[11/10, 1:25 PM] Bintu: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN ATTAJIRI* *NA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* ___ *MANAZARTA WRTS ASS* Pege 37&38 'Kamshi turaran ta ne ya sheda masa zuwan ta gurin. Cikin nutsuwa ya d'ago kansa daga barin karanta jaridar da ke hannunsa. 'Bata fuskarsa yayi yana yi mata wani irin kallo na tuhuma. Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba ta fara kokarin zama a kujerar dake fuskantar sa. A tsawa! ce ya dakatar da ita daga abinda take shirin yi. "Ka da ki sake ki zauna anan gurin.'' Ya fada yana zare mata gabad'aya idanuwansa yanda ya tsani mutuwarsa haka ya tsane ta Fatima tayi masa illah a rayuwarsa. Da hannu ya nuna mata hanya da fadin." Fita ki bani gurin tun kafin ranki ya 'baci." Ta girgiza kai still da murmushin a fuskarta ta ce." Ai ko babu komai ka tsaya ka saurare ni domin kaji da abinda nake tafe, idan ban ci albarkacin Shukura ba sai na ci arzikin zumuncin dake tsakaninmu." Tsaki ya ja ya koma ya zauna tare da cigaba da karanta jaridar dake hannunsa. Gurin yayi shuru na minti biyar kafin ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta kalle shi wani irin bala'in son sa na ratsa dukkan sassanan jikinta, ita ce tayi wauta a wancan lokacin, gashi yanzu yayi mata nisa tayi-tayi ta shawo kansa ta kasa, saboda babu wacce ya tsana sama da ita.'' "Maganar Shukura nake tafe da ita." Ta yi maganar idonta a kansa. Shuru bai d'ago kansa ba ballananta ya bata amsa. sai ta d'ora da fadin." Aiki na samo mata a babban kotun birnin tarraya ina fata ba zaka watsa min 'kasa a ido ba." Babu walwala a fuskarsa ya ce." Babu wani aiki da Shukura za tayi, buri na na ga na aurar da ita ga wanda ya da ce, saboda haka wannan maganar ki ajiye ta a gefe.'' "Me kake nufi kenan.? ta fada d'a b'acin rai a tare da ita. Ya ce." Ban amince da kud'irin ki ba." Sai ta fusata! "Amma dai ka san ba kai kad'ai ka ke da iko da ita ba ko? "Yes na sani da ni da ke muka haife ta amma abinda nake so shi za a yi idan kuma akwai matakin da zaki d'auka bisimillah." Fuska a tur'be ta mi'ke tsaye! "Shikkenan tunda haka ka ce zan nuna maka nawa ikon a kanta." Fuuu! ta bar gurin ranta a mugun b'ace! Dogon tsaki! ya ja ya bita da mummunan kallo har sai da ta fita daga gurin. Ya d'auke kansa yana jan ajiyar zuciya tare da tuno kuttun 'bakin cikin da ta k'unsa masa a can baya. ******* Da azama ta shiga d'akin sai dai me? tuntube tayi da ita a raku'be jikin dirowar gado ta hada kanta da gwiwa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya! Gabanta na fad'uwa ta ambaci sunanta a sanyaye ta ce." Shahida ba zaki fada min abinda ke damunki ba ko? kullum sai ki 'buya a daki kina kuka idan maganar Saminu ce ai ta mutu ki daina damun kanki mutu'kar ina raye ba zan bari mahaifinki yayi miki auran dole ba." Jin yanda take tausar ta da kalamai masu sanyi ya sanya ta sassauta kukan da take yi ta sa hannu ta goge hawayen dake gudana a fuskarta ta ce." Baba ba zaki iya magan ce min matsala ta ba, watakila ma idan na fad'a miki damuwa ta ki kira ni mahaukaciya, shiyasa na gwammace damuwar da nake ciki ta zama ajali na." Maganar ta doke ta sosai! kafafuwanta su kayi sanyi sai ta nemi guri ta zauna tare da fadin." Shahida wace irin damuwa ce wannan ? wacce har ki ke ikirarin ta zama ajalin ki, kada dai a kan mahaukacin mutumin nan ki ke nema ki kashe kanki."? Jin abinda Baban tace yasa ta 'kunshe bakinta da tafin hannunta domin ta hana kukan dake k'okarin kufce mata fita. Ta dinga girgiza kanta zafafan hawaye na sharara a fuskarta, murya a sar'ke da yanayin harshenta ta ce." Ki daina kiran sa da wannan sunan domin bai cancanta ba wallahi shi din ba mahaukaci bane kuma zan iya sadaukar da farin ciki na akan sa." Jikinta ya 'kara yin la'asar jin furucin da yarinyar tayi. ya kamata ta daina tsawwala wa domin ba ta san abinda Allah ya lullu'be ba amma babu shakka al'amarin yana bata tsoro mutu'ka! Ta ce.'' To na ji na daina kiran sa da mahaukaci ko zaki iya fad'a min abinda ya same shi domin tabbas ruwa baya tsami banza Shahida baki ta'ba shiga damuwa ta kwana da kwanaki ba irin wannan ko shakka ba nayi akansa ne." Hanci taja tana jin wani irin rashin dadi a tare da ita ta ce." Yau tsayin kwana goma kenan ban sanya shi a idona ba tun bayan korar da akayi masa daga mazauninsa shikkenan ban sake ganinsa ba, ko na je bakin kasuwar haka zan dawo gida gabad'aya ma mutane sun watsar da kayan sa a bola sai filin gurin tunda mai motar ya d'auke abar sa." Wani irin sanyi ta ji a zuciyar ta amma ba ta nuna a zahiri ba, sai ta shiga girgiza kai cikin alhini da damuwa ta ce." Ayya! Allah sarki shi yasa ashe kwana biyu na ga ba kya kai masa abinci ashe abinda ya faru kenan amma na tausayawa mutumin nan wallahi." Zuciyar ta ta 'kara yin rauni! kukan da take dannewa ya kufce! ta ce." Ni yanzu ban san ya zanyi ba zuciyata tana so ta gan shi ban san a wane hali yake ciki ba, ya kamata a taimaka masa." Kallon tausayi takewa yarinyar domin kuwa Allah ya jarabce ta da soyayya a in da bai da ce ba sai dai addua kawai. Ta ce." Ki share hawayen ki ki daina kuka insha Allahu zan taya ki da addua kuma zan sanya ayi miki saukar al'kur'ani a kan lamari idan da rabon zaku sake had'uwa sai Allah ya had'a ku a wani guri na daban." Hannunta ta ri'ke da fadin." Na gode Baba Allah ya saka miki da alkairi, insha Allahu nima zan dage da addu'a Allah ya bayyana mana shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." ******* "Alhaji Sammani mai leshi wani d'an kasuwa ne wanda ya kasance abokin hurd'ar Hujaj ta 'boye! shima yana caca kuma yana samun alkairai sosai yana kasuwancin ne kawai domin kawar da hankalin jama'a daga kansa. Tarin kud'ad'an da yake bin Hujaj ba za su lissafu ba, domin gabad'aya duniya ta juya masa baya komai nasa ya tsaya cak! sai buge-buge! yake yana yawon malamai k'auyuka da zaurukan malamai ba irin wanda bai je ba domin a duba masa me yake faruwa da rayuwar sa. Kimanin miliyan biyu da rabi Alhaji Sammani yake bin sa, kuma a wannan lokacin ya bu'kaci da ya bashi kud'insa domin yin wata bu'kata! Ya rasa ina zai tsoma rayuwarsa yayi nan yayi can fagau-fagau! ya zama wani shashasha! har ya fara surutai a hanya, shawarar da ya yanke shine sanya gidansa a kasuwa domin ya biya bashin kudin da ake bin sa! [11/14, 11:03 AM] Bintu: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* ______ *MANAZARTA WRTS ASS* Pege 39&40 To koda ya sanya gidan nasa a kasuwa bata canza zani ba. Domin kuwa duk dillalin da yazo ya duba gidan ba ya yi masa 'kima ta mutunci. duba da yanayin unguwar ta gargajiya ce. bayan haka kuma gidan irin ginin taka haye ne irin ginin 'yan kanci! duk fulastar ta zaizaye! ramuka ciki da wajan gidan, sannan kuma duka d'akuna uku ne sai tsakar gida madaidaici da kicin da band'aki. Wannan dalilin yasa gidan bai yi wani daraja ba. wanda yazo daga k'arshe ne ma yayi wa gidan 'kima ta mutunci ya saya miliyan daya da dubu dari biyu, amma duka na bayan sun taya ne a wula'kance! Ganin ba yanda zai yi ne ya sanya ya sallama a hakan, idan ya so sai ya biya bashin miliyan d'aya tare da alkawarin cika sauran a cikin 'yan kwanaki kad'an domin akwai wasu kudi da yake sanya rai a kansu duba da cewa malaminsa ya tabbatar masa da samuwar su. Alhaji Sammani ya nuna rashin amincewar sa akan hakan. A cewarsa ya za ayi yai masa wasa da dukiya duba da cewa shi a dunkule ya bashi, amma zai tsinka masa kud'i a cikin miliyan biyu da rabi an bashi miliyan d'aya mai zai yi da ita a wannan lokacin da yake bukatar kud'in masu kauri da zai yi order amma za a zo masa da wasa! ba tare da 'bata lokaci ya nufi police station. domin shigar da 'kara mutukar akan kudi ne baya saurarawa kowa ciki kuwa har da 'yan uwansa. "Alhaji Sammani ban yi tunanin za kayi min haka ba wallahi, yanzu ni ka kawo police station? na d'auka ai kai mai rufa min asiri ne a kowane hali. Alhaji Sammani me akayi akai miliyan biyu da rabi da har zaka tozarta ni." Murmushi yayi ya ce" Alhaji Jamilu ni kaina ban so hakan ba amma duk kaine ka janyo duba da ganin yanda kake min yawo da hankali alhalin na sheda maka cewa ga bukatar da zanyi da kudin nan. shin wai ko so ka ke ka talautani ne kamar yanda ka talauta kanka." Murmushin takaici yayi ya ce." Kana da damar da zaka fad'i duk abinda kake so, amma ka sani sai kayi nadamar abinda kayi min.'' Ya zakud'a kafad'arsa da nuna alamun bai damu ba ya ce." Kud'i na kawai nake bu'kata a yanzu gani a zaune ga kuma Yalla'bai shi zai zama shaida zan kar'bi miliyan d'aya ba don raina ya so hakan ba sai don samun maslaha a tsakaninmu, sabida haka ka fadi lokacin da zaka cikan kud'i na." Shuru yayi gumi sai karyo masa yake. D.P.O Ya ce." Alhaji Jamilu kai muke saurare." Kansa ya d'ago ido jawur! ya ce." karshen watan nan insha Allah zan biya Alhaji Sammani Kud'insa." D.P.O yayi rubutu cikin wata takarda ya bashi ya sanya hannu. Ya kalle shi da fadin." Wannan shine 'karshen magana Alhaji Jamilu, iyakar adalci anyi maka kada lokaci ya cika ka zo da wata magana, hukuma ba zata saurare ka ba idan baka cika al'kawari ba to zamu d'auki mataki na gaba." Ya ce." Babu damuwa Allah zai rufa asiri." Daga haka bai saurari jin wani abu daga gare su ba ya tashi fuuuuu! ya fita daga ofis din. Duk suka bi shi da kallon mamaki! **** A shirye ya fito ya same ta zaune a falo tana kallo. kafin ma yayi magana ta riga shi da fadin." Ranka ya dade ina son magana da kai." Tunda ya ji haka sai yayi murmushi ya nufe ta ya samu guri ya zauna tare da fuskantar ta. cikin zuciyarsa yake raya cewa maganar dai d'aya ce amma ba zai yi saurin yanke hukunci ba tukkuna. Ta gyara zaman ta da fadin." Hajiya Fatima ta kawo k'arar ka akan Shukura wai ta samo mata aiki amma ka hana shine nake so na ji dalili." 'Bacin ransa ya danne ya ce." Hajiya ki cire kan ki a cikin wannan maganar don Allah. domin ba ni da wannan ra'ayin, babban buri na shine Shukura ta samu miji nayi mata aure amma ni ba zan yarda da wannan tsarin ba." Ta ce." Sabode me? kenan karatun da tayi ya tashi a banza?" Ya ce." Bai tashi a banza ba mutukar za tayi amfani dashi ta hanyar da ta dace. nufi na anan shine ta tarbiyan tar da yaran ta sannan tayi biyayyar aure." Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Hakane kai ma kana da hujja amma ai har yanzu ba ta samu tsayayye ba, mai zai hana ka bar ta domin ta ci gajiyar karatun da tayi." Girgiza kansa yayi, alamun bai amince ba. ya dan kalli agogon dake daure a hannunsa ya ce." Wannan maganar mu bar ta kawai Hajiya kawai ki cigaba dayi mata addua'a." Ta ce." To shikkenan Allah ya za'ba mata miji nagari." Ya amsa da "ameen." Kallonsa tayi lokacin da yake kokarin tashi ta ce." Yanzu kuma ina ka nufa? kwana biyu dai na ga ka zauna a gida ka huta sosai na ji dadin hakan." Ya ce." Kano zan tafi amma iyakaci na kwana biyu zuwa uku zan dawo saboda akwai tafiyar da zanyi zuwa Swaziland insha Allah." Ta ce." To Allah yayi jagora ya tsare ka a duk in da zaka shiga. Sai dai ba zan fasa yi maka maganar aure ba, Alhaji Habu mutukar ka naso ka cika cikakken mutum to dole kayi aure idan ba haka ba to jama'a ba za su daina zargin ka ba." Murmushi yayi ya ce." Na kusa aure Hajiya insha Allahu kiyi min addua." Fuskarta cike da annuri ta ce." Alhamdulillahi haka nake so na ji to ubangiji Allah ya baka tagari.'' Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina." ******** Tsabar fargaba da tashin hankali ya haddasa masa matsanancin ciwon kai! wanda duk dauriyarsa sai da ya kwanta! hankalin Talatu ya tashi domin ko banza idan ya fita ya samo wani abu yana rage mata wata wahalar! ta shiga nan, ta fita can. yawon cin bashi domin samun abinda za su ci da yara. Ganin saura 'yan kwanaki wa'adin ya cika ya sanya ya yanke shawarar sanar da ita halin da ake ciki ko da taimakon da za tayi akan lamarin. Tashin hankali kenan! maimakon ta tausaya masa halin da yake ciki sai ta shiga surfa masa rashin mutunci da tsiya iri-iri da tozarci! a cewarta shi ya siyi hakan da kud'insa saboda haka ita babu wani taimako da za tayi masa domin shi kadai yake cin kud'insa hakkinta da na yara baya saukewa! saboda haka matsalarsa ce! a halin da ake ciki 'ya'yansa ne kawai suke tausaya masa domin sune suke jinyarsa! Talatu ba ta bi ta kansa harkokin gabanta kawai take. Jamila ce ta yanke shawarar zuwa ta fad'a mata halin da mahaifin nasu yake ciki na rashin lafiya, da kuma irin tashin hankalin da suke ciki. Kasa hakuri tayi hawayen takaici suka k'wace mata! ko shakka ba tayi fargaba da tashin hankali ne suka janyo masa ciwo! me za ayi da wannan hali irin na mahaifinsu, duniya ta sani suma 'ya'yansa sun sheda cewa abinda yake aikatawa haramun ne, anyi anyi dashi ya bari ya'ki! kullum sake tsunduma kansa yake a masifa! yau shine cin bashin wancan. gobe shine cin bashin wannan. kuma kudi ba kad'an ba! to yanzu dai yayi kankat! gidan da yake tutiya dashi ya sarayar dashi kuma bukatarsa ba ta biya ba, dama karshen kwad'ayi jin kunya! Mutumin da ya sayi gidan ya bada notice saura 'yan kwanaki, kana kuma ga wani can a gefe yana jiran miliyan daya da rabi wannan wane irin tashin hankali ne? Ido jawur! ta fito tsakar gidan da hijab a hannunta, Jamila na biye da bayanta itama kallo d'aya za kayi mata ka hango damuwa a tare da ita. Baba dake tsige alayyahu ya kalle su tana girgiza kanta, babu shakka ruwa baya tsami banza duba da yanayin fuskokinsu, bayan haka kuma ta zargi wani abu ne yake faruwa da mahaifin nasu duba yanda ta ji suna magana 'kasa-'kasa kamar ba sa so wani ya ji abinda suke tattaunawa. Cikin dushewar murya! da yanayin harshenta ta ce." Baba zan je na duba babanmu bashi da lafiya shine Jamila ta zo ta fad'a min." Cikin alhini ta ce." Allah sarki to ai ba kuka za kuyi ba addu'a za kuyi masa Allah ya tashi kafad'arsa ai cuta ba mutuwa ba ce; shin wai me yake damunsa ?" ta karasa maganar tana kallon jamilan dake kokarin mayar da k'wallar idonta. A sanyaye ta ce." Ciwon kai ne mai tsanani! amma da likita ya duba shi ya tabbatar mana da cewa jininsa ne ya hau?" "Allah sarki! ai abinda ake ta fama dashi kenan. Allah ya bashi lafiya." Gabad'aya suka amsa da "Ameen." 'Dari biyar ta mi'ka wa Shahidan da fadin." Kuyi kudin mota amma ki dawo da wuri kar ki bari dare yayi miki kin ji ko ." A sanyaye ta ce." Insha Allahu." Hanyar fita suka nufa ta ce." Jamila ki gaishe min da mai jikin kinji ko." Ta ce." Insha Allahu zan fad'a masa." Girgiza kanta tayi bayan fitar su, tausaya musu take na rashin samun nagartaccen uba! idan Jamilu bai yi hankali ba yanzu yaushe ne zai yi ? gashi Allah ya bashi zuria duk mata wannan shine abin dubawa. Lokacin da suka isa gidan yana bacci shi kadai a dakinsa, ita kuwa Talatu sai sabgoginta take, Hadiza bata nan ta je bikin 'kawarta, gidan a bushe 'kamas! yanzu ne Talatun take kujuba kujubar d'ora girki bayan ta je tayi fafutukar ciyo bashi a mak'ota! Babu arziki ta kalle su da fadin." Au! ita ki kaje kika jajibo me za tayi? ko kuma za ta iya biya masa bashin dake a bin sa ne." Ta ce." Haba Talatu wannan ba magana bace dani da Anty Shahida duk d'aya muke kuma itama tana da hakki na je na fada mata ne domin ta zo ta duba shi saboda yana matsayin mahaifinta. Tsaki! ta ja ta shige dakin girki ta bar su a tsaye a gurin da takaicin ta. To sai gefin magriba ya tashi daga baccin babu laifi da dama-dama jikin nasa. fitowa yayi domin daura alwala nan ya gansu a zaune a tsakar gidan sunyi jugum jugum! jikinsa ya k'ara yin sanyi! kunyar had'a ido yake dasu, da sauri ya dauki buta ya kama hanyar band'aki. Sai suka dinga rige rigen yi masa sannu! kansa kawai ya iya daga musu yayi saurin shiga band'akin Talatu ta bishi da zabgegiyar harara! "Baba ya jikin naka.''? Ba tare da ya kalle ta ba ya ce." Da sauki alhamdulillhi wanene ya fada miki bani da lafiya?" Ta goge hawayen da ya zubo a fuskarta ta ce." Jamila ce ta je ta fada min shine na ce bari na zo na duba ka, Baba Asabe ma ta ce ayi maka sannu.'' "Ina amsawa ai na ji sauki ki tashi ki tafi kada dare yayi." Ya fada yana dan kallonta ganin yanda take kuka sai abin ya bashi tsoro lallai baya shakka ta samu labarin abinda yake faruwa; sai kawai ya sunkuyar da kansa 'kasa ya san takaicin abin ke damun zuciyarta. Aikuwa ya tsinkayi maganarta. "Baba wace irin rayuwa ka jefa kanka a ciki? wace irin rayuwa kake so ka jefe mu a ciki shin wai baka tausaya mana ne?" Shuru yayi bai ce komai ba. Ta ja majina! tare da cigaba da cewa ." Gabadaya ka zubar da kima da mutumcinka a gari, babu wanda bai san irin harkar da kake ba, shifa arziki na Allah ne, wallahi ubangiji ba zai ta'ba azurtaka da haram ba! ko ya azurtaka din 'karshen nadama da jin kunya! shin meye ribar abinda kake? gashi ka jefa kanta cikin masifa da bala'i ka jefe mu a ciki, a yanzu ina muka ga miliyan daya da rabi? babban tashin hankalinmu wannan gidan da ya rage maka shima ka sarayar dashi yanzu da mu da kai ina zamu kama?" [11/17, 8:09 PM] Bintu: _••MAJNUN!••_ *'BOYAYYAN ATTAJIR!*🛩️ ~~~~~ *NA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *MANAZARTA WRTS ASS* ~~~~~ Tukwici ne gare ku mutana ne💕 _*1-AUTAR MANYA*_ _*2-ZEEY KUMURYA*_ _*3-AYSHA BARNO*_ Pege 41&42 Cike da fuffuka! irin wacce ya saba ya nuna ta da yatsa da fadin." Kada ki yi min maganar banza da wofi mana; don uwaki ni za ki zauna kina tsarawa magana, ke din guda nawa kike? me ki ka sani a rayuwa da har zaki zo kina kawo min 'kabli da ba'adi, to wannan shine gargadi na dake na karshe! kada wani abu ya sake faruwa ki zo kina min wasu zantuka ranki sai yayi mummunan 'baci! wallahi." A sanyaye ta ce." Kayi hakuri Baba." tsawa! ya daka mata ya nuna mata hanyar fita da fadin." Fita ki bani guri shashasha kawai." Da sauri ta fito tana share hawaye! Talatu ta ja tsaki da fadin." Aikin banza yarinya kina wahalar da hawayenki a wofi wannan mahaifin naku ai ya riga yayi nisa domin ba zai ta'ba gane hanya ba, don haka kowacce ta nemi madafa don duk wanda ya dogara da Jamilu 'bacin rai ne zai kashe shi." Hadiza ta ce." Talatu duk lalacewarsa ubanmu ne babu yanda za mu yi dole mu shiga damuwa." Ta ce." To ai sai ku yi karo karo ku biya masa bashin da ake bin sa shashashai kawai ana nusar da su suna baud'ewa." To in ban da rigima irin ta Talatu ya za suyi ? za su je su rufe shi da duka ne? ai ya riga ya gama yi musu illah! a rayuwarsu dole kuma suyi hakuri su cigaba da yi masa addu'a domin ba a canzawa towo suna. A na kiran sallar isha'i mai adaidaita sahu ya sauke ta a bakin titi. Kud'insa ta bashi ta fara kokarin tsallaka titin da nufin shiga layinsu, dan gabadaya Hankalinta yayi gida ganin garin yayi duhu, gashi babu wani cikkaken haske akan titin. tana kokarin tsallakawa kawai ta ji ana jan gefen hijab d'in ta. A razane! ta juyo sai tayi saurin ja da baya tana kallonsa gabanta na wani irin fad'uwa! Yana nan yanda yake sai dai an samu sauyin tufafi a jikinsa, amma fuskarsa tana nan cike da 'kasumba sumar kansa ka a cukurkud'e! Yana sanye da tazarce na shadda bulu sai dai ta kod'e sosai tayi haske sai wani takalmi sosa a kafarsa shima ya sud'e! amma babu datti a tare dashi. Murmushi kawai yake mata yayin da yake mata wani irin kallo. Ita kuwa gabanta sai bugawa! yake tana kallonsa tana so ta tabbatar da cewa shine ko kuma aljani ne domin al'amarin ya 'bata tsoro mutuka! Maganarsa ta dawo da ita hayyacin ta. "Shahida ni ne Baban-baba kina mamakin gani na ko?" da d'an k'arfi yayi maganar saboda ya san lalurar ta. Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke har yanzu da ragowar tsoro a tare da ita ta ce.'' Baban Baba kai ne da gaske ko dai idona ne yake min gizo." Ya sake matsowa kusa da ita a nutse ya ce." Ni ne dai masoyinki na san kin yi kewata ko? nima ina can hankali na yana kan ki." Wasu hawaye masu zafi suka 'kwace mata ta ce." Alhamdulillahi Allah Na gode maka daka 'kar bi addu'a ta." Yana murmushi ya ce." Ai d'azu akan idona kuka fito tare da wata abokiyar ki sai na ga fuskokinku cike da damuwa! ganin haka ya sa jiki na yayi sanyi na ce lallai akwai abinda yake faruwa, wannan dalilin ya sa na ce sai na zauna na jira dawowarki kafin na tafi." Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta. Ya dan sake matsowa daf da ita da fad'in." Ko ba zaki iya fad'a min damuwarki ba."? Ta kalle shi tana girgiza kai. Ya tausasa murya da fadin." Ina sauraranki ki sanar dani abinda yake faruwa domin ganin ki cikin damuwa da tashin hankali ya sanya ni cikin wani hali." Ita dai a tsorace take dashi dan sai waiwayen bayanta take. Shima ya fahimci hakan ya ce." Kina jin tsoro na ko."? Zuciyarta ta karye sai kawai hawaye suka shiga gangarowa ta sanya hannu tana sharewa wasu na biyo baya! sai jan majina take. Wani irin ciwo zuciyarsa take masa. tuntuni ya tsani zubar hawayen ta ita ce ba ta fahimci hakan ba. Ya rasa yanda zai yi a gurin yana jin kamar ya rungume ta ya rarrashe ta, sai dai ya daure ya shirya kalaman rarrashi ya fara kwantar mata da hankali har ya samu ta daina kukan. Ta kalle shi; nan ta fahimci cewa yana cikin damuwa da kukanta, sai ta sassauta fuskarta ta d'an yi kasa da kanta ta ce." Ka fara fad'a min ya akayi rayuwarka ta sauya ? wani almajiri dai ya tabbatar min da cewa an tashe ka daga gurin da kake rayuwa to tun daga lokacin ba a 'kara ganin ka ba. shin dama kai din ba mahaukaci bane?" Murmushi yayi, ya ce." Ni ba mahaukaci ba ne Shahida." Da sauri ta kalle shi tana mamakin furucinsa, koda yake ba abun mamaki bane a gurinta tunda dama can ita ba ta yi masa wannan kallon. Ya cigaba da cewa " Rayuwa ce ta mayar dani haka amma yanzu alhamdulillhi na gode Allah tunda ya mayar min da alkairi ya had'a ni da uban gida wanda ya dauke ni aiki a garin abuja, ina masa gadin gidansa ni nake kula da masu shiga da fita! wannan shine ya sauya min rayuwata na dawo cikkaken mutum kamar kowa tunda bani da fargabar ci da sha da kuma gurin kwanciya komai ya d'auke min, nutsuwa ta zo min ban yi tunanin kowa ba sai ke domin ina ganin zaki iya amincewa mu rayu a inuwa d'aya." Hannu tasa ta rufe fuskarta kunyarsa ce ta rufe ta. Ya raunata murya da fadin." Ko kina ganin nayi miki tsufa ne? ko kuma kina gudun kada 'yan uwanki da 'kawayenki su yi miki dariya."? Hannunta ta cire tana girgiza kai ta ce." A'a wallahi bana shakka kuma bana jin kunyar mutane su gan ni tare da kai! so na gaskiya nake maka, kuma wallahi zan iya rayuwar aure da kai a cikin kowane hali, ina rokon Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninmu." Ya amsa cike da walwala da farin ciki. Ya ce." To yanzu ya za a yi nayi magana da mahaifinki domin jibi nake so na koma bakin aiki na." Shuru tayi tana Nazari! Ya ce." Shahida akwai matsala ko?" Kanta ta d'aga murya a sanyaye ta ce." Mahaifi na yana cikin matsananciyar damuwa da rashin lafiya! gashi bama jituwa da juna kullum cikin yi min tsawa! yake tunkararsa da wannan maganar zai yi wuya domin bashi da fahimta, ita ma Baba Asabe tana da tata matsalar. Ya ce." Ko zan iya sanin matsalar."? Shuru tayi tana jin nauyin fad'a masa! dole duk d'an halak yayi kishin iyayansa. Ya ce." Ki daina shakkar fada min damuwarki Shahida ni dake mun riga mun zama d'aya." Shuru tayi ta kasa magana. Ya d'anyi murmushi da fadin." Ki fad'a min kada kiji komai, ni mai rufa miki asiri ne a kowane yanayi." A sanyaye ta fara bashi labarin abinda yake faruwa. Shuru yayi na minti uku kafin ya ce." Ina ganin wannan ba a abun damuwa bane insha Allahu, ni zan yi iyakar bakin 'kokari na akan al'amarin ina da alfarma sosai a gurin maigida na zai nemi alfarma a gurinsa insha Allah ba za ku tozarta ba." Ta ce.'' Kudin fa suna da yawa." yayi murmushi da fadin." Ba zai gagara ba insha Allahu rabbi.'' Ta dinga kallonsa ta na tunanin yanda za ayi har a samu a biya wannan kudi masu yawa, to amma tunda ya ce Allah ya gama magana. Har 'kofar gida ya rakata suna tafe suna hira ta fahimtar juna sosai ta saki jikinta dashi, ta kuma samu sassauci a kan fargaba da tashin hankalin da take ciki. Sai dai har yanzu tana mamakin sauyawarsa. Cike da farin ciki biyu ta shiga gidan. Sai kawai ta riske su a tsaitsaye a tsakar gidan har da kawu Musa a cikinsu, da alama akwai maganar da suke. Gabanta ne ya fadi! ganin fuskokinsu babu walwala ko kad'an! Kafin ma tayi magana ya rufe ta da fada! ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Sai kawai ta fashe da kuka ta durkushe a gurin tana shashshe'ka! Baba Asabe ta ce." Ka kyale ta haka tunda dai Allah yasa ta dawo lafiya shikkenan magana sai ta wuce." Ya ce." Idan gidan uban nata take so ta koma ai sai ki had'a mata kayan ta, amma idan ba haka ba mai zai sanya ta dinga wahalar damu, kawai ina zaman zamana an taso ni a tsaye 'karfe goma na dare idan ba shashashan uba ba waye zai bar 'yar sa tana gantali a hanya irin haka." Ta ce." Na ce ya isa haka don Allah kada mak'ota su ji abinda yake faruwa, tunda dai ta dawo magana sai ta mutu." 'Kwafa! yayi da girgiza kai ya kalle ta da fadin." Ni zan tafi gida sai da safe." Ta ce." To Allah ya tashe mu lafiya" Ya kama hanya ya fita da takaicin abin a cikin ransa. Saliha kuwa bayan fitarsa tsaki ta ja ta shige daki tana surutai! Ya rage da ita sai Baba Asabe a tsakar gidan. Ta ce." Ai sai ki tashi kuma kukan da kike bashi da amfani domin sai da na ce miki kada kiyi dare duba da yanayin garin da kuma lalurarki idan shi Jamilun bashi da hankali to mu muna dashi" Cikin b'acin yanda suke cin fuskar mahaifinta ta ce." Baba ku daina daukar alhakinsa haka don Allah." Sai ta ri'ke baki da mamaki a tare da ita ta ce." 'Karya akayi masa kenan?" Girgiza kai tayi ta ce." Tuntuni na dawo fa babu ruwan Babanmu shine ma ya ce na tashi na tafi kada dare yayi min." Ta ce." To a ina kika tsaya har goma na dare." Kai tsaye ta ce.'' Ina tare da Baban Baba." Gabanta yayi mummunan fad'uwa!" Baki na rawa ta ce'' Baban-Baba kuma?" Ta amsa da "Eh." tana kokarin tashi tsaye. Ta cigaba da cewa." Ya zo ne saboda ni, kuma mun tattauna maganganu masu muhimmanci! wallahi Baba baki ga yanda rayuwarsa ta sauya ba dama na ce miki ba mahaukaci bane." Baba Asabe jikinta yayi sanyi sosai kawai ta dinga kallonta ta gaza cewa komai, mamaki da al-ajabin al'amarin kawai take. A daran ranar dai da 'kyar Baba ta iya rintsawa tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki na al'amarin yarinyar da wannan mutumin da take zargin wani abu a kansa. Mamakin ta ya kara tsananta lokacin da Shahidan take sheda mata irin maganar da suka tattauna dashi. wato Maganar aure da kuma taimakawa mahaifinta da zai yi." Ta kalle ta da fadin." Shahida anya kina da hankali kuwa.? Kafin tayi magana Saliha ta kyalkyale da dariya da fadin." Ras! take tsabar iskanci ne wallahi! amma Baba ki kyale ta kawai jiki magayi ta je ta aure shi jikinta zai gaya mata." Baban ta girgiza kai da fadin." A'a Saliha ba za ayi haka da ni ba, domin yarinyar nan amana ce a hannuna ban bari ta an aura mata Saminu abbatuwa ba to kuwa ba zan bari ta auri mahaukaci ba." A hankali suke maganar dan kada ta ji." Ta kalle su ranta a masifar 'bace ta ce." Baba na san duk kokarin ki kada nasha wahala a rayuwa! wallahi nayi imani da Allah mutumin nan ba zai azabtar dani ba, yana sona ina sonsa mai zai sanya ki dinga mugun tunani akan al'amarin, ni dai mutukar kina so ki ga farin ciki na to ki amince da abinda nake so kuma ki bini da addu'a. Sai kawai tayi shuru tana kallonta gabadaya jikinta ya mutu ta rasa yanda za tayi ta kamo bakin zaran. [11/25, 10:02 AM] Bintu: pege 43&44 "Ranka ya d'ad'e wannan mutumin da ka sa nayi maka binkice a kansa har ila yau magana d'aya ce kamar dai wancan lokacin; ma'kotansa da jama'ar unguwa ba su ba da kyakykyawar sheda a kansa ba, duk wanda zai bud'e baki yayi magana baya fad'in alherin sa, ranka ya da'de wannan shine labarin da nasa mu a kansa cewa d'an ca-ca ne wasu ma suna zargin yana harkar bariki." Cikin ladabi ya 'karasa maganar da yake tafe da ita. Jaridar dake hannunsa ya ajiye a gefansa, ya mayar da hankalinsa gare shi ya ce." Sule ka tabbatar da Gaskiyar maganar nan? kasan duniya ta lalace mutane basa kunyar sharri! yarda da amincewa ne yasa na sanya ka gudanar min da wannan binkicen, ba naso daga baya wata magana fito." "Ranka ya dad'e hakane wallahi ba za a ta'ba had'a baki dani a cutar da kai ba, duk maganar da na fada gaskiya ne akan Hujaj sai dai ma'kotansa sun bada sheda arziki akan mahaifinsa, sun tabbatar min da cewa shi mutumin kirki ne domin har ya rasu bai ta'ba aikata alfasha ba." Ya ce."To godiya nake Sule za ka iya tafiya." Har ya niyyar tashi sai ya koma ya zauna yana d'an shafa 'keyarsa tare da sinne kai. "Sule Ya akayi ne? da alama akwai magana a bakinka ." 'Dan murmushi yayi ya ce." Ranka ya dad'e na jima ina mamakin al'amarin tun a karon farko da ka sanya ni wannan aikin, sai nake tunanin wani abu, na ce kodai mun kusa samu uwar d'aki ne?" Maganar ta sanya shi dariya ya ce." Sule ai na d'auka za ka bukaci zuwa gida ne domin dubo iyali ashe ba hakan bane.?" Da murmushi a tare dashi ya ce." Da wannan maganar ma Alhaji amma ina bu'katar ka bani wannan amsar idan babu damuwa." Shuru yayi na minti biyu kafin ya ce." Hakane maganar ka Sule, yarinyar mutumin nan nake so na aura insha Allahu." Da walwala a tare dashi ya ce." Ma sha Allah Alhamdulillhi ranka ya d'ade Allah ya sanya alkairi yasa za ayi damu Allah kuma yasa abokiyar arziki ce." Ya amsa da "Ameen suma ameen." Shuru gurun yayi na minti biyu kafin ya ce." Amma Alhaji baka ganin hakan zai janyo maka wata matsalar duba da cewa uban yarinyar bashi da kirki! akwai ma'kiya wad'anda suke jiran 'kiris su samu abun yayatawa a gari." Murmushi yayi ya ce." Sule kada ka damu da hakan, insha Allahu alkairi ne zai biyo bayan al'amarin, ba mu nufi kowa da sharri ba, duk wanda ya nufe mu dashi to babu shakka sharrinsa zai koma kansa." Ya ce." Wannan haka yake fatan alkairi Alhaji tabbas idan hakan ta kasance za mu fi kowa farin ciki." "Ma sha Allah." Abinda ya fada kenan; ya dauki jaridar da ya ajiye ya dan kishingida kan kujerar da yake zaune, ya ce." Ina fatan ka shedawa Labaran cewa bayan sallar la'asar za mu fita." Yana k'o'karin tashi ya ce." Eh Alhaji na sheda masa umarinka tuntuni." To bayan fitar Sule da minti goma kira ya shigo wayarsa. Koda ya ga wanda yake kiran sai ya ajiye ya cigaba da abinda yake. Sai da ta kira sau uku tukkuna ya daga, shuru yayi bai ce mata komai ba. "Daddy ina kwana." ta fada cikin rawar murya. A dakile ya amsa. Sai ta fashe da kuka tana bashi hakuri "Daddy don Allah kayi hakuri ka ji." Gyaran murya yayi babu walwala a tare dashi ya ce." Shukura kin zama mara ji ko? Fatima ta na yi miki hud'ubar banza kina dauka, kamar ni ubanki na baki umarni ki tsallake! ki fita ba tare da izini na ba, har na fita baki dawo ba shin me kike so ki zama?" A sanyaye ta ce." Daddy wallahi ba 'kin bin umarnin ka nayi ba, tsoro nake na fad'a maka gurin da zan je, na san ba zaka bari ba shiyasa na tafi amma ai Hajiya ta sani na fad'a! mata. "Shukura saboda kin san bana tsallake maganar Hajiya shiyasa ki ke had'a ni da ita ko?" "Ba haka bane Daddy." Ya ce." Nayi 'karya kenan." "A'a Daddy ba kayi 'karya ba kawai dai na ga itama Mamana tana da hakki a kaina babu laifi idan na je in da take." Ya ce." Ok to ki tattara kayanki gabad'aya ki koma gurinta kada na dawo na same ki a gidana." Tana kuka take bashi hakuri! Ya ja tsaki! da fad'in." Wallahi kiyi hattara da wannan uwar taki bata da kirki! sannan magana ta dake ta 'karshe shine kiyi gaggawar fito da mijin aure a cikin masu sonki domin ba zan lamunci sakarci ba." Yana gama maganarsa sai ya kashe wayar ya ajiye ransa a 'bace! Shiru tayi da wayar a hannunta tana tunanin abinda zai biyo baya, ta san halin mahaifin ta kaifi daya ne, baya magana biyu, mutum ne shi da bai yarda da shiriri ta ba, ita kuwa a yanzu dai babu wani wanda zata nuna a matsayin wanda za ta aura domin har yanzu ba ta samu wanda yayi dai-dai da rayuwarta ba, tunani mai zurfi ta shiga domin nemo hanyar warware matsalarta. **** "Baba yau fa zai zo da daddare ku gaisa sannan kuma mu je da shi can gidanmu su gaisa da Babanmu domin gobe yake so ya koma gurin aikinsa." Ta ce." Waye zai zo?" domin ita har ga Allah ta manta da maganar da sukayi da safe. Ta d'an 'bata fuska da fadin." Har kin manta ko?" Girgiza kanta tayi ta ce." Ke shahida magana mai muhimmanci ita nake ajiyewa a cikin raina domin abubuwan da suka dame ni suna da yawa." Ta 'karasa maganar tana kokarin kwance lalitar dake d'aure a k'ugunta. Sunkuyar da kanta tayi idonta yayi ja! alamun ranta ya 'baci! Ita kuwa Saliha dariya kawai take mata tana 'yan 'kananun maganganu wanda ta san ba za ta ji ba. Wutar nepa a ka kawo Saliha da sauri ta kunna musu fanka domin zafi ake a garin. Ita kuma Shahida ta je ta dauko hijaban ta domin ta goge. Ta kalle ta da fadin." Kin san dutsen gugar nan yana da jan wuta Shahida da ki bari na gama kallon labarai idan an gama sai kiyi gugar ki." Ta ce."Baba idan su ka dauke wutar fa.''? Ta ce." A'a ba zasu dauke ba insha Allahu, ke Saliha kunna min talabijin din NTA KANO zaki kai." Ta ce." To." da sauri ta janyo 'yar yawo (cover socket) ta jona kayan kallon tana kokarin gyara Area domin hoton ya fito. Shahida d'aki ta shiga ta kwanta ta shiga tunanin masoyinta. An gama labaran, 'karshen kawai suka riska. A in da mai gabatarwa yake fad'in kanun labaran 'karshe, cewa wannan Attajirin d'an kasuwar Alhaji Saddiku wanda aka fi sani da *'Dan gaske* zai yi rabon shinkafa a babban company sa dake sharad'a, za a fara rabon abincin da karfe hudu har zuwa karfe goma na dare. Baba Asabe ta ce." Wannan karon ma sai na je ko Allah zai sa na da ce." Saliha ta ce." Da rabon kiyi asarar kudin motarki, har kin manta 'bakar wuyar da ki kasha a wancan lokacin" Ta ce." Wuya ai mai shigewa ce 'yar nan a wannan zamanin shinkafa 'yar gwamanti babban buhu ai ko kwana zanyi a gurin ba zan damu ba mutukar zan samu, saboda haka yanzu ma zan tashi na shirya sai ki kula da masu shige da fice. Girgiza kanta tayi a zuciyarta ta ce." Wanda ya 'ki sharar massalaci ai yayi ta kasuwa! samun shinkafar nan ai sai mai tsananin rabo. "Baba ina za ki je kuma?" ta fada tana kokarin tashi zaune. Tana gyara hijab din dake wuyanta ta ce." Unguwa zani amma ba zan dade ba insha Allah." Ta ce." To don Allah kiyi sauri ki dawo kada kuma ya zo ba kya nan." "To." kawai ta ce ta kama hanya ta fita da sauri tana mamakin wautar yarinyar. **** Gurun cike yake da mata da maza dattijai da matasa matan aure kai harda 'yan mata, dama irin wannan na faruwa mutane babu uzuri sai su tarkato 'ya'ya da jikoki a zo a bi layi kowa kansa ya sani idan kai ka samu ba zaka bari d'an uwanka ya samu ba, wannan shine abinda yake cutar damu wato son kai. Gurin yayi cikar kwari! hayaniya ce kawai take tashi wasu ma fad'a suke yi akan bin layi mussaman mata wasu babu kamun kai! don ma da akwai masu tsaro (securities) da abinda za ayi a gurin sai yafi haka. Duk yana kallon abinda yake faruwa ta cctv camera ya umarci yaransa cewa su je su raba number kowanne ya san matsayinsa lokaci yana cika afara rabo." Abinda ya faru kenan mutum goma ke raba number 'bangaran maza mutum biyar 'bangaran mata mutum biyar. Baba Asabe dai ita ce ta dari hud'u da talatin da shida😂 ta tambayi cewa ita ce ta nawa ? ya fada mata cewa sai an bawa mutum dari hudu da talatin da biyar kana za a zo kanta, amma bata sare ba! ta gyara tsayuwarta a gurin tana adduar Allah yasa tana da rabo. Wasu na fita wasu na shigowa haka ake ta turmutsutsu! a gurin, duk wanda rabo ya zo kansa ana bashi yake jan buhun ya fita daga gurin da yake kan titi ne abun hawa baya wuya. Gefin magriba ya sauko 'kasa yana sanye da farin yadi dinkin tazarce, yadin mai taushi ne wanda kallo d'aya zaka san mai tsada ne, kansa sanye da hulu zannar bukar mai adon bakin zare da ja! kafarsa sanye da bakin takalmin mai gidan yatsa. bai yarda ya fito haka ba sai da ya sakaye idonsa da farin gilashi. Da sauri Sule ya je ya bud'e masa mota! tunda ya ga ya fito ya san fita za su yi. Duk saurin Sule sai da wasu daga cikin mutanan dake gurin suka ganshi. Kafin ki ce kwabo sun yanyame! motar! wani za'kwa'kuri a cikinsu ya 'bude murya sosai dan da alama maro'ki ne ya fara yi masa kirari. "Damuna uwar albarka." Alhaji Saddiku mai dubun nasara! kai ne 'ki gudu sa gudu mazan fama! Allah yayi maka arziki muna amfana dashi! Allah ya 'kara suturtaka *'DAN GASKE!* 'Dan da aka haifa da kyakykyawar Aniya." Da murmushi a fuskarsa yake d'aga musu hannu cikin nuna alamun jin dad'in addu'onin da suke masa! Sule da Labaran suna ta k'ok'arin ganin sun kori mutanan da sukeyi dafifi a jikin motar, da 'kyar suka matsa sannan ya samu ya shiga motar ya zauna amma duk da haka hannu yake daga musu cike da jin dadin adduarsu. Motar tana daf da fita ya hangi dattijuwar matar da ba zai ta'ba mance fuskarta ba. tana tsaye ita ce a kusan 'karshen layi. Baba Asabe ganin yana kallon gurin da suke da sauri ta daga masa hannu tana fadin." Alhaji Allah yayi maka albarka hakika kana aikata alheri muna rokon Allah ya kai mizani, Allah ya yi wa dukiyarka Albarka." Ya amsa da "Ameen ya rabbi." Ya kalli Laraban da fadin." Ka fita ka samu daya daga cikin yaran dake wannan aikin, cewa su ware Dattijawa maza da mata a sallame su duba da raunin da suke da shi." "An gama ranka ya d'ad'e." Da sauri ya fita daga motar ya je ya cika umarni ya dawo ya zauna a mazauninsa, Sule ya ja motar suka fita. Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce." Ranka ya dad'e "Gadon 'kaya za mu nufa ne?" Ya ce." A'a Adakawa za mu je." Gabad'aya sukayi shuru babu wanda ya sake magana, sai dai Labaran da Sule cikin tunani suke! a duk lokacin da suka shigo garin KANO maigidan nasu sai ya je unguwar Adakawa kuma baya yarda su shiga dashi cikin unguwar a bakin titi yake sauka ya ce su tafi zai dawo gida da kansa. Wannan abu na nasu mamaki mutu'ka! [12/7, 8:06 PM] Bintu: 45&46 "Wai ana sallama da Shahida." Yaron ya fad'a yana wasa da garegaran dake hannunsa. Saliha dake zaune a tsakar gidan tana kula da masu shige da fice domin sayan abinci ta hararin yaron tana shirin magana sai ga Shahidan ta fito daga daki. Sai tayi shuru tana yi mata wani mugun kallo. Yaron ya ce." Yawwa Shahida ki zo ana kiran ki a waje." Da dan 'karfi yayi maganar. saboda ya san lalurarta. Da sauri ta ce." Ka je ka ce gani nan zuwa." Yaron ya juya ya fita cike da wasa a tare dashi. Dama tayi wankata tsaf ta shirya cikin atamfah mai sauki kudin, sai kawai ta fesa turare mai dadin 'kamshi ta sa hijabi a jikinta, ta fito cike da farin ciki a tare da ita. Saliha ta bi ta da harara da fadin." Shashasha! mara hankali kawai." Yana tsaye a soron gidan ya shirya babu laifi doguwar jallabiya ce a jikinsa ruwan madara amma ta kod'e sosai, da ba'kar hula mai raga-raga a kansa, kafarsa sanye da takalmi d'an madina kore sai hannunsa dake makale da carbi mai madannai! yayi mata kyau sosai, ta tsuguna har 'kasa tana gaishe shi. Ya amsa yana mata wani irin duba mai tattare da abubuwa da yawa. Cikin nutsuwa ya ce." Ki tashi mana." Ta mi'ke tsaye tana murmushi, a hankali ta ce." Yau kafi koda yaushe kyau." Murmushin farin ciki yayi ya ce." Na gode sosai Gimbiyata." Tana wasa da yatsun hannunta ta ce." Baba Asabe ta je unguwa ya za ayi kenan?" Ya ce." Hakan ba matsala ba ce idan babu damuwa sai mu je can gidan naku nayi magana da mahaifinki." Ta ce." Shikkenan hakan yayi." Suna fitowa kofar gidan. adaidaita sahu yana sauke Baba Asabe da 'katon buhun shinkafarta. Ta fito da kudi ta bawa direban da fadin." Don Allah ka taimaka ka shigar min dashi gida." Ya ce."To babu matsala Baba." Tana juyowa ta gan su a tsaye. Gabanta yayi mummunar fad'uwa! Wani irin kallo take musu fuskarta babu annuri ko kadan. A sanyaye ta ce."Baba sannu da zuwa." A dakile ta amsa tana kokarin shiga gidan, ya zube gwiwa a 'kasa yana gaishe ta. wuce shi tayi ba tare da ta amsa gaisuwarsa ba. Sosai ya ji babu dad'i amma sai ya danne! ya tashi tsaye yana buge rigarsa! Shahida kuwa idonta sun ciko da ruwan hawaye ta ji ciwon wulakancin da tayi masa. "Kayi hakuri don Allah." Ta fada tana kokarin mayar da hawayen dake kokarin kwace mata. Ya ce." Babu komai kada ki damu. zubar hawayenki shine damuwa ta, saboda haka kiyi kokarin hana su zuba." Ta daure tana kokarin mayar da hawayen ta ce." Bari na je na sanar da ita." Ya ce." To babu matsala. Gidan ta shiga ta same su suna mayar da magana. Baban tana cewa." Ai mutumin nan yana da kirki sosai wallahi shine ya bada umarnin cewa a sallami dattijai irinmu saboda raunin da muke dashi, da ba don haka ba da tuni ina can cikin 'kila wa 'kala." Saliha ta ce." Ai ya taimaka wallahi ban yi tsammanin zaki samu ba." Tana kokarin magana Shahidan ta katseta ta hanyar fadin." Baba wannan fa ba rayuwa ba ce, tunda ubangiji ya girmama dan adam babu wanda ya isa ya wulakanta shi, a matsayinki na mai hankali bai kamata kiyi masa haka ba, ban ji dadi ba wallahi." ta kai karshen maganar cikin rawar murya. Ta ce." Rashin kunya za kiyi min Shahida?" Ta girgiza kai "A'a ni ba nufi na kenan ba, kawai kuskuran ki nake nuna miki." Ta ce." Ai ba tun yau ki ka saba nuna min kusukura na ba Shahida ki cigaba da yi min abinda ranki yake so. Ta share hawayen da ya soma fita ta ce." Allah ya baki hakuri! dama zan fada miki ne cewa. Za muje can gurin Babana tare dashi." Ba tare da ta kalle ta ba ta ce." Sai kun dawo." Ga mamakinta sai ta ga ta juya ta fita. Suka kalli juna ita da Saliha ta ce." Gatse fa nayi mata." Saliha ta ce." Don girman Allah Baba ki kyale 'yar iskar yarinyar nan da mahaukacin mutumin nan jiki magayi." Baban ta shiga girgiza kanta tana tu'ajibun al'amarin. Gidan duhu sosai! babu haske. dukkaninsu suna rumfa a zaune yunwa na sasakarsu! yau Talatu dai ta ranste tace kowa ya ci aljihunsa! domin ta gaji yawon cin bashi gashi babu mai ko anini a cikinsu, tunda ba sana'a suke ba, bahaushe ya ce duk lalacewar mutum yana da rana. Talatu tana iyakar bakin ko'kari a kansu, yau dai ta gaji! 'kokari take ma ta biya bashin da ta ci a baya wanda kullum ta Allah ake mata sallama ba dare ba rana. Motsin shigowarta gidan ya sa Hadiza tayi saurin kunna fitilar wayarta tana fadin." Waye?" Ta ce." Ni ce Shahida." Talatu tayi karaf ta ce" Wa ce Shahida kuma. ba dai kurmar yarinyar nan ba, domin na ji kamar muryarta." Hadiza ta ja tsaki mai tsayi ta tashi ta shiga daki ta kwanta. tunanin yanda za a yi ta samu abinci kawai take, tana ganin saurayinta kawai zata kira a waya ta fad'a masa halin da take ciki. A wulakance ta kalle ta kafin ta ce." Ke kuma daga ina da wannan daran?" "Da ga gida nake." tafada a takaice. Ta ce." Ayyo! to ina fatan dai lafiya?" "Gurin Babanmu na zo tare da wanda zan aura za su yi magana." Gabanta ya yanke ya fad'i! ta ce" Waye wanda zaki aura din? wane sakarai! asararran ne mara mafad'i." Jamila ta ce."Haba Talatu abinda ki ke fa bai dace ba, kefe uwa ce idan ba zaki fadi alheri ba to kiyi shuru." "Rufe min baki ba'kar munafuka algunguma." ta katse ta a zafafe! Jamila ta mik'e ranta duk a 'bace ta kama hannunta suka fita tsakar gidan. "Don Allah Aunty Shahida kiyi hakuri da abinda Talatu take miki wallahi ba na jin dad'i." A jiyar zuciya ta sauke ta ce."Jamila Mahaifiyarku ba ta k'aunata ban san abinda nayi mata ba. amma ki sani wallahi ta na cin albarkacin ki, da ba don haka ba da tuni na dauki mataki a kanta." Ta ce.'' Ki cigaba da hakuri watarana sai labari yanzu ina mutumin da ku ka zo tare?" Ta ce." Yana can waje a tsaye kuma wallahi da gaske ya ke aure na zai yi." Ta ce.''Amma na ji dadi wallahi. mu je na gaishe shi kafin Baban ya dawo" Tare su ka fita suka same shi a tsaye a jikin bango (garu) yana danna 'karamar waya nokia da aka d'aure ta da kyaure. Jamila wani irin kallo take masa a tsorace! kwata-kwata mutumin bai kwanta mata a rai ba, ganinsa wani iri babu sutturar arziki gashi tsoho gemunsa da tsalli-tsallin furfura! "Ina wuni." Ta fada tana dan sunkuyar da kanta. Ya amsa fuskarsa a sake yana dan tsokanarta. Tana 'yar dariya ta ce." Ga aunty na nan; don Allah ka rike mana amanarta! kaga tana da lalura ta rashin ji a kula mana da ita. Murmushi yayi ya ce." Kada ki damu 'kanwata zan ri'ke amana insha Allahu; yanzu ina so ne nayi magana da babanku domin da gaske na ke." Tana k'okarin magana Hujaj ya k'araso gurin! kallonsa yayi sama da 'kasa da fadin." Malam menene? ka tsaya min a kofar gida tare da yara na." Ya d'an rusuna da fadin." Barka da dare Baba." A takaice ya amsa da "Barka dai" Gurin yayi shuru dukkaninsu jikinsu yayi sanyi! Ya kalli Shahidan da fad'in."Waye wannan ki ka kawo min?" Ta ce." Shine wanda nake so na aura, mun daidaita junanmu shine ya ce yana da kyau ya zo ya gaishe ka, kuma akwai alherin da yake tafe dashi." Bud'ar bakinsa sai ya ce." Ni da kai na nace ki fito da mijin aure, amma kin san dai a yanzu ba ni da kud'in da zanyi miki wata hidima ko? don haka maganar aure a tattara a ajiye a gefe guda. idan kuma zai aure ki babu kayan daki falillahil-hamdu." Ya ce."Babu komai Baba Shahida nakeso ita kanta ba wani k'yale-k'yale ba, buri na kawai ka bani ita. Wani irin kallo yake masa yana raya abubuwa da yawa a ransa! wannan mutumin da yake gabansa da ka gani talaka ne duba da yanayinsa, amma kuma ya yaba da nagartarsa kuma ba 'karamin yaro bane, Shahida 'yarsa ce mai rangwamin ga ta, shiyasa bai wani ci buri a kanta ba, amma zai so nagari ya aure ta ko dan ya kula da ita saboda lalurarta. Ya ce." Na baka yarinyar nan amana. sai abu na gaba wane alheri ne yake yafe da kai bayan wannan." Fuskarsa cike da annuri ya ce."Alhamdulillhi na gode sosai insha Allah zan kula da amanarka. bayan haka kuma Shahida ta shaida min irin halin da ka ke ciki na rayuwa, zanyi iyakar bakin kokari na akan lamarin. Ya ce." Wane irin taimako za kayi min? da ka ganinka dai talaka ne, wanda baka ajiye ba, baka bawa wani ajiya ba, shin ko akwai wata hanyar da ka ke samun kudi a b'oye kake yawo a tsiyace! kana da hanyar miliyan biyu da rabi ne?" Ya girgiza kai cikin rashin jin dadin maganganunsa ya ce." Eh insha Allahu, ina da alfarma a gurin maigidana, mutum ne shi mai tausayi da taimako insha Allahu zai duba uzuri na." Nan da nan fuskarsa ta washe ya ce." mutukar kuwa hakan ya tabbata baka da matar aure sai wannan yarinya na baka ita halak malak." Bai yi mamakin jin haka daga gare shi ba, ya ce."Shikkenan Baba na gode sosai, yanzu abinda za ayi shine ka bani number wayar mutumin da yake bin ka bashin kud'in koda maigidana zai bukaci magana dashi idan na koma can abujan." Ya ce." Don ta lamabar waya ai babu matsala sai na baka yanzu. Ya shiga fad'a masa lambar shi kuma yana d'auka a 'kwara'babbiyar wayar dake hannunsa da aka d'aure ta da kyaure. Sai bayan ya gama fada masa lambar wayar ne ya kalle shi da fadin." Da gani kai ba yaro bane ga alamun shekaru nan a tare da kai. shin kana da aure ko kuma yarinyar nan ita ce matarka ta farko?" Ya ce." Nayi aure shekarun baya har 'yata ta girma ta zama budurwa amma tana can garinmu." Ya ce." Ina kenan?" "Katsina a cikin karamar hukumar jibia, nan ne mahaifata. Ya ce." Ma sha Allah. kayi kokarin ganin ka fitar dani a wannan masifar ni kuma nayi maka alkawari sati guda yayi yawa gurin daurin auranka da yarinyar nan. Ya ce." Insha Allahu zanyi kokari." Gidan ya shige zuciyarsa fes! yau haihuwa za tayi masa rana. A tsakar gida ya same ta a tsaye. kamar wacce take jiran shigowarsa babu sannu da zuwa ta ce." Maganar da Jamila ta zo fad'a min gaskiya ne?" A lalace ya kalle ta kafin ya ce." 'kwarai kuwa yau haihuwa za tayi min rana dake da yaranki kun zama yuyuyu! sakarkaru kawai." Yana 'kare maganarsa ya bude dakinsa ya shiga ya bar ta a tsaye a gurin cike da d'umbun mamaki! A hanyar su ta komawa gida take tambayarsa ashe ya ta'ba aure har da haihuwa, ya tabbatar mata da gaskiyar magana ya ce." Amma yarinyar ta na can garinsu kamar yanda ya shedawa mahaifinta. Cike da 'kauna da begen juna su kayi sallama da juna tare da alkawarin cewa gobe da wuri zai zo ya gaisa da Baba Asabe kafin ya tafi. Lokacin da ta shiga gidan, muryoyinsu ta ji a can cikin daki harda Kawu Musa. gabanta ya fad'i! jin kawu Musa a gidan ba alheri ba ne. Saliha ta fito tsakar gidan ta sameta a tsaye ta kasa shiga dakin. Ta dan d'aga muryarta da fadin." Matar mahaukaci kin dawo kenan?" Kallonta kawai tayi amma ba tace mata komai ba, ba don ba taji haushin kalaminta ba. Suka fito daga dakin a tare, Baba Asabe na sake jadadda masa matakin da zata dauka akan al'amarin, ya yin da shi kuma yake nuna mata cewar tabi a hankali domin ba ta da k'arfi akan yarinyar kamar ubanta. Ya kalle ta suka had'a ido! sai tayi saurin sunkuyar da kanta kasa. Ya d'an bud'e muryarsa da fad'in." Shahida wannan rayuwar ki ka za'bawa kanki ko?" Shuru tayi hawaye na 'kok'arin kufce mata. Ya cigaba da cewa." Shin me ki ka hango a tare da wannan mutumin wanda shi ba mai hankali ba kuma ba mahaukaci ba, a matsayin ki na mara lafiya zaki za'bi wannan rayuwar da mara galihu. wanda ba a san asalinsa ba." Baba Asabe ta d'ora da fadin" Yo idan ba rashin hankali ba ina ke ina auran mahaukaci mutumin da ba a san daga ina ya ke b......gurin ta bari tana wani irin kuka! duk suka bita da kallon mamaki! lallai al'amarin yarinyar ya fi karfin tunaninsu. [12/8, 12:47 PM] Bintu: 47&48 To a daran ranar Talatu dai da kyar ta iya rintsawa, domin ta jima tana tunani akan al'amarin, ka da fa tana zaune baki a sake yarinyar da ta tsana! tayi mata zarra! tunda gashi tun kafin aje ko'ina Hujaj ya fara yi mata habaici ita da 'ya'yanta, dole ta je ta bincika domin sanin ainihin mutumin da ya ke neman auran yarinyar. Shahida da 'kunci! da 'bacin rai ta tashi. tsakanin Baba da Saliha jira take wani ya ce mata kule tace cas! domin gabad'ayansu a ciki take dasu, saboda suna kiran masoyinta da mahaukaci. Ta shiga d'akin ta same ta a kudindine a cikin bargo amma ba bacci take ba. kawai ta tsirawa rufin dakin ido! Ta d'an bud'e muryarta ta ce." Shahida ki tashi ki karya kummalo mana kina kwance kina tunane tunane mara amfani ko?" Ta mike zaune tana kallonta ta ce." Baba ina neman alfarma a gurinki." Kallonta tayi tana ayyana wani abu, labarin gizo dai baya wuce na koki, amma sai ta ce." To Allah ya sa zan iya. Ta ce." Don girman Allah da darajarsa ki kar'bi wannan al'amari da zuciya d'aya! wallahi nayi imani da Allah cewa alheri ni, nayi istahara akan al'amarin, Baban Baba ba zai cutar dani ba, mutumin kirki ne kuma ba mahaukaci bane kamar yanda ku ke zato, yau ce kawai ta mayar dashi haka, amma tunda ya samu ubangida ya koma mutum kamar kowa, arziki da rashi duk daga Allah suke, kiyi min addua kawai Allah ya sa hakan alheri ne. Gabadaya ta gama kashe mata jiki da kalamanta, a yanda ta shirya ta kuma kudire a ranta cewa sai bayan ranta wannan al'amari zai tabbata, amma wannan maganganun da tayi gabadaya gwiwarta tayi sanyi, babu shakka akwai wani abu da Allah ya rufe, kuma sha'anin aure irin wannan ba'a tsawwala wa domin idan ka tsananta sai ayi babu kai. Ta ce." Shikkenan Shahida na rabu dake da abinda ki ke so Allah ya sa hakan alheri ne dake damu baki daya. Cike da tsantsar farin ciki ta ce." Na gode sosai Baba insha Allahu za muyi farin ciki gabadayan mu, amma ki shirya an jima kadan yana tafe zai zo ku gaisa kafin ya tafi Abuja gurin sana'arsa. Ta na kokarin fita daga dakin ta ce." Shikkenan Allah ya kawo shi lafiya. Zama tayi kan kujera 'yar tsuguno jikinta duk a mace! Saliha ta ce." Baba Lafiya dai?" A sanyaye ta ce." Lafiya lou Saliha al'amarin Shahida da wannan mutumin ne yake ban tsoro. Ta ce." Tuntuni na ce miki ki daina damuwa amma kina kokarin janyowa kanki matsala! duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka." Ta ce." Na yi fatan alheri ai Allah ya ba su zaman lafiya." Shuru tayi ba ta amsa da ameen ba, kawai ta cigaba da feraye kabewar dake gabanta. ** To kamar yanda Talatu ta kudire a ranta cewa za ta je tayi tambaya a kan lamarin, da asubah zakara ya bata sa'a ta fita can wani 'karamin k'auye ta nufa gurin wani malami, wanda ya duba mata al'amarin ya kuma tabbatar mata da cewa shi bai ga komai ba face alheri domin kuwa babu da na sani ko bak'in ciki a cikin al'amarin, sai farin ciki. Jikinta a sa'bule ta dawo gida da tunanin yanda za tayi ta wargatsa auran. *** Cikin nutsuwa ta fito ta same shi a tsaye a soran gidan, sosai tayi farin cikin ganinsa tsaf dashi cikin shadda bulu mai duhu tazarce har k'asa da hula da takalmi ya dora rigar sanyi a sama saboda yanayin garin sanyi ya fara busawa, ta tsuguna har kasa tana gaishe shi, ya amsa a nutse yana mata wani irin kallo wanda ya sa ta jin kunyarsa ta kasa tashi tsaye. Ya ce." Kin yi min kyau fiye da tunaninki. Murmushi tayi ta ce." Ni ma haka idan na gan ka cikin suttura cike da kamala sai na yi ta mamaki kamar ba kai ba, wanda da yawa mutane suke maka kallon mahaukaci! lallai babu shakka wannan ubangida naka dole a jinjina masa domin ya taka muhimiyyar rawa a rayuwarka, ya sanya ni cikin farin ciki mara mislatuwa domin ni yayi wa tagomashi yayi wa bajinta ba zan gushe ba face na cigaba dayi masa addu'a har karshen rayuwata." Ya dinga jin wani irin farin ciki na kwarara a zuciyarsa, ya ce." Za ki gaisa da maigidana insha Allahu sai kiyi masa godiyar alherin da yayi miki, duk da cewa yana da labarinki amma lokaci kad'an ya rage ku gaisa da juna da ikon Allah." Ta mi'ke tsaye tana gyara mayafinta da ya sauka a kafadarta ta ce." Ina fatan zuwan wannan rana. Kawu Musa ne ya shigo da shirin zuwa kasuwa a tare dashi. Ya tsaya suna gaisawa babu yabo babu fallasa yake kallon mutumin, shima mamakin sauyawarsa yake, kamar bashi ne wannan mahaukacin ba mai yagaggun kaya da kwanciya cikin 'kazanta. Ya ce." Ai babu damuwa mu je ciki sai ku gaisa sosai tsayuwa a soron bashi da amfani." Cike da jin dadi ya ce." Na gode sosai Kawu." Ita kuwa Shahida babu wanda ya kai ta jin dadin ganin yanda Kawu Musa ya saki fuskarsa su gaisa da Masoyinta cikin farin ciki. Babu yabo babu fallasa ta shimfida masa tabarma ya cire takalminsa ya zauna a nutse ya ke gaisata, ta amsa babu walwala a tare da ita domin dai har yanzu zuciyarta ba tayi na'am dashi ba kawai dai ta hakura ne saboda samun farin cikin yarinyar. Ita kuwa Saliha a fakaice take kallonsa tana k'unshe dariya, hular kansa da takalminsa soso da ya cire a gefanta su takewa dariya. wanda duk abinda take yana kallonta kuma yana mamakinta a zuciyarsa. Kawu Musa shi yake masa tambayoyi, cikin nutsuwa yake bashi amsa daidai da tambayar da yayi masa. Kawu Musa ya ce." To Allah ya tabbatar da alheri a cikin al'amarin. tunda ka riga kayi magana da mahaifin yarinyar ai shikkenan, dama shike iko da 'yarsa, tunda ya baka mu kuma za mu zama masu addua da fatan alheri, amma mun baka amana ka rike ta da kyau, marainiya ce bayan haka kuma ka duba lalurarta. Ya ce." Nayi alkawarin haka insha Allahu. Baba Asabe ta ce." Da zai yiwu sai ka kama haya a cikin unguwa ka ajiye ta a kusa, idan yaso ka dinga zuwa daga can abujan. Ya ce" Hakan ba zai yiwu ba Baba, ni dai buri na ku yarda dani, ku amince cewa zan rik'e amanarku, ni kuma nayi alkawari insha Allahu idan ban rik'e ba Allah ya hukunta ni". Ta ce." To ai shikkenan Allah ya sa mu dace amin." Gabadaya suka amsa da "Ameen ameen." Da zai tafi ya ajiye mata dari biyar, ta ce."A'a zo ka dauki kudinka bawan Allah ka 'kara guziri, kai da za kayi tafiya" Yayi sauri yasa takalmansa ya kama hanyar fita Shahidan ta bi bayansa da sauri. 'Yar 'karamar waya tacno ya bata ya ce ta ri'ke zai dinga turo mata sak'on gaisuwa, saboda ya san lalurarta, ta kar'ba ta na godiya sai murmushi take ganin yanda aka samu daidaito ta kowane b'angare! a yanzu burinta bai wuce ace sun mallaki juna ba. **** "Eh ni ne Alhaji Sammani mai leshi kasuwar wambai.'' Ya fad'a yana gyara wayar a kunnansa. Daga daya 'bangar ya ce." Ma sha Allah. dama na kira ne akan maganarka da Abokinka Jamilu Hujaj." Ya ce." Eh hakane to ina sauraranka, Allah yasa alheri ne. Murmushi yayi a nutse ya ce." Alheri ne insha Allahu." Yayi shuru na second daya kafin ya ce." Nawa ne sauran kud'in naka ne?" Cike da karsashi da kwarin gwiwa ya ce." Ba saura bane ai domin a miliyan biyu da rabi an bada miliyan daya ka ga kuwa ya wuce saura." Ya ce." 'Kwarai kuwa, yanzu idan na fahimta cewa kudinka da suka rage a hannun abokinka Miliyan daya da rabi kenan?" Ya ce." 'Kwarai kuwa." ya fada yana gyara tsayuwarsa a cikin shagon. Ya ce" Babu matsala ka tura min account number zan sa maka insha Allahu." Mamaki ya rufe shi! ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ya ji wayar ta tsinke! ya dinga kallon fuskarsa wayar yana mamakin in da Alhaji Jamilu ya samu wannan hanyar, shin waye wannan mutumin? amma bari ya tura account din ya gani, domin bai gama amincewa da maganar mutumin ba, ya na so ya tabbatar ne kawai. Ko minti biyar bai yi da tura account d'in ba ya ji alert kudi sun shigo, yana dubawa ya ga kud'insa cif miliyan biyu da rabi! Cikin tsantsar mamaki! ya nemi guri ya zauna jikinsa sai kyarma yake dama Jamilu ya sha sheda masa cewa shi ba 'karamin mutum bane. Text ne ya shigo wayarsa ya bude yana dubawa. Sai jikinsa ya 'kara mutuwa karanta abinda yake k'unshe. _"Ga kud'inka nan Alhaji, ka mayar masa da miliyan dayan da ya baka Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba."_ Hannu na rawa ya fara kokarin kiran wayar sai dai sai kash a kashe take, ya kira ya kai sau bakwai bata shiga ba, sai ya hakura ya fara laluben lambar abokin nasa domin fada masa halin da ake ciki. " Na san da hakan, domin kafin a tura maka kudink'a sai da aka sheda min, Yau ka tabbatar da cewa ni din ba 'karamin mutum bane ko?" ya fada cike da izzah da ginshera! Alhaji Sammani ya ce." Wai don Allah ina ka samo wannan mutumin domin daga jin muryarsa bai yi kama da abokanan hurd'ar mu ba." Murmushi yayi kafin ya ce." Haihuwa ce tayi min rana saboda haka mu bar maganar kawai, kai kayi nufin tozarta ni Allah bai nufa, sai ka tura min abinda yayi saura nawa dake hannunka, daga haka ala'karmu ta yanke." Ya na gama maganarsa ya kashe wayar yana jan tsaki, account number ya tura masa yana jiran ya ji alert. Cike da kwarin gwiwa ya fito daga d'akinsa! ya bankad'a labulan dakin yana kiran sunanta. Ba ta amsa ba sai ido kawai da ta zuba masa. Ya ja mugun tsaki kafin ya ce." Na yarda ke ce ki ka karya ni, ba tun yau ba malamina ke sheda min hakan, rabon wad'annan yaran nake zaune dake, amma ki sani, Mariya ta fiye min ke duk da bata raye ina alfahari da ita, domin ta haifa min yarinyar da ta share min hawaye, ba zan ga ji da sheda miki cewa ke da yaranki baku da amfani a guri na ba." Yana gama maganarsa ya saki labulan ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa fes! gabadaya duk wani damuwa da lalure-lalure da yake sun tafi sakamakon shigowar kud'i, a maimakon ya je ya mayar wa da dillali kudin ya bashi takardar gidansa, kawai sai ya cigaba da fantamawa da kud'in, ya gwammace ya zauna a matsayin d'an haya a gidan, domin zuwa yayi ya bashi kudin hayar shekara biyu dubu dari biyu da ashirin, yasa abinda ya rage a aljihunsa ya cigaba da buga barikinsa. Baba Asabe tayi-tayi dashi kan cewa a je ayi binkice a can garin nasu amma fafur! ya'ki a lokacin har ya so yayi mata rashin kunya! Kawu Musa ya ce kawai ta kyaleshi kamar yanda ya fad'a mata cewa uwarsa da ubansa ne kawai za su fad'a masa magana ya ji akan wannan al'amari to tunda basa raye babu wanda ya isa domin dai yarinya 'yarsa ce shi yake da iko da ita! Baba Asabe har kuka tayi saboda tsabar 'bacin rai tana jin takaicin abinda mutumin yake mata, wato ita ta gama yi masa wahala yana nuna mata iko. kawai sai ta barwa Allah al'amarin, ta tsananta da addua. 'Bangaran masoyan kuwa sun sha'ku sosai ta waya domin kalaman soyayya suke aikawa da junansu babu dare babu rana. Ranar juma'a 20/3/2021 aka d'aura auran, babu laifi d'aurin auran ya tara mutane, amma duk yawancinsu mutanan Hujaj din ne, sai wakilan ango guda biyu da suka bada sadaki, kuma suka kar'bi auran bisa yarjewar addinin musulunci. [12/10, 9:53 AM] Bintu: 49&50 'Yan Allah ya sanya alhari da 'yan gulma sai shige da fice suke a gidan, ita dai Baba Asabe kallonsu kawai ta keyi saboda ta san mafi akasarinsu, ba alheri ne ya shigo dasu ba, domin da kunnanta ta ji wasu mata suna maganar cewa; ai auran kawai aka d'aura amma babu lefe babu komai, asali ma angon yana da matsalar k'wak'walwa sannan ba shi da wani cikakken asali. ire-iren wannan zantukan jama'a suka ke'be guri guda suna yi. Amarya kuwa sam ba ta sanya damuwar komai a cikin ranta ba, ta na ji ko babu lefe za ta iya zama da masoyinta burinta ya cika za su rayu cikin inuwa d'aya. Kitso akayi mata 'kananu irin na bare-bare sai k'unshin salatif da makociyarsu tayi mata, ta sanya sabuwar atamfa wacce ya kawo mata a din'ke da mayafi da takalmi, Rabi makociyarsu wacce tayi mata k'unshi itace tayi mata kwaliyya dai-dai gwargwado tayi kyau tana ta murmushi, mutane na ta'ba ta suna mata Allah ya sanya alheri. Can gidan Hujaj kuwa Talatu kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ganin yanda al'amarin auran ya kasance, babu lefe babu wata hidima da ango yake wa amarya. babban farin cikin ta da ta samun labari cewa ai angon ma bashi da hankali asalinsa mahaukaci ne kawai ya d'an samu sau'ki ne! wannan al'amari yayi mata dadi sosai, kawai sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da sabgoginta, ko gidan bikin ba ta je ba, Jamila ce kawai tayi wanka ta shirya ta tafi. ita da sauran yaran suna gida duk wanda ya shigo sai sun labarta masa abinda yake faruwa. Da magariba Hujaj ya shigo gidan; kalau dashi cikin sabuwar shadda babba riga da 'yar ciki, komai sabo ne a jikinsa sai walwala yake kamar bai ta'ba shiga wani rikici ba. A tsiyace! ta kalleshi kafin ta ce." 'Karya banza da wofi ina zaune labarin komai ya same ni da har kake wani fuffuka kana murna ka dauki 'yarka ka bawa mahaukaci wanda ba a san asalinsa ba." Ya ce." Ai gwara ita akan ke da 'ya'yanki, Talatu daf ki ke da ki bar gidan nan, ki rubuta wannan ki ajiye mutsiyaciya kawai duk kin tsiyata ni, zan dai auro wacce take dai-dai da arziki na." Ta buga cinya da fad'in" Ai wallahi 'karya kake Jamilu, ai na ci gida ko ka sake ni ba zan fita ba ina nan daram dam." Ya ce." Tunda gidan ubanki ne ai sai ki zauna sakarai shashasha! kawai." 'Kwallah ta ciko idonta tana rawar murya ta ce. " Shashasha ba, ai ka santa. A sukwane ya gaura mata mari! wanda sai da ta ga gilmawar taurari! ya nuna ta da yatsa da fadin." Wallahi ki ka sake wata magana a bakin auranki domin dama na ga ji da zama da ke mahaukaciya kawai." D'aki ta shige tana wani irin kuka mai tsuma zuciya! Hadiza tana kwance a kan gado tana danna wayarta, uffan ba tace ba, gabad'aya ma hankalinta yana kan hirar da take da saurayinta. Bayan sallar isha'i Hujaj ya dira a gidan, Baba ta shimfid'a masa tabarma suka gaisa kamar abin arziki. Shahida ta fito ta gaishe shi, ya amsa kafin ya ce ta nemi guri ta zauna. Gurin yayi shuru na minti biyu yayi gyaran murya da fad'in." To Alhamdulillhi, bu'katata ta biya gurin ganin na auran da yarinyar nan a in da ya da ce! wannnan mutumin ya fitar dani kunya saboda haka ko da yana tsince-tsince ne akan bola zan iya bashi auran 'ya ta saboda yayi min abinda ba zan mance ba. Shahida 'ya tace, ni ne ubanta ni nake da iko a kanta, saboda haka babu wani mahalukin da ya isa yace ga yanda zan yi da abinda nake da iko a kansa. Ta ce." Dakata! Jamilu." Ya kalle ta ido cikin ido. Ta cigaba da cewa." Ai na dauka arziki ne ya kawo ka gidan nan ashe rashin kunya ka zo kayi min." Ya ce." A'a ba nufi na kenan ba. Ta ce." Idan ba nufinka kenan ba mai zai sanya ka dunga wasu maganganu masu kama da jirwaye." Ya ce." Surutai nake ji a gari cewa wai na d'auki 'yata na bawa mahaukaci wanda ba a san daga ina ya fito ba, naga dai ni na hai fi abata, kuma wannan maganar nasan daga gidanan ta fito." Ta tsira masa ido kawai tana kallonsa, ya cigaba da cewa."Kamar yanda na fada da farko cewa." Mutumin nan sanadiyarsa na fita daga cikin rud'ani, to wallahi ko doke-doke yake yana tsince-tsince a bola hakan ba zai hana ni na bashi yarinyar nan ba, dalili ya rufa min asiri na a lokacin da yake daf da tonuwa". Jiki a sanyaye ta ce Allah ya sanya alheri. Ya amsa da "Ameen ya cigaba da cewa." Gobe da sassafe zai zo ya d'auke ta su tafi can abujan inda yake aiki, yayi alkawarin cewa bayan an kwana biyu, zai zo ya dauke ni domin na je naga mazauninsu, na amince da maganarsa dari bisa dari! ke Shahida wannan mutumin daga yau shine uwarki shine ubanki! kuma mijinki, yi nayi bari na bari, ke ki ka ganshi kina so ki ka amince da auransa, saboda haka kada naji wata magana ta biyo baya wannan shine abinda zan fad'a miki." Ta d'aga kanta da fadin." Insha Allahu zanyi kokarin yi masa biyayya Baba a cigaba da yi mana addua'a." Ya kalli Baba Asabe da fad'in." Ko akwai nasihar da za kiyi mata domin tafiya nake so nayi da ita can gidana da wuri za su wuce." Ta ce."Ai ka riga ka gama yi mata nasiha Jamilu ni kuma a suwa! a matsayinka na ubanta ai ka gama komai.'' Ko a jikinsa, ya kalli Shahidan da fad'in " Ki shiryo ki fito ina waje ina jiranki." Ya mi'ke tsaye tare da zura hannu cikin aljihu, dubu uku ya d'auko ya ajiye a gabanta da fadin " Allah ya bamu alheri.'' Cike da rashin kuzari ta bishi da kallo tana Allah wadai da mugun halinsa. Ta juya ta kalle ta tana zaune ta kasa tashi ballantana ta shirya kamar yanda ya umarce ta. Ta d'an bud'e muryarta da fad'in." Ki tashi ki sanyo mayafi ki bishi Shahida ai magana ta 'kare, ni dai nayi iyakar bakin kokari na akan lamarin, ba zanyi miki baki ba sai dai adduar Allah ya tabbatar da alheri." Wani irin kuka ya kufce mata sai kawai ta rungume ta a jikinta tana fadin." Baba don Allah ki yafe min kada ki k'ulla ce ni, ki cigaba da yi min addua." Tana kuka sosai ta ce " Shahida addua a kanki ai yanzu na fara, ba zan daina ba har sai ranar da Allah ya dauki raina, amma har a cikin raina ban so kiyi wannan rayuwar ba, na so ki auri miji nutsatstse mai hankali d'an gari mafi kusa dani wanda zai kula min dake da lalurarki, amma hakan bai samu ba, sai wannan kaddara to ina rokon Allah yasa ta zama alheri." Sosai suka rungume juna suna ta kuka! Saliha ta dinga kyalkyala musu dariya tana yi musu vedio, da 'kyar suka rabu da juna kowanne zuciyarsa babu dadi, mussaman Baba Asabe da har yanzu abin bai kwanta mata a rai ba. Ita kuwa Shahida kukan rabuwa da ita kawai take, amma a cikin zuciyarta ba ta tunanin komai face alheri domin ba ta tsammanin cewa masoyin nata zai cutar da ita. To tun a mota ta sha jinin jikinta gabad'aya sai tayi sanyi jikinta ya mutu! ta dinga kallonsa a fakaice! tana jin wani irin tsoro a cikin zuciyarta. Gabad'aya kamar tunda aka hallice shi bai ta'ba dariya ba, fuskarsa murtuk! sam ya ma'ki yarda ya kalle ta ballanatana ta samu sararin yi masa wata magana, tun bayan da ya d'auko ta daga gaban mahaifinta ya rikid'e! ya zama mara farin ciki ko a motar ma bai yarda ta zauna a kusa dashi ba, cewa yayi taje can ta zauna cikin mata 'yan uwanta. Ta dinga tunane-tunane marasa kyau a cikin zuciyarta! amma ba ta bari abinda take rayawa a ranta yayi tasiri ba, kawai sai dinga nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Tunda take bata ta'ba doguwar tafiya irin wannan ba shiyasa gabad'aya! jikinta ya mutu! ta gaji sosai! sai addua take Allah ya sa su sauka lafiya! ko ta samu ta mi'ke k'afafunta! Matar dake kusa da ita ta bata pure water "Kar'bi ruwa 'yan mata naga kamar kin gaji." Ba ta ji maganarta ba kawai dai ta ga tana mi'ko mata ruwa. Da sauri tasa hannu ta kar'ba ta bud'e baki za tayi magana, ya juyo daga mazauninsa wata muguwar harara ya daka mata fuskarsa a mugun had'e! Sai tayi saurin sunkyar da kanta gabanta na wani irin fad'uwa ta mayarwa da matar ruwan da sauri! jikinta sai rawa yake. Matar ta bi ta da kallon mamaki! sai kuma ta ta'be bakinta ta ajiye ruwanta da fadin."Kin yi wa kanki." A galabaice suka isa abuja! yanda ta fahimta kamar tafi kowa galabaita watakila saboda rashin sabo ne. Ya riga ta fita daga motar yana tsaye yana jiranta ta fito. a gajiye likis ta fito, nan ta ga yanda ya sa bakin gilashi a idonsa tare da rufe kansa da bakar hular sanyi. ta dan tsaya a gefansa tana bin tashar da kallo! ga rana ta k'wallare! jama'a kowa na gabatar da abinda yake gabansa. Hannunta ya ri'ke! ya jata suka nufi wata rumfar kwano gurin wata mai sayar da abinci bayerabiya. cikin harshen turanci suka gaisa kafin ya shedawa matar cewa ga ajiyar yarinya ya kawo mata ta bata abincin da zai isheta anjima zai turo a d'auke ta, wanda zai zo ya d'auke ta sunan Sule." Ta Amsa da "to kafin kalle ta da fad'in." Zo ki zauna." tana nuna mata wata kujera. Gabanta ya dinga duka yana daka! hawaye suka ciko idonta! ita dai ba ta ji abinda suke cewa ba amma ta fahimci kamar barin ta zai yi a gurin ganin yanda matar ke kallonta tana nuna mata gurin zama. Ta ri'ke hannunsa tana girgiza masa kai! wasu zafafan! hawaye suka kufce mata. Saurin d'auke kansa yayi ya cire hannunsa daga nata ya kalli matar da fad'in." Tana da matsalar kunne ba sosai take ji ba." Da kansa ya ja hannunta ya kai ta ya ajiye a kan kujera, fuska a murtuke ya ce" Zan je wani guri ne shiyasa na kawo ki anan na ajiye amma zan turo a dauke ki kada ki damu." Bai jira tace wani abu ba yayi saurin barin gurin ko waiwayenta be yi ba. Duk kyawun abincin bai bata sha'awa ba, gabadaya ma ba ta cikin nutsuwarta, tsoro da fargaba sunyi mata dabaibaiyi, tunani ma ta rasa wane kala za tayi, sa'i da lokaci ta ke share hawaye tana bin tashar da kallo da nazarin wace rayuwa za ta fuskanta a nan gaba. Ekeke matar dake sayar da abincin kenan, ta kalleta a karon da ba zai lissafu ba, domin tun tana lallabata ta ci abincin har ta gaji ta zuba mata ido! sai dai haka kawai take tausaya mata idan ta tuna cewa kurma ce ba ta ji sosai, ta yi tunanin abubuwa da yawa akan yarinyar, ta tunanin mutumin yayi kawalcinta ne domin ya dinga biyan buk'atarsa! Sai daf da magariba Sule ya je domin d'aukarta! Ko kusa ko alama bai gane ta ba ballantana yayi tunanin wani abu, ko da yake can baya da ya je binkice lokacin da abin ya faru duhun dare ya shigo da kuma cikowa ta mutane shine dalili. Su ka gaisa da Ekeke kafin ya sheda mata shine Sule ya zo tafiya da yarinyar." Ta ce." To kud'in abinci dubu biyu sai kudin jira dubu uku, duk da ba taci abincin ba ita wannan ba damuwarta bane. Sule bai ja doguwar magana ba ya ciri kudinta ya bata. Jiki a sanyaye take binsa tana ta addua a cikin zuciyarta. ba ta 'kara firgita ba sai da ta ga shirgegiyar motar da ya bude mata wai ta shiga. Ai sai hawaye suka fara zuba kuka sosai take! tana waiwaye a gurin, ta tsorata don gani take kamar sa ce za ayi." Yayi -yayi da ita ta shiga amma fafur! ta' ki shiga sai kuka take tana nema ta tara musu mutane a gurin. Wayarsa ya fito da ita ya kira maigidan nasa ya sheda masa halin da ake ciki. Ya ce ya bata wayar suyi magana. Nan ma da kyar ta karbi wayar jikinta sai rawa yake. Da muryar da ya aro yayi mata magana da karfi yanda za ta ji. "Shahida ki shiga mota Sule zai kawo ki gidan da nake aiki wato gidan maigidana kamar yanda nayi miki bayani a can baya. zamu zauna a gidan ne a wani sashe da aka bamu, ina nan ina jiran zuwanki." Hankalinta ya kwanta jin muryarsa, a sanyaye ta ce." To." ta mika masa wayar tana godiya a cikin ranta domin wallahi tayi tunanin Sule sace ta zai yi. [12/10, 12:09 PM] Bintu: 51&52 Girman gidan da tsaruwarsa ya firgitata sosai, sai ta 'kara shiga rud'ani zuciyarta ta cigaba da yi mata tunane-tunane marasa kyau! wani 'bangaran na zuciyarta na nuna mata cewa Baban- Baba mutumin arziki ne ba zai cutar da ita ba. Tafiya mai tsayi su kayi a cikin gidan domin kwalta ce a shimfid'e har sai da suka kusa kai wa karshen gidan, sannan taga yayi parking, sai ta dinga kalle-kalle a gurin, tsit! sai shuke-shuke da kukan tsintsayen dake sauka a kan ciyayi gabanta ya cigaba da fad'uwa, cikin zuciyarta take ta nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! ya bud'e mata 'kofar motar, alama yayi mata ta fito da hannunsa. 'Kin fitowa tayi ido jawur! take kallonsa kafin ta bud'e baki cikin yanayin maganarta tace." Ina ne nan din.? Ya ce." Gurin da zaki zauna ne maigida ne ya ce a kawo ki nan" Sai ta kasa fahimtar inda maganarsa ta dosa. kawai dai ta zuba masa ido tana ayyanawa abubuwa da yawa aran ta. Cikin wayo da dubara ya ce." Ai yana ciki yana jiranki kamar yanda ya fad'a miki a waya." shima ya fadi maganar ne kawai! ba tare da ya san abinda ke faruwa ba. Jin abinda ya ce yasa ta d'an ji 'kwari a jikinta, ta fito daga motar, yayi mata jagora zuwa wani ke'bantaccen sashe, ya bude mata ta shiga da bisimillah a bakinta! tare da jin fad'uwa gaba a tare da ita. Tana shiga ya mayar da k'ofar ya rufe da key. ya bar gurin da saurin gaske. Shuru falon babu alamun motsi! sai dai tsaf ko'ina a tsare babu datti a ko'ina. Falo ne mai girma da kujeru masu kyau da labulaye! sai dak'in bacci guda biyu da kicin da bandaki duk a falon. a hankali ta zauna kan kujera mai cin mutum d'aya tana sake nazarin falon, gefe guda kuma zuciyarta sai bugawa take, shin ko daga ina mijin nata zai fito oho! "Yallabai komai ya kammala, yarinyar tana wannan sashen daka umarce ni dana ajiye ta." Sule ne ke wannan maganar lokacin da yake zaune a gabansa. Ya cire farin gilashin dake sakaye a idonsa ya kalleshi sosai kafin ya ce."Matata ce Shahida." Da sauri Sule ya kalle shi da dumbun mamaki a tare dashi ya ce." Matarka Yallabai?" Yayi murmushi da fadin."Kwarai kuwa a jiya nan aka daura min aure da ita, itace yarinyar mutumin nan da nasa kayi min binkice a kansa." Sule ya dinga jinjina al'amarin ya ce." Wallahi Yallabai ban gane komai ba, ita kanta yarinyar ban gane ta ba, sai dai nayi ta mamakin dalilin da yasa ka 'kebance ta a gidanka, sai na ce to ko da wani abu ne wanda kake shiryawa." Ya ce." K'warai kuwa Sule kai din yaro na ne amintacce wanda na yarda dashi, nasan cewa ba zaka mance wahalhalun da nasha a can baya ba, auren farko ban yi dace ba, na biyu ma haka, wannan dalilin yasa gabad'aya nake tsoron duk wata 'ya mace saboda kaidi da sharrinsu, da yawa 'yan uwa da abokanan arziki suna fad'in ai ba duka suke da mugun hali ba, bahaushe yace wanda maciji ya sara idan ya ga bakin tsumma dole ya razana! a cikin zuciyata na cire aure gabad'aya daga raina! sabida samun zaman lafiya na, daga baya surutai na jama'a yayi yawa a kaina cewa ba girma na bane na zauna babu aure! wannan dalilin yasa na janye kudirina, auran wannan yarinyar nayi shi ne da manufofi da yawa. saboda haka kai kad'ai ne a gidan nan kasan wannan yarinyar matata ce, akwai wani shiri da nake akan lamarin duk don na gwada ta, da tarbiyarta." numfashi ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Matata ce, amma za ta zauna a matsayin matarka na d'an wani lokaci, ina nufin ko da wani daga cikin iyali na zai tambaye ka sai ka amsa da cewar matarka ce, shikkenan, amma babu ruwanka da zuwa sashen, sai dai idan ni na aike ka gurinta." Sule ya sauke zazzafar ajiyar zuciya, a sanyaye ya ce." To shikkenan Alhaji Allah ya sa a dace da tagari, ina yi maka fatan alheri ubangiji Allah yasa anyi kenan." Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina Sule za ka iya tafiya sai na neme ka." Godiya yayi sosai kafin ya tashi ya tafi cike da mamaki a tare dashi, ko da yake bai ga laifin maigidan nasa ba, duba da cewa a can baya mata sun wahalar dashi don yayi hakan ba laifi bane. Kuka taci sosai! ganin duhu dare ya shigo gashi babu haske a falon, ko'ina yayi duhu! sai labulan tagogin dake falon ta janye haske ya shigo, hakan yasa iskar sanyi ta dinga shigowa, jikinta ya dinga kyarma! da sauri ta takure jikinta akan kujera tsoro na sake kanainaye ta, bud'e tagogin da tayi sai idanunta ya dinga yi mata gizo ta dinga ganin gilmawar abubuwa da yawa. da sauri ta je ta sauke labulayen ta koma ta zauna, babu abinda ya fi damunta irin sallar magariba da isha'i! ga yunwar da take mugun sasakarta! Jin motsi kamar ana ta'ba 'kofa ya sa gabanta ya tsananta fad'uwa! ta tsirawa kofar ido! duk da bata da tabbacin ganin fuskarsa saboda duhu amma a jikinta take jin shine zai shigo. Ya shigo da sallama ciki-ciki. ba ta ji ba amma ta ga inuwarsa. Tsaye ta mi'ke! har yanzu jikinta bai dawo daidai ba. Ya kunna hasken 'karamar wayarsa, nan ya hangeta a tsaye ta tsura masa ido, lokaci guda ya fahimci firgici da tsoro a tare da ita. Sunanta ya kira babu walwala a fuskarsa. Ta amsa cikin rawar murya. Ya ce." Zo ki kar'bi wannan ledojin kayanki ne a ciki." A sanyaye ta 'karasa kusa dashi tasa hannu ta kar'bi manyan ledejojin dake hanunsa. Bayansa ta bi ganin ya nufi d'aya daga cikin d'akunan dake falon. Ya juyo ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya ce." Nan d'akina ne kuma ina bukatar sirri! ki d'auki wancan dakin ya zama naki." ya fada yana nuna mata d'aya dakin. Yana gama maganarsa ya bud'e ya shiga ya barta a tsaye da ledoji a hannu. Ta jima a tsaye a bakin kofar dakin tana tunane-tunane! daga bisani ta fara laluben hanya tunda ya shige dakinsa da hasken sai falon ya dawo inda yake duhu sosa! ta nemi kan kujera ta zauna ba tare da tayi tunanin shiga dakin ba, saboda tsoro take ji tana ganin gwara ta zauna a falon shi yafi mata alheri, amma haki'kanin gaskiya Baban-Baba yayi mata bazata! ba ta ta'ba tunanin zai mata wannan wulakacin ba, hawaye masu tsananin zafi suka shiga kwaranya a saman fuskarta. Fitowa yayi daga d'akin ya ji shashshekar kukanta! Tausayi ta bashi amma bai nuna ba, ya d'aga muryarsa sosai!" Ke menene? ki ke wa mutune kuka" A zabure! ta juyo tana kallonsa! sai kuma ta sunkuyar da kanta amma ba ta fasa zubar da hawaye ba. Ya ja tsaki! da fad'in." Ko yunwa ki ke ji ?" Kai ta daga masa alamun hakane sannan tayi namijin 'kokarin fad'in." Ina so nayi sallar magariba da isha'i." Ya ce." To waye ya hana ki? da duk zaman da ki ke a gidan ba kiyi sallar ba?" Ta ce." Duhu ko'ina babu haske." Ya ce." Ki bud'e wannan ledojin da akwai fitila da batiri a ciki sai ki kunna." Da sauri ta fara dubawa, ya kunna mata hasken wayarsa har ta saita fitilar ta kama, sannan ya kashe wayarsa, ya kama hanyar fita, ta bishi da wani irin kallo zuciyarta sai bugawa take. Tana d'aura alwala a bandakin dake cikin falon ta dinga jin motsinsa kamar yana shigowa da abu, sai da ta fito ne ta fahimci cewa kayan abinci ne. Nan falon ta gabatar da sallolinta, ta jingina jikin kujera tana kallon shiga da ficensa tsakanin kicin da dakinsa. Gani tayi ya zo ya zauna a daya daga cikin kujerun dake falon, ido ya zuba mata, sai ta kasa jure hada ido dashi, domin yanzu gabadaya tsoro yake bata, ya sauya sosai! ya dawo Baban-baba na asali wanda ta san shi a lokacin da yake kwanciya a 'kasan mota! Gyaran murya yayi kafin ya kira sunanta yanda za ta ji.'' Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba. Ya ce." Nan ne gurin da maigidana ya bani domin na zauna da iyalina. bayan haka kuma sa'i da lokaci za ki dinga zuwa kina gaisawa da kakarsa wacce take zaune a cikin gidan, za ki dinga taimaka mata da wasu abubuwa duk da cewa akwai masu aiki amma kema zaki shiga sahun su, akwai kayan abinci a kicin komai da komai na bukata maigidana ya bani kudi nayi miki sayayya! a cikin ledojin nan akwai kayan sawarki kala hud'u da mai na shafawa da sabulun wanka da wanki da sauran tarkacen ku na mata, abinda babu kada kiyi 'kwaron baki sai ki sanar dani, amma ina so ki zauna da masu gidan nan lafiya! mussaman maigidana domin shi ya mayar dani cikakken mutum kamar kowa, wannan dalilin yasa nake so kiyi masa biyayya kamar yanda za kiyi min, duk wani abu da yake bukata kiyi masa.'' A sanyaye ta ce." Insha Allahu zanyi iyakar bakin kokari na, ni dai buri na ka ri'ke ni amana kamar yanda kayi alkawari! Tsaki ya ja kafin ya mi'ke tsaye ya ce." Wace amana kuma? ki daina wannan maganar, domin kada ki manta fa ke kamar siyan ki nayi a gurin mahaifinki, saboda haka ki daina wannan maganar." Wani irin kallo take masa tana jin maganganunsa na amsa kuwwa! a kunnanta "Kada ki manta fa ke kamar siyan ki nayi a gurin mahaifinki, don haka ki daina maganar amana." Wannan magana ta jima tana yi mata yawo a k'wa'kwalwarta. Jin yunwa na nema ta halaka ta yasa babu shiri ta dauki fitila ta nemi hanyar kicin ta je tana laluben abinci, aikuwa ta samu fulas cike da dambun shinkafa wanda yaji kayan had'i! ga ledojin ruwa nan pure water ta dauka ta fito da fulas din abincin a hannunta. [12/12, 1:06 PM] Bintu: 53&54 A ta'kaice dai Shahida ita kad'ai ta kwana, domin tun da yayi fitar nan, bai dawo ba, tun tana jin tsoro har ta hak'ura ta barwa Allah al'amarin, sai dai bakinta bai daina addu'a ba har san da bacci 'barawo ya sace ta. Motsin shigowarsa da asubah ya tashe ta, sai ta mik'e zaune da sauri tana laluben fitilar da gurin bacci ta fad'i a gurin, batiran duk suka watse Shigowarsa yayi daidai da lokacin da ta gama gyara fitilar haske ya mamaye falon. Ya kalle ta babu walwala a tattare dashi ya ce." A nan ki ka kwanta ne?" Kanta ta daga masa alamar ."Eh." ya kama hanyar d'akinsa ba tare da ya sake wata magana ba, wannan ya sake tabbatar mata da cewa ba a gidan ya kwana ba. Jiki a sanyaye tayi alwala ta fito anan falon dai ta gabatar da sallah, ta jima tana addu'a tana kuka sosai take neman sassauci a gurin mai duka domin ba ta ta'ba tunanin cewa zata fuskanci irin wannan matsala ba. Sai da gari ya waye sosai ya fito cikin shiri ya d'ora rigar sanyi babbah da sabuwar hula irin sanyi ya rufe kunnuwansa sannan ya rufe idonsa da gilashi b'aki, tsira masa ido tayi domin gani tayi kamar yayi haske ba kamar can baya ba sai dai har yanzu wannan k'asumbar tana nan duguzaza! tare da tsalli-tsallin furfura. Ganin yanda take kallonsa sai ya sha kunu! ya ce." Na zama tibi ne?" Ba ta ji abinda ya fad'a ba amma yanayin yanda yayi maganar yana tsatstare ta da ido ta fahimci cewa ransa a 'bace! sai ta d'auke kanta tana mamakinsa a cikin zuciyarta. Gyaran murya yayi sosai ya bud'e ta domin ta ji abinda zai fad'a mata. "Zan tafi can kudu wani aiki kamar yanda maigidana ya umarce ni, don haka za ki cigaba da zama anan babu wata matsala tunda akwai ci dasha saboda haka ki kwantar da hankalinki, amma ban amince ki je ko'ina na ba, abinda na aminta dashi zuwa gaishe da kakar maigidan kamar yanda na fad'a miki da farko. Tsoro ta cire a ranta ta kalle shi sosai kafin ta ce." Shi maigidan naka bai san cewa kai ango bane zai tura ka wata uwa duniya, kada fa ka manta amana ka d'auko ni a gaban iyaye na mai yasa tun kafin tafiya tayi nisa ka sauya hali, wallahi ban yi tunanin haka daga gare ka ba." Hannu ya d'aga mata da fad'in." Za kiyi min rashin kunya ne?" ta girgiza kanta. ya cigaba da cewa; idan na zauna a gidan me zanyi miki da har ki ke wannan maganar." Sunkuyar da kanta tayi tana mamakinsa. Ya cigaba da cewa'' Ai ban ta'ba ganin makwad'aicin uba irin naki ba, wanda bai san k'ima da mutumcin 'ya'yansa ba. domin ya ba ni auranki ne a matsayin fansa a gare shi, ke da bakinki kuma ki kayi al'kawarin girmama maigidana saboda alherin da yayi miki keda mahaifinki, amma har kina da bakin fad'in wata magana a kansa, to ki iya bakinki idan ba haka ba ranki zai yi mummunan 'baci! Kuka take sosai! ta ce." Yanzu mai ya kawo wannan maganar? wato ka naso ka nuna min cewa maigidan ka ya fi ni kenan, kada fa kamanta bani da kowa a wannan gari sai kai, ban san ko'ina ba, sannan akwai rashin sabo wannan shine dalilina na fad'in wannan maganar amma bada cin mutunci ba. Tsaye ya mi'ke tare da fad'in" Ni dai na fad'a miki ki kiyaye! kuma ki iya bakin ki, maigidana ya fi kowa daraja a guri na ciki kuwa har dake, mutukar kina so na shirya dake to ki girmama shi kuma ki san irin maganar da zaki dinga fad'a a kansa. Cikin shashshe'kar kuka ta ce." Kayi hakuri zan kiyaye insha Allah, yanzu kwana nawa za kayi?" Ya ce."Sati biyu zanyi." a sanyaye ta ce." To Allah ya kiyaye hanya ya bada abinda aka je nema." Ya amsa da amen kafin ya d'ora da fadin." Akwai komai na bukata, idan wani abu ya 'kare to kiyi wa Sule magana wanda ya kawo ki nan, abokina ne zai yi miki komai kafin na dawo" Ta ce." To shikkenan.'' hanyar fita ya nufa, sai ta mi'ke domin yi masa rakiya ya dakatar da ita da fadin." Koma ki zauna bana bukata." Ta koma ta zauna tana kallo ya bud'e kofa ya fita tayi saurin zuwa ta bud'e labule tana le'kansa, juyo wa yayi suka had'a ido, sai tayi saurin sauke labulan gabanta na cigaba bugawa. Kamar yanda ya sanar mata da cewa akwai komai na bu'kata hakane. koda ta duba kicin din komai da komai da akwai, sai ta kunna karamin gas din da ta gani a ajiye. ta d'ora ruwan shayi, sannan ta feraye dankalin hausa ta soya dai-dai cikinta, a kicin d'in ta had'a shayin ta zauna tana sha tare da had'awa da dankalin da ta soya. Tunani ne yayi mata yawa, gabad'aya ta rasa a ina zata ajiye wannan al'amari! ashe Baban-baba mayaudari ne ba ta sani ba? ita dai har ga Allah ta ke k'aunarsa take kuma yi masa kallon mutum mai mutunci da amana, ashe kallon kitse takewa rogo, tun ba aje ko'ina ba ya fara gwada mata wasu dabi'u marasa kyau! hawaye ta share! tana tunanin Baba Asabe, watakila dama abinda take ta guje mata kenan shiyasa hankalinta bai kwanta da al'amarin ba, tabbas duk abinda ya fad'a akan mahaifinta gaskiya ne, beyi masa sharri ba, domin ita kanta ta san ba suyi sa'ar uba ba, sai yanzu take sake gazgata maganarsa, domin duk uban arziki mai kishin 'ya'yansa ba zai dauki aure ya baiwa irinsu Baban-baba wad'anda basu da asali ma'ana ba a san daga inda suke ba. Sosai ta ci kuka ta koshi a kicin din, ta ajiye al'amarin a matsayin kaddararta, domin a yanzu duk abinda za ta fito ta fad'a a banza babu wanda zai saurare ta. Wanka tayi ta shirya cikin atamfah riga da siket daga cikin kayan da ya kawo mata jiya, tasa hijabi a jikinta ta kama hanyar fita, tana so ne ta je ta gaisa da masu gidan kamar yanda ya umarce ta kafin ya tafi. Sai da tayi tafiya sosai sannan ta fito harabar gidan, nan taga mutane rukuni-rukuni a wata rumfa yawanci maza ne matan basu da yawa, suna zazzaune, daga can bakin gate kuma ma'aikata ne masu tsaro sun kai bakwai harda masu bindigu a hannu. Da sauri ta d'auke kanta. tana jin fad'uwar gaba, lallai duk yadda akayi wani abu ne zai faru a gurin, da alamar suna jiran fitowar maigidan ne. Wata hanya ta bi duk da cewa bata san ina za ta shiga ba kawai dai tayi hasashen nan ne hanyar da zata shiga cikin gidan. Wani lafiyayyan k'amshin turare ya daki hancinta. da sauri ta d'ago kanta tana kallon hanyar lokacin da suka fito tare da escort dinshi guda biyu. ido suka had'a da saurin gaske tayi kasa da kanta jikinta yayi bala'in mutuwa! ganinsa. cikakken mutum kamili mai halin dattako! yana sanye da farar shadda kal dinkin tazarce da jar dara a kansa as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi, yayi kyau sosai ba'a magana domin gabad'aya shekarunsa sun 'buya sakamakon gyaran fuskar da akayi masa wanda ya sake k'ayata fuskarsa, gemu kad'an ya bari wanda ya kwanta luf da furfura kad'an-kad'an. Duk sai ta dabarbace! domin wani irin kwarjini yayi mata, tun kafin ya karaso gurin da take ta zube 'kasa tana gaida shi da yanayin maganarta. Bai amsa ba sai dai yayi mata alama da hannunsa ma'ana ta tashi, kasa mi'kewa tayi kanta yana 'kasa tana kallon kyakykyawar kafarsa cikin ba'kin takalmi maigidan yatsa. Ganin ta kasa tashi yasa ya wuce ya bar ta a gurin, yaransa suka rufa masa baya. Tashi tayi tana buge jikinta zaninta duk ya kwashi datti! a sanyaye ta juya tana kallon bayansu har suka 'kurewa ganinta, ta sauke ajiyar zuciya mai zafin gaske. A hankali ta tura kofar falon wacce ta kasance ta gilas. sallama tayi a nutse da yanayin maganarta. Hajiya Saude tayi saurin kallon bakin k'ofar tare da amsa sallamar. kallon rashin sani take mata, ita kuma duk sai ta daburce! ganin kallon da matar take mata. A sanyaye ta isa har gurin da take ta zube 'kasa tana gaishe ta, Cikin wani irin yanayi ta amsa gaisuwar tana mamakin daga ina yarinyar take, domin ita duk a tunaninta irin nakasassun da suke zuwa gidan neman taimako ne, da jin yanayin maganarta ta kurame ba sosai take fita ba. Ta sauke ajiyar zuciya cike da d'an tausayin yarinyar a tare da ita ta ce." Ai yanzu maigidan ya fita idan taimako ki ka zo nema yana waje can zaki tsaya." Ganin tayi shuru ba ta amsa ba, yasa ta bud'e muryarta ta sake maimaita maganarta . Cikin jin nauyi ta ce." Sunana Shahida ni ce matar Baban-baba." Jim tayi kafin ta ce." Ayyo! amaryar Sule ce ashe. sai tasa dariya da fad'in ai jiya nan yake sheda min cewa ya k'ara aure har maigidan ya bashi gurin zama a cikin gidanan Allah ya sanya alheri ai mu nan da Sule muke kiransa." Murmushi tayi ba tace komai ba, sai dai cikin zuciyarta take ta auna maganganun matar ashe dama sunansa Sule na gaskiya. Hajiyan ta cigaba da cewa." Ai Sule mutumin kirki ne sosai ki ri'ke shi da kyau sosai! kuma ki zauna da kishiyarki lafiya." Gabanta ya fad'i jin maganar kishiya, ta dinga kallonta lokacin da take jaddada mata nagarta da kyawun halinsa, sai ta ji wasu zafafan! hawaye suna nema su kufce mata. Da k'yar! ta iya danne damuwarta, ta ce." Hajiya ko da akwai wani abu da zanyi miki?" Girgiza kanta tayi ta ce." A'a babu komai, sai dai ki zauna ki d'ebe min kewa ai na ji dad'in zuwanki gidan nan saboda zaman kad'aici yana damuna, Shukura kuma ba gwanar zaman falo ba kullum tana daki da waya a hannu." Sunkuyar da kanta tayi tana nazarin maganganunta, to shin maigidan bashi da aure ne? ko kuma ba a gidan yake zaune ba? bata da mai bata amsa sai kawai tayi shuru, tare da tsirawa tv ido kallon kawai take amma ba sosai take jin abinda ake fad'a ba. Cikin riga da wando na bacci ta fito daga d'akinta. ganinta a zaune yasa tayi turus! tana kallonta babu annuri a fuskarta ta kalleta da fadin." Hajiya wannan wacece kuma?" ta fada tana nuna ta da yatsa. Tana shirin bata amsa ya shigo, duk sai su kayi shiru suna kallonsa, a nutse ya zauna kan kujera yana kallon Shukuran dake tsaya da alamun rashin gaskiya a tattare da ita. "Kin yi sallah?" tambayar da ya yi mata kenan. Sai ta hau diri-diri kafin ta ce." Daddy bani da tsarki ai." Shuru yayi be ce komai ba, da shagwaba ta ce" Daddy don Allah ka bari na je gidan bikin nan, kamar hakan bai dace ba tunda Aunty Samira 'kanwar mommy ce kuma kai ma 'kanwarka ce ka taimaka Daddy don Allah." ta 'karasa maganar tana karyar da kai. Shuru yayi bai ce uffan ba, ta kalleta da fadin." Hajiya kisa baki don Allah" Kallonsa tayi da fad'in.'' Alhaji Habu ina nema mata alfarma." Yanda ta fad'i maganar cikin 'kaskantar da kai ya bashi dariya! Ya ce" Na amince amma ba don halinta ba, kuma ban yarda da kwana ba, aje a dawo." Tsalle ta buga da fad'in." Daddy na gode Allah ya 'kara girma." Duk abinda suke tana takure a gurin tana kallonsu, sai dai ba sosai take jin abinda suke tattaunawa ba. ita gabad'aya zaman sa a gurin shi ya 'kara firgitata! ta kasa gane wane yanayi take ciki, haka kawai mutumin yake cika mata ido. Hajiya ta nuna ta da yatsa da fadin." Yallabai wannan ita ce amaryar Sule fa, wallahi da farko na dauka irin masu zuwa neman taimako ne, sai da ta gabatar min da kanta tukkuna na tuna amma ga dukkan tana da matsalar rashin ji kurma ce" Kallon da yake mata ne yasa duk ta tsargu! ta kasa kwakwkwaran motsi. A hankali ya kalli Hajiyan da fadin." Ya sunanta?" "Shahida sunanta, ai na ce na samu abokiyar hira duk da cewa ba ta ji sosai hakan bai zai hana ta d'ebe min kewa ba." Ya ce." 'Kwarai kuwa nima wannan ne dalilin da yasa na bashi guri a gidan nan, na ce ya zauna saboda ki samu walwala. Ta ce." Maganar auranka dai shuru Alhaji kullum sai kace kana kan hanya.'' Shukura da sauri ta ce." Hajiya ai daddy ba sabon aure zai yi ba, Mommyna zai dawo da ita.'' Wani irin kallo yayi mata kafin ya mi'ke ba tare da ya ce musu komai ba ya haura samansa. Hajiya ta ce." Shukura mahaifinki ya tsani ayi masa maganar Fatima mutukar kina so ki ga b'acin ransa to ki ambaci sunanta, wannan k'iyayyar tayi yawa." A sanyaye ta ce."Wai Hajiya me ya faru ne? na lura daddy ya tsane ta sosai kuma yana da ri'ko! kome tayi masa ai sai yayi hakuri tunda na shiga tsakani, sannan da dangantaka a tsakaninsu." Ta ce." Shukura labarin yana da tsayi sosai! amma babu shakka Fatima ta yi abubuwa da yawa marasa kyau a can baya! wanda ba su da amfani, saboda haka tayar da al'amarin yana nufin 'bacin ran mu gabad'aya. A sanyaye ta ce." Shikkenan to Allah ya kyauta." ta amsa da "Ameen ya rabbi." Shahida na zaune tana satar kallonsu, yanayin fuskokinsu da yanda suke magana a hankali cikin rashin walwala yasa ta gane cewa lallai abinda suke tattaunawa ba mai dad'i bane. **** To kwana d'aya biyu har ta saba! kullum idan ta tashi za ta gyara gurinta, kafin tayi wanka ta shirya jikinta tsaf! sai ta karya kummalo ta nufi cikin gidan a can take yini tare da hajiya, idan lokacin shiga kicin yayi ta je ta taimakawa masu aiki, sosai Hajiya take jin dadin zama da ita, wannan dalilin yasa ta umarce ta cewa duk abinda take bukata kada tayi 'kwauron baki ta tambaye ta, anan take cin abinci rana da dare. sai tayi sallar isha'i take tafiya gurinta, sai dai abinda yake damunta yanda Shukura ke 'kyamarta! hantara! kyara! wataran harda zagi! kuma kullum ita ke zuwa ta gyara mata d'akinta ta wanke mata bandaki da sauransu, amma bata ta'ba godiya ba, wannan abu yana damunta sosai! Kasancewar ta samu caji a wayarta yasa ta tura masa text na gaisuwa da kalaman soyayya! tana jiran amsarsa, shuru bai bata amsa ba, jikinta ya 'kara yin sanyi gabad'aya bata da wani kuzari, yau kwanansa tara da tafiya babu wata magana da ta ta'ba shiga tsakaninsu ta hanyar sadarwa. Cikin kwana goma da tayi a gidan ta sauya fatarta tayi luff! tayi kyau daidai gwargwado kuruciyarta ta sake bayyana, Shahida bata da wani kyau na ku zo a gani, sai dai tana da dirin jiki mai kyau akwai cikar kirji tare da kyakykyawan k'ugu ko'ina a jikinta a cike yake bata da rama kuma tana tsakatsaki ita ba doguwa ba sannan ba gajeriya ba, tana da yawan gashi cikkake irin na asalin hausawa, bakikirin! haka take d'aure shi da ribbon ya taru sosai a kanta, tana yanayi da Nafisa Abdullahi jarumar finafinan hausa, sai dai har taso tafi Nafisa cika da kwarjini. ba ta da makusa bayan matsalar kunne (rashin ji) da Allah ya hallice ta. Yau kwana goma sha biyu kenan da tafiyarsa, tana lissafi saura kwana biyu ya dawo,sai murna da farin ciki take, domin ita kad'ai ta san irin halin da take shiga a duk lokacin da za tayi bacci! tsoro take ji ita kad'ai a wannan gurin, koda wani abu ba zai shiga tsakaninsu ba, idan tana jin motsinsa a gidan rahama ne. Shuru lokacin da ta shiga falon, sai sallama take babu wanda ya amsa, cikin zuciyarta take tunanin ko Hajiyan na d'aki bata fito ba, sai ta yanke shawarar shiga dakin. a lokacin ne yake saukowa daga sama cikin pyjamas (kayan bacci) irin masu falmaran amma babu ta ciki kirjinsa wanda ya ke cike da kwantaccen gashi 'baki duk a waje! Da saurin gaske ta kawar da kanta! tana jin wani irin fad'uwar gaba, 'kafafunta ne suka shiga kyarma! ta zube a k'asa tun kafin ya 'karaso gurin da take. "Alhaji Ina kwana?" tafad'a cikin sar'kewar murya. Bai amsa ba da hannu yayi mata alamar ta tashi. Tashi tayi amma ta gagara kallonsa, gabad'aya ma tsigar jikinta ce take tashi ganinsa haka. Gurin cin abinci ya nufa ya zauna domin karya kummalo. Ita kuma jiki a mace ta kama hanyar fita, ya tsirawa bayanta ido, duk da cewa a cikin hijabi take hakan bai hana shi ganin 'kirar jikinta ba, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! yana danne abinda ke taso masa. muryarsa ya bud'e sosai kafin ya kira sunanta. Juyowa tayi tana kallonsa, yayi mata alama da hannu ta je gurinsa. Gabanta ya tsananta da fad'uwa, shin idan ta je me za tayi masa? abinda take rayawa kenan a zuciyarta. amma tuno gargadin mijinta yasa a sanyaye ta nufi gurin nasa kamar yanda ya umarce ta. [12/14, 11:49 AM] Bintu: 55&56 A nutse ta d'an tsaya a jikin daya daga cikin kujerun cin abincin, amma bata yarda ta kalleshi ba, kanta yana 'kasa, sai dai a jikinta taji ana kallonta. gabanta ya dinga fad'uwa tana kiran innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! 'kadaicewarsu, a falon su biyu yana nufin abubuwa da yawa, saboda haka sai tayi ta maza! ta d'ago kanta ilai kuwa sai ta ritsa shi ya zuba mata ido wanda har ya fara sanja kala, ya 'kan'kance ya kuma yi ja! ta sake shiga rud'ani mara misaltuwa! cikin yanayin maganarta ta ce." Yallabai ko kana bukatar wani abu ne?" Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nuna mata tarin abincin dake shirye a teburin alama yayi mata wai ta had'a masa abin kari. Cikin rashin kuzari ta fara abinda ya umarce ta, gurin tsiyaya shayi (tea) ya zubo mata a hannu saboda gabad'aya ta kasa nutsuwa sakamakon kallon kurillan da yake mata. Yarfe hannun tayi, tana d'an ya mutse fuska! babu zato babu tsammami ta ji ya kama hannun yana dubawa! da saurin gaske ta k'wace hannunta tana d'an harararsa, gefe guda kuma kafafunta sai rawa suke domin ba 'karamin tsorata tayi da abinda yayi ba. "Sannu.'' a hankali ya furta duk da ya san ba lallai ne ta ji ba. Ba tare da tace masa komai ba, ta juya da sauri ta bar gurin. kallo ya bita dashi yana ayyana abubuwa da yawa a tare da ita. Cikin mutuwar jiki da faduwar gaba ta isa sashenta, ta zube kan kujera tare da dafe goshinta. Sam 'kunar dake hannunta bata dameta ba akan abinda ya faru a tsakaninsu, shin wai mai yake shirin faruwa ne? gabad'aya mutumin bai kwanta mata a rai ba, duba da irin mugun kallon 'kurrila da yake mata, bayan haka kuma menene hujjarsa na ri'ke mata hannu a matsayinsa na babba mai hankali ai ya san hakan ba daidai bane, tunda yafi kowa sanin matsayinta a gidan, matar aure ce kuma matar yaronsa. Gaskiya al'amarin ya sanya ta cikin rud'ani haka ta yini tana tunane-tunane! Wajajen tara na dare text ya shigo wayarta, da yake tana samun chaji a can cikin gidan, tunda gurinta babu wuta haka take zama cikin duhu sai hasken wannan fitilar da ya kawo mata ranar da suka zo gidan. Farin ciki ya cika mata zuciya ganin mijin nata ne ya turo mata sa'kon, cikin rawar hannu ta bud'e domin karantawa! Hawaye ne suke 'kwace mata ganin abinda yake rubuce. _"Ba zan dawo jibi ba, saboda maigidana ya umarce ni na zauna tsayin sati uku na kula masa da wasu harkokinsa ."_ Tana kuka ta rubuta masa amsa kamar haka. _Don Allah ka dawo wallahi ina cikin matsala da kewarka akwai abubuwan da suke shirin faruwa."_ Ya dawo mata da amsa kamar haka. _"Maigida na ya wuce komai a guri na, ba zan iya yin jayayya dashi ba saboda haka kiyi hakuri kawai"_ Kasa bashi amsa tayi sai uban kukan da take shirga! wai shin ita ya za tayi ne? wannan lamari da faru ya fara sanya ta cikin shakku da fargabar zama a gidan. Kwana tayi cikin zullumi da tunani da kuma rashin madafa, amma tasa a ranta cewa Allah shine madogara a gare ta. Washe gari ta shirya tsaf cikin doguwar riga ja mai adon duwatsu tayi kyau sosai sai dai rigar ta d'an matseta daga 'kasa kasancewarta mai cikakken 'kugu, koda ta ga haka sai tayi tunanin cire rigar ta sanja wata sai dai duk kayanta sunyi daud'a wanki suke bukata gashi har yanzu ba ta ga Sulen ba ballanantana ta tambayeshi sabulu. hakanan ta yafa mayafin rigar ta nufi cikin gidan domin gaishe da Hajiya kamar ko da yaushe. Sai dai yau ma shuru babu Hajiyan babu Shukura! cikin zuciyarta take tunanin ina suka tafi, can taji motsi a hanyar kicin ta juya da sauri, sai tayi ido hud'u da Sule ya fito daga kicin din da wani abu a wuyansa, hannunsa rike da babban tire ya shiryo abincin akai. Gaisawa sukayi take tambayarsa masu gidan, nan yake sheda mata cewa sun je biki za suyi kwana uku ko hud'u kafin su dawo." "Eh hakane fa, ta manta shaf ta ji suna maganar biki wanda za suyi a cikin gari. 'Dan tsayawa tayi har ya gama shirya teburin cin abincin, sannan ta kalleshi tare da sheda masa bukatarta. Ya ce." Babu damuwa insha Allah zan kawo miki idan anjima. Tana shirin magana suka hangi sakkowarsa daga sama. yau ma yana cikin kayan bacci masu taushi masu kama dana sanyi domin har da hula. waya ce a kunnansa da alama da wani yake magana. Koda ya sauko kai tsaye gurin cin abincin ya nufa. Sule ya bishi gurin da saurin gaske. Da har tayi niyyar fita sai kuma wata zuciyar ta hana ta domin tana gudun 'bacin ran mijinta tana kuma so ta zauna lafiya dashi, wannan dalilin ne ya sa ta tsaya amma har yanzu tana jin haushin abinda yayi mata jiya. Sule ya risina tare da mi'ka gaisuwarsa, ya amsa hankalinsa na kan wayar dake hannunsa. Sule ya fara 'kokarin zuba masa abinci, sai ya dakatar dashi tare da bashi umarnin tafiya. Ya bi umarni cikin sauri ya kama hanya ya fita. Ta kai minti biyar a tsaye tana dawurwura! kafin ta yanke shawarar zuwa ta gaishe shi. Duk abinda take yana kallonta ta gefen idonsa. A nutse ta tsuguna da fadin." Yallabai ina kwana ka tashi lafiya?" Ya d'an saci kallonta da gefen ido kafin ya amsa a ciki, wanda yake da tabbacin ba lallai ne ta ji ba. Itama ganin bakinsa ya motsa yasa ta mi'ke tsaye zata tafi. Kawai ta ji sunanta rad'au! a bakinsa. Ta ja ta tsaya tana kallonsa gabanta na bugawa. Da hannu ya nuna mata gurin zama. ma'ana ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun dake gurin. Kasa zama tayi, domin tana ganin kamar hakan bai dace ba. Ya bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce." Ki zauna nace ko bana son gardama." Ganin yayi maganar da yanayi na bacin rai! yasa taji wani iri kwata-kwata ba taso ta 'bata masa rai! Ido cike da ruwan hawaye ta ce" Kamar hakan bai dace ba. "Ni na baki umarni." yafad'a yana tsatstsare ta ido! A sanyaye ta ja kujera ta zauna amma ta gagara kallonsa, bayan kwarjinsa sai mugun 'kamshin turaransa da duk ya cika gurin. sai jikinta ya sake mutuwa ta dinga wasa da hannayenta. Muryarsa ya bud'e sosai tare da kiran sunanta. Ta amsa tana d'an kallonsa, kafin ta sunkuyar da kanta kasa tana sauraran abinda zai biyo ba. Ya ce." Ya hannun naki?" "Da sauki." tafada a ta'kaice! Gurin yayi shuru na minti uku. d'ago kanta tayi ta ritsa shi ya 'kura mata ido wannan karon ma idonsa ya sauya kala yayi ja! tare da 'kan'kancewa! sosai ta shiga rud'ani! sam bata 'kaunar wannan kallon da yake mata. Ta tsinkayi maganarsa yana cewa; 'Kin san kina da kyau kuwa ?" Shuru tayi ba ta iya magana ba, sai mugun mamaki! da yake kasheta. Ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! kafin ya sake bude muryarsa yanda za ta ji ya ce." Zuba min abinci." A hankali ta fara zuba masa abincin tana Allah wadai da wannan hali nasa. shi kuma sai kallon hannunta yake, wannan dalilin yasa duk ta daburce amma dai yau ba ta zubar da komai ba. Bayan ta had'a masa sai ta kalleshi, as'usul ita d'in dai yake kallo! 'bata fuskarta tayi kafin ta ce." Zan tafi Yallabai. Kai tsaye ya ce." Zauna ki ta ya ni ci." Ta kalleshi da tsantsar mamaki a tare da ita lallai ma wannan mutumin da alama bashi da kamun kai Fita tayi daga tsakanin kujerun. Ya kira sunanta, ta kalle shi ba tare data amsa ba. Babu walwala a tattare dashi ya ce." Hau sama ki gyara min gado na. Taji wani irin miyau! ya tsinke a bakinta tsabar tashin hankali. Baki na rawa ta ce." Yallabai kamar hakan bai dace ba, kana yin wasu abubuwan da basu cancanta da kai ba. Ya ce" Na san ke matar aure ce, kuma matar yaro na, to ina so ki sani; shi mijin naki a 'karkashi na yake, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka kada ki sake yi min jayyaya akan umarni na. Jikinta yayi sanyi tana sake tuno jan kunnen da mijin nata yake mata akansa. Abincinsa ya fara ci ba tare da ya sake kallonta ba. Ta saci kallonsa ta gefen ido, sai ta ga babu walwala a fuskarsa. A hankali ta kama hanyar matattakalar bene tana addu'ar neman tsari a zuciyarta. Tsaruwar d'akin sam bashi ne a gabanta ba, babban burinta ta gama abinda take yi ta fita. Tana tsaka da gyara shimfid'ar gadon ya shigo dakin. Gabanta ya tsananta fad'uwa! duk sai ta rasa abinda za tayi, ta dinga sauri tana jere filo sam ta'ki kallonsa sai sanda ta ji kamar yana murzawa 'kofar mukulli (key) sannan ta zabura! ta kalle shi, lokacin ya rufe 'kofar ya nufi inda take. [12/15, 12:28 PM] Bintu: 57&58 A tsorace take kallonsa a lokacin da yake 'kokarin zuwa gurin da take tsaye. Cikin wata irin tafiyar isa da ta'kama! ya tsaya daf da ita hucin numfashinsa na dukan fuskarta. hannu ya sa cikin aljihu. kafin yasa d'aya hannun ya rungumota jikinsa! rikon tsauri! yayi mata da hannu d'aya yana sumbatar gefen fuskarta. Wani irin hauka da buge-buge! ta shiga yi duk domin ta 'kwaci kanta daga hannunsa! ta samu gefen kafad'arsa ta gartsa masa cizo! wanda yayi sanadiyar sakinta, sai ta matsa gefe tana mayar da numfashi tare da wani irin kuka! mai ciwo! jikinta na kyarma! tsigar jikinta gabad'aya ta tashi. Kallonta yake da idanuwan da suka sanja launi! ta zabga masa muguwar harara! cikin tsananin jin ciwo da takaicin abinda yayi mata ta ce." Wallahi ka ji kunya! ashe dama baka da kirki ko?" Ya tsira mata rikitattun idanuwansa dake cike da tsantsar fitina ta shekara da shekaru! gabad'aya yarinyar ta gama tayar masa da hankali. Ta je ta rarumi gwangwanin turare a kan madubi ta jefa masa tana kuka ta ce." Sai Allah ya saka min abinda kayi min, kuma sai na fad'awa mijina." Ya 'bata rai! kafin ya bud'e muryarsa sosai ya ce" Kafin ki fad'a masa ni zan riga ki, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka ki fice min daga daki" Da k'arfi ya k'arasa maganar yana nuna mata hanyar fita da hannunsa. Ta sake d'aukar wani gwangwanin ta je fa masa wanda ya sauka a goshinsa, tana zubar da hawaye ta ce" Ban yafe ba daka ta'ba ni." yanda ta ke rawar jiki da yanda take kuka har cikin ranta ya tabbatar masa da cewa ta ji ciwon abinda ya yi. Sai ya mi'ke da azama ya nufe ta, ta zabura! a guje tayi hanyar fita, garin kici-kicin bud'e kofar ta zame ta fad'i a gurin, rintse idonta tayi ganinsa a tsaye a kanta ya yi mata rumfa. Ta rufe fuskarta da tafin hannunta "Don Allah kada ke ta min haddi, ka dubi darajar aure kada ka sake ta'ba ni." tafad'a jikinta na wani irin rawa. Hannu biyu yasa ya d'ago ta ta mi'ke tsaye, ya tsirawa fuskarta ido, hawaye sai tsare suke a saman fuskar, harshe yasa yana tsotse hawayen, gabad'aya k'afafunta suka kasa d'aukarta, sai k'o'karin zubewa take a gurin, yana tallafota. Yanzu ma haukan ta sake yi masa tasa dukkanin 'karfinta ta dinga dukansa a k'irji har sai da ya saketa, ta zube a gurin tana wani irin kuka mai cin rai! Tayi tur! da wannan rayuwa da take. tayi Allah wadai da ita. Ya tsuguna gabanta tare da k'okarin daidaita yanayinsa ya ce." Ko na kwanta dake mijinki babu abinda zai ce, saboda iko na ne, ke kuma baki da wata daraja! sannan na ji kina maganar aure! to ki daina daukar wannan auran naku da mutunci, domin duk ina da labarin yanda akayi shi, da kud'i na aka fansheki a gurin mahaifinki, saboda haka ina da iko da damar nayi duk abinda nakeso dake. Wani irin kallo take masa bakinta ya mutu murus! gabad'aya ta rasa a wane mizani za ta ajiye maganarsa. Ganin tayi sanyi ta gagara magantuwa yasa ya mi'ke tsaye, anan ne ta girmansa ya bayyana sosai! ya tashi, saboda yanayin kayan dake jikinsa masu kwanciya a jiki ne, wannan dalilin yasa girmansa fitowa, gaskiya ta tsorata! da yanayin, sai tayi gaggawar d'auke idonta tana kiran sunan Allah a zuciyarta, tunda ta ke, bata ta'ba ganin girman namiji irin haka ba sai akan wannan mutumin da yake kokarin keta mata alfarma. "Tashi ki fitar min a daki.'' Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta, da sauri ta tashi har dankwalin kanta yana fad'uwa, anan ne ya ga tarin sumar kanta, ya sake shiga rud'ani, domin a rayuwarsa yana masifar son mace mai gashi, kawar da kansa yayi daga barin kallonta ya nuna mata hanyar fita da fadin." Yanzu nan zan kira mijin ki na sheda masa irin zagi da cin mutumcin da ki kayi min." Ya fadi maganar ne yanda za taji. Muguwar harara! ta buga masa kafin ta ja dogon tsaki! ta fita ta barshi a tsaye da kwantaccen murmushi a fuskarsa. Jiki a mace ya nemi guri ya zauna tare da dafe kansa, gabad'aya jikinsa ya rikirkice sha'awa ta shekara da shekaru ta taso masa, bai san ya zai yi ba a halin yanzu. Yinin kuka da damuwa tayi, duk ta tsargi kanta da kanta, sa'i da lokaci idan ta tuna al'amarin sai gabanta yayi ta fad'uwa, adduar kariya kawai ta lazumta domin ita kad'ai ce magani a gare ta. Wajejan goma da rabi na dare ya turo mata text cewa ta kiyayi 'bacin ransa idan ya dawo domin ya ji labarin abinda tayi wa maigidansa saboda haka tayi gaggawar zuwa ta bashi hakuri. Amsa ta bashi kamar haka; "Da kasan abinda ya faru a tsakanina dashi ba zaka fad'i haka ba maigidanka mutumin banza ne don haka ni ba zan bashi hakuri ba. Sai ya bata amsa da cewa; Ashe kuwa auranki yana gargada domin kuwa mutukar ba ki je kin bashi hakuri ba wallahi zan iya sakin ki." Jikinta yayi sanyi jin abinda ya ce. sai tayi shuru tana tunanin yanda za ayi ta je ta bashi hakuri bayan tasan shine mara gaskiya. Ya sake turo mata da wani sakon, cewa; "Lallai kada ta tsallake umarninsa a daran nan taje ta bashi hakuri. Agogo ta duba sha d'aya saura na dare, ya za'ayi ta iya fita a wannan daran. gaskiya sai dai da safe, shima don ba yanda za tayi ne. Yau cikin hijabi har 'kasa ta shirya jikinta, babu walwala a tare da ita nufi cikin gidan. Zaune a falo ta same shi kan wani keke irin na motsa jiki, yana sanye da singileti da wando iya gwiwa, cigaba yayi da motsa jikinsa ba tare da ya kalle ta ba. Tsugunawa tayi a gefansa da fadin." Ina kwana?" shuru yayi be amsa ba ya cigaba da abinda yake gabansa. "Don Allah kayi hakuri." Tafada cikin yanayin maganarta, gabadaya duk tayi sanyi ta fara nadamar wannan auran. Ya cire 'karamin towel din dake rataye a wuyansa. fuskarsa ya goge! kawai ya jefa mata towel din a jiki. Sai ta bi towel din da kallo tana mamakin abinda yayi. kallonsa tayi. suka had'a ido sai tayi saurin kawar da fuskarta. Ya tashi daga kan keken ya nufi gurin cin abinci ba tare da ya ce mata komai ba. Ganin haka sai ta ajiye masa towel din ta kama hanyar fita tana neman tsari dashi. Sunanta ya kira tana daf da fita. Ta juyo tana kallonsa fuskarta sam! babu fara'a. "Zo ki zuba min abinci" hankalinsa na kan wayarsa yayi maganar. Girgiza kanta tayi ta koma da baya domin bin umarinsa. Ta had'a masa komai ta ajiye a gabansa kafin ta ce." Zan iya tafiya?" Kansa ya girgiza alamun A'a. sai ta tsaya tana kallonsa da jiran umarni na gaba. Sai da ya mula tukkuna ya ajiye wayar hannunsa kafin ya kalle ta a sakarce ya ce." Kinyi kyau cikin hijabi." Tayi shuru dai ba tace uffan ba. Gabadaya girmansa ya zube a idonta. Ya ce'' Na ga kina ta wani rufe-rufe me ki ke b'oyewa ne?" Ta ce." Babu komai." Girgiza kansa yayi ya ce."Ban yarda ba gaskiya, ba zaki fita ba sai kin cire wannan hijabin na duba ki." Taji wani irin fad'uwar gaba! ta kalle shi idonsa k'ur! a kanta kamar tsohon maye! Ta ce" Shigowata ban kai minti goma ba kuma iyakata nan falon me kake tunanin zan d'auka?" Ya daga kafad'a da fad'in." Ni dai ban yarda ba saboda haka ki cire idan kuma kinyi gardama to zan cire miki da kaina. Cikin rawar murya ta ce." Kai fa uba ne, ka haifa kasan mai kyau da mara kyau, yanzu idan akayi wa 'yarka abinda kake min za ka ji dad'i?" "Ba zan ji dadi ba gaskiya" Serious ya fadi maganar. Ta ce." To mai yasa ka keyi min haka?" Shuru yayi be ce komai ba illah kofin shayi da ya d'auka yana kur'ba! Ta ce" Zan iya tafiya?" Ya ta'be baki "A'a nifa har yanzu ban yarda dake ba, mutukar zaki shigo nan to ki dinga sa mayafi wannan hijabin akwai munafurci a ciki. Cike da takaici da mugun haushinsa ta ce." Ba hali na bane sata, kuma ba zan fara anan ba, don haka ka daina d'aukar alhakina. Bagarar da maganar yayi ya cigaba da kur'bar shayinsa. Yanda ya ke wulakantata hakan yana yi mata ciwo mutu'ka! sai kawai ta kama hanyar fita a karo na biyu ya dakatar da ita da fadin." Har yanzu ban baki izinin fita ba don haka dawo ki tsaya." Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta koma da baya ta tsaya tana facing d'in shi, ya 'kura mata mayunwatan idanuwansa masu je fata cikin tashin hankali. Sai da ya gama karyawa tsaf! sannan ya tashi ya fito daga tsakanin kujerun ya nufi gurin da take tsaye. Ta ji fad'uwar gaba sosai! amma ba ta karaya ba, domin kuwa tasan duk shaid'ancin mutum bai fi karfin addu'a ba, tana da tabbacin cewa sai ta samu rinjaye a kansa. Daf da ita ya tsaya yana lumshe mata shu'uman idanuwansa. Ta kawar da fuskarta tana cigaba da nanata addu'ar neman rinjaye a bakinta. Ya sanya hannu da nufin cire hijabin jikinta. Ba tare da jin nauyi ba ta buge hannunsa da karfin gaske! bahaushe ya ce ." Idan babba ya zubar da girmansa yaro zai iya hawa kai ya tattaka. Ya dube ta da fad'in" Ba ki ji nauyin abinda ki kayi ba?" Zum'bura bakinta tayi tana d'an ture shi da 'kokarin so ta fita daga tsakaninsa domin ya babbake gurin yayi mata rumfa. Ya sake kama 'kasan hijab din a karo na biyu, sai ta sake wancakalar da hannunsa, ta tsinci kanta da nuna shi da yatsa da fadin" Wallahi zan baka mamaki yanzu nan!" cikin zafin zuciya ta fad'i maganar jikinta na wani irin karkarwa! Bai wani tsorata ba, sai ma sake matse ta da yayi jikin bango (garu) ya tallafo fuskarta da hannunsa d'aya, aikuwa karan hancinsa dake daf da bakinta ta gartsawa cizo! tana nema ta gutsire masa saman hanci! babu shiri ya matsa gefe yana shafa gurin da ta cije shi wanda yayi sheda tare da rurucewa! Zazzafar harara! ta buga masa kafin ta ja masa dogon tsaki! tana 'kun'kuni! ta wuce ta bar shi a tsaye a gurin yana bin ta da kallo har ta bud'e 'kofa ta fita. [12/16, 7:25 PM] Bintu: _'Karshen littafi na d'aya kenan, sai mu tara a cikin littafi na biyu, wanda ya kasance na kud'i #500 vip 1k za a tura kudin ta wannan account din...0542382124...Binta umar gtbank, idan kati za a turo sai ayi min magana ta WhatsApp da wannan numbers.. 07084653262.or 08089965176. BINTA UMAR ABBALE_ 59&60 Ya jima yana jinyyar karan hancinsa kafin ya daina masa ciwo, sai dai sa'i da lokaci idan ya tuna abinda ya faru tsakaninsa da yarinyar sai yayi murmushi! cikin zuciyarsa yake addua'a akan Allah yasa ta cinye jarrabawarsa, domin d'an zaman da su kayi tare sonta da k'aunarta ya gama mamaye jini da gangar jikinsa. A na ta 'bangaran kuwa daina walwala tayi a gidan, motsi kadan za ta tsorata, domin tana fargabar kada ya kawo mata farmaki har gurinta. Bata sake saki jikinta ba sai da su Hajiya suka dawo sannan. ta warware amma duk da haka Hajiyan sai da ta lura da wani abu, sai take tambayarta ko akwai abunda ke damunta ta daina sakewa, da sauri ta ce "babu komai wallahi kaina ne kawai yake ciwo." Hajiya ta ce'' Ai fa na ga alama saboda ba haka muka tafi muka bar ki ba, to amma kin shedawa mijinki domin naga kina da k'wauron baki'' Murmushi tayi ta ce." Eh na fada masa har ya siyo min magani na sha." Ta ce."To Allah ya raba lafiya." domin ita Hajiyan a tunaninta ko ciki ne da ita. Ta ce." Ki je ki kwanta ki huta ai sai da lafiya ake komai." Sosai tayi farin cikin hakan, sakamakon ganin saukowarsa tasan tabbas idan yana gurin ba zata iya sakewa ba. Ya zauna kujerar dake fuskantarta. sai ta sunkuyar da kanta a hankali ta ce." Ina kwana?" ya d'aga mata hannu ba tare da ya amsa ba. Hajiya ta kalle shi da fadin." Yarinyar nan bata da lafiya har nake zargin ko ciki ne da ita?" Gabansa ya fad'i ya kalle ta da fadin." Wane irin ciki kuma Hajiya duka-duka yaushe su kayi auran?" Murmushi tayi da fad'in." Yo tsakanin mace da miji ai sai Allah, ai yanzu kamar tuntu'be akeyi dashi a hanya, shine nake tambayarta mijinta ya sani, ta ce" Eh har magani ya siyo mata." Ya kalle ta tare da bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce" Ke da gaske ciki ne dake?" Kunya duk ta rufe ta, sunkuyar da kanta tayi tana jin nauyi don gani take kamar maganar tayi kama da ta rainin hankali! kwana d'aya kacal da aurensu ya dauk'e mata miji ya kai shi uwa duniya, zai zo yana tambayarta sai dai idan shine yayi mata cikin. ita da zuciyarta take magana. Hajiya Saude tasa dariya da fadin." Kai ma dai da wani abu, to idan shine a tunaninka za ta fad'a maka ne? ni ma hasashe kawai nake. Ba tare da ya ce komai ba ya dubi agogon dake daure a hannunsa, ya kalle ta da fadin " Hajiya zan fita" Ta ce" To Allah ya bada sa'a." ya amsa da "ameen yana kokarin tashi. Shukura ta fito daga d'akinta. Sai ya tsaya yana kallonta, ta ce." Daddy ina kwana?" ya amsa babu yabo babu fallasa. Ta ce."Hajiya ta fad'a maka sakon mommyna." Ya kalli Hajiyan domin jin 'karin bayani. Ta ce" Neman magana ne kawai irin na Hajiya Fatima, mun shirya dawowa gida ne shine take ba mu sa'kon gaisuwarta gare ka. Bai ce komai ba ya kama hanyar fita, sai suka bi shi da kallo jikinsu a sanyaye Hajiya ta riga tasan halinsa tun yana yaro mutukar ya bar abu to bar shi har abadah, wannan dalilin ne yasa take tausayawa Hajiya Fatima duba da irin wahalar da take sha a kansa ya'ki sauraranta, shekara da shekaru da rabuwar auransu, ta'ki aure ita lallai tana jira yazo ya mayar da ita d'akinta, in da shi kuma ya ci alwashin sai dai ya mutu babu aure mutukar sai ya zauna da ita ne. 'Yan uwa da ita kanta kakar tasa sunyi-sunyi har sun ha'kura, domin mai daki shi ya san in da yake masa oyoyo, shi kadai ya san irin wahalar da ta bashi a lokacin da suke tare. **** BAYAN KWANA BIYAR Tana zaune 'kasan kafet tana cin abinci wanda ci kawai ta ke yi saboda ta kori yunwa ba wai don abincin babu dadi ba, A'a sai don ta san mutukar ta kwanta da yunwa to tabbas zata tashi a galabaice! shiyasa take tuttura abincin tana had'awa da ruwa. Motsi ta ji ana kokarin bud'e kofar shigowa, gabanta ya yanke ya fad'i! ta tsirawa kofar ido tana addua a zuciyarta, domin ba ta kawo cewa mijinta bane ta fi tunanin maigidan ne da yake kai mata hari a duk lokacin da su had'u sai ya san yanda yayi ya ta'ba jikinta, wannan abu yana yi mata ciwo mutuk'a! ita ba abun ta zazzage shi ba tana cikin gidansa, sai dai duk sanda ya ta'ba jikinta ko ya cire mata dankwali sai ta yini tana share hawayen takaici wanda ya ajiye ta ma bai ta'ba ri'ke mata hannu ba amma shi kuwa har ya samu sararin rungumeta yana tatta'ba wasu abubuwa na jikinta. Da 'karamar wayarsa yake haske falon ya hange ta zaune kamar kace kyatt! ta ruga a guje! Ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah a cikin ranta da sauri ta je ta rungumeshi kawai sai ta fashe da kuka! tana sake matse shi a jikinta. Wani yanayi ya shiga amma bai bari yayi tasiri a tare dashi ba. yasa hannu ya cire ta daga jikinsa hanyar dakinsa ya nufa ba tare da ya ce mata uffan ba. A sanyaye ta je ta zauna tana kallon d'akin dake rufe don bayan shigarsa mukulli yasa ya kulle ba tare da ya tsaya ya saurareta ba. Kwanan 'kunci da 'bakin ciki tayi ido luhu-luhu! ta tashi don ba ta iya shiga kicin ba kwanciya tayi lamo kan kujera zazzabi na neman rufe ta. Tsayin kwanaki uku da dawowarsa uffan be ce mata ba, ko ta gaishe shi baya amsawa, fushi yake sosai! da ita. idan ya fita tun safe baya shigowa sai dare wajejen sha biyu. Sosai ta shiga damuwa matsananciya tun tana zazza'bi! sama-sama har ya kai ta 'kasa! ta dinga kwara amai, yana daki ya ji kakarinta! da sauri ya fito ya tarairaye ta bayan ta gama aman ya wanke mata baki ya kai ta kan kujera ya kwantar. Kicin ya shiga ya had'o mata shayi tea. da kyar ta iya shan rabin kofi ta koma ta kwanta tana lumshe idonta, gabad'aya yanzu ta daina sonsa tunda bashi da imani. Tsayin kwana uku yana kula da ita kafin ta warware sosai! sai aka koma 'yar gidan jiya, yana amsa gaisuwarta amma baya tsayawa suyi doguwar magana da juna ballantana ya ji damuwarta. Wannan abu yana mata ciwo sosai! cikin ranta sai nadamar auransa take. **** "Saliha jiya nayi mafarki da Shahida cikin wani yanayi mara dad'i." Baba Asabe ke wannan maganar lokacin da take d'ura man gyada a kwalba. Hankalinta na kan wayar dake hannunta Ta ce."Hum Baba Asabe kenan." Ta ce."Ko za ki yi mata magana ne da wayarki." Ta ce'' Baba raba ni da yarinyar nan don Allah na san dai mahaukacin nan ya fara cin ubanta." Ta ce." Saliha fata nagari lamiri, ba na jin dadin irin wannan maganganun da ki ke akan Shahida. Murmushi tayi kafin ta ce" Bari na tura mata text (sak'o) na san idan ta gani za ta bada amsa, tunda kin san dai idan an kira ta a waya ba lallai ne ta ji ba. Ta ce."To shikkenan Allah yasa mu ji alheri. Ba tare da ta bawa maganar muhimmanci ba ta amsa da "ameen" ***** _"Ke Shahida dama ba komai ne yasa na turo miki wannan text din ba. Baba Asabe ta dame ni wai lallai ta na so ta ji lafiyarki, saboda haka sai ki bata amsa."_ Wannan shine abinda Saliha ta rubuta. Tana hawaye take tura amsa kamar haka. _"Wallahi ina nan lafiya lou Saliha ki kwantar mata da hankali ki ce ina gaishe ta da kyau zan kuma zo ba da jimawa ba"_ Daga dakinsa ya fito ya ga tana kuka! sai tayi saurin share hawayen amma ba su daina zuba ba. Ya zo ya 'karbi wayar yana dubawa. Tausayi ta bashi ganin irin amsar da ta bayar, hakan ya sake tabbatar masa da cewa lallai zata ri'ke masa sirrin gidansa cikin ko wane hali. Bai nuna farin ciki a fuskarsa ba, sai ma yasa wayar cikin aljihunsa ya ci kunu sosai! ya zauna yana fuskantar ta. Zaman da yayi ta san DA WATA A 'KASA, sai ta sunkuyar da kanta tana neman sassauci gurin Allah. Ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji ya ce." Maigidana ya sake tura ni legos domin wani aiki! zan tafi yanzu don na kammala duk wasu shirye-shirye, saboda haka ina sake gargad'inki da kakkausar murya! ki kula da abinda zai 'bata masa rai! domin ya fi karfin komai a guri na, bayan haka kuma da kud'insa na aure ki, yana da iko dani da abinda na mallaka! duk abinda yake buk'ata kiyi masa, ki kula da kakarsa da kyau! wannan shine gargad'in da zanyi miki.'' Hawaye wani na bin wani ta ce." Don Allah kada kayi min haka, ka nema min alfarma a gurinsa ka tafi dani duk in da za kaje domin ina bukatarka a kusa dani, bayan haka kuma wannan mutumin bashi da hali mai kyau! farautata yake a duk sanda ya tura ka wani gari." Ya mi'ke tsaye! cikin fad'a ya ce" Sharri za kiyi masa? me zai yi dake? ina abin burgewa da sha'awa a jikinki da har zai farauce ki, to shikkenan misali a ce maganarki gaskiya ce, ni na amince ki bashi kanki a madadina domin bani da wata cikakkiyar lafiyar da zan kwanta dake, na fad'a miki wannan mutumin ya fi karfin komai a guri na, saboda haka na amince a duk lokacin da ya buk'aci wani abu a gurinki ciki kuwa harda kwanciya dake, to kada kiyi masa jayayya domin yin hakan na barazana da auranki, ki amince masa kai tsaye kuma ki sakar masa jiki sa'anan kiyi k'o'karin faranta masa, ki ji a ranki kamar kina tare dani, wannan shine abinda za kiyi ki faranta min rai. *WASA FARIN GIRKI!🥰* Ko ya zata kasance? ina fatan za ku biyo ni domin karanta cikakken labarin, don wannan sominta'bi ne, kada ku manta akwai labari a 'kasa jingim! don haka masoya kada ayi 'kasa a gwiwa gurin biyan kudi domin jin yanda za ta kasance. Ni ce taku a koda yaushe *BINTA UMAR ABBALE* MARUBIYAR *1-NANA KADIJA* *2-YARO DA KUDI* *3-GIMBIYA BALARABA* *4-BABBAN YARO* *5-MASHAHURI* *6-LADIDI KWADAGA* *7-RUWAN DARE* *8-SADAUKI OMAR* *9-NIDA YAYA SADAM* *10-YAR BANGAR SIYASA* *11-DA WATA A KASA* *12-MADADI* *13-KWARYA TABI KWARYA* *14- GA IRINTA NAN* *15-MATSALARMU A YAU* *16-GOJE*