11/13/22, 10:30 AM - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹rayuwar zainab❤‍🩹 By zainab kabir jaen Elegant online writers📚📖 Free page Page one Dukanta yake ta Ko'ina ihu take tana neman dauki dan allah kayi Hakuri insha allah bazan sakeba Amma duk wannan Rokon da take masa besa yadena dukanta ban Tun tana kuka har muryarta ya dena futa hankalinta yayi mutukar tashi Don tasan yau kasheta kawai zai yi Gabadaya jikinta yai laushi da kyar kukan ma yake futa saida ya gaji dan kansa ya kyaleta Janyota yai, yai wurgi da ita a kofar bed room dinsa Sannan ya juya daki ya koma Bango yake duka yana fadin I hate you natsaneki na tsaneki kuma bazan taba sonki ban Toilet ya shiga yafi minti Talatin yana wanka kafin ya fito gaban madubi ya tsaya mai yasha fa masu kamshi sannan ya nufi wardrobe dinsa masha kayan sojojine dayawa nagani aciki Daya daga ciki ya dauko ya shirya sannan ya nufi gaban madubin yadau turare mai sanyi kamshi ya fesa masha allah shine abinda na furta Sanda Naga irin kyawun Halitta irin na wannan saurayin yana da ma tsagaicin tsawo farine tas fuskar sa madaidaiciyace me dauke da dogon hanci da manyan fararen idanu dan karamin pink lip dinsa yafi komai daukar hankali a tattare dashi Sumar kansa bakace sidik tana kwance luf da ita hakama sajensa kai masha allah captain al'ameen kenan nidai haka nace duk yanda akai guy din yanada alaka da yan Indian 🥱🥱🥱🥱🥱🥱🥱 #zainab kabir jaen (zee baby ) 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹rayuwar zainab❤‍🩹 By zainab kabir jaen Elegant onliine writers📚 Free page Page two A hankali yake tafiya har ya Iso wajan parking din motocin gidan wata farar honda Naga ya nufah yaransan sane suka taso da sauri suna Sara masa Hannu ya daga musu ya shige motar suma motocin su suka shiga alayi suke tafiya har suka iso bakin gate din dasauri wani soja dayake gadin gidan yazo ya bude Musu kai tsaye Barack din sojojin suka nufa Tunda ya shiga sojoji suka fara sara masa har yashiga office din daya kasance mallakinsa office din yatsaru sai tashin kamshi yake captain al'ameen kenan matashi mai jida kudi ga kyau ga ilimi Kowa tsoransa yake a gurin dan baya daukar raini har Shugaban ninsa Baya ragawa ..................................... Adaya bangaren kuwa bayan ya hankadota kofar dakin dakyar ta lallaba tatafi bangaren daya kasance namasu aikin hi Dan Kuka take sosai tarasa wata irin tsana hamma al'ameen yai mata wani daki tashiga madaidaici tana kuka toilet ta nufah tasamu ruwan zafi tai wanka tafito Ta dauki wata kodaddiyar atamfar ta duk tsamin dauda takeyi amma ko ajikinta ahaka tasa tazauna tana tunanin rayuwar Shin yaushe zata samu farinciki allah yajikan nannen ta kuka takeyi har yanzu zainab kenan baiwar allah ................................ ❤‍🩹Shin wacece zainab❤‍🩹 Wata yarinya naga tana tafiya waddah akalla batafi shekara sha biyar ba a duniya tana tafe tana hawaye wani gida naga tashiga gidan nakasane wanda da labule akai kofar shiga gidan Daki naga tashiga ta tadda nanne tana ta murkususu tana dafe da cikinta cikin kuka take cewa nannena nasamo miki magani bari injika miki a hankali tace Allah yai miki albarka zainab allah yakawo miki farinciki arayuwar ki a hankali ta goge hawayen daya bata mata fuska Tace ameen nanne tadauko kofi tajika mata maganin ta tallafota ta bata ba'a dau lokaci ba cikin nanne ya lafa bacci ya dauketa ita kuma ta dauki robar bararta ta tafi bara don samomusu abinda suci Amma har magariba nera hamsin tasamu kai tsaye ta wuce shago tasiyo garin kwaki na talatin sugan ashirin ta shigo gidan Akan dadduma tatarar da nanne yajiki tai mata ta dau buta itama Tagabatar da sallar magariba tazo kusa da nanne tazauna da tausayi ta kalleta tace kindawo Tace eh nannena amma tunda nafita naira hamsin nasamu shine nasiyo miki gari kici kinga bakya jin dadi hawaye nanne ta goge tace allah ya bayyanamiki iyayenki kihuta da wannan wahalar itama hawayen ta goge tace nanne nifa banda iyayen bayanke da Baffah allah yai masa ....... #zainab kabir jaen (zee baby) More comments more writing i love u my lovely fans😀😀 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹rayuwar zainab❤‍🩹 By zainab kabir jaen Elegant online writer📖📚 Free page Page three Da suna sona bazasu yardaniba tun da suka haifeniba haka kuka tsinceni allah yaji kanka baffah na shine gatana da bai taimakeni.ba da yanzu bana duniyar ma dan haka ni wannan rayuwar tafimin dadi nanne na mubar maganar nan kisha garin nan murmushi nanne tayi azuciyar ta tana fadin zainab kenan Ko baki fada ba ai ansan kina cikin wahala wlh Afili kuma tace toh diyata kwakin tajika tamikawa nanne duka kadan tasha tamiko mata badan ta koshiba saidan tasan inbata shaba zainab din bazata shaba Dauka tayi ta shanye ta wanko kofin takai shi ma ajiyarsa sannan tai alwala tai sallar isha sannan ta kwanta Washe gari da wuri tatashi tagyara gidan tsaf sannan ta tafi barar ta dari biyu tasamo da murna tatafi wajan mai kunu tasiyi na dari tasiyo musu kosan dari tayo gida Nanne na ganinta tai murmushi tace sannu dadawowa diyata nima anjima tare zamu fita barar tunda nasamu saukin jikinnawa tace toh nanne nan suka karya suna ta shira cikin farinciki kamar ba abinda ke damunsu da yamma tare suka fita a Inda suka saba zama anan suka zauna Da gudu motocinsa suke shigo cikin garin Suka wuce su tare da fallatsa musu ruwan cakwalkwalin dake gurin ita zainab ma besameta sosai ba amma yasamu nanne dayawa ta.mirror din motarsa yaga abinda yafaru a hankali ya tsaida motar sa suma sauran tsayawa sukai Ahankali ya fito yazo.ya tsugunna agaban nanne yace kiyi hakuri mama bamu lura da ku bane itadai zainab mamaki take jin wannan dan indiyan yana hausa Nanne ce tace bakomai yarona allah yai maka albarka yace amin mama yan dubu dubu ya zaro yabasu guda goma nanne takarba tana ta samasa albarka Yace mama kutashi nai maidaku gida nanne tace to dan albarka haka kurin yaji tausayin matar yarufeshi jinta yake kamar amminsa duk abinda ake bai kalli inda zainab take bare yasan da ita a gurin Captain al'ameen kenan To rayuwa ta sauya musu don dan birni kamar yanda zainab tarada masa ya tsaya musu dan yanzu sundena bara duk sati yanazuwa ya kawo wa nanne ziyara da abin Arziki sosai shidai haka kurin yaji ya tsani yarinyar nanne waddah ko sunanta ma bai sani ba Saboda shegiyar kazantarta shikuma yatsani kazanta arayuwar sa.yalura batason tsaftace jikinta amma kullum ka taddah ta tana aikin gida rannan yana zaune da kyar nanne tasa ta tai wanka tacanja kaya wannan kenan Tafiya ce ta tasomai ta shekara uku yazo yayi sallama da nanne ,nanne harda kuka dazai tafi dubu hamsin yabasu dazai tafi Bayan tafiyarsa.nanne sana'a tafara amma sai ake kin siye wai ana.zargin su mayune.ahaka.har suka cinye kudin yazamana yanzu saidai sufita bara wataran su samu wataran su kwana haka Yanacan amma.kullum tunanin wane hali.nanne take yakeyi gashi yarasansa dasuka san gidan duk anmusu canjin wajan aiki Ashekara ukunnan sunsha wahala rayuwa tai ta juyi dasu wataran sai suyi kwana biyu basuci komai ba aita kyararsu agarin amma zainab batada burin dayawuce taga nanne cikin farinciki bayan shekara uku Da tafiyarsa ciwon nanne yatashi tabata maganin harta gaji amma haryanzu ina gashi ba kudin zuwa asibiti don abinda zasucima karfinsu yake fi............ 🥱🥱🥱🥱🥱🥱🥱 Bacci #zainab kabir jaen(zee baby) More comments more writing Karku manta littafinnnan fah paid book ne gameso tamin mgn ta private dan munkusa gama free page nagode 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹rayuwar zainab❤‍🩹 By Zainab kabir Jaen Elegant online writers📚📖 Free page Page 5 Dafarko kisa aranki aiki kikazo Gidan nan bawani Abu ba koda wasa kikasake wasu daga cikin yan aikin gidannan yasan cewa ke matatace zaki gani Kuma sannan bana bukatar indinga ganin wannan mummunar halittar taki koda wasa kika bari naganki wlh zaki fuskanci hukunci mai tsananani kina jina Ahankali dagyada kai sannan yace kuma akwai baba kande me aiki da kuma asabe zaki koma bangarensu dazama Dan nan ne bangaren masu aiki kinaji na Ahankali tace eh hamma Allah yabami ikon cika duk sharadinka yace wannan kuma yarage naki asabe yakira yace ga sabuwar me aiki nakawo zaki koya mata aikin dazata dingayi kanta akasa tace toh yallabai Tashi tai itama tabita abaya tanuna mata dakin da zata zauna ta shiga haka kurin asabe taji kaunar yarinyar aranta gata karama ankawota aiki a tunaninta bazata wuce shekara sha biyar ba ahankali tace kanwata yasunan ki tace sunana zainab tace toh zainab nan ne dakin da zaki zauna gobe in Allah yakaimu inkin huta sai innuna miki aikin da zakiyi tace toh anty ngd Dakin tashiga, dakine madaidaici yana dauke da gado da wadrope tsummokaranta ta ajiye agefe sannan tashiga bandakin ta dauro alwala tagabatar da sallar La asar baba kande ce tashigo tace diyata kece sabuwar mai aikin da yallabai yakawo tace eh mama sannan ta tsugunna ta gaisheta ta amsa tana samata albarka cewatai bari inkawo miki abinci tace toh mama ngd Bayan fitar baba kande nannen tace tafado mata arai kuka tafara baba kande ce tashigo tace aa diyata me yasameki tace bakomai baba Guri baba kande tasamu ta zauna akusa da ita tana fadin bakyason aikin ne iyayenki sukai miki dole girgiza kai tayi tace toh meyafaru tace nanne na saita fashe da kuka meyasamu nanne taki nan takwashe lbrnt ta gayamata amma koda wasa bata fada mata aurenta da captain ba baba kande ta tausayamata tajawota jikinta tana fadin kidena kuka diyata kidaukeni a matsayin nanne ki kinji tace toh mama tana share hawaye Abangaren captain kuwa ya sanar da iyayensa batun aurensa sunyi farinciki sosai kasancewar dama suna so yayi aure a Nigeria basa son zamansa shikadai Yace musu yarinyar ce batada kowa shiyasa akai auren da gaggawa bai sanar dasu ba Abbie yayi fada amma bewani zafafa ba ya watsar yakira kanninsa ya sanar dashi shima yayi murna sosai Tana kicin taji kara Waya waddah idan captain yana bukatar wani abu yake kira toh anty asabe bata nan kuma baba kande bacci take dagawa tai tasanar dashi basa nan amma bejira yaji mai zatace ba yace akawomin coppe tare da kashe wayar Hartayi kamar bazata kai ba gudun kartai lefi yasata daukan coppe din takai mai kanta akasa tashiga falon gware tai da mutum yazo futowa cikin rashin Sa a coppe din ya zube gabadaya ajikin farar shadarsa ransa yayi bala in baci yace kewata irin dabbace zaki zubama mutun Abu mezafi ajiki banza dakiyaye kawai Yar kauye kazama dake ma uban wayace kikawomin abu Kina tunanin zanci abinda yafito daga hannunki ne kuma tasa tana bashi hakuri shine yarufeta da wannan dukan ❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹 Cigaban labari ❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹 ...................................... Tana cikin wannan tunanin bacci yadauketa ba Ita tatashi ba sai gab da sallar magariba tashi tai ta dauro alwala jitai anfara kiran sallah dadduma tashinfida tagabatar da sallah Tana idarwa asabe tashigo tace kitaso mushiga kicin za ayiwa yallabai girkin dare cewa tai toh anty asabe kichen din suka shinga Asabe tana nunamata abubuwa ahaka har suka gama girkin tsaf sannan asabe tajera mai a dining suka wuce suka gabatar da sallar isha i suka zauna suna hira Asabe ce tace nikwa kanwata intambayeki mana tace inajinki anty asabe tace kinga yanda kike da wannan kyan wlh dakina gyara kanki da anga mace anan Kinga yallabai ma ya tsani gazanta shiyasa zaki masu aikin sama masu tsaftane ni nayi mamakima da yabarki agidanan haryanzu ta dafata tace akudin aikin ki kikawo nasiyo miki kayyayyakin sawa da sabulai da mayuka nagyaran jiki wlh sai kinga yanda zaki koma kidauke ni amatsayin yayarki kinji hawaye ta goge tace ngd anty asabe kuma gobe zankarbi kudin awajen mama kande inbaki tace toh kanwata ngd asabe irin mutananne masu tsafata kuma ta iya gayu sosai Dan zainab had sha a war tatake wataran kuma tayi alkawarin kodan tadawo da darajarta agurin hamman ta zatayi tsafta #zainab kabir Jaen Gaskiya comment dinku tana kadan akan littafin rayuwar Zainab Ina godiya agareki maman Ahmad da ummu raees da takwarorina da anty mamy khabir maryam Yusuf anty Maimoon ina godiya agareku Allah yabar zumunci 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹rayuwar zainab❤‍🩹 By zainab kabir jaen Elegant online writer📚📖 Free page Page 4 Bismillahir rahmanu rahim To yaune captain zai dawo daga Tafiyar da yai yana sauka kai tsaye gidan su yafara nufah dan yaga halin.da nanne take.ciki zainab.yatarar akanta sai kuka take tana tofah mata adduo'in da suka zo bakinta Zubewa.yai agaban nanne yana fadin mama bakida lfy meyasameki, nanne dai bata iya cewa komai salati kawai take zainab ce tace ciwon cikinta ne yatashi.nabata magani taki warkewa takarashe tana sakin wani irin kuka mai cin dai Ahankali yace kamata mukai ta asibiti nanne ce tarike hannunsa tana.fadin wannan.ciwon nawa bana tashiba ne dan allah yarona kamin alkawari bayan raina zaka dauki zainab daga garinnan kamin alkawari zaka nemomata iyayenta sannan zaka zamemata gata dan allah inaso ka.aureta dan hakan ne zaisa inmutu ina mai farinciki Mamakine ya cika shi dama ba nanne ce tahaifi zainab ba zanin kayan da aka tsinceta dasu ta Mika mai tace wannan shine kayan da aka tsinceta dasu tafada dakyar ahankali yace nanne namiki alkawari amma nanne kitashi mutafi asibiti insha allah bazaki mutu kibarta bama Kalmar shahada take karantowa kullu nafsin zaikatull maut hakika duk wani.mairai mamacine allah ya dauki ran nanne wani ihu zainab.tasa tana fadin nanne karki mutu kibarni ke kadai ce nake da ita narokeki nanne zubewa tai a gun asume😭😭😭 Shikansa ya girgiza da mutuwar nanne zainab ta matukar bashi tausayi saidai tunanin dayake alkawarin daya daukarwa nanne taya zai cika shi meyasa bata zabi kowa ba saishi innalillahi wainna ilaihi rajiun shine abinda yake nanatawa Bazai iya auren yarinyar nan ba gaskiya baitaba tsanar wani abu ba kamarta mutanene.suka fara shigowa nan akai wa nanne wanka aka kaita gidan ta nagaskiya sai fatan allah yaji kanta mukuma allah ya kyautata makwancinta mukuma allah yasa mucika da imani abinda yabashi mamaki shine Ana kai nanne kowa ya watse yarage daga shi sai yarinyar ahankali take bude idanuwan ta da sukai mata nauyi akansa ta sauke su a hankali tace hamma al'ameen dagaske nanne tatafi ta barni koh takarashe tare da sakin wani kuka mai cin rai daban tausayi😭😭 Tabashi tausayi sosai ahankali yace kiyi hakuri nanne dai lkcnta yayi tashi mutafi kinji ba musu tatashi ta bishi dan yanzu shine madafarta kuma tayi alkawarin duk rintsi duk wuya zata jure duk wani kalubale dazata fuskanta a bangarensa hayaniya sukaji awaje mutane yagani a tsai tsaye da abin duka wai sai sun kasheta watoh maitartasu tasa sun fara cinye junan su to kafin tafara cinsu sai sunkasheta kafin yai Wani yunkuri har mutane sun rufu akanta suna duka zuciyar maza ce ta motsa bindaga ya fito da ita yadinga harbin sama ja da baya sukai a tsorace cikin bacin rai yace duk wanda ya kara tabata na rantse da allah saina fasa kansa da harsashin bundugarnan yakarasa gurin ya dagota duk ta galabaita duk da Sun tsora hakan baisa sunyi shiru ba wani ne yace yazaka zo har rugarmu kace zaka yimana ikoh to kai mekake yunkurin yimata ahankali yace inason ku dauramin aure da ita a Hanoi dubu hamsin ya zaro yabata a matsayin sadaki agurin kuwa aka daura auren inda mlm sani da mlm ado sukai wallicin auren watsewa sukai dukansu a mota yasa ta suka bar rugar da matsananci gudu Kai.tsaye hospital ya wuce da ita likitoci suka rufu akanta wata norse yasa tana kula da ita harzuwa sanda za,a sallamota satinta guda aka sallameta yazo yadauke ta baccine ya dauke ta amotar sa Jin tsayuwar motarne yasata farkawa kallon gidan take kallo baki saki gaba yai tana binsa abaya tayaba da tsarin gidan falon gidan suka shiga nan kallo yakoma sama gaba daya ta tsorata da girman gidan Kan kujera yazauna itakuma akasa tatakure guri daya kallo daya yai mata sannnan yace zangaya mike sharadina nazaman gidannan inkin kiyaye ki zauna lfy inkuma baki kiyaye ba zaki gani #zainab kabir jaen More comments more writing Ina godiya agareku ummu ra ees da takwarorina da ummina da mauncy ilove you my lovely fans 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹rayuwar zainab❤‍🩹 By Zainab kabir Jaen Free page📖📚 🅿️.....6️⃣ Washe gari kamar yanda tafada takarbi dubu hamsin tabawa anty asabe tashiga kasuwa tasiyo mata atamfofi da dogayen riguna guda biyu mayafi da takalmi mayuka na gyaran jiki taje wajan anty lady ta hadomata domin kuwa kayanta suna da kyau ga sauki itakanta saida takara mata dubu ashirin kai tsaye gurin dinki tawuce da kayan tace ai mata dogayen riguna da riga da sket tasiyo mata su under ware agajiye tashigo gida zainab naganinta takarbi kayan tana murmushi tace sannu da zuwa anty asabe tace yauwa kanwata ga kayanki nan saida na kara miki dubu ashirin ma amma su kyauta na baki murna ce tacikata tarasa me zatai kawai ta rungume anty asabe tasa kuka tace ngd anty asabe Allah yabiyaki ta sharemata hawayen fuskarta tana fadin ke kanwata ce Dan haka babu godiya a tsakanin mu asatinnan me dikin zai dinka miki kayan tace toh anty asabe Allah ya biyaki yabaki miji nagari tace ameen kanwata kema Allah yabaki miji nagari afili tace amin azuciyarta kuma tace nikam Allah yabani miji nagari saidai fatan Allah yasa yasoni yadena yimin wannan tsanar Kamar yadda anty asabe tafada asatin tela yai mata dinki kayan sunyi kyau sunyimata das saboda me dinkin kwararren telane to kayan gyaran jikin tafara amfani dasu kafin wata daya tayi wata muguwar canzawa ga anty asabe tana kara koyamata wasu abubuwan a wannan lkcn captain baya nan ya tafi England inka ga zainab sai ka rantse ba itace zainab din nanne me bara ba tazama wata Yar gayu fatar ta harwani tsantsi take tana sheki mayuka gyaran gashin da tasiyo mata agurin anty lady b masu kyau sutake amfani dasu kasancewar tana da yawan gashi da tsawo yasa bata kitso Dan dama nanne ce take matsa mata taimata kalba itama ba a iya gama ta a ranar kanta yayi kyau yayi baki duk dattinnan babu tazama wata Yar gayu duk inda ta wuce kamshin humra da turaren lady b ne yake tashi itakanta yanzu tafi jin dadin jikinta da take tsafta Dan akalla arana in batai wanka hudu ba zatayi uku tayi kiba tadan kara girma hakoranta sunyi tas dasu inba saninta kai ba ma inkaganta bazaka ganeta ba To yau sungama aiki da wuri Dan haka wanka tai ta dauki wata doguwar riga tasa simple make up tai kwalliyar ta amshe ta running tai da mayafin doguwar rigar tasaki jelar gashinta tana reto a gadon bayanta ta dau falat shoe tasa tatafi garden din Gidan tazauna tana ta tunanin rayuwar ta ahankali motocinsu suke shigowa Gidan wajan ajiye motoci suka nufa sukai parking kowa yafito daga nesa ya hango ta a garden din da mamaki yake kallon gurin Dan shidai yasan ba mai zuwa garden din inba su basma ne suka zo nigeria ba toh wannan ai tafi basma girma duk yanda akai bakuwa Ahankali ya karasa garden din kujera dake fuskantarta ya zauna yace sannu baiwar Allah ta Dan tsorata da ganinsa amma sai ta dake cikin siririyar muryarta tace yauwa ina wuni ta durkusa aransa yace dama wannan balarabiyar tanajin hausa yace amma baiwar Allah bansanki ba gurin wa kikazo a Gidan nan shikansa mamakin kansa yake daya zauna yake tambayar yarinyar kawai jiyai ta burgeshi gata kyakkyawa kamshin turaren ta yafi komai tafiyar mai da ahankali dan yana da matukar San kamshi da tsafta ahankali cikin siririyar muryarta tace ni wai gurin anty asabe nazo yace bata nanne kikazo kika zauna anan ke kadai Dan shi harga Allah be San cewa zainab bace kwata kwata kwalla ce tataru a idonta wai ace mijinta ne yakasa ganeta cikin kinkina tace dama ni ni ce zainab din nanne da mamaki yake kallonta wai zainab ce takoma haka duk da dai bawani girma takara ba amma tazama Yar gayu ga kyau saikace balarabiya sai yaga tanamai kama ma da basma Yar Gidan ammiensa tunanin yakawar aransa ya hade rai kamar bashine me murmushi yanzu ba yace yace wayabaki damar zama anan gun cikin hawaye tace hamma Dan Allah kayi hakuri tashi yai yabar gun amma bedena mamakin yanda yarinyar takomaba kamar ba itace kazamar nan ba me warin datti har ya shiga gidan bedena mamaki ba Yana tafiya itama tatashi takoma cikin Gidan tana hawaye wai ace Mijin ta yakasa ganeta itadai tasan tanajin kaunar hammanta aranta kuma tana fatan itama yasota ko yayane Toh tundaga ranar basu kara haduwa ba amma koda yaushe da tunanin yarinyar yake wuni yayi danasanin abinda yai mata yake da daya daukota ya gyarata ya sata a mkrnt ai bazatai kazantar ba dama da rashin kulawa a da din saiyaji kamar bai kyauta ma nanne ba berike amanar data bashi ba duk da dai bayajin son yarinyar amma saiyaji wani mugun tausayinta yana ratsashi yayi alkaqawarin zai zamemata gata kamar yanda ya daukarwa nanne alkawari amma taya yanzu tsoransa yarinyar takeji tana mai kallon mugu ne Wanda bai iya rike amanar daya dauka ba amma zaiyi duk mai yuwa yaga yagoge hakan a tattare da ita Yau bayan sun gama aiki wanka tai ta dauko wasu Riga da siket na atamfa tasa ta dau dankwalinta dayi daurin ture kaga tsiya baba kande tace kai diyata wannan kwalliya haka kamar zaki gasar kyau ta duniya murmushi tai tace kai baba kande harna kaiki iya kwalliya baba kande ce ta aikwa sanda Ina kamarki bakiga kyauna ba. Samari har fada suke akaina murmushi tai tace wannan gaskiyane baba kande bari inje dining in debo abinci Dan yunwa nakeji fitowa tai tana tafiya ahankali tana tafiya kanta akasa tuntube tai da kafar mutum tatafi tagal tagal zata fadi cikin zafin nama ya taro ta tafado a kirjinsa wani bakon yanayi sukaji ya ziyarce su kalon juna suke ko kifta ido basayi sunfi 30 minute ahaka sannan ta dauke Idonta tana kokarin dagashi tace hamma kayi hakuri wlh ban lurabane ahankali yace kidinga kallon gabanki inkina tafiya in bahaka wataran saikin jiwa kanki ciwo a ahankali ta gyada kai dakin shi ya wuce inda ita kuma ta wuce dakin su tana ta tunanin abinda yafaru dasu wani farinciki taji ko bakomai hamma yafara tausayinta tsalle tai tana dariya tunda tasan da Dane da duka ne hukuncinta nikwa nace kai madam daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaki shima abangarensa wani farinciki taji yana ziyartar Sa ❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹A daya bangaren kuwa ammi ce zaune tunda diyarta ta bata yanzu kusan shekara sha shida kenan amma haryanzu takasa mantawa kullum cikin tunanin ta take basma ce tashigo dakin tazauna kusa da ita tana fadin ammiena tunani kike koh a ahankali tace a,a basma ba tunani nake ba Abbie ne yashigo yana fadin maman yara kiyi hakuri kidena wannan tunanin insha Allah indai Ummina tana Raye zamu ganta Dan ajikina ina jin wataran zan hadu da diyata yafada da murmushi akan fuskarsa Dan ya kwantar mata da hankali yace danki fah captain yace Yananan zuwa a watananan tace tare da matartasa zaizo yace wlh bansani ba amma dazu Yaya yake fadamin tace son kenan nayi kewar shi dayawa wlh yace kedai bari da Abbie da abbu wato baban captain uwarsu daya ubansu daya haka ma ammie da momy yaya da kanwane Dan captain ma yafi shakuwa da ammi Yanzu lbrn yafara masoyan zainab Ina godiya agareku bisa yanda kuka nuna damuwarku akaina INA matukar godiya agareku INA matukar kaunar Ku More comment more typing #zainab kabir Jaen (zee baby) 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹rayuwar zainab❤‍🩹 By zainab kabir Jaen Free page📖📚 🅿️..........7️⃣ A bangaren su captain ❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹❤‍🩹 Yadage da nemarmata iyayen ta badare ba rana yasa anbuga jaridu da hoton kayan da aka tsinceta dakuma yanda baffah ya tsinceta a dokar daji amma shiru kakeji gidan talabijin gidan radio kodayaushe cikin sanarwa suke amma ina balabari Yanzu yadan fara sakar mata fuska duk da dai basosai ba boarding schools yasamomata inda zatai shekara shida ta kammala ranar daya sanar mata bakaramin farinciki taiba don dama bata da burin da wuce taga itama tasamu ilimi tace hamma ngd Allah ya biyaka da gidan aljannah be mgn ba ya shige daki Washe gari yace tashirya zai kaita shopping tasiyo abubuwan dazata bukata amkrnt siyaya sukai kamar ba a son kudin komai dazata bukata ansiyo mata sannan suka dawo da anty asabe taga kayan bakaramin mamaki tai ba anya yallabai yarinyar nan ba Yar uwarsa ba ce don taga inka kura musu ido zakaga har wata kama suke barin yanzu da tacanja amma saita kawar tace ya za ai ya dauko kanwarsa yasa abangaren masu Ai ranar Monday Yakama zata fara zuwa mkrnt don haka shirye shirye taketayi Dan yace karta wuce karfe bakwai bata shirya bakwai daidai kuwa ya fito lkcn harta shirya yana fitowa ta durkusa har kasa ta gaisheshi ya amsa tare dayin gaba ta bishi abaya duk abinda Yakama aiwa dalibai inza a sasu amkrnt yayi mata sannan yace tazo yanason mgn da ita bayan tazo yacemata kikiyaye kanki dayin kawaye dayawa karatu kikazo bawasa ki kare mutuncinki a maysayinki na matar .......... Shiru yai ya shiga mota yace kinji dai nafada miki tace insha Allah hamma zan kiyaye yaja motarshi yai gaba itakuma principal tasa aka kaimata kayanta hostel mutum biyune adakin da da fatima Mohd da kuma hamidah mika'il yaran masu kudine Dan duk mkrnt shakkarsu ake Dan ko yan ss 3 basa yimusu su kyale yarane yan gayu inka gansu saikace wasu irin yan matannan ba yan jss 1 ba To zaman zainab agurinsu yasa takara wayewa duk rashin mgnrta yanzu ta koyi surutu da tsiya agunsu saidai kuma in muskilancinta yatashi bata mgn sosai kai saikayi zaton Yar sarkice yan mkrntar ma duk haka suke cemata zee beauty kowa soyake ta kulashi Dan akwaita da shiga rai yau suna daki itada su hamidah suna duba littafin English saboda gobe akwai test wata Yar ss 3 ce tazo tace kai kutashi ga kayan anan Ku wanke min acikinsu babu waddah ta dago ta kalleta tacemin kujimin yan iskan yara saboda kunga kowa amkrntar nan yana shakkar Ku shine kuke ganin Ku kun isa ko to wlh Baku tashiba sai na yaga littafin nan wlh Fatima ce ta dago ayangance tace madam kin ishemu fah kinzo sai wani shouting kikemana aka Fatima Mohd tace ubanwaye ma zaimiki wanki wlh baki isa ba muma namu wankemana akeyi zainab kuwa ko inda take ma bata kallaba tace ah lallai yara kun isa ke wato me girman kai ina mgn kin min shiru dagowa tai tace ke dallah dakata mufah muna da abinyi ne wazai kulaki my friend Ku juyo mucigaba da karatun mu shiru kuwa sukai suka cigaba kafin zainab tai wani yunkuri taji ta zabga mata mari cikin zafin rai hamidah tarama mata kafin hamidah ta sauke hannu Fatima itama ta Dora suka hadu sukai mata duka tafita tana zaginsu sukwa ko ajikinsu tashi sukai sukai shirin Islamiyya yanzu izzun su ashirin hadda zainab kuma goma suka fito suna tafiya acikin filin mkrnt suka karasa masallaci don daukar darasi bayan antashi suna daki aka kirasu wai wannan Yar ss3 takai karar su suka tashi sukaje aka tambayesu meyahadu su nan kuwa suka fadi duk abinda yafaru fada mlmr tai musu tace ba yayarku bace ana yawan kawomin kararku Ku kiyayeni suka bata hakuri suka tashi yau Suka kammala jarabawar kammala jss1 dinsu zasu wuce ss 2 kowa sai murna yake zai tafi gida hamidah ce tace Besty wlh banason tafiya gabadaya inna tafi zanyi missing dinku zee ce tace Hummm Besty kenan Ai saina fiki amma Ai hutun badewa za ai ba tace hakane motar su Fatima ce tafara zuwa sannan tasu hamidah kamar yanda tasaba driver ne yazo daukarta Nan suka tafi suna kewar junansu tana shigowa Gidan da anty asabe tafara cin karo aikwa da gudu ta rungumeta tana murna tace nayi missing dinki anty asabe ina mama kande tace tatafi kauye yallabai ma yatafi India wajan iyayenshi ni kadaice a gidan naji dadin dawowarki tace nima haka anty asabe Kuyi hakuri da wannan pls ❤‍🩹‍rayuwar zainab❤‍🩹 fans ina yinku Allah yabarmin ku #zainab kabir Jaen(zee baby) Yau naso yimuku posting dayawa saboda naji dadin comment dinku najiya Baiwar Allah da tafadamin mgn ce tasa wlh nakusa gama wa ban San gama gogeba na biyemata kuyi hakuri🙏🙏🙏🙏 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹Rayuwar zainab❤‍🩹 By zainab kabir Jaen 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana ,fadakarwa ,ilimantarwa da kuma nishadantarwa(R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin kishi Alkalaminmu yancin mu FREE PAGE📖📚 🅿️.....8️⃣ To har hutun yakare ko saudaya basu hadu da captain ba har hutun yakare kudi ya turo yasa driver yakaita tai shopping din abinda take bukata a mkrnt aikwa komai zata siya saitasiya itada da friend dinta ranar da zata koma mkrnt jitai farinciki kamar ya kasheta saboda zataga kawenta harga Allah ita yanzu ji take kamar batada wani aure akanta jinta take dai dai dasu hamidah kuma yanzu bakasafai ma take tuna wani captain ba Dan yanzu tafara sanin ciwon kanta kuma tayi alkawarin saita kwatarwa kanta enci agurinsa duk abinda yai mata saita rama To ita akafara kawowa mkrnt sananan hamidah da Fatima dagudu suka rungume juna suna murna bayan sun huta kowa yafito da tsarabar daya kawo Dan uwansa kamar yanda zainab duk abinda tasiya saida tasiyo musu suma haka suka tashi suka gyara dakinnasu sannan kowa ta kwanta tana baccin gajiya To sun fara jss 2 dinsu a sa,a duk mkrnt kowa jiyake dasu don sun zama kamar taurari ga kyau ga ilimi ga kuma iya gayu Akwai wani ancul dinsu anacemai ancul aboki matashi ne maiji da Da ilimi da kudi ga iya gayu yana masifar son zainab amma yanayin tsiwarta yasa yake shakkar fadamata su hamidah yasamu yasanar musu sukuma suka sameta suka fadamata danjin amsar da zata bashi Ku biyoni a page 9 ngd Ina miko gaisuwa agareku masoyana Allah yabarminku ya biyamuku bukatunku na alkhairi #zainab kabir jaen 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹Rayuwar Zainab❤‍🩹 Story & writing Zainab Kabir Jaen *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana,fadakarwa,ilimantarwa dakuma nishadantarwa(R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin kishi Alkalaminmu yancin mu FREE BOOK📖📚 🅿️........9️⃣ Numfashi ta sauke ahankali ta ce "ni fa in gaya muku ba soyyaya ce agabana ba karatu na zo yi" a zuciyarta kuma ta ce 'ya zanyi da auren dake kaina?' su Hamidah ne suka sata agaba suna ta lallashi akan ta yarda dashi suma Ai baza su goyi bayan ya hanata karatu ba. Da suka isheta da surutu tace taji ta yarda wani lhu suka Sa suka ce dama ana so ana kaiwa kasu tashi tai tana binsu suna gudu suna ta dariya data gaji ta zube akan katifa suma zubewa su ka yi suna maida numfashi. Da yamma da ta tashi bata jin dadi ciwon marar tane ya tashi magani ta sha don haka bata je makaranta ba da ta tashi wanka ta yi ta gyara jikinta ta yi simple make up sannan tasa katon hijabinta ta zauna tana jiransu Hamidah su dawo su d'an zaga makaranta. Da sallama kuwa suka shigo ta amsa tana harararsu ta ce "ai na kuka tsaya kun san jiran Ku nake suka ce wlh ancul ne ya tsaidamu wai kina ina muka fada masa bakya jin dadi gashi nan ma yazo yi miki ya jiki. Ki fita yana jiranki ta ce "ni dai gaskiya ba in da zani da kyar suka lallabata ta fita da ta je suka gaisa ya mata ya jiki tace "da sauki" yace "toh ga tarin maganganu a bakina Gashi kuma bakida lfy" murmishi ta yi tace ancul Ai na warke" ,yace "kin tabbata" ta ce "eh ancul" yace "to da farko dai Zainab tunda yayanki captain al'ameen ya kawo ki naji duk duniya babu "ya macen da ta yi min sama dake nayi kokarin sanar dashi a lkcn sai kuma na fasa naga gwara in fara sanar dake inkin aminta sai na tura iyayena gidanku Ai maganar sai kuma kwarjininki ya yi min yawa na kasa fada miki ina fatan zaki amsheni hannu biyu". Wani numfashi ta sauke aranta tana saka tace mai tana da aure ko kuma ta rabu dashi a'a wata zuciyar tace mata ke kina da tabbacin hamma zai zauna dake a matsayin matane gwara ma ki lallaba ki samu Wanda yake sonki inya so ko hamma ya sake ki bakida wata damuwa. Wannan shawarar ta dauka ta ce mai kawai sai tayi tunani yace "ba komai Sweetyna Allah yasa naji alkhairi na baki kwana uku ina jiran amsa". To ranar da kwana uku ta cika ancul aboki yazo nan ta shaida mai ta amince wasa-wasa soyyaya mai karfi ta shiga tsakanin su a makaranta babu Wanda bai san lbrn soyayyarsu ba don haka yanzu sai suka kara wani iyayi don ba mai tabasu ancul aboki ya kyale. Yanzu suna shirin yin jarabawar mita daga jss three amma tun randa hamma ya kawota bata kara ganinsa ba kuma duk sanda zata je Hutu bayanan yayi tafiya ita yanzu ma mantawa take dashi amma kuma koda yaushe yana turo mata kudi tasai abinda take bukata sun zana jarabawar kammala jss three dinsu lfy inda suka koma gida dan jiran sakamako sun dade suna Hutu agida kafin result dinsu ya fito sunci Dan haka suka fara shirin tafiya ss one. Zuwan ancul aboki hudu a hutun Sa su ka yi anty Asabe ta dinga tsokanarta tana cewa "Ashe kina candy sai aure" ita dai sai dai tayi dariya. Sun fara karatun su a sa'a kuma sun samu nasarori masu yawa kuma yanzu sun haddace karatun alqur'ani mai girma sun jajje musa baka kuma dai sune sun samu kyaututtuka masu yawa yanzu suna ss 3 sun zama manyan yan mata masu jidakansu da aji shirya-shiryan fara neco suke da waec inda za su hada bikin saukar su da candynsu, gabada daya sun Shiga busy shirye-shirye kawai suke da karatu ana gobe zasu fara exam kusan kwana su ka yi suna karatu sun fara exam a sa'a sun kammala sai fatan jiran sakamako ranar da suka kammala jarabawar ranar aka yi musu saukar karatunsu an kirata an mata kyaututtuka ancul aboki ma yai masa tata kyautar ba zato ba tsammani kawai taga hamma ya taso ya mika mata tasa kyautar ita a tunanin ta bata taba kawowa zai zo na ya kara girma da kyau bayan anyi hotuna kowa yakama gabansa suka rabu ita da kawayenta cike da kewa da kuma kuka da kyar suka rabu da juna da alkwarin kowa zai ziyarci kowa. A haka suka dau Hanya cikin kewar juna tunda suka dau hanya ba wanda ya yi wa Dan uwansa mgn ahaka har suka isa gida. Kuyi haƙuri da wannan Ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci Inai wa duk wani Dan " kungiyar Royal Star fatan alkhairi Allah ya bar zumunci Allah ya daukaka K'ungiyarmu mai albarka #Zainab Kabir Jean 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹Rayuwar Zainab❤‍🩹 Story & writing By: Zainab Kabir Ja'en *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* {R.S.W.A} https://www.Face book.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c *Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa,ddakuma nishadantarwa* (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi *Alkalaminmu yancin mu* FREE BOOK📖📚 🅿️..........🔟 ………Kowa b'angarensa ya nufa, tunani yake wai Zainab d'insa ce ta koma haka? Hummm taya yanzu zai nuna mata yan da yake jinta a ransa? yana jinta kamar Yar Uwarsa, jinta yake kamar su Basma. Tashi yayi ya fita falo yasa Asabe takira masa ita, aikuwa da sauri ta ce "to yallabai" ta tafi ta kirata lokaci ta shirya cikin wani arnen les blue mai adon pink, an zuba masa stone tayi kyau sosai doguwar Riga ce, bata d'aura d'an kwali ba, ta dan yafashi akanta ta fito, a zaune ta sa me shi akan kujera, a kasan k'afarsa ta zauna tare da cewa "barka da hutawa Hamma, ya ce "yauwa barka," dai shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani ya ce "dama na kiraki ne domin in fad'a miki ki d'ebi kayanki daga b'angaren masu aiki ki maida daya part d'in, sa bo da ya kamata kisan cewa bafah matsayinki d'aya da sauran masu aiki ba. Mamaki ne ya kamata wai ita Hamma yake ban-ban tawa da matsayin masu aiki, ba tayi mai musu ba tasa su Anty Asabe suka ta ya ta d'iban kayan, ta maidasu can. Tun da ta dawo kullum sai sunyi waya da ancul aboki, sai dai kuma taki basa damar yazo ko sau d'aya sa bo da Hamma yana nan yayi nacin har ya gaji, gashi kullum sonta k'aruwa yake a zuciyarsa Yau ya yanke shawarar ko taki ko taso sai yaje gidansu, dan yana kishirwar ganinta, ya shirya tsaf cikin dakakkiyar shaddarsa marun, kana ganinsa kaga had'ad'd'en matashi mai ji da ilimi, a marun d'in matarsa ya fita kai tsaye gidan su ya nufa. Ita sam bata san da zuwansa ba, ta idar da sallah taji Anty Asabe tana cemata tazo b'akonta yazo, gabanta ne taji ya fad'i amma sai ta dake ta fita garden d'in gidan cikin natsuwa, tun daga nesa ya hangota blue black din hijabine a jikinta yayi mata kyau sosai abinka da farar fata, kafeta yai da ido har ta karaso tai masa sallama tare da jan daya daga cikin kujerun gurin ta zauna ta gaishe shi cike da girmamawa sannan ta ce "zuwa ba sanarwa kawai sai dai naji kazo kaga ko kwalliya banyi maka ba, murmushi yayi tare da fad'in "aike ko baki kwalliya ba kyau kike, dan nikam kin fimin kyau a haka abar k'auna. Shiru suke cikin farin ciki da annashuwa duk da dai ita tana cikin tsoran kada Hamma ya zo ya taddashi bata san me zata ce masa ba Allah, Allah take yatafi aikuwa tana cikin wannan tunanin sai ga motocinsu sun shi go gida zumbur ta mik'e alamun tsoro suka bayyana a fuskarta amma dakewa tai a hankali yake fitowa daga motar idanunsa basu sauka a koina ba sai akan Zainab d'insa kuma zaune ita da wani duk da dai bai san abin da ake kira da kishi ba amma nan da nan ransa yai wani mugun baci yana cikin kakin sojojinsa cikin natsuwa yake tafiya ya karaso gurin ya ce "keee me kike anan, d'aure fuska tayi ta ce "bakona ne, ancul d'in mu ne, kuma shi nake sa ran zan aura, ita kanta tayi mamakin kanta data iya fadin maganar kallonta yake cikin bacin rai nan da nan idanunsa suka kada sukai ja cikin tsawa ya ce kafin na irga uku kibar gurin nan ai kafin ya karasa sa bo da tsorata tabar gurin shika ancul aboki tsayawa yai ganin ikon Allah daga gani wannan dai Yayan Zainab ne dan ga kamanan bare ya ce kishi ne, dan haka a ahankali ya ce "kayi hak'uri Yayanmu wallahi na tambayeta yafi saunawa ta barni nazo nagana da iyayenta amma taki yarda ni kaina banso nafara zuwa gurin ta ba tare da neman izini ba amma wallahi ba wai nazo da niyyar yaudarar ta bane ni aurenta zanyi. Wani kallo Hamma yai mai tare da fad'in "okey ba matsala zan yi magana da iyayen mu ya ce "to yayanmu ngd," Barin gurin yayi kai tsaye part d'inta ya nufa yaje ya taddata tana ta rusa kuka kanta ya damko ya ce "da aurena akanki kike kula wani, ina amfanin iliminki? to yau shi ne jan kunne na farko kuma na k'arshe da zan miki wallahi na k'ara ganinki da wani, abin da zan miki bazai miki kyau ba ki bari in ba aurena akanki saiki kula kowane kare ko kina tunanin akwai wanda zai aureki bakida cikakken asalai ne? burina a kullum bai wuce naga na samo miki iyayenki ba na maidaki `Ya mai enci kamar kowa, amma ke wato soyayya ce a gabanki koh? ya ce ko kina tunanin shi saurayin naki zai aureki inyasa wacece ke? to wallahi ki nutsu kisan me yake miki ciwo...... Kuyi hakuri da wannan Ina godiya agareku masoyana Allah ya bar kaunar Inayi wa duk wani Dan kungiyar Royal Star fatan alkhairi. Allah ya kara dauk'aka " kungiyarmu mai albarka. #zainab kabir Jaen 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹Rayuwar Zainab❤‍🩹 Story & writing By: Zainab Kabir Ja'en 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A}http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishadantarwa (R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin kishi Alkalaminmu yancin mu. FREE BOOK📖📚 🅿️........1️⃣1️⃣ Ya saketa tare da barin gurin, kuka tasa mai cin rai, a yanzu Hamma ya tuna mata wace ce ita, ada ta shagala ta daina wannan tunanin, sam bata ga laifinsa ba, sa bo da a kalamansa ba abin da yayi karya, ita d'in mara asali ce, mara gata! shi yayi mata duk wani gata a rayuwarta, ko haka ya barta ba abin da zata ce masa tunda ya suturta, ya bata ilimin addini dana boko, to ita kuwa mai zai sa ta k'i mishi biyyaya! Tayi alk'awarin zata bauta masa har karshen rayuwarta, amma ta yaya? Tana mutukar son ancul aboki, kuma tasan ko ba dade ko ba jima Hamma sai ya saketa! Dan tasan bazai iya zama da ita ba, tashi tai ta d'auro alwala ta gabatar da sallar nafila tana addu'ar Allah ya baiyana mata iyayenta. Shi kuwa a b'angarensa yana shiga daki ya fara farfashe kayan D'akin yana huci, zuciyar maza ta b'aci sai da yaga yafara jiwa kansa ciwo ya dakata, yana fad"in "why? Meyasa zata min haka? da aurena akanta ! Zuciyarsa ce ta ce mai "kai to me ye naka aciki tunda ba sonta kake"afili ya ce sa bo da kare mutuncin aurene badan haka ba ina ruwana da ita, d'ayar zuciyar kuma ta ce mai "ko dai ka fara sonta, tun da kaganta da wani kaji haushi," da karfi ya ce noooo bazai yuwu ba. Wanka ya shiga ya shirya cikin k'ana nan kaya ya fita, motarsa ya nufa yabar gidan ya tafi gidansu abokinsa Kamal,yana zuwa Kamal ya ce "yau kaine a gidanmu Captain lafiya kuwa naga kamar ranka a b'ace?" murmushi yayi tare da fadin lafiyar kenan" Kamal ya ce no fad'a min gaskiya kodai-kodai....." harararnsa yayi ya ce kaga "Malam dakata ni mene had'ina da ita 'murmushi Kamal yai ya ce calm down abokina me ya faru ? "Ahankali ya labarta masa abin da yafaru, ya ce "ni ba wannan ne damuwata kaga akwai aurena akanta ba " numfashi kamal ya sauke ya ce "abokina naji abinda ya faru kuma gaskiya bata kyauta ba amma kaima da laifinka in kana sonta kawai ka rik'e matarka hannu biyu ba hujja bace, kace ta jira sanda ka saketa ta kula wani kuma inka lura Zainab yarin ya ce mai bukatar tallafin wani tunda ta rasa iyaye tana son wanda zai jata a jiki ya dinga fad'a mata gaskiya amma yanzu duk abin da yazo kanta shi zatayi, karkayi la'akari da cewa baka sonta,ka d'auketa kamar su Basmah zaka gani ba wanda zatayi shawara dashi sai kai wani gauran numfashi ya sauke, ya ce "abokina nagode da shawararka agareni kuma insha Allah zanyi aiki da ita" ya ce "bakomai abokina nima in ka saki inaso kaji Yayanmu "duka ya kai mai yana fad'in " ba kada dama wallahi Allah ya shiryeka, sun dade suna shira dan anan Captain yayi sallar isha'i To tunda abin ya faru basu kara ganin juna ba, yau ta yanke shawarar zataje ta bashi hak'uri akan abin da ya faru. Da sallama ta shiga dakin, yana zaune a falonsa, ya d'ago ya kalleta ya amsa sallamar, ta masa kyau sosai, cikin wata abaya take ammata ado da duwatsu har kasa tayi rolling da mayafinta ta tufke gashin kanta yai kamar tayi acuci, tayi kyau sosai, agefan k"afarsa da zauna ta ce "Hamma ina wuni," cikin sakin fuska ya ce "kin yini lafiya kanwata" tayi mamakin sunan da taji ya kirata dashi amma sai tace "lafiya kalau Hamma, "ya ce "masha Allah" ta sun kuyar da kai tare da fad'in "dama Hamma nazo ne in baka hak'uri akan abin da ya faru, dan Allah kayi hak'uri, sai ga hawaye yafara wanke mata fuska😭😭 "A hankali ya sakko ya durkusa a gabanta ya ce "daina kuka kinji kanwata na dad'e da yafe miki ya karasa fad'a yana goge mata hawayen daya b'ata mata fuska ya ce "daina kukan haka, ki daina b'atamin wannan kyakkywar fuskar taki kanji kanwata yimin murmushi, tai ta ce "to Hamma nagode. Ya ce "mukulla kawance daga yau kin zama kanwar Captain " ta miko hannunta suka d'aura . Tun daga ranar ya zamana ko da yaushe indai yana nan suna tare duk ranar week end sai sun fito yawo yanzu gaba d'aya ji suke basu da wata damuwa ita ce yanzu take kula da b'angarensa, cinsa da shansa wataran ma har wanki take mai gabada ta mai dashi dan gata, amma ita har zuciyarta tana yi mai ne a matsayin Yayanta ba wai don tana Matarsa ba, don ita mantawa take wai shi mijinta ne. Kullum sai sunyi waya da ancul aboki idan ya ce mata zai zo sai tace ya bari Yayanta ya bashi dama a haka yake ta hak'uri Wannan kenan ............✍️ Kuyi Hakuri da wannan Ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci Ina yiwa duk wani Dan k"ungiyar royal star fatan alkhairi Allah yakara daukaka k" ungiyarmu mai albarka #Zainab Kabir Jaen {@GARKUWAR ROYAL STAR} 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://www Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana,fadakarwa,ilimantarwa,dakuma nishadantarwa,(R.S.W.A)Ruwa Ka"dai ke maganin kishi. *Alkalaminmu ƴancin mu.* FREE BOOK📖📚 🅿️.....1️⃣2️⃣ ........ Yau Uncle Aboki yacemata,shifah gaskiya yagaji,yau zaizo yasami Yayanta ya mishi magana, dan shi gaskiya yanason ganinta,Tarasa yanda za tayi da shi don gaskiya tana matukar son sa,amma bata son ɓacin ran Yayata,yace "kinyi shiru baki ban amsa ba,"tace "shikenan Allah yakawo ka lafiya", yace "zanzo karfe biyar nasan lokacin yadawo koh?," tace"eh yadawo,"yace"," toh Sweetyna kimin kwalliya mai kyau kinji abar kauna",murmushi tai,tace "toh abin kauna zanyi maka". Karfe hudu dai dai a kofar Gidan nasu yai mai,horn ya yi,wani Soja yataso da sauri ya bude,yana ganinshi ya ganeshi,yace "barka da zuwa ranka ya dade", murmushi Uncle Aboki yay yace "barka dai,Dan Allah Captain yadawo gidane?," da sauri yace eh ranka yadade, yadade da dawowa ai", Uncle Aboki yace " toh Dan Allah kamin magana dashi,kacemasa ya yi bako," da sauri yace "toh bari namasa magana. Wayar shi ce yaji tana kara da sauri yakara gurin ,tare da fadin " hello " a dayan ɓan garen sojan yace" Ranka ya Dade kana da bako yana dakin baki", a hankali yace "ina xuwa toh " ya fada tare da kashe wayar, tashi yay kai tsaye falon bakin ya nufa Sallam yay Uncle Aboki Ya amsa mai cikin girmamawa, suka gaisa sannan Captain yace "amma abokina ban ganeka ba?", "Ankul Aboki yace"da farko ni dai sunana Abubakar Abdullahi,Amma ana kirana da Uncle Aboki,ni Malamin Ƙanwarka ne Zainab Al'ameen, kuma magarnar gaskiya nazone kabani izini domin nafara zuwa wajanta zance,"nan take Captain yaganeshi wato wannan Malamin na sune daya taba ganinsu tare,tabbas shine sai yanzu yaganeshi!" Nan da nan ya hade rai kamar hadarin gabas yace "toh ni dai Zainab Ƙanwace a gurina kuma iyayen mu ba anan suke ba, Dan haka bani da damar yanke hukunci akanta!, " numfashi Uncle Aboki ya sauke tare da fadin" Yayanmu wallahi! Ina sonta Kuma aurenta zanyi Yayanmu Dan Allah kaban izini na fara zuwa gurinta Dan Allah, " shima Captain numfashin ya sauke, a ransa yana tunanin taya zai bawa wani kato damar zuwa wajan matarsa zance?, abinda bazai yuyu bane,afili kuma sai yace " bari in turo ma ita ta fadamaka gaskiya ya karasa fada yana mikewa, musabaha sukai Uncle Aboki yace" nagode Yayanmu", yace "no bakomai" . Tana zaune agefan gadonta taji Sallamar sa, Amsawa tayi cikin sanyi murya tace "Hamma sannu da dawowa kayini lafiya "zama yai, ya amsa sallamar cikin murmushin da ya tsaya iya lab'b'ansa sannan yace ", kinyi bak'o kinsan da zuwansa?," sunkuyar da kanta tai k'asa Tace" eh Hamma nasan da zuwansa!,"kallonta yay yace mene hadinki dashi? ",Kanta akasa tace "dama Hamma sai kuma tayi shiru," yace "dama me", tace "Hamma Saurayina ne" tafada k'irjinta yana dukan uku uku, yace " Zainab kiji tsoran Mahaliccinki,kinsa nema akan nema Haramune koh?," ahankali ta d'aga kai alamun "eh", yace" amma meyasa kike kula wani Namijin alhalin kinsan dawani auren akan ki? To Ki nutsu kisan meyake miki ciwo, ni Zainab ina samun Iyayenki zan sauwake miki Aurena dake kanki ki auri duk Wanda kike so, amma yanzu, ba dai dai bane ki take k'a'idojin Ubangiji, kiji tsoran Allah, ki tuna cewa zaki mutu zaki koma ga mahaliccinki!". Gaba daya jikinta yayi sanyi nan da nan hawaye ya wanke mata fuska a hankali tace "Allah na tuba Hamma kayi hakuri Dan Allah", a hankali yace ni na yafemiki Ƙanwata amma ki fada masa gaskiya kinji Ƙanwata ," tace "Toh Hammana insha Allah " yace "good" yana falon baki yana jiranki", Tace" toh Hamma". Wannan kenan...............📝📝 Kuyi Haƙuri da wannan Ina godiya Agareku masoyana, Allah ya bar zumunci. Ina yiwa duk wani d'an Ƙungiyar Royal star fatan Alkhairi. Allah yakara d'aukaka Ƙungiyarmu mai albarka. #ZAINAB KABIR JAEN {@GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY AND WRITTING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://www.Facebook.com/Royal-star-writer's-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fa"dakarwa,ilimantarwa,dakuma nishad'antarwa(R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin k'ishi. Alkalaminmu "yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️.............1️⃣3️⃣ Zainab ce ta sunkuyar da k'ai tana goge hawaye, ta ce "To Hamma", Murmushi ya yi shi ma ya ce "Good tashi kije" tashi tayi jikinta a sanyaye ta nufi falon bakin, Sallama tayi a sanyaye, Uncle Aboki daya Dade yana jiranta da fara'arsa ya d`ago ya kalleta, ya ce "barka da zuwa abar kauna, tun dazu da Yayanmu ya tafi nake ta kallon hanya, shi ne kika shanyani ko?" ya fad'a kamar zai yi kuka, Zainab murmushi tayi ta ce "barka da zuwa Uncle", Mamaki ne ya kamashi rabon da ta kirasa da wannan sunan tun kafin su fara Soyayya da ita, danne mamakin nasa yayi suka gaisa sun d'an taba hira ba sosai ba, sannan Zainab ta ce "Uncle ina son magana da kai" "To abar kauna ina jinki" Cewar Uncle. Hawayenta ta goge, Sannan a hankali ta Zayyane masa labarinta tun daga sanda Baffah ya tsinceta har zuwa Aurenta da Hamma, sannan ta karasa da ce wa "Uncle Allah ya gani ina sonka kuma banyi haka da niyyar yaudararka ba, nasan ko ba dad'e ko ba jima Hamma zai sakeni shi yasa na karbi soyayyarka, sa bo da nasan kai ma zaka zame min gata koda Hamma ya sakeni," ta karashe tare da fashewa da matsanancin kuka! wata Uwar zufa ya goge haƙiƙa ko Mara lmani yaji labarin Zainab da gwagwarmayar da tasha a rayuwa dole ya Tausaya mata amma ya sani Hajiyarsa ba zata tab'a bari ya auri Zainab ba tunda batada asali to shi kam ya zai yi ke nan?, A hankali ya sauko ya durkusa agabanta ya ce "Zainab haƙiƙa kin ga rayuwa wanda duk mara lmani in yaji labarinki sai ya Tausaya miki! Amma kinyi kuskure da ki kayi soyayya da auren wani akanki ni Zainab masoyinki ne kuma ina nan ina jiranki duk sanda Hamma ya sauwake miki ni kuma a shirye nake na aureki", cikin kuka ta ce "na gode da soyayyarka agareni," sallama su ka yi ya tafi cike da tsananin begen juna, tashi tayi ta koma cikin gida zuciyarta na suyar rabuwa da Uncle din nata. A bangaren Hamma kuma yana komawa part dinsa yaji zuciyarsa tana zafi, band'aki ya shiga ya sakarma kansa shower ko ya samu ya ji sauƙin abunda ya to kare masa zuciya , Amma lna ji yake kamar ana ƙara masa zafin zuciyar wanka yayi ya fito ya shirya cikin wata dakakkiyar blue din shaddah ta amshe shi abinka da farin mutum, wayoyinsa ya d'iba da makullin mota ya fito a falo ya ganta a zaune ta zabga tagumi kallo daya yayi mata ya d'auke kai ya cigaba da tafiya, da sauri ta taso ta karaso gabansa ta ce "Hamma fushi kake dani pls kayi hakuri kaji,?" cikin tsawa ya ce "ban hanya!" ya fada yana zaro mata ldanuwa ai kuwa ta tsorata da sauri ta matsa, shi kuwa gogan na kara cigaba da tafiyarsa kuka tasa, ita kuwa ya zatayi bazata iya jure Hamma ya yi fushi da ita ba ta shiga uku d'akinta ta Shiga ta yi wanka kanta ne taji yana mata ciwo ga wani irin sanyi da take ji, bargo taja ta lulluba kafin wani lokaci zazzabi ya rufeta. Shi kuwa Captain ya na fita gidansu Kamal ya wuce, yana zuwa Kamal ya ce "abokina naga ranka a bace ko dai Madam din ce?" murmushin karfin hali yayi ya ce "kawai yanayi ne ya zo a haka, na zo ne mu tattauna akan batun neman iyayen yarinyar nan, numfasawa Kamal din yayi ya ce "abokina kawai za mu bada sanarwa ne a Gidan Television da Radio da Jaridu ko Allah zai sa mu dace, shi ma Captain Numfashi ya sauke ya ce "haka ne abokina gobe in Allah ya kaimu sai muje mu kuma bada sanarwar ko?". Wannan ke nan .........📝📝 Kuyi haƙuri da wannan. Ina godiya agareku masoyana Allah ya bar zumunci. Ina yiwa duk wani d'an k"ungiyar Royal Star fatan alkhairi. Allah ya kara daukaka k'ungiyarmu mai albarka. #ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR} 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY: ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://wwwfacebook.com/royal-star-writer's-association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa, ilimantarwa, dakuma nishadantarwa.(R.S.W.A) Ruwa kadai ke maganin kishi. Alk'alaminmu 'yancinmu. FREE BOOK📖📚 🅿️..........1️⃣4️⃣ Sun dad'e suna fira, kafin daga bisani yayi masa sallama ya tafi, daya fito kai tsaye shopping ya wuce yayi mata, d'an gaba d'aya ya mance da sun yi fad'a kafin ya fito, yana shigowa Gidan part d'inta ya nufa da sallama ya shiga, amma yaji shiru ganin bata falo yasa ya nufi bedroom d'inta, ganinta yayi a k'udundune da blanket da murmushi dauke a fuskarsa ya haura saman gadon, ya janye blanket din wani hucin zafi yaji ya daki fuskarsa a kidime yace "kanwata me yake damunki? bakida lfy?me yasa baki fada min ba? a tare ya jero mata tambayar, amma ko d'aya ba wadda ta iya amsa masa d'an gaba d'aya ta fara fita a hayyacinta, gaba d'aya ya nannadeta kai tsaye hospital ya kaita nan da nan likitoci suka rufa akanta, yana ganin wani Doctor ya fito ya nufe shi yana fad'in "Doctor me yake damunta? ta farfad'o?" Likitan ne yayi murmushi ya ce "karka damu typhoid ne ya ke damunta amma yanzu an mata allurai ta samu bacci nan da lokaci kankani zata tashi", cikin damuwa yace "to Doctor nagode, likitan ya ce "no ba komai nasa wata nurse ta kula da ita zaka iya tafiya yallab'ai" murmushi yayi ya ce "ba damuwa zan shigo goben", hannu ya mika mai su ka yi musabaha sannan ya fito daga Hospital din. A wannan Daren gaba d'aya bacci yayi k'aura acikin idanuwansa, da asuba ya gabatar da sallarsa, akan dadduma bacci ya d'aukeshi bashi ya farka ba sai karfe goma ko break fast bai tsaya yayi ba ya shirya a gurguje, Hospital d'in ya fara zuwa ya dubata lokacin da ya shiga d'akin bacci take dan haka ya tafi akan zai dawo anjima, Kamal ya kira ya tambayeshi "Abokina kana gida?" A daya ɓangaren Kamal ya ce "E ina nan tun dazu nake jiranka," ya ce "wallahi Abokina bacci ne ya d'auke ni, kuma dana tashi sai da na biya ta Hospital na duba Madam bata da lafiya," cikin jimami Kamal ya ce "ayyah Abokina me ya sameta?" captain ne ya ce "typhoid ne wallahi" Kamal ya ce "ayyah Allah ya bata Lafiya in mun dawo ma je na dubata". Wannan ke nan..........📝📝 Kuyi haƙuri da wannan. Ina yiwa duk wani d'an k'ungiyarmu Royal star fatan alkhairi Allah ya bar zumunci. Ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci. Allah ya kara d'aukaka k'ungiyarmu mai albarka. #ZAINAB KABIR J'AEN {@GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 {R.S.W.A}https://www.Facebook.com/Royal-star-writer's-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishadantarwa (R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin kishi. Alkalaminmu yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️.............1️⃣6️⃣ ............Yau ta yanke shawarar zata jira shi har zuwa sanda zai dawo, daan haka a falo ta zauna bayan ta gabatar da sallar isha'inta ta zauna akan doguwar kujera tana jiransa har ƙarfe 12 bai dawo ba wasa-wasa har barci ya fara ɗaukanta ba alamun sa, anan falon bacci ya ɗauke ta, shikwa a ɓangaransa bashi ya dawo ba sai ƙarfe 1:30 yana yin parking ɗin motar shi ya hango haske a falo mamaki ne ya kama shi kenan ba tai bacci ba falon ya shiga da sallama ɗauke a bakinsa ,hango ta yayi a kwance akan doguwar kujerar falon ƙarasa wa yayi gabanta ya tsugunna yana kallon ta shidai yasan ba son Yarinyar nan yake ba amma yana jinta acikin jiki da jininsa ji yake tamkar in babu ita bazai iya rayuwa ba yana jinta kamar ƙanwarsa da suka fito ciki ɗaya, ya yi wa kansa alƙawarin kulawa da ita har ƙarshen numfashinsa, gaba ɗaya ya ɗauke ta be sauƙe ta a ko ina ba sai akan gadon part ɗinsa, wanka yayi ya kwanta akan doguwar kujerar part ɗin nasa ,da asuba ita ta fara tashi mamaki ne ya kamata ganinta a ɗakin Hamma ita dai tasan a falo ta kwanta hango shi tayi akan kujera ta zuba masa ido wani irin son Hamma ne yake ratsata amma tasan ba zata taɓa samun shi ba saƙƙowa tayi daga kan gadon tashiga toilet ta ɗauro alwala. A ɓangaren sa kuwa tunda ta tashi yasani ganin ta tada sallah yasa shima ya miƙe ya ɗauro alwala ya tafi masallaci kasan cewar yau bazai fita da wuri ba yasa bai dawo da wuri ba, ita kuma tana idar da sallah ta tashi ta gyara part ɗinsa tas sannan tasa turare kichin ta shiga ta haɗa musu break-fast shigowa yayi kichin ɗin ya same ta tana soya dankali da ƙwai a hankali yace" barka da aiki ƙanwata", murmushi tayi ta ce"barka dai Hamma" sannan ta tsugunna har ƙasa ta ce "Hamma ina kwana?" shima murmushin yayi yace "Lafiya ƙalau ƙanwata ya ƙarfin miki" ta ɗan shagwaɓe fuska tace"da sauƙi bayan kwana biyu kamanta dani" ,murmushi yayi sannan yace "waya faɗa miki ƙanwata?ke kin taɓa ganin inda mutum ya manta da ƙanwarsa? to ina tare dake aikine yamin yawa wallahi amma kullum kina raina ,turo baki tayi gaba bata kulashi ba marairaice murya yayi yace " please ƙanwata ki ya fema Yayanki kinji dan Allah kimin murmushi kona ji daɗi araina" ,murmushi tayi sannan tace"Hamma ni bakamin laifin komai bafa na ya femaka ma in kayi min" shima murmushin yayi sannan yace "to ƙanwata na gode na tana di gift ɗin dazan baki amma saikin gama aikin ki zan baki tace" to Hamma"yana zaune a kichin ɗin yana ta yata hira a haka har ta ƙarasa aikin sannan suka ɗiba suka jera a dining ,tace "Hamma bari inje part ɗina nashirya kajirani fa karka tafi" yace "to ƙanwata ina jiranki amma fa kiyi sauri kinga nakusa makara" tace"toh Hamma ganinan ......... Wannan kenan........📝📝 Kuyi haƙuri da wannan. Inayiwa duk wani ɗan ƙungiyar Royal star fatan alkhairi Allah yabar zumunci. Ina godiya a gareku masoyana Allah yabar zumunci. Allah ya ƙara ɗaukaka ƙungiyar mu mai albarka. #ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY: ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.} http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fa"dakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad"antarwa.(R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin kishi. Al"kalamin mu "yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️................1️⃣5️⃣ Ba damuwa yanzu kana gida ne cewar captain, "a d'aya bangaren Kamal yace" eh ina gida ka karaso kad'aukeni dan bazan fita da motor ba, "captain ya ce" ok ba damuwa gani nan zuwa, ya fad'a yana katse kiran, "kai tsaye gidan su Kamal ya nufa, horn yayi gate man d'in gidan yazo ya bud'e mai yana fad'in "barka da zuwa Yallab'ai, "Captain ya kalleshi da murmushi ya ce, "yauwa Baba barka dai, an tashi lafiya, "Lafiya kalau" cewar Baba mai gadi bayan sun gaisa, "kai tsaye parking space d'in gidan ya nufa yayi parking din motarshi sannan ya shiga gidan, da Nadiya yafara cin karo kanwar Kamal, "da sauri ta ce " lah Mommy kinga Yaya Al'ameen yazo, Yaya Al'ameen sannu da zuwa, "murmushi yayi ya ce" yauwa k'anwata, sannan ya wuce suka gaisa da Mommy, sun dad'e suna shira sannan ya tashi ya ce " mom bari nak'arasa part d'in Kamal, "tace toh son kak'i kawo min matarka dai naganta koh?, "murmushi yayi ya ce "Mom zan kawo miki ita next week insha Allah, "murmushi ta yi ta ce Allah ya kaimu da rai da lafiya, "Ameen ya ce sannan ya k'arasa part d'in Kamal da yake shirin fitowa, "yace ka iso kenan?, to mu k'arasa, "ya ce na dad'e ai ina gurin Mommy muna fira, "Kamal ya ce" ok badamuwa mu wuce, "nan suka juyo suka nufi falon gidan, "Mommy su kai wa sallama sannan suka fito suka tafi gidan radio da jaridu gidan talabijin duk suka bada sanarwa, "sannan suka juyo suka nufi asibitin zaune suka sameta tana shan tea, ya jiki sukai mata sannan suka nufi gurin Dector "kai tsaye office d'in Likitan suka shiga da sallama a bakin su, ya amsa da murmushi a fuskarsa sannan ya basu gurin zama suka zazzauna sannan suka gaisa captain ne ya ce" doctor ya jikin nata?, "murmushi Likitan ya yi sannan ya ce" jikinta da sauki yanzu ma zaku iya tafiya da ita, "captain ya ce" to Doctor badamuwa mun gode, "sannan ya basu sallama suka nufi gida, bayan ya sauke ta ya maida Kamal gida sannan ya dawo A falo ya ganta kwance akan kujera doguwa, "ya k'araso kusa da ita ya ce " k'anwata ya jikin?, "ta ce da sauki Hammana, "ya ce masha Allah Mom d'in su Kamal tace tana so ta ganki insha Allah next week zan kai ki Cikin muryarta, ta marasa lafiya ta ce" to Hamma Allah ya kaimu lokacin, "tashi yai ya nufi part d'insa, "itama b'angaren nata ta nufa, su Aunty Asabe da Baaba Kande ne suka shigo suka dubata, sun dad'e kafin suka tafi, "wanka tashiga sannan ta gabatar da sallar magariba tun daga Wannan Rana ganin Hamma ya yi mata wuya dan da safe kafin ta tashi ya fita ba ya dawo wa sai wajan karfe sha d'aya lokacin kuma ta dad'e da yin barci, "aiki ne yayi masa yawa ga shi ta b'angaren cigiyar iyayenta da ya bayar, amma tana ransa gaba d'aya a wannan lokacin sai taji ta damu da rashin ganinsa. Wannan kenan......... Kuyi hakuri da wannan . Inayiwa duk wani d'an k'ungiyar Royal star fatan alkhairi Allah ya bar zumunci. Ina godiya agareku masoyana Allah ya bar zumunci. Allah yakara d'auka ka kungiyar mu mai albarka . #ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py _c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad'akarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa.(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalamin mu 'yancin mu. FREE BOOK 📖📚 🅿️................1️⃣7️⃣ Da sauri ta 'karasa part d'in nata ta shirya, sanda ta fito har ya gama shiryawa kallonsa tayi yayi kyau sosai a hankali ta bud'e baki tace "sorry Hamma na dade ko?" yace "a'a 'kanwata ba komai zauna muyi break fast sauri na ke yi" tace " to Hamma" tunda suka fara break din kowa ya yu shiru dan kowa da tunanin da yake, bayan sun kammalla ta d'ebe kwanunka ta kai kitchen sannan ta zo taraka shi har bakin motarsa ya tafi ita kuma ta koma cikin gidan, Hamidah ce ta kirata ta d'aga da murnarta tana fad'in "hello 'kawata wato kin manta dani kwana biyu ko?" a d'aya 'bangaren Hamidah ta ce "'yar rainin wayo ai ni fushi nake dake kuma yanzu ma sa'a ki ka ci na kiraki" marairaice fuska tayi kamar Hamidar na wurin tace "kai bloody me nayi miki kuma?" Hamidah tace "yaushe rabon da ki zo ki gaida Mamanmu?, yanzu ma gaba d'aya kin yada mu jiya da mu ka yi waya da sis Fatima tace ita ma rabon da kuyi waya harta manta" cikin sanyi murya tace "dan Allah sis kuyi ha'kuri kunsan koda yaushe kuna raina kuma in Allah ya yarda ina nan zan zo kin ji? Bestyna" cikin murna Hamidah tace "to my bloody sai kin zo" tace "insha Allah" sun dade suna waya kafin suyi sallama, bayan ta katse kiran ta tashi ta gyara gidan ta tafi ɓangaren su Mama Kande acan ta yini suna aikace aikacen su kamar yanda suka saba, bayan sun yi sallar magariba Anty Asabe tace "ni kuwa 'kanwata kinga yanda kika koma? ki fada min gaskiya mene tsakanin ki da yalla'bai na fara zargin wani abu!, Da farko ya d'aukeki daga 'bangaren masu aiki ya mai dake part ďin kusa da nasa sannan kuma ya hanaki kula saurayinki mene dalili? ki fadan gaskiya 'kanwata babu 'boye-'boye a tsaninmu ke 'kanwata ce", sunkuyar da kai tayi tace "a zahirin gaskiya na boye muku wani 'bangare a labarina nan ta bata labarinta har zuwa aurenta da Hamma har i zuwa kawo yanzu, murmushi Anty Asabe tayi tace "Alhamdullilah amma na ji daďin wannan auren naku dan wallahi kunyi matu'kar dacewa Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi Allah ya bayyana miki iyayenki Allah kuma ya dai-daita tsakaninku" dariya tayi tace "kai Anty Asabe wannan murna haka to Allah ameen" nan suka cigaba da hirarsu cikin nishad'i dan har ga Allah suna jin junansu a rai. A d'ayan ɓangaren Abbie ne zaune yana ta tunanin rayuwa, Basma ta shigo tace "Abbie hutawa kake yu anan?" ya ce "wallahi Basma tunanin y'ar uwarki nake yi yau shekaru sha tara ke nan amma har yau shiru babu ita babu dalilinta ga Ammin ku kullum ciki damuwa, ga wannan lallura dake damunta na rasa yanda zanyi kuma ni har yanzu ban fidda ran zan ganta ba, gaskiya Hajiya Falmata ta cuceni!nayi Dana sanin saninta Allah zai bi min ha'kina insha Allah" ya fad'a yana goge 'kwallar da ta taru a idonsa ita ma Basma haweyen daya wanke mata ta goge ta san iyayenta basu da wata damuwa da ta wuce 'batan yayarta kuma kullum inta kai goshinta 'kasa sai tayi addu'ar Allah ya bayyana ta iyayenta su huta cikin sanyi murya tace "Abbie insha Allah a jikina ina jin Allah ya kusa bayyana mana Anty Ummi" murmushi ya yi yace "Allah yasa 'yata" tace "yauwa Abbie dama ina son zuwa Nigeria wajan Hamma Al'ameen" yace "to amma ba yanzu ba" ta ce "to Abbie". Su waye Al'ameen? .......... Wannan ke nan.......✍️✍️ Kuyi haƙuri da wannan. Ina yiwa duk wani d'an 'kungiyar Royal star fatan alkhairi Allah ya bar zumunci. Ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci. Allah ya 'kara d'aukaka k'ungiyarmu mai albarka. Ina godiya a gareku takwarorina Ummu Raees, kakata, Mauncy, da dai sauransu. #ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: RAYUWAR ZAINAB COMMENT PAGE 18 Masha'allah Hussain Allah y Sanya alkhairi y Bada zaman lpy t Bada zuri'a mai albarka🤲🏻🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 Kaji illar kawayen banza su hure maki kunne su hanaki girmama uwayen mijinki dama shi kanshi mijin sannan Kuma m daga karshe su kashe maki aure y Allah ka kare mu daga sharrin gurbatattun abokanai 🤲🏻🤲🏻🙏🏼 Masha'allah Hassan kaikam k dace d mace Allah y Kara maku hakuri d juna Allah y Baku zuri'a mai albarka🤲🏻🥰💃🥰🥰🥰 Masha'allah Allah y raya al'ameen ga tafarkin tsira y kare shi d kariyar shi yasa mai jinkan iyayen shine🤲🏻🙏🏼 Kai gsky naji dadin wannan abun Hassan d hassana ga Kuma Hussain d Ussaina💃 Allah y Baku zaman lpy Kuma y baka iKon yin adalci a tsakanin matan ka🤲🏻💃💃💃 Hussaina Allah y sauke ki lpia🤲🏻🥰💖💖💖💖💖💖 Masha'allah Garkuwar royal 🌟 Allah y Kara hazaka d basira d qarfin👀ya kare ki d sharrin masu sharri🤲🏻Kuma Allah y Kara daukaka d Nisan kwana🤲🏻🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Muna godiya sosai Daga fateemah🥰🌹 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Tsokaci,, dama mu mata abinda ke cutar mu kenan bakin kishi aduniyar nan mata mafi akasarinsu kishi sukasa alamarinsu yayinda su maxan daake kishin akansuma yawanci Bata tasu sukeba baxaki tsaya kiyi abinda yakawoki duniyaba saidai kibata lokacin ki abanxa akan wata aiyanzu kishin kwatar miji ake kema kixama sarauniya agurinsa bawai Kita shirmen kishi dawata ba wlh mata mukula mudawo haiyacinmu,, Kunga irinta ai kamar masu Hali irinna hajiya falmata wlh akwai ire irensu harma da wainda suka fisu kiga mace aduniya batada abokiyar gaba samada kishiyarta yesss baace kada kiyi kishi ba kishi halal me ga kowacce mace kuma halittane Amma saikisan irin Wanda xakiyi kiga mace tabata lokacin ta gabun malamai dasunan mallakar muji ko nakasa kishiya wlh wannan ba maslaha bace aikiyi tsaftataccen kishi tahanyar dawoda martabarki ga mijinki shine kawai kainifa macen dadake biye biyen malamai wlh batakai maceba tunda bakisan yadda xaki kwaci kanki ahannun wataba saikin hada da xagon kasa wannan kinrako mata duniyane kamarsu hajiya falmata wlh sunyi asara akwai iri irensu dadama harma da wainda suka fisu aikata mummunan aiki duk abinda muke gani akarance karancenmu wlh akwai mata masu aikata mafiyinsa axahiri kuma karshensu Dana sani da nadama Kalubale garemu Mata ☹️☹️☹️ 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 {R.S.W.A} http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad'akarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️..................1️⃣9️⃣ Yau cikin Usaina ya cika wata tara da sati biyu, a ranar ta tashi da matsanan cin ciwon mara, aka d'auketa a ka kaita hospitalspital nan likitoci suka tabbatar da haihuwa ce, nan aka rufu a kanta, ba'a fi minti ashirin ba ta haifi santaleliyar 'Yarta mace farinciki a wajan a halinta ba'a magana, ana wajan Usaina ana ta yimata sannu da barka ana juyowa wajan jaririya aka ga babu ita babu dalilinta, tashin hankali a wajan a halin nan ba'a cewa komai tun ana d'aukar abin wasa yazamana abin ya koma gaske, daga likitoci har i zuwa ma'aikatan gurin kowa yana cikin tashin hankali, nan aka shigar da report wajan 'yan sanda bincike ake ta ko'ina har rufe asibitin a kayi amma ina da Alhaji Hussain yaga abin ya'ki 'karewa ya hakura ya fauwalawa Allah, Usaina ta rame sosai, hawan jini yakamata da k'yar aka dinga kar'bo mata rubutun dangana ta hak'ura, amma har yanzu bata koma yanda take daba. A 'bangaren Hajiya Falmata koda tasamu nasarar d'auke jaririyar kai tsaye wata 'kawarta ta kaiwa ajiya kafin tasamu abin ya lafa taje ta jefar da Yarinyar duk abinda ake ko a jikinta dan ko jaje bata yiwa Uwar Yarinyar ba a cewar ta ita ba abinda ya shafeta bane. Bayan abin ya lafa ta tambaye shi kan zataje saro kayayyaki ya barta nan ta d'au Yarinyar taje wani daji a Yankin jigawa mai gatari ta yarda ita ba tausayi ko kad'an a ranta, ita dai burinta ta samu burinta ya cika bayan ta dawo sai ta fito da wani salo na shiga jikin Usaina sa bo da taji sirrinta, Allah yasa ita Usainar bame surutu bace barin ma da Yarinyar ta ta 'bata shi yasa bata samu yanda take so ba. Bayan 'batan 'Yar tasu sai da Hajiya Usaina tayi shekara hud'u sannan ta samu wani cikin, wannan karon 'kasar waje Abbie ya fitar da ita da yaga tana da cikin saida ta haihu 'yarta Basma ta girma sannan ta dawo Nigeria Hajiya Falmata ba'kin ciki kamar ya kashe ta. bayan shekara biyu ta kuma samun ciki haba Hajiya Falmata kamar tayi hauka wannan karon nan ba'kin cikin ta kasa 'buya yayi. Kun san yaro ba hankali Basma ce ta tafi 'bangaren Hajiya Falmata aikwa nan tace shegiya gwara da kikazo 'Yar uwarki sa ce ta nayi na yar ke kuma kashe ki zanyi shegu a halin tsiya, d'agowar da za tayi taga Alhaji Hussain a tsaye yana kallonta idon sa yayi jawur cikin rauni yace" Falmata me nayi miki? me Usaina tayi miki? kika raba mu da farincikin mu!nan ya zube a kan gwiwoyinsa yana kuka mai cin rai, hankalinta yayi matu'kar tashi ta rasa mai zata yi kuka tasa tana fad'in Alhaji kayi ha'kuri ka rufamin asiri, "wani irin duka ya kaimata sai da yayi mata jina-jina sannan yasa 'yan sanda suka kamata yau kimanin shekara ashirin amma har yanzu tana kurkuku. Hajiya Usaina da taji labarin ba 'karamin kuka tayi ba ta yiwa Falmata Allah ya isa yafi a 'kirga. Bayan Basma ta haifi yara uku Yasmeen, Intisar,da Hanan, amma har yanzu suna kulafacin 'Yarsu su suna fatan Allah ya bayyana ta. Mommy kuma tunda ga kan Al'ameen bata 'kara haihuwa ba dan haka duk wata soyayya suka tattara ta a Kansa. CIGABAN LABARI..... Wannan kenan........✍️✍️ Kuyi ha'kuri da wannan. Ina godiya agareku masoyana Allah yabar zumunci. Ina yiwa duk wani d'an 'kungiyar Royal star fatan alkhairi Allah yabar zumunci. Ina godiya agareku rayuwar zainab fans. Allah ya'kara d'aukaka kungiyar mu mai Albarka. #ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: tofah kardai daga haihuwar ya aga Babu kamar wata allura 🤔🤔🤔🤔🤔 kaiii gaskiya dasa hannu barina Kira Yan kato da gora 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️ gaskiya hajiya falmata kiguji karshenki takan San duniya kiraba ya da mahaifiyar ta wannan kayan xunubin har ina😥😥😥 karshenta kenan dama gidan kurkukun anyi mummunan karshe dman karshen masu Hali irin nata kenan masu San duniya 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: tofah kardai daga haihuwar ya aga Babu kamar wata allura 🤔🤔🤔🤔🤔 kaiii gaskiya dasa hannu barina Kira Yan kato da gora 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️ gaskiya hajiya falmata kiguji karshenki takan San duniya kiraba ya da mahaifiyar ta wannan kayan xunubin har ina😥😥😥 karshenta kenan dama gidan kurkukun anyi mummunan karshe dman karshen masu Hali irin nata kenan masu San duniya 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY&WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 {R.S.W.A} http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️...............2️⃣0️⃣ Tun daga ranar basu ƙara had'uwa da Hamma ba, yau da wuri ya dawo a falo ya same ta tana kallon Indian fim, murmushi yayi yace"sannu da hutawa" ita ma murmushi tayi tace "yauwa sannu Hamma ka dawo lafiya?" yace"lafiya ƙalau ƙanwata bari inje in watsa ruwa kema ki shirya za muje gidan su Kamal" da murnar ta tace"to Hamma" d'akinta ta shiga ta shirya cikin wata blue black d'in shadda ta yafa mata milk colour d'in mayafi, tayi kyau sosai kamar ka sace abinka da farar fata. Da ta fito Hamma tagani yana shirin fitowa kallon-kallo suka fara yiwa junansu domin kuwa shima shaddar daya sa kalar ta tace sak kamar sun had'a baki, murmushi suka sakar ma junansu sannan Hamma yace"shine kika sa irin kayana ko?" murmushi tayi ta shagwa'be fuska tace"kai Hamma ko kuma kai kasa irin kayana ba" dariya yayi yace"to naji mutafi yamma tanayi" nan suka jera suka nufi mota haba wa duk inda kake neman da cewa kaga wannan ma'aurata kasan sun kai dan sunyi bala'in da cewa,a zuciyata nace Allah Ubangiji ya 'kara had'a kawunansu, yau ba da sojan daya tafi daga shi sai Zainab gidansu Kamal suka nufa kai tsaye bayan sun isa suka shiga Mommy suka tarar a zaune Nadiya tana yanke mata farce, da murna Nadiya ta tari Zainab tana mata oyoyo nan suka gaisa da Mommy da yaya Kamal, Nadiya ta janye ta sukai part d'inta Kamal ma suka tafi part d'insa shida Captain ,hira sosai Nadiya da Zainab suka yi nan danan suka saba, basu suka bar gidan ba sai bayan magariba da al'kawarin Nadiya zata ziyarci Zainab ita ma. A gajiye suka dawo dan haka kowa ɓangaren shi ya nufa, basu 'kara had'uwa ba sai washe gari, nan yake sanar mata yana so zaije ya gaida su Ammi shi tace "nima hamma zan bika please" "yace to ba damuwa insha Allah zaki" "tace to Hamma na gode" A 'DAYA BANGAREN Abbie ne zaune yana karanta jarida kawai yaga NASA cigiyar wata Yarinya da hoton ta tana 'karama da kuma hoton ta na yanzu kawai sai ya tsinci kansa da karanta labarin Yarinya mi'kewa yayi yana fad'in"Ummina ce ita ce wallhi ita ce!" Ammi ya ƙira ya nuna mata nan take ta yanki jiki ta faɗi. Yanzu muka fara Shin su Abbie zasu samu damar had'uwa da d'iyar su kuwa? Shin Zainab ce Yarinyar da suka ga labarinta a jaridar?. Shin Hamma zai kar'bi Zainab a matsayin abokiyar rayuwar shi?. Shin ina labarin Ancul Aboki?. Shin in Zainab ta had'u da Iyayenta ya Hamma zaiji sanda yasa Ammin sa ce Mahaifiyarta?. Wannan amsoshin suna tattare a cikin wannan littafi namu mai albarka. Wannan kenan✍️✍️✍️ Kuyi ha'kuri da wannan. Ina godiya agareku masoya rayuwar zainab. #ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: toh fa su hamma wato anga xee taxama mutum andaina kyararta da hantararta dacin xalinta ko wato kaga tayi fresh Takoma mace harda wani kanne ido kk😏😏 toko xamu amsheka saimun wahalarda Kai kaji abinda mukaji 😡 garadai kafita da ita taga gari garima yaganta kotayi kasuwa tunda Kai kace dibarmata lokaci kayi kafin aga iyayen ta yakamata kabarta ta sakata ta wala taxama mace Mai yanci itama😍😍😍 Masha Allah xee xee wahala takusa Yanke Miki insha Allahu ubangiji yabaiyanar wa iyyayenki ke kema kiji dadin iyaye ahayye xanaxo Bari inshafa hoda warrrrrrrrr💃💃💃💃💃💃💃💃💃 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, da kuma nishad'antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️...................2️⃣1️⃣. Kiran sunan ta yake cikin tashin hankali "Usaina ki tashi dan Allah", ruwa ya d'ebo ya yayyafa Mata nan taja wani dogon numfashi sannan ta bud'e idonta a hankali,da sauri ta tashi tana fad'in"ina 'Yata take tana ina,"number da akasa in anji labarin iyayenta a kira ita sukai ta kira amma switch off tashin hankali nan Abbie yace su shirya gobe za su tafi Nigeria,nan da nan kuwa suka shirya suka d'unguma sai garin Adamawa,Alhaji Hassan ma shi da Iyalin sa duk sun zo dan Alhaji Hussain ya kira shi ya fad'a mai yanda ake ciki,Hamma lokacin baya Nigeria ya d'anyi tafiya zuwa Germany domin duba wasu company d'inshi na can,dan haka bai san wainar da ake toyawa ba. Yauce ranar da Hamma zai dawo dan haka tun safe ake gyare_gyaren gidan sun shirya Abinci kala-kala ita dasu Anty Asabe ko'ina na gidan tas dashi 'kamshine kawai ke tashi, part d'inta ta koma domin ta shirya don yanzu tasan sun kusa Ƙarasowa,cikin wata farar Abaya ta shirya wadda taji stones ta tifke gashin kanta da ribbon fari tayi rolling d'in Mayafin rigar,Tubarakallah zo kuga had'uwa tayi kyau ma tuka flat shoe tasa ta fito,Ƙarar durar motocin su da taji ya tabbatar mata da isowar su dan haka ta tafi falo ta tsaya tana jiran shigowar sa Yana shigowa falon ya ganta a tsaye sai murmushi take ware hannuwan sa yayi alamun ta taho aikuwa da gudu ta taho ta rungume shi tana yi masa sannu da zuwa jakar hannunshi ta kar'ba ta ajiye mai sannan ya nufi part d'inshi ya watsa Ruwa sannan ya fito ta gabatar masa da abinci, sannan tasa aka kaima sojojin gidan nasu . Wannan kenan.......✍️✍️ Kuyi hakuri da wannan banajin dad'ine ina kwance da 'kyar na lalla'ba nai muku wannan ina barar addu'ar Ku. #ZAINAB KABIR JA'EN. {@GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://www Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa.(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalamin mu 'yancin mu. FREE BOOk📖📚 🅿️......................1️⃣8️⃣ ________________________ Waye captain Al'ameen? ________________________ Al'ameen Hassan d'a ne a gurin Alhaji Hassan , d'a guda d'aya da iyayenshi suka mallaka a duniya shi yasa duk wani gata suka bashi, Mahaifinshi d'an asalin garin Adamawa ne su biyu iyayen su suka Haifa shida 'kaninsa Alhaji Hussain tagwayene su,tun tasowar su komai tare suke yi sun shaku sosai, in d'aya ba shida lafiya to d'aya ma sai ya kamu, a haka har suka girma sunyi karatu mai zurfi inda suka karanci 'bangaren kasuwanci, iyayensu suka basu jari, a hankali kasuwancin su ya bun'kasa Alhaji Hussain ne yazo Kano yi musu sare-sare nan ya had'u da Falmata soyyaya ce ta kullu a tsakaninsu har sukai alkawarin aure, Sanda ya sanar da iyayenshi cewa sukai ya bari Yayanshi ya nemo shima amma sai ya dage ba yanda suka iya haka suka yarda nan akai biki, da farko Falmata ta nuna baruwanta daga baya da ta had'u da 'kawaye yan duniya ta goge sai ta dawo tafi kafin kowa shekarar su biyar bata ta'ba haihuwa ba,gaba daya Alhaji Hussain damuwa tayi mai yawa na yanda Falmata ta koma bata ganin kowa da gashi, shi kanshi wataran tsoranta yake yi, a wannan halin Yayan shi ya tafi Turkey domin duba company su na can, a can ya had'u da Hassana 'Yar gidan wani hamsha 'kin mai kud'ice a haka suka 'kulla soyyaya mai 'karfi ba da dad'ewa ba a kai bikin su ya taho da ita Nigeria suna zaune lafiya da mijinta da danginsa kasan cewar ita maca ce mai hakuri,kowa yabonta yake ana haka ta samu ciki, zo ku ga murna a wajan Alhaji Hussain kamar matarshi akace tana da ciki kulawa take samu ta kowani 'bangare sai dai Sam basa shiri da Falmata sa bo da ita halinta bai mata ba. Bayan cikin ta ya tsufah ta haifo san kacecen d'anta namiji, yaro ne kyakkyawa fari tas dashi da suna yazo yaron yaci suna Al'ameen wato sunan Kakanshi Mahaifinsu Alhaji Hussain duk wani gata na duniya yaron yana samu a gurin iyayenshi ta kowani bangare tun daga kanshi mommy bata 'kara haihuwa ba. 'Kanwar Mommy wato Ussaina ta tafi karatu shi yasa bata taba zuwa Nigeria ba saida Alhaji 'karami yayi shekara biyar a duniya sannan yazo gidan Yayarta ta dad'e a gidan sosai a wannan zaman da tayi suka fara soyyaya da Alhaji Hussain kowa yaji dad'in wannan lamari ,sanda Hajiya Falmata taji anyi bala'i na 'kin 'karawa ta wannan dalilin har saida Alhaji Hussain yayi mata saki d'aya ganin haka yasa ta saduda bawai dan ta hakura a zuciyarta ba ,anyi biki na kece raini a ka kai amarya d'akin ta tana zaune da mijinta lafiya, shekararta biyu ta samu ciki ganin wannan cikin ba 'karamin d'agawa Hajiya Falmata hankali yayi ba tayi al'kawari sai ta salwantar da cikin ta ko yaya dan haka tai ta 'kullawa da kwancewa nan ta yanke shawara in har aka haifi d'an ko 'Yar zata sa a yarda su taga ta tsiya tasan yanzu tana yin yun'kuri za'a kamata amma ta yake shawara yanzu jira kawai take Hussaina ta haihu ta ida aikinta. Wannan kenan .....✍️✍️ Kuyi hakuri da wannan. #ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad`akarwa,ilimantarwa, da kuma nishad`antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad`ai ke maganin `kishi. Al`kalaminmu yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️................2️⃣2️⃣ Bayan ya kammala cin abinci suka d'an ta'ba hira kafin daga bisani ya ce mata "zan tafi gidan su Kamal akwai maganar da zamu tattauna dashi. "murmushi tayi ta ce" kai Hamma ko hutawa ba kayi ba to ka gaidamin da Nadiya da Mommy, ya ce" to K'anwata insha Allah maganar ce mai mahimmaci kinji K'anwata amma ai bazan dad'e ba "murmushi tayi ta ce" to Hamma badamuwa adawo lafiya, "murmushi yayi ya ce"Allah yasa K'anwata. "kai tsaye gidan su Kamal ya nufa, yana zuwa yayi parking d'in motar shi a parking space na gidan, sananan ya shiga gidan nasu, "bakowa a falon dan haka ya samu d'aya daga kujerun falon ya zauna. number Kamal ya kira ya ce" ka k'araso part d'ina su Mom basa nan sun tafi biki, "ya ce ohk ganinan. Yana k'arasa wa part d'in nashi ya ganshi a zaune yana aiki a laptop d'insa, "gefen gadon yasamu ya zauna sannan ya ce" Abokina aiki kakeyine?, idon Kamal yana kan aikin da yake ya ce "wallahi Abokina wasu file nake shigarwa nama kusa k'arasawa, "Captain ya ce" ohk badamuwa ka k'arasa sai muyi magana, rufe computer yayi ya ce" nagama ai, ya ce" dama na zo ne akan maganar iyayen Yarinyar nan Zainab har yanzu shiru fa akeji kana ganin anya kuwa zamu samu iyayenta nan kusa?, "numfashi Kamal ya sauke kafin ya ce" Abokina kar mu fidda rai da samun iyayen Zainab ni a jikina inajin cewa za'a ga iyayenta kasan shi abu irin wannan sai a hankali dole mu bi lamarin a sannu insha Allah zamu samu nasara, "shima numfashin ya sauke ya ce" Allah ya taimakemu burina inga iyayen Yarinyar nan in mika musu 'yarsu, "murmushi Kamal yayi ya ce" to ya maganar aurenka dake kanta?, "hararar shi yayi ya ce" bansani ba d'an raini wayo. Fitowa suka yi suka tarar Mom harta dawo ita da Nadiya da murnar ta ta ce "lah Yaya Al'ameen Kaine a gidan namu ina wuni?, "murmushi yayi ya ce " lafiya k'alau k'anwata ya karatu?, ta ce" karatu alhamdulillah ina Anty Zainab?, "ya ce "Wallahi tana gida ta ce" tana gaisheki. ta ce" ina amsawa ka gaidamin da ita nima, ya ce" insha Allah sannan ta zauna suka gaisa da Mom kafin ya nufi gida. Wannan kenan............... Kuyi hakuri da wannan kunsan yanayi na rashin lafiya kawai dan kar ink'i yi muku typing ne amma banda lafiya. #ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR} 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad'akarwa,ilimantarwa, da kuma nishad'antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️...................2️⃣3️⃣. ………Bashi ya iso gida ba sai wajajan sallar isha'i, sanda ya shigo harta tafi part d'inta ta kwanta dan haka bata san sanda ya dawo ba. Washe gari da asuba ta tashi tai ayyukanta ta tafi part d'insa ta gyara masa, a kwace ta tarda shi yana kwance amma idonsa biyu murmushi tayi sannan ta ce "barka da safiya Hamma har yanzu baka fita ba dama?" Tashi yayi zaune sannan ya ce "wallahi kuwa K'anwata ban tashi ba kin tashi lafiya?" "Lafiya Alhamdulillah Hammana" ya ce "toh masha Allah bari inje in watsa ruwa yau bana jin dad'i ne sosai kuma su Ammi sun zo Nigeria harda Mommy ma suna gidan Granny" ji tayi gabanta yayi wata mummunar fad'uwa, amma sai ta dake ta ce"da gaske Hamma kace mun fasa zuwa can d'in?" yace"eh K'anwata sai dai muje Adamawan amma ni gobe zanje in yaso ke ma tafi daga baya" ta ce "toh Hamma bari in had'a maka kayan" ya ce "toh" sannan ya shiga wanka ita kuma tana shirya masa kayansa a akwatinsa ta tafiya Wayarsa ce take ta ringing dan haka da sauri ya fito ya d'aga oganshi ne daga gurin aiki dan haka cikin girmamawa ya d'aga ya ce"barka da wannan lokaci Ranka ya dad'e" a d'aya 'bangaren Ogan nasu yace "barka dai Captain Al'ameen,sannan ya cigaba da cewa dama nakiraka ne in sanar da kai akwai wani aiki daya tashi na ujila kuma kai akasa a kan tafiyar tafiyar one week ce kayi ha'kuri nasan ko gama hutawa bakai ba kasan aikin namu akwai wahalar" cikin muryarsa mai tsananin kwarjini ya ce "ba damuwa Oga insha Allah yanzu zan taho"sannan ya katse kiran kallon shi tayi ta ce " Hamma yanzu ka fasa zuwa gaida su Ammin?" zuwa yayi ya tsugunna a gabanta yace" 'kanwata aiki ne ya tashi na gaggawa tunda kika ga Oga ya sani a aikin to aikine me mahimmanci ya zanyi dole in ha'kura inya so inna dawo sai mu tafi tare koh?" Murmushi tayi duk ranta ba dad'i tace "toh Hamma" A gaggauce ya shirya sai da tayi mai rakiya har bakin motar shi sannan ta koma gida, kai tsaye wajan su Anty Asabe ta wuce sukayi aikin su kamar yanda suka saba sannan suka samu ke'bewa da Anty Asabe, bayan sun zauna ta ce"Anty Asabe dama kayan nan na wajan Anty Lady nake so da mayuka da sabulai da kuma su dilka da turarrauka nawa duk sun 'kare" murmushi Anty Asabe tayi ta ce"ai kayan ne suna da kyau sosai baki da damuwa zan mata magana sai a aiko miki dashi har gida" "yauwa Anty Asabe shi yasa nake sonki" sun dad'e suna shira sannan ta kira Fatima da Hamida sun sha hira sannan ta tafi part d'in ta ta kwanta. Kwanci tashi ba wuya Yau takama satin Hamma d'aya da tafiya yaune ya kama ranar da zai dawo dan haka suka yi mai kayan tarba kamar yanda suka saba,kamar yanda yayi tsammani haka kwa ya tarar ita tafara tar bar shi. Washe garin daya dawo kuwa suka d'aga Adamawa shida ita... To fahhhhhhh Wannan kenan.......✍️✍️ Kuyi ha'kuri da wannan.... #ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR🌟}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, da kuma nishad'antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️.................2️⃣4️⃣. ............Da yamma li'kis suka isa garin Adamawa a hotel suka kwana, wannan ne karo na biyu da suka kwana a d'aki d'aya washe gari suka 'karasa gidan su Granny kowa nan nan yake da ita tun daga kan su Mommy har su Abbie da Abbu, haka kurin Ammi taji son Yarinyar ya kamata, ita ma a 'bangaren Zainab ji tayi tana son Ammi sosai, haka su Basma ji suke kamar su mai da ta ciki wannan yace "Anty me kikeso" haka suka cika ta da surutu ita dai kawai sai dai tayi murmushi. Kwanan su biyu yau da zuwa ta saba da kowa na gidan barin ma Granny da Basma tunda suka zo basu samu damar ke 'bewa da Hammanta ba gaba d'aya sai taji ta damu matu'ka shima a 'bangaren nasa gaba d'aya daure wa kawai yake amma ya yi kewarta matu'ka tunda yazo shima sai yau ya samu zama da su Abbie dan shi baisan dalilin zuwan su ba kwata-kwata. Abbu ne ya fara magana tare da fad'in "Son dama dalilin zuwan mu Nigeria shine Yarinyar wajan Abbien ka da ta 'bata ita muka ga an buda ta a jarida to munyi ko'karin Tuntu'bar number wayar da muka gani a jiki amma abin yaci tura kullum muka kira a kashe shine muka yanke shawarar tuntu'barka tunda kai a Nigeria kake ga jaridar Abbu ya d'akko ta mi'ka masa" tunda Abbu ya fara bayanin yaji gabansa nata fad'uwa amma sai ya daure har zuwa sanda Abbu ya mi'ka masa jaridar, a hankali yake bud'ewa, gaba d'aya yaware idonsa akan jaridar a zabure ya mi'ke yana 'kara zare ido "me hakan ke nufi? suna nufin Zainab ita ce Yarinyar Ammi data 'bata innalillahi" abinda ya dinga maimaitawa kenan . Abbie da Abbu ne suka tashi a tare suna fad'in "kasan Yarinyar ne?" Kallon su yake yi sannan yace "kwarai kuwa Abbie nasan ta" amma ina so a had'a kowa da kowa da maganar bata iya mu kad'ai bace" har Abbu zai yi magana Abbie ya dakatar da shi. Wannan kenan.......✍️✍️ #ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: to jamaa ga takwara ga hammanta fa xaaje adamawa ta yola💃💃💃💃 shin mexai wakana kuma tsakanin su baridai mubaxa idanuwa mugani🥱🥱🥱 Kuji hamma meye nawani kewar ta niba bansan shishshigi da kankanba kamanta wulakanci dakadinga matane Toni ban mantaba idan Maye yamanta? wato kaga xee taxama mutum ko harwani kewanta kake to Koda xamu amsheka saimun wahalarda dakai kamar yadda dafarko kakasa rike amanarta daaka bar maka wannan Abu yamin ciwo idan natuna Wai harda duka abaya😢😢😢 inajin haushinka kamar na shakeka Amma bakomai lokacinne xakaxo hannu very soon🥱💃💃 Ahayye xanaxo Bari inshafa hoda warrrrrrrrr ahayye xanaxo Bari inshafa hoda warrrrrrrrr ahayye shikenan faduwa taxo daidai da xama wayyooooo takwara dadi Ina xansa raina finally kinso gida ashekema yargatace gaba da baya Amma wancan katon yanayi da gemu kamar jelar tsatso yaita cutarki abaya harda kaiki bangaren masu aiki wayyiiihuuuuuuuuuu dadiiiiiii💃💃💃💃💃💃💃💃💃😋😋😋😋😋 wayyyyyoooooooo hamma kashiga uku kaxo hannu aidole sainunyi ramuwa baa taba Xaynabu Abu Mai tagwayen suna axauna kalau gashidai Yar uwar kace kaita gana Mata abaya kaiiii gaskiya hakan yamin sugar 😋😋😋😋😋😋😋 kekuma xee kitsaya ki jajirce ka kwatarwa kanki yanci bawai xuruf kixurmaba kamar injin taliya😡😡😡😏😏😏😏 kixama mace cikakka Mai class kiwanashi kafin ki amince masa yasan cewa yesss kema kinsan yancinki na mace eheee💃💃💃💃 mexan gani haka???🤔🤔🤔 saida naxauna na takarkare na Mike akujera Yar tsuguno xansha karatu harda kulle kofa Amma Naga Abu dan mitsitsi kamar jelar tsatso😔😔😔 gaskiya matarnan kinada lutiyar fitina😥😥 yanzu wannan wacce irin rowace haka maimakon kibari muga murnan su Abbie da yadda hamma xai rude yaga xee amatsayin family dinsace Naga farin cikin takwara Amma kinwani katsaemu kinbarni da tunanin yadda xaa karke💃💃💃💃💃 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 https://www.facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/?ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad'akarwa,ilimantarwa dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. 🅿️...................2️⃣5️⃣. ______________________Ta hanyar cewa "Yaya kar mu katse mai hanzari Son zamuyi yanda kace", ya ce "toh Abbie" a babban falon Granny kowa ya hallara tun daga kan iyayen har zuwa "Yayan kowa so yake yaji dalilin had'uwar tasu Hamma ne ya juya yaga bai ga Zainab ba dan haka yace ma Basma" je ki kiramin Antyki" Basma ce ta ce "Yaya wlh tunda tatashi yau batada lafiya" yace "eh duk da hakan kirawota" tace "to Yaya,sannan ta juya ta tafi kiranta, Kanta a 'kasa tashigo falon duk jikinta a sanyaye yau sam ta rasa me yake mata dad'i gefen Hamma ta zauna sannan kowa na gurin yayi tsit ana jiran aji me ya faru a ka had'a wannan taron na gaggawa Abbu ne ya fara magana yana cewa "Assalamu alaikum," nan kowa ya amsa masa sallamar cikin girmamawa sanna ya cigaba "to kamar yanda muka sani idan wani abu ya tashi a family muna k'ok'ari muga an had'a taro irin wannan domin a magance matsalar, to wannan taro yasha bamban da wancan wannan taro an had'ashi ne akan Yarin yar wajan K'anina Hussain data b'ata toh mun samu jarida akan wani bawan Allah yana neman Iyayen Yarin yar to munyi iya k'ok'ari domin mu tuntu'bi layin wayar da muka gani amma kullum a kashe, shi ne mika yanke shawarar tahowa Nigeria domin mu bin cika, to yau muka zaunar da son a kan zance ya ce "yasan wani abu akan Yarin yar amma yana so a had'a kowa da kowa domin jin yanda lamarin ya kasance dan haka son muna sauraranka" gaba d'aya hankalin kowa ya juya kan shi kowa ya zuba masa ido ana jiran aji mai zaice, Cikin sanyin jiki ya ce "Mommy, Ammina, Abbu,Abbie, ku gafarceni bakowa bace Yarinyar da ake nema ba sai Zainab matata" cikin zaro ido kowa na falon yake kallonsa, ya kuma sunkuyar da kai ya cigaba " 'kwarai Abbu ita ce na 'boye muku wasu abubuwa akan aurena bakowa bane yasan cigiyar iyayenta ba sai ni" nan ya kwanshe labarin tun had'uwar shi da Nanne har zuwa aurenshi har kawo yanzu sannan ya cigaba" abisa rashin sani na cutar da 'Yar Uwata ta jini kuma 'kanwata nayi nadama nadama mara amfani Ammina ki yafe min, sannan ya d'auko zannin goyon da Nanne ta bashi kafin ta rasu ya mi'ka musu kowa a falon kuka yake gaba d'aya in kana gurin tausayin su sai ga kamaka Ammice ta ce "k'warai kuwa Zainab 'yata ce wannan shi ne zanin goyan da aka jefar ta dashi Yarinya ta taho gareni inji d'uminki!" Da gudu Zainab ta taho ta rungume Ammi tana wani irin kuka mai cin rai Ammin ma rike ta tayi tana kuka kowa tausayin 'Ya da Uwar ya kamashi rabon da taji farin ciki irin na yau tunkan Nanne ta mutu ji tayi wani sanyi na ratsata jinta kwance a jikin Mahaifiyarta abin da tarasa shekara da shekaru, da 'kyar aka samu aka lalla'ba su sukayi shiru. Abbu ne ya cigaba da cewa "k'warai Allah AL hakimu ne ya Yarin yar da mukai shekaru muna nema ashe tana tare damu k'warai kuwa tana tare damu tunda tana tare da jinin mu Allah mun gode maka" Abbu ya cigaba shima da fad'in "babu abinda zamu cewa Allah mad'aukakin sarki saidai muce Allah mun gode maka da ni'imar daka saukar mana wannan rana ta zamo ranar farin ciki a garemu ranar da bazamu tab'a mantawa da ita ba Allah ya bayyana mana Yarin yar mu da muka dad'e muna nema Allah mun gode maka" kowa a falon farin ciki yake Zainab tashi tayi ta dinga rungume kowa yau wani farin ciki take ciki, ina ma Nanne na tana nan ta fad'a a ranta, ashe Hamma dan Uwana ne shi yasa naji ina mai soyyayar yaya da 'kanwa" saida ta rungume kowa amma sai ta tsaya tana kallon Hamma yau jitayi ta kasa rungumarsa murmushi ya sakar mata ya bud'e hannuwan sa alamun tazo aikuwa da gudu taje ta rungumeshi tana dariya bayan komai ya lafa ne, Abbie ya ce "to yanzu ya matsayin aurenku yake shin kanason matarka ne yanzu tunda da naji kace kamata al'kawari kana ganin iyayenta zaka sauwa'ke mata in kana sonta shi ke nan sai abar maka matar ka"da sauri Abbu ya ce"dakata Abbie baza'a tauyemin Yarin ya ba kaji son kai wato in d'anka yana so shi ke nan to ba'a isa ba, 'Yata shin kina son zama da mijinki?"cikin zallar Yarinta tace"ni dai Abbu bana son shi ina da Wanda nake so shima ya sani" Abbie ne yace "kaji maganar banza da auren naki like cewa akwai Wanda kike so?" hawaye ne ya wanke mata fuska ta ce"dan Allah Abbie kuyi ha'kuri bawai na fad'a ne don na 'bata muku bane kayi hakuri "Abbu ne duk da baiji dad'in abin ba amma ya dake ya ce"dakata Husain mene abin d'aga murya Yarinyar nan ita zata za'bi mijin da zata zauna dashi kuma ai shi yayi mata Al'kawari da bai mata ba ya sota ya ri'ki matarsa ai da hakan bazai faru ba dan haka son inaso ka sauwa'ke mata yanzu basai anjima ba" gaba d'aya Hamma baisan a wane yanayi yake ciki ba anya kuwa zan iya zuciyar shi ta ayyana mai haka,d'aya 'bangaren na zuciyar shi yace "to kai sonta kake yi" nooo ya fada bawani dogon tunani yayi mata saki d'aya Tur'kashi Wannan kenan...........✍️✍️ #ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Yeeeeeeeeee💃💃💃💃💃💃💃tafaru ta kare 😥😥😥😥😥😥 Kutayani kukan farin ciki wayyooooo takwara wayyooooo dadi🫂🫂🫂🫂🫂🫂 gaskiya Dole muyi patyn ganin iyayen takwara yau ranar farin ciki ce kowa Dole ya wataya agidan nan💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Allah sarki nanne naso kina nan kiga yadda yarki ubangiji ya dauka kata ya nuna Mata iyayenta na insuli abinda kk Dade kina fata saigashi bayan Babu ranki yarki tahadu da iyayen ta gashi alameen dakika bawa aamanarta Dan uwantane na jini saidai daga farko bai rike ananar taba 😥😥😥😥😥😥 Waw waw waw dax very good my besty gaskiya kin birgeni yanzu nasan cewa lallai xee ce gara kinuna wa hamma kinsan kinsan yancinki na yamace dama wannna ranar nake jira wayyiiihuuuuuuuuuu💃💃💃💃💃😹💃😹💃😹💃😹💃😹💃😹💃😹 Lallai hamma xakai nadama saki ko😡😡😡no worry muje xuwa Rafi wataran tulun xai fashe xamu saita maka xamane💃💃💃💃 Anaso ana kaiwa market😏😏😏 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Wallahi kuwa anaso ana kaiwa kasuwa nima ai zee ta burgeni😅 ba kadan ba Ku futo Mu wataya💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Yau ranar Mu ce ina kuke takwarorin zee 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Wayyo zainab gsky natayaki farin cikin ganin iyayyenki💃💃💃💃💃💃💃 amma banso kika rabu da hammanki ba 😞😞😞😞😞😞 Masha Allah muna godiya Allah yakara basira da xaqin hannu tare da lapiar ido 👁️ gaskiya muna jin dadi labarin nan sosae much ❤️ Allah yakara lapia Mae amfani 🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY&WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. FREE BOOK📖📚. 🅿️..............2️⃣6️⃣ _________________Kowa a gidan jikin yayi sanyi kuma da sakin, bawanda ya lura Hamma ya zame jikinsa daga gurin Sam tunda yayi sakin ya rasa mai yake mai dad'i duk jinsa yake wani iri shiyasa ya zame ya bar wajan, ita kanta Zainab bata ta'ba tunanin Hamma zai sake ta ba ta fad'ane kawai hakan yana nuna kenan Hamma bai ta'ba sonta ba duk gaba d'aya taji ranta ya 'baci duk son da takewa Hamman taji yana fita a ranta wani tsanar sa taji a ranta tayi Al'kawarin sai ta rama wulakancin dayayi mata. Muje zuwa Tun daga ranar da abin ya faru yabar garin Adamawa ya koma Kano dan ji yayi garin yayi masa zafi,sai dai kuma har yanzu ya'ki yardar ma Kansa cewa son Zainab ya keyi. Abbu ne ya had'a walimar dawowarta 'yan uwansu daga ko'ina sunzo aka gabatar wa da kowa ita farin ciki kamar ya kashe ta ganin yanda take da family yanzu jinta take bata da wata damuwa wannan kenan Yanzu kusan wata d'aya rabota da Kano tana cikin 'Yan uwanta kowa ji yake da ita sosai Ammi da Abbie ji suke kamar su mai data ciki motsi kad'an kaji sun ce "Ummina" yanzu ta zama wata Babbar Yarinya ta kira Ancul Aboki ta sanar masa da ganin Iyayenta da kuma mutuwar auren ta,dan haka soyayya suke yi sosai Basma ce ta shigo d'akinta ta zauna a gefan gadon ta tace "Anty bacci kike yine?" Juyowa tayi ta kalleta tace "a-a wallahi sister Waya nagama yi da Ancul" kawar da fuska Basma tayi tace "OK" dan ita har ga Allah tafi ma Yayarta sha'awar ta koma gidan Hamma Al'ameen dan tafi dacewa da shi,shira suka d'an ta'ba sannan ta tashi ta tafi. A 'bangaren Captain kuwa tunda ya dawo ya rasa me yake mai dad'i gaba d'aya gidan baya mishi dad'i wani kewar Zainab ne ya addabeshi ya saba da'ita sosai komai ita ta keyi mishi amma yanzu sai dai masu aiki wani ba'kon lamari yaji yana ziyar tarshi akanta tun yana dannewa har abin yafara fin 'karfinshi ya rame sosai, gidan su Kamal yaje, Kamal yace "kai Abokina kwana biyu ina ka shigane ka kyaleni" murmushi yayi yace"kai dai bari Abokina wallahi abinne sai a hankali,kasan naga Iyayen Yarinyar nan kuwa?" Kamal dayake kwance ya tashi yace "me kake shirin fad'a min ne kana nufin kaga iyayen matarka?" Kallon shi yayi yace " hakane Abokina naga iyayen Zainab "nan ya kwashe abinda ya faru tun daga farko har k'arshe ya sanar dashi. Kasa maga Kamal yayi sannan yace " kana nufin yanzu dai kasake ta bayan sanin cewa ita 'K'anwar kace? Captain kai wane irin mutum ne to nidai wallahi babu ruwa na ni ban ta'ba tunanin furta inkaga Iyayenta zaka saketa da gaske ne ba,kalli yanda ka koma kana son Yarinya amma ba'kin halinka ya'ki bari ka yarda kana sonta"fad'a yake yi tu'kuru Captain zuba masa ido yayi sai daya gaji sannan ya koma nasiha, numfashi Captain ya sauke sannan yace "Abokina bazaka gane halin dana ke ciki ba wallahi inna ce a yanzu bana bu'katar rayuwa da Zainab nayi karya ina matukar bu'katar da ban ta'ba sanin ina sonta ba sai yanzu a da na d'auka tausayinta nake amma yanzu na fahimci tazama wani 'bangaren a rayuwata" ya 'karashe idonsa yayi jajir,Kamal yace "to ai kariga ka'bata komai yanzu dai kai zaka san yanda zakai ka shawo kan matar ka ka mai data d'akinta,dama abinda nake fad'a maka kenan wataran zakayi dana sani amma ka'ki yarda" sun dad'e suna tattaunawa akan batun sannan ya tafi gida wayarta ya kira,tana kwance taga shigowar kiran tayi mamaki sosai to mai zai mata daya kirata ita fa Allah yagani ko muryarsa bata son ji d'agawa tayi tare da fad'in "hello dawa nake magana?" Shiru yayi "wai tana nufin batada number ta" a ransa ya ayyana hakan,data gaji da magana sai ta katse kiran ta ajiye wayar ta tashi tashiga kichin domin had'awa Ancul Aboki kayan motsa baki domin yau zai zo,data gama sai ta shirya tayi kyau sosai a falon ba'kin gidan ta sauke shi suna zaune suna shira yake sanar mata cewa"wani satin zai turo Iyayenshi ta sanar ma da su Abbu" tace "to Hubbina" kamar yanda ya fad'a haka kuwa akayi ya turo Iyayenshi an tsaida ranar biki wata biyar masu zuwa, sanda Hamma yaji labari ji yayi kamar zaiyi hauka saida ya kwanta a asibitin likata ya sanar masa cewa ya rage damuwa domin kuwa jininsa ya hau sosai bawanda yasan halin dayake ciki daga shi sai Kamal. A d'aya 'bangaren kuwa Amarya sai kewaya dangi take na nesa dana kusa yanzu biki ya rage wata biyu ta ko'ina shirye-shirye akeyi. A 'bangaren Hamma ciwo yaci 'karfin sa har zuciyarsa ta fara ta'buwa Kamal yayi-yayi dashi ya yarda a sanar da iyayenshi ya'ki yarda, yau yana zaune yafara tari saiga jini kuka yasa yana fad'in "Allah ka yafemin nasan son Yarinyar nan shine ajalina amma bayanda zanyi tunda bata sona Allah ka ciremin sonta ya Allah!" Wannan kenan...............✍️✍️ #ZAINAB KABIR JA'EN. {GARKUWAR ROYAL STAR🌟}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Allah sarki hamma Wlh yabani tausayi. Zee kuma tabani hashi wlh ta manta dukkan alkhairinda yayi mata a rayuwanta shine sanadin zamanta komai na rahuwa amma ta saka masa da wannan 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Kai 😢😢🥺🥺🥺😩😩😭😭gsky hamma naban tauyayi matuka zainab zatayi nadama sosai na Abundatayi Amma shima da laifinsa Amma duk da haka zee bata kyautaba kurciya kedamuntashiyasa 🥺😩. But everything will be sold out we move wani salo ne sister zainab Allah yakara basira da ilimi mai Amfani muna godiya sosai ❤️🙏🏻🙏🏻 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Hmmmm Allah sarki hamma Allah yabaka lapia gsky zainab bata kyauta ba 😥😥😥😥😥 Xamu gani yau ko xamusha biki ancle ne ango ko hamma 😄😄😄😄😄😄 Muna godiya Allah yakara lapia mae amfani Allah yakara basira da xaqin hannu ya kuma kara lapiar ido 🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/?ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. 🅿️.................2️⃣7️⃣. __________________Yana kwance Kamal ya shigo domin a jikinsa yaji cewa akwai abinda yake damun Captain,a lokacin daya shigo Captain baya gane wake kanshi da sauri ya d'auke shi bai zame ko'ina da shi ba sai hospital,nan likitoci suka rufu a kansa domin ceto ransa,gaba d'aya Kamal yarasa inda zai sa ransa yaji dad'i shikam ya zaiyi Abokinshi taurin kaine dashi in yace kaza to bazai canja ba ya san matu'kar ya gawa iyayenshi sai sun sami matsala "ya zanyi" ya fad'a a ransa. Likitocin sun kai awa d'aya sannan suka fitowa Kamal ne ya 'karasa wajan likitan cikin tashin hankali yake cewa "doctor ya jikin nasa?" Likitan yaja numfashi sannan yace "munyi iya 'ko'karin mu mun ceto rayuwar shi amma in bai dena sa damuwa a ransa ba gab ake da rasa ransa a dena barinshi shi kad'ai saboda babu bu'katar ya dinga tinani" Kamal ne yace "insha Allah likita zamuyi iya bakin 'ko'kari muga mun kiyaye"likitan yace " yasamu barci yanzu zuwa anjima zai farka saika Shiga ka ganshi" Kamal yace "to likita na gode sosai". A daya 'bangaren Amarya sai shirye-shirye suke yi ita da su Basma ta sanar dasu Fatima da Hamida suma sun zo gidan su na Adamawan,kwana biyu jin ta take ba tajin dad'i kwata-kwata sai taji ranta yana 'baci ga yawan fad'uwa da gabanta keyi tana ta dai yin addu'a,Basma ce ta shigo tace "Anty ga Yaya Aboki yazo"kallon ta tayi tace "da gaske kike koda wasa?" Basma ce tace "wallahi Anty da gaske yana falon ba'ki" tace "bai fad'amin zai zo ba wallahi gani nan ya kyauta" a gurguje ta shirya duk da dama a shirye take amma saida aka 'kara gyarawa,da sallama ta shiga d'akin ba'kin a zaune ta tarda shi yana danna Waya yana ganin ta ya saki murmushi yace "my shine kika barni inata jiranki ko" cikin shagwa'ba tace"to Hubby ba kaine baka fad'a min zaka zo ba" yace "sorry matar wallahi jinayi kawai ina son ganin matata shiyasa na taho" tace "humm hubby kamar kasan nima nayi kewarka" yace "da gaske? "Tace eh hubby" yace "yauwa tawan mene tsare-tsaren da zakuyi a bikin kinga fa yanzu saura sati uku,ni dai tsare-tsarena shine Abokina Musaddik ya had'a mana dinner,nima kuma akwai dinner da zanyi sannan ga party za'a yi Indian day ma amma shi sai an d'aura aure da daddare sannan Momma ma ta had'a nata partyn" zaro ido tayi tace"wai hubby kana nufin duk wanna partyn da za'ayi nima in yi wani ai sun isa mu dai anan walima zamu yi sai kuma kamu shikenan Wanda ka lissafa ai sun isa" murmushi yayi yace "shikenan matar jibi za'a kawo lefe fa" tace "to hubby" sun sha soyyayar su sannan ya tafi,ita kuma ta cigaba da shirye-shiryen ta mai gyaran jiki Mommy ta d'auko Basma tace "itama sai an mata" dan haka tare ake yi musu ta janza sosai dama kuma ga shi tana amfani da malato soup din Anty lady da body scrub gaba d'aya ta canja sosai kamar ba ita ba, an kawo lefe na gani na fad'a a kwatuna set uku ne sannan ga fridge lefen dai sai dai hassada amma sunyi kyau. A 'bangaren Hamma kuma tunda aka Sallamo shi daga asibiti yana tare da Kamal Sam Kamal baya barin shi da damuwa ya dan rage damuwa yanzu jikin nashi Alhamdulillah har sun koma aiki shida Kamal duk labarin bikin ana fad'a masa da bikin ya rage. Sati d'aya ya tafi shida Kamal,kwanan sa biyu da zuwa amma ko sau d'aya bai hadu da ita ba ranar dinner cewa yayi "shi fa baza shiba" Kamal ba yanda bai yi dashi ba ya'ki zuwa,Mommy ce takira shi tace "Son na fahimci kana cikin damuwa ka dubi yanda ka rame" murmushi yayi yace "Mom na d'an yi rashin lafiya ne shiyasa kikaga na rame amma bayan haka ba abinda ke damuna" tasan 'karya yayi mata amma sai ta 'kyaleshi saboda ba taso ta matsa mishi, ranar partyn da Ammi ta had'a ne yaje sanda yaga Zainab da Ancul Aboki ji yayi wani abu ya tokare masa 'kirji numfashin sa yana neman d'auke wa da 'kyar ya lalla'ba ya bar gurin Kamal sai gani yayi bayanan da haka gida yadawo ya tar dashi a kwance ya dafe saitin zuciyar shi Kamal yace "wato Captain ka za'bi ka kashe kanka to kasani wallahi ka mutu a wannan halin daidai kake da wanda ya kashe kansa tunda nayi-nayi ka bari a sanar da Iyayenku a halin da kake ciki ka'ki bazan tsaya in zuba ido ina kallo ka mutu ba"kallon shi yayi yace " please ka mi'ko min maganina" tashi yayi ya d'auko mai ya d'ago shi ya bashi sannan bacci ya d'auke shi, zuba masa ido Kamal yayi tausayin Abokin nashi duk ya cika shi yarasa ta yanda zai 'bullowa lamarin. Ana gobe d'aurin aure 'Yan uwan na nesa dana kusa duk sun zo ana ta shagali da daddare kowa shirin tafiya dinner yake yi shi kuwa Hamma Al'ameen yana kwance ciwon shi yana neman tashi domin ya sadda'kar daya rasa Zainab d'insa da suka had'u da shi daga tace"Hamma ina wuni"ko jiran ya masa ma ba tayi ba tayi gaba,Kamal ne ya shigo yace "Abokina ka tashi mu fita tunda bazamu partyn yau ba" shiru yaji ya kuma magana yaji shiru 'karasa yayi yace "wai kana nufin har kayi bacci?" Amma me yana ta"bashi yaga yayi lagab alamun ba numfashi a jikin shi wani ihu yasa Wanda ya karad'e gidan da gudu kowa ya 'karaso part d'in Kamal ne yake jijjigashi yana fad'in "Abokina in da wasa kake ka tashi bazaka mutu ta sanadiyyar soyayya ba katashi! " da gudu Ammi da Mommy suka rufu a kanshi suna kuka Zainab ce 'karshen shigowa tana shigowa taji Ammi tana cewa "Yarona ya za'a yi ka mutu ka barmu dan Allah ka tashi" ai tana jin haka ta yanke jiki ta fad'i a gurin sumammiya. Tur'kashi ya zata kaga Kuyi ha'kuri da wannan Wannan kenan........✍️✍️ #ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR🌟} 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY&WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/?ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. 🅿️...................2️⃣8️⃣. ____________________K'arar fad'uwar Mutum da akaji shiya tabbatar da zuwanta, gaba d'aya aka d'auke su akayi hospital dasu,kowa a gidan kuka yake yi dan ganinsu shi ke nan su Hamma sun mutu, likitoci sunyi iya 'kokarinsu domin su dawo da numfashin Hamma amma abin ya gagara sun dai tabbatar da yana raye, ita kuma awarta d'aya ta farfad'o kuka takeyi sosai tana fad'in "dan Allah Hamma karka mutu ka barni wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba!" da 'kyar aka lallasheta,Ancul Aboki ma yazo gurin tun sanda aka sanar dashi abinda ke faruwa, Kamal ne ya sanar dasu irin halin da Captain yake ciki tun farkon rashin lafiyarshi har yanzu kowa tausayin shi ya cika zuciyar shi Mommy ce ta rarrafa gaban Ancul Aboki tari'ke 'karfarshi tana fad'in "dan Allah ka taimaki Yarona ka ceto rayuwarshi na rok'eka, shi kad'ai muka mallaka a duniya dan Allah" ta k'arasa tare da fashewa da wani ma tsanancin kuka mai ban tausayi, numfashi Uncle Aboki ya sauk'e tare da fad'in "Mommy kiyi ha'kuri ki dena kuka indai nine na barma Captain matarshi,sa bo da na fahimci cewa suna 'kaunar junansu" ya share hawayen daya gangaro masa a idonsa dan shi Allah ya gani yana son Zainab, kowa hamdala yayi a gurin Abbu ne yayi magana tare da fad'in "Yarona ba' abinda zamu ce maka sai Allah yasaka da alkhairi kuma ina ro'kon alfarma ka akan zanyi hukunci a kanka kamar d'an dana haifa zan had'a auren ka da Basma 'kanwar Zainab,Ancul Aboki ya rasa me zaice ma wannan mutane masu karamci kawai saiya zube a gaban Abbu ya ce "Abbu nagode da karamcinku a gareni Allah yasa haka shi ne yafi. "alkhairi"ameen kowa ya amsa a gurin. Gurin Likita Abbu da Abbie suka tafi domin tattauna yanda za'ai nan likitan ya ce "Alhaji ni a ganina a fitar dashi 'kasar America ko a can Allah zaisa a dace" Abbie ne ya ce "yanda kace Likita sai a shirya fita dashi d'in" ya ce "toh Alhaji insha Allah." Rana bata 'karya sai dai Uwar d'iya taji kunya, a ranar 9/2/1999 aka d'aura auren Captain Al'ameen Hassan da Amaryar Zainab Hussain akan sadaki dubu d'ari wanda Abbie ne ya wakilice shi, sanan aka d'aura auren Abubakar Abdullahi(Ancul Aboki) da zan kad'e d'iyar Amaryar sa Basma Hussain wadda ita sai a yau tasan da batun auren taci kuka amma ba yanda zatayi dole ta ha'kura tayima iyayenta biyyaya shagalin biki kuma an bari sai Hamma ya samu Lafiya. Washe garin d'aurin auren jirginsu ya d'aga zuwa America ita da Hamma kai tsaye a babban asibitin garin suka sauka ita take kula dashi da duk abinda yake bu'kata kafin ayimai aiki in andace shi ke nan, kullum suna waya da K'anwarta Basma tana 'kara kwantar mata da hankali suna waya dasu Ammi ma da su Abbie kowa fatan samun nasara yake musu. Yau ce ranar da takama za'a yima Hamma aiki duk familyn nan sun hallara a America kowa fatan samu nasara yake yi ranar da azumi Zainab ta tashi sai addu'a ake tayi masa sunsa a Nigeria anata yi mai sauka da addu'aoi a masallatai sai dai fatan samun nasara. Wannan kenan..........✍️✍️ Kuyi ha'kuri da wannan. #ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/?ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. *Al'kalaminmu 'yancin mu.* 🅿️..................2️⃣9️⃣. __________________To cikin ikon Allah an yi mai aiki cikin nasara Likitoci sun tabbatar da cewa yana tashi zai tashi cikin 'koshin lafiya,amma zai samu sati d'aya kafin ya farfad'o, nan aka ci gaba da bashi kulawa ta musamman tana zaune a gefansa hawaye take ta sharewa a ranta tana tunanin lallai duniya ba'a bakin komai take ba, kalli Hamma a kwance kamar matacce "Allah ina ro'konka kabawa Hamma lafiya" hannunsa ne taga yana motsi da sauri ta 'karasa ganshi lokacin su Abbie duk basa nan suna hotel d'in da suka sauk'a a hankali yake bud'e ido duk da sun masa nauyi, haske ne yayi masa yawa dan haka ya kara maida su ya rufe da gudu ta fita ta kira Likita a tare suka shigo a hankali ya kuma bud'e idon nasa a kanta ya sauk'e su tarame tayi duhu kamar ba'ita nan abinda ya faru yafara dawo mai aka ana i gobe d'aurin auren ta ya sameta yake cemata "ta temake shi tace bata son auren nan wallahi in ba ita bazai iya rayuwa ba" nan ta bud'i Baki tace ni wallahi Hamma in fad'a maka kwata-kwata babu sonka a raina soyyayar dana kemaka ta Yaya da K'anwa ne dan haka kaga babu batun soyyaya"yace "shikenan na gode" 'kwa'kwalwarsa ce take zai yana masa hakan dan haka ya juyar da kansa daga barin kallon ta dan zuwa yanzu yasan tazama mallakin wani shin mema take yi a gurinsa wani haushinta yaji yana ji ko ganinta baya son yi,da sauri da 'karaso gurin nasa tace "Hamma ka tashi alhamdulillah Allah na gode maka" kallon ta yayi sannan ya saukar da idonsa 'kasa a hankali cikin sanyin murya tace "dan Allah Hamma kamin magana kaji" cikin muryarsa dabata fita yace "me kikeyi anan gurin ina mijinki?" "Bawani bane mijinta face kai" Ammi ce take fad'a lokacin da suke shigowa, ha'ki'ka badan Ammi ce yaji tana fad'a ba bazai ta'ba yarda ba hakan yana nufin Zainab matarshi shi aka aurawa "garin yaya hakan ya faru?" Yun'kurin tashi yake yi Kamal ya 'karasa ya d'agoshi yana fad'in "to mijin Zainab 'karshe dai kayi likimo an aura maka ita sai kawarke ai" dariya kowa yasa a d'akin nan aka fara yimasa ya jiki yana amsawa "da sau'ki" to satin sa d'aya ya warware sosai saidai abinda ba'a rasa ba,a 'bangaren Zainab kuwa ta fahimci Hamma share ta kawai yake yi in yana shira yana dariya daya ganta sai ya had'e rai abin yana damunta sosai amma sai ta bayar da ko fushi yake da ita. Yauce ranar da'aka sallamesu dan haka gaba d'aya jirginsu ya d'aga zuwa Nigeria kwannan su biyu da dawowa kowa ya warware gajiya Abbu ya yata rasu harda Ancul Aboki da Kamal dan yanzu Kamal tazama d'aya daga cikin wannan familyn suna ganin bazasu iya 'boye masa duk wani abu daya shafesu ba, bayan an bud'e taro da addu'a sannan Abbu yafara jawabai kamar haka "to abinda ya tara mu anan shine magana ce akan batun auren ku da yanda abubuwa suka faru da farko dai wannan Yaro Abubakar babu abinda zamu cemaka sai Allah yasaka maka da alkhairi ya kuma had'a kanku kaida matar ka domin kayi abinda ba kowa ne zai iya ba kayi ceton rai Allah yasaka maka da alkhairi" "Ameen" kowa ya amsa a gurin sannan Abbu ya cigaba "to bisa yanda abubuwa suka faru mun tsaida satin sama kowa zai tare da matar sa ke kuma Basma yanda muka sanki mai biyyaya karkiga had'a auren ki a kayi kice zaki wulakanta mijinki kimasa biyyaya" tace "insha Allah Abbu zan kasance mai biyyaya a gareku" yace "to Allah yai muku albarka ya baku zuri'a d'ayyiba" aka amsa da amin bayan an watse kowa ya kama gabansa Hamma ya samu Ancul Aboki yayi masa godiya bisa karamcinsa a gareshi sannan yayi mishi fatan alkhairi a auren shi sannan ya tafi. To tundaga ranar Zainab bata 'kara ganin Hamma ba saida ta tambayi Basma take shaida mata ai yakoma Kano sai ana saura kwana biyu tariyar su zai dawo hawaye ta share sannan tace "sis bakya ganin yanzu Hamma ya dena sona" dafata Basma tayi sannan tace "haba Anty ai ke zaki bada labarin son da Hamma yake miki kawai dai inaga ko fushi yake ta abin da kikayimasa a baya amma wallahi Hamma bazai iya dena sonki ba" sai a lokacin taji zuciyar ta samu sau'ki amma tasan yanda zata 'bullo masa. Wannan kenan.......✍️✍️ Kuyi ha'kuri da wannan. #ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR🌟}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Rawa d girgiza💃💃💃 zanyi gabanki in daddara😁😁 kai naji dadin feginan wlh sosai hamma ashe dai kaine mijinta har abada sai dai muce Allah y bada xaman lpy mai daurewa. Allah y kara basira d karfin ido👀 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/?ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. 🅿️............3️⃣0️⃣. ___________________To yau tun safe aka hada-hada a gidan sa bo da yau ne ranar da za'ayi walima, Amare su tare a gidajensu, su Hamida da Fatima duk sun zo, haka itama Basma ta gayyato 'kawayenta domin yanzu sun sasanta kansu ita da mijinta, kowa a gidan murna yake Basma ce ta kira Zainab take cewa "Anty Zainab Hamma fa yazo tun jiya kun had'u?" Murmushi tayi wanda yafi kama da ya'ke ta ce "a-a nasan dai yazo amma bamu had'u ba, ki rabu dashi fushi yake yi kuma zai sakko ne" murmushi Basma tayi sannan ta ce "haka ne kam Anty, Ancul Aboki ya ce " yana gaisheki" mantawa nai ban fad'a miki ba" duka ta kai mata ta ce "wato Ancul Aboki ko ba Mijina ko Hubbyna" dariya tayi ta ce "kai Antyna" murmushi tayi ta ce "ai gaskiya ce Yarin ya ta girma" duk dariya suka sa a dai-dai lokacin Hamma yazo wucewa domin zashi ya gaida Ammi had'a baki sukai suna fad'in " Hamma ina kwana" murmushi yayi ya ce "lafiya kalau Basma kintashi lafiya?" ta ce "lafiya kalau Hamma ance min jiya kazo zamu mu gaida ka kuma a kace ka fita kaida Yaya Kamal" ya ce "haka ne K'anwata mun je duba wani companyn su Abbie ne anan" ta ce "to Hamma Allah ya temaka a gaidamin da Yaya Kamal kafin mu had'u" ya ce "to zaiji" sannan ya wuce idon Zainab ya cika da k'walla wato yanaji tana gaishe shi amma ya shareta shi ke nan, Basma ce ta dafata ta ce "kiyi ha'kuri Antyna nasan be kyauta ba amma ki rabu dashi kisan yanda zakiyi ki shawo kan mijinki kar kice kema zaki d'au zafi kinji" ta ce "to K'anwata na gode" murmushi tayi ta ce " ba komai Anty bari in k'ara inje in d'auko mana kayan mu a part d'in Mommy mu mai dashi part d'in mu tun kan mutane su cika" ta ce "to K'anwata" Basma ta zame mata wani 'bangaren na rayuwar ta ta wuce iya K'anwa agareta ta zama K'awa kuma 'Yar Uwa, part d'in su ta wuce tana har had'a musu kayan su. To da misalin karfe biyar na yamma harabar gida na gani a cike da mutane kowa ka ganshi farin ciki yake yi waige-waige nakeyi inga ta inda zan hango Angwaye da Amare amma ban gansu ba har na k'osa da zanyi tafiya ta kamar ance in kalli gefena nan na hangi Amaren suna tahowa ana ta watsa musu furanni haba ai saida na kusa sumewa sa bo da yanda naga sun had'u shigar indiyawa sukai Amaren cikin ja da adon milk sari Angwayen kuma cikin jar Riga da milk colour d'in wado zo kuga kyau idan akace muku ba indiyawa ne agurin ba bazaku ta'ba yarda ba, wajan zaman da aka tanadarwa Amaren da Angwayen nan suka nufa suka zauna har lokacin ba'a dena zuba musu furen ba, bayan sun zauna Malaman da aka gayyato domin suyi lecture suka fara can na hango tawagar Zainab fans da Hamma suma sun iso k'ar kashin jagorancu Ummu Rae'es da takwarorin Zee nan na basu gurin zama na gabatar musu da abinci suka zauna suka fara kwasa guri yayi guri domin 'Yan Uwa na kusa dana nesa duk sunzo Ancul Aboki ma 'Yan uwan shi duk sunzo wa'azi ake me ratsa jiki kowa a gurin jikinsa yayi sanyi su Basma kam harda kuka. Bayan an gama aka gabatar da abubuwan ta bawa kowa yai yayi hani an sannan a aka watse Abbu ne yakirasu tayi musu nasiha sannan kowa Mijinta ya d'auke ta a mota ya tafi da ita sai dai muce Allah ya basu zaman Lafiya. Wannan kenan........✍️✍️ Kuyi ha'kuri da wannan. #ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR🌟}. 11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹 STORY & WRITING BY:ZAINAB KABIR JA'EN 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟. http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/ref_c Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi. Al'kalaminmu 'yancin mu. 🅿️............3️⃣1️⃣. _________________Tunda suka tafi ba wanda ya kula kowa, kuka take ta rerawa dan a gaskiya ta sha'ku da su Ammi a haka suka isa gidan, ga ba d'aya gidan ya canza mata anyi masa gyara sosai gidan suka shiga kowa 'bangarensa ya nufa mamaki ne ya cikata ganin komai na d'akin sabo ne akwatuna tagani saiti-saiti, wajan set haud'u sunyi kyau sosai a ranta ta ce "kenan Hamma yayi min lefe?" Murmushi tayi sannan ta shiga wanka ta shirya cikin kayan bacci masu kyau tabi lafiyar gado tai kwanciyar ta. Washe gari ta tashi ta gabatar da ayyu kanta sannan tayi wanka tai simple make up d'in ta falo ta fito a zaune ta tar dashi yana danna computer 'karasawa tayi ta ce "ina kwana Hamma" kallon ta yayi tayi masa kyau amma cikin had'e rai ya ce "lafiya" ya cigaba da abinda yake abin ya k'ona mata rai amma sai ta dake ta ce "Hamma ga break fast d'inka fa tun d'azu na gama" k'ara b'ata rai yayi yace "ni fa na k'oshi tun d'azu nayi break fast d'ina" kallon sa tayi na wani lokaci sannan ta ce "shikenan" ranta yayi bala'in 'baci ita bata san me tayi masa ba yake mata wannan wulak'ancin amma ba komai zata jure bar ya sakko, tashi tayi ta koma part d'inta break fast d'in da ba tayi ba kenan. To yau kusan watansu d'aya a haka bayacin abincinta kuma baya kulata gaisuwa ce kawai take had'a su, Basma ta kira ta fad'a mata halin da take ciki tana kuka tace "Basma na gaji da wula'kancin da Hamma yake min wallahi Basma yanzu baya sona kwata-kwata, nagaji-nagaji Basma!" ta k'arasa cikin kuka da k'yar Basma ta rarrasheta ta dena kuka ta ce "ni wallahi Anty laifinki nake gani a ce har yanzu kin kasa shawo kan Mijinki ni wallahi yanzu nida Mijina zaman mu muke lafiya in akace miki ba auren soyyaya mukai ba bazaki yarda ba duk abinda nake so shi yake min yasiyamin fa sabuwar mota inna fara fita zanzo gidan lki sai na nuna miki dan Allah Anty kiyi iya bakin k'ok'arinki nasan ki" ta 'karashe da zolaya, murmushi Zainab tayi ta ce "kai wannan Yarinya bakida kunya wato Mijina ko ke mai miji" dariya sukayi gaba d'aya sannan sukai sallama ha'kik'a tayi d'amarar shawo kan Mijinta ta kowace hanya tashi tayi ta nufi falo a zaune ta hango shi a kan kujera yana waya da alama daga wajan aikin sa yake kiran, bata lura ba kawai taji tayi sufa da 'bawon ayaba nan kuwa ta fad'i a k'asa war was k'arar data k'walla ita ta juyo da hankalinsa kansa bai san ya akayi ba kawai ya gansa a gabanta gaba d'aya narkewa mai tayi sai kuka take yana bata ha'kuri, hijabi ya d'akomata yayi hospital da ita tundaga ranar yake kula da'ita sosai duk ta narke masa ta 'kara tabbatar da son da Hamma yake mata domin yanzu baya barinta tayi kowane irin aiki, harta warke yanzu zamansu suke lafiya duk fushinnan Hamma ya dena ya rungumi matarsa suna zaman zu lafiya cike da so da 'kaunar juna. Bayan shekara ashirin Wata ham shak'iyar mata na gani a zaune daka ka ganta kasan hutu da jin dad'i ya ratsata, wata Yarinya naga tafito wadda bazata wuce shekaru sha bakwai a duniya ba ta nufo matar tana kuka ta ce "Momma kinga YQya Ashman ya k'wacemin waya ko" Ashman dake fitowa ya ce "wallahi Mommah Yarinyar nan tunda aka bata waya yanzu bata karatun arzi'ki shiyasa na 'kwace" sai a lokacin na k'arewa matar kallo bakowa bace face Zainab yanzu ta zama wata Hajiya gata tayi kyau in ka kalleta baza kace ta haifi su Ashman ba kallon shi tayi ta ce "haba Yaya babba kayi ha'kuri ka maida mata wayar ta in naga bata karatu da kaina zan kwace kaji Babana" cewa yayi "to Momma ta" ya mi'ka mata wayar bayan ya tafi Zainab tayi wa d'iyar tata fad'a sosai akan karatu sannan ta ce "taje ta kira mata papi a lambu" ta ce "to Momma" yaran Zainab had'u, Ashman ne babba wanda yaci sunan Abbu sai Aisha wadda taci sunan nanne ana kiranta da Ashna, sai 'yan biyun ta Hasana da Usaina sukuma ana kiransu da Ammi k'arama da Mommy k'arama yaran sun tashi cikin kulawa sosai BQba kande tana zaune a tare dasu Anty Asabe tayi aure yanzu Yaranta biyar hakama Fatima ita ta auri Kamal Abokin Hamma Hamida kuma d'an Uwansu ta aura ko wacce tana da yara biyu, Basma ma Yaranta hud'u tana zaune da mijinta Lafiya yanzu wannan family suna zaune cikin farin ciki da annashuwa sun mance duk wata damuwa Hamma ne ya shigo ya tadda ta a zaune ya zo ya zauna a kusa da ita ya ce "Amarya ta" dariya tayi ta ce "kai Hubby ka ganni tsofai-tsofai dani kace min Amarya har na kusa jikoki" dariya yayi ya ce " 'Yan matana ai bakya tsufa har yanzu ganin ki nake kamar Yarinya" dariya suka sa dukkan su cikin farin ciki da nishad'i Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah A yau na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai suna rayuwar Zainab ina fatan abinda muka fad'a dai-dai Allah ya bamu ikon amfani dashi abinda muka yi kuskure Allah ka gafarta mana ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci. Mu had'u a sabon littafina mai suna ❤‍🩹RASHIN MAHAIFIYA❤‍🩹 Na gode #ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}.