Haske writer's association [Home of expert & perfect writer's 💡] Bismillahir Rahmanir Raheem. Da sunan ALLAH mai rahma mai jin k'ai, tsira da aminci da dukkan yabo su tabbata ga shugabanmu ANNABI MUHAMMAD ( sallallahu alaihi wa alihi wasallam), ALLAH ina rok'onka yadda nafara book d'in nan lafiya kabani ikon gamawa lafiya. *WATA SOYAYYA*♥️🩸♥️ Writer: Oum Hanan Free pages Fiction story *mg's skincare* Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩 Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️ Shin kinafama da Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata? Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫 Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare duk wnd yy using set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali😘just start placing ur orders dearies DNT be left behind Available product👇 Herbal whitening black soap:3k Beauty kit:11k Blacksoap/molato whitening soap: 3500 Bridal kit:20k Muna maraba da masu siyan daya ko sari Chat 08062991549 Call 08064532391 Facebook: mg's skincare Instagram:glow_with_mgs Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩 Then @mgs skincare gat you covered 💯 Now is time to glow😍 Pamper ur skin🦵 Shine like bride👰🏻‍♀ Glow🧖‍♀? 💯 tested nd trusted🤝 Guarantee Sannan munada frames masu kyau shima siyan daya ko sari 07046881166 08062991549 Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549 Mungode🤝 01 SHIMFID'A. Malam Abdullahi Modibbo madugu haifaffen garin yola ne bafulatanine usul iyaye da kakanni yayi shura sosai wajen noma da kiwo kamar yadda ya gaji sana'ar a wajen mahaifinshi Ard'o Modibbo, ahalinsu babban ahali ne ta yadda kowa ke son had'a zuri'a dasu. Abdullahi yayi aurenshi tun lokacin iyayenshi na raye ya auri wata yarinya mai suna Dije a wata ruga dake mak'oftaka dasu. Lokacin da Dije tayi haihuwarta ta farko a lokacin ne ALLAH ya d'auki ran mahaifin Abdullahi wato Ard'o Modibbo sakamakon ciwon ciki daya turnuk'eshi rana lokaci d'aya ya rasu, bama iya rugarsu ba rugogi da dama sunji rasuwar shi musamman iyalanshi mai d'akinshi Asiya tafi kowa jin mutuwarshi inda daga baya ta fawwalawa ubangiji lamuranshi. Abdullahi sun cigaba da rainon yaransu mai suna Basheer inda suke bashi cikakkiyar kulawa gefe d'aya kuma yana cigaba da kula da mahaifiyar shi da kuma kasuwancinshi na noma da kiwo. Tsakanin Ard'o Modibbo da mai d'akinshi Asiya duka baifi tsiran wata biyar ba itama ALLAH ya karb'i abarshi, daga nan Abdullahi yazama ba uwa ba uba sai y'an uwa da abokan arzik'i, ta b'angaren haihuwa kuma tun daga kan Basheer ko b'atan wata Dije bata k'ara yiba saida Basheer yayi shekara takwas lokacin ma harya fara makaranta dayake Malam Abdullahi yanason karatun boko dan haka lokacin da yaji wasu suna saka yaransu a makarantu shima yasa Basheer duk da a lokacin ana gudun karatun bokon, saida yayi shekara takwas sannan kwatsam Dije taji alamun ciki a jikinta dan har sun fitar da ran sake wata haihuwar saikuma ALLAH ya kawo musu wani cikin Malam Abdullahi yayi murna k'warai ya kuma yiwa ALLAH godiya itakuma Dije kunya ya hanata bayyana nata farin cikin amma cikin ranta tayi farin ciki mara misaltuwa tana kuma addu'ar ALLAH yasa ta haifi mace saboda tun kafin tayi aure take sha'awar yara mata. Cikin ikon ALLAH kuma data tashi haihuwar sai ALLAH ya bata d'iya macen, sunyi murna sosai sunyi godiya ga ALLAH yarinya taci suna Maryam inda mafi yawancin y'an uwa ke kiranta da mairo, anan suka cigaba da kula da yaransu har itama Maryam din ta taso suna matuk'ar k'aunar juna itada d'an uwanta Basheer. Tunda ta taso itama ta nuna sha'awar irin karatun da yayanta yake dan haka Malam Abdullahi yayi mata alk'awarin insha ALLAHU itama zatayi shi idan ta isa sawar. Koda lokacin data isa shiga makarantar yayi, Malam Abdullahi yafara maganar nan Dije wadda suke kira da Ayyah tayi tsalle ta dire tace ita sam batasan zancen ba ba za'a saka mata d'iyar ta mace a makarantar kafirai ba namijin ma dayake yi ALLAH ya yafe musu. Sada aka sha artabu sosai tsakaninta da Malam Abdullahi sannan ta yarda shima d'in bawai da son ranta bane fin k'arfi akayi mata. Y'an uwa ma a lokacin sukayi ta k'ananun maganganu Malam Abdullahi ya toshe kunnuwanshi baibi ta kansu ba, yasa Maryama a makarantar su Basheer suka cigaba da tafiya tare kuma masha ALLAH suna da k'wak'walwar gane abinda ake koya musu ba laifi. Lokaci ya cigaba da tafiya kuma har lokacin Basheer da Maryam suna karatunsu na boko gefe d'aya kuma gata allo da dama suka bud'i Ido sukaga suna zuwa dan tun basu san inda kansu yakeba ake zuwa dasu. Basheer yasamu kammala primary school d'inshi inda yabar Maryam na cigaba da zuwa, ya shiga secondary school ya cigaba da karatunshi. Bayan wani lokaci Maryam ta kammala primary d'inta, Malam Abdullahi ya fara shirin tafiyarta secondary a nan fa Ayyah ta tubure ita yarinyarta bazataje gaba da primary ba d'iyar ta aure zatayi tunda ga manema nan sunata b'arkowa tako ina ga kuma surutan jama'a da suke tayi na cewa yak'i aurar da ita, to tarihi dai ya maimaita kansa dan a nan d'inma Malam Abdullahi ya nuna mata shine gaba da ita kuma a k'asanshi take haka nan kuma surutan mutane ba damuwarshi bace ya samar mata secondary ta d'ora daga inda ta tsaya, kan dole Ayyah ta kawo idanu ta zuba musu dan sanin kanta ne Malam baya d'aukar wargi duk boren datayi bai hanashi bin ra'ayinshi ba. Maryam ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali, har zuwa lokacin data gama k'aramar secondary wato j.s.s 3, taso ta d'ora zuwa senior amma Malam ya hanata dan zuwa lokacin shima yaga dacewar tayi aure saboda shekarunta sun ninka ma yadda suke aurar da yaransu mata duk yadda ta dinga masa nacin ya barta ta cigaba yak'i yace idan tayi auren in ALLAH yasa mijin data aura mai sha'awar yin karatun ne saitayi a gidanshi. Ita dama Ayyah murna fal cikinta, haka Maryam ta hak'ura a hakan ma ta godewa ALLAH da wanda ta samu d'in ta cigaba da zaman gida. Duka cikin masu neman auren natama bamai rabo a ciki dan wani can daban yazo tayi kuma na'am dashi, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba magabata suka shiga maganar, lokacin shi Basheer yana jami'a, anyi biki lafiya an tashi lafiya an kaita gidan mijinta dake nan cikin yolan. Tsiransu ba yawa da Basheer dan shima auren wurin yayi saboda iyayen wadda yakeso d'in da suka nemi ya turo saboda aure zasu yiwa d'iyar su idan bai shiryaba zasu aurarwa da wani gashi kuma suna masifar son junansu hakan yasa ya uzzurawa su Malam Abdullahi shifa lallai aure zaiyi gashi baima yi wani nisa sosai a karatunshi na jami'a daya fara ba. Da farko dai Malam bai yardaba sai daga baya sannan ya amince, akasha bikinshi da Hafsat k'anwar abokinshi. Anan gidan yafara zama inda ya gyara d'aki akasa amarya a ciki. Ya cigaba da karatunshi gefe d'aya kuma yana d'an tab'a kasuwanci, dama kuma business yake karanta a school. Haihuwar farko da Hafsat tayi ta haifi 'ya mace wadda taci sunan Ayyah wato Khadeejah, har lokacin suna nan a cikin gidan, Khadeejah tanada shekara uku Hafsat ta k'ara samun wani cikin zuwa lokacin Basheer yasamu cigaba harya gina musu d'an k'aramin gida suka koma ciki. Namiji ta haifa lokacin da cikin ya isa haihuwa, akasa masa Ameen sunan baban Hafsat kenan. Har zuwa lokacin itakuma Maryam ALLAH bai bata haihuwa ba. Shima Ameen shekararshi uku ta k'ara samun wani cikin. , kuma wani ikon ALLAH wannan cikin yafi bata wahala akan sauran guda biyun sosai take laulayi danma Ayyah na taimaka mata da yaran dan kusan can suke yini wani lokacin ma har kwana suke a can hakan yasa ayyukan gidan nata suka ragu. A daidai wannan lokacin ne itama Maryam tasamu nata cikin zokuga murna wajen bayin ALLAHn nan suka yiwa ALLAH godiya tasha gata sosai a wajen mijin da sauran y'an uwa ta cigaba da rainon cikinta cikin kulawa. Ranar da Hafsat ta haihu a ranar ALLAH ya yiwa Malam Abdullahi rasuwa, dama ya d'an kwana biyu yana fama da jikin, sunyi matuk'ar girgiza da rasuwar nan ta Malam Abdullahi, saidai dole mutum ya d'auki dangana dan ita mutuwa rigar kowa ce kowa saiya sanyata sai abin ya had'e musu biyu ga farin cikin samun k'aruwa ga kuma gagarumin rashi da sukayi a familyn su na madugu. Da ranar suna ta zagayo sai aka maidawa jaririn sunan Malam wato ABDALLAH. Tsiran Hafsat da Maryam duka sati biyu itama ta haifo yaronta namiji bayan doguwar nak'uda datayi, itama d'in dai sunan Malam d'in aka maidawa yaron. Rayuwa ta cigaba da tafiya da dad'i ba dad'i har Basheer ya kammala masters d'inshi ya d'ora harkokin kasuwancinshi. Bayan wasu shekaru. Arzik'in Basheer wanda yazama Alh a yanzu ya hab'aka sosai ubangiji ya sawa kasuwar shi albarka, yayi fice sosai sunanshi kuma ya zaga ko ina, daga kan Abdallah Hafsat bata k'ara haihuwa ba saida akayi shekara biyar sannan ta k'ara haihuwar d'iya mace mai suna Hauwa'u daga Hauwa'u saikuma Mabrookah saikuma twins datayi duka mata wanda daga sune bata k'ara wata haihuwar ba. Maryam ma bayan nata Abdallahn tayi Zakiyyah, Hameedah, Kulthum da Hannah wanda itace y'ar auta itama domin daga kanta ne haihuwar ta tsaya. Tun tasowar Abdallah Ammi (Hafsat) ke fama dashi saboda rashin jin maganar shi ga surutu gashi duk maganar datazo bakinshi fad'ar ta yake ba abinda ya dameshi. Ganin harkokin kasuwancinshi sunfi a kano shi Alh Basheer d'in yasa ya siya gida ya tattaro iyalan nashi gaba d'aya suka dawo kano. Har Ayyah yaso tahowa da ita tace a'ah ita sam bazata biyoshi ba zata zauna gurin danginta, amma har a yanzun yanada burin d'auko mahaifiyar shi ya zauna tare da ita hankalinshi zaifi kwanciya idan tana gabanshi duk da can d'inma akwai d'iyar k'anwar ta dasuke zaune tare bazawara ce batada aure. Alh Basheer ya mallaki manyan kamfanoni a cikin birnin kano dama Nigeria gaba d'aya sannan yanada hannun jari a kamfanunnuka da dama na gida dama na waje. Ya k'ara gina wani k'aton gidan a unguwar nassarawa G.R.A. part daban daban suka tare a ciki. (Sauran haife haifen da Hafsat tayi duk a kano tayisu Khadeejah, Ameen da Abdallah su kad'ai aka haifa a yola). Bayan dawowarsu kano Khadeejah tasamu miji anan tayi aure yaranta biyu ma a yanzu haka Afnan da Nu'aym sai Amin da ake shirin bikinshi a halin yanzu. Ameen tun yana yaro yake da sha'awar yazama banker dan haka gaba d'aya karatunshi akan aikin banki yayi shi kuma Abbie kamar yadda suke kiran Alh Basheer dashi bai hanashi ba saima k'warin gwiwa dayake bashi duk da dai yaso ya karanci business kodan yasamu mai taimaka mashi amma bai tauyeshi ba yabashi damar zab'in ambition d'inshi tunda ga Abdallah shi saiya karanci business d'in, kuma Alhmdulillah burinshi ya cika na zama banker d'in. Mrs Salees Mu'az 💝 Maryam Ibraheem Aleeyu [Ummee] *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* 2/14/22, 08:38 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* ♥️🩸♥️ HASKE WRITER'S ASSOCIATION (Home of expert & perfect writer's) Writer: Oum Hanan The writer of DR SAIF Free page Fiction story 02 Shikuma Abdallah tun tasowar shi yakeda sha'awar zane zane koyaushe zaka ganshi da pen da paper yana zana bishiyoyi, gidaje, da tsuntsaye flowers,da sauran zane, ko assignment aka basu a school indai na drowing ne shine yake winning shikuma saiya taso da son yazama architecture. Lokacin da Abbie ya zaunar dashi ya tambayeshi nashi ambition d'in kai tsaye yace masa mai zane yakeso yazama, cikin rarrashi Abbie ya nuna masa ya karanci business administration dan ya taimaka masa kan harkokin kasuwancinshi ba wani b'oye b'oye dan tun yana d'an mitsitsinshi bai iya b'oye abinda ke ranshi koma meye fito dashi yake koda kuwa wanda zai gayawan bazai masa dad'i ba yacewa Abbien shi wllhy zane yakeso kuma shi zaiyi idan kuma aka takura masa karatun ma zai bari gaba d'aya 😡🤣 sanin halin darunshi yasa Abbie yace me yayi zafi? yaje yayi ALLAH ya bada sa'a, dan baya d'aya daga cikin iyayen dasuke takura yaransu kan abinda sukeso ko yaushe yana duba maslahar yaran ne sannan nefa aka samu zaman lafiya. Kamar Ameen din shima yasamu cikar burin nashi alhmdulillah yaje yayi karatun kuma ya fito da good results Arch. Abdallah Basheer Madugu kenan inkiya Modibbo, mutum magananne ba ruwanshi da wani miskilanci irin na Mr hukunci😂 ( Dr Saif) ga masifa da neman tsokana halayyar nan tashi dai tun yana yaro bata sauya ba, saurayine d'an kimanin shekaru 30 kyakkyawa ne na ayi kwatance dashi kunsan dai fulani tubarkallah akwai baiwar kyau, dogo ne sosai kuma sam bashida jiki sai afkin tsayin da faffad'an k'irji da ALLAH yayi masa baiwa, mugun d'an hayagaga ne idan kuma ka ganshi ya nutsu yana zane saika rantse da ALLAH bashi bane saboda yadda yake maida duk wani attention d'inshi kan abinda yake, tamkar hawainiya haka yake wajen canza kala yanzun nan zaiyi abu saikuma yakoma tamkar bashi yayiba kokuma wani tym d'in ka ganshi yazama wani silent kamar bashi ba. Akwai yayar Ammi da suke uwa d'aya uba d'aya datake aure a garin kaduna da nata iyalin tanada 'ya'ya sosai dan yaranta sun kusa goma maza da mata amma duk sunyi aure mazan da matan sai guda uku ne yanzu a gabanta Ja'afar dayake saurayi kusan sa'an Abdallah saidai Abdallahn ya girmeshi da wata biyu, saikuma twins d'inta itama wad'anda zasuyi kusan sa'anni dana Ammi dan familynsu akwai y'an biyu sosai, matane dukansu Hassanar Janan ake kiranta itakuma Hussaina Jauhar identical twins ne su dan in bakayi musu cikakken sani ba to kuwa bazaka iya bambance su ba , ba kamar na Ammi da sam basu kama kamar ba twins bama idan ba an fad'awa mutum ba. ta b'angaren halayyar sune kawai ake ganesu dan ita Janan tanada sauk'in kai da sanyin hali ga hak'uri da kawaici sab'anin Jauhar datake matsiwaciya ga rashin kunya da d'an banzan surutu, suna first year d'insu ne a higher level inda Janan take kano gidansu Abdallah tana karatunta a B.U.K wato Bayero university Kano itada Hassana da Hussaina, itakuma Jauhar acan Kadunan take nata karatun a poly. Sunada kyau mai d'aukar hankali ga diri da ALLAH yayi musu da kyan sura komai nasu iri d'ayane. Itama Maryam wadda suke kira da Momy a yanzu ta aurar da Zakiyyah Hameedah da Kulthum d'in sai auta Hannah datake gabanta a yanzu tana karatu saikuma Abdallahnta da shima baiyi auren ba yake aiki a wani babban company na babansu wanda ake sarrafa fata. Wannan shine tarihin madugu family a tak'aice ga kuma su Jauhar dasu Abdallah suka had'a alak'a ta jini dasu ta b'angaren Ammi. A yau alhamis Abdallah yake dawowa daga k'asar Italy wani course dayaje duka na wata biyu duk akan aikinshi na zane a yaune kuma yake dawowa k'asar. Tun safe Hassana da Hussaina ke kaida kawowa wajen yin girke girke kasancewar basuda lecture ita Janan tun 7@m tabar gidan. "Dan ALLAH sis ya kikaji gidan nan da Yah Abdallah baya nan?". Hussaina ce tayi maganar tana blending aya da coconut a blander. "Hmm very nice wllhy 👌". Hassana tabata amsa lokacin datake k'ok'arin zuba yankakkiyar hanta a cikin pot d'in dake kan gas cikin kayan miyan da akayi blending d'insu sama sama. Y'ar dariya Hussaina tayi tace "Zakije d'auko shine a airport?". Ido Hassana ta d'an zaro tace "Wllhy ba inda zanje tab! maybe Yah Ameen ne kawai zaije fa". "Nima dai zan masa addu'a daga nan ALLAH ya saukeshi lafiya". dariya suka saka gaba d'ayansu suka cigaba da aikinsu. Maganar Yah Ameen sukaji daga falo yana yiwa Ammi sallama zaije airport ya d'auko Abdallah tayi masa fatan dawowa lafiya. KANO NIGERIA. Mallam Aminu kano airport. K'arfe 10@m jirginsu Abdallah yayi landing, bayan wani lokaci mutanen dake ciki suka fara saukowa. Mutum na shida dake cikin jerin masu saukowa idanuna suka kai kanshi 'Masha ALLAH' itace kalmar dana ambata lokacin dana ganshi, kyakkyawa saurayi fari tas mai had'e da sirkin jaa kwantaccen sajen daya k'awata fuskar shi ya k'ara fito da ainahin kyawun da ALLAH yayi masa, sai matse d'an k'aramin pink lips d'inshi yake wanda yake tamkar ya turasu da jambaki a tak'aice dai ya hadu ta ko ina komai yaji masha ALLAH. Sanye yake cikin k'ananun kaya na kamfanin DKNY wandon da rigar duk blue black ne sai black jacket daya d'aureta a k'ugunshi k'afarshi sanye cikin bak'in boot hakama hannunshi d'aure yake da bak'in agogon fata na kamfanin Gucci sai bak'ar P.cap dake kanshi wadda ya juya gaban hular baya ya toshe idanunshi da bak'in google hakan yasa ba'a ganin k'wayar idanunshi wata doguwar luggage ce goye a bayanshi ta gayu, cikin takunshi na mai cikakkiyar lafiya da kazar kazar yake saukowa daga step d'in jirgin harya k'arasa sauka gaba d'aya k'ugunshi ya dafe da hannu d'aya d'aya hannun kuma yakai kan P.cap d'in dake kanshi ya fara wuwwurga idon inda zaiga wani nashi saidai ba wani wanda yasani tsadaddiyar wayarshi dake hannunshi ya shiga dubawa da nufin kiran Yah Ameen yana shirin yin dialling number Yah Ameen d'in yaji daga bayanshi an dafa kafad'arshi hakan yasa ya juya dan ganin kowaye sukayi ido hud'u da Yah Ameen yana murmushi tareda mik'o masa hannu alamun suyi musabaha shima hannun ya mik'a masa sannan sukayi hugging juna cikeda murnar ganin juna da sukayi. Bayan sun saki juna ne Abdallah yace "Nifa ban ganeba bros yana ganka kai kad'ai, kana nufin kace kai kad'ai kazo taryana?". "Dawa zaka ganni da? kaidai ba buk'atar ka akaika gidaba?". Yah Ameen ya amsa masa. "Two months bana gida bros amma sai kai kad'ai ai kamata yayi ace an cika airport d'in nan da masu tarona ko". Gaba Yah Ameen yayi yana fad'in "Ai dayake ga d'an shugaban k'asa ko let's go malam inbaka zuwa inyi tafiya ta". Bayanshi yabi yana fad'in "Kaga Habeeb ma yace zaizo baizoba saina masa rashin mutunci wllhy". Baki Yah Ameen ya tab'e yace "Wannan kuma kunfi kusa". Suna zuwa inda motar Yah Ameen take ya bud'e back seat ya jefa luggage d'in ciki yadawo ya bud'e front seat ya shiga Yah Ameen yayiwa motar key suka bar wajen, kujerar dayake kai ya kwantar yayi relaxing sosai akai tareda tallafe kanshi da duka hannayenshi idanunshi a rufe har lokacin bai cire glasses d'in ba, juyowa Yah Ameen yayi ya kalleshi baidai ce komai ba ya juya ya cigaba da driving d'inshi, saida suka fara nisa sannan Yah Ameen ya shiga tambayar shi kan abinda ya kaishi Italy d'in yana a hakan yake bashi amsa daga nan kuma suka shiga hira ya shiga bashi labarin yadda ya gudanar da course d'in nashi a can. Da haka har suka k'arasa bakin wani k'aton gida yayi horn aka bud'e gate d'in ya danna hancin motar tashi ciki. Babban parking lot d'in dake farfajiyar gidan ya shiga wadda ke d'auke da manya manyan motoci da suka had'a dana Abbie na Yah Ameen d'in dana uban gayyar Abdallah saikuma ta Ammi guda biyu, yayi parking. "Wow I'm very happy wllhy, gida na daban ne Bros". Abdallah ya fad'a yana tashi zaune, shidai Ameen bai kulashi ba ya bud'e motar ya fita shima bud'ewar yayi ya fita yana k'ara bin gidan da kallo kamar wanda yayi wasu shekaru baya ciki, Baba maigadi da isya mai bawa flowers ruwa suka k'araso suna masa barka da dawowa hannu yaba kowanne sukayi musabaha yana amsa musu sannan suka koma bakin gate inda suke zaune kan benci suna hira. Tare suka jera da Yah Ameen zuwa general parlor d'in gidan suka shiga d'auke da sallama a bakinsu. Ammi da fitowarta kenan daga kitchen suka shigo ta saki murmushi tana amsa sallamar. "Oyoyo Amminaaaaa". ya fad'a da k'arfi yana dariya tareda bud'e hannayenshi ya nufeta da sassarfa ya rungume ta, kai kawai Ameen ya girgiza ya nemi waje ya zauna, cikin farin ciki Ammi ke fad'in "Oyoyo my son welcome back andawo lafiya?". ta k'are maganar tana d'agoshi daga jikinta. "Lafiya Ammi saidai kewarku danayi I miss you so much wlhy". ya fad'a yana karyar dakai. Murmushi Ammi tayi tace "Toh koma dai meye ai gashi ka dawo sai fatan nasara kuma kan abinda akaje yi, yanzu ga dinning can an shirya maka wanka zaka fara yine kokuwa?". Glasses d'in daya cire tun shigowarshi ya mak'ala a gaban rigarshi yace "Ammi zan fara yin wankan kawai saboda nagaji over wllhy". "To shikenan oya aje ayi wankan". Ammi tace tana barin wajen, juyawa yayi zai fita sai lokacin yaga Ameen ma ashe baya falon, har zai fita ya hangi su Hassana a tsaye sunyi tsamo tsamo kamar wad'anda sukayiwa sarki k'arya sai raba ido suke, tsaye yayi yana kallonsu kafin yace "Tsayuwar me kuke a nan dan ubanku, wato sannu da zuwan da zakuyi min shine ya gagara ko". Da sauri suka had'a baki wajen yimasa sannu da zuwan suka d'ora da fad'in dama yanzu zasuyi masa. K'wafa kawai yayi yana hararar su ya nuna Hussaina yace ta karb'o masa key d'in d'akinshi wajen Ammi, cikin hanzari ta nufi upstairs itakuma Hassana ta lallab'a tabar wajen kafin ya lalubo wani abun yace tayi. Key d'in ta karb'o takawo masa ya karb'a ya fita yana cillashi sama, k'irjinta ta dafe tana sakin ajiyar zuciya sannan ta nufi d'akinsu. Mrs Salees Mu'az 💝 Maryam Ibraheem Aleeyu HASKE WRITERS ASSOCIATION💡💡💡 TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A ZAFAFAN LITTAFAI MASU SAKA SHAUK'I, FADAKARWA K'AYATARWA NISHADANTARWA HAR GUDA 7!!! GA SHIRI NA MUSAMMAN INA MASU SON KOYAN GIRKUNA DA MASU SON KARA SANIN SIRRIN MALLAKE MAI GIDA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 KUDIN RAJISTA - 500 (NAIRA DARI BIYAR GABA DAYA) *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 2/14/22, 08:40 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* ♥️🩸♥️ *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *TOP TEN TAKUN HASKE BATCH [A]* Writer: Oum Hanan The writer of DR SAIF 🩸 Free page Fiction story 03 Wani part d'in naga ya nufa ya bud'e k'ofar ya shiga wasu k'ofofi biyu suka bayyana ta k'arshen ya bud'e ya shiga wani madaidaicin falo ya bayyana sam babu tarkace a cikinshi amma yayi kyau sosai ya tsaru, set d'in kujeru ne fari da purple sai curtains suma fari da purple saikuma plasma medium size dake jikin bango kusa da TV stand da akayi adon wasu k'ananun flowers akai, purple d'in grass carpet ne shimfid'e a tsakiyar kujerun sai k'aramin center table akai da kuma can tsakanin 3sitter da 2sitter kowace kusurwa ka kai idanunka a jikin bangon falon zaninnika ne kala kala a lik'e wanda zai tabbatar maka da cewa mamallakin d'akin mai zane ne, tsaf komai yake a muhallinshi sai tashin k'amshi yake da alamu dai mai gyaran saida yayi taka tsantsan dan gudun hayagagar Abdallah 😃. Wata k'ofa dake hannun damanshi ya nufa ya tura ya shiga bedroom d'in, shima dai bawani babba bane irin sosai d'in nan madaidaicin gadone dayaji tattausan bedsheet da blanket da aka d'ora akai, sai clothes ta jikin bango saikuma mirror dake cike da kayan shafe shafe da uban turaruka tamkar wata mace sai k'aramin carpet dake shimfid'e a k'asan gadon, daga kan kayan gadon zuwa curtains da wallpaper dake jikin bangon duk fari da purple ne shima bedroom d'in da alamu fav color d'in mai d'akin ne tako ina an k'awata jikin bangon da drowing na tsuntsaye da fulawoyi sai inda fuskar gadon take da aka lillik'a hotunanshi kala kala. P. cap d'in ya cire kwantacciyar sumarshi ta asalin fulani ta bayyana wadda ta kwanto har bayan wuyanshi bak'a wuluk, ya wulla saman bed d'in ya kwance jacket d'in itama ya wullata ya zauna bakin gadon ya sunkuya yana kwance igiyar takalmanshi kafin ya ciresu fara tas din k'afarshi ta bayyana mai d'auke da zara zaran y'an yatsu wadda tayi gumi kad'an, tashi yayi ya cire kayanshi ya shiga bathroom sharp sharp ya fito bayan yayi wankan farar riga yasa mara nauyi mai yankakken hannu da farin wandon three quarter Arabian perfumes dake cike kan mirror d'in ya feffesa ya d'auki farar P. cap ya saka dan shi d'in ma'abocinta ne, wayarshi ya d'auka ya zura farin slipper mai taushi ya fita ya rufo k'ofar ya nufi falon su Ammi hannunshi d'aya cikin aljihun wandonshi kanshi a k'asa yana duba number Habeeb abokinshi ne sosai tun a unguwar da suka fara zama tare sukayi primary school sukayi secondary har zuwa lokacin da kowa ya tafi k'asar da zaiyi karatu, sun shak'u sosai ta yadda har iyayensu ma suka k'ulla alak'a ta zumunchi a tsakaninsu, shikuma Habeeb d'an kasuwa ne gashi dai yayi karatun amma kuma kasuwanci yake abinshi zai d'an girmi Abdallah amma tsiran bamai yawa bane. Lokacin daya shiga falon a lokacin ne kuma Habeeb yayi picking d'in wayar yana fad'in "Habeeb Umar Marafa ke magana who is the line?". Saida ya d'an cije baki sannan yace "Ubanka ne akan layi ni zakawa iskanci Habeeb?". Dariya Habeeb ya shek'e da ita, K'wafa Abdallah yasaki lokacin daya k'arasa dinning table d'in yaja kujera ya zauna yana fad'in "Dan ubanka ya mukayi dakai jiya? yana maganar yana janyo plate gabanshi tareda tsiyayar coconut juice a glass cup yakai bakinshi ya fara sha Cikin dariya Habeeb yace "Kasan ALLAH A.B seriously wani important issues ne ya tasomin wanda dole sainaje wajen naso inje airport in taroka amma karka damu zan shigo anjima ko zuwa dare ne insha ALLAH". "Okay saika shigo d'in". Abdallah ya fad'a tareda yin hanging d'in kiran, wayar ya ajiye ya bud'e wata warmer yaga tuwon shinkafa a ciki fari tas an sakashi a farar leda. "Tuwo kuma? yace yana b'ata fuska gamida ture warmer d'in gefe ya shiga k'walawa Hassana kira da uban k'arfi, lokacin suna zaune kowacce da handout a hannunta suna dubawa sukaji kiran da sauri kowacce ta aje littafin hannunta tareda zaro ido suna kallon juna kowacce gabanta na bugawa, jin ya k'ara k'wala wani kiran yasa Hassana ta zabura ta fita cikin sauri har tana hard'ewa Hussaina ta bita da kallo tana addu'ar ALLAH yasa dai bawani laifin sukayi ba saita kasa cigaba da duba littafin ta shiga tsumayen dawowar Hassana. A tsorace ta isa gurin dinning d'in inda Abdallah ke zaune yana jefo mata harara, d'an nesa dashi ta tsaya jikinta na rawa kanta a k'asa cikin rawar murya tace "Yah Abdallah gan......."Uban waye yace kuyi min tuwo? Indawo k'asar yau ku tareni da tuwo saboda bakuda mutunci dan ubanku". ya katseta cikin hargagi. "Wllhy Yah Abdallah.... kallon dayayi mata yasa tayi shiru kamar zatayi kuka, Ammi dataji hayaniyar Abdallah ta fito daga kan upstairs d'in ta tsaya tace "Wai meyake faruwa ne anan Modibbo?". "Ammi tuwo nefa sukayi min wai su rasa me zasu girkamin sai tuwo kuma sun san bana cinshi". Kai Ammi ta dafe tana fad'in "Modibbooo meyasa kake hakane? shin ka bud'e sauran warmer's d'in kaga abinda ke ciki? wannan tuwon mafa na Abbienku ne yace yana sha'awa nayi masa kuma bansan wanda ya d'aukoshi ya kawo nan ba kake faman tada jijiyar wuya akai, dan ALLAH ka dinga sassautawa zuciyarka". daga haka ta juya ta koma bedroom d'inta. Wata warmer ya janyo ya bud'e yafara zuba had'add'iyar fried rice dake ta tashin k'amshi kad'an ya zuba ya zuba cows low a gefe da cinyar kaza, ganin har lokacin Hassana na tsaye kanta a k'asa tana tsoron tafiya yace tayi wani laifin. "Zaki bar wajen nan ne kokuwa saina tashi kanki". yace yana k'ok'arin d'iban abincin a spoon batare daya kalleta ba, kamar wadda ke jira kuwa tabar wajen da sauri. Tana shiga bedroom d'insu ta saki ajiyar zuciya tana zama kusa da Hussaina datake kallonta, Hussaina tace "Wai kiran meyake miki ne haka?". "Hmm waifa kawai dan yaga tuwo shine na wannan kiran wai ubanwa yace muyi masa tuwo". Baki kawai Hussaina ta tab'e tace "ALLAH ya kyautawa mutumin nan wllhy, nifa maybe inyi tafiyata gidan Aunt Deejah wllhy wannan bala'i har ina". "Idan ma kinje zaki dawone yarinya, kuma tunda ya dawo d'in nan kuma ai babu sauran sakewa, dad'ina da Yah Ameen kenan ba ruwanshi dakai indai ba gani yayi zaka kauce hanya ba". Karatun da basu cigaba dashiba kenan suka shiga gulmar Yah Abdallah 😅. ^√^√^√^√^√^√^? Yana gama cin abincin ya tashi ya fita part d'insu ya koma ya shiga d'akinshi ya kwanta, barci yakeso yayi saboda gajiyar dayake ji a jikinshi bai dad'e da kwanciyar ba kuwa barcin yayi awon gaba dashi. JANAN. A gurguje tayi wanka bayan dawowar ta school yau tagaji sosai ga yunwa dan batayi breakfast ba ta fita kuma sam ita ba kasafai take cin abinci a makaranta ba, sama sama ta shafa lotion da body spray ta zura doguwar rigar wani yadi mara nauyi ta yafa mayafi mai d'an girma akan rigar tasa slippers ta fita zuwa dinning table a falo. Tana saka kai falon ta hangoshi akan kujera yayi wani zama shi ba'a kwance yakeba haka kuma ba'a zaune ba, hannunshi d'aya rik'e da juice yana sipping a hankali d'ayan kuma rik'e da waya yana danne danne, wani irin mugun bugawa gabanta yayi tayi saurin dafe k'irji tareda ja baya da niyyar komawa inda ta fito taji yace "Come here dan ubanki". a haka yayi maganar batare daya d'ago kaiba. "Innalillahi wa inna ilaihi rajioun, wllhy sam ta manta yau mutumin nan zai dawo da gidan Aunt Deejah zata wuce inyaso ta dinga zuwa school d'in daga can. Kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki ta fara takowa inda yake kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, gefe tasamu ta tsuguna a hankali cikin sanyin muryar ta dayake halittarta tace "Yah Abdallah sannu da zuwa". Sipping d'in lemon dayake sha ya k'ara yi sannan batare daya d'ago daga kallon wayar dayake ba yace "Sai yanzu kikaga damar yimin sannu da zuwan dan ubanki? tun k'arfe nawa na dawo gidan nan saboda bakida mutunci ko? Ji take tamkar tasaka kuka, ta tsani wannan zagin dayake musu wllhy gashi hakan kamar wata d'abi'ar shice ya zagi mutum shiba komai bane a wajenshi. A marairaice tace "Wllhy Yah Abdallah bana gidan tun 7@m natafi school sai yanzu nadawo". Zaune ya tashi ya aje lemon kan k'aramin center table dake gefen kujerar dayake zaune, crossing legs d'inshi yayi yana kallonta yaga kanta a k'asa. "Munafuka, nasan har cikin ranki bakiso nadawo gidan nan ba ko? so kikayi flight d'in ya tarwatse dani a sama ko? muguwa". Haka ALLAH ya yita da saurin kuka hakan yasa yanzun ma hawaye suka taru cikin idanunta saidai bata barsu sun kai ga zubowa ba dan suma d'in idan yagani saiya sauke mata wani bala'in nashi, ko wanda ba musulmi ba dai bazata yimasa wannan fatan ba bare shi dayake matsayin musulmi kuma d'an uwanta na jini sai neman jafa'in tsiya ya iya dan wannan neman jafa'ine wani time d'in idan yasaki magana fitar tusa ma tafita dad'in ji wllhy. Ganin yadda ya tsura mata ido yasa ta girgiza kai tace "ALLAH Yah Abdallah ba haka bane". "Koma dai meye nadawo fece daga wajen nan". Tashi tayi ta koma bedroom haka ta matse yunwarta saidata lek'o taga ya fita sannan taje ta zuba abincin bata zauna a falon ba ta shige bedroom a can taci abincin. ^√^√^? Da dare Habeeb yazo ya d'aukeshi suka fita suka d'anyi yawo sukaga gari, gari ya gansu, sai wajen k'arfe 10pm Habeeb ya dawo dashi ya tafi. Sai a lokacin suka gaisa da Abbie. Tunda ya dawo ya hana su Janan sakat gashi haka zai baro part d'insu yazo yayi zaune a falon duk abinda zasuyi idonshi akai, kuma bazai gani ya k'yale ba saiya tanka, hakan yasa duk suka daina zaman falon da sun dawo school kowacce zata shige bedroom indai ba dole ce zata fito dasu falon ba. ^√^√^√^√^? Duka baifi sati da dawowa ba yafara shirin zuwa Kaduna gidan yayar Ammi mamansu Janan hajiya Ameenah wadda suke kira da Mama, yana matuk'ar son zuwa gidan saboda yadda Mama take nuna masa k'auna yasamu labarin tunda aka haifeshi take nuna masa soyayya ALLAH ya had'a jininta da nashi hakama mijinta Alh Isma'eel yanason Abdallah sosai saboda yana yawan zuwa gidan tun yana yaro hakan yasa suka shak'u sosai. Mrs Salees Mu'az 💝 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡💡💡 TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A ZAFAFAN LITTAFAI MASU SAKA SHAUK'I, FADAKARWA K'AYATARWA NISHADANTARWA HAR GUDA 7!!! GA SHIRI NA MUSAMMAN INA MASU SON KOYAN GIRKUNA DA MASU SON KARA SANIN SIRRIN MALLAKE MAI GIDA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 KUDIN RAJISTA - 500 (NAIRA DARI BIYAR GABA DAYA) *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 2/14/22, 08:41 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* ♥️🩸♥️ HASKE WRITER'S ASSOCIATION 💡 (Home of expert & perfect writer's) TOP TEN TAKUN HASKE BATCH {A} Writer: Oum Hanan From the writer of DR SAIF 🩸 Free page Fiction story 04 A ranar dazai tafi bayan ya gama shirinshi ya shigo cikin falon dan yiwa Ammi sallama shi Abbie tun safe dazai fita sukayi sallama dashi. Ash color d'in wandone a jikinshi da black color d'in riga round neck mai dogayen hannu wadda ta d'ameshi ta fito da cikakken k'irjinshi, wani siririn abune mai d'an fad'i na sak'a ash color mai taushi ya nad'e wuyanshi dashi, d'aya yayi gaba d'aya yayi baya, agogon sark'a ne a hannunshi shima kalar ash sai bak'in takalmi dake k'afarshi na zallar fata, ya toshe idanunshi da bak'in glasses k'amshin Arabian perfumes kawai ke tashi daga jikinshi. Anan falo ya samu Ammi dasu Hassana harda Janan a d'arare suka had'a baki suka gaisheshi baima amsaba ya zauna kusa da Ammi yana fad'in "Ammi ni zan wuce". "To a gaishe mana dasu kwana nawa zakayi?". "To gani dai Ammi amma bazan dad'e ba". yayi maganar yana d'an sosa kanshi da key d'in motarshi dake hannunshi. "To ALLAH ya kaimu, kadawo dai da wuri kaga ga shirye shiryen bikin d'an uwanka da za'ayi". "Insha ALLAH Ammi". daga haka ya mik'e tsaye yana jan wandon dake jikinshi sama, Ammi ma tashi tayi ganin haka yasa suma su Janan suka tattashi da niyyar rakashi, ganin yadda suketa fara'a yasa har yayi gaba saikuma ya juyo ya kallesu. D'an yatsanshi manuniya ya d'ora kan bakinshi kamar mai tunani kafin yace "Kamar fa murna kuke zan tafi ko?". Tuni kowacce ta d'inke fuskarta daga yanayin murmushi dasuke a da sukayi saurin girgiza kai Kad'a kai yayi yace "Duk zakuci ubanku ne zan dawo ai". K'aramin tsaki Ammi taja tace "Dan ALLAH ya isa haka wuce katafi ALLAH ya kiyaye murna kuwa ai dole suyita a yadda kake takura musu d'in nan". Saidaya hararesu sannan ya fice daga falon basu bishi bama suka koma suka zauna suna k'usk'us a tsakaninsu itadai Janan tana gefe ALLAH nagani tayi murna da barinshi gidan kafin kuma ya dawo ya d'ora daga inda ya tsaya duk rashin son hayaniyar ta saiya samu abinda ya lak'aba mata yace tayi. Ammi ma daga bakin k'ofar falon sukayi sallama tadawo shikuma ya nufi wajen motarshi da Isya ya goge masa ya shiga saida yayi addu'o'e sannan ya tada motar ya fita dama already maigadi ya bud'e masa gate. Sauka lafiya Abdallah madugu🤩. Ana yin sallahr la'asar ya shiga unguwar, bai shiga gidan ba saida ya tsaya yayi sallah a masallachin dake jikin gidansu Maman sannan ya shiga bayan an idar, Maman na zaune a falo itada Hajiya Yaya wato mahaifiyar Alh Isma'eel d'in dake zaune a gidan Hajiya Yaya akwai fad'a kuma dama basu cika shiri da Abdallah ba saboda yadda idan yazo yake cin zalin Jauhar gashi y'ar gaban goshinta ce. Tashi Mama tayi ta tareshi da murnar ta sam bakinta ya kasa rufuwa Hajiya Yaya kam kicin kicin tayi da fuska ta juyar dakai gefe. Zama yayi kusa da kujerar da Mama take yana gaisheta cikin farin ciki ta amsa tareda tambayarshi mutanen gidan ya amsa yana kallon Hajiya Yaya data b'ata fuska, tashi yayi ya nufi wajenta yana dariya gamida fad'in "Hajjaju ikon ALLAH, wai bakiyi murna da ganina bane? yayi maganar yana zama kusa da ita. "Banyi ba". ta fad'a kanta tsaye. Dariyar ya k'ara saki tareda zaro ido na iya shege yace "Why Hajiya?. Banza tayi masa, hakan yasa yace "Ohhh na manta fa bakyajin turanci, cewa nayi saboda me bakiyi murna da ganina ba". Mama dai dariya kawai take ta tashi da kanta ta nufi kitchen dan samar masa abinda zaici. "Ka fini sani ai fitinanne yanzu zakazo ka takurawa yarinyar nan Johar". Baki kawai ya tab'e ya tashi ya koma inda ya taso ya zauna yana fad'in "Shine damuwarki?. K'ala batace masa ba shima saiya tattarata ya watsar, Mama ta fito daga kitchen d'in hannunta d'auke da tray da warmer guda d'aya sai plate da spoon sai kuma drink da cup, gabanshi ta ajiye da kanta tayi saving d'inshi dambun shinkafa dayaji vegetables da spices sai k'amshi yake tashi kad'an ta zuba masa saboda tasan yanayin cikinshi bai wani cika cin abinci sosai ba barshi dai da kayan k'walam saikace wani mace, had'add'en lemon ayar dake cikin jug ta zuba masa ta ajiye a gabanshi, itadai Hajiya Yaya sai kallon Mama take tana tab'e baki shiyasa yake tata rashin mutuncin shi yadda yaga dama tunda duk abinda yayi Maman bata gani, daga k'arshe ma tashi tayi tabar falon ta shige d'akinta. Abincin yafara ci ya d'auko wayarshi ya kira number Ja'afar, bata dad'e da fara ringing ba akayi picking. "Yane wai kana inane?". Abdallah ya fad'a bayan ya amsa sallamar Ja'afar. "Ka ganni nan a hanyar gida na kusa k'arasowa ka iso ne?". "Eh mana nazo, saika k'araso d'in". "Okay Tam". Ja'afar ya fad'a sannan sukayi hang up a tare. Hira suka cigaba dayi da Mama har lokacin da Ja'afar ya k'araso, hannu ya bashi suka gaisa ya d'auki trolley d'in Abdallah na kayanshi suka wuce part d'in Ja'afar d'in tare. Dukansu wanka suka k'ara yi suka shirya cikin k'ananun kaya suka k'ara ficewa ganin gari a motar Ja'afar saidai Abdallah ne yake driving. Yawo sukayi sosai cikin garin daga k'arshe suka yada zango wajen shan ice cream, sun dad'e a wajen suna hira ayi ta arzik'i ayi ta tsiya kuma duk Abdallah ne ke takalar fad'an. Tafe suke a hanyar dawowar su yanzun ma Abdallah ke tuk'in anci sa'a a hankali yake tuk'in dan sam Abdallah bai iya bin mota a hankali ba sharara gudu yake yadda ranshi keso. Da uban gudu wata mota ta taho tamkar zata tashi sama duk yadda Abdallah yaso kauce mata sai data gogi motar su dan dama ya hangota ta mirror, batare da mai motar ya tsaya ba ya k'arawa motar tashi gudu, a fusace Abdallah ya mulmulo wani uban ashar ya k'unduma masa tare da k'arawa motarsu gudu shima dayake titin ba yawan motoci hakama ba mutane sosai. Wuta yake bawa motar sosai kamar yadda wancan mai motar ma yake k'ara nashi gudun, sai masifa yake yana sakin zagi ganin haka yasa Ja'afar ya fara fad'in "Dan ALLAH Bros kabari tunda dai ba abinda ya samemu". Baki Abdallah ya cije yace "Bazan barshi d'in ba dan ubanka gobe ma yaji dad'in yiwa wasu haka". "Dan ALLAH nace fa kasani ko yanada wani uzurin ne, duk da uban gudun dayake saida ya juyo ya harari Ja'afar kafin yace "Uzurin yaci ubanshi kasamin ido kawai malam tunda kai banza ne mara zuciya, ido kawai Ja'afar yasa masa yasan Abdallah farin sani wata magiya da ban baki bayi masa sukeba idan ba niyyar yin abu yayi ba, duk gudun mutumin nan saida Abdallah ya k'ureshi yana zuwa yasha kan waccan motar ya taka wani wawan birki jikake k'uuuuuuu wanda daga shi har Ja'afar saida sukayo gaba sukayi baya, dan dole motar ta tsaya cikin hanzari Abdallah ya bud'e murfin motar ya fita a fusace ya nufi gurin motar yayin da shima mai motar ya bud'e ya fito daidai lokacin da Abdallah ya k'arasa yana zuwa ya d'aga hannu da nufin kaiwa wannan saurayin mai motar mari Ja'afar daya k'arasa wajen yayi saurin rik'e hannunshi yana fad'in "Dan ALLAH Abdallah kayi hak'uri ayi magana ta fahimta". "K'yaleshi ya mareni ya marowa kanshi bala'i dan duk danginka sainasa an d'auresu wlhy". wancan saurayin ke fad'ar haka yana wa Abdallah wani irin kallo. Hannunshi ya warce daga rik'on da Ja'afar yayi masa, ya wani kad'a kai tareda sakin wani d'an iskan murmushi ya dafe k'ugunshi da hannu d'aya d'ayan kuma ya shiga nuna k'irjinshi yana fad'in "Ni? ni zakasa a d'aurewa dangi? kabar bala'i ya kwana lafiya d'an samari bank'i mu kwana muna bala'i dakai a wajen nan ba bakasan waye Abdallah ba amma bari in fara marin naka idan ka d'aure min dangin daga nan zakasan waye ni". ya k'are maganar yana cije baki gamida d'aga hannu zai kai masa mari Ja'afar ya k'ara hanzarin rik'e hannun yayin da wancan saurayin yaketa balok'ok'on Ja'afar ya saki Abdallah ya mareshi, a fusace Abdallah ya juya ya kalli Ja'afar yace "Idan banci ubanka anan wajen ba kace d'an iska ne ni Ja'afar dallah malam sakarmin hannu, wani dattijo dake can gefe a wajen yin sana'ar shi ta faci yake kallonsu tun d'azu ganin abin yak'i ci yak'i cinyewa ne yasa ya tsallako titi hannun da suke inda suketa faman tada jijiyar wuya kamar zasu fara kokawa, yana zuwa Abdallah ya fara janyewa dan yaga kamar yafi wancan zafin zuciya. "Dan ALLAH kayi hak'uri saurayi tunda dai ALLAH yasa ba abinda ya sameku ka kyaleshi kuyi tafiyarku". "Dan ALLAH Baba ka sakeni sonake ya fad'amin waye uban nashi a garin nan kamar yadda yake ik'rari angaya masa ina gudun bala'ine k'aramin aikina ne in tub'e anan mu bugu dashi wllhy, yaci darajar ka kawai tsoho naci uwarshi a rashin mutunci wllhy". Murmushi kawai dattijon yayi yana nan shima da irin Abdallahn a gida mai shegen zafin ran tsiya. "To nagode sosai dayaci darajar tawa yaro kamashi ku tafi ALLAH ya huci zuciyarshi". yayi maganar yana kallon Ja'afar daketa kallon ikon ALLAH ko fiye da haka akace Abdallah zaiyi bazaiyi musu ba yasan shi kamar yunwar cikinshi. Hannunshi ya kama ya nufi inda motarsu take ya shigar dashi driver seat dama a bud'e take dan lokacin daya fita baima tsaya rufe murfin ba. Komawa Ja'afar yayi inda dattijon yake yayi masa godiya harda alkhairi yayi masa na kud'i, shima dattijon godiya yayi sosai, a fusace wancan saurayin ya shiga motarshi ya bata wuta ya zagaye motarsu Abdallah yabar wajen da gudu da kallo Abdallah yabi motar yasaki k'wafa yana jijjiga kai zuciyarshi sai zafi take masa. Dawowa Ja'afar yayi ya shiga motar ya kalli Abdallah daketa cije lips yana rurrufe ido baki ya bud'e da nufin yin magana Abdallah ya dakatar dashi da fad'in "Uwarka zanci wllhy idan kasake kai min magana wllhy banza mara zuciya". Murmushi kawai Ja'afar yayi yana d'an tab'e baki yace "To naji bazanyi magana ba kar aci uwata yanzu dai ka tuk'a mutafi gida kaga magreebah takawo kai". "Bazanyi driving d'inba, kai zakayi". yace kanshi tsaye yana wani girgiza k'afa "A kanka zan zauna to inyi tuk'in". Ja'afar ya fad'a yana dariya. Mrs Salees Mu'az 💝 Maryam Ibraheem Aleeyuh (Ummee) HASKE WRITERS ASSOCIATION💡💡💡 TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A ZAFAFAN LITTAFAI MASU SAKA SHAUK'I, FADAKARWA K'AYATARWA NISHADANTARWA HAR GUDA 7!!! GA SHIRI NA MUSAMMAN INA MASU SON KOYAN GIRKUNA DA MASU SON KARA SANIN SIRRIN MALLAKE MAI GIDA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 KUDIN RAJISTA - 500 (NAIRA DARI BIYAR GABA DAYA) *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 2/14/22, 08:41 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* ♥️🩸♥️ *HASKE WRITER'S ASSOCIATION 💡 (Home of expert & perfect writer's) *TOP TEN TAKUN HASKE BATCH {A}* Writer: Oum Hanan From the writer of DR SAIF 🩸 Free page Fiction story 05 Fita yayi daga motar ya zagaya front seat inda Ja'afar yake shima lokacin ya fito shi ya shiga shima Ja'afar ya zagaya driver seat ya shiga ya zauna ya tada motar suka cigaba da tafiya. Tunda suka tafi Abdallah bai k'ara magana ba duk da Ja'afar yana takalarshi da hira amma yai masa bakam kamar ba dashi yakeba ganin haka yasa shima yaja bakinshi yayi shiru. Suna shiga unguwar ana kiran sallahr magreebah dan haka Ja'afar yayi parking anan k'ofar gida sukayi alwalah suka shiga masallachin dan sauke farali. Bayan an idar suka fito tare har lokacin Abdallah bai yiwa Ja'afar magana ba shima kuma bai kulashi ba dan yasan idan y'an tsiyar suna kanshi to duk surutun mutum bazai tanka masa ba. Tare suka jera har k'ofar gidan Ja'afar yayi knocking k'ofa saboda yanasa ran zai k'ara fita shiyasa bai shiga da motar ciki ba. Babban falon gidan suka nufa Abdallah na gaba Ja'afar na biye dashi kamar makaho da d'an jagora, lokacin da suka shiga ba kowa a falon sai TV dake a kunne akan tashar sunnah TV inda suke haska wa'azin Dr Umar sani rijiyar lemo, dukansu waje suka samu suka zauna ba wanda yayi magana, daidai lokacin Mama ta fito falon ta gansu zama tayi tana fad'in "A'ah yaushe kuka shigo gidan?". Ja'afar ne kawai ya bata amsa da fad'in "Yanzu muka shigo Mama". Kallonta ta maida kan Abdallah da har lokacin baice uffan ba yayi relaxing kan kujerar ya d'aga kanshi sama yana kallon Pop d'in falon da suka wadatu da fitilu masu haske, sai faman girgiza k'afa yake idanunshi a rufe. "A'ah waya tab'o wannan d'an tutsun nawa Ja'afar?". Dariya Ja'afar yayi yana kallon Abdallah daya d'ago kai yana hararar shi yaba Mama labarin abinda ya faru ya k'are da fad'in 'Nace masa maybe yanada wani uzurin ne na gaggawa shiyasa' murmushi kawai Maman tayi tace "Abdallah ho, tunda dai ALLAH yasa ba abinda ya faru daku ai sai a godewa ALLAH ko ta bakin na Ja'afar k'ila da wani uzurin dazaije ya gabatar". "Amma kowane uzuri ne ai ya kamata ace ya tsaya yabamu hak'uri ko?". "Gaskiya kam bai kyauta ba ayi dai hak'uri". K'wafa yayi yana cije baki yace "Wllhy badan dattijon nan ba da sai naci........"Easy dai Alajiii". Ja'afar ya katseshi yana dariya dan yasan k'aramin aikinshi ne ya danna zagi yanzun nan. Tashi Mama tayi ta bar falon tana dariyar Abdallah shifa duk abinda yazo bakinshi fad'a yake wani lokacin saidai kai ya barka da jin kunya. Shima Ja'afar tashi yayi yacewa Abdallah ya tashi su wuce side d'inshi yak'i kulashi sai waya daya zaro yafara dannawa, baki Ja'afar ya tab'e ya wuce ya barshi anan. Ja'afar na barin falon na hango wata matashiyar budurwa mai kama da Janan sak ba abinda ya rabasu, sanye take cikin riga da siket na atamfa wad'anda suka d'an kamata kad'an kalar atamfar bak'i da orange ne sai touch d'in green kad'an tayi d'aurin nan na malha wanda ya k'awata zagayayyiyar fuskar ta sai k'aramin vail datayi rolling dashi fuskarta fayau ba wata kwalliya powder ce kawai sai lipgloss data shafa wanda yasa y'an k'ananun lips d'in nata keta faman k'yalli da d'aukar ido, hill shoes ne sosai a k'afarta black color sai k'aramar jaka data sak'ala a hannunta, so simple kwalliyar tata amma ta bada ma'ana. Tunda ta doso wajen wani sassanyan k'amshi ya gauraye ko ina. Wanda ta gani a zaune ne yasa gabanta yayi mugun bugawa, cak ta tsaya tana tunanin abinda ya kawo wannan Mr arrogant d'in gidan nan kamar sunce suna gayyatar shi? yanzu zaizo ya fara takura mata dasa mata ido, k'aramin tsaki taja cikin ranta ta d'auke kai ta nufi wani dogon corridor dazai sadata da bedroom d'inta dan duk zatonta bai ganta ba saboda kanshi na k'asa yana latsa waya batasan yana kallonta tun shigowarta ba ta k'asan idanunshi saboda tun dosowarta falon yaji bugun zuciyarshi ya canza yasan kuma itace, d'agowa yayi lokacin da take daf da shigewa corridor'n murya ya d'aga sosai yace "Ke zo nan". yayi maganar yana mata alamun tazo da hannunshi. Cak ta tsaya tareda turo baki gaba, tasan halin bala'i da masifarshi hakan yasa ta juyo ta nufo inda yake zaune, tsaye tayi a kanshi lokacin data k'araso tana faman zumb'urar baki. Ajiye wayar yayi a kusa dashi ya d'aga kai ya kalleta a fusace yace "Ke bakida tarbiyya ko k'asa dan ubanki". ya k'arasa kamar zai tashi tsaye, cikin sauri ta durk'usa k'asa. Cikin tsare gida yace "Daga ina kike yanzu da magreebahr nan?". Shiru tayi tak'i magana sai b'ata rai take tana faman kumbura baki. "Ba zakiyi magana ba". yace cikin tsawa "Naje biki nefa na friend d'ina". kamar zatayi kuka take maganar tana hararar shi ta gefen ido. Baki ya cije yace "Biki kikaje? kuma sai yanzu kikaga damar dawowa ko saboda bakida mutunci, k'wafa yayi yana kad'a kai yace "Zanyi maganinki ne very soon ware daga nan". kamar wadda ke jira kuwa ta tashi da sauri har tana gurd'ewa da takalminta mai uban tsini, dan tasan k'aramin aikinshi ne ya kai mata duka yanzun nan ba abin damuwa bane a gurinshi. Zama ya cigaba dayi a wajen har lokacin da Ja'afar ya dawo Mama ma ta dawo ta zauna suka cigaba da hira, Hajiya Yaya dai tana d'aki abinta bata fitoba tasan matuk'ar ta fito sai d'an banzan yaron nan yasata magana dan haka tai zamanta a d'aki. Suna nan zaune Alh Isma'eel yadawo gidan da sallama ya shigo falon suka amsa masa dukansu suna masa sannu da zuwa, sosai fuskarshi ta washe da fara'a lokacin dayaga Abdallah cikin fara'a yake fad'in "A'ah my son saukar yaushe?". "D'azu nazo Daddy". Ya bashi amsa. Ganin fuskarshi ba yadda ya saba ba yasa Alh Isma'eel yace "Wai waya tab'o min mutumina ne haka?". yayi maganar yana kallon Mama daketa murmushi k'warai da gaske tanajin dad'in yadda mijin nata ke nunawa y'an uwanta kulawa musamman Abdallah da idan ba an fad'a maka ba zakayi zaton shine ya haifeshi saboda yadda suka shak'u da juna. Cikin murmushi Mama tace "To gashi nan dai wannan mutumin naka mai wuyar sha'ani wani ne ya tab'o shi daga waje". Murmushi Alh Isma'eel yayi yana mik'ewa tsaye yace "Tofa! zo nan ka fad'amin waye ya tab'aka". Tashi Abdallah yayi Alh Isma'eel ya k'araso wajenshi ya sak'alo hannunshi a kafad'arshi suka fice waje yana k'ara tambayarshi. Bayan sallahr esha'e aka had'u a dinning table akayi dinner, sanin Abdallah na gidan yasa Jauhar tak'i fitowa yin dinner sai bayan da aka gama sannan ta fito ta d'iba nata a plate ta shige d'aki. ^√^√^√^√^√^√^√^ Kwanan Abdallah biyu amma duk yabi ya gallabi Jauhar ya hanata sukuni, ko fita baya barinta yauma ta shirya zata fita tana fitowa ta ganshi zaune a farfajiyar gidan akan farar kujera ya fatattakota yace ba inda zata duk yadda ta dinga magiyar ya barta yak'i yace ba inda zata aikuwa taji haushi sosai haka dolenta takoma cikin gidan kamar zatayi kuka harga ALLAH ta matsu yakoma garinsu ita bataga ubanda yazoyi nan bama wllhy aikuwa zaisan ya hanata fita wlhy. Kome Jauhar zata yiwa Abdallah madugu 😅. Bayan tashin shi a nan ya shiga part d'in Ja'afar dan yin wanka, shirt d'in jikinshi ya cire da dogon wandon jeans d'in dake jikinshi ya rage dagashi sai boxer dama ba singlet a jikinshi ya shiga bathroom. Bathtub ya cika da ruwa na sanyi dana zafi ya daidaita d'umin ya shiga ciki, yana kai hannu cikin ruwan da niyyar d'ebowa yaji wani abu ya tsikareshi a hannu runtse Ido yayi lokaci d'aya yana saurin fito da hannun daga cikin ruwan tareda kai idonshi ciki dan ganin meye idanunshi suka nuna masa wata k'atuwar kunama bak'ikk'irin a tsorace ya mik'e tsaye yana zaro ido cikin matuk'ar mamaki da al'ajabi tabbas lokacin daya shiga cikin ruwan ba komai a ciki to ta ina kunama ta shigo? Fita yayi daga ciki ya figo towel ya d'aura koda ya k'ara kai dubanshi cikin ruwan ba kunama ba alamarta, mamaki ne ya k'ara kamashi lallai akwai ayar tambaya akan wannan al'amarin anya ba Jauhar ce da wannan aikin ba? yess tabbas itace saboda ya hanata fita, lallai zaici ubanta kuwa muguwa. Fitowa yayi daga bathroom d'in ya bud'e trolley d'inshi ya ciro bak'ar shirt da farin wando yasa duk da halin dayake ciki saidaya d'auki farar P. cap data zame masa ta k'a'idah yasa 😂 dan zuwa lokacin hannun yafara masa rad'ad'i turare ya fesa ya fita ya rufo k'ofar d'akin ya fita harabar gidan sai faman cije baki yake yana tunanin irin hukuncin da zaiyiwa wannan muguwar yarinyar. Yana fita compound d'in Ja'afar ya shigo gidan. "Muje ka kaini hospital Ja'afar". ya fad'a lokacin da Ja'afar ya k'araso wajenshi, idanunshi sun kad'a sunyi jawur yana rik'e da hannunshi wanda yake masa uban zugi da zafi. "Meya faru ne Bros na ganka haka?". Ja'afar yace yana kallonshi da mamaki ganin yadda ya koma ga fuskarshi datayi jaa. "Zaka wuce ne muje ko tambayata zaka tsaya yi?". Baki kawai Ja'afar ya tab'e ya d'aga hannayenshi sama yana fad'in "ALLAH ya baka hak'uri". Tsaki kawai Abdallah yaja yayi gaba inda motar Ja'afar take, yana zuwa ya bud'e front seat ya shiga yaja murfin ya rufe da k'arfi, Ja'afar shima daya k'araso ya shiga driver seat ya kunna motar kafin daga bisani yajata suka bar gidan. Sai daya hau kan babban titi sannan Ja'afar ya k'ara waigowa ya kalli Abdallah dayake ta matse baki yana huci, dariya ce taso kamashi duk da baisan abinda ya sameshi ba mazewa yayi yace "Wai dan ALLAH Bros meyake faruwa? meyasamu hannun naka?". K'wafa Abdallah ya saki yana jijjiga kai yace "Ni yarinyar nan zatayiwa haka? in hanata fita tayi min k'ofi? na rantse yau sai Jauhar ta gane kurenta". Sai a lokacin Ja'afar ya fahimci inda akalar maganar take wato Jauhar ya hana fita unguwa itakuma tayi masa halin nasu na y'an biyu lallai ta tarowa kanta match. Dariya ce taso kama Ja'afar ya wani maze ya shiga sosa kanshi da d'aya hannun da baya tuk'in dashi kafin kuma dariyar ta sub'uce masa ya shiga k'yak'yatawa harda dukan sitiyarin, haka ya hasala Abdallah ya kaiwa Ja'afar naushi a baki yayi hanzarin gocewa yana dariya. M? *TOP 10, TAKUN HASKE💡* _INA MASOYA MA'ABOTA SON HASKAKA ZUKATANSU? KU MATSO KUSA GA DAMA TA SAMU DA ZAKU KWASHI GARAB'ASAR DA ZATA HASKAKA MAKU ZUKATA DAGA QUNGIYAR HASKE WRITER'S, QAYATATTUN SHIRE_SHIRE HAR GUDA UKU DA KUMA HA'DA'DDUN LITTAFAI GUDA BAKWAI, DUK AKAN NAIRA 500 KACAL DOMIN FARANTA MAKU_👇🏼 ? *IBTISAM:- AYUSHA MUH'D* ? *WASU MAZAN:- BILLY S FARI* ? *AZAAD JUNAID:- JEEDDAH ALIYU* ? *ZO GARE NI:- HAJJA CE* ? *KUKAN ZUCI:- SLIMZY* ? *NIDA RAHEEMAH:- ASMY B ALIYU* ? *WATA SOYAYYAH:- OUM HANAN* ? *SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE:- CHIEF DEEJARH BERVER* ? *SHIRIN YANDA ZAKU GYARA JIKINKU, TSAFTA DA MATSALOLIN JINI:- UMM A'ISHA* ? *SHIRIN HAD'A MAGUNGUNA:- MAMAN KHADIJA* _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N500)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_ 2083371244 ZENITH BANK AISHA M. SALIS SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼 +447894142004 IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA WANNAN LAMBAR👇🏼 07043079282 SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼 07065283730 _GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU 550F TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_ +227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey. MUN GODE. 2/14/22, 08:41 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*♥️🩸♥️ *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* 💡 (Home of expert & perfect writer) *TOP TEN TAKUN HASKE BATCH {A} 2022* Writer: Oum Hanan From the writer of DR SAIF 🩸 Free page Fiction story 06 ^√^√^√^√^√^ Wani private hospital Ja'afar yakai Abdallah inda wani abokinshi yake aiki, kai tsaye suka samu ganin Dr Naseer yayi mashi allura yabashi duk taimakon daya dace ayi masa, Ja'afar dai sai danne dariyar shi yake kar yaja abinda za'a zagi uwarshi da ubanshi yanzun nan dan yadda yake a zuciyen nan kamata yayi mutum yayi baya baya dashi. Har suka koma gida ba wanda yace uffan dan yasan yana magana maybe Abdallah ya huce a kanshi shiyasa yayi gum da bakinshi har suka k'arasa. Yana yin parking Abdallah ya b'alle murfin motar ya fice a fusace ya nufi main parlor na gidan a zuciye, Ja'afar ya bishi da kallo yana tunanin abinda yasa har Jauhar tayi masa haka kuma tasan halinshi sarai koma me yayi mata ita ta jawa kanta, fita yayi daga motar ya shige side d'inshi. Ko sallama baiyiba ya afka falon inda Hajiya Yaya take zaune kan kujera tana kallo dayake Mama bata nan, bai kalleta ba kai tsaye ya nufi bedroom d'in Jauhar, da kallo Hajiya Yaya ta bishi tana fad'in "Kai kai meye haka zaka shigo mana waje ba sallama, bada Abdullahi nakeba wai". Sam baibi ta kanta ba ya shige corridor'n dazai kaishi bedroom d'in Jauhar. "Yau naga jaraba da rana tsaka, wannan yaron kanshi d'aya kuwa? tsaki kawai tasaki ta maida kanta kan TV'n datake kallo. Tana zaune a tsakiyar gadonta da books a barbaje a gabanta amma ba book d'in take karantawa ba wayace a hannunta tana dubawa, ta canza shigarta da wasu riga da wando plain ash color ba komai a kanta sai gashinta mai uban yawa da tsayi bak'ikk'irin dayake ta shek'i, ba zato taji an turo k'ofa da k'arfi an shigo manyan idanunta ta zaro ganin wanda ya shigo d'in a tsorace ta mik'e tsaye tana kallon Abdallah saidaya murza key sannan ya k'araso bakin gadon tareda kai hannu kan k'ugunshi yana kwance belt d'in dake d'aure lokaci d'aya yana fad'in "Ni zakiwa k'ofi Jauhar? dan uwarki ni sa'anki ne da zakimin k'ofi". ya k'are maganar da kai mata duka da belt d'in tayi saurin gocewa ta shiga dire dire akan gadon tana yayyarfe hannu da fad'in "Dan ALLAH Yah Abdallah kayi hak'uri dan girman ALLAH wllhy bazan k'ara ba wayyo Mama wayyo Hajiya". tayi maganar cikin ihu. Baki ya cije ya k'ara kai mata wani dukan yana fad'in "Yau sai kinmin k'ofin maciji a gidan nan sannan zan yarda ke muguwace dan ubanki". Hannu tasa ta toshe bakinta d'ayan kuma sai yayyarfa shi take tana girgiza masa kai, haka sukai ta faman tsere shi a k'asa itakuma akan gadon har lokacin kuma baiyi nasarar dukanta ba, Hajiya Yaya dataji ihun Jauhar da saurinta ta taso ta taho bedroom d'in saidai tana zuwa tajishi ansa key daga ciki. "Kai dan ubanka ka bud'e d'akin nan, mugu kawai wato muguntar taka ce ta motsa kazo zaka sauketa akan yarinyar da bataji ba bata gani ba ko". magana take tana bubbuga d'akin saidai ba alamun za'a bud'e haka ta gaji ta juya tana ta faman bambamin fad'a tana zai fito ya sameta ne dan ubanshi yaro saikace mahaukaci. Har zai bita kan gadon databi duk ta tumurmushe shi saikuma ya fasa ya juya, tana shirin sakin ajiyar zuciya dan duk zatonta fita zaiyi saitaga sab'anin hakan kan couch taga ya zube yayi wani irin zama, k'afa d'aya ya d'ora kan hannun kujerar d'ayar kuma ya ajiyeta a k'asa yana faman girgizata hannunshi rik'e da belt d'in, yana sauke numfashi idanunshi akan Jauhar data zauna kan pillow ta toshe bakinta da hannu d'aya kanta a k'asa tana satar kallonshi ta k'asan ido. "Jauhar". ya ambaci sunanta a hankali kamar wanda zai fad'a mata wata maganar arzik'i, d'agowa tayi ta kalleshi batare data amsa ba, cikin ranta banda ALLAH ya isa ba abinda take ja masa ko wannan dire diren daya sata ai sai ALLAH ya saka mata mugu da wata R d'inshi dabata fita (Abdallah na daga cikin mutanen da basu iya harafin R ba). "Zaki amsa ne kokuwa saina tashi kinga tsayina". yayi maganar yana shafa belt d'in hannunshi. "Na'am". ta amsa da sauri. "Kinaso inci uwarki a d'akin nan?". Kai ta girgiza masa tana matso hawayen munafunci. "Good, sonake kimin na maciji ya sareni in tabbatar dake d'in bak'ar muguwa ce, k'aryar mugunta kike yarinya kunama ai k'aramin alhaki ce (Kunji mutumin naku fa 😂). Kanta ta cusa tsakanin cinyoyinta. Yana shirin yin magana kamar ance ya juya ya hangi snake daga wajen wardrobe d'inta ba irin babban nan bane amma kuma da d'an girmanshi ba laifi, ido ya zaro ya mik'e da sauri ganin yafara shirin yowa wajenshi belt d'in hannunshi ya jefar yayi wata irin sufa kan gadon lokacin Jauhar ta mik'e tsaye akan gadon aikuwa yabi ta kanta suka fad'a kan gadon sai gashi d'are d'are akanta fuskarsu daf data juna idanunshi cikin nata idanun cikin zaro ido yace "Ke dan ubanki bakida hankali maciji fa nagani yanzu". "Yah Abdallah kaine fa kace inyi na snake". tace tana b'ata fuska gefe d'aya kuma dariyar ta take matsewa ganin yadda ya tsorata ashe ba namiji bane bama sai afkin cika baki ya iya". "Wawuyar yarinya kawai ke dan ubanki ba'ayi miki wasa?". Baki ta tura tasa hannayenta a k'irjinshi tana turawa tace "Nidai ka d'agani Yah Abdallah nauyi wllhy". "Wancan snake d'in dake d'akin fa?". Cikin dariya Jauhar tace "Ka tashi kagani Yah Abdallah ya tafi fa". K'wafa yasaki ya tashi a hankali yakai dubanshi inda snake d'in yake yaga ba komai, kad'a kai yayi lallai ma yarinyar nan zataci ubanta belt d'inshi ya d'auka ya kalli Jauhar da har lokacin take kwance bata tashi ba sai k'yalk'yalar dariya take abinta. "Zanyi maganinki yarinya, sainasa an karya miki k'ofin naki inga ta yadda zaki dinga cutar da mutane shegiya muguwa". daga haka ya bud'e k'ofar ya fice, har lokacin Jauhar dariya take wlhy ya bata dariya sosai ganin yadda yayi ashe duk kuri ne kawai irin na maza dama wani tym d'in mata sunfi mazan jarumta su sai afkin cika baki suka iya. Falon ya fito yana maida belt d'in, tun daga nesa Hajiya Yaya take jefo masa harara murmushi kawai ya sakar mata ya zauna kujerar dake facing tata yace "Yadai hajjaju zaman me kike anan ne?". yayi maganar yana d'age mata gira "Zaman k'aniyarka nake d'an banzan yaro kai bak'in mugu me Johar tayi maka ka daketa? kaidai wannan yaro anyi mamugunci wlhy". Baki ya tab'e yace "Tamuce ta had'omu dan haka ki zuba Ido kawai kiyi kallo wannan jikar taki batada kunya Abdallah kuma ba'a tab'a shi a zauna lafiya idan taimin ubanta zanci wllhy". ya k'arasa maganar yana mik'ewa tsaye da nufin barin falon, da kallo Hajiya Yaya ta bishi tace "To zakabar gidan nan kuwa tunda cin zaline ya kawoka mara mutunci kawai". "Idan nayi ra'ayin tafiya ba, ki share kawai hajjaju". yace lokacin dayake k'arasa ficewa daga falon yana k'ara gyara zaman belt d'inshi. "Mtsww, ALLAH ya shiryaka". tashi tayi ta tafi bedroom d'in Jauhar dan ganin abinda yayi mata wannan uban ihun dataji tanayi tasan ba banza ba yanzu haka ma tana nan kwance azzalumi kawai (kai Hajiya 🤣). ^√^√^√^√^√^ Da Mama ta dawo Hajiya ta fara mata maganar. "Kijawa wannan mugun yaron naki kunne wllhy karya k'ara gigin tab'amin jikata idan ba hakaba kuma zamusa k'afar wando d'aya dashi". (Lokacin da Hajiya ta shiga bedroom d'in Jauhar itama munafukar bata nuna ba dukanta yayi ba harda hawayenta da k'yar Hajiya ta lallab'ata tayi shiru). "Me kuma yayi Hajiya?". "Meye ma baiyi ba? yaron nan dan tsabar zalunci yasamu yarinyar nan ya dinga duka ba laifin zaune bana tsaye saboda mugunta to wllhy nagaji ai ba jaka bace dazai dinga kilarta haka nan batare da wani dalili ba". "Hajiya yarinyar nan fa ita take jan abinda Abdallah yake mata ko meye shifa idan ba'a shiga harkarshi ba baya kula mutum duk ita take ja". "Dama haka zakice mana saboda bakison laifin shi, idan ance Johar tanada tsokana itakuma Janan fa? yarinyar daba ruwanta itama nasamu labarin takura mata yake". "Ayi hak'uri Hajiya zan masa magana". "Atoh dan bazan lamunci hakaba". tayi maganar tana gyara medical glass d'in dake idonta. Tun daga ranar Abdallah da Jauhar basu k'ara had'uwa ba har akayi kwana biyu. Tun safe ya fita daga gidan yaje wajen wani friend d'inshi da sukayi school tare a outside Khaleel dama d'an Kaduna ne shine yakai mashi ziyara can suka yini sai yanzu da yammacin nan yadawo gidan. Tunda ya danno hancin motar shi ya hango Jauhar itada wani saurayi a compound d'in gefen wasu flowers akan fararen kujeru sai k'aramin table a tsakiya da aka jera drink's kaloli daban daban da snacks. Parking yayi ya k'ura musu ido ta glass d'in gaban motar zuciyarshi na masa wani irin tuk'uk'i, ido ya lumshe ya k'ara bud'esu akansu Jauhar da suke hirarsu cikin nishad'i da farin ciki, lips d'inshi ya cije yana kad'a kai bari yaje ya d'an tab'a tsokana ko kad'an ce yaga ta yadda za'ayi zancen dan ubansu itada saurayin. Fita yayi ya rufe motar, yana sanye ne cikin bak'in wando da red colour d'in riga sai black tied daya matse wuyanshi dashi ya matse k'ugunshi da bak'ar belt bak'in takalmi sawu cikine a k'afarshi sai black watch dake d'aure a tsintsiyar hannunshi mai cikeda kwantaccen gashi sassanyan k'amshi ke fita daga jikinshi. Kai tsaye ya nufi inda su Jauhar suke yana kad'a key d'in motarshi, saidaya fara d'auko wata kujerar sannan ya k'arasa inda suke daf da saurayin ya aje kujerar ya zauna tareda sallama yana mik'awa saurayin hannu sukayi musabaha, sosai Jauhar ta b'ata fuska tasan tunda wannan mutumin yazo yanzu zai b'ata gayyar duk saita rasa abinyi. Shima saurayin mai suna Saleem mamakin abinda ya zaunar da Abdallah yake a wajen duk da dai bai sanshi ba amma koma waye ai kamata yayi ace suna gaisawa yabar wajen amma harda neman wajen zama 🤔😬. Kallon Jauhar Saleem yayi data kasa samun nutsuwa sai hararar Abdallah take ta gefen ido tana d'an tura baki. "My love yayanki ne wannan?". "Nabi My love da gudu ubanka zakaci". Abdallah yayi maganar cikin ranshi a fili kuma yace..... Mrs Salees Mu'az 💝 Maryam Ibraheem Aleeyuh 💡 *DAGA TASKAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 💡💡💡💡💡💡💡💡💡 *_OHH NI IBTISAM WANNAN SOYAYYAR TA YAYA UMAR ITA AKE KIRA DA WATA SOYAYYA DUK DA HALIN ABDALLAH YA BANBANTA DA WASU MAZAN, KUKAN ZUCIN DA AZAAD JUNAID YA JIMA YANA YI AKAN SALIMA YAYI KAMANCECINIYA DA NA HAKEEM TAURARON NIDA RAHIMA BURINSA DA KALAMANSA AKODA YAUSHE ZO GARE NI.....TOP 10 KENAN DAGA ƘUNGIYAR HASKE YAR UWA KAR KI SAKE KI BARI AYI BABU KE_* *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *HAKA KUMA ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALAR JINI, DA MA MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. *HASKE MAGANIN DUHU*🤝🏻 2/14/22, 08:42 - Ummi Tandama😇: *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) *WATA SOYAYYA* ♥️🩸♥️ Writer: Oum Hanan From the writer of DR SAIF 🩸 Free page Fiction story. 07 ^√^√^√^√^√^ "Baki tab'a bashi labarina ba? baki tab'a fad'a masa waye ni a wajenki ba?". Yayi maganar yana k'ank'ance idanunshi akan Jauhar. Murmushin yak'e kawai Jauhar tayi tace "Amm Saleem wannan kamar yaya yake a wajena da Maman mu da mamanshi ya da k'anwa ne so yazo kawo mana ziyara ne a Kano suke da zama". ta k'are maganar tana d'an hararar Abdallah da yaketa sakin murmushi yana wani tsotsar baki kamar mai shan sweet, shima Saleem murmushin yak'en yayi yace "Eyyah ALLAH sarki". daga haka yaja bakinshi ya tsuke yana satar kallon Abdallah ta gefen ido wanda ya sunkuyar da kanshi yana danna waya, ido suka had'a da Jauhar data had'e rai sosai sai faman hararar Abdallah take ta gefen ido. Shiru gurin ya d'auka, kafin Abdallah ya d'ago kanshi ya kallesu duk sai suka bashi dariya y'ar dariyar iya shege ya saki yana d'an tab'e baki ya matso inda drink's da snacks d'in suke wanda da alamu ma ko tab'a su ba'ayi ba ya bud'e ya tsiyaya a glass cup dake wajen ya koma yayi relaxing kan kujerar yayi crossing legs nashi yafara shan lemon yana danna waya, wani takaici ne ya kama Jauhar wllhy abinda mutumin nan yake sam baya kyautawa taya zaizo ya sameta da saurayi suna hira yazo ya wani zauna tsabar neman bala'i irin nashi wllhy ta gaji da zamanshi a gidan nan jitake tamkar ta iza k'eyarshi ya koma garinsu. Saleem dai kallon ikon ALLAH kawai yake zuwa yanzu dai ya tabbatar bawai iya gaisuwa bace ta kawo mutumin nan harda neman masifa da biyu yazo wajen kuma, haka suka cigaba da zama ba wanda ya k'ara magana Abdallah daya shanye lemon ya ajiye cup d'in ya d'auki lafiyayyen meat pie ya fara ci, Saleem dai mamaki yagama cikashi itakam Jauhar kome akace Abdallah zaiyi bazatayi musu ba gashi dai One in town, first class handsome guy duk inda ake neman cikakken saurayi mai cikar sura kyawun fuska dana jiki Abdallah ya had'a ga brain ga ilmi ga kud'i dan yana samun kud'i sosai a sana'ar shi, amma wani time d'in idan yayi wani abun zakace bai tab'a shiga class ba shiyasa dayawa daga cikin y'an uwansu wad'anda suka san halayyarshi basu cika damuwa ba idan yayi musu wani abun, shi kawai haka ALLAH yayi shi baya d'orawa kanshi pressure yana da hawa kai ga wanda zama ya had'asu tare, amma wani lokacin yanada dad'in zama idan akayi sa'a y'an buyagin nashi basu kusa 🤣. Ji kawai sukayi ya k'yalk'yale da dariya har yana d'an dukan goshinshi, shidai Saleem zuwa yanzu ya daina mamakin Abdallah ya zura masa ido kawai yana kallon ikon ALLAH ya kuma fara tunanin ya tashi yayi tafiyarshi idan ALLAH yasa Abdallah yabar gidan yadawo wannan jaraba dame tai kama yazo ya musu katak'e katak'e a waje suna tsaka da soyayyarsu. "OH my God, wllhy ana tsiya a media dan ALLAH abokina duba wani posting da akayi a Facebook yanzu". Cikin dariya Abdallah yayi maganar yana karkatowa kusa da Saleem tareda haska masa screen d'in had'add'iyar wayarshi a fuskar Saleem d'in daya shak'a ya tumbatsa kamar zai fashe tsakani da ALLAH wannan guy d'in bai kyauta masa ba yazo yana cikin tsinkar fulawarshi ya katse masa komai jiyake kamar ya tashi yaita dukan Abdallah 😂 cikin had'e rai Saleem yakai idanunshi kan wayar batare daya karanta abinda yake nuna masa d'in ba ya kauda kanshi yana fad'in "Zan wuce My love sai mun k'ara had'uwa". "Buk'atar maje hajji sallah". Abdallah ya fad'a a ranshi dama so yake ya tafin, dan haka yanajin ya fad'i haka ya mik'e tsaye yana gyara zaman tied d'inshi fuskarshi d'auke da wani shegen murmushi ya mik'awa Saleem hannu alamun su gaisa, da k'yar yabashi hannu suka k'ara yin musabaha har lokacin da murmushi saman fuskarshi, ledar da aka rufe snacks d'in ya bud'e ya d'auki doughnut da samosa guda d'ai d'ai yayi gaba yana dariya. Duk da kallo suka bishi Jauhar kamar idonta zai fad'o saboda harara, kallonta tadawo dashi kan Saleem da shima ya dawo da nashi idanun kanta. "Wai dan ALLAH My love wannan guy d'in waye? meyake nufi da wannan abinda yayi?". Tsaki taja cikin jin haushi tace "Dan ALLAH kayi hak'uri Saleem mutumin can fa da kake gani bawai k'alau yakeba yanada d'an tab'in hankali a k'wak'walwar shi". Cak ya tsaya tareda runtse Ido lokacin dayake daf da shigewa cikin falon ALLAH ya hore masa ji kamar maciji hakan yasa har yaji abinda ta fad'a wato ma mahaukaci ta d'aukeshi? kai kawai ya kad'a ya ida shigewa falon yana cije lips d'inshi tamkar zai huda. "A'ah no wonder mana haba shiyasa naga abin yayi yawa to ki dinga dai taka tsantsan dashi My love duk da dai ni ban gama ma yarda wai tab'in hankali gareshi ba tsabar tantiranci ne kawai yake d'awainiya dashi". ya k'arasa maganar yana shirin tashi tsaye. "Yanzu tafiya zakayi kenan?". tace cikin tura baki kamar zatayi kuka. "I'm sorry Jauhar munada appointment da wani da zamu had'u kinga ma yafara calling d'ina, yace yana nuna mata wayarshi dake hannunshi wadda ta tafara ringtone. Mik'ewa tayi ta taka masa har wajen motarshi sukayi sallama ya shiga ya tayar tana nan tsaye har saida ya fice daga gidan sannan ta juyo a fusace ta nufi falon bata tsaya bi takan kayan dake kan table d'in ba ta shige falon. Tana shiga ta sameshi akan kujera 2sitter ya mik'e k'afarshi akan k'aramin center table da labtop akan cinyarshi dama nan ya barta kan kujera lokacin dazai fita ga dukkan alamu wani binciken yake saboda yadda ya maida hankalinshi sosai kai dan baisan ma ta shigo ba saiji yayi an tsaya masa akai ana huci, d'agowa yayi ya kalleta cikin fushi ta fara magana "Gaskiya Yah Abdallah ka dainamin irin wannan ya za'ayi kazo wajen bak'o na kayi masa haka yanzu gashi nan kaja ya tafi kuma daga gani ranshi ya b'aci wllhy". "Ya dad'e ran nashi bai b'aci ba dan ubanshi, ke ki bini fa a sannu wllhy". Ido ta zaro jin kai tsaye ya zagar mata saurayi "Kai kai kai ka zageshi?". Dama a kusa yake k'iris yake jira dan haka da sauri ya dangwarar da labtop d'in ya mik'e a zafafe ya matsa daf da inda take tsaye har sunajin hucin numfashin juna yace "Na zageshi d'in akwai abinda zakiyi ne? nace na zageshi Jauhar zaki da'u mataki ne". ya k'arasa maganar yana turata da k'irjinshi tayi baya kamar zata fad'i ya k'ara binta yana fad'in "Nace zaki d'auki mataki ne Jauhar?" A tsorace tace "ALLAH saina had'aka da Daddy idan ka k'ara". juyawa tayi tana cigaba da fad'in "Aikin banza aik.......ba zato ba tsammani taji ya fisgota haka yasa ta katse maganar dataso fad'a ba shiri kafin tayi tunanin abinda zai mata taji ya zuro hannayenshi ya kamo nata hannayen ya bank'aresu baya ba shiri tasaki k'arar azaba tana runtse idanunta kanshi ya zuro ta gefen wuyanta ya d'ora hab'arshi akan dokin wuyanta ta yadda kwantaccen quarter million d'in dake hab'ar tashi yasamu damar tab'a wuyanta ta k'ara tamke idanunta kamar zata saki kuka saboda zafin da hannayenta ke mata. "Dan ubanki wa kike cewa yanada tab'in hankali d'azu?". K'asa k'asa yayi maganar cikin kunnenta yana k'ara matse hannayenta dake rik'e cikin nashi hannun tabbas da wani zaizo a lokacin zaiyi tsammanin wata maganar arzik'i yake fad'a mata, ido ta zaro gabanta na fad'uwa dama yajita ne shikenan ta shiga ukunta. "Baza kiyi magana ba saina karya wad'annan hannayen naki?". yace yana k'ara bank'aresu harda cije baki. "Wayyo ALLAH dan girman ALLAH Yah Abdallah kayi hak'uri na rantse maka bazan k'ara ba wayyo ALLAH nah". da k'yar ta harhad'a kalmomin ta fad'a saboda azaba hawaye har sun cika idanunta suna daf da zubowa. Wata y'ar dariya yayi yace "Wai ni Abdallah nine mahaukaci ko to kibari in k'ara ganinki da wannan ramammen saurayin naki ko wani daban anan ne zakiga tsantsar hauka da tashin hankali dan ubanki b'ace daga nan". yayi maganar tareda sakar mata hannu ya d'aga kanshi daga wuyanta. Kamar wadda ke jira tabar wajen harda had'awa da gudu hawaye shab'e shab'e a fuskar ta, k'ugu ya kama da hannayenshi duka ya bita da kallo. Saidata tabbatar takai kusa da bedroom d'inta sannan ta leqo da kanta tace "ALLAH ya isa mugu kaidai anyi azzalumi wllhy bazan tab'a yafewa ba kuma". Inda ya tashi ya koma ya zauna ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana girgizasu idanunshi akanta yace "Uwarki zanci la'ada waje wllhy kibari mu k'ara had'uwa Jauhar". Fuska ta yatsina tana d'an tab'e baki tareda kwaikwayar sunan Jauhar d'in daya fad'a "Wai Jauhar, dan ALLAH wai yaushe zaka iya R ne Miss Abdallah Madugu". Baice komaiba sai dariya kawai dayayi ya d'auki labtop d'inshi ya k'ara mik'e k'afarshi ya cigaba da aikinshi. "Mugu kawai". Tace cikin tura baki tana share hawayen fuskarta da bayan hannunta ta shige bedroom d'inta tana k'ara yimasa ALLAH ya isa saboda hannayenta dataji suna amsawa dole saita musu ruwan zafi kuma wllhy saita d'auki mataki akai kuma saita fad'awa Mama abinda yayi mata. _D'inbin godiya gareku masoya hak'ik'a banida bakin magana, kunyi nagani na kuma yaba da irin soyayyar da kuke nunawa book din nan wanda har yaso ya zarta ta book din DR SAIF 🩸 nagode sosai ina ganin sak'onnin ku na gaisuwa ALLAH ya saka da alkhairi yabar mu tare ina yiwa kowa fatan alkhairi ALLAH yasa mudace Amin_.🤩😍🥰 *1luv* Mrs Salees Mu'az 💝 Maryam Ibraheem Aleeyuh {Ummee} *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 2/14/22, 08:44 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* ♥️🩸♥️ *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* 💡 (Home of expert & perfect writer's) *TAKUN HASKE BATCH {A} 2022* Writer: Oum Hanan From the writer of DR SAIF 🩸 Free page Fiction story 08 Bedroom d'in Mama ta shiga bayan tayi wanka ta gasa hannayenta dasuke mata rad'ad'i ta shafa man zafi sai faman jera masa ALLAH ya isa take cikin ranta. "Waya tab'o min autata ne na ganta haka?" Mama tayi maganar tana kallon Jauhar data b'ata rai kamar wadda zatayi kuka, zama tayi kusa da ita tana fad'in "ALLAH Mama kiyiwa Yah Abdallah magana kar ya k'ara yimin irin haka wllhy". "Me kuma yayi yanzu shida kullum sai ansamu laifin da akace yayi?". Cikin tura baki tace "Kawai fa yazo ya sameni da Saleem yazo ya wani zauna tsabar neman fitina ya hanamu sakat harda zuba drink yasha da snack saida yaji yace zai tafi fa sannan ya tashi ya bar wajen". Kai kawai Mama take girgizawa kafin tafara dariya. "Mama dariya ma kikeyi?". tace tana tura baki kamar zata saki kuka. "Abin ne ya bani dariya Jauhar lamarin Abdallah sai dua'e tun yana k'araminshi haka ake fama dashi wllhy da rawar kai shikuma haka ALLAH yayi shi". "Ni Mama ba ruwana da wani rawar kanshi kawai ayi masa magana ya daina shiga harkata wllhy". "Taya kuwa zai daina shiga harkarki yana d'an uwanki zanyi masa magana dai ai ba'a haka tashi kije". Tashi tayi ta fita daga bedroom d'in tana faman cika tana batsewa. Washegari. 4:30pm. Wasu y'an mata na hango a falon su Jauhar su uku kowacce taci ado na kece raini dukansu kyawawa ne masha ALLAH, gabansu kayan ciye ciye ne kala kala da lemuka. Jauhar na hanga tana saukowa daga upstairs taci kwalliya cikin shadda ash color doguwar riga datasha aikin stone work sai walwali take d'aurinta data saba na malha siririn gyale data nad'e kanta dashi red colour sai takalmin k'afarta Tom's shima red sai sauran abubuwan datayi using dasu irin su sark'a d'an kunne da abin hannu da zobe da agogo duk red colour ne tayi kyau k'warai masha ALLAH duk da dai ba wata kwalliyar kirki a fuskar tata powder ce kawai da kwalli sai lipgloss da eye shadow kad'an data goga saman idanunta ash color sai zuba daddad'an k'amshi take, hannunta rik'e da wayarta. "Hi guys get up". ta fad'a lokacin data k'arasa saukowa downstairs d'in. "Wow! kinyi kyau sosai fa Jauhar". d'aya daga cikinsu mai suna Abeedah ta fad'a kafin sauran ma su fara yaba kyawun datayi bayan sun tattashi tsaye cikin murmushi tace "Thank you so much my friends". tayi maganar tana shiga gabansu tareda d'aga wayarta suka shiga yin selfie, kaloli daban daban sukayi sannan kowa ta d'auki bag d'inta suna shirin tafiya. ALLAH ALLAH take subar gidan kafin wannan mai almatsutsan yadawo yazo yawani tare musu a gida ya takura musu kawai. A hankali yake takowa zuwa cikin falon yana sanye da riga da wando farare k'al rigar mai gajeren hannu hakan yabawa cikakkun fararen damatsen shi damar fitowa k'afarshi sanye da bak'in boot Rolex watch ne black color d'aure a tsintsiyar hannunshi sai bak'ar P cap d'inshi ta gado dake sanye a kanshi, cikin takunshi na mai cikakkiyar lafiya ya shigo falon kanshi a k'asa yana danna waya sai d'aya hannun daya sokeshi cikin aljihun wandon, cak ya tsaya yana kallonsu lokacin daya gansu suma d'in tsayawar sukayi suna kallonshi dukansu lokaci d'aya suna yaba kyau da tsari irin na gayen a zuciyoyinsu, Jauhar kam tuni tayi kicin kicin da fuska dan bataso yace zai kawo mata k'auli a gaban k'awayenta tasan k'aramin aikinshi ne yace ba inda zata fita, kamar yasan abinda take tunani kuwa ya shiga takowa inda take bayan ya zura wayarshi a aljihun wandonshi, wata irin tsayuwa yayi yai bake bake a gabanta ya soke hannu d'aya a aljihu yayin da d'ayan kuma ya dafa bayan wuyanshi yana kallon Jauhar data had'e rai tana tura baki sudai k'awayenta Abeedah da Maryam da Ameerah tsaye sukayi suna kallonsu, cikin tsare gida yace "We're are you going?". kai ta juyar tana tura baki gabanta sai fad'uwa yake tsoronta d'aya kar ya dizgata gaban su Abeedah. "I said we're are you going?". ya fad'a cikin d'aga murya yana k'ara matsawa daf da ita, baya ta d'an ja cikin tura baki tace "Bikin friend d'inmu zamuje". "Bikin friend d'inku?". ya maimaita yana mata wani irin kallo. Kai kawai ta d'aga masa tana satar kallon su Maryam da suka maida gaba d'aya hankalinsu kansu suna mamakin waye kuma wannan? sudai Ja'afar kawai suka sani a matsayin yayanta to waye wannan kyakkyawan handsome man d'in?. "To bazaki ba". ya fad'a kanshi tsaye. "What?". Tace cikin yatsina fuska tana d'an hararar shi. "Baki buk'atar maimaici kinji me na fad'a, kewai baki gajiya da yawo ne uban me kike fita kiyi a wajen?". Dire diren k'afafu tafara kamar zatayi kuka take fad'in ita wllhy saitaje, Ameerah datafi sauran son iyawa da neman suna ta matso inda yake cikin kwarkwasa da yanga tana wani kashe murya tace "Please mai kyau a taimaka a bar k'awarmu taje mana bawani dad'ewa zamuyi ba, uhmm?". Inda take tsaye ya juyo ya kalleta sama da k'asa yace "Wace ke?". "I'm Ameerah Muhammad Ali Jauhar is my best friend". "Ware daga nan to uwar shisshigi ko kinji nasaki a maganata". kunya ce ta kama Ameerah sosai jin abinda yace mata, a kunyace ta koma gefen da sauran suke tsaye tanajin tamkar ta nutse k'asa saboda kunya wane irin mutum ne wannan? Kallon Jauhar yayi datake ta faman jijjige jijjigen jiki tana itafa bai isa ya hanata fitaba,yana shirin magana Hajiya Yaya ta shigo falon jin maganganu. "Meyake faruwa ne anan naketa jin surutai d'an lazumin danake ma kun hanani". kafin ta k'araso wajen Jauhar ta k'arasa wajenta tana fad'a mata Yah Abdallah ne yace wao bazata fitaba. "Yau naji jaraba, waikai Modibbo meyake damunka ne? kai a rayuwar duniyar nan idan baka takurawa yarinyar nan ba bakajin dad'i akan wane dalili zaka hanata fita?". cikin fad'a tayi maganar suna k'arasowa inda yake tsaye itada Jauhar d'in data fara matso k'wallah. "Saboda bai dace taje wajen ba". yace yana kallon Hajiya. "To saitaje kuwa inga mai hanata fita dan k'aniyar mutum haba wannan bala'i har ina kai idan bakaja abinda aka tada jijiyar wuya ba bakajin dad'i ku wuce kuyi tafiyarku inga mai hanaki". "Yeeee I love you so much Hajiyata muaahhhh". ta fad'a cikin murna tana sakarwa Hajiya kiss a kumatunta. "Wuce kuje ALLAH ya kiyaye". Hajiya ta fad'a tareda juyawa ta koma d'akinta tana cigaba da mita. Gaba su Maryam sukayi suka fita falon, ta kusa dashi Jauhar tazo ta wuce tana wani taku d'ai d'ai tana yatsina fuska saidata harareshi sannan sannan ta fita. "I like this". ya fad'a yana wani murmushi gamida fad'awa saman kujera. A motar Abeedah da sukazo a ciki suka fita, Abeedahn ke driving sai Jauhar a front seat Maryam da Ameerah a back seat, suna d'aukar hanya suka fara tambayar Jauhar dan ALLAH waye wannan? sai santin shi suke suna ya burgesu wllhy harda Ameerah wadda gayen yayi matuk'ar tafiya da ita duk da irin gwanya mata d'in datayi. Cikin tab'e baki tace "Hmmm wlhy yaron k'anwar Mama ne yazo ya gallabeni bayajin magana wllhy ni kad'ai ke taka mashi birki dan ni bana yarda ya nunamin wani iko da Saleem yazo ma kinsan meyayi masa kuwa? Kai suka girgiza gaba d'ayansu anan tabasu labarin yadda akayi ranar dariya sukasa gaba d'aya Abeedah harda dukan sitarin motar tana fad'in "So funny, amma dai wannan gayen yasan takan tsiya wlhy amma fa very very handsome guy ne wllhy ya had'u over". "Bakiji komaiba indai Yah Abdallah ne wllhy". Nan ta shiga basu labarinshi aikuwa sukaita dariya suna fad'in wllhy yanayin actions d'inshi na burgesu daga yadda take basu labarin nashi. Har suka kusa k'arasawa hirar Abdallah suke ita Jauhar ma shiru tayi ta k'yalesu kafin daga bisani kuma su fad'a wata hirar daban. Wajen Hall d'in da ake kamun k'awar tasu suka isa, tayi parking suka fiffito suna shirin shiga cikin Hall d'in Maryam ta dafe k'irji tareda k'walalo ido ta tsaya tana kallon can gefen Hall d'in daba kowa a wajen, suma tsayawar sukayi suna mamakin abinda ya tsayar da ita d'in "Wai meye kika tsayar damu anan Maryam? mu shiga ciki mana". Abeedah tayi maganar tana kallon Maryam dan su duk hankalinsu baikai kan abinda Maryam d'in tagani ba. "Wancan ba Yah Abdallahn da muka gani a gidanku bane da kike bamu labarinshi ba". Duk kallon inda take nuna musu sukayi aikuwa idanunsu suka hango musu Abdallah d'are d'are a saman motarshi harda wani kishingid'a hankalinshi kwance kayan d'azu ne dai sai bak'in glass kawai daya b'oye k'wayar idanunshi dashi sai jefa car key d'inshi yake sama yana cafewa, gaba d'ayansu saida gabansu ya fad'i musamman Jauhar suka zaro ido suna kallonshi mutum saikace aljani yaushe yazo wajen nan kuma ya akayi yasan inda zasuzo? Durowa yayi daga kan motar ya zare abin sauraron dake mak'ale a kunnenshi ya ratayashi a wuyanshi ya k'araso inda suke tsaye cirko cirko kamar zakaru🤣 sai wani d'an banzan murmushi yake yana tsotsar baki. "Surpriiiise". ya fad'a lokacin daya k'arasa daf da Jauhar, da bak'in ciki kamar zai kasheta. Had'e rai yayi kamar bashi ke murmushi yanzu ba ya kalli Jauhar yace "Wuce mutafi gida". Sanin halinshi datayi shi wani tutsu da bore da mutum zaiyi bayi masa sukeba yasa tayi tunanin kawai bari ta bishi ta lalama yadda zai barta dan haka ta kwantar da murya a marairaice tace "Dan ALLAH Yah Abdallah kayi hak'uri I promise you bazan dad'e ba zan koma gida dan ALLAH". "Da zan barki da banyi wahalar zuwa nan ba oya let's go malama". "Please Yah Abdallah". tace kamar zatayi kuka tana karyar dakai. Hannayenshi ya zube duka cikin aljihun wandonshi ya k'ara matsawa daf da ita ya had'e rai sosai yace "Zaki wuce muje ne kokuwa sokike saina d'auke ki yanzu a gurin nan?". Ganin abinda yayiwa Ameerah d'azu yasa yanzu sukayi gum dasu ba wadda tayi k'ok'arin tanka masa karya dizgasu gaban bainar jama'a. "Naga alamun d'aukar kikeso ko". Yace yana k'ok'arin sunkuyawa tasan kad'an daga cikin aikinshi ya sungumeta yasa tayi saurin matsawa ta fara tafiya a fusace dan takaici harda k'walla. Mrs Salees Mu'az 💝 *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 2/14/22, 08:57 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* ♥️🩸♥️ *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer). *TOP TEN TAKUN HASKE BATCH A 2022* _Sa kud'i kad'an ki debi hani'an😂😍_ Writer: Oum Hanan From the writer of DR SAIF 🩸 Free page Fiction story *Na sadaukar da wannan page d'in ga duk wani masoyin book din nan wanda nasani da wanda ban saniba alkhairin ALLAH ya kai muku a duk inda kuke nagode ALLAH ya saka da alkhairi ♥️🩸♥️*. _Gaisuwa ta musamman ga kungiyata ta haske da duk wani member dake cikinta ALLAH ya barmu tare ya k'ara dank'on zumunchi Ameen👍😍🥰_ ```Sak'on gaisuwa daga Abdallah yace a sanar daku masu zaginshi da masu cewa bashida hankali duk yana nan juyowa gareku😂 yanaso yagama da Jauhar ne ya dawo kanku saikun jishi lol. Sako daga Abdallah Madugu (Modibbo).``` 10 Dariya Ja'afar yayi yace "Abu d'aya ne kawai a sameta a bata hak'uri kawai". Cikeda rainin hankali yace "Waye zai bata hak'urin?". "Waye kuwa banda kai". Ja'afar ya mayar masa da amsa. "Saidai inci ubanta dai wlhy amma bazan bata hak'uri ba taimin laifin kuma inbata hak'uri?". "To yazaka yi? haka nan zaka daure yanzu dai bari inje in fad'awa Mama". nan Ja'afar ya fita yabar Abdallah sai faman cije baki yake yana sakin k'wafa. Koda Ja'afar yaje ya fad'awa Mama abinda Jauhar tayi ranta b'ace ta nufi bedroom d'in Jauhar ta shiga bugawa amma bata bud'e ba bugun duniyar nan tayi amma Jauhar tayi shiru abinta dan tasan kan abinda ake mata bugun kuma wllhy bazata sakeshi yanzu ba saiya d'and'ana kud'arshi, Hajiya ma dataji bugun yayi yawa ta fito ta tambayi Mama abinda yake faruwa Mama ta sanar da ita itama d'in da ita akaita bugun tana faman lallab'a Jauhar kan ta bud'e duk a banza dole haka suka hak'ura suka bar k'ofar d'akin. Komawa Ja'afar yayi side d'inshi yasamu Abdallah yaja k'afafunshi ya koma kan gadon ya rufe k'afafunshi da blanket yana danne danne a waya, dariya ce sosai ta kama Ja'afar aikuwa ya shiga k'yalk'yala ta harda dafe ciki, d'agowa Abdallah yayi a fusace ya kalli Ja'afar yace "Na rantse idan natashi sainaci ubanka cikin d'akin nan Ja'afar wato dariya ma kake min ko?". "Yo taya bazan maka dariya ba da alamu dai yau nan zaka yini dan wllhy munje ba irin bugun da ba'a yiwa yarinyar nan ba tak'i bud'e k'ofar". "Haba dai?". Abdallah yace yana zaro ido "Wllhy da gaske nake maka bansan dai ya za'ayi ba amma dai yanzu ba wannan ba bari in kawo maka breakfast kayi d'an gurgu". ya k'arasa maganar cikin dariya, throw pillows dake kan bed d'in Abdallah ya rarumi d'aya ya jefa masa yana zaginshi, fita yayi yaje dinning ya had'o masa breakfast ya kawo masa kan bedside ya ajiye yana fad'in "Gashi nan". "Bani brush". Toilet Ja'afar ya shiga ya matso masa maclain a toothpaste ya kawo masa da wata roba da ruwa yayi brush d'in sannan yayi breakfast d'in. Komawa Mama ta k'arayi ta bubbuga amma Jauhar tak'i bud'ewa sosai ran Mama ya b'aci da wannan iskancin na Jauhar. Wasa wasa dai har kusan Azhar Abdallah na nan zaune, ya cika yayi famm sai faman masifa yake daga zaunen Ja'afar namasa dariya dayaga bazai iya zaman d'akin ba saiya fice ya bar masa d'akin yayi alk'awarin bazai k'ara shiga harkar taba tunda batada mutunci muguwa kawai, gobe goben nan ma zai koma Kano yabar mata gidan dan ubanta ALLAH ne ya jefo da Daddy gidan yazo d'aukar wasu file daga office anan Mama take sanar dashi abinda ke faruwa da kanshi yaje ya buga d'akin yayi magana, sai dataji maganar shi sannan ta bud'e bedroom d'in Mama tamkar zata rufeta da duka saboda fad'a Daddy ma fad'an ya shiga yimata da dalilin dayasa tayi masa haka cikin tura baki ta fad'a musu abinda yayi mata Daddy da kanshi ya tasata yace taje ta bashi hak'uri. Yana zaune har lokacin da kayan barci a jikinshi, suka shiga bedroom d'in tunda suka shiga yake hararar ta harta k'arasa bakin gadon ta tsaya Daddy ya k'araso shima yana fad'in "Ashe sai k'anwar taka tamaka tsiyar tasu My son". "Ai wllhy Daddy ko? bai cigaba ba sai k'wafa daya saki yana jijjiga kai. Murmushi Daddy yayi tareda dafa kafad'arshi yace " I'm sorry d'an gidan Daddy Jauhar tayi laifi bashi hak'uri Jauhar". Daddy yayi maganar yana kallon Jauhar dake tsaye tana faman d'add'age hanci cikin tura baki tace "Kayi hak'uri Yah Abdallah". banza yayi bai kulataba Daddy yace "Ka amsa mana Abdallah ka hak'ura?" "Saboda kai Daddy dasai nakusa targad'a yarinyar nan wllhy". ya fad'a kanshi tsaye (Kutt lallai Abdallah a gaban mahaifin yarinya kace zaka targad'a ta🤔🙄 saboda bakada man kai 😅🤣). Baki ta murgud'a masa ta juya tayi ficewarta yabita da kallo yana kad'a kai. Bayan fitar Daddy ya tashi yayi wanka ya d'aura alwalah ya fito ya canza kaya ya gabatar da sallahr Azhar dan tuni masallatai sun riga da sun idar. Tun daga nan basu k'ara had'uwa da Jauhar ba washegari yayi shirin tafiya Kano. Jauhar na zaune a falo kan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana sanye cikin riga da siket na atamfa Cote d'ivoire tayi d'aurin ture kaga tsiya😂 da waya a hannunta tana buga candy crush saga, daga upstairs ya sauko sunyi sallama da Daddy yaudai shigar manyan kaya yayi riga da wando na shadda sea green mai matuk'ar tsada sai walwali take tana d'aukar ido bai dai saka hula ba sai takalmi da agogo duk kalar shaddar yayi matuk'ar yin kyau wannan mayen turaren nashi dai na biye dashi ta bayanta ya zagayo kawai ji tayi an dungure mata kai har d'an kwalinta na fad'owa kan cinyarta da sauri ta waiga dan ganin waye duk da bata raba d'aya biyun idan ba Abdallah bane shine kad'ai zaiyi mata haka a gidan, tsaye ta ganshi a bayan kujerar ya kama k'ugunshi da hannayenshi duka biyun yana kallonta, d'an kwalinta ta d'auka ta fara k'ok'arin d'aurawa tana tura baki tace "Dan ALLAH meye haka Yah Abdallah?". "Ture kaga tsiya naga kinyi shine na ture inga tsiyar taki". K'aramin tsaki taja cikin ranta tace Banida lokacinka ni ayi mutum ace bashida aiki sai jan masifa ALLAH yayi mata maganin mutumin nan. Yana shirin k'ara yin wata maganar Mama ta fito Ja'afar ma ya shigo janye da trolley d'in Abdallah, farin cikine ya kama Jauhar sosai dan ita sam batasan yau zai tafiba to umma ta gaida assha ALLAH raka taki gona, Hajiya ce ta fito falon itama ta zauna Abdallah ya kalleta yace "Hajjaju zan wuce saina k'ara kewayowa kuma zanyi missing d'inku wllhy musamman ke Hajiya". "Kasha zamanka dan ALLAH ka dinga kiran waya ana gaisawa kawai nikam bawani mussun d'inka da zanyi". "ALLAH Hajiya? anya bazan fasa tafiyar nan ba". "Ka fasa kuma?". Jauhar ta fad'a da sauri tana zaro ido waje. "Nasa dake ne malama?". yace yana hararar ta, baki ta tab'e tana yatsina fuska ta maida kanta kan wayarta Hajiya kam cewa tayi "A'a Modibbo kaje kawai ALLAH ya kiyaye hanya yabada ladar zumunchi". daga jin yadda tayi maganar kasan kora da haline take masa 🤣. Dariya Ja'afar da Mama suka sa shikuma gogan ya wani tab'e baki yana d'age kafad'a yayi hanyar fita daga falon Hajiya da Jauhar suka rakashi da murmushin farin ciki, kai Abdallah case ne yasin 😂 kazo gidan mutane ka addabesu yaudai Jauhar ranta fari k'al Hajiya ma na tayata murna wannan jaraba har ina. Har bakin motarshi sukayi masa rakiya Mama tace sai biki idan ALLAH yakai rai amma Jauhar da Jauhar zasu fara tahowa kafin bikin, back seat Ja'afar ya bud'e yasa masa trolley d'inshi yabashi hannu sukayi musabaha sannan ya shiga motar ya tayar yabar gidan suna d'agawa juna hannu duk sai Ja'afar yaji ba dad'i abokin fad'an nashi ya tafi dan Abdallah ba wanda ya ragawa gashi dai bak'unta yazo amma duk sai daya addabi y'an gidan 😃 Ja'afar d'inma ba tsira yayi ba to yau dai Kano ta d'auka za kuma a komawa Janan dasu Hassana. Sauka lafiya Abdallah Madugu 🤩. ^√^√^√^√^√^ KANO. Babu wadda gabanta bai fad'i ba cikinsu Janan lokacin daya dawo dama duk suna zaune a falo ya shigo dan haka al'adar gidan take ana yawan zama a falo ayi hira harda Ammi da Abbie aji matsalar kowa ayi wasa da dariya, a d'arare suka yimasa sannu da zuwa da d'ai d'ai da d'ai d'ai kowacce ta samfe daga falon dan karma sutafi lokaci d'aya yace kamar sunga wani dodo dayake hankalinshi ma nakan Ammi suna gaisawa da tambayar yadda yabaro su Mama yasa baima lura da fitarsu ba. Anata shirye shiryen bikin Yah Ameen su Abdallah sune kan gaba a komai yaso ya wakiltashi ma shida Habeeb suje su tattauna da y'an mata k'awayen amarya kan events d'in dazasu gabatar da tsare tsarensu da kud'in da za'a basu Yah Ameen yace sam 🤣 Abdallah bazai jeba yaje ya kwanto masa ruwa dan kad'an daga aikinshi idan sukayi abinda bai gamsheshi ba ya k'ukk'urma musu zagi 😅 abokanshi na jiki sosai Sameer da Miftahu su sukaje suka zauna da k'awayen Fareedah sukayi tsare tsaren bikin. Ana sauran kwana biyar bikin Ja'afar da Jauhar sukazo Kano saboda wani aiki dazai kawo Ja'afar d'in lokacin sai Mama tace kawai sutaho da Jauhar itakuma sai ana gobe d'aurin aure sannan zata taho. Janan tayi murna k'warai da ganin y'ar uwarta suka rungume juna cikeda farin ciki sunyi missing d'in juna sosai su Hassana ma sunyi murnar ganinta nan fa suka zauna aka shiga chapter dariyarsu kawai kakeji da shewarsu Janan dai yawanci saidai tayi murmushi kawai idan abu yabata dariya saboda ita sam batada hayaniya kuma batada surutu kamar sauran. Duk yinin ranar datayi a gidan bataga Abdallah ba ita hakan ma saiyafi yimata dad'i dan tasan indai suka had'u tofa sai ansamu abinda zai had'asu. Koda dare ma da za'ayi dinner badashi akayi ba wai sun fita shida Habeeb da Ja'afar. A ranar da daddare sukayi waya da Abeedah itama ta shigo Kano bikin wata cousin d'inta tana gayyatar ta nan tayi mata alk'awarin insha ALLAHU zatazo ta fad'a mata address d'in gidan sukayi sallama. Washegari ita kad'ai aka bari a gidan daga ita sai Ammi su Janan duk sun tafi school, bayan ta tashi barci tayi wanka ta shirya cikin jallabiyyah k'irar Turkish red colour mai adon duwatsu masu k'yalli a gaban rigar ta yafa mayafin rigar ta zura bak'in plat shoe ta fito bayan ta fesa turare. Mrs Salees Mu'az 💝 Maryam Ibraheem _😳😳 KIN SIYE 'YAR UWA?, KINA DA TANADINKI AHANNU?, KINA SO?, ZAKI KI KOYA?, SHIN KE CIKAKKIYAR MACECE? IDAN AMSARKI ITACE *EHHH..😅* 'YAR UWA INA YIMAKI SAMBARKA, I DAN KUMA AMSAR ITACE *A'A😥* TO MAZA KI HANZARTA KIYI REGISTER DA👇_ *TOP 10, TAKUN HASKE, BATCH A, INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI, 1-ZO GARENI NA HAJJACE, 2-IBTISAM NA AYUSHA MOH'D, 3-WASU MAZAN NA BILLY S FARI, 4-AZAAD JUNAID NA JEEDDAH ALIYU, 5-WATA SOYAYYAR NA OUM HANAN, 6-NI DA RAHEEMAH NA ASMY B ALIYU, 7-KUKAN ZUCIYA NA SLIMZY,💃💃💃KAI KA KAI....!😱TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N500 KACAL, GA KUMA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU DA KUKA ZABEMU, 1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍DAGA CHIEF DEEJARH BARVER, 2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI HA'DA MAGUNGUNAN NI'IMA DANA KARIYA DAGA CUTAR INFECTION DA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA DAGA MAMAN KHADIJA, 3-SHIRIN KOYOR DA TSAFTA, GYARAN JIKI, GYARAN GIDA, SAMUN WARAKA DAGA MATSALTSALUN JINI DA SAURANSU DOMIN ZAMOWA FITILAR GIDANKI DAGA UMMI A'ISHA* _WOHOHOOO..DUKA FA AKAN NAIRARKI 'DARI BIYAR KACAL ZAKI MALLAKI REGISTER  A *TOP 10, TAKUN HASKE BATCH A* SAI KIGA KIN ZAMA QASAITATTAR MACE, ISASHSHIYA KUMA ZINARIYA AWAJEN MIJINKI!_ _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N500)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_ 2083371244 ZENITH BANK AISHA M. SALIS SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼 +447894142004 IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA WANNAN LAMBAR👇🏼 07043079282 SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼 07065283730    _GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU 550F TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_ +227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey. MUN GODE. 2/14/22, 08:57 - Ummi Tandama😇: 11. ^√^√^√^√^ Dinning table taje tayi breakfast ta taso kenan Ammi ta shigo falon inda take taje ta gaisheta kafin ta fara kame kamen tambayar unguwar datake so tayi hakan da Ammi tagani ne yasa tace "Yadai Jauhar me kikeson tambaya ne kiketa faman kwana kwana?". "Wllhy Ammi wata k'awata ce itama jiya ta shigo Kano bikin cousin d'inta shine ta gayyaceni dama kuma tun a KD ta fad'amin shine nakeso inje". "Jauhar nifa banason wannan yawace yawacen kosu Janan dakike gani ba inda suke zuwa daga school saikuma idan fita ta kama dole". A marairaice tace "Dan ALLAH Ammi ki barni please ALLAH ko magreebah bazan kaiba dan ALLAH". Shiru Ammi ta d'anyi kafin tacee "Toh naji amma kifara zuwa ki tambayi Modibbo naga shine yake a gida idan yabarki sai kije". "Kai Ammi dole saina tambayeshi?". ta fad'a a shagwab'e tana b'ata fuska. "Eh, haka tsarin gidan yake y'an uwanki ma haka suke idan Daddy yana gida a tambayeshi idan kuma baya nan toga wakilanshi nan Ameen ko Modibbo dan haka indai kinason zuwa to kije ki tambayeshi tunda Ameen baya nan". Baki ta tura ta tashi ta gyara gyalen jallabiyyahr jikinta ta zura takalminta ta fita daga falon dan dole zata tambayeshi wllhy kawai dan tanason zuwa ne amma ita harga ALLAH batason su had'u ma so tayi har a gama biki su tafi bata ganshi ba. Side d'insu shida Yah Ameen ta nufa k'ofar Yah Ameen a kulle tashi kuma a bud'e take saidai an d'an karota kad'an, saidata harari k'ofar kafin ta tura ta shiga bakinta d'auke da sallama can ta hangoshi zaune a tsakiyar doguwar kujera ya d'ora wata k'atuwar farar paper akan k'aramin table d'in dake gabanshi sai pen da color kaloli daban daban masu yawa cikin wani farin abu dogo kamar cup na roba, duk wani hankali da nutsuwar shi ya maidasu kan zanen dayake, yana sanye da 3 quarter bak'i da farar riga mai hula marar hannu green color yasa hular a kanshi saidai ya d'anyi baya da ita kad'an wanda hakan ya bayyanar da kyakkyawar tattausar sumarshi daga gaba, sai data k'are masa kallo sosai yadda ya nutsu idan ka ganshi a haka zakayi zaton ko d'an yatsa akasa masa a baki bazai ciza ba nan kuwa sai tsabar rashin ji da d'aukar magana tamkar wani k'aramin yaro. A hankali ta taka ta isa kujerar dake gefenshi ta zauna bai waigo ya kalleta ba kamar ma baisan an shigo falon ba zanen dayake kawai ne a gabanshi, baki ta d'an tab'e kafin tace "Yah Abdallah Ammi ce tace inzo in tambayeka zan fita idan ka yarda". Baice uffan ba bai kuma juyo ya kalleta ba yadai d'ago kanshi ya k'urawa zanen dayayi kan takardar gabanshi ido ya d'ora pen d'in akan lips d'inshi. "Kaji Yah Abdallah". ta k'ara fad'a tana kallonshi da alamu yau y'an mulkin ne a kanshi, bayanshi ya kwantar a bayan kujerar dayake zaune ya shiga girgiza k'afa kamar bazai tanka bama yanzun saikuma yace "Bazaki jeba Jauhar". "Dan ALLAH Yah Abdallah". ta fad'a da siyar shagwab'a kamar zatayi kuka. Ido ya bud'e mata sosai yace "Nace bazakiba wai dan ubanki ke amarar inace dabaki da aiki sai zuwa biki to bazaki jeba get out of my room". Tana shirin k'ara yin wata maganar yayi mata wani kallon dayasa dolenta ta had'iye abinda tayi niyyar fad'a, a fusace ta mik'e tsaye tana huhhura hanci kamar wadda zata d'auki wani mataki a kanshi, kai ya d'age yana kallonta kafin yace "Zaki dakeni ne?". Tsaki kawai taja a hankali ta fice daga falon nashi da sauri kafin ya yunk'uro yaci k'aniyarta, da kallo ya bita yana girgiza k'afafunshi har yanzu kan yarinyar nan rawa yake ya kamata ya saita ta bai saniba ko shiga harkarta da yake ne yasa ta rainashi haka k'wafa yayi sannan ya taso ya cigaba da duba art d'in d'inshi ko zaiga wani gyaran. A bakin k'ofar falon ta tsaya tana shirya k'aryar dazata yiwa Ammi dan dole saitaje bikin nan fa abu d'aya zatayi tacewa Ammi yabarta zuwan to idan kuma Ammin ta tambayeshi fa? wani sashen na zuciyarta ya tambayeta, kai ba lallai bane ta tambaya hakan kawai zatayi dan haka ta nufi falon su Ammi ta canza fuskarta daga b'acin rai zuwa murna, da murnar ta ta shiga falon kamar gaske tasamu Ammi anan inda ta barta kusa da ita ta zauna tace "Ammi ya barni zuwa amma yace indawo da wuri". sam Ammi bata kawo k'arya take mata ba tace "To barkan ki kinci sa'a indai Modibbo ne ba k'aunar fita yakeba haka su Hassana ke fama dashi dama Janan wannan fice ficen bai dameta ba, saiki tashi kije ki shirya". "Yanzu kuwa Ammi". ta fad'a da sauri tareda barin falon ta shige bedroom d'in su Hassana inda kayanta suke, dama a shiryen ta take tsaf dan haka bata buk'atar wani shirin saidai kaya dazata canza. Wani dakakken lace tasa lemon green rigar bubu ce tayi mata kyau sosai d'aurinta data saba tayi, ta yafa k'aramin gyale kalar lace d'in a gefen kafad'arta agogo da d'an kunne duk lemon green ne sai bak'in takalmi mai d'an tudu datasa da k'aramar jaka itama black color sai datayi selfie kala kala sannan ta fito tana zuba k'amshi, bata samu Ammi a falon ba dan haka ta bita bedroom tayi mata sallama ta fito bayan Ammi taja mata kunne kar takai dare, ALLAH ALLAH take tabar gidan dan haka komai cikin hanzari tayi shi ta shiga wata mota da Ammi tabata key d'in taja tabar gidan. ^√^√^√^√^ Daf da magreebah tadawo gidan tana shigowa harabar gidan a motar shima Abdallah ya kunno hancin motar shi gidan, Ido ta runtse cikeda fad'uwar gaba tayi saurin yin parking ta fito daga motar ta d'auki bag d'inta ta nufi ciki da saurinta, shima parking din yayi ya fito yana kallon Jauhar datake ta uban sauri dan tsakanin parking lot d'in da k'ofar da mutum zai shiga general parlor d'in gidan akwai y'ar tazara, bai tsaya ya d'auki babbar jakar dake back seat ba wadda kayan daya karb'o daga wajen tailor ke ciki ba na biki yabi bayanta yadda take sauri haka shima yake saurin kasancewar shi namiji kuma mai cikakkiyar lafiya yasa ya cimmata tana daf da isa k'ofar falon sai gani tayi yasha gabanta yayi mata tsaye aka ya rik'e k'ugunshi da hannayenshi duka yana kallonta, kana ganinta kaga marar gaskiya saboda yadda take wuri wuri da zare ido. "Wato danace kar kije saida kikaje ko? ke wai ba'a fad'a miki magana kiji ne?". "Ahmm.... Yah Abdallah bafa Jauhar bace". tace cikin in ina da sanyin murya irin na Janan d'in tana k'ara yin k'asa da kanta. Tsayuwar shi ya k'ara gyarawa yana shafa sajen fuskarshi yace "Who?". Gefen wuyanta ta shiga sosawa a hankali tace "Uhmm.... Janan ce fa". "Okeyyyy Janan ko?". yace yana murmushi yana wani jijjiga kanshi. Kai kawai ta d'aga cikin ranta tana addu'ar ALLAH yasa yace ta wuce ta tafi gabanta sai fad'uwa yake. Dariya kawai taga ya shiga yi cikin dariyar yake fad'in "Bakida hankali yarinya wato a zatonki bana bambance tsakaninki da Janan ne? bari kiji to in fad'a miki abinda baki saniba koda kikeji mutane na cewa basu ganeku to nibana cikinsu tun kuna jariranku nake ganeku bare yanzu da halayyarku tasha bambam keda y'ar uwarki tafiki hankali da nutsuwa da jin magana ko lokacin da kuke zanin goyo Mama saita duba shaidar jikinku take ganewa amma ni kallo d'aya zanyi muku in tantanceku dan haka muje garden ki fad'amin dalilin dayasa na hanaki fita kika fita dan ubanki". Kamar zatayi kuka tace "Da gaske nefa Yah Abdal......."Zaki wuce muje ne kokuwa?". yace yana d'an d'age rigarshi yafara k'ok'arin kwance belt d'in dake d'aure a k'ugunshi. Da sauri tayi gaba yabi bayanta kamar makaho da d'an jagora data d'an waigo saitaga hannayenshi akan belt d'in da haka har suka k'arasa inda garden d'in yake suna shiga ya nemi kujera ya zauna ya d'ora d'aya kan d'aya yace ta masa frog jump tsaye tayi tana kallonshi alamar abinda yace bai gamsheta ba. "Bazakiyi bane?". ya fad'a yana k'ok'arin mik'ewa tsaye. "Zanyi fa Yah Abdallah". tace da sauri tana ajiye bag da key d'in motar kan grass carpet d'in dake ko ina a cikin garden d'in. Haka tanaji tana gani ta tattare rigarta ta fara frog jump d'in kamar tafasa ihu haka take ji shikam yana kame kan kujera yafara latse latsen waya yana murmushi. Lokacin da suke k'ok'arin shiga garden d'in shikuma a lokacin Yah Ameen ya shigo compound d'in yana yin parking kuwa daya fito ya nufo garden d'in dan yasan bai wuce wata muguntar Abdallahn zaiyi ba shi duk zatonshi ma Janan ce, farin cikine ya kamata lokacin dataga Yah Ameen ya shigo tasan zai k'waceta a hannun wannan mugun shi sam baima ga Yah Ameen d'in ba dayake ya juya masa baya ne sai maganar shi yaji yace "Meye haka Abdallah? ya zakazo kasa yarinya tsallen kwad'o metayi maka?". Waigowa yayi ya kalli Yah Ameen ta bayanshi yace "K'yaleni kawai in casata Bros bakasan me tayi min ba". Hararar shi Ameen yayi yace "Kaji tsoron ALLAH wllhy Abdallah kowa yasan Janan batada hayaniya magana ma ba damunta tayi ba amma saboda zalunci saida kasan yadda kayi ka k'ak'aba mata wani laifin ko". "Bros bafa Janan bace wllhy". "Karka rainamin hankali mana Malam". Ameen ya fad'a yana d'an hararar Abdallah. "Wllhy Bros ba Janan bace Jauhar cefa ka tab'a ganin nasa Janan haka?". "Idan muguntarka ta motsa uban waye baka yiwa? yanzu ita wannan daga zuwa biki kuma metayi maka?". Juyawa yayi yana kallon Jauhar data daina tsallen kwad'on take kallonsu sun d'anyi nesa da ita bama ta jin abinda suke fad'a saida ya harareta sannan yace "Ammi ce tace tazo ta tambayeni zata fita unguwa shine nikuma na hanata ashe k'arya taje tayiwa Ammi tace na barta ta fita shinefa sai yanzu tadawo". Jauhar Yah Ameen ya yafito da hannunshi alamun tazo yana fad'in "To ayi hak'uri dai tsallen kwad'o saikace wasu maza, kekuma karki k'ara irin haka Jauhar kinji ko". ya k'arasa maganar yana kallon Jauhar data k'araso wajen, kai ta d'aga masa murmushi yayi yace ta taho su shiga cikin gida inda ta baro ta koma ta d'auko jakarta da key d'in mota tazo suka nufo hanyar fitowa daga garden d'in basu bi takan Abdallah ba daya k'ara kishingid'a kan kujerar har lokacin da waya a hannunshi. M&S💝 2/14/22, 08:58 - Ummi Tandama😇: 12. ^√^√^√^√^√^? Anci gaba da gudanar da shirye shiryen biki tun daga ranar kuma Jauhar bata k'ara saka Abdallah a idanunta ba dan bai cika zaman gidan bama. Ana gobe kamu ranar laraba kenan duk suna zaune a falo harda Ammi maganar bikin ake tayi ana k'ara shirya yadda zai tafi Hassana ta kalli Ammi tace "Ammi munyi waya da Mubarak d'azu yace ya kammala d'inkunan aje a karb'a". "Toh ai saikuje ku karb'o d'in ko keda Jauhar ne, je d'akin Modibbo idan yana nan kice idan ya tashi fita yazo". Ammi tayi maganar tana kallon Jauhar dake kwance tana danne dannen waya. Zaune ta tashi tana lalubar gyalen kanta daya zame kan kujerar ta d'auka ta mik'e tsaye ta yafashi kan long skirt d'in dake jikinta black color da body hook mai dogayen hannu red colour ta zura plat shoe takalminta dake gaban kujerar black ta fita daga falon zuwa aiken Ammi. A kulle tasamu k'ofar falon nashi saidata dad'e tana knocking ba'a amsa mata ba dan haka kawai ta murd'a handle d'in k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama ta duba tagani ko yana nan dan duk zatonta baya nan turus tayi hangoshi datayi kan kujera yayi relaxing sosai akan kujerar dayake ya d'ora k'afafunshi kan center table daya janyoshi kusa da k'afafun nashi k'aramar paper ce da pen a hannunshi batasan tsiyar dai dayake zanawa ba. "Lallai gayen nan yaci uwar rainin hankali wllhy shine dan wulak'anci yanaji tana knocking yayi bakam dashi kamar bayaji dan tsabar wulak'anci? takawa ta shiga yi zuwa inda yake tana wani yatsina fuska jin alamun an shigo yasa ya tashi ya zauna sosai kan kujerar yana kallon Jauhar data tsaya kusa da wata kujera d'an nesa dashi ta dafa bayan kujerar, k'aramin tsaki taja cikin zuciyarta ganin irin shigar dayayi milk wandone a jikinshi wanda da kad'an ya wuce cinyarshi gashi ya d'ameshi sai light ash color d'in riga mai k'aramin hannu shara shara baifi mab'allai biyu ne suke a b'alle ba daga k'asa sauran duk bai b'alle suba hakan ya bayyana faffad'an k'irjinshi mai cike da yalwar kwantaccen gashi bak'i sid'ik sai P cap daya d'ora wadda ta zame masa kamar ibadah, dubeshi dan ALLAH sam ba tsari wannan shigar tashi duk ya wani bayyanar da surorin jiki, cikin zuciyarta tayi maganar tana k'ara jan wani tsakin gamida juyar da kanta gefe tana tab'e baki. Rai had'e yake kallonta yana k'ara tsare gida yace "Meya kawoki nan?". Tana daga tsayen tace "Ammi ta aikoni tace idan katashi fita ka biya ta cikin gida". Sai daya cije baki yana wani k'ank'ance ido kafin yace "Ke bakida tarbiyya ko? dan uwarki haka akewa manya magana kinzo kin min tsaye akai tsabar bakida ladabi ko". Wata shegiyar dariya tasaka ta rainin hankali harda d'an tafa hannayenta tace "Wai manya, suwaye manyan?. dariyar ta k'ara saki ta cigaba da fad'in "Amma dai an cuci manya wllhy kabar manya irinsu Yah Ameen masu rik'e girmansu suyi magana amma ba kai....... yunk'urowar dayayi a fusace yana cije lips yasa ta dakata da abinda tayi niyyar fad'a ta juya ta fice da gudu tana dariya, k'wafa kawai yayi ya koma ya zauna yau bai cikin mood d'in hayaniya da har gaban Ammi saiya bita yaci ubanta mara kunyar yarinya kawai". Tana komawa falon Ammi tace Jauhar da Hassana suje su shirya sai subi Modibbo ya saukesu shagon tailor d'in dake musu d'inkuna zasu karb'o d'inkunan su na biki saboda driver baya nan ta aikeshi kasuwa. Tunda Hassana taji da wanda aka had'asu tafiya ta shiga bedroom ta fara shiryawa kafin yazo ya tashi hankalin kowa na gidan itakam Jauhar koda ta shiga bedroom d'in saitayi zamanta tana cigaba da buga game d'inta da Janan ma tace mata bataji Ammi tace zasu fita da Yah Abdallah ba kuma ta zauna bata gyara ba banza tayi mata ta cigaba da abinda take yi. Mayen k'amshin turarenshi ne mai bala'in dad'in k'amshi da sanyaya zuciya ya fara yiwa falon sallama kafin mamallakin turaren ya biyo baya bakinshi d'auke da sallama, sanye yake cikin bak'in wando da red shirt mai dogon hannu sai black falmaran daya d'ora akai daga kan takalmin k'afarshi zuwa agogon hannunshi duk black color ne sai dark space daya toshe idanunshi dashi sumar kanshi tasha gyara sai k'yalli take simple dress ne amma sai fitinannen kyau dayayi mara misaltuwa. Yana shigowa falon itakuma Ammi ta sauko downstairs d'in kusa da ita ya k'arasa yana fad'in "My sweet Mommah ance kina nemana". "Eh, zaka fita dasu Jauhar ne ka saukesu wajen Mubarak zasu amso mana d'inkunan mu na aiki driver ne kuma bai dawoba har yanzu". "Toh Ammi ina jiransu suyi sauri dan ALLAH nima ina saurine". "Gasu nan zuwa". Ammi ta amsa masa tana kallon Hussaina data kawo kai cikin falon tareda fad'in taje ta kirawo su Jauhar d'in yayin da shikuma ya juya ya fita daga falon. Motar dazai fita da ita ya bud'e ya shiga ya zauna yana jiransu, wucewar y'an mintuna basu fitoba hakan ya hasala shi ya tsani jira a rayuwar shi badan Ammi ce ta tsayar dashiba da zaiyi tafiyarshi ne kawai, wani uban horn yafara saki mai shegen k'ara wanda duk saidaya rud'a mutanen gidan da gudu Hassana ta fito compound d'in jikinta sai rawa yake ta bud'e motar ta shiga a fusace yace "Ina yarinyar nan kuma?". cikin rawar murya tace "Gata nan yanzu zata fito". "Dan ubanku da kunsan baku shiryaba kukasa aka tsayar dani". Itadai Hassana shiru tayi kanta a k'asa ita bataga abin tada jijiyar wuya ba anan ALLAH dai ya kyautawa halin Yah Abdallah. Sai data gama shirinta tsaf cikin doguwar rigar atamfa kalar bak'i da milk ta yafa black vail k'arami tasa bak'in takalmi plat ta fita, takaici ne ya kama Abdallah ganin yadda Jauhar ke tafiya hankalinta kwance tana wani taku d'ai d'ai wato shi ta tsaidashi k'wafa kawai yayi yana cije baki. Tana zuwa ta bud'e back seat inda Hassana take ta shiga ta zauna, a fusace Abdallah ya juyo yace "Uban waye drivern ku anan?". Baki Jauhar ta tab'e ta juyar dakai ba inda zata fita saidai yayi haukan nashi yagama saidai Hassana ta koma front seat d'in. Hannu Hassana tasa ta zunguro Jauhar ta juyo tana kallonta da Ido Hassana tayi mata alamun takoma front seat d'in tana marairaice fuska, kamar zata shareta saikuma ta bud'e ta fita ta koma gaban. tsaki yasaki kafin ya tada motar suka bar gidan. Tunda suka tafi ba wanda yayi magana shi ya maida hankalinshi kan driving Jauhar kam latse latsen waya take ta faman yi, a haka dai har zuwa lokacin daya saukesu a shagon ya k'ara gaba. Bayan sun karb'a suka shiga tricycle zuwa gidan Aunt Deejah dan kaimata nata d'inkunan dama wajen d'inkin su d'aya sai yamma suka bar gidan. ^√^√^√^√√^√^ Ranar alhamis kamu bayan la'asar su Jauhar suka fito zasu tafi inda ake kamun y'an matan ne kawai su manyan sunyi gaba tana tsaye bakin motar itada Hussaina suna jiran Janan da Hassana su fito su wuce, doguwar rigar atamfa ce a jikinta orange color da fari sai bak'i da aka d'an ratsa kad'an kanta ba d'ankwali sai rolling datayi da bak'in gyale k'arami takalmin k'afarta hill ne sosai mai igiya rigar ta d'ameta sosai daga sama k'asan kuma shima ya bud'e sosai tayi kyau sosai cikin shigar. Kiran daya shigo wayarta ne yasa ta maida kanta kan wayar dan ganin waye, baki ta tab'e ganin kowaye gefe d'aya na zuciyarta na tunanin abinda yasa ya kirata kamar bazatayi picking ba saikuma tayi ta kara wayar a kunnenta sarai tasan waye amma tayi kamar bata ganeba tana d'agawa tace "Wake magana?". "Ubanki ne, wannan dressing d'in naki baiyiba kije ki canza wani". Ikon ALLAH wannan isa dayawa take, d'agowa tayi ta shiga wuwwurga idanu ko zata hango wannan sarkin y'an k'ok'arin saidai bashi ba alamun shi ko mai kama dashi babu hasalima ba namiji ko d'aya cikin compound d'in daga maigadi sai mai bawa flowers ruwa ko daga ina yake hangota oho masa. Cikeda rainin hankali tace "Wai waye ne nifa ban ganeba kayimin bayanin kanka". "Bayanina bazai miki dad'i ba Jauhar idan kuma so kike in fito zan fito d'in amma ki shirya zuwana kinsan halina sarai basai anbaki labari ba, kije ki canza tun kafin aji kanmu dake". tana shirin magana taji k'itt ya kashe wayar. Tsaki tasaki tana kallon Hussaina data tsura mata ido tana kallonta. "Ya akayi ne sis?". Hussaina ta tambayeta. "Hmm kibari kawai nida wannan isasshen mana kinji wai dress d'ina baiyiba inje in canza wani ko ina ruwanshi da shigata oho". "To kije ki canza d'in mana Jauhar hanyar lafiya abita da shekara fa". "Ba inda zanje bazan canza kayan ba, Ina ruwanshi dani to tsabar neman bala'i irin nashi". cikin jin haushi tayi maganar harare harare kamar mai laifin yana wajen ne. "Na had'aki da ALLAH kije ki canza d'in yadda yace Jauhar ALLAH har yanzu bakiyiwa Yah Abdallah cikakken sani ba muda muke zaune dashi mu mukasan halin bawan ALLAHn nan please". Ta bud'e baki zatayi magana kenan wani kiran ya k'ara shigowa tana shirin yanke kiran Hussaina tayi mata alamu da ido ta d'aga k'aramin tsaki taja tayi picking tareda kai wayar kunnenta. "Jauhar! kinaso in b'ata kwalliyar nan taki ko? bai bari tayi magana ba ya cigaba da fad'in karki kuskura inzo in sameki wajen bar ganin ina lallab'aki idan kika bari nafito uwarki zanci wllhy kibari kuma inzo in sameki anan, zakije ne kokuwa in fito?". Kamar saki kuka dan haushi tace "Zanje". saidaya saki wata dariya kafin yace "Good girl kin taimakawa kanki". daga haka ya yanke kiran. Tsabar takaici jitake tamkar ta had'iyi zuciya ta mutu, a fusace ta nufi k'ofar falon taje zata shiga kenan Janan da Hassana sukuma sunzo fitowa suka had'u a bak'in k'ofar falon ba wanda ta kula tayi shigewarta ciki suka bita da kallo. M&S💝 2/14/22, 08:58 - Ummi Tandama😇: 13. Kallo suka bita dashi gaba d'ayansu Hassana tace "Ikon ALLAH ga wata y'ar uwar Yah Abdallah mai almatsutsai k'alau fa naga ta fito da fara'arta". "Dama ai tafiyarsu d'aya dashi ai". Janan ta fad'a tana murmushi gamida kama hannun Hassana suka fice daga falon. Saida sukaje wajen motar ne suke tambayar meya faru da Jauhar sunga ta shiga gida a fusace anan Hussaina ke sanar dasu wayar da Yah Abdallah yayi mata yace saita canza dressing d'inta na jikinta baiyiba, dukansu saida sukayi mamaki ko ina ruwanshi da shigar datayi koda yake ba abin mamaki bane indai Yah Abdallah ne idan yaso neman rigimarshi ko mutum bai shiga sabgarshi ba toshi zaisan yadda yayi ya shiga ta mutum ALLAH dai ya shirya musu wannan yayan nasu. Haka dole ta canza shigar tata tasa riga da siket na atamfa ruwan toka da touch d'in bak'i da fari ta yane kanta da gyale mai d'an girma ruwan toka shima, tana faman zumb'ure²n baki ta fito ta samesu har sun shisshiga motar Janan da Hussaina a back seat sai Hassana a front seat dama ita zatayi driving d'insu dan duk tafisu iyawa saboda tafisu rawar kai har gara Hassana ma akan Janan da Hussaina, tana shirin shiga motar wayarta tayi k'ara batare data duba mai kiran ba tayi picking ta kaita kunnenta lokacin data k'arasa shiga motar ta zauna kan kujerar. "Perfect! shigar tayi". taji an fad'a daga d'aya b'angaren, sai lokacin ta ciro wayar taga number data kirata tsaki kawai tasaki tareda katse wayar ta d'orata kan cinyar Hassana tayiwa motar key sukabar gidan sai faman k'ink'uni take. Sai bayan magreebah suka dawo gidan. ^√^√^√^√^√^√^ Washegari juma'a ranar za'a gabatar da dinner tun safe gidan yafara d'aukar bak'i na nesa dana kusa Momy Maryam ma ta k'araso itada nata yaran Abdallah da Hannah sai Aunt Zakiyyah da Aunt Hameedah ita Aunt Kulthum bata samu zuwa ba saboda tsohon ciki datake d'auke dashi. Hakama Mama ta k'araso itada Aunt Zaleehah babbar yayar su Jauhar da mai binta Aunt Fatee sai sauran mazan daza suzo ranar asabar wato ranar d'aurin aure. Tunda suka k'araso gidan ya k'ara kacamewa Abdallah Madugu da Abdallahn Momy Maryam dama bayan y'an uwantakar abokai ne sosai jininsu yayi bala'in had'uwa shima d'an warai ne irin Abdallah Madugu yanada wasa da dariya kuma shi idan bawai ka shiga harkarshi ba ba ruwanshi dakai sab'anin Abdallah d'an neman fitina da abokin fad'a ga tsokana. Su hud'u ne a falon Abdallahn Ja'afar sai H.U Marafa wato babban aminin Abdallah saikuma shi Madugu uban tafiyar sai Abdallahn Momy Maryam gaba d'aya sun hargitsa falon da plate plate na abinci da sukaci da cups da suka sha ruwa da lemuka sun baje sai hira suke kafin ka shigo falon zakayi zaton sunkai kusan su goma a ciki saboda yadda hayaniya ta cika ko ina Ja'afar nema mai d'an sauk'i a cikinsu danshi bai cika hayaniya ba sosai. Bayan magreebah aka fara tafiya hall d'in da za'ayi dinner dama iya ta y'anmata da samari ce dinner ko ina ka waiga a cikin gidan y'an uwa ne maza da mata y'an matan su da samarinsu kowa yaci ado mai k'ayatarwa sai walwali suke suna haskawa, Janan, Jauhar, Hassana, Hussaina da Hannah shigarsu iri d'ayace wani had'add'en material ne mai tsada dark peach color da adon tsalli tsallin flowers green color Ammi ta d'auki nauyin siyanshi da d'inkinshi gaba d'ayansu d'inki iri d'aya akayi musu riga da siket sai head d'in kansu da akayi musu d'auri green kowacce tasha makeup masu ra'ayin heavy makeup anyi musu hakama wad'anda light sukeso duk ayi musu sunyi kyau sosai sai selfie suke kashewa yayin da k'amshi ke tashi duk ta inda suka gifta. Can part d'insu Ameen ma haka yana d'akinshi da abokanshi suna shiryawa shima Abdallah yana nashi d'akin shida Habeeb da Ja'afar da Abdallahn Momy Maryam sai wasu y'an uwa da ba za'a rasaba da suke d'akin, had'add'un shaddoji kuma tsadaddu kawai kake gani a d'akin kowa da yanayin shigarshi wadda ta dace dashi, Abdallah wata bugaggiyar shaddace a jikinshi rantsattsiya sai k'yalli take zubawa da d'aukar ido maroon color daya ciza sosai kasancewar shi fari yasa kalar ta haskashi sosai anyi masa d'inki irin na zamani daidai jikinshi harda babbar riga k'arama irinta samarin zamani da akeyi yanzu ya murza hula zanna bukar data hau da shaddar sosai hatta links d'in dayayi amfani dashi ya shiga da kalar shaddar sai bak'in takalmi halfcover da bak'in agogon fata daya haska farin hannunshi mai cikeda gargasa, madarar kyau dai yayita a wannan lokaci sai k'amshin Arabian perfumes ke tashi a jikinshi duk da suma sauran ba bayaba wajen kyawun da sukayi saida suka shiga yana kyawun da Abdallah yayi shi d'in na daban ne a cikinsu. ^√^√^√^√^√^ Taheer guest palace. Hall d'in wajen aka kama inda yasha adon decorations masu kyau da d'aukar ido da k'ananun fitilu da aka mammak'ala jikin fulawoyi da suke bada haske kala kala red, green, purple da sauran kaloli masu kyau da ban sha'awa gurin ya k'ayatu matuk'a. Cike wajen yake wanda ya had'a wayayyun y'an mata da samari y'an boko kowa kagani yaci ado na kece raini kowa yanason nuna shi wanine a wajen. Ango da amarya suna zaune a inda aka tanadar musu inda akafi k'ayatawa amarya tasha kyau harta gaji cikin bride gown white color shima Yah Ameen d'in shigar farar shadda yayi sai murmushi yake faman saki bakin sam yak'i rufuwa. Babban abokin ango Sameer shi aka kirawo ya bada d'an tak'aitaccen tarihin ango da turanci sai babbar aminiyar amarya Nusaiba da itama tazo ta bada tarihin amarya a tak'aice, daga nan aka shiga gabatar da abinda ya tara mutane a wajen, tuni wajen ya hargitse saboda music d'in da aka saki aka fara gwangwajewa. A.B Madugu, H.U Marafa, J.I Turaki da kuma A.A Zakeer su kad'ai aka bawa filin cashewa nan fa suka fara kwasar rawa musamman Abdallah Madugu dayafi kowa zak'ewa rawarshi yake bil haqqi da gaskiya Ja'afar ne kad'ai yake d'an takawa a hankali. "Anya mutumin can baici kaiba kuwa dan ALLAH dubi irin rawar dayake, wai Ammi bata tab'a baku labarin ya d'an samu matsala a brain d'inshi ba tym d'in dayana yaro?". Jauhar ce tayi maganar bayan taja tsaki idanunta akan Abdallah dayake ta d'iban shokky 😂. Sosai Hassana ta k'yalk'yale da dariya tace "Wllhy sis bawata matsala dake k'wak'walwar shi kawai shi haka yake in kikace zaki biyewa Yah Abdallah da abinda yake zaki iya kamuwa da hawan jini ma wllhy shiyasa tsakaninmu dashi ido". ta k'arasa maganar tana kai hannu kan idanunta, wani tsakin Jauhar ta k'ara saki tana tab'e baki. Cikin rawar ya hango Jauhar da wani saurayi sun fita daga cikin Hall d'in baki ya cije yana binsu da kallo kafin ya zame jikinshi ya fita daga filin rawar da zuwa yanzu aka cikashi sosai yabi bayansu cikin takunshi na k'akk'arfan namiji da ubangiji ya azurta da cikakkiyar lafiya. Gaba d'ayansu basu san da tahowarshi ba bare zuwanshi saboda sun juya bayansu sai saukar wani azababben rank'washi da Jauhar taji a tsakiyar kanta, ba shiri tasaki k'arar azaba tareda dafe wajen da hannunta tana juyawa dan ganin waye duk da dai zuciyarta bata raba d'ayan biyun wannan fitinannen ne, k'ik'am ta ganshi yayi mata tsaye yana k'are mata kallo hankalinshi kwance bakace shiya aikata ba, cikeda mamaki saurayin yace "A'a Malam lafiya kuwa? ya zakazo ka sameni da yarinya ka daketa meye had'inka da ita?". Zagaye Jauhar yayi ya k'arasa gaban saurayin yai masa tsaye akai ya kama k'ugunshi da hannayenshi duka biyun yana wani kallonshi a d'age yace "Zaka rama mata ne?". "Ba zancen zan rama mata bane amma meye dalilinka nayin haka?". saurayin yace yana wa Abdallah wani irin kallo na mamaki. Gabanshi ya k'ara matsawa sosai yana wani irin murmushi gamida shafa sajen fuskarshi yace "Ko zamuyi fad'a ne?". "Fad'a kuma? me yai zafi? akan me zanyi fad'a dakai?". lokaci d'aya saurayin ya jero masa tambayoyin yana kallon shi. Tsayuwar shi ya gyara gaban saurayin yace "Karka damu ganina dakayi da wannan babbar rigar zan iya cireta mu bugi juna dakai yanzun nan d'an saurayi". Shidai zuwa yanzu saurayin ya fara tunanin duk yadda akayi Abdallah baida cikakkiyar lafiya ta k'wak'walwa gashi dai very handsome guy fari kyakkyawa dan haka yafara masa kallon tsoro yana girgiza masa kai. "Saita hanya". Abdallah ya fad'a yana kaucewa daga gabanshi tareda nuna masa hanya da hannunshi, da sauri kuwa saurayin yabar wajen yana waiwayen inda yabarsu tsaye. Takowa ya shiga yi inda Jauhar ke tsaye har lokacin hannunta dafe da kanta dan harga ALLAH ba k'aramin shigarta rank'washin yayiba ga takaici daya cikata kamar ta mutu dan haushi. "Munafuka da kukazo nan d'in uwar mi zakuyi?". baki ta tura gamida sakin tsaki ta juya da shirin barin wajen ya fincikota ya matso da ita daf dashi har sunajin hucin numfashin juna da k'amshin turarukan juna da suka cika k'ofofin hancinansu. "Ba'a tafiya idan ina magana, ya kamata kisan wannan". Wani k'ululun abune ya tokare mata a wuyanta baiyi gaba ba haka kuma baiyi baya ba ALLAH nagani Yah Modibbo yana mugun takurawa rayuwarta batasan ya zatayi dashiba ya zamar mata alak'ak'ai. "Bakya jine". yace yana k'ara matsar da fuskarshi kusa da tata tamkar mai shirin had'esu. Da k'yar ta had'iye abinda ya tokare mata batason su raba abin fad'a a cikin mutane ita yau batajin fitina gashi kanta na mata ciwo saboda hayaniyar wajen datayi yawa. "Kayi hak'uri to". ta fad'a tana cije lips jitake tamkar tai ta wanka masa mari tsabar haushin da datake ji. Sakinta yayi yace "Wuce muje". "Kaje zan taho". tace cikin had'e rai tana hararar shi ta gefen ido Cikin zaro ido yace "Inje ina? k'afata k'afarki wuce ko in d'auke ki kuma kinsan koban rantse ba zan iya ko?". Gaba tayi batare datayi magana ba tasani sarai tsaf zai iya d'aukar nata kamar yadda ya fad'a d'in yabi bayanta yana murmushi. M&S💝 *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* 2/14/22, 08:59 - Ummi Tandama😇: 14. Tana gaba yana biye da ita a baya. "Bakiji ba". ya fad'a daga inda yake, banza tayi masa tamkar bataji abinda yace ba ta cigaba da tafiyarta k'wararan taku biyu yayi sai gashi ya taddo ta gefenta ya tsaya suka jera yace "Nace ba". Nan ma shiru tayi kamar bata jishi ba a fusace yace "Jauhar zanci ubanki a wajen nan wllhy ya ina miki magana kinyi banza dani kurma ce ke kome". Sai data harari gefen dayake tana tura baki tace "To wai ba kunne ne yake jiba, zaka ishi mutane jarababbe". ta k'arasa maganar k'asa k'asa cikin k'unk'uni yadda bazai jiba. "Idan an tashi kar kibi motar kowa sai tawa kin gane". "Why?". tace tana tsayawa. Shima tsayawar yayi a gabanta ya d'age kafad'a yana d'an tab'e baki yace "Haka dai na fad'a idan kuma kikayi gigin bin wata mota ba tawa ba kinsan sauran ki gwada kigani". bai bata damar magana ba yayi gaba yana wani irin taku. Da wata muguwar harara tabi bayanshi jitake tamkar ta janyoshi taita dukanshi batasan ya zatayi da wannan bawan ALLAHn ba, tsaki taja tabi bayanshi lokacin harya shige cikin Hall d'in. Tana komawa su Hassana suka fara tambayar ta inda taje ba wanda ta kula a cikinsu dan a wuya take ranta a b'ace yake suma da suka gaji sai suka k'yaleta suka maida hankalinsu kan ango da amarya da aka taso suka fito filin rawa dan takawa. An rak'ashe sosai anyi nishad'i anci ansha da abinci da abinsha masu dad'i da akayi order, k'arfe sha d'aya da y'an mintuna aka tashi daga dinner cikin rububi Jauhar tabi danta gujewa Madugu saidai abinda bata saniba hankalinshi gaba d'aya yana kanta saiji tayi caraf an rik'e hannunta an fita da ita daga taron mutanen, kamar sakara haka tabishi batare datayi magana ba to tace me? shifa hayaniyar mutum da wani bore da mutum zaiyi bashi zaisa ya fasa abinda yayi niyyar yiba. Can gefe inda ba yawaitar mutane suka nufa inda motarshi take, suna zuwa yaga yaga Abdallahn Momy Maryam da Habeeb Umar Marafa suna tsaye jikin motar suna jiranshi, front seat ya bud'e yayi mata alamun ta shiga da hannunshi ba musu ta shiga ya rufe ya zagaya yaga Habeeb Marafa ya shiga back seat Abdallahn Momy Maryam ma na shirin shiga hannu yasa ya janyo rigarshi ta baya yana fad'in "Wai ina zaku? dallah malamai ku fito". juyowa A. Zakeer yayi yace "A'a ban ganeba ba tare mukazo dakaiba". "Eh tare mukazo amma ba d'an iskan dazan maida yanzu kowa yaje ya nemi mai maidashi gida kaima fito dan ubanka". yayi maganar yana cakumo Habeeb Marafa ya fito dashi shima, sakato sukayi suna kallon wannan d'an jujun abokin nasu. "Amma kaidai anyi mara mutunci wllhy kasan fa bamuzo da mota ba a motarka mukazo shine zaka mana iskanci A.B Madugu?". Habeeb Marafa ne yayi maganar yana hararar Abdallah daya juya baya yana shirin bud'e driver seat, juyowa yayi yace "Kuje ku nemi Ja'afar ubanwa yace karku d'auko mota niba d'an iska bane dazaku maidani wani direbanku". bai saurari abinda zasuce ba ya bud'e ya shiga ya yiwa motar key yabar harabar hall d'in suka bishi da kallo harya fice, k'wafa A. Zakeer yayi yace "Gayen nan fa ya raina mana hankali Habeeb". "Rabu da d'an iska bashi da mutunci fa zo muje ga Ja'afar can da alamu ma mu yake nema". ya fad'a yana jan hannun A. Zakeer suka nufi inda Ja'afar yake tsaye yana dube dube suna k'arasawa Ja'afar yace dama su yake nema yayi zaton sun tafi da Abdallah tsaki A. Zakeer yayi yace "Rabu da mara mutuncin can yayi tafiyarshi wai bazamu maidashi driver ba". Kai kawai Ja'afar ya girgiza yana murmushi ya shiga motar suma suka shisshiga ya tayar sukabi sahun sauran motocin daketa ficewa daga wajen. Tunda suka tafi ba wanda yayi magana saida suka d'an fara yin nisa sannan ya juyo inda Jauhar take taci d'aci tana faman harare harare murmushi yayi ya juya ya maida hankalinshi kan driving d'in dayake kafin yace "Ya kikaga rawar d'azu?". 'Ji wani shirme kuma dan ALLAH' tace cikin zuciyarta tana jan k'aramin tsaki. "Kinji". ya k'ara tambayar ta, takaici kamar me Jauhar kamar ta daddalla masa mari meye abin burgewa a rawar? baisan ma haushin shi taji ba d'azun lokacin da yake rawar. Kai tsaye tace "Batai ba". harda tsartar da yawu dan k'arin bada haushi. Maimakon taga yaji haushi sai taga yayi murmushi ya juyo ya kalleta ya k'ara maida kanshi kamar bazaiyi magana ba saikuma taji yace "So tired wllhy jikina duk ciwo yake". "Saikace wani yasashi yayi rawar". ta fad'a cikin ranta tana hararar shi ta gefen ido, bai k'ara magana ba itama ta maida kanta kan wayarta dake hannunta har suka k'arasa gida, yana yin parking tayi hanzarin ficewa ta shige falo bata saurari cewar dayake ba wai bazata tsaya tayi masa godiya ba saboda mutuncinta ragaggene, tsaki kawai taja lokacin datake k'arasa shigewa cikin falon. Wanka kawai tayi tasaka nyt dress tabi lafiyar gado dan cikinsu ma ita kad'ai ce ta dawo, ta gaji matuk'a dama ga kanta dake ciwo dayake ba k'aunar magani take ba yasa bama ta nemeshi ba tayi kwanciyar ta. Yana shiga part d'inshi A. Zakeer da Ja'afar suma suka shigo dama saida suka biya suka ajiye Habeeb Marafa a gida sannan suka wuto, bai kalli inda sukeba ya cigaba da cire kayan jikinshi tunda suka shigo A. Zakeer yake hararar shi ba kallonshi yayi ba baima san abinda yakeba sai daya d'ago kai yaga yadda yake hararar shi dariya yasaki yace " Ya Broth har kun dawo?". "Ban saniba d'an iska mara mutunci yanzu daka taho ka barmu bambancin mu kad'an ne dakai ai". Baki ya tab'e yana zame wandon shaddar jikinshi yace "Bakasan wadda na d'auko bane da baka zageni ba". "Tafimu muhimmanci kenan?". A. Zakeer ya tambaya. "To dama kunada wani muhimmanci ne a gurina?".yace yana k'ok'arin shigewa toilet danyin wanka, k'aramin pillow A. Zakeer ya d'auka ya jefa masa yayi saurin shigewa toilet d'in yana dariya. ^√^√^√^√^√^√√^√^√^√^√^√^√^√^ Washegari asabar aka d'aura auren Al'ameen Basheer Madugu da amaryarsa Fareedah Mustapha Ahmad akan sadaki dubu d'ari, daga nan aka d'ora da yinin biki da mata suke yi aka cigaba da gudanar da shagalin biki har zuwa yammacin ranar inda kuma aka tafi d'aukar amarya. Anan unguwar Ameen yayi ginin gidanshi basuda nisa dasu Ammi dan a k'afa ma ana zuwa gidan gidanshi yayi kyau sosai masha ALLAH ginine na zamani da aka tsarashi sosai k'arami ne kuma bashida irin girman nan sosai, Jauhar tana sane tak'i zuwa gidan amaryar dan tasan indai ta fita wannan d'an takurar sai yasan abinda yayi mata ya b'ata mata rai shiyasa tayi zamanta, aikuwa kamar tasani dan saidaya dinga dubata duk inda yaga taron y'an mata saiya dubata daga k'arshe dai ya hak'ura. Yana shirin komawa cikin gidan ya hango Jauhar tsaye itada wani saurayi a kusa da wata mota, tsaye yayi yana k'are musu kallo kamar zaije wajen saikuma ya tsaya ya fasa dan ya gano kowaye suke tsaye dashi abokin Yah Ameen ne kuma yana ganin mutuncin shi sosai daba abinda zai hana yaje yayi masa d'iban albarka, zuciyarshi wani irin zafi take masa tana tuk'uk'i baisan meyasa ya tsani ganin Jauhar da kowane irin namiji ba lallai zaici uban yarinyar nan kuwa tunda batajin magana nan ya tsaya yana jiranta sai cije baki yake yana kad'a kai. Janan da fitowarta kenan Muhammad ya tareta dama tun ranar dinner ta kula da irin kallon dayake mata na k'urullah to hardai aka tashi bai samu damar yi mata magana ba sai yanzu tana fitowa sukaci karo da ita yayi nasarar janta can inda motarshi take dan yad'a manufarshi dan sosai yarinyar tayi masa duk da bawai ya santa bane sosai amma yaga alamun yarinyar tanada hankali da nutsuwa irin macen daya dad'e yana addu'ar samu ALLAH ya had'a shi da ita gata very beautiful girl son kowa k'in wanda ya rasa. Duk jinta take a takure tsayuwar nan da sukayi saboda bata saba ba duk shi kad'ai yayi kid'anshi yayi rawarshi saidai eh ko a'a wata maganar kuma saidai tayi murmushi kawai dayaga dai kamar a takure take saiya nemi tabashi phone number dinta sai suyi magana ta waya ita tsoron bada number ma take haka yasa tace masa bata fito da wayarta ba kuma bata rik'e number a kanta ba ganin tanata masa hanya hanya ne yasa shi yazaro wani k'aramin card cikin wallet d'inshi ya mik'a mata yace ta kirashi yaga number tata ya batane kawai amma yasan ba lallai ne ta kirashi din ba zai karb'i number tata ma a wajen Ameen sai suyi magana, duk akan idon Abdallah Madugu haka ke faruwa kai kawai yake kad'awa yana cije lips d'inshi tareda sauke numfashi yana lumshe ido yana tausayin gayen can idan har zuciya ta d'ebeshi yaje wajen dan zai manta da koshi waye yamasa d'iban albarka mai citta saidai ko meye zai faru ya faru yasan dai Yah Ameen zai tuhumeshi kan ya ciwa abokinshi mutunci ya shirya kuma tsaf dan kare kanshi kuma baya shayin hakan ta faru. Harya fara takawa zai nufi wajen dan ya kasa jurar kallonsu saikuma yaga ya shiga mota ya tayar yabar wajen da alamu gidan angon ya nufa, k'wafa kawai yayi yana bin motar da kallo, saman motar dake kusa dashi wadda baima san kota waye ba ya d'ane yana jiran zuwanta yaji dalilin dayasa ta rainashi haka. A hankali ta shiga takowa zuwa gidan dan tama fasa zuwa gidan amaryar, sam bata ma kula dashi ba tana shirin gota inda yake sai muryar shi dataji yace "Come here". Gabanta ne yayi wani irin fad'uwa ta juyo tana kallonshi ALLAH ya zuba mata tsoron bawan ALLAHn nan Hassana da Hussaina tasan suna tsoranshi amma ita kanta shaidace basa masa tsoron da ita take masa, sosai jikinta yafara tsuma ta nufi inda yake, tana zuwa ta durk'usa k'asa jikinta sai b'ari yake tun jiya data ganshi a wajen dinner yana kwasar rawa bata k'ara ganinshi ba. M&S💝 2/14/22, 10:29 - Ummi Tandama😇: ©? *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* *WATA SOYAYYA.....* 15. √^√^√^√^√^√^? Duk yinin yau basu had'u ba bare tayi tunanin wani laifin tayi masa koda yake idan y'an zalincin nashi suka motsa da wanda yayi laifin dama wanda baiyiba duk had'awa yake itadai ALLAH ya kub'utar da ita shine kawai addu'ar ta. Hannu yasa ya turo hular kanshi gaba yana wani girgiza k'afa yace "Stand up". yayi maganar yana mata alama da hannunshi nata tashi tsaye, tsayen ta tashi kanta a k'asa tana wasa da card d'in da Muhammad ya bata gabanta sai harbawa yake. Kanshi a k'asa yana wasa da zoben azurfar dake hannunshi na dama batare daya d'ago kaiba yace "Ban hanaki tsayawa da samari ba?". "Yaushe kuma sukayi haka da ita ko duk cikin neman fitinar tashine? tayi maganar cikin zuciyarta, to kokuma dai ya zaci Jauhar ce? "Ba magana nake miki ba?". ya fad'a cikin tsawa yana k'ok'arin dirowa daga saman motar, a tsorace ta d'ago kai idanunta har sun fara tara ruwan hawaye ta shiga girgiza masa kai da fad'in "Ba Jauhar bace Yah Abdallah Janan cefa". "Rainamin hankali zakiyi dan ubanki". yace yana k'arasawa inda take tsaye, ganinshi a gabanta ya k'ara rikitata sai faman girgiza kai take tamkar k'adangaruwa tama kasa yin maganar "Firstly bani wannan card d'in na hannunki". yace yana mik'a mata hannu, da sauri ta mik'o masa cikin rawar hannu ya kuwa fisgeshi ya kekketashi harda cije lips ya zubar dashi nan k'asa ya d'ago yana kallonta da yadda jikinta keta faman shaking kamar wadda aka tsoma cikin ruwan k'ank'ara, wani d'an tunani shima yayi cikin ranshi anya kuwa ba Janan d'in bace da gaske da Jauhar ce bazatayi wannan rawar jikin ba kuma ido cikin ido zata kalleshi harta fad'a masa maganar da duk taga dama idan ma kasheta zaiyi ya kasheta, wannan tunda tazo bata yadda sun had'a ido dashi ba amma dan ya k'ara tabbatarwa saiya k'ara matsawa daf da inda take tsaye ta d'an ja baya ya k'ara binta yana fad'in "Ta cire mayafin ta ya duba yagani (Duk cika bakin dayake yi na shi kad'ai yake bambancesu batare daya sha wahala ba yaudai ya gaza dan ya kasa tantancesu d'in, almuri dama k'arya ne 🙄😬). Amma akwai abinda zai gani wanda zai gane idan ta tabbata Jauhar d'in ce kuwa saiya yanka mata kazar wahala yanzun nan bada dad'ewa ba. "Zaki cire ne ko sai jikinki ya gaya miki". ya fad'a a fusace yana kai mata mari ALLAH yasa tayi hanzarin gocewa sai gefen bakinta daya samu, ba zato taji ya fige gyalen datayi rolling dashi tayi saura daga ita sai bak'ar jallabiyyahr jikinta ALLAH yasa ma da hula a kanta da haka zai bud'e mata gashi da daren nan, jikinta ta k'ank'ame sosai tana danne kukan daya taho mata. Saman k'irjinta ya k'urawa ido so yake yaga d'igon tawadar ALLAH d'in daya tab'a gani a k'irjin Jauhar wadda take da d'an girma ba laifi saidai kuma ba komai a wajen saboda akwai haske sosai a wajen yasa yagani hakan ya tabbatar masa da cewa Janan d'in ce kenan da gaske, tsaki yaja ya kasa bata vail d'in kuma, A. Zakeer dayake ta bulayin nemanshi tun d'azu bai ganshi ba sai lokacin ya hangoshi shida Janan a tsaye kanta a k'asa kamar ma kuka take, wajen ya k'araso yana fad'in "Azzalumi kana nan kanata zaluncin ko, inata nemanka tun d'azu". ya ida maganar yana warce vail d'in dake hannun Abdallah Madugu ya damk'awa Janan yace ta tafi gida da sauri ta karb'a kuwa ta yafa tabar wajen shikuma yaja hannun Abdallah yana masa magana k'asa k'asa wanda sam banjin abinda yake fad'a masa naga dai sun shek'e da dariya tareda tafawa suka nufi wajen wata mota da wasu y'anmata biyu ke tsaye a jikin motar. Haka nan Janan taji zuciyarta na mata zafi game da abinda Yah Abdallah yayi mata duk daba yaune karo na farko da irin hakan tafara faruwa ba meye Yah Abdallah baya musu? duka zagi cin mutunci ba irin wanda basa gani idan y'an buyaginshi na kusa, ba wasu mutanen kirki ma a gidan duk an yoye an tafi gidan amarya, da kuka ta k'arasa bedroom d'insu raguwar zuciya gareta batada wuyar yin kuka kan sofa ta zauna tana share hawayen fuskarta bata kula ma da Jauhar ba wadda ke kwance kan bed tana chatting a wayarta, wayar ta ajiye ta taso ta isa inda Janan take ta zauna kan hannun kujerar tareda dafa kafad'arta, da sauri ta d'ago dan ganin kowaye dan batayi zaton da mutum ba a d'akin. "Meya faru sister? kukan me kikeyi?". ta tambayeta cikin damuwa. Shiru tayi ta cigaba da share hawayen ta saida Jauhar ta k'ara maimaita tambayar sannan cikin rawar murya tace "Yah Abdallah ne.......Anan ta bata labarin duk abinda yafaru yanzu a waje, tsaki Jauhar taja tace "Dole ya rainaki wllhy ya riga yaga gurin kwananki ya zaki dinga b'are baki kina kuka a gabanshi? wllhy yarinya gara tun wuri ki rage wannan d'an banzan tsoron nashi da kikeji tunda ALLAH ya had'aku zama dashi gida d'aya shifa ba'a masa alkunya wllhy mugu azzalumi kawai shi idan baiyi mugunta ya takurawa jama'a ba baiji dad'i ba ki k'yaleni dashi ji yadda dan ALLAH har bakinki ya d'aga". ta ida maganar tana shafa gefen bakin Janan daya d'an d'aga kad'an saboda marin daya kaimata d'azu bai sameta ba yasamu gefen bakinta. "Ki barni dashi saina rama miki, naga alamun soyake a k'ara maimaita abinda ya faru a KD dan wllhy tsaf zan kame k'afar mugu da hannayenshi harda idanun inga ta mugunta kuma inyi tafiyata ba wanda yasan nina aikata". Girgiza kai Janan ta shiga yi da sauri tace "Rufamin asiri sister da wannan aika aikan naki tsaf zaice nice nayi masa bamai fitar dani kuma ki k'yaleshi kawai wata rana da kud'i aka had'ashi akace yayi hakan bazaiyi ba". Baki Jauhar ta tab'e tace "Saifa yaji a jikinshi ko yayane dama ai inajin haushinshi jiya bakisan me yayi minba". "Karki sake wllhy sister idan kika sake kika tab'a shi nikuma abinda zan miki saiya zarta nashi wllhy kinfi dai kowa sanin halina basai wani ya fad'a miki ba". "Bak'ar muguwa wlhy sister kin fini sanin takan mugunta nawane kawai ya fito fili". Jauhar ta fad'a cikin dariya tana dukan kafad'ar Janan itama Janan d'in dariyar tayi daga nan kuma suka shiga hirar y'an uwantaka. √^√^√^√^√^? Washegari biki ya tashi dangi na kusa dana nesa duk sun kama gabansu sai y'an tsirari dake gidan aka shiga gyare gyaren gida da inda duk aka b'abb'ata. Jauhar taso tabi Mama Ammi ta hana tace saita k'ara kwanaki tunda ta dad'e batazo gidan ba, bawai da son ranta ba ta amsa dan harga ALLAH batason zaman gidan tunda tasan mawuyacin abune basu dinga had'uwa da Yah Abdallah ba itakuma abinda bataso kenan bataso ranta ya dinga b'aci a banza a wofi. A washegarin ranar Ja'afar da Mama sukayi sallama dasu Ammi suka kama hanyar KD Jauhar tamkar ta bisu take ji, lokacin da suka rakosu ma compound wajen mota tayi tsammanin zata ganshi a wajen saitaga bashi alamu sun nuna baya gidan ne taji dai Ammi na tambayar Mama sunyi sallama da Modibbo kuwa Mama tace eh sun riga sunyi sallama tun jiya da dare saboda yau zai fita da wuri kuma baisan yaushe zai dawo gidan ba, baki kawai Jauhar ta tab'e lokacin da suke maganar. Momy Maryam ma kwana d'aya ta k'ara ta tafi itada yaranta da sukazo tare, Hannah sun shak'u sosai da Jauhar a d'an kwanakin nan da sukayi tare dama ita kad'ai ce basu san juna ba sunyi exchanging numbers dan gaisawa. Aunt Deejah dama bata kwana sai sintiri data dinga yi kullum tazo ta koma tunda aka fara bikin. Typing wahala 🥺😑 Mu had'u a next page dan jin yadda zata kaya. Me kuka fara hangowa game da labarin? Inason jin ra'ayin ku Ina buk'atar comments ko in tahi yajin aiki🧐🚶🧑‍? Dan ALLAH wai Abdallah Madugu baya burgeku🙄 kowa sai inji yace ya tsaneshi 😥 masu sonshi suyi k'uri'a nasan da zero zai tashi😂😂 Mrs Salees Mu'az 💝 Maryam Ibraheem Aleeyuh [Ummee] 2/14/22, 10:29 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Oum Hanan Page 16. *TOP TEN TAKUN HASKE BATCH A* A. Zakeer ma baibi su Momy Maryam ba yace saiya k'ara y'an kwanaki tunda yasamu hutu a gurin aikinshi suna nan tareda Abdallah Madugu suna iya shegen su dan shima A. Zakeer d'in ba baya ba na Abdallah Madugu ne yafi fitowa fili. Gida yakoma ba kowa sai masu gidan kawai saikuma Jauhar da A. Zakeer da suke nan har yanzu. Sam Jauhar bata fitowa daga bedroom ko abinci ne saidai akai mata idan ta fito ta gaida Ammi tayi komawarta saikuma idan Abbie yadawo ta fito ta gaisheshi duk tana yin hakan ne dan gujewa Yah Abdallah dan tasan indai suka had'u sai sunyi fad'a tamkar wasu tom and jerry, saidai taji maganar shi a falo. √^√^√^√^√^? Bayan kwana biyu. Tana kwance a bedroom kiran Saleem ya shigo wayarta, murmushi tayi takai wayar kunnenta bayan tayi picking suka gaisa suka shiga hirarsu ta masoya daga bisani yake fad'a mata zai shigo Kano gobe wani aiki zai kawoshi tabashi address d'in gidan datake zaizo, tayi murna sosai suna gama wayar kuwa ta tura masa address d'in ta WhatApp. Washegari tun safe tasamu Ammi ta sanar da ita zuwan bak'on da zatayi, Ammi tace to ya kamata a samar masa abinda za'a tareshi dashi dan haka tun wuri Jauhar suka shiga kitchen itada mai taya su Ammi aiki suka fara shirye shiryen tarbar bak'o. Daf da Azhar suka kammala komai ta amshi key d'in sit room na saukar bak'i wanda ke cikin compound d'in gidan mai tayasu Ammi aiki taje ta jera komai a dinning table itakuma ta shiga wanka, bayan ta fito ta gabatar da sallahr Azhar dan lokacin ta ya riga yayi sannan ta zauna shiryawa ta dad'e sosai tana k'ak'ale² wajen yin kwalliyar duk da dai bawata kwalliyar kirki bace amma ta d'auki lokaci tana gyara fuskar ta tayi kuma kyau sosai ta shirya cikin doguwar rigar atamfa A shape purple and white color tayi d'aurinta data saba na malaha ta d'aura agogon fata purple sai fashion d'an kunne data saka ta fesa turarukan su Hassana data gani birjik kan mirror tana cikin neman mayafin dazai shiga da atamfar ta tuna ba'a kai drink's ba dan haka bayan ta d'auko gyalen shima purple da fararen duwatsu a jiki ta yafa sai data k'ara fesa wani turaren sannan ta fito ba kowa a falon dan Ammi bata cika zaman falo ba tafi zama can upstairs su Janaan kuma har yanzu basu dawo daga school ba kitchen ta wuce kai tsaye ta bud'e fridge ta d'auko exotic da hollandia da wasu guda biyu na gwangwani sai ruwan faro roba biyu, kan tray ta d'orasu ta fita ta nufi sit room d'in dan kaiwa. Tayi mamaki k'warai dataga d'akin a bud'e sai tayi tunanin ko Atika ce bata rufe ba tunda ita tabawa key d'in takai kayan kuma bata dawo mata da key d'in ba. Tsaye tayi cikeda mamaki tana binsu da kallo Abdallahn Momy Maryam ne da Habeeb Marafa akan kujera sunyi d'ai d'ai suna danne dannen waya sai Madugu uban tafiyar shikuma a k'asan carpet yake ya kishingid'a kan filon kujera shima dai wayar ce a hannunshi sai hira da suke d'an tab'awa jefi jefi, mamakin abinda ya kawosu d'akin take koma meye ita ba damuwarta bace shida abokan nashi duk ba'a gabanta suke ba suma kana ganinsu kasan y'an a mutu ko ai rai ne, kamar yadda take kallonsu haka suma suka d'ago suna kallonta Abdallahn Momy Maryam da Habeeb kansu suka maida kan wayar hannunsu suna cigaba da abinda suke Madugu kam kasa d'auke idanunshi yayi a kanta matuk'a gaya kwalliyar ta tafi dashi ba kad'an ba, wani kallon sama da k'asa tayi musu ta d'auke kai tareda jan k'aramin tsaki ta nufi inda dinning table yake dan ajiye tray d'in da drinks da ruwan yake. Cak ta tsaya tana zaro ido ganin yadda duk aka lalata wajen an hargitsa komai nakan dinning d'in, da sauri ta k'arasa wajen ta ajiye tray d'in daga kan plates da spoon d'in data gani akai duk da ragowar abinci ta tabbatar koma meye aikin gama ya riga yagama amma duk da haka sai data shiga bubbud'e warmer's d'in dake jere dan tabbatarwa gaba d'aya ba komai ba abinda ba'a tab'a ba wani gaba d'aya an cinye wani kuma an d'iba an rage, Ido ta runtse sosai cikeda b'acin rai mara misaltuwa zuciyarta na wani irin tafarfasa ko ba'a fad'a mata ba tasan Abdallah ne da wad'annan y'an korar tashi suka yimata wannan cin mutuncin tsabar takaici batasan lokacin da k'walla ta cika mata idanunta ba. Wani irin juyowa tayi a fusace ta nufo inda suke, gaban Abdallah Madugu taja birki tayi masa tsaye akai tana faman huci, ganin haka yasa Habeeb Marafa ya mik'e yana fad'in "Get up Baaba mu fita kafin su k'onamu da ranmu cikin d'akin nan". yayi maganar yana kallon Abdallahn Momy Maryam da shima ya mik'e shidai bai fahimci saboda me Habeeb d'in ya fad'i haka ba, wani kallo ta rakasu dashi ji take kamar ta shak'osu amma badasu zatayi ba da ogan nasu zatayi. Sai bayan fitarsu ne Habeeb yake bawa Abdallah labarin dramar Jauhar da Abdallah idan suka had'u, dariya kawai Abdallah yayi yana gyad'a kai cikin zuciyarshi yake kissimawa anya ba soyayya bace ba kuwa dole ya dasa ayar tambaya?. Sai bayan fitarsu sannan Abdallah ya mik'e tsaye yana jan wandon jeans d'in dake jikinshi sama, yadda tayi masa tsaye haka shima yayi mata tsaye suna kallon juna ido cikin ido fuskarshi a had'e kamar yadda tata take, a zafafe ta fara magana tana fad'in "Nagaji Yah Abdallah nagaji da irin wad'annan abubuwan da kake min meyasa kai baka k'aunar a zauna lafiya ne mutum saikace shaid'an to wllhy nagaji zan maka abinda sai kayi dana sanin sanina a rayuwar ka". Wata irin mik'a yayi ta shak'iyanci ya k'ara matsawa kusa da ita sosai tamkar zai had'e jikinshi da nata yace "Zakimin k'ofine kamar yadda kika saba? kin dad'e baki min abinda zanyi dana saniba Jauhar naci uwar k'ofin naki da kike tak'ama dashi wane d'an iska zaki kawo gidan nan?". "Ina ruwanka da wanda zan kawo? a gaban idonka zan kawoshi kuma ba abinda zaka iya Yah Abdallah". Wata y'ar banzar dariya yasaki yana kad'a kai gamida cije lips yana wani shafa sajenshi yace "Ki kawoshi Jauhar nikuma zan nuna miki yadda ake karya k'asusuwan mutum a gabanki zan karya banza ba abinda kuma aka isa ayi". Duk da yadda zuciyarta ke tafasa hakan bai hanata sakin dariya ba tana wani girgiza kai tace "Da kuwa kaima anyi maka yadda kayi masa ko ance maka bashida gata ne meye tak'amarka? duk abinda kake gadara dashi to shima yana dashi kuma dole zaizo gidan nan a gaban idanunka". "Yazo mana Jauhar ke dashi d'in zan had'a inci ubanku". yace yana murmushi gamida yin hanyar fita daga falon. "Ni malam ka daina b'ata min suna wllhy k'ato dakai baka iya R ba". takaici yasata fad'ar haka dan ta rasa abinda ma zatace masa, juyowa yayi yana murmushi yace "Zan iya R amma sai ranar da kika shiga hannuna". daga haka ya juya ya fice, dogon tsaki taja tana binshi da kallo a fusace itama ta fita daga d'akin ko inuwar shi bata gani ba da alamu ya shige part d'insu wanda yanzu yazama nashi shi kad'ai tunda Yah Ameen ya tashi. (To abinda dai ya faru har Abdallah yasan Jauhar zatayi bak'o shigowarshi gidan kenan yaga Atika tanata faman shige da fice daga cikin gida zuwa d'akin bak'i, dayake ya dad'e cikin motar bai fitoba bayan yayi parking, kamar zai wuce bayan fitowarshi saikuma ya tsaya ya tambayi Atika wadda ta fito daga sit room d'in anan take fad'a masa ai y'an biyun Janaan ce zatayi bak'o shine ake shirya masa table, shine ya karb'i key d'in dan neman fitina fa shine ko part d'in nashi bai shiga ba ya kira Abdallah a waya yace ya fito ga wani party an shirya musu, suna shirin shiga sit room d'in shima Habeeb yazo gidan suka shiga tare suka sha gararsu😂.) Kai tsaye cikin gidan ta koma dan wllhy saita fad'awa Ammi wannan abin da sukayi mata, tana shirin hawa upstairs dan zuwa wajen Ammi ta hango Ammin zata sauko dan haka ta zauna kan kujera tana jiranta ta sauko, tana ganin Ammi ta k'arasa saukowa ta fashe da kuka da sauri kuwa Ammi ta k'arasa kujerar datake ta zauna ta dafa kafad'arta tana tambayarta lafiya take kuka haka? cikin kukan tace "Ammi abincin da aka had'awa Saleem ne Yah Abdallah da d'ayan Yah Abdallahn yayan Hannah da wannan abokin nashi sukaje suka hargitsa komai duk sun cinye abincin sun lalata wajen". "Su su Modibbon?". Ammi ta fad'a cikin mamaki tana kallon Jauhar datake ta shasshek'a sai yanzu abin yake k'ara b'ata mata rai. Kai ta kad'a tace "Eh Ammi wai kuma idan ya sake yazo saiya had'amu nida shi yaci ubanmu kuma saiya karya masa k'asusuwan jikinshi". girgiza kai kawai Ammi take ta dafe kanta batasan yaushe Abdallah zai daina wannan halin nashi ba a fili tace "ALLAH ka shirya min Modibbo, kiyi hak'uri zanji dalilin dayasa sukayi haka yanzu dai lokaci ya k'ure amma duk da haka bari a shiga kitchen a samar masa d'an wani abu sharp sharp kafin yazo". "Ai yace bazai dad'e ba Ammi kawai a k'yaleshi tunda nakai ruwa da juice sun isa kawai". Tsaki Ammi tayi tace "Amma dai su Modibbo basu kyauta ba wllhy kiyi hak'uri kinji y'ar gidan Ammi yanzun nan zan kirasu saina musu ba dad'i tunda su manyan kwabo ne". Kai Jauhar ta gyad'a tana tura baki, tana mik'ewa kiran Saleem ya shigo wayarta bayan tayi picking ya sanar da ita zuwanshi kallon Ammi tayi ta fad'a mata Saleem d'in ya k'araso Ammi tace taje ta shiga dashi kar a barshi yayita tsayuwa, sallama tayiwa Ammin ta fita. Tana fita Ammi ta kira number Abdallah lokacin duk suna falonshi a zaune jira yake kawai yaji zuwan wannan lange langen saurayin nata yaje ya hanasu sakat ya hana zancen saikuma ga kiran Ammin yana yin picking tace suzo dukansu tana nemansu yanzun nan bata saurari abinda zaice ba tayi hang up d'in wayar. D'agowa yayi ya kalli su Habeeb yace "Ammi fa tana kiranmu da alamu Jauhar taje ta fad'a mata abinda yafaru". Zumbur Habeeb Marafa ya mik'e tsaye yana fad'in "ALLAH yasa dama tafiya zanyi sai anjimanku". "Rik'omin d'an iska dan ubanka bada kai akayi laifin ba". Madugu yayi maganar yana kallon Abdallahn Momy Maryam da sukafi kusa da Habeeb, aikuwa yai ram dashi yana dariya. Mrs Salees Mu'az 💝 2/14/22, 10:29 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 17. Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Haka suka tasa k'eyar Habeeb har falon Ammi, a jere suka shiga bakinsu d'auke da sallama tunda suka shiga Ammi ke binsu da kallo kana ganinsu kaga marasa gaskiya saboda yadda kowannen su kanshi yake k'asa. 3sitter suka zauna dukansu sukayi shiru, kai kawai ta girgiza kafin tace "Kun kyauta abinda kukayi, nace kun kyauta waye shugaban aikata hakan?". Da sauri duk suka nuna Madugu Abdallahn Momy Maryam ya d'ora da fad'in "Wllhy Ammi ina bedroom a kwance ya kirani yace wai inzo muci abinci". "Nima Ammi shigowata kenan ya kirani wai inzo an shirya mana party". Habeeb ya fad'a yana kallon Ammi da idanunta ke kan Abdallah Madugu da kanshi ke k'asa sai faman shafa k'eya yake dan duk iya shegen shi idan har Ammi ko Abbie na fad'a shiru yake sai sun gama yabada hak'uri, k'aramin tsaki Ammi taja tace "Wai Modibbo sai yaushe ne zaka daina jawowa kanka raini a wajen Jauhar ne? duk abinda yarinyar nan take yimaka kai kake siya da kud'inka saboda shiga harkarta dakake saikuma ta maka rashin kunya kazo kana faman balok'ok'o da tada jijiyar wuya, ku tashi kuje Ammi ta fad'a cikin bada umarnia tare suka mik'e tace Abdallah ya koma ya zauna bata gama dashi ba, Habeeb da Abdallah suka fita suna k'unshe dariyar su. "Me kace zaka yiwa bak'on Jauhar idan yazo!". Ammi ta tambayeshi tana masa wani irin kallo zaka had'asu ita dashi kaci ubansu kuma saika karya masa k'asusuwan jikinshi ko? Shiru kawai yayi yana shafa gefen wuyanshi, tunda Ammi taji yayi shirun nan tasan ya fad'a d'in dan da bai fad'a ba zai k'aryata idan tsireshi ma za'ayi a tsire, kai kawai ta girgiza kafin ta d'ora da fad'in "Dan ALLAH Modibbo ka dinga nutsuwa mana wai nikam meyasa ma baka fita office ba? to wllhy idan kasake kaje inda suke saina b'ata maka rai wlhy kaji na fad'a maka tashi ka b'ace min daga nan, kuma har Jauhar tabar gidan nan ban yadda ka k'ara shiga harkarta ba indai ba gaisuwa ce zata had'aku ba kaji na fad'a maka "Kiyi hak'uri Ammi". ya fad'a a shagwab'e, ganin bata kulashi ba ya k'ara fad'in "Please Amminah I'm sorry bazan k'ara shiga harkarta ba wllhy nayi miki alk'awari". "Yayi kyau, tashi kaje". abinda Ammi ta fad'a kenan. Tashi yayi ya fice yana satar kallon Ammi duk abinshi yana gudun b'acin ran iyayenshi baya k'aunar abinda zai b'ata musu rai. Tsaye yayi hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi yana kallon bak'uwar motar dake cikin compound d'in wadda ya tabbatar ta saurayin Jauhar ce, a hankali kuma ya maida kanshi kan sit room inda suke wani irin zafi da zogi zuciyarshi ke mashi jiyake tamkar ya shiga ya karta masa rashin M saidai kuma Ammi ta riga tayi masa shamaki da hakan dan haka yabar wajen da sauri yana cije lips tun kafin zuciya ta d'ebeshi yaje yayi aika aika dan a yadda yake jin zuciyarshi zai iya illata wannan siririn saurayin nata. Saleem dai sai ruwa da lemo kawai yasha dan bata bari ma yaga alamun wai anyi girki ba komai sai data kwashe ta gyara wajen, yaso fahimtar kamar ranta a b'ace yake yadda yaga yanayinta tace masa ba komai kawai kanta ne yake d'an ciwo yayi mata ALLAH ya sauk'e ya d'ora da tambayar ta tasha magani ta amsa masa kawai da Eh tasha. Bai dad'e ba sosai yace zai tafi dan karya takura mata gashi dama a ranar zai juya dad'in dad'awa kuma ba guri d'aya zaije ba hakan yasa yayi mata sallama suka fito tare danyi masa rakiya. Suna tsaye jikin motar Saleem d'in suna sallama Abdallah ya fito daga part d'inshi ya canza kaya light blue d'in shaddace a jikinshi sai P cap itama light blue daya d'ora (Nifa nafara gajiya da P cap din nan 🧐 manyan kayan ma sai ansa musu P cap dan hegantaka 😬🤨). Tunda ya fito wannan mayen turaren nashi dai data sani ta saba shak'arshi kuma a duk lokacin da suka had'u ya cika ko ina, matuk'a take son k'amshin turaren dan haka ta k'ara bud'e k'ofofin hancinta tana shak'a, gefe d'aya kuma banda fad'uwa ba abinda gabanta keyi tsoronta d'aya kar yazo inda suke yayiwa Saleem rashin mutunci musamman dataga yanayin fuskarshi ranshi a had'e yanata wani cin d'aci yana basarwa kamar ba Abdallahn data saniba tunda shi mawuyacin abune kaga fuskarshi a murtuke sai jefi jefi, shima Saleem d'in gudun cin mutuncin ne yasa yayi saurin shigewa mota, duk Abdallah na ganinsu tsaki kawai yaja ya isa inda motarshi ke parke ya shiga ya tayar yabar gidan, sosai Jauhar tayi mamakin hakan tayi zaton zaizo ya musu tujara kamar yadda ya saba saikuma taga sab'anin hakan koma dai meye ta godewa ALLAH dabai kunyatata ba. Haka sukayi sallama da Saleem ya tafi itakuma ta juya ta shige ciki. √^√^√^√^? Tun daga lokacin Abdallah ya daina shiga harkar Jauhar kuma suna had'uwa a cikin gidan amma baya kulata abin yana bata mamaki sosai da ganin wannan canji da aka samu kuma tayi murna sosai da hakan amma fa abin yana d'aure mata kai sosai ganin yadda da ko sau goma zasu had'u to saiya takaleta sunyi bala'i dashi koma dai meye damuwarshi ce ba tata ba, ji yadda ya koma wani salihi kamar mutumin kirki tasan nan da y'an kwanaki nutsattsun zasu gudu y'an buyagin su dawo. Kwana biyu da tafiyar Abdallahn Momy Maryam itama Jauhar ta tafi inda Ammi tasa driver ya maidata, Abdallah baisan ta tafiba saida akayi kwana biyu yaga sam baya ganin giccinta yasan lallai bata gidan. Some days after. Ammi ta nemi ganin Ameen da Aunt Deejah dan yin wata shawara. Suna zaune a bedroom d'in Ammin, Ameen na zaune kan sofa Aunt Deejah da Ammi kuma suna zaune a bakin gado, bayan gaisawa da aka k'ara yi Ammi tace "Abinda yasa na kiraku inaso inji ra'ayinku ne kan abinda zuciyata ke ayyana min kafin inyiwa Abbien ku maganar, numfashi ta d'an sauke kafin tace "Ina neman shawararku akan had'a Modibbo da Hussaina aure (Jauhar) danake niyyar yi me kuke gani?". Da sauri duk suka kalleta kowa yayi shiru yana nazari cikin ranshi. "Uhum Ina sauraronku naji kunyi shiru, dan gaskiya aure ya kamata ayi masa ko ALLAH zaisa ya nutsu ya gyara d'abi'unshi Ammi ta fad'a. Aunt Deejah ce ta fara magana tace "Gaskiya Ammi ina ganin had'in Abdallah da Jauhar akwai matsala kinga dai yanada zafi itama haka kuma za'ayi had'in nan ne dan k'arfafa dank'on zumunchi kar azo garin neman gira kuma a rasa ido Janaan ita tafi dacewa da Abdallah saboda tanada sanyin hali tanada hak'uri kuma". Kai Ammi ta shiga kad'awa kafin ta maida kallonta kan Ameen da harya fara imagining d'in Abdallah da Jauhar a matsayin miji da mata fire 🔥 kenan🤣 inajin duk unguwar ma sai sun tasheta ba iya gidansu ba. Ganin Ammi ta kalleshi yasa yace "Maganar Aunt Deejah tana kan hanya Ammi kamar yadda kikace kinaso kiga ya nutsu to saidai fa a had'ashi da Janaan itace daidai shi anfiso a had'a zafi da sanyi ba zafi da zafi ba saikiga anzo anata dana sanin had'awar". "Gaskiya ne amma baku ganin zai dinga cutar da ita saboda hak'urinta ni shaidace kan Janaan batada matsalar komai amma ina ganin fa kamar zaiyi amfani da hak'urin datake dashi ya dinga k'wararta, da ace yanada wata budurwa ma daban fara maganar had'in nan ba to matsalar bashi da ita buyagin shima baya barinshi yayi wata soyayya". Murmushi Ameen yayi yace "Karki damu Ammi wuyarta dai yaganta a matsayin matarshi yanafa da hankali Ammi kawai dai iya shege ne ke d'awainiya dashi bawani abu ba insha ALLAH ba komai". "Hakane Ammi kawai ayi musu addu'a ALLAH yasa hakan yazama alkhairi nifa tunani na d'aya ta yadda za'a tunkareshi da maganar yanzu". Aunt Deejah ce tayi maganar tana kallon Ammi. "Karku damu insha ALLAHU zai yarda ai Modibbo bada ganan ba wajen jin magana tsiyarshi ce dai bata sallah". ta k'arasa maganar tana dariya, Ameen da Aunt Deejah ma duk dariyar sukayi Ameen yace "Ammi kinsan halin kayanki kenan ko". Kai kawai Ammi ta girgiza tana murmushi tace "Ai haline tun na yarinta yak'i barinshi farko nayi zaton idan ya girma zai daina ashe abin ba haka bane ALLAH dai ya shirya min shi". da 'Ameen' suka amsa kafin su cigaba da tattauna maganar yayin da Ammi ta k'uduri niyyar yiwa Abbie maganar da dare idan yadawo tana fatan abin yazame musu alkhairi gaba d'ayansu. Tofa!🤔😩 Janaan da Abdallah Madugu. Masu son auren Madugu da Janaan su d'aga hannu😀 Mrs Salees Mu'az 💝 Maryam Ibraheem Aleeyuh {Ummee} 2/14/22, 21:22 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 18 Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* ALLAH yayi dai Ayyah ta yadda zata dawo Kano gidan d'anta wato Abbie da k'yar da sid'in goshi ta amince ya dad'e yana mata nacin tadawo kusa dashi tak'i yarda amma duk da haka Abbie bai daina mata naci ba duk lokacin dayaje garin gaisheta kokuma idan sukayi waya da haka dai harta amivt tonce zata dawo d'in, a yau zata dawo dan haka tun safe gidan aka tashi da shirye shiryen tarbar babbar bak'uwa Ayyah. Daf da Azhar direban daya kawo Ayyah ya k'araso gidan, isowarsu yasa Ammi, Hassana, Hussaina da Janaan suka fito compound d'in dan tararta. Wata kyakkyawar tsohuwa ce mai kimanin shekaru 70 ta fito daga cikin motar, kasancewarta cikin hutu daya ratsata hakan ya b'oye tsufan nata wanda idan mutum bai saniba zaiyi zaton batafi irin sittin da y'an kai ba cikin kyakkyawar shiga ta alfarma, kallo d'aya zakayi mata kaga tsantsar kamarsu dasu Abdallah, cikin girmamawa Ammi ta rissina tana mata barka da zuwa ta amsa mata cikin sakin fuska tana dafa kafad'arta akwai kyakkyawar alak'a da fahimtar juna tsakaninta da surukar tata. "Oyoyo Ayyahnmu". Hassana da Hussaina suka had'a baki wajen fad'a tareda rungumeta, Janaan dai tana gefe tana murmushi cikeda sha'awarsu. "A'a ya kika tsaya taho mana Hassana". Ayyah ta fad'a cikin murmushi tana kallon Janaan bayan su Hussaina sunbar jikinta, a hankali Janaan ta k'araso inda Ayyah take rungumota Ayyah tayi jikinta haka nan take k'aunar yarinyar ALLAH ya had'a jininsu kuma sau d'aya ta tab'a ganinta wani hutun semester da suka samu driver ya kaisu itada Hassana da Hussaina tun daga lokacin taji yarinyar tayi mata musamman saboda hak'urinta dakuma sanyin halinta, kwanansu biyu suka dawo. Cikin gidan gaba d'aya suka rankaya suka shiga bayan Hassana ta karb'i jakar kayanta da drivern yabata, saida suka rakata har wani k'aramin part da aka tanadar mata wanda zata zauna yasha gyara sosai sai tashin k'amshi yake duk fita sukayi sai Ammi da aka bari sai data shiga bathroom ta had'a mata ruwan zafi ta fito ta sanar da ita tayi wanka saitayi sallah sannan tazo taci abinci. Sai data shimfid'a mata pray mat sannan tabar bedroom d'in. Tana kan dardumar bayan ta idar da sallahr Janaan tayi sallama Ayyah ta amsa tare da bata iznin shiga, kusa da ita ta tsuguna tace "Ayyah Ammi tace ki fito ga abincin angama shiryawa". "Gani nan zuwa Hassana bari in shirya". "Toh Ayyah saikin fito". Janaan ta fad'a cikin murmushi tareda fita daga d'akin Ayyah ta bita da kallo. Bayan wani d'an lokaci Ayyah ta fito falon duk a dinning table d'in ta samesu dan dama suma basuyi launch d'in ba, tana isa Janaan tayi hanzarin tashi taja mata kujera ta zauna. "ALLAH yayi miki albarka". Ayyah ta fad'a bayan zamanta, da Amin suka amsa gaba d'ayansu sannan Hussaina ta tashi suka shiga yin serving d'insu itada Janaan, kasancewar ansan Ayyah da son tuwo hakan yasa akayi mata tuwon masara lafiyayye dayake kona semovita bataso tafison na masara kokuma na shinkafa miyar busasshiyar kub'ewa akayi mata wadda taji naman rago da man soyayyen man shanu duk k'amshin miyar ya cika wajen, Hassana ma da tuwon yabata sha'awa tace shi zataci, hararar wasa Ayyah ta jefa mata tace "Magulmaciya". Y'ar dariya kawai Hassana tayi tana janyo plate d'in da aka zuba mata tuwon gabanta ta fara ci. Bud'e k'ofar falon da akayi ne duk yaja hankalinsu Ammi bakin k'ofar dan ganin waye duk da dai sun d'auki haske saboda jin k'amshin mayen turarenshi daya fara gauraye ko ina na cikin falon Abdallah Madugu ya bayyana sanye cikin bak'in wandon jeans da white shirt long sleeve mai round neck dayasa wadda ta fito masa da faffad'an k'irjinshi ya nad'e wuyanshi da wani dogon abu mai taushi na sak'a black color farin takalmin sawu cikine sanye a k'afarshi ya manna farin glasses na gayu a idanunshi yayi matuk'ar yin kyau duk da dai fuskarshi a tamke tam ya shigo saidai ganin wadda ke dinning wato Ayyah yasa ya saki fuskar tashi ya nufi dinning table d'in. Yana k'arasawa yaja kujerar kusa da Ayyah ya zauna yana fad'in "Hajjaju mutan makkah saukar yaushe?". "Ka ganni nan dai ban dad'e da zuwa ba maigidan". Ayyah tabashi amsa fuskarta a sake cikeda jin dad'in ganin Abdallahn dan duk a cikin jikokinta kaf mata da maza ba wanda take nunawa so irinshi hakan ya samo asaline kuma saboda sunan Malam Abdullahi Modibbo da aka maida masa wato mijinta saikuma Abdallahn Momy Maryam da shima take kulawa dashi sosai duk dan saboda sunan maigidanta da suke dashi, dan ma dai wani lokacin halinshi na had'ashi da ita haka take biye mashi suyita fad'a wani lokacin ma fad'an nasu abin dariya. Tunda ya zauna wajen su Janaan duk sukasha jinin jikinsu kowacce ta sunkuyar da kai tana juya spoon cikin plates d'in abincin har Hassana datake ta faman yiwa Ayyah surutu saitaja bakinta ta tsuke, plate d'in Ayyah ya kalla ya wani yatsina fuska yace "Kinji matsalarki Ayyah dan ALLAH meye daga zuwa zaki fara wani cin tuwo? Dan ubanku wayace kuyi mata tuwo?". Yayi maganar yana rarraba idanunshi kansu Hassana da Janaan wanda duk suka tsure kowacce kanta a k'asa. "Modibboo, waye baisan Ayyah da son tuwo ba? shiyasa fa akayi mata". "Rabu da wannan maigidan nawa d'an rigima, ina ruwanka ninake so nace ayimin". Ayyah tayi maganar tana kallon Abdallah. Plate d'in tuwon ya janye yana fad'in "Ayyah baza kici tuwon nan bafa". "A'a nikam dawo min da abuna". Tace tana k'ok'arin amsar plate d'in, kallon Hassana yayi ya zabga mata harara yace "Kema dan ubanki mayar da tuwon nan ki ajiye munafukai na k'ara ganin kunyi mana tuwo a gidan nan sainaci ubanku dukanku". "Yaa salam! Wai meyake damunka ne haka Modibbo? Dan ALLAH tashi kabar wajen nan kuma kabawa Ayyah tuwonta tun kafin ranka ya b'aci". Ammi tayi maganar a fusace tana kallonshi. Plate d'in ya tura mata yana wani yatsina fuska, itadai Ayyah murmushi kawai take gamida girgiza kai, Ammi kam k'wafa tasaki ta maida kanta kan abincin datake ci, har yanzu tamkar yaro haka Abdallah yake wani lokacin ALLAH dai ya shirya mata shi. "Bani abinci". Abinda kawai yace kenan yana kallon Janaan, da sauri ta mik'e kuwa kamar wadda ke jira ta zuba masa dambun shinkafa dayaji vegetables da spices sai hanta da aka yanka hanta k'ananu a ciki ta tura masa plate d'in gabanshi bayan tasa masa spoon, su Janaan dai sai tashi sukayi suka bar wajen dan gaba d'aya zamanshi a wajen ya takura musu, kad'an ya tsakuri abincin ya ture plate d'in coconut juice d'in da aka zubawa Ayyah a glass cup shiya d'auka yana shirin kaiwa baki Ammi tayi saurin cewa "Ah meye haka wai Modibbo? tashi kabar wajen nan tunda neman magana ya kawoka". Ganin ba alamun wasa saman fuskar Ammi yasa ya ajiye ya yagi tissue ya fita yana goge bakinshi, duk da kallo suka bishi Ayyah ta girgiza kai tace "Halin dai yana nan har yanzu". "Me za'a fasa Ayyah? Modibboo ai sai addu'a har yanzu bai daina halayyar shiba". "Zai daina ne Hafsat". Ayyah ta fad'a tana murmushi, kai kawai Ammi ta girgiza itadai taga ranar dazai nutsu ya daina wannan harigidon nashi amma tasan idan ALLAH ya taimaka yayi auren maybe ya daina. √^√^√^√^√^? Yau sati d'aya kenan da zuwan Ayyah gidan sun shak'u sosai da Janaan kullum suna tare da ita a bedroom d'in Ayyahn suna hira indai ba school dan yadda suke zama suyi hira ma basuyi dasu Hassana. Yauma suna cikin bedroom d'inta, Ayyah na zaune kan gado ta mik'e k'afafuwanta Janaan tana zaune daga wajen k'afafunta tana shafa mata man zafi a k'afafun saboda takura mata d'in da suke cikin kwana biyun nan da ciwo, tuni Ayyah take faman kissima abubuwa da dama akan Janaan da Abdallah a cikin ranta saidai bata saniba ko akwai wanda yake nemanta dan haka ta bugi cikinta da fad'in "Nikam Hassana wai yaushe za'a kawomin jikana mu gaisa ne bake d'in ba basu waccan uwar surutun ba(Hassanar Ammi). Murmushi kawai Janaan tayi a kunyace tace "Ayyah ai babu kowa fa". Cikin jin dad'i Ayyah tace "Kina nufin bakida tsayayye?". Cikeda sanyin muryarta na halitta tace "Ayyah karatu mukefa nibana kula kowa har gara su Hassana suna d'an kula samari". Kai Ayyah ta shiga jijjigawa tana murmushi da yardar ALLAH zata isar da k'udurin zuciyarta. "ALLAH ubangiji ya kawo mafi alkhairi". Cewar Ayyah, Janaan bata amsaba sai k'asa data k'ara yi da kanta cikeda kunya. K'ofar bedroom d'in aka bud'e Abdallah ne ya shigo bakinshi d'auke da sallama sanye cikin blue black d'in jallabiyyah mai hula wadda tayi mugun haska farar fatarshi, kai Ayyah ta d'aga tana amsa sallamar tashi, bakin gadon ya k'arasa ya d'auke wata ledar magunguna dake kan bedside drawer ya zauna, tunda ya shigo Janaan tabar abinda take gabanta sai fad'uwa yake bataso taga sun had'u waje d'aya da Yah Abdallah zuciyarta wani irin bugu take. "Ke! tashi kibar wajen nan". Yayi maganar cikin had'e rai yana kallon Janaan. "Ina ruwanka da ita? kaidai rigimarka tafi k'arfinka wllhy maigidana". Janaan kuwa kamar jira take dama ta rufe bottle d'in man zafin ta sauka daga kan gadon cikin rawa rawar murya tacewa Ayyah "Ayyah bari inje in dawo". Bata jira komaiba ta fice daga bedroom d'in, Ayyah ta bita da kallo kafin tadawo da kallonta kan Abdallah tace "Zamusa k'afar wando d'aya dakai fa tunda nazo na lura kana takurawa yaran nan musamman ma Hassana". "Nifa raini ne banaso Ayyah, suna ganin kafara sakar musu fuska zasu rainaka nikuma cin uban yarinya zanyi". Ya ida maganar yana zame hular jallabiyyahr dake kanshi. Tsaki kawai Ayyah taja tana girgiza kai, nan ya cigaba da zama yana tayata hira duk rabin hirar fad'a ce kuma yak'i tashi ya tafi sai daya dad'e sannan ya fita yayi shirin fita office. 2/16/22, 07:41 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 19 Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Bayan sallahr la'asar ya shigo gidan bayan yadawo office yayi wanka ya huta. Pen da paper ne a hannunshi ya shigo falon Ayyah kawai ya samu a falon ta k'urawa TV ido wanda ake haska news na turanci kusa da ita ya zauna yana fad'in "Tsohuwar nan akwai fitina wllhy saikace wadda ke gane abinda ake fad'a". "Aifa kadawo kenan d'an nema". Tayi maganar tana kai masa rank'washi a kanshi yayi saurin gocewa yana dariya bata sameshi ba, bata k'ara bi takan Abdallah ba ta cigaba da kallon news d'inta tana k'ara gyara zaman farin medical glasses d'in idonta itadai kawai hotunan da ake haskawa take kallo. Zamanshi ya gyara yafara zane a paper daya shigo da ita sai jefi jefi dayake satar kallon Ayyah data maida hankalinta gaba d'aya kan kallon datake, dan haka batasan bikin dayake ba. Ameen ne yayi sallama ya shigo falon yaci gayunshi sosai cikin bugaggiyar shadda mai kyau da tsada sai k'yallin amarci yake ga k'amshi dayake ta zubawa, kusa da kujerar Ayyah da Abdallah ya zauna yana gaida Ayyah ta amsa masa tana tambayarshi lafiyar Fareedah. "Lafiya k'alau wlhy Ayyah tace a gaisheki". Yayi maganar yana lek'a paper'n da Abdallah yake zane dan ganin abinda ya d'auke masa hankali haka baki ya bud'e tareda zaro ido yace "Lallai Abdallah Ayyah kinga iskancin da yaron nan yake miki kuwa?". Ya k'arasa maganar yana warce takardar daga hannun Abdallah dake ta dariya ya nunawa Ayyah zanenta ne rad'au a jikin takardar tamkar ka kirata ta amsa hatta irin d'aurin d'ankwalin dake kanta iri d'ayane saidai dan iya shege yadda ya zana glass d'in fuskarta k'ato wanda har ya kusa cika rabin fuskar, karb'ar takardar tayi ta shiga dukanshi da ita tana fad'in "Amma kai dai anyi d'an k'aniyar yaro wllhy shine dan wulak'anci ka zanani haka, dariya kawai Abdallah yake yana kare dukan datake kai masa da hannunshi Ameen ma dariyar yake tayashi dan ba k'aramin dariya zanen yabashi ba lallai ALLAH yayiwa k'anin nasa wata baiwa ta musamman indai zane mutum keso ya fita sosai to ya nemi Abdallah shiyasa manyan masu kud'i da masu kamfanoni da sauran wad'anda za'a yiwa gine gine suke yawan nemanshi saboda yadda ya iya tsara gini har outside ake d'aukarshi yaje ya gano gida ko kamfani yazo ya zana irinshi kuma sak batare dawani bambanci ba. Ana cikin haka Abbie shima ya shigo falon tareda sallama, ganin yadda Ayyah take faman dukan Abdallah da takarda yayi dariya yana fad'in "Meyake faruwa ne? Ayyah yau keda mutumin naki ne kuma". Juyowa Ayyah tayi tace "K'yaleni da wannan maigidan nawa kaga tsiyar daya min yanzun nan". Tayi maganar tana nunawa Abbie takardar hannunta, karb'a yayi ya duba yaga abinda aka zana d'agowa yayi ya kalli Abdallah daya sunkuyar da kai yana shafa sumar kanshi yace "Gidanku Modibbo tsohuwar tawa kayiwa haka dan k'aniyarka". Dariya Abdallah yayi ya d'ago yace "I'm sorry Abbie color kawai za'asa mata kaga yadda zata k.....ganin Abbie yayo kanshi yasa cikin sauri ya mik'e tsaye ya dira ta bayan kujerar ya fice daga falon yana dariya dama tsokanace kawai ta kawoshi ba wani abu ba, da kallo duk suka bishi Abbie ya girgiza kai yana murmushi ya zauna kusa da Ayyah yana mata sannu da gida kafin su shiga gaisawa. √^√^√^ Ammi ce kawai da Ayyah a falon a zaune dan su Hassana duk suna school. "Nikam Hafsat akwai mata muhimmiyar magana danake so muyi dake ina fatan zaki bani had'in kai da goyon baya akan maganar". Ayyah ta fad'a tana kallon Ammi. "Insha ALLAHU Ayyah me kikeso ayi miki?". Ammi tace tana maida hankalinta gaba d'aya kan Ayyah. Shiru Ayyah ta d'anyi kamar bazatayi magana ba kafin tace "Maganace kan maigidana da wannan yarinya Hassana y'ar wajen yayarki, nutsuwa Ammi ta k'ara yi sosai jin Ayyah ta d'auko maganar data dad'e tana ranta takeso kuma tayiwa Abbie maganar duk da dai bata tabbatar da abinda Ayyahn zata fad'a ba maybe ba abinda take hasashe bane, cigaba Ayyah tayi da fad'in "Na yaba sosai da halayyar yarinyar nan hak'uri da kawaicinta da kuma sanyin halinta na burgeni matuk'a wanda har hakan yasa nayi kwada'yin shigarta cikin zuri'ata kuma bada kowaba da mai sunan Malam dan k'ara k'arfafa dank'on zumunchi tsakaninmu Ina fatan zan samu had'in kanki". Ajiyar zuciya Ammi ta saki tareda fad'in Alhmdulillah cikin zuciyarta kamar Ayyah tana zaune sukayi wannan tattaunawar itadasu Deejah, cikin murmushi tace "Wllhy Ayyah na dad'e da wannan tunanin cikin raina kuma ma har munyi maganar dasu Aminu nace zan samu Abbien su da maganar kuma har yau ALLAH bai bud'i bakina na masa zancen ba, had'in yayi sosai Ayyah ubangiji ALLAH yasa alkhairi zamu k'ulla". "Amin Amin, saidai kuma wannan rikitaccen maigidan nawa nasan da k'yar zai amince sai ankai ruwa rana dashi". Murmushi Ammi tayi tace "Karki damu Ayyah insha ALLAHU Modibbo bazai bamu matsala ba nasan halinshi sarai duk abin nan nashi yanajin maganar mu sosai kuma bayason ranmu ya b'aci". "To masha ALLAH, ALLAH yasa muga alkhairi". Ayyah ta fad'a cikin jin dad'i daga nan suka d'ora da hirarsu ta surukai masu ganin mutuncin juna. Da dare lokacin da Abbie yaje gaida Ayyah a bedroom d'inta bayan sun gaisa ne ta d'auko masa maganar shima yaji dad'i sosai yayi murna ya kuma d'ora da addu'ar fatan alkhairi,anan suka tsayar da maganar za'a samu Abdallah da maganar da ita kanta Janaan d'in. Ko Madugu zai karb'i tayin Ayyah, Ammi da Abbie?. Two days after. Tunda Janaan taji an aiko Hassana wai su Ayyah na nemanta a falon Abbie gabanta yaketa faman fad'uwa batasan dalilin kiranba tanada matuk'ar tsoro da gudun laifi dan haka tsoronta d'aya kar ace ko wani laifin tayi wanda bata saniba, doguwar rigar abayah ce a jikinta black color sai k'aramin hijab iya kafad'arta datake sanye dashi white color da akabi ko ina na jikin hijabin da stones masu k'yalli. A d'arare tayi sallama ta shiga falon nan ta hangi Abbie da Ammi akan doguwar kujera a zaune Ayyah ma zaune kan kujera 1sitter da carbi a hannunta tana ja kamar yadda koda yaushe zaka sameshi dashi a hannunta, da k'yar ta k'arasa inda suke ta zauna a k'asa saitin inda k'afafun Ammi suke ta sunkuyar da kanta tana musu barka da hutawa cikin rawar murya duk suka amsa mata cikin sakin fuska, baifi minti d'aya da shigowarta ba aka k'ara bud'e k'ofar falon aka shigo tareda yin sallama, k'amshin turaren shi kawai daya baza musu a falon Janaan ta shak'a ta gane wanda ya shigo bai wuce Yah Abdallah ba tuni gabanta ya k'ara tsananta fad'uwa itafa harga ALLAH bata son abinda zai dinga had'asu ita dashi batak'i bama idan cikin mutane ne shima d'in saiya zama dole kamar wannan lokacin. Coffee color d'in yadi ne a jikinshi mai kauri riga da wando wanda aka yiwa aiki da bak'in zare wanda ya zauna sosai jikin yadin da kad'an rigar ta wuce cinyarshi, sumar kanshi tasha gyara sosai anyi mata wani style na gyara mai k'ayatarwa kasancewar shi fari yasa yadin yayi matuk'ar haskashi, hannunshi d'aya soke cikin aljihun wandonshi d'ayan kuma yana rik'e da wayarshi ya k'arasa inda suke shikuma kusa da k'afar Ayyah ya nema ya zauna ya gaishesu kawai ya cigaba da latse latse a wayarshi kanshi a k'asa,wani aiki sai Abdallah Madugu 🤔tunda dai yaga anyi zaman nan yasan abune mai muhimmanci yataso amma saboda shegantaka yazo ya fara danne dannen waya kuma shi iya gaskiyarshi kenan hakan kamar bawani laifi bane yake gani, dukansu kallonshi suke banda Janaan data kasa ko d'agowa dan karma su had'a ido dashi, gyaran murya Abbie yayi yace "Ajiye wayar nan Modibbo magana zamuyi very important daku". "Okay Abbie". Ya fad'a tareda d'ago kanshi ya kashe wayar ya ajiyeta gefenshi ya maida hankalinshi kansu danjin abinda suke tafe dashi. Saidaya nemi Ayyah ta fara yin magana tace masa ta bashi dama yayi jawabi kawai. Da bismillah Abbie ya fara ya d'ora da yiwa ANNABI MUHAMMAD sallallahu alaihi wa alihi wasallam salati sannan ya fara fad'in abinda ya tarasu a wajen. "Kamar yadda kukaga munyi kiranku nan zamane da muke fatan ya zame mana alkhairi gaba d'aya mu daku muna fatan kuma zakuyi mana biyayya kamar yadda aka umarci y'ay'a suyiwa iyayensu". Kai kawai Abdallah ya jinjina yayin da Janaan tace "Insha ALLAH". Cikin y'ar rawar murya har zuwa lokacin bata d'ago kaiba. "Masha ALLAH. Abbie ya fad'a ya d'ora da fad'in "Modibboo! Daga yau inaso ka fara yiwa Janaan kallo a matsayin matar da zaka aura dan munaso mu had'aku aure kaida ita". Duk yadda Janaan taso nuna jarumta da nuna abin bai dameta ba lokacin da maganar Abbie ta shiga cikin kunnenta hakan ya gagara dan da wani irin mugun sauri ta d'ago kanta tana kallon Ammi da itama d'in take kallonta daga irin kallon datake mata tasan cewa alfarma take nema a wajenta na karta musawa maganar da Abbie yazo da ita duk da Ammin tasan mawuyacin abune Janaan d'in tayi hakan, saitaji kamar duk ta d'add'aure tane da jijiyoyin jikinta dan haka ta maida kanta k'asa idanunta cike fal da k'walla sai wani fat fat gabanta keyi da tsabar tsorata da maganar tanajin tamkar a mafarki hakan ke faruwa. Shikam Madugu kallo d'aya idan kayi masa bazai sa mutum ya gano ainahin abinda ke fuskarshi ba sai b'ata fuska kawai yake ya had'e ran nan gabas da yamma kallonsu kawai yake d'aya bayan d'aya kafin yace "Nifa Abbie ban gama fahimtar kuba ana nufin aure za'a had'ani da wannan yarinyar wadda ko cikakken energy bata dashi(Kai Madugu 🤦🙄) ya k'are maganar yana nuna k'irjinshi da hannunshi da Janaan d'in datake jin tamkar ta tashi taga mafarki ne take ba gaske bane. "K'warai kuwa har mun riga da mun yanke hukunci akanku". Ayyah ta bashi amsa. Kai ya shiga girgizawa yana fad'in "Habaaa mana Ayyah nifa banason yarinyar nan saboda banason raini ya shiga tsakaninmu da ita impact ma ni ba yanzu zanyi aure bama dan ALLAH ku canza magana please". "Dole kuwa haka zakayi hak'uri da wannan zab'in da mukayi maka bawai sonka ne bamayi ba a'a tsananin son naka da mukeyi ne yasa muka zab'a maka matar da muke ganin ba wadda ta dace dakai irinta saboda hak'urinta dan ba kowacce mace bace zata iya zama da rigimamme irinka ba dan haka kayi hak'uri kawai ka amsa da hannu bibbiyu insha ALLAHU alkhairi ne". Ayyah ce tayi maganar tana kallon Abdallah. "Nifa kawai a ruguje wannan maganar inba hakaba wllhy saina tada hankalin kowa a gidan nan kowa yasan halina b....tsawar da Abbie ya daka masa ce yasa shi yin shiru bai k'arasa abinda yayi niyyar fad'a ba kafin Abbie yayi magana Ayyah ta rigashi da cewa "Kayi hak'uri maigidana wannan abinda kag....."Nifa nace bazan aureta ba auren dole zakuyi min n..... kyakkyawan marin da aka sakar masa a kuncinsa ne yasa bai k'arasa maganar daya faro ba, gurin da aka mareshin ya dafe tareda d'aga kanshi ya kalli Abbie dake tsaye a kanshi yana huci wanda sam baisan lokacin daya taso daga inda yake zaune ba, cikin b'acin rai Abbie ke fad'in "Ayyahn kake fad'awa haka saboda bakada mutunci? Ashe dama bakada kirki ban saniba? To bari kaji abinda zan fad'a maka aure kaida Janaan babu fashi ba gudu baja da baya ban haifi d'an dazai dinga raina mahaifiyata ba, yana shirin d'orawa Ayyah ta katseshi da fad'in "Ya isa haka koma ka zauna". K'wafa Abbie yayi ya koma inda ya taso ya zauna yana kallon Abdallah daya k'ara had'e fuska har lokacin bai cire hannunshi daga inda Abbie ya mareshi ba, Janaan kuwa k'asa k'asa take kukanta cikeda d'imbin tararrabin wannan babban al'amarin dayake tunkarota aure itada Yah Abdallah? Bala'i kenan tarasa ta yadda zata fassara lamarin nan mai kama da almara. "A karo na farko zan baka umarni kuma dolenka kabi ko kanaso ko bakaso dole zaka auri Hassana kayi rayuwa da ita a matsayin matarka kum.....Bai k'arasa jin abinda zatace ba ya mik'e tsaye da sauri harda buga k'afa ya nufi hanyar fita daga falon. "Modibbo! Modibboo!! Ammi ta shiga kiranshi amma sam bai juyoba ya fice, tashi Abbie yayi yana shirin binshi Ayyah ta dakatar dashi komawa yayi ya zauna yana fad'in "Ayyah ki k'yaleni inci uban yaron nan tunda bashida mutunci". Kai ta girgiza tace "Rabu dashi ya gama haukan nashi dama aiya saba aure ne dai babu fashi ku zuba masa ido kawai". Kai kawai Abbie da Ammi suka jinjina mata, kallonta ta maida kan Janaan ta kira sunanta a hankali tace ta d'ago ta kalleta da k'yar Janaan d'in ta d'ago kai ta zube idanunta da sukayi jawur kan Ayyah. "Kiyi hak'uri kinji Hassana kar wannan buyagin nashi ya dameki muna rok'on alfarma dai a wajenki dan ALLAH kibamu had'in kai insha ALLAHU aurenku alkhairi ne kiyi mana wannan alfarmar karki gujewa wannan auren". "Insha ALLAH Ayyah". Janaan ta fad'a cikin rawar murya ruwan hawaye na k'ara taruwa cikin idanunta batasan meyasa har su Abbie sukayi tunanin had'ata da Yah Abdallah ba to taya ma zasuyi zaman auren? Tambayar datake ta faman nanatawa cikin ranta kenan. "Tashi kije ALLAH yayi miki albarka". Maganar Ayyah ta katse mata tunanin datake, cikin sanyin jiki ta tashi ta fita daga falon, saida suka k'ara d'an tattaunawa sannan Ayyah ta fita daga falon ta koma nata bedroom d'in. 2/17/22, 16:17 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Oum Hanan Page 20. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* √^√^√^√^√^? Da k'yar Janaan ta isa bedroom d'insu saboda jirin dataji yana d'aukarta tana shiga ta zube kan gado ta saki kukan da tun d'azu take rik'eshi, Hassana dake gaban mirror tana shafa lotion dan fitowarta kenan daga wanka ta taso ta nufo inda Janaan take kwance wajen kanta ta zauna ta dafa bayanta tana tambayarta abinda yake damunta, bata amsa mata ba ta cigaba da kukanta yayin da Hassana ta cigaba da tambayar ta, a haka har Hussaina itama data fito daga wankan ta samesu, itama wajen ta k'arasa ta zauna tana tambayar Hassana meye yasamu Janaan d'in?. "Wllhy ban saniba sister nima haka dai naga ta shigo ta kwanta tanata kuka kuma inata tambayarta meyake faruwa tak'i magana". Hassana ta fad'a tana kallon Hussaina. Ganin yadda duk suka damu da kukan datake sunata faman tambayarta kamar suma zasuyi kukan hakan yasa ta mik'e zaune suka sata a tsakiya suka zuba mata ido duk suna kallonta dan jin abinda zata fad'a, hannu Hussaina takai fuskar Janaan ta share mata hawayen dake gangarowa saman kumatunta tace "Please sister dan ALLAH ya isa haka kiyi shiru ki fad'a mana meye damuwarki kin tayar mana da hankali wllhy say something mana please". Cikin rawar murya sf nida Yah Abdallah". "Eyeee". Hassana ta fad'a da k'arfi tana zaro ido Hussaina ma k'irji ta dafe tana fad'in "Bala'i aure da Yah Abdallah?". Kai Janaan ta jinjina musu tana share hawaye, shiru duk sukayi aka rasa mai magana kowa da sak'e sak'en dayake a cikin zuciyarshi, ajiyar zuciya Hussaina ta saki tace "Dank'ari! Dole kiyi kuka sister zaman minti d'aya ma idan mutum yayi da Yah Abdallah ai saiya wahala bare zaman aure na din din din da ake saka ran sai mutuwa ce zata raba?. "Hmmm ganemin hanya dai sister ni wllhy narasa abin fad'a ma ciwon kaine dai zakisha shi dan Yah Abdallah ma yafi headache wllhy ni bansan ma meyasa su Ammi sukayi wannan tunanin ba wllhy kaiii Yaa ALLAH". Ta k'arasa maganar tana dafe goshinta. Anan dai suka cigaba da jajanta lamarin suna k'ara kwantar mata da hankali. √^^√^^√^^? Kai tsaye inda yayi parking motarshi bayan dawowar shi gidan ya nufa ya bud'e ya shiga ya zauna ya tayar ya shiga danna uban horn mai azabar k'ara wanda ya gigita Baba maigadin harya rasa ta inda zai fara bud'ewar da k'yar dai ALLAH ya bashi sa'ar bud'ewa aikuwa da gudu ya fice daga gidan tamkar zai tashi sama, Baba maigadi yabishi da kallo yana tunanin waye kuma ya tab'o wannan hargitsattsen mutumin?. Da mugun gudu ya dinga jan motar zuciyarshi namasa zafi, meyasa za'ayi masa haka saboda me za'a had'ashi da wadda sam zuciyarshi bata tab'a jin sonta ba yana daf da fallasa sirrin zuciyarshi a gurin wadda yakeso yake k'auna kuma yake muradin tazama matar aurenshi? Dan me za'ayi masa kutse cikin al'amuranshi? Yasan tunda Ayyah ta shiga maganar shikenan zance ya b'aci dan yasan Abbie bazai tab'a juyawa umarninta baya ba saboda yadda yake mata matuk'ar biyayya da kyautata mata. "Oh My God". Ya fad'a da k'arfi yana cije baki gamida dukan sitarin motar so yayi fa cikin month d'in nan yaje yayi surprising d'inta ta yadda zai gigita tunaninta dan yasan zatayi mamaki matuk'ar mamaki. Gefen titi ya gangara yayi parking ya had'a kanshi da sitarin ya shiga tunanin ta yadda zai b'ullowa lamarin kamata yayi yasamu Janaan d'in yaci uwarta tunda munafuka ce ita idan bata sonshi dan me bazata fito ta fad'a ba ita ga mai ladabi da biyayya ko zaici ubanta kuwa, da sauri ya k'ara tada motar yayi reverse ya koma gidan. √^^√^^√^^?. A kasalance ta fito falon dan d'aukar ruwa a kitchen fridge d'in bedroom d'insu kuma duk babu ruwa sai drinks hakan yasa ta fito d'auka a kitchen, gaba d'ayanta yau batada walwala jinta take tamkar wadda tayi wata da watanni a kwance ba lafiya duk wani kuzarinta babu a hakan ma dan Ayyah ta sameta har bedroom ta k'ara kwantar mata da hankali da k'yar ma tasamu tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na wani plain material light blue ta saka k'aramin hijab kalar kayan. Bata samu kowa a falon ba dan haka ta wuce kai tsaye k'ishirwa take ji sosai, tana daf da shiga kitchen d'in taji anyiwa hannunta wani irin fisga dayayi mugun tsorata ta tunda sam bataji motsi ko shigowar wanda ya kamata d'in ba,amma koda bata d'aga kai ta kalla ba tasan kowaye, idanunta ta d'an runtse saboda damk'ar dayayi wa hannun nata ba k'arama bace da iya k'arfinshi ya rik'eta. Bata turje ba sam dan tasan duk turjewar datayi hakan bashi zaisa ya saketa ba sai kawai ta cigaba da binshi da sauri dama kuma da saurin yake janta ko kallonta bayayi. Da k'afa ya tura k'ofar falon shi bayan isarsu part d'in suna shiga yayi wurgi da ita kan kujera bayanta ya bugi bayan kujerar, Ido kawai ta runtse gam zuciyarta cikeda wani irin tsoro sai harbawa take, k'aramin fridge d'inshi dake falon ya isa ya bud'e ya d'auko k'aramar robar ruwa na Eva ya b'alle murfin yakai bakinshi ya shiga sha. A hankali ta bud'e idanunta ta zubesu a kan Abdallah daya d'aga bakin robar yana shan ruwa, da azama tayi saurin kauda idanun nata tayi k'asa dasu tareda sakin wata b'oyayyiyar ajiyar zuciya tanajin tamkar tayi fiffike tabar d'akin tsabar zullumin abinda zai mata. Kad'an ya rage ruwan ya rufe ya cilla robar kan kujera, wata k'aramar kujera ya turo da k'afarshi zuwa gaban Janaan ya tako inda take ya k'ara matsar da kujerar gabanta sosai yayi wani irin zama na rashin mutunci. Tuni bugun zuciyarta ya k'ara tsananta taji tamkar ta saki fitsari saboda tsoro kanta a k'asa batayi gigin d'agowa ba bare har su had'a ido dashi bak'ak'en maganganu ne dai tasan zata shasu da zagi idan ma tayi sa'a bai had'a mata da duka ba. "Look at me". Ya fad'a cikin wata irin hargitsatstsiyar murya data k'ara tsoratata, kasa d'agowa tayi saboda idanunta da suka ciko da k'walla. "I said look at me". Ya fad'a cikin tsawa kamar zai daketa, a firgice ta d'ago ba tare data saniba ta kalleshi, sosai ya k'ara tsare gida ya wani k'ank'ance mata ido na tsabar masifa yace "Tun yaushe kika fara sona?". Wani iri taji tambayar yaushe tafara sonshi kuma? Lallai Yah Abdallahn nan shida a zatonshi sonshi take?. "Zaki fad'amin ne kokuwa sainaci ubanki". Taji amon muryar shi cikin kanta. A hankali cikin rawar murya tace "Yah Abdallah ban fahimci abinda kake nufi bafa ni?". "Okeyyyy kice mahaukaci ma kika maidani ko?". Yayi maganar yana kaiwa bakinta duka da sauri ta goce tana dafe bakinta bai sameta ba, k'wafa ya saki ya k'ara gyara zamanshi yace "Janaaan ki fadamin dalilin dayasa lokacin dasu Ayyah ke maganar had'amu aure baki fito kin nuna musu bakya sona ba?". Kamar zatayi kuka tace "Amma Yah Abdallah tayaya zan bijirewa maganar su Ammi koda ace ban......"Shut up munafuka ya katseta cikin hargagi shirun tayi ta sunkuyar da kanta k'asa, cigaba yayi da fad'in "Kega mai ladabi da biyayya ko? Tun wuri ki fito ki nuna musu bakya ra'ayin auren nan tunda ni ba za'aji magana taba idan ba hakaba kuma ko? Baki kawai ya cije yana jinjina kai, tsaye ya mik'e ya soke hannayenshi cikin aljihun wandonshi yace "Tashi kibar d'akin nan". Zumbur ta mik'e kuwa tamkar wadda ke jira kuwa dama kamar akan k'aya take, ta gefenshi ta rab'a ta wuce da sauri tun kafin ya canza shawara ya mata lilis dan kad'an daga cikin aikinshi. Ruwan da bata shaba kenan duk da matsananciyar k'ishirwar datake ji kuwa ta koma bedroom, kai tsaye bathroom ta wuce bayan shigarta, gefen bathtub ta zauna ta shiga raira kuma mai tsuma zuciyar mai saurare, batajin duk wannan kurarin zaisa ta musantawa su Abbie mutumin daya d'auketa tamkar d'iyar daya haifa da cikinshi, tako wane b'angare baya bambanta ta da y'ay'an daya haifa duk da dai bawani dad'ewa tayi a gidan sosai ba amma ya mata alkhairi masu tarin yawa da bazasu fad'u ba to danme ita zata watsa masa k'asa a ido? Ta b'angaren Ayyah ma tanajin tamkar ta isa da itane tanajin sam bazata iya bata umarni ta k'etara shiba tsabar yadda take ganin girma da k'imarta, sannan uwa uba kuma Ammi wadda takejin tamkar ita ta tsuguna ta haifeta saboda k'aunar datake nuna mata idan ta bijirewa maganarsu kamar tayi musu butulci ne wanda bata fatan hakan ta kasance, zatayi biyayya kuma zata jure duk wasu halayen Yah Abdallah ko don jin dad'insu zatayi iya yinta taga ta kyautata musu ALLAH ya bata ikon yin biyayya kamar yadda ta k'udurce a ranta. √^^√^^√^^√^^√^^? Gaba d'aya yinin ranar Abdallah bai k'ara neman kowa ba a gidan kamar yadda ba wanda ya nemeshi dan haka Ayyah tace a k'yaleshi yagama fushin nashi ya sauko da kanshi dan haka ba wanda ya k'ara bi takanshi . Sai k'arfe 12:10@m sannan yadawo gidan dama saidaya siyo take away d'inshi a wani restaurant, bayan dawowarshi yayi wanka yaci fried chicken and rice daya siyo kad'an yaci ma yaji duk ya ginsheshi gefe ya tureshi ya tashi ya nufi fridge ya d'auko exotic ya tsiyaya a tambulan d'in dake saman fridge d'in ya koma ya zauna yana sha, bayan ya gama ya d'aura alwalah yayi raka'ah biyu sannan ya kwanta bayan ya karanto addu'ar kwanciya barci anan fa barci ya k'auracewa idanunshi ya shiga tunanin mafita na wannan al'amarin daya tunkaroshi, saidaya dad'e yana sak'a da warwara a zuciyarshi sannan ya yanke shawarar abinda zaiyi basai sun k'ara ganinshi bama har su aura masa itaba. Ta b'angaren Janaan ma haka barci ya gagari idanunta duk juyin da zatayi magana d'aya ce ke yawo cikin brain d'inta wai zata auri Yah Abdallah mutumin da suke mugun jin tsoronshi baya wasa dasu ko kad'an, tun tasowar su ta fahimci bashida dad'in zama wai kuma a haka shine zai zama mijinta? To takai tsoron nashi ina? ALLAH dai ya kawo mata mafita ta alkhairi cikin rayuwar ta. Mrs Salees Mu'az 💝 2/19/22, 19:12 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 21. Paid book Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Washegari ma bai shiga gaida kowaba a gidan tun wuri ma ya fice daga gidan ya nufi office dama yanada appointment dawasu dazasu bashi contract na zanen wata ma'aikata da za'ayi musu. Zaune yake a had'add'en office d'in nashi wanda yaji kayan alatu wanda ake k'awata manya manyan office's dasu, daddad'an turaren jikinshi ne ya had'u da sanyin AC dake cikin office d'in ya bada wani kalar k'amshi mai dad'in gaske mai kwantar da hankali, yana kan k'atuwar chair office ya d'an dafe kanshi da hannunshi sai faman jujjuyawa yake, so yake yaje ya bawa su Ammi hak'uri ya kuma amince da buk'atar su ta auren Janaan yayin yunk'urin yin hakan yafi sau nawa wata zuciyar na hanashi yin hakan da nuna masa kawai ya bijire idan sukaga haka zasu janye maganar, tsaki ya saki a karo na ba adadi zuwa yanzu dai zuciyar dake hanashi d'in ta rinjayi waccan dan haka ya janyo wayarshi dake kusa da labtop d'inshi akan babban table d'in gabanshi ya fara neman number Habeeb yayi calling d'inta, harta gama ringing ta katse ba'a d'auka ba ya k'ara kira nan d'inma ba'a d'aga ba. "D'an iska ko gidan uwarshi yakai wayar da aketa faman kira bai picking ba". Yayi maganar a fili yana k'ara gwada kiran a karo na uku, sai daf dazata tsinke sannan Habeeb yayi picked up aikuwa kamar jira yake ya shiga d'ura masa zagi wai uban meyasa yak'i d'aga masa waya yanata kira tun d'azu? Tsaki kawai Habeeb yaja yace "Kanada matsala wlhy Madugu dan ubanka kasan uzurin daya hanani yin picking d'in akan lokaci?". "Wane uzuri daya wuce iskanci dayake damunka, koda wani abu daya wuce wannan?". "Ban saniba dallah meye kake kirana?". "Kana gidane?". Abdallah ya tambaya "What happened?". Cewar Habeeb. "Idan ban d'ura maka ashar ba Marafa ya ina tambayar ka kana tambayata". Sanin halin abokin nashi yasa bai wani damuba saima dariya daya k'yalk'yale da ita yana fad'in "I'm sorry A.B Madugu ina gida amma ina daf da fita fa zanje inyi signing wajen kayan nan dana baka labari nayi order". "Owk ka jirani ina zuwa yanzun". "Alright! But kayi sauri fa inba hakaba zaka samu nayi tafiya ta". "Ka tafi mana kagani idan banci uwarka ba banza". Abdallah ya fad'a yana sakin k'wafa, wata dariyar Habeeb ya saki sannan yayi hang up d'in kiran yana cigaba da dariyar shi a fili yake fad'in "ALLAH ya shiryamin abokina, shidai bai tab'a ganin mai irin halayyar A.B Madugu ba yanzu saiya cazawa mutum kai dan yanzu zai zama mutumin kirki minti goma sunyi yawa ya hargitse tamkar wani mai jinnu, yanzu zakaga ana hirar arzik'i dashi anjima kad'an saiya botsare aga kamar bashi ba idan bazai manta ba sun tab'a had'uwa da wata budurwa a wajen shan ice cream cousin d'in wata abokinsu ta nuna tanason Abdallah rimi rimi ya nuna kamar ya yarda suka shiga hira da yarinyar kamar abin arzik'i baiyi auneba kawai yaji yana zagin yarinyar duk da yana d'an nesa dasu hakan bai hanashi jiba yanada yak'inin dai yarinyar ce tayi masa wata maganar da bata gamsheshi ba shiyasa ya antaya mata zagi yabar wajen yarinyar ta bishi da kallon mamaki da tunanin wannan wane irin mutum ne haka? Lokacin da Habeeb ya isa inda yake har ya shiga mota shima ya shiga suka tafi nan Habeeb ya dinga faman tambayarshi abinda yarinyar tayi masa tunda ya danna masa zagi yaja bakinshi ya tsuke (ALLAH ya shirya 🤦 mutum saikace d'an maguzawa😬). Wata dariyar Habeeb ya k'ara saki yana girgiza kai lokacin daya gama tuna labarin duk cikin abokansu shi kad'ai ne yakeda juriyar zama da Abdallah shiyasa har sauran suke ganin kamar ko tsoronshi yakeji kuma a zahiri ba haka bane kawai dai yasan akwai mutane irinshi masu wahalar zama duk da dai basu cika yawa ba gaskiya da kuma jininsu da ALLAH ya had'a tun yarinta. Cikakkun mintuna goma ne suka kaishi gidansu Habeeb parking yayi a harabar gidan ya kulle motar, harya fara tafiya yaji muryar maigadin gidan ya biyoshi yana gaisheshi hannu kawai ya d'aga masa yayi gaba abinshi harya d'an fara nisa kuma saigashi yadawo inda maigadin yake hannu ya zura a aljihun wandonshi na baya ya ciro kud'i masu yawa wanda shi kanshi baisan ko nawa bane ya mik'awa maigadin hannu biyu yasa ya karb'a bayan ya rissina ya shiga zuba masa godiya da addu'o'e wanda sam Abdallah bai tsaya jinsu ba bare ya amsa ya nufi inda part d'in Habeeb inda yake kafin a k'arasa cikin gidan, da niyyar knocking ya tab'a k'ofar amma saiyaga ta bud'e shiga, anan falon yasamu Habeeb kwance kan kujera dagashi sai boxer da waya a hannunshi bai aune ba yaji an dakar masa k'eya yayi saurin tashi zaune yana dafe wajen tareda kai kallonshi kan Abdallah dake tsaye a kanshi yana hararar shi. "ALLAH ya isana kawai mugu". Abinda Habeeb ya fad'a kawai shima yana hararar Abdallahn, wuceshi Abdallah yayi ya zauna kan kujerar dake facing ta Habeeb yayi crossing legs nashi yana kallon Habeeb tareda fad'in "Dama k'arya kakemin dakace fita zakayi ko, shine naganka daga kai sai gajeren wando ko a haka zaka fita mara mutunci". Dariya Habeeb yayi yace "Ko d'aya wllhy zan fita d'in amma zuwa anjima nagane idan ba haka nayi makaba saika d'auki wani lokaci bakazo ba". K'wafa Abdallah yayi yana shirin yab'a masa bak'ar magana Habeeb ya tari numfashin shi da fad'in "Yane wai mutumina naganka duk kamar ba'a nutse kake ba what happened to you?". Saidaya hura iskar bakinshi ya dafa hannayenshi a gefe da gefen kujerar sannan yace "Ka bari kawai Marafa yaji nayiwa y'an gidan kuma banaso asan cewa ina gidanku kuma koda an nemeka an tambayeka karka sake ka fad'i cewar ina nan duk neman da za'ayi min kuwa, idan kuma ka sake ka bayyana hakan kasan halina sarai basai wani ya baka labari ba Marafa k'aramin aikina ne in kamaka in maka bugun tsiya dan haka ka kame bakinka". "Ai dayake ga wawa sai in tsaya ka dakeni ko". Habeeb ya fad'a yana hararar Abdallah, baki ya cije yace "Ka gwada kagani mana, tsaki Habeeb yaja yace Wai tsaya ma in tambayeka, wannan guje gujen duk na meye hala wani babban laifin kayiwa su Abbie kazo zaka nemi mafita a gurina". "Auren dole zasuyi min ". Ya fad'a kai tsaye yana kallon Habeeb dayayi masa k'uri da ido yana kallonshi, da mamaki Habeeb yace "Auren dole kuma? Kamar wata mace? Kai bansan iskanci fa kayimin bayani dalla dalla yadda zan fahimta". Baki kawai Abdallah ya tab'e gamida d'age kafad'a batare dayace komi ba. Da mamaki Habeeb yace "Aure? Da wace yarinyar to?". "Janaan mana". Abdallah ya bashi amsa. Ido Habeeb ya zaro tareda fad'in "Ah haba dan ALLAH Janaan dai dana sani ta gidanku?". "Munada wata Janaan d'ince dan ubanka". Amsar da Abdallah ya bashi kenan yana sakin k'wafa. Dariya Habeeb yayi yana kad'a kai kafin ya maida fuskarshi tazama serious yace "In baka shawara Madugu?, Ido kawai Abdallah ya tsura masa baiyi magana ba, ganin haka yasa Habeeb ya cigaba da fad'in "Dan ALLAH A.B karka guji yarinyar nan tanada duk wasu qualities da mutum keso matar aurenshi ta kasance dasu, kaga tanada hankali hak'uri kawaici da sanyin hali itace daidai dakai wllhy idan mukaci sa'a saikaga ta dalilinta ALLAH ya shirya mana kai". "Wato ga rik'akk'en d'an iska ko?". Abdallah ya fad'a yana dallawa Habeeb harara. Y'ar dariya Habeeb yayi yana girgiza kai yace "Nidai bance ba kai inama ka damu da matan bare kayi iskancin kawai dai halayenka ne idan ba mace irin Janaan d'in kasamu ba mai hak'uri da wuya zaman yayi dad'i bawai fatan hakan nake maka ba misali twin sister d'inta Jauhar ko tanada zafi kaima haka so had'inku gaskiya is not perfect kaida ita kayi hak'uri dan ALLAH ka karb'i auren yarinyar nan ka kuma yiwa su Abbie biyayya". "Malam ka k'yaleni ni auren ne gaba d'aya ban shiryawa yinshi ba yanzu kuma akwai wadda nakeso lokacin da zan bayyana ne baiyiba". "Wace ita?". Habeeb ya tambaya. "Basai kaji ba". Haka kawai Abdallah ya fad'a yana kishingid'a akan kujerar dayake zaune. Duk yadda Habeeb yaso fahimtar da Abdallah abin ya faskara yak'i saurararsa sam k'arshe dai da Habeeb d'in yaga yana neman b'ata masa lokaci gashi zai fita sai yayi watsi dashi ya tashi ya hau shirinshi dama yasan bazai saurareshi ba yadda yake da shegiyar kafiyar nan, ko sallama baiyiwa Abdallah ba lokacin dazai fita shi a lallai fushi yake dashi shima Abdallahn ko a kwalar rigarshi ya dad'e baiyi fushin dashi ba, wanka ya shiga bathroom yayi ya fito ya shirya cikin kayan shan iska na Habeeb ya kwanta bayan ya kashe wayoyin shi duka. √^^√^^√^^√^^? Tun Ammi na zuba idon ganin Abdallah ya shigo gidan harta daina, rashin shigowar tashi kuma ta fara damunta har Abbie tayiwa maganar ya nuna mata karta damu ta k'yaleshi kawai tunda fushi yake dasu idan yayi yagama zai nemesu amma duk da haka dai Ammi ta kasa hak'ura saidata Hussaina part d'inshi tagani ko yana nan tadawo tace baya nan part d'inma a kulle yake duka ga layukan wayarshi duk a kulle bataso kuma Ayyah ta farga da halin da ake ciki Abdallah bai kyauta musu ba. Mrs Salees Mu'az 💝 2/21/22, 09:24 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 22 Paid book Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Kwana d'aya ba Abdallah ba labarinshi ga layukan wayarshi da har yanzun suke a kashe, zuwa yanzu dai hankalin Ayyah da Abbie dasu Hassana yafara tashi. Ammi kuwa tafi kowa shiga damuwa a gidan saboda tasan halin d'anta duk inda yaje to kuwa zai dawo gida saidai idan baya k'asar ne gaba d'aya kokuma baya garin shi sam ma irin yawace yawacen nan na samari bai cika yiba to ina yaje haka??? Tambayar da kowa yake nanatawa cikin ranshi kenan. Habeeb dai ganin fushin nashi ma bai d'ad'a Abdallah da k'asa ba yasa ya sauko tunda baiga amfanin shiba, shi wanda akayi dan shi baima san anayiba dan kayi fushi da Abdallah ai kayi ta banza baisan kanayi ba. Ya zuwa yanzu dai Abbie ma daya nuna kamar bai damu da rashin Abdallah ba yafara fito da tashi damuwar k'arara tunaninshi d'aya ina Abdallah ya tafi haka? shi kanshi shaida ne yaronshi bai iya kwanan wani wajen ba wato ya nuna musu basu isa dashiba kenan shikuma zai nuna masa su suka haifeshi suke kuma iko dashi bashi yake iko dasu ba ALLAH dai yadawo dashi gidan. Kullum Ameen cikin neman inda Abdallah yake duk y'an uwa na nesa dana kusa an kikkira an tambayesu ko Abdallahn yazo nan sunce a'a hakan ya k'ara d'aga hankalin su Ammi sosai. ∆√∆√∆√∆√∆√∆√? Yau kimanin kwana uku da yini d'aya kenan ba labarin Abdallah, Ameen duk inda yasan Abdallah yanada alak'a dasu yaje amma baya can. A gajiye ya shigo gidan nashi saboda yawon dayasha a mota na neman Abdallah, cikeda farin ciki Fareedah matarshi ta tareshi ta bashi kulawar da duk wata macen k'warai ya dace tabawa mijinta a duk lokacin daya dawo gida. Saidaya nutsu sosai ya huta sannan ta tambayeshi labarin Abdallah, sai daya sauke nannauyan numfashi kafin yace "Abdallah shiru wllhy har yanzu bansan ina d'an banzan yaron nan ya shigeba wlhy yaro kamar wani aljani". Shiru Fareedah tayi alamun tunani zuwa can tace "Nikam mezai hana ka nemi wannan best friend d'in nashi Habeeb Marafa yake kowaye ne". "Woww very very good idea, meyasa tun tuni banyi tunanin Habeeb ba?". Murmushi tayi tana d'an tab'e baki gamida d'age kafad'a tace "Atoh sai anyi magana kuce kunfi mata basira bayan kuma kwanyar mu nakawo light". "Very light ma my Feedy wllhy sam banyi tunanin neman Habeeb ba saboda yadda kaina ya d'auki zafi thank you so much bani wayata in kirashi tun yanzu". Wayarshi dake kan center table ta d'auko masa yafara laluben number Habeeb yayi dialing d'in number bayan ya nemota. Habeeb dake zaune a office d'inshi yana ganin kiran Yah Ameen ya kasa d'agawa dan fargabar abinda zaice masa musamman da Abdallahn ke k'ara jaddada masa karfa ya sake koda bincike zai biyo ta kanshi ya sanar dasu inda yake yanzu gashi Yah Ameen na kiranshi kuma ko kaffara bazaiyi ba yasan kan maganar Abdallahn ne gashi yana matuk'ar ganin girman Ameen d'in saboda mutum ne shi mai kama girmanshi idan ya d'aga ma baisan me zaice masa ba......Wani kiran ne daya k'ara shigowa kusan karo na uku ya katse masa tunanin dayake, hannu yakai kan wayar ya d'aukota yayi picking yakai kunnenshi tareda sallama. A nutse suka gaisa da tambayar mutanen gida da al'amuran kasuwa kafin Ameen ya d'ora da tambayarshi labarin Abdallah, shiru Habeeb yayi kamar bazaiyi magana ba yana tunanin ya fad'i gaskiya ne kokuwa yace bai saniba amma idan ya fad'i gaskiya kamar baiyiwa Abdallah adalci ba tunda yayi masa alqawari bari dai yace bai d'in ba kawai, gyaran muryar da Ameen yayi ne yasashi fad'in "Gaskiya Yah Ameen bansan inda A.B yake ba nima two days d'in nan inata traying wayarshi bata shiga bansan meke faruwa haka ba". Tuni jikin Ameen yayi sanyi wato inda yake tunanin ma za'a sameshi d'in baya nan? Yaa ALLAH baisan kuma ina zai nemo yaron nan ba ga hankalin su Ammi da Ayyah dashi kanshi Abbien duk a tashe yake ido ya lumshe ya bud'e yace shikenan Habeeb nagode daga nan sukayi sallama. "Can d'inma baya nan". Fareedah data k'ura masa ido tun fara wayarshi ta tambaya, kai kawai Ameen ya girgiza mata baiyi magana ba. "Nikam ina ganin ka k'ara bibiyar Habeeb d'in nan tunda kaga fa Abdallah bashida wani babban aboki daya wuce shi so kaga komai idan zaiyi zai fad'a masa". Jinjina mata kai kawai yayi alamun yarda da maganar ta bari kawai yayi masa dirar mikiya a office d'inshi maybe idan yaganshi a gaban shi ya fad'a masa gaskiya da wannan tunanin Ameen ya yanke shawarar abinda zaiyi. √^√^√^√^√^√^? Washegari kuwa kamar yadda Ameen ya tsara yana fita daga gida ya nufi office d'in Habeeb bayan anyi masa iso ya shiga bakinshi d'auke da sallama, sosai gaban Habeeb ya fad'i ganin zuwan bazata d'in nan da Yah Ameen yayi masa, hannu ya mik'a masa sukayi musabaha bayan ya zauna, gaba d'aya Habeeb a d'arare yake daka ganshi kaga marar gaskiya sai zare ido yake, tashi yayi da nufin kawowa Ameen ruwa da lemo a fridge ya dakatar dashi yace sauri yake ya gode ya zauna magana zasuyi. Komawa Habeeb yayi ya zauna yana kallon Ameen da shima yake kallonshi, numfashi Ameen ya sauke yace "Habeeb tambayar ka zanyi ka fad'amin tsakaninka da ALLAH kasan inda Abdallah yake kokuma baka saniba? karka manta fa su Ammi nacan cikin damuwa da rashin tabbas na halin dayake ciki please karka b'oyemin Habeeb". Gaba d'aya Habeeb saiyaji tamkar Yah Ameen ya d'aureshi da jijiyoyin jikinshi ne yana matuk'ar ganin girmanshi da k'imarshi musamman dayake zaune yanzu a gabanshi saiyake jin bazai iya masa k'arya ba. Kai ya shiga gyad'awa tareda fad'in "Hakane Yah Ameen A.B yana gidanmu kuma kosu Hajiyata bata saniba afwan please shiya nemi hakan daga wajena ayi hak'uri". Ajiyar zuciya Yah Ameen ya sauke yace "Karka damu laifinka d'aya daka biyewa wannan shashashan yaron kai kanka kasan tsiyar Abdallah fa bai kamata ka biye masa ba yanzu dai duk ba wannan ba yana gidan naku a yanzu haka?". Kai kawai Habeeb ya gyad'awa Yah Ameen alamun eh, tsaye Yah Ameen ya tashi yana fad'in "Thank you so much Habeeb bari inje gidan naku in tafi da d'an banza marajin magana". Dariya kawai Habeeb yayi yace " Ayi masa a hankali dai yayanmu please nima akwai bak'in dazamu gana dasu yanzu dana biyoka mun tafi tare". "Karka damu nagode". Ameen ya fad'a tareda fita daga office d'in ya shiga mota ya nufi gidansu Habeeb. Kai tsaye side d'in Habeeb Ameen ya nufa bayan yayi parking a compound d'in gidan, a rufe yasamu k'ofar tsayawa yayi bakin k'ofar yafara knocking amma ba'a bud'e ba ya cigaba dayi amma shiru, saidaya b'ata mintoci masu d'an dama sannan yaji alamun antaho bud'ewa. Three quarter din wando ne a jikinshi milk color mai igiyoyi a jikin aljihunan wandon sai farar riga mai hula mai yankakken hannu yayi baya da hular bai sata a kanshi ba sai farin slippers mai taushi sosai dake sanye a farar k'afarshi, sweet ce a bakinshi yaketa faman tsotsa kamar wani yaron goye, ido ya zaro sosai lokacin da idanunshi sukayi tozali da Yah Ameen dake tsaye yana wurga masa wani irin kallo da sauri yayi baya Yah Ameen yabi bayanshi, tsaye yayi a tsakiyar falon ya wani had'e rai yana kallon Ameen daya zauna kan kujera da shima d'in yake masa kallo mai kama da harara. "Malam samu guri ka zauna magana zamuyi dakai". Yah Ameen yace Ba musu kuwa ya zauna d'in a kujerar kusa da Yah Ameen d'in shiru ya biyo baya kafin Yah Ameen ya katse shirun da fad'in "Meka aikata haka Abdallah? wane irin hukunci ne haka ka yanke batare dakayi tunanin meye zaije yadawo ba?". cewar Ameen yana k'urawa Abdallah ido. "Haba Yah Ameen bakaji abinda suke shirin yimin bane for God sake taya za'ayi min haka saikace wata mace ko wanda yazo irin zamanin da d'in nan kum........"Hakan dakayi a tunaninka shine daidai? kokuma shine maslahar dakake ganin zata fissheka? Yah Ameen ya katse masa maganar daya fara, kasan irin tashin hankalin dasu Ammi suka shiga kuwa haba Abdallah kasan girman hakkin iyaye akan y'ay'ansu kuwa ya kamata ka tsaya kayi tunani su Ammi basu cancanci haka daga wajenka ba dan ALLAH ka karb'i tayin da sukayi maka na auren Janaan karka watsa musu k'asa a ido ALLAH ya gani nima inason aurenku da Janaan saboda yarinyar akwai hankali ga hak'uri please Abdallah". Cikin sigar lallashi Yah Ameen ya k'arasa maganar yana kallon Abdallah dayake ta faman had'e rai yana d'an tura baki, a marairaice yace "To saboda ALLAH kuma sai ayimin haka Yah Ameen? nifa yarinyar nan matsayin k'anwa na d'auketa kuma yanzu sai ace za'a had'ani aure da ita". Murmushi Yah Ameen yayi yace "Ai ikon dasuke dashi a kanka shiyasa har sukayi tunanin hakan, Abdallah iyaye ba abin wasa bane karkayi abinda daga baya zakazo kana dana sani ka amince?". Ga mamakinshi saiyaga Abdallahn ya d'aga kai alamun ya yarda, lallai dole yayi mamaki saboda sanin halinshi na taurin kan tsiya da shegiyar kafiya amma kuma harya yarda yanzu. Cikeda farin ciki Yah Ameen yace "Masha ALLAH thank you very very much my brother yanzu ka tashi ka shirya muje kabasu hak'uri ka kuma fad'a musu ka amince da duk zab'in da sukayi maka shine daidai". Tsaye ya tashi ya shiga bedroom d'in Habeeb bayan y'an wasu mintuna ya fito ya shirya cikin wandon jeans blue black da dark blue d'in riga mai dogon hannu, sai baza k'amshi yake a gaba Yah Ameen ya tasashi suka fito ya rufe part d'in maigadi yabawa key d'in ya shiga motar Yah Ameen suka tafi da niyyar zai dawo ya d'auki tashi motar dake gidan. Suna tafe a hanya Yah Ameen na k'ara yimasa nasiha da nuna masa falalar bin iyaye da duk maganar da suka fad'a indai bai haura shari'ar musulunci ba, shidai yayi kwance kan seat d'in daya kwantar ya tallabe k'eyarshi da hannayenshi biyun yana sauraron Yah Ameen da haka har suka k'arasa gidan. Sosai su Ammi sukayi murna da ganinshi amma duk da haka saidata nuna masa b'acin ranta akan abinda yayi ya kuma bata hak'uri hakama Ayyah da kuma Abbie daya dawo gidan bayan shigowar su. Janaan kuwa tunda taji shigowar shi gabanta yake fad'uwa kasa fita ma tayi sam saisu Hassana ne sukaje suka masa barka da dawowa itadai tana d'aki tana faman sak'e sak'e a ranta. Mrs Salees Mu'az 💝 2/24/22, 16:22 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 24. Paid book Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Gudu gudu sauri sauri haka ta dingayi yana binta, shidai Baba maigadi da kallo kawai ya bisu baiyi azarb'ab'in tare Abdallah ko dakatar dashi ba saboda yanayin yadda yaga Abdallahn duk da yana girmama shi da ganin mutuncin shi amma yasan tsaf zai iya fad'a masa wata maganar da zata dad'e tana masa ciwo dan bai iya saita kanshi ba yayin dayayi fushi. Tana k'arasawa bakin k'ofar falon shima ya k'arasa ganin batada sauran wani gudu kuma kawai tayi surrender so take tayi masa bayani yadda zai fahimceta amma tasan bazai bata wannan damar ba. "Ni zaki rainawa hankali Janaan? dan ubanki sa'anki ne ni ko abokin wasanki da har zaki tsaya da wani a waje bayan dasa ranata a kanki har kina masa dariya". ya k'are maganar yana nuna k'irjinshi da hannunshi d'aya d'ayan kuma rik'e da belt d'in, kai kawai take girgiza masa ta rufe bakinta da hannunta tana k'unshe kukanta, kyawawan mari biyu ya sauke mata a kuncinta na hagu dana dama wanda ya gigita tunaninta, belt d'in ya d'aga zai kai mata duka ta k'wak'ume k'ofar tamkar zata shige cikinta tareda sakin wata siririyar k'ara mai k'arfi wadda Ayyah da Ammi da suke zaune a falon sukaji ta da sauri kuwa suka taso suka bud'e k'ofar dan ganin abinda yake faruwa. Saboda yadda ta matse da jikin k'ofar hakan yasa su Ammi na bud'ewa tayi taga taga zata fad'i k'asa saida Ayyah tayi saurin rik'ota ta had'ata da jikinta, a rud'e Ammi ke fad'in "Lafiya Modibbo meya faru meya had'aka da Janaan d'in?". "Ammi wasu take kulawa a waje ayi mata gargad'i idan ba hakaba wllhy zan karya yarinyar nan". "Kamar ya tana kula wasu a waje?". Ayyah ta fad'a cikin rashin fahimta tana d'ago kan Janaan datake kuka sosai ga bakinta daya fashe saboda marin datasha ga fuskar tata harta fara d'agawa. Cikin kuka Janaan tace "Ayyah Anas nefa wani d'an layin nan muke school d'aya shine yau na biyosu ban tsaya jiran driver ba shinefa na manta handout d'ina a motar ya fito ya kawomin". A fusace Ammi tace "Bakada hankali ne Modibbo, kan wannan abin zaka mata irin wannan dukan? mahaukacin inane kai? dan ubanka aure aka d'aura maka da ita dazaka yiwa mutane wannan haukan?". "Ammi ninaga abinda nagani dariya fa yarinyar nan take masa wato ga banza mahaukaci ta ajiye a gefe na rantse idan na k'ara ganinta dawani abinda zan mata saiya zarce wannan dan ubanta". cikin huci ya k'are maganar yana k'ok'arin maida belt d'in k'ugunshi. "Zoka kasheta Modibbo, nace zoka kasheta yanzu dan ubanka shashasha marar hankali kawai, inbanda hauka kawai daga ganinta da wani a tsaye saika hauta da duka ko kayi binciken abinda ya tsayar dasu? tunda akayi maganar aurenku ka tab'a kiranta koda na minti biyar ne kunyi magana da ita a matsayinta na wadda zaka aura? shine danka ganta dawani a tsaye zakazo kana nuna wani kishi na banza da wofi to wllhy ka kiyaye ni kaji na fad'a maka sakarai kawai ka dinga sassautawa ranka kana yak'i da zuciyarka tun kafin ta kaika ta baroka". K'ala Ayyah bata iya tofawa ba tayi tsaye kawai tana kallon zafin rai da zuciya irin na Abdallah anya basuyi wauta ba kuwa dasuka had'ashi da Janaan? ashe da labarinshi kawai take ji wajen su Hassana na bala'in shi itadai nata Abdallahin ba haka yakeba sam bashida hayaniya ga hak'uri da kawaici shikuma wannan kowa ya d'ebo a zuciya? dangin uwa kona uba ALLAHU A'ALAM, ALLAH masani. Hassana da Hussaina ma wad'anda suka fito tun d'azu saboda hayaniyar dasukaji na tashi a k'ofar falo, jikinsu banda tsuma ba abinda yake saboda tsoro, Janaan kam har yanzu hawaye take tana kuka k'asa k'asa Ayyah na d'an bubbuga bayanta alamun rarrashi. Hannun Janaan Ayyah ta kama suka koma cikin falon Ammi tabi bayansu da sauri suma su Hassana suka take musu baya tun kafin yayo kansu su shiga uku. Ido ya lumshe ya shiga sauke numfashi a hankali a jere a jere kafin daga bisani ya nufi part d'insa yana k'ara gyara zaman agogon hannunshi na fata daya karkace. Zazzaune suke a falon bakajin sautin komai sai kukan Janaan k'asa k'asa, har lokacin tana jikin Ayyah. Numfashi Ayyah ta sauke tace "Yau naga bala'i ganin idanuna haka dama maigidan nan nawa yake Hafsat?". 'Hmm gara dai da kika gani da idanunki tsohuwa da idan muna fad'a miki halinshi ai gwasalemu kike kega mai sunan mijinki'. Hassana ce tayi maganar cikin ranta tana tuna lokaci zuwa lokaci idan suka kaiwa Ayyah ziyara a yola idan suna mata hirar Yah Abdallah bashida dad'in zama saita faman kareshi tana ita maigidanta ba haka yakeba. Cikeda damuwa Ammi tace "Wllhy Ayyah lamarin Modibbo ya wuce duk yadda kike tunani abinda yasa na k'arfafa yin auren nashi kenan bansan ina ya kwaso wannan bak'ar zuciyar tashi ba iya sanina dai mai sunanshi ba haka yakeba yanzu dan ALLAH kuduba abinda yayi mata?". Kai kawai Ayyah ta shiga jinjinawa tana shirin magana Janaan tace "Ammi bafa ni kad'ai yayiwa haka ba". Idanuwa duk suka zaro Ammi tace "Ban ganeba me yayi masa Janaan?". Sai data share hawaye sannan tace "Ammi wllhy bakuga dukan dayayi masa ba da k'yar Baba maigadi dayaji hayaniya ya lek'o da kuma driver'n su suka k'waceshi suka sashi a mota". "Innalillahi wa inna ilaihi rajioun". Ammi ta fad'a tana dafe goshinta, Ayyah ma kai ta dafe tana girgiza kai, kai jama'a Abdallah kanshi d'aya kuwa? anya ba abinda ke damun k'wak'walwar shi kuwa?. "Yaron d'an gidan waye?". Ammi ta tambayi Janaan. Kafin Janaan tayi magana Hussaina tace "D'an gidan Alh Hamisu ne Ammi". Kai kawai Ammi ta jinjina batace komaiba. Kallon su Hassana Ammi tayi dasukayi tsuru tsuru tace "Kuje ku rakata tayi wanka sai akai mata abinci taci ta kwanta ta huta". Da 'Toh' suka amsa suka mik'e Janaan ma ta tashi suka nufi bedroom d'insu. "ALLAH dai ya sanyaya masa zuciyarshi wannan masifa dame tai kama, irinsu ne suke d'aukar mataki cikin fushi daga baya suzo suna dana sani". Ayyah tayi maganar tana kallon Ammi datayi tagumi. "Amin dai Ayyah, ni tunanina ma yaron nan bansan ya zamuyi dasuba hankalina duk ya tashi wllhy". "Ah dole fa za'aje a basu hak'uri tunda anyi musu laifi bari baban nasu yadawo saiyaje yasamu mahaifin yaron". "Shikenan Ayyah". Ammi ta fad'a cikin damuwa batasan yaushe Abdallah zai daina janyo musu magana ba kwanakin baya ma saida akayi wani case da iyayen wani yaro dawani abu ya tab'a had'osu ya masa dukan tsiya hardasu rauni yayi masa case d'in har police station saida akaje da k'yar dai Abbie yasamu case d'in ya mutu bayan yayiwa Abdallah gargad'in karya sake ya k'ara janyo musu fitina idan kuma ya janyo d'in zasu k'yaleshi da hukuma suyi duk abinda sukaga dama dashi babbar matsalar ma kuma shi baya tsoron hukumar a hakan ma kuma ana d'aga masa k'afa ne saboda mahaifinshi Alh Basheer wanda ake ganin k'ima da mutuncin shi a garin dama k'asar baki d'aya. Wanka Janaan tayi ta fito ta shirya cikin doguwar rigar plain material mara nauyi orange color tasa hula orange tayi sallah, tana idarwa Hassana ta mik'a mata plate d'in abincin data zubo mata jallof d'in macaroni da kifi, kai ta girgiza cikin sanyin murya tace "Bazan iya ciba bakina ba dad'i sanyi ma nakeji kamar zazzab'i ke son rufeni ga kaina yana min ciwo sosai". ta ida maganar tana k'ara rufe jikinta da hijabin jikinta datayi sallah. Gaba d'ayansu tausayinta ne ya kamasu dama wannan uban marin datasha ai dole kai yayi ciwo gaskiya lamarin nan da buk'atar su Abbie su k'ara dubashi tun kafin fa ayi auren kenan inaga anyi ankai masa ita gidanshi?. "Please sister kici ko kad'an ne dan ALLAH kinga fa haka kika fita d'azu ma da safe bakiyi breakfast ba". Hassana ta fad'a tana k'ara mik'a mata plate d'in, Hussaina ma baki tasa suka cigaba da rarrashinta da k'ara kwantar mata da hankali da haka suka samu ta d'an yafici abincin kad'an tasha paracetamol ta kwanta. Bai kara shigowa gidan ba fita yayi ya shigo da motarshi cikin compound ya koma part d'inshi, wanka yayi, yayi sallah ya kwanta batare daya tuna da abinda yayi ba danshi da iya gaskiyarshi yayi hakan kuma bawai don yana sonta ko kishinta yayiba kawai gani yake ta raina masa hankali ne inba rainin hankali ba taya ansa musu date d'in biki kuma tazo kan layi tana kula wani harda yimasa dariya? sai yanzu yakejin wani takaici ma dabai lakad'a mata dukan tsiya ba ta yadda bazata k'ara marmarin kula wani ba. Da wuri yau Abbie ya dawo kamar yasan abinda yaronshi yayi, Ammi bataso sanar dashi ba lokacin so tayi saiyaci abinci ya huta sannan ta fad'a masa rashin mutuncin da Abdallah yayi amma ganin yadda yanayin ta yake alamun tana cikin damuwa yasa ya tambayeta abinda yake damunta haka tunda bai saba ganinta hakaba dan Ammi macece mai sakin fuska da fara'a ga mutanen gidan da duk wanda zama ya had'asu da ita. Nannauyan numfashi Abbie ya sauke yace "Wai dan ALLAH meke damun Modibbo ne Hafsat? inbanda shirme da shashanci daga zuwa saika hau mutum da duka batare da binciken abinda ya tsayar dasu d'in ba shi idan baiyi neman magana ba bayajin dad'i, tsaki ya k'ara saki yana sauke numfashi ya zaro waya a aljihu yafara laluben number Abdallah yana fad'in "Bari in kirashi yazo muje yabasu hak'uri dan ubanshi tunda shi bayajin magana". Baikai ga kiran number ba Baba maigadi yayi sallama daga bakin k'ofar falon, Abbie ya bashi iznin shiga. Shigowa yayi ya tsuguna daga can bakin k'ofa yace "Barka da hutawa Alh". "Yauwa barka dai Baba lafiya dai ko?". "Eh to Alh wannan mak'ocin namune yace ayi masa iso gurinka zakuyi magana Alh Hamisu". "Okay, shikenan gani nan fitowa". Tashi Baba maigadi yayi ya fita bayan ya amsawa Abbie. "Kingani ko Hafsat? yanzu ina amfanin haka dan ALLAH". Abbie ya fad'a rai a b'ace yana kallon Ammi. Kai ta girgiza tace "Babu fa ayi hak'uri dai Abbie kaje ka sameshi d'in". Tashi Abbie yayi ya gyara babbar rigar shaddar dake jikinshi sannan ya fita kiran da Alh Hamisu yake masa. A compound d'in ya sameshi zaune kan fararen kujerun dake kusa da wasu shuke shuken furanni, bakinshi d'auke da sallama ya k'arasa wajen tareda mik'a masa hannu sukayi musabaha. Mrs Salees Mu'az 💝 3/2/22, 08:19 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 25. Paid book Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Shima Abbie kujera yaja ya zauna suka shiga gaisawa da tambayar iyalai dakuma kasuwa duk a mutunce, shiru suka d'anyi nawasu y'an sakonni kafin Alh Hamisu ya katse shirun nasu da fad'in "Wato Alh Basheer d'azu bayan nadawo office nakejin wani labari a gurin iyalina wanda sam banji dad'in shiba shine nace bari dai inzo inji yadda batun yake da kuma abinda ya faru tsakanin yaron wajena da naka yaron kar in yanke hukunci cikin rashin sani dan dukan nan saidaya kaishi ga asibiti". "Gaskiya ne Alh Hamisu yaron wajenka bashida laifi ko kad'an babban mai laifin Modibbo ne kuma koda bakazo ba zan taso k'eyar shi muzo har gida mubaka hak'uri, anan Abbie ya zayyanawa Alh Hamisu abinda ya faru kamar yadda Ammi ta fad'a masa ya d'ora da neman afwarshi. "Ba komai Alh Basheer ALLAH ya kiyaye gaba bari in koma". ya ida maganar yana mik'ewa tsaye tareda k'ara bawa Abbie hannu suka k'ara gaisawa Abbie yace "Ya kamata mu shiga dakai ciki iyalina su k'ara baka hak'uri dan haka nazo nasame su cikin damuwar abinda yayi mahaifiyata ma har gida tace zataje". Alh Hamisu ma cewa yayi basai ya shigaba komai ya riga ya wuce amma Abbie ya takura masa dole sai sun shiga haka dole yabi bayan Abbien zuwa general parlor na gidan. Har lokacin Ammi tana zaune a falon cikin zullumi dan batasan da abinda Alh Hamisun yazoba, amma ganin yanayin fuskarshi a sake kamar ma wani abu bai faruba yasa taji tasamu nutsuwa, a mutunce suka gaisa dashi tabashi hak'uri Abbie yace ta kirawo Ayyah ma su gaisa. Ayyah ma tazo sun gaisa itama ta bada nata hak'urin yace duk ba komai ALLAH ya kiyaye gaba komai yawuce, dayake tsaffi akwai son labari 🤣 nan Ayyah ta dinga janshi da tad'i, Abdallah Abbie ya kira a waya yana yin picking yace "Idan kaga dama kazo general parlor inason ganinka". bai jira amsar da Abdallah zai bashi ba ya katse kiran. Yasan dai kiran kona meye bai wuce hukuncin daya d'auka ba kan wannan yaron, tashi yayi daga kwancen dayake dagashi sai boxer ya d'ora farar jallabiyyah akan gajeren wandon ya d'auki wayarshi ya fita bayan ya kulle part d'in. Da sallama ya shiga falon Alh Hamisu da Ayyah ne kawai suka amsa masa sallamar da k'arfi Ammi da Abbie kuwa ciki ciki suka amsa suna binshi da harara, gefe d'aya yasamu ya zauna k'asan carpet yana k'ara bin Alh Hamisu da kallo ko ba'a fad'a masa ba yasan mahaifin yaron nan ne duk da bawai wani tsayawa yayi ya kalli Anas d'in sosai ba amma yaga kamarsu tattare da mutumin dake zaune. Rai a had'e Abbie yace "Modibbo! ga Alh Hamisu nan mahaifin yaron d'azu da rashin hankali yasa ka dakeshi dan haka saika bashi hak'uri kan laifin dakayi musu". "Hak'uri kuma Abbie?". Abdallah yace yana d'an tura baki. ""Eh, hak'uri idan kuma zaka nuna bamu isa dakai bane to". Ammi ta fad'a tana hararar shi. "Zaka bayar ne kokuwa?". Abbie ya fad'a. "Kayi hak'uri". yace yana juyar dakai gefe. "Ba komai Abdallah ya wuce sai a kiyaye gaba, bari inkoma Alh Basheer". Alh Hamisu ya fad'a yana mik'ewa tsaye, godiya Ammi da Ayyah suka k'ara yimasa sukace kuma zasu shiga su duba Anas d'in daga nan ya fita Abbie yabi bayanshi danyi masa rakiya. Abbie yana fita yadawo, zama yayi ya shiga yiwa Abdallah fad'a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba daga k'arshe kuma ya koma nasiha da rarrashi dan lamarin na Abdallah saida rarrashin. Upstairs Abbie ya hau yabar Abdallah dasu Ammi da Ayyah suma suka d'ora da tasu nasihar, a haka dai kamar ya d'auka dan harda yimusu godiya 😅 sannan ya tashi zai fita har yaje bakin k'ofar falon ya tsaya tareda waigowa yace "Ayyah zan samu damar ganin amaryar tawa kuwa?". takaici ya hana Ammi cewa komai Ayyah kam dak'uwa ta jefa masa tana fad'in "Gidanku, saikace gaske kamar ba d'azun nan kagama bata kashi ba to kasha zamanka bata buk'atar ganinka". Baki ya d'an tab'e tareda d'age kafad'a yana murmushi ya ida ficewa daga falon dama neman magana ne kawai irin nashi. √^^√^^√^^√^^√^^? Kusan kwance Janaan ta yini ranar zazzab'in dai ya sauka sai ciwon kan dake damunta wanda yak'i sauka ga jikinta da sam batajin k'warinshi, gefe d'aya kuma tararrabin yadda zasu k'ara had'uwa da Yah Abdallah ne cike da zuciyarta. Ayyah duk bayan y'an mintuna saita lek'ata hakama Ammi tanajin dad'in yadda suke bata kulawa sosai gasu Hassana ma dasuke ta nasu k'ok'arin ganin ta manta da damuwarta. After Asr. K'arar wayar tace ta tasheta daga barcin daya fara surarta, wayar ta janyo a k'asan pillow ta duba mai kiran sunan My Bloody ya bayyana bisa screen d'in wayar, murmushi ta d'anyi sannan tayi picking takai kunnenta lokaci d'aya tanayin sallama, amsa sallamar Jauhar tayi tana tambayar Ammi da sauran y'an gidan Janaan ta amsa mata tana k'ara jan blanket d'in data lullub'a saboda zazzab'in dataji yana son dawo mata itama ta shiga tambayar su Mama da Hajiya. "Amma dai bakida lafiya My Bloody naji muryar ki haka?". Murmushin k'arfin hali Janaan tayi kamar tana gabanta tace "K'alau nakefa kawai dai gajiyar school ne ke aiki dani". bataso ta fad'a mata abinda ya faru d'azu dan tasan tsaf zata iya kiran Yah Abdallahn suyi ba dad'i. "Wayyo sannu Bloody haka muketa fama wllhy muma, bari in barki haka to ki gaida su Ammi da twins". "Zasuji insha ALLAH take care love you". "Love you too". Jauhar ta fad'a tareda datse kiran, haka nan jikinta yabata y'ar uwar tata ba gaskiya ta fad'a mata ba kamar yau tafara yin school d'in? itadai bata yardaba dan haka ta kira number Hassana dan jin gaskiyar lamarin. Lokacin suna kitchen suna shirye shiryen d'ora dinner itada Hussaina dakuma Atika dasuke yi tare kiran ya shigo wayarta barin yankan salad d'in datake tayi ta d'auki wayar dake saman drawer a kusa da ita ta d'aga, bayan sun gaisa Jauhar take tambayar Hassana ko akwai wani abu dake damun Janaan sunyi waya taji kamar tana cikin damuwa kuma ta tambayeta tace ba komai shiyasa ta kirata ta tambayeta. Lek'e lek'e Hassana ta shigayi tana hango falon ta k'ofar kitchen d'in dan wani lokacin kamar aljani haka yake saidai kawai ka ganshi a gabanka. "Munafunci ya tashi kenan". Hussaina ta fad'a cikin dariya tana kallon Hassana, dak'uwa Hassana ta jefa mata tana hararar ta itama Hussaina ta rama dak'uwar ta juya ta cigaba da aikinta. K'asa Hassana tayi da murya tace "Bawani gajiyar school datayi Yah Abdallah ne ya daketa". Ido Jauhar ta zaro sosai cikeda mamaki tace "Duka kuma Hassana? me tayi masa to?". "Hmm bari kawai sister Yah Abdallah saidai addu'a, dayake yau ita kad'ai taje school saboda mu bamuda lectured so da aka tashi bata jira driver ba saita biyo wani Anas d'an layinmu sukayi dropping d'inta to data fito saita manta handout d'inta a motar shine ya fito ya kawo mata sai suka tsaya suna y'ar hira saiga Yah Abdallah yadawo wllhy ingaya miki haka yakama yaron mutane yayi masa lilis wai wayace ya tsaya masa da iyalinshi da k'yar maigadin gidanmu da drivern su yaron suka k'waceshi.(Kai Hassana 🤦kamar a gabanta akayi komai). Cikin b'acin rai Jauhar tace "Shine itama ya daketan?". "Wllhy ingaya miki lafiyayyun maruka yayi mata saida fuskarta ta d'aga ya fasa mata baki kuma, gata can kwance yau yini tayi zazzab'i da ciwon kai". Hassana ta bata amsa. "Shikenan sister sai anjima ki gaida su Ammi da Abbie sai munyi waya". bata jira abinda Hassanar zata fad'a ba ta kashe wayar saboda ranta dayake a b'ace wllhy Yah Abdallah mugune kawai dan yaga su k'annen shine saiya dinga zalintarsu ai ALLAH yana nan kuma saiya saka musu ita kad'ai ta dinga zazzaga masifa a d'aki daga k'arshe dataga ba amfanin masifar tunda wanda ake domin shi bai saniba dan haka ta rarumi wayarta data aje bayan gama wayarsu da Hassana ta lalubo number Abdallah ta danna masa kira. Lokacin yana kwance tsakiyar gadonshi ya tada kanshi da pillow da laptop akan ruwan cikinshi yana duba tsarin wasu new design d'in wasu company's da suka shigo a k'asar America, three quarter ne kawai a jikinshi ko riga babu sai P cap d'inshi ta gado 🤣 dake sanye a kanshi, k'amshin nan dai daya tsumu dashi shike ta faman tashi kowane lungu da sak'o na d'akin, hannu yakai ya d'auko wayar datake ajiye a gefenshi kan gadon ya duba mai kiran nashi sunan dana ganine yana yawo saman screen d'in yasana zaro ido saboda mamaki har yayi picking yakai kunnenshi ina can ina tunanin ma'anar sunan maganar daya fara ce tasa nadawo hankalina na cigaba da d'auko muku rahoto. "Malama meye na kirana?". yace yana cigaba da duba pictures d'in dayake gani da hannu d'aya. "Dalilin dayasa ka tab'amin y'ar uwata nakeso inji". tayi maganar cikin tsiwa da rashin kunya. "Dalili kikeso kiji?". ya tambaya Kai tsaye tace "Eh" harda murgud'a baki kamar yana wajen ne. Murmushi yayi yana wani cije lips ya rufe laptop d'in ya ajiyeta gefe tareda kai hannu kanshi ya zame P cap din ya shiga yamutsa lallausar sumar kanshi yace "Kibari mu had'u Jauhar zan fad'a miki dalilina". Tsaki tasaki tace "Mugunta dai batada kyau, kawai dan kaga yarinya tana da hak'uri saika dinga cin zalinta kum....."Koke dabaki da hak'urin bakifi k'arfin insa bulala in miki dukan tsiya ba yarinya". ya katse maganar data fara. Wata irin dariyar rainin hankali tayi tace "Wa? ai wllhy ko a mafarki karkayi tunanin dukana duk ranar dakayi gigin tab'a lafiyar jikina kuwa to kaima bazaka kwana da lafiya ba". "Haka kikace ko? to muzuba mugani ni da ke har yanzu sunan Abdallah Madugu kikeji bazaki tabbatar da sunan ba sai ranar dana miki kamun kazar kuku wllhy". yayi maganar yana cije baki tareda gyara kwanciyarshi daga rigingine zuwa rufda ciki. Cikin tab'e baki tace "Kai kasan duk wannan kuma damuwarka ce batawa ba nidai abinda nasani karka k'ara gangancin tab'amin y'ar uwata wllhy". "Idan ba'ayi hakan ba kuma fa? me zakiyi? zaki d'auki mataki ne?". "Matakai ma ba mataki ba wllhy". tace kanta tsaye. "Zaki cimin uwa Jauhar, koni zakici mu had'u a......."Tirrr ALLAH wadaran naka ya lalace". ta fad'a da sauri tareda jan tsaki ta kashe wayar batare data bari ya k'arasa abinda yayi niyyar fad'a ba. Mrs Salees Mu'az 💝 3/2/22, 08:20 - Ummi Tandama😇: WATA SOYAYYA 💝 Oum Hanan Page 26 *TOP TEN TAKUN HASKE BATCH A* Tasan shi sarai yanzu saiya fad'i maganar dazata dad'e tanajin kunya tunda shi ba kunyar ce ta isheshi ba. Dariya kawai yayi lokacin dayaga tayi hanging call d'in wani irin nishad'i da farin cikine masu tarin yawa yaji suna ratsashi cikin b'argo da zuciyarshi harma da ilahirin jikinshi baki d'aya ya lumshe ido yana jin yadda zuciyarshi ke harbawa da sauri sauri, laptop d'in dabai k'ara dubawa ba kenan ya cigaba da kwanciya a haka idanunshi a rufe yana sauke numfashi a hankali a hankali muryar ta kad'ai dayaji ta haddasa masa shiga wani hali mai wuyar fassara. √^^√√^√^^√√^? A ranar da daddare Ammi da Ayyah da Hassana datayi musu rakiya sukaje suka duba Anas wanda ke kwance ciwon k'irji ya sakoshi gaba saboda dukan da Abdallah yayiwa k'irjin nashi, sun dubashi tareda k'ara bada hak'uri sannan suka dawo gida. Abbie ma saidaya tasa k'eyar Abdallah a gaba suma sukaje suka duboshi, farko ma togewa yayi bazashi ba saida Abbie yayi masa tsiya tsiya sannan ya bishi sukaje tare. A cikin halin zazzab'in da Janaan take ko sannu bai mataba lokacin ita kad'ai ce a d'akin yazo ya titsiyeta lallai saita fad'a masa dalilin dayasa ta fad'awa Jauhar abinda ya faru, cikin rawar jiki data murya wanda zazzab'i da kuma tsoron Abdallah ya haifar mata ta shiga yimasa rantsuwa ita sam basuyi maganar da Jauhar ba batasan kuma wanda ya fad'a mata ba yak'i yarda wai k'arya take, ana haka Ammi ta shigo duba jikinta ta ganshi yana tuhumarta yayi mata tsaye akai aikuwa Ammi ta hau kanshi da fad'a ta korashi daga bedroom d'in. √^√^√^√^√^√^√^√√^√^√^√^√^√^√^√^√^√^√^? Tun daga wannan lokacin Janaan ta daina kula kowa a makarantar tasu dama kuma bata shiga harkar kowa inba karatu dake had'asu da wasu mazan ba shima saita daina ta shafawa kanta lafiya dan gani take tamkar Yah Abdallahn zaizo har school d'in ya ganta, harkar lafiya a bita da shekara tunda shi bayayin uzuri a rayuwa. A gurguje please 🙇 Kwanaki sunata k'ara tafiya yayin da bikin Abdallah da Janaan keta k'ara matsowa, kuma har a yanzun koda sau d'aya bai tab'a gwada kiran Janaan sun keb'e sunyi magana ba a matsayinta na wadda zai aura, ita kanta Janaan d'in bawai son had'uwarsu take dashi ba harga ALLAH ma batason ya nemeta d'in. Ammi ma bata matsa masa lallai saiya dinga kiranta suna zance ba saboda wasu dalilanta da ita kad'ai ta barwa kanta sani. A yanzu baifi saura 3wks da y'an kwanaki ya rage biki ba, Abdallah ya gama gininshi tsaf wanda dama ya dad'e yanayi a unguwar zoo road ginine na musamman daya zana abinshi da kanshi inda ya d'auko tsarin gidan a k'asar Cyprus dayaje gano wani ginin company wanda mai kamfanin ya d'auke shi, anan yaga gidan kuma yayi masa kyau matuk'a dan haka ya d'auko hotonshi plat house ne gidan bashida irin girman nan sosai amma dole tsarin gidan ya burge mutum ya narka dukiya dashi kanshi baisan adadinta ba kuma alhmdulillah kwalliya ta biya kud'in sabulu dan duk wanda ya shiga gidan kokuma yaga hotonshi saiya burgeshi yayi santin shi Habeeb Marafa ma da Abdallahn Momy Maryam sunce irinshi zasuyi Abdallah yace ba d'an iskan daya isa yayi irinshi suma suje sugano kalar nasu suyi amma dai ba irin wannan ba sukace tunda ubanshi ya basu kud'in yin ginin ai saiya hanasu, kai wad'annan yara ALLAH shirya 🤦. Ko lefe baiyi tunanin had'awa ba kawai harkokin gabanshi yake saida Ammi tayi masa maganar tace ya tura mata kud'i za'a had'o kayan lefen, mak'udan kud'ad'e ya turawa Ammin dan bashida matsalarsu ubangiji ya hore kuma ya sawa sana'ar tashi albarka, yana tura mata kud'in ta turawa Hauwa'u k'anwar Abdallahn mai binshi a haihuwa wadda su Hassana ke kiranta da Aunt Jeeddah ita zata had'o lefen komai da komai dayake tana yin order na kayayyakin na mata kasuwancin datake kenan hakan yasa Ammi ta wakiltata kan had'a lefen. Wannan karon da kanta ta shirya tafiya had'o kayan bayan ta nemi yarjewar mijinta ya amince. Cikin y'an kwanaki kad'an kuwa Aunt Jeeddah ta had'o komai harda k'arin tata gudunmawar data saka a ciki set biyune na akwatinan masu shida shida set d'aya peach color d'aya set d'in kuma ash color mai haske su kansu jakunkunan abin tsayawa a kalla ne bare kuma kayan dake dank'are a ciki kowacce saida aka shak'eta da kaya na alfarma masu matuk'ar tsada da asalin kyau, kai tsaye gidan Ammi aka wuto da kayan tunda itace uwar y'a nan fa aka baje kaya ana kallo dama su Aunt Deejah da Aunt Jeeddahn da Mabrookah wadda su Hassana sukebi duk suna gidan da sauran y'an uwa da abokan arzik'i da suka zazzo. "Masha ALLAH" kalmar da kowa ke fad'a kenan lokacin da ake ganin kayan kowa santi yake tareda yabawa Aunt Jeeddah data zab'o kayan, ba abin kushewa sai san barka tareda zaman lafiya mai d'orewa ga ma'auratan. Janaan dai tana mak'ure a gado tanajin hayaniyar mutane tareda sa albarka ganin abin take tamkar a mafarki wai itada Yah Abdallah ne zasu zama k'ark'ashin inuwar aure tana rok'on ALLAH ya bata hak'uri da juriyar zama da Abdallah, Hassana ce taje ta tsegunta mata yadda lefen yake tanata faman santi itadai murmushi kawai tayi tana sauraron Hassana. Haka Abdallah da suka shigo gidan da Habeeb bayan tafiyar bak'in ya rage sai y'an gida kawai ba kunya ya zauna ya baje kayan ya musu filla filla yana gani harda cewa Aunt Jeeddah idan baiga abinda yayi masa ba saiyaci ubanta kuma saita biyashi kud'inshi ko mijinta ya biya a hakanma wai tasu tazo d'aya dashi yana d'an mata mutunci, duk dariya akayi a falon Aunt Jeeddah tace "To gasu nan dai ko kai iya zab'en dazakayi kenan Yah Modibbo". Baki ya tab'e yana cigaba da d'add'aga kayan Habeeb na tayashi gani. "Very good thank you so much, kinyi k'ok'ari sosai". yayi maganar yana cigaba da dubawa, mamaki ne ya kama kowa a wajen dan sunsan halinshi sarai ko godiya bai cika yiwa mutane ba. "Nagode Yah Modibbo". Aunt Jeeddah ta fad'a tana murmushi, d'agowa yayi ya kalli Hussaina yace "Ina Janaan? kirawota taga kayan, idan akwai abinda baiyiba a canza". "Haba Yah Abdallah ina kaga an tab'a yin haka? cikin mutane amarya tazo tana ganin kayan lefenta". Aunt Mabrookah ce tayi maganar tana kallon Abdallah. "Ina ruwanki? banason shisshigi malama". ya fad'a yana hararar ta, baki ta d'an tab'e tana juyar da kai gefe. ""Wai dan ubanki ba magana nayi miki ba". yace a fusace yana kallon Hussaina, da sauri ta zabura ta nufi bedroom d'insu inda Janaan take. Kallonshi Aunt Jeeddah tayi tace "Haba Yah Modibbo dan ALLAH ka k'yaleta kunya kawai zaka bata wllhy kasanta akwai kunya". Harara ya zabga mata yace "Wato nine sarkin marasa kunya kenan ko, to ko itace sarkin kunya na duniya saitazo ta gani dan ubanta salon nan gaba tace wasu abubuwan basuyi mataba". "Dama ina kaga kunyar?". Aunt Deejah tace tana hararar shi, baice uffan ba ya cigaba da dubawa. Har lokacin Janaan tana kwance kan bed da waya a hannunta kamar ma wani assignment take dubawa a ciki Hussaina ta shiga ta zauna bakin gadon tana kallon Janaan tace "Aike daga angonki sister yace wai kizo kiga kayan lefen yanzu". "Inzo inga lefe kuma?". Janaan ta tambaya cikin mamaki tana kallon Hussaina tareda ajiye wayar hannunta. "Eh wllhy, haka yace". Hussaina ta bata amsa. "Amma dai da wasa yake ko?". Janaan ta k'ara tambaya gabanta yana fad'uwa, dariya Hussaina tayi tace "Wllhy bawani wasa kinsan dai ba wasa yake damuba bare kice kitaho kawai muje a wuce wajen". "Amma saboda ALLAH Hussaina cikin mutane sai inje in fara kallon kayana saboda nice k'arshen mara kunya duk gasu Ammi da Ayyah a falon". A marairaice tayi maganar kamar zatayi kuka. "Ammi da Ayyah fa basu falon Aunt Deejah ce kawai saisu Aunt Jeeddah saikuma Aunt Fareedah su kad'ai ne". "Duk da haka dai Hussaina nidai dan ALLAH kibashi hak'uri dan ALLAH kice masa kunya nakeji". Tashi Hussaina tayi tana fad'in "Bari inje to zagi ne dai zamusha nidake". ta fita daga bedroom d'in. "Yah Abdallah tace dan ALLAH kayi hak'uri kunya takeji wllhy". cikin y'ar rawar murya Hussaina tayi maganar bayan isarta falon. "Kice mata idan tabari nazo d'akin nan saina mata ba dad'i har inbada sak'o tace min wai tanajin kunya". yacewa Hussaina a fusace, da sauri ta k'ara juyawa sudai su Aunt Deejah suna zaune suna kallon ikon ALLAH kuma ba wanda yayi magana sai Aunt Jeeddah cema tace "Dan ALLAH Yah Modibbo ka k'yale yarinyar nan". baiko kulata ba ya cigaba da abinda yake, Habeeb kam cewa yayi "Dan ALLAH Jeeddah ku k'yale wannan d'an banzan ba mutunci ne dashi ba yanzu idan batazo ba saiyayi mata abinda gara tazo d'in tunda duk dai y'an gidane ba bare ace za'a dinga maganar tayi rashin kunya". Ba shiri Janaan ta tashi ta yafa k'aramin gyalen doguwar rigar dake jikinta maroon color ta biyo bayan Hussaina dan tana gudun abinda za'a cimata mutunci. Duk da kallo sukabi Janaan da yawansu tafara basu tausayi tun yanzu zama da Abdallah sai mai hak'uri. Tsugune tayi gaban kayan ta sunkuyar da kanta ita batayi magana ba kuma bata fara duba kayan ba. "Malama ki bud'e ido kiduba sosai kigani abinda baiyiba ki fad'a banason munafunci". da k'arfi yayi maganar hakan yasa ba shiri Janaan ta zabura ta fara d'add'aga kayan batare datana tantance kyansu ba wannan jaraba dame tai kama, wata akwati ya janyo ya bud'e yaga bra and panties ne kawai a ciki bra d'aya ya d'auka yana kallon Janaan yace "Wannan size d'inki ce?". Oh My God! Yaa salaam 🤦 Abdallah ba man kai yasin, gaba d'aya ido y'an falon suka zaro wasu harda dafe kai, Habeeb ma goshinshi ya dafe yana hararar Abdallahn da hankalinshi kwance bakace shiya fad'i maganar ba danshi iya gaskiyarshi ya fad'a so baiga wani abin jin kunya ba su kansu kunyace ta kamasu bare Janaan dataji tamkar ta nutse cikin k'asa tsabar kunya da takaici. "Kai dan ubanka tashi kabar wajen nan tunda bakada kunya fitsararre kawai". Aunt Deejah tayi saurin fad'a kafin ya k'ara b'aro musu wata maganar datafi wannan, zaiyi magana Aunt Deejah ta nuna masa k'ofa da hannunta tana hararar shi. Mrs Salees Mu'az 💝 3/2/22, 08:20 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Oum Hanan Page 27 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 {Home of expert & perfect writer's} *TOP TEN TAKUN HASKE BATCH A* Tashin yayi ya fita Habeeb ya mara masa baya, goshi Aunt Deejah ta dafe tana girgiza kai tace "ALLAH ka shirya mana Abdallah". duk da Amin suka amsa Fareedah tayi dariya tana fad'in "Ai wannan k'anin mijin nawa ba damane wllhy Janaan saidai ayita hak'uri ALLAH dai ya bada zaman lafiya dawwamamme". da Amin suka amsa dukansu, Aunt Deejah tayi kiran Janaan tashi tayi ta nufi inda take ta zauna kusa da ita cikin muryar rarrashi tace "Kar duk wad'annan abubuwan da Abdallah yake su dameki kinji Janaan haka ALLAH yayishi kuma bamuda damar canzashi kedai kiyi ladabi da biyayyar zaman aure insha ALLAHU zakici riba, ubangiji yasa alkhairi a zaman aurenku ya kad'e dukkan wata fitina da sharrin shaid'an la'ananne ALLAH kuma ya k'ara miki hak'uri da juriyar zamantakewar ku dashi tashi kije ALLAH yayi miki albarka". Nan d'inma dai amsawa sukayi da Amin d'in, Janaan ta d'ago kanta dake sunkuye cikin sanyin murya tace "Nagode k'warai Aunt Deejah ALLAH ya sakada alkhairi". "Amin Amin k'anwata". Aunt Deejah ta fad'a tana murmushi, tashi Janaan tayi tabar falon sukuma suka harhad'e kayan da duk Abdallah yabi ya barbaza su. Abbie ya hana Alh Isma'eel Daddyn su Janaan yin komai dangane da kayan d'aki ya d'auki nauyin yin komai yace shima d'iyarshi ce dan haka yadda zaiyiwa su Hassana idan aurensu ya tashi haka ma zaiyiwa Janaan. Ba k'aramar dukiya aka narkawa Janaan a gidan ba two bedroom d'inta kowane saida aka cikashi taf da tsadaddun furniture da Abbie yasa akayi masa order sannan falo wanda yafi ko ina had'uwa duk da dai ba tarkacen kaya akasa ba amma ya had'u over, ga kitchen d'inta da aka shak'eshi shima da kayan electric kala kala abin sai wanda yagani dan bazai misaltu ba gara kowa ya k'iyasta cikin ranshi (Lol). Masha ALLAH Abbie dai yayi bajinta ba kad'an ba saidai fatan ALLAH ya saka masa da alkhairi yabada ladar zumunchi Amin. Hakama side d'in Abdallah dake gidan ya k'awatashi sosai da kayan more rayuwa, shikuma falo d'aya ne k'ato da bedroom d'aya sai wani d'aki daya zuba kayan motsa jiki iri iri a ciki gida dai ya had'u masha ALLAH sai fatan zaman lafiya. √^√^√^√^√^? Ammi ta shiryawa su Janaan dasu Hassana tafiya KD dan yimusu sallama, Abdallah taso ya kaisu yakawo mata uzurin ranar yanada bak'in dazai gana dasu hakan yasa tayiwa driver magana ya kaisu. Kwanansu biyar suka dawo, sosai Janaan taso su taho da Jauhar amma tak'i tace ba inda zata bisu sai lokacin bikin yayi dayake harsu Maman duk can Kano zasuje ayi bikin, farko dai sunso takoma can ayi bikin a d'auko amarya daga can Abbie ne yace sam hakan bamai yiwuwa bane saidai su suzo nan ayi komai tunda shima d'iyarshi ce, Alh Isma'eel yaji dad'in hakan kuma Abbien ya k'ara k'ima da mutunci a idanunshi dan duk wanda zai kula da naka ya nuna masa k'auna to kaima mai k'aunarka ne. Hassana da Hussaina sunsha rabon I.V card bayan dawowarsu dan Janaan kin zuwa tayi kuma dama bawasu k'awayen kirki gareta ba duk nasu Hassana ne ita takamaimai ma bazata nuna yarinya d'aya ba tace k'awarta ceba saidai mutunci kawai daf da bikin nema aka kawo wata sabuwar student department d'insu kuma wajen zamansu d'aya ma Hafsat Yusuf datake yawan shigewa Janaan d'in to itama ganin batada wani aibu kuma abinda ya kaita shi takeyi yasa ta sakar mata fuska suka fara mutunci sosai har take kiranta da Mommy kasancewar sunan Ammi kenan Hafsat itakuma take cemata daughter. Cikin d'an lokaci kad'an suka shak'u sosai da ita. Ko wajen rabon invitation d'inma tare sukayi dasu Hassana ita da kanta tace idan lokaci yayi suyi mata magana dan haka duk wasu shirye shirye da ita akeyi kasancewar tanada saurin sabo da mutane yasa nan da nan suka saba dasu Hassana harda ma Ammi da Ayyah. Tuntuni Janaan ke fama da Jauhar tazo ayi komai da ita amma fur tak'i yarda tace ba inda zatazo wai sai lokacin dasu Mama zasu taho, har fushi Janaan d'in tayi tace koda bikin ma karta sake taga k'afarta Jauhar tace wannan ne kuma bata isaba amma yanzu kam dai bazata zoba haka nan duk take jin duk batajin dad'in wannan auren da y'ar uwar tata zatayi ta kuma rasa dalilin hakan amma tafi alak'anta hakan da wanda zata aura d'in kasancewar ba shiri suke ba. Gyara sosai Ammi take yiwa Janaan gyaran jikine kawai sai magungunan sanyi datake ta banka mata masu matuk'ar kyau dan su tafi buk'ata fiye da magungunan mata da wasu iyayen na wannan zamani suke d'irkawa yaransu y'anmata idan zasu aurar dasu. Gyaran kam ya amshi jikinta masha ALLAH dan wani irin kyau ta k'ara kan wanda take dashi fatar jikinta ta k'ara yin smooth sai sulb'i da k'yalli take tamkar bayan maciji ga daddad'an k'amshi na musamman da aka tsumata dashi ya zauna sosai a jikinta da kayan sawar ta. Ranar laraba Mama ta iso dawasu daga cikin yayyen su Jauhar saikuma Hajiya Yaya, gida yafara d'aukar bak'i sai hidima ake ana faman shige da fice, Momy Maryam ma da nata iyalan a ranar suka sauka nan fa gida ya k'ara kacamewa. Ranar alhamis akayi bridal shower amarya tasha kyau sosai, basu fita ko ina ba cikin compound d'in akayi decorations na k'wayaye da balloons kala kala abinda yaba kowa mamaki Abdallah dai yace ba wata dinner da za'ayi waleemah kawai za'ayi ta wadatar, kowa saida yasha mamakin hakan dan anyi zaton a yadda yake da rawar kan nan za'ayi party's kala kala ne saikuma gashi yabawa mutane kunya. Duk yadda Abdallahn Momy Maryam da Habeeb sukayi dashi ya fad'a musu dalilin dayasa yace ba za'ayi party ko d'aya ba yak'i yace dai ba komai kawai ra'ayinshi ne hakan, aikuwa yasha zagi dan gaba d'aya ba haka sukaso ba so sukayi warwasa sosai a wannan bikin amma d'an iskan yayi musu buk'ulu a cewarsu fa amma dan nima nafison waleemahr. Madugu ashe akwai sauran hankalin(Lol). Baki kawai Jauhar ke tab'ewa lokacin da ake maganar ai ango ya hana yin party ko d'aya saidai ayi waleemah, aikin banza mutum sai shegen felek'en tsiya da ba'a san halinshi ba dai saiyace zaiyiwa mutane iyayi, ita kad'ai take maganar cikin ranta haushinshi takeji wllhy. Tunda su Jauhar sukazo batasa Abdallah a idanunta ba da alamu ya shiga busy taji dai muryarshi a falo suna magana da Mama da Ammi lokacin tana bedroom ita hakan ma saiyafi mata dan tasan mawuyacin abune su had'un bai takali abinda zasu raba hali dashi. Washegari bayan an sauko masallacin juma'a aka d'aura auren *ABDALLAH BASHEER MADUGU (MODIBBO)* da *HASSANA ISMA'EEL TURAKI (JANAAN)* Akan sadaki dubu d'ari a babban masallacin juma'a dake nassarawa d'aurin auren daya tara manya manyan k'usoshin gwamnati y'an kasuwa da rik'akk'un y'an boko duk tawagar Abbie ce data Daddyn su Janaan ga kuma tawagar Abdallah data Yah Ameen masha ALLAH d'aurin aure yayi jama'a ya kuma kafa tarihi a cikin birnin na Kano. Can na hango ango Abdallah cikin shiga ta alfarma farar shaddace k'al tamkar takarda sai faman yarari take tana zuba k'yalli da d'aukar idanu y'ar ciki da wando sai babbar riga madaidaiciya wadda akayiwa wani fitinannen aiki mai matuk'ar kyau da light blue d'in zare hakan yasa ya murza hula zanna bukar da akayiwa ado da light blue d'in zare dakuma fari, hakama agogon hannunshi na fata shima light blue ne yayi matuk'ar yin kyau ga wani k'amshi na musamman dayake zubawa, fuskarshi wasai bakace wai auren had'i bane akayi masa sai gaggaisawa yake da jama'a suna masa fatan alkhairi yana amsawa cikin fara'a dan dama Abdallah yanada sakin fuska sosai da faram faram da jama'a kawai dai tsiyarshi ce dai da bata sallah ta bakin Ammi (Lol). Waleemahr ma da akace za'ayi ba'a yinba sai yini da mata suka cigaba dayi a cikin gida bayan d'aurin aure a ranar kuma za'a mik'a amarya gidanta hakan yasa tunda ALLAH yasa taji an d'aura auren tafara kuka duk yadda taso danneshi kuwa har taso b'ata kwalliyar fuskarta wadda aka samu akayita da k'yar dan cewa tayi bataso tana ganin abinne kamar almara ba'a zahiri ba wai yau itace ta shiga sahun manya an d'aura aure, auren ma da Yah Abdallah mutumin da bala'in tsoronshi datake ji yasa ko inuwa d'aya batason su had'a amma saigashi inuwar aure ta had'asu dashi. Su Hassana ne y'an rarrashi da Jauhar wad'anda suke abokan wasa kuma suka samu abinyi suka shiga tsokanarta. Ansha shagali sosai a yinin ranar kafin da yamma aka fara shirye shiryen kai amarya, wanka aka sata ta k'ara yi aka shiryata cikin atamfa exclusive red colour mai had'e da ratsin milk da fari riga da zani ne simple d'inkine mara ado aka nad'eta da jar lafayah mai matuk'ar kyau da akayiwa bakin lafayahr ado mai d'aukar hankali da manya manyan fulawoyi kalar milk da golden, k'amshi kawai take zubawa duk ta inda ta motsa. Hassana, Hussaina, Jauhar da Hannah su sukasa amaryar a tsakiyarsu suna tayata kukan rabuwa da gida, da k'yar aka rik'ota aka kaita inda su Abbie suke zaune da sauran y'an uwa da abokai dabasu kai ga tafiya ba anan kowa ya tofa albarkacin bakinshi bayan angama wani abokin Abbie babban malamine ya rufe da doguwar addu'a ta zaman lafiya ga ma'auratan, daga nan kuma aka dawo da ita cikin gidan wajensu Ammi da Mama da sauran y'an uwa suma d'in dai kowa yayi mata nasiha daidai gwargwado da nuna mata zaman aure ba zama bane irin wanda tasaba yinshi a gidan iyaye ba yanzu ALLAH ya d'ora mata wani nauyi a kanta wanda idan ta kula dashi tabi ALLAH da manzon sa ta saukeshi zai zama hanyar shiga aljannarta, sosai nasihohin suka shiga jikinta suka ratsa k'wak'walwar kanta cikin ranta kuma ta d'auki d'amarar bin mijinta cikin kowane hali dan samun dacewa. Jauhar zamanta tayi tace bazataje kai amarya ba duk yadda su Hassana suka dinga yimata magiya akan taje tace ba inda zata su k'yaleta tayi kwanciyar ta kan bed tana sharar hawaye data rasa na meye, kai tsaye dai bazata kirasu dana rabuwa da Janaan ba tunda dama ba tare suke ba. Haka suka gaji suka k'yaleta suka fita daga bedroom d'in tareda bin sahun wad'anda suke tafiya gidan amaryar inda compound d'in ke cike da hamshak'an motoci masu rai da motsi. Mrs Salees Mu'az 💝 3/2/22, 08:21 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 28 Oum Hanan *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* 💡 (Home of expert & perfect writer's) *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Inda compound d'in ke cike da hamshak'an motoci masu rai da motsi na y'an uwa da abokan Abdallahn wad'anda sukayi masa matuk'ar kara a hidimar bikin, sai faman jidar mutane ake ana tafiya. "Masha ALLAH, masha ALLAH la quwwata illa billah, kalmomin dana dingaji suna tashi kenan daga bakunan y'an rakiyar amarya lokacin da aka isa gidan saboda matuk'ar kyau da gidan yayi musamman dayake tarwai tamkar rana saboda hasken fitilun da suka k'awata gidan hatta shuke shuken gidan an musu k'awa da k'ananun fitilu wad'anda suke kawowa suna d'aukewa kaloli daban daban white, purple, green, red, blue da sauran kaloli masu ban sha'awa tako ina sai san barka k'aryar mahassada. Basu k'ara rud'ewa ba saida suka shiga cikin gidan idanunsu suka nuna musu irin yadda cikin yake duk sai suka ida rud'ewa lallai ba k'aramin kud'i Abdallah ya narkar a gidan nan ba ga tsarin gidan ba wanda ya tab'a ganin irinshi lallai masu abu da abinsu. Had'add'en bedroom d'inta dayaji wasu muggan furniture masu azabar kyau aka direta, sannan mutane suka shiga zazzagayawa dan kashe kwarkwatar idanunsu. Bayan wani d'an lokaci aka fara tafiya da kad'an kad'an duk aka watse bayan sunsha tarin addu'o'e na zaman lafiya ya zamana saisu Hassana kawai da ragowar y'an mata y'an uwansu tunda dama ba k'awaye gareta ba sai Hafsat Yusuf kawai da itama takawo amarya, suma d'in shirin tafiya suka fara duk da yadda Janaan ke rok'onsu tareda had'asu da ALLAH karsu tafi tsoro takeji Hassana da Hussaina ne suka k'ek'ashe k'asa sukace sam bazasu zauna ba tafiya zasuyi sunfi kowa sanin halin Yah Abdallah k'aramin aikinshi ne yazo ya zazzagesu, wata y'ar k'anin Ammi da suke y'an uwa Amatullah itakuma ta dage kan saisun tsaya angwaye sunzo an sayi baki sannan su tafi. "Alamu sun nuna bakisan waye angon nan ba Amatu ki rufawa kanki asiri kitaho mutafi wlhy tun kafin suzo". Hussaina ce tayi maganar tana gyara yafen mayafin ta. "Rabu da ita sister da rabon yau ta kwana cikin takaici kenan aini banga abinda zai jamin zama a gidan nan ba har Yah Modibbo yazo ya sameni". Hassana tace tana saka takalminta. Kallon Amatullah Hannah tayi tace "Kinga Amatu ki tashi mutafi dan ALLAH dare na k'ara yimana fa idan kuma nan zamu barki to mu saimu tafi". Ganin dai ba wanda ya goyi bayan a zauna d'in yasa itama ta mik'e ta hau laluben gyalen ta akan gadon, ji take tamkar karta bar gidan tsabar yadda yayi mata kyau hakama maigidan ya matuk'ar yimata kasancewar bata wani yimasa cikakken saniba saboda bata dad'e da dawowa karatu daga Europe ba amma sau d'aya data saka idanunta cikin nashi yayi matuk'ar tafiya da ita. "To aita hak'uri dai Aunt Janaan dan yanzu kinzama Auntien mu tunda kin auri yayanmu, ALLAH ya bada zaman lafiya ya k'ara miki hak'uri akan wanda kike dashi". Hannah ce tayi maganar tana kama hannun Hassana datake share hawaye suka fita daga nan suma sauran suka take musu baya tana jinsu da d'ai d'ai da d'ai d'ai suka fice daga bedroom d'in sukaja mata k'ofar. Wani kukan ta k'ara fashewa dashi tana k'ara matse jikinta saboda tsoron daya fara shigarta tun yanzun bata saba rayuwa ita kad'ai a waje ba, a hankali ta janye mayafin lafayahr dake kanta ta shiga k'arewa d'akin kallo da irin yadda aka tsarashi tabbas Abbie yayi namijin k'ok'ari dole ta jinjina masa bedroom d'in tamkar ba'a nan k'asar mutum yakeba dole ta cigaba dayi masa addu'ar gamawa da duniya lafiya gamida cikawa da imani. √^√^√^√^√^√^√^? 9:55pm. Mutum biyar ne cikin lafiyayyar motar samfurin Corolla l.e ta yayi sabuwa dal sai shek'i take da d'aukar ido musamman data kasance black color ce, daf da bikin ya siyeta dan bai tab'a amfani da ita bama sai yau d'in kuma yanzu da suke shirin rakashi gidanshi. Abdallahn Momy Maryam ne ke driving d'in sai Habeeb Marafa dake gefenshi, back seat kuma Eng. Mujaheed ne da Arch. Mas'oud Garba duk abokan Abdallah ne saishi kuma mai gayya mai aikin wato ango Abdallah Madugu daya lafe a bayan kujerar yasha gayunshi cikin dakakkiya kuma bugaggiyar shadda mai yarari wadda kallo d'aya zakayi mata kasan ba k'aramin kuka naira tayi ba wajen siyanta, ash color ce mai d'an duhu sai hular daya murza a kanshi data hau da shaddar sosai, d'aure tsintsiyar hannunshi da Rolex silver motar duk ta cakud'e da k'amshin turarukan jikinsu masu dad'i fuskarshi a sake sosai ya shiga cikinsu sai raha ake ana wasa da dariya sai shak'iyanci suke irin nasu na abokai da haka har suka k'arasa gidan kasancewar babu maigadi yasa Habeeb ya fita daga motar ya bud'e gate d'in suka shiga ciki, bayan yayi parking suka firfito kowanne cikin nashi salon gayun. Tunda suka fito suke santin tsaruwar gidan daga bisani suka d'unguma dukansu suka nufi babbar k'ofar da zata sada mutum da general parlor na gidan, nan d'inma bakinsu baiyi shiruba suka cigaba da yabawa tareda taya abokin nasu murna. Tun lokacin dataji dirin mota an shigo gidan ta runtse Ido tareda k'ara takurewa waje d'aya tana k'ara maida mayafin lafayahr yadda yake ada, bugun zuciyarta na k'ara tsananta tasan baya wuce Yah Abdallahn ne ya shigo tsoron had'uwarsu dashi take batasan ya zata kasance ba tsakaninsu ALLAH ya rage mata tsoron wannan bawan ALLAHn a cikin ranta addu'ar datake akoda yaushe kenan. "Malam sauri mukefa kayi mana jagora inda amaryar taka take mu tofa albarkacin bakinmu musan inda dare yayi mana". Arch. Mas'oud Garba yace yana ajiye babbar ledar hannunshi akan center table d'in dake tsakiyar falon. "Kuje ina? yau naga mahaukata dan ubanku d'akin matar tawa zaku shiga? kowa ya ware nagode da rakiya abokai". Duk ido suka zubawa Abdallah dariya ma yabasu dan duk cikinsu babu bak'on Abdallah a ciki bare mutum yace zaiba kanshi wahala wajen jin haushin abinda ya fad'a d'in sun san zai aika abinda yafi ma haka. "Amma kaidai anyi mara mutunci wllhy wato korar mu ma kake ko?". Habeeb ya fad'a yana hararar shi. "Yo bazan koreku ba? kowanne yaje ya nemi wajen kwanciya garadan banza ba wanda keda mata aje a rungumi pillow nidai kam yau.....cikin sauri Abdallahn Momy Maryam ya katse maganar da Abdallah yayi niyyar fad'a gudun kar yayi musu b'aram b'arama kad'an daga aikinshi. "Dan ALLAH yimana gori Madugu, dan ubanka batare muke zaman tuzurantakar ba sai yau da ALLAH ya d'aga ka kasamu y'anci muma very soon duk zamu angonce mubaka mamaki mara mutunci koba hakaba guys?". Eng. Mujaheed ne yayi maganar yana rarraba idanunshi akan sauran, duk suka amsa kuwa da fad'in "insha ALLAH". Baki Abdallah ya tab'e yana turo hular kanshi gaba yace "Ku kuka sani dai munafukan banza, oya let's go muje in taka muku". "Ka wuce kawai malam muyi maka jan kunne a gabanta karka aikata mata wani d'anyen aikin tayi zaton dasa hannunmu a ciki". cewar Habeeb Marafa. "Kajawa wa kunne? k'yaleni ma wanda su Abbie sukayi min da wannan tsohuwar na kusa 1hr yau d'in nan durk'ushe a gabansu kamar mai d'aukar darasi duk akan waccan yarinyar". Dariya suka saki gaba d'ayansu Arch. Mas'oud Garba yace "Yanzu dai abokina a tak'aice mubar maka gidanka ko ba'a buk'atar mu?". Kai tsaye Abdallah yace "Eh bana buk'ata, bazaka tafi bane kai?". yace yana kallon Abdallahn Momy Maryam wanda ya hakimce akan kujera yana danna waya. "Ah tafiya kai tunda ba gidan ubana bane". yace yana hararar Abdallah lokaci d'aya yana mik'ewa tsaye, suka k'ara barin falon harda Madugun sallama sukayi suka shiga motar Habeeb da dama tun d'azun tana gidan lokacin da aka kawo amarya, yana nan tsaye har suka bar compound d'in ya k'arasa ya rufe gate d'in ya koma cikin falon ya rufe k'ofar daga nan duk k'ofofin da suke a bud'e ya rurrufesu ya kashe k'wayaye sannan ya d'auki ledar da har lokacin take ajiye kan kan center ya nufi bedroom d'in daya tabbatar Janaan d'in tana ciki. Handle d'in k'ofar ya kama ya bud'e ya shiga bakinshi d'auke da sallama, can ya hangota ta mak'ure waje d'aya kana ganinta kasan a tsorace take saboda irin yadda tayi musamman dataji shigowar tashi duk saita sake rud'ewa, saidaya d'an ja lokaci yana k'are mata kallo kafin ya fara takawa inda take zaune, kan bedside drawer ya ajiye ledar hannunshi sannan ya zauna kusa da ita yana fad'in ta cire lullub'in kanta d'in nan shi bayason gulma. Tofah! farawa da iyawa 😅, ita ba abin tayi masa musu ba yaci k'aniyarta ta shiryawa abinda yafi hakan daga gareshi hakan yasa a hankali tasa hannu ta cire lullub'in still dai bata d'ago ta kalleshi ba. "Look at me". yace murya ba alamun wasa a hankali cikin nutsuwa ta d'ago kanta ta saka k'wayar idanunta cikin nashi sosai yake kallonta kamar wadda zai cinye d'anya so take ta janye nata idanun amma tana tsoro kar cibi yazama k'ari dan haka ta cigaba da daurewa tana kallonshi da idanunta da sukayi matuk'ar canza kala saboda kukan datasha "Kuka kike ko?". ya jefa mata tambayar har lokacin idanunshi na kanta, da sauri ta girgiza masa kai tana k'ok'arin b'oye wasu sabbin hawayen da suka fara tsattsafowa cikin kwarmin idanunta sai daya tab'e baki sannan yace "K'arya zakimin Janaan? kukan na meye? wato ga dodo an had'aki dashi ko". nan ma kan ta shiga girgiza masa hakan ya hasalashi cikin tsawa yace "Wai bakida bakine Janaan? ko k'adangaruwa ce ke? kinaso in b'ata miki rai cikin daren nan ko?". Kai ta girgiza kafin kuma da sauri cikin rawar murya tace "A'a Yah Abdallah ba kuka nayiba". "Damuwarki ce". yace yana tab'e baki gamida d'age kafad'a ya d'ora da fad'in "Tashi kije kitchen ki d'auko plates da cups". Amsawa tayi da "Toh" sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi k'ofar fita yabita da kallo sai fama take da lafayahr jikinta ta kasa sarrafata tamkar zata tad'iyeta ta fad'i k'asa hakan yasa ya kirata ta juyo ta dawo inda yake inda yayi crossing legs nashi yana wani girgizasu yace "Ki tabbatar kin cire wannan abar idan kin fita karki sake kidawo min da ita nan". kallon rashin fahimta ta shiga yimasa dan bata gane abinda yake nufin ta cire ba. Mrs Salees Mu'az 💝 3/2/22, 08:21 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Oum Hanan Page 29 *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Shima d'in ganin kamar bata gane me yake nufiba yasa yayi mata nuni da idanunshi kan lafayahr jikinta yana fad'in "Wannan abinda aka nad'eki dashi d'in kamar gawa". Kai ta jinjina masa sannan ta juya ta fice, fitilun falon ta kunna ta shiga k'are masa kallo ba k'aramin tafiya yayi da itaba gashi kalar kujerun da curtains d'in falon da sauran wasu abubuwan da aka k'awata falon dasu favorite color d'inta ne wato pink and white, dube duben inda zataga kitchen d'in ta shiga yi amma bata ganiba gashi kuma tanajin tsoron zuwa ta tambayeshi hakan yasa ta cigaba da dubawa har tayi sa'ar ganin wata k'ofa data d'an shiga wani corridor dalilin dayasa ma tun farko bata gantaba kenan, wajen ta nufa ta bud'e k'ofar ta shiga kyakkyawan kitchen ya bayyana wanda yaji kayan amfanin wuta kaloli daban daban masu kyau da matuk'ar tsada. Wajen ajiyar plates ta nufa inda suke jere lodi lodi tamkar na siyarwa biyu ta d'auka da glass cup dogaye ta fita taja k'ofar ta k'ara kashe fitilun falon sannan ta koma bedroom d'in, yana nan zaune inda ta barshi yana latse latse a wayarshi gabanshi ta ajiyesu ya d'ago kai yana kallonta ganin abinda yake kallon yasa ta kalli jikinta baki ta dafe sam ta manta dayace ta cire lafayahr jikinta cikin hanzari ta juya ta koma falon ta cire ta k'ara dawowa gefen gadon tasamu can nesa dashi ta zauna ta takure waje d'aya jinta take duk ta takura saboda rashin mayafi dababu a jikinta, tashi yayi ya d'auko ledar daya ajiye a bedside drawer ya zauna a k'asa ya bud'e ya d'auko wata k'atuwar kaza dataji kayan miya da vegetables ya d'ora kan plate d'in, waigawa yayi ya kalleta yace "Sauko kici?". Batada da damar yimasa musu hakan yasa ta sauko ta zauna gefenshi duk a d'arare naman ya yago yakai bakinta bayan shima yaci, kai ta girgiza masa tareda juyar dakai gefe alamun bazata ciba k'asan ranta kuma duk mamakin shi ya cikata kodayake ba abin mamaki bane indai Yah Abdallah ne ruwa biyu ne kuma hawainiya wajen canza kala. "Kin juyo kin karb'a kokuwa banason munafunci fa". yayi maganar da k'arfi, da saurinta kuwa ta juyo. "Open ur mouth". yace, ba yadda ta iya dole haka ta bud'e bakin yasa mata naman, haka ya dinga d'ura mata shima yana ci saboda yunwar dake cikinshi rabonshi daya sawa cikinshi wani abu tun breakfast shima bawani na kirki yayi ba, so take tace masa ta k'oshi amma ta kasa sai dan kanshi daya tambayeta ta d'aga kanta fresh milk ya zuba mata ya mik'a mata ta karb'a ta fara sha, k'adan tasha ta ajiye cup d'in taci sa'a kuma baiyi magana ba. Bayan sun gama ya had'e komai ya fita dasu daga bedroom d'in, zaune tayi ta rasa ma abinda zatayi, ganin shiru shiru bai dawo d'akin ba yasa ta tashi ta rage kayan jikinta ta shiga bathroom tayi wanka ta fito d'aure da towel da hijab sama sama ta shafa cream ta d'auko night dress doguwar riga mai kauri milk color mai net a gaban rigar, tana shirin sakawa bayan ta cire hijabin jikinta saigashi ya shigo ido ta runtse gam ta rasa yadda zatayi gashi ta riga ta cire hijabin ga towel d'in bawani na kirki ba duk ta dabarbance ta tsaya cak ita batasa rigar ba kuma bata maida hijabin ba sai rigar data k'ara k'udundune ta a hannunta gabanta sai fad'uwa yake. Fari k'al d'in three quarter ne a jikinshi da farar riga mai yankakken hannu sai farin slippers mai taushi dake sanye a k'afarshi sai tashin k'amshi yake mai matuk'ar dad'i wanda tun kafin ya shigo yafara yiwa bedroom d'in sallama, inda take tsaye ya k'arasa yasa hannayenshi duka kan kafad'unta ya juyo da ita tana facing d'inshi k'ara k'asa tayi da kanta kunya tako ina na dukanta tamkar ta nutse cikin k'asa takeji, hannu yasa ya karb'i rigar ya warwareta yasa hannu zai fige towel d'in tayi saurin damk'ewa tana girgiza masa kai kamar zata saki kuka. "Ke! dallah malama cire hannunki bak'auya kawai dan zan taimaka miki ma insa miki rigar". yace cikin zare ido yana k'ara jan towel d'in. "Dan ALLAH Yah Abdallah kabari zansa da kaina". da k'yar ta harhad'a maganar ta fad'a saboda tsoro da kunya da suke dukanta. "Why?". ya tambayeta cikin silent voice kamar bashi ba. "Nidai kawai Yah Abdallah kunya nakeji". tace cikin rawar murya. "Nabi kunyar da gudu Janaan, kinaso inci uwaki cikin daren nan ko". Kai kawai take girgiza masa hakan ya k'ara bashi haushi matuk'a dan ya tsani wannan girgiza kan datake tamkar wadda batada bakin magana. Baya ya d'an ja daga kusa da ita yace ta d'ago ta kalleshi, haka nan ta d'ago kai ta kalleshin kamar yadda yace d'in ganin ya d'ora hannunshi saman zip din three quarter'n dake jikinshi yasa ta zaro ido sosai batasan lokacin datace "Me zakayi Yah Abdallah?". K'ok'arin zipping d'in wandon yake hankali kwance yace "Ah wai da cire miki zanyi nima kigani yadda zanga naki jikin kinga munyi 50 50 kenan ko". Ido ta k'ara k'walalowa sosai jin abinda ya fad'a kuma ya aikata d'in bawani babban abu bane a wajen shi itadai ta shiga uku da wannan mijin nata wai shi komai baya sakayawa ne? komai gaba gad'i yake yinshi ba abinda ya shafeshi a tsorace tace "A'a Yah Abdallah please karka cire". "To kibari insa miki rigar nan ko in cire gaba d'aya kayan jikina yanzun nan kinsan zan iya ko?". ya k'are maganar da sigar tambaya. Kai ta jinjina masa kawai alamun Eh cikin ranta tace 'Abinda yafi hakan ma zaka iya'. kusa da ita ya k'ara matsowa tareda mik'a mata hannu alamun ta bashi rigar, dolenta ta mik'a masa tareda rufe idanunta sosai gabanta na fad'uwa haka tanaji tana gani ya zare towel d'in ya cillar dashi gefe, wani irin numfashi taji ya fisga kamar wanda numfashin yake k'ok'arin k'wace masa kafin daga bisani ya saka mata rigar yaje ya kashe fitilar bedroom d'in yadawo inda take tsaye k'ik'am kamar gawa ya jata kan bed tareda kunna bedside lamp blue color. Duk wani tsoro saida aka tattaro mata shi a lokacin dan bata tab'a d'aukar Yah Abdallah zai nemi wani abu da wuri haka a wajenta ba amma amma dubi daga kawota yau yana shirin yimata abinda bata tab'a kawoshi nan kusa ba, jikinta ta matse sosai cikin bala'in tsoro lokacin dataji ya kwantar da bayanta akan gadon. "Dan ALLAH Yah Abdallah kayi hak'uri please". tace cikin rawar murya hawaye na taruwa cikin idanunta. "Nace zan miki wani abu ne?". ya fad'a cikin had'e rai yana kallonta ta cikin hasken dump light d'in. B'oyayyiyar ajiyar zuciya ta saki wadda ita kad'ai taji abarta, saikuma duk kunya ta kamata karma yayi mata wata fassarar yanzu. Baki ya d'an cije tareda sakin wata y'ar dariya yace "Bakida hankali ma yarinyar nan kinsan dai idan nayi niyyar yin wani abu dake duk wani kuka da magiyarki bazaisa in fasa yimiki abinda nayi niyyar yiba ko? yau dai na d'aga miki k'afa amma banda gobe dan ni ba mahaukaci bane da zan zuba miki ido banci sadakina ba". Kai tsaye yayi maganar yana kwanciya tareda jawota jikinshi ya shiga lalubarta, ganin yadda take ta masa nok'e nok'e yasa ya k'ara cewa "Ki maida hankalinki Janaan making love kawai zanyi dake idan kuma kika k'i bani had'in kai har wancan d'ayan dabaki so zanyi inga ta tsiyarki". bai jira cewarta ba ya rungumota gamida saka bakinshi cikin nata ya shiga bata wani irin passionate kiss mai wahalar fassararuwa ga wanda ake yiwa, ganin haka yasa cikin hanzari naja k'afafuna nabar musu bedroom d'in tun kafin yasani nutsewa k'asa dan kunya (Lol). Cikin ikon ALLAH dai kamar yadda ya fad'a d'in baiyi mata komaiba amma fa tasha murza ta bala'i duk yabi ya gajiyar da ita, daga k'arshe kuma bacci ya kwashesu gaba d'ayansu tana jikinshi. A daren ranar sam Jauhar bata runtsa ba sai faman juye juye data dinga yi har Hassana ta jita ta tashi take tambayar ta abinda ke faruwa ta kasa barci tace ba komai kawai dai ta kasa barcin ne, kuma ba k'arya tayi ba haka d'inne takamaimai bazatace ga abinda ya hanata yin barcin ba. ^^√^^√^^√^^√^^√^^ Da asubah shiya fara tashi sai daya tasheta sannan yabar bedroom d'in ta bishi da kallo harya fice batasan time d'in da murmushi ya k'wace mata ba wanda batasan dalilin yinshi ba. Tashi tayi ta shiga bathroom ta tsarkake jikinta ta d'auro alwalah ta fito ta d'aura zani kan rigar barcinta, saidata fara raka'atainil fajr sannan ta gabatar da sallahr asubah, nan kan dardumar ta zauna tana Azkar d'inta data saba Abdallah kam bata k'ara jin d'uriyarshi ba. Sai misalin shida da kusan rabi sannan ta rufe da addu'aen ta tana mai rok'on ALLAH ya sanya albarka cikin wannan auren nata yabata zaman lafiya mai d'orewa da kwanciyar hankali ya kuma bata juriya da hak'urin zama dashi a kowane irin hali. Barci ta koma saboda gajiyar datake ji a jikinta sai kusan k'arfe goma sannan ta farka, wanka ta shiga bathroom tayi ta fito ta shirya cikin riga da siket na atamfa green color mai zanen ganyayyaki ajiki powder kawai ta shafawa fuskarta sai kwalli da lipstick datasa dama k'arshen kwalliyar ta kenan turaruka masu dad'in gaske ta feshe jikinta dasu sannan ta shiga gyaran bedroom d'in bayan tagama da nan takoma falon nan ma ta gyara ko ina ta kunna burner ko ina ya d'auki k'amshi daga nan kuma ta shiga kitchen tafara had'a breakfast. Bayan tagama ta gyara kitchen d'in sannan ta fara shirya breakfast d'in a dinning koda tagama zaune tayi cikin falon tana tsoron zuwa ta tasoshi bayan haka kuma ma batasan inda part d'in nashi yakeba, tana nan zaune taji motsin fitowarshi waigawa tayi inda ta jiyo motsin nashi dayake ta bashi baya, nan ta hangoshi yana nufo inda take dagashi sai farin gajeren wando da farar singlet sabbi k'al da farin slipper sanye a k'afarshi, wata masifaffiyar kunya ce ta kamata tayi saurin kauda idanunta ta juyar da kanta cikin ranta tana jinjina tsantsar rashin kunya irinta Yah Abdallah. Kusa da ita ya zauna bayan k'arasowar shi, zamowa tayi har k'asa ta gaisheshi da lafiya kawai ya amsa mata ya d'ora da fad'in ina breakfast yanajin yunwa. "Yana dinning Yah Abdallah". ta amsa masa kanta a k'asa wata irin kunyarshi na shigarta idan ta tuno abinda ya faru tsakaninsu jiya saidai shikuma a yadda ta ganshi kamar ma ba abinda ya farun ita kad'ai ke hidimar ta. Mrs Salees Mu'az 💝 3/2/22, 19:29 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 30 Paid book Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* ^^√^^√^^√^^ "Saukomin dashi nan k'asa". ta tsinkayi muryar shi cikin kanta, amsawa tayi tareda tashi ta nufi dinning d'in shikuma ya cigaba da danne dannen waya. Saidata shimfid'a sabuwar leda sannan ta jera masa komai a kai tana shirin barin wajen taji yace "Nizan had'awa kaina kike nufi kokuwa?". juyowa tayi ta kalleshi taga har lokacin wayar yake kallo, dawowa tayi ta had'a masa tea ta zuba masa Irish d'in data soya da stew d'in hanta sai wainar k'wai. K'asa ya sauka ya tank'washe k'afafunshi yafara karyawa, Janaan dai tana rakub'e a gefe ta sunkuyar da kanta tanajin kanta duk wata iri kamar ba ita ba. "Kinyi breakfast ne?". taji amon muryar shi yana tambayar ta. Kai ta girgiza masa da sauri kuma tace "A'a" ganin irin kallon dayake mata na zaici k'aniyarta. "Taso kizo kiyi". abinda yace kawai kenan ya cigaba da juya tea d'in dake cikin mug, tanaso tayi masa musu tana tsoro dan sam batajin yunwa haka dai ta matso ta zauna tafara had'a tea d'in itama haka ta dinga sha kamar bataso shikuma bai k'ara bi takan taba yana gamawa ya tashi yabar wajen. Wajen ta gyara bayan tagama tayi wanke wanke ta k'ara gyara kitchen d'in sannan ta koma bedroom d'inta ta zauna tayi shiru ita kad'ai duk kewar Ammi dasu Hassana ta cikata, tana nan zaune taji tashin motarshi daga cikin compound ta window ta lek'a taga ya fice daga gidan, dawowa tayi ta zauna ta cigaba da sak'e sak'e cikin zuciyarta. Ba laifi tasha bak'i a ranar dan akwai y'an uwansu na wajen uwa dana uba duk sunzo sun k'ara ganin gida da wad'anda ma basu samu zuwa ba a jiya da aka kawota, hakan ya d'ebe mata kewar datake fama da ita na kad'aitaka. √√^^√√^^√√^^√√ Sai bayan sallahr Esha'e sannan Abdallah ya dawo gidan lokacin tagama komai ta gyara gidan inda bak'in dasukazo aka b'abb'ata tayi wankanta ta shirya tsaf cikin wani yadin material mai rawa riga da wando rigar iya gwiwarta rapper blue black ne yadin da akayiwa ado da k'ananun flowers orange color tayi rolling da k'aramin gyale kalar kayan tayi matuk'ar yin kyau duk da dai bawata kwalliyar kirki bace a fuskarta amma tayi kyau ainun, sai k'amshin turaruka masu dad'in gaske take wanda ya had'u dana asalin fatarta yabada wani kalar k'amshin mai dad'in shak'a. Sama sama ya amsa mata sannu da zuwan datayi masa ya wuce side d'inshi, bai dad'e ba sosai ya fito cikin riga da wando marasa nauyi na shan iska farare tas yanata k'amshi da alamu wanka yayi. Ganin d'azu da safe yace ta sauko masa da breakfast kan carpet hakan yasa yanzun ma tafara k'ok'arin dawo masa dashi k'asan nan kuma yace tabar masa shi akan dinning d'in ta d'auka ta k'ara mayarwa wato shidai ba'ayi masa gwaninta haka halinshi yake. Kamar dai yadda Abdallah yayi alk'awarin bazai d'agawa Janaan k'afa ba hakan ce ta faru kuwa a daren ranar ya maida Janaan cikakkiyar mace tasha matuk'ar azaba a hannunshi duk da yadda taso daurewa hakan ya gagara dan sosai tasha kuka abinta hakan kuma baisa ya sarara mata ba dan tamkar ma tana k'ara ingizashi ne. Ta b'angaren Abdallah kam yayi matuk'ar farin ciki da yadda yasamu Janaan kuma ta kaishi wata duniya ta daban wadda bai tab'a shigarta ba kuma tasamu babban matsayi a cikin zuciyarshi. Sam batayi tsammanin samun rarrashi daga gurinshi ba bayan wakanar komai amma ga mamakin ta sai taga ya zage yanata rarrashi da ban baki bayan ya k'ara shigar da ita jikinshi sosai, ganin haka tasamu damar k'ara shigewa jikinshi tanajin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta duk da kuwa rad'ad'in dake ziyartar ta ta k'asanta wanda take jin tamkar an watsa mata barkono. A wannan daren suka tsarkake jikinsu sannan suka koma barci tana jikinshi duk da dai a d'ar d'ar take dashi dan tasan yanzun nan zai canza kamar bashi ba shiyasa take baya baya dashi. ****** Number Jauhar ta kira Janaan ta kira dan jin dalilin dayasa har yanzu batazo taga inda take ba tarasa meke damun y'ar uwar tata haka, tana picking kuwa ta sakar mata kuka, sosai Jauhar ta shiga tashin hankali ta shiga tambayarta abinda ya faru take kuka hala itada wannan mijin nata ne mara alk'ibla cikin kuka Janaan tace "Ni karki k'ara sa mijina a ciki ba ruwanshi kuma inajin dad'in zama dashi". "A hakan?". Jauhar ta fad'a cikin zaro ido kamar tana gabanta. "Eh a hakan nakeji". Janaan ta fad'a tana share hawayen fuskarta, baki Jauhar ta tab'e tace "Sannu fa, ALLAH ya had'aki da aiki wllhy nidai yanzu fad'amin abinda ya saki kuka malama". Ajiyar zuciya Janaan ta saki tace "Amma saboda ALLAH kin kyautamin kenan Bloody ba'a kawoni dake gidana ba kuma har yanzu bakizo kinga inda nakeba why? meyasa kika tsani aurena da Yah Abdallah ne har haka Bloody?". ta k'arasa maganar cikin sanyin murya sosai. "A'a fa karki k'alamin sharri malama yaushe nace banason aurenki dashi? bake kikaji kika gani ba ina ruwana ni". "To naji yanzu yaushe zakizo dan ALLAH". Janaan tace. "Gobe dama zamu shigo dasu Hassana dan zuwa jibi nakesa ran komawa Ammi ce ma ta tsayar dani da tuni natafi wlhy". cikeda farin ciki Janaan tace "ALLAH ya kaimu goben dan ALLAH kuzo da wuri Bloody wllhy nayi missing dinku over". "Insha ALLAH". Jauhar ta fad'a sannan suka katse kiran a tare. Washegari tun sassafe Janaan ta fara shirye shiryen tarbar su Jauhar jitake tamkar taje ta taho dasu, dama da wuri Abdallah ya fita ranar. Ganin shiru shiru har kusan sha biyu na rana basu zoba hakan yasa ta kira layin Hassana ta tambayeta ko sun fasa zuwa ne tanata jira tun d'azu tace gasu nan yanzu suka fito driver zai kawosu sai lokacin taji dad'i a ranta dan duk zaton ta sun fasa zuwane. Da sauri ta nufi k'ofa lokacin dataji ana knocking ko tsayawa tambayar waye ma batayi ba ta bud'e cikeda tarin farin ciki da Jauhar ta fara cin karo cikin tsananin murna ta rungumeta kafin sukayi joining gaba d'ayansu dasu Hassana suka rungume juna ALLAH nagani sunyi masifar kewar y'ar uwar tasu, daga nan kuma suka rankaya suka shiga cikin falon suka zazzauna sam bakunansu sun kasa rufuwa musamman ma Janaan nan fa suka shiga hira baji ba gani da k'yar ma ta tashi ta kawo musu abin tab'awa suka d'ora daga inda suka tsaya bayan sunje sun zazzagayo gidan sun k'ara gani. Gaba d'ayansu suka shiga kitchen lokacin lunch, ganin sunada yawa yasa suka tarki yin sakwara aikuwa cikin k'ank'anin lokaci suka kammala ta da miyar ganye ragowar doyar da suka kirb'a kuma sukayi yam balls sai had'add'en kunun aya da kwakwa da sukayi suka jera komai bisa dinning table bayan sun gyara kitchen d'in sannan sukaje sukayi sallahr Azhar da aka kira tun d'azun banda Jauhar datake fashin sallah. Bayan duk sun idar suka hau kan dinning dan yin lunch sunaci suna hira har suka gama suka gyara kan dinning d'in suka k'ara bajewa nan cikin falon suka cigaba da hirarsu. K'arar bud'e k'ofar falon ce tasa duk suka maida hankalinsu kan k'ofar da aka bud'e, Abdallah ya bayyana sanye cikin riga da wando farare na kamfanin POLO takalmin k'afarshi ma POLO shima fari kayan sunyi matuk'ar amsarshi yayi kyau ainun, tuni falon ya d'auki shiru kamar basu bane masu dariya da shewa saboda dad'in hira, kauda kai Jauhar tayi tana wani mele baki kamar wadda taga kashi. A hankali ya shiga takowa har zuwa tsakiyar falon sannan ya tsaya tareda bud'e hannayenshi yana kallon Janaan da bata fahimci abinda yake nufiba sai kallonshi da itama take yi. "Taso mana". yace yana murmushi gamida ware manyan idanunshi akan Janaan, tanaso tayi masa musu ga kuma tsoro fal cikinta ga kunya data dabaibayeta haka dai ta tashi kamar kazar da k'wai ya fashewa cikin ciki ta nufeshi kanta a k'asa tana zuwa tayi yunk'urin tsugunawa shikuma ya hanata ta hanyar kamota ya sanyata cikin k'irjinshi ya maida hannayenshi ya rufe, lamo tayi tareda lumshe ido tana shak'ar daddad'an k'amshin dake tashi a jikinshi wani sanyi na ratsa zuciyarta wanda ya aikawa dukkan sassan jikinta, Hassana da Hussaina kam tamkar zasu nutse tsabar kunya data mamayesu duk k'asa sukayi da kansu dan bazasu iya ganin wannan tab'arar ta Yah Abdallah ba, Jauhar ma da akayi sa'a ta waigo da kanta inda suke tsaye suka had'a ido da Abdallah dayake ta wani lumshe ido yana bud'ewa hannu ya d'aga mata tareda d'age mata gira yana wani munafukin murmushi tareda shafa bayan Janaan da d'ayan hannun, wani k'ululun bak'in cikine yakama Jauhar tamkar ta tashi ta kama dukansu da duka takeji, k'aramin tsaki kawai taja tana tab'e baki ta k'ara maida kanta inda yake da farko, kan Janaan ya d'ago yana fad'in "Daga yau irin wannan oyoyon nakeso koma a gaban waye kinji HASKEN ANNURI". Kai kawai Janaan ta d'aga masa ba kuma dan zata iya d'inba sai dan gudun laifi, gefe d'aya na zuciyarta kuma mamakin sunan daya kirata dashi take uwa uba kuma dad'in da sunan yayi mata. Hannunta ya kamo har zuwa inda su Jauhar suke zaune, har lokacin Hassana da Hussaina basu d'ago kansu ba a hakama suka gaisheshi ya amsa sama sama, Jauhar kam dama batayi niyyar gaisheshi d'in ba yaja hannun Janaan. "Mtsww, kunya tayi a rayuwa gaskiya kuma wanda baida ita baiji dad'in shiba wlhy". kunnenshi ya d'auko masa sautin muryar Jauhar ta fad'a k'asa k'asa, murmushi yayi tareda sakin hannun Janaan yadawo inda Jauhar take zaune rank'wafawa yayi samanta cikin d'age mata gira yace "Yadai yarinyar nan kamar kinajin ba dad'i fa". Waigowa tayi ta sakar masa wani irin kallo tace "Kamar ya inajin ba dad'i akan wane dalilin?". Baki ya tab'e tareda d'age kafad'a alamun shima bai saniba, tsaki Jauhar ta saki cikeda k'unar rai, murmushi yayi ya tashi yabar wajen ya koma inda Janaan ke tsaye ya kama hannunta suka nufi side d'inshi. Tunda ya dawo ya hana Janaan sakat tanaso ta fito wajen su Jauhar ya hanata sunyi bulunbuk'wi a d'aki ba damar kuma ta fito ta barshi. Su kad'ai suka cigaba da hirarsu duk da dai can cikin k'asan ran Jauhar abin ya k'ona mata rai wanda batasan dalilin jin hakan ba. Sai lokacin da aka fara kiraye kirayen sallahr Asr sannan suka fito. Mrs Salees Mu'az 💝 3/5/22, 18:40 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 31 Paid book Oum Hanan *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* Yayi shirinshi na zuwa masjeed jallabiyyah black color sai k'amshi yake, lokacin suma su Jauhar sun tashi da niyyar zuwa yin sallahr akayi sa'a idanunsu suka had'u ya kashe mata ido kuwa yana wani murmushi data kasa fassarashi ya fice daga falon. Tsaki kawai taja ta juya ta nufi bedroom danyin alwalah duk suka bita da kallo kafin suma su mara mata baya. Daya dawo daga masallacin ma ba wanda ya nema ya shige side d'inshi ya rufe. Sai daf da sallahr magreebah sannan su Jauhar suka tafi cikeda alhinin rabuwa Janaan harda y'ar k'wallarta. √√^√√^√√^√√^√√ A gurguje please 🙇. Kwanaki sunci gaba da gangarawa inda kai tsaye Janaan bazatace tanajin dad'in zama da Abdallah ba hakama bazatace bataji ba saboda shi wani irin juyayyen mutum ne mai wuyar ganewa bashida hagu bare dama sau tari abune zatayi masa na kyautawawa amma saiya juya abun ya maidashi baibai yazama laifi a wajenshi amma duk da haka dai bata gaza ba kuma bata fasa yimasa d'in indai ta tabbatar tayine dan ta kyautata masa kuma tanada lada a gurin ALLAH duk wani abu da zaiyi baya damunta. Babu wata sakewa a tsakaninsu sosai kuma ta kasa daina tsoronshi wannan kam a jinin jikinta yake bata saniba dai ko nan gaba. Ta cigaba da zuwa school d'inta, kullum tare suke tafiya saiya ajiyeta sannan ya wuce office idan antashi kuma tadawo a napep ranar da y'an kirkin kuma suke kanshi saidai ta ganshi kawai yaje d'aukarta. ****** Jauhar dai ansamu matsala tsakaninta da Saleem kuma bawani abune ya had'asu ba kawai dai mahaifinshi ne ya nuna ra'ayin aura masa d'iyar k'aninshi lokacin dashi Saleem d'in ya gabatar da Jauhar a gurinsu a matsayin wadda yakeso ya aura. Yaji ba dad'i sosai kuma yayi iya bakin k'ok'arinshi wajen ganin mahaifin nashi ya barshi ya auri zab'in ranshi amma fur Alh Kabiru yak'i farko yaso ya bijire daga baya kuma da ya hak'ura. Ga mamakin Jauhar sam bata wani damu da rabuwar tasu ba dama can batajin wani feelings a kanshi batasan meyasa ba kawai dai suna soyayya ne har wani lokacin takan zauna tayi ta tunanin meyasa batajin sosai cikin ranta kuma yadda take tuna Abdallah shi bata tunanin haka duk da dai aduk lokacin data tuna Abdallahn saitayi tsaki saboda yadda yake shiga harkarta ya takura mata koda yake yanzu abin ya ragu sosai ba kamar da ba tarasa dalilin dayasa take yawan tunawa da wannan d'an buyagin mutumin. *NOTE* I'm sorry reader's! nasan da yawanku kunso kuji irin rayuwar da za'ayi a gidan Abdallah Madugu tsakaninshi da Janaan da irin dramar da za'a buga saidai kuma dole in tak'aita saboda tun farko an tsara kowa zaiyi gajeren labarine ta yadda masu karatu zasu karanta cikin marmari batare da abin ya gunduresu ba, kuma mugama cikin lokaci so shiyasa na tak'aita shi ba lallai saina fito nace ga abinda ya faru a gidan ba anyi kaza kaza kawai dai inaso ku kimanta a cikin ranku ku k'iyasta maza masu hali irin na Abdallah duk da dai nasan basuda yawa amma dai za'a iya samu ya auri mace mai hak'uri da kawaici irin yadda zaman zai wakana da irin hak'urin da zatayi basai lallai na fito na bayyana komaiba saboda hakan zai daukemu lokaci mai tsawo gaskiya kuma ba'a son hakan ta kasance fatan zaku duba mun gode sosai da had'in kanku wajen yimana comments ALLAH ya sakada alkhairi ♥️. Nagode. Bayan wasu watanni. Zaman Abdallah da Janaan yayi dad'i sosai Janaan tayi matuk'ar k'ok'ari wajen ganin ta canza Abdallah kuma alhmdulillah cikin kaso 100 ya rage wajen kaso 80 na abubuwan dayake ita kanta tayi mamaki k'warai amma idan ta tuna irin jajircewar datayi saitaga hakan ba abin mamaki bane dan sai datayi ta maza ta rage tsoronshi hakan yasa idan taga yayi abinda ba daidai ba harta gyara masa tun yana d'ura mata zagin daya saba yimusu da masifa da buyaginshi daya saba harya dawo ya fara d'auka ganin bata fasa ba. Cikin lokaci k'ank'ani Janaan ta siye zuciyar Abdallah tsaf da kyawawan halayenta gamida ladabi da biyayyar datake masa tasamu babban matsayi cikin zuciyarshi wanda bai tab'a tunanin zata sameshi a gurinshi ba,haka itama Janaan d'in mamaki take ganin yadda Abdallah ke nuna mata tsananin kulawa da soyayya wadda bata tab'a samunta a wajen rikitaccen mutum irin Yah Abdallah ba sai gashi kuma komai yazo mata da sauk'i ba yadda tayi zatoba tasan kuma hakan bazai rasa nasaba da yadda ta dage da addu'o'e ba dama ance addu'a takobin mumini tayi yak'inin da bata had'a addu'a ba zaman nasu sai a hankali duk da dai farkon auren tasha wahalar shi, a yanzun ma bawai ya daina bane gaba d'aya ance mai hali baya fasa halinshi ana d'an tab'awa 😀. Ta b'angaren su Ammi ma abin ya basu mamaki ganin Abdallah yana zaune lafiya da matar da suka zab'a masa koda yake y'an uwa da dama basu yi zaton hakan ba ALLAH natuba Abdallah ko wadda yakeso ce ya zab'a da kanshi ai zamansu sai addu'a bare kuma wadda ba zab'inshi ba, daidai da sau d'aya bata tab'a kawo masu k'arar shiba kuma kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin kwanciyar hankali da nutsuwa abin ya matuk'ar yimusu dad'i suka cigaba da binsu da addu'ar zaman lafiya mai d'orewa da tarin albarka a rayuwar su. Har zuwa yanzu Jauhar tak'i sakarwa kowa fuska danyin soyayya da ita, duk da yadda samari ke bibiyarta tak'i ba kowa dama haka nan take jin tagama soyayya a duniya duk wanda zasu had'u dashi yayi mata maganar soyayya saitaga baiyi mata ba bai kuma kai quality'n irin namijin datake da burin aure ba dan haka ta ajiye maganar soyayya a gefe ta maida hankalinta kacokam kan karatun ta. Kullum ta ALLAH sai sunyi waya da Janaan idan ita Janaan d'in bata kiraba ita Jauhar d'in zata kira danjin lafiyar juna. ******** ★★? Janaan na hanga zaune a falonta dayasha gyara sosai sai k'yalli yake yana tashin k'amshi tako ina, Sosai nake k'are mata kallo ganin yadda ta k'ara kyau sosai kan wanda take dashi ada hasken fatarta ya k'aru sosai kuma fatar ta k'ara yin smooth sai wani glowing take ga k'amshi na musamman da koya ta motsa jikinta yake tashi. Sanye take cikin farin wandon three quarter mai d'an fad'i sai half vest pink color ba komai a kanta sai manyan twist dake kanta wanda ya sauka har kan kafad'unta gaba d'aya hankalinta ya tafi kan cup d'in dake kan cinyarta sai faman sha take tamkar mayunwaciya har wani lumshe ido take tana kad'a kai alamun tana mugun jin dad'in abin. K'ofar falon aka bud'e Abdallah ya shigo bakinshi d'auke da sallama, shigar k'ananun kaya ne a jikinshi bak'in wando da shirt mai dogon hannu red colour ya matse wuyanshi da tie black color, sanye k'afarshi cikin boot red yayi matuk'ar yin kyau wannan mayen turaren nashi na biye dashi kamar bodyguard gaba d'aya hannayenshi soke suke cikin aljihun wandonshi ya shiga takowa idanunshi kyarr akan Janaan wadda sam batayi zaton shigowarshi yanzu ba ganin bai dad'e sosai da fita ba hakan yasa cikin hanzari tayi saurin b'oye cup d'in hannunta a bayanta gabanta na fad'uwa sai faman zare ido take tana murmushin yak'e, daga yadda tayi masa sannu da zuwan yasan batada gaskiya hakan yasa yana k'arasawa inda take yaja tunga yayi mata tsaye akai yayi crossing hands d'inshi a faffad'an k'irjinshi yana kallonta batare dayace komi ba. K'asa tayi da kanta tana shafa gefen wuyanta ALLAH yasa dai bai gantaba ita kanta wannan shan kwakin datake ya isheta baso take ba to amma ya zatayi da ranta itakuma haka ALLAH ya tsaro mata nata cikin d'an kimanin watanni biyu da rabi babu abinda take sha'awa sama da garin kwaki Abdallah yayi masifa da bala'in yayi buyagin nashi da hayagagar duk a banza saidai idan baisa k'afa ya fita daga gidan ba. Ganin baice uffan ba yasa ta d'ago kai ta kalleshi taga yadda ya tsareta da ido yana mata wani kallon tuhuma. "Bakida gaskiya Baby". ya fad'a kanshi tsaye, soshe soshen kai ta fara kamar zatayi kuka itama d'in batace komaiba ALLAH ALLAH take yabar kanta ta cigaba da shan abinta yawunta har gudanya yake. Hannu yakai bayanta inda ta sak'e cup d'in ya d'auko shi ya kalli kwakin dake ciki kusan cike, dawo da kallonshi yayi kan Janaan data tsure saboda tsoro sai wuri wuri take da idanu cikin had'e rai sosai yace "Ban hanaki shan wannan abin ba Baby? dan kinga ina lallab'aki shiyasa kike bijirewa maganata ko to bari in dawo miki Abdallah na na asali inci k'aniyarki tunda yanzu bakijin magana". A marairaice cikeda shagwab'a tace "Dan ALLAH Yah Abdallah kayi hak'uri please bazan k'ara ba ka....."Kima k'ara kiga yadda zanyi dake a gidan nan duk abincin gidan nan kirasa abinda zaki dinga ci sai kwaki saboda kijamin magana a wajen mutane ko". ya katse Janaan. "Yah Abdallah bayin kaina bane fa kafi kowa sanin hakan". tace kamar zata saki kuka. "Nafi kowa sani kuwa tunda nina d'ura abina amma kibari ki juyemin abinda ke cikinki nayi alk'awarin aje miki buhu buhu yadda zakifi jin dad'in sha tunda shi kikeso". Baki Janaan ta tura sosai jin abinda ya fad'a wato ita baya sonta kenan, dariya ta bashi hakan yasa ya shiga darawa yana cije lips gamida kamota jikinshi ya rungumeta sosai yana shak'ar daddad'an k'amshin dake tashi a jikinta, itama lamo tayi tana shak'ar nashi turaren idanunta a rufe wani tsananin son mijinta na k'ara ratsata ada gani take ba yadda za'ayi Yah Abdallah yasota har taji dad'in zama dashi sai gashi kuma alhmdulillah komai yazo mata cikin sauk'i batada matsalar komai dashi sai wanda ba'a rasaba wanda kuma zaman aure ya gaji hakan zo mu zauna zo mu sab'a tana fatan ta rayu da mijinta har k'arshen rayuwarta. Daga nan kuma salon labarin yafara canzawa ya d'auketa cak suka nufi bedroom ganin suna shirin zubewa k'asa. √^√^√^√^√^√•••••••? Rayuwa ta cigaba da tafiya da dad'i ba dad'i dama haka rayuwar ta gada watarana zuma watarana mad'aci ayi kuka ayi dariya da haka har lokacin da kowa zai amsa kiran ubangiji subhanahu wa ta'alah ubangiji ALLAH yasa mudace yasa ranar mutuwar mu tazama ranar farin cikinmu ALLAH kasa mu cika da Imani yabamu sa'ar tafiya alfarmar sayyadil wujuud sallallahu alaihi wa alihi wasallam (Amin ya Rahman). Mrs Salees Mu'az 💝 3/5/22, 18:41 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*💝 Page 32. Paid book *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*. © Oum Hanan Tun kafin cikinta yafara girma ya kaita ta ziyarci y'an uwa Yola suka fara zuwa suka sauka gidan Momy Maryam taga y'an uwa ta zazzagaya sosai kwanansu biyar anan Yolan suka wuce Kaduna gidansu Janaan. Tunda sukaje Abdallah yake gumawa Jauhar takaici iri iri rashin kunya kala kala kuma tasan da biyu yake hakan,su Mama kuwa sai sallamawa zaman falon sukayi Hajiya Yaya ce ma wani lokacin takan ce baza'a takura mata da zaman bedroom ba ta fito falon ba jimawa kuwa zata gudu tana faman mita Abdallah na mata dariya. Gaba d'aya Jauhar ta k'osa sutafi kafin zuciyarta ta buga duk da dai bata gaji da ganin y'ar uwar tata ba amma mijinta yaja mata, ita kanta Janaan d'in yana matuk'ar bata kunya saidai ba yadda ya iya dashi a haka suka gama kwanakin su suka tafi. Shak'uwa ce mara misaltuwa ta k'ara shiga tsakanin Madugu da Janaan duk wanda ya gansu dole yayi mamaki saboda sanin halin shi sai gashi kuma yabawa marar d'a kunya irinsu Aunt jamila da sauran y'an team d'inta 😄 bani na fad'a ba🥲. •••••••••••••? A haka Janaan ta cigaba da rainon cikinta wanda tun yana y'an watanni da basu wuce hud'u ba yayi girma sosai idan mutum yagani sai yace yayi wata biyar koma shida school d'inta kuwa tuni ta ajiyeta gefe saboda laulayin datake kullum batada cikakkiyar lafiya hakan yasa dole ta hak'ura duk da yadda takeson karatunta sosai. Sosai Abdallah yake bata kulawa taban mamaki wanda kowa yagani sai abin ya d'aure masa kai wai Abdallah ne yake yiwa mace haka?. Ganin yadda take matuk'ar shan wahala yasa Ammi da Ayyah suka nemi Abdallah ya maidata gabansu lokacin cikinta yanada wata takwas amma idan mutum yagani zai iya rantsewa ya shiga cikin na goma bama tara ba saboda yadda yayi mugun girma ga kumburi datake fama dashi, Nan fa Abdallah ya k'ek'ashe k'asa yace sam shi babu inda zaikai matarshi ko haihuwa tayi ba inda zata saidai azo a zauna musu saida Ammi tayi masa jan ido sosai harma da Abbie wanda Ammi ta fad'a masa ya kuma ga dacewar Janaan d'in ta dawo gabansu, haka nan dai bawai da son ranshi ba ya maida ita da siyayyar kayan baby daya uban jidosu kamar hauka. Kwana d'aya biyu shima sai gashi wai yadawo gidan da zama bazai iya zama acan ba matarshi ba, haka yasa aka gyara masa side d'in daya bari ya zauna a ciki. Sosai su Ammi kejin dad'in irin d'imbin kulawar da Abdallah yake bawa Janaan duk da dai harda rashin kunya yake had'awa saidai su kauda kai amma suna jin dad'in hakan sosai. Yauma suna bedroom d'in data sauka bayan zuwanta kusa dana Ammi, yana zaune a tsakiyar gadon ya jingina bayanshi da pillow ya mik'e k'afafunshi dogon wando ne a jikinshi plain ruwan zuma da farar riga mai gajeren hannu, Janaan na kwance kanta akan cinyarshi hannunta cikin nashi hannun yana mammatsa mata su saboda kumburin da sukayi suma hatta fuskarta ta d'add'aga matuk'a gaya yake tausayawa matar tashi ko ba'a fad'awa mutum ba yasan tanajin jiki ya matsu yaga ta haifar masa da abinda ke cikin nan nata kota huta da wannan wahalar. "Yayanah". yaji muryar Janaan ta ambaci sunanshi cikin sanyin muryarta wanda a yanzu ta k'ara yin sanyi sosai saboda wahalar ciki. "Na'am MAI SANYIN". yace shima a hankali bayan ya sunkuyo da kanshi saitin kunnenta, murmushi tayi jin sabon sunan daya mak'ala mata kuma yau dama kullum da kalar sunan dayake fad'a mata wani ma idan ya fad'a sai abin yaba mutum dariya. Bata bud'e idanunta da suke a lumshe ba tace "Idan na haihu wani suna za'a sawa babyn?". "Kibari ALLAH ya saukeki lafiya mana Baby saurin me kike uhmm?". "Nidai kawai inaso inji ne Yah Modibbo". tace cikin muryar shagwab'a, murmushi yayi yace "Idan namiji ne zan maida sunana ne idan kuma baby girl ce zataci sunanki ok?". Da mamaki tace "Sunan mu fa Yayanah?". "Basuyi bane?". ya maida mata da tambaya maimakon amsa yana d'age kafad'a daga zaunen dayake. "Nikam gaskiya dai.....bai bata damar k'arasa abinda yayi niyyar fad'a ba ya sunkuyo tareda zura bakinshi cikin nata ya shiga bata zazzafar sumba daga nan kuma ya shiga ragewa kanshi zafi cikin dabara batare daya takurata ba dama a kusa yake an kwana biyu ba'a had'u ba 🙃. Tunda cikin Janaan ya shiga watannin haihuwar shi su Ammi suke zuba ido amma shiru haka dai suka cigaba da jiran haihuwa da kuma addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya Abdallah da kanshi yake kashe ayyukan gabanshi ya kaita asibiti ganin likita da kuma yin awo. Lokacin da akayi scanning aka tabbatarwa da Abdallah twins ne a cikin Janaan, tamkar zaiyi hauka saboda tsabar murna suna dawowa kuwa ya fesawa su Ammi labari suma sunyi murna sosai tareda fatan sauka lafiya. √•√•√•√•√•√•√•√ A firgice Jauhar ta farka daga wani mummunar mafarkin datayi a daren ranar ganin y'ar uwarta cikin wani hali marar dad'i kai tsaye bazatace ga yanayin da Janaan d'in take ciki ba kawai dai ta ganta cikin wani hali mai wuyar fassara gaba d'aya sai jikinta yayi sanyi taji gabanta sai fad'uwa yake addu'o'e ta k'ara yi ta k'ara komawa ta kwanta da k'yar barci ya d'auketa bayan dogon lokaci data d'auka idanunta biyu ta kasa komawa barcin. Washegari kuwa tana idar da sallahr asubah ta dokawa Janaan kira a waya, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da taji Janaan d'in tayi picking kuma muryarta lafiya lau sai lokacin hankalinta ya kwanta sosai Janaan ta shiga tambayarta lafiya kuwa kira da asussuba haka? kawai cemata tayi ba komai kawai ta kirane dai taji lafiyar ta daga nan sukayi sallama. Tun daga lokacin Jauhar taji gaba d'aya hankalinta ya koma kan y'ar uwarta burinta tasa ta a idanunta duk hankalinta yayi Kano dan haka tasamu Mama da maganar tanason zuwa Kano, Mama tayi mamaki k'warai ta tambayeta dalili tace kawai ita haka nan take so taje taga Bloody d'inta, da farko Mama bata yardaba tace ta bari Janaan d'in ta haihu tunda ta kusa amma ta shiga yimata magiyar dan ALLAH ta taimaka ta barta tunda sun samu hutu a school da k'yar Mama ta barta tace zata fad'awa Daddy aji ta bakinshi. Da dare take fad'awa Daddy zancen tafiyar da sukayi da Jauhar baija da nisa ba yace ALLAH ya kiyaye hanya ayiwa Ja'afar magana ya kaita. Kwana biyu da yin maganar Jauhar ta shirya inda driver ya tafi kaita saboda Ja'afar aiki yasha masa kai a office hakan yasa bai samu kaita ba. Sai ganinta kawai sukayi katsam dan bata sanar da kowa zuwanta ba itama kuma Mama da sukayi waya da Ammi ta manta bata fad'a mata ba. Rungume juna sukayi sosai lokacin data k'araso cikin tsananin murna da soyayyar y'an uwantaka dake ratsa jininsu, ta tausayawa Janaan sosai ganin yadda takoma kamar ba itaba tamkar tayi mata kuka, nan suka had'u a bedroom d'in Janaan d'in har da Hassana da Hussaina sunata hira a haka Abdallah ya shigo ya samesu tun kafin ya shigo d'in k'amshin shi ya bayyana musu mai shigowar hakan yasa su Hassana duk suka mik'e tsaye suna jiran ya shigo su fita Jauhar kam tana nan a inda take kusa da Janaan tasan shi dinne saboda yadda bugun zuciyarta ya canza lokaci d'aya gabanta sai wani fat fat yake tamkar zai fasa k'irjinta ya fito waje batasan meyasa hakan ba kokuma dan ta dad'e bata ganshi bane oho murmushi kawai Janaan take saki tun kafin shigowar shi ALLAH sarki Yah Abdallah gaskiya wanda bai zauna dashi ba bazai tab'a fuskantar shiba yanada dad'in zama ga wanda bai saniba kuma yanada hawa kai da addaba itadai a yanzu batada kamar shi kulawar dayake bata ko auren soyayya sukayi sai haka ba abinda zatace sai alhmdulillah ubangiji ya karb'i addu'arta yabata zaman lafiya da nutsuwa a gidan aurenta. Yana shigowa Hassana da Hussaina suka fita daga bedroom d'in kansu a k'asa sudai duk da ake cewa Yah Abdallah ya canza har yanzu basu tabbatar ba dan zagin dayake musu bai dainaba yadai d'an ragu ba kamar da ba. Farar rigace a jikinshi long sleeve mara nauyi sai wandon jeans blue black saita gadon tashi wato P.cap white color dake kanshi idanunshi kyarr akan Jauhar da tun shigowarshi ta had'e rai sosai itama idanunta cikin nashi kowa da abinda yake sak'awa cikin ranshi yayin da kowa ya kasa fassara irin kallon da d'an uwanshi ke jifanshi dashi, sai taga duk ya canza mata kamar bashi ba yayi y'ar k'iba abinshi sab'anin da dayake sai uban tsayin kawai kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin tarin nutsuwa da kwanciyar hankali gashi ya k'ara fari akan wanda yake dashi da masha ALLAH musamman da bak'i sid'ik d'in sajen daya k'ara k'awata fuskar tashi da gemunshi na gayu wanda suke shan uban gyara da mayuka masu matuk'ar kyau da tsada. Ido ta runtse gam zuciyarta na wani irin rawa lokaci d'aya ta saki y'ar k'aramar ajiyar zuciya dako Janaan dake kusa da ita bata jitaba. A hankali ya shiga takawa inda suke zaune bayan ya soke hannayenshi cikin aljihun wandonshi, yana takowa ne yayin da bugun zuciyarta ke k'ara tsananta tayi ta maza ne kawai ta basar ta juyar da kanta gefe tana girgiza k'afafunta data d'ora d'aya kan d'aya, k'erere yayi musu akai yayi musu tsaye idanunshi akan Jauhar data juyar dakai wani side d'in. Rai a had'e ba alamun wasa a muryar shi cikin harshen fulatanci yace "Ke tashi ki fita zanyi sirri da matata". Da sauri ta juyo ta kalleshi tanajin tamkar ta tashi ta daddalla masa mari saboda mugun haushin daya bata. "Bazaki fita bane? ko bakya jin yaren danayi magana dashi?". yace still dai da fillacin yana zaro hannayenshi dake aljihu ya kama k'ugunshi da duka hannayenshi, a fusace Jauhar ta mik'e tsaye sama da k'asa ta kalleshi itama cikin fulatanci tace "Dan ALLAH idan ka tashi ka cinyeta gaba d'aya k'arewar sirri mtwss". taja k'aramin tsaki ta nufi k'ofar fita bedroom d'in. "Cinyewa ta nawa kuma? ki zuba ido kiyi kallo had'iyeta zan dinga yi ina dawo da ita tsabar yadda nake sonta kwarkwar d'in yarinya kawai". Tsaye tayi a bakin k'ofar bayan ta janyo k'ofar da k'arfi duk yadda taso hana hawayen idanunta zuba saida suka zubo zafi zuciyarta keyi mata tarin tambayoyi ne cike fal cikin ranta amma batada wanda zai amsa mata su, jin takun tafiya kamar an nufo wajen tasan baya wuce Ammi ko Ayyah. M&S 💝 3/7/22, 21:16 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*💝 Page 33. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022* © Oum Hanan. Da sauri tasa hannu ta goggoge idanunta sannan tabar wajen cikin sassarfa ta nufi bedroom d'insu Hassana. "Yah Modibbo wai sai yaushe ne zaku daina y'ar tsama da Bloody dan ALLAH?". Janaan tace tana kallonshi. "Ranar datayi hankali". yabata amsa kai tsaye yana zama kusa da ita. "Da da yanzu fa ba d'aya bane Yah Modibbo yanzun surukar kace fa". "Idan ban bige miki baki ba kice......kukan shagwab'a tasa masa wanda yasa ya kasa cigaba da maganar ya janyota jikinshi yana fad'in tayi masa shiru zai gaisa da baby's d'inshi. Tunda Jauhar ta fahimci abin na Madugu wulak'anci ne saita daina shiga bedroom d'in Janaan dan bayan wannan ya k'ara zuwa ya sameta suna zaune suna hira da Janaan lokacin su su Hassana suna school ranar ma kam baiyi mata magana ba sai gani tayi ya rungume Janaan d'in yasa bakinshi cikin nata ita kanta Janaan d'in abin yazo mata unexpected, abin yayi matuk'ar k'ona mata rai tashi tayi ta fita tanata faman masifa harda cemasa jarababbe da cikin ma bazai bar mata y'ar uwa ta huta ba ( Hajiya Jauhar 🤣). Tunda daga lokacin ta janye shiga bedroom d'in saidai su had'u a falo dasu Ammi ayi hirar cikin jama'a tasan dai duk iskancin shi da rashin kunyarshi bazaiyi a gaban su Ammi ba amma abinda ya bata mugun mamaki rannan a gaban Ayyah yayi hugging d'in Janaan ya k'ara mata da peck a goshinta Ayyah sai kauda kai tayi k'arshe kuma ta tashi ta bar falon tun daga nan ta sallamawa Madugu da aikinshi lallai a hakane har ake cewa yayi hankali? indai hakane kam da sauranshi ALLAH ya shiryashi. Friday morning. Tun bayan sallahr asubah Janaan takejin jikinta ba daidai ba ga ciwon baya da mara kad'an kad'an dake damunta idan suka murd'a mata saikuma su saki. Abdallah daya shigo lokacin dazai fita office yaga yanayinta duk ya rud'e ya dinga tambayarta ko tanajin wani ciwo ne cikin dauriya ta nuna masa ba komai batason tun yanzu ta nuna gazawarta ta tayarwa da mutane hankali, tsugunawa yayi yayi kissing d'in cikin ya tashi yayi kissing d'in goshinta ya gangaro kan dogon hancinta sannan ya dire kan bakinta doguwar sumba ya bata sannan ya saketa saidaya k'ara yin hugging d'inta sannan yayi mata sallama yana fad'in ta kular masa da kanta. K'ofar daya fita tabi da kallo fuskarta d'auke da mad'aukakin murmushi tana matuk'ar son Yah Abdallah yazama wani b'angare na rayuwarta a yanzun ALLAH ya bata ikon cigaba dayi masa biyayyar aure ninkin ba ninkin akan wadda take masa a da, siririyar k'ara ta saki tareda dafe k'asan mararta wadda ta tsinka mata idanunta ta rufe gam tana ambatar sunan ubangiji so take ta d'aga k'afar taje ta zauna amma ta rik'e da k'yar taja k'afafun nata da sukayi mata matuk'ar nauyi ta nufi bakin gado ta zauna tana cije baki. Ajiyar zuciya ta saki lokacin da ciwon marar ya saketa, nan ta cigaba da zama sai yayi kamar ya saketa saiya k'ara dawowa k'arshe dai k'asan tiles ta sauko ta durk'ushe nan k'asa tana salati idanunta a runtse, cikin haka ALLAH ya shigo da Ammi dan ta dubata taga halin datake ciki nan taga yadda Janaan take da sauri ta k'arasa inda take hankalinta a tashe ta dafa kafad'arta tana tambayar ta abinda ya sameta sam Janaan batayi magana ba sai cije baki datake ta faman yi na azaba hakan ya tabbatarwa da Ammi lallai nak'uda ce, da sauri taje ta sanar da Ayyah suka taho tare Ayyah tace kamata yayi a tafi asibiti dan haka zataje ta sanarwa driver ya fito da mota itakuma Ammi ta shirya kayan da za'a tafi dasu. Hakan kuwa akayi Ayyah ta fita Ammi kuma ta fara shirya kayan baby's dana Janaan d'in da duk wasu abubuwa datasan za'a buk'ata acan a rud'e take yin komai cikin hanzari tana faman jerawa Janaan sannu wadda har lokacin take durk'ushe a k'asa idanunta a rufe tana ambaton ALLAH batayi zaton abun zaiyi worsting haka tun yanzu ba, sam Jauhar batasan bikin da akeba sai lokacin da Ammi ta kamo Janaan zasu fita itama ta fito falon suka had'u sosai hankalinta ya tashi ta shiga tambayar Ammi meya samu Janaan d'in Ammi tace mata haihuwa ce zasu tafi asibiti ne zasuje itada Ayyah itakuma ta zauna a gidan, Jauhar taso binsu Ammi ta hanata tace suma ba dad'ewa zasuyi ba insha ALLAH suna fatan ace da sunje ta haihu haka suka tafi suka bar Jauhar cikin jimami na ganin halin da y'ar uwarta ke ciki. Suna zuwa aka karb'i file d'inta dama inda take zuwa ante natal ne aka shiga da ita labour su Ammi na zaune gaba d'aya hankalinsu a tashe yake indai kanada mai nak'uda dama hakane hankali bazai tab'a kwanciya ba har sai kaga ALLAH ya bud'i ido lafiya fatansu ALLAH ya sauketa lafiya ya kawota mai sauk'i kuma. Tunda aka shiga da Janaan take faman abu d'aya haihuwa shiru ba ita ba alamunta sai tsabar wuya datake sha, a hakan kuma tayi matuk'ar dauriya duk da haihuwar fari ce sam bata irin ihuce ihuce nan sai salati da ambaton ALLAH kawai take amma fa tana shan azaba wadda tunda uwarta takawo ta duniya bata tab'a jin irin misalinta ba. Ammi batayi niyyar kiran Abdallah ba karta tayar masa da hankali so tayi sai an haihu sannan ta kirashi tayi masa albishir amma ganin lokaci yanata k'ara shud'ewa abu yak'i ci yak'i cinyewa har lokacin bata haihu ba yasa Ammi tace ta kirashi ta fad'a masa nan kuma ta dinga neman number tashi switch off sai Abbie ta kira ta fad'a masa. Meeting d'in daya shiga yasa ya kashe wayoyin nashi bayan fitowar tashi kuma bai kunna wayar da wuri ba sai bayan wani lokaci daya kunna yaga kiran Ammi rututu har dana Abbie 2miscal, Ammi yafara kira ta sanar dashi suna hospital Janaan zata haihu sosai hankalinshi ya tashi nan da nan ya tattara duk abinda yake ya ajiye a gefe kasancewar dama yasan asibitin dama nan yake kaita ake duba lafiyar ta. Da gudu ya figi motar shi ya nufi asibitin, a reception yasamu su Ammi da Abbie harma da Yah Ameen dan lokacin da Ammi ta kira Abbie ta fad'a masa suna tare dashi sai suka taho tare. D'akin da Janaan take yaso shiga su Ammi suka hanashi nan suka cigaba da jira amma shiru sai shige da fice likitocin keyi a d'akin hakan ya k'ara d'aga hankalin su Ayyah. Jauhar kasa hak'ura tayi gaba d'aya hankalinta yak'i kwanciya dan haka su Hassana na dawowa daga school data fad'a musu suka shirya driver ya kaisu. Kowa kagani a gurin yayi jigum al'amarin yafara basu tsoro, Jauhar kam tuni ta fara kuka gani take tamkar zata rasa y'ar uwar tata, bayan wasu awanni da suka shud'e babban likitan dayake tsaye a kanta ya fito ya nufo inda suke tun kafin ya k'araso wajensu su suka tareshi kowa da tambayar dayake jefa masa game da Janaan anan yake sanar musu da cewa dole saidai ayi mata C.S haihuwar tazo mata da gardama bazata iya haihuwa da kanta ba, dan haka mijinta zaisa hannu ko iyayenta ayi mata abinda ya dace gaba d'aya sai jikinsu ya k'ara yin sanyi Abdallah kam tubure musu yayi harda cewa ba d'an iskan daya isa ya farka masa cikin mata zata haihu da kanta insha ALLAH sune dai basuyi abinda ya dace ba ya shiga masifa da bala'i ido kawai Dr Jabeer ya k'ura masa yana kallon ikon ALLAH lallai wannan gayen d'an tujara ne duk da alamu sun nuna shine mijin nata yasan tsayin lokacin da suke kanta kuwa? yasan irin k'ok'arin da sukayi na ganin ta haihu da kanta kuwa amma abin yaci tura? kokuwa zai koya musu aikinsu ne?. A fusace Abbie yace "Kai Modibbo banson shashanci da hauka mana kai wane irin yarone kasan tsahon lokacin da yarinyar nan ta d'auka cikin azaba kuwa tun safe ake abu d'aya ba irin k'ok'arin da basuyi ba ganin ta haihu amma shiru zakazo kayi mana buyagin naka daka saba anan karb'a kayi signing ko in b'ata maka rai yanzun nan". Abbie ya k'arasa maganar cikin tsawa, haka nan yana huci da kumbura baki ya karb'i takardar yayi signs ya koma gefe ya cigaba da kai kawo ranshi fal tausayin matarshi. Sunaji suna gani aka gangaro Janaan kan gadon da ake d'ora patient zuwa d'akin da za'ayi mata theater suka bita da addu'ar ALLAH ya raba lafiya Abdallah kamar zai bita d'akin haka yayi tsaye ya goya hannayenshi a bayanshi ya rasa abinda yake masa dad'i, Jauhar kam wani kukan ta k'ara saki lokacin dataga an fito da Janaan su kansu su Hassana hawaye suke. Abdallah tsaye yayi a k'ofar jiyake tamkar ya afka d'akin yaga halin da matarshi take ciki da k'yar Yah Ameen yaje ya dafo kafad'arshi ya dawo dashi inda suke, nan ma zaune yayi kan kujera ya dafe kanshi da hannu bibbiyu wanda yake mugun sara masa. Alhmdulillah cikin ikon ALLAH ubangiji ya basu nasarar ciro baby's d'in baby boy da baby girl, kyawawan yara manya manya farare tas masu kama da ubansu sak tamkar Abdallah yayi kaki ya tofar tamkar yaran larabawa masha ALLAH duk nurse's d'in sun rikice sai santin yaran suke. Nan da nan aka shiryasu cikin fararen kayan sanyi aka fito aka sanar dasu Ammi fad'ar irin farin cikin da wannan ahali suka shiga a wannan lokacin b'ata bakine gaba d'aya wajen ya rikice sai tashin hamdala kakeji musamman da sukaga yaran, suna fitowa suka shiga tambayar nurse's d'in lafiyar maijego suka shaida musu tana nan lafiya ba wata matsala bata farka bane dai har yanzun an kaita d'akin hutu. Ba kunya Abdallah ya had'a yaranshi ya rungume kyawawan yaranshi yanajin wani irin farin ciki mara misaltuwa yana ratsa k'wak'walwar shi zuwa gangar jikinshi wai yau shine da yara har biyu lallai wannan kyauta ce wadda ba wanda ya isa yayiwa wani mutum ita sai jallah wa azzah wanda kud'i ko mulki na mutum basu isa su siyeta ba alhmdulillah kawai yake jerawa cikin ranshi yayin da idanunshi suka ciko da k'wallar farin ciki, Ayyah ce ta karb'i baby girl d'in tana fad'in "Bani ita nan fitsararre". "Barni inji d'uminsu please Ayyah". yace yana kallon Ayyah. "Shima kawoshi zakayi mara kunya". Ammi tace tana kawo hannu ta karb'i baby boy d'in ba yadda ya iya amma yanajin tamkar a bar masa su cikin jikinshi su dawwama a haka, bisa kujera ya zame yana sakin wani murmushi lokaci d'aya yana shafa sumar kanshi yanzu kuma burinshi yasa Janaan a cikin idanunshi yaga halin datake ciki. Bayan wani lokaci Janaan ta farka, saidai farkawar tata tazo da matsala. M&S💝. 3/9/22, 20:15 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*💝 Page 34. Paid book *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*. ©Oum Hanan. _I'm sorry reader's yanayin labarin ne yazo da haka dazan iya dana canzashi tun farko so sorry mutuwa rigace da kowa saiya sakata a jikinshi, ni kaina page din nan ya tab'a min rai sosai ina ganin abin tamkar gaske 😭 ubangiji ALLAH yasa mu cika da Imani yabamu sa'ar tafiya alfarmar annabi rahma (S.A.W.)🙏._ Wani azababben ciwon ciki ta farka dashi wanda irin zaburar data dinga yi sai dayasa gadon datake kai ya dinga jijjiga kamar zata fad'o k'asa, ba k'aramin tashi hankalin likitocin yayiba abin ya matuk'ar tsorata su. Su Ammi ma basu san abinda yake faruwa ba dan basu fad'awa kowa ba burinsu kawai Janaan d'in ta tashi suga lafiyar jikinta, da k'yar da taimakon ALLAH suka samu suka shawo kan al'amarin ta d'an samu nutsuwa kad'an amma jikinta wani irin rawa yake kamar mazari ga wani irin numfarfashi datakeyi sun rasa daga ina matsalar take sister d'inta kawai take ambata da Yah Abdallah dan haka d'aya daga cikin likitocin yazo ya tambaya waye Abdallah dakuma sister d'inta a rud'e suka shiga tambayarshi lafiya kuwa ake nemansu? Anan ya sanar dasu maijegon ce take ta ambatarsu cikin sauri Abdallah da Jauhar sukabi bayan likitan zuwa d'akin da Janaan take ciki lokaci d'aya suka isa inda take da mugun sauri suka tsuguna gabanta a tare zuciyarsu tayi mugun rauni ganin yanayin halin datake ciki kuka Jauhar ta fashe dashi ta kama hannunta ta damk'e cikin nata hannun tace "Meya sameki haka Bloody?". Batayi magana ba sai kallonta data maida kan Abdallah wanda ya k'ura mata ido cikin rarraba maganar saboda hakin datake tace "Yayanah! ina yaranmu da muka haifa inaso in gansu please". juyawa Abdallah yayi ya kalli Dr'n dake tsaye shikuma ya kalli wasu nurse's biyu dake tsaye a gefenshi sun san ma'anar kallon dan haka suka nufi inda yaran suke a wani gadon daban suka daukosu suka kawosu aka sa mata su gefe da gefenta, duk da irin rawar da jikinta yake da numfashin ta daketa faman kaida kawo bai hanata rungume yaran sosai a jikinta ba wata irin k'aunar su da soyayyar su na ratsata saidai a yadda take jin jikinta tamkar bazata rayu dasuba, kuka kawai Jauhar take mai shiga rai Abdallah kam bakinshi ya mutu uffan ya kasa cewa sai idanunshi da suka kad'a sukayi jawur jijiyoyin kanshi sun tashi rad'a rad'a wani dunk'ulallen abu mai tauri ya tokare masa mak'oshinsa yak'i gaba yak'i baya. "Suna kama da Yah Abdallah nah ko?". Janaan ta fad'a da k'yar tana kallon Jauhar fuskarta d'auke da kuka mai had'e da murmushi ita kad'ai tasan azabar datake ji cikin jikinta, Kai kawai Jauhar ta jinjina mata yayin da wasu sabbin hawayen suka shiga rige rigen zubowa kan kumatunta cigaba Janaan tayi da fad'in "Bloody ga amanar yarana a hannunki duk da nasan zaki basu gata fiye da wanda zan basu inajin alamun rayuwata tazo k'arshe dan ALLAH ki kulamin da Yah Abdallah nah ki.......Da sauri Abdallah yasa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata yayin da idanunshi suka cika taf da k'walla. "I'm sorry N00R kiyi shiru dan ALLAH insha ALLAHU zaki tashi kar zafin ciwo yasaki sambatu mana zaki tashi mu cigaba da rayuwar mu cikin farin ciki da yaranmu zaki k'ara haifa min wasu twins d'in please *JANAAAN* kiyi shiru da bakinki kinga numfashin ki ba daidai yake ba stop crying please inane yake miki ciwo yanzu?". ya k'arasa maganar yana share mata hawayen da suka fara zubowa a idanunta yana share mata shikuma nashi hawayen na d'iga a fuskarta batare daya saniba saboda yadda idanunshi suka rufe fuskar tata ma dishi dishi yake ganinta. "Ba zafin ciwo bane Yah Abdallah bakusan ya nakeji bane inajin kamar ana huramin wuta a cikina Yah Abdallah ko ina na jikina ciwo yakemin". da k'yar ta k'arasa maganar tana fashewa dawani irin kuka tareda kamo hannun Abdallah ta kifashi akan fuskarta tana cigaba da kukan wanda sanadin hakan yasa numfashin ta sark'ewa tuni likitocin sukayo kanta dama tuni an kwashe yaran an maidasu gadon da suke da, da k'yar suka samu Abdallah da Jauhar suka matsa gefe farko ma cewa sukayi su fita tamkar kurame ba wanda ya kulasu dole suka k'yalesu wani irin kuka Jauhar take tamkar zata shid'e, basu san ya akayi ba waye ya fad'awa su Ammi sai ganinsu kawai sukayi sun shigo d'akin kowa hankali a tashe lokacin ansa mata oxygen dan taimakawa numfashin nata amma ina duk da haka fama take Abdallah kasa hak'uri yayi ya ratsa ta tsakiyar likitocin da suke kanta ya isa inda take ya durk'ushe a gabanta hannunta ya kama ya damk'e gam yana kuka sosai basuyi aune ba sukaga tasa d'aya hannun ta fincike oxygen d'in ta cillata k'asa a hankali bakinta yafara fad'ar kalimatush shahadah wanda k'arasowar Abbie wajen ya cigaba da d'ora mata tana fad'a har takai ga fad'in sallallahu alaihi wa sallam daga nan kuma komi nata ya tsaya cak (Ubangiji kabamu ikon cikawa da mafificiyar kalmar nan 😭🙏🙏). Gaba d'aya d'akin rud'ewa yayi Abbie ne kawai da Yah Ameen masu dauriya duk da suma d'in k'arfin haline kawai amma can k'asan ransu wani irin d'aci sukeji mara misali ganin abin suke kamar a mafarki wai Janaan ce ta rasu? ALLAH Al HAKEEM shi kad'ai yasan hikmarshi tayin hakan duk abinda ubangiji yayi to lallai akwai hikmah a cikinshi. Saida sukayi aune aunensu dan tabbatar da gasken ta rasu kuwa? abu d'ayane dai binciken nasu yake nuna musu Janaan lokaci yayi ubangiji yayi ikonshi akanta. Mayafin dake jikinta babban likitan yaja ya rufe mata gaba d'aya jikinta sannan sukabar d'akin kowanne da y'ar guntuwar k'wallarshi hak'ik'a sun tausayawa ahalin mai haihuwar nan suna tayasu jimamin rashinta tareda fatan ALLAH yabasu hak'urin rashi. Duka gaban gadon suka k'arasa gaba d'ayansu kuka suke mai cin rai musamman Jauhar wadda muryarta tafi ta kowa d'agawa tana rungume jikin Ammi da itama take kukan bata tab'a tsintar kanta a cikin makamancin halin nan ba jitake dama itama ALLAH ya d'auki rayuwarta a yanzun tabi y'ar uwarta ta huta, tamkar k'aramin yaro haka Abdallah ya dinga kuka yayi zaman dirshan a gabanta kanshi akan cikinta yana fad'in shi matarshi bata mutu ba likitocin ne munafukai kuma duk saiya d'auresu sai sunyi shari'a dasu kai daga jin irin maganganun dayake na rashin kan gado kasan bawai a cikin hankalinshi yake yinsu ba kamar wani zautacce, ganin hakan yasa Abbie ya d'agoshi ya rungumoshi jikinshi "Abbie Janaan ta mutu da gaske? Kai kawai Abbie ya gyad'a masa zuciyarshi tafara rauni da ganin halin da yaronshi yake ciki shima kamar yayi kukan yakeji saidai kuma shi namiji ne sunada dakakkiyar zuciya fiye data mata kuma bai kamata ace shida zai rarrashesu ba shima yanayi amma hak'ik'a rasuwar yarinyar nan ta tab'ashi fiye da tunanin mai tunani. "No Abbie nooo matata bata mutuba dan ALLAH kuce ta tashi please". yayi maganar da k'arfi yana kallon gadon Janaan bai jira abinda Abbie zaice ba ya zame daga jikinshi ya nufi inda Yah Ameen yake tsaye yana fad'in "Please Brother kayi wani abu mana ka fad'amin da gaske Janaan ta rasu?". k'wallar data taho masa yayi saurin maidawa ya kamo hannayen Abdallah yace "Janaan ta amsa kiran ubangiji Abdallah ka nutsu ka fahimta Janaan bata raye kayi mata addu'a ALLAH yaji kanta ya raya abinda tabari". Kai Abdallah ya shiga kad'awa kamar irin ya fahimta d'in nan ya bud'e baki zaiyi magana kenan sai gani sukayi yayi luuuu jikin Yah Ameen idanunshi a k'akk'afe cikin hanzari Abbie ya k'araso suka tareshi daidai lokacin da itama Ammi taji Jauhar dake jikinta ta langab'e mata duk jikinta ya saki hakan ya tabbatar mata da itama ta suma kamar Abdallah salati gurin ya d'auka yayin da tashin hankalinsu ya k'ara nunkuwa fiye da da, da k'arfi Yah Ameen yacewa Hussaina wadda keta gurshek'en kuka kamar ranta zai fita taje ta kira musu Dr, da gudu tayi hanyar fita daga d'akin sukaci karo da Dr'n zai shigo suka dawo ciki tare. •√•√•√•√•√•√•√•√•√? Gado biyune kawai a d'akin na marasa lafiya suna facing d'in juna Abdallah da Jauhar ne kwance akan gadon kowanne hannunshi mak'ale da drip, tashin hankali ba dad'i jama'a iya yanzu kawai dana kalli fuskar Abdallah sai daya bani tausayi saboda yadda naga ya zuge lokaci d'aya Abbie da Yah Ameen su kad'ai ne a d'akin kowa ya zuba tagumi sun rasa abinda yake musu dad'i a duniyar nan dama haka lamarin ubangiji yake idan yaso jarabtar mutum fatansu dai ALLAH ya basu ikon cin wannan jarrabawar. Abdallah ne yafara farkawa da kuka ya farka yana wasu maganganu dasu Abbie basujin abinda yake fad'a saboda k'asa k'asa yakeyi, da sauri Yah Ameen ya fita kiran Dr ba jimawa suka dawo tare kamar yana jiran shigowar su ya fincike drip d'in ya fara k'ok'arin tashi wai zaije wajen Janaan Dr'n da Yah Ameen su suka dinga rirrik'eshi yana zamewa a dole saiya sauka Abbie dake kusa dashi yanata masa magana amma yak'i kulashi burinshi kawai su sakeshi ya fita. "Abdallah". Abbie ya fad'a da k'arfi sosai har d'akin yana amsawa, yaune karo na farko da Abbie ya tab'a ambatar sunan Abdallah gatsau ba tare dayace masa Modibbo ba kamar yadda suka saba fad'a shida Ammi, tuni Abdallah ya nutsu ya k'urawa Abbie ido hawaye na sauko masa kan kumatunshi wani na bin wani tamkar an kunna famfo, a hankali cikin nutsuwa da tsananin tausayin Abdallah Abbie yace "Abdallahi! ka nutsu ka bani hankalinka nan Hassana ta rigamu gidan gaskiya ta tafi gurin wanda yafimu sonta da k'aunarta shiya bamu ita kuma ya karb'i abarshi shin kanada ja ne akan hakan? kokuma dan wani yabaka aron abinshi yazo daga baya ya karb'a zakaji haushi? mutuwa gaskiya ce Abdallah kuma rigace dani dakai dasu da kowa da kowa saiya sanyata babu wata rai da bazata d'and'ani d'acin mutuwa ba kullu man alaiha faaan kowa saiya tafi mutuwa ta d'auki shugaban dayafi kowa ANNABI MUHAMMAD sallallahu alaihi wa sallam ta d'auki annabawa ta d'auki manya manyan sahabbai ta d'auki tabi'ai ta d'auki tabi'uttabi'ina ta d'auki manya manyan malamai da sauran muminai to waye bazata d'auka ba Abdallah? Hassana ta samu shaida da yabo ta mutu ranar juma'a ta cika da kalimatush shahadah me kuma musulmin k'warai yake fata banda wannan? kayi hak'uri mutuwa akwai d'aci kuma gyambo ne da warkewar shi sai a hankali kayi mata addu'a ALLAH yaji kanta yayi mata rahma yasa taje a sa'a ya had'a fuskokinku da alkhairi kaji Modibbo". Abbie ya k'arasa maganar cikin sigar lallashi yana kallon Abdallah wanda alamu suka nuna nasihar Abbien tayi matuk'ar tasiri a zuciyarshi da gangar jikinshi gaba d'aya. Jauhar ma tun lokacin da ake fama da Abdallah na saiya fita itama ta farka, a hankali k'wak'walwar ta tafara tariyo mata abinda ya faru wanda take fata da addu'ar ace mafarki ne ba gaskiya ba yanzu shikenan twin sister d'inta ta tafi ta barta ita kad'ai? shikenan bazata k'ara ganinta ba ta mata nisan da har abada bazasu k'ara had'uwa ba sai a darussalam? wani kuka tasaki mai k'arfin gaske harda shasshek'a kamar zata shid'e tareda dafe kanta dayake mugun sara mata wanda yayi mata mugun nauyi take jinshi tamkar ba nata ba da sauri Yah Ameen ya nufo wajenta. Mrs Salees Mu'az 💝 3/11/22, 23:55 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 35. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*. ©Oum Hanan. Da gawar tata suka tafi duk wanda ka kalla idanu sunyi ja sun kumbura wasu kam suna kan yine har yanzu irinsu Jauhar da Hassana da Hussaina da kuma Aunt Deejah wadda bata dad'e da zuwa ba baby girl d'in na hannunta shikuma namijin yana hannun Ammi har suka k'arasa gida Abdallah yayi shiru kamar mai nazarin wani abu kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin tsantsar tashin hankali da rashin nutsuwa sai wata irin ajiyar zuciya yake saukewa akai akai Yah Ameen ne dake zaune kusa dashi yake yawan dafa kafad'arshi alamun rarrashi bai tab'a tunanin haka Abdallah yake son Janaan ba sai ayau da babu ranta. Suna komawa aka fara shirye shiryen had'ata ayi mata sallah a mik'ata gidanta na gaskiya, sai bayan la'asar sannan al'ummar annabi masu d'imbin yawa suka sallaci gawarta sannan aka d'auketa zuwa gidanta na gaskiya tafiyar da babu dawowa ALLAH yasa muyi kyakkyawan k'arshe dan sayyadil wujuud 🙏. Abdallah kamar zaiyi hauka a lokacin dan makarar ya rirrik'e yana kuka da k'yar aka b'amb'areshi ya durk'ushe a wajen ya cigaba da kukan Habeeb da Abdallahn Momy Maryam wanda ya samu isowa yanzun suka kamashi suka d'agashi suna rarrashi duk da suma hawayen suke hak'ik'a mutuwar Janaan ba mutum d'aya ta tab'a ba kowa jimantawa yake kuma tasamu shaida mai kyau a wajen mutane da dama, daga nan suka nufi inda mak'abartar take suna rik'e dashi. Mama tayi dauriya sosai ko d'igon hawaye babu a idanunta sai na zuci datake itace ma take rarrashin Ammi, Hajiya Yaya kam kuka ta dingayi sosai lokacin da suka k'araso abu d'aya kesa zuciyar mutane karyewa idan aka kalli jariran data bari wanda basu san komaiba shikenan sun rasa gatan UWA, UWA ta daban ce a rayuwar nan kowa tausayin yaran yakeji, musamman da akaga sunata neme nemen abinci zam-zam aka basu sannan aka tauna dabino aka basu ruwan daga nan kuma Habeeb yaje ya siyo madara bayan an dawo daga kai Janaan. An cigaba da karb'ar gaisuwa mutane tako ina b'arkowa suke b'angaren Abdallah ne Abbie Ammi Mama Yah Ameen da sauran y'an uwa da abokan arzik'i hak'ik'a Janaan tana shan addu'o'e daga bakunan mutane da dama duk wanda ya santa alkhairinta yake fad'a kowa ya bud'i baki saidai ya yabeta ko hakan da Ammi da Mama sukeji yana d'an rage musu rad'ad'in rasuwar Janaan Hafsat Yusuf ma k'awarta ta school tazo itada mahaifiyarta tasha kuka ba kad'an ba tanajin wata irin kewar k'awar tata ALLAH yayi bazasu gama karatun tare ba. Jauhar kullum tana k'ule a d'aki sam ko fitowa batayi bedroom d'in da Janaan ta sauka lokacin data dawo gidan nan ne yazama wajen zamanta ta tasa kayan Janaan d'in a gaba tana kallonsu tana kuka ratuwarsu ta baya tana dawo mata kafin Janaan d'in tadawo gidan Ammi takan tuna irin hak'uri da kawaicin da ALLAH ya azurta ta dashi ko takalarta tayi da fad'a bata kulata sau dayawa wani abun na Janaan d'inne amma saitayi ruwa tayi tsaki tace natane haka zata bar mata batare data damuba ALLAH yasa hak'urinta ya amfaneta, cikin kwana biyu Jauhar ta rame saboda tunani datasa a ranta da kuma rashin cin abinci batacin komi sai ruwan Lipton shima sai wani daga cikin Aunt Deejah ko Jeeddah ko Aunt Mabrookah ko sauran yayyensu sunzo sun tasata a gaba sannan za'a samu tasha da k'yar duk tabi ta tsangwami kanta. Yadda ake fama da Jauhar haka Habeeb Yah Ameen Abdallahn Momy Maryam suke fama da Abdallah yazama kurman k'arfi da yaji sam ya daina magana saidai yaita bin mutane da kallo, ko gaisuwa akayi masa saidai ya amsa dakai gashi baya cin komai duk ya zabge ya lalace duk faman da sukayi dashi kuwa k'arshe ma sai tashi yayi ya shige bedroom d'inshi ya rufo k'ofar saida takai sun had'ashi da Abbie yazo har d'akin bayan yasa an had'a masa tea mai kauri sosai yataho dashi, yanaji ana bugawa yayi kunnen uwar shegu dasu yak'i bud'ewa duk a zatonshi su Abdallah ne sai dayaji muryar Abbie sannan ya bud'e. A hankali cikeda da rarrashi Abbie ya fara yimasa nasiha da nuna masa wannan abinda yake duk bashi bane addu'a ya kamata ya dinga yimata ALLAH ya sadata da rahmarshi cikin hikmah irin tasu ta manya yasamu Abdallah yasha tea d'in sosai shik kanshi yayi mamakin wanda yasha daga nan Abbie ya k'ara d'ora masa da wata nasihar mai shiga zuciya saida Abbie yaga ya k'ara samun nutsuwa sosai sannan yabar bedroom d'in, maganar bacci kuwa babu ita yadda ya kwanta haka yake tashi ganin baccin ba samuwa yakeba kawai saiyayi alwalah yayi sallah tareda rok'arwa Janaan da sauran musulmi gafara da rahmar ubangiji. Wani lokacin Abdallahn Momy Maryam da Habeeb sukan zauna suyita kallon Abdallah yadda ya canza lokaci d'aya mutum magananne ga masifa da bala'i da shak'iyanci kala kala amma dubi yadda ya koma wani salihi kamar bashi ba lallai idan ubangiji yaso zai iya canza mutum lokaci d'aya kokuma ya canza mutum ta sanadiyyar wani kamar yadda Abdallah ya canza sanadin rasuwar Janaan. Abdallah taron mata dake cikin gidan baya hanashi shiga yaga yaranshi haka yake ketasu har saiya dangana da inda suke sun zama sanyin idaniyarshi yana jinsu fiye da komai a cikin zuciyarshi a yanzu baahi kad'ai ba kowa na familyn yana nunawa yaran soyayya suna iya bakin k'ok'arinsu wajen ganin sun basu kulawa tamkar mahaifiyarsu na raye. ✓✓✓✓✓✓✓✓••••••••••••✓✓✓✓✓✓✓? Ranar Bakwai. A yau Janaan take kwanaki bakwai da rasuwa yayin data kama ranar rad'in sunan twins anyi yanka kamar yadda addini ya tanadar ba'a canza musu sunaba an barsu da sunansu dama ance twins da sunansu suke zuwa, saidai ita Hussainar duk Janaan suka fara kiranta dashi a tak'aice dai Janaan ta tafi Janaan ta dawo fata dai ALLAH yasa tayi d'abi'un mai sunan. A ranar Habeeb da Abdallahn Momy Maryam suka lodowa yaran siyayyar kayayyaki kala kala masu kyau da tsada. Washegari Mama da sauran yayyen su Jauhar da Hajiya Yaya suka fara shirin komawa Mama taso Ammi ta bata little Janaan ko Hassan wanda suke cewa Irfaan ta tafi da d'aya daga cikinsu Ammi ta rok'i alfarmar abar matasu duka dan ALLAH bataso a rabata da yaran nan ganin yadda duk ta damu yasa Maman tace shikenan a barsu d'in, Ammi taji dad'i sosai sam bataso a raba yaran nan tafiso su tashi tare. Da Jauhar aka shirya tafiyar amma jin ance yaran anan za'a barsu saita tubure ita wllhy ba inda zata bazata tafi tabarsu little Janaan ba abin yabawa kowa mamaki amma duba da yadda tayi mugun sabo da yaran ba abin mamaki bane kullum tana mak'ale dasu ta goya wancan data saukeshi ta maida d'ayan gaba d'aya rabin d'awainiyarsu itace Mama ta kanyi mamakin hakan sosai a yadda tasan Jauhar da d'an banzan son jiki da lalaci ko aiki sai anyi fama da ita takeyi amma dubi yadda ta zage hidimar yaran kaf ta d'auketa batare da nuna k'osawa ba duk yadda aka kad'a aka raya Jauhar tace ba inda zataje bamai rabata da yaran nan k'arshe ma kuka ta saka musu saboda mutuwar Janaan data dawo mata sabuwa fil a cikin zuciyarta, ido kawai kowa na wajen ya zuba mata kafin Hajiya Yaya tace "Ke bamuson sakarci mana kin tashi kin shirya kokuwa kinata b'ata mana lokaci tun d'azu ku kiramin Abdullahi yazo yayi mana maganinta yanzu tunda batajin magana". ta k'are maganar tana kallon Hassana. "Hmmm Hajiya Yaya ko Abdallah yazo yanzu ba abinda zai iya yimata kura tayi lafiya ai rasuwar Janaan duk ta canzashi". cewar Ayyah, cikin kuka Jauhar tace "Wllhy ko yazo ba inda zanje saidai idan dasu zamu tafi Kadunan". ido kowa ya zuba mata lallai abin na Jauhar da gaske take, cikin lallashi Mama tace "Haba auta ta kinga kina zuwa school idan kika zauna nan ya zakiyi da makarantar gashi hutun da kuka samu ya kusa k'arewa ki shirya mutafi idan aka samu wani hutun sai Ja'afar ya kawoki kinji". kafad'a Jauhar ta nok'e alamun a'a har hakan ya basu dariya murmushi Ammi tayi tace "Dan ALLAH Yaya a barta d'in har hutun nasu ya k'are sai Modibbo ko Aminu wani a cikinsu ya maida ita". Kan dole dai Maman ta amince bataso kad'aici yayi mata yawa. Abdallah ne yayi sallama ya shigo falon yana sanye da farar jallabiyyah da dogon wandon shadda fara, fuskar nan tashi fayau saboda ramar dayayi waima a hakan yadan ciko sai dogon hancinshi daya k'ara fitowa sosai ga uwar k'asumba data fara cika fuskar tashi wadda bata samun wani gyaran kirki, Kai tsaye kusa da Mama ya nufa ya zauna batare daya yiwa kowa magana ba. "Yadai mai sunan manya?". Mama tace tana kallonshi fuskarta d'auke da murmushi, kanshi ya kwantar a kafad'arta yana sakin ajiyar zuciya duk binshi akayi da kallo Jauhar kam kukan datake ta daina ta kalli yadda ya wani shasshake tsaki taja cikin ranta wai yaushe mutumin nan zai girma ne fisabilillahi ya rasa ina zai kwantar da kanshi sai wajen surukarshi ALLAH dai ya kyauta masa ya girma baisan ya girma ba, d'agowa yayi ya kalli Ammi yace "Ammi ina suke?". kowa yasan suwa yake nufi dan haka Ammi ta bashi amsa da "Suna d'aki barci suke". "Ke kuje ku daukomin su duk yau bamu gaisa ba". ya ida maganar yana kallon Hassana da Hussaina da suke kusa da Ayyah. "Ban gane a d'auko masa suba yaran suna barcin za'a tashesu". Hajiya Yaya da bata gani ta k'yale ta fad'a tana masa wani irin kallo. "Hajiya banason magana please a fitomin da yarana in gansu". yace cikin sanyin murya da rasuwar Janaan ta haddasa masa ita. Baki kawai Hajiya Yaya ta tab'e cikin ranta take ayyana wannan yaro dai bazai tab'a canzawa ba, kallonshi ya maida kansu Hassana ranshi a had'e sosai hakan yasa cikin sauri suka tashi suka tafi bedroom d'in Ammi inda su little Janaan suke, Ammi da Ayyah dai basu tanka masa ba su Aunt Deejah ma basu kulashi ba. Basu dad'e ba sai gasu sun d'auko su anyi musu shigar kayan sanyi overrole da hulunansu an nad'esu da shawul mai taushi gaske sai k'amshi suke zabgawa, zamanshi ya gyara suka d'ora masa su a cinyarshi har lokacin basu tashi ba sai baccinsu suke sha, tuni yanayin fuskarshi ya canza ta washe lokaci d'aya duk saiya manta da kowa na wajen ya shiga yimusu wasa kamar sunsan abinda yake, sudai mutanen dake wajen sai suka tsaya kallon ikon ALLAH gaskiya Abdallah bashida kunya. Mrs Salees Mu'az 💝 3/13/22, 07:08 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*💝 Page 36. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*. ©Oum Hanan. Takaici yasa Jauhar jan tsaki batare data san tayi d'inba, in banda shirme na Yah Abdallah ya za'ayi ka dinga yiwa yara y'an 8dys wasa a hakan ma kuma barci suke inyayi maka wani abun kamar d'an fari. D'agowa yayi da sauri ya kalli Jauhar wadda suna had'a ido tayi saurin kawar da nata ido ya k'ura mata sosai harya bud'e baki zaiyi magana kome ya tuna saikuma yayi shiru ya maida kanshi kan yaran yana taune lips d'inshi na k'asa, ya dad'e a zaune a wajen har wasu daga cikin y'an falon suka tattashi shi yana zaune hankalinshi gaba d'aya yana kan twins. Dole haka su Mama sukayi sallama suka tafi batare da Jauhar ba tace babu mai rabata da twins d'inta. ****** Jauhar tana burge Ayyah da Ammi sosai harma da Abbie saboda yadda take yiwa yaran nan matuk'a take nuna musu tsananin so da k'auna bataso ko k'uda ya tab'asu duk wata d'awainiya da hidimar su ta d'auketa tsaf kamar irin dama can ta saba da rainon yara ko taimakon su Ammi wani lokacin saitace bataso saitaji uwar bari sun caza mata k'wak'walwa sannan take nufo Ammi dasu waya gaya miki Jauhar 🤣 rainon twins wasane is not easy fa aradu 😪. Abdallah kanshi yana matuk'ar jin dad'in yadda Jauhar d'in take yiwa yaran nashi ya fito ya nuna ne dai bai tab'a ba amma yana yaba k'ok'arin ta a zuciyarshi dan duk lokacin daya shigo gidan ganinsu zai samesu a wajenta tana hidima dasu. ***★★?*** To haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya yau da gobe kayan ALLAH gidan yafara komawa kamar da sun fara sabawa da rashin Janaan walwalar gidan tafara dawowa duk da dai sai a hankali har yanzun twins sun fara girma madarar ta karb'esu sosai sunyi dumi dumi dasu gwanin sha'awa kullum kyawunsu k'ara fitowa yake haka kuma kamanninsu da Abdallah na k'ara bayyana shak'uwar Jauhar da yaran na k'ara k'arfi kowa nan nan yake dasu suna ganin gata sosai kuma har yanzu basu daina basu tausayin rashin UWA da sukayi ba duk da ba abinda suka nema suka rasa kullum Abdallah ya fita da kalar abinda zai shigo musu dashi na daga kayan sawa masu kyau da tsada dana kwalliyar yara da kayan wasa duk da har yanzun basu gama sanin menene wasan bama. Daf da hutun su Jauhar zai k'are Mama tayiwa Ammi waya ta fad'a mata ya kamata Jauhar ta dawo haka nan tafara shirin komawa school dan Monday zasu koma saura kuma kwana uku litinin d'in, Ammi na fara yiwa Jauhar maganar tafiyarta ta nuna sam batasan zancen ba inkuwa aka tilasta mata ta tafi saidai ta tafi da twins d'inta ba kalar lallashin da Ammi batayi mata ba amma ta tubure gashi sam Ammi batada zafi bare ta b'ullo mata ta bayan gida sai Maman ta k'ara kira ta fad'a mata yadda sukayi da Jauhar d'in ta kuma kawo shawarar me zai hana abar musu Jauhar d'in sai a samar mata gurbin karatu a B.U.K inda su Hassana suke ta cigaba dayi anan, shiru Mama tayi tana tunani shikenan fa idan Jauhar ta koma can batada wani yaro kenan a gabanta sai Ja'afar shikuma ba za'ayi la'akari dashi ba tunda namiji ne ba mazauni bane kuma batason Ammin ta tambayeta wani abu a matsayinta na y'ar uwarta jininta ta hanata amma dai zata yiwa Daddy maganar duk abinda ya yanke shikenan duk da tasan dai da wuya ya hana d'in inyaso ita saita d'auko Kauthar babbar d'iyar Zaleeha babbar yayar su Jauhar dama tana yawan zuwa tayi kwanaki kafin takoma gidansu. Hakan ta fad'awa Ammi tace yadda sukayi da Daddyn zata kira ta fad'a mata, godiya Ammi tayi sannan sukayi sallama kowa ya kashe wayar. Kamar yadda Maman tayi alk'awari bayan dawowar Daddy tayi masa zancen, shikam baima ja da nisa ba yace tayi zamanta a can d'in nan da can d'in duk d'aya ne ALLAH yasa zaman nata a can shine mafi alkhairi, Hajiya Yaya ce dai dataji maganar tayi k'orafin nata data saba ya za'ayi ace duk yaran can zasu tare taso hanawa Daddy ya lallab'ata da k'yar ta yarda amma fa tana ta faman maganganu da mitarsu ta tsaffi musamman idan Mama tana wajen itadai uffan bata cewa harta gaji ta daina. Lokacin da Jauhar taji labarin da Ammi take fad'a mata tayi matuk'ar farin ciki da murna itafa burinta kasancewa da yaran nan batason abinda zai rabasu ko kad'an su kansu yaran da ita suka bud'i ido dan haka suka fara sabawa da ita. Tsakaninta da Abdallah ido ne babu mai cewa d'an uwanshi kanzil kowa harkar gabanshi yake hakan yana mata dad'i sosai da baya takalarta duk da dai tun kafin bikinshi da Janaan ta lura ya janye mata. Yah Ameen Ammi tayiwa maganar karatun Jauhar dan haka yafara yimata cuku cukun samar mata gurbin karatu a Bayero University Kano, ba'a d'auki dogon lokaci ba komi ya kammala harsun fara tafiya tare dasu Hassana da k'yar take tafiya tabar yaran saikuma d'awainiyarsu takoma kan Ammi saidai idan tadaw ta d'ora. Abdallah sai gani yayi tafara zuwa school kai kawai ya jinjina yana tab'e baki lokacin daya hangosu ta windown bedroom d'inshi driver zai kaisu wato tadawo nan kenan gaba d'aya shima d'in kai tsaye bazaice bayason zamanta anan ba ko dan yaranshi abu d'aya dai yasani wanda yakejin baison ta zauna anan wanda shi kad'ai ya barwa kanshi sani. 1Yrs After. Cikin ikon ALLAH su Jauhar har sunyi graduation itada su Hassana dama classmate ne, twins suna gudunsu ko ina dole subawa mutum sha'awa idan ya gansu sunyi mugun sabo da Jauhar abin nasu har mamaki yake bawa mutane saboda tsananin yadda suka shak'u. Auntie Fareedah ma matar Yah Ameen sun samu k'aruwar baby boi wanda yaci sunan Abbie suke masa alkunya da Aabeed. Abdallahn Momy Maryam dai yayi wuff da Hassana 🤣 yayin da Habeeb shikuma ya kafa ma Hussaina k'ahon zuk'a tun tana d'ari d'ari dai dashi harta amince dan farko tsoron Yah Abdallah ne yasa tak'i yarda to shi ranar daya gansu ma a compound ko bi takan su baiyiba sai bayan da suka gama zancen ne Habeeb ya shiga side d'in Abdallah anan yake tambayar shi meye had'inshi da Hussaina ya gansu tare bayani Habeeb yayi masa tsaki yayi yace "Banzaye haka zaku k'are naji ma wancan shegen wai Hassana yakeso yara k'ananu ku auresu kuce kun auri me?". had'e rai Habeeb yayi yace "Ba ruwanka malam a haka muka gani mukace munaso kasa ido kawai kayi kallo". "Saikuyi tayi ai manyan banza". yace tareda zamewa ya kwanta kan kujerar dayake kai zaune. Cikin kwanakin kuma saiga maganar Ja'afar ta b'ullo shikuma wai Hannah yakeso k'anwar Abdallahn Momy Maryam, hak'ik'a y'an uwa dayawa sunji dad'in wannan al'amari ganin zumunchi zai k'ara had'uwa kenan kowa fatan alkhairi yake da addu'ar ALLAH yasa aga lokacin. Ganin abu duk na gidane yasa aka had'e bikin kawai lokaci d'aya kuma gaba d'aya angwayen a shirye suke dan duk cikinsu ba wanda bashida gidanshi duk angama komai sai lefe da sauran abubuwan da ba za'a rasaba. Duka watanni hud'u aka tsayar idan ALLAH yakai rayuwar, su Hassana fa ansamu dama soyayya ba kama hannun yaro musamman data samu d'an soyayya haka suke zuba love abinsu Hussaina kuma itace mai kunyar saikuma ALLAH ya bata marar kunya dan shima Habeeb d'in duk jirgi d'aya ya kwasosu dasu Abdallahn. Jauhar dai har yanzu ba tsayayye sam bata ma kula masu son nata duk wanda yayi mata maganar aure sai tace ita ba yanzu zatayi aure ba ba soyayya ce a gabanta ba haka nan take jin duk soyayyar ta fita a kanta anya Jauhar 🤔🤣. Abbie da kanshi ya kira Abdallah ya nuna masa ya kamata fa yasamu wadda zai aura bai kamata yayi ta zama haka ba, ya amsa da to ne kawai amma shikam bai shiryawa yin aure yanzu ba bai saniba dai ko nan gaba, Jauhar saidai taje Kaduna da ziyara shima kuma saidai su tafi dasu little Janaan suyi kwana biyu su dawo Kano, Abdallah ya tab'a yunk'urin hanawa saida Ammi taci mashi shi ganinshi dan me za'a dinga kwasar yara ana faman yawo dasu ko a cikin Kanon indai zataje gidajen su Aunt Deejah dasu Jeeddah dasu take tafiya, Abbie yana yawan tuntub'arta batun aure sai tace masa ba yanzu ba shidai koda yaushe lallashinta yake da nuna mata zuwa yanzu ya dace ace tana d'akin mijinta saidai tace masa kawai zata duba insha ALLAH shiyasa take jin kunyar had'uwa dashi bataso ya kalleta a matsayin wadda batajin maganar shi ko marar jin maganar na sama da ita. ★★★★ "Nifa Ammin yara akwai wani tunani daya fara d'arsuwa a raina amma ban saniba ko abinda nake tunani kema kinyi hasashen hakan". Abbie yayi maganar yana rufe laptop d'in dake kan cinyarshi tareda k'urawa Ammi ido danjin abinda zatace. "Wane tunani ne wannan Abbie?". Ammi ta tambaya. Gyaran murya yayi yace "Game da Modibbo da y'ar uwar mai rasuwar nan Hassana bakya wani tunani a kansu?". "A'a Abbie wani tunani kayine a kansu?". ta fad'i hakan ne kawai danjin abinda zai fad'a amma tunda taji yafara maganar tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i. "K'warai kuwa Ammin yara ina ganin ta inda aka hau ta nan ake sauka Abdallah ya rasa matarshi itakuma wannan yarinyar har yanzu tak'i tsayawa ta saurari masu son nata bare harta fitar da wanda take so shine nake ganin mezai hana a karo na biyu a k'ara aura masa ita kinga zai dinga ganinta kamar Janaan tunda kamarsu d'aya kuma komai nasu iri d'ayane shi kanshi sai hankalinshi yafi kwanciya idan ita d'in ya aura ko don saboda yaranshi itace kawai bazaiyi d'ar ko tararrabi ba dan yaranshi suna hannunta itama kuma yanzu rabata da yaran nan ai yak'i ne babba inaga shine musabbabin ma da har yanzun tak'i fitar da wanda zata aura d'in amma idan itace muma hankalinmu kwance munsan wadda suke hannunta yadda mahaifiyarsu zata rik'esu da tana da rai itama haka zatayi musu amma ke meye shawarar ki akai".(Kai Abbie wannan magana haka ba jan numfashi duk nagaji 😬🙃). Jinjina kai kawai Ammi take alamun gamsuwa da maganar Abbie itafa koda sau d'aya bata tab'a kawowa ranta wannan maganar ba cikeda jin dad'i tace "Gaskiya ne Abbie wannan tunanin naka yayi daidai wllhy kuma shawara ce mai kyau fatanmu dai ALLAH yasa su amince dan dukansu ba kanwar lasa bane dan ma rasuwar Janaan tasa duk sun d'an rissina ba laifi". "Insha ALLAHU zasu amince kuma insha ALLAH alkhairi ne zan kira Alh Isma'eel d'in a waya mu tattauna batun ALLAH ya zab'a abinda yafi zama alkhairi". "Amin Amin Abbie". Ammi ta amsa cikin farin ciki dagani maganar da Abbie yazo da ita ba k'aramin dad'i tayi mata ba. A hasashenku waye zai bada mtsl tsakanin Madugu da Jauhar? A kafta🤣. Mrs Salees Mu'az 💝 3/13/22, 07:08 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 37. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*. ©Oum Hanan. Cikin kwana biyu maganar duk ta karad'e kunnuwan manyan cikin familyn na son had'a Abdallah da Jauhar aure da Abbie yake sonyi a karo na biyu kuma kowa yayi na'am ya bada goyon bayan yin hakan, sudai kam ma basu san wainar da ake toyawa ba ba sai a yau ne da Abbie yayi shirin sanar dasu dan yana sone a had'a bikin gaba d'aya danasu Ja'afar ayi a huta gaba d'aya. Kamar yadda akayi lokacin Janaan hakan ce ta k'ara kasancewa wannan karon akayi zama irin wancan tarihi zai maimaita kanshi kenan😅 har Jauhar ta hallara kiran da akayi mata Madugu ne kawai baizoba, Abbie yana shirin k'ara kiranshi a waya saikuma ya bud'e k'ofar falon ya shigo yana sanye cikin bak'in wando plain da farar riga mai dogayen hannuwa wadda ta d'an kamashi kad'an ya nad'e wuyanshi da abubuwan daya saba nad'ewa black color sai bak'in agogon fata dake d'aure a hannunshi wanda ya haska farar fatarshi sosai sai k'amshi yaketa uban zabgawa wanda har yanzu Jauhar bata san wani irin mayen turare bane wannan mai masifar k'amshi haka gashi k'amshin mai sanyi bamai hawa kaiba har wani irin yanayi take shiga mai wahalar fassararuwa idan taji wannan k'amshin na Abdallah, guri yasamu ya zauna yana k'ara gaishesu kowa ya amsa fuska a sake tunda ya shigo Jauhar ta kauda kanta dan karma yasa ran zata gaisheshi, shima d'in sau d'aya ya saci kallonta ta gefen idonshi yayi saurin kauda idanunshi wani abu na k'ara taso masa game da ita gashi ta k'ara zama big girl kyawunta ya k'ara fitowa ga tsabar gayu da iya kwalliya daya zauna mata. Shiru wajen ya d'auka kafin Abbie yayi addu'a yafara sanar musu abinda ya tarasu a wajen, cikin sauri Jauhar ta d'ago kai tana kallon su Ammi yayin da gogan ya wani maze sam babu alamun maganar ta girgizashi hankalinshi kwance har wani wasa yake da bezar abinda ke nad'e a wuyanshi yake wanda ya sauko kan k'irjinshi ta k'asan ido yake kallon Jauhar dan ganin wani irin action zata d'auka, b'ata fuska tayi sosai a shagwab'e tana d'an yatsina fuska tace "Aure kuma Abbie da Yah Abdallah?". Kai Abbie ya jinjina mata yana murmushi cikin ranshi yana addu'ar ALLAH yasa ta amince dan indai bataso bazai mata dole ba ya d'ora da fad'in "K'warai yarinyata munga hakan shine maslaha abinda kuma yafi dacewa kenan ki maye gurbin y'ar uwarki dan kulawa da yaranta da kuma basu ingantacciyar rayuwa fiye da kowace mace a duniyar nan me kikace?". ya k'are maganar da sigar tambayarta dan jin ta bakinta. To Jauhar dai ta gado yayanta Abdallah🤣 dan itama ba b'oye b'oye ba kunya da kawaici a al'amurata dan haka tayi k'asa da kai duk da tanajin kunya da nauyin abinda zata fad'a d'in a gabansu Abbie wasa ta shiga yi da y'an yatsun hannunta da sukasha jan lalle wanda saboda kamun dayayi yazama maroon color ya zauna sosai a farin hannunta, jin tayi tak'i magana Abbie yace "Karfa kice zakiji kunya Hussaina kuma kar kiyi la'akari damu muka haifi Modibbo ki fito ki fad'a mana gaskiyar abinda ke cikin ranki kinji autar Mama". Baki ta d'an tura kafin tace "Ni gaskiya a'a Abbie bana sonshi". Ido suka zaro dukansu musamman Ayyah da kamar ya fad'o k'asa, Abdallah kam ido ya lumshe cikeda b'acin rai yana taune lips d'inshi tamkar wanda yake shirin hudashi lallai yarinyar nan batada mutunci a gaban idanun su Ammi take cewa bata sonshi ta kalli tsabar idanunshi tace bata sonshi a gabanshi zata gane dashi take magana shi tayiwa haka dan mai garinsu. "Murmushi kawai Abbie yayi duk da dai cikin ranshi sam baiji dad'in abinda ta fad'a d'in ba yace "Kikace bakya sonshi ko?". Kai ta d'aga tace "Eh Abbie bana sonshi". tace hankalinta kwance dan ita bata d'auki hakan wani abu ba a ganinta tambayar ta akayi ta bada amsa kuma ance ta fad'i abinda ke ranta Abbie yana shirin yin magana yaji Abdallah cikeda bala'i yana fad'in "Ki kalli tsabar idanuna saboda bakida mutunci kice baki sona dan ubanki me kike tak'ama dashi? nace me kike tak'ama dashi ne Jauhar". Kallon sama da k'asa tayi masa tana wani yatsina fuska tace "Abinda kake tak'ama dashi kaima kuma na fad'a d'in bana sonka ko ana so dole ne?". tayi maganar cikin rashin kunya da tsiwa tana kallonshi, wani irin numfashi ya zuk'a tareda lumshe shanyayyun idanunshi cikeda b'acin rai da k'uncin zuciya datasan irin halin da zuciyarshi ke shiga idan ta furta wannan kalmar ta BANA SONKA da bata fad'eta ba yanajin tamkar zuciyarshi zata fashe tayi bindiga ne, itama a fusace tace "Nace bana sonka d'in Yah Abdallah akwai abinda zakayi ne? banayi a k'ara gaba ko za'a samu wadda zata taya". Huci yaja sosai sosai yana cije leb'e tareda jinjina kai yace "Okayyyyy haka kikace ko? good nikuma zan aureki kota tsiya ne inga matakin dazaki d'auka stupid d'in yarinya kawai". ya ida maganar yana fincike abinda ya nad'e wuyanshi dashi ya cillar dashi a k'asa tamkar shine mai laifin ranshi na masa suya da tuk'uk'i. Baki Jauhar ta bud'e da niyyar maida masa martani Ammi ta daka musu wata tsawa ranta a matuk'ar b'ace tace "Ku rufa mana baki shashashan yara kawai yanzu a gaban mu kuke wannan musayar yawun ko kunya bakuji, ke Jauhar ba sama yake dake ba da har kike bud'e baki kike fad'a masa maganar da duk tazo bakinki". Kamar Jauhar zatayi kuka ta bud'e baki zatayi magana Abbie yace su tashi dukansu subar wajen kar wanda ya k'ara magana a cikinsu, a tare suka tashi tsaye kamar kububuwa haka Abdallah ya fice daga falon da sauri tamkar zai tashi sama Jauhar ta rufa masa baya. Ajiyar zuciya Abbie ya sauke yace "Anya kuwa wannan had'in zai yiwu kuwa Ayyah Hussaina ba irin y'ar uwarta bace zamansu bazaiyi dad'i da Modibbo ba". Jinjina kai Ayyah tayi tace "Hak'ik'a tun farko sai danayi wannan tunanin kar azo ayi abu daga baya kuma azo ana dana sani ya kamata dai a k'ara duba lamarin gaskiya". "Insha ALLAH ba wata matsala Ayyah sai alkhairi dazai biyo baya da anyi auren zasu daidaita tsakaninsu ne duk wadda Modibbo zai aura bayan Jauhar ne muyi musu kyakkyawar addu'a kawai ALLAH ya basu zaman lafiya ya rage musu zafin zuciyar nan tasu". Duk sunyi na'am da maganar Ammi daga nan kowa ya kama gabanshi saikuma zama na biyu idan buk'atar hakan ta taso. ✓•✓•✓•✓•✓ Kai tsaye side d'inshi ya nufa ya tura k'ofar da k'arfi ya shiga bai tsaya a falon ba ya wuce bedroom d'inshi yana shiga ya fad'a bisa bed yayi ruf da ciki idanunshi a rufe zuciyarshi na masa wani irin zafi wai shin Jauhar tasan tsahon lokacin daya d'auka yana dakon soyayyar ta kuwa? shin batasan itace BUGUN NUMFASHI DA ZUCIYARSHI BA? duk abinda yake mata kawai yana yine saboda alamunta daya gani batada kunya bazasu tab'a daidaitawa da itaba, Jauhar tun tana y'ar shekara hud'u zuwa biyar ya kware mata a soyayya a lokacin dayaso bayyana mata kuma aka shigo masa da zancen auren Janaan bai tab'a kawowa zuciyarshi auren wata ba bayan Jauhar ko a kanshi bai tab'a kawowa zaiyi rayuwar aure da wata d'iya mace ba sab'anin Jauhar amma saboda lamarin ubangiji juya k'addara da sarrafata ba'a hannunmu yakeba sai gashi rabon su little Janaan yasa sunyi aure da Janaan sun samu kyakkyawar shekara d'aya a matsayin ma'aurata daga baya ubangiji yazo yayi ikonshi akanta ta tafi ta barshi da yara biyu, koda su Abbie basuyi masa tayin auren Jauhar ba shi zai nemi hakan lokaci yayi dazai fallasa sirrin zuciyarshi lokaci yayi daya kamata ya bayyana mata ciwon daya dad'e yana fama dashi a zuciyarshi dama gangar jikinshi ya daina k'warar kanshi haka saigashi a gabanshi take ta maimaitawa da nanatawar bata sonshi saboda ita d'in batada mutunci aikuwa zai nuna mata kalar nashi rashin mutuncin dama yayi k'aurin suna a wajenta dole ma saita aureshi (Tsohon k'ok'ari🤔🙄). Tsaki ya dinga ja daga kwancen dayake kafin daga bisani ya tashi ya nufi wata drawer sai daya lalubo key d'inta cikin wata drawer ta kusa da ita sannan ya bud'e ya d'auko wani k'aton dairy ya koma kan gadon ya zauna tsakiyar gadon sannan ya fara bud'e littafin shafi na farko yana bud'ewa na fara cin karo da hotunan wata kyakkyawar yarinya y'ar kimanin shekaru biyar fara tas da ita wajen guda goma k'ananu kaloli daban daban wasu sanye take cikin k'ananun kaya wasu kuma manya gasu nan dai dayawa wani tana rik'e da teddy bear wani tana dariya wani ta shagwab'e fuska ta turo baki kamar zatayi kuka style kala kala wani ma dana gani kukan take ta cika bakinta da Pop corn ta bud'e bakin gaba d'aya abin dariya, saidana k'ura mata ido sannan nagano ashe Jauhar ce ta hoton, sassanyar ajiyar zuciya ya saki tareda lumshe ido yakai hannu kan hotunan yana shafasu daki daki yake tariyo lokacin da akayi kowane hoto shi kad'ai yake murmushi yana hango time d'in dayake d'aukarta kowane pic da digital camera d'inshi da Daddy ya siya masa kafin yabar k'asar Nigeria lokacin yana Kaduna da zama wajen Mama (Su Madugu ashe an dad'e da folawa Jauhar almuri 🤣🤣). Sam fuskarshi ta kasa barin murmushin dayake ya cigaba da bud'o sauran hotunan yana kallo kowani k'asan hoto akwai zanen flower masu matuk'ar kyau da ban sha'awa had'i da special words na tsantsar soyayya da zallar k'auna cikin tataccen speech wani kuma da fulatanci da kuma wani yare dana kasa tantance shi kamar chaina kamar indiyanci 😂 wani irin yanayi yakeji tattare dashi ya b'ata lokaci mai tsaho a haka batare daya sani d'in ba k'arshe ma daya gaji da zaman saiya zame ya kwanta kan pillow ya dora littafin a tsakiyar k'irjinshi ya rufe ido yana tunano yadda suke ada da irin tsananin shak'uwar da sukayi wanda idan bazai manta ba lokacin daya tafi outside karatu har rashin lafiya tayi sosai saboda kewarshi datayi yayi d'awainiya dasu Janaan sosai tun suna zannuwan goyonsu musamman Jauhar da tun farko tafi shiga ranshi har wankin kashi da fitsari ba wanda baiyi musu ba dan tare dashi Mama tayi jegonsu ya dad'e a haka yana tuna baya kafin barci yayi awon gaba dashi Abdallah dai an shiga shauk'i🥲🤣. Ya dad'e yana barcin kafin ya tashi maida littafin yayi inda ya d'aukoshi ya k'ara kullewa sannan ya shiga bathroom danyin wanka. Mrs Salees Mu'az 💝 3/13/22, 21:16 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 38. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*. ©Oum Hanan. Yana cikin shiryawa bayan fitowar shi daga wanka yaji ya taka wani abu da k'afarshi daga bakin gado, sunkuyawa yayi yakai idanunshi kan abinda ya taka d'in abin d'aure gashi ne na yara mai kyau sosai pink color ido ya k'ura masa tabbas wannan beat d'in na Jauhar ne kuma wajen d'auko littafin nan ya fad'o dashi bai saniba bazai manta ba lokacin dazai tafi k'asar waje had'uwarsu ta k'arshe yace tabashi abinda zai dinga tunawa da ita dube duben abinda zata bashi ta shiga yi saidai ba komai a jikinta wanda zata bashi dan haka kawai tasa hannu ta cire beat d'in da aka d'aure mata tulin gashinta a baya ta warware shi ta kama hannunshi ta damk'a masa murmushi yayi ya sumbaci goshinta a wancan lokacin, yanzun ma murmushin ne ya sub'uce masa yakai beat d'in bakinshi yayi kissing d'inshi sannan ya maidashi inda yake ya tashi ya cigaba da shirinshi baisan abinda ya canza Jauhar ba ada tanada hak'uri ko surutu bata dashi kafin tafiyar shi amma yana dawowa da d'okin yazo ya ganta yaga gaba d'ayanta ta canza tazama fitinanniya mara kunya ga tsiwar tsiya tun daga lokacin ya fita sabgarta. Tsaf ya shirya cikin k'ananun kaya riga da wando farare tas na kamfanin ADIDAS wanda akayi musu ado da jan layi layi a gaban rigar dakuma gefe da gefen wandon Pcap yasa red colour ya zura farin slippers mai taushi sosai ya fesa turare ya fita yaja k'ofar. Kai tsaye cikin gidan ya nufa baisamu kowa a falon ba kuma dama sarakan rashin jin gidan basu nan Aunt Jeeddah ce tazo ta kwashesu wai zasuyi kwana biyu da k'yar ma Abdallah ya bari itama Jauhar jitake tamkar ta bisu gidan dama bada son ranta aka tafi dasu ba. Bedroom d'in Jauhar ya wuce kai tsaye yana zuwa yakama handle d'in k'ofar ya bud'e ya shiga, tana zaune a gefen gado da waya a hannunta tana danne danne ta zame mayafin kanta wanda ya bayyana da lallausar gashin kanta bak'a wuluk ta asalin fulani datayi doughnut dashi a baya, da sauri ta d'ago kai ta kalleshi lokaci d'aya tana laluben gyalenta a gefenta ta had'e rai sosai tana harararshi ta gefen ido, bai damuba ya cigaba da takawa zuwa wajen gadon saida yaje daf da inda take sannan ya tsaya ya d'ora k'afa d'aya kan gadon d'ayar kuma tana k'asa ya d'an rank'wafa yana kallon Jauhar data had'e fuska take masa wani irin kallo tace "Wai meye ma'anar haka Malam?". Wani d'an iskan murmushi yayi tareda d'age kafad'a ya juya gaban Pcap d'in kanshi ya koma baya yace Nima ban saniba kawai dai nazo in jaddada miki maganar aurena dake ne ba fashi dan haka ki shirya zan aureki zan kaiki gidana dolenki kuma ki zauna". Itama d'in murmushin tayi cikeda rainin hankali tace "Ana aure dole ne ko k'arfa k'arfa zaka nunamin ban saniba". "Yeah! zan miki k'arfa k'arfa da k'arfin ikona a kanki, dan kin samu ma zan taimaka miki in aureki kike rainamin hankali shekararki nawa babu mashinshi ni koda sunzo ma bazaki iya kula kowa ba Jauhar saboda nine anan d'inki". ya ida maganar yana nuna saitin zuciyarta da d'an yatsanshi manuniya. Sosai maganar ta daketa batada mashinshi fa yace yasan irin mazan dake kara kaina a kanta kuwa, a fusace ta mik'e tsaye tace "Yah Abdallah ka fita daga d'akin nan dan ALLAH ka fita na rok'eka kuma zan tabbatar maka da inada mashinshina bama d'aya ba ba biyu ba kawai ra'ayin kulasu ne daba nayi aure kuma bazan aureka ba kayi abinda zakayi". Tsaye ya mik'e ya cusa hannayenshi duka cikin aljihun wandonshi ya juya mata baya yace "Mu zuba ni da ke Jauhar za'aga wanda zaici nasara". daga haka ya fice daga bedroom d'in da sauri, yana fita ta fad'a kan gadon tareda sakin wani irin kuka ranta na mata k'una ta rasa ta yadda zatayi ta fito da soyayyar Yah Abdallah daga zuciyarta tun batasan mecece itaba batasan meye SO ba take jinshi cikin zuciyarta sunanshi kawai aka ambata yakan sata cikin farin ciki mara misali tanason Yah Abdallah kamar ranta lokacin da maganar aurensu da y'ar uwarta ta taso k'iris ya hana zuciyarta fashewa ta tsinci kanta cikin wani irin mawuyacin hali ta danne ne dai kawai saboda kar mutane su ranfo ta amma a lokacin ko barcin kirki bata iyawa sai data kai zuciyarta nesa wajen ganin bata canzawa y'ar uwarta ba a lokacin saboda yadda zuciyarta take mata zafi idan ta tuna masoyinta shi zata aura shikenan ita ta tashi a tutar babu duk dakon soyayyar nan tashi datayi tun tana k'aramar ta ta tashi a banza kenan a yadda yadawo mata a marar mutunci itama a haka ta karb'eshi a yanzu gani take koda ta auri wanin Madugu to gangar jikinta ya aura amma zuciyarta da dukkan wani tunanin ta suna wajen Abdallah batasan ya zatayi ba shin ta amsa tayin su Ammi ne kokuwa dai ta bijire kanta ya kulle itakam. Saida taci kukanta ta k'oshi ta rarrashi kanta da kanta ta fad'a tunanin abinda ya kamata tayi cikin haka barci ya kwasheta cikeda mafarkai kala kala kuma rabi duk na Abdallah ne. **★★**★★** Two days after. Jauhar tasamu wani sabon saurayi da suka had'u a shopping malls taje yiwa su Irfaan siyayyar sweet da chocolate suka had'u shikam dagani ya girmewa Abdallah sosai kawai dai irin y'an boko d'in nan ne wanda ya dad'e baiyi aure ba sunanshi Auwal zarewa tunda ya ganta yabi ya rud'e bataja da tsayi ba tabashi phone number d'inta tareda address din gidan shiya biya kud'in datayi siyayyar sai dayaga tashin motar ta sannan shima ya shiga tashi motar yabar wajen. Su Ammi basu k'ara tada maganar ba hakan yasa Jauhar tayi tunanin ko sun bar maganar ne gaba d'aya shikam Abdallah hankalinshi yana kai kuma yayi alk'awarin koda su sunbar maganar saiya k'ara taso da ita dan a yanzu burinshi bai wuce yaga ya mallaki Jauhar a matsayin matarshi ba dan haka kota yayane yanajin saiya mallaketa. Sau biyu suna waya da Auwal zarewa kuma ya nemi zuwa gidansu dansu gana da ita bataji ko d'ar ba tabashi damar zuwa ranar dazai zo ta sanar da Ammi ga mamakin ta kuma Ammin batace komaiba tace ALLAH ya kawoshi lafiya. Sai yamma yazo bayan sallahr la'asar anan compound suka zauna kusa da wasu shuke shuken furanni kan fararen kujerun roba dake wajen ta kawo masa ruwa da lemo da snacks bayan sun gaisa ya bata yabata tarihinshi in brief da kuma aikin dayake tunda suka zauna Jauhar ta lura shegen surutu gareshi gashi bataso wannan mara mutuncin yadawo gidan ya sameshi batasan abinda zai masa ba bataso a dalilinta aci masa mutunci shikuma ya dage sai zuba yake sam batayi zaton zai dad'e hakaba horn d'in dataji daga bakin gate ne yasa gabanta ya fad'i cikin ranta ta shiga addu'ar ALLAH yasa Yah Ameen ne ko wani dai ba Abdallah Madugu ba, aikuwa dai addu'ar tata bata ciba dan ana bud'e gate d'in motar Abdallah ta danno cikin gidan. "Innalillahi wa inna ilaihi rajioun". ta fad'a cikin ranta tana k'ara gyara zamanta duk ta tsorace kuma badan komaiba saidan gudun cin mutuncin da Abdallah zai iya yiwa Auwal tasan da wuya yagani bai tanka ba sai yanzu take dana sanin yarje masa datayi yazo gidan data sani gidan Aunt Deejah ko Jeeddah ko Mabrookah taje suka had'u tsaki ta saki tana d'an dukan goshinta, jin tsakin datayi yasa Auwal tambayar ta lafiya kuwa? murmushin yak'e kawai tayi tace masa lafiya k'alau ba komai hankalinta gaba d'aya yana kan Abdallah dake k'ok'arin fitowa daga mota bayan yayi parking, kasancewar shi Auwal d'in ya bashi baya hakan yasa baiga mai shigowar ba baikuma juya dan ganin waye d'in ba. Had'add'en farin yadin filtex ne a jikinshi riga da wando rigar iya gwiwarshi shara shara ne yadin hakan yasa har singlet d'inshi fara tas bata b'uya ba k'afarshi ma farin takalmi ne na zallar fata sai farin agogon fata daya d'aura a tsintsiyar hannunshi ta gadon ce dai a kanshi itama fara da adon bak'i a gaban (Nasan dai kun fahimta 🤣). Tsaye yayi bayan fitowarshi daga motar yayi crossing hands d'inshi a k'irjinshi ta k'asa ma yayi crossing legs d'inshi ya zuba musu ido yana kallonsu ransa na masa zafi meyasa Jauhar batajin magana ne? duk hak'urinshi saitaja abinda zaizo yana bambami da tada jijiyar wuya dan me zata kawo wani cikin gidan da maganar aurenshi a kanta, ido suka had'a da Jauhar tayi hanzarin kauda nata idanun cikeda fargaba addu'ar ta d'aya ALLAH yasa yayi wucewar shi salin alin batare daya kulasu ba wanda tasan mawuyacin abune hakan ta faru Abdallahn ne zaiga abinda baiyi masaba ya kauda kai bai tanka ba aikuwa da an canza masa suna saidai kuma wani ikon na ALLAH. Kai Jauhar ta sunkuyar lokacin daya fara tahowa. "Shikenan ta faru ta k'are". tace cikin ranta time d'in daya k'araso inda suke shima ya janyo wata kujerar ya zauna bayan ya mik'awa Auwal hannu sunyi musabaha a mutunce Jauhar har yanzu bata d'ago kaiba. "Ahmm dalilin daya kawoka gidan nan nakeso inji Malam". yace idanunshi akan zoben azurfar dake hannunshi na dama yana wasa da ita. Ko bai tambaya ba yaga kamanni na jini tsakanin Abdallah da Jauhar yasan yayanta ne shiyasa cikin girmamawa yace "Nazo wajen Jauhar ne dan mu gana saboda inaso in aureta idan ALLAH yayi". Kai kawai Abdallah ya shiga jinjinawa kafin yace "Bakasan matar aure bace ne tanada miji?". Da sauri Auwal ya zaro ido ya shiga bin Abdallah da Jauhar da kallo itama Jauhar da sauri ta d'ago kai ta kalli Abdallah daya maze kamar wanda ya fad'i gaskiyar nan cikeda mamaki yace "Tanada aure fa kace?". Wani kallon rainin hankali Abdallah yake masa kafin yace "Kana tantama ne? to nine mijinta yau kwana biyu da d'aura mana aure bata tare bane saboda wani dalili fatan kagane?". Kallon Jauhar Auwal yayi wadda tayi wuri wuri tamkar hakane d'in gaskiya Abdallahn ya fad'a kai ta shiga girgizawa tana fad'in "Wllhy Auwal ba haka bane karka yarda da abinda ya fad'a yana jin haushi ne ance za'a had'amu aure nace bana sonshi". Yaa ALLAH yau kuma ta nan Abdallah ya b'ullo tayi zaton zaizo a fusace yaci masa mutunci saikuma taji akasin hakan. Shidai Auwal saiya rasa maganar wazai kama tawa kuma zai bari, ganin kamar Auwal ya yarda da maganar Jauhar yasa Abdallah tashi tsaye yace "Bari inyi abinda zaisa ka yarda tunda naga tantama kake". gani kawai sukayi ya nufi Jauhar basu san me zaiyi ba yana zuwa yasa hannu ya janyo nata hannun ya mik'ar da ita tsaye kafin tayi tunanin abinda zaiyi mata taji ya zura bakinshi cikin nata ya shiga kissing d'inta. "Innalillahi wa inna ilaihi rajioun". Amma dai wannan yarinya ta cuceshi wllhy yanzu ashe da matar aure yake tare bai saniba ALLAH zai saka masa kuma yasan bazai kamashi da laifin kula matar aure ba tunda bai saniba me yake damun matayen yanzu ne sam babu tsoron ALLAH a lamuransu. Auwal ne ke wannan zancen zucin ranshi a b'ace sosai gameda abinda Jauhar tayi masa ita ko tsoro ma bataji a gansu? Tamkar ta mutu saboda tsananin b'acin rai wani dunk'ulallen abu ya tsaya mata a wuya idanunta suka cika da k'wallar bak'in ciki me Yah Abdallah yakeso ya zama ne shi idan zaiyi abu kawai gaba gad'i yake yin abinshi ba tunanin komai ko abinda zaije yazo, k'ok'arin k'wacewa ta dinga yi da kici kici ya saketa amma saboda irin rik'on tsauri dayayi mata hakan yasa ta kasa k'wacewa, Auwal dai yana zaune shi bai tashi ya tafi ba bai kuma kallesu ba ya sadda kanshi k'asa yana dana sanin zuwanshi gidan nan. Saida yayi iya son ranshi sannan ya saketa sai wani lumshe ido yake yana murmushi, dab'ar takoma ta zauna kan kujerar d'aya fincikota ta tashi sai lokacin hawayen da suka taru cikin idanunta suka samu damar zubowa kan fuskarta. "Woww like sweet". Yace yana murmushi gamida tsotsar bakinshi yabar wajen da sauri, da k'yar ta d'ago kai ta kalli Auwal tana shirin yin magana ya d'aga mata hannu batare dayace komi ba ya tashi yabar wajen da sauri, batayi yunk'urin binshi ba harya shiga motarshi maigadi ya bud'e masa gate ya fice daga gidan da sauri (Maigadi dai baiga aika aikar da Abdallah yayi ba lokacin ya zagaya band'aki). A hankali tasa hannu ta goggoge idanunta a fusace ta tashi bata nufi cikin gidan ba sai side d'in Abdallah data nufa, tana zuwa ta banka k'ofar falon a shiga baya ciki dan haka kai tsaye ta nufi bedroom d'in tasan dai bazai wuce can ba. Yana tsaye gaban mirror yana cire links d'in hannunshi ta shigo bedroom d'in, kai tsaye inda yake ta nufa tana zuwa tasa hannu ta turashi tana fad'in "Me kake tak'ama dashi ne Yah Abdallah meyasa kakemin haka ne? nace me yasa kakemin haka idan baka b'ata raina ba bakajin dad'i ko nace bakajin dad'i ko. Ta k'are maganar cikin k'araji tamkar wata zararriya, dariya kawai yayi ya zagayeta da nufin komawa wajen mirror n ta k'ara turashi ya had'u da bango taje daf dashi tamkar zata shige jikinshi hakan daya gani yasa ya d'age hannayenshi sama tareda zaro ido waje yace "Fyad'e zakimin Jauhar?". Cikeda b'acin rai tanajin tamkar taita marinshi ko zata huce daga iskancin dayake mata tace "Y'ar iska ka maidani Yah Abdallah? Nace y'ar iska ka d'aukeni? Eh fyad'en zan maka Tayi maganar da k'arfi tana k'ara turashi, ido ya k'walalo waje na shak'iyanci ya k'ara d'age hannayenshi yana wani d'an runtse Ido da kauda kai gefe yace "Wayyo Ammi kizo zatamin fyad'e wayyo Ayyah". Ya fad'a da k'arfi yana y'ar dariya Ganin kamar ma ya maida ita wata sha ka tafi mara hankali yasa kawai ta sakeshi tabar bedroom d'in da gudu tana hawaye. Dariya ya k'yalk'yale da ita kafin yace "I love you so much Jauhar har k'arshen numfashina muaahh". Yace yana jefawa hanyar data fita kiss ya cigaba da rage kayan jikinshi yana murmushi. Mrs Salees Mu'az 💝 3/16/22, 11:24 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 39. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*. ©Oum Hanan. Tun daga lokacin Jauhar take baya baya da Abdallah tsoron had'uwarsu dashi take gani take tamkar zai k'ara yimata kiss ne agaban y'an gidan shiyasa ko suna zaune a falo ana hira dataji alamun shigowar shi zata tashi da sauri ta shige bedroom d'inta kar yaja mata abin kunya tunda dai shi ko d'igo bashi da ita. Abbie sunyi waya da Daddy ya fad'a masa duk abinda ya faru lokacin da sukayi musu maganar auren dan haka gara a hak'ura kawai har ALLAH ya fito mata da miji tayi aurenta shima Abdallahn haka, sam Daddy baiji dad'in hakan ba yace kuma a barshi da Jauhar d'in zaiyi mata magana, shidai Abbie har sukayi sallama yana k'ara nanatawa Daddy da rok'on alfarmar kar yace zai takurawa Jauhar ta auri Modibbo idan bata yardaba kawai a k'yaleta Daddy yace ko d'aya ba matsa mata zaiyi ba abarshi dai da ita. Jauhar Daddy ya kira bayan ta gaisheshi yafara mata nasiha da rarrashinta akan maganar auren Abdallah tareda nuna mata alfanun wannan had'in da suke son suyi karta bashi kunya dan ALLAH taje tasamu Abbie ta bashi hak'uri ta kuma sanar masa ta amince da auren Abdallah adole kawai ta amsawa Daddyn danta faranta masa amma bawai dason ranta ba. Bayan dawowar Abbie Jauhar taje ta gaisheshi sannan ta bashi hak'uri tareda fad'a masa ta amince da zab'in da sukayi mata cikin hikmah Abbie ya bugi cikinta yana son yaji ko Daddy ne ya tilasta mata amincewar Jauhar ta nuna ba ruwanshi kawai dai tanaso ta kyautata musu ne hakan yayiwa Abbie dad'i sosai ya shiga yimata addu'a tareda sanyawar albarka a rayuwar aurensu da Modibbo. Tana komawa bedroom ta fad'a kan gado ta shiga raira kuka wanda ita kanta batasan na meye ba na farin cikine ko akasin hakan ta rasa wanne take yi daga ciki farin cikinta bai wuce auren mutumin daya dad'e cikin rayuwar ta wanda tun tana k'wailarta take jinshi cikin ranta fiye da kowa tun bata gane meye ma'anar hakan ba harta fahimta shiyasa duk wani d'a namiji dazata gani indai zataga Abdallah kota tuna dashi saitaga wancan d'in baikai ba Abdallah ya kereshi tako wane b'angare, bak'in cikinta kuma bai wuce aurenshi dazatayi a matsayinshi na mijin y'ar uwarta ba saidai kuma bazata ja da ikon ALLAH ba yafisu sanin hikmar yin hakan dama can ubangiji yayi sai Janaan ta fara zaman aure dashi kafin ita koma dai meye ita zab'in ubangiji take nema. An tsaida sa ranar Abdallah da Jauhar daidai lokacin bikin su Hassana suma za'a had'a ayi tare, Abdallah kasa b'oye farin cikinshi yayi lokacin da aka tsaida maganar auren ga d'okin zuwan lokacin daya dinga yi kamar shine aurenshi na farko da zaiyi hakan yaba wasu daga y'an gidan mamaki sosai suka shiga tunanin kodai dama can Abdallah Jauhar yakeso aka bashi Janaan ba wanda dai ya fito da maganar suka barta cikin zuciyoyinsu. Kwanakin biki nata k'ara matsowa yayin da Ammi ta shiga gyaran d'iyoyinta magungunan sanyi ne sadidan take d'ura musu wanda bazai cutar dasu da lafiyar jikinsu ba, saikuma gyaran jiki da shima aka samu wata y'ar maiduguri k'awar Aunt Deejah ce kuma mak'ociyarta dan haka suke tafiya can gidan Aunt Deejahn itakuma take samun su a gidan duk nok'e nok'en da Jauhar take na ita batason wannan gyaran hakan baisa Ammi ta k'yaleta ba. Aikuwa cikin lokaci k'ank'ani duk suka canza kowacce ta k'ara yin kyau fatarsu ta canza gyaran ya karb'esu sosai. Shiri sosai Abdallah yakewa wannan auren wannan karon ma Jeeddah yabawa kwangilar had'a lefen ya kuma sakar mata kud'i bana wasa ba yace bayason k'ananun kaya komai manya zatasa masa idan kuma yaga abinda baiyi masaba tasan sauran dan haka Aunt Jeeddah ta dage sosai ta had'a masa lefe na garari set biyu masu shida shida kamar dai na Janaan saidai kayan ciki sun bambanta sosai ta wajen kyau da kuma tsada. Gidan Aunt Deejah aka kai kayan washegari aka kawosu a ranar ma aka kawo na Hussaina shima Habeeb yayi k'ok'ari sosai kayane gasu nan tamkar za'a bud'e kanti, bayan kwana biyu kuma aka kawo na Hassana daga Yola itama d'in dai duk d'aya kaya sunyi masha ALLAH sai fatan zaman lafiya kuma. Duk wata hanya dazata had'ata da Abdallah bata binta dan bataso su had'un kuma shima d'in a y'an kwanakin yana busy sosai sam bai cika zaman gidan ba ko shigowa yayi baya dad'ewa yake k'ara fita batasan uwar dayake a wajen ba. Hidima akewa auren nan sosai baga b'angaren amarya ba baga na angwaye ba anata shirye shiryen yadda bikin zai kasance, wannan karon ma tare dasu Hassana sukaje Kaduna sukayi kwana biyu suka dawo saboda lokaci daya k'ure ga kuma gyaran jikin da Ammi takeso a k'arasa musu. Ana saura kwana biyar biki Ammi ta aiki Jauhar gidan wata aminiyarta zata kai mata wani sak'o kasancewar su Hassana basa nan yasa ita kad'ai ta fito zata tafi, riga da siket ne a jikinta na atamfa sun d'an kamata kad'an tayi rolling da k'aramin gyale light purple kalar atamfar kenan tayi matuk'ar yin kyau fatarta sai wani glowing take tana shek'i ga k'amshin daya zauna a jikinta dama kayan sawarta gaba d'aya. Tana shirin bud'e k'ofar motar taji kamar an tsaya an bayanta juyowa tayi dan ganin waye tayi tozali da Abdallah yayi mata k'erere a gabanta sama da k'asa ta kalleshi yana sanye da farin wandon three quarter da ash color d'in riga mara hannu mai hula k'afarshi sanye da farin takalmi sandals mai mad'auri, kallonta yake sosai hannayenshi zube cikin aljihun three quarter'n dake jikinshi. "Lafiya?". Jauhar tace tana wani yatsina fuska, Kai ya d'age shima yana wani kallonta up and down matuk'a gaya kwalliyar ta tafi dashi ga atamfar tayi mugun haskata ga wani kyau data k'ara na musamman ga kuma daddad'an k'amshin dayake buso shi wanda yasashi d'an lumshe ido ya bud'e yana kallonta da shanyayyun idanunshi. "Ina zakije?". "Inda ka aikeni". Tabashi amsa kai tsaye batare da shayin komaiba mamaki yasashi zaro ido ya ciro hannu d'aya daga aljihun wandonshi ya nuna k'irjinshi dashi yana fad'in "Ni kike fad'awa haka Jauhar? sa'an wasanki ne ni? kan bala'i, yace yana rik'e k'ugunshi da duk hannayenshi bayan ya tamke fuska sosai ya nuna mata hanyar komawa cikin falon tareda fad'in "To shige ki koma ba gidan ubanda zakije". "To wai ina ruwanka da fitar da zanyi ka takurawa rayuwata fa Malam". Tace cikin tsiwa tana harararshi. Batayi aune ba kawai taji ya finciki hannunta da k'arfi yayi hanyar komawa da ita tutturjewa ta shiga yi tana son k'wace hannunta amma ta kasa saboda irin rik'on da yayiwa tsintsiyar hannun nata wanda har zafi suka fara yimata saboda tsabar damk'a tana tutturjewar tana komai sai daya kaita har cikin falon ya wurgata kan kujera. "Subhanallah! Meye haka Modibbo? Lafiyarka kuwa?". Ammi da fitowarta kenan daga kitchen ta fad'a tana kallon Abdallah dake tsaye akan Jauhar ya kama k'ugunshi, a fusace yace "Ammi ki gayawa yarinyar nan kija mata kunne ta daina fad'ar duk abinda yazo bakinta a kaina idan ba hakaba wllhy wataran zan raunata ta a banza Ammi". "Innalillahi me yayi zafi haka, me kikayi masa Jauhar?". Ammi ta tambaya tana kallon Jauhar daketa harare harare tana tura baki, kamar zatayi kuka tace "Wai Ammi kawai daga ganina zan fita ba tambayar ina zanje wai indawo ba inda zani". Goshi Ammi ta dafe tace "Haba Modibbo nice fa na aiketa gidan Hajiya Zuhra zata kai min wani sak'o meyasa kai baka tsayawa yin bincike akan komai ". "To kuma Ammi daga tambaya saita fad'amin magana dan ubanta abokin wasanta ne ni? Kuma saboda tsabar batada hankali da wannan shigar zata fita tana yawo a gari". Cikeda tsiwa Jauhar tace "To ina ruwanka da fitar da zanyi inba sa ido ba kuma meye laifin shigar danayi kai idan baka takurawa mutane ba bakajin dad'i". "Kina jinta ko Ammi? Kinajin abinda take fad'amin ko". Yayi maganar yana nuna Jauhar da d'an yatsanshi tareda sakin k'wafa yana jijjiga kanshi. "Kai dallah ku rufewa mutane baki shashashai kawai aure fa kuke shirin yi amma bazaku bar wannan abinda kukeyi ba zan sassab'a muku yanzun wllhy ke kuma Jauhar banason rashin kunya Modibbo yayanki ne kuma yake shirin zama mijinki dan haka ki dinga saita bakinki a kanshi kinji na fad'a miki, Kai kuma nasha gaya maka ka dinga kama girmanka wannan abinda kakeyi shike k'ara janyo maka raini a wajenta kullum kamar k'ananun yara ku dinga saka mutane magana wuce ka tafi naka waje". "Ki kawo sak'on inkai miki". Yace yana kallon Ammi. "Ka wuce kayi tafiyarka banaso". Baki ya bud'e zaiyi magana Ammi ta dakatar dashi tana kallon Jauhar dake ta faman ture turen baki tace "Tashi ki maida min sak'ona bedroom d'ina idan su Hassana suka dawo su saisu kai". "An fasa kaiwa Ammi?". Jauhar ta tambayeta, cikin gatse Ammi tace "Eh tunda wanda yafi kowa iko dake ya hana ai dole ki hanu tashi ki maidamin abuna. Abdallah daya san dashi Ammi take baiyi magana ba sai sajenshi daya shiga shafawa yana tattare fatar goshinshi sama. Tashi Jauhar tayi ta kalli Abdallah da shima yake kallonta wani irin kallo tayi masa sannan ta nufi upstairs dan maidawa Ammi sak'on nata, saida taje tsakiyar stairs d'in sannan ta waigo taci sa'a kuwa idanun Abdallah na kanta wata k'atuwar harara ta sakar masa tareda murgud'a masa baki, baki ya bud'e yana zaro ido kafin cikin hanzari ya haura ta bayan kujerar inda yake tsaye ya bita da gudu kan upstairs d'in da gudu itama ta kwasa, Ammi kam zaune tayi kan kujera tana kallonsu itada su Irfaan da suka shigo yanzu daga wajen Ayyah suna kallon mahaifinsu na gudu akan stairs 🤣 Ita ta rasa ma abinda zatace musu wllhy. Da gudu ta k'arasa bedroom d'in ta banko k'ofar da k'arfi shikuma daidai lokacin daya k'arasa, tsayawa yayi cikin haki ya rik'e k'ugu yana kallon k'ofar, kai ya jinjina yana shirin barin bakin k'ofar yaji tace "Kuma bazan yafe gudun daka sani ba Abdallah". Murmushi yayi yana kad'a kai gamida cije lips d'inshi na k'asa yace "Abdallah kai tsaye ko? Zan rutsaki ai kin kusa shiga hannuna, kwarkwar d'in yarinya kawai". Daga haka ya sauka downstairs, sumar kanshi ya shiga shafawa yana kallon Ammi da itama take kallonshi ya bud'ewa su little Janaan hannayenshi sun san ma'anar hakan dan haka da gudu suka nufoshi suka rungumeshi suna masa surutunsu irin na yara wanda abubuwa dayawa ba'a sanin abinda suke fad'a. "Sannu, ALLAH ya shiryeka Modibbo ka gama gudun?". "ALLAH Ammi yarinyar nan batada kunya kiyi mata fad'a". Baki Ammi ta tab'e tace "Matsalarku ce kuje can ku k'arata bazaku dinga sani magana ba kamar k'ananun yara". Y'ar dariya kawai yayi ya sunkuyo ya sumbaci forehead d'insu sannan ya fice. Mrs Salees Mu'az 💝 3/16/22, 20:39 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 40. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.* ©Oum Hanan. Tun daga ranar Jauhar bata k'ara bari sun had'u da Abdallah ba duk hanyar datasan zasu had'u kauce mata take har zuwa lokacin da y'an biki suka fara hallara a gidan. Gidanshi da suka zauna da Janaan nan aka k'ara gyarawa sosai gaba d'aya kayan ciki fitar dasu akayi aka zuba wasu sabbi komai da komai wadancan kuma na Janaan d'in aka dawo dasu gidan Ammi aka zubasu a wani d'aki daba komai anan cikin compound. Ranar alhamis da safe sukaje akayi musu gyaran gashi sannan akayi musu k'unshi. Da yamma kuma akayi kamu anan compound d'in gidan wanda aka k'awatashi sosai inda ya cika da mutane mak'il kamar irin ranar yinin nan amare sun fito d'as inda sukayi kwalliya da kayan sak'i wanda amare kesawa kalar ja da adon bak'i a jiki light makeup akayiwa kowacce sai tashin k'amshi suke, an gabatar da kamu lafiya k'alau aka tashi daf da magreebah bayan anyi rabon abubuwa masu tafiya suka tafi masu shiga ciki suka shiga. Jauhar harta fara gajiya duk tayi tib'is da ita tana kwance saman gado bayan tayi wanka ta d'an tsakuri abinci y'an mata ne birjik cike da d'akin y'an uwansu. Hassana da Hussaina kam ansamu dama suna can wajen angwayen su dan Abdallahn Momy Maryam ma tun ranar yazo shida wasu daga cikin abokanshi sauran mutanen kuma sai ranar d'aurin aure zasu biyo baya. Kan dole Habeeb yayi sallama da Hussaina ya tafi saboda kiran da babanshi yake masa, wajen shiga gidane Hussaina ta had'u da Abdallah yace ta kira masa Jauhar a cikin gida da sauri ta amsa da to ta wuce kafin ya tuhumeta fitowar datayi ta tsaya da Habeeb dan tasan sarai zai iya ba ruwanshi da amintakar dake tsakaninsu da Habeeb d'in. "Auntie Jauhar angonki fa na kira a waje". Hussaina ta fad'a lokacin datake zama gefen gadon da Jauhar take. "Waye haka kuma?". tace cikin yatsina tana b'ata fuska bayan ta d'ago kanta. "Ke kuji min y'ar rainin hankali angon naki ne baki saniba?". wata y'ar uwarsu ta fad'a, tsaki taja ta maida kanta tana fad'in "Kice masa bazanzo ba". kai tsaye. Ido Hussaina ta zaro da wasu na kusa da ita da hankalinsu ke kansu da sauri Hussaina tace "Bazakije bafa kikace?". "Eh ki fad'a masa haka kedai ai y'ar aike ce". Kai Hussaina ta jinjina ta tashi tana fad'in "Kin fad'i gaskiya ni y'ar aike ce amma Yah Abdallah ba lallai ya tuna da hakan ba shiyasa zan tsaya daga baya baya in fad'a masa". ta fita daga bedroom d'in. Tana zuwa ta fad'a masa abinda Jauhar tace, kai ya shiga kad'awa kafin yace ta tafi, wayarshi dake hannunshi yana danne danne yafara nemo number ta ya danna mata kira, Itama wayar na hannunta lokacin kiran ya shigo dayake da wani sabon sim card ya kirata bata gane number shi ba tayi picking takai kunnenta tareda yin sallama saboda masifa dake cinshi da k'yar ya amsa sallamar datayi ya fara balbala mata bala'in ta rainashi har ya aiko a kirata tace bazata zoba saboda batada mutunci, itama a fusace take fad'in "Wai to idan nazo me zanyi maka haka nan zaka damu mutane da jarabar aike". K'wafa yayi yace "Haka kikace ko to ki shirya zuwana yanzun nan kinsan ba gudun abin magana nake ba wllhy tsaf zan d'auko ki kowa ya ganki kafin in fito dake nan inci uwaki tunda bakida kunya". K'aramin tsaki taja tace "Ina jiranka idan kuma bakazo ba baka cika sunanka Abdallah Madugu ba". daga haka ta katse wayar. "Kutt shikenan Jauhar kin kwanto mana kura bala'i da kanshi ai bakeba muma nan idan har yazo d'akin nan tamu ta samemu dan haka wllhy ba abinda zai zaunar dani a d'akin nan karku babbaka mu da ranmu gara tun wuri in fece". wata y'ar yayan su Ammi Aliya ta fad'a tana mik'ewa tsaye tareda kama hannun Hussaina suka fita daga bedroom d'in, dayake sauran bawani cikakken sani suka yimasa ba itama d'in wani zuwa ne daya tab'a yi Yola yakai musu ziyara aikuwa duk saida ya gallabi y'an gidan akwai yayyenta mata masu jida kansu marasa jin magana duk saidaya saita musu zama a lokacin tun daga nan suke shakkar shi, Abdallah case 🤦😂. D'an yatsanshi ya ciza lallai ma yarinyar nan baisan meyasa ta rainashi har haka ba bari ta shigo hannunshi zatasan da wanda takeyi, cikeda karsashi ya tashi ya nufi hanyar dazata sadashi da cikin falon zai nuna mata shi Abdallah Madugu ne, yana shiga falon yaga mata da yawa wasu na kallo wasu cin abinci yayin da wasu sukayi group sai zabga hira ake ta y'an uwantaka, bai tankawa kowa ba ya nufi hanyar dazai isa bedroom d'in Jauhar sukaci karo da Ammi itakuma zata fito baya yayi yana y'an kame kame ganin yadda Ammi ta tsura masa ido da alamun tambaya a fuskarta. "Ina zakaje da daren nan Modibbo?". Hannu yakai kan lallausar sumar kanshi ya shiga shafawa d'ayan kuma ya cusashi a aljihun wandonshi yace "Ammi wajen yarinyar nan mana wai har in aiko a kiramin ita tace bazata zoba tsabar ta raina ni Ammi". galala Ammi ta tsaya tana kallonshi kafin tace "To daka taho nan zuwa zakayi ka d'aukota kokuma dai me zakayi?". Ba rissinawa ba komai yace "Eh Ammi zan gyara mata zamane naga rainin hankalin nata ya wuce misali". Tsaki Ammi taja ta nuna masa hanyar fita tana fad'in "Dallah malam wuce ka tafi harkar ka kiran uban me kake mata da daren nan harda tasowa wai kazo ka d'auketa saboda bakada kunya wai dan ALLAH Modibbo yaushe zaka girma ne ka daina abinda kake?". Baki ya tura yace "Dan ALLAH Ammi ki k'yaleni da.......hanyar fita data k'ara nuna masa yasa yayi shiru ya juya ya fita daga falon, da kallo Ammi ta bishi tana girgiza kai tasan halin kayanta shi yanzu ba abin kunya bane a gurinshi ya d'auko Jauhar duk uban mutanen nan yazo ya keta ta cikinsu ba ALLAH dai ya zaunar dasu lafiya inba hakaba wllhy za'a ga kwamacala kala kala ita Jauhar rashin kunya shikuma ba hak'uri da rangwame ko yaya akayi masa abu saiya rama haka zaije yaita wahalar da ita a banza indai bata daina yimasa rashin kunya ba zata sameta kuma tayi mata magana rashin kunyar datake masa tayi yawa inzata gyara ta gyara idan kuma bazata gyara ba to itace a wahale. Yana fita yaga har lokacin Abdallah da Hassana suna nan anata lobayya, wajen ya nufa a fili yake fad'in "Kaima tashi zakayi dan ubanka tunda nima ban yiba, tunda Hassana taga ya nufosu gabanta ya shiga fad'uwa tun kafin ya k'araso ma ta mik'e tsaye dan tasan sauran zancen yana zuwa kuwa yace mata "Ke dan ubanki wuce ki shiga gida". da sauri kuwa tabar wajen jikinta na rawa, harara Abdallahn Momy Maryam ya zabga masa yace "Malam ya haka daga zuwa zaka korar min mata bayan bamu gama soyayyar mu ba". "Ai yadda banyi ba ba ubanda ya isa yayi wllhy shima wancan d'an iskan daya nan wlhy saina koreshi". ya fad'a yana zama kusa da Abdallahn, tsaki Abdallahn Momy Maryam yayi cikeda jin haushin korar masa sweetie dayayi yace "Banza d'an bak'in ciki wato yadda bakayi ba muma baza muyiba ance maka kowa ma irinku ne kullum bakuda aikin yi sai fad'a kamar wasu kaji". "Da bakasan kajin bane". Madugu yace yana lallatsa wayarshi, k'wafa Abdallah yayi ya tashi yabar wajen Madugu ya tuntsure da dariya ya bishi yana masa magana yayi masa banza. ✓•✓•✓•✓•✓•✓ Washegari juma'a aka tashi da hada hadar d'aurin aure duk da dai na azahar ne d'aurin auren. Bayan an sauko masallacin juma'a aka d'aura auren ABDALLAH BASHEER MADUGU (MODIBBO) da amaryarshi HUSSAINA ISMA'EEL TURAKI (JAUHAR) saikuma na HABEEB UMAR MARAFA da HUSSAINA BASHEER MADUGU daga k'arshe kuma aka d'aura na ABDALLAH ALIYU ZAKEER da HASSANA BASHEER MADUGU kowanne akan sadaki naira dubu d'ari d'aurin auren daya tara d'aruruwan mutane da manya manyan mutane babu wanda babu malamai ne masu mulki ne rik'akk'un y'an boko ne da k'usoshin gwamnati da manya manyan masu kud'i wad'anda sukaci kuma suka tada kai nan fa marok'a suka samu abinyi musamman da sukaga anata musu b'arin naira tamkar ba'a san zafin nemanta ba. Anko sukayi su ukun wato Madugu da Habeeb da Abdallah komai da sukayi amfani dashi iri d'ayane hatta wrist watch d'insu iri d'ayane na silver wanda shi kad'ai ma idan mutum yaji kud'inshi saiyayi mamaki, kowanne ka kalla fuskarshi taf da fara'a da farin cikin angwancewa sai gaggaisawa suke da jama'a ana musu fatan alkhairi. A can Yola ma a ranar aka d'aura auren JA'AFAR ISMA'EEL TURAKI da amaryarshi HANNATU ALIYU ZAKEER, shima yayi mutane sosai na ban mamaki daga nan Ja'afar da Daddy da wasu y'an uwa na jiki suka nufo Kano. Ranar ma amaren kaya iri d'aya suka sa wata dakakkiyar shadda fara dogayen riguna da akayi musu wani tsadadden aiki irin na y'an Senegal sunyi kyau sosai tunda aka d'aura auren kowacce jikinta yafara sanyi ganin yau dole ne subar gidansu da suka rayu tsahon lokaci a ciki shikenan kuma sun shiga wata sabuwar rayuwa kenan. An cigaba da shan shagalin biki wanda gidan ya cika mak'il ba masaka tsinke harda wad'anda ba'a gayyata ba irinsu Mom sayyeed da Aunt jamila dasu haleemah d'ayyabu da wasu daga cikin y'an TOP TEN dai irinsu bazan kama suna ba dai 😝😅. Abinciccika gasu nan kaloli daban daban sai wanda mutum ya zab'a da kalar lemuka kala kala can na hango su Mom sayyeed da Aunt jamila a lungu sunata aswaki da naman kaji suna korawa da exotic ( bani na fad'a ba ango Madugu ne ya hangoku🤐). Kasancewar bikin Ja'afar daya had'e lokaci d'aya yasa Mama batazo Kano ba tasan dai Ammi na tsaye akan komai na yaranta. Tunda yamma aka fara shirye shiryen kai amare wad'anda tuni suka fara kuka saboda ganin dai da gasken tafiyar zasuyi ga kuma tsoro da fargabar shiga wata sabuwar rayuwa wadda basu saba da itaba dad'in dad'awa kuma nasihar dasu Abbie da Ammi da sauran y'an uwa sukayi musu hakan ya k'ara sanyayar da jikinsu musamman Hassana da zatayi nesa dan ita yola za'a kaita. Jauhar kam tuburewa tayi ita dole saidai a kaita dasu Irfaan ba za'a kaita ita kad'ai ba da k'yar aka shawo kanta da rarrashi akace idan tayi kwana biyu za'a kawo mata su, suma d'in kukan suke tayi ganin za'a rabasu da ita da k'yar da dabara aka fita da Jauhar aka shigar da ita mota aka tafi ana tafiya da ita itama Hussaina motocin da zasu d'auketa sukazo haka suka k'ank'ame juna itada Hassana. Mrs Salees M 3/17/22, 12:10 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 41. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*. ©Oum Hanan. Sunsha kukan rabuwa sosai da k'yar aka b'amb'are Hussaina daga jikin Hassana aka fita da ita sunata kuka tunda suka taso suke tare daidai da rana d'aya wata a cikinsu bata tab'a tafiya tabar y'ar uwarta ba komai zasuyi tare su kwana su tashi tare ayi fad'a a shirya yau ALLAH ya kawo rabuwarsu auren kenan ai kabar kowa naka iyaye y'an uwa da abokan arzik'i shiyasa masu karin magana sukace aure yak'in mata, koda aka fita da Hussainar ma Hassana bata fasa kukan ba kwanciya tayi kan gadon ta cigaba da raira kukanta. ***** Wad'anda suka kai Jauhar basu wani dad'e ba anga gida dai ansa albarka daga nan kuma motocin da suka kaisu suka juya dasu aka barta ita kad'ai, sai bayan tafiyar sune sannan ta bud'e kanta ta shiga k'arewa d'akin kallo ya matuk'ar yimata kyau duk da dai bawai yaune ganinta dashi na farko ba amma kasancewar ya k'ara shan gyara ga me sabbin furniture hakan yasa ya k'ara yin wani irin kyau na musamman ya burgeta sosai haka kayan ciki sunyi mata masifar kyau. Abdallah shi kad'ai ya taho abinshi bayan dogon gargad'i da nasihar dayasha daga bakin Abbie da Ammi dakuma Ayyah, saida ya biya ya siya kazar amarci da fresh milk da ruwa saboda ba komai a fridge d'in sannan ya wuce gidan. Da kanshi ya fito ya bud'e gate d'in gidan ya shiga da motar ya k'ara rufewa, ledar dake kan front seat ya d'auka ya rufe motar sannan ya wuce cikin gidan yana jin zuciyarshi wasai tamkar wanda aka yiwa albishir da gidan aljannah sai faman doka murmushi yake, tanajin motsin shigowa tayi sauri ta k'ara jan gyalenta ta rufe fuskarta ta cikin mayafin take kare masa kallo lokacin daya shigo cikin salon gayunshi daya saba tafiya da hankalin y'an mata shadda light coffee da hula kalar shaddar basai anyi maganar k'amshi ba dan wannan a zaune take tsadadden k'amshin shi dake masa rakiya a ko ina yauma yana biye dashi harya zarta na kullum, masha ALLAH Yah Abdallah badai d'aukar wanka ba wllhy koya yasa kaya saiya haskasu koda kuwa yasane bada niyyar kwalliya ba ya had'u tako ina idan ka ganshi kamar ya had'a jini da larabawa. Inda take ya nufa yana zuwa ya zauna a bakin gadon bayan ya ajiye ledar hannunshi yace "Da zaki taimaki kanki ki cire wannan lullub'in na kanki kisha iska". ta cikin mayafin ta murgud'a masa baki, batare datayi zato ba taji ya fisge mayafin ya jefar akan gadon yana fad'in "Malama ki cire wannan abinda kike ta fama dashi kamar matar liman". baki ta tura kawai batayi magana ba. "Wow she's very very beautiful baby, kinyi kyau ba kad'an bafa". bata kulashi ba sai juyar dakai gefe datayi tana ta wani cin magani hakan saiya bashi dariya ma baki ya tab'e ya tashi ya d'auki ledar daya ajiye ya fita ta bishi da kallo tareda k'ara d'auko gyalenta ta k'ara lullub'awa saidai bata rufe fuskarta ba. Kitchen yaje yasamu plate ya juye naman kazar ya d'auko cup biyu da fresh milk d'in yadawo d'akin cup d'in ya ajiye da madarar a bedside drawer ya haye da naman kazar kan gadon ya ajiye a gabanta yana fad'in "Gyaramin zaman nan naki malamar k'arya shine saida kika k'ara yafa wannan gyalen ko? baki ya cije yasaki k'wafa yana murmushi yace "Ki gama yafe yafen k'aryar naki Jauhar badai mayafi ba? dariya ya saka kafin kuma ya had'e fuskarshi tam yaci serious ya d'auki naman yakai bakinta, girgiza kai tayi ta kauda kai gefe tace "Nifa na k'oshi Yah Abdallah bazan iya cin komai ba yanzu". Cinyar kazar ya yaga ya fara taunawa yana fad'in "ALLAH sai kinci kazar nan Jauhar bazan b'ata kud'ina a banza ba ko kici ko in yanka miki ta wahala yanzu nan". Cikeda gajiyawa tace "Wai ana dole ne dan ALLAH tunda nace na k'oshi basai a k'yaleni ba". "Zakiga dole kuwa yanzu yanzun nan yarinya ganin idonki wllhy ko kici da arzik'i kokuma kici ta tsiya saiki fad'amin wanda kika zab'a". yace yana ajiye naman hannunshi yafara cire links d'in hannunshi yana tattare hannun rigarshi kamar wanda zaiyi dambe ido kawai ta zuba masa tana kallon ikon ALLAH taga abinda zaiyi, d'agowa yayi ya kalleta bayan ya gama tattare hannun rigar tashi yace "Tsiya kikeso ko arzik'i? idan tsiyace kinsan na iyata harda ta siyarwa wllhy danneki zanyi in miki d'ura ta rashin arzik'i koda kuwa zakiyi amai idan kuma arzik'i kike nema shima na iyashi kwando kwando idan mutum ya nemi hakan". zab'i ya rage naki tsiya ko arzik'i?". ya ida maganar yana d'age mata gira, da kanta ta shawarci zuciyarta gara taci ta arzik'in dan tasan sarai zai iya aikata abinda ya fad'a d'in yayi ma wanda ya fishi sun gani, idanun daya tsura mata ne alamun yana jiran amsa yasa ta tura baki takai hannu tafara cin kazar tana faman yamutsa fuska dan ALLAH nagani a k'oshe take duk da bawai wani abincin kirki bane a cikinta amma a cushe yake wani irin murmushi ya saki shima ya d'auki wanda ya ajiye din yakai bakinshi yana fad'in "Good yarinyar kirki maza cikamin cikinki". d'agowa tayi ta kalleshi taga bama ita yake kallo ba ya maida hankalinshi kan naman dayake ci, kad'an taci ta cire hannunta alamun ta k'oshi. "K'ara naman nan Jauhar kafin in b'ata miki rai yanzun". yace batare daya kalleta ba, kamar zatayi kuka ta maida hannunta ciki ta cigaba daci wannan mugunta dame tai kama shi tuni ya cire hannunshi ya daina ci waya ce ma a hannunshi yana dannawa amma ita yasata sai jibgar nama take kamar wata jaka, haka ta dinga turawa saida taji kamar zatayi amai sannan ta marairaice kamar mai shirin sakar masa kuka tace "ALLAH na k'oshi inajin kamar zanyi amai". wayar ya kashe ya ajiye sannan ya d'auke plate d'in ya ajiyeshi a k'asan carpet ya d'auko cup da fresh milk d'in ya zuba. "Koramin da wannan". yace yana mik'a mata cup d'in, yawun bak'in ciki ta had'iya tana jin kamar ta shak'oshi dan takaici gaba d'aya zamanshi a wajen ya gundureta, a fusace ta karb'i cup d'in takai bakinta tafara sha saidata shanye tas sannan ta mik'a masa kofin tana goge bakinta da hannunta karb'a yayi shima ya zuba ya shanye ya k'ara zuba wata ya shanye tas sannan ya sauka daga kan gadon ya had'a komai ya fita ta bishi da kallo. Bai dad'e ba yadawo d'akin tana nan inda ya barta ko cikakken motsi batayi, hularshi ya d'auka wadda ya cire tun shigowarshi bedroom d'in ya cokarata a kanshi tazo har gaban goshinshi ya kwashi links d'inshi daya cire da wayarshi baice mata komai ba ya juya ya fita daga d'akin yaja mata k'ofar. "Umma ta gaida Assha". ta fad'a tana kallon k'ofar daya fita tana gatsina baki murna fal zuciyarta ALLAH yasota baice zai kwana anan ba ya addabeta tasan da saiya sanya mata ciwon kai. Tashi tayi rage kayan jikinta ta fad'a bathroom tayi wanka bayan ta fito ta shafe jikinta da had'add'iyar khumra da kolacca ta asalin maiduguri mai mugun k'amshi ta k'ara da body spray a kowace gab'a ta jikinta sannan tasa night dress riga da wando farare k'al masu kauri tasa k'aton hijab ta kabbara sallah, Esha'e tayi sannan tayi shafa'i da wutr tayi Azkar da addu'o'en ta data saba ta tashi ta nad'e pray mat d'in ta maida inda ta d'auko ta cire hijabin shima ta ninkeshi ta ajiye sannan ta kashe k'wayayen d'akin gaba d'aya ko dump light bata kunna ba saboda akwai hasken farin wata daya ratso ya shigo d'akin ta window kasancewar net ne kuma watan baiyi nisa ba da haskenshi sosai ta daidaita A.C yadda take so. Gadonta ta haye ta karanto addu'ar kwanciya barci taja duvet ta rufe k'afafunta ta d'auki wayarta ta kunna data sak'onni suka fara tururuwar shigowa saboda kwana biyun datayi bata hauba kad'an ta duba daga ciki bata samu damar yin replying bama saboda barcin dake cin idonta saboda tsabar gajiya dake tattare da ita, ganin dai hammar datake ta faman dokawa tak'i k'arewa ga wayar na shirin sullub'ewa yasa ta kashe datar ta ajiye wayar gefen pillow ta lumshe idanunta yanayin nayi mata dad'i sosai barci ya fara fisgarta daga haka harya d'auketa sosai ta shiga sauke numfashi a hankali a hankali alamun barci yayi dad'i kenan. Cikin barcin taji kamar ana tab'a k'ofar bedroom d'in kasancewar bata cika nauyin barci sosai ba yasa taji, da sauri ta tashi zaune gabanta na fad'uwa, aka turo k'ofar aka shigo tun daga tsayin shi data gani ta inuwar shi ta gane kowaye k'aramin tsaki taja cikin ranta tana tunanin abinda ya dawo dashi kuma yanzu da daren nan, makunni ya laluba ya kunna fitilun d'akin yayi tsaye a wajen yana k'are mata kallo tamkar wanda bai tab'a ganinta ba daga shi sai three quartern wando ko riga babu faffad'an k'irjinshi mai cike da yalwar kwantaccen gashi ta bayyana sai slippers a k'afarshi, sosai Jauhar ta had'e rai tace "Lafiya kuwa?". "Ita ta kawo hakan". yace kai tsaye yana k'ara gyara tsayuwar shi. "To mekazo yi dan ALLAH yanzu da daren nan?". Jauhar tace tana d'an hararar shi k'asa k'asa. "Hakk'ina zaki bani". yace ba alamun wasa saman fuskarshi. Sosai gaban Jauhar yake bugawa amma ta maze ta k'ara shan kunu sosai (Jauhar kenan Madugu wani shan kunu baya masa ko koko zakisha ba damuwarshi bace 🤣😝). "Hakk'i kuma? wani irin hakk'i ban ganeba". Wani d'an iskan murmushi ya saki tareda cije lips d'inshi yana wani shanye idanuwa yace "Bayani zanyi miki kokuma gwadawa zanyi kigani a aikace?". ya fad'a yana tunkarar gadon yana mammatsa damtsen hannunshi har wani tsotsar bakinshi yake tamkar mai shan sweet, baya Jauhar ta fara ja tana fad'in "Wai meye ma'anar haka Malam dan ALLAH ni ka kashemin fitila ka fita barci nakeji". cikin tsiwa da masifa tayi maganar tana k'ara jan blanket d'in tana rufe jikinta gabanta sai dukan uku uku yake. "Nima barcin nazo muyi ai baki gane bane". ya fad'a lokacin dayake k'arasawa wajen gadon yafara jan blanket d'in data lullub'a dashi, ganin wata masifarta bazata kaita ko ina ba yasa ta marairaice kamar zata sakar masa kuka tace "Dan ALLAH kayi hak'uri please Abdallah ina fashin sallah nefa yanzu". dariya yayi yace "Rainamin hankali zakiyi Jauhar? sai watan gobe kike menstruation Al Muharram kenan 12 ga wata right?". yace yana kashe mata ido tareda d'age mata gira lokaci d'aya yana janye lullub'ar datayi yayi wurgi da ita k'asa. Mrs Salees M💝 3/17/22, 20:24 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 42 Paid book *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.* ©Oum Hanan. Mamaki ne ya kusa sumar da Jauhar a zaune kai jama'a Abdallah bala'i ne anya mutumin nan bashi da shafar jinnu a jikinshi kuwa? ta yaya yasan watan datake period harma da kwanan watan datakeyi?. Jin ya hawo kan gadon ta k'ara tsurewa tana matse jikinta sai girgiza masa kai take tana son yin kuka tace "Da gaske fa nake maka wasa yake min yadawo wannan watan please ka k'yaleni dan ALLAH". "Ok bari in duba in gani sai in tabbatar". kafin tayi tunanin abinda zaiyi mata taji ya finciko k'afafunta da k'arfi sai jinta tayi a kwance kafin tayi wani yunk'uri yabita ya danne yafara k'ok'arin cire mata riga duk yadda taso hanashi ta kasa y'an hannayen nata ma datake ta k'ok'arin tureshi ya had'esu guri d'aya ya danne da gwiwarshi a haka yasamu damar cire mata riga, tuni ta fara hawaye musamman daya kasance ko bra babu a jikinta duk albarkatun k'irjin nata gasu nan a sarari muraran wanda hakan ya k'ara haukata Madugu bedsheet d'in gadon ya yaye ya lullub'a musu ya cigaba da k'ok'arin cire mata dogon wandon kayan barcin dayayi saura a jikinta ganin ya sakar mata hannayen yasa ta fara son k'watar kanta d'an tsayawa yayi cikin haki yace "Kokawa zakiyi dani Jauhar? malama ciremin hannunki a nan wajen". "Dan ALLAH dan annabi kayi hak'uri na tuba wllhy". duk da yanayin dayake ciki saida yayi y'ar dariya yace "Dan ALLAH karki tuba yanzu Jauhar nafiso mu zuba ni da ke, harni kike kira da Abdallah gatsau ko na turo a kiraki kice bazaki zoba saboda kin maidani shashasha saikin biyani kazata da kika cimin yarinya bakici a banza ba". ya ida maganar yana sab'ule wandon gaba d'aya, sosai ta k'ara rikicewa ta rik'e hannayenshi gam cikin zubda k'walla tace "Ka yafemin dan ALLAH wlhy bazan k'ara yimaka rashin kunya ba na rantse maka da ALLAH ka......ganin tana b'ata masa lokaci da shegen surutun nan nata yasa kawai yayi maganinta ta hanyar zura bakinshi cikin nata ya kama harshenta gam yana masa wani irin tsotsa bayan ya zame hannayenshi data rik'e ya k'ara ja musu abin rufa. Duk da irin azabar dayake gana mata hakan bai hana bakinta mutuwa ba sai antaya masa uwar magiya take tana bashi hak'uri wai ta daina masa rashin kunya har abada sam Abdallah bai kulata ba duk da dai kukan datake yana tab'a ranshi sosai amma so yake ya horata yabata kashi ta yadda idan akace tayi masa rashin kunya zataji fargabar yi dan haka bai tsaya uban kukan datake ya masa tasiri a ranshi ba ya cigaba da mata sambad'e bad'e da kashe arna baji ba gani, magiya take masa har data hauka wasu abubuwan ma batasan tana fad'ar suba tsabar wahala gashi bakin nata ya kasa yin shiru harda ALLAH ya isa ta dinga had'awa kuma a shirmen ta tanaso ya k'yaleta ne 🤭. Ganin ba sarki sai ALLAH yasa tayi gum da bakinta sai uban b'are masa baki datake tana kuka mai k'arfi iya gaskiyarta ko zaiji tausayinta ya k'yaleta amma inaa Madugu yayi nisa sambatu kawai yake zuba mata har dana iskanci, sai daya fanshe duk wata rashin kunya datake masa ya tabbatar ta jigatu tayi laushi ta galab'aita sannan ya sarara mata zuwa lokacin ko d'an yatsanta bata iya d'agawa tsabar jigata, koda yasamu nutsuwa ma bai d'agata ba sai nauyinshi daya k'ara sakar mata sosai wanda ta fara nishi da k'yar da k'yar cikin dasasshiyar muryarta wadda bata fitowa sosai tace "Dan ALLAH kayi hak'uri ka d'agani numfashina zai d'auke wlhy". hawaye shab'e shab'e tayi maganar hardasu majina. Baki ya cije yana murmushi cikin sauke numfashi yace "To ya kikaji Baby, zaki k'ara min rashin kunya? tun kafin ya k'arasa fad'a tayi saurin girgiza kai, kai ya jinjina yana wani tab'e baki yace "Meye sunana daga yau?". yace yana zura hannu yayiwa k'irjinta wata wawar damk'a wanda yasata zabura ta k'ara fashewa da kuka iya k'arfinta saidai dayake muryar tata a dashe take yasa bai fitoba sosai cikin kukan tace "Yah Abdallah sunanka, ALLAH bazan k'ara ce maka Abdallah ba dan girman ALLAH ka taimakeni ka k'yaleni haka Yah Modibbo". "Ai ban gamaba tukunna d'an saurara min, kanshi ya d'ora a wuyanta yasa bakinshi cikin kunnenta yace "To yadai kina sona yanzu? kuma kinyi farin ciki da wannan auren?". "Wllhy ina sonka kuma nayi murnar auren nan". "Gud to yanzu fad'amin da wane suna zaki dinga kirana?". Jauhar jitake tamkar tayi kukan kura ta b'arar dashi taita dukanshi dan tsabar mugunta banda azabtar da ita d'in da yayi yanzu kuma yazo ya danneta yana mata wasu tambayoyi na hauka ALLAH mutumin nan da k'yar idan baici kaiba abin nashi yayi yawa, da k'yar tana nishi tana komai tace "Yah Abdallah, ALLAH na daina cemaka Abdallah kawai". fuska ya yamutsa yace "Me wani Abdallah? sunan soyayya nakeso malama". cikin hanzari tace "Sweet honey". "Wow nice name! wannan yayi yanzu zuwa gaba sai a canza wani ko?". ya k'are maganar da sigar tambayarta tareda d'an cizon gefen kunnenta cikeda mugunta wanda ba shiri ta saki wata siririyar k'ara wasu hawayen na k'ara zubo mata, saidaya bata kyakkyawar sumba sannan ya d'agata kafin tayi wani yunk'uri taji yayi sama da ita har saidata k'ank'ame shi tareda runtse idanunta, toilet ya nufa da ita ya had'a ruwa masu d'umi yasata, kuka take sosai dan dai ba k'ara sai a lokacin dan rashin mutunci wai ya nuna tausayinta yakeji harda cewa ta taimakeshi tayi shiru idan ba hakaba kuma shima zaiyi kukan takaici yasa batasan lokacin data tsayar da kukan nata ba ta d'ago jajayen idanunta da suka kumbura ta watsa masa wata uwar harara wadda tasa ya zaro ido yana dafe k'irjinshi cikin dariya yace "Wllhy ki cigaba da hararata yarinya nikuma bazan gaji da sassama miki jiki ba akan gado". k'aramin tsaki tasaki wanda ta tabbatar dayaji shi saiya san abinda yace kai wannan bawan ALLAH ba k'aramin fitinanne bane wllhy tasan harda k'eta ya had'a mata da zallar mugunta sai ALLAH yayi mata sakayya. Shiya taimaka mata ta tsarkake jikinta duk da anayi ana fad'a shima yayi nashi wankan ya d'aukota suka fito, har lokacin hawaye basu daina zuba daga idanunta ba, ba k'aramin jin jiki take ba ALLAH yasani ya cutar da ita jitake tamkar k'asanta ba'a jikinta yake ba ga k'irjinta dayake mata mugun zafi wanda sukayi jawur saboda jarabar Abdallah. Duk yadda taso tasa kayanta kafin su koma barcin yace sam bai yardaba a yadda suke a haka zasu kwanta salon idan zaiyi second round saita sashi wahalar cire kaya dan mugunta, bazata iya da kwatirar Abdallah ba ta gaji iya gajiya hutu take buk'ata da barci dan haka ta k'yaleshi suka kwanta a hakan yana rungume da ita a jikinshi. Barcin wahala ne ya d'auketa shikam Abdallah sam barcin ma gagarar idanuwanshi sukayi wani irin farin ciki mara misali suna ratsa b'argo da zuciyarshi harma da dukkan jikinshi gaba d'aya wai yau gashi ga Jauhar a matsayin ma'aurata harma wani abu ya shiga tsakanin su kasa jurewa yayi saida ya zameta daga jikinshi yaje ya d'auro alwalah ya maida wandonshi ya fita ya d'auko jallabiyyah a nashi bedroom d'in yadawo yayi sallah raka'ah biyu ya k'ara jaddada godiyarshi ga ubangiji mad'aukakin sarki daya mallaka masa burin ranshi wanda tun baisan menene kanshi ba yake da burin a cikin zuciyarshi yau ALLAH ya amsa rok'on shi ya mallaka masa BURIN ZUCIYARSHI. Bayan ya kammala ya tashi ya komawa ya kwanta ya k'ara k'wak'umeta tamkar mai shirin maidata cikinshi har saidata bud'e ido ta saki k'aramar k'ara saboda azabar zogin daya ziyarci k'asanta baki ta b'are zata sakar masa kuka yayi maganinta ta hanyar tura mata harshen sa karta jik'a masa aikin rarrashi yanzun nan dan shima barcin ne a idonshi. **** Shiya fara tashi da asubah saidaya bata peck a goshinta sannan ya shiga bathroom yayi wanka ya d'aura alwalah ya fita masjeed. Harya dawo tanata barcinta da k'yar yasamu ta tashi tana tashi kuwa ta dira masa kukan k'asanta zai cire wai dariya ta bashi ma dama ta tab'a gani k'asan mutum ya cire? wankan ma da k'yar tayi shi dan saidaya tsoratar da ita yace zai maida ita gado yanzun nan kuma tasan abinda zai faru hakan yasa ta rage kukan sannan tayi wankan ya d'aukota tayi sallah tana hawaye anya gabanta bai samu matsala ba kuwa jinshi take kamar ma ba'a jikinta yake ba tana idarwa ta k'ara dira masa wani kukan. "Ya ilahee wai Jauhar menene haka dan ALLAH kiyi hak'uri mana". ya fad'a yana dukan goshinshi Janaan sam batayi masa wannan iya shegen ba ya rasa ganewa kukan tsakani da ALLAH take kokuwa dai raki ne da shegantaka take masa. Tea mai zafi ya dafa ya had'o mata mai kauri ya kawo mata karb'a tayi ta shanye ya maida cup d'in yana dawowa ya sameta ta k'ara b'arke masa baki ta cigaba da wani kukan. "Oh my God kinga Jauhar idan ban maidake kan gadon nan nayi till down dake na ranar nan ba kice ba sunana Abdallah ba ya zaki maidani wani sakarai shashasha tun d'azu muke abu d'aya dake kin k'i yin shiru". Takaici ne ya kamata wato rarrashin ta dayake shine abin gajiyawa shi baiga irin d'anyen aikin daya aikata mata ba, cikin rashin kunya tace "Wllhy bakada tausayi kuma bazan yafe cutar dakayi min ba ALLAH ya sakamin". maimakon taga yaji haushi saitaga yayi dariya kawai yace "Nima ALLAH ya sakamin ciwon jikin dakika sani". k'aramin tsaki taja wanda bata bari ya fito waje ba ta juya ta cigaba da kukanta bilhaqqi da gaskiyarta. Abdallah dai tun yana d'aukar abin iskancin Jauhar ne harya fara yadda d'in k'warai akwai matsala dan haka ya kira Mabrookah dan nurse ce a wani private hospital baima tsaya amsa gaisuwarta ba yace tazo ta duba masa Jauhar tambayar shi take yi lafiya ya daka mata tsawa wai idan bazata zoba ta barshi zai nemi wata, tunda Mabrookah taji haka ta ayyana a ranta yayansu ya cika aiki maigidanta ta kira a waya ta sanar dashi zataje ta duba matar Yah Modibbo yayi mata waya batada lafiya yace ALLAH ya kiyaye ta hau shirin tafiya. A bakin gate tayi masa waya yazo ya bud'e mata suka shiga cikin gidan tare tana tambayar shi abinda ya samu Jauhar d'in bak'ar magana ya yab'a mata wadda tasa taja bakinta ta tsuke har suka shiga ciki, bedroom d'inshi yanufa yace ta shiga ta fara dubata yana zuwa. Mrs Salees Mu'az 💝 3/19/22, 08:17 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 43. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.* ©Oum Hanan. Tana shiga ta sameta a baje akan dardumar data idar da sallah idanun nan luhu luhu sunyi jawur alamun kukan datasha bana wasa bane, tana ganin Mabrookah ta k'ara fashewa da wani sabon kukan zama tayi kusa da ita ta dafa kafad'arta cikin muryar rarrashi tace "I'm sorry Jauhar meyake damunki haka ya dokamin tun d'azu wai inzo bakida lafiya meya faru?". shirun da Jauhar tayi yasa ta gane koma meye yana da alak'a da kwanciyar aure da yayanta yayi da ita dan haka tace ta kwanta ta dubata bayan ta d'auko hand gloves a jakarta tasa, nan fa Jauhar tace sam batasan maganar ba ta kad'a ta raya amma k'ememe Jauhar tak'i yarda wai ya za'ayi k'anwar mijinta ta dubata kaji manya 😅 da k'yar da dabara Aunt Mabrookah tasamu Jauhar ta kwanta a nutse ta shiga dubata sai data tsorata ganin yadda gurin yayi lallai Yah Modibbo bashida tausayi dubi yadda ya maida yarinya dan ALLAH ita kanta ba k'aramin tausayawa Jauhar tayi ba dole yarinya tayi kuka wllhy kasa daurewa tayi cikin tausayawa tace "Jauhar garin yaya haka ta faru? duk yadda akayi gardama kikayi masa ko yayi miki irin wannan zuwan na rashin hankali?". "Wllhy Aunt Mabrookah bawata gardama danayi masa tsabar mugunta ce kawai kuma dai kunsan halinshi". Jinjina kai Mabrookah tayi tace "Gashi yaja miki aiki dan wllhy sai anyi miki d'inki". Ido Jauhar ta zaro daga kwancen tace "Na shiga uku Aunt Rookah dan ALLAH kawai ki k'yaleni basai kinmin ba tsoro nakeji wllhy". ta k'are maganar tana hawaye "To ta zakiyi Jauhar? dole haka zaki daure ayi miki idan ba'a yiba akwai matsala gashi ma banzo da kayan d'inkin ba bari in fad'a masa ya siyo". bata saurari cewar Jauhar ba ta fita daga bedroom d'in Jauhar ta bita da kallo cikin zuciyarta tana jawa Madugu ALLAH ya isa haka nan yaja mata ita ba haihuwa ba ba komai ba za'ayi mata d'inki wlhi Man d'innan gaba d'ayanshi matsala ne. Mabrookah tana fita taci karo da Abdallah ya fito daga side d'inshi cikin riga da wando marasa nauyi light blue ganinta yasa ya tsaya yace "Ya akayi kin dubata?". Kai ta kad'a masa kawai. "Yadai ba wata matsala dai ko?". "Gaskiya akwai Yah Modibbo dan ALLAH ya akayi haka". Hannun kujera ya dafa ya hard'e k'afafunshi yana kallonta bayan ya had'e rai sosai yace "Ban gane ya akayi haka ba me akayi?". "Amma dai Yah Modibbo meyasa kayi haka ka......"Idan banci ubanki cikin gidan nan ba kice shege nake Mabrookah ya zakizo ki dinga min kame kame tuhuma ta kike ne akan abu ya shiga tsakanina da matata kokuwa?". wani aiki sai Abdallah Madugu 😝. "Nifa ba haka nake nufiba Yah Modibbo". Mabrookah ta fad'a tana tura baki ya taso ta da safiyar nan kuma weekend ne ba aiki yazo kuma yana zaginta. "Me kike nufi to?". yace yana hararar ta. Wani abun tayi niyyar fad'a amma ganin irin kallon dayake mata kad'an daga aikinshi ya mauje ta ba ruwanshi da aurenta ko kuma ya d'ura mata ashar hakan yasa tace "An samu matsala dole sai anyi mata d'inki". "Shine abin tsayawa kina min kame kame anan wajen? wuce kije kiyi aikinki kibar min gidana yanzu". "To ai ban taho da kayan aikin ba saidai in rubuta maka ka siyo". "Ok turomin text message inje in siyo". ya fad'a yana zaro wayarshi dake cikin aljihu, a nan ta tura masa abinda take buk'ata saida yaji shigar message d'in sannan ya juya ya fita yana fad'in ta koma ta kula masa da matarshi da kallo ta bishi kafin ta girgiza kai a fili tace "ALLAH ya shirya mana wannan yayan namu ta juya ta koma bedroom d'in, dariya ma Jauhar ta bata ganin yadda ya wani shasshake tamkar mai wata uwar jinya nan ta zauna ta cigaba da rarrashinta da nuna mata haka aure yake dama kuma kowacce mace saita taka wannan matakin kafin tazama cikakkiyar mace, itadai Jauhar jinta kawai take amma ita tasan nata mijin daban yake mugunta ce kawai da tsabar k'eta ya had'a mata. Ba'a jimaba sosai ba yadawo gidan ya kawowa Mabrookah abinda ta rubuta masa da kuka da komai akayiwa Jauhar d'inkin sai faman raki take zubawa ba'a dad'e da gamawa ba barcin wuya ya d'auketa batasan lokacin da Mabrookah ma ta bar gidan ba. Ba laifi tasha tarairaya a wajen shi a ranar amma fa anayi ana fad'a kamar wasu zararru idan yayi fushi ma saiya bar mata d'akin gaba d'aya ba'a dad'ewa kuma sai taga ya dawo idan tace meya dawo dashi yace ba dan halinta ba abinci ma shi yaje yayi musu take away haka sukayi ta budurinsu su kad'ai a gida ba mai kwab'a musu. Sai yammaci sosai sannan ya fita saboda wani uzuri kan harkar office d'inshi tasa ya fita, tunda ya fita tana kwance sai daf da magreebah sannan ta tashi tayi wanka ta k'ara shiga ruwan d'umi ta d'aura alwalah lokacin data fito har an fara kiran sallah dan haka kawai ta gabatar da tata ta shafa lotion mai k'amshi da khumra ta zura doguwar riga mara nauyi purple da pink ta d'aura k'aramin gyale pink tasa barima k'arama a kunnenta purple color tayi kyau sosai fuskarta fayau sai powder da kwalli da lipstick data shafa. Gefen gado ta zauna ta d'auki wayarta tana chatting taji dad'in jikinta sosai ba kamar d'azu ba har yanzu bata daina tuna irin gwale gwalen da Yah Abdallah ya bata ba gaskiya mata suna azabtuwa musamman ita data had'u da miji irin Abdallah. Tana zaune taji shigowar shi, bata d'aga kai ba bare ta kalleshi ta cigaba da danne dannen wayarta ta dai amsa sallamar dayayi k'asa k'asa, kusa da ita ya zauna yana fad'in "Yaa ALLAH! Nagaji sosai Baby". ganin bata kulashi ba yasa ya juya ya kalleta yace "Ke wai sai wani cin d'aci kike kina shasshareni meya faru?". baki kawai Jauhar ta tab'e ta juyar dakai gefe, murmushi yayi shima ya tab'e bakin yace "To naji ba za'a kulani ba a bani abinci inci yunwa nakeji". Sai lokacin tace "Waye zaiyi girkin? ka manta jinyar jikina nake?". "Yanzu dai a tak'aice bazan samu komaiba kenan?". yayi maganar da sigar tambaya yana kallonta kai tsaye tace "Eh babu kaje ka siyo mana abinda zamuci". cikin turo baki tayi maganar da y'ar shagwab'a. Murmushi kawai yayi daya tuna wani abu lokacin Janaan da kanshi ma yace kar tayi girki amma yana dawowa ya tarar tayi ALLAH yaji kanta yayi mata rahma yasa aljannace makomarta yayi mata addu'ar cikin ranshi, ta zaci zaiyi mata masifa da buyagin daya saba sai kuma taga ya mik'e ya fita daga d'akin lallai yau y'an mutuncin ne a kanshi taci sa'a da bai kaimata duka bama koya fad'a mata bak'ar maganar daya saba gwalo tayiwa bayanshi lokacin daya fita tana y'ar dariya. Tana nan zaune har aka fara kiran sallahr Esha'e tashi tayi ta bada farali sannan tayi shafa'i da wutr, bata tashi daga kan dardumar ba ta cigaba da yin Azkar, tana nan zaune ya shigo d'akin a bakin k'ofa ya tsaya yace "Malama taso ki fito falo kici abincin". Bata kalleshi ba tace "Ka kawomin nan ni anan zanci". k'ugunshi ya kama da hannayenshi duka yace "Idan ban shigo d'akin nan na....shiru yayi bai k'arasa ba ya juya ya fita yana fad'in shi ba bawanta bane ai. Binshi tayi a baya itama tana fad'in aikuwa ya zama bawanta tunda har tasashi abinda baiyi niyyar yiba yanzun, tasan bai jiba dasai ya juyo ya maida martani a k'asan carpet taga ledoji guda biyu harda plate da cup a wajen an ajiye yana zaune akan kujera ya hard'e k'afafu yana girgizawa dariya ce ta kamata batasan lokacin data fara yiba tana kallonshi, maimakon taga yaji haushi ya taso mata saitaga shima ya fara dariyar yana kallonta. k'arasawa tayi ta sauko da pillown kujera k'asa ta zauna ta fara shirin bud'e ledar taga ya sauko k'asa shima ya zauna ya janyo ledar gabanta ya bud'e ya ciro take away d'in ya juye had'add'iyar fried rice d'in ciki kallonta yayi bayan ya gama juyewa yace "Matso nan muci daga yanzu indai ina gida tare zamu dinga cin abinci". Bata kulashi ba ta d'auki spoon zata fara cin abincin a fusace taji yace "Wai bada Jauhar nake ba ina magana kinmin shiru wllhy ki kiyaye ni na kwanta dake kinsan sirrina k'aniyarki zanci wllhy yanzun nan". baki ta turo batace komaiba tafara cin abincinta dan yunwa take ji, k'wafa yayi shima ya d'auki spoon d'in ya fara ci kafin kuma ya tashi yaje ya kunna TV ya kamo tashar MBC Action yadawo ya zauna suka cigaba daci ba wanda ya k'ara magana a cikinsu har suka gama, suna gamawa ta haye kan kujera ta lafe sai shine ya kauda kayan wajen yadawo ya zauna ya cigaba da kallonshi itakuma ta cigaba da latsa wayarta ba wanda ya k'ara tanka wani a cikinsu. Wayar hannunta ce ta sullub'e saboda barcin daya d'auketa, yana kallonta yaga har tayi barci tashi yayi ya gyara mata kwanciyar ta tareda zazzafan peck a goshinta ya koma ya zauna kafin lokacin dazai tashi saboda film d'in da sukasa a tashar ya d'auke masa hankali sosai. Sai kusan goma da rabi na dare sannan ya tashi ya kashe TVn da fitilun falon ya d'auketa cak bai nufi nata bedroom d'in ba ya nufi nashi da ita. Kan k'aton gadonshi ya shimfid'eta yana kwantar da ita kamar jira take ta tashi ta ganta a nan ta had'e rai sosai tana k'ok'arin tashi take fad'in "Meye haka Yah Abdallah ya zaka kawoni nan kuma?". Yana cire rigar jikinshi ya bata amsa da "Me idanunki suka gane miki". Cikin sauri ta tashi saidai zugin da k'asanta yayi yasa ta saki k'aramar k'ara ta koma ta zauna idanunta na cika da hawaye, gajeren wando kawai ya bari ya k'araso inda take ya maida ita ta kwanta yabi bayanta gaba d'aya ta gama rud'ewa duk zatonta wani abun zaiyi mata gashi bata gama warkewa ba tuni ta fara son k'watar kanta tareda fad'in "Dan ALLAH Yah Abdallah kayimin rai kaga ban warke ba wllhy wajen yana min ciwo sosai please Yah Abdallah". ta k'are maganar cikin kuka na tausayin kanta, shima cikin kunnenta yace "Nima ba wani abu nace zanyi miki ba ki k'yaleni kawai in rage zafi abina inba hakaba kuma kinsan dai waye Abdallah sarai bakya buk'atar tuni". bai jira abinda zatace ba ya shiga k'ok'arin cire mata kayan jikinta, shiru tayi ta daina k'ok'arin k'watar kan nata kamar yadda ya fad'a d'in tasan waye shi wani boren mutum da masifarshi bazasu k'waci mutum a hannun Abdallah ba indai har bashi yaga dama ba dan haka ta saddak'ar kawai ta mik'a kai. Mrs Salees Mu'az 3/19/22, 18:54 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 44. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.* ©Oum Hanan. Saidaya jagwalgwala ta son ranshi sannan ya k'yaleta harya gama a bired'enshi bata kulashi ba damuwarta dai itace taga ya k'yaleta tun kafin ya birkice mata yafara neman inda zai cutar da ita. Sai anan ta kwana ranar tana jikinshi ko yaya ta motsa da niyyar barin jikinshi zai k'ara matseta da haka harta hak'ura suka cigaba da barcinsu. Da asubah bayan ya tashi yayi wanka yayi alwalah saidaya gama shirin fita masallaci sannan ya tasheta yabar bedroom d'in, da k'yar ta iya tashi saboda jikinta dayayi tsami duk gab'ob'inta ciwo suke mata itama sai datayi wankan ta d'aura alwalah sannan tabar d'akin saboda ba hijab anan, bedroom d'inta ta koma tayi sallah saidata karanta abinda ya sauwak'a daga alqur'ani mai girma cikin k'ananun surorin sannan ta k'ara komawa ta kwanta. Shima daya dawo masallacin yaga bata d'akin bai nemeta ba ya koma ya kwanta yanaso ya d'an rage barci ne kafin anjima yau dole zai fita saboda zai gana dawasu mutane a office. Cikin barcin nan na bayan asubah da Jauhar ta koma tayi wani mafarki daya bata mamaki ya kuma tsorata ta, a mafarkin an nuna mata Janaan ne cikin kyakkyawar shiga da kamala fuskarta sai annuri take alamu tana cikin farin ciki a maganganun da Janaan d'in tayi mata suna alamta mata kar ta cigaba da wannan rayuwar auren data fara ta kyautatawa mijinta saboda shine aljannarta kar tayi la'akari da yadda yake tayi k'ok'arin janshi a jikinta hakan zai k'ara musu kusanci kuma idan da wani hali nashi ma da bataso ta hakan ne zai canzashi ba irin yadda take masa, Janaan tayi maganganu masu dama a cikin mafarkin Jauhar wanda sukayi bala'in sanyayar mata da jikinta haka ta tashi jiki duk ba k'wari taso tayi barci ta more dan dama idan ta koma irin wannan barcin na bayan asubah tana dad'ewa bata tashi ba har k'arfe sha biyu tana kaiwa amma wannan mafarkin datayi yasa ta tashi batayi niyya ba, zaune tayi a tsakiyar gadon daki daki take auna maganganun da Janaan tayi lallai da tayi shirin yin kasassab'a ita ko a kanta bata kawo kyautatawa Abdallah wani abu bane duk da yana matsayin mijin nata gani take idan ma tayi masa ai baisan tayi ba tunda shi ba'ayi masa gwaninta gaskiya ne ya kamata ta gyara ALLAH ubangiji ba ruwanshi indai batayiwa mijinta ladabi da biyayyar aure ba saiya kamata da laifi wanda bata fatan hakan gashi kuma dama tanason mijinta a kanshi tafara sanin menene SO kuma danta samu ma ubangiji ya cika mata burinta na mallakarshi zatayi wasa da damarta? tasan mata nawa ne suke rububin samunshi? wato ALLAH nema yasota da abin baiyi nisaba da haka zatai ta zabga masa rashin mutunci tana ganin kamar daidai take gaskiya taso tayi wrong. Ta d'an jima anan zaune tana a faman tunani kafin ta tashi ta nemi k'aramin hijabi tasaka ta fita kai tsaye kitchen ta wuce ta fara tunanin abinda zata had'a na breakfast. Tea ta dafa wanda yaji kayan k'amshi da na'a na'a sai k'amshi yake ta soya dankali da k'wai da y'ar miyar hanta sai kunun gyad'a datayi bata tab'a kula ma da narkad'add'iyar gyad'ar ba sai yanzu tasan kuma aikin Ammi ne tasan ta dason kunun gyad'a shiyasa ta kawo mata. Bayan ta kammala ta shirya komai a dinning table ta gyaran ko ina ta kunna burner gidan duk ya d'auki k'amshi daga nan kuma ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga ta wani yadin material mai rawa ruwan zuma tana cikin fesa turaruka taji an bud'e k'ofar bai shigo ba sai lek'o da kanshi dayayi yace "In shigo ko in koma?". dariya ya bata ta d'anyi murmushi ta ajiye kwalbar turaren hannunta ta nufo inda yake tana zuwa ta durk'usa har k'asa tana gaisheshi mamaki yasa ya kasa amsawa sai baki daya bud'e yana kallonta ita kanta kunyar hakan taji dan bata tab'a gaisheshi ba, shima d'in tunanin hakan yake shidai a tarihin rayuwarshi duk zaman da zasuyi da Jauhar bata gaisheshi daga harara sai bak'ar magana abin ma dariya ya bashi dan haka ya shiga darawa batare daya amsaba yakai hannu ya d'agota yana fad'in "Taso nan y'ar rainin hankali wannan canjin fa daga ina yake? Jauhar kin tab'a gaisheni kuwa a tarihin rayuwar mu?". yayi maganar yana dafa kafad'unta. A shagwab'e tace "Tunda dai yau d'in na gaisheka ai saika amsa Yah Abdallah". "Eh to kuma hakane, kin tashi lafiya?". A hankali ta amsa da lafiya lau kafin ta d'ora da fad'in "Dan ALLAH Yah Abdallah kayi hak'uri ka yafemin duk abubuwan danayi maka kafin auren mu da kuma yanzu d'azu baccin dana koma nayi mafarki da Bloody tazo min a kyakkyawar suffa kuma ta nuna min abinda nake ba daidai bane forgive me please". ta k'arasa maganar tana kwantar da kanta akan k'irjinshi. K'ara shigar da ita yayi jikinshi ya rungumeta sosai yana sakin ajiyar zuciya yace "Jauhar bazaki gane bane da kinsan yadda kike a zuciyata da abubuwa dayawa bazakiyi minsu ba shin kinsan kece mace ta farko a duk fad'in duniyar nan dana fara so?". da mad'aukakin mamaki ta d'ago kanta tana kallonshi yana sonta fa taji yace abubuwan da duk yake mata fa duk ya sunansu, ganin tayi sakato tana kallonshi yasa yayi murmushi yaja kumatunta batayi auneba taji yayi sama da ita ya mata wata d'auka in a bridal style yana fad'in "Zo muje in nuna miki wani abu da bakisan dashi ba". idanunta ta runtse gam tareda k'ara k'ank'ameshi yana tafe yana sakar mata kiss a duk inda yaci karo dashi a fuskarta har suka k'arasa d'akin, kan bed ya kwantar da ita yaje inda ya ajiye littafin nan nashi ya d'auko kusa da ita ya zauna ya d'ora mata littafin akan cinyarta da ido yayi mata alamun ta bud'e ta gani, cikin sanyin jiki ta fara bud'ewa ta fara cin karo da hotunan ta lokacin da take yarinya da irin kalaman da ake rubutawa a k'asan kowane hoto duk da dai turanci da fulatancin kawai take iya ganewa da ma'anar kalmomin, kalmomin sunyi mata girma da nauyi a kanta kalmomi ne da duk wanda yasan me ake nufi dasu yayin da ake fad'a masa zai tsinci kanshi cikin wani irin yanayi na farin ciki tun tsahon wane lokaci Yah Abdallah yake sonta kenan?, idanunta ne suka kawo hawaye ta d'ago ta kalleshi tana jin tamkar ta fashe da kuka, gira kawai ya d'aga mata yayi mata alamu da idanunshi ta cigaba sunkuyar da kai tayi ta cigaba da dubawa tana hawaye tana bud'e wani shafi taci karo da beat d'inta na d'aure gashi wanda bazata tab'a mantawa dashi ba saboda yadda take sonshi duk cikin abin d'aure gashinta tafi sonshi har tsiya Mama take mata kasa daure kukanta tayi ta ajiye littafin ta fad'a jikinshi tareda sakin kuka lumshe ido yayi yana k'ara matseta sosai a jikinshi yana tapping bayanta alamun rarrashi lokaci d'aya yana sakar mata kisses tako ina, cikin wata irin kasalalliyar murya yace "I love you very very much Jauhar ina sonki har k'arshen numfashina ban tab'a rayuwa da son wata d'iya mace ba saike Jauhar please ki soni kema koda kwatan son danake miki ne". "Nima ina sonka Yah Abdallah tun bansan kainaba bansan meye soyayya ba nake jinka sama da kowa a cikin zuciyata wllhy Yah Abdallah zuciyata ta kusa tarwatsewa lokacin da zancen had'a aurenku da Bloody yazo kunnena barci ya k'auracewa idanuna tun lokacin danake yarinya nakejin wani abu a cikin zuciyata gameda kai wanda narasa tantance meye shi d'in har saidana girma na fahimci SOYAYYA CE I love you too Yah Abdallah". ( Finally kowa tashi ta fito 😘🤣). Kamar zai maidata cikinshi haka ya k'ara matseta saboda dad'in kalmar data fad'a. Sun dad'e sosai a haka kafin ta zame jikinta ta kalleshi gira ya d'age mata yana mata wani irin kallo murmushi tayi ta sadda kai k'asa wani irin dad'i na ziyartar ta jinta take wasai yaudai ta fidda abinda ya dad'e yana cin ranta, shima d'in wani farin ciki yake ji ya amayar da abinda ya d'auki tsahon shekaru yana b'oyeshi. "Dama ka iya magana ta hankali Yah Abdallah?". Sai data fad'i maganar ta zaro ido tana rufe bakinta, baki ya cije yana y'ar dariya yace "Ki cigaba yarinya har yanzu a Abdallah na nake yanzu zan miki sambad'e bad'e kuma kinsan kalar horon da zanyi miki". dariya tayi kafin kuma ta d'an d'aure fuska tace "Amma Yah Abdallah inaso ka share min wata tantama danak.....kafin ta k'arasa taji ya finciko ta ta k'ara fad'awa jikinshi kafin tayi tunanin abinda zaiyi taji ya had'e bakinshi da nata, kissing d'inta yayi sosai kafin ya saketa yana murmushi yace "Yadai Baby na share tantamar yanzu?". baki ta d'an tura tace "Nifa ba itaba Yah Abdallah kace kana sona kuma naga ba'a tab'a jin kanku da Bloody ba bata tab'a zuwa tace kayi mata abu ba shin itama sonta kakeyi kenan?". Murmushi yayi ya kwantar da kanta a cinyarshi yana shafa gashin kanta yace "Kishi kike da matacciya Jauhar? koda yake Janaan ta mutu ne amma bata mutu a cikin zuciyata ba, naga amfani dake cikin hikmar yin biyayya ga iyaye Jauhar tun farko na fad'a miki Jauhar ban tab'a son wata mace ba bayan ke to hakama Janaan babu d'igon soyayyarta ko d'aya a zuciyata a lokacin dana aureta amma Janaan tanada hak'uri tanada kawaici da son farantawa duk wanda ya rab'eta na k'untatawa Janaan da irin halayena da kowa ya sansu amma bata tab'a yunk'urin yimin rashin kunya ba ko makamancin hakan ba kullum k'ok'arin ta taga na zama abin yabo a gurin mutane abubuwa dayawa ba wanda yasan anyi su kuma harta koma ga ALLAHn daya halicceta bata tab'a fad'awa kowaba har dukan Janaan nayi farkon aurenmu zagina dama ta saba dashi tun kafin muyi aure wani abun idan nayi mata saidai tayi murmushi kawai kota zauna tayi kuka a haka har ALLAH ya bata nasara a kaina tarin kulawar ta a kaina da yadda ya maidani kamar wani jariri hakan yayi matuk'ar tasiri a kaina na daina k'untata mata ta shiga raina fiye da zaton mai zato kuma bawai dan ina sonta ba kawai dai ina tausayinta ne ban tab'a cewa Janaan tayi wani abu ta musamin koda kuwa ita d'in baiyi mata ba kullum sabbin dabaru take kawowa na yadda zata zauna dani lafiya batare da mun samu matsala ba Shiru yayi ya had'iye wani abu daya tsaya masa a mak'oshinsa hawaye sun cika kwarmin idanunshi yayin da mutuwar Janaan ta dawo masa sabuwa dal kamar yaune yake ganinta kwance babu rai a jikinta, itama Jauhar d'in kukan take kamar ranta zai fita kewa da alhinin rabuwa da ita na k'ara shigarta hak'ik'a Janaan tana da hak'uri duk abinda kayi mata bazata d'aga kai ta kalleka ba bazata manta ba lokacin da suke nursery zuwa secondary school duk Jauhar d'in ce ke shigar mata fad'a idan taga za'a cuceta gashi ita za'a k'wara amma saidai tayi kuka bazatayi magana ba kota tankawa mutum ba har hakan yake bawa Jauhar d'in haushi dole tayi kukan rashin y'ar uwarta. Hannu yasa ya share hawayen da suka cika masa ido ya cigaba da fad'in "Mistake kad'an zatayi min zan kai hannu jikinta ko inci mata mutunci amma hakan bazai hanata fita hakk'ina ba, Janaan tanada hak'uri Jauhar nafi kowa sanin hakan duk da ban d'auki dogon lokaci sosai da itaba ALLAH yakai rahma kabarinta. Kota yayane Jauhar mu dinga jin maganar iyayenmu yanzu dana bijire lokacin ban aure taba da ke d'in danake ta hank'oron in samu d'in kije ki auri wani inyi biyu babu amma cikin k'udurar ubangiji na amshi aurenta farko na k'untata mata daga baya kyautatawar ta a gareni ya tasirantu a gareni na daina duk abinda nake mata cikin hikmahr ubangiji kuma saiya d'auke abarshi har hakan ya jawo hankalin iyayenmu sukayi tunanin had'amu aure dake cikin ruwan sanyi wannan kuma duk ya samo asali ne da biyayyar danayi tun farko, Jauhar iyaye sunada babban hakk'i a kanmu zuciya ta daina yaudararmu muna ganin kamar basu isa damu ba duk rashin mutuncina da ake gani nasan darajar iyayena kuma ina ganin amfanin rashin bijire musu danake ALLAH ya k'ara mana hak'uri da juriyar yimusu biyayya har k'arshen rayuwarmu". Da "Amin" ta amsa cikin kuka ta tashi zaune tana share masa hawayen idonshi. Mrs Salees Mu'az 💝 3/20/22, 21:20 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 45. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.* ©Oum Hanan. Falo ta jashi inda ta shirya breakfast d'in, cikin farin ciki da nishad'i sukayi tare dama bai barta ta zauna a wani wajen ba tana kan cinyarshi shi ya ciyar da ita itama haka suna hirarsu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa kamar basu ba, wayarshi data fara ringing ne yasa ya tuna fa daya bar mutane tun d'azu suna jiranshi da k'yar ta barshi ya fita farko ma mak'ale masa tayi dole saidai su tafi tare da k'yar ya rarrasheta ya gudu, kowanne a cikinsu farin cikinsu yak'i b'oyuwa musamman da kowa ya fitarwa d'an uwanshi abinda yake ranshi tsahon lokaci. Bayan ya fito meeting d'in ya kunna wayarshi sink'i sink'in tarin sakonni ne suka shiga shigowa wayar tashi duk daga Jauhar kalamai kala kala masu dad'i da tsayawa a rai kasa hak'ura yayi kawai ya tafi gida jinshi yake tamkar sabon mutum gaskiya zama da masoyi akwai dad'i, lokacin daya koma yasamu ta gyara gida ko ina k'al k'al ga had'add'en lunch data shirya masa taci uwar kwalliya tamkar mai shirin zuwa party sai tashin k'amshi take yaga tarairaya da gata a ranar dan hatta wanka ita ta tayashi yayi sannan ta tayashi ya shirya sun k'arar da ranar ne gaba d'aya a tare cikin farin ciki da kyautatawa juna. Tun daga lokacin zaman Abdallah da Jauhar ya canza yayi dad'i sosai saidai fa duk da haka wani lokacin ya birkice mata kamar bashi ba tun tana d'an biye masa wani lokacin suyi harta daina ta fahimci dai wasu daga cikin halayen nashi bazai tab'a barinsu ba idan ma taga take takenshi ma saita fita harkarshi gaba d'aya musamman ma idan daga waje aka tab'oshi idan yadawo mata gidan a hargitse ta dinga kaffa kaffa dashi kenan bata zama ma kusa dashi saidai ta keb'e kanta nan d'inma bata tsira ba saiyace wai ta maidashi mahaukaci kenan mafi yawancin lokuta ma ita dariya yake bata dama ance mai hali baya canza halinshi saidai wani abun ya ragu shiyasa taci maganin zama dashi. Jauhar harta gaji da yiwa Ammi magiyar adawo mata dasu Irfaan gabanta kullum tayiwa Ammin maganar sai tace tabari ta d'an k'ara dad'ewa tukunna sai a kawosu ko kwanaki dataje gidan saida taso tahowa dasu amma da Ayyah suka hana wai ba yanzu ba kuma a zahiri rabuwa da yaran ne kawai basuso saboda suna d'ebe musu kewa tunda yanzu ba kowa a gidan to motsinsu da sukeji suna jin dad'i sosai Ammi ma kam ta yanke shawarar koda zata bada su saidai Jauhar d'in ta d'auki guda d'aya tabar mata d'aya. ****** Tunda suka gama sunna yake ta fama da ita ta tashi suje suyi wanka tak'i ta shagwab'e masa ita duk ya gajiyar da ita yaje yayi wankanshi kawai ita hutawa zata k'ara yi, jiranshi ake dama yanason fita dan haka ya k'yaleta kawai ya shige bathroom dan tsarkake jikinshi. Tana nan kwance idanunta a lumshe bacci nema keson d'aukarta saboda tsabar gajiya da Abdallah ya tara mata mugun horar da ita yake ta wannan b'angaren ko laifi tayi masa yanzu saidai ya kalleta kawai ba duka ba zagi amma zaici k'aniyarta a gado, yau d'inma tuwo tayi shine yayi mata wannan hawan k'awarar duk ya gaji da ita, wayarshi dake bedside ce ta fara ringing hakan yasa ta bud'e ido kamar bazata d'auka bama saikuma takai hannu daga kwancen datake ta d'auko wayar ta duba mai kiran taga number ce kawai ba suna har zata maida ta ajiye saikuma dai tayi picking takai kunnenta tareda yin sallama. "Halooo My Babyyy". Muryar mace ta daki dodon kunnenta, zumbur ta tashi zaune da sauri ta manta ma da gajiyar datayi cikeda bala'i tace "Wace y'ar iska ce take kiran mijina, shegu masu bibiyar mazajen mutane ko wacece ke ALLAH ya ts....... k'it taji anyi saurin kashe wayar baki ta cije cikeda b'acin rai ta yarfar da blanket d'in datake lullub'e dashi ta sauko daga gadon tsaye tayi da wayar a hannunta tana cizon yatsa saboda takaici dama Abdallah wasu matan yake kulawa a waje har tana kiranshi da Baby? Daidai lokacin ya fito daga bathroom d'in da towel d'aure a k'ugunshi sai k'arami dake kanshi yana goge sumar kanshi ganinta a tsaye yasa tana faman girgije girgijen jiki ga kuma wayarshi daya hanga a hannunta shima tsayawar yayi daga k'ofar bathroom d'in yace "Ke kuma lafiyar ki kuwa ko abinne bai isheki ba inzo in k'ara wani ". Yace yana d'age mata gira, Harara ta zabga masa tace "Wace y'ar iska ce take kiranka a waya Yah Abdallah dama kula mata kake a wajen ko? saboda iskanci har wani Baby take kiranka". K'aramin towel d'in dake kanshi ya cillar kan sofa a harzuk'e shima yace "Me kike nufi Jauhar? Ki fito kai tsaye kice Abdallah kai d'an iska ne mai kula matan banza a waje". "Nidai ban fad'a ba karka kaini gaba kuma wllhy koni ko wayar nan yau d'in nan saina fasata". Ta k'are maganar tana d'aga wayar sama zata bugata da k'asa ganin haka yasa ya nufeta cikin hanzari yana fad'in "Karki fasamin waya Jauhar, ke idan bala'i kikeji dashi fa na fiki iyawa mu rigima gaba muka bata ba baya ba, kafin ya k'arasa kuwa ta saki wayar k'asa screen d'in ya bugu da tiles zancen ace ta fashe ma b'ata baki ne ita kanta saida ta saki wayar ne ta tsorata ta dafe bakinta tana zaro ido tana bin wayar dake k'asa da kallo, tun kafin ya k'arasa ya cije baki ya d'aga hannu da nufin yana zuwa ya wanka mata wani wawan marin dazaisa ta gigice saidai yana zuwa ya kasa marin nata sai huci dayake, hannayenta tasa duka a kanta ta sunkuyar da kanta ta runtse ido gam tana jiran jin saukar duka saikuma taji akasin hakan a hankali ta d'ago kai ta kalleshi idanunshi sun kad'a sunyi jawur hannunshi ya saki yace "Bazan dakeki ba Jauhar saboda nine zanji zafin a zuciyata amma na rantse saina miki abinda gara in miki dukan tsiya dashi". Tunda taji ya fad'i haka gabanta yayi wata irin fad'uwa dan sarai tasan abinda yake nufi da hakan bai wuce ya tara mata gajiya ba dama kuma a gajiyen take dan haka da sauri ta durk'usa ta k'asan shi zata gudu yasa hannu d'aya ya cafkota d'ayan kuma ya cire towel d'in dake k'ugunshi yayi cilli dashi ya malk'wayota har saidata saki k'ara yayi sama da ita tun kafin ya k'arasa wajen gadon ya cillata kan gadon kamar wanda ya cilla kayan wanki 😅 ta d'aya gefen gadon ta fara k'ok'arin sauka dan harga ALLAH tasan idan har ta shiga hannunshi to ta gama yawo, daidai lokacin da shima ya hau gadon ya janyota yadawo da ita ya kwantar da ita yabita ya danne bayan ya had'e hannayenta ya matsesu da k'arfi wad'anda take k'ok'arin tureshi dasu tana kuka da fad'in yayi hak'uri ALLAH batayi niyyar fasa wayar ba tsautsayi ne kawai shikuma fad'i yake shi tsautsayin yaci ubanshi da baisan inda zai sauka ba sai akan wayarshi.(Sunan labarin WATA SOYAYYA ya fara fitowa reader's, suna tsananin son juna amma hakan baya hanasu bawa junansu wahala). Cikin tsananin mugunta da k'eta Abdallah yake sarrafa Jauhar ta rasa ina zatasa kanta kukan ma ba jinshi yake ba kamar wani kurma haka ya koma mata bare tace zatayi masa magiya ita ta fara ma yimasa magiya shida yake punishment d'inta tasan ma baji zaiyi ba, kukanta ta cigaba dayi cikin tsananin azaba da son a taimaka mata amma babu mai taimaka matan to waye ma a gidan dazai taimaka mata? Haka Abdallah ya cigaba da cin karenshi ba babbaka saidaya tabbatar data ladabtu tayi laushi ta nutsu sosai sannan ya k'yaleta ya d'agata bai kalli inda take ba ya d'auki towel d'in daya cillar ya k'ara d'aurawa ya nufi bathroom dan sake wani wankan. Da ido ta bishi harya shige toilet din, wani irin zugi k'asanta yake mata da k'irjinta daya sarrafasu cikin mugunta batasan yaushe zasu daina wannan abin da Abdallah ba su zama kamar sauran ma'aurata hawaye ne suke sauko mata wani na bin wani, a haka Abdallah ya fito daga wankan tayi zaton bazai kalleta ba saikuma taga ya nufota ya d'auketa cancak ya nufi bathroom da ita ruwan d'umi daya had'a lokacin dazai fito yasata a ciki saidata d'an dad'e sannan yayi mata wankan da kanshi ya nad'ota a babban towel ya dawo da ita kan gadon, wardrobe d'inshi ya bud'e ya d'auko mata riga da wando three quarter pink sai farar riga mai kamar vest dayake duk rabin kayanta ma sun dawo d'akin nashi musamman English wear, da kanshi ya shiryata harda fesa mata turare kuma har lokacin ba wanda yayi magana a cikinsu dan komai dayake ma fuskarshi ba walwala yaci d'aci yanata faman had'e rai kamar wanda akasa dole. Bayan yagama shima ya shirya cikin k'ananun kaya na kamfanin Gucci sunyi matuk'ar amsarshi kasancewar su black color itadai tana kwance tana binshi da ido harya gama ya d'auki P cap bak'a ya d'ora ya manna glasses shima bak'i ya fesa turare sannan ya fita yabar d'akin, duk zatonta ko tafiya yayi saitaga yadawo hannunshi d'auke da madaidaicin tray ya ajiye kan bedside batare dayayi magana ba ya juya ya d'auki key d'in motarshi akan mirror ya fita yaja mata k'ofar batare daya kalli ko inda wayar take ba. Hawaye taji sun cika mata idanunta har yanzu bata gama dawowa daidai ba ga kanta dake sara mata tsabar matsar datasha a hannun Madugu cikinta duk ya rarake kamar bataci komaiba shima kuma tasan dalilin dayasa yakawo mata abinda ya kawo d'in duk da bataga ko meye ba saboda duk lokacin daya kusanceta bayan sungama saita nemi abinci. Da k'yar taja jikinta ta d'auko tray d'in juice ne na gwangwani na zallar Mango sai snacks da tea mai kauri sai tururi yake sai wani k'aton biscuit guda d'aya da short bread. "Saikace wata jaka ya wani tulo mata uban abinci". Ta fad'a a fili tana tura baki kafin ta fara ci a ranta ta k'udurce wajen Ammi zata gudu wllhy saidai yadawo ya tarar bata nan. Saidata cika cikinta tayi k'at sannan ta tashi nan tabar tray d'in bisa gadon ba abinda ta d'auke ta tafi bedroom d'inta da k'yar take takawa tana zuwa ta canza kaya jikinta da atamfa fitted d'in riga sai zani mara ado Cote d'ivoire kalar milk da coffee da bak'i ta yafa bak'in mayafi tasa plat shoe shima bak'i da side bag k'arama bak'a ta fito taja kowace k'ofa sannan ta fita taja k'ofar falon ta kulle ta fita daga gidan gaba d'aya tasamu mai napep ta hau ta nufi unguwar su Ammi. Bayan wasu y'an awanni yadawo gidan dayake shima akwai key a wajenshi wanda yake had'e da key d'in da motarshi ya bud'e ya shiga, ko ina sai daya duba bai gantaba a gidan ba inda bai lek'a ba ya tabbatar dai da bata gidan gaba d'aya, tsaye yayi a tsakiyar falon ya dafe k'ugunshi da hannu d'aya yana cizon yatsa amma dai yarinyar nan taci uwar rainin hankali wlhy tayi masa laifin sannan kuma tabar gidan saboda ta maidashi wani gaula marar wayo k'wafa ya saki yana jijjiga kai ya fita da sauri ya k'ara shiga motarshi ya figeta da uban gudu ya nufi gidan Ammi yasan dai can kad'ai zataje har gaban Ammin zaije yayi mata rashin M tunda ta rainashi. Mrs Salees Mu'az 💝 3/20/22, 21:21 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 46. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.* ©Oum Hanan. A falo tasame su dukansu, Irfaan da little Janaan sunsa Ayyah a tsakiyarsu sai hira suke mata wadda wasu abubuwan duk ba fahimta take ba amma haka take biye musu sunata dariya Ammi kuma waya take itama tana zaune a falon tayi sallama ta shigo da gudu su Irfaan sukabar wajen Ayyah suka nufi Jauhar suka mak'alk'ale ta suna dariya saboda murnar zuwanta, Ammi da Ayyah kam ido kawai suke binta dashi suna addu'ar ALLAH yasa dai lafiya dan duka yau kwana biyu kenan da zuwanta ya kawota ta yini da dare yazo ya d'auketa kuma indai zatazo tare suke zuwa da Abdallah, tsugunawa tayi da k'yar saboda k'asanta ta rungumo yaran jikinta tareda yimusu kiss a goshinsu tsananin k'aunarsu na k'ara ratsata, mik'ewa tayi ta kama hannayensu suka isa kusa da kujerar da Ammi take kai suka zauna ta kalli Ayyah tana gaisheta, amsawa Ayyah tayi ta d'ora da tambayar ta lafiya kuwa ina shi Modibbon yake ko ita kad'ai tazo?. Tana sane ta cewa Ayyahn lafiya k'alau ba komi yana sauri ne shiyasa bai shigoba ya wuce amma zaizo su tafi. Kai Ayyah ta kad'a ta mik'e tacewa su Irfaan suzo suje d'akinta su tayata zama k'ememe suka k'i saboda ganin Jauhar da sukayi wucewa tayi ta nufi bedroom d'inta tana fad'in "Zaku nemeni ne har inda nake dan gidanku wato kunga mamanku ko". sudai hankalinsu ma gaba d'aya yana kan wayar Jauhar wadda bayan sun zauna ta kamo musu game sunayi, juyawa tayi wajen Ammi da nufin gaisheta taga ta tsura mata ido tana mata kallon ban yarda dakeba baki ta d'an tura ta sunkuyar da kanta hakan yasa Ammi ta tashi tsaye ta amshi wayar Jauhar ta had'a kansu little Janaan tace su tafi d'akin Ayyah farko k'in tafiya sukai saida ta k'ara basu wayar sannan Irfaan yakama hannun Janaan suka tafi, upstairs ta nufa tana fad'in "Ke kuma ki biyoni inji abinda ya had'aki da mijin naki". tashi tayi tabi bayan Ammi da k'yar take hawa stairs d'in gaskiya Abdallah yagama da ita wlhy. "Meya had'aki da Modibbo Jauhar?". Ammi ta tambayeta bayan sun shiga bedroom d'in nata sun zauna. "Ni yaji nayi Ammi". tace cikin tura baki da shagwab'a, Ido Ammi ta zaro tace "Kinsan me kike fad'a kuwa Jauhar? yaji fa kikace me Modibbon yayi miki?". "Ammi wllhy watace ta kirashi a waya harda cemasa wai Baby tsabar its tantiriya ce wllhy Ammi kuyi masa fad'a ya daina kula matan wajen duk y'an......"Ke dallah rufe mana baki sakarya kawai, Ammi da haushi ya k'umeta ta fad'a cikin fad'a tana hararar Jauhar cigaba tayi da fad'in "Shikenan kuma dan wata yarinya can ta kirashi sai kiyi yaji saboda abin yajin bashida yawa to tashi zakiyi yanzu ki koma inda kika fito kinji na gaya miki idan na fahimceki dai a tak'aice fasa masa wayar kikayi shikuma yayi miki d'anyen kan daya saba ko wai dan ALLAH sai yaushe ne zaku girma Jauhar ku daina abinda kukeyi d'in nan wayarshi kika fasa masa ko?". Sunkuyar dakai tayi kamar zatayi kuka, ga fad'an Ammi ga kuma can d'aya wajen da Abdallah ya masa muguwar shiga wanda ya isheta da zafi dan ma dai taji ya d'an ragu ba kamar d'azu ba. Tsaki Ammi tayi tana girgiza kai tace "ALLAH ya shirya ku, zaman aure rabi da kwatanshi duk hak'uri ne Jauhar shin ke ba zakiyi koyi da y'ar uwarki ba ALLAH yaji kan rai tunda suke da Modibbo daidai da rana d'aya bata tab'a kawo mana wani complain daya shafi zaman aurensu ba kuma nasan sarai Modibbo yana mata abinda bataso d'in amma saboda tanada hak'uri ta kauda kai har ALLAH yasa suka rabu lafiya duk lokacin da zan tambayeta ya zaman nasu yake saidai kiji tace lafiya k'alau bawata matsala, bance idan kinga yana cutar dake kiyi shiru ba amma Jauhar daga wata mace ta kirashi shikenan saiki fasa masa waya ke ga mai kishi ko maza nawane wad'anda mata ke bibiyar rayuwarsu yanzu wuyar ta dai aga ALLAH ya rufawa mutum asiri shikenan kuma mata sun samu nayi kuma wad'anda yasani da wanda bai saniba haka zasuyi ta son samun shiga a wajen shi, tabbas zanyi shaidar Modibbo ta nan wajen sam mata basa gabanshi bare harya tsaya yana kulasu barshi dai da halayenshi wanda kuma Janaan tayi iya bakin k'ok'arinta ganin ta saita masa su kuma alhmdulillah ansamu cigaba dan ALLAH Jauhar ki zama mai hak'uri da kauda kai a rayuwar aurenki da ace ba'a hak'uri damu kanmu bamu zauna har mun haifeku ba da tuni kowacce mace tana gidan iyayenta hak'urin shiya zaunar da iyaye da kakannin mu a gidajen aurensu lafiya mijinki yana sonki kiyi k'ok'ari ki k'ara dasa wata sabuwar soyayyar wadda ako ina yake zai dinga jinki a ranshi anaso a koda yaushe mace ta dinga tsayawa tana karantar abinda mijinta yakeso da wanda bayaso kiyi k'ok'ari duk abinda kikaga bayaso kin gujeshi wanda kuma yakeso ki k'ara k'aimi wajen yinshi musamman irin masu halin mijinki sunada wuyar sha'ani so dole sai anyi hak'uri an kauda kai sai kiga an zauna lafiya indai bawai miji yana cutar da matar bane". shiru Ammi tayi tana sauke numfashi kafin tace "Ince dai bai tab'a lafiyar kiba ko dan nasan halinshi sarai indai yayi fushi ko meye a kusa dashi a kanshi yake sauke fushin nashi. "Ni abinda yayi min ba gara yayimin dukan ba Ammi". tace kamar zata saki kuka, Ammi bata tsaya tambayar ta abinda yayi mata d'in ba tunda sirrinsu ne tsakaninsu na miji da mata ta cigaba da yiwa Jauhar nasiha da koya dabarun zama da miji musamman masu halayya irinta Abdallah. ★★★________★★? Tunda Baba maigadi yaji irin horn d'in da aketa faman zabgawa yakawo a ranshi Abdallah ne dan tun kafin aurenshi ma da Janaan indai aka b'ato masa rai a waje haka yake zuwa ya ishi y'an gidan da uban horn harma da mak'wafta duk yabi ya rikita Baban, cikin hanzari kuwa ya tashi ya bud'e masa ya danno hancin motar da uban gudu yayi parking a compound ya fito ya nufi k'ofar babban falon gidan, bai samu kowa a falon ba hakan yasa ya haura upstairs yasan dai bata wuce can d'in suna zaunen Ammi nacewa Jauhar tazo tayi maza ta koma kafin ya dawo yasamu bata gidan sukaji an turo k'ofar an shigo dukansu d'aga kai sukayi suga mai shigowar sukaga Abdallah ran nan nashi a had'e, a tsorace Jauhar tayi saurin tashi tayi bayan Ammi da gudu ta b'uya sam ta manta ma da ciwon datake ji a k'asanta, kai tsaye bayan Ammin ya nufa zai damk'ota Ammi tasa hannu tana kareta da fad'in "Meye haka ne Modibbo a gaban nawa zaka daketa". ganin dai da gasken yake yasa Ammi ta daka masa tsawa hakan ya dakatar dashi ya tsaya yana huci da fad'in "Dan ALLAH Ammi ki k'yaleni in casa yarinyar nan tunda batada mutunci ta rainani ta fasamin wayar kuma ta fito bada iznina ba uban me tazo yi gidan nan?". "Kayi hak'uri yanzu fad'an danake mata kenan bata kyautaba yanzu ma nace mata ta tashi ta tafi kafin ka koma gidan baka sameta ba". Cikin takaici yace "Ammi tasan meye a cikin wayar nan? tasan irin muhimman abubuwan dake cikinta dan hauka daga wata banza can ta kira saita fasa min waya tasan matayen dake bibiyata kuwa idan na fita wanda har office suke bina dazan basu fuska ma har gida zasu bini kullum da kalar macen dazata kiraka amma saboda ni ba'a gabana sukeba ban tab'a bi takan suba amma duk da haka basu k'yaleni ba kamar ma k'ara yawansu ake wllhy Ammi kija mata kunne inba hakaba kuma, bai k'arasa ba sai k'wafa dayayi cikin huci yana kad'a kai sai yanzu ne yake k'ara jin haushin fasa wayar nan da Jauhar tayi masa akwai important abubuwa masu yawa da suka shafi office d'inshi wad'anda dama yake shirin yin copying d'insu ya maida laptop d'inshi k'arin bak'in cikin ma kuma babu a d'aya wayar tashi dama biyu ne amma wadda ta fasa d'in tafi tsada. "Tunda dai nabaka hak'uri ai shikenan kayi hak'uri bazata k'ara ba, ki bashi hak'uri kema". Ammi tace tana d'an juyawa ta kalli Jauhar wadda ta mak'ure a bayanta, kamar wata saliha murya a sanyaye tace "Kayi hak'uri Yah Abdallah dan ALLAH bazan k'ara ba". "Yo kima k'ara mana yarinya, wllhy abinda nayi miki d'azu ba komai bane next saikin kwanta gadon asibiti sannan ne zan huce". Kai Ammi kawai ta girgiza taga alamun idan ba fita yayi daga d'akin ba maganar ba mutuwa zatayi ba dan haka tace masa "Kaje falo ka jirata zata fito yanzun ku tafi a dinga hak'uri dai da juna dan ALLAH". harya juya zai tafi idanunshi suka sauka kan Jauhar datake masa gwalo tana dariya k'asa k'asa aikuwa da sauri ya juyo itadai Ammi gani kawai tayi ya damk'o Jauhar ya sauko da ita daga kan gadon batare datasan yaushe ya juyo ba saikuma k'arar da Jauhar d'in tayi wadda ta ankarar da ita, gaba d'aya ma mantawa yayi da Ammi tana wajen ya mana Jauhar a jikin bango ya matseta da k'irjinshi yana fad'in "Saita biyashi wayarshi". (Abdallah kuna sani ciwon kai fa aradu kaida matarka 🤦😭 nakusa k'areku dai in huta 😪). Baki kawai Ammi ta kama tana kallonsu ta rasa ma abinda zatace musu wllhy tsabar takaici wannan idan mutum ya biye musu sai sun sashi hawan jini ciwon kai kuwa kullum ne indai kana tare dasu saidai ka nemi sudrex d'inka a kusa ka dinga sha, tashi tayi ta fita daga bedroom d'in tana fad'in "Su kashe kansu itakam bazata iya ba". "Wayyo ALLAH dan ALLAH Ammi kidawo ki ceceni a hannunshi dan ALLAH kayi hak'uri Yah Modibbo". "Saikin biyani wayata fa yarinya bazaki min asara a banza ba in k'yaleki kinsan nawa na siya wayar nan kuwa?". A wahalce saboda kamun dayayi mata tace "Dan ALLAH toka matsa sai muyi magana ta nutsuwa". Bayan kuwa yayi yana fad'in "Nayi miki sauk'i kawo d'ari uku na cika sauran". yayi maganar yana mik'a mata hannunshi kamar wanda zata bashi a lokacin, a marairaice tayi fuskar tausayi tace "Haba Yah Modibbon Jauhar nida d'ari ukun waye ya ajiye wani amma zan duba account d'ina ko 100k aka samu sai inbaka haka yayi". ta ida maganar cikin lank'washe murya tana wani karkace kai ita a tausaya mata d'in nan, dariya yayi yana kad'a kai yace "Ni zakiwa wayo Jauhar? in raineki da hannuna kice zakimin wayo lallai yarinya bakida lafiya koba yanzu ba saikin biy.....Bai ankare ba kawai yaji tasa hannu biyu ta janyo kwalar rigarshi kafin yayi wani tunani yaji ta cusa bakinta cikin nashi ta kamo harshen shi tana masa wani irin tsotsa tareda sa hannunta tana yamutsa lallausar sumar kanshi wanda hakan tuni ya sukurkutar da Abdallah sai k'ara matsawa yake jikinta yana k'ara kamota sam ya manta ma dawani fad'a dayake. Kissing d'in juna suke sosai ganin suna shirin zubewa k'asa ne yasa Abdallah yaja Jauhar kan bed suka zauna a bakin gadon suna cigaba da sha'aninsu sun fara mantawa ma a ina suke. Tsahon lokaci suka d'auka a hakan kafin Jauhar ta zare bakinta da k'yar saboda yadda shi kamar ma lokacin ne yafara jin dad'in abinda yake d'in, numfashi suka shiga saukewa gaba d'ayansu a tare suka zube akan gadon rabinsu saman gadon daga cinyoyinsu kuma zuwa k'afafunsu duk a k'asa yadda yayi kwanciyar ya tallabe kanshi da hannunshi haka itama tayi suna facing d'in juna ido cikin ido suke kallon juna suna murmushi. Mrs Salees Mu'az 💝 3/20/22, 22:21 - Ummi Tandama😇: Skip to content Bakandamiya Hikaya Navigation Menu Siradin Rayuwa 1 | Babi Na Daya by Sumayyah AbdulkadirMarch 1, 202230 Comments Views: 266 2.5 (45) 21 Muharram (Hijriyyah) Da Karfe Shidda Na Yamma Agogon Garin Miami Dr. Al’ameen Bello Makarfi, ke kwance cikin sofa mai juyawa dama zuwa hagu, idanun shi a rufe suke tamkar mai barci, amma a zahiri ba barcin yake ba, shi kadai ya san hakikanin abin da ke damunsa. Alal hakika rigimar matar shi IHSAN ne ya ishe shi a yau. Shi kam tun barin sa kasar haihuwar shi bai sake waiwayar ta ba balle ya tuna ta da sunan zama na din-din-din ba. America, ta bude wani shafin rayuwa mai dimbin tarihi da nasarori a tare da shi, ta maida shi wane, ta zamo silar dukkanin nasarorinsa a rayuwa ta warkar da bakin cikin kuruciyar da ya zo Miami da shi ta kuma shafe rayuwar shi ta baya, ta wanke tsanar kan shi da yake a da can, shin a kan me zai bar ta? Sai dai wani bangaren na zuciyarshi sam, ya ki amince mai da hakan. Idan ya yi hakan ya tabbata hakkin yarinyar kadai na iya wargaza masa farin cikin da yake takamar ya samu a Miami; Shekaru goma kenan cif da rabuwarta da iyayenta, shi kuma goma sha biyar cif in har lissafin da yake daidai ne bai rage ba, sun turo ta karatu sun sarke da soyayyar da har ta kai su ga aure ba tare da sanin iyayen ko dayan su ba. Ta jure rashin soyayyar nan ta iyaye a tare da ita tsayin shekarun nan wadda ta fi komai dadi da muhimmanci ga dan adam, idan shi namiji ya iya ya jure, ita Ihsan mace ce, ya kuma tabbatar ta yi hakuri kan hakuri ba don komai ba sai don masifaffen son da take masa. To shi don me ba zai nemo mata wannan soyayyar ba, ko don albarkacin wadda take masa? Shi kansa ya san a yanzun zuciyarsa ta yi sanyi da takaicin kuruciyarsa ta gida. Tunanin Daddy din shi ya addabe shi, ko an harbe shi? Ko har yanzu yana kulle a kurkuku (Prison)? Zuciyarsa ke bijiro masa da cewa, yanzu ne ya dace ya je ya tallafi mahaifiyarsa da ‘yan uwansa duk da ya san a kowanne hali mahaifiyarsu za ta iya kula da su, kasancewarta mace mai dumbin arziki. Yana ganin yanzu ne ya dace Hajiyarsu ta huta da guminsa, shi a yanzu ya san Allah ya yi masa ludufi da nasibi ta kowanne fanni a rayuwa; Bar ta kasancewarsa mamallakin shahararren asibitin kwakwalwa wato “MERITIME? da ke cikin birnin Miami, hakan nan shi ne babban likita a sashen kwakwalwa (consultant) a babban asibitin garin Miami (Jackson Memorial) da ke Florida. Har ila yau, Dr. M.A.B (Senior lecturer) ne da ke daukar daliban “Medical Psychology? a jami’ar da ya yi karatu (University of Miami), kuma masani a kan duk wata larura da ta shafi kwakwalwa. Don haka kasar America ke ji da shi, suna lailayar shi da ruwan arziki kasar su na amfana da dumbin baiwa da fasaharshi. Baya ko tuna kasar shi ta haihuwa (Nigeria) balle iyayen shi da ya tafi da niyyar barin su har bada, don yana ganin ba abin da zai masu, ‘ya’ya irinsa ba abin bukata ba ne, don haka bashi da amfani a gare su. Ga ingantacciyar kauna da kulawa daga matarshi abin kaunar shi Ihsan, yalwataccen gida a Miami, motocin hawan da ko a U.S. sai wane da wane. Kenan duk wani buri da dan adam zai iya ciwa rayuwar duniya, ya samu. To amma zai so ya mutu ba tare da sanin halin da iyayen shi ke ciki ba? Ba tare da ya kara sa wani jinin shi a idanun shi ba? Bai sake sanin halin da kanwarsa SARATU-INTISAR ke ciki ba, shakikiyarsa kuma kanwarsa da ya NAKASTA? Mafarke-mafarken da yake na Daddy a dan tsukin kadai na tayar masa da hankali, ya kasa nutsuwa kwata-kwata wanda hakan ya janyo masa yi wa wani mara lafiya (Patient) rubutun magungunan da ba su dace da lalurarsa ba, ba don Ihsan ta lura ba da an yi mamakin shi M.A.B ne da wannan danyen aikin. To haka ko rubutu yake yana daburcewa ya rasa me zai rubuta? Gaba daya hankalinsa ya yi gida ya kuma tabbatar kwanciyar hankalinsa kadai ya bude ido ya gan shi a gida. Baya jin zai sake samun nutsuwa bai baro Turai haka nan ba. Anya ma kuwa babu hakkin Dady din shi a kan shi? Mutumin da ya wanzar da ran shi da lafiyar shi cikin wahala, domin nema masu farin ciki, anya ya cancanci hukuncin da ya yanke masa? Bar ta so da gatan da yake nuna masa throughout sauran kannensa to haka Hajiyarsa, ya tuno yadda a kullum take gaya masa ba ta son ya yi nisa da ita, ya fiye mata duk sauran ‘ya’ya taran da ta haifa a duniya! Sai ya ji kansa ya yi wani irin gingiringim, idanuwansa sun yi mai nauyi, baya ko iya bude su. Ya lumshe ido cikin wani sabon yanayi a tare da shi. Allah kadai ya san halin da zuciyarsa ke ciki. Ihsan ta karaso rike da tambulan mai garai-garai cike da danyar madarar shanu mai sanyi (fresh) wadda shan ta ya zamewa likita Ameenu lazim a duk yammaci, a gida ne ko ofis. Sanye take cikin fararen kayan wanka (bikini), gashin kanta ke digar da ruwa tabbacin daga wanka ta fito. Ganin yanayin da Al’ameen ke ciki sai ta ja dan karamin tebur da ke gabansa ta ajiye kofin. Sannu a hankali ta kwanta jikin Al’amin sannan ta marairaice kamar za ta yi kuka ta ce, “Ameenu isn’t this enough? America is not our motherland?. Don Allah mu koma gida…? Sai kuka. Shiru ya yi cikin tunani, shi kam bai san ma abin da zai ce mata ba ma. Zuwa gida? Ai shi ne mai cewa a je ba ita ba yanzun. Bai ce komai ba, baya ga dora hannu cikin gashin kanta, don in ta soma yi mai wannan rigimar ta “a dawo gida…? da kyar yake iya samun kanta. Hakika tana ba shi tausayi, dole su baro MIAMI a wannan watan. ***** 1 GA WATAN SAFAR (HIJRIYYAH) Jirgin American Airways ya sauke su a birnin Ikko da karfe tara daidai na safe. Sai da kowa ya fita amma Al’ameen da Ihsan ba su ko motsa daga “seat? dinsu ba. Gaba dayansu jikkunan su sun yi sanyi, domin a take zazzafan zazzabi ya rufe Ihsan, ba su san da fuskokin da za su aro su dubi iyayensu ba. Sai da wata ma’aikaciyar jirgin ta yi masu magana cewa za a rufe jirgin, sannan ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa namiji ne, ya rungume matarsa da hannunshi na dama a yayin da na hagun ke rike da ‘yar kyakkyawar jakarta ‘Japanese? a haka suka soma tako matattakalar jirgin cikin nutsuwa har suka taka kasarmu mai dimbin albarka. Dole idan ka kalle su sai ka maimaita su kuma yi bala’in ba ka sha’awa. Kwarjini da cikar zati irin na Al’ameen da ke sanye cikin edpensive Italian suit, kalar baki da ratsin fari sol sun taimaka ainun wurin kara fiddo ilhama da cikar zatin shi, ya saya kwayar idon shi cikin bakin dark-spaces da ganinsa dai ka ga bakon Ba’amurke. To haka itama Ihsan din tamkar aljana take don kyau, baby face gareta mai dauke da kayatattun idanu tare da kyakkyawan dogon karan hanci da gassun gira mai tsari. Yarinya ce ‘yar gajeriya mai jiki kuvul-kuvul, kamar na tarwada saboda tsabar hutu tamkar ba bakar fata ba, domin tun fil’azal ita brown ce, sai kuma zaman kasar sanyi da jin dadin samun gwarzon miji irin Al’ameen Bello, da suka kara wanke ta tas. Dr. M.A.B zai yi wuya ka fassara daga kabilar da ya fito a lokaci daya, kamannin shi na da ruda tunani da sanya shakku, bi-ma’ana (by appearance) ba za ka kira shi Bahaushe ba sam-sam duk da cewa ya fi son yin magana da harshen Hausa a kodayaushe fiye da duk wani harshe da ake magana da shi a duniya. Hakan nan ba za ka ce shi din Balarabe ba ne, domin baya da tarin nannadaddiyar suma irin tasu kullum kansa cikin saisaye yake, amma ya bar siririn saje a gefen fuskarshi abin nan da ake kira Man’s pride. Mutum ne dogo siriri, don tsayi har ya rankwafa, wanda mutane da dama ke (kuskuren tsammanin) cewa yanayi ne don kwalisa, amma Al’ameen Bello komai nashi natural ne babu artificial. Idanun shi abin so ne, ba ga mata kadai ba har maza ‘yan uwansa will not keep wishing they were like him (Ba za su bar fatan ina ma a ce sune shi ba). Idanuwa ne manya kuma lumsassu, tamkar kuma an diga masu zaiba har wani maiko-maiko suke. Bai kama da Turawan ma sam-sam shi dai kawai Al’Ameen ne, haka Allah ya yi sa. Da wuya ka karanci zuciyar Al’ameen Bello, ko matar shi ba ta iya gane wasu al’amuran shi. Mutum ne murdadde mai yin komai straight forward (kansa tsaye) ba tare da tunanin illar da abin zai haifar ba, mai tsayawa a kan mgana daya, ba kankanin abu ke sa shi canza ra’ayi ba. Kuma mutum mai tausayi da masifaffar kyauta. Ya sha sauka daga mota in ya ga wani a gefen titi yana jiran bus a Miami, ya kira shi ya danka mai mukullin ya ce, “Tafi.? Shi kuma ya sayi wata. Tun Ihsan na masifa har ta gaji ta kyale shi don ta lura abin a cikin jinin shi ne. Ita kanta ba karamar barna yake wa kayan ta ba wurin baiwa masu karamin karfi dake tareda su. Sau tari, tana kwance a mike ya kan dafa mata abinci, ya dauko ya kawo mata yana sanya mata a baki, yana mai lallashinta ta ci sosai. Cewa yake wannan hakkinshi ne ya ciyar da matarshi, tunda a Alkur’ani mai tsarki babu inda aka ce mace ta ciyar da mijinta hakan nan bai son mata suke wahala, domin su ne uwayen al’umma duk wata wahala a wuyan su take. Idan suna nakuda ji yake kamar ya taya su. In yana fada mata irin wannan kallon shi kawai take ta yi dariyarta mai isar ta ta ce wata rana zai daina ne, don yana ganin ba su da kowa ne a nan inda suke sai junansu. Shi wani irin mutum ne da bai bambancewa cikin mu’amalarshi da kowa, abin nufi, mai kudi da mara kudi, mace ko namiji. Dr. Al’ameen Bello kowa nasa ne. Don haka ya sha fama da mata iri-iri a zamanin karatunsa, daga Turawan zuwa ‘yan sauran kasashen duniya da karatu ya hada su. Ihsan A.A kadai Allah ya bai wa sa’ar koda yake zan iya cewa, Al’ameen ya auri Ihsan ne domin ceton ta daga masifar son shi da ta sanya kanta, amma ba wai don wani mashahurin so na Allah ko na Annabi ba. Ihsan Abubakar Argungu, ‘ya daya tal ga mataimakin Governor na (Central Bank of Nigeria), Dr. Abubakar Argungu. Iyayenta mazaunan Abuja ne na din-din-din duk da cewa dukkansu aiki ne ya kawo su a garin, daman an ce wai birnin Tarayyah ne. Kasancewar Ihsan ‘ya daya jal ga iyayenta ya sanya duk wani buri na Dr. Argungu da mahaifiyarta Ann Hathaway wadda ta kasance Kirista ‘yar uslin Birnin Gwari, akan Ihsan yake. Mahaifiyarta Ann ce mamallakiyar bankunan Savannah da ECOBANK da ake damawa dasu a halin yanzu a kowacce jiha ta Najeriya, don haka gaba da baya Ihsan ‘yar gata ce ta karshe gun iyayenta baya ga watsi da ta yi da su kan son Al’Ameen Bello. Iyayenta sun turo ta karatun medicine ne a University of Miami, inda ta hadu da Al’ameen, wanda a lokacin ke ba da lacca cikin makarantar bangaren masu karantar lafiyar kwakwalwar dan-adam. Tun daga wannan lokacin Ihsan ba ta kara nutsuwa ba sai da ta zamo friend din Aminu. A hankali a hankali ta yi amfani da hilarta wajen jan ra’ayinsa gare ta tana bayyana masa yadda take son shi wani zubin har tana kuka take rokon shi ya aure ta gudun kar ta sanya kanta cikin gurbatacciyar rayuwa. Ga Al’ameen mutum mai tsananin tausayin mace, tun ba in tana fidda mai hawaye ba, sai dai sam a lokacin bai da ra’ayin aure, tunda kuwa zai sada shi ne da gidan da ya baro baya ko son tunawa. Yaya ma za ai ya yi aure, ba tare da sani da yardar mahaifansa ba da baya da kamar su? Don haka ya rungumi Ihsan suka tsunduma watsewarsu ba tare da tunanin illar da hakan zai haifar ba. Wannan ya fi komai dadi ga Ihsan domin dama ita ba auren ne a gabanta ba, illa tana tsoron idan ta bijiro mai da irin soyayyar da ta zaba musun ba zai amince ba, kasancewarsa mutum mai tsananin kamewa daga barin jin dadin rayuwar Turai a ko’ina kuma a cikin kowanne hali ya sami kansa, duk zalamar yarinya kuwa haka za ta ga Aminu Bello ta kyale domin abin da ya kai shi kadai yasa a gaba. To itama Ihsan din kowa da ke tare da su ya yi mamakin yadda ta samu Ameenun haka a hannu, ba mamaki, domin an ce kowacce ‘ya mace da kissarta ake haifarta, hakan nan Ihsan tun tana mitsitsiyarta take koyan kissa gun uwarta har girmanta iri-iri ba wadda ba ta iya ba, don haka duk saurayin da ta kimsawa kanta sha’awarsa ta same shi ta gama kuma da kyar ne yake kubuta daga tarkonta. To haka shi ma Al’ameen, ta tabbatar sha’awarshi ya fi son shi yawa a tare da ita kamin su yi aure, sai dai a dan zaman da ta yi da shi ta koyi kaunarsa saboda wasu kualities nasa da ke burge ta da ba duk maza Allah ya mallakawa ba. Don haka ne ma duk wulakancin da yake mata in ya bushi iska ko ya yi sabuwar girlfriend take hakuri tana shanyewa, don ta tabbatarwa kanta tana samu nutsuwa 100% and beyond a tare da Al’ameen fiye da duk wasu maza da ta taba mu’amala da su gida da wajen. Hakan nan tana ganin Al’ameen ko a cikin maza daban ne wurin nuna kauna. Samun maza irin su a matsayin MIJI sai mai sa’ar gaske. Ba ta taba haduwa da namijin da ke gamsar da ita ba har ya kure ta kamar Al’ameen ba. Ba ta taba haduwa da namijin da ya san darajar diya mace kamar Al’ameen ba. Don haka ta kara manne masa ta like masa tare da kara zage damtse wurin nuna masa ingantacciyar kauna da kulawar da ta sa shi dole ya so ta, ta kuma shiga yakar macen duk da ta gani tare da shi ba tare da shi din ya sani ba ma. Ta kuma alkawartawa ranta, ruwa ko iska baya raba su. Daga baya ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa Musulmi ne, da kuma irin horon da Daddy dinsu ya yi masu, wanda da a ce yana tare da shi, hakan ba zai taba faruwa da shi ba. Ya roki Allah ya yafe masa ya kuma nemi Ihsan da ta yi Istibra’i su yi aure, ita kuma ganin lokacin Aminun na sonta kamar me ta ce ba ta san wannan ba, jin hakan shi kuma ya fita harkarta kwata-kwata, ko a tunaninta kuma ko a mafarkinta a lokacin ba ta kawo Al’ameen zai iya rayuwa ba tare da ita ba. Ta kuma tabbatar gab yake da ya shafe ta kwata-kwata a babin rayuwarsa in har bata amince su yi auren ba, ta amince ta saduda cewa shi din mai ra’ayin kansa ne, don haka ba ta isa ta sashi ko ta hana shi ba. Suka yi auren su mai tsafta ba tare da sanin iyayen ko dayansu ba. Daga baya ne ita Ihsan ta aikawa Ann cewa ta yi aure da wani likita Al’ameen. A lokacin hanyoyin sadarwa basu yi kamarin da suka yi yanzu ba. Ann din ta aiko mata da zagin cin mutunci ta waya da e-mail kan don me ta auri Musulmi ba ta auri dan Addininta ba, bayan ta yi mata alkawarin muddin ta tashi aure Kirista za ta aura, don wai sun fi rikon aure. Shi kuma mahaifinta ya ce kwata-kwata ba ta kyauta musu ba ta dauke su ba a bakin komai ba tunda kuwa har za ta iya ta yi aure ba tare da sani da amincewarsu ba, don haka ta je Al’ameen din ya maye mata gurbinsu. To Ihsan ranta ya baci sosai da iyayenta a ganinta gata ta yi wa rayuwarta ai, domin shi kansa auren ai mutunci ne ko bature yana daraja aure, da dai ta ci gaba da gurbatacciyar rayuwar turai da babu komai cikinta sai lalacewa, kuma ba su yi mata uzuri da soyayyar da ta rinjaye ta ba sun manta an ce luv is overall, wato soyayya tana gaba da komai. Wannan ya faru shekaru uku da suka gabata, tun daga lokacin Ihsan ba ta kara waiwayarsu ba, duk da cewa daga baya su din sun neme ta amma ta share su, don tana ganin son Ameenu ya fiye mata komai, ko in ta sauraresun me za su yi mata? Za su hana ta aurensa ne? To gara ita, shi din ko sanar da su bai yi ba, tunda kuwa a lokacin ya riga ya shafe gida kwata-kwata daga kundin tarihinsa illa sabuwar rayuwar da ya gina a gaba. Sai suka hade abinsu suka dunkule junansu wuri guda suka bude sabon shafin rayuwa cike da soyayya mai ban sha’awa. Daga Al’ameen har Ihsan kowa na son Da, musamman ita Ihsan da take ganin haihuwa da Ameenu ne kadai zai dorar da dangantakarsu. Tana ganin in ta haihu da shi zai mallaka mata dukkan so da kaunarsa da har yanzu kwakwalwarta take gaya mata bata mallaki komai a ciki ba duk da cewa da wuya a karance shi, amma hakika ta san bata da dukkan so da kauna a zuciyarsa. Hana rantsuwa za ta iya cewa ‘yana son ta? kadai. Wannan ita ce matsala ta farko da suka fara cin karo da ita a rayuwar auren su, kuma in har suna da matsala a auran to wannan ce. Lokacin da Al’ameen ya soma complain (korafi) wai abortion (zubar da ciki) da ta-yi ta-yi ya shafi lafiyar mahaifarta, cikin kwafa kuma sai ya ce ko ciki har nawa ta barar oho. Da haka suka fara fada, ta ce ya san tana bare-baren cikin ai ya neme ta da watsewa, don ita tun farko ai aure ta ce su yi. Yadda ta lurra Al’ameen mutum ne mai masifar son yara, ko tafiya suke bisa hanya ya ga yaro sai ya tsaya ya dauke shi ya yi kissing ya ba shi choculate da baya rabo da saye cikin kantuna. Ranar da Ihsan ta yi nadamar aurenta da M.A.B shi ne ranar da ya ce da ita wai shi dama tun ranar da ya soma saninta ya yi mamakin maza nawa ta sani? Shi ba irin matar da ya so aure ba kenan a rayuwarsa, amma ya zai yi da kaddara? A wannan ranar ne Ihsan ta yi kuka wanda rabonta da shi tun na sallamar ta da iyayenta shekaru goma a baya. Kewar iyayenta ya zo mata. Ta tuna masifaffen gatan da take da shi a wurin iyayenta da yadda suke sonta, suke kula da ita, suke gudun duk wani bacin ranta. Yau ga namiji kwaya daya na yi mata yawo da hankali. Sai take tambayar kanta ko me Al’ameen ke takama da shi da yake gara ta haka? Ba ya takama da komai illa jarababben son da take masa. Ta tabbatar duk wani cin mutunci ma in da a gaban iyayenta take zai zo da sauki fiye da nan din da yake ganin ba ta da kowa sai shi. Sai dai ta kudurce a ranta koma me zai mata ko duka ne ba za ta taba rabuwa da shi ba. Daga baya Al’ameen da Ihsan duk sun amince ba hayaniyarsu ko tashin hankulansu ne za ya ba su haihuwa ba, illa ma ya rugurguza masu kyakkyawar rayuwar da suke ciki, ta so da fahimtar juna, sai suka dangana. Shi Al’ameen yana addu’a ita ko Ihsan Addinin nata ma gashi nan ne, sallah sai in ya takura mata za ta yi in baya nan ko a hadu a gaba. Tun daga wannan rigimar da suka yi Ihsan ta soma yi wa Ameenu korafi da koken su koma gida ta ga iyayenta ta kuma roki gafararsu, tunda shi ba ya son nasa. Shekaru bakwai ta yi tana karatu, shekarun su uku da aure kuma a cikin shekarun tana aiki a asibitin (Baptis Health) da ke South Florida, cikin birnin Miami matsayin karamar likitar zuciya (cardiologist) kuma kwararriya a fannin heart-transplantation Da fari hankalin Al’ameen ya tashi da wanann sabon abu ko ko ya ce rigima da Ihsan ta kinkimo mishi har ya dinga ganin bekenta, to amma shi ma da ya yi tunani mai kyau sai ya ji shi din ma ba abin da yake so irin dawowar, ya kuma bude ido ya gan shi a gaban Daddy din shi ya ga SARATU-INTISSAR din da ta sa shi barin gida, ko a wanne hali take yanzun? Yaya take gudanar da rayuwarta a hakan? Uwa-uba tausayin Ihsan, yau shekaru goma kenan ba ta kara sa iyayenta a idanunta ba, shi kuma shekaru goma sha biyar kenan sai ko yau da jirgin da suka shigo ya sauke su a birnin Ikko. Ihsan Abubakar matashiya ce da jin dadi ke boye mata shekaru a kullum, amma a zahiri shekarunta ashirin da tara cif, don dai gajera ce kawai ba a fiya kimanta shekarunta ba, a yayin da Dr. Al’ameen Bello ke da talatin da biyar da wasu ‘yan watanni. Daga Ihsan har Ameenu kowa na ji da kyau, sai dai nesa ba kusa ba Al’ameen ya darawa Ihsan tsari. Kusan kyawun Ihsan ya fi yawa a fuska, amma ba ta da wannan fasalin na ‘ya mace sai ko ‘yar lafiyayyar fuskarta da Ameenu ke matukar so. Sanye take cikin English wears ruwan hanta riga da wando masu kauri, amma da yake ta baro Miami a yau ta dora bakar after dress kirar Oman a kai, bata da sumar kai mai yawa don haka sau da dama gashin kanta cikin tarin attachement yake. To yau ma hakan, sai dai ta yane kanta da gyalen abayar yayin da kyawawan tafin kafarta ke sanye cikin wani rantsatstsen ‘high hill shoe? bakin takalmi (mai tsayin dunduniya) mahadin jakarta kirar Japan. In ka dauke zobban diamond kwaya uku da ta yi wa kyawawan yatsunta ado babu komai a hannunta don ‘yar jakarta na hannun Al’ameen ne har suka shiga jirgin da zai kai su Abuja. A Abuja Al’ameen ya riga Ihsan sauka don ta tsaya make-up dinta da baya karewa. Hannuwan shi duka biyu zube cikin aljihu ya doshi reception wato wajen karbar baki duk da dama shi bai yi tsammanin zuwan wani nashi ba. Nan ya hango wata mata sanye da malfa mai tsananin kama da matarsa, ko ba a gaya mai ba ya tabbatar Ann ce mahaifiyar Ihsan. Kallo daya ya yi mata ya dauke kai a ransa ya yi mamakin yadda mahaifiyar Ihsan ta kasance Kirista amma ba ta taba gaya mai ba, domin ya hango cross a sarkar da ke wuyanta. Har ya yi gaba sai kuma ya yi tunanin bai kyauta ba, ya juyo ya komo inda suke daidai lokacin da Ann ta rungume diyarta suna ta kukan dadi tamkar ba wani sabani da ya faru tsakanin su, sai ya yi fatan hakan ta kasance a gare shi shima. Ihsan ta saki mahaifiyarta ta yi mata nuni da Al’ameen da ya harde hannuwa bisa kirji yana kallon su kawai ta ce shi ne mijinta Al’ameen. Duk kin da Ann ke wa auren Ihsan da Al’ameen, amma kwarjini da kamala irin na Al’ameen Bello, ba ta san yaushe ne ta sami kanta a mai mika masa hannu ba, ya mika mata nasa a ransa ko cewa yake wai kakar ‘ya’yana ne wannan Inyamurar kuma suruka ta ke mika min hannu mu gaisa kamar a turai? DA YA SANI? Wai me yasa har kullum yake gamuwa da DA NA SANI MARA AMFANI NE a rayuwarsa? To haka suka gaggaisa da sauran ‘yan uwanta ma gaisuwar hand shake fuskar shi ba annuri sam-sam sun nemi da ya bi su gidan su a Garki, domin ya gana da mahaifinta inda shi kuma ya nuna uzrinsa yana cike da dokin ganin nasa iyayen shima. Sai dai in ya huta ita ma Ihsan din ta huta zai zo su gaisa da shi din, ya kuma dauki Ihsan din zuwa gidan iyayen shi. Next >> How much do you like this story? Share the story: Click to share on Facebook (Opens in new window)Click to share on Twitter (Opens in new window)Click to share on LinkedIn (Opens in new window)Click to share on Pinterest (Opens in new window)Click to share on Telegram (Opens in new window)Click to share on WhatsApp (Opens in new window) 30 thoughts on “Siradin Rayuwa 1 | Babi Na Daya? Avatar Sadiya Kabir Alhassan March 1, 2022 at 10:27 pm REPLY Allah ya kara basira ya kara lafiyar rubutu da fadakarwar da akeyiwa Al,umma. Wannan littafin ya kayatar dani kwarai da gaske Dan bangajiya da karantashi akwai darasi mai tarin yawa a cikin sa. Avatar Latifatbello March 2, 2022 at 7:16 am REPLY Allah ya taimaka @takori Avatar Amina Mamser March 2, 2022 at 8:33 am REPLY mashaAllah daughter Ubangiji Allah ya kara basira, da fasaha,hakika Siradin rayuwa littafi ne dake cike da darussa da ke ilmantarwa,Al’amin na Ihsan gaa kuma zabin iyayen shi Intisar,bari mu bi muji wake nasara. Avatar Fatima March 1, 2022 at 11:09 pm REPLY Allah ya kara basira Avatar Fatima March 1, 2022 at 11:12 pm REPLY Allah ya kara basira Avatar Lubabatu Bashir March 1, 2022 at 11:52 pm REPLY Allah ya kara basira da zaqin hannu Avatar Alawiyya Nasir March 2, 2022 at 6:47 am REPLY Masha Allah Anty summy my favourite writer Allah ya Kara basira Avatar Rukayyah mukhtar sada March 2, 2022 at 9:23 pm REPLY Masha Allah aunty sumy Allah ya Kara basira da Zaki hannu I like you Avatar Naimah March 2, 2022 at 7:00 am REPLY Sannu da kokari, Allah ya kara basira Avatar Nasare March 2, 2022 at 7:08 am REPLY Masha Allah, Allah ya sanya alheri ya kara basira? Amin ya rabbi Avatar Ramatu Mustapha Abubakar March 2, 2022 at 7:29 am REPLY Allah ya qara basira da zaqin hannun rubuta,haqiqa dukkan rubuce-rubucen ki babu na yarwa,suna fadakarwa, ilimantarwa tare da nishadantarwa. Muna godiya qwarai, Allah ya qara lafiya. Avatar Rahma Nahaja March 2, 2022 at 7:27 am REPLY Allah ya kara baseera Takori muna godiya Avatar Shafa'atu Isah March 2, 2022 at 7:42 am REPLY Allah ya Kara basira Takori Avatar Amina Disina March 2, 2022 at 7:52 am REPLY Masha Allah Avatar Samirah March 2, 2022 at 7:57 am REPLY Masha Allah,Allah ya kara basira Avatar Halima isah usman March 2, 2022 at 8:00 am REPLY Kai masha Allah, wannan book din ya kayatar yakuma fadakar ,zamu dauki darasi acikinshi kalakala. Allah y kara basira our takori Avatar Zainab Abdullahi March 2, 2022 at 8:01 am REPLY Maasha Allah Allah ya qara basira Avatar Oum Al'ameen March 2, 2022 at 8:43 am REPLY Masha Allah Karatun littafin ki Takori ba regrets, akwai fadakarwa Avatar Sa'adatu Sani zakka March 2, 2022 at 9:06 am REPLY Allah ya Kara basira ameen Avatar Maryam Gambo March 2, 2022 at 9:07 am REPLY My very own Siradin rayuwa🙌 my favorite the best of all times Allah ya qara basira sis. Avatar Khadijah sani Baba March 2, 2022 at 10:11 am REPLY Masha Allah among my best novels siradin rayuwa Avatar Binta Abba March 2, 2022 at 12:41 pm REPLY An educative piece of work. Avatar Zainab Abdullahi barde March 2, 2022 at 1:29 pm REPLY Masha Allah summy Allah yakara basira Avatar Umaima March 2, 2022 at 3:06 pm REPLY Allah ya biyaki takorinmu. Avatar Bilkisu Aminu usman March 2, 2022 at 5:02 pm REPLY MashaAllah,lallai akwai chakwakiya bakadan ba,muna biyeda ke Allah ykara basira da daukaka Avatar Zainab ibrahim Makwashi March 2, 2022 at 8:09 pm REPLY Masha Allah Aunty Allah ya kara basira da zakin hannu Avatar SUMAYYAH ABDULKADIR March 3, 2022 at 1:11 pm REPLY Nagode muku bakidaya, jazakumullah bikhair Avatar Hadiza Adamu March 3, 2022 at 10:18 pm REPLY Masha Allah, Allah ya Kara basira Avatar Fatima m March 7, 2022 at 5:25 pm REPLY Ma sha Allah. Allah ya qara basira Avatar Hafsatmusajibrin March 20, 2022 at 9:21 am REPLY Kai Allah ya qara basira I so much like ur write ups Leave a Comment Your email address will not be published. Required fields are marked * Name * Email * Website Comment * Save my name, email, and website in this browser for the next time I comment. Subscribe to weekly updates PREVIOUS Rayuwata | Babi Na Daya NEXT Ta Ki Aure | Babi Na Uku © 2022 Bakandamiya CLICK HERE TO INSTALL THE APP × 3/21/22, 20:59 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*💝 Page 47. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.* ©Oum Hanan Sun dad'e a haka kowanne yana aikawa da d'an uwanshi sak'on dake cikin zuciyarshi ta cikin idanuwansu a tare suka k'ara kauda kansu suka kalli P.O.P d'in saman d'akin suna sauke numfashi a tare kowanne fuskarshi d'auke da murmushi, kiran wayarshi da akayi ne yasa ya tashi zaune ya karkace yana zaro wayar a aljihun wandonshi itama tashi tayi tana kallonshi yadda yake gyad'a kai yanata rangaji daga zaunen saboda dad'in wak'ar dayake ji wadda kuma itace akan ring tone d'in nashi wak'ar Nura M Inuwa wadda yake cewa (Wanda baiso ku tambayeshi dame yake more rayuwa abadan bana daina yin so gaskiya ko dame yazo mini). Yana son wak'ar sosai har wayar ta katse baiyi picking ba aka k'ara kira sai lokacin ya d'aga tareda rungumo Jauhar ta gefenshi ya fara magana cikin harshen turanci, yana wayar yana sakarwa Jauhar kisses a gashinta da goshinta zuwa fuskarta harya gama ya kashe wayar tashi yayi ya nufi wata speaker dake d'akin yayi connecting da wayarshi yasa wak'a speaker tafara dukan kid'a mai dad'i Jauhar dai na zaune bakin gado tana kallon ikon ALLAH taga me Yah Abdallah zaiyi kawai taga yafara taka rawa yana fad'in "kwana biyu bai d'an taka ba". wato duniyar dai tayi masa dad'i kenan😂 rawar shi yake bilhaqqi da gaskiya cikin kwanciyar hankali sai dariya Jauhar take masa. Hannu ya mik'o mata yana d'age mata gira alamun ta taho itama tayi kafad'a ta nok'e masa alamun a'a tana dariya har inda take ya k'araso yana rawarshi ya janyo hannunta ta taso ya fara malk'waya hannayenta yana juyi da ita irin na India tun tana nok'ewa har itama wak'ar tafara tsumata dan haka suka cigaba da takawa tare yana rawar amma bakinshi bai zauna k'alau ba sai kissing d'inta yake. Ammi da takaicinsu yasa ta komawa falo ta zauna saiji tayi kid'a na tashi daga bedroom d'inta ba k'akk'autawa da sauri ta tashi ta haura upstairs d'in dan duk zatonta ko Abdallah ne yake dukan Jauhar shine ya kunna kid'a saboda kar ajishi sarai kuma tasan zai iya amma abin mamaki da ban haushi tana bud'e k'ofar ta shiga ta samesu sunata rawa hankalinsu kwance tamkar su kad'ai ne a gidan tsaye tayi tasaki baki tana kallonsu dan duk basu kula ma da zuwanta ba amma dai yaran nan sun iya tsiya wllhy yanzu fa data fita ta barsu suna fad'a amma tadawo ta gansu sunsa kid'a sunata tik'ar rawa? lallai idan mutum ya biye musu zaisha kunya saisu sawa mutum hawan jini, Jauhar ce tafara ankarewa da Ammi dake tsaye bakin k'ofa tana kallonsu hakan yasa ta daina rawar shikam Abdallah da hankalinshi baikai kaiba sai juyi yake yana k'ara juya Jauhar ganin ta tsaya a hankali murya k'asa k'asa tace "Yah Abdallah Ammi ce ta shigo fa tana bakin k'ofa". da sauri ya tsaya tareda kai kallonshi bakin k'ofar yaga Ammi kuwa a tsaye kai ya d'an sunkuyar yana shafa k'eya yana d'an murmushi sukayi tsaye a wajen, k'arasa shigowa Ammi tayi tana fad'in "To kuzo ku wuce kutafi gidanku bada niba wannan kayan takaicin". ta k'are maganar tana nuna musu hanyar fita daga bedroom d'in da hannunta, marairaicewa Jauhar tayi tace "Ammi shinefa yace saina biyashi wayarshi amma idan nayi rawa zai yafemin". Ido Abdallah ya zaro yace "Wllhy Ammi k'arya yarinyar nan take ita t......dakatar dashi Ammi tayi tace "Koma dai meye ku kuka sani kuzo kubar gidan nan wllhy bazaku samin hawan jini ba ina zaman zamana wllhy maganar da kuke sani kosu Irfaan albarka kuma na k'ara ganin k'afafunku nan kusa a gidan nan saina b'ata muku rai kuzo ku wuce kuje can gidanku ku k'arata". A tare suka koma wajen gadon ya d'auki glasses d'inshi da P Cap da key d'in motarshi ya fita daga bedroom d'in yana cewa Ammi sai anjima bata kulashi ba sai kallo data bishi dashi itama Jauhar d'ankwalinta ta d'aura ta yafa mayafinta ta d'auki jakarta kanta a k'asa tazo tayiwa Ammin sallama ta fita sai yanzu take k'ara jin kunyar rawar da Ammi ta samesu sunayi duk Yah Abdallah ne ya jawo mata wllhy. Sai bayan fitarsu nema abin yabawa Ammi dariya girgiza kai tayi ta shiga bedroom d'in tana murmushi cikin ranta tana k'ara binsu da managarciyar addu'a ta k'ara samun zaman lafiya da daidaito a tsakaninsu dakuma zuri'a dhayyibah mai albarka. D'akin Ayyah sukaje Abdallah ya gaisheta yaga yaranshi daga nan ma tare suka fita dasu Janaan d'in yace Ayyah ta fad'awa Ammi zasuje sudawo yaran kuwa sai murna suke. Suna tafe suna hirarsu irin ta masoya cikin nishad'i da annashuwa har tafawa suke idan abin yayi musu dad'i, ba zato kuma taji ya bige mata baki yana fad'in shine tayi masa k'arya a wajen Ammi ko tace shiya sata rawa. Baki ta tura masa cikin shagwab'a tace "ALLAH Sweetheart ka cika cin zali wllhy". Hannun da baya tuk'i dashi yasa ya matse mata hannu cikeda mugunta harda cije lips d'inshi ta saki k'aramar k'ara kuwa tana yarfe hannu tare dasa masa kukan shagwab'a saidaya k'ara matse hannun sosai sannan ya sakeshi yasa hannu ya rungumo kafad'unta yana d'an jijjigata gamida cewa "I'm sorry RAYUWA TAH na yarda yau kibani punishment a gado yadda nake baki kinji y'ar albarka". ya ida maganar yana sumbatar goshinta, duk abinda suke hankalin yaran ma gaba d'aya baya kansu yana can wajen game da suke bugawa. Wani irin kallo tayi masa na sama da k'asa kafin tace "Lallai ma Sweetheart to nak'i wayon, kaima dakake min wannan punishing d'in ALLAH na ganinka kuma saiya sakamin". ta k'are maganar cikin tura baki kamar zatayi kuka tana jefa masa hararar wasa. Dariya yasa sosai har yana d'an dukan sitarin motar da hannunshi yace "ALLAH kinga gurin kwanana yarinyar amma bari mu koma gida zan saita miki zamanki sosai". baki kawai ta gatsina masa tareda kai hannu ta shafi sajen fuskarshi wanda yake matuk'ar burgeta shikuma yaja karan hancinta fuskarshi d'auke da murmushi kafin ya maida hankalinshi kan tuk'in dayake. Yawo suka sha sosai a ranar sun zazzagaya park park na shak'atawa sunsha ice cream sannan suka tsaya a wani babban boutique clothing store ya jidar musu kayan sawa da takalma tamkar wad'anda suke fatararsu, daga kuma suka zarce wani babban super market ya dinga jidar musu uban kayan zak'i dasu biscuits kamar hauka har saida Jauhar ta gaza yin shiru da bakinta tace "Kai jama'a Yah Abdallah dan ALLAH a dinga tausayin kud'i haba". harara ya dalla mata yace "Ina ruwanki malama kud'inki ko nawa banason sa ido fa". yadda ta saba gatsina masa baki haka ma tayi masa a lokacin yayi k'wafa kuwa yana kad'a kai yace "Ni kikewa haka ko? ALLAH ya kaimu gida lafiya saina kusa karkatar miki dashi ta yadda idan akace watarana kiyimin haka baza kiyiba". Gaba tayi tana fad'in itama haka zatayiwa nashi, duk dariya mutanen dake wajen sukayi kafin sukazo wajen biya ya biya kud'in suka tafi. Bayan sun maida yaran ma gida ba gida suka nufa ba sunje gidan Aunt Deejah da gidan Aunt Jeeddah dakuma Aunt Mabrookah suka dire kuma a gidan Habeeb lokacin ma Habeeb d'in yana gida murna a wajen Hussaina kamar me ta rungume Jauhar cikin jin dad'in zuwansu nan ta shiga cika musu gabansu da lemuka da kayan ciye ciye ta tsuguna har k'asa tana gaida Abdallah amsawa yayi yana k'are mata kallo ganin yadda duk tabi ta rame sai dogon hancinsu irin na gado daya k'ara fitowa sosai apple juice ya d'auka yana bud'ewa yace "Ke meya ramar dake haka? kai dan ubanka me kake mata?". maganar yana kallon Habeeb, kafin Habeeb yayi magana ya k'ara juyawa wajen Hussaina yace "Fadamin gaskiya idan yana miki wani abu inci miki ubanshi yanzun nan, goshi Jauhar ta dafe tana d'an girgiza kai ALLAH ya shirya mata wannan mijin nata idan ba Abdallah ba waye zaizo har gidan mace ya dinga zagin mijinta a gabanta, k'asa Hussaina ta k'ara yi da kanta tace "Ba komai Yah Abdallah banida lafiya ne wlhy". juyawa yayi ya kalli Habeeb yace "Shege ai tunda naga idanunka nasan bakada gaskiya hala har ka d'irka mata ciki ne". wata masifaffiyar kunya ce ta kama Jauhar da Hussaina suka sunkuyar dakai Habeeb ma kunyar ce ta kamashi ganin ga Jauhar a wajen ya maze dai yana murmushin yak'e yana kallon Hussaina da kanta ke k'asa, shikam gogan baisan ma sunayi ba lemonshi kawai yake sipping hankali kwance ya bararraje akan kujera ko kunya bayaji gidan k'anwa ne 🤦. 'Gaskiya bakin Yah Abdallah bai gasu ba sam lokacin da yana jariri' Jauhar ta ayyana a ranta ta mik'e tsaye ta kamo hannun Hussaina tace tazo su shiga daga ciki kafin ya k'ara b'aro musu wata maganar datafi k'arfinsu. "Kai dai kaji kunya wllhy, banza ko kunyata bakaji kake irin wannan maganar a gabana". Kai tsaye Abdallah yace "Ubana ne kai da zanji kunyarka? jiya ma munyi waya da Abdallah yace suna hospital Hassana ba lafiya itama nasan bai wuce cikin ba shegu jarababbu". Hararar shi Habeeb yayi yace "Kai ubanwa yafika jaraba ma A.B Madugu fad'awa wanda bai saniba". dariya Abdallah yayi bai dai maida martani ba suka cigaba da hirarsu irin ta aminai da suka dad'e tare ayi fad'a a shirya kuma duk yawancin fad'an Abdallah ne yake janshi dayake Habeeb d'in ya karance shi kuma yaci maganin zama dashi abubuwa dayawa idan yayi masa ko d'aga kai bayayi bare ya kalleshi. Sai bayan sallahr Esha'e sannan suka bar gidan Jauhar tayi matuk'ar gajiya dan ba k'arya sun yawatu yau d'in nan ta langab'e a jikinshi zata masa barci yace sam bata isaba shi dayake ta garari yana tuk'in baice yagaji zaiyi barci ba sai ita aikuwa tashi zatayi dolenta ta tashin tana murza ido barci da gajiya sun had'e mata. Suna komawa wanka sukayi tare sukayi shirin barci, ganin take takenshi yana neman wani abu a wajenta ya hanata sakat yasa ta marairaice masa tace "Haba Yah Modibbo dan ALLAH ka tausaya min mana ka barni in huta bakaga yadda kayi min d'azu bane gashi yanzu munsha yawo duk mun gaji". "Malama ki bani hakk'ina kawai, kedai kika gaji amma ban dani dayake yawone ai kin iya bina to saina fanshe ladan wahalar tuk'a ki d'in danayi". yace yana d'ora k'afarshi kan cinyoyinta dake mik'e samb'el ba abinda ya rufesu dan wandon kayan barcin da kad'an ya wuce pant. "Please kibani ko d'ayane sai in hak'ura ko cikin dare ne na k'ara wani". Shure shuren k'afafu ta fara lokaci d'aya tana sa masa kukan shagwab'a wanda ta k'ara rikitashi, shima k'asa yayi sosai da murya ya shagwab'e mata yace "Please My sugar nine fa Abdallahn nan naki bawan ALLAH". Dariya tayi tace "To saika fad'i wani abu daidai tukunna". "Meye shi?". Ya tambaya yana k'ara nanik'arta kawai dai yana biye mata ne bawai dan idan ta hanashi d'in zai hanu ba. "Fad'i Jauhar zaka fad'a daidai". "Meye abin wahala a sunan naki? Nace Jauhar to". Ya fad'a da harafin 'R' d'inshi da bata fita daidai. Dariya tasa sosai tana fad'in "Eyyah ka fad'i Yah Abdallah ba daidai ka fad'a ba kai yanzu Jauhar d'in ne yake maka wahala?". Ita a dole wayo take so tayi masa harya gaji yabar maganar kusantar ta, zabura yayi ya haye kanta gaba d'ayanshi yana fad'in "Ke nabi Jauhar da.......Batare daya k'arasa ba ya zura bakinshi a nata ya cafko harshenta yafara masa wani salo daya hargitsa Jauhar wadda batare data saniba ta biye masa suka shiga farantawa juna rai. Mrs Salees Mu'az 💝 3/22/22, 19:29 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝 Page 48. THE END. Paid book. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.* ©Oum Hanan. Washegari da k'yar Jauhar ta iya tashi saboda tsamin da jikinta yayi ga gajiyar yawon da suka sha ga kuma wadda Abdallah ya tara mata dan barcinsu rabi da rabi ne a wannan daren duk yabi ya addabeta da fitinarshi. Langab'e masa tayi tace ba abinda zata iyayi wlhy jikinta ko ina ciwo yake dan haka da kanshi ya shiga kitchen safiyar ranar yayi musu breakfast duk da dai tea ne kawai ya dafa shima baiyi irin na Jauhar ba sai wainar k'wai daya soya wadda itama duk ta fara k'onewa ya shirya a dinning table ya shiga gyaran gidan duk tana lafe cikin bargo barci take so tayi duk ya hanata da uwar kwarafniya shi bai yadda ba aiki yake, tashi tayi ta sauko daga kan gadon ta fito falon. Tsakiyar falon ta hangeshi daga shi sai bak'in gajeren wando yana mopping duk ya had'a uban gumi batasan lokacin data tuntsure da dariya ba harda tafa hannu tace "Oh yau maza na aiki fa a gidan nan gaba d'aya an hanamu zaman lafiya". D'agowa yayi yana cije baki tareda sakin k'wafa yace "Idan ban sakar miki aikinki ba kice ba sunana Abdallah ba ya zan tak'ark'are ina miki bauta kizo kina min dariya ko sannu babu". Baki ta dafe tana k'unshe dariyarta da hannu d'aya d'ayan kuma tana d'aga masa shi alamun bada hak'uri saida ya saki wata k'wafar sannan ya cigaba dayi, d'aya daga cikin k'ayatattun kujerun dinning inda take tsaye taja ta zauna tana kallonshi tana k'unshe dariyarta dan karya ganta da anyi kad'an sai a tashi tsaye a rik'e k'ugu ana goge gumi abin dole yabaka dariya, ai gara dai kaji yadda akeji in ana aikin, nan akayi ta fama dashi ya yarda a d'auko y'ar aiki yace sam bai yardaba shi baya ra'ayin y'ar aiki ba yadda ba'ayi dashi ba yace bayaso kuma dama tun lokacin Janaan wani zuwa datayi tazo gidan taga yadda take shan aiki ga girki ga gyaran gida tace mata ya kamata a samo mata y'ar aiki wadda zata dinga tayata aikace aikacen gida koda batayi mata girki ba Janaan tace ai Yah Abdallah ne bayaso shiyasa bata d'auka ba tayi masa maganar yace bayaso, baki kawai ta tab'e a lokacin gani take idan itace bai isa yayi mata wannan mulkin ba dan dai yasamu Janaan d'in ne saigashi itama ya hana d'in kuma ta hanu d'in farko dai taso tayi masa bore taga dai ya fita bala'i dole ita ta rissina ta mik'a wuya dan a zauna lafiya, amma magana ta gaskiya dai tana shan aiki gyaran gidan ma kad'ai wani uban aikine amma idan ta tuna bautar aure take kuma ta hakane zata samu lada sai taji baya damunta. Magana ta gaskiya Janaan ba k'aramin hak'uri tayi da bawan ALLAHn nan ba sai yanzu take k'ara tabbatar da hakan datake zaune dashi musamman ita Janaan da batada baki bata iya masifa ba ita d'inma datake da tsiwa da masifa dole take shafawa kanta lafiya dan bazata iya da bala'in Abdallah ba. "Ka manta da burner Yah Abdallah". ta fad'a cikin sigar tsokana bayan yagama mopping d'in, a gajiye yace "Meye haka kuma? shima mopping d'in akeyi dashi?". "No abin saka turaren wuta". ta bashi amsa, harara ya zabga mata ya jefar da mopper a tsakiyar falon yace "Aini ba bawanki bane in miki ciki in miki goyo? kwankwaso na ciwo kawai yake dan mugunta kin sani aikin daba nawa ba salon anjima idan nazo raya sunnah in kasa tab'uka komai, wuceta yayi ya shige bedroom yanata masifa kamar ita tace dole saiyayi aikin, tashi tayi ta maida mopper inda take mopping d'inma gaba d'aya saita canza wani dan bawani yi yayiba bai mata yadda yakeso ba, itama bedroom d'in ta shiga danyin wanka. Tare sukayi wankan suka shirya tare sannan suka fito yin breakfast tafara serving d'insu, tashin farko tana zuba tea d'in taji k'amshin ya bambanta da nata, kallonshi tayi ko zaiyi magana taga hankalinshi ma gaba d'aya yana kan wayar hannunshi yana danne danne haka dai ta zuba musu madara da Milo tasaka musu cube sugar tasa tea spoon a cup d'inshi ta tura masa gabanshi, again dai tana bud'e plate d'in taga waina bak'a tana kallonta ido ta zaro tace "Yaa subhanallah". d'agowa yayi daga kallon wayar dayake yace "Lafiya?". Kallon plate d'in tayi tace "Amma Yah Abdallah meye wannan dan ALLAH haka akeyin wainar k'wai dama?". Wayar hannunshi ya ajiye yace "To koyamin zakiyi? y'ar iya meye bamu iyaba a girke girken naku zakimin iyayi". baki ta tura tace "Nidai to wllhy bazan ciba". "Karki ci d'in yarinya". yace yana janyo plate d'in ya gutsura yasa a baki ido ya dinga zarewa yana kallonta dan tashin farko wani uban gishiri ne yayi masa sallama wanda ya gauraye duk ilahirin bakinshi mai uban yawa dan lokacin dazai zuba bada spoon ya zuba ba bakin robar ya karkata ya antaya shi, ido itama ta tsura masa duk yadda yaso had'iyewa ya kasa da sauri ya furzar da ita akan dinning d'in Jauhar dariya kawai take tana kallonshi tashi taga yayi duk zatonta zuwa zaiyi ya wanke bakinshi sai gani tayi ya nufota yana zuwa ya d'auketa cak d'inta ya d'ora akan dinning d'in ya tsaya a gabanta itadai da ido kawai take binshi taga abinda zaiyi sai gani tayi ya tallabo fuskarta ya had'a bakinshi da nata, k'ok'arin k'wacewa ta shiga yi saboda uban gishirin da itama ya ratsa nata bakin amma saboda yadda ya kama harshen nata kam yasa ta kasa k'wata. Baki ta tura kamar zatayi kuka lokacin daya cire bakinshi dariya ya fara yimata shima ta diro daga dinning d'in ta bishi da gudu suka shiga zagaye falon yana mata dariya ganin ta kasa kamashi gashi kuma tagaji yasa ta zube k'asan carpet tana sauke numfashi shima tsayawar yayi yana kallonta kafin ya k'araso inda take ya d'auketa suka koma dinning d'in a tak'aice dai ranar sai tea d'in kawai suka sha wainar sam bata ciyu ba dan haka ranar da wuri ta had'a launch saboda cikin bai d'auka ba da safe 😀. ★★★★★★__________________★★★★★★ Rayuwa tayiwa su Jauhar dad'i saidai d'an abinda ba'a rasaba na akasin hakan dama rayuwar gaba d'ayanta k'alubale ce kuma jarrabawa dan haka a koda yaushe idan ubangiji yaso zai jarabci bawanshi da kalolin k'addarori masu kyau da kishiyar hakan fatan mu dai ALLAH ubangiji ya bamu ikon cin jarrabawa aduk lokacin da aka jarabcemu. Jauhar ta dad'e bata haihu ba dan ak'alla saida sukayi kusan shekara hud'u harta fara saka damuwa a ranta sannan cikin iko na ubangiji ALLAH ya bata cikin a lokacin Hassana da Hussaina kowacce yaranta biyu, sai little Janaan da tuni tadawo wajenta Irfaan shidai yazama d'an wajen Ammi dan k'in badashi tayi. ALLAH cikin ikonshi lokacin data tashi haihuwa itama sai ALLAH yabata twins d'in duk maza wad'anda suka biyo ubansu sak ba abinda suka baro nashi fad'ar irin murna da farin cikin da wannan familyn sukayi ma b'ata baki ne Abdallah harda kwaso shokky agaban Ayyah datake gidan dan dama ita tadawo gidan lokacin da cikin nata ya tsufa kuma haihuwar ma a gida tayi ta ALLAH yakawo mata da sauk'i. Sukam ba'a canza musu suna ba Hassan da Hussain sunan da sukazo dasu ake kiransu. Tun daga nan kuma kamar an bud'e mata haihuwar ne dan su Hassan ko shekara basu rufa ba ta k'ara samun wani cikin to dama d'an adam ba'a iya masa nan kuma ta tada hankalinta ta dinga kuka duk saboda cikin harda ik'rarin zata zubar dashi ya za'ayi duka yara basufi wata goma ba ta k'ara samun wani cikin da wanne zataji da rainonsu koda rainon cikin, aikuwa dai a ranar taga bala'i ruwa ruwanshi a wajen Abdallah tamkar wani zararre haka ya koma mata daga k'arshe dai dataga ba sarki sai ALLAH dolenta ta hak'ura bazata iya da jarabar Abdallah ba ta cigaba da rainon cikinta dakuma yaranta. Abdallah namijin gaske ne dan yana tsaye akan iyalinshi yana basu kulawa duk wani hakk'insu yana iya bakin k'ok'arin shi wajen ganin ya sauke shi kuma a ko ina Jauhar tana alfahari da mijinta dan d'ayane tamkar da dubu yasamu cigaba ta b'angarori da dama kuma yanada zuciyar taimakon al'umma musamman gajiyayyu masu rauni da marasa lafiya musamman ya kafa wata k'ungiya ta taimakon marasa k'arfi da marayu shiyasa ako yaushe yake k'ara ganin bud'i da alkhairai a sana'arshi. Dama masu iya magana kance barewa batayi gudu d'anta yayi rarrafe ba kuma kamar kumbo kamar katan ta dan Irfaan kaf halayen Abdallah lokaci dayana yaro ya kwashesu tsaf shima idan yayi wani abun saidai kawai Ammi ta bishi da ido dan yana tuno mata da k'uruciyar Abdallah ne fatan ta dai ALLAH yasa yabi k'uruciya karya d'ore har girmanshi dan ga babanshi nan yara hud'u gana biyar a ciki amma har yanzu Jauhar fama take dashi idan ya rikice mata idan yayi wani abun ko k'aramin yaro bazaiyi ba saidai ta kalleshi kawai tasa masa ido, amma fa yana da dad'in zama ita kanta tasan da haka kawai dai wani lokacin ne sai a hankali kuma dama zaman tare saida hak'uri bawai duk abinda mutum yakeso yake samu ba ALLAH ya k'ara mana hak'uri da juriyar zama da mazajen mu lafiya 🙏. Mace ta haifa lokacin data haihu ita kuma saita biyo kamannin Jauhar d'in sunan Ammi taci wato Hafsat suke mata alkunya da Mahnoor. Yah Ameen ma yanzu haka yanada yara uku itama dayake matar bata haihuwa akai akai su Hassana ma kowacce ta ajiye iyali, abokantakar Abdallah da Habeeb da d'aya Abdallahn tana nan saima abinda yayi gaba suma sun sa hannu tare suke tallafawa al'ummar musulmi. Bayan haihuwar ta dawasu watanni ya shirya musu tafiya yawon bud'e ido k'asashen waje shida iyalanshi gaba d'aya da Irfaan aka shirya tafiyar amma k'ememe yace shifa ba inda zaije kawai a k'yaleshi Abdallah yaso tursasa shi Ammi tace ya k'yaleshi d'in kawai tunda yace bazaije ba. Fatan dawowa lafiya ABDALLAH BASHEER MADUGU FAMILY 💝😍. Alhmdulillah Alhmdulillah Alhmdulillah ALLAH nagode maka daka bani ikon sauke wannan nauyin dake kaina, abinda na fad'a daidai ubangiji ya had'amu cikin ladar wanda nayi kuskuren rubutawa ya yafemin ina rok'on afwar duk wanda na b'atawa yayin rubuta wannan littafin kuma mun gode sosai da had'in kan da kuka bamu ALLAH yabar zumunchi ya had'amu a aljannah kamar yadda ya had'amu a nan 🙏👏👏 Ina yiwa kowa fatan alkhairi Bissalam. Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 (Oum Hanan)