*SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* 🌻🌻🌻 _"Ƙungiyar Marubuta masu tasawa, Rubutunmu shi ne tafiyar da ke wuce lokaci, mu ne masu ɗaukar harshen gobe a yau. Marubuci ba ya zana kalma kawai, sai dai ya zana mafarki a zuciya, ya maida shi haske ga al'umma. Wannan shi ne alwashinmu a matsayin mu na matasan marubuta. Taken mu shine ɗaga darajar Marubuta masu tasawa."_ 🌻🌻🌻 🌻SYou Na sadaukar da wannan littafi ga ’yan’uwa marubuta na cikin ƙungiyarmu mai albarka — *Future Writers Association*. Ku ne ginshiƙin kwarin gwiwa da hasken tafiyata a duniyar rubutu. Wanan Littafin yafi ƙarfin Shafi ko alƙalami; wani ɗan ɓangare ne daga zukatanmu da ke ɗauke da mafarki, ƙalubale da burin da muke fatan cimmawa tare. Allah ya ka ɗorar mana da haɗin kai, ka bunƙasa ƙungiyarmu, ka ba mu ikon sauya al’umma ta hanyar kalmomi. *–Fatan alheri da ƙauna.* *[Sayyid writer Legend]* بسم الله الرحمن الرحي SHAFI NA FARKO (P. 01) Durƙushe nake, gaban kawu Mudi yana zubamun bulalal da nake jinta kamar saukar ruwan dalma a jikina. Yata ƙarƙare sai zubumun bulalal yake iya ƙarfinsa, idanuwa na suna a murje kamar baza su zubar da hawaye ba. A cikin raina kuma faɗi nake. “Ya ubangiji ka gama Mus’ab da masifar duniya, da ta lahira. Ya ubangiji kasa yayi saɓani da Alkhairi, yayi ido huɗu da tsautsayi , da asara.” Wata bulala da ta shigeni ce, tasa ƙwalla fitowa daga idona ba tare da na shirya ba. Da sauri nayi ƙasa dakaina, ina goge ta da hijabi na. Mai na yiwa Mus’ab a duniyar nan ya tsane ni har haka?, a kullum burinshi yaga ana jibgata kamar sabuwar jaka, ko nace tsohuwa tunda na saba da dukan. Tabbas nasan, ina da taurin kai, da kafiya, haka naci, amma kwata-kwata bani da rashin kunya. To yanzu ma ko ina da rashin kunyar, zan tsaya a waje na fara yiwa mutane rashin kunya ba tare da sunyi mun komai ba. Mahaukaciya nake ko me?, su kuma iyayen tarbiya, gidan da yafi na kowa tarbiya. Daga ance musu gani can waje, ina yiwa mutane rashin kunya. Shine zai sani gaba da duka. “Tashi ki bani waje.” Muryar kawu mudi ta shiga kunnuwa na, tashi nayi na nufi cikin ɗakin mu. Nasan Mamana ba zata ce mun ko sannu ba, hakan yasa na kwanta kan doguwar kujera, ina kuka na a hankali, zuciya ta cike da ƙarin tsanar Mus’ab. Ƴan mintina kad’an, Sadiya da Ummi suka shigo ɗakin namu, lokacin Mamana na cikin d’aki. “Gaskiyya Yaya Mus’ab baya kyautawa, kullum shi burinshi yaga an dake ki, ko da yaga kina yin rashin kunyar ai shi mai yi miki faɗa ne.” Wani haushin Ummi ya ƙara kamani, ita yayanta bazaiyi ƙarya ba kenan, sai nice nake ƙarya tunda gashi sun yarda nayi rashin kunyar. Ni daga ganin mutane, suka tambayeni gidan Alhaji Idi me mai. Na nuna musu gidan, d’aya cikin su yace. “Mungode ‘yan mata.” Ni kuma nayi dariya shikenan kawai sabida Mus’ab ya tsaneni, yasa aka jibgeni kamar ba daren jiya yasa Yaya Iliyasu ya mareni ba. Sadiya ce, ta bawa Ummi amsa. “Nikam gaskiyya abinda Yaya Mus’ab yake yayi yawa, shi fa bazai hanamu abu ba, sanan bazai sa a hana mu ba. Ita kad’ai yake sawa a daka, itama kuma ba sabida soyayya ba, sai dan ‘yar tsamar dake tsakanin su. Duk gidan nan Yaya Mus’ab ne kawai ke nuna ware, yana nuna ku kaɗai ne ƙannansa, kuma sauran yayin mu ba haka suke ba.” “Sadiya gidan ku da wanan maganar, kar nasake ji kinyi ta. Gaba ɗaya gidannan babu wani mai ware, domin dukkan ku jini ɗaya ne, Hajja itace asalin ku. Kuma shi Mus’ab ai yanayin sa ne a haka, bai da son mutane kwata-kwata.” Ummanah dake cikin ɗaki ta faɗa. Nikam takaici ya isheni, na yadda Ummanah bata taɓa jin haushin Mus’ab, juya musu baya nayi na kwanta. Tun ina jin maganarsu sama-sama har bacci ya d’auke ni, zuciyata cike da tsanar Mus’ab. Ƙarfe 1:45 dai-dai natashi, domin nasan da zuwa islamiya hakan yasa natashi a lokacin. Banɗaki na shiga na watsa ruwa, tare da ɗaura alwala na fito na tada sallar azhar. Ina idarwa na shiga Kitchen na lodo abinci, dan gaskiyya babu laifi Allah ya horemun ci, kamar yadda Mus’ab ke dizgani cikin mutane. Yake cemun (Gara uwar ci). To kam gaskiyya ina da cin abinci, sai dai kuma idan naci yanzu fa zai iya zama naci har na dare, dan bani da yawan cin abinci akai-akai, lokacin farko dai xanci har sai yabawa mutane mamaki. Ina gama ci na zura hijabi na, nayi makaranta, a tsarin gidan mu (Gidan Galadima) duk lokacin tafiya makaranta sai an shiga ɗakin Hajja, an gaida ta, kama da makarantar safe, rana, da kuma ta dare, sabida ɓacin rai da hausin ɗan gaban goshinta, wanda nafi tsana sama sa kowa a duniya yasa nakaɗa kai na tafi banje na gaida ta ba. Ko a islamiyyar ma haka na zauna, kamar wacce aka yiwa mutuwa. Tsana da haushin Mus’ab na lugude a zuciyata. Ko da na dawo ma banje ɗakin Hajja ba, ɓangarenmu na nufa nayi kwanciyata. A ɓangaren Hajiya Hajja kam, tana ganin kowa na shigowa gaisuwar tafiya amma babu ni, babu alamu na. Hakan ya matuƙar damunta, tana nan zaune ‘yan islamiyya suka fara dawowa. Ganin sun ƙare babu ni yasa tace da Iki. “Ikirama, kira mini Salame.” Tashi Iki tayi ta nufo ɓangarenmu, ina kwance kan doguwar kujera tashigo ɗakinmu. “Salma, kizo inji Hajja.” “Kice mata banzo ba….” ban ƙarashe ba, naji an make mini baki tare da faɗin. “Zanci ubanki Wallahi, Hajja kike cewa ace baza kizo ba. Sai kin ƙara tabbatar da cewa baki da kunya ko.” cuṅo baki nayi gaba, tare da sakkowa daga kan kujera, banko ɗauki mayafi ba na fice. Dabda ɓangaren Hajja, na hango Mus’ab yana tafiya a hankali, kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki. Idanunshi sunyi jazur, kamar gauta. A fili nace. “Allah yasa wanan ciwon kan ne ajalinka.” A bakin ƙofar ɗakin Hajja na tsaya, tare da cewa. “Gani.” “Naganki tijararra, naganki.” Juyawa nayi zan koma ɓangaren mu, ba tare da na ce ko ƙala ba, tunda ni yau bakina jinshi nake kamar an ɗora masa kwaɗo, babu abinda nake ji sai tsanar Mus'ab, Hajja ta ƙara cewa. “Yanzu salame, tafiya za kiyi.” “Toh Hajja mene zance miki, bayan wanan kafirin la’ananne jikin naki, yasa ‘ya’yanki suna dukana, sun mai dani kamar wata jaka, kowacce a ka siyo.” “Yanzu Salame,Mus’abun kike kafurtawa, har da la’ana. To fice ki bani waje.” “Daman bani na kowa kaina ba, kice kika nemeni.” na faɗa tare da fice, a hanya na ƙara cin karo dashi, har yanzu bai kai ga shigowa ba. Dogon tsaki naja tare da cewa. “Duk wanda ya ɗauke zalunci a matsayin sana’a, rayuwarshi zata ƙare a jinya.” nikaina nasan da’a ce ba'a wanan halin Mus’ab yake ciki ba, da kafin na ƙarashe wanan maganar na kwashe haƙora na a hannu. Ci gaba yayi da tafiyarsa, nima nayi ɓangarenmu, a raina ina nanata addu’a ta ‘yar kullum. “Allah yagama Mus’ab da masifar duniya.” *Asalinmu* Dafarko dai sunana: Salamatu Yunusa Galadima. Kakan mu shine Galadiman, bawai Galadima na fadar sarki ba, a’ah sunane kawai yace. Mahaifina Yunusa shine ɗa na Uku wajen Galadima, Yakubu shine babba, wanda muke kira da Abban ciki. Sai kuma Aisha wacce muke kira da Mami, sai Mahaifina Yunusa wanda kowa ke kiranshi da Abba, sai kuma Halima wacce ake kira da Ummah, sai Abbas da ake kira da Alhaji ƙarami, daga shi sai Ilyasu da ake kira da yaya Ilyasu, shi kam shine baya son ace masa Kawu, shiyasa ake ce masa, Yaya ilyasu, sai kuma autan su Kawu Madu. A taƙaice da Galadima kakanmu yana da ‘ya’ya bakwai, maza biyar mata uku. Kuma duka wa’yan nan ‘ya’yan sun fito daga matarsa guda ɗaya, (Hajiya Hajja). Kakanmu Galadima, tsohon mai kuɗi ne. Domin ko gidansa wanda muke ciki yanzu, yana da girman da kowanne part zau dauke mata hudu. Kafin rasuwarsa shiya bawa kowa ɓangaren da zai zauna, domin bayason yaga yaranshi su raba giadaje. Yace yana da burin ganin mun tashi a zuri’a ɗaya. Abban ciki ne ya fara aure, matarshi yar kano ce mai suna Jamila. Muna ce mata Maman ciki, idan mutunci yana yawa to ya yiwa Mamam ciki yawa, tana son mu, tana kaunar mu. Duk abu indai Maman ciki ce bata taba ware mu da yaranta, sanan mijinta shine babba. Kuma ta dau girman, domin har su Ummanah Yaya suke cemata, tana da yara guda biyar. Mai sunan Hajja ce babba, wacce yanzu take aure a Abuja, da yaranta guda biyu, yanzu gaba daya gida ance da ita, Yayar Abuja. Sai kuma Yaya Amira wacce ke aure a Zaria, ɗanta guda daya ne. Shekarar da ta ƙare ne, a ka aurar dasu, su hudu a cikin gidan. Daga ita Sai Mus’ab, shine babba a maza a ɓangarensu, sai kuma mai binsa Mai sunan kakanmu. Daga shi Sai Ummi dake auta a bangarensu. Sai kuma ‘ya’yan Mami guda shida, su kam ba’a gidan Galadima suke ba, kuma basa amfani da sunan Galadima kamar yadda mukeyi. A tsarin wanan gidan, yadda mahaifanmu ke amfani da Galadima haka muma mukeyi, kwata-kwata bama amfani da sunan iyayen mu, yadda mahaifina ke amfanu da Yunusa Galadima, haka nake amfani da Salma Galadima. Kuma kowa na cikin gidan haka yake amfani dashi. Legends pen. (08165383931 / 08129553971). *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* بسم الله الرحمن الرحي SHAFI NA BIYU (P.02). Mu hudu ne wajen Mahafinmu, Yaya Asma’u ce babba. Wacce tana cikin ‘yan matan da aka aurar shekara da ta kare. Sai kuma Muhammadu dake bin ta, sai ni sai Mai sunan Hajja. Wacce itace autar mu muna ce mata Iki. Itama Ummah bata gidan Galadima, amma kuma yaranta maza uku, duka a gidan Galadima suke, sai matan ne a wajenta, wa’yanda sune ƙanana dan muma nun girmesu. Aliyu, shu’aibu sai Kuma mai sunan Galadima. Sai kuma ɓangaren Alhaji ƙarami, shi ‘ya’ya uku gareshi, Yaya Khadija ce babba. Itama tana cikin wa’yan da aka aurar shekarar da ta ƙare, daman uku ne a cikin gidan Galadima. Sai kuma ɗaya daga gidan Mama. Sadiya ce ke bin Yaya Khadija, Sai kuma ƙanwarta guda daya. A cikin jikoki 27 da Allah yabawa Hajja, sai Allah ya jarabce ta da son guda daya, fiye da sauran jikokin. Har ake tunanin ta mafi son shi a kan wasu yaran na ta. Mus’ab Galadima. Tun haihuwarsa take nuna masa muguwar ƙauna, fiye da tsammani. Dan ko sanda yana jariri yayi kuka, nan Hajja zata fara balbalin bala’i, Ƙarshe dai Maman ciki, ba tajira lokacin yaye yazo ba ta miƙawa Hajja abunta. A cinyar Hajja ya taso, ɗangata, ɗan lele, rigimamme, mara kuma jin magana, sabida gata da ya samu wajen Hajja, kowa bai kyale ba a lokacin ƙuruciyarsa, har da kawunansa wa’yanda basuyi aure ba lokacin. Haka rayuwa tai ta tafiya, har a kazo lokacin da muka diro duniya, mu uku ne a set ɗinmu. Sadiya ce babba, sai kuma Walidah, ni ce ƙarama cikinsu. Tun tasowa ta, nake mugun son Kakata Hajja. Ina ƙaunar Hajja sosai da sosai, itama ganin haka yasa take ƙaunata. Sa dai Mus’ab ba ya ƙaunata ko kaɗan. Haka rayuwa tai ta tafiya, har a kazo lokacin da muka diro duniya, mu uku ne a set ɗinmu. Sadiya ce babba, sai kuma Walidah, ni ce ƙarama cikinsu. Tun tasowa ta, nake mugun son Kakata Hajja. Ina ƙaunar Hajja sosai da sosai, itama ganin haka yasa take ƙaunata. Sa dai Mus’ab ba ya ƙaunata ko kaɗan. Da zarar nazo wajen Hajja, zai fara dukana, ni kuma Allah yasa mun taurin kai, kafiya, naci, da kuma rashin haƙuri. Shekaru d’ai-d’ai har goma ne tsakanin ni dashi, amma a wanan lokacin da nake da shekara uku, shi kuma yake da goma. Da zarar ya dake ni, ko ya buge ni, ko ya harare ni, kai ko kallon banza yayimun sai fa na rama. Wanan ramawar da nake itace abun da ta kara haifarwa da Mus’ab tsanata, ni kuma wanan tsanar tashi itace ta raini tawa. Mus’ab bashi da kunya, ko yayunsa maza ma yi musu yake. Wanan rashin haƙuri nawa, yawan faɗa da ƙarata da Mus’ab ke kaiwa Hajja. Shi yaja ta fara yi mun faɗa, har tana hanani zama a ɓangarenta, da nazo zata fara cewa.”Ni Salame, wanan halin rashin haƙuri naki ya fara isata na. Ke kenan bazaki zo ba, sai kin addabarmun yaro?.” Cikin kuka nake cewa. “Hajja shine yake duka na.” “Ke kuma da baki da kunya, shine sai ki rama ko?.” haka kullum muke fama da Hajja, har naji zuwa ɓangaren nata ya fara fita a kaina. Abinda na kwana, na tashi da sanin shi shine. Mus’ab yana masifar son ganin ya kai ƙarata, dan tu ina ‘yar mitsitsiya idan ya dakeni, nayi masa Allah ya isa, sai yazo ya ce. “Ya ganni a waje, ina yiwa wani Allah ya isa.” haka za’asani gaba, ai ta jibga kamar sabuwar jaka, nai ta kuka kamar marainiya. Irin wa’yannan abubuwan, sune suka taru suka haifar da muguwar ƙiyayyar Mus’ab a zuciyata. Ƙiyayya irin mai girman gaske, sanan da yanda yake yiwa kowa rashin kunya, yasa na ƙara jin haushin sa. Sai da Ummanah ma Allah ya jarabce ta da ƙaunar Mus’ab. Ƙauna ta gaske, bata taɓa ganin laifinsa duk abunda zaiyi, ko da kuwa ya dakeni, ko yayi mun sharri an dake ni. Haka zan zauna nai ta kuka, amma ko a jikinta. Kamar yanda na faɗa. “Gidan Galadima gidane na haɗin kai, ƙaunar juna.” gida ne da babu wani ware, kowa yana son kowa,sanan kowa yana da set na, sakwanin haihuwa. A bangaren rayuwa, gida ne na masu rufan asiri, ba zaka ce mana masu arziƙi ba. Amma duk wani ci, sha, suttura, wajen zama, wajen karatu, munfi ƙarfinsu. Muna rayuwa a nutse cike da tarbiya, kowa na ƙaunar kowa. A ɓangaren kyau kam. Duk cikin gidan Galadima babu wanda yakai yayata Asma’u kyau. Duk da ance tana kama dasu Yaya Khadija, amma kowa yasan tafi kowa kyau A cikin wanan gidan. To ni da ita muna ɗiban kammani, ko da baza’ace nike biye mata a kyau ba. Bazan huce ta uku ba a cikin gidan Galadima. A maza kam a bayyane take, Mus’ab Galadima yafi kowa kyau, dan har wani shigen kama yake da wanan jarumin na indiya. (Aditya Roy Kapur) kawai shi Mus’ab yafi Aditiya faffadar fuska, kasancewar ta Aditiya ‘yar tsurut ce. Amma ni bana ganin wanan, sabida girmam tsanar da nayi mishi. Nikam zance ban taɓa jin yakira sunana ko sau daya ba. Yoo mutumin ma da harkar arziƙi ba ta haɗa ku ba, ta ina zai kira sunanki?. A haka har mu kazo matakin gama firamare, zuwa sakandire. Mukam a gidan mu ba’a cewa mace ba zatayi karatu ba. Sabida iyeyenmu nan duk da iliminsu, sai dai kuma ba’a taɓa samun wacce taje gaba sakandire ba, domin da zarar sunje matakin siniya samari zasu fara ɓulɓulowa kamar ruwa. Hajja kam cewa take. “Tun da samarin nan sunzo, to aurar da yaran nan, sabida lokaci daya mazaje ki zu war wa mace, da zarar sun kare to tsiyayewa zasuyi kamar hawaye.” Hakan ce ta faru kuwa, da zarar ‘yan matan gidan mu sunkai senior, zakiji anyi musu baiko. Suna kammalawa za’ayi bikinsu, wasu mazajen na barin su su ci gaba, wasu kuma basa ci gaba. Auren da’akayi shekarar da ta gabata, shine aure na uku da akayi, sabida idan aka tashi sai a hade mutum biyar, ko uku, maza da mata. A yanzu mukam mun shiga Ss1. Mu uku abun mu, sanan an saka ran aurar damu tare dasu Mus’ab, da wata buduruwarsa Junaidiya. Yarinyar kamar tsinken sigari haka take, ni ina mamakin yadda Mus’ab yake son yarinyar nan, duk kudinshi, duk gayunshi, duk ajinshi. Sai kuma wani lokacin nace, menene nawa?. A zuwa yanzu, tsanar Mus’ab ta danne ƙaunar da na kewa Hajja. Dan ko ɓangarenta banni xuwa, indai Mus’ab na garin. A kwanakin baya nai ta biyewa Mus’ab, ina zaginsa da masa rashin kunya, shi kam sai ya dakeni sosai, sanan yasa kawunnai na, ko yayumun su zaneni. Bansan mai yasa kaf ahalin Galadima, ake yarda da maganar Mus’ab ba, ni kuma ake kin yarda tawa. Ko dan shi yanayin magana cike da nutsuwa, niko da hayaniya nake magana. Sanan ina ƙaryatashi a gabansu. Haka za’aita jibgata kamar jaka. Akwai wataran da nayi niyar daukan fansa a kan Mus’ab, Naje har ɓangarensu lokacin Maman ciki na kitchen. Da sallama nashiga Kitchen tare da faɗin. “Maman ciki, aiki akeyi.” “Eyh, diyar ciki.” dariya nayi, sabida sunan da take kirana dashi kenan. “Ummi bata dawo ba kenan?.” “Ke wai lafiyanki, kike mun tambayoyi haka.” Murmushi nayi sanan nace.”Babu komai, sai anjima.” “Dawo mana, ɗiyar ciki.” Naji ta fada murya a sanyaye, alamun taji babu dadi. Haka kawai naji zuciyata ta karye, nafasa yin abinda ya kawo ni. Abinda ya faru kuma, jiya da daddare har yaja Yaya ilyasu ya mareni. Mun dawo daga makarantar magariba, sai wani dan ajinmu Walid ya tareni a lokon baya. Yana tambayata a kan buduruwarsa, wacce take ƙawata. Muna cikin magana, Mus’ab yazo wucewa, da sauri Walid yace. “Salma ga yayanki.” kallon Mus’ab nayi nace. “Naganshi, yayi kyau kamar rago.” gyaɗa kai yayi yahuce, kasancewar lokon da mutane. Shi kam bazaiyi abinda xai zubda mai da mutunci gaban mutane ba. Ina shigowa harabar gida, naganshi yafito daga bangaren Hajja. Da sauri na nufin ɓangaren nata, amma yarikemun hannu, juyowa nayi zan mai masifar da nasaba. Naji ya tsinkeni da mari. "Allah ya isa, Allah yagamaka da masifar duniya.” addu’ata ‘yar kullum gareshi, wacce shi kan shi ya haddace ta. “Zaki ci gidanku.” ya fada tare da jana ciki, ihu na fara kur mawa, ko Allah zaisa maman ciki tajiyo ni, amma Allah bai nufita ba. Kai tsaye inda Yaya Ilyasu yake yakaini. “Yayana, nagaji da abinda yarinyar nan keyi. Har ta kai ga abokaina sun fara mun magana a kan rashin kunyar da takeyiwa mutane a waje.” Da sauri na ɗago, tare da faɗin.”Wallahi karya yake, Mus’ab kai azzaulumi ne.” Yaya iliyasu ne ya tare ni da cewa. Legends pen. (08165383931/ 08129553971). *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* بسم الله الرحمن الرحي SHAFI NA UKU (P.03). “Tabbas kuwa, wanan ba rashin kunya bace. Salma mai yasa kike haka?.”Cike da jin haushi na sake buɗe baki nace. “Wallahi, karya yake min. Kawai ya tsaneni ne.” ban rufe baki ba naji, an ɗaukeni da mari. Tabbas marin ya shigeni, domin har wasu taurari nagani. Suna yawo a sama, daga nan ɗaki na huce. Ban san mene zanyiwa Mus’ab na huce wanan kayan haushin, sai dai kuma ɗaukar fansar duk kusanci dashi ne, nikam ina neman tsarin ubangiji da zuwa kusa dashi, ni ko a laira idan za’ayi mana Hisabi so nake tazarar mu ta kasance nisan sama da ƙasa. Idan kuwa har akace sai nuna gab da juna, ni mai iya yafeshi ce. Duk lokacin da Mus’ab, ya matso kusa dani wani irin turnuƙuƙi nakeji daga cikin zuciyata. Wani irin zafi kamar ana soyata. Idan nace na tsani Mus’ab, to na tsaneshi, bana fatan ko da rana daya naji na samu sasssuci daga tsanar da nayiwa Mus’ab. Yau ta kasance Lahadi, babu makarantar boko sai islamiyya. Muna zaune a compound muna wasa, har yanzu zuciyata cike da ɗacin marin da Yaya ilyasu yayimun jiya, kamar ance Salma fita waje haka naji zuciya na na fusgata. Kyawawan samari ne guda biyu, suna tsaye daga gefen gidanmu. Kyawawa ne sosai da sosai, cike da nutsuwa na fara tafiya zuwa inda suke, kamar wacce aka saka. ”Ƴan mata barka.” Daya cikinsu ya faɗa fuskarshi da murmushi. “Ina wuni.” na faɗa kasancewar sha-biyu ta kawo kai. “Lafiya ƙalau, dan Allah ko kin san gidan Alhaji idi me mai.” ɗaga kai nayi sanan nace. “Ai kuna kusa ma, gida na uku daga gidanmu.” “To inane gidan naku?.” ɗayan da baiyi magana ba tun dazu ya faɗa, cikin wata murya mai sanyi da zaƙi. “Kaji mazan arziƙi, ba irin su Mus’ab masu maganar mata ba.” na faɗa a raina, a fili kuma nayi murmushi na ce. “Wan can mai jan get ɗin shine namu, to daga na kusa da mu mai ƙofa, sai wancan mai ɓakin get na farko, to mai baƙin na biyu shine.” “Mungode Ƴan mata.” nayi murmushi, kamar an cemun juya idanuna suka faɗa cikin na Mus’ab, Ya harɗe hannye a ƙirjinsa yana kallonmu. Irin kallon da yakemun naji zuciyata ta buga da ƙarfi, da sauri nashiga gidansu Nana. Sai dai ko minti biyar banyi a gidan ba, iki tazo tace wai nazo inji kawu Mudi. “Innullahi, mai wanan mutumin yaje yace nayi kuma ni.” iki dai ba tace mun komai ba ta huce, na bita jikin a sanyaye. A tsakar gidan mu, na tarar dashi hannunsa rike da bulala ga Mus’ab can tsaye. “Kawu gani.” “Tsugunna ƙasa.” “Kawu mai nayi.” “Bazaki tsugunna ba.” ban kai ga tsugunnawar ba ya fara dukana, da iya ƙarfinsa, babu imani ko tausayi. Yana dukana yana faɗin. "Ke mara kunya mara tarbiyya ko, kina yin rashin kunya a gida ana kyaleki. Yanzu abun naki yakai harda fita waje, kiga mutane tsaye suna magana ki hau yimusu rashin kunya ko?.” zallan mamaki ne ya hanani cewa komai, wacce irin tsana Mus’ab yayi mini, mai nayi masa haka da zafi?, haka kawu mudi ya ci gaba da zabgamun bulal, har kuka shigo farkon labarin. *Cigaba* Nanata addu’a ta nakeyi.”Allah yagama Mus’ab da masifar duniya.” na jiyi sautin Walida, tashigo bangaren mu tana rusa kuka, Abinda ya fara zuwa raina shine. Mus’ab ya mutu, afili na furta. "Allah ka tabbatar.” shigowa tayi ɗakin mu tana faɗin. “Ummah, Yaya Mus’ab ne ya faɗi, ciwon kansa.” wani sanyi naji ya ratsa zuciyata, wanda kwata-kwata yau banji shi ba, tun bayan haɗuwata da wanan samari guda biyu. A gigice Ummanah ta fito, kamar wacce a ka ce mata, ni ko Yaya Asma’u sun faɗi. “Innullahi wainna illahir raji’un, Allah ka kawowa yaron nan saukin wanan ciwon kan.” Ummanah ta fada tana ficewa, da ido na bita ina taɓe baki. “Allah yasa har mutuwarsa.” na fada tare da kwanciya abuna, ban farka ba sai kiran sallar asuba. Tashi nayi na shiga toilet, na daura alwala nayi sallah. “Ummah ina kwana?.” Na fada daga inda nake, amma naji shiru. “Ina kwana.” still shiru, tashi nayi nafito falo tunda ita Ummanah na anan take zama lazimi, tun sallar asuba har bakwai. Rashin ganinta a falon yayi matukar razana ni, dakinta ta nashiga kai tsaye nan ma batanan. A kid’imi na fito xuwa b’angaren Abbanah, dakinshi na shiga na tarar dashi xaune da carbi hannunsa. Kallo ɗaya yayimun yasan da damuwa a tare dani. “Salma lafiya?.” “Abbanah, ina Umma?.” Murmushi yayi sanan yace. “Yayanku ne ba lafiya a asibiti suka kwana.” A jiyar zuciya na sauke, ni kam na ma manta da wani Mus’ab ba lafiya. Hanya na kama zanfita yace. “Ki hada musu breakfast, kuje ke da walida.” cuno baki nayi gaba, tare da ficewa. Kitchen na shiga na fara hada breakfast, cikin ƙanƙanin lokaci na soya doya da ƙwai, zuciya ta nayi mun tuƙuƙi. Nasan yadda Mus’ab ke mugun ƙaunar doya da ƙwai, domin ko a baya a ka kaiwa Hajja ba taci sai dai ta ajiye masa, har na zuba a plast sai kuma na tuna Mus’ab bai cin yamboll (Ƙosan doya), cikin hanzari na jawo doya nashiga ferayewa. A gaggauce na dadatsa ta na ɗora ta a kan gas, tare da balbala uwar wuta. Zuba doyar nayi a plast tare da tea na miƙawaya Abbabah, na ɗibi iya cikina, na ɗibawa Hajja sai kuma wani bangare na zuciyata ya rayamun kar na kaiwa Hajja, domin ita ke daure masa gindi. Amma fa inason Hajja ko ya ne, fita nayi zuwa ɓangarenta hannuna riƙe da doyar. Tana zaune jigom kamar wacce aka yiwa mutuwa, ina kyautata zaton jiya batayi bacci ba.”Ina kwana?.” na faɗa, ina shiga dakin. “Lafiya.” “Gashi.” na fada tare da miƙamata. “Babar taki ta dawo ne?.” girgixa kai nayi, sanan nace. “Nina soya.” “Menene kika soya?.” “Doya ne da ƙwai.” Murnushi tayi sanan tace. “Kin ɗibi na Asibiti.” a da kile nace. “Uhm.” daga haka na juya na fice. Ina zuwa na tarar doya ta tayi, aikuwa na sauke na fara dakawa, cikin ƙanƙanin lokaci na dake ta. Na yanka albasa da attatuhu na zuba a ciki, na kawo maggi da kuri na zuba a ciki, nasan baicin kifi hakan yasa na dakko kifin gwangwani na zuba a ciki, na hau mulmulawa. Cikin ƙanƙanin lokaci na mulmule ta tas, na kaɗa kwai na hau soyawa. Ina gama soyawa na juye a plast, nasan duk masifa yana shan ruwan zafi hakan yasa naki da fawa dasu. Zuba tea din nayi a kofi, na zuba doya da yamboll dina, na hauci. Sai dana ƙoshi, na hade ragowar doyar na juye a baƙar leda, na jefe a kwandon shara, zuciyata fari tas. Abbanah ne ya kirani ɗakinsa, bayan na zauna ya kalleni yace. “Salma, kije ki shirya kuje asibitinan yanzu.” “Abba wallah, ƙafata ciwo takemun sosai…” wani kallo da ya watsamun yasa na haɗiye yawon bakina, da ragowar maganar tas, na tashi na nufi daki, dogon hijabin Ummanah na dauka na zura, aikuwa yazo mun har ƙasa ina jaa. Ban ko damu ba, nashiga kicin na dakko plast din nasa a leda, a bakin ƙofar dakin na tsaya nace. “Kudin mota.” “Tasowa zanyi na kawo miki?.” a jiye ledar nayi, nashiga dakin ya bani dubu biyu, ba godi ba nagode na kadai na tafi, tunda dai bani na tambayeshi ba. Ɓangren su Walida na nufa, na sameta tsaye.”Mai kike jira?.” na tambayeta. “Lami nake jira ta gama abinci na tafi dashi; ina zaki ke?.” ta tambayeni , donin kowa zaiyi mamaki idan nace, Mus’ab zanje kai wa abinci. "Abba ne yasani girki, wai na kai asibiti, amma tunda ga wanan kawai kizo mutafi." na faɗa da biyu a raina, domin banason ya zamana abinda Ummi zata tafi dashi, Mus'ab ɗin nacin sa, anyi ba'ayi ba kenan. Ɗaki tashiga ta saka Hijabi itama, mu ka fice. A bakin titi mu kasami napep muka shiga, kasancewar kowa yasan asibitin da ake kai Mus'ab, ba ma shi kaɗai ba, kowa da kowa na gidan Galadima. A bakin asibitin mai napep ya sauke mu, naira duba daya na bashi ya ɗau ɗari biyar, yaban ɗari biyar. Muka rankaya cikin asibitin, har zuwa bakin ɗakin. A dai-dai na naja na tsaya, namiƙa wa Walida ledar nace."Shiga da'ita, idan kinfito ina bakin nan." "Haba salma, kishigo mana." "Wallahi walida ba zan shiga ba, ko da ace dubashi da xanyi, itace hanyar samun saukin shi da huri.” Ba tak’ara cewa komai ba, ta amshi ledar ta shige dakin ni kuma naja na tsaya, kamar wata mai gadi. Ina tsaye kusan mintina biyar, Ummanah ta leƙo sai ji nayi ance. "Sannu tabbatacciya." da sauri na juya, domin banma ji sanda aka buɗe ƙofar ba, da ruguwa zanyi a guje. "Ummah ina kwana." "Bansani ba, zaki shigo ko sai nazo nan na tsinke ki da mari." ta kowa na farayi a hankali, har zuwa bakin ƙofar ɗakin, a raina ina faɗin. "Lallai Walida da ni take zancen." Yana Kwance idanunsa na kallon ƙofa, aikuwa cikin rashin sa'a muka haɗa ido, aikuwa na murguɗa masa baki, tare da maka mai harara, game da yi masa gwalo a lokaci guda. Karo na farko a rayuwarsa da yaga nayi abu ya burgeshi, a cikin zuciyarsa yaji hakan. "Maman ciki ina kwana." "Lafiya ƙalau ɗiyar waje." kamar kullum dai dariyar mukayi, na matsa kusa da walida ko zama ban ƙarasa yi ba na maka mata mintsine tare da faɗin."Wallahi kinyi da ni." da sauri tace. "Wallahi bani na ce kinzo ba, Yaya Mus'ab ne." "Wallahi Walida ƙarya kike, aina yasan nazo." "To nima bansani ba, daga Mama ta tambayeni ya mutan gidan, nace lafiya. Sai ta ƙara cewa ke ya kike, nace ke kikayi girkin ma, shine Ummah ta ce mai yasa baki biyoni ba, ni kuma nayi shiru. Sai ji nayi yace tare kuke, na girgixa kai amma yace wai tare muke Ummah ta duba." Hararar ta nayi na ce. "Ni ban yarda ba." Ƴan minti na kaɗan na miƙe tare da cewa. "Zamu tafi." dai-dai lokacin shikuma ya buɗe baki ya ce. " Abinci..." Wani murmushi nayi tare da zama, Ummanah kuwa ta sakko tana faɗin. "Walida kun manta da tea." "Wallahi umma ba ni nayi komai ba, ko ledar ma sai a bakin ɗakin nan ta bani na riƙe." "Ai shikenan, Ummanah ta faɗa tana kwance ledar. Legends pen. (08165383931/08129553971). Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000. Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* SHAFI NA HUƊU (P.04). بسم الله الرحمن الرحيم "Wallahi umma bani nayi komai ba, ko ledar ma sai a bakin ɗakin nan ta bani na riƙe." "Ai shikenan, Ummanah ta faɗa tana kwance ledar. Bude idanu tayi, ganin yamboll kuma ta tabbatar wanan din aiki na ne, domin kowa ya kwana ya tashi da sanin cewa. Mus'ab bai cin yamboll. "Yunwa na keji." Mus'ab ya fada, wata dariyar mugunta ta tawomun wacce da kyar na iya tsaida ta, har sai da shi kanshi yaga alamun ina dariya. "Salma, mene kikayi haka, kinsan baya cin yamboll ko?." Hade rai nayi, sanan na ce. "Ummah shi ka dai ne damu." "Eyh shi dake ba da doya akeyi ba ko?." "A'a Ummah, yafi sauƙi ne." "Ke zanci gidanku wallahi, a gama dafa doyar azo a daka shine zakice yafi sauƙi?." "Wai menene?." Maman ciki ta tambaya, "Yamboll ta yo." Ummanah ta ba ta amsa, " Ai shikenan mu bari mu ci, ku kuma ku fita ku nemo mana tea, da kayan madara." Tashi nayi na amshi kudin, walida ta biyo ni har mun kai bakin kofa, Ummanah ta ce. "Saura ki siyo ruwan sanyi." Dariya nayi na fice, Mus'ab kam zuciyarsa kamar ta fito waje, ji yake kamar ya makeni da duka. Mun siyo kayan shayin mun dawo cikin asibitin naji ana cewa."Ƴan mata." kamar nasan murya, amma duk da haka naki tsaya wa, duba da yanayin yawan mutanen dake wajen bai zama lallai ni din ake kira ba. "Ƴan mata, bakya jina wai." a ka sake fada kusa dani, da alama mutumin yazo inda muke. A hankali na waigo idanuna suka sauka a kansa, daya cikin matasan da suka zo layin mu jiya, suka tambayi Gidan Alhaji idi me mai. Wanda baiyi magana sosai ba, ina tuna lokacin da yace. "To ina ne gidan naku?." Murmushi nayi masa sanan nace."Ina yini." shima murmushin yayi, cikin zazzakar muryarsa yace. "Lafiya kalau ƙanwata; me kikeyi anan?." "Ɗan-uwan mu ne ba lafiya, aka kwantar dashi anan." "Ayyah, Allah sarki muje na duba shi." Wani irin abu naji a zuciyata, amma kuma baxan iya masa musu ba, hakan yasa na ce. "Toh muje." jerawa mu kayi muka fara tafiya, Walida ta shige gaba mu kuma muna baya, duk naji nayi wanan fiyau. Ya cika wajen baki daya, a raina na ce. "Idan wanan yace yana so na, wallahi sai nayi sadaka, sabida yana da kyau, gashi ɗan gayu, mai aji, murya mai zaƙi. Nipa an gama tashin kai na." A haka muka ƙara so daƙin, walida ce ta ce. "Bari na sanar da su." gyada kai yayi, ni kuma naji ni a ta kure. Ban yarda da abinda Walida za ta ce ba, hakan yasa na ce. "Bari na bi ta." "A'ah ki jira mana." kallonshi nayi, idanuna sunyi wani kala na ce. "Ban san me za ta ce ba." "Mai kike tsoro to?." "Za fa ta iya ce musu, Saurayina ko wani abu." Murmushi yayi, sanan ya ce. "To menene a ciki, ko ki na da wani saurayin ne?." ƙasa nayi da kai na, ba tare da na ce komai ba. Shi kuma ya ƙara cewa. "Ko akwai ne." girgixa kai kawai nayi, dai-dai lokacin da Walida ta fito. Sai a lokacin na fahimci cewa, kofar bata yin ƙara idan a ka bude ta, shine yasa dazo banji lokacin da ummanah ta buɗe ba. "Ku shigo." ta faɗa, ni kam kamar munafuka haka na zama. Idanunsa a rufe yana kallon sili muka shigo, Maman ciki ce ta. "Ga waje mana basai ka xauna a ƙasa ba." "A'a Mama bari na zauna anan; ina kwana, ya mai jikin." "Lafiya ƙalau, mai jiki da sauƙi." su ka amsa tare. "Allah ya ƙara lafiya." "Amin, Mus'ab ga baƙo fa." Mama ta faɗa, a hankali ya buɗe idonsa ya sauke su akan mu, kasancewar ya tsugunna kusa da inda nake zaune. Kallo daya ya gane fuskar gayen, wa'yanda yaganni dasu jiya, tasowa gayen yayi zuwa idan gadon yake, tare da mi ƙawa Mus'ab hannu sukayi Musabaha."Ya ƙarfin jikin?." "Alhamdulillah." Mus'ab ya fada a da ƙile. "To Allah yaƙara afuwa." "Amin." "Zan huce, Allah yakara lafiya." "Amin-Amin, an gode." Su Umma suka fada, shi kuma ya nufi ƙofa. Walida ce tayi magana da ƙarfi yanda kowa zaiji."Salma kije ki raka shi mana." kamar mara laka haka na tashi, ina raba idanu nayi waje. A bakin ƙofa na tarar dashi. "Salma..." ya faɗi sunan, tare da ja cikin wani irin salo mai dadi. Sai naji kamar shi kadai ya iya kiran sunana. "Zan tafi, ngde da kulawa. Sunana Masrur, sanan wanan asibitin na mahaifina ne, kuma yana karkashin kulawata saboda haka, an dauke muku komai." "Mun gode, amma da ka barshi dan wallahi ban san ta yadda zan fadawa iyayena haka ba." "Salma..." ya ƙara kiran sunan na, a nutse na ɗago na kalleshi. "Ina sonki." Kara ɗagowa nayi na kalleshi, idanunsa suna kaina, da sauri nayi kasa da nawa a raina na ce."nima ina sonka." amma afili kuwa shiru nayi na kasa cewa ko uffan."Bazan ta kureki ba, zanbaki lokaci kiyi tunani. Ga lambata nan." ya faɗa yana miƙomin wani kati, hannu nasa na amsa sanan nace. "Nagode." ka ɗa kai yayi ya tafi, ni kuma na koma ciki. Kamar wata ɓarauniyar da tayi sata aka kamata haka na shiga cikin ɗakin. Sai dai duk cikinsu babu wacce tace da ni ko uffan, hakan yasa nayi matuƙar damuwa. A hankali na ce."Umma, mai walida ta ce muku?." banza Umma tayi dani kamar ba taji ni ba, kuma nasan taji, hakan yasa na koma ga Mama. "Mama mai walida ta ce?." "Mai kikaji wani yace miki?." Na girgiza kai na ce."Bakomai." "To kuma, ko kinyi wani abun ne?." na girgiza kai kawai, can 'yan mintina na ce. "Walida ta so mu tafi." ba ta kai ga magana ba likita ya shigo ɗakin. Bayan sun gaisa yace da su Ummah. "Ban san wane likita ke duba Mus'ab ba, kuma ko ma wane akwai matsalal da ba daga likitan mu take ba, dagashi yaron ku take." "Matsala kuma likita?." Mama da Ummanah suka tambaya, har wani hade baki sukeyi. Ni kam a raina na ce. "Allah yasa matsalal mutuwa ce." maganar likitan ce tasa na dago na kalleshi. "Eyh matsala, domin gaskiyyya ba aina hin ciwon dake damunshi ake fada ba, kuma da masaniyar sa domin ko magungunan da ake bashi, na asalin ciwon sa ne. Kunga kuwa sun hada baki da likitan suna ɓoye muku. Wani daɗi naji a raina, domin nasan babban ciwon ne kadai ake boyewa iyaye ba'aso su ji sabida kadan hankalinsu ya tashi. "To yanzu likita wane ciwo ne, na gaskiyya dan Allah." Ummanah ta fada kaman zatayi kuka, wani ƙululun abu ya tsayamun a ma ƙoshi yanda matarnan ta damu da Mus'ab ko ni bata damu dani ba, ji yanda take magana kaman zatayi kuka. Abban ciki ne yayi sallama, tare da Kawu mudi da kuma Yaya ilyasu. Shigowa sukayi baki dayansu, nida walida muka koma can gefe muka basu basu waje, kasancewar dakin babbane. "Kai ka sa tsohuwar mutane cikin damuwa." Yaya ilyasu ya faɗa. Likitane ya ci gaba da cewa."Kamar yanda na fada muku, matsalal shi ba ciwon kai bane kwata-kwata." da sauri Abban ciki yace. "To menene?." "Matsala shi a ciki take." "To amma mai yasa duk bayanan ku na baya yake nuna kai." "A'ah ranka yadaɗe, ko a file na asibiti cike ne, sanan magungunan da yake sha ma na ciwon ciki ne, kawai su na ambatar kai ne domin ɓoye muku." Ina daga gefe na fara addu'ar, Allah yasa afendes ne yanda za'a yanka shi karshe a ce ya mutu. "To yanzu likiti menene cutar?." Abban ciki ya ƙara tambaya, Likitan ne ya fara duba takardun hannusa, nikam hankali na kanshi. " I need you to stay calm, please. Cutar tashi ba wata babba bace, amma kuma lokutan da ta dauka a jikinshi ta kara girma. "Doctor, kana firgita mu Menene matsala?" Legends pen. (08165383931/ 08129553971). Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000. Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* SHAFI NA BIYAR (P.05). بسم الله الرحمن الرحيم " I need you to stay calm, please. Cutar tashi ba wata babba ba ce, amma kuma lokutan da ta dauka a jikinshi ta kara girma. "Doctor, kana firgita mu Menene matsala?" " He have been diagnosed with a rare condition called Hypersexual Hormonal Disorder HHD. It means His body produces an unusual level of sex hormones beyond control. That’s why kake yawan jin wani irin zafi, idan kana ciwon cikin. Kuma irin wannan sha'awar ba irin wacce ake iya da ƙilewa ba ce,da ƙile ta da yayi na kwanakin baya yasa ta zama babba har haka." "Wannan wace irin cuta ce haka, nifa bangane komai ba?." Mama ta tambaya cike da ruɗani. "Nima dai." Ummanah ma ta faɗa. Yaya Ilayasu ne, ya kallemu ni da Walida yace."Ku fita." Sim sim sim kamar munafukai muka fice, ni dai burina a ce mutuwa zaiyi. Bayan munfita ne likitan ya kalli su Mama yace. "Yana fama da wata irin cuta mai suna Hypersexual Hormonal Disorder. (HHD). Ma'ana jikinsa yana fitar da wani nau'in sinadarin sha'awa fiye da kima. Wanan ne dalilin da yasa yakw yawan jin wani irin zafi, da kuma wata sha'awa mai ƙarfi wacce har ta kan iya kayarda shi ƙasa." "Inullahi wa'inna illahir rajiun." su Mama suka shiga maimaitawa, likitan yakara da cewa."Tun farko bai bari anyi dogon bincike ba, a kan rashin lafiyar tashi, gashi har abun ya zama worst haka, ko kunyar ku yake ji oho." "To amma fisabillillahi, ko da yanajin kunyar mu bashi da 'yan uwa maza. Kawai sabida rashin kula da lafiya." Ummanah ta fada cike da damuwa. "To yanzu likita menene ai nayin maganin cutar?." Abban ciki ya tanbayeshi. "There’s no drug-based cure yet. But in most studied cases, emotional stability and natural intimacy especially within marriage. help the body regulate the hormones over time. Auren na iya zama magani a gareshi." "Shikenan likita, insha Allahu za'ayi." Abban ciki ya faɗa, likitan yakara da cewa."Yanzu za'a rubuta mishi drugs da zai na amfani dashi, zasu taimaka sosai da sosai." "To mungode." Ummanah ta fada, likitan yasa kai ya fita, Mus'ab kam idonshi a kulle angama to na mai asiri yanzu kowa sai yasan halin da yake ciki. "Yanzu fa Mus'ab da ka mutu d Wanan ciwon, baka da maraba da wanda yakashe kansa, kasani kuwa." Maman ciki ta fada murya a sanyaye, Ummanah ta dora da cewa. "Mus'ab, a duniyar nan babu kamar iyaye, ba'a ɓoye musu komai domin kowacce mafita tana daga garesu, ka bar ganin mun girma har mun haifi kamarku, duk wata matsala idan tataso mana, idan har mijinmu bazai iya magance mana ba, to iyayen mu muke nufa da ita." Tashi Abban ciki yayi ya fice, domin yasan duk abinda zai iya fada, Maman ciki da Ummanah zasu faɗeshi. "Kuyi haƙuri..." ya faɗa cikin sanyin murya, Ummanah ce tace. "Dan Allah ko dan gaba ku kiyaye baki ɗayanku." "Tom insha Allahu." Yaya Ilyasu ya faɗa, sanan yace dasu Ummah. "Jiya masu neman auren Sadiya sun sake zuwa, a kace dasu sudawo yau." "Lallai ne, Sadiya lokaci yayi." Maman ciki ta fada, inda Yaya ilyasu yace. "Saura Walida da kuma Salma, su kam kamar ma ba za su kai candy ba." "Eyh kam, bazasu kai candy ba." Ummanah ta fada, Maman ciki tayi murmushi. Can sai ga Abban ciki ya shigo,rike da ledar magunguna. " Gashinan, suma sai kayi wasa da shan su." Maman ciki ta amsa ba tare da ta cw komai ba. "Ni zan koma gida, zan samu Hajja nayi mata bayani, Muji abinda zata ce." "Tom shikenan."Maman ciki ta fada, shikuma yasa kai ya fice. Muna zaune daga gefe ya fito, da sauri muka taso tare da cewa."Abba zamu tafi muma." "A'ah ku xauna mana, ko za kuyi musu wani aikin." "Ai Abba zamuyi girkin rana, sanan mu na da islamiya." na fada sabida ni hankali na, na kan na koma gida nayi sadakar alewa, zan kaɗeɗen saurayi kamar Masrur ya ce yana so na, shine sabida nice nafi kowa butulci ba xanyi sadaka ba. "Shikenan ." ya fada tare da fita, Walida ce ta koma daki tayi musu sallama, nikam bayan Abba nabi sabida tsoron karma ya tafi ya barmu. Muna ƙarasawa gida na sauka nayi ɓangaren mu, ban ƙarasa ba naji muryarshi na cewa. "Ki cewa Abbanki ya same ni ɓangaren Hajja." "Thom." na ce sanan na ci gaba da tafiya, shi kuma ya juya ga walida. "Kira mun sauran kawunnanki." itama "Tho." ta ce, ta tafi kiransu. Ina shiga na tarar da Abbanah ya gama shiryawa. "Abba mun dawo." "Toh sannu da dawowa, ya jikin na sa?." "ya warke." na faɗa a gajar ce, sai kuma na ƙara ce wa. "Abban ciki, ya ce ka same shi ɓangaren Hajja." "Ya dawo?." "Eyh, shine ya dawo da mu." "Okay." daga haka ya fice, ni kuma nayi cikin ɗaki. A ɓangaren Hajja kam, gaba ɗayansu ne zaune sun sa Hajja a gaba da kallo. "Ni wai lafiyan ku?, kun haɗu kuma kun bini da idanu." Hajja ta faɗa, sai kuma ta ce. "ko dai Mus'abu ne ya mutu?." "A'ah Hajja, ba mutuwa yayi ba amma akwai matsala." "Tsarin ubangiji muke nema a kan kowacce matsala." Hajja ta faɗa, Abbanah kuma ya ce. "Yanzu Salma ke ce mun ya warke." "Eyh hakane, su za su ga kamar ya warke. Amma a bayanin da likita ya yi mana, ya ce ba cutar ciwon kai ba ce ke damun Mus'ab tun farko, ya ɓoye mana ne." "Waye ya ɓoye mana?." Abbanah ya faɗa cike da fushi, dan shi a tunaninshi likitan ne yanzu ya je suyi ɗauki ba daɗi, dan duk gidan Galadima babu wanda ya kai Abbanah fushi, da zafin zuciya. "Shi Mus'ab ɗin." "Innullahi wa inna illahr rajiun, yanzu wace cuta ce haka zata kashemun jika na, ɗan lele nah?." "Mus'ab, na fama da wata cuta wai ita Hypersexual Hormonal Disorder. (HHD). Ma'ana dai jikinsa ya na fitar da wani nau'in sinadarin sha'awa fiye da kima. Shi ke haifar masa da wanan ciwon cikin." Kuka Hajja ta saki tare da faɗin."Nashiga uku na, shiyasa nake ce wa yaron nan cike ke masa ciwo ba kai, sabida idan ciwon yayi zafi ciki ya ke riƙewa ba kai ba. Amma ya ce wai A'ah, yanzu idan ciwon ya kashe shi ina yake so na sa ka kaina." "Kiyi haƙuri Hajja." kawu Mudi ya faɗa. Abban ciki ya ɗora da cewa. "A yanzu likita ya ce hanyar samun sauƙi guda ɗaya ce, ayi masa aure." Abbanah ne ya ce. "Abinda ke raina kenan, dama ai akwai yarinyar da ya ke nema ko?." gyaɗa kai Abban ciki ya yi, sanan ya ce. "Amma ya na da kyau idan anje neman auren a sanar da iyayen komai." "Salan su hana shi, to wallahi ba da yawo na ba." Hajja ta faɗa. "Yaya ba fa cewa sukayi ya na da Mentel disorder ba, kuma ba cewa su kayi ya na sa yawan buƙata ba. Dan haka wanan ai ba matsala ba ne." Abbanah ya faɗa, Hajja ta cafeshi da ce wa."shine dai, yanzu ina so ku tashi daga nan kuyi gidan iyayenta a ba su komai da komai harda sadaki." "Shikenan, amma ni ai babu ni za'a je ko?." Abban ciki ya faɗa da alamun tambaya ga Hajja. "Uhmmm." ta faɗa a gajarce, sai kuma ya ƙara cewa. "Su ma masu neman auren Sadiya fa?" "Naga dangin Mahaifiyar ta ne, ɗan gidan Yayar Mahaifiyarta uwa ɗaya uba ɗaya. Ba najin sun cancanci a hana su, duba da Mahaifinsa kowa yasan shi, tarbiyar gidansu ba ɓoyayye ya baci." Abbanah ya faɗa. "Sanan yaron yana zuwa nan sosai da sosai, haka mahaifiyarsa." Itama Hajja ta faɗa. "Shikenan, sai a ba su watanni. Amma kuna ganin za' a haɗe dana yaron nan." "A'ah kar ku fara, banason auren sa ya huce wata biyu fa." Hajja ta faɗa cike da damuwa. "Shikenan." kawai suka ce sanan suka fice, dole sai sunyi tasu shawarar a waje. Ina shiga cikin ɗakin mu, nayi ɓangaren Ummanah. Ƙasan kayanta na shiga du bawa, nasan nanne wajen ajiyar kuɗinta. Cikin sa' a na gano su, naira dubu daya na dauka na ƙara da ɗari biyar cikin canji mota na, na fita siyo alewa sadaka. Shagon bayan gidanmu na je, na siyo lolipop mai tsinke, har leda biyu a cewa ta "idan zaka gode wa Allah, ka gode ma sa da babban masaki sai ya ƙara ma ka da wanda ya fi wanan girma." Ina dawowa harabar gidan mu, na fara ƙwalawa yara kira ina faɗin."Sadaka, sadaka." cikin ƙan ƙanin lokaci yara su ka fara ta ruwa cikin gidan mu. Daga na cikin gida har na waje, ni kuwa faɗi nake. "Duk wanda ya karɓa ya ce Allah yabar ƙauna." ai kuwa da sun amsa za kiji suna cewa. "An gode, Allah ya bar ƙauna." na cafe da. "Amin." abuna, zuciyata shar, Allah ya bani zankaɗeɗen saurayi da ga sama. Walida ce ta fito wajen da na ke sadakar, ta kalli ne ta ce. "Sadakar mecece haka kuma?." Jin wani yaro ya ce. "Allah ya bar ƙauna, yasa ta bi ni da idanu, ni kuwa na murje na ce. "Menene a ciki?." "Ce wa yayi yana sonki?." ta tambaye ni. "Ba ke uwar munafukai ba, a faɗa miki kije ki ya ɗa mutum." "Ya za'ayi na ya ɗa ki?." "Walida da ban san halinki ba." na faɗa ina ci gaba da sadaka ta. "Wallahi ba zan fada ba." "To ce wa yayi ya na so na, har da ba ni lambarsa." na faɗa hankali kwance. "Lallai ne, ki na cikin Alheri. Kin san Sadiya ma an ba da ita?." "Naji ƙishin-ƙishin dai." Na faɗa, ni dai hankali na na kan 'yan sadaka. Ganin kamar ta ji babu daɗi ya sa na ce. "Yanzu ke ma sai ki yi wa, Haidar magana kawai a kwashe mu." "kina ganin Haidar zai yi aure yanzu?." ta tambayeni cike da damuwa. "Mai zai hana shi tun da ya na sonki, ko ma ba za yi ba menene a ciki. Sai ki bawa wasu dama." "Ni kam na fi sonshi." "Sai ki zauna ki jirashi, ni dai wallahi ko yanzu a ka ce za'a ɗaurawa Masrur ne bin shi zanyi, na zauna na yi uban me a gidan?." Na faɗa ina murguɗa baki, kamar gaban iyayen nawa nake. Ƙarar tsayawar Napep ya samu ɗagowa tare, Su Ummah mu ka gani. Wani irin abun naji tsurum a zuciyatah, ga uban ledar alewa a hannuna, ga yara sun zangaye ni su na faɗin."Allah ya bar ƙauna." Legends pen. (08165383931/ 08129553971). Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000. Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* SHAFI NA SHIDA (P.06). بسم الله الرحمن الرحيم Ƙarar tsayawar Napep ya samu ɗagowa tare, Su Ummah mu ka ga ni. Wani irin abun naji tsurum a zuciyatah, ga uban ledar alewa a hannuna, ga yara sun zagaye ni, su na faɗin."Allah ya bar ƙauna." Sakkowa su ka fara yi daga cikin Napep ɗin, idanu na suka sauka a kan sa, a raina na furta. "Ya dawo bai mutu ba." na ja tsakin da ya fito fili, har Walida ta kalle ni, sai kuma na sake ce wa. "Kai ka ɗai dai za ka ci tsiyarka, ni kam lokacin ta shi na daga gidan Galadima ya yi." "Sadakar me a ke yi kuma?." Umnanah ta tambaya, bayan sun ƙaraso inda muke tsaye. Buɗe baki nayi zan fara wa'in- wa'in yaron da yake gaba na ya ce. "An gode, Allah ya bar ƙauna." da sauri nayi ƙasa da kai na, ban san da wane ido ne zan kalli Ummanah ba, Maman ciki kam ce wa tayi."Ƙaunar wa?." Shiru mu kayi nida Walida, nasan dai Walida ganin ina wajen yasa ba ta faɗi komai ba, amma da ba na wajen tuni ta shai da musu. Ummanah ce ta ce."Ku shigo da kayan." sanan ta huce, Maman ciiki ma ta huce. Ido nasa na kalleshi, wata irin tsanarshi mai nauyi ta durga a ƙirjina, ni ke nan ba zanyi masa mugun fa ta ya kama shi ba, duk da haka ba zan gaji ba."Allah ka gama shi da masifar duniya da ta lahira." na sake faɗa ina daukan kayan. Ɓangaren Hajja suka nufa, mu kuma mu kayi bangarensu. A raina naji dadin dawowar Ummanah, ko ba komai zan ɗauki wayarta na kira Masrur. Ban daddara ba, na mai da lolipop ɗita jakar islamiya ta, a ce wa ta idan na fita nayi sadakar a bata, dan wallahi sai na nunawa Allah godiyata da yabani kyakyawan saurayin kamar Masrur. Ƙarfe ɗaya da rabi nayi shirin Islamiyya, bayan na ɗau jaka ta na fito falo na ce da Ummanah. "Na huce." tsaya ki mika wa Mus'ab doyar nan. Turɓune fuska nayi sanan na ce. " Na ma kara fa." "To sai kin kai, ko abinda ya fi makara kika yi. Wai ni Salma yaushe ne zaki dai na yi wa Mus'ab wanan ƙiyayyar ne?." "Au ni ce nake ƙinsa?." Na faɗa a raina, a fili kuma na ce. "Ni ba ƙinsa na ke ba, kawai ba na son kowacce kalal alaƙa ta haɗa ni da shi." "Sabida ba ɗan-uwanki ba ne ko me?." "Umma kawo na kai."Na faɗa domin son tsayar da waccan maganar. "Salma ba fa ke ce kika haife ni ba, kin san da haka?." shiru nayi, ni ba na son a ci gaba da maganar, domin har cikin rai na ba na son wani abu da ya shafi Mus'ab a rayuwata. Ina tsaye ta gama soyawa ta miƙo mun."Sa a plast ki miƙa mai." ban ce uffan ba, na ɗau plast ɗin na zuba. Ga ba daya na juye a plast din na kama hanya na fice, na fito daga ɓangarn mu zan nufi ɓangaren su na ga Sadiya ta dawo. Washe baki nayi da faɗin. "Ka ga amarya, shine kika kwashe ƙafa ki ka tafi, wato sai da a ka ce an basu shine ki ka dawo." Dariya tayi sanan ta ce. "Wallahi dazu Amina ta ce mun, Mal isah ya ce sai ya ɓallani, shine ki ka ga na kwaso ƙafa na dawo." Dariya nayi sanan na ce."Ba kunya ki ka tafi gidan su saurayi ki ka zauna." "Yoo kunyar wa zanji, ina shan zumar ƙauna." ta fada ta na fari da ido."Uhm bari na mika wanan ɓangaren Hajja, amma kafin nan tsaya ki amshi sadakar ki." na fada ina a jiye plast ɗin a ƙasa. "Sadakar me?." ta tambaya ne da mamaki. "Allah ya kawo mun masoyi, na kece rai ni." Na faɗa ina miƙa mata alewan."Ki ce mun kusa barin gidan Galadima." "Mun kusa fa." na fada ina hucewa, ita ma tayi bangarensu. A hankali nayi sallama, amma ba'a amsa ba hakan yasa na shigo ciki kai tsaye. "Yanzu Mus'ab da wanna ciwon ya kashe ka fa?." Naji muryar Hajja na faɗa. Ahankali na ji ya yi magana cikin sanyin muryarshi."Hajja ai ina shan magani, ba zai kashe ni ba." "A'a nidai Mus'ab, gwanda kawai ayi auren nan. Irin wanwn ciwon na ku, aure ne kadai mafita." Nan take kwakwalwata ta gano mun cutar da ke damunshi, kuma gashi ɗazu naji likita ya ce tayi Worst. "Chaɓ, irin su ne muke ji a Novel kenan? Wa'yanda matansu ke ramewa sabida yawan sha'awarsu." wata muguwar dariya ce ta tawo mun da ƙyar na iya tare ta, sabida tinawa buduruwar da zai aura nayi kamar tsinken sigari haka ta ke. "Sai dai ta koma tsinken kwa-kwa." na fada a fili, ina dariya ƙasa-ƙasa na shigo dakin. "Baki iya sallama ba." Hajja ta fada ta na hararata, nima hararar na mayar ma ta sanan na ce. "Kun can kuna hirar ku ai ba za ku ji ba." "Ke dalla me yasa baki da hankali." hararar na mayar kanshi, sanan na ce. "Ni ce ma kai." azabure ya ta so ya yo kai na xai da ke ni. Hajja tayi saurin riƙeshi, tare da fadin. "A'a Mus'ab na hana ka." Koma wa yayi ya zauna ya na haki. "Ai da ka dake ni, wallahi sai ka yi da nasani, domin yanzu Allah yakawo mun mai tsayamun, wallahi Mus'ab idan ka dake ni har kotu sai mun je." Na faɗa tare da ajiye plast ɗin na juya. "Lallai yarinyar nan tabbata ki ke ji, to wallahi zaki zo ki same ni." Hajja ta faɗa, shi kuma ya ce. "Da kin barni na ɓallata." "A'a Mus'ab, ka dai na wanan saurin hannun." Shiru yayi bai ƙara ce wa komai ba. Ni kam ina fita na kaɗa kai na yi makaranta abu na. A hanya nai ta yiwa yara sadaka, haka 'yan ajinmu. Duk wanda na bawa sai na ce ya ce."Allah ya bar ƙauna." Kasancewar Ajin mu ba daya dasu Walida ba, ya sa ban fiya tsaya su tafiya ba. Allah bashii dawowa ma, ita kam Halima ba ma islamiyar mu ɗaya ba, ita hadda ta ke yi. A haka na shigo cikin layinmu, zuciyata fes sai dai ƙara hango Musrur da nayi ya ƙarawa zuciyar ta wa haske, a nuste na ci gaba da tafiya har inda ya ke. Da mayalwacin murmushi a fuskar sa ya tare ni da faɗin."Sannu da dawowa ranki ya daɗe." Wani sanyi na ji da ya ce ranki ya daɗe. "Yawwa sannu, Yallaɓai." na faɗa sabida kar na ce ranka ya daɗe ya zama kamar na kwaikwaiye shi gwanda na zo da sabon salo abuna. "Uhm, i apprecite this name." "You deserve it." na mayar mai cikin harshen turanci nima, domin ban son ya ga gazawa ta, ta kowanne fanni, domin yasan bani ka ɗai nayi sa'ar samunshi ba, shima ya yi sa'ar samu na. "So how was the school." "Alhmadulilah Yallaɓai, how was your work." "Everything great, ya mai jiki." "Jiki gashi can ya na fama." Na faɗa, in i don't care, ban son ma ya sake mun maganarshi. "Tun ɗazu ina ta expecting kiranki." Murmushi nayi kafin na ce."Ina ta jiran Ummanah ta dawo da ga asibiti kafin na kira." "Ouh, bakya da waya!?." Ya fada da mamaki ƙarara a fuskarshi. Sai naji na zama wata kala, dama bance ba. "Yaka ma ta na sama miki." Da sauri na girgiza kai. "Abbanah duka ne zai yi, kaba ri with time za'azo lokacin da zaka bani." Murmushi ya yi sanan ya ce. "I'm so glad to have you in my life." Ƙasa na yi da kai na, sanan na ce."Same here." Kamar an ce Salma juya, idanu na suka sauka a kan shi, a raina na ce. "Ko uban me yake yi a nan, oho." "Fulani, wanan kamar mara lafiyan nan ko?." "Fulani.." na sake maimaita sunan, ya masifar yimun daɗi. Na ma manta da abinda ya tambaye ni. "ko ba shi ba ne?." ya sake tambayata. "Yeah, shine." Na faɗa. "Oh ya warke sosai, gida ɗaya kuke kenan?." "Uhm, family house ne." Na bashi amsa, ni ban son maganar wan can Mutumin. "But you look alike kamar blood brother na ki." da sauri na girgiza kai sanan na ce. "Godforbid, cousin brother ne." Dariya ya yi sanan ya ce."Mene na Godforbid ɗin?." "Ni kam, i really hate this Mus'ab, mahaukaci ne fa ɗa zu fa ce wa ya yi wai zai dake ni." nan da nan ya haɗe rai, sanan ya ce. "Du ka kuma?." Na ɗaga kai sanan na ce. "Ai bashi da hankali." "Da'alama faa." shima ya faɗa. "Yallaɓai bari na shiga gida, Ummanah na jira na." "Okay, Fulani take good care I love you." "I love you too." Na faɗa tare da juyawa da sauri, har na kusa shiga gida ya ce."Am, Fulani kar ki manta ki kirani faa." Daga kai kawai nayi na huce, Mus'ab na tsaye bakin gate nazo zan huce, sai da na kalleshi wata sabuwar tsanar ta sake dirga a raina, sanan na ce. "Allah ubangiji ba danni ba, ba dan Halina ba, ba dan laifuka na ba, ka gama Mus'ab da katuwar Masifa ko iya duniya ne, masifa wacce za ta azbtar da shi." Legends pen. (08165383931/ 08129553971). Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000. Ranar litinin zamu fara posting paid pages, posting kullum, za'a fara siyar da complt ma ranar litinin, zaku iya fara payemnt tun yanzu Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931 *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* SHAFI NA BAKWAI. (P.07).. Sanarwa! Ranar litinin zamu fara posting paid pages, posting kullum, za'a fara siyar da complt ma ranar litinin, zaku iya fara payemnt tun yanzu Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. بسم الله الرحمن الرحيم "I love you too." Na faɗa tare da juyawa da sauri, har na kusa shiga gida ya ce."Am, Fulani kar ki manta ki kirani faa." Daga kai kawai nayi na huce, Mus'ab na tsaye bakin gate nazo zan huce, sai da na kalleshi wata sabuwar tsanar ta sake dirga a raina, sanan na ce. "Allah ubangiji ba danni ba, ba dan Halina ba, ba dan laifuka na ba, ka gama Mus'ab da katuwar Masifa ko iya duniya ne, masifa wacce za ta azbtar da shi." "Ke wai baki san wanan masifar da like jawa Yaya Mus'ab ba, Mala'iku su na amsa da ce wa Walaki ba." Kallon Sadiya da ke zaune kan doguwar kujera a falon mu nayi sanan na ce. "Wallahi Sadiya ni dan ta tawa mai sauƙi ce, indai har Mus'ab zai shiga Masifar da nake masa fata." "A'ah, dan Allah ki rage wanan muguwar tsanar." "Wallahi Sadiya duk safiyar ubangiji, wata sabuwar tsanar Mus'ab ke huda zuciyata." "Allah ya kawo miki sauƙi."Banza nayi da ita, sanan na miƙi zuwa ɗakin Ummanah. Wayarta da ke jikim chaji a soket na je ɗauka, amma ƙwalam ba ta nan. "Nasan tana dakin Abbanah, bari na je na ce tabani zanyi karatu." Na faɗa a raina tare da fice wa. Ban kai ga ɗakin ba naji muryar Ummanah na ce wa. "To yanzu zuwa yaushe zaku jira su?." "Eyh, zamu jira su zuwa sati ko fi. Dole dai idan su ka gama shawararsu su nai me mu." "Nima amma Alhaji, ciwon yaron nan ya mugun damana, gani nake kamar zasu ɓata mana lokaci. Kasan Likitan yadda ya nuna, yana buƙatar aure cikin gaggawa fa." "Gaskiyya ne, ciwon nan na shi na buƙatar iyali kusa-kusan nan, Allah dai ya bamu yadda zamuyi." Abbanah ya faɗa, dai-dai lokacin da nayi sallama. Ummanh ca ta amsa da faɗin. "Salma shigo ma na." shigar nayi kaina a ƙasa, sanan na ce. "Ummanah ina son nayi karatun hadda, idan babu damuwa." "To ai wayar na ɗaki." "A'ah Umma, ba ta jikim soket." "Eyh, ba nan na ajiye ba. Ki duba gefen fulo." Tashi na yi a raina ina ce wa. "Ko mai yasa ban duba nan ba oho." wani ɓari da ga zuciyata ya ce. "Rabon kiji wanan maganar ta su." afili na furta. "Mene haɗi na da maganar." kasancewar babu mai ba ni amsa, ya sa nayi shiru na ci gaba da tafiya zuwa ɗakin mu. Wayar na gefen gadon, hakan yasa na ɗauka na fara loda lambar ta shi, wacce tsabar yawan dubawa yasa na hadda ce ta. Bugun farko ya ɗaga wayar, kamar ya san ni ce ya fara magana. "Fulani barka da dare." idan na ce banyi mamaki ba, kuma kusan ƙarya ne. Domin yadda ya kira sunan da ƙarfin gwiwarsa, irin yana da tabbacin ni ɗin ce."Ba ita ba ce." Na faɗa ina murmushi. "Haba Fulani, tun kafin ki kira zuciyata ke cemun Next call is your future wife." Murmushi nayi sanan na ce. "Yakake?." "Not good." ya bani amsa, a ɗan tsorace na ce. "What's going on." "Fulani I'm missing you, so badly." "Same here, Vida mia." "Oh what a sweet name, amma naji dadin sunan." kunya ta ka mani, na ce."Amma Fulani yafi daɗi." "No, wanan ma yayi daɗi i really appreciate it." "Thanks you." na fada, cikin ƙarewar magana. "Fulaninah." Sassanyar muryarshi ta sake faɗa. "Vida Mia." Nima na faɗa, cike da sabuwar soyaya, a raina ina cewa. "Ni kam na dace, a rayuwar soyayya, domin Masrur ko babu ci babu sha, zan zauna dashi ko dan kyakyawar fuskarsa. Duk da Walida ta ce wai rawar kai ce, amma nafishi kyau." "Fulani, ina da tarin tambayoyi." "Tambayoyi kuma?." Na faɗa kai tsaye. "Yeah Fulani, amma ba tambayoyi masu damuwa ba, na soyayya ne." Murmushi nayi sanan na ce. "Tom ina jinka." "Fulani mai kika fara ji ranar da kika ganni." Shiru nayi ina sauraron zuciyatah. A hankali na fara ce wa."Ina zaune a harabar gida, na ji kamar ana kirana a waje, na tashi na fito, idanuwa na suka sauka a kan ka. Kyakywar farar fuskar ka ce ta fara burgeni." sai kuma nayi shiru. "Ci gaba mana Fulaninah." "Shikenan." Na faɗa, shi kuma yayi dariya. "Ni kam Fulani idan na faɗamiki ranar da na fara ganinki za ki yi mamaki sosai." "Yaushe?." Na tambayeshi. "Fulani, wajen 3weeks back. Na gan ki ke da ƙawayenki, kun dawo daga school. Tun lokacin na fara bin ki, ina ganin ki." Murmushi nayi mai sauti sanan na ce."Kasan maganar da nayi da ku, sai da Mus'ab ya ja a ka dake ni." "Fulani, wai mai kika yiwa Mus'ab ne?." "Nima ban sani ba, kawai dai na san ya tsane ni, nima haka." "Amma ya kama ta ku daina haka, ba kya ganin yadda kuke kama ne." "Ni kam har abada ba zan so Mus'ab." "Nima bance ki so shi ba, amma ku fahimci juna." cike da jin haushi na ce."Ko da a kwai wani abu da fahimtar juna dashi za ta yi mun?." "Ɗan-uwan ki ne fa." "Dan Allah mu bar maganar shi haka." Na fada kamar zanyi kuka."Shikenan, yanzu tambaya ta gaba. Mutum nawa kika yi dating kafin ni?." Shiru nayi ina son tuna wa, sai kuma na ce."Wani yaro ne Hafiz, tun muna aji biyu a islamiya daga baya kuma mu ka rabu." "Faɗa kuka yi?." Ya tambaye ni. "A'a, kawai yau da gobe da kuma girma." "Okay, Wa kika fi so a ƙawayenki?." "Ai ni bani da ƙawaye da suka huce 'yan uwana, Walida da Sadiya." "Wacece wacca nagan ku tare a asibiti?." "Walida, na bashi amsa." "Okay, yanzu yi mun naki kafin na ciga ba." "A wacce unguwa kake?." tambayar da ta fara zuwa bakina ba tare da na shiryawa fitarta ta ba. "Gwari avenue." Na girgiza kai, alamun naji."Akwai wata?." ya tambayeni, na ce."Eyh, mai ya baka kwarin gwiwar zuwa layin mu." "Zuciyatah." Dariya nayi sanan na ce."Na gama." "Ina da wasu masu yawa, amma naga dare yayi." "Uhm." Na faɗa, sabida bana son wayar ta kare. "Ki kwanta, sai Allah ya tashe mu. Kisani ina matuƙar ƙaunarki." "Nima haka." Na faɗa tare da gyara kwanciyatah, fuska ta ɗauke da murmushi ya katse wayarshi. Haka na kwanta ina ta murmushi, kamar wata sabuwar kamun hauka. Washe gari.. Da sassafe na tashi, sabida ina son zuwa boko duk da ba wani abu ake mana ba, sabida muna Ss2 ne kuma anyi exam ɗin third term har angama. Boko dai ajin mu ɗaya da Sadiya, amma Walida ta na Science ne, ni da Sadiya Muna art. Ita sadiya ma commerce take, kawai wasu subject ɗin mukeyi tare. Ni dai na ce ba zan wahalal da kaina a kan Karatun boko ba, dan yanzu ba wani aiki a ke samu ba, gwanda na karanci har kar kasuwanci abu na. Zaune nake a cikin class, na ware gefe na zauna hirar mu da Vida mia nah ta na dawomun ina murmushi ni kadai abu na. Safiyya ce ƙanwar Samira wacce Mus'ab zau aura ta shigo ajin mu, wata muguwar dariya ce ta tawo mun, ganin ta na tafiya kamar cokali. To a haka ma tafi Samira ƙiba, ga mamaki naga ta na yo inda nake, kau da kai nayi daga saitin inda take tawo wa."Salma Galadima." ta faɗa, bayan ta ƙara so inda nake, cike da haɗe rai na ce. "Ya a ka yi?." murmushi tayi sanan ta ce. "Lafiya ƙalau, ai yanzu mun zama 'yan uwa." "kun dai zama 'yan uwa, ni mene alaka ta da ku, har da wanda zaku aura." "Ai ko ba komai ɗan uwanki ne ko." "Kinga Safiyya, tashi ki bani waje." Na faɗa a tsawa ce, saukar da murya tayi sanan ta ce."Kiyi haƙuri, tambayar ki na zo yi fa." "Me zaki tambayeni?." "Dan Allah Kifaɗamun gaskiyya, nasan ba kya ƙarya kuma ba za kiyi ba." kallonta nayi sanan na ce. "Wai me zan fada miki." "Nasan kin san Mus'ab su na soyayya da Samira, to amma tun farko ba wata soyayya ba ce ta a zo a gani, dan bai taɓayi ma ta maganar aure ba. Kawai dai soyayyar tasu ta bazo ne, kowa ya sani to kwatsam su Abbanku su ka zo da maganar aure, bayan su Babban mu sunyi shawarar ba shi, sai ga wani zance ya fito. Wai Mus'ab yana dauke da wata cuta, kuma duk macen da ya aura za ta sha wahala a kan wanan cutar tashi, dan Allah ki faɗamun gaskiyya, nasan ba zaki ɓoye ba, sanan kin san Yayata ba wani kiɓa gare ta ba, kuma wallahi ba xan taɓa cewa daga bakinki na ji ba, ko a gidanmu." Legends pen. (08165383931/ 08129553971). Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000. Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ SHAFI NA TAKWAS. (P.08). بسم الله الرحمن الرحيم "Nasan kin san Mus'ab su na soyayya da Samira, to amma tun farko ba wata soyayya ba ce ta a zo a gani, dan bai taɓayi ma ta maganar aure ba. Kawai dai soyayyar tasu ta bazo ne, kowa ya sani to kwatsam su Abbanku su ka zo da maganar aure, bayan su Babban mu sunyi shawarar ba shi, sai ga wani zance ya fito. Wai Mus'ab yana dauke da wata cuta, kuma duk macen da ya aura za ta sha wahala a kan wanan cutar tashi, dan Allah ki faɗamun gaskiyya, nasan ba zaki ɓoye ba, sanan kin san Yayata ba wani kiɓa gare ta ba, kuma wallahi ba xan taɓa cewa daga bakinki na ji ba, ko a gidanmu." Tsuru-Tsuru nayi da idano, tabbas nasan komai da ta faɗa gaskiyys ne, Amma idan na fad'a mene makoma ta, nayi munafunci, ko nayi taimako?. "Wallahi, Salma ba zan ta ɓa cewa a bakin ki naji ba." Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke, sanan na ce."Kin san bani da alak'a kyakyawa da Mus'ab, abubuwan shi ba su shafe ni ba, kuma ba na saka kaina, domin nasaka SAKATA na kulle duk wata ƙofa da za ta had'a wani abu tsakani na da abinda ya shafi Mus'ab." "Nasani, Amma ba zaki rasa sani wani abu a kai ba, bani zaki yiwa ba Salma, 'yar uwata da rayuwarta." Shiru nayi ina tunani a cikin zuciyata, mai zai sa na ɓoye gaskiyyar nan, mene ruwana da tonan asirinsa, idan ma na rufa mai aairi ban tsane shi ba, gwanda na to na masa asiri ko mutuwa ne ma yayi, karewa. "Duk abinda na fad'a miki, idan har kika fad'awa wani ni ce na fad'a miki. Ubangiji ya gama ki da Masifa a rayuwa." da sauri ta gyad'a kai sanan ta ce. "Na yarda wallahi, babu wanda zaiji ke ce kika fad'amun." "Eyh, tabbas Mus'ab na dauke da cutar da ni kaina ban ma san sunan ta ba. Amma ta danganci iyali, itace wacce ke sa mata su rame sosai. Yanzu shigowarki zaki ga ina dariya, ganin ki ne yasa na tuno yayarki shine nay dariya." Shiru tayi, ni kam sai a lokacin na tu na ɓaranɓaramar da niya, daman ni a kwai mugun surutu, da fad'i ba a tambayeka ba."Shikenan na gode, kuma insha Allahu babu wanda zai ji maganar nan da ga bakin ki ta fito." "Shikenan na gode." daga haka ta tashi ta fice, ni kuma na maida hankali kan abinda nake kafin ta shigo. Haka na zauna a jin sukuku, idan wani ɓangarena zuciyata ya nuna mum abinda nayi ba dai-dai ba ne, sai wani b'arin ya ce. "Kinyi d'in, shi dai-dai yake miki." Muna tashi daga makaranta mu ka yo gida, ni dai burinah naje nayi waya da Vida.mia nah, ya fi mun wanan zancen Mus'ab ɗin. Sai dai ina shiga ɗakin Ummanah ta aika ni ɓnagren sa, na kai mai Abinci. "Wai Ummah ke ce kike da haƙƙin ciyar da Mus'ab ne?." Wani banzan kallo ta watsa mun wanda ya sani ficewa, ni ban san me Mus'ab kewa Ummanah ba ta ke mugun son sa haka. Ɓangaren Hajja na fara zuwa, bakina ɗauke da Sallamah na shiga ɗakin na ta. Ciki-ciki ta amsa mun, ni kam bai dame ni ba. "Ya na nan?." "Waye?." ta tambayeni, kamar ba ta san wanda nake nema ba. "Mus'ab." na faɗa a daƙile. "Allah magani maƙoci maye ni uwar su Yunusa matar Galadima, wanan yarinyar baki yi ba wallahi." "Yana nan?." Na sake fada. "Yana ɓangaren uwarsa." Murgu ɗa baki nayi na huge, har na fita sai naji ban kyauta ba, Hajja fa ba ita ta kemun abinda Mus'ab ke mun ba, dawowa nayi na ajiye plast ɗin sanan na zo inda take na zauna."Hajja." na kira sunanta. "Na'am Uwatah." ta faɗa. "Hajja, kin ware mutum ɗaya cikin jikokin, kin nuna shi kaɗai kike so, kika damu da shi, kuma hakan kan haifar da tsana cikin zuri'ar ki." kallona tayi sanan ta ce. "Salame ai ni kin nuna mun ban isa da ke ba, kin nuna mun ke ware cikin jikokina, sabida kin dauki tsanar duniya kin ɗora a kan wanda kika kamar na damu da shi." ganin Hajja ba zata fahimci abinda na ke so ta fahimta ba, yasa na kwashe ƙafafuna nayi waje. Ji nake kamar kar na shiga ɓangaren nasu, sabida nasan Maman ciki ba ta nan, walida kuma ba ta dawo ba, har na kai bakin ƙofa wani ɓangarena na zuciyata yace da ni."Yanzu fa yunwa yake ji, kuma yana jiran abincin nan, ke baki da hankali zaki kai masa yaci yayi maganin yunwar, kinga fa kin taimakeshi kenan." Da sauri na ce."Allah kar kasa ko rana daya na zama mai taimako ga Mus'ab." ina fadin haka na canja hanya zuwa ɓangaren su Sadiya, a zauren su na ɓoye plast din kar a gani, nasan da zarar angani topa sai nai kai mai. Sadiya na zaune tsakar gida na shiga, washe baki nayi ganin wayar Anty a hannunta, a fili na ce. "Antyn ba ta nan?." "Yanzu ta je gidan Anty Nadra, wai ta kawo kayan kitchen." "Su amarya, ni ɗan a ramun minti ɗaya nayi waya." Na faɗa, ban jira cewarta ba na dau wayar, a zuwa yanzu na haddace lambar Masrur tas a kaina, kira na danna bayan na loda lambar. Kamar ko yashe bugu ɗaya ya ɗauka tare da faɗin."Fulani nah." Wani sanyi naji a raina, sanan na ƙara yardarwa raina Masrur soyayyar gaskiyya yake mun, domin dana kirashi yake gane nice. "Na'am Vida mia." "Fulani, yau nayi kewarki sosai." "Nima haka, na si kiranka da safe amma ban sami lokaci ba har na tafi makaranta." "Nima Fulani na tanadi morning messages ɗina, sai kuma na tuna wayar Ummanah ce." dariya nayi jin ya faɗi Ummanah kamar yadda nake faɗa."Me ya baki dariya haka?." ya tambayeni, murya cike da so da ƙauna, wanda ban san lokacin da na fara gane su ba. "Wai Ummanah, irin yadda nake faɗa." Dariyar yayi shima sanan ya ce. "To ba Ummnah ba ce." da sauri na ce. "Eyh, Ummanah ni kaɗai." "Wallahi ban yadda ba." ya faɗa kamar zaiyi kuka, dariya yabani, ai kuwa na shiga yin abata babu ko ƙaƙautawa, sai da na gama sanan ya ce. "Dariya kike mun ko?." shima dai kamar zaiyi kukan. "Ni kai ne ka ban dariyan." "To me nayi na baki dariya?." "Kana magana kaman za kayi kuka." "To ai kukan zan miki, tun da kina rabani da Ummanah." "Ni dai ba zan baka Ummanah ba gsky." na fada, kuka har cikin raina da gaske."Shekrar ki nawa?." Naji ya tambaye ni. "Sha takwas da wata ɗaya." dariya yayi sanan ya ce. "Menen wata ɗaya?, sha takwas kawai hajiya." "Hajiya kuma?." na tambayeshi."Eyh mana, Hajiyata, Fulanita." "Wai nikam suna nawa ne da ni?." "Dubu biyu." ya bani amsa, kamar yasan tambyar da zan masa kenan. "To faɗo su muji." "Tom ki shirya." "Na shirya ai." Na bashi amsa a matse. "Fulani." "Ɗaya." yayi dariya sanan ya ce. "Gimbiya." na c e. "Biyu." ya k'arayin dariya, sanan ya ce. "Mai gadon zinare." "Uku." "ki daina lissafawa." na ce. "Thom." "Habibiya, Hajiya, Uwar 'ya'yana, Matata, mai ɗaki na, abar ƙauna, wacce nake so." Dariyar da nayi ce ta tsayar dashi. "Mai ya baki dariya?." Shiru nayi sanan na ce. "Duka kuma wa'yanan nawa ne?." "Ai baki taaya na gama ba." bude baki nayi da niyar yin magana, naji sallamar Anty, sai a lokacin na tuna inda aka aiki ni, da sauri na ce."Kasan aike na akayi?." "Ta ina zan sani baki fad'an ba, ina zaki." "Wai Mus'ab a ka ce na kaiwa abinci, tun ɗazu." "Maza-maza tashi ki kai ma sa." Tashi nayi ina fad'in. "idan na dawo zan kira ka, ko a wayar Ummanah ne." Sanarwa! Ranar litinin zamu fara posting paid pages, posting kullum, za'a fara siyar da complt ma ranar litinin, zaku iya fara payemnt tun yanzu Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. ci gaba "Shikenan sai anjima, love you." A jiye wayar nayi tare da fitowa, kai tsaye nayi ɓangarensu. Da sallama na shiga ɓangaren na su, sanin Walida ba ta dawo ba, kuma tun safe Maman ciki ta fita yasa na nufi ɗakin na shi, yana zaune kan kujera yana faman lallatsa da laptop ɗin shi, daman kowa yasan Mus'ab da aiki da na'ura, domin ko aikin da ya ke yi na na'ura ne. Suna da babban kamfani, wanda suke aiki da na'ura mai kwakwalwa sanan ma aika cin farin kaya ne, na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC. Ciki-ciki nayi sallama, yayi kamar bai ji ni ba, nima kuma ban sa ke maimaitawa ba. Ajiye plast ɗin abincin nayi tare da juyawa, sai dai kiran suna na da yayi yasa ni tsayawa, ba tare da juyowa ba."Ke Salame." bantaɓa jin ya faɗi suna na ba, idan an tambayeni ma zance ba lallai yasan sunan, ashe shima salamen yake cewa, sunan da na tsana. Ƙin amsawa nayi jin Salame ya ce, na ci gaba da tafiya. "Ba da ke nake ba." ya faɗa a fusace amma cikin sanyin murya. "Ai ba suna na Salame ba." Na faɗa, zuciyata namun wani tuƙwiƙi domin ko kalma ɗaya bana ƙaunar ta haɗani dashi. "Ke ya dama wanan, ɗauki tsintsiya ki sharemun ɗaki." a wane sukwane na juyo nayi mai wani kallon. "Kana shaye-shaye ne?." Ganin ina ta kallonsa, idanu na kamar sa faɗo ƙasa tsabagen harara ne yasa shi cewa. "Ba da ke nake ba, ko baza kiyi ba ne?." "Wallahil azeem ba zan ba." na faɗa a fili, kallo na yake cike da mamaki, rashin kunyar tawa har ta kai nan kenan?."A karo na ƙarshe, ki ɗau tsintsiya ki sharemun nan." "Mitcheww." naja wani dogon tsaki, tare da yin gaba. Sai dai ban kai ƙofa ba naji an riƙomun hannu, ina juyowa a ka ɗauke ni da mari, wanda nima banyi wani dogon tunani ba, na ɗauke shi da nawa marin. Sai ƙarar ya bada Tas! Tas Legends pen. (08165383931/ 08129553971). Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000. Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* SHAFI NA TARA (P.09). بسم الله الرحمن الرحيم "Mitcheww." na ja wani dogon tsaki, tare da yin gaba. Sai dai ban kai ƙofa ba na ji an riƙo mun hannu, ina juyowa a ka ɗauke ni da mari, wanda nima banyi wani dogon tunani ba, na ɗauke shi da nawa marin. Sai ƙarar ya bada Tas! Tas. Da mugun mamaki ya ɗago ya kalleni, ni kuwa sai haki nake kamar wata zakanya, banyi au ne ba kuwa naji ya kwarfeni da ƙafarsa na faɗi ƙasa Tim!, ai kuwa ya bini da duka. Ya fusa ta iya fusa ta, nima kuma na fusa ta iya fusa ta domin baki na bai mutu ba, faɗi na ke. "Shege, mugu, azzalumi, kuma wallahi zai ka ga gatana, wallahi sai munyi shari'a da kai." shi kuwa duka na ya ke amma da ƙafa, cikin sa'a na riƙe kafar ta sa, na gan tsara masa wani mugun cizo, kuma nak'i ci kawa har sai da na had'o da fata, da sauri ya janye k'afar tare da matsawa, nan take zuciyata ta ce mun. "Faɗan bai k'are ba." ai kuwa na tashi da mugum guda na ɗane bayan shi kamar wata biranya, na shiga gantsara masa cizo a wuya, shi kuwa faɗi ya ke. "Baki da hankali ne?, sauka a kai na." Salatin da Ummanah ta saki ne ya sa jiki na wani irin mutuwa, kirjina ya shiga bugawa da k'arfi-k'arfi. "Sannu 'yar biri." sai a lokacin na fara ƙoƙarin dirga ƙasa, idanunta suka kai kan ƙafarshi da ke fitar da jini, ga kuma shatun haƙorana a wuyansa. "Kashe shi zakiyi kenan." miri-miri nayi da idanu tare da fad'in. "Ina shigowa ya kifa mun mari." Ba ta ko kula ni ba ta shigo ɗakin tare da kama hannuna ta shiga jana a ƙasa, kamar kayan wanki. "Nashiga uku na lalace." kawai nake iya fad'a a raina domin nasan yau na bushe har hanjina. "Ummanah dan Allah kiyi haƙuri, wallahi shine ba shi da gaskiyya, wai sai na share masa d'aki daga na ce bazan share ba shine ya mare ni." Sai da na fad'a kuma, na tuna ɓaran-b'aramar da nayi, ni a rayuwata kwata-kwata ban iya ƙarya ba, komai gaskiyya nake fad'a kai na tsaye. "Shine kika fara gantsara masa cizo ko, ke ga mahaukaciya, karya ko?." "Wallahi Ummanah ba haka ba ne, mari na yayi." ban ƙarasa rufe baki ba, naji saukar mari tare da bulala, ina ihu ina kororoto amma Umma ƙara zanbad'a mun ta ke. Daman Ummanah kwata-kwata ba ta iya duka ba, duk lokacin da ta dake ni sai tayi mun rauni, shi yasa Abbanah yayi mun fad'a kan na kiyaye abinda zai ɓa ta ma ta rai, to lokacin da ta da ke ni ma na ƙarshe a kan Mus'ab ne, kai Mus'ab ya zama masifa a rayuwata. Tun ina kuka da bata haƙuri, har na yi shiru gaba ɗaya duk wani ƙarfina ya ƙare, sai da ta ga ji dan kan ta sanan ta kyale ni tare da fice wa, ta bar ni kwance ina kuka. Nayi kusan minti goma a zau ne, zuciyata na ta saka mun abubuwa kala-kala, ta ce mun "in je ina bu ga masa dutse a kai, sai dai ko mene ayi mun.", ta ce mun."In je in ƙa re mai tana di, zagi ta uwa ta uba" ko hakan zai kawo karshen zumuncin nan." abubuwa kala-kala, ƙarshe na yanke mafita guda d'aya na tarka ta na bar gidan baki daya, na je gidansu Masrur ko a 'yar aiki ya kai ni, daga baya mu yi aurenmu. A b'angaren Ummanah kam, ta na ga ma duka na ta nufi ɓagarensu Mus'ab, ya na zaune kan kujera ya rasa mai ke masa dadi, sallama tayi d'akin ya amsa. "Yanzu kai Mus'ab yarinya k'arama za ka tsaya har ta mare ka, ba ka b'abbalata." "Ummah kiyi hak'uri, bana son na dake ta nayi mata rauni." "Da ba ka ballataba, ai ko shi Abban na ku idan yazo ya ji abinda ta yi sai ya ɓallata, kuma ya na dawo zan faɗamai." "Ummah dan Allah kiyi hakuri, laifina ne da nasa ta sharar." "To wallahi daga yau, har zuwa ranar da zaka bar gidan nan ita zata ke maka sharar ɗakin, kuma ka ci abinci idan zaka ci." ta faɗa ta na ta shi, alamun shi ma ya ɓata ma ta rai,a tsakar gida su ka haɗu da Maman ciki, ganin yanda ran Ummanah ke haɗe Maman ciki ta ce."To mai kuma ya faru da 'ya'yan naki?." "Bari ke dai, lamarin Salma ya fara isa ta, yarinyar nan kullum rashin arziƙinta ƙara gaba ya ke." "Salma yarinya ce fa har yanzu, wai bakya tuna lokacin da aka haife ta ne?." wata harara Ummanah ta watsa Maman ciki, sanan ta ce."A'a ban haife ta ba, yawo nake da ita a ciki." "Allah yabaki haƙuri, yanzu ta na ina?." "Ta na can ta na jinyar jikinta." daga haka Ummanah ta huce, tabar Maman ciki da sakkaken baki, ɗaki ta nufa ta ajiye jakar ta tare da shiga bayi, sauri-sauri take ta fito tazo ɓangaren namu. Ni kam tun da na yanke shawarar barin gidan, na shiga haɗa kayana, bayan na cika akwatina sanan na jawo wata katuwar jaka na shiga zuba wasu kayan ciki, har da jaka da takalmi na. Bayan na gama na shiga d'akinta, inda take ajiye kudinta na nufa, naira dubu uku na dauka, sai kuma nayi tunanin dubu uku tayi mun yawa, nan da Gwari avenue baifi 2500, haka yasa na ajiye dari biyar na fito, ina kokarin janyo jaka da akwati na ta shigo, kallo na kawai tayi ba tare da ta ce."Ci kan ki ba." ta huce ciki, ni kam na ci gaba da jan kayana. Ina daf da bakin ƙofa naji an cafke ni, juyuwar da xanyi na ganta da wayar charger ta computer Abbanah, ba wata-wata ta hau zabga mun, ni kuma ina rusa ihu. Mamam ciki ta shigo da sauri ta na fad'in."Innullahi wainna illahir rajiun, Menene haka dan Allah?." "Barni na targad'a yarinyar nan, nayi mata rau ni." "Kiyi ma ta rau ni, sabida me, haba dan Allah." Nikam narkewa na ƙarayi a jikin Maman ciki, ina faɗin."Wallahi sai na bar gidannan ba za'a kasheni ba." "kiyi shiru ke kuma." Maman ciki ta faɗa, Ummanah kam ajiye bulal tayi tare da shigewa ɗakin, kallona Maman ciki tayi sanan ta ce. "Je ki mai da kayan, kuma kar ki sake irin wanan abun ko da wasa." "Wallahi Mama bazan ko ma ba, duka na zata ci gaba, ni kawai a bar ni." "Ki je ki mayar na faɗa mi ki." Maman ciki ta sake faɗa. "Wallahi ko kin mayar sai na dake ki, kuma har can ɓangaren zan zo." Kuka na fara, maman ciki ta ce. "To ai ba ɓangarena zan kai ki ba, muje." tunda ta ce haka, ɓangaren Hajja zata kai ni. Ai kuwa can ɗinne, Hajja na gani na haka ta fara sababi. "Amma wanan uwarta ki ba ta da hankali, to wallahi ahir ɗinta." Ni kam wata tsanar Mus'ab ce sabuwa ta sake fidda rashe a cikin zuciyata, a kan shi anyi mun dukan da ba'a taɓa kwatanta mun ba, an kira mahaifiyata sa mara hankali, duk a kan Mus'ab, kai Mus'ab ya zama tauraruwa mai wutsiya a inda nake." Maman ciki ce tai ta ba Hajja haƙuri, sai da ta ga tay shiru sanan ta ta shi ta tafi. "Tashi ki haɗa ruwan ɗumi." Hajja ta faɗa tana kallona, bayan fitar Maman ciki, ba musu na miƙe nayi Kitchen, a heater na ɗora ruwan ɗumin, sai da yayi sanan na sauke na shiga na watsa ruwa, naji daɗi sosai a jikina, na zo nabi lafiya kujera na kwanta, banko sassauta da tsinewa Mus'ab, har bacci ya ɗauke ni. Sai wajen la'asar sanan na tashi, zaune na ganshi kan ɗaya kujera dake kallon tawa, amma hankalinshi na kan wayarsa yana dannawa, inaga ma baisan ni ce kwance kan ɗaya kujerar ba, miƙewa nayi ina turu baki, ina hararshi ƙasa-ƙasa, Allah ya gani na tsani Mus'ab, bana ko ƙaunar ganinshi domin a yanzu na fuskanci Mus'ab so yake ya rabani da Ummanah, domin a kwanciyar nan ta wa na ƙara tabbatar da hakan, indai nasamu saɓani da Ummanah tofa a kan lamarin Mus'ab ne, ko mene ribarsa oho, wani ɓari na zuciyata ya ce. "Mutumin da baya sonki, mene ribarsa idan bai rabaki da iyayenki ba?." a fili na furta. "Kurwata kur, mai ɗa ya ci ɗanshi mara ɗa ya ci ƙoƙon tsuliyarshi." Wani kallo ya watsamun, sanan ya ci gaba da danna wayarsa, nima na mayar mai da kallon da hausawa suke cewa. "Harara a duhu." tun da bai san inayi ba. Bayi na shiga na ɗaura alwala, na fito na ta da sallah, har na kamalla yana zaune, yana danna waya."Mai bautar waya." na faɗa a raina, tare da shiga ɗakin da Hajja ke ciki. "Hajja abinci." Na faɗa daga tsaye. "Ke fa matsalata dake rashin kunya da rashin mutunci, haka ake yi a gidanku." na cuno baki gaba sanan na ce. "Ke kuma matsalal ki mita da sababi." "Nayi mita nayi sababin, na rantse yanzu zaki ficemum a ɓangare." Shiru nayi nasan zata aika, kaddam ne daga aikin Hajja."To yanzu Hajja mai zan ci?." "Shiga kitchen, ki dafa taliyar yara ina da ita lodi-lodi." Kicin ɗin na nufa, na shiga haɗa indomie na, ina mamakin yadda Hajja ke cin indomie, a yanzu haka akwai sama da katan biyar a cikin kicin ɗin, ina tsaye har ta kamalla, na juye a faranti na dawo falon, yana nan zaune kaman mutun-mutumi, yana faman bautar waya. Bayan na ajiye na shiga ɗaki, nayi narai-narai da fuska na ce. "Hajja tawa." Baki buɗe take bina da kallo, kamar ta ga sabuwat hallita. "Hajjana, dan Allah wayarki zaki bani, na kira malamin mu na sanarshi bani da lafiya ya sa banzo ba." ita Hajja ba ta wami damu da waya ba, kuma kullum wayarta cike da katin waya, haka su Sadiya za su zo da Walida suyi ta ɗauka suna kiran samarinsu, ni kam bantaɓa ba sai yau, ko da yake yanzu na fara soyayyar. Dawo falon nayi, sabida naji ana cewa."Waya sa saurayi kana cin ainci tafi tsargawa." Nan da nan na danna masa kira kamar ko yaushe, sai dai yau kiran na shiga ya katse, kafin na gama tantance mai ya faru naga kiranshi ya shigo, murmushi nayi tare da kai lomar indomie baki na, bayan na ɗaga kiran."Fulani mai lambobi da yawa." Ya faɗa bayan na ɗaga."Mijin Fulani, mai gane Fulani a ko yaushe." Na faɗa cikin wani irin salon magana, dani ban ma san na iya ba, ko dan Mus'ab na nanne? Oho mun. "Fulani, yau kuma wayar wa aka samu?." Ya tambaya cike da kulawa kamar ko yaushe."Wayar Hajja ta ce." Na bashi amsa cikin cool voice, wanda ni dai ban san lokacin da na iya ba."Uhm, Ummanki, Hajjanki, to ni wai wa za'abani?." "Salma Galadima mana, ita za su baka, ni dai kabarmun Hajjana, da Ummanah." "Ai kam na barsu, tun da zasu bani abinda nafi ƙauna." Dariya nayi na ce."Zasu baka mana, mussaman Ummanah." "Yau mai Fulani ke ce?." Dariya na ƙarayi, sanan na ce. "Indomie ɗin Hajja na dafa." "Yau kina ɓangaren Hajja ne?." "Can zan kwana, ƙilama na dawo nan." "Kai Fulani, ai Umma ba za taji daɗi ba." "Uhm, zataji mana. Ai yanzu munafukai sun shiga tsakanina da ita." Dariya yayi, har ana jiyo sautin shi sosai ta waje, sanan ya ce."Fulani munafukai kuma." "Uhm, munfukai masu bacci da ido ɗaya." Na faɗa ina ƙara kai indomie bakina, gaskiyya na yarda waya da saurayi ana cin abinci tafi tsargawa."Su waye haka to?." ya tambayeni. "Na ce maka masu bacci da ido ɗaya." "Su ba su da suna?." "Uhm..." "La'ila ha ilallahu muhammadu rasulillahi, amma Salame baki da mutunci, Mus'ab ɗin na zaune kika saka taliyar yaran gaba kika cinye, shi dayake kawo wa baki zuba masa ba." Muryar Hajja ta tare ni daga niyar bawa Masrur amsa, dariya yayi ta cikin wayar tare da ce wa. "Fulani sai anjima." ban iya bashi amsa ba ya kashe wayarsa, sakamakon wani abu da yatsayamun a maƙoshi yaki tafiya, jin wai Mus'ab ke kawo wa Hajja indomie ɗin da nake ci yanzu, yau nice naci abinda Mus'ab ya kawo. Da wani mugun sauri na tashi na nufi banɗaki, domin kwararar da indomie din da naci, amma ina ciki na yariƙe ta katamau, duk yunƙuri na amai yaƙi fita, a dole na wanke bakina na koma ɗakin, ina ta faman cika da batsewa."Ke lafiyanki?." Hajja ta tambayeni. "Haba Hajja ai sai ki ce mun ga wanda ya kawo indomie ɗin, amma kika barni na ci haram." "Uwariyanki Salame, abincin ne haram?." "Habba Hajja, Haba Hajja ni dai baki kyauta mun ba." Sallama Babban ciki naji, sai kuma Abbanah ya na ta faman faɗa, ban ma iya ƙarasa tantance abinda yake faɗa ba, na tashi nayi ɗakin Hajja da nasan Ummanah ce ta faɗa masa abinda nayi ya zo ɓallani. "Har mu mutanen nan zasu mayar ƙananan mutane, har mu za'ayi wanan cin fuskar." Abbanah yake faɗa, shi dai Babban ciki yayi shiri ya zauna kan kujera, Alhaji ƙarami da kawu Madu ne suka shigo sai Yaya ilyasu, babu Abinda nake tamaimaitawa a raina sai. "Innullahi wa inna illahir rajiun, yau kashi na ya boshe. Duka wanan taron a kai na." "Lafiyanku wai?." Hajja ta tamabaya, bayan su gama zama. "Iyayen yarinyar da Mus'ab zai aura ne suka aiko, wai sun gano yana da wata cuta dan haka sun fasa bashi aurenta." Legends pen. (08165383931/ 08129553971). Daga gobe zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000. Payment via. 8129553971 OpaY Sani Muhammad lawan. Shaidar biya. 08165383931. *SAKATA*❤️⚓️ 🌻Stroy and written🌻 By Sayyid writer (Legend)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* SHAFI NA GOMA (P.10). بسم الله الرحمن الرحيم "Har mu mutanen nan zasu mayar ƙananan mutane, har mu za'ayi wanan cin fuskar." Abbanah yake faɗa, shi dai Babban ciki yayi shiri ya zauna kan kujera, Alhaji ƙarami da kawu Madu ne suka shigo sai Yaya ilyasu, babu Abinda nake ta maimaita wa a raina sai. "Innullahi wa inna illahir rajiun, yau kashi na ya bushe. Duka wanan taron a kai na." "Lafiyan ku wai?." Hajja ta tamabaya, bayan su gama zama. "Iyayen yarinyar da Mus'ab zai aura ne suka aiko, wai sun gano yana da wata cuta dan haka sun fasa bashi aurenta." Wani irin dum! Naji a ƙirjina, a fili na furta"Na shiga uku." dan tsorona kar naji an faɗi sunana, ance ni na faɗa. "Shikenan sai sun kashe mun jikan, sai sun raba shi da duniyar, Mus'ab idan ka mutu ina zan sa kai na, ina zan sa rayuwata." Hajja ta faɗa tana matse ƙwalla, Abbanah ne ya ce."Hajja ki yi haƙuri dan Allah, iyayen yarinyar nan ba su kyauta ma na ba, kuma sun nuna su ƙananan mutane ne, amma zamu ɗau mataki a kan hakan." Abbanah ya ƙarashe maganar da alaman karaya, zuciya ta ce ta tsinke lokaci guda, ganin fuskar Abbanah da ta Hajja a haka, ga Abbanciki da Alhaji ƙarami sun zuba ta gumi, kawu Madu da Yaya ilyasu tsaye carko-carko,"Duk ni naja wanan abun." na faɗa a rai na. "Yanzu ya za'ayi kenan?." Hajja ta faɗa ta na ci gaba da kukan, Ummanah da Maman ciki sai Anty mamansu Walida ne suka shigo su ma, idanun Ummanah sunyi jawur, kamar ni a kace ba za'a ba wa Masrur ba, ina ga ma tayi kuka. Zama su ka yi su ma, Hajja ta sake maimaita abinda ta faɗa, cikin sharɓar hawaye. "Hajja zamu sake bashi zaɓi idan yana da wata, sai muje mu nema mai, idan babu sai aduba cikin 'yan Uwa." Abbanah ya faɗa, ni da ke cikin ɗaki na ce. "Sai dai ko can waje, ko ku bashi Walida da ke ƙanwarsa, tunda dai Sadiya an ba da ita, ni kuma ga Masrur abu na, daman ita ce soyayyarsu ke ƙasa na dabo." "Nikam Abba ba ni da wani zaɓi a yanzu." Mus'ab ya faɗa, wani kukan Hajja ta ƙara saki, sanan ta ce. "Shikenan, ya cire rai da auren. Ubangiji ka wadaran yarinyar nan da iyayenta." "Hajja kiyi haƙuri,amma ni ina da shawara." Ummanah ta faɗa."Kai Umma kin fiya shiga abinda ba ruwanki." na faɗa daga can inda nake a cikin rai na. "Wace shawara ce haka?." Hajja ta tambaya, zama Ummanah ta gyara sanan ta fara magana. "Mus'ab dai ɗan mune na gida, kuma tun da wanan maganar ta fara fita ta na zaga gidajejen wa'yanda a kaje nema masa aure, to haka za tai ta zagayawa, ƙarshe ko ina su hana bayan an gama tozarta shi." "Hakane wallahi, abinda yake ta faman sani kuka kenan." Hajja ta tare Ummanah, Abbanah kuma kallon ummanah ya yi sanan ya ce. "To mai kike gani?." Shiru ta yi na 'yan mintina, sanan ta sauke wata ajiyar zuciya. "Mai zai hana mu haɗa aurensa da Salma, tun da muna da ita a cikin gida, kun ga dai Sadiya har anyi mata bai ko, ita kam ina ga ko saurayi ma ba ta dashi." Ai ban san lokacin da nayi wani tsalle ta tagar Hajja na dirgo falon, sai gani kamar wacca aka jefo. "Wallahi Ummanah ina da saurayi, ina da wanda na ke so, ko Hajja za'a tambaya yanzun nan na gama waya dashi, a gaban ma shi Mus'ab ɗinne, dan Allah kar ku auran Mus'ab." Gaba ɗaya na rikice, na manta a gabansu wa nake, haka shima Mus'ab, ji yake ana magana kamar ihu, amma kwakwalarsa kam dai ta ɗauke, babu abinda yake nanatawa a ransa sai. "Ummah karki yi mun haka, bana son yarinyar nan, natsane ta, bana ko son ganinta." Abbanah ne ya da ka mun wata tsawa, wacca ta sani haɗiye maganar da nake shirin yi, amma jikina sai karkarwa yake, hawaye na bin kuncina, zuciyata na wanu irin tsalle kamar zata fito waje. "Amma Allah yayi miki albarka da wanan shwarar." Hajja ta faɗa ta na murmushi."Har mu za'ayi wa hulaƙanci, jikoki 27 Allah yabani, ba a isa a hulaƙantani kan ɗaya ba." Hajja ta sake faɗa, Abban ciki kam cewa ya yi. "Tabbas wanan shwarar tayi, sai dai yakama ta a duba ita yarinyar." "Har wani haƙƙi take dashi, da ya huce ta yi mana biyayya." Abbanah ya faɗa cike da ɓacin rai, dan shi maganar da Abban ciki yayi ma ta ɓata masa rai."A'a Yaya, a duba yarinyar nan." Alhaji ƙarami ya faɗa. "Yanzu idan ace yarinyar wajenka na nemi ayi wa haka, cewa zakayi a'a ko me?." Hajja ta faɗa kamar zata yi kuka."Ni Hajja ba haka nake nufi ba, kuma kin sani da Mus'ab da Salma da kowane yaro dake cikin gidanan, ɗaya nake ɗaukansu, bantaɓa banbanci su a kan komai ba, Sabida haka na taso naga yayuna sunayi, duk cikin mu wanda bai godewa Abban ciki da Abbah ba sai Allah ya saka musu, tun tasowar mu suke tsaye a kan mu, har zuwa kan yaranmu dan haka bana banbance tsakanin 'ya'yansu da nawa yaran, amma Hajja ki kalli yanda Salma ke yi, a bata damar idan wanda take dashi ɗin ya dace, sai a bawa Sadiya Mus'ab ɗin." "Ai har gwanda sadiyan." Mus'ab ya faɗa, bayan ya dawo daga suman da yake."Ni kam Alhaji ƙarami sai nake ganin kaman Salman ce ta fi cancanta, domin ita nata saurayin da take iƙirarin tana da shi, bai ko taɓa zuwa ya gaida ku, bare kuma mu Mata, sanan idan har Salma ba ta taimaki ɗan uwanta ba, wa zata taimaka?." Ummanah ta faɗa, shiru Alhaji ƙarami yayi, sai kuma a lokacin Kawu Madu ya ce."Tabbas hakan yayi, kuma wanan shine amfani da ranar zumunci da zaman lafiya, mu ɗin ahali ne guda, a kullum burin mahaifinmu mu zama tsintsiya ɗaya, gashi Allah ya amsar addu'arsa ta hanyar bamu mataye na gari, nima ina goyan bayan wanan abun." Maman ciki dai ba ta iya cewa komai ba, tabbas tana farin ciki da hakan, kuma ta ƙara yadda Ummanah macece ta gari, sai dai kuma tana tausayina, domin ta san ba na son Mus'ab kuma shima bai so na. "Yanzu zuwa yaushe za'asa ɗaurin auren?." Abban ciki yayi magana, wani irin ihu na saki tare da zubewa ƙasa, domin nasan tun da Abban ciki yayi na'am da maganar to fa sai dai wani hukunci na ubangiji fasa wanan auren. Shi kan shi Mus'ab ji yake kamar ya ƙwalla ihun, dan yana buƙatarsa sosai."A haɗe shi da na Sadiya wata biyu." Abbanah ya bashi amsa. "A'ah wallahi, tun da ita ta gida ce sati uku ko biyu ya isa, domin kusan ba lafiya ba ce dashi." Hajja ta faɗa."Hakane kam Hajja, ni a ganina kwana goma sha huɗun zaifi." Ummanah ta bawa Hajja amsa. "Shikenan, Allah ya nuna mana." Abban ciki ya faɗa, tare da tashi, haka kowa ya tashi sai a lokacin Maman ciki ta kula da cewar bana numfashi, da sauri tayo kaina tana faɗin. "Yarinyar nan fa ta suma." Dawowa su kayi kaina, banda iyayen mu maza da suka fice, Anty ce ta samu ruwa ta bawa Maman ciki ta shafa mun, can bayan 'yan mintuna na sauke ajiyar zuciya tare da buɗe ido, suka sauka a kan Ummanah, ai kuwa na tsala ihu tare da tashi zan fice, da sauri suka riƙeni har da ita Ummanah ɗin, turza ƙafa kawai nake bana iya magana. "Innullahi wa'ina illahir rajiun." kawai Hajja ke maimaitawa, kowa yayi shiru sai karatu da ake mun, tunaninsu Aljannu na tayar, nikam kawai zafin ƙiyayya ce, ta samun harda haushin Ummanah, domin zuciyata babu abinda take nuna mun sai, zallan tsanar da Ummanah tayi mun, gwada kawai na bar musu gidan, son da nake su daina karatun yasa na tsaya da abinda nakeyi, hakan yasa suma su ka tsaya. "Dan Allah kar ku auran Mus'ab, bana son shi, Ummanah mai yasa ko da yaushe kika zaɓi ki ba ƙanta mun." Saukar marin da naji a fuskata ya sa nasaki wani fitsari mai mugun zafi, da gudu na ƙara kwasa zan fice, Mamman ciki ta roƙoni. "Nutsu Salma, idan aka barki ina zakije da gudun." Shiru nayi ina kallon tare da zazzaro idanu, kamar wata karya. "Ku kyaleta da gidansu, yanzu zan saka a ɓaɓɓalamun ita wallahi." Hajja ta faɗa tana hararata. "Kuma wallahi Mus'ab ne, insha Allahu sai kin aure shi, kinyi biyayyar aure, kin haifa masa 'ya'ya, wanan rashin zama ƙarƙashin inuwa ɗayan naku, bi'izinillahi sai ya zama Alheri a rayuwar ahalin gidan Galadima." Wani mugun Haushin Hajja yazo ya dirja a ƙirjina, gaba ɗaya na rasa menene yake mun daɗi, kukan ko shirun?."Tashi muje." Umanah ta faɗa a tsawa ce, tashi nayi kamar mara laka a jikina, ji nai iska na ƙoƙarin dauka na tayi wurgi dani, dan gaba daya na koma 'yar tsurut. A waje muka ci karo da su Walida sun tawo da gudu, ban ko kallesu ba nayi ɓangarenmu, suka rufamun baya har zuwa cikin ɗaki. "Salma mai ya faru?, ance kin ta da Aljanu a ɗakin Hajja." ji nayi a zuciyata, daman Aljannun nayi ko na ƙarya ne, nayiwa Hajja mugun duka, amma mu tara lokaci na gaba."Wai muna tambayarki, kinyi shiru." "Ku tashi ku kyaleta, mugun hali take ji." Ummanah da ta shigo ta basu amsa, tashin su kayi suka fice, na haɗa kai da gwiwa tare da fashwewa da kuka mai ƙara ina faɗin. "Wallahi bazan auri Mus'ab ba, wallahi ko za'a kasheni da duka." ba ta ko kalleni ba ta ci gaba da abinda take, ni kuma na ƙara cewa. " Wallahi ko tsinemun ne sai dai ayi." A ɓangaren Mus'ab kam, Mama ce ta kalleshi, sanan ta ce. "Ka tashi mu huce ko kaima kukan zakayi?." bai ce uffan ba ya tashi yayi gaba, ai kuwa suna shiga ɓangaren su ya zube a ƙasa tare da faɗin. "Mama Wallahi ba zan auri yarinyar nan ba." Bai kai ga rufe baki ba, Mama ta ce. "Wallahi Mus'ab ko bayan babu raina, ka ƙi auren yarinyar nan, ko ka musguna mata bayan aure, ban ya fe maka ba." To jama'a, mun iso iyakar free pages, kuma daga nan zamu faɗa cikin labarin, cikin rigima da zallar ƙiyayya. Gashi dai ance za'ayi musu aure, shin Mus'ab zai bari ya auri yarinyar da bai so, ko Salma za ta auri namijin da tafi tsana?. Idan har anyi auren, yaya zaman zai kasance, ya Salma zatayi da soyayyar Masrur? sakata ce zallan kiyayya da dumin ƙaddara! Paid pages suna ɗauke da abubuwa masu matuƙar yawa, da ɗaure kai. N500 kacal. Masu buƙatar complt kuma 1k ne. 8129553971 Opay Sani Muhammad lawan. Shaidar biya ta nan 08165383931. Paid pages zai fara zuwa ranar Monday, masu buƙatar complt 1k. Paids page. PAGE 11 idan kika fitarmun da labari Allah ya isa ban ya fe ba. (11). Kallon Mama yayi, idanun sa cike da tsoro da fargaba.”Mama, dan Allah.” “Wallahi Mus’ab na gama magana, kai wane irin mutumin ne, kasan taimakon da mahaifiyar yarinyar nan tayi maka.” Shiru yayi, domin bai da abinda zai ce, amma gaskiyya babu wani abu da zai sa ya auri yarinyar nan, yaushe ma ya taɓa ganinta a matsayin mutum, mai hankali, har da zai zauna da ita matsayin mata, wai sun sa ma wasu ke magana a kai, Salma faa, yarinyar dai bai taɓa jinta a rayuwarsa ba, shi a tarihin rayuwarshi yadda zai iya tuna sau ɗaya ma ya taɓa ganin wani abu daga yarinyar da yaji ya burgeshi; shine lokacin da yake kwance a asibiti, da ta harareshi ta murguɗa mai baki, bayannan bai taɓa jin wani abu da ya taɓa burgeshi a yarinyar nan ba, shine za’a maka mai ita a matsayin mata. Tashi yayi ya nufi cikin ɗakinshi, tare da waɗawa kan gadonsa ya rufe idonsa, shi yanzu Mus’ab, da ‘yan mata ke rubibinsa, ‘yan mata ke faɗa a kansa, shi za’abawa wanan ƙwailal yarinyar a matsayin mata. “Wallahi bazai yu ba.” Ni kam tun da na shiga ɗaki, na zauna na rafka uban tagumi, ni ba mai tunani ba ni ba marar tunani ba, gani nan dai zaune kamar an sassaƙa ni, na kasa yin tunanin komai bare ma na sam mafita, kusan awanni biyu ina wanan zaune, na ƙurawa waje guda ido, kamar mai kallon wani abu. Mamace ta fito, da’alama ɓangaren Hajja za taje, ita kanta ganina a wanan wajen, kuma cikin yanayin da ta barni, ya matuƙar tsorata ta, amma ta maza ta huce, ta na fita na miƙe nayi cikin ɗaki na ɗauki wayarta, lambar Masrur na danna. Bugu ɗaya ya ɗauka, dan yana da lambar tun da Ummanah ce. “Fulani, ina kika shiga haka, I really missed you. Daga muna waya kika ce kina zuwa shikenan, ina ta jin babu daɗi, kaman wani abu na faruwa dake.” Wani irin kuka ne mai ƙarfi ya ƙwacemun, wanda yasa shi ƙara cewa.”Fulani lafiya? Fulani talk..!” kukan na ci gaba da yi, yana ta faman bani haƙuri, daƙyar na iya haɗiye kukan na ce. “Kazo ka ɗauke ni dan Allah.” “Fulani ina zan kai ki?.” “Gidanku muyi aure, wai Mus’ab za’a auran.” kamar saukar aradu haka yaji maganar tawa, da sauri ya ce. “Fulani banji mai kika ce dai-dai ba.” Majina na haɗiya, sanan na ce. “Kaji, dan Allah.” “Fulani, ki sa ke faɗan naji, ni wallahi banji ba.” Kukan na ci gaba da yi iya ƙarfina, ya rike ce gaba ɗaya, yana tambayata.”Na ce kazo ka tafi dani, wai Mus’ab za’a auran.” “Innullahi Fulani, waye da wanan maganar.” Jin tambayar nayi ta zo da rainin hankali, kawai na kashe wayata na ci gaba da kukana, can dabara tazo mun na kira Yayatah, nasan ita kaɗaice jinina, ita ce zata fahimce damuwatah. Tana ɗagawa na fashe da kuka, a firgece ta ke magana. “Salma lafiya, salma waye ya mutu.” “Yaya sun kashe ni, Yaya na shiga uku.” gaba ɗaya ta firgice, a ruɗe take tambayata. “Salma nutsu kimun magana, mai ya faru, wani ya mutu, ko Mus’ab ne?.” “Allah ya kashe shi na huta.” na tare ta da faɗa, shiru tayi tasan maganar a kan shi ce. “Salma, mai ya faru?.” “Yaya, wai aure za’ayimun, kuma Mus’ab.” Tabbas ta ji maganar, kamar saukar tsawa lokacin ruwa, domin duk wanda ke gidan Galadima ya kwana ya hantse da sanin ƙiyayyar dake tsakanin Mus’ab Galadima da kuma Salma Galadima, amma mai yasa a ka yanke wanan hukumcin. Ajiyar zuciya ta sauke, sanan ta ce.”Salma yimini bayani dan Allah.” “Wai wane bayani Yaya.” “Mai yaja auren, kuma mai ya kawo maganar.” gani nai kamar tafi damuwa da shi, hakan yasa na ce. “Idan na mutu, kece zakifi kowa rashi.” daga haka na kashe wayar, nayi wurgi da ita gefe, na shiga tunanarwa kai na mafita.” Ina zaune Sadiya da Walida suka shigo, ta shi nayi na nufi cikin ɗakina, sabida banason ganin kowa cikinsu domin duk kansu munafukai ne, ba barin Walida ma. “Haba Salma, ko kowa yayi miki laifi, gani nake mu ba ma cikin masu wanan laifin Salma.” Sadiya ta faɗa, shiru nayi dan zan iya sauraron maganar Sadiya a kan ta Walida. “To menene?.” na faɗa, fuska fal da hawaye. “kiyi haƙuri Salma, ki zauna ki nemi mafita.” Walida ta faɗa, tana koƙarin matso ni. “Ku kyale ni kawai, gwanda na mutu domin rayuwata ba ta da amfani, da zama da Mus’ab a matsayin mata da miji, gwanda zamana a gidan bariki.” ina faɗin haka na shige ɗakina. Tabbas dole na bar gidan Galadima, domin zama a gidan ba nawa ba ne, barin gidan shine hanya ta farko, kuma mafi sauƙi ta ƙin auren Mus’ab, amma idan na bar gidan Galadima ina zani, ina na nufa?, na san dai ba zan je gidan dake da alaƙa da Galadima ba na zauna, sai dai ko dangin Mamana. Haka nai ta famam tunanuka kala-kala, a ƙarshe na yanke shawarar haƙura da duk wani jindaɗin duniya, na haƙura da komai, gida mai kyau, abinci mai kyau, suttura mai kyau, gwanda naje nayi rayuwa a matsayin mabaraciya mara komai, a kan na zauna na auri Mus’ab. Kayan jikina na kalla, leshi ne mai kyan gaske, tashi nay na shiga ɗaki na cire, gwanda na fita a matsayin mara gata mara komai. Canja shi nayi da wani bakin material ɗin na, mara nauyi kuma mara kyau dan ya dad’e, ni kaina na kwana biyu ban sa ka shi ba, haka ɗan kunnen kunnena na cireshi, na saka wata ƙaramar barima, dan tabbas na haƙura duk wani jin daɗin duniya, gwamda na fita nayi bara, nayi sana’a na samu kuɗin kai na, wani silafas na ɗauka na saka, na fito kamar wata almajira. Sai da na leƙa sosai, na ga ba kowa sanan na fita a guje, dai-dai lokacin da Yaya Ilyasu ya fito daga ɓangarensa, da sauri shima ya yo wajen amma ina, kamar nasan za’abiyu ni na shige gidan ku sa damu, ganin ba kowa a wajen ya sa ya koma. Inda ya ci karo da Ummanah ta fito daga ɓangaren Hajja. “Lafiya dai ko, naga ka shigo kana zare ido.” Ummanah ta zolayeshi. “Wallahi gani nai kamar an fito daga ɓangarenki, anyi waje kuma na leƙa ban ga kowa ba.” “Ɓangarena kuma?.” Ummanah ta faɗa tare da shiga ciki. “Salma, Salma.” ta fara ƙwalamun kira, amma shiru. “Wai daman Salman na nan?.” Yaya Ilyasu ya tambayeta. “Eyh, anan na barta.” “chaɓ, aikuwa ita ta fice.” ya faɗa tare da yowa waje, gidajen kusa da mu ya fara shiga, amma ko ina sai a ce bana nan, ko ban shigo ba. A ɓangarena kam, ina shiga gidan na ɓoya bayan ƙofa, ban fi minti biyu ba na fito, tunanin inda zani na fara, sai dai kuma dare ne. “Ina na nufa?.” Na tambayi kai na, tuna wa nayi da wani ɗaki da ke zauren gidan Alhaji idi me mai, ɗaki ne da ke babban zaurensu, a rufe ma yake, amma mu da idan muna wasa mun san hanyar da muke shiga ɗakin ta cikin ta ga, nan na yanke shawara zuwa na shiga zuwa da safe, babu wanda ya kula da ni, ya ga shi ga ta ko hucewa ta, dan ko mutum ma ya ganni banjin zai iya gane ni, dan nayi kala da mabarata. A hankali na shiga gidan, na ɗane tagar na shige cikin ɗakin da sauri, ba tare da kowa ya ganni ba, duk ƙurar dake d’akin ba ta dame ni ba, haka na samu waje na kwanta ina faman tunanin makomata, gobe idan na tashi ina nufa?, Tun Ummanah da Yaya Ilyasu na duba na asirrance, har abu ya fito gida kowa da kowa ya shiga nemana, abu har maƙwaftan mu. Hankali kowa ya tashi cike har da na Ummanah da Mamana ciki, dan ita Maman ciki har da hawayenta, Hajja kam salati tasaki tare da cewa.”Kai amma wanan yarinya anyi ‘yar jakar uba, har tayi wayon da zata ce zata bar gida?.” Walida da Sadiya suke yawo gida-gida nemana, fuskarsu sharkaf da hawaye. Ina jin sanda su ka shigo gidan, Alhaji idi me mai nemana, amma kasancewar babu wanda ya san na shigo, hakan yasa a ka ce da su ba na nan, Mama ce ta ɗauki waya ta fara kiran mutane ita da Anty, ita kam Ummanah ta tsaya tsaye kamar gawar sababi, tunani take ina zan iya zuwa?. “Walida ina ne gidansu saurayin na ta.” Ummanah ta tambaya. “Wallahi Umma ban sani ba, ita ma kan ta ba ta sani ba, domin ranar da mu ka zo asibiti ranar suka fara haɗuwa.” “Haba, ya ma za’ayi ta je gidansu sauray, dole tana gidajen ‘yan-uwa, kuma ina kyautata zataon ƙarasawa ne ba tayi ba, shiyasa kowa yake cewa ba ta zo ba.” Anty ta faɗa, dan dai kowa yasan bazan iya bin saurayi ba. “Yanzu mai Salma take son ta zama?.” Ummanah ta faɗa kamar za ta yi kuka. “Babu wani abu sai Alheri, Allah ya riga da ya tsara komai tun kafin yanzu.” Anty ta sake faɗa, dan ita Maman ciki ta zabga ta gumi. Abbanah ne ya shigo, kasancewar Yaya ilyasu ya kira su duka ya faɗa musu, kana ganin Abbanah kasan ya je ƙarshe a fusata, bayansa Abban ciki ne, shima ranshi ya ɓaci sosai. Hannun Abbanah riƙe da wata babbar leda wacce ba wanda yasan menene a ciki.” Wai mutane da ka kira a waje na menene?.” Abban ciki ya faɗa yana tambayar Abbanah. “Yaya ka kyaleni, ba ita gani take ta isa ba, to wallahil azim cikin daren nan za’a ɗaura musu aure, kuma ban laminci ko da an nemo ta ta dawo gidanan ba, sai dai ta huce can gidan mijinta.” legend’s pen Page 12 Duk yanda Ummanah ta kai ga son auren nan, sai da ta ji ya zo mata wani kala, ko ba komai ta so ta gyarani, tayimun abubuwa, sanan ga kayan kitchen da na gado, kar kuma abun ya zama shiga haƙƙi. Ko da yake, a farayin auren, sanan a sameni. “Amma kana ganin hakan zai fi.” Abban ciki ya tambaya, a fusace Abbanah ya juya. “Kaga Yaya, ban neme yardar ka ba, ko shawarar ka, da Mus’ab da Salma babu wanda bani da iko a kansa, dan haka yanzu xanyi amfani da ikona, wallahi cikinsu babu wani da ya isa ya maidamu ƙananan mutane.” Shiru Abban ciki yayi, domin fa tun suna ƙanana daman tsoro Abbanah yake, sabida yana da fushi da zafin zuciya, sama da kowa a gidan. Yaya Muhammadu yaya na ne ya shigo, ya kalli Abbanah sanan ya ce.”Abba ga limamin.” bai rufe baki ba, su Yaya Amira suka shigo, kowa da mamaki yake kallonta, an zaci Salman ce ta je gidan. “Asma’u tana gidan ki ne?.” Maman ciki ta tambayeta, girgiza kai tayi sanan ta ce. “Abbanah yayi mun waya lallai-lallai na zo yanzu, kuma ina jin bani kaɗai bace, dan ina hanya yayar Abuja ta kira ni ta ce wai lafiya, Abba ya ce lallai gobe ta zo, shine na ce mata nima ina hanya, inaga gaba dayan mu ya ce mu zo.” “Salma ta jawa kanta.” Anty ta faɗa, dan ita tafi tausayin Salma. “Wai anganta ne?.” Yaya Asma’u ta ƙara tambaya, girgixa kai Maman ciki tayi, sanan ta ce. “Auren dai za’a ɗaura.” “Ikon Allah, Ita kuwa Salma ina ta je haka?.” “Koma ina ta je zata dawo ta tarar da hukunci, duk wanda bai ji bari ba, ai yaji hoho.” Ummanah ta faɗa. A can waje kam, maƙota Abbanah ta taro, har da wasu cikin abokansa, inda limami ya ɗaura aurena da na Mus’ab Galadima, kan sadaki naira dubu dari biyu, wanda Abbanah ne ya bayar da kansa. Cikin ƙanƙanin lokaci, ahalin Galadima da ke kusa su ka hallara gabaki ɗayansu, Yayar Abuja ce babu, sai kuma Yaya Amira ta zaria, sai ni da kuma Mus’ab, wanda babu wanda ya nemeshi baki ɗaya. Gaba ɗayansu suna zaune a falon Hajja, bayan Abban ciki ya buɗe taro da addu’a, kasancewar ya saba hakan a duk wani taro da za’ayi, Abbanah ne ya ɗora da cewa. “A yau, Allah ya nufemu da ɗaura auren Mus’ab da Salma, wanda mutane da dama su ka shaida hakan, to abinda yasa na tara ku a nan, kowa da kowa shine; ina so nayi amfani da wanan lokaci domin na sanar da ku cewa, in dai har Salma taƙi biyayya ga auren Mus’ab, ko kuma taƙi zama a gidan Mus’ab, to na sallamata, na cire ta lissafin ‘ya’yana, wanan magana ce wacce na yanke ta, kuma babu canja magana dan duk kusan ba halina bane, sanan shima Mus’ab ku sanar masa, idan har ya sake wanan yarinyar tafi ƙarfinsa, ta kai ga har saɓani ko saki ya shiga tsakani, to wallahi shima nida shi ne” “Toh, amma yanzu ita Salman ta ina?, kawai sai ayi wanan hukuncin ba tare da an nemi lafiyarta ba, sanan mai ya kawo maganar auren haka cikin gaggawa.” Mami wacce take yaya a wajen Abbanah ta faɗa. “Wanan su zasu iya yi miki bayani, amma abinda yasa na na ɗaura auren yanzu shine; daga Salma har Mus’ab babu wanda ya isa, ya nuna bamu isa ba, babu wanda ya isa cikinsu, ya ma yar da mu ƙananan mutane.” “Yunusa, tambayarka nayi mene asalin abinda ya kawo auren?.” ta sake maimaita masa, dan ita ma akwai zafin kai.”Ni ce na haɗa, nina haɗasu auren.” Hajja ta faɗa, dan tasan a zafin kai irin na Mami, da ba’a ɗaura auren ba tsaf zata iya hanawa. Shiru Mami tayi, tun da Hajja tayi magana kuma ai shikenan. “Amma kuma yana da kyau a nemi inda take dai.” Ummah wacce take ƙanwar Abbanah ta faɗa. “Eyh, dole za’a ba zama nemanta, amma ta kwana da sanin ba za ta sake zama a waje na ba.” Ummanah ta faɗa. “Ni a kawo ta waje na.” Maman ciki ta tare Ummanah. “Amma ni cewa nayi cikin gidan ne ba zata ƙara zama ba.” Abbanah ya faɗa. “A’ah Yaya, ba za’ayi haka ba, dole Salma zata zauna da mu, kafin shi Mus’ab ɗin ya haɗa mata lefe, da sauran kayyaki, sanan kaima akwai haƙƙin kayan ɗaki da na gado a kanka, sanan duk wasu abubuwa da aka gudanar a bikin sauran ita ma za’ayi a nata.” Yaya ilyasu ya faɗa, tun da ya fuskamci dai babu wanda zai iya faɗawa Abbanah, shiru yayi sanan ya ce.”Da komai da komai kar ya huce kwana goma.” daga haka ya tashi ya fice, shi dai Abban ciki mamakin yadda ya ƙwace mai girma kawai yake. *Mus’ab* A ɓangaren shi kam, tun da Maman ciki ta ce dashi, idan har ya sake ya fasa auren, ko ya musguna mun ba ta ya fe ma sa ba, ya samu waje ya zauna. “Shikenan wanan auren ya tabbata, ya zama na dole, domin yasan tun da a kazo wanan matakin, komai ya ƙare. Ya zai yi da rayuwarsa, ya zai yi da auren ƙaddarar da a ka ɗaura masa, Zuciyar da ya sa wa SAKATA ya rufe, zai buɗe da soyayyar wanan ƙaramar yarinyar?. “Mai yasa to na damu da kukan da naga tana yi?.” Yayi wa kan sa wanan tambayar. “Tabbaa naji kukan da take yi har cikin zuciyata, kuma naji babu da “Amma Mus’ab, mene laifin Salma a wajenka?.” Wani ɓari daga cikin zuciyarsa yayi masa wanan tambayar. “Yarinyar ba ta da kunya.” ya bawa kan sa amsa, shi ba ma wanan ba.”Mai yasa yake jin kukan da take yi har cikin zuciyarsa, shin shi ɗin ba mutumin arziƙi bane, da zai ji ma ta tausayin aurenta ko me?.” Tabbas ya damu da wanan kukan na ta. *Salma* Ina zaune cikin ɗakin, naji shigowar su Walida da fitarsu amma ko a jikina, domin ina zaune na gama tsara yanda zanyi da rayuwata, bara ne zanyi na ‘yan kwanaki kafin na samu miji nayi aure, shima Masrur ɗin duk naji ya ficemun a rai, garin zan bari baki ɗaya ya fiyemun. Ina nan zaune naji suna koƙarin kulle gidan, alamun sha biyu ta gota, sai a lokacin naji wani mugun tsoro ya ka mani, yanzu idan sukayi bacci ɓarawo ya shigo fa?, ni ce a farko ni zai fara ɗaukewa, hakan yasa na rufe idona tare da yin addu’a, idona a rufe har bacci ya ɗaukeni. Kiran sallar farko na buɗe idona, dake ba wani dogon bacci na samu nayi ba, ina jin matasan gidan sun fita sallah na miƙe, gwanda na fita da duhun nan, sabida idan gari ya waye kowa zai ganni, kuma nasan zancen ɓata na ya yaɗu ko ina, tagar na ƙara kamawa na ɗage tare da dirga ƙasa na bi ƙofa na fice, sai dai ban fito a sa’a ba, domin dai-dai lokacin Yaya Muhammadu da ya fito a makare ya nufa massallacin, tun fitowa ta na ganeshi, ƙoƙarin komawa na fara shi kuma ya ce. “Wace anan?.” da sauri na koma zan shige, amma yayi saurin sa hannu ya riƙe ni, kuka na fara tare da faɗin. “Yaya dan Allah ka cika ni.” a fusace ya ce. “Salma!.” shiru nayi bance komai ba.”Ba magana nake miki ba, ina kika je, kin san halin da kika sa iyayyen mu?, gaba ɗaya gidan Galadima jiya babu wanda ya runtsa, kowa yaja carbi yana ja, wasu kuma sai sallah suke suna roƙon Allah ya bayyanaki.” “Ni babu inda naje, a ɗakin shirgi na gidan Alhaji idi na shiga, kuma ka cika ni na tafi, na bar muku gidanku, na bar muku ahalinku… Legend’s pen Page 13. Saukar marin da naji a fuskata ya sani haɗiye yawon baki na babu shiri, jana ya farayi ni kuma ina turjewa tare da faɗin.”Wallahi bazan koma ba, idan na koma Allah yatsinemun, ka cika ni.” Shi kam kawai jana yake ta ƙarfinsa, domin nima nasa ƙarfina ina neman fusgewa, na kwasa da gudu. Dai-dai ƙofar gidan mu na saka ƙarfi na fusge tare da kwasa da gwado, shi kuma ya rufamun baya, ji nai a rinƙo hannuna; ina juyowa aka kifeni da mari, tun daga saukar marin nasan Kawu Mudi ne. “Dan ubanki baki da hankali ko?.” takaici ya isheni, na fara jan hannuna zan ci gaba da tafiya, cika ni yayi tare da faɗin. “Je ki.” aikuwa nasa ƙafa na fara tafiya, danni gaba ɗaya gidan Galadima sun fitar mun a rai, bana son kowa, kowa baya burgeni, dan Wallahi a kan na auri Mus’ab gwanda naje nayi bara, ƙara riƙeni yayi tare da kifamun wani marin, daman haushin Kawu Mudi nake ji, dan shine kullum cikin dukana yake, shima ja na ya farayi ina turjewa, da sani na na kama hannunsa na gantsara masa wani mugun cizo. Duk zafi cizon baisa Kawu Mudi ya cika ni ba, sai da ya dangana ni da cikin gida. Gani na a harabar gidan ya sa na kurma wani mugun ihu wanda ya ratsa gidan gaba ɗaya. Ummanah na zaune kan dadduma ta jiyo ihun nawa, da mugun gudu ta taso zuwa harabar gidan, fitowar dai-dai da fitowar Maman ciki da Anty, gaba dayansu su ka zo kai na,Maman ciki na faɗin. “Ina a ka gan ta?.” Banza Kawu Mudu yayi musu ya shige ciki, Yaya Muhammadu ne ya ce. “Ɗakin shirgi na gidan Alhaji idi me mai ta shiga.” nan suka hau salati da salallami, Ummanah ba ta ƙara cewa komai ba ta huce, Maman ciki ce ta kama hannuna zuwa ɓangarenta, Anty kuma ta koma ciki, Allah ya gani ita Anty ba ta son auren nan, ba wai dan wani abu ba, kawai tasan yadda muka tsani juna nida Mus’ab, da ace shi yana so na to da sauƙi, amma duka ba ma son junan mu, amma addu’ar ta ita ce. “Allah yatabbatar da abinda yake Alheri.” Ɗaki Maman ciki ta huce dani Walida na bin bayanmu, sai da mu ka shiga ta zaunar da ni kan kujera ta fara magana cike da hikima da dabara. “Salma! Salma!! Salma!!!, sau nawa na kira sunanki?.” Kai na a ƙasa na ce. “Uku.” “Salma mai kika aika ta haka, kin san fushin da kika ɗaukar wa kan ki, kin san adadin tsinuwar da mala’ikun Allah suka yi miki a kan ɓata ran iyayenki da kika yi, Yanzu mene amfanin gudun da kikayi, sabida ka da ki auri Mus’ab?, to idan hakane kinyi a banza, domin ko awa biyu ba kiyi da tafiyar ba a ka ɗaura miki aure da shi Mus’ab ɗin, kinga kuwa auren ku haɗin Allah ne, wata SAKATA da kuka sakawa zuciyoyinku, ba zata hana Allah aiwatar da abinda yayi niya ba, sanan ba zata canja komai daga abinda ke rubuce a littafin ƙaddararku ba.” Tun lokacin da naji ta ce banyi ko awa biyu da barin gida ba, aka ɗaura mun aure da Mus’ab, ban sake tsintar ko kalma ɗaya daga maganganun ta ba, wani abu mai nauyi naji ya durga a kai na, zuciyata ta fara bugawa da wani irin ƙarfi. Fat! fat!!, idanuwa su ka fara mun yaji, hawaye su ka ɗauke, sai wani zugi da radaɗi nake ji daga cikinsu, kalmar da na ƙara ji ita ce. “Yanzu Salma mene ribar abinda kikayi, banda ɓatawa kanki suna, ko kin san duk macen da ta taɓa sa ƙafa tabar gidan iyayenta, ta tashi daga matsayin mace mai daraja.” Buɗe baki nayi da niyar cewa. “Gwanda na dauwama a matsayin mara daraja, a kan na dauwama a matsayin matar Mus’ab.” sai dai jin baki na ya gagara buɗuwa ya sa nayi shiru.”Yanzu Salma ina zaki kai fushin iyayenki na kan ki?.” “Tana ina?.” Muryar Abbanah ta kara ɗe gidan, ɗage labulen ɗakin yayi, hannushi riƙe da bulala mai girma, take idanuna suka fara zubar da ruwa. “Kayi haƙuri dan Allah.” Maman ciki ta faɗa, Abbanah bai ko kalleta ba yayo kai na, ji kake zit, ya fara sauke mun bulala a jikina, ta na shiga ta da wani irin zafi, duka na yake kamar Allah ne ya aiko shi, babu tausayi babu imani, tun ina zubar da hawaye har hawayen ya ƙare, na koma nishi kawai, sai dai zuciyata na ƙara tsanar Mus’ab, shikenan ya shiga, ya fita ya rabani da iyayena, ko aina yake na san yana can yana farin ciki da jindaɗi. “Yah Allah ka saka mun, kabi mun haƙƙinah a kan Mus’ab, ka gama shi da masifar duniya ya Allah.” *Mus’ab* Kwata-kwata bai iya bacci ba, zuciyarshi taƙi bari ya runtsa, taƙi saurar masa da tunanin halin da nake ciki, ayyana masa take. “Yanzu ina Salma, tana wane hali, ta kwanta, ta ci abinci, ya zatayi da wanan sanyin da akeyi, sauro ba zai cije ta a inda take ba, idan ta haɗo da ɓata gari fa?.” Shi kan shi ya rasa mai ya haifar masa da wanan damuwa da ni ɗin cikin ƙanƙanin lokaci?. Haka yayi kwanan zaune, yana ta faman tara da kwashewa, sai gab da asuba wani ɓarowan bacci ya ɗauke shi, kuma ba’a samu wani ya tashe shi ba. Cikin bacci ya fara jin sautin kuka na, zuciyarsa na wani bugawa da ƙarfi, runtse ido yayi sanan ya buɗe su, rau yaji kukana. Da sauri ya tashi ya buɗe window ɗin ɗakinshi, ni ɗin ce Abbanah ke duka, tabbas yaji daɗin ganina da a kayi, amma kuma dukan da kukan nawa ya tsaya masa a rai, gani yake kamar shi yajamun komai, da bai yi rashin lafiyar ba, da ba za’a auramun shi ba, shiru yayi yanajin saukar bulal a cikin su zuciyarsa.”Mus’ab, mene na damuwa da yarinyar nan haka?.” yaji tambayar a cikin kunnuwansa, da sauri ya wai ga ko wani ne yayi masa maganar, amma ba kowa sabida ko ƙofar ɗakin bai buɗe ba. Ganin kamar Abbanah bai da niyar kyaleni ya sa shi buɗe ƙofa ya fito waje da sauri. “Abba a yi haƙuri dan Allah.” Wani maƙoƙon abu ne ya tsayamun a maƙoshi, tare da wata sabuwar tsanarshi da ta ninka ta baya, sau dubu da ɗari biyar. “Munafuki, wutar Allah ta cika.” Na faɗa a zuciyata, tare da galla mai harara a fili. “Mus’ab, ka karbe bulalal nan.” Mamam ciki ta faɗa, dan gaba d’aya ta gama rud’ewa da irin dukan da Abbanah ke mun, ni kam a yanzu zafin tsanar Mus’ab, ya ninka zafin dukan da abbanah ke mun, hannu ya kai zai karb’a Abbanah ya ce. “Karka kuskura, Anty ce ta shio ita da Alhaji k’arami. “Kayi hak’uri Yaya dukan babu abinda zai gyara, hukunci kuma ka ga ma yiwa Salma shi, tun da ka d’aura ma ta aure.” Alhaji k’arami ya fad’a. “Kyaleni kawai.” Abbanah ya faɗa, yana ci gaba da dakuna, ga mamakin kowa sai kawai ganin Mus’ab a kayi ya faɗu kaina, ya lulluɓeni da jikinsa, ya kare ni baki ɗaya. Ganin hakan yasa Abbanah ajiye bulal ya fice, ni kuma wani ƙululin takaici ya isheni, wai yau Mus’ab ne ya ceceni, citon munafuncin, domin ko da ƙur’ani a ka bani zan iya rantsewa da shi, zuciyar Mus’ab fara take tas! Abban na fita, Mama da Anty sukayo kai na. “Salma kinjawa kan ki fushi mai tsanani, kin san yadda mahaifinki da mahaifiyarki su ke, mai yasa kika buƙaci haka, yanzu Umman naki ke cewa, ba zaki sake zama wajenta ba, shima kuma tun jiya ya faɗi haka, dan Allah salma menen ribarki anan?.” Anty ta faɗa, tabbas jikina yayi sanyi, a kan hukuncin da iyayena suka yanke, amma kuma koma menene Mus’ab ne ya ja, kallonshi nayi yadda yayi wani tsuru-tsuru. “Ko menene ribarshi na haɗa ni da iyayena oho?.” legend’s pen Page 14. Kallona yake ta ƙasan ido, yanda na daku naji jiki, abun ya matuƙar ta ɓa shi, ga kuma hukuncin da iyayena suka yanke a kaina, duk wanan a kan shi, tabbas yana buƙatar neman shawara ko mafita a kan lamarin nan, amma kuma zuciyarsa ta addaba masa ta wani ɓangaren, tunani da yawan damuwa da al’amurana, tun daga jiya har yau, tunawa da yayi baiyi ko sallar asuba, ya sa shi ya tashi da sauri, duk da wai ba gari ne yawaye ba, dan wasu masallatan ma yanzu su ka idar. Ficewa yayi zuwa ɗakinshi, ya ɗaura alwala ya gabatar da sallah, sai dai ga matuƙar mamakinsa, sai ya tsinci kan sa da addu’a gare ni. “Ya Allah, ka kawo sauƙi a lamuran Salma, ka ba ta haske a rayuwa, ka sauƙaƙa zuciyar iyayenta da ta ta.” Sai bayan ya idar yayi da addu’ar ma, wani mamaki ya kamashi, sai kuma ya kaudar da tunanin ta hanyar cewa. “Tabbas yanzu Salma na cikin halin da take buƙatar addu’a.” “Salma, ta shi ki je ki watsa ruwa, ko zaki ji daɗin jikinki, sanan ki rama sallolin da ke kanki.” Sai a lokacin na tuna ko Sallar magribar jiya ban yi ba, ga isha’i da kuma asubar yau. Tasi nayi jikina babu ƙwari kwata-kwata, ƙafafuna sunyi tsami. A hankali na nufi hanyar ban ɗakin,dai-dai lokacin da a ka buɗe kofa a ka shigo, Hajja ce, bayanta kuma Ummanah ce, kallo ɗaya na yiwa Hajja na ɗauke kai, Ummanah ko kallo ban ishe ta ba. “Sannu.” Naji muryar Hajja ta faɗa, ji nayi kamar na shaƙota na tsinka ma ta mari, ko zan ji ni dai-dai. Shigewa ban ɗakin nayi, na gasa jikina da yayi tsami sosai, sanan na ɗaura Alwala na fito, ɗakin Walida na shiga tana zaune ta rafka uban tagumi. “Bani kaya na sa.” na faɗa a daƙile, danni gaba daya gidan Galadima haushin kowa nake ji, gani nake gaba ɗaya sun tsane ni, tuno wa nayi da auren Mus’ab da ke kai na. Hannu na ɗora a ka tare da runtuma ihu na zube a ƙasa. Shigewa ban ɗakin nayi, na gasa jikina da yayi tsami sosai, sanan na ɗaura Alwala na fito, ɗakin Walida na shiga tana zaune ta rafka uban tagumi. “Bani kaya na sa.” na faɗa a daƙile, danni gaba daya gidan Galadima haushin kowa nake ji, gani nake gaba ɗaya sun tsane ni, tuno wa nayi da auren Mus’ab da ke kai na. Hannu na ɗora a ka tare da runtuma ihu na zube a ƙasa. Da sauri Walida ta watsar da kayanta, ta yo kai na tare da faɗin. “Salma lafiya?.” Banza nayi ma ta na ci gaba da kuka na, kuka wiwi kamar wacce a kayiwa mutuwa.”Salma wai kukan mai kikeyi haka, sai ka ce wacce ta ga ranar mutuwarta.” “Ni da wanan mummunar ranar, ai gwanda naga ranar mutuwar Hajja.” dariya walida tayi, sanan ta ce. “Salma Allah ya shirye ki, yanzu fa ke matar aure ce, mata a wajen Mus’ab Galadima, matashin da kika daɗe kina fatan zama matarsa.” “Allah ubangiji ya tsine miki albarka Walida, wallahi na tsani Mus’ab, na tsaneshi fiye da yadda kike tunani, kuma wallahi ba zan taɓa zama matar Mus’ab ba.” “Matar Mus’ab dai, kin gama zama, sai dai kuma idan ya ƙara auren ki zama uwar gida.” Tashi nayi na shaƙu wuyanta, ji nake kamar na kasheta ko na huta da wanan maganganun nata masu kamar sa saukar ruwan zafi a jikina. “Dalla cika ni, mahaukaciya.” rufe idanuna nayi, abu kamar wasa ya zama babba, tun Walida na ɗaukan faɗan ƙarami, har ta fara mai da mun da martanin duka, ni kuwa na taƙarƙare ƙarfina sai labtar ta nake, ita ma kuma ta fara ramawa. Ƙarar hayaniyar da suka ji a ɗakin ne yasa su shigowa, da mamaki suke ganin yanda muke faɗa da junanmu, abinda ba mu taɓa tun girman mu. “Walida!, Salma!, me kukeyi haka?.” Maman ciki ta tambaye mu. “Wai kawai daga ina magana ta shaƙemun wuya.” “To na ce kiyi mun magana, kuma wacce magana kika zo kina mun, ina ce ba tsokanata kikeyi ba, wai matar Mus’ab.” “To dan ta ce matar Mus’ab shine ne, ba matar tasa ba ce, ko dan baki da ku bane, za ki zo kinawa mutane shirme anan.” Ummanah ta faɗa cike da fushi. ”A’ah, to ita Walidan mai ya kai ta yi mata wanan maganar.” “Duk ya isa haka, ke Salame ki shirya ki biyo ni ɓangarena.” “A’a, ni Hajja ba zanje ɓangarenki ba.” “To gidan ubanwa zaki?.” Ummanah ta faɗa kamar zata dake ni. “Ɓangarenmu.” na faɗa tare da cuno baki. “To wallahi idan har kika ga kin dawo waje na da zama, to bana raye ne, Salma na sallamaki, na barwa duniya ke, tun da haka kika zaɓa, kin zaɓi dubiya a kan yi mana biyayya.” “A’ah ya da haka, bana son ƙara jin wanan maganar.” Hajja tari numfashin Ummanah. “Wai so kike sai kinyiwa yarnyar nan baki ne zakiji dadi?.” Maman ciki ta tambayi Ummanah, sanan ta ɗora da cewa.”Idan fa rai yaɓaci, hankali baya gushewa.” “Shiyasa na ce dole a raba ta da yarinyar nan, nasan nan ke zaki riƙeta, amma mugun halinta ba zai barta ta zauna ba.” Hajja ta faɗa.”To ai wajen naki ma Hajja ba zama zata yi ba.” Maman ciki ta faɗa. “To ina za’a kaita?.” Zallan mamaki ne ya kusa kasheni, wai ni da gidan ubana a ke neman inda za’a ajiye ni, kamar wata kayan wanki, “taya za’ace bazan tsani Mus’ab?.” na tambayi kai na. “Ni ba zan tsoma muku baki ba, amma gidan mijinta shine inda ya dace ta zauna.” maganar Ummanah ta dawo dani daga tunanin da nakeyi. “Ba fa yarinyar nan zata bar gidan nan ba, sai anmata duk duk wani abu da ya kamata, sanan haɗe bikin nasu za’ayi da Halima, sabida shi yaron yana son tafiya karatu ƙasar waje.” “To yanzu Hajja ya za’ayi?.” Maman ciki ta tambayi Hajj, bayan ta gama magana.”Ta ci gaba da zama nan, idan zaman nasu yaƙi daɗi, ko ita ko Walidan wata sai ta dawo ɓangarena.” Hawaye naji sun fara zubomun a fuskata, wani ni ce a ke yiwa haka, a kan wani ya shigo rayuwata, tabbas Mus’ab ya zama annoba a rayuwata, ya zama fitana, ɗakin Walida na koma na zauna, tare da zabga uban tagumi. *Masrur* Waye Masrur, mai ya kawo Masrur rayuwata?. legends pen Page 15. *Masrur* Waye Masrur, mai ya kawo Masrur rayuwata?. Kamar yadda ya faɗamun a farko, sunanshi Masrur, kuma wanan asibitin na mahiafinsa ne, kuma shi ke kula dashi. Masrur shine ɗa, ɗaya tilo a wajen mahaifinsa, ɗan-gata ne na ƙarshe, mara kuma jin magana. Irin su Masrur ne matasan da kan shafe shekara da shekaru suna bautawa mace, a kan su sameta na rana ɗaya, lokaci ɗaya. Masrur irin mazan nan ne mazinata, shi kan shi bai san adadin ‘yan matan da yayiwa fyaɗe ba, wayanda kuwa yayi zina da su, sun fi cikin buhun hatsi, karuwai kuwa yana da su sunfi guda asirin, ya ƙware sosai a yaudara. Wanan shine Mus’ab. Mai ya kawoshi rayuwata. Ranar Wata Asabar, mun dawo daga makarantar hadda ta safe ni da Walida, lokacin Sadiya tayi gaba sabida tana sauri zasu je gidan yayar Anty, gidansu saurayinta. Shi kuma dai-dai lokacin ya fito daga wani babban shagon aske da ke bakin titin mu. Waya ce a hannunshi yana dannawa, amma idanunsa na sauka a kanta yaji ya kasa ɗauke su, zallan kyau ne kawai ya ɗebeshi, sakamakon sauran ‘yan matan da jikinsu ne ke ɗibarsa. “Wanan tayi yarinya.” ya raya a ran sa, amma shaiɗaniyar zuciyarsa ta ce masa. “Wanan ita ce dai-dai, ka rai ne ta da soyayyarka, yadda zaka juyata yadda ka so.” Ba shiri ya fara bin mu a baya, har zuwa lokacin da mu ka shiga gida. Tun daga wanan ranar Masrur yake sintirin bin bayana, har sai da ya gama fahimtar komai a kan rayuwata, ranar da muka fara magana, ranar ya tsara hakan, sanan layin da ya bani, ni kadai ke kiran shi da shi, shiyasa duk lokacin da na kira yake kama sunana kai tsaye, a kullum mugun kudurin shi a kaina ƙara girma yake, yau da gobe yana ƙara jin sabuwar sha’awa a kai na, wacce bai san ta zama soyayya ba. Matsalal shi da Mus’ab kuma ita ce. Masrur ya taɓa yiwa wata yarinya fyaɗe, wacce take ‘yar aikin gidan su abokin Mus’ab, to a lokacin da aka yi case ɗin, Mus’ab baya ƙasar, sai da yadawo ya samu labari, kuma gayen da aka nuna masa yayi masa kama da Masrur, kasancewar an ɗauki shekaru, Mus’ab ya manta asalin kamar gayen, shiyasa kawai ya watsar da lamarin masrur, ko dan irin shigar kamalan da ya gani a tare da shi. *Wanan kenan* Zaune nake kan doguwar kujera, na kafa uban tagumi, tambayar zuciyata nake. “Ina Mafita?.” sai dai zuciya tayi banza dani, kamar ba da ita nasaba neman shawara a kan komai ba, so nake nayi tunani amma na kasa, abu ɗaya ke dawowa zuciyata, shine: na zama matar Mus’ab. Ji nake kamar na cire kayana, nai ta ihu kamar mahaukaciya, ko kuma na kama gini nai ta duka, ko zanji sauƙi a zuciyata. Ikram ce ta shigo, janye da ƙatuwar akwati wacce nasan ta kayana ce. “Ke wanan fa?.” “Ummah ce ta ce a kawo miki, wai kayanki ne?.” “To ina sauran?.” “Wai an haɗe miki su, da su za’a haɗa da lefenki a kai gidan mijinki.” Ji nayi kamar ta watsa mun huta, na kai hannu na ɗaka ma ta duka, ta fice da gudu tana faɗin. “Ke da Allah.” Ni kai nasan kwana biyu na koyi saurin hannu, wanda da ba haka nake ba. “Uhm, bawanan ne ga ba na ba.” Na faɗa a fili, domin nasan ba shi bane a gabana, tunani nake son yi amma na kasa. “Salma ya kama ta ki rage wanan mummunar addu’ar ga Yaya Mus’ab, domin ance idan kayi addu’a ga wani bawan, mala’iku suna amsa da cewa Walaka, idan macece Walaki.” Tuno lokacin da Sadiya ta faɗamun wanan maganar nayi. “Ke ni Wallahi indai Mus’ab zai ga mu da masifar duniya, to ba wani abu ba ne, dan nima na gamu da ita, Sadiya ba zaki gane yadda natsani Mus’ab ba.” Amsar da na bata a lokacin kenan. Tabbas addu’a ta ta amso amma a kai na, domin tabbas Mus’ab ya kasance masifar da aka gama ni da ita. Wanan wace irin rayuwace, nayi masa addu’a ta faɗa kai na, nayi masa mugunta sabida ya mutu da ciwo, ya juye kai na. Tabbas addu’a ta ta amso amma a kai na, domin tabbas Mus’ab ya kasance masifar da aka gama ni da ita. Wanan wace irin rayuwace, nayi masa addu’a ta faɗa kai na, nayi masa mugunta sabida ya mutu da ciwo, ya juye kai na. Kuka na fara, hawaye suna bin kunci na, ga tilin kayana da aka kawomun daga gidan ubana a gaba na, duk wanda ya ganni dole ya tausayamun. Yana tsaye bakin taga yana kallon yadda nake zubda hawaye, yana jin zubar hawayen a cikin zuciyarsa. Tabbas ya kamu da tausayina mai girma, domin duk wani kuka na, ko zubar hawaye na, yana jinsa a zuciyarsa, ji yake kamar ya je ya kamani ya gogemun hawayen, ji yake kamar ya je ya bawa Abbanah hakuri kan su janye auren nan, in dai hakan zai sa na daina wanan kukan. Ficewa yayi zuwa bangaren Hajja, tana zaune daki tana faman lisssfin bikin Mus’ab, wai zata gayyato ƙawayenta na ƙuruciya, suyi ashobe abunsu, kuma so take Abban ciki ya kawo mata atamfar turmi ashirin tarabawa kawayen na ta. Kallon shi tayi, yadda ya shigo sim-sim kamar mara gaskiyya. “Mus’abunah mene ya kuma faruwa?, dan nasan wanan fitinanniyar matar taka batta bari mu zauna kalau.” Zama yayi kusa da ita, sanan ya ce. “Bakomai Hajja, kawai gani nake dan Allah a fasa wanam auren Hajja, bana son naga yarinyar nan ta na kuka.” baki buɗe Hajja take kallonshi, tun da ya fara magana, har ya dire. “Eyh Lallai ne, salau, sallamu, tun kafin a kai ta gidan naka, ka fara cewa baka son ka ga tana kuka?.” “Ni ba haka ba Hajja, gani nake kamar an shiga haƙƙinta.” “Lallai ne Mus’ab, to idan kamanta bari na tuna maka, yarinya fa an d’aura muku aure, yanzu komai na ta yadawo ƙarƙashin ka, cin ta, shan ta, sutturarta, da duk wani sauran nauyinta, rashin yi mata duk wani abu na al’adar aure shine shiga haƙƙinta, dan haka tun wuri kaje ka fara shirya komai, wajen xama da kayan lefe.” Shiru yayi, shi wajen zama ai sai dai ya bawa wani, sanan kayan lefe ma ba matsala ba ne, ko yanzu yayi waya kafin awa ɗaya sai an had’a mai komai da komai, amma yanda za’ayi zaman?, shi gani yake a ta bangarenshi babu matsala, tayi rayuwarta yayi ta sa, ko gaisuwa karta haɗasu, ko abinci ba zai buk’ata daga wajen ta ba. “Kaji abinda na ce maka?.” Gyad’a kai yayi ya tashi ya fice, Yaya Asma’u ya kira a waya, daman ita ce kawarsa a kaf Galadima. Tana zaune ta ga kiransa ya shigo, dariya tayi har sai da mijinta yak kalleta.”Mus’ab ne.” ta faɗa tana ɗaukan wayar. “Ango, Ango. Angon salame na Hajja, Yayana kuma mijin ƙanwata.” Tsaki yaja tare da cewa. “Asma’u mai yasa ba zakiyi hankali ba.” dariyar ta ƙarayi sanan ta ce. “Hankali har ya huce na baka ƙanwata ka aura?.” Legends pen Page 16. “Ba wanan maganar ba dan Allah, ki nutsu.” zama ta gyara sanan ta ce. “Tom, na nutsu ina jinka.” “Idan za’a haɗa lefe, kamar nawa ce za tayi.” “Na talakawa ko na masu kuɗi.” ta tambaya tana dariya, a fusace ya ce. “Na dai-dai ahalin Galadima.” “A’ah, mai yayi zafi bawan Allah da zaka gayamun ba suger.” “Zaki faɗamun ko na kashe wayata.” “Yi haƙuri, idan za’ayi ƙarami 1.5million zata isa, idan kuma ana son matsaiakaci 2million, tsaka tsaiya kuma 3million, idan kana son wanda zai yi kyau ba’ayi almubazaranci ba, amma kayan sunyi yadda za’a faɗa 5million, idan kuma ka na son mai yawa 10millon.” “Account dinki zai iya ɗaukan 7million?.” ita kanta ta ji mamakin 7million ɗin da ya fada, amma sanin yana da kuɗi, zai iya fin haka yasa ta ce. “Na wa kam bai ɗauka, amma bari na baka namiji na.” “Okay, zan samiki 7millinon sai ku haɗa yanda ya dace.” daga haka ya kashe wayar. “Lallai salma anyi goshi,amma ta tsaya tana iskanchi.” Yaya Asma’u ta faɗa, sanan ta kalli mijin ta ta ce. “Zan bawa Mus’ab account dinka, zai sa mun kuɗi zamu haɗow Salma lefe.” “Okay badamuwa, sai na bar miki atm ɗin.” wayarta ta ɗauka ta kira Yaya ta Zaria, ta shaida mata komai.”Eyh, Lallai Mus’abun Hajja.” Yaya ta Zaria ta faɗa. “uhm bari ke dai, ran ‘yan maza yaɓaci, yanzu goben kawai nan xaki shigo.” “Shikenan sai mu fita da huri.” daga haka su kayi sallama. Maman ciki ce ta shigo ta ganni ina ta faman zubar da hawaye, ga kuma tulin kayana a gaba na. Zama tayi kusa dani tare da faɗin. “Salma.” a hankali na ce. “Na’am.” “Ya kamata ki nemi yafiyar iyayenki, domin suna matuƙar fushi dake, hakan kuma ba ƙaramin abu ba ne.” Murya ta a hankali na fara magana.”Amma Mama mai yasa ummanah ba ta so na,a kullum ta zaɓi abinda bana so a kan wanda nake so, ba ta damuwa da farin cikina.” “A’a, wanan maganar ba gaskiyya ba ce Salma, babu yanda xa’ayi mahaifiyar da ta haifi mutum ya zamana ba ta son shi, kin san irin sadaukarwa da iyaye domin farin cikin ‘ya’yansu, kin sam irin yanayin da iyaye ke shiga idan su kaji kukan ‘ya’yansu?, tabbas kinyi wa mahaifiyarki fahimta ba dai-dai ba, kiyi gaggawar tuba wajen Allah, sanan ki cire wanan tunanin a ranki.” Shiru nayi, zuciyata na koƙarin gano mun lokaci ɗaya da Ummanah ta taɓa yin wani abu da yayi dai-dai da ra’ayina, amma shaiɗaniyar zuciyta ta kasa hango mun, bayan tulin abubuwan Alheri da mahaifiyata ta mun, da kuma wanda take shirin yi mun. “Ki tashi ki matsar da kayan naki, insha Allahu ba zaki ƙara sati biyu cikin gidannan ba, zaki tafi naki gidan.” “Lalai matar nan.” na fada a rai na, ni ina mamakin yadda zasu ajiye ni gida ɗaya da Mus’ab, kuma har washe gari su dawo sai su sameshi da rai, ko da cikkakiyar lafiya. Tashi tayi ta fice, tun da ta ga na shiga tunani, Allah yasa nayi tunanin abinda yake Alheri, buɗe baki nayi da niyar cewa ta bani aron wayarta na kira Masrur, sai dai tuna wa da nayi da ƙaddarararen auren Mus’ab a kaina ya sa nayi ƙus.”Magana kikayi Salma?.” girgiza kai nayi alamun A’h, ta sa kai ta fice. Tana shiga ɗaki ta kira wayar Mus’ab. “Kazo duk inda kake, ina son ganinka.” ta faɗa bayan ya ɗaga wayar. “Ina ɗakina.” “To na ce dai kazo.” Tashi yayi ya fito zuwa ɗakin na ta, tana zaune kan kujera, shi kuma ya zauna ƙasa. “Mama gani.” Kallonshi tayi, kusan minti biyar sanan ta ce.”Mus’ab, ko kasan kai ne sanadiyar rashin fahimtar dake tsakanin Salma da iyayenta, musamman ma mahaifiyarta?.” da sauri ya ɗago kai, ya kalli Mama ta kuwa ɗaga masa kai alamar “Eyh” sanan ta ce. “Ka san yadda mahaifiyar Salma ke son ka, ko ni irin son da zan maka kenan, kai ne ka cusa ƙiyayyarka a zuciyar Salma, ka kuma raine ta, domin a farkon tashin Salma ta na son ka, amma bakin halin irin na ka ya ja ka haifar da tsana mai girma a zuciyarta, ka kawo rashin fahimta tsakaninta da iyayenta, Mus’ab haƙƙine a kan ka, ka ɗinke ɓarakar nan, haƙƙine a kan ka ka raini Salma, ka goge wanan tsanar, ka mayar da ita Soyayya, sanam ka kawo iyayenta ita a matsayin masoyiyarka,kuma wacce tayi biyayya ga iyayenta, shine kadai hanyar da zai sa su sakko daga wanan fushin da sukeyi a kan ta.” “Shikenam Mama, insha Allahu zanyi duk wanan abubuwan, zata tabbatar na kawo Salma a matsayin mai biyayya, zan yi haƙuri da duka halayenta, sanan zan goge duk wata ƙiyayyata a zuciyarta, nayi miki wanan alƙwarin Mama.” “Allah yayi maka albarka, ya kuma da fa.” “Amin ya Allah.” Ta shi ya yi zuwa ɗakinsa, bayan ya kwanta ya yi shiru, ya na so ya amsarwa zuciyarsa sabon yanayin da yake ji. Tabbas bai san so ba, amma yana jin kamar zuciyarsa ta faɗa soyayya da Salma.”Amma ai ance soyayya ba ta shiga sai wani abu ya ɗauki hankalinka, to ni mai ya ɗauki hankali na a tare da Salma?.” Ya yi wa kansa Kan sa wanan Tambayar, amma sanin babu mai ba shi amsa ya sa shiru, domin ya san haka zai dauwama cikin shirun, ji ya yi zuciyarshi na azal zalal sa lallai sai ya je yaga Salma, ko ta dai na kukan, ko ba ta dai na ba?. Ba yan da ya iya, dole ya ta shi ya fita, a bakin taga ya tsaya yana kallon Salma, wacce ta baje kayan ta a ƙasa tana kallon su tsaf, tana faman tunani kala kala. “Way’anan su ne ‘yan kayan da aka kawo mun, sauran kayana masu kyau fa, nufin su idan naje gidan mijin kwalliya zanyi masa ko me?.” na tambayi kai na, a lokacin da na ke kallon kayan, ji nayi kamar mutum a kai na, hakan ya sa na ɗaga kai na, sai dai babu kowa, na ci gaba da kallon kayana, idona na kai wajen window kawai na ga mutum yana kallo na ƙir. Legends pen. Page 17 Murguɗa masa baki nayi, tare da galla masa uwar harara, har da jan tsaki, dan nasan a cikin gidansu dai bai isa ya taɓa lafiyata ba, ga matuƙar mamakina sai na ga yayi murmushi. Wani ƙululun abu ya tsaya mun a maƙoshi, ji nayi kamar na ta shi na fara dukan sa, har sai ya dai na motsi, ko zan ji wani abu ya ragu a zuciyatah. Ɗauke kai nayi, na mai da shi kan kayana, a zuciyata ina faɗin. “Wai wanan ne mijina ni Salma, gaskiyya nayi asarar Kyakyawan matashin saurayi, mai kyau da jini a jiki, wato Masrur, an haɗani da wanan lange langen.” domin ni tabbas zuciyata rayamun take idan na kama Mus’ab da duka, tsaf zan iya ɓallashi, ban san ba ko tsanar da nayi masa ce ta sa nake ganin shi kamar tsinken kwa-kwa. Juyowa nayi na sake kallon tigar, yana tsaye kamar an dasa shi, sai dai wanan lokacin wayarsa yake kallo ba ni ba, hararsa nayi, tare da murguɗa masa baki, na mai da hankalina kan kayana. “Na tashi na je na amso kayana wajen Ummanah, ko kuma na bar su kawai, tun da ba ta son gani na?.” “Allah ya isa Mus’ab, ko a haka ka cuceni, ka sa mahaifiyata da mahaifina na fushi da ni, ka raba ni da iyayena, ka haramtamun shiga ɓangarenmu.” Wasu ƙanan hawaye na ga suna zubowa ta idona, da sauri na juyar da kai na, ba na son ya ga hawaye a idona, dan nayi alƙwari Mus’ab bai isa ya ga gazawa ta ba, yaƙin yanzu ya fara, mu zu ba mu gani, shege ka fasa tsakani na da shi. Bai ga hawayen da ke idona ba, amma yasa wayarsa ne yana recording ɗin na video, mussamman lokacin da na sake juyowa, na murguɗa masa bako, tare da harara. Ta cikin wayar yake kallona, tare da yin murmushi, ya yanke iya wajen da nayi harar da murguɗa baki, ya yi saving. Kiran Abdul ne ya shigo wayarsa, Abdul shi ne babban abokin Mus’ab a duniyar nan, tun su na ‘yan ƙanana suke yin abota, mai cike da so da ƙaunar juna, suna raba duk wani sirri tsakaninsu, su magance damuwarsu, su bawa junansu shawara. Ba wai ba su da wasu abokan ba ne, amma su biyu ta su tafi zuwa ɗaya, ganin abubuwa na ƙoƙarin cunkushewa Mus’ab ya sa ya kira Abdul, a iya sanin Abdul ya san an ɗaura mai aure daren jiya, amma ya ce zai ma sa bayanin komai. “Ango! Ango.” Abdul ya faɗa bayan Mus’ab ya ɗau wayar, haka kawai Mus’ab ya tsinci kansa da yin murmushi jin an kira shi da Ango. “Man how far?.” Mus’ab ya faɗa, har lokacin da murmushi a fuskarsa, amma ya matsa daga jikin window ɗin, ya nufi ɗakinsa. “Normal ango, ya kwanan angon ci.” “Me yasa kake da matsala har haka ne.” Dariya Abdul ya yi sanan ya ce. “Yanzu fa nake ƙoƙarin ƙarasowa, motan da nake son fita da ita ne ba a wanke ba, sai da na jira.” “Kai kuma da ke an ce dole sai ita zaka hau?.” Mus’ab ya ba shi amsa. “No ba haka ba ne, na kwana biyu ban hauta ba, anyway gani na ƙara so.” “Okay, kar ka shigo, bari na fito ni.” “Okay.” Abdul ya faɗa tare da kashe wayar, shi har yanzu so yake ya gasgata cewar an ɗaurawa Mus’ab aure, gaba ɗaya jiya ya dawo daga cafoniya, wayar da ya kira Mus’ab ya faɗa masa ya dawo, shine yake sanar mai wai an ɗaura mai aure. Mus’ab ɗin ne ya buɗe motar ya shigo, kallonshi Abdul ya yi sanan ya ce. “Ya na ga karame, kai da kake ango, na mayi tunanin zaka ce gidanka na G.R.A zan zo?.” “You think am joking ko?, kayi tunanin wasa nake ko?.” “To Mus’ab ba dole nayi tunanin wasa kake ba, dan ma ban ce ka hauka ce ba.” Zama Mus’ab ya gyara sanan ya ce. “Man, harkar asibitin nan ce ta tashi.” “Garin ya haka?.” “Ciwon ya tashi sosai, har na shiga critical condition, ban san inda ya ke ba, sanan asalin doctor ɗin shi ya duba ni, ya faɗa musu komai da komai, sanan ciwon ya zama very worst, sabida daɗewa da ya yi a jikina.” “Yaushe abun ya faru, kuma shi likitan ya ce ayi maka aure?.” Abdul ya je fa mai tambayar. “Yes, last week. Ciwon ya matuƙar tsorata Mama da Umma, Abba ne ya tambayi likitan maganin ciwon, sai ya ce best solution shine aure.” “Yanzu samiran ka aura?.” Girgiza kai ya yi sanan ya ce.”Iyayenta sun sami labarin wai inda cuta, sai su ka ce sun fasa ba ni.” “What!, how comes.” “Wallahi i don't know Abdul, kawai haka su ka ce.” Kwantar da muryar Abdul ya sa ke yi, sanan ya ce.”Mai yasa duk ba ka faɗamun ba, yanzu kuma wa ka aura?.” “Abdul ka na calfoniya, sanan contract ɗin da kake aiki a kan sa babban contract ne, yanzu ba ga shi ina faɗa maka ba.” “Yanzu wa ka aura?.” Abdul ya sake dawo masa da tambayar.”Wa aka auran dai, Salma ƙanwata.” wata irin juyowa Abdul ya yi, tabbas ya girgiza da jin sunan Salma a matsayin wacce Mus’ab ke aure, domin ko ƙudajen da ke yawo gidan Galadima zasu iya shaida tsantsanar tsanar dake tsakanin Mus’ab Galadima da Salma Galadima. “Wa ka ce wai.” Abdul ya sa ke tambayarsa. “Salma Galadima, ƙanwata.” “When a kayi auren?.” “Daren jiya, an saka auren, in the next two weeks amma yarinyar ta fara ƙoƙarin barin gida, kasa Abbansu da zafin zuciya, ya sa aka ɗaura auren daren jiya.” Shiru Abdul ya yi, ya san Mus’ab bai ƙaunar Salma, Salma ba ta ƙaunar Mus’ab, zallan ƙiyayya ce mai zafi, sai dai kuma ɗumin ƙaddara ya haɗa su, ya haɗa su waje guda bayan Sakata da su ka garƙamawa zuciyoyinsu. Legends pen. Page 18 “Kasan wani abu?.” Mus’ab ya tambayi Abdul. “Sai ka faɗa.” Abdul ya bashi amsa. “Ni kake tausayi ko Salma?.” Kallon Mus’ab Abdul ya yi sanan ya ce. “Dukkan ku, amma kai ne babban abun tausayi, domin kai babbane, kasan aure ka san ta zama matarka, dole zaka saurara a wani abun, amma ita fa, she will still behave as how she is before, babu wani abu da zata canja.” “Kasan wani abu?.” Mus’ab ya sa ke yin tambayar.”Wane abu?.” “Ban san so ba, amma tabbas zuciyata ta kamu da son Salma, tun daren jiya.” “Mai ka ke ji game da ita.” “Komai nawa ita, tunani ita, bacci ita, zuciyata za tai ta azalzalta a kan na je na ganta, idan na ga tana hawaye har cikin zuciyata nake jin su, idan ta kalleni ta harareni, ta murguɗamun baki daɗi nake ji, nayi mata video a waya ta, a yanzu shi nake son sake gani ko zanci sauƙi a raina, ji nake kamar nayi ni sa da ita, ina jin zan iya dauwama ina kallonta.” “Ka faɗa soyayya, mai shiga lokaci ɗaya, mai kuma ƙarfi abokina, sai dai ko a mafarki ban ta ɓa tunanin ƙiyayyarka ga Salma za ta zama ƙauna haka.” “Nima hakan, har yanzu na kasa gasgata zuciyata, na kasa yarda da hakan.” “Tun da har ka fara son Salma, komai zai zo da sauƙi, ita macece ƙiyayyarta ƙarama ce, daga lokacin da ka ɗauke, ƙauna da kulawa ko ɗora ma ta, shikenan yau da gobe za ta gane, za ta so ka, fiye da yadda kake son ta.” Shiru Mus’ab ya yi, zuciyarshi ta shiga tuno masa lokacin da ya dake Salma, lokacin da yayi mata targaɗe a hannu, lokacin da ya tsige mata kitson kanta guda ɗaya, kawai sabida ya ga tayi kuka, tabbas ya san Allah ya jarabce shi da son ganin Kukan Salma, yana mugun jindaɗi idan ya ga tana kuka, sai dai a jiya da yau, kukan ya zama abu mafi azabtar da shi, abu mafi soya zuciyarsa, a hankali ya bude baki ya ce.”Salma na da riƙo, ta riƙe ni a kan abubuwan da nayi ma ta, ka na ganin Salma za ta so ni?.” Shiru Abdul ya yi, tabbas Mus’ab ya azabatar da Salma, ya ci zalin Salma, ya na tuna lokuta da dama, da yake hana shi hakan, amma Mus’ab yaƙe ƙashi ƙasa ya ce sai ya yi, yanzu gashi Allah ya jarabce shi da son Salman. “Allah ya gama ka da Masifar duniya.” Sautin muryar Salma ya shiga kunnensa. Shiru Abdul ya yi, tabbas Mus’ab ya azabatar da Salma, ya ci zalin Salma, ya na tuna lokuta da dama, da yake hana shi hakan, amma Mus’ab yaƙe ƙashi ƙasa ya ce sai ya yi, yanzu gashi Allah ya jarabce shi da son Salman. “Allah ya gama ka da Masifar duniya.” Sautin muryar Salma ya shiga kunnensa, kamar yanzu ta ke faɗa, wanan addu’ar ta ta ‘yar kullum gare sa lokacin da yake dukanta ko cin zalinta. “Yanzu, a ce Salma ce masifar duniyar da take roƙon Allah ya gama ka da ita fa?.” Abdul ya faɗa, da sauri Mus’ab ya juyo ya kalleshi.”Wanan shime tunanin da nake yi a yanzu haka, amma insha Allahu ba haka ba ne.” Da fa kafaɗar Mus’ab Abdul ya yi, sanan ya ce. “Kar ka damu Man, komai zai zo da sauƙi, Salma ba za ta zama babbar damuwa ba, Allah zai shiga lamarin.” “Ina jin kamar haƙƙin Salma ne zai bibiye ni.” “kar ka faɗi haka, a kwai addu’ar iyaye, sanan kuma ka tu na biyayya ka yi, ka san duk mai biyayya bai ta ɓa ta shi a ban za.”Shiru Mus’ab ya yi, zuciyar sa na azalzallashi a kan ya je ya ga Salma, wayarsa ya zaro ya ƙura video ɗin da ya yi mata ido, kusan minti biyar bai ɗauke idonsa a kai ba, “Yanzu mene abun yi, yaushe za ta tare.” “Su Hajja sun ce, dole sai anyi mata duk wasu al’ada da ake yiwa sauran ‘ya’yan da aka aurar, sanan ina tunanin haɗe su za’ayi da Sadiya, Walida ce ban jim za’a haɗe da ita, kaman ba ta da tsayayye.” “ka na so ka ce, ba za a bani walidan ba.” “Dan Allah ba na son shiga harkar yara.” Mus’ab ya faɗa yana mai da hankalinshi kan wayar sa. “Kai ai uwar mata ka ɗakko.” Abdul ya ba shi amsa, Mus’ab dai ba kulashi ba, ya ci gaba da abinda yake yi. “Shikenan zanje na nema da kai na.” “To ni dai kar ka sani a lamarinku.” “Daman ai ba zan sa ka ba, yanzu ka gama yin kalal tausayi a nan, soyayyar ƙarama yarinya za ta hauka ta ka.” Murmushi Mus’ab ya yi kawai, shi kuma Abdul ya fice daga Motar. Kai tsaye ɓangarenmu ya nufa, Ummanah na kitcehen tana haɗa abincin rana, ta amsa sallaman da yake yi. “Umma ina wuni.” Abdul ya faɗa, bayan ya zauna a kan kujera. “Lafiya ƙalau Abdul, saukar yaushe.” “Jiya da daddare, sai kuma naji abun alheri, to Allah ya sanya alheri.” “Amin amin.” Ummanah ta fada, Shiru ya ɗanyi na ‘yan mintina sanan ya ce. “Ummah daman nima wata magana na zo da ita.” “Tom Abdul ina jinka, amma ka tabbatar ba ta shafi Salma ko mus’ab ba.” girgiza kai ya yi, sanan ya ce. “Tawa buƙatar ce nima.” “Tom, ina jinka.” gyaran murya ya yi sanan ya ce. “Ummah daman gani nayi, tun da anyi auren su Mus’ab, sanan za’a haɗe tarewar da bikin Sadiya, mai zai hana abani dama ne nemi Walida, ko Allah xai sa mu fahimci juna, duk sai a had’e mu.” har cikin ran Ummanah taji mugun dad’i, domin da lamarin Walida ta kwana a ran ta, ko azkhar d’in ta na safiyar yau ta sa Walida sosai a ciki. “Amma gaskiyya Abdul ka kyauta sosai da sosai, kuma kayi tunani mai kyau, Insha Allahu zaku fahimci juna.” “Bakomai Ummah.” ya fad’a kan sa a ƙasa. “Yanzu dai sun tafi islamiya na san, amma da yamma ka dawo, sai ku tattauna, nima yau zan sami Abban na su da maganar, bayan kun tattauna sai ka turu ayi kawai a huce wajen, Allah ya yi muku albarka, ya baku zuri’a ta gari.” “Amin Ummah.” ya fad’a tare da ta shi ya fice, Mus’ab na cikin mota ya ƙurawa video na ido yana kallo, ya riƙe wayar da dukkan ƙarfinsa kamar wani zai ƙwace, a haka har Abdul ya dawo, bayan ya shiga duka ɓangarorin hadda na Hajja, ina zaune ya shigo ɓangaren Mama, yana wani sunkuyr da kai kamar sabon munafuki, har da mun magana, amma ko kallon arziƙi ban masa ba. “Babban Yaya zan huce.” Kallonsa Mus’ab ya yi sanan ya ce. “Babban Yaya a ina?.” murmushi ya yi kawai, bai ƙara ce mai komai ba, fitowa Mus’ab yayi daga motar ya nufi cikin gida. “Ai gaida Amarya.” “Wai wane shaƙiyanci kake ji da shi ne haka Abdul?.” Mus’ab ya juyo ya tambayeshi. “A sauka lafiya ango, yanzu zanyi announcement a cikin friend's ɗinmu.” banza Mus’ab ya yi masa, dan ya rasa gane kan Abdul ɗin. Legends pen. Page 19 Ina zaune a falo na saka indomie a gaba na, ina jiram tayi sanyi na fara ci, dan bana jin zan iya cin wani abu mai nauyi, lokacin Maman ta fita ɓangaren Hajja. “Ina Maman?.” Na ji muryarsa a kunne na, wani ƙululun abu naji ya tsaya mun a maƙoshi, jin shi kusa da ni ya ƙara ɓatamun rai, turarensa mai warin akuyoyi ya daki hancina, su ka had’u su ka haifar mun da wani mugun yanayi. “Salame magana na ke.” kai zo ka ga baƙi wajen zuciyata, ji nayi kamar na kama ƙafafunsa na ja su ƙasa, ya kife. Na hau kan sa na fara duka. “ Ba dake nake ba wai?.” “Mus’ab ka matsa daga kusa da ni, kafin na kifar da kai ƙasa.” Dariya ya yi mai sauti sanan ya ce. “Zaki iya?.” wani ƙululun abu na sake ji, ban san san da zuciyata kwashe ni ba, na ja ƙafafun amma sai naji su digirgir, kamar wata bishiya, dariya ya sake yi, sanan ya ce. “Sa ke ja.” cokali mai yatsu da zanci indomie ɗin da shi na ɗauka, na sai ta kafaɗarsa da iya ƙarfina na cika masa, dariyar dai ya sake yi, sanan ya ce. “Sai kuma me?.” “Natsane ka Mus’ab, na tsane ka, mai son ka ma na tsane shi.” Tabbas ya ji kalmar tsanar har cikin zuciyarsa, domin ta shige shi yadda bai yi tsammani ba, jin kalmar ya yi kamar an so ka maaa mashi a ƙahon zuciya, da yasan kalmar da zan faɗa mishi kenan, sa tun farko ya barni na kai shi ƙasa, ko zanji daɗi, ƙila ma hakan yasa nayi murmushi, wanda a yanzu shine abinda yake matuƙar ƙauna a tare dani. “Salma, sake jan ƙafafun nawa, zan faɗi Wallahi.” ya faɗa cikin sanyin murya, irin sanyi da ban ta ɓa tunanin yana da shi ba, shiru nayi ban ce ko ƙala ba, danni babban abinda ke damuna shine ganinshi kusa da ni, da ba dan kar ya ga gazawa ta ba, dan bar ma sa ɗakin zanyi, to amma idan yaga haka, shikenan ko da yaushe haka zai dinga yimun, duk da na ƙuddurce cewa, idan an kai ni gidansa, kullum ina ɗakin da a ka bani, abinci ma Sai dai na sa Sadiya ta dinga bawa driver din ta yana kawomun kullum, amma a nan bai sa na bar mai ɗakin ba. “Kinji Salma, ki ƙara ja wallahi zan faɗi.” “To kar ka faɗin mana, ni kawai ka matsa daga inda na ke, na tsane ka Mus’ab.” “Ya salam, wanan kalmar tsanar ta na shigar masa har zuciya, tana dukan zuciyarshi da ƙarfi, kaman ana buga ganga, mai zaiyi wa yarinyar nan ta dai na faɗin wanan tsanar, baya son ta.” maganar da yake yi kenan a zuciyarsa, ni kuwa na ƙureshi da ido, babu abinda nake gani sai muni a fuskar, har wani kama na ga yanayi da gaggon biri, ga tsinannen turaren sa mai warin akuyoyi, ya addabe ni, ga indomie na nan na shirin yin sanyi. Hannu na sa na fara tureshi, tare da faɗin.”Ka matsa ni.” kasa matsawa yayi, gaba ɗaya zuciyarshi ta karye, yana ganin zallan ƙiyayya a idanuna. Hannuna na sa gaba ɗaya na turashi ya yi ƙasa, sai dai ya jawo ni mun fadi tare. “Allah ya isa Mus’ab, Allah ya gama ka da masifar duka duniya.” na fada tare da ta shi, ina jin sabuwar tsanar Mus’ab a zuciyata, ga wani sabon salo da ya fito da shi na shiga sabgata, wanda zai ƙaramun tsanarsa, ya ƙaramata girma da faɗi. Bai san ni duk abinda zai sani kusanci da shi, neman tsarin Allah nake da shi ba, amma zai wani fara yimun magana na munafunci. Indomie na na ɗauka, na zauna kan kujera na fara ci, Shi ma ta shi ya yi, ya zauna kan kujerar da ke kallon tawa, ya fara danna wayarsa. Hankali na kwance na ke cin indomie na, bani da wata damuwa ko matsala, domin ni duk girman matsala idan na zo cin abinci a jiye ta nake yi a gefe, dan haka Mus’ab bai kai girman matsalal da zai hana ni cin abinci ba, ko kuma ina ci ina tunaninsa. “Salma ba bismillah.” banza nayi dashi kamar banji ba, ba na ciki da kayan iskancin Mus’ab, dan na ga neman magana yake, na kulashi ya je ya ce na mai rashin kunya a sake jibgata, bayan yanda nake ji a jikina.”Salma kalma ɗaya a kai na.” ɗagowa nayi na kalleshi, sanan na ce.”na tsane ka.” “Ni kuma ina sonki Salma, ina sonki, so ba ƙarami ba, so mara misaltuwa.” “Salma ba bismillah.” banza nayi dashi kamar banji ba, ba na ciki da kayan iskancin Mus’ab, dan na ga neman magana yake, na kulashi ya je ya ce na mai rashin kunya a sake jibgata, bayan yanda nake ji a jikina.”Salma kalma ɗaya a kai na.” ɗagowa nayi na kalleshi, sanan na ce.”na tsane ka.” “Ni kuma ina sonki Salma, ina sonki, so ba ƙarami ba, so mara misaltuwa.” “Lallai Mus’ab, ya ƙware a munafurci.” Na faɗa a rai na, dai dai lokacin kuma Ummanah ta shigo, kallon mu tayi, sanan ta ɗauke kai. “Tana nan?.” “Nima yanzu na shigo, ina tambayarta ta mun banza.” Mus’ab ya bawa Ummanah amsa, yana kallo na ta gefen ido, tare da yi mun dariya. “Ba ki ji ba, ana tambayarki.” Ta faɗa a tsawace. “Ni yaushe ya tambayeni, Wllahi ƙarya yake.” “Salma kin ci ubanki, idan baki sani ba yanzu Mus’ab mijinki ne, ba kowace magana da rashin kunya zaki dinga yi masa ba, yanzu mala’ikun Allah zasu yi fushi da ke.” “Mai kuma tayi, ita da ba ta huce laifi?.” Maman ciki da ta shigo yanzu ta faɗa.”Rashin kunya take masa.” Ummanah ta ba ta amsa. “To wanan ai tsakaninsu ne, mene na shiga.” “Eyh, lallai ne.” Ummanah ta fada tare da shigewa dakin Maman ciki, bin ta tayi a baya cikin ɗakin. Ganin haka yasa na fi ce, shima Mus’ab ɗin ya biyo ni. “Salame, ina zaki?.” Banza nayi masa, dan bai kai na kula shi ba, bare kuma na bashi amsa. “Karfa ki fita.” juyowa nayi na kalleshi, sanan na ce. “Sai na fita, banza kawai.” Murmushi ya yi tare da bin bayana, ni kuma na fice zuwa ɓangaren Hajja. Tana zaune kan kujera na shigo babu ko sallama, faɗawa nayi kanta tare da fashewa da kuka. “Innullahi, wacece wanan haka.” kukan na ci gaba da yi ba tare da na ce ma ta ko ƙala ba, har Mus’ab ɗin ya shigo, ganin shi ya sa Hajja cewa. ”Mai kuma Ka yi ma ta?.” “Ni kam mai zan ma ta Hajja, sai dai ki tambayeta mai ta yi mun dai.” “Ni Hajja kice ya dai na zuwa inda nake, ya kyale ni, yayi nesa dani.” “Eyh, lallai ne Salame, lallai ba ki da hankali, mijin na ki zaki ce ya yi ne sa da ke, wai ni yarinyar nan menene a kan ki.” Kukan na ci gaba da yi, dan ba zan iya da hukuncin son zuciya da Hajja ke yi a ko yaushe ba, haka na gama Kuka na, na tafi ɗakin baccinta na kwanta.”Da ina ɓangarenmu babu wanda ya isa ya takuramun haka Gaskiyya Mus'ab ya cuceni." Haka na kwanta raina a ɓace ina ta juye-juye kan gado, sai dab da sallan magariba na miƙe, Hajja ce ka ɗai zaune a falon shi ya fice, ban ko kalli inda take ba nima na fice, ina jin ta tana cewa."Kyaji da shi, azababbiya." Legend’s pen Page 20. Hanyar ɓangarenmu na nufa, sai dai kuma tunawa da nayi bani da wani hurumi da ɓangaren yasa na canja tafiyata zuwa ɓangaren Alhaji ƙarami, Anty na cikin kitchen ta amsa sallama ta, sanan ta ɗora da faɗin. "Wa nake gani kamar amaryar Mus'ab." juyawa nayi na kalli baya, ko ni da wata mu ka shigo. Dan ni har ga Allah na manta da wani auren Mus'ab a kai na. "Kin ci gidanku Salame, mai kike juyawa gani?." "Matar Mus'ab ɗin man.." sai kuma na tuna cewar ni ɗin ce matar Mus'ab ɗin, dariya tayi daga cikin kitchen ɗin, dan ta fahimci abinda ya faru, ɗakin Sadiya na huce, kamar yadda nayi hasashe tana zaune tana faman wayar, Allah ya jarabci Sadiya da mugun son waya, sai suyi waya da Sadeeq sau 20 a rana ɗaya ko gajiya ba sa yi. Zama nayi kan kujera, tana wayar ina sauraronta. Daga nan kuma na faɗa duniyar tunanin kai na. "Allah sarki ni, an raba ni da wanda nake ƙauna, dai-dai lokacin da na fara jin daɗin soyayya, an haɗa ni da wanda na tsana, wanda ya tsane ni, iyayena sun watsar da ni, sun nuna mun ni ba 'yar gata ba ce, ni ba 'yar da ake so ba ce, za'a tura ni gidan namiji babu gata babu soyayyar iyaye, a haka namiji zai karɓe ni a matsayin hulaƙantacciya, mara gata, ta ina shima zai mutun ta ni, ta ina zai ga daraja ta." hawaye ne su ka fara zuba a kunci na, ba tare da na sani ba. Sadiya da ke waya ce ta kalli yadda nake lake nani tare da zubar da hawaye, katse wayarta-ta ta yi ta taso inda na ke, sai kawai ji nayi an dafa kafaɗuna tare da faɗin. “Salma, kiyi haƙuri ki dai na wanan kukan babu abinda zai miki, iyayen mu sun ga ma yanke hukuncin su, kuma har sun aiwatar, kiyi haƙuri kiyi biyayya, mu du ka mun san bakya son Yaya Mus’ab, shima baya son ki, amma ɗumin ƙaddara ya shiga rayuwarku, kuma ba ku san mai Allah ya tanadar ba.” “Amma Sadiya shikenan iyayena sun nuna bani da gata, bani da daraja?, haka za’a kai ni gidan miji a hulaƙance, miji irin Mus’ab da ba shi da mutunci?.” “Salma waya gaya miki haka, babban gata da iyayenki su kayi miki tun zuwan ki duniya, su ka baki ilimi da tarbiya, su ka aurar da ke. Tsaya kiji Mus’ab fa ɗan gida ne, wallahi ba isa ya yi wani abu dan ya cutar da ke ba, sai yanda kika dama zakiyi.” “Sadiya, ni fa ba na so Mus’ab ya dinga zuwa inda nake kwata-kwata, wallahi ko iska iri daya ba na son mu dinga shaƙa da Mus’ab.” “To ai kin san ba zuwa zaiyi ba, ba zai zo inda kike ba.” “Waya faɗa miki, ɗan iska ne fa, ɗazu har da jawo ni jikinsa.” na faɗa ina tsartar da yawo.”Ubanki Salma, mijin naki kike cewa haka?.” “Allah ya tsare, wallahi Mus’ab ba zai ta ɓa zama mijina ba, sai da na gawa ta.” ba ta kai ga buɗe baki ba Walida ta shigo da mugun gudu tana dariya, matsawa nayi gudun kar ta faɗa kai na, tare da jan tsaki, ita kam ba tabi ta kaina ba, sabida farin cikin da takeyi. “Albishirinki.” ta faɗa tana kallon Sadiya alamun da ita ta ke. “Goro fari ƙal-ƙal.” “Ni ma na kusa aure, tare da ku zan bar gidan Galadima.” har cikin rai na naji ma ta daɗi, amma ganin yadda ta yi banza da ni, ya sa nima nayi banza da ita. “Kai naji daɗi sosai da sosai, waye a cikinsu.” girgiza kai tayi sanan ta ce. “Ina dawo daga islamiya a ka ce Umma na kira na, ina zuwa ta ce na je nayi wanka na shirya na zo, aiuwa na je na shirya na dawo, ta ce mun baƙo zanyi, idan mun fahimci juna shikenan, kin san waye baƙon?.” Ba sadiya ka ɗai ba, nima da ba ni ake bawa labarin ba na matsu na ji. “Waye ne, ke matsalal ki gutsira zan ce.” “Uhm, Yaya Abdul abokin Yaya Mus’ab.” Tsaki na ja a fili, duk uwar ɗarin, ni na tsane Mus’ab na tsani abokansa. “Kai Alhmdulillah, amma naji daɗi sosai, ai Yaya Abdul mutumin kirki ne sosai.” Sadiya ta faɗa, dan son kawar da tsakin sa na yi. “Na gode sosai da sosai, daman ai na san ke zakiyi farin ciki, dan ke baki da zuciyar baƙin ciki.” Gaskiyya maganar Walida ta shige ni, tana nufin nj baƙin ciki nake mata, mai zan yi wa baƙin ciki a gayyar Mus’ab, idan ma na ƙyale ta ai ta ci banza wallahi. Miƙewa nayi tare da zuwa inda take, na tsaya ƙiƙam a kan ta, ban ma san ta inda zan fara ba, ji nake kamar na rufe ta da duka. Sadiya ce ta taso zuwa inda mu ke tare da faɗin. “A’a faaa, Salma ki koma inda kike.” “Kyale ni Sadiya, wallahi sai na yiwa yarinyar nan mugun duka, ban da hauka ma irin na ta menene abun baƙin ciki a Abdul, gayyar tsiya, gayyar marasa mutunci, to ni wallahi ko yayan na ta bai isheni kallo ba, bare kuma gayyar abokansa.” Miƙewa tayi ita ma tare da faɗin. “Gayyar rashin mutunci ai bai huce ke ba, da baki san darajar mijinta ba.” wani maƙoƙon abu ya tsayamun a rai. “Walida ki shiru mene haka wai?.” “Sadiya bar ni na faɗa ma ta, ita gani take kamat tsoronta ake ko?, idan kuna tsoronta ni ba tsoronta nake ba, ke gani kike alfarma ki ka yiwa Yaya Mus’ab ko me?, to ki sani idan a farko kinyi masa alfarma zaki aure sa, sabida iyayenki zasu haɗa ku, to daga baya shi yayi miki, domin duk macen da ta sa ƙafa ta bar gidan iyayenta to darajar ta taƙare, ta zama banza mara daraja, kuma duk namiji mai daraja ba zai aure ta ba.” “Sadiya bar ni na faɗa ma ta, ita gani take kamat tsoronta ake ko?, idan kuna tsoronta ni ba tsoronta nake ba, ke gani kike alfarma ki ka yiwa Yaya Mus’ab ko me?, to ki sani idan a farko kinyi masa alfarma zaki aure sa, sabida iyayenki zasu haɗa ku, to daga baya shi yayi miki, domin duk macen da ta sa ƙafa ta bar gidan iyayenta to darajar ta taƙare, ta zama banza mara daraja, kuma duk namiji mai daraja ba zai aure ta ba.” Tabbas naji maganganun Walida har cikin kwa-kwalwata. “Wai ni ce mara daraja, kuma duk namiji mai daraja ba zai aure ni ba.” ban san lokacin da na kai hannuna na tsinkawa Walida wani mugun mari ba, tare da ƙara ma ta wani, ita ma a fusace ta kai hannu ta kifamun mari, nan da nan faɗa ya kaure, ina dukanta, tana duka na abu kamar wasa ya zama babba, Sadiya na tsakiya, ni kuma har ita nake haɗawa na jibga. Idan mutum ya shigo zaiyi tunanin duka mu ukun ne ke faɗan. Legends pen. Page 21. Sadiya ganin abun ya fi ƙarfinta ne, ya sa ta fita zuwa tsakar gidansu, tayi mamakin rashin ganin Anty a kitchen, sai dai ba ta san shigowar Walida ta ce mata, Ummanah na neman ta a ɓangaren Hajja. Leƙawa ɗakin ta kuma yi, ganin muna faɗan kamar ba mu ta ɓa sanin Juna ba, ya sa tayi waje, cikin sa’a ta ci karo da Yaya Mus’ab, da kuma Abdul. “Yaya Mus’ab, ana faɗa Walida da Salma.” da sauri suka biyo bayanta zuwa ciki. Yaya Mus’ab ne ya shiga raba mu, Walida na ganin shi ta cika ni, mussaman ganin Abdul da ta yi. Ni kuwa idanu na sun rufe, ci gaba da dukanta ta nayi. “Wai ba zaki bari ba ne.” Ya faɗa a tsawace. “Ba zan bari ba ɗin.” na ba shi amsa nima da ƙarfi, haushin ganin zan kunyata yayanta a gaban abokinsa, ya sa Walida ta kai mun duka ita ma, ai kuwa nayi tsallen albarka na ƙara shaƙe ta, nan faɗa ya dawo sabo. Duk da Mus’ab yana tsakiya, amma hakan bai hanani kai wa Walida naushi ba, sai a lokacin Abdul ya yi magana. “Wai ke Salma mene haka, mai yasa bakya jin magana?.” duk wata fusata ta jawo ta na yi, na ɗago a fusace na kalleshi. “Ka ga Malam ban shiga sabgar ka ba, dan haka kar ka yi shishigin shiga ta wa, aikin banza kawai.” “Wai Salma mene haka?.” Sadiya ta faɗa, ganin lamarin nawa ba na ƙare ba ne.”Dalla malama ke ma rufe mun baki munafuka, ai duk bakin ku ɗaya.” ina faɗin haka na fice, na kuma ƙudurce a raina, gaba ɗaya na fita sabgar Walida da Sadiya har abada, a hanya na ci karo da Ummanah, da Maman ciki, har da Anty, su ma ɗauke kai na yi, da niyar ba zan musu magana ba, dan ni na fita sabgar ‘yan gidan Galadima gaba ɗaya. “Uwarki na ce.” Ummanah ta faɗa tana riƙe hannuna. “Kuka na fara, ina faɗin . “Ni ki cika ni.” Anty ce ta ce. “Wai Salma mene ke yawo a kan ki dan Allah?.” “Ni Anty kawai su kyale ni, ni ba na son kowa.” Maman ciki ce ta riƙe ni, ta fahimci irin yanayin da nake ji a zuciyata, irin yanayin da za ka ji, baka son kowa, kawai kaɗaici kake buƙata. “Cika ta, mai da ita ɓangaren Hajja, kowa ya fita sabgarta.” Maman ciki ta faɗawa Ummanah. “Wai Salma ce ta haife mu, ko mune muka haife ta, sai abinda take so zamuyi?.” “Ba wai haka bane Yaya.” Anty ta faɗa. “To ya ne, ku ba ni ita na tafi da ita, za ta ci ubanta.” ni haka kawai sai naji ma na fi son ɓangarenmu, shine babu wanda ya isa ya zo ya takura mun. “Ta je can ɗin, ina ga zai fi.” Maman ciki ta faɗa, tare da cika ni, mu ka nufi ɓangaren mu nida Ummanah, muna shiga na nufi ɗaki na, na kwanta tare da rufe idona. A can ɓangaren Anty kam, ina fita Mus’ab ya kalli Walida da Sadiya ya ce. “A yanzu sai kunyi ma ta uziri, sai kuma kun fita sabgarta har zuwa lokacin da za ta gane abinda take ba dai-dai ba ne.” “Ni kam na fita sabgarta har abada ma.” Walida ta faɗa, shiru yayi bai ce komai ba suka fi ce. “Kinga da baki biye ma ta ba, da yanzu ba ki zubar da mutunci a gaban wanda zaki aura ba.” Kallon Sadiya da ta yi magana Walida ta yi sanan ta ce. “Haba Sadiya, shikenan ita sai tai ta yi wa mutane iskanci?.” “Ba haka ba ne, kin san dai tun ba yanzu ba akwai tsana mai girma tsakanin Salma da Yaya Mus’ab, to kuma a ce shine mijinta, dole ta shiga damuwa fa.” “Shi bai tsane ta ba?, amma yanzu ga shi ya ajiye komai.” “Walida abinda zaki duba, Yaya Mus’ab namiji ne, kuma babba, yafi Salma hankali, amma ita ma wata rana za ta gane, za kuma ta karɓi Ƙaddarar da ta haɗa su aure.” “Ai shikenan, amma wallahi na fita sabgarta gaba ɗaya.” *Mus’ab* “Mus’ab, akwai aiki babba a kan ka, lamarin yarinyar nan ba ƙaramin aiki ba ne.” Abdul ya faɗawa Mus’ab, da ya kifa kan shi a kan sitiyarin mota.”Nasani Abdul, ina tambayar zuciyata mai yasa ta faɗa soyayyar Salma da huri haka, mai yasa?.” “Kamar ko da yaushe shi so babu ruwanshi, da yaga wuri faɗawa yake, kawai ka yarda da zuciyarka, ka amshi soyayyar Salma, sanan ka yi yaƙin yadda za ta so ka, amma ba wai ka tsaya ka na ja inja da zuciyarka ba.” Shiru Mus’ab yayi, har yanzu yana tantama yadda zuciyarshi ta faɗawa soyayyar Salma mai girma, da nauyi har haka. “zaka sauka ne, ko mu huce gidanmu.” “Kai ne hotel, yau a can zan kwana, ina son restful night, ina son nayi tunani, nayi shwara da zuciyata.” “Kai malam a nigeria kake ba wata ƙasar ba, faɗi inda xaka kwana ba hotel ba.” “Kai ni Malali.” Jan motar Abdul ya yi, zuwa makeken gidan Mus’ab da ke Malali G.R.A, gida ne gaske, mai girman gaske, gida ne da ya tsaru, aka kashe kuɗi. Horn Mus’ab ya yi, mai gadin gidan ya fito ya buɗe, su ka shiga ciki.”Ranka ya daɗe barka da zuwa.” buzun mai gadin ya faɗa, cikin hausarsa ta ‘yan koyo. “Yawwa barka.” Abdul ya faɗa, dan shi Mus’ab tun da su ka fara tafiya bai ce komai ba, har yanzu da su ka ƙara so. “Man.” Juyuwa Mus’ab ya yi, ya kalli Abdul da ya yi maganar.”Zan huce, sai da safe.” “Ba tare zamu kwana ba?.” Mus’ab ya faɗa cikin sanyin murya. “Ka ci kai.” Abdul ya faɗa yana juyawa cikin motarsa. Murmushi Mus’ab ya yi tare da cewa. “Sai da Safe, ka tawo mun da breakfast.” “Sai dai nasa Salma ta yi maka.” banza Mus’ab ya yi masa kamar bai ji shi ba, ya shige cikin gidan, shi kuma ya ja motarsa ya yi waje. Falon ka ɗai abun tsayawa a kalla ne, wani irin globe ne a ɗakin, ɗaukan ido ya ke da ƙyalli, kai ka ce da gold a ka yi shi, wasu manyan A.C ne a ɗakin, su kan su design and decorated ones ne, kujerun da ke cikin ɗakin sun yi masifar karɓar ɗakin, makekiyar TV da ta cika bango guda, ta ƙara haskaka ɗakin. Legends pen Page 22. Wanka na sake yi, na shirya cikin wata baƙar doguwar riga, nayi kyau sosai abuna, duk da ba wai kwalliya na yi ba, amma na shafa mai da powder har da man leɓe, na ɗauki ƙaramin mayafin doguwar rigar nayi mishi wata kalal yafa mai kyau, wacce nake gani a nayi a TV, ta shi na yi na gabatar da Sallar magriba, sanan na fito falo. Da ido Ummanah ke kallona, tana so ta yi magana, amma ta na jiran ganin gudun ruwana, zama nayi kan kujera na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, na zubawa TV idanu, na yi kai na alƙwarin ba su Mamaki. “idan mu suna tunanin sun aura mun Mus’ab, dan na shida damuwa, to na dai na damuwar, wanka da gayu zan fara, idan akwai mai bakin ciki to ya mutu, zan nuna musu na kwantar da hankalina, zanyi rayuwa kamar ban da mu ba, a ɗaga bikin har zuwa mu yi candy, kafinan zan samu hanyar da zan bi, amma wallahi ba zanyi zaman aure da Mus’ab.” “idan mu suna tunanin sun aura mun Mus’ab, dan na shida damuwa, to na dai na damuwar, wanka da gayu zan fara, idan akwai mai bakin ciki to ya mutu, zan nuna musu na kwantar da hankalina, zanyi rayuwa kamar ban da mu ba, a ɗaga bikin har zuwa mu yi candy, kafinan zan samu hanyar da zan bi, amma wallahi ba zanyi zaman aure da Mus’ab.” Wanan shine alwashin da na ɗauka. Ina zaune Abbana ya shigo,kallona yake sosai, dan shi a farko ma ya yi tunanin baƙuwa muka yi. “Wanan kuma lafiya?.” ya tambayi Ummanah. “Nima yanzu naga ta fito a haka, jira nake na ji mai zai ta ce.” “Ni babu abinda zan ce, kawai ba zan yi wanka na shirya ba, ni da ba mutuwa a ka yi mun ba, ba takaba na ke ba.” “Kya dai ji da shi.” Ummanah ta faɗa, shi kuma Abbanah ya yi ɓangarenshi, ina nan zau ne a kan kujerar, bayan na ɗauki wayar Ummanah ina dannawa, na hakimce kamar wata baƙuwa. Walida ce ta yi Sallama, ban ko kalleta ba bare na ɗago, ita ko kallon na take tana faman mamaki.”Wai Yaya Mus’ab yana nan?.” wani sanyi naji a raina, nan ta ke na fara addu’ar. “Allah yasa ya ɓata ko masu garkuwa da mutane sun ɗauke shi.”. Ummanah ce ta fito daga cikin ɗakinta tana faɗin. “Walida mai kike cewa.” “Wai Yaya Mus’ab ne bai shigo ba, gashi har tara ta gota.” “Innullahi, to ki ce ta kira wayarsa mana, ke ban wayata na kira shi.” ban ce komai ba, na miƙa mata wayar tare da miƙewa, ina tafiya ɗas, ɗas, na nufi kicin zuciyata fara sol. “Wayar ta shi tana ringing ba’a ɗauka ba.” Ummanah ta faɗawa wayar na kare a kunneta.”Mu ma mun ki rashi ba ta shiga ba.” Walida ta ba ta amsa. Hijabi Ummanah ta saka ta nufi ɓangaren Hajja, dai-dai lokacin da na fito daga kitchen riƙe da plate, ina ‘yar waƙata. “Ko kun kama suna da mu, ai ko ku ƙi kama suna da mu, mu mun samu dai-dai da mu, ko kuna ƙin mu to fa dubu sunayi da mu, kun ji ga ta, to ai subarma coge ma sun ta fi, Alla ba mu sa’ar zuwa su ‘yan adawar mu dukka abar su gadin gari, hehehe.” kallona kawai ta yi, ba ta ce komai ba ta fice, dariya nayi tare da faɗin. “Da an isa a tan ka.” Zama nayi na lodi abincina son rai na, na buɗe firji na kandami lemu, shima nai ta sha kamar raƙuma, ina gama na yi gyatsa, dai-dai lokacin Ummanah ta shigo tare da faɗin. “Duba mun lambar Abdul abokin Mus’ab a nan.” ta faɗa tare da miƙo mun wayarta ta. “Ai baki da ita.” “A’a Salma ina da ita du ba.” ban san lokacin da na yi suɓutar bakin cewa. “Hajja ce fa take da ita.” sai bayan na faɗa na shiga dana sani, kai wanan mugun surutu nawa bai yi ba, bai da wata rana, kallona ta yi sanan ta ce. “kin san Hajja na da ita, amma baki faɗa ba.” “Ai Ummah ita ma babu tabbas, cewa na yi ita yakamata a ce tana da ita.” “Ta shi ki je ki duba wayarta ki ga ni.” Ta shi nayi ina murna dan wallahi sai na gogeta, har na kai bakin ƙofa ta ce.”Ji ra ni.” ban so ba na tsaya mu ka tafi, dai-dai lokacin da muka ƙarasa walida ta kira lambar, ta duba wayar Hajja ne ta ga lambar Abdul ɗin. “Wai ya kai shi gidansa na Malali, a can zai kwana.” “Ba dole ya ce a can zai kwana ba, gida ana haɗa masa zafi, ni ka wai azo a ba shi matar sa su ta fi.” wani ban zan kallo na watsawa Hajja. “Kai wanan tsohuwar ba tayi ba kwata-kwata.” na faɗa a rai na, ita kuwa Ummanah kamar jira take ta fara na ta sababin. “Nima abinda na gani Hajja, kawai a ba shi ita su huce.” “Gaskiyya Hajja ba za’ayi haka ba, ai dai yi haƙuri, ai ‘yan kwanaki ne ya rage.” Ni kam daga Ummanah har Hajjan, har da Maman cikin ma jin su nake, naga wacce zasu kai gidan Mus’ab ɗin, ban san ba ko su na da wata Salman da ban san ta ba. Anty ce ta kalleni sosai, sanan ta ce. “Ita kuma ina za ta?.” “Wayasan ma ta, gata nan dai ki tambyeta.” Ummanah ta ba ta amsa, sai a lokacin hnkalin kowa ya yo kai na kuma. “ina zaki?.” Maman ciki ta tambaye ni. “Ina ga mijinta za ta bi.” “Ni dai Hajja ki dai na mun irin wanan, wane mijin zan bi?, sai dai na ki wanda ya mutu.” “Uwarki ubanki.” Ummnah ta faɗa, tare da kokarin kai min duka, juya kai na yi na nufi ɓangarenmu. “Anya lamarin auren nan, bai sa yarinyar nan ta kwaso Aljanu ba?.” Anty ta faɗa cike da sarewa. “Waya sani ma, ko kwanan da ta yi a ɗakin shirgi na gidan Alhaji idi me mai ba.” In ni maman ciki, Ummanah kam cewa ta yi. “Wallhi babu wa su Aljanu, wai halin Salma wanene ba ku sa ni ba?, tabbata ce kawai ta yi mata yawa.” Haka dai su ka yi ta maganganun su, karshe Kowacce ta yi ɓangarenta, ni kam ina zuwa ɓangarenmu na watsa ruwa na kwanta, ko addu’a ban ba, nayi kwancinyata. Legends pen. Page 23 Kamar ko yaushe, kiran Sallar farko ya ta shi, bayan daddan mafarkin da ya yi, wai shi da Salma a bakin wani tafkeken kogi, ga yara ƙanana guda biyu masu kyau, wa’yanda su ke mugun kama da Salma a gaban su suna wasa. Salman ta wane kashe murya ta na masa waƙa, gwanin ban sha’awa. Toilet ya nufa bayan ya tashi, wanka yayi ya zura jallabia, ya nufi massallacin da ke jikin gidan, bayan ya gabatar da nafulfulinsa ya bi jami’in Sallah da a ka tayar, bayan an idar da Sallah ya ɗaga hannu sama ya na roƙo Allah, dauwamamen zaman lafiya tsakaninsa da Salma, zuri’a ta gari, Allah ya ba su soyayyar juna, Allah ya kuma sawa Salma tausayi da soyayyarsa. Bayan ya dawo ne ya duba wayarsa, ya yi matuƙar mamakin ganin yawan missed calls a wayarsa na ‘yan gidansu, a gaggauce ya fara shirin tafiya gida, gwanda kawai ya je dan bai ma san mai zai ce mu su ba idan ya kira. Ina idar da Azkhar din safe na shiga toilet, wanka na yi sosai abuna, bayan na fito na hau shiri cikin lafiyayyar atamfa ta, shartoon mai matuƙar kyau da tsada, zama nayi na tsara light make up a fuska ta, na kashe uban ɗauri, na sha multi lips, sai ka rantse sabuwar amarya ce, ni kai na nasan na zuba uban kyau, domin na daɗe ina kallon kai na a gaban mirror, sanan na fito zuwa falo. Ɗakin Abbanah na nufa bakina ɗauke da Sallama, amsawa ya yi tare da faɗin ”shigo.” na kuwa shiga, ina ganin shi sai da ya kalleni tas, amma bai ce komai ba. “Abbanah ina kwana?.” “Lafiya ƙalau, ya rashin biyayya.” narai-narai da idanu tare da faɗin. “Wane rashin biyayya kuma Abbanah?.” “Na auren Mus’ab, ko kin yi mun biyayya ne?.” Ya katse ni da amsa, mai dauƙe da tambaya. Shiru na yi, dan ba ni da amsar ba shi wallahi, ku san minti biyar sanan ya ce. “Ta shi ki je, ki sa ni dai iyaye sune komai.” tashin na yi, domin ni bani da abin cewa, na san Ummanah na kitchen kai tsaye na nufi nan, ta na tsaƙa da zubawa doya a cikin plast ta ji na ce. “Ina kwana?.” ju yo wa ta yi takalle ni, ita kam sai da ta tanka ni. “Salma wai mai kike nufi da wanan saye-sayen kayan da kike?.” “Ni ba komai Ummah, shikenan zan zauna damuwa da ɓacin rai su kashe ni, wasu haka su ke so.” “Mitchew.” ta ja tsaki ta ci gaba da abinda ta ke. “Wanan ki kai wa Hajja, wanan kika ɓangarensu Mijinki a ajiye mai, saura idan kin je ki hau kan wuyansa.” “Ummah wane mijina?.” kallo na tayi cike da ɓacin rai, sanan ta ce. “ba za ki ɗauka ba?.” “Ni fa ban san wani mijina ba?.” “Ga shi can a ɗakin da kika fito.” shiru na yi na san na kai ta bango, dan Abbanah ta ke nufi. Daukan na Hajja na yi, snan na ɗau na shin na fice. Dai-dai lokacin da ya gama parking motarsa a harabar gidan, ta cikim motar yake kallona, irin kyan da na yi, yadd nake tafiya, duk wani taku guda ɗaya da na yi, tare ya ke tafiya da bugun zuciyarsa. Fitowa ya yi cikin sauri ya yo inda nake, ban kula da shi ba sai ji na yi ance.”Salame.” Dai-dai lokacin da ya gama parking motarsa a harabar gidan, ta cikim motar yake kallona, irin kyan da na yi, yadd nake tafiya, duk wani taku guda ɗaya da na yi, tare ya ke tafiya da bugun zuciyarsa. Fitowa ya yi cikin sauri ya yo inda nake, ban kula da shi ba sai ji na yi ance.”Salame.” Wani malolon abu ya tsaya mun a maƙoshi, ga takaicin ya yi mun magana, ga Haushin xuwa kusa da ni da ya yi, ga tsanarshi dake rayuwa a cikin zuciyata, ga kuma sunan da ya kirani da shi wai. “Salame.” a fusa ce na juyo, ban wani mai da hankali na kalleshi ba na ce. “Mus’abu fitinanne.” na san dole sai ji haushi, kowa ya san shi da son girma, domin duk gidan Galadima babu mai kiran sunan kai tsaye, sai dai ko iyayenmu, amma hatta da yayunshi mata ma haka suke cewa. “Yaya Mus’ab.” ni ka dai ce ban taɓa cewa Yaya Mus’ab ba, kuma yana sa ne da wanan abun, yana cikin abubuwan da ke ƙara ma sa jim haushi na, dan a lokacin da na ke ƙarama yana mugum jin haushin sunansa da na ke kira. Ga mamaki sai na ga ya yi murmushi tare da cewa. “Kin yi kyau, kina da kyau Beb.” wani mugun abu ne na ji ya na neman dakatar da numfashi na.”Wai Beb, A’a ted.” na faɗa ina galla ma sa harara. “Shima ya yi kyau.” “Allah ya tsine maka Mus’ab.” na faɗa tare da shigewa ɓangaren Hajja, fuska ta fal da hawaye. “To sarauniyar kuka, mai kuma a ka yi daga safiyar.” zama na yi sanan na ce. “Ga shi.” “Ina tambayarki ya a ka yi, kina cemun ga shi.” “To Hajja kuna gaya miki babu abinda zaki yi, ƙarshe ma sai dai ki ba ni rashin gaskiyya.” “Allah sarki Salame, ban tsaneki har haka ba, kin san duk cikin jikokina daga Mus’ab sai ke, kawai rigimar ki ce ta yi yawa, ni kam ba na son rigima da kika ganni nan.” “Ai shikenan.” Na faɗa ina ƙoƙarin ta shi.”Baki faɗan mai ya faru ba, kuma wanan kwalliyar ina xaki?.” “Babu inda xani, wai Mus’ab ne ya ganni a waje wai na yi kyau, ni dai Hajja ki faɗa masa dan Allah ya fita shirgin rayuwata, ya barni da fushin da yasa iyayena suke yi da ni.” riƙe haɓa ta yi, sanan ta ce. “Eyh, lallai Salame har yanzu baki da hankali, kin ta ɓa ganin Mijin da ya fita shirgin matarsa?, sanan fushin da iyayenki ke yi da ke ai ke ce kika ja, kin ƙi yi musu biyayya, kin nuna ba su isa da ke ba, salame kowaye dole zai yi fushi da ke.” ƙarasa miƙewa na yi, naga ranar da Hajja za ta y adalci a kan abinda ya shafi Mus’ab.”Au kin bawa banza ajiya ta ko, ai shikenan Allah ya shirya ki.” ni dai ban ce komai ba na fice, a harbar gidanmu na ga Sadiya da Walida cikin shirin unifoam, da alama boko zasu tafi, wani abu ne ya tsayamun a rai, ko a haka a ka tsaya Mus’ab ya zalunce ni, ya cuceni, ya gama dani. Legends pen. Page 24 Wuce su na yi, dan tun kallon farko da na yi musu ban ƙara kallon inda su ke ba, haka suma kallona suke yi cike da mamaki.”Ni kam Walida Salma mai ya shiga kanta tsakanin jiya da yau, ki ga gayun da take ci, wanan atamfar ina ta bikin Yaya alisha ce, wacce mu ka ce zamu sa da bikin Amiran Mama.” “Uhm ita ce, akwai abinda ke damunta da ya wuce tabbata da rashin arziƙi.” Walida ta bawa Sadiya amsa, cikin ko in kula. “Ai shikenan Allah ya kyauta, amma nima fa daga yau na gama zuwa makaranta, tun da dai aurena saura kwana 11.” Dariya Walida ta yi sanan ta ce.” yau ma ai sai da a ka ce kar mu je, muka ƙi.” “Ai na yi na ƙarshe, sai kuma exam.” daga haka suka fice daga gidan. Ina shiga ɓangarenmu na ɗaura hannu a ka na fara rusa ihu, da burgima a ƙasa.”Wai na shiga uku na lalace, Allah ya isa ban ya fe ba, Wallahi Mus’ab ka cuceni.” abinda na ke faɗa kenan cikin kukan, Abbanah na gani tsaye a kai na yana kallona, da sauri na haɗiye kukan amma ban ta shi ba. “Ni kike wa Allah ya isa.” wani giririm na ji maganar ta sa, “wai shi nake wa Allah ya isa.” da na ci ka ‘yar asara. “Abba kai kuma?.” “Nima tun da ni na wakilci ɗaurin auren na ku.” da sauri na hau girgiza kai ina faɗin. “Wallahi Abba a’a.” “To wa kike wa.” da sauri na ce. “Mus’ab.” ai kuwa ya kifamun marin da na ji shi har tsakar kai na. “Salma!, Salma!!, Salma!!!.” ya kira sunana sau uki ajere. “Sau nawa na kira sunanki.” Baki na na rawa na ce. “Sau uku.” “Ta shi ki biyo ni ɗaki.” tashin na yi, a rai na ina faɗin. “Ni Salmatu ba ni da sa’a a kan Mus’ab kwata-kwata.” *Mus’ab* Bayan na ce. “Allah yatsine ma sa.” huce ɓangaren Hajja ya yi dariya ya huce cikin, shi bai san mai ya sa ba ya ga rashin kunyar tawa ma sonta yake, shi fa ya ƙago a kai masa ni gidansa, ko rashin kunyar zan dinga masa zai ji daɗi, dan ajiye ni zai yi, yaita tsokanta. Da sallama ya shiga ɓangaren na su, Maman ciki ta fito daga kitchen, ta yi masa wani kallo guda ɗaya ta shige ɗaki, da sauri ya bi bayanta yana faɗin. “Mama ina kwana?.” “Lafiya ƙalau, ai ga shi ka gani.” shiru ya yi, ya san kam dai bai kyauta ba.”Mama dan Allah ki yi haƙuri, wallahi mantawa na yi ban sanar da ku ba.” “To yanzu ni me na ce maka?.” “Babu komai, amma na san ban kyauta ba kiyi haƙuri.” “Sai ka bi matan gidan da ka ɗagawa hankali jiya, ka basu haƙuri.” daga haka ta ci gaba da abinda ta ke, zama ya yi ya fara breakfast, sai bayan ya gama ya tashi zuwa ɓangarenmu. Ya shigo a dai-dai, lokacin Abbana ya kira sunan. “Salma.” a hankali na ɗago na kalleshi, sanan na ce. “Na’am.” “Kin san waye Mus’a yanzu a wajenki?, shi ɗin mijinki ne, a yanzu ko da na baki umarni, shima kuma ya baki wani daban, na san zaki bi a maimakon nawa, sabida ni ta wa ta ƙare da ke, sai dai biyayya, amma shi biyayyarki gareshi, shine nemam Aljannarki.” Dai-dai lokacin ya shigo gidan, sai dai Abba ya jira suka gaisa da Ummanah sanan ya ce da shi. “Mus’ab shigo nan.” yana ta raba idon ganina a falon, Abba ya ce ya shigo, ya so ya yi mamakin ganina zaune a ɗakin Abban. “Abba ina kwana?.” “Lafiya ƙalau Mus’ab.” ganin ya gaida mahaifina, kuma ga shi gaban mahaifin nawa ya sa na ce. “Ina kwana?.” Murmushi ya yi sanan ya ce. “Kin ta shi lafiya?.” banza na masa ban shi amsa ba, tun da ya samu arziƙin gaisuwar ma ya gode Allah. “Salma ga Mus’ab nan, mijinki, yayanki wanda ko babu aure Mus’ab mai riƙe ki ne, zan miki nasihar da ko ranan tariyarki ba zan miki kamar ta ba, ki bi Mus’ab sau da ƙafa, ki bi Mus’ab sau da ƙafa, Salma idan har ki ka sake kika ta da wani abu a gidan aurenki, to wallahi babu ni babu ke, na sallami ki, kuma banyi alfahari da haihuwarki ba.” Wani irin abu na ke ji maganganun Abbanah na saukar mun da su, ya tabbata sun danƙawa Mus’ab ni, ya tabbata Mus’ab ya yi nasara a rayuwata, ai shikenan, na sallama sallama komai, na sallama rayuwar duniyar, zan bi Mus’ab sau da ƙafa, ko cewa ya yi Salma kashe kan ki zan kashe. Abinda nake faɗa a cikin zuciyata kenan, a fili kam Abbanah ne ke ta mun faɗamun, da nasiha a kan Mus’ab. “Tashi ki je.” mi ƙewa na yi jikina babu kwari na nufi cikin daƙi na na kwanata, me zan yi?, tunanin yadda zan yi Mus’ab biyayya, ko kuwa tunanin zama a gidan Mus’ab?, na haƙura da komai na rayuwa.”Shikenan dai Mus’ab ya ci nasara a rayuwata, ya raba ni da farin ciki, ya rabani da jin daɗi, ya raba ni da iyayena, ya raba ni da ‘yan uwana, sai mai kuma?, ya raba ni da rayuwar shine kadai abinda ya ragewa Mus’ab.” Shigowa ɗakin ya yi bakin shi ɗauke da Sallama, banza nai ma sa kamar banji ba, zama ya y gefen gadon da nake kwance, sanan ya ce. “Salma.” ban ko ɗago bare yasa ran samun amsa. “Salma ki yi haƙuri.” sai a lokacin na samu damar yin magana.”Mus’ab!, Allah ya isa tsakanina da kai, Mus’ab ka zama masifa a rayuwata, na tsane ka Mus’ab, wallahi natsan ka, kuma wallahi ba zan ta ɓa tarewa a gidanka ba, idan za’a kashe ni sai dai a kashe, amma gidan ka babu wanda zai kai..” ban ƙarashe maganar ba, ya jawo ni jikinshi, ya rungume ni iya ƙarfinsa kamar zai mai dani jikinsa, ai kuwa na buɗe baki na gantsara masa wani azababben cizo. “Salma ki yi haƙuri.” sai a lokacin na samu damar yin magana.”Mus’ab!, Allah ya isa tsakanina da kai, Mus’ab ka zama masifa a rayuwata, na tsane ka Mus’ab, wallahi natsan ka, kuma wallahi ba zan ta ɓa tarewa a gidanka ba, idan za’a kashe ni sai dai a kashe, amma gidan ka babu wanda zai kai..” ban ƙarashe maganar ba, ya jawo ni jikinshi, ya rungume ni iya ƙarfinsa kamar zai mai dani jikinsa, ai kuwa na buɗe baki na gantsara masa wani azababben cizo. ƙara matse ni ya yi, duk da cizon da nake gantsara masa, wani haushi ya isheni. “Ni ka cika ni, maye kawai.” “Salma da ki ci gaba da faɗan wa’yancan maganganun, gwanda ki yi ta cizo na, raɗaɗin zafin cizon zai fi mun sauƙi a kan na maganganun, domin shi na cizo a fata ta zan ji, shi ko maganganun a cikin zuciyata ne, Salma mai na yi miki haka da zafi?.” Legends pen. Page 25 “Natsane ka Mus’ab, zuciyar ta ka ta yi bindinga.” na faɗa ina fin cike jikina, zama ya yi kan gadon, tare da haɗa kan sa da gwiwa.”Ta shi ka fitar mun daga ɗaki.” banza ya yi mun, kamar ba da shi nake ba, daman ya sa ba wanan iskancin, ka ma sa magana ya yi banza, kuma yana cikin abubuwan da ke ƙaramun tsanar shi, duk da ni ban da mu da maganarsa ba, hasali ma maganarsa ta yar mun da tsanarsa ke yi, amma hakan da yake wa ‘yan uwana, yana mugun ƙaramun tsanar shi, zama na yi can gefen gadon. “Wai Mus’ab ya yi nasara a kai na, Salma ki farka, Mus’ab ƙaramin ɗan rigima ne, ki nuna mai nasarar sa ta bogi ce.” “To me zan yi?.” Na tambayi ɗaya ɓarin zuciya ta da ya yi mun waccar tambayar. “Yan da kika fara zaki ɗora, babu abinda ya dame ki, ki watsar da Mus’ab da lamarinsa.” Ta shi na yi zan shiga toilet. “Salma.” ya kira sunana a hankali, ban tsaya ba, kuma ban juyi ba. “Ina son ki, ina ƙaunar ki.” shigewa ta toilet na yi.”Wai yana so na, to ni ba na son sa, munafuki.” Wanka na yi na fito, lokacin ya bar ɗakin gaba ɗaya, shiryawa na yi cikin wani doguwar riga material, na sa ka baƙar hula na ha ye gado abuna, bacci ya dauke ni cikin ƙanƙanin lokaci. Ban farka ba sai bayan azhar, na shiga ban ɗaki na daura alwala na gabatar da Sallah, falo na fito dake ɗakina ta cikin falo ya ke, Ummanah ce zau ne kan kujera, sai wata da alama baƙuwa ta yi, tsugunnawa na yi ƙasa tare da faɗin. “Ina yini.” “Lafiya ƙalau, Ita ce amaryar?.” ta amsa mun gaisuwa ta, sanan kuma ta tambayi Ummanah. “Eyh ita ce.” Ummanah ta bata amsa, sanan ta kalle ni ta ce. “Ki je akwai abincin Mus’ab a basket, ki ɗauka ki ka mai sa, yana ɓarin sa na ɓangaren Hajja, daman yanzu ya kira yana jira.” jin maganar ta ta na yi wani gingirigin, “wai na kai masa abincin a basket, daman jira ya ke, har da yin waya, shi awa?.” “Mijinki.” wani ɓari daga zuciyata ya bani, datacciyar amsa, Allah ya gani mantawa nake Mus’ab miji na ne, ganin nake kamar cew a ka yi za’ayi mana auren, ko wani abu, domin da’a ce ina tunawa na san zan rage masa wani abun. Kitchen ɗin na nufa, kamar yadda ta ce abincin na cikin baske ɗin, food plast ne guda biyu babba da ƙarami, da alama dai akwai na shinkafa da akwai na miya, sai salad sai kuma plate da cokali. “Ikon Allah.” na faɗa a fili, har na kai hannu zan ɗauka, mugunta ta dirga rai na. “Yaji.” na faɗa tare da ajiye abincin, abinda muke zuba ya ji na ɗakko, na ɗauki cokali na ɗebi yajin nan cikin cokali na afka a ciki, na ƙara ɗiba na afka, nasa cokalin na juya miyar sosai na mayar na rufe tare da yin murmushi, fuska ta na gyara dan nayi alwashin biya ɓangaren Maman ciki, Walida ta ga yanda nake gayu, ko za ta mutu dan baƙin ciki sai dai ta mutu. “muguwa.” na faɗa a fili, bayan na ɗau kwandon na fice, suna Compound ita da Abdul, sai yanzu na tuna ashe ɗazu iyayen Abdul ɗin sun zo, sunma ansaka musu rana, an bada sadaki. Ɓangaren Hajja na nufa kai na tsaye, na zo dai-dai bakin ɗakin na shi na ajiye kwandon tare da juyawa. “Ba zaki ƙarashe ladan na ki ba.” na ji muryarshi ta faɗa, banza na masa na shige d’akin Hajja. “ke dai kin dai na yin Sallama ko?.” zama na yi a kan kujera ban ce mata ƙala ba, na yi alƙwarin ba xan ƙara ma ta magana ba, ba ita ka d’ai ba, mutane dayawa cikin gidan Galadima. “Ta shi ki fita.” Gyara zama na na yi, alamum babu inda zani. “Ba zaki zo kina gaba da ni ba, kuma kina zamar mun ɗaki.” ban dai ce ma ta komai ba, haka ta ci gaba da sababin ta, wallahi sai na bar ma ta bangare, amma ban ce ma ta Hajja ci kanki ba. Lamarin nan ya matuƙar ɓa ta ran Hajja, jira kawai ta ke wani ya shigo ta faɗa mai, cikin sa’a Mus’ab ya shigo hannunsa riƙe da plate ya zubo abincin a ciki, da alama ko fara ci bai ba, ya zo neman magana. “Yawwa Mus’abu gwanda da ka shigo, zo ka fitar mun da yarinyar nan.” “Me ta yi Hajja?.” “Gaba take da ni, tun da ta shigo ba ta ce mun ci kan ki ba, kuma ta zauna mun ɗaki.” “Toh Hajja dan ta ce miki komai ba, menene na damuwa, ki bar ta ta ci shirun ta, ke ma kin huta da saki magana, yarinya kamar ɓera ba jin magana ta ke ba.” wani malulun abu ne ya tsaya mun a rai, “Allah ya isa tsakanina da Mus’ab, Allah ya yi mun arzik’i wallahi sai na yi shari’ah da Mus’ab, wai ni ya ke kira b’era.” “Ai shikenan, amma kar ta sa ke zuwa inda na ke, kai ko kun tare gidan ku in dai ba hankali ta yi ba, kar ka kawon ita.” Mi k’ewa tsaye na yi, sanan na ce. “Insha Allahu, Hajja ni da ɓangaren ki har abada.” ina fad’in haka na fice abu na, dariya ya yi bayan na fice. “Hajja kinga kin ɓa ta ran ta ko.” “Ni ba nawa ran ta ɓa ta ba.” “Amma Hajja matar ɗan lelen ki ce fa. “ “Ka ga ba na ciki da shegan ta ka, kar ta ƙara zuwa ɗin.” Abincin ya shiga juyawa tare da fara ci, lomar farko ta daɗe masa harshe. Da mugun sauri ya ta shi ya nufi waje zai zubar, ni kam tun da na fita na je bakin ƙofa na tsaya, a ƙalla ko sau daya na yi nasara a kan sa, na tsaya na ji ihunsa bayan ya ci uban ya jin da na zuba, bana jin maganar su kwata-kwata, da yake na yi nisa da su, ganin ya fito da gudu ya nufi kwandon shara, ya sa na kyalkyale da dariyar, sai da ya gama tofe tofen yawonsa ya ɗago ya kalleni, ai kuwa na hade rai tare da gallamasa harara. “Zaki shigo gidan ne.” ya faɗa yanda zan ji. “Wallahi Mus’ab sai sai gawa ta ta shiga gidan ka.” dariya ya yi sanan ya ce. “ke da ƙafarki zaki shiga gidana.” “Mus’ab, Wallahi na yi kuɗi sai na yi ƙararka gaban alƙali, mugu kawai.” Legends pen. Page 26 “Salma ko mai naki son shi na ke, burgeni ya ke,Salma ke ta wa ce, ni na ke ni har abada.” “Mus’ab, Wallahi na yi kuɗi sai na yi ƙararka gaban alƙali, mugu kawai.” “Salma ko mai nake son shi na ke, burgeni ya ke,Salma ke ta wa ce, ni na ke ni har abada.” “Wallahi Mus’ab na fi ƙarfin ka, wai an gaya maka Salma matar kowanme kalan mutunci, Salma matar mutumin mai nagarta ce, Salma matar mutumin mai kyan hali ce.” ina fad’in haka na fice, tsaya wa ya yi yana mai maita maganganuna. “Mai yarinyar nan ke nufi, mai maganganun yarinya ne ke nufi?.” ya shiga tambayar kan sa, amma sanin babu wanda zai iya ba shi amsa, ya sa ya koma ciki. Kasa ma cin abincin ya yi baki ɗaya, yana ta faman tunani kala-kala. Ni kam ina fita nayi ɓangaren Anty, baki na washe ɗauke da Sallama na shiga, duk sabida na nunawa kowa ba na cikin damuwa, domin na gama yin shwara, matsalal Mus’ab ƙarama ce, ba ta isa ɓatamun rai ba. Walida da Sadiya suna zaune a tsakar gida, walidan na gayawa Sadiya wai gobe ko jibi za’a kawo kayan lefenta, ni da ke ba auren ba ne a gaba na, ko a barbaɗen takalmi na, Sadiya ya ce ta amsa Sallamar ta wa, amma ko kollonta ban yi ba na shige ɗakin Anty. “Daman na faɗa miki, naga ta ci uwar kwalliya.” Walida ta faɗawa Sadiya. “Uhm lallai Salma, wani abun ta ke shiri.” ta ɓe baki Walida ta yi sanan ta ce. “ita ta sa ni, yanzu dai mu dawo maganar yanda zamu haɗe event's din mu.” “Kin san babu yadda za’ayi a ce mun yi event's babu Salma ko?.” Sadiya ta bawa Walida amsa, dan ta ɗazu ma maganar da suke yi kenan, ita Walida ta ce ta san bazan ba, ita kuma Sadiya ta ce sai dai ayi gaba daya kowa da kowa, har ƙawayena da ‘yan uwana. “Wallahi Sadiya ba zan tsaya yarinyar nan ta yi mun rashin kunya ba, sai dai ke ki gaya ma ta.” “Nima ba zan gaya ma ta ba, nasan dai kamu dole a haɗe za’ayi, sanan na faɗamiki ni bazan dinner ba, dan shima na gaya masa, Albarkar aure na ke nema, shi wanan cocktail ɗin muyi magana da su Yayan Abuja muji.” “Ni dai gsky zamuyi dinner, dan ya faɗamun ma, su yaya kuma sun ce za su haɗa mana, White party na iya ‘yan gida, kinga shi cocktail ɗin sai muyi da ƙawayen mu.” “Ai zasu iya ma ta magana a kai.” “Ni Sadiya wai me yasa dole sai anyi da ita?.” “Ke wallahi idan baza’ayi da ita ba Walida sai dai na haƙura, kowa ya san mu tare, tare mu ke komai, duk sauran yayin mu tare su ke komai da bikinsu shine mu zamu ware, A’ah gaskkiya.” “To amma ai ita ta fara ware wa.” “Sai muyi ma ta uziri, Walida ko ke ce a matayinta abinda zaki yi zai iya kai wa haka.” “Ai shikenan, amma ni banga abin yin uziri a nan ba.” Ni kam tun da na shiga ban ma tsaya bin ta kan su ba, bare na ji mai su ka ce, wajen Anty na je mu ka gaisa sanan na ta shi na tawo. Wasa wasa abubuwa na ta gaba, gidan Galadima na ta shirye-shiryen aurar da ‘yan mata uku, an kawo lefen Walida akwati 12, an kawo na Sadiya ita kuma 13 da kuma fridge, yanzu saura nawa ake jira, Mus’ab kam ya yi ƙirmishi shi, ya dai ce kawai a gidansa na Malali zamu zauna, ni ba na ma son ya yi mun lefen, domin wallahi ba sa wa zan yi ba, kai ba ma zuwa gidan na sa zan ba, bare na sa ka kayan. Yanzu ma wasan ɓoya na fara da shi, dan tun ranar da mu ka haɗu ɓangaren Hajja, na sai mai ya ji a miya, ba mu ƙara haɗuwa ba. Ban ma cika fita ba, na tattare rayuwata na maida ta waje ɗaya, Hajja ita ma ban ƙara sa ta a idona ba, ita ma ba ta ƙara sani ba, jiya daddare ma ina ji ta aiko Kawu Madu ya ce na zo, ganin kamar ina bacci ya sa ya ce a ƙyale ni, amma yau da safe na je. Gama karin kumallo na kenan Ummanah ta tilastamun zuwa wajen Hajjan, a rai na na ƙudiri aniyar ba inda za ni, ɓangaren Anty zan je mu gaisa ita ma na kwana biyu ban je ba, Maman ciki ce dai kullum sai na leƙa, wajen ƙarfe ɗaya haka, nasan ba ya gidan gaba ɗaya. Dogon hijabi na bula har ƙasa sanan na fice, inda na ƙudiri niyar zuwa nan na nufa kai tsaye, rabo na da fitowa waje a irin wanan lokacin har na manta ma, cikin rashin sa’a shi ma ya fito mu ka yi kiciɓus, ɗauke kai na yi kamar bangan shi ba, na yi hanyar ɓangaren Anty. Ji na yi an riƙemun hannu, tsayawa na yi ba tare da na juyo ba na ce. “Cika ni.” “Masoyiyah, mai nayi miki kika ɓoyemun ganin ki.” ji na y kamar na lailayo ashariya na ƙunduma ma sa, amma na san kai na za ta kwaɓe.”Mus’ab dan Allah cika ni, aike na a ka yi.” sai bayan na fada na ji wani mugun da na sa ni, yanzu Mus’ab har ya kai na yi mai ƙarya, shi wa?. “Cika ni Malam.” “Wai ba ki san haƙƙoƙin miji a kan ma ta ba ne?.” “Ban sa ni ba, ai ban je islamiya ba.” “Salma nayi kewar ki sosai, dan Allah ki bini mu tare yau.” “Allah ya isa tsakani na da kai, wallahi ko a lahira ba zan yafe maka ba, kuma wallahi natsane ka.” cika ni ya yi, ni koma ɓangarenmu ina zubar da hwaye, Ummanah na zau ne ta ce “Har kin dawo?.” Sallamar Mus’ab ce ta katse ma ta maganar da take yi, amsa ma sa ta yi ya sa mu waje ya zau na, ku san mintina biyar sanan ya ce. “Ummanah na kawo miki k’arar Salma, ba wai dan ki da ke ta ba, sai da kin fahimtar da ita irin fushin mala’ikun da take ɗibarwa kan ta, ta na yawan ce mun Allah ya isa, ina guje ma ta kar ya shiga bakinta.” “Allah ya isa, ka na mijin na ta?, bar ta mala’ikun Allah suyita fushi da itan, tun a duniya za ta karɓi sakamakonta.” “Ummah dan Allah ki yi haƙuri, Salma fa yanzu duk wanan fadan ba shi take buƙata ba, doguwar nasiha ta ke buƙata.” “Mus’ab nasiha har ta yaushe, kullum za’ayi ta ma ta nasihar, yarinya ce ita ko me, shekara sha takwas fa za ta shiga.” “Duk da haka Ummah, salma yarinya ce ƙarama wallahi.” “Shikenan zan yi ma ta, amma wallahi ka ce zaka je gida ka na ma ta wanan soloɓiyancin ƙara rai na ka za ta yi, Salma ba kunya ba ce da ita.” “Shikenan Ummah ngde.” ya faɗa tare da ta shi ya fice. Ƴar aiken Hajja ce ta yi Sallama tare da faɗin. “Wai Salman ba za ta zo ba ne, inji Hajja.” “Au wai Salma baki je kiran Hajjan ba?.” Ummah na ta faɗa, sanan ta shi ta shigo ɗakin da na ke. “Salma.” ta kira suna na. “Na’am.” “Ta shi zamu yi magana.” miƙe wa na yi zaune, amma idona na kallon ƙasa. “Kin san menene aure?.” “Na sa ni Ummah, zama miji da mata a gida ɗaya, biyayya ga miji.” “To amma kin sa ni kike wanan abun.” “Ummah wallahi bana son Mus’ab, ba na son shi.” “Salma ki koyi yanda zaki so Mus’ab, domin shine wanda ƙaddara ta xaɓa miki, kuma banu yanda xaki yi.” Shiru na yi, ni wai mai yasa ƙaddara ta zaɓa mun Mus’ab, ko da ƙaddara ta za ɓa mun shi, amma har yanzu zuciyata ta ƙi yadda da hakan, bare kuma na yi tunanin yadda zan so shi, wanda ba ma na fatan hakan, ba na fatan na so Mus’ab ko guda ɗaya, ko na sakan ɗaya, na fi son na dauwama ina ƙin Mus’ab. “Ki ta shi ki je Hajja na kiran ki.” “Ummah ita ce ta ce kar na sake zuwa inda take.” “To yanzu ai ta buƙaci ki sake zuwa ko, ai sai ki je.” miƙe wa na yi, ban san uban da zan yi wa matar nan ba ta da mu na zo, kar she kuma ba xamu kwashe ta daɗi da ita ba. Na yi mamaki da ban same shi a falon ba, tun da na ji muryar shi da ina ciki, na ji sama-sama duk da ban sam me ya ke cewa ba, wucewa na yi ɓangaren Hajjan, babu ko sallama na shiga har cikin falon na ta. Ita da Mus’ab ɗin ne a ɗakin suna zaman gulma. Tsaya wa na yi a bakin ƙofa ba tare da na ce ƙala ba. “Salame na za ci kwana biyun da ba ki shigo ba hankali kika yi, ashe ba haka ba ne?.” “Hajja, idan har na cika jinin gidan Galadima ba zan ƙara shiga sabgarki ba, ko ta wani wanda ya ke da hannu a kan wanan auren zaluncin da a ka yi mun.” “Uwarki za ki fara fita sabgarta ba wani ba, shegiyar yarinya.” Juyawa na yi na fice, ni wallahi na tsani kowa a gidan Galadima, dan na fuskanci kowa murna ya ke za’a aura mun mutumin da nafi tsana a rayuwata. “Hajja, ina jin kamar na haƙura da auren yarinyar nan, ko zan samu rayuwarta ta yi fari, ban san me Allah ya tana da ba, amma wallahi tun da a ka ce za’a hada auren mu da ita na ji na kamu da son ta, so mai girma da nauyi, Hajja ina son Salma, amma Salma ba ta so na, kullum kara tsana ta ta ke, Hajja son Salma zai iya ajala na idan har ta ƙi ni. Wani tausayin sa ne ya ratsa zuciyar Hajja. “Allah sarki Mus’abu na, insha Allahu babu abinda son Salame xai haifa ma sai Alheri, ba ka bina bashin rantsuwa amma Salame za ta so ka, so mai girma fiye da wanda kake ma ta.” duk da ya san hakan ba lallai ba ne, amma ya matuƙar jindaɗin maganar. “Hajja ni ko son bai kai wanda nake ma ta ba, amma ta so ni.” “Insha Allahu, kawai ka dage da addu’a sosai, yanda na san ka da ibada ka ƙara dagewa a kai, akwai ayoyin ƙur’ani da dama wa’yanda suke kawo sauƙi, duk tsanani cikin su akwai. Rabbi inni lima anzalta illahi min khairi faqeer, da wasu ayoyin.” “Shikenan Hajjatah, ngde.” Ina fito wa daga ɓangaren Hajja, naga ana sakko da manyan akwatuna daga boot da cikin motar da ban san ko ta wace ba.”Na shiga uku, ba dai kaya na ba ne?.” Legends pen. Page 27. Ina fito wa daga ɓangaren Hajja, naga ana sakko da manyan akwatuna daga boot da cikin motar da ban san ko ta wace ba.”Na shiga uku, ba dai kaya na ba ne?.” “idan ba kayan ki ba na wane, wace ta rage ba’a kawo ma ta ba?.” ɓarin zuciyata ya yi mun wanan tambayar. “Shikenan ka shi na ya bushe, duk gujewa auren Mus’ab da na yi sai anyi.” ɓangarenmu na nufa, na shige ɗakina na kwanta, gaba ɗaya duniyar ta dai na mun daɗi, komai ya tsayamun cak, ba na jin daɗin komai. Bacci na ke ya zo mun, amma idanuna sun ƙeƙashe, kuka na ke so na yi, nan ma idanu na sun ƙeƙashe, murza idanu na na ke ko kukan zai zo amma shiru, sai yau na tabbatar da cewa idan ka ga mutum yana wa ta shin hankali kuka to ƙaramin ta shin hankali ne, idan babban ya zo neman kukan ake a rasa. Yanzu wanan kayan lefe na ne aka kawo, Mus’ab mutumin da na tsana fiye da kowa, na ƙi jinin shi fiye da kowa shine ya zama mijina, sai yau zuciyata ta amsa cewar Mus’ab ya zama mijina, amma gaba daya da zuciyata ba ta yarda ba, ina cikin ɗakin na ji Sallamar Yaya Asma’u, a rai na na ce. “Hum Munafuka ita ta shirya kayan kenan.” ban ƙarashe ba na ji ta shigo ɗakina, na kuwa kawar da kai na baya. “Salma Amarya, an kawon kayan lefen ki fa, ki fito ki ga abim arziƙin da mijin ki ya yi.” “Wallahi Yaya Asma’u ban ta ɓa tunanin haka kike ba, ina ji a jikina ko kowa zai ki farin cikina babu ke a ciki, ko ba dan komai ba, sai dan kasancewar uwar mu ɗaya uban mu ɗaya, sanan nice na ke bin ki a haihuwa, amma kin nuna ba haka ba ne, wallahi ba zan ta ɓa mantawa da wanan abun da kika yi mun ba.” tabbas jikin ta ya yi sanyi, amma kuma ba ta san mai ta yi mun haka ba, zama ta yi gefen gadon sanan ta ce.”Salma mai ya faru.” “Mene ma bai faru ba, kin san yadda natsani Mus’ab, bana ƙaunar Mus’ab, amma a ka ɗaura mun aure da shi, ba zaki iya kare ni ba gaban iyayen mu, ba za ki iya supporting ɗina ba, kin zo kina murna ƙarshe ma ke ya bawa kuɗi kika masa lefe.” “Salma faɗamun munanan hali guda uku na Yaya Mus’ab, ni kuma zan shige miki gaba wajen an raba auren.” shiru na yi, so na ke na faɗa ko da za ta tsaya mun ɗin, amma kuma ban san ta ina zan fara ba. “Yaya ni ba na son sa na tsane shi, kamar yadda ya tsane ni.” “Salma Yaya Mus’ab mutumin ƙwarai ne, mutum ne na kirkine wanda duk macen da ta same shi za ta ji daɗi ko da baya son ta, bare kuma ke Salma. Idan tsoron ki ba ya sonki to ki dai na domin Yaya Mus’ab ya faɗawa ƙaunar ki, yana sonki, ya kuma damu da ke, domin kullum sai ya tambaye ni kalal abinda kike so, Sai ya tambaye ni abinda kike so.” “Ni duk ba na so, na tsani Mus’ab Wallahi, kuma kullum ƙara tsanar shi na ke.” “Kin haɗa kan ki da aiki, idan ma za ki dai na ki dai na, aure ne an riga an ɗaura, kuma kin san zancen mutuwarsa ma babu.” “Allah ya isa wallahi.” na faɗa tare da juyawa, sanan ita ma na kudire a rai na na fita sabgarta har ga ba da abada, ta shi ta yi ta fice ni kuma na sake kwantawa, sai dai babu baccin babu kukan. Kowa ya ga kaya sai ya yaba, domin akwati goma sha shida ne, sai adudu guda uku, komai dai-dai da ni. A ɓangaren Hajja aka ajiye kayan, zuwa dare za’a dawo da su ɓangarenmu kamar yadda a ka yiwa na kowacce. Sadiya ce ta samu Yaya Asma’u da ke zaune a falo a can ɓangaren Hajja.”Yaya Asma’u, lamarin Salma yana ƙara gaba, a yanzu ta fita sabgar mu baki ɗaya” sanan muna so zamuyi maganar cocktail da zamu haɗa, kayan da zamu sa da adadadin mutanen da zamuyi inviting amma ta ƙi kulamu.” “To sai ku kyale shegiya, kuyi ba ita.” “Ai Yaya Mus’ab ya ce lallai sai mun yi da ita, duka mazajen za su zo da abokansu, sanan shi y Kama wajen.” “To kawai ku faɗawa Ummah, dan nasan ita kaɗai za ta tursasata, Abbah ba zai ta kura ma ta ba tun da dai bidi’a ne.” “Yanzu ku ba zaku iya ma ta magana ba, idan muka fadawa Ummah za ta iya dukan ta.” “To ai gwanda a dake ta tun da ta mai da kan ta jaka, ko shi Yaya Mus’ab ɗin ya yi magana da ita, dan ni ba zan ƙara shiga shirgin yarinya ba ta zageni.” Ina zaune a ɗaki, bayan na gabatar da Sallar isha’i na ya shigo, ban amsa sallamar sa ba, bare na ɗago na kalleshi. Zama ya yi gefen gado na, kasancewar ɗakin nawa daga gado sai sif, sai kuma dreesing mirrior ne kawai a ciki. ”Salma, kin kammala?.” banza na yi da shi. “Salma ki yi wa Allah, ki yi wa Annabi, ki tsaya muyi magana, dan darajar iyayenki.” ɗagowa na yi na kalleshi alamun ina jin shi. “Salma, ‘yan uwanki sun shirya muku event, mai yasa ba zaki hallarta ba?.” “Sabida ban da ra’ayi.” “Bangane ba ki da ra’ayi ba, Salma wanan abu ne da kin san ya zama kamar al’ada ko?.” “Su ai ‘ya’yan ga ta ne, ‘ya’yan da ake so a ka basu wa’yanda suke so, ni wanne a ka yimun a ciki, har wane haɗe kai suka yi, su kai ma dai ni bare, to ba za ni ba.” daga haka na miƙe daga kan daddumata na haye gadao. “wallahi babu abinda zai kai ni, kenan ma ina murna da auren?.” haka ya gama xaman sa ya ta shi ya fice. Abu kamar wasa baki na ta matsowa, shirye-shiye na ƙara gaba, sai dai har yau ban sa ko abu ɗaya na cikin lefenan a idona ba, ban san wane kalal abubuwa ba ne a ciki, haka kuma Ummah ba ta ta kuramun sai na ga ni ba. Yau laraba, yau ne za’a gabatar da cocktail ɗin da suka shirya, ni dai ina zaune ɗakin mu ko lalle ban yi ba, babban daɗin da na ji Ummanah da ta tarka ta ni ta watsar, ko uffan ba ta ce mun a kan lamarin bikinan. Ina zaune ɗaki bayan na gama cin uban kuka na, tunawar da na yi duk masifa ta nan da kwana uku, an dauke ni an kai ni gidan Mus’ab, na kwana a gidansa na ce albarka cin sa. Sallama a ka yi, yayan Abuja ce da su Yaya Aleesha, haɗe girar sama da ta ƙasa na yi, ba na ma so wani cikin su ya yi mun magana a kan waccan shirmen. “Salma, wajen ki mu ka zo.” ɗagowa nayi na kalle su sanan na ce.”Ina jin ku.” “Salma, mun zo mu faɗa miki gskyr da kowa ya ka sa faɗa miki.” “A matsayin ku na wa?.” sororo su ka tsaya suna kallona, ni kam ko a jikina indai iskanci ne ai gidansu ka tarar. Legends pen. Page 28 “Salma yanzu abinda kike yi kina tunanin ya da ce.” Yayar Abuja ta faɗa, wanda ita sai ynzu ma ta yi magana tun da su ka shigo. “Wai ni me na yi ni yanzu, kuka ku ka ga Ina yi, ko ihu na ke ina cewa ba na son auren?.” “Ba mu ga kina haka ba, amma Salma kin nuna wa kowa ba kya son auren nan.” “To Yaya zan yi ƙarya ne?, ba na so.” “Nifa ga ni nake magana da mara kunyar yarinyar nan ba shi da wani amfani, mu ta shi mu sami uwarta mu gaya mata.” Yaya Aleesha ta faɗa, na ɗago na watsa ma ta uwar harara, damam su ‘ya’yan Maman kwata-kwata ba su da kunya, sai raina ‘yan gidan Galadima, ko da muna dangin ubansu ne oho?. “Duk wanan bai ta so ba, Salma za’a zo ayi miki lalle ja da baƙi, sanan zaki je cocktail din Anjima.” “Yaya, dan Allah a bar zancen Cocktail din nan, ba na so wallahi, suyi abun su kawai.” “Shikenan, bari a turo mai lallen.” shiru na yi ban ce komai ba, hakam ya nuna kenan a turo. Ta shi suka yi suka fice, ni kuma na kwanta. Ƴan mintina kaɗan mai lallen ta shigo, ban nuna wani ɓacin rai ba na miƙa mata hannun ta fara zana mun ja da baƙin, cikin ‘yan awanin ta gama zana mun ta fice. Su Yayan Abuja kuwa suna fita Mus’ab ya tare su, daman shi ne ya turo su. “Ya kuka yi da ita?.” “Ta ce ba zata je ko event ɗaya ba, amma yanzu za’ayi ma ta lallen.” Bai ji dadin haka ba kwata-kwata, duba da yanda abokan su dayawa za su zo, haka za su ga Abdul da amaryarshi, shi kuma ko oho. “Ka kyale ta, tun da a ka samu nasara za tayi lalle to saura ma za ta yi.” “Bari na je kawai.” daga haka ya fice, ita kan ta ta yi mamakin yadda Mus’ab ya rikiɗe ya koma masoyi ga Salma, bayan kowa ya san ba sa ga maciji. “Allah kenen.” ta faɗa tare da hucewa Wajen karfe hudu na fire lallen nawa, ban ko tsaya na kalleshi sosai ba, sabida kar ma na ga ya yi kyau na ji daɗi, gado na ƙara komawa na kwanta, amare da kam sun ta fi make-up. Ummanah ce ta shigo ɗakin, da sauri na ta shi daga kwancinyar da na ke, rabonta da shigowa ɗakina ai an kwana biyu, sai dai kawai ta kirani ta ba ni magani na sha, tasan idan wani ne ya kawo ba sha zan yi ba. Zama ta yi kan gadon sanan ta kira suna na. “Salma.” ɗagowa na yi na kalleta, sanan na ce. “Na’am. “Salma, ki na son kullum ki dinga baƙanta mun, ki na son na zauna da ɓacin ranki ko?.” da sauri na girgiza kai, ina zubar da hawaye. “A’ah Ummah.” “Salma a yanzu zamana da ke ya zo ƙarshe, zaki ta fi gidan mijinki, amma kina so ki tafi ki barni da ɓacin ranki ko?.” “A’ah Umma.” “Na miki shiru ko za ki yi hankali, amma Salma kin ƙi ko?, kowa sai ya yi magana a kan ki za ki ji daɗi ko?. “ “A’ah Umma.” “Salma a yanzu ni ka ɗai na san yadda nake ji a jikina, kuma na tabbatar miki idan na je asibiti cewa za’ayi jinina ya hau, Salma kin san ɓacin ranki ne ya haifarmun ko?, Salma ko mutuwa na yi a yanzu wallahi kece.” da sauri na ɗago idanu na masu cike da hawaye na ce. “A’ah Ummah, dan Alah ki yi haƙuri.” “Salma kin fi son duk lokacin da na tuna ki maimakon na ji sanyi a rai na sai dai na ji a kasin haka, Salma kin fi son duk inda za’ayi magnar ki a aibata ki?.” “A’a Umma ki yi haƙuri.” “kin san ai abinda ya kama ta, ki ta shi ki halallarci abubuwan biki.” “Tom Umma wallahi zani komai, kiyi haƙuri amma banda na yau, wallahi da na miƙi jiri ya ke ɗi ba na.” “Salma ke kika jawa kan ki komai, bari na kira likita ya duba ki.” “To.” kawai na ce na kwanta tare da rufe idona, ita kuma ta ta shi ta fice, na kudire a raina tabbas zan hallarci komai na bakin, ko dan na cika umarnin mahaifiyata ta yi farin ciki da ni, amma wallahi babu murmushi daya ko fara’a a fuskata. Mintuna kadan likitan ya zo, duba ni ya yi ya bani magunguna har da yimun allura bacci, sabida kwata-kwata ba na iya bacci, mintuna kadan kuwa bacci ya dauke ni. Sai wajen karfe 12 na dare na farka, miƙewa na yi na shiga toilet na ɗaura alwala, na biya ba shi salloli uku da ke kai na, ban nemi abInci ba na sake kwantawa. Washe gari. Wasai na ta shi babu inda ke mun ciwo, dama na ɗauki aniyar gyara, zan hallarci komai na bikin da su ka tsara, ai hallarta ba ita ke nuna cewa ina son Mus’ab. Ina cikin gyaran gado na ya shigo bakin sa dauke da Sallama, ban amsa ma sa ba,na ci gaba da abinda na ke.”Ya jikin na ki?.” kallon shi na yi kamar ya san tambayar shi na ke son yi aina ya san ban da lafiya. “Jiya Ummah ta sa ni na kira likita, bayan ya fito ne yakw cemun rashin ƙwarin jiki ne da kuma rashin bacci su ka haifar miki da ciwon kai.” ci gaba na yi da aiki na ban ce ma sa komai ba. “Jiya anyi cocktail, kin san wacce ta zauna amadadinki?.” ji nai rai na ne neman ɓaci, ina ruwana da wacce ta zauna amadadina?. “ƙawarki ce.” A fusace na ce. “To ina ruwana da wacce ta zauna amadadina, mene ya dameni dama aurenta ka yi zai fi ma.” dariya ya yi sanan ya ce. “Salame ashe ana kishi.” wani abu naji ya maƙalen mu a maƙoshi, ni Salma na gamu da alheri, Mus’ab dole sai ya sa ni magana. “Dan Allah Mus’ab ka fita sabgata, ka fita a harkata dan Allah.” ta shi ya yi ya fice, na ci gaba da abinda na ke, ‘yan mintuna kaɗan sai gashi ya shigo da abun breakfast. “Yau tare da matata zamuyi karin kumallo.” “Dole sai ya sa na zage shi zai ji dadi.” amma Ummanah ta mun Allah ya isa, duk ranar da na ƙara zagin Mus’ab, ko na yi masa Allah ya isa. “Habibty ki zo muyi breakfast.” fi cewa na yi daga ɗakin na fito falo, mutane ne a falon ta cikinsu na ratsa nayi kitchen. “Ummah ina abin brealfast dina?.” Legends pen. Page 29 “Wanda Mus’ab ya shiga da shi ciki na uban waye.” shiru na yi kawai na kama hanya na fice, ko ina na gidan a cike yake da mutane, ɓangaren Maman ciki na shiga, shima cike da mutane har ya so ya fi namu cika, da kyar na kutsa inda ta ke na ce. “Amma a bani abin karyawa.” “Yanzu fa Mus’ab ya fita da abincin ya ce ke zai kai wa.” shiru na yi a raina ina cewa. “Shi dai wanan ina ga ko ina sai da yabi ya ce zai karɓaemun abinci.” fi cewa na yi na nufi ɓangaren Hajja. “ina maƙil.” na faɗa a raina ganim inda ya cika ya cike da mutane, ta dole na koma ɓangaren mu. Yana cikin dakin inda na bar shi zau ne, zama nayi daga gefe na fara cin ƙosan da ke cikin plate din, fuskata a daure kamar zan kai mai duka. Haka na ci na sha tea din, da magani na na kwanta. Sai wajen karfe hudu na shiga wanka, mai kawai ma shafa sai powder ita ma sama-sama, kayan da zan sa ma kawon mun a ka yi, na dauka na saka ko abun na din kan ma da kaina na nada, sanan normal naɗi na yi ba kalal na amare ba. Da kan shi ya zo ya fita ni, yau ko ina sai yabona ake ni dai na hade rai kamar wacce a ka yiwa mutuwa. Haka mu ka je wajen event din, ban yi murmushi ko na secon daya ba, har a ka ta shi, washe gari kuma a ka yi daurij auren su Walida da Abdul, Sadiya da Umar, da yamma kuma a ka yi kamu wanda iyayn mu su ka shirya. Harabar gidan mu a ka yi uban decoration. Yu dai dole sai da a kayimum make-up sabida anfi karfina, amma gaba daya kamar ko yaushe banyi wata dariya ko murmushi ba. Haka a ka gama event wajen karfe 07:30 a ka watse, amare suka shirya kowacce za’a huce da ia gidan mijinta, zo kaga kuka wajen Salma Galadima, ihu nake kuka nake kamar wacce ta ra sa iyayenta duka biyu. Duk kukan nawa haka a ka fice da ni daga gidan Galadima mu ka nufi Malali G.R.A. Kuka na ke kuma duk ‘yan cikin motar sun yi mun banza, babu mai ce mun ci kan ki, a haka mu ka shiga makeken gidan malali. Kowa sai yabo da santin gidan ya ke, amma ni ban ko kalli waje daya cikin gidan ba. Haka suka gama abun su su ka barni ni ka ɗai, kuka na nake yi hankali na kwance, hankali na ya koma yadda za’ayi Mus’ab ya sake ni, na san babu wani abu da zai sa Mus’ab ya sake ni, sai dai idan na takura, amma idan ya sake ni na je ina, nasan Abbanah ba zai karɓe ni ba, amma dai dole ya sake ni. Ina wanan tunanin naji alamun shigowarsa, da alamu shi kadai ne tin da babu hayaniyar abokai, tun da zu na ke som rufe dakin amma na jira ya zo muyi magana, dan wallahi ba zan kwana da auren sa ba. Ina zaunen ya shigo, bai ƙarasa zama ba na yaye mayafi na, na dago na kalleshi. “Mus’ab, ka ga ka ci nasara an kawo ni gidanka, babu abinda ya yi saura, dan haka ka taimake ni ka sake ni.” kallo na ya ke yi sosai, bai ta ɓa tunanin zan kawo maganar saki a duk tashin hankalin zaman da zamuyi ba, ya zama dole ya ja mun kunne a kan maganar sakin nan. “Salma, Saki kike magana?, to ki cire wanan a ranki domin auren mu aure na har abada, babu abinda xai rabamu.” Washe gari. Buɗe ido na yi, na ƙarewa ɗakin Kallo. “Yau dai na kwana a gidan Mus’ab, matsayin matarsa.” Kuka na fara yi ina kwancen, sai da na ɗauki kusan minti 30 ina kwance ina hawaye, sanan na ta shi, kallon ƙofar ɗakin na yi, na tuna kulle ƙofar da na yi bayan ya ta shi zuwa waje, toilet na shiga na watsa ruwa, sanan na ɗora alwala, na fito na ta da Salla, zama na yi gefen gado ina kallon ɗakin, yanda ya ke da girma kuma ya tsaru, an kashe zallan dukiya a ɗakin. “Salma, mene mafita?.” na yi wa kai na wanan tambayar, shiru na yi ina son na sami mafita, nasan dai wanan ƙaddararen auren yanzu a ka fara shi, duk da cewar idan na ta da har gitsi zai mutu. “To me zai hana na ta da har gitsin, ko zan tayar a sa’a auren ya mutu.” Ta shi na yi na buɗe kofar ɗakin na fito falo, falon kam ya tsaru shima, ya sha ado sosai da sosai, ga wasu hotona nan da na shi da a ka yi musu frame na gaske mai kyau da ɗaukan ido, duk da dai ni ba su ɗauki na wa idon ba. Zama na yi kan kujerun ɗakin, na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ina jiran ya fito mu kwashe uwar sabada, ko Allah zai sa na da ce. “Ina kwana Salame.” miƙewa na yi tsaye, tare da juyawa na kalleshi. “Mus’ab, kar ka ƙara so inda nake.” Tsayawa ya yi yana kallona sosai, cike da mamaki, daƙyar ya iya tambaya ta. “Me ya sa.” “Mus’ab kar ka zo ku sa da ni, na tsane ka.” Murmushi ya yi, snn ya ce.”Kiyi haƙuri Salma, ba ni na jaranci kai na da son ki ba,Allah ne ya jarabce ni, kuma ba ki isa ki canja nufin ubagijia ba.” “Ni ma kuma shi ya jarabci ni da ƙin ka, da tsanarka. Mus’ab ka saki ni, ka sake ni na tafi gidanmu ko da iyaye na za su kashe ni, sai dai su kashe ni,amma bazan zauna a matsayi matarka ba.” Matsowa inda nake ya yi, tare da kama hannuna. Da sauri na fincike hannuna tare da faɗin.”Kar ka kuskura ka ƙara ta ɓa ni Mus’ab, idan ba haka ba wallahi zan yi maka abinda ba ka yi tunani ba.” Dariya ya yi, sanan ya ce. “Me za ki iya yi mun Salma?.” Tsaki na ja sanan na ce. “Natsane ka Mus’ab, kuma wallahi sai ka sake ni.” “Salma ki dai na yawan rantsuwar nan, kuma kalmar tsana da na ce tana mun zafi ki dai na faɗa, dan Allah kar ki dai na faɗa, ki mayar da ita lazimi.” wani malolon abu ne ya sakko mun zuwa maƙoshi, na kai hannu na jawo da ƙarfi tare da faɗin. “Wallahi babu inda zaka sai ka sake ni.” “Wallahi Salma banga wani abu da zai sa na sake ki ba, ko da ba na sonki, zan yi biyayya ga iyayena tun da sun ba ni ke, bare kuma ina son ki.” Hannu na kai na ƙara jawo shi baya, tare da faɗin.”Ka sake ni.” shima hannun ya sa ya fin ciki jikin shi, kawai na kai hannu na shaƙe shi. “Wai Salma ba ki da hankali har haka?.” Legends pen. Page 30 “Ba ni da shi Mus’ab, kuma hankali na da rashin sa ba zai da me ka ba, kawai ka bani takarda ta.” “Salma na ce miki fa bazan sake ki ba, ban san dai mai ya shiga kan ki ba, har kika dai na haddace maganganuna.” “Wallahi ko ta ƙarfi ne sai na ƙwaci takarda ta, ko ta faɗa ne.” Dariya ya yi mai sauti sanan ya ce. “Yanzu Salma kina da ƙarfin da zaki ƙwaci abu a hannuna, abun ma kamar saki?.” Shiru na yi ina tunani.”shi fa saki abu ne da a ke yin shi da ba ki, ban isa na ƙwata ba, amma idan na yi masa rashin arziƙi ai zai fusata ya sake ni, na san shi da zafin zuciya.” “Salma babu abinda zaki yi mun na sake ki wallahi, idan zaki zauna da ni a matsayin mijinki ki zauna, idan ba zaki zauna ba kiyi duk abinda kika ga dama, sakarya kawai.” jin ya kira sakaryar nan ya sa nayi wani tsallen albarka na sake shaƙo shi, na shiga jijiga shi, duko ko ta ina, wai ni faɗa nake da shi. Shi kam ya bar ni ni kaɗai na yi kiɗa na na yi rawata, idan na gaji zan dai na. Gaba ɗaya faɗan baya mun daɗi, hakan ya sa na cika shi na nufin wajen hotonan mu da suke ɗakin, wanda yaje a ka yi editing a ka haɗa mu na nufa, daman haushin hoton na ke ji, dan zaka iya rantsewa tare a ka ɗauke mu hoton. Ta ƙarfi na sa na fara fin ciko hoton ina buga shi da ƙasa frame ɗin na karye wa.”Salma kar ki ƙara karyamun hoto.” “Wallai sai na fa sa komai na gidan nan, muddin baka sake ni ba, mugu azzalumi, mai son ganin rayuwar mutum ta yi baƙi.” “Ko meye ki kirani da shi Salma, amma wallahi ba zan sake ki ba, na san na yi miki laifi da kike magana a baya na baki haƙuri amma kin ƙi saurare na ma.” Ban za na yi da shi na ci gaba da fasa hotonan, har da makeken agogon bango mai tsadar da ke ɗakin, ina gama wa na nufi makekiyar tv bango da ta cika bangon ga ba ɗaya, da sauri ya zo ya sha gaba na tare da faɗin. ”Allah Salma ba ki isa ba, kar ma ki fara.” juyawa na yi na ɗako ƙaton frame ɗin da ke ƙasa na dawo. “Salma ba fa ki isa b..” bai ƙara sa ba na maka masa frame ɗin, tare da faɗin. “Wallahi har kai sai na yi wa rauni, ba sakarya ba?, ba ka ga komai ba daga aikin Sakarya ba.” riƙe ni ya farayi yana faɗin. “ki yi haƙuri ni ba sakarya na ke nufi ba.” ƙwace jikina na yi, na juya kan centre table na glass da ke tsakiyar kujeru.” Shi ma kuwa na maka masa frame, amma kamar ban buga masa komai ba, na ƙara maka masa, shiru ba alamun tsagewa bare ya fashe, haka nai ta maka ma sa amma shiru abu ya ƙi fashewa, juyowar da zan yi na ga babu Mus’ab, babu tv bango, ƙwafa na y tare da shigewa kitchen, gidan babu wani makami na gaske, da zan yi amfani da shi, dan Wallahi har su dining table yau sai na fasa. Zama na yi kan kujera ina faman tunanin mai zan yi amfani da shi na fasa wanan kayan, gwanda kowa idan ya ji labarin haukan da na yi zai sa a sake ni, kitchen ɗin na sake komawa ko akwai muciya ko taɓarya, amma babu su babu alamun su, ga shi shima matsora ci ya gudu, da ko shi na mammakawa frame ɗin ai zan rage takaici, amma yanzu idan ban faffasa kayan gidan nan ba, ba lallai na sake samun dama irin wanan, kuma nayi alƙwarin sai Mus’ab ya sake ni. Idanuna ne suka sauka a kan wokaƙe.”Mai zan yi da su?.” na tambayi kai na. “In kashe Mus’ab, chaɓ rufamun asiri, da zai mutu sai na fi kowa murna, ina ga har sadaka zan yi, amma ba zan iya kashe shi ba, na tattaro wa kai na uban zunubansa, ga kowa ma cewa zai yi ni na kashe shi, ƙarshe nima a kashe ni, ina riba anan?.” ni kaɗai nake wanan hirar a cikin zuciyata, ni banƙi yanzu na fita na ga ya faɗi ya mutu ba, amma dai ba na so na kashe shi da kai na, ba zan iya kashe kowa ba, ko mai tsanar da na yi masa, amma Mus’ab ya cuceni, ya gama da rayuwata, ya zamar mun masifa da annoba, idan har bai sake ni ba, ya gama da rayuwata har abada, hawaye na ji suna bin kunci na, da sauri na gogesu tare da faɗin.”Kuka ba naki ba ne Salma, ki tsaya ki ƙwaci ‘yancin ki.”Goge hawayen na fara yi da sauri-sauri, nima na san kuka ba na wa ba ne, Salma ba raguwa ba ce, ko me Mus’ab yake ji da shi, sai ya makamun Saki na yau, sai na ko ma gidan Galadima yau, ko mai zai faru. Huƙar na ɗauka na fito, sai na yanka kujerun gaba daya, na bi gadon na yanka katifarsa gaba ɗaya. Fitowa falon na yi, dai-dai lokacin da shi ma ya fito daga ɗaki, kallo na yake hannuna riƙe da huƙa, simi-simi ya huce ta jikin bango ya tun ƙari ƙofa, ni kuma na tun ƙari kan kujera. Buɗe ƙofar ya yi na ji Sallamar Abbanah. Fitowa falon na yi, dai-dai lokacin da shi ma ya fito daga ɗaki, kallo na yake hannuna riƙe da huƙa, simi-simi ya huce ta jikin bango ya tun ƙari ƙofa, ni kuma na tun ƙari kan kujera. Buɗe ƙofar ya yi na ji Sallamar Abbanah. “Innullahi wa ina illahir raji’un.” na shiga maimaitawa, shikenan ta wa ta ƙare, yau ko Abba ya kashe ni ko ya tsinemun. Kallon ko ina yake, yanda na fasa frame, ga kuma huƙa a hannuna, sai da ya gama kallon ko ina tass, sanan ya ce.”Salma.” har wani karkarwa jikina yake na ce. “Na’am Abba.” “A’ah cewa za ki yi na’am yunusa.” kuka na fara tare da faɗin. “Abba ka yi haƙuri dan Allah.” “Ke zan bawa haƙuri Salma, sabida ni na gama yi miki komai, na zo ne na faɗa miki kalma guda ɗaya wacce ita kaɗai ta rage ban faɗa miki ba.” “Innullahi, shikenan Abbanah tsinemun zai yi, ina na kama a duniyar nan, ina nufa, me zan yi a duniya iyayena sun tsinemun.” na shiga maimaitawa a zuciyata. “Salma.” ya sake kiran sunana, na ɗago da idona cike da hawaye. “Abba kar ka tsinemun dan Allah, Abba kar ka tsinemun.” “Salma ba zan miki baki ba, amma wallahil azim ki sani duk ranar da kika kashe aurenki, to kamar ni kika kashe ne, Salma zan sallama ki, zan yafe ki a cikin ‘ya’ya na, zai zama babu ni babu ke.” “Innullahi wa inna illahir rajiun, Abba na tu ba ka yi haƙuri, Abba na tu ba.” “Wane tu ba za ki yi Salma, ke da kike yin ƙurin kisan kai, Ina zaune a ɗaki na ji zuciyata na azalzalta na zo gidanki, Salma da banzo ba kashe shi za ki yi?.” “Abba wallahi ba kashe shi zan yi ba.” Legends pen. Page 31 “Salma ji abinda kika yi, mahaukaciya kika zama, to wallahi na faɗa miki abinda zan faɗa miki.” daga haka ya juya, bai ko bi ta kan Mus’ab da ke ba shi haƙuri ba, zubewa na yi a ƙasa ina kuka mai tsuma zuciya, kuka na ke babu ƙaƙƙautawa. Har Mus’ab ya dawo daga rakashi da ya fita yi, duk da nasan bai kula shi ba, shi ma Mus’ab ɗin bai kula ni ba, ya shiga kwashe kayan da na ɓa ta, har ya gama bai ce mun komai ba. Ina zaune ina kuka na ya fice bai ce mun ci kan ki ba, zuwa lokacin ni yunwa ta hana ni kukan, ta hanani na yi tunanin wata mafitar, ta hana ni na yi komai. Har wani jiri-jiri na ke ji, kai na na wani juyawa, kamar wacce zan faɗi daga zaune, ban san ko ƙarfe nawa ba, amma daga yanayin garin nasan 12 ta kawo kai, ga shi rabona da abincin arziƙi tun jiya da safe. Ina nan zaune ƙasa na kifa kai na da kujera na ji yana buɗe ɗakin, har sauri na ke na ɗago kai na na kalle shi, wani san yi naji a zuciya ta ganin shi da leda, da alamu take away ya yi mun, gani nai kamar baya ya ke yi ba shigowa ɗakin ba, mi ƙewa na yi zuwa inda yake na sa hannu na amshi take away d’in, da mamaki ya sakar mun ni kuwa na ba je a ƙasa na fara ci, sai da na ta shi da take-away d’in gaba d’aya na sha ruwa, sanan na miƙe na fita da take-away ɗin, na huce ɗaki ban ko kalle shi ba. Zama nayi kan gado, ina sauke ajiyar zuciya tunawa da na yi Abbanah bai tsinemun ba, amma dai ya ce idan na kashe aure na kamar shi na kashe, to idan auren na wa ya mutu da kan sa fa?, ai ba ni na kashe auren ba, kin san ƙuma zan masa, domin hausa sun ce. “idan tsuntsu ya yi shiru, ba wai ya manta da harbin sa ba ne.” girki zan yi iya cikina, shara da wanke guri zan yi idan na ɓa ta, wanka da gayu zan yi abuna, amma ko kalma ɗaya ba zai ƙara ji a bakina ba, ba zan yi abinci da shi ba, ba gaisuwa ba adawo lafiya. Idan ya gaji da kan sa zai galla min saki uku abuna, na shiga sabuwar rayuwa. Duk da a yanzu ina jin na tsani Masrur, amma na san zan sami wani saurayin mu sha ƙauna, bacci na ji yana son kwashe ni hakan ya sa na kwanta abu na. Ban ta shi ba sai wajen ƙarfe biyu na rana, wanka na shiga tare da d’aura alwala na gabatar da sallar azhar, ta shi na yi zuwa wajen kaya na wanda suke a cike taf, kallon su na yi tas na ga an haɗe su da wasu sababbi da alama su ne na lefen, zama na yi na ware na wa da kuma na lefen, na sakko da babbar akwati na juye na lefen a ciki na matsar da su gefe, dan ba zan ta ɓa amfani da komai na sa ba har na bar mai gida. Wata doguwar rigar atamfa na ɗauka na zura, bayan na yi simple and light make-up ɗina, na kashe uban ɗauri tare da uban turarruka, sai ƙamshi nake zubawa na fito falon, yana zaune yana danna system ɗin shi da alamu aiki yake yi da ita. Ƙamshin turare na ne ya fara dukan hancin sa, da sauri ya d’ago kai ya kalleni. “Masha Allah.” ya fada a ran sa, ya bi ni da idanu yana kallon yadda kyau na yi kyau, haka na zo na huce shi na shige, kallon store din da yake shaƙe da kayan abinci na yi, nan da nan shiga hada jallop na taliya, raba guda daya na yi gida biyu dai-dai ciki na, ina tsaye cikin kitchen din har na gama na juye ta a plate, shi kuwa yana faman santin hucewa ta ‘yan mintina kadan yaji ƙamshi na fito wa daga kitchen din, wata yunwa ce ta taso masa nan da nan ya fara hadiyar yawu, duk da haka yana gargadar kan shi da cewa. “Mus’ab kar ka ba da kan ka, idan ta kawo ka ce ba ka ci, dan da alama maganganun Abba sun ratsa ta.” Yana cikin wanan maganar ya ga fitowa ta rike da plate da drinks, huce shi na yi na shige dakina tare da garƙama mukulli. Baki sake yake kallona na har na sa key, ta shi ya yi ya shiga kitchen ko na bar masa a kitchen din, amma babu komai tukunyar ma na jiƙata da ruwa. Girgiza kai ya yi, tare da yin ƙwafa ya koma ya zauna sai dai kuma ya kasa yin aikin gaba daya, mugun kwad’ayin taliyar ya ta so ma sa, haka ya yi ta sintiri a cikin falon, karshe ya yanke shwarar ya shiga ya dafa da kan sa. Ina zaune cikin daki bayan na gama cin taliyar, ƙauri-ƙauri na fara ji alamun abu yana ƙonewa, da sauri na ta shi na fito da tunanin ko ni nabar abu a kan huta, sai dai ganinshi da na yi a kitchen din ya matuƙar ba ni dariya, maze wa na yi ina ajiye plate din na fara wanke shi da tukunya da ƙananan abubuwan da na yi amfanj da su. “Salame wanan zalunci ne.” ko kallonshi ban yi ba, bare kuma na ba shi amsa, sai ma a rai na da na ce. “kaɗan ka gani Mus’ab.” gajiya ya yi ganin taliyar ba za ta yi ba ya sa ya kashe gas din, ya fice yana tsaki nima tsakin na mayar masa, daga haka na huce daki ban ƙara fitowa ba sai bayan magari ba. Baya dakin a lokacin, ban san inda ya nufa ba, kuma ban damu ba ni dai na yi zamana a kan kujera na ƙurwa Tv ido ina kallo Mbc bollywood da suke haska favorite film din Kabhi kush Kabhi gham, an zo waƙar da nafi so na fi ƙauna, ji nake kamar na shiga Tv a yi rawar da ni, ina cike da nishaɗi irin wanda na dade ban yi ba, danni Allah yasa mun ƙaunar ‘yan bollywood, ina zaune ina girgiɗa kai ina bin waƙar, kamar ance juya na gan shi tsaye kai na baki kamar gonar auduga, ta shi na yi da kan kujerar na matsa gefe tare da shan kunu kamar ba ni ce ke yin dariya yanzu ba.”Baby Salame, mutanen bollywood.” banza na yi da shi tare da kauda kai na daga kallon Tv din gaba daya, amma kuma na yi alkwarin ba zan ta shi daga dakin ba, dan yasan bai isa dan ya zo ba na ta shi. “Salma kiyi haƙuri dan Allah da abubuwan da na yi miki, ki karbi soyayya ta wallahi, ina sonki Salma, ina matukar kaunar ki, Allah ya jarabci zuciyata da azababben sonki.” “Mus’ab ba na son ka, ba ka da abubuwan da nake so, a tare da kai babu komai da nake so.” “Salma na tambaye ki, wani kalal mutum kike so, mai kudi ko talaka, fari ko baki?, duk wanda kike so haka zan koma.” “Mus’ab ba na son ka, ba ka da abubuwan da nake so, a tare da kai babu komai da nake so.” “Salma na tambaye ki, wani kalal mutum kike so, mai kudi ko talaka, fari ko baki?, duk wanda kike so haka zan koma.” “Mus’ab, ba na so mai kudi, ba na son talaka. Mutum nagartacce mai kya hali, wanda zan amfana da shi na ke so.” Shiru ya yi, yana tambayar zuciyar Sa menene kyan hali, menene nagarta, wanda ya rasa su har Salma ta ki shi a kan su. Ni kuwa ina fadamai haka na ta shi na huce daki na, ina mai jin haushin kai na, a kan biye masa da na yi, har na ke masa magana. Haka a bangaren sa gaba daya tambayr kan sa yake, menene kyan hali, menene nagarta?, har bacci ya dauke shi. Legends pen. Page 32. Washe gari. Kamar yanda nayi jiya haka nayi, wanka na zuba ado da gayu na shi ga kitchen, dankaki na ferayi guda bakwai kacal, na soya na hada tea kofi daya na dauka na shige daki na ci, shi hakan bai da meshi ba kwata-kwata, kalamar Nagarta da kyan hali ita ta fi damun sa, haka ya yi wanka ya shirya ya fice. Kai tsaye gidan Galadima ya nufa, ɓangaren Hajja ya fara shiga. Bayan sun gaisa ne Hajja ta ce. “Ya rigimammiyar matarka.” murmushi ya yi sanan ya ce. “Wallahi Hajja rigima sai wacce ta manta.” “Ai na sa ni, sai ka yi hakuri fa, ka kuma dage da addu’a Allah ya sassauta ma ta wanan tsanar ta ran ta, amma lamarin Salma da girma ya ke.” “Hakane kam Hajja, amma duk fushi ta ke da ku baki daya.” “Ai ni ce nan na hana zuwa gidanta, kar ta yi wani rashin arziki mutane su ta fi da ita a baki, wanda ta yi lokacin biki ma ya isa, fushi kuwa za ta yi ta gama.” “Hakane Hajjata, bari na je na gaida mutanen gidan ko.” “To, amma ka biyo kafin ka ta fi.” “Shikenan Hajja.” daga haka ya mike ya tafi, bangaren su ya nufa, bayan sun gaisa da Abban ciki ya koma daki da Mama, yana so ya tambayeta amma ya kasa, yasan a kan shi za ta karar da komai. “Ya Salman.” murmushi ya yi sanan ya ce. “Tana nan ƙalau.” “Babu wata matsala dai ko?.” “Eyh babu Mama, amma ina da tambaya guda daya dan Allah.” “Ina jinka.” “Mama menene nagarta, menene kyan hali?.” Murmushi ta yi tasan Salma ce ta yi masa maganar, amma sai ta ce. “Mene amfanin wanan tambayar, ko da tun da ba ka sa ni ba?.” Shiru ya yi, daman ya san a kan sa zata karar da komai. “Tambayr ka fa na yi?.” “Ina son sani ne.” “Tsanar da ka yi ma ta, da cin zalinta da ka yi a baya shi ya ja ta ce maka baka da kyan hali.” Shirun ya sake yi, tare da miƙewa ya yi alƙwarin ba zai ƙara zuwa wajen Mama da irin wanan tambayar, dariya ta yi sanan ta ce. “To ango Salame, kar dai amanta da amanar da a ka baka.” shiru ya yi ya fice, ɓangarenmu ya nufa kai tsaye, Abban mu ba ya na Ummanah ce kawai sai yaya Asma’u, bayan sun gaisa kamar ko ina amma Ummanah ba ta tambayi ya na ke ba. “Ummah ba ki tambayi Salma ba.” banza ta yi masa, sai Yaya Asma’u ce ta ce. “Ya matar ta ka.” “Bansani ba.” “Eyh ka ce ba ka sani ba mana, sanda ina maka lefe gaishe ni ne kawai ba ka yi ba.” “Dan Allah ta shi k ba ni waje zan yi magana da Ummah.” ta shi ta yi ta shege daki ta ci gaba da hade kayanta. Bayan ta ta shi ne Ummah ta ce.”Lafiya dai ko Mus’ab?.” “Lafiya kalau Ummah, daman tambaya zan yi miki dan Allah.” “Toh Mus’ab,ina jinka.” ta fada ta na gyara zamanta. “Umma menene nagarta, menene kyan hali?.” Kallonshi Umma ta yi sanan ta gyara zama ta ce. “Nagarta, ita ce yin abin da ya dace, koda babu mai kallo. Mutum mai nagarta yana aikata gaskiya da adalci, yana tausaya wa mutane, yana kiyaye alkawari, kuma baya cutar da wani ko da yana da dama. Nagarta kamar haske ce a zuciya tana haskaka rayuwar ka da rayuwar wasu.” “Na’am Ummah kyan hali fa?.” “Kyan hali kuma, shi ne dabi’ar kirki da ake gani a ayyukan ka da hulɗarka da mutane. Yana nufin ka zama mai ladabi, hakuri, biyayya, girmama na gaba da kai, ka dinga magana da kyau, ka kuma daina zagi ko faɗa da mutane. Idan mutum na da nagarta da kyawawan halaye, zaka fi kyau fiye da tufafi masu tsada ko kuɗi masu yawa. Saboda mutane suna mantawa da abin da ka ce, amma ba za su manta da yadda ka sa su ji ba. Nagarta da kyan hali su ne ado na gaske da babu mai iya cire maka.” “Nagode Ummah, kuma insha Allah zan zama mai nagarta da kyan hali.” “Mus’ab waya ce ba ka da nagarta da kyan hali?, duk misalan da na bayar na nagarta da kyan hali a kan halayen ka na dauka, ka na da nagarta, kyan hali, cika da kamala.” “Umma tun da Salma ta ce ban da su, da alamu na ga za ta wani ɓangaren.” “Yanzu kai fisabillilahi Mus’ab zancen Salma ka sa a ranka har ka zo ka na tambayata, kai wanan yarinya ba ta da hali kwata-kwata.” “A’a ba haka ba ne Ummah.” “Mus’ab idan har za ka saka haukan Salma a ran ka to za ta iya cewa kai din ba musulmi ba ne, lamarin Salma addu’a yake buƙata kawai, da kuma yi mata zuru.” “Shikenan Ummah ngde.” daga haka ya tashi ya fice, Ummah ce ta kira Yaya Asma’u da ke daki ta ce.”Asma’u ina so kije gidan Salma, ki ci mun ubanta sanan ki hada ni da ita a waya.” “Toh Umma, na ji duk yadda kuka yi da shi, ni ina mamakin yadda Yaya Mus’ab ya faɗa soyayyar Salma har haka.” “Asma’u nima na yi mamaki, amma kuma ba a mamaki da lamarin ubangiji kuma isnha Allahu ita ma sai ta so shi, fiye da yadda ya so ta.” “Allah yasa.” Mus’ab daga bangaren mu, bangaren Anty ya nufa,nan ma sun gaisa sanan ya fice zuwa gida. Ina zaune a falo na cakare ado abuna, hankali na na kan Tv, daga kitchen kuma na ɗora abincin, ƙamshin abincin na ta shi a gidan. Sallama ya yi na amsa ciki-ciki, dan ba ma zai ji na amsa din ba. “Barka da gida Salame.” ban kula shi ba, ban kuma juyo na kalle shi ba. “Tai ma ka mun da ruwa na sha.” nan ma banzan na masa, ganin ba zan ba ya sa ya miki ya nufi fridge ya ɗauki ruwan shi ya sha, ya dawo ya zauna. “Salma yau na sha rana, Mama da Hajja da Anty da Umma suna gaida ke.” wani hawaye na ji na shirin tawo mun, ashe gidan Galadima ya je ya bar ni a wanan gidan na sa, mai kama da na fatalwa, wanan shine amfaninn auren kenan yazo ya turkeni kamar tikinya ko. “Kai da Allah.” na fada a zuciyata. Legends pen. Page 33 “Salma mai kike so na yi, na kyan hali ko na nagarta, ki fadamun dan Allah.” “Wai Mus’ab ina shiga sabgarka a gidanan ne, me yasa kai kake shiga tawa, ba ka da zuciya ne ko me.” “Salma a kan ki ba ni da zuciy kwata-kwata wallahi, Salma ba ni na ɗorawa rai na son ki ba, ubangiji da ya hallice ni ne.” Banza na yi da shi, ni ban san me zan ce masa ba, kawai ya yi nesa da ni, amma tun da ba shi da zuciya ai shikenan ni dai ba zan kula shi ba. Ta shi ya yi ya nufo inda na ke, ban aune ba na gan shi ya tsugunna a gaba na. “Salma ki yi wa Allah, ki yi wa ma’aiki, ki sassauta mun wanan tsanar, ki yafe ni ki karbi tu ba na dan Allah.” “Ni ka ta shi daga inda na ke kawai.” “Salma, ki yi hakuri.” “Mus’ab ba zan ta ɓa yafe maka ba, ni kawai ka rabu da ni.” shiru ya yi, ya rasa me zai mun, ya yi fushi ya kyale ni, ya sake gwadawa, ko me zai yi.” Ta shi na yi na nufi kitchen duba abincina, na bar shi wajen a durkushe, ina dalili zai zo ya yi mun makirci, ni akwai abin da zai sa na yafewa Mus’ab a duniya kowa, ai ganin shi na yi yana masharsharar mutuwa ban jin zan ya fe masa, fito wa ta daga kitchen bayan na duba abincin ya yi dai-dai da fara knocking din kofar da a ka yi, shi ya ta shi ya nufi ƙofar ya bude, wa zan gani idan ba Yaya Asma’u ba. Ta shi na yi na nufi kitchen duba abincina, na bar shi wajen a durkushe, ina dalili zai zo ya yi mun makirci, ni akwai abin da zai sa na yafewa Mus’ab a duniya kowa, ai ganin shi na yi yana masharsharar mutuwa ban jin zan ya fe masa, fito wa ta daga kitchen bayan na duba abincin ya yi dai-dai da fara knocking din kofar da a ka yi, shi ya ta shi ya nufi ƙofar ya bude, wa zan gani idan ba Yaya Asma’u ba. Yana ganin ta shigo ya sa kai ya fice, ni kuwa nayi cikin daki da sauri, yanda take zare idanu tana bina da wani kallo kamar sabuwar mayya ya sa nasan ba alheri ya kawo ta ba, da alama jibgata ta zo.”Karki kulle dakin nan na gaya miki.” tsayawa na yi ina kallonta sanan na ce. “Ya aka yi?.” “Ubanki a ka yi.” ta fada bayan ta zo inda na ke. “Shige muje.” dakin na shige a rai na ina mamakin munafunci irin na Mus’ab, ya je ya kai gulma kuma ana zuwa ya gudu. Zama ta yi a kan gadon ni kuma na tsaya a kanta ƙerere. “Zaki zauna ko sai na ci ubanki.” zama na yi can nesa da ita, ina turu ba ki gaba. “Ni ba na ce ba zan kara neman ku ba har abada, to ku mai ya kawo ku waje na?.” “Ke dalla malama rufemun baki, shashasha da ba ta san me ke ma ta ciwo ba, ba ki san aure ba da darajarsa, to Wallahi Salma ki kula ki kama kan ki, aure ba abun hulakantawa ba ne, miji ba abin yarwa ko hulakanta wa ba ne, haka iyaye ba ababen wasa ba ne, ba kuma mutane da za a kiyiwa biyayya ba ne, dan wallahi muddin kika ci gaba da baƙanta musu, zaki ga wahala ne a rayuwarki wahala ta gaske.” ƙaurin da ke ta shi daga kitchen ne ya katse ma ta maganar da ta ke. “Me kika dora a huta, ta shi ki je ki kashe yana ƙauri.” “Abinci ne.”na fada ina kokarin mikewa. “Ke sai yanzu kike yin abincin ranan sai yanzu, mijin na ki haka kike gana mai azaba, salma kiji tsoron Allah.” shiru na yi kawai na tashi, a raina ina cewa “wa zai masa girkin ba dai ni ba wallhi.” kamar ta san abinda nake fada ta ce. “Salma kina yin girki da shi?.” “Yaya ni zan masa girkin?.” “A’a, ni zan zo na masa dan ubanki.” ta fada tana danna wayarta, fita nayi zuwa kitchen din na kashe girkin na dawo. Tun kafin na kara shiga dakin na ji tana cewa. “To wallahi Umma ko girki ma iya cikinta ta ke yi, ba ta ba shi.” ban ji mai Ummah ta ce ba, amma nasan fada ta ke. “Bari ta shigo.” “Innullahi wa inna illahir rajiun.” na shiga maimai ta wa, jikina sai ɓari yake na kasa shiga dakin gaba daya, sai da na dau kusan mintuna 10 a haka sanan na shiga dakin. “Sai yanzu kika gama tsayuwar? To ki zo ga Ummah.” ta fada tare da mikamun wayar, karba na yi hannuna na rawa na fara magana. “Ummah ina kwana.” “Bansani ba Salma, bansani ba.” “Ummah kiyi hakuri dan Allah.” “Salma mai kike so ki zama, mai kike nema a rayuwa haka, mijinki kullum kina masa ra shin azirki, Salma kullum kina ba ta ran iyayenki, kina tunanin zaki samu riba a haka?.” “A’a Ummah.” “Salma kin fusata mahaifinki, kin kai shi karshe ya sare da lamarinki, so kike nima na yi haka, mu barki da duniyar, mu barki da halinki?.” “A’a Umma Wallahi bana masa fada, bana masa rashin kunya.” “Amma ai bakya ba sa abinci, bana jin ma ko gaishe shi kina yi?.” “A’a Ummah.” “Salma ba zan ƙara ce miki ki gyara ba, ki yi komai da kika ga yada ce, amma ki sani Allah na ji kuma yana gani.” “Ummah ki yi hakuri dan Allah.” ɗif naji an kashe wayar ga baki daya, kuka na ci gaba da yi iya karfina babu mai rarrashe na babu mai ce mun dai na. “Salma idan kinga dama kin yi hankal kanki, idan ba ki yi ba ma kan ki, amma ki sani duk ranar da kika kashe auren ki, tsakanin Ummah da Abba babu mai karɓar ki, kuma kin san duk duniya babu inda zaki ji dadin zama, kamar gaba iyayyenki.” shiru na yi ina ci gaba da kuka na, a zuciyata ina cewa. “To yanzu me nake, ni ina son in rabu da iyayema lafiya, amma Mus’ab ya na so ya ga haka ba ta faru ba.” Legends pen. Page 34 “ki ta shi kije, ki dora wani abincin, kuma daga yanzu ki tabbatar kina kowanne girki da shi, safe rana dare, ki kai mai kan dinning ki ajiye masa.” “Tom.” kawai na ce na ci gaba da kuka na, haka tai ta bani shawarwari, amma ciki ban ji wacce zan iya dauka ba, domin shwararwarin na ta sun tafi kan macen da ke so miji ya so ta, ni kam ban ga abinda zai sa na so Mus’ab ya so ni ba, mai zan yi da soyayarsa, mai zan yi da ita. Har ta gama ta tafi ban dai na kukan ba, sai da na yi mai isa ta har na ji kai na ya fara mun ciwo sanan na yi shiru, wani wahalallen bacci ya yi gaba da ni. Ban ta shi ba sai bayan biyar daman lokacin hudu ta yi, ta shi na na yi wanka, amma yanzu ban yi wanan azababben make up din ba, yunwa nake ji hakan yasa na nufi kitchen, yana fallon yana aikin latsa computer, ban kalli inda yake ba bare ma na san da zaman sa. Taliya na dora jollop na hada drinks, ina kitchen din komai ya kammala, na zuba mai a plate na dauka na fito falon, kan dinning na je na ajiye mai tun da can a ka ce na dinga ajiye mai, sanan na koma kitchen na dakko nawa na yi cikin daki. Murmushi ya yi, sanan ya ta shi ya nufi dining din yana ci yana santi abun sa, lallai Salame ta iya girki abunta, shi kam ya ji dadi sosai ko iya girkinan zam dinga ba shi kullum, haka ya ci ya gatse sanan ya kai plate din kitchen ya dawo kan system din shi. Ni kam ina shiga daki na sa abinci na a gaba na ci na sha drinks dina, hankali na kwance na gama na fito kitchen na wanke kwanika na, na gyara kitchen dina, tabbas wanan xaman ya ishe ni na gaji iya gajiya, ko makatanta ko wani abun, amma kuma ai ko waec da neco ba muyi ba, ina zancen zuwa makaranta?, ko ance na je ma ba zan je ba, dan ba zan iya shiga cikin ‘yan ajinmu ba a matsayin matar aure, matar auren ma ta mus’ab wanda kowa yasan yadda na tsane shi. A bangaren Mus’ab kuma bayan ya gama ci Abdul ya kira shi a waya, bayan sun gaisa ne Abdul ya ce. “Boss yaushe xa ka koma aiki?.” “Ba ku sa ba fa, sai na samu soyayyar gimbiya ta ko zai dauke ni shekaru, nine mai gidan kai na babu wanda zai neme ni ko ya hukunta ni.” Dariya Abdul ya yi, sanan ya ce. “Sai an nemo soyayyar gimbiya, akwai hanyoyi da dama na neman soyaya, ka yi amfani dasu mana.” “Wane irin hanyoyi Abdul?.” “Akwai kyautatawa, nuna so, nuna kula, ka dinga bauta mata, i mean ka dinga nuna mata so, dan baitin nan na waka ka yi mata, ka dinga daukan ta kuna fita dinner, da sauran abubuwa.” Shiru Mus’ab ya yi, tabbas wanan shawarwarin idan ya gwada su za’a iya da cewa Amma ya san Salma na da matsla, ba lallai wa’yanan abubuwan su burge ta ba, ya santa da tsatsauran ra’ayi, amma ba a ƙin ta mutum zai gwada hakan, godiya ya yi wa Abdul tukunna su kayi Sallama. Fito wa na yi falon ba yan na idar da Sallar isha, nasan dai-dai lokacin MBC Bollywoood ke saka fina-finan indiya masu kyau, jikin sa’a na ga sun daka jodha akbar na Ashwarriya da hrithick roshan, film ɗin da har yau ban ta ɓa ganin karshen sa ba, godiya na yi wa Allah na sa a rai na yau kam sai na ga karshen film dinan, tin da dai nan ba dauke huta a ke ba, ina zaune hankali na na ka ya shigo ya zauna ne sa da ni, can ƙasa na fara jin muryar shi kamar mai waƙa, dan mai da hankali na yi, sai ji nai ya na cewa. “Na ƙyasa kalal ki, drees da tsarin zubinki sun ka tsuma ni.” sai a lokacin na fahimci waƙa ya ke yi, dariya na so na yi amma na maze, na ci gaba da kallona. “Bege na son ki na riƙe, ki zare Sakata ki na bayyana miki ƙauna.” a rai na na ce. “Sakata na zura ta kenan ba zan ta ɓa zare ta ba har abada.” na faɗa a cikin rai na, dan ban na ma nuna mai ina sauraron shi ba.”Ke na hango jiki a take ya hau ɗari, sai na rugo ƙafafuwana cikin sauri, ungo-ungo kyauta gareki mai alkhairi, bude ki duba zuciya ta kamu da kauna.” ya ƙarashe tare da miƙo mun wata lead, kallo daya na yi mishi shida ledar na watsar, dan a ganina ban da lokacin shirmen sa. “Salma ki kar ɓa mana is for you.” “Mus’ab ba na bukatar komai da ga gareka, sabida ba’a tsiya ce ka ganni ba.” “Nima ai ban ce a tsiyace na gan ki ba, ranki ya dade, kyauta ce wacce ba’a tsammani na yi miki.” Ta shi na yi na shige cikin daki, dan ba ni da lokacin biyewa shirmen Mus’ab, na so kallon ƙarshen jodha akbhar amma bai bar ni ba. Tun da shiga ban ƙara fito wa ba, gado na haye na kwanta tare da yin addu’a, shima Mus’ab din a bangaren shi dakin shi ya huce, ya na ƙudurtawa a zuciyar shi ba zai sare ba, ba zai haƙura ba. Bud’e idona nake ƙoƙarin yi, amma na ji idanu na sun yi mun nauyi, kaina ya na mun wani irin zugi, da alama da matsanan cin ciwon kai na ta shi, ina lissafe yau sati na biyu a gidan Mus’ab, tun ranar da na fara girki da shi ya kuduri ta shi ni duk asuba, duk asuba sai ya zo ya buga mun daki, yanzun ma bugunshi ne ya tashe ni sai dai na tashi da ciwon kai mao tsanani, ƙara rufe idon nawa na yi ko zan ji sauƙi, amma babu alamun sauki.”Hasbunallahu wani’imal wakeel.” na faɗa ina daga kwancen. Legends Pen. Page 35 A ɓangaren Mus’ab ganin har ƙarfe 7:30 babu motsi na a falo bare kuma kitchen ya sa shi sake zuwa bakin ƙofar ɗakin. “Salma, kin ta shi kuwa.” Kuka na fara, ina faɗin “kai na.” “Salma me kike cewa?, ba na jinki.” “Kai na.” na fada tare da fashewa da kuka. “Ina zuwa.” ya fada tare da matsawa daga jikin kofar, ‘yan mintuna kadan na ji yana bude kofar, ashe yana da extra key a hannun shi amma bai ta ba budewa ba ko da wasa, shigowa ya yi tare da fadin mai kike cewa. “Kai na.” “Ya salam sannu kin ji.” ya fada tare da ficewa, can ya dawo rike da ruwan zafi na tea.”Salma ta shi ki sha, bari naje pharmacy na duba miki magani, kina da ulcer?.” “A’a.” ficewa ya yi, ni kuma na fara shan ruwan zafi, ina cikin sha ya dawo rike da ledan maganguna. Ajiye mun ya yi tare da fadin “Ga su ki sha.” ɗauka na yi na bude na sha da ruwan zafin sanan na kwanta shi kuma ya fice, sai ƙarfe sha biyu da rabi na farko, lokacin ciwon ya ɗan safafa mun, na miƙe na shiga ban ɗaki na daura alwala tare da yin wanka, sallar asuba na yi dan ban iya yi ba, na saka doguwar riga na fito falo dai-dai lokacin da ya fito. “Sannu Salma, ya jikin?.” “Da sauƙi.” “Ga take away can a kan dinning zaki iya ci?.” ban ce mai komai ba na nufi dining din, bayan na xauna na fara bude take away din, dankali ne da plantain, sai kum tea a plast da alamu shi ya dafa abunsa, sai da na fara zuba tea din na sha sanan na fara cin dankalin, ban wani ci sosai ba, na ta shi na dawo kan kujera na zauna. “Ya.ƙarfin jikin.” “na warke fa.” “To ai haka ake so Hajiya Salame.” “Wai kai Mus’ab ba ka iya shiru ne a rayuwarka?.” dariya ya yi, sanan ya ce. “Ai ke din ce ban so kiyi shiru kwata-kwata.” Tsaki na ja tare da mikewa na shige daki, har da banko kofa. Tsayawa nayi cak, ganin dakin ba yadd na bar shi ba, angyara shi sosai har da gadon, ga magani na nan har da bottle water a kan centre table na cikin dakin. Karo na farko, abu na daya da Mus’ab ya yi wanda na ji ya so ya burgeni, haka kwai abun ya tsaya mun a rai, amma kuma ban duba ba. Har dare ban sake fitowa ba, sabida jikina babu kwari kuma bana jin wata yunwa. Washe gari ma haka ce ta kasance, ya yi mana order abin kare, ya gyara gidan gaba daya har daki na, a takaice dai sai da na yi sati ina wanan jinyar, Mus’ab na mana aikin gida. Ranan da na fara jin na warke da kaina na y duk wasu abubuwana, har na hada mana breakfast kamar yadda na saba, a kan dining na ajiye masa na shige daki na ci nawa. Ina zaune cikin dakin ya shigo, nesa da inda nake ya zauna tare da kiran sunana,’yan mintuna bayan ya zauna. “Salma, a yanzu mun dauki wata da watanni cikin gidanan, amma ba kya yimun ko da maganar arziki ce, Salma ko gaisuwa wanan ba ta hadani da ke, ba ki da aiki sai yi mun tsaki kamar ba mijin ki ba, Salma na miki hakuri da sa ran gobe za ki canja amma kullum jiya iya yau.” Ban bari ya ƙarasa ba na ce. “Idan Saki na zaka yi Mus’ab ka sake ni, har yanzu ka sa ni ina zaune ne bisa umarnin mahaifna da kuma biyayyarsa, amma ba na ƙaunar ka ko ɗis.” Shiru ya yi, ya kuma ra sa mai zai ce mun amma tabbas lamarin Salma bana kare ba ne, sa’anin auren mu sunan kowacce na da juna biyu, amma shi ko kallom arziki bai sa mu. Mi kewa ya yi ya fice, ni kuma na ci gaba da abinda na ke. Haka ya zauna gaba daya ya rasa mai ke ma sa dadi, ta ina zai fara lamura na, an ce kulawa na sa ka soyayya, amma ni kara mun kiyayya ta yi, an ce hakuri amma shi da alamu na shi ba riba, wani bari daga zuciyarsa ne ya ce. “Ka da ka sare Mus’ab, akwai abubuwa da yawa da ba kayi ba, akwai hanyoyi da dama, ka yi ma ta kyautar da baza ta iya banza da ita ba, waya, ko wani abu, ka fita da ita ta ga gari, ka dinga bata nishadi.” “Salma ba bina za ta yi ba, nasan babu inda za ta bini muje, tama ki bani dama na nuna ma ta kulawar ko soyayya.” “Ka bi ta hanyar Mama da Ummah, kar ka nuna musu ta yi maka wani abu, amma ka sa su gane ba ta jin maganar ka.” “Amma ai haka zai ba ta ran ta, zai ja su yi ma ta fada.” “A’a Mus’ab, suma sun san gyara a ke so ba za su yi ma ta fadan da za su ji haushi ba.” “Shikenan bari zan gwada.” Hirar da Mus’ab ke yi kenan da zuciyarsa, haka ya yi ta kwashewa da debewa har ya samar da matsaya guda daya, wacce za ta bude ma sa hanyar samun sa’a. Mota ya shiga kai tsaye ya nufi gidan Galadima, kamar ko da yaushe bangaren Hajja ya nufa, bayan sun gaisa ta tambaye shi matar shi, ya ce. “Hajja a dai ci gaba da mana addu’a kawai, amma lamarin ta sai hakuri.” “Wane sabon iskanci kuma ta tsuru da shi?.” “Hajja, Salma ba ta mun magana duk tsahon lokacin nan, sai dai ta dinga bani abinci kamar ya wane maye, amma babu ko kalma daya ta magana.” Dariya Hajja ta yi sanan ta ce. “Daman matarka gwana ce wanan fannin na gaba da mutane, ina kai ne ka ce wai ba matsala ba ne danna ta yi banza da ni, ina ga wanan ba abun damuwa ba ne Mus’abu.” “Hajja ba za ki ga ne ba, Hajja lamarin na ta ya yi yawa fa.” “ka kara hakuri kawai.” Mikewa ya yi ya fice kawai, bangaren Ummanah ya nufa, bayan sun gaisa ne ya ce. “Ummah dan Allah ina neman alfarma wajennku, ku tai maka kuje gidana, bawai fada ba ne ko matsala, amma ku yiwa Salma nasiha.” “Wane sabon abun kuma ta tsiro da shi.” “A’ah Umma, kawai rashin maganar ta ta ya yi yawa, har yanzu ko gaisuwa fa ba ta hada mu.” “Duk wanan lokacin Mus’ab.” Gyada kai ya yi sanan ya ce. “Duka wallahi Ummah.” “Shikenan bari na yi magana da Yayan sai ka kai mu ko da daddare ne.” “Shikenan Ummah, amma dan Allah kar ku fadawa su Abba.” “Ba zamu fada musu ba Mus’ab.” Ta shi Ummaha ta yi ta nufi bangaren Maman ciki, bayan ta gama gaya ma ta komai ne Maman ciki ta ce. “To mene amfanin zuwan dan Allah, yarinyar nan ai ta yi kokari, tun ta na cewa ba za ta tare ba har ta tare, ta ce ba za ta zauna ba ta zo ta zauna, ta ce sai ya sake ta, yanzu ta daina maganar sakin, wanan din ma za ta dai na.” “Salma ba za ta dai na gaba ba, kin san da mitsiya cin riko, kamar yar zamanin kafirai, ba fada zamu yi ma ta ba ko duka, nasiha ce kawai.” “Shikenaan muyi sallan magariba ya zo ya kai mu.” Komawa bangaren mu Ummanah ta yi ta same shi zaune. “Mus’ab bari muyi sallah sai ka kai mu ko.” “Tom shikenan Ummah.” Ya fada tare da mikewa ya fice. Legends pen. Page 36 Ina zaune a cikin daki na naji ana bude kofar main falo. “ko gidan ubanwa yaje oho?, sai yanzu ya dawo.” Na fada a rai na, ina jiya ya shigo na cancare mai, kwana biyu ina dan jin dadin yi masa rashin mutunci, kofar dakin nawa ya bude tare da shigowa. “salma muna da baki?.” “Baki kuma?, ka na da baki dai, ni wa nake da shi da zai zo ko gidana ne?.” “Salma wa’yanan bakin manya ne, ki zo karki jawa kanki fada, ni ba ruwana.” Yana fadin haka ya fice. “Na shiga uku, su waya ya kwasa mana?.” Na fada tare da mikewa, kofa na nufa zan fita sai kuma na tuna ko maza ne, hakan yasa na dawo na zura hijabi na fita. Da gudu nayi inda suke ina dariya da fadin. “Ummah.” Hade rai Ummanah ta yi, na koma wajen Mama ina fadin. “Mama ku ne, mai makon ku shigo sai ku zauna anan?.” “Ai Salma ba zama ya kawo mu ba, gaisawa da ku mu ka zo yi kawai.” “Bari na kawo muku ruwa.” Na fada tare da kokarin ta shi. “Ga ki a haka kamar mai hankali da nutsuwa, ko kuma wacce ke zaune kamar matar auren gaske.” Zama na yi tare da cewa. “mai kuma ya ce na yi, shi shikenan idan bai hadani da ku ba ya jin dadi?.” “Ni a kace miki na ce wani abu?.” Ya fada da saurin baki. “Wai Mus’ab tsoron yarinyar nan kake ko me?, kai ka fada ta kashe ka, Salma abinda kike yi kina ganin dai-dai ne?.” “Mama dan Allah me na yi, me nake ma sa wallahi tun da Abba ya zo gidanan ko magana ban kara masa ba, bare na ba ta mai rai, Abba ya yi fushi da ni, ina masa girki, ina ajiye mai a kan dinning, ina share-share.” “Amma ai abincin a kan dinning kike ajiye ko da yaushe, ko da bana gidan kuma cikin plate, ba wai food plast ba, kina hadawa da ruwa?.” “To ance indinga baka ruwa ne, ai abinci kawai a kace, kuma Yaya Asma’u cewa ta yi indinga maka girki ina ajiye maka a kan dinning.” “yanzu Salma dan ance ki dinga ajiye masa a kan dinning sai a ka ce ki zuba a faranti ki ajiye masa, kuma dan baki da hankali ruwa sai ance ki ba shi, yarinya ce ke?.” Ummanah ta fada kamar za ta da ke ni. “Yanzu kai Mus’ab wanan ai kukan dadi kake, tana baka abinci, ba ta zagin ka, ba ta ma rashin kunya, mai kake bukata?.” “Haba Yaya ita ba ta da hankali, dan ance ta kai abinci kan dinning sai ta dinga kaiwa, dan ba a ce ba’a ce ma ta ruwa ba sai ta ki kai wa?.” “To yanzu da ta na bar ma sa a kitchen fa?.” “Ba fa da kika zo ba, wani abun dai ya kawo ki.” Ummanah ta fada tana harara Maman ciki. “Yanzu Ummah ni ba wanan ba, ko kallo na ba tayi ba gaisuwa, babu wani hakkina da ta ke saukewa, idan zan kwana ina mata magana to ba za ta kulani ba, karshen amsar da zan samu ita ce ta yi mun tsaki ta bar mun wajen.” Da dukkan alamu ran Mus’ab ya kai karshen ba ci, har ya yi wanan furucin bai sa ni ba. “Salma!, Salma!!, sau nawa na kira sunanki.” Ummanah ta fada fuskarta a hade. “Sau biyu.” “To kar ki ba ri na kira na uku, dan ba zan kira sh da alheri ba, na fada miki.” “Yanzu Ummah me zan yi?.” “Kinga Salma ki kwantar da hankalinki, ki yi iya abinda kika ga za ki iya, wanda ba za ki iya ba ki barshi, yau da gobe za ta sa ki iya, ba kwa ganin Zuwa yanzu kiyayyar da ke tsakanin ta da shi ta sauka fiye da rabi, komai ma a haka zai zama tarihi.” Cewar Maman ciki kenan. “Salma ba irin yaran da ake cewa yau da gobe za ta sauya ba, ya zuwa yanzu watansu nawa da aure, amma ace har yanzu ba ta san ta bawa mijinta ruwa ba, ruwa dai wanan abun banza.” “Dan Allah kar ku ta kura ma ta, Salma ki yi abinda za ki iya, ki yi kokari ki canja Allah ya yi miki albarka.” “Amin.” Na fada tare da ta shi na huce ciki, bayan ita ma ta miki tana fadin. “idan ka ga dama ka zo ka mayar da mu.” Kofa mu ka nufa tare da ita, ina iya lissafa lokutan da na fito wajen compund dinan, domin kullum ina ciki ba na fita, a ciki kuwa Ummanah ce ta kalli Mus’ab ta ce. “Ka bata ‘yan kwanaki, idan ba ta canja ba akwai shirin da zan yi maka, wanda zai ka ci riba insha Allah.” “Shikenan Ummaha ngde.” Ya fada yana ta shi, a ranshi yana mamakin Ummanah wacce irin mata ce, wacce ba ta dauki na ta a na ta ba, wacce ba ta fifita farin cikin dan ta a kan na wani ba. Sai da suka shiga mota na koma cikin daki na. “Me zan yi yanzu ni Salma, me zan yi?, na dinga gaishe shi da zuba masa abinci a plast na hada mai da ruwa, amma ai hakan ba zai rage tsanar da na masa ba, yana nan a kan wanan matsayin na Mus’ab, mutumin da na tsana kamar mutuwa ta. Kitchen na shiga bayan na dauke abincin shi da ke plate a kan dinning, plast na sakko da shi wanda ina ga banta ba amfani da su ba, na zuba abincin a ciki na gyara na kai kan dinning tare da ruwa da cup, sanan na shige daki na na kwanta. Ya ji dadin ganin wanan, da alama za’a samu canji yanzu lokaci ne da zai nunawa Salma mene so, lokaci ne da zai zubawa Salma ruwan soyayya a zuciya, lokaci ne da zai koyawa Salma soyayyarsa, lokaci ne da zai yi yakin ganin ya kuri duk wata kiyayay ta zuciyar Salma ta dawo soyayya, shima ya fara ji a jikinsa da gaske Salma za ta so shi, ko da bai kai rabin wanda yake ma ta ba, yana fatan ko da rana daya Salma ta bude ba ki ta ce. “Ina son ka Mus’ab.” Ranar bai san irin farin ciki da zai yi ba, bai san irin sadakar da zai yi ba, bai san irin sallolin godiyar Allah da zai yi ba. 37. Washe gari. Kamar yanda nake ta shi ko yaushe haka na tashi, bayan na yi wanka na, na caba ado kamar yadda nake ma fito falo, nasan bayanan bai dawo daga gudu da yake ba, daman ko da yaushe na saba sai ina cikin kitchen zai dawo ya zo ya tsaya a kaina ya na ta zuba mun surutu ina ja mai tsaki, har na gama. Ina shiga kitchen din kamar an hankadomun abu haka naji ‘yan uwana sun fadomin a rai, Walida da Sadiya, Yaya Asma’u da yayar Abuja su Iki da sauran, tabbas na yi kewarsu kima na yi butulci na watsar da su baki daya, duk da nima sun watsar da ni amma hali na ne, ina tuna farkon aure na da su ka dinga kiran Mus’ab su na cewa a bani waya ina kin amsa, ciki har da Walida kuwa. Amma nima ai bana cikin tawa nutsuwar kuma suma duk makiya na ne, suna farin ciki da auren Mus’ab auren kaddarar mummuna da a ka yi mun. Haka nai ta aiki na ina faman tunani, ga kuma Mus’ab dai bai shigo da huri ba, koma ya shigo bai zo kitchen din ba, haka kawai na ji na matsu ya zo. Tsaki na ja tare sa cewa. “Uban mene na wa, da zuwan na shi.” Ina fadin haka na ci gaba da aikina ina yaki ce zuciyata da tunanin shi, ina gab da kammalwa ya shigo kitchen. “Salame mai ake dafa ma na?.” Kamar ko yaushe din banza na yi da shi, na ci gaba da aikina. “Salame ina jin yunwa ayi sauri.” “Ina kwana?.” Na fada ba tare da na juyo ba, murmushi ya yi har ina jiyo sautin shi, sanan ya ce. “lafiya kalau gimbiyata, kin ta shi lafiya?.” “Cewa a ka yi na gaishe ka, ba na biye maka ai ta surutu ba.” Na fada a rai na, a fili kuma dai na masa banza ban tan ka mai ba. Yana tsaye yana ta zuba har na kammala girki na, na zuba na shi plast da tea na zuba nawa a plate, juyowa na yi na gan shi tsaye, matsamun hanya ya yi tare da cewa. “Bari na fita da plast din.” Ajiye ma sa na sa na yi, na dauki na wa dake ni a cup na zuba nawa, sai na dauki cup da plate na fice, dakina na koma na zauna na fara cin abincina, bayan na kammala na dawo kitchen na fara kokarin wanke kwanin ka da na yi amfani dashi, amma sai ya shigo. “Ki bari na yi wanke-wanken Gimbiyata.” “kabar shi dan Allah.” “A’a ni gaskiyya na yi niya kawai ki bari.” “Mus’ab ba na son yawan magana, dan Allah ka kyale ni.” “Nifa A’a sai dai mu yi tare.” “Dan Allah ka bari, ka je ka yi wani abun mana.” Cika mun ya yi ya fice, ni kuma na ci gaba da abinda nake. Yan mintuna kadan na kammala na fito falo, tsaye na gan shi rike da moper yana mopping, almun ya yi shara ya gama. “Kai duk rashin jin maganata Mus’ab ya fini wallahi.” Na fada a rai na, ina nufar wajen Tv na fara gogewa, sai ya zama kamar tare muke aikin yanayin can barin ina yin can barin. “Gimbiya kin gam mu kamar wasa best couples.” Ni a rayuwata ban san lokacin da Mus’ab ya zama mai yawan surutu ba, kuma kowa na cewa Mus’ab ya na da surutu ba zai ta ba yarda ba. “Gimbiya idan kana tare da wanda kake so, ka na zama mai yawan surutu ne ba tare da kai ma ka sa ni ba, kawai dadin soyayya ke di ban ka.” “To ni mai ka ji na ce maka?.” Murmushi ya yi sanan ya ce. “Nasan a ran ki kina mamakin yadda na zama parrot haka.” “Ni ban yi ba, kawai sai na zauna na yi tunani ka?.” “Ko ba ki yi yanzu ba, wata rana za ki yi.” Bude ba ki na yi da niyar yin tsakin da na sa ba, amma kuma sai na ji na kasa, mikewa na yi na shige daki na kwanta, can mintuna ina zaune daki na ji am shigo, da sauri na dago tare da janyu blanket na rufe jiki na, ina kallonsa ya na murmushi har ya zauna gefen gadon. “Barka da rana, ranki ya dade.” Shiru na yi ban da niyar magana dan ban ma san me zan ce ma sa ba, wai “barka da rana.” “Ina neman wata alfarma ne Gimbiyatah.” Shiru na kuma yi, amma kuma ya gane ina sauraron sa. “Ina so nu dan fita mu ga gari, zaman kwana biyu ya yi yawa.” Har cikin rai na na ji dadi, ko ina zamu dan wallahi kamar a kan ƙaya na ke a zaune.”Kishirya nima bari na je na shirya.” Ban ce komai ba dai har ya fice, na dau yan mintuna kafin na ta shi, shiryawa na yi cikin riga sa skert na wata atamfa, na yi kyau sosai da sosai ko abu daya ban dauka daga lefensa ba haka na yi shiri na, kuma har yanzu ko dan kunnen ban ta ba dauka daga lefensa ba. Fitowa falo na yi na sami waje na zauna ina kallon Tv, ban fi minti biyar da zama ba ya fito cikin shirin shi, ba zance ya yi kyau ba ko bai yi kyau ba, sabida ni ba wani kallon arziki nake masa ba, amma dai na kwana na tashi da sanin Mus’ab ɗan wanka ne kuma dan gayu. “Yanzu wanan kwalliyan duk na mene, so kike mu fita maza su biki da ido?.” kallon kai na yi, ni kwalliyar na yi ne, fuskata ko powder babu, multi lips ne kawai ke shinning, na san dai fuskar ta yi smooth sosai da sosai, sai kuma mai da kallona kan shi, shi uban kayan da ya saka da alama ma sababbi ne, amma ya zo ya ce wai wanan uwar kwalliyar. “Mus’ab, zamu fita ne ko ba zamu fita ba?.” Legend's pen. Page 38. “Zamu fita ranki ya dade, amma kyanki ya yi yawa sosai da sosai.” hanya na kama na fice, ban masan mai zance masa ba neman maganar kawai yake so, ni wallahi muryar Mus’ab har cikin kwakwalwa ta nake jin ta, biyo ni ya yi a baya zuwa parking space, burki na ja na tsaya, sabida ban san wani mota zai shiga ba, tun da ga sunan burjik kaman na siyarwa.”Ranki ya dade wanne zamu shiga?.” “Wai dan Allah kai ba ka iya rayuwa ne sai ka mun magana?.” dagowa ya yi ya kalleni tare da yin murmushi. “Ranki ya dade idan ban kulaki ba wa zan kula?, yanzu ki zaba mana motar da zamu hau.” “Ta farkon.” Na fada dan san kawar da zancen, idan za’a kasheni da wuka ma bansan wacce nake nufi ba, kawai dai na fada ne. “Angama Hajju.” Ya fada tare da nufar motar, kawar da kai na na yi gefe ba na ma so naga wacce ya dakko din, sai da na ji alamu ya zo inda nake yasa na juya. Kai tsaye back seat na nufa da budewa, amma sai naji su a rufe, tsaki na yi na bude front seat fuska ta a hade na shiga. “Ina muka nufa frist?.” “Kai ma ba kasan inda zaka kai mu ba?.” Na bashi amsa kai na a kasa. “Nasani ko kina da inda kike son zuwa Gimbiyata.” “Muje park.” “Okay.” Ya fada tare da saita motar zuwa hanyar park din, cikin mintuna kalilan mu ka isa duk da a hankali yake tukim cike da kwarewa. Ƙofar Gamji park mu ka je, park din da muke mafarkin zuwa nida su Walida, har cikin rai na ji dadi amma ban iya nuna masa hakan ba, bayan ya yi parking my ka fito sai ji nai ana ta ɓamun mayafi, kafin na karasa juyowa na ga ashe shine yake gyaran mun inda ya sauka bansani ba, duk inda muka yi a park din ya na manne da ni, kuma ranshi a hade kamar zai yi kuka ko zai daki wani, a raina na ce. “Ko uban mai a kayi masa oho?.” Bayan mun gama zagayen mu ka samu wajen da ake zama muka zauna, yana faman danna wayarsa ni kuma ina wasa da wani game da ke wajen ina kuma kallon gefe da gefe, kamar nasan wancan mutumin da ke zaune, duk da ta baya yake amma tabbas ina ji kamar na san shi, ya so ya yi kama da masruru amma ba shi ba ne, sabida idan masruru ne akwai wani yanayin bugu da nake ji a zuciya ta mai nuna zallan so da kauna, mai nuna girma da zafin soyayya, kuma nasan har yanzu idan na gan shi haka zanji, duk da rabo na da tuna wani mutun wai shi masrur tun kafin na shiga gidan Mus’ab, amma na san a yau na yi ido biyu da shi zan ji soyayyarshi a zuciyata, sabida shine mutum na farko da na fara so, kuma wa’yancan da alama shaye-shaye suke, masrur kam na kwana da sanin mutumin kirki ne. “Salma me kike kallo, tunanin me kike?.” ido na mayar kan sa sanan na ce. “Bakomai.” “Kin san wani a cikinsu ne?.” da sauri na girgiz Kai na ce. “Ko ɗaya.” “Okay, mu tafi ko?.” “Uhm.” na fada ina mikewa, daii-dai lokacin da suna samarin su ka ta shi, sakamakon zuwan wasu manyan karuwai, kana ganin yan matan nan kasan karuwai ne masu lasisi, duba da irin shigarsu, atamfa ce amma dinkin da ake kira. “Fan ɗarinka tsirara. “ domin duk wani waje da yake bai kamata ya fita jikin mace ba ta su nasu a waje yake, sai gaisawa suke da mazan har da rike hannu, gaba na ne ya fadi amma bana soyayya ba, na tsoro sakamakon ganin masrur da na yi, hawaye na ji sun fara zubumin ban san na mene ba, amma kuma ban hanasu ba cikin sa’a shima idanunsa suka sauka a kai na, bayan na juya inawa Mus’ab magana. Ƙamewa ya yi yana kallona, tabbas ni ce tare da wanda a ka bani a matsayin miji, gamu nan cike da so da kaunar juna, daman yaudararsa na yi ko kuma yau da gobe ce ta sa na fara son Mus’ab din. Ji ya yi kamar yazo ya mun magana, sai dai kuma yanayin da ya ke, gashi kuma ni na juya na bi mijina, yana kallon lokacin da Mus’ab ya budemun gidan gaba na shiga, ya rufe sanan ya juya ya bude nasa ya shiga muka tafi. Kallona Mus’ab ya yi sanan ya ce. “Wai kukan na mene haka?.” Banza na yi masa, nasan duk shi ya ja rashin samu na ne ya sa Masrur shiga wanan halin, halin da ni kai na nai fatan na shiga a kan na zama matar Mus’ab. “Kiyi hakuri idan na miki wani abun?.” Goge hawaye na na yi, sakamakon parking da na ga munyi a bakin wani shago. “jirani.” Kawai ya ce ya fice, bin bayan shi na yi da kallo na ga shagon da ya shiga an rubuta. Apple fix by Legend. Da alama shagon siyar da iphone, kau da kai na na yi, na shiga tunani da mamakin ganin masrur amma ban ji wa’yanan yanayin da na yi imanin jin su ba’ mai hakan ke nufi, wai na daina son Masrur ko me, to idan na dai na son Masrur wa nake so, ko kuma wa zan fara so?. “Mus’ab.” Na ji zuciyata ta fada da karfi, nima cikin karfi da sauri na ce. “A’a wallahi.” Legends pen. Page 39. Bude kofar na ji yanayi, da sauri na dauke kai da kallonshi haka kawai naji banson ganin sa ma, har ya shigo ya ja motar ban ce mai kala ba. “Dare ya yi amma ba sosai ba, zamu iya fita dinner?.” Allah ya gani rai na a bace yake, kuma ba ma na son fita amma kuma ina tuna kalmar opportunity come once, ga shi kuma ni ban ma san ya a ka yi ba na ji ina son bin na shi. “Zuwa ina?.” “Do you have place in your mind?.” Girgiza kai na yi sabida ba ni da wani waje, kuma ko ina da shi ma ba zan iya fada ba, dan na ga sakin fuskar da na masa kwana biyu ya samu sake a wajena, amma zan canja. “Okay mu shirya din sai muje inda Allah ya yi.” Bance komai ba kawai na mai da hankali na kan titi, har mu ka isa gida ban ce komai ba. Yanayin parking na bude zan fita. “Ranki ya dade take this.” Ya fada yana mikomun leda. “Mene a ciki?.” “Ki duba ki gani ma na.” “Ka bar shi kawai.” Na fada zan fi ce. “Kiyi hakuri dan Allah ki kar ba.” A yatsine na sa hannu na amsa na yi cikin daki, ina zuwa na dire leda kan gado na shiga toilet, wanka na sake na yi Sallah sanan na kwanta, wajen 30min na ji ya na mun knocking. “Ranki ya dade na shirya fa.” Ya tsine fuska na yi, ni ba na son fitar ma ba ki daya. Sakkowa na yi daga kan gadon na shiga toilet na wanke baki na fito, doguwar rigar material na dauka na sa ban ko sa ka mai ba bare wani abu a jikina, ban san meyasa ba kawai na ji ba na son sakawa, ko dan ba na son ya na yawan yi mun magana ne oho. A falo na sameshi yana tsaye cikin english wear, ya yi kyau sosai, tabbas yana kama da Aditiya roy kapur na india, ban ta ba gani ba sai yau. “Ranki ya dade na yi kyau kenan?.” Tsaki na yi tare da kau da kai. “Nagode.” Ban ce komai ba na fita shi ma ya biyo ni, front seat na zauna, bana son yawan jan maganarsa shiyasa nake kare komai, ban san me yasa ba kwata-kwata ba na jin dadin, kamar wani abu zai faru a can inda zamu. Shiga ya yi ya fara jan motar, wacce mu ka fita da ita da zu ba ita ba ce wanan wata ce da ban. Country Hill Restaurant 21a Dan marna street unguwar rimi. Mu ka nufa, tabbas ko a da idan na zo hucewa ta wajen yana burgeni, amma ban ta ba ko mafarkin shiga ba sabida nasan sama ta yi wa yaro nesa, nasan a gida babu wanda zai bar mu zuwa wajen, sanan mijin da zan aura ba lallai mai irin wanan yawace-yawacen ba ne, amma Mus’ab kwana biyu yana kokarin cikamun duk wasu buri ka na. Vip mu ka shiga, komai aka kawo mana shi a mutumci da cafasity din mu, wajen a nutse a gyare ya yi masifar kyau da burgeni. Menu din wajen ya mikomun mai cike da jerin da ɗaɗan girke-girken da ke wajen, komai mai tsada ne kuma mai dadi. “Ka zaba mana kawai.” na fada sabida har yanzu ban jin wani kwarin jiki na ko dadi. “Mai yasa?, ki za ɓa mana tare fa da mijinki kike ba saurayi ba.” tsaki na ja cikin rai na, na kara dubawa. Haka na zabi abinda nasan zan iya ci da cinyewa na ba da, ‘yan mintina kalilan aka kawo mana. Awanni kadan muka dauka a can mu ka kama hanya mu ka dawo. “Ranki ya dade mai yasa bakya son sakik jiki da ni ne, ba dukan ki zan yi ba, ba zagi ba, ba harara ba.” Shiru na yi ban ce komai ba har mu ka shiga gida, haka na fito daga motar na yi cikin falo. “Dan Allah ki tsaya na yi magana da ke, ba danni ba ba dan halina ba, dam darajar iyayenmu.” tsyawa na yi cikim falon bayan na sami waje na zauna. “Salma, zan fada miki abinda ke zuciyatah, zan gaya miki girman Soyayyarki a zuciyata, ko da ba zaki so ni ba zan so ki rage wata kiyayya ta da ke cikin zuciyarki.” Ya yi shiru na ‘yan mintuna sanan ya ce. “Salma... akwai kalmomi da ba su da sauki a furtawa, amma yau zan furta su. A baya na sakawa zuciyata Sakata, na rufe ta ruf ba wai cike da ƙiyayyarki ba, sai dai na san ban ta ba sonki ba, kamar yadda ban ta ba ƙin ki ba... Na gina katanga tsakanin ni da ke saboda ganin Hajja na nuna miki Soyayya irin tawa, Salma ba ki ta ba yimun komai ba na ƙi, ban ta ɓa kai ƙarar ki dan na tsane ki ba, sai dan ki gyara, ina so ya zaman gaba daya cikin gidan Galadima kin fi kowa nutsuwa da hankali, sai dai naga kinfi kowa rashin ji da taurin kai, duk lokacin da a ka dake ki ina jin babu dadi, sai dai ina saka ran zaki gyara. Salma ban ta ba jin sonki ba, kamar yadda ban ta ba jim tsanar ki ba, zance masrur kuma ba mutumin arziki ba ne tun ranar da na ganku tare ma gane shi, shine wanda ya yi rapping mai aikin gidansu Abokin, shiyasa na dage wajen kai karar ki tare da biayyarku a ko yaushe, Salma ban ga ba jin zan iya zare Sakatar da ke cikin zuciyata a kan ki ba, amma daga ranar da na ji iyayenmu sun yanke hukunci ha ɗa aurenmu... sakatar zuciyata ta zare da kanta. Legend's pen. Page 40 “Na fara jin ki a cikin kowanne sashi na rayuwata. Muryarki na karade kunnena ko da ba kya kusa da ni. Abincina baya daɗi sai na tunaki, Fuskar ki ce nake gani ko da idona na a rufe, kece kike zuwar mun cikin mafarki, ke ce yanzu ke ce har ibada a zuciyata. Salma, wallahi bana miki so na yau da kullum bana miki so irin wanda ke ƙarewa da jiki. Ina miki so mai tsarki, irin wanda idan na mutu, ya kamata a rubuta a kabarina: ‘Ya mutu yana sonta!’” Ya juyo ya kalle ni kai tsaye, idonsa a cike da hawaye masu zafi, amma yana dariya da kuma murmishi, sanan ya ci gaba da cewa.”Idan har ana iya so har fuska ta canza kama, to Salma ni na kai nan. Ina rokonki kada ki saka ni cikin duhun da ba zan iya fita daga cikinsa ba, ki bani dama daya, ko da karama ce, domin zan kashe raina wajen nuna miki ƙimar ki a wurina.” Dago ido na yi na kalleshi, zuciyta na mun wani abu da na kasa banbance mene, kawai na dauke shi a matsayin tsana mai girma, baki na na rawa amma zuciyata ta bude ta na kokarin yin maganar da ni kai na ban san me zan ce ba. “Mus’ab… naji kuma na saurari kalaman ka. Amma ka tuna, ba duk kyawun magana ke tsinkewa cikin zuciyar da bata so ba. Na riga na saka wa zuciyata sakata. Na rufe ta da ruf da ƙiyayya. Ban taba sonka ba, kuma banza taba sonka ba, na san dai na karɓe ka a matsayin mijin kaddara, mijin da iyaye da ‘yan uwa su ka yimun, amma ba jagoran zuciyata ba na karbe ka a matsayin mijin da iyayena suka zaba. Amma ko yau a ce babu ran iyayenmu, babu wani abu da zai sa na kara zama ko na awa ne a tare da kai,So ba dole ba ne. Kuma ni ban zauna da kai saboda so ba. Na zauna da kai ne saboda biyayya ga iyaye, amma zuciyata ba ta son ka, kuma ba ta da wajenka.” Shiru dakin ya yi,ba ka jin komai sai numfashin Mus’ab, ni kuwa mamakin kai na ya cika nibda nayi wa’yanan furucin sai ka ce mai shafar aljanu, maganar zarar bunu ce yau na tabbatar da zan iya da na gogeta yanzu, sabida gaba daya ba ta kama ta ba. “Salma nagode.” na ji ya fada, shiru na yi zuciyata tsinke ga ba daya. “Mai ya kai ki wanan maganar Salma?.” nasan tabbas wanan magamganun ba daga cikin zuciyata suka fito, domin ni kai na nasan a yanzu wanan tsnar mus’ab din babu fiye da rabi a zuciyata. To mai ya kai ni wanan maganat. “innullahi wa ina illahir raji’un.” na fada a cikin rai na, tare da dagowa sai dai babu Mus’ab babu mai kamar shi cikin. “Ya hayyu ya ƙayyum.” na maimaita ina jin hawaye na zuna a idona, wa’yanda ban san na mene ba kuma ban tare su na hana su zuba, sai dai na yi masu isata sanan na ta shi na koma daki, maganganun da na fada masa na ta dawo mun a kai na, kamar yanzu na fade su, Salma kin sha roƙon Allah ya gama ni da Masifar duniya, to Salma Allah ya gamani da masifar kaunarki, wacce na san shine amsar addu’arki. “Mus’ab… naji kuma na saurari kalaman ka. Amma ka tuna, ba duk kyawun magana ke tsinkewa cikin zuciyar da bata so ba. Na riga na saka wa zuciyata sakata. Na rufe ta da ruf da ƙiyayya. Ban taba sonka ba, kuma banza taba sonka ba, na san dai na karɓe ka a matsayin mijin kaddara, mijin da iyaye da ‘yan uwa su ka yimun, amma ba jagoran zuciyata ba na karbe ka a matsayin mijin da iyayena suka zaba. Amma ko yau a ce babu ran iyayenmu, babu wani abu da zai sa na kara zama ko na awa ne a tare da kai,So ba dole ba ne. Kuma ni ban zauna da kai saboda so ba. Na zauna da kai ne saboda biyayya ga iyaye, amma zuciyata ba ta son ka, kuma ba ta da wajenka.” Maganganun da suka ta shi Mus’ab kenan daga baccin da ya samu ya yi bayan sallar asuba, amma gaba daya daren jiya bai iya ko runtsawa ba, Salma ba ta son shi kuma ba zata ta ba son shi ba, anzo gejin da yake ji ya kamata ya sauwake ma ta kawai ya huta ta huta, yasan dai yana son ta amma ya zama dole ya bar ta sabida ba ta son shi kuma ba za ta so shi ba. Ban daki ya shiga ya watsa ruwa ya shirya, kallon agogo ya yi bayan ya kunna wayarsa, karfe 09:19 gida kawai zai je. Nima jiya bacin rabi da rabi na yi, ban samu mai tsayi ba sai ba yan sallar asuba, nayi matukar mamakin rashin ta shi na da Mus’ab ya yi, jikina ya yi san yi ya mutu gaba daya, na yi dana sanin wa’yan can maganganun kuma a shirye na ke na yi zaman aure da shi, ko da ba na son sa zan zauna da shi. Wanka na yi na saka bakar doguwar riga na nufi kitchen hada breakfast. Ina kichen ina sa ka ran shigowarsa ya zo ya yi mun magana, amma babu shi babu alamun shi. Na ji ni gaba daya wata sukuku a kitchen din, haka har na kamalla na kai masa kan dinning, shiga ta daki na ji alamun ya fita da sauri na fito ko ya taba abincin amma bai ko kalleshi ba. Kai tsaye gidan Galadima Mus’ab ya nufa, byan sun gaisa da Hajja ya y bangarensu, nan ma su ka gaisa ya yi namu bangaren. Daki ya shiga ya jira Ummanah bayan sun gaisa sa Abbanah, shigowa Ummanah ta yi ta zauna tare da fadin.”Mus’ab lafiya dai ko?.” ya dau mintuna kafin ya yi magana. “Ummah na zo wajen ki ne a matsayin uwa ba matsayin maman Salma ba, na zo wajen ki ne dan nasar da ke hukuncin da na yanke, ina tunanin zan sauwakewa Salma.” “Ya salam, Mus’ab mai Salma ta sake yi, ina tunanin ka ce mun abubuwa sun yi sauki, nima kuma ina magana da kai ne a matsayin uwa ba matsayin uwat Salma ba.” “Eyh Ummah sun yi sauki,amma Salma ta ki canjawa.” nan ya bata labarin duk maganganun da ta fada masa daren jiya, sanan ya dora da cewa. “Na yi mamakin ganin breakfast yau, Sanam kuma tun ajiyan na ga alamun rashin jin dadin fadin maganar, amma kuma Ummah gsky ta fada.” “Mus’ab, zan doraka a kan wani tsari guda daya, kuma zaki bishi insha Allahu za ka yi nasara, sanan ka yi addu’oin da a ka ba ka?.” Shiru ya yi m, tare da girgixa kai. “Tabbas Ummah ban yi addu’a ko daya ba, a rashin ganin dai-dai a al’amuran Salma har da rashin kai kuka na ga ubangiji, na yi sake da addu’a Ummah, kwata-kwata bana yin addu’a, ba na ta shi cikin dare na kai kuka na ga ubangiji, na fada masa bukatu na na kuma rokeshi ya kawo mun sauki da mafita a cikin al’amurana Ummah.” “To ka gani ko, amma duk da haka ka je ka rubuta takarda kar ka ba ta ka ajiye ma ta.” Legends pen Page 41. “Ummah ban gane ba?”. Mus’ab ya tambayi ummah.”Ka rubuta takarda ka ajiye ma ta, nasan za ta ji tsoron bude takarda, sanan kar ta zama ta saki, ta zamna ka rubuta cewar ta yi hakuri ba zaka iya sakin ta ba, amma zaka je ka nemi wacce za ta so ka, ma’ana dai zaka kara aure, sanan ka fita sabgarta gaba daya, ka hada kaya cikin sati biyu, kabar ma ta gidan. Zan maka matar da zaka aura ku bar gari da ita, wanan shine umarnina kuma duk ka bi su dole.” Dagowa ya yi ya kalli Ummah, sanan ya ce.”Ummah aure kuma?.” “Aure Mus’ab.” ta fada tare da ta shi ta bar shi a wajen. Ta shi ya yi ya nufi gida cike da mamaki, mai Ummah ke nufi?. Ina zaunen na zuba uban ta gumi, gaba duniyar ba ta mun dadi jina ke kamar na rasa wani abu mai muhimmanci a rayuwata, Sallama ya yi na miki da sauri tare sa fadin. “Sannu da zuwa.” bai kalle ni ba bare ya amsa kawai ya shige dakin sa, da mamaki na ke bin bayan shi da kallo. “Ni Mus’ab ke wa haka, laifi na ne ma da na yi mai sannu da zuwa.” Na fada tare da shigewa daki, ina zaune ina faman bacin rai na ji ya shigo, wani sanyi na ji a rai na ina cewa. “Wallahi sai na rama wanan jan ajin da ya yi mun.” “Salma, ga wanan.” na ji muryarshi a cikin kwakwalwa da kwanyata, dago kai na yi na kalleshi na ga abinda yake mikomun, takarda ce wacce tasa gabana ya yi mugun bugawa Durum. “Saki.” na fada a zuciyata, na ce. “innullahi wa’ina illahir rajiun.” na fada ina kai na ƙasa. “Salma ga shi.” “Wai mene?.” “ki karba ki ga duba mana.” “Ajiye a can.” na fada ina kau da kai, ajiyewar ya ya juya ya fi ce. “Na shiga uku ni Salam, Mus’ab zai ja mun tsinuwar iyaye, na shiga uku.” na fada a fili ina zubar da hawaye. “Ai saki sai mace ta gani ko?, to ni bangani ba dan haka ban saku ba, babu inda zani wallahi.” na fada ina rusa ihu, kuka na ci na gode Allah sanan wani wahalallan bacci ya yi gaba da ni, sai bayan la’asar na ta shi, yau ko wankan ban yi ba na yi alwala na ta da sallar azhar da la’asar, ko fito wa ban yi ba sabida ban ma jin yunwa ba bare na je kitchen, ni duk tunani na yana kan tsinuwar Abbanah, Ummanah kuwa kisan gilla ne za ta yi mun. “Mus’ab ya cuceni ni Salma ya gama dani, ya gama da rayuwata.” Abinda na ke ta maimaita wa kenan a cikin a raina, sai bayan magariba na iya shiga kitchen na dora ruwan zafi na sha na dawo daki, na zauna kamar mai yin takaba ko idda. Har wajen karfe goma babu Mus’ab a cikin gida, kuka sosai da sosai nake yi a fili bama a zuci ba, ni ban san me ya dame ni ba, rashin sa ne ko kuma sakin da ya yi mun, ko tsoron tsinuwar Abbanah da dukan Ummanah. “Ni dai Salma na shiga uku na lalace.” na fada a fili cikin Kuka, mai na yiwa mus’ab da zai hade mun komai lokaci guda?, har wajen sha biyu na dare ban ji shi ba, lokacin kuma baccin dole ya dauke ni sabida gajiyar da idanuna suka yi da kuka. Shi ta shi Sallar asuba sabo ne, idan har ka saba to dole sai ka ta shi, hakan ce ta faru da ni domin tin ina gida na sa ba, ga kuma da na yi aure Mus’ab ya sabar da ni, bayan na fito daga ban daki ina kokarin ta da Salla na ji alamun zai fita. “Ya dawo kenan, sai da ya bar ni ko barayi ne za su shigo sai su kashe ni ko?.” na fada a rai na kafin na tayar da Sallan, ina idarwa na fito na shiga kitchen ko zai zo muyi sulhu, nasan ance idan miji ya kwana daya zuwa biyu zuwa uku yana sakkowa daha fushi kila ya janye sakin da ya yi mun. Ina jin shi ya shigo cikin falon yana zagaye, ‘yan mintina kadan bayan na fito na gan shi da jakkun kuna cike da kaya. “Ina zaka?.” na fada ina zuwa inda yake. “Ina ruwanki.” ya ban amsa ba tare da ya kalle ni ba. “Ni kuma ka bar ni aina?.” “Baki duba takarda da na baki ba?.” shiru na yi tsuru-tsuru. “Mus’ab idan na koma gida iyayena tsinemun za su yi, Ummanah kashe ni za ta yi, ka rufan asiri dan Allah.” “Kiyi hakuri Salma na gama yanke hukunci na, kintsane ni, bakya so na, zama da ni babu abinda zai miki, na gama yanke hukunci wanda shine zai fi alheri a gare ni har da ke.” “Yanzu ka yarda iyayena su tsine mun, kayarda?, za ka ji dadi idan ka ga an tsinemun Mus’ab, menene ribarka idan haka ta faru da ni, wane dadi za ka ji?.” Legends pen. Page 42. “Salma nima biyayya na ke, amma tin da haka ne ki zauna a gidan ba sai kin koma gidan Galadima, ni na bar miki gidan halak malak ki yi ta rayuwa a ciki.” Shiru na yi, mai kuma zan ce bayan wanan, ya bar ni na zauna a gidan ni ka dai, to ni ai har shi ina son gani a gidan ba wai gidan kawai ba, ya zan fada masa haka?. Ji na yi yana jan akwatin kayan na sa zai fice.”Yanzu tafiya za ka yi?.” “Tafiya zan yi mana, ai na bar miki gidan ki yi zamanki kinga babu wanda zai tsine miki tin da kina cikin gidan.” shiru na yi har ya fice, ina jin an bude masa gate ya fice na rotsa wani ihu mai karfi. “Na shiga uku na ni salame na lallace, ina zan sa kai na da rayuwata, Mus’ab ya sake ni ya tafi ya bar ni, na shiga uku na, na lalace.” Abinda nake fada kenan cikin ihun na wa, kuka nake babu mai jina babu mai kawo mun dauki sai Allah, “ina zan saka rayuwata a wanan gidan babu miji babu aure?.” haka nai ta kukana bahu mai ji na, har lokuta su ka ja naji anfara kiran sallan azhar, ta shi na yi na shiga daki na kwanta kai na nayimun wani azababen ciwo, mai sa jira da juwa ko ka na kwance, rufe ido na ke ina son bacci ya dauke ni ko zan ji sauki amma ina babu bacci babu mai kamarsa, ina kwancen na ke jin ciwon kan da jiri dakin sai juyawa yake, kuka na fashe da shi amma fa hawaye ya dauke mun, domin nasan yau na karar da hawaye na har na gobe da jibi. Ina cikin wanan halin wani bacci mai cike da wahala ya kwashe ni. Mus’ab kam na fita gidan sa na gwari avenue ya huce, domin Ummanah ta ce masa jar ya nuna kowa ba ya gidan tare da ni, kawai sai dai kowa ya ji maganar aurensa, wanda nan da kwana biyi za ta fito a gidan galadima, ma’ana sa rana da kuma shirye-shirye. Bikin wata biyu za’a daga sa rana ba wani lokaci mai tsayi za’a ja ba, ya bar komai a hannunta shi kuma ya shiga rokon Allah, da kai wa Allah kukan sa a kan lamaruna da wasu abubuwan na shi, ya san da yabar ibada ya yi sakaci wajen kai wa Allah kukansa, ayoyin da Hajja ta ba shi duk ya yi sake da su.”Rabbi inni lima anzalta illaihi min khairil faqeer.” da sauran ayoyin al Qur’ani mai girma, cike da yakinin ubangiji zai duba lamuran sa. Ban ta shi daga wanan wahalalen baccin ba sai karfe biyar na yamma, lokacin ciwon kan ya ragu sai kuma yunwa dake kwazarzabar ciki na, amai nake ji amma ba na koshi ba na yunwa, ban samu sauki ba sai da na fara kwara aman nan, mai yawa na yi shi wani kore shar da shi, sanan na dawo na sa tea da bread a gaba na na fara sha, baki na babu dadi amma haka nake cusawa ko sabida yunwar cikina. Haka rana ta daya ta zo ta huce babu Mus’ab a gidan, na damu na kuma shiga wahala a kwana na biyu, na yi kuka har sai da idona ya fara zafi da yaji, kai na ya fara ciwo. Na yi nadamar kalamai na yi dana sani mai girma, nayi matsananciyar kewar Mus’ab, muryar shi da nake cewa kamar ta gyare, yawan maganar shi da nake cewa yana damu na, kallonsa da yake yawan yi mun nake ce mai kamar maye, nayi matukar kewar su, a rana ta uku na gane cewa da ban yi kuka ba, ban damu ba domin kasan yin komai na yi, idan ka ga ni na rame na yi baki, kasan idanuna sunyi baki sosai kamar na zana kwalli, jikina duk ya fige babu wanan ado da gayun babu wanan kwaliarsa, na rame na fige kamar kazar mayu abincin ma sau daya nake ci a rana shima sai naji uwar azaba nake iya ci. Gidan ya yi kaca-kaca bana iya dauke ko tsinke domin da ciwon kai da jiri da nake yini nake kwana. Haka rana ta hudu ma ta kasance, gaba daya Salma ta rame ta lalace kamar ba Galadima ba, naga rayuwa na yi na dama, na kuma tabbatar da zuciyata ta kamu da ƙaunar Mus’ab ko da karama ce. Ganin gidn na shirin zama bola ya sa na fara gyaran shi, ta kitchen na fara na yi kusan awa guda ko fi a cikin kitchen ina ta faman aiki kamar mara laka ajiki, haka na gama na dawo falo shima na kwashi kusan awa da motsi ina gyara shi, daga nan dakin da nake kwna na gyara akwai kusan ɗaku na biyar da ban ta ɓa shiga ba bare na san mene a ciki, a iya ƙasa kenan bare kuma sama wanda daga ni har shi ba ma rayuwa a ciki, dakin da naga yana shiga na nufa nasan na shi ne, kai tsaye na shiga nasan idan naga wani abu na shi zan rage wanan matsananciyar kewarsa da na ke. Bude dakin na yi cikin sa’a ya bude na tura kai, ƙamshin turaerensa da nake cewa kamar na tumakai ya daki hanci na, sai dai yau jin shi na yi kamar yafi komai na duniya ƙamshi mai dadi, dakin ya na da girma sosai da sosai, ya sha ado da gyara, frames din da na farfasa gaba dayansu an gyara su an manne su a dakin, zama na yi a kan katifar na ji zuciyata na wani iri bugawa da karfi, fiye da yadda nake ji lokacin da nake son Masrur. Legends pen. Page 43 Tabbas idan haka soyayya take a wancan lokacin ban so Masruru ba sai dai ko burgeni yake ko wani abu, amma yadda nake ji Mus’ab har cikin ɓargo da ƙashina ban ji masrur haka ba, hannu na sa na kai wajem frame din hotnan mu mai ni da shi guda daya na ciro, sanan na ciro mai hoton shi guda daya na hada nai waje da su zuwa daƙin na sakale su, ko hoton na shi kadai nake kallo ai zan rage wani abu na kewarsa, amma tabbas ina son ganin Mus’ab, ina son jin muryarsa, ina son jin motsinsa. A ɓangaren Mus’ab kam ya dage sosai da sosai da sallolin dare da yawan na filfilo, ya mai da komai na shiga ubangiji. Yana jin kewata, ya na son ganina ya na son sanin halin da na ke ciki, amma yasan wanan hukunci da ya dauka shine dai-dai, ko bakomai zai gane idan ina son sa ko kuwa ba zan ta ba son sa ba. A cikin gidan Galadima kuwa, rana daya Ummanah ta fito sa zancen auren Mus’ab, Maman ciki na zaune ita da Anty da matar Yaya ilyasu a bangaren Hajja, Ummanah ce ta ce.”Hajja na san ke kin san wanan maganar, amma su sauran ina tunanin ba su sani ba.” “Wace magana ce haka?.” Hajja ta tambaya duk da ta san sun yi magana jiya, Abbanah ya ke ce mata Mus’ab zai kara aure sun je su nema mai aure, ta yi fada sosai ta kuma ce ba zai yi ba, amma bisa wasu dalilai da ya fada mata ta amince. “Zancen auren Mus’ab mana.” da kallo duk suka bi Ummanah, Maman ciki ta ce. “Wane Mus’ab din, kuma wane aure?.” “Yoo nima jiya Yunusa ke sanar da ni, wai sun je nemawa Mus’ab auren yarinyar da ya so kwanakin baya kuma an ba shi, nayi fada kamar na ari baki amma sun ki ji na.” Mikewa tsaye maman ciki ta yi sanam ta ce. “Nifa bangane ba ko kadan, wace yarinya zai aura, Salman fa?.” “Salma ta ki mai da hankali ta yi zaman aure, ku duba sakwan nin auren su yadda kowa ya nutsu, ita Sadiya ma har ta shiga watan haihuwa amma ita fa, ta zauna sai wahalal da bawan Allah ta ke, kun san yadda yake fama da rashin lafiyarsa, ko dan ku baya zuwa ya fada muku.” Ummanah ta fada, tana fito da duk wani ɓacin ran da ke zuciyarta. “Amma gaskiyya baki kyauta ba, Yaya wanan ba dai-dai ba ne, ranan tare da ke fa ya ce sun fita har park sun ne ai a hankali komai zai yi dai-dai.” Anty ta fada cike da fushi.”Ki fa da ma ta dai, to wanam auren gaskiyya ba zai yu ba.” Maman ciki ta fada ranta a bace, ita dai matar Yaya ilyasu ba ta sa baki ba, tun ita ce karama cikinsu. “Ai kwai kuyi hakuri, Salma ta tsaya a matsayin uwar gida, amma kubar shi ya yi wanan auren.” Ummanah ta fada kamar ba ‘yarta za’ayiwa kishiya ba. “Ni kai na bana son auren, kuma nace indai har Salame ta canja kafin wanan lokacin za’ a fasa.” Cewar Hajja. “Ni kawai Hajja a fasa, a karawa Salma lokaci.” “Lokaci fa kika ce, yanzu fa wata tara da auren su kenan.” Ummanah ta fadawa Maman ciki da ta ce a karamun lokaci, shiru dakin ya yi an rasa mai magnar arziki. Cikin kwana daya maganar karin auren Mus’ab ta zagaye ahalin Galadima, kowa ya ji sai ya ce. “Salma ba ta yi ba.” zaton kowa da a ka ji mu shiru kwana biyu na yi hankali, ashe-ashe ba haka ba ne. Ina can ina fama da rayuwa ban sani ba, ban san ta inda zan sani ba, kawai dai na daukar wa kaina masifar shiga dakin Mus’ab Kullum, har kwanciya nake wasu lokutan a kan gadonsa, na yi kuka har na gaji na gode Allah, na fita hayyacina na rame sosai da sosai, damma yanzu ina samu na ci abinci shi yasa na dan rage kan jamewar nan. Zaune naki cikin wani daki mai mugun duhu, kamar haske bai ta ba ratsa shi ba, ganin nan a zaune kamar andaure ni da igiya mai tauri, ina kuma jin azaba a jikina, kamar dai igiyar ta wuta ce ko karfe da ya sha huta ya yi ja a ka daure ni da shi, ciko cikon kwacewa nake amma na kasa ko kadan, wata kara mai firgitarwa ta karade kunnena, ji na yi ana jana kamar tsintsiya ko kayan wanki, dai-dai wani wajen dubu a ka tsaya sai ga wata tsohuwa ta fito daga cikin duhun, idanuwanta jajaye kamar wuta ko garwashi. Cikin wata muryar mara dadin ji kamar ihun gyare, tsohuwar ta ce."Ke ce 'yar da ta ki bin umarnin iyayenta? Ke ce wadda aka haɗa aure, kika tozarta miji, kika hulakanta shi, kika nuna iyayenki ba su da daraja?.” Tuni na ji cikina ya wani yi kuuuuu kamar zan yi kashin wuta, sabida yanda na ji kamar ‘ya’yan hanjina na konewa, kokarin bude baki nake na karyata, amma murya ta ta makale, hannaye na na fara dagawa alamun roko. A take ƙasan wajen ya ɓalle, na fada cikin wani ramin da yafi wanda nake zafi, zafin kamar wuta na tashi daga ƙasan da na ke kai. Sanan ga jikina daure da wanan igiyar mai zafi, sai a lokacin na fara jin zuciyata ta fara magana. “Tabbas Allah ya bani uba, ya bani uwa amma na wulakanta su. Sanan ya ba ni miji, mai so na da kauna ta amma na raina shi, na hana masa soyayya, na ƙuntata masa, na sashi kuka." Kuka na fara mai ban tausayi ina fadin. “Allah Na tuba!, Allah na tuba, Allah ka karbi tuba na, Allah kasa mjina da iyayena su yafe ni.” Ina cikin wanan kukan na ji ƙarar saukar bulala mai zafin gaske a jikina, kuka na fara mai ta ba zuciya, sai naji kukan nawa na zama biyu daga ido na yi na ci karo da Ummanah tana kuka ta na cewa. Legends pen. Page 44. “Salma, ke ce ƙaddara ta, amma me kika yi mun na sakkayya a rayuwa ? Mun miki aure da fatan zaman lafiya, da kuma biyayya a garemu, sai kika mayar da gidanki wuta, kika kuntaci mijinki, kika azabce shi, Salma duk abinda kika gani anan bai kai rabin kwatan azabar da ubangiji ya tana darwa miki da masu irin hilinki, idan har ku ka koma gareshi ba ku tuba ba, miji babban abu ne ba na rainwa ba ko hulakantaw, haka iyaye ma.” Hawaye ne ke zubo daga idanuwa na kamar ruwan sama. Na bude baki ina son na roki Ummanah gafara, amma sai na neme ta na rasa. A daidai wannan lokacin na farka daga baccin da yau dauke ni a dakina bayan na dawo daga dakin Mus’ab, ihu na saki jikina na rawa gumi yajikani sharkaf, zuciya ta kamar za ta faso kirjina ta fito, mikewa nayi ina kuka kamar zan shide. “Ya Allah! Na yi kuskure na yi kuskuren hada kiyayya da aure, auren da kai ka zaba mun, ya Allah ka gafarta mun, Na raina iyaye, na tauye hakkin mijina, ka ba ni damar gyara.” Addu’ar da na shiga yi kenan ina kuka. Ta shi na yi cikin sauri na shiga ban daki, na daura alwala na ta da sallar nafila, bayan na idar na daga hannu sama na fara addu’a. "Ya Allah, Ya Ubangijina, kai ne Mai gafara, kai ne Mai jin ƙai Wallahi na yi kuskure, na yi sakaci da ni’imar da ka bani, na wulakanta iyaye da mijina, wanda bai cancanci hakan ba. Allah ka gafarta min, na gaza, na raina su, na tsaya akan girman kai da ƙyama... amma yanzu na gane. Ya Allah ka wanke ni da hawayen tuba, ka tsarkake zuciyata daga hassada da ƙyama, ka cire wannan ƙiyayyar da ta hana ni ganin alkhairi. ka zaremun wanan Sakatar da ta rufemun ganin Alkhairan Mijina,Ka sake zuciyata kamar yadda kake sake shuke-shuke a lokacin damuna. Ka juyo da ni, ka ba ni damar yin gyara a kan barnar da na yi. Allah ka sa iyayena su yafe min, ka sa mijina ya ji tausayina, ya yafe min, ya nuna soyayya gareni, ka maida wannan auren daga tilas zuwa rahama, daga wulaƙanci zuwa soyayya. Ka bani ƙarfi da hikima da ladabi na zama mace ta gari. Na gaji da yin girman kai, Allah na gaji da rashin biyayya, Wallahi na gaji.” Na fashe da kuka mai ƙarfi daga cancikin kasan zuciyata, na jingina kai na da katakon gadona, zuciya ta na bugu da sauri, ina jin wani haki. Zuciya ta na ƙuna da tsoro da nadama, duk wani abu da na taɓa yi na ke dauka bai komai ba ne, yanzu ya dawo mun da nauyi a zuciyata kamar dutse. "Ya Allah! Idan kana da hukunci a kaina, ka sauya mun ya zama rahama, Idan ni ce jarabawa ga mijina, ka mayar da ni salama gare shi. Ka juyo da ni Allah, kai ne Mai canza zukata, ka zaremun Sakatar ta wa zuciyar.” Na kara rushew da wani kukan kamar zan shide, sabida nauyi da na ji zuciyata ta yi mun, na rusunar da kaina ƙasa, ina ci gaba da roƙon gafara a wajen sarki mai duka. Yan awanin kadan naji wani sanyi ya na shiga zuciyata, naji wata nutsuwa wacce na dade ban ji irnta ba na shiga ta, wanan jire da hajijiyar ya dauke gaba daya, kai na kamar andauke dutsen da a ka doramun, haka zuciyata ma kamar an zare wanan babban karfe da ya tokare mun komai, wasayau haka naji kaina sa zuciyata. Mikewa na yina nufi sip di ta, wanan ledar da ya bani ranar da muka fita na dauka na bude, ga matukar mamakina sai naga wayar kirar iphone 17promax, wayar da ake ya yi a yanzu. “Mus’ab ya cika mutumin arziki, ya cika miji na gari.” Na fada ina murmushi da hawaye, kunnata na yi ta kama bayan na sata a chaji, da akwai layi airtel wanda da alama anyiyyi amfani da shi a ciki, shi ya kamata na fara kira, amma ban da lambar shi, lamabar Ummanah da Abbana ce a kaina kawai sai kuma ta Yaya Asma’u, da sauri na shiga saka lambar nasan ita kadai ce za ta ba ni lambarsa kai tsaye a kan dai Ummanah ko Abbanah, bugu daya ta dauka tare da fadin. “Salamu alaikum.” Amsawa na yi da fadin. “Wa’alaiki Salam, Yaya ni ce.” “Salma.” “Na’am.” Na fada tare da fashew da kuka. “Salma lafiya mai ya faru, mai a ka yi miki?.” Kukan na ci gaba da yi, sai da na yi sosai sanan na ce. “Yaya na tuba na bi Allah, na bi iyayena da mijina, na gane na yi babban laifi nayi kuskuren kin biyayya ga umarnin iyayena, da mijina, Yaya na tuba.” “Alhamdulillah Salma, Alhamdulillah addu’ar mu ba ta fadi kasa banza ba Salma, Allah ya yi miki albarka Salma.” “Amin Yaya.” “Yaya ina son kiran Ummah, ina son kiran Abbah, ina son kiran Yaya Mus’ab, amma ina jin tsoro.” “Salma karki ji tsoron kowa, mussaman Abba babu abinda zai miki, kowa zai ji dadi.” “Turumin da lambarsu har ta Yaya Mus’ab din.” “Shikenan Salma.” ta fada tare da kashe wayar, lambar Abba na danna tun da daman ina da ita a kai na, ina ni ta shiga hannuna ya fara karkarwa. Sai da ta ji ringi sau biyu kafin ya ɗaga. "Assalamu Alaikum." Ya fada da Muryarsa mai sanyi, hawaye ne suka fara gangaro daga idona, baki na na rawa na ce. "Wa’alaikum salam Abba..." Shiru ya biyo baya. Nasan ya gane wace a kan layin, kuka na ci gaba da yi, sai can ya ce. "Salma ke ce?.” jan hanci na yi cike da kuka, na ce. "Ni ce Abba… Ni ce... Abba don Allah… Don Allah ka gafarce ni… na yi kuskure, na sabawa umarninka… na yi abin da bai kamata ba. Na raina shawararka… Na bijirewa zabinka, na kau da kai daga tsoronka..." Sai kuma wani kuka ya ci karfina, cikin kukan na ci gaba da cewa. “Abba na gane kuskurena, Yanzu na fahimta, na fahimci cewa kai ka fi sanin alkhairi a gareni fiye da kai na. Duk da ba ka daɗe da magana ba, zuciyarka ta fi nisan tunani na ka yi hakuri Abba.” “Salma. me ya sa kika yi haka? Me ya sa kika ɗauka zan taɓa maka wani zabi da zai cutar da ke? Ni mahaifinki ne kuma rayuwarki gaba ɗaya amana ce a gareni…" Shiru na yi ina sauraron muryar Abbanah, muryar da ita kan ta kam saukarmin da natsuwa. “Salma na yafe miki, ban ta ba kwana da fushin ki ba, bake ka dai ba duk cikin ‘ya’yana da na ‘yan uwana babu wanda na ta ba kwana da fushin sa, Rayuwa darasi ce, kuma idan kika koyi darasi, to kin gyara gaba. Allah Ya sa ki zama cikin masu tuba da gyara.” Fahsewe na karaye da wani kukan sanan na ce. "Na gode Abba, na gode, Wallahi zan gyara. Zuciyata ba za ta sake bijire maka ba, zan zama 'yar da za ka yi alfahari da ita."* “Ko a hakan ma na yi alfahari da ke Salma, sabida kin yi lafi kuma kin dawo kin tuba, ko ubanginjin mu yana son ba yi masu tuba, Allah yakarbi tuban mu ba ki daya.” “Amin ya Allah Abbanah.” Na fada tare da sauke wayata a kunne. Kallon su Abban ciki da su Mama Abba ya yi, daman lokacin suna bangaren Hajja baki daya, kan maman ciki da dage ba za’ayi wanan auren ba. “To kinga ni, kinga ni, yanzu a yanda kika ji muryar Salma kin san ta yi tuba na gaske.” Shiru Ummanah ta yi wa Mama, zuciyarta fari sol da jin magana ta da kuma neman yafiar da na ke. Legends pen. Page 45. “To yanzu ina son a janye maganar auren nan na Mus’ab.” Hajja ta fada tana kallonsu, murmushi Ummanah ta yi sanan ta ce. “Hajja daman babu wani aure dai zai yi, kawai an yi hakan ne domin a sanya ma ta tsoro kuma da’alamu hakkarmu ta cin mu ruwa.” Dariya kowa ya yi daga haka su ka ci gaba da hira. Har zuwa lokacin da Abbanah ya fita sakamakon kiran da abokinsa ya yi masa. Ji na yi zuciyata na gaya mun na bude wanan takardar a jikina nake jin ba za ta zama ta saki ba, na duba nagani. Ta shi na yi naje inda ya ajiye ta, gaba na na faduwa kirjina na dukan uku-uku na dauka, sai da na zauna kan gado sanan na budeta na ci karo da rubutu kamar haka. “Amincin Allah ya tabbata a gareki ranki ya dade, ina rubuta miki wanan takardar da zuciya mai cike da soyayyarki, da kuma begen ki. Salma ban sake ki ba, kuma ba na jin zan sake ki, zan iya zama dake a duk irin kiyayyar da kika yi mun.” Wani sanyi na ji a raina tare da fadin. “Na daina kin ka, nima zan so ka fiye da yadda kake so na.” na ci gaba da karanta takardar. “Sai dai Salma zan dauki wata hanya mafi sauki a gareni da ke, ita ce Zan kara aure. Salma zan kara aure, zan kuma tafi na barki na zauna tare da amaryata na gode sosai.” Wani ihu na saki tare da yarda takardar, da sauri na lalubu wayata na kira Yaya Asma’u, bugu daya ta dauka tun da ta gani lambar. “Hello Yaya.” Na fada cikin kuka. “Salma ya a ka yi kuma, Abban bai hakura ba?.” “Wai aure Yaya Mus’ab zai kara.” Shiru ta yi kamar ba ta ji na. “Hello Yaya, magana na ke.” Shirun da ta kara yi ne ya bani amsata cikakkiya. “Yaya dan Allah da gaske.” “Salma kin yi wasa da damarki. Kin yi wasa sosai, Mus’ab na sonki kuma ya so ki, amma kin nuna masa zallan kiyayya mai zafi, wanda kalamanki sai da su ka nemi kashe shi, aure zai kara ina ga cikin satinan ne ma bakin,bai fada miki ba?.” Kuka na fara wani sabo mai fitowa daga cancanki kasan zuciyata, na dama da na sani su ka cika ni, Sakata ba ta yi mun rana ba, Sakatar da na zurawa zuciyata ba amfane ni ba. “Ina son Mus’ab, ina kaunar Mus’ab, ina mugun kishin Mus’ab.” Lambar shi da Yaya Asma’u ta turumun na shiga kira, sai dai gaba daya a kashe ba ta shiga, kamar layin na wa ne a ka yi blocking din shi daga kiran, sabida da na kira take faduwa, wani irin zafi na dinga ji a kirjina, kamar zafin wutar garwashi, kuka na fara da ban san lokacin tsayuwarsa ba, kuka ne daya ke ta ba kashin zuciyata. “Na yi wasa da dama ta, na kasance ‘ya mara biyayya, da a ce na zama mai biayyya da duk abun ba zai faru ba, da na samu alheri da ribar biyayya a duniya, kamar yadda su Walida su ka samu.” Kuka na na ci gaba da yi, wazan kira na sa ya kira mun shi, na fadamai na yi na dama na yi da na sani, kuka na ci sosai da sosai, sai da na gaji sanan na nemi Yaya Asma’u da ta turamun lambar Maman ciki, tana turumun na kira lambar, bugu daya a ka dauka naji sasanyar muryar Maman ciki ta na fadin. “Salamu alaikum.” Kuka na fashe dashi ba tare da na iya amsawa ba. “Salma, Salma ke ce?.” “Ni ce Mama.” Na fada cikin kuka. “Salma mai ya faru, dukan ki ya yi.” Cikin kukan na ce. “A’a Mamah, mamah ku yi hakuri dan Allah, na tuba ba zan sake bijire muku ba.” “Salma babu abinda ki ka yi mana, mun ya fe miki.” ”Mama ki ce ya yafemun dan Allah, ko waya na kira shi ba ta shiga, Mama ki ce mai na tuba dan Allah, ina son shi wallahi.” Murmushin jin dadi ta yi, sanan ta makawa Ummanah harara, su Anty su ka yi dariya. “Shikenan Salma, zan ce ya yafe miki shikenan ko?.” “A’a Mamah.” “To menene kuma?.” “Mama ba ya gidan ku san sati biyu kenan.” “Salma ya gudu ne sabida tsoran kar ki mai wani abu.” “Mama babu abinda zan masa wallahi, ina son sa sosai, dan Allah ya yi hakuri.” “Shikenan Salma, ki ta shi ki shirya ki gyara jikin da gidan ga shinan zai so.” “Toh Mama na gode.” Na fada zan kashe wayar. “Kina ji Salma?.” “Ina ji Ummah.” “Duk wani abu da kika san ya ta ba baki kyauta ki yi amfani da shi, ki yi amfani da kayan lefen ku, ya ce dani babu wani abu na shi da kika ta ba amfani da shi.” “Shikenan Mamah zan yi, har girki zan masa.” “Allah ya yi miki albarka.” “Amin.” Na fada tare da sauke wayar a kunne, na san na cancanci hukunci kishiya a gurin Mus’ab, sabida na nuna mummunar tsanar. Yanzu abunda nake fata shine, samun soyyayarsa a karo na biyu. Ta shi na yi na shiga gyara gidan, cikin sauri da nutsuwa na ke kowanne aiki gaba daya gidan, cikin kankanin lokaci na gama gyaran gidan. Shinkafa da miya na dora, bayan na soya doya da kwai, na yi farfesun naman rago, na kuma yi papped chicekn na kaza, na hada masa lafiyayyane drinki, na jere komai kan dining na je na shirya. Wata doguwar rigar abaya mai kyau wacce ba a cikin lefe ya ban ita ba, lokacin biki ya bani da hannunsa, ban ma san ya a ka yi ta zo nan ba, shiri na yo tsaf gwanin ban sha’awa na sha light make up abuna, sai dai ganin awanni babu Mus’ab ya sa jikina ya mutu, ina cikin wanan tunanin ne wayata ta suma ringing dauka na yi tare da sawa a kunne. “Hello Salma fito bakin gate yanzu.” Bangane wanda ya yi magana kamar dai Mus’ab kuma kamar ba shi ba, mayafi na na dauka na fita compound, Abdul ne mijin Walida da mamaki matuka nake kallonshi har naje inda yake. “Lafiya, ina Yaya Mus’ab din.” “Shi ya ba ni umarnin dakko ki, muje zaki gani.” Legends pen. Page 46. Shiga cikin motar na yi hankalina a tashe, ina ta faman tunani ko dai bai hakura ba, ko kuma a gida za’ayimun fada oho, har mu ka shigo cikin unguwarmu, unguwar da na yi natukar kewarta kamar ba zan sake shi ga ba, kowacce na shekara dari banzo ba, taron mutane na gani a kofar gidanmu da yawa, nan da nan na bude baki cike da tsoro na ce. “Abdul mai ya faru?.” Hannu ya sa ya nuna mun Mus’ab bayan ya yi parking sanan ya ce. “Zai miki bayani.” Sauka na yi na nufi inda yake, idanun sa sun yi jazur kamar garwashi, da alama ya yi kuka, inda yake na nufa ina sauri kamar zan ta shi. Hannuna ya kama ya shiga jana zuwa cikin gida, ko ban da hankali na san mutuwa a ka yi a gidan Galadima, duba da irin mutane da kuma kukan da su ke, cikin gida mu ka shiga bangaren Hajja. “Ba dai Hajja ba ce ta mutu na shiga uku ina zan sa rai na da hakkin Hajja.” Ganin Hajja da sauran ‘yan uwana gaba daya a bangaren Hajjan ya sa na ji wani sanyi, cika ni ya yi zai juya. Kallon mutanen dakin nake daya bayan daya, ko zanga wanda babu. “Ummanah! Ummanah.” Na fada a rude, hannuna ya nuna mun dakin Hajja, alamun ta na ciki sosai, juyowa na yi na kalleshi a hanakali na matso inda yake. “Nifsil hayyat.” Na kira shi, juyowa ya yi ya kalleni, ba na iya tantance yanayin da yake. “Mai ya faru?.” Sautin muryar Ummanah na ji bayan ta sauke wata nannautar a zuciya sanan ta ce. “Kar ka ta fi ka bar ni, kar ka ta fi ka bar mu, Alhaji yaranka Salman ka, Asma’unka da su Muhammadu, ka ce za ka rayu da mu, zaka zama bango a garemu, Alhaji idan ka ta fi ina zan sa rai na , ina ‘ya’yanmu za su sa ransu.” Suuuh na ta fi kasa jikake tim, da sauri Mus’ab ya yo kai na tare da rungume ni cikin jikinsa kam, kamar wani zai kwace ni, cikin kuka na ke cewa. “Abbanah ne ya mutu!, Abbanah ya mutu, Abba mai yasa, Abba mai yasa zaka ta fi da huri, Abba mai mu ka yi maka zaka tafi kabarmu da huri, Abba dadin mai zamu ji a duniya idan babu kai, Abba dan Allah ka dawo, Abba kar ka tafi ka barmu, Abba kai ne gatan mu Abba kai ne jagoran mu Abba ba yanzu ba dan Allah, Abba ka yi alfahari da ni ko sau daya.” Matseni Mus’ab ya sake yi a jikinsa yana kuka sosai da sosai, kamar yadda kowa na bangaren Hajjan ke yi. “Salma Abba bai mutu ba fa, Abba zai dawo Abba ba zai ta fi yanzu ba, Abba shine bangon mu gaba daya, Abba shine karfin gidan Galadima, wallahi Abba bai mutu ba.” Muryar Walida na ni da sauri na kwace jikina daga kan mus’ab na yi inda take tare da rungume ta ina kuka, ina fadin. “Walida dan Allah kar Abba ya mutu.” Muryar wani kawun su Abban mu ka ji ya ce. “Za’a shigowa da gawar ku yi Sallama da shi.” Ji na yi kamar ya bugamun guduma a kaina jin ya kira Abbanah da gawa. Amma ban iya magana ba aKa shigo da makara dauke da Abbanah a kwance daure da farin likafani, da sauri na yi wajen da su ka ajiye shi ina kuka ina fadin. “Abba yanzu kai ne ka tafi ka bar ni? Ka tafi ba tare da ka yi mun kallon ƙarshe ba?, kallo a gidan mijina cike da soyayya, Abba har yanzu ina jin sautin muryarka yana kirana da ‘yar aljannata, yanzu fa shiru, shiru Abba ba zan ƙara ji k ce min komai ba?.” Wata Kwalla ta ci ka idona, Mus’ab ya zo ya rungume ni. Kowa na zagaye da Abbanah yana masa addu’a cikin hawaye, Yaya Asma’u dai na dakin Hajja ta suma gaba daya, Sadiya ma ta fa di tun da ta ji ance wai Abba ne ya mutu, Abban ciki ku ance kwantawa ya yi a kasa yana kuka kamara karamin yaro, yanzu ma ana tunanin hawan jini shi ya tashi an kira masa likita, Mus’ab ne ya kara rungume ni, ina kuka na ci gaba da cewa. “Abba, ni ba zan iya ba, ban san rayuwa ba, ban san komai ba, ka yi mini komai. Kai ne jagora na, ka fi zama uwa fiye da uba. Kana tare da ni ko da yaushe. Abba, me ya sa za ka bar ni da huri haka? Me ya sa ba ka jira na dawo na rungume ka, na ce maka na gode ba, na gode da kyauta miji da kabani. Abba Na gode da ka bani rayuwa da tarbiya da soyayya. Dago idanuna na yi na kalleshi kwance cikin likkafanin. “Abba, ka tafi da damuwata, na yi maka laifi, Abba, na fusata ka, Abba ka yi fushi da ni, ji nake kamar har yanzu ban nemi gafarar ka ba Abba. Dan Allah Abba, ka yafe min, Idan ruhinka na jina, idan kana kusa dani, ka gafarce ni, na maka rashin biyayya a wasu lokuta, Ina sonka Abba, har abada, har abada zan riƙe sunanka, zan rike tarbiyar ka da Umarnin ka Abba, Ruhinka ya sami rahamar ubangiji Abba, na yi alkawari zan yi rayuwar da za ka yi alfahari da ita. Zan zama abin alfahari gare ka, domin kai ba kowane uba bane, kai uba ne na gaske…” Legends pen. Page 47 “Mus’ab dauke yarinyar nan.”Yaya iliyasu ya fada muryar shi na rawa, alamun kuka yake yi, kamani Mus’ab ya yi zai dagani, ai kuwa ina mikewa na zube kasa tum. Bayan su Hajja da kowa ya zo ya ci kuka a ka fita da Abbanah zuwa gidan na gaskiyya, kowa na gidan Galadima ya san ya yi baban rashi, kowa da kowa ya san Abba shine karfin gidan Galadima, Abban ciki likita ya duba shi ya tabbatar da cewa hawan jininsa ne ya tashi, sabida mutuwar ta yi matukar ta ba shi, sadiya kuma a wanan faduwar da tayi aka huce da ita asibiti, kuma wanan hucewar ta samu sauka, kyakyawan dan ta namiji, wanda ya zo duniya ranar da Abbanah ya bar duniyar. Dama haka rayuwa take, lokacin da wani ya tafi kokacin wani ke zuwa, lokacin da wani farin ciki lokacin wani ke bakin ciki, Ummanah kam an samu ta yi shiru, amma gaba daya ba ta iya ko da magana, sai zubar hawaye ta ke. Yaya Asma’u ta yi suman har ta gaji ita ma ta dawo kukan. Tun faduwar da na yi ban bude idona ba sai can yamma, ban san a inda nake ba amma nasan ba asibiti ba ne,” Abbanah ya mutu.” Na fada tare da fashewa da kuka, ina cikin kukan ya shigo sai a lokacin na fahimci da kin shi ne na bangaren Hajja, ga hotonsa nan ga kuma wanu hoton nawa, ta shi nake kokarin yi na je na rungumeshi amma rashin kwarin jikina ya hanani ta shi, zama ya yi kusa da ni yana kallo na. “Salma kinga yadda Allah yake hukuncinsa ko?, ya dauke mana Abba lokacin da ba muyi tunani ba.” Kuka na fashe da shi tare da fadin. “Ka yafemun dan Allah, na sani har da hakkin ka ke bibiyata a rayuwa, na yi furucin ko yau babu ran Abbanah ba zan kara zama a gidanka da matsayin matar aure ba, sai ga shi Allah ya dauke shi bayan ya jarabci ni da matsanancin son ka, dan Allah kar ka sake ni.” Tasowa ya yi ya rungume ni tare da fadin. “Tun da ranan Abba ban sake ki ba Salma, sai yanzu bayan amanar ke da ta sake dawowa a hannu, Abba ya kira ni dazu bayan kin kira shi, ya kara bani amanarki Salma.” Kuka na fashe da shi sosai ina rungume a jikinsa. “Sadiya ta sauka, ta samu namiji.” Na ji dadi a rai na nasan ko ba komai sunan Abbanah za’a mayar amma na yi danasin rashin biyayya ga iyaye na, da na yi biyayya da yanzu nima ina lokacin da zan haihu kuma zan mayarda sunan Abbanah, to yanzu ma ina cikin yake bare ya yi wata tara na haihu, idan ma na haihu ban lallai na farko ya kasance namiji ba. Sai dare na fito daga dakin, zuwa lokacin na samu sauki sosai, na shigo cikin yan uwana kowa na jimamin mutuwar Abbanah. Ban sami zama tare da Ummanah ba sai dare, bayan na sha kuka na nemi ya fiyarta. Haka rana daya ta zo ta huce, ya tabbata babu Abbanah a duniyar, rana ta biyu ta sake zuwa ta huce, babu Abbanah, rana ta uku ta huce. Ya zuwa yanzu kowa na gidan Galadima ya yarda babu Abbanah ya tafi, ya amsa kiran mahalincinsa, sai dai mutuwar ta bar mana abubuwa mai girma domin Hajja dai ciwon ta ya ta shi, ta shi mai tsananin na gaske, ya zamana mgana ba ta iyawa, Abban ciki ya daina walwala gaba daya, ko magana ba ya iya wa sosai, Ummanah ma hakan take, kowa na gidan Galadima ya samu sauyi. Haka a ka yi kwana bakwai, yaron wajen Sadiya mayar ma sa da sunan Abbanah, mun ji dadi sosai da sosai, washe gari kowa ya kama shirin tafiya gida, ciki kuwa har da ni Salma matar Mus’ab. Bayan mun yi Sallama da kowa mu ka koma gidanmu, duk da muna cikin jimamin rashin Abba hakan bai hana mun nuna kauna da kulawa ga junanmu ba. Na sake neman yafiyar Mus’ab kuma ya yafemun, sanan ya roki ne alfarmar mayar da wanan abun tarihi, ko da wasa ba ya son sake tayar da maganar cewa a baya na taba kinsa. Mun fara rayuwa cike da soyayya da kulawar juna, Mus’ab ya zama bango na ya zama gata na, ya dauke ni a matsayin amanar da Abbanah ya ba shi, wata biyar da mutuwar Abbanah Allah ya yi wa Hajja rasuwa, wacce tun lokacin da Abbanah ya rasu ba ta sake jin dadi ba, mun yi kukan rashin ta sosai da sosai, tsakanina da yan uwana kowa ya karbe ni hannu biyu kamar wani abu bai ta ba faruwa ba, haka tsakanina sa Ummanah soyayya da kulawa ta ke nuna mun sosai da sosai, ta so komawa gidan su bayan rasuwar Hajja, amma su Abban ciki suka ce. “A’a sam.” Ta dole ta zauna gidan Galadima, ba tare da ta taba rasa komai na bukata ba. Mus’ab ne baban jika na miji a gidan Galadima cikin kankanin lokaci ya maye gurbin Abbanah a gidan Galadima, ya zama shine bango gidan Galadima. Ni kam tun rasuwar Abbanah na canja, daga asalin Salma da kuka sanni, na zama saliha mara yawan magana, mara yawan fada bare hayaniya, babu abinda na sa a gaba sai bautar sa yiwa mahaifiyata biyyaya da mijina, girmama iyaye da yan uwa, har gidan su Walida na je da sadiya mu ka yafe juna, su ka fadamun su ba su ta ba fushi da ni ba, ni ce dai na watsar da zumunci. Watanni kadan da mutuwar Hajja, nasamu haihuwar ‘ya mace wacce a ka saka mata sunan Hajja, muna kiranta da little, soyayyarmu nida Mus’ab ta zama abin kwantace a wajen kowa, domin ko ina ban iya boye son sa, haka shima ba iya yawa, naga amfani da ribar biyayya ga iyaye, kamar yadda shima ya ga amfanni da ribar kai kuka wajen ubangiji. Tammata bi hamdillah. Allah na gode maka da kabani damar kammala wanan labarin na Sakata cikin koshin lafiya, yadda na fara shi da bismillah, na karashi da Alhamdulillah. Kuskuren da ke ciki Allah kayafe mana, gyaran da ke ciki Allah ka bamu ikon amfani da shi. Labarin Sakata; labari ne da kike nuna illar rashin biyayya ga iyayye da kuma ribar biyayaa ga iyayen, da amfani da girman Addu’a. Na gode sosai daga bibiyar ta tun farko har zuwa karshe. Allah yasa mu dace, yayi mana kyakyawan karshe. Legends pen 08129553971/ 08165383931