Compiled By Golden Pen Writer's Association. 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene One_ ~*Page 1*~ A kwance take, sanye cikin English wears na riga da skirt ja da rantsin fari a jikin shi, kayan sun amshi yanayin jikin ta kasancewan ta ba mai jiki sosai ba, sannan sun zauna ɗas a jikin ta tare da baiyana k'uruciyan ta. *HUNAYDA* Kenan, ƴar matashiyar da baza ta gaza shekara goma sha bak'wai ba (17years). Farin earpiece ne a kunnen ta, a lokaci ɗaya kuma hankalin ta na kan wayan ta k'irar Tecno Camon 12. Kana kallon ta zaka fahimci hankalin ta gaba ɗaya na kan wayan ne, domin ko k'ifta idon ta bata yi, jifa-jifa takan yi murmushi, a lokaci ɗaya kuma takan lumshe idon ta tare da runtse su na ƴan wasu dak'ik'u sannan ta buɗe tare da sake mai da hankalin ta kan screen ɗin wayan. Daga kitchen Hajiya Hauwa ce mahaifiyar ta, wanda suke kira da *Ammi*, take ta k'ok'arin haɗa musu abincin dare, inda yar autan nata *Hajna* da baza ta wuce shekara goma ba (10years) take taya ta wasu aiyukan. Ganin aiyukan suna neman kwaɓe mata, yasa ta ɗaga murya tare da fara kiran sunan ta. "*Hunayda!* *Hunayda!!* *Hunayda!!!*" Amma babu alaman motsin mutum ballantana tasa ran anji kiran har a amsa mata. Maida kallon ta kan Hajna da take k'ok'arin gyara kayan miya tayi, a sanyaye ta kira sunan ta; "Hajna!". "Na'am Ammi". Ta amsa tare da dakatawa daga abin da take. "Je ki duba min Aunty ki, ko tana banɗaki ne". "Tohm!". Ta amsa tare da tsame hannun ta, ta nufi ɗakin da sallama, ta tura k'ofan ta shiga, inda ta same ta kwance ruf da ciki, ta kafe idon ta akan waya. Ganin bata san da shigowan ta ba yasa ta k'arasawa tare da ɗan girgiza ta, a lokaci ɗaya kuma take sanar da ita sak'on Ammi na kiranta. Cikin jin haushin katse ta da tayi ga karatun littafin da take ta watsa mata harara. "Sai kije ai ina zuwa, kin sake baki kina kallo na, ko baki taɓa gani na bane?!". "Um um". Ta amsa tana ficewa daga ɗakin cikin rashin jin daɗin canjawan ɗabi'un ƴar uwar tata, domin da sam bata ko mata tsawa bare k'yaranta. A sanyaye ta k'arasa madafan inda ta sanar da Ammi wai tana zuwa. Kallon ta take tare da yin nazarin sauyawan ta. "Dama idon ta biyu?". Ta jefo mata tambaya. "Eh". Ta amsa. "Toh me take yi, duk wannan ihun kiran ta da nake?". "Wayan tane dai na gani a hunnun ta, sai earpiece dake kunnen ta". "Shikenan, je ki kwashe kayan gugan da Magaji ya kawo ki jera min a wardrobe, idan tazo ta k'arasa markaɗen". "Toh Ammi". Ta faɗa cike da ladabi tare da shigewa cikin hanzarin domin aiwatar da umarnin mahaifiyar nata. A can ɗaki kuwa Hunayda sai da ta k'washe tsawon mintuna biyar sannan ta ajiye wayan tare da fitowa cikin rashin walwala. "Gani Ammi". Ta faɗa a dai-dai lokacin da ta k'arasa k'ofan kitchen ɗin. Kallo ɗaya ta mata taji ranta bai mata daɗi ba, domin waƴannan sabbin ɗabi'un da take gani tattare da ita sun fara isan ta, wanda tana iya k'ok'arin ta amma ta rasa gane kanta da inda ta dosa. Cikin takaici ta dube ta. "yanzu Hunayda Fisabilillah kina k'wance a ɗaki tun safe baki da wani aiki sai latse-latse a waya! Tunda Abban ku ya sai miki wayan nan kika haɗu da Sahabat kuka ɗinke, ɗabi'un ki sun canja gaba ɗaya! Idan tazo baku da aiki sai ku kulle kanku a ɗaki kuna labaran Social Media, mussaman WhatsApp da Littatafan Hausa, ni ban san irin wannan zamani naku ba Hunayda! Idan karance-karancen littattafai ne ai nayi shi, kuma ban daina ba har sai da na haife ki hidiman raino ya sani watsi da karatun littafi, wanda har abada bazan iya biyan wayannan marubuta ba, domin sun taka rawar gani sosai a cikin rayuwa ta, na koyi darasi masu tarin yawa wanda iyayena basu koyar dani ba, kama daga yanda zan k'yautata ma miji na tare da sauke duk wani hakkin shi daya rataya a wuyana, zamantakewa na da mak'ota, tsakani na da dangin miji na, yanda zan k'yauta ta ma iyayena domin samun kyakkyawan k'arshe, da ma sauran abubuwan da dama na rayuwa!". Daɗa zunɓuro bakin ta tayi, tunda ta fara magana inda gaba ɗaya sauraron ta take amma hankalin ta yana can kan wayan ta da ta bari. "Ki shige ki ɗauki kayan miyan can ki ida gyara su, sannan ki markaɗe su. Idan kin gama ki asa bisa wuta sannan ki fidda kayan salad ki fara yanka su. Bari na watsa ruwa ina zuwa". Bata jira cewar ta ba ta fice daga kitchenɗ'in tare da nufan ɗakin ta. Tana tsaye a kofar kitchen ɗ'iin cikin jin haushi da bakin cikin aikin da mahaifiyarta ta bata umarni. K'aramar tsaki taja. "Ni shikenan a gidan nan bani da ƴancin kaina!? Sai dai inyi ta bauta, Abba ya kawo ƴan aiki amma kin ce a'a, tsakani da Allah Ammi sai kace bakya sona, ba dama kiga na zauna hakanan sai kin k'irk'iri wani aikin da zaki nemo ki lik'a min!". Mita ta cigaba da yi tana aikin cikin jin haushi tare da yin komai cikin rashin nutsuwa, yanda taga dama ba tare da nutsuwa ba. ******* A cikin aji a yayin da malami yake cikin karatun Qur'ani mai girma, inda duk ɗalibai sun maida hankalin su kan sauraron malamin da kallon yanda bakin shi yake motsawa, domin suma su samu daman mai-maita abinda ya faɗa dai-dai ba tare da kuskure ba. A lokacin kuma Sahabat da take zaune a bencin baya hanun ta rik'e da Qur'ani Izu sittin, wayanta ne rik'e a hannun ta. Ta cikin Qur'anin inda baza'a iya hango shi ba, hankalin ta na ga wayan ta da sam ba ta iya jiyo duk wani abinda yake faruwa cikin ajin, duk da kuwa yanda sauran ɗalibai yan uwan ta suke ɗaga murya wajen bitan karatun da malamin nasu yake biya musu da zazzak'an muryar shi cikin suratul Maryam. Gaba ɗaya littafin ya tafi da duk wani imaninta, a lokaci ɗaya kuma tana imagining abinda take karantawa da ita yake faruwa, wajen da ko a yaushe yake ainihin ɗaukan hankalinta tare da tafiya da imanin ta a littafin, sosai take jin daɗin yanda daren nasu na jaruman littafin ya birge ta, tsawon awa uku yana kan amaryan shi sannan ya samu nutsuwa, inda ya dakata ba dan ya gaji ba sai don tausayinta da yaji ganin tayi laushi. A dai-dai lokacin kuma ta runtse idonta, nan take taji wani abu na fita daga k'asan ta. Runtse ido tayi tana jin wani irin daɗi a lokaci ɗaya kuma cikin ta ya fara murɗeta. Kashe wayan tayi tare da k'wantar da kanta saman benci, idonta a runtse, gaba d'aya tsikar jikin ta a tashe yake. A daidai lokacin kuma Mallam Jamil idon shi ya kai kanta. "Wacece a k'wance ana karatu?!". Bata d'ago ba har sai da abokiyar zaman ta a bencin takai hannu ta taɓa ta. A sanyaye ta ɗago da kai tare da zuba idanunta kan Mal. Jamil. "Yaya ana karatu kika kwanta? Ko baki jin daɗi ne?". Sauran ɗaliban ajin kuwa duk sun bar abinda suke tare da zubo mata ido. Idon ta sun kaɗa sunyi ja, cikin daskararriyar muryanta ta amsa. "Eh Mal. Cikina ne ke min ciwo". "Subhannallah!". Ya faɗa cike da tausayawa. "Allah ya baki lafiya. Sai kije Office ki karɓi magani ko?". "Toh". Ta faɗa inda ta sake komar da kanta kan bencin. Bayan sun sake biya mai yaji karatun ya musu sallama ya fita. Dama shine last period, dan haka yana fita ɗalibai suka fara fita suna kama hanyar gida, ita ma haka ta fito cikin rashin walwala ta nufi gida ba tare da ta jira k'annen nata ba. Tun kan ta k'arasa shiga ta jiyo dariyar mahaifiyar nata da shewa ita da Aminiyar ta Hajiya Saudat. "Kai Aminiya ta, ai ina faɗa miki wallahi littafin nan yayi wuta, kinyi mutuk'ar k'ok'ari, gaba ɗaya kar kiga yanda duk group ɗin da kika shiga na WhatsApp littafin ake nema, kai baki taɓa rubuta littafin da ya samu masoya kaman wannan ba tawan!". Jin Abin da suke faɗa yasa ta dakatawa tare da sake sauraron su. "Ai ni kaina abin na bani mamaki, k'awata, kinsan jiya na amsa waya sama da mutum goma duk akan page ɗin jiya suna yabawa tare da jinjina min. Kai ban taɓa tunanin littafin *NI DA SHI* zai samu ɗunbin wannan masoyan ba. Sharhi dana gani har ban iya karatan su ba, ke ban faɗa miki ba, akwai wacce ta ce in tura mata account namba na banda katin waya dana samu". "Kai! Toh ai dole k'awata, ai kin tafi da imanin mu ne gaba ɗaya, ni kaina banda Abban Yusra na kusa ai ban san yanda zan k'are ba". Dariya suka sake bushewa dashi tare da tafawa. A dai-dai lokacin kuma da Sahabat ta kasa ɗaga k'afan ta jin maganganun da yake fitowa daga bakin mahaifiyar nata. Dama itace Marubuciyar *NI DA SHI*? toh me yasa bata amfani da asalin sunan ta a matsayin marubuciyar da duk wanda ya santa zai gane ta dashi? Cikin k'arfin hali ta k'arasa shiga ɗakin da Sallama cikin sanyi jiki. Dakatawa sukyi da dariyar da suke tare da maida kallon su kanta a tare. "A'a, yan makaranta!". Hajiya Saudat ta faɗa tana murmushi. "Ina wuni?". Ta faɗa cikin rashin walwala. "Lafiya". Ta amsa tana k'ara faɗaɗa fara'arta. "Ina wuni Ummi?". "Lafiya lau". Ta amsa da fara'a. "Ina kika baro su Na'eef da Suraiyyan?". "Suna baya suna zuwa". Ta faɗa tare da shigewa cikin ɗaki. Da kallo suka bita inda suka sake mai da hankalin su kan firar su, sai dai sun rage murya saboda kar ta jiyo su. Jakan makarantarta ta ajiy ta faɗa kan gado tare da kai hannu ta k'asan maran ta. Lumshe idon ta tayi tare da cigaba da motsa hanun ta. Ba tafi minti biyar ba ta samu nasarar gamsar da kanta. Samun nutsuwar da tayi yasa ta dawowa cikin haiyacin ta, nan take taji takaicin kanta tare da jin wani bak'in cikin abinda ta aikata. Vibration ɗin wayanta ne yasa ta saurin tashi ta jawo jakan, inda ta ciro shi da sauri tare da nufan can k'uryan ɗaki ta amsa kiran. Filo ta ɗauka tare da cusa kanta ciki a lokacin ɗaya kuma ta rage muryan ta saboda kar su jiyo ta. ******** Cikin kulawa ya dube ta tare da k'wantar da murya. "Tun jiya da dare nake ta binki, Salma ki faɗa min abin da yake damun ki amma kin k'i, sai amsa min kike da ba komai, kar ki manta fa duk duniya baki da wanda ya kaini, a matsayina na mijinki kuma uban ƴaƴan ki, bana jin ak'wai abin da yayi saura daza mu ɓoye a tsakanin mu". Dad'a had'a girar sama da k'asa tayi tare da ture bakin ta tana kumburi. "Ni nace maka ba komai. Ba komai, idan ak'wai ai zan faɗa maka, kaina ne kawai ke min ciwo, amma tun jiya ka dame ni da magana ɗaya, please ka barni haka inji da ɗaya mana!". Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin yanda take mishi magana gaba ɗaya kaman ba Salman shi ba, mai tausasa murya da kwantar da kai a duk lokacin daza ta mai magana. "Shikenan". Ya faɗa cikin sanyi jiki. "Ni zan fita". "Sai ka dawo". Ta faɗa ba tare da ta dubi inda yake ba. Girgiza kai yayi cikin sanyi jiki ya fice daga gidan cike da jimamin canji daya gani tattare da matarshi. Bayan addu'ar fita daga gida da yayi, ya fice tare da buɗe madaidaiciyar motan shi k'irar 206 fara sol! Tasha wanki sai k'yalli take. Tuk'i yakeyi, amma zuciyar shi sam ba daɗi. Istighfari ya cigaba da maimaitawa a laɓɓenshi har ya isa masana'an tashi. Domin Yana mutuk'ar son matar shi, baya son abin da zai kawo wata ɓaraka cikin zamantakewan su, dan haka gaba ɗaya hankalinshi a tashe tun jiya, amma yayi juyin duniyan nan ta faɗa mishi matsalar amma tak'i. Bayan fitan shi tsaki taja tare da hararar bayan shi. "Namiji har namiji amma baka iya awa biyu da mace kuna mu'amalan aurataya! ?. Ni wallahi hakuri na ya k'are kwata-kwata da komai da komai kagama daɗewa baka wuce 30-40 minutes! Dubi littafin *GIMBIYA TA* dana karanta jiya a WhatsApp, da *ZAZZAFA* dana karanta a Wattpad yanda suke yin dogon zango da matayen su, har fiye da awa huɗu zuwa awa biyar suna mu'amala amma banda ni, haba wallahi da sake!" . Haka tayi ta sambatu ita kaɗai kamar sabuwar kamu. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:* "Allah Almighty has said: 'The son of Adam denied Me and he had no right to do so. And he reviled Me and he had no right to do so. As for his denying Me, it is his saying: 'He will not remake me as He made me at first' (1) - and the initial creation [of him] is no easier for Me than remaking him. As for his reviling Me, it is his saying: 'Allah has taken to Himself a son,' while I am the One, the Everlasting Refuge. I begot not nor was I begotten, and there is none comparable to Me.'" (1) i.e., bring me back to life after death. [Bukhari (also by an-Nasa'i).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ تَعَالَى: كَذَّبَنِي ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، وَشَتَمَنِي وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: لَنْ يُعِيدَنِي كَمَا بَدَأَنِي، وَلَيْسَ أَوَّلُ الْخَلْقِ بِأَهْوَنَ عَلَيَّ مِنْ إِعَادَتِهِ، وَأَمَّا شَتْمُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَدًا، وَأَنَا الْأَحَدُ الصَّمَدُ، لَمْ أَلِدْ وَلَمْ أُولَدْ، وَلَمْ يَكُنْ لِي كُفُوًا أَحَدٌ رواه البخاري (وكذلك النسائي) *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene One_ ~*Page 2*~ Motsin da taji alaman za a shigo ya sata sauri datse wayan tare da b'oye ta cikin rigar ta. Tashi tayi tare da fara k'ok'arin cire Uniform d'in jikin ta. Da kulawa ta dube ta, "wai me yake damun ki ne Sahabat? Naga kin shigo gida yau a sanyaye?". Ba tare da ta kalle ta ba ta cigaba da cire Uniform d'in. "Babu komai Ummi, kawai kaina ke ciwo amma ya daina ma". "Toh Allah ya sauwak'a!". "Amin!" Ta amsa tare da sake duban ta. "Idan kin canja kayan kije ki fara rage mana aiki a kitchen kafin su Surayya su k'araso sai su taya ki". Girar sama da k'asa ta had'a jin abin da ta ke fad'a. "Ummi ina fa son zuwa gidan su Hunayda ne in dubo ta, domin yau banga taje makaranta ba". Wayan ta d'aga tare da dubawa taga 4:30 Pm. "Toh shikenan, amma kar ki zauna, kinga dai nayi bak'uwa, sannan da ta tafi zanyi Typing ne so da kin duba ta ki dawo". Dad'a zunb'uro baki tayi, ba tare da ta amsa ba. Bayan ta tabi da harara tare da fara k'unk'uni. "haka kawai sai dai kizauna ke baza kiyi komai ba sai dai ki ta bamu Umarnin sai kace bayin ki! Ni wallahi na fara gajiya, haba! shikenan ke baza kiyi komai ba tun safe mutum ya tashi yayi ta bauta kenan kaman bawa. Ni wallahi gwara inyi aure na in tafi gidan miji inyi mai licence amma na gaji!". Toh fa! kunji fa wata babban magana wai shin yima iyaye hidima bauta ne da ba lada? Ina Sahabat, kije ga Mal.Jamil, na san zai miki cikaken bayanin kan hakkin iyaye kanki. Bayan ta gama rage kayan jikin ta, fitowa tayi daga ita sai d'aurin k'irji da zani ta zo ta gitta su ba tare da ta kalle inda suke ba tayi wucewar ta kitchen, bucket ta d'auka tare da juye ruwan zafi dake wuta ta nufi band'aki dashi. Bayan wucewar ta dukkan su dakatawa suka yi da hirar da suke, wanda duk akan littafi ne da kallo suka bita. Hajiya Saudat ne tayi murmushi, "kai *Hibba!* mun kusa yin sirikai fa". "Hmmm", tayi murmushi, "hajiya ni kaina girman yarinyar nan na bani mamaki kaman ana hura ta, duka-duka fa bata wuce shekara goma sha shida da d'an d'oriyar watanni ba, domin bata ma kai da rabi ba, amma kinga yanda ta zama wata uwar mata". Dariya Hajiya Saudat tayi, "toh Allah dai ya basu mazaje na gari". "Amin!", ta amsa. Bayan ta fito daga wanka shiryawa tayi cikin riga da zani na atamfa, d'inkin zanin six pieces da rigan ta d'inkin Borno style, kayan su mata k'yau, a nutse ta zauna ta tsara k'walliyan ta tare da feshe jikin ta da turare, sannan ta d'auki mayafin ta da takalmi da suka dace da kayan nata ta sa. Wayan ta d'auka tare da soke ta k'ugun ta sannan ta fice. A falo ta ja birki inda suke zaune har lokacin suna k'wasar fira, ranta gaba d'aya dama baya son Hajiya Saudat saboda yanda taga kaman ita take tunzura mahaifiyar nata take sata sauran aikace-aikacen gida. "Ni zan wuce Ummi". "Toh ki gaishe ta, kar ki zauna dan Allah Sahabat". "Toh!", ta amsa in ta d'an dubi inda take zaune, "Umman Yusra sai anjima". "Yauwa!", Ta amsa", "sai kin dawo Sahabat, a dinga kula dai da yan iskan samarin kan hanya. Allah ya kare a dawo lafiya!". Amin ta amsa tare da ficewa tana sake jin haushin maganan nata, "Wai a ringa kula da yan iskan samarin kan hanya" Ce mata aka yi gurin su zanje ko kuwa?". Haka tayi ta mitan ta dai ta ida fita daga gidan, a bakin k'ofa suka yi kicibis da su Surayya, da gudu Na'eef ya k'araso yayi mata Oyoyo, "Aunty Saha munje ajin ku muna ta jiran ki bak'ya nan, shine Aunty Surayya tace mu jira ki, shine muka zauna muna ta jiran ki amma bamu ganki ba". Dariya tayi, "toh Na'eef Gani nan yanzu ka ganni. Yau ban jira ku ba nayi tafiya ta, yanzu kaje gida ka cire Uniform, Surayya tayi ma wanka ak'wai ruwa a wuta", ta fad'a tare da kallon inda take tsaye. "Barina je anguwa in dawo Sis". "Toh Aunty sai kin dawo, amma ina zaki irin wannan k'waliyya haka? Kinga yanda kikayi k'yau kuwa!". Dariya tayi, "toh na gode, idan na dawo k'yaji. Me zan siyo ma?". Ta tambaye shi. "Chaculate!", ya amsa yana tsalle. "Toh shikenan zan kawo ma". Da gudu ya shige cikin gida, inda Surayya take biye da shi. "Hibba! dole fa mu tashi tsaye da yima yaran nan addu'a Allah ya shiga tsakanin su da wayannan samarin zamanin masu rud'in yara su lalata musu rayuwar". Cewar hajiya Saudat "Ke dai bari k'awata, ni shi yasa nake takatsan-tsan da duk wani motsin Sahabat, saboda Allah ya mata diri da garab'an jiki. Kinga wannan yasa fa ko waya bazan yarda ta rik'e ba gaskiya, ni ina tunani ma sai taje gidan auren ta, saboda wannan waya.....", ta d'aga wayan ta tana jujjuyawa. "....Illan shi yafi amfanin shi yawa. Domin duk abin da kake nema zaka samu cikin shi, idan alkhairi ne zaka samu ko akasin shi". Ajiyar zuciya hajiya Saudat ta sauke. "Amma yanzu ke kina ganin hajiya hanata rike waya shine mafita? Ni inaga fa ba shi bane mafita. Domin yaran nan da kike ganin idan har suka tasa ma ka hana su rik'ewa sai kiga sunje samarin sun sai musu kuma suna rik'ewa a b'oye ba tare da kin sani ba. So kinga ba daga nan take ba fatan kawai Allah ya shirya mana zuri'a, amma ni rayuwar nan ma tsoro take bani , domin kinga Mallam Usman mak'wafcin mu nan yar shi Saliha haka saurayin ya sai mata waya sama da shekara ba tare da sanin iyayen ba, toh haka dai har mahaifin ya fahimta, k'arshe kar kiga tijaran da ya mata ya karb'i wayan nan amma abin mamaki yarinyar nan ba ayi wata ba saurayin nan ya sake sai mata wani, ta cigaba da rik'ewa ba tare da sanin iyayen nata ba. Ke ni yaran nan har tsoro suke bani". "Toh Allah ya k'yauta. Hakan kam yana faruwa sosai, Allah dai ya kare mana zuri'a". "Amin!", ta amsa. "Kin san fa hajiya duk wani burina da tunanina yana kan Sahabat, cikin yaran nan gaba d'aya nafi jin ta a rai na. Bani da buri da ya wuce in ganta cikin farin ciki...". Shigowan su Na'eef ne yasa su dakatawa daga maganan da suke. ****** Duk wani aikin da Ammi ta bata Ulumarnin yi kafin ta dawo haka tayi shi na ganin dama ko ince ko oho, dan haka cikin k'ank'anin lokaci ta gama tare da tattare kayan data b'ata ta zuba su gun wanke-wanke, share kitchen d'in tayi sama-sama ta rage wutan abincin dake wuta tare da lek'awa d'akin Ammi. Hajna ce a falo tana k'ok'arin sa turaren wuta a d'an k'aramin k'yak'yawan kasko. Harara ta b'alla mata, "ni zan shiga wanka, ki duba abinci dake wuta idan yayi ki sauke". "Toh", ta amsa cikin rashin jin dad'in abinda yar uwar nata take mata, domin ita har bata so Ammi ta aike ta kiran ta domin idan har ta tadda ta da wayan ta a hannun ta, ta Isar mata da sak'on toh wuni zata yi k'yarar ta da mata tsawa. ******* Bayan fitowan ta daga gida taku kad'an tayi ta ja ta tsaya daga gefe tare da fitowa da wayan ta k'irar tecno Spark 4, yan latse-latse tayi tare da karawa a kunne. "Hello Dear", ta fad'a bayan an d'aga wayan ta d'ayan b'angaren aka amsa. "Hi Sweedy! Har kin fito ne?". "Eh na fito!". "Good! Gani nan k'arasowa ki jirani". "Toh", ta fad'a tare da katse wayan. Tafiya ta fara yi cikin takun ta mai d'aukan hankali. Cikin mintunan da basu gaza biyar ba ta iso inda suka saba had'uwa, tsayuwar ta yayi dai-dai da Goga Parking d'in shi, batayi k'asa a gwiwa ba ta k'arasa jikin motan inda ya bud'e mata k'ofa, mazaunin gaba ta shiga tare da rufe k'ofan ya k'ara ma mota giya suka hau hanya. Kaman ko yaushe gurin shak'atawa suka nufa. ******* Bayan Ammi ta fito daga wanka ta shirya cikin doguwar rigar ta na wani jan material, kayan sun amshe ta kasancewan ta farar fata, sun kuma b'oye k'uruciyar ta domin daga ido baza ka ce tana da ya kaman Hajna bama ballantana Hunayda. Kitchen ta nufa da hanzari jin abinci na k'auri. Da sauri ta k'arasa tare da murd'e switch d'in gas ya mutu, bud'e tukunyar tayi tare da duba dahuwar abincin gashinan a ido ba sai ta tab'a ba bai dahu ba amma babu ruwa cikin tukunyan sai k'onewa da ya fara yi. Ranta ne taji ya b'aci amma ta danne tare da fara duba Yankan kayan salad d'in data sata. "Subhannallah!", Ta fad'a ganin irin yanda ta yanka mata. Wai me yake damun Hunayda ne? Me take Nufi ne? Tambayoyin da suka cika mata zuciyan ta kenan, domin wasu irin yankan da tayi fato-fato da sai ka d'auka fad'a akayi da ganyen. A fusace ta nufi d'akin ta tare da tura k'ofa ta shiga. A tsaye ta same ta daga ita sai towel alaman ta fito daga wanka, tana zaune gaban dressing mirror wayan ta na hannun ta. Jin Yanda aka turo k'ofan ya sata saurin mik'ewa game da ajiye wayan. "Me yake damun ki ne haka Hunayda?! Ina hankalin ki yake ne?! Ko dan na tursasaki kinyi aiki baki yi niyya bane yasa zakiyi yanda kike so, wanda ko Hajna baza tayi wannan b'arnar ba!?". D'an Sosa k'eya tayi tare da sunar da kai k'asa. "Ammi me nayi?". Domin ita har ranta bata ga laifin data yi ba, sai dai tasan tayi aikin cikin gaggawa. "Au!, me kikayi kike tambaya na?". "Yanzu ace dafa farar shinkafa yau ya gagare ki, baza ki iya tsayar da ruwan da zai wadace shi ya dahu ba?". Dahm! K'irjin ta ya buga domin sai Yanzu ta tuna fa bayan ta tafasa ta tsane ta mai da tukunya ta aza a wuta ba tare da tasa ruwa a ciki ko kad'an ba. "Ammi dan Allah kiyi hakuri wallahi na manta ne dana tafasa na tsane na mayar tukunyan bansa ruwa ba". Takaici ne ya kama ta jin abinda ta fad'a. Wanda gaba d'aya ma ta rasa abinda zata ce mata sai wani kallo da take watsa mata. "Su kuma kayan salad d'in fa? Kin manta suma baki yanka ba ko?". "Um'um!". Ta fad'a tana sunkuyar da kanta domin tsoron Ammi ne ya kamata, ganin b'acin rai kwance a fuskan ta wanda ita baza ta iya tuna sanda taga fushi har haka daga gare ta ba. "Shikenan!", ta fad'a cikin tak'aici, "Idan abu da kike me k'yau ne, ki cigaba Hunayda, Allah ya gani ina iya k'ok'arina kanki, kuma wannan abu tun ba yau ba kin saba yin su kuma ba tare da wani matsala ba, amma saboda kina aikin daya fi nawa lada na d'ago ki yasa kimin yanda kike so ko?!". Girgiza kai tayi idon ta ya ciciko da k'walla; "Ba haka bane Ammi, dan Allah kiyi hakuri kar kiyi fushi dani, Insha Allahu bazan sake ba na tuba". Ta k'arasa maganan ta had'e hannun ta guri guda. "Shikenan!", ta fad'a tare da jin tausayin ta, kuma a lokaci d'aya zuciyar ta yake sanar da ita dole ta mata uzuri ta kuma ringa nusar da ita a hankali, saboda ba d'abi'an ta bane, da tana k'ok'arin yi mata komai cikin tsari da nutsuwa koda bata sata ba, zata mata duk abinda ya kamata. "Ki ringa kula Hunayda, Dan Allah na rok'e ki, kinga ke mace ne gidan wani zaki je, idan baki nutsu kin koyi duk wayannan abubuwan ba idan kika je naki gidan wa zai miki? Kiyi k'ok'arin yin amfani da abinda kika karanta da wanda ake fad'akar da ku a makaranta koda yaushe, saboda watarana idan da rai da safiya ke ma uwace kuma na tabbata baza ki so yarki ta miki abinda kike yi min yanzu ba, baza ki tab'a son haka ba kuma nima bana miki fata. Dan haka ki k'ara kula, domin idan kayi dai-dai zaka ga sakamakon ka, idan kayi ba dai-dai ba ma zaka gani. So ki kula sosai kuma kar ki maida hankalin ki kan abinda ba zai amfane ki ba". Jikin tane yayi sanyi da nasihar mahaifiyar nata. A sanyaye ta furta; "Insha Allahu Ammi zan kula, na gode". "Yauwa maza ki sa kaya ki fito, wannan b'arnar da kikayi mu gani ko za a iya gyarawa". "Toh!", Ta amsa tare da fara kintsawa a sanyaye, domin maganganun mahaifiyar nata ya shige ta, kuma tabbas ta gamsu, gaskiya take fad'a mata sai dai fatan Allah ya miki Albarka, "ki dauki abinda yake mai amfani cikin littatafan da kika karantawa masu amfani, sannan kiyi watsi da marasa amfani, domin ko wani littafi babu inda bazai miki nuni da nashi darasin ba sai dai idan anyi shi ne domin nishad'i ba ilimintarwa ko fad'akarwa ba". Amma ita sam bata jin zata iya daina karanta littafi. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* On the authority of Zayd ibn Khalid al-Juhaniyy (may Allah be pleased with him), who said: The Messenger of Allah (may the blessings and peace of Allah be upon him) led the morning prayer for us at al-Hudaybiyah following rainfall during the night. When the Prophet (may the blessings and peace of Allah be upon him) finished, he faced the people and said to them: "Do you know what your Lord has said?" They said: "Allah and his Messenger know best." He said: "'This morning one of my servants became a believer in Me and one a disbeliever. As for him who said: 'We have been given rain by virtue of Allah and His mercy,' that one is a believer in Me, a disbeliever in the stars (2); and as for him who said: 'We have been given rain by such-and-such a star,' that one is a disbeliever in Me, a believer in the stars.'" (2) The pre-Islamic Arabs believed that rain was brought about by the movement of stars. This Hadith draws attention to the fact that whatever be the direct cause of such natural phenomena as rain, it is Allah the Almighty who is the Disposer of all things. [Bukhari (also by Malik and an-Nasa'i).] عَنْ زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ الْجُهَنِيِّ، رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: صَلَّى لَنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَاةَ الصُّبْحِ بِالْحُدَيْبِيَةِ، عَلَى إِثْرِ سَمَاءٍ كَانَتْ مِنْ اللَّيْلَةِ، فَلَمَّا انْصَرَفَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ، فَقَالَ لَهُمْ: هَلْ تَدْرُونَ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ؟ قَالُوا: اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: أَصْبَحَ مِنْ عِبَادِي مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ، فَأَمَّا مَنْ قَالَ: مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللَّهِ وَرَحْمَتِهِ، فَذَلِكَ مُؤْمِنٌ بِي، كَافِرٌ بِالْكَوْكَبِ، وَأَمَّا مَنْ قَالَ: مُطِرْنَا بِنَوْءِ كَذَا وَكَذَا، فَذَلِكَ كَافِرٌ بِي، مُؤْمِنٌ بِالْكَوْكَبِ رواه البخاري (وكذلك مالك والنسائي) *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene One_ ~*Page 3*~ A zaune suke a wasu fararen kujeru, gefen su ruwa ne da d'aid'aikun jama'a suke d'an giftawa, a dai-dai wannan yammacin da iska mai dad'in gaske yake kad'awa cikin nutsuwa da saukar da yanayi farin ciki ga duk wanda ya shak'e ta, duk wanda ka gani gurin da yar budurwan shi gefe ko matar shi. Ice cream ne gaban su da sauran tarkacen kayan ciye-ciye. Zaiyad saurayi ne mai ji da tashe tare da ji da kanshi, d'an shekaru 25 a duniya, yana zaune ne cikin shigar sa ta k'ananun kaya na riga da wando, wanda duka kayan sun kasance farare sol, kayan sun karbe shi sosai, takalmi da agogon shi duk farare ne, sai bak'in glass d'in daya sa a idon shi, wanda ya dace da yanayin fuskar shi. D'aukan ice cream d'in yayi a cokali tare da nufan bakin ta dashi yana murmushi. Bata yi k'asa a gwiwa ba ta bud'e bakin ta ya zuba mata ciki, lumshe idon ta tayi tare da motsa d'an k'aramin bakin ta, ta fara tsotse wa. Haka suka cigaba da ba ma junan su cikin kwanciyar hankali suna murmushi. Sun dauki tsawon lokacin kafin suka gama, kallon ta yayi yana murmushi. "My Saha, idan muna tare bana son mu rabu, saboda bana gajiya da kallon k'yak'yawan fuskar ki mai kawar min da duk wani b'acin rai, tare da dasamin farin ciki". Lumshe ido tayi tana murmushi ba tare da ta ce komai ba, kalamun shi sun faranta mata rai mutuk'a, wannan yasa koda yaushe take sake jin wutar k'aunar shi na ruruwa a zuciyar ta. Agogon hannun shi ya duba tare da maida kallon shi kanta, "lokaci yayi ya kamata ki koma gida, domin bana son ki kasance cikin matsala My love". Murmushi tayi tana mik'ewa. "Ya kamata, ganin ka ya kan sani mantawa da komai". Murmushi yayi, "ina aiki na dakyau kenan, abinda ya kamata kenan, dama tuntuni kika barni nake kid'a na da rawa na ni kad'ai". Dariya suka yi tare da jerawa suna hiran su ta soyayya har zuwa inda yayi parking motan. Sai da yabud'e mata ta shiga ya rufe, sannan ya zaga ya shiga tare da rufewa ya tayar suka kama hanya. Nesa da gidan su Hunayda ya goga parking, inda sukayi sallama cikin jimamin za suyi kewan juna. Dubu biyar ya d'auka tare da mik'amata ta siya kati. Karb'a tayi had'e da mai godiya ta fice a motan hannun ta rik'e da yar k'aramar ledar daya mata orde ice cream d'in da su choculate. Da sallama ta shiga cikin gidan, Ammi dake tsakar gida ta amsa mata cikin sakin fuska. "Ina Wuni Ammi!", Ta fad'a tare da d'an rusunawa. Da fara'a ta amsa mata. Hunayda dake kitchen ne ta fito tana kad'e ruwan hanun ta da ta gama wanke-wanke kenan. Had'a ido sukayi tare da sakar ma juna murmushi. "Welcome!". Ta fad'a tana k'arasowa inda take. "Yauwa! Wai yau lafiya bakije makaranta ba?". Ta tambaya a lokacin da suka nufi k'ofar d'akin su. "Lafiya!" Ta amsa. "Ammi ne taje anguwa, kuma bata dawo da wuri ba, babu key da za mu rufe gida shiyasa ba muje ba". "Ok! Ai su Aisha suna tambaya na ke nace may be ko bakiji dad'i bane, toh dana duba ko zan hango Hajna itama ban ganta ba". "Hakane, muna tare an barmu mu biyu a gida". "Daga ina kike ne? irin wannan k'amshin naga sai k'yalli kike!". Ta fad'a cikin sigan zolaya. "Uhumm! ke dai bari, daga Green park muke ni da rabin raina, yanzu ya sauke ni nan ya wuce". "Wai ke Sahabat ba k'ya tsoron ranar da asirin ki zai tonu?". "Hmmm!", ta sauke ajiyar zuciya, "ke dai bari , ai Allah ma ya kare amma da na boni da Ummi, kar ma Uncle Zakari yaji labari da kashina ya bushe". Gyad'a kai tayi, "toh kinji ko, ina fad'a miki kiyi a hankali fa". "Hunayda kin san fa so tunda kema kina yi, baza ki gane yanda nake ji akan zaiyad ba ina mugun son shi kin sani fa!". "Hakane na san so, amma kuma ni ai duk samarin dazan yi da soyayyar da zamu d'ana duk a waya muke gama shi, sai idan ko mun had'u hanyar makaranta amma kinsan tsorona ma bazai barni inyi k'arya har in fice daga gida inbi saurayi wani gurin ba". Ajiyar zuciya ta sauke, "toh kin gani ko ke da kike da freedom d'in rik'e wayan kenan, amma ni kina ganin yanda Ummi take da ra'ayin nan zata barni rik'e waya nan kusa kuwa? Kai da kamar wuya!. So kin gani da zan samu wannan daman nima bazan ringa satan hanya ina fita ba, idan ma zanyi toh bazai zama koda yaushe ba. Amma yanzu ko wayan zan amsa fa sai a b'oye da kuma dabara kamar wata b'arauniya". "Toh ai sai kiyi hakuri zuwa lokacin da Ummi zata Amince miki". "Ke dai mu bar zancen, barina tashi, sai mun had'u a WhatsApp anjima, yanzu ni zan wuce kafin a kira magrib". Ta fad'a tare da mik'ewa tana gyara gyalen ta, a lokaci d'aya kuma ta mik'a mata ledan dake hannun ta, "Ga tsarabar ki, barina d'auki Chaculate ma Na'eef kafin in in shiga dashi duka gida a dasa min ayar tambaya". Dariya tayi tare da d'aukan hijab ta zura domin tayi mata rakiya. Bayan ta ma Ammi sallama, suka fita tare domin ta mata rakiya. ****** Kaman ko yaushe bayan sallar isha'i, Abdulkareem ya nufi gidan shi kai tsaye, bayan ya saya ma yaranshi tsaraba kaman ko yaushe tare da mai d'akin nashi. Da sallama ya shiga cikin gidan, da gudu Husna, yarinyar yar shekara hud'u da k'anin ta Abubakar da suke kira (Mussadiq )da ba zai wuce shekara biyu ba, suka nufo shi tare da kiran; "Abba Oyoyo Abba Oyoyo!". Da murmushi ya shiga d'aga su d'aya bayan d'aya, yana dariya tare sumbatan su a goshi. Bayan ya sauke su da d'an musu wasa ya. mik'a musu Bobo da Biscuit d'in da ya kawo musu, murna su ka shiga yi inda ya karb'a tare da fara k'ok'arin bud'e musu. Duk abinda suke Salma na zaune tana karatun littafi a wayan ta, cikin kwalliyan ta na riga da wando na Pakistan, wanda rigan ya kai mata gwiwan ta, gyallen shi tayi d'auri da ta karkato dashi gaban goshin ta inda gefen kanta ya baiyana tare da fito da bak'i sutuk d'in gashin kanta daya sha gyrara yake ta k'yalli. Tunda ta juyo muryan shi taji ranta ya b'aci tuno daren su na jiya dashi, dan haka ta sake maida hankalin ta kan abinda take karantawa tare da yin kaman bata ma san da shigowan shi ba. Duban su yayi yana murmushi. "toh kuzo muje d'akin ku ko, yan albarka!". Ya fad'a tare da kama hannun su ya bud'e kofan d'akin tare da ganin shigan su kafin ya jawo musu k'ofan ya nufi inda take zaune, gaban shi na fad'uwa a lokaci d'aya kuma k'waliyar ta, ya mutuk'ar k'ayatar dashi tare da jin wani abu ya tsarga mishi. Salma k'arshe ne wajen kaman ta komai kuma mace ne da duk namijin zai yi burin samun ta matsayin uwar y'ay'an shi, domin tana da ilimin ta na addini tare dana boko dai-dai gwargwado, tsafta, iya girki da kula da kanta wannan yasa idan ka kalle ta baza ka tab'a tunanin ma ta ajiye d'a d'aya ba. Zama yayi a hannun kujeran da take zaune tare da sak'alo hannun shi saman kafad'un ta, a hankali ya furta; "My Salma, wani laifi nayi ne da ko kallo na ba a son ayi ballantana in samu tarb'a?". Hannu ta tasa tare da cire nashi daga kafad'an ta. "Ban san ka shigo ba ai, Sannu da zuwa!". Murmushin tak'aici yayi sannan zuciyar shi ta mishi zafi k'warai da yanda ta nuna mai, amma yayi kokarin danne zuciyar shi tare da had'iye abinda ya taso mishi. "Yaya kuka wuni?". "Lafiya lau". Ta amsa. "Amma ina kike ajiye wayan ki yau? Na kira inji lafiyar ku tunda ke baki neman kiji na isa lafiya ba, amma baki d'aga ba kuma baki yi ko flashing ba". Yatsina fuska tayi, "tunda kaji shiru ai muna cikin k'oshin lafiya". K'aramar ajiyar zuciya ya sauke ba tare da yace komai ba, ya kalle ta, "A taimaka min da abinci, domin yau sai naci in iya watsa ruwa, rabona da abinci tun break fast". Dad'a d'aure fuska tayi, "ni ban dafa abinci ba, su Mussadiq ma indomie na dafa musu, kai kuma na san baka son ta shi yasa ban dafa da kai ba". Da mamaki ya kalle ta. "Amma me yasa baki dafa ba bayan ak'wai komai a gidan?". "Bana jin dad'in jikina ne!". Ta bashi amsa tana shan k'amshi. "Amma kuma yanzu kika ce min kuna lafiya". "Uhumm!". Ta fad'a tare da mik'ewa, "nifa gaskiya Abban Husna na fara gajiya da k'wak'wanka da bin diddigi, haba, tunda ka shigo sai tuhumana kake kaman wacce tama sarki k'arya! Haba! ka barni inji da abinda da yake damuna mana!". Ta k'arasa fad'a tare da shigewa cikin d'akin su Husna ta barshi zaune a gurin, baki bud'e. Mamaki ne fal ranshi. Wai me yake faruwa ne haka? Zugi ne wannan ko yin kanta? Ko kuwa Aljanu ne suka shafeta? Amma yau Salma ce take treating d'in shi haka?! Wacce take tarairaiyan shi tare da nuna mai dukkan kulawa tare da soyayya, yau ita ce take mai irin haka, to me ya mata? Tambayan da ya tsaya mai a rai kenan! Wanda dashi ya wuni. Duk ciwon da take fa bata tab'a barin shi yaci abinci a waje, haka zata daure ta shiga kitchen ta dafa mishi. Ya d'auki tsawon wasu mintuna agurin yana ta tunani, kafin yayi dauriyan tashi ya shiga bed room d'in su. Yana jiyo muryanta gurin su Husna suna karatu. Wannan ya sake tabbatar mishi lallai dashi take wannan fushin. Toh laifin me na mata haka da baza ta fito ta fad'a min ba? Rage kayan jikin shi yayi ya fad'a toilet domin ya watsa ruwa, jikin shi a sanyaye. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🙆🏻🤷🏻‍♀ *_MENENE RIBA TA ❓_* 🤷🏻‍♀🙆🏻 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ *~ ✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽~* *~We are bearier's of so golden pen~*🖊 *~We write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da sauke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Two_ ~*Page 4*~ Sahabat na fita daga gidan su Hunayda ta tari mai machine ya kai ta layin su, dan ta isa gida da wuri, kasancewar ba wani nisa sosai, yasa suka isa cikin ƙanƙanin lokaci, tana sauka ana kiran sallar maqrib. Da sallama ɗauke a bakinta ta isa ɗan madaidaicin gidan na su, ba kowa a tsakar gidan, hakan yasa ta shiga falon kai tsaye. "Sahabat ina kika tsaya, ban gayamiki ki dawo da wuri ba, ki ɗaura girki?!". Ummi ta faɗa, wacce take zaune akan kujerar dake falon, wayarta na hannun ta tana latsawa ,da alama har Hajiya Saudat tabar gidan bata tashi daga gurin ba. Turo baki Saha tayi tana ƙara jin haushin mahaifiyar tata. "Ba inda na tsaya, da naje na tadda Hunayda bata jin daɗi ne shi ne na tsaya". Tayi maganar cike da jin haushi da tsoro, bata yadda sun haɗa ido ba dan kar ta gane ƙarya tayi mata. "Ayyah Allah ya bata lafiya, to sai ki je kiyi sallah ki ɗaura muku abinda zaku ci". Fuuu! ta wuce ɗakin su, ba tare da ta ce komai ba, dan tsabar haushin Ummin da take ji. "Shikenan mutum komai sai yayi, duk inda naje sai an jira na dawo, ke kenan latsala waya, baki iya yin aikin komai ni na fara gajiya! Ni ce wannan, ni ce wancan! haba! mutum an maida shi jakin dole", a ranta tayi maganar cike da jin haushi. Tana shiga ɗakin Na'eeb ya rugu ya rungume ta,"Oyoyoo! Aunty Sahabat kin dawo, ina chocolate ɗi na?" Cikin fushi ta ce,"Na dawo!". Ta miƙa mishi, bai bi ta kanta ba ya fita yana murna da jin daɗi. Suraiyya ma tai mata sannu da zuwa, "Aunty Sahabat ina da assignment". "ki ƙyale ni da wani Assignment, da wanne zanji!?". Cikin faɗa- faɗa tayi maganar, ganin yadda tayi maganar ba daɗi yasa ta sassauta murya. "Suraiyya ki bari sai gobe da safe, kin ga yanzun zan ɗaura mana abinda zamu ci, kuma idan na gama da abinda zanyi". "Ba komai Aunty Saha,muje na tayaki wani abun". "Yawwa!" Bayan ta idar da sallah ta fito zuwa kicin ɗin, har lokacin Ummi na gurin tana ta faman latsa waya, basu ce mata uffan ba, suna ta aikace-aikacen su amma tamkar bata san suna gidan ba. ******************** *Wanene Zaiyad* Zaiyad Kabir Safana shi ne cikakken sunan Zaiyad, mahaifin shi Kabir Safana haifaffan ɗan jahar kaduna ne, dan kasuwa ne wanda yayi fice a jahar kaduna. Tun zaiyad na ƙarami mahaifiyar shi ta rasu, wanan dalilin yasa Alhaji Kabir Safana ya ɗau son duniya ya ɗaurawa Zaiyad, baya ganin laifin shi ko kaɗan, yana sakar mishi kuɗi yayi yadda yake so ba mai taɓa shi. Zaiyad ba wani mai kyau ba ne irin na azo a gani, sai dai ba laifi yana da nashi irin kyaun, shi ba baƙi ba sanan kuma ba fari ba, amma kuma ɗan gaye ne. Shi yasa Zaiyad ya taso cikin rashin jin magana da sangarci, sai yadda yake so, sai abinda yake so. Gaba ɗayan unguwar Rimi daga kan layin Isa Gaita harda sauran layikan, ba wanda bai san waye Zaiyad ba gurin ɓata yaran mutane, baya shaye-shaye sosai amma ta fannin ɓata yaran mutane ko ince yaudara dan sai da yarda mace, ya ƙware sosai ta fannin yaudara, duk wayau mace sai dai bai kwallafawa ranshi ita ba, cikin salon shi zai sa mace ta amince da shi, yadda bata isa takai ƙarar shi ba. Ranar da ya haɗu da Saha a central market, taci ado kasancewarta mai son ado ce, da shigar ƙananan gaya ko atamfa ce ɗamaman ɗinki ake mata, da soyayya ya isa gareta, bai sha wata wahala gurin shawo kan ta ba, wanda har zuwa yanzun bai baiyana mata manufar shi ba, kullum nuna mata yake yi shi kamili ne. Wanan kenan akan Zaiyad Kabir Safana. Zaiyad ne kwance akan doguwar gujerar da ke falon, idan ka ganshi zaka ɗauka bacci yake yi, amma a zahiri lamo kawai yayi.Kwakwalwar shi ke ƙara nuna mishi hoton yadda dirin Sahabat yake, lips ɗin ta yadda take sarrafasu idan tana magana shi yafi ɗaukar hankalin shi. Ɗan tsaki yayi iya leɓan shi haɗe da cizon leɓan, sanan ya ce cikin raguwar muryar shi mai cike da kasala. " Da sannu!! zaki shigo hannu yarinya, ban taɓa daɗewa da mace ba tare da na cin ma burina ba irin ki, amma na kusa cin ma haƙa." ******************** Bayan fitar Sahabat Hunayda ta ɗauko tsarabar da ta kawo mata, kiran Hajna ta fara. "Hajna! zo ki amsa". Ammi, wacce ke zaune a gurin ta kalle Hunayda cikin kulawa ta ce, "Hunayda ina kika samu chocolate haka da yawa?". "Ammi, Saha ce ta kawo min". "Ita ina ta samu, na gansu da yawa". Shiru Hunayda tayi na ɗan dakiƙu kafin ta ce, "Ban sani ba, amma siyowa tayi". "To ku kula dai Hunayda,rayuwar yanzun ta zama abinda ta zama sai kun kula". Cikin sanyin murya ta ce,"To Ammi." Hajna ta zo cike da jin daɗi ta amsa tana sha, kallon yanayin ƴar uwarta ta ya sauya yasa ta ce mata, "Aunty Hunayda kin tuno lokacin da Abba ke kawo mana irin wannan, ki min wayau ki shanye?". Dariya suka yi dukan su harda Ammi. Suna nan zaune aka kira sallah suka tashi suka yi, bayan duk sun idar suka ƙarasa yin aikin su sannan suka zauna a falon jiran mahaifin su. Da sallama ya shigo ɗakin, cikin jin daɗi da farinciki suka amsa mishi. "Sannu da zuwa Abba". Hunayda da Hajna suka faɗa a tare, Hajna ta amshi ledar dake hannun shi. Cikin sakin fuska da nuna kulawa ya ce, "Yawwa ya kuka wuni?". "Lafiya lau Abba". Ammi dake gefe zuciyarta cike da farin ciki tayi mishi sannu da zuwa. "Ya gidan Ammin Hajna?". "Lafiya lau ya aiki?" "Alhmdllh! sai godiya". Sannan suka zauna suka dan taɓa fira cikin so da ƙaunar juna, sannan su Hunayda suka yi musu sallama suka tafi ɗakin su. *Wacece Hunayda?* Maryam shi ne ainihin sunan Ammi mahaifiyar Hunayda ƴar kaduna ce,a unguwar badikko.Hamza shi ne ainihin sunan Abbah,wanda shi ma ɗan kadunan ne unguwar hayin ɗan mani. Maryam cikin so da ƙauna ta taso gurin iyayenta, su biyu mahaifin su ya haifa, yayan ta Ibrahim sai ita, mahaifin Hamza(Abba) abokin mahaifin Maryam ne(Ammi), tamkar ƴan uwa haka suke, dan abotar su tun yarinyata, sai kuma gashi yaran su sun fara soyayya a tsakanin su,dukkan su wa wani bako suka yiba kandy kowanan su yayi,dan ƴan kasuwa ne iyayen na su, atamfofi suke saidawa a kasuwa. Maryam tana da tarbiyyarta wacce ta samu daga iyayenta, sai da ta kammala aji uku na Mutawassiɗa na isalamiya, haka shi ma Hamza yayi nashi karatun, kasancewar ba wani karutun boko suke yi ba yasa suka aurar da Maryam tun tana shekara goma sha takwas. Hamza ya gina musu ɗan madaidaicin gidan su, a Kurmin Mashi, wanda ba wani nisa sosai a tsakin unguwar da su. Ana ɗaura aure aka kawo amarya gidan mijin ta. Zaman mutunta juna da girmamawa suke yi, har Allah ya bata cikin Hunayda. An haifi Hunayda da shekara ukku da rabi aka haife Hajna, wanda a yanzun shekarun Hunayda goma sha bakwai kenan. Hunayda mai kyau ce, ita ba mai qiba ba ita ba siririya ba, tana da zati dai-dai ƙirarta, sannan tana da haske ba irin mai yawan nan ba, daidai-daidai. Hunayda yarinya ce mai shauƙi,(Wacce abubuwa ke saurin birgesu), amma tana da tsoro,tana da rauni sosai da shagala. Haɗuwar su da Saha ya samo asali ne sakamakon burgeta da take yi, tana sha'awar yadda take rayuwarta, yadda take kwalliya, shiga da dai makamanta su, tana son yin wasu abubuwan amma tsoro ke hana t, tana son soyayya da labarin soyayya, wanan dalilin yasa tayi ƙokari a karatun ta na candy, dan samon waya, domin mahaifin ta Hamza(Abba) yace sai ta kammala candy zai bata waya, Hakan kuwa ta faru, tana gamawa ya siyo mata waya sabuwa Camon 12, yanzun watan su ɗaya da kammala candy. Hunayda taji daɗin samun wayar nan, haka ma Aminiyarta Saha, ita ke turo mata littafai ta WhatsApp. Primary daban suka yi, a candy ne suka haɗu, Gombe International school, a nan suka haɗu, sannan kuma islamiyar su ɗaya, kasancewar makarantar haɗe da isalamiya ne. Wanan kenan akan Labarin rayuwar Hunayda. ******************** Bayan ya fito daga toilet ya saka kaya mara nauyi a jikin shi sannan ya fito, har zai shiga ɗakin yaran inda yake jin surutun ta, sai kuma ya fasa ya nufi kicin, haka nan ya ɗaura indomie ɗin dan yunwar da yake ji. Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama dafawa ya fito, a falo ya ganta tana danna waya, xama yayi kan kujerar dake fuskan tata bai ce mata komai ba ya fara cin abincin shi. Ƙamshin turaren da taji ne yasa ta tabbatar ya shigo falon, lumshe ido tayi domin tana bala'in son ƙamshin turaren shi, tsaki tayi a ran ta ce; "Idan ka ganshi ka ɗauka wani jarumin namiji ne, ga kwarjini amma na banza, tirr! da miji irin ka, ni dai ban yi sa'ar miji ba". Bayan ya gama cin abincin ya tashi ya maida kwanan kicin yasha ruwa sanan ya dawo kusa da ita ya zauna. Cikin marairaicewa ya ce,"Salma! kin san ganin fushin ki yadda yake wahalar da zuciyata kuwa? Pls ki tausayamin Matata, ki tausayawa mijin ki, ki daina wannan fushin, idan kuma wani laifi nayi miki ki gayamin, zan gyara kuma na baki hakuri da hannu biyukin ji?!". Ya ƙarasa maganar cikin sigar naiman yafiya. Wani uban tsaƙi taja a ranta, "Wai zaka gyara, tayaya?, haka kake ba zaka taɓa canzawa ba, ni da lafiyata haka kawai ka ɗinga ƙwarata". "Dan Allah!". Katse mata tunanin da take yi yayi, kallon wulaƙanci tayi mishi sannan ta ce; "Ni ba komai ka ƙyale ni plss, ni ban san takura da naci haba!", ta faɗa tare da turo baki. "Ban yarda ba, akwai wani abu, ki gayamin, wanan fushin ba lafiya ba". "To ai sai kayi". Tashi tayi tabar gurin. Dafe kanshi yayi wanda yake jin yana sara mishi, a hankali a hankali zuciyar ta fara mishi zafi, "Meke faruwa ne?!". "Taya zata ce min ba komai, bayan akwai wani abun? Taya take ganin zan jurewa fushin ta akai ta na *MENENE* *RIBA* *TA ??* anan na ganin fushin ta?". Tashi yayi ya bita ɗakin, yana zuwa ya ganta a kwance har lokacin wayar na hannunta, yana kwanciya kan gadon ta tashi. Tsaki tayi, "Mtseeww! ni wllh naci ne ban so, da takura, haba mutum kamar maye, duk inda nayi ka biyo ni kamar bindi!". Ta tashi ta fita tana tsaki. Kallon tsoro ya bita da shi, dan lamarin yanzun tsoro ya bashi, dan tunda yake da Salma bata taɓa yi mishi magana cikin rashin kunya irin haka ba, balle tsaki. "Anya kuwa ba Aljannai ba ne suka taɓa ta!?". ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷‍♀ *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ *~ ✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽~* *~We are bearier's of so golden pen~*🖊 *~We write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* https://www.facebook.com/groups/156937942662161 ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN.*~👇...... ✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da sauke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say: "The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path [un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire." [Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: إِنَّ أَوَّلَ النَّاسِ يُقْضَى يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَيْهِ رَجُلٌ اسْتُشْهِدَ، فَأُتِيَ بِهِ فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ قَاتَلْتُ فِيكَ حَتَّى اسْتُشْهِدْتُ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ قَاتَلْتَ لِأَنْ يُقَالَ: جَرِيءٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ تَعَلَّمَ الْعِلْمَ وَعَلَّمَهُ وَقَرَأَ الْقُرْآنَ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: تَعَلَّمْتُ الْعِلْمَ وَعَلَّمْتُهُ، وَقَرَأْتُ فِيكَ الْقُرْآنَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ تَعَلَّمْتَ الْعِلْمَ لِيُقَالَ: عَالِمٌ، وَقَرَأْتَ الْقُرْآنَ لِيُقَالَ: هُوَ قَارِئٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ، فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ وَسَّعَ اللَّهُ عَلَيْهِ، وَأَعْطَاهُ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ كُلِّهِ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: مَا تَرَكْتُ مِنْ سَبِيلٍ تُحِبُّ أَنْ يُنْفَقَ فِيهَا إِلَّا أَنْفَقْتُ فِيهَا لَكَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ فَعَلْتَ لِيُقَالَ: هُوَ جَوَادٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ، ثُمَّ أُلْقِيَ فِي النَّارِ. رواه مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي) *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Two_ ~*Page 5*~ Cike da tunanin abinda ke damun Salma Abdulkareem ya kwanta, dan har ya fara tunanin ko bata da lafiya ne, dan bai taɓa tunanin makamancin irin wannan saɓanin zai shiga tsakanin su da Salma ba, ko a mafarki bai yi ba.A haka cike da ɓacin rai bacci ya ɗauke shi. Kiran Sallar asubar farko a kunnen Abdulkarim, yana ji ya tashi daman baccin ya gundure shi, gefen gadon ya duba, wayam ba Salma, saɓanin yadda ya saba ganinta, idan bata jikin shi tana gefe, guntun tsaki yaja mai cike da ban haushi. Ɗakin yaran ya nufa a hankali ya buɗe kofar ya shiga, kwance ya ganta a tsakiyar yaran tana baccinta hankali kwance, ɗan murmushi yayi wanda bai kai zuci ba ya ce, "Allah ya baki lafiya Salma, idan wani abun ne yake damun ki, Allah yai miki maganin shi yasa ki gane gaskiya". Ya daɗe a tsaye yana kallon su, sai da yaji an kira sallah na biyu sannan ya juya ya tafi masallaci. Bayan ya dawo zai shige ɗakin su yaji motsin ta alamar ta tashi, murmushi yayi na taikaici, "wato shi kaɗai ta canja mawa, komai na halaiyarta yana nan". Ɗakin ya shiga ya fara shiri dan yau da wuri yake so ya fita, yana jin ta ita da yara suna ta hayaniyan su cikin walwala. Salma kuwa yana fita ɗaga ɗakin ta tashi dan yin sallah, abin yabi jikin ta, ana kiran sallah take tashi, ranta fes ta tashi tayi sallah sai dai tana tuno shi a ranta zata yi tsani cikin takaici. Bayan ta idar ta shiga kicin, indomie kawai ta dafa ma yara ita kuma ta dafa lipton ta soya ƙwai. Abdulkarim yana jin su ita da yara tana shirya su, bayan sun gama shirin makaranta su ka fito falo. Shi ma fitowan yayi da shirin shi na office, su Husna na ganin shi suka rugo suka rungume shi. "Ina kwana Abba?" "lafiya lau kun tashi lafiya?" Falon ya ƙarasa ya zauna ya ɗau Mussadiq yana mishi wasa. Ta gefen ido ta kalle shi tare da da kintsa fuskan ta sannan a hankali ta furta "Ina k'wana." Har ranshi baiji dad'in yanda tayi ba ammaya waske tare da qaqalo murmushi cike da kulawa ya dube ta. "Lafiya lau Madam, dafatan kin tashi lafiya?". Ya faɗa yana kallon ta, ciki-ciki ta amsa da. "lafiya lau." "Ina breskfast ɗina?". "Banyi da kai ba". Ta amsa a takaice tana kallon gefe. Kallonta yayi na yan dakiku kafin ya gyada kai. "Ok sai na dawo". Ya faɗa tare da miƙewa ya fita. Su Husna har ƙofa suka raka shi. *ASALIN SU.* Salma Ɗahiru Bala, shi ne cikakken sunan Salma, ƴar wani ƙauye ne dake yankin Kaduna ta yamma. Buruku ƙaramin gari ne, zaman lafiya da son juna shi ne ɗabi'ar mazaunan Buruku. Garin Buruku basu da wadataccen makarantun islamiya da na zamani, su kansu mutanan garin basu son karatun haka suke rayuwa tsangangan, sai ka ga babban mutu ko matashi amma bazai iya rubuta koda sunan shi ba, haka ta ɓangaren islamiya sun fi ba makarantar allo muhimmanci. Mahaifin Salma Ɗahiru Bala, mutum ne mai son ilimi a rayuwar shi, kasancewar shi bai yiba yasha alwashin yaran shi sai sunyi. Babban ɗan shi namiji wanda ya fara ɗaura burin akan shi, sai Allah yasa shi baya son karatun ko kaɗan, Ɗahiru yayi-yayi da shi har ya haƙura, sai mace mai bi mishi ita ma dai Ɗahiru baiyi ƙasa a gwiwa ba gurin ganin tayi karutu, nan ma abin yaƙi domin ita rayuwar bariki ta ɗaukar wa kanta, haka nan ya ƙara hukuri ya ɗau kaddara har ya cire rai akan burin shi da kudurin shi na son ganin yaran shi sun yi karatu. Salma ita ce ta uku a gurin iyayenta.Yarinya ce mai fasaha da basira, ga saurin ɗaukar abu, tun tana ƙarama take ba mutane mamaki dan duk abinda akayi a gabanta komai wuyar shi zata ɗauka. Ɗahiru ya fahimce hakan daga ƙareta saidai bai damu ba dan sauran ma haka suka taso da fasaha da kaifin kwakwalwa, duk da kasancewar tafi su. Salma tana da shekara goma wata ƙanwar mamanta taje da ita cikin garin kaduna, anan Salma taga yara na zuwa makaranta, sai son karatu ya shiga ranta. Suna dawowa kuwa taje ta samu baban ta maganar tana son ya sakata makaranta, wai ranar kamar Dahiru ya zuba ruwa a ƙasa ya sha dan murna da jin daɗi, tun a ranar yakai ta makarantar primaryn garin, aji ɗaya suka saka ta ganin ta ɗan girma. Salma kuwa ga son karatun gashi guru wa ce by nature, sai abin ya fara ba malaman mamaki jin abinda ake yiwa ƴan aji ukku Salma ta iya, ana koyar da su arabic a makarantar, ganin kaifin basiri irin na Salma yasa malaman suka kai ta aji huɗu. Ɗahiru kuwa yayi farin ciki ya kuma godewa Allah. Shekara huɗu da shigar Salma primary ta gama, nan Ɗahiru ya fara tunanin saka ta candy, Malaman suka bashi shawara da ya kai ta cikin garin Kaduna ta cigaba a can, dan na nan ɗin ba wani koyarwa sosai. Ɗahiru yana da yaya a cikin garin kaduna unguwar Sunusi, shi da kan shi yakai ta ya damƙa musu amana. Haruna shi ne yayan Ɗahiru uwa kawai suka haɗa da shi.Haruna ɗan kwangila ne yana da shi dai-dai gwargwado, mutum ne mai son mutane da mutunta su. Yaji daɗin zuwan Salma gurin shi dan yana son ɗan uwan shi,gashi daman yaran shi huɗu mata duk sunyi aure. Maryam matarshi ita har tafi shi jin daɗi da zuwan Salma dan Salma tana da shiga rai. Ba ɓata lokaci suka kai Salma makaranta haɗe da islamiya da bokon ma. Salma kuwa ta maida hankali sosai gurin karatun ta, sannan tana jin daɗin zama da su domin tamkar ƴar cikin su suka ɗauke ta, duk lokacinda suka samip hutu tana zuwa gida gurin iyayen ta. Cikin shekara uku Salma ta haddace izufi arba'in da biyar na al-qur'ani. Lokacin tana ta gama ji uku na candy.Mahaifin ta yaji daɗi matuƙa sanan ya godewa Haruna. Salma yarinya ce mai natsuwa ga hankali da zurfin tunani, ga riƙo da addini, way'annan halayen nata suke sa duk wanda ya zauna da ita sai ya ƙaunace ta. Tana da kyau dai-dai misali, irin manyan kyawun nan gareta, gata fara da yalwataccen gashin kai dana ido.Salma na da tsabta sosai komai nata acan-acan. Wata rana tana tafiya cikin shigar kayan makarantarta, hijabi ne ruwan madara sai wandon pink, cikin natsuwa take tafiya. Tun daga nesa Abdulkarim ya hangota, yanayin yadda take tafiya cikin natsuwa shi ya fara gani, sannan ya fita daga cikin motorshi. Yana kallon ta har ta samu abin hawa ta hau, bin su ya dinga yi har suka isa unguwar su, ta ba mai mashin ɗin kuɗin shi sannan ta ƙarasa, duk yana biye da ita bata sani ba, tafiya ƙatan tayi ta isa gidan su, yana ganin ta shiga gidan yayi parking, ya daɗe ganin ko zata ƙara fitowa da ya tabbatar gidan su ne, ya juya, cike da tunanin ta dan tun daga kallo ɗaya ta tafi da shi. Abdulkarim Khalil Yahaya shi ne cikakken sunan Abdulkareem, mazauna garin Kaduna ne a unguwar Mu'azu, anan aka haife shi kuma nan ne iyayen shi ke da zama. Shi ne Auta gurin iyayen shi yayyan shi duk mata ne su biyu,shi ma su ukku ne a ɗakin su.Yaro ne matashi mai jini a jika,kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar da hakan. Domin iyayen shi nada shi,a kamfanin baban shi yake aiki. Ga nutsuwa shi ma yasha addini ya ƙoshi domin ita Kaduna garin addini ce indai kana son yin ilimi zaka yishi,tamkar a misra,ga boko ga addini duk Abdukareem ya haɗa su shiyasa yake da gwarjini kamar zaki ga kyau,ga gata baya da matsalar komai a rayuwar shi. Kai tsaye gida ya nufa. Dama iyayen shi basu da burin da ya wuce ace Abdukareem yayi aure, sun mishi maganar ya ce bai samu wacce yake son ya aura ba ne, mahaifiyar shi Hafsa har ƴan mata take kawo mishi amma yace basu yi ba. Yana zuwa ya sanar da ita yaga wacce tayi mishi, sai farin ciki, kasa haƙuri mahaifin shi ya dawo gida suka yi,sai da suka kira shi suka sanar mishi. Abdul yayi mishi kwatancen gidan su Salma domin yaje ya nemar mishi auran ta. Shi ma mahaifin dan zumuɗi bai bari lokacin tashi yayi ba ya fito, yana zuwa gidan yasa akayi mishi Sallama da Haruna sai aka ce baya nan, yace anjima zai dawo. Bai koma gida ba sai da ya haɗu da Haruna, dukkan su sun yabawa juna ta ko'ina, musamman Haruna, dan irin mijin da yake son Salma ta samu kenan. Haruna bai ɓoye mishi komai ba akan ba shi ya haife Salma ba, har abinda yasa ta zo gurin shi, da matakin karutun ta, duk ya fada mishi, amma ya tabbatar mishi mahaifin ta bashi da matsala ko kaɗan, ya bashi izini ya fara zuwa idan suka amincewa juna sai a sanar da mahaifin nata. Har cikin gidan Abdul ke shiga suyi hira, ranar da Salma ta fara ganin shi zuciyarta ta kamo da son shi,nan da nan muguwar soyayya ta shiga tsanin su,kullum kwanan duniya sai sun haɗu,duk ranar da basu ga juna ba cikin su ba wanda zai iya barci. A SS two Abdul ya biya mata kuɗi ta zana jarabawar kammala candy, daman ya biya mata tayi jamb, dan shi kanshi yana son karatu, gashi Salma karutu shi ne abincin ranta, a lokacin ta haddace al-qur'ani gaba ɗaya, ita ta zo na ɗaya a musabaƙa, kyaututtuka kuwa tasha kuɗi sama da biliyan dan ko mahaifin Abdul rabin miliyan ya bata. Mahaifin ta Ɗahiru kuwa ranar sai da yayi kuka dan murna, ga labarin Salma ta samu miji, shi da kanshi yace a sa sati biyu, tabar makarantar haka tayi ta cika mishi burin shi Abdul ya nuna yana son idan sunyi aure yana son ta cigaba ta karatun ta, ba wanda ya hanashi. Anan aka shiga shagalin biki, ranar ɗaurin aure aka yi walima da wa'azi, tun ƙarfe biyar aka kai ta gidan mijin ta, daman ita ba ƙawaye gareta ba. Zaman so da ƙauna suke yi, Salma tana mutunta shi da girmama shi fiye da kowa a rayuwarta, haka shi ma, Salma ta samu gurbin karatu a KASU (Kaduna state university). Shekarata ɗaya da fara zuwa ta samu cikin Husna, Abdul yayi murna sosai dan shi mai son yara ne. Bayan Salma ta haifi Husna ta cigaba da karatun ta, Husna na da shekara biyu ta haifi Mussadiq, yana cika shekara ɗaya ta kammala karatun ta inda tayi short service. Taso yin aiki ya hana ta ta kuwa hanu domin bata musu da shi akan duk abinda ya ce mata, har lokacin suna zaman su cike da kulawa da kyautatawa, ganin zaman na mata yawa tunda ba makaranta, yara idan su ka fita makaranta tun bakwai basu dawowa sai shidda na yamma, yasa ta fara karatun littafin hausa, wannan shi ne dalilin sauyawar Salma lokaci daya, ganin mazan novel yanda suke yin dogon zango yayin mu'amalansu ta auratayya da matan su. A tunanin ta cutan ta kawai yake domin duk wani abu da zai iya shigan tsakanin su bai wuce awa d'aya a yayin da take ji a novel miji yakan kai sama da awanni 4-5 suna mu'amala da matan shi ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 Of Golden Pen Writers Association Team Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~✍ _~We Love U All~_❤ 🙆🏻🤷🏻‍♀ *_MENENE RIBA TA ❓_* 🤷🏻‍♀🙆🏻 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ *~ ✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽~* *~We are bearier's of so golden pen~*🖊 *~We write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say:* *"The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path [un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire."* *[Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)]* *عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: إِنَّ أَوَّلَ النَّاسِ يُقْضَى يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَيْهِ رَجُلٌ اسْتُشْهِدَ، فَأُتِيَ بِهِ فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ قَاتَلْتُ فِيكَ حَتَّى اسْتُشْهِدْتُ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ قَاتَلْتَ لِأَنْ يُقَالَ: جَرِيءٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ تَعَلَّمَ الْعِلْمَ وَعَلَّمَهُ وَقَرَأَ الْقُرْآنَ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: تَعَلَّمْتُ الْعِلْمَ وَعَلَّمْتُهُ، وَقَرَأْتُ فِيكَ الْقُرْآنَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ تَعَلَّمْتَ الْعِلْمَ لِيُقَالَ: عَالِمٌ، وَقَرَأْتَ الْقُرْآنَ لِيُقَالَ: هُوَ قَارِئٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ، فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ وَسَّعَ اللَّهُ عَلَيْهِ، وَأَعْطَاهُ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ كُلِّهِ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: مَا تَرَكْتُ مِنْ سَبِيلٍ تُحِبُّ أَنْ يُنْفَقَ فِيهَا إِلَّا أَنْفَقْتُ فِيهَا لَكَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ فَعَلْتَ لِيُقَالَ: هُوَ جَوَادٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ، ثُمَّ أُلْقِيَ فِي النَّارِ. رواه مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي)* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da sauke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene One_ *Page 6* Har Sahabat ta gama dafa abinci Ummi na zaune a guri ɗaya tana abu ɗaya, takaici ya kama Saha, ko magana bata mata ba, ta zubawa Surayya da Na'eef itama ta zuba. "Sahabat! ki zubo min abincin ki kawo min nan, na fara jin yunwa". Saha, wacce lokacin har ta fara cin abincin ta ja tsaki, "Oh Allah! wai ni Ummi in dai ina gidan nan bata taɓa bari na na huta ba? Abin na ta yayi yawa, komai Sahabat! Bata iya taɓuka komai sai zaman danna waya!". "Saha kina ji na?". "Gani nan", ta tashi ta fita cike da jin haushi, abincin ta zubo mata. "Yawwa Saha Allah ya miki albarka". "Amin". Kamar yadda ta saba bayan ta gama abinda zata yi, tayiwa Ummi sallama ta kulle ɗakin, kasancewar ita kaɗai ke kwana a ɗakin. Wayarta ta fito da shi ta kunna, tana kunnawa ta buɗe data ta shiga WhatsApp, saƙon Zaiyad ta fara dubawa. _"Kin dawo gida lafiya sweet?"_ _"Kewar ta dame ni, pls mu ƙara haɗuwa gobe kinji."_ Murmushi tayi tana ƙoƙarin yin reply wani saƙon ya shigo. _"Yau baki zo da wuri ba, ina ta jira har hankali na ya fara tashi"_ _"Srry sweet ban gama aiki da wuri ba ne, amma yanzun ga ni, any latest?"_ _"Sonki ya fara min yawa, tamkar na zauce, mu haɗu gobe, idan ban ganki ba zuciyata ciwo zata min"_ _"Ini sonka fiye da komai a duniya Zaiyad, ka turo gidan mu ayi magana."_ _"Na turo! waiyo daɗi, kash! yanzun matsalar Dady baya gari, amma ki ban nan da wata ɗaya, lokacin ya dawo."_ _"To Allah ya dawo da shi lafiya."_ _"Kina so na kamar yadda nake son ki kuwa.?"_ _"I love u! how many times kake son na faɗa u are my life."_ _"Den prove it! ke da ko kiss baki taɓa min ba"_ _"Idan kana so a shirye nake da aikata duk abinda kake so, wanda zai saka cikin farin ciki."_ _"Komai?"_ _"Uhm"_ _"To yanzun zamu haɗu goben ne?"_ _"Ba lallai ba, dan ba makaranta gobe, Ummi ba zata barni na fita ba, amma zanyi try insha allahu"._ _"Yawwa my love kiyi ƙoƙari tabarki dan ina matsanaicin son ganin ki, tamkar nayi tsuntsuwa na zo."_ _"Nima ina son ganin ka, ka san bana gajiya da kallon ka."_ _"Yanzun dai turomin photon ki masu kyau."_ _"Okkk my love."_ Tana fita ta buɗe saƙon Hunayda. _"ke fah ba mutunci gareki ba, mutum yai miki magani ki wani share, kuma kina gani sannan kin san dan ke nake tsayawa har wannan lokacin ban sauka ba."_ _"Sorry! Sahiba kin san idan muna chat da Zaiyad ne bana raba hankali na biyu."_ _"Kina da matsala Saha, ki rage wannan son fa, irin shi ne ake samun matsala."_ _"Ba wata matsala, kuma da kike cewa haka dan baki san irin son da yake min ba ne, ke kamar baki san so ba, ko da yake baki taɓa haɗuwa da wanda ya iya soyayya ba ne shi yasa."_ _"Hm! kinji ki, ba haka ba ne, yadda kowa yake ɗaukar abu ne, Zaiyad ɗin shi autan maza ne ko me? koma duk iyawar shi wani ya fi shi, ke ni dai yanzun turomin littafai masu daɗi."_ _"Naki wasa ne, bari wata rana zan haɗa ku dai ki ganshi, kina ganin shi zaki tabbatar," littafin Ni da shi da ƙauna ce ta tura mata._ _"Zaki iya karantawa kuwa?"_ _"Me zai hana.?"_ _"Littafan sun haɗu ne a ba dai daɗi ba."_ _"Shine bazan iya ba, sauran dana iya karantawa fa."_ _"Su daban ne, amma ki karanta, bari naje gurin love idan kin tafi to saida safe, raguwa kawai baza ki iya kai ɗaya kina chat ba."_ Photo nan ta tura mishi," Ga su my love." Saida ya gama ƙura ma hotunan ido yana jin wani abu a ranshi mai wuyar misaltuwa, lasar laɓen shi yayi, sanan ya ce; _"Wow! Sweet, kyawunki yana tsorata ni, Allah yayi halitta gaskiya, ke ko cikin su mata kinyi fice, kinga dirin ki kuwa! duk namijin da ya same ki yayi sa'a, za'ai dai mu kira shi ɗan baiyawa."_ _"Mijin na kuma, ai kai ne mijin nawa."_ _"Na gode sweet!"_ _"Na me?"_ _"Da kika ƙara tabbatar min da ni kike son na zama mijinki, ɗazun ban yarda da kika ce na turo ba, amma yanzun na yarda kuma na amince tabbas kina so na, kamar yadda nake son ki, ke ce muradi na."_ _"Sweet zaka fasa min kai da kalaman ka, wani irin so zan ma wanda bazan so ka zama uban ƴaƴanah ba..."_ Sai gurin uku da wani abu sannan ya barta ta kwanta. *Wacece Sahabat??* Zuwaira shine ainihin sunan Ummi, ƴar asalin jihar Kaduna ce, unguwar Rafin Gusa, su biyu ne gurin iyayen ta, ita ce babba sai ƙanin ta Zakari, kasancewar su biyu ne gurin iyayen su yasa tarbiyyar su da ilimin su bai wahalar da iyayen ba, dan suna da rufin asiri dai-dai bakin gwargwado, mahaifin ta ƙaramin ma'akaci ne na gwamnati, mahaifiyarta koyarwa take yi faramari. Zuwaira(Ummi)tayi karatu har gaba da sakandiri, ita da ƙaninta zakari. Isma'il Ridwan sunan mahaifin Sahabat, shi ma ɗan Kaduna ne, mahaifan shi duk sun rasu shi kaɗai yake gurin babban yayan mahaifin shi yake, wanda suke zaune a Abakwa, mutum ne kamili wanda ya san darajar mutane, kuma ya iya zama da su, rayuwa mai sauƙi yake yi, yana karatu kuma yana gyaran motor, domin rufawa kan shi asiri da wanda yake gurin shi. Bayan ya kammala karatun shi ya samu aikin gomnati, shekarar shi biyu da samun aiki ya haɗu da Zuwaira, taje bikin wani abokin shi, nan da nan suka amince wa juna, soyayya da shaƙuwa ta shiga tsakanin su. Ya turo magabatanshi aka yi maganar aure, lokaci nayi aka ɗaura auran Zuwaira da Isma'il. A Kurmin Mashi suka zauna, unguwar su Hunayda tazara kaɗan ne a tsanin gidajen su. Zaman lafiya da soyayya Zuwaira da Isma'il suke yi, suna nuna wa juna soyayya da kulawa, bayan shekara ɗaya da rabi da yin auran su aka haifi Sahabat, cikin so da ƙauna Sahabat ta taso gurin iyayenta.Sahabat na da shekara uku da rabi aka haifi Suraiyya, soyayya da shaƙuwa irin da wa da ƙani ke tsanin Sahabat da Suraiyya. Bayan haihuwar Suraiyyah da shekara uku da rabi aka haifi Na'eef. Yara sun fara tasowa cikin tarbiya ta kulawar iyayen su, rana ɗaya kwasam Isma'il yayi haɗarin motor Allah ya amshi abinshi, lokacin Na'eef na da shekara shidda, lokacin ita kuma Sahabat na da shekara goma sha huɗu tana aji uku na secondry. Sun yi kuka iya iyawar su, Saha da Suraiyya su na da wayo, Na'eef ne bashi da waiyo a lokacin. Rayuwa ta sauya musu, gonmati na biyan su kuɗi duk wata, shi yasa basu samun wata matsala ɓangaran amfanin kuɗi, sannan Zakari yana taimaka musu, haka iyayen ta, basu da wani matsala ta bangaran kuɗi sai dai kewa. Tun daga wannan lokacin Ummi ta fara rubutu na littafan hausa ta online, bata da kunyar rubuta batsa a littafin ta ko kaɗan, bata tunanin abinda hakan zai haifar mata a gaba, ɓaro-ɓaro take baiyana komai na rayuwar ma'aurata. Tunda ta fara rubutun nan rayuwarta ta sauya gaba ɗaya, bata kula da komai sai wannan rubutun, gaba ɗaya hankalin ta da natsuwarta duk ta ba rubutu. Ummi tana mugun son Saha a rayuwarta, shi yasa duk yadda rubutu ya shagalartar da ita bata manta da kula da kiyayewa akan Saha ba, bata barin ta da wata ƙawa sai Hunayda, bata barin ta fita idan ba makaranta ba, sai gidan su Hunayda, shi ma ba kasafai ba,Tsoron kar ruɗin Zamani yaja Saha yasa Ummi ta hana ta riƙe waya. Sahabat; kyakyyawa ce dai-dai iya kyau tana da shi, tana da idanu wanda shi ya ƙara mata kyau, ita ba baƙa ita ba fara ba, amma tafi Hunayda haske kaɗan, da tsawo shi ma idan ba a jere ka gansu ba baza ce ta fi ta ba, tana da ƴar qibarta dai-dai ba can ba, dan ta wuce a kira ta siririya, kuma bata kai a kira ta mai qiba ba, tana da zati dai-dai bakin gwargwado. Sahabat Yarinya ce mai son ado da shigar yayi, tana da tarbiyya da girmama mutane, amma tana da tsiwa da rashin haƙuri da juriya, wannan halin ne yasa ba zaka ce tana da tarbiyya ba, ga surutu kuma bata son raini, tana da son girma, ban-bancin su da Hunayda kenan, dan ita Hunayda tana da tsoro kuma tana da hakuri da kau da kai. Wannan halin yasa Saha idan ta ya buɗe na rashin tsoro, takan aikata duk abinda taji ranta yana son aikatawa.Ƴar soyayya ce, bi ma'ana tana son soyayya tun kafin ta fara soyayyah, film ɗin soyayyah yake birgeta, raguwar zuciya gareta, ma'ana mai saurin yadda da amincewa akan duk wani shafa larabi shuni, shi yasa Zaiyad yai saurin kama ta da maganganun shi, ko na ce shafa larabi. Wata rana Ummi ta aike ta unguwar su, akan hanyarta na dawowa ta haɗu da Zaiyad a mator shi, ya ɗauko ta, tun kafin Zaiyad ya ce yana son ta,ya shiga ranta, dan a tsarin Saha tana son namiji ɗan gaye wanda ya iya wanka kuma mai kyau, shi kuwa zaiyad duk ya haɗa su. Tun kafin ya sauke ta ta sake mishi fuska, ko da ya tambaye ta zai samu damar zuwa gidan su idan dare yayi, ta ce mishi ba'a barin ta fita, ta gaya mishi inda zasu haɗu gobe, zata fito idan zata makaranta sai su haɗu. Bayan ta amince mishi, suka fara zuba soyayya, Saha na son Zaiyad sosai a rayuwarta, shi ne first love ɗin ta, daga nan ya sai mata waya a ɓoye, suna fita yawo irin wanda masoya ke yi, duk wanan abun Ummi bata sani ba. Tun asuli Saha tana da sha'awa amma tana haƙuri da juriya, wayar da Zaiyad ya siyan mata ne ta fara WhatsApp, a inda ta fara karanta littafan hausa, sai abun ya tsanan ta, akan littafin *Ni da shi*, wanda mahaifiyar ta, Ummi ta rubuta, wanda yanzun takan gamsar da kan ta. _~We Love U All~_✍ [1/13, 9:12 PM] Masha Allah 👏🏽: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:* *"A prayer performed by someone who has not recited the Essence of the Qur'an (1) during it is deficient (and he repeated the word three times), incomplete."* *Someone said to Abu Hurayrah: [Even though] we are behind the imam? (2)* *He said: Recite it to yourself, for I have heard the Prophet (may the blessings and peace of Allah be up on him) say:* *"Allah (mighty and sublime be He), had said: 'I have divided prayer between Myself and My servant into two halves, and My servant shall have what he has asked for. When the servant says: 'Al-hamdu lillahi rabbi l-alamin' (3), Allah (mighty and sublime be He) says: 'My servant has praised Me.' And when he says: 'Ar-rahmani r-rahim' (4), Allah (mighty and sublime be He) says: 'My servant has extolled Me,' and when he says: 'Maliki yawmi d-din' (5), Allah says: 'My servant has glorified Me' - and on one occasion He said: 'My servant has submitted to My power.' And when he says: 'Iyyaka na budu wa iyyaka nasta in' (6), He says: 'This is between Me and My servant, and My servant shall have what he has asked for.' And when he says: 'Ihdina s-sirata l- mustaqim, siratal ladhina an amta alayhim ghayril-maghdubi alayhim wa la d-dallin' (7), He says: 'This is for My servant, and My servant shall have what he has asked for.'"* *(1) Surat al-Fatihah, the first surah (chapter) of the Qur'an.* *(2) i.e. standing behind the imam (leader) listening to him reciting al-Fatihah.* *(3) "Praise be to Allah, Lord of the Worlds."* *(4) "The Merciful, the Compassionate."* *(5) "Master of the Day of Judgement."* *(6) "It is You we worship and it is You we ask for help."* *(7) "Guide us to the straight path, the path of those upon whom You have bestowed favors, not of those against whom You are angry, nor of those who are astray."* *[Muslim (also by Malik, at-Tirmidhi, Abu-Dawud, an-Nasa'i and Ibn Majah)]* *عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: مَنْ صَلَّى صَلَاةً لَمْ يَقْرَأْ فِيهَا بِأُمِّ الْقُرْآنِ، فَهِيَ خِدَاجٌ ثَلَاثًا، غَيْرَ تَمَامٍ، فَقِيلَ لِأَبِي هُرَيْرَةَ: إِنَّا نَكُونُ وَرَاءَ الْإِمَامِ، فَقَالَ: اقْرَأْ بِهَا فِي نَفْسِكَ، فَإِنِّي سَمِعْتُ النبي صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ:{ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ } قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:{ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ } قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: أَثْنَى عَلَيَّ عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:{ مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ } قَالَ اللَّهُ: مَجَّدَنِي عَبْدِي - وَقَالَ مَرَّةً: فَوَّضَ إِلَيَّ عَبْدِي، فَإِذَا قَالَ:{ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ } قَالَ: هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ:{ اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ } قَالَ: هَذَا لِعَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ. رواه مسلم (وكذلك مالك والترمذي وأبو داود والنسائي وابن ماجه)* ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ *_Scene three _* ~*Page 7*~ Tun da ya isa gurin aikin shi ya ke tunanin me yayi mata take mai irin wannan azabar har da wani canza gurin kwana, amma tunanin shi ya kasa gane wani irin laifi ya aikata da zai fuskanci wannan hukuncin daga gure ta, haka dai ya gama tunanin shi, ya k'udurce yau idan yaje gida zai lallab'ata ko zata fad'a masa laifin da yayi mata. Ita kuwa tana can sai faman karatu take yi tana dad'a jin tsanar shi na shiga ranta, musamman ma idan aka zo wannan fannin, gani take kamar ba rayuwar aure su ke yi ba. A b'angaren Saha kuwa ta kai kusan 6:00 tana bacci, vibration d'in wayar ta shine ya farkar da ita, ko ba a fad'a mata ta ba ta san sahibul qalb d'in ta shi yake kiran ta, don idan ba shi ba babu wanda yake kiran ta sai dai chatting. Cikin bra d'inta ta kai hannu tare da zaro wayar ta kara a kunnen ta. "Hello sweet heart kin tashi ma kuwa?". Cikin bacci bacci ta ce, "Uhmmm yanzu dai ka tashe ni". Lumshe idon sa yayi saboda wani mugun feeling din ta da ya taso mishi. "Kai wannan yarinyar zata kashe ni". Ya fad'a can k'asan mak'oshin sa. "Baby na, me ka ce?". "Babu abunda nace, ki tashi kiyi sallah mana in yaso sai mu cigaba da wayar, ko ki hau online saboda ina son kasancewa tare da ke Saha". Babu wani kunya ta ce, "Baby ina yin period ne, bari kawai na zo online d'in". Tuni ta murje idon ta don yin chatting da Zaiyad, amma tana kunna data taji Ummi na kwalla mata kira. "Saha wai baki ji ina kiran ki bane!? Kiyi sauri kizo ki d'aura breakfast su Sumayya su shirya, kada su makara zuwa makaranta!". "Innalillahi! Ai shikenan kuma na shiga uku, garin ya waye kenan anyi ta k'walla maka kira ana sa ka aiki, gaskiya na fara gajiya, haba! Kai kenan aiki kamar machine fisabillilahi, mtwssss!". Ta ja uban tsaki had'e da durowa daga saman gadon ta nufi k'ofar fita. Nan da nan ta had'a musu breakfast ta zubawa kowa na shi sannan ta zuba musu wanda za su tafi makaranta da shi, har Ummi ta zubawa don ta san indai bata zuba mata yanzu ba ta dinga kwalla mata kira kenan. "Aa'a'a 'yar albarka! Kice har kin gama had'a breakfast, sannu Saha!". "Uhmm har na gama had'awa, ga naki nan ni zan shiga ciki nayi wanka". "Kai Saha tun yanzu zan ci kuwa?". Tayi maganar tana kallon wayar ta. "Eh ni dai Ummi gashi nan na zubo zan wuce". "To shikenan babu matasala, sannu da aiki yaya Saha". Ta fad'a saboda ta ga yanayin yarinyar kamar ya d'an sauya, ita kanta ta san Saha tana k'ok'ari a gidan ba na wasa ba, shi yasa idan tayi wani abun kawai take d'an share ta. Tana shiga d'aki ta ciro wayar daga k'asan kayan ta wanda tun da zata fita ta danna ta silent, nan take ganin miss calls d'in Zaiyad, wajen 10 mis calls yayi mata. "Allah sarki love d'ina am really sorry", ta fad'a tana kwab'e fuska irin cikin shagwab'ar nan, nan ta kunna data suka fara plan d'in yadda za su had'u. ***** Ita kuwa Hunayda tunda Saha ta turo mata littafan ta fara karantawa, ba ita tayi bacci ba sai gurin 1 din dare sannan ta samu runtsawa, wajen 4:30 ta tashi daga bacci, ganin lokacin Sallah bai k'arasa ba ya sa ta janyo wayar ta ta cigaba da sana'a, dan littafin ji take kamar kar ta daina karanta shi. Ni kuwa nace tabbb! irin wannan abu haka tun kafin ma ayi sallah, Allah ya shiryar mana da zuri'a. Bayan tayi sallah ne ta d'an koma bacci, bata dad'e da kwanciya ba sai ga Hajna ta shigo cikin d'akin. "Aunty! Aunty! Ki tashi Ammi na kiran ki". Wani juyi tayi tare da buga wani uban tsaki tace; "To naji kar ki ishe ni malama, ga ni nan zuwa, haba mana sai wani kwalla mun kira kike yi". Hajna wanda take sanye cikin uniform d'in makaranta ta keb'e baki had'e da barin d'akin. "Hunayda wai wani irin bacci kike ki yi har Hajna ta tashi ta fara shirin tafiya makaranta amma ke kina kwance kin barta da komai ko, kin san dai kafin na sallami Abban ku daga ciki kamata yayi ace kin taya ta ta shirya saboda kar ta makara, amma ina! kina can kina bacci ko, k'ila ma baki yi bacci da wuri ba wallahi!". "A'a Ammi ba fa haka bane, kaina ne yake yi min ciwo shi yasa ban tashi da wuri ba na d'an kwanta bacci". "AI dole kanki yayi ciwo tunda baki da aiki sai na kallon waya, sha-sha-sha kawai! Wallahi na kusa fara k'wace wayar nan idan dare yayi, don na fuskanci a 'yan kwanakin nan ba kya yin bacci da wuri!". "Ammi don Allah kiyi hak'uri ina fa yin bacci da wuri". Bayan sun gama duk abunda suke yi, Hunayda ta taya Ammi suka gyara gidan yayi tasss da shi sannan suka yi breakfast d'in su, suna gama tace wa Ammi bari taje tayi wanka, tana shiga d'akin ta d'au wayar ta aka cigaba da sana'a wato karatun littafi. Can edge d'in gadon ta na hango ta ta wani cure guri d'aya sai lumshe ido take yi (ni kuwa nace da zan iya sai naga me ake gani haka). Dropping wayar tayi tare da had'e kai da gwiwa ta k'ara curewa guri d'aya ta ce; "Wayyo Allah ciki na! Na shiga uku ni Hunayda me nake gani, dama haka ake yi? Tabbbd'ijan! Shegiya Saha, dole ta ce zan iya karantawa? Ashe al'amari ne a cikin littafin, anya zan iya cigaba da karantawa kuwa, idan ba haka ba sha'awa zata kashe ni wallahi". Wayar ta d'auka tare da fita daga gurin karatun ta bud'e data, ai kuwa tana hawa taga Saha na online, ta fara yin typing kamar haka; "Shegiya, dama na san kina online ana tare da Zaiyad ko? Ke dama haka littafin nan yake? Tabbd'ijan, gaskiya writer d'in shegiya ce ta iya rubutu sosai wallahi, ke amma fa wani abun ma wallahi ban san haka ake yin shi ba sai yau!". Sai da ta d'au kusan 10 minutes sannan tayi mata reply. "Wallahi kuwa kamar kin sani muna tare da shi, hmmm ai dama sai da na fad'a miki zaki iya karantawa saboda littafin na manyan yara ne". "Gaskiya kam bafa ta b'oye komai, komai fito da shi take yi". "Eh mana, yanzu a ina kike?" "Ina gurin da suka yi aure mana, har sun tafi Dubai ma". 😳"Kai wai har kin kawo nan wai?". "Eh mana ke jiya har wajan 1:30 fa ina karatu, kuma ina tashi na d'ora". "Gaskiya ne, kina k'amshi ina bin ki da humra, shegiya kice abun ba wasa!". "Ke, amma fa gaskiya ina jin daina karantawa zan yi, ke kin ji wani mugun sha'awa da nake ji kuwa? Kamar na mutu, gaskiya bari zan yi, wai, ina bazan iya ba!". "Ke dalla can banza, ba sai ki rik'a samarwa da kanki nutsuwa ba, kuma wallahi kada ki bar wani karantawa, ai gwara ki san komai yadda kawai idan kika je gidan miji kin san yadda zaki sarrafa shi, ai ni wallahi na k'agu ayi maganar mu da Zaiyad yaga yadda ake love". "Kamar ya samarwa da kaina nutsuwa kuma?". "Mtsww ke fa banza ce, ki bari idan mun had'u zan fad'a miki yadda zaki dinga yi". "Okk tom shikenan ba wata matsala, sai mun had'un, bari na shiga wanka". "okk tom bye". **** Da misalan k'arfe d'aya da rabi na rana Saha ce sanye cikin uniform d'in islamiyya, babu komai a fuskar ta sai lipstick da ta shafa, ta kuma saka kwalli, hijab d'in ta saka sannan ta fito daga d'aki rike da jakar makaranta a hannun ta, can ta hangu Ummin su tana ta faman danna waya. "Kai wai ita Ummi kullum cikin danna waya, bata da lokacin da zata ware yin wa'innan sabgogin nata, amma ace mutum kullum abu d'aya, mtswww!". Note:plss iyayen yara writers da wa'inda ma ba writers ba kai har ma da riders plsss mu dinga ware lokacin da zamu dinga yin abubuwan mu, mu bari sai mun gama duk wani responsiblity namu na cikin gida kafin mu hau online, ku shiga wps don karatu ko kuma typing, ko karatu online plsss....wallahul musta'an Allah yasa mu dace AMIN ya Allah. "Ha'a Saha naga yanzu fa d'aya da 'yan minutes amma har kin fito?". "Eh zan biya gidan su Hunayda ne kafin mu shiga makarantar, saboda zata koya min wani karatu da aka yi mana jiya, gashi an bada assingnment kuma ban yi ba". "To bari sai su Na'eef sun dawo daga makaranta zuwa 2:30 sai ku wuce gidan su Hunaydan tare ko?". "A'a Ummi sun tawo daga baya, aikin fa yana da wahala". "To ai gani nayi sai kun yi sallar la'asar kuke shiga shi yasa". Tana fad'in haka messege ya shigo cikin wayar ta, tuni ta manta da sha'anin Saha, sai da ta gaji da tsayuwa sannan ta ce, "Ummi na tafi?". "To Saha sai kin dawo, su Surayya sun tawo daga baya". Tana fita ta hango car d'in shi a can k'arshen layin su, da sauri ta k'arasa, tana zuwa ya bud'e mata ta shiga, ya rufe ya ja su suka tafi. "Yanzu baby na ina kike so mu je?". "Uhmm... duk inda muka je ai babu matsala". "To muje gida na kenan?". "Gidan ka kuma? Gaskiya A'a, kawai dai mu je wani gurin shak'atawa haka, ko da Gamji ne tunda ai hira kawai zamu da'n tab'a". Hannun shi ya d'ora kan nata yana murzawa ya ce, "Amma dai baki manta da alk'awari ba dai ko?". Ji tayi gaba d'aya jikin ta ya mutu, ga wata muguwar sha'awa da ta taso mata, cikin ranta take ayyana; "Dama haka ake ji?! Tabb, ashe dai gaskiyar Ummi ana jin dad'i sosai". D'ago da idon ta da suka fara canza kala tayi ta kalle shi ta ce, "Ban manta ba baby na ina sane". Itama ta d'ora dayan hannun ta kan nashi tana murzawa. "Shegiya wallahi ta kamu, wannan baza tayi wahalar shigowa hannu ba". "To yanzu mu wuce gidan nawa?". "Ba..by duk..yadda..ma kayi dai-dai ne". Ta fad'a in a lustfull tone. Wani smile ya saki tare da juya kan motar shi su kayi gidan na shi. Suna isa ya shiga ya bud'e musu sannan ya dawo suka shiga cikin gida, yayi parking car d'in shi inda ake ajiye motor. "Tom remember my promise dai gaskiya". "Amma bazan shiga ciki ba gaskiya". Don kar tayi tunanin wani abu yasa ya ce; "To shikenan ba matsala, amma mu koma bayan mota". ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [1/13, 9:14 PM] Masha Allah 👏🏽: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:* *"Allah (mighty and sublime be He) says:* *'The first of his actions for which a servant of Allah will be held accountable on the Day of Resurrection will be his prayers.' If they are in order, then he will have prospered and succeeded; and if they are wanting, then he will have failed and lost. If there is something defective in his obligatory prayers, the Lord (glorified and exalted be He) will say: 'See if My servant has any supererogatory prayers with which may be completed that which was defective in his obligatory prayers.' Then the rest of his actions will be judged in like fashion."* *[At-Tirmidhi (also by Abu Dawud, an-Nasa'i, Ibn Majah and Ahmad).]* *عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ عَمَلِهِ صَلَاتُهُ. فَإِنْ صَلُحَتْ فَقَدْ أَفْلَحَ وَأَنْجَحَ، وَإِنْ فَسَدَتْ فَقَدْ خَابَ وَخَسِرَ، فَإِنْ انْتَقَصَ مِنْ فَرِيضَتِهِ شَيْءٌ، قَالَ الرَّبُّ عَزَّ وَجَلَّ: انْظُرُوا هَلْ لِعَبْدِي مِنْ تَطَوُّعٍ فَيُكَمَّلَ بِهَا مَا انْتَقَصَ مِنْ الْفَرِيضَةِ، ثُمَّ يَكُونُ سَائِرُ عَمَلِهِ عَلَى ذَلِكَ. رواه الترمذي وكذلك أبو داود والنسائي وابن ماجه وأحمد* ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* *♣scene three * *page 8* Car d'in ya bud'e suka fito a tare, nan ya bud'e mata bayan motar ya ce; "You are welcome, her majesty". Wani irin dad'i taji saboda yadda yayi maganar ba k'aramun fasa mata kai yayi ba, shiga tayi ta zauna tare da sakin wani deep breath (Abun ka da sabon shiga farkon yi). Zagayawa yayi shima ya shiga ya zauna yana fuskantar ta. "Sahabat!", ya kira ta da full name d'in ta, dararan oily eyes d'in ta zuba mai tace "Na'am baby na me ya faru?". "Ina mugun bala'in sonki, zan iya aikata komai akan ki, zan yi miki duk wani abu da kike so, hope dai kema kina so na haka?". Ya k'arashe maganar yana d'ora hannun shi kan kolumatun ta na gefe d'aya. Hanu takai kan nashi tace; "Love! nima ina yi maka irin son da kake yi min, kai zan iya ce maka ma nafi son ka Zaiyad, you are my every thing, plsss stay with me muyi spending life time d'in mu together". "Shegiya, ko ba life time ba I will spend my life time da ke amma ba na aure ba". Ya fada a cikin zuciyarshi. A fili kuma ya ce; "Why not baby, ai kawai kiyi tunanin mun fara spending life time d'in mu". Ya fad'a had'e rungumota jikin shi, wani sabon hali taji ta tsinci kanta a ciki, saboda yau ne na farko da namiji ya fara yi mata haka, amma da yake giyar soyyaya na d'iban ta haka ita ma tayi hugging d'in shi har da su Ilove you my sweety. D'ago da face d'in ta yayi ya fara dosar fuskar ta da niyar kissing d'in ta, amma ko k'okarin hana shi ba tayi ba, shi kuwa tuni ya k'arasa ya had'e bakin su guri d'aya yana zuba mata sihirtaccen kiss, ita kuwa hajiya Saha sai sauke numfashi take tana jin zuciyar ta na mata nauyi har ta fara tafiya bata ma san inda kanta ya ke ba, zip d'in ta yake k'okarin ziping ta hango time ta cikin agogon mota wanda yake mak'ale a jikin radio na motor, ai bata san lokacin da ture shi ba ta ce; "3:30 yanzu Zaiyad, kuma ka san sai na biya ta gidan su Hunayda kafin na wuce". Kallon ta yayi da shanyayyun idon sa ya ce, "Ha...ba.. ma...na.. Saha you and your islamiya abubuwa, let have fun mana". "A'a ka bari sai next meeting". Ta fad'a had'e da durowa daga motar ta koma gidan gaba tana gyara hijab d'in ta, haka nan shima ya koma gurin zaman driver ya zauna yana maida numfashi, ba yaso yayi forcing d'in ta, ya fiso yayi komai da ita cikin had'in kanta shi yasa kawai ya rabu da ita. Suna isa kusa da layin su Hunayda ya sauke ta, ai kuwa tana fitowa ta hango Hunayda can tana tahowa itama da kayan islamiyya jikin ta, nan ta jira ta ta k'araso. "Hmmmm! Saha kenan yauma anyi sana'a, ni dai zan ga ranar da zaki daina sneaking d'in fita, me ye naga kin yi wani furgaifurgai da ke?". "Hmmmm ke dai bari, ai sai mun zauna, wannan zancen Hunayda na samun natsuwa ne". Suna tahowa na hango wani d'an matashi wanda bazai wuce shakara 29 zuwa 30 ba, dogo ne kuma yana da haske amma ba sosai ba, kuma yana da kyaun shi na dai-dai misali, shi ba mai irin asalin kyaun nan ba kuma ba mai muni ba da bulala rik'e a hannun shi da alama malamin makarantar ne. "Su Saha da Hunayda yau an makara, don haka dole ayi muku dukan makara". Ya fad'a in a jokeful way yana kallon fuskar Hunayda. "A'a malam mun zo dai a dai-dai, bamu makara ba". "Ya akayi k'anen ku suka riga ku zuwa toh? "Kawai muna tahowa ne babu komai". Duk maganar nan da ake yi Saha ce ke yi amma ita Hunayda ba abunda ta ce, nan yace musu idan aka tashi kafin su tafi gida yana son magana da Hunayda, amsa mishi da to suka yi kafin su wuce aji. "Ke anya kuwa malama Suhail ba son ki yake yi ba?", "Hmmm ke dai bari nima na ga alama". "Tabbb me zaki yi da malamin islamiyya,Allah ya kauta!". "Allah ko ?". Ta fad'a in I don't care manner. Haka dai suka cigaba da hirar su har suka shiga aji... ************ Bayan an tashi su Hunayda daga makaranta, nan malam Suhail yake fad'a mata shi son ta yake yi kuma da aure, don haka zai zo gida yayi magana da Abban ta idan ta amincie, zata je tayi tunani tace mishi. Su Hajna da Surayya da kuma Na'eef sune a gaba, while Saha da Hunayda suna bayan su. "Tabbb! ai wallahi kar ki yadda, wannan d'an k'auyen zaki yi soyyaya da shi, ko d'an zuwa outing d'in nan baza ku ri'ka zuwa ba, tabb! gaskiya ban goyi bayan haka ba, ina da sake!". "Saha amma kuma ai yana da hankali, kuma babu ruwan shi he is so silent, kuma ko ya ce zai je outing d'in da ni ai kin san bazan iya zuwa ba, besides, bance miki na yadda ba tukunna don haka ki daina damun kanki sai nayi tunani. Ke ba ma wannan ba, fad'a mun yadda zan dinga yi idan naji sha'awa". Kunnen ta Saha ta kamo ta fad'a mata abu a kunne wanda ni ban samu damar jin shi ba. "Kai! Allah kuwa Saha?". "To ba sai ki tsaya wasa ba, hmmm kin san yau Zaiyad har kissing d'ina yayi". "Me ne! kissing fa Sahabat!". "EH man....". "Yaya Saha don Allah kizo mu wuce gida, kusan fa magrib ake k'ok'arin kira". "Eh wallahi ya Hunayda ku zo mu tafi plss". "To jarabbabu har da wani kusan had'a baki, sai ku wuce mu tafi ai". Inji Saha tayi maganar a irin kar ku dame mun nan. Nan suka yi hanyar gida, dama anzo kan kwanar rabuwa amma hira ta k'i k'arewa. "Saha wai a ina kuka tsaya yau ne? ina ta jira ku dawo gashi ni ko abinci ban d'ora ba". Surayya ce ta ce, "Mun taho suka tsaya a kan kwana ita da Aunty Hunayda suna ta hira". "Yanzu Saha duk hirar da kuka sha tun d'azun sai da kuka tsaya hira akan hanya?". Don ta kawar da zancen ya sa ta ce; "me za a dafa don tasan dole ita zata dafa,nan.ta shiga kitchen ta fara shirya musu abunda za su ci. A b'angaren su Hunayda ma sai da Ammi tayi musu fad'a amma sai dai ita har ta gama abinci ta ajiye ta gama komai nata, gida yayi tsaf da shi(ni kuwa na ce ko don ita mai miji ce, kai amma anya, kawai dai ma tana da kula ne). *********** Zaune take a palo ta sha riga da siket d'in ta na atamfa wanda ya karb'i jikin ta, sun zauna dass sunyi mata kyau sosai, rik'e take da mug da alama dai na'ana'a tea ne a ciki while yaran suna daga gefe suna cin abinci ga kuma mbc 3 an saka musu suna kallo,ita kuwa sai faman danna waya take yi ,bayan sun k'oshi abunka da hali irin na yara har suka fara wasa da abincin, amma Salma bata san halin da ake ciki ba tayi nisa wurin karanata *NIDA SHI* sai wani sakin smile take yi. Yana shigowa tun kafin ya bud'e bakin shi yayi sallama ya ga sun yiwa palon kaca kaca da shinkafa, ga duk sun burkita palon sai wasa suke yi, ita kuwa hakima bata san wainar da ake toyawa ba, kallon inda take yayi yaga gaba d'aya ma bata san ana yi ba, wai kunu a mak'ota. Sallama ya fara yi amma sai da yayi sau biyu kafin ta jiyo, shima har sai da yaran suka fara oyoyo abba sannan ta d'ago firgit ta kalle shi. Yau kam ta k'ular da shi, ko kallon inda take bai yi ba yayi shigewar shi, ita ma nan ta juya had'e da keb'e baki, mai da kai tayi zata cigaba kamar ance ta kalli d'akin ta ganshi yayi kaca-kaca. "Innallillah dama haka yaran nan suka yiwa wajan nan?". Bata gama tamabayar kan ta ba taji ya ce; "Salma ina abinci na, don yunwa nake ji". Yau kam yaci sa'a an dafa da shi, (ni kuwa na ce ko dai shauk'in novel ne😜) "Ka shiga kitchen akwai a tukunya sai ka zuba". Tayi maganar kamar ba ita tayi ba, ta maida kai ta cigaba da abunda take yi. "Gurin nan kuma wa zai gyara shi, wai shin Salma me kike yi ne ma a jikin wayar nan da ina miki magana kina ji na, kin mai dani d'an iska a cikin gidan nan, ko don kinga ina kyale ki ne iye!!!". Da sauri ta juyo ta kalle shi don jin yadda ya d'aga murya, don ita ba don kar ace tayi k'arya ba da sai tace bata tab'a ji yayi mata magana irin yadda yayi mata yau ba. Tana k'unk'uni ta tashi ta shiga kitchen ta zuba mai abincin tazo ta dongwarar da abincin kafin ta tattare gurin, sannan ta samu guri ta zauna tana fad'in, "Duk abi a takura mutum, bayan bayi mai abunda ya kamata ake yi ba, kalli fa ji yadda ake love", ta fad'a tana kalon wayar ta kamar ba ita tayi maganar ba. Shi kuwa kawai kallon mamaki yake yi mata yana mamakin, " Me yasa ta fad'an haka?me take nufi da shi? duk kular da yake bata". "Amma just ko d'an two hours d'in nan baza a iya da kai ba, babu wani armashin arzik'i!", ta fad'a tana mik'ewa da alamar d'aki zata shiga, wucewa tazo yi ta inda yake zaune, yayi saurin rik'o hannun ta ya ce; "SALMA wai me ke faruwa ne? me nayi miki wanda baza ki iya fad'a mun ba sai dai kiyi ta mun habaici kamar ba zaman aure muke yi ba?". "Ni kawai ka sake mun hannu don ko na fad'a maka ba iya yi mun zaka yi ba, don haka kawai a barshi!" ta fad'a tana fuzge hannun ta. "Gaskiya baby yau ba k'aramun burge ni kika yi ba, kin nuna kina so na kuma naji dad'in haka, amma plss gobe ma zamu had'u ko?". Gyara zaman wayar tayi a kunnen ta ta ce, "Ummm anya kuwa bana jin Ummi zata barni na fita gobe, saboda na fita da yawa a 'yan kwanakin nan kuma bana so ta fara zargin wani abu". Jin foot steps a guraren k'ofar ta ne yasa tayi saurin saka wayar cikin bra. Ai kuwa ji tayi Ummi ta ce, "Saha lafiya kuwa naji kamar kina magana". Ta fad'a tana turo k'ofar d'akin. "Wayyo Allah na Ummi wallahi cinnaka ne ya ciji ne shi yasa nake ta mita". "Cinnaka kuma a d'akin nan, me ya kawo shi toh? Ko da yake yanzu kaka ce babu mamaki ma idan an gansu, sai ki shafa maklin k'ila ya rage zafi". "To Ummi, zan shafa" "Yauwa ga doya can na fere miki ki tashi da wuri ki had'a musu breakfast..... ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [1/15, 11:00 AM] Sumayya Sumy B: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:* *"A prayer performed by someone who has not recited the Essence of the Qur'an (1) during it is deficient (and he repeated the word three times), incomplete."* *Someone said to Abu Hurayrah: [Even though] we are behind the imam? (2)* *He said: Recite it to yourself, for I have heard the Prophet (may the blessings and peace of Allah be up on him) say:* *"Allah (mighty and sublime be He), had said: 'I have divided prayer between Myself and My servant into two halves, and My servant shall have what he has asked for. When the servant says: 'Al-hamdu lillahi rabbi l-alamin' (3), Allah (mighty and sublime be He) says: 'My servant has praised Me.' And when he says: 'Ar-rahmani r-rahim' (4), Allah (mighty and sublime be He) says: 'My servant has extolled Me,' and when he says: 'Maliki yawmi d-din' (5), Allah says: 'My servant has glorified Me' - and on one occasion He said: 'My servant has submitted to My power.' And when he says: 'Iyyaka na budu wa iyyaka nasta in' (6), He says: 'This is between Me and My servant, and My servant shall have what he has asked for.' And when he says: 'Ihdina s-sirata l- mustaqim, siratal ladhina an amta alayhim ghayril-maghdubi alayhim wa la d-dallin' (7), He says: 'This is for My servant, and My servant shall have what he has asked for.'"* *(1) Surat al-Fatihah, the first surah (chapter) of the Qur'an.* *(2) i.e. standing behind the imam (leader) listening to him reciting al-Fatihah.* *(3) "Praise be to Allah, Lord of the Worlds."* *(4) "The Merciful, the Compassionate."* *(5) "Master of the Day of Judgement."* *(6) "It is You we worship and it is You we ask for help."* *(7) "Guide us to the straight path, the path of those upon whom You have bestowed favors, not of those against whom You are angry, nor of those who are astray."* *[Muslim (also by Malik, at-Tirmidhi, Abu-Dawud, an-Nasa'i and Ibn Majah)]* *عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: مَنْ صَلَّى صَلَاةً لَمْ يَقْرَأْ فِيهَا بِأُمِّ الْقُرْآنِ، فَهِيَ خِدَاجٌ ثَلَاثًا، غَيْرَ تَمَامٍ، فَقِيلَ لِأَبِي هُرَيْرَةَ: إِنَّا نَكُونُ وَرَاءَ الْإِمَامِ، فَقَالَ: اقْرَأْ بِهَا فِي نَفْسِكَ، فَإِنِّي سَمِعْتُ النبي صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ:{ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ } قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:{ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ } قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: أَثْنَى عَلَيَّ عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:{ مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ } قَالَ اللَّهُ: مَجَّدَنِي عَبْدِي - وَقَالَ مَرَّةً: فَوَّضَ إِلَيَّ عَبْدِي، فَإِذَا قَالَ:{ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ } قَالَ: هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ:{ اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ } قَالَ: هَذَا لِعَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ. رواه مسلم (وكذلك مالك والترمذي وأبو داود والنسائي وابن ماجه)* ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ *_Scene three _* ~*Page 7*~ Tun da ya isa gurin aikin shi ya ke tunanin me yayi mata take mai irin wannan azabar har da wani canza gurin kwana, amma tunanin shi ya kasa gane wani irin laifi ya aikata da zai fuskanci wannan hukuncin daga gure ta, haka dai ya gama tunanin shi, ya k'udurce yau idan yaje gida zai lallab'ata ko zata fad'a masa laifin da yayi mata. Ita kuwa tana can sai faman karatu take yi tana dad'a jin tsanar shi na shiga ranta, musamman ma idan aka zo wannan fannin, gani take kamar ba rayuwar aure su ke yi ba. A b'angaren Saha kuwa ta kai kusan 6:00 tana bacci, vibration d'in wayar ta shine ya farkar da ita, ko ba a fad'a mata ta ba ta san sahibul qalb d'in ta shi yake kiran ta, don idan ba shi ba babu wanda yake kiran ta sai dai chatting. Cikin bra d'inta ta kai hannu tare da zaro wayar ta kara a kunnen ta. "Hello sweet heart kin tashi ma kuwa?". Cikin bacci bacci ta ce, "Uhmmm yanzu dai ka tashe ni". Lumshe idon sa yayi saboda wani mugun feeling din ta da ya taso mishi. "Kai wannan yarinyar zata kashe ni". Ya fad'a can k'asan mak'oshin sa. "Baby na, me ka ce?". "Babu abunda nace, ki tashi kiyi sallah mana in yaso sai mu cigaba da wayar, ko ki hau online saboda ina son kasancewa tare da ke Saha". Babu wani kunya ta ce, "Baby ina yin period ne, bari kawai na zo online d'in". Tuni ta murje idon ta don yin chatting da Zaiyad, amma tana kunna data taji Ummi na kwalla mata kira. "Saha wai baki ji ina kiran ki bane!? Kiyi sauri kizo ki d'aura breakfast su Surayya su shirya, kada su makara zuwa makaranta!". "Innalillahi! Ai shikenan kuma na shiga uku, garin ya waye kenan anyi ta k'walla maka kira ana sa ka aiki, gaskiya na fara gajiya, haba! Kai kenan aiki kamar machine fisabillilahi, mtwssss!". Ta ja uban tsaki had'e da durowa daga saman gadon ta nufi k'ofar fita. Nan da nan ta had'a musu breakfast ta zubawa kowa na shi sannan ta zuba musu wanda za su tafi makaranta da shi, har Ummi ta zubawa don ta san indai bata zuba mata yanzu ba ta dinga kwalla mata kira kenan. "Aa'a'a 'yar albarka! Kice har kin gama had'a breakfast, sannu Saha!". "Uhmm har na gama had'awa, ga naki nan ni zan shiga ciki nayi wanka". "Kai Saha tun yanzu zan ci kuwa?". Tayi maganar tana kallon wayar ta. "Eh ni dai Ummi gashi nan na zubo zan wuce". "To shikenan babu matasala, sannu da aiki yaya Saha". Ta fad'a saboda ta ga yanayin yarinyar kamar ya d'an sauya, ita kanta ta san Saha tana k'ok'ari a gidan ba na wasa ba, shi yasa idan tayi wani abun kawai take d'an share ta. Tana shiga d'aki ta ciro wayar daga k'asan kayan ta wanda tun da zata fita ta danna ta silent, nan take ganin miss calls d'in Zaiyad, wajen 10 mis calls yayi mata. "Allah sarki love d'ina am really sorry", ta fad'a tana kwab'e fuska irin cikin shagwab'ar nan, nan ta kunna data suka fara plan d'in yadda za su had'u. ***** Ita kuwa Hunayda tunda Saha ta turo mata littafan ta fara karantawa, ba ita tayi bacci ba sai gurin 1 din dare sannan ta samu runtsawa, wajen 4:30 ta tashi daga bacci, ganin lokacin Sallah bai k'arasa ba ya sa ta janyo wayar ta ta cigaba da sana'a, dan littafin ji take kamar kar ta daina karanta shi. Ni kuwa nace tabbb! irin wannan abu haka tun kafin ma ayi sallah, Allah ya shiryar mana da zuri'a. Bayan tayi sallah ne ta d'an koma bacci, bata dad'e da kwanciya ba sai ga Hajna ta shigo cikin d'akin. "Aunty! Aunty! Ki tashi Ammi na kiran ki". Wani juyi tayi tare da buga wani uban tsaki tace; "To naji kar ki ishe ni malama, ga ni nan zuwa, haba mana sai wani kwalla mun kira kike yi". Hajna wanda take sanye cikin uniform d'in makaranta ta keb'e baki had'e da barin d'akin. "Hunayda wai wani irin bacci kike ki yi har Hajna ta tashi ta fara shirin tafiya makaranta amma ke kina kwance kin barta da komai ko, kin san dai kafin na sallami Abban ku daga ciki kamata yayi ace kin taya ta ta shirya saboda kar ta makara, amma ina! kina can kina bacci ko, k'ila ma baki yi bacci da wuri ba wallahi!". "A'a Ammi ba fa haka bane, kaina ne yake yi min ciwo shi yasa ban tashi da wuri ba na d'an kwanta bacci". "AI dole kanki yayi ciwo tunda baki da aiki sai na kallon waya, sha-sha-sha kawai! Wallahi na kusa fara k'wace wayar nan idan dare yayi, don na fuskanci a 'yan kwanakin nan ba kya yin bacci da wuri!". "Ammi don Allah kiyi hak'uri ina fa yin bacci da wuri". Bayan sun gama duk abunda suke yi, Hunayda ta taya Ammi suka gyara gidan yayi tasss da shi sannan suka yi breakfast d'in su, suna gama tace wa Ammi bari taje tayi wanka, tana shiga d'akin ta d'au wayar ta aka cigaba da sana'a wato karatun littafi. Can edge d'in gadon ta na hango ta ta wani cure guri d'aya sai lumshe ido take yi (ni kuwa nace da zan iya sai naga me ake gani haka). Dropping wayar tayi tare da had'e kai da gwiwa ta k'ara curewa guri d'aya ta ce; "Wayyo Allah ciki na! Na shiga uku ni Hunayda me nake gani, dama haka ake yi? Tabbbd'ijan! Shegiya Saha, dole ta ce zan iya karantawa? Ashe al'amari ne a cikin littafin, anya zan iya cigaba da karantawa kuwa, idan ba haka ba sha'awa zata kashe ni wallahi". Wayar ta d'auka tare da fita daga gurin karatun ta bud'e data, ai kuwa tana hawa taga Saha na online, ta fara yin typing kamar haka; "Shegiya, dama na san kina online ana tare da Zaiyad ko? Ke dama haka littafin nan yake? Tabbd'ijan, gaskiya writer d'in shegiya ce ta iya rubutu sosai wallahi, ke amma fa wani abun ma wallahi ban san haka ake yin shi ba sai yau!". Sai da ta d'au kusan 10 minutes sannan tayi mata reply. "Wallahi kuwa kamar kin sani muna tare da shi, hmmm ai dama sai da na fad'a miki zaki iya karantawa saboda littafin na manyan yara ne". "Gaskiya kam bafa ta b'oye komai, komai fito da shi take yi". "Eh mana, yanzu a ina kike?" "Ina gurin da suka yi aure mana, har sun tafi Dubai ma". 😳"Kai wai har kin kawo nan wai?". "Eh mana ke jiya har wajan 1:30 fa ina karatu, kuma ina tashi na d'ora". "Gaskiya ne, kina k'amshi ina bin ki da humra, shegiya kice abun ba wasa!". "Ke, amma fa gaskiya ina jin daina karantawa zan yi, ke kin ji wani mugun sha'awa da nake ji kuwa? Kamar na mutu, gaskiya bari zan yi, wai, ina bazan iya ba!". "Ke dalla can banza, ba sai ki rik'a samarwa da kanki nutsuwa ba, kuma wallahi kada ki bar wani karantawa, ai gwara ki san komai yadda kawai idan kika je gidan miji kin san yadda zaki sarrafa shi, ai ni wallahi na k'agu ayi maganar mu da Zaiyad yaga yadda ake love". "Kamar ya samarwa da kaina nutsuwa kuma?". "Mtsww ke fa banza ce, ki bari idan mun had'u zan fad'a miki yadda zaki dinga yi". "Okk tom shikenan ba wata matsala, sai mun had'un, bari na shiga wanka". "okk tom bye". **** Da misalan k'arfe d'aya da rabi na rana Saha ce sanye cikin uniform d'in islamiyya, babu komai a fuskar ta sai lipstick da ta shafa, ta kuma saka kwalli, hijab d'in ta saka sannan ta fito daga d'aki rike da jakar makaranta a hannun ta, can ta hangu Ummin su tana ta faman danna waya. "Kai wai ita Ummi kullum cikin danna waya, bata da lokacin da zata ware yin wa'innan sabgogin nata, amma ace mutum kullum abu d'aya, mtswww!". Note:plss iyayen yara writers da wa'inda ma ba writers ba kai har ma da riders plsss mu dinga ware lokacin da zamu dinga yin abubuwan mu, mu bari sai mun gama duk wani responsiblity namu na cikin gida kafin mu hau online, ku shiga wps don karatu ko kuma typing, ko karatu online plsss....wallahul musta'an Allah yasa mu dace AMIN ya Allah. "Ha'a Saha naga yanzu fa d'aya da 'yan minutes amma har kin fito?". "Eh zan biya gidan su Hunayda ne kafin mu shiga makarantar, saboda zata koya min wani karatu da aka yi mana jiya, gashi an bada assingnment kuma ban yi ba". "To bari sai su Na'eef sun dawo daga makaranta zuwa 2:30 sai ku wuce gidan su Hunaydan tare ko?". "A'a Ummi sun tawo daga baya, aikin fa yana da wahala". "To ai gani nayi sai kun yi sallar la'asar kuke shiga shi yasa". Tana fad'in haka messege ya shigo cikin wayar ta, tuni ta manta da sha'anin Saha, sai da ta gaji da tsayuwa sannan ta ce, "Ummi na tafi?". "To Saha sai kin dawo, su Surayya sun tawo daga baya". Tana fita ta hango car d'in shi a can k'arshen layin su, da sauri ta k'arasa, tana zuwa ya bud'e mata ta shiga, ya rufe ya ja su suka tafi. "Yanzu baby na ina kike so mu je?". "Uhmm... duk inda muka je ai babu matsala". "To muje gida na kenan?". "Gidan ka kuma? Gaskiya A'a, kawai dai mu je wani gurin shak'atawa haka, ko da Gamji ne tunda ai hira kawai zamu da'n tab'a". Hannun shi ya d'ora kan nata yana murzawa ya ce, "Amma dai baki manta da alk'awari ba dai ko?". Ji tayi gaba d'aya jikin ta ya mutu, ga wata muguwar sha'awa da ta taso mata, cikin ranta take ayyana; "Dama haka ake ji?! Tabb, ashe dai gaskiyar Ummi ana jin dad'i sosai". D'ago da idon ta da suka fara canza kala tayi ta kalle shi ta ce, "Ban manta ba baby na ina sane". Itama ta d'ora dayan hannun ta kan nashi tana murzawa. "Shegiya wallahi ta kamu, wannan baza tayi wahalar shigowa hannu ba". "To yanzu mu wuce gidan nawa?". "Ba..by duk..yadda..ma kayi dai-dai ne". Ta fad'a in a lustfull tone. Wani smile ya saki tare da juya kan motar shi su kayi gidan na shi. Suna isa ya shiga ya bud'e musu sannan ya dawo suka shiga cikin gida, yayi parking car d'in shi inda ake ajiye motor. "Tom remember my promise dai gaskiya". "Amma bazan shiga ciki ba gaskiya". Don kar tayi tunanin wani abu yasa ya ce; "To shikenan ba matsala, amma mu koma bayan mota". ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [1/15, 11:02 AM] Sumayya Sumy B: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:* *"Allah (mighty and sublime be He) says:* *'The first of his actions for which a servant of Allah will be held accountable on the Day of Resurrection will be his prayers.' If they are in order, then he will have prospered and succeeded; and if they are wanting, then he will have failed and lost. If there is something defective in his obligatory prayers, the Lord (glorified and exalted be He) will say: 'See if My servant has any supererogatory prayers with which may be completed that which was defective in his obligatory prayers.' Then the rest of his actions will be judged in like fashion."* *[At-Tirmidhi (also by Abu Dawud, an-Nasa'i, Ibn Majah and Ahmad).]* *عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ عَمَلِهِ صَلَاتُهُ. فَإِنْ صَلُحَتْ فَقَدْ أَفْلَحَ وَأَنْجَحَ، وَإِنْ فَسَدَتْ فَقَدْ خَابَ وَخَسِرَ، فَإِنْ انْتَقَصَ مِنْ فَرِيضَتِهِ شَيْءٌ، قَالَ الرَّبُّ عَزَّ وَجَلَّ: انْظُرُوا هَلْ لِعَبْدِي مِنْ تَطَوُّعٍ فَيُكَمَّلَ بِهَا مَا انْتَقَصَ مِنْ الْفَرِيضَةِ، ثُمَّ يَكُونُ سَائِرُ عَمَلِهِ عَلَى ذَلِكَ. رواه الترمذي وكذلك أبو داود والنسائي وابن ماجه وأحمد* ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* *♣scene three * *page 8* Car d'in ya bud'e suka fito a tare, nan ya bud'e mata bayan motar ya ce; "You are welcome, her majesty". Wani irin dad'i taji saboda yadda yayi maganar ba k'aramun fasa mata kai yayi ba, shiga tayi ta zauna tare da sakin wani deep breath (Abun ka da sabon shiga farkon yi). Zagayawa yayi shima ya shiga ya zauna yana fuskantar ta. "Sahabat!", ya kira ta da full name d'in ta, dararan oily eyes d'in ta zuba mai tace "Na'am baby na me ya faru?". "Ina mugun bala'in sonki, zan iya aikata komai akan ki, zan yi miki duk wani abu da kike so, hope dai kema kina so na haka?". Ya k'arashe maganar yana d'ora hannun shi kan kolumatun ta na gefe d'aya. Hanu takai kan nashi tace; "Love! nima ina yi maka irin son da kake yi min, kai zan iya ce maka ma nafi son ka Zaiyad, you are my every thing, plsss stay with me muyi spending life time d'in mu together". "Shegiya, ko ba life time ba I will spend my life time da ke amma ba na aure ba". Ya fada a cikin zuciyarshi. A fili kuma ya ce; "Why not baby, ai kawai kiyi tunanin mun fara spending life time d'in mu". Ya fad'a had'e rungumota jikin shi, wani sabon hali taji ta tsinci kanta a ciki, saboda yau ne na farko da namiji ya fara yi mata haka, amma da yake giyar soyyaya na d'iban ta haka ita ma tayi hugging d'in shi har da su Ilove you my sweety. D'ago da face d'in ta yayi ya fara dosar fuskar ta da niyar kissing d'in ta, amma ko k'okarin hana shi ba tayi ba, shi kuwa tuni ya k'arasa ya had'e bakin su guri d'aya yana zuba mata sihirtaccen kiss, ita kuwa hajiya Saha sai sauke numfashi take tana jin zuciyar ta na mata nauyi har ta fara tafiya bata ma san inda kanta ya ke ba, zip d'in ta yake k'okarin ziping ta hango time ta cikin agogon mota wanda yake mak'ale a jikin radio na motor, ai bata san lokacin da ture shi ba ta ce; "3:30 yanzu Zaiyad, kuma ka san sai na biya ta gidan su Hunayda kafin na wuce". Kallon ta yayi da shanyayyun idon sa ya ce, "Ha...ba.. ma...na.. Saha you and your islamiya abubuwa, let have fun mana". "A'a ka bari sai next meeting". Ta fad'a had'e da durowa daga motar ta koma gidan gaba tana gyara hijab d'in ta, haka nan shima ya koma gurin zaman driver ya zauna yana maida numfashi, ba yaso yayi forcing d'in ta, ya fiso yayi komai da ita cikin had'in kanta shi yasa kawai ya rabu da ita. Suna isa kusa da layin su Hunayda ya sauke ta, ai kuwa tana fitowa ta hango Hunayda can tana tahowa itama da kayan islamiyya jikin ta, nan ta jira ta ta k'araso. "Hmmmm! Saha kenan yauma anyi sana'a, ni dai zan ga ranar da zaki daina sneaking d'in fita, me ye naga kin yi wani furgaifurgai da ke?". "Hmmmm ke dai bari, ai sai mun zauna, wannan zancen Hunayda na samun natsuwa ne". Suna tahowa na hango wani d'an matashi wanda bazai wuce shakara 29 zuwa 30 ba, dogo ne kuma yana da haske amma ba sosai ba, kuma yana da kyaun shi na dai-dai misali, shi ba mai irin asalin kyaun nan ba kuma ba mai muni ba da bulala rik'e a hannun shi da alama malamin makarantar ne. "Su Saha da Hunayda yau an makara, don haka dole ayi muku dukan makara". Ya fad'a in a jokeful way yana kallon fuskar Hunayda. "A'a malam mun zo dai a dai-dai, bamu makara ba". "Ya akayi k'anen ku suka riga ku zuwa toh? "Kawai muna tahowa ne babu komai". Duk maganar nan da ake yi Saha ce ke yi amma ita Hunayda ba abunda ta ce, nan yace musu idan aka tashi kafin su tafi gida yana son magana da Hunayda, amsa mishi da to suka yi kafin su wuce aji. "Ke anya kuwa malama Suhail ba son ki yake yi ba?", "Hmmm ke dai bari nima na ga alama". "Tabbb me zaki yi da malamin islamiyya,Allah ya kauta!". "Allah ko ?". Ta fad'a in I don't care manner. Haka dai suka cigaba da hirar su har suka shiga aji... ************ Bayan an tashi su Hunayda daga makaranta, nan malam Suhail yake fad'a mata shi son ta yake yi kuma da aure, don haka zai zo gida yayi magana da Abban ta idan ta amincie, zata je tayi tunani tace mishi. Su Hajna da Surayya da kuma Na'eef sune a gaba, while Saha da Hunayda suna bayan su. "Tabbb! ai wallahi kar ki yadda, wannan d'an k'auyen zaki yi soyyaya da shi, ko d'an zuwa outing d'in nan baza ku ri'ka zuwa ba, tabb! gaskiya ban goyi bayan haka ba, ina da sake!". "Saha amma kuma ai yana da hankali, kuma babu ruwan shi he is so silent, kuma ko ya ce zai je outing d'in da ni ai kin san bazan iya zuwa ba, besides, bance miki na yadda ba tukunna don haka ki daina damun kanki sai nayi tunani. Ke ba ma wannan ba, fad'a mun yadda zan dinga yi idan naji sha'awa". Kunnen ta Saha ta kamo ta fad'a mata abu a kunne wanda ni ban samu damar jin shi ba. "Kai! Allah kuwa Saha?". "To ba sai ki tsaya wasa ba, hmmm kin san yau Zaiyad har kissing d'ina yayi". "Me ne! kissing fa Sahabat!". "EH man....". "Yaya Saha don Allah kizo mu wuce gida, kusan fa magrib ake k'ok'arin kira". "Eh wallahi ya Hunayda ku zo mu tafi plss". "To jarabbabu har da wani kusan had'a baki, sai ku wuce mu tafi ai". Inji Saha tayi maganar a irin kar ku dame mun nan. Nan suka yi hanyar gida, dama anzo kan kwanar rabuwa amma hira ta k'i k'arewa. "Saha wai a ina kuka tsaya yau ne? ina ta jira ku dawo gashi ni ko abinci ban d'ora ba". Surayya ce ta ce, "Mun taho suka tsaya a kan kwana ita da Aunty Hunayda suna ta hira". "Yanzu Saha duk hirar da kuka sha tun d'azun sai da kuka tsaya hira akan hanya?". Don ta kawar da zancen ya sa ta ce; "me za a dafa don tasan dole ita zata dafa,nan.ta shiga kitchen ta fara shirya musu abunda za su ci. A b'angaren su Hunayda ma sai da Ammi tayi musu fad'a amma sai dai ita har ta gama abinci ta ajiye ta gama komai nata, gida yayi tsaf da shi(ni kuwa na ce ko don ita mai miji ce, kai amma anya, kawai dai ma tana da kula ne). *********** Zaune take a palo ta sha riga da siket d'in ta na atamfa wanda ya karb'i jikin ta, sun zauna dass sunyi mata kyau sosai, rik'e take da mug da alama dai na'ana'a tea ne a ciki while yaran suna daga gefe suna cin abinci ga kuma mbc 3 an saka musu suna kallo,ita kuwa sai faman danna waya take yi ,bayan sun k'oshi abunka da hali irin na yara har suka fara wasa da abincin, amma Salma bata san halin da ake ciki ba tayi nisa wurin karanata *NIDA SHI* sai wani sakin smile take yi. Yana shigowa tun kafin ya bud'e bakin shi yayi sallama ya ga sun yiwa palon kaca kaca da shinkafa, ga duk sun burkita palon sai wasa suke yi, ita kuwa hakima bata san wainar da ake toyawa ba, kallon inda take yayi yaga gaba d'aya ma bata san ana yi ba, wai kunu a mak'ota. Sallama ya fara yi amma sai da yayi sau biyu kafin ta jiyo, shima har sai da yaran suka fara oyoyo abba sannan ta d'ago firgit ta kalle shi. Yau kam ta k'ular da shi, ko kallon inda take bai yi ba yayi shigewar shi, ita ma nan ta juya had'e da keb'e baki, mai da kai tayi zata cigaba kamar ance ta kalli d'akin ta ganshi yayi kaca-kaca. "Innallillah dama haka yaran nan suka yiwa wajan nan?". Bata gama tamabayar kan ta ba taji ya ce; "Salma ina abinci na, don yunwa nake ji". Yau kam yaci sa'a an dafa da shi, (ni kuwa na ce ko dai shauk'in novel ne😜) "Ka shiga kitchen akwai a tukunya sai ka zuba". Tayi maganar kamar ba ita tayi ba, ta maida kai ta cigaba da abunda take yi. "Gurin nan kuma wa zai gyara shi, wai shin Salma me kike yi ne ma a jikin wayar nan da ina miki magana kina ji na, kin mai dani d'an iska a cikin gidan nan, ko don kinga ina kyale ki ne iye!!!". Da sauri ta juyo ta kalle shi don jin yadda ya d'aga murya, don ita ba don kar ace tayi k'arya ba da sai tace bata tab'a ji yayi mata magana irin yadda yayi mata yau ba. Tana k'unk'uni ta tashi ta shiga kitchen ta zuba mai abincin tazo ta dongwarar da abincin kafin ta tattare gurin, sannan ta samu guri ta zauna tana fad'in, "Duk abi a takura mutum, bayan bayi mai abunda ya kamata ake yi ba, kalli fa ji yadda ake love", ta fad'a tana kalon wayar ta kamar ba ita tayi maganar ba. Shi kuwa kawai kallon mamaki yake yi mata yana mamakin, " Me yasa ta fad'an haka?me take nufi da shi? duk kular da yake bata". "Amma just ko d'an two hours d'in nan baza a iya da kai ba, babu wani armashin arzik'i!", ta fad'a tana mik'ewa da alamar d'aki zata shiga, wucewa tazo yi ta inda yake zaune, yayi saurin rik'o hannun ta ya ce; "SALMA wai me ke faruwa ne? me nayi miki wanda baza ki iya fad'a mun ba sai dai kiyi ta mun habaici kamar ba zaman aure muke yi ba?". "Ni kawai ka sake mun hannu don ko na fad'a maka ba iya yi mun zaka yi ba, don haka kawai a barshi!" ta fad'a tana fuzge hannun ta. "Gaskiya baby yau ba k'aramun burge ni kika yi ba, kin nuna kina so na kuma naji dad'in haka, amma plss gobe ma zamu had'u ko?". Gyara zaman wayar tayi a kunnen ta ta ce, "Ummm anya kuwa bana jin Ummi zata barni na fita gobe, saboda na fita da yawa a 'yan kwanakin nan kuma bana so ta fara zargin wani abu". Jin foot steps a guraren k'ofar ta ne yasa tayi saurin saka wayar cikin bra. Ai kuwa ji tayi Ummi ta ce, "Saha lafiya kuwa naji kamar kina magana". Ta fad'a tana turo k'ofar d'akin. "Wayyo Allah na Ummi wallahi cinnaka ne ya ciji ne shi yasa nake ta mita". "Cinnaka kuma a d'akin nan, me ya kawo shi toh? Ko da yake yanzu kaka ce babu mamaki ma idan an gansu, sai ki shafa maklin k'ila ya rage zafi". "To Ummi, zan shafa" "Yauwa ga doya can na fere miki ki tashi da wuri ki had'a musu breakfast..... ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* *♣Scene Four* *page 9* ***** Ko bayan data kammala girkin, kasa daurewa tayi, toilet ta shige, hankalin ta gabaki ɗaya yana kan wayar ta, masalan ma data bar datar a kunne, tana jin lokacin da saƙon ni suke shigo mata akai akai, wani bayan wani, duk da a sace take duba saƙonnin, lokaci guda kuma tana ci gaba da girkin. Saƙonnin zaiyad sunfi yawa, yana yaba mata, yanda ta shayar dashi daɗi yau, yana mai ƙara ƙwarzanta mata, haɗi da yi mata wasu alƙawurran na zama tare da ita har abada. A ɓangare guda kuma, group ne na inda ake turo masu litattafan da yake sanya su nishaɗi, har ta ƙagara dare yayi, inda Ummin tata zata sake masu sabon post yau, tasan mai zafi ne, Tunda har taga hankalin Ummin gabaki ɗaya yau yana kan typing ɗin da take. Bata wani ci abincin kirki ba, ta kasa zaune ta kasa tsaye, so take ta samu ta keɓe, ko zata samu damar yin magana da zaiyad ɗinta. Akai akai take sakin murmushi ita kaɗai, har Ummin da take zaune tana cin abinci taso ta lura, yau ta fahimci Sahar tana cikin wani irin shauƙi, to shauƙi mana zata ce, yau Sahan ce tayi saurin amsa mata da cewa me za'a dafa? Ba tare da ta nuna ɓacin ranta a fili ba? "Ummi kaina ne yake man ɗan ciwo, gashi har ciki na naji yana katsawa, zanje in ɗan kwanta." Da kallo Ummin ta bita, har yanzu ta gaza gane inda Sahar ta dosa, Amman zuciyar ta tana mai ayyana mata abubuwa da dama game da ita. Saidai bata jin in zata iya wani tsayawa ta bincika sosai, in tayi la'akari daga makaranta sai gidan su Hunayda Sahar ke zuwa. Balle tace ko wasu sabbin ƙawaye ne tayi,kuma ita ba waya ce da ita ba, balle tace ko ta haɗu da sherin social media ne. "Sannu to Sahabat, yanzu zan aiko Surayya da magani ta kawo maki" Abunda Ummin ta faɗa mata kenan, itama tana mai miƙewa ta shige ɗakin ta. Ko da Surayya ta shiga ɗakin da magungunan a hannun, sai ta tadda Saha bata cikin ɗakin, saidai motsi data jiyo cikin banɗaki, murya cen ƙasa ƙasa tana magana, alamun bata so wani yaji. Baƙin ƙofar ta matsa, tana mai bubbuga ƙofar toilet ɗin "Aunty Saha wai ga maganin inji Ammi" cewr Surayyan, ta ƙarashe da magana da ɗan ƙarfi,tana mai mamakin yanda yayar tata ke magana ita kaɗai a banɗaki. "Ajiye man bisa mirror, zan fito in ɗauka" Saha ɗin ta faɗa daga cikin toilet ɗin. Girgiza kai Surayya tayi, tana mai juyawa ta ajiye maganin haɗi da ruwa. Ta haye saman gadon tayi kwanciyar ta, gami da jan bargo da addu'a. (Dayake yanzu Ummi ta haɗe su ɗaki guda, domin Surayya ta dinga faɗa mata halin da Sahan ke ciki, kuma har yanzu Saha bata taɓa bari Surayya taga wayar tata ba) "Baby ke dawa haka? Ba kin faɗa man kina cikin toilet ba?" cewar Zaiyad dake kwance bisa gadon nashi, daga shi sai short nicker da ƴar singlet fara, daka ganshi kasan yana cikin wani yanayi, saboda a kallo guda zakayi ma halittar shi sai ka janye idanu. Yana enjoying duk wasu maganganu dake fitowa daga bakin Sahar tashi, murmushi yake saki akai akai, jin yanda Sahan bata jin ko ɗar wajen faɗa mashi wasu kalaman. Kenan taji daɗin moment ɗinsu na ɗazu? "Babyna ai bakiga komai ba, abunda kikayi mani ɗazu ya daɗa tabbatar mani da irin soyayyar da kike mani har cikin ranki, please baby ki bari in turo maki wani ɗan video nan kaɗan, Amman dan Allah kada ki bari wani ya gani, dakin kalla ki goge" ya faɗa cikin wani irin taushin murya, yana yi yana karya kai, kaman yana gabanta ne. "Haba Sweet heart, kai kanka kasan ba yanda za'ayi in bari wani ya gani, infact ma dai ai kasan ba wanda yasan ina da waya nan gidan, ko chaji a toilet nake Sanyawa ko in naje gidan su Hunayda" "Oowhp na manta wallahi shaf baby, ashe fa nine ma na siya maki wayar?" ya faɗa yana mai sake sakin wani killer smile. Ba tare da ta kawo komai a cikin ranta ba tace "Eah mana dear, ashe ka manta fa" "Na manta baby, kinsan kyauta tsakani na dake ma yanzu aka fara, please kiyi man alƙawarin mallakaman zuciyar ki da abunda duk kika mallaka, nayi alƙawarin shayar dake daɗi, da kuma kyaututtuka marasa misali" "Kada ka damu indn wannan ne ka samu, saidai ni da ina tsoro Zaiyad, kasan Ummina akwai ta da ganewa, ga kula, kuma ina tsoron Uncle ɗina.." "Shiiiit my Habat, kada kiji tsoron komai, ina tare dake indn wannan, kuma koma menene ya faru na ɗauki alhaki, kuma zan tsaya dake a kowanne irin hali, Dad ɗina kawai nake jira ya dawo azo ayi wacce za'ayi, kawai in mallake ki, in huta da wannan rowar taki" Cikin ɗan zaro idanu ta dafe ƙirji, "Rowa kuma Sweet heart?" "Eah mana rowa, gashi ko ɗazu ma kinyi mani? Baki yarda dani ba? Kuma kika ƙi shiga gida na? Saboda kina jin tsoro kada in ci ye ki? Ko in miki fyaɗe?" Rau-rau tayi da idanu, jin kaman yaji haushin abunda tayi mashi ɗin. "Ba ƙin yarda dakai nayi ba dear, kawai dai lokaci ne yayi, ai nasan ba zaka taɓa cutar dani ba, irin yanda kake sona, dan haka insha Allahu babu Abunda zaka nema a gareni ka kasa samu, kawai dai ku jira lokaci" Gyara kwanciya yayi, yana mai sauke miƙa, har saida sautinshi ya fito ta cikin wayar. Lumshe idanu Saha tayi, har cikin zuciyar ta saida taji wani iri, me ya hana ta ɗazu ta tsaya ko da kaɗan ne ta ɗanji Abunda ake ji?" Katse mata tunani yayi da cewa "Promise? Zaki bani dama mu tabbatar ma kanmu irin soyayyar da muke ma juna? Zai zo gida na? Zaki shiga?" Saida ta ɗan yi jimmm, sannan tace "Eah dear, Amman ba yanzu ba" "Why?" ya faɗa shima a hankali, cikin wani irin sexy voice. "Kawai hakanan" "baki yarda dani ɗin ba kenan? " Na yarda dear" To ki amince dani kawai, zaki sha mamaki, insha Allahu ba'a wuce nan da wata guda za'ayi auren mu, muddin kika bani *Haɗin kai* " Ta yarda ta amince mashi 100%. Tayi imani cewa wannan ita ce soyayya, kaman yanda taga Umminta na rubutawa, bata ɗaukn hakan a matsayin komai, tuno wani moment da Umman tata ta rubuta jiya a Page ɗinta, sai taji ta yarda ta amince, koda sau ɗaya ne itama tana buƙatar taji abunda ake ji. "Na yarda na amince" ta faɗa a hankali. Ihun murna ya saka a hankali, burin shi na daf da cika, lasar leɓe ya fara, ji yake kaman gashi cen ma a wata duniyar. "Yes no matter how ma dai Sweet heart, ya kamata mu sake haɗuwa kusa kusan nan" "Eah to kusan nan dai babu inda zanje, Kaga gobe Alhamis, jibi juma'a to gata Asabar akwai bikin ɗiyar ƙanwar babanmu, nasan Ummata ba zata je ba, sai mu haɗe acen kawai" "Really?" ya faɗa cikin murna da jin daɗi. "For sure my love" itama ta bashi amsa. Dariya ya saki yana mai mamakin Sahabat ɗin, wannan ƴar yarinyar, dududu atatarta 17yrs ko da ɗan fi, Amman har ta iya kalaman soyayya haka, kodayake yana ganin litattafan soyayya a wayar ta, kuma ya tabbata acen ne zata koye su. Zagewa yayi ya shiga shirya mata kalaman yaudara, yanayi yana gamsar da kanshi da hannu, ta dalilin muryar Sahabat ɗin mai cike da taushi da yake jiyo wa. Jin motsin kaman an shigo ɗakin nasu ne, ya sanya ta datse kiran ba shiri, haɗi da soka wayar cikin riga, ta kunna fanfo ta shiga watsa ma fuskar ta ruwa. Tana fitowa ta tadda Ummin tata tsaye itama hannun ta riƙe da wayar. An riga an ɗauke wuta, Shiyasa take haskawa da fitilar wayar. "Ya jikin ne? Bakiyi bacci ba har yanzu?" cewar Ummin. "Eh Ummi naji sauƙi ai tun sanda nasha maganin, yanzu ma kwanciya zanyi, sai da safe" tayi saurin tarar numfashin Ummin, lokaci guda tana mai kare magungunan da suke ajiye bisa mirror da bayanta. Gyaɗa kai Ummin tayi, tana mai juyawa ta fice, gami da cewa "Allah ya tashe mu lafiya, zo ki kulle ɗakin" Bayanta tabi ta dasa ma ƙofar makulli, gami da zaro wayarta ta maida earpiece ɗin, haɗi da latso kiran nashi. Ita kanta mamakin kanta take yi, wai yau ita ce harda iya haɗa baki da wani namiji, Amman koda yake shi ne take da burin aure ai, kaman yanda ya shaida mata cewa ai shine zai aure ta nan ba da jimawa ba. dan haka ba wani abu bane, shine dai zai mallake ta. Kafin ya ɗauki wayar ne, saida ya tura mata wani ɗan short video na xxx, ya lura yanzu ya fara shawo kanta da kalaman yaudarar shi. Sannan ya amsa wayar, daidai lokacin da ita kuma ta kwashe magungunan daga bisa mirror, ta shiga tayi floshing nasu, sannan ta dawo ta haye gadon, tana mai kashe murya a hankali ta cikin bargo, saboda kada Surayya ta jiyo ta, wadda ta riga tayi bacci tuni. Kuma Surayyn irin yaran nan ne masu nauyin bacci, ko fitsarin dare ba kasafai take iya tashi ba. Ci gaba sukayi da yin wayar daga inda suka tsaya. Kafin suyi sallama, saida ya tabbatar mata da cewa ta buɗe WhatsApp akwai saƙo, ko basu haɗu online ba zasuyi magana zuwa gobe, domin shi yau ya riga da ya samu gamsuwa da ita ba tare da ta ko sani ba. Kashe wayar yayi yana mai sakin wata irin shegiyar dariya, ayyanawa yake a ran shi, ai duk yanda zaiyi ya samu gararta da ni'imar ta sai yayi, balle yanda yaji taushin leɓenta ɗazu, daga ji zata shayar dashi kalar daɗin da yake burin samu daga gareta. Ita kuwa tana hawa online Hunayda ta fara dubawa ko tana online ɗin, ilai kuwa tana online. Dan haka tace mata kada ta sauka, ta jira ta akwai wani abu da zata turo mata. Hunayda dariya take tayi, saboda littafin da take karantawa ya kai mata iya maƙura, dan haka ne ma ta ɗauka abunda Saha ɗin zata turo mata yafi littafin daɗi. Wara idanu tayi sosai akan video ɗin da yake playing, wanda ya kasance na fararen fata ne. Gabanta da zuciyar ta ne kawai suke bugawa, me take gani haka? Wane irin al'amari ne wannan? Take hannun ta ya shiga kyarma da rawa. Runtse idanunta tayi, tana mai ayyano kalar daɗin da zai kasance suna ji. Tana haka ne har clip ɗin ya ƙare, kuma kunnawa tayi tana mai natsuwa cikin bargo ta sake binshi bit by bit. Abunda zayyad yake nufin zaiyi mata kenan? Anya kuwa zata iya? To Amman ita kanta tayi imanin wannan shine soyayyar, kuma in basu koya tun yanzu ba sai taushe? Hannun ta na rawa tayi forwarding ɗinshi zuwa ga account ɗin Hunaydar, wanda har Yanzu take ganin ta online tasan kuma jiran ta take yi Jikinta yayi sanyi ƙlau, ko hannun ta bata iya ɗagawa, ayyanowa abubuwa da dama take yi cikin zuciyar ta, gani take kaman ita ce da Zaiyad, yanzu abunda Umminta da Abban ta suke yi kenan ada? Yanda dama irin hakan ne Ummi ke nufi? Ba zata iya jurewa ba, tasan tana cikin irin matan da Ummin tata ke rubutawa, wanda koda za'ayi awanni ana faranta masu ba zasu taɓa gajiyawa ba. To itama ta ɓangaren Hunayda abun haka take, saidai ita sam wani iri take ji anjikinta, tabbas ita kanta ta sani Amminta ba irin wannan tarbiyyr ta bata ba, Amman ya Zatayi? Tana so ta bari, Amman bata jin zata iya, Saha na son jin daɗin ta, ko rabi bata kalla ba, taji wani iri abu na fito mata, kaman tana menstration. Hannu ta kai a hankali zuwa ƙasan nata, saidai madadin taga jini, sai taji wani irin yauƙi da sulɓi, me hakan ke nufi? Gashi ta gaza tashi ma, balle ta shiga ban ɗakin. Abunda Saha ta faɗa mata ɗazu ne a kunne ya faɗo mata arai, da wannan ƴan dubarun tabi ta gamsar da kanta, sai kuma ta koma gefe, gabanta naci gaba da faɗuwa sosai. Menene haka take aikatawa? Ko dama ashe mace zata iya bin wata hanya domin satisfying kanta? Da kyar ta tashi, tana mai faɗa wa banɗaki, ruwa ta tara, tana mai mixing nasu da Hot water ɗinta Ammin su ke ajiye masu na tsarki, sannan tayi wanka gabaki ɗaya ta fito. Saidai har yanzu ta gaza tantance kalar tunanin da take yi. Shin anya tana aikata abu mai kyau kuwa? Anya Saha itama tana kyauta wa? Idan ta sake Ammi ta kamata da irin waɗannan halayyar tasan dambunta zatayi ta rarraba ma maƙota.. ******* A hankali ya kai zaune gefen gadon, yana mai kai hannu bisa bargon data kwanta ta duƙunƙune ciki. "Salma tashi magana zamuyi dake" Ɗan guntun tsaki taja ciki ciki, lokaci guda tana mai sakin miƙa, haɗi da yin hamdala, sannan ta tashi zaunen. Bata kalle shi ba, kaman yanda hakan bai dame shi ba, ko ba komai yasan daru take ji ɗan tsakanin nan. Dan haka sai bai kula ta ba, ya gyara zaman shi, yana mai kamo mata hannuwa duka. "Please Salma ki bani aron hankalin ki nan" ya faɗa cikin marairaicewa. Sai ya bata tausayi, ita kanta ta tabbata mijin nata yana sonta, kuma yana iya bakin ƙoƙarin shi wajen bata dukkanin kulawar da ta dace, bata neman komai ta rasa, kawai dai matsalar shi da yake raggo a shimfiɗa, ita kuma tana hangen muddin ta cigaba da zama dashi a haka akwai cutar wa. "Salma dan Allah ki faɗa man, idan a zamantakewa ta dake akwai ta inda na Gaza maki? Ci ne bakya samu? Ko sha? Sutura? Ko kwanciyar hankali? Dan Allah ki bani amsa, na Gaza da ganin fushin nan naki, sai nake ganin kaman Allah zai iya kamani a bisa hakan." Maganganun nashi sun ratsa ta, ɓangare guda kuma sai taji wani irin haushin shi, kuji fa abunda yake faɗa, wai ta ina ya gaza dani? Zamewa tayi a hankali zata koma kwancen, sai kuma yayi saurin sake damƙe hannun ta. "Please salma for God sake" Idanunta ta sauke cikin nashi. Ita kanta tasan tayi dace da namiji na nuna ma sa'a, kuma kaman yanda ya faɗa, baya da matsala sai ta fanni guda, ba zai iya tsawon zango da mace ba, ba zai iya daurewa ya haƙure ya bata abunda take so ba. Duk iya nacewar da take wajen siyan magungunan mata tana sha, domin ta gyara mashi kanta, amman ina shi Sam ba haka yake ba, ada tana zargin kanta ko ta gaza ne ta fannin gyara? Sai daga baya ta kula cewa duk mazan litattafan da take karantawa sunfi nata juriya, dauriya da iya nuna soyayya a gado irin ta auratayya. Girgiza kanta ta shiga yi, lokaci guda tana mai cewa "Komai nake nema ina samu, saidai..." Sai kuma tayi shiru, ta kas a idasa faɗar Abunda tayi niyya, kunya kuma sai ta rufe ta. "Sai me Salma? Ɗazu fa ina ji kina ta gaya man magana ciki ciki, duk da ba zan iya fahimtar inda kika dosa ba, Amman sai nake ganin kaman ina shiga haƙƙin ki ne, ta fannin mu'amalar auratayya dake, dan haka dan Allah kiyi haƙuri, na Gaza, ni kaina nasan baki samun yanda kike so a gareni, Amman dan Allah kiyi haƙuri, idan ma lafiya ce bana da ita, na maki alƙawarin zan nemi magani insha Allahu" Ga mamakin shi, sai kuma yaga ta ɗago kai, tana mai ɗan motsa fuskar ta, murmushin gefen fuska ta saki, lokaci guda tana mai sauke kanta ƙasa, cikin wata irin kunya kuma. "Nagode Abban Husna, nima kayi haƙuri idan na ɓata maka rai, naji ba daɗi ne, kuma kaga kai kaɗai ke gareni.." Saurin rufe mata baki yayi da tafukan hannayen shi, shi kanshi yasan yana son Salma, kuma yasan itama tana sonshi, ya yadda kuma da tarbiyyarta, irin haka ne sai kaga mace na ƴan biye biye da ƴan leƙe leƙe, ta fara cenza hali ne, ta dalilin karance karancen daya kula kaman ta fara yi, saidai zai bi komai a sannu kan hankali, domin ya gano menene abunda take nufi, magani ne kuma yayi alƙawarin zai nema insha Allahu, indai wannan itace matsalar tsakanin shi da ita. Daren kuwa ba ƙaramin ƙoƙari Abdul yayi ba, wai duk dan dai ganin ya shawo kan matsalar matar tashi, saidai duk ƙoƙarin da yayi ɗin, har ta kai ga ko yatsan shi ya kasa motsawa saboda gajiya, ita a ɓangaren Salma hakan baiyi mata ba, ta tabbatar ma kanta mijin nata dai raggo ne, Sam baisan ta yanda zai mu'amalanci mace ba, kada ma akaita ga daɗewar, camon ta yanda zai sarrafa tama bai sani ba, Idanunta ta runtse, tana mai ayyano Isham na cikin *Ambaliya* wanda ta karanta jiya jiyan nan. Shi kam ba haka yake ba, kalamai da sambatun da ake cewa yana ma Muneera ma kaɗai ya isa, gashi sai yayi mata style ya kusan kala goma, Amman ita da ƙyar Abdul ke lallaɓa wa yayi biyu, wani lokaci ma ɗayan nan tilo shi kaɗai zai mata. Dogon tsoki taja, tana kai ture hannun shi da yake bisa jikin ta, tashi tayi ta shige toilet, bata san irin wannan al'amari ba, haushin Abdul takeji, kaman ta rufe shi da duka haka take ji, ina amfanin namiji irin shi? Ita ta tabbata su Husna da Musaddeq ma rabo ne, Amman inda daɗewa ke sanyawa a samu ciki, da ita ba zata taɓa samu ba. Shi kau Abdul ta ɓangaren shi, numfashi kawai yake saukewa, a ganin shi yayi iya yinshi, yayi iya ƙoƙarin shi, amman gashi duk ga alama hakan baiyi ma Salma daɗi ba, toh ya take so yayi? So take ya dinga fidda jini ne? Gaskiya ba zai iya ba, bari safiya tayi ayi wacce za'ayi a gama, yanzun ma dan dare ne, sauti nada ƙarfi da tun yanzu sai ta gane itace bata da godiyar Allah, ba shine Baida ƙoƙari ba. Lumshe idanun shi yayi a hankali, lokacin da yaji ta fito sai sakin tsaki take yi, an koma ruwa kenan? Sulhu da sasanci baiyi ba kenan? Bai ko ƙara kulata ba, shima ya miƙe, yana mai shigewa toilet ɗin, jikin shi a matuƙar sanyaye, kaman wanda baya da lakka. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* *♣Scene Four* *page 10* ******** Kwana biyu suka kwashe suna ƴar shariya, saidai har cikin ran Abdul abun na damun shi, kuma yasha alwashin neman magani, domin yana so ya gane idan wannan lalurar tashi ita ce kawai matsalar shi da Salma, ko kuma akwai inda ta sanya gaba. Yayin da ita kuma Salma kullum abun nata sai ci gaba yake yi, cikin kwana biyun nan har ta kai ga wata ƙawarta, wadda dama ita ce ta sanya ta turba ta karance karance litattafai masu harka a ciki (A cewarsu) bata bin litattafai, *First night* sune pages ɗin da Ƙawar tata take turo mata. Wani group aka saka ta, mata ne zallah, da yawansu kuma group ne da ire-iren waɗannan marubutan suke ciki, sharhi kuwa kullum shan shi ake yi, wasu ma voice note zasu turo, tsabar son asan cewa sun karanta Page ɗin kuma ya ƙayatar dasu. Sai ya kasance ko girki take, rabi da kwatan hankalin ta na kan waya. Tana kallon yadda Abdul ke yawan shigowa da magunguna da jiƙe jiƙe, domin akwai inda yaje akace mashi sanyi ne da zafi ke damun shi. Haka ya dage wajen shan magani, so yake ya kai sati, kafin ya jaraba Sa'ar shi, duk yanda yake jin Salmar tashi na sambatu idan tana karatu "Kaga namiji malam, yo Allah na tuba wannan ai sujadda ce kawai ba zata yi mashi ba tsabar biyayya, saboda yana wadata ta da abunda yake shine auren" ya kan yi dariya idan yaji ta faɗi haka. Saidai yasan insha Allah wannan matsalar tsakanin shi da Salma ta kusa zuwa ƙarshe. Ita kuma a ɓangaren Salma dariya kawai take yi, ta riga ta ayyana ma kanta cewa mijin nata ya gaza ta wannan fannin, masalan yanzu da take ganin firar wasu daga cikin matan auren, duk style ɗin da sukayi da mijin su a daren ranar, da wuri suke hawa online, domin kowa tazo ta baje kalar tata fasahar, Abunda ke ƙara tsuma Salma kenan, dole ne yau tayi ma Abdul bore, koda kuwa me zaiyi, lallai yau sai ya kwatanta koda awa biyu ne tare da ita. Haka akayi kuwa, da daddare Abdul ya shigo ya tadda suna zaune sun kallo su duka, Husna ce ma zaune da home work gabanta sai jagwalgwalawa take yi, yayin da musaddiq kan yago mata littafin, sai ta kai mashi duka ita kuma, a sa'ili guda kuma tana kai ma Maman tata ƙara. Amman duk abun nan da suke yi, salma saidai tace "Musaddiq ba nace ka bari ba wai? Matsa daga nan mana." yaron da dududu yake shekara biyu da ƴan watanni, baima fahimci me take cewa ba. Ana haka ne Abdul yayi sallama, da sauri ya isa ga stool yana mai ajiye baƙar ledar dake hannun shi. Musaddiq ya ɗauka, yayin da ya daidaita tsayuwar shi bisa kan Husna ɗin. "Yaya Husna home work kike yi ne?" ya tambaye ta fuska sake. Dariya tayi tana mai cewa "Eah Dady, aunty ɗinmu tace duk wanda baiyi ba zata buge shi, tun ɗazu nake cema Momy tayi mani, Dady Amman sai latsa waya take yi, tama ƙi kallo na, Dady zo kayi mani kada Aunty ta doke ni" Maganar yarinyar ta ratsa shi, ɗan kallon shi ya kai kan Salma, wadda tayi ma kaman bata san da zuwan nashi ba. Ɗan ƙutawa yayi yana mai zama bisa sofa. Sai kuma ya ajiye Musaddiq ya zamo ƙasa dirshan yana mai duba ma yarinyar tashi aikin. Saida ya tabbatar sun kammala home work ɗin, kuma ta iya, sannan yace mata taje kitchen ta ɗauko mashi plate. Da kanshi ya sake ɗauko ledar ya juye naman dake ciki, sannan ya ajiye lemunan gefe, naman kaji ne guda biyu an gasa su an yayyanka. Ɗauka yayi ya miƙa ma Husna babbar cinya, sannan ya yago ya lallatsa ya sanya ma Musaddiq ɗin a baki, wanda Tunda ya ɗauki yaron yaji tsamin kashi na tashi daga cikin pampers ɗin. "Husna je kice da Momy ɗinku tazo taci abinci" Abunda ya faɗa ma yarinyar kenan, ya maida kanshi ƙasa ga cin naman shi da bama Musaddiq ɗin. Ba ko kunya haka Salma ta taso, kusa dashi ta zauna, tana mai sanya hannu cikin plate ɗin, har yanzu fa idanun ta na bisa screan ɗin wayar. Girgiza kai yayi bai dai ce mata komai ba. Yau ma yasha alwashin sasanci, idan bai manta ba, yau satin shi guda kenan yana shan magani, kaman yanda akace mashi. Saida suka kammala, Salma na nan zaune ya tashi ya ɗauke yaran, saida ya wanke ma Musaddiq kashin da yayi, ya sanya mashi wata pampers ɗin. gami da kaisu makwancin su, ya lulluɓe su ya tofa masu addu'a. Sannan ya dawo falon inda salman ke zaune. Yanzu ya tadda ta ta ajiye wayar, saidai tayi zugum hannun ta dafe da fuskar tata. A hankali ya kai hannuwan nashi yana mai janye mata tagumin da tayi. "My Salma lafiya kuwa? Me ke damun ki? Ko har yanzu fushin da ake yi dani ne ba'a huce ba?" Sauƙin kai irin na Abdul na daga cikin Abunda ke karya lagon Salma, koda tayi niyyar yi mashi wani abun sai ta gagara, masalan idan yana kallon ta da mayatattun idanun nan nashi masu rikita ta. Saidai irin yadda ya gaza ta fannin mu'amalantar tata kan ƙara Sanyawa taji har yanzu haɗuwr tashi bata kai mata 100% ba. A hankali ta girgiza kai, ita kanta tana tuhumar kanta, menene dalilin ta nayi ma Abdul wannan abun duk da take yi? Tasan da babu kyau, kuma ita kanta tarbiyyarta bata bata haka ba, saidai idan ta hau online taji yanda kowacce mace ke kwarzanta mijin ta, duk sai taji kaman ta muzanta ne, sai taga kaman ita ya gaza da ita ne. Kuma Allah ya sani tana da buƙata mai yawa, to saidai fa ya kamata ace tayi la'akari da cewa kowa da irin halittar da Allah yayi mashi. Ajiyar zuciya ta kuma saukewa mai nauyi, a take Abdul shima ya murmusa, ko ba komai yasan Salma akwai ilimi addini, shi kanshi yana rasa dalilin wani lokacin da take birkice mashi ya kasa gane kanta, saidai ma ko menene ya tabbata yana da nasaba da ƙawaye da take haɗuwa dasu a WhatsApp, "To menene Tell me mana? Akwai wani abu da kike buƙata kuma? Ko baki ƙoshi bane?" ya faɗa cikin ɗan zaulaya. Ɗan murmushi tayi mashi, "Babu komai Abban Husna, an dawo lafiya?" ta samu kanta da cewa. Har ga Allah, har cikin ranshi yaji matuƙar daɗi. Muƙewa yayi tsaye, yana mai miƙa mata hannun shi, alamun ta kama ta miƙe. Batayi musu ba, wajen bashi nata hannun itama ya ɗago da ita. Fuskar shi ya kai daidai tata, yana mai sakar mata wani irin lallausan murmushi. "Fatan an huce ko my dear?" gyaɗa mashi kai tayi, Abban Husna don Allah kayi haƙuri abubuwan da nake yi maka... " Saurin toshe mata baki yayi da hannun shi," ya wuce kawai Momyn Yara, yanzu muje muyi wanka ko? Sai mu kwanta, Nidai na gaji yau" Ƙasa ƙasa take kallon shi, sai kuma taji kaman babu daɗi kenan duk haƙurin da tayi na sati guda yauma yana nufin babu yanda zai mata kenan? Ji tayi ya shiga jan hannun ta har zuwa cikin bedroom ɗin, bakin gado ya zaunar da ita, yana mai ficewa ya kulle ko ina, sannan ya dawo ya wuce toilet ya haɗa masu ruwan wanka. Ita dai da idanu kawai take binshi. Abdul ɗinta namiji ne, irin wadda kowacce mace take da burin ta mallaka, babu Abunda take nema ta rasa shi, hasali ma ko wata hidima ta kama ta zuwa, daga nata dangin har na mijin nata Abdul, babu wadda zata nuna mata sanya sutura da riƙe waya mai tsada ƙirar IPhone 11pro max, wanda Abdul ɗinne da kanshi ya tura ma wani ƙanen shi da yake karatu china ya siyo mashi ita acen da sauƙin kuɗi ba kaman nan ba.ƴan kunne da salƙar nan na gwal Abdul duk ya mallaka mata, to ita kuwa me take nema ne? Wata zuciyar ce ta dinga mata irin wannan huɗubobin. "Idan ke baki kwantar da hankali, kuma kika dena ɗaga mashi hankali ba, zai rabu dake ya nemo wata wanda tayi daidai da buƙatar shi, shi namiji ne, ba'a mashi haka, ko bai rabu dake ba, ai zai iya neman wata, ya aure ta kina ji kina gani, kuma dole ki zauna, dukkan abubuwan da yake yi maki dole ya raba biyu, kwanan da akeyi dake kina rainawa shima dole a raba shi biyu, sai muga ya kuma zakiyi?" wata zuciyar ta raya mata haka. Ai batasan lokacin da ta miƙe ba, tana mai binshi toilet. Inaaa ai dole ta gyara halin ta, idan ma bai bata ba, dole haka zata haƙura ta lallaɓa mijin ta. Ta tadda shi ya gama haɗa ruwan wankan kenan. Bai kula ba, saidai kawai yaji hannun ta bisa jikin shi, zagaye shi tayi gabaki ɗayanshi, tana mai kwantar da kanta ta bayan shi. "Abban Husna Nifa na gaji ba zan iya wankan ba" ta samu kanta tana mai faɗa cikin shagwaɓa. Sororo yayi, anya kuwa Salmar shi ce wannan? Anya kuwa kunnen shi yaji daidai? Juyowa yayi gareta, yana mai fuskantar ta. "Momyn Husna ba gani ba? Ai sai in miki kome kike so, farin cikin ki kawai nake nema ni" Dariya tayi, tana mai kama mashi tsinin hancin shi, ji take kaman ayi mai gabaki ɗaya a wurin kawai, masalan idan ta tuno firar wata mata ɗazu da take cewa a group, ita mijinta jarumi ne, tun daga ban ɗaki idan suka fara abu, har saman gado, kai harma asuba, wani lokaci haka daya dawo daga sallar asuba ake dasa abu ɗaya. Wani irin miyau Salma ta haɗiye, ita kanta tasan ko haka tace ma Abdul ba zai taɓa yarda ba, shi mutum ne ma mai tsari, komai a tsanake yake yinshi, wanda ita kuma sai take kallon hakan a matsayin gazawa. Haka dai sukayi wankan su suka gama, har yanzu Salma ta zuba ido taga ta inda Abdul zai fara mata, ta kai matuƙa iya geji, ta tuno da jarumn wani littafi, salon shi da iya aikin shi kaɗai ya isa yaja hankalin mace ta so shi. Saidai saɓanin yanda Salma ta zata, ko bayan da sukayi addu'a suka kwanta, baya Abdul ya juya mata, baccin shi ya shiga kwasa haiƙan, ya gaji ne sosai, yau kanshi ya ɗauki chaji, aikin kamfani ba kowa bane zai iya aiwatar dashi, saboda ko naira ta ɓace sai an tuhume ka, gashi idan kamfani zata fidda kaya, dole ne kayi tsaye wajen ganin iya adadin kayan da aka fitar. Juye juye Salma ta dinga yi, wani irin haushin Abdul take kuma ji, ji take kaman ta rufe shi da duka, ji da'allah yanda ya saki baki yana ta sakin numfashi, shi dai ta tabbata ba zai cenza ba kenan? Wai kodai sai ta zaunar dashi ne ta bashi Page ɗin ya karanta da kanshi zai gane yanda gwarazan maza suke tafiyar da matan su a kan shimfiɗa ne? In bashi ba ita ta taɓa ganin namiji mai juya ma mata baya? Ita ko a litattafai ji tayi ana cewa miji rungume matarshi yake suyi bacci,bayan sun gama harka har asuba, wata ma cewa ake da ƙirjin mijinta take matashi ko fillow,bayan sun kwashe tsawon awanni huɗu suna abu ɗaya kenan. Hannu ta sanya ta fara bubbuga shi. "Abdul Abdul" cikin bacci ya jiyo ta, sai ya tashi zaune yana murtsike idanu, "Menene Salma?" "Menene fa kake tambaya ta? Kasan dai dukkan mazan da suka amsa sunan su maza, suna cen suna biya ma matansu buƙata ko? Amman gashi kai kazo ka sheme man saman gado kana kwasar baccin ka" Ta faɗa tana mai Zumɓura baki gaba. Bai kula ba, saboda babu haske a ɗakin, saidai yanayin yanda yaji tayi maganar yasan an kusa komawa ruwa. "Yi haƙuri Salma, na gaji ne sosai wallahi, ki bari bayan sallar asuba" "Gaskiya a'a, kawai idan ba zakayi ba sai ka faɗa man, ɗan minti ashirin ɗin ma da kake yi gashi yanzu ka gagara" Maganar tata kam ta bashi mamaki, anya Salman shi ce kuwa? Koda yake ai ba yanzu ne ta fara irin waɗannan abubuwan ba. "Nidai wallahi na fara gajiya, gara in fito maka a mutum, wannan shine auren fa, idan har ba zaka iya ba, gara ka sauwaƙe mani inje in nemi daidai dani.." "Subhanallah salma, kanki ɗaya kuwa?" yayi saurin faɗa, yana mai lalubo wayar shi ya kunna ya haske ta. Sai ta kauda fuska tana mai cewa "Ah to ai gaskiya ce" Shiru ne ya biyo baya, yayin da zuciyar Abdul keta bugawa. Dole ne ya raba Salma da wayar nan, wayar na neman zame mashi bala'i, watau ta fara karance karance kenan irin wanda yake jin labari? Tana haɗuwa da ƙawayen banza, masu tura matan mutane zuwa ga halaka ko?" Matsawa yayi sosai zuwa kanta. Yana mai tallafo kanta, " Ya Rab Salma, why? Haka kika fi so?" ya jefa mata tambaya. Gyaɗa mashi kai tayi. Shima sai ya jinjina kai alamun to bari in maki yanda kike so, Amman ba zan kashe kaina ba. Duk yanda Abdul yayi ƙoƙari yau ga Salma bata yaba ba, bata kuma gode ba, hasalima wancen Hisham ɗin take tunowa. Ana cikin haka ne taji Abdul ya zaren jikinshi daga gareta, ba yanda ta iya, ai sai ta saki kuka sosai, hankalin Abdul yayi mugun tashi, matsalar Salma na neman gagarar shi, ya zaiyi ne wai? Ga matsalar wajen aiki da yau da sukayi lissafi anyi shoi na wajen miliyoyi kuma shi ke da alhakin hakan. Ga matsalar registration na ƙanen shi maƙudan kuɗi ake nema a hannun shi, wanda mahaifiyar shi ta ƙafe akan lallai sai shine zaiyi mashi, ga kuma matsalar cikin gida ta salma. Dafe kai yayi sosai kanshi ke juya mashi, ya rasa yanda zaiyi. Miƙewa yayi ya shiga toilet. Yana fitowa bai kula Salma dake ta kukan ƙorafi ba, ita lallai baiyi mata yanda saura kema matan su ba. Duvet ɗinshi kawai ya ɗauka, yana mai komawa falo, salma ta saba dawowa falo ta kwanta, yau sai ya kwammace ya bar mata ɗakin gabaki ɗaya. Ya fara gajiya sosai da matsaltsalun Salma, zuciyar shi na raya mashi abubuwa da dama, wanda baya san ya ɗauki shawara ko ɗaya daga cikin wanda zuciyar tashi ke bashi, domin yasan hakan ba zaiyi ma Salmar daɗi ba. Saidai ba yadda zaiyi, muddin bata gyara ba, shi kuwa dole ne ya nema ma kanshi mafita, ai yasan lafiyar ta lau, Tunda da ba haka take ba, balle yace ko tana cikin irin matan nan da basa gajiya da ɗa namiji. Da kyar ya samu bacci ɓarawo ya ɗauke shi, itama Salmar kwanciya tayi tana mai zuzzunɓura baki da ƙunƙuni, ta sare da lamarin Abdul, bata ji idan ya cika cikakken ɗa namiji kyaun da haibar a fili ce, Amman idan aka je other Room fa saidai a hankali, dole ne ta fidda kunya ta tambayi ƙawayen nata, ko kuma tabi marubuciyar *ambaliya* domin taji idan akwai wani siriri da zata bada, wanda itama zata samu irin Abdul ya dinga mata irin yanda Hisham kema matarshi. *****' Kaman yanda Ammin tata tace mata, yau tun da safe ta shiga kitchen ta toya masu doya da kwai ɗinɗa Ammin tata tace mata, sai ta haɗa masu shayi mai kyau. Ammin ce ta leƙa ɗakin nasu ta tadda ta zaune bisa gado, duka hankalin ta na kan wayar tata. Ta fara gajiya da wannan latse latsen wayar na Hunayda, ga karance karance abubuwa marasa ma'ana. Tsaye tayi tana kallonta, wanda bata ma san tana wajen ba. Ta daɗe kafin ta juya tabar ƙofar ɗakin tana mai girgiza kai. Tana lura da Hunaydan koda ta gama haɗa kalacin, bata wani ci na kirki ba, gashi har Hajna ta shirya zuwa islamiyyar ta safe Amman ita tana zaune. Tasan yanda Zatayi mata, tasan ta inda zata ɓullo nata, ai in tasan wata batasan wata ba. Sake dawowa tayi, aikuwa ta balbaleta da faɗa, dan dole ta ajiye wayar ta tashi ta fara shiryawa. Wayar Ammin ta ɗauka domin duba ire iren litattafan da Hunaydan Ke karantawa, wanda ta tabbata Saha ce kan gaba wajen turo mata. Saidai me wayar an kulle ta da pass words, tasan saboda Hajna ne tayi hakan, ajiye wayar tayi tana mai juyawa ta fice daga ɗakin. Wayar ta ta ɗauko itama bayan ta shiga ɗakin, ta kai zaune bakin gado bayan ta latsa kiran wata number. "Hello Hajiya Gambo mun tashi lafiya?" Ɗaya ɓangaren akace "Lafiya Lau Hajiya Hauwa, fatan mun tashi lafiya?" "Lafiya lau wallahi sai godiya, ya iyali da kuma su Sulaym?" "Sulaym suna lafiya ai kinsan tana makaranta bata ma kai ga dawowa ba" "Oh ke duniya, Sulaym fa har ta shiga university fa ko?" cewr Ammi. Daga cen ɓangaren wadda aka kira da Hajiya Gambo tayi dariya. "Hajiya Hauwa kenan, ince ko kin manta Sulaym taba Hunayda kusan shekara guda? Kin manta lokacin da kika zo sunan Sulaym kina amarya, ba ko cikin Hunayda?" Dariya Ammi tayi "Ahaf, aifa wallahi na manta shaf, ashe fa Sulaym gaban Hunayda take, Amman yaran nan fa ba wani sanin juna sukayi ba sosai Hajiya, kinga ba zasuyi zumuncin da mu iyayen su mukayi ba" "Ai laifinki ne Hajiya Hauwa, kece baki barinsu suna zuwa gaida iyayen su, kuma gashi ke bakya kawo su, kullum idan kika zo sai kice suna makaranta, gashi ma sun gama amma har yanzu haka, gara gara ma Hajna yanzu ita ce ke makaranta" Dariya Ammi ta sake yi, "Insha Allahu ƙawata ki kwantar da hankalinki, yara dai zasu zo yi maki hutu har Katsina, Amman sai Hajna ta samu hutu, yanzu dai ba ma wannan maganar ta sanya na kira ki ba, wai ya rubutu kuwa? Har yanzu kina yi ne?" "Toh kinji hajiya, Allah na tuba me za'a fasa ne? Har yanzu muna ɗan taɓawa, saidai kinsan yanayin jiki gashi kuma Baban su Sulaym ba cikakkar lafiya ba Shiyasa wani lokaci sai in kwana biyu ban rubuta ba, kinsan yanzu ci gaba yazo, an maida rubutun online, to idan na rubuta na wallafa, sai in samu kuma in maida shi online, inda nan ma kuma akwai masu karantawa" Itama Ammi ta ɓangaren ta sai ta miƙe, "Yauwa Hajiya Gambo dama gaɓar da nake so azo kenan, dama Hunayda ce ta nace ma karance karancen nan, to kinsan Baban su yana da ra'ayin riƙau, yace makarantar bokon nan dai ta gama, sai idan tayi aure taci gaba, gashi kuma har yanzu Hunaydan dududu nawa take? Shine nake so idan ba damuwa, ki saka ta group ɗin litattafan ki, indai har ƴan mata zasu iya karantawa ba matsala" "A'ah ba wata matsala insha Allahu, ai nima har Sulaym na karantawa wallahi, kinsan fa Rubutun namu ma ai mun fi so ƴan mata na karantawa, ni bana daga cikin irin Writers ɗin nan na zamani da rubuce rubucen batsa ya rufe masu ido, ke in tabbatar maki ma, gabaki ɗaya ƙungiyarmu bama irin waɗannan rubuce rubucen, abu mai amfani da zai amfani goben yaran mu shi muke rubutawa, yanda zasu kula da kansu, da kuma girke girke da haɗa mayuka da sabullai, sai kuma yanda zasu zauna da kowa lafiya, da kuma rayuwar duniyar nan, sai rayuwar gidan aure da zasu iya fuskanta nan gaba. Kaman yanda bana son rayuwar yarana ta ɓaci, haka ma bana son rayuwar yaron kowa ta ɓaci ta dalili na" Wannan magana tayi ma Ammi daɗi, saboda haka ne tayi ma ƙawarta godiya, haɗi da Sallamar cewa lallai ta saka Hunayda cikin wannan group na Hajiya Gambo. Tasan Hajiya Gambo tsohuwar marubuciya ce, hasalima tana daga cikin marubutan da suka amshi kambun girmamawa ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, haka kuma tana wakiltar manyan marubuta, zuwa taron ƙara ma juna sani da kuma haɓɓaka Rubutun zube, da adabin baka. Tana ajiye wayar Hunayda ta shigo ɗakin sanye da kayan islamiyya. "Ammi na shirya zan wuce, Hajna tayi tafiyar ta ta barni" Ammin ce ta haɗe fuska tamau, "to ba dole tayi tafiyar ta ba? Kin tsaya caccakar waya, kuma bayan kinsan da zuwa makarantar? Sai ki tafi, Allah ma yasa malamin ku ya zane ki, gobe ai ba kin ƙara ba" Haka Hunayda ta fito jikin ta duk a sanyaye, bata so take ɓata ma Ammin tata rai, ta sani sarai Amminta tsaye take kan su, da tarbiyyarsu, to saidai Page ɗin da Saha ta turo mata ne jiya ya tsumata sosai, Page ɗinɗa har wanka saida yaja mata tayi cikin dare, duk da hakan bata ji ta gamsu ba, saida ta buɗe video ɗinɗa Sahar ta sake turo mata jiya, wanda ita har yanzu ma dai ta rasa inda take samo su wlh, bata so take kallo, Amman idan suna fira da Sahar kan ƙara jan hankalinta zuwa ga kallo da karantawar. Ta sani sarai yau Sahar ba zata je islamiyya ba, wai suna da biki, inda ta ɗan guntsa mata cewa zata haɗe da Zaiyad mutumen nata, duk yanda sukayi zata zo ta bata labari. Hankalin Hunaydan kan ƙara tashi, ita dai ko da wasa wallahi ba zata iya aikata abunda Saha ke aikatawa ba, tana tsoron Amminta da Abban ta, saboda haka ne ta sake ɗaga ƙafa har bakin makarantar. Daga nesa ta hango shi yana taron makara. Malam Suhail ne, saboda haka sai duk taji ba daɗi, Tunda ya furta mata kalmar so, sai take takura a gaban shi, tana hango Hajna daga cikin makaranta tana mata dariya, ta raya a ranta cewa ko ranƙwashi ɗaya ne sai ta bata idan suka koma gida. Yanda yayi ma kowa bulala uku a hannu haka itama yayi mata, saidai ya sassauta mata wajen bugawa da ƙarfi. Yanayi yana tsare ta da kallon tuhuma, na cewa kullum ita sai ta makara, saidai ta sauke kanta ƙasa kawai tana mai shigewa islamiyyar. Tana jin kunya da nauyin shi, saidai bata so ta bari sonshi ya kamata, kaman yanda Saha ke faɗa mata cewa tafi ƙarfin malamin islamiyya. A cikin ranta kuwa rayawa take yi cewa, lallai bakin iyaye abu ne daya kamata kowa ace ya guje shi, gashi dai Ammin tata cikin ɓacin rai ta mata addu'ar a doketan, kuma gashi yabi ta, saida akayi mata bulala uku a hannu, duk da tasan har cikin zuciyar Ummin ba Zataso ace an doke ta ba. Yau ma dai saida Malam Suhail ɗin ya biyo ta, yana mai jaddada mata cewa baya so ne yake tsayawa da ita a waje haka kan hanya, saboda haka ta bashi damar ya tura gidan nasu, ga mamakin ta, maimakon ma taji ya bata haushi kaman yanda ya doke ta ɗazu, sai yayi mata kwarjini sosai a fuska, Gaza mu santa mashi tayi, tunda ma yau Saha bata nan, kawai sai ta amsa mashi, tana mai ce mashi kada yace da saninta aka je gidan nasu, Dariya yayi, ya kula akwai ƙuruciya sosai da wauta a cikin al'amarn ta, duk dai da haka shi yaji ya amince, indai zata aure shi da zuciya ɗaya, insha Allahu shikam babu abunda zai hana shi auren ta. Yayinda ita kuma take rayawa a ranta cewa idan Saha taji ko ya zata ce? Gaskiya koma dai me zata ce gara tace, Amman ita ta gaji da ƴan matse matse da ulƴan kalla ce kallace, gara kawai taje tayi mai digi, wanda har lada sai ta samu, kuma gashi tayi sa'a malam Suhail ɗin nata akwai tarin sani da ilimi a cikin kanshi, ta fanni guda kuma gashi ɗan gayu, wanda zamu iya cewa idan da halin yaran zamani gareshi, toh fa da babu abunda zai kaishi makarantar islamiyya koyarwa, zai ga ne ai kaman yafi ƙarfin hakan. ******* Taji daɗin yanda Ummin tata take shaida mata akan cewa ta kula da su Surayya da Na'eef, ita ba zata samu damar zuwa ba, kuma dama bikin dangin baban nata ne, wanda dama ta sani da wuya Ammin taje, kayansu suka haɗa akwati guda, duk da cikin gari ne inda ake bikin, saidai Ummin tace ba zata lamunci kai komi ba, har zuwa kwana biyu da za'ayi ana shagalin bikin. Haka ta basu kuɗin a Bus, wadda zata kaisu har ƙofar gida, jama Sahabat ɗin kunne Ummi tayi sosai, duk da tasan cewa Sahabat ɗin dai akwai ɗan rashin ji, saidai ta tabbata bata kula kowa, balle ma samari, wanda ko wayar har yanzu ta ƙi barinta ta riƙe, to yanda duniyar social network ɗin nan ma ke cike da ƙalubale iri iri yaushe zata bar ɗiyar ta ta shige ta? Ai saidai idan tayi aure, wannan kam zata iya bari, Amman ita kanta tasan irin rubuce rubucen da take yi, ko ƴaƴan ƙannenta bata so su kasance suna karantawa, na daga cikin dalilin ta na cenza suna kenan daga Maryam zuwa Hibba. Bakin tanƙamemen gidan Mai Bus ɗin ya ajiye su, zuciyar Sahabat wanke tas, wanda tun da sanyin safiya dama tayi ma Zaiyad text akan cewa yau fa zasu haɗu, dan haka sai yayi mata shiri mai kyau, jiya kwana suka yi a waya yana mata ƴan abubuwa, wanda har saida ya sanya ta fidda kayan nata, yana ce mata ta ayyano shi yana kusa da ita, subhanallah, abubuwa dai iri iri, saidai ta shige toilet, domin sai zuciyar ta ke raya mata ko Surayyan ba bacci take ba tana sauraren ta. Ƴan uwan baban su sunyi murna da zuwan su, sai suke tuna masu da ɗan uwansu marigayi, dama kuma gashi Ummin ba barinsu take zuwa ko ina ba, sai in irin hakan ta tashi, ita duk a tunanin ta zatayi ma Allah wayau ne. Yau kam sai Allah, domin tun da sanyin marece aka fara shirin kai amarya ɗakin ta bayan an ɗaura aure, inda daga cen ne za'a kwashi mutane aje wajen dinner. Sahabat na gaba gaba, duk da ƙawayen amaryar sun fita a shekaru, saidai ba zasu nuna mata raɓar jiki ba, kusan ma zamu iya cewa tafi wasu da dama cikin ƙawayen cika da haɓɓaka. Hakan take kuma a ɓangare guda tun ɗazu Zaiyad keyo mata wayan cewa ta kwatanta mashi wajen da ake dinner ɗin. Aikuwa ba shayin komai ta kwatanta mashi. Ihun murna ya saki, lokacin da text ɗin ya shigo, ya hararo cewa yau akwai shan gara, dole ne ya huce gajiya da tarin buƙatun shi akan yarinyar, masalan ma da yaga cewa ya shawo kanta da sauri, har alƙawarin kwatanta mashi abunda ya tura mata jiya a waya tayi. Ankai amarya lafiya, bayan isha'i ne aka fara shirin tafiya dinner, dama ba kowa zai je ba, kuma gashi ita ta shige cikin ƙawayen amarya, inda har anko ma duk Ummi tayi mata, a cewarta kada ace ta raba zumuncin dake tsakani. Babban Hotel ne daya amsa sunanshi kaf faɗin garin na Kaduna, an ƙawata wurin sosai da kayan ado da manyan speakers na kiɗa. Zaiyad da tun ɗazu ya isa, a waya ya kira Saha, sai gata ta fita domin shiga dashi wurin. Maimakon ya bita, saima jan hannun ta yayi zuwa bayan motocin da suke fake a wajen. "Menene haka Sweet heart? Kada fa wani ya gammu" ta faɗa cikin ɗan zaro idanu, lokaci guda tana yi tana waige waige. "Is ok my Habat!, babu wanda zai gammu nan we are safe" Ɗan girgiza mashi kanta tayi, har yanzu hannuwan ta suna cikin nashi, ya tallafo gefen ƙugun nata ɗaya da hannun shi ɗaya zuwa cikin jikin nashi. Jikin ta na gogar nashi jiki, har yanzu kyarma take yi, bata so a samu matsala, masalan ma da bikin yake na dangin mahaifin ta. Lura da hakan ne da yayi, ya sanya shi buɗe motar tashi back seat ya saka ta shima ya shige, sai a lokacin ne ta saki ajiyar zuciya, tana mai kai kanta saman kafaɗar shi, ba tare data san tayi hakan ba. Shi kuwa daɗi yaji sosai ya fara shawo kan Sahabat ɗin, ko ba komai ya sani turaren da yayi amfani dashi mai ƙarfi ne yana fizgar hankalin mace zuwa gareshi, shi ɗin dai ne yake shafawa, duk lokacin da yaso samun kan yarinya. Karkacewa yayi, yana mai fiddo wani ɗan ƙaramin chewing gum daga aljihun shi. Guda biyu ne kacal, saboda haka ya sanya mata ɗaya a baki shima ya sanya ɗaya, har yanzu kanta na saman jikinshi. Kalamai masu daɗi yake fesa mata, ta narke sosai a ƙaunar shi sai wani irin yamm take ji sosai a jikin nata, lokaci guda kuma video ɗin da yake turo mata tana kalla suka shiga playing a ƙwayar idanun nata. Zataso ta kwatanta, masalan yanzu da suka keɓe tsakanin su su biyu, babu mai ganin su, ɓangare guda kuma update ɗin Ummin nata na jiya yana sake dawowa tiryan tiryan a kwakwalwar ta, masalan inda take bayyana irin daɗin da mace take ji idan ta kasance da namiji. To ita me zai hana ta itama? Shine fa zai aure ta, ga Zaiyad ɗin ya haɗu, abun alfahari ne a gareta kuma cewa tana tarayya da namiji kaman Zayyad ɗin. Bata dawo daga tunanin da ta tafi ba, taji hannun shi a gadon bayan nata, ƙoƙarin zipping rigar ta yakeyi, ga mamakin ta, babu wani yunƙuri na hana shi da tayi, Saima sake gantsarewa da tayi, domin yaji daɗin zagewa. Ta ko ina hancin shi na bisa jikin ta, sun shagala sosai, da taimakon desire chewing gum da ya saka mata take tauna bata sani ba, ta miƙa mashi kanta sosai da sosai, enjoying moment ɗin take a hankali, inda shi kuma cikin salo da ƙwarewa a yaudara ya dinga raɗa mata Kalamai, wanda zasu taimaka mashi wajen yarda cewa shi ɗin nata ne, kuma kome ma yayi mata a yanzu, shi ɗin dai ne zai aure ta. Lallai Ummanta nayi gaskiya, ashe haka ake ji? Abu ɗaya ne bata yarda ba, ya kusance ta takanji ance ana shan wahala sosai da sosai a yi na farko, Amman inda ba haka ba, babu Abunda zai hana ta miƙa mashi ragamar kanta a wannan daren na yau, inda wajen yake tsit, baka jin sautin komai, sai tashin kiɗa daga cen nesa da inda mitocin nasu suke. Hasken fitilar motar data dalle wurin, shi yayi sanadin firgitarsu sosai da sosai, daga irin duniyar da suka wulla, sai tayi saurin ture shi ga inda yake nufa ɗin, gyalenta ta jawo tana mai gyara lulluɓin ta, jikinta sai ya ɗauki rawa, tunani take an gansu, saboda haka ne tayi saurin ɓalle motar ta fito tana mai zare idanu. Ashe wasu ƴan party ɗin ne da basu samu isowa da wuri ba sai yanzu, sun ma riga sun wuce zuwa ciki kai tsaye, da sauri tayi zipping rigar tata zuwa sama, bayan ta maida hannun bra ɗin tata da ya zame mata. Sai lokacin ta lura da shima ashe ya fito, ya jingina kanshi bisa fuskar motar yana maida numfashi da sauri da sauri, saboda ya kai iya matuƙa, kuma bai taɓa kawo ma ranshi cewa ba zai samu yadda yaso ba a lokacin... ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:* *"Allah (mighty and sublime be He) says:* *'The first of his actions for which a servant of Allah will be held accountable on the Day of Resurrection will be his prayers.' If they are in order, then he will have prospered and succeeded; and if they are wanting, then he will have failed and lost. If there is something defective in his obligatory prayers, the Lord (glorified and exalted be He) will say: 'See if My servant has any supererogatory prayers with which may be completed that which was defective in his obligatory prayers.' Then the rest of his actions will be judged in like fashion."* *[At-Tirmidhi (also by Abu Dawud, an-Nasa'i, Ibn Majah and Ahmad).]* عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ عَمَلِهِ صَلَاتُهُ. فَإِنْ صَلُحَتْ فَقَدْ أَفْلَحَ وَأَنْجَحَ، وَإِنْ فَسَدَتْ فَقَدْ خَابَ وَخَسِرَ، فَإِنْ انْتَقَصَ مِنْ فَرِيضَتِهِ شَيْءٌ، قَالَ الرَّبُّ عَزَّ وَجَلَّ: انْظُرُوا هَلْ لِعَبْدِي مِنْ تَطَوُّعٍ فَيُكَمَّلَ بِهَا مَا انْتَقَصَ مِنْ الْفَرِيضَةِ، ثُمَّ يَكُونُ سَائِرُ عَمَلِهِ عَلَى ذَلِكَ. رواه الترمذي وكذلك أبو داود والنسائي وابن ماجه وأحمد *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* *♣Scene Four* ~*Page 11*~ Wannan karon, irin fushin da Abdul ya ɗauka da Salmar tashi kam yayi tsanani. Duk wata hulɗa da zata haɗa shi da ita ya kauce mata. Hatta da ruwan wanka da abinci baya saurara daga gareta. Komai shine yake yi ma kanshi, haka kuma yayi ma yaran shi. Hatta da wanka shine yake masu tun da safe idan ya tashi, yayi ma Husna shirin makaranta, ya saka ta gaban mota yaje ya ajiye ta, sannan ya wuce zuwa wajen aiki, idan rana tayi, haka zai ajiye abunda yake yi, yaje ya ɗauko ta, ya biya ya siya masu abinci a restaurant sannan ya wuce gida, haka zai tasa su gaba ita da musaddiq suci abincin, sai sun gama ci ne sannan zai mata shirin islamiyya, wata yarinyar maƙautansu da take tafiya da ita tazo ta ɗauke ta, sai a lokacin ne zai samu ya koma bakin aikin shi. Duk wannan abun da yake Salmar na kallon shi, wai ta barshi ne ya ɗana irin wahalar da mace ke sha a cikin gida, wanda itama idan tazo da tata buƙatar namiji ya kasa yin kataɓus a gareta, bayan duk waccen wahalar aikin gidan da take sha. Iyakarta tayi wanka ta shirya, sai shiga kitchen da take yi, ta sama ma kanta abunda zata kai bakin salatin ta. Ko gyaran gidan bata damu da tayi ba. Ita duk a ganin ta, da hakan ne zai iya gane kuskuren da yake aikata mata. Abunda basu sani ba, su duka suna matuƙar shan wahala da wannan zaman doya da manja da suke yi. Ta fannin Salma kuwa, yanzu hatta da ƴan kuɗaɗen da Abdul ɗin ke bata na buƙatar ta, wanda dasu ne take amfani ta sanya data sai suka dawo suna gagarar ta. Yayin da shi kuma Abdul cen wajen aiki suka fara mashi ƙorafi, inda Allah ya taimake shi ma, kuɗaɗen da sukayi waibuwa a kamfanin an riga da an gano inda suka shige. Kullum manager ƙorafi yake na rashin maida hankali kan aikin na Abdul. Tuni fa ya fara ramewa, ya fita hayyacin shi, duk inda Kaga Abdul kai kasan baya cikin walwala. Ita kuwa Salma da ƴan kayayyakinta da bata ɗinka ba, su ta dinga ɗauka tana kaima wata dillaliya kusa dasu nan tana siye tana bata kuɗin, domin kawai ta siya data ta hau online, saboda bata da rashin ci dai balle sha. Group ɗin da tafi jin daɗi a ko yaushe nan tafi shiriricewa. Matan aure ne da zawarawa cike taf da group ɗin, komai tattaunawa akeyi a ciki, kai hatta da abincin da suka ci sai sun ɗauki photon shi sun tura, ga maganganu marasa ma'ana da suke yawan yi, ga litattafai masu munin karantawa. Ita kuwa Salma a hakan komai yayi mata zam. Ƙorafinta ta tura, gami da irin zaman ko in kula ɗin da suke yi da mijin ta, inda ta ƙara da cewa babu abunda baya yi mata amman, komai, ci, sha, sutura mai tsada, waya mai tsada, muhalli da kuma kulawa da dangin ta. Kwanaki ma har ya fara shawarar siya mata ƴar ƙaramar mota saboda kai Husna makaranta. To Amman ita matsalar ta dashi kawai wajen shimfiɗa ne. Yanzu yama daina kula ta, ko inda take baya kalla,tana so a sake bata wasu shawarwarin masu ƙarfi. An bata shawarwari sosai da sosai, inda tayi ta jin daɗi, tana kwashe dukkan wani harafi na shawara da aka bata, saboda da yawa wasu ce mata suke ta cigaba da nuna mashi kuskuren shi, ai wannan abun babu abunda aka haɗa dashi, wata ma har ce mata take wai "Aini Namiji wallahi idan har ba zai iya gamsar dani a shimfiɗa ba, to gara a tasa mun naman balangu inta ci, ko ba komai dai nasan zan maida kwaɗayi na". Nan dai suka ci gaba da tattaunawa, da bata shawarwari marasa ma'ana. Wata da tafi kowa zaƙalƙalewa a group ɗince ta bita private chat. Bayan sun gama gaisawa ne ta nuna ma Salmar irin tausaya mata da tayi, nan ta nemi Salmar data bata dama ta zama ƙawarta. Cikin kwanaki kaɗan suka wani irin ɗinke da matar data kasance bazawara, auren ta biyu, amman ta ɓoye ma Salmar, wajen ce mata aurenta ɗaya, kuma shima matsalar dangin shi ce, nan salma ta saki baki tana gaya mata, ita dai bata da matsala da dangin Abdul, kowa na sonta na ƙaunar ta, hatta da mahaifiyar shi. Kafin kace me, Salma ta kwashe duk wani sirri nata kaf da abdul ta faɗa mata, hatta da yanayin yanda Abdul ɗin ke kwanciya da ita, da yanda bata kula shi yanzu, Amman wai duk da haka babu Abunda baya kawowa gidan shi, nama kuwa idan ka buɗe frezer ɗinta kaman yayi magana, banda sauran kayan ciye ciye da maƙulashe,da kuma yanayin aikin Abdul ɗin, harda abubuwan da yafi so mace tayi mashi, da kuma wanda baya so mace tayi mashi. Wata irin shaƙuwa sukayi da matar da take da suna Jameela, kafin kace me har Salma ta bata adireshin ta, da kuma wai lokacin da zata zo gidan ta iske Abdul, domin ta ganshi, nan tayi mata alƙawurran shawarwari da kuma wasu magunguna da zata bata, wai ta sanya ka Abdul ɗin a cikin abun sha. ********** Cikin kwana biyun da Saha tayi gidan biki, sau biyu suna haɗuwa da Zaiyad, yaro da kuɗi kenan, ɗan gayu mai tashe da faɗa aji. Duk wata hanya da Zaiyad zai bi yaja hankalin Saha ya bita kuwa. Ya zuwa yanzu tana jin babu abunda zai iya raba ta da Zaiyad ɗin nata, kai koda Ummi ce kuwa. Ta fannin karatun littafi kuwa sai abunda yaci gaba. Kwana biyun da sukayi basa gida, sau uku Ummin tata ke sakin update a kullum, wannan ya nuna bata aikata komai cikin gidan nata sai typing, domin ta burge Fans. Comment kuwa da take so, tana masifar shan shi, wasu su zaga wasu su yaba, Amman da yawa cikin fans ɗin nata, suna jindaɗin abunda take yi, kaman yanda suke mata comment suna mai ƙarfafa mata guiwa akan ta cigaba, ai wannan ma faɗakantarwa ce a hakan. Ta kan ce, "Ahh to! duk wanda yaji ba zai iya ba sai ya barshi kada ya karanta" ko kuma tace "Ai bata sanya Uban kowa ya karanta ba", wani Page ɗin ma da tasan mai zafi ne, ta kan yi kandako a saman Page ɗin, da *"If you read, you are on your own"* Wannan abu nama fans ɗinta matuƙar daɗi, da yawa ma tarawa suke sai dare yayi su karanta, matan auren wasu su nemi mazajen su, wasu kuma su biya ma kansu buƙata daga haka, wasu ƴan matan kuwa da hannu ko wata hanyar suke bi wajen samun gamsuwa. Ummi kuwa ba tare da tasan cewa, duk wani abu data rubutu a nan duniya sai Allah ya tada ta akan shi ba ranar gobe ƙiyama, sannan duk wanda yabi wata hanya da ba daidai ba wajen gamsar da kanshi, to fa tana da kamashon zunubi. Duk abunda ake yi Sahan na kallo, domin tana cikin group ɗin Ummin, Amman ba tare da sanin Ummin ba. Kullum wayar Sahabat a silent take, hatta da hasken wayar ta kashe shi duka ta maida shi a (A) Ana gama shagalin biki suka tattara suka dawo gida, abun baima Sahabat daɗi ba, domin ya bala'in takurata wajen haɗuwa da Zaiyad ɗin nata, saidai ta shige toilet suyi ta waya, ko kuma tayi ta playing xxx video ɗin da Zaiyad ɗin ke turo mata, wai tayi course akan su, idan sunyi aure ta dinga practicing a kanshi. Abun na mata daɗi, sai take yarda ma kanta cewa lallai Zaiyad ɗin kullum a shirye yake da auren nata. Bata tsagaita da tura ma Hunayda pages ba, da kuma video's ɗin. Duk da ita kanta Hunaydan idan ta gama kalla, kuma ta tabbata ta samu gamsuwa, abun na mata ciwo, gashi cikin kwana biyun har Malam Suhayl ya turo gidan su wajen Abban ta. Ba tare da ɓata lokaci ba, abban ya basu haƙuri da cewa Hunayda tayi ƙarama da aure, saidai malam Suhayl zai iya cigaba da zuwa gidansu da rana wajenta, kafin nan da ta cika ko shekara sha takwas ne, sannan sai ayi masu auren. Ko a hakan aka tsaya yama malam Suhayl daɗi, dama kuma shi ɗinma ba wani aikin kirki gareshi ba, karantarwar ce kawai a Islamiyya, kuma mafi yawanci kowa yasan malaman islamiyya dan Allah suke yi. Saboda haka ne yake ma kanshi fatan zuwa lokacin da Abban Hunaydan ya ɗiba, shima ya samu abun yi, tunda ya riga ya kammala karatun shi, harda bautar ƙasar shi ma. Sahabat taji matuƙar haushi, inda har saida ta balbale Hunayda da bala'i da masifa, akan me zata amsa ma malam Suhayl ɗin? Sam ba ajinta bane, ina ma laifin ta samu kaman Zaiyad ɗin nata? Koma wanda ya fishi? Ko ba komai dai ita gani take kaman Malam Suhayl bai iya soyayya kwatankwacin ta Zaiyad ba, kuma ma wai abunda ya ƙara bata haushi, shine wai zance ma saidai ya dinga zuwa da rana! Ita ko Hunayda da kallo tabi Saha ɗin, har saida ta gama bambamin faɗan nata, sannan tace mata, "Idan kin gama ni zanje na ɗora ma Ammi girki, kinga yau bata nan, mu kaɗai ta bari cikin gidan, kuma so nake in kammala kafin lokacin makaranta yayi" ta faɗa tana mai miƙewa zata wuce. Da hannu Sahan ta jawo ta, "Kinga malama bar wani sauri, ita Ammin me yasa bata tsaya tayi abincin ba kafin ta fita. Nifa Shiyasa nake bala'n jin haushin mahaifan nan namu, su kullum suna kan waya, suma basu iya taɓuka komai, wai saidai lallai kai ace kayi, kaman wani bawa, mtseww" ta ƙarashe tana mai jan tsoki. Galala Hunaydar tayi tana kallon ta. "Anya kuwa Sahabat? Kin fa fara cenza hali wallahi, to ke in kina jin haushin Ummin ki, Nidai gaskiya bana jin haushin Ammi na, kuma Ammina tana yimin hakan ne domin in iya, karatu ne dai kinsan sai dare yayi nakeyi yanzu saboda Ammi tana neman ta hana, kuma nima gaskiya na fara gajiya, ina tunanin dena karatun ma baki ɗaya, indai irin waɗanda kike turo mani ne. Malam Suhayl rannan daya zo ya duba wayata yaga litattafan hausa faɗa ya dinga yiman, yana jawo man ayoyi, Allah ma ya sanya bai karanta ko kaɗan bane ai da na bani, tunanin in dena nake gaskiya, tunda babu wanda babu batsa ciki, ni kuma ina shiga cikin wani yanayi, bana so in dinga aikata ba daidai ba, kaman yanda kike yi keda Zaiyad" Ai tana ƙarashewa Saha ta miƙe cike da bala'i, "Ke asiri zaki tona min? To wama yace maki bama aikata daidai ni da Zaiyad? Soyayya ce, to matar malam nace ko shi malamin naki ya faɗa maki inda aka haramta soyayya? naga ai kuma kuna yi ko?" ta faɗa cike da masifa, har tana riƙe ƙugu. Girgiza kai Hunayda tayi, dayake ita ɗin mai sanyi ce, sai tace mata" Allah ya baki haƙuri malama, ba nufi na kenan ba, kuma koda muna soyayya ai bama yin irin taku, har yanzu ko yatsa ma malam Suhayl bai taɓa riƙewa ba, balle ma ni zan iya ce maki har yanzu ban san soyayya ba, koda nake tsayawa tare da malam Suhayl, kawai dai wanda yace yana sonka, ai yafi wanda yace shi maƙiyinka ne" Tana gama faɗar haka ta juya ta shige kitchen. Itama Saha da tsabar masifa ta kwashi wayarta, tana mai ficewa daga gidan faɗi take "ai dan kinga ma ina biyo ki ne har gidan ku, kike neman gaya man magana, har ma zaki tona man asiri game da Zaiyad, da a gaban wani kika faɗi haka fa? Lallai ma yarinyar nan, dole ne kema in dinga ɓoye maki wani abu, kuma littafi ma daga yau na dena turowa, haka ma video's ɗin. Saboda idan aka gani a cikin wayarki, cewa zakiyi ni na tura maki, kinga kin tona man asiri kenan" Tana wannan masifar har ta isa gida. Tura wayarta tayi cikin riga, sannan ta shige. Kaman kullum daiUmmin zaune take da baƙin ta, wai Fans ne suka kawo mata ziyara, daga cikinsu ma harda shatara ta arzuƙi, wai suna jin daɗin labarin ta, tana koya masu salo salo na kwanciya da ogannin nasu. (Hmm Fans kenan) Ko kallonsu Saha batayi ba, ta nemi shigewa ɗakin nasu Da sauri wata daga cikinsu ta buɗa baki tana cewa "Wannan fa Aunty Hibba? Ƴarki ce?". Kai Ummi ta gyaɗa masu, tana mai ɗaga murya ta kwala ma Saha kira. "Sahabat!!. Sahabat!!" "Na'am" ciki ciki ta amsa tana mai fitowa daga ɗakin nasu. "Ki gaida ƙawaye na mana, ko baki gansu ba?" cewar Ummin. Tana Zumɓura baki tana komai ta gaishe su, wata daga ciki ce tayi saurin cewa "Aiko kaman na taɓa ganin photon wannan a Dp ɗin wata cikin group ɗinki Aunty, kai ita ma ce wallahi" Gaban Sahabat ne ya buga damm!! Cikin in ina ta ƙarƙaro yaƙen dole tana mai cewa "a,, 'a aunty baani ba... Ce. Ni. Bana ma da wayaa" Da mamaki matar ta maida kallon ta kan fuskar Ummi. Gyaɗa mata kai tayi cikin son tabbatar mata "Kwarai ma kuwa Maman Aisar, ai bama barinta da waya yanzu, bata ma taɓa riƙe waya ba, kinsan ai sharrin zamanin nan na yanzu, saboda haka sai tayi aure, cen mijin ta ya siya mata. Gaskiya ba ita bace, ƙila dai kama ce ko?" Gyaɗa kai Saha keyi kaman ƙadangaruwa, tana tsaye sai kyarmar ƙafafu take yi. Ita kuwa matar sai ta haɗiye wani irin miyau, tana mai murmusawa itama tace to" ƙila kamar ce, Amman tabbas dai na taɓa gani wallahi" Da sauri Sahabat ta shige ɗaki, tana mai dafe baki da ƙirji, "Waih! Allah ya soni ni Sahabat, wannan shegiyar matar, ai data tona man asiri, ni me ya kaini ma sanya pic ɗina? Koda yake ai na cire tun ma ranar, ashe har ta gani, mayya kawai, to ta Allah ba taki ba, munafukan banza, ai wallahi duk sai kun shiga wuta, kuna karantawa kuna zuga ko? Harda wani kwaso ƙafafu wai kun taho godiya? Sai kace wani wa'azi ko hadisai take faɗa maku, ga masu rubutun Allah da Annabi cen, wanda ba zaka taɓa jin kalmomn batsa ba, bakwa son karantawa, amman idan aka fito ana maganganu kunfi kowa nuna ku na Allah ne, daga ku har Ummin Allah zai kama ku" Har matan nan suka bar gidan, wadda aka kira da Maman Aisar tana al'ajabi. Sai bayan fitar su ne suka hau gulmar Ummin, wai wayau zatayi ma Allah, ita tana nufin ta kimlace tata, Amman tana ɓata na wasu, Allah dai ya shirya mana, amman yanda matar nan ke tsula tsiya a labaranta akace yarinyar ta na karantawa ai data sha kunya. (Nace ai kuma kuna da laifi, da bakwa karantawa da basu rubuta ba, Allah ya kiyashe mu da kai kanmu wuta") ********** Ita kuwa Hunayda da Allah shi kyauta tabi Saha, lamarin Saha na bata tsoro, ina duk tarbiyyr da Umminta ke iƙirarin tana yi mata? Ina duk kullen na Ummin tata?. Da haka ta shige kitchen ɗin, zuciyar ta ba daɗi da irin yanda ta ɓata ma Sahar rai, ba da niyya tayi ba, saidai ba zata taɓa bari Sahar ta koya mata yima Ammin tata rashin kunya ba. Ko da suka haɗu Islamiyya, tana gani Sahar tana galla ma malam Suhayl harara, sai duk taji ba daɗi, tayi niyyar bata haƙuri. Hakan yasa da aka tashi ta tsaida Sahar domin ɓata haƙuri, Amman sai ta sake yaɓa mata wasu maganganun, harma tana ce mata "Sannu shekiya uztaziya, ai dole ki nuna man Allah, kiyi mun wa'azi, tunda zaki auri alhuda huda, ai yanzu zaki ma iya cewa musulunci na ma bai cika ba". Tana gama faɗar hakan ta sanya kai tayi wucewarta, a gaba idanun ta Zaiyad ya faka da mota ta shige, dayake Surayya yau da Na'eef basu zo islamiyyar ba, bata san me ya hana su ba, ko ina suka nufa kuma oho, abun na Saha ya fara tsanani, ta kai ma ko Kunyar jama'a bata ji, wajen shiga motar wanda har yanzu ya gagara turawa gidan su, gashi kuma in sun keɓe ɗin ta sani abunda ba daidai ba suke aikatawa. Da haka ta isa gida, zuciyar ta ba daɗi, saidai koda ta isa gidan, Ummin ta ke shaida mata cewa ta shirya tunda su Hajna sun samu hutu, zasu je Katsina gidan ƙawarta Hajiya Gambo, daganan zata kakkaisu sauran gidajen ƙawayen nata domin su gaida su. Sai taji zuciyar ta tayi sanyi, ko ba komai zata ɗan huta da darun Saha, wata ƙila ma kafin ta dawo Sahar ta huce, da wannan zummar ta taka tana mai isa ɗakin nasu ta cigaba da har haɗa masu kayayyakin da tasan zasu buƙata... ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ ♣ _Scene Four_ ~*Page 12*~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) says: 'Fasting is Mine and it is I Who give reward for it. [A man] gives up his sexual passion, his food and his drink for My sake.' Fasting is like a shield, and he who fasts has two joys: a joy when he breaks his fast and a joy when he meets his Lord. The change in the breath of the mouth of him who fasts is better in Allah's estimation than the smell of musk." [Bukhari (also by Muslim, Malik, at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: الصَّوْمُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي، وَالصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَلِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ، وَفَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ. رواه البخاري (وكذلك مسلم ومالك والترمذي النسائي وابن ماجه) ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Four_ ~*Page 12*~ Hunayda kuwa taso ace kafin wucewarsu zuwa Katsinan sun haɗu da Saha, saidai hakan bai yuwu ba. Da misalin ƙarfe taran safe duk sukayi sallama da Ammin tasu, inda Abban su ne ya bada mota a kaisu. Saida Ammin taja masu kunne sosai, kafin ta damƙa amanar kula da Surayya hannun Hunaydan. Tafiya ce da zamu iya kiran ta a nutse, domin Ammi tace ma Driver bata yarda yayi mata gudu da yaranta ba, ba sauri ake ba, balle aje ayi gaugawa. Suna cikin motar ne Hunaydan ta danna ma Sahar tata kira. Tana zaune gidan ƙunshi ana zana mata jan lalle, wanda Zaiyad ɗin yace mata yana so, kuma shine ma ya bada kuɗin, wai a cewar shi yana matuƙar son ƙamshin lallen.wayarta ce tayi tsuwwa alamun kira ya shigo. Kallon ta ta kai kan wayar, lokaci guda tana mai janye idanun ta, gami da jan tsoki kaɗan. "Kinji dashi ai, ki gama gaya man magana kuma ki nemeni yanzu? Me zan maki?" ta faɗa a hankali, iya kan laɓɓan nata. "Me kika ce?" cewar matar dake zana mata lallen. Ba tare da Sahar ta kalleta ba tace "Ba dake nake ba". Sauke kanta ƙasa tayi taci gaba da zana mata lallen. Hajna dake zaune gefe ce ta cigaba da girgiza kai a hankali. Halin Yayar tata gabaki ɗaya yana bata tsoro, ko a gida fa ba'a san tana da waya ba, gashi taja mata kunnen akan idan ta sake ta faɗa, wallahi sai ta ɓaɓɓalla ta, gashi ita kuma abunda Sahar keyi yanzu ya fara bata mamaki, a kan idonta take waya da samari a cikin ɗaki, ko kuma ta shige bayi tayi ta waya, ko tayi ta karance karance marasa amfani. Har ta buɗe baki da niyyar yima Sahar magana, sai wayar Sahar ta sake ɗaukar tsuwwa. A hasale ta juya tana kallon Hajnar. "Zo ki duba man, kibi a hankali kar ki ɓata mun waya". Shiru Hajnar tayi mata tana mai ɗauke kanta gefe, gami da turo baki gaba. "Waike dan ubanki ba dake nake magana bane? Ki kiyaye ni fa Hajna, naga kaman kin fara raina man wayau" Sake tura baki tayi gaba. "Wayar ma da Ummi bata san kina da ita ba? Wallahi ba dan ina jin tsoron ki dena ƙara man kuɗin tara ba, ai da sai na tona ki" Ta faɗa itama ciki ciki. "Me kike cewa? Ba dai zagina kike yi ba ko? Ah ke! wallahi sai in ɓaɓɓalla yarinya yanzun nan" Bata ko kula ta ba, ta miƙe tana mai isa kusa da Sahar, dama ita ba'a sanya mata ƙunshin ba, tace ba zatayi ba, a makaranta an sanya masu dokar yin lalle, saboda haka ne ma har ya fita ranta. Amman duk da hakanan Ummin bata bari Sahar ta taho ita kaɗai ba. Saƙon Hunayda ne tana shaida mata kada ta jita kwana biyu shiru, sunyi tafiya ne zuwa Katsina, Amman zasu dinga waya, ta kira ta bata kusa. Taɓe baki tayi tana mai cewa "Umma ta gaida assha" Duk da Hajnar na mamakin me ya shiga tsakanin Sahabat ɗin da Hunayda, Amman tsoro ya hana ta tambaya, kuma ko ba komai yanzu ta samu Sahar na ƙara mata kuɗin break akan wanda Ummi ke bata, Amman taja mata kunne akan idan ta faɗa ma Ummin aka gane tana da kuɗi, ba zata sake bata ba,dukda itama tana mamakin inda Sahar ke samun kuɗaɗe masu yawa har haka. Saida aka kammala ma Sahar ƙunshin, harma ta wanke kafin suka bar gidan, Ita kanta matar dake ƙunshin mamakin Sahar take yi, yarinya tana abu kaman wata matar aure? Ko kafin su bar gidan ƙunshin tayi waya da saurayin ta ya kai sau biyar, kuma shagwaɓar take zuba mashi son ranta, harma tana cewa sai ya ƙara kuɗi akan wanda ya bada. Da addu'ar shiriya ta bita, domin dai tasan irin zafi da tsananin Ummin tasu, Amman ace ƴar yarinya kaman wannan tana fira da maza irin haka. ********* Sun samu tarba fiye da zaton su, babban gida ne daya amsa sunan shi gida, babu ce kawai babu ciki. Nan danan matar ta shiga hidima dasu, sannan ta kira ɗiyar ta mai suna Sulaym ta haɗa su. Dayake Sulaym yarinya ce mai natsuwa, saidai akwai wayewa a tattare da ita, itama bata da hayaniya sosai, saidai tana da walwala da saurin sabo da mutane. Dan danan ta saki jiki dasu Hunaydan. Saida suka ci abinci suka huta, kafin Driver ɗin ya juya, a cewar Hajiya Gambon idan zasu koma da kanta zata je har gida ta maida su. Saida ta cika Driver ɗin da abun arzuƙi, Hajiya Gambo ba dai kirki ba. Zaman gidan yayi ma su Hunayda daɗi, domin rayuwa ce ake cikin gidan ba takura, ga wuraren shaƙatawa a cikin gidan, idan kuma sun so su fita, Hajiya Gambon ce ke kwasar su da kanta tana kaisu duk inda zasu masalan ma Katsina da take cike da mutane masu mara da kunya da karamci, Hunayda da Sulaym sun ɗinke, kusan zamu ce sun zama ƙawaye, hatta makaranta da Sulaymin ke tafiya wani lokaci tare da Hunayda suke zuwa, komai a tare suke yi. Gashi Abunda ke birge ta, idan kitchen Hajiya Gambo zata shiga tare suke shiga, domin ita tace tana da ƴan mata ba abunda zai sanya ta ajiye mai aiki. Komai na tafiya kaman yanda Hajiya Gambo ta tsara. Daga zuwan su Hunayda gidan ko sati biyu ba'a rufa ba, sai gashi hannun Hunayda ya goggoge da yin wasu abubuwan, sannan ta ƙara sani akan abubuwan kitchen, wanda suke amfani da wuta. Zamu iya cewa Hunayda har ta manta da batun Sahabat, al'amurransu suke yi cikin kwanciyar hankali. Kullum sai sunyi waya da Ammin su, tana daɗa ja masu kunne akan yin biyayya da iya zama da mutane. *Sumayya Abdullahi Babayo* marubuciya ce data shahara a fannin rubutun hausa irin na zamani, sannan tayi fice wajen tsara labarai da kuma fiddo ma'anarsu a fili, sannan da bayyana kura kuran da abu mara kyau kan haifar. Wannan ne ya sanya ta samu lambobin yabo da dama, da kuma kambun girmamawa. Rubutu take mai cike da tsafta da tsari, ana alfahari da irin litattafan ta ko a social media ɗin, bata taɓa yin rubutun littafi ta wallafa ba, saidai tana yin rubutun tane online, ga duk mai sha'awar karantawa, ko ina ya nema zai samu. Wannan ne ya sanya hatta da BBC Hausa saida ta bata kambun girmamawa. Ƙungiyar su ɗaya da Hajiya Gambo. Kusan ma zamu iya cewa, tana daga cikin wanda Hajiya Gambo ta tsaya tsayin daka wajen ganin al'amurranta sun tafi daidai, masalan ma da take mai biyayya, girmama wanda tasan sun fita, da kuma natsuwa da kula da iyalin ta, ba tare da ta bari harkar rubutunta ta taɓa lafiyar zaman auren nata ba. Kaman yanda Ammi suka tsara da Hajiya Gambo, hakan ce ta faru, domin kuwa Hajiya Gambo sun zauna da Sumie a pc a tsanake sun tattauna, daga nan ne Sumie ta buƙaci da abata numb Hunaydan, gami da yin adding ɗinta a special group nata, da kuma inda take tuttura litattafai. Daga ƙarfe takwas na dare, Sulaym kan zauna karatu, ita kuma Hunayda sai ta shiga group ɗin Sumiee B. Inda take ganin irin tattaunawa mai muhimmanci da akeyi, da kuma ƙara wayar da kai akan al'amurran duniya da suka shafi girki da kula da kai da tsaftar jiki. Duk abunda su Hunayda keyi akan idon Hajiya Gambo ne, idan ta samu lokaci kuma ta kan zauna dasu taji damuwoyinsu, takan bincika wayar su sosai kuma akai akai, sannan ta sake basu wasu shawarwarin. Sosai zaman Katsinan yayi ma Hunayda daɗi, ba dan gida gida bane, da sai tace tafi jin daɗin nan. Yanzu tana kallon Saha online tana turo mata litattan data saba turo mata, da kuma videos wanda tayi imanin Zaiyad ɗinne ke turo ma ita Sahan. Wani lokaci ta kan biye mata su gaisa sama sama, har Sahar ke mata ƙorafin wai ta manta da ita. Amman har ga Allah yanzu ta samu natsuwa, duk karance karancen da takanyi, wanda suke jawo mata matsala taji har bata iya tsallake karantawar, ko domin ta samu gamsuwa, takan guje masu, domin ya zuwa yanzu ko Sahar ta turo mata gogewa take yi kawai, ko don ma kada Hajiya Gambon ta gani. Sahar dai ya zuwa yanzu ta ɗan fahimci wani abu, hankalin Hunayda ya karkata wani waje, taso taja Hunaydan a hanya da take, tana so idanun Hunaydan su buɗe kaman yanda nata suka buɗe, tana so Hunaydan ta dinga jin daɗi kaman yanda takeji itama. Taso ace ma Hunaydan ta samu namiji kaman Zaiyad, ta yanda itama zata ji daɗi, ta more rayuwar ta kaman yanda take yi itama. saboda haka ne ta ɗauri aniyar sake juyo da karkato da hankalin Sahan ɗin zuwa gareta, sannan taci ɗammarar raba Hunayda da wannan malam Salim ɗin, da idanun shi kaman na Mayu. Sahabat abu yaci gaba, ya zuwa yanzu ko Zaiyad bai nemeta ba, da kanta take neman shi, tayi imann cewa da Zaiyad kaɗai zata iya rayuwa. Babu inda bata mallaka ma Zaiyad a jikin ta ya taɓa, har gidan shi ya kan kai ta suji ɗumin juna, kaman yanda ya kan ce, ai wannan shine soyayyar. Kullum dai maganar shi ɗaya Dady ɗinshi yake jira, har yanzu bai dawo ba, sannan ya ƙara da cewa baya so a gidan su asan da zaman shine, yafi so manya su fara shiga al'amarin, ta yanda zai sake samun karɓuwa kai tsaye. Kullum Ammi tayi sabon post, idan tana karantawa Zaiyad kawai take assuming, ji take dama shine yake mata kwatankwacin abunda Ammin tata takan rubuta. Wannan ya ƙara taka muhimmiyar rawa, wajen ganin akalar Sahabat ɗin ta ƙara warwarewa. (Hibba baki san kanki kike cutar wa ba, Amman akwai ranar nadama) ********** Ya kai kusan minti biyu yana kwaɗa sallama. Har saida ya gaji ya kutsa kanshi cikin falon. Dama ya dakata ne daga waje, saboda ganin baƙin takalma a ƙofar shiga falon. Har yanzu hankalin su baikai kanshi ba, da yake nufar hanyar shiga bedroom nasu. "Oyoyo Dady you are welcome" cewar Husna dake wasa da teddy a ƙasan falon ita da musaddiq. Wurgar da teddy ɗin tayi, tana mai miƙewa da gudu ta nufi ɓangaren da Abdul ɗin yake Cak ya tsaya, yana mai juyowa a hankali ya kai kallon shi kan Husnar dake tsaye kusa dashi, ta kama ƙafafun shi ta maƙalƙale. A hankali ya zuƙunna, yana mai ɗango Husnar, ya shiga ɗan juyi da ita, yayin da yarinyar keta faman kyalkyala dariya. Shima Musaddiq ɗin ganin haka, sai ya dunguro a hankali yana mai ɗaga ma Dadyn nashi hannu, alamun shima ya ɗaga shin. Ajiye Husnar yayi ƙasa, sannan ya ɗaga Musaddiq ɗin kaman yanda yayi ma Husna. Saida yaji kaman kanshi ya fara juyawa, sannan ya direshi, yana mai rungumo yaran nashi zuwa cikin ƙirjin nashi, cike da soyayya da ƙaunar yaran nashi. "Ya gida my kids? Kunci abinci? Wasa kuke?" duk ya jero masu tambaya, kaman wasu manya, cikin salon muryar shi ta cikakken namiji. Husnar ce ta fahimci me yake nufi, saboda haka ne ta shiga girgiza mashi kai "A'a Dady, Momy bata bamu abinci ba, tace sai ka dawo zaka siyo mana" yarinyar ta faɗa kai tsaye, ba tare da shayin komai ba. A hankali ya juyar da kanshi zuwa ga ɓangaren da Salmar ke zaune, ita da baƙuwar da har yanzu bai shaida fuskar ta ba, saboda ko sau ɗaya bai kalli inda suke ba. Idon shi cikin bata, abunda yasa tayi saurin janye idon nata kenan, tasan tana son Abdul, kuma Abdul ɗin irin namijin da kowacce mace keda nuradin kasancewa dashi kenan, saidai Sam baya da cikakken quality a bisa gado. Maida kallon shi yayi bisa fuskar yaran nashi. Yana mai sakar masu ɗan murmushi, saboda Sam baya so yaran su fahimci kaman akwai wani abu tsakanin shi da Momyn ɗin tasu, masalan ma Husnar da take da bala'in wayau "Kuje ku zauna ko? Zan cenza kaya sai inzo in dafa maku indomie" ya faɗa yana mai raba jikinshi dana yaran. Ai dagudu suka koma tsakar falo suna tsallen murna, masalan Husnar da ta ɗan fahimci me Dadyn nata yace. Shi kuwa daga haka, kai tsaye ɗakin ya shige, yana mai jin wata irin ƙaunar yaran nashi a cikin ranshi. Da kallo Jamilar tabi Salma tana mai jinjina kai a hankali. Kallon farko da tayi ma Abdul ta gano tsantsar wautar da Salmanke tafkawa, kai tun ma tako ƙafar ta a karon farko cikin gidan, ai Abdul ɗin ba da irin su ake saka ci ba. Amman sai ta kalli Salmar gami da cewa "Wannan shine mijin naki?" Ɗan taɓe baki Salmar tayi "Shine ko kin sanshi ne?" Girgiza kai Jamilar tayi, "Ban sanshi ba, amman sai naga ai baya da kamannin Raggon da kike faɗa a kanshi" "Humm! Haka dai kika ce Jamila, dandai ba ke bace a gadon, da zaki faɗi haka, Amman ki bari duk lokacin da hakan ta kasance dake zaki gane ne" Salimar ta faɗa itama cikin I dont care tone. "Zakuwa ta kasance, kuma zan bi dashi kaman yanda yake so" Jamilar ta faɗa a cikin ranta Gyaɗa kai Jamilar tayi, tana mai ɗan ɗaga idanun ta a hankali tabi ƙayataccen madaidaicin falon daya sha kayan alatu da kallo. Komai yayi, komai yaji, gidan da mai gidan, komai ya mata yanda ake so. Abubuwa da yawa take rayawa a cikin ranta. "Amman please Salma kije kiji ya ya dawo, ba zanji daɗi ba in kika ƙi zuwa dan Allah" Girgiza kai Salma tayi, alamun ba zata ba. Nan fa Jamilar tayi ta roƙon ta, har dai lokacin data ajiye wayar tata bisa kujera tana mai ce mata "inazuwa" Tana ganin ta shige ɗakin, tayi saurin ɗaukar wayar Salmar, gami da yin minimixing ta shiga contact. Bata sha wahala ba, wajen ɗaukar number ɗin Abdul ɗin, bayan ta tabbatar ita ce mallakin mijin Salmar. Bata daɗe da ajiye wayar ba Salmar ta fito. Zama tayi tana mai faɗin "ki share shi kawai ƙawata, ai yama shiga toilet, yanzu dai idasa faɗa man yanda zanyi amfani da magungunan nan" Ƙasa ƙasa Jamilar ta shiga yi mata bayani, ba wasu magunguna bane masu kyau, hasali ma da kanta ta haɗa su a gida, Amman sai ta dage tana ta kambama ma Salmar magungunan, harma ce mata take sunansu *tazarce* Suna zaune ɗin dai Abdul ya sake fitowa daga ɗakin, yayi wanka ya cenza kaya. Yayi matuƙar kyau, sumar shi ta kwanta luf-luf gwanin ban sha'awa. Da ɗan kallo Jamilar ta bishi, tana mai yaba kyau da haiba irin ta Abdul ɗin. Ita a hakan yayi mata, kuma duk ƙulla ƙullar da zatayi domin ganin ta kwaci Abdul ɗin a hannun Salmar zatayi, balle ta fahimci ga yanda al'amurran suke. Indomie da kwai ya dafa ma yaran, da kanshi ya zaunar dasu a bisa dining yana ba Husnar, yayin da Musaddiq ɗin yake zaune bisa tashi cinyar. Jamila dai taƙi tafiya, sai ɗibar Salma da fira take, har kai lokacin data kula Abdul ɗin ya kammala komai yana ƙoƙarin ficewa, sannan nayi maza tayi ma Salimar sallama ta fice, gami da yi mata alƙawarn zasuyi magana online. Cikin jin daɗi Salimar ta amsa mata, har tana raka ta bakin gate ɗin gidan, gami da sake yi mata godiya, na ƙoƙarin gyara mata zamantakewar auren nata da take ƙoƙarin yi. Tun daga nesa ya hango kaman ana tsayar dashi. Saboda haka ne ya goga parking daga gefen titin, yana mai ƙare ma fuskar tata kallo. Bai shaida ta ba, saboda bai kalli inda take ba ko a cikin gidan. Kanta ta sunkuya dashi daidai saitin inda yake. "Dan Allah malam ko zaka taimaka ka fidda ni hanya? Tun ɗazu nake takawa ban samu abun hawa ba" ta furta cikin wata irin murya mai taushi, lokaci guda tana ɗan farfara idanu gami da ɗan yamutsa fuska alamun gajiya. Ɗan jim yayi, baya son irin hakan, Amman taimako wani abu ne, beside ma ba cewa tayi ya kaita gida ba, iyaka hanya ne zai kaita. Saboda haka ya gyaɗa mata kai alamun ta zagaya ta shiga, sannan ya sanya hannu daga ciki yana mai ɓalle mata murfin gaban motar. "Come in" ya furta cikin wani irin cool voice. Daidaita zamanta tayi a gaban motar, tana jin wani irin daɗi, da alfaharin gashi daga haɗuwa dashi yau zata fara yaɗa manufarta, wannan jin daɗin da Salma ke iƙirarin tana samu, tabbas itama zata samu irin shi, koma muce wanda ya fishi, domin dukkan abubuwan da Abdul ɗin keso, Salmar ta riga ta faɗa mata from A to Z. Saboda a haka ne, ta murmusa cike da ƙwarin guiwa, daidai lokacin da Abdul ɗin ya yima motar key yana mai daidaita tafiyar tashi bisa titin... ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Four_ ~*Page 13*~ Kwarjini yayi mata sosai, masalan da take ta satar binshi da kallo, ganin yanda yake sarrafa stearyn motar hankalin shi kwance. Har kai lokacin daya gangara gefen titin, yana mai ɗora hannun shi kan murfin ƙofar motar, yatsun shi na bisa fuskar shi. Idanun shi a ɗan kulle ya juya yana mai kallon ta. "Ina ganin anan zaki iya samun abun hawa ko?" ya faɗa a hankali, saboda baya buƙatar ɗaga murya, tunda suna kusa ne da juna. Sai ta samu kanta da gyaɗa mashi kai a hankali, ji take bata son rabuwa Sam dashi, ƙamshin daɗaɗɗen turaren shi na dokar mata hanci. Ɓalle murfin motar tayi a hankali, tana mai cewa dashi "Nagode Allah ya saka da alkhairi, ba zan taɓa manta alkhairinka a gareni ba" "Ba damuwa" ya maida mata amsa, yana mai janye idanun nashi daga ɗan kallon da yake mata. Saida ya tabbatar ta sauka ta rufo ƙofar, kafin yaja motar tashi yana mai barin wajen. Kai tsaye wajen aikinshi ya koma. Aikin nashi aiki ne mai wahala, yana buƙatar natsuwa, yana buƙatar mai kwantar mashi da hankali, Amman sai gashi ita Salmar tashi Sam ba abunda ke gabanta ba kenan. Yanzu ta kai ga har ta fara wulaƙanta shi gaban ƙawayen ta. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, yana mai dire biron dake hannun nashi. Lamarin Salma ya fara bashi tsoro, gashi har mutanen da yake tare dasu sun fara fahimtar halin da yake ciki, kowa cewa yake rashin natsuwar da yake ciki, ƙila daga gida ne, gashi akai akai ya kan fita yaje ya duba yaran nashi. Gaskiya ya kamata ya zauna da Salma, gara ya sani, idan har ta gaji da zama dashi ne, ba zai takura mata ba, ba zai tilasta mata ba, gara su san abun yi daga shi har ita. Duk yanda yake sonta, muddin akaci gaba da tafiya a haka, dole ne zai gaza. Ƙarar wayar shi ce ta katse mashi dogon tunanin da yake yi. Saƙo ne ya shigo wayar, ganin baisan number ɗin ba, har zai ajiye wayar hankalin shi ya kai kan kwantaccen tsararren rubutun dake jiki. _"Assalamu Alaikum Wa Rahmatullai Ta'ala Wa Barakatuhu Ya Ma'abocin Karamci Da kuma tausayi. Haƙiƙa naji daɗin ƙaramcin ka gareni, wannan ce ta sanya ni samun number ɗinka domin sake yi maka godiya, nagode kwarai Allah ya saka da mafifucin Alkhairin sa, ya kuma raya maka zuri'a Husna da Musaddiq. Ina fatan zaka huta lafiya, ka kuma kasance cikin farin ciki da annashuwa"_ Sake bin saƙon yayi da idanu, haƙiƙa ba gizo idanun nashi suke yi mashi ba. Wacece wannan? Hada sunan yaran shi fa ta ambata. Shaf ya manta daya rage ma wata hanya jiya. Saboda haka ne ya sanya shi saurin dialling number ɗin. Saida ta gyara murya sosai kafin ta amsa, tana mai wani narkewa bisa gado. Sautin amsa sallamar tata ya daki dodon kunnen shi sosai. "Zan iya sanin ko wacece please?" Ya furta, bayan ya gama amsa mata sallamar tata. "Ba lallai ka gane ba, amman kasan ance yaba kyauta tukuici" Ɗan murmushi ya saki. "Naji kin ambaci sunan yara na ne, dalilin kiran kenan, ko ba komai na tabbata kin sanni, shine nake so inji ke wacece, kuma alkhairin me na aikata maki?" Sake narkewa tayi, tana mai sakin wani irin ƙayataccen murmushi,wanda har saida ya jishi a kunnen nashi. "Hakan shi zai daɗa tabbatar mani da cewa alkhairi a jinin jikinka yake, kai ma'abocin shine. Gashi kai kayi, Amman har ka manta, saboda dan Allah kayi." Ɗan muskutawa yayi, bai gane inda zantukan nata suke dosa ba, hakan ce ta sanya shi saurin cewa "Kinga aiki nake kika katse mani, kada ki riƙeni da yawa please" Maganar tashi tayi mata daɗi, a yanda ta ganshi jiya sai tayi tunanin zai wahalar shawo kai, Amman daga fara maganar dashi ta tabbata ma kanta yana da sauƙin kai. A karo na biyu da ta ayyano irin wautar Salma. Allah ya baki miji irin wannan, amman kina wasa da damarki. "Ba zan riƙe ka ba Abban Musaddiq, saidai zanso ace na samu lokacinka mai yawa, duk da na lura da cewa tsada ne gareshi" Itama ta sake furta wa cikin wani irin salo. Ya fara gajiya da maganar, gashi dama kanshi cikin zafi yake. Sai yayi saurin ce mata. "Idan ba zaki faɗa ba, zan iya kashe kiran, saboda na faɗa maki ina da ayyukan yi a gabana" Jin hakan da tayi ne ya sanya ta saurin tashi zaune, to ya haka kuma? Ita da take ganin abubuwa sun fara tafiya daidai? Sai kuma ya rikiɗe mata? Saurin cewa tayi "Yi haƙuri Abban yarana, nice wadda ka rage ma hanya jiya, Naji daɗin hakan ne, Shiyasa na nemeka domin in sake maka godiya, jiya naga kaman kana sauri ne, ban samu damar yi maka ba" "Ba damuwa, wannan ba komai bane ai" ya furta shima, bayan ya fahimci wadda yake maganar da ita, dama kuma ko a jiyan yana kula da yanda take satar kallon nashi. Duk sai taji ba daɗi. "Nagode! Zan so ace na sake kira lokacin da kake free domin mu ɗan tattauna wani batu." Ta furta a hankali, tana mai miƙewa ta fara takawa, duk sai taji ma ta kasa sukuni, kaman tana gabanshi ne. "Na dai san kinsan ina da mata, kaman yanda naji kin ambata sunan yara na, saboda haka kinga bana da wani time, daga na bautar Allah, sai na aiki na da iyali na. So na gode, zanso ki bar maganar tattaunawar nan hakanan please" Ya faɗa yana mai ƙoƙarin datse kiran, saboda shi bai ga alaƙar shi da ita ba, da har zata so ɗauke mashi hankali daga kan aikin nashi. "Idan wani ya ƙi ka da yini, wani da kwana yake sonka, tunda Salma ta fara yi maka haka, me zai hana ka jaraba wata?" zuciyar shi ta shiga raya mashi. Girgiza kai ya fara yi a hankali, yana son Salma, baya jin idan zai iya haɗa ta da wata a rayuwar tashi, zai so ace Salmar ta hankalta ta gyara, da zaifi kowa jin daɗi, farin ciki da annashuwa. Kasaƙe tayi da waya a hannu. Ya da haka kuma? Zuciyar tace ta shiga raya mata "ai dama irin waɗannan mazajen suna da wuyar samu, ki daure ki shawo kanshi tukunna, kada kiji haushi" Gyaɗa kanta ta fara yi cikin gamsuwa da zancen zuciyar tata. Sake daddanna mashi saƙo tayi, tana mai turawa, sannan ta faɗa saman gadon nata, tana mai sauke ajiyar zuciya, gami da dafe ƙirji. Koda yaga shigowar saƙon, bai kula tashi ba, haka ya cigaba da aikin shi, har ya kammala ya kama hanyar zuwa gidan nasu. Saida ya gaido iyayen nashi, kafin ya juya akalar motar zuwa gidan nashi, riƙe da ledar chips daya siyo wa yaran nashi. Saida ya kammala komai na al'ada sannan ya kwanta, har yanzu babu wata alaƙa tsakanin shi da Salma, ita ala dole fushi take, shi kuma tunda baiga abunda yayi mata ba, ya kuma yi lallashn duniya akan ta bar fushin nan ta ƙiya, Shiyasa ya share ta shima, yana kallo ta, tsakanin shi da ita saidai kallo. Duk dai abun buƙata zai siyo ya ajiye, amman ko nairar shi ya dena bata. Ba don komai ba kuma, sai dan ta gane irin kuskuren da take neman tafkawa, sannan ta gane ba kwanciya ce kaɗai rayuwar zaman aure ba, kaman yanda tasha faɗa tana ji a litattafai. Wayar ya ɗauko da niyar maida ta silent, idanun shi suka kai kan saƙon ɗazu. "_Mai son tsuntsu shi yake binshi da jifa, ina maka fatan nasara da sa'a a duka rayuwar ka, sannan ina mai roƙon alfarmar a ɗan dinga kula ni, koda sau ɗaya ne a rana. Jameela Jameel"_ Ɗan murmushi yayi, mata a wannan zamanin sun fita daban, ace wai ana zamanin da mace zata kai kanta wajen namiji, har rana roƙon shi daya taimaka ya kula ta. Wannan wace irin rayuwa ce? Kuma bayan tasan yana da aure, da mata harda yara biyu. Ɗan tsoki yayi yana mai kashe wayar ma baki ɗaya, mata kenan, gashi da ɗaya ma wace Allah cika, balle ya jawo ma kanshi jaye jaye. Kusan zamu iya cewa cikin kwana biyun nan, babu ranar da Jameela bata kiran Abdul, tun yana share wa, har ta kai ga yana ɗan biye suyi fira, chatting ne kawai baya yi da ita. Amman ɗan fira haka, kaman na minti biyu sukan yi. Idan ya dawo gidan ya kan tadda yaran shi da kayan wasanni ko kuma kayan ciye ciye, suna ce mashi aunty Jameela ce ta kawo. Saidai yayi murmushi kawai. Domin ya zuwa yanzu ya fahimci Jameelar Ƙawar Salma ce, shine take neman ta ƙwace mata miji smman dayake Salmar sa karya ce, sai gashi bata ko kula ba. Wannan kaɗai ya samu abun riƙewa, koda Salimar zata kula ta hankalta kuma. Wani lokaci Salmar kan bada kai bori ya hau, Amman da an kammala sai kuma mita, da gunguni, baya biye mata, in da sabo ya saba, sai gashi bata tsinana mashi komai a cikin gidan, amman ta iya tayi shaye shayen magungunan ta, ta kuma kai kanta ko kunya bata ji. Duk yana kula da abubuwan da yake yi Amman ya share ta. Shi dai kawai abunda ya sani, ba zai kashe kanshi ba, tunda haka ta zaɓa sai a cigaba a yanda take so ɗin. ************* Kaman kada su tafi haka suke ji su duka. Cikin week end Hajiya Gambo ta zuba su duka cikin mota, harda Sulaym, da yanzu ta zama aminiya wajen Hunayda. Sai Kaduna garin gwamna. Hunayda ta ƙara kyau, clean da kuma gogewa tarayyar ta da Sulaymin. Ga abubuwa data koyo zaman ta a gidan Hajiya Gambon. Sannan tarayyar ta da Sumie B. Abun gwanin ban sha'awa. Duk Abunda taga bata gane ba, ta kan tambayi Aunty Sumie ɗin. Har ta kai da ta kan ce mata Aunty na, ita kuma Sumiee tace mata Ƙanwata. Ammi taji matuƙar daɗin ganin yaran tana, sai godiya take zuba ma Ƙawar tata, nan fa suka buɗe babin sabuwar fira, inda Hunaydan taja Sulaym zuwa ɗakin nasu. Labarin malam Suhayl ta shiga bata, har ta kira mata shi a waya suka gaisa. Sulaym taji matuƙar daɗi, ganin duk wasu halaye da taga Hunayda dasu, ta idasa kakkaɓe mata su. Ta yaba da Malam Suhayl ɗin, inda ta sake ba Hunaydan shawara akan ta kula da Malam Suhayl ɗin, domin daga ji shi mutum ne mai daraja, masalan ma kasancewar shi malamin Islamiyya mai ɗinbin sani. Sai Hunaydan taji ta ƙara son Sulaym ɗin, masalan ma da take bata shawarwari nagari, saɓanin Sahabat da kullum ita tunanin ta, tayaya zasuji daɗi, suyi enjoying rayuwar su, sai yanzu ne take gane Sam rayuwar tata batayi kamanceceniya da Sahabat ba. Tasha alwashn kulle duk wata ƙofa da Sahabat ɗin zata ɓullo mata, wajen ganin ta sake tunzura ta ga aikata abunda ubangijn ta zai yi fushi da ita. Sun ci abinci sun huta, kafin Hajiya Gambon tace zasu koma. Aiko nan Ammi ta cika su da shatara ta arziƙi itama, duk da tayi ma su Hunaydan soyayya mai yawa suma a A.A Moda, da kuma Umar Store. Sun rabu suna masu kewar juna. Tun daga ranar Ammi taga cenji a cikin halayen Hunayda. Komai ba sai tace ta tashi tayi ba take yi, hatta da maida hankali kan waya kullum da take yi, yanzu duk ta rage sosai, girki mai daɗi, tsafta da komai Hunaydan yanzu ba baya ba. Idan Malam Suhayl yazo, rabi fira rabi karatu ita da Surayya. Tare suke zuwa cen wajen nashi suyi ta yarintar su. Abunda kan ƙara ma Malam Suhayl ƙwarin guiwar mallakar Hunaydan. ************ "Sahabat! Sahabat! Sahabat! Wai ke lafiyar ki ƙlau kuwa? Kwana biyun nan fa na gaza gane maki Saha, kullum yini kike a banɗaki, wani lokaci ma sai inji kina ta maganganu ke ɗaya, kodai aljanu ne suka kama ki?" Cewar Ummin tasu, tana maganar tana bubbuga kyauren toilet ɗin ɗakin nasu Sahar. Saurin cusa wayar ta tayi cikin ɗan ƙaramin wandon dake ƙasan doguwar rigar tata, dama takan sanya shine idan tana son ɓoye wyarta, nan ne aljihun da take tura wayar, bayan ta maida ta silent. Da sauri ta fito tana mai fiƙi fiƙi da idanu, alamun rashin gaskiya. "Ummi ban lafiya, kwanan nan atini nake fama dashi sosai wallahi" ta faɗa itama tana mai sosai kai. "Atini fa kika ce? Tun yaushe kika fara?" Ummin ta maida mata da amsa. "An kwana biyu Ummi" itama ta mayar mata, har yanzu jikin ta ɓari yake, ta kula yanzu Ummin tata ta sanya mata idanu, kaman ma bata yarda da ita ba, to kodai Hajna munafukai taje ta faɗa ma Ummin wani abu ne? "Maganar da nake ji kina yi cikin bayan gidan fa?" Ummin ta faɗa, tana mai ƙureta da idanu. "A..a'..a Ummi nishi ne nake, shine sai in dinga cewa way... Yyo, saboda akwai zaf.. I" ta faɗa cikin in'ina daga ji bata da cikakkar gaskiya. "Shine sai ki dinga magana a toilet dan kina sakarya? Ba zaki iya zuwa ki faɗa man ba, in baki kuɗi ki amso magani?" Ummin ta faɗa, tana mai juyawa ta nufi nata ɗakin. A baya Sahar ta bita, tana mai yi mata gwalo da ƙunƙuni, faɗi take cikin ranta, duk bake bace ke rubuta abunda zai sanya mutum cikin wani hali? Yanzu ma ai update ɗinki nake karantawa ne, Shiyasa kika ji ina ta surutai, ai dole ne ma in nemi Sweet heart, domin bana jin zan iya bacci yau da wannan Bomb ɗin da kika haɗa man. Kuɗi Ummin ta bata, tana mai cewa tayi maza taje asibiti, a duba ta, kada ta daɗe, su Hajna sun kusa tasowa daga makaranta. Da to tabi Ummin. Tana mai juyawa ta fice. Murna take da jin daɗi, ko ba komai ta samu mafakar fita. Sauri sauri tayi ta shirya, tana mai cema Ummin sai ta dawo. Da a dawo lafiya ta bita, tana mai ƙara jan kunnen ta akan ta kula. Kaman yanda yake al'adar shi, yau ma da mota ya tsaya ɗan nesa da gidan su Sahar, da an sha kwana sai gidan su Sahar. Tunda ta kira shi yake ihun murna, ya ɗan kwana biyu bai haɗu da ita ba, acewarta wai Ummi ta sanya mata ido, tare da sabunta dokoki ta. Motar ta faɗa kai tsaye, motar yaja yana mai kamo hannun ta cikin nashi. Ba kunya ta matsa sosai zuwa jikin nashi, dayake glassan motar tint ne, sai babu wanda zai iya hango abunda suke yi cikin motar. Ajiyar zuciya mutumin ya sauke, ba wannan ne karo na farko ba, da yake ganin yarinyar na shiga motar, wadda ba zai iya shaida wanene a ciki ba. Ya san yarinyar marainiya ce, kuma ba zaiba uwar ta wata shaidar banza ba, sannan yasan tana iya ƙoƙari ta wajen kula da yaran, toh saidai zamani fa ya cenza, zamani ne da yaran suke ganin kaman sunfi iyayen wayau. Sai gashi ana zuwa da mota ana ɗaukar yarinyar. .............. "Sweet heart ki barni hakanan, tun kafin ki sanya motar nan ta ƙwace man" cewar Zaiyad ɗin da yake tuƙin motar da hannu guda, gudan hannun kuma yana tallafe da ƙugun Sahar. Sauka tayi tana mai komawa kujerar ta. "Ni ɗince yau full my Dear. Naji bama iya bacci sai na ganka" Ta furta tana mai maida numfashi, lokaci guda tana mai zame hijab ɗin dake jikin ta. "Shine aka zo kaman za'a gama dani?" ya maida mata shima, yana mai sakin wani irin Killer smile. "Huh! Ka bari kawai, wani littafi ne na karanta mai zafi, idan munyi aure zamu dinga yin irin yanda suke yi dear" ta faɗa itama kai tsaye, ba tare da wata kunya ba. "Ki bari dan Allah? Me zai hana mu kwatanta yau to? Ko sauri kike yi kaman kullum?" Gyaɗa mashi kai tayi. "Ba yanzu ba dear, ai su aure sukayi.." "Muma ai auren zamuyi, so ina ganin gara mu koya tun yanzu" yayi hanzarin katse mata maganar da take yi. Har gidan shi suka shiga, ba yanda baiyi ba juyin duniya Sahabat ta ƙiya, saidai abunda ba'a rasa ba, saida su dukan su suka samu abunda suke so, sannan ya ɗaga mata ƙafa, duk da har yanzu Sahabat bata bari Zaiyad ya kusance ta ba, Amman babu abunda basa aikatawa. Ya zuwa yanzu Sahar ta mugun sakin jiki da Zaiyad ɗin, a ƙarairayin da yake shirga mata kullum. Bata jin Kunyar ya gantaba ko sutura, zuciyar ta kullum ƙara ƙeƙashewa take yi. Har ta kai yanzu ta kan yi aiki da yatsunta, domin biya ma kanta buƙata, idan kuma sun haɗu haka Zaiyad ɗin keyi nata. (Duk acikin irin busar sarewa ta shaiɗan da yake yi masu, tare da ragamar Rubutun litattafan banza da Ummin ta take yi, wanda shine silar faruwar komai, ba tare da ankarewar ta ba) Saida suka gama abunda zasuyi, sannan suka baro gidan cikin jin daɗi. Chemist ya kaita, aka rubuta mata magani, tare da bata ya biya kuɗin, sannan ya ƙara mata wani, wai tukuicin rowa da batayi bashi, duk da yasan tabbacin tana sonshi ɗin kenan. Kafin ya maida ta kusa da gidan ya dire ta. A gaban mutumen da take zaune bisa ƴar tsohuwar tabarmar shi ta sake gittawa ta shige gidan. Yayi da shima Zaiyad ɗin ya ja motar shi yana mai barin wurin, tare da raya ma zuciyar shi cewa yana daf da cimma buƙatar tashi akan Sahar. Girgiza kai mutumen yayi, ya zama dole wajibi ya sanar ma mahaifiyar wannan yarinyar, ko hakan zai sa ta ɗauki mataki, idna kuma ɗan uwanta ne, ya kamata dai ace an sani. Ƴar butar shi dake ajiye gefenshi ya ɗauka, gami da fara ɗaura alwalar sallar la'asar. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) says: 'Fasting is Mine and it is I Who give reward for it. [A man] gives up his sexual passion, his food and his drink for My sake.' Fasting is like a shield, and he who fasts has two joys: a joy when he breaks his fast and a joy when he meets his Lord. The change in the breath of the mouth of him who fasts is better in Allah's estimation than the smell of musk." [Bukhari (also by Muslim, Malik, at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: الصَّوْمُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي، وَالصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَلِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ، وَفَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ. رواه البخاري (وكذلك مسلم ومالك والترمذي النسائي وابن ماجه) *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Four_ ~*Page 14*~ ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ ******* "Assalamu alaikum wa rahmatullah" Karo na biyu kenan da daɗaɗɗar sautin nata na shiga kunnen shi. Shi kanshi baisan dalilin shi na amsa kiran nata ba, ba wannan ne karo na farko da take kiran nashi ba, saidai ganin baya da wata alaƙa da ita ne, ya sanya yake kauda kai, da kuma sharewa. Baya son yanda take shisshige mashi, sai yake ganin wannan ai kaman cin amana ne, tunda ta kasance ƙawar Salmar shi. "Yayana ka amsa man sallamar mana please" "Wa'alaikumus-salam". Shima ya amsa mata a taƙaice. Shiru ne ya biyo baya, na tsawon ƴan second. Sai cen ne tayi ƙarfin halin cewa; "Ya iyali ya su Musaddiq?" "Duk suna lafiya, ya naku mutanen gidan?" Cikin wani irin farin ciki ta amsa, zuciyar tata ɗauke da addu'a. Bata so ya watsa mata ƙasa a ido, so take ta samu gurbi a cikin zuciyar tashi, saidai taga hakan ba mai yuwuwa bane. Ta ƙagara ta ganta a cikin gidan nashi, a matsayin matar shi. Bata jin idan zata iya bari wani dalili ya hana ta kai ga cin nasara. "Yayana dan Allah kada kace na dameka, ni kaina bansan me ya shiga kaina ba akanka, bansan dalilin da ya sanya nake jin ka har cikin raina ba, kada Kaga laifi na, kasan shi so makaho ne, kuma baya shawara, dan Allah ka tausaya ma baiwar Allah, tun ranar da ka rage man hanya, nayi mantuwar zuciya ta tattare dakai, ka taimaka ka dawo man da ita dan Allah" Ta ƙarshe cikin sanyin murya, kaman zata saki kuka, abun daga zuciyar ta ne yake fitowa. Jin yayi shiru bai ce komai bane, ya sanya ta sakin wata irin wawuyar ajiyar zuciya. "Nasan wata ƙila nayi laifi, saidai wannan ba magana ce daya kamata inyi a waya bace, Amman na gaza jurewa ne, idan ban faɗa ba, zan iya shiga wani halin, ka taimaka kada ka maido man ƙoƙon bara ta, nasan baka rasa komai ba wajen salma, amman dan Allah ka taimaka mu raba wannan kyautatawar da take maka. Insha Allahu nayi alƙawarn zama da duk wani wanda ya shafe ka lafiya" A hankali ya sauke wayar daga kunnen shi, yana mai latse ta ya kashe ta baki ɗaya ma. Maganganun nata sun ratsa mashi kwalwa, me hakan yake nufi? Yana hango natsuwa da kamala tattare da yarinyar, Amman me yasha kan shi? Duk da ga fuska bata kama da budurwa, amman kalaman nata, suna nuni da tsantsar ƙaunar ta gareshi. Baiso kalaman nata suyi tasiri a cikin zuciyar shi, dalili daya sanya ya tattara komai nashi kenan ga zuwa gida. Yanda ya bar falon, haka ya kuma dawowa ya tadda shi, su Husna da Musaddiq ma sun riga sunyi bacci. Saboda haka ko inda take zaune bai kalla ba. A daƙile tayi mashi sannu da zuwa, baima zata ba, hakan ya sanya ya zauna a hankali bisa sofar dake kallon tata, yana mai ce mata "Yauwa Madam ya gida ya yara, ya kuma kaɗaici? Koda yake ai kince bakya jin kaɗaici in waya na riƙe a hannun ki" Ɗan murmushi tayi iya fuska, har yanzu idanun ta na kan wayar. Miƙewa yayi zuwa ɗakin, yau dama dama ta gyara gado, Amman ai da sai in ya dawo ne yake gyarawa, wani lokaci ma sai yace ta tashi ya gyara, sannan take tashi ta tsaya, yana gyarawa ta koma tayi kwanciyar ta. Da kallo yake bin ɗakin. Kaman ba ɗakin mutane ba. Ko ina kaya, ga yana da ta fito duk ta kama POP ɗin dake ɗakin, abunda bai taɓa gani ba. Kayan shi ya rage, daga shi sai ƴan ciki. Zagewa yayi ya gyara ɗakin tsaf, sannan ya kwashe yaran daga falon ya maida su ɗaki, bai ƙasa a guiwa ba, ya gyara falon tsaf, duk tana zaune tana caccakar waya, sai dariya take yi ita kaɗai, tana buɗe audio na mutane tana shan dariya. Nan ma bai kula ta ba, ya shige toilet ya wanke, sannan yayo wanka, yazo ya murza mai yana mai hayewa gado. Saidai me, yana kai kafaɗar shi ƙasa, tunanin Jameela yayi mashi sallama. Sai a lokacin ya manta da wayar ma ashe ya kashe ta. Yana kunnawa text ɗinta na shigowa. _Ba dai zan gaji ba, kayi man lamuni gobe inzo Office ɗinka_ Ɗan murmushi ya saki. Mata kenan da ƙarfin hali suke. Baya so ya saki jiki da Jameela, daga baya kuma tazo mashi da tsurfa, kwatankwacin wadda Salma tazo mashi da ita yanzu. A hankali ya lallatsa reply ya mayar mata. _Your Address, Amman ba dai Office ba_ Cikin second sai ga reply ɗinta, da exact Address nata. Gidan su Baida wuyar kwatance. Saboda haka yayi alƙawarin neman ta gobe. So yake gashi gata ya bata haƙuri, baya so alaƙar tasu tayi nisa, ko dan gudun Salma tace yaci amanar ta. Shi kanshi ya sani, yana masifar son Salma, Amman Salma ta zaɓi hanya marar ɓullewa. "Ok i'll meet u 2mrrw by 4pm" Ya sake tura mata. Ba jimawa sai ga reply nata. "You are always Welcome my love. Sleep tight" Ya maimaita karanta saƙon yafi sau biyu, sai cen ya saki dariya, yana mai furta "Mata! Salon yaudarar ku daban ce" Sai kusan ƙarfe sha biyu salma ta shiga ɗakin, shima har ta kwanta latsa waya take yi, wai style take gani na kwanciya, dayake group nasu ana tutturo su da yawa. Dalili kenan da yasa take ji bata iya barin yin WhatsApp koda kuwa za'a mutu. Gashi tana ta samun friends ta ko ina, kasancewarta yanzu ta idasa gogewa, ko ina shiga take ana damawa da ita yanzu. Ta ɓangare guda ga Jameela tight friend tata, wanda kaf, duk wani sirri nata kwashewa take ta faɗa mata, ita kuma wai tana bata shawarwari. Hatta da gyaran gida, da wankin toilet ɗin da yayi mata daga dawowar shi, saida ta kwashe ta faɗa ma Jameelar. Ita kuma sai bugun cikinta take ƙara yi. Tana ƙudurcewa a ranta, zata gane bata da wayau. Cikin farin ciki Jameela ta tashi ta fara murza dulka a jikin ta. ko ba komai so take ta fita daban a idanun shi, duk da kasancewarta ba kyakkyawa ba, saidai zama da namiji fiye da ɗaya, ya sanya ta gane inda maza suka fi so. Bata kwanta ba, saida ta tabbatar da ƙalƙale ko ina, ta sani Salma ta ɗara ta kyau nesa ba kusa ba. Amman ina amfanin kyawun da ba gyara.? Saboda haka ne ta kwanta cike da farinciki. Tun da safe ta tashi ta fara toye toye da kimtse kimtse. Duk da kasancewar gidan su masu rufin asiri, ba dai makusa, kuma Maman ta tsaye take akan gyaran gida. Sam ita ba mace bace mai hayaniya, saidai ko ita kanta bata jin daɗin halin Jameelar, duk da yanzu haɗuwarta da sabon saurayin nata, kaman yanda tace. Ta lura ta fara cenzawa sosai. Ƙarfe uku daidai bakin mirror tayi mata, bayan ta gama gyare ko ina, tare da sharewa da tsaftacewa. Ita dai maman tata sai binta take yi da kallo, duk da taji daɗi, amman sai take jin tsoron sabon saurayin na ɗiyar ta ya sake kufce masu, a karo na barkatai. ******** "Sweet heart gaskiya nidai tsoro nake ji, Ummi zata yayyanka ni, wallahi duk ranar data gane, kuma kaga Hotel ɗin nan akwai ƴan sa idanu, saboda haka dan Allah ka maida ni gida kawai haka, hakan ma ai ya isheka, ko ba komai Kaga yau daga ni har kai lafiya ƙlau muke jin kanmu... " Saurin katse mata maganar da take yayi. " My Habat! Haba me yasa kike haka ne? Wannan fa yawa ne wallahi, kinsan ko nawa na kama ɗakin nan? Beside ma wa zai gammu? Na faɗa maki gidana an fara sanya man idanu ne, har ma an kira Dad ɗina wai an faɗa mashi ina kawo mata da abokai a gida, shine ya kira fa yana ta man faɗa, wai ni rashin haƙurin me nake, ai daya dawo zai je gidan ku kawai, wajen su kawu a gama magana" Da sauri Sahabat da kalle shi. "Dagaske kake dear?" shima gyaɗa mata kai ya shiga yi. "Eah da gaske mana, just remain a little ki shigo gida na, as my Bride" shima ya ƙarasa cikin zaulaya da iya yaudara. Sai Sahabat ta samu kanta tana mai jin daɗi, bata san sadda ta kai hannu ta jawo shi zuwa jikin nata ba. "I wished so my dear" ta furta a hankali. Cikin wani irin sauƙi shima ya fara kai hannu saman jikin nata. Sun jima a haka, hatta da rigar ta saida ya raba ta da ita, ƙoƙarin kai hannu yake inda ba'a so, tayi saurin riƙe hannun. "Not now dear" ta furta a wahale. Yana da matuƙar wahala ta iya daurewa ra riƙe kanta, masalan idan tana tunano yanda take ji ana wassafawa a littafi, da yanda take ji ana labarin farkon yi. Akwai zafi, kuma ance tafiya na cenzawa, to ita me zai kaita ta bari yayi amfani da ita? Duk da dai zuciyar ta na raya mata tana so, ai akwai inda ta taɓa ji a littafi, ance akwai abunda ake ba mutum ya tura ƙasan nashi, sai ya koma ya haɗe kaman budurwa, gashi irin saƙonnin da take ji daga Zaiyad ɗin, abun bai misaltuwa,tana jin kaman ma yafi sauran mazan da take kallo a cikin video ɗin da yake tura mata. Shima a wahale yake kallon ta. Ya kai matuƙa wajen buƙatuwa, ya kai geji. A ɗan hasale ya ture ta daga bisa jikin nashi, ya matuƙar jin haushi, duk yanda yaso da daurewa yau ya kasa, dole ne ma yaje ya nemi wata, dole ya samu mai rage mashi zafi. Kunna motar yayi a fusace, yana mai jan motar daga ƙofar Hotel ɗin. Yaso yau ya kammala komai, ya gaji da yi mata ƙarya, Amman yaga yarinyar tsoron Ummin tata ya shige ta sosai, me zai sa ya tsaya yana ɓata ma kanshi lokaci? Shi dai ba zai taɓa mata fyaɗe ba, saboda yasan illar yin hakan, kuma asirin shi na iya tonuwa watarana. Amman in ita ce ta amince fa? In ita ta kai kanta fa? Har ya isa kusa da gidan nasu, yana mai goga parking. Sannan ya juya ya kalle ta. "You can go, kada kuma ki sake kirana, zanje in ta addu'a Allah ya cire man sonki a cikin raina, Tunda babu yadda da amana tsakani na dake, kuma sai yau ne na gane baki sona, ashe dama yaudara ta kike, Tunda har kike tsorona, kuma kike faɗa man wai Ummin ki, ashe baki yadda da soyayya ta ba? To ki sani, zanje in samu wadda take sona da gaske, wadda koda yanka ta zanyi gutsi gutsi in cinye, ba zata taɓa tanka man ba. Nagode da kika nuna man rashin soyayyar ki a zahiri, kinga ba sai su Dad sunsha wahalar zuwa gidan ku ba" Yana gama faɗar haka, ya sake jan motar shi a fusace. Sai ta fashe da kuka. Zaiyad bai taɓa mata haka ba, laifin me ta aikata mashi? Dan ta hana shi kanta? Me yake so tace ma Ummi?. A sanyaye taja ƙafar ta tana mai shige wa gidan, magariba ta kawo jiki sosai, daga taje saloon ta dawo, shine taje ta biye ma Zaiyad, bayan an gama salon ɗin ta kira shi suka ɗan fita. Koda ta shiga gidan, sa'a taci Ummi ta tashi yin sallah, saboda haka sai basu haɗu ba har ta shige ɗakin nasu. Tana cikin tashin hankali, sai bayan data kammala sallah ne, sannan Ummin ta leƙo tana mai cewa, ta fito taci abinci. Haka taci abincin a ɗarare. Ummin har taso ta kula, sai ta wayance da cewa wai kanta ne ke mata ciwo, saboda jan da akayi mashi. Addu'a Ummin tata tayi mata. Tana mai ɗauko mata magani ta bata tasha. Sannan tace taje ta kwanta. Maimakon ta kwanta ɗin, sai ta shige toilet tana mai danna kiran Zaiyad. Tayi mashi kira ya kusa hamsin bai ɗaga ba, kuka take sosai, saidai mara sauti, son Zaiyad zai kashe ta. Ta yadda zata bashi dukkan wani abu da yake so daga gareta, indai zaibar jin haushi, kuma ya dawo gareta, sannan kada yaje wajen wata, kaman yanda ya faɗa. Sai ta samu kanta da kiran Layin Hunayda. Har ta fara bacci taji kira ya shigo wayar tata. Ɗagawa tayi cikin muryar bacci "Hello Saha" ta faɗa a hankali, gudun kada ta tashi Surayya. "Hunaida ki taimaka man, Zaiyad ya rabu dani, ya gujeni, please ki faɗa man ya zanyi? Na kira wayar shi yaƙi ya ɗaga, nayi mashi text ba reply" ta faɗa cikin kuka ƙasa ƙasa. Ɗan tashi zaune Hunaydan tayi. Mamaki take sosai, to me Sahar take so tayi mata? Ta gama bashi kanta, ai dole ne ya guje ta. Kuma inma bata manta ba, rabon ta da Saha an kwana biyu, dama ita Ammi ba barinta take yi zuwa gidan su Sahar ba. Sahar ce mai zuwa, to itama ta ɗauke ƙafar ta, saboda tana bata shawara akan Zaiyad, na ta rabu dashi ba mutumen kirki bane, inda itama Sahar ke bata shawara ta rabu da Malam Suhayl, wai tafi ƙarfin shi. "Ya isa hakanan Saha, ki bar kuka, ko me kenan gobe ki shigo mu tattauna" cewar Hunaydan. Tana mai ɗan kallon sashen da Surayya ke kwance. Da kyar ta lallaɓa ta tayi shiru, akan cewa gobe zata je gidan su Hunaydan suka rabu. Kashe wayar Hunayda tayi tana mai girgiza kai. "Allah shi kyauta" Abunda ta faɗa kenan a fili. Tana mai addu'ar Allah yasa Sahar ba kanta ta miƙawa Zaiyad ba. ********* Cikin sabuwar motar daya cenza ƙirar 406 ya goga parking ƙofar ɗan madaidaicin gidan. Da kallo yake bin gidan. Gida ne daidai misali na masu rufin asiri. Saidai ko ina daga gaban gidan tsaf yake, share kwal. Ya yaba da tsaftar mutanen gidan, shi mutum ne mai son tsafta a rayuwar shi. Janye idanunshi yayi, yana mai ɗora su bisa fuskar wayar tashi daya zaro. _"Ina waje"_ Abunda ya rubuta kenan yana mai tura mata. _"You are welcome Abban Musaddiq. Ka ƙaraso daga ciki mana"_ Abunda ta rubuto mashi kenan. Saurin maida mata yayi da _"Noo ina sauri ne"_ Shi da yaje katse alaƙa, meye nashi na shiga cikin gida? Ko minti biyu ba'a yi ba, sai gata ta bayyana, tana ta faman kyalli da ɗaukar idanu. Daga ciki ya sanya hannu, yana mai buɗe mata murfin motar. Zama tayi a hankali, bakin nata ɗauke da bismilla. Lokaci guda kuma tana mai haske shi da wani irin murmushi. Ɗan kauda kanshi yayi gefe kaman bai gani ba. Salma yake tunawa, wane irin sone Salma batayi mashi ba? Wane irin so ne Salma bata nuna mashi ba? Wace irin kulawa ce Salma bata bashi ba..? Katse mashi ɗan guntun tunanin tayi, ta hanyar cewa "yau gaka a gidan su Jameela, saidai baƙo a tsaitsaye, kaƙi shiga ko Mama ce ka gaida, koda yake nasan watarana zaka shiga ne" ta faɗa, tana mai ɗan murza yatsun ta, fuskar ta ƙasa, idanun ta na bisa hannun nata da ya sha ƙunshi ja. Ɗan murmushi yai, yana mai cewa "Mu hanzarta fa, Salma na jira na" "Aunty na zaka ce" tayi saurin tarar numfashin shi. Ɗan jinjina kai yayi gefe. "Humm namiji kenan, wai shi nan ƙoƙari yaje in gane Salma na kula dashi, baisan kaf labarin gidan nashi a tafin hannu na yake ba" ta faɗa a cikin ranta. A zahiri kuma, sai ta sake dakin murmushi a karo na biyu. Sake gaishe shi tayi, cikin wani irin ladabin da bata dashi tun cen baya. Dayake bai sani ba, sai yaga abun wani iri. Irin yanda take ta bashi kulawa, shi yaja hankalin shi, sai ga Abdul da ɗan biye ma Jameelar sama sama suka taɓa fira. Inda tayi ta ƙoƙarin cusa mashi kanta. Ba laifi, ba kaman yanda ta zata ba, ya ɗan bata kulawa, duk da akai akai yake kallon agogo. Kayan ciye ciyen data haɗa mashi ta kwaso mashi, wai ya kai ma yara. Bai musanta ba ya amsa, gami da yi mata godiya, ai ko ba komai kaso mai son naka, kuma yana ganin kaman kulawar da su Husnan suka gaza samu wajen Salma, jamilar zata iya kulawa dasu. Sai gashi kafin yabar ƙofar gidan, saida ya sake mata sosai, ta hanyar abubuwa da kalaman da Salmar ta faɗa mata yana so tayi amfani. Cewa yayi zai kira ta, dazaran ya natsu. Gaban idanun ta yaja motar shi, tana ɗaga mashi hannu har ya ɓace ma ganin ta. Juyawa tayi zuwa cikin gidan, hankalin ta kwance, fuskar ta ɗauke da murmushi, tana rayawa a ranta cewa muddin ta shiga gidan nan, kashin Salma ya gama bushewa... ********** Koda Sahabat taje gidan su Hunayda basu kwashe da daɗi ba, duk shawarwarin da Hunaydan taba Sahar, babu wanda take jin zata iya ɗauka a cikinsu. "Ki rabu dashi kawai Saha, dama ba sonki yake ba, kin tabbata har ga Allah babu wata alaƙa data shiga tsakanin ku? Saha kin ba Zaiyad kanki ne? Kin amince mashi?" kalaman da Hunaydan tayi ta nanata ma Sahar kenan da suka ƙara tunzura ta. Gani take tama raina ta, wannan ma ai cin fuska ne. Ya tazo mata da matsala, zata sanya ta gaba tana mata tambayoyin banza da wofi? Kenan ita ga wadda zata auri malami ko? Wannan ce ta sanya ta itama yayyaɓa ma Hunaydan magana. Na cewa ko ta bashi, miye ruwanta? Ai wlh data tsaya kula irin su Malam Suhayl sau ɗaya, gara ta kula irin su Zaiyad so dubu, duk da yake ɗan iskan, ai dai shi da kuɗin shi, da kuma gatan shi,kuma da tasan abunda zata faɗa mata kenan, da batayi gigin sake ɗauko ƙafar ta ta tako gidan su Hunaydan ba. Saidai Hunaydan ta bita da murmushi da Addu'a. Yanzu Hunayda ta fara gane kanta, tarayyar ta da malam Suhayl, Sulaym da kuma Aunty Sumiee B. Ya ƙara taimakawa wajen daidaituwur rayuwar tata, a bisa siraɗi madaidaici. Ko karance karance yanzu ta dena yi, inba littafin Aunt Sumie ba, sai kuma girke girke da ake yi masu turorial, da kuma litattafan addini da malam Suhayl kan tura mata cikin wayar tata. A take ta danna ma Sahar blocking, bayan fitar ta gidan nasu. Inda har saida Ammi ta leƙo, wai me tayi ma Sahabat ta fita tana ta fushi? Murmushi kawai tayi ma Ammin, tana mai cewa "Ammi ba komai fa, ƙyale ta kawai gaskiya kawai na faɗa mata, shine taji haushi ta tafi" Girgiza kai ammin tayi, tana mai cewa "Gaskiyar me? Bana son haka fa Hunayda, da tana da waya, da kin kira ta kin bata haƙuri, ni bana son faɗan nan wallahi, kuna yara bakwa iya kai zuciya nesa" Da kallo ta bi Ammin, tana mai raya ma ranta cewa "Ammi da zaki san halin da Sahabat ta jefa rayuwar ta, da baki sake barinta ta tako ƙafar ta gidan nan ba, koma menene ni bazan tona mata asiri ba, taje, ai duniya ce ta fi bagaruwa iya jima ai" Saha tasha matuƙar wahala kafin Zaiyad ya yarda ya sauko, shima saida ya kafa mata sharaɗin cewa da kanta zata kai mashi kanta, sannan tayi mashi alƙawarin cewa duk abunda ya nema zai samu. Dayake so ya rufe mata idanuwa, kuma huɗubar shaiɗan na tasiri kanta, shaiɗan na kaɗa mata ganga bisa tsakiyar kai. Cikin sauri ta bada kai bori ya hau, ta hanyar ce mashi yayi mata kwatancen inda zata iske shi. Aiko ba daɗewa sai ga Address ɗin gidan ya bayyana a saman secrean na wayar tata. Ƙudurcewa tayi a ranta cewa, gobe duk wayo, da ƙaffa kaffan Ummin tata, sai tasan yadda akayi ta ɓalle taje ga Zaiyad farin cikin rayuwar tan..... © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) says: 'Fasting is Mine and it is I Who give reward for it. [A man] gives up his sexual passion, his food and his drink for My sake.' Fasting is like a shield, and he who fasts has two joys: a joy when he breaks his fast and a joy when he meets his Lord. The change in the breath of the mouth of him who fasts is better in Allah's estimation than the smell of musk." [Bukhari (also by Muslim, Malik, at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: الصَّوْمُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي، وَالصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَلِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ، وَفَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ. رواه البخاري (وكذلك مسلم ومالك والترمذي النسائي وابن ماجه) *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Four_ ~*Page 15*~ Ba ƙaramin yaƙi yayi da zuciyar shi ba, wajen ganin bai ba Jameela dama akan shi ba, saidai inaaa! ya riga ya makaro, ita zuciya a kullum mai kyautata mata take so. Ita kanta Salmar ta kula da yanayin Abdul ɗin ya cenza, yanzu fushin da take yi dashi ma, gani take kaman bai damuwa, sai ya zauna yana yima yaran shi wasa amman ko inda take baya kallo. Har firarraki zata ji yana yi masu, ko ya kwashe su su fita, ko ya kaisu cen gidan nasu. Butsu Butsu sai taji wayar shi tayi ƙara, bai ɗagawa a gabanta, sai ya tashi ya ficewarshi waje ya amsa wayar, saɓanin da da ko wanene ya kira shi a gabanta yake amsawa, saboda tsabar soyayyar shi gareta da kuma yarda da junan da sukayi ma kansu. Abun sai kuma ya dawo yana ɗan bata tsoro, hankalin ta ya fara tashi, me Abdul ke shiryawa, masalan da taga fafa ya fara tada ginin shi, na filin dake jikin gidan, sai ya fasa bangon tsakar gidan ya haɗe su, duk abunda yake yi, iyakar shi da ita kallo sai kuma amsa mata gaisuwa idan tayi mashi. Ta yaran shi kawai yake yi. So take ta gyara komai, tsoron ta guda ace Abdul ɗin wani salon ya ɓullo mata dashi, bata iya jure wannan halin da suke ciki. Saboda haka ne ta miƙa kokenta a group ɗin masu, tare da naiman shawara. Nan fa aka shiga bata shawarwari, Jameela ce mai zaƙal ɗin cewa ta cigaba da share shi, da kanshi zai nemeta, yayin da wasu suke ce mata kada tayi haka, ta nemi mijin nata su sasanta. Dayake ta ɗauki dukkan yardar ta taba Jameelar, sai take ganin kaman Jameelar ce kaɗai mai ƙaunar ta. Nema tayi da Jameelar tazo gidan ta su tattauna, Amman sai Jameelar take faɗa mata wai bata lafiya, duk da haka bata haƙura ba, sai tace ma Jameelar tayi mata kwatance zata je gidan nasu, daganan sai su gaisa da mama ta kuma duba jikin Jameelar. Ba musu ko shayin komai Jameelar tayi mata kwatance. Koda taje, sun jima suna fira, tare da gaisawa da maman tata. Suna taren ne kiran wayar Abdul ya shigo wayar Jameelar. Saurin ɗauka tayi, tana mai ficewa daga ɗakin. Saida ta kammala wayar ne ta koma ɗakin. Da murmushi Salmar ke bin Jameelar. "Ya dai? Kodai Ogan ne ake ɓoye man?" ta faɗa da murmushi. Itama Jameelar ɗan yaƙe tayi tana mai cewa "Laa kuji mata da sharri, meye na ɓoyo kuma? Sha kuruminki, har gida zan kai maki shi ai" tafawa sukayi, suna masu ci gaba da tattaunawar su. Duk yanda Jameelar zatayi wajen ganin Salmar ta ƙara dagula lissafinta tsakanin ta da Abdul tayi. Ta kuwa ci nasara. Domin Salma dai sai abunda yaci gaba. Yanzu maganganu take yaɓa ma Abdul, tana biye ma dokin zuciyar ta ne, tare da zuga da shawarwarin ƴan social media irin su Jameelar. Shi dai Abdul wani lokaci ya kan ce "Allah ya kyauta" sannan yabar gidan. Ƙarin aure a gareshi dole ne, koda kuwa Jameelar bata kawo mashi kanta ba. Duk da Salma take ganin ƙarin buɗi tattare da Abdul ɗin, domin yanzu ya kai wani matsayi a ma'aikatar tasu, hakan baisa ta kwantar da kai ga Abdul ɗin ba. Gani take kullum ya gaza, har ƙarar shi ta kai gidan su, wai ya dena mata komai, kuma ko a shimfiɗa ya dena kula ta,bata ko ji kunyar faɗin hakan ba, tunda tana amfani ne da cewar su Jameelar, gani take kaman shawarwarin nasu sune mafitar ta. Mahaifiyar ta da kanta ta ɗauko mayafi zuwa gidan Salmar, saidai saɓanin abunda Salmar ta faɗa ne ta tagani. Tunda da kanta ta shiga kitchen da store ɗin gidan. Ai bata san sadda ta kaima Salmar duka ba, idan ba rashin godiyar Allah ba, me ta nema ta rasa? Akwatinta cike suke da kaya sababbin da ko ɗinka su batayi ba, haka store ɗin nata, cike yake da kayan masarufi daidai da magi ƙwaya ɗaya ba zata siya ba a waje. Ai sai ta sanya waya ta kira Abdul ɗin, koda yazo bai shaida ma Mahaifiyar tata abunda yake tsakani da, kawai dai yace a ƙara yi mata faɗa, tana biye ma ƙawaye ne a waje. Nan kuwa uwar tata ta rufa a kanta, faɗa, zagi da wulaƙanci iri iri babu wanda Salma bata gani ba. Ai sai ta ƙullaci Abdul, sai abun ya ƙara tsamari, shi ba dakai ƙara ba, shi da amsar hukunci. Wannan duk bai dame shi ba, kawai ya ɗauki hakan a matsayin wata Jarabawa ce a rayuwa data same shi, kuma yana ƙoƙarin ganin yaci jarabawar. Babu wanda ya taɓa faɗa ma halin da yake ciki a waje, dama hasalima shi ba mai abokai bane da yawa, kasancewr irin aikin nashi, da har dare yana kaiwa wani lokaci. Koda yaje da zance ƙarin aure gidan nasu, babu wanda yayi yunƙurin hana shi, duba da yanayin shi, ba sai ya fito ya faɗa ba, ko ramar dake jikin shi kaɗan ya isa ya shaida ma mutum halin da yake ciki. Addu'a iyayen nashi suka bishi da ita, tare da fatan nasara, domin ya zuwa yanzu dai Abdul ɗin ya fara zama wani abu, riƙe mata biyu ba zai yi mashi wahala ba. Ranar da komai ya ƙara rincaɓewa ita ce; ranar da Abdul ya kawo ma su Husna chocolate da biscuit da yawa yake shaida masu inji Auntyn su, watau amaryar da zaiyi kwana kusa. Nan fa Salma ta ruɗe, kuka take tayi, tare da aibace aibace. Kalmar daya faɗa mata cewa "Abunda ka raina shi wani ke so, kuma inda wani yaƙi da yini, nan wani keso da kwana" Tashin hankalin da Salmar ta shiga bai ƙilguwa, ko bayan daya fice, Jameelar ta kira tana kuka, saidai Jameelar tace ta kwantar da hankalinta, ƙila barazana ce yake yi mata domin ta gyara, saidai ko alama, ta tada mashi hankali, har sai yace ya zanye maganar auren. Haka akayi, kwana biyu ba kwanciyar hankali a gidan. Husna da Musaddiq ma ya kwashe su, ya kaisu cen gidan su. Abaya kawai ta zara tayi gidan su, wai tayi yaji, aikuwa dawa Allah ya haɗa maman tata ba da ita ba. Ta inda take shiga ba tanan take fita ba. Sannan tace tayi gaugawar komawa ɗakin ta ma, tun kafin mahaifin nata ya dawo ya same ta. Lallai ta yarda Salmar bata da hankali, ta yarda duk ta watsar da tarbiyyr da sukayi mata a gida. Dama a haka Abdul ɗin ke zama da ita, Amman bai taɓa kai ƙarar ta ba? Lallai Abdul ya cika suruki, wanda ko wacce uwa zata so ace ya auri ɗiyar ta. Saboda haka ne ta sanya waya tana mai kiran shi, haƙuri ta dinga bashi harma yaji kunya, yace ba komai dan Allah suma suyi haƙuri in ransu ya ɓaci. Ba ariziƙi ta koma gidan, tare da gargaɗin cewa daya dawo ta tabbatar ta bashi haƙuri, ba'a aure ita aka aure ta? Sai take ganin kowa ya juya mata baya ne, ita ba'a kula da lalurar ta, ba'a kula da damuwar ta, saboda tana mace komai sai ace ita ce ƙasa? Ita za'a taka? Wallahi kuwa indai haka ne, Abdul bai zaɓa ma kanshi zaman lafiya ba. Hidimar biki ta kankama. An kammala ginin gudan sashen amaryar, inda har yanzu bata kwantar da hankalinta ba, balle ma tasan wacece amaryar. Kuma dama ko a shimfiɗa ta dena neman shi, shima idan yaje haka take kulle ido ta gaigaya mashi maganganu marasa daɗi, Shiyasa ma yanzu ya dena neman ta. Sai ya sanya mata idanu, aure ne dai babu fashi, saidai duk abunda take jin zatayi tayi. **************** "Kiyi haƙuri Hunayda, nima ba'a son raina ba zan tafi in barki, saidai hakan ya zame man wajibi je, karatu zan tafi yi ba wani abu ba, kuma zamu dinga yin waya, sannan insha Allahu zan dawo in iske ki kaman yanda na barki, zuwa lokacin shekarunki sun rufa ma yanda Abban ki ya ɗibar mana, kinga zuwa lokacin zamu iya auren mu cikin kwanciyar hankali, na samu aiki, zan iya riƙe ki da duk wasu buƙatun ki" Suhayl ɗin ya faɗa cikin shigar lallashi. Share hawayen fuskar ta tayi, sai take ji kaman idan ya tafi shikenan ba zai dawo ba, ta saba dashi, ta fara koya ma kanta sonshi, kwatsam rana guda yazo mata da maganar zai tafi wata ƙasa ƙara karatu? "ki dena kuka, dariya ya kamata kiyi My Nayda, farin ciki shi ya kamace mu, shekara biyu kawai zanyi, insha Allahu da na kammala zan kawo takardun, ƙanen Babana yayi mani alƙawarin aiki mai tsoka, wanda insha Allahu har wani ma sai mun taimaka" Gyaɗa kanta ta shiga yi cikin gamsuwa, a hankali ta shiga kwararo mashi addu'a, har yanzu fuskar tata babu walwala sam a tattare da ita. Saidai bata da yanda Zatayi, kaman yanda ya faɗa ɗinne. Hakan ba ƙaramin ci gabansu bane. Saidai idan ya tafi dawa zata dinga fira? Wa zai dinga ƙara mata karatu?. Kaman yasan tunanin da take yi, yayi saurin cewa "Saidai ina roƙon wata alfarma guda ɗaya My Nayda, dan Allah ki zam mai kula, ki riƙe man alƙawari na, banda biye ma ƙawayen banza, banda yada karatun ki, wanda kin sani dashi ne zaki bama yaran da zamu haifa tarbiyya, ki man alƙawari My Nayda zan dawo in iske ki, natsattsa, kamammiya kaman yanda na tafi na barki". Ya ƙarashe shima yana mai karya kai, zuciyar shi tayi rauni, masalan da yaga wasu siraran hawaye na kuma biyo fuskar tata, daga cikin idanun nata. Ji yake kaman ya kamata ya rungume, kaman ya share mata hawayen, kaman ya ɗora bakin shi saman goshin nata. Saidai inaaa, ba zai iya ba, yasan hakan haramun ne a gareshi, yasan hakan ba da cewa bane, koda ba'a haramta ba, baya jin zai iya, tarbiyyarshi bata bashi haka ba, balle yasan wutar Allah mai zafi ce, wadda ɗan adam ba zai iya daure mata ba. Cikin tabbatar da alƙawarin nata take gyaɗa mashi kai. Ba zata taɓa guje nashi ba, kaman yanda itama bata fatan ya guje matan. "Kaima kayi man alƙawarin ba za ka kula kowa ba acen, ba zaka barni ba, ba zaka yi man kishiya ba, ba zaka taɓa haɗa son wata da nawa ba, idan kayi man hakan insha Allahu, nayi alƙawarin kamewa da tsare maka komai nawa, har sai ka dawo munyi aure" ta samu kanta da faɗa Shima cikin son maida hawayen daya taho mashi yake gyaɗa mata kai. HUNAYDA daban ce, komai nata a nutse take yinshi, kalaman ta masu taushi, yana mai jinjina ma Amminta, irin tarbiyyr data bata, tare da ƙoƙarin kiyaye yaran nata daga faɗawa halaka da ruɗin zamani. Cikin wani irin yanayi sukayi Sallama, ita dai Hunayda kuka take marar sauti, yayin da Suhayl ke tafiya yana waiwayen ta. Ba dan tafiyar tazo mashi a bazata ba, babu abunda zai hana shi tsayawa tsawon yini yana lallashin ta. A haka masoyan biyu suka rabu suna masu marmarin juna, sai ɗaga mata hannu ya ke, yayin da ita kuma ko kallon shi ta gaza yi. Har ya ɓace daga cikin layin nasu. Sannan ta tashi ta faɗa cikin gidan nasu tana mai rusa kuka. Ita kanta Ammin tayi mamaki da Hunaydan ke faɗa mata yanda sukayi da Suhayl. Ashe ɗiyar tata soyayya take har haka? Har tayi zurfin da zata dinga rusa kuka irin haka, saboda tafiyar saurayi. Da Addu'a da shawarwari tabi Hunaydan, har saida taga ta ɗan dayaye, sannan ta umurceta akan ta shiga ɗaki ta kwanta ta huta. Jiki a mace ta shige ɗakin, ji take kaman ta rabu da Suhayl kenan rabuwa ta har abada, gani take kaman Suhayl ɗin zaifi Ƙarfinta idan ya dawo. Da haka har bacci kaɗan ya sace ta, tana mai tunanin Suhayl da irin yanda rayuwar ta zata zama, idan akace ba Suhayl ɗin. *********** Sanye take cikin kayan islamiyya. Hijabin ta har ƙasa, fuskar tata Sanye take da liƙaf baƙi. Cikin sauri take takawa har zuwa bakin titin inda zata tari Napep ɗin. Tun bayan data samu ta gilla ma Ummin tata ƙaryar cewa an saka ta cikin masu musabaƙar karatun Alƙur'ani ta bana, dan haka cen zasu yini suna bita, abinci ma saidai suci ce, sai Ummin tata take ce mata, ta tafi idan su Hajna sun taso daga Lesson zata kai mata abincin. Saurin tarar Ummin tayi da cewa "A'a Ummi, ta dawo daga Lesson ta gaji, kada a takura mata, ki bani kuɗi kawai na siya cen inci. Insha Allahu ƙarfe shidda a gida Zatayi mana, alabasshi idan na dawo sai in ci mai yawa in ƙoshi Ummi" Ummin bata kawo tunanin komai ba, ta ɗauko kuɗi a jikkarta, tana mai miƙa ma Sahar cikin jin daɗi, irin yanda take maida hankali kan karatu, duk da take mai nukura, Amman sai gashi yanzu harda ita wai cikin gasa, kai Allah na gode maka. Da fatan alkhairi tabi Sahar, tana mai shige wa kitchen, domin yau kenan saidai ita Zatayi girki dole, Saha bata nan, haka ma Hajna, sai Na'eef kawai wanda ya rage a cikin gidan. *"Malali Lowcost"* Sahar ta faɗa a hankali, tana mai ɗan waige waige, kada ace wani ya ganta. Bata jira cewar mai a daidaita ɗin ba ta faɗa ciki kawai. Da kuɗin abincin da Ummi ta bata tayi amfani wajen biyan mai adaidaitan. Bayan ya sauke ta gaban wani madaidaicin gida. Wayar ta ta zaro daga cikin riga, tana mai danna kiran sahibin nata. Dama jira yake yi, saboda haka a kira na biyu ya ɗaga cikin wata irin annashuwa yake faɗin "Ya dai my Habat? Har kin iso kenan?" "Eah na iso, gani ƙofar gidan" ta faɗa itama, tana mai ɗan waige waige. Ƙarar buɗe ƙofa taji cikin seconds, kaman dama yana bakin ƙofar ne. Da kallo yake binta sama da ƙasa, cikin wata irin dariya ta rainin wayau. "Wow! Kunga malama ta fa, gashi tazo ɗaukar karatu" ya faɗa cike da rainin wayau, lokaci guda yana tafa hannu. Mai makon Sahar taji ba daɗi, sai itama tayi dariyar, tana mai yaye hijabin dake sanar rigar tata. Ƴar riga ce amless kalar ja, tsawon ta iya guiwa, duk tabi ilahirin surar jikinta ta shafe, komai na jikin ya bayyana, hatta da hannun brezier ɗinta da take kalar baƙa. *"Woooh ko kefa My Habat, yanzu kinfi kyau, wow! Wannan shiga haka duk ni kaɗai akayi mawa, in more inta kallo?"* Ya faɗa yana mai saƙalo hannun nata cikin nashi, zuwa cikin gidan, bayan ya maida gidan ya kulle. Sai taji wani irin daɗi, Zaiyad ya cika namiji, ganin shi cikin farin ciki ba ƙaramin nishaɗantar da ita yayi ba. Bisa kujera ya zaunar da ita, yana mai amsar hijab da ƴar jikkar tata ya wurga su bisa sofar. Bai ƙyaleta hakanan ba, faɗa wa yayi bisa jikin nata, Amman bai sakar mata nauyin shi ba. Numfashin sune ya gauraya. Saurin ɗauke kanta gefe tayi, tana son Zaiyad ɗin, sai take jin kanta kaman ma gata cen ta shiga gidan nashi a matsayin matar shi. Wasu abubuwa ya fara mata, yana mai faɗin wasu kalamai na ƙauna a gareta., tana mai tashi tsaye, ta shiga gyara wuyan rigar tata. "Toilet zan shiga My Love" Ɗan maida numfashi yake sama sama. "Muje in raka ki kenan.?" Ya faɗa cikin wani irin salo, yana yi yana kashe ido guda. Ɗan girgiza kanta tayi cikin kunya, tun da ta sako ƙafar ta gidan ta gaza yi mashi cikakken kallo. Duk da ba yau ta fara ganin namiji a tuɓe ba riga ba, amman kasancewr ita Kunyar soyayya daban take. Wando ne short sosai iya cinya, jikin nashi babu riga, sai yalolon gashin da yake kwance luf, jikin ilahirin kyakkyawar farar fatar jikin nashi. Zaiyad ɗin namiji ne cikakke, dayake yana yin jim sosai, sai ya kasance jikin nashi a murɗe yake, ga 6packs daya ajiye a bisa cikin nashi. Juyawa tayi tana mai nufar bed room ɗin nashi. Ba yau ta fara shiga ba, Amman bata san dalili ba, wata irin faɗuwr gaba ce ta ziyarce ta. Ita kanta tasan bata kyauta ba, tasan hakan ba daidai bane, saidai ta biye ma huɗubar shaiɗan ne, da yake raɗa mata cewa ai ba wani abu bane a wajen budurwa dan tazo wajen saurayi, haka taji Ummin ta ta faɗa cikin wani littafinta, har ta ƙara da cewa hakan shine wayewa da kuma nuna tsantsar ƙauna ga masoya, ya kasance koda yaushe suna jin ɗumin juna. Ko bayan data fito daga toilet ɗin, bata koma falo ba, ta samu gefen gadon nashi ta zauna, tana mai fiddo wayar ta daga cikin rigar ta, wadda ta mayar tun kammala wayar da Zaiyad, dayake hakan ya zame mata al'ada. Ta kusan minti talatin bata ji ɗuriyar shi ba. Sai cen ya shigo ɗauke da tray babba, a saman shi plate guda ɗaya na dafaffiyar indomie, wadda taji kayan haɗi da kwai, sai ƙamshi take yi. Gudan plate ɗin kuma kayan marmari ne ya yayyanka. Sai cokulla da suke ajiye bisa babban tray ɗin, tare da Jog mai haɗe da kofuna, cikin shi lafiyayyen Banana and Milk shake ne. "Here is your delicious yummy my Habat" Ya faɗa a hankali, yana mai dire tray ɗin gefen gadon kusa da ita. Sauke wayar tayi a hankali bisa cinyar ta, tana mai haske shi da ɗan murmushi. Sai suka zama kaman turawa, irin kular da mazajen turawa keba matayen su, a haka take hango kansu cikin ƙwayar idanun nata. Shima murmushin yayi mata, yana mai ɗauke wayar tata zuwa bisa stool. Gyara zama sukayi su duka. Sannan ya kalle ta,yana mai cewa "Feel free dear, and eat your food, here is your home, or u want me to feed you, uhmm.?" ya ƙarashe cikin salon da yana yana tafiyar da ita. Idanunta na kan abincin take ɗan girgiza mashi kai, Amman duk da hakanan saida ya cida kanshi, sannan yake cida ta, da cin abinci yayi daɗi ma, jawo ta yayi zuwa bisa jikin nashi, yana bata yana ba kanshi, hannun shi guda ɗaya na bisa jikin nata yana mata abubuwa marasa daɗi, wanda take jin daɗin su, take kuma hararo yanda Ummin ta ke wassafa daɗin hakan. Duk da haka Saha bata kula da kuskuren da take neman tafkawa ba. Ko bayan da suka gama cin abincin, kallo ya kunna masu a laptop ɗin tashi, yayin da suka gyara kwanciya bisa madaidaicin gadon nashi. Bisa ƙirjinshi fa take kwance, yanzu har ƴar hular tata ya zame mata, kalamai na soyayya suke zuba ma junan su, tana jin daɗi idan yace wannan gidan gabaki ɗaya, da mallakin gidan nata ne. Sai take ji ko Sama da ƙasa zasu haɗe bata jin zata iya rabuwa da Zaiyad ɗin. Sun nutsa cikin kallo ne sosai, sinadaran da ya zuba a cikin abincin suka fara tasiri kanta, tare da son zuciyar ta, da kuma shauƙin abunda take yi. Dayake Zaiyad ɗin ya ƙware a yaudara, sai gashi Sahar da kanta ta fara yi mashi wasu abubuwa, shi kuma sai ya dinga tutture hannayen nata, yana mai cewa "A'a my Habat, ba yanzu ba, ki bari sai munyi aure" totaly nuna mata yake baya so, yayin da Idanunta suke kan secrean na laptop ɗin, take kwaikwayar abunda turawan suke yi tana mashi. Wanda dama haka ya tsara, dan haka ne ya kunna ɗin, domin hakan ya ƙara jan hankalinta, inda suke cikin ɗaki su biyu, kuma bisa gado ɗaya, sannan jikin nata na gogar nashi. Wanda sun sani cewa hakan haramun ne, keɓancewar mutane gida biyu, mabanbantan jinsi, kuma ba muharramai ba. Dama haka yake so, a hankali ya fara biye mata, sai abun ya dinga mata daɗi, dama tasan Zaiyad ba baya ba wajen irin hakan, dayake ba yanzu ne ya fara yi mata ba. Abun fa ya fara yawa, tuni aka ture laptop gefe. Saidai me? Jin indaya dosa, sai zuciyar ta ta fara raya mata tsoro. Ture shi ta shiga yi tana kuka, Amman ina baya ma ko jinta, inda yayi niyya saida ya isa. Ƙara ta saki, tana mai rushewa da kuka sosai, duk yanda taso ture shi ta kasa, sai taji kaman yana da ƙarfin dawakai goma ne. Shi kuwa ba abunda yake mata sai sambatu, Sam baya ko jin kukan nata, kawai dai abunda yayi ƙoƙarin kiyayewa shine ji mata ciwo, ko kuma wahalar da ita. Saida ya gaji dan kanshi, sannan ya sauka yana mai komawa gefe, numfashi yake saukewa sosai, yayin da yake ji ɗakin na juya mashi. Ya samu yanda yake so, yanda ya zata haka yaji, tayi mashi daidai, ba zai iya lissafa ko ta nawa bace ita, irin su suna da yawa, Amman bai ji wadda ta kai Sahabat ɗin ba. Yayi da ita kuma take kukan biye ma zuciyar ta, danasani da nadama suka rufe ta, yanzu idan Ummi ta gane ya zatayi da ita? Yanzu idan ta samu ciki fa? Ba ta aure take yi ba, tunda tasan shine zai aure ta, ya dai san ba wani taje ta kai mawa ba. Tasha kuka sosai, har Idanunta suka kumbura, saidai cikin ƙanƙanin lokaci Zaiyad ɗin yayi amfani da irin tsantsar soyayyar da take mashi, da kuma yarinta dake kan Sahabat ɗin, sannan da kalaman yaudara wajen shawo kanta. Faɗi mata yake yi cewa komin rintsi komin wuya, yana tare da ita, ba zai taɓa barinta ba, kuma shine zai kasance miji a gareta, dan haka kada taji komai wannan shine somin taɓi, dan haka duk abunda take so, daidai yake da yayi mata. Kuma dan yana na farko ne taji zafi, nan gaba da wurin ya warke zataji babu zafi, saidai daɗin da ake faɗa kullum. Da wannan har ta ɗan saki jikinta, ya taimaka mata ta gyara jikinta, sannan ya bata wani ointment ta shafa a wurin. Ta ɗanji sauƙi, koda ta dawo ta kwanta, tuni bacci ya kwashe ta. Kallon ta yake yi cikin wani irin yanayi, yana mai jinjina yarinta da saurin sakin jiki da Sahar tayi dashi, ya tabbata nan gaba kaɗan zata dinga kawo mashi kanta, bai shirya ƙyaleta hakanan ba, har sai ya gama kwashe romon nata, kafin nan zai ajiye ta ya ɗauki wata... ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [2/13, 8:29 AM] Sumayya Sumy B: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *On the authority of Ibn Abbas (may Allah be pleased with them both), from the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him), among the sayings he related from his Lord (glorified and exalted be He) is that He said:* "Allah has written down the good deeds and the bad ones." Then He explained it [by saying that] "he who has intended a good deed and has not done it, Allah writes it down with Himself as a full good deed, but if he has intended it and has done it, Allah writes it down with Himself as from ten good deeds to seven hundred times, or many times over. But if he has intended a bad deed and has not done it, Allah writes it down with Himself as a full good deed, but if he has intended it and has done it, Allah writes it down as one bad deed." *عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فِيمَا يَرْوِي عَنْ رَبِّهِ عَزَّ وَجَلَّ، قَالَ: إِنَّ اللَّهَ كَتَبَ الْحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ، ثُمَّ بَيَّنَ ذَلِكَ: فَمَنْ هَمَّ بِحَسَنَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا، كَتَبَهَا اللَّهُ لَهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، فَإِنْ هُوَ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا، كَتَبَهَا اللَّهُ لَهُ عِنْدَهُ عَشْرَ حَسَنَاتٍ، إِلَى سَبْعِمِائَةِ ضِعْفٍ، إِلَى أَضْعَافٍ كَثِيرَةٍ، وَمَنْ هَمَّ بِسَيِّئَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا، كَتَبَهَا اللَّهُ لَهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، فَإِنْ هُوَ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا، كَتَبَهَا اللَّهُ سَيِّئَةً وَاحِدَةً. رواه البخاري ومسلم* [Bukhari and Muslim.] *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 16*~ Salma dake zaune tana danna waya babu abinda take sai kai ƙorafin Abdul wajen Jameela, ita kuwa Jameela ƙara zugata take yi akan ta cigaba da abinda take yi mishi zai tsorata ya dawo ya bata haƙuri. mussadiq dake zaune yana zazzage dakakken barkonon data gama cin soyayyen ƙwai dashi bata ɗauke ba tas ya juye a jikin shi amma Salma bata lura ba. Shigowar Ƙawarta Habiba wacce suka haɗu a sabon group ɗin data shiga wanda wata ƴar ƙanwar maman ta ta saka ta, ita bata wani damu ma da group ɗin ba domin baya wani birge ta ganin anfi turo hadisai da kuma Ayoyin Alƙur'ani hakan yasa bata wani damu dashi ba, akan group ɗin har faɗa sai da suka yi da ƙanwar tata kasancewar Salmar ta girme ta. To a shekaranjiya ne ma da aka turo wani video mara kyawun gani aka dinga cece kuce a group ɗin shine fa Salmar ta dinga tarewa wacce ta tura ɗin ganin sunyi mata caaa akai, shine fa Habibar da yake ita ɗin Admin ce ta cire su duka daga wacce ta turo ɗin har Salmar dake goye mata baya. Hakan ya ƙara tunzira Salmar shine tabi Habibar private taci mata mutunci ganin hakan ne yasa ita Habibar yin dariya kawai, ba tare data kula ta ba. Lokaci zuwa lokaci Habibar ta kan yi mata magana idan taso ta amsa idan bata ga dama ba ta share ta, shine fa jiya Salmar taga wani status da Habibar tayi na tallan magun-guna shine itama tace tana so,daga nan tayi mata kwatancen gidan ta shine ta kawo mata. "Assalamu Alaykum, masu gidan suna nan kuwa?", ta ƙara kwaɗa sallama a karo na biyu. Salma taja tsaki ƙasa-ƙasa sannan ta amsa da; "wa'alaikumus salam, waye ne yake kwaɗa sallama haka?, ya shigo mana". Jin hakan yasa Habibar shigowa, Salma ta tsaya tana kallon ta ganin baƙuwar fuska, gata mace ce wacce take zata kai shekaru talatin da biyu zuwa da uku. Habiba ta zauna sannan tace; "baki gane ni ba ko?", Salma ta ɗago daga kallon screen ɗin wayar ta da take yi ta ɗaga kai alamar eh, Habiba tayi murmushi tace; "Nice wacce muka haɗu a *Matan ƙwarai* Maman Afnan". Sai lokacin Salma ta faɗaɗa murmushin ta sannan tace; "sannu da hany.....", ihun da Musaddiq ya ƙwala ne yana sosa idanu hankalin su ya kai kanshi, duk ya wanke jikin shi da garin barkonon. "Kan ubancan, amma wallahi wannan yaron akwai ɗan iska mara mutunci yajin nawa ka maida shi haka?", da sauri Habiba ta dakatar da ita ta hanyar faɗin; "haba Maman Husna kije ki wanke mishi ne sai ki dawo", Salma tace; "aikuwa wallahi be isa ba sai dai ya jira Uban shi ya dawo ya wanke mishi". Habiba tace; "ba za'a yi haka ba, nuna mini Toilet ɗin naje na wanke mishi", da hannu ta nuna mata hanyar tana me cigaba da danna wayar ta, Habiba ta ɗauki yaron ta kufi toilet ɗin dashi. Shima duk datti haka dai ta daure ta wanke mishi sannan ta sake mishi wanka, yadda ta barta haka ta dawo ta same ta, Habiba ta jinjina kai tana me mamakin halin na Salma. " a taimakawa bawan Allah da man shafawa da kaya", tana daga zaunen ta ƙwalawa Husna kira wacce ke ɗaki, da sauri yarinyar ta fito, ta kalle ta tace; "ki ɗaukowa wannan ɗan iskan kaya ki kawo a saka mishi", ita kanta yarinyar duk da bata da wayo sai da tayi jim sannan ta nufi ɗakin da sauri gudun masifar mahaifiyar tata. Babu jimawa ta dawo hannun ta ɗauke da riga da wando ta miƙawa mahaifiyar tata, Salma ta zabga mata harara sannan tace; "a hannu na kika ganshi ko hannun wannan matar?", Husna tayi saurin miƙawa Habibar kayan tana me komawa ɗaki, Habiba tabi yarinyar da kallo cike da tausayawa. Ita ta sakawa yaron kaya sannan ne Salmar ta maido da hankalin ta gare ta suka gaisa sannan tace; "yauwa Maman Afnan ina kayan", Habiba ta jinjina kai tace; "ai Maman Husna ke kanki kina buƙatar gyara haka kike zaune a gidan naki?". Cikin haɗe fuska tace; "to yanzu kuma meya faru?", Habiba tace; "haba Maman Husna ki kalli kanki ki kalli yaran ki, sannan ki kalli gidan ki babu wanda ya sami cikakkiyar kulawa, ki duba kiga yadda kike tafiyar da al'amuran ki, babu wata cikakkiyar natsuwa tunda nazo waya take hannun ki baki sauke ba, yaron ki yayi ɓarna maimakon kice Allah ya shirye shi kin bishi da aibantawa to ki sani wannan hanyar da kika ɗauko ba zata ɓulle dake ba sannan kuma bakin uwa akan ƴaƴan ta dafi ne idan kika cigaba da aibanta abinda kika haifa zaki dawo kiyi dana sani, lokacin daya lalace ke zaki fi kowa shiga tashin hankali dan haka dan Allah ki maida hankalin ki kan abinda ya kasance dolen ki, ki rage bawa waya imanin ki gaba ɗaya ni dai roƙo na a gare ki kenan da kuma shawarar da nake baki". Cike da rashin kunya Salma tace; "tallan magani kika zo ko kuwa saka idanu akan abinda babu ruwan ki? Wannan fa rayuwa tace, idan har zaki bani kaya na siya ki bani idan ba zaki bani ba ga hanya bana son salo da kinibibi", Habiba ta saki murmushi tana faɗin; "dama nasiha ce nayi miki tunda baki ji ba ai shikenan". "nace miki ina da buƙata ki tattara kayan ki, ki fice kawai bana da buƙatar kayan naki ma", Habiba ta miƙe cikin sanyin jiki tace; "Allah ya baki haƙuri". Salma taja tsaki tana faɗin; "kawai mutanen yanzu sai gulma da kinibibi suka iya basu iya komai ba daga kawo talla mata har ta samu damar gaya mini magana ki shigo gidana kice wani zaki mini sanabe, to a ƙara gaba dama can ba wai kin dame ni bane". Abdul dake tsaye bakin ƙofa yana jiyo su yayi saurin matsawa ganin Habibar tana ƙoƙarin fitowa, yana me takaici da tsoron halin matar tashi. Ganin Habibar ya ƙara tsunduma shi cikin kaɗuwa da rashin kuzari, a ƙalla zata bawa Salma shekara biyar zuwa shida amma shine take mata wannan rashin mutuncin ya ilahi! Me Salma ta zama ne?". Habiba kuwa ta raɓe gefen shi ta wuce tana me gaishe dashi, cikin rashin kuzari ya amsa yana me faɗin; "kiyi haƙuri baiwar Allah ni kaina yanzu bana gane kanta gaba ɗaya a ganin da nayi miki na san ke macece me kamala ki ƙara haƙuri wata rana sai labari". Habiba tayi murmushi tace; "kada ka damu kuma insha Allahu zanyi iya ƙoƙari na ganin ta gyaru kuma ni komai ya wuce a waje na, Allah ya ƙara maka haƙuri da juriya ko baka faɗa ba na san cewa kana cikin tashin hankali da rashin walwala da nutsuwa amma komai yayi farko zai yi ƙarshe", tana gama faɗin haka ta juya ta fice daga gidan. Jiki a sanyaye yayi sallama ya shiga, ko ɗagowa bata yi ba balle ta kalle shi, shima kuma tsabar takaicin abinda ta yiwa wannan matar yasa be kula ta ba, wanka yayi sannan ya dafawa yaran nashi abinda zasu ci. Da kanshi ya tasa su a gaba suka ci suka ƙoshi sannan ya fice daga gidan ya nufi wajen sahibar sa Jameela wacce a yanzu yana damuwa da lamuranta sosai kuma zuciyar shi ta fara aminta da ita. Koda ya isa ƙofar gidan su Jameelar ta waya ya kira ta, ita kuwa Jameela bata jima da gama waya da Salma ba wacce ke faɗa mata yadda komai ya wakana tsakanin ta da Habiba. Cike da nishaɗi tace; "yayi dai-dai ta hannun dama na kada ki yadda wata ta shigo ta nemi raina ki, kika sani ko idan ta sami dama sai kiga ta fara sako miki gulma da sauran su gwara da kika ci ƙaniyar ta". Salma tayi murmushi tana me jin daɗin yabon da aminiyar tata tayi mata haka kuma ya ƙara mata ƙarfin gwiwa wajen ganin ai bata yi wani abin aibu ba. Haka Jameela ta cigaba da zuga ta har sai da ta tabbatar Salmar ta ɗauke komai data kitsa mata sannan ta katse wayar. Ganin kiran abin ƙaunar nata yasa tayi wani miskilin murmushi tana faɗin; "Salma kashin ki ya bushe kin kaɗe har ganyen ki", cikin kissa da kwarkwasa ta ɗaga tana ƙara kashe murya tace; "Abban Mussadiq barka da yamma". Abdul ya ɗanyi ajiyar zuciya sannan yace; "ki fito ina ƙofar gidan ku", kamar ta saka ihu haka take ji amma ta maze sai faɗin; "gani nan zuwa ban minti biyar", tana katse kiran tayi shewa tana juyi cikin murna da farin ciki. Shaf-shaf ta faɗa wanka, sai da ta ƙalƙale jikin ta sosai sannan ta fito, ta shafa mai sannan ta hau shiryawa kwaliyya sosai ta zauna ta tsara sannan ta fesa jikin ta da wani irin fitinannen turare me shegen ƙamshi da ɗaukar hankali. Riga ta saka ta material ɗin da ake kira rariya wanda aka yiwa ɗinkin doguwar riga ta ciki kuma ta saka dogon wando baƙi da riga ƴar ƙarama, tayi kyau babu laifi domin kuwa me yawan kwalliya ba'a ganin munin shi. Cikin taku me ɗaukar hankali ta nufi waje, kamar yadda ta zata idanun shi na kan ƙofar gidan yana kallon ta ina zata ɓullo, koda ta fito sai da ta zubo mishi wani murmushi me jan hankali sannan ta fara takowa zuwa gare shi. Cikin mutunta juna suka gaisa tana tambayar shi yasu Salma da kuma Husna, ya amsa da suna lfy sannan ya ɗora da cewa; "ni na rasa wannan sirrin ƙamshin naki Jameela", jameelar tayi murmushi tana sauƙar da kai ƙasa. "gaskiya ya kama ta ka turo kaga Baba na ya fara magana akai", ta kaudar da waccen maganar, ya juyo yana kallon ta sannan yace; "ai dole ma nayi na turo, amma abinda nake so shine na gama inda zaki zauna tukunna, ya kama ta ma kije ki gani saboda abinda kike buƙata". Tayi murmushi tace; "kada ka damu in dai yayi maka nima yayi mini, dan duk abinda kake so ina son shi", sosai yaji daɗin maganar tata, matsalar shine ta iya kalamai masu sanyaya zuciya wanda ya rasa daga wajen matar shi Salma a yanzu. Sai da aka fara kiraye-kiraye sallar magrib sannan suka yi bankwana, haka Jameela ta kuma haɗa shi dasu Sweet da chocolates a cewar ta ya kaiwa yaran ta, haka ya tafi cike da farin ciki domin kuwa yanzu idan yana tare da Jameelar ya kan manta da duk wata damuwar da Salmar take ƙunsa mishi a gida. ************ Sai da ta ɗauki awa biyu cikakku tana barci sannan ta farka, cikin jikin shi take kwance suna shaƙar barci kai zaka ce irin ma'auratane masu tsananin ƙaunar juna. Ba zata ce bata ji daɗin kasancewar su ɗazu ba sai dai kuma zuciyar ta cike yake da tsoron abinda zai je ya dawo idan Ummi taji abinda ya faru. Hannu ta kai ta yaɓa saman girar shi zuwa idanun shi, lallai Zaiyad ya nuna mata shi cikakken namiji ne wanda kowacce mace take burin samu. Idanun shi ya buɗe sannan ya kalle ta, cikin muryar barci yace; "my Habat har kin tashi", ta saki murmushi tace; "kai my love tun ɗazu fa nake barci", yayi murmushi yana miƙewa yace; "muje muyi wanka". Kamar tace a'a sai kuma ta tuna da littafin Ummin nata inda take cewa jaruman littafin tare suke wanka, tayi dariya wato dai Zaiyad shine dai-dai ita kenan wanda zai bata kulawa sosai. Bata idasa tunanin ba taji anyi sama da ita, shagwaɓe fuska tayi tana faɗin" kai My love ka sauke ni zan iya tafiya da kaina", ya ƙara haɗa ta da ƙirjin shi yana faɗin; "ai naga kin tsaya tunani da shakkun so da kulawar da zaki samu ni kuwa so nake na tabbatar miki da irin son da nake miki ne". Ta ƙara shigar da kanta cikin ƙirjin shi tana me farin ciki da murnar samun Zaiyad ɗin a matsayin masoyin ta, a wajen wankan ma haka ya dinga jagwalgwala ta sai da ya gama son ranshi sannan suka yi wankan suka fito. Kayan jikin ta ta maida sannan ta fito falo, a zaune ta same shi saman kujera ya kalle ta yace; "kai My Habat kinyi kyau sosai nazo na maida ke gida ko?". Ta kalli agogo ƙarfe huɗu da mintina, ta girgiza kai tace; "ai da sauran lokaci na cewa Ummi sai shida", yayi dariya yace; "ba zaki shiga islamiyya ba kenan?". " ka bari sai shida saura sai kawai ka ajiye ni a bakin makaranta", ta ƙarasa tana yamutsa fuska, haka suka ƙarasa zaman tare har shida saura sannan ya ɗauke ta har ƙofar makarantar tasu. Suna cikin mota suka hango an fara fitowa hakan na nuna an tashi kenan, Zaiyad ya buɗe locker dake motar ya zaro ƴan dubu-dubu guda takwas ya miƙa mata. Tayi murmushi ta amsa tana faɗin; "thanks my love", ya ɓata fuska yana faɗin; "ni bana son irin wannan godiyar", tayi dariya sannan ta haɗe bakin su. Zaiyad kuwa kamar jira yake ya cafke harshen ta suka hau sumbatar juna, tsayin lokaci suka ɗauka a haka sannan suka saki juna suna maida numfashi. Zaiyad ya maida numfashi yana faɗin; "My Habat wannan irin salo haka, gaskiya na more sosai da samun ki, ji nake kamar kada mu rabu". Sahabat tayi murmushi tace; "gobe ma ai zan fito mu sake haɗuwa", cikin jin daɗi yace; "dats my Habat", haka suka yi sallama ta fita kasancewar da ɗalibai a wajen yasa babu wanda ya damu da fitowar ta dan babu wanda ya lura da ita ma. Har cikin makarantar ta kutsa sannan suka haɗu da Hajna da Na'eef da alamu ita suke nema, nan ta riƙo hannun su suka nufi gida. Koda suka shiga gidan kamar yadda ta zata haka ta tarar da Ummi hannun ta riƙe da waya tana faman dannawa, tana ganin su tace; "yauwa Sahabat tunda kin dawo ɗan wanke tukunyar can ki ɗora mini ruwan wanka". Sahabat kamar ta fasa ihu haka take ji shiyasa fa bata so ta dawo gidan nan saboda aikin da Ummi zata dinga saka ta, haba ita kenan aiki kamar engine. ************* Hunayda ke zaune tayi tagumi tana tunanin Malam Suhayl bata taɓa tunanin zata so wani har haka ba, ashe dama haka soyayyar take gashi daga tafiya ko kwana biyu be yi ba amma ji take kamar an shekara, taja wata irin nannauyiyar ajiyar zuciya. Ammi dake tsaye a kanta tace; "Hunayda!", cikin sauri ta ɗago ta kalli Ammin nata sannan tace; "na'am Ammi". "Hunayda ya kamata kiyi haƙuri haka ki dinga maida hankali akan sauran al'amuran dake gaban ki, kada ki manta tafiya fa ba mutuwa bace kuma insha Allah Malam Suhayl zai dawo ya same ki, haba kinji ta Suhayl". Hunayda tayi saurin rufe fuskar ta tana dariya cike da kunyar abinda Ammi ta faɗa. Ammi tace; "yanzu kije kiyi wanka sai kizo ki share tsakar gida kinga yamma tana daɗa yi", babu musu ta amsa da to tana nufar ɗaki domin cika umarnin mahaifiyar tata. Ammi tayi murmushi tana bin ƴar tata da kallo, yanzu Hunayda ta natsu kamar ba ita ba, lallai dole ta godewa Allah ta kuma godiya ƙawarta Hajiya Gambo tare da Sumayya Babayo Abdullahi wa'inda suke taimaka wajen sai-saita ƴar tata har ta dawo nutsuwar ta. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [2/24, 9:56 AM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) said: 'Spend (on charity), O son of Adam, and I shall spend on you.'" [Bukhari (also by Muslim).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ، أُنْفِقْ عَلَيْكَ . ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 17*~ Jameela tayi sallama ta shigo cikin gidan, da sauri Salma ta ajiye wayar dake hannun nata ta tarbo ƙawar ta ko ince aminiyar ta, sosai suke farin ciki da ganin juna. Salma tace; "ai na ɗauka da wasa kike ba zaki zo ba", Jameela tayi wata irin dariya sannan tace; "ai zuwa ya kama ni dole wace ni ai dole nazo", ta ƙarasa tana bin gidan da kallo. Da hannu ta nuna ɓangaren da Abdul ke mata gini tace; "wancan fa da naga an tada ginin, ƴan haya zai zuba?". "ina fa wai nan na amarya ne", Salmar ta faɗa tana taɓe baki, Jameela itama ta taɓe baki sannan tace; "au ashe da gasken yake kenan ai na ɗauka wasa yake yi wallahi, amma wannan amarya zata ga rashin mutunci,yanzu duk wannan tsantsara ginin da ake yi nata ne?". Salma ta taɓe baki tana faɗin; "bar namiji munafiki, rigar ƙaya ki saka ya soke ki, ɗan bushiya sai kin goya shi ya sakar miki ƙaya, ƙanin ajali kenan kobe kashe ki ba ya barki jinya, ai duk wacce ta riƙi ɗa namiji uba zata mutu marainiya". 🙄Bani na faɗa ba inji oga Salma babu ruwa na a ciki🙊. Jameela tayi shewa tace; "ashe kina fahimta ai lallai kin fara shigowa gari ai na ɗauka har yanzu kina nan cikin duhun kan naki". Salma ta jefa mata harara tace; "aiko yanzu bayana zaki biyo dan na tabbatar a wayewa da rashin mutunci na ɗara ki". Jameela tayi munafikin murmushi tace; "a'a fa tukunna dai Salma ai a halina idan aka kasa casa'in to ko kaso ɗaya baki gama sani ba, yanzu dai muje ki nuna mini ɗakin amaryar taki". Salma tace; "au wai ke tunanin ki zan bari ta shigo ne ai ina hakan ba zai taɓa yiwuwa ba", Jameela tace; "kuma fa hakane amma shiya kamata ki tadawa ɓalli har ya fasa". Salma ta juyo ta kalle ta tace; "ke wallahi ina yi mishi kawai dai kunnen uwar shegu yayi dani amma zan kuma dagewa zai san kaidin mace nada yawa". Jameela tace; "ai dama kaidin mace yawa gare shi dan ina da tabbacin koke baki gama sani ba balle shi da yake namiji,lalala cancanɗi gaskiya masha Allah". Sosai suka zagaya part ɗin komai yayi two bedroom da kuma falo sai kitchen da bayi komai yayi zam-zam abinda ya rage kawai fenti da pop shikenan. Aikuwa komai yayiwa Jameela yadda take buƙata, suna tafe tana kuma zuge Salma akan irin rashin mutuncin da zata dinga yiwa Abdul ɗin. Ita kuma da yake sauna ce sai naɗewa take yi kamar ana biya mata fatiha, sosai kuma yake zama a kanta. Haka har suka koma falon Salmar suka zauna, fira suke sha sosai har zuwa azahar sannan Salma ta shiga kitchen ta girka musu taliya suka zo suka ci. Sun gama kenan Jameela ta dube ta tace; "wai ya maganar wannan munafikar fatan dai baki kuma yi mata magana ba ko?". Salma tace; "tun yaushe nayi blocking ɗin ta ai naga ba zamu dai-dai ta ba, na ɗaga mata red card", suka saki shewa suna tafawa. Sai uku da rabi sannan suka ji shigowar me gidan shida yaran, cikin dabara Jameela ta ƙara gyara ɗaurin dake saman kanta. Da sallama a bakin shi ya shigo riƙe da hannun Mussadiq da kuma Husna, Jameela ce ta amsa tana me jefa mishi wani kallo cike da so ƙauna. Salma kuwa tsaki taja ta juyar da kanta hakan ya hana ta hango Jameelar yadda take bawa filawar ruwa. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke yana me ƙaran binta da kallo, sanye take da baƙar abaya sai gyale wanda shita naɗa a kanta tayi ɗaurin zamani, shigar da Abdul ke matuƙar so kenan. Ya maida kallon shi kan salma da har lokacin take sanye da doguwar riga ta barci alamu ya nuna tunda ya fita har ya dawo bata yi wanka ba. Mamakin shi ɗaya taya akayi Jameela ta san shigar da yafi so, taya ba zata sani ba bayan matarka sauna ta karance mata tas🙄. Cike da kasala ya ƙaraso domin irin gajiyar da yayi ga kuma halin da Jameelar ta jefa shi wanda inama ace Salmar ce tayi wannnan shigar da yafi jin daɗi. Cikin wata iriyar murya Jameelar ta gaishe dashi ai sai da ya nemi waje ya zauna yana me sauke numfashi. Ya saci kallon Salmar ya kamata ace zuwa yanzu ta harbo jirgin nasu amma da yake ƴar can kwanar ce bata fahimci komai ba. Ko sannu da zuwan da ƙyar ya samu daga Salmar, ya kalli Husna yace; "yau kuma fushi ake yi dani ko sannu da zuwan ba zan samu ba". Ke da bakya wajen idan kin tanka to Salma ta tanka, ya juya ya kalli Jameela wacce har lokacin shi take kallo ji yayi kamar ƙasa ta buɗe ya shige. Cikin sauri ya nufi bedroom ɗin su, Salma tabi hanyar da yabi da harara tana jan dogon tsaki, Husna da Musaddiq kuwa ɗakin su suka wuce domin canza kaya. Ya ɗan jima a ciki a tunanin shi ko Salma zata biyo shi amma shiru haka ya haƙura ya fito, suna a yadda ya barsu alamu ya nuna kenan bata shiga domin taimakawa yaran ba. Ɗakin yaran ya shiga, ya sami Husna har ta cire nata kayan tana taimakawa Musaddiq ɗin domin shima ya cire nashi. Hannun su ya riƙo suka fito tare, tsabar haushi ko kallon inda Salmar take beyi ba, ya fice abin shi. Jameela na ganin ya fita, tayi shewa tace; "kina wuta matar nan, gaskiya kina birge ni ai kada kiyi mishi da wasa kwata-kwata". Salma ta ƙara hura hanci jin abinda Jameelar ta faɗa tace; "ai masifa da bala'i yanzu ya fara gani cikin gidan nan wallahi". Jameela tayi mata jinjina tace; "wallahi kina birge ni ƙawata bari na tashi na tafi gida", Salma ta taɓe baki tace; "tun yanzu?. Jameela ta miƙe tana ɗaukar ƴar ƙaramar jakarta tace; "gwara ke a gidan ki kike nifa Mama na can na jira na", haka Salma ta rako ta har bakin get yayin da Jameela ke ƙara zuga ta. ******************* Yanzu Sahabat liƙafa ta cigaba domin kuwa a koda yaushe tana gidan Zaiyad don ƙaryar da tayi akan musabaƙa da zasu je hakan yasa Ummi barin ta ba tare da wani tunani ba. Ta ɓangaren su kuwa rayuwar su suke kamar ta miji da mata kullum ya kan ɗauke ta haka suke wuni tare bayan sun gama holewar su ya kaita bakin makaranta inda anan zata jira ƙannen ta suzo su wuce gida. Kuɗi da sauran abubuwan ƙwalam da maƙulashe babu abinda Zaiyad baya siya mata, idan ka ganta yanzu tayi kyau har wani ƙyalli take domin kuwa ruhin ta da gangar jikin ta na samin abinda take so. Hajna kuwa ga abin magana amma babu bakin yin ta, daga um sai um wai uwar gulma tayi cikin shege, ita dai ta zubawa ƴar uwar tata idanu ne tana tsoron yi mata magana yayar tata ta dena ƙara mata kuɗin tara hakan yasa taja baki ta tsuke. Yau Alhamis dan haka babu yadda Saha bata yi ba amma Ummi ta hana ta fita ko'ina hakan ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba. Tana shiga ɗaki taja dogon tsaki, dan ita yanzu ji take dai-dai da Ummi ganin cewa abinda Ummin ta sani itama ta sani. "yanzu mutum ba dama ya sami ƴancin kanshi, sai ayi ta faman damun shi mtsew, ashe abinda take mini baƙin ciki kenan, ita da mutuwa ta ɗauke nata shi yasa nima take so ta hana ni hutawa da jin daɗin rayuwa ta, mtseew gidan ku amma baka da sakewa", cewar Sahar kenan cikin zunɓurar baki. Allah ya shirye ki Sahabat, da alamu kinyi nisa bakya jin kira🙄. Sai da ta kuma tura ƙofar ta rufe sannan ta ciro waya ta fara kiran layin nashi, be ɗauka ba har ta katse, babu jimawa sai gashi ya biyo kiran. Tana ɗagawa ta sakar mishi wani kuka irin na shagwaɓa har da sheshsheƙa, Zaiyad ya ruɗe gaba ɗaya. "haba matar Zaiyad me yake faruwa ne?", cikin shagwaɓa tace; "ba Ummi bace ta hana ni fitowa", ya ɗan yi jim sannan yace; "babu komai Allah ya kaimu asabar ɗin". "nifa yanzu ina son ka ji nake kamar ba zan iya rayuwa babu kai ba", faɗar Sahabat kenan. Zaiyad yayi murmushi yace; "kada ki damu insha Allah Daddy yana dawowa zamu yi aure". Sosai hakan ya faranta ran Sahar har tayi murmushin da haƙoran ta suka bayyana, kaɗan suka yi fira sannan suka suka yi sallama. Haka ta tura wayar cikin rigar ta sannan ta fito, abin ban haushi shine Ummin tana zaune da waya a hannun ta tana dannawa kamar ko wane lokaci. Saha tayi ƙwafa a ranta tace; "anjima za'a sake sakar mana me zafi kenan?". Ummi ta kalle ta tace; "Saha aje a ɗora abinci, yanzu Hajna ta tafi siyo Kabeji, kafin ta dawo kin ɗora kinji ƴar albarka". Saha ta ɗan turo baki gaba sannan ta wuce kicin ɗin tana ƙunƙunai, wanda ita Ummin bata ma lura da me take ba. ****************** Ammi data shigo ɗakin ta kalli ko'ina tayi murmushi, a koda yaushe tana ƙara godewa Allah akan shiryar mata da yarinya da yayi. Wayar Hunaydar ta hango saman dressing mirror ɗin ɗakin nata, cikin sauri Ammi ta ɗauka. Koda ta bincika babu wani abu wanda zai nuna ma na ɓatanci ne, hakan yasa ma Hunaydar bata sakawa wayar Password ba. Hunayda ta fito daga bayi hannun ta riƙe da Izal, tayi murmushi tace; "Ammi sannu da hutawa". "sannu da aiki ke kuma ƴar albarka", Ammi ta faɗa cike da jin daɗin yadda ƴar tata take yanzu. Hunayda ta ɗan langaɓe kai, Ammie tayi murmushi tace; "ya akayi me kike son cewa". Hunayda tayi murmushi tace; "dama Ammie ina so ne na idan babu abinda zan miki gobe zamu je kasuwa nida Surayya". Ammie tace; "babu komai Allah ya kaimu sai dai zamu je tare ne daku sai ku zaɓi abinda kuke so ko?". Hunayda tayi murmushi tace; "shikenan yadda kika ce Ammi", tana faɗin hakan ta ɗauki wayar ta fice daga ɗakin. Koda taje ɗakin su Surayya har ta gama gyara ɗakin don haka bayi kawai Hunayda ta wanke. Ta koma ta zauna kusa da Surayya tace; "Ammi ta amince tace ma tare zamu je", Sosai Surayyar tayi murna da shiriyar ƴar uwar tata. Ita kanta Hunaydar yanzu tafi jinta cikin walwala saboda komai tana yi ne ba tare da shayi ko shakkar wani ya ganta ba amma da kullum cikin tsoro take da fargaba. Ammie kuwa Hunayda na fita tayi murmushi me cike da farin ciki, tun ba yanzu ta fahimci Hunayda tana cikin masu son ƙalƙali da kuma sha'awar kayan ado hakan shine ya kusa jefa ta a halaka. Sai dai yanzu Alhamdulillahi ta fahimci yarinyar tayi hankali sosai, ita kuma tayi alƙawarin indai ta lura da wani abu daya birge Hunaydar to zata yi ƙoƙari ganin ta mallaka mata kalar wannan abin koda be kai wancan ba. (To ƴan uwa sai ki lura wace kalar ƴa ko ɗa Allah ya baki idan har me zara ne sai kiyi ƙoƙarin ganin kin wadata shi ko kin wadata ta da abinda take buƙata ko yake buƙata gudun gurɓataccen aboki yazo ya janye miki shi ko gurɓatacciyar ƙawa tazo ta janye miki ita Allah yasa mu dace). ************* Yau daren Juma'a Sahabat dake kwance tayi wani juyi cike da shiga wani yanayi mara misaltuwa, ta maida kallon ta kan Surayya dake faman barci hankali kwance taja tsaki. Wayar ta dake hannun ta ta sake matso da ita tana me cigaba da karanta littafin da mahaifiyar ta ke karanta wai shi *RAYUWAR BARIKI* har yaso ya ɗara *NI DA SHI* don wannan ma na kuɗi ne kuma tana ɗaya daga cikin wacce ta biya har nera dubu ɗaya ta siya amma Ummin bata gane ta ba domin kuwa kati ta tura ba VTU ba hakan yasa Ummin bata gane ta ba. Sosai littafin yake hargitsa duk wata ko wani me rai da lafiya, hannu tasa ta shafi ƙirjin ta jin ta kawai take wani iri. Da ƙyar ta iya ƙarasa page ɗaya, ɗayan kuma tace ssi gobe idan taje wajen sweethert ɗin ta. Lamo ta kwanta ta ɗora hannun ta saman marar ta, wani irin ciwo take mata gashi maganin ciwon yayi mata nisa. Miƙewa tayi ta shige bayi da sauri, ta kunna wutar bayin sannan jiki na rawa ta hau kiran shi. "My Habat ya akayi ne na jiki a irin wannan lokacin?", ya tambaye ta dan yau basu jima ba ta kashe datar ta saboda littafin da Ummi ta saki,shi kuma hakan dama ya bashi domin kuwa ya sami wata chicks ɗin yana ƙoƙarin tsara ta ne. Habat tace; "Sweetheart ba zan iya barci ba shine na kira ka ko akwai abinda zaka yi mini". Yace; "ok to yanzu ki buɗe datar ki zan kira ki", ta amsa da to tana me katse wayar, tana kunna datar ko minti uku bata yi ba kiran shi ya shigo. Ta ɗaga suna kallon juna don video call ne, ganin yadda idanun ta yayi ja sai ta bashi tausayi domin shi yasan Sahar tana daga cikin mutane masu tsananin sha'awa. "Yanzu ki miƙe ki cire kayan ki", babu musu ta miƙe ta cire kayan tsaf, yana daga kwancen ta kafa mata idanu. Kullum sukan kasance tare in dai ta sami fitowa amma har yanzu be ji ta ishe shi ba, lallai yarinyar tana da zaƙi da yawa🙈. Hannu yasa saman marar shi yana me shafawa yana lumshe idanu, don ganin da yayi mata haka ba ƙaramin tayar mishi da hankali yayi ba. A haka ya dinga faɗa mata magan-ganu wa'inda wani har sata yake tana yi,wai ta dinga assuming shine ke yi mata. Ta haka ya samu damar biyawa kan shi buƙata itama ya biya mata, nan suka yi sallama cike da kewar juna sannan ta katse kiran. Hakan nan ta kunna famfo ta tara ruwa tayi wanka dan hakan shine rufin asirin ta, ga ruwan me sanyi amma gudun abinda zai je ya dawo yasa tayi wankan a haka ta maida kayan ta sannan ta zo ta kwanta. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) said: 'Spend (on charity), O son of Adam, and I shall spend on you.'" [Bukhari (also by Muslim).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ، أُنْفِقْ عَلَيْكَ . *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 18*~ Hunayda ke gaba inda Hajna ke bayan ta, duka suna sanye da dogon hijab me hannu kalar Uniform duk suma sauran ɗaliban da suka fito daga makarantar kalar hijab ɗin dake jikin su kenan. Gaban Hunayda ya faɗi ganin Sahabat tsayr gaban mota, inda na ciki kuma ya zuro hannu ya riƙe mata nata hannun, ita kuma sai murmushi take yi. Kasa motsi tayi tana mamakin rayuwar da Sahabat ɗin ta ɗaukarwa kanta, Sahabat kuwa sai da suka yi sallama sannan ɗagowar da zata yi sai akan fuskar Hunayda. Duk da gaban ta ya faɗi amma sai ta ɗaure fuska ganin kallon da Hunaydar ke jefa mata, Hunayda kuwa kallon mamaki, tsana da kuma jimami duka shi take bin Sahabat dashi. Amma duk da haka ta ƙudiri aniyar yi mata nasiha ko zata ji ta dena, dan haka cikin sauri ta ƙarasa kusa da ita da niyar magana amma abin ban haushi Sahabat data lura da Hunaydar magana take son yi mata sai tayi saurin wuce ta. Hunayda tabi bayan Sahabat da kallo, tana ƙara jinjina halin da ƙawar tata ta jefa kanta me wuyar fita. Taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta ja Hajna suka wuce jikin ta a sanyaye. Koda suka isa gida sai da Ammi ta lura da canzawar tata, har sai da ta kai ga Ammin ta tambaye ta amma tace mata babu komai. Dole Ammi ta haƙura domin kuwa bata so tana takura mata dan yaran yanzu sai Allah kawai. Suna zaune suna cin abinci Hajna tace; "Ammi kin san meya faru yau kuwa?", Ammi tace; "a'a auta sai kin faɗa mini". Hajna ta kalli Hunayda wacce ke cin abinci a sanyaye domin duk cikin minti ɗaya sai abinda Sahabat tayi ya dawo mata ƙwaƙwalwa. Hajna tace: "yau munga Aunty Saha ta fito daga wata mota kuma na ciki har riƙe mata hannu yayi, sannan ko makaranta bata zo ba sai da aka tashi sannan motar ta ajiye........", bata sami damar ƙarasawa ba domin wani dundu da Hunayda ta sakar mata a baya. Babu shiri Hajnar ta ƙwalla ƙara sannan tari ya biyo baya domin dukan ya shige ta, ita kanta Hunaydar bata san lokacin data yi mata wannan aika-aikar ba. Ammi ta dakawa Hunayda tsawa; "Baki da hankali ne? Wannan wane irin duka ne ko kema irin abinda Sahabat ɗin take aikatawa kike aikatawa kina tsoron ta tona miki asiri yasa kika mata wannan dukan?". Hunayda ta girgiza kai, idanun ta kamar zai kawo ruwa, Ammi ta kuma daka mata tsawa; "dalla tashi ki bawa mutane waje kina girma kina rashin hankali", cikin sauri Hunaydar ta miƙe ta bar wajen ƙwalla na zubo mata. Tana zuwa ɗaki ta fashe da kuka wanda ita kanta bata san takamai-mai ta meye ba, shin na faɗan da Ammi tayi mata ne?, na zargin da Ammi ta jefa a kanta ne?, tausayin dundun da ta yiwa ƙanwarta ne ko kuwa tausayin halin da ƙawar ta ke ciki ne?". Nace; "kya tambaye ni Hunayda taya zan sani ni kuwa🙄. Sahabat kuwa tana ɓacewa ganin Hunaydar taja tsaki tana faɗin; "aikin banza yarinya ƙarama sai iyayi", haka taje ajin su Na'eef sannan ajin su Surayya. Kamar koda wane lokaci Ummi na zaune da waya a hannun ta, Sahabat ta kuma jan tsaki tana faɗin; "wallahi Ummi wata rana sai an sace ta hankalin ta na kan waya bata sani ba". Sahar ce ta share gidan, sannan tayi alwala din yin sallah, tana idar da sallar ta fito don ta ɗorawa ƙannen nata ruwa, Ummi har tayi sallah ta dawo ta zauna. Tsabar haushi Sahar ko kallon ta bata yi ba ta wuce, Ummi tace; "Saha ɗan zubo mini abinci mana", sai da ta turo baki sannan ta amsa da to. Sai da ruwan yayi zafi sannan tace; "Surayya ki fara yiwa Na'eef sai kema kiyi kinji, ki maida mini nawa idan kin juye", Surayyar ta amsa da to. Tana shiga ɗaki wayar ta fara vibrating, cikin sauri ta zaro ta daga ƙaramin wandon da take sakawa a jikin ta me aljihu. "My Habat na kira ne naji ya kika je gida?", ya faɗa in cool voice. Tace; "lafoya lau nazo gida sai dai kewarka da nake yi". "ɗazu fa muka rabu, kuma gobe zamu sake haɗuwa", ya sake bata amsa, tace; "umm hakane amma aini ko kwana zamu yi tare ba zan gaji da kai ba". Yayi wata ƴar iskar dariya irin ta ƴan duniya sannan yace; "nima ai ba zan taɓa gajiya dake ba kin san irin son da nake yi miki kuwa?". jin alamar tahowa yasa tayi saurin katse wayar ta maida cikin wandon, Surayya data shigo ta kalle ta sannan tace; "ruwan ki yayi zafi". Batace komai ba ta fice, Surayya ta girgiza kai tana neman shiriya ga ƴar uwar tata dan alamu ya nuna bata jin kira yanzun. ******** ******* Hunayda ta tashi ta ɗora alwala domin yin sallah, Hajna kuwa na saman gado tana kwance. Bayan ta shigo itama Ammi ta shigo, Hunayda dake riƙe da Sallaya tayi saurin saukar da kanta ƙasa. "Ammi na bata haƙuri tun ɗazu", Ammie tayi murmushi tace; "kada ki damu ai ya wuce kinji", Hunayda tayi ajiyar zuciya. "yanzu kiyi sallar sai ki kwanta kuyi barci sai da safe", tana gama faɗin hakan ta fice daga ɗakin. Hunayda ta tada kabbarar sallar isha'i wacce bata yi ba saboda halin da take ciki, tana idarwa ta ɗora da shafa'i sannan tayiwa ƙawarta addu'a akan Allah ya shirye ta. Sai da tayi Addu'a ta shafe jikin ta sannan ta nemi waje ta kwanta, tana me kara neman tsari Allah akan duk wani abinda zai cutar da ita ko ƴar uwar ta. Sai tsakiyar dare sannan ta tashi, sai da tayi murmushi tunawa da Malam Suhayl domin shiya saba mata da tashi wannan lokacin. Haka ta janyo wayar ta cike da hope ta sake dannawa number ɗin shi kira sai dai kamar koda wane lokaci is not reachable. Haka ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi bayi ta ɗoro Alwala tazo ta tada kabbara, raka'o'i guda biyu tayi kamar yadda manzon Allah(S.A.W) ya faɗa; "Idan ɗayan ku ya tashi da daddare to ya buɗe sallar sa da raka'o'i guda biyu sauƙaƙa", Muslim ya ruwaito. Haka ta buɗe Alqur'ani me girma ta fara karantawa cikin natsuwa da fitar sauti me daɗi wanda ke ratsa zuciya da gangar jiki baki ɗaya. Ammie dake ɗakin ta itama tana nata ibadar sai da ta ɗaga hannu ta kuma godiya ga Allah akan shiryartar mata da yarinya da yayi tana me kuma jinjinawa mutanen da suka taimaka wajen faruwar haka. Sai da aka kusan kiran sallar asuba sannan ta tashi ta kawo raka'a ɗaya wato witri tana zaune tana istigfari aka fara kiraye-kirayen sallah dan haka ta miƙe taje ta tada Hajna akan ta tashi sannan ta koma ta tada raka'atanil fajr. Tana idar da sallar asuba ta kuma cigaba da karatunta har zuwa shida sannan ta miƙe ita da Hajna suka fita domin aikin gida wanda har Ammi ta fito itama. Sai da suka gaishe ta sannan Hunayda ta fara ƙoƙarin ɗora ruwa, Hajna kuma ta fara shara suna dai ƙoƙarin taimakawa mahaifiyar tasu. ************ Jameela ta ƙara damƙe hannun Husna tace; "kada ku damu ku shiga ciki wajen Mama yanzu zan shigo nima kunji", babu musu Husna ta rike hannun Musaddiq suka yi cikin gida domin sun san gidan dan suna zuwa da Abban su sannan sun ɗan saba da mahaifiyar Jameelar. Jameela ta kai kallon ta wajen Abdul tace; "gini yayi kyau Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi, komai yayi dai-dai". Rabon da ya samu irin wannan godiyar da addu'ar har ya manta amma yau gashi ya samu a bakin wata wacce ma be kai ga auren ta ba. Cikik farinciki yace; "na gode sosai da sosai, yanzu zuwa nan da sati ɗaya za'a zo saka rana". Jameela tayi murna sosai har farin cikin ta ya kasa ɓoyuwa, haka suka ɗan taɓa fira kan yace ta shiga gida ta turo masa su Husna. Ta amsa da to sannan ta tafi, tana shiga ta tarar dasu suna ta wasa nan ta miƙar dasu, ruwan zafin da Mama ta ɗora shi ta juye domin tayi musu wanka. Ta kuwa rangaɗa musu wanka sannan ta shafe su da mai, ta ɗauko wata doguwar riga wacce ta ɗinka da wani ragowar atamfa ta sakawa Husna, Mussadiq kuma kayan ƙanin ta ta saka mishi yayinda nasu kuma na linke ta saka a leda baƙa ta basu a hannun su. Tana riƙe da hannun su, suka fito yaran sun birge Abdul ganin yadda sika fito tas dasu kamar lokacin da mahaifiyar su take kula dasu. Duk da beyi magana ba amma ya nuna yaji daɗin haka a fuskar shi, Jameela tace; "to gasu ko? Sai anjima idan mun yi waya". "yanzu harda musu wannan aikin, kuma kika wahalar da kanki?", ta langwaɓar da kai tace: "ayya na ɗauka cewa yaran ka yara na ne shiyasa amma idan nayi laifi ayi mini haƙuri". Wai! Lallai wannan ta shirya samun babban matsayi a wajen shi ganin yadda take ƙoƙarin kyautata mishi. "yauwa dan Allah gobe ma ka kawo mini Husna", ya juyar da kai yace; "Allah ya kaimu", ta ɗaga mishi hannu tana godiya a haka har ya bar ƙofar gidan. Koda suka isa gidan Salma na nan a jaɓe tana faman danna waya tana dariya, cikin murna Musaddiq ya nufi inda take. "Mama munje wajen Aunty tayi mana wanka", Salma ta ɗago ta kalle shi sai da zuciyar ta ta buga ganin yadda yaron aka mishi wanka sosai wanda a da baya samu. "wace Aunty kenan? Kuma tare da waye kuka je?", yaron ya kuma cewa; "tare da Abba kuma wajen wannan Auntyn me zu.........", cikin sauri ta daka mishi tsawa tana ture shi daga jikin ta har ya kai ga faɗuwa. Ran Abdul a ɓace yazo ya ɗaga shi sannan ya kalle ta yace; "Bafa tsoron ki nake ji ba dan kinga ina ƙyale ki, wallahi duk rashin mutuncin da zaki yi ya tsaya kaina idan ya haura kan yarana zan ɗauki matakin da baza ki taɓa jin daɗin shi ba". Salma cikin masifa tace; "nayi ɗin kayi duk abinda zaka iya, ko an faɗa maka ina tsoron matakin da zaka ɗauka a kaina ne?, banzan Ragon Namiji kawai". Abdul da zuciyar shi ta kai matuƙar ɓacewa ya ɗaga hannu ya kwashe ta da mari sannan ya nuna ta yace; "haka kika ce ko?, to ki sani ni nake auren ki ba wai ke kike aure na ba", yana gama faɗin haka ya wucewar shi. "to dan ka rabu dani sai me ga maza nan a gari wa'inda suka fika komai da komai, me ake da miji soloɓiyo kalar ka wanda be san haƙƙin matar shi ba *meka taɓa mini a rayuwa?*". Jin wannan kalma ta ƙara fusata shi yayo kanta kamar zai dake ta, sai kuma ya fasa ya juya yayi ficewar sa daga gidan gaba ɗaya ma. Nan Salma ta dinga balbalin masifar ta har ta gaji kamar mahaukaciya tayi ɗakin su Husna kan su ta nufa ta rufe su da duka tana faɗin; "wallahi baƙin cikin uban ku ba zai taɓa kashe ni ba shegu matsiya ta🙊". Habiba data shigo gidan ta girgiza kai yana ƙara kwaɗa sallama, amma ina Salma nacan na masifa bata ma san abinda take yi ba. Sai da duk tayi musu duka sannan ta saka su suka cire kayan dake jikin su ta ɗeba ta watsar. Tana fitowa taga Habiba ƙara haɗe rai tayi tace; "ke kuma baƙar munafika meya kawo ki gidan nan?", Habiba cikin sanyin murya tace; "ai kya bari na zauna sai kiji meya kawo ni ko?". "zama? Ai babu wajen zaman munafikai a cikin gidan nan ki tattara ki bar mini gida tunkan na saka ayi miki rashin mutunci, banza mara zuciya". Habiba tace; "tunda haka kika ce zan fita sannan ina miki fatan shiriya Allah ya shirya ki yasa ki gane gaskiya, dama kaya ne aka samu kalar naku masu shegen kyau shiyasa nace bari in kawo miki". "nace bana so ko ana ciniki dole ne? Mtseww aikin banza aikin wofi kun girma amma baku san kun girma ba, kin kasa riƙe girman ki wallahi anji kunya", jiki babu ƙwari Habiba tace; "Allah ya baki haƙuri zan fita amma ki sani banyi zuciya ba ni jinki nake kamar ƙanwa ta ko nace ƴar dana haifa dan haka duk ranar da kike buƙatar taimako na kina da numberta ki kira ni", tana gama faɗin haka ta fice daga gidan. Tana juyo yadda Salma ke lailayo mata zagi, haka ta fice daga gidan tana kuma ƙara ɗaura ɗamarar taimakon ta dan daga gani rayuwar ta a da ba haka take ba. Im madai Aljanu inma kuma wani ke zuga ta wannan shine tunanin ta. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) said: 'Spend (on charity), O son of Adam, and I shall spend on you.'" [Bukhari (also by Muslim).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ، أُنْفِقْ عَلَيْكَ . ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 19*~ Yau Ƙanin mahaifin Abdul da kuma abokin shi suka je maganar saka rana, babu ɓata lokaci suka tsaida wata ɗaya wato kwana talatin kenan. Salma tana zaune Abdul ɗin ya shigo ko samin arziƙin kallon shi yau bata yi ba domin kuwa wani littafi daya ɗauke mata hankali tsabar batsa ce da maɗigo kawai a ciki. Abdul ya dube ta yadda ta maida hankali akan wayar sai ka ɗauka hanyar shigar ta aljanna ne a ciki. Ya zauna a saman kujera sannan ya dube ta yace; "haba Salma yanzu abin naki ya wuce min sharri ya kai mahalaka, mijin ki ya dawo ace ko kallo be ishe ki ba". Ta ɗan ɗago ta kalle shi cikin yanayin ko in kula sannan tace; "to me kake so nace maka kuma?", ya girgiza kai yana miƙewa tsaye sannan yace; "Allah ya taimake ki ya baki sa'a". Ɗakin su Husna ya shiga abin ban haushi yadda ɗakin yake kaca-kaca komai yana yadda yake tsayin lokaci yana tunanin tun ranar sati daya share ɗakin be kuma ganin shara ba. Ya kalli Husna dake zaune yayin da Musaddiq ke kwance daka gansu ka san yunwa na ɗawainiya dasu, da hannu yayi musu nuni akan su zo, da gudu suka nufo shi ba tare da yace komai ba ya jasu suka fice. Yana tafe yana tunanin halin rayuwar daya faɗa shida yaran shi, lallai duniya abin tsoro ce haka mace bata da tabbas kamar wutar nepa, zata gatan taka yadda sai kaji cewa kai ɗin sarki ne da babu kamar shi ranar data botsare maka a ranar zaka tabbatar da almajirin dake bara a gefen tasha ya fika galihu. A ƙofar gidan yayi parking inda ya buɗe musu suka fice, su kansu yaran sunyi farin ciki domin sun san Auntyn tasu tana kula dasu sosai. Ya ɗan jima a tsaye kafin ta fito daga gidan, yauma dai wankan doguwar riga tayi baƙa tayi wacce taji stones a gaban rigar da hannun rigar, gyale fari tayi rolling dashi wanda ya ƙara ƙawata kwalliyar tata. Tunda ta fito yake kallon ta, a rayuwar shi yana ƙaunar yaga mace tayi wannan shiga, ya sauke ajiyar zuciya a lokacin da muryar ta, ta ratsa dodon kunnen shi yayin yi mishi sallama. Cikin sanyin murya ya amsa, nan suka gaisa cike da mutunta juna, "iyaye na sunzo ɗazu kuma mahaifin ki ya tsaida lokaci nan da wata ɗaya", zoben dake hannun ta take wasa dashi fuskar ta kuma ɗauke da murmushi. "au kunya ta kike ji ne?, lallai ma", da sauri ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta, tana me sakin dariya, hakan ba ƙaramin birge shi tayi ba wanda har yasa shi yin dariyar shima. Jameela kuwa ta langwaɓar da kai, idanun ta a ƙasa sannan tace: "na san dai ba lallai kaci abinci ba dan haka yanzu ka shigo sai kaci tukunna ka tafi", yayi jim yana tunani ya san idan yace yaci abinci a gida yayiwa kanshi ƙarya gaskiya idan kuma yace beci ba ai abin kunya ne ace yana da mata amma kuma beci abinci ba har zuwa wannan lokacin kuma hakan zai zubar da ƙimar matar shi a idanun Jameelar. Jameela tace; "yau dai ina neman alfarmar cin abincin ka anan gidan dan Allah kada kace mini kaci a gida", ya kalle ta bashi take kallo ba amma kuma yadda tayi da fuskar ta sai ta bashi tausayi dan haka yace; "shikenan muje". Ɗakin dake zauren gidan wanda ƙannen Jameelar suke kwana nan ta kaishi dama tuntuni ta shiryawa hakan dan haka ta share ɗakin tass harda ƙamshin turare dake tashi. Tunda ya shiga yaji wani irin farin ciki ya ziyarci ran shi domin kuwa Allah yayi shi da son ƙamshi amma ta dole yanzu ya haƙura domin dai Salma ta dena sa turare a gidan. Kan darduma wacce Jameelar ta shimfiɗa ya zauna, gaban shi ta jere da kololi wanda suke shaƙe da abinci. Daba dan kada yaga zaƙewar ta ba da da kanta zata zuba mishi amma ina bata so tayi abinda zai fahimci cewa kunyar ta ragaggiya ce dan haka dole ta miƙe ta fice daga ɗakin a ranta tana faɗin; "me nake ci na baka na zuba saurin me nake, ai inda jirgin sama yaje kunkuru ma zai je, za'a zo wajen ne idan na sawa kaina haƙuri". Abdul kuwa tana fita ya buɗe kololin wainar shinkafa ce me kyau gashi da zafin ta, ɗayar kular kuwa miya ce ta alayyyaho wacce taji ƙashi ga wani irin ƙamshi da take yi, ɗayar kuma danbun nama ne haɗaɗɗe yaji kayan ƙamshi sosai, sai filet ɗin da aka yanka su abarba da lemo da kankana da dai sauran su, sai jug guda biyu wanda ɗaya ke ɗauke da lafiyayyen kunun aya yaji madara da kayan ƙamshi ɗayan kuma zoɓo ne shima me kyau da ƙamshi, sai gorar swan water guda biyu. Abdul cikin jin daɗi ya buɗe ciki ya kwashi gara, inajin yama manta gidan surukai yake, gani a gefe ko ɗan san mini beyi ba😏. ya gama ci kenan Jameela tayi sallama ta shigo, ya miƙe cikin basarwa yana faɗin; "bari nazo na koma wajen aiki", Jameela tayi murmushi tace; "nagode sosai", be amsa ba ya nufi hanyar fita itama tabi bayan shi. Har ƙofar gida ta raka shi, yasa hannu cikin aljihu ya ciro kuɗi ƴan ɗari biyar-biyar ya miƙa mata yace; "ga kuɗin lallen nan", ta amsa tana faɗin; "na gode sosai",haka suka yi sallama sannan ta koma gida. Husna da musaddiq idan ka gansu ba zaka ce wai ba gidan su bane har sunfi sakewa a nan sama da can gidan nasu. Sai da Jameela ta ƙara shiryawa sannan tace da husna; "Yauwa Husna zo mu tafi ko?", yarinyar wacce ke sanye da doguwar riga ta nufo wajen ta ta kama hannun ta nan suka yiwa Mama sallama suka tafi. Koda suka isa shagon, wajen babba ne sosai don waje ne na manyan mutane da hamshaƙai da suke garin na Kaduna. Sai da suka fara wucewa wajen masu wanke kai aka wanke musu sannan fa suka dawo suka fara bin layin ƴan ƙunshi da kitso, babu jimawa sosai aka zo kansu domin kuwa mutane ne da yawa suke aiki a wajen. Wasu suka kama kan Husna wasu na Jameela, masu lalle ma suka kama nasu aikin cikin ƙanƙanin lokaci aka gama yi musu. Me wajen Hajiya Fatima Batula matar senator na kaduna north, kasancewar akwai sanayya tsakanin ta da Jameelar tace; "yau babu gyaran jiki kenan?". Jameela tayi murmushi tace; "wallahi naso na yi to kuma bana so na daɗe a nan ne domin ina so mu biya kasuwa daga nan sannan zan koma gida nayi girki, amma biki na idan ya matso zan zo ayi mini gyaran jiki na musamman". Hajiya Batula tace; "an saka lokaci kenan?", Jameela tace; "nan da wata ɗaya insha Allahu", Hajiya Batula cike da farin ciki tace; "ah lallai idan ya matso ki kirani ni kuma zan baro Abuja nazo nayi miki gyara na musamman irin wanda nayiwa Her Excellency Hajiya Amina Hassan minister of health". Jameela ta kama baki tace; "wai! Wace ni ina naga kuɗin da zan biya ki har kiyi mini kalar wannan a'a kawai kiyi mini dai-dai kuɗi na". Hajiya Batula tayi dariya tace; "ke dai kada ki damu daya matso kamar saura sati biyu ki kira ni a waya kawai", Jameela tace; "shikenan an gama ranki shi daɗe", zuwa lokacin ya bushe dan akwai sanyin Ac a wajen, wata me aiki a wajen tazo ta wanke musu sannan aka shafa musu muhallabiya nan fa yayi raɗau dashi. Jameela ta kalli Hajiya Batula tace; "gaskiya ina son aikin ma'aikatan ki domin sun ƙware sosai", Hajiya Batula tayi dariya yayin da take zaro ƴan dubu-dubu daga jakar ta ta miƙawa Husna sannan tace; "gashi kya sai Chocolates ko kinzo na shagon ya ƙare gaba ɗaya". Jameela tace; "ai kuwa mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi, sai na kira ɗin na gode", nan suka yi sallama cikin mutunci da girmamawa don Hajiya Batula bata da ɗaukar kai, hakan yasa mutane ke son mu'amala da ita. Sai da suka biya ta kasuwa Jameela tayi siyayyar ta sannan suka wuce gida a lokacin har magrib ta matso. Suna isa gida kayan kawai ta ajiye sannan ta shiga kitchen domin kamawa mahaifiyar tata girkin daren, kowa ya yaba da ƙunshin nasu nan kuwa Jameela ta dinga washe baki tana basu labarin Hajiya Batula. Sai da suka yi sallar Magrib sannan suka zauna cin abinci, suna cikin cin abincin Abdul ya kira ta akan gashi yazo ɗaukar yaran. Jameelar ta fara fita, nan cikin lallami da lallashi ta roƙe shi akan ya shigo yaci abinci tukunna, "kaga daga nan ma sai ka gaishe da Mama", duk yadda yaso kaucewa abu ya gagara hakan yasa ya amince kawai. Yanzu kam Tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya 😋 taji man shanu ga nama zuƙu-zuƙu. Nan fa ya ƙara kwasar garar shi ko kallo na beyi ba😭. Sai da yaci yayi nak ya godewa ubangiji don rabon shi da abinci irin wannan har ya manta, nan Jameela tayi mishi jagora zuwa ciki ya gaishe da Maman. Ya ajiyewa Maman ƴan kuɗaɗe sannan suka fito, Jameela na riƙe da hannun Husna Abdul kuma na riƙe da hannun Musaddiq. Ta buɗewa Husna baya ta shiga sannan ta saka mata ledar dake hannun ta, yana daga cikin mota ita kuma ta tsaya a bakin motar. "na gode sosai na kuma ji daɗi Allah ya kaimu lokacin da zan mallakeki ki zama taqa gaba ɗaya", Jameela tasa hannu ta rufe fuskar ta, tana dariya. Wayar shi ya kunna torch yana faɗin; "Lah haka dama lallen yayi kyau amma baki faɗa mini ba", tayi murmushi tana saukar da kai ƙasa. Oh jameela green snake🤸 Haka yayi sallama da ita cike da nishaɗi da jin daɗi domin kuwa Jameelar tana ƙoƙari wajen ganin ta kyautata mishi tare da yin abinda yake so domin kawai ta sake kama shi a hannun ta, kuma tabbas tana ganin cigaba tunda gashi har yana yaba mata sannan ita kanta ta san ta samu matsayi me girma a zuciyar shi. koda ya isa gida Salma bata falon hakan ya tabbatar mishi da tana ɗakin su kenan, shi da kanshi ya shirya su Husna suka kwanta barci sannan ya musu addu'a ya rufo ɗakin. Da sallama ya shiga ɗakin, tana kwance saman gado tana ɓaɓɓaka dariya sannan kuma tana sauraren Voice wanda ake turo mata. Ko sallamar bata amsa ba shima hakan be wani dame shi ba domin yanzu ya saba da halin matar tashi dan haka dressing mirror kawai ya nufa ya ajiye wayoyin shi da makullan shi sannan ya nufi bayi. Sai da ya gama duk abinda zai yi sannan ya fito, raka'a biyu yayi wato shafa'i kafin yayi shirin kwanciya har lokacin kuma Salmar na kwance tana faman dariya da tura voice da kuma saurara. "ai wallahi yau yanda nake ji na idan Salim be kwana a kaina ba to sai mun raba dare dan yau babu ɗaga ƙafa", maganar da yaji kenan wata tana faɗa wacce har sai da ya ɗan dakata. Salma kuwa bata wani damu ba sai ma fara recording tayi inda take cewa; "ai wallahi shine dai-dai kada ki saurara mishi yayi miki cin da Fu'aid yayiwa Sukainah a *Ni da shi*, ni mkaina dan nasan ba zan samu bane shiyasa sai dai raina kawai ya ɓace amma page ɗin yau yayi wuta wallahi". Abdul sai da dardumar hannun shi ta faɗi tsabar mamaki da al'ajabi cikin fushi da ɓaci rai ya nufi inda take. Salma duk rashin kunyar ta, tana tsoron Abdul dan haka ganin yadda ya nufo ta yasa ta miƙe cikin sauri. Me zai faru? Sai kun cigaba da biyomu kawai domin jin yadda zata wakana tsakanin ma'auratan nan masu son junan su a baya da kula da tattali kafin a samu akasi😥. *** ****** ****** Ummi ke ƙoƙarin kulle gida domin yau suna da taron su na *MUNA WUTA* na Kaduna state wanda ɗumbin marubutan batsa ne kawai a ciki kai harda na maɗigo duka shine suka haɗa ƙungiya wanda ainihin ƙungiyar ta samo asali ne daga jahar Gombe sai Kano, Abuja yanzu kuma ta shigo Kaduna, asalin ta Gombe sun buɗe tane saboda nasiha da kuma jan kunne da akasarin mutane masu karatu, malamai da kuma sauran marubuta suke yi musu akan su ji tsoron Allah su dena, to ganin hakan dan su ƙara bawa mutane haushi shine suka kafa ƙungiya inda duk bayan wata uku sukan samu waje su haɗu, dalilin sa mata sunan *MUNA WUTA* kuwa shine masoyan su dakan fasa musu kai, suke zuzuta su alhalin basu san cewa masoyan nasu suke komawa su zage su ba da yake mahaukata ne su kawai sai suka ɗauka suka ɗorawa kai suna ganin cewa ai hakan shine dai-dai sannan sai kayi haka za'a sanka a duniyar marubuta na Online, wannan shine dalilin samuwar sunan a yayin da ma gani suke wa'inda keyi musu magana hassada ce da baƙin ciki, to wa'innan dalilan sune dalilin saka wannan suna a matsayin sunan ƙungiyar. Wannan shine taro na farko da za'a yi a jahar Kaduna inda kowacce jaha daga cikin sauran jahohin ta turo da wakilanta, Gombe, Kano da Abuja duka. Ummi kam ai ɗauki kwalliya ta gani ta faɗa dan ta jima rabon ta da irin wannan kwaliyyar murna fal ranta domin zata shiga cikin wa'inda suka ɗarata a rashin kunya da rashin mutunci da silar lalata yara, hakan yasa idan kaga fuskar ta sai ka ɗauka albishir akayi mata da kujerar hajji kyauta. Tana fitowa lungu ta haɗu dashi, ɗan dattijo ne dan ya fara tsufa ya ɗan rankwafa ƙasa kaɗan sannan ya gaishe da ita domin kuwa ta kan yi musu ihsani shida ƴan majalisar shi. "Mal Mukhtar ya iyali?", ya amsa da; "lafiya lau Hajiya fatan an fito lafiya?", tayi murmushi tace; "lafiya lau ya akayi ne?". Sai da ya ɗan ƙara gyara tsayuwa sannan yace; "dama wani abu ne naga yana faruwa da ƴar ki shine nace bari na faɗa miki domin kuwa yaran yanzu sai Allah". Ummi ta ɗan ɓata rai sannan tace; "me kenan Mukhtar", ganin ta bashi dama yasa ya ƙara gyara tsayuwa yace; "akan Sahabat ne kusan kullum wani me mota ke zuwa ya ɗauke ta, sannan kuma ya kan dawo da ita kuma ko yau ma ƙannen kawai ta tura makaranta suna tafiya yazo da mota ya ɗauke.........". ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) said: 'Spend (on charity), O son of Adam, and I shall spend on you.'" [Bukhari (also by Muslim).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ، أُنْفِقْ عَلَيْكَ . ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 20*~ Ummi cikin sauri ta ɗaga mishi hannu, cikin masifa tace; "yanzu Malam Mukhtar har yawpn gulmar ka ya tsallake kan mutane ya kawo kan ƴata?, to wallahi ka sani ba zan ɗauka ba domin kuwa ni ban haifi ƴar iska ba ya za'ayi kullum ina ƙoƙarin kyautata muku amma ku kuna ƙoƙarin bin jinina da ƙazafi, to bari kaji idan har hakan ya kuma faruwa sai na ɗauki tsattsauran mataki akan ka", shi dai Malam Mukhtar babu abinda yake yi sai ƙoƙarin bata haƙuri domin ya san ya ɓata damar shi. Ummi ta ja dogon tsaki ta wuce shi tana faɗin; "mutanen yanzu basu tsoron Allah kwata-kwata, wai kai kana da naka laifin amma ka danne na wani kake son hangowa kuma wai ma har da sharri". Haka har ta ƙarasa bakin titi ta tare Napep ta nufi Hall da suke taron, Allah-Allah take yi taje ko zata sami sauƙin abinda ke damun ta. Me keke Napep na sauke ta, ta fara jiyo hayaniyar mutane inda ake shige da fice na jama'a, cikin zumuɗi ta nufi ciki da sauri me Napep ɗin ya fito yabi bayan ta yana kiran ta. Sai da ta ja tsaki sannan ta juyo, yace; "Hajiya kuɗi na", ta kuma jan wani tsakin sannan ta ciro dubu ɗaya ta miƙa mishi ya ciro canjin ta ya miƙa mata sannan ya juya ya tafi yana mamakin me ake a ciki da har ya ɗauke mata hankali, ya ɗaga kafaɗa yana faɗin; "Ina ruwa na mane 🤷". ita kuwa Ummi cikin sauri ta nuna pass get sannan ta shige ciki, waje ne Babba domin babban ɗakin taro ne da ake ji dashi a garin kaduna. An ƙawata wajen sosai ga kujeru nan a jere ga kuma mutane ana ta hada-hada, babu abinda Ummi take banda wurga idanu ta ina zata hango ƙawarta amma sam bata hango ta ba hakan yasa ta fara takawa zuwa ciki. Abinda ya bata mamaki shine jin me riƙe da speaker ɗin tana sanar da isowar ta, inda take cewa; "ga ɗaya daga cikin manyan marubutan da ƙungiyar *Muna wuta* take ji dasu wanda rubutun su har yanzu yana zagaya duniyar internet wato *Hibba* marubuciyar *Ni da shi*", aifa sai ga waje ya ɗauki ihu da tafi. Nan fa Ummi taji wani abu yana flying saman kanta, ji tayi har tafiyar ta sai da ta canza taku. Manya-manyan cikin su haka suka dinga gaisawa da Ummi sannan aka bata wajen zama a saman high table inda daman aka tsara cewa nan ne wajen zaman manyan ƙwarin ƙanana kuma suna ƙasa. Ta kalli gefen ta, sannan tayi dariya tace; "ai ina ta neman ki Afra amma ban ganki ba ashe kina nan sama", matar wacce zasu yi sa'a da Ummin tayi murmushi sannan suka sake gaisawa. Wata ƴar figigiyar mace ita aka kira ta hau saman domin yin jawabi, nan fa ta shiga godiya sannan ta fara sakin zance kamar a club su kuwa sauran babu abinda suke sai dariya da tafa mata. Figigiyar macer tace; "ai mu abin alfaharin mu ne duk wanda zai zage mu sai dai ya karawa kanshi zunubi kuma koyar da yadda ake harka yanzu muka fara, ni nan Asmy ina nan zan rubuta littafi a wannan watan wanda ko miji na ya karanta idan bana kusa sai ya afkawa ƴata 😥". Nan fa waje ya ɗauki sowa ana faman ihu da murna, ta cigaba da cewa; "Kuma ina nan zan rubuta ɗin wa'inda suka fasa zagin nawa ba ƴan halas bane", nan ta ringa kutuntumo ashar su kuma suna jin cewa ai ta kai ƙarshe kawai. Bayan ta gama nata jawabin haka wata wacce daga gani ita ko auren farin ma bata yi ba amma kana jin magan-ganun ta ka san sun wuce shekarun ta. Koda aka zo kan Ummi itama tayi nata jawaban cike da batsa da rashin tarbiya sannan ta ɗora da yi musu albishir ɗin tana gama *Ƙasan Cibiya* zata fara wani sabo wanda yafi wannan kawo wuta. A ƙarshe aka naɗa sababbin shuwagabanni wa'inda zasu wakilci ƙungiyar a nan kaduna inda aka bawa Ummi treasurer. Shugabar da aka naɗa musu me suna Bihal ta miƙe tayi godiya sannan tayi fatan komawar su gida daga nan aka sami zabiya inda take badawa suna amsa mata. *Muna Wutaaa.......*. *Suna binmu da fetur*. *kowa yace bamu ba*. *ɗan hassada ne*. *meye a cikin duniyar?*. *Banda a hole*. *daga duniya sai kaduna*. *in tayi ƙamari Abuja*. *kusa shagalin ku duniya ce*. *Muna wuta suna bin mu da fetur* Haka take faɗa su kuma suna mata amsa mata, sai da suka gama sannan aka ɗauki tafi kafin kuma a fara kacaniyar cin abinci me rai da lafiya ana yi kuma ana gaisawa cike da farin ciki ga waƙa irin ta batsa dake tashi a hankali a hankali gefe masu rawa da shafe-shafen jiki suna ta yi kowa na ƙoƙarin ya gwada iya rashin tashi tarbiyar da kuma ƙwarewar shi a fitsara. Ni dai abin ya ishe ni haka kada na ɗauko abinda yafi ƙarfin kunne na hakan yasa na kwashi slippers ɗina a hannu na sannan na fice amma sai da na ɗauki take away ɗaya na ɓoye a baya na kada su gani su ƙwace😏. A waje na haɗu dasu Aunty Umme inda suke zaman jira na don mu wuce gidan Abdul na Salma da Jameela baban Husna da Mussadiq😂. ******** ********** Salma tayi tsalle ta dire sannan ta kwasa tayi waje da gudu, Abdul na ganin ta fita ya zauna yana dafe kanshi yana kuma faɗin; "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un". Ya jima a zaune gaba ɗaya duniyar yaji tana juya mishi, gani yake gaba ɗaya matan yanzu tsoro suke bashi har Salma ce yanzu zata iya fira a gaban shi irin wannan with confidence🤔 Ina ilimin nata?". Ni kuwa nace; "an rufe border dashi mana😎. Kwata kwata barcin ma kasa yi yayi a daren gashi baya jin zai iya faɗawa wani sirrin gidan shi amma gaskiya yana neman mafita. Wata zuciyar tace mishi; "mafitar kenan ka ƙara aure ko zata yi hankali", ganin hakan ba zai fishe shi ba yasa kawai ya tada kabbarar sallah. Salma kuwa sai da ta jita a ɗakin yaran nata, ta jingi na da jikin ƙofar tasu tana me maida numfashi, lallai yau ta tsorata da mijin nata. Ta jima tana saƙe-saƙe kafin kuma ta nufi kan gadon nasu ta kwanta, sai dai abin ban haushi tana kwanciya taji ƙasa a bayan ta. Wani dogon tsaki taja kafin ta tashi zaune, yanzu dama Abban Husna be share ɗakin nan ba yau ya gyara?", abinda ta faɗa kenan. Dole haka ta tashi ta ɗauko wani zanin ta shinfiɗa a saman sannan ta kwanta, sai a lokacin ta kalli kan yarinyar tata, kitso ta gani ƙanana-ƙanana masu kyau gwanin ban sha'awa ta kai hannu saman kan ta shafa, kitson ba ƙaramin birge ta yayi ba ta kai hancin ta taji yana wani irin ƙamshi me daɗi na mayukan daya sha, hannu tasa ta janyo hannun yarinyar lalle ne gashi nan a saman fatar yarinyar wanda ya tsaru yayi kyau haka ma ƙafar shi kanshi hannun ƙamshin muhallabiya yake yi, Salma ta taɓe baki tana me juyawa. Idanun ta ya sauka kan ledar dake gefe wacce Jameela ta bawa Husnar da zasu taho, kamar ta kwanta sai kuma wata zuciyar tace duba kiga meye a ciki. Da sauri ta tashi ta ɗauko ledar ta buɗe, dogayen riguna masu kyau guda biyu ƴan kanti ɗaya pink da milk ɗayar kuma ɓaki da ash sosai kayan suka yi kyau duka a cikin ledar su, sai riga da wando ƴan kanti guda biyu suma, sai t-shirt da wando jeans kala uku, agoguna guda biyu ƙanana sai babba ɗaya sai kuma takalma dai-dai Husnar ɗaya me ɗan tudu ɗaya flat, na maza kamar ƙafar Musaddiq suma guda biyu masu kyau ɗaya slippers ɗaya cover shoe, sai turare manya guda uku masu ɗan tsada da kuma tarkacen kayan kwalliya. Salma cikin mamaki tace; "waye kuma ya basu wa'innan kayan, wannan dai rigunan da riga da wandon na Husna ne wannan kuma na musaddiq, wa'innan fa?", ta faɗa tana nuna turaruka guda uku da kuma agogo ɗaya. "ABBAN HUSNA",amsar da zuciyar ta ta bata kenan dandanan kuwa taji gaban ta ya faɗi lallai ma wacece wannan kenan. Kenan da gaske wai auren zai yi? Lallai akwai tashin hankali a gidan nan Allah ya kaimu gobe sai ya gaya mini wace tsinanniya ce ta bashi wannan kayan, haka tayi ta zuba surutun ta ita kaɗai. Tayi can tayi nan ji take zuciyar ta na saƙa mata irin rashin mutuncin da zata yi mishi kasa haƙuri tayi dan haka tayi post a group ɗin su wai shi *Matan Manya* Nan fa suka dinga bata shawarwari wanda kusan duk akan kada ta yarda ne. Wata har cewa tayi ta kwashi kayan kawai ta ƙona tun daren nan wata tace mata taje yanzu ta mishi rashin mutunci wata kuma tace ta bari sai da safe. Ita kanta tafi aminta akan ta bari sai da safen kawai dan haka tayi godiya sannan ta kashe datar ta nemi waje ta zauna tana ƙara saƙa yarda zasu kwashe da safe. Har akayi kiran Assalatu idanun ta biyu dan haka bayin su Husnar ta shiga ta ɗoro alwala sannan tazo tayi sallah. Da sallama ya shigo ɗakin ganin ta a tsaye yasa ya juya kawai ba tare da ya ƙaraso ciki ba, ita kuma kuma taja tsaki sannan ta nemi waje ta zauna. Sai da aka idar da sallah a masallatai sannan ta tashi su Husnar suka je suka yi sallah, wayar ta ta janyo ta hau online inda ta ƙara cin karo da shawarwarin ƙawayen nata. Gari yana fara haske ta jiyo motsin mijin nata a kitchen wanda hakan ya tabbatar mata da ya tashi kenan, dan haka cike da ƙarfin gwiwa ta miƙe hannun ta riƙe da kayan ta fito. Har ya fito da kayan karin a hannun shi, kallon kallo suka yi kafin ya ratse ta gaban ta ya wuce. Wannan abin ya ƙara baƙanta ranta dan haka cikin sauri ta dawo gaban shi sannan ta jefar da kayan a ƙasa cikin gadara tace; "waye ya baku wa'innan kayan?". Ya kalle ta cike da mamaki kan yabi kayan da suka zubo daga cikin ledar da kallo, bece mata komai ba sai ajiye kayan karin da yayi ya nufi ɗakin yaran inda ya tarar har sun shirya ya riƙo hannun su suka fito falo nan ya zaunar dasu ya zuba musu abin karin. Ganin yadda yayi banza da ita yasa ta ƙara fusata cikin jin haushi tace; "wai ba tambayar ka nake yi bane, nace waye ya baka wannan kayan?". Be kula ta ba sai kofin da yake cike da kunun daya dama ya ɗauka da nufin kaiwa bakin shi, cikin ingizawar da zuciyar take mata tasa ƙafa ta bige kofin wanda kofin be sauka ko'ina ba sai fuskar Musaddiq kasancewar yana gefen Abdul ɗin ne, yaron ya tsandara ihu. Abdul yayi kanshi da sauri, kunun ya ɓata fuskar yaron sosai ga kuma shi kunun da zafi ga kofin irin mug ɗin nan ne, wani irin abu ya haɗiya sannan ya kalli Husna yace; "jeki bayi ki wanke mishi, daga nan ki shiga ɗakin ku ki kwantar dashi sannan kema ki zauna a ɗakin", yarinyar ta amsa da "to Abba", ta ja hannun Musaddiq ɗin suka wuce. Abdul yana ɗagowa ya kwashe Salma da mari dama da hagu, ta saka hannu ta dafe kuncin ta cikin masifa tace; "ni ka mara to wallahi sai na rama banza mugu azzalumi lusari kawai, wallahi sai na ram.....", bata rufe baki ba ya kuma ɗauke ta da wani marin. Jijiyoyin kanshi sun fito ruɗu-ruɗu tsabar ɓacin rai, cikin haɗuwar numfashi yace; "shege ka fasa in kin fasa ramawa", aikuwa Salma na jin hakan tayi kukan kura tayi kanshi shi kuwa ya saka mata ƙafa ji kake timmm a ƙasa. Ta bugu sosai hakan yasa ta miƙe da ƙyar, cike da gajiya da halinta Abdul yace; "wallahi idan baki bar wannan hanyar da kika ɗauko ba kina tattare da wahala,banza wacce bata san inda yake mata ciwo ba, kina so ki san inda muka je har aka bada kaya ne ko, to ba wani waje bane face wajen matar da zan aura nan da wata ɗaya ke kuma sai ki zauna ki cigaba da mugun halin da kika ɗauko", yana gama faɗin hakan ya shige ɗakin su Husna ya barta a tsaye kamar wacce aka shuka. Cikin jin haushi tace; "au haka kace to wallahi sai na tada hankalin ka a gidan nan, sai dai kowa ya rasa nasa farin ciki, babu wacce ta isa ta shigo gidan za kuma ka gani". Kamar mahaukaciya haka ta janyo wayar ta, number ɗin Jameela ta nemo ta danna kiran ta, koda ta ɗaga cikin kuka take sanar da ita abinda ya faru. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [3/9, 9:36 AM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) says: 'Fasting is Mine and it is I Who give reward for it. [A man] gives up his sexual passion, his food and his drink for My sake.' Fasting is like a shield, and he who fasts has two joys: a joy when he breaks his fast and a joy when he meets his Lord. The change in the breath of the mouth of him who fasts is better in Allah's estimation than the smell of musk." [Bukhari (also by Muslim, Malik, at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: الصَّوْمُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي، وَالصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَلِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ، وَفَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ. رواه البخاري (وكذلك مسلم ومالك والترمذي النسائي وابن ماجه) ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 21*~ Abdul kuwa ɗakin su Husna kawai ya shiga, a tsaitsaye ya same su sai zare idanu suke yi, ba tare da yabi ta kansu ba ya ɗauki jakar kowanne ya rataya mishi sannan ya riƙe hannun su suka fice daga gidan. Salma kuwa ɗaki ta wuce tana kuka tana sanar da Jameela, ita kuwa Jameela babu abinda take yi in banda murmushi ganin tarkon data ɗana ya yi babban kamu, Salma na gamawa Jameela ta zunduma ashar sannan tace; "kika yarda har ya dake ki, to wallahi yana dawo wa kici kwalar sa", Salma tace; "ni ai da gida kawai zan tafi". Cikin sauri Jameela tace; "a'a ba za'a yi haka ba, kada ki sake ki bari yaci ki a yaƙi ai an daina wannan yayin kin san mutane me zasu ce sannan can gidan idan kinje ba zasu goyi bayan ki ba", Salma jiki a sanyaye tace; "hakane kuma to ke yaushe zaki zo". Jameela tace; "zan zo amma da wata babbar magana zan zo insha Allahu", Salma tace; "shikenan ina nan ina jiran ki Allah ya kawo ki, kin san jiya anyi taron *Muna Wuta* na Kaduna state?". Salma ta ɗan taɓe baki tace; "naga ana ta magana a whatsapp dana hau jiya da daddare", Jameela ta ɗora da cewa; "aikuwa abu ya ƙayatar an bawa Hibba ma kambu na girmamawa". Salma tace; "ai ta cancanta domin yarinyar akwai bada wuta wallahi, amma ni yanzu ba wannan bane damuwa ta damuwa ta shine yadda Abban Husna zai fasa wannan auren". Jameela taja tsaki tace; "to ki zauna baƙin cikin ɗa namiji ya kashe shi, kinji zan turo miki da video clip din ki kalla", Salma tace; "shikenan ina jira", a haka suka yi sallama. Salma ta faɗa saman gadon tana me ajiyar zuciya, babu batun wanka ko wanke-wanke balle gyara inda ta ɓata, ta shafa cikin ta jin yana kukan yunwa, cikin sauri ta tashi ta fice, tana shiga kitchen ta hau buɗe-buɗe ta kuwa tarar da Abdul ɗin ya rage mata nata abin karin haka ta juyo kunun ta kuma kwashe ragowar doya da ƙwan daya bari a food flask. Bedroom ta shige a tsakiyar kan gado anan ta ajiye abin karin nata ta kuma janyo waya ta buɗe data ta hau whatsapp tana karyawa tana chating. Ganin Jameela ta turo mata da wannan video clip ɗin yasa ta buɗe ta hau kalla, yadda aka yi abin ba ƙaramin birge ta yayi ba, garin murna harta zunguri kofin kunun ya kife a nan saman gadon. Ta kalle shi sai kuma taja tsaki, da hannu ta ɗauka ta cilla shi ƙasa sannan ta cigaba da abinda take yi ba tare da ta damu ba, tana kallo tana jin ina ma itace a wajen, nan fa ta turawa group ɗin su na *Manyan Mata* da kuma *MU HAƊU A SAMAN GADO* ai fa nan aka fara fira akai wa'inda basu gani ba suka kalla suna nasu sharhin yayin da wa'inda suka kalla suke ƙara yi musu sharhi akai. Salma dai a nan ta wuni babu abinda yake tada ta sai cikin ta idan kuma ta ci to nan zata dawo ta kwanta, tana me cigaba da latsa wayar. Ƙarfe uku Abdul ya kwaso yara daga makaranta, gidan ya nufo amma gaba ɗaya bashi da walwala dan be san me zai zo ya tarar ba gashi a office an dawo da yi mishi warning akan yadda yanzu aikin shi yayi ƙasa sosai. Su kansu yaran idan ka kalle su babu wani kuzari a tattate dasu, ba wai rashin cin abinci bane domin sai da suka biya gidan wata yayar Abdul ɗin suka ci abinci sannan suka wuto gidan. Da sallama suka shiga amma babu wanda ya amsa hakan yasa suka kutsa kai ciki, Abdul yabi falon da kallo cike da baƙin ciki yadda ya bar komai haka ya dawo ya same shi har kunun daya zube ya bushe ga ƙuda duk sun gama bin wajen, abincin da basu ci ba kuwa yana nan a yadda yake kuma dan wulaƙanci a buɗe yake. Ya kalli yaran sannan yace; "ku wuce ɗakin ku", shi kuma ya wuce nata ɗakin, yana shiga yaci karo da kofin data cillo tun safe, ya kalli kofin sannan ya kalle ta. Cikin jin haushi ya daɗa mata duka a gadon baya, Salma dake faman ƙalƙala dariya babu ɓata lokaci dariyar ta koma, fuska ta dago taga waye ishashshe da mai wanda har ya kai ya dake ta. "lallai ma wuyan ka ya isa yanka, ni kake duka Abdulkareem to wallahi ka sani ni ba baiwar ka bace kuma ka duki auren kane". "in dai dan wannan irin rayuwar auren ce sai me dan na daki aure na Salma, wallahi kin bani mamaki kuma kin yiwa kanki, yanzu dan rashin mutunci sai ki kasa kwashe kayan da kika ɓata a falo, nan ma kuma kin lalata amma baki san ki gyara ba to wallahi wannan abubuwan naki ya fara isa ta dan haka ko dai ki gyara ko kuma na ɗauki mummunan mataki akan ki banza shashasha kawai", yana gama faɗin haka ya fice a ɗakin. Ɗakin su Husna yaje inda ya tarar dasu sun gama shiryawa zuwa islamiyya, dan haka ya jasu kawai suka fice daga gidan gaba ɗaya. Salma kuwa babu abinda ya dame ta banda alwashi da take ci akan mijin nata na yadda zata ɗauki fansa akan abinda yayi mata don bata jin zata iya ƙyale shi. ********* *********** Sahabat tana gama girki ta wuce ɗaki, kwanciya tayi kawai tare da jan tsaki, yau saura kwana biyu ƙaryar da ta yiwa Ummi ya ƙare domin kuwa an kusa gama rehersal ɗin masu tafiya musabaƙar da tayi ƙarya dasu. Ta ɗaga kai ta kalli agogo ko ina Ummi ta tafi yau oho?", kayan ta ta tuɓe ta ɗauki haɗin sabulun da take wanka dashi me gyara fata da ƙamshi ta fice domin yin wanka. Ta kai minti talatin a bayin tana wanke jikin ta sannan ta gama ta fito, ta tsane soson ta shanya a sama tana ƙoƙarin shiga ɗaki Ummi tayi sallama ta shigo ita da tawagar mutanen da suka rako ta. Duka idanun su na kan Sahabat kasancewar towel ɗin jikin ta ɗan ƙarami ne ko gwiwa be ƙarasa ba ga kuma sirrin kyau da take ƙara yi wanda duk aikin gyarawa Zaiyad din ta da take yi. Tana gama yi musu sannu da zuwa ta wuce ɗaki, Matar da idanun ta kamar ya faɗo tayi saurin lashe leɓen ta tana faɗin; "masha Allah". Ummi kuwa abinda Malam Mukhtar ya faɗa mata ne ya faɗo mata a rai ganin yadda yarinyar tata take ƙara cika da kyau. Amma koma meye zata ƙara sawa Sahabat ɗin idanu don ganin meke faruwa duk da ta yarda da tarbiyar data bawa ƴar tata. Ummi ta kalli tawagar tata tace; "to na gode da wannan rakoni da kuka yi, yanzu sai ƙarshen sati insha Allahu idan mun haɗu a meeting". Matar nan ta kalli Ummi tace; "wai ni Hibba waccen yarinyar fa ƴar ki ce", Ummi ta washe baki tace; "eh Shukra ƴa tace Sahabat kenan itace babba", Shukra ta kuma lashe baki sannan tace; "aikuwa dai yarinyar masha Allah, ga wannan a bata ta siya ƴan kayan make up", Ummi ta washe baki domin kuwa Shukra irin matan mayace mijin ta babban soja ne sai dai be cika zama a gari ba hakan yasa ta faɗa harkar banza wato mace tabi mace daga baya kuma ta shiga harkar rubutu inda take bada tata gudummawar wajen ganin ta ɓata yaran jama'a. Shukra nada masoya sosai domin littafin ta har ya fi na Ummi rashin mutunci dan yanzun ma itama ambata awward sannan kuma an bata muƙami itace chairwomen na ƙungiyar gabaki ɗaya, ta kan yi amfani da masoyan ta masu biyota gida domin su ganta, to anan ne idan taga wacce tayi mata ta kan kashe ko dubu nawa ne dan ganin ta mallaki yarinyar, ita da wacce aka bawa shugabar ƙungiyar gaba ki ɗaya wato *Hapcy* tafiyar su ɗaya kusan ma aminai ne sannan wajen wannan harkar ma tare suke yi. Kuma Shukra duk wacce ta gani take muradi tofa sai ta same ta kota halin ƙaƙa ne kuma duk ustazanci da kamewar yarinyar, ainihin sunan ta shine Kareema Hassan laɗɗo, ainihinta ƴar garin Adamawa ce, saboda haka kyakkyawa ce sosai kuma ba wata me ƙiba bace a girme Ummi zata ɗarar mata domin ita Shukra ɗanta ɗaya ne kuma yana can ƙasar waje yana karatu. Yau tunda ta ɗora idanun ta akan Sahabat taji yarinyar ta gama birge ta tana kuma muradin kasancewa tare da ita dan haka dole wannan labari yaje kunnen Hapcy domin su san yadda zasu yi. Ummi ta ƙwalawa Sahabat kira, jin hakan yasa Shukra kafawa ƙofar ɗakin su Sahabat ɗin idanu tana fatan fitowar ta domin ta ƙara samin damar ganin yarinyar. Sahabat ɗin ce ta fito cikin sauri jikin ta sanye da wando jeans kalar blue da kuma riga pink sai ta ɗora top fara a sama, wani irin jan numfashi Shukra tayi domin ji tayi kamar ta janyo ta ta rungume haka take ji. Ummi tace; "ga kyauta daga Hajiya Kareema" Ummi ta ƙarasa tana nuna mata Shukrar, Sahabat ɗin ta kalli Shukra tayi murmushi sannan tace; "nagode sosai". Shukra ta janyo ta ta rungume tana faɗin; "kada ki damu ai kin wuce haka a wajena", Ummi kuwa murna fal ranta ganin ƴar tata ta sami shiga wajen manyan mutane kamar Shukra, ita kuwa shukra haɗuwar jikin nasu yasa gaba ɗaya wutar kanta ta ɗauke dan haka ta ɗan shafa bayan Sahabat ɗin. Sahabat kuwa jin sabon abu wai harda wani runguma cikin sauri ta janye jikin ta, Shukra ta ƙara faɗin; "ina wayarki in saka miki number ta duk abinda kike buƙata ki kirani kawai kada ki biye Ummin ki". Ummi tayi saurin tarar numfashin Shukra wajen faɗin; "ai bata da waya ni bana bari suna riƙe waya ba yanzu ba". Shukra tace; "abin mamaki yarinya kamar wannan ace bata da waya a hannu gaskiya akwai abin mamaki, amma hakan yayi kyau to shikenan abinda za'ayi shine zan dinga neman ki data mahaifiyar ki, kinji". Sahabat ta daga kai kawai cike da mamakin irin kallon da Hajiya Kareemar take binta dashi, sai da Ummi ta gama godiyar ta sannan suka yi sallama. Shukra ta kalli Sahabat ta marairaice fuska tana faɗin; "haba Beauty babu rako?", Sahabat ta kalli Ummi, Ummi ta mata nuni da taje kawai domin ita har ranta ta yarda da Shukrar. Sahabat tabi Shukrar a baya har zuwa waje, Shukra dama ita kaɗai ya rage bata tafi ba itama kuma Sahabat ɗin ce ta hanata tafiya. Ta riƙo hannun Sahabat ɗin tace; "dan Allah kada ki ji nauyi na ki ɗauke ni kamar ƙawarki kinji, zan dinga jin lafiyar ki wajen Ummin ki sannan zan dinga kiranki a wayar ta ki saki jikin ki dani kinji". Sahabat ta ɗaga mata kai, Shukra ta shafa fuskar Sahabat ɗin sannan tace; "dat's my girl", daga haka tace; "zan tafi amma bada jimawa ba zan dawo saboda ke kinji, take care", ta karasa tana me bawa Sahabat ɗin peck a kumatu. Sahabat kuwa tama kasa motsi ganin abin yafi ƙarfin ta, Shukra kuwa motar ta ta shiga ta ɗagawa Sahabat ɗin hannu sannan taja motar ta tafi. Sahabat kuwa ganin Shukrar ta bace yasa taja tsaki tana faɗin; "karuwar banza kawai", daga haka ta juya zuwa gida. A falo ta sami Ummi sai faman irga kyaututtuka da kuma kuɗaɗen data samu take yi, Sahabat ta zauna kusa da ita sannan ta ajiye mata kuɗin da Shukra ta bata . Ummi ta kalle ta tace; "har ta tafi kenan", Sahabat ta amsa da; "eh, ta tafi", Ummi tace; "Allah sarki Hajiya Kareema". Kuɗin ta ɗauka ta kuma miƙawa Sahabat ɗin sannan tace; "gashi nan ki riƙe gobe sai kuje kasuwa keda Surayya ki siyo abinda kike so", Sahabat ta amsa da; "to". Tana shiga ɗaki ta ciro wayar ta, abin mamaki shine da har yanzu Zaiyad be kira ta ba, ta san dai a duk lokacin da ya ajiye ta ƙofar makarantar su to ya kan kira yaji yaya taje gida amma kuma yau shiru kome ya faru kuma oho?. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [3/12, 8:32 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: "Allah (mighty and sublime be He) says: 'The first of his actions for which a servant of Allah will be held accountable on the Day of Resurrection will be his prayers.' If they are in order, then he will have prospered and succeeded; and if they are wanting, then he will have failed and lost. If there is something defective in his obligatory prayers, the Lord (glorified and exalted be He) will say: 'See if My servant has any supererogatory prayers with which may be completed that which was defective in his obligatory prayers.' Then the rest of his actions will be judged in like fashion." [At-Tirmidhi (also by Abu Dawud, an-Nasa'i, Ibn Majah and Ahmad).] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ عَمَلِهِ صَلَاتُهُ. فَإِنْ صَلُحَتْ فَقَدْ أَفْلَحَ وَأَنْجَحَ، وَإِنْ فَسَدَتْ فَقَدْ خَابَ وَخَسِرَ، فَإِنْ انْتَقَصَ مِنْ فَرِيضَتِهِ شَيْءٌ، قَالَ الرَّبُّ عَزَّ وَجَلَّ: انْظُرُوا هَلْ لِعَبْدِي مِنْ تَطَوُّعٍ فَيُكَمَّلَ بِهَا مَا انْتَقَصَ مِنْ الْفَرِيضَةِ، ثُمَّ يَكُونُ سَائِرُ عَمَلِهِ عَلَى ذَلِكَ. رواه الترمذي وكذلك أبو داود والنسائي وابن ماجه وأحمد ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 22*~ Koda daddare da Abdulkareem ya dawo be shiga inda take ba, itama kuma bata wani damu ba amma tana nan ta ƙudurci aniyar sai ta rama. Sai da ya yiwa su Husna addu'a suka kwanta sannan ya dawo falon ya kawar da duk kayan dake wajen tun na safe sannan ya share ɗakin ya kwanta saman doguwar kujera. Wajen sha biyu amma Salma taji Abdulkareem shiru be shigo ba, tashi tayi ta fito falo kamar ance ta kalli saman kujera ta hango shi kwance yana barci. "lallai ma wannan ya raina mini hankali, ni ina can ina jiran shi na shuka mishi rashin mutunci ashe yana nan yana barci abin shi to wallahi duk da haka baka tsira ba", abinda Salmar ta faɗa kenan. Ƙofa ta buɗe ta fita, wajen tankin gidan ta nufa, ta tara ruwa a cikin bokiti sai da ya kusa ciki sannnan ta ɗauko ta nufi ciki dashi babu wani dogon tunani ko wani abin ta ɗaga ta watsa mishi a jiki. Abdulkareem ya miƙe cikin sauri yana jan salati, ganin Salma a tsaye ga bokiti a hannun ta ya ƙara bashi mamaki. Salma cikin tsiwa tace; "wallahi baka isa ba, maza ka tashi ka bar mini kujera tunda naga Ubana ya siya mini ita ba wani ƙato ba". Abdulkareem kuwa ya rasa me ma zai ce tsabar mamaki da tsoro, domin yanzu kam Salma tsoro take bashi, ba tare da yace mata komai ba ya nufi hanyar bedroom. Da gudu tazo ta hankaɗe shi ta shige ciki ta murza key, bema ɓata lokaci wajen bugawa ba haka ya tsaya a wajen cike da takaici yana kuma mamakin halin Salmar. Dole ya kwana ɗa kaya jiƙaƙƙu, ga kuma ɓacin rai dake damun shi, koda asuba dan mugunta bata buɗe ƙofar ba zuwa safiya kayan ya bushe hakan yasa ya wuce kitchen kawai ya haɗa musu abin kari. Kafin ma Salma ta farka daga barci ya gama abin karin sun karya sun fice dan haka basu haɗu ba, koda ta tashi tayi sallah sannan ta fito domin neman abinda zata ci. Komai na kitchen ɗin a wanke a goge kuma a share babu inda bata duba ba amma bata sami abinci ba hakan ya bata haushi. "wato yau bema girka abincin dani ba kenan? Aikuwa wallahi zai dawo ya same ni a cikin gidan nan", haka tayi ta mitar ta sannan ta buɗe kwalin indomie ta ɗauko guda biyu ta dafa sannan ta soya ƙwai ta ɗora a sama. Allah ya taimake ta cikin flask akwai ragowar ruwan zafi shi ta zuye ta haɗa tea sannan taje falo ta zauna ta hau karyawa. Abin mamakin ma tana gamawa ta tashi ta bar kwanukan a nan ta koma uwar ɗaka, tana me cigaba da karanta sabon littafin *Hapcy* wanda take yi wai shi *Ƙasan cibiya* sosai littafin yake kawo light. Tana gamawa ta ɗora dana *Hibba* wato *Saman gado* inda gaba ɗaya littattafan suke tafiya da imanin ta, ga wata irin sha'awa dake taso mata. Kwanciya tayi lamo tana tunanin ina zata sami biyan buƙatar ta, ganin babu sarki sai Allah yasa tayi shawarar idan mijin ta ya dawo zata je ta bashi haƙuri ya biya mata buƙata. Aikuwa cikin sauri ta hau gyaran gida, kan kace me komai ya zauna a muhallin shi, tana gamawa ta ɗora girki me rai da lafiya sannan ta tsantsara kwalliya tana jira Abdulkareem ɗin ya dawo. 🤣To ga Salma fa yau ana jiran oga me awa ɗaya shin ya zata kaya?? Ni dai bari nayi gidan su *Sahabat*🤣🤣🤣. ****** ******** Tana kwance saman ƙirjin shi yayin da shi kuma yake rungume da ita kai zaka ɗauka wasu shahararrun masoya juna ne kuma ma'aurata. Saha ta shafa fuskar shi tace; "zanyi kewarka gaskiya, yanzu da muka saba da juna sai nake gani kamar ba zamu sake haduwa ba". "ai ni wannan rabuwar tamu daɗin ta zanji ko babu komai zan samu damar kawo Zeezee cikin gidan nan babu shayin komai",abinda Zaiyad ɗin ya faɗa kenan a cikin ranshi. Amma a fili kuwa cewa yayi; "kada ki damu My Habat ai zamu dinga haɗuwa idan kin fito makaranta". Saha tace; "eh hakane amma ni nafi sabawa da mu wuni tare", Zaiyad ya saki murmushi sannan yace; "kada ki damu My Habat nan bada jimawa ba zaki zamo tawa har abada". Cikin farin ciki tace; "hakane kuma Allah ya kaimu lokacin yanzu bari na tashi na tafi", ba tare da damuwa ba ya ɗauko dubu shida ya miƙo mata yace; "ki ɗauki drop". Cikin sanyin jiki Sahabat tace; "Sweetheart yau ba zaka kaini bane?", ya gyara kwanciya sannan yace; "am sorry kaina ke ciwo", Saha tace; "to Allah ya sauwaƙe",daga haka ta tattara nata ya nata ta bar gidan. Zaiyad na ganin ta tafi ya kira Zee ya shaida mata gobe insha Allahu suna tare tun safe har zuwa yamma. Sahabat kuwa Keke ta ɗauka drop har bakin makarantar su, nan ta sallami me Keken sannan ta tsaya jikin wani shago har aka sako ɗaliban sannan ta shige cikin su. Kamar yadda ta saba a bakin get suka haɗu dasu Suraiya domin gargaɗin da tayi musu akan su dena zuwa ajin su neman ta gudun tonuwar asirin ta. Ta riƙo hannun su har gida suna tafe suna fira duk da dai Suraiya nada tambayar da take so ta yiwa ƴar uwar tata amma tana tsoron abinda zai biyo baya hakan yasa taja baki tayi shiru kawai. Suna shiga gidan suka tarar da Ummi tana faman amsa waya na masoyan ta akan sabon littafin data fara, tana ganin su Sahabat ɗin tayi saurin katse wayar. Sahar ta taɓe baki tana faɗin; "aikin banza bayan na riga da na san kina yi kuma har comment nayi miki a group ɗin ki har kuma kin amsa mini", Ummi tace; "me kika ce?", Sahabat tace; "cewa nayi sannu da gida Ummi na". Ummi ta washe baki tana faɗin; "yauwa sannun ku ƴaƴan albarka, kuje ku cire hijab ɗin Saha kizo ki share tsakar gida, Suraiya ke kuma ki kwashe abincin can a cikin cooler tana gamaa faɗin hakan ta cigaba da danna wayar tata. Sahabat taja tsaki ƙasa-ƙasa tana guna-guni haka dole ta cire hijab ɗin taje ta hau shara tana gamawa ta ɗoro alwala taje tayi sallah, koda ta idar sai da ta duba wayar ta amma babu kiran Zaiyad. Jin Ummi na ƙwala mata kira yasa ta maida wayar jikin ta, ta fice zuwan amsa kiran Ummi ɗin. "Ummi gani", Sahabat ta faɗa lokacin data ƙarasa kusa da mahaifiyar tata, Ummi ta miƙo mata wayar tata tana faɗin; "ga Hajiya Kareema na son magana dake". Sahabat cikin ranta tace; "ga dai me shafe mutane kawai zaki ce", ta amsa ta kara a kunnen nata, bayan tayi sallama. Shukra tayi wata ajiyar zuciya jin muryar Sahabat ɗin take yi har cikin ranta, ta amsa itama cikin salon tata muryar. Sahabat cikin ladabi ta gaishe da ita yayin da Shukra ke jin kamar ta janyo ta jikin ta har wani ƙara maƙale wayar take yi. "Beauty shine ko nema na bakya yi ko ni in nan duk kewar ki ta dame ni", Sahabat taji wani irin bambaraƙwai wai namiji da suna Salamatu 🤣🤣🤣🤣. Uhum", shine abinda Sahar ta iya faɗa kawai, Shukra cikin salo ta kuma cewa; "to naji yanzu yaushe zaki zo", Sahabat tace; "Ummi bata bari na fita". Shukra tayi ɗan jimm sannan tace; "zan tambayi Ummin taki da kaina, yanzu faɗa mini me kike buƙata", Saha tace; "babu komai". Cikin shagwaɓa Shukra tace; "a'a ni dai ban yarda ba ki faɗa mini me kike so", Sahar bata san lokacin da tace; "Fura da nono", Shukra tace; "an gama zaki zo ki tarar da fura kuwa, bawa Ummin ki waya". Saha ta miƙawa Ummin nata wayar, tana jin lokacin da Ummi ke cewa; "Allah ya kaimu goben da rai da lafiya", nan Sahar ta tafi ta bar su inda suka juya akalar firar zuwa ga litttattafan nasu, kowa na yaba aikin kowa". Saha kuwa koda tazo kwanciya babu kiran Zaiyad ba alamar shi, koda ta kira shi user busy abin ya bata mamaki sosai. Data ta buɗe inda ta duba taga tun shekaranjiya be hau ba, to kodai har yanzu kan nashi beyi sauƙi bane. Group ɗin su Ummi ta shiga inda ta tarar Ummin tana ta yi musu lecture akan zaman aure da yadda ake kwanciyar aure, Saha ta taɓe baki sannan tace; "mata dai babu hankali wai macer da bata da aure ita zata koya muku yadda zaku zauna da mijin ku lafiya", su kuwa sai faman godiya suke mata. Nan ta kuma wani group wai shi *Kaduna Chicks", babu abinda suke yi sai batsa, kowacce tana turo hoton ta tsirara ko video ɗin ta. Shiru tayi har zuwa lokacin da Admin yazo ya fara zubo musu Bluefilm nan fa Sahar jiki na rawa ta hau saukewa sai da ta gama sannan ta fita a group ɗin, Zaiyad ta kuma dubawa amma har lokacin baya online, ta kashe data sannan ta kunna wa'innan Videos ɗin tana kalla yayin da gefe ɗaya kuma take ƙoƙarin gamsar da kanta. Ba ita ta sami natsuwa ba sai wajen ɗaya, sannan ta miƙe zaune tana tunanin yadda zata zuba ruwa a jikin ta a yanzu, haka dole ta tashi ta fice. Cikin sanɗa ta hau jan ruwa sai dai bata san Ummin nata tana kallon ta ba, sai da ta shige bayi sannan Ummi ta fito tana mamakin me zai jawa Saha ɗin wanka yanzu. Sahar kuwa tana gama wankan ta fito, tana daf da shiga ɗaki taga Ummi a tsaye saura kaɗan ta faɗi ƙasa tsabar tsoron da taji. Ummi tace; "ke kam meya kaiki wanka yanzu?", Sahar tace; "Ummi zafi nake ji ne shiyasa", Ummi tayi shiru kamar me nazari sannan tace; "shikenan shiga kije ki kwanta", tun kan Ummi ta ƙarasa har Saha ta shige ɗaki ta rufo. Ummi ta jinjina kai sannan tace; "lallai dole na kuma zage damtse wajen saka idanu akan ki Sahabat domin na fara zargin ki nima". Saha kuwa bayan ta rufe ƙofa sai da ta tsaya ta maida numfashi sannan ta nufi kan katifar tasu ta kwanta dan ko kaya bata tsaya sakawa ba. Washe gari da safe, Saha ta lura da yadda Ummi ta dinga binta da kallo hakan yasa duk ta tsargi kanta, ganin bata da mafita yasa ta basar. Wajen sha ɗaya ta shirya domin zuwa gidan Shukra, Ummi tace; "kada ki kai yamma ki dawo da wuri sannan ki kula, Allah ya kiyaye hanya", Saha ta amsa da ameen tana me ficewa. Sai da tayi tafiya me ɗan nisa sannan ta iso bakin titi, zuciyar ta ke bata shawara ta fara zuwa ta dubo Zaiyad kan ta wuce hakan yasa kawai ta ɗauki drop na Keke Napep inda ta nufi gidan shi dake Badarawa. addu'ar ta Allah yasa yana nan sai dai ganin motar shi yasa ta fahimci yana nan ɗin kenan, Allah sarki! Wataƙila kan ne ke damun shi. Ta daɗe tana ƙwankwasa amma ba'a buɗe ba har zata juya sai kuma ta tura ƙofar aikuwa ta buɗe dan haka ta tura kai ta shiga dan bata zargin komai akan Zaiyad ɗin. Zaiyad kuwa na can shida Zee ɗin shi suna soyewa wannan dalilin yasa beji ƙwanƙwasa ƙofar da Sahabat take yi ba. Sahabat ta nemi kujera ta zauna sannan ta fara ƙoƙarin kiran Zaiyad ɗin, ba'a yi picking ɓa amma tana jiyo ƙarar wayar daga ciki hakan ya bata tunanin wata ƙila ciwon kan ne yayi tsanani da ba zai iya tashi ba. Babu wani shakka ko ɗar ta nufi bedroom ɗin, daf da zata shiga ta ɗan buge ɗan canter ɗin da aka ajiye flower vase hakan yasa hoton dake gefe da kuma flower ɗin ta faɗo. Cikin sauri Saha ɗin ta tsugunna ta ɗauko Allah yasa ta roba ce dan haka cikin sauri ta maida ita inda take tare da ɗan ƙaramin hoton Zaiyad ɗin. Cikin sauri ta nufi ciki tana faɗin; "Sweetheart, ba dai jikin bane ko", ta ƙarasa faɗa tare da ƙoƙarin tura ƙofar bedroom ɗin. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [3/15, 9:08 AM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say: "The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path [un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire." [Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: إِنَّ أَوَّلَ النَّاسِ يُقْضَى يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَيْهِ رَجُلٌ اسْتُشْهِدَ، فَأُتِيَ بِهِ فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ قَاتَلْتُ فِيكَ حَتَّى اسْتُشْهِدْتُ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ قَاتَلْتَ لِأَنْ يُقَالَ: جَرِيءٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ تَعَلَّمَ الْعِلْمَ وَعَلَّمَهُ وَقَرَأَ الْقُرْآنَ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: تَعَلَّمْتُ الْعِلْمَ وَعَلَّمْتُهُ، وَقَرَأْتُ فِيكَ الْقُرْآنَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ تَعَلَّمْتَ الْعِلْمَ لِيُقَالَ: عَالِمٌ، وَقَرَأْتَ الْقُرْآنَ لِيُقَالَ: هُوَ قَارِئٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ، فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ وَسَّعَ اللَّهُ عَلَيْهِ، وَأَعْطَاهُ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ كُلِّهِ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: مَا تَرَكْتُ مِنْ سَبِيلٍ تُحِبُّ أَنْ يُنْفَقَ فِيهَا إِلَّا أَنْفَقْتُ فِيهَا لَكَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ فَعَلْتَ لِيُقَالَ: هُوَ جَوَادٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ، ثُمَّ أُلْقِيَ فِي النَّارِ. رواه مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي) ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 23*~ Tana tura ƙofar Zaiyad na turowa dan haka a wajen suka ci karo, cikin sauri ya rungume ta haka da dabara ya ja ta zuwa falo. Yana zama ta zauna saman ƙafar shi sannan ta shafo fuskar shi tace; "nayi kewar ka Sweetheart sosai", ya riƙo hannun ta sannan yace; "nima nayi kewar ki sosai, yanzu sai ina dan na san akwai insa zaki je". Sahabat tace; "zan je Unguwar Rimi ne wajen ƙawar Ummi na", Zaiyad yace; "to Allah ya kiyaye hanya". Saha tace; "korata kake yi ne wai?", Zaiyad yayi saurin girgiza kai yace; "a'a, kawai dai bana so ki shiga cikin matsala ne, muje na sama miki abin hawa". Saha ta shafa gefen fuskar shi sannan tace; "nayi tattaki tun daga gida domin kawai na ganka amma ka kasa bani komai daga gare ka", kan Zaiyad yayi magana Saha ta haɗe bakin su inda ta shiga kissing ɗin shi. Zee dake leƙe ta jikin kafar makulli ta girgiza kai cike da kishi tana faɗin; "zaka dawo ka same ni ne". Da ƙyar Zaiyad ya iya control ɗin kan shi dan Saha ta wuce duk ƴan matan shi ya san da cewa ita ɗin daban take, dan ma dai shi ɗin baya gani ya ƙyale ne amma da be kula ZeeZee ba domin kwata-kwata bata kai Saha ba. Hannun su sarƙe dana juna, Saha ta kalle shi tace; "meya faru kwana biyu ka canza mini, baka son kira na yanzu Sweetheart ko ka fara gajiya dani ne?". Zaiyad ya girgiza kai sannan yace; "kik gane ne bana son abinda zai kawo zargi tsakani na da Dad nafi so idan yazo ya tabbatar da cewa kece zaɓin ɗan nashi", Saha tayi murmushi jin abinda Zaiyad ya faɗa. Ya kamo hannun ta yana shafawa cikin salon yaudara yace; "ina ma ace zamu kwana a haka da zan fi kowa jin daɗi", Saha ta miƙe da sauri tana faɗin; "bari na tafi na bar me Keke Napep a waje", ba tare da ya miƙe ba ya cillo mata kiss, ta fice tana dariya. Koda ta shiga Keke murmushi kawai take saki idan ta tuno yadda Zaiyad ke matuƙar son ta da kuma ƙaunar ta. Dai-dai wani tamfatsetsen gida tace ya sauke ta, sai da ta ƙara duba takardar hannun ta domin tabbatar da gidan ne kuwa, lallai shine, kuɗin ta ciro ta bawa me Keken sannan ta fara ƙwanƙwasa get ɗin. Ta ƴar kafa me gadin ya leƙo, tace; "nazo wajen me gidan ne?", komawa yayi ciki ya kira wayar Hajiyar. Hajiya Kareema dake tsakiyar aikata masha'ar ta, taja tsaki tana me shafa gashin yarinyar sannan tace; "bari na amsa wayar", ba tare da ta jira amsar yarinyar ba ta ƙarasa kusa da wayar, ganin me gadi ne yasa ta kuma jan tsaki sannan ta ɗaga, nan ya sanar mata da zuwan baƙuwar, tace ya barta ta shigo. Ya buɗewa Sahabat get ɗin ta shigo, tun daga farfajiyar gidan ta fara haɗiyar miyau domin irin kyawun da gidan yayi mata, ko'ina interlocks ne a shinfiɗe a wajen sai dai gefe da gefe inda aka shuka shukoki domin su ƙara ƙawata gidan. Hanyar data gani wacce ta miƙe samɓal ita ta cigaba da bi har ta iso ƙaramar farfajiyar gidan, a hankali ta tura ƙofar ta shiga dogon corridor wanda tun daga nan ta fara jin sanyin Air Conditioner tana ratsa ta, Sahabat ta lumshe idanu jin har tsigar jikin ta na tashi. Sai da tayi tafiya me nisa kaɗan sannan ta iso waje me kama da varender wanda aka sakawa labule me zare-zare yana kuma walwali, a hankali ta ɗaga bakin ta ɗauke da sallama. Numfashinta ya kusa ɗaukewa ganin wani irin haɗaɗɗen falo, komai na ciki lemon green da milk ne har long chairs ɗin dake falon, ga ƙaton tibin bango wanda yake ta aikin shi, ƴan mata biyu ta samu a zaune, suna ganin ta suka zuba mata idanu, tayi murmushi sannan tace; "sannun ku", babu yabo ba fallasa suka amsa da "yauwa. "Amm, Hajiya fa ko tana nan?", Sahabat ta tambaya, ɗaya ta kalli ɗaya sannan suka juyo suka ƙara zubawa Sahabat idanu har ta fara tsarguwa. Ta kalli kayan jikin ta, riga t shirt ja sai pencil skirt baƙi inda ta ɗora top har ƙasa me baƙi da ja a sama, mayafi ma baƙi ta yafa sosai shigar tayi mata kyau abinka da ƴar duma-duma😉. "amm.....nace dan Allah Hajiya na nan?", ta sake tambaya a ɗan ƙufule dan ita gani take kamar sun raina wankan ta. Sai lokacin suka dawo daga duniyar yabo da kwaɗayin tsarin halittar yarinyar dan suna ganin ta sun tabbatar zasu girmeta. Baƙar me ƴar siririyar mara kuma tsayi tace; "eh tana ciki, Suhy ɗan kira ta", ta ƙarasa tana kallon baƙar me tsayi. Wacce aka kira da Suhy tace; "to zauna ina zuwa, Zuby ki bata wani abun mana", ta miƙe ta nufi wata ƙofa itama ta glass ce wanda Sahabat tana iya hango komai ta nan, inda kuma karamin wajen.hutawa ne me kyau da tsari. Sahabat tabi Suhy ɗin da kallo, riga ta saka me kama da vest sai wando legines iya gwiwa, eh to babu laifi dan tana da ƙugu sai da fa babu komai a ƙirjin. Ta kai kallon ta kan Zuby wacce ke ƙoƙarin shigewa Kitchen ita kam babu gaba babu baya amma duk da haka sai faman iyayi take ita a dole ga mace, dan ita riga ce iya cinya ta saka wacce a mutunce sai dai ka saka ta da wando. Kan ta gama tunanin har Zuby ta dawo hannun ta ɗauke da lemo da kuma glass cup sai ƙaramin bowl cike da kayan ƙwalama. Koda ta ajiye kasancewar rigar samanta a buɗe yake hakan yasa Sahabat ta hango brezier guda biyu da Zuby tayi ciko da ita. Saha ta matse bakin ta, tana faɗin; "kai Saha idanun ki ya cika kallon abinda babu ruwan shi", ta faɗi hakan a ranta tana me murmushi. Bayan Zuby ta ajiye ta koma saman kujera ta zauna tana me zubawa Sahabat ɗin idanu, Sahabat kuwa hankalinta ta mayar kan plasma dake aiki. Wani irin fitanannen ƙamshi ne ya dinfaro falon wanda babu shirin Sahabat ɗin ta juya domin kallon inda take jiyo ƙamshin. Hajiya Kareema ce tana tafe hannun ta riƙe dana wata budurwar ƴar kyakkyawa mara tsayi, sai dai tayi ɗoɗar sunan wani mulki namu daga gani kasan mai ke aiki dan har wani kashe idanu take yi. Sahar ta taɓe baki ganin Hajiya Kareemar sanye da wando da riga, ita kuma yarinyar sanye da riga doguwa ta ɗame ta. Hajiya Kareema na ganin Sahabat ta fara sakin murmushi tana faɗin; "Lale maraba da Beauty", Saha tayi murmushi tana me saukar da kanta ƙasa. Hakan ne yayi sanadiyar rashin ganin lokacin da Hajiya kareema ta kai bakin ta saman ƙirjin wannan yarinyar yayin da hannun ta kuma yake saman ƙugun ta, ta shafa kaɗan sannan ta sakarwa yarinyar kiss a ƙirjin ta, sannan ta sake ta. "Amm..... Safeena kije gida kawai zamu yi waya zuwa anjima kinga yanzu nayi baƙuwa me mahimmanci, Suhy ki bata wannan jakar babu yawa wannan kuma gashi ki yiwa ƙannen ki tsaraba". Safeena ta washe baki tana murna, bata taɓa tunanin harka da manyan hajiyoyi haka yake ba sai yanzu lallai ne dole ta godewa ƙawarta Suhy wacce ta ɗora ta akan wannan harkar. *Zuby ainihin sunanta shine Zubaida haifafiyar garin Katsina ce karatu ya kawo ta nan kaduna inda ta haɗu da Suhaila(Suhy) wacce take ita kuma ƴar Jos kasancewar halin su yazo ɗaya na son kuɗi wannan shine silar da suka ƙulla abota kuma suka fara gantalin su cikin garin kaduna, sun haɗu da Hajiya karima inda nan ta zama Mummyn su yayin da suke biya mata buƙata itama tana biya musu nasu, yawan carry over da suke dashi yasa aka kore su daga jami'ar dake kaduna shine fa suka tare gidan Hajiya Kareemar kuma har lokacin iyayen su basu san da an sallame su a makaranta ba( iyaye ya kamata ku dinga kula da makarantun yaran ku dan sau da yawa akan kori ƴaƴan naku amma baku sani ba Allah yasa mu dace)*. _Safeena kuwa talauci ne yayi musu katutu, ga mahaifin su da Allah ya yiwa rasuwa, hakan yasa suka shiga cikin ƙunci wannan dalilin yasa har makaranta suka dena zuwa, ga Safeena tana ƙaunar cigaba da karatu wata rana sai ta haɗu da Suhaila dama sune ke yiwa Hajiya Kareema farautar ƴan mata, bata wani sha wahala ba wajen shawo kan Safeenar, yau shine ranar da suka fara ita da Hajiya Kareemar_. Ragowar kuma ta kan ja ra'ayin masu zuwa ganin ta wato masoyan littattafanta na batsa da maɗigo wannan shine ta hanyar da takan samu ƴan mata. "haba Beauty kamar ba ƴar gida ba kin ƙi sakin jiki kici abinci ko dan ganin wa'innan ne", Saha ta girgiza kai. Hajiya Karima ta kalli Suhy da Zuby fuska ɗaure domin ita kanta ta lura da kallon da suke bin Sahabat ɗin dashi tace; "maza ku wuce naku ɗakin", ba dan ran su yaso ba suka nufi ɗakin suna me baƙin cikin hana su kallon yarinyar. Hajiya kareema ta taso ta dawo kusa da Sahabat ta zauna, sannan ta riƙo hannun Sahabat ɗin cikin salon yaudara da iskanci tace; "haba Beauty na faɗa miki ki dauke ni kamar Ummi mana bana jin daɗin yadda kike jan baya daga gare ni", Sahabat kuwa ta kasa cewa komai tsabar mamakin iskancin matar. Cikin dabara ta ƙwace hannun ta sannan ta ɗauki glass cup ɗin ta kai bakin ta, Hajiya Kareema kuwa har lokacin hankalin ta be wani dawo dai-dai ba, gashi dama bata gama samin natsuwa da Safeena ba Sahar ta zo gashi kuma zama da tayi kusa da Saha ya jifata wani hali. Saha kuwa banda jan tsaki babu abinda ta ke yi itafa ta fara lura da take-taken wannan matar kamar ƴar maɗigo ce, batama san a ina Ummi ta haɗu da ita ba, gashi dama can ita ƴan maɗigon ba birge ta suke yi amma zata zuba mata idanu taga gudun ruwan ta. Ko minti biyar bata ƙaraba ta miƙe akan zata tafi, Hajiya Kareema jikin ta har rawa yake yi wajen kwasowa Saha kayan kwalliya turarrurruka, atamfa da abin hannu wai gashi nan taje tayi gayu dasu. Saha tace; "nagode sosai", Hajiya Kareema ta riƙo hannun ta tace; "kada ki damu ni me son ki ce, ni dai ina roƙon ki da kada ki juya mini baya", Saha ta ɗaga kai. Hajiya Kareema taja Sahar zuwa waje inda suna tafiya tana samun damar murza lallausan tafin hannun Saha ɗin, da Saha na gyara tafin hannun ta sosai don ta san Sahibinta na so wato Zaiyad. A harabar gidan ta tsaya sannan ta ƙwalawa Idris driver kira, babu ɓata lokaci yazo ta miƙa mishi key na mota sannan tace; "gashi ka kai mini Sweet Baby na gida", Saha ta bita da wani kallo wai Sweet Baby. Mota jibgegiya High lander ita ta buɗewa Saha baya ta shiga, sannan Idris ɗin yaja motar, tana tsaye tana ɗagawa Saha hannu har suka fice daga gidan. Hajiya Kareema ta sauke ajiyar zuciya sannan tace; "ai tunda na ƙwallafa rai akan ki sai na sami abinda nake so yarinya ki gama gudun ki", ta faɗa tana ƙarasa shigewa ciki. Tun daga falo ta fara ƙwalawa su Suhy kira, Suhy da Zuby da suke manne da juna dan suma ganin Sahar ba ƙaramin tayar musu da hankali yayi ba. Hajiya Kareema ta kuma ƙwala musu kira babu shiri suka saki juna suka yo waje domin jin me yake faruwa, Hajiya kareema na ganin su ta ƙara kusa dasu ta janyo Zuby jikin ta yayinda ta haɗe bakin ta dana Suhy da sauri nan suka shiga aikata masha'ar su. *wa'iyazubillah* ********** *********** Kwanaki nata shuɗewa inda a yanzu saura kwana uku a ɗaura auren Abdulkareem da Jamila, babu masifar da Jamila bata yi ba amma Abdulkareem yaƙi fasa auren saima Allah yake a kawo masa amaryar sa koya sami sauƙi. Yauma ƴan uwan shi ne suka kawo mata kayan faɗar kishiya, Salma ta tuna da huɗubar Jameela inda take cewa kada ta yarda ta raga musu dan suma munafikai ne. Salma tabi matar yayan shi da kallo bayan ta gama ɗaga mata kayan wai nan tana nuna mata, Salma tayi yaƙe sannan tace; "ina zuwa", sun ɗauka tukwuici zata basu har suna washe baki dan basu san me take yiwa Abdulkareem ɗin ba dan baya zuwa gida ya faɗa musu. Salma kuwa galan na kalanzir ta ɗauko da ashana, suna zaune sai ganin ta suka yi da kalanzir da ashana ta buɗe galan ɗin ta fara tsiyayawa saman kayan. Duk suka zuba mata idanu, sai da ta gama tass sannan tace; "kune munafikai wato ko harda ku za'a haɗa baki a kawo wata cikin gidan nan to zaku ga aiki da cikawa kuma na tabbatar muku yadda na ƙona kayan nan haka zan ƙona amaryar zaku san dani kuke magana", tana gama faɗar haka ta cilla asha saman ƙaramin akwatin. Da sauri ƴan uwan suka ɗauke ragowar biyun da kada suma su kama yayin da ƙanwar Abdulkareem ɗin ta yi waje da gudu domin ɗebo ruwa tazo ta sheƙawa akwatin da yake ci. Cikin fushi Gwaggon su tace; "Salma wannan wane kalar rashin hankali ne?, bafa kanki aka fara kishiya ba kuma ba'a kanki za'a gama ba kiyi haƙuri mana komai zai zo ya wuce amma kina ƙona dukiyar mijin ki kamar wani kayan bola babu damuwa babu komai". Salma cikin rashin kunya tace; "dakata Safiya ai ban ga hakan a cikin gidan ki ba idan kina so ki nuna mini zahiri sai kije ki cewa Habu ya ƙara miki wata daga nan nima zan yarda da abinda kike faɗa amma ke kina zaune a gidan ki tsofai-tsofai dake kin kanainaye naki mijin da asiri da tofe-tofe da jiƙe-jiƙe ni kuma sai ki kwaso ƙafa kizo don ki taimaka wajen a kawo mini kishiya to wallahi ki kwashi ƙafafun ki dake da ƴan koron naki kan nayi muku na cikar shekara", bata gama rufe baki ba Ƙanwar Abdulkareem ɗin ta kwashe ta da mari, Salma ta buɗe baki zata kuma magana ta ƙara kwashe ta da mari. Cikin fusata tace; "ko Yaya Abdulkareem ba zai kalli Gwaggo ya kirata da sunan ta ba balle ke da kike cin arziƙin zama dashi, wallahi kika sake kika kuma kallon Gwaggo da sunan zaki yi mata rashin kunya sai mun lalllasa ki a gidan nan kuma aure babu fashi sai mun shigo da Amarya gidan nan ko ki so ko kada ki so banza ballagaza ke waye yace kada ki kama naki mijin tunda kin saki wata kuma ta cafke a waje ba shikenan ba Shashasha soloɓiyo". Gwaggo ta dakatar da ita tace; "barta Halima ta cigaba da abinda take yi idan har hakan shi take ganin dai-dai lallai Salma kin canza dole Abdulkareem ya ƙaro aure abinda kika faɗa mini kuma kije dan kanki, mu haƙuri mu kazo baki tunda baki so shikenan bama neman tashin hankali kuzo mu tafi". Salma ta taɓe baki tace; "ku kwashe kayan tsiyar ku ku tafi dashi dan babu abinda zan yi dashi, ke kuma wallahi sai na rama mari na", ta ƙarasa tana nuna Halima, Halima tace; "a shirye nake ai ina jira mahaukaciya ƙazama kawai", haka suka tattara kayan suka tafi dashi. Koda suka koma gida zancen da aka dinga maimaitawa kenan inda wasu suka dinga kare ta akan zafin kishi ne wasu kuma suka dinga zagin ta, har ma akwai wanda suka so komawa gidan suyi mata rashin mutunci mayan suka hanasu. Ita dai wacce ta riƙe Abdulkareem ɗin bata ce komai ba sai dai fuskar ta zai nuna maka bata ji daɗin hakan ba, koda Abdulkareem yazo Halima ita ta tare shi ta faɗa mishi hankalin shi ya tashi sosai har ƙasa ya durƙusa yana bata haƙuri, Gwaggon tace babu komai ai ya wuce. Kaya kuwa sai dai ƙannen nashi ne suka saka omo suka wanke su tas bayan sun bushe suka maida akwatin suka ajiye, Mariƙiyar shi ita ta amsa ta ɓoye ƙasan gadon ta dan shi Abdulkareem ɗin har yace musu ma su raba a tsakanin su ta hana. Salma kuwa nan ta kira Jameela ta bata labarin abinda ke faruwa, Jameela ta hau yi mata kirari tana ƙara Zugata, ita kuwa Salma sai washe baki take yi ganin cewa Jameelar na matuƙar sonta. Salma tace; "wai yaushe zaki zo gida na ne?",Jameela tayi murmushi tace; "nan bada jimawa ba, amma idan na tashi zuwa zan zo miki da abin mamaki ne". Salma da bata fahimta ba ta kwashe da dariya tana faɗin; "kamar kin san ina son surprise", Jameela tace; "shi yasa zan zo miki dashi ai", nan suka yi sallama. Jameela taja tsaki tana faɗin; "mahaukaciya keda kike cikin gidan mijin ki maimakon ki riƙe shi hannu biyu amma kin tsaya wasa matan da yanzu kamar su kai kansu gidan miji haka suke ji ƴan mata sunyi yawa a gari ga zaurawa suma amma kin wani tsaya sanya ai zaki ga aiki da cikawa ne", ta ƙarasa tana miƙewa daga inda take. Koda daddare Abdul be nunawa Salma komai ba itama bata nuna mishi ba, hasalima yanzu ɗakin Amarya yake kwana dan tun ranar data neme shi ya nuna mata bata isa ba suka ɓata gaba ɗaya, nan ta hana shi shiga ɗakin babu arziƙi ya tattara ya koma ɗakin amarya. Allah yasa ma sai gobe zasu zo danki, daga gobe kuma dole ya canza wajen kwana haka ya kwanta yana me janyo wayar shi ya hau fira da abar ƙaunar shi. Washe gari aka zo aka yi danki, inda nan ma sai da Salma ta nuna halin ta dan sai da suka tafi da ita a baki. Ita kuwa babu abinda ya dame ta, ji take wannan shine dai-dai kuma har yanzu ta yarda da maganar Jameela akan Abdulkareem ɗin zai iya tsorata yace ya fasa. Dangin amarya kuwa sai da suka kulle ɗakin tsaf sannan suka tafi da makullin gudun abinda zata iya aikatawa bayan sun tafi. Abdulkareem ranar sai cikin motar shi ya kwana, washe gari kuwa ko idanun shi Salma bata gani ba yana dai jiyo hayaniyar ta a ciki nan ya wuce can gidan su dama tuntuni ya kai su Husna can acan ya karya sannan yayi wanka ya canza kaya. Sai dare sannan ya koma nashi gidan, abin mamaki yau tsabar masifa ma Salma ko wayar bata danna ba dan wani irin zafi zuciyar ta yake yi mata. Kamar ba zai shiga inda take ba sai kuma ya shiga, hannun shi ɗauke da leda, yayi sallama ko kallon shi bata yi ba ta dai amsa sallamar. Ya saba da halin ta yanzu dan haka yace; "ga kayan ki nan na fitar biki tunda baki amshi akwatin ba, na kaiwa su Husna nasu, dan Allah Salma ki dena abinda kik........". Cikin fushi ta shaƙi wuyan shi sannan cikin ihu tace; "ka fita ka bani waje Abdulkareem!!!", sosai abin ya bashi mamaki dan be taɓa jin sunan nashi a bakin ta ba. Ganin yadda ta koma kamar mahaukaciya yasa ya bamɓare hannun ta daga jikin shi ya juya zai fice, ta ɗauki ledar da jefa mishi a jiki ya juyo da sauri, cikin sanyin murya kuma tace; "dan Allah ka ɗauke bana so", ta ƙarasa muryar ta na rawa. Sosai ta bashi tausayi, a wajen ta zauna ta fara kuka, ance soyayya daban take dole Abdulkareem yaji wani abu ya caki zuciyar shi ya san da cewa Salma itace macer da yaso so na gaskiya. Da sauri ya ƙaraso inda take ya ɗago ta, Salma da kamar ma bata hayyacin ta abu ɗaya take ambata shine; "ka tafi ka bani waje kawai", be saurare ta ba haka ya ɗauke ta ya kaita har saman gadon ta ya kwantar. A hankali yake shafa gashin kanta tana sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya yace; "Salma kiyi haƙuri duk abinda ya faru kece kika janyo mana, ki ɗauki aure na a matsayin hukunci daga ubangiji ki sassautawa kanki haka mana, na san da cewa kina sona har yanzu dan auren soyayya muka yi dake amma meyasa kika canza mini lokaci ɗaya?". Bata ce komai ba sai dai har lokacin hawaye na zuba daga idanun ta, haka ya dinga kwantar mata da hankali cikin dabara kuma cikin taimakon Allah taji ta ɗan sami sauƙi. Ranar dai tsakanin Abdul da Salma sunyi kwanan farin ciki duk da babu abinda ya shiga tsakanin su, asuba suka tashi inda yace; "ki tashi yanzu kiyi sallah", babu musu ta tashi tayi. Yana dawowa haka suka kuma shan barcin su cike da ƙaunar juna, Abdul yayi ƙoƙari wajen kaudar da damuwar da Salma take ciki. Sai takwas suka tashi, nan suka shiga kitchen tare suka samawa cikin su abinda zasu ci, sai da suka gama sannan yace; "yanzu ki tashi muje mu gyara gidan nan kinji", fuskar ta cike da damuwa dan ta tuna ko jiya sai da Auntyn ta ta kira ta akan zasu zo su taya ta gyara tace bata so suyi zaman su. Abdul ya riko hannun ta yace; "kada ki damu Matata ki muje muyi aikin mu", tayi murmushin da be kai zuciya ba sannan ta miƙe. Sunyi aiki sosai da sosai dan irin yadda gidan yayi datti, har wajen azahar basu gama ba gashi da an idar da azahar ɗin za'a ɗaura auren, har ma abokanan shi sun fara kiran shi. Ya cire hannu daga wankin da suke yi ya kalle ta cikin damuwa yace; "bari nazo na shirya na tafi amma zan kira miki su Aunty Maryam kinji kada ki damu", tayi murmushin yaƙe tace; "to. Ta bishi da kallo har ya shige ɗakin, kasa cigaba tayi da wankin ta tsaya kawai, ita ba tunani ba ita ba aikin ba. Har yayi wanka ya shirya tana tsaye, ƙamshin da hancin ta ya fara kawo mata ne yasa ta ɗaga kai ta kalle shi, kamar ta ɗora hannu akai tayi ihu haka take ji. don mijin ta data gani sanye da farar shadda ƙarr da ita wacce aka yiwa aiki da zare me ruwan ƙasa yayi kyau sosai wular kanshi da takalmin shi sau ciki duka ruwan ƙasa ne, ga wani irin ƙamshi dake tashi a jikin nashi wanda ya buɗe gidan. Yayi mata murmushi sannan ya matso kusa da ita ya bata kiss a goshi yace; "zan tafi kada nayi latti azo ana jira na", ta ɗaga kai kawai. Ya kwanto ta jikin shi sannan yace; "babu rako ma Sweet", ba dan taso ba ya riƙe hannun ta har zuwa bakin get ɗin gidan, ita dai binshi take kawai da kallo. Shigowar ƴan uwan ta nan suka hau yi mishi tsiya yana dariya, Salma kuwa babu eh babu a'a, sai da suka gaisa cikin sakin fuska sannan suka wuce suka barsu. Yace; "zan tafi", ta ɗaga mishi kai ya langwaɓar da kai yace; "babu addu'a", tace; "Allah ya kiyaye hanya yasa a ɗaura lafiy....." bata ƙarasa ba hawaye suka fara zubowa daga idanun ta. Ya ciro handkerchief ya hau goge mata sannan yace; "kiyi haƙuri ki dena zubar da hawayen ki haka Salma haba Uwargida ki zama jaruma mana, ki zauna kusa da wayar ki anjima zan kira ki", ta ɗaga kai kawai ya kaiwa lips ɗin ta kiss sannan ya sake ta ya fita. Ta daɗe tsaye a wajen tana sharar hawaye, zuciyar ta kamar zata tsago ƙirjin ta ta fito haka take ji, ga wani iri da numfashin ta keyi yanzu shikenan zasu zama su biyu wajen mijin ta. A sanyaye ta koma cikin gida inda ta tarar da ƴan uwan nata har sun gama wankin sun ɗora mata abinci. Auntyn ta Aunty Maryam ta balla mata harara tace; "ji yadda kika maida kanki ko?", Salma ta sauke kanta ƙasa. Aunty Jidda tace; "mijin ki na son ki amma kin bi kin sa duk ya juya miki baya ai wallahi da ba dan ya kira Abban Aarif ba da ba zan zo ba ki zauna kici haukar ki shashasha kawai". Aunty Maryam tace; "barta Jidda wallahi ta cigaba da ɓata mishi rai ya sako ki, ki koma gida dama Abba yace ai ki bari mijin naki ya sako ki ki dawo gida sai kin gane baki da wayo". Aunty Sameeha tazo ta riƙe hannun ta sannan tace; "kai Jidda da Maryam ku bar mini ƙanwa haka, kinji zo muje ciki kije kiyi wanka na tsantsara miki kwalliya kema kada amarya tazo ta raina ki". Maryam da Jidda suka yi dariya suka ce; "Allah matar yaya Salman ce bata da hali kwata-kwata". Nan dai Sameeha taja hannun Salman suka shiga ciki, da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta shiga tayi. Tana fitowa wayar ta ta hau ƙara, ganin me kiran sai da gaban ta ya faɗi, amma haka ta daure ta ɗaga, a can ɓarin taji yace; "Uwargida an ɗaura", ba tare da tace komai ba ta katse wayar kawai ta saki kuka. Aunty Sameeha ta hau rarrashin ta tare da yi mata nasiha, ita dai Salma yanzu gani take ma Sameehar ba son ta take yi ba. Haka tayi banza da ita, su Aunty Maryam ne suka shigo ganin yadda Salmar ke kuka Sameehar na lallashin ta abin ya basu haushi nan suka hau Salmar da faɗa babu arziƙi ta goge hawayen ta, Aunty Sameehar ta hau yi mata kwalliya. Shaddace ruwan toka wacce taji aikin wuta da stones doguwar riga ce tayi kyau sosai, nan Aunty Sameehar ta kashe mata ɗauri me kyau, Aunty Maryam tace; "da kyawun ki da komai amma kin zauna kin ɓata wayon ki gashi mijin naki akwai ƙoƙari wajen siyo miki kayan kwalliya, nan dai suka ƙara yi mata nasiha sosai. Sai lokacin Salma taji hankalin ta na ɗan kwantawa ga kuma jikin ta da yayi sanyi jin yadda ƴan uwan nata suke mata wanka me kamar jirwayi, ga wasu ayoyi a alƙur'ani da suka janyo mata su wanda Salma duka ta san ma'anar su dan ba jahila bace, basu ƙyale ta ba sai da suka tabbatar da ta fara dawowa hayyacin ta sannan suka ce ta tashi ta fita. Babu musu ta miƙe ta fita inda tana fitowa mijin nata yana shigowa da abokanan shi, nan fa suka hau tsokanar ta wai ta zama tsohuwa ita dai murmushi kawai take yi domin bata da kuzari, gashi ta kira number din Jameela amma bata ɗaga ba. Haka ta tura mata da text akan an ɗaura auren ta taya ta da addu'a, Jameela na ganin saƙon ta saki shewa tana dariya. Sun yi barkwanci sosai tsakanin ango da abokanan shi kafin aka ɗauki hotuna har zuwa wani lokaci sannan suka fice daga gidan. kamar yadda al'adar kaduna take, sai da aka gama dinner ƙarfe goma sannan aka nufo da amarya gidan ta, a lokacin kuwa Salma na saman dadduma dan tun wajen takwas ƴan uwan nata suka bar gidan inda aka bar mata ƙanwar ta Fiddausi da kuma Fatima, to su ɗin ma kowacce tana kan waya tana faman fira da saurayi. Jin guɗa yasa gaban Salma faɗuwa dan bata je dinner ba saboda kunyar ƴan uwan Abdulkareem ɗin da take yi na ganin irin rashin mutuncin da tayi musu. Sallama taji a falon ta wanda ya bata tabbacin an kawo mata amarya ne, ta kalli su Fatima sannan tace; "Fatima muje falo", dole suka ajiye wayoyin suka fito duka. Nan aka gabatar da Amarya ga Uwargida aka kuma damƙa amanarta gare ta tare da ƴan nasihohi, Salma cikin sanyin murya tayi godiya tare da jaddada musu insha Allahu zata riƙe amana ƙarshe tayi addu'a sosai wanda hakan yasa ƴan uwan amaryar jin ta birge su, duk da sukar ta da ƴan jere suka kai amma yanzu ta wanke wancan Jameela kuwa ba haka ranta yaso ba amma babu yadda zata iya. Haka suka tashi suka tafi suna yaba halin ta wasu na cewa ladaf tayi dan babu yadda zata yi wasu kuma suna cewa halin tane hakan. Salma kam suna fita ta koma ciki kan daddumarta tana ƙara neman yafiyar Allah akan abinda ta aikata tare da neman taimakon Allah. Anya kuwa tuban gaskiya kika yi Salma🤔. Sai wajen sha ɗaya sannan ango ya shigo gidan, Salma na jiyo haniyar su har suka gama duk abinda zasu yi.na al'ada sannan aka yi addu'a aka watse. Nan Ango yace; "amarya tashi kiyi alwala muyi sallah", kasancewar ba yarinyar bace ta san hakan babu musu ta tashi tayo alwala. Sai da suka gabatar da sallah raka'a biyu nan yayi addu'ar da manzon Allah ya koyar sannan ya tambaye ta game da addinin ta babu laifi ta ɗan bashi amsa. Yayi.murmushi yana me tuna lokacin da suke amare shida Salmar shi yadda ta amsa mishi tambayoyin cike da birgewa da kuma nutsuwa. Ya riƙo hannun Jameelar yace; "zo muje wajen Auntyn ki", Jameelar kam haushi taji sosai amma ta dake tace; "to muje", ya ɗauko ɗaya daga cikin ledojin dake ajiye a saman center table kana suka fice. Da sallama suka shiga ɗakin, ganin haske a ciki ya tabbatar mishi da cewa idanun Salmar biyu, ya kalli Jameelar yace; "zauna anan bari na shiga na kira ta", Jameela ta taɓe baki sannan ta zauna yayin da shi kuma ya shiga don kiran Salmar. A Zaune a saman gado ya same ta , ta zuba tagumi yayin da Fatima da Fiddausi ke fama barci abin su hankali kwance. Yadda ya ganta ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, yana yin sallama ta ɗago ta kalle shi sannan ta amsa. "kizo falo ina son ganin ki", be jira cewar ta ba ya fito itama kuma bata ce komai ba ta miƙe ta biyo bayan shi gaban ta yana faɗuwa. Koda ta fito kan amaryar yana sauke a ƙasa dan haka bata ganin ko fuskar wacece, Salma taje ta zauna saman one seater, Abdulkareem yayi addu'a sannan ya ɗora da yi musu nasiha akan su zauna lafiya ya kuma ce jameela itace ƙarama dan haka ta girmama Salma yayin da yace Salma ita kuma ta kama girmanta sannan ta su.riƙe juna amana babu wacce tafi wani a wajen shi duka so da ƙauna ne ya haɗa su kuma dukan su so iri ɗaya yake yi musu su zauna lafiya. "sannan batun kwana ya kuke ganin za'a dinga yi", Salma tace; "ta zaɓa duk yadda ta zaɓa shikenan". Abdul yace; "a'a kece babba dan haka ke ya kamata ki zaɓa", Salma tace; "shikenan bibbiyu ina ganin hakan yayi ai?". Abdul yace; "to kamar yadda addini ya tanadar budurwa ana yi mata sati ɗaya ne bazawara kuma kwana uku, don haka zan yi mata kwana uku tukunna sai kuma a koma kwana bibbiyu, Amarya ke hakan yayi miki?". Jameela tace; "eh yayi tunda haka ta zaɓa a barshi a hakan amma da sai nace kwana biyu gaskiya yayi.mini yawa dan ba zan iya jure rashin miji na a kusa dani ba har tsayin kwana biyu bayan na san can inda yake ba wai kula yake samu ba". Dum gaban Salma ya faɗi, dan tabbas muryar Jameela take jiyowa idan har kunnen ta ba ƙarya yake yi mata, Abdul kuwa kasa cewa komai yayi fatan shi ɗaya kada Salma ta tanka dan baya so su fara hayaniya tun yanzu dan haka ƙoƙarin shi na kauda maganar yasa ya miƙe sannan yace; "taso muje". Jameela har ta miƙe Salma tayi sauri ƙarasawa gaban ta, ta ɗaga mayafin data rufe fuskar ta dashi, cikin kiɗima da mamaki tare da ruɗewa tace; "Jameela!!!! Kece matar da miji na ya aura yau, Jameela kece kika aure mini miji??". Jameela tayi wani munafikin murmushi tace; "nice mana Ƙawata Aminiya ta ya san ranki, ai dama nace miki zan zo.miki da abin mamaki ya kika gani?". ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [15/03, 09:08] Yaya Umar: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say: "The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path [un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire." [Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: إِنَّ أَوَّلَ النَّاسِ يُقْضَى يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَيْهِ رَجُلٌ اسْتُشْهِدَ، فَأُتِيَ بِهِ فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ قَاتَلْتُ فِيكَ حَتَّى اسْتُشْهِدْتُ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ قَاتَلْتَ لِأَنْ يُقَالَ: جَرِيءٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ تَعَلَّمَ الْعِلْمَ وَعَلَّمَهُ وَقَرَأَ الْقُرْآنَ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: تَعَلَّمْتُ الْعِلْمَ وَعَلَّمْتُهُ، وَقَرَأْتُ فِيكَ الْقُرْآنَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ تَعَلَّمْتَ الْعِلْمَ لِيُقَالَ: عَالِمٌ، وَقَرَأْتَ الْقُرْآنَ لِيُقَالَ: هُوَ قَارِئٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ، فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ وَسَّعَ اللَّهُ عَلَيْهِ، وَأَعْطَاهُ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ كُلِّهِ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: مَا تَرَكْتُ مِنْ سَبِيلٍ تُحِبُّ أَنْ يُنْفَقَ فِيهَا إِلَّا أَنْفَقْتُ فِيهَا لَكَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ فَعَلْتَ لِيُقَالَ: هُوَ جَوَادٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ، ثُمَّ أُلْقِيَ فِي النَّارِ. رواه مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي) ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 23*~ Tana tura ƙofar Zaiyad na turowa dan haka a wajen suka ci karo, cikin sauri ya rungume ta haka da dabara ya ja ta zuwa falo. Yana zama ta zauna saman ƙafar shi sannan ta shafo fuskar shi tace; "nayi kewar ka Sweetheart sosai", ya riƙo hannun ta sannan yace; "nima nayi kewar ki sosai, yanzu sai ina dan na san akwai insa zaki je". Sahabat tace; "zan je Unguwar Rimi ne wajen ƙawar Ummi na", Zaiyad yace; "to Allah ya kiyaye hanya". Saha tace; "korata kake yi ne wai?", Zaiyad yayi saurin girgiza kai yace; "a'a, kawai dai bana so ki shiga cikin matsala ne, muje na sama miki abin hawa". Saha ta shafa gefen fuskar shi sannan tace; "nayi tattaki tun daga gida domin kawai na ganka amma ka kasa bani komai daga gare ka", kan Zaiyad yayi magana Saha ta haɗe bakin su inda ta shiga kissing ɗin shi. Zee dake leƙe ta jikin kafar makulli ta girgiza kai cike da kishi tana faɗin; "zaka dawo ka same ni ne". Da ƙyar Zaiyad ya iya control ɗin kan shi dan Saha ta wuce duk ƴan matan shi ya san da cewa ita ɗin daban take, dan ma dai shi ɗin baya gani ya ƙyale ne amma da be kula ZeeZee ba domin kwata-kwata bata kai Saha ba. Hannun su sarƙe dana juna, Saha ta kalle shi tace; "meya faru kwana biyu ka canza mini, baka son kira na yanzu Sweetheart ko ka fara gajiya dani ne?". Zaiyad ya girgiza kai sannan yace; "kik gane ne bana son abinda zai kawo zargi tsakani na da Dad nafi so idan yazo ya tabbatar da cewa kece zaɓin ɗan nashi", Saha tayi murmushi jin abinda Zaiyad ya faɗa. Ya kamo hannun ta yana shafawa cikin salon yaudara yace; "ina ma ace zamu kwana a haka da zan fi kowa jin daɗi", Saha ta miƙe da sauri tana faɗin; "bari na tafi na bar me Keke Napep a waje", ba tare da ya miƙe ba ya cillo mata kiss, ta fice tana dariya. Koda ta shiga Keke murmushi kawai take saki idan ta tuno yadda Zaiyad ke matuƙar son ta da kuma ƙaunar ta. Dai-dai wani tamfatsetsen gida tace ya sauke ta, sai da ta ƙara duba takardar hannun ta domin tabbatar da gidan ne kuwa, lallai shine, kuɗin ta ciro ta bawa me Keken sannan ta fara ƙwanƙwasa get ɗin. Ta ƴar kafa me gadin ya leƙo, tace; "nazo wajen me gidan ne?", komawa yayi ciki ya kira wayar Hajiyar. Hajiya Kareema dake tsakiyar aikata masha'ar ta, taja tsaki tana me shafa gashin yarinyar sannan tace; "bari na amsa wayar", ba tare da ta jira amsar yarinyar ba ta ƙarasa kusa da wayar, ganin me gadi ne yasa ta kuma jan tsaki sannan ta ɗaga, nan ya sanar mata da zuwan baƙuwar, tace ya barta ta shigo. Ya buɗewa Sahabat get ɗin ta shigo, tun daga farfajiyar gidan ta fara haɗiyar miyau domin irin kyawun da gidan yayi mata, ko'ina interlocks ne a shinfiɗe a wajen sai dai gefe da gefe inda aka shuka shukoki domin su ƙara ƙawata gidan. Hanyar data gani wacce ta miƙe samɓal ita ta cigaba da bi har ta iso ƙaramar farfajiyar gidan, a hankali ta tura ƙofar ta shiga dogon corridor wanda tun daga nan ta fara jin sanyin Air Conditioner tana ratsa ta, Sahabat ta lumshe idanu jin har tsigar jikin ta na tashi. Sai da tayi tafiya me nisa kaɗan sannan ta iso waje me kama da varender wanda aka sakawa labule me zare-zare yana kuma walwali, a hankali ta ɗaga bakin ta ɗauke da sallama. Numfashinta ya kusa ɗaukewa ganin wani irin haɗaɗɗen falo, komai na ciki lemon green da milk ne har long chairs ɗin dake falon, ga ƙaton tibin bango wanda yake ta aikin shi, ƴan mata biyu ta samu a zaune, suna ganin ta suka zuba mata idanu, tayi murmushi sannan tace; "sannun ku", babu yabo ba fallasa suka amsa da "yauwa. "Amm, Hajiya fa ko tana nan?", Sahabat ta tambaya, ɗaya ta kalli ɗaya sannan suka juyo suka ƙara zubawa Sahabat idanu har ta fara tsarguwa. Ta kalli kayan jikin ta, riga t shirt ja sai pencil skirt baƙi inda ta ɗora top har ƙasa me baƙi da ja a sama, mayafi ma baƙi ta yafa sosai shigar tayi mata kyau abinka da ƴar duma-duma😉. "amm.....nace dan Allah Hajiya na nan?", ta sake tambaya a ɗan ƙufule dan ita gani take kamar sun raina wankan ta. Sai lokacin suka dawo daga duniyar yabo da kwaɗayin tsarin halittar yarinyar dan suna ganin ta sun tabbatar zasu girmeta. Baƙar me ƴar siririyar mara kuma tsayi tace; "eh tana ciki, Suhy ɗan kira ta", ta ƙarasa tana kallon baƙar me tsayi. Wacce aka kira da Suhy tace; "to zauna ina zuwa, Zuby ki bata wani abun mana", ta miƙe ta nufi wata ƙofa itama ta glass ce wanda Sahabat tana iya hango komai ta nan, inda kuma karamin wajen.hutawa ne me kyau da tsari. Sahabat tabi Suhy ɗin da kallo, riga ta saka me kama da vest sai wando legines iya gwiwa, eh to babu laifi dan tana da ƙugu sai da fa babu komai a ƙirjin. Ta kai kallon ta kan Zuby wacce ke ƙoƙarin shigewa Kitchen ita kam babu gaba babu baya amma duk da haka sai faman iyayi take ita a dole ga mace, dan ita riga ce iya cinya ta saka wacce a mutunce sai dai ka saka ta da wando. Kan ta gama tunanin har Zuby ta dawo hannun ta ɗauke da lemo da kuma glass cup sai ƙaramin bowl cike da kayan ƙwalama. Koda ta ajiye kasancewar rigar samanta a buɗe yake hakan yasa Sahabat ta hango brezier guda biyu da Zuby tayi ciko da ita. Saha ta matse bakin ta, tana faɗin; "kai Saha idanun ki ya cika kallon abinda babu ruwan shi", ta faɗi hakan a ranta tana me murmushi. Bayan Zuby ta ajiye ta koma saman kujera ta zauna tana me zubawa Sahabat ɗin idanu, Sahabat kuwa hankalinta ta mayar kan plasma dake aiki. Wani irin fitanannen ƙamshi ne ya dinfaro falon wanda babu shirin Sahabat ɗin ta juya domin kallon inda take jiyo ƙamshin. Hajiya Kareema ce tana tafe hannun ta riƙe dana wata budurwar ƴar kyakkyawa mara tsayi, sai dai tayi ɗoɗar sunan wani mulki namu daga gani kasan mai ke aiki dan har wani kashe idanu take yi. Sahar ta taɓe baki ganin Hajiya Kareemar sanye da wando da riga, ita kuma yarinyar sanye da riga doguwa ta ɗame ta. Hajiya Kareema na ganin Sahabat ta fara sakin murmushi tana faɗin; "Lale maraba da Beauty", Saha tayi murmushi tana me saukar da kanta ƙasa. Hakan ne yayi sanadiyar rashin ganin lokacin da Hajiya kareema ta kai bakin ta saman ƙirjin wannan yarinyar yayin da hannun ta kuma yake saman ƙugun ta, ta shafa kaɗan sannan ta sakarwa yarinyar kiss a ƙirjin ta, sannan ta sake ta. "Amm..... Safeena kije gida kawai zamu yi waya zuwa anjima kinga yanzu nayi baƙuwa me mahimmanci, Suhy ki bata wannan jakar babu yawa wannan kuma gashi ki yiwa ƙannen ki tsaraba". Safeena ta washe baki tana murna, bata taɓa tunanin harka da manyan hajiyoyi haka yake ba sai yanzu lallai ne dole ta godewa ƙawarta Suhy wacce ta ɗora ta akan wannan harkar. *Zuby ainihin sunanta shine Zubaida haifafiyar garin Katsina ce karatu ya kawo ta nan kaduna inda ta haɗu da Suhaila(Suhy) wacce take ita kuma ƴar Jos kasancewar halin su yazo ɗaya na son kuɗi wannan shine silar da suka ƙulla abota kuma suka fara gantalin su cikin garin kaduna, sun haɗu da Hajiya karima inda nan ta zama Mummyn su yayin da suke biya mata buƙata itama tana biya musu nasu, yawan carry over da suke dashi yasa aka kore su daga jami'ar dake kaduna shine fa suka tare gidan Hajiya Kareemar kuma har lokacin iyayen su basu san da an sallame su a makaranta ba( iyaye ya kamata ku dinga kula da makarantun yaran ku dan sau da yawa akan kori ƴaƴan naku amma baku sani ba Allah yasa mu dace)*. _Safeena kuwa talauci ne yayi musu katutu, ga mahaifin su da Allah ya yiwa rasuwa, hakan yasa suka shiga cikin ƙunci wannan dalilin yasa har makaranta suka dena zuwa, ga Safeena tana ƙaunar cigaba da karatu wata rana sai ta haɗu da Suhaila dama sune ke yiwa Hajiya Kareema farautar ƴan mata, bata wani sha wahala ba wajen shawo kan Safeenar, yau shine ranar da suka fara ita da Hajiya Kareemar_. Ragowar kuma ta kan ja ra'ayin masu zuwa ganin ta wato masoyan littattafanta na batsa da maɗigo wannan shine ta hanyar da takan samu ƴan mata. "haba Beauty kamar ba ƴar gida ba kin ƙi sakin jiki kici abinci ko dan ganin wa'innan ne", Saha ta girgiza kai. Hajiya Karima ta kalli Suhy da Zuby fuska ɗaure domin ita kanta ta lura da kallon da suke bin Sahabat ɗin dashi tace; "maza ku wuce naku ɗakin", ba dan ran su yaso ba suka nufi ɗakin suna me baƙin cikin hana su kallon yarinyar. Hajiya kareema ta taso ta dawo kusa da Sahabat ta zauna, sannan ta riƙo hannun Sahabat ɗin cikin salon yaudara da iskanci tace; "haba Beauty na faɗa miki ki dauke ni kamar Ummi mana bana jin daɗin yadda kike jan baya daga gare ni", Sahabat kuwa ta kasa cewa komai tsabar mamakin iskancin matar. Cikin dabara ta ƙwace hannun ta sannan ta ɗauki glass cup ɗin ta kai bakin ta, Hajiya Kareema kuwa har lokacin hankalin ta be wani dawo dai-dai ba, gashi dama bata gama samin natsuwa da Safeena ba Sahar ta zo gashi kuma zama da tayi kusa da Saha ya jifata wani hali. Saha kuwa banda jan tsaki babu abinda ta ke yi itafa ta fara lura da take-taken wannan matar kamar ƴar maɗigo ce, batama san a ina Ummi ta haɗu da ita ba, gashi dama can ita ƴan maɗigon ba birge ta suke yi amma zata zuba mata idanu taga gudun ruwan ta. Ko minti biyar bata ƙaraba ta miƙe akan zata tafi, Hajiya Kareema jikin ta har rawa yake yi wajen kwasowa Saha kayan kwalliya turarrurruka, atamfa da abin hannu wai gashi nan taje tayi gayu dasu. Saha tace; "nagode sosai", Hajiya Kareema ta riƙo hannun ta tace; "kada ki damu ni me son ki ce, ni dai ina roƙon ki da kada ki juya mini baya", Saha ta ɗaga kai. Hajiya Kareema taja Sahar zuwa waje inda suna tafiya tana samun damar murza lallausan tafin hannun Saha ɗin, da Saha na gyara tafin hannun ta sosai don ta san Sahibinta na so wato Zaiyad. A harabar gidan ta tsaya sannan ta ƙwalawa Idris driver kira, babu ɓata lokaci yazo ta miƙa mishi key na mota sannan tace; "gashi ka kai mini Sweet Baby na gida", Saha ta bita da wani kallo wai Sweet Baby. Mota jibgegiya High lander ita ta buɗewa Saha baya ta shiga, sannan Idris ɗin yaja motar, tana tsaye tana ɗagawa Saha hannu har suka fice daga gidan. Hajiya Kareema ta sauke ajiyar zuciya sannan tace; "ai tunda na ƙwallafa rai akan ki sai na sami abinda nake so yarinya ki gama gudun ki", ta faɗa tana ƙarasa shigewa ciki. Tun daga falo ta fara ƙwalawa su Suhy kira, Suhy da Zuby da suke manne da juna dan suma ganin Sahar ba ƙaramin tayar musu da hankali yayi ba. Hajiya Kareema ta kuma ƙwala musu kira babu shiri suka saki juna suka yo waje domin jin me yake faruwa, Hajiya kareema na ganin su ta ƙara kusa dasu ta janyo Zuby jikin ta yayinda ta haɗe bakin ta dana Suhy da sauri nan suka shiga aikata masha'ar su. *wa'iyazubillah* ********** *********** Kwanaki nata shuɗewa inda a yanzu saura kwana uku a ɗaura auren Abdulkareem da Jamila, babu masifar da Jamila bata yi ba amma Abdulkareem yaƙi fasa auren saima Allah yake a kawo masa amaryar sa koya sami sauƙi. Yauma ƴan uwan shi ne suka kawo mata kayan faɗar kishiya, Salma ta tuna da huɗubar Jameela inda take cewa kada ta yarda ta raga musu dan suma munafikai ne. Salma tabi matar yayan shi da kallo bayan ta gama ɗaga mata kayan wai nan tana nuna mata, Salma tayi yaƙe sannan tace; "ina zuwa", sun ɗauka tukwuici zata basu har suna washe baki dan basu san me take yiwa Abdulkareem ɗin ba dan baya zuwa gida ya faɗa musu. Salma kuwa galan na kalanzir ta ɗauko da ashana, suna zaune sai ganin ta suka yi da kalanzir da ashana ta buɗe galan ɗin ta fara tsiyayawa saman kayan. Duk suka zuba mata idanu, sai da ta gama tass sannan tace; "kune munafikai wato ko harda ku za'a haɗa baki a kawo wata cikin gidan nan to zaku ga aiki da cikawa kuma na tabbatar muku yadda na ƙona kayan nan haka zan ƙona amaryar zaku san dani kuke magana", tana gama faɗar haka ta cilla asha saman ƙaramin akwatin. Da sauri ƴan uwan suka ɗauke ragowar biyun da kada suma su kama yayin da ƙanwar Abdulkareem ɗin ta yi waje da gudu domin ɗebo ruwa tazo ta sheƙawa akwatin da yake ci. Cikin fushi Gwaggon su tace; "Salma wannan wane kalar rashin hankali ne?, bafa kanki aka fara kishiya ba kuma ba'a kanki za'a gama ba kiyi haƙuri mana komai zai zo ya wuce amma kina ƙona dukiyar mijin ki kamar wani kayan bola babu damuwa babu komai". Salma cikin rashin kunya tace; "dakata Safiya ai ban ga hakan a cikin gidan ki ba idan kina so ki nuna mini zahiri sai kije ki cewa Habu ya ƙara miki wata daga nan nima zan yarda da abinda kike faɗa amma ke kina zaune a gidan ki tsofai-tsofai dake kin kanainaye naki mijin da asiri da tofe-tofe da jiƙe-jiƙe ni kuma sai ki kwaso ƙafa kizo don ki taimaka wajen a kawo mini kishiya to wallahi ki kwashi ƙafafun ki dake da ƴan koron naki kan nayi muku na cikar shekara", bata gama rufe baki ba Ƙanwar Abdulkareem ɗin ta kwashe ta da mari, Salma ta buɗe baki zata kuma magana ta ƙara kwashe ta da mari. Cikin fusata tace; "ko Yaya Abdulkareem ba zai kalli Gwaggo ya kirata da sunan ta ba balle ke da kike cin arziƙin zama dashi, wallahi kika sake kika kuma kallon Gwaggo da sunan zaki yi mata rashin kunya sai mun lalllasa ki a gidan nan kuma aure babu fashi sai mun shigo da Amarya gidan nan ko ki so ko kada ki so banza ballagaza ke waye yace kada ki kama naki mijin tunda kin saki wata kuma ta cafke a waje ba shikenan ba Shashasha soloɓiyo". Gwaggo ta dakatar da ita tace; "barta Halima ta cigaba da abinda take yi idan har hakan shi take ganin dai-dai lallai Salma kin canza dole Abdulkareem ya ƙaro aure abinda kika faɗa mini kuma kije dan kanki, mu haƙuri mu kazo baki tunda baki so shikenan bama neman tashin hankali kuzo mu tafi". Salma ta taɓe baki tace; "ku kwashe kayan tsiyar ku ku tafi dashi dan babu abinda zan yi dashi, ke kuma wallahi sai na rama mari na", ta ƙarasa tana nuna Halima, Halima tace; "a shirye nake ai ina jira mahaukaciya ƙazama kawai", haka suka tattara kayan suka tafi dashi. Koda suka koma gida zancen da aka dinga maimaitawa kenan inda wasu suka dinga kare ta akan zafin kishi ne wasu kuma suka dinga zagin ta, har ma akwai wanda suka so komawa gidan suyi mata rashin mutunci mayan suka hanasu. Ita dai wacce ta riƙe Abdulkareem ɗin bata ce komai ba sai dai fuskar ta zai nuna maka bata ji daɗin hakan ba, koda Abdulkareem yazo Halima ita ta tare shi ta faɗa mishi hankalin shi ya tashi sosai har ƙasa ya durƙusa yana bata haƙuri, Gwaggon tace babu komai ai ya wuce. Kaya kuwa sai dai ƙannen nashi ne suka saka omo suka wanke su tas bayan sun bushe suka maida akwatin suka ajiye, Mariƙiyar shi ita ta amsa ta ɓoye ƙasan gadon ta dan shi Abdulkareem ɗin har yace musu ma su raba a tsakanin su ta hana. Salma kuwa nan ta kira Jameela ta bata labarin abinda ke faruwa, Jameela ta hau yi mata kirari tana ƙara Zugata, ita kuwa Salma sai washe baki take yi ganin cewa Jameelar na matuƙar sonta. Salma tace; "wai yaushe zaki zo gida na ne?",Jameela tayi murmushi tace; "nan bada jimawa ba, amma idan na tashi zuwa zan zo miki da abin mamaki ne". Salma da bata fahimta ba ta kwashe da dariya tana faɗin; "kamar kin san ina son surprise", Jameela tace; "shi yasa zan zo miki dashi ai", nan suka yi sallama. Jameela taja tsaki tana faɗin; "mahaukaciya keda kike cikin gidan mijin ki maimakon ki riƙe shi hannu biyu amma kin tsaya wasa matan da yanzu kamar su kai kansu gidan miji haka suke ji ƴan mata sunyi yawa a gari ga zaurawa suma amma kin wani tsaya sanya ai zaki ga aiki da cikawa ne", ta ƙarasa tana miƙewa daga inda take. Koda daddare Abdul be nunawa Salma komai ba itama bata nuna mishi ba, hasalima yanzu ɗakin Amarya yake kwana dan tun ranar data neme shi ya nuna mata bata isa ba suka ɓata gaba ɗaya, nan ta hana shi shiga ɗakin babu arziƙi ya tattara ya koma ɗakin amarya. Allah yasa ma sai gobe zasu zo danki, daga gobe kuma dole ya canza wajen kwana haka ya kwanta yana me janyo wayar shi ya hau fira da abar ƙaunar shi. Washe gari aka zo aka yi danki, inda nan ma sai da Salma ta nuna halin ta dan sai da suka tafi da ita a baki. Ita kuwa babu abinda ya dame ta, ji take wannan shine dai-dai kuma har yanzu ta yarda da maganar Jameela akan Abdulkareem ɗin zai iya tsorata yace ya fasa. Dangin amarya kuwa sai da suka kulle ɗakin tsaf sannan suka tafi da makullin gudun abinda zata iya aikatawa bayan sun tafi. Abdulkareem ranar sai cikin motar shi ya kwana, washe gari kuwa ko idanun shi Salma bata gani ba yana dai jiyo hayaniyar ta a ciki nan ya wuce can gidan su dama tuntuni ya kai su Husna can acan ya karya sannan yayi wanka ya canza kaya. Sai dare sannan ya koma nashi gidan, abin mamaki yau tsabar masifa ma Salma ko wayar bata danna ba dan wani irin zafi zuciyar ta yake yi mata. Kamar ba zai shiga inda take ba sai kuma ya shiga, hannun shi ɗauke da leda, yayi sallama ko kallon shi bata yi ba ta dai amsa sallamar. Ya saba da halin ta yanzu dan haka yace; "ga kayan ki nan na fitar biki tunda baki amshi akwatin ba, na kaiwa su Husna nasu, dan Allah Salma ki dena abinda kik........". Cikin fushi ta shaƙi wuyan shi sannan cikin ihu tace; "ka fita ka bani waje Abdulkareem!!!", sosai abin ya bashi mamaki dan be taɓa jin sunan nashi a bakin ta ba. Ganin yadda ta koma kamar mahaukaciya yasa ya bamɓare hannun ta daga jikin shi ya juya zai fice, ta ɗauki ledar da jefa mishi a jiki ya juyo da sauri, cikin sanyin murya kuma tace; "dan Allah ka ɗauke bana so", ta ƙarasa muryar ta na rawa. Sosai ta bashi tausayi, a wajen ta zauna ta fara kuka, ance soyayya daban take dole Abdulkareem yaji wani abu ya caki zuciyar shi ya san da cewa Salma itace macer da yaso so na gaskiya. Da sauri ya ƙaraso inda take ya ɗago ta, Salma da kamar ma bata hayyacin ta abu ɗaya take ambata shine; "ka tafi ka bani waje kawai", be saurare ta ba haka ya ɗauke ta ya kaita har saman gadon ta ya kwantar. A hankali yake shafa gashin kanta tana sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya yace; "Salma kiyi haƙuri duk abinda ya faru kece kika janyo mana, ki ɗauki aure na a matsayin hukunci daga ubangiji ki sassautawa kanki haka mana, na san da cewa kina sona har yanzu dan auren soyayya muka yi dake amma meyasa kika canza mini lokaci ɗaya?". Bata ce komai ba sai dai har lokacin hawaye na zuba daga idanun ta, haka ya dinga kwantar mata da hankali cikin dabara kuma cikin taimakon Allah taji ta ɗan sami sauƙi. Ranar dai tsakanin Abdul da Salma sunyi kwanan farin ciki duk da babu abinda ya shiga tsakanin su, asuba suka tashi inda yace; "ki tashi yanzu kiyi sallah", babu musu ta tashi tayi. Yana dawowa haka suka kuma shan barcin su cike da ƙaunar juna, Abdul yayi ƙoƙari wajen kaudar da damuwar da Salma take ciki. Sai takwas suka tashi, nan suka shiga kitchen tare suka samawa cikin su abinda zasu ci, sai da suka gama sannan yace; "yanzu ki tashi muje mu gyara gidan nan kinji", fuskar ta cike da damuwa dan ta tuna ko jiya sai da Auntyn ta ta kira ta akan zasu zo su taya ta gyara tace bata so suyi zaman su. Abdul ya riko hannun ta yace; "kada ki damu Matata ki muje muyi aikin mu", tayi murmushin da be kai zuciya ba sannan ta miƙe. Sunyi aiki sosai da sosai dan irin yadda gidan yayi datti, har wajen azahar basu gama ba gashi da an idar da azahar ɗin za'a ɗaura auren, har ma abokanan shi sun fara kiran shi. Ya cire hannu daga wankin da suke yi ya kalle ta cikin damuwa yace; "bari nazo na shirya na tafi amma zan kira miki su Aunty Maryam kinji kada ki damu", tayi murmushin yaƙe tace; "to. Ta bishi da kallo har ya shige ɗakin, kasa cigaba tayi da wankin ta tsaya kawai, ita ba tunani ba ita ba aikin ba. Har yayi wanka ya shirya tana tsaye, ƙamshin da hancin ta ya fara kawo mata ne yasa ta ɗaga kai ta kalle shi, kamar ta ɗora hannu akai tayi ihu haka take ji. don mijin ta data gani sanye da farar shadda ƙarr da ita wacce aka yiwa aiki da zare me ruwan ƙasa yayi kyau sosai wular kanshi da takalmin shi sau ciki duka ruwan ƙasa ne, ga wani irin ƙamshi dake tashi a jikin nashi wanda ya buɗe gidan. Yayi mata murmushi sannan ya matso kusa da ita ya bata kiss a goshi yace; "zan tafi kada nayi latti azo ana jira na", ta ɗaga kai kawai. Ya kwanto ta jikin shi sannan yace; "babu rako ma Sweet", ba dan taso ba ya riƙe hannun ta har zuwa bakin get ɗin gidan, ita dai binshi take kawai da kallo. Shigowar ƴan uwan ta nan suka hau yi mishi tsiya yana dariya, Salma kuwa babu eh babu a'a, sai da suka gaisa cikin sakin fuska sannan suka wuce suka barsu. Yace; "zan tafi", ta ɗaga mishi kai ya langwaɓar da kai yace; "babu addu'a", tace; "Allah ya kiyaye hanya yasa a ɗaura lafiy....." bata ƙarasa ba hawaye suka fara zubowa daga idanun ta. Ya ciro handkerchief ya hau goge mata sannan yace; "kiyi haƙuri ki dena zubar da hawayen ki haka Salma haba Uwargida ki zama jaruma mana, ki zauna kusa da wayar ki anjima zan kira ki", ta ɗaga kai kawai ya kaiwa lips ɗin ta kiss sannan ya sake ta ya fita. Ta daɗe tsaye a wajen tana sharar hawaye, zuciyar ta kamar zata tsago ƙirjin ta ta fito haka take ji, ga wani iri da numfashin ta keyi yanzu shikenan zasu zama su biyu wajen mijin ta. A sanyaye ta koma cikin gida inda ta tarar da ƴan uwan nata har sun gama wankin sun ɗora mata abinci. Auntyn ta Aunty Maryam ta balla mata harara tace; "ji yadda kika maida kanki ko?", Salma ta sauke kanta ƙasa. Aunty Jidda tace; "mijin ki na son ki amma kin bi kin sa duk ya juya miki baya ai wallahi da ba dan ya kira Abban Aarif ba da ba zan zo ba ki zauna kici haukar ki shashasha kawai". Aunty Maryam tace; "barta Jidda wallahi ta cigaba da ɓata mishi rai ya sako ki, ki koma gida dama Abba yace ai ki bari mijin naki ya sako ki ki dawo gida sai kin gane baki da wayo". Aunty Sameeha tazo ta riƙe hannun ta sannan tace; "kai Jidda da Maryam ku bar mini ƙanwa haka, kinji zo muje ciki kije kiyi wanka na tsantsara miki kwalliya kema kada amarya tazo ta raina ki". Maryam da Jidda suka yi dariya suka ce; "Allah matar yaya Salman ce bata da hali kwata-kwata". Nan dai Sameeha taja hannun Salman suka shiga ciki, da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta shiga tayi. Tana fitowa wayar ta ta hau ƙara, ganin me kiran sai da gaban ta ya faɗi, amma haka ta daure ta ɗaga, a can ɓarin taji yace; "Uwargida an ɗaura", ba tare da tace komai ba ta katse wayar kawai ta saki kuka. Aunty Sameeha ta hau rarrashin ta tare da yi mata nasiha, ita dai Salma yanzu gani take ma Sameehar ba son ta take yi ba. Haka tayi banza da ita, su Aunty Maryam ne suka shigo ganin yadda Salmar ke kuka Sameehar na lallashin ta abin ya basu haushi nan suka hau Salmar da faɗa babu arziƙi ta goge hawayen ta, Aunty Sameehar ta hau yi mata kwalliya. Shaddace ruwan toka wacce taji aikin wuta da stones doguwar riga ce tayi kyau sosai, nan Aunty Sameehar ta kashe mata ɗauri me kyau, Aunty Maryam tace; "da kyawun ki da komai amma kin zauna kin ɓata wayon ki gashi mijin naki akwai ƙoƙari wajen siyo miki kayan kwalliya, nan dai suka ƙara yi mata nasiha sosai. Sai lokacin Salma taji hankalin ta na ɗan kwantawa ga kuma jikin ta da yayi sanyi jin yadda ƴan uwan nata suke mata wanka me kamar jirwayi, ga wasu ayoyi a alƙur'ani da suka janyo mata su wanda Salma duka ta san ma'anar su dan ba jahila bace, basu ƙyale ta ba sai da suka tabbatar da ta fara dawowa hayyacin ta sannan suka ce ta tashi ta fita. Babu musu ta miƙe ta fita inda tana fitowa mijin nata yana shigowa da abokanan shi, nan fa suka hau tsokanar ta wai ta zama tsohuwa ita dai murmushi kawai take yi domin bata da kuzari, gashi ta kira number din Jameela amma bata ɗaga ba. Haka ta tura mata da text akan an ɗaura auren ta taya ta da addu'a, Jameela na ganin saƙon ta saki shewa tana dariya. Sun yi barkwanci sosai tsakanin ango da abokanan shi kafin aka ɗauki hotuna har zuwa wani lokaci sannan suka fice daga gidan. kamar yadda al'adar kaduna take, sai da aka gama dinner ƙarfe goma sannan aka nufo da amarya gidan ta, a lokacin kuwa Salma na saman dadduma dan tun wajen takwas ƴan uwan nata suka bar gidan inda aka bar mata ƙanwar ta Fiddausi da kuma Fatima, to su ɗin ma kowacce tana kan waya tana faman fira da saurayi. Jin guɗa yasa gaban Salma faɗuwa dan bata je dinner ba saboda kunyar ƴan uwan Abdulkareem ɗin da take yi na ganin irin rashin mutuncin da tayi musu. Sallama taji a falon ta wanda ya bata tabbacin an kawo mata amarya ne, ta kalli su Fatima sannan tace; "Fatima muje falo", dole suka ajiye wayoyin suka fito duka. Nan aka gabatar da Amarya ga Uwargida aka kuma damƙa amanarta gare ta tare da ƴan nasihohi, Salma cikin sanyin murya tayi godiya tare da jaddada musu insha Allahu zata riƙe amana ƙarshe tayi addu'a sosai wanda hakan yasa ƴan uwan amaryar jin ta birge su, duk da sukar ta da ƴan jere suka kai amma yanzu ta wanke wancan Jameela kuwa ba haka ranta yaso ba amma babu yadda zata iya. Haka suka tashi suka tafi suna yaba halin ta wasu na cewa ladaf tayi dan babu yadda zata yi wasu kuma suna cewa halin tane hakan. Salma kam suna fita ta koma ciki kan daddumarta tana ƙara neman yafiyar Allah akan abinda ta aikata tare da neman taimakon Allah. Anya kuwa tuban gaskiya kika yi Salma🤔. Sai wajen sha ɗaya sannan ango ya shigo gidan, Salma na jiyo haniyar su har suka gama duk abinda zasu yi.na al'ada sannan aka yi addu'a aka watse. Nan Ango yace; "amarya tashi kiyi alwala muyi sallah", kasancewar ba yarinyar bace ta san hakan babu musu ta tashi tayo alwala. Sai da suka gabatar da sallah raka'a biyu nan yayi addu'ar da manzon Allah ya koyar sannan ya tambaye ta game da addinin ta babu laifi ta ɗan bashi amsa. Yayi.murmushi yana me tuna lokacin da suke amare shida Salmar shi yadda ta amsa mishi tambayoyin cike da birgewa da kuma nutsuwa. Ya riƙo hannun Jameelar yace; "zo muje wajen Auntyn ki", Jameelar kam haushi taji sosai amma ta dake tace; "to muje", ya ɗauko ɗaya daga cikin ledojin dake ajiye a saman center table kana suka fice. Da sallama suka shiga ɗakin, ganin haske a ciki ya tabbatar mishi da cewa idanun Salmar biyu, ya kalli Jameelar yace; "zauna anan bari na shiga na kira ta", Jameela ta taɓe baki sannan ta zauna yayin da shi kuma ya shiga don kiran Salmar. A Zaune a saman gado ya same ta , ta zuba tagumi yayin da Fatima da Fiddausi ke fama barci abin su hankali kwance. Yadda ya ganta ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, yana yin sallama ta ɗago ta kalle shi sannan ta amsa. "kizo falo ina son ganin ki", be jira cewar ta ba ya fito itama kuma bata ce komai ba ta miƙe ta biyo bayan shi gaban ta yana faɗuwa. Koda ta fito kan amaryar yana sauke a ƙasa dan haka bata ganin ko fuskar wacece, Salma taje ta zauna saman one seater, Abdulkareem yayi addu'a sannan ya ɗora da yi musu nasiha akan su zauna lafiya ya kuma ce jameela itace ƙarama dan haka ta girmama Salma yayin da yace Salma ita kuma ta kama girmanta sannan ta su.riƙe juna amana babu wacce tafi wani a wajen shi duka so da ƙauna ne ya haɗa su kuma dukan su so iri ɗaya yake yi musu su zauna lafiya. "sannan batun kwana ya kuke ganin za'a dinga yi", Salma tace; "ta zaɓa duk yadda ta zaɓa shikenan". Abdul yace; "a'a kece babba dan haka ke ya kamata ki zaɓa", Salma tace; "shikenan bibbiyu ina ganin hakan yayi ai?". Abdul yace; "to kamar yadda addini ya tanadar budurwa ana yi mata sati ɗaya ne bazawara kuma kwana uku, don haka zan yi mata kwana uku tukunna sai kuma a koma kwana bibbiyu, Amarya ke hakan yayi miki?". Jameela tace; "eh yayi tunda haka ta zaɓa a barshi a hakan amma da sai nace kwana biyu gaskiya yayi.mini yawa dan ba zan iya jure rashin miji na a kusa dani ba har tsayin kwana biyu bayan na san can inda yake ba wai kula yake samu ba". Dum gaban Salma ya faɗi, dan tabbas muryar Jameela take jiyowa idan har kunnen ta ba ƙarya yake yi mata, Abdul kuwa kasa cewa komai yayi fatan shi ɗaya kada Salma ta tanka dan baya so su fara hayaniya tun yanzu dan haka ƙoƙarin shi na kauda maganar yasa ya miƙe sannan yace; "taso muje". Jameela har ta miƙe Salma tayi sauri ƙarasawa gaban ta, ta ɗaga mayafin data rufe fuskar ta dashi, cikin kiɗima da mamaki tare da ruɗewa tace; "Jameela!!!! Kece matar da miji na ya aura yau, Jameela kece kika aure mini miji??". Jameela tayi wani munafikin murmushi tace; "nice mana Ƙawata Aminiya ta ya san ranki, ai dama nace miki zan zo.miki da abin mamaki ya kika gani?". ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [25/03, 14:02] Yaya Umar: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say: "The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path [un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire." [Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)] عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: إِنَّ أَوَّلَ النَّاسِ يُقْضَى يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَيْهِ رَجُلٌ اسْتُشْهِدَ، فَأُتِيَ بِهِ فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ قَاتَلْتُ فِيكَ حَتَّى اسْتُشْهِدْتُ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ قَاتَلْتَ لِأَنْ يُقَالَ: جَرِيءٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ تَعَلَّمَ الْعِلْمَ وَعَلَّمَهُ وَقَرَأَ الْقُرْآنَ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: تَعَلَّمْتُ الْعِلْمَ وَعَلَّمْتُهُ، وَقَرَأْتُ فِيكَ الْقُرْآنَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ تَعَلَّمْتَ الْعِلْمَ لِيُقَالَ: عَالِمٌ، وَقَرَأْتَ الْقُرْآنَ لِيُقَالَ: هُوَ قَارِئٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ، فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ وَسَّعَ اللَّهُ عَلَيْهِ، وَأَعْطَاهُ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ كُلِّهِ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: مَا تَرَكْتُ مِنْ سَبِيلٍ تُحِبُّ أَنْ يُنْفَقَ فِيهَا إِلَّا أَنْفَقْتُ فِيهَا لَكَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ فَعَلْتَ لِيُقَالَ: هُوَ جَوَادٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ، ثُمَّ أُلْقِيَ فِي النَّارِ. رواه مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي) ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Five_ ~*Page 24*~ Cikin fushi Salma ta ƙaraso kusa da Jameela ta fincikota, tace; "wallahi baki isa ba dole ki bar mini miji na, na baki amana shine zaki ha'ince ni?". Jameela ta taɓe baki tace; "wannan kuma matsalar ki ne, ke in banda hauka kalar taki taya zaki sami miji kamar wannan amma ki zauna wasa", Salma kuwa babu abinda take banda jijjiga Jameela tana kuka. Abdulkareem kuwa da yaga abin ba zai ƙare ba, da kanshi ya hau raba su, da ƙyar ya fincike Jameelar a hannun Salma. Salma kuwa lokaci guda ta fita hayyacin ta, babu abinda take yi sai kuka idanun ta sam sun rufe faɗi take; "macuciya Allah ya isa tsakani na dake". Abdulkareem dai jan hannun Jameela yayi suka fice daga ɗakin, Fatima da Firdausi wanda hayaniyar su Salmar ya tayar dasu, Fatima ta riƙo Salma wacce ke kwance saman tiles tana kuka tace; "Aunty kiyi haƙuri". Salma tace; "Fatima ku tafi ku bani waje, mutane gaba ɗaya macuta ne basu da amana, Fatima kije nace", dole haka Fatima ta tafi ta barta. Salma bata tashi daga wajen ba har aka yi kiran sallar asuba, haka ta miƙe jikinta babu ƙarfi ta shiga bayi tayi alwala ta hau darduma ta fara sallah. Sai da ta idar sannan ta tashi su firdausi domin suma suyi sallah, kan kujera ta koma ta kwanta tana tariyo rayuwar su ta baya ita da Abdulkareem ɗin. Har gari yayi haske sannan su Firdausi suka fito suka shiga kitchen domin haɗa abiɓ kari, Salma na kwance tana jinsu amma saboda yadda zuciyar ta da jikinta babu daɗi yasa ko ɗago kai bata yi ta kalle su ba. Sai da suka gama sannan Fatima tazo ta tsugunna kusa da ita tace; "Aunty Salma mun gama, zamu kawo miki naki ne nan?", Salma tace; "kuci kawai idan zanci zan muku magana", Fatima ta ɗan yi jimm sannan tace; "shikenan". Fiddausi ta jera abincin saman tray sannan ta nufi part ɗin amarya dashi, sai dai me tana zuwa ta samu a kulle dan haka ta bubbuga. Ɓangaren Amarya da Ango kuwa suna zuwa ɗaki Jameela ta mantar dashi wata Salma haka suka sha love ɗin su a matsayin su na sababbin amare. A lokacin da Firdausi ta buga ƙofar suna bayi suna wanka tare, Jameela cikin salon ɗaukar hankali tace; "Annurin zuciyata bari na duba naga ko waye", da gayya ta saka ƙaramin towel ta fito a haka kai a jiƙe don ta san Salma ce kuma tana so ta baƙantawa Salmar rai. Sai dai kash! Tana buɗewa taga Fiddausi dan haka ta haɗe rai, Fiddausi kuwa ta ƙaƙalo murmushi tace; "barka da safiya Amarya dama Aunty ce tace na kawo muku abin kari". Jameela ta harare ta sannan tace; "kije kice mata bama buƙatar abincin ta domin iya abinda na bashi da daddare jiya da wanda ya bani ya ishe mu yinin yau", tana gama fadar haka ta maida ƙofar ta rufe. Fiddausi ta kama baki tana mamakin halin Amaryar, haka ta maida kayan zuwa ɗakin Salma wacce bama ta san anyi ba, Fatima tana karyawa taga Fiddausi ta tulin abinci ta dawo. "meya faru kuma?", Fiddausi ta faɗawa Fatima duka abinda ya faru, Salma tana jinsu sai dai bata da ishashshiyar lafiyar da zata amsa musu. Haka suka dinga didimar su har sai da Maman su tayi kiran su akan su koma gida sannan suka tattara kayan su suka tafi. Ɓangaren amarya da ango kuwa bayan ta koma tace; "matar ka ce tazo yi mini gargaɗi wai kona bar gidan nan ko ta kashe ni", yayi murmushi me ciwo cikin ɓacin rai yace; "da kuwa na ɗauki mummunan mataki akanta". Jameela tayi munafikin murmushi, sai da suka taimakawa juna suka shirya sannan Jameela ta shafa cikin ta tace; "Haskena yunwa nake ji fa". Yayi ɗan jim sannan yace; "bari naje na amso a wajen Maman Husna idan ta girka", ba tare da tace komai ba ya juya ya fice. Da sallama ya shiga ɗakin, komai a gyare yake fes dashi, Salma tunda ta ɗago ta kalle shi ta maida kanta tana rufe idanu, zuciyarta kamar ta tsago ƙirjin ta, ta fito haka take ji dama ace zata iya ɗaukar wuƙa ta soka mishi ya mutu kawai kowa ya huta. Abdulkareem kuwa mamaki yake yi da tunanin sauyin halin Salma wato ko gaisuwa ba zai samu ba, cikin haɗe fuska yace; "ina abin karin mu". "Lallai namiji munafiki ne", abinda Salma ta faɗa kenan a ranta amma a fili tace; "bar girka daku ba", tana faɗar haka ta juyar da kanta gefe. "wai wannan wane kalar hali ne kika ɗauko Salma kamar kwana biyu kin dena yanzu kuma mugun halin yana so ya dawo?, Salma ni kike wulaƙantawa ko, har Jameela zaki je ki yiwa kashedi akan ta bar miki gida idan ba haka ba zaki kashe ta ko? Yanzu ban isa dake ba ko to kiyi duk abinda kike ganin zaki yi sai dai ki sani yadda na ɗauki wulaƙanci a da yanzu ba zan ɗauka ba domin kuwa da da yanzu da bambamci", yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin. Salma ta saki kuka wai ko zai sanyaya mata rai akan abinda Abdulkareem ɗin ya aikata mata, lallai rayuwa kenan. Yana fita ya koma ya cewa Jameela tayi haƙuri ta ɗora musu abin kari, cikin kissa tace; "ayya Haskena kada ka damu ni da nazo neman aljanna", yaji daɗi sosai a da ya san yaji kalan kalaman nan daga wajen Salma sai dai a yanzu da Jameela ta faɗa sai ya tabbatar da cewa ya cutu na samun rashin kulawa daga matar shi. Suna gama karyawa jama'a suka fara zarya domin ganin ɗakin amarya hakan yasa Abdulkareem ficewa daga gidan gabaki ɗaya. Salma na kwance zazzaɓi ya rufe ta kuma tana jiyo zuwan kowa har dangin su Abdulkareem ɗin amma babu wanda ya leƙo yace ci kanki nan fa ta fara zubar da hawaye domin ta san cewa Jameela ta cuceta kuma ta kaita ta baro domin kuwa itace silar da ta dinga yiwa dangin Abdulkareem ɗin rashin mutunci yanzu gashi sun dena ganin farinta yayin da Jameelar kuma ta sami damar shigewa ƴan uwan mijin nasu. Har dare Salma na kwance abinda yake tayar da ita sallah, su Husna ma an dawo dasu gidan amma abin mamaki babu wanda ya shigo inda take. Haka Salma ta kwanta cikin baƙin ciki, domin kuwa yaran ta ma gudun ta suke yi, wannan ya ƙara tayar mata da hankali. Ta kira yayyin nata tayi musu complain amma kowa cewa yake yi Allah ya ƙara ita ta jawa kanta. Ranar ma dai Salma bata yi wani barcin kirki ba domin kuwa ga rashin lafiya ga kewar yaran nata da mijin ta haka ta kwana a wahalce. Da safe kuwa da ƙyar take iya buɗe idanu saboda yadda suka kumbura gashi sunyi jajur dasu, ga wani irin ciwo da kanta yake yi. Abinda ke ƙara bata mamaki rashin shigowar mijin nata inda take tun jiya da safe da yazo ɗakin nata karɓar abinci be kuma takowa inda take ba. Haka ranar ma ta wuni a kwance sai dai idan taji yunwa ta janyo flask ɗin ruwan zafi ta zuba tasha sai kuma sallah. Kuma yanzu abin ya fara bata tsoro domin kuwa yaran nata sai dai ta jiyo hayaniyar su ɓangaren Amaryar haka duk wani wanda zai zo wajen ta. Tana neman me bata shawara a rayuwar ta, duk da ta san meya kamata tayi amma tana buƙatar me ɗora ta akai, Kuka kam da yana magani da yayiwa Salma har hawayen nata ma da ace suna ƙafewa da sun ƙafe kuwa tsabar kuka ta rasa inda zata saka rayuwar ta, kwana biyu kenan amma duk ta fige ta lalace. Washe gari zata amshi girki a hannun Jameela duk da dai amarya ce kuma tun daren farko basu kuma haɗuwa ba, ita Salma ko ƙofar ɗakin ta bata fita komai a ɗaki take yi dan tana da kitchen da bayi a ciki. Har lokacin bata da wata cikakkiyar lafiya, dan haka babu abinda tayi na gyaran ɗaki ko kuma girki ko dai wani abin. A haka Abdul yazo ya same ta, ya baje hanci ya shaƙi ƙamshin da yanzu Jameela ta sabar mishi amma maimakon haka sai ƙari da yaji domin kuwa har amai yau Salma sai da ta kwara shi. ya ja tsaki cike da jin haushi, ya kalli yadda ta kwanta can ƙuryar gado, ba dan Jameela ta koro shi ba babu abinda zai kawo shi wajen wannan matar wallahi. Ya ɗan matsa kusa da ita yace; "Maman Husna", Salma da tun shigowar shi tana kallon shi ta amsa da ƙyar yace; "ina abinci na". Ta ɗan yi jim sannan tace; "nifa babu abinda na dafa", ya ja dogon tsaki sannan ya fice, wajen Jameela ya koma ya marairaice mata inda ita kuma ta cika mishi ciki da abinci tana ƙara jan shi da fira sai da ya raba dare sannan ya baro ɗakin nata. Salma ta kalle shi sannan ta kalli agogo ɗaya saura, ta koma ta kwanta domin kuwa amai ne ya tada ita, Abdulkareem kuwa cikin alamun rashin gaskiya yace; "tunda baki dafa kin bani ba ai dole ne naje inda za'a bani". Salma tana jin shi amma ta kanta take yi dan haka bata tsaya bashi amsa ba, haka ya nemi waje ya kwanta. Wajen ƙarfe uku na dare jikin Salma ya ƙara tashi sosai, haka ta miƙe cikin jiri amma kan ta kai bayi aman yazo dan haka anan ta tsugunna ta fara kwara shi. Abdulkareem cikin barci yaji kakarin amai, dan haka ya sauko ganin Salma na amai a wahalce ya ɗaga hankalin shi sosai ya tallabota har ta gama sannan ya ɗaga ta ya nufi bayi da ita. Shi ya taimaka mata ta gyara jikin ta sannan ya kaita saman gadon ya kwantar da ita shi kuma yazo ya gyara wajen da tayi aman. Koda aka idar da Sallar asuba da wuri Abdulkareem ya dawo daga masallacin yazo ya ɗauke ta domin tafiya asibiti. Ɗakin Jameela ya ƙwanƙwasa ta buɗe ƙofa jikinta sanye da hijab wanda ke nuni da sallah ta idar. "Maman Husna ba ta da lafiya zamu je asibiti", ya faɗa mata, Jameela tace; "Innalillahi! Meya same ta? Bari na shirya mu kaita tare". Abdulkareem ya lumshe idanu yana jin daɗin yadda take nuna tsantsar ƙaunar ta ga shi da matar shi da ƴaƴan shi duk da ƙasan zuciyar shi yana gargaɗin shi akan Salma ma haka ta nuna da farko. Jameela data fito daga ɗakin tayi saurin tallabo Salma tana faɗin; "Haskena bari na riƙe ta", Salma taji wani abu ya caki zuciyar ta. Haka Jameela ta taimaka mata har suka isa motar Abdulkareem ɗin ya saka ta a ciki suka fice daga gidan. Wani asibitin kuɗi suka je wanda yake kusa, sun sami ƴan aikin dare basu tafi ba dan haka su suka yi mata duk abinda ya dace. Da yake asibitin kuɗi ne kafin gari yayi haske har sun gama mata komai an ɗaura mata drip ta sami barci ma. Ganin ƙarfe shida da rabi yasa Jameela tace; "Haskena bari naje gida ka san yara na suna da makaranta yau idan na shirya su suka tafi na sama musu abinda zasu ci sai na dawo". Yace; "muje na kaiki nima sai nayi shirin zuwa wajen aiki, tunda ta sami barci", haka suka miƙe suka fice daga ɗakin. Salma da duk taji abinda ke faruwa ta girgiza kai hawaye yana biyowa ta idanun ta, ga zafin ciwo ga kuma zafin kishi da kuma karayar zuciya data samu daga ƙawar tata kuma aminiyar ta. Tayi tunanin zasu dawo tare amma koda ta farka Jameela ta samu a zaune, Jameelar tana ganin ta farka tace; "sannu, mun dawo kina barci shine Haskena yaga zai yi latti yace bari kawai ya tafi". Salma bata ce komai ba banda kauda kai da tayi kawai, Jameela ta taɓe baki tace; "da kin haƙura kin bini a sannu da nima zan sassauta miki sai dai ki sani duk iya ɗaga hankalin ki da shige da ficen ki babu wanda zai yi tasiri a kaina dan haka ki kwantar da hankalin ki kawai, Abdulkareem yanzu sai Jameela haka Jameela sai Abdulkareem", tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin. Salma taja dogon tsaki tana me dangwarar da kofin data ɗauko domin haɗa abin kari, lallai dama bahaushe yace mutum mugun ice. Tana cikin wannan tunanin taga an turo ƙofa an shigo, ta ɗaga kai tana kallon wacce ta shigo, itama kuma Salmar take kallo tana murmushi. Salma ta zaro idanu, idan bata manta ba Habiba ce wacce ta taɓa kawo mata tallan kayan mata har tayi mata wa'azi akan irin yadda take tafiyar da gidan ta da ƴaƴan ta ta zauna ta wanke matar tas batare data duba shekarun ta ba. ************ ************** Ummi tace; "Saha wai wane sabon al'amari kika shigo mini dashi cikin gida ne?", Saha ta saukar da kanta ƙasa tace; "babu komai Ummi kawai yanayin zafin garin ne", Ummi tayi jimm tana kallon ta sannan tace; "shikenan". Saha ta sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya sannan ta wuce ɗakin su bayan ta ajiye bokitin, cikin sauri ta maida ƙofar ta kulle sannan ta faɗa saman katifar tasu. Lallai Ummi tana daf da gano ta, dole ta canza taku gudun kada Ummin ta fara zargin ta, wata zuciyar tace mata; "ba Ummin ke janyo miki ba". Ta maida idanu ta rufe tana tuno page ɗin jiya na littafin *MACE DA MACE* wanda wata marubuciya *Shukra* take rubutawa jiya aka fara turo shi group ɗin *MATAN HARKA* wanda Sahar take basaja a cikin shi kuma shine group ɗin da duk wata marubuciya me batsa da lesbian da kuma makarantan su suke ciki, Sahar ma da ƙyar aka saka ta a ciki sai da ta biya 5k sannan. Saha ta sake juyi tana me kallon ƴar uwar ta dake kwance a saman gadon, ita lesbian ba wani damunta yayi ba amma yadda marubuciyar ta tsara shi da yadda ake yabon abin dan jiya firar da suka yi kenan a group din sai taji tana sha'awar aikatawa ko yaya ne dan taji ya ake ji a cikin shi. Ta tashi zaune tana son taɓa Suraiya dake barci tana kuma tsoron abinda zai je ya dawo, ta ɗan ja tsaki tana faɗin; "dole ne nima na ɗan ji me akeji a ciki, amma bata haka zan biyo ba to yanzu ma waye zai koya mini yadda ake yin lesbian ɗin?", ta ƙarasa tana buga uban tagumi. Ganin bata da mafita dole ta kwanta domin dai tana jin tsoron taɓa ƴar uwar tata gudun farkawa kuma ta tona mata asiri sai dai dole zata canza taku inda zata janyo ƴar uwar tata da kuɗi da kuma kayan ƙwalama. Sai dai dole tana buƙatar me ɗorata akan hanya don haka ta yanke shawarar tuntuɓar wata yarinya wai ita *fici* ganin yadda jiya ta zaƙalƙale a group ɗin ya tabbatar mata da cewa ƴar hannu ce, da wannan shawarar barci ya kwashe ta. Koda safe bata farka da wuri ba dan haka Suraiya ce ta ɗora abin kari ta gama ta maida ruwan wanka sai da yayi zafi ta juye tayi sannan tazo ta hau tashin ƴar uwar ta. Saha tayi miƙa sannan ta miƙe, idanun ta ya sauka kan ƙanwarta ɗaure da towel nan da nan sheɗan ya fara ƙawata mata ƙanwartan. Suraiya kuwa ganin yadda yayarta ke kallon ta tace; "Aunty Saha ki tashi kiyi wanka kizo mu karya Ummi zata aike mu fa". Cikin sauri Sahabat ɗin ta dawo hayyacinta, sai taji muryar yarinyar kamar ana ƙara mishi zaƙi ne, ta saki munafikin murmushi sannan ta miƙe ta fice, ko wajen wankan surar ƙanwarta kawai take tunawa bata taɓa jin sha'awar mace ƴar uwar ta ba sai jiya zuwa yau kuma abin ban haushi wai ƴar uwar ta. Koda ta fito nan ta fara lissafin watannin da ya rage su Ummin su tafi taron ƙungiyar tasu, saura wata uku da ƴan kwanaki dan haka tana saka ran kan wannan lokacin xata shawo kan ƙanwarta inda zasu more kan Ummin ta dawo duk da dai bata da tabbas ɗin akwai daɗi ko babu. Ummi kuwa tana komawa ɗaki ta watsar da tunanin Sahar ta fara tunanin yadda zata tsara page ɗin gobe yafi na yau daɗi don jiya tasha comments ta kuma sami ƙuɗi sosai da sosai. Shukra har jinjina sai da tayi mata, Ummi kam ta karanta littafin Shukrar jiya dan haka itama yana ɗaya daga cikin abinda ya fara ɗaga hankalin ta. Sai dai ita bata da burin yin wannan harkar dan haka ta watsar dashi, safiya nayi kuwa ta baje saman kujera ta fara aikin nata wato typing. Saha data gama shiryawa cikin doguwar riga ta atamfa me ruwan shuɗi tayi kyau sosai gashi ɗinkin ya zauna a jikin ta dan ada ɗin kin yayi mata yawa amma ƙara buɗewar da tayi sai ɗinkin ya dawo ya zauna a jikin ta sosai kuma ya kamata. Suraiya kuwa riga da wando na pakistan ta saka me kalar pink da ratsin milk, itama tayi kyau dan yanzu ta fara girma sai dai ita tsayi gare ta saɓanin Saha da take da jiki yanzu. Ummi ta kalle su ta washe baki sannan tace; "ah lallai ƴan mata na sun yi kyau", Surayya ta rufe idanu tana murmushi, Ummi ta miƙawa Saha kuɗin tace; "gashi Hajiya Kareema ta aiko miki dashi jiya tace ki siya abinda kike so, na san dai akan kayan kwalliya zasu ƙare", Saha ta saka hannu ta amshi kuɗin. "ku siyo abinda ya kamata, kema ga naki sai ki taimaka mata ta siyo ɗan kayan ƙaleƙalen dan itama yanzu naga ta fara girma", Ummin ta faɗa cikin salon tsokanar Suraiyyar. Sahar ta haɗa duka ta amsa tana faɗin; "an gode sosai, insha Allahu zamu siyo kamar yadda kike bukata", itama Suraiya tayi godiya. Ummi tayi murmushi tace; "kada ku damu, ku dai ku tabbata kun dawo gida da wuri sannan banda shashashanci da kule-kulen maza a hanya", Saha tace; "to", tana jan hannun Surayyar suka fice. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [4/13, 8:49 PM] Sumayya Sumy B: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَال*َ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ اللَّهَ إِذَا أَحَبَّ عَبْدًا دَعَا جِبْرِيلَ، فَقَالَ: إِنِّي أُحِبُّ فُلَانًا فَأَحِبَّهُ، قَالَ: فَيُحِبُّهُ جِبْرِيلُ، ثُمَّ يُنَادِي فِي السَّمَاءِ فَيَقُولُ: إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ فُلَانًا فَأَحِبُّوهُ، فَيُحِبُّهُ أَهْلُ السَّمَاءِ، قَالَ: ثُمَّ يُوضَعُ لَهُ الْقَبُولُ فِي الْأَرْضِ. وَإِذَا اللَّهُ أَبْغَضَ عَبْدًا، دَعَا جِبْرِيلَ فَيَقُولُ: إِنِّي أُبْغِضُ فُلَانًا فَأَبْغِضْهُ، فَيُبْغِضُهُ جِبْرِيلُ ثُمَّ يُنَادِي فِي أَهْلِ السَّمَاءِ: إِنَّ اللَّهَ يُبْغِضُ فُلَانًا فَأَبْغِضُوهُ، قَالَ: فَيُبْغِضُونَهُ، ثُمَّ تُوضَعُ لَهُ الْبَغْضَاءُ فِي الْأَرْضِ. رواه مسلم (وكذلك البخاري ومالك والترمذي)* *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:* *"If Allah has loved a servant [of His], He calls Gabriel (on whom be peace) and says: 'I love So-and-so, therefore love him.'" He (the Prophet - peace and blessings of Allah be upon him) said: "So Gabriel loves him. Then he (Gabriel) calls out in heaven, saying: 'Allah loves So-and-so, therefore love him.' And the inhabitants of heaven love him." He (the Prophet - peace and blessings of Allah be upon him) said: "Then acceptance is established for him on earth. And if Allah has abhorred a servant [of His], He calls Gabriel and says: 'I abhor So-and-so, therefore abhor him.' So Gabriel abhors him. Then Gabriel calls out to the inhabitants of heaven: 'Allah abhors So-and-so, therefore abhor him.'" He (the Prophet - peace and blessings of Allah be upon him) said: "So they abhor him, and abhorrence is established for him on earth."* _[ Narrated; Muslim also by al-Bukhari, Malik, and at-Tirmidhi).]_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Six_ ~*Page 25*~ Taku kad'an suka yi bayan fitowar su daga gida suka yi nasarar samun mai adaidaita sahu. Kai tsaye kasuwar Central ya sauke su inda Sahabat take rik'e da hanun Surayya tana d'an murza su a hankali wani bak'on yanayi take ji a jikin ta a lokaci d'aya kuma zuciyar ta na k'wadaito mata son aikata abinda ta karanta a littafin *MACE DA MACE.* Surayya kanta tayi mamakin yanda take ta haba-haba da ita, bata karaya ba sai da suka isa wani tafkeken shagon Cosmetics, Mayuka masu tsadan gaske dasu Powder, turare, da sauran kayan makeup ta zage ta ringa ibar mata abin tsoro ya koma bata bayan sun kammala taga kud'in data fidda ta biya duka kayayyakin wanda tun a nan sun cinye kudin da Ummi tasu ta basu. Bayan sun gama da nan shagon suka nufi shagon kayan ciye-ciye da kwalamulashe ta nufa da ita, inda nan ma ta zage ta ibar mata su chocolate, sweet, biscuit da sauran su, Surayya kamar mutum mutumi ta zama domin gaba daya abin gani take kamar shirin film domin duk abinda ta dauko zata kalle ta da murmushi ta mik'a mata tare da fad'in. "My Sister wannan test d'inki ne" a haka har suka qarqare suka doshi wani Boutique inda ta siya mata Riga da skirt na English Wears masu tsada da k'yau guda biyu. Fitowa suka yi tare da nufan bakin hanya domin hawa adaidaita sahu ya sada su da gida. har a lokacin tana rik'e da hanun Surayya. "Assalamu Alaikum, Ranki shi dade, barka da da wannan lokacin" Abinda kunnuwar ta suka jiyo mata kenan da wani murya mai kama da busar sarewa, a tare suka juyo da Surayya tare da zuba mishi ido. K'warjinin da ya mata yasa bata san lokacin da bakin ta ya bud'e har ta amsa mishi sallamar da "Amin wa'alaikas salam" "Wow yanda komai yaji, haka Voice dinta yake nasan ciki kuma sai tafi haka" a zuciyar shi yake wannan zancen a zahiri kuwa wani lallausar yaudararriyar murmushin shi ya sake da har sai da gefen kumatun shi ya lotsa tare da mik'a hanun shi mai d'auke da zaran-zaran yatsu da nufin karb'ar ledar dake hanun ta cikin salon muryar shi ya ce; "Gimbiya wannan ba girmar ki bane rik'e shi, sai mu bayin ki" Qamshin turaren shi ya mutuk'ar birge ta kuma ya mata kamaceceniya dana abin k'aunar nata *Zaiyad*. Shigar shi ta mutuqar birge ta shiga ce ta qananan kaya daya dace da siffan jikin shi, Fari ne dogo, hancin shi d'an matsakaici, Sajen daya zagaye fuskar shi, ya qara ma fuskar k'yau da haiba wandaya sha gyara ya kwanta lub yana ta zuba shek'i. Dimple ne ya qara qawata fuskar tashi domin duk sanda yayi magana sai ya lotsa. "Na gode" ta fad'a ba tare da ta sakar mishi ledar ba. Kallon shi ya maida kan Surayya, " Sister na kawo in taya ki tunda Auntyn mu tak'i kawo nata." ya fad'a cikin narkar da muryar irin ta shagwab'ab'u. Kallon ta Surayya tayi inda taga bata ma kallon inda suke hankalin ta naga kan hanya. Ba tare da ta mik'a mishi ba yasa hanun ya karb'i babbar ledar dake hanun hagun ta. Sakar mishi tayi inda ya dube ta yace "Bismillah ranki shi dade, idan baza ki damu ba in sauke ki, domin bai kamata rana ya ringa samun rabon shi a jikin wannan lallausar fatar fatar ba." Ji tayi wani yamm kalamun shi suna fasa mata kai tare da jin kanta na qara girma. "A'a ka bar shi kawai na gode" "Haba gimbiya bai kamata ki hana bawar ki yi miki hidima ba a daidai lokacin daya dace ba tare da wani dalili ba instead ki bada Umarni kawai." Lumshe ido tayi tare da kai duban ta gun Surayya, "Sis muje." Ta fad'a a tak'aice tare da bin bayan shi har gurin da yayi parking d'in dalleliyar motar shi, gidan gaba ya bud'e mata ta shiga sannan ya bud'ewa Surayya baya ta zauna zagawa yayi ya tadda motar suka d'au hanya inda yake tambayar ta anguwar su ta fad'a mishi a tak'aice. "Abinda bata tab'a ba shi yau tayi domin har qofar gida sai daya sada ta wanda bata san lokacin da suka iso ba saboda irin kalaman dayake tsara mata wanda kuma suke tasiri a zuciyar ta, tana kuma mamaki dama ak'wai namijin daya iya jere kalamai kamar Zaiyad d'inta? Kalaman shi sun shagalar da ita sosai da sosai kunnuwar ta kuma basu gaji da sauraron su ba, wannan yasa sun so su wuce ma Surayya ce ta ankarar dasu inda yayi baya tare da goga parking a daidai qofar gidan. Bayan musayar namba waya da suka yi, sabbin rafa yan d'ari biyar ya dauka tare da mik'a mata na 20k a sanyaye ta qarb'a tare da yin godiya, bud'e murfin motar tayi ta fito wanda Surayya tuni ta riga tayi shigewar ta cikin gida, yana tsayawa ta balle murfin motar tayu shigewar ta domin irin yanda taji yana sakar magana kai tsaye gaba daya sai taji ta a takure. Saukar ta yayi dai-dai da fitowar Baba Mariya daga gida zata anguwa, da mamaki ta dube ta tare da bin bayan motan da kallo hanun ta rik'e da bakin ta lallai abinda jama'a suke fad'a a kan Sahabat dama da gaske ne ashe? Tunda gashi ta gani da idon ta. An sauke ta ga siyayya ga kuma maqudan kud'ad'e a hanun ta Yooo wannan zamani da ake ciki idan ba fasiqanci za ai dake ba wani namiji ne da bai ko tura gidan ku ya nemi izini ba zai ringa miki irin wannan hidimar? Gaisuwar Sahabat d'inne ya katse mata tunani. Inda ta amsa da "Lafiya Saha" Har ta ratsa ta zata wuce tayi saurin tsaida da ta. "Uhumm nace ba Saha." Cak ta tsaya tare da d'an yin baya a daidai lokacin kuma da take qoqarin saka kud'in cikin Purse d'in dake hanun ta. "Kiyi hakuri, zan shiga abinda ba ruwa na amma ina ganin wannan shine zaman tare saboda hakkin maqotaka ya wuce wasa sannan irin zaman amanan da akayi da mahaifin ki mutumin kirki Allah ya qara masa rahma, ya gafarta masa zunuban sa." "Amin" ta amsa jikin ta a sanyaye domin tana mutuk'ar ganin girmar Baba Mariya, tana da kamala da kamun kai sosai sannan kome na anguwa tana tashi tsaye abinda ya shafi zamantakewa da mak'wafta da sauran su duk wani abinda zai taso sune a gaba-gaba. Cigaba tayi da magana "Saha maganganun dana ke ji a kanki sam bana jin dad'in su duk da bangani ba a zahiri amma masu fad'ar na tabbatar da baza su mik'a qage ba ko sharri, sannan yanzu kuma na ga saukar ki a mota da kuma yanayin dakika sauka.". Ta fad'a tare da nuna hanun ta, "Saha dan Allah kiyi hakuri ki rik'e maraicin ki, ki duba girmar Allah. Ki sani duk abinda kika yi na alkhairi ko akasin sa sai an isarwa mahaifin ki. Mahaifin ki mutumin kirki ne mai qoqarin ganin ya k'yautatawa duk wanda ya rab'e shi, baida abokin fad'a ko gaba tsawon zamana dashi a anguwar nan tun kafin yayi aure ban tab'a ganin wani abun asha dayayi ba. Samarin zamanin nan ba abinda yake gunsu sai rud'u da yaudara ki yi tunani, har yau banji ance ga garon tambayar ki ba, amma koda yaushe sai dai ace ga shinan an dauke ki mota an sauke ki nan aikin kenan abubuwa marasa dad'i bazan b'oye miki ba naso zuwa in samu mahaifiyar ki kan zancen amma kuma wai-wai nake ji amma kinga yanzu da ido na ya gane min ban bari ki wuce ba na tsaida ki. Dan Allah Sahabat ki kula ki kame kanki, ki tsare mutunci ki na ya mace Dana iyayen ki, ki kare martabar ki domin duk namijin da yake miki soyayya ta gaskiya tsakani da Allah bazai fara tsaida ki hanya ba yana hure miki kunne da kalamun shi na yaudara face ya dangana da gidan ku ko ya nemi wani naki domin neman izinin hakan. Wannan shine kuma addinin, da al'adar mu suke tafiya akai, kuma yin hakan shi ne siya ma kanki daraja a idon duniya da kuma shi kanshi namjin idan Allah yayi mijin ki ne, saboda maza ba tabbas suke dashi ba. Sun aure ka tare sun same ka a mutunci ma sun wulaqanta ka idan ba'ayi sa'a ba ballantana." Sahabat da tunda ta fara maganar kanta yake qasa da farko maganganun sun b'ata mata rai, suka koma bata mamaki sako zancar mahaifin ta kuma ya sanyaya mata jiki. Tabbas duk maganganunnta haka ne amma kuma fa Baba Mariya baza ta gane ba domin wani al'adar neman aure etc duk wannan a zamanin su ne yanzu ana Digital life ne komai is modern ake yi. A sanyaye ta amsa da "Na gode Baba Mariya" "Allah ya miki albarka dan Allah a ringa hattara" Shigewa tayi tana yatsina fuska dai-dai zata shiga ta lura da Ummi tsaye a qofar gidan da alama ta dade da tsayuwar. "Me kuke zantawa da Baba Mariya?" Gaban tane ya fad'i amma ta dake wai nasiha ta tsaya min tare da bani dogon tarihi akan Abban mu, halin shi me k'yau ne muyi koyi dashi kaza-kaza ni jin ta kawai nake bana game me take fad'a na kwaso rana." A nutse Ummi ta dube ta tana karantar tanayin ta. "A zahiri kuma ta amsa da Allah sarki Baba Mariya kenan." "Shege ni." Farouk ya fad'a tare da dukan siterin motan bayan ya sauke ta yabar anguwar. "Lallai Zaiyad dole kamin Katanga kak'i sake min cikar nan, koda sau d'aya ne kak'i ka barni na lasa naji nima, kai kad'ai kake more wannan ni'imar dana hango, Wallahi dole ka ringa haske da fresh abokina. Dole nima na lasa kalar zumar nan." Haka yayi ta sambatu har ya isa gida ******* ******** ****** Ganin ta take kamar a mafarki, har ta ida shigowa d'akin tare da jingina jikin gadon fuskar ta dauke da murmushi "Barka da safiya Salma, yaya jikin Allah ubangiji ya baki lafiya. D'azu zan shigo bakin gate nayi karo da Abban Husna bayan mun gaisa shine yake sanar dani kece baki ji dad'i ba, Allah ya baki lafiya." "Amin." ta amsa jikin ta a sanyaye Runtsa ido tayi wasu zafafan hawaye suka fara sauka tana tuno maganganun Habiba wanda data saurare ta da tabbas tasan da bata cikin wannan matsalar amma tayi fatali da ita da dukkan zancen ta. "Na rik'e Jameela ta zama siteri na sai yanda ta juya ni nake bi akan gida na." Zancen zucin da take kenan. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ [4/13, 8:50 PM] Sumayya Sumy B: 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ عَنْ مَسْرُوق*ٍ . قَالَ : سَأَلْنَا ـ أَوْ سَأَلْتُ عَبْدَاللهِ (أَيْ ابْنَ مَسْعُودٍ ) عَنْ هَذِهِ الايةِ : : ولَا تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ قُتِلُوا في سَبِيلِ اللهِ أَمْواتاً بَلْ أَحْياءُ عِنْدَ رَبِّهِمْ يُرْزَقُونَ )) ـ قَالَ : أَمَا إِنَّا قَدْ سَأَلْنَا عَنْ ذَلِكَ ، فَقَالَ)) أَرْواحُهُمْ في جَوْفِ طَيْرٍ خُضْرٍ ، لَهَا قَنَادِيلُ مُعَلَّقَةٌ بِالعَرْشِ ، تَسْرَحُ مِنَ الجَنَّةِ حَيْثُ شَاءَتْ ، ثُمَّ َ تَأْوِي إِلي تِلْكَ القَنَادِيلِ ، فَأَطَّلَعَ إِلَيْهِمْ رَبُّهُمْ اطِّلَاعَةً فَقَالَ : هَلْ تَشْتَهُونَ شَيْئاً ؟ قَالُوا : أَيَّ شَيْءٍ نَشْتَهِي ، وَ نَحْنُ نَسْرَحُ مِنَ الجَنَّةِ حَيْثُ شِئْنا ؟ فَفَعَلَ ذَلِكَ بِهِمْ ثَلَاثََ مَرَّاتٍ ، فَلَمَّا رَأَوْا أَنَّهُمْ لَنْ يُتْرَكُوا مِنْ أَنْ يُسْأَلُوا ، قَالُوا : يَا رَبِّ ، نُرِيْدُ أَنْ تَرُدَّ أَرْوَاحَنَا في أَجْسَادِنَا ؛ حَتَّى نُقْتَلَ في سَبِيلِكَ مَرَّةً أُخْرَي . فَلَمَّا رَأَى أَنْ لَيْسَ لَهُمْ حَاجَةٌ تُرِكُوا . (رواهُ مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي وابن ماجه* *On the authority of Masruq (may Allah be pleased with him), who said:* *We asked Abdullah (i.e. Ibn Masud) about this verse: "And do not regard those who have been killed in the cause of Allah as dead, rather are they alive with their Lord, being provided for (Qur'an Chapter 3 Verse 169)." He said: "We asked about that and the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said: 'Their souls are in the insides of green birds having lanterns suspended from the Throne, roaming freely in Paradise where they please, then taking shelter in those lanterns. So their Lord cast a glance at them (1) and said: 'Do you wish for anything?' They said: 'What shall we wish for when we roam freely in Paradise where we please?' And thus did He do to them three times. When they say that they would not be spared from being asked [again], they said: 'O Lord, we would like for You to put back our souls into our bodies so that we might fight for Your sake once again. And when He saw that they were not in need of anything they were let be.'"* *(1) i.e. at those who had been killed in the cause of Allah.* _[Narrated; Muslim also by at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah.]_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Six_ ~*Page 26*~ "Kiyi hakuri Salma nasan kina cikin qunci da b'acin rai wanda banason in qara zama silar qara miki wani b'acin rai kamar yanda kika fad'a baki son ganina a inda kike, baki son inzo inda kike, na ma kaina alqawarin nisantar ki har zuwa lokacin daza ki gane gaskiya nasan ko baki sake ganina ba zaki tuna dani watarana Allah shi ya jarabce ni da jin ki a zuciya ta wanda shi yasan hikimar hakan. Dan haka ina mai baki hakuri kan shiga rayuwar ki da nayi na takura miki, yanzu ma da ba rashin lafiya naji an anbata ba bazan rab'a inda kike ba. Ina miki fatan samun lafiya mai daurewa tare da miki fatan samun nasara a rayuwar ki. Na barki lafiya" Bata jira cewar ta ba tayi ficewar ta a d'akin. D'akin ne taji yana juyawa da ita, duk da ak'wance take runtsa idon ta tayi wasu hawaye na bin k'uncin ta. ****** ****** ***** Misalin qarfe 2:00 na rana Abdul-Kareem ya dawo inda ya tadda Jameela zaune bakin inuwa tana yan latse-latse a wayar ta, bata san da isowar shi ba yasa hanun ya qarb'e wayar yace; " Allah yasa kema ba wai irin karance-karancen litatttafan ku na hausar nan ba kike?" Fari tayi da ido tare da saisaita muryar ta cikin sigan daukar hankali tace; " Abinda ban tab'a ba ma kenan Haske na, gaba d'aya littattafan Hausa mussamman na yanzu da aka maidashi online ba abinda yake sai b'ata tarbiya domin batsa suke zubawa kawai a cikin ta." Tohfa yau ga inda ake yi, Jameelar dake sa har dubu ta sai littafi guda, mussamman idan ak'wai harka, fin haka ma zata iya biya domin ko ba komai yana rage mata zafi. Ganin ta harbo logon shi yasa ta dad'a narkar da muryar. " Haske na ai ko ina karantawa idan har baka so dole na ajiye saboda farin cikin ka shine nawa, dole in bi duk abinda kake so, sab'a maka kai tsaye kamar ina sab'awa mahallaci nane. Idan kuma so kake in fara karantawa toh." Maganganun ta sun mutuqar tafiya da hankalin shi, ji yayi ya rungume ta amma gilmawar da mutane suke yasa shi dai-dai ta kanshi tare da kama hanun ta yace "Allah ya miki albarka, na gode da dukkanin halaccin ki gareni." "Amin." ta fad'a tana kashe shi da wani murmushi, "Yaya mai jikin ya tambaya?" "Jiki Alhamdulillah! Doctor yana son ganin ka, yana Office d'in shi bayan mata gwaje-gwaje an cigaba da mata qarin ruwa a halin yanzu dai tana barci." "Alhamdulillah!" Ya fad'a "Muje Office d'in nashi", langwab'e kafad'a tayi, sannan tace: "A'a kaje kawai zan jira ka a nan idan ka fito sai mu shiga gurin nata." Jim ya d'an yi, ba haka yaso ba. "Shikenan yanda kike so haka za'ayi amarya." Kai tsaye office din likita ya nufa bayan ya nemi izinin shiga, ya mishi iso da nashi gurin zama, gaisawa suka yi inda ya gabatar mishi da kansa. Binciken File d'in ta yayi game da fara kora mishi bayanai kan abinda yake damun ta. "Bayan gwaje-gwaje da aka gabatar mata, sakamakon ya fito inda aka same ta da matsanacin gwambon ciki (Chronic Stomach Ulcer) sai Malaria da shima an same ta dashi amma ba yawa. Jinin ta ya hau sosai wanda tun maraice shi muke ta qoqarin ganin ya daidaita abin yaci tura, amma da yardar Allah yanzu munyi qoqarin yi mata allura dazai sa tayi barci tare da hutawa sosai bayan magungunan da aka bata da drip muna fatan za'a samu progress idan ta farka. Sai dai ak'wai buk'atan kiyaye duk wani abubuwa da dama saboda samun lafiyar ta mai dorewa mussamman kiyaye abinda zai ringa b'ata mata rai." "Shikenan Doctor Insha Allahu za'a kiyaye na gode sosai, za a iya ganin ta?" "Eh, zaka iya shiga sai dai ayi a hankali kar a tashe ta." "OK, na gode" ya tashi ya fito jiki a sanyaye tare da jin tausayin ta mutuqa "Ke kika siya ma kanki damuwa Salma, kin je kin dauko halaiya da d'abi'un da ba taki ba kin yafa. Ya za ayi ki zauna lafiya?" Maganar da yake a zuciyar shi kenan har ya iso inda Jameela take. ******** ******** ******** Hunayda ce k'wance kan d'an madaidaicin gadon ta daya sha zanin gado mai taushi kalar fari da pink sai daukan ido yake, ta gyara shi gwanin ban sha'awa littafin *NAJWA* na Fhareedaty ta kammala karantawa wanda Aunty Sumiee ta ke musu posting littattafan yan qungiyar nasu mai cike da hikima basira da hikima wanda a iya rayuwar ta bata tab'a haduwa da littatafai masu cike da d'unbin basira kamar ire-iren su ba ta tun daga kan littafin *AMINTA* zuciyar ta ya kamu da son ta har ranta, wanda baza ta iya fasalta qaunar data ke mata ba a rayuwar ta mussaman irin muhimmin rawar data taka a rayuwar ta wajen ceto ta daga fad'awa tarkon Sahabat, Dan haka koda wasa ba ta bari littattafan da duk ta turo ya wuce ta ta qaru tare da daukan darasi daban daban wanda littattafai ne da suke tafiya da zamani masu cike da soyayya, fad'akarwa game da nishad'antarwa tabbas ba abinda za ta iya biyan wayanan bayin Allah sai godiya game da aduar gamawar su da duniya lafiya a hankali ta runtsa ido iskar fankar dake sama yana ratsa ta, ta fara lisafo sunan su a hankali *"UMMU SALMA na Ummu Yusuf, KAREENATY ( Khadija One love), HURU'AINI (Shamsiyya Yar Musa), RAYUWAR ALEESHA (Maryam A Shahada), JINNUL ASHQUE (Harira Aliyu/ Yar fillo), YAN UKU (Queen Indo) WANDA YACE TUKUNYAR WANI....( Ummity Yusuf), BANFI K'ARFIN TA BA. (Oum Deedat), SHABIHATY (Bintu Ahmad), A GIDAN MU( Shatu) KAICO NA (Nasbat Gaa...." Maganar Ammi da taji ne ya dakatar da ita. Cike da murmushi Ammi ta qarasa shiga cikin d'akin tare da zama a bakin gadon tace, "Wannan lisafe-lisafen danaji kinayi na sunayen mutane fa?" Murmushi tayi game da mik'ewa ta gyara zaman ta tare da cire ear piece d'in dake kunnen ta wanda take sauraron cool music d'in Abdul D one wanda yanzu shine mawaqin da yake birge ta mutuqa, saboda waqoqin shi gaba d'aya na soyayya ne kuma cike suke da nutsuwa ba hayaniya. "Ammi Sunayen haziqan marubutan qungiyar *Golden Pen Writers Association ne da littattafan* su dana karanta wanda nake qoqari a koda yaushe in haddace sunayen su tare da littafin su, saboda babu wacce ban dauki darasi ba a cikin labarin ta abin da yake bani mamaki Ammi shine, wasu daga cikin marubutan nan fa Yan Mata ne amma kuma idan suna baka darasi kan zamantakewar aure, maqota da tsakanin ka da dangin miji zaka ce sun shekara hamsin cikin gidan aure. Lallai na yarda wannan baiwa ce da Allah yake bama wanda yaso kuma a lokacin daya so, wallahi Ammi babu batsa babu rashin kunyar na wasu marubutan mussaman wasu daga cikin marubutan online da suke kiga sun fito da komai baro baro ba sakayewa." Cikin jin dadin bayanan yar nata ta sake fad'ad'a murmushin ta tare da dafa kafad'ar ta, "Nayi farin cikin jin haka daga gare ki Hunayda, irin nunin da nake miki kenan a can baya. Alhamdulillah na godewa Allah daya amsa min rok'o na na kuma godewa wayannan bayin Allah da suka d'ora daga tarbiyar min dake, babu abinda zance sai hamdala da godiya gare su tare da musu aduar ganin farin ciki a rayuwar su ta nan duniya zuwa har cikin aljanna ya kare musu zuri'ar su daga gurb'atattun mutane da abokai ya daukaka darajar su. Ke kuma a koda yaushe kiyi qoqari kiyi amfani da abinda yake dai-dai cikin duk abinda kika karanta domin d'an Adam tara yake bai cika goma ba sannan ki nemi littafi ki ringa rubuta duk littafin da kika karanta sunan shi dana marubuciyar shekarar da aka rubuta da darasin da littafin yake dauke dashi, kinga sai ki adanawa yaran ki ki kuma basu labarin wayannan marubuta kamar yanda na baki nawa, domin kinga zamanin ku online ce tafi yawa bamusan me gaba zata haifar ba kuma idan muna raye." "Allahumma Amin Ammi, lallai na gode da shawarar nan kuma insha Allahu yanzu zan ma fara ba sai anjima ba, amma abinda yake dad'a qara ma wayannan marubuta qima da daraja ido na shine wannan rubutun da suke ficika basa karb'a wallahi, rubutu suke fisabilillah da dukkanin qarfin su, tunanin su zuwa aljihunsu wasu daga cikin su ma datar watarana gagarar su take, amma wasu daga cikin Fans sai kiga da an k'wana biyu ba ayi posting ba zasu fara qorafi ba tare da la'akarin wani abu makamanci wannan ba domin wasu daga ciki ma cajin waya sai sun biya kud'i an musu, idan basu da wuta mussaman matsalar qasar nan da ko yaushe cikin matsalar wutar lantarki ake." "Kinsan harka da jama'a sai a hankali, kowa da kalar fahimtan shi da kuma hangen nesa, amma magana ta gaskiya ku masu karatun ya kamata ku ringa k'yautata musu, domin kaman maluman ku suke idan kuka k'yautata musu Allah sai ya albarkaci abinda kuka karanta daga gare su." "Haka ne Ammi, Allah ya bamu ikon k'yautata musu." "Amin" ta amsa Amma Ammi abinda ke daure min kai shine littattafan batsar nan da ake rubutawa naga k'wanaki ana ta yawo a social media wai suna taron qungiyar marubutan irin tasu wanda suka yi a nan Kaduna suna masu alfahari da kasancewar su masu rubutun *ADABIN BARIKI* shin Ammi dama ak'wai wani sigan rubutu ne haka? Ni ban tab'a ji ba duk kuwa da dad'ewar da nayi ina d'aukar darasi a Hausa." "*ADABIN BARIKI KUMA?" Ammi ta tambaya da mamaki "Eh! Adabin bariki! Domin yanzu abin dad'a gaba-gaba yake duk da matakin da wasu daga cikin qungiyoyin online writers d'in suke dauka na hana turo irin wayannan littattafan cikin groups din su, an samu saukin abin kam sosai da sosai ba kaman can baya ba daza ka ringa cin karo da pages din su ta ko ina. " "Lallai kice yanzu duniyar online yazo da wani salon mai wuyar fassaruwa ga marubuta, zuwa masu karatu. Gaskiya banda masaniya akan haka amma kinsan ilimi kogi ne kuma na dade rabona da karatun littafi sama da shekara goma sha biyar. Amma zanyi qoqari in fara sannan dan kuma bincika wannan adabin barikin ta inda aka samo shi ." "Tohm Ammi, amma dana fi kowa farin ciki idan kika fara bibiyar littafin nan kinga Ammi da *Banfi k'arfin Ta Ba* zaki fara kiga yanda rayuwar Suhan, da Yaya Ameen kiga son zuciya da cuta gurin Mom zjwa su Maree wanda Mom ta gada gurin iyayen ta da kakan ta sannan kiga mai zuciyar yan Aljanna irin su Ummah Allah sarki, tsatsan hakuri, da daukan qaddara." Ta qarasa maganar kamar zatayi kuka "Dariya sosai Ammi tayi lallai ko zan karanta ni gashi ai har kin lasa min Zuma a baki naji na k'wadaita. Amma yanzu tashi kizo ki shirya na aike ki gidan Mariya ki karb'o min d'inki na jiya tace zata kammala amma naji ta shiru kar ta min halin teloli." Dariya tayi sannan ta mik'e tare da fara qoqarin kintsawa. "Shikenan Ammi bazan je Hajna bata tashi a barci ba?" "Bata tashi ba, kije karki zauna, ki dawo yanzu ga sauran kud'in nan ki bata. Ki gaishe ta kuma" ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷           *_MENENE RIBA TA ❓_*                                                            🙆🙆🙆              © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~  ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf*  ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan*  ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI*   ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD*  ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO*  ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF  KO  MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *_Ya Allah wannan cuta ta coronavirus kayi mana maganin ta, ka tsare mu kayi mana katangar ƙarfe tsakanin mu da ita, ya Allah ka tamake mu, ya Allah ka sassauta mana, ya Allah mun tuba ka yafe mu, ya Allah mu masu lefi ne ka yafe mana laifukan mu. Amin ya rabbil alamin..._* *_Ƴan uwa mu zauna a gida mu kare kan mu, muyi ta istigifari muna neman sassauci daga Allah, ya kawo mana ƙarshen wannan annoba, Amin ya rabbi.. Ya Allah wainda basu da yadda za su yi wajen ciyar da kan su, ya Allah ka kawo musu mafuta_* *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:* "Allah said: 'I have prepared for My righteous servants what no eye has seen and no ear has heard, nor has it occurred to the human heart.'" Thus recite if you wish (1): "And no soul knows what joy for them (the inhabitants of Paradise) has been kept hidden (Qur'an Chapter 32 Verse 17)." (1) The words "Thus recite if you wish" are those of Abu Hurayrah. [*Bukhari, Muslim, at-Tirmidhi and Ibn Majah*.] نْ أَبي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ :* قَالَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى الله عَلَيْهِ وَ سَلَّمَ قَالَ اللهُ أَعْدَدْتُ لِعِبَادي الصَّالِحِينَ مَا لَا عَيْنٌ رَأَت وَ لَا أُذُنٌ سَمِعَتْ وَلَا خَطَرَ عَلَى قَلْبِ بَشَرٍ فاقْرأُوا إنْ شِئْتُمْ : فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَّا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ رواه البخاري و مسلم والترمذي وابن ماجه* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* *_♣️scene 7_* *page 27* Saha tana shiga cikin gida direct ɗakin su ta wuce tana tuna irin maganganun da baba Mariya ta ƙara tunatar da ita, ba wai bata san su bane, a'a kawai dai gani take a yanda take jin kanta kuma ta saba da Zaiyad bata jin zata iya dena kasan cewa da shi nan kusa, kuma bama wannan ba tasan dai nan kusa Ziyad zai turo zuwa gidan su ayi maganar auren su to ko me zai  sa ta damu har ta kai ga dena faran ta ran masoyin nata duk da yanzu taga ba kamar da ba ya d'an fara canza mata. Deep breath ta sauke, kafin ta fara rage kayan da ke jikin ta don duk a gajiye take, faruk ne ya faɗo mata a rai "Shi kuma wannan handsome guy ɗin ko waye oho, amma anya kuwa zan iya haɗa shi da Zaiyad kuwa? Gaskiya bana jin zan iya tunda shima na tabbar da ni kaɗai yake mu'ammala to ko me zai sa naci amanar shi". _Ni kuwa nace ohoho Saha baki dai sani ba amma kafin ki akwai wasu, sannan bayan ki ma akwai wasu_ Haka dai tayi ta magana ita kaɗai har Surayya ta shigo cikin ɗakin " Kai ya Saha na gode sosai da irin siyayyar da kika yi mun yau, naji daɗi sosai wallahi Allah ya bar zumunci ya kuma ƙara haɗa kan mu". Wani lustful kallo Saha ta watsawa Surayya kafin ta kamo hannun ta tace "Haba ƴar uwa, don nayi miki siyayya  shine kike yi mun duk wannan godiyar sai kace wata bare". Saurin janye hannun ta tayi tana mata kallo me wuyar fassarawa kafin ta ce"Ai abun da ba ki yi ne da kika yi shi yanzu kin ga kuwa dole ai na gode miki ko ba komai". "To naji kar dai ki ƙara mun wata godiya". "Dama Ummi ce ta ce kizo mu haɗu mu ɗora Abinci". "Okk munje" ta faɗa tana miƙewa daga inda take zaune. "Sahabat." With full of fear akan fuskar ta ta juyo ta kalli Ummin ta da jin yanayin yadda ta kira ta. " Waye ya ajiye ku a mota, Surayya tace min a mota kuka dawo?" "Ammm..... Umm.... Wallahi Ummi muma ba mu san shi ba kawai dai bayan mun gama siyayya ne a wani kanti ya takura mana wai dole sai ya kawo mu gida, muka ƙi yadda amma sai da yayi insisting shiyasa ma na bari ya kawo mu har nan ƙofar gidan, kuma ki tambayi Surayya ma". Kallon ta ta mayar ɓangaren Surayya"Wallahi Ummi haka ne, abunda ya faru kenan". "Yanzu Saha duk abunda nake faɗa miki baki jin magana ta ko?so ki ke sai kun ja mun magana a unguwar nan, don na tabbatar maganar da Baba mariya take miki kenan, ko ba haka bane? " Hake Ummi don Allah kiyi Haƙuri wallahi baza mu sake maimaita abu shigen irin haka ba Allah kuwa". "To nidai ina faɗa muku ku dinga taka tsantsan, don duniyar nan yanzu ba abun yarda bace. Ku shiga ku ɗora mana abinci. _Haba malama basai yanzu ya kamata ki fara saka mana ido ba, don ni wallahi nayi nisa kuma in sha Allahu sai na cimma buri na na auren Habibi na abun alfahari na_. Cewar Sahabat da tayi maganar cikin zuciyar ta. Bayan sun kammala abincin sun zuba shi a kula Saha ta nufi ɗaki don watsa ruwa a jikin ta saboda yanayin zafin da garin ya ɗauka, bayan ta fito ta shirya cikin wata riga mara nauyi. "Ke Surayya baza kiyi wankan yanzu  ba ne? " Eh wallahi ya Saha sai munzo kwanciya tukunna, nafi jin daɗin baccin. **** Bayan sallar isha'i duk sun gama cin abincin Ummi ta shige ɗaki don tayi shirin kwanciya, suma su Sahan ɗaki suka wuce don su kwanta, suna shiga Surayya fara shirin yin wanka nan fa Saha ta fara kallon ta tana haɗiyar yawo har ta shige toilet ɗin, bayan ta fito tana shirin saka kaya Saha bata san san da tace"Haba Surayya me makon ki kwanta a haka shine sai kin wani saka nightyy". Da mamaki Surrayan take kallon yayar tata. _kai anya Saha bata samu matsala ba kuwa, ji fa abunda take cewa ya za ayi na kwanta daga ni sai towel_ A fili kuma ta ce"Bangane ba Ya Saha me kike nufi". Saurin lumshe ido tayi jin ta kwafsa, "Aa ina nufin ki saka kaya marasa nauyi mana". "Okkk... Ai wainnan ɗin ma basu da nauyin". "To sai da safe". Ta faɗa tana juyawa while deep inside her  ji take kamar ana ƙara mata wutar sha'awar Surayyan. Ita kuwa ko a gefan slipper din ta. itama  hayowa kan katifar tasu tayi ta kwanta. 12:20pm Sahabat dai abun dai har yanzu babu sauƙi, don kuwa har ƙarawa kanta tayi saboda sai da karanta pages ɗin da Ummin ta ta saka da raguwar team ɗin su kafin ta fara tunanin kwanciya banci amma ina bacci yace ai baki isa ba, Sha'awa kuma tace salama alaikum,tayi ta kiran lambar masoyin nata amma sam taƙi shiga wannan dalilin ne yasa ta ƙara shiga wani hali, wanda yasa zuciyar ta ta dinga raya mata why not ta gwada biyan buƙatar ta da Ƙanwar tata, a hankali takai hannun ta ta fara shafa Surayyan tana mata wasu irin abubuwa masu wuyar fassarawa, da kuma tsayawa a zuciya ba tare da tayi tunanin ko me zai je ya dawo ba. Surayya cikin bacci taji wani baƙon yana yi yana ziyar tar ta ai kuwa zunbur ta tashi tana me ture yayar tata tare da faɗin"Ya Saha meye haka⁉️ me kike shirin aikatawa!!!?? Ita kuwa Saha ina hankalin ta yayi nisa sai ƙara cakumo Surayyan take yi. "Plss ki barni wallahi idan banyi ba mutuwa zanyi". Hawaye shaɓe shaɓe kan fuskar Surayya tace "Wallahi sai dai ki mutu amma bazan taɓa baki goyan bayan yin wannan ƙazantacciyar alaƙar da ni ba, duk kuwa da ba wani masaniya nake da shi akan hakan ba amma nasan a islamaiyya ana yawan kawo mana fatahohi na malaman fiqihu akan irin wainnan alaƙun, don haka ki rabu dani idan ba haka ba wallahi sai na faɗawa  Ummi idan har kika kuskura kika ƙara taɓa ni, kuma ko yanzun ma sai na faɗa mata abunda kika yi niyyar yi, shiyasa ki kai ta mun siyayya saboda kar na faɗa, to da wancan da wannan ba ɗaya bane, kuma wallahi daga yau na dena karɓar komai daga hannun ki da sunan cin hanci sai na faɗawa Ummi komai da safe". "Surayya na roƙe ki kada ki gaya Ummi wallahi bazan ƙara takura miki ba kinji ma na rantse yanzun ma sharrin sheɗan ne, amma wallahi ba hali na bane kuma bana yi". "To kina karance karance, da kalle kalle da kuma bin samari ta ya ba zaki faɗa cikin irin wannan rayuwar ba, ko an gaya miki da nake bani da shekaru ban san abunda kike yi ba, to wallahi duk abunda kike yi ina sane kuma sai na faɗima Ummi zuwa safiya". Ta ƙarashe maganar tana jan bargon da yake gefan gadon tare da ɗaukan pillow tayi kasa tayi sabuwar shimfiɗa sannan ta kwanta. "Ya Allah wani irin hali na saka kaina, what if Surayya ta faɗawa Ummi, wallahi nasan kashi na ya bushe na shiga uku na, Zaiyad duk kai kasa ni cikin wannan halin gashi yanzu ka dena kula dani sam..." Haka suka kwana ranar, ita Surayya tana bacci rabi da rabi while ita kuma Sahabat Sha'awa da fargaba duk ya dame ta. Washegari da safe da wuri Surayya ta tashi tayi sallah don ta ƙudiri niyyar sai ta sanarwa da Ummi abunda Sahan tayi mata jiya, bayan sun kammala break fast ba wanda yace wa kowa komai, while ita kuma Ummi har yanzu bata fito daga ɗaki ba, sai kusan 8:30 ta fito tayi wanka ta shirya daga gani akwai gurin da zata je. Bayan sun gaishe ta suka fara break fast, suna gamawa Ummi ta ɗauki waya tare da kunna data tana bin irin comment ɗin da tasha jiya tare da yin replying haɗe da duba wasu messages ɗin nata. Nan fa Surayya ta matso "Ummi dama wata magana zan faɗa miki, wani abu ne ya faru jiya da daddare". Tabb ai kuwa Saha ji tayi kamar ta saki zawo a gurin saboda yadda cikin ta ya murɗa mata ga wani gumi da wanke mata fuska. "Plsss Surayya ba kya ganin  ba haka nan nake zaune ba, ki bari sai anjima zuwa da yamma sai muyi magana don yanzu ma idan na gama fita zanyi kinji ko". Wani irin baƙin ciki ne ya ziyarci Surraya, ita kuwa Saha kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Nan ta tashi fuuuuu tayi cikin ɗakin su. Tana shiga ta fasa kuka me cin zuciya"Yanzu shikenan ita Ummi bata da lokacin sauraren mu, bata da lokacin jin matsalar mu, bata da lokacin jin cikin mu,ya muka kwana ya muka tashi a wani hali muke ciki duk be dame ta ba, to ai shikenan ni kuma wallahi tunda har bata bari na faɗa mata yanzu ba sai dai idan ta gano da kanta, ni kuma in sha Allahu zanyi duk yadda ya kamata ganin na kare kaina daga halaka, tunda ita ya Sahabat ta kasa riƙe tarbiyar da Abbu ya bamu kafin Allah yayi mai rasuwa". ****  ***** **** **** Abdulkareem yana fitowa daga office ɗin ya tarar da Jamila a tsaye bakin ƙofar, yana fitowa tayi saurin ƙarasawa gurin da yake. "Haske na me likitan ya ce? Ta faɗa tana mai wani fari da ido irin na ƴan barikin nan". "Ke dai bari kawai abun babu daɗi wallahi, sai dai fatan Allah yasa Salma ta cire duk wani abu dake ranta ku zauna lafiya". "Uhmmm to Amin, don ko ɗazu ma da nace zan haɗa mata abun kari, sai da ta hantare ni tace bata so, baka ji irin maganganun da  ta dinga faɗa mun ba wallahi". Ta ƙarashe maganar tare da matso wasu hawayen ƙarya da kuma munafurci.. "Tabbb abunda tayi miki kenan? Kuma dama likita yanzu ya gama faɗa mun  ciwon ta harda na yunwa, to wallahi kuwa inda baza ta zauna lafiya dake ba sai dai ta tafi gidan su, don bazai yuwu ta dinga kawo mun hargitsi a cikin gida na ba, ta kuma hana ni kwanciyar hankali, bazan ɗauka ba wallahi, yanzu ba da bace, haba mana me take so nayi mata, duk ba halin ta bane ya ja mata sai yanzu zata zo tayi wa mutane rashin hankali da hauka". Ya ƙarashe maganar yana nufan hanyar ɗakin nata. "Aaa ina kuma zaka je? " Dubo ta zanyi kafin na kira wani daga can gidan su yazo ya dinga kula da ita don gida zamu koma tare da ke". Wani shu'umin murmushi tayi kafin tace"Haba mana kayi haƙuri, dama nima cewa nayi muje gida idan nayi girki sai mu dawo tare ko"? "To shikenan babu matsala amarya ai duk abunda kika ce shi za ayi". Nan suka ɗau hanyar gida, sai da suka yi kusan 3 hours kafin suka kama hanyar dawo wa, yanzun kam harda su Husna. Ita kuwa Salma tana ɗaki a kwance gaba ɗaya ta gama cika, ga wani baƙin ciki da ya cika ta, ta jira shi har ta gaji da jira, har ta kira su Fatima suka kawo mata abinci. Da sallam suka shigo cikin ɗakin, ko kallon inda suke Salma bata yi ba ballnatana ta amsa sallamar su, sai su Fatima suka amsa musu. Guri ya samu ya zauna kafin ya ce"Ya jikin naki? Ciki ciki da amsa "Da sauƙi" . "To gaskiya Salma sai kin Kula, kina cin abinci sannan kuma ki kwantar da hankalin ki saboda likita yace kina da ciwon ulcer da kuma hawan jini.don haka duk wata damuwa sai kin ajiye ta Jamila ba baƙuwar zafi bace idan kika kwantar da hankalin ki to zaku zauna lafiya wallahi, saboda ɗazu ma ta faɗa mun cewar ta haɗa miki abun kari amma kika ce baki so sannna kuma kika bita da munanan kalamai wanda yayi matuƙar ɓata mun rai". Wani irin zafi zafi da baƙin ciki Salma taji yana taso mata, ga wani mugun abu da ya tsaya mata a maƙogaro yaƙi wucewa, ga kuma kishi da taji shima ya taso mata. _"Lallai ma wannan matar banda ƙwace mun miji da tayi shine kuma take mun sharri tana haɗa ni da shi to kuwa wallahi bazan yarda ba_". Muryar jamila ce ta katse mata tunanin ta"Wallahi kuwa Haske na gwara ka faɗa mata ni bani da wata matsala idan har tana so mu zauna lafiya to zamu zauna". "Na sani ai Sweety, kar ki damu ai komai zai daidaita". "Kutumar uba" Salma ta faɗa tana daga kan gadon,bayan kin aure mun miji sannan kizo kina haɗani faɗa da shi to wallahi baki isa ba". "Uhmmm ni ba karya bace irin ki don haka bazan yi faɗa dake ba a asibiti ba". Kafin Jamila ta rufe baki Salma ta yunƙura tasheƙa mata mari kasancewar tana kusa da ita. "kika mare ni? Kika mare ni, wallahi bazan yarda ba". "Aa Jamila dakata, salma kika mare ta? " Na mare ta me zaka iya yi Abdulkareem? Shima marin Salmar yayi "Ga abunda zan iya yi nan, na rama mata". Fisge ruwan da yake hannun tayi ta tashi kafin taci kwalar shi "Ka mare ni akan wannan tsinnaniyar matar taka, macuciya azzaluma, ma ci amana, maƙaryaciya." "Salma ki sake ni bana son wannan haukan naki! " Wallahi sai dai ka zaɓa ko ita, ka sake ni kawai!! " "Haka kika ce na sake ki ko? " Eh ka sake ni bazan iya zama da kai ba saboda baza kayi adalci a tsakanin mu ba". "Haka dai kika ce ko? " Eh na haka na ce" . "To ki je zan turo miki da takardar sakin ki, na sake ki saki ɗaya." *~_From the everlasting golden pen, of golden pen writer, association of MENENE RIBATA AND ALLAH GATAN MARAYA _~* *©️2020* ~_WE LOVE YOU ALL_~❤️ 🤷‍♀🤷‍♀🤷           *_MENENE RIBA TA ❓_*                                                            🙆🙆🙆              © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~  ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf*  ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan*  ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI*   ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD*  ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO*  ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF  KO  MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ عَنْ مَسْرُوق*ٍ . قَالَ : سَأَلْنَا ـ أَوْ سَأَلْتُ عَبْدَاللهِ (أَيْ ابْنَ مَسْعُودٍ ) عَنْ هَذِهِ الايةِ : : ولَا تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ قُتِلُوا في سَبِيلِ اللهِ أَمْواتاً بَلْ أَحْياءُ عِنْدَ رَبِّهِمْ يُرْزَقُونَ )) ـ قَالَ : أَمَا إِنَّا قَدْ سَأَلْنَا عَنْ ذَلِكَ ، فَقَالَ)) أَرْواحُهُمْ في جَوْفِ طَيْرٍ خُضْرٍ ، لَهَا قَنَادِيلُ مُعَلَّقَةٌ بِالعَرْشِ ، تَسْرَحُ مِنَ الجَنَّةِ حَيْثُ شَاءَتْ ، ثُمَّ َ تَأْوِي إِلي تِلْكَ القَنَادِيلِ ، فَأَطَّلَعَ إِلَيْهِمْ رَبُّهُمْ اطِّلَاعَةً فَقَالَ : هَلْ تَشْتَهُونَ شَيْئاً ؟ قَالُوا : أَيَّ شَيْءٍ نَشْتَهِي ، وَ نَحْنُ نَسْرَحُ مِنَ الجَنَّةِ حَيْثُ شِئْنا ؟ فَفَعَلَ ذَلِكَ بِهِمْ ثَلَاثََ مَرَّاتٍ ، فَلَمَّا رَأَوْا أَنَّهُمْ لَنْ يُتْرَكُوا مِنْ أَنْ يُسْأَلُوا ، قَالُوا : يَا رَبِّ ، نُرِيْدُ أَنْ تَرُدَّ أَرْوَاحَنَا في أَجْسَادِنَا ؛ حَتَّى نُقْتَلَ في سَبِيلِكَ مَرَّةً أُخْرَي . فَلَمَّا رَأَى أَنْ لَيْسَ لَهُمْ حَاجَةٌ تُرِكُوا . (رواهُ مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي وابن ماجه* *On the authority of Masruq (may Allah be pleased with him), who said:* *We asked Abdullah (i.e. Ibn Masud) about this verse: "And do not regard those who have been killed in the cause of Allah as dead, rather are they alive with their Lord, being provided for (Qur'an Chapter 3 Verse 169)." He said: "We asked about that and the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said: 'Their souls are in the insides of green birds having lanterns suspended from the Throne, roaming freely in Paradise where they please, then taking shelter in those lanterns. So their Lord cast a glance at them (1) and said: 'Do you wish for anything?' They said: 'What shall we wish for when we roam freely in Paradise where we please?' And thus did He do to them three times. When they say that they would not be spared from being asked [again], they said: 'O Lord, we would like for You to put back our souls into our bodies so that we might fight for Your sake once again. And when He saw that they were not in need of anything they were let be.'"* *(1) i.e. at those who had been killed in the cause of Allah.* _[Narrated; Muslim also by at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah.]_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* *~Scene 7~* *Page 28* "Innallilahi wainnailaihi raji' un, na shiga uku na lalace! Yanzu Abdulkareem saki na kayi akan Jamila? Dama akwai ranar da zata zo kaci mun mutunci haka? Wallahi sai Allah ya saka min. Ke kuma Jamila in sha Allahu abunda kika yi mun Allah bazai barki ba, saboda Allah ba azzalumin bawan shi ba ne". Ta ƙarashe maganar tana komawa kan gadon tare da saka kuka kamar ranta zai fita. Jamila ce ta kama hannun su Husna zasu bar ɗakin, ranta fari ƙal abunda take so yau ya faru, ji take inama zata iya rawa a gurin, da sai ta ɗan taka saboda yadda lamarin ya mata daɗi. _Ohhh Jamila akwai barikanci_. "Ki sakar mun ƴa ai ba ke kika haife ta ba da zaki kama hannun ta ku tafi saboda tsabar munafurci". Abdulkareem kam tunda ya furta kalmar sakin sai kuma yaji jikin shi yayi sanyi ya kasa magana ma, har saida Salman tace wa Jamila ta sakar mata yara. "A guri na za su zauna. Jamila wuce mu tafi gida". Wani kukan Salma ta ƙara fashewa da shi, ji take kamar ranta zai fita. "Shikenan an rabani da yara na, na shiga uku ni yanzu ya zanyi, Fatima ku temaka mun, ku hana shi tafiya da su Husna ko idan na gansu Hankali na zai dinga kwanciya". "Aunty kiyi haƙuri akwai Allah". Haka dai Salma tayi ta kuka tana dana sanin abunda ya faru yanzu, ga kuma wani zazzaɓi da ya ƙara rufar mata. A ɓangaren su Jamila kuwa suna fita Abdulkareem yayi gida dasu, bayan sun shiga gida ya samu guri ya zauma tare da haɗe kai da gwiwa yana jin ciwon abunda ya aikata. _"Salma duk ke kika ja mana wallahi, ga abunda kika janyo nan, har sai da kika sa na sake ki, nace miki bana so bana so amma sai da kika tunzura ni na aikata abunda Allah baya son shi, to yanzu wa gari ya waya, ai gashi nan kin cuce ni mu da yaran mu, kin saka za su zama  marasa uwa, duk da na san Jamila zata basu kulawa, amma baza ta so su kamar yadda ke da kika haife su ba_". Haka dai yayi ta mitar shi cikin ranshi. "Haske na, na kawo maka abincin ne ka ci ko kafi samum nutsuwa?" Yaji muryar Jamila ta daki kunnen shi. Kallon ta yayi yana wani ɗan yatsina fuska kafin ya ce"Please Jamila ki ɗan bani lokaci kaɗan, i want to be alone, i want to be my self, please". Ya faɗa yana haɗe mata hannayen shi guri ɗaya.. "Sweat heart kenan" Ta faɗa tana shafa gefan kumatun shi. "Ka ɗau duk lokacin da kake buƙata nayi maka uzuri, na kuma fuskanci irin halin da kake ciki". "Nagode sosai" ya faɗa kafin ya kwanta akan kujerar....          ****    ****    ****     **** "Surayya don Allah, don girman Allah, don sonki da manzon Allah (S. W. A) kar ki faɗawa Ummi abunda ya faru tsakani na dake jiya da daddare na roƙe ki, don Allah, wallahi kema kin san idan taji maganr nan kashe ni ne kawai Ummi ba zata yi ba, so plss ki rufa mun asiri kema wata rana sai ki ga Allah ya rufa miki asirin, kuma ko ba komai ni fa ƴar uwar ki ce ta jini". "Ya Saha kenan, ai in sha Allahu in Allah ya yarda bazan aikata abunda kike aikatawa ba ballantana ma har na ɓoyewa Ummi, ke kanki kin san abunda kike aikwata ba daidai bane, don Ummi bata yin abunda ya kamata akan mu sai akace ki bi hanyar lalata rayuwar ki? to ki sani idan da akwai lefin Ummi to kema akwai naki, domin kuwa ke ba jahila bace Allah ya hore miki ilimin islama dana boko dai dai gwargwado, amma ke kin kasa amfani da shi, da jahili ne yayi irin wannan abun sai ace mai ai jahili ne be yi karatu ba, be san abunda yake yi ba, to ke kuma me za a kira ki umm? Duniya ce ta ishi kowa riga da wando, ni dai In sha Allahu zan yi ƙoƙarin kare mutunci na, amma ki sani akwai ranar da za ta zo dole sai kin girbi abunda kika shuka wallahi, kuma zancen faɗawa Ummi tunda har bata bari na sanar da ita yau ba, to kuwa sai dai ta farga da kanta, Allah ya kyauta amma gaskiya idan bacci kike to ki farka, ki kuma san halin da kike ciki yauwa". "Haba Surayya ya zaki ce haka, wallahi zaiyad kaɗai da shi nake mu'ammala kuma shima don yace zai aure ni ne shiyasa". "Ya Saha kenan, a barshi ma a auren naki zai yi, sai kuma aka ce saboda zai aure ki ki sakar mai jikin ki yayi yadda yake so da ke ummm? Haka addinin ki yace kiyi, to ai ko aure kika yi bazai yi ɗaukin ki ba, saboda ya riga da ya san komai game da ke, kuma bazai daraja ki ba, sai ya dinga zargin anya ma kuwa baza ki bi wasu mazan idan baya nan ba, tunda haka kuka yi kafin kuyi aure, ko kuma ke ki dinga zargin shi da hakan. Allah dai ya kyauta kawai". "Amin" Saha ta amsa mata don ita gani take Zaiyad bazai yi mata haka ba... _Ni kuwa nace tabbb kin tafka babban kuskure_ "Saha ni na fita sai na dawo, kawun ku zai zo anjima ya kawo mana kayan abinci munyi waya da shi ni kuma bazan iya jiran shi ba jira na ake yi idan yazo kuce ina gaida shi don Allah!!! Sahan leƙowa tayi daga ɗakin su kafin tace" to Ummi sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya. Bayan fitar Ummi da kamar awa ɗaya, sai ƙanin Abbun su Saha yazo gidan. Gaida shi suka yi cikin mutunci da girmamawa. "Ina Ummin taku take ne? " Wallahi kawu bata daɗe ta fita ba, wai anata jiran ta ne, tace tana gaida ka". Ɗan jimm yayi kafin ya ce"To ina amsawa, muje ku tayani ɗebo kaya a waje. Boot ɗin motarshi ya buɗe ya ciro buhun shinkafa  su kuma su Saha suka ɗebo cartoon ɗin indomie dana su spaghetti da macarooni da dai sauran kayan abinci zuwa cikin gidan. 10 minutes ne ya ɗauke su gurin shigo da kayan, bayan sun gama ya basu wasu kuɗi da ina tunani za su kai 20k ya ce"Gashi nan idan ta dawo ku bata wainnan kud'in cafane". "To shikenan kawu Insha Allah zan bata, mun gode sosai." Sahabat ne ta d'an marairaice tace "Kawu kafin ka tafi ko zaka ara min wayar ka na kira ta". "Affff wai har yanzu bata baki waya ba?" " Eh Kawu". "To shikenan in Allah ya yarda zan samo miki ko ƙarama ce, saboda ai wayar tana da amfani, what if wata matsalar ta taso muku bata gidan fa ya zaku yi kenan? Ya ƙarashe magnar yana miƙa mata wayar. " Hello Ummi ". " Na'am Saha, har yazo kenan? "Eh, dama cewa nayi me za a dafa ko may be ba a kusa zaki dawo ba. " Ai kuwa dai, ku dafa white rice and stew kawai". "To shikenan sai kin dawo". Nan ya karɓi wayar yayi musu ƴar nasiha kafin ya wuce. Yana tafiya Saha ta fara shiri daga gani fita za tayi sai wani sauri take yi. "Ammm Surayya zan je gidan su Hunayda yanzu zan dawo". "Uhmmm sai kin dawo". Tana fita ta nemi me adaidaita saho yayi gidan Zaiyad da ita saboda tun jiya take gwada no. Shi amma yaƙi shiga, bayan me adaidaita sahu ya ajiye ta bakin ƙofar gidan Zaiyad ɗin nan taci karo da wata sabuwar picanto pake a wajan, sai mamakin ko waye me motar oho, ko may be abokin shi ne, haka dai ta gama tunanin ta har tashige cikin gidan kuma ƙofar a buɗe take , tana shiga ta jiyo shewar Zaiyad ɗin da alamun fitowa ma zai yi daga ɗakin shi. Shi kuwa sun gama harka da zeeee suna shirin fitowa. liƙe da juna suka fito while bakin su yana cikin na juna suna tafiya suna abun su ko a gefan slipper nasu. Ita kuwa Saha tun da suka fito ta suma a tsaye ko motsi ma ta kasa yi. Sai da suka sakko daga stairs sannan Zaiyad ya hangota, ai kuwa da sauri ya saki zeeee"Sa.... ha... bat... Me kike yi a nan?? "Dama abunda kake yi kenan Zaiyad? dama cin amanata kake yi, shiyasa ka dena ɗaga waya ta saboda ka gama yayi na ko? Shiyasa ka kashe wayoyin ka saboda kar na dame ka, ba a gabanka nake ba yanzu, na gode sosai".ta faɗa, tana share hawayen da suka wanke mata fuska. "Ba haka bane don Allah ki tsaya mana kiji Saha". 🖐️"Ya isa haka Zaiyad babu abunda zaka faɗa mun kaji ko, enough, na gaji dajin ƙaryeyya kin ka". Fuuu ta fita daga palon "Umma ta gaida ashha ya faɗa yana keɓe baki". "Wannan kuma wacece Zaiyad? " Wata tsohuwar hannu na ce, batta can da yawar ta, can ta matse mata a matse matsin matsalar ta wallahi....." Bayan mai adaidaita ya sauke Saha direct ta shige gida gaba ɗaya ba a cikin hayyacin ta take ba. Ita kuwa Surayya har ta ɗora tafashen nama don girikin rana. Wannan dalili ne ya saka, Saha na shiga ƙamshin tafashen ya daki hancin ta, nan da nan taji ƙanshin gaba ɗaya ya hargitsa mata kai, nan fa zuciyar ta ta fara tashi da gudu tayi toilet nasu tana kwarara amai kamar ƴan hanjin ta za su fita, sai da ta amaye kafff abunda tayi breakfast da shi kafin ya sarara mata. Ita kuwa Surayya sororo tayi tana ganin ikon Allah. Bayan ta fito ta baje a gado tana sake fashewa da kuka. "Shikenan ya cuce ni ya gama dani, wallahi sai Allah ya saka mun, azzalumi macuci kawai". "Wai me ya faru ne ya Saha? "Surayya Zaiyada ya gama da rayuwa ta, kuma wallahi bazan yafe mai ba Allah ya isa tsakani na  da shi mugu kawai.. Ita dai Surayya bata sake ce mata komai ba sai Allah ya kyauta nan ta koma palo ta cigaba da kallon ta, har nepa suka ɗauke wuta. Haka dai ranar Saha ta wuni tana jin kasala ga kuma baƙin cikin abunda Zaiyad yayi mata abun ya haɗun mata huɗu da biyar.. Ita kuwa Surayya har ta gama abincin ta ta zuba su a kula. Ummi bata dawo ba sai wajen qarfe shida na yamma, ana shirin kiran sallar magrib. "Surayya tun yaushe nepa suka ɗauke wuta ne, na dawo waya ta babu charge gashi na tarar babu wuta". "Wallahi Ummi sun daɗe kam, don kusan awa huɗu kenan". "To Allah yasa su dawo da ita nan kusa, wai ina Saha ne tunda na shigo ban ganta ba? "Tana ɗaki kamar bata jin daɗi ne, ga wannan Kawu yace mu baki". "Allah sarki, shidai baya gajiya, tunda mahaifin Ku ya rasu kullum cikin dawainiya da hidima yake. Wannan yasa kuke rayuwar ku cikin wadata kamar sanda mahaifin Ku take raye. Allah ya saka musu da alkhairi, Ku kuma Allah ya muku albarka ya gafartawa mahaifin ku." " Amin Surayya." ta amsa had rants taji farin cikin aduar Ummi a yau. " Ai kuwa an gode, Bari na dubo Sahar". "Saha me yake damun ki ne? Ummin ta faɗa tana shafa jikin ta. " Suhannallahi"Ummin ta faɗa jin jikin Sahan da zafi sosai. "Kin sha magani kuwa?" "A'a Ummi ban sha ba" tayi maganar cikin muryar marasa lafiya. "Ayya sannu tashi kici abinci sai ki sha ko panadol ne kafin zuwa gobe idan jikin be yi sauƙi ba sai mu tafi asibiti. Bayan Saha tayi Sallah taci abinci ta sha magani, nan Ummin take ta jera mata sannu, ko 15 minutes ba ayi ba Saha taji abincin na taso mata, ai kuwa da gudu tayi toilet nan ta fara amayar da abunda taci ko narkewa ma basu fara yi ba. Itama Ummin bayan ta ta biyo. "Sannu Saha, dama kinyi amai ne ɗazu? " Eh Ummi nayi". "Ayya sannu ko? May be malaria ce take damun ki, zuwa gobe zamu gwada zuwa asibiti mu gani". Jinjina mata kai kawai Sahan tayi, don ita kaɗai tasan abunda yake damun ta. Haka ranar suka kwana jikin Sahar babu daɗi, don yau ɗakin Ummin ma suka kwanta. _Ni kuwa nace ba wuta, ballantana ayi typing dole aja yara jiki_ Har safiya nepa basu kawo wuta ba, Ummi kuwa sai mita take yi. Bayan sun ci breakfast nan ma Saha ta ƙara amayar da shi, ga kuma jikin ta babu zafi sanyi ƙalo sai wani bin kujera take kamar me jaririn ciki. Nan fa Ummi ta fara shan jinin jikin ta tana yiwa Sahar wani irin kallo me wuyar fassarawa. "Saha shiryawa zaki yi mu tafi asibiti kawai, don jikin nan naki ya fara bani tsoro wallahi" "To Ummi" tayi maganar ko a jikin ta. Bayan kamar one hour Saha ta gama shiryawa suka nufi  asibiti, lokacin da likita ya kawo wa Ummi result ji tayi gaba ɗaya komai ya ɗauke mata, duniyar tayi mata zafi, dena gane komai tayi sai wani zufa take yi, har wani gudawa gudawa taji yana shirin kama ta a asibitin. Haka nan dai ta daure ta kama hannun Sahar suka yi gida saboda kar ta kwafsa a asibiti. Ita dai Saha bata gane kan Ummin nata ba, har suka ƙarasa gida. Suna shiga ta cilla ta kan kujera tare da faɗin. *"SAHABAT KI FAD'A MIN UBAN WA YA MIKI CIKI⁉️⁉️⁉️😡😡.......*"              ***    ***    ***    *** "Kai Ammi kinga yadda kayan suka yi miki kyau kuwa?" "Wallahi kuwa nima na gani tun da na saka kayan ina shiryawa a jikin dressing mirror, ai ta iya ɗinki sosai, ga itama atamfar tana da kyau". "Gaskiya kam, ai yau sai Abba ya kasa gane ki tabbb". Hunayda ta faɗa tana guntse dariyar ta. "Gidan ku Hunayda" Ammin ta faɗa itama tana dariya. "Ai kam dai Ammi wallahi kinyi kyau sosai". "Allah ko Hajna? "Sosai kuwa" "To na gode muku da yaba kwalliya ta, kuma idan kunje gidan miji haka zaku dinga yi , ba aje ayi ta zama da ƙazanta ba". Suna cikin haka wayar Hunayda ta fara ringing, da mamaki take kallon screen ɗin ganin sunan malam Suhail. Da sauri ta shige cikin ɗakin su tana kara wayar a kunnen ta. "Salama Alaikum" ya faɗa daga can ɓangaren. Sai da ta lumshe ido kafin ta ce "Wa alaikumusalam". Shima anashi ɓangaren haka ne, ga wani farin ciki da ya ziyar ce shi jin muryar sahibar tashi. "Hunayda ya kike? ya gida? Ya su  Ammi da Abba da Hajna kuma? "Duk suna lafiya lau, ina wuni". Be amsa gaisuwar tata ba yace "Kiyi haƙuri rashin network ya hana mu kasancewa tare nayi kewar ki sosai wallahi". "Uhmm Allah sarki babu komai nima nayi kewar ka, ya karatun? " karatu Alhamdulillahi, mun kusa kammalawa ma in sha Allahu". "To Allah ya bada sa'a, don Allah ka dawo da wuri". "In sha Allah zan dawo har muyi aure Hunayda, ke de wai ki kula da kan ki...... ~_From The Everlasting Golden Pen Of Golden Pen Writers Associotion Team Of MENENE RIBA TA AND ALLAH GATAN MARAYA_~             _~WE LOVE YOU ALL~_❤️❤️ 🤷‍♀🤷‍♀🤷‍♀             *_MENENE RIBA TA ❓_*                                                            🙆🙆🙆              © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~  ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf*  ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan*  ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI*   ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD*  ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO*  ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF  KO  MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ،* عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:  مَنْ صَلَّى صَلَاةً لَمْ يَقْرَأْ فِيهَا بِأُمِّ الْقُرْآنِ، فَهِيَ خِدَاجٌ ثَلَاثًا، غَيْرَ تَمَامٍ، فَقِيلَ لِأَبِي هُرَيْرَةَ: إِنَّا نَكُونُ وَرَاءَ الْإِمَامِ، فَقَالَ: اقْرَأْ بِهَا فِي نَفْسِكَ، فَإِنِّي سَمِعْتُ النبي صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ:{ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ } قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:{ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ } قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: أَثْنَى عَلَيَّ عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:{ مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ } قَالَ اللَّهُ: مَجَّدَنِي عَبْدِي - وَقَالَ مَرَّةً: فَوَّضَ إِلَيَّ عَبْدِي، فَإِذَا قَالَ:{ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ } قَالَ: هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ:{ اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ } قَالَ: هَذَا لِعَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ. رواه مسلم (وكذلك مالك والترمذي وأبو داود والنسائي وابن ماجه)* *On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: * "A prayer performed by someone who has not recited the Essence of the Qur'an (1) during it is deficient (and he repeated the word three times), incomplete." Someone said to Abu Hurayrah: [Even though] we are behind the imam? (2) He said: Recite it to yourself, for I have heard the Prophet (may the blessings and peace of Allah be up on him) say: "Allah (mighty and sublime be He), had said: 'I have divided prayer between Myself and My servant into two halves, and My servant shall have what he has asked for. When the servant says: 'Al-hamdu lillahi rabbi l-alamin' (3), Allah (mighty and sublime be He) says: 'My servant has praised Me.' And when he says: 'Ar-rahmani r-rahim' (4), Allah (mighty and sublime be He) says: 'My servant has extolled Me,' and when he says: 'Maliki yawmi d-din' (5), Allah says: 'My servant has glorified Me' - and on one occasion He said: 'My servant has submitted to My power.' And when he says: 'Iyyaka na budu wa iyyaka nasta in' (6), He says: 'This is between Me and My servant, and My servant shall have what he has asked for.' And when he says: 'Ihdina s-sirata l- mustaqim, siratal ladhina an amta alayhim ghayril-maghdubi alayhim wa la d-dallin' (7), He says: 'This is for My servant, and My servant shall have what he has asked for.'" (1) Surat al-Fatihah, the first surah (chapter) of the Qur'an. (2) i.e. standing behind the imam (leader) listening to him reciting al-Fatihah. (3) "Praise be to Allah, Lord of the Worlds." (4) "The Merciful, the Compassionate." (5) "Master of the Day of Judgement." (6) "It is You we worship and it is You we ask for help." (7) "Guide us to the straight path, the path of those upon whom You have bestowed favors, not of those against whom You are angry, nor of those who are astray." *Narrated  by Muslim and also by Malik, at-Tirmidhi, Abu-Dawud, an-Nasa'i and Ibn Majah* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Eight_    ~*Page 29*~ Wani irin dummm taji maganan Ummeen nata kaman saukan aradu akan ta,cikin kid'ima da rashin fahimta ta d'ago da kai ta zubawa Ummee ido tana tantaman abinda kunnenta suka jiyo mata yanzu gaskiya ne ko kuma mafarki take? Saukan wani bahagon  mari da Ummee ta kifa mata shiya dawo da ita daga suman zaunen da tayi kuma ya tabbatar mata ba mafarkin take ba, da ido take kowa na parlour ga bakinta na rawa amma ta kasa furta ko kalman A. Cikin wani irin tashin hankali da Ummee bata san dashi a duniya ba ta tsinci kanta a ciki jikinta sai karkarwa yake cikin d'aga murya tace" Saha magana nake miki uban wa ya miki cikin nan ki gaya min nace?"ta karasa da wata irin murya. Kuka mai cin rai wanda yafi karfin a kira shi dana nadama Saha ta fashe shi tana jin zuciyar ta kaman ya fito haka yake ta harbawa da sauri-sauri,yanzu shikenan Zaiyad ya yaudare ta ya gama da ita,ciki fa ina zata je da ciki?gashi tun ba'a je ko ina ba ya watsar da ita ya samu wata.... Ummee kuwa zuciya ne yazo mata wuya ganin tana  tambayan ta maimakon ta bata amsa ta kama mata kuka mara amfani,duka kawai ta rufe ta dashi ko ta ina abinda bata tab'a yi ba kenan domin Ummee na matukar kaunar yayan nata tana yi tana magana" ba zaki gaya min uban da yayi miki cikin nan ba ko Saha ina magana kina jina? Wallahi gwara in kashe ki kowa ya huta ba zaki dasa min bakinciki ba,ba zaki b'ata min suna ba" sai haki take tana suratai da itama bata san ma'anar su,Saha kuwa ko ihu batayi ba bare neman ceto saboda radadin da zuciyar ta ke mata yafi karfin dukan da Ummee ke mata,Suraiya dake gefe itama tana kuka tana bawa Ummee hakuri amma ko jinta bata yi. Duka tayi mata sosai amma Sahabbat bata da niyyan cewa komai,Ummee dan kanta ta gaji ta kyale ta ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi can kuma ta fashe da kuka mai cike da d'acin zuciya tace" Innalillahi wa inna ilahi rajiun!!! Na shiga uku yau me zan gani wannan wace irin bakin rana ne haka a rayuwa ta? Sahabbat kin cuce ni kinci amanar tarbiya dana baki me nayi miki zaki saka min da wannan mummunar sakamakon?".kuka ne ya ci karfinta ta kasa karasa maganan taci gaba da kukanta ita da 'yan mata ta babu mai rarrashin wani. A bangaren Salma kuwa bayan fitan Abdul da Jameela tun tana kuka su Fatima suna bata baki har suga idonta ya kafe tayi baya luuuu ta fad'a kan gadon babu numfashi a tare da ita,ihu su Fatima suka saka suna ambatan sunan ta tare da girgiza ta babu wanda yayi tunanin kiran doctor a cikin su,a haka su Aunty Maryam da Aunty Jidda suka shigo suka same su. Da gudu suka karaso ciki tare da tambayan meke faruwa? Abinda ya faru Fatima ta fara fad'a musu sai dai Aunty Maryam bata tsaya jin karshen zancen ba ta garzaya zuwa office d'in Doctor ta kira shi suka taho tare da wasu nurses 2,ba b'ata lokaci suka fara kokarin ceto rayuwarta bayan sun kora su Aunty Jidda waje dan su samu daman yin aikin su. Suna fita Aunty Maryam ta kira gida cikin kuka ta zayyane musu abinda yake faruwa,ba sufi 15 mints da waya ba sai ga iyayen su da Yayan su namiji sun shigo asibitin cikin tashin hankali suna tambayan ya jikin nata kuma tana wani d'akin dan su shiga su ganta,Fiddausi ce tayi karfin halin basu amsa cewa ga d'akin da take amma Doctors suna ciki har yanzu basu fito ba. Cike da jimami suka nemi guri suka zauna jiran tsamani zuciyoyin su cike da fargaba Maman ta sai share hawaye take,sun kai good 20 mins da zama sannan suka ga an bud'e kofan d'akin da take ciki Doctor ya fito yana goge zufan dake goshin sa nurses na take masa baya,gaba dayan su suka taso sukayi kan shi suna tambayan ya jikin nata? Cikin natsuwa yake bin fuskokin su da kallo daya bayan d'aya amma baiga fuskar Abdul a cikin su ba dan haka no wasting of timw ya tambaya " ammm nace ba ina mijin nata yake akwai abubuwan da nake so mu tattaunawa dashi". Su Aunty Maryam zasu bada amsa Abban su yayi saurin cewa baya nan an kira shi a wajan aiki amma zai iya gaya mishi ko menene dan shi mahaifin tane,office d'in shi yace su je zai masa bayani a can yana fad'an haka yayi gaba Abba ya rufa masa baya har office d'in. Suna shigowa Doctor ya zauna tare da nunawa Abba kujera yace ya zauna,a d'osane ya zauna dan shi ba zama ne a gaban shi ba halin da 'yar shi take ciki shine a gaban shi,bayani ya fara mishi na yanayin cutan nata kuma yace a kiyaye abinda zai b'ata mata rai komin kankantar sa domin yanzu haka anyi mata wani abinda ya bata mata rai sosai ne bayan warning da yayiwa mijinta amma Allah  ya kawo da sauki domin sunyi nasaran shawo kan matsalar a yanzu sai dai su kiyaye gaba. Godiya Abba yayi mishi ya fito daga office d'in jiki a sanyaye,suna ganin fitowar shi duk suka mike tsaye suna jiran suji me Doctor yace, a takaice ya fad'a musu abinda yake damunta da kuma yanda Doctor yayi warning kan kiyaye bacin ranta. Mama ba abinda take sai hawaye,da daddaya suka fara shiga suna dubo yanayin jikin nata gudun kada su tashe ta daga baccin hutun da take,matan duk in sun shiga da kuka suke fitowa saboda yanda cuta ta maida lokacin guda kaman ba Salma 'yar gayu ba.tun daga wannan rana iyaye da 'yan uwan Salma suka shiga bata kulawa ta musamman suna tarairayan ta sannan suna matukar kokari na ganin basu bar ta tayi tunanin past rayuwar ta ba. Salma ta kanyi pretending na bata tuna komai abinda ya danganci rayuwar ta na da but yana damunta kuma kullum cikin dare ta kan tashi tayi ta kuka tana yiwa Jameela Allah ya isa sannan tayi ta nafila cikin dare tana kaiwa mai sama kukanta tare da neman ya sassauta mata radadin dake cinta a rai,cikin ikon Allah kamin ta cika wata 2 a gidan su sosai zuciyar ta ta rage jin zafin abinda Abdul yayi mata. A gidansu Saha kuwa wannan rana babu wanda ya runtsa saboda tashin hankali kowa da irin tunanin da yake,ita Saha abubuwa sun gama cakude  mata tana tunani ta fad'awa Ummee gaskiya ne ko kuma ya zatayi gashi sai gwada layin Ziyad take amma yaki shiga hakan ya tabbatar mata da cewa yayi blocking din number ta,tun tana da karfin kukan har karfin ta ya kare ta kwanta lamo sai ajiyar zuciya take tana tuno yanda ta fara had'uwa dashi da yanda yayi amfani da Kalmar aure ya yaudare ta har ya cimma burin shi akanta take" Hunayda....." Ta furta can kasan makoshi Allah sarki k'awa ta gari kuma masoyiya,inama ta d'auki shawaran da take bata tun farko da haka bata faru gare ta tana ganin hakan shine so da wayewa. "Dole in fad'awa Ummee gaskiya meye amfanin b'oyewa tunda komai ya gama lalacewa ya daina sona ko kuma ince ya gama dani,dubi yanda muka rabu jiya dashi amma har yanzu ko text din shi ban gani ba bare kira...Ya Allah na cuci kaina..." ta cigaba da maimaitawa kuma duk a bayyane take wad'an nan kalaman suraiya da take kwance a gefen ta sai hawaye take sharewa saboda tausayin 'yar uwarta. Ummee tana kwance a d'akinta sai kuka da tsinewa wanda ya lalata mata 'ya take duk taka tsantsan da take a kan ta sai da yayi nasara "wai wani d'an tsinanniya ne shi? Duk yanda akayi ba d'an halal bane d'an kwararo ne Allah ya isa tsakanina da kai..." Karan wayarta shi ya dakatar da ita ta juyo tana kallon wayar dan tashin hankali da take ciki yau bai barta ta tuna da wata waya ba bare tayi typing. A hankali ta kai hannunta na dama ta d'auko wayar na hagun kuma tana share hawayen ta dashi tana duba screen d'in wayar taga wata fitattaciyar fan d'in tace da tafi kowa iya sharhi kan kowanne update da zatayi gata da iya turo mata recharge card kullum dan wai taji dad'in yi musu update, dan haka Ummee tana matukar ji da ita cikin fans d'in ta bata ganin kiranta ta kyale amma yau tana gani har tayi mata 2 missed calls ta.kasa d'agawa ta san ba zai wuce ta tambaye ta ya yau suka ji shiru babu sabon update kaman yanda ta saba musu dashi ba. Bayan kaman minti 5 wani kiran ne ya kara shigowa na wata fan d'in a zuciye Ummee ta kashe wayar baki d'aya dan yau ita kad'ai tasan halin da take ciki. Kamin gari ya waye Ummee ta tsayar da shawaran ta kira kawun su yazo ko in Sahabbat ta gan shi zata iya fadan wani abu game da cikin jikin ta kasancewar suna tsoron shi sosai duk da dai wani bangare na zuciyar ta na kwabar ta akan yin haka sai dai dole ne tayi dan bata da wani mafita sai wannan. Da washe gari Saha sallah kawai tayi ta koma ta kwanta saboda jikinta duk ciwo yake mata ga wani zazzafan zazzabi daya rufe ta sai nishi take hawaye na bin gefen idonta,Suraiya ita tayi akin komai a gidan abinda ya had'a da girka abin karya har zuwa sauran aikace-aikacen gida,koda ta shigo dan sanarwa Ummee ta gama saida ta girgiza ganin yanda fuskan ta ya kumbura suntum saboda kuka da rashin bacci cikin ita da Saha bata san wacce tafi wata ba. "Kije ina zuwa Suraiya" tace tana tashi daga kwancen da tayi ta zauna,wayarta ta d'auka ta kunna sai da ya gama booting sannan ta nemo no Kawu ta danna mishi kira,bayan sun gaisa tace tana son ganin shi yanzu in babu matsala. Nan ya shiga tambayan ta lafiya dai ko? Da eh ta amsa mishi ta katse kiran ta zauna jiran shi tare da rabka tagumin da hannu 2, Kawu bai dad'e ba ya kamo hanyan zuwa gidan nasu jin muryan ta a shake ya san babu lafiya,a kofar gidan yayi parking na motan shi sannan ya fito ya nufi cikin gidan. Sallamar shine ya dawo da Ummee hayyacinta kamin ta amsa har Suraiya ta amsa ta fito tana mishi sannu da zuwa,both Ummee da Saha kowanne su sai da suka ji fad'uwarta gaba,Ummee nata na fargaban ya zai d'auki zancen ne while Saha kuma nata na tunanin meya kawo shi gidan su da sassafen nan,ko kuma yaji labarin abinda ya faru ne? Kai ta girgiza da wuri tace" nasan Ummee ba zata fad'awa kowa wannan maganan ba saboda......" Banko kofar d'akin nasu da akayi yasa ta firgita ta mike jikinta na wani irin rawa ganin Kawu su d'auke da wata sharb'eb'iyar wuka da ake yanka musu ragon layya dashi ga fuskan nan a murtuke kaman mala'ikan mutuwa yasa ta kusan sake zawo a jikinta. Baya-baya ta farayi yana binta har suka karasa jikin bango,ganin babu wajan guduwa yasa ta durkushe a wajan ta fara kuka tana yarfe hannaye tare da rokon shi,hannu daya ya d'aga mata alaman tayi shiru ai kuwa ba shiri ta had'iye sauran kukan sai jikinta da yake karkarwa. A hankali ya karaso gaban ta ya durkusa yana mata wani kallo daya kara hargitsa mata hanjin cikin ta yace" abinda naji Ummee ku ta fad'a gaskiya ne?" Kasa magana tayi sai ido da ta d'ago ta kalli Ummee dake tsaye a bakin kofan shigowa,lafiyayyaen mari daya kifa mata wanda ya haddasa mata kurumta na 'yan seconds kamin jin nata ya dawo cikin razanannen murya da bata san Kawun nasu dashi ba taji ya daka mata tsaya yace" zaki amsa min ne ko kuwa?" Kamin ya karasa tayi saurin gyad'a mishi kanta yace" good! Gaya min wanene shi?" Sanin halin shi yasa ba b'ata lokaci ta bud'i bakin ta na rawa tace" Za.....Za....Zaiyad". "Good kin san inda zamu same shi?" Ya kara jeho mata tambaya,nan ma gyada mishi kai tayi. Ya juya ga Ummee dake tsaye yace " ku same ni a mota" yana fad'an haka ya raba ta gefen Ummee yayi waje,wata muguwar harara Ummee ta jefe ta dashi sannan ta juya fita,jiki a mace Saha ta mike ta jawo hijabinta ta saka ta fito tana Jan kafa a lokacin Ummee har ta fita dan haka itama bata tsaya a tsakar gidan ba tabi bayan Ummee, gidan gaba Kawu ya nuna mata da hannu alamun ta shigo nan babu musu kuwa ta shiga tana shiga Kawu yaja sukayi gaba. Kallonta kawo yayi da suka hau babban titin,jiki na rawa ta fad'a mishi sunan anguwan su Zaiyad dan tasan nufin sa kenan,suna zuwa cikin anguwan ta fara mishi kwatance har suka iso kofar gidan yayi parking ba Ummee kad'ai ba harda Kawu wajan mamakin ya akayi Saha ta san nan wajan har take zuwa bayan basa zuwa ko Ina daga makaranta sai islamiya. Suna fitowa daga cikin mota Zaiyad shima yana fitowa daga cikin gidan sanye da farar jallabiya kan zai je restaurant ya sayo musu breakfast shida Zee shi. Wani mugun firgita yayi ganin Saha da iyayen ta amma da yake d'an duniya ne nan da nan ya had'iye ya bisu da kallon wa kuke nema? Kawu ne ya d'aure zuciyar shi ya d'an matso yayi mishi sallama,amsawa yayi har da d'an dukawa ya gaishe su wanda yin hakan har saida yasa Kawu shakku,Zaiyad dariya ya fara a cikin zuciyar shi d'an ya lura da yanda yanayin Kawu ya canza lokaci daya duk da haka Kawu ya daure yace" bawan Allah kasan wannan yarinyan"? Kallon Saha yayi a yatsine kaman yaga kashi sannan ya girgiza kai yace" A'a Baba ban santa hasalima yau na fara ganinta,me yasa ka tambaya Allah yasa dai lafiya?" A razane Saha ta d'ago tana kallon shi dan kunnenta sun kasa gaskata cewa wai yau Zaiyad d'in tane yake cewa bai tab'a ganin ta ba? Kamin tayi wani yunkurin magana taji Kawu na cewa" kada ka nemi raina mana hankali dan kaga ina binka a hankali,dole kace baka santa ba tunda ka gama lalata ta harda guzurin ciki". "Innalillahi wa inna ilahi rajiun!!! Yarinya kiji tsoron Allah dan kinyi abinki a wani waje kada kizo ki shafa min kashin kaji" ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020*             _~We Love U All~_❤ 🤷‍♀🤷‍♀🤷 *_MENENE RIBA TA ❓_* 🙆🙆🙆 © *2020* 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* ~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_ ~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍ ♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.* ♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.* ♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.* ♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.* ♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.* ♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).* ~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_ ~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!* ♣ _Scene Eight_ ~*Page 31*~ *LAST PAGE* Sahabbat sosai take nunawa Ummee cewa ta karanta abinda take rubutawa domin ko kad'an ta daina bawa Ummee wani girma saima nuna mata da take idonta ya riga ya bud'e babu abinda bata sani ba a rayuwa,wannan sabon halin nata kullum sai yasa Ummee zubar da hawayen nadama,WhatsApp d'in ma tuni ta goge shi a wayarta saboda shine musababin halin da take ciki yanzu. Kawu ya kawo musu labarin an kama Zaiyad kuma ya amince ya amsa laifin shi sannan Baban shi yace dole ya aure ta bayan ta haihu, Ummee tayi farinciki da jin haka ko ba komai asirin su zai rufu amma tasan akwai babban kalubale gaban ta wajan fuskantar mutane da yan uwa saboda ta sani ko a wajan 'yan uwan ta ba zata tsira ba bare a je ga dankin Baban su Saha. Ita kuma Saha tunda taji labarin bai dame ta ba saima kara kaimi tayi wajan yiwa Ummee iskanci son ranta dan wani lokacin in taga Ummee zaune a parlour sai ta zo itama ta zauna d'an nesa da ita tayi ta maimaita novels na Ummee wanda zai sata ta bar wajan ba shiri dan kunya ne yake lullub'e ta ji kaman ta nurse kasa,yau ma ganin Ummee zaune yasa tazo ta zauna tana" wash na kwana 2 ban karanta sabin novels masu saka ni nishad'i ba amma bari in karanta na bayan saboda bana gajiya da karanta wannan novel d'in saboda dad'in ta". Ummee tana jinta bata tanka mata ba kamin ta ankara taji ta fara karanta wani zazzafan page data rubuta wanda sai da fans dinta a ranan suka cika mata waya da recharge card saboda yanda ta zuba shaid'ancin a ciki abun ba'a magana. A zuciye Ummee ta kwace wayar tayi jifa dashi ya fad'a kan kujera tace" ya ishe ki haka Sahabbat kada kiga ina kyale ki kina abinda kika ga dama hakan ba wai yana nufin kin gagare ni bane kuma kada ki manta har abada nice mahaifiyar ki....." Ummee kenan na san kece mahaifiya ta shiyasa Kika ga ina kokarin nuna miki yanda zaki gyara lahirar ki,ko kunnuwanki sun gaza sauraron abinda kika rubuta da hannun ki saboda munin su amma kuma a haka wasu yaran da basu fi 13 ko 15 years ba suma sun karanta kuma yana cigaba da yawo a social media Allah kad'ai yasan shekarun da za'a dauka kamin ya b'ace sannan duk wanda ya karanta ya lalace ta sanadiyan novel dinki kina da naki kason a kowani abinda ya aikata" kukan Ummee daya tsaanan ta shiya hana ta karasa abinda tayi niyya tayi shiru ta zuba mata ido tana share nata hawayen. "Nayi nadama Saha nayi nadaman ban tab'a yin irin shi ba a rayuwa ta bana cikin kwanciyar hankali kullum idan na tuna cewa babu yanda zanyi na goge abinda na rubuta kullum kara yaduwa yake kuma zunubai na kara hauhawa suke abin yana kara firgita ni,koda yaushe cikin istigifari nake ko Allah zai yafe min " Ummee ke fad'an haka cikin marairaicewa" Allah zai yafe miki Ummee na tunda kinyi nadama kuma kinyi tuban gaskiya, Ummee nima ko yaushe a cikin ta nake na biyewa son zuciya da rudin shaidan na b'ata rayuwata Allah ka yafe min...." Rungume juna sukayi dukan su 2 suna kuka kaman ransu ya fita kana ganin su zaka san sunyi tsatattaciyar nadama. Zaiyad saida yayi sati 1 a hospital bed sannan ya samu sauki aka sallamo shi ya dawo gida zuciyar shi na masa ciwon abinda Baban shi yayi mishi wai ace mahaifin shi da kan shi ya mika shi ga police maimakon ya kare shi,tunda ya dawo yake ta cincin magani shi a dole fushi yake ,Baban shi yana ankare da shi amma bai kula shi ba saida yayi kwana 2 da dawowa sannan ya kira shi suka zauna dashi a parlour harda Maman shi sannan ya fara bayanin dalilin da yasa ya kira su yace" na dad'e ina jin rad'e-rad'in abinda kake aikatawa amma banyi saurin yanke hukunci ba saida naga zahiri shiyasa na bari police suka koya maka hankali ka sani Zaiyad shi zina da kake gani bala'i ne banda azabar Allah dake jiranka acan kiyama anan duniya kuma bashi ne in kayi da 'yar wani sai anyi da 'yar ka na tabbata ba zaka so ace wani ya aikata maka abinda kakewa 'ya'yan mutane ba. Kai ba yaro bane haka kuma kai ba jahili bane amma ka biyewa son zuciya ka yi gaggawar tuba ka koma ga Allah tun kamin lokaci ya kure maka,munyi magana da shi Baban yarinyan kan cewa tana haife cikin dake jikinta za'a d'aura maka aure da ita". A razane ya d'ago yana kallon Baban shi dan yanda yaji saukan maganan kaman saukan guduma a tsakiyan kan shi tayaya za'a ce za'a aura mishi Sahabbat duk dacikin 'yan mata da yayi mu'ammala dasu babu wacce yake jinta a cikin ran shi kaman ita amma gaskiya ba zai iya auran ta ba domin ba shida burin daya wuce ya samu sweet sixteen kuma virgin ya aura sai gashi Baban shi yana son rusa mishi tsari,a raunane ya d'ago yace" nayi kuskure Baba ka yafe min amma dan Allah ina rokon alfarma kada kace inyi aure yanzu wallahi ban shirya ba". "Haba Alhaji taya zaka ce ya auri yarinyan da ta gama wastewar ta harda cikin shege,kasan mutane da sharri kai kuma ka biye su ba tare da wani bincike ba".cewar Hajiya kenan dan tunda ya fara maganan take ta faman tab'e baki. Murmushi Baban yayi yace" wannan maganan da kikayi shi ya kamata ki tambaya zai baki amsan cewa cikin nashi ne ko ba nashi ba,kai kuma bud'e kunnen ka kaji in kaga ba'a d'aura auren ka da yarinyan nan ba ka tabbata ita tace bata son ka dan haka tashi ka bani waje mutumin banza kawai". Zuciyar shi a jagule ya mike ya fita daga parlour kuma ya d'auri d'amaran yaki da ita Sahabbat har sai tace bata ce bata son shi da kanta. Yana zuwa d'akin shi a fusace ya ficiko wayar shi dake jikin charging ya fara neman layin Sahabbat,kusan 5 missed calls ya mata amma bata d'aga ba. A zuciye yayi cilli da wayar yana huci shi kad'ai yaso ace ta d'aga wayan nan domin abinda yayi niyyan yi mata sai tayi nadaman sanin shi da tayi a rayuwar ta. Saha kuwa tana bacci bata san ya kira ba saboda wayar tana silent duk da yanzu kowa ya san tana da waya amma ta kasa cire shi a silent saboda sabo,tana tashi daga bacci taga missed calls d'in Zaiyad saida taji fad'uwar gaba kasancewar tayi iya kokarin ta ta cire tunanin shi a ranta kuma ko lokacin da Ummee ta bata labarin hukuncin da aka yanke na had'a su aure abin bai wani d'aga mata hankali ba amma yanzu gainin kiran nashi yasa taji duk hankalin ta ya tashi. Tana shirin tashi taje wajan Ummee dan ta fad'a mata domin yanzu bata da abokiyar shawara sai Ummeen ta itama Ummee yanzu sai take jinta kaman ba ita ba saboda tana samun time ta zauna tare da yaran ta suyi hira ta fuskanci matsalalolin su ba kaman baya da bata da lokacin kowa saina fans nata,kara shigowan kiran Zaiyad ne ya hana ta tashi ta tsurawa wayar ido tana ji kaman kada ta d'aga saida ya kusan tsinkwa sannan ta d'aga ta kara a kunne ta ba tare da tace komai ba tana jira taji me zaice mata taji ya fara mata ihu a kunne yace" Sahabbat or whatever you are I don't care abunda nake so dake shine ki bud'e kunnen ki da kyau ki saurari me zance miki tun kamin dare yayi miki ki maza ki cewa wannan tsohon naki ba kya son auren nan if not kika yarda akayi auren nan wallahi sai na lahira yafi ki jin dad'i in yayi aiki mai kyau sannan kuma....." Dakata Zaiyad kada kace zaka cika min kunne da haushinka na banza ce maka akayi ni son auren naka nake? Amma tunda har kayi kuskuren nuna min kin auren nan a zahiri toh wallahi sai dai ka mutu dan wannan auren babu fashi". Tana gama fad'an haka ta katse wayar tana huci yau wai Zaiyad ne yake mata wannan bala'in dan ance ya aure ta amma da saboda ya cimma burin shi akan ta kullum sai ya ambato mata maganan aure da yanda zasuyi rayuwar su in sunyi. ************************* Salma duk an watse an barta a gidanta tana zaune shiru tana jiran zuwan angon nata tare da fatan ya kasance mata irin mijin dasu *muna wuta* suke fad'a a novels din su,sai sak'a da warwara take na meye ya rike shi har yanzu bai iso gare ta ba duk da yanda yake nuna d'auki sa akanta amma gashi har 11 ta wuce shiru,gajiya tayi da zaman ta kwanta bata dad'e da kwanciya ba bacci yayi awon gaba da ita sai kusan 12 sannan ya shigo gidan direct d'akin nata ya shigo saida ya zauna a bakin gadon sannan ta farka suna had'a ido ya sake mata murmushi mai sanyi yace" amarya ayi min afuwa na tsaya sallama da abokai nane" Tashi tayi daga kwancen tana d'an murmushi ta zauna sannan tace" kada ka damu ba komai".nan yace ta sauko suci abinci daya shigo dashi,bata musa ba ta sauko kasa da kanshi ya d'auko musu plates,cups da spoons sannan ya juye gasassun kaji daya siyo musu a plate yana ce mata bismillah ya fara durawa cikin sa bai ko tsaya ya lura da tana ci ko bata ci ba,saida yaci yayi Kat sannan ya cika glass cup da fresh milk ya shanye yayi gyatsa sannan ya mike ya shige bathroom dake cikin d'akin ya wanke hannun shi ko brush bai tsaya yi ba bare wanka ya zo ya haye gado yacewa Salma tazo su kwanta bayan ya rage kayan jikin shi. Cike da sanyin jiki take kallon shi yanda bai tsaya ya kimtsa jikin shi ba yazo ya kwanta gashi ko nafila basuyi ba tace" ba muyi sallah nafila ba kuma ina son yin wanka kamin in kwanta" haba ke kuma wani wankan bayan wanda da kikayi a gidan ku? Maganan nafila kuma mayi anjima ai nafila sai dare ya raba ake yin ta".zatayi magana ya katse ta yana nuna tana b'ata mishi lokaci take,da kyar ya barta ta wanke hannunta ta dawo ko tattare wajan bata samu daman yi ba ya jawo ta suka kwanta. Bayan komai ya lafa Salma idon ta 2 tana kallon yanda yake ta sharan baccin shi hankali kwance ko tsarkake jikin shi baiyi ba ya baje da bacci,ita ba wannan ne yake bata takaici ba sai na yanda ya rinka nuna mata shi a matse yake kaman wanda zaiyi wani abin kirki amma basu fi 30 mins ba wai har ya gama komai ya kama bacci,toh shi kuma haka yake ko kuma yau din ne yayi hakan saboda gajiyar biki? Abdukareem ta tuna a daren su na farko ko wasa kad'ai ya kai gud 1 hr yana yi da ita sannan ya kai ga wani abun amma shi wannan ko wasan ma bai iya ba kuma bai wani tabuka mata abin kirki ba illa kara kunna mata wuta da yayi ya kwanta abin shi. Haka ta rinka juyi har kusan asuba sannan bacci yayi nasaran d'aukan ta,koda sukayi sallah asuba zata koma bacci yace shi da sassafe zai fita dan haka ta d'aura mishi breakfast yanzu,duk da tana jin bacci na cin idon ta amma haka ta hakura ta fito kitchen ta had'a breakfast mara nauyi tana yi tana tuna ranan ta na farko a gidan Abdukareem shine ya shiga kitchen yayi musu breakfast in short sai da tayi good 1 week bai barta ta shiga kitchen ba. Istigifari tayi a bayyane saboda a tana matar wani bai kamata tayi tana tunanin tsohon namiji ba,tana gamawa ta kai komai kan dinning ta shiga ta tarar da shi fitowar shi kenan daga wanka ta tsaya tana kallon yanda yake shafa mai sauri-sauri bata ankara ba taji yace" baki iya gaisuwa bane zaki zo ki wani zuba min ido haka?" Saurin gaishe shi tayi daga inda take tsayen,maimakon ya amsa binta yayi da wani mugun kallo yace" saboda rashin tarbiya daga tsayen zaki gaishe ni sai kace ni sa'an kine". Cike da mamakin yanda yake treating d'in ta daga jiya zuwa yau ta durkusa ta gaishe shi,bai amsa ba ya fito parlour ya hau kan dinning ya bud'e abincin da ta girka mishi yaga kwai ne kawai ta soya mishi sai bread da ruwan lipton,ture abincin yayi ya fara kwala mata kira da dukan karfinsa,har tuntube take wajan fitowa dama tana nan durkushe a inda ya barta mamakin abinda yake mata bai barta. "Wannan wani irin shashanci ne,wannan shirmen shi kike kira girki sai kace wani d'an goye kika samu zaki wani soyo min kwai 1 ki kawo min shi a matsayin abincin?" Jin ya ambaci sunan kwai 1 yasa ta d'aga ido ta kalle shi da mamaki yace mata" me kike min irin wannan kallon ko karya nayi miki ke ga mai gara kada in cinye miki ko?toh wallahi ina gaya miki ki gyara halin ki dan saboda ni ba zan d'auki wannan shashancin ba"yana gama banbanin shi ya fice ya bar mata gidan. Hawaye ne ya zubo mata tasa hannu da wuri ta share tana rarrashin kanta kan cewa ba haka yake ba maybe wani abin ne ya bata mishi rai,gyaran gida ta hau yi duk da ko Ina tsab yake dan su Aunty Jidda saida suka gyara mata ko ina jiya kamin suka tafi,tana gamawa ta fad'a wanka bata d'auki dogon lokaci ba ta fito ta zauna gaban mirror tayi simple makeup sannan ta saka wani atamfan ta na super wax mai golden da pink a jiki anyi mata dinkin doguwar riga yasha stone work ta gaba sosai kayan.sukayi mata kyau,turaruka ta fesa sannan ta fito parlour lokacin kusan 8:30na safe dan haka kan dinning ta wuce ta had'a tea har ta bud'e kwai data soya mishi amma ta kasa ci saboda yanda take jin zuciyar nata a cunkushe tea kawai ta sha ta dawo kan kujera ta kwanta tana tunanin abubuwa da suka faru daga daren jiya zuwa yau da safe bata san da me zata fassara shi ba,tana cikin tunanin bacci ya sace ta kasancewar jiya da daddare baccin ta kad'an ne. Tana cikin bacci su Aunty Jidda suka shigo kusan su shida,tashin ta sukayi suna tsokananta wai ango ya hana ta bacci ya tara mata gajiya dole tayi baccin safe,ita dai bata kula su ba saima hankalinta data mayar kan su suka gaisa a mutunce. "Kuzo Kuga girkin ango" wata cousin din su mai suna fareeda take fad'a musu lokacin da karambanin ta ya kai ta kan dinning ta bud'e abubuwa da suke wajan tana kallo " ai dama yanda naga Alhaji Naseer yana ta rawar kafa akan ki nasan zaki sha tarairayan" cewar Aunty Maryam kenan ita dai bata ce komai ba sai yake da take ta bin su dashi,zuwan su ya debe mata kewar dan sai hira da raha suke tayi rana nayi kuma suka shiga kitchen suka girka cous-cous da vegetable soup sannan suka hada coconut nd pineapple juice suka ci suka zubawa ango rabon shi a sabobin warmers masu kyau sai kusan 4 sannan suka tafi ba dan Salma ta so ba. ****************** A gidan Abdukareem komai sai kara tabarbarewa suke kan yanda Jameela take gallazawa su Husna amma har yanzu bai sani ba domin Jameela ta kware wajan iya munafurci sannan yanzu ta koma ruwa tsundum shima babu abinda ya fahimta kasancewar ta iya takunta,in a gaban shine nuna mishi take babu wani d'a namiji sai shi amma daga ya fita wajan aiki kuma ta riga da ta san lokacin fitan shi da dawowan shi yasa yana fita itama take saka kafa tayi ficewar ta bayan ta tsamma yaran abinci ta kulle su a d'akin su. Abdukareem har yanzu Salma tana makale a zuciyar shi dan ma Jameela tana d'auke mishi hankali da salon ta,sosai yaji wani abu a zuciyar shi lokacin da labarin auren ta yazo mishi amma ganin yanzu ta zama matar wani yasa ya rage tunanin ta zuciyar sa itama Jameela data ji labarin Salma tayi aure abu 2 taji a ranta na farko taji dad'i kuma tayi nasaran kwace Abdukareem a hannunta na har abada kuma hakan ya tabbatar mata ba zata kuma dawowa suyi rayuwa tare ba sannan abu na 2 bata ji dad'i ba da Salma ta samu mijin aure da wuri haka taso ace ta kwashi shekaru ba aure kaman yanda ita tayi a baya. """""""""""""""""""""" Zaiyad kullum sai ya kira Saha yaci mata mutunci kan wai lalle sai ta fad'a a gidan su kan bata son auren duk da itama bata raga mishi in yace as sai tace mishi cas,tun abin yana damunta harta saba wani lokacin tana ganin kiran shi ba zata d'aga ba. Cikin Sahabbat yanzu ya shiga wata na 7 duk wasu laulayi ta daina su sai girman da cikin nata yayi kaman ba cikin fari ba,zagi da tsegumi ta sha su daga wajan mutanen anguwan su harda ma 'yan uwan su kowa da abinda yake fad'a,wasu suce sakacin ummee ne wasu kuma suce dama Sahabbat idon ta a bud'e yake ka haifi d'a ne baka haifi halin shi ba. Ummee duk tana jinsu amma ta d'auke kanta tayi kaman bata san sunayi ba cos abinda yake gaban ta yafi mata mahimmaci ga 'yan kungiyar su na*muna wuta* sun saka ta a gaba kan ta dawo da rubutu ko kuma zasu karbe matsayi da aka bata a bawa active ones,nan ita kuma ta nuna musu ta daina rubutun kwata-kwata su cire ta a kungiyar ma gaba 1.bata san 'yan kungiyar nasu basu da mutunci ba saida suka fara kiranta daya bayan d'aya suna ce mata sunji 'yar ta tayi cikin shege ko shiyasa ta ajiye rubutun basu kad'ai ba harda fans dinta masu zugata a lokacin da take rubutu sai gasu suna kiran ta sunayi mata izgili suna dariya abin da yayi sai ta canza sim card kawai ta bar wanda duniya ta san ta dashi. A wannan lokacin Malam Sulaym ya dawo daga karatu da good result bai sha wahala ba ya samu lecturing a nan ABU zaria a fannin Arabic a wannan lokacin aka saka ranan auren su da Hunayda wata 2 kacal masu zuwa. "Ammee ina neman izinin ki zan kaiwa Sahabbat kati koda ba zata zo ba saboda a da banida aminiya kamarta"Hunayda ce tsugune a gaban Ammee take neman izinin cikin ladabi. "Ba zan hana ki ba hasalima hakan yana da kyau Allah yayi miki albarka" Ameen Ammee" ta amsa tana mikewa ta shiga d'akin su hijabi kawai ta saka ta fito Ammee ta bata kud'in napep ta fita. A kofar gidan su Saha mai napep d'in ya sauke ta,kudin shi ta bashi sannan tayi sallama ta shiga ciki Ummee ta gani zaune a tsakar gida tana taya Suraiya tsifa har kasa Hunayda ta durkusa ta gaishe ta kaman yanda ta saba kallon sha'awa Ummee ta bita dashi tana amsa gaisuwan tana mata fad'an me yasa ta d'auke kafa a gidan su sannan tana tuna lokacin da suke tare da Saha haka take itama. "Ki shiga tana ciki" cewar Ummee da toh ta amsa tana mikewa tana tsokanan Suraiya wai sun fara zama seniors a islamiya shiyasa ba'a ganinsu. Kaman yanda ta saba da haka ta fad'a d'akin tana mita" kina jina shine kikayi lakwas a daki kaman wata mara gask...."maganan ne ya makale mata ganin Sahabbat ta turo katon cikinta a gaba tana zaune tana mata murmushi amma idonta cike tab da hawaye tace" hakane Hunayda ina nan a daki ko a tsakar gida bana iya zama saboda rashin gaskiya ina tsoron kada mutane suzo su ganni,kinga abinda son zuciya ya jawo min kina bani shawara amma ina miki kallon bagidajiya ga sakamako ban na sam......" Kuka ne yaci karfin ta kasa karasawa da gudu Hunayda tazo ta rungume ta ta fashe da kuka sosai itama tana" Inna lillahi wa inna ilahi rajiun Sahabbat yaushe hakan ya faru me yasa baki name ni ba" da wani ido zan kalle ki Hunayda bayan irin abubuwan da nayi miki akan fad'a min gaskiya da kike ki barni in girbi abinda na shuka" sun dad'e suna kuka ba mai rarrashin wani da kyar suka rarrashi junan su sukayi shiru. Bayan Saha ta bata labarin duk abinda ya faru sannan itama Hunayda ta bata labarin bayan rabon su da katin auren ta da ta kawo mata tace yanzu saura wata 1 ya rage bikin nasu,sosai Saha ta taya ta murna tace sai dai ita ba zata iya zuwa ba saboda watan haihuwar tane lokacin bikin,addu'an Allah ya sauke ta lafiya tayi mata sun dad'e suna hira sannan tayi musu sallama ta tafi tare da alkawarin zata kuma dawowa kamin bikin nata. A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah dan yau ake walimar auren Hunayda wanda ya kayatar sosai saboda ya tara manyan malamai,da washe gari aka d'aura auren su bayan sallahn juma'a Mallam bai yarda anyi wani bidi'a ba dan haka bayan sallahn isha'i aka mika ta gidan mijinta bayan ta sha dogon nasiha daga wajan iyayenta. (Sai muce happy married life Hunayda). """"""""""""""""""""""""""""'''""''''''''' Rayuwar Salma a gidan Naseer ba abin cewa saboda abin kullum kara muni yake domin Naseer irin mutanan ne da zaka gansu a nesa kaman mutanen Kwarai amma da zaka kebe dasu zaka san ba haka suke ba domin ada kamin ta aure shi akace ga halin shi ba zata tab'a yarda ba domin ya kasance cikin mazajen nan ne masu nunawa mace so kaman su lashe ta amma da zaran kin shigo kuma shikenan kin zama bola saima son nuna iko da kokarin maida mace baiwa,duk wani d'auki da soyayya daya yake nuna mata a waje tunda ta shi ko a ido bata ga ya nuna mata ba balle a aikace. Na 2 kuma tunda suka cinye garan da akayi mata a gidan su ta daina cin wani abu mai dad'i gashi da kudi amma ko shinkafa baya saya sai garin masara wai yafi dad'i bare tasha tea mai madara ga bakin magana da yake yab'a mata sai in dare yayi yazo mata da bukatar shi wanda a dole Salma take bashi kanta domin in har ya kusance ta toh da ciwon mara take kwana domin Naseer in har ya biya nashi bukatar toh ita ko oho gashi baya wuce minti 15 ko 20 gaba daya. Salma duk ta rame saboda bakinciki amma ta had'iye kayanta domin ko su Aunty Jidda bata tab'a fad'awa matsalar ta ba saboda tayi abaya bata ji dad'i ba shiyasa tayi gum da bakin ta,ga kewar yaranta dake cinta a cikin ranta yau sama da wata 8 rabon da ta saka su a idon ta,duk yanda tayi yaki da zuciyar ta na ganin batayi tunanin Abdukareem ba abin ya faskara sai yanzu tasan lalle tayi sake ta rasa gwarzon miji kaman Abdukareem babu abinda ta nema ta rasa a gidan shi duk wani gata da jin dad'in duniya babu wanda bai nuna mata ba amma ta biye shirmen yan *muna wuta* gashi sun kaita sun baro nadama tayi shi yafi cikin trailer amma haka ta daure ta rungumi kaddara ta zauna domin ta tabbata alhakin Abdul ne yake bibiyanta. ********************* Cikin dare Saha suna kwance da suraiya suna bacci kaman a mafarki ta rinka jin ciwon ciki kad'an-kad'an har abin yayi yawa ya tashe ta a bacci,cike da azaba ta d'aura hannunta akan tirtsesen cikin nata tana cizon leb'e da kyar ta yunkura ta tashi zaune taji duk zaninta ya b'aci ga kuma fitsari da take ji ya matse ta bangoi ta rinka bi har zuwa bathroom d'in ta cire zanin daya b'aci ta gyara jikin ta ta tsuguna dan yin fitsain taji cikin nata ya wani irin murdawa har bayan ta ya amsa,tana durkushen ta fara kokarin fitsain taji yazo mata da wani nishi mai karfin gaske wanda tunda take a duniya ba ta tab'a jin irinsa ba. Kokarin danne nishin take saboda azaba da take ji sai dai ina nishin yafi karfin dannewa tana yi kuma tana jin abu yana zuwa,wani nishin ne yazo da karfi wanda yafi na bayan sai ji tayi muryan baby na callara kuka da iya karfin shi zubewa tayi a wajan tana maida numfashi ko dagowa batayi ba dan abinda ta haifa saboda yanda take jin jikinta kaman ba nata ba. Ummee tana zaune kan sallaya tana lazimi wanda yanzu kullum dare sai ta tashi tana neman yardar mahallacin ta, taji kaman kukan jariri sa kunne ta karayi taji da gaske take ji jiki na rawa ta fito tsakar gida ta ji daga bayan gida kukan jariri ke fitowa kaman ta kifa haka take sauri wajan nufan bayan gidan tana bud'ewa taga Saha kwance da jariri,da gudu ta karasa ta d'aga ta tana ambatan sunan ta a galabaice ta amsa. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi jin tana da rai dan ita a yanda ta ganta batayi tsammanin da rai a tattare da ita ba,gyara su tayi tsab ta kai su d'aki ta miko mata baby amma ta kasa sa hannu ta karb'a kallo 1 ta mishi ta d'auke kanta gefe ganin yanda yaron yake tsananin kama da Zaiyad,kuka ta fashe da shi sosai tana jin dama mutuwa tayi da ganin wannan rana shikenan ta tabbata uwar shege kukan tane ya tashi suraiya daga bacci taga Ummee rike da yaro suna kuka dukan su,cike da murna ta karb'i yaron a hannun Ummee tana kallon kyakkyawan fuskan shi. Da washe gari Ummee ta kira number Kawu ta fad'a mishi cewar Saha ta haihu shima a take ya kira Baban Ziyad ya fad'a mishi. "Allah ya isa tsakanina da kai Zaiyad ka min tabon da ba zai tab'a goguwa ba a rayuwa ta ba kasani sai Allah ya saka min,ga dan ka nan kazo ka d'auke abinka" text din da Saha rubutawa Zaiyad kenan. Ya karanta text din yafi a kirga bai tab'a jin wani emotions game da abinda yake aikatawa ba sai yau kuma a take Allah ya saka mishi son ganin yaron a ran shi. Baban shi yasa shi a gaba har zuwa gidan su Saha ganin baby da kaya sha tara na arziki,baban bai shiga ba yace shi ya shiga haka dole shi ya shiga akawo mishi yaron shi bayan sun gaisa da Ummee, ido ya tsurawa yaron yana kallon photo copy shi,yaso yaga Saha amma ko mai kama da ita bai gani ba dan tana can daki tana kukan daya zama mata jiki tun da ta haihu ta maida shi ibada Ummee tayi tayi har ta gaji ta zuba mata ido shiyasa yanzun ma bata takura kan ta fito ba,haka ya karaci zaman shi ya tafi. Sati na zagayowa aka rad'awa yaro suna Muhammad raguna har 2 Baban Zaiyad ya aiko kuma a ranan aka d'aura auren su sai dai an bar tarewan nata bayan ta gama wanka. **************** Jameela sai kukan kissa take a gaban Abdul dan zaiyi tafiya na kwana 2 zuwa Kano wanda aka tura shi daga wajan aikin su yana ta faman rarrashin ta tana nuna mishi kwana 2 yayi yawa ba zata iya rayuwa babu shi ba,da kyar ya lallab'a tayi shiru da zai fita ma saida ya nemi ya gana da yaran shi amma tace ta tura su gidan su gaishe da Mamanta cike da jin dad'i yanda take kula da yaran shi ya fita ya shiga mota tana tsaye harya tada mota ya fita tana d'aga mishi hannu tana shigowa ta daka wani uban tsalle ta d'auko wayanta cikin sauri ta kira wani no ta tsaya jiran a daga,ana d'agawa tace" baby ya tafi kazo kawai kuma sai bayan kwana 2 zai dawo" tana gama wayan ta nufi d'akin su Husna tana bud'e kofan saida suka firgita sun zuwan ta ba alkhairi bane ai kuwa saida ja kama kunnen su taja tace su zauna kada su fita sai ta kira su suka amsa da toh duk da suna jin yunwa kuma son fad'a mata amma saboda tsoro suka kasa yi . mata magana har ta fice ta rufe su harda murza key sannan ta shiga shiryawa cikin wasu arnen kananan kaya ta zauna jiran kwarton nata,bata dad'e da zama ba kuwa sai gashi nan ya iso cike da murna ta tare shi suka shige ciki abin su suka fara badalar su cikin kwanciyar hankali. Shi kuma Abdul koda ya isa office d'in su director su yace an d'aga tafiya sai next week,cikin sauri ya nufi gida dan kawowa Jameela wannan daddadan labarin koda ya shigo yaga sabuwar mota da bai sani ba amma bai wani dame shi ba ya wuce cikin sauri har ya nufi hanyan bedroom dinsu yaji kaman kukan yaran shi koda ya matso bakin kofan nasu yaji kukan daga d'akin yake fitowa murda kofan yayi amma yaji ta a kulle saida ya lura yaga an saka key cikin sauri ya murda key ya bud'e kofan ba shiri yayi baya saboda abinda idon shi ya gani yaran shine kwance male-male cikin amai ga jikin su duk daud'a ko almajirin kan hanya ya fisu haske da gudu ya shigo d'akin yana daga su amma ba magana saboda duk sun galabaita a fusace ya nufi d'akin su dan ya samu Jameela tayi mishi bayanin meye dalilin ta rufe mishi yara a daki kuma tace basa gidan,tun kamin ya karasa d'akin ya fara jin wani irin nishi daya saka shi fad'uwar gaba a bakin kofan d'akin yayi suman tsaye ganin Jameela da wani kwance tsirars kan gadon na sunnan su suna aikata masha'a. Wani flower vase da hannun shi ya Ture ya fad'i kasa ya tarwatse shiya dawo dasu daga duniyar da suka lula tsoro,firgici da tashin hankali karara a fuskan Jameela shi kuwa kwarton nata karkarwa ya fara yana neman hanyan gudu,Abdul idon shi ya rufe ko ta kan shi bai ba yayi kukan kura yai kanta ya shake ta yana maimaita Kalmar" why....why!!!!" A takaice dai Jameela saida ta sha bakar azaba a hannun Abdul sannan ya mika ta ga police su Husna kuma saida suka kwanta gadon asibiti saboda ulcer da yayi musu mugun kamu,jamerla daga karshe kotu aka mika ta aka yanke mata hukunci kan abinda tayiwa su Husna. ****************** Salma yau tunda ta tashi gaban ta ke faduwa haka ta daure ta fito ta d'aura d'umamen tuwon miyan kuka data rage musu na breakfast,bayan ta gama ta kawo ta ajiye kan dinning zata shiga ciki ta kira Naseer suka had'u a hanya ya sha wanka yace mata shi Katsina zai wuce auren 'yar abokin shi dan haka sai dai ita taci bashi da lokaci abokanen shi suna jiran shi ,da addu'a a dawo lafiya ta bishi amma ko amsawa bai yi ba ya fice abin shi. Tunda ya fita Salma ta zauna shiru saboda gaba daya bata jin dad'in jikinta dan haka ko kallon d'umamen batayi ba, kusan karfe 10 taji wayarta ya fara ringing wanda ya kara mata fad'uwar gaba da kyar ta kai hannu ta d'auki wayan amma taga bakuwar number tana d'agawa taji muryan wani mutum yake ce mata tare da Alhaji Naseer suka yi tafiya amma ko Kano basu wuce ba sukayi hatsari kuma ya rasu,tashin hankali sosai Salma ta shiga taji mutuwar nan har cikin ranta,haka aka dawo da gawan Alhaji Naseer akayi mishi sutura Salma ta fara takaba. A gurguje pls Saha ta tare a gidan Zaiyad an barwa Ummee yaron data haifa wanda kullum in ta kalle shi sai ta zybar da hawaye itama Saha zaman su ita da Zaiyad sai a slow kowa na kallon hanjin dan uwan shi babu yarda ko kadan tsakanin su kullum ciki zargin juna suke ga dangin miji sun saka ta a gaba da zai da habaici,haka Salma itama ta gama takaba wanda Abdul kullum cikin irga kwanaki yake yake dan haka tana gamawa aka maida auren su ta dawo ta rungumi mijinta da yaranta hannu 2-2. Alhamdullilahi anan muka kawo karshen wannan short novel namu da fatan ya isar da sakon da muke son isarwa. Allah ya bamu ladan ilmantarwa dake ciki ya yafe mana kurakuren dake. Kaman yanda Allah ya nuna mana wannan wata mai alfarma ya nuna mana karshen ta lafiya. Allah ya bamu lafiya tare da wadatan yin ibada Ameen. ~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~ © *2020* _~We Love U All~_❤