*KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. _Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, godiya ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai da ya ba mu aron rai da lafiyar da mu ka kawo wannan lokacin da rai da lafiya. Ina roƙon Allah yadda ya bani ikon fara rubutu littafin nan lafiya da aminci Allah ya sa na gama lafiya, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani al’umma baki ɗaya, ya Allah kar ya bani ikon rubutu ɓarna ko abinda ya saɓa addinin mu amin._ _Wannan labari mai suna KIRAN RABO ƙirƙirarre ne, ban yi shi dan wani ko wata ba, in ya yi kama da labarinki ko labarinka ayi haƙuri rashin sani ne._ _Ban yarda a canja min labari zuwa wata siga daban ba, ban amince a juya min labari zuwa wata fuska ba ba tare da izini ba!._ *SHIMFIƊA.* _*Hausawa suna cewa da mutuwa, aure da arzuƙi ƴan uwan juna ne. Ni kam na ce a haɗa da RABO domin shima yana daga cikin waɗanan ukun. RABO in ya yi kira ko kana cikin mahaifiyar ka sai ka amsa shi ka fito duniya. KIRAN RABO ya kan canja ƙaddara daga baƙa zuwa fara, KIRAN RABO ya kan mayar da wasa ya zama gaske, KIRAN RABO yana mayar da abinda ba zai yu ba ya zama mai yuwa. Wani yana shigowa rayuwar wani dan ya zama silar amsa KIRAN RABON sa, wani yana fita daga rayuwar wani dan hakan ya zama silar amsa KIRAN RABON SA. Ya ake gane rabo ya yi kira? Ba a ganewa, sai bayan Allah ya yi ikon sa a kai ake fahimtar daman can kiran rabon ka amsa. Ana amsa KIRAN RABO a lokacin da ba a san an amsa shi ba, ba a jin kiran da kunne balle a kasa kunne a nutsu dan a saurari lokacin da rabo yake kiran ka. Kamar yadda bawa ba ya sanin lokacin da mutuwar sa, lokacin auren sa, lokacin da ƙaddara ta kira shi haka ba a sanin lokacin da RABO yake kira sai dai ka tsinci kan ka a lokacin da ka amsa. KIRAN RABO lokaci ne dashi kamar dai yadda mutuwa take da lokaci!.*_ https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t *Book 1* *P 01* _"Tsinanne ɗan iska, a haka zaka ƙare rayuwarka. Yara duk sun zama ɓata gari saboda rashin kulawar iyaye"._ _"Ka daina furta irin wannan maganar don Allah, in kana aibata yaran wasu kamar na ka ka ke aikabata. Mun haifa mu ma, don Allah ka daina ba hali ne mai kyau ba."_ Numfashi ta sauke tunawa da abinda ya wuce a shekarun baya, sai yanzu take fahimtar illar da take cikin irin wannan kalamai da iyaye suke yiwa yaran da ba nasu ba. Sai yanzu take fahimtar dalilin mahaifitarta da a kullum take kwaɓar mahaifinsu ga barin aibata ƴaƴan wasu da yake yi. Tabbas yanzu ta fahimta tunda gashi reshe ya juye da mujiya. A zaune take a ƙaramar harabar gidan akan sallaya babba mai girma. Ita da wani mutum ne a zaune amma gabaɗaya hankalin ta baya tare da shi ta tafi tunanin abinda ya wuce saboda abin ya zo akan gaɓar da zata yi tunanin ne. Kallon farko zaka yi musu ka fahimci zaman taɗi suke yi kamar yadda samari da ƴan mata ke yi, ko yadda zawarawa suke yi. A yadda take kallon sa yana magana zaka tabbatar da kalaman da yake faɗa basu yi mata daɗi ba sam, fuskarta mai yawan fara'a ta canja gabaɗaya ta cushe waje ɗaya saboda yadda kalaman suke sosa mata rai. Shima kallon ta yake yi cikin ƙarfin guiwar sanar da ita saƙon da yake zuciyarsa, domin abinda yake ransa kenan kuma shi yake faɗa kuma ya zama dole ta sani. Babbar mace ce matashiya wacce a a shekaru zata kai shekaru talatin da biyar a duniya, fara ce irin haske mai ja kaɗan, tana da haske sosai da manyan idanu masu haske da ɗaukar hankali lokaci guda. Tana da dogon hancin da ya ƙarawa fuskarta kyau. Kai tsaye in ka kalle ta baza kace ta kai shekarun da take kai ba saboda ƙaramin jiki ne da ita, sannan ga madaidaicin kyaunta da yake ɗaukar hankali har ba a fahimtar shekarun ta saboda hakan. Jin Muktar ya gama maganar tasa sai tayi murmushin yaƙe wanda ake kira da yafi kuka ciwo ta kalli wanda yake zaune kusa da ita cikin murya mai sanyi ta ce, "Abinda ka ke tunani kaima a kaina kenan?." Yayi murmushi ya ce, "abu ne a bayyane ai Aysha. Ke kin san da gaske nake ina so na aure ki, amma maganar da take yawo a kan ki bana tunanin iyayena zasu amince da auren ki. Shiyasa na zo ayi ta ta ƙare kawai." "Yanzu zuwa kayi ka ce min ka fasa aure na kenan?" Ta tambaya tana kallon sa. Duk da ba yau aka saba ba, amma yanayin yadda yake magana yana bata mamaki. "Kusan Hakan." Ta girgiza kai ta ta ce, "to ka tashi ka koma ta inda ka biyo, saƙon da ka ke son isar min ka isar sai ka je ko?." Ya bi fuskar ta da kallo ya ce, "ki yi haƙuri ba daga ni bane, in magana tayi yawa akan mutum ko kana son alaƙa dashi dole ka dakata. Na so auren ki amma zancen nan ya zaga ko ina. Har da masu cewa shiyasa baki aure ba saboda duk abinda miji yake yiwa matar sa ƙanin ki OMAR yana yi miki." Ta rantse ido cikin ɗacin kalmar ta ce, "kar ka sake magana akan ƙanina, kaje tunda dai ka fasa ai shikenan ko?." Ta faɗa cikin rashin damuwa dan ta saba indai fasa aurenta ne. Yayi dariyar rainin hankali ya ce, "Daman an ce bakya son laifinsa, daman an sanar dani ko me za a ce baza ki taɓa ganin laifinsa ba, ke lallai ga mai ɗan uwa. Taƙadarin yaron da ya adabi mutanen Kano gabaɗaya, wai shi ki ke jin haushi dan an faɗi magana a kansa saboda kawai ɗan adam baya son gaskiya."    "Ka gama!?." Ita dashi a tare suka juya zuwa inda suka ji anyi maganar zuciyar ko wannen su ta buga a take. Wara idanu tayi ganin wanda idanunta suke gani dan gabɗaya bata so yazo ya riski maganar ba, shikenan yanzu ƙaramin abu zai koma gingimeme a wajansa. Yana zaune akan ɗan tudun ƙofar gidan ya harɗe ƙafafunsa, ga ƙatuwar wuƙa a hannunsa yana shafa ta a hankali yana kallon ƙasa kamar ba shine ya yi maganar ba. Juyo idon sa yayi ya watsa masa wani kallon da ya saka gaban Muktar ya faɗi nan take ya shiga hankalinsa. Wani irin kallon raini da ƙasƙanci yake yi masa yana taune laɓɓansa cikin ɓacin rai. Wuƙar ya fara wasawa a jikin ƙaramin dutse da yake kai a nutse cikin salon mugunta. Saurayi ne wanda a shekaru bai wuce talatin ba, kallo ɗaya zaka yi masa ka shaida kamar da ya ke yi da Aisha, duk da kyuansa ya fi fitowa akan nata amma suna kama sai dai banbacin halitta ta mace da namiji. Dogo ne mai cikar zati da kuma kyakykyawar halitta, kallon farko zaka yi masa ka shaida kwarjininsa, dan lokaci ɗaya zai cika maka idanu tsoronsa zai mamaye maka zuciya har ya kai mutum ga sauke idanu ƙasa. Namiji ne wanda ake kira na miji, ƙaƙƙarfa kuma mai jikin ƙarafafa, sai ka rantse da Allah Aisha ƙanwarsa ce saboda gabaɗaya ya zama shine yayan itace ƙanwar. Yana da haske sosai, fuskarsa tana da haske irin sosai ɗin nan, yanayin rigar da take jikinsa ƙarama ce zaka hango fatar jikinsa da ta kasance fara tas har tafi fuskarsa haske. Yana da manyan idanu sosai wanda ake kira kwala-kwala masu ban tsoro, idanunsa zagayayyu ne masu girma, in ya wara su yana magana kamar zasu fito saboda girman su. Kallo ɗaya in ka yiwa idanunsa baza ka so ka sake kallon idon ba musamman in ransa a ɓace ya ke. Yana da hanci amma ba irin mai tsayin nan sosai ba kuma ba gajere ba ne, yana da zagayye cikakken baƙin gashi a fuskarsa, wanda suka ɓoye ƙuruciyar sa suka bayyanar da kwarjini a tare dashi. Yana da kwantaccen gashi a kansa wanda ya tara, in ka kalli gashin lokaci ɗaya zaka fassara shi a gashin buzaye ko fulani, dan yadda ya ke a kwance baƙi zai saka ka tabbatar ba gashin hausawa ba ne. Yana da yalwar gashin gira irin wacce take a cushe gata baƙa sosai. Haka fuskar sa itama a cike take da gashi mai yawa wanda kana gani ka san baya samun gyara yadda ya kamata. OMAR kenan! wanda ake yiwa laƙabi da DAMISA wasu kuma su ce MADUGU, wasu kuma ce JAN WUYA. Ɗan daba ne lamba ɗaya, ɗan daba ne mai lasisi wanda ya samu goyan baya daga iyayen ƙasar wato ƴan siyasa. Duk da dabancin ta sa mai tsari yake yi amma yana daga cikin ƴan dabar da ake matuƙar tsoron su a faɗin Kano. Kaf yankin ƙofar nasarawa shine shugaba, babu wani ɗan daba da zai aikata ba daidai ba a wannan area sai Damisa ya sani. Kuma saboda shine kawai ake jin tsoron yin faɗa a arear saboda in ya tashi ɗaukar fansa bai iya ba, shiyasa ba a cika koda sace-sace a unguwar ba saboda ya zama kamar kura da nama ya shigo zai kama. A shekarun baya ya yi faɗace-faɗace duk da bai taɓa kisa ba amma ya yi ƙanin kisa, a yanzu ne ya canja tsari da salon dabancin shiyasa wasu mutanen suke gani kamar ba ɗan daban gaske bane. Aisha da take zaune ganin Muktar ya firgita da ganin ƙanin nata cikin bada umarni ta ce, "Omar ka tashi ka shiga gida babu ruwan ka." Jin abinda Yayar ta sa ta ce sai ya miƙe tsaye yana kallon ta, shigowa ciki yayi sosai yayi kamar zai wuce ta kawai ya ɗuka ya damƙi wuyan Muktar  ya miƙar dashi tsaye. Nan take jikinsa ya soma, yana kallom Omar yana karkarwa dan daman an faɗa masa Omar indai akan Yayarsa ne babu abinda bazai yi ba. Omar ya kalli cikin idonsa cikin dakakkiyar muryarsa irin ta jarumai mazajen gaske ya ce, "maimaita abinda ka faɗa mata naji." Jikin Muktar rawa yake yi sosai, ji yake kamar ya yi fitsari saboda tsoro ya kasa furta komai saboda tashin hankali. Aisha da take tsaye itama t ce, "Omar meye haka ne? Ka sake shi!?" Ta faɗa cikin ɗaga murya. A fusace ya kalle ta ya ce, "DIDI ki matsa baya, babu abinda zai hana ban farka bakin wannan mutumin ba. Nan gaba na ga da wanne bakin zai furta irin abinda ya ce yanzu" ya dawo da kallon sa ga Muktar shi ya ce, "Tunda ya tako har cikin gidan mu babu abinda zai hana ban ɗauki mataki a kansa ba. Ko na datse masa harshe, ko na farka cikinsa." "Wayyo Allah na shiga uku!. Aisha don girman Allah ki taimake ni, ki ce ya ƙyale ni, ki taimaka min kar......" maganar da ta maƙale saboda wuƙar da ya kawo kusa da wuyan sa ya ce, "kana cigaba da magana wallahi sai dai uwar ka ta haifo wani." Ɗif ya yi ya kulle bakinsa da jikinsa yana karkarwa sosai nan da nan hawaye suka fara ambaliyya daga idanunsa saboda tsoro. Didi ta ƙaraso wajan ta riƙe hannunsa ta ce, "Omar ka ƙyale shi ya tafi na ce ko?." "Bazan ƙyale shi ba. Ba shi yana da zarrar zuwa har gidan nan yake cewa ya fasa aurenki ba? Inda iya wannn kalmar ya faɗa da sauƙi, amma har magana mara daɗi ya faɗa a kanki. Didi ko duniya ce zata taru yau babu abinda zai hana ban farka cikin mutumin nan ba." "To ba ni aka faɗawa magnar ba ina ruwan ka...? Malam ka cika shi ya tafi bana son wannan ɗabi'ar" Ta faɗa da ƙarfi tana son cire hannun Omar daga wuyan Muktar amma ta kasa. Kallon Muktar ɗin ya yi da yake hawaye kamar ƙaramin yaro jikinsa na rawa sosai ya ce, "ka ci albarkacin ta a yau ka sha, amma kar ka sake idanuna ya sake ganin fuskar ka, In kayi wannan gangancin zaka yi dana sanin zuwan ka duniya." Kai yake ɗaga kamar ƙadangare saboda tsoro Omar ya ce, "baka da baki!?." Yadda yayi maganar cikin tsawa ya ake firgita shi ya ce, "na....ji....ka yi....ha...ku....ri." Omar ya cika masa wuya ya kalle shi ya ce, "durƙusa ka bata haƙuri." Babu ɓata Lokaci ya zube a ƙasa ya ce, "Ki yi haƙuri Aisha, na tuba ki yafe min." A fusace Omar ya ce, "sunan ta ka ke faɗa kai tsaye babu girmamawa? Sa'ar ka ce?." Jiki na karkarwa Muktar ya ce, "ki yi haƙuri Mama, Allah ya wuci zuciyarki." "Haifar ka tayi da zaka ce mata Mama!?" Ya sake faɗa yana cakumar rigarsa. Muktar ya fashe da kuka mai sauti ya ce, "Ki yi haƙuri Anty, ki yi haƙuri don Allah." Omar ya sake shi ya nuna masa ƙofa ya ce, "bar nan." Ai bai sake magana ba ya fita a guje ko takalman sa bai ɗauka ba saboda tsoro. Omar ya kalli inda Didi take ganin bata wajan ya san ta shiga gida ya kalli yaransa da suke ƙofar gida ya ce, "duk ranar da ya shigo area nan kar ya fita da lafiya." Dukkan su suka haɗa biki suka ce, "An gama Damisa, a fito Lafiya Magudu uban matsiyata." Ya jiyo idanunsa masu ban tsoro ya kalle su ya ce, "Zaku iya wucewa anjima sai ku zo" yana gama faɗa ya shiga gida yana jin su suna amsawa.         Yana shiga tsakar gidan Didi ta tare shi ta ce, "Omar me yasa ka ke min haka ne? Omar me yasa ka ke son saka min ciwo ne wai?." Zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce, "kar ka ce komai sai na baka dama. Ya ka ke so nayi ne? Me ka ke so ka zama ne Omar? Yau gabaɗaya satin ka biyu da fitowa daga prison bayan ka shafe kwana goma a ciki, so ka ke ka kuma komawa ne?." "Didi...." Ta katse shi ta ce, "ba wani Didi, babu wani Didi kar ka ƙarasa. Omar me ka ke son zama ne don girman Allah? Ɗan ta'adda ka ke so ka zama ko me? A gaban idona ka dinga zancen zaka farkawa wani ciki?." "Duk abinda ya faɗa miki naji, in ya fasa auren ki ya faɗa cikin magana mai daɗi mana sai ya faɗa da wulaƙanci?. Na rantse da girman Allah ba dan ke ba sai na yiwa bakinsa illa." "To waye zai aure ni bayan kowa tsoron ka yake ji? Da irin wannan dabi'ar taka ka ke so na yi aure Omar?. Wanne iyaye ne zasu amince ɗansu ya aure ni bayan ina da ƙani irin ka?." Ganin idon Yayar tasa ya fara kuka da hawaye sai ya lumshe idanunsa ya buɗe ya kalle ta ya ce, "Didi don ina so ki yi aure ba haka yana nufin zan juri ko wacce kalma a kanki ba, Wallahi ko waye yayi ƙoƙarin ɓata miki rai shima sai nasa da na danginsa ya ɓaci." Didi ta ce, "waye yace maka raina ya ɓaci?Gaskiya ya faɗa Omar kowa a unguwar nan kallon da suke min kenan. Ban taɓa aure ba muna zaune da kai a gida ɗaya gani suke kamar ni da kai wani abun mu ke aikatawa mara kyau shiyasa rashin auren baya damuna. Shekaran jiya matar Alhaji Yusuf ni da ita ta faɗa min ido cikin ido. Kaga na damu...? Ban damu ba saboda ni na san ba haka bane, suna yiwa abun kallon baibai ne, kuma babu wanda ya isa ya ce zamana da kai a gidan nan akwai haramci, sai dai su yi tunanin banza su daina. Aurena kuma lokaci ne kawai bai yi ba." Bai yi magana ba kallon ta yake yana kuma hakaito kamannin matar da ta ambata a idanunsa yaji ta ce, "kowa tsoron zuwa ya ce zai aure ni yake yi saboda kai Omar, kaf ƙofar nasarawa da kewaye tsoronka suke ji iya kallon idanunka ma tsorota su yake yi balle ka yi musu magana. A haka ka ke cewa burin ka nayi aure?." Ya sauke numfashi yana kallon ta kafin ya dafa kafaɗarta ya ce, "Didi lokaci ne kawai bai yi ba, in yayi zaki yi aure. Kawai bazan yarda ki auri ɗan kutmar uba bane, dan ko kina auren nasa ya raina miki hankali ni mai iya ganin bayan sa ne." Ta cire hannunsa daga kafaɗarta ta ce, "Omar ka daina furta wannan kalmar, ka daina cewa zaka ga bayan mutum don Allah ka daina." Leɓensa ya ciza ya kalle ta ya ce, "Didi kamar uwa ki ke a wajena, in na kira ki da uwata ban yi laifi ba. Ina so ki sani babu wani ƙato ɗan ƙatuwa da ya isa ya ɗaga miki yatsa ban karya shi ba, kuma shi wannan da ya fita na ƙyale shi ne yanzu saboda ke amma ai zamu haɗu ko da sanayya ko da ganganci. Itama matar Yusuf ɗin zamu gauraya" yana faɗa ya juya ya shiga wata ƙofa da take farko  a cikin gidan. Idanu ta wara waje jin abinda ya ce cikin ɗaga murya ta ce, "Omar kar ka yiwa matar nan komai fa, matar aure ce kar ka sake ka yi wannan gangancin!." Bata ji maganar sa ba daman ta san bazai ce komai ba. Waje ta samu ta zauna tayi tagumi hawaye na sakkowa daga idanunta. Tana matuƙar son ƙaninta Omar, tana matuƙar ji dashi bata so taga wani abun ya same shi. Amma Omar ya wuce tunanin mai tunani, duk yadda ka ke tunanin rashin jin Omar ya wuce haka. Baya ji tun yana yaro, baya bari in aka ɓata masa tun bai kai haka. Yana da zafi sosai, iya kallon idanun Omar zai saka ka firgice balle ka buɗe bakinsa ko ya yi maka barazana. Kaf unguwar tsoron sa ake ji ko almajiri baya iya shigowa gidan yayi bara saboda dashi. Babu maƙociyar da take shigowa gidan saboda shi, baya ɗaukar raini kuma yason munafurci da gulma. Bashi da ɓoye-ɓoye kuma girman ka baya hana shi magana, shiyasa gidan kullum shiru sai Didi kawai ita kaɗai saboda kowa tsoron sa yake ji ba a iya zuwa. In kaga mutane a gidan to tabbas baƙi ne, shima haka zai ta cin magani yana zare musu idanu dan ya tsani ya ga anyi baƙo ko baƙuwa. Hawaye taji yana share mata sai ta kalle shi bayan ya canja kaya zuwa ƙananun kaya ya tsuguna a gabanta ya ce, "duk wanda ya zama silar zubar hawayen ki sai na zama silar zubar jini a jikinsa, Didi kin san bana kisa, ban taɓa kashe rai ba. Amma akan hawayenki zan iya farke maƙworagon ko waye" ya faɗa yana wara idanunsa yana kallon ta. Murmushi kawai tayi ta miƙe tsaye ta ce, "baza ka ci abinci ba?." Shima ya tashi tsaye yayi yana kallon ta ya ce, "Zamu zo anjima dasu goje mu ci, yanzu zan je na dawo." "Ina zaka je?." "Wani ɗan aiki zan je nayi." "Wanne aiki ne?." Ya kalli idanunta ya ɗauke kai  dan baya yi mata ƙarya kuma shi baya ɓoye mata komai na sa. Ya ce, "mutanen Yakasai ne suka ƙwacewa wani na mu waya sannan suka kashe shi, Ke kin san sai naje mun zauna dasu." Ta girgiza kai tace, "don Allah Omar...." Ya dakatar da ita ta hanyar faɗim, "Didi sai na je fa, amma nayi miki alƙawari bazan yi faɗa ba indai ba sune suka so hakan ba. Magana kawai zamu je mu yi domin na ja musu kunne akuyar su ta kiyayi ramata." Kallon sa take yi bata ce komai ba shima haka kafin ya ja baya ya ɗauke idanunsa daga kanta ya ce, "Zan dawo yanzu Didi." Yana faɗa ya fita cikin takunsa na ƙasaita ya bar ta a tsaye tana kallon sa. Hawaye ta share ta ɗaga kai sama bayan ta ɗaga  hannu ta ce, "Ya Allah ka kiyaye min marayanka, Allah ka kare shi. Ya Allah ka sassauta masa wannan zuciyar da yake fama da ita, ya Allah ka cire masa son wannan ɗabi'ar daga zuciyarsa." Ido ta share tare da sauke ajiyar zuciya ta shiga falo. ••••••••• *ABUJA* *SENATOR SAGIR SANI SHATIMA RESIDENT.* Senator Sagir shine Sanatan Kano ta tsakiya mai ci yanzu, wayeyen mutum ne mai ilimi da kuma son ilimin boko. Kaf ma'aikata gidan sa daga masu degree sai masu master, daƙyar ake samu ya ɗauki mai kwalin diploma aiki, saboda a ganin mai wannan matakin karatu jahili ne bai san komai ba, shi kuma yana ganin aiki da wanda bashi da ilimi ba ya haifar da komai sai dana sani. Kaf masu aikin gidan mata da zama sun iya english, in suna turanci ba ka ce masu aiki ba ne saboda haka ne tsarin mai gidan. Ya raina wanda bashi da ilimin boko, yana kuma ganin wanda bashi da ilimin boko babu inda zai je a rayuwa sai dai ka ƙare a bara. Ba ya mu'amala da wanda ba shi da ilimin boko, in kuwa ya yi to ta zama dole kuma sai dai a ɓangaren siyasa. Bai damu da ilimin addinin ka ba, shi dai indai kana da na boko ko kafiri ne kai ka fiye masa musulmi. Matar shi ɗaya tal wacce yake so kamar rai, yana da yara guda uku. Nabil, Narma sai Najwa.        Babban falo ne mai kyau da tsari, kai da ka kalli falon ka san na manya mutane ne na na ƙananun mutane ba, ya tsaru iya tsaruwa duk da babu tarkace a cikin sa. Yanayin tsarin sa zai saka ka tabbatar da falon ba na ƙananun mutane bane ba. Wata kyakykawar budurwa ce fara tas a zaune a falon, sanye take da riga iya guiwa kanta babu ɗankwali hakan sai ya bayyanar da yalwar sumar da take da ita. Tana da kyau wanda a kallo ɗaya zaka fahimta saboda kyawun halittar da Allah ya yi mata. Barr Narma Sagir Sani shatima kenan wacce ake yiwa laƙabi da Barr Nass. Second born a wajan Senator Sagir, ƴar kimanin shekaru ashirin da shida. Bata da ƙiba daga sama amma Allah ya yi mata baiwar ƙira mai kyau daga ƙasa, tana baiwar sura wacce in ka kalla za ka so ka sake kallo saboda yadda ta tsaru. Barr Nass manager director ce a ɗaya daga cikin kamfanin mahaifin ta. Sananniya a social media musamman a instagram da X. "Daddy Ina so zan shiga Kano next week" ta furta cikin muryarta irin ta ƴan gayu ƴaƴan Daddy da Mummy. Kallon ta ya yi a lokacin ta kai abinci bakinta ya ce, "me ake yi a Kano?." Ta ɗan yi farrr da idanu wanda hakan ya zamar mata jiki ta ce, "arewa24 sun yi inviting ɗina then..akwai bikin friend ɗina Samra kamar ma ka san Dad ɗin ta. Bashir na Gwaggo ne babanta." Dad ya kalle ta yana girgiza kai ya ce, "yes, i knew him. But, how many days are you planing to spend in Kano?." Ta ajjiye spoon ɗin hannunta ta ce, "Uhumm two to three weeks. At least two weeks." Daddy ya girgiza kai bayan ya haɗe fuska ya kalle ta sosai ya ce, "Narma!." Jin yadda ya kira sunan ta sai ta kalle shi ta ce, "Dad." "You know i don't want you to go to Kano, right?." "Yes dad, but it's necessary. And dad I'm not a little gril fa, I know what I'm doing. Zan iya kare kaina daga duk abinda ka ke gudu, so just calm down." Kallon ta yake yi kafin ya kalli wacce take zaune a gefe sa ya ce, "Kina Jin abinda take cewa baza ki yi magana ba?." Mum ta kalle shi ta ce, "wannan maganar tsakanin ku ne babu ruwana a ciki. Ta faɗa min batun zuwa Kano nace sai ta jira umarninka." Dad ya kalle ta ya ce, "Narma kin san abinda ya faru last a zuwan ki kano ko? An yi attacking ɗinki kin tuna wannan? Ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu bamu san meye ya faru ba." "Yes Dad ban manta ba, amma hakan ba zai saka na daina zuwa Kano saboda wanda ban san su ba." Dad ya bita da kallo kafin ya ce, "well, I will think about this." Kamar zatayi kuka ta ce, "Dad don Allah kar ka ce bazan je ba." "I'm not saying that, but sai nayi tunani." "Okay, thank you" ta faɗa tana tashi ta hau sama tana danna waya. Senator ya bi ta da kallo bayan ta wuce ya kalli Maman ta ya ce, "Kina ganin ya kamata na barta ta je Kano?." Mum ta ce, "yeah ka barta mana, na san Samra ƙawarta ce sosai bai kamata ace bata je ba. Sai ka bata security su kula da ita." Ya girgiza kai ya ce, "Okay zan san abinda zan yi" ya faɗa yana tashi shima ya saman yana tunani. Anya zai iya barin Narma taje Kano? Garin da aka kusa hallaka masa ƴar da yafi ƙauna a duk duniya?. Ko da zai bari taje sai ya haɗa ta da wanda yake tunanin zai kular masa da ita sosai. Narma ce ta sakko cikin shirin fita, sanye take silk adire kalar ja wanda aka yi masa ɗinki mai ɗaukar hankali. Gabaɗaya ya bi jikinta ya kwanta yana bayyanar da zallar surar da take jikinta, hatta bra ta da saka ana ganin shatin ta komai ya fito kamar bata saka kaya ba. Duk namiji mai lafiya in ya kalli Narma a wannan shiga sai ya ji yanayin da bai shiryawa jin sa ba har ƙwaƙwalwarsa. Ɗauke idanu daga kan Narma a wannan lokaci abu ne mai wahala, sai mai juriyar gaske ne zai kawar da ita daga idanunsa.Ta tsaru a cikin rigar, ta kuma yi mata kyau kamar ka ɗauke ta ka gudu. Kallon Mum tayi da take zaune ta ce, "Mum zan je shoprite" ta faɗa tana gyara zaman hular kanta. Mum bata kalle ta ba ta ce, "ki taho min da diet stick ɗina ya ƙare." "Okay Mum" ta amsa tana fita. A harabar gidan ta tsaya tana ƙarewa motar ta kallo, ta san ta ce a wanke mata amma sai ta ga kamar ba a taɓa ba. Cikin ɗaga murya ta ce, "Ina Kashim!?." Kashim jin maganar ta ya fito cikin sauri da rawar jiki ya ce, "ga ni Ma'am." Nuna masa motar ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ya kalli motar ya kalle ta ya ce, "i'm sorry ma'am, bani da lafiya ne shiyasa......" dakatar dashi ta yi ta ce, "in ka ƙarasa wallahi sai na mare ka." Jin abinda ta ce sai ya kalle ta dan kuwa a shekaru ita ba sa'ar sa ba ce, ko yayanta Nabil ya girma balle ita. "Who do you think you are...? You won't wash my car, and now you're telling me you're not feeling well?. Damn your sickness!" Ta faɗa cikin ɓacin rai tana kallon sa. "I'm sorry" ya furta a sanyaye yana kallon ta. Narma ta saka baƙin glasses ɗin hannunta ta ce, "ko mutuwa ce a kan ka kar ka sake aikata wannan gangancin, in na ce ayi kawai ayi in ba haka ba you must regret about it." "In sha Allah, Sorry Ma'am." "Zan ƙyaleka saboda wannan ne karo na farko da ka yi haka, kar ka sake maimaitawa" ta faɗa tana barin wajan kafin ta ce, "And make sure you've washed it before i get back" ta faɗa tana karɓar key ɗin motar Mum ta shiga. A guje gate man ya buɗe mata gate ta fita a guje. Sai bayan ya kulle gate ɗin ya kalli Kashim ya ce, "ka yi sauri ka ƙoƙarta ka wanke kafin ta dawo, yarinyar nan bata da kirki, a iya watan nan masu aiki goma ta kora ta kuma ɗauko guda goma. Ka yi haƙuri ka yi kar ta ci maka mutunci a banza." Kashim ya ce, "wallahi bani da lafiya." "Haka zaka yi haƙuri. Kuma wallahi ba a wanke musu mota a gidan nan car wash ake zuwa, kawai saboda ta samu hanyar ciwa wani mutunci ne ya saka ta ce ka yi. Dan ita tana so ta ga tana ciwa mutum mutunci. Ta waje guda take da kirki wani lokacin, in ta ga mutum a kwance babu lafiya a nan zata ɗan tausaya masa. Amma sai ciwo ya kai ciwo, bata ɗauki ƙaramin ciwo a komai ba." Kashim ya yi ajiyar zuciya ya wuce jiki a sanyaye. Inda an sabo da wulaƙanci da cin fuska da ƙasƙantar da mutum da yanzu sun saba a wajan Narma. ••••••••••• *KADUNA STATE* *ALHAJI ABDALLAH AHMAD RESIDENT.* Alhaji Abdullahi sannen ɗan kasuwa ne mai ji da kuɗi da iko da kuma alfarma a faɗin ƙasa nigeria. Yana da matuƙar kirki da daɗin mu'amala ga kowa, ko ma'aikatan gidan sa ya ɗauke su kamar ƴan uwan sa baya wulaƙanta su ko tozarci ko yaushe cikin wasa da dariya suke. Mutum ne wanda ya san ya kamata, bashi da wulaƙanci ko kaɗan kamar ba mai kuɗi ba, in ka ga fushinsa akan abu tabbas ransa ne a ɓace. Mutum ne mai kyautatawa iyalan sa da matuƙar ƙaunar su, baya bari iyalan sa su yi kukan babu ko ya ya abin yake. Haka kawai zasu kulle gidan a bar ƙasar kawai dan jin daɗin ƴaƴan sa da walwalar su. Babu abinda iyalan sa suka nema suka rasa, kuɗi, mota, fita ƙasashen waje da sauran kayan more rayuwa ya tanadar musu dashi. Shiyasa suka kasance ƴan gata gaba da baya. Matar sa ɗaya mai suna Zeenatu, uwar gidan sa mai suna Bilkisu Allah ya yi mata rasuwa shekaru masu yawa da suka wuce. Yaran sa shida, biyar daga wajan Zeenatu ɗaya tal daga uwar gidansa. Ahmad shine babba, Jawad, Jidda, Nayla, Jalila, Jalil. Yara ne masu tarbiyya da sanin ya kamata, dukkan su sun tashi a turbar tarbiyya mai kyau, ilimi, addini da kuma kyakykyawar rayuwa.           Kyakykyawar farar budurwa ce ƴar kiminin shekaru ashirin da huɗu zaune a ƙasaitaccen falo mai kyau da girma tana danna waya. Falon yana da girma sosai ya kuma tsaru matuƙa, kana ganin falon ka san na masu kuɗi ne ba na talakawa ba. Tana da haske da kyawawan idanu da ƙaramin baki mai ɗaukar hankali, tana da ƴar ƙiba kaɗan ba mai yawa ba, yanayin jikin ya dace da ita sosai dan komai ya yi daidai da halittar ta. Tana zaune tana danna waya fuskarta ɗauke da kyakykyawan murmushin da yake bayyanar da dimples ɗinta, kana kallon ta ka san duk abinda take kallo a wayar yana bata nishaɗi sosai. A yanayin ta zaka hangi tsantsar nutsuwa da kuma fara'ar da take da ita. Hauwer Abdallah Ahmad kenan, wacce ake yiwa laƙabi da NAYLA.          "Nayla me ki ke kallo haka ki ke dariya?." Juyawa tayi ganin wacce tayi mata magana sai tayi dariya cikin murya mai daɗin saurare ta ce, "Mama ina kallon comady ɗin ƴan TikTok ne. Abiy ya fito?." Wacce ta kira da Mama ta zauna a kusa da ita tace, "Yanzu zai fito." "Gani na fito." Jin muryar mahaifin nata mafi soyuwa a gare ta sai ta miƙe tsaye tana murmushi ta ce, "Abiy sannu da zuwa." Ya dafa ta ya ce, "Yauwa Mamana. Ya aka yi ki ke nema na?." Zama yayi bayan ya zaunar da ita tana murmushi ta ce, "Ina so daman zan je Kano cikin gari wajan Hajja na yi kwana biyu." Nan da nan annurin fuskar sa ta gushe ya ɗago ya kalle ta ya ce, "Nayla!." Gabanta ya faɗi jin a yadda ya faɗi sunan ta, kasancewar bai cika faɗa ba sai dai ya ce Mamana. Ta kalle shi ta ce, "Na'am Abiy." "Meyasa ki ke son zuwa Kano ko yaushe? Meyasa bakya son zaman gidan nan?." Nayla ta kalle shi bayan ta rausayar da kai ta ce, "Ba haka bane ba Abiy, waya mu ka yi da Hajja tace min yaushe zan zo shine nace mata sai na kammala nysc. Kuma yanzu Abiy na gama services, tahfiz ɗin ma da na shiga na gama shiyasa nake naje" ta faɗa cikin yanayi na shagwaɓa wanda zai tabbatar da ita ɗin ƴar gata ce. "Amma kin san bana son zuwan ki Kano ko yaushe ko?." "Na sani Abbiy, amma Hajja kakata ce tana so na je na dinga gaishe ta. Kuma duk dangin Ummana a can suke, suna jin daɗi in naje na gaishe su." Abiy yayi shiru bai ce komai sai kallon ta da yake yi ganin haka sai ta sunkuyar da kai tana addu'ar Allah ya sa ya barta ta. Abiy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "zan bar ki ki je amma baza ki jima a can ba, sannan ban yarda da yawo ba." Nan take tayi murmushi mai bayyanar da kyaun ta da ƙuruciya tace, "in sha Allah Abiy. Na gode sosai." Ganin tana farin ciki shima sai ya yi murmushi sannan ya tashi ya yi musu sallama ya fita. Nayla ta kalli Mama da farin ciki ta ce, "Mama bara naje na fara shirin tafiya Kano." Mama tayi murmushi ta ce, "to sai kin dawo. Sannan kar ki damu da yace kar ki jima, in kika tafi ba sai ya gan ki ba?." Nayla tayi dariya ta ce, "Kuma fa haka ne Mama, bara naje na dawo" ta faɗa tana tashi da sauri ta shiga ciki. Da muguwar harara Mama ta bita bayan ta ja tsaki ta ce, "na rantse da girman Allah sai kin bar gidan nan, yadda uwar ki ta barshi kema sai kin bari. Wannan soyayyar da yake nuna miki sai ta koma ƙiyayya nan ba da jimawa ba. Sai na saka kin zama abin ƙyama a idanun mahaifinki. Irin wahalar da uwarki ta bani a gidan nan sai kin an ninka miki ita a gidan aurenki. Bazan taɓa bari samarin da suke tururuwar son auren ki su aure ki ba, in suka aure ki ai ban yi riba ba, ɗiyar Bilkisu ta rayu a cikin gidan aure mai ɗauke farin ciki bayan ni ta wahalar dani a nawa gidan auren?. Hmmm ai duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha, wallahi sai kin gwammace ba a haifo ki ba. Mu je zuwa Nayla!." *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Tsakanin Narma, Nayla da Omar waye zai amsa KIRAN RABO..?🤩 Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t Book 1 P 02            Omar ko da ya fita a ƙofar gida ya tarar da yaran sa su uku suna jiran fitowarsa, suna ganin ya fito sa suka miƙe ya ƙaraso cikin su yana kallon su sannan ya ce, "ehmm matan Alhaji Yusuf na wa?." Ɗaya daga cikin su ya ce, "Alhaji Yusuf nan baya?." Ya ɗaga masa kai alamun eh ya sake cewa, "Matar shi ɗaya ce." Omar ya girgiza kai bayan ya saka hannu a aljihu ya ce, "mu je gidan." Tafiya suka fara yi yana tsakiyar su fuskar nan tashi a tamke matuƙa, babu alamun fara'a a tare dashi gabaɗaya babu damar kawo wasa ko raini a kan fuskarsa. Duk inda ya wuce kallon sa ake yi amma babu damar ayi masa magana saboda kwarjinin da yake dashi.         "kai Ummaru!." Aka faɗa daga bayansa ya tsaya cak tare da juyawa dan ya san kaf unguwar mace ɗaya ce ke ɓata masa masa ta kira shi da Ummaru. A hankali ya juya kamar yadda ya yi tunani kuwa ita ce ya sake haɗe fuska ya ƙarasa wajan ta yaran sa suka rufa masa baya ya kalle ta ya ce, "Omar sunana, in baza ki faɗa ba ki ce Tiger." Ta harare shi ta ce, "bazan faɗa ba, ko zaka saka ni na faɗa ne?. Na faɗa Ummaru." Ɗan kawar da kai ya yi ya ɗan saki fuska kaɗan domin yana matuƙar girmama tsohuwar da babu abinda zai hana bai yi mata warning ɗin da baza ta sake ganganci ce masa Ummaru ba. Hajja ta kalle shi ta ce, "Kwana biyu baka shigowa mu gaisa ko?." Ya kalle ta ya ce, "zan zo." "Allah ya kawo ka, a daina rashin ji a san an girma dai. Ka gaishe da Aisha mutuniyar kirki." Bai ce komai ba ya juya suka cigaba da tafiya yana ɗan murmushi jin abinda Hajja ta ce wai a daina rashin ji. Tafiya suke yi har ƙofar gidan Alhaji Yusuf kamar yadda suka yi niya. Ɗaya daga cikin yaran sa ne yayi sallama a ƙofar gida aka amsa daga ciki. Kafin ka ce kwabo mutane sun taru a wajan saboda mamakin ganin Omar a ƙofar gidan a tsaye, wannan dalilin ya saka aka tsaya kallo dan a ga me zai faru. Alhaji Yusuf ya fito ganin Omar shi kansa sai da gabansa ya yanke ya faɗi dan bai san dame yazo ba. Ya dake bai nuna tsoro ba ya kalli wanda ya yi sallamar ya ce, "Lafiya?." Omar jin maganar sa sai ya ƙaraso yana kallon sa ya ce, "Ka jawa matar ka kunne, kar ta dake faɗar abinda ta faɗa in ba haka ba zata yi dana sani." Alhaji Yusuf ya ce, "me tayi maka?." "Har gwara ace ni ta taɓa da zata fi zama lafiya, in ka tambaye ta zata faɗa maka. A dai ja mata kunne saboda gudun gamuwa ta gaba" abinda ya ce kenan ya tafi daga wajan. Yaron sa mai suna Tk ya kalli Alhaji Yusuf ya ce, "a ja mata kunne, Tiger gargaɗi ɗaya kawai yake yi. Tunda kaga yazo har nan tabbas Didi aka taɓa, ka tambayi matar ka abinda ya haɗu su zaka fahimta" yana gama faɗa ya bar wajan aka bar Alhaji Yusuf da sakaken baki yana bin su da kallo.         Kamar yadda ya faɗa cikin unguwar Yakasai suka shiga kasancewar magriba gabato garin a cike yake da ƴan kasuwa da ake dawowa. Har inda ya san ƴan dabar yakasai suna zama suka shiga, kai tsaye ya hango wanda yake nema ya ƙarasa wajan su yana kallon su kamar yadda suke kallon sa. Zama yayi a cikin su yana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ya kalli babban su ya ce, "Meyasa akuyar ka ta shiga gidana ta cinye min dusa?." Kallon sa ya yi ya ce, "Tiger ban fahimce ka ba." Tk da yake tsaye a baya ya ce, "Tiger yana magana akan yaron da aka kashe a nan bayan kun kwace wayarsa, ɗan arear Tiger ne." Kallon Omar ya yi ya ce, "Tiger afuwa ban mu san na ku bane da hakan bai faru ba. Ka gan shi nan yanzu maganar ma mu ke yi" ya faɗa yana dukan kan yaron. Omar ya kalli wanda aka nuna masa kafin ya dawo da kallon sa ga Jijiya ya ce, "Wanne mataki aka ɗauka akan hakan?." "Babu abinda mu ka yi a yanzu." "Ya zama dole a hukunta shi! Bazai kashe banza ba, kai ka san bazan ƙyale ba." Jijiya ya ce, "Haba Tiger duk an zama ɗaya fa, kuskure ne kuma baza a sake maimaitawa ba." Ya sauke ajiyar zuciya ya sake kallon Jijiya ya ce, "ya san an zama ɗayan ya kashe rai?." "Tiger kana da abin mamaki, meye aibu a kashe rai kamar yau aka saba?." "Ko ku bari hukuma tayi aikin ta ko mu mu yi aikin mu, wanne ku ka zaɓa?." Jijiya ya kalli Tiger ya ce, "yadda ka ce haka za a yi." Omar ya miƙe ya ce, "ku tashi mu je wajan ƴan sanda" Wanda ya aikata laifin yayi tsiru-tsiru da ido jin ana zancen ƴan sanda ya kalli Jijiya ya ce, "Haba Jijiya ai ba a yi min adalci ba." Jijiya ya kalle shi ya ce, "Kenan na bar ka da Tiger ya hukunta ka?." Kai ya sunkuyar cikin rashin abin yi, ya kalli Tiger da yake kallon wani wajan daban. Ya tuna kwanaki da wani ya aikata irin abinda ya aikata yaƙi yarda ya kai kansa ga ƴan sanda, aka bar shi da Omar yana da ƙafafunsa basa takuwa saboda sun tashi aiki. Omar ba ya kisa, amma za a yi maka abinda zaka gwammace kashe ka aka yi. Ajiyar zuciya yayi ya ce, "mu je ga hukumar." Omar ya koma gefe kamar ma bai san ana yi ba, tare suka tafi police station aka gabatar da mai laifi kamar yadda maganar ƙwace wayar ta zaga duniya saboda irin kisan da aka yiwa wanda aka ƙwacewa wayar. Video aka yi masa aka yaɗa a duniya ana tabbatarwa da mutane wanda ya yi kisan ya shiga hannu, kuma za a yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata.          A nan suka yi sallar magriba gabaɗaya, DPO yana ta yabawa Omar akan abinda ya yi, duk da an saba ire-iren wannan laifin ya kan kawo wanda ya aikata don a hukunta shi.  Shi kuwa ko maganar kirki samu daga gare shi ba burinsa a hukunta shi in ba haka ba shi ya ɗauki mataki.  Ya tsani yadda ake ƙwacewa mutane waya kuma a cutar dasu, kai da abin ka a ƙwace maka kuma a cuce ka saboda tsabar zalinci. In da iya ƙwacen ne ma da sauƙi, amma bayan a ƙwace sai an cutar da kai. Shiyasa baya ɗagawa kowa ƙafa akan ƙwace, ko da kana daga cikin yaran ka aikata sunan da ake kiran sa zai yi tasiri a kan ka. Damisa ƙi sabo!. Suna idar da sallah suka koma unguwar su kamar yadda suka saba. Waɗanda suka kalli video da aka yaɗa sai kallon Omar suke yi suna mamakin yadda wani lokacin yake yin aiki irin na masu hankali wani lokacin kuma ya yi aiki irin na ƴan daba. Tare suka shiga gidan da yaran sa su uku har shi na huɗu. A lokacin Didi tana zaune akan sallaya a tsakar gidan tana sauraron abinda ake faɗa a video da aka yaɗa na yaron da Tiger ya saka aka kama. Ganin shigowar su sai ta kalle shi ta ce, "ka ɗauko mu ku abinci." Bai ce komai ba ya nemi waje ya zauna dan sun san bazai dauƙo ba. Goje ne ya ɗauko abincin da kansa dan gidan ba baƙon su bane, babu inda basa shiga dan sune kamar ƴan aiken ta. Abincin ya kawo kowa ya zuba abincin yana ci. "Omar amma abinda ka yi ka kyauta sosai, ina nan ina fargabar kar ka ɗauko min magana ashe gyara ka je kayi. Da haka ka ke yi da ba ayi maka wani kallo na daban ba" Didi ta faɗa tana kallon sa. Numfashi kawai ya sauke bai ce komai ba sai tayi murmushi bata damu da shirun na sa ba ta ce, "Tukur meyasa bakwa yiwa mai gidan ku faɗa ne? Meyasa bakwa faɗa masa gaskiya?." Tk ya kalli Didi yana murmushi dan itace kawai take ce masa tukur a zauna lafiya, Tk shine sunansa ba Tukur ba. Ya ce, "Didi Tiger fa ba yadda ki ke tunani ya ke ba, mutum ne mai son zaman lafiya in kinga an samu matsala dashi akasi aka samu."         "Ba wani nan, kawai kana kare mai gidan ka ne, kuma bakwa faɗa masa gaskiya" ta kalli sauran da suke cin abinci suna murmushi ta ce, "Sai murmushi ku ke yi babu mai faɗa masa gaskiya a cikin ku, na tabbatar in Omar ya watsar da makaman sa kuma za ku watsar, domin kuwa ya zamar kamar shi ne komai na ku, in ya ce ayi kuna yi, In ya ce a bari kuna bari. Da tattara ku ya yi ku ka koma kasuwa duk da hakan bai faru, da nima na huta da ɗauko min maganar da ku ke yi." Ƴar dariya suka yi dukkan su dan in da sabo sun saba da wannna maganar ta Didi. Shi kam ko motsin kirki bai yi ba balle yayi magana abinci kawai yake ci. Da kansu suka kwashe mata kayan aka shiga dashi kitchen kafin su miƙe tsaye Goje ya ce, "Tiger zamu wuce." Shima tashi yayi suka fita gabaɗaya ta bisu da kallo tana yi musu fatan shiriya. Sallah i'sha tayi bayan ta idar ta kunna tv kasancewar suna da wutar solar, rana tsaka ta ga Omar da masu haɗawa aka haɗa a gidan. Da ta takura masa da tambayar inda samu kuɗi sai ya ce sadaka aka bashi. Ta kuma san gatse ya yi mata, kawai bazai faɗa bane shiyasa ta haƙura. Babu jimawa ya shigo da sallama ta amsa ya samu waje ya zauna ta kalle shi ganin yayi shiru yana kallon hoton da yake kafe a falon. Hoton su ne shida ita da mahaifiyar su a ranar da ya cika kwana bakwai a duniya. Ganin abinda ya ke kallo ya saka ta kalle shi ta ce, "ko dan saboda ita nake so ka gyara rayuwarka ka koma mutum kamar kowa saboda tayi alfahari da kai a ranar tashin qiyama. Ko dan saboda Mama da Baba...." Kafin ta ƙarasa ya kalle ta ya ce, "iya Mmaan dai, ki cire na ƙarshen." Da mamaki take kallon sa ta ce, "wai tsaya! Omar Baba ba shine ya haife ka? Meyasa baka so a dinga zancen sa kamar ba uban ka ba?." "Bai cancanci na dinga tunawa dashi ba ko kaɗan." "Mahaifin?." "Shi fa" ya bata amsa kai tsaye. "Me ya yi maka?." "komai ma" ya bata amsa yana ɗora ƙafa kan ɗaya.          "Omar ko dan saboda ƙasa da ta rufe idanunsa ya kamata ka manta da abubuwa da suka wuce a baya. Kuma abinda ka ke fushi a kai baka san an yi ba labari aka baka, amma ka ara ka yafa." Ya sauke ajiyar zuciya bai yi magana ba, ganin hakan sai ta canja batun ta ce, "Baba Adamu ya yi min waya ɗazu yana tambayarka na ce baka nan." "Waye haka?" Ya faɗa yana danna waya. Ta sake kallon sa ta ce, "Baba Adamu fa nace maka." Ya kalle ta yana ɗaga yalwatacciyar gashin girarsa ya ce, "Shine nace waye haka?." "Yayan mahaifiyarka." Ya girgiza kai ya ce, "ban san shi ba." Banza tayi masa bata sake magana ba dan in ta biye masa ranta ne zai zo ya ɓaci da irin waɗanan kalaman na sa marasa control. Jin ta yi shiru sai ya girgiza kansa ya ce, "ba dan ba dan ba ko....hmm." Jin abinda ya ce sai ta kalle shi suka haɗa ido ya ce, "bani da dangi a kaf duniyata, ke kaɗai ce dangina a kaf rayuwata." "Hmmm Omar kenan!." Ta faɗa kawai bata tanka masa ba, in ta biye masa taurin kansa ɓacin rai zai jawo mata, shi kuma ko a jikinsa gaskiyar abinda yake zuciyarsa ya ke faɗa. Tv take tana kallon a lokacin aka hasko fuskar wacce ta kunna tv domin ta a daidai lokacin tana cewa, "Sunana Narma Sagir Sani wacce ku ka fi sani da Barr Nass." Murmushi Didi tayi ta ce, "haka kawai Allah ya ɗora min soyayyar yarinyar nan a zuciyata. Bana kallon shirin nan amma saboda a shafin ta na instagram na ga ta ce yau za a saka interview ɗin da aka yi da ita ya saka na zauna." Kallon wacce take kallo yayi yana mamakin ko meye abin so a yarinyar nan da Yayarsa take son ta oho. Kallon sa tayi ta ce, "yarinyar nan bata burge ka?. Tana ƙoƙari wajan karɓar cases na ƙananun yara, sannan an ce bata taɓa yin rashin nasara ba a duk case ɗin da zata yi." Kallon tv ya yi ya kalli Didi ya ce, "Tunda ke tayi miki shikenan ai." Dariya tayi ta dafa kafaɗar sa ta ce, "ɗazu da safe da baka nan Oga Mansur ya sake zuwa gidan nan. Don Allah Omar ka daure ka koma harkar aikin kayan nan, aikin ya karɓe ka kana da nasibi sosai akai meyasa baza ka dogara da kanka ba?." "Bayan Allah akwai wanda na dogara dashi ne?" Ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba. Ta girgiza kai ta ce, "Babu, amma in da sana'ar aikin yin takalman nan ka ke yi sai an fi ganin girmanka da martabarka, saboda kowa ya san harkar sa'anarka ka ke yi babu mai yi maka wata magana ta banza. Aikin ya karɓe ka, ka iya fiye da tunanin mai tunani, meyasa ba zaka riƙe iyawar ka ba?." "Ni da ba sarki ko gwamna ba martaba da girman me zan nema? Tunda ina girmama kaina hakan ya ishe ni. Kuma ko a yanzu babu wanda ya isa ya yi min maganar banza, ai na wuce a kalli idona a yi min maganar da bata kwanta min ba. Ai ko kura ta rame ta wuce rainin karnuka, kuma duk lalacewar giwa ai tafi ƙarfin suya, balle giwar da lafiyar ta babu abinda ya same ta."  Zata sake magana ya ce, "Didi zaki ɓata bakin ki ne kawai, na wuce zama a ƙarƙashin wani, in zan yi sai dai nawa na kaina." Ta girgiza kai ta ce, "Tunda kai ba kowa bane zama a ƙasan wani ya zamar maka dole, kuma waɗanda ka ke so ka bawa haushi a rayuwa baza ka taɓa ɓata musu rai da ɗaukar wuƙa ko adda da zaman prison ba. Murna ma zasu yi in suna ganin har yanzu kana cikin wannan ƙasƙantacciyar rayuwar. Amma in ka gyara rayuwarka ka koma makaranta, Allah ya ɗaukaka duk mai son ganin ka wulanƙanta a wannan gaɓar ne zai ji haushi." Kallon idanun ta yayi na wani lokaci sai kuma yayi murmushi wanda fararen haƙoransa da suke a jere reras suka bayyana ya ce, "Didi baza ki gane ba." Kallon sa take yi ta ce,"Kar na gane Omar, Sai aukin iya karin magana kamar goyan Kaka." Murmushi ya sake yi ta sake kallon sa ta ce, "Murmushi yana sake fito da asalin kyaun ka Omar, Meyasa baka son yin murmushi sai wa ni kawai?." "Ba kowa ya cancanci ya gani ba." "Sai ni sai matarka?." Kallon ta ya yi jin kalmar mata da ta saka, ya ɗan sosa walwatacciyar girar sa kamar yadda ta zama al'adar sa na ɗora yatsu biyu akan goshin sa ya ɗan murza kaɗan amma bai ce komai ba. Didi ta ce, "Hmm! Zan ga matar da zaka aura dai Omar." "Au za a samu wacce zata aure ni?." Ta wara ido da mamakin kalaman sa ta ce, "Meyasa ka ce haka?." "Haka nan" ya bata amsa a taƙaice. "Za a samu mana Omar. Shiyasa nake so ka ajjiye wannan ɗabi'ar ta ka, in kana a haka ba ko wanne uba ne zai baka auren ƴar sa ba." Ya taɓe baki ya ce, "nima ba a wajan ko wanne uba zan nemi aure ba." Murmushi ta sake yi jin abinda ya ce dan kuwa ba a kayar dashi a bada amsa. Bata sake cewa komai ba sai sauraron muryar Narma da ake hira da ita akan yadda take gabatar da aikin ta da sauran rayuwar ta. "Gobe zan je Abuja." Kallon sa tayi jin abinda ya ce ta ce, "Abuja? Me ake yi?." Ya ɗora ƙafa kan ɗaya wani baƙin zare da yake ɗaure a ƙafarsa ya bayyana, yana ɗaure a tsintsiyar ƙafarsa kamar sarƙar ƙafa ta mata. Ya yi masa kyau sosai ya haska farar ƙafarsa matuƙa. Ya ce, "aiki." Didi ta ce, "wanne irin aiki ne haka? Wai me yake kai ka Abuja akai akai haka Omar?. A mota zaka je ko a  jirgi?." "Hmmm Didi kenan" ya faɗa yana ƴar ƙaramar dariya kana ya ce, "ai na wuce zuwa Abuja a mota tun tuni." Ta fuskance shi sosai ta ce, "Omar me yake kai ka Abuja haka? Daga fitowar ka daga prison ka je Abuja sau uku kenan. Me ka ke yi a can?." "Aiki ne yake kai ni." "Wanne irin aiki?" Ta faɗa tana yi masa kallon tuhuma kafin ya yi magana ta ce, "yaushe ka fara aiki babu labari? Yaushe ka fara ɓoye min abu?." Shiru yayi bai amsa mata ba ta ce, "Omar da kai nake fa, yaushe ka fara aiki babu labari sannan wanne irin aiki ne haka?." Kallon ta yayi ta ƙasan ido ya ce, "kin san ni ba ɗan kidnapping ba ne ba ko?." "Nima ban ce ba, amma me yake kai ka Abuja haka?." "Aiki ne yake kai ni can Didi." Wayarsa da take ƙara ya saka bata sake magana ba shi kuma ya miƙe ya fita. Mamaki take yi wanne irin aiki ne ya kai shi Abuja haka? Anya babu abinda yake ɓoye mata game da rayuwar sa?. Babu mai bata amsa sai shi ta kuma san babu lallai ya amsa mata.          Bai jima ba ya dawo ya koma inda ya tashi ta ce, "tunda baza ka faɗa min ba kaje ka kulle mana gidan kar a shigo mana." Kallon ta ya yi a kaikaice ya ce, "ai ko shekara gidan nan zai yi a buɗe babu halittar da zata iya shigowa da niyar cutarwa. Ko aljani sai dai wani gidan ba dai wannan ba." "Har da aljanu a masu tsoron na ka kenan?." "Hmmm!" Shine abinda ya furta kawai yana ɗan sakin fuskar sa kaɗan. "Ko bara almajiri baya shigowa saboda kawai ana jin tsoronka, ni dai ina nan ina yi maka addu'ar canji daga wajan Allah, wannan ɗabi'a har ina? In sha Allah canji yana nan zuwa rayuwarka. Ina yi maka fatan ka amsa kiran ƙaddararka da kuma rabo. Maƙota babu mai shigo min saboda kai, kowa tsoron ka yake ji." Bai ce komai ba yayi shiru muryar Narma na tashi a falon hakan ya saka ya sake kallon Tv kafin ya yi tsaki ya ɗauka kansa zuciyarsa na wani tunani daban. Babban burinsa a rayuwa bai wuce Didi tayi aure ba, amma auren ya gagara saboda baƙin fentin da yake ganin mahaifin su ya shafa musu. Shekarar ta talatin biyar amma bata taɓa aure ba, da an fara batun auren sai ya lalace, ya rasa meye dalilin hakan. Shi ba ya hango lamarinsa yana daga cikin dalilin da ya hana Didi aure, kawai abinda yake hange daban kuma ya tabbatarwa kansa da shine silar da ya hana Yayar sa yin aure. Numfashi ya sauke da ƙarfi hakan ya saka ta kalle shi ta ce, "ka je ka kwanta, Nima gobe ina da aiki zan yi jollop rice ta mutane ɗari, bacci zan yi." Tashi tayi ta barshi a falon ta shiga ɗaya daga cikin daƙuna da yake falon guda biyu. Tana shiga ta tsaya a jikin ƙofa tana goge idanunta cikin tausayin ƙanınta da ita kanta, Tabbas mahaifin su shine silar shigar Omar wannan hali saboda yawan aibata yaran mutane da yake yi Allah ya ɗorawa na sa. Amma ta tabbatar da Allah ne ya rubuta faruwar hakan a gare su, tana kuma sake gode masa yadda aka so su wulaƙanta a duniya basu wulakanta ba sun samu rufin asiri daidai gwargwado. Shi kansa Omar ɗin yadda aka so ya lalace bai kai haka ba, duk da ta san tasirin addu'arta ne da ta malaman islamiyyar da take zuwa su taimaka mata da addu'a kansa. Duk da ana kallon su a matsayin masu cin kuɗin haram amma ita ta san ba haram suke ci ba shiyasa maganar mutane akan wannan baya damun ta. Da wannan tunanin tayi alwala ta fito falon ta samu baya nan ta kashe kayan wuta na falon ta koma ciki.              Washe gari. Kamar yadda Omar ya saba bai cika bacci bayan sallar asuba ba, gari yana haske ya fita motsa jiki bayan ya dawo yayi wanka ya shirya. A lokacin Didi ta fito tsakar gidan shima ya fito ya shirya cikin ƙananun kaya kamar ko yaushe. Riga ce fara a jikin sa sai ta sama da ya ɗora baƙa mai zip amma bai kulle zip ɗin ba ya zama ana ganin farar. Sai dogon baƙin jeans da ya saka, sai takalmi wanda ya rufe ƙafarsa gabaɗaya. Kallo ɗaya in kayi masa baza ka ce yana taɓa dabanci ba saboda gabaɗaya yanayinsa bai gwada hakan ba, wani lokacin kana kallonsa zaka tabbatar da tantiri ne, wani lokacin in ka kalle shi sai kaga kamar ba shi ba. Murmushi tayi tana kallon sa kafin ya ce, "Ina kwana Didi." Sai da ta ƙaraso kusa dashi sannan ta ce, "Ka tashi lafiya?." "Lafiya lau, na shirya zan wuce, a yau zan dawo ba kwana zan yi ba." "Baza ka ci abinci ba?." "Uhum bana jin yunwa." Ta girgiza kai ta ce, "To Allah ya dawo da kai lafiya." "Amin. In akwai abinda ki ke so su Tk suna nan." Tayi murmushi ta ce, "To a dawo lafiya." Ya ɗaga kai kafin ya juya ya fita daga gidan. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t *Book 1* *P 03* *ABUJA* *11:00am.* Senator Sagir Sani yana zaune a babban falo mai kyau da ƙayatarwa ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana ƙadawa. Su biyu ne shi da wani abokinsa mai kuɗi da mulki kamarsa. Yanayin yadda suke magana zai baka tabbacin sun saba sosai. Sen Sagir ya kalli abokin na sa ya ce, "Wallahi shine abin ya dame ni, bana son zuwan Narma Kano gabaɗaya, kai ka san abinda ya faru kwanaki." Minister ya kalle shi ya ɗan dariya ya ce, "Haba Senator, yanzu meye abin damuwa a nan? Wancan lokacin ma ai akasi aka samu yanzu kuma baza a maimaita irin sa ba. Duk jam'ian tsaron da suke Kano sai hankalinka ya tashi dan Narma zata je can?." "Kai baka san yadda na tara maƙiya bane shiyasa ka ke faɗar haka." Minister ya sake yin dariya ya ce, "ko shekara zata yi a Kano babu abinda zai sameta, akwai fa masu tsarom lafiyar ta ka manta ne?. Akwai police da za a bata, in ta kama a bata sojoji ma duk normal ne ba abin damuwa bane." Sen ya kalle shi ya ce, "kuma fa haka ne. Ni na san da wanda zan haɗa ta." "To ka gani, meye na damuwa?." Wayar Senator ce tayi ƙara ya duba kafin ya saka a kunne ya ce, "Ya shigo mana." Sauke wayar ya yi ya kalli minister ya ce, "Yanzu mutumin zai shigo." Minister ya ce, "Waye kenan?." "Masu bada ransu a kan mu mana, wanda nake faɗa maka ina da shi a Kano." Minister zai yi magana Omar ya bayyana a falon da sallama cikin dakakkiyar muryarsa. A tare suka kalle shi suka amsa Senator yana kallonsa yana murmushi har ya ƙaraso ya zauna akan kujera kamar yadda suke akan kujera kana ya ce, "Barka da safiya Senator." Murmushi ya yi sosai ya ce, "Tiger! Ka tashi lafiya?." Omar ya ɗaga kai sannan ya ce, "lafiya lau" ya kalli Minister da yake kallonsa ya ce, "Barka da safiya." Minister yayi murmushi ya ce, "barka." Sen ya kalli minister ya ce, "minister wannan shine Tiger! Babban makami na a garin Kano, Tiger ga Minister" ya faɗa yana kallon Omar da burgewa. Minister ya ƙare masa kallo ya ce, "wai shine Tiger ɗin da ka ke bani labari ko yaushe?." Sen ya amsa yana kallo Minister shi kuma ya zare glasess ɗin idon sa yana kallon sa ya ce, "Wow! He seems really nice, babu wanda zai kalle shi ya ce he's the one. Kalle shi fa kyakykyawa kamar balarabe." Sen yayi murmushi ya ce, "shiyasa ake masa laƙabi da damisa, komai cikin nutsuwa ake gabatar dashi babu hayaniya balle ɓata lokaci." Minister ya sake kallon Tiger da yake kallon wani wajan daban kamar ba dashi suke magana ba, fuskar nan a cushe kamar ko yaushe. Minister ya ce, "Dan samari ka burge ni fa, gabaɗaya yanayin ka ya bani mamaki sosai." Kallon Miniter ya yi a kasalance ya ce, "na gode." Sen ya kalli Minister ya ce, "jiya baka ga ya saka an kama wani da ya ƙwacewa wani waya sannan ya kashe shi ba? Maganar da take trending kenan a media ai." "Yeah...yeah..I saw it. Ya bani mamaki sosai Sentor." Yayi murmushi ya kalli Tiger ya ce, "Tiger!." Ya jiyo ya kalle shi ba tare da ya amsa ya ce, "Daman magana ce akan zaɓen chairman da za a gabatar da kano. Kai ka san na mu shine a DPD so bama buƙatar wata damuwa da zata haifar mana da matsala shiyasa na kira ka." Omar ya kalle shi ya ce, "kamar ko yaushe zan maimaita, babu abinda zai faru. Amma mun jima da daina tayar da hayaniya a wajan zaɓe, an daina jiwa kowa ciwo, amma na tabbatar da komai zai tafi yadda ake so." Minister ganin yadda Tiger yake magana sai ya murmusa ya ce, "Tiger I like your confidence." Kallo minister yayi amma bai ce komai ba dan ba kasafai ya cika so ayi masa turanci ba, ba komai yake fahimta yadda ya kamata ba shiyasa baya so ma ayi. Senator ya sake kallon sa ya ce, "na san in kace babu matsala babu ɗin, shiyasa nake matuƙar jin daɗin aiki da kai." "Na gode" ya furta a taƙaice ba tare da ya saki fuska ba balle murmushi. Sen ya ce, "Magana ta gaba; Akwai daughter na da zata zo Kano biki next week,ina so duk inda zata je ka kasnace a kusa da ita saboda an taɓa attacking na kashe ta kwanaki baya. Nafi yarda da kai akan jami'an tsaro dan na san zaka fi bani abinda nake so. Kuma mutanen Kano duk sun sanka babu wanda zai kawo mata raini in tana tare da kai, Kana ganin kana da damar Hakan?." Tiger ya girgiza kai yana tunani, aiki da Sen yana matuƙar kawo kuɗi, shi kuma yana buƙatar su a yanzu. Zai karɓa ne kawai saboda kuɗi da yake so wanda ya ke adanawa saboda bikin Didi zai iya zuwa ko yaushe, kuma shine uba shine uwa a gareta, duk abinda ya kamata shi zai yi. Hakan ya saka ya ce, "Akwai dama, amma bana kwana a wani wajan in ba gida ba. Zan iya zama tare da ita daga safe har dare amma a gida zan kwana." "No problem, buƙata ta daman ka kasance da ita din a duk inda zata je, If possible ka zama mai kai ta ko ina." "Ka ɗauka an gama" ya faɗa yana kallon sa. Sen ya yi murmushi ya ce, "Dakyau Damisa!." Ɗan sakin fuska yayi kaɗan ya juya suka haɗa ido da Minister da tun ɗazu kallon sa yake yi dan shi mamaki yake bashi sosai, maganarsa da yanayin komai ya yi masa. "Hello Dad, how are you?" Narma ta faɗa tana shigowa falon amma sai ta tsaya cak ganin mutane biyu a zaune. Minister ya kalleta ya yi murmushi ya ce, "Our Barrister." Tayi murmushi ta ce, "Daddy good morning." "Morning my dear, how's your day going?." "Been good Dad. Ina ilham?." "Ilham tana Canada, tayi miki wayo ta tafi phd." "Oh Dad! I'm so tired from studying, I really need some rest" ta faɗa tana ɗan sauke numfashi kaɗa tare da juya ido alamun gajiya. Minister ya yi murmushi ya ce, "As your wish." Kallon Tiger tayi da yake zaune kamar bai san ma ta shigo ba amma a zuciyarsa yana so ya tuna inda ya san maganarta, dan tunda tayi sallama ya ɗau murya amma ya kasa gane a ina yana santa. Ita kuma Narma ta ɗauka tare suke da Minister hakan ya saka ta ce, "Hiiii" ta faɗa tana kallon Tiger wanda ya ɗago idanunsa ya watsa shi a cikin nata. Da sauri ta kawar da kai jin idanunsa a idonta kamar jan wutar lantarki, mamaki take yi waye wannan haka da idanunsa suke da ban tsoro a kallo ɗaya haka?. Shima ya ɗauke kansa ba tare da ya amsa ba dan lokaci ɗaya ya gane itace wacce suka gani da Didi jiya a tv. Sen ya kalle ta ya ce, "Narma ina aikin?." Cikin shagwaɓa ya ce, "Dad I need to talk to you about something ." "Alright, ki koma gida zan shigo in na gama." "Dad ka yi sauri." "Okay Daughter." Yana faɗa ta fita da sauri. Kallon Tiger ya yi sannan ya ce, "She's my second daughter Narma, Itace wacce nake maka magana a kai. Itace wacce na amince da kai na baka ragamar kula da ita." Omar ya kalle shi ya ce, "babu damuwa." Ya girgiza kai cikin gamsuwa dan ya gama amincewa da aikin Omar. Sen ya ce, "Akwai inda zaka je in ka bar nan?." Omar ya ɗaga kai alamun eh ba tare da ya yi magana ba. "Okay I think it's okay, zaka iya tafiya. In yaso in lokacin tafiyar na ta yazo zan sanar da kai. Zan tura maka kuɗin mota." Minister ya kalli Omar kafin yayi magana ya ce, "Tiger ya kamata ace ni na biya kuɗin motar zuwa garin nan, zan iya samun account number ɗina ka?." Omar ya kalle shi kai tsaye ya ce, "Me zai hana?." Ya karanto masa account number shi kuma ya saka masa kuɗi. Omar da ya ji ƙarar shigowar saƙo wayar sa ya ce, "na gode." Minister ya ce, "you deserve it, kar ka damu. Yadda ka ke yin komai a nutse ya burge ni sosai, Nima zan so na shiga cikin wanda za a dinga taimakawa." Omar bai ce komai ba ya kalli Sen da yake kallon sa sai ya ce, "Zamu yi magana Tiger, na san in kana nan babu matsala." Miƙewa Omar ya yi ya ce, "A duk inda nake matsala bata zama, koda tana wajan da naje zata kama gaban ta.Kamar yadda ruwa da wuta basa haɗuwa waje ɗaya haka ni da matsala bama zama waje ɗaya." Sen yayi murmushi cikin jin daɗi ya ce, "ni na san da wannan." "Na bar ku lafiya" ya faɗa yana fita da hanzari cikin takunsa na isa da ƙasata. Minister ya kalli Sen bayan ya fita ya ce, "Amma wannan yaron sam bai yi kama da ƴan daba irin na mu ba, Anya kayi bincike akansa sosai?. Ka duba fuskarsa fa, irin kyawawan mazan nan ne masu kwarjinin tsiya." Sen yayi dariya ya ce, "kai ka san bazan fara mu'amala dashi ba in ban san shi ba, na san shi tun da jimawa na kuma san komai akansa. A kaf kano tsoron yaron nan ake ji in dai a ɓangaren daba ne, har ta kai ta kawo ƴan sanda su kan neme taimakonsa a ɓangaren kama wani ko wani abun. Duk yadda ka kai ga jin kai jan wuya ne da yazo waje ya kalle ka ya ce ta shi ka bi wannan ɗan sandan sai ya je. Dabarsa mai tsafta ce duk da a sanin da nayi masa a baya yafi haka jagaliyanci. Jikinsa mai matuƙar tsafta ne, baza ka taɗa ganinsa ka ce ɗan daba bane, amma kallo ɗaya zaka yi masa gabanka ya faɗi." Minister ya ce, "Amazing! Ya burge ni sosai fa, especially yadda yake magana da izza kamar shi ne senator ɗin." "Bai yarda da wulaƙanci ba, tun farkon haɗuwa ta da shi ya faɗa min wannan. Kai baka ganin akan kujera nake akan kujera yake baka yi mamaki ba?." "Nayi mamaki sosai, na saba ganin thugs suna warin wiwi da sun ganka su zube a ƙasa suna magana mara kan gado, But he's different gaskiya." "That's why I choose him, kar ka yi mamaki in nace maka bai jima da fitowa daga prison ba." Minster ya ce, "a yadda ka ke bani labarinsa prison a wajan irin su ai is just normal, kamar a shiga gida ne a fito." "Ya yi hidima a lokacin zaɓe, yana daga cikin wanda suka bani kujerar da nake kai. Sannan ka san shi baya kisa a lamarinsa, in ya zauna a ake zaɓen ma ganin sa zawo yake saka maza balle ya ɗauko wuƙa. In kaga ya zubarwa da mutum jini shi ya so, Minister, totally Tiger is different" Minister ya yi murmushi ya ce, "I see. But yana da karatu?." "Bashi da ilimi, bana tunanin ya yi SSCE." "Ya aka yi ka ke mu'amala dashi kai da baka zama inuwa ɗaya da wanda bashi da karatu?." Sen ya yi dariya ya ce, "shi ai daban da sauran mutane. Shi rayuwarsa ya ke sadaukar min, dan in aka kashe shi akan aikin da yake yi min an kashe banza da wofi, kuma ina amfani dashi ne daga lokacin ya wuce shikenan. In ba dan haka ba shi da ganina sai dai in a waya." Dariya suka yi gabaɗaya minister ya ce, "Yaran ba su da hankali, muna gina rayuwar mu suna ɓata ta su." "Rashin ilimin kenan." "Kaga in ka haɗa Narma dashi babu sauran damuwa." Sen yayi dariya suka tafa kafin Minsiter ya ce, "Yaushe zamu yi bikin Narma ne?." Sen ya ce, "tana da damuwa, taƙi mayar da hankali a kai. Akwai ɗam Sarkin Gombe yana sonta amma wai Gombe tayi mata nisa, Ina jin dai da Asharfa ɗan gidan gwaman Katsina za a yi." Minister ya ce, "wow! yaron yana da hankali sosai." "Sosai ma kuwa, Maganar baza tayi nisa ba ina so ta nutsu sosai ne." "Hakan yana da kyau, a barta ta zaɓi abinda ta ke so." Daga nan suka cigaba da tattauna abinda ya shafe su kafin Dad ya shiga ciki minister ya fita. Dad yana shiga falon Narma ya kalla ya ce, "Daughter waye ya baki izinin yiwa Tiger magana a falo? Waye shi ɗinki da zaki kalle shi ki ce masa hiii? Shi bai miki magana ya girmama ki ba sai ke zaki yi masa magana?. What kind of nonsense is the?." Narma ta turo baki gaba ta ce, "Dad who's Tiger? I don't know him." "Guest ɗin da kika zo kika samu tare dashi a falo." "Ohh Dad! daman shine tiger din? But ba kace ɗan daba bane ba?." "Yes he's." "But dad, he looks so handsome and decent." Yayi tsaki ya ce, "look Narma! Ya kamata ki san matsayin da ki ke dashi, dan bai yi kama da ɗan daba ba ba haka yana nufin in kin ganshi ke zaki yi masa magana ba. Babu ruwan ki dashi, aiki yake yiwa babanki ya biya shi, bana son magana ta sake haɗa ki dashi kin ji ko?." Narma ta ce, "Okay Dad, Ka san halina, ni mutane ma ba isa ta kallo suka yi ba balle shi da ba mutum ba, Na dauƙa tare da Daddy suke tha's why na yi magana. But ba shine jiya ya saka aka kama wani a Kano ba?." Hararar ta yayi sai ta yi ziping bakinta ta ce, "Sorry Dad." Ya sake kallon ta ya ce, "what is your problem?." "Dad I need money." "Shine dalilin da ya saka ki ka bini falo?." "Yes. Zan yi order ashobi na bikin Samra." Yayi tsaki ya ce, "okay zan tura miki." Tayi murmushi ta ce, "thank you dad." "Ya maganar saurayinki Ashraf?." Narma tayi dariya ta ce, "yau zai zo." Sen ya ce, "zuwa yanzu ya kamata ayi magana ayi bikin ku ko?." Tayi farrr da ido ta ce, "okay dad." Da mamaki yake kallon ta jin ta amsa abinda bata taɓa amsawa ba ya ce, "are you ready?." "Sure" ta amsa tana kifta ido cikin murmushi. Sen ya kalli Mum ta da take shigowa falon ya ce, "My dear your daughter she's ready to get married." Mum ta yi dariya tace, "ya kamata daman ai" ta faɗa tana zama akan kujera. Narma tayi dariya ta ce, "Dad ya maganar zuwa kano?." Sen ya ce, "Yauwa maganar zan yi miki daman, Kin ga tiger ba?." "Yes dad." "To da shi zan haɗa ku a Kano ya zama escort ɗinki kuma driver, duk inda kika shiga yana tare dake na tabbatar bazai bari wani abu ya same ki ba." Mum ta ce, "Tiger! Kana so kace da ɗan daba zaka haɗa min yarinya?." Sen ya ce, "Nafi yarda dashi akan police, zai kula da ita bazai bari wani abu ya same ta ba." Mum ta ce, "this is bad idea Sen, Ta ya zaka haɗa ɗan daba da daughter suna shaƙar numfashi ɗaya? Matsayinsu ai ba ɗaya bane. Ta ya zai shiga motar da Narma take ciki? Hakan ai babban abin kunya ne kuma is so disgusting" ta faɗa tana yatsina. "Na sani, na kuma sam abinda nake yi. Kuma daman su aikin su su yi a biya su, in ba dan zai kula da ita ba ai ko kusa da ita bai isa yazo ba balle har ya samu damar yi mata magana. To na yarda da aikinsa hundrent percent, in nace kar ya bari wani ya kalle ta ma zai iya shiyasa na zaɓe shi. Kar ki damu wannan ba komai bane aiki ne kawai." Narma ta ce, "Dad ni tsoronsa ma nake ji, kuma ta ya za ka haɗa ni dashi bayan bana tunanin ya taɓa zuwa school?." Dad yayi dariya ya ce, "Daman ai ya kamata ki ji tsoronsa, yadda ki ke jin tsoronsa haka ake jin tsoronsa a duk inda ya je, Ganin sa kawai a kusa dake babu wanda zai iya yi miki magana. Kuma ba maganar school, dan bana tunanin ya yi secondry school." Mum ta wara idanu ta ce, "da jahili zaka haɗa min yarinya? Gaskiya ban amince ba." Dad ya ce, "haba dear, ki yarda dani mana na san abinda nake yi fa." Narma ta ce, "amma Dad sai ayi min dariya in aka gan mu tare." "Kar ki damu kowa ya san aiki yake miki a ƙasan ki yake." Narma ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "well, a wanne Guest house ɗin zan zauna? Kasan akwai friends ɗina da zamu zauna tare." Sen ya ce, "bana tunanin zan bar ki ki zauna a guests house, Ina tunanin ki tafi hotel kawai." Narma ta ce, "okay Dad, yadda ka ce" ta tashi tana hawa sana dan ta ɗauko jaka ta tafi aiki. Mum ta kalli Sen ta ce, "amma my dear meyasa zaka haɗa ta da wani ɗan daba for god sake? Meye haɗin ta dashi? Iya wannan bad smell ɗin ma da suka yi ai sai ya saka tayi ciwo, gaskiya hakan bai yi min ba." Sen ya ce, "wannan ɗan daban ba irin wanda ki ka sani yake ba, kuma aiki ne na lokaci kaɗan da ya ƙare shikenan ba sake ganin ta zai yi ba. Ni nasan matsayinsa bai kai ace yana jan Narma a mota ba, kawai zamu jure ne saboda lafiyar ta. Zai iya bada ransa akan kula da Narma, ko da kashe shi aka yi a maimakon Narma an fa kashe banza." Mum ta ce, "in ba dan aikin ba ina shi ina haɗuwa da Narma? Ai sai dai a tv." Sen to yayi dariya ya ce, "na san abinda nake yi kar ki damu." Ya faɗa yana tashi ya hau sama bayan ya saka waya a kunnen sa. ******* Nayla tana zaune tana shan tea tana danna waya Abiy ya fito falon yana kallon ta yana murmushi. Itama murmshin ta yi ta ce, "Abiy har ka fito?." Abiy ya ce, "To Mamana ta gama shirin tafiya Kano ba dole na fito ba." Nayla ta wara idanu da mamaki ta ce, "Abiy kai zaka kai ni?." Yayi murmushi ya ce, "Mun yi magana da Salisu jiya bazai samu damar kai ki ba, sannan Yayan ki Jawad baya nan balle ya miƙa k, Kin san ni bana barin sauran direbobin gidan nan su kai ku waje mai nisa dole ni zan kai ki." Mama ta shigo yana falon tana faɗin, "Abiy ban da dai kana so ka wahala ga direbobi a gidan nan sai kaje da kanka?." Nayla ta ce, "Abinda na gani kenan Mama." Ya girgiza kai ya ce, "kin san bana son driver ya kai ta Kano in ba Baba Salisu ba, nafi yarda ta tuƙinsa akan kowa. Jawad yana wajan aiki balle ya kai ta, Ahmad ma baya nan balle ya kai ta." Mama ta girgiza kai fuska da murmushi amma zuciyarta cike da baƙin cikin abinda ya ce. Abiy ya kalli Nayla ya ce, "ta so mu je, so nake ta je lafiya ta kuma dawo lafiya, ni badan ta matsa ba ai babu inda zata je saboda bana so tayi nisa da gida." Nayla tayi murmushi ta ce, "Abiy ai bazan jima sosai ba zan dawo." "Shikenan Mamana yadda ki ke so." Ta ajjiye mug ɗin hannunta ta shiga ɗaki sai gata ta fito da jaka ta tafiya ta kalli Mama ta ce, "Mama zan tafi" ta kalli Jalila ƙanwarta da Jalil ɗan autan su da suke fito tace, "zan tafi." "Allah ya kiyaye" suka faɗa a tare. Jalil ya ce, "Ya Nalya kar ki daɗe, in bakya na gidan nan babu daɗi." Murmushi ta yi ta shafa kansa tace, "an gama auta. Me zan taho maka dashi?." "Wannan donut ɗin da muka taɓa ci...." Ya faɗa yana jan sunan dan ta tuna. Ta yi dariya ta ce, "kar ka damu auta in sha Allah." Jalila ta ce, "Ya Nayla ni dai kunun Hajja nake so." Nayla ta yi dariya ta ce, "tun daga Kano zan yi dakon kunu...? Lallai sannun ki Jalila." "Allah ba don school ba sai na biki." "Wani lokacin sai mu je tare." Mama ta ce, "Nayla har na fara kewarki." Nayla ta ce, "Nima haka Mama" ta faɗa tana Rungumeta. Abiy da yake kallon su cikin murmushin haɗin kan ƴaƴan na sa ya ce, "to mu je." Nayla ta saki Mama tana cewa, "Abiy motata fa?." "A Kano zan bar ki ki ja mota? Gaskiya Nayla da sauran ki baki san ina ne Kano ba." Tayi dariya suka fito har harabar gidan ta shiga mota tana ɗagawa Mama hannu suka fita. Mama ta girgiza kai tana kallon bayan motar har suka fice ta ce, "Nayla lokaci dai, ki jira ki sha mamaki dan wallahi! wallahi! sai ma farraƙa wannan soyayyar da yake miki. Ki je ki dawo, sai na tabbatar da kin je gidan auren da zaki sha wahala, So nake ki ƙare a wahala har abada, bana so ki san daɗin aure ko kaɗan. Ina nan ina jiran ki!." *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t *Book 1* *P 04* Nayla da Abiy tafiya suke a mota a hankali kafin ya kalle ta ya ce, "Ummina." Ta kalle shi ta ce, "Na'am Abiyna." "In kin je Kano ban da yawo kin ji?." Ta ɗaga kai sannan ta ce, "in sha Allah Abiy." "Kin ga abinda ya taɓa faruwa dake a shekarun baya shiyasa na tsani zuwan ki kano, ki kula ba ko yaushe zaki gida fita ba." Nayla ta ce, "zan kiyaye in sha Allah Abiy." "Yauwa. Allah ya yi miki albarka ya jiƙan Ummanki." Ta amsa da amin kafin ya kalle ta ya ce, "zan saka miki kuɗi a account ɗinki duk abinda ki ke so sai ki siya." Tayi murmushi ta ce, "Thank you Abiy." Shima murmushin ya yi kana ya ce, "Ya batun Sadiq ne? Ban ji kin ce komai ba." Ta turo baki tace, "Abiy ya cika takura, kuma shi wai in na aure shi bazan yi aiki ba ni kuma gaskiya a'a" ta faɗa da shagwaɓa tana juyar da fuska gefe tana ƙifta idanu. Murmushi ya yi cikin ƙaunar ɗiyar ta sa ya ce, "Gaskiya bazai yu ba, ya kamata ki turo min shi mu tattauna." Ta sake ƙifta idanu wanda hakan ya zama ɗabi’arta tace, "A'a Abiy, ka ƙyale shi kawai." "To na ƙyale shi. Sai waye kuma?." Tayi dariya ta rufe fuskar ta alamun kunya ya sake yin murmushi suka cigaba da tafiya. Awa biyu da mintina ne suka kawo su Kano, har ƙofar gidan Hajja ya faka motar ya kalli Nayla bayan ya tsaya ya ce, "Ki shiga ki sanar da Hajja zan shigo mu gaisa." Nayla ta amsa ta fito ta ɗauki jaka ta shiga gidan dan ta sanar da Hajja zuwan Abiy ɗin. Da sallama ta shiga cikin muryar ta mai zaƙin gaske, Hajja da take alwalar sallar azahar ta amsa yana kallon wacce ta shigo. Nan da nan fuskar Hajja ta washe Nayla ta tafi a guje ta faɗa jikinta ta ce, "Hajja ta." Hajja tayi dariya tace, "Hauwa'u ke ce da ranar nan? Sannu da zuwa mutanen zazzau. To ɗaga ni kar ki karya ni." Nayla tayi dariya ta ce, "Abiy yana waje zai shigo ku gaisa." Hajja ta tashi daga inda take ta ce, "maza jeki ki ce ya shigo, ai ban san shi ya kawo ki ba." Nayla ta juya ta fita ba jimawa suka shigo tare da Abiy. A falo suka same ta Abiy ya zube a kan carpet ya gaishe ta. Hajja ta amsa da fara'a suka ta ce, "ya yara?." "Lafiya lau Hajja." "To ma sha Allah, Allah ya taimaka ya tsare." Ya amsa da amin kafin Hajja ta kalli Nayla ta tace, "Hauwa'u maza kawo masa ruwa a fridge, Yau Salma bata nan ta shiga kasuwa sai zuwa anjima zata dawo." Nayla ta ce, "Hajja ni fa shiyasa bana son zuwa wani lokacin, Na faɗa miki ki daina ƙara u ɗin nan a gaban sunana bana so." Hajja bata kula ta ba saboda sirikinta da yake wajan. Abiy ne ya yi murmushi ita kuma ta tashi ta ƙarasa wajan fridge ta kawowa Abiy ruwan roba harda lemo. Ya ɗauki ruwan ya riƙe a hannun sa. Hajja ta ce, "Na gode fa Abdullahi da ka kawo min ƴar rigimata." Abiy yayi murmushi cikin girmamawa ya ce, "Babu komai Hajja, Allah ya ƙara lafiya." "Amin ya Allah, Allah ya gafartawa Bilkisu." Da Abiy da Nayla suka amsa da amin kafin Abiy ya ce, "To Hajja zan wuce, ina so na shiga Kaduna kafin duhu ya yi." Hajja ta ce, "Da wuri haka? Na ɗauka sai anjima har zan yi waya a kawo maka gurasar Kano ka kaiwa yara." Yayi murmushi ya ce, "Babu komai Hajja, a kan hanya nake daman ita kawai na sauke zan koma." Hajja ta ce, "ikon Allah, daga zuwa har zaka koma kamar ba waje mai nisa zaka koma ba? Baza ka zauna ka ci abinci ba?." Murmushi ya sake yi ya ce, "Hajja kamar wani baƙo? Babu komai wallahi" ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ajjiyewa Hajja kuɗi sannan ya fita Nayla ta bi bayan sa. Yana jin godiyar da Hajja take yi yana murmushi har ya fita. Nayla da take bayansa ta tsaya kusa da shi ta ce, "Abiy Allah ya kiyaye hanya, Allah ya sauke ka Lafiya." "Amin Mamana, ki kula kin ji? Banda yawo. Kin ga yadda gari yake babu tsoro ƙwacen waya yayi yawa, duk inda zaki je kar ki yi dare kuma ki sanar dani. Ki kuma tabbatar driver Hajja ne ya kai ki ban yarda da hawa keke ba kin ji?." "İn sha Allah Abiy, Kuma daman Hajja bata barin fita da daddare." "Yauwa." "Allah ya kiyaye a gaishe da Mama" ya amsa yana shiga mota ya tafi.         Wajan Hajja ta koma tana cewa, "Hajja me ki ke dashi a gidan nan? yunwa nake ji wallahi." Hajja ta ce, "Sarkin ci, shiyasa ki ke ƙiba ai. Duba Salma tayi abinci kafin ta shiga kasuwa." Falon Hajjan ta shiga dan a ciki kitchen yake dan gidan Hajja gidan ƴan gayu ne. Hajja ta biyo bayanta sai ta same ta ta shiga da kayan ta ɗakin da take sauka in tazo sannan ta fito. Hajja ta kalle ta tace, "Baki zuba abincin ba?." "Sallah zan fara yi tukunna, wai Hajja ya gidan yau babu wuta ne?." "Wata waya ce ta solar ta katse har yanzu dai ba a zo an gyara ba." Nayla ta wara idanu ta ce, "wai kina nufin babu wuta a gidan nan?."          "Eh yanzu dai kam babu, Wataƙila sai gobe ko jibi." Nayla ta ce, "Innalillahi! Wallahi da na sani bazan zo ba sai an gyara, Ga wayata babu chaji ina zan saka?." Ta faɗa ido na cikowa da hawaye cikin shagwaɓa. Hajja ta harare ta tace, "Sarkin shagwaɓar tsiya, gabaɗaya Abiy ya shagwaɓaki. Ki yi sallah tukkuna sai a san abinda za a yi." Nayla ta ce, "wallahi Hajja gabaɗaya raina ya ɓaci, bana son zama babu chaji" ta faɗa tana komawa cikin ɗakin tana mita ta yi alwala ta fito tayi sallar azahar sannan ta ci abinci.        Kallon Hajja tayi da take kallon ta itama ta ce,"babu masu chaji a unguwar nan na kai?." Hajja ta ce, "a sace miki wayar ai." Nayla ta ce, "ni fa shiyasa ban cika son zuwa Kano ba wallahi, da na san babu wuta ai da na taho da power bank ɗina. Yanzu tsakani da Allah ta ya zan iya rayuwa babu chaji?." Hajja ta ce, "In kin huta zuwa la'asar sai ki shiga wajan Aisha ki saka chaji." Nayla ta ce, "wace haka?." Hajja ta kalle ta tace, "Didi." Nayla ta wara ido ta ce, "wannan mutumin yana nan zan shiga gidan? A'a rufa min asiri kar ya naushe ni, Itama Didin in ta shigo gaiahe ki ma gaisa." Hajja tayi dariya ta ce, "babu abinda zai yi miki, ki huta sai ki shiga." Nayla ta ce, "ni tsoronsa nake ji Hajja, Zuwana na ƙarshe harara ta ya dinga yi dan kawai ina hira da Didi. Didin ta fishi kirki shi bashi da mutunci, daman gashi da zubin abin tsoro." Hajja ta ce, "ke dai baza ki ce bashi da kirki ba, dan ya taimake ki taimakon da babu wanda ya taɓa yi miki shi a rayuwa." Ta turo baki ta ce, "ni wallahi ban so kuna tuna min wannan maganar" ta faɗa tana tashi ta shiga ɗaki. Hajja tayi dariya zuciyarta cike da farin cikin ganin jikarta ta.           Didi kuwa cikin lokaci kaɗan ta kammala sana'ar abincin da mutane suka saka order, mai delivery ya tafi kaiwa kowa tayi wanka ta gyara gidan kamar ba ita ce tai aikin ba. Sana'arta karɓe ta, tun tana yi da kaɗan-kaɗan har ta kai ta kawo wata ran sai ta yi abinci pack ɗari da hamsin ko ɗari biyu. Sosai ta ke samun alkhairi tana kashe matsalolin gabanta, babu abinda zata cewa Allah sai godiya. Shiyasa kullum in ka ganta fes da ita, daman ga ta ƴar gayu in ta yi kwalliyya sai ka kalle ta ka sake kallo saboda babu abinda ya fi ƙarfinta. Tana zaune bayan ta idar da sallar la'asar tana ta zullumin rashin kiranta da Omar bai yi ba tunda ya tafi Abuja, ta kuma san hakan ba halin sa bane ba. Sallama aka yi ta amsa tana jiran a shigo. Nayla ta shiga falon bayan ta sake yin sallama Didi ta amsa tana murmushi kafin ta ce, "kaii Nayla! Saukar yaushe?." Nayla tayi murmushi ta ƙarasa ta zauna ta ce, "ɗazu da azahar nazo Didi, Ina yini." "Lafiya lau Nayla, ya hanya?." "Alhamdu lillah." "Ma sha Allah, sannu da zuwa. Tunda kika koma Wancan lokacin baki sake dawowa ba, na cewa Hajja Nayla tayi mana yaji kenan." Nayla tayi murmushi ta ce, "Wallahi Abiy ne sam baya son zama na a Kano, kuma ga makaranta shiyasa dole ina can. A cikin kwanakin nan na kammala tahfiz ɗin da na shiga shiyasa." Didi tayi dariya ta ce, "baya so ki yi nisa dashi ne." Nayla murmushi ta yi kafin ta ce, "Didi don Allah zan saka chaji." Didi ta ce, "Kamar wata baƙuwa Nayla? Jeki ki saka mana." Nayla ta tashi ta saka chaji ta dawo ta zauna. Didi ta kalle ta ganin sai murmushi ta yi sai tayi murmushi itama ta ce, "kwanaki na ga kun sha biki sai rawa ki ke, na ce Nayla akwai son rawa." Nayla ta kulle fuskar ta tana dariya ta ce, "Didi ashe kin ga status ɗin." "Na gani tunda gashi na faɗa miki." Nayla ta sake yin dariya amma bata ce komai ba. Didi ta ce, "yanzu kuma na gama aikin abincin order bara na duba miki abinci." Nayla ta ce, "Na ƙoshi Didi, ina zuwa gidan Hajja na ci abinci." Didi ta ce, "Daman ke ai bakya cin abincina, baki taɓa ci ba, kullum kin ƙoshi ki ke cewa." "Ba haka bane ba wallahi, ina zuwa na ci abinci bana jin yunwa." "Amma dai zaki mana shekara ko?." Nayla ta wara ido ta ce, "taɓ! Ai ko sati biyu bana tunanin zan yi a nan." Didi tayi dariya ta ce, "Abiy yafi so ya dinga ganin ki kullum, da gaskiyarsa." Nayla ta murmusa tana jin daɗin zama da Didi, saboda mace ce mai fara'a da wasa ga saurin sabo. Ta zama tamkar jikar Hajja itama, tana matuƙar girmama Hajja sosai, ko me yake damunta Hajja take iya faɗawa ta bata shawara. Shiyasa duk wani mai zuwa gidan Hajja ya san Didi saboda gidan zuwan ta ne, ko biki ake a ɓangaren Hajja Didi na zuwa kuma an santa sosai. Didi ta miƙe ta shiga ɗaki tunawa akwai abinda zata yi tabar Nayla a zaune tana ƙarewa falon kallo.          “Wacece ke!?.” Abinda taji an faɗa kenan cikin kakkausar murya. A hankali ta juyo a firgice suka haɗa ido nan take gabanta ya yanke ya faɗi. Kafin ta tattaro abinda zata ce ya ware murya cikin tsawa ya ce, "Nace Wacece ke!? Me kika yi a zaune a na wajan?." Nayla tsabar tsoro bata san ta miƙe tsaye ba, jikinta na rawa nan da nan ido ya cika da hawaye abin ka da ƴar shagwaɓa. "Goje!, Tk!, Bash! kuna Ina!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallon ƙofa, sai gasu sun shigo falon da hanzari. Nayla ya nuna musu ya ce, "ya akayi wannan ta shigo gidan nan? Wacece ita? Kenan in bana nan barin kowa ku ke yi ya shigo!?." Goje ya kalli Nayla da har lokacin jikinta yake rawa cikin tsawa ya ce, "Ke daga ina ki ke!? Waye ya baki izinin shigowa gidan nan?." Numfashi take ja daƙyar hawaye na sakkowa daga idonta, ta saka magana balle ta iya cewa wani abun. "Ba magana ake miki!?." "Cha....ji....na....ka...wo..." a fusace Omar ya ce, "Nan gidan kawo chaji ne? Ku fitar min da yarinyar nan yanzu." Didi da take banɗaki take jiyo amon maganarsa da hanzari ta fito dan da tasan zai shigo baza ta bar Nayla ita kaɗai ba, ta san sai an yi haka. Tana fitowa falon ta ce, "Kar wanda ya taɓata." Cak suka tsaya da ƙarasowa inda Nayla take ta jawo hannunta zuwa kusa da ita sai kawai ta fashe da kuka ta kwanta a jikin Didi. Didi ta shafa kanta ta ce, "yi haƙuri Nayla, da na san zai dawo yanzu da ban barki ke kaɗai ba, Zauna" ta faɗa tana zaunar da ita akan kujera. Omar ta kalla fuska babu walwala ta ce, "kai wai meyasa ka ke haka ne? kenan bazan yi baƙi ba sai wanda ka sani?. Haka kawai daga dawowarka kazo ka fara yiwa ƴar mutane ihu ba tare da ka santa ba? Kenan bazan yi baƙuwa ba lallai sai ka santa? Meye haka ne?." Kallon Didi yayi amma bai ce komai ba ta kalli su Goje ta ce, "kenan ku ne masu yi masa gadina, sai baƙin da ku ka ga dama sannan zasu zo su ganni ko?." Zasu yi magana ciki tsawa ta ce, "ku fice ku bani waje!." Dole suka cika umarninta suka fita. Didi ta dawo da kallonta gare shi ta ce, "kar ka sake ganin baƙuwata ka sake yi mata ihu, in kai baka buƙatar baƙi ni ina buƙatarsu, wajena tazo ba wajanka ba dan haka babu ruwanka da ita." Wani irin yake ji a jikinsa da zuciyarsa, ya zubawa Didi ido cikin abubuwan da suka tarar masa a ƙirji. Na farko kukan da Nayla take yi yana daga cikin abinda yake sake harzuƙa shi, a ganinsa dan shagwaɓa shi zata saka a gaba tana yiwa kuka, me aka yi mata?. Na biyu faɗan da Didi take masa a gaban baƙuwa yafi komai ɓata masa rai. Ta fi kowa sanin baya so ayi masa faɗa a gaban mutane balle kuma mace baƙuwa wacce bai santa ba, babban abin haushin ma ko gaisawa bata tsaya sun yi ba ta fara yi masa faɗa akan wata wacce bata da alaqa da ita. Kallon Nayla ya yi a fusace ya ce, "dalla malama ki yiwa shiru ko na yanka bakin ki!." Wata irin firgita Nayla tayi sai gata ta dawo ƙasa daga kan kujera ta cure waje ɗaya jikinta na tsuma. Babu zato babu tsammani ta ji maganar shiyasa ta gigice. Didi ta sake fusata ta kalle shi ta ce, "Omar fita ka bar min falo." Ido ya waro waje jin mamakin abinda tace, a daidai lokacin da Nayla ta kalle shi sai ta sake gigicewa ganin idanunsa kamar za a saka hannu a cire saboda girma. Kafin ya yi magana ta sake cewa, "na ce ka fita ko!?." Bai ce komai ba ya juya ya fita a zuciyarsa yana tabbatar da dole ma ya hukunta Nayla duk da bai santa ba. Didi ta koma kusa da Nayla ta riƙe ta ta ce, "yi haƙuri Nayla, taso ki zauna." Ta faɗa tana taso da ita ta zaunar da ita akan kujera ta kawo mata ruwa mai sanyi ta ce, "sha ruwa." Ba musu ta karɓa tasha tana sauke ajiyar zuciya. Didi ta kalli gaishe ta sai ta bata dariya ganin hawaye shaɓe-shaɓe fuskarta har tayi ja kamar wacce aka yiwa duka. "Yi haƙuri kin ji, haka nan yake shi in yaga baƙo ko baƙuwa in bai san su ba shikenan sai faɗa. Ki nutsu ai ya tafi ki goge hawayen nan." Nayla ta goge idanunta tana jan numfashi amma har lokacin a tsorace take. Sai da Didi taga ta nutsu sosai sannan ta sake cewa, "kar ki damu bazai sake yi miki haka ba." Nayla ta ce, "ai bazan sake zuwa ba ma Didi, bara na ɗauki waya ta na tafi." Didi tayi dariya ta ce, "Wallahi babu inda zaki je, kuma in baki shigo gidan nan ba shi zan saka ya ɗauko min ke a wajan Hajja." Nayla tayi gum bata ce komai ba amma zuciyarta cike take da tsoron sa, bata taɓa ganin halitta ta mutane wacce take tsoro kamar sa ba. Ganin ta yi shiru sai Didi ta tashi ta shiga kitchen ta ɗauko abincin da ta dawo kusa da Nayla ta ce, "ko zaki kai masa abincin?." Yadda Nayla tayi da idanu cikin firgici ya bawa Didi dariya ta ce, "wasa nake kwantar da hankalinki" ta faɗa tana fita tana dariya dan wallahi yadda ta tsorata dariya ta bata. Setroom ɗin da yake gidan wanda ya kasance ɗakinsa ta nufa, kafin ta ƙarasa ya fito har yayi wanka ya canja kaya zuwa na shan isa, dan rigar jikinsa ko hannu bata dashi sai wando wanda ya wuce guiwa da kaɗan. Kallon sa tayi ta ce, "sai mu koma ka ci abinci." Bai kula ta ba sai ma sake tamke fuska da yayi yana kallon ƙofar ɗakin da alama tana ciki tunda ga takalmin ta nan. Didi ta ce, "Magana nake maka Omar." Nan ma ya share ta dan tsakani da Allah in ba dan ita bace da yanzu ba wannan labarin ake yi ba, ta bashi haushi sosai. Itama sai ta ɗaure fuska ta ce, "ina yi maka magana kayi min banza." "Me zan ce miki? Kin nuna waccan abar ta fi ni" ya faɗa cike da jin haushi. "To haka kawai daga ganin yarinya sai ka fara yi mata ihu baka san ta ba baka san daga inda take ba? kai baza a yi baƙi a gidan nan ba kenan?." Ya kalle ta ya ce, "duk wanda zai zo gidan nan munafuki ne, yana zuwa yaga ya muke rayuwa ni dake." Didi ta ce, "in ma hakan ne babu ruwan ka, kar wata baƙuwata ta sake zuwa kayi mata abinda ka yi yanzu, Wajena suka zo ba wajanka ba." Ya kalle ta ya taɓe baki ya nuna kansa da yatsa ya ce, "ni ki ka yiwa faɗa a gaban wata yarinya, ni kika yiwa tsawa har ki ka ce na bar miki falo kuma duk a gabanta. Ni ko Didi?." Didi ta kalle shi dama ta san zai ji haushi ta ce, "kaine ka jawo, lokacin da ka shigo da kun gaisa ka shiga ɗaki inda nake ai da hakan bai faru ba." Ya girgiza kai cikin ƙunar rai, baƙin ciki yake ji zuciyarsa, kamar shi tiger Didi ta yi masa faɗa akan wata banzar yarinya wacce bai ma santa ba. Ya kalli Didin da take kallon sa cike da ɓacin rai ya ce, "ni wai kika kora a gaban wata, ni Omar hmm....." ta kalle shi ta ce, "meye hmmm? Kar ka cutar da ƴar mutane, kar ka saka a zubar mata da jini."         "In ki ka ce kar ayi ɓata bakinki ke yi, zata san ta shigo gidan mu ta saka chaji har an yi min faɗa a gabanta. Nan gaba aka ce ta shigo baza ta yi wannan marmarin ba." Ganin yadda yake cize baki yana maganar ya saka Didi ta ajjiye abincin da ta taho masa dashi ta riƙe hannunsa ta ce, "Omar kar ka saka ka cutar da ita, na faɗa maka kar ka yi mata komai." A fusace ya cire hannunsa daga nata ya ce, "to meyasa zaki yi min faɗa a gabanta? Meyasa?. daga wani gari na dawo ko tsayawa baki yi mun gaisa ba ki ka fara yi min faɗa." Didi ta ce, "shikenan nayi kuskure, amma kar ka yi mata komai na sake faɗa maka." Kai ya girgiza dan maganar bata wani shige shi ba ganin haka Didi ta ce, "wai baka gane ta ba ma?." Kallon ta yayi alamun na san ta ne daman, ta ɗaga kai dan tana fahimtar saƙon ido in ya yi mata tunda ya saba ta ce, "ka san ta mana, Nayla ce fa jikar Hajja. Yarinyar da aka taɓa ƙoƙarin yi mata fyaɗe ka cece ta ka dawo da ita wajan Hajja?. Ka tuna har ka dinga yiwa Hajja faɗa akan ne aka barta ta fita ita kaɗai bayan a san baƙuwa ce bata san gari ba, ka tuna?." Kallon Didi yayi jin abinda take cewa dan ya tuna abinda ta ce ɗin tsaf a ransa, har hango lokacin yake yi a idanunsa da yadda komai ya faru. Amma bazai gane ta ba, dan a yanzu ma ba ganin fuskarta ya yi sosai ba, gwara ma a da ɗin ya san fuskarta saboda suna haɗuwa bayan abin ya faru tana yawan zuwa wajan Didi kafin ta bar garin. Bazai manta da ita ba dan ta silar ta ya fara yankewa wani ɗan yatsa a duniya, tabbas a kanta ya fara zubar da jini saboda ceto. Batu ake na shekara tara zuwa goma baya ta ya zai gane ta banda abin Didi?. "Ni ban san ta ba, ina kallonta a matsayin wacce ki ka yi min faɗa a gabanta" Abinda ya ce kenan ya wuce ya barta a wajan tayi dariya tana jinjina son girma, da son mulki, da zafin kai irin na ƙanin nata, abincin ta shigar masa dashi ɗakim sannan ta koma wajan Nayla. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t *Book 1* *P 05* Didi da ta bar wajansa wajan Nayla ta koma ta zauna kusa da ita ta ce, "na bar ki ke kaɗai ko?." Ganin Nayla a tsorace har lokacin sai ta tausasa murya ta ce, "har yanzu a tsorace ke ki ke? Ki nutsu mana." Nayla ita dai gaban ta faɗuwa yake saboda duk abinda suke faɗa tana ji, tana ji Didi tana ce masa kar ya yi mata komai duk shine ta sake firgita. Dana sanin shigowa gidan ta mamaye mata zuciya, ji take ina ma bata shigo ba ta haƙura da chajin wayar. Didi ta kalli Nayla ganin har lokacin tsorace ta ke sai tayi dariya ta ce, "Wallahi dariya ki ke bani, yadda ki ka firgita haka kamar kin ga wani abin tsoro, In kina nuna kina tsoronsa har haka sai ya fi cewa zai latsa ki. Omar fa yana da sauƙin kai, kawai shi bashi da saurin sabo ne, amma na tabbatar miki kafin ki bar Kano zaku saba, Zaki yi mamakin yadda yake da hira da kuma yawan murmushi." Murmushin yaƙe kawai Nayla tayi dan kawai tana jin ta ne, amma ta yaya zasu saba da dashi bayan abinda ya faru. Didi ganin tayi shiru ta dinga jan ta da hira kaɗan-kaɗan tana amsawa duk da har lokacin a tsorace take matuƙa. Agogo ta kalla sai ta kalli Didi ta ce, "Didi bara na ɗauki wayata na tafi saboda zan kira Abiy na ji ya koma gida lafiya." Didi ta kalle ta tace, "Ko dai kina so ki gudu saboda Omar?." "A'a Didi, Abiy zan kira na tabbatar yana jiran kira na." "To Shikenan. Ina jiranki da daddare ki zo ki taya ni hira." Nayla ta ɗaga kai kawai ta tashi ta ɗauki wayarta da charger tayi hanyar fita Didi na bayanta. Tana fitowa daga falon yana shigowa gidan idanunsa ya faɗa cikin na ta. Nayla bata san lokacin da wayar charger sun suɓuce a hannunta ba, wayar ta faɗi ta ɗan yi ƙara amma bata duba ba jikinta ya cigaba da rawa. Hannunta Didi ta riƙe ta bayanta, Nayla ta sunkuyar da kai cikin tsoro. Didi ta kalle shi bata ce masa komai ta kalli Nayla ta ce, "Nayla don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga kin yar da wayarki" ta faɗa tana sunkuya ta ɗauki waya da charger ta riƙe mata hannunta har suka bar cikin gidan. Ai Nayla bata iya cewa Didi komai ba, tana bata wayar ta kwasa a guje ta yi hanyar gidan Hajja. Didi tayi dariya ta dawo cikin gidan tana dariya suka sake haɗuwa da shi cikin dariya ta ce, "Kaji tsoron Allah ka daina tsorara yaran mutane don Allah, haba wannan bala'i daga haɗa ido da kai duk ta ruɗe?. Ni ban ga meye abin tsoron a nan ba." Bai ce komai ba ya sake shiga cikin gidan tayi dariya ta bi bayansa tana jinjina ƙarfin tsoron da Nayla take masa. Nayla a haka ta faɗa cikin gida a firgice Hajja da Salma da suke zaune a falo suka ganta kamar an cillo ta Hajja ta ce, "ke lafiya?." Nayla ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Hajja har abada bazan sake shiga gidan Didi ba, na gama shiga gidan ko me za a bani." Salma ta wara ido ta ce, "shiyasa daman da Hajja ta ce min kina can nace wallahi bazan je ba, in yaga ka shiga gidansu kamar zai yanka naman ka haka yake ji. Sam baya so ya ga an shiga gidan, ba ya ƙaunar kowa ya shiga gidan su daga shi sai Didi." Nayla ta ce, "wallahi Salma fitsari ne kawai ban yi ba, yau ni naga bala'i ganin idona. Salma duba min wayar nan ki ga ko screen ɗinta ya samu damuwa, dan yadda ta faɗi a hannuna da na ganshi na tabbatar daƙyar bai fashe ba. Wannan halitta ta mutumin nan akwai ban tsoro, ga ido kamar na aljanu." Salma ta karɓi wayar da take miƙa mata dubawa kana ta ce, "Wallahi ya tsage. Wannan bala'i har ina? daga gidan su ya jawo miki asarar sama da naira dubu ɗari biyu. Dan screen ɗin wayar ki in bai yi haka ba ya kusa." Nayla ta faɗi akan kujera ta dafe kai ta ce, "gabaɗaya ban shigo Kano da ƙafar dama ba, da fari gidan nan babu haske, ga tashin hankalin da na haɗu dashi sannan ga asara." Hajja da take jin ta take kallon ta tayi dariya ta ce, "wai duk tsoron Ummarun ne ya saka ki ka firgice haka?." Salma ya ce, "ba dole ba Hajja, wannan mutumin kallon sa ma tsoro yake bawa mutane balle kuma ya harare ka ko yayi magana. Ni na jima ban ga mutum bai baƙin hali kamar sa ba, sai kyaun fuska kamar shi ya tsara kansa, amma zuciya da hali baƙaƙe." Hajja ta ce, "ai kam yana da kirki sosai, kaf unguwar nan ni kaɗai ce nake kiransa da Ummaru ya amsa har yayi min magana. Duk da nima ɗin kafin ya amsa sai ya ce bana son sunan amma sai na faɗa, kuma zai gaishe ni wani lokacin da fara'a sannan ya tafi. Kawai shi baya so a raɓi yayarsa ne saboda mutanen unguwar nan suna yi musu wata fassara mara daɗin ji. Shiyasa sa baya son kowa ya shiga gidan su dan baya ƙaunar munafurci da gulma." Nayla ta ce, "to mu ina ruwan mu da wata fasaara da ake musu Hajja? Shima ya san in ba dan Didi ɗin ba waye zai shiga gidan nan? To Didi tana da kirki sosai, tun ɗazu naso fitowa amma ta hana ni ta ce sai yanzu zan fito, shima ƙaryar zan kira Abiy ne ma ya saka ta ƙyale ni. Har tana cewa na dawo da daddare, to in ba aljanna ake bayarwa ba me zai kai ni gidan nan na ta?." Salma ta ce, "bashi da mutunci bai san mutunci ba, ai ko dan yayarsa ya kamata ya dinga ɗagawa mutane ƙafa. Ni fa shiyasa wallahi bana ma shiga gidan dan bana so na haɗu dashi kwata-kwata, In ta shigo gidan nan ta dinga yi min mitar bana shiga inda take, kin san ni babu ɓoye-ɓoye kai tsaye na ce mata Omar yana gidan bazan iya shiga ba.." Nayla ta ce, "ina yaga kirki? shi ai abin alfaharinsa ne ma a shiga gidan su. Nima ba dan chaji ba da sai dai ta shigo ta ganni, duk abinda zata ce bazan je ba." Hajja tayi dariya ta ce, "ke dai kawai ya firgita ki ne Hauwa'u." "Wallahi sosai Hajja, haka na saka Didi a gaba ina kuka tana rarrashi." Hajja tayi dariya sosai ta ce, "ke fa babu abinda zaki cewa Omar wallahi, ya taimake ki a lokacin da ake gab da tuntsurar miki da budurcinki. Ba dan shi ba da yanzu ana zancen an yi miki fyaɗe shekarun baya." "Hmmm!" Shine abinda Nayla tace kawai tana sauke numfashi. Salma ta ce, "Kai Hajja! daman wai shine ya taimake ta?." Hajja ta ce, "Ke duk labarin da ake yi baki sani ba?." "Ban taɓa tsayawa na fahimta ba ai." "Shine wallahi. Haka ya ɗauko ta kamar jaririya saboda a tsorace take sosai sai kuka take yi daman ita sarkin shagwaɓa. Gashi babu riga a jikinta sun yaga rigar atamfar da take jikinta, hakan ya saka shi ya cire rigarsa ta sama ya saka mata sannan ya dawo da ita." "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Don Allah Hajja ki daina faɗar haka bana so wallahi" Nayla ta faɗa da ƙarfi tana runtse ido. Salma ta sake cewa, "Hajja wai kina nufin rigarsa ya sakawa Nayla?." Hajja ta ce, "ƙwarai kuwa." "Tab! amma ya cuce ta wallahi." "Meye na cuta shi da ya yi taimako? Kuma magana ake ta shekaru takwas ko tara baya." "To Hajja shekara tara baya a ƙalla tana da shekara sha uku ko sha huɗu." Hajja ta kalli Nayla da har lokacin idon ta yake a kulle ta ce, "Kuma da yake tana da girman jiki ƙirjinta a cike yake shiyasa ma suka so lalata ta." Nayla tashi tayi ta bar falon cikin takaici da baƙin cikin wannan labari, ta tsani ta ji ana bada labarin nan ko kusa. Salma ta ce, "Gaskiya Hajja ki daina bada labarin nan, hakan yana nufin fa ya gama ganin halittarta tun shekarun baya. Yanzu kallon raini yake mata shiyasa ma yake tsoratata." Hajja ta ce, "to sai me? Da ya gani ɗin wani abun yayi mata? Da ya barta a wajan su da ba lalata ta zasu yi ba?. Ni tun daga lokacin nake ƙaunarsa saboda abinda ya yi mata, daga ranar ya fara riƙe amfani da makami dan a kanta ya fara zubar da jini, akan taimakon ta ya fara saka makami a jikin mutum. Haka yazo gidan nan yana faɗa kamar ƙanwar sa aka ao cutarwa. Ni yayi min, kuma har gobe ina kallon sa da wannan ƙimar." Salma tayi shiru bata ce komai ba Hajja ma tayi shiru dan da alama tana taya ƴar uwarta kishi dan ance ya ɗauko ta babu riga. Ita kuma bata ga abin fushi ba, taimako ne kuma ya wuce wataƙila ma shi ya manta. Omar kuwa bayan Nayla ta fita shima fita ya yi bai dawo ba sai bayan an yi sallar magriba as usually shi da mutanen sa. A falon ta suka baje suka ci abinci kamar yadda ya saba ciyar da su kafin ya sake fita. Bai dawo ba sai tara na dare ya same ta a zaune da waya a hannunta tana dannnawa. Kallon sa tayi bayan ya shigo ta ce, "baka faɗa min me ya faru a Abujaa ɗin ba." Zama yayi ya kalle ta ya ce, "wani ɗan aiki zan yi zuwa wani satin." "Allah yasa ba harkar siyasa ba ce ba." Murmushi yayi kaɗan amma bai ce komai ba. Ta kalle shi ta ce, "ina so ka gane ƴan siyasar nan amfani suke yi da ku wajan lalata rayuwarku su kuma su inganta ta ƴaƴan su, ku ɗauki makami ku je ku yi musu yaƙi su kuma su gina yaran su da ilimi. Kuna nan kuna wahalar banza kuna haƙilo ƴaƴan su suna gida cikin ac da kwanciyar hankali, ku kuma sun mayar da ku ƴan wahala waɗanda ba su san darajar kan su ba. In da gaske yaƙin neman zaɓen su ke yi su fito a yi da ƴayan su mana. Baza su yi ba saboda rayuwar ƴaƴan su ba irin ta ku bace, aikin ku ku salwantar da rayuwarku a kan su, su kuma su gina na su." Kallon Didin yayi ya ce, "Didi kenan." "Ko nayi ƙarya ne?." "A'a" ya faɗa yana ɗauko wayar sa ƙirar iphone yana dannawa. Didi ta kalle shi ta ce, "Ni wai ya aka yi ka ke iya operating ɗin waya? Gashi ko labarai ne da turanci sai na ji ka karanta ka faɗa min, ya abin ya ke?." Ya kalle ta da mamaki ya ce, "Oh dan bana so ana yi min magana da turanci shiyasa ki ke yi min kallon ban iya ko?." Ta yi ƴar dariya ta ce, "A'a ban ce ba. Kawai dai na san ko secondary school baka yi handling ba, duk da ka ce jarabawa ce baka yi ba." Ya kalle ta ya ce, "Ai kin san jarabawar ce ban yi niya ba, kuma mutum nawa na rubutawa waec ana biyana?. Ko ke da ki ke taƙama da wani NCE ko diploma sai mu zuba, wallahi sai na kai ki ƙasa ko motsi baza ki iya ba. In kina mamaki a feɗe biki biri har wutsiya." Ta yi dariya sosai ta ce, "Wane mutum! Ku ai gifted ne, ku karatu yake bi kuna guduwa. Da ka tsaya ka yi karatu ko Omar, da ba ƙaramin amfana za a yi dakai a ƙasar ka ba." "Babu niya, tunda sai wanda yake da ilimin boko ne yake zama wani a duniya zan ta zama a yadda ku ke kallona." Didi ta ce, "Allah ya ke bawa kafirai arzuƙi a duniya balle musulmi mai bauta masa?. Allah yana bada duniya ga wanda yake da wanda baya so, lahira ce sai rabo. Ba sai mai karatun boko ne yake zama wani ba Omar, in dai Allah ya saka maka albarka zaka iya zarce wanda ya kai matakin professor. Ilimin yana da amfani ne saboda goyayya da mutane." "Mutane haka suke ɗauka, wanda bai yi boko ba babu shi babu arzuƙi a duniya. Turanci ne kaɗai ilimi a nigeria, duk ilimin ka in baka iya shi ba a banza ake kallon ka. Mu baza mu yi karatun ba, kuma baza mu yi turancin ba, in Allah ya ce yes sai na ga ɗan shegiyar da zai ce no. Ko yanzu in niya zan je a bani takardar da ku ke taƙama da ita, kawai babu niya ne." Didi ta yi dariya cikin tsokana ta ce, "Ni dai ina so naji ya akayi ka ke iya karanta turanci? Ko duk zaman social media ɗin ne ya kawo haka?. Yadda ka ke zama ko yaushe cikin danna waya da kuɗi ka ke samu da ita da ka ji daɗi." Murmushi ya yi kaɗan bai ce komai ba. Ta ce, "tsokanarka nake, ko a shekarun baya kana cikin wanda makaranta take ji da ku." Bai bata amsa ba sai girgiza ƙafa da yake yi, ta kalli ƙafar ta sa ta ce, "wai ni meye benefit ɗin wannan baƙin abun da ka saka a ƙafarka? Gashi dai yana yi maka kyau sosai, amma adon mata ne." Taɓe baki ya yi bai ce komai ba ta ce, "ko da yake ko mace aka gani da sarƙar ƙafa wata fassara ake mata daban." "Ni kam yana burge ni." "Sai matarka ta saka." Bai ce komai ba cikin tsokana ta ce, "Wai kuwa ka san me aure yake nufi?." Wani kallo ya ɗago ido yake mata na kin raina min hankali, Didi ta sheƙe da dariya ta ce, "to kai ba abokai ne da kai ba, ba wani waje ka ke zuwa ba ta ya zaka fahimta daidai?." Murmushi ya yi bai kula ta ba dan bazai kulata ba. Kira ne ya shigo wayar Didi ganin sabuwar number sai ta ɗauka masu siyan abincin ta ne, ta saka a speaker daga can ɓangaren aka yi sallama jin muryar namiji sai ta amsa a sanyaye kafin ya ce, "don Allah da Aisha nake magana?." Didi ta ce, "eh itace. Wake magana?." "Sunana Abdulhamid." "Allah sarki!." "Aisha ina so ki bani lokaci ina so zan yi magana dake." Didi ta kalli Omar da ya kafa mata idanu ta ce, "Magana da ni? Akan me?." "Alkhairi. Magana a waya baza ta yu ba ikon ganin ki nake so ki bani." Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "To san sanar da kai." "Yauwa na gode, don Allah ki saka lokaci mafi kusa in hakan zai samu." "Shikenan, zan maka text." "Na gode sosai, ki kwana lafiya" Didi ta amsa shi kuma ya kashe wayar. "A ina ya samu number ki?" Omar ya tambaya yana kallonta. "Omar ta ya zan sani? Ni dai kawai ya kira ni ne." "Me ya ke nema?." "Omar ta ya zan sani? A gaban ka fa ya kira ni." Omar ya ce, "wanne lokaci zaki ba shi?." "Bana ce ba." Ya kalli Didi cikin bada umarni ya ce, "ki faɗa masa yazo jibi, jibi juma'a kenan, ina gida nan zan so na zauna a tatauna dani. In da tsiya ya zo gidan ya tarar, in arzuƙi ne ya kawo shi ana yi masa maraba." Tayi murmushi ta ce, "to babban Yaya." Jin abinda tace sai yayi murmushi amma bai ce komai ba. "Kai yaushe zaka yi auren ne?." Ya ɗan juya idanunsa ya ce, "kwana biyu meyasa ki ke yi min zancen aure ne?." Tana murmushi ta ce, "ai ka kai ka yi ɗin ne Omar, santalelen saurayi kamar ka ga kyau ga kwarjini ai dole ayi maka zancen aure." "Ni wallahi bana kawo zancen aure a raina ko kaɗan." "Ko me yasa?." "Sai na fara aurar da ke" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Ƴar dariya tayi ta ce, "Ko kuma ni na fara aurar da kai ba." Bai yi magana ba ta miƙe tsaye tana kallon sa duk da ya kere mata a tsayi sosai ta ce, "burina naga kayi aure ka haifa mana mai sunan Mama Omar, duk macen da ta same ka zata yi sa'a, a haka ne ake kallon ka a baibai amma ni da na san ka, na san sa a tana tare da wacce zaka aura, musamman in ka ɗauki nasihar da nake yi maka a kullum." Fuska sake yake kallon ta ya ce, "Yanzu in aka aure ni ba a yi sa a ba kenan?." "Eh to, kusan hakan zan ce." Yayi murmushi mai sauti ya kalle ta ya ce, "ina zuwa." Fita yayi daga gidan gabaɗaya. Kasancewar unguwar akwai duhu da ya fito ƙofar gidan daga wajan gidan su ne kawai mai haske sauran wajan babu haske. A hankali yake takawa yana jiyo magana na tashi ana daga inda yake nufa, muryar maza ya ji suna cewa, "hmm to Omar da Aisha meye basa aikatawa, kai a banza ta kai yanzu bata yi aure ba?. Wannan ingarmar namijin da take kwana dashi waje ɗaya ta tashi ba dole mugun abu ya faru ba." Ɗaya daga cikin su ya ce, "wai don Allah da gaske ku ke?." Na ukun ya ce, "to kai gani ka ke wasa ne? Baka ganin yaron ko kula mutane baya yi saboda ya san iskancin da yake yi?. In da ma ace iya dabancin ya tsaya da sauƙi, to har da lalata da ƴar uwarsa. Ai ba a banza ta kai wannan shekaru babu aure ba, tana samun duk abinda ƴa mace take samu a gidan mijinta a wajansa. Kai baka ganin da an zo neman aurenta sai a gudu ba? Wannan mugun abun da suka binne ake tonowa." "Kuma fa ashe gado ya yi, ubansu tantirin ɗan iska ne tsohon ɗan giya. Ai barewa baza tayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, nan gaba zaman unguwar nan sai Omar ya hana mu." Omar yana jinsu ya runtse idanu cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya, ya koma da baya ya hangi yaransa a gefe yayi musu alamun da su yi shiru kar su yi magana su zo inda yake. Nuni ya yi musu da kowa ya kama mutum ɗaya a cikin ƴan majalisar da suke gulmarsu. Cikin sanɗa suka ƙarasa inda suke sai caraf ko wanne ya riƙe mutum ɗaya. Omar ya tako ya bayyana a gabansu ransa a ɓace sosai duk suka kalle shi cikin firgici da tsoro. Alama yayi musu da su sake su, dukkan su suka sake su ya bisu da kallo dan dukkan su manya ne a haife zasu haife shi. Babu wanda yayi ƙoƙarin miƙewa a cikin su saboda duk sun tsorata matuƙa suna kallon Omar. Abin ka da wanda yake gulmar wani kuma ya kama shi, wanin ma kuma irin Omar." Tsakiyar su ya shiga ya zauna tare da ɗauko ƙaramar wuƙa a ƙasan takalmin yana shafa ta a hankali ba tare da ya kalle su ba. Duk sun ruɗe, jikinsu ya fara ƙyarma cikin tsoro. Zaman da ya yi a cikin su yafi komai tsorata su, ga wuƙa kuma a hannunsa. Ajiyar zuciya Omar ya yi, ya daidaita kansa kana ya ce, "Ku maimaita hirar da naji kuma yi yanzu." Tsit suka yi kowa ya kasa cewa komai, Omar ya kalli ɗaya daga cikin su sai kawai ya zube a ƙasa saboda tsoro jikinsa na rawa sosai. "Ku maimaita na ce" ya sake faɗa a kausashe yana kallon su. Nan ma suka yi shiru ya girgiza kai ya ce, "kenan kun san ba daidai ku ke faɗa ba ko? Shikenan, tunda baza ku yi magana ba bara na saka a saka ku magana." Kallon na gefen sa ya yi nan take suka taho da wuƙa suka ƙaraso wajan. Omar ya sake kallon mutanen yaga duk sun tsorata gasu kuma manya dan suna cikin manyan unguwar. Ɗaga musu hannu yayi alamun kar ya ƙarasa inda mutanen suke ya ce, "Maganar da ku ka faɗa a kaina da Didi naji kuma zan ɗauki mataki akan hakan, abinda ya saka bazan iya yi muku komai ba kun girma iyayen wasu ne ku. Ba dan ina jin tsoro ko kunya ba, sai dan haka na yi niya." Bash ya ce, "Damisa ai in babba bai ji tsoron hawa jaki ba, jaki bazai ji kunyar kayar dashi ba." "Allah ya baka haƙuri" ɗaya a cikin su ya faɗa yana kallon Omar. Omar zai yi magana wani matashin saurayi ya ƙaraso wajan ya ce, "Baba lafiya?." Omar ya kalle shi ya kalli wanda ya kira da Baba bai ce komai ba yana jira ya ji ne zai ce. Murya na rawa Baba ya ce, "lafiya lau." Yaron ya ce, "lafiya naga wannan a tsakiyar ku da wuƙa a hannunsa?." Omar Bash ya kalla yayi masa alamun da a kawo yaron, ai kuwa suka damƙe shi aka ɗukar dashi a kusa da Omar. Cikin takaicin da ya ke ji a zuciyarsa ya fara tsinke fuskarsa da mari cikin tsananin fusata. Ya jawo rigarsa ya kalle shi ya ce, "ku hana iyayen ku yin magana a kaina da rayuwata, in ba haka ba wallahi duk abinda nayi musu ku yi kuka da kan ku." Ya sauke numfashi cikin baƙin cikin da yake ji a zuciyar sa ya ce, "ina yiwa mutum alfarma sau ɗaya tak a rayuwarsa, to na yiwa iyayenka, na ga girman su duk da basu duba girman su ba suke faɗar ko wacce magana a kaina, ina gargaɗin ka da su kansu akan abin yazo ƙarshe daga yanzu, In hakan ya sake faruwa bazan ɗagawa kowa ƙafa ba" ya faɗa yana sakin yaron tare miƙewa zai bar wajan. "Me ka ke taƙama dashi?." Yaron ya faɗa yana kallon sa." Juyowa kawai yayi bai ce komai ba ya juya ya bar wajan, inda zai je ɗin ma ya fasa dan in ya tsaya wallahi zai iya yiwa yaron kaca-kaca da fuska kawai ya bar wajan yafi alkhairi. *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t *Book 1* *P 06.*       Duk abinda ya faru a kan idanun Nayla da Salma da suka ta dawo daga unguwa aka ajjiye su a farkon layin suka shigo a ƙasa. Sai da suka tabbatar ya shiga gida sannan suka shiga wajan Hajja Salma tana faɗin, "Shi wai wannan bawan Allah babu abinda ya iya sai mugunta?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "wa kenan?." Nayla ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Waye in ba wannan basamuden na gidan Didi ba, Hajja kin ga yadda ya kama fuskar wani yaro yana mara kamar Allah ya aiko shi?." Hajja ta ɗan yi tsaki ta ce, "wai a cikin ku Hauwa'u da Salma wacece take son Ummaru ne?." Salma da take shan ruwa sai da ta ƙware jin abinda Hajja ta ce ruwan ya dawo mata ta fara tari. Nayla ta kalle ta ta ce, "Sannu Sis, dole ki ƙware fa, wannan kalami na Hajja sai ya saka zuciyarka ta daina aiki na wucin gadi. Wai so, Allah na tuba meye abin so a wannan mutumin? Sai dai hasken fata." Salma da ta dawo daidai ta kalli Hajja ta ce, "So fa Hajja?." Hajja ta kalle su ta ce, "bai kai a so shi ɗin bane ba?." Nayla ta taɓe baki ta ce, "ya kai, amma a wajan ƴan jagaliya kamarsa. Da ilimin mu da komai Hajja ki faɗi wannan maganar a kan mu? Wannan ai kamar babban saɓo ne wallahi." Hajja ta ce, "to tun ɗazu ku ke maganarsa har yanzu kun kasa dainawa, wanda ake so shi ake yawaita magana a kansa ai." Nayla ta kalli Salma suka ƙyalƙyale da dariya Nayla ta ce, "Shi tantirancin sa ne ya saka mu ke magana a kansa, kuma abin alfaharin sa ne ma mata masu class kamar mu suna maganarsa. Batun so kuma Allah ya tsari gatari da saran shuka, Allah na tuba ya wuce na zaunar dashi na koya masa karatu?. Wai a taƙaice ma yayi makaranta kuwa? Dan irin su wallahi basu cika karatu ba, addini ma gararar su yake yi."            Hajja ta murmusa kawai bata ce komai ba Salma ta ce, "to ina ya ga lokacin yin wani karatu kullum ana yawo da wuƙa? Kuma wallahi laifin ƴan unguwar nan ne da ba a samu wani shegen da yafi shi hauka ya koya masa hankali bane shiyasa yake abinda ya ga dama. Haka kawai ya kama mutum yana zabga masa mari ga iyayensa a zaune." Hajja ya ce, "na faɗa muku Omar bashi da matsala, kuma tunda ki ga haka ɗayan biyu ne, in ma an zagi mahaifiyarsa ko kuma an yi magana mara daɗi akan Aisha." Hajja ta kuma cewa, "kun san mutanen hausawa da wani banzan tunani, tunda Aisha bata taɓa aure ba kuma suna zaune gida ɗaya da ƙaninta shikenan ake musu kallon ƴan iska. Majalisar maza ake zama ana dasa gulmar su wai neman junan su suke yi." Nayla ta buɗe idanu ta ce, "a'uzubillahii! Kaji wani jahilci don Allah." Hajja ta ce, "Wannan maganar ba baƙuwa ba ce ba a unguwar nan, sau da yawa za a zo neman aurenta amma da wanda yazo neman auren ya tafi shikenan bazai dawo ba an je an zuga shi an ce ai tana bin ƙaninta suna lalacewa a gida. Jinkirin aure bashi da daɗi, dan babu yadda zaka canja ƙaddararka ne amma wanda yake cikin irin yanayin shi kaɗai ya san halin da yake ciki. Aisha kam tana ganin jarabawa, wanann ya zo sai an fara abu kamar na kirki sai a watsar, gobe ma wani yazo shima ya gudu." Salma cikin tausayi ta ce, "Allah sarki Didi! Amma duk masu faɗar wannan kalami mai munin tsiya ba su yi mata adalci ba, kuma sai Allah ya yi musu hisabi." Hajja ta ce, "tunda ku ga yana wannan hukuncin daƙyar ba maganar yaji suna yi ba, dan shi zaki iya zagin shi ya wuce ki amma kar ki taɓa Aisha, sonta yake kamar ya bata ran da yake dashi ta haɗa da nata, saboda Aisha itace kamar uwarsa da ubansa." Nayla ta ce, "gaskiya indai haka ne yayi daidai wallahi, in ma ƙara ya kai su gaban hukuma ai daidai ne. Wannan wanne irin ƙazafi ne mai baƙin muni haka?." Salma ta dawo kusa da Hajja ta zauna ta ce, "Hajja to ina ƴan uwan su ne?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "ke bacci nake ji, in Allah ya kaimu gobe na baku labarin asalin su Aisha da Ummaru." Nayla ta ce, "kai Hajja ki faɗa mana yanzu mana." Hajja ta harare ta ta ce, "yanzu da nace wata tana sonsa cikin ku sai kuka ce a'a, in ba so ba meye na son jin labarinsa?." Nayla ta gimtse fuska ta ce, "Hajja ki daina kawo batun nan ko da wasa don Allah, kawai muna so mu sani ne ba dan wai wani abun ba. So ki ke Daddy yaji labari ya zane mu?" Ta faɗa tana kallon Salma suka ƙyalƙyale da dariya. Hajja tunda taji sun ce Daddy ta san mahaifin Salma suke nufi babban ɗanta kenan. Hajja ta ce, "ko shi daddyn in ɗaya tana son Umar ɗin ina ruwansa?." Salma ta wara idanu ta ce, "Maza ki yi istigifari Hajja, dan wannan babban saɓo ne." Hajja tayi dariya ta girgiza kai ta ce, "Ni ko labarin gidan Daddyn ma baku bani ba, kun shigo kuna yi min hirar saurayin Hauwa'u" ta faɗa tana kallon Nayla da tsokana. Nayla ta ce, "Hajja ki daina cewa saurayina, saurayina yana Kaduna ba a Kano yake ba. Sannan ba sunana Hauwa'u ba Hawwa nake, ki dinga cire u ɗin nan don Allah." "Bazan cire ba, Hauwa'u zance, Kuma na faɗa Umar saurayinki ne." Nayla rai ta ya ɓaci amma ganin Hajja tsokanarta take yi sai tayi dariya suna hira da Salma dan Hajja ya shiga ɗaki.         *Kaduna.* Abiy da Mama a zaune a falo, Abiy yana cin abinci Mama na gefensa ganin ya kammala cin abincin sai ta kalle shi ta ce, "ɗazu Nayla ta kira ni, na ce mutanen Kano ya Hajja." Abiy ya murmusa ya ce, "nima daga dawowa ta gidan nan zuwa yanzu sau biyar ta kira ni, Ai naga alama tana son zama wajan Hajja sosai." Mama ta yi murmushi ta ce, "itama Hajjan tana matuƙar jin daɗin zama da Nayla ai, kasan Nayla ba dai hankali da iya magana ba." Abiy ya murmusa kawai bai ce komai ba kafin ta ce, "Kwana nawa ka bar ta yi ne?." "Sati ɗaya." "Haba Abiy, ina laifin ka barta tayi sati uku tunda dai ta kammala service ɗinta kuma baka samar mata aiki ba. Tahzif ɗin da ta shiga ma ta kammala tana gida a zaune. Hajja na son zaman ta a can, ita take ɗauke mata kewar mahaifiyar ta da ta rasa take kallon Nayla tamkar Bilkisu." Abiy ya kalle ta ya ce, "Bana son zaman ta a Kano ne gabaɗaya, kar ki manta abinda ya so faruwa da ita a shekarun baya, ba dan Allah ya kiyaye ba da an cutar da ita. Tun daga nan zaman ta a Kano ya gama fita daga raina, da ina da iko ma ko kwana ɗaya baza tayi a can ba, to ban isa na rabata da dangin mahaifiyarta da suke can ba. Kuma suna tsananin son Nayla da ƙaunar ganinta, dole ne na barta ta je gare su." "Na sani Abiy, Amma ai komai ya wuce kuma yanzu Nayla ai tana da hankali da wayon da abinda ya faru a baya bazai faru yanzu ba sai dai ƙaddara. Hajja tana sonta, tun farko ta nuna maka ka bar mata Nayla kawai dai ka ƙi ne. Kuma suma sun yi mana kara a kanta sosai." Abiy ya ce, "har abada bazan iya barwa kowa Nayla ba, ke bama Nayla ba kaf ƴaƴana biyar har Nayla shida bana tunanin zan iya barin su su je  wani wajan su zauna gaskiya. Sai dai aje ayi ziyara a dawo, ni ne na haife su haƙƙin riƙe su a hannuna yake." "To ka ƙara mata lokaci kafin ta fara zuwa aiki ta zauna a Kano wajan Hajja." Abiy ya sauke numfashi ya ce, "zan yi tunani a kan hakan na gani, amma a yanzu dai sati ɗaya na bari tayi, in naga zan ƙara mata sai na ƙara mata, In naga bazan iya ba ta dawo gidan mahaifinta." Mama tayi murmushi ta ce, "Hakan yayi, Allah ya kaimu." Ya amsa da amin kafin ya tashi ya shiga ɗaki ya bar Mama a zaune a wajan.         "Nayla hmmm! Ai wallahi sai na raba ku, yadda ta bar gidan nan a bana tunanin zata sake dawowa cikin sa, in ma ta dawo na ɗan lokaci ne kawai amma sai nayi amfani da wayo da dabarar da na nisanta ka da Nayla. Sai na san yadda na yi Nayla ta je gidan mijin da zai ci ubanta, ya hanata walwala ya kuma hanata jin daɗi. Burina Nayla ta rayu a gidan auren da zata sha wahala kamar ydda uwarta ta wahalar dani, Zan fashe wahalar da na sha akanta!." Girgiza kai Mama take yi tana hasaso lokacin da wannan buri na ta zai cika. Bata nufin Nayla da ko wanne irin sharri ko makirci, ta raini Nayla daidai da yadda ta raini ƴaƴanta, ta bata tarbiyya da rayuwa mai kyau. Ita babban burin ta Nayla ta yi aure a inda zata sha wahala kuma sai tabbatar da ta cika wannan buri na ta hankalin ta zai kwanta, ta yi ƙwafa ta miƙe zuwa daƙi. Washe gari Kano. Washe gari Alhamis Nayla da azumi ta tashi kasancewar ta mai ibadar azumin litinin da alhamis, ranta a jagule gabaɗaya bata da walwala saboda rashin chajin waya, daman gidan Daddy da suka je da daddare ne ya saka ta cikar wayarta kuma ta ƙarar gashi yanzu kuma babu wuta kuma ba a gyara solar Hajja ba. Hajja na kula da ita tana zaune a falo tayi shiru masu yiwa Hajja aiki suna ta aikace-aikacen su kafin kammala su bar wajan. Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u baki da lafiya ne? Ko ki karya azumin." Ta kalli Hajja ta ce, "Rashin chaji bala'i ne Hajja, duk shi ya saka ni a wannan yanayin." Hajja ta ce, "ki kaiwa Aisha ta saka miki mana." Nayla ta dafe ƙirji ta ce, "har kin saka gabana ya faɗi, ni in sake shiga wannan gidan...? Ai har abada." Hajja ta ce, "To a ina zaki saka chajin?." "Bara Salma ta tashi mu ji ya za a yi." Salma ce ta fito da kayan bacci ta kalli Nayla ta ce, "meye naji kina maganata?." "Salma chaji nake so wallahi, Ke kin san bana son zama babu chaji." "Ga power bank ɗina can ki saka, amma ba zai yi miki da yawa ba dan shima babu chajin." Jin haka sai taji daɗi ta saka chajin amma duk da haka bai mata ba dan da gani chajinsa ya kusa ƙarewa. Sallama aka yi aka shigo falon duk suka kalli wanda ya shigo. Ganin Daddy ya saka Nayla ta miƙe tana cewa, "Lah Daddy sannu da zuwa." Kallon ta yayi yana murmushi ganin fuskar ƙanwarsa Bilkisu a kan fuskar Nayla ya ce, "yauwa Hawwer, yanzu ma ki ka tashi kenan?" ya faɗa yana kallon Salma da ta fito daga kitchen da kofin shayi. Hajja ta ce, "Yanzu kam suka tashi dan ko wanka ba su yi ba." Gaisawa suka yi da Hajja kafin suma su gaishe shi ya kalli Nayla ya ce, "Jiya kun je bamu haɗu ba, ya services ɗin naki?." "Daddy ai na gama, yanzu aiki nake jira." "Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya kawo miji na gari." Hajja ta amsa da amin kafin ta ce, "Duk sun girma sai aure, su huɗu ne gasu nan kan su ɗaya. Hauwa'u, Salma, Ummimi da Zainab." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne wannan, Allah ya kawo namiji na gari." Hajja ya ce, "Amin. Amma ga mazaje nan a gidajen ku meye amfanin su?. Zaratan samari nawa muke dasu?." Salma da Nayla suka kalli juna Daddy ma dariya ya yi ya ce, "basu da amfani kan Hajja, muna jira wani ya furta yana son ƴar uwarsa ne sai ayi." "Har sai an jira? Lallai kace zan rarraba su ga duk wanda naso. Duk wanda na ce na bawa ɗaya a cikin su ai babu wanda zai musa ko?." "Babu kam Hajja." "Yauwa, to ku jira zan fara watandarsu tunda na ga ku kun yi sanyi." Dariya Daddy ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Ya gidan babu wuta? Naga kina gumi ki kunna ac mana." Nayla cikin shagwaɓa ta ce, "ba solar ta lalace ba har yanzu ba a gyara ba." Daddy ya ce, "Subahanallah! Har yanzu ba a gyara ba daman? Ke Salma meye amfaninki da baki faɗa min ba?" Ya faɗa yana ɗauko waya tare da kiran masu aikin solar suka tabbatar da zasu zo a lokacin. Nayla murna kamar tayi me saboda zata samu chaji yadda take so. Daddy sallama ya yi musu bayan ya basu kuɗi ita da Salma ya tafi.         Omar kuwa a safiyar yana zaune a falon Didi yana cin indomie ita kuma ta kitchen tana wanke-wanke. Sallama akayi tare da shigowa falon ya ɗago yana kallon wanda ya shigo. Ɗiff yayi ganin wanda yake tsaye a bakin ƙofar shi bai shigo ba kuma bai koma ba. Omar bai amsa sallamar ba sai ma ɗauke kai da ya yi. Didi jin sallama kuma bai bada amsa ba ya saka ta fito falon tana kallon inda yake kallo. Da Yayan Mahaifiyarsu ta haɗa ido Baba Adamu sai kuwa ta saki fara'a ta ce, "Lah Baba kai ne tafe? Sannu da zuwa." Ƙarasowa tayi shima ganin ta sai ya shigo yana murmushi ya ce, "Ni ne Aisha." "Sannu da zuwa, Ka zauna mana Baba." Ya zauna yana satar kallon Omar da yake cin indomie kamar bai san ma ya shigo ba. Gaisawa suka yi da Didi ya ce, "ya kike ya sana'ar taki? Fatan komai Lafiya." "Lafiya lau Baba, ɗazu nake zancen gobe juma'a zan zo mu gaisa in sha Allah." "Allah sarki, Allah ya baki ladan niya." Ta amsa da amin ya kalli Omar ya ce, "Omar ina kwana." Wani iri Didi taji na rashin jin daɗi ganin babban mutum kamar Baba Adamu shine yake gaishe da Omar. A sanyaye ta kalli Omar da kamar bai ma ji abinda aka ce ba ta ce, "Omar magana ake maka, ka gaishe da Baba." In bowl ɗin da yake hannunsa ya amsa shima ya amsa. Didi ta ce, "Omar!." "Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Baka ji abinda nace ba ne?." "Naji mana." "To ka gaishe shi." Ya kalle ta ya ce, "bazan ba." Zata sake magana Baba Adamu ya girgiza mata kai alamun tayi shiru ya kalle shi ya ce, "Omar ina kwana." Nan ma ya sake yi masa banza Didi zata yi magana Omar ya ce, "Bana iya girmama wanda bai girmama mahaifiyata ba, bana iya girmama wanda bai tashi nuna min mu masa bane sai da haƙora talatin suka fito a bakin mu. Kar ki ɓata bakinki Didi, kema kin san bazan yi ba." Baba Adamu ya ce, "Omar kayi haƙuri, kuskure ne an yi shi a baya kuma na nemu afuwar ku." "Ita wacce ƙasa ta rufe idonta fa, itama ka nemi afuwarta ne?"Omar ya faɗa yana kallonsa da rikitattun idanunsa. Baba Adamu ya ce, "Ina yi mata addua'ar samun gafara a wajan mahaliccinta." Omar ya ce, "yadda bakwa son mu wallahi nima bana son ku, yadda ku ka wulaƙanta mahaifiyar mu dan kawai tana auren mahaifin mu babu wanda zan iya ganin darajarsa wallahi, kum...." "Omar!" Didi ta katse shi da ƙarfi tana kallon sa. Kallon ta yayi sai ya fasa faɗar abinda zai ce kuma bai tashi daga inda yake ba, dan bai isa yazo ya same shi ya tashi ya bar masa wajan ba. Baba Adamu ya ce, "ƙyale shi Aisha. Daman magana ce nazo da ita akan sabon company na da na buɗe, in Omar ɗin yana so sai yazo mu fara aiki gabaɗaya." Kallon ƙasan ido ya yiwa Baba Adamu kamar zai yi magan sai ya fasa ya cize bakinsa cikin ƙunar zuci. Didi ta washe baki ta ce, "Lah yaushe aka buɗe Baba?." "Satin da ya wuce." "Allah ya sanya alkhairi ya sa albarka, Me zai hana ya zo? Zai ma yi aikin...."  "Gwara na koma bara akan titi da dai nayi aiki a ƙarƙashinsu wallahi" Omar ya katse a yana ɗaga mata hannu. Zata yi magana ya ce, "Didi! Ke kin san waye ni, babu ɓoye-ɓoye, babu kare, wallahil azim bazan yi ba. Wato nayi aiki a ƙarƙashin su a samu damar wulaƙanta ni a zage ni ko? Kema kin san bazai yu ba, ai ko rahama ake rabawa a company na amince ta wuce ni na samu a wani wajan daban. Hanyar samun ta ai yawa ne dashi." Baba Adamu ya ce, "babu laifi Omar. Amma duk lokacin ka ji kana da ra'ayi ƙofa buɗe take, Kuma har abada baza ka taɓa goge mu a rayuwarka ba, mu ɗin dai mu ne gatanka saboda mu ne jinin mahaifiyarka." Omar ya taɓe baki ko kaɗan baya jin nauyi da girman Baba Adamu duk da ya girma sosai. Ya ce, "Allah ne gatan mu gaba da baya, babu wata halitta da zata zama gatan mu a duniya in ba Allah ba." Murmushi Baba Adamu yayi dan ya san shine ya jawo kuma ya san halin Omar da shegen riƙo da taurin kai, shekara sama da goma sha ana abu ɗaya amma har yanzu yaƙi sakin jikinsa. Baba Adamu ya ce, "Aisha zan tafi, akwai abinda ki ke buƙata ne?." Didi cikin sanyin jiki ta ce, "Babu komai Baba, in akwai zan sanar da kai a waya." "To akwai kayan abinci da nazo miki dashi, zo mu je yara sai su shigo dasu" ya faɗa yana miƙa mata rafar ƴan dubu-dubu guda biyu ta saka hannu biyu ta karɓa ta ajjiye. Omar ya kalle shi  ya ce, "duk wanda ya ganni ya ganta ya san ba ma tare da yunwa." Babu wanda ya kula shi Didi ta kalle shi sannan ta bi bayan sa tana hararar Omar saboda kallon da ta ga yana yi mata. Ba jimawa aka shigo da madara da milo da sugar da butter, kwai, taliya, doya, dankali, platain, da sauran abubuwa. A guje yaran suke ajjiyewa suna fita saboda Omar da yake kallon su daga falon. Tana shigowa gidan yana fitowa daga parlon ya ce, "babu abinda za a ci a cikin kayan nan, ko ki mayar masa da tsiyarsa ko kuma na kwasa na zubar wallahi." Ta Harare shi ta ce, "wallahi bazan mayar ba, kuma baza a zubar ba Omar ba. Yayan mahaifiyata ne ya bani ba wani bare ba." Da mamaki yake kallon ta ya ce, "ba gwara ace wani baren ne ya bayar akan ace shine ya bayar? Didi kar mu yi haka dake, ba za a ci abubuwan nan a gidan nan ba." "Wallahi sai an ci!" Ta bashi amsa a kausashe tana kallonsa. Idanunsa sun yi ja saboda ɓacin rai ya kalle ta ya ce, "Akwai abinda babu a gidan nan ne? Faɗa masa aka yi yunwa tana tare damu ne da zai kawo mana wannan tarkacen?." "Omar wai meye ya sa baka yafiya ne kai?." Ta kalle shi ganin sai wuci yake kamar zaki, idanun nan nasa sun yi ja haka jijiyar kansa ta miƙe kana kallon sa kasan ran masa ya ɓaci. "Tambayarka nake, meyasa baka yafiya ne?." Bai iya yi mata magana ba sai wuce zai fita tayi saurin riƙo hannunsa ta ce, "Yayan mahaifiyarka ne in ka saka aka yi masa wani abun tamkar Mama ka yiwa, sannan ka tuna Mama baza ta taɓa alfahari da kai a yadda ka ke ba Omar. Zata yi alfahari da kai in ka kasance na gari, amma a haka baza taɓa alfaharin haihuwarka ba." Runtse ido yayi cikin ƙunar zuci ya zame hannunsa daga riƙon da tayi masa ya bar gidan da sauri. Da kallo ta bishi bayan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ya Allah ka shirya min ƙanina Omar, Allah ka yaye masa wannan baƙar zuciyar da yake fama da ita, Allah ka bashi ikon manta abinda ya riga ya wuce ya kama abinda yake gabansa, Amin." Kayan take ɗauka a hankali tana shiga dasu dan ta san in zasu shekara a wajan bazai taɓa ba,  gabaɗaya jikinta ya gama yin sanyi itama, abubuwan da suka faru a baya suna yi mata yawo a zuciyarta. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t *Book 1* *P 07.* *Abuja.* Zaune suke a babban falo na alfarma su biyar suna cin abinci cikin yanga da iyayi, kai da ka gansu ka san kuɗi da ilimi ya gama zama a jikin dukkan su. Duba da irin shigar da take jikin Narma zaka tabbatar da wayayyun ƴan boko ne. Dad ya kalli Nabil ya ce, "Nabil ka san lokacin lissafi a store ya kusa ko?." Nabil ya kalli mahaifin na su ya ce, "Yes Dad, na sani." "Ya kamata a dakata da karɓat kaya sai mun kammala lissafi." "Okay Dad za a yi." Ya kalli Najwa ya ce, "Najwa yaushe zaki koma London?." Najwa ya kalle shi ta ce, "Sai nan da three weeks Dad." Kafin ya bada amsa Mum ta ce, "My Dear tunda dai sun samu hutu lokaci ya yi da zamu je Paris. Akwai birthday party ɗin friend ɗina, za a yi surprising ɗin ta a can, so ina so nayi attending." Narma ta kalli Mum tana turo baki ta ce, "Mum ni babu inda zan je gaskiya, beside ni Kano zan je." Najwa ta ce, "Yaya Narma wai me zaki yi a Kano ne?." "Samra's wedding." "Friend ɗinki sai aure suke yi amma ke kin tsaya wasa." Narma tayi murmushi ta ce, "na kusa." Mum ta ce, "to ke ki tafiyar ki Kano ni da Najwa zamu je Paris." Najwa ta ɗan ɓata rai ta ce, "Paris Mum?." "In baza ki je ba kin huta, ai ba hanya ce ban sani ba." Najwa tayi dariya ta ce, "dole na ma." Mum ta kalli Nabil ta ce, "Nabil ka faɗawa Zuhra sai mu je tare, I hope Asim sun samu hutun school?." "Yes Mum, sun yi hutu." "Okay" ta furta tana cigaba da cin abincin ta. Dad ya kalle Narma ya ce, "Yaushe zaki je Kano din?." Narma ta kalle shi ta ce, "Ranar Sunday zan tafi." Dad ya kalle ta ya ce, "Ranar yaushe zaku fara events ɗin?." "Wednesday." "Okay. Narma ban da yawo ke kaɗai ba, kin yanayin Kano ba wani security ne dashi ba. Dan ma kin takura ne da babu abinda zai saka na bar ki ki je." Narma tayi shiru bata ce komai na dan kar ma tayi magana a hana ta zuwa. *Kano.* Didi share Omar tayi dan ta san yinin ranar a ɓacin rai zai yi shi in tace zata biye masa itama ranta ne zai ɓaci. Aikace-aikacenta ta cigaba da yi gabaɗaya abubuwan da suka wuce suna yi mata yawo a kanta, duk yadda ta so ta kawar itama ta kasa hakan ya sanya idanunta zubar hawaye tunawa da iyayen su da suka rasa a shekarun da suka wuce. Bata sake tunanin Omar ba dan ta san bazai dawo ba ransa a ɓace yake da ita sosai ta fi kowa sanin hakan. Ta kuma san in ba dan ita ɗin babu babu halittar da yake ɗagawa ƙafa, shi bai san kara ba, bai kuma son alfarma ba. Haka ranar ta yini sukuku bai dawo ba har yamma, ko da ya shigo bai ce mata komai ba daman ta san bazai ce ba ɗakinsa ya shiga bai jima ba ya fito ya sake fita. Sai bayan sallar magriba kamar yadda ya saba shigowa ko yaushe sannan ya shigo kamar baza ta yi masa magana ba ganin ya haɗe rai sai kuma ta ce, "Baza ka ci abinci ba ne?." Kallon ta yayi yana shan ruwa ya ce, "Na daina cin abincin gidan nan har sai abinda ya kawo ya ƙare." Ta rausayar da kai ta ce, "Omar! Omar!! Wai wacce irin zuciya ce da kai ne don Allah?." "Wacce Allah ya yi min Didi." "Shikenan naji. Amma abinda na dafa yau ko abu ɗaya a cikin abinda ya kawo ban taɓa ba. Kazo kaci abincin ka." Ya kalle ta alamun bai yarda ba ta ce, "da gaske nake, ka san ai bazan maka ƙarya ba. Ka je ka ɗauko abincin, ka kira su Tukur su ci ga na su." Shiru yayi kamar zai ci ɗin sai kuma ya girgiza kai ya ce, "su dai zasu zo su karɓa, ni kam bazan ci ba." Duk sai Didi ta damu a tausashe ta ce, "in baka ci ba me zaka ci?." "Assalamu alaikum, Damisa na dawo." Jin muryar Bashir a cikin yaransa ya saka shi ya fita tsakar gidsa sai ga shi ya dawo da packs da alamun abinci aka siyo masa. Didi ta kalle Bashir ta ce, "Bashir ku zo ku ɗauki abinci." Bash ya ce, "An gama babbar Yaya, godiya mu ke Allah ya saka da alkhairi." Kitchen ɗin ta shiga ta ɗauko musu ta bashi shi kuma ya fita. Lokacin da ta dawo ta tarar grill tilapia fish ne da chip a cikin pack ɗin irin mai sauce ɗin nan da ake siyarwa yana ci hankalin sa kwance. Daman ta san shi masoyin kifi ne sosai, bai damu da cin nama ba akan yadda yake son cin sa ba. Numfashi ta sauke ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa ta zauna akan kujera. Wani pack ɗin taga ya miƙo mata sai tayi murmushi, daman ta san bazai taɓa siyan abu bai siya da ita ba, koda a waje ne in ya ci itama sai ya kawo mata. Ganin bata karɓa ba sai ya ajjiye mata ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya maganar saurayinki?." Dariya ya bata sosai, wai saurayinta a ganin ta ai sai dai ace bazawari ba saurayi ba, ita mantawa da take itama tana cikin sahun wanda za a kira da budurwa. Ganin tana dariya sai ya kalle ta ya ce, "me ya baki dariya?." "Kaine ka bani dariya Omar, wai saurayina. Ina laifin ka ce mai neman aurena? Saurayi ai sai dai irin ku masu neman yara su aura." Shima sai ya ɗan saki fuska yana kallon ta ya ce, "Yaushe zai zo ɗin?." Ta ce, "ba ka ce gobe ba? ya ce goben zai zo in sha Allah." "Ya yi" ya faɗa yana ɗauko waya yana dannawa. Abinda ya faɗo ƙasa ta kalla garin ɗauko wayar ya faɗo daga aljihunsa. Ta kalle shi ta ce, "Omar me nake gani a kusa da ƙafarka?." Kallon wajan ya yi sannan ya kalle ta ta ce, "Omar baka daina shan sigari ba daman?." "Na daina Didi, ɗazu ne da raina ya ɓaci shine...." "Shine ka sha?." "Uhum." "Omar ba ka ce min ka daina ba?." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Didi na daina wallahi, ɓacin rai ne kawai." Shiru tayi alamun ranta ya ɓaci, ya kalle ta ya ɗauke kai ya cigaba da abinda ya ke yi. Jin shirin na ta yayi yawa ya sake kallon ta ya ce, "Didi yau ne kawai, kuma daga yau har abada bazan sake ba." Kawai sai ta fara kuka ta ce, "amma ka ce min ka daina ko? Ka san bana so. Yaushe ka fara yi min ƙarya? Ina yarda da duk abinda ka ce min saboda na san ƙarya ba ɗabi'arka ba ce, amma gashi ka fara Omar." Ya tausasa murya ya ce, "ai na faɗa miki dalilina Didi, kuma bazan sake ba faga yau nayi miki alƙawari, ki daina kuka." Ajiyar zuciya tayi ta kalle shi bata ce komai ba. Ɗauke wacce ta faɗi ƙasa tayi ta miƙe ta ce, "Zan shiga na kwanta." Ya miƙe shima yana kallonta ya ce, "ki daina kuka to, bazan sake ba in sha Allah." Ya share mata hawayen da kansa ta kalle shi tace, "na daina Omar." Da hannu yayi mata alamun tayi murmushi sai tayi murmushin shima yayi murmushi ya fita ya barta a wajan. Ajiyar zuciya tayi ta shiga ɗaki bayan ta kashe hasken falon. Washe gari. Kasancewar Juma'a ce da wuri ta tashi dan tana yin abincin sadaka duk ranar, nan da nan ta haɗa shinkafa da wake da dafaffan kwai ta zuba a disposable packs kamar yadda take yi in an idar da sallah ta fita da kanta ta rabawa yara. Lokacin da ya shigo ta gama tana zubawa a packs ɗin ya kalle ta ya ƙaraso ya ce, "Didi wai ba za a samu mai taya ki aikin nan ba?" Ya faɗa yana karɓa tare cigaba da yin abinda yake yi. "To Omar ko wacce mace tsoron shigowa gidan nan yake yi saboda kai, kai kanka in kaga baƙuwa ka dinga faɗa kenan taya zan samu mai ta ya ni aiki?." "Gabaɗaya mutanen unguwar nan munafukai ne, musamman ma matan." Jin abinda ya ce sai tayi murmushi ta bar masa ya cigaba da abinda yake yi dan tasan bazai barta ta cigaba ba. Sai da ya gama sannan ta kalle shi ta ce, "Amma dai ba da ƙananun kaya zaka je masallaci ba?." Zai yi magana ta ce, "Don Allah ka saka manyan kaya, don Allah na don ni ba." Hannu ya wanke bai ce komai ba ya shiga ɗakinsa. Sai gab da lokacin sallah sannan ya fito yana fitowa ta fito itama daga falo ta bishi da kallo tana murmushi. Ya yi mata kyau cikin yadi milk colour, abin ka da namiji mai kyau, duk da bai saka hula ba amma yayi kyau sosai. Murmushi tayi ta ƙaraso inda ya ke ya ce, "ƙanina mai kyau ne wallahi, Allah ya sa kayi budurwa yau." Taɓe baki yayi bai ce komai ba kuma bai yi murmushi ba. Ta kalli gashin kansa ta ce, "ya kamata ka ɗan rage gashin nan na kanka, kalli fuskar ka ma, gashin yayi yawa kamar wani buzu." "Shi ne" Abinda ya ce kenan yana juyawa ya fita ta bishi da kallo tana murmushi. Hijjabi ta saka ta fita bayan ta rufe ƙofar gidan ko makulli bata saka ba dan ta san babu wata halitta da zata iya shiga gidan da sunan sata. Kai tsaye gidan Hajja ta shiga a lokacin Nayla tana zaune kusa da Hajja sun saka ta a gaba ita da Salma sai wai ta basu labarin lokacin haihuwar Salma. Sallamar Didi ya saka suka amsa Nayla ta ce, "Didi." Didi ta harare ta ta ce, "daman kin ce min baza ki sake zuwa ba gashi kin tabbatar." Nayla tayi dariya sosai, Didi ta kalli Hajja ta ce, "Hajja ki shaida mun yi faɗa da Nayla." Hajja ta ce, "ko ɗazu sai da tayi zancenki, amma wai baza ta shiga ba saboda Omar. Na ce Omar ya raba Yaya da ƙanwarta." Didi tayi dariya suka gaisa da Hajja suma duk suka gaishe ta amsa da murmushi ta ce, "Hajja mutuminki shine yake firgitata, na faɗa mata kuma ta daina jin tsorosa babu abinda zai mata amma ta kasa. Kuma da zata zauna a garin nan na wani lokaci suna sabawa shikenan. Wahalar sabo ne dashi kawai." Salma ta ce, "Didi ko iya wannan idanun na sa ma ai ya isa ka ji tsoro balle ya buɗe baki." Didi tayi dariya ta ce, "yanzu saboda shi sai ku daina zuwa wajan Yayarku?." Salma ta ce, "ai Didi lamarin na sa ne akwai ban tsoro." Nayla ta ce, "Ke da bai taɓa tarfa ki kamar yadda ya yi min bama kenan, ina jin in ke ya yiwa abinda ya yi min suma zaki yi." Didi ta ce, "ai na faɗa miki shi zan saka yazo ya ɗauko min ke in baki koma ba, zaki gani kuma." Hajja ta ce, "wai! ranar sai Hauwa ta suma." Suka yi dariya gabaɗaya kafin Didi ta ce, "Hajja dahuwar awara zaki koya min, wacce nake kaiwa ana yi min bata yiwa Omar daɗi." Hajja ta ce, "shikenan kin kama Hauwa har wuya. Ja hannunta ki je ta dafa miki, ta iya dafa awara nesa ba kusa ba. Itama irin Omar ɗin ce, tsabar son cin ta da take yi sai da ta iya dafawa." Didi ta kalli Nayla ta ce, "Alhamdu lillah, ki ce shiga gida ya kama ki." Nayla ta wara ido ta ce, "ai gwara ki aiko min da kayan nayi miki a nan sai na aiko miki da ita, kuma ban iya mai yawa ba ƴar kaɗan na iya dafawa." Didi ta ce, "ai wallahi gida zamu je ki yi min nima na koya, babu wani na aiko miki dashi baki isa ba." "Allah Didi tsoronsa nake ji, in na ganshi hantar cikina kaɗawa take yi." Suka yi dariya gabaɗaya Didi ta ce, "Tsoron nake so na cire miki, ki saba dashi shima yayanki ne kamar yadda nake yayar ki." Hajja ta ce, "ai na faɗa mata in da amana ai ruwa bazai dafa kifi ba, Ita da ya saɓo ta a kafaɗa ko riga babu itace mai faɗar haka a kansa." Nayla ta dafe kai cikin takaicin kalaman Hajja ta ce, "Wai Hajja don Allah meye haka?." Didi ta yi dariya ta ce, "Hajja kina bata kunya." "Kunyar ƙarya ce, ai ba ƙarya nayi ba a kafaɗar ya ɗauko ta ko? Kuma ai gaskiya ne rigarsa ya saka mata." Didi ta ce, "Gaskiya Hajja ki daina tuna mana maganar nan kunya mu ke ji." Hajja tayi dariya ganin Nayla sai ɓata rai take yi, ita kuma tana sane take faɗa saboda ta tunzura Nayla ɗin. Didi ta miƙe tana dariya ta ce, "Nayla ina jiranki." Nayla ta ɗaga kai dan babu yadda zata yi ne amma bata son haɗuwa da Omar. Bayan Didi ta fita Nayla ta kalli Hajja ta ce, "Haba Hajja! Meyasa zaki ce mata na iya don Allah? Kin san tsoronsa nake ji." Hajja ta ce, "ke ni fa saboda kyautatawarsa akan ki ne ce ki je, sannan Didi jikata ce kamar ki, tana sona tana son ku gabaɗaya." Nayla ta kalli Salma ta ce, "Salma zamu je?." Salma ta wara ido ta ce, "ai na rantse da Allah baza ni ba, Ke dai ki je." Nayla ta zauna kamar zata yi kuka zuciyarta cike da fargaba. Didi na rabon abinci a ƙofar gida ta hango Nayla tana tahowa a nutse sai tayi murmushi tana kallonta, ita dai Nayla na matuƙar burge ta sosai, bata sani ba ko dan tana kyau ne ya saka haka oho. Babban abinda yake burge ta game da Nayla shine shigarta, bata taɓa yin shigar banza. Kayanta ta basa wuce doguwar riga, riga doguwa har guiwa da siket, butterfly da sauran kayan mutunci na zamani. Wannan dalili ya saka take sonta sosai, gata kirki. Tare suka ƙarasa rabon abincin da Nayla suka shiga cikin gidan Nayla sai ɗari-ɗari take yi. Didi ta kalle ta tace, "kwantar da hankalinki baya nan, ya kai yamma bai dawo ba." Ajiyar zuciya tayi Didi tayi dariya suka fara haɗa awara kamar yadda ta ce. Didi tana gefe tana kallon ta har suka markaɗa a blender aka tace aka fara dafawa. Didi ta ce, "bara na gyara kayan miyar nan mai sauce nake so nayi." Nayla ta ce, "ashe kina son awara, nifa saboda son da nake mata ne ya da na iya dafawa, dan tunda na taɓa ganin gashin kai a cikin wacce ake yi min a gida na daina bari masu aiki su yi min." Didi ta ce, "ni bata dame ni sosai ba, mutuminki ne masoyin awara, bai damu da nama ba kamar yadda ya damu da awara. Zai iya ci miki awara da safe da rana da daddare, Sam shi nama bai dame shi ba, da rayuwar nama da babu duk ɗaya, har gwara kifi ma." _Shiyasa yake gabjeje mana ashe soya beans yake afakawa cikinsa_ Nayla ta faɗa a zuciyarta. Didi ta ce, "kuma kar ki ɗauka da yawa yake ci, kin san ɗan iyayi ne, ƴar kaɗan in ya ci zata ishe shi kawai  sonta yake yi. Da ita da jollof rice mai kifi, da noodles, da pasta and stew. Inda safe ne kuma doya da ƙwai in ta huce ya ci ta da ketcup ko yaji, har mamakin inda ya iya cin ketcup yake yi. Noodles ma sai ya ci ta tun safe har dare kamar yaro. Wani lokacin kuma baya cin ahinci sai dai ya shafa coffee ko ya yini yana cin apple da kankana." Nayla ta yi murmushi kawai tana mamakin ko ita ina ruwanta da abinda yake so. Didi ta ce, "yau so nake yaci har ya barta, bara na haɗa sauce ɗin." Nayla ta ce, "bar shi nayi miki kafin awarar tayi, tunda kin gyara kayan miyar bara ayi blending, ni gyara su ne bana so." Didi ta ce, "yau Omar zai ci abincin ki kenan." Tayi dariya kawai ta fara haɗa sauce ɗin tana yi suna hira. Nan da nan suka gama Nayla ta tace awarar ta kalli Didi ta ce, "Zamu bar ta haɗa jikinta sai mu soya. Ita kuma sauce ɗin in kina da mayonnaise ki zuba mata, ko in kin zo serving ki zuba ni dai tana min daɗi." Didi ta ce, "ai kam na gode sosai Nayla, Kin ga nima na koya saboda gaba, ashe ma babu wahala." Tayi murmushi ta ce, "bara naje gidan Hajja." "To ki dawo mu ƙarasa don Allah." "Zan dawo yanzu Didi" ta faɗa tana fita da sauri. Didi sallama ta jiyo daga tsakar gidan hakan ya saka ta kashe gas ta fito tana amsawa. Gabanta sai da ya faɗi ganin wanda ya yake tsaye a tsakar gidan ta daure tayi murmushi ta ce, "Kawu kai ne tafe? Sannu da zuwa." Wanda ta kira da Kawu ya yi murmushi ya ce, "Yauwa Aisha, ke kaɗai ce a gidan?." "Eh ni kaɗai ce Kawu, Omar bai dawo daga masallaci ba. Shigo kawu." Kawu ya yi ajiyar zuciya dan yana daga cikin masu tsoron Omar ya shiga falon da sallama. Didi ta amsa ya zauna suka gaisa ta ce, "Ya Mutanen gidan?." "Lafiya lau Aysha. Daga masallaci nake na biyo mu gaisa na kawo miki kafin bikin ƙanwarki" ya faɗa yana miƙa mata katin. Didi da murmushi ta ce, "bikin wa za a yi Kawu?." Kawu ya ce, "Bikin Ramla." Jin sunan Ramla sai da gabanta ya faɗi itama sai tayi murmushi ta ce, "Kai ma sha Allah! Allah ya nuna mana lokacin." "Amin ya Allah, Amma zaki zo ko?." "Zuwa kai Kawu, in ban zo ba waye zai zo?." Yayi murmushi ya ce, "gaskiya ne, ku ne yayyen amarya." Tayi murmushi ya miƙe tsaye ta ce, "Kawu ko ruwa baka sha ba ka miƙe." Kawu ya ce, "sauri nake yi, babu komai ba sai na sha ruwa ba. Na ce Omar bai shirya aure bane?." Ta kalle shi ta ce, "Gaskiya bai shirya ba." "In ya shirya akwai ƙannensa zai iya zuwa ya nema." Jin abinda Kawu yace sai tayi murmushi tana murna da Omar baya nan da an shiga uku da wannan furuci na Kawu. "Didi!" Omar ya faɗa yana shigo falon. Ganin wanda yake parlon sai ya tsaya cak yana kallonsa kafin ya girgiza kai ya kalli Didi da ita kanta bata so ya shigo ba, Kawu kuwa ya gamq tsurewa saboda tsoro. Karaf Didi tayi ta ce, "Omar ga Kawu, ya biyo mu gaisa ya kawo katin biki ƙanwarka Ramla." Idanu ya waro waje ya ce, "ni bani da wani Kawu a duniya, kuma bani da ƙanwa, bani da ƙanwa a duniyar nan kar ki sake cewa ƙanwata!." Kawu yayi tsitt bai ce komai ba zuciyarsa rawa kawai take yi saboda tsoro. Kallon Kawu ya yi ya ce, "Baka san baƙi ba sa zuwar mana gıda ba?." Kawu ya ce, "Omar ni ne fa." "Kaine wa? Na ce kai ne?" Ya faɗa a zabure yana fito da idanunsa waje cikin fusata. Didi ta kalle shi ta ce, "Omar meye haka?." "Didi wai meyasa ki ke min haka ne? Su waye waɗannan da ki ke bari suna shigo mana gıda?. Waye shi? waye na mu?" Ya faɗa yana ɗaukar iv da aka kawo ya watsar dasu a tsakiyar falon. "Omar Kawu ne fa." "Ke ki ka san wani Kawu ni ban san shi ba, bani da wani Kawu a duniya" ya faɗa idanunsa a waje yana karkaɗa yatsansa. Kallon Kawu ya yi ya ce, "ka manta abinda na yi maka wancan lokacin ko? Baka ji ba ka sake zuwa gidan nan ko?. Shikenan zan maka tabon da baza ka sake marmarin zuwa ba." Kawu ya tsorata sosai ya ce, "ka yi haƙuri Oma...." "Kar ka sake faɗar sunana, haƙuri kuma ban san shi ba!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallonsa. Didi ta kalli Kawu ta ce, "Kawu yi haƙuri, ka tafi kawai Kawu." Ganin Omar zai fita ta ce, "Omar kar ka fita daga falon nan, Kawu mu je na rakaka." Omar jikinsa rawa yake saboda ɓacin rai ya fita daga falon. "Omar! Omar ka dawo!" Ta faɗa da ƙarfi amma ina ya fita daga gidan. Kawu ya ce, "Aisha tsoro nake ji kar ya saka ayi min wani abun, haka kwanaki ya saka aka kusa hallaka ni." Ganin Kawu ya tsorata sosai sai ta ce, "babu abinda zai maka Kawu, tunda nace babu abinda zai yi babu ɗin, Kayi haƙuri." "Ni zan bada haƙuri da na zo tunda na san baya so, ki yi haƙuri duk laifina ne ni na jawo wannan tsanar da yake mana." Didi ta ce, "Mu je kawu." Har ƙofar gida ta raka shi, ta ka ga su Bash kuwa suna jiran fitowarsa. Kallon su tayi ta ce, "Kar wanda ya yiwa Kawu komai, in kuma wani abun ya same shi duk sai ranku ya ɓaci, ku faɗawa Damisar na ku ni nace a ƙyale shi. Kawu shiga motarka." Kawu jiki na rawa ya ce, "A'a Aisha." "Kar ka damu Kawu babu komai." Kawu dai tsoro ne ya saka shi shiga motar ya bar unguwar a guje. Didi gidan ta shiga cikin ɓacin rai ta shiga falo tana mamakin baƙar zuciya irin ta Omar da baya mantawa. Bai bar dangin uwa ba, haka ma dangin uban bai bar su ba. Har gwara ma na uwa tsanar da ya yi musu bata kai wacce ya yiwa su Kawu ba. A lokacin ya shigo tsakar gidan ya tsaya yana zagaye ransa a matuƙar ɓace zuciyar sawuya, fuskarsa tayi wani irin ga jijiyoyin kansa sun tashi. Abokin karawa kawai yake nema ya wuce a kansa. "Assalamu alaikum, Didi na da......" Maganar Nayla ta maƙale saboda wanda suka haɗa ido dashi a cikin gidan. "A'uzubillahi minal shaiɗanir rajim!" Nayla ta faɗa a tsorace cikin gigicewa dan bata san ma ta yi ta'awizin ba. Omar ya sake wara ido a kan fuskarta cike da mamaki da fusata ya ce, "Shaiɗan!" Ya faɗa yana kallon Nayla tare da takowa zuwa inda take. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 08.*           Nayla baya take ja yana takowa inda take idanunta a waje ƙirjinta yana up and down saboda tsoro da tashin hankali. Shi kuma yana takawa inda take saboda ɓacin rai da zallar haushi da takaici a zuciyarsa. Sai da ta jingina da bango ya dakata da bin bayanta, jikinta na rawa kar kar kar bakinta na motsawa amma ta kasa magana. "Ni ki ke yiwa korar shaiɗanu? Wacece ke! Waye ya turo ki gidan nan!?." Tsawar da ya yi ya sake firgita Nayla ta runtse idanunta cikin fargaba da tashin hankalin da bata taɓa shiga irin ta ba. Numfashita ya kusa ɗaukewa ganin ƙaramar wuƙar da ya zaro daga ƙasan takalminsa ya ɗago ya ɗora wuƙar akan wuyanta yana sake wara idanunsa waje ya ce, "Wacece ke!?." Nayla bata taɓa shiga tashin hankali kamar yadda take a ciki yanzu ba, ƙafafunta sai rawa suke yi saboda tashin hankali, zuciyar tacike da dana sanin abinda ya shigo da ita gidan. "Omar!" Didi ta faɗa da hanzari tana zuwa ta janye Omar daga kusa da Nayla da take zubar da hawaye. Sharaf Nayla ta faɗi a numfashi ta na sama da ƙasa saboda tashin hankali. "Baka da hankali ne Omar? Kashe ta zaka yi?." A fusace ya kalle ta ya ce, "Wacece ita? Ban ce kar na sake ganinta a gidan nan ba?." "Gidanka ne da sai wanda ka ke so ne zai shigo? Na ce gidanka ne!?." "Ba gidana ba ne, amma ina da ikon hana duk wanda bana so shigowa cikinsa. Ban son sake ganin wannan yarinyar a gidan nan, bana son sake ganin ta!" Ya faɗa da ƙarfi yana nuna Nayla da take zaune a baya kamar sumammiya. Didi ta fusata sosai ta ce, "baka isa ba, baka isa ka hana baƙina shigowa gidan nan Omar. Wai kai Meya ke damunka? Meye a cikin kanka? Meyasa baka aiki da hankali ne kai?." Idanu ya sake warawa waje yana kallon Didi jin kalamanta musamman na ƙarshe ta ce, "eh na faɗa, Meyasa baka aiki da hankali? Meyasa ko yaushe zuciya ce take sarrafa tunaninka ba ƙwaƙwalwarka ba?." Kai yake girgizawa Didi ta sake cewa, "wacce irin zuciya ka ke da ita ne kai? Meyasa baka mantuwa baka yafiya?." "Eh bana yafiya, kuma bazan yafe ba. Iya yau kin cece shi ya sha, amma wata rana zamu haɗu a lokacin da babu ke ko?." "Ƙanin mahaifinka ne, ko ka ƙi ko ka so dole ka kira shi da Kawu." Ƙasa ya yi da muryar da yana girgiza kai cikin ƙunar rai ya ce, "Har abada bani da dangin mahaifi, bani da dangin mahaifiya, kamar yadda na rasa iyayena suma ki ɗauka sun mutu. Ke kaɗai na sani dangina, bayan ke babu wata halitta a duniyar nan da ta rage da zan kalle ta matsayin dangi!" Ya ƙarashe maganar da ƙarfin gaske. "Ƙarya ka ke Omar, ƙarya ka ke. Kawu ƙanin mahaifinka ne duk da abinda ya aikata maka ba a canjawa tuwo suna. Baba Adamu Yayan mahaifiyarka ne, duk da abinda ya yi maka ba a canjawa tuwo suna. In dai har ka manta da dangin iyayenka to zaka manta da wanda suka haife ka Omar!." Hannu ya saka ya daki kansa ya juya ya sake juyowa ya kalle ta ya ce, "iyayena sun rasu dan haka bani da wani a duniyar nan in ba ke ba." "Nima ɗin baka ɗauke ni komai ba Omar, tunda baka yin abinda nake so." Sake kallon ta ya yi ya ce, "na rantse da Allah Didi, in na sake ganin ƙafar wani dangin Baba a gidan nan ranar bazai kwana lafiya ba. Zan iya ɗagawa dangin Mama ƙafa, amma bazan taɓa ɗagawa dangin mahaifina ƙafa ba. Ke kin san waye ni, kin kuma san abinda zan yi da wanda bazan yi ba." Didi sai ta kasa magana dan baza ta iya da taurin kansa ba, tayi murmushin takaici kawai ta kalli Nayla da take zaune a wajan har lokacin kamar bata numfashi. Da sauri ta ƙarasa inda take ta ɗago ta jikinta ta ce, "Nayla! Nayla buɗe idon ki don Allah." A hankali Nayla ta buɗe ido tana kallon Didi sai jikinta ya cigaba da rawa ta ƙanƙame Didi tana kuka sosai. "Yi haƙuri Nayla, ki daina kuka don Allah ki yi haƙuri" ta faɗa tana shafa bayanta a hankali cikin tausayinta da mugun takaicin halin Omar. Omar takaici kamar ya kashe shi haka yake ji, cikin tsananin ɓacin rai da takaici da tsawa ya ce, "in na sake ganin yarinyar nan a gidan nan bazan ƙyaleta ba." Cikin ɓacin rai da fusata Didi ta ce, "Sai ta shigo! Omar sai ta shigo in ka dama ka kasheta ka kaima ka ga in za a barka da rai. Na gaji da wannan shirmen na ka, kullum kana girma amma kana cin ƙasa, sam baka aiki da hankali balle ka san abinda zaka yi." Runtse idanu yayi yana jin zafin kalamanta, Babban abin haushin ma a gaban yarinyar da ta taɓa yi masa faɗa kwanaki a gabanta, yau ma gashi an maimaita har tana cewa yana shirme baya aiki da hankali. To shi wanne gangancin ne ma zai bari ya bar yarinyar da lafiyarta? ai in bai taɓa lafiyar jikinta ba bazai ji daɗi ba. Bai taɓa jin haushin wata halitta kamar ita ba, saboda itace mace ta farko da aka yi masa faɗa a gabanta. Zai sake magan ta dakatar dashi cikin fushi ta ce, "Dallah Malam fita ka bani waje kafin na tsinke ka da mari." Sak ya yi yana kallon ta jin wai zata mare shi, kallon ta yake yi cikin mamaki dan abinda ta faɗa bata taɓa furtawa shi ba sai a lokacin. Ganin kallon mamakin da yake mata sai ta ce, "ko kana ganin ban isa na mare ka ɗin ba ne? In kana ganin ban isa ba ka cigaba da tsaya min kai wallahi sai na mare ka." Kai yake gigirzawa yana kallon Nayla da take kwance a jikin Didi tana sauke numfashi ya ce, "na gama haddace fuskarta, duk abinda ya faru tayi kuka da kanta" yana faɗar hakan ya fita daga gidan cikin baƙin ciki da ƙunar zuciya. Wai kamar shi Omar Tiger Didi take cewa zata mara a gaban wata yarinya, ƙarshe ma akan yarinyar take zancen zata ta dake shi.          Didi ta kalli Nayla bayan ya fita ta ce, "Nayla yi haƙuri don Allah ki nutsu, ki dawo nutsuwarki ji." Tashi tayi da sauri ta ɗauko mata ruwa mai sanyi ta bata, ai kam Nayla ta sha ruwan nan sosai dan tana buƙatarsa. Hijjabin jikinta ta cire mata ta riƙeta ta ce, "taso mu shiga ciki." Daƙyar Didi ta iya ɗaga ta suka shiga falon Didi ta zaunar da ita akan kujera ta kunna mata fanka sannan ta zauna kusa da ita tana yi mata firfita. Bata sake magana ba sai da taga Nayla ta ɗan nutsu hawayen da take yi ma ya tsaya sannan ta sake kawo mata ruwa ta ce, "karɓi ki sha Nayla." Nayla kallon ta tayi sai ta ɗan zabura Didi ta riƙe ta ta ce, "kar ki ji tsoro, babu abinda zai miki baya cikin gidan ma gabaɗaya. Yi haƙurk ki sha ruwa." Ba musu ya sake karɓat ruwa ta sha tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu. Didi ta kalle ta ganin ta dawo nutsuwarta sai ta dafata ta ce, "ki yi haƙuri Nayla, ban saka ki shigowa gidan nan dan ki shiga wannan yanayin ba, wallahi ban san zai dawo ba da ban ce ki zo ba. Ki yi haƙuri don girman Allah, da na san hakan zai faru da ban ce ki zo ba." Nayla jin yadda take mata magiya cikin sanyim murya sai ta ce, "Haba Didi, don Allah ki daina yi min magiya haka babu komai Didi." "Dole na roƙeki ki yafe min ai Nayla, da ban je har gida na taho dake ba da haka bai faru ba, tun farko kin nuna bakya so amma na takura miki. Gashi na saka ki a halin tsoro da fargaba wanda ya kusa sakawa ki suma ki fita daga hankalinki, ki yafe min kin ji? bazan sake takura miki akan zuwa gidan nan ba." Nayla ta ce, "babu komai Didi, don Allah ki daina bani haƙuri." Didi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "ransa ne a ɓace sosai kin tarar dashi akan gaɓa shiyasa, zaki ga ni kaina bai ƙyale ni ba saboda in ransa ya ɓaci ya kan rasa hankalinsa na wani lokaci sai daga baya yake fahimtar abinda ya faru. Bayan fitar ki baƙon da ya zo shine silar ɓacin ransa, na tabbatar ba dan haka ba da bazai kalle ki ba, saboda nayi masa magana ranar da ya yi miki wannan abun." Nayla ta riƙe hannun Didi ta ce, "babu komai Didi ya wuce." Ta yi murmushi ta ce, "na gode. Amma ki rage tsoronsa har haka, ki koyi dakewa koda zaku haɗu a wani waje" tayi murmushi ta ce, "Dan na san baza ki sake shigowa gidan nan ba, Nayla ban ga laifinki ba Omar abin tsoro ne a wajan wanda bai san shi ba, amma in ka san shi normal mutum ne kamar kowa" ta faɗa tana ƴar dariya tana kallon Nayla da take yaƙe. Didi ta ce, "ina jin aure zan masa wataƙila zafin kansa ya ragu." Nayla bata san san da murmushi ya subce mata ba, ta wara ido ta ce, "Aure! Kuma sai a samu wacce zata aure shi? Taɓɗi! amma sai dai mai taɓin hankali." Sai bayan tayi magana ta fahimci a bayyane tayi maganar. Didi tayi dariya sosai ganin ta saka Nayla murmushi ta ce, "Ni da nake cewa ƴar gida za a yi dake? Shikenan tuwo na mai na, Yayar amarya kuma Yayar ango." Wani irin numfashi Nayla ta sauke mai nuni da ta rasa abinda zata ce. Didi tayi dariya ta ce, "wato kin kasa magana ma kenan?." Nayla tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Didi ta ce, "mu je na raka ki wajan Hajja in na soya awara sai na kawo miki." Ai kamar jira Nayla take ta miƙe tana neman hijjabinta. Didi ta bita da kallo dan ƙananun kaya ne a jikinta ta ɗora dogon hijjabi ta fito ta ce, "Irin wannan kyau haka Nayla? gaskiya ina yiwa ƙanina kamu." Taɓe fuska Nayla tayi ta kalle ta tace, "Didi wallahi kina saka zuciyata cikin fargaba, don Allah ki daina faɗar haka bana so." Didi tayi dariya tana cewa, "na daina faɗa, yi haƙuri." Nayla ta saka hijjabin ta, itama Didi ta saka suka fito. Ganin tana dafe kai ya saka Didi ta ce, "ciwon kai ko?." Ta ɗaga mata kai alamun eh, Didi ta ce, "sannu, Allah ya ye." Ta amsa da amin suka fita ƙofar gidan. Nayla ganin Didi bata rufe gidan ba sai ta ce, "baki kulle ƙofar ba." Didi tayi murmushi ta ce, "a tunanin ki za a shiga ayi mana sata ne? Gidan su Omar Damisa ne fa, gidan nan ko almajiri baya shiga yayi bara balle ɓarayi." Nayla ta ce, "Ya ci suna Tiger ɗin ai, ba shi da sabo." Didi ta yi murmushi Nayla ta girgiza kai bata kuma cewa komai ba amma zuciyar ta tana jinjina girman baƙin halin sa.             A zaune suka samu su Hajja ita da Salma suna cin abinci. Didi ta ce, "Hajja ga Nayla na dawo da ita na kuma yi mata laifi, a taya ni roƙon ta tayi haƙuri." Hajja ta ce, "me ya faru ke da ƙanwarki?." Didi ta ce, "ita da Omar suka gamu wallahi, gamuwar bata yi daɗi ba sam kuma duk ni ce sila. Ni nazo har goda muka tafi, da ban mata dole ba da baza ta je ba, yanzu haka kanta ciwo yake yi." Salma ta yi dariya ta ce, "Shiyasa ni da gidanki sai kallo daga nesa." Didi ta zaunar da Nayla ta ce, "ki yi haƙuri Nayla." Nayla ta ce, "Haba Didi, tun a can ki ke bani haƙuri, don Allah ki bari." "Na bari, Na gode sosai Allah ya baki miji na gari. Zan koma gida yanzu amma zan shigo anjima." Nayla ta ce, "to Didi." Didi ta fita zuciyar taduk babu daɗi akan abinda Omar ya yi mata. Ai Didi tana fita Nayla ta zare hijjabinta ta cillar ta ɗaga wuya sama ta kalli Salma ta ce, "Salma duba wuya na ki ga babu yanka da wuƙa." Salma ta kalli wuyan ta ce, "babu komai, Meye ya faru?." Nayla ta ce, "wannan mutumin an yi ɗan tijara kuma ɗan bala'i. Ina shiga ban ma kula dashi ba fa, ina ganinsa sai nayi ta'awizi ashe yaji haushi, wai korar shaiɗan nayi masa, to meye marabarsa da shaiɗan ɗin?." Salma ta ce, "shine ya shaƙe ki?." "Ke faɗar tashin hankalin da na shiga ai ɓata baki ne, ba na jin ma abinda yake cewa saboda tsoro da fargaba. Kawai naga ya ɗora min wuƙa a wuya daga nan ƙwaƙwalwata taje hutun rabin lokaci, dan numfashi na kaɗan ya rage bai ɗauke ba." Salma ta ce, "to shi wai bashi da hankali ne ko ne? Faɗa masa aka yi in yayi miki wani abun ƙyale shi za a yi?." Nayla ta ce, "shima ya san wasa yake yi ai, babban abin mamakin ma wallahi har ita Didin bai bari ba, kin ji yadda yake zazzaga bala'i kamar ba ita yayarsa ba?. Sai magana yake akan shi bashi da dangi da sauran su." Salma ta ce, "wannn mutum dai ya zama annoba a unguwar nan, almajiri fa baya shiga gidan saboda tsoro." Nayla ta ce, "haka Didi take faɗa min yanzu, ke ni naga bala'i ai. Ruwa kuwa ina jin na sha yafi leda uku." Hajja da take jin ta tayi dariya ta ce, "kin cika tsoro ne kawai Hauwa'u." "Hajja tsoro halak ne, dan naji tsoronsa ai ban yi laifi ba, da tuni an kawo miki ni ya yanka min wuya." "Haba dai, shima ai bazai fara ba, tsorataki yake yi kawai." Salma ta ce, "amma abin yayi yawa wuƙa fa? Wai bashi da dangi ne?." Hajja ta ce, "kin taɓa ganin wanda bashi da dangi?." Salma ta ce, "to suna ina? Ai ko dan wannan jagaliyancin da yake yi ya ci ace na gaba dashi sun tsawatar masa." Hajja ta yi murmushi ta ce, "wai ba gidan babar ku Sa'adatu zaku je ba?." Nayla ta miƙe ta ce, "bara na canja kaya mu tafi" ta faɗa tana shiga ciki dan ta canja kaya su tafi.         ***** Didi haka ta koma gidan gabaɗaya zuciyarta da jikinta babu ƙarfi, haka ta soya awarar da suka gama ta rage wata ta saka a fridge dan ta ga da yawa sosai, ta zuba wata a food flakas ta zuba sauce ɗin ta fita da kanta ta kaiwa Hajja, Hajja take sanar da ita su Nayla  sun fita itama ta koma gida.        Kamar yadda baƙon ta ya ce zai zo bayan la'asar hakan ce ta kasance, ita ta manta da zuwan na sa sai da yayi mata waya ya ce gashi nan ya tawo ta tuna. Dole ta miƙe tayi wanka tana fatan Allah ya sa shine na ƙarshen masu zuwa neman aurenta. Ba jimawa ta gama shiryawa ya zo ta sauke shi a harabar gidan dan bata shiga da baƙo ciki saboda bakin mutane. Sun jima suna tattaunawa kuma ta yaba da kalamansa da nutsuwarsa da alama da gaske yake, ya kuma faɗa mata duk abinda ake faɗa a kanta shi kuma bai damu ba ya amince da auren ta a haka. A nan ya yi masa kwantancen gidan Kawu da lambar wayarsa dan yaje su tattauna inda dai gaske yake, bai jima sosai ba ya yi mata sallama ya tafi da alqawarin zuwa gidan kawu. Haka kawai ta ke jin kanta da farin ciki fiye da sauran masu zuwa neman aurenta, zuciyarta lokaci ɗaya taji tayi na'am da shi sosai ta kuma ji daɗi da har ya tafi Omar bai shigo ba, duk da ya san labarin Omar ɗin da komai amma a yanayin da Omar ɗin ya ke a ranar tsaf zai kwafsa. Bata da uwa kuma ta da abokin shawara a kusa sai Hajja, Hajja ce maƙociya, kaka, uwa a gareta. Hakan ya saka ta gama abinda take yi ta rufe gidan ta shiga wajan Hajja. Hajjan kawai ta samu a zaune tana jan carbi tana kallon tashar madina. Didi ta ce, "Hajja ƴan matan basu dawo ba?." "Ba su dawo ba Aisha, amma na san suna hanya tunda magriba ta taho." Didi ta ce, "Hajja yau ma wani yazo da batun aure, abinda ban taɓa yi ba yau nayi, domin na tura shi wajan Kawu su yi magan." Hajja fara'ar ta ta ƙaru ta ce, "Alhamdu lillah! Aisha ai abinda ki ka yi daidai ne, shi kansa zai yaba da hankaliki da kika tura shi wajan na gama dake." Didi ta ce, "Hajja ban taɓa jin na gamsu da duk masu zuwa neman aure na wani lokaci ɗaya ba sai shi." Hajja cikin farin ciki ta ce, "lokacin aurenki ne yazo Aisha shiyasa. Duk masu baki da kunu da suke ta magana a kai in yanzu Allah ya rubuta shine lokacin ki sai yanzun zaki yi aure." Didi ta ce, "sunan saAbdulhamid kuma bashi da mata, ya sanar dani sun rabu matar da yara biyu kuma suna hannunta. Ya ce a yi bincike akan rabuwarsu da matar indai akwai damuwa a kansa bazai sake zuwa ba. Ma'aikacin gwamnati ne a wata babbar ma'aikata." Hajja ya ce, "Alhamdu lillah! In sha Allah komai ya zo ƙarshe. Ai dai ka miƙa lamarinka ga Allah baka da sauran damuwa, Zaɓi na gari Allah ya yi miki shiyasa ya jinkirta miki auren, ko bani da rai zaki ce na faɗa miki Aisha." Didi ta ce, "Allah ya sa Hajja." Ta amsa da amin Didi ta ce, "Sai dai Omar nake ji, in ya san na kai batun nan wajan Kawu babu zaman lafiya. Ɗazu ma fa shine yazo waje na kawo min katin bikin Ramla ƴarsa shine Omar ya tarar dashi, Wannan tsinin ɓacin ran Nayla ta tarar." Hajja tayi dariya ta ce, "yayi faɗansa ya gama dole sai an nemi maganatan ki a fannin aure, shi kansa da yake wannan abubuwan bara maganar auren na sa ta zo dole sai ya neme su. Babu mutumin kirkin da zai bashi auren ƴarsa ba tare da ya nemi danginsa ba." "Hmmm! Ina jin wannan ranar a zuciyata Hajja, ranar da Omar zai je ya nemo dangin mu saboda batun aurensa. Allah Hajja gani nake akan Omar ya neme su zai iya fasa aure, zai iya zuwa ya nemi wacce ba zasu damu da danginsa ba ya aura." Hajja tayi dariya ta ce, "haka ki ke gani, amma zai neme su da kansa. Ban da abin Omar tunda har suka fahimci a baya basu kyauta ba kuma suke ƙoƙarin gyara laifin su ai ya kamata ya yafe musu." Didi ta ce, "Omar da kafiya, taurin kai, zuciya, riƙo, zafin rai, zafin zuciya ai aminan juna ne, Allah kaɗai ya san yadda zamu kwashe dashi in yaji na tura shi wajan Kawu."   "To banda abin Omar in baki tura shi wajan Kawu ba wajan wa zaki tura shi?." Didi tayi dariya ta ce, "ya ce an faɗa min shi bai yi hankalin da zai bada aurena ba." Hajja tayi dariya sosai ta ce, "a shekaru dai yayi, amma ina hankalin da Ummaru zai bada aurenki?." Didi tayi murmushi Hajja ta ce, "ki cigaba da yi masa addu'a, kamar uwa ki ke a wajansa, ki ta yi  masa addu'a wata rana sai labari." "In sha Allah Hajja, addu'akullum ana yi masa har taimakon malamai nake nema akansa, in sha Allah canji zai zo. Ba dan malam Salahudden ya rasu ba ai da shine maganin Omar, yana matuƙar girmama malamin." Hajja ta ce, "a yanzun ma zai dawo hankalinsa in sha Allah, nan gaba shima mu sha biki." Didi ta ce, "wai! Omar da mata." Hajja ta ce, "ba abun mamaki bane, kuma cikin ikon Allah daƙyar in ba ta silar mace zai canja ba." Didi ta ce, "wai ta hanyar soyayya?." "Kina ganin bazai yu ba ne?." "A'a, amma lamarin ne akwai firgici, wacce yarinya ce zata so Omar a haka?. Ga halinsa na bayyane ga zafin zuciyar da yake da ita?." Hajja ta ce, "kadai Allah ya bamu lafiya, Allah ya yafi gaban komai." Didi ta ce, "Haka ne Hajja. Bara na koma magriba tayi in Nayla ta zo a gaishe su" Hajja ya amsa tana sake yi mata addua'a tana amsawa ita kuma ta fita tana jin Hajja kamar mahaifiyar ta saboda kirki da karamcin ta. Nayla sai bayan i’sha aka dawo dasu daga gidan ƙanwar mahaifiyarta ya wacce suke cewa Mama. Ɗanta mai suna Abbas shine ya dawo dasu har gida sannan suka shiga wajan Hajja tare. Yana yin sallama Hajja ta ce, “wa nake ganin kamar Abbas?.” Yayi dariya ya ce, “ni ne Hajiya Hajja, kin wuni lafiya?.” “Lafiya lau mara kunya, baka zuwa ka gaida mutane sai dai in zaka kawo babbarka sannan ake ganinka, yanzu ma na san saboda Nayla ne ka shigo ko?.” Yayi ƴar dariya ya ce, “Haba Hajja, ni da nazo ki bani dambun nama sai ki fara ƙorafi?.” Hajja ta ce, “nayi ɗin, baka zuwa gidan nan kai kwata-kwata sai da dalili.” Yayi murmushi ya kalli Nayla da take jona chaji kasancewaar an gyara musu wutar gidan. Hajja ta bishi da kallo tana kallon abinda yake kallo ta ce, “ya ƙannen naka da Yayar?.” “Lafiya lau Hajja, kowa yana gaisheki.” “Ina amsawa da kyau.” Daga nan suka yi shiru ya sake kallon Nayla da take aikinta ba ta shi yake yi ba. Hajja ta ce, “Hauwa ga saƙo ki can Aisha ta kawo miki tun yamma.” Nayla ta kalli Hajja ta ce, “to.” Abbas ya miƙe ya ce, “Hajja ni zan koma, sai Allah ya dawo dani.” “Allah ya kiyaye.” Ya kalli Nayla ta ya ce, “Hawwa zan tafi.” Ta kalle shi ta ce, “To Yaya Ab ka gaida gida.” “Bazaki raka ni ba?.” Ta shagwaɓe fuska ta ce, “na gaji Yaya.” Yayi murmushi ya ce, “ki huta.” Itama murmushin tayi ya fita daga falon. Salma ta bi shi da kallon ta kalli Nayla ta ce, “Nayla anya Yaya Abbas bai ƙyasa dake ba?.” Nayla ta wara idanu ta ce, “rufa min asiri ki bar zancen nan.” Hajja ta ce, “babu zancen a rufa miki asiri ai gaskiya ta faɗa, ni kaina na lura da yana sonki Hauwa’u.” Gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba ta kalli Hajja ta ce, “don Allah Hajja ki daina faɗar haka, ni ɗan uwana ne babu wannan batun a tsakanin mu. Kuma kun san shi yana da wasa da dariya babu lallai abinda ki ke zargi ne. Ga su Yaya Muhmmad da su Yaya Aliyu, da Yaya Khaleed duk ba a ce haka ba sai shi?.” Hajja tayi murmushi ta ce, “Mai Babban suna da Ali babu wanda ya nuna wani abu a kan ki kamar yadda Abbas ya nuna, daman ni ina son auren zumunci kuma in sha Allah a cikin zuri’ata sai an yi auren zumunci ba ɗaya ba ba biyu ba. Da kaina zan cewa Abbas ya samu Daddyn ku da maganar ki.” Nayla kamar tayi kuka ta ce, “Don girman Hajja ki bar zancen nan, wallahi ni bana so” ta faɗa tana tashi ta shiga ɗaki dan ita in akwai abinda ta ƙi jini bai wuce auren zumunci ba. Haka kawai baya burgeta balle tayi tunanin zata yi nan gaba. Balle ma kuma Abbas da ya kasance mai ƙirar mazan da ta tsana, bana son namijin da gym ya nuna shi, ita ta fito son mai normal ƙira ba murɗaɗɗe ba. Didi tana zaune har takwas na dare Omar bai shigo ba duk sai ta damu ta ɗauko waya tana kiransa amma wayar ma taƙi shiga. Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ta amsa tana kallonsa ganin fuskarsa tana nan kamar ɗazu a ɗaure tamau. Didi ta ce, “ina ka shiga ina ta jiran ka tun dazu?.” Kamar ba zai ce komai ba sai daga baya kuma ya ce, “ina nan.” “Ka zauna kaci abinci.” Kai ya girgiza alamun baya ci sannan ya ce, “meyasa baki kira ni ba lokacin da baƙonki yazo ba?.” Ta kalle shi ta ce, “na san ba zaka dawo ba saboda ranka a ɓace yake sosai, Yanzu ka zauna kaci abinci.” “Bana son cin komai.” “Ko abincin rana baka ci ba na san kuma kai ba mai son abincin waje bane, ka zauna na kawo maka awara nayi maka da kaina.” Jin yadda take magana murya a sanyaye sai ya ɗago ido ya kalle ta ta ƙaraso inda yake ta ce, “ka zauna don Allah, ba don ni ba.” Ba shi da mafita dole ya zauna ta wuce kitchen sai gata ta dawo da lafiyar jollof rice da kuma ƙaramin plate na awara ta ajjiye masa. Kallon shinkafar ya yi ya ce, “bazan ci shinkafa ba, wannan ya isa” ya faɗa yana ɗaukar ƙaramin plate ɗin awarar ya riƙe a hannunsa ya ɗora ƙafa akan ɗaya.” Fara ci yayi kusan mintina biyar kafin ya kalle ta ya ce, “Amma ya yi daɗi sosai, kuma babu yaji.” Didi tayi murmushi ganin ya sake ta ce, “na san baka son yaji ai shiyasa sauce ɗin ma babu abinda zai saka ta yaji.” Kai ya girgiza cikin izza da ƙasaita ya kalle ta ya ce, “ina jinki.” Didi ta ce, “Kamar yadda kaji sunansa haka sunansa yake, ma’aikaci ne ya taɓa aure amma basa tare da matar. Kuma alamunsa ba da wasa yazo ba gaskiya.” Ya girgiza kai ya ce, “haka ake so. Yanzu ya maganar ta tsaya?.” Ido ta zuba masa sannan ta ce, “ka san ba ni zan bayar da kaina ba ko? To na tura shi wajan Kawu.” Cak ya dakata da abinda yake yi ya kalle ta suka haɗa ido tayi sauri ta ce, “babu yadda na iya ne, ya nemi ganin dangin babana dole na yi masa kwatancen gidan Kawu. Kai ka san ai ba ni zan aurar da kaina ba dole a nemo ganin dangina.” Ajjiye plate ɗin hannunsa yayi bai ce mata komai ba ya miƙe tsaye ya fita. Daman ta san ƙarshen cin abincin na sa yazo kenan tunda ta ambato maƙiyansa, taji daɗi da bai yi magana ba dan ta san da faɗa zasu yi dashi. Su Bashir ta kira ta basu abincin sannan ta shiga tayi shirim kwanciya. Tunanin baya ne yake dawo mata dawo mata cikin kanta, ta yi ajiyar zuciya tana tuna abinda ya wuce. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 09.*          Ranar asabar da daddare Omar da Didi suna zaune a falo yana aikin danna waya ita kuma tana kallon tv, bata ce masa komai ba ganin ya ƙi ya saki rai, sai ɗaure fuska yake yi ba kamar jiya ba, bata so ta yi masa wata maganarta tsokano shi hakan ya saka ta yi shiru. Shirun ne yayi yawa  hakan ya saka ta kalle shi ta ce, "Omar." Ya ɗago manyan idanunsa ya kalle ta sai ta langwaɓar da kai ta ce, "don Allah ka daina buɗe idanunka akan fuskar mutane, wannan idanu naka sai ya firgita mutum cikin dare." Bai yi magana ba ta ce, "zan faɗa maka wata magana amma kar ranka ya ɓaci don Allah." "To" ya amsa a taƙaice kafin ta ce, "Ɗazu Kawu ya kira ni, maganar AbdulHamid ce. Ya samu Kawu ɗazu da yamma, shi kuma ya ce ya bashi lokaci zasu ɗan yi bincike a akansa." Ta ɗauka da ta kira sunan Kawu ransa zai ɓaci kamar kullum amma sai taga yayi murmushi mai ƙayatarwa da daɗin kallo. Murmushi yana yi masa kyau matuƙa, yana fitowa da asalin kyaunsa da kwarjininsa. Ya ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi." Sai taji daɗi sosai a ranta ta har hakan ya bayyana a fuskar ta ta ce, "Amin Habibin Mama. Yaushe zaka nemo taka matar? Kaga in Allah yayi aurena dashi sai a haɗa gabaɗaya ko?." Kallon ta yayi tare da ɗaga yalwatacciyar gashin girarsa ya ce, "Tare mu ka zo duniyar da zamu yi aure tare?." "Ba tare muka zo ba, amma zan so mu yi aure tare." "Ke kika fara zuwa duniya, ke zaki fara aure." "Ai abin ba daga nan yake ba, yara nawa aka haifa a bayana duk suna yi aure har yaran su duk sun girma?." "Su daban Omar daban" ya faɗa yana kallonta. Didi ta ce, "to naji, Amma ya kamata dai kaima ka fara neman matar aure, kaga in nayi aure gidan nan bazai maka daɗi ba, waye zai maka girki ka ci da sauran su?." Omar ya ce, "kin san dai na iya girki ko?." "Na sani, amma yadda baka zaman nan zaka so ace kana dawowa abinci zaka ci ba sai ka dafa ba."  "Ni wannan bai dame ni ba, ki yi auren dai kawai yafi komai a yanzu." Tayi murmushi cikin tsokana ta ce, "faɗa min wacece budurwarka, baka ɓoye min komai amma baka taɓa faɗa min wacce ka ke so ba." Murmushi ya saki mai sauti yana kallon ta ya ce, "Ni aka ce miki ina da budurwa?." Didi ta harare shi ta ce, "Santalelen saurayi mai kyau da kyaun zati kamar ƙanina ai bazai rasa budurwa ba. Ina jin ka ya sunanta." "Aisha" ya faɗa cikin gatse yana kallon ta da murmushi. Dariya tayi jin sunan da ya faɗa ta ce, "ka ce takwara ta ce ma, Yaushe zata zo na ganta?." Bai ce komai ba kuma bai daina murmushi ba ta ce, "Wai! zan so naga mace da Omar zai so, zan so naga lokacin da Omar zai fara soyayya. Allah ka bani aron rai da lafiyar da zan ga Omar na matuƙar son wata mace bayan Didinsa. Wacce kalar mace ka ke so? fara ko baƙa?." Kallon ta yake cikin mamaki ganin yadda ta saka shi a gaba tana yi masa wannan tambayoyi kamar wanda ya ce mata neman aure yake yi. Murmushi ya yi ya ce, "ni wai na ce miki aure zan yi ne?." "Ko baka ce ba na san zaka yi." "To ba yanzu ba." Tayi murmushi tana kallon sa ganin shima murmushin ya ke yi ta ce, "Allah ya kaimu lokacin, Allah ya kawo macen da zata gyara min kai ka hau kan hanya mai kyau ka sauka daga wacce ka ke kai." "Hmmm" shine abinda ya furta kawai amma murmushi yake yi. Sai kuma tayi ajiyar zuciya alamun akwai abinda ta tuna amma bata ce komai ba. Ganin yanayinta ya canja sai ya so ya kawar da damuwarta ya ce, "ai ki kiyaye ganin matar da zan aura, sai na baki mamaki." Jin abinda ya ce sai fara'arta ta dawo ta ce, "Allah ya nuna mana lokacin, Allah yasa baza a samu matsala a aurenka. Allah yasa kar ka nemi wacce za a ce tafi ƙarfin ka." Ga mamakin ta sai taga yayi dariya kaɗan ya ce, "har akwai macen da tafi ƙarfin namiji ne a duniya?." Didi ta ce, "sosai ma kuwa, akwai inda kai baza kaje kace ma a baka aurenta ba, saboda matsayin ku ba ɗaya ba ba." Ya girgiza kai ya ce, "ni kam ban ga macen da za a ce tafi ƙarfina ba, sai dai in bana sonta." Kallon sa take yi jin da gaske yake yi ta ce, "kai dai Omar ayi shiru kawai, amma akwai matan da sun fi ƙarfin ka nesa ba kusa, tazarar ku kamar tazarar sama da ƙasa. Kyaun da ka ke dashi ba komai ba ne." Taɓe baki yayi kawai bai ce komai ba, amma shi kam a wajan sa bai ga macen da za a ce tafi ƙarfinsa ba, in dai yana sonta tana sonsa to bata fi ƙarfinsa ba.         A wannan lokacin Nayla tana ƙofar gidan Hajja hannunta har rawa yake yi wajan kiran number Salma, tana ɗauka ta ce, "Salma ya naga gate ɗin gida a kulle?." Daga can ɓangaren Salma ta ce, "Wallahi mun fita, mun je dubiya kuma bamu taho ba." Nayla ta ce, "Innalillahi na shiga uku, Salma fitsari nake ji kamar nayi hauka. Yanzu ina zan shiga? Kin san ba kowa na sani a unguwar nan ba."  Salma ta ce, "Wallahi bamu taho ba, ki shiga gidan Didi kawai." "Gidan Didi kuma? Ni ce zan shiga gidan Didi?." "To ba lalaura ba ce? Ita kaɗai ki ka sani a unguwar kawai ki daure ki shiga." Tsabar haushi Nayla kashe wayar tayi ta fara zaga wajan saboda fitsarin da take ji kamar zai zubo. Haka kawai ta shiga gidan Didi Omar ya ganta yayi mata tsawar da zata yi fitsarin a wando, me ya kai ta shiga gidan Didi..? ai gwara ta yi fitsarin a wando ta san a wandon ta yi. Runtse ido tayi saboda yadda take a matse sosai, kawai sai ta fara hawaye cikin matsuwa da rashin mafita. Hango ƙofar gidan Didi take yi daga inda take, kamar wacce aka bawa umarni ba shiri ta kwasa a guje ta afka gidan.    Kamar a cilla ta ta shiga falon da sallama, idon ta bai faɗa kan kowa ba sai Omar da ya kalli ƙofar yana kallon wacce tayi sallama. Idanunta ne ya faɗa cikin nasa, ga mamakinta murmushi yake yi kuma ganin ta bai saka ya daina ba sai ma ɗauke kai da yayi daga kallon ta. Didi ganin ta ƙame a jikin ƙofa sai ta miƙe ta ce, "Nayla lafiya na gan ki a firgice haka?." Nayla a wahale ta ce, "Didi fitsari nake ji." Didi ta ce, "maza shiga ki ciki mana" da sauri ta wuce ta shiga ɗakin Didi. Didi ta koma ta zauna tana kallon Omar da har lokacin fuskarsa a sake take bai yi wani abu da zai tsorata Nayla ba. "Ita wannan yarinyar kullum sai ta shigo ne?." Jin abinda ya ce sai ta ce, "Eh mana, tana sona ne nima ina sonta, tana girmama ni nima ina girmamata." Kai ya girgiza kawai, yana tuna a gaban ta Didi ta dinga yi masa faɗa harda cewa zata mare shi. Sallamar Nayla ya saka bai ce komai ba ta fito falon kamar munafuka tana kallon Didi. Didi ta ce, "ƙaraso ki zauna." Zama tayi a tsorace ta kalli Didi ta ce, "Su hajja ne basa nan, ni kuma naje gidan ƙanwar Abiy sai yanzu na dawo." Didi ta ce, "Ayya. To ki shiga kitchen ki zuba abinci in zaki ci." "Na ƙoshi" ta faɗa kanta yana ƙasa dan har lokacin yana zaune bai tashi ba. Didi ta kalli Omar da ba su yake kallo ba ya dai hakimce ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana kaɗawa. Murmushi tayi tace, "Yayanki Omar ya ci awarar da kika dafa yana ta santi." Nayla ta ɗago tana kallon Didi haka kawai gabanta yake faɗuwa, babban abin mamakin faɗuwar gaban da take ji ta banbanta da irin wacce take ji in ta ganshi. Nayla dai bata ce komai, Didi tayi murmushi ta kalli Omar da yake murmushi sosai da alama akwai abinda ya bashi dariya a wayarsa. Didi ta ce, "Omar!." Ɗago idanunsa yayi ya kalle ta suka sake haɗa ido da Nayla tayi saurin kawar da kai jin faɗuwar gaban da take ji tana neman wuce tunaninta. Hasken idanunsa kawai take a gani a idanunta, tana mamaki daman idanunsa suna da haske haka ko kuma dan yau ransa ba a ɓace yake ba?. Muryar Didi taji tana cewa, "itace fa ta dafa awarar da ka gama ci." Bai ce komai ba, amma yana mamaki meyasa Didi take son saka shi a lamarin yarinyar nan ne? Dan tsabar neman waje irin na Didi wai Yaya Omar, shi kaf duniya babu wanda yake ce masa Yaya. Wayarsa take ƙara ganin mai kiran sai ya tashi ya fita daga falon. Didi ta bishi da kallo sannan ta kalli Nayla da itama kallon sa take yi Didi ta ce, "Yau kin yi mamakin mutumin naki ko?." Nayla tayi murmushi kawai bata san meyasa ta kasa furta komai ba. Ji take kamar an ɗaure mata baki harshenta ya sarƙe ta saka cewa komai. Didi ta ce, "wallahi ɗazu ya gama yabon awarar ki wai kar na sake kaiwa inda ake yi na dinga yin irinta, yau tsokanarsa nake tayi shiyasa yake ta murmushi." Nayla ta ce, "abin mamaki, ban ɗauka yana dariya ba." Didi tayi dariya ta ce, "dariya har da ta ƙeta in dai Omar ne, kawai bashi da saurin sabo ne kwata-kwata, amma da zaku saba ke kan ki da kinga canji daga halayensa. Yana da hira sosai in ya so, zaku zauna ku yi hira cikin raha da wasa da dariya. Inda zaku saba murmushinsa bazai miki wahalar gani ba, kafin a saba ɗin ne ana jimawa." Nayla ta girgiza kai kawai ta sake kallon inda ya tashi sai take ji a zuciyarta dama ya dawo ta sake gani yana murmushi.       Shi kuwa Omar ganin kiran Senator ya saka shi ya fita ya ɗauja da sallama, suka gaisa Senator kamar ko yaushe ya ce, "Tiger gobe Narma zata sauka a Kano, jirginta zai sauka bayana azahar in sha Allah. Akwai wanda na bashi number ka zai kira ka ya kai ka airport ɗin, in ya nuna maka ita sai ka karɓi motar ku wuce. Zan tura maka address ɗin gidan da zata sauka." Omar ya ce, "Allah ya kaimu." "Amin. Tiger please kar kayi wasa da wannan lamari, ka kula da Narma kar ka bar wani wanda baka yarda dashi ba a kusa ita. Akwai wanda basa son su ga Narma a Kano, na san baka da wasa shiyasa na zaɓe ka akan police." "In sha Allah babu damuwa, sai dai in a samu damuwa daga wajanta." "kar ka damu zan ja mata kunne sosai, in kaga abu ba daidai ba ka kira ni." "In sha Allah" ya sake amsawa a taƙaice kafin su yi sallama ya kashe wayar. "Zan wuce" yaji an faɗa daga bayansa muryata na rawa sosai alamun a tsorace take. Juyowa yayi ya kalle ta kanta yana ƙasa jikinta na ɗan rawa kamar wacce aka jonawa lantarki. Didi ya gano fito daga falo ta nufo inda Nayla take tsaye. Bai ce komai ba kuma bai motsa ba har sai da Didi tazo wajan ta ce, "Omar ka bata hanya mana." Magana yake so yayi amma sai ya fasa ya shiga ɗaki Nayla ta fita a guje, Didi tana dariya ta bi bayan ta sai da ta ga ta shiga gidan Hajja sannan ta dawo.      Tana shiga ta dinga yiwa Salma masifa akan me ta san zasu fita bata faɗa mata ba, Salma ta ce, "Anty bala'i, na kira ki ban samu ba, kuma ba ga shi kin shiga gidan su mai baki tsoro ba?." "Ke kin san halin da nake ciki da na dawo? Fitsari kamar ya kashe ni bani da zaɓin da wuce na shiga gidan." Salma tayi dariya tana bin ta da kallo ta ce, "ya ban ga fitsari yana bin jikinki ba? Dan na san gamuwar ku dole ki yi fitsarin wando." Nayla ta ce, "kee abin mamaki, yau bai min komai ba, hasalima da na shiga suna hira da Didi murmushi bawan Allah nan yake yi. Wai daman yana murmushi?." Salma ta ce, "mai zai hana ya yi? Kawai ba kowa yake yiwa bane." Nayla ta ce, "naga alama" ta faɗa tana shiga ɗaki tana sake hango murmushinsa a idanunta. Washe gari har rana ta fito Nayla ta kasa mantawa da fuskar Omar yana murmushi, da ta rufe ido shi take gani da lokacin da suka haɗa ido hasken idanunsa ya shiga cikin nata ido. Gabaɗaya ta kasa mantawa da abin ta kwana, tayi-tayi ta manta amma abin ya ci tura.          Omar kuwa lokacin da driver ya kira shi ko Didi bai sanarwa ba ya fita, ya same shi yana jiransa a mota ya shiga motar suka ɗauki hanyar airport. Mutumin yana ta jan Omar da hira shi kuwa ba amsawa yake ba yayi shiru abinsa. A cikin airport suka ajjiye motar Omar ya fito ya jingina da motar shima driver ya fito yayi kamar yadda Omar ya yi. Kallon Omar ya yi ya ce, "Abokina sai kayi haƙuri da yarinyar nan bata ji, tana da rawar kai sosai sannan tana da gadara duk abinda yake so shi za a yi mata." Omar ya ɗago ido ya kalle shi mutumin ya ce, "Wallahi sai kayi haƙuri dan bata da kunya ko kaɗan, mulki take ji dashi da isa, hatta buɗe ƙofar mota zata ce kai zaka yi mata. Ga tsawa da kyara kamar waɗanda ta haifa." Omar ya girgiza kai kawai mutumin ya sake cewa, "Ni ai naji daɗi da aka ce wannan karon ba ni zan dinga kai ta inda take so ba, wallahi sai sha biyu na dare zata yi min waya na baro gidana nazo na siyo mata pizza ko shawarma. Ta tara ƴan mata irinta ƴaƴan manya a gidan suna ihuu kamar ba dare ba." Omar duk yana jinsa kawai bai san me zai ce masa ba ne, amma duk abinda yake faɗa baya tunanin ko babanta zai yi masa shi balle ita. Drivern ya ce, "Abokina gata nan ta fito, Hajiya Narma kenan shugabar masu shigar banza nigeria." Omar ya ɗaga kai yana kallon inda yake kallo, Narma ya hango cikin atamfa fitted gown ta atamfa ta kama ta sosai ɗakyar take motsawa, mayafi ne siriri ta yafa shi a kafaɗa, hannun rigar gabaɗaya da net aka yi shi hakan ya bayyanar da farin dantsen hannunta, hatta pink colour ɗin bra ɗinta ana gani. Tahowa take fuskar ta ɗauke da baƙin glasess, gabaɗaya ilahirin jikinta a bayyane yake, daga wrist ɗinta zuwa hips ɗinta an kama shi ɗam, a kuma cike sosai. Duk yadda ka kai ga kushe sai ka yabi surar Narma, dan Narma akwai sura ma sha Allah, shiyasa take ɗaukar hankalin maza nan take. Omar gani yayi wanda suke tsaye ya ƙarasa da sauri ya karɓi trolly bag ɗinta ya saka a bayan mota, sannan ya buɗe mata bayan motar ta shiga. Omar ya bawa key ɗin motar ya ce, "Allah ya fushsheka lafiya mutumina, ni daga nan zan wuce." Omar ya kalle shi ya ce, "na gode. Amma kazo mu je gidan tare ban gane kwatancen ba." "To mu je" ya faɗa yana buɗe motar ya shiga shi kuma ya shiga gaba. Drivern ya kalle ta ya ce, "Hajiya barka da zuwa." Danna waya take yi ta ce, "barka." Bata sake magana ba shima bai sake ba ya kunna motar suka bar cikin airport ɗin. Tafiya suke babu wanda yake magana a ciki su, ƙhamshin turarenta ya gama mamaye motar gabaɗaya. Wayar Omar ce tayi ƙara ya duba yaga Didi ce ya ɗauka yana cewa, "Na fita zan dawo anjima." Abinda ya ce kenan ya cire wayar daga kunnesa, hakan ya saka ta ɗago kai tana kallon inda Omar ɗin yake. "kai meye ma sunan ka?." Driver ya ce, "Yahya Hajiya," "Waye wannan muna tafiya yana amsa min waya?." Yahya ya ce, "baƙo ne Hajiya, bai san dokokin ki ba." "Ka sanar dashi" ta faɗa tana cigaba da danna wayarta. Omar bai ma kalle shi ba ya cigaba da danna waya a haka suka isa katafaran gidan da yake cikin nasarawa gra, mai gadi ya buɗe masu ƙofa suka shiga. Yahya ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofa ta fito ya ɗauki jakar ta yabi bayan ta a guje. Omar ya bushi da kallon mamaki dan shi bai ga abu ɗaya da zai iya yi mata ba, daga buɗe ƙofar da ɗaukar jakar. Yana nan tsaye Yahya ya dawo ya kalle shi ya ce, "Abokina wannan matar bata da kunya na faɗa maka, gwara ka ja girmanka, in ba haka ba zata yi maka abinda bazai maka daɗi ba. Ba a waya a mota in tana ciki, ka kiyaye." Omar ya girgiza kai ya ce, "wai abinda ka ke yi mata nima shi zan yi?." "Fiye da haka ma." "Ba a haifi yarinyar da zan yiwa wannan abun ba." Yahya yayi dariya ya ce, "Tunda har ka karɓi aiki da Hajiya Narma sai kayi haƙuri kawai, duk abinda ka ke faɗa yanzu a baki ne, amma zaka tabbatar da magana ta gaskiya ce." Kallon idon Yahya ya yi ya ce, "nayi maka kama da wanda yake wasa?." Kwarjini ya yiwa Yahya sosai sai ya girgiza kai ya ce, "A'a, amma ina baka shawara." Omar ya ɗauke kai suka yi sallama da Yahya ya tafi. Fanfo ya gani daga can gefen compound ɗin kuma yana fa buƙatar yin sallah, ya ƙarasa yayi alwala, ya juya yana kallon gidan a nan ya ga wani ƙaramin masallaci da mai gadin da ya buɗe musu ƙofa a ciki, Omar ya nufi wajan kai tsaye da niyar yin sallah. Narma ce ta fito ta canja shiga zuwa riga mai jikin roba ta kama, sannan daga sama wuyan a buɗe yake ana iya hango saman ƙirjinta. Narma ta ce, "kai!." Bai ko kalle ta ba balle ya saka ran dashi ta ke, ta sake cewa, "da kai nake." Nan ma Omar bai kalle ta ba sai ma cigaba da tafiya da yayi, mai gadin da yake zaune a cikin masallacin ya taso da sauri ya tari Omar ya ce, "Abokina magana Hajiya take maka." Omar ya kalle shi ya ce, "magana?." "Eh, gata can tana magana." "Ba da ni take ba." Muryar Narma ya ji a bayansa ta cewa, "Waye kai ina yi maka magana baza ka amsa ba?." Nan ma bai motsa ba balle ya kalle ta. Shan gabansa tayi tana kallonsa daga sama har ƙasa ta ce, "ba kai ne Tiger ba? Kana ji ina yi maka magana zaka yi min banza waye kai?." Ganin yayi shiru bai amsa ba ya dai zuba mata ido har hakan ya saka ta janye idanunta ta ce, "charger zaka je ka siyo min yanzun nan, ka bar shiga masallacin ka je ka siyo min." _Tashin hankali, haka za a yi da yarinyar nan?, ni zata tsayarta ce zata aika? Ni take yiwa tsawa? Lallai kafin na gama aiki da ita sai dai a kai gawar ta Abuja._ Abinda yake aiyanawa kenan yana ƙare mata kallo cikin ɓacin da ya baya bayyana akan fuskarsa. Ta buɗe baki zata yi magana ya ce, "in kika sake yi min magana sai na yi ball dake a wajan nan, sa'anki ne ni ko yaron ki ne..? bani waje!?" Ya faɗa da tsawa idanunsa na waje yana kallon ta. Narma bata san ta daka tsalle ta koma gefe ba sai sautin tsakinsa ta ji ya shiga masallaci yana ayyana dole ma ya kira baban yarinyar nan bazai juri wannan shirmen nata ba, ko ya ajjiye aikin da ya karɓa ko a wayi gari yayi mata illa. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 10.* Narma suman tsaye tayi ta bishi da kallo cikin faɗuwar gaba, ba a taɓa yi mata tsawa ba sai yau, tsawar ta ratsata sosai shiyasa bata san ta koma gefe ba. Sai da ta dawo hankalinta ta kalli ma'aikatan gidan ta ga kowa kallon ta yake yi rai a ɓace ta wuce cikin gidan a guje. Tana shiga babban falon gidan ta ɗauki waya hannu na rawa ta kira mahaifinta. Yana ɗauka kafin ya yi magana ta ce, "Dad waye wannan ka haɗa ni dashi? Dad tsawa fa yake yi min ina yi masa magana yayi min banza. Kuma tun airport ko sannu da zuwa bai yi min ba, kamar ma bai san ya ɗauko ni a mota ba. Gaskiya Dad bazan jure zama da wannan mutumin ba na gaji." Senator da yake sauraren ta sai da ta gama ya ce, "ƙyale ni dashi zan kira shi yanzu a waya, kin sauka lafiya?." Da shagwaɓe ta ce, "lafiya lau Dad. Charger na ce ya siyo min na bar tawa a gida kaga yadda ya yi min tsawa kamar ni ce nake aiki a ƙasansa? Babban abin ɓacin ran a gaban maids ɗin gidan nan. Gaskiya Dad i can't toleret this kind of nonsense."  Dad ya ce, "don't worry my dear, zan kira shi yanzu."  "And let him come and say sorry to me Dad." Senator ya yi murmushi ya ce, "hold on, i'm coming." Kashe wayar tayi ta nemi waje zauna tana lissafa kalar wulaƙancin da zata yi masa.          Omar kuwa tun yana sallah yake jin kiran waya na shigowa wayarsa, bai katse sallar ba sai da ya idar sannan ya duba wayar ganin mai kiran sai yayi ƙaramin tsaki ya taso ya fito daga masallacin. Car park ya ƙarasa, daga gefe akwai madaidaiciyar gazebo ta shan iska da kujeru a ciki nan ya shiga ya zauna, yana zama wayarsa ta ɗauki ƙara ya ɗauka ya saka a kunne.         Daga can ɓangaren Sen ya ce, "Tiger." Omar ya amsa suka gaisa kafin ya ce, "Tiger Narma ta kira ni ta ce kayi mata tsawa dan ta ce a siyo mata charger." Omar ya ce, "ba ɗan aiken ta bane ba ni, haka zalika ni ba yaron ta bane. Saboda kai na karɓi aikin nan, kai ta wajan da take so shine abinda ka ce zan yi, amma ba wai dan ta saka ni a gaba tana yi min ihu ba. In a haka za a tafi gaskiya zan ajjiye aikin nan sai a samo wani, ni bazan jure ba." Senator ya ce, "bata san waye kai bane shiyasa, Amma zan mata magana za a samu mai yi mata aike da siyo mata abinda take so, kai dai kai nake so ka dinga kai ta inda zata je." Omar ya ce, "bazan dinga zama a nan ba gaskiya, zan dinga tafiya in zata fita sai ta sanar dani nazo na kaita." Senator ya ce, "Daman ni abinda nake so shine ka kaita ka kula da lamarinta a duk inda take." Omar ya yi shiru Sen ya ce, "ina zuwa" ya faɗa yana yanke wayar. Omar yana nan zaune bai san me ya faru ba sai yaga Yahya wanda suka rabu ya dawo ya shiga gidan ba jimawa ya dawo ya hau mota ya fita. Taɓe baki yayi dan a kaf duniya bai ga macen da zata aike shi ba in dai ba Didi ba. Tsabar raini shi zata dinga yiwa tsawa ta ɗauka shi yaron ta ne?. Bai jima sosai a zaune a wajan ba kawai ya tashi bayan ya bawa Yahya key ɗin motar da ya bashi ya fita daga gidan. A can Abuja kuwa Dad yana yanke wayar Mum ta kalle shi a fusace ta ce, "ni fa tun asali ban so ka haɗa riƙaƙƙen ɗan daba da ƴata ba, ta ya ya za a ce kaf jami'an tsaron da suke Kano ka rasa da wanda zaka haɗa ta sai da ɗan daba?. Waye shi da zai mata tsawa har yake ganin yafi ƙarfin ta aike shi? Ba a ƙarƙashin ka yake ba?." Nabil da yake zaune shima rai a ɓace ya ce, "abinda zan ce kenan Mum. Ta ya zai mata tsawa har kuma Dad ka biye masa ka ce wai in zata yi aike ta aiki Yahya? Kenan shi ya fi ƙarfin ta aike shi ko me?. Gaskiya Dad wannan ba wanda za a zauna dashi bane, ina bayan Mum ka salleme shi kawai a tura mata wani ya dinga kaita duk inda yake so. Wani ƙazami dashi har yana da bakin da zai ce wai baza ta aike shi ba? Waye shi?." Mum ta kuma ɗora da cewa, "ba kowa bane face ɗan iska gari na banza da wofi, matsayin numfashi su ma ba ɗaya bane amma Dear ya saka tana shaƙar gurɓataccen numfashinsa a mota ɗaya. Tsakanin ta dashi shine mahaifinta ya biya shi ya ne ya tayar da hayaniya a wajan zaɓe da sauran su, amma matsayin ya haɗa mota ɗaya da Narma sam-sam bai tashi ba." Dad yayi murmushi yana kallon su ya ce, "na fi ku tsanar kusancin da ya samu da Narma saboda bashi da wannan matsayin kuma bazai taɓa samun sa ba har abada. Tsakanin Narma dashi kamar tazarar sama da ƙasa, turaren da Narma take sakawa sai ya siyi danginsa kaf balle kuma agogon da take ɗaurawa a hannunta. Ban haɗa shi da Narma dan ya yiwa Narma wani abun ba, na haɗa ta dashi ne na ɗan lokaci saboda lafiyar ta da zaman ta lafiya a Kano. Ke kin san wancan lokacin abinda ya faru da ita, tare musu hanya aka yi ana ƙoƙarin saceta in ba dan Allah ya tsare ba da yanzu wataƙila bata gidan nan. Shi kuwa kaf kano a san shi, in baka san shi ba ka san sunan shi, ana faɗar sunansa shikenan duk iskancin da ka ke ki dashi ka ajjiye. Saboda haka kawai na bashi Narma ya dinga kai ta duk inda zata je, in ba dan haka ba haɗa ido ma bai kai matsayin da Narma zata yi dashi ba." Nabil ya ce, "Amma Dad akwai police a Kano da zaka ɗauka a haɗa ta dasu ta je duk inda take so, suna da bindiga shi kuwa bashi da ita, sun san aikin su shi kuwa me ya sani ban da wasa da wuƙa?. Gaskiya Dad ban ji daɗi ba, wani ƙazamin bagidaje dashi har yana da zarrar da kana yi masa magana yana cewa wai zai ajjiye aikin saboda baya son raini? Just Imagine, wani banza shashasha talaka ne yake faɗawa ƴar senator haka." Dad ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "kar ka damu Nabil na san abinda nake yi, kar ka samu damuwa, wani lokacin yawo da irin su Tiger yafi amfani akan yawo da police. Na san abinda nake yi fa kar ka samu damuwa." Mum dai kawar da kai tayi zuciyar ta cike da haushin wannan hukunci na senator, gashi wani banza talaka yana wulaƙanta mata yarinya.      Wayar Narma ce ta sake zuwa ya ɗauka ya saka a speaker muryarta karaɗe falon ta ce, "Dad zan fita da daddare amma an sanar dani ya fita, Dad i'm so done with his attitude, Ko 24 hours ban yi ba ya fara bani cikon kai? Gaskiya i can't." Dad ya ce, "whice time you want to go?." "By 8." "Alright, i will let him know, i will send you his number in kina son fita ko yaushe you can give him a call." Narma ta ce, "Dad what's so special about this guy that you're willing to share my contact info with him?."Dad ya ce, "kar ki damu" abinda ya ce kenan ya yanke wayar yana kallon irin kallon da su Mum suke masa amma bai kula su ba dan shi kaɗai ya san amfanin Tiger su baza su gane abinda yake nufi ba shiyasa.           Shi kuwa Omar ko da ya bar gidan a napep ya koma unguwar su ya sauka a bakin layin ya shiga ciki a ƙafa. Babu wanda yake yiwa magana kamar yadda babu mai yi masa magana tafiya kawai yake yi cikin takun isa da ƙasaita da nuna zallar izza. "Ummaru wucewa zaka yi? To na gode." Kallon inda aka yi maganar yayi yaga Hajja da hijjabi zata shiga gidan ta da alama dawowar ta kenan daga wani waje. Zai yi magana ta ce, "in baza ka shigo mu gaisa ba na gode" ta faɗa tana shiga cikin gidan. Shi fa wallahi baya son shiga gidan mutane, ga Hajja yana ganin kırkinta da mutuncinta amma shi gabaɗaya baya son shiga gidan. Ƙaramin tsaki ya yi ya shiga gidan fuskarsa a ɗaure ya yi sallama a car park ɗin gidan. Nayla da ta ji sallama ta amsa tana juyowa ido ta ya faɗa cikin nasa, bata san ta saki tea flaks ɗin da yake hannunta ba sai sautin fashewar kwalba tayi. Ido ta wara waje tana kallonsa shi kuma kallon sencond biyar ya yi mata ya ɗauke kai ya jiyo muryar Hajja tana cewa, "Ummaru shigo mana." Shiga falon ya yi Hajja tana cewa, "na ɗauka ai baza ka shigo ba, ko gaishe ni ɗin da ka ke yi yanzu ka daina." "Ina yini" ya furta a taƙaice ta amsa ta ce, "lafiya lau Ummaru, ya gida?." "Lafiya" ya amsa a taƙaice yana kallon ƙasa. Hajja ta ce, "Hauwa'u filas ɗin shayin ki ka fasa? Naji ƙarar fashewar kwalba. Ki saka shi a shara kawai, Allah ya sa baki ji ciwo ba" Hajja ta faɗa yadda Nayla zata ji. Maganar da Hajja tayi ne ya dawo da ita hankalinta, ta ɗauki flakas ɗin ta saka a shara ta taho a hankali zata shiga falon shi kuma zai fito. Ɗifff tayi ta ja numfashi mai nauyi, ƙiris ya rage ƙirjinsu ya haɗu waje ɗaya, ya kalli fuskarta na wasu sacanni murya a can ƙasa ya ce, "ki ƙauracewa ganina" abinda ya ce kenan tayi saurin yin baya shi kuma ya fita yana ji Hajja tana yi masa magana.       Nayla ta shiga tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "na shiga uku, Hajja daman yana shigowa gidan nan?." Hajja ta ce, "yana shigowa mana." Nayla ta ce, "Allah ya taimaki Salma da take bacci bata ganshi ba, wai har da ce min na ƙauracewa ganinsa. Ni dai ban san ƙaddarar da take haɗa mu ba wallahi, gabana sai faɗuwa yake yi." Hajja ta ce, "shiyasa ki ka fasa min filas ɗin shayi ai, sai ki kira babanki Daddy ya bayar a kawo mana sabo saboda gobe zaki azumi." Nayla dai numfashi take sauke a hankali, abinda yake bata mamaki faɗuwar gaban da take ji ba ta tsoro ba ce kamar wacce take ji farkon haɗuwarsu, muryarsa take ji a kunnenta tana hango yadda ƙirjinsu da ya kusa haɗewa da na juna. Lumshe ido tayi ta buɗe a bayyane ta ce, "Allah mai iko." Hajja ta kalle ta sai tayi tsaki ta cigaba da kallon tv tana kallon tashar saudia.            Omar yana shiga gidan a tsakar gidan ya samu Didi ta juyo tana kallon sa ta ce, "shigowa ba sallama kuma Omar?." Bai amsa mata ba ta kalle shi ta ce, "ina kaje ne?." Bai ce komai ba ya shiga falon ya zauna, itama bata bi bayan sa ba sai da ta gama abinda take yi sannan ta shiga ta samu yana cin abinci. Bata yi masa magana ba har ya gama dan ta san shi ba mutum ne mai son yin magana in yana cin  abinci ba, sai da ya sha ruwa ya sauke numfashi kaɗan sannan ta kalle shi ta ce, "ina ka je?." Kallon ta yayi ya tashi zaune sosai ya ce, "na fara wani aiki ne, amma ina ganin dole na ajjiye shi kafin na shaƙe yarinyar." Didi ta ce wanne aiki ne?." "Zan faɗa miki, na karɓi aikin saboda ke ne kawai, na san aikin zai kawo kuɗi sosai ga hidimar bikin ki tana zuwa." "Waye ya ce maka hidimar bikina tana zuwa?." "A jikina naji hakan." "Allah ya sa. Amma ka faɗa min wanne irin aiki ne?." Bai ɓoye mata ba ya faɗa mata komai da kuma wacce aka haɗa shi da ita, ya ɗora da cewa, "ni wai yarinyar nan zata yiwa tsawa" yayi wani murmushi ya ce, "ko babanta bana tunanin zai yi min tsawa na ƙyale shi balle ita, a kaf duniya ke kaɗai zaki aike ni naje bayan ke babu wata halittar." Didi da ta saki baki tana kallon sa cikin mamakin da ya sumar da ita a wajan ta ce, "Omar Senator Sagir ɗan takarar gwamnan Kano kuma sanata mai ci yanzu! Omar Meyasa ka kai kanka irin wannan wajan don Allah?. Na san halin ka baka da haƙuri ko kaɗan, kar zuciyarka ta kai ka ga aikatawa yarinyar nan wani abun na shiga uku." Ya kalle ta ya ce, "kema kin san bazan ɗauki raini ba ai ko? Kuma bazan ɗauki iskanci ba. Ko Wacece ita daidai nake da ita wallahi, dan ubantq sanata ne hakan bazai hana na tsaga mata fuska ba da aska ba. In ta ja mutuncinta zamu zauna lafiya, in bata ja ba sai dai ko yi haƙuri kawai zaki ji labarin ina prison." Didi a ruɗe ta ce, "Omar don girman Allah ka ajjiye aikin nan ka rufa min asiri, shi uban yarinyar wanne ganganci ne ya saka ya haɗa ka da ita? Omar ya san halin ka kuwa? Ya san baka da juriya kuwa? Ya san kana ɗaukar makami kuwa Omar?." Ganin Didi ta ruɗe hankalinta ya tashi sai ya ce, "kar ki damu Didi, babu abinda zai faru, in kin ga wani abu ya faru yarinyar tazo da rainin hankali ne wanda kin san bazan jure masa ba. Ko da ita nake yiwa aiki bata isa ta yi min abinda bai yi min balle babanta nake yiwa aiki, Kuma shima baban nata alfarmata ya nema a wannan ɓangaren, sai da na amince zan yi sannan ya turota." Ganin ya miƙe tsaye Didi ma ta miƙe ta ce, "Omar ka yi masa waya ka ajjiye aikin nan." "Didi ki nutsu don Allah, babu abinda zai same ni." "Wallahi a jikina nake ji haɗuwarka da ita bazai zama alkhairi ba wallahi, don Allah ka ajjiye aikin nan." Ya bita da kallo ya ce, "Didi yarinyar da ki ke gani ce a social media fa, wacce ki ke cewa tana burge ki kin ganeta?." Didi ta wara ido waje ta ɗauki wayarta da sauri ta dubo page ɗin Barr Nass ta nuna masa ta ce, "wannan ce?." Hoton Narma ya gani cikin kayan lauyoyi sun yi mata kyau matuƙa fuskar ta sai sheƙi take yi da annuri, wani iri yaji a jikinsa ya janye idanunsa ya kalli Didi ya ce, "ina faɗa miki itace kuma kina nuna min hotonta." Didi ta ajjiye wayar ta ce, "na shiga uku, Omar don Allah ka ajjiye aikin nan ka ji? Yarinyar nan kowa ya yi mata shaidar bata da kunya, a social media ma faɗa ake yi da ita balle kuma a zahiri, kuma kai ka ga tana ganin a ƙasanta ka ke aiki." Murmushi ya yi ya ce, "Didi kar ki damu babu abinda zai faru." Didi a sanyaye ta ce, "Tsoro nake ji Omar, bana son wani abu ya same ka shiyasa." "Babu komai." Shiru tayi bata ce komai ba shi kuma ya fita ya bar mata falon tana kallon sa. Tana mamakin wannan ƙarfin hali na Omar, yarinya kamar wannan ƴar manya ita yake cewa in tayi masa wani abun sai dai ta samu labarin yana prison kenan bazai ƙyaleta ba, ta san daman bazai ƙyale ɗin ba wallahi sai dai a kulle shi. Ita dai duk fargaba ta gama cika mata zuciya, saboda babu wanda ya san halin Omar kamar ta, tsaf zai jawo mata maganar da zata kwana tana kuka. A haka ta koma ta zauna jiki babu ƙwari.       Narma kuwa bacci ta yi sosai bata tashi ba sai magriba tayi sallar la'asar sannan tayi magriba, sakkowa tayi ƙasa ta samu har mai aiki ta haɗa mata abinci ta zauna taci abinci, ta ɗauki waya tana amsawa kafin ta tashi ta koma sama. Ta window ta leƙa ta ga Yahya a zaune ta ɗaga murya ta ce, "kai!." Ɗago kai yayi ya kalle ta ya ce, "Hajiya." Narma ta ce, "ina sabon driver nan yake?." Yahya ya ce, "Hajiya ai tun ɗazu da ya tafi bai dawo ba." Kai ta girgiza ta koma tana mamakinsa da ƙarfin hali irin nasa. Shi ba kowan kowa ba amma ya dinga yi mata iskanci kala-kala. Sai da tayi sallar i'sha sannan ta fara shiri, sun yi da ƙawayenta zasu ne yawo hakan ya saka ta shirya cikin doguwar riga wacce jikinta take kamar roba mai tsaga a baya, daga hips ɗin akwai wani maɗauri kamar mayafi daka ɗaure shi aka ɗaura a tsakiyar rigar. Rigar baƙa ce hakan ya saka ta haska jikinta sosai, ta ɗauki hula ta saka sannan ta ɗauko ƙaramin mayafi ta ɗora akan hular. Kallon kanta take yi, dan ta kanta san tayi kyau itama sosai, ta fesa turare masu daɗin gaske sannan ta sauka falon ƙasa a lokacin takwas daidai. A daidai wannan lokacin Omar ya shigo cikin gidan ya kalli Yahya suka gaisa yana cewa, "yanzu Hajiya yake tambayarka." Omar ya ce, "gani ai, tana ina?." "Tana ciki bata fito ba." Omar ya kalli agogon wayar sa ya ce, "ƙarfe takwas aka ce min, yanzu kuma takwas da mintina biyu, In takwas da sha biyar tayi wallahi babu inda zan je." Shi dai Yahya kallon sa yake yi da mamaki, ganin sun haɗa ido sai Yahya ya ce, "ban san ko sunanka ba amma ƙarfin halin ka yana bani mamaki." Omar ya kalle shi ya ce, "Omar sunana." "Koda na ji, yanayinka da maganarka da ta masu suna Omar ka yi kama, Daman da wahala ka ga masu suna Omar ba irinka ba, ko kaɗan ba sa lamuntar raini." Ɗan murmushi Omar ya yi kawai amma bai ce komai ba. Narma ce ta fito tana duba waya tana cewa, "wai ina driver nan yake ne? Bana son wulaƙanci da iskanci fa, dan ya raina ni ni ce zan zauna ina jiran sa?." Inda yake ta kalla ta ga ya kalle ta ya ɗauke kai kafin ya ƙarasa wajan motar ya buɗe mazaunin driver ya shiga ya zauna ita kuma ta ja ta tsaya. Ƙwanƙwasa glass ɗin gaban motar tayi ya sauke glass ɗin ƙasa. Wani irin kallo take masa na raini da ƙasƙanci ta ce, "Malam ka sakko ka buɗe min, ko kana so kace ni zan buɗe?." "Baki da hannu?" Ya faɗa ba tare da ya sake kallon ta ba. "Ina dashi, kai nake so ka buɗe min." "Ashe baza ki je" ya sake kallon agogo ya ce, "kina da mintina bakwai in lokaci ya cika babu inda zan je." Kallon sa take yi shi kuma ya kalli glass ɗin gaban motar kamar motar sa, fuskarsa ɗaure matuƙa ga wani kwarjini da fuskar take fitarwa. Duk da tana jin tsoronsa musamman yadda ya ɗaure fuska amma hakan ya saka ta kuma cewa, "ni kuma indai baka buɗe min ba bazan je" ta faɗa tana komawa gefe ta ja ta tsaya tana so ta ƙure shi iskancinsa. Shi kuwa kallon ta yayi zuciyarsa a sama matuƙa, abu ɗaya kawai ya sani ko zata mutu ta dawo wallahi bazai buɗe mata mota ba sai dai kar ta je. Zama ya cigaba da yi a cikin motar sai kace motar ta Didi ce. Agogo yake kallo yana jira lokacin da ya bata ya cika ya fita ya bar gidan. Su dai ma'aikatan gidan kallon ikon Allah suke yi, mamakin Omar su ke yi ɓangare ɗaya suna jin daɗi an samu daidai da Narma, suna tsaye suna so su ga waye zai ci wasan. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 11.* Kowa a wajan kallon ta yake yi ana kuma jira a ga Omar zai fito ya buɗe mata motar ko bazai fito ba. Ga mamakin su Omar bai fito ba yana zaune a cikin motar kamar motarsa, ita kuma tana tsaye har lokacin tana jira ya fito ya buɗe mata. Mamakin sa take yi ganin bai sauko ya buɗe mata ba kenan bazai yi ba? In haka ya faru wacce irin kunya zata ji a gaban ma'aikatan gidan?. Wayarta ce tayi ƙara ta ga ƙawayenta da suke jiran ta zasu fita ne, ta buga uban tsaki ta kashe wayar tana sake kallon sa babu alamun ma zai fito dan ko kallon inda take ma baya yi. Shi kuwa Omar ƙoƙarin daidaita ɓacin ransa yake yi dan in ya fita a yadda yake jin zuciyarsa tsaf zai sharara mata maruka masu zafi, shi kuma ba haka yake so ba, yana so su rabu lafiya ko dan alƙawarin da ya yiwa Didi, sannan yana so su rabu lafiya ko dan kuɗin mahaifinta da ya karɓa. Shiru na kusan mintina biyar hakan ya yi daidai da saursa minti biyu ya kama gaban sa. Yahya ne ya ƙaraso wajan motar  a sanyaye ya ƙwanƙwasawa glass ɗin gefen Omar, Omar glass ya sauke yana kallon sa ya ce, "Omar don Allah kazo ka buɗe mata ka huta." Omar ya kalle shi ya ɗauke kai dan babu amfanin ma yi masa magana. Yahya ya juya ga Narma ya ce, "Hajiya bismillah" ya faɗa yana buɗe mata amma sai ta bishi da banzan kallo na wulaƙanci ta ce, "Wallahi shi zai buɗe min, in kuma bai buɗe min ba daga yau ya bar aiki a gidan nan, sai naga waye ubansa a Kano da yake min wannan wulaƙanci. Shashasha dashi ƙazami." Buɗe kofar taga an yi sai tayi murmushi ta ɗauka zai buɗe mata ne, ga mamakin ta kai tsaye inda take ya nufa fuskarsa a ɗaure, yana zuwa ya kalle ta ya ce, "in kika sake furta abinda kika furta ɗazu sai kin yi dana sanin haɗa ido dani a rayuwarki, in kuma kina ganin wasa nake yi ki maimaita abinda ki ka ce yanzu" ya faɗa ciki tsawa yana tsare ta da idanunsa masu ban tsoro da kwarjini. Ɗiff Narma tayi tana kallon idanun sakamar yadda ita yake kallo, da sauri ta ɗauke kai daga kansa, ganin ta yi shiru ya cize baki yana karkatar da baki irin yadda ƴan daba suke yi ya nuna ta da taysa ya ce, "ki san irin maganar da zaki dinga faɗa min in kina so kan ki da zaman lafiya, In kuma kina so na huda cikin ki sai ki cigaba." Yahya ya kalla ya cilla masa key ɗin motar shi kuma ya chafe, Omar bai ce komai ba ya juya ya fita daga gidan. Wata uwar ƙara Narma tayi ta shiga cikin gidan a guje ta faɗa kan kujera ta fashe da kuka mai ƙunar rai. Wai ita Narma wani banzan ɗan daba, ɗan shaye-shaye ya yiwa wannan wulaƙacin a gaban ma'aikata, kawai saboda Dad ya bashi damar haɗa ido da ita shine yake zaƙewa. Ita Narma mai capacity wani ɗan tasha ya wulaƙanta a gaban masu aiki a ƙarƙashin ta. Hannu na rawa take kiran Dad, yana ɗauka kawai ta fashe masa da kuka. Dad ya ruɗe sosai ya ce, "Oh Narma, what wrong? Why are you crying like this?." Kuka take yi sosai cikin baƙin cikin da take ji a zuciyarta. Sai da tayi kukan ta gaji murya na rawa ta ce, "Dad i was really disrespected by that guy in front of the maids, Dad ƙawayena suna can suna jira na amma yayi tafiyarsa. Dad gaskiya ni bana son aiki dashi, ka barni da wanda muke tare dasu a nan." Dad ya ce, "stop crying and talk to me, what happened?." Narma ta bashi labarin abinda ya yi mata sannan ta ce, "Dad wai waye shi da yake min haka ne?." Dad ya ce, "ba kowa bane fa ce ɗan daba kuma ɗan tasha, ba kowa bane fa ce ƴan bangar siyasa wanda mu ke amfani dasu wajan cikar burin mu. Bana son yin wasa da Tiger shiyasa kika ga ina biye masa duk abinda ya ce, zaɓen gaba nake ji ke kin san kujerar da nake nema, irin su Tiger makami ne sosai a tafiyar mu shiyasa ki ka ina biye masa. In ba dan haka ba shi waye? Ko inda motarki take bai isa yazo ba, lafiyarsa nake so ya bani wajan kare ta ki shiyasa nake jure duk abinda yake miki. Sorry my daughter kar ki damu da wannan, abu ne ƙarami da mun ci zaɓe shikenan bazai sake ganin koda fuskarki ba. So wipe your tears my dear, i know what i'm going to do." Narma ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "But Dad if he doesn't stop bothring me and upset me, i will have him arrested wallahi." Dad ya ce, "kar ki damu, ni zan san abinda zan yi. Yanzu kin zuwa dinner ɗin?." "Na fasa." "Gobe ƙarfe nawa zaki je arewa 24 ɗin?." "Zuwa 11am." "Okay ki kwantar da hankalinki ki huta kin ji? Babu abinda zai sake faruwa." Amsa tayi kawai ta kashe wayar zuciyarta na aiyana mata irin abubuwan da ya kamata ta yi masa wanda zata huce.        Shi kuwa Omar yana fita ya tarar da Bash a machine ya ɗauke shi suka bar wajan zuciyarsa na faɗa masa gwara ya bi shawarar Didi ya ajjiye aikin nan in ba haka ba wallahi zai yiwa ƴar mutane illa. A haka suka je unguwar yana sauka akan machine wayarsa tana yin ƙara, ko bai duba ba ya san Senator ne hakan ya saka kawai ya danna ya kara a kunne. Kafin Sen ya yi magana ya ce, "batun aikin nan na ajjiye shi bazan yi ba, matuƙar zata dinga ɗaga min murya tana faɗa min magana mara daɗi bazan jure ba, gwara na ajjiye shi a huta kawai. In ban ajjiye ba zaka tarar da abinda bazai maka daɗi ba, ba a ɗaga min murya na ƙyale, ba a yi min ihu a kai, ba a yi min maganar banza. Dan tana ƴarka baza ta yi min abinda bana so na ƙyale ba." Sen wani takaici ya tokare masa maƙogwaro amma bai nuna ba ya ce, "Tiger ya kamata ka san ƴata ce yarinyar da ku ke tare." "To dan tana ƴarka sai me? Dan tana ƴarka sai na bari tayi min abinda yake so? Ta tambayi waye ni a garin nan, babu wanda yake ɗaga min murya balle rashin kunya ko zagi. Sanin ƴarka ce ya saka nake faɗa maka, ka ja mata kunne. Senator ba haka Tiger yake ba, Tiger baya jure koda ɗaga murya ne balle maganar baki." Sen ya danne ɓacin ransa ya ce, "na ɗauka yadda ka ke girmama ni zaka girmama ƴata." Omar ya ce, "in da ta so zamu girmama juna, bata girmama ni ba nima bazan girmamata ba. Shiyasa na ce a bar aikin nan kawai." Numfashi Sen ya sauke ya ce, "na zaɓeka ne saboda na san zaka iya kular min da ita sosai, na zaɓeka akan jami'an tsaro masu bindiga amma na ga kamar hakan bai maka ba." "Kawai bana tolerating nonsense ne" ya bashi amsa kai tsaye ba tare da wani tunani ba. Tolerating nonsense, Senator ya maimaita a zuciyarsa cike da mamaki,  wai daman har yana da karatun da ya san ne kalmar take nufi, kuma dan bashi da hankali shi yake faɗawa haka akan ƴarsa?. Lallai ya zama dole ya san abin yi, da an kammala zaɓe zai saka a yi masa abinda zai manta ma ya taɓa sanin Sen a duniya. Sen ya ce, "Amma Tiger meye buɗe mota? Da ka buɗe mata kun tafi da shikenan." Wani murmushi ya yi na rainin hankali kana ya ce, "a kaf duniya Yayata kaɗai zan iya yiwa haka, bayan ita babu wani ko wata a duniya da zan buɗewa mota. Ka faɗa mata indai sai na dinga buɗe mata mota zata shiga ta je inda take so to baza ta je ko ina ba." Duk da ba a zafafe yake maganar ba amma kalamansa ciwo suke yiwa Sen sosai kawai bashi da zaɓi ne. "Is okay, ka koma ka kai ta yanzu." "Bazan iya ba, na riga na dawo gıda sai dai wani lokacin." "Well, gobe zata je interview ƙarfe sha daya na safe." "Allah ya kaimu" ya amsa a daƙile dan wallahi gabaɗaya ma aikin ya fita daga ransa, dan ya san cigaba da aiki da ita babbar damuwa zai haifar, tabbas zai iya zama silar komawar sa prison dan wallahi bazan sasssuta mata ba. Bayan ya kashe wayar gida ya shiga wajan Didi, ganin ta a zaune kamar ba ita ba ya saka shi ya ƙarasa ciki fuskar nan a tamke sosai ya ce, "Didi lafiya?." Ta kalle shi ta ce, "kaina ne yake min ciwo Omar, har zazzaɓi nake ji." "Mu je a dubaki" ya faɗa  yana kallon ta. Girgiza kai ta yi ta ce, "kar ka damu na sha magani zan warke." "Ki zo mu je a baki magani" ya sake maimaitawa yana kallon ta. Kallonsa itama tayi dan tasan baya ƙaunar ya ji tana ciwo kwata-kwata, yafi so da ta ce babu lafiya ayi maganinsa. Maganin da ta sha ta nuna masa ta ce, "na sha magani." "Waye ya baki?." "Jikar Hajja Salma, ka san karatun lafiya tayi." Shiru yayi kawai jin ance jikar Hajja kawai sai fuskar Nayla ta zo idanunsa ba tare da ya san dalili ba, ya kulle ido ya buɗe akan fuskar Didi ya ce, "yanzu da sauƙi?." "Sosai ma." "Allah ya ƙara lafiya" ya furta a sanyaye. Ta amsa da amin tana kallon sa tana mamakin abinda ya ɓata masa rai. "Ki je ki kwanta" ya katse mata tunani yana kashe tv ɗin. "Bana jin bacci Omar, Zaman kaɗaicin nan damuna yake yi sosai, in ka fita sai ni kaɗai, na danna wayar na gaji, nayi kallon na gaji." Bai ce mata komai ba ya zauna daga nesa da ita yana kallon ta. Gabaɗaya jikinsa yayi sanyi baya so yaji tana yin ciwon kai balle harda zazzaɓi, baya so yaga Didi na rashin lafiya, gabaɗaya sai ya damu kansa kamar shi ya ɗora mata. Didi ta kalle shi ganin yana kallon ta tace, "kar ka damu fa, da nayi bacci na tashi zan ji daɗi." Kai ya ɗaga mata kawai bai ce komai kuma bai daina kallon ta ba. Ganin ya damu sai ta miƙe ta ce, "ka kashe hasken falon zan je na kwanta." Kai ya ɗaga mata kawai ta shiga ciki dan kawai ta kwantar masa da hankali. Shiru yayi yana tunani, bai san dalili ba kawai fuskar Narma ta kawo masa ziyara a idanunsa, yadda take kallon sa tana tsaye da mamaki a idanunta na kalaman da take faɗa masa shi yake gani. Tsaki ya yi ya kawar da tunanin daga zuciyar sa yana zaune bai tashi ba. Bai kashe hasken ba kuma bai tashi ba dan bazai iya tafiya ya bar Didi ita kaɗai ba, in ya tafi sai yaga kamar ciwon zai same ta sosai. A kan kujera yayi bacci ba tare da ya san hakan ba sai dan bazai iya tafiya ya bar ta ba.          Ƙarfe huɗu na dare ta farka kamar kullum, tayi mamakin ganin haske a falo a kunne, ta leƙo ta ganshi a kwance yana bacci hankalinsa kwance. Murmushi tayi ta ƙaraso ta kashe hasken falon ta koma ɗaki ta yi alwala ta tayar da sallah. Sai da aka kira asuba sannan ta ƙaraso inda yake ta kalli gefen sa taga ya ajjiye ƙaramar wuƙa da wani ƙarfe da alama a jikinsa suke, ta girgiza kai ta tashe shi ya buɗe ido ta sanar dashi lokacin sallah ya yi sannan ta koma ciki shi kuma ya tashi ya fita. Bayan an idar da sallah ya dawo har ɗakin ta ya shiga kamar yadda yayi tunani tana kan sallaya ya ce, "Didi ina kwana." Murmushi ta yi ta ce, "ka tashi lafiya mai bacci a falo?." Murmushi shima ya yi sannan ya ce, "ya jiki?." "Na ji sauƙi sosai. Yau baka tashi sallar dare ba, ko baccin ne?." "Kawai ban tashi ɗin bane, Allah ya ƙara lafiya" abinda ya ce kenan ya wuce ya fita daga falon nata. Kamar yadda Sen ya ce masa ƙarfe sha ɗaya bai jira sha ɗayan tayi ba ya tafi dan shi mutum ne mai girmama lokaci, baya son african time kwata-kwata, shiyasa in kace masa ƙarfe goma to tabbas goman zaka ganshi, in ka san ƙarya ka ke ma gwara kar ka faɗa masa. Tare da Tk suka je har cikin gidan ya nemi waje ya zauna bayan suka gaisa sama-sama da masu aikin gidan. Su kam mamaki suke yi ganin da alama ba a kore shi ba akan abinda ya yi jiya, suna jinjina ƙarfin hali da kuma sa'ar da yake da ita, in ba haka ba waye zai yiwa Narma haka ya kwana lafiya. Yahya ne ya zo zai zauna kusa dashi Tk ya ce, "kai yanee?." Yahya ganin Tk da yanayin sa ya saka shi yin sak ya miƙawa Omar hannu ya ce, "Omar barka da safiya." Kallon sa ya yi suka gaisa Tk ya ce, "to kama gabanka." Kallon sa Omar kawai ya yi sai Tk ya yi shiru shi kuma ya kalli Yahya ya ce, "ka zauna." Ba musu ya zauna ya ce, "ban ɗauka ma zan ganka kazo yau ba duba da abinda ya faru jiya, na ɗauka shikenan kwantiragin aikinka ya ƙare." Omar bai amsa masa ba sai agogo da ya kalla sha ɗaya saura mintina goma sha biyar. Numfashi ya sauke ya ce, "tana da sauran mintina sha biyar." Yahya ya ce, "don Allah Omar na tambayeka." Kallon sa kawai yayi alamun ina ji shi kuma ya ce, "don Allah ne ka ke taƙama dashi ka ke yiwa ƴar sanata haka?." Omar ya ɗauke kai daga kallon sa ya ce, "ka tambayi sanatan." Zai sake magana kawai suka ga an taho a guje an zube a gaban Omar yana cewa, "Madugu uban tafiya, madugu uban matsiyata, a hauka a zame ka hau mutum ka zauna daidai. Gadon ƙaya ka ke wallahi duk wanda ya hauka babu shi babu bacci, wando ƙarfe ka ke saka ka sai wanda ya shirya. Ba ayi maka wargi ka ƙyale, jan wuya jinin Didi, Allah ya ja da ran yayar mu." Kallon wanda ya zube a gaban na sa ya ke yi ya kalli Tk sai Tk ya ce, "Damisa ai kunama ne ɗan yankin su Jijiya." Kai ya girgiza kawai ya kalli yaron da ya miƙe ya ƙaraso wajan Tk yana cewa, "kai ashe babbar giwa ce da kanta a wajan nan, ina na sani ina can ina shirme." Yahya ya maimaita sunan Damisa yana kallon Omar Tk ya ce, "eh Damisa, shine dai wanda ka ke jin labari a radios shine a zaune a gaban ka! Kayi hattara domin taken Damisa ƙi sabo." Yahya ya girgiza kai yana mamakin to me ya haɗa shi da Sanata kuma? Lallai dole ya yi jiji da kai, wannan kirari dake kwarara masa, kuma ga sunan sa da yayi tambari kusan kowa ya san shi, ko baka san shi ba kasan sunan sa. Yahya ya sake kallon sa ganin maza buyu suna gefensa a tsaye shi kam sai aikin danna waya yake yi yana kuma kaɗa ƙafa, in ka shigo gidan sai ka ɗauka mai gidan ne a zaune saboda yadda ya kame kai baza ka ce ma shi bane. Mamaki Yahya yake yi sam bai yi kama da ƴan daba ba sai ma kama yake yi da jaruman gaske, kallo ɗaya zaka yi masa kayi tunanin babban hamshaƙin mai kuɗi ne ko ɗan mai ƙudi saboda yanayin fatarsa da kyaun da Allah ya bashi, in ka sake kallon sa sai ka ɗauka soja ne, saboda kwarjini da ƙirarsa. In ka kalli fuskarsa kaga yalwar gashi sai ka ɗauka wani babban ma'aikacin gwamati ne ko hamshaƙin ɗan kasuwa. Dan ƙananun kaya ya saka harda takalmi sau ciki, kai baza ka kalle shi kace Damisan da ke zance bane. Narma kuwa tsaf ta shirya cikin riga da siket ɗnkin straight siket, ya kamata sosai ɗakyar take jefa ƙafarta saboda yadda ya kamata, ta yafa mayafi babu laifi ta saka da ɗan saka mai girma amma chantily ne gabaɗaya ana ganin jikinta. Wayarta taji yana ƙara ta duba ganin mai kiran sai ta ɗauka aka yi mata magana ta kashe ta ɗauki wayar ta ta sakko daga saman. Harabar gidan ta fito duk ma'aikatan gıdan suka ƙarasa suka gaishe ta maza da mata, shi kam yana zaune abin sa gefensa Tk shida kunama. Kallon agogo ya yi yaga saura mintina biyar a lokacin da ya bata ya tashi ya tawo wajan Tk da kunama suna take masa baya, ya buɗe motar ya shiga ya yi mata key bai ce mata komai ba. Narma sai da gabanta ya faɗi ganin yanayinsa a yau ya saka taji wani iri a zuciyarta, gudun kar abinda ya faru jiya ya faru ya saka ta buɗe bayan motar ta shiga Tk ya shiga gaba shi kuma ya ja motar suka fita. Ƙhamshin turarenta ya gama cika motar, ga ƙhamshin mai daɗi da tsayawa a rai bai ce mata komai ba itama bata ce masa komai ba. "Tk." "Allah ya ja da zamanin Madugu." "Ina ne Arewa24?." "Nan gaba ne babu nisa." Bai sake magana ba ya cigaba da tafiya Tk na nuna masa. Yadda ya furta magana ta biyu sai ta kalle shi tana mamakin wai shine ya yi maganar ko ba shi ba, ganin shi ne yake maganar sai ta girgiza kai tana tunanin anya wannan ɗan daba ne kamar yadda Dad yake faɗa? Anya shine Tiger ɗin da ake faɗar tsagerancinsa a duniya?. Kai gaskiya da sake tana tantama akan sa. A bakin gate suka tsaye ta kalle shi kamar zata yi magana sai kawai ta fasa dan so take taga iya gudun ruwan sa. Fita tayi ta shiga ciki kamar yadda bata yi magana ba babu wanda ya kula ta. Suna zaune shi da Tk duk da ba magana suke yi ba kowa harkar gabansa yake yi, shiru babu ita babu alamun ta kusan mintina talatin. Agogo ya kalla ya ga sha biyu na rana har ta kusa ya sake kallon inda ta shiga ya yi tsaki. Mintina goma ya ƙara mata in bata fito ba zai yi tafiyarsa ai ba driver bane ba shi da zata ajjiye shi a waje bata fito ba.  Ita kuwa an jima da gama interview tana sane tayi banza dashi tana so taga ƙarfin iskancin sa shiyasa tayi zaman ta. Gajiya tayi da zaman ita kanta, bacci take ji hakan ya saka ta fito a lokacin ya kunna motar zasu bar wajan kenan. Ganin ta fito ya saka shi ya dakata ta buɗe ta shiga tana cewa, "wai da ban fito ba kenan tafiya zaka yi?." Tk ya ce, "to Damisa yaron ki ne da zai zauna yana jiran ki?." Narma ta ce, "kai ba da kai nake magana ba, kayi min shiru kafin na ɗauki mataki akan ka." "Mataki akan wa? Wai ni Tk? Gaskiya....." Kallon sa Omar yayi hakan ya saka ya ce, "Tuba nake Madugu ta zo ta rainin hankali ne." Narma ta zo iya wuya saboda ɓacin rai cikin masifa ta ce, "Kai wai waye kai? Me ka ke dashi da ina magana zaka yi min banza?. Me ka ke dashi da zaka tafi ka barni a kan titi iyeee!" Ta faɗa da ƙarfin gaske wanda hakan ya saka Omar taka burki da ƙarfi. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 12.* Yadda ya taka burki da ƙarfi sai da tayi gaba kamar zata kifa kafin ta koma daidai ta zauna, ya jiyo ya kalle ta suka haɗa ido bata ɗauke idonta shima bai ɗauke ba ya ce, "in kika sake yi min magana a motar nan wallahi sai kin sauka, ki aikata ki gani." Mamaki yake bata da tsoro, ita da motar gidan su shine yake cewa in ta yi wani abun ba daidai ba sai ta sauka? Lallai wannan anyi ɗan rainin hankali, rainin hankali mana, in ba haka ba ita zai kalla ya ce in bata yi shiru ba sai ta sauka daga motar da babanta ya siya. Sai kuma ta kasa magana tayi shiru ya cigaba da jan motar yana aiyana wallahi in ta sake masa magana sai ta fita daga motar sai dai ta hau abin hawa ta koma. (Omar akwai ƙarfin hali). A haka suka koma gida motar tsitt babu wanda yake magana a cikin su sai ƙhamshinta da ya cika motar gabaɗaya. Yana tsayawa a gidan ta buɗe motar ta fita, ta kalle shi bayan ta fita shima ya fito ta ce, "zan ga abinda ka ke taƙama a duniyar nan, zan ƙure maka gudu, zaka fahimci ni ba sa'ar wasan ka bace ba." Tk ne ya zabura ya yi kanta Omar ya ɗaga masa hannu alamun ya ƙyale ta, ya juyo ya kalle ta ya ce, "cigaba." Wani irin baƙin ciki ya zo ya tokare mata a maƙogwaro, kenan ya mayar da ita shashasha mara hankali kenan ta cigaba da magana mahaukaciya. Juyawa tayi a fusace ta shiga cikin gidan ta cillar da mayafin jikin ta a haukace. Wayarta ce tayi take ƙara ganin sunan Ashraf ya saka bata ɗauka ba ta tashi ta hau sama a guje raina a ɓace matuƙa. Da wannan ɓacin ran tayi sallah sannan ta yi wanka ta kwanta bacci zuciyarta nayi mata saƙa da kwancewa akan abinda zata yiwa Omar dan ta huce. Bata farka ba sai bayan la'asar, ta tashi ta sake sabon wanka ta sako riga da wando na shan isaka ta sakko ƙasa da niyar cin abinci. Kamar yadda ta zata mai dafa mata abinci ta dafa abinci ta ajjiye, ta a dining table zauna ta zuba abinda take so ta fara ci. Wayar ta ce ta sake yin ƙara ganin mai kiran sai ta ɗaula ta ce, "ina ciki." Abinda tace kenan aka yanke wayar ba jimawa aka shigo falon. Kyakykawan saurayi ne fari tass siriri mara jiki ya shigo yana kallon ta daga inda take zaune tna cin abinci. Kallon sa tayi sai ta miƙe ta ɗauko plate ɗin abincin ta shigo cikin falon tana cewa, "Welcome Baby." Ƙare mata kallo yake yi dan shigar da tayi ta yi masa kyau a idanunsa sosai. Surar Narma tana daga cikin abinda yake ɗaukar hankalinsa a kan Narma, duk lokacin da zai yi arba da ita sai yaji shauƙin son kasancewa da ita cikin yanayi na soyayya. Ya so hakan ya kasance tsakanin su amma taƙi ba da haɗin kai, da ya yi magana sai ta ce ya jira sai bayan auren su, shi kuma gani yake kamar bazai iya jurewa ba. Ɗan hugging ɗinsa tayi daga gefen kafaɗarsa kana ta zauna a akan kujera ta ɗora ƙafa kan ɗaya tana cigaba da cin abincinta. Zama Shima ya yi yana kallon ta cikin yanayin da ya ke kasancewa da duk lokacin da suke tare, yanayin sa na sake yin gaba in ta yi hugging ɗinsa ko ta yi masa kiss sai ya ji kamar zai zauce. Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce, "What wrong? Naga fuskarki da alamun damuwa." Yatsine fuska tayi ta ce, "Wani banzan driver Dad ya haɗa ni dashi yake raina min hankali, wai ni yake ɗagawa murya har yana cewa in na sake magana sai na fitar masa a mota." Ashraf ya ce, "Like Seriouly? Ke ɗin yake faɗawa haka?." Bata amsa ba sai murmushin takaici da tayi tana girgiza kai. "Waye shi haka?." "Wani ɗan iskan mutum ne dan daba wai shi tiger, ni yake yiwa tsawa saboda Dad yana son ya dinga kai ni ko ina nake so." "Kuma Dad ɗin ya san da haka?." "Yes he knew, but today i won't inform him, i want to take action independently and how him my capabilities." Ashraf ya ce, "That's good my Love, you should teach him a lesson so he understands you deserve respect and won't tolerate any nonsense." Kallon sa tayi taga yana kallonta ba, iya fuskarta yake kallo ba duka jikinta yake kallo sai tayi murmushi ta ce, "zan koya masa hankali." "Nima zan taya ki." Murmushi tayi tana kallonsa  tace, "yaushe ka zo Kano?." "Ɗazu." Kai ta girgiza ya ce, "yaushe zaki fara event ɗin Samra?." "Lahh ka tuna min, gobe ne fa, ko makeup artist ban nema. He looks into her eyes yana wani lumshe ido then he say, "My Narma event without makeup you looks magnificent." Tayi murmushi ta ce, "Duk da haka dai zan yi kwalliya." Ya bita da kallo ta ɗauki waya ta kira tana magana da turanci nan da nan ta yi booking makeup artist za a zo har gida ayi mata home service. Ashraf ya jima suna hira kafin ya tafi dan shima a gajiye yake ya tafi ya huta da niyar in anjima zai dawo. Narma bayan ya tafi sama ta hau ta buɗe balcony gidan tana kallon ma'aikatan gidan ɗaya bayan ɗaya tana mamakin rashin ganin Omar, wato ko ya taimaye ta ya ji babu inda zata je shine yayi tafiyar sa kamar itace take aiki a ƙarƙashin sa. Wayarta duba taga number sa Dad ya turo mata kawai ta dubawa number ido kafin ta girgiza kai tare da yin tsaki ta koma cikin falon.       Omar kuwa ko da suka bar wajan shi da Tk ba gida suka koma ba sai da suka je wani wajan bai koma gida ba sai bayan la'asar. Yana shiga kai tsaye wajan Didi ya shiga, ya same ta a zaune tana shan magani ya ƙarasa ya zauna ya ce, "Ya jikin?." Ta kalle shi ta ce, "Jiki da sauƙi sosai, na sha magani." Ya girgiza kai ya ce, "kin tabbatar babu abinda yake damın ki?." Ta ɗaga kaii alamun eh. "AbdulHamid zai zo in anjima, ka zauna ku gaisa." Da to ya amsa mata a taƙaice kafin ya tashi ya fita daga falon. Ba jimawa AbdulHamid ya ce masa gashi ya zo ta ce ya shigo ya shigo da sallama ya samu ta ajjiye kujeru gıda biyu kamar wancan lokacin. Zama ya yi suka fara gaisawa cikin girmama juna ya faɗa mata duk yadda suka yi da Kawu da jiran sa da yake yi dan ya ce zai neme shi. Ta girgiza kai ta ce, "Kawu ya faɗa min komai, bayan ka bar wajansa ya kira ni a waya." "Haka nake so naji. Amma Aisha na tambaye ki." Ta kalle shi ta ce, "ina ji." "In Kawu ya baki dama kina ganin zaki iya aurena?." Murmushi ta yi ta ce, "Allah nake roƙa ko yaushe ya zaɓa min mafi alkhairi, sai gaka kazo, in dai har kai ba alkhairi bane Allah bazai bani ikon zaɓarka ba." Ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne, Allah ya tabbatar mana da alkhairi baki ɗaya." Ta amsa da amin. Omar ne ya zo wajan ya ƙaraso yana kallon su ta kalli Omar ta kalli AbdulHamid da yake kallon sa ta ce, "AbdulHamid ga Omar ƙanina kuma Yayana." AbdulHamid ya miƙawa Omar hannu suka gaisa ya ce, "Omar ya aiki?." "Alhamdu lillah" ya bashi amsa a taƙaice yana sake kallon sa dan haka kawai ya ji ya burge shi. Didi ta ce, "Ina zuwa haka?." Ya girgiza kai ya ce, "akwai inda zan je." AbdulHamid cikin wasa ya ce, "ko wajan ƙanwarta mu zaka je?." Kallon sa ya yi ya ɗan saki fuska amma bai ce komai ba kuma bai yi murmushi ba. Barin wajan Omar ya yi AbdulHamid ya kalli Didi ya ce, "ma sha Allah, babu wanda zai ce ƙanin ki ne, kallon farko in aka yi masa za a ace Yayan ki ne dan ya cancanci zama yayan naki. Yana da kwarjini sosai kana kallon sa kaga jarumi." Didi tayi murmushi ta ce, "Omar kenan." Shima murmushin ya yi yana mamaki dan shi yadda ake bashi labarin Omar ɗin sam bai yi kama da haka ba, ba dan ya sani ba ma da bazai ce shine Omar tiger dake bashi labari ba. AbdulHamid bayan sun yi sallama da Didi ya fito zai shiga mota sai ga wani babban mutum mai ƙaramin jiki ya ƙaraso inda yake, ya yiwa AbdulHamid sallama ya amsa da girmamawa. Mutumin ya kalle shi ya ce, "Bawan Allah don Allah wajan Aisha ka zo?." AbdulHamid ya ce, "Eh, wajan ta nazo." "Neman aurenta ka ke yi kenan?." "Haka ne." Ya girgiza kai ya ce, "kuma ka san duk abinda da suke faruwa a akan ta?." Abdulhamid ya ce, "a'a, sai ka faɗa min." Sai kuwa ya gyara tsayuwa cikin son isar da gulma ya ce, "Ko da naji, da ganin ka yaro ne ɗan mutunci baza ka kawo kan ka gidan nan ba sai dai rashin sani. Wato Aisha da Omar da ka ke gani abinda suke aikatawa a gidan nan Allah ne kawai ya sani, ya hana kowa shiga gidan ko almajiri baya shiga ya yi bara, da shi sai ita kullum su kwana su tashi. Baligi mara aure da baligar mace a waje ɗaya ai dole a samu matsala, zan iya yi maka rantsuwa da Allah masha'ar su kawai suke aikatawa a cikin gidan. Shiyasa ba ya barin kowa ya shiga gidan, irin yaran nan ƴan mata na unguwa ko kallon ƙofar gidan basa yi saboda shi. Gashi tantirin ɗan iska ajin ƙarshe, kai da ka gashi ma ai ka ga zubin ƴan iska." AbdulHmaid kallon sa kawai yake yi cikin tsananin mamaki ya ce, "Baba ba ƙaninta ba ne? Aka ce uwa ɗaya uba ɗaya suke." "Hmm ƙaninta ne mana, amma zama suke yi kamar mata da miji. Kuma bayan shi ma ta kan kawo wasu cikin gidan shiyasa take samun kuɗi tana siyan abinda take so. To in ba mazan banza ne suke bata kuɗi ba wannan sana'arta ta ta siyar da abincin order wata riba ce da ita da zata dinga wannan kashe-kashe kuɗi? Ai kana gani ka san da walalin giro a miya, ba a haka kawai ta kai wannan shekarun bata yi aure ba. Akwai mai biya mata buƙatarta daga gefe." AbdulHamid ya sake kallon sa ya ce, "to Baba yanzu me ka nufi da labarin nan da ka bani?." "Ina nufin ka rabu da Aisha kaje ka samu yarinya ƴar mutunci ka aura, gabaɗaya unguwar nan babu wanda ya sana salin su, kwatsam suka tare a cikin ta kuma wayi gari dasu. Ba a ganin dangin uwar su dana uban su balle a saka ran suna da dangi. Kaga a haife na haife ka, kamar ɗana ka ke bazan ga abinda zai cutar da kai na bari ba, kayi gaggawar daina zuwa wajan Aisha kafin girman ka da mutuncin ka ya zube a idanun mutane." Yayi murmushi ya kalli gefensa kawai idanunsa ya faɗa cikin na Omar da alama duk yaji abinda suke tattaunawa. Sai kuwa ya ce, "Yauwa Omar ƙaraso ga Baba yana bani bayani akan ku." Mutumin yana ji an ce Omar ya kalli wajan da sauri ya ganshi kuwa a tsaye yana kallon sa ya Kalli AbdulHamid murya na rawa ya ce, "Aisha ai mutuniyar kirki ce, ga sanin ya kamata, ga girmama na gaba da ita. Don Allah ba abinda nake faɗa maka kenan ba?." Ba AbdulHamid kaɗai ba Omar ɗin kansa sai da yayi murmushi jim abinda Baba ya ce, bai nuna ba haka ya tako cikin ƙasaita yana zuwa ya kalli mutumin ya ce, "Waye kai a layin nan?." Jikinsa ya soma rawa kar kar kar saboda tsoro. Omar ya kalli gefe yana girgiza kansa kafin ya sake kallon sa fuska babu walwala ya ce, "nace maka waye kai a layin nan?." Murya tana rawa ya ce, "Malam Salihu." "Mai kiran sallah?" Omar ya tambaya yana kallonsa. Jiki na rawa ya amsa AbdulHamid ya ce, "Yanzu Baba kana da matsayin mai kiran sallah ma a unguwar nan amma ka ke faɗar irin wannan maganar akan yaran wasu? Ko baka da yara matsayinka na babba wannan ba girman ka bane balle na tabbatar kana da yara kaima da ka ke burin aurar dasu. Ko da da gaske abinda ka faɗa gaskiya ne ka taɓa gani da idon ka?." Shi dai yayi shiru sai hannunsa da yake rawa sosai. Omar ya kalle shi ya ma rasa abinda zai yi masa, baya son yiwa manya wani abun ko ya yi niya sai ya kasa amma babu abinda zai saka ya ƙyale Malam Salihu, sau biyu kenan yana kama shi da irin wannan munafurcin a kan su. Malam Salihu ya ce, "Ni fa wasa nake maka yaro, so nake naga ko maƙaryatan unguwar nan sun faɗa maka haka, dan Aisha mutuniyar kirki ce." Omar ya ce, "Zaka tabbatar da mutuniyar kirki ce in nayi maka illa yanzun nan." Malam Salihu ya ce, "Ka bashi haƙuri don Allah" ya faɗa yana kallon Abdulhamid. Shima ya kalle shi ya ce, "Baba ai ko ya yafe nima bazan yafe ba, matar da zan aura ka ke yiwa ƙazafi a gaban idanuna. Ko shi ya ƙyake ka ni sai hukuma ta raba mu da kai." Tk da goje Omar ya hango da ido yayi musu alama su riƙe Malam Salihu, caraf Tk ya kamo shi daman haushinsa yake ji shekaran jiya ya yi masa munafurci hakan ya saka ya ce, "Malam Salihu yau ka zo hannu, ƙarshen munafurcin ka ya ƙare." AbdulHamid ya kalli Omar ya ce, "Omar ka ƙyale shi kawai kar ka yi masa komai, ka bar shi da halin sa." Omar kallon sa ya yi jin yana bashi umarni kamar wani wanda ya haifa. Omar ya ce, "ai ba a dakatar dani in nayi niyar abu sai nayi." Ya yi murmushi ya ce, "kar ka manta kamar yayan ka nake tunda yayar ka zan aura." "Ko ita bata faɗa maka bana bari ba?." Ya yi murmushi ya ce, "a yi min wannan alfarmar." Kallon sa ya yi zai sake magana sai kawai ya fasa ya kalli su Tk da suke tsorata Malam Salihu ya masa alama da su ƙyale shi ya juya ya shiga gida, shi kuma ya hau mota ya tafi yana mamakin munafurci irin na mutane.        Omar yana shiga gida wayarsa ta fara ƙara ya duba ya ga number ce ya ɗauka, ana fara magana ya gane Yahya ne ya sanar dashi Narma zata fita in anjima. Bai amsa ba ya yanke wayar dan ransa a ɓace yake sosai ko wajan Didin bai koma ba. Sai bayan sallar i'sha yaje gidan ya tarar da Narman ma ta hau mota ta tafi wai ta gaji da zaman jira ita ba baiwarsa bace ba. Tsaki ya yi da ya san hakan mai zai fito dashi daga gida yanzu. Gabaɗaya zuciyar saa cushe take akan kalaman Malam Salihu, duk da ba haka aka saba ba amma ya ji zafi sosai. Ɓacin ran da yake ji ya saka shi takowa a hankali yana tafiya ya saka pcap wacce ta rufe fuskar sa. Narma kuwa a ƙasan gadar ƙofar nasara motar da take ciki ta mutu, tayi-tayi ta kunna ta kasa kunnawa gashi bata da number kowa balle ta kira azo a tafi da ita gıda. Tsaki tayi ta fito daga motar tana kallon hanya, wajan babu mutane sai mota da take wucewa kuma babu haske sosai hakan ya bata tsoro. Napep take so ta tare ta hau ta tafi amma bata san ma ya ake tare mai napep ba dan ba taɓa hawa tayi ba, bisa kuskure ko tsautsayi bata taɓa hawa napep ba. Shiyasa take kallon su ɗaya bayan ɗaya suna wucewa ta rasa me zata yi. Abu taji an saka mata a bayanta kamar wuƙa zata juya aka ce, "kina juyawa wallahi sai na farɗe miki bayanki, kawo wayar hannunki." Narma jiki ya fara rawa hannu na karkarwa ta kuma kasa miƙar wayar. "Baza ki bayar ba sai na kashe ki?." Hannunta rawa yake yi garin ta miƙa masa wayar garin ya yanke ya da wuƙar a hannuta. Narma tayi ƙara tana kallon hannunta, shi kuma ya yi cikin duhu a guje bai sake waiwayen ta. Hannunta jini yake yi tana kuka ga tsoron tashin hankali, sai rawa jikinta yake yi dan bata taɓa tsintar kanta a irin wanna tashin hankalin ba sai a lokacin. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 13.* Omar tun daga nesa ya gane motar ya kuma ganta a tsaye a wajan, a hankali ya ƙaraso kamar zai gifta sai yaji tana kuka tana cewa, "a taimake ni don Allah, a taimaka min jinina zai ƙare." Ɗaga pcap ɗin ya yi ya kalle ta suka haɗa ido ganinsa ta matso kusa dashi a gigice da fitar hankali sosai ta ce, "Tiger sun ƙwace min waya, sun yanke ki a hannu, jinina zai ɗare ka taimaka min zasu kashe ni." Ya kula gabaɗaya a gigice take har tana riƙe shi bata san ma tayi hakan ba saboda tsoro. Kallon hanyar ya yi ya sake kallon ta yaga yadda take hawaye shaɓe-shaɓe tana riƙe da hannu kamar wacce aka guntulewa hannu, kallon ɗan yankan da yake hannun ta ya yi tare da yin tsaki a bayyane har lokacin bata saki rigarsa. "Take me to hospital please, ka kaini ayi min TT kar na samu ciwo." Kamar ba zai yi mata ba magana ba sai yaji ta ce, "Don Allah ka ɗauke ni daga nan, tsoro nake ji, ka taimaka min don Allah." Yadda take kuka tana ƙoƙarin shege masa jiki ne ya saka ya riƙe hannunta ya janye ta ya buɗe gaban motar ya ce, "shiga." Ba musu ta shiga jikin ta na shaking sosai ya buɗe mazaunin driver yana kunna motar ta tashi ya ja motar ya nufi asibiti mafi kusa. Wani private hospital suka ƙarasa ya ajjiye motar ya kalle ta yaga sai kuka take yi ta riƙe hannunta, shi wallahi mamaki take bashi, ɗan wannan yankan take yiwa kuka kamar wacce aka yanka sosai. Ya kalle ta ya ce, "Fita ki je." Ta buɗe murfin motar ta kalle shi ce, "nayi bleeding sosai in na tashi jiri zan yi." "Ko" ya furta a bayyane yana kallon ta. Fita ya yi daga motar ya ce, "Fito" ya furta a kausashe dan ya ga tana neman mayar dashi ɗan aikinta, jin yadda tayi magana ya saka ta sakko amma tana fitowa tayi kamar zata faɗi, da hanzari kuwa ta riƙe shi tana cewa, "na ce maka i'm dizzy bazan iya tafiya ba." Ɗan tsaki ya yi ya janye ta a jikinsa ya kalli bayan sa yaga ma'aikatan asibitin nan ya yi musu magana suka riƙe ta suka shiga da ita. Bai shiga ba ya tsaya a jikin motar sai ga wacce ta shiga da ita tazo tayi masa magana dole ya shiga. Yana shiga ya ganta sai kuka take yi an ɗaure hannun da bandage, likitan da ya gama yi mata dressing wound ɗin ya kalle shi ya ce, "Oga ka taya mu rarrashinta taƙi yin shiru." Kallon ta ya yi suka haɗa ido sai wani juya ido take yi kamar mage. Ƙaramin tsaki ya yi Narma ta kalle shi ta ce, "kayi clearing bill ɗin, wayata da atm ɗina duk sun ƙwace." Sai a sannan ya tuna ma da batun wayar ta bai ce komai ba ya yi musu transfer a take suka fito tare da ledar magani a hannun nurse ɗin wai baza ta iya riƙewa. Sai tafiya take kamar mara jini ita a lallai an yanke ta, gabaɗaya haushi take bashi yadda take langwaɓewa kamar wacce aka jiwa ciwon kirki. Suna zuwa gaban motar ta shiga bayan motar shi kuma ya shiga gaba ya ja motar da gudun gaske. Da yake kwanciya tayi bata san inda suka nufa ba sai da taji ya tsaya yana niyar fita, ta miƙe ta gansu a wani waje mai duhu ta ce, "ina zaka je?." Kallon ta ya yi jin yadda tayi maganar a firgice bai amsa ba, "don Allah ka je dani bazan iya zama ni kaɗai ba, wallahi i'm scared." Nan da nan jikinta ya fara shaking cikin tsananin tsoro tana ganin kamar abinda ya faru zai sake faruwa. Narma ganin ya yi mata banza yana niyar fita sai itama ta fito da sauri ta ce, "bazan iya zama ba, don Allah ka je dani tsoro nake ji." "Inda zan je ba wajan zuwan ki bane" ya faɗa without looking her. "Ni dai zan je, don Allah ka je dani." Kallon ta ya yi sai kawai ya yi gaba ta bishi a baya, kanta har sarawa yake yi saboda ciwon da ya fara yi mata. Wani waje taga sun shiga sai gasu a gaban dandazon ƴan daba sama da su ashirin a wajan sun baje wayoyi da atm cards da kuɗi. Wajan banda warin wiwi babu abinda yake yi, ga hayaƙin taba ya cika wajan. Ganin an shigo suka miƙe duk suka fito da makamai ɗaya daga cikin yana cewa, "wanne mai ƙarar kwanan ne yazo inda bazai fita ba?." Narma ta ɓuya a bayasa gabanta na faɗuwa tana dan sanin shigowa wajan. Haske shi suka yi da fitila shi kuma ya ɗaga pcap ɗin kansa, ganin fuskarsa ta bayyana sai suka haɗa baki suka ce, "Damisa!." Babban cikin su ya ce, "Allah ya ja zamanın Damisa ƙi sabo, mu je madugu uban tafiya, barkono ka fi ƙarfin shiƙa. Allah ya sa ba laifi mu ka yi ba, na ganka kwatsam babu sanarwa." Omar ya bisu da kallo yana kallon wayoyin da suke ƙasa ya ce, "waye ya ƙwace waya a ƙasan gada?." Ɗaya daga cikin su ya ce, "Madugu ai ƙasan gada da yawa, daidai ina ka ke nufi?." Narma ya juya yana kalla ya ce, "fito." Sai ta riƙe rigarsa tana kwanciya a bayansa jikinta na rawa sosai. Hannunta ya jawo kafin ya saki hannun na ta ya ce, "waye ya karɓi wayarta?." Wanda ya ƙwace mata wayar ya kalle ta ya ce, "afuwan Jan wuya ni ne." Da hannu ya yi masa alamun da ya zo, ba musu ya taso yazo yana zuwa ya daki ƙewarsa ya ce, "Sai ka ji mata ciwo?." Ya sunkuyar da kai ya ce, "afuwan madugu ban san antyn mu ba ce." Harararsa ya yi ya kalli Narma da tayi tsuru ya ce, "bata haƙuri." Kallon Narma ya yi ya ce, "ki yi hakuri Anty." Firgita tayi da maganarsa jin ta wani iri kana ji ka san a buge ya ke, ta yi tsalle cikin tsoro ta koma bayansa ta riƙe shi jiki na rawa. Omar ya runtse ido jin jikinta a bayansa a kwance, wani iri yake ji baya so tana riƙe shi ɗin nan, shi in ba Didi ba babu macen da ya taɓa haɗa jiki da ita, ko ita tunda ya girma bai haɗa jiki da ita ba sai dai ya riƙe hannunta ko su gaisa da safe, shiyasa yake jin wani iri a jikinsa in ta riƙe shi. Daurewa ya yi ya ce, "ɗauko min wayar, sannan kar ka naga an taɓa mata komai." Ba musu ya juya aka fara bincike wayar sai ga iPhone 16 kalar pink da atm ɗinta a baya an ɗauko ya miƙa masa yana cewa, "wallahi Allah ne ya taimaka Magudu da yanzu ba labarin nan ake yi ba, na je inda za a kwashe kuɗaɗen ciki baya nan." Omar ya karɓi wayar yana kallon su ya ce, "sauran wayoyin fa?." Wanda yake zaune ya ce, "Damisa ganimar yau ce." Ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya kana ya ce, "tattaro min su duka." A tare suka haɗa baki suka ce, "Haba Damisa wannan yawa ka ke yi fa, wannan ba halin ka bane." Fuska ya sake ɗaurewa ya ce, "Ku tattaro min ko na tattara har da ku." Babban ciki ya ce, "gaskiya Madugu hakan bai yi ba, ka san wahalar da muka sha....." kallon da ya yi masa ya saka ya ce, "Kawai dan kaine wallahi, amma da ka san babu wani da ya isa ya saka mu bada wayar nan koda gwamna ne wallahi, ku bashi." Tattaro wayoyin suka yi suka zuba a wata jaka aka miƙa masa ya karɓa yana kallon su duk sun ɗaure fuska alamun basu ji daɗin hakan ba. Ya sake kallon su ya ce, "Ku riƙe kawai" ya faɗa yana miƙa musu. " ka je dasu kawai, amma kawai dan babu yadda zamu yi da kai ne." "Ban son wannan ɗabi'ar da ku ke yi, in ba ku daina ba...." Sai ya katse maganar ya karkaɗa musu yatsansa. Ya motsa zai bar wajan ta sake riƙe shi gam. Tsaki ya yi ya ce, "Malama ki sake ni!." Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka ta sakinsa amma duk da haka tana rike da gefen rigarsa suka fita daga wajan. Bayan motar ta shiga a tsorace ya cilla mata wayar ta ya ce, "Kano ba Abuja bane ki san inda zaki dinga shiga." Bata ce komai ba ya ja motar kai tsaye police station ya wuce. Nan ma sai da ta bishi ya samu dpo yana niyar fita suka gaisa ya bashi wayar ya ce, "wayoyin da aka ƙwace yau ne, ku saka a duniya a mene masu su a basu wayar." Dpo ya kalle shi ya ce, "ina wanda suka ƙwace wayoyin su ke?." "Ni dai wayoyin na kawo maka in na mayar shikenan." Ya karɓa ya ce, "amma samun masu aikata laifin ya fi samun wayoyin amfani. Tiger da zaka taimaka a kama su da kayi babban aiki." Ya kalli Dpo ya kafin ya ce, "a fara bawa kowa haƙƙinsa tukunna, zan faɗa maka inda zaka same su wani lokaci, amma ba yau ba." Dpo ya ce, "babu damuwa. Da za a samu shugabanni kamar ka ai da Kano ta zauna lafiya. Ga ka dai kowa ya san ka amma baka ɓarnar da ƴan uwanka suke yi, ban san meyasa ake kiran ka da ɗan daba ba, dai kai ba shi ba ne." Bai ce komai ba ya fito ya shiga mota itama ta shiga ya ja motar ya nufi gidan da Narma ta sauka. Yana tsayawa a harabar ta buɗe motar ta fito jiki a sanyaye dan kanta ciwo yake yi mata matuƙa saboda kukan da tayi. Fitowa Shima ya yi tana niyar shiga ya ce, "kin ga." Ba musu ta tsaya cak ta jiyo tana kallon sa ya tako inda yake ya miƙa mata key ɗin motar. Ta kalli key ɗin da yake bata ta kalle shi ta ce, "kaje da ita." "Karɓi" ya sake faɗa yana miƙa mata fuskarsa a ɗaure yamau. A shagwaɓe ta ce, "hannuna yayi nauyi bana iya ɗaukat komai, maganin ma wahala nake sha wajan riƙewa." Ledar hannunta ya buɗe ya saka mata key ɗin ya juya ya fita daga gidan. Ajiyar zuciya tayi bayan ya fita tana kallon sa ta ce, "kamar wani mai hankali, ba dan shi ba da waya ta ta tafi kenan" ta faɗa tana shiga falo. Kunna wayar tayi tana ajiyar zuciya kiran Dad ya shigo, ɗauka tayi daga can Dad ya ce, "Narma ina kika saka wayarki? Ina ta kira tun ɗazu bana samun ki." Narma ta ce, "Dad!" Sai ta saka kuka hankalinsa ya tashi ya ce, "me ya faru? Tiger ne ya sake miki wani abun?. Talk to me mana kin saka ni a ruɗani." "Dad tare ni aka yi a under the flyover, they snatched my phone and my atm card. Dad sun yanke ni a hannuna jini yana ta flowing" ta faɗa tana jan kalmar ƙarshe tare da fashewa da kuka. "Innalillahi! Daughter me ki ke cewa? A ina haka ya faru? Ina shi Tiger ɗin yake?." Ba ta yi magana ba sai kuka, kawai ya yanke wayar ya kira ta video call ta ɗauka ta ganshi a zaune shida Mum harda Najwa a rikice suke ce mata ne ya faru. Narma ta ce, "Dad ba da shi ne fita ba, ni kaɗai na fita." "Are you mad Narma? Nace baki da hankali ne. Me na faɗa miki akan fita ke kaɗai? Ban yi miki warning akan haka ba?." Ganin yana faɗa sai Mum ta ce, "My dear ka yi mata a hankali baka ganin tana da ciwo ne?. Daughter calm down ki faɗa mana abinda ya faru." Narma ta ce, "na jira shi bai zo ba sai na hau mota na fita, ina cikin tafiya sai motar ta tsaya na fito daga motar sai ga wani ya saka min wuƙa ya ce na bashi wayata, da zai ƙwace wayar ne ya yanke ni....!" Ta faɗa tana hawaye. Dad ya ce, "oh my god! Yanzu ya jikin naki?. Kin je asibiti?." Mum cikin faɗa ta ce, "'ni banga amfanin wannan banzan Tiger ɗin ba, ban ga amfaninsa da ka bashi ragamar kula da yarinya ta ba. How com yana matsayin driverta ya barta ta fita ita kaɗai?. Gaskiya dear bazan iya tolerating wannan shirmen na sa ba, zan tura mata da poliçe da zasu kula min da ita. Kalli hannunta fa, kalli girman ciwon da ka ji mata akan wayar one million." Narma ta goge ido ta ce, "No Mum, ya taimake ni. Ban san ya aka yi ba ina wajan sai na ganshi yazo, he took me to the hospital and had my wound dressed, then muka je har inda masu ƙwacen wayar suke zama ya kaɓo min wayar har suka bani haƙuri. Sai da ya dawo dani sannan ya tafi." Jin haka gently Mum ta ce, "kina nufin har inda wanda suka ƙwace miki wayar ya je ya karɓo miki?." "Yes Mum, har da atm card ɗina ma an bani. Ba ma iya phone ɗin ba duk wanda aka karɓawa waya yau ya karɓa ya kaiwa police station za a neme masu shi." Dad ya kalli Mum ya ce, "Now you understands why I have trusted him right? You should see the benefit of being him with Narma?." Narma ta yi shiru ya kalle ta ya ce, "na tabbatar da ace tare ku ke babu wanda zai ce zai miki wani abun." "I see, Dan suma bashi respect sosai har mamaki nayi." "You see. Kina ji, yanzu ki je ki huta ki yi bacci sosai da safe sai mu ƙarasa maganar." Narma ta ce, "but Dad I'm scared wallahi, please can you convince him to come and stay with me? In yana kwana a nan zan fi samun tsaro sosai." Dad ya ce, "don't worrry, yanzu ki kwanta." Amsawa tayi ta kashe wayar ta tashi ta sha magani ta kwanta. Dad bayan ya kashe wayar ya kalli Mum ya ce, "kin ga abinda nake faɗa miki ko?. Ɗan iska sai da ɗan iska irinsa ake zama lafiya." Mum ta ce, "na fahimta, amma ya cika zaƙewa ne da yawa baya bata girmanta." Dad ya yi murmushi ya ce, "ƙyale ni dashi, tunda har ya taimake ta ai komai ya yi kyau." Omar kuwa a haka ya koma gida jikinsa duk babu ƙarfi, ƙhamshin turaren Narma ya gama kama kayan jikinsa gaba da baya. Duk ya takura ya kuma damu saboda turaren ya ishe shi duk da yana da daɗin ƙamshi sosai, amma ya takura masa so yake ya cire kayan ya huta. Yana shiga gidan ya ga Didi a tsaye, ta ƙaraso inda yake ta ce, "Tun ɗazu nake jiran dawowaka, ko abinci baka ci ba." Kallon rigarsa tayi kasancewar ta blue mai haske ta ce, "Omar me nake gani a jikinka kamar jini?." Kallon rigar ya yi ya kalle ta zai yi magana ta ce, "Omar kar ka ce min faɗa ka yi." Omar ya ce, "Ban yi faɗa da kowa ba Didi, taimako nayi, kar ki damu." Kallon fuskarsa tayi sai taga bai yi kama da wanda ya yi faɗa ba, dan ta san in faɗa ya yi jiyoiyin kansa ma zasu tona masa asiri saboda ɓacin rai. "Wa ka taimaka haka?." "Wata yarinya aka ƙwacewa waya kuma aka yanke ta a hannu shine na taimaka mata." Da mamaki take kallonsa ta ce, "ƙhamshin turarenta nake ji a jikinka haka?." Ɗan kulle ido ya yi ya buɗe dan bai so ta ji ƙhamshin ba ya ce, "shi shine." "Wanne irin taimako ne wannan da ƙhamshinta zai dinga tashi haka a jikinka?." Ya kalle ta ganin tana kallon sa kamar bata yarda ba ya ce, "kin san bazan miki ƙarya ba ko?." Didi ta ce, "na sani, ban ce kana ƙarya ba, ina so na tabbatar ne kawai." "To ki yarda" ya furta mata a taƙaice ya wuce ya kyale ta. Mamaki abin yake bata, taimako ya yi, taimakon ma mace ya taimaka kuma ga ƙhamshinta a jikinsa, wanne irin taimako ne wannan haka?. Babu mai bata amsa hakan ya saka ta ƙyale shi da tambaya ta shiga ciki. Washe gari. Da labarin abinda Tiger ya yi aka tashi, kusan duka mutanen da aka ƙwacewa waya a daren jiya an basu kayar su, musamman wanda aka ƙwacewa a arear da ya karɓa. Ana ta saka masa albarka dan an faɗi sunan sa ance Omar wanda aka fi sani da Tiger. Nayla na zaune kusa da Hajja tana kallon labaran tana murmushi. Hajja ta kalle ta tace, "ke lafiya ki ke murmushi?." Ta kalli Hajja ta ce, "Hajja Omar ƙanin Didi shine ya karɓo wayoyin da aka ƙwacewa wasu jiya, Wallahi shine abin ya yi min daɗi sosai." Hajja ya ce, "indai irin wannan abubuwan ne ya saba, inda iya haka yake tsayawa da ya zama mutumin kirki sosai, to shima shegen kansa ne. Lokacin da yake cikin ƴan daban kaca-kaca baza ki so ki ji irin abinda yake yi ba, ya zubar da jinin mutane da yawa ba kaɗan ba. Allah sarki Aisha, ya wahalar da baiwar Allah nesa ba kusa ba, itace zuwa wajan ƴan sanda, itace zuwa prison, ita zuwa inda yake zama. Kaii...sai dai Allah ya biyata kawai, amma Omar ya wahalar da ita har yanzu yana kan bata ciwon kai." Nayla tana ji tayi shiru amma Allah ya sani ya yi bala'in burgeta, haka kawai taji tana so ta ganshi ko da kuwa zai yi mata tsawa. Hajja ta sake kallon ta taga sai murmushi take yi ta ce, "Wai murmushin ne har yanzu?." Nayla ta ce, "wani abun na gani a wayar." Hajja ta ɗauke kai sai Nayla ta ce, "Hajja an ce Didi ma tayi rashin lafiya, bara naje na duba ta." Hajja ta kalle ta ta ce, "Keda bakya son shiga gidan?." "Hajja ai lalura ce kuma tana da kirki sosai." "Ki jira Salma ta dawo sai ku je." "A'a Hajja, kamar wata baƙuwa?, bara naje dai" ta faɗa tana ɗaukar hijjabi ta saka, ta ɗauki wayarta fita Hajja ya bita da kallon mamaki. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://www.tiktok.com/@nanahaleemawriter?_t=ZS-8zaZqblsrGp&_r=1 *Book 1* *P 14.* Nayla sai da tazo ƙofar gidan Didi sai kuma gabanta ya faɗi matuƙa, ta runtse ido tare da ajiyar zuciya ta shiga gidan da siririyar sallama. Yana tsaye a tsakar gidan dube-dube da alama akwai abinda yake nema, jin anyi sallama ya juya kai tsaye suka haɗa idanu da Nayla. Sanye yake da riga mai siririn hannu kamar singlet amma tafi singlet girma da rufe jiki. Sai dogon wando mai jikin Damisa dan sai ka ɗauka da fatar Damisa aka yi shi. Murɗaɗen jikinsa duk a bayyana haka farar fatansa a bayyane take tana ɗaukar ido, ga wanda bai san shi ba dole in yaga fatarsa sai ya tsaya yana kallo saboda haskenta. A cikin sakan biyar ta ƙare masa kallo har lokacin kallon ta yake yi duk da tana jin tsoro amma ta daure ta ce, "ina kwana." Bai amsa ba bai kuma daina kallon ta ba yana mamakin wannan yarinya da shegen naci take, bata jin magana duk da ya yi mata warning bata daina zuwa gidan ba. Janye idanunsa ya yi bai ce komai ba, jin bai amsa ba sai ta ce, "Didi tana nan?." Nan ma yayi mata banza sai jikinta ya ɗan yi sanyi, daman gashi a tsorace take dashi gashi yayi mata banza. Kallon inda take ya yi yaga tana tsaye ya ce, "in zaki shiga ki shiga, in fita zaki yi ki bani waje!" Ya faɗa da ƙarfi bata san ta wuce shi a guje ba sai sautin tsakinsa taji tayi ajiyar zuciya. Bata tarar da Didi a falo ba sai ta zauna kamar munafuka ta kasa sakewa, motsin shara taji ana yi sai ta miƙe ta kalli window ga mamakin ta shine yake share gidan a nutse, sai ta tsaya tana kallon sa tana murmushi wanda bata san tana yi ba. Didi da ta fito ta ga Nayla na kallon window sai ta yi murmushi tana daga bayanta ta ce, "Nayla." Firgigit tayi ta kalli Didi ta ce, "Didi yaushe ki ka fito?." "Ta ya zaki san lokacin da na fito kina kallon mutumin ki yana shara? Ya baki mamaki ko?" Ta faɗa suna zama a kan kujera. Nayla sai taji nauyi kallon sa da ta tsaya yi amma bata nuna ba ta ce, "Sosai ma kuwa, kawai ji na yi ana shara sai na leƙa ashe shine, kawai sai na tsaya ina kallonsa." Didi tayi dariya ta ce, "ai dole ki tsaya, In ya so ya ga dama shi yake yin komai a gidan nan hatta girki, har inda na kwanta shine zai gyara kuma baza ki ce namiji ne ya yi ba. Amma in bai ga dama ba abinda ya ci abincin ma ni zan ɗauke." Nayla tayi murmushi tana kallon Didi ta ce, "shi dai sai ka rasa ka gane wanne iri ne, in ya yi gabas sai ya karkace." Didi ta ce, "shiyasa nake faɗa miki yana da kirki fiye da tunaninki, yana da hira sosai. Kawai bashi da saurin sabo ne kuma baya son baƙi kwata-kwata." Nayla daɗi take ji a zuciyarta ana hirar Omar hakan ya saka ta sake gyara zama ta ce, "ina fa kirki a nan Didi, har gaishe shi nayi yayi min banza." Didi ta ce, "bazai amsa ba ai, in kinga ya amsa to tabbas kun sana dashi matuƙa. Naga alama dai tsoron na sa ya ɗan ragu a zuciyarki." Nayla ta ce, "hmm ina fa, wallahi akwai daurewa nayi nazo na gaishe ki, kwana biyu kin yi rashin lafiya." Didi tayi dariya ta ce, "ai kuwa na gode sosai Nayla, Naji daɗi matuƙa Allah ya bar zumunci." Nayla ta amsa da amin amma a zuciyarta kawai so take a cigaba da zancen Omar. Ƴar hira Didi take janta da ita akan labarin mutanen Kaduna da Hajja tana amsa mata da lafiya kowa yake. Shigowarsa suka gani ya canja kaya zuwa jeans blue da farar riga mai layi-layi a jikinta, riga ta mai dogon hannu ce, sai ya tattare hannun rigar zuwa guiwarsa hannun, farin hannunsa da gashin da yake a kwance a hannun ya bayyana sosai, hakan da yayi sai ya ƙara masa kyau sosai. Nayla kallon sa take yi kawai cikin burgewa, daga sama yana da faɗi duk da ba faɗi sosai ba, amma daga ƙasa ɗan ƙarami dashi kuma a tsuke kana ganin sa kaga halittar cikakken namiji jarumi. "Ina zuwa haka Alhaji Omar?." Didi ta tamabaya tana kallon sa da murmushi. Ya kalle ta bayan ya ɗage gira ya ce, "Yaushe ki ka fara sanin inda zan je?." Tayi dariya ta ce, "abin ne da mamaki, naga ƙarfe sha biyu ma bata yi ba ka shirya. Ko wajan yarinyar nan zaka je?." Agogo ya kalla ya ce, "A'a sai anjima." "To ina zuwa ko abinci baka ci ba?." "Bana son cin komai, zan je wani waje wataƙila bazan dawo ba sai dare." Didi ta girgiza kai ta ce, "Allah ya kiyaye Alhaji Omar Faruk." Murmushi ya yi yace, "Amin." Murmushin da ya yi shine ya saka narkar da Nayla a kogin kallonsa har bata san ta tallafi haɓar ta tana kallonsa ba, ya gama tafiya da ita daga shigarsa, da maganarsa, uwa uba murmushin da yake sakawar Didi. Sai da ya fita sannan ya kalli Didi taga tana neman wayarta sannan ta miƙe ta ce, "Didi bara na koma." Didi ta ce, "da wuri haka? Na ɗauka sai anjima." Nayla ta ce, "zan dawo anjima in sha Allah, ai yanzu na rage tsoronsa." Didi tayi dariya ta sake yi mata godiya ta raka ta har waje sannan ta dawo. Nayla sai da ta tsaya a gate ɗin gidan Hajja ta dinga sauke ajiyar zuciya. Namiji mai murɗaɗɗen jiki irin na sa sam basa burgeta, hasalima itace mai kushe duk wani namiji mai irin wannan jikin, bata ƙaunar su tafi son namiji mai normal jiki ba wannan murɗewar ba. Wannan halitta tana daga cikin dalilin da ya saka bata so ace Abbas yana sonta, dan ta san baza ta so shi ba saboda jikinsa dan shi ya fi Omar murɗewa. Amma yau Omar ya burgeta, ya tafi da imaninta fiye da tunanin ta har mamaki abin yake bata. Har hango kanta take yi ta kwanta a ƙirjinsa tana hasahen wanne irin yanayi zata ji a wannan lokacin. Da ta rufe ido murmushinsa take gani, sau biyu kenan taga yana murmushi, hakan ya shiga cikin tarihin ta dan tun daga murmushin farko da ta gani ya yi komai ya canja, faɗuwar gaban da take ji akansa ta canja salo zuwa harbawar zuciya a duk sanda tayi araba dashi. A haka ta shiga gidan zuciyarta na bugawa sossi. Shi kuwa Omar yazo zai fita sai kiran Sen ya shigo wayarsa ya ɗauka yana shiga ɗakin sayana amsawa. Gaisawa suka yi Sen ya ce, "Tiger Narma ta faɗa min duk abinda ya faru jiya, gaskiya i'm so proud of you, naji daɗin taimakon da ka yiwa Narma sosai." Omar ya ce, "babu komai. Amma ka ja mata kunne Kano ba Abuja bane, akwai masu ƙwace sosai wanda za su yi mata illa ma kafin su ƙwace ɗin. Ta kula in zata fita ta daina kaiwa dare, in ta kai dare ma kar ta sake ta tsaya a ko ina. Allah ne ya taimaka da har motar zasu ƙwace musamman in suka lura da bata san gari ba." Sen ya ce, "ai ganganci ne irin nata, na faɗa mata duk inda zata je ta kira ka amma bata ji." Omar ya ce, "tafiyar mu baza ta zama ɗaya ba, ni bana son ɓata lokaci ko kaɗan, kuma dai yanayinta bai yi daidai da nawa ba." Sen ya ce, "kar ka damu yanzu ta fahimci abinda nake nufi." Omar ya ce, "babu komai." "Yau zata je biki zata kira ka." "Allah ya kaimu." "Amin. Akwai saƙonka na kyautatawar da ka yi mata jiya, naji daɗi sosai." "Na gode" ya bashi amsa a taƙaice kafin Sen ya kashe wayar. Ɓangaren Narma a daren sai da tayi mafarkin Omar, da ta farka sai kawai ta ɗauka taimakon ta da ya yi ne ya saka haka. A haka ta tashi ta shirya dan a ranar zasu fara bikin Samra. Ƙawayenta guda uku ne suka zo gidan, ganin hannunta a ɗaure suka dinga yi mata sannu kafin ta sake a fara hira. Da wuri mai kwalliya tazo aka fara yi musu kwalliya, sai da aka yiwa duk ƙawayenta sannan aka yi mata a lokacin an idar da magriba. Narma tayi kyau cikin ankon kamu dukkan su dogayen riguma suka yi marasa kama jiki, amma Narma fitted gown tayi wacce ta kama ta matuƙa, sannan saman rigar gabaɗaya net ne a jiki ana ganin jikinta. Ganin yadda tayi kyau duk suka ruɗe suna zugata ita kuma tana jin daɗi tana fari da idanu. A lokacin Ashraf ya zo gidan haɗa ido da ya yi da Narma ji ya yi kasala ta saukar masa lokaci ɗaya, ya haɗɗiye yawu ya bita da kallo ya ce, "Beb ke ce?." Gira ta ɗaga masa ya ce, "you look so magnificent." Mursmushi tayi ya matso aka fara yi musu hotuna masu kyau. Ashraf ya ce, "Amma dai ni zan kai ki ko?." Narma ta ce, "Dad ya ce Tiger ne zai kai ni." "Tiger again?." "Yes, sai dai mu haɗu a can." Ya girgiza kai ya ce, "Okay normal, sai mun haɗi din." Daga nan suka yi sallama ya fita su kuma suka fara sallar i'sha. Narma dai sai da ta cire rigar gabaɗaya sannan ta iya sallah bayan ta idar ta mayar. A cikin ƙawayen ta wacce suke kira da Safna itace babbar ƙawar Narma, ta kalle ta taɓe baki ta ce, "Narma ya kamata ki daina wannan ɗinkin fa, yanzu an daina wannan matsewar musamman ke da kike da halitta irin wannan." Narma ta ce, "kina da matsala Safna, to in ban nuna halittar da Allah ya yi min ba meye amfanin ta?." "Ki adana sai ki yi kwalliya a gidan mijinki." "Ke baki ga yadda Ashraf ɗin ya ruɗe da ya ganni haka ba? Da iya surata nake sake kama zuciyarsa. Kuma in bai ga abinda nake dashi ba ta ya ya zai yi mararin aurena?." Safna ta ce, "amma hakan ba daidai bane, wannan shigar zata iya jawo miki abinda ba kiyi tunani ba Narma. Ina yawan faɗa miki wannan maganar amma bakya ji, su Nasreen su daina zugaki, wallahi cutar ki suke yi. Da wannan shigarta ki babu lallai ki samu wanda zai aure ki saboda Allah." Gabaɗaya suka yiwa Safna can akan abinda ce ita dai tayi musu banza suka ƙaraci surutun su. Ɗaya daga cikin su da ta fita ta shigo yana cewa, "Nass yanzu da bouncers ki ka dawo yawo?." Narma ta ce, "a ina?." "Gashi nan" ta faɗa tana nuna musu Omar ta window wanda ya ke tsaye yana amsa waya. Narma ta kalle su ta ce, "shine Tiger fa, na san kin san sunan na sa ko?." "Ni kuwa na san sunan, ban dai san fuskarsa ba amma na san sunansa ko ɗazu media akan maganarsa ta yamutse." "Yes shine. Ai na baku labarin abinda ya faru jiya, shiyasa Dad yake so ya dinga kai ni duk inda nake so." Safna ta kalle shi ta ce, "amma kin cuce shi, a ina ya yi kama da bouncers don Allah? Ki ga mutum ɗan daidai dashi ki haɗa shi da waɗanan jibga-jibgan halittar?." Suka yi dariya gabaɗaya Nasreen ta ce, "Gaskiya dai ta cuce shi, wannan ai ko rabin bouncers bai kai ba, yanayin jikinsa ma sha Allah." Safna ta ce, "kuma gashi bai yi kama da yadda ake faɗarsa ba. Kalle shi fa fari kyakykawa mai zubin buzaye." Nass ta ce, "ni kaina mamaki nake yi anya kuwa ɗan daba ne kamar yadda ake faɗa?. Amma jiya na gani da idona." Narma ta sake cewa, "mu je mu tafi, ɗan rainin hankali ne yanzu sai na neme shi na rasa." Ɗaya daga cikin su tace, "Dan ya raina miki hankali?." Nasreen ta ce, "baki yi maganinsa bane." A haka suka fito harabar gidan ko wacce ta sha makeup kuma duk sun yi kyau. Dukkan su da mota suka zo, ko wacce ta shiga motarta suka fita ita kuma ta shiga bayan motar. Bai ce komai ba ya buɗe mazaunin gaba ya shiga ƙhamshin turarenta ya sake kai amsa ziyara a hancinsa. Kamar zatayi masa magana sai ta kasa shi kuma yana so yaji inda zasu je. Narma da ta fahimta sai ta faɗi sunan event center ɗin da location ɗin, bai ce mata komai ba ya kunna motar suka fita. Kallon gefen fuskarsa ta samu kanta da yi yana kallon gabansa hankali kwance fuskar sa babu fara'a ko kaɗan. "Na gode" taji bakinta ya furta ba tare data sani ba. Kamar bai ji ta ba haka ya yi, ya cigaba da tafiya har suka zo inda ta ce kafin a buɗa masa gate ya shiga ta fito daga motar. Har zata wuce taji ya ce, "zaki gama yaushe?." Kallonsa tayi suka haɗa ido ta ga fuskarsa babu alamun wasa ta ce, "nan da two hours." Bai sake cewa komai ba ta tsaya tana kallonsa ganin hakan sai ya kalle ta sai ta wuce shi ta shiga ciki. Samun kansa ya yi da kallon ta tana tafiya, ya yi saurin janye idanunsa jin baƙon yanayi ya na kawo masa ziyara. Bai zauna a wajan ba fita ya yi ya koma gida a yadda ya lissafa ƙarfe goma kenan zasu gama. Ƙarfe goma da wani abun kuwa ya dawo ya samu ƴan mata suna ta fitowa ƴaƴan manya kai da ka ga yaran ka san yaran masu kuɗi ne manya ba ƙananu ba. Hango ta ya yi tana tahowa tana dariya gefen ta Ashraf ne shima dariyar yake yi. Dauke kai ya yi ya kawar da fuska daga kallon ta ya lumshe ido, ido ya sake buɗewa a lokacin ta zo wajan, kallon motar tayi ta gane ta sai ta ce,  "Ka je kawai zamu tafi da Beb." Kallon baki da hankali Omar ya yi mata ya kalli Ashraf da shima shi yake kallo yana mamakin daman wannan ne tiger ɗin. Narma ta sake cewa, "ka je kawai." Wani irin kallo yake mata alamun bazai ma yi magana ba ganin hakan Ashraf ya ce, "kai ba Drivern ta bane? To ta ce kaje zan kaita ka tafi mana." Kallon Ashraf ya yi bai ce komai ba dan bashi da lokacin sa. Narma ta ce, "ƙyale shi Beb, mu je ka kai ni na gaji....." bata ƙarasa ba maganar ta maƙale jin ya ce, "Ko ki zo ki shiga ko na ɗauko ki." Mamaki suka juya suma kallon sa ganin kamar ba shi ya yi maganar ba, ya ɗago ido yana kallonta ta ƙasan ido ya ce, "bana son ɓata lokaci, ki zo ki shiga ina da abinda zan yi. Ni ba ɗan aikin ki bane da zaki ajjiye ni ina yi miki magana kina yin banza ba!." Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka Narma ta ɗan ji tsoro amma ganin Ashraf na wajan sai ta danne ta ce, "ba fa zan shiga ba, a motar mijin da zan aura zan tafi." Ashraf ya ce, "malam ka tafi daman ai aikin ka kenan ko? To Narma tace bata so ba sai ka ƙyale ta ba?." Kallon Narma ya yi yana cize baki ya sake kallon Ashraf ya ce, "in na sake magana ka saka min baki sai kayi dana sani. Wallahi sai na saka ka haɗɗiye haƙorinka." "Me zaka yi?." Omar bai bashi amsa ba dan yadda yake jin zuciyarsa zai iya karya shi wallahi. Fitowa ya yi daga motar ya matso kusa dasu ya ce, "ka sake yin maganar zaka ga abinda zan yi. Ke kuma kafin na irga uku ki shiga mota in ba haka ba wallahi sai na mare ki!" ya faɗa yana nuna ta da yatsa idanunsa a waje. Tsoro ya bayyana a tare da ita bata san ta buɗe motar ta shiga ba ya bar Ashraf a wajan ya shiga motar suka fita. "Wai kai meye haka ne? Ina ruwanka da ni, bani nace ka bari ya kai ni ba?. Biyan ka ake yi, ina da ikon da zan ce bana son abu kuma dole ka yi min. Haba duk kabi takura min, ni wallahi na gaji." Tsayawa ya yi ya jiyo yana kallon ta kafin ya duƙa ƙasa ya ɗauko wata wuƙa mai madaidaicin girma, ya buɗe motar ya fito ya buɗe bayan motar inda take ya saka mata wuƙar a wuya kamar yadda ya yiwa Nayla ya ce, "in kika sake yi min magana wallahi sai na yi miki illa. Ni zaki dinga yiwa ihu? Sa'an ki ne ni?." Ɗiff Narma tayi tana tuna yankan jiya ma taji azaba balle ya yanke ta a wuya. Kallon idonsa take yi yana kallon nata ya sake cewa, "in kika sake magana wallahi da ƙafa zaki koma, In na yi rantsuwa bana karyawa, ki kiyaye ni duk lokacin da na ce wallahi!." Shiru tayi bata ce komai ba yaja tsaki ya ce, "stupid girl" ya faɗa yana barin wajan ya sake komawa motar ya ja motar suka tafi. Har suka je gıda Narma bata ce komai ba a tsorace take dashi ko motsin kirki ta kasa, ya buɗe motar ya fita ya barta a cikin motar bai sake kallon inda take ba ya fita daga gidan. Narma haka ta koma gidan jikinta duk a sanyaye a daren ta kira Dad ta faɗa masa abinda ya yiwa Ashraf sannan ta kwanta amma zuciyarta cike yake da tunaninsa, wai wanne irin ƙarfin guiwa yake da ita haka?. Da wannan tunanin bacci ya ɗauke ta. Shi kuwa Omar yana komawa text ya rubutawa Sen dan wallahi ya cigaba da zama inda Narma take bai dan adadin abinda zai aikata mata ba, gwara kawai su nemi wani shi kam ya gaji. Sen yana ganin text ɗin sa ya kira shi ya faɗa maaa abinda ya faru shi kuma ya nuna jin daɗin sa akan hakan, dama amfanin kula da ita ɗin kenan, kuma shi Omar bai san Ashraf ba dole a samu damuwa in ya gansu tare. Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar ya kwanta yana tunani, fuskar Narman yake gani a idonsa ya ja tsaki mai tsaho ya kulle ido da ƙarfin gaske. Kwana biyu bai je ba saboda Sen ya ce ya bari Ashraf ɗin ya dinga kai ta dan haka kwana biyu babu inda yake sai dai ya fita ya dawo kawai. Ita kuwa Narma biki suke sha Ashraf yana kai ta duk inda take so amma ta kasa daina tunanin Omar ko kaɗam, da ta rufe ido shi take gani musamman lokacin da yake kallon idanunta. Ranar asabar Ashraf ya koma Omar bai sani ba yana zaune a ɗaki ya ga baƙuwar number tana kiran sa, ɗauka ya yi ya saka a kunne bai yi magana ba Narma ta ce, "Hello Tiger, Narma ce." Jin hakan sai ya gane ta ya ce, "ina ji." "Ashraf baya anjima zan je biki." "Okay" ya furta mata kafin ta sake magana ya yanke wayar. Saurin katse da wayar ya yi jin zuciyarsa na wani irin harbawa lokacin da Narma ta fara yi masa magana, magana take cikin yanga da iyayi hakan ya saka yaji wani iri har bai san ya yi hanzarin kashewa ba. Shin wai me yake Shirin faruwa dashi ne?. Meyasa ya kasa daina tunanin ta? Meyasa yake jin wani iri da ta kira shi yanzu? Lallai dole ya san dalilin hakan kafin abun ya yi nisa. Ɓangaren Narma murmushi ta samu kanta da yi bayan ya kashe wayar a bayyane ta ce, "muryarsa mai daɗi, zan so naga yana murmushi." Sai kuma tayi tsaki ta ce, "Ko Ina ruwana ma oho, da ya yi murmushi da kar ya yi shi ya sani. Ni so nake na manta dashi amma na kasa, ko meyasa na kasa mantawa dashi oho min" ta faɗa a bayyane tana tashi ta shiga ɗaki har lokacin muryarsa take ji a kunnen ta. Tofa, Omar da Narma, ga kuma Nayla a gefe. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://www.tiktok.com/@nanahaleemawriter?_t=ZS-8zaZqblsrGp&_r=1 *Book 1* *P 15.*        Nayla kuwa yanayin da take ji akan Omar ya fara damunta domin ko yaushe a cikin tunaninsa take, ko yaushe a cikin ganin murmushinsa take da zarar ta kulle. Ga faɗuwar gaba da take addaba mata, ko ya taji an kira wani mai irin sunansa sai ƙirjinta ya buga. Ɗakyar ta jure kwanaki uku bata ganshi ba, a safiyar ranar bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da siket, rigar har guiwa ta saka mayafi ƙarami a kanta ta fito falon. Salma ta kalle ta tace, "Sai ina?." Ta kalli Salma ta ce, "Zan je gidan Mama Zaliha." Hajja ta kalle ta ce, "Sai kin dawo, amma dai kar ki yi dare." Nayla ta ɗaga kai alamun to, Salma ta ce, "Amma da kin faɗa min da na raka ki." "Na ji jiya kina cewa bakya jin daɗi shiyasa, ni kuma tun jiya ta kira ni ta ce nazo." Salma ta ce, "Da motar Hajja zaki je?." Nayla ta ce, "A'a, napep zan hau." Hajja ta ce, "ke bana son shirme, kin san babanki baya son kina hawa abin hawa na haya ko? Meyasa baza ki bari a kira Sayyadi ya kai ki ba?." Nayla ta ce, "Hajja ai ba jima zan yi ba, yanzu zan dawo" ta faɗa tana fita da sauri dan kar Hajja ta hanata. Nayla tana fita daga gidan kallon ƙofar gidan Didi ta ta yi gabanta ya faɗi sosai, a hankali ta fara takawa zuwa ƙofar gidan faɗuwar gabanta na tsannanta, wani irin yanayi baƙo a gare ta yana ratsa ilahirin jikinta. Ƙofar ɗakinsa a buɗe take tayi sallama ta shiga gidan amma shiru babu alamun motsi. Tana gab da shiga falon ta ji an ce, "wace a nan!?." Da sauri ta jiyo suka haɗa ido, Sarai ya gane itace tun wucewarta ya ganta, yana sane ya ce wace a nan dan yarinyar ta soma zuwar masa wuya. Nayla ta ce, "ni ce, ina yini." Bai amsa ba ya ce, "Haka ake shiga gidan mutane babu sallama?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "nayi sallama." "Mtsww! To me ya kawo ki?." "Wajan Didi na zo." "Tattara ƙafafunki ki bar gidan nan Didi bata nan." Jin abinda ya ce sai ta ɗago ta ga shima ita yake kallo fuskarsa a ɗaure sosai. A hankali ta tako ta zo ta wuce shi ya bita da harara ya koma ciki. Haushin Didin ita kanta yake ji tun safe ta wani fita gidan biki, bikin ma kuma wai gidan Kawu tsabar lalacewa. Ga Nayla da ta ke neman tunzura zuciya sa, ta dame shi da shige da fice a cikin gidan su. A bayyane ya ce, "wannan yarinyar akwai nacin tsiya." Nayla ba ƙarmain daɗin ganinsa taji ba ta dinga sauke ajiyar zuciya tana tafiya fuskarta da murmushi, ji take kamar an yi mata babbar kyauta mai matuƙar daɗi kasancewar ta ganshi har sun yi magana. A haka ta hau napep ta tafi gidan Mama Zaliha dan kar ta koma Hajja ta fahimci wani abun da baza ta je ba. Omar shiryawa ya yi cikin manyan kaya na yadi baƙi mai gajeran hannu kansa babu hula, gidan ya kulle da makulli sannan ya tafi wajan Narma da niyar kai ta inda ya ce zasu je. Narma tun shigarsa tana tsaye a balcony tana kallon sa, wara idanu tayi tana kallon sa cikin shigar manyan kaya dan ya yi mata kyau sosai. Bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba, duk da ƙananun kayan suna karɓar sa kamar jarumin india, amma kyaun da yayi a manyan kaya ƙarshe ne. Gani tayi kamar kwanakin da ɗauka bata ganshi ba ya sake yin kyau ga wani class na musamman da ya ƙaro, duk da fuskarsa babu annuri amma ya yi mata kyau sosai. Gazebo ya shiga ya zauna akan kujerun da suke cikin ta. Yadda ya zauna ya ɗora ɗafa kan ɗaya yafi komai tafiya da ita, bata san tayi murmushi ba a bayyane ta ce, "Tiger!." Sakkowa tayi daga saman ta fito harabar gidan tana kallon inda yake, samun kanta tayi da nufar wajan da yake cikin salon tafiyar ta ƴan gayu. Har ta isa bai sani ba sai tsayuwarta ya gani da ƙhamshin turarenta. Ɗago ido ya yi ya kalle ta, ta yi kwalliya cikin straight gown, ta kawo mayafi mai kauri amma mara girma ta saka, tayi ɗauri da ta ja shi baya gaban gashin ta ya fito sai hakan ya ƙara mata kyau sosai. "Ina yini" ta furta tana kallon sa shi kuma tuni ya janye idanunsa dan ya kasa gane abinda yake ji in yana kallon ta musamman in itama kallon sa take yi. Miƙewa ya yi ba tare da ya amsa ba, a shagwaɓe ta ce, "na gaishe ka kayi min shiru, kuma saboda kirkin da ka yi min ya saka na gaishe ka." Lumshe ido ya yi ya buɗe jin yadda maganarta ta tatsa har cikin zuciyarsa, wani irin sanyi yake ji a jikinsa yanayinsa na canjawa. Sake haɗa ido suka yi ya janye ido bai ce komai ba. Narma ta ce, "baza ka amsa gaisuwar ba?." Ɗan ƙaramin tsaki ya yi ya ce, "lafiya." Daga haka ya yi gaba ta bishi da kallo duk sai taji haushin kanta da ta yi abinda ya dizaga ta. A hankali take takowa dan ɗakyar take motsawa saboda yadda ta kamata rigar, daga wajan guiwarta an kama rigar sosai ta tsuke. Baya ta juya tana yiwa mai gadi magana a nan ya hango doguwar tsagar bayan rigar wacce ta bayyana farara digadiginta, har abinda ya rab digaginta da cinyarta a bayyane yake. Ɗauke kai ya yi daga kanta yaja dogon tsaki ba tare da ya san dalili ba, ta buɗe motar ta shiga shi kuma ya ja motar suka fita. Babu wanda yake magana a cikin su kamar ko yaushe, shi titi yake ita kuma danna waya amma lokaci zuwa lokaci tana ɗagowa ta kalle shi sai ta cigaba da abinda take yi. Shopping complex suka shiga kamar yadda ta ce, ya tsaya a harabar store ɗin ta buɗe ta fita bata ce masa komai ba. Fitowa ya yi shima ya shiga dan akwai abinda yake so ya siya. Bata san ya shigo ba sai ganin sa tayi a ɓangaren turare ya ɗauki ɗaya na maza sannan ya ɗauki ɗaya na mata. Ƙarasowa wajan tayi ta kalle shi shima ya kalle ta amma bai ce mata komai kafin kuma tayi magana ya wuce. Wajan kayan shayi ya je ya ɗauki coffee sannnan ya ɗaukarwa Didi milo dan ya san ta akwai son Milo, haka kawai ma sha take yi. Kafin Narma ta gama shi ya biya kuɗi ya koma mota ya zauna yana duba turaren da ya siya. Ba jimawa sai gata nan ta fito bayan ta da mai riƙe da ledar da ta yi siyayya. Yana daga zaune buɗe baya aka saka mata sannan ta shiga motar suka tafi. Jira yake yaji ta ce ga inda zasu je yaji tayi shiru shi kuma bazai tambaya ba. Ta wani ƙaramin cafe suka zo wucewa Narma ta ce, "ɗan tsaya a nan zan siyi donut." Faka motar yayi ta shiga ciki bata jima sosai ba ta dawo ta shiga motar. Wani almajiri ne yazo wucewa yana bara Omar ya sauke glass ya miƙa masa kuɗi shi kuma yana addu'a, Omar ya ɗaga glass ɗin bai ko kalle ya ba. Donut ɗin ta buɗe sai ta kalle shi ta ce, "Ga donut" ta faɗa tana miƙa masa ledar. Kai ya girgiza mata kawai ya ja motar suka tafi. Wayarsa ce tayi ƙara ya kalla yaga Goje ne yake masa waya sai ya ɗauka ya saka a kunne Goje ya ce, "Damisa babbar Yaya ce babu lafiya, yanzu ta dawo daga unguwa." "Subahanallah! Me ya same ta?" Ya tambaya a gigice. Goje ya ce, "Bamu sani ba, kawai mun ga saukarta daga napep tana jiri kamar zata faɗi." "Gani nan" ya faɗq yana yanke wayar tare da ƙara speed ɗin motar. Kallon sa Narma take tana mamakin Wacece babu lafiya haka ya damu?. Sannan mamakin kanta take yi wai ita Narma itace driver yake amsa mata waya a mota bata ɗauki mataki ba, ita kanta ta san ta canja. Gani tayi sun wuce hanyar su ta kalle shi ta ce, "gida fa zan je." Ai ko kula ta ma bai yi ba sai da ya ganshi a ƙofar gidan su ya fita a gigice ya shiga gidan. A kwance ya samu Didi kana ganin ta ka san bata da lafiya, ya tallafo ta jikinsa ya ce, "Sannu Didi, tashi mu je asibiti." Ta kalle shi ta ce, "A'a Omar, ba sai naje ba." "Wallahi sai kin je, ki tashi mu je ko na ɗauke ki wallahi." Jin abinda ya ce sai tayi murmushi ta miƙe ya riƙe hannunta suka fito, gidan ma a buɗe ya barshi saboda su Bash suna nan. Motar da taga ya buɗe mata gaba ne ya bata mamaki, duk da tana cikin ciwo bayan ya shigo sai sa ta ce, "Omar motar waye wannan?." Narma da take baya ta maimaita Omar a zuciyarta tana cewa, _Dama sunan sa Omar? Suna mai daɗi. Shiyasa yake da fushi mana da yawa masu suna Omar haka suke._ bai bata  Didi amsa ba ya ja motar ta ce, "wai yaushe ma ka iya mota Omar?." Kallon ta ya yi ya ce, "Don Allah ki yi shiru baki da lafiya" ya faɗa yana taɓa goshinta yaji zafi sosai. Narma da take baya ta ce, "Sannu, ya jiki?." Didi kanta ciwo yake ɗakyarta iya waiwayowa bata ma iya gane wacece sosai ba, ta ɗaga kai kawai daga nan tayi shiru. Narma dai mamaki take yi ko wacece wannan? Ya ruɗe tunda aka ce bata da lafiya, gata kuma har yana haɗa ta da Allah akan tayi shiru cikin rarrashi, lallai ko wacece tana da mahimmaci a gare shi. Asibitin da suka je aka yiwa Narma dressing nan suka je ya fito da kansa ya riƙe Didi suka shiga asibitin. Narma ganin yadda jikin Didi yake rawa sai ta bata tausayi sosai daman ita akwai tausayin mara lafiya hakan ya saka ta fito itama ta bi bayan su. Kwantar da Didi aka yi akan gado aka yi mata allura kafin a ɗauki jininta a gwada a dawo a fara yi mata treatment ɗin malaria. Ɗakin gado biyu ne a ciki amma Didi ce kawai a kwance, Narma tana jingine da bango tana kallon Didi da aka gama saka mata ruwa bacci ya ɗauke ta. Hannun Didi ya riƙe wanda aka sakawa ruwan ganin zai faɗi ya ajjiye a gefen ta ya zare mata hijjabin jikinta ya sake taɓa wuyanta. Ƙaramin tsaki ya yi jin har lokacin da zazzaɓin ya ce, "Sai da nace mata kar ta fita amma taƙi ji." Narma ita dai kallon sa take yi domin mamaki yake bata sosai, gabaɗaya ya sauya mata ya yi sanyi damuwar rashin lafiyar wacce bata san alaƙar su ba ta canja shi. Kana jin yadda yake magana kasan ko wacece wannan ya damu da ita sosai. Kallon gefen ta ya yi yaga tana kallonsa sai a lokacin ma shi ya tuna da ita dan wallahi tunda yaga yadda Didi take ya manta da wata Narma a bayan mota. Sai Narma tayi murmushi ta ce, "Zata samu sauƙi in sha Allah." Kai ya girgiza bai ce komai ba, amma yaji ta burge shi sosai. Awa ɗaya suka kwashe a asibitin dan shi bazai iya tafiya ya bar Didi ba, ita kuma Narma duk ta gaji sosai. Bai ma lura da yanayin ta ba, abinda ya sani ko babanta ne zai zo bazai bar Didi ya tafi wani waje ba. Ya kalle ta ya ce, "zan kira waya azo a mayar dake gida yanzu." Narma ta ce, "A'a, ka bari ta farka sai mu tafi gabaɗaua, jikinta bai yi worst ɗin da za'a yi addminting nata ba." Shiru kawai ya yi bai sake cewa komai ba. Fita ya yi ya yi sallar magriba ya dawo a lokacin Didi ta buɗe ido. Bayan ya dawo ya ƙaraso inda take ya riƙe hannunta ya zaunar da ita akan gadon ya ce, "ya jikin?." Didi ta ce, "na ji sauƙi sosai, ciwon kai ya rage sai rashin ƙarfin jiki da babu." "Shima zaki daina ji in sha Allah." Ba sake magana ba ya fita jim kaɗan ya dawo ya kalle ta ya ce, "zamu tafi gida, ga magani da allurai an bayar, ai kin ce jikar Hajja ta iya allura ko?." Didi ta ɗaga masa kai, ya riƙota ta tashi tsaye ya saka mata hijjabi da kansa ya riƙe hannunta ya ce, "Mu je gida." Kallon Narma tayi ta ce, "Ka bar baƙuwar ta ka." "Wacce baƙuwa?" Ya furta yana kallon Narma dan wallahi ya sake mantawa da ita. Narma ta ɗan saki fuska kaɗan ta biyo bayan su. Yanzun ma Didi ya buɗewa gaba ta shiga, Narma ta shiga baya suka sake komawa gidan Didi. Narma tana mamaki kenan itace bazai buɗewa ƙofa ba tunda gashi yana buɗewa wacce bata sani ba. Suna tsayawa Narma ta ce, "Allah ya ƙara sauƙi." Didi ta kalle ta ta ce, "Amin. na gode Barr Nass." Narma bata yi mamaki yadda ta santa ba tayi mata murmushi ta fita. Bayan sun shiga Didi ta ce, "ka bar ni kaje ka mayar da ita gida, tayi ƙoƙari sosai wallahi." Ya kalli Didi ya ce, "zan kai ta, so nake na tabbatar kin samu lafiya." "Na samu lafiya Omar, ka je ka mayar da ita ba kowa ne zai yarda da irin haka ba." Bai ce komai ba ya fita ya shiga motar bai ce mata komai ba har suka je gidan. Fitowa yayi daga motar bayan ta fito ta kalle shi ta ce, "Allah ya ƙara lafiya, a gaishe ta." Dan kawai kallon sa take yi ne ya saka taga bakin sa ya amsa da amin, amma maganar ko kan harshensa bata zo ba balle laɓɓansa. Ya miƙa mata key ta girgiza kai ta ce, "kaje da motar saboda kana da mara lafiya, kaje da ita kawai." Kai ya girgiza ya ce, "bana buƙata" ya faɗa yana sake miƙa mata key ɗin. "Ka je dashi." Ya girgiza kai ya ce, "bani da buƙata, na gode." Murmushi tayi jin yana yi mata godiya ta karɓi key ɗin har ya juya ta ce, "Omar!." Wani iri ya ji a jikinsa, ya waiwayo ya kalle ta ta ce, "Ranar da aka yanke ni a hannu kaine ka biya kuɗin asibiti, na manta ban biya ka ba. Please ka bani account number ɗin ka na tura maka." Kamar zai yi magana sai ya fasa ya ɗaga kai kawai yana juyawa ya fita, ta bishi da kallo tana murmushin da bata san dalili ba. Mai gadi ta kira ta bashi key ɗin motar ta ce ya kwaso mata kaya ya shigar mata dasu ita kuma ta shiga ciki.         Omar kuwa haka ya koma gida sunansa da ta kira yake ji har cikin zuciyarsa bai san lokacin ba, ya yi murmushi Didi ta kalle shi ta ce, "murmushin me ka ke yi?." Ya ƙarasa shiga yana kallon ta ya ce, "ya jikin naki? Na ɗauka ma kin yi bacci kin huta." "Ban yi bacci ba." "Abinci fa?." "Na ɗan ci, Hajja ce ta ta aiko min da abinci yanzu." Ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "To yanzu ki ki kwanta ki huta. Sai da nace miki kar ki je gidan bikin nan kika ƙi ji, wataƙila wani abun suka yi miki dan ki yi rashin lafiya daman ba son ki suke yi ba." Tayi ƴar dariya ta ce, "naji, ko ma meye dai ƴan uwana ne." Ya taɓe baki bai yi magana ba. Tana  so tayi masa maganar Narma da inda ya koyi mota amma bata jin ƙarfin jiki hakan ya saka ta tashi taje ta kwanta shi ma ya fita zuciyarsa cike da tunani kala-kala. Washe gari bai fita ba har yamma sannan ya je gidan dan yaga kiran Narma bai ɗauka bane. Lokacin da ya je gidan shiru babu komai duk bai ga masu aikin ba bai damu ba ya yi zamansa a inda ya saba zama. Ihu ya dinga ji daga cikin gida, da farko ya ɗauka kunnensa ne amma sai yaji abun ya yi yawa ihu ake sosai ana neman taimako. Kamar kar ya shiga sai kuma ya miƙe ya shiga falon gidan dan bai san abinda ya faru a ciki ba, a daidai lokacin Narma ta sakko a guje daga ita sai towel ƙarami wanda ko cinyar ta bai gama ɓoyewa ba, kanta babu ɗankwali tana ihu kamar wacce aka biyo. Ganinsa a tsaye sai kawai ta yo inda yake ya yi saurin yin baya dan yaga ƙoƙarin rungume shi take yi. "Geckos a toilet ɗina, ka taimaka min ka kashe shi tsoronsa nake ji." Takaicin da Omar ya ji ji yayi kamar ya tsinke ta da mari ya tsaya kawai yana kallon ta cike da takaici. Wai tsaka take yiwa wannan ihum, da farko ya ɗauka wasu ne suka shigo gidan da niyar cutarwa take kukan neman ceto. "Ka taimake ni ka je ka kashe ta don Allah" Ta faɗa tana niyar yin kuka. Kallon inda ta sakko ya yi dan shi kam dai bazai hau saman ba. Mai aikin ta mace ce ta shigo tana cewa, "Hajiya lafiya?." "Geckos zaki kashe, maza jeki toilet ɗina." Da sauri ta hau saman shi kuma ya fita bai sake kallon ta ba. Zama ya yi yana amma gabaɗaya ita yake gani a idanun sa ɗaure da towel ta nufo shi a guje, runtse ido ya yi ya buɗe ya tashi zaune sosai ya tuna lokacin da ta riƙe shi da aka ƙwace mata waya, ya sauke numfashi yana jin sabon yanayi a tare dashi mai wahalar fasaarawa. Bai jima sosai sai ga mai aikin ta ta ƙaraso ta ce, "Wai kazo." Ya kalle ta ya ce, "na zo?." "Eh, haka Hajiya Narma ta ce." Kai ya ɗaga  mata kawai ta tafi shi kuma ya sake gyara zama dan bazai shiga ba. Bata isa ta aiko a kira shi ba kuma ya je, dan ta ga yana sake mata bata isa ta raina shi ba. Ga mamakinsa sai gata ta fito cikin riga roba mai bin jiki ko ina na jikinta yana rawa. "Wannan yarinya bata da hankali!" Ya furta yana yana rufe idonsa. Ƙarasowa tayi ta ce, "Tiger daman tambayarka zan yi ya jikin mara lafiya shiyasa na kira ka ɗazu, da baka ɗauka ba shiyasa kayi tunanin akwai inda zan je." Omar ya miƙe tsaye jin tana tambayar lafiyar rabin ransa ya ce, "ta ji sauƙi." "Allah ya ƙara lafiya, ka gaishe ta." "Zata ji." "Baka tura min account details ɗin ba." Ya kalle ta suka haɗa ido ya ce, "zan tura." Miƙa masa ledar jiya tayi ta ce, "ka barta a mota jiya, da na ce kwaso min kaya sai aka haɗa min har ita. Nace wannan ai saƙon Tiger ne ba nawa ba." Kallon ledar ya yi dan shi wallahi ya manta da ita gabaɗaya, karɓa yayi bai yi magana ba. Narma ta ce, "Zaka iya tafiya babu inda zan je." Nan ma bai yi mata magana ba yana mamaki a ransa lallai ma ta samu sake, har zaka iya tafiya take ce masa wato ga yaronta. Ƙwafa ya yi kaɗan zai wuce ta ce, "Meyasa baka son yi min magana? Jiya naji kana ta magana amma ni baka yi min." Bai jiyo ba balle ya tanka ba ya wuce, a nan ya ga Ashraf a tsaye yana kallon su da alama ya jima da zuwa gidan. Bai ko kula shi ba ya fita daga gidan. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. Masu nema daga farko ga WhatsApp link nan. https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t *Book 1* *P 16.* Narma wajan Ashraf ta ƙaraso da yake kallon ta har tazo inda yake ya kalli Omar da ya fita ya kalle ta ya ce, "me ki ke yi a wajansa?." Narma ta ce, "mu je ciki" ta faɗa tana wucewa shima ya bi bayan ta. A falo ta zauna shima ya zauna yana kallon ta ya ce, "Ina tambayarki, me ki ke yi a wajansa har kina yi masa murmushi haka?." Narma ta kalle shi ta ce, "ba na faɗa maka abinda ya faru ba akan ƙwacen waya? Tun daga nan na gane yana da kirki shine mu ke gaisawa. Kuma jiya ne da ya kaini shopping complex ya yi mantuwa a mota shine na bashi." "Kawai dan ya taimake ki sai ki fara sakıin jiki dashi? To daman taimakon ki a dolensa ne ko baya so, saboda aikinsa ne, biyansa aka yi dan ya kula dake. Ki san matsayinki Beb, ke fa ba gama garin mutane bace you have to know that." "Na sani, kuma ni ba wani abun ne ya kaini wajansa ba." "Gaskiya ya kamata ki koma gida, zaman Kanon ya isa haka tunda dai an gama bikin da ya kawo ki. Ta ya zaki dinga tsayawa kusa dashi kina yi masa murmushi kamar wani mate ɗinki?. He's just your driver, driver ɗin ma ɗan daba shashasha, mara ilimi, ƙazami, jahili ne wanda bai san komai ba sai...." Narma bata san ta katse shi ba ta ce, "Ashraf stop please! na faɗa maka dalilina na zuwa wajan sa why are you insulting him like that?." Da mamaki yake kallon Narma ya kafa mata ido ya kasa koda motsa idon yana kallonta, sai a sannan ta fahimci abinda ta ce cikin mamakin kanta ta kalle shi itama kafin tayi magana ya ce, "just because i insulted him that's why you are upset?." Jin a yadda ya yi tambayar cikin jin haushi sai ta ce, "Ba haka bane, kawai bana so ka dinga yi min faɗa ne akan abinda na faɗa maka dalili. Ka san wacece ni ai, na san abinda zan yi." Shi dai mamakin ta yake yi sosai dan Narma tana neman canjawa daga yadda ya santa, amma sai bai nuna ba ya ce, "Well, is okay" ya faɗa cike da jin haushi yana ƙoƙarin miƙewa. Riƙe hannunsa ta yi ta ce, "Are you upset?." Miƙewa tsaye ya yi itama ta miƙe tana riƙe da hannun sa ya ce, "kin nuna min driver ya fi ni a wajan ki Narma." Ta buɗe idanu ta ce, "haba Beb, what are you saying? Ni ban haka nake nufi ba." "No! driver ki ya yafi ni, you show me my limit. Saboda na zage shi ki ke yi min shouting ko?." "Sorry beb, ba haka bane" ta faɗa da shagwaɓe tana kallonsa. Lumshe ido ya yi kafin ya buɗe ta kwanta a jikinsa ta ce, "kar ka ji haushi, i'm sorry." Hugging ɗinta back ya yi na wasu seconds kafin ta janye jikinta tace, "Smile." Murmushi ya yi yana kallon ta ya ce, "I love you." Itama murmushi tayi ta ce, "I love you too." Waya ya ɗauka ya yi musu selfie suka yi kyau kuwa kafin ya kalle ta ya ce, "ina zaki je yau?." "Babu ko ina, na gaji kaina na ciwo so bana son fita." "Okay yanzu zan je wani aike da Abba ya yi min, so in na dawo zan dawo." Murmushi ta yi ta ce, "okay sai ka dawo." Har bakin mota ta raka shi ya shiga ya fita ita kuma ta koma ciki. Omar lokacin da ya koma Didi tana a falo zaune ya shiga shima ya zauna ya ce, "ya jiki?." Ta kalle shi ta ce, "da sauƙi Omar." Ledar hannunsa ya miƙa mata ta karɓa ya ce, "jiya na kai yarinyar can wani kanti sai na siyo miki, na san ki da son turare da kuma son milo." Murmushi tayi ta buɗe turarenta ga kuɗin sa a jiki naira dubu talatin da uku ta ce, "Omar wannan turare mai tsada haka?." "Eh, ki dinga fesawa in sirikina zai zo." Dariya tayi ta ce, "Ka raina ni." Shima murmushi ya yi kafin ya ce, "Ya maganarsa kuwa?." "Sun gama magana da Kawu to rashin lafiyar nan tawa ban sammu mun tattauna sosai ba, ko mai yake faruwa zan faɗa maka." Kai ya girgiza kafin ta kalle shi ta ce, "Omar yaushe ka iya mota?." Murmushi ya yi ɗan daman ya san sai ta tambaya, ya gama sanin halinta ko wanne motsi in ta yi zai fahimci me take nufi kamar yadda ta sa nasa. Ya kalle ta yaga shi yake kallo, kafin yayi magana ta ce, "Omar kana bani tsoro fa, a ina ka san Sen har ya baka ƴarsa kana yawo da ita?." "Didi" ya faɗa yana gyara zama ya kalle ta sosai ya ce, "na san abinda nake yi fa, kar ki damu kanki." Ta ce, "nima ban ce baka sani ba Omar, amma abubuwan ne suke bani mamaki sosai." "Kar ki damu, babu komai sai alkhairi." "Allah ya sa hakan" ta furta tana buɗe turaren dan ya yi mata ƙhamshi sosai. Bai sake magana ba ya tashi ya fita itama bata sake cewa komai ba saboda kanta ya fara yi mata ciwo. Da daddare Hajja ta shigo ita da Nayla da Salma dan su duba Didi, kamar ko yaushe yana zaune a falon shi da ita duk da ba hira suke ba ita tana abinda yake gabanta shi kuma yana ta danna waya. Sallamar su ya saka suka kalli masu shigowa Didi da fara'a ta ce, "Hajja kece da kan ki?." Hajja ta ce, "Aisha an ce baki da lafiya harda su kwnaciya a asibiti ai dole nazo." "Sannu da zuwa" ta faɗa da fara'a tana kallon Hajja. Hajja ta zauna suka gaisa da Didi kafin ta kalli Omar suka haɗa ido ta ce, "Omar Faruku mazan fama, ja daku ba dai rago ba. Wannan hakimcewa da ka yi a falo sai ka sa a ɗauka mai gidan ne ai." Samun kansa ya yi da sakin murmushi mai sauti haka kawai yake jin farin ciki a zuciyarsa ba tare da ya san dalili ba, ya kalli Hajja ya ce, "Ina yini." "Lafiya lau Ummaru, Na ɗauka ai baka ganni ba da naga ka ɗauke kai." Bai ce komai ba kuma fuskarsa bata bar murmushin ba. Nayla suman zaune tayi ganin yana murmushi a karo na uku da ta ga yana yi, sai taji ƙirjinta yana sama da ƙasa wani irin abu yana fizgar ta zuwa gare shi kamar ta saka igiya ta jawo shi haka take ji. Daƙyar ta iya ɗauke ido daga kansa suka gaisa da Didi kafin ta kalle shi ta ce, "ina yini." Jin ta gaishe shi sai Salma ma ta gaishe shi ya ɗago ido ya kalli Nayla da take kallon sa kamar zai amsa sai ya yi shiru. Hajja ta ce, "Kana ji ana gaishe ka fa." "Ni bana son gasuwa ni kam, Lallai sai an gaishe ni?" Ya faɗa yana kallon Hajja kafin ya kalli Didi. Hajja ta kalli Nayla ta ce, "to kin ji sai ki daina gaishe shi. Daman ai dodon ki ne ko yaushe cikin tsorataki yake." Didi ta ce, "Omar meye haka? Gimamawa ce zata saka a gaishe ka, kai wanne irin mutum ne da komai baka so?." Salma ta taɓe baki cikin jin haushi, daman in banda karanbani irin na Nayla ina ita ina gaishe shi? Gabaɗaya haushin kanta take ji da ta biye mata itama ta gaishe shi, ita kuma tayi haka ne saboda kar Hajja tayi mata faɗa tace bata gaishe shi ba. Hajja ta ce, "ƙyale shi, wataƙila in ya amsa ɗin ma tsoro zai bawa Hauwa'u." Nayla ta sauke ido ƙasa zuciyarta babu daɗi akan abinda ya yi mata, amma bata gajiya za kallon sa daƙyar ta iya sauke idon ta ƙasa. Nayla ido na ƙasa ta ce, "daman in an gaishe shi baya amsawa." Kallon wacce Hajja ta nuna da Hauwa'u ya yi yaga Nayla ce ta sunkuyar da kai sai yaji wani iri a ransa kamar bai kyauta ba, ɗauke kai ya yi daga kallon ta ya kalli Didi da take kallon sa ya ce, "Lafiya lau, shikenan na amsa ko? To ki daina hararata" ya faɗa yana miƙewa ya fita daga falon. Hajja tayi dariya ta ce, "ja'irin yaro, zan ga matar da zaka aura ai, sai na fara yi mata huɗuba na zama da kai kafin ta shigo, dan Omar jarbin ƙwai ne jansa sai me nutsuwa." Didi ta ce, "Ai Hajja dodo da donanniya zamu haɗa kawai" ta faɗa tana kallon Nayla cikin wasa tana dariya. Hajja ta ce, "shikenan ba, ayi maganin tsoro da rashin son gaisuwa." Suka yi dariya gabaɗaya yanzu har Nayla. A baya in aka yi irin wannan maganar haushi take ji, amma yau sai taji daɗi a zuciyarta har tana murmushi zuciyarta na taya ta murmusawa. Basu jima sosai ba suka yi mata sallama suka tafi bayan Salma tayi mata allura. Basu jima da fita ba aka yi sallama tare da shigowa falon. Da mamaki Didi take kallon wacce ta shigo ta ce, "wa idona yake gani kamar Barr Nass?." Narma tayi murmushi ta ƙaraso ta ce, "ni ce." Didi ta ce, "ki zauna mana." Narma ta zauna tana kallon Didi itama ita take kallo ta ce, "Sannu da zuwa." "Yauwa, ya jiki?." "Jiki da sauƙi na samu lafiya, Bara na kawo miki ruwa." "Ki barshi kawai, daman cewa nayi bara nazo na gaishe ki na barki babu lafiya." Didi taji daɗi sosai a ranta tace, "kai amma na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci." Ta amsa da amin. Didi ta ce, "yanzun nan kuma ya tashi amma na tabbatar yanzu zai dawo." Kafin Narma tayi magana suka ji sautin murya sa yana magana dasu Bash tare da shigowa falon. Haɗa ido suka yi da Narma tayi masa alamun hiii da hannu, ya kalli Didi da take murmushi ta ce, "yanzun nan yazo, ta ce ta zo gaishe ni." Narma kallon sa take yi shi kuma bai yi magana ba kuma bai zauna ba, kuma koma inda ya fito ba. Narma kallon sa take yi kafin ta ce, "Yayan ki ne?." Didi tayi dariya kaɗan ta ce, "kusan hakan, tunda ya fini tsaho da suffar manya, Yayana ne." Narma ta kalle shi a lokacin ya kalli Didi ya ce, "ina abincin su?." Didi ta san su wa yake nufi sai ta ce, "yana nan, ka jira na sallami baƙuwa sai na ɗauko maka ko?" Ta faɗa tana harararsa ganin ko kula ta bai yi. Komawa ya yi ya bar falon bai ce komai ba, to me zai ce? Shi sam bai iya magana da baƙi ba, kuma ga gidan na su ba baƙi ake yi ba ko yaushe shiru babu mai zuwa, shi kuma damn ya son baƙi, shiyasa bai iya magana da baƙo a cikin gidan ba. Bayan ya fita Didi ta ce, "in baƙi sun zo sam baya sakewa, sai ya yi ya abu kamar yaro." Narma tayi murmushi kawai bata ce komai ba dan taji haushin ƙin kula ta ɗin da ya yi. Ai ko babu komai tunda har ta tako har gidan su ta zo ya kamata ko hello ya ce mata. Didi ta ce, "na jima ina bibiyarki a instagram, ko yaushe cikin fegin ki nake har Omar ya gane ya kan ce ke dai kina son yarinyar nan. Yadda ki ke tsayawa ƙananun yara musamman akan fyaɗe yana min daɗi sosai." Narma ta ce, "na gode" ta faɗa tana murmushi kaɗan. Miƙewa tayi ta kalli Didi ta ce, "zan koma, dama nazo na duba ki ne." Didi ma ta miƙe tana yi mata godiya har bakin mota ta rako ta. Narma ta yiwa motar key ta buɗe mazaunin driver ta shiga tana sake kallon gidan ko zata ganshi, babu shi babu alamunsa duk sai taji babu daɗi ita ba haka taso ya faru ba. Ajiyar zuciya tayi ta kunna motar amma taƙi tashi tana neman yi mata yadda tayi mata har aka ƙwace mata waya. Tsaki tayi ta fito daga motar a lokacin ta hango shi sai ya ƙaraso ta bashi hanya ya shiga gaban motar, yana shiga ya kunna sai ta tashi ya zauna bai fito ba. Zagayawa tayi ta buɗe gaban motar ta shiga tare da saka seat belt shi kuma ya ja motar yana mamakin dalilin shigar ta gaba maimakon baya mazaunin ta. Tafiya suke bai bari ya kalle ta ba dan kallon ta yana yi masa illa a jikinsa, sanye take da kayan bacci riga da wando masu santsi rigar tana da tsaho tazo har guiwa amma ƙaramin hannu ne da ita. Sai wandon da yake dogo har ƙasa ta yafa mayafi ƙarami a kanta. Har suka je gidan bai ce mata komai ba sai da ya tsaya sannan ya ce, "mun gode." Cikin shagwaɓa ta ce, "Sai yanzu zaka ce? bayan har gidan ku naje ko ka kula ni? Ina tausayin mara lafiya kuma sister ka ce shiyasa naje gaishe ta amma kayi min banza kamar baka sanni ba. Da na sani ban je." Yadda take maganar sai da ta saka shi yin ajiyar zuciya, ya kalle ta yaga shi take kallo ya ce, "mun gode" ya sake faɗa yana janye ido daga kanta. "Amma sai yanzu ka ce, ko magana fa baka yi min ba." Shiru ya yi dan bai san me zai ce mata ba kuma, ita kuma ta kafe shi da ido tana mamakin abinda take aikatawa amma umarnin zuciyar ta kawai take bi. Shiru ya ratsa motar kafin ya kashe motar ya ce, "zan koma" ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe ƙofar. "Baza ka bani haƙuri ba?" Ta faɗa tana kallon sa da narkakkun idanunta. Kallon ta ya yi zuciyarsa na bugawa sosai, ya tsaya cak da buɗe ƙofar kamar an hana shi ya sauke ajiyar zuciya yana dana sanin biyo ta ma da ya yi. "Sai da safe" abinda ya ce kenan ya buɗe motar ya fita dan ya ga so take ya tarwatsa masa tunani. Narma ta bishi da kallo ta kwanta a kujerar motar tana sauke ajiyar zuciya cikin sabon yanayin da bata san daga ina yake zuwa ba. Haka kawai taji tana son ganin sa shiyasa ta tashi zuwa gidan su, ganin na sa da tayi sai taji kamar wani sabon yanayin wanda yafi na ɗazu tsayawa a rai da shauƙi a ranta. Ta kwashe mitina goma a haka kafin ta buɗe ƙofar ta fito bayan ta zare ɗin ta shiga cikin gida. Kiran Dad take gani yana zuwa video call ta zauna a falon ta ɗauka tana kallon sa ta ce, "Hii Dad." "Hiii Baby, how was your night." "It was fine.." "Good. Yaushe zaki dawo ne?." Narma ta ɗin yi jim kafin ta ce, "maybe next week." Dad ya ce, "no, kin shirya ki taho Monday." Cikin shagwaɓa ta ce, "Dad ina son zaman Kano sosai." "Dole ki dawo akwai aiki a company da yake jiranki kin manta ne?." Shiru tayi tana tura baki gaba kafin ya ce, "kin fita ne?." "Yes Dad, naje gidan su Tiger sister shi babu lafiya na gaishe ta." Dad ya wara ido ya ce, "What? Kin je gidan su Tiger?." Narma ta ce, "Yeah, yanzu ya dawo dani." "Kina cikin hankalin ki kuwa?." Shiru tayi bata ce komai ba Dad ya fara faɗa ya ce, "meye haɗinki dashi da zaki je gidan su gaishe da sister shi? Waye na ki? He's just your driver not your friend. Wai what is your problem ne Narma? Ina hankalinki ya tafi ne?." Ganin yadda Dad ya ke faɗa sosai sai ta ce, "I'm sorry Dad, kawai naje ne saboda bata da lafiya sosai, sannan...." Dad ya katae ta ya ce, "Then what? Narma Tiger is not your mate, na faɗa miki reasons ɗina na barin ki tare dashi ba wai dan ya kai matsayin ya zauna ɗin bane. Aikin sa ya kula da lafiyarki na biya shi, ba dan ki ji gidan su im wani babu lafiya ba. Ke ko mutuwa ya yi matsayin kin wuce ki je gaisuwa kin gane?." Narma ta ce, "Dad ka san ina tausayin mara lafiya shiyasa." "Na sani, na san halin ki na tausayi mara lafiya amma ba irin famliyn Tiger ba. Wanda yake daidai dake ko ya fiki matsayi shi zaki tausayawa ba shi ƙasƙantacce ba. Aikin driving ɗin ma da ya samu daga gare ni ina da dalilina, ke kin san da ko mai gadin gidan da ki ke bai isa ya zama ba." "Is okay, I'm sorry." "Sorry for yourself. Dan haka ranar Monday ki siyo ticket ki dawo gida. Ki zo ayi maganar auren ki kawai, akwai mutane da yawa suke so su aure ki." Narma ta ce, "Okay." "Ki je ki ci abinci sannan ki kwanta." Ta sake amsawa sannan ta kashe wayar tana turo baki ta hau sama. Shirin kwnaciya tayi amma babu bacci a idanun ta hakan ya saka ta tsaya a varander tana kallon motoci zuciyarta cike da tunanin Omar. Omar a irin yanayin Narma ya ke tafiya, zuciyarsa gabaɗaya ta cushe babu abinda yake gani sai ita, kuma ta burge shi sosai zuwan ta gidan su ba ƙaramin girma ya bata a idanunsa ba, duk wanda ya san da Didi bata da lafiya har yazo ya duba ta ai abin ka girmama shi ne balle ita ga yadda matsayinta yake, ga kuma yadda ake faɗar rashin kırkinta. Kuma batu ake na Didi rabin ransa aka zo akazo dubawa, dole ya ji daɗi. Gaskiya in ya ce bai ji daɗin zuwanta gidan su ba ya yi ƙarya, har zuciyarsa ya ji daɗi haka ya samar mata da matsayin sosai a wajan sa. A karo na farko a rayuwarsa wata mace ba Didi ba ta burge shi, a karo na farko ya ji yana ganin girman wata mace ba Didi ba a zuciyarsa. Koda ya shiga gida Didi ma zancen ta take yi, tana aikin faɗar ashe tana da kirki har haka ake mata kallon mara kirki, shi dai bai ce mata komai ba dan shi kaɗai ya san abinda yake ji a jikinsa a haka ya tafi ya kwanta, sai dai babu bacci babu alamun sa saboda tunani. Nayla ma a irin yanayinsa take, gabaɗaya murmushinsa take gani a idanun ta zuciyarta na bugawa sosai, ajiyar zuciya tayi a bayyyane ta ce, "wannan wanne irin yanayi ne?." Babu mai bata amsa, ta sake yin shiru tana kallon bangon ɗakin, ta kulle ido ta buɗe tana jin sautin muryarsa da yadda ya amsa gaisuwarta. Murmushi tayi ta ce, "he's so handsome." Salma da ta shigo ta kalle ta ta ce, "waye ya kama zuciyarki haka?." Nayla ta kalle ta Salma ta ce, "tun ɗazu na shigo kina tunani kina ta murmushi alamun kin faɗa soyayya, sai naji kina yabon kyaunsa, waye shi?." Gaban Nayla ya faɗi, sai a lokacin ta farga da hakan yana nufin soyayya, kenan son Omar take yi?. Tuna hakan sai ta wara idanu waje Salma ta ce, "meye na buɗe idanu, ai duk wanda yaga yanayinki a kwanakin nan ya san akwai bayani. Kenan ɗan Kano kika samu ko? Yaya Abbas yana can yana haukan sonki wani ya ɗauki zuciyarki." Nayla ta haɗɗiye yawu ta ce, "Salma ba haka bane." "To faɗa min ya ne?." Shiru tayi bata ce komai ba, ta juya baya ta kwanta tana tunanin lallai dole ta bar Kano tun kafin dare ya yi mata. Hajiya Nayla ita soyayya ai duk inda ki ke yana tare dake. lol 😝😂 *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t *Book 1* *P 17.* Nayla haka ta tashi sukuku ta rasa abinda yake yi mata daɗi, zuciyar tayi mata nauyi sosai yanayin ta gabaɗaya ya canja. Kallo ɗaya zaka yi mata ka hango canji a yanayinta, kasancewarta ba mace bace mai nuƙu-nuƙu ba, ko ya yanayinta ya canja zaka fahimta, kana ganinta ka san ta canja. Tana zaune a falon Hajja tama juya cokalin a cikin tea ita bata sha ba kuma ita bata daina juya cokalin ba. Hajja ta kalle ta ta ce, “Hauwa’u lafiya ki ke kuwa?.” Ta kalli Hajja ta ce, “Lafiya lau nake Hajja, Kawai yau na tashi bana jin daɗi ne.” Salma da take gefe tayi dariya ta ce, “ba wani nan, Hajja soyayya ta fara shiyasa yanayinta ya koma haka.” Nayla ta ce, “Samla ki ji tsoro Allah, ni dai ban ce miki ba.” Hajja tayi dariya ta ce, “rabu da ita Hauwa, in ma da gaske soyayyar ki ka fara meye a ciki ai kin kai ki yi ne.” Nayla ta ce, “balle ma ba haka bane” ta faɗa tana ɗaukar wayarta jin tana ƙara. Abiyna shine ya bayyana akan screen ɗin, tayi murmushi ta ɗauka ta saka a kunne ta ce, “Abiy barka da safiya.” Daga can ɓangaren Abiy ya ce, “Kin tashi lafiya Mamana?.” “Lafiya lau nake Abiy, ya su Mama?.” “Lafiya lau kowa yake, sai kewar ki mu ke yi.” Tayi murmushi kafin ta yi magana ya ce, “Ya Hajja tana Lafiya?.” “Lafiya lau Abiy.” “Ki gaishe ta da kyau.” Ta amsa kafin ya ce, “yaushe zaki dawo ne? Sati ɗaya na ce ki yi amma naga kin yi shiru ban ji kina zancen dawowa gida ba.” Haka kawai gabanta ya faɗi ta ce, “Abiy na ɗauka sai nayi sati biyu.” Abiy ya ce, “A’a baza ki ba Mamana, ki zauna cikin shiri ko yaushe zan iya ce miki zan turo a ɗauke ki. Ki zo gida ki fara aiki ki in makaranta zaki koma ki makaranta in aure zaki yi ki yi aure.” Nayla da zuciyar take harbawa ta ce, “To Abiy.” “Yauwa, ki zama cikin shiri zan turo a taho min dake hutun ya isa.” Nayla ta amsa kafin Abiy ya yanke wayar. Hajja ta kalle ta ta ce, “Hauwa kina son zaman Kano baban ki yana son ki zauna a kusa dashi. Yaushe ya ce zaki tafi?.” Nayla a sanyaye ta ce, “yace na zauna a shiri ko yaushe zai turo a ɗauke ni. Wallahi Hajja bana son tafiya.” Hajja tayi murmushi ta ce, “haƙuri zaki yi ko koma, nima bana son tafiyar ki amma mahaifinki shine yake da iko akan ki sama da kowa, ki koma ɗin wani lokacin sai ki dawo.” Ajiyar zuciya tayi kawai tuna tunanin in ta tafi Kaduna ya zata yi da ganin Omar kenan?. Ɓangaren Abiy yana yanke wayar Mama da ta shigo ta zauna ta kalle shi ta ce, “Abiy kana son Nayla ta dawo sai, na ɗauka zaka barta ta sake yin kwana biyu.” Ya kalle ta ya ce, “iya hakan da na bari ma nayi ƙoƙari, ke kin san bana barin yara su je wani waje, ba wai dan ba yarda da tarbiyyar wajan da zasu je ba sai dan kawai bana so. In ba Hajja ɗin ba babu inda zan iya barin Nayla ta je yayi wannan kwanakin.” Mama ta girgiza kai ya ce, “haka ne, amma da ka bari ta sake kwana biyu Itama tana son zaman Kanon. Kuma yanzu bata fara aiki ba kuma ba karatu take ba, tana da lokacin da zata zauna wajan Hajja.” Abiy ya ce, “na yi iya yina ai, gwara ta dawo gida wani lokacin ta koma.” Mama ta ce, “haƙuri zaka sake yi, itama Naylan tafi jin daɗin zaman can akan zaman nan.” Da mamaki Abiy ya kalle ta ya ce, “Haka Naylan ta ce miki?.” Mama ta ce, “eh haka ta ce. Ta ce min ita da zaka barta ta koma Kano ma tafi son haka.” Abiy ya zuba mata ido yana kallo cikin mamaki kafin ya ce, “na tambayeki.” “Ina ji.” “Meyasa bakya son zaman ta a gidan nan ne? Akwai abinda take tsare miki?.” Mama ta wara ido cikin tsoro ta ce, “Abiy yau ni ka ke faɗawa haka? Me Nayla zata tsare min a gidan nan saboda Allah?.” Abiy ya ce, “to meyasa ko yaushe in ina zancen zata dawo ki ke so na barta ta zauna?.” Mama ta ce, “ba haka bane, kawai ina duba yadda kakarta take sonta ne, da kuma yadda ita Naylan take son kakarta. Kuma kar ka manta Hajja mahaifiyar Nayla ta rasa, Nayla take kallo a matsayin ƴarta da ta rasa shiyasa kawai.” Abiy ya ce, “nima uwar gidana na rasa, Nayla nake kallo a matsayin matata da muka zauna tare tun auren saurayi da budurwa. Nayla kaɗai Allah ya bata matsayin ƴa kafin ta bar duniya, ita nake kallo nake a madadin matata. Dan haka Zeena kar ki sake yi min magana irin wannan, a duk lokacin da nayi maganar Nayla ta gida dawo in baza ki taya ni cewa ta dawo ba ki kar ki sake saka min baki kin gane?.” Ganin ya fusata sosai sai ta ce, “Allah ya baka haƙuri, ba da wani abun nake faɗ ba.” “Na dai faɗa miki” yana gama faɗar hakan ya tashi ya bar mata falon ta bishi da kallo. Kai ta girgiza dan wallahi sai ta samu makamin da zata nisanta Nayla da mahaifinta, dole ma tayi wani abun kafin lokaci ya ƙure mata. •••••• Omar kuwa da safe wajan Didi ya shiga ya tabbatar da lafiya lau take ya hanata dafa abinci da kansa ya dafa musu noodles suka ci, bayan sun kammala ne ta kalle shi ta ce, “Yaushe zaka gama aiki da Barr Nass?.” Omar ya kalle ta cikin rashin fahimta ya ce, “Wace haka?.” Ta harare shi ta ce, “ban sani ba. Yarinyar da ka ke kaiwa unguwa mana.” “Oh! Ni in kika ce Barr Nass ɗn nan ɓatar dani ki ke yi. Ban sani ba, amma na san cikin kwanakin nan ne.” Didi ta girgiza kai ta ce, “to Allah ya taimaka, ni so nake ayi a gama lafiya kar a samu matsala da kai.” Ya yi murmushi kawai bai ce komai ba alokacin wayar sa ta ɗauki ƙara. Number ce ya kalli wayar sosai kamar ya santa number hakan ya saka ya ɗauka ya saka a kunne, “Hello Tiger.” Narma ta faɗa daga cikin wayar, lumshe ido ya yi jin muryarta mai daɗi a kunnesa ya ce, “ina ji.” Narma tayi murmushi ta ce, “Daman na san abinda zaka ce kenan. Na kira ka ne in kana da time zuwa bayan azhar zamu fita.” “Okay, Allah ya kaimu.” “Amin. A gaishe da Sister ace ina yi mata ya jiki.” “Okay” ya sake furtawa a taƙaiice, Narma tayi dariya ta kashe wayar. Kallon Didi ya yi da take kallon sa kafin ya yi magana ta ce, “Omar kafin ita ka taɓa waya da mace kuwa?.” Ya girgiza kai ya ce, “Gaskiya ban taɓa ba Didi, sai dai masu rubuta wrong number su kira ni suna neman wani. Itace mace ta farko da na taɓa waya da ita gaskiya.” Didi ta ce, “koda na ji, shiyasa ka ke mata magana a daƙile kamar kai ne oga itace driver ta ka.” “Bana son rainin wayo ne, kin fi kowa sanin haka.” “Nafi kowa sani kam Alhaji Omar.” ya yi murmushi mai sauti kafin ya tashi ya bar mata wajen. Sai da yayi sallar azahar ya shirya cikin ƙanunun kaya masu kyau wanda suke masa jikinsa sosai. Kiran Narma ne ya sake shigowa wayarsa ya kalli number dan daga ɗazu zuwa yanzu ya gane number, ya ɗauka ya saka a speaker ya ajjiye a kusa dashi bai ce komai ba. Narma ta ce, “Tiger ina jira.” “Okay” ya amsa a taƙaice kafin ta kashe wayar ma ya yanke wayar. Wajan Didi ya shiga ya samu bacci take yi ya fito ƙofar gidan yana ƙoƙarin kiran Bash a waya. Ba jimawa Bash ya zo ya ɗauki shi a machine suka wuce gidan. A ƙofar gidan ya ajjiye shi ya ce yaje kawai zai taho ya tafi shi kuma ya shiga cikin gidan. Da su Yahya ya gaisa da masu gadin gidan kamar ko yaushe, bayan sun gaisa ya hakimce a inda yake zama. Ga mamakinsa sai gata ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tana nufo shi. Kasa ɗauke ido ya yi daga kanta, tayi matuƙar kyau cikin lace ja mai adon duwatsu. Riga da siket ne a jikinta ta yafa mayafi a kafaɗa ɗaya da wayarta a hannu. Kafin ta ƙaraso ƙhamshinta ya zo inda take, ya miƙe ta kalle shi ta ce, “Zamu iya tafiya?.” Kai ya ɗaga mata ta bashi key ɗin wata motar daban ba wacce suke hawa ba ya ƙarasa ya kunna motar yana jira ta shiga. Ga mamakin sai yaga ta buɗe gaban motar ta shiga, bai yi magana ba ya ja motar suka fita ma’aikatan gidan sai kallon ikon Allah suke yi. Titi ya hau ba tare da ya san inda zasu je ba, kallon fuskar sa take yi cikin tsantsar shauƙin da bata san daga inda yake zuwa ba, wani irin bugu zuciyar ta take yi ba tare da ta san dalili ba. A haka ta kwana ta tashi cikin wannan yanayi na bugawar zuciya, tsananin kewarsa da take take ji ya saka ta ce zasu fita da wuri ba dan ta san inda zata je ba, yanzu gashi gata amma sai take jin yanayin kamar ya fi na baya shiga rai. “Ina zamu je?.” Jin muryarsa ya saka ta janye ido daga kansa ta jingina da kujera ta sauke ajiyar zuciya tare lumshe ido, a hankali ta buɗe ta ce, “nima ban sani ba.” Kallon ta ya yi da mamaki suka haɗa ido sai ta ce, “mu je gaba akwai wani restaurant sai mu shiga, yunwa nake ji.” Bai sake magana ba ya cigaba da tafiya har suka zo inda take nufi. Shiga suka yi ya ajjiue motar yana jira ta fita. Kallon sa yake ji tana ji a jikinsa shiyasa yaƙi kallonta, bai san meyasa ta canja haka ba. Narma ta ce, “mu je tare.” Kai ya girgiza bai kalle ta ba ta ce, “Don Allah.” Kallon ta yayi ya rasa meyasa ta canja gabaɗaya, ya rasa meyasa take masa irin wannan abubuwan kamar wacce take tare da wani mijinta. “Bazan je ba” ya faɗa kai tsaye. Narma taji babu daɗi a zuciyarta, ta buɗe ta fita ya bita da kallo dan iya tafiyarta ma abar ɗaukar hankali ce. Ba jimawa sai gata da wani waiter a bayan ta da ledoji, ta shiga motar sannan ta karɓa ta kalle shi ta ce, “mu je.” Fita suka yi ta sake kallon shi ta ce, “Zaka kai ni zoo park? Amma mu shiga tare kaji!” Yadda tayi maganar kaɗan ya rage bai saki motar ba, amma kasancewar sa akwai dakiya da basarwa bai nuna ba ya ce, “ni bazan shiga ba.” “Don Allah Omar!.” Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya ɗauki hanyar Zoo park. Ba ya cewa komai yana ji tana kallonsa ya rasa meyasa take son kallon sa haka kawai. Narma kuwa tunani take yi, ko shima yana jin irin abinda yake ji akan sa oho. A haka suka ƙaraso bakin zoo park, ta kalle shi ta ce, “mu je don Allah.” Yana kallon gabansa ba tare da ya kalle ta ba ya ce, “babu inda zan je.” “Don Allah” ta faɗa tana kallonsa. “Bazan je ba!.” “Ba don ni ba, don Allah, don Annabi.” Numfashi ya sauke ya kalle ta, baya son magiya ko kaɗan, magiya tana daga cikin abinda Didi take masa ta cuce shi ya yi abinda ba ya so. Ba tare da ya kalle ta ba ya buɗe motar ya fito ta biyo bayan sa tana murmushi. Shi ya biya kuɗin ticket suka shiga ciki. Tafiya suke yi tana gaba yana baya, sam yaƙi yarda su jera su tafi tare, da tazo kusa dashi zai ɗan tsaya har sai ta wuce sannan zai biyo ta. A haka ta suke ta tafiya, suna zuwa waje-waje baya cewa komai dan shi kam ya gaji. Mamaki yake yi ma da ya amince ya biyo ta, mamakin kansa yake yi kamar ba shi ba wani abun yana niyar canja shi. Da aka zo wajan tiger sai Narma ta yi murmushi ta kalle shi sai ta ga ba wajan ma yake kallo ba. Ta yi murmushi ta ce, “Tiger i like your acting” daga haka tayi gaba. Bai yi tunanin me ta ce ya wuce shima. Waya ya tsaya yana amsawa hakan ya saka ta tsaya tana kallon sa cikin annushuwa mai yawa, ko tare da Ashraf take bata jin wannan abinda take ji a kansa, shiyasa ta kasa fassara shi har yanzu. Basu jima ba suka fita suka mota tare da ɗaukar hanya. Har lokacin bai ce mata komai ba itace dai take kallon sa kamar ta cinye shi. Lokacin sallah ne yayi hakan ya saka yake gudu har suka ƙarasa gidan ya tsayar motar. “Na gode.” Kai ya ɗaga kawai bai ce komai ba. Ta yi gyaran murya ta ce, “Gobe zan koma Abuja.” Kallon ta ya yi ta ɗaga masa kai ta ce, “Daddy ya ce na koma ni kuma ban gaji da Kano ba.” Maimakon ya amsa mata abinda ta ce sai ya ce, “Allah ya kaimu.” “Amin ya rabbi. Ƙarfe sha biyu jirgina zai tashi, zaka zo ka kaini airport?.” Yadda take maganar a shaƙe ya saka shi ya kalle ta, sai ta marairaice ta ce, “please!.” “Allah ya kaimu” ya sake faɗa a taƙaice. Ta amsa da amin ta ajjiye masa abinda ta siyo ta ce, “ga naka nan, in baka so ka kaiwa Sister. Sai gobe” ta faɗa tana buɗe motar ta fita. Kafin ta shiga gidan ya fito ya ce, “Makullin.” Tsayawa tayi tare da dawowa, ta karɓi key ɗin tana kallon sa bata ce komai ba ta wuce ciki zuciyar tahar zillo take yi daga ƙirjin ta saboda bugawar da take yi. Bai bar gidan ba sai da yayi sallar la’asar sannan ya fita daga gidan ya nufi gidan Didi. Narma tana kallon sa har ya fita ta jingina da bango idanunta a lumshe ta ce, “Wayyo Allah, ne nake ji haka akan wannan mutumin? Meyesa bana so ya yi nisa dani? Meyasa nake so naji yayi magana? Ina haushinsa da nake ji a baya ya tafi?.” Babu mai bata amsa ta buɗe idanunta a bayyane ta ce, “me hakan yake nufi?.” Gate ɗin gidan take kallo kamar shi take kalla kafin ta ja baya ta ta koma ciki. Omar da ya koma ya bawa Didi kayan gabaɗaya, Didi ta karɓa tana godiya dan shi kam ta san ba ci zai yi ba. Didi tana ta yabon Narma shi dai bai ce komai ba ya yi shiru yana kallon wani waje daban yana mamakin yanayin da yake ji a kanta da abubuwan da take yi masa ita kanta Narma. Bai bari tunanin ya yi tasiri a kansa ba ya tashi ya fita daga gidan domin samu ya manta da maganar. Washe gari. _Tiger don’t forget my flight is at 12pm._ abinda ya gani kenan a wayar ɗsa, ya sake maimaitawa karantawa ya fahimci abinda take nufi. Sake karantawa ya yi a karo na uku sai ya ja tsaki ya cillar da waya ya ce, “iyayi, baza a yi magana da hausa ba sai da turanci, sai ka ce an faɗa mata na iya oho.” Wanka ya yi ya saka manyan kaya daman ya sanar da Didi zai mayar da ita bai shiga wajan ta ba kai tsaye ya tafi. Ta sama ta hango zuwan sa ta ƙare masa kallo tun kafin ya shigo tana murmushi. A haka ta sakko ta same shi, ta ƙarasa tana sallama da masu aikin a yatsine kamar bata so. Mai gadi ya saka mata jakar ta booth ta shiga motar. Kamar jira yake yi ya shiga shima suka tafi. Bai ce mata komai ba daman ta san bazai ce ba ita kuma hakan da yake yi ba ƙaramin burge ta yake yi ba. Murmushi tayi bai kalle ta ba abinda yake gabansa kawai yake yi. Wayarta ce tayi ƙara ta duba taga sunan Dad ta ɗauka ta saka a kunne kafin ya ji ta ce, “Yes Dad, gani nan zuwa.” Shiru yaji ta sake yi kafin ya ce, “shine.” Daga nan bai sake ji ta ce komai ba ta yanke wayar. Shigar su Airpot ba jimawa ya ƙarasa ɓangaren domestic kamar yadda suka ɗauko ta a wancan lokacin. Tsayar da motar ya yi ta zuba masa ido tana kallo. Kamar bai san kallonsa take yi ba ya share yana kallon glass ɗin gaban motar. Ganin kallon ya yi yawa ya juyo fuska a ɗaure ya ce, “Kina bina bashi ne? Kin ishe ni da kallo.” Murmushi ta yi bata ce komai ba kuma bata daina kallo sa ba. Ƙaramin tsaki ya yi jin hakan sai ta ce, “Faruq!.” Wani irin bugawa zuciyarsa tayi ya kalle ta da manyan idanunsa da suke da haske a wannan lokacin. Itace mutum na farko da ta taɓa kiransa da wannan suna, kowa ya san Faruk sunan sa ne amma babu wanda ya ke faɗa masa sai dai Omar ko sunayen da aka san shi da shi. Ganin yana kallon ta sai ta ce, “Zan tafi, amma na kasa gane yanayina haka kawai bana so na tafi.” Bai amsa mata ba ta sake cewa, “Amma zan dawo, naji daɗin kwanakin da nayi a Kano tare da kai. Da farko nayi maka wata fahimta daban please ka yafe ni, abinda nayi maka ya wuce.” Shi wallahi mamaki take bashi yana tunanin anya ba ƙwaya ta fara sha ba, to in ba aikin ƙwaya ba ina ita ina bashi haƙuri? Laifin me tayi masa da take bashi haƙuri? A matsayin sa nawa da zata bashi haƙuri?. Daga yin kwana takwas tare dashi har tayi masa laifin da zata bashi haƙuri?. Katse shirun ta yi ta ce, “Faruk say something..” Kallon ta ya yi ya ce, “zaki rasa jirgi.” Ta kalli agogo ta ga saura mintina ashirin jirgi ya tashi ta kalle shi ta ce, “in na rasa zan iya neman wani.” Ganin bazai magana ba sai ta buɗe motar ta fito, ga mamakinsa da kanta ta ɗauko jakarta a bayan mota ta riƙe handbag ɗinta ta dawo kusa dashi ta ce, “thank you for being always by my side, thank you for your helpful.” Ya fahimci abinda take nufi rass, ya gane abinda ta ce kawai shi sam baya so ayi masa turanci ne. Inda ace zasu cigaba da zama a Kano tare sai ya karta mata warning akan yi masa turanci, baya ra’ayi ya fi son ayi magana da yaren da ya iya. Kallon ta ya yi ya ga abaya ta saka, a karo na farko da ya ganta da abaya amma duk da haka an yi shaping abayar ta zauna daidai da jikinta ko wanne lungu na jikin ta ya shiga cikin abayar ya zauna dasss kamar a jikinta aka ɗinka. “Allah ya kiyaye hanya.” Narma ta ce, “Amin. Can you do me a favor please?.” Kallon ta ya yi da mamaki da kuma takaici, shi ba ya son turanci amma ita ya ga alama in bata yi ba bata jin daɗi gabaɗaya. Narma ta ce, “Smile please.” Ko kallon ta ma bai yi ba balle ya yi murmushi, sai ma sake haɗe gira da ya yi ya ɗauke kai. Murmushin ita take yi dan iya wannan ɗauke kan ya biya ta ta ce, “I like your acting Faruk. Anyway, na tafi ka bawa Yahya key ɗin motar sai na sake dawowa a karo na biyu.” Kai ya ɗaga mata ta fara tura jakarta gaba tana tafiya ya samu kansa da binta da kallo. Juyowa tayi ta kalle shi ganin yana kallon ta sai ta yi murmushi ta ɗaga masa hannu alamun bye, bai ko motsa ba sai ma buɗe motar da ya yi ya shiga ya tafi ita kuma ta girgiza kai tana tafiya. Wannan ɗabi’ar ta sa ta ko in kula tana matuƙar burgeta. A haka ta ƙarasa ciki ta tana jin wani abu mai kama da kewa na shiga jikinta. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 18.* Omar tuƙi yake yana tuna murmushin Narma tayi da ta juyo tana ɗaga masa hannu, bai san ya yi murmushi ba sai da ya kalli inda ta zauna har lokacin ƙhamshin turarenta bai daina tashi daga motar ba. Haka yake tafiya har ya koma gidan ya tarar Yahya yana nan ya bashi key ɗin motar ya fito zuwa gida. Da ya koma bai shiga wajan Didi ba ɗakinsa ya shiga ya kira Sen a waya domin ya sanar dashi aikin da ya saka shi ya kammala lafiya. Sen kamar gaske ya yaba sosai kafin su yi sallama ya kashe wayar yana jin wani abu mai nauyi a zuciyarsa. Gajiya yayi da zaman kasancewar rana ta yi ga yunwa da yake ji dan bai karya ba. Yana fitowa daga ɗakin Nayla tana shigowa gidan, kai tsaye idanunsa ya faɗa cikin nata da mamaki. Saurin janye ido tayi saboda abinda taji yana sukar zuciyarta, bata iya jure kallonsa ko ya ya yake. "Ina yini" ta furta cikin sanyi tana niyar gifta shi. Ga mamakin ta sai ta ji ya amsa hakan ya saka ta juyo tana kallon sa shi kuma yana kallon waya, ji ya yi ana kallon sa hakan ya saka ya kalle ta sai ya ga tayi murmushi ta ɗauke ido ta shiga wajan Didi. Didi ganin ta ya saka ta murna suka zauna suna hira kafin Nayla ta ce, "Didi gobe zan koma Kaduna in Allah ya kaimu, sallama na shigo nayi miki." Didi tayi sak cikin rashin jin daɗi ta ce, "da wuri haka?." Nayla ta ce, "wallahi, naso Abiy ya barni na ƙara kwanaki amma ya ce a'a na dawo." "Wallahi na ɗauka zaki kai gab da ramadan a garin nan tunda naga azumi ya kusa. Allah ban ji daɗin tafiyar nan da zaki yi ba Nayla." Nayla ta ce, "ni kaina ban taɓa jin bana son tafiyar ba kamar wannan lokacin, sosai nake jin bana so na bar Kano." Didi ta ce, "in kin tafi sai yaushe?." Nayla ta ce, "Wallahi ban sani ba Didi." Didi ta ce, "Allah ya kiyaye hanya ya kai ki lafiya." Ta amsa da amin Didi ta tashi ta shiga ɗaki sai gata da turaren da Omar ya siyo mata ta kawo mata ta ce, "Na rasa me zan baki Nayla, ga turare sabo ne mutuminki ne ya siyo min shi shekaran jiya." Nayla ta karɓa ta ce, "na gode sosai Didi." "Haba tsakanin mu babu godiya Nayla. Wallahi duk ji nake yi bana so ki tafi." Nayla kam murmushi take yi ko babu komai ta samu abinda ya fito daga hannun Omar. Shigowa falon ya yi fuskar nan a tamke matuƙa kamar zai yiwa Didi magana sai ya fasa ya juya zai koma. Didi ta ce, "Omar Nayla ce zata tafi gida gobe." Tsayawa ya yi ya kalli Didi bayan ya ɗora yatsunsa a goshi ya ɗan murza kaɗan ya ce, "Wace haka?." Wani irin yarr Nayla taji a jikinta, haka nan idanunta suka taru da hawaye, kenan yana nufi bai ma san sunan ta ba. Didi ta nuna Nayla ta ce, "gata a zaune." Omar ya tsaya kawai yana kallon Didi cike da takaici. To ina ruwan sa da tafiyar da zata yi banda abin Didi da take son saka shi a sabgar yarinyar, shi kuma tunda tayi masa faɗa a gabanta wallahi yake jin haushinta, ya tabbatar ba zai daina jin haushin ta ba har abada. Bai ce komai ba ya fita Didi ta kalli Nayla ganin tayi shiru ta sunkuyar da kai sai ta ce, "Yi haƙuri Nayla, Omar ne sai addu'a. Ta bakin Hajja ta ce carbin ƙwai ne, jan sa sai mai nutsuwa." Murmushin yaƙe tayi kaɗan tayi mata sallama ta fito zuwa ƙofar gidan. Yana zaune a ƙofar gidan da yaran sa suna magana, Nayla ta wuce da sauri sai da taje gate ɗin gidan Hajja sannan ta tsaya tana sake kallon sa. Wayar ta ta ɗauko ta yi zooming ɗinsa sosai tayi masa hoto ba tare da ta san dalilin aikata hakan da tayi ba. Wajan Hajja ta shiga ta nuna mata turaren da Didi ta bata kafin su shirya tafiya gidan su Salma dan tayi musu sallama. Har suka je suka dawo Nayla bata da walwala, Salma tayi-tayi ta faɗa mata abinda yake damunta tace babu komai. A haka suka dawo wajan Hajja Salma tana ta ciwon bakin taƙi faɗa mata damuwarta, Hajja tace bata son komawa Kaduna ne ta ƙyale ta kawai. Ɗakin da Nayla take kwana Salma ta shiga ta ɗauki wayar Nayla da take gefe ta ce, "bara na tura hotuna." Nayla bata ce komai ba Salma ta fara duba wayar. Ɗagowa ta yi ta kalli Nayla kafin ta ce, "Wannan ba hoton Tiger ba ne?." Jin hakan sai gaban Nayla ya faɗi, ta kalli Salma dan bata da mafita ta riga ta gani. Cikin borin kunya Nayla ta ce, "Hotonsa kuma?." Salma ta haska mata fuskar wayar ta ce, "gashi nan." Nayla ta ce, "oho ban ma san na ɗauka ba." Salma ta bita da kallon rashin yarda ta ce, "gashi har zooming ɗinsa akayi ki ce baki san kin ɗauka ba?." Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Salma ta ce, "me ki ke nufi da ɗaukar hotonsa Nayla?." Tayi shiru bata ce komai ba Salma zata sake magana ta ce, "Don Allah Salma ki yi shiru, ki bar ni naji da abinda yake damuna don Allah. Na ce miki ban sani ba ai, ga wayar nan a hannunki ki goge mana." Salma ta ce, "ai ko baki ce ba sai na goge" ta faɗa tana goge hoton ta ajjiye mata wayar ta fita bata sake magana ba. Washe gari ƙarfe sha ɗaya na safe Abiy ya iko da driver. Nayla na shan tea taga kiran drivern gidan su sai da gabanta ya faɗi, ta ɗauka nan yake sanar da ita yana waje ta kashe wayar. Kallon Hajja ta yi da salma ta ce, "Hajja ya zo zamu tafi" ta faɗa a sanyaye tana ajjiye kofin shayin hannunta. Hajja ta bita da kallo ta ce, "Zo Hauwa'u." Ba musu ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, Hajja ta riƙe hannunta tace, "faɗa min damuwarki." Sai kawai ta rungume Hajja ta ce, "bana son tafiya Hajja, bana son tafiyar nan, wani iri nake ji a zuciyata Hajja. Bana so na tafi wallahi." Hajja ita kanta zuciyarta sai tayi rauni, tana matuƙar ƙaunar Nayla saboda kasancewar ta marainiya, kuma a cikin ƴaƴanta mahaifiyar Nayla ce kawai ta rasu, tana kallon Nayla kamar ƴarta da ta rasa. Hajja cikin shigar rarrashi ta ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka, kin ga bakya koma gida masa kina yi masa kuka ba, bazai ji daɗi ba. Ki yi haƙuri ai zaki sake dawowa nan gaba in sha Allah." Nayla ta ce, "Bazai bar ni na kusa ba Hajja, Abiy baya so nayi nisa dashi" ta faɗa tana kuka sosai wanda ya bawa Salma mamaki kawai ta zuba mata ido. Hajj ta ce, "kewar mahaifiyarki yake yi shiyasa baya so ki yi nisa dashi, gani yake kamar zai rasa ki kamar yadda ya rasa ta. Ki daina ku ka kin ji?." Ta goge ido ta ce, "To hajja." Hajja ta ce, "Akwai saƙo a kitchen ki kaiwa Abban naki, sannan akwai wani ma a bokiti ki bawa Maman taki kin ji?." Nayla ta ɗaga kai tana tashi ta ɗauko ta ajjiye a kusa da ita. Ta ƙarasa jikin socket ta zare chargerta, ta shiga ɗaki ta ɗauko trolly bag ɗinta da handbag ta fito bayan ta saka mayafi. Salma tana tsaye tana kallon ta tace, "Nayla wallahi mamaki ki ke bani, kamar yau kika taɓa zuwa wajan Hajja zaki koma ki ke wannan kuka?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "Ki kaiwa Salisun abin kari ya karya kafin su wuce." Salma ta wuce zuwa kitchen ta haɗa masa ta fita ta kai masa. Nayla bata ce komai ba amma ta san ita kanta wannan kukan ba wai na rabuwa da Hajja bane kawai, tabbas akwai manufarsa a ƙasan zuciyarta, amma ta kasa gane meye shi. Sai da aka bashi lokaci ya gama, ya shigo da kayan da kansa ya gaisa da Hajja sannan ya fita. Hajja har bakin gate ta rako Nayla, Salma ta ɗaukar mata jaka suka fita ta saka a cikin booth ɗin motar, Nayla ta kalli Hajja ta ɗaga mata hannu kafin Hajja ta koma. Kallon gidan Didi tayi sai ta hango Didin na ƙarasowa inda take, murmushi Nayla tayi tana kallon ta Didi cike da tsokana ta ce, "Kukan tafiya daga Kano ki ke yi Nayla? Ko da yake ai dole, ɗan ƙauyen Kaduna ai dole ya yi kuka in zai bar birni." Dariya Salma da Nayla suka yi Didi ta ce, "na ɗauka zaki sake shigowa mu yi sallama." Nayla ta ce, "kar na tsayar dashi ne shiyasa." "Allah ya kiyaye hanya Nayla, ko Kano zata yi kewarki balle mu da muke cikin ta." Murmushi tayi ta amsa da amin tana ji ina ma tana da zarrar tambayar Omar da ta ce ina yake. Tana shirin shiga mota ta hange shi ya fito daga gidan yana kalle-kalle da alama Didi yake nema, hannu Didi ta ɗaga masa sai ya ɗaga kai alamun ya ganta ya juya bai sake kallon kowa. Nayla ita hakan ma ya yi mata, ko babu komai ta ganshi kafin tafiyarta Kaduna. Bayan motar ta buɗe ta shiga tana yi musu sallama suna yi mata addu'a ya ja motar suka bar cikin unguwar zuciyarta sam babu daɗi. ••••••••• "Dad zaman Kano ya yi min daɗi sosai, I feel like na sake komawa cikin kwanakin nan" ta faɗa tana cin Apple. Mum ta kalla kafin ta ce, "Mum wai ya ba ku je Paris ɗin ba?." Mum ta ce, "mun fasa." Sen ya kalli Narma ya ce, "Tunda kin dawo lafiya haka nake so. Tiger ya kira ni tun jiya yana shaida min kin taho babu abinda ya same ki." Narma sai ta saki murmushi jin an ambace shi ta ce, "Classy boy kenan!." Da Sauri Mum ta kalle ta jin abinda ta ce taga murmushi ma take yi. Mum ta ce, "I hope bai cutar dake ba?." "Babu abinda ya yi min, ya kula dani sosai fa Mum." Mum ta sake kallon ta tace, "amma da farko ai ya raina ki, yana ganin kanku ɗaya dan kuna haɗa numfashi dashi a mota, yanzu a ina zai ganki ma balle ku zauna mota ɗaya?." Dad ya ce, "bai isa ba wallahi, ita dashi ai sai dai taimako shima ba daga hannunta ba, sai dai daga hannun personal assistant ɗinta." Mum ta ce, "Yana da jin kai yaron kamar wani ɗan sarauta, yana talaka, illirate, useless and dirty ya dinga irin wannan abun. I so much hate him wallahi, just imagine nonsense like him sayiing he won't open the car for her. Oh God! har yanzu na kasa mantawa da abin nan. Shi ba abin alfaharinsa bane ace ya buɗe mata mota? Talaka bashi da hankali sam, talakan ma irin sa jahili da bai san komai ba." Dad ya murmusa ya ce, "saboda ƴan iska irinsa na garin Kano ya saka na haɗa ta dashi, gashi kuma ta dawo lafiya." Mum tace, "kana ganin scar mark ɗin hannunta kana cewa ta dawo lafiya? Ta dawo dai babu laifi amma ba lafiya ba." Narma gabaɗaya bata jin daɗin zagin nan da suke yi masa ko kaɗan. Dad ya kalle ta ya ce, "block his number then delete it, Matsayinsa bai kai ya samu number ki ba kin gane?." Narma gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ta ɗauki wayar ta miƙe tsaye ta ce, "Okay Dad" abinda tace kenan ta hau sama zuciyarta a cushe cikin jin abinda iyayen ta suke faɗa akansa. •••••••• Nayla basu shiga ba sai la'asar, a gajiye take tana shiga Jalil da suke kira aura ya ɗafe ta yana muryar ganinta. Dariya take yi ya riƙe jakarta ya shiga da ita. Drivern ya kai mata kayan zuwa cikin falon. Abiy ta samu a zaune yana kallonta da murmushi sai ta saki fara'a ta ƙarasa wajan sa ta zauna akan carpet ta ce, "Abiy na." Yayi murmushi ya bata hannu suka gaisa ya ce, "Ummina kin dawo?." "Na dawo Abiy. Barka da yamma." "Barka dai Mamana, ya hanya?." "Lafiya lau Abiy. Na same ku lafiya?." "Lafiya lau. Ya ki ka bar Hajja?." "Hajja tana nan lafiya, tana gaishe ku." Mama da take kallon ta ta ce, "Nayla sannu da zuwa." Kallon Mama tayi ta ce, "Mama nayi kewar ku wallahi." Mama ta ce, "ai gashi kin dawo." Baban Yayan su ne ya shigo da suke kira da Yaya ganin Nayla sai ya ce, "A'a mutanen Kano, saukar yaushe?." Ta kalle shi ta ce, "yanzu na dawo Yaya. Ina yini." "lafiya lau Nayla, ya Hajja?." "Tana gaishe ku." Nayla ta ɗauko saƙon Abiy ta bashi, bawa Mama nata saƙon. Abiy yana ta murmushi ganin gurar kano mai kyau kana gani ka san sabuwa ce ta saka yi masa. Ga Dambun nama a cikin wani ƙaramin bokiti. Yana ta murmushi yana sake girmama matsayin Hajja a wajan sa. Mama ta buɗe nata kayan ta ga girki ne su kuka da kuɓewa da daddawa. Mama ta yi godiya tana ta murmushi. "Twiny." Nayla jin abinda akace ya saka ta kalli wacce take shigowa ta ga Jidda ta ce. Nayla ta ce, "Twiny yaushe ki ka zo?." Ƙarasowa tayi ta zauna kusa da ita ta ce, "Jiya nazo. Kuma guess what? Kano zamu koma da zama." Wara idanu Nayla tayi ta ce, "da gaske?." "Wallahi da gaske, Ke dai ki je ki huta zan shigo mu sha labari." Nayla ta kalle ta tana cewa, "gaskiya bana so ki bar Kaduna, in kika koma Kano ya zanyi?." Jidda ta riƙe hannunta suka yi ciki suna hira. Murmushi Abiy ya yi yana jin daɗin zumuncin da yake tsakanin ƴaƴansa, duk da Nayla ce kaɗai ba uwa ɗaya suke da sauran ba amma in ba sani ka yi ba bazaka banbance ba uwa ɗaya ce ta haife su ba. Kowa ya san Jidda da Nayla tasu tafi zuwa ɗaya saboda sa'anni ne kuma masu suna iri ɗaya. Kwana goma sha huɗu Jidda ta bawa Nayla, tare suka tashi komai tare. Komai tare suke yi Aure ne Jidda ta riga Nayla shine abinda ya raba su. Da daddare suna zaune akan dining da Abiy da Mama da Nayla, Jidda, Jalila, Jalil autan, Yaya Jawad wanda Nayla ke kira da Ya J. Hirar Kano kawai ake yi suna dariya kafin Abiy ya kalle ta ya ce, "Kin dai je Kano hankali ya kwanta." Nayla tayi murmushi ta ce, "Gidan Hajja akwai daɗi Abiy." "Ai dole ya yi miki daɗi Nayla. Yaushe zaki fara aiki ne? Ko school ki ke so ki koma?" Sai ya kalle ta sosai ya ce, "Ko kuma aure?." Gabanta ya faɗi, a da in an yi zancen aure bata jin faɗuwar gaba, amma yanzu ta rasa dalilin faɗuwar gaban da take ji ko yaushe. Nayla ta kalli Abiy ta ce, "duk wanda Allah ya zaɓar min Abiy? Amma nafi so na fara aiki tukunna." Abiy ya ce, "Alright, zaki fara a cikin kwanakin nan in sha Allah." Nayla ta yi murmushi sannan ta kalli Yaya Jawad ta ce, "Yaya J aiki da wahala ko?." Dariya ya yi ya ce, "ɗauka ki ke sauƙi ne dashi? Hmm zaki gani yarinya." Abiy ya ce, "ƙyale shi tsorata ki yake yi." Tayi dariya tana cin abinci amma zuciyarta tana Kano musamman gidan Didi, a gidan Didin ma Omar take tunani. Abiy ya ce, "Amma maganar aure ma ya kamata ayi ta Mamana, bayan tafiyar ki ina ta samun masu neman aurenki, harda Abbas cousin ɗinki." Gabanta ya faɗi sosai ta wara ido ta ce, "Abiy Ya Abbas yazo nan?." "Yazo. Ya tabbatar min da yana neman auren ki ko ke bai sanarwar da yana sonki ba. Hakan da ya yi ya min daɗi sosai, duk da ɗan uwanki ne amma bai nemi soyayyar ki kai tsaye ba ya biyo ta wajena." Nayla tayi shiru gabanta yana faɗuwa sosai ta ji Abiy ya ce, "yana da kyau ki yi tunani, zan basu damar magana dake dan mutane uku kenan har Abbas. Kin ce a ajjiye batun Sadiq ko? To an ajjiye, bayan shi akwai uku har Abbas yayan ki. Bana son yawan tara samari kema kin sani, ya kamata ki san abinda zaki yi. Abinda ya jawo rabuwarki da Jidda kenan, dan haka kema yazo kan ki, ki nutsu ki yi addu'a." Nayla jikita yayi sanyi ta kalli Abiy ta ce, "to Abiy, ka taya ni addu'a." "Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi Mamana." Suka amsa da amin kafin ya ce, "ina jin next week sai muje umra ko kwana goma mu yi sai mu dawo." Ihu suka yi cikin murna, Abiy ya yi murmushi ya tashi ya hau sama. Yana jin daɗi in yaga iyalansa suna farin ciki, hakan yana ƙara masa jin daɗi a zuciyarsa. *Bayan Kwana biyu.* Omar ya yi ƙoƙari ya yakice tunanin Narma ya koma sabgoginsa, baya bari tunaninta ya hana shi wani abun dan tun bayan tafiyarta basu sake koda waya ba, hakan kuma ya yi masa daɗi dan baya son abinda zai hana zuciyarsa sukuni. Ɓangaren Narma duk yadda tayi ta jure share Omar ta kasa, tayi-tayi amma abin ya girmi tunaninta. Har ta kai ta kawo ta fara ware kanta a gida da wajan aiki, saboda gabaɗaya bata son magana sai aikin tunaninsa da ganin fuskar Omar a idonta. Ta rasa meyasa take jin abinda take ji a kansa, gabaɗaya ta kasa sarrafa kanta akan tunanin Omar. Yau ta kama Sunday bata je aiki ba tana kwance a ɗaki sai ga Mum ta shigo, ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce, "Narma tashi zaune." Ba musu ta tashi ta kalle ta ta ce, "me yake damunki? Tunda kika dawo daga Kano baki da walwala, me ya faru?." Narma ta ce, "babu komai Mum, kawai bana jin daɗi ne." "Kin je asibiti ne?." Ta girgiza kai alamun a'a, Mum ta ce, "meyasa baki je ba?." "Zan je Mum." Mum ta ce, "good. Yanzu ki zo ga Ashraf nan a falo yana jiranki" Mum tana faɗa mata haka ta fita. Haushi taji ya tokare mata zuciya jin wai Ashraf ne yazo. Yanzu ta rasa meyasa yake ɓata mata rai, haushi yake bata yanzu, kwata-kwata bata son magana dashi. Ɗankwali kawai ta ɗaura ta fito falon cikin shigar ta kullum ta same shi a zaune, yana ganin fitowar ta ya miƙe tsaye har ta ƙaraso ya ce, "Why Narma? Bakya picking calls ɗina, bakya responding messages ɗina. Me yake faruwa?." Narma ta ɗan yi ajiyar zuciya ta ce, "babu komai." "akwai komai, ki faɗa min abinda yake faruwa. Gabaɗaya kin canja, ko a Kano ba haka ki ke ba." "Na faɗa maka babu komai, kawai bana jin daɗi ne, yanzu Mum tace naje naga Dr." Ashraf ya bita da kallo ganin yadda take yi masa in yazo gidan yanzu ta canja, yadda take welcoming ɗinsa gabaɗaya ta canja. Ya ce, "Amma kin canja Narma, da ba haka ki ke ba yi min gabaɗaya. Yadda ki ke welcoming ɗina in na zo gidan nan yanzu kin daina. Nayi miki laifi ne?." Narma ta ce, "baka yi mun laifin komai ba, kawai bana son yawan magana ne." Ashraf ya nuna kansa ya ce, "Har ni bakya son magana dani?." "Ba haka nake nufi ba." Ya ce, "Okay, zan barki ki huta zuwa kwana biyu zan dawo mu yi magana." Narma ta ce, "thank you" ta faɗa tana komawa ɗaki ya bita da kallon mamaki. Tana shiga ta cire ɗankwalin kanta cillar ta ce, "Aikin banza kawai, Bana son magana dashi gabaɗaya." Ajiyar zuciya take yi kafin ta ɗauki wayar ta tana kallon number Omar. Kira tayi ba tare da tunanin komai ba tana jira a amsa. A lokacin Omar yana zaune a ɗakinsa ya ga waya na shigowa, bai manta number ba yana gani ya gane ta kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka ya saka a kunne. Narma ta yi ajiyar zuciya jin ya ɗauka sannan ta ce, "Hello Faruk." Omar ya yi ɗiff jin muryarta har cikin jininsa, wani irin yanayi yake ji yana ratsa gangar jikinsa. Kafin ya yi magana ta sake cewa, "Ka manta dani ko? Tunda na tafi ko waya baka yi min ba." Nan ma Omar ya yi shiru bai amsa ba, ta kwantar da murya ta ce, "Faruk na san kana ji na, kawai baka son magana da ni ne." Omar ya rasa abinda zai ce mata, bai saba waya da mace ba balle ya san abinda zai ce mata sai kawai ya ce, "kin je lafiya?." Da shagwaɓe ta ce, "yau kwana na nawa da dawowa sai yanzu zaka tambaya?." "Uhum!" Shine abinda ya ce kawai bai yi magana ba. Narma ta ce, "ina nan na kasa mantawa da tunaninka, bana iya komai a ko yaushe sai tunaninka, na kasa gane me yake damuna." Omar ya yi shiru yana jinta yana mamakin kenan itama tana tunaninsa, to akan me?. Narma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ka manta dani ko? Ni ban manta da kai ba." Nan ma bai yi magana ba kuma bai bata wata alama da zata fahimci ya ji ba. Narma ta ce, "baza ka yi min magana ba?." "Ina jinki" ya faɗa dan shi bai san me zai ce mata ba wallahi. Narma ta ce, "zan zo Kano ina so na haɗu da kai." "To" shine abinda ya furta kawai sai yaji ta yanke wayar, ya bi wayar da kallo yana mamakin son ganin sa da take yi da kuma dalilin kiransa. Narma kuwa ta kashe wayar ne saboda jin an buɗe ƙofa an shigo Mum ta bita da kallo ta ce, "wai me yake damunki? Me Ashraf ya yi miki ne?." Narma zata yi magana Mum ta ce, "ki zo." Ko ɗankwalin bata ɗaura ba ta biyo Mum ta samu Dad falon sama yana kallo tahowar su. Zama tayi Dad ya kalle ta ya ce, "me yake damunki Narma me Ashraf ya yi miki?." Narma ta ce, "ni bai yi min komai ba." "Amma meyasa ki ke treating reletionship ɗinku like that? Kin san yana sonki ai kema kina sonsa. Shine future husband ɗinki, meyasa ki ke masa haka ne?." Narma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Dad!." Dad ya kalle ta ya ce, "ina jinki." Narma ta ce, "Ni yanzu gabaɗaya bana son Ashraf, bana tunanin zan iya aurensa! In fact akwai wanda nake so zan aura ba shi ba" ta faɗa kai tsaye tana kallon Dad da yake kallon ta. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 19.* Dad ya bita da kallon mamaki ya kalli Mum da take kallon sa itama kafin ta sake kallon Narma ya ce, "Bakya sonsa yanzu?." Ta ɗaga kai alamun eh kamar zata yi kuka. Dad ya ce, "meyasa? Ya yi miki laifi ne?." Narma ta ce, "bai yi min komai ba Dad, kawai zuciyata bata sonsa yanzu." Mum ta ce, "to wa ki ke so?." Narma ta kalle ta ta ce, "Wani ne Mum, zan faɗa miki in muka gama daidaita kan mu." Dad ya ce, "Waye shi?." "Dad zan faɗa maka, but not now" she said it from the bottom of her heart, and her voice trembled with emotion. Dad ya ce, "to shi Ashraf ya zaki yi dashi? Kin san yana sonki ko?." Narma ta ce, "to Dad saboda yana sona sai na cutar da kaina?." "Amma bazai ji daɗi ba dai ko?." "Amma Dad rayuwata ce." "Is okay. Shi wanda ki ke so ɗin a Kano ku ka haɗu?" Dad ya tambaya da kulawa yana kallon ta. Narma tayi murmushi ta ce, "Yes Dad." Ya kalli Mum yana murmushi kafin ya sake kallon ta ya ce, "Alright, ki je ki huta in ya so daga zamu sake yin magana." Narma in a trembling voice ta ce, "Dad zaka amince min na aure shi?." Dad ya yi murmushi ba tare da damuwa ba ya ce, "why not my baby? Tunda kina sonsa ai shikenan. Ki je ki huta." Da sauri Narma ta miƙe ta shiga ciki cikin farin ciki. Dad yana dariya ya kalli Mum ya ce, "ashe wannan ne dalilin da ya saka Narma bata son dawowa daga Kano, she's in love." Mum ta yi dariya ta ce, "nayi mamaki fa, ka duba yadda take da Ashraf amma tunda ta ce bata so bata son ɗin ne. Ka san ita free and open ce, bata ɓoye abinda yake damunta ko kaɗan. Gaskiya zan so naga waye wannan da ya kama zuciyar Narma very cheap haka." Dad ya ce, "Oh love! Kin manta a ranar da na fara ganinki na fara sonki? Uhum kin manta?" Ya faɗa yana kallon Mum da murmushi. Mum tayi dariya ta ce, "I will never forget that time, shi ake kira da love at first sight." Dad ya yi murmushi ya ce, "indai Narma zata yi farin ciki hakan ya yi min dadi." Hira suka cigaba da yi cikin farin ciki da son samawar da ƴarsu abinda take so.   ••••••••               Omar bayan ta kashe wayar gabaɗaya kashe masa jiki tayi, ya rasa abinda abinda yake yi masa daɗi. Tana faɗa masa tayi kewarsa, to wai me hakan yake nufi ne? Sannan bata manta dashi ba? Shi ya ɗauka a kwanakin da ya wuce ta manta da shi kamar yadda yake ƙoƙarin mantawa da ita. Ajiyar zuciya ya yi a bayyane ya ce, "ko meyasa ta ce tayi kewa ta oho." Wajan Didi ya shiga ya samu tana amsa waya, daga yadda take mayar da amsa ya tabbatar da Yayan mahaifiyar su ne. Kamar bazai zauna ba sai kuma ya zauna, ta gama wayar ta kalle shi ta ce, "Baba Adamu ne, yana magana ne akan kayan ɗakin bikina." Ya kalle ta a kaikaice ya ce, "Haka aka ce masa bani da kuɗin da zan miki kayan ɗaki?. Didi ya kamata ki ja musu kunne fa su daina shiga lamarina da naki, Ina ruwan su ne wai?." Didi ta ce, "da ruwan su mana Omar, iyayen mu ne." "Iyayen ki dai, ni kam babu ni. Kuma babu abinda za a karɓa daga wajan su komai ni zan yi in sha Allah. In kuma ki ka ce sai kin karɓa wallahi na bar garin nan baza ki sake ganina ba, sai ki zauna dasu ki cigaba da rayuwa tunda su ki ka zaɓa. Tayi murmushi tana kallon sa a ranta tana ayyana bai san hidimar aure bane, in ba dan haka ba bazai furta komai shi siya yi ba, shida ba sana'a yake yi ba an ina zai samu kuɗi?. Ita har mamaki take yi da bata ji yana zancen bashi da kuɗi dan ta san dai ba abinda yake yi balle tace kuɗi na shigo masa. Sannan tana mamaki in ya siyo mata kaya ya kawo mata, kayan sakawa ko na abinci haka yake siyowa ya kawo mata. In ta tambaya ya ce ta san ba satar mutane yake yi ba. Tana ji yana ta yi mata mita tayi masa shiru bata ce komai ba dan bazata tanka masa ba indai akan dangin su ne baya gane gaskiya, ko me zata ce bazai amince ba gwara ma tayi shiru. Haka ya dinga faɗa lokacin da aka kai kuɗin aurenta gidan Kawu kamar shine babba itace ƙarama, wai meyasa ba a kawo masa ba ai ya isa ya aurar da ita. Ita dai bata tanka ba tayi masa banza dan tana tankawa zai hargitse ya tashi garin Kano. Ajiyar zuciya tayi tana ayyana rigimar Omar yawa ce da ita. "Kai ma sha Allah, Allah ya kaimu garin madina. Allah ka sa ina da rabon zuwa wannan gari, Allah ya sa ko a radio na ci wata gasar da za a kaini Madina. Omar kalli yarinyar nan ka gane ta?" Ta faɗa tana nuna amsa wayarta. Bai yi musu ba ya kalla ya ga yarinyar sanye da baƙar abaya tayi rolling kanta fuskarta ɗauke da murmushi. Ɗauke kai ya yi ya ce, "a'a." Ta harare shi ta ce, "Nayla ce fa, jikar Hajja." Tsaki ya yi ya ce, "itama dai ban san ta ba." "Yarinyar da ka dinga bawa tsoro a gidan nan? Kai Omar har yaushe ta bar Kano da zaka ce ka manta ta?. Yarinyar da ka ceta lokaci......" katse ta ya yi ta hanyar faɗin, "to wacece ɗina da zan kasa mantawa da ita? Mun haɗa dangi ko kuma akwai wani abu tsakanina da ita?." Didi ta yi dariya ta ce, "babu komai. Amma na san baka manta ta ba, kawai halin wulaƙancin naka ne ya motsa." Ɗauke kai ya yi yana mai jin haushin Nayla a ransa, ita kanta Didi haushinta yake ji, haka kawai ta dinga nuna masa yarinyar kuma ta ce lallai sai ya game ta kamar wata ƙanwarsa. Fushi ya yi ya tashi ya bar mata falon bata ma wawaye shi ba ta cigaba da harkokinta dan in ta saka lamarin sa a zuciyarta ciwo zata yi.         ••••••• Nayla kuwa kamar yadda Abiy ya faɗa kaf ɗinsu suka tafi Umra, suna garin Madina suna ibada kafin su tafi makka. Nayla gabaɗaya bata da karsashi zaman, saboda zuwa lokacin ta tabbatar da son Omar take yi, so ba wai na wasa ba na gaske wanda ake kira so. In ta tuna waye Omar da halayensa, ta tuna waye Abiy sai gabanta ya faɗi tsoro ya mamaye mata zuciya ta kasa sukuni gabaɗaya. Ta saka tunanin Omar a ranta ta hakan ya saka ta rame, bata ma zaman hotel ko yaushe tana masallaci tana kaiwa Allah kukan ta amma abin babu sauƙi sai sake gaba da yake yi. Duk ƴan uwanta sun fuskanci canji a lamarinta, in suka tambaya sai ta ce babu komai. A wannan yanayin suka shiga makka suka yi umra Abiy bai ji Nayla tana zancen zata je Makka mall ba, dan ya san indai suka zo sai Nayla taje Makka mall ta yi siyayya ta dawo. Suna zaune a falon hotel ɗin su gabaɗayan su Abiy ya kalle ta ya ce, "Mamana zo nan." Ba musu ta ƙarasa inda yake ta zauna, ya kalle ta ya ce, "ban ji kina zancen zaki je Makka mall ba, lafiya ki ke?." Nayla ta ce, "bana son zuwa ne, duk abinda zan siya zan siya a nan ba sai naje can ba." Yadda take magana a sanyaye ya saka ya kalle ta da kulawa ya ce, "Mamana me yake damunki? Na lura da rashin walwalarki, kina ware kanki ke kaɗai bakya son zama cikin mu, sannan baki da ƙwarin jiki, sannan kuma kin rame. Me yake damunki?. Duk lokacin da muka zo ƙasar nan har neman ki mu ke yi muna rasawa saboda yawo, amma gabaɗaya yanzu ki canja. Me ya faru?." Zuciyar Nayla harbawa take yi sosai, idonta ya kawo ruwa kafin ta farga har hawayen ya sakko. Abiy ya damu ganin tana kuka ya ce, "Sanar dani damuwarki Mamana." Nayla ta goge ido ta ce, "Babu abinda yake damuna Abiy." "Yaushe ki ka fara yi min ƙarya Mamana?." Ta sunkuyar da kai ya kalli ƴan uwanta ya ce, "in kuma kina so su bamu waje sannan ki faɗa min sai su bamu waje." Nayla ta kalli Abiy ta ce, "A'a Abiy, babu abinda yake damuna." Abiy ya murmusa ya ce, "Mamana kina da damuwa, damuwar ma ba ƴar kaɗan ba. Ki faɗa min abinda yake ranki." Nayla ta sunkuyar da kai ta rasa abinda zata ce, saboda ko giyar wake ta sha bazata faɗawa Abiy abinda yake damunta ba, da ta faɗa masa gwara abinda take ji ya kashe ta. Dabara ce tazo mata sai ta ce, "Ummana, mafarkinta nake yi a kwanakin nan Abiy" ta faɗa tana fashewa da kuka. Duk sai kowa jikinsa ya yi sanyi ba kamar Abiy da take kusa dashi, fuskarta ya riƙe ganin yadda take kuka sai baice komai ba ya kwantar da kanta a kafaɗarsa ya bata dama tayi kukan. Ita kuwa Nayla kukan rashin mafita da tausayin kanta kawai take yi, sai da tayi mai isar ya sannan ta tsagaita kukan ya ɗago ta daga jikinsa ya ce, "Kina yi mata addu'a?." Nayla ta ɗaga kai alamun eh ya ce, "To ki yi haƙuri, addu'a itace kawai soyayyar da zaki nuna mata kin ji?." Ta ɗaga kai alamun to ya share mata hawaye ya ce, "Yanzu ki shirya ki tafi kasuwar ki yiwa Hajja da Salma siyayya, ko baza ki basu tsaraba ba?." Sai tayi murmushi ta ce, "zan basu." Ya yi murmushi ya ce, "to maza riƙe twnity ɗinki ku tafi kasuwar." Ta ɗaga kai Abiy ya ce, "ki saki ranki bana son wannan ɗabi'ar da kika ɗauko kin ji." Tayi murmushi ta ce, "To Abiy." Ta kalli Jidda da take kallon ta ta ce, "Twiny mu je?." Jidda ta ce, "Zo mu je ɗaki ɗauko kuɗi sai mu je." Tare suka fita zuwa ɗakin su dan nan wajan Abiy ne, ɗakin suka shiga basu jima ba suka fita. Sai da suka je reception na hotel ɗin sannan Jidda ta riƙe hannu Nayla ta ce, "Twiny." Nayla ta kalle ta dan ta san daman sai ta tambaye ta, in akwai wanda ya san halinta a gidan su to Jidda ce. Jidda ta ce, "Twiny kin san dai ban yarda da abinda ki ka cewa Abiy ba ko? Ai ba yau kika sana mafarkin Umma ba, Meyasa baki taɓa shiga damuwa ba sai a wannan lokacin?." Nayla ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Jidda ta ce, "Twiny ki faɗa min damuwar ki don Allah." Nayla ta fashe da kuka ta rungume Jidda tana kuka sosai. Jidda ta riƙe ta tana shafa bayanta a hankali dan ta san ƴar uwarta ta tana da babbar damuwa. Sai da ta bari ta gama kukan sannan ta ɗago tagoge idanun ta ta ce, "mu je mall mu dawo." A haka suka tafi dukka su babu mai walwala a tare dashi, sun jima sosai duk da basu yi wata siyayya ba, sai dan kawai kasuwar da nisa  inda suke. Ɗakin su ita da Jidda ne kawai sai matar Yaya Anty Halisa dan Jidda babu mijinta suka zo. Da suka dawo Anty Halisa bata nan hakan ya saka Jidda cire mayafi ta zauna kusa da Nayla. Kallon ta tayi sosai ta ce, "Faɗa min damuwarki." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "Twiny wani ne." Jidda ta ce, "me wanin ya yi miki?." Tayi shiru bata ce komai ba. Jidda ta ce, "kin faɗa soyayya ko?." Nayla ta kalle ta sai hawaye ya sakko mata, Jidda ta riƙe hannunta ta ce, "tun a Kaduna naga yanayinki ya yi min kama da wacce ta fara soyayya, kuma na tabbatar a Kano ki ka yi gamo da ƙaddararki. Waye shi? Ya san kina sonsa?." Kai ta girgiza tana kuka ta ce, "ban san sonsa nake yi ba Twiny, da na san zan fara sonsa da ban je Kano ba, da na yi zamana tare da Mama da Abiy a gida, wallahi da bazan je ba." Jidda ta ce, "ƙaddarar kenan ai. Kuma ita soyayya ai ba kai make sakawa kanka ita ba, Allah ne, kuma yin kanta take yi a zuciyar ɗan adam." Nayla kuka take yi sosai tana cewa, "ban san ya zanyi ba, kullum cikin kewar ganinsa nake, kullum cikin son jin muryarsa nake amma ko number wayar sa bani da ita Twiny. Meyasa soyayya zata yi min haka? Meyasa zan fara son wanda bani da tabbaci akan zai so ni?. Twiny ko kallo ban ishe shi ba, hasalima maganar minti ɗaya bata taɓa haɗa mu dashi." Jidda cikin sanyi ta ce, "Waye shi?." Ɗagowa tayi daga jikin Jidda ta ce, "Ki yi haƙuri Twinny, zan faɗa miki amma ba yanzu ba." Jidda ta ce, "kina addu'a?." "Ina yi sosai." "Ki sake dagewa kina faɗawa Allah damuwarki, in ba alkhairi bane Allah ya cire shi daga rayuwarki, in kuma alkhairi ne Allah ya daidai ku." Da jajayen idanun ta ce, "gwara na yi addu'ar Allah ya cire min shi ɗin, dan ko yana sona bana tunanin Abiy zai amince." "Me zai hana ya amince?." Nayla ta girgiza kai tana aiyana dan bata san waye bane shiyasa take faɗar haka. Jidda ta ce, "yanzu dai tashi mu je mu shiga mataf ki sake faɗawa Allah damuwarki, zama bai kama mu ba ai Twiny." Nayla ta miƙe tsaye Jidda ma ta miƙe sai Nayla ta ce, "yau ban ji kina waya da Baby ba." Jidda tayi murmushi ta ce, "yana can Kano yana neman gida, ya dage sai unguwa ɗaya yake so kuma gidan sai wanda ya yi masa wai ai kuɗinsa ne, siya zai yi ba haya ba." Nayla tayi dariya ta shiga tayi alwala Jidda ma tayi suka fita zuwa masallaci.         A ɓangaren Abiy bayan fitar su Nayla kowa ya fita ya zama daga shi sai Mama ya yi shiru bai ce komai ba. Mama cikin ƙarfin hali ta ce, "ka yarda da abinda Nayla ta ce maka?." Abiy ya kalle ta ya ce, "koda abinda ta faɗa yana damunta to tabbas akwai wani abun da yake damunta bayan wannan." Mama tayi murmushi ta ce, "ka fahimta kenan, nima na ga haka a tare da ita sosai." "Amma me kike gani yana damunta?." "To in na faɗa sai ka ce ba haka ba, gwara nayi shiru kawai." Abiy ya ce, "kina nufin Hajja?." Kafin Mama tayi magana ya ce, "kinga mu bar zancen nan, domin bazan amince son zaman Kano ne ya mayar da Mamana haka ba. Akwai dai abinda yake damunta amma ba wannan ba." Mama ta yi shiru kawai bata ce komai ba amma ya zama dole ya nemo damuwar Nayla ko dan ta san meye in zata amfane ta tayi amfani da ita. •••••••• Narma gabaɗaya ta susuce soyayya tayi mata mugun kamun da bata yi tunani ba, ta koma wani iri ko yaushe cikin tunani take da faɗuwar gaba. Yanzu gashi in ta kira Omar ɗin ma baya ɗauka, gabaɗaya sai ta sake shiga damuwa ta yi wani iri kamar ba ita ba. Iyayenta duk sun lura da yanayin ta ranar Mum tayi nufin sake tambayarta. Ɗakin ta ta shiga ta same ta tayi tagumi ta zauna a gefen ta ta ce, "Narma." Narma ta kalli Mum ta ce, "faɗa min abinda yake damun ki kika zama haka." Narma ta ce, "Mum nima ban sani ba, amma Ina sonsa sosai Mum, Ina ji in ban aure shi ba zan iya mutuwa." Mum ta riƙe fuskar ta tace, "Waye shi? A Ina yake?." Narma ta ce, "A Kano yake, kuma yanzu na samu labarin baya jin daɗi Ina so naje na duba shi Mum." Mum ta bita da kallo mamaki ta ce, "anya shima yana sonki kuwa?." "Yana sona sosai Mum, yana sona. Tunda Dad baya nan gobe da safe zan je Kano zuwa jibi sai na dawo kin ji Mum?." Mum ta bita da kallo cikin tausayin yanayin da take ciki ta ce, "is okay, sai Najwa ta rakaki." "No Mum bana so kowa ya ganshi mamaki nake so na baku, ni kaɗai zan je." Mum ta ce, "shikenan dai. Amma jibi zaki dawo da safe, kuma ban amince da wannan Tiger ɗin matsayin driver ba. Ki kira drivern Kano su zo su ɗauke ki ki gama abinda zaki yi ki dawo kin gane?." Jin abinda Mum ta ce sai gabanta ya faɗi, amma da yake an barta zuwa Kano bata damu ba ta amince da hakan. "Kar ki damu Daughter, zaki auri wanda ki ke so kin ji?." Kai ta ɗaga cikin farin ciki Mum tayi hugging ɗinta tana rarrashi kafin ta fita barta. Narma tana fita ta tashi ta kalli kanta a madubi tana so ta gane itace ko kuwa ba ita bace, domin ta san ta canja, halayya ta da kamanninta duk sun canja saboda Omar. Mamaki take yi wai daman zata iya fara soyayya da wanda bai ma san tana yi ba? Soyayyar ma kuma da mutum irin Omar. Itace fa Narma da maza suke so ta yi musu replying message balle kuma ta yi magana dasu, amma ga Omar ya haukata ta lokaci ɗaya ta fita daga hankalin ta. Ajiyar zuciya ta yi ta lumshe ido tayi tana sake buɗe ido a bayyane ta ce, "Faruk gani nan zuwa."         Washe gari. Jirgin ƙarfe takwas ta hau dan haka da wuri ta shiga kano, tana fitowa taga Yahya wanda ya san da zuwan ta tun a daren jiyaa. Gida aka kai ta daƙyar ta iya haƙura aka yi sallar azahar ta hau mota ta nufi gidan Didi kai tsaye. Sai da taje ƙofar gidan sannan ta kira Omar a waya. A lokacin yana kwance a ɗaki abubuwa sun yi masa yawa, ya kasa gane abinda ya damunsa gabaɗaya wani irin yanayi ya damu zuciyar shi da gangar jikinsa. Kiran ta ya shigo wayarsa ya kalli wayar, bai yi saving ba amma ya gama haddace ƙarshen number ta ko dan kiransa da take yawan yi a kwanakin nan ne bai sani ba. Kai ya dafe bai ɗauka ba yana kallo har ta katse, wani kiran ya sake shigowa kamar bazai ɗauka ba sai ya ɗauka. Narma da ta fara kuka yana ɗauka ta ce, "Faruk Ina ƙofar gidan ku." Da hanzari ya miƙe zaune ya ce, " ki ka ce?." "Uhum, Ina ƙofar gidan ku." "Me kika zo yi gidan mu?." "Ina kiran ka baka ɗauka shiyasa nazo." Kasa magana ya yi ya tashi ya fita ya kuwa hango motar ta a ajjiye a gefe, ganin sa sai ta buɗe motar ta fito. Kallon ta ya yi itama shi take kallo ta ɗauki wayar hannunta sake kiransa ya ɗauka ta ce, "na ƙaraso ko zaka zo mota mu yi magana?." Omar yace, "meyasa kika zo?." Narma tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Da yake yana kallon ta tana kallonsa sai ya ce, "ki koma gida zan zo." "Na san ba zuwa zaka yi ba" ta faɗa tana yanke wayar ta nufo gidan, yana kallon ta tana tahowa zuciyar sa cike da tsoro da kuma tsantsar mamakin zuwan ta gare shi. Sai da ta shigo gidan sannan ta zuba masa ido tana kallon sa ko kofta ido bata yi. Numfashi ta sauke ta kawar da kai gefe tana jin haushin zuciyarta da ta saka ta fara son wannan mutum mai shegen shariya da nuna ko in kula kamar sa. Narma ta kalli gidan ta ce, "Sister fa?." "Bata nan" ya bata amsa babu ɓata lokaci dan ya ƙagu ya ji abinda tazo dashi. Tayi shiru bata ce komai ba, hakan ya saka ya ce, "Ina jinki, me ya kawo ki Kano har kika zo nan?. Kar ki ɓata min lokaci ki faɗi abinda yake ranki." "Babu abinda ya kawo ni Kano, na zo Kano saboda kai kuma saboda kai zan koma." Narma ta gyara tsayuwa tana kallonsa ta ce, "ban san me zan ce maka ba, ban iya ɓoye-ɓoye ba haka zalika ban san wani abu tsoro ba indai a kan abinda yake zuciyata ne. Abinda na sani kawai Ina sonka Faruk! Ina sonka so na Aure!." *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 20.* Wani irin dumm Omar yaji a zuciyarsa, ya zubawa fuskarta ido yana kallo ba cikin mamakin da ya gama ɗaure masa jiki. Ya kasa motsi sai kallon idanunta da yake yi kamar yadda take kallon sa. Narma tayi murmushi tare da hawaye ta ce, "kayi mamaki ko?." Sai ta girgiza kai ta ce, "nima kwana nake Ina mamaki, kwana nake Ina tambayar kaina Narma ta ya hakan ya faru. Kullum tambayar kaina nake yi Narma meyasa ki ka shiga wannan rayuwar, meyasa ki ka fara son wanda bai damu dake ba. Da wannan tunani nake kwana nake tashi tunda na bar garin nan har yau da nake tsaye a gabanka." Narma ta ce, "Ina sonka, Ina sonka!. Ban san me zan ce maka ka yarda ba amma abinda nake ji a raina kawai Ina so nayi rayuwa da kai a matsayin mijina, ban damu da abinda zai biyo baya ba, ina so na rayuwa da kai daga nan har a tashi duniya. Ban damu da abinda kowa zai ce ba, kawai Ina so na dinga duba gefena na ganka a tare dani ko yaushe, ban damu da kowa ba, ban damu da komai ba. Da zuciyata kawai na damu, abinda yake cikinta kuma soyayyar ka ce, Ina son ka!" Ta faɗa tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta. Kai ta girgiza tace, "ba wasa nake yi ba wallahi, zan iya aurenka na zauna da kai a ko wanne yanayi. Please Faruk! ka amince dani as your life partner, wallahi ina sonka!" Abinda take faɗa kenan kamar zata zubar da hawaye. Bai yi zato ba, bai yi tsammani ba, ya tafi duniyar tunani kawai yaji ta kwanta a jikinsa ta rungume shi sosai tana kuka. "Innalillahi!" Ya furta a bayyana yana riƙe hannayenta ya janye ta daga jikinsa ya ce, "Narma!."  Kallon sa tayi karo na farko da ya kira sunan ta, bata ɗauka ya san sunanta ma tunda bata taɓa ji ya faɗa ba sai yanzu. Hasalima bashi da sunan da yake faɗa mata tunda ba magana yake yi mata ba. Ganin irin kallon da yake mata ya yi kama da na fushi da fusata sai jikinta ya yi sanyi. A kausahe Omar ya ce, "Ki bar wannan abin da kike yi, Ko da wasa kar ki sake kuskuren cewa zaki riƙe ni, bana son wannna shirmen kin fahimta!?" Ya faɗa a fusace yana nuna ta da yatsa. Kai ta girgiza ta ce, "I'm sorry!." Omar ya ce, "Sannan ki koma gida, ki bar cikin gidan nan yanzu. Abinda ki ke so baza ki same shi daga gare ni ba." Narma ta narke fuska ta ce, "Kana nufin baza ka iya sona ba?." Ya ɗaga mata kai alamun eh kana ya ce, "in ma wasan kwaikwayo kika shirya ki dakatar dashi bazai yi tasiri a kaina ba. Kar ki sake zuwa cikin gidan nan ba tare da kin sanar dani ba, bana so na sake ganinki, ki fita daga gidan nan kafin na nuna miki asalin waye ni." Kallon sa kawai Narma take yi jin yana ambatar wasan kwaikwayo, yanzu kenan soyayyar da take yi amsa ce ya ɗauka wasan kwaikwayo ko bayyana masa ɗin da tayi ne ya zama wasan kwaikwayo?. Narma murya na cracking ta ce, "Wallahi Ina sonka, wallahi i'm ready to marry you. Ban damu da abinda zai biyo baya ba indai zan samu cikar burina na amince zan zauna da kai a ko wannan yanayi." Kuka take yi mara sauti duk sai ta sake dagula masa lissafi, shi bai san da wacce makama zai ɗauki maganarta ba dan shi gani yake kamar akwai abinda ta shirya shiyasa ta zo masa da wannan maganar. In ba haka ba kai tsaye tazo ta furta tana son shi kamar ba mace ba? Macen ma irin ta mai aji da kuɗi da mulki na siyasa? Ta ya zai amince da wannan tatsuniyar mai kama da wasan yara?. Kuma shi wata mace bata taɓa kallon sa ta furta masa wannan kalma ba, bai taɓa tsayawa da wata mace na adadin mintinan da yake tsaye da Narma ba. Shifa Didi kawai ya sani, itace komai na sa, Bai taɓa alaƙantuwa da ko wacce mace ba in ba ita ba. Shiyasa yake jin kansa uncomfortable saboda ita ce mace ta biyu a rayuwarsa da ya samu kusanci da ita, da ita ya taɓa haɗa jiki, da ita ya taɓa tsayawa suna doguwar magana, da ita ya fara zama waje ɗaya shida mace, itace ta fara furta masa kalmar so a rayuwarsa. Jin kansa yake yi yayi nauyi, nauyi yake a zuciyarsa dan yanayin ya zama baƙo a gare shi. Da wannan tunanin ya ce, "kina ji.....!" Baya tayi tana kuka kamar wacce ta rasa hankalinta ta ce, "ba wasa nake maka ba, ba ƙarya nake maka ba, ba yaudararka nake ba, ba plan na shirya maka ba. Wallahi Ina sonka da gaske ba da wasa nake ba. Dama ana cire zuciya da na cire zuciyata na nuna maka abinda nake ji a kan ka. From the moment i saw you in our house fell in love with you, saboda zuciyata bugawa ta dinga yi da na ganka, na ɗauka kwarjini kayi min a lokacin, amma a yanzu na fahimci sonka nake yi. I'm not joking about my feeling, it's not a game or drama or whatever you think about it. I truly love you" ta haɗe hannayenta waje ɗaya ta ce, "Please believe me" ta faɗa tana zubewa a wajan tana kuka sosai. Kama ƙugu Omar ya yi yana kallon ta, wai shi Omar wata mace take ɗuke a gabansa take kuka da sunan tana sonsa. Ya kasa banbance yanayin da yake ciki, tausayinta yake ji ko haushi take bashi shi kam bai sani ba. Bugawar zuciyarsa yake ji na tausayinta ne ko na meye dai shima ba sani ba. Ba ya so Didi ta dawo ta tarar da ita a wannan yanayi, hakan ya ya buɗe baki zai yi magana amma ya kasa. Shi bai san ya ake rarrashin mace ba har ta daina kuka, bai taɓa ganin kukan mace a gaban idanun kamar haka ba sai a wannan lokacin, bai san ta ya zai fara ba kwata-kwata. Ya sake kallon ta ya ce, "ki bar kuka ki tashi daga wajan nan." Bata daina kukan ba amma ta miƙe tsaye ya ce, "na ce ki bar yi min kuka bana so!" Ya faɗa cikin tsawa kaɗan wacce ta sakata haɗɗiye kukan nata. Ya kalle ta ya ce, "Yanzu ki je gida zan zo zamu yi magana anjima." A sanyaye ta ce, "ka tabbatar zaka zo?." Ya ɗaga mata kai alamun eh. Ta kalle shi ta ce, "in ma baka zo ba zan dawo, Ina so naji amsar ka akan abinda na faɗa maka. Bazan koma Abuja ba sai na ji amsar ka." Bai ce komai ba sai cize bakinsa da ya yi, ya kalli fuskarta ya ga ta koma ja sannan da gaske ta ɗan rame kaɗan. Wuce shi tazo yi ta sake kallon shi ya ce, "Faruk ka kawar da duk tunanin da ka ke yi a kaina, da gaske nake Ina sonka." Kulle ido ya yi ya buɗe sai yaga ta bar wajan da alama ta fita. Ƙarasowa ya yi ya ganta ta fita a guje ta ƙarasa mota ta shiga ta ja motar da ƙarfin gaske. "Wai ni za a yaudara" ya faɗa a bayyane bayan motar ta fice daga layin. Sai kuma kalamanta suka dinga dawo masa cikin kansa ya kulle ido ya ce, "ni dai ba sonta nake yi ba, kawai na kasa mantawa da tunanin ta ne. Wannan film ɗin da tazo ta shirya kuma duk zai ƙare." "Kai kuma kai da wa ka ke magana kai kaɗai?"Didi ta faɗa tana shigowa gidan. Da sauri ya buɗe ido ya kalle ta ya daidaita nutsuwarsa kana ya ce, "kin dawo?." "Eh na dawo" ta bashi amsa tana wucewa bata ce masa komai ba. Daɗi yaji da ta bata tarar da Narma ba da bai san me zai ce mata ba. Bai shiga inda take ba ya koma ɗaki yana tunani kala-kala akan abubuwan da suka faru wanda yake kallon sa kamar a mafarki, tsaki ya yi kawai cikin tunanin da ya rasa wanne zai kama ya yi. Didi bata sake ganin sa ba sai bayan sallar magriba ya shigo cikin gidan. Duk da yadda yaso ɓoye abinda yake ransa sai da Didi ta fahimta. Ta kalle shi sosai ta ce, "lafiya ka ke kuwa?." Ya girgiza kai ya ce, "lafiya lau." Bata ce komai ba ya zauna yana kallon ta yana ji kamar ya faɗa mata yaji me zata ce, amma kuma yana ji kamar ba sai ya faɗa mata ba yaudara ce kawai ake so a shirya masa. Didi ganin yana kallon ta kuma bai yi magana ba sai ta ce, "ya dai?." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Didi a misali namiji kamar ni wacce irin mace ce zata iya cewa tana sonsa?." Didi da mamaki ta ce, "kamar ya kenan?." "Ina nufin ko wacce mace ma zata iya son namiji kamar ni?." Didi ta ce, "ita soyayya ai baka sanin lokacin da ka ke fara ta Omar. A yadda ka ke a haka in ƙaddarar soyayya ta gifta sai ka fara son ƴar gwamnan garin, kuma so bana wasa ba na gasken gaske, kuma dai kaga a zahiri ka san tafi ƙarfinka amma soyayya bata duba wannan Omar. Ko kuma ita ƴar gwamna ta fara sonka so mai tsananin gaske, so na gaskiya ba wai na wasa ba, saboda ba ita ta yi sonka a zuciyarta ba Allah ne da kuma taimakon zuciya. To soyayyar ce yanzu duk ta gaskiya ta gushe sai dai sama-sama, kafin a samu soyayyar gaskiya a yanzu an samu ta ƙarya sau dubu, kuma da yawa yaran manyan mutane yanzu ƙwarya tabi ƙwarya ake yi, me ka kai me za a kawo maka. A dah dai ɗan mai kuɗi ya auri ƴar talaka, ƴar mai kuɗi ta auri talaka kuma an zauna lafiya. Amma yanzu wannan zamani ya gushe Omar." Yayi shiru jin kalaman Didi sai ya kalle ta ya ce, "misali ace ƴar mai kuɗin unguwar nan ta ce tana sona zaki amince da gaske takr?." Didi ta yi dariya ganin da gaske yake maganar sai bata saka wasa a ciki ba ta ce, "zan amince mana Omar, ai ba ita ta halicci kanta ba, kuma ba ita ta saka son naka a zuciyarta ba, babu yadda Allah baya tsarawa ɗan adam ƙaddara da rabonsa. Allah ne  ya kaddara hakan kuma babu wanda ya isa ya canja faruwar sa. Kuma da yawa in yaran masu kuɗi mata suka fara soyayya da wanda bai kai matsayin su ba yawanci soyayyar gaskiya ce, saboda mata rauni gare su, soyayya tana saurin kama zuciyarsu." Shiru ya yi kawai bai ce komai ba yana tunanin kenan dai da gaske Narma zata iya fara sonsa ko dai hasashen Didi ne kawai?. Didi ta ce, "kai dai ka bar so kawai Omar, nima ba wai sanin soyayyar na yi ba, amma so babban abu ne. Kai ta addu'a Allah kar ya ɗora maka son wacce tafi ƙarfinka, daga lokacin da ka fara son wacca tafi ƙarfinka daga lokacin zaka san meye azabar so. So ai mugun abu ne wani lokacin." "Ni ai Didi na faɗa miki bana tunanin akwai wacce tafi ƙarfina a duniya, in har akwai ɗin sai dai in bata sona." Didi tayi dariya tana jinjina maganar sa ta ce, "ko tana son naka iyaye da ƴan uwa sai sun dakusar da soyayyar." Ya yi shiru bai ce komai ba yana ɗan girgiza kai ba dan ya yarda ba. Disi ta ce, "wai me ya kawo wannan maganar ma yau?." "Zan faɗa miki" ya fɗa  yana tashi ya fita ya barta da tunani dalilin yin wannan maganar, ita da ta san baya magana akan soyayya, ko akan mace baya magana balle irin wannan ta soyayya. Ko tsokanarsa ta yi wani lokacin ko tanka mata baya yi, amma tunda ta ji ya yi wannan maganar tabbas akwai dalili.         Yana fita yaga message ɗin Narma ta rubuta, _Daman na san baza ka zo ba, in na rasa raina kaine sila Faruk! Da Ina da iko da na cire son da make maka tuni na ajjiye shia a gefe. Amma babu komai na gode._ Sai yaji wani irin abu ya tsirga masa mai kama da tausayi sosai, ya sauke ajiyar zuciya yana jin zuciyarsa na bugawa sosai cikin rashin sanin dalili. Shi dai bazai je inda Narma take ba gaskiya, in ya je dagula masa lissafi zata yi ya rasa abinda zai ce mata gwara ya ƙyale ta in ta gaji ta koma gida. "Kenan in da gaske so na take su masu kuɗi babu ruwan su da cewa in mace ta fara cewa tana son namiji zubar da aji ne? Tunda gashi tun daga Abuja ta ɗauko ƙafa tazo Kano saboda ta furta min tana sona. In kuma yaudarata take yi ta taro match wallahi, za tayi dana sanin aikata abinda ta aikata. Amma taya zan gane soyayyar gaskiya ce ko ta ƙarya?." Shafa kansa yake yi ya kasa gane inda zai kama dan ya kamo bakin zaren. "To wai ni me nake ji a kanta?" Ya faɗa yana shafa ƙirjinsa daidai inda zuciyar take, yana jin wani irin abu yana fizgarsa daga ta ciki. Da wannan tunanin ya kwanta yana ta juyi ya rasa abinda yake damun sa.         Narma yanayin ta babu daɗi, raba dare tayi tana kuka zuciyarta ma bata shawara kala-kala, har shawarar kashe kanta tayi ta fasa, tayi shawarar fita taje gidan su Omar ta kasa. Ta jima tana kuka daƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta.          Ya jima yana bacci har goma na safe sannan ya tashi, bai fito ba sai da ya yi wanka jikinsa duk a sanyaye yake ya rasa abinda ya kamata ace ya yi. Lokacin da ya shiga wajan Didi ta idar da sallar walha ta kalle shi ta ce, "yau ka sha bacci, da fari na ɗauka ka fita ashe kana nan." Ya girgiza kai ya ce, "na jima ban yi bacci ba ne jiya, daƙyar na iya tashi sallar asuba." Didi ta ce, "ga idanunka nan har yanzu da sauran bacci. Ga abinci can in zaka ci." Ya girgiza kai ya ce, "bana son cin komai gaskiya." Didi ta ce, "na lura gabaɗaya a sanyaye ka ke, me ya faru ka koma haka?." Ya bita da kallo yana tunani. Bashi da aboki a duniya sai ita, babu mai bashi shawara sai ita, babu wanda yake iya faɗawa damuwarsa sai ita, babu da wanda ya saba sai ita ɗin dai. Itace kawai mafitarsa, dole ya faɗa mata abinda yake faruwa ko zai samu wata makama a wajan ta. Niyar zama yake yi aka shigo falon sai ya fasa zama yana kallon wacce ta shigo. Didi ta miƙe tsaye ganin wacce ta shigo cike da mamaki,  shi kansa sai da gabansa ya faɗi balle Narma da take kallon sa. Didi ta ce, "Barr Nass." Wajan Didi ta ƙarasa ta ce, "Sister laifi ne dan mace ta fara soyayya? Laifi ne dan ma fara son wani a lokacin da ban shirya ha? Laifi ne dan na fara son wani ba tare da na san hakan ba?." Didi da mamaki take jin abinda take cewa ta girgiza mata kai ta ce, "A'a." Ta nuna mata Omar ta ce, "Amma Faruk ya kasa gane da gaske ina sonsa, wallahi sister daga Abuja na taho nan akwai dan na furta masa kalmar Ina sonsa. Ina sonsa da gaske, ki faɗa masa ba yaudararsa nake yi ba. In ya cigaba da tafiyar dani a haka a yadda nake jin sonsa zan iya mutuwa!" Ta ƙarasa faɗa a sanyaye tana kwantar da kanta a kafaɗar Didi. Didi suman tsaye tayi tana jin sautin kukan Narma a kunnenta, tunani take yi wai ko dai mafarki take yi? Sai kuma taga ai ko a mafarki abinda take ji bai kamata ace yazo gare ta ba. Omar ɗin ta ake magana akai, kuma ƴar Senator ɗan takarar gwanma ce take wannan maganar. Tabbas wannan maganar indai ba mafarki bane to tabbas wasan kwaikwayo ne. Bata iya bata amsa ba ta ji Narma ta ɗago daga jikin ta ta ce, "Sister bazan yi ƙarya dan na yaudare shi ba, ki kalli idona wallahi da gaske Ina son sa. Tun farkon ganina dashi na fara jin wani abun a kansa, da ya zo ɗauka na a Airport a nan na sake jin abinda naji. Da ya taimake ni a lokacin da aka ƙwace min waya a nan na tabbatar da ya shiga zuciyata. Ba wasa nake yi ba, ba yaudara na shirya ba, gaskiya nake faɗa Sister." Shi dai Omar yana tsaye kaiwa bai fita ba kuma bak ce komai ba yana kallon ikon Allah. Didi sai a lokacin ta samu damar kallon Narma ta ce, "Wai Omar ɗina ki ke so?." Ta ɗaga mata kai alamun eh, Didi ta zuba mata ido kafin ta kalli Omar da yake kallon su sannan ta ce, "Narma kalaman naki ne kamar a mafarki, Omar ɗin ki ke so?" Ta faɗa tana sake nuna mata shi da yake tsaye. Narma tayi murmushi ta lura sun kasa gane abinda yake ji a kansa, ta ce. "Shi nake so, saboda son da nake masa aka fasa maganar aurena da Ashraf ɗan gov katsina state, na faɗawa iyayena Ina da wanda nake so su bani lokaci, yanzu sun bani lokaci suma jira na kai musu shi matsayin wanda nake so. Wallahi a yadda nake ji bazan iya auren wani in ba shi ba, ki taimaka min, kece kawai hope ɗina Sister. Nazo har nan jiya na bayyana masa amma ya ce min A'a!." "Tirƙashi!" Didi ta furta tana sake kallon Narma dan ta tabbatar a hankalin ta take, sannan ta kalli Omar da yake jin su bai ce komai ba. Motsawa yayi zai fita Didi ta ce, "Ina zaka je?." "In na tsaya me zan yi Didi? Me zan ce in na tsaya? Gwara na tafi" ya faɗa yana kallon ta. Narma ta kalle shi ta ce, "kana ganin kamar wasa nake yi ko?" Sai tayi murmushi ta ce, "dole zaka ji haka saboda a saba namiji ne yake bayyana cewa yana son mace kafin ita tace, ni kuma sai gashi nice nazo ina yin abinda mazan ma baza su yi ba. Ni ban iya ɓoye abinda yake raina ba, in dai akwai zan faɗa ne kawai na huta. Kuma ban ɗauki dan nazo har gidan ku na ce ina sonka da wani abun ba, gaskiya na faɗa ba ƙarya ba. Amma wallahi ko dm namiji ya yi min a social media sai na shekara ban buɗe ba, namiji sai ya shekara biyu yana so nace masa hii amma ban ce ba. Duk wannan ajin da nake dashi soyayyarka ta kawar da ita Faruk!. Kuma har yanzu kace kana tantama? Didi kina ji fa" ta faɗa tana kallon Didi da take ganin abun kamar almara. Didi ta ce, "Ko da gaske ki ke, ko da wasa kike Narma kin fi ƙarfinki ce kina son Omar, ke ba irin matan da ya kamata ace suna son Omar bace. Kuma amsar da ya baki ta a'a itace daidai Narma, dan ke ba daidai dashi bace, ki tuna matsayin ki dana mahaifinki." Narma ta ce, "ni dai in har yana sona duk wannan ba damuwa ta bace, iyayena suna son duk abinda nake so, ko yanzu na kai musu shi nace shi nake so zasu yi maraba da zuwan sa. Kuma na sanar dasu ma fara sonsa kuma sun yi min fatan alkhairi." Didi ta ce, "Omar ɗin ki ka ce kin fara so?." Narma tayi murmushi ta ce, "Didi kema ɗauka ki ke ƙarya nake ko?." "A'a Narma ban ce ba, amma maganar ce dole ta saka mana shakku a zuciyar mu." Narma ta ce, "me zan yi da zai goge shakkun? Na shiga social media nayi video ce Ina sonsa? Ko gidan tv zan je ma bada labarin yadda ma fara son sa?. Ko kuma na sanar da iyayena su zo su nemana min auren sa?. Wanne zan yi da zai tabbatar da ba ƙarya nake ba?." Didi ganin Narma ta gigice sai ta kwantar da murya ta ce, "Ki kwantar da hankalin ki Narma, yanayin matsayin da kike dashi ne dole ya saka mu tantama a kan ki." "Shiyasa nace me zan yi ya goge?." Didi ta ce, "babu ko ɗaya da kika lissafa. Na amince da gaske kina son Omar so na gaskiya kuma so na aure." Narma a sanyaye ta ce, "Amma shi ya ce ƙarya nake yi." Didi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Narma ban san me zance miki ba a yanzu, amma ki koma gida zan yi ƙoƙari na shawo kansa ya faɗa min abinda yake ji ransa a kanki, in yana ji zai karɓi soyayyar ki shikenan, in baya ra'ayin hakan sai dai ki yi haƙuri." Narma ta goge idon tana murmushi ta ce, "Hakan ma na gode. Amma Didi in kika samu labarin wani abu ya faru dani wallahi Faruk ne sila, soyayyarsa itace silar da zata jefa ni ko wanne irin yanayi. Yin acting ɗin ƙarya akan soyayya ba ajina bane, bazan taɓa iya furta ina son mutum ba indai ba da gaske nake ba Didi. Abu ɗaya kawai na sani, ina sonsa koda shi baya sona, zan rayu dashi koda baya sona." Kallon Omar Narma tayi ta matso kusa dashi ta ce, "zan koma gida, zan je na samu likitoci naji zasu canja min zuciya. Indai zasu iya zan amince a cire tawa a saka min wata indai zan rabu da abinda nake ji. In kuma baza su iya ba ina tabbatar maka wani abun zai same ni akan abinda nake ji a kanka. Na tafi, amma ka sani zan dawo, zan dawo dan jin amsarka. Bazan iya rayuwa da wani in ba kai ba, bazan taɓa iya rabuwa da kai ba" ta faɗa tana ficewa a guje kamar walƙiya. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 21.* Didi tana kallon ta har ta fice ta dafe ƙirji ta kalli Omar da yake tsaye har lokacin ta ce, "wai da gaske ba mafarki nake yi ba?." Ƙoƙarin fita ta ga yana yi ta ce, "Ina zaka je?" ya juyo yana kallon ta ta ce, "Dawo, ai fita bata kama ka ba Omar. Daman shine silar magangangun da kayi min jiya? Daman akan Narma ne Omar?." Yana daga wajan da yake tsaye ya ce, "na rasa abinda zan ce ne Didi, ban san me zan yi ba, ban kuma san a wanne matsayi zan ajjiye hakan ba." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Omar ni na amince da gaske Narma tana sonka." Ya kalle ya ce, "ta ya kika tabbatar a lokaci ɗaya haka?." "Kalamanta, yanayinta, matsayinta. Omar a matsayin da Narma take dashi a Nigeria baka kai matsayin wanda zata yiwa wasa da hankali ba, ko ta yaudare shi ba. Soyayya bata duba cancantar mutum ko kuɗi ko mulki, dan zuciyarta faɗa a soyayyarka abu ne mai sauƙi tunda ba itace tayi kanta ba. Mace kamar ta baro Abuja kawai saboda ta zo ta ce maka tana sonka daga ji ka san wannan abin ya kai zuciya." Kallon Didi yake yi har ta gama magana kana ya ce, "in kuma film aka shirya fa? Ni Ina ganin kamar da wata manufa hakan ya faru. Ta ya za a ce lokaci ɗaya ta baro garin su tazo ta ce tana sona? Har yaushe ta sanni? Yaushe muka yi sabon da zata fara sona? Yaushe muka yi mu'amala tare da hakan zai faru?." Didi ta murmusa ta kalle shi ta ce, "Wacce manufa kenan? Me ka ke dashi da Narma zata yaudare ka Omar? kai waye a Nigeria da za a yi amfani da ita wajan yaudararka?. Da gaske na san ana amfani da mace a yaudari mutum amma sai mutum ya kai inda ya kai ake aika masa haka. Allah na tuba kai wanne matakin rayuwa ka taka da za a yi amfani da ita a cuce ka? Ai in ma cutar taka za a yi sai dai ayi amfani da mata irin na lunguna ba dai ita ba." Ganin ya yi shiru bai ce komai ba ta kuma cewa, "Zancen yaushe ta fara sonka duk daga baya ne, zuciya tana fara son wanda mutum bai taɓa gani ba, ana fara soyayya a iya jin murya kawai. Mace na fara son namiji in taji muryarsa a tv ko radio, haka namiji yana fara son mace in yaji muryar ta koda a hanya ne." Shi Omar mamaki abin yake bashi shiyasa ya kasa magana, ya sake kallon ta ya ce, "wai da gaske yana faruwa a gaske ko sai a film? Ni ban amince da soyayyar ba, ban amince akwai wani abu soyayya a duniya ba. Ina jinta tamkar tatsuniya, ina jin labarin soyayya kamar iska da zata zo ta wuce ba tare da ka ganta ba, ina jin labarinta tamkar tafiyar ruwa. Ban amince akwai soyayya ba Didi, ni ban yarda akwai ta ba balle har na yarda da son da wata take min." Didi tayi murmushi tana girgiza kai ta ce, "Zaka amince da akwai soyayya Omar, zaka tabbatar da soyayya gaskiya ce a lokacin da ka fara son wacce ka ke so, daga wannan lokacin zaka tabbatar da soyayya ba film bace ko wucewar iska. Yanzu babu abinda ka sani sai ni, soyayyar Yaya da ɗan uwanta kaɗai ka sani, baka san ko wanne irin so ba sai ita, baka san son ko wacce mace ba sai ni, baka jin ko wacce mace a zuciyarka sai ni ɗin. A yanzu baza ka gane ba, sai zuciyarka ta fara son wata mace sannan zaka tabbatar. Yanzu meye mafita akan Narma?." "Mafita kamar ya?." "Ya zaka yi da ita?. Misali ace da gaske tana son naka, ya zaka yi mata?." "Haƙuri zata yi Didi, me zan yi mata?." Didi ta ce, "Haka nake so naji ka ce, domin Narma ba kalar wacce zaka yi gangancin fara so bace, in ka bari zuciyarka ta yaudare ka ka fara sonta wallahi kaine a ruwa domin kaine zaka sha wahala. Mallakar Narma abu ne mai wahala a wajan namiji irinka, in kuma kaga hakan ya faru to sai dai tsananin rabo." Omar ya murmusa kaɗan ya ce, "ban san meyasa kike faɗar wannan maganar ba, ni ban cancanci a soni ko a aure ni bane?." Didi ta girgiza kai ta ce, "ka cancanta mana, ka cancanta a wajan wanda ka cancani kaso a soka. A wajan Narma, ko a wajan masu matsayin na ƙasa da ita wallahi baka cancanta ba Omar. Ba maganar hasken fata ake yi ba, ba maganar kyau ko sajen fuska da ƙirar jiki ake ba Omar. Magana ake ta karatu da kuma kuɗi, magana ake ta asali mai kyau, in ma asali na kuɗi ko na sarauta. Omar duka wannan baka dashi, kaga kenan a wajan ta baka cancanta ba, ba ita kaɗai ba har masu biye mata." Ransa yaji ya ɗan sosu akan maganar Didi, ya zuba mata ido yana kallon ta kafin ya ce, "Shi mutumin da bashi da karatu ko bashi da kuɗi ba mutum ba ne?." Didi ta ce, "Mutum ne mana Omar, amma a gidan Senator Kano central ba mutum bane wallahi." Kallon Didi yake yi kawai bai ce komai ba, kamar zai yi magana sai ya fasa bai ce komai ba ya kawar da kai gefe. Didi ta tausasa ta ce, "Ka bata haƙuri Omar, in mahaifinta yaji tana sonka ma wani babban tashin hankalin ne, kar kaga kuna waya dashi ko kana zuwa inda yake yana yi maka dariya. Wallahi dariyar nan ta manufa ce Omar, ba tsakani da Allah yake sonka ba amfani yake yi da kai. Da zarar ya ji ƴarsa na sonka duk wannan zai gushe, saboda ba matsayin ku ɗaya ba." A fusace Omar ya ce, "Saboda ita muslma ce ni kafiri shiyasa ki ke kiran ba matsayin mu ɗaya ba?." Mamaki ya bawa Didi ganin yaji haushin abinda tace, har ya kasa ɓoyewa ya nuna mata hakan. Didi ta ce, "a wajan su gwara kasancewar ka kafiri akan kaje a yadda ka ke kace kana sonta Omar." Didi ta ta sake tausasa murya ta ce, "Ni don Allah ka rufa min asiri kar ka bari wannan kalaman nata ya yi tasiri a kanka, yadda na sanka baka bawa kowa ƙofa a rayuwarka itama kar ka bata, ka ɗauka komai ba komai bane ka manta da ita, ka toshe duk hanyar da zata bi wajan neman ka." Omar ya zuba mata idanunsa yana zagawa dasu a fuskarta ya ce, "Yanzu kika gama faɗa min baka sanin lokacin da soyayya take shiga zuciyarka, nima in soyayyarta zata shiga zuciyata zan hana ne?." Gaban Didi ya faɗi jin kalamansa, tsoron ta ɗaya kar taje ya fara son Narma ta shiga uku. Didi ta ce, "Addu'a zaka yi Allah kar ya baka ikon fara sonta." Baice komai ba ya fita yana mamakin wannan kalamai na Didi masu kama da rainin hankali.  Didi da kallo ta bishi a bayyane ta ce, "Wai Narma ke son Omar...Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya Allah ka kiyaye min ƙanina daga faɗawa tarkon soyayyarta, gwara ce itace take sonsa da ce shine yake sonta, gangancin fara son Narma kamar ganganci da rayuwarsa ne. Ya Allah kar ka bashi ikon fara son wannan yarinya" ta faɗa kamar zata yi kuka. ••••••        Narma da zazzaɓi mai zafi ta sauka a Abuja, ta kira Najwa ta ce tazo ta ɗauke ta, ba jimawa sai gata ganin yanayin da take ciki sai ya bata tsoro ganin da gaske bata da lafiya kawai ta wuce asibiti. Sai bayan sun je asibitin an bata taimakon gaggawa sannan ta kira Mum ta sanar da ita. Awa biyu tayi a asibitin suka koma gida an samu  zazzaɓin ya sauka. Bacci tayi sosai bayan sun koma dan har da maganin bacci aka bata, ta jima sosai tana bacci har dare sannan ta farka, da yake ta san ba sallah zata yi bata yi ƙoƙarin yin sallah ba tana kwance tana tuna kalaman Omar masu kama da sukar mashi a zuciyarta. Tashi tayi ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta, wai itace take son namiji kamar Omar, ɗan daba wanda bashi da komai bai san komai ba sai riƙe wuƙa. Ita Barr Narma, manager director ta kamfanin mahaifinta, ita Narma da take juya kuɗin mahaifinta da suka haura billions wai itace take son wani da bashi da komai har yake mata wulaƙanci. Turarukan da suka kan madubin ta watsar, ta jawo madubin ya faɗi kasa ya tartwase a wajan, ta faɗa kan gado tana fashewa da kuka. A guje Mum, Dad, Najwa da Nabil suka shigo  daƙin. Dawowar Dad kenan sun rako shi sama wajan ta suka ji sautin fashe-fashe daga ɗakin. Ganin yanayin da take ciki ya saka su ƙarasowa da gudu kowa yana tambayarta abinda yake faruwa. Bata iya magana ba sai kuka da take yi a jikin mahaifinta mai tsuma zuciya. Duk sun yi shiru suna surarem kukan da take yi, sai da tayi mai yawa sannan ta tsagaita sai ajiyar zuciya da take yi. Najwa ta kawo mata ruwa Dad ya bata tasha yana kallon ta a nutse. Sai da yaga ta nutsu sosai sannan ya ce, "Me yake damun ki Daughter? Me ya faru kika shiga wannan yanayin?." Narma murya a shaƙe ta ce, "I'm in love Dad." Dad ya kallo Mum ya sake kallon Narma ya ce, "kina nufin ki ce duk wannan damuwar da kike ciki saboda soyayya ne? You're in love, that's why you looks like this?." Bata yi magana ba sai lumshe ido ta tayi a jikin Dad bata ce komai ba. Dad ya yi shiru bai ce komai ba Mum ta kalle ta tace, "Narma taso mu je ki ci abinci." Bata samu damar magana ba ta miƙar da ita tsaye suka fito falo ta zaunar da ita. Tea ta zuba mata ta miƙa mata ta ce,"Oya take it." Narma a sanyaye ta ce, "I want to brush my teeth first." "Okay, Najwa kai ta bathroom." Najwa ta riƙeta ta miƙe tsaye, Dad ya ce, "take her to my bathroom, sai an gyara ɗakin ta, ki buɗe drawer akwai sabon brush." Da to ta amsa suka wuce zuwa ɗakin Dad. Basu jima ba suka dawo, Narma ta zauna tana shan tea ɗin kaɗan-kaɗanan tana tunanin yadda suka yi da Omar. Sai da shanye tea ɗin tass suna ta yi mata sannu. Sai da ta gama ta nutsu sannan Dad ya ce, "akwai abinda ki ke so?." Ta girgiza kai alamun babu ya ce, "okay, tell me your problems. Who is the guy you are in love with?." Ta yi shiru bata amsa ba, Mum ta ce, "Narma Dr ya tabbatar mana da kina cikin damuwa shine ya haifar miki da zazzaɓi ɗazu, yanayin muka same ki a ɗaki ya tabbatar min da maganar Dr gaskiya ne. Waye wanda ki ke so haka?." Shiru tayi bata ce komai ba, Nabil yayanta ya ce, "Narma feel free ki faɗi abinda yake ranki, kar ki damu zamu yi supporting ɗinki hudrend percent." Narma tayi ajiyar zuciya ta ce, "Dad ku taya ni da addu'a saboda kamar bazai karɓi ni ba." Mum ta ce, "what! Kina nufin daman ke kike sonsa ba shi yake sonki ba?." Narma ta ɗaga kai alamun eh. Mum cikin wani yanayi ta ce, "damn it! Ta ya hakan ya faru Narma?." "I don't know" ta faɗa kamar zatayi kuka. Dad cikin rarrashi ya ce, "ɗan waye? Ɗan sarkin Dubai ne?" Ya faɗa yana kallon ta, dan a ganinsa duk wanda Narma zata so har haka kuma bai san tana yi ba, bai ma karɓeta ba, a ganinsa sai dai ɗan sarkin Dubai. In ba haka ba to waye zata iya wannan son da ya saka mata zazzaɓim damuwa? A ganinsa ko ɗan president albarka. Narma ta katse shi ta ce, "Not at all. Dad...!" Ta faɗa tana jan sunan tare da kallon sa. Ta ce, "promise me you will allow me to marry him at any cost." Dad ya riƙe hannunta ya ce, "I promise you zaki aure shi indai yana sonki, abinda bazan amince ba shine in baya sonki bazan yarda ki aura shi ba." Ta yi murmushi ta ce, "Dad I'm Barr Nass don't forget, i will attract his attention." Dad ya yi murmushi ya ce, "anything for you my daughter. Kema ki yi min alƙawarin damuwarsa baza ta sake baki damuwa har ki yi ciwo ba." Narma ta girgiza kai ta ce, "in sha Allah." Rarrashinta suka dinga yi suna bata baki har ta ware ana hira da dariya da ita. Bayan Kwana biyu. Narma ta tabbatarwa da kanta Omar shine farin cikin ta dole ta san ya zatayi kafin ta rasa ranta, duk da tayi ƙoƙarin ajjiye damuwar ta kamar yadda ta yiwa mahaifinta alƙawari amma soyayyar tana nan a tare da ita. Ta daure bata nemi Omar a kwanakin ba tana so taga zai kira ta ko bazai kira ta ba. Abin mamakin bai kira ba kuma bai yi mata koda text ba, sai ta tabbatar da gaske bai ɗauki maganar ta da mahimmaci ba tunda gashi ya share ta bai kira ya ji ya take ba. Shi kuwa Omar shi kansa ya san ya damu da lamarin Narma, daurewa kawai yake yi yana nuna bai damu ba amma a zuciyarsa ya damu da ita sosai ma kuwa. Bai san dalilin da ya saka ya damu ɗin ba, shi ba sanin so ya yi ba balle ya ce sonta yake yi. Bai taɓa ƙoƙarin kiranta ba, dan shi kansa ya san bazai iya neman ta ba ko meye zai faru, dalilin da ya saka ya jure rashin jinta ya share ya bar tunaninta. Kamar ko yaushe yana zaune cikin ƴan uwan sa ƴan daba ana meeting akan ƴan wata unguwa suna faɗa kuma ana cewa ƴan unguwar su ne. Yana zaune yaji kiran waya amma bai duba ba har suka gama meeting ɗin da bai ce komai ba, hankalin sa baya tare dashi shiyasa bai ce komai ba. Ana gamawa ya tashi ya nufi gida. Yana shiga ɗaki wayarsa sake yin ƙara ya ɗauko tare da zubawa number ido, har lokacin bai yi saving ba dan baya so ba, kawai baya so ya bada wata ƙofa da wani abun zai shiga ransa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka tayi shiru bata ce komai ba shima bai ce komai ba. Nunfashinta kawai yake ji yana sauka a hankali, saukar numfashinta sai ya saukar masa da kasala sosai ya yi shiru bai ce komai ba. "Da ban kira ka baza ka kira ni ba ko? Ka san damuwar da na shiga a kanka kuwa? Ka san har asibiti na kwanta saboda kai?. Saboda Ina sonka ka ke min haka ko Faruk? Shikenan na gode" ta faɗa a sanyaye. Lumshe ido ya yi zuciyarsa na bugawa sosai, in ya ce bai ji daɗin maganarta ba ƙarya yake yi, in ya ce bai ji maganar ta na shiga zuciyarsa ba ƙarya yake yi, in ya ce bai ji rauni ya mamaye zuciyarsa ba ƙarya yake yi. Buɗe ido ya yi har lokacin bata sake magana ba yana dai jin nunfashin ta kamar ɗazu. Shiru ya rasta tsakani har mintina biyu sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "shikenan ka gaishe da Didi." "Ya hanya?" Ya tsinci muryarsa ya faɗa ba tare da ya shirya ba. Narma jin maganar sai tayi ajiyar zuciya mai nauyi ta ce, "hanya ba lafiya ba, ni kaina ba lafiya nake ba Faruk." "Ayya Allah ya bada lafiya" ya faɗa a hankali. Narma ta ce, "Amin,Thank you." Nan ma ya sake yin shiru bai ce komai ba, Narma ta ce, "Okay byee" ta faɗa tana yanke wayar da sauri. Shiru yayi yana kallon wayar yana mamakin kansa da ya tambaye ta hanya, to Ina ruwansa?. Numfashi ya sauke, ya saka a ransa tausayinta yake ji shiyasa haka da wannan tunanin ya share wancan. •••••••         Mutanen Saudia sun dawo Kaduna, Nayla har lokacin bata dawo daidai ba domin abinda take ji yafi ƙarfin zuciyarta. Nauyi take ji kamar dutse aka ɗora mata a ƙirjinta, wani lokacin numfashi wahala yake mata saboda nauyin da zuciyarta tayi mata. Washe garin da suka dawo Twiny ta juya Kano saboda mijinta ya gama komai na gida. Sai ta sake zama shiru-shiru bata da abokin shawara, gashi tana son zuwa Kano amma tana tsoron Abiy kasancewar bata jima da dawowa ba. Kamar yadda ta zaɓarwa kanta kullum tana ɗaki a zaune sai ga autan su ya shigo ya ce Abiy yana kiran ta. Sai da ta daidaita nutsuwarta sannan ta fito ta same shi a falon da shi kaɗai yana kallon tv. Da sallama ta shiga ya amsa yana bita da kallo tare da tattara nutsuwar sa gabaɗaua a kanta. Sai da ta zauna sannan ya ce, "Mamana dawo kusa dani" ya faɗa yana nuna amsa kan kujerar da yake. Ba musu ta tashi dawo kusa dashi ya fuskance ta ya ce, "Mamana baki da lafiya ne?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "bana son body language, ki yi min magana." "Lafiyata lau Abiy." Abiy ya ce, "ƙarya ki ke yi, tun a Saudia kika canja gabaɗaya. A wancan lokacin na karɓi dalilinki ne kawai saboda kar na takura ki, amma ba dan na amince da abinda ki ka ce ba. Me yake damun ki kika koma haka? har rama naga kin yi, me ya faru?." Nayla tayi shiru bata ce komai ba Abiy ya ce, "ban kai na ji damuwarki ba?." Da sauri ta ce, "A'a Abiy." "To faɗa min." "Babu ne shiyasa." "Kar ki yi min ƙarya Mamana, ƙarya ba halin ki bane. Ki faɗa min gaskiya kafin na gano da kaina." Nayla ta ce, "da gaske nake Abiy, babu abinda yake damuna." Abiy ya yi shiru yana kallon ta cikin nazari, bai yarda da abinda ta ce ba, ya san kawai bazata faɗa bane amma zai san yadda zai yi mata. Ya sauke numfashi ya ce, "shikenan. Ga offer ki" ya faɗa yana miƙa mata takarda. Nayla murmushi tayi cikin farin ciki ta karɓa Abiy ya ce, "Federal inland revenue service ne. Ranar Monday zaki je ki gama duk abinda ya kamata." Nayla cikin farin ciki ta ce, "Abiy na gode, Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna." Murmushi ya yi ya ce, "Amin Nayla. Sai zancen shagon ku keda Twinyn ki, za a ƙara muku jari ku cigaba da juya kuɗin, Kwana biyu ma ke bakya zuwa." Nayla farin cikin samun aiki duk ya cika mata zuciyata, burinta a rayuwa kawai ta yi aiki shiyasa Abiy ya samar mata. Ta ce, "Abiy ni na rasa me zance saboda murna." Murmushi ya yi kawai yana kallon ta ya ce, "Nayla kenan. Akwai abinda ki ke so bayan wannan?." Nayla tana murmushi ta ce, "babu komai Abiy. Kawai Ina so na kaiwa Hajja tsarabarta ne." Murmushi ya yi ya ce, "Nayla sarkin zuwa Kano, Ke dai kina son shiga Kano." Tayi dariya ta ce, "Kano da daɗi Abiy." "Shikenan, in kin shirya sai ki je gobe ki yi kwana biyu ki dawo." Farin cikin da Nayla taji ko da ya miƙo mata offer bata ji ba, hakan ya bayyana a kan fuskarta sosai da murya ta ce, "Na gode Abiy, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan mahaifa, Allah ya jikan Ummana." Murmushi ya yi ya ce, "Amin. Bani offer ɗin kinje ki shirya." A guje ta miƙe ta shiga ɗaki tana murna. Cikin murna ta yi ajiyar zuciya ta zabura ta buɗe trolly bag ta fara zuba tsarabar Hajja da ta Salma har da Didi ma. Wata maroccon jallabiya ta maza ta ɗauko kalar baƙa mai kyau da santsi ta kalla ta ce, "zata yi masa kyau sosai." Murmushi take kamar shashasha, tana hango in Omar ya saka rigar ya zai koma. Da haka ta gama zuba kayan a jakar tafiya Kano. Wayarta taji tana ƙara da ta duba sai ta ga Abiy ne, tana ɗauka ya ce, "Mamana ki bar zuwa Kano gobe a gama settling aikin nan da kika samu, in aka gama kafin ki fara aiki sai ki je ki dawo. Yanzu ake sanar dani gobe ake so ki je." Sai jikinta ya yi sanyi ta ce, "to Abiy" daga haka ya yanke wayar ita kuma ta zauna gabaɗaya murna ta koma ciki. Nayla Anya kuwa🤔 *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 22.* Kwance tashi babu wahala a wajan Allah, a hankali zuciyar Narma ta fara rinjayar zuciyar Omar, tun tana kira yana ƙin ɗauka har ta kai in bata kira shi bama baya jin daɗi. Gashi da shegiyar izza shi bazai iya kiranta ba, in ta kira kanta ta yiwa, in bata kira ba bazai kira ba. Tun yana ƙaryata kansa akan yana sonrta har ya amince da gaske yana sonta, kuma shima ya shirya auren ta kamar yadda ta shirya aurensa. Ranar da ya bayyana mata kamar zata yi hauka saboda murna, duk da bai yi wasu dogayen kalamai ba, kawai ya ce mata shima zai iya aurenta daga nan bai ƙara koda kalma ɗaya ba. Narma ta dinga murna tana farin ciki, shi kansa farin ciki yake yi, duk da wani lokacin sai ya ji kamar soyayyarta ta bar zuciyarsa, bayan kwana biyu sai ta dawo. Duk da basa haɗuwa amma babu laifi sun saba a waya, da yake ba aikin yi ne dashi ba in dai zata kira shi zata same shi, shine dai bai cika kiran ta sosai ba. Yau ta kama ranar juma'a kamar ko wanne sati Didi ta kammala abincin sadaka ta rabawa yara ta koma tana hutawa ya shigo bayan an sakko daga masallaci. Da kallo take binsa ya zauna ta ce, "har an sakko?." Gira kawai ya ɗaga alamun eh kafin ya kalle ta sosai ya ce, "Didi." Ta kalle shi  ba tare da ta amsa ba, ya ce, "ta ya zan iya gane Ina son wata?." Da kallon rashin fahimta ta bi shi ta ce, "ban gane ba, me ka ke nufi?." "Ina nufin in na fara son wata ta ya zan fahimci hakan?. A taƙaice ya ake gane soyayya?." Didi da kallo take bin sa cikin faɗuwar gaba, babban tashin hankalin ta bai wuce kar ya ce yana son Narma ba, amma tunda ya tambaya zata faɗa masa dan tafi kowa sanin bai san soyayya ba. Didi ta ce, "To nima Omar ba wani sani nayi ba ai." "Amma baza ki kasa yi min bayani yadda zan gane ba ai ko?" Ya faɗa yana tsare ta da ido. Didi ta ce, "Zuciyarka zata dinga bugawa a yayin da ka ganta, zaka dinga ɓata lokacin ka wajan saurarenta, zaka dinga jin shauƙi sosai koda sautin muryarta ka ji, zaka dinga jin zaka iya yin komai dan ka mallaketa. Sannan....." dakatar da ita ya yi ya ce, "iya wannan da ki ka faɗa ma ya isa." Kallon fuskar ta yayi, cikin rashin tsoro ya ce, "Hakan yana nufin ina son Narma, daman na tambaye ki ne dan na tabbatar kuma na tabbatar ɗin." Cikin tashin hankali Didi ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Omar ka san abinda ka ke faɗa kuwa?. Kana son Narma ka ce fa? Don Allah ka faɗa min wasa ka ke yi." Da mamaki ya ke kallon ta jin tayi dogon salati ya ce, "wannan salati haka Didi na meye? Bata cancanci na sota ɗin ba ne?." "Omar kai ne baka cancanci ka sota ba, Omar ita ba ajinka bace, don girman Allah ka rufa min asiri ka bar maganar nan, Ina kai ina soyayya da ƴar gidan sanata Omar?." "Kin zo a makare Didi, domin kuwa wannan asirin naki bazai rufu ba. Ina sonta kuma zan je har gaban sanatan na faɗa masa." Didi numfashi ta ja kawai tayi shiru bata ce komai ba, dan babu amfanin maganr, ta san kuma wallahi sai ya aikata tunda ya faɗa. Hawaye yaga tana yi ya tausasa murya ya ce, "don Ina sonta shine ki ke kuka?." Didi ta ce, "Omar bana so wani abun ya same ka, Ina ji a jikina soyayyarta bazata zama alkhairi a gare ka ba." "Kin san gaibu ne Didi?." Jin tambayar da ya yi mata ya saka take kallon sa da mamaki, kenan dai da gaske son Narma yake yi tunda gashi yana yi mata wata bahaguwar tambaya. "Ban san gaibu ba Omar, amma auren ka da ita da kamar wuya." Omar ya murmusa ya jingina da kujera ya ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "ki taya ni addu'a kawai, amma kin san tunda na ɗauki hanya bazan karkace ba. Zan je har gidan su har gaban sanata na nemi auren ta, kin san bana jin tsoro komai kuma bana tsoron kowa. Ki kwantar da hankali ki daina kuka, babu abinda zai same ni sai alkhairi." Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "ai shikenan" ta faɗa cikin rashin mafita dan ta san bazai bari ɗin ba kamar yadda yace. Ganin ta a yanayin damuwa sai ya yi ƙoƙarin kawar mata da tunani ya ce, "Ya zancen AbdulHamid? Kwana biyu bana ganinsa." Didi a sanyaye ta ce, "Ta ya zaka ganshi kullum kana ɗaki kana soyayya?." "Hmm! Saura wata nawa bikin?." "Ban sani ba" ta bashi amsa a taƙaice tana miƙewa ta shiga ɗaki ta bar masa falon. Murmushi ya yi dan ya san haushinsa take ji, shi kam tunda ya ɗaura ɗammaara bazai kwance ba. Kiran Narma ne ya shigo wayarsa ya ɗauka ya ji ya ce, "Faruk na shigo Kano, Ina so mu yi magana da gaggawa, kuma zuwa dare zan koma Abuja. Na karo Mum gaisuwar rasuwa ne." Daƙyar ya ce, "maganar meye?." "Ni dai Ina so mu haɗu, zaka zo ko nazo gidan ku?." Numfashi ya sauke kana ya ce, "kina ina?." Narma ta ce, "Ina guest house, amma ba wanda ka sani ba. Ina zaka zo zan baka address ɗin, ko kuma naje wancan da ka sani sai mu haɗu." Shiru yayi yana nazari akan zuwan kamar bazai ce komai ba, ta san halinsa akan wannan shirun yanzu sai ya ɓata mata lokaci har lokacin tafiyar su ya yi. Ta ce, "please na faɗa maka da wuri zamu bar Kano." "Zan zo" ya bata amsa taƙaice kafin ya kashe wayar. Ba jimawa yaji ƙarar messege ya miƙe ya fita daga falon.         Da kayan jikinsa ya tafi tunda Didi ta laqaba masa saka mayan kaya ranar juma'a. Bashir ne ya kai shi a machine ya kuma saka shi ya tsaya ya jira shi ya fito su tafi. Kafin ya zo Narma ta sanar da zuwan da hakan ya saka kai tsaye aka masa iso zuwa harabar gidan. Kiran ta ya yi a waya ya ce, "ki fito." Narma a sanyaye ta ce, "don soyayyar ka da annabi Muhammad S.A.W ka shigo, ba don halina ba" ta faɗa dan ta san zai ce bazai ce bazai shiga ba. Jin magiya da tayi masa sai ya kashe wayar bashi da zaɓin da ya wuce shiga inda nuna masa matsayin nan ne hanya. Tafkeken falo ne mai kyau da tsari, babu haukan ado a cikin sa amma ya tsaru irin sa ake kira da luxury parlour. Tana tsaye a falon cikin riga da siket na atamfa ta yi mata matuƙar kyau. Kasancewar atamfar baƙa ce sai ta haska farar fatarta sosai. Ta ɗame kamar ko yaushe, daƙyar take iya motsawa a cikin siket din. Rigar kuwa tsabar kamata da tayi gabaɗaya ana ganin saman ƙirjinta, gashi bata da tsaho in ta ɗaga hannu ana hango cibiyarta. Kallon farko in kayi mata zaka ga shigar ta ƙara mata kyau, amma in ka nutsu zaka fahimci fidda tsaraici ƙarara a tare da ita. Bai san yana kallon ta sai da yaji ta a jikinsa ta rungume shi da sunan welcome hug. Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, shi bai yi hugging nata ba kuma bai ƙoƙarin cire ta a jikinsa ba. "Nayi kewar ka" ta faɗa tana kwance a jikisa tana jin farin ciki da nutsuwa na shiga jikin ta. Maganar da ta faɗa ne ya saka shi janye ta daga jikinsa yana binta da shegiyar harara. Da yatsa ya nuna ta ya ce, "gargaɗi na karshe zan miki, kar ki sake aikata haka, kar ki sake cewa zaki riƙe ni, kar hakan ya sake faruwa in ba haka baza ki sake ganina a inda ki ke ba!." Narma ta shagwaɓe ta ce, "I'm sorry, I just missed you ne shiyasa." Ƙaramin tsaki ya ja sai ta ce, "i'm apologize fa, smile please." Sake bashi haushi tayi dan shi baya son magana da turanci, duk abinda ta ce yaji amma baya ra'ayin ayi masa magana yaren. Murmushi tayi ganin ya sake tamke fuska, ita hakan ma yana matuƙar burge ta wallahi, sake ƙara mata ƙaunarsa yanayin sa yake yi a zuciyarta. "Have a seat" ta faɗa tana nuna masa wajan zama. Kallon ta yayi da birkitattun idanunsa, yana ayyana dole ya taka mata burki akan turancin nan kafin hakan ya saka ya tsane ta. Bai musu ba ya zauna ta zauna nesa dashi kaɗan ta ce, "kayi kyau Faruk! Sai naga kamar ana ƙara maka kyau ne sosai." Kallon ta ya yi jin wata magana mai kama da zagi dan ya wuce zolaya, shi bai ce tayi kyau ba sai ita zata faɗa? Ina kyaun a wajansa. Daman ta gama shirya center table ta kalle shi bata damu da rashin bashi amsa ba ta ce, "bismillah." Kallon abinda ta nuna ya yi ya kalle ta ya ce, "ki faɗa min dalilin ki na kira nan." Ta langwaɓar da kai ta ce, "Amma ka sha ko ruwa ne ko? Ni wallahi kamar baka yi kewata ba sai ɗaure fuska ka ke, don Allah kayi murmushi." Kallon ta ya yi suka faɗa ido ya ce, "zuwan da nayi bai nuna miki abinda kike tunani ba?." Sai ta yi murmushi cikin zallar shagwaɓar da take sake canja masa yanayi ta ce, "haka ne my Faruk. Da kace zaka zo naji matuƙar farin ciki, domin kuwa na san tabbas na babban samu matsayi a wajan ka." "To Ina jinki." Narma ta gyara zama ta ce, "Yaushe za ka zo Abuja ku haɗu da Dad ɗina? Ba a matsayin Tiger ba, a matsayin Faruk inlwa ɗinsa. Yaushe zaka zo?." Bata ji ya amsa ba hakan ya saka ta ce, "Ina so kaje don ya san da zaman soyayyar mu Faruk, bana son yin aure da wuri, amma tunda na fara sonka nake ji a zuciyata ina son yin aure da gaggawa." Omar ya kalle ta yana wani tunani, ya rasa meyasa in ta yi zancen aure wani lokacin zuciyarsa bata karɓa, sai ya dinga ji kamar shi bazai aureta ba, sai ya dinga ji shi kamar ba aurenta yake son yi ba akwai abinda yake zuciyarsa ba aure ba. Ya kawar da tunanin ya ce, "na faɗa miki na shirya yin aure ne yanzu? Kuma shi ne ya ce nazo?." "A'a, ni nake so kazo saboda ya san da kai ayi maganar aure a wuce wajan kawai." Kai ya girgiza ya ce, "baza ki samu matsala ba?." "Babu wata matsala." "To zan duba na gani, in na samu lokaci zan sanar dake sai ki faɗa masa." Narma tayi murmushin jin daɗi ta ce, "thank you my Husband to be. I can't wait to be your wife, I feel like na jawo lokacin da zaka kasance miji a gare ni. Ranar da aka ce na zama matar ka bazan iya bacci ba." Gyara zama y yi ya ce, "Narma!." In ya faɗi sunan nan kamar ya soka mata abu a zuciya haka take ji, bata taɓa jin wanda yake faɗar sunan ta daidai kamar sa ba. Ta narke tana kallon sa ya ce, "kar ki sake yi min wani yare in ba hausa ba in muna tare kin gane?." Jin yadda ya faɗa a kausashe sai ta nutsu sosai ta ce, "in sha Allah bazan sake ba. I'm sorry..." hararar da ya yi mata ya saka ta tsorata sosai ta ce, "ka yi haƙuri" ta faɗa a sanyaye. Bata taɓa zaton soyayya zata saka ta tsoron wata halitta irin Omar ba, tsoronsa take ji matuƙa bata son abinda zai ɓata masa rai ko kaɗan. Shiyasa take kiyaye dokikinsa dan a zauna lafiya. "Yaushe zaka saba dani ne Faruk? Ka kasa sakin jiki dani har yanzu. Ina sonka, da kai kaɗai nake so na rayu. Don Allah kar ka dinga amfani da rauni na akan sonka kana cutar dani." Kallon ta ya yi bai san lokacin da ya yi murmushi ba, kamar shashasha itama sai tayi murmushi ta ce, "na gode da wannan kyauta Faruk." Miƙewa tsaye ya yi alamun zai tafi ta ce, "Zaka tafi ko ruwa baka sha ba." "Zan sha wani lokaci" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba, dan in yana kallon ta wani ne yake shiga jiki sa take sai yanayinsa ya canja. Miƙewa itama ta yi ta kalli window ta kalle shi ta ce, "Ga irin wajan zaman ka can a wancan gidan, naga kana son zama a gazebo, dole gidan auren mu kasance da gazebo saboda ka shiga ka huta" ta faɗa cikin son burgewa. Kallon ta ya yi kafin ya ɗauke kai ya ce, "kina tunanin samunta a aurena?." Narma jin ya bata amsa sai ta sake karya murya cikin iyayi ta ce, "ko ba yanzu ba ko nan gaba. Kuma gidana da nake ginawa akwai." "Gidan ki!" ya maimaita yana yi mata kallon bakin da hankali kafin ya sake cewa, "kina tunanin in Allah ya ƙaddara na aure ki ni Omar zan zauna a gidan da yake naki? Hmmm baki san Omar ba har yanzu, ki yi gaggawar canja tunaninki a kan hakan" ya sake cewa, "In har da gaske kina son auren Omar ki san irin tunanin da zaki yi" ya faɗa dan ya tuna mata, dan shi ba irin mazan da suke zama a gidan mata bane, gwara ya yi mata gargaɗi da babbar murya. Narma a sanyaye ta ce, "Ina yi mana fata a rayuwar auren mu mu samar da ita." "Dakyau!" ya furta yana fita ta biyo bayan sa tana ta yi masa shagwaɓa yana sharewa kamar bai gani ba ko kamar baya jin shagwaɓarta a jikinsa, yana ji kawai bazai nuna bane, dan in ya nuna mata shine a ruwa. A haka suka yi sallama ya fita ya samu Bashir na jiran sa suka koma gidan Didi.          Bayan fitar Omar Didi tana zaune rana ta buɗe sosai tana shan iskar fankar solar taji anyi sallama. Amsawa tayi tana jiran mai shigowa sai kawai suka haɗa ido da Nayla. Didi ta wara ido ta ce, "Nayla!." Nayla tayi dariya ta ƙaraso kusa da Didi ta zauna ta ce, "Na'am Didi." Didi da farin ciki ta ce, "Saukar yaushe? Wannan bazata haka." "Saukar ɗazu. Ina yini." Didi ta amsa da fara'a tana tambayar ya mutanen gida ta tabbatar mata da kowa lafiyar sa lau. Didi ta ce, "wallahi nayi kewar ki Nayla, haka kawai nake ji bana so ki bar Kano." Nayla tayi dariya ta ce, "wallahi nima bana son barin Kano Didi, amma ya zama dole dan yanzu na fara aiki ma a can." "Ma sha Allah, amma na taya ki murna Nayla. Allah ya sanya alkhairi ya kaɗe fitina." "Amin ya rabbi. Na gode sosai Didi." "Amma kwanaki zaki mana ko?." Nayla tayi dariya ta ce, "Ranar Sunday da safe zan tafi, kin manta na ce Ina aiki?." Didi ta ce, "kai! Wallahi ban ji daɗi ba. Amma babu komai in sha Allah ɗan Kano zaki aura, kin ga sai dawo Kano gabaɗaya mu dinga ganin ki." Nayla tayi murmushi amma a zuciyar tana aiyana in sha Allah ƙaninki zan aura Didi, amma a bayyane sai bata ce komai ba. Didi ta kalle ta tace, "an sha saudia. Ina fatan kin roƙawa mutumin ki shiriya a wajan Allah kamar yadda na ce, kin yi min?." Wani iri taji a zuciyarta, domin kuwa babu ranar da zata fito ta koma bata ambaci sunan Omar a addu'arta ba, ba wai tana cewa Allah ya bata shi bane, tana roƙon Allah ya shirya shi ya cire masa dukkan abinda yake yi ya dawo mutum kamar kowa. Ita kanta bata san sau dubu nawa tayi masa addu'a ba. Har ɗawafi ta yi akan Allah ya canja Omar, ta yi ɗawafi bama sau ɗaya ba. A bayyane ta ce, "Nayi masa sosai Didi, ba ma shi kaɗai ba har da ke. A jikina nake jin Allah zai amsa da gaggawa." Didi ta ɗaga hannu ta ce, "Allah Amin" ta kalli Nayla ta ce, "na gode Nayla, Allah ya bar zumunci." Nayla tayi murmushi ta amsa da amin. Didi ta kalle ta tana murmushi ta ce, "wallahi Nayla haka nan Allah ya saka min ƙaunarki, Ina jinki kamar ƙanwata." Nayla ta murmusa ta ce, "nima Ina jinki kamar yayata Didi." Didi tayi murmushi ta ce, "Amma Nayla naga kin rame, kin yi rashin lafiya ne?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "haka ake cewa na rame amma ni bana gani, lafiya ta lau kawai kiɓar nake so na rage." Didi tayi dariya ta ce, "ai baki da kiɓa Nayla, gaki nan ƴar chubby dake in kika rame ai baza ki yi kyau ba. Gaskiya ki daina." Nayla tayi dariya kawai bata ce komai ba sai ledar da ta shigo da ita ta miƙawa Didi ta ce, "ga tsabar ki." Didi ta karɓa ta ce, "Nayla harda tsaraba? Ai ni iya addu'ar da kika yi min itace babbar tsaraba a wajena." Didi ta buɗe ta ga doguwar riga irin mai babban mayafin nan da ake yayi, original ƴar Saudia dan a yanayin jikinta ma zaka tabbatar da ba fa irin ƴan Nigeria ba ce. Sai zamzam da chocolate da kuma cross shoe. Didi ta fara godiya Nayla ta ce, "Didi yanzu ki ka ce ni ƙanwarki ce ko? Don Allah ki bari." Didi bata daina ba ta cigaba da addu'a tana yi mata godiya. Nayla ta sake bata leda ta ce, "Ga na...." Sai ta rasa wanne suna zata kira shi, Omar zata ce ko Tiger? Didi kallon ta take yi tana so ta ji na waye, Nayla ta ce, "Na Yaya Omar." Didi tayi dariyar tsokana ta ce, "A'a, harda su kaza a cin danƙoo? Kuma yaushe Omar ɗin ya zama Yaya Omar?." Nayla tayi murmushi ganin tana tsokanarta, ta karɓa ta buɗe taga doguwar riga irin ta maza mai dogon hannu, ga wata cover ƙarama mai kyau a ciki, ta ɗauko ta buɗe idon ta ya faɗa kan lafiyayyar azurfa mai bala'in kyau. Didi ta kalle ta a sanyaye ta ce, "Nayla duk wannan na Omar ne? Azurfa da take da tsada a nan ƙasar ma balle a Saudia?. Bayan azurfa ma harda doguwar riga ga wani abu ma a ciki ina ji" ta faɗa tana fito da ƴar ƙaramar kwalba ta oil perfume ta ce, "ga turare. Nayla hidimar bata yi yawa ba?." Nayla ta ce, "Haba Didi wallahi babu komai, an zama ɗaya kar ki damu." Didi tayi ta ce, "To Nayla, mun gode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci, Allah ya baki miji na gari." Nayla ta amsa da amin kafin Didi ta ce, "Su Omar an samu azurfa, daman hannun nasa babu komai kamar ba saurayi ba, kin taimaka kin fito dashi ya zama mutum shima kamar kowa. Kwanaki ya je kasuwa zai siya aka ce masa azurfa mai kyau daga ko dubu talatin ta fara, ya dawo na ce ya baka siyo ba wai ai ba hauka yake yi ba, ta sha zaman ta." Nayla tayi murmushi kamar yadda Didi take murmushin itama tana sake yiwa Nayla godiya. Basu ji sallama ba kawai sun ganshi ya shigo falon, Didi ta kalle shi ta ce, "shigowa babu sallama Omar?." Kallon Didin ya yi kafin ya kalli wacce take zaune a kusa da ita yana aiyana wacce baƙuwa ce tazo musu gida. Nayla tunda taji an shigo an kuma ce Omar ta nutsu ta sunkuyar da kai ƙasa. Sake kallon Didin ya yi ya ce, "Nayi sallama baki ji ba ne." Ajiyar zuciya Nayla tayi jin murya sa a kunnen ta, ido ya cikowa da ƙwallar kewarsa da take ji. Didi jin ajiyar zuciyar da tayi sai ta kalle ta a tausashe tace, "Nayla ki bar jin tsoron Omar don Allah, wannan ajiyar zuciya ta meye haka? Kar ki dinga cutar kanki fa." Nayla bata ce komai ba domin Didi baza ta gane ba, ita ba ajiyar zuciyar tsoron sa take yi ba, ta soyayyar da take yi masa ce. Ta kalli Omar ta ce, "ga tsaraba Nayla ta kawo maka daga Saudia." Sarai ya gane Nayla ɗin ya haddace sunanta tsaf a wajan Didi, har mamakin haddace sunanta da yayi yake yi, da zarar ta ce Nayla fuskarta zata zo idonsa. Bai san me yasa hakan ba amma ya ɗauki hakan a yawan kiran sunanta da Didi take yi ne, da kuma faɗan da ta yi masa a gabanta. Basarwa yayi kamar bai gane ba ya ɗage gira sama ya ce, "Wace haka?." Wani iri Nayla taji a zuciyarta, amma jin muryarsa na kore waccan damuwar. Didi ta Harare shi bata yi magana ba ta ce, "ga tsarabar sai kayi mata godiya, nima ta gwangwaje ni da doguwar riga. Kuma irin ta jikinta sak, ni sai yanzu ma na lura" ta faɗa tana nuna masa. "Kin gode" ya faɗa yana niyar juyawa. Didi ta ce, "kai baka gode ba?." Ya kalli Didi ya kalli Nayla da take zaune kamar munafuka, shi fa wallahi haushi take bashi ba kamar in ya tuna faɗan da Didi tayi masa a gabanta, tayi masa faɗa tana wajan kuma ta hana shi ɗaukar mataki sannan ta shigaba da shigowa gidan su. Lokaci ɗaya yaji haushinta na sosa zuciyarsa. Ya ce, "ai ban roƙa ba ko?." Didi taji babu daɗi cikin takaici da jin kunya take kallon sa, in da ba a gabanta bane ba da sauƙi, amma a gaba idon mutum akwai cin fuska sosai. Sai ya samu kansa da kallon Naylan da take zaune, baƙin gani ya yi domin kuwa murmushi take yi ga kuma hawaye yana sakkowa daga idanun ta. Ƙaramin tsaki ya yi dan haushi yaso ya bata, duk da yaga hawaye amma hawayen bai kama da na jin haushi ba. Ganin kallon da Didi take yi masa sai ya ce, "an gode" daga haka ya fita ta harari bayansa ta ce, "kaji dashi bahagon mutum kawai. Ni mamaki ma nake yi da Narma ta iya dakon soyayyarka zuwa yanzu, ko da wanne yanayi ka ke soyayyar oho." Dam gaban Nayla ya buga bata san ta ɗago tana kallon Didi ba, ganin tana hawaye jikin Didi ya yi sanyi ta ce, "yi haƙuri kinji Nayla, don Allah ki yi haƙuri." Nayla bata ce komai ba dan labarin soyayyar tasa take so taji. Ganin Didi bata sake cewa komai a kai ba sai Nayla ta ce, "Didi yana da budurwa ne?." Didi ta ce, "yana da wahala dai, Omar Ina ga wata budurwa kema ban da abin ki. Ɗazu dai ya gama furta min da gaske yana son yarinyar kuma ya shirya aurenta ta ko wanne hali. Ko waye zai bashi auren ƴarsa oho." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Nayla ta faɗa a bayyane ba tare da ta sani ba. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025              ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 23.* Jin dogon salatin da Nayla tayi Didi ta kalle ta da mamaki, Nayla tayi saurin cewa, "Kuma itama tana sonsa? Taɓ bata san waye shi bane." Jin abinda ta ce sai Didi tayi dariya ta ce, "wallahi tana son Omar matuƙa Nayla, har nan tazo ta zube min akan na saka baki Omar ya saurareta. Amma tsabar wulaƙanci irin nasa a gaban idanunta yake cewa in ma yaudarar sa tazo yi yafi ƙarfinta. Shi da ita ya ce mata shi bazai yi soyayya da ita ba kar ta sake gangancin furtawa, kuma fa ƴar manya mutane ce wallahi, mahaifinta shine Senator Kano central a yanzu. Omar yana yiwa mahaifinta aikin siyasa, kin san ƴan siyasa suna son irin su Omar a tafiyar su. To shine fa da zata zo Kano ya ce Omar ne zai dinga kaita duk inda zata je saboda ya yaba dashi, daga nan dai sai ta fara sonsa." Nayla tana ji amma bata fahimtar me take cewa, tayi tsitt zuciyarta na bugawa a guje, sai goge ido take yi bata so hawayen da ya taru a ciki ya zubo. Didi ta cigaba da faɗin, "A hankali dai shima ya fara sonta, sonta ya fara dai ko ba so bane shi ya sani. Ban da hauka irin na Omar ina shi ina wannan yarinyar? To baya jin magana, ya ce min tunda ya ɗauki hanya bazai karkace ba, ni wallahi tsoro nake ji kar a cutar dashi.." Nayla bata iya magana ba tayi shiru zuciyarta na bugawa sosai har zazzaɓi take ji yana neman rufe ta. Jin tayi shiru sai Didi ta ce, "ki daina tsoron sa don Allah, abinda ya yi miki da yanzu bazai miki ba." Nayla tayi murmushin yaƙe ta ce, "ba tsoron sa nake ji ba Didi, kawai na tafi tunani da mamakin sa ne. Daman zai iya son wata mace? Lallai tayi sa'a ko wacece." "Mtsww! Meye abin sa'a dan Omar yana son wata? Rashin sa a ne ma ai wata ta fara sonsa ni a wajena. Meye abin so a Omar don Allah?. Farar fata ko kyaun fuska? Allah dai ya shirya kawai." Nayla tayi murmushi bata ce komai ba dan kanta ya yi mata nauyi sosai kwanciya take da buƙatar yi. Miƙewa tsaye tayi ta ce, "Didi bara na koma wajan Hajja." Did ta ce, "To Nayla. Na gode Allah ya bar zumunci. Zan aiko miki da mutuminki shinkafa da wake shi nake dafawa." Nayla tayi murmushi ta ce, "to Didi" ta faɗa tana fita kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki. Tana fitowa tsakar gidan taji muryarsa ya yi ƙaramin tsaki ya ce, "to ni ƙaramin yaro ne da wani abun zai same ni a hanya? Lafiya naje gida." Nayla tana takowa inda yake tana jin zuciyarta na cigaba da bugawa dan ta san da budurwarsa yake waya. Tana zuwa kusa dashi ta ji ya ce, "kar ki dame ni!" Sai ya yanke wayar fuskarsa ba yabo babu fallasa. Ya ɗago ido suka haɗa ido daidai lokacin da hawaye ya sakko daga idanun ta. Kallon ta yake yi da mamakin abinda ya saka ta kuka tunda yaga tana hawaye a wajan Didi, kusan ko yaushe in zai ganta kuka take yi bai sani ba ko kukan ne yake mata daɗi. Da sauri tazo zata wuce doguwar rigar jikinta harɗe ta zata faɗi tayi saurin dafa bango bata faɗi ba, yana tsaye shi dai yana kallon ikon Allah dan kallon ta yake yi. Da sauri ta fice shi kuma ya yi tsaki ya ce, "tunda ba a nutse ki ke ba ai dole ki nemi faɗuwa, yarinyar ta cika rawar kai" ya faɗa yana shiga ɗaki. Nayla a guje ta shiga falon Hajja ko kula Hajja da Salma bata yi ba ta wuce ɗaki a guje ta faɗa akan gado tana sakin kuka mai sauti. Hajja da Salma suna jiyo sautin kukan nata Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma wai me yake damun ƙawar ki ne?." Salma ta ce, "Wallahi Hajja ban sani ba, amma tun waccan tafiyar ta na lura tana cikin damuwa, dana tambaya sai ta ce babu komai." Hajja ta ce, "ki duba har rama tayi fa, gaskiya tana cikin damuwa ya kamata ki tambayeta ki ji abinda yake damunta. Ko ki yiwa takwararta magana tunda ku biyu ne ƙawayen ta." Salma cikin damuwa ta ce, "to Hajja. Amma tabbas tana da damuwa, ki duba da farin ciki ta fita amma ta dawo a wannan yanayi. Gaskiya akwai abinda yake damunta sosai." Hajja ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba amma tana tunanin abinda ya damun jikar ta ta. Nayla kuwa kuka take yi kamar ranta zai fita, in ta tuna Omar yana son wata mace sai taji sabon kuka da hawaye yana ambaliya daga idonta. Zuciyarta fara harbawa take yi kanta na juyawa, kanta ya yi nauyi haka ƙirjinta ma ya yi mata nauyi sosai. Shikenan ita a haka zata gama rayuwa da dakon sonsa, tunda gashi yana da wacce yake so kuma har yana cewa zai je ya samu mahaifinta. Shikenan ta ta ta ƙare, sai dai ta mutu da sonsa ba tare da ya sani ba. Kalaman Didi take tunowa ta fara girgiza kai ta ce, "Ko da zan mutu ni bazan ce ina sonsa ba, bazan faɗawa Didi Ina sonsa ba, bazan faɗa ba" ta faɗa tana kuka sosai tana kwanciya a kan gadon jiki na rawa. Sai da tayi kuka mai isarta sannan ta iya yin shiru ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta zauna tayi shiru tana salati. Wayarta ta ɗauko ta kira Baba Salisu da ya kawo ta ta shaida masa gobe yazo ya ɗauke ta fasa kaiwa ranar Sunday. Salma ce ta shigo bayan ta gama wayar ta zauna kusa da ita ta ce, "Nayla a duniya a baki da ƙawaye masu baki shawara kamar ni da Twiny, ana kallon ki an san kina cikin damuwa, ki faɗa min abinda yake damunki." Kallon Salma tayi jin ta ce Twiny sai ta ce, "Sayyadi...Driver Hajja, yana nan ya kai ku gidan Twiny?." Salma ta ce,"yana nan." Nayla ta miƙe ta yafa mayafin doguwar rigar ta ce, "na fasa kaiwa jibi a garin nan gobe zan koma Kaduna, muje ya kaimu ko zuwa anjima ne ma dawo." Tare suka fito suka faɗawa Hajja inda zasu je tayi musu a dawo lafoya suka fita. Jidda tayi murnar ganin Nayla a gidan ta suka baje a falo dan sun saba da Salma sosai. Salma ta kalli Jidda ta ce, "Jidda wani abun da yana damun Twiny ki wallahi, nayi-nayi ta faɗa min taƙi faɗa. Tsabar damuwa wai Nayla ce take cewa ta fasa yin kwana biyu a Kano gobe zata koma Kaduna. Kowa ya ji wannan magana sai ya yi mamaki sai kuma ya tambaya meyasa." Twiny ta kalli Salma ta ce, "tun a Saudia muka yi maganar nan da ita, amma abin yawa yake sake yi yana bani mamaki" ta kalli Nayla ta ce, "Nayla don ki faɗa min waye wannan da ki ke so." Salma ta ce, "wai zaman akan soyayya ne? Da yake bata faɗa min ba ta ce kawai mu zo nan." Jidda ta kalle ta ta ce, "akan soyayya ne Salma, wani take so shi bai ma san tana sonsa ba." "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lallai Nayla tana cikin azaba mai tsanani." Jidda ta ce, "tayi addu'a a Saudia amma ta ce soyayyar bata raguwa sai ma sake sonsa da take yi, nace ta nemi zaɓin Allah in shine alkhairi Allah ya kawo silar da zai fara sonta shima. Amma sai tayi murmushi ta ce ko da yana sonta auren sa da ita da wahala ya yu." Suka kalli Nayla a tare da take hawaye Salma a raunane ta ce, "Nayla waye wannan?." Nayla ta goge ido ta ce, "Sanin waye bashi da amfani, ku taya ni addu'a kawai Allah ya kawo min mafita. Twiny bani paracetamol kaina ciwo yake yi." Ba musu ta tashi ta kawo mata haɗi da ruwa ta sha kafin Jidda ta ce, "amma faɗa mana zai iya sakawa ki ji sauƙi a zuciyarki, kin san babu wanda zai ji labarin daga bakin mu." Nayla tayi murmushi ta ce, "qaunar da zaku nuna min shine ku yi min addu'a." Ganin ta dage taƙi faɗar waye sai suka ƙyaleta suna ta hira har ita, dan ta ɗan sake amma da ta tuna sai hawaye. Sai tara na dare suka baro gidan Twiny zuwa gidan Hajja. A nan Hajja take faɗa mata ga abinci Didi ta kawo mata kaɗam ta iya ci ta ajjiye ta kalli Hajja ta ce, "Hajja gobe zan koma Kano, na kira driver Abiy zai mayar dani gida." Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u an fasa kaiwa jibin?." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Na fasa Hajja. Na tuna akwai abinda zan yi a gidan, kuma ranar ranar litinin Ina da aiki." Hajja ta ce, "To Hauwa'u Allah ya kiyaye hanya ya nuna mana goben, Allah ya yi miki maganin damuwarki." Ta amsa da amin daga nan bata sake cewa komai ba, Salma tana kallon Labarina ita kuma ta miƙe ta shiga cikin ɗaki. Kamar yadda ta fada washe gari da ƙarfe goma na safe driver ya zo daga Kaduna, sai da ta bari ya huta ya ci abinci a wajan Hajja bayan sallar azahar suka ɗauki hanyar Kaduna. Ko a can kasancewar babu wanda ya san da dawowata, da yake ta asabar ce Abiy yana gida shi da Yaya Ahmad tayi sallama a falon ta shiga. Yaya ya ce, "A'a, mutanen Kano." Murmushi tayi ta ƙaraso ta zube akan carpet ta ce, "Abiy ina yini." "Lafiya lau Mamana, ya kika baro Hajja?." "Lafiya lau, tana gaishe ka. Ga saƙo ta ce a baka." Ya karɓa yana cewa, "Hajja bata gajiya da hidima in dai aka je sai ta bayar? Na kuwa gobe sosai. Zan yi mata waya na yi godiya." Da Yaya suka gaisa kafin ya ce, "mutanen kano, ba sai gobe zaki dawo ba daman?." Ta yatsine fuska ta ce, "Gajiya nayi kawai na kira Baba Salisu na ce ya zo ya taho dani yau." Ya yi dariya ya ce, "ikon Allah, zaman Kanon ne kuma ya ishe ki?." Tayi dariya kaɗan Abiy ya ce, "nima nayi mamaki, bata faɗa min ma zata taho ba, sai Salisu ne yake cemin ita zai ɗauko tayi amsa waya jiya, na ce to sai ka dawo. Gaskiya zan faɗawa Hajja taci tarar ki kin gudo kin barta." Nayla tayi dariya ta miƙe ta shiga wajan Mama. Itama tayi mamakin ganin ta suka gaisa daga nan ta koma ɗakinta tana sauke ajiyar zuciya. Zaman Kano ai ba nata bane, indai tana son kanta da zaman lafiya dole ta bar shi. Da daddare Mama ta shiga wajan Nayla ta same ta ta yi shiru ita kaɗai. Zama tayi kusa da ita ta ce, "Nayla." Nayla ta kalle ta ta ce, "Na'am Mama." "Tunanin me ki ke yi haka?." "Babu komai Mama." "Haba Nayla, kowa ya ganki ya san kina cikin damuwa mai yawa. Meyasa baza ki faɗa min ba? Ko dan bani na haife ki ba?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "A'a Mama ba haka bane, babu damuwar ne shiyasa." Mama ta zo kusa da ita ta riƙe hannunta ta ce, "uwa nake a wajanki, na haife ki na yi jika dake Nayla. In baza ki iya faɗa min damuwar kiba wa zaki faɗawa? In baki furta min abinda yake damunki ba wa zaki fadawa?. Uwa ce fa ni, ko bani da maganin damuwarki in nayi miki addu'a Allah zai amsa." Nayla kalaman Mama suka karya mata zuciya ta fara share hawaye. Mama ta sake nutsuwa ta ce, "faɗa min Ina jinki." Nayla ta ce, "Mama babu komai, in akwai zan fada miki bazan ɓoye ba." Mama tayi murmushi ta ce, "shikenan Nayla. Allah ya yi albarka, ki fito ki ci abinci" daga haka ta tashi ta fita tana tabbatarwa da kanta ƙarya Nayla tayi mata, amma zata tambayi Jidda dan ta san ita ta san dalilin damuwar Nayla. •••••••• Washe gari Didi ta shiga gaishe da Hajja ta kuma yiwa Nayla sallama dan fita zata yi kar ta shiga bata nan tarar da Nayla ta tafi, tayi mamaki sosai Hajja ta bata labarin a yadda ta shigo gidan da yadda ta ce ita ta fasa zama. Didi ta ce, "Allah ya sa ba Omar ne ya tsorata ta ba, dan ke baki ji ajiyar zuciyar da tayi da ta ganshi ba. Ni wallahi tsoron nasa da take ji ya fara bani tsoro." Hajja ta dinga dariya tana faɗin ba wani tsoro kawai akwai abinda yake damunta ne. *Abuja* Kamar ko yaushe suna zaune gabaɗaya suna hira Narma ta kalli Dad ta ce, "Dad." Ya kalle ta ya ce, "Narma." Narma ta ce, "mun gama magana da Faruk ya ce zai zo ku gaisa." Sai kuwa Najwa ta ce, "Awwnn! Ki ce shima dai yanzu da gaske yana yi ko Sis?." Aka yi dariya Dad da fara'a ya ce, "da gaske ki ke?." Ta ɗaga kai alamun da gaske kafin ta ce, "yana so ka bashi date da time ɗin da zai zo." Dad ya ce, "wow! wannan abin farin ciki ne sosai. Inda zai iya zuwa ranar Monday zan so hakan, zan kira minister mu zauna tare domin mu tarbe shi" sai kuma ya kalle ta ya ce, "Ko kuma ranar Monday da aiki?." Narma ta ce, "Dad ko yaushe ne zai zo indai a kaina ne. Zan faɗa masa in ya amince ranar monday ɗin zai zo." Mum da take dariya ta ce, "oh my god! Narma....." Narma tayi dariya ta ce, "Mum I love him so much, my feelings for him are impossible to hide" ta faɗa tana murmushin sannan ta ce, "then he loves me too." Nabil yayan ta ya ce, "Ma sha Allah, muna taya ki murnar samun wanda ki ke so." Tayi murmushi ta ce, "thank you bro, let me go and call him" ta faɗa tana tashi ta shiga ciki a guje. Dad yayi dariya suna tattauna yadda za'a tarbi siriki in yazo. Narma na shiga ɗaki Omar ta kira bai ɗauka ba, ta sake kira bai ɗauka ba sai ta ƙyale shi dan baya son tana tara masa kira. Wajan mintina kaɗan da kiran ya kira ta ta ɗauka da sauri ta saka a kunne sai ta ce, "kashe na kira ka." Daga can ɓangaren Omar ya ji abinda ta ce ya maimaita a zuciyarsa, me take nufi kenan? bashi da kuɗin da zai iya kiran ta kenan sai dai ita ta kira shi?. Kafin tayi magana ya yanke wayar, Narma ta kira sau adadi yaƙi ɗauka. Narma ta tayar da hankalinta ganin yaƙi ɗauka, ta je WhatsApp ta tara masa message tayi masa text message shima ba reply. Tun tana kiran sa har ta gaji ta kuma kasa gane laifin da tayi wanda ya saka ya yanke mata waya ya kuma ƙi ɗauka. Shi kuwa Omar yayi haka ne dan ya koya mata hankali nan gaba bazata sake cewa ya kashe ta kira shi ba. Yana ganin message ɗinta da kiran yayi banza ko kallo bai yi ba dan ya yi alqawari bazai ɗauka ba, kuma bazai kira ta ba, zata san waye Tiger. Sunday ta wuce, Monday ta wuce Omar baya ɗaukar wayarta kuma baya kiranta. Narma hankalinta ya tashi sosai sai ƙarya ta yiwa Dad ta ce ya ce ranar Monday baya nan. Sai ranar talata da yamma ya ga kiran na zuwa bai ɗauka ba sai da ta katse sai ya kira ta da hanzari ta ɗauka, tana sakawa a kunne ta ce, "laifin me nayi maka haka? Me nayi ka ke hukunta ni da wannan hukuncin Faruk?." "Gobe in na kira ki sai ki sake cewa na kashe ki kira ni. Banda kin raina ni saboda kinga ina surarenki har ke zaki ce min wai na kashe ki kira ni? Nuna min ki ke yi bani da kuɗin da zan kira ki?." Jin yadda yake maganar da tsawa sai Narma ta ce, "I'm sorry...." Cikin tsawa ya katse ta ya ce, "kin manta gargaɗin da nayi miki ko?." Narma ta ce, "yi haƙuri, na saba da yin English ne ko yaushe shiyasa, Amma zan dinga kiyayewa. Kayi haƙuri don Allah." "Mtsw! Faɗi matsalarki" ya faɗa kai tsaye yana sauraren ta. "Ka yi haƙuri, nayi kewarka, kuma Ina sonka, Ina ƙaunarka." Sai ya ɗan sassauta murya bayan ya ja tsaki ya ce, "Ina jin ki." "Daman tun ranar asabar na faɗawa Dad maganar zuwan ka ya ce in kana dama kazo Monday...au litinin, shine na kira na sanar dakai a lokacin." "Yanzu sai me?." "In zaka iya zuwa gobe yana jiran zuwan ka." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "bazan zo gobe ba, amma zan zo ranar alhamis hakan ya yi?." Narma tayi murmushi ta ce, "Ya yi Faruk ɗina, na gode Allah ya barmu tare na haifa maka yara masu kama da kai." Samun kansa ya yi da murmushi mai sauti har taji murmushin nasa. Omar ya ce, "na faɗa miki ban shirya aure ba ko? Ban ma san yaushe zan yi ba." Narma ta ce, "ai fata nayi mana ko?" Ta faɗa cikin shagwaɓa tana narkar da murya. Shagwaɓar da take yi yana ƙara masa karkasashi da yanayin da ya saba ji in suna waya. Jin ya yi shiru sai Narma ta ce, "baka ce amin ba, baka so na haifa maka yaran ne?." Murmushi ya sake yi har Narma tayi mamakinsa, dan ta san sai a gama waya dashi bai yi maganar kirki ba balle murmushi. Ya ce, "Ki jira lokaci." "Alhamdu lillah! Faruk yana son ya auri Narma har ya haɗa jini da ita. Wannan abin farin ciki ne." Nan ma murmushi ya sake yi amma bai ce mata komai ba, tana ta yi masa zance shi kam baya tanka mata sai ya ga dama, sai da ya gaji ya ce, "Zamu yi magana anjima" daga haka ya yanke wayar yana shafa gajin fuskarsa yana murmushi. Ajiyar zuciya ya yi ya miƙe ya shiga wajan Didi da niyar faɗa mata zai je gidan sirikai. *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *Book 1* *P 24.* A zaune ya samu Didi tana waya ya zauna a kujerar da ya saba zama ya harɗe ƙafa yana kallon ta tana cewa, "Ya jikin na ki?." Shiru tayi ana bata amsa sannan ta ce, "Allah ya ƙara lafiya Nayla, a gaishe da su Mama." Ta Amsa daga nan ta yanke wayar. Ambatar Nayla da tayi ya saka shi ya tuna fuskar ta a lokacin da take hawaye, sai ya samu kansa da jin wani iri a zuciyarsa ba tare da ya san dalilin haka. "Omar ya aka yi?." Maganarta ta katse shi ya kalle ta ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ranar alhamis zan je Abuja wajan mahaifin Narma." Didi ta kalle shi ta kasa cewa komai sai kallo, ta zuba masa ido bayan ta tallafi haɓarta da hannayenta. Ta ce, "Omar!." Jin yadda ta kira shi ya saka ya kalle ta sai ta ce, "Ka shirya aure ne? Yanzu in aka ce an baka aurenta kana da abinda zaka aure ta?." Ajiyar zuciya ya yi ya sauke ƙafasa daga kan ɗaya, ya sarƙe hannayensa waje guda ya kalle ta ya ce, "ni ai na faɗa mata ban shirya aure ba, tana so iyayenta su san da ni ne kawai." Zuba masa ido tayi tana kallonsa, a tausashe ta ce, "Omar anya baka yi ganganci da rayuwarka ba? Anya baka saka zuciyarka a tsaka mai wuya ba?. Sai nake ji kamar akwai wani shiri da yarinyar ta shirya maka Omar." "Didi babu wani shiri sannan babu abinda zai faru, Ina sonta kuma zan je wajan iyayenta matsayin mai sonta." "Omar kenan, ta ya iyayenta zasu karɓe ka a matsayin mai son ƴar su?. Tausayi ka ke bani wallahi, domin wanna hasashe naka ba mai yuwa bane Omar." Kallon ta ya yi ya ce, "Didi bana so kina ce min haka, wai ita wacece da zaki dinga cewa tausayi nake baki a kanta?." "Ita ba tsarar ka bace ba Omar, ita ba daidai da kai ba ce ba Omar." Kallon Didin ya ke yi na wani lokacin kafin ya ce, "Didi!." "Omar." "Bakya son abinda nake so ne?." "Omar Ina so mana." "Meyasa ki ke faɗar abinda ki ke faɗa indai haka ne." "Hmmm!" Didi ta faɗa a taƙaice bata ce komai ba. Omar ya ce, "kawai ki ta ya ni da addu'a." Didi ta ce, "Omar addu'a ko yaushe Ina yi maka ita ai, Allah ya baka abinda ka ke so in alkhairi ce." Shiru ya yi Disi ta ce, "kuma kaima ka dinga addu'a, kana da ƙoƙarin ibada na sani, amma ka ƙara daga yadda ka ke Omar. Ka cigaba da yaƙi da shaiɗan kana tashi cikin dare, wani lokacin shaiɗan yana galaba a kanka. Ni shiyasa nake son ka samu mace nutsatstsiya mai ilimi wacce zata cigaba da taimaka maka wajan bunƙasa ibadar ka." Kallon Didi ya ke yi har ta gama magana kafin ya ce, "oh kina nufin dai ban cikin masu ibada? Kina so ki ce mace ce zata saka na yi ko ta hana?." "Ni ban ce baka yi, in na ce baka ibada ai ƙarya nake yi. Ko a unguwar nan an shaida sallah bata wuce ka a masallaci, sannan ni shaida ce, tunda ni nake rayuwa da kai. Ko a gaban Allah zanyi shaidar kana da ibada daidai gwargwado. Ina so ka ƙara ne kawai Omar, amma batun mace zata saka ka yi ko ka bari wannan zai faru." Taɓe baki ya yi bai ce komai ba ya yi shiru, ya lura adawa take yi da Narma shiyasa bai tanka ba. Didi ta ce, "To a yadda ka ke ɗin nan Omar in ba dan kana ibadar ba ai da ban san ya zaka zama, Allah sai ya dubi maraicina ya taimake ni ya saka maka son ibadar a zuciyar. Malam Salahudden kuma shine sila, shi ya ɗora ka a kan hanya gashi yanzu baya duniya ka ɗore akan abinda ya ɗora ka a kai. Inda ace ibadar ma bata dame ka ba ai da yanzu ka kashe ni da raina." Ƙala bai ce ba, ya share ta yana kallon wani waje daban kamar ba da shi take maganar ba. ••••••• Nayla lokacin da Didi ta yanke wayar taji sallamar Omar hakan ya saka ta yin shiru tana sauke numfashi a hankali. Dawowar ta daga office kenan ta samu kiran wayar Didi. Tashi ta yi ta shiga banɗaki tayi wanka lokacin har anyi magrib, ta fito ta yi sallah sannan ta fito falo. Tana fitowa Auta ya tare ta ya ce, "Anty Nayla ki zo in ji Mama." Da to ta amsa tabi bayan sa zuwa ɗakin Mama ta shiga da sallama. Amsawa tayi tana kallon ta har ta shiga kafin ta ce, "Abiy ya ce a sanar dake kina da baƙo in anyi sallar i'sha." Nayla ta ce, "To" ta faɗa a sanyaye tana juyawa zata fita, Mama ta ce, "Nayla bakya son faɗa min damuwarki ko?." Nayla ta kulle ido ta buɗe ta juyo a hankali ta ce, "Mama ki yi haƙuri, ba na ƙi faɗa miki bane, kawai babu damuwar ne shiyasa."  Mama ta ce, "Shikenan jeki." Nayla ta fito zuwa falo ta zuba abinci tana ta jagalgala shi amma ta kasa ci. Daƙyar ta iya cin kaɗan kafin ta tashi ta shiga ɗaki ta zauna kawai babu abinda take yi. Cikin wannan tunani har aka yi sallar i'sha ta tashi tayi sallah bayan ta idar hijjabi ta saka kawai akan kayan jikin ta dan na shan iska ne ba canja kaya zata yi ba. Sallama akayi a ɗakin nata ta juyo taga Yaya da kansa ya kalle ta ya ce, "Nayla ga baƙon ki can a babban falo, ki yi sauri yana jiran ki." Kai ta ɗaga kawai bata ce komai ba. Ya kalle ta sosai ya ce, "Nayla wai me yake damunki ne?." Murmushin ta ƙaƙalo ta ce, "Yaya na gaji ne kawai, zaman office ko wahala." Dariya ya yi ya ce, "Yanzu kika fara aiki ai Nayla, maza ki zo yana jiran ki." A hankali take takowa zuwa babban falon gaban ta yana faɗuwa sosai. Da sallama ta shiga kanta ta na ƙasa ya amsa har ta ƙaraso ciki ta zauna. Kanta yana ƙasa ƙafarsa kawai ta iya gani ta haka ta fahimci a inda yake zaune. Nayla ta ce, "ina yini." Murmushi ya yi ya ce, "kin yini lafiya Nayla?." "Lafiya lau" ta amsa a taƙaice. "Ya aiki?." "Alhamdu lillah" ta sake bashi amsa tana wasa da hannun ta. "Ma sha Allah. Sunana Omar ...." Bata bari ya ƙarasa ba ta ɗago da sauri suka haɗa ido dashi. Saurin ɗagowar da tayi ne ya saka shi ya dakata daga maganar da yake yi yana kallon ta. Ajiyar zuciya tayi ta sauke ido ƙasa ganin ba wancan Omar ɗin bane suna ne yazo ɗaya. Murmushi ya yi ya ce, "me ya baki mamaki?." Kai ya girgiza alamun babu komai ya ce, "Sunana Omar Mansur Garkuwa, ni ɗan garin Kaduna ne iyaye da kowa nawa yana cikin garin nan. Amma Ina aiki da NCC a Abuja a can make da zama." Nayla jin sa take ba fahimta take yi ba, shi kam yana ta magana yana gabatar mata da kansa amma ba ji take yi ba saboda hankalin ta baya tare da ita. "Nayla!." Jin ya kira sunanta ta ɗago suka haɗa ido ya ce, "Ina sonki, auren ki nake da burin yi shiyasa na samu mahaifin ki da maganar ya ce nazo na same ki yau. Ina fata zaki amince dani." Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi." Murmushi ya yi ya amsa da amin ya ce, "ki saka min number wayarki" ya faɗa yana miƙa mata wayar. Karɓa tayi ta saka number ta miƙa masa wayar. Ya ƙarba ya ce, "na gode sosai Nayla, na gode da damar da kika bani." Murmushi tayi kaɗan kafin ya bata kuɗi ta ƙi karɓa tace ta gode. Babu yadda bai yi ba amma ta ce bazai karɓa ba dole ya haƙura ya ƙyaleta suka yi sallama ta koma cikin gida. A falon cikin gida ta tarar da Abiy ana zaune kamar ko yaushe shida Yaya da Yaya Jawad da Auta da kuma Jalila da Mama. Abiy ya kalle ta ya ce, "baƙon naki ya tafi?." "Eh Abiy, ya tafi." Abiy ya kalli Yaya ya ce, "A NCC yake aiki kuma bazai wuce sa'an ka ba, na san mahaifinsa a nan Kaduna suke gabaɗayan su. Familyn Mansur Garkuwa ne. Yaron babu laifi gaskiya, yana da hankali ana ta yabonsa sosai." Yaya yace, "Family Garkuwa Abiy? Lallai manyan mutane." "Sosai kam. Amma ni yadda ake yabon kirkin yaron ne ya burge ni ba familyn sa ba." "Ita samarin ma har sun yi mata yawa Abiy. Wannan shine na huɗu kenan fa, ga cousin ɗinta Abbas." Abiy ya murmusa ya ce, "bari kawai Babana, ka san bana son wannan yazo wannan ya tafi. Abinda ya jawowa Jidda aure ba tare da Nayla ba kenan" ya kalli Nayla ya ce, "Nayla bana son tara samari, bana son wannan saurayi yazo wannan saurayi ya tafi kema kin sani, kamar yadda na bawa wannan Omar ɗin dama zan bawa sauran dama a ciki ki zaɓi wanda ki ke so ki yi auren ki. In kuma Yayanki Abbas ki ke so shikenan." Nayla ido ya ciko da hawaye ta turo baki ta ce, "To Abiy." Yaya J ya ce, "ke dallah meye na wani hawaye?." Ta goge ido tana kallon sa, Abiy yana dariya ya ce, "Nayla ce fa. Tunda kin fara aiki Nayla aure zaki yi, in Abuja kika tafi sai a nemi transfer ki koma can, in Kano ne sai ki koma can, in a nan ne dai duk ɗaya." Kanta na ƙasa sai ajiyar zuciya da tayi, ta miƙe Jalila na ta tsokanarta, Nayla ta harare ta ta miƙe ta shiga ɗaki. Mama ta bita da kallo ba tare da ta tanka ba. Familyn Garkuwa kawai take maimaitawa a zuciyarta, ta ya zata bar Nayla ta auri ɗan Familyn Garkuwa?. Kaf wanda aka lissafa a cikin masu neman aurenta wallahi baza ta bari ta aure su ba, har cousin ɗinta Abbas bazata bar auren ya yu ba. In ma ta bari ta aure su taje ta huta kenan taji daɗin zaman aure, ai wallahi yadda bata ji daɗin zaman aure ba Nayla ma baza ta ji daɗin zaman aure ba, duk yadda zata yi zata yi don ganin Nayla ta sha wahala a gidan aure, baza ta bari a kai Nayla inda zata ji daɗi ba wallahi. In ta bar hakan ya faru mahaifiyar Nayla ta ci bulus kenan, ita ta wahalar da ita a gidan aurenta kuma sai ta bar ƴar cikinta ta ji daɗi...? Wannan ai ba abu ne da zai yu ba wallahi. Kai ta girgiza tana cize baki tana tunanin abinda ya kamata ace ta yi. ••••••• Thursday 10:00am       Didi kallon Omar take yi ganin ya sha kwallaiya cikin manyan kaya riga da wando da hula, ya yi matuƙar kyau kamar ba Omar ɗinta ba. Omar ya kalle ta ya ce, "Didi mun shirya sai Abuja." Didi jikinta gabaɗaya a sanyaye ya ke ta ce, "to Omar, Allah ya kiyaye hanya." "Amin. Don Allah ki daina sanyin jikin nan bana so." "Omar ji nake kamar akwai abinda zai faru wallahi, bana so ka tafi Omar." Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Babu abinda zai same ni, kar ki damu." Kai ta girgiza ta ce, "kai da wa zaku je? Kana da abokan da zasu raka ka?." "Ni ina da abokai ne? Sai dai yara su Bash." "Dasu Bashir ɗin zaku je?" Ta tambaya da mamaki tana kallon sa. Gira kawai ya ɗaga mata sai gasu sun shigo kowa ya ci manyan kaya, Bashir da Goje ne, daman sune na hannun damansa, ba kamar Bashir. Da kallo take bin su sai suka bata dariya ganin yadda suka yi wani iri dasu harda kwalli suka ranbaɗa su a lallai za a je gidan sirikai. Ganin Didi na dariya sai suna suka yi dariya dan sun fahimci canjin da suka yi take yiwa dariya. Didi ta ce, "lallai su Bashir an ci kwalliya. To ina Tukur? "Babbar Yaya ai baza a barki ke kaɗai ba." "Shi zai yi gadina kenan. To a mota zaku tafi?." Omar ya ce, "eh a mota zamu je." "Allah ya kiyaye" ta faɗa tana kallon su kafin su fita ita dai gani take wani abun zai faru dasu dukkan su. *Abuja.* Ana ta shirye shiryen tarbar in-law, Dad ko fita bai yi ba yana gida saboda tunda ya ga Narma tana matuƙar sonsa ya san ba ƙaramin mutum ta ɗauko ba. Ya gayyato Minister don tarbar sa suna zaune a falo suna hira. Narma ta ci kwalliya sai murmushi take yi, bata kawo matsala a zuciyarta ko kusa, a ganin ta tunda tana son Omar dan yazo gidan sunba abin damuwa bane ba. Narma ta sakko daga sama Mum ta bita da kallo tana murmushi ta ce, "my daughter, kin yi kyau." Tayi murmushi ta ce, "thank you Mum. Yau rana ce mai mahimmaci a wajena shiyasa nayi kwalliya."  Mum ta ce, "dukkan mu rana ce mai mahimmaci, ko haɗuwarki da Asharaf baki wannan farin cikin da ki ke yi yanzu ba." Jin Mum ta ambaci Ashraf sai ta murmusa kawai tana tuna yadda suka ƙare dashi jiya, yana jajjada mata wallahi sai ya aureta babu wanda ya isa ya aure ta in ba shi ba. Dad ne ya shigo yana kallon Narma ya ce, "Daughter bai zo bane?." Narma ta kalli Dad ta ce, "bai ƙaraso ba Dad." "Okay zamu yi sallah." Ta amsa Dad ya fita don su yi sallah. Su Omar basu suka shiga Abuja ba sai ƙarfe uku na rana, duk sun jigata saboda zama mota, kai tsaye hotel suka je suka kama ɗaki a nan suka huta zuwa la'asar suka yi sallah kowa ya sake gyarawa sannan suka nufi gidan su Narma. Lokacin da su Omar suka je ƙofar gidan Narma ya kira a waya ya ce mata gasu sun zo. Mai gadi ta kira a waya ta bashi umarnin buɗe musu su shigo. Mai gadi ya kalli su Omar bayan sun gama waya da Narma ya ce, "Hajiya ta ce ku shiga." Ya faɗa yana bisu da kallon mamaki. Yadda ake ta zuzuta su, tun safe aka ce musu za a yi baƙi ya ɗauka zai ga motoci sun cika estate ɗin sai ya gansu taxi. Buɗe musu ya yi suka shiga gate ɗin farko suka shiga na biyu. Narma ya gani a tsaye da alama jiran su ta ke yi,da sassarafa ta ƙaraso inda suke dan takalmin ƙafarta ma silifa ne, tana zuwa ta kalle shi da murmushi ta ce, "Barka da zuwa Faruk." Su Bash dai sunan tsaye suka yi, basu ɗauka inda Ogan nasu ya kawo kansa ya kai haka ba. Duk da sun san gidan, suna zuwa tare dashi wani lokaci. Kenan a gidan Sanata yake neman aure? Kuma wannan kyakykyawar budurwar ita yake so?. Gaskiya sun jinjina ƙarfin guiwa irin ta Omar, gashi babu damar magana balle su tanka, sun san halinsa. Narma ta ce, "mu je falon." Bayan ta suka bi tana tafiya tana yiwa ma'aikatan gidan faɗa, su kuma sai gaishe su suke yi suna ana bata haƙuri. A babban falon ta kalli Omar ta ce, "Dad sun je masallaci, tun ɗazu suna jiran zuwan ka baka zo ba, yanzu zasu dawo." Omar ya girgiza kai ya zauna ko ɗar a zuciyarsa baya ji. Yadda ya zauna ya harɗe ƙafa sai ka ɗauka Sen ɗin ne da kansa, su Bashir kallon ikon Allah kawai suke yi, basu ɗauka lamarin ogan nasu ya kai haka ba. Nan take aka cika gaban su Omar da abin sha da abin motsa baki. Narma ta fita ta koma cikin gida dan ta sanar da Mum zuwan su. Bash ya kasa haƙuri bayan ta fita ya ce, "Sai da kai Tiger, wallahi Madugu ƙwarin guiwar ka yana burge ni sosai. Allah ya bani ikon koyi da kai, Allah ya zamanin Jan wuya na mu." Omar bai ko kalle shi ba kaɗa ƙafa kawai yake yi, babu abinda suka taɓa abinda aka kawo musu. Su Bashir suna son cin koda Apples ɗin da aka ajjiye ne, amma waye ya isa ya taɓa bayan ga Boss a gefe bai taɓa komai ba? Sai dai kallon. Dariyar Dad suka jiyo suna shigowa falon shi da minister. Turus suka yi ganin su Omar a zaune a kan kujera suna kallon masu shigowa. Kallo ɗaya Sen ya gane Omar ya kalle shi da mamaki ya ce, "A'a Tiger, saukar yaushe? Zuwa babu notice?" Ya faɗa yana ƙarasowa fuskarsa ba yabo babu fallasa......... Senator ya haɗu da In law😂😂🫸🏼 *Book 1 free ne* *Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal* *VIP group 1k* *VIP2 on ArewaBooks.* *domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp* wa.me/2349030398006 wa.me/701 809 8175 Dm to subscribe yours. Nana Haleema❤️ *KIRAN RABO.* #Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11. *_Godiya ta musamman ga waɗannan mutane masu karamci, kirki, daraja da kuma alkhairi._* 1-Halimahz 2-Oum Nabil 3-Jamila Umar Janafty 4-Oum Mumtaz 5-Maryam Kitty 6-Aisha Muhammad Alto 7-Autar Manya 8-Mai Dambu 9-Maryam Jumare 10-Maryam Hadeja 11-Zainab Kano 12-Aunty Nice 13-Gureenjoh. _Ina miƙa godiyata a gare ku, Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya bar zumunci ya cikawa kowa burinsa na alkhairi amin._❤️❤️ *Book 1* *P 25.* Omar bai tashi tsaye ba kuma bai ce komai ba, su ma su Bashir ganin Boss bai tashi tsaye ba sai suka gyara zama. Sen ya ƙaraso yana bin su da kallo, ransa ya ɓaci ganin su a zaune akan kujera kamar wasu baki masu mahimmaci. Minister ya kalli Omar ya kalli Sen ya ce, "Ina baƙin da aka ce mana sun zo?." Sen ya ce, "to nima dai ban ga kowa ba, nayi tunanin zan ga Bakuwar mota a car park amma ban gani ba." Kallon su Omar ya yi ya ce, "ku jira ni daga waje zan gana da baƙi yanzu. Bana son irin wannan zuwan babu notice, ni ban san ma ya akayi aka bar ku kuka shigo ba wallahi. Mtsww..." Sai kuma ya ɗaga murya ya ce, "Auwal!." Da sauri wanda aka kira da Auwal ya shigo, Sen ya kalli su Omar ya ce, "kai su BQ, in na gama ganawa da baƙi sai su zo. A taƙaica waye ya bar su suka shigo? Irin waɗanan baƙin ba ni nake faɗa muku zuwan su ba?. Waye ya shigo da su?." "Hajiya Narma ce" ya bashi amsa da girmamawa. "Narma!" Ya maimaita cikin mamaki. "Itace.." Sen ya tafi tunani, ya kalli Omar ya sake kallon Auwal ya kuma maimaita sunan Narma. Omar da ya ke jinsa yake kuma kallon reaction ɗinsa ya murmusa ya ce, "babu wasu baƙi da zasu zo Sen, mu ɗin nan dai mu ne baƙin." Da sauri Sen ya juya yana kallon Omar ya ce, "ban gane ba." "Ba kana jiran zuwan sirikan ka bane?" Omar ya faɗa yana kallonsa kamar yadda shima shi yake kallo. Kasa magana Sen ya yi sai kallon Omar da yake yi cikin mamaki. Omar ya ce, "to ai ni ne." Sen ya yi ƙaramin tsaki tare da tamke fuska ya ce, "kai kar ka ga Ina wasa dakai, Ina baka damar zuwa gidan nan ko yaushe ka raini ya shigo tsakaninmu, ka tsaya matsayin da na baka. Ku tashi ku bar min falo!." Narma ce ta shigo falon ta ce, "Dad!." Kallon ta ya yi cikin fusata ya ce, "Ina baƙin naki suke? Sannan kece kika buɗewa waɗanan falon nan suka shigo?." Narma cikin shagwaɓata ce, "ni ce mana. Kuma Dad ai sune baƙin nawa, Tiger shine Faruk ɗina, your inlaw." "What!!" Sen ya faɗa da ƙarfin gaske yana kallon Narma da take kallon sa, ya kalli Omar da yake zaune har lokacin kamar falon babansa, ya kuma kalli minister da yake tsaye ya rasa ma abinda zai ce. Kallon Narma ya sake yi cikin wani irin yanayi ya ce, "kin san abinda ki ke faɗa kuwa? Are you out of your senses Narma?." "Dad da gaske nake, he's your son in-law." Sen ya nuna Omar da ya miƙe tsaye a lokacin bakinsa har rawa yake yi ya ce, "Wai wannan?." Narma ta ce, "yes Dad, I love....." Ai bata ƙarasa ba ya tsinke ta da marin da sai da ta koma ta daki bango. "Narma!!" Ya faɗa da ƙarfin gaske yana riƙe kafaɗunta ya jijjigata cikin fusata ya ce, "kalle ni, ki dawo hankalinki, ki kalli waɗanda suke gabanki ki daina furta min shirme. Narma ki dawo hankalinki!" Ya faɗa yana sake jijjigata da ƙarfi. Narma da ta dafe kunci tana kallon mahaifin nata cikin gigicewa, bai taɓa dukanta ba a rayuwarta ba sai a wannan lokaci. Omar da yake tsaye ya gaji da wannan surutun ya ce, "tana cikin hankalinta, da gaske take ni ɗin sirikin ka ne." Da wata irin fusace Sen ya juya ya nuna da yatsa Omar ya ce, "kar ka sake saka min baki, da ƴata nake magana" ya jiyo ga Narma ya ce, "faɗa min prank ki ke yi ko? Ko kuma April fools joke ne?." Narma in her trembling voice ta ce, "Dad it's not a pranks, da gaske nake maka ni na gayyato shi. Shine wanda ku ke zaman jiran zuwansa. He's my Faruk!." Muryar Mum Narma taji ta ce, "Narma what are you saying?." Ta kalli Mum da take tsaye tashin hankali ya gama bayyana a tare da ita, Narma ta ce, "Mum da gaske nake, shine Faruk ɗina, kuma shi nake so. Sannan....." Ai bata ƙarasa ba Sen ya sake tsinke ta da marin da sai tayi ƙara saboda shigarsa jikintq. Minister ne ya riƙe shi ya ce, "easy mana, control yourself. A kan wannan zaka dinga dukan Narma? Haba kamar ba kai ba" ya faɗa yana nuna Omar shima ransa a ɓace. Kallon Omar ya yi da yake tsaye ƙyam yana kallon su one by one. Sen ya girgiza yana nuna Omar ya ce, "meye ma sunanka?." Omar ya bishi da kallo cikin ko in kula ya ce, "ka fini sani." Sen ya kalle shi ya ce, "shaye-shayen da ka ke yi ya taɓa maka ƙwaƙwalwa ko?. Dan in ba mara hankali ba babu wanda zai yi abinda ka yi. Har kana da zarrar ɗauko ƙazaman ƙafafunka kazo gidana da sunan neman aure?. Na jima Ina jin ana cewa kawai mahaukatan da haukan su ya wuce ace musu mahaukata sai dai dadbobi, ban yarda ba sai yanzu. Look at you..." Sai kuma ya dafe kai ya rasa ma abinda zai ce. Narma da take kuka ta ce, "Dad ni ce na gayyato shi, kuma ni sonsa nake yi...." Maganar ta maƙale saboda zaburar da Sen ya yi zai yi kanta Minster ya riƙe shi, Sen ya kalle shi ya ce, "kana jin abinda take faɗa? Kana jin abinda take cewa?." Minster ya ce, "ba itace mai laifi ba ai, ga mai laifi nan a tsaye a gaban ka. Ita meye nata da zaka dinga dukanta? Shi zaka daka ai ba ita ba" ya faɗa yana nuna masa Omar da yake tsaye yana kallon su. Minister ya sake cewa, "Akwai abinda ya shirya shiyasa ya yi amfani da asiri wajan mayar da Narma haka, don't judge her Sen, bata san tana faɗa ba, it's the spell he cast on her that's working." Narma ta ce, "Ni bai yi min ko wanne asiri ba, ni ce na fara sonsa kuma har yanzu ina sonsa. Babu wani abu da ya shirya a kaina, yana sona kamar yadda nake sonsa" ta faɗa da ƙarfi tana daga inda take. Sen ya rasa abinda zai yi ya kalli Omar da yake tsaye yana kallon sa ya ce, "kai kuma ka san ƴata ce ka amince har ka ke sonta?." "Ga zahiri kana gani" Omar ya faɗa yana kallon sa kamar yadda yake kallon sa. Kasa magana Sen ya yi na wani lokaci kafin ya ce, "ƴar tawa ka zo nan da ka ce min kana so. Ƴata zaka yiwa asiri? Saboda na haɗa ka zama da ita a waje ɗaya shine ka samu damar yi mata tsafi?." Omar ya ce, "ƴarka zaka tambaya, in asiri nayi mata ma ta sani." "Shut up! Ina magana kana magana dan ka raina ni?." "Kaine ka haife ni?" Omar ya bashi amsa kai tsaye yana kallon sa kamar yadda yake kallon sa. "Ko a matsayin diver Narma baka isa ka zo ba, haɗa numfashin ka da na ta babban zunubi ne saboda tazarar ku kamar sama da ƙasa ne. Na baka ita ne saboda wani buri nawa har ka dinga yawo da ita a mota na wani lokaci, amma ba dan haka ba ko a mai aikin gidan nan baka isa kazo ba. Bana ɗauka mutum aiki sai yana da matakin diploma a karatu, kai kuwa fa?." Omar ya kalle shi ya ɗora yatsun sa biyu akan goshin sa kamar ko yaushe ya ce, "ban zo a mai aiki ka ba, amma nazo a sirikinka." Ai Sen ji ya yi kamar ya zuba masa ruwan zafi, jikinsa har rawa ya ke yi, ya zare ido ya ce, "me ka ke dashi? Waye kai a duniya?. Ko matsayin mai gadin gidan nan baka dashi, mai aikin gidan nan dukkan su graduates ne, meye matakin karatun ka? Faɗa min me ka ke dashi a duniya?.." Omar ya ɗan yi murmushi kalle shi ya ce, "abinda nake dashi ka ke so ka ji?" Ya kalli Narma da take wajen tana kuka ya sake kallon Sen ya ce, "zuciyar ƴarka, ita nake dashi." Fusata Sen matuƙa ya yi ya kai hannu kamar zai mare shi amma sai ya fasa yana jin zuciyarsa kamar ana zuba masa ruwan zafi saboda ɓacin rai. Minster ne ya ƙaraso yana kallon Omar ya ce, "Dan kaji last time na yabe ka sai aka ce maka ka kai matsayin da zaka zo gidan nan neman aure?. Kana da hankali kuwa?." Omar shima shi ya ke kallo ido cikin ido ya ce, "babu tabbacin kowa yana da hankali tunda ba ganin hankali sa ake yi ba." Sen ya zabura ya yi kan Omar Minster ya riƙe shi Sen yana cewa, "ka barni nayi maganin wannan mahaukacin, bar ni na kashe shi kuma na kashe banza wallahi. Ni zai dinga yiwa hauka a cikin gida? Kalle shi fa?." Minister ya ce, "ba class ɗin ka bane." Ya kalli Omar cikin ƙunar rai ya ce, "baka da maraba da dabba a idona, amfanin ka a gare ni na biya ka kaje ka sadaukar da rayuwarka domin cigabana da na ƴaƴana. Saboda wannan kawai nake nuna maka so a baki dan bai kai zuciyata ba, in ba dan haka ba baka ka kai ka ce kana son mai aikin cikin gidan nan ba. Jahili ne kai baka da ilimin komai, babu inda zaka je a rayuwa a haka zaka ƙare rayuwarka a gagari akan titi. Ko riƙe gidan ku baka iya yi, Yayarka itace take ciyar da kai ba kaine ka ke citar da ita ba. A haka ka samu zarar ratso cikin gidan nan ka ce kana son Narma!? Ka san wacece Narma?." Omar ransa ya ɓaci sosai, tunda aka fara maganar sai yanzu ransa ya ɓaci hakan ya saka shi zubawa Sen ido bai ce komai ba. Ganin ya yi shiru Sen ya ce, "Ni Senator ne, Mahaifiyar Narma tsohuwar ƴar majalisa ce. Narma lawyer ce, ta kai matakin masters a karatu, tana kuma riƙe da company guda a ƙarƙashinta. Tana juya biliyoyin kuɗaɗe wanda sai ta saka hannu kuɗin zasu fita. Tana aiki da babban kotun Nigeria, tana da ikon da zata yi ko wacce irin shari'a a faɗin ƙasar nan. Faɗa min kai waye?. Ɗan daba ne, mai garari akan titi, ɗan shaye-shaye, jahili, wanda bashi da ilimi balle a saka ran zai kai wani mataki a nan gaba?. Ko kana so kace ban san labarin uwarka hiv ce ta kashe ta ba...." Ai bai ƙarasa ba Omar ya damƙi wuyan Sen jikin sa na rawa. Narma da take gefe ta yi tsalle ta zo wajan, Nabil da Minster suke ƙoƙarin cire hannun Omar daga wuyan Sen amma sun kasa. Wani irin wuci Omar yake yi, ransa bai taɓi ɓaci a duniya kamar yau ba, bai taɓa jin tsanar abu lokaci ɗaya kamar tsanar Sen ba, bai taɓa ji zai iya aikata komai ba kamar yadda yake ji zai iya shaƙe Sen har sai ya daina numfashi. Daƙyar suka cire hannun Omar daga wuyan Sen. Sen yana fitar da numfashi daƙyar Omar ya nuna shi da yatsa ya ce, "ka san irin kalaman da zaka faɗa a kaina, in ba haka zaka fara dana sanin sanin Omar a rayuwarka." Minister mamakin ƙarfin halin Omar yake yi ganin ko tsoro ma shi baya ji. Har gidan Sen yazo ya shaƙe masa wuya kuma yana faɗar magana mara daɗi. Sen da ya kammala dawowa hankalinsa ya nuna ya ce, "kaine zaka yi dana sanin sani waye ni a duniya, zan nuna maka banbancin dake tsakanin aya da tsaƙuwa, zan nuna maka banbancin da yake tsakanin sama da ƙasa. A yau zaka tabbatar da ka tafka babban kuskure a cikin rayuwarka, zan shafe danginka kaf da kai kanka." Waya Sen ya ɗauko yana dannawa hannunsa har rawa yake yi saboda ɓacin rai. Narma ta riƙe hannu Omar tana ja cikin fitar hayyaci ta ce, "Faruk ka zo mu tafi, ka zo mu tafi kawai ni zan bika duk inda zaka kaini. Ni Ina sonka har yanzu kuma zan aure ka. Ka zo mu tafi, na zaɓi na zauna da kai akan zama a gidan nan." Marin ta Nabil ya yi, ya janye ta gefe tana kuka ya riƙeta gam yadda baza ta iya ƙwacewa ba. Omar ya kalli Sen muryarsa ta koma can ƙasa saboda ɓacin rai ya ce, "ka ce babu inda zan iya zuwa ko?" Sai ya girgiza kai ya ce, "zan tabbatar maka da zan iya kaiwa irin matakin da ka ke kai a yanzu, zan iya zuwa inda kai baka isa ka je. Abinda nake so da kai ka kasance a raye." "Har abada! Kai da zuwa irin matsayin da na taka a rayuwa har Allah ya tashi duniya. Ko da ace  a lahira ana mulki baka isa kayi irin abinda na yi ba, a lahirar ma baka isa ka zo inda nake ba. Aljanna ma akwai irin ta mu, akwai irin ta ku. In ka ci sa'a ka shiga aljanna ko a cikin ta baza ka hangi inda nake ba, na yi maka nisa mai tsahon gaske a lahira balle kuma a duniya. Kana jahili wanda ko jss bai kammala ba wanne mataki zaka je? A haka rayuwarka zata ƙare, daman domin ku yi mana amfani Allah ya halicce ku, kuma kun yi mana amfani rayuwar mu ta yi kyau. Sai kaje ka cigaba da zaman chamber ana shan wiwi." Kallon sa yake yi shima kallon sa yake yi, kowa ransa a ɓace yake ba kamar Omar da yake yi kamar ya murƙushe Senator. Sen ya ce, "Narma ba daidai dakai take ba, kar kayi mafarkin mallakarta a cikin rayuwarka domin daga yau zaman duniya bazai sake yi maka daɗi ba, zaka koma rayuwa irin ta gidan yari har ƙarshen rayuwarka. Zan iya kashe ka kuma na kashe banza wallahi, bana son aikata hakan ba dan ina tausayin ɗaukar ranka ba, sai dan nafi so wahala ta yi ƙasa-ƙasa da ƙasusuwan jikinka. Wahala da baƙin ciki nake so su ga bayanka ba bindiga ko wuƙa ba. Sai ka yi dana sanin wannan rana a rayuwarka, sai kayi dana sanin sanin waye Senator Sagir a cikin rayuwarka." Omar ya yi murmushi yana kallonsa ya ce, "wahala bata kisa, babu wahalar da zaka bani wacce zata kashe ni Sagir!. Babu inda zan je, zan kasance da raina, zan cigaba da rayuwa fiye da yadda na yi a baya. Zan kuma kai matakin da kai baka kai shi ba a rayuwarka, abinda nake so da kai kawai ka kasance a raye Sagir!" Ya faɗa yana girgiza kai yana kallonsa. A lokacin ƴan sanda suka shigo Sen ya kalle su ya ce, "yayi attacking ɗin kashe ni, sannan ya yi ƙoƙarin sace Narma. A tabbatar da rayuwarsa ta ƙare a prison" ya faɗa yana kallon Omar da shima shi yake kallo. Narma ta fincike hannunta daga na Nabil tayi inda Omar yake a gigice, Sen ya riƙeta gam tana kuka tana ƙoƙarin ƙwacewa tana cewa, "A'a Dad! kar ka aikata haka, ka ƙale shi don Allah. Ni nace yazo ba shi ya zo da kansa ba, ni ce nake sonsa Dad, ni nake so na aure shi. Don Allah kar ka yi masa komai Ina sonsa...!!" ta faɗa cikin kuka sosai tana ƙoƙarin fincikewa. Ƴan sandan wajan Omar suka nufo shi kuma kallon Sen ya ke yi, ya kalli Narma da take kuka ya sake kallon Sen ya ce, "zan tabbatar maka da abinda na faɗa, in har kana so ka tabbatar kar ka bari ka mutu! Ka kasance a raye, sai na shayar da kai mamakin da baka taɓa shiga irinsa ba a rayuwa." Sen a fusace ya ce, "ku tafi dashi daga gidan nan!" Ya faɗa cikin tsawa matuƙa. Kallon Narma Omar ya yi itama shi take kallo tana faɗin, "please Faruk!." Ɗauke kai ya yi daga kanta, ya sake kallon mahaifinta kafin ya girgiza kai akwai bai ce komai ba. Fita aka yi da su Omar aka saka su a mota, fitar motar daga cikin gidan ya yi daidai da zubewar Narma a ƙasa ta faɗi summiya. End of book 1! _To fa Book 1 ya tiƙe a nan!!. Ya ku ke ganin abin zai kasance? Omar zai auri Narma bayan duk abinda ya faru? Nayla fa? Omar zai aureta ko kuma zata cigaba da dakon soyayyarsa?. Burin Maman su Nayla zai cika ko bazai cika ba? Shin Omar zai kai matakin da ya faɗawa Sen ko bazai kai ba?. To wai meye asalin su Omar? Meyasa ya tsani danginsa? Meyasa ya tsani dangin uwa da uba?. Didi zata yi aure ko baza ta yi ba?. Wanne irin rabo ne zai kira Omar? Wanne irin Rabo ne zai kira Nayla? Wanne irin rabo ne zai kira Narma?._ _Duk amsoshin tambayoyin nan suna cikin Book 2&3, labarin yana da tsaho doguwar tafiya ce, zamu shiga jirgin book 2&3 ya lula damu cikin duniyar KIRAN RABO dan jin abinda zai kasance. Free ya ƙare book 2&3 naira 500 for regular group, vip kuma naira 1000 ne kacal. Akwai vip2 zai zo a arewabooks in sha Allah. domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp wa.me/2349030398006 wa.me/234701 809 8175 Dm to subscribe yours._ _Na gode da soyayyarku a gare ni da littafin nan, Allah ya ƙara zumunci. Allah ya sa ku nuna min ƙauna ku gigita ni da shiga paid group._😩❤️❤️ Nana Haleema❤️