BK 2 52 Jamila ta fashe da wani irin kuka tana tsuma, ta ce "Na shiga uku, yanzu Aljani ne ya kwanta da ni?" "Eh amma a jikin bil'adama ya shiga, ya yi amfani da ke" ta gaya wa Jamila kai tsaye, ba tare da ta ji nauyin hakan ba. "Na shiga ku, yanzu waye zai aure ni a haka? Ya zan yi. Na lalata rayuwata" Hajiya Sa'a ta riƙo hannun Jamila ta ce "Na sha gaya miki, matsoraci ba ya zama gwani Jamila. Shi fa auren nan ba dole ba ne ba. Idan kina tare da ni duk abin da ki ke so za ki samu a tare da ni. Idan ma auren ki ke so miji sai kin zaɓa, kuma tsaf za a yi miki gyara babu wanda ya isa ya gane an taɓa amfani da ke. Kuma ƙungiya ta bayar da kuɗinki na shekara. Su na gurina zan din ga baki a hankali saboda kar a gane. Ki kwantar da hankalinki, ki ƙwarara jikinki, kar wani abu ya razana ki. Kuɗi kin same su kin gama ki saki jikinki ki mori duniya. Ke ce yarinya mafi ƙanƙanta a cikin ƙungiya. Ni dai ina matuƙar ƙaunar ki ne. 'yar uwakki na so na kawo, amma abu bai yiwu ba, ina tausayawa rayuwar da ku ke yi a gidanku ne. Ki cire duk wata damuwa daga zuciyarku, ki cire tsoro da tausayi baki ɗaya za ki je inda ba ki taɓa zato ba. Jamila ta ɗaga kai ta yi wa Hajiya Sa'a wani irin kallo, da ita kaɗai ta san ma'anarsa. Ta share hawayenta ta ce "To shikenan" Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Yauwwa Daughterna, tashi mu je na gasa ki, ki karya likitan ƙungiya zai shigo ya duba ki" Jamila ta ja jikinta da ƙyar, Hajiya Sa'a ta kama ta suka je banɗaki. **** Yau kwana na huɗu kenan, Sayyid yana cikin wannan yanayin. Babban abin da yake damun Nana rashin cin abinci da kuma salla da ba ya yi, daga bacci sai zaman shiru. Ba ya cewa uffan, sai dai ya yi ta bin ta da kallo. Ta din ga Addu'a Allah ya taimake ta, ko Ummi ba ta zo gurin ta ba, balle ta san halin da suke ciki. Ƙarfe tara na dare ta na zaune a ƙasa inda ta ajiye fulo tana kallonsa a kwance a kan katifar. Ta ɗaga hannayenta kamar za ta yi addu'a, ta karanta suratul mulk, da ayatul kursiyyu, da Suratul falaƙi da Nasi. Ta tofa a hannunta, ta ƙarasa kusa da shi a ɗan tsorace ta shafa masa a fuskar sa. Ta ja da baya tana jira ta ga abin da zai yi, amma ta ga bai yi komai ba. Ta nemi guri ta kwanta tana ta tunani a ranta. A cikin bacci ta ji ana ture ta, ta buɗe ido da sauri, ta ga yana ƙoƙarin kwanciya a gefen ta, duk da yadda gurin ya matse su. "Sayyid" ta kira sunansa. "Na'am" Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta riƙo hannunsa ta ce "Mene ne?" "Na kasa bacci, kin bar ni nikaɗai a kan katifa" Cikin farin ciki da kulawa, ta shafa bayansa ta ce "Gani na yi ka na numfashi da ƙyar, kamar na matse ka shi yasa na saukko nan" "Ma vie" "Na'am Shugabana" "Yunwa nake ji, kamar ban taɓa cin abinci ba" "Bari na yi sauri na dafa maka wani abin, amma zo mu je ka wanke bakin ka, ka ga yanzu tsakiyar dare ne"  Ya yinƙura ya tashi, ta kama shi, yana ta jiri, saboda yunwa ga rashin lafiya, ga kuma mutuwar jiki. Ta kai shi banɗaki, ya wanke bakinsa, ta dawo da shi ya zauna. Ta feraye doya a cikin ɗakin, ta ɗaukko gas ɗin ta, ta ajiye a bakin ƙofa ta ɗora. Ta ɗaukko mafici tana ta yi masa fifita. "Rayuwata" "Sayyid" "Kamar yau ba mu ci abincin safe ba ko?" Nana ta ce "Kwanan ka huɗi fa ka na bacci. Babu abin da zan ce wa Allah sai godiya, da ka farka" ya yi shiru bai kuma cewa komai ba. Ta sauke doyar ta dafa masa shayi, ta ajiye tana jira ya sha iska, ta ba shi da kanta. Amma bai jira ta ba, ya din ga hannu baka hannu ƙwarya. Sai dai hakan ya yi wa Nana daɗi, ganin ya ci Abinci da yawa yau. Ya gama ci, ta dafa ruwa ta kama hannunsa zuwa banɗaki, tamkar jaririn goye ta yi masa wanka. Shi kansa a lokacin ya din ga jin wata lafiyayyiyar iska na shigar sa. Ta saka ya yi alwala, ya fito ya zauna ya fara jero sallolin da ake bin sa. Ta ce "Sayyid kar ka ce sai yi a yanzu duka, sallolin da yawa.ka bari ka din ga ramawa a hankali. Ya jinjina mata kawai kawai, tun yana yi a tsaye ya kasa tsaiwar ya koma yi a zaune. Ta yi shiru tana kallonsa, ta wasu guraren suna da kamanceceniyar halayya ita da shi. Duk yanayin da yake ciki, muddin ba hankalinsa ne ya gushe gaba ɗaya ba, ba ya wasa da salla ko kaɗan. Hakan ya sanya take jin ko a ainihin rayuwarsa haka ya siffantu da kiyaye salla a kan lokaci. Har ƙarfe uku da rabi, dan kansa ya ce "Ba zan iya ƙarasawa ba, numfashina" Ta ce "To ko za ka yi a kwance?" Ya girgiza kai ya ce "Na fi so na yi a zaune, ko a tsaye" Ta ɗage masa labule, ganin yadda yake ta gumi. Ta shimfiɗa masa sallaya a bakin ƙofa, ta jera masa fululluka, ya kwanta.ta zauna a gefen sa tana yi masa fifita. Ta ɗora hannunta a goshinsa tana karanta masa abin da Allah ya sa ta tuna a zuciyarta. Hannunsa ta ji yana saka wa a rigar ta, duk da idonsa a lumshe yake. Murmushi ta yi ta ci gaba da abin da take yi. Jin yana yi mata cakulkuli, ya sanya ta kwanta a jikinsa tana dariya. Shi ma dariyar ya yi. Ya ce "Ki kwanta a kusa da ni" ya yi maganar yana nuna mata kusa da shi. Kafin ta yi magana ta ga an dalle su da fitila. Cikin hanzari ya juya kansa, ya ɓoye fuskarsa a cinyar Nana, gashin sa ya kwanta a kan filon. Nana ta saka hannu ta kare fuskarta. Muryar Barira ta ji ta ce "Yi haƙuri dan Allah, jin motsi ya yi wa na fara jin tsoro, shi ne na fito na duba, ku yi haƙuri. Ta kashe fitilar ta koma ɗaki. "Sayyid ka yi haƙuri, na san ba ka ji daɗi ba, ka yi haƙuri" Ya yi mata shiru, kuma bai ɗago daga kan cinyarta ba. Ta shafa gashin ta ce "Shugabana, ka yi magana mana, ko na ji daɗi, kwana huɗu ka na bacci, ba ka yi mini magana dan Allah kar laifin wani ya shafe ni" Sai kuma ya juyo a hankali, ta ce "Yauwwa Rayuwata" "Kin daina aman?" Ta ji ya tambaye ta babu tsammani. "Eh na daina" "Allah ya sa ki haihu wannan karon " "Amin, kuma Allah ya baka lafiya na haɗa jariraina biyu, babba da ƙarami" Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah, kafin ki haihu, idan na ji sauƙi zan nemi aiki, na kula da ku da kaina" "To Allah ya amince. Amma Sayyid ina kuɗin nan da na gani rannan, a cikin wardrobe ɗin ka? Da na haɗa mana kaya ban gan su ba. Da sai mu ɗauka a yi maka magani, kuma mu canza gida" "Ai Habu ya karɓa, ranar da ya zo na ƙarshe, ya karɓi kuɗin Nigeria da yawa, ya bar mini wasu, ya ce na Nijar ne. Kuma da kin duba kayan nawa sosai, su na ciki" "A'a ni ba na caje maka kaya, idan Allah ya kaimu gobe, sai a lissafa mu gani idan za su isa." Ya ce "To. Kwanta ki yi bacci" ya yi maganar ya ƙara matsa mata. Ta kwanta tana murmushi. "Sayyid, idan har ba a ga su Habu ba, ina ga da ni da kai zamu je Nijar, mu nemi danginka da kanmu" Ya yi shiru bai yi magana ba, ta ɗan taɓa shi ta ji har ya yi bacci. ***** Jamila a dole ta saki ranta, jikinta ta ɗan samu ƙwari, ya daina yi mata wannan mugun ciwon da yake yi mata. Raɗaɗin ma duk babu. Sai dai tana jin ƙasan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banɗaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar. Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta ɗaga. Muryar Abba ta ji ya ce "Ƙanwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?" Wani irin abu mai zafi ya taso mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce "Yaya Abba ba ni da lafiya" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?" Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta. Da ƙyar ya lallaɓa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo. "To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?" "Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ƙoƙarin ta,kar ka yi mata zancen dan Allah" "No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji Ƙanwatax "To shikenan na gode sosai" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta. ***** Yana zaune a cikin mota, yana ƙoƙarin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen ɗin wayar, ya ga baƙuwar lamba. Ya ɗauki wayar ya ɗaga ya saka a kunnensa. "Hello" muryarta ta doki dodon kunnensa. Ɗan waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce "Wa ke magana?" A raunane ta ce "Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode" ta kashe wayar. Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ƙi shiga, ya yi ya yi, amma ta ƙi shiga, sai haƙura ya yi ya ja motar. Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana ɗaga labule, ta hango ya ja motar ya tafi. Video call ɗin Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta ɗaga cikin fara'a tana faɗin "Hajiya Mummy, ya ibada?" "Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini ɓacin rai da damuwa" Cikin rashin fahimta, ta ce "Ni ɗin kuma? Me na yi?" "Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faɗan wai ke ba ki san ƙaddara ba ne? Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa ɗa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura" "Mummy ki na ji na, network ɗin ki mai ƙarfi ne ko?" Ta ce "Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki" "Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga lamarina ya ƙarfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata. Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa." "Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?" "Ki bari dai ki dawo ɗin" "To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daɗin abin da ki ka yi ba sam" Shukura ta lallaɓa ta, ta ajiye wayar. ***** Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banɗaki. Barira ta ce "Nana ki yi haƙuri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne" Nana ta ce "Babu komai" Sajida ta ce "Uban me ki ka haska ki ka gani?" Barira ta kwashe da dariya ta ce "Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani ɗin. Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?" Nana ta ɗaga ta kalle ta. "Tun da ku ka zo dama bamu taɓa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai" Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi ɗakin su. Sajida ta tuntsure da dariya ta ce "Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki" "Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar ɗaki ɗaya ba" Duk abin da suke faɗa a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba. Bayan ta gama wanke banɗaki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya ɗaukko sauran kuɗin nan, ya ajiye a gaban ta. Ta kalle shi ta ce "A ina ka ɓoye ne, ban gan su ba?" Ya yi murmushi ya ce "Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka yawa, Habu ne ya karɓa". Nana ta duba kuɗin, sai tarin kuɗin nijar, na Nigeria ba su dubu ɗari da goma ba. Ta ce "Sayyid, idan ka ɗan ƙara hutawa, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne, za mu koma Asibiti a sake duba ka. Da za su kai da na haɗa da sauran na guri na, a fara yi maka allurar nan ko guda ɗaya ce" "A'a, kin manta yanzu mu zamu din ga sayen Abinci. Idan su ka ƙare ba mu da hanyar samun kuɗi. Kuma da akwai isassun kuɗi, gara mu bar gidan nan, da a yi mini magani" "Ni kaina Sayyid ba na son gidan nan. Mama za ta aiko mini buhun barkono, idan aka kawo, na ga ana ciniki, sai mu ci gaba da sayarwa". Ya jinjina kai ya ce "To, in anjima ki raka ni masallaci" Ta kalle shi ta ce "Da gaske masallaci za ka je?" "Eh, ina son zuwa masallaci. Idan ki ka raka ni, sai ki dawo" Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, Alhamdillah sauƙi yana samuwa. In sha Allah zan kai ka. Bari na ajiye kuɗin nan, idan na raka ka ma, dan Allah zan je gidan Ummi" ya jinjina kai. Har za ta tashi ya riƙo ta, ya cire hijjabin da yake jikinta. Ƙonuwar da take wuyanta ya gani, ya ƙura wa gurin ido sosai sannna ya ce "Mene ne wannan?" Ta ɗan basar ta ce "Ba komai fa, ɗan ƙonewa ne kawai na yi" "Ba ɗa ba ne ba, me ya kai ruwan zafi wuyan ki? Waye ya zuba miki?" "Ba wanda ya zuba mini, sha nake yi ya zube" kawai ya rabu da ita, ba dan ya gamsu da amsar da ta ba shi ba. Ta tattare kuɗin nan, na Nijar ta zuba su a cikin jakar gidan Sarkin Baka. Na Nigeria kuma ta haɗe su, ta saka a cikin kayan ta. Ana kiran salla, ya yi alwala, Nana ta ba shi mayafin rawaninsa, ya yafa a kan sa. Nana ce ta fito tsakar gida. Barira ta gani, tana girki sanye da wata 'yar riga, milik ce amma ta yi baƙi saboda dauɗa, ko brezia babu a jikinta. Ga gashin hammata ya fito zaro-zaro idan ta ɗaga hannunta. Zanin jikinta ma baƙi ƙirin, tamkar an yi matsar man ƙuli da shi, sai annakiya take yi. Nana ta ce "Barira, dan Allah ko za ki gyara, zamu wuce" Barira ta ce "Bismillah ki wuce mana" "A'a ai ni da mijina ne" "Ku wuce ba wani abu ai" Nana ta yi shiru tana jinjina tumasanci da rashin sanin ciwon kai, na mutanen gidan. Babu yadda ta iya, haka ta kammo hannun Sayyid, ya fito ta rufe ɗakin. Ya ja mayafin ya rufe fuskarsa da rawanin, saboda yanzu ba ya iya naɗa shi, saboda numfashinsa. Tun da ya fito Barira take kallon sa, ta na son ganin ainihin fuskarsa, amma ya sunkuyar da kai, kuma ya rufe fuskar sa suka fice. Su na tafe Yana hutawa, saboda haki, a hankali har suka isa masallacin. Ta ce "Za ka jira ni na je gidan Ummin na dawo?" "Zan koma gida da kaina" "Har ka gane hanya?" Ya ce "Eh ki gaishe ta" Nana ta ce "Ai ba daɗewa zan yi ba ma" Ya shiga Masallaci Nana kuma ta tafi gidan Ummi. Su Nana na fita, Barira ta buga banɗakin tsakar gida ta ce "Ke Sajida kashin danƙo ki ke yi ne? Ki na manne a banɗaki yau mijin 'yar rainin hankalin nan dai ya fito. Ashe dole ta ɓoye shi, fari ne tas wannan gashin da na gani, da gaske nasa ne." Sajida ta fito da buta a hannunta ta ce "Kai haba, ban gama ba ne shi yasa ban fito ba, zogala na ci da ƙuli ya ruɗa mini ciki" "Aikuwa kin rasa, ba ki gan shi ba. Sai na ga kamar mata na rako, da na tuna Gali, ga baƙi ga ƙeya" Sajida ta ce "Ba gara Gali ba da nawa mijin? Ke Gali na da tsawo, ni nawa ga gajarta ga muni" "Gaskiya Sajida mijinki akwai muni kam, dogon baki kamar dangin burrai" Sajida ta tsuke fuska ta ce "Ba na son iskanci kuma. Gara shi dai a kan Galin, da ki ka ce ba ya iya tsinana miki komai a shimfiɗa. Kalarsa kalar... Kafin ta ƙarasa Barira ta ƙunduma mata Ashariya, take faɗa ya kaure, suka ci wa junan su mutunci tsaf, suka tona wa kan su Asiri. Suka gaji dan kan su, suka haƙura. **** Nana ta bawa Ummi labarin barkono da za a kawo mata. Ta ce "Amma Ummi sai dai a kawo miki nan, can ɗakinmu babu gurin da zan ajiye a can" "Bakomai a kawo, kuma nan da nan za ki ga an saye shi ba, ai unguwar nan fuskar jama'a ce, idan ka kasa kaya za ka samu alkhairi" Su na tsaka da hira, babu zato babu tsammani sai ga Saleh ya afko cikin gidan. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Nana, bayan da ta gan shi babu tsammani. Duk ya ƙara lalacewa. Turus ya yi yana kallon Nana, cikin mamaki ya ce "Nana, dama kina nan?" "Eh" ta amsa a taƙaice. "Nana da yanzu nine mijinki, amma ki ka guje ni" Ummi ta haɗe rai ta ce "Saleh Nana fa matar aure ce, dan haka babu ruwan ka da ita dan Allah" Saleh ya ce "Dan matar aure ce, kuma shikenan ba za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce wani baroroji aka aura miki ko?" Nana ta haɗe rai ta tashi ta ce "Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama" Ummi ta ce "Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki ba" Nana ta ce "Gaskiya sai kin bar mini, ki zo ɗakina, ki ɗauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ƙaramin kwano za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan" Ummi ta ce "Hajiya Nana, an sake haɗiyar wake kenan, to Allah ya inganta" "Dawa na haɗiya ba wake ba" Tsulum Saleh ya sake cewa "A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi" A ƙufule Ummi ta ce "Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu. Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuɗinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?" Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yauƙi, har da man shanu, Nana sai haɗiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta durƙusa ta ci a gurin. Ummi ta shiga ɗaki, ta ɗaukko wa Nana dambun kifi ta ce "Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na ɗebar miki" Nana ta karɓa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce "Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi na gode sosai" suka yi sallama Nana ta fita. Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta. Ta ƙara saurin da take yi, amma ya cimma ta. "Nana dan Allah ki saurare ni". Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa bayani ba ya fahimta. "Nana ki tsaya ki ji mana" "Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?" Ganin tana ɗaga murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya. Tana zumbuɗa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaɗai ƙwal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta. "Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?" "Ba zan iya shiga nikaɗai ba" Ta miƙa masa hannu ta ce "Taso mu tafi" ya miƙa mata hannunsa. Sai dai tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta. Da suka je gidan, danƙam da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba ɗaya suka yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta riƙe da na Sayyid. Kawai ta ja hannunsa, suka nufi ɗakin su. "Nana kun dawo" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga ɗakinta, saboda kar su wuce ba ta gan su ba. "Eh sannun ku" daga haka ya tura ƙofar ya fara shigewa. Suna shiga ɗakin matan suka saka shewa, ɗaya ta ce "In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne" Nana su na shiga ɗaki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce "Nana ba ki da gaskiya" Gabanta ya faɗi cikin tsoro ta ce "Me na yi?" "Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa da ƙarfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke ɓoye mini ko?" Haɗe rai ta yi ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa. Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce "Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ƙi ya tunkaro rayuwata da ke ba, ki daina fushi" "To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya" ta faɗa a hasale. Ya girgiza kai ya ce "Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba, idan na sani zamu samu saɓani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi. Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba. Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu yana cin abinci. Sayyid na matuƙar son zuwa masallaci salla, amma dole yake haƙura. Saboda da gayya matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana fitowa sai su yi shiru su zura masa ido. Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ƙaunar zaman gidan nan ko kaɗan. Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki. Ummi da kanta, ta je ta ɗauki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba ɗaya saboda Saleh. Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi. Tun Yamma Nana, ke ƙoƙarin shirya duk abin da za su buƙata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri. Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaɓi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai ɗaga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saɓani suka samu, ƙaramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya fara nema ya faɗi. Tana ƙofar ɗakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata maƙwabciyar su kitso. Suke zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a ɗaki. Barira ta kada baki ta ce "Amma ta mayar da mijin nan tasono, ƙarya take yi gantalinta kawai take tafiya. Meye matan auren ba sa yi yanzu?" Sajida ta ce "A'a Barira, ki daina cewa ƙarya ne" "Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai ɗauke mutum ya kai shi wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taɓa yadda ba, iskanci ne kawai da ƙaryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai. Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ƙura wa Barira ido, ko ƙiftawa ba ta yi. Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma ta ɗan tsorata ta ce "Nana lafiya kuwa?" Ayshercool 08081012143 53 "Barira, kin taɓa haihuwa?" Nana ta tambaye ta. "A'a me ki ka gani?" "Amma dai ki na ganin mata su na ɗaukar ciki su haihu. Kuma kin yarda da abin da suke faɗa cewar haihuwa akwai wahala, duk da ba a bakin mutum ɗaya ko biyu ki ka ji ba. Kin yarda wannan ciwon na haihuwa akwai shi, duk da ba ki taɓa yi ba?" Barira ta ce "Eh mana, ai wannan kowa ya san haihuwa akwai wahala" "Kin yadda akwai ciwon haihuwa, amma ba ki yadda akwai na aljanu ba, saboda Allah bai jarabce ki ba, har ki ke ƙarar da cewa matar mutane yawon iskanci take tafiya? Duk wanda zai shaide ta, barin mijinta ne, tun da yake zaune da matarsa a haka, ke mene ne naki da za ki ce mutuniyar banza ce? Idan aka rutsa ki shaidar ina take tafiya iskancin za ki faɗa? Idan aka faɗi abu, ko baki yarda ba gara ki yi shiru ki ce Allah ya kyauta, musamman larura. Idan ba haka ba maganganu irin naki za su iya zama cutarwa a gare su". Jin Nana yau ta saka musu baki a magana ya sanya suka din ga goyon bayan abin da Nana ta faɗa gaskiya ne. Da fari jikin Barira ya yi sanyi, daga baya ganin kowa ya hayayyaƙo mata, ya sanya ta hau bala'i, har abin ya koma faɗa. Ita kuwa Nana tun da ta gama zazzagar abin da yake ranta, ta kammala girkinta, ta kwashe kayanta, ta koma ɗaki ta bar su da mayar da zance. Dama ga zafin laulayi, ga takaicin mutanen da ake tarawa a gidan babu dalili, ga kuma zafin ƙazafin da Barira ta yi wa matar, da ita kanta Nana ba ta sani ba, amma maganar da ta yi ta ji sanyi a ranta. Yana daga kwance a kan katifa ya ce "Rayuwata" Ta ɗaga kai ta kalle shi ya ce "viens(zo) yana yi mata alama da hannunsa. Ta ƙarasa gabansa ta zauna. "Dan Allah ki daina shiga maganar mutanen nan, ki daina kula su. Ni na daɗe ban ji mutanen da ba na ƙauna kamar su ba. Ba na son su zo su yi miki abin da ba zamu ji daɗi ba" Ta jinjina kai ta ce "Haka ne, ka yi haƙuri nima ban so na shiga ba, haka kurum na ji maganar ta su kamar da ni suke yi. Sayyid ni da kai mun san azaba da raɗaɗin larurar nan. Ire-iren waɗannan maganannun da yadda wasu suke ganin kamar ciwon nan ƙarya ne, ya sanya da yawa masu larurar da dama a cikin wata damuwar ciwon ya yi musu illa, tun da ba a yarda da ciwon ba balle a ɗaukar musu mataki." "To ai ba su ce da ke suke ba" Murya a sanyaye ta ce "Sayyid, duk lokacin da aka yi maganar irin wannan larurar, ina jin tamkar da ni ake. Nima wasu lokutan na kan shiga ɗimuwa, na bar gida a gano ni a wani gurin, duk da ni ban taɓa kwanaki ba a ganni ba. Ta kai ta kawo har a zahiri ina ganin abubuwan nan. Sayyid kai ma fa wasu lokutan ina yi a gabanka ka na gani, to yaya za a ce mutum yana sane ya din ga mayar da kansa mahaukaci? Wanda kuwa duk aka samu da yin ƙaryar irin wannan ciwon, yana buƙatar kai shi gurin likitocin ƙwaƙwalwa, Sayyid ciwon nan babu daɗi, akwai wahala" ta yi maganar hawaye na zirarowa daga cikin idanunta. Ya tashi zaune ya kai hannunsa jikinta zai rungumota, zafin zazzaɓin jikinta ya ziyarce shi. Ya kalle ta a tsorace ya ce "Ba ki da lafiya?" Ya furta maganar haɗe da haki, saboda yadda ya ji zafin a bazata. Da sauri ta ɗora hannunta a ƙirjinsa ta ce "Sayyid dan Allah ka din ga ɗaukar al'amurana da sauƙi. Ga shi har girki na yi, ina komai nawa lafiya. Ka san lallaɓawa muke yi, ba ka da cikakkiyar lafiya. Ka daina saurin tsorata ko fusata. Ya saka hannun sa yana ƙara danne hannunta a saitin zuciyarsa. Yana iya ƙoƙarin sa a kan ya din ga saita al'amuransa. Amma ya rasa dalili duk abin da ya shafi Nana, kai tsaye yake jin sa a tsakiyar zuciyarsa. Ba ya iya yi masa shinge ko ya dakatar da shi. Yana so Nana ta haihu da shi, amma wahalar da ya ga tana sha, sai da ya ji dama cikin ya zube ko zata huta. ***** Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya faru da ita. Mama kuwa baki ya ƙi rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince. Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buɗe ido, ta sake ganinta, a wannan gurin da suka je da Hajiya Sa'a. "Jamila" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta. "Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?" Gaban Jamila ya faɗi ta ce "Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?" "To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai" "Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ƙalau nake " Suwaiba ta ce "To ai shikenan" **** Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha ɗaya, a gurin ganin likita. Wajen sha ɗaya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna. Ya karɓa ya duba a tsanake, ya duba Bp ɗin Sayyid, ya duba ƙirjinsa da stethoscope. Nana ta ce "Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?" Bai kalli Nana ba ya ce "Me yasa ba ku dawo follow up ba" Ta ce "Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo ɗin. mu na ta ƙoƙarin kuɗin allurar su haɗu ne, ko ba su haɗu ba, zamu yi ƙoƙari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi booking a fara yi masa" Likitan ya ce "Ki na ji na 'ya ta?" Ta ce "Eh" "Ai mijinki ne ko?" Sayyid ya jinjina kai. "To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuɗin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sauƙi sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da ɓacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ƙwarewa a kan aiki a cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief. Ya rubuta musu lambarsa ya ce "Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya din ga ganina." Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa. Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya miƙa wa likitan. Likitan ya karɓa ya duba. Ya yi murmushi ya ce "Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke" Nana ta yi murmushi ta ce "Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi ɗin dai" "A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa" Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ƙi tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen. Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata magungunan da za ta yi amfani da su. Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa riƙe murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce "Saura kwana nawa ki haihu?" Ta kwashe da dariya, ta ce "Ina na sani, ko cika wata ɗaya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya bar mana, ya bamu ɗa na gari" Ya amsa da "Amin." A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su. Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banɗaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa ya yi, yai shiru yana ƙare wa ɗakin kallo. Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta ɗauki cylinder gas, ta ce "Sayyid gas ya kusa ƙarewa, idan zaka iya fita in anjima sai mu je titi tare mu ɗuro" Ya ce "To" "Bari na sake ɗumama miyar" Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce "Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Shaidar me?" "Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faɗa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da muka je bayar da shaida. Wataƙila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida." Nana ta numfasa ta ce "Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai ɓullewa ba" Sajida ta ce "Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma" "Allah ya kyauta" Har Nana ta yi haɗin salak ɗin ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad ɗin nan, na rufe sauran anjima zan sake ci" "Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?" Ta ɗan waro ido ta ce "Dama ka gani?" "Eh ina kallon ki" Ta ɗan yi murmushi ta ce "Idan babu yajin, ba zai yi daɗi sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?" "Ba sauƙi" "Subhanallah, ba sauƙi kuma?" Ya ce "Eh, kin je ki na hira da likita a gabana" "Amma ko ba komai, ya kwantar mini da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ƙwarin gwiwar da yakamata na samu" ta yi maganar ƙwalla na cika mata idanu. Ya girgiza mata kai ya ce "Kar ki bari su zubo". "To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?" Murmushin sa mai matuƙar ƙayatarwa ya yi, ya ce "Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda tawa ce nikaɗai. sourire (smile) ki yi murmushi mana" ta noƙe kafaɗarta tana tura baki,ta juya masa baya. Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da kansa a kan kafaɗarta. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa ilahirin jikinsa. Ta maze cikin yaƙe ta ce "Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?" Ya girgiza kai ya ce "Babu komai" "A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka, haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid" Ya ɗan sake yin guntun murmushi ya ce "Damuwa ai akwai ta, ba na son ɗaga miki hankali ne kawai. Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da ɗawainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai ɗauke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai". Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta riƙo hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur. "Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama haƙƙina, na san ba a banza Allah ya haɗa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sauƙi. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa. Kafaɗarta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha, duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi. Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan ɗumi banɗaki ya yi alwala. "Za ka je masallaci ne?" "A'a a nan zan yi" "To yi sallar. Nima sai na yi muje mu ɗuro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti, na din ga haɗawa da shi" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla. Yana kallon ta ta idar, ta buɗe jakarta ta ɗebo sauran kuɗin da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta haɗa su da waɗancan kuɗin. Kawai ta ga kayan wardrobe ɗin a hargitse. Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taɓa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe ɗin ba. Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuɗin nijar a ciki. Ta laluba ta ɗauki ledar, da kuɗin Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe ɗin gaba ɗaya, tana ƙara haskawa da fitilar wayarta. Yana tsaye yana kallon ta. Muryarta na rawa ta ce "Sayyid" Ya kalle ta. "Kuɗinmu, kuɗin da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka ɗauka?" Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya riƙe ta. Jikinta yana tsuma take ƙoƙarin fizgewa amma ya riƙe ta yana girgiza kai ya ce "Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buɗe ɗakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe ɗakin kawai." "Sayyid ba a yi mana adalci ba. Kuɗin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba ɗaya wace irin masifa ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?" Ya riƙe ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina ɗaga murya, akwai Allah" Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raɗaɗin satar da aka yi musu. Ba iya kuɗi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na ɗakin an ɗauka, ya san kuma hakan sabon ƙalubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuɗi a yanzu. Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana ɗaukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata shocking. Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ƙafafuwanta su na lanƙwashewa, goshinta kuma yana tsatstsafo da gumi. Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ƙurzunu-ƙuruzunu, tamkar dutse. Gurin baƙi ƙirin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki ɗaya. Ta ɗaga kanta ta ga ba ta iya gano ƙarshen ɗakin. Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga Ƙaisar a zaune lulluɓe da wani abu mai haske sosai. "Ƙaisar. Ba ka da lafiya?" Ta yi maganar tana nufar inda yake. Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa "Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba ɗaya" ya yi murmushi ya ce "Mu na rashin lafiya mana, guba na ci" Ta waro ido ta ce "Guba kuma? Me yasa?" "Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani." "Kuma ka sha? Wai meye alaƙar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?" "Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai" "Fushi da ɓacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai, saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library ɗi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama. Duk ba wannan ba, duba can." Ta ɗaga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library ɗin Ƙaisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance. Tsohon nan ya ɗaɗɗaure shi da wata irin igiyar ƙarfe. Ƙasan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ƙasa. Nana ta zabura a rikice, ta ce "Wannan ai Sayyid ne" "Ƙwarai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai abu ɗaya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan" Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ya ce "Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaɗin. Kalli" ya yi maganar yana sake nuna mata gurin. Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ƙuri da ido ta ce "Kamar na san wannan" "Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma albishir da nake yi miki, da ƙanwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ƙungiyar asiri. Ɗayar kuma wannan bararojin da ta taɓa baki magani, ta aura mata ɗanta, wanda yake baƙin aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taƙaice miki ma, a kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba ɗaya. Shikenan bissalam" "Ƙaisar" sai kuma ta yi ido huɗu da Sayyid. "Kin tashi?" Ta yinƙura ta tashi zaune, tana kallon ɗakin. Sayyid ya ce "Ƙaisar ɗin ba shi da lafiya ne?" Ya yi maganar yana tsare ta ido. "Wane Ƙaisar ɗin?" "Tambayata ki ke yi?" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ƙasa, sai kuma abin da ya faru ya faɗo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe ɗin, tana zazzage kayan tana kuka. "Kuɗin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a gaba tana kallo. Ya yi mata shiru ya ƙi kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faɗa za su yi. Cikin ƙanƙanin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi. Barira na kwance a ɗakinta, ta yi ɗaiɗai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ƙafafuwanta. Har ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce "Gali meye haka, za ka din ga karta mini faratanka, ina cikin bacci ne?" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ƙeyarsa a can ƙarshen gado, yana bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya. Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari. Bayan ta fito daga banɗakin, kanta ko ɗan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo. Ta haska Nana ta ce "Nana lafiya kuwa?" Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiɗe ta zama wata irin ƙatuwar mage, baƙa ƙirin, girman ta ya yi na tunkiya ƙosashiya da ita, ta yo kanta tana buɗe haƙora. Da gudu Barira ta shiga ɗakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali. "Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?" Ba ta ce masa uffan ba, ta duƙunƙune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ƙyar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta. Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haɗa kai da gwiwa. Ya yinƙura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya ɗauke ta. Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan. Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu. Kwanki biyu da sace kuɗin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuɗin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. Kuɗin Nijar ɗin kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin ɗin nan, ba tare da ta rushe gaba ɗaya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata ɗaya dubu goma sha biyu take sayen su. Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi haƙuri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin. Kwana biyar da kwashe kuɗin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haɗo mata da su, take ta cancana musu. Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daɗi, yana ta numfarfashi. Abin Duniya ya ƙara damunta, ya kuma ƙi cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari. "Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ƙarfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ƙarfin mutum". Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?" Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri" "Ni fa ba na son kurman baƙi, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan" "Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah" Bai fi mintuna biyar ba, wani irin hayaƙi, mai azabar yaji, ya turnuƙe gidan. Nana da take lafiya ƙalau ma, ta fara tari. Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai ɗauke, ta ɗaukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi, da nufin ta je ta ga me ake ƙonawa yake wannan uban hayaƙin haka. Amma ya riƙe hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da hayaƙi. "Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?" "Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke" Barira ta ce "Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba, da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu. Washegari ma, azabar hayaƙin nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai ɗauke saboda azaba. Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da wuta ta afka hayaƙin nan. A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki. Nana ta ce "Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a ɗaki. Yana da matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa" Ta kalli Nana ta ce "Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba" Nana ta ce "Kamar yaya kenan?" "Kamar yadda ki ka ji" "Ni dai koma mene ne, ki yi haƙuri idan ba ki yadda ba, zo mu je ɗakin ki ga halin da yake ciki" "Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ƙarfin duk wani maye wallahi" Nana ta ce "Barira mu ne mayun da ki ke faɗa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk dauɗa?" "Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji zaƙin kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci ubansa, miyagun banza kawai" "Mu ne mayun Barira?" "Eh ku ne, ko na ce ke" Nana ta ƙarasa daf da Barira ta damƙi tsintsiyar hannun Barira ta ce "Ki ka ce ni mayya ce?" Barira ta yinƙura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faɗi ƙasa. Ayshercool 08081012143 54 Ihu Sajida ta saka, tare da sauran matan da suke zaune, tamkar ana bajekolin kasuwar ƙauye, suka dare ganin daga riƙe hannun Barira da Nana ta yi, ta faɗi ƙasa. Faɗuwar da ba su da tabbacin, tana raye ko mutuwa ta yi. Wasu suka yi waje da gudu su na ihu, tamkar garken tumakin da ba su san inda suka dosa ba. Nana kuwa idanunta a rufe, ta nufi ɗakin su tana tangaɗi, Sayyid kuwa da ƙyar ya lallaɓa ya tashi yana ƙoƙarin fitowa, amma mai afkuwa ta riga ta afku. Nana na shiga ɗakin ta faɗa jikinsa, ya taro ta. Gaba ɗaya jikinta ya saki kuma ya yi sanyi ƙalau, shaidar Ƙaisar ya buge ta. Ya ɗauki wayarta, ya tura wa Ummi saƙo. Tuni aka kira mijin Barira, jikinsa na rawa ya shigo gidan, tare da rakiyar wasu mazan. Ya durƙusa a kan Barira ya taɓa ta, ya ɗago ta, sai dai ya ga tana numfashi, sai dai idanunta a kakkafe, ya girgiza ta yana kiran sunanta "Barira. Barira ki buɗe idonki. Ki na ji na?" Barira ba ta motsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Sai dai numfashinta yana fita normal. Mijinta ya ce "Dan a samo adaidaita sahu mu tafi Asibiti" Ɗaya daga matan da abin ya faru a gaban su ta ce "Wane Asibiti, ai ko an je Asibiti babu abin da za a gani, Nanan za a janyo daga ɗakin, a yi wa dukan tsiya a sanya ta tsallaka ta, shi ne za ta tashi, kama mata kurwa ta yi" Ɗaya daga mazan ya ce "A'a ba za a dake ta ba, a kai ta dai gurin hukuma, a san abin yi." Mijin Barira ya ce "Wane irin kar a dake ta, kana kallon halin da matata take ciki" Ya miƙe ya nufi ƙofar ɗakin su Nana, cikin ɗaga murya ya ce "Kina ina, ki fito ki tsallake mini mata, ki sakar mata kurwa" Sai dai ya ji shiru, babu wanda ya yi magana. "Ki fito ko na shigo wallahi" Wani ya ce "Kar a yi haka Gali, ka ga matar aure ce, bai kamata a bi abin da mata suka faɗa ba, kamata ya yi a zurfafa bincike tukuna, kar a ɗauki doka a hannu, a zo daga baya a ji kunya" Gali ya ce "Malam ni dai ba zan ji kunya ba da yardar Allah, kalli halin da yarinyar nan fa take ciki. Idan ta mutu fa? Wallahi ba zan yarda ba" A fusace maƙwabcin na su ya ce "To a je Asibiti mana a duba, sai haƙilo ka ke yi, matarka matarka. Kamar ba nan ka ke jibgarta, ake ƙwatar ta da ƙyar ba, sai da aka haɗa ka hukuma ka daina, auren da ko shekara biyu bai yi ba, a lokacin ba ka yi tunanin ta mutun ba sai yanzu?" A fusace Gali ya ce "Kar ka gaya mini maganar banza mana, ina ruwan ka da dukan da nake yi mata, dama munafunci ne ya sanya ku ke yi mana sulhun?" Ummi ce ta yi sallama, Sajida ta yi caraf ta ce "Yauwwa ga yayarta, ita ce dama ta kawo ta gidan nan" Cikin mamaki Ummi ke bin dandazon jama'ar da kallo. Ta ce "Wai lafiya me ya faru?" Mijin Barira ya ce "Mene ma bai faru ba, kin kawo mana mayya ta kama mini kurwar mata. Dan haka sai ki shiga ki fito da ita ta tsallaka ta" Tuni idon Ummi ya cika da hawaye, saboda ba ta ƙaunar tashin hankali ta ce "Wallahi mu ba mayu ba ne ba. Nana ƙanwata ce, akwai dai abin da ya faru amma ba wai Nana ta kama kurwar wani ba" "To ƙarya aka yi mata? Ba ga Bariran can a kwance ba, ta tashi mana". Cikin tashin hankali Ummi ta ce "Wallahi kaf zuriyarmu babu mayu, Nanan ma matsalar mutanen ɓoye ne da ita, amma ba maita ba, bari na duba ta" Ta nufi ɗakin da su Nana suke. Tuni gidan ya sake ɗinkewa da mutane, ya cika fal wasu suna a fito da Nana, a zane ta a saka ta tsallake Barira. A zaune ta tarar da Sayyid, rungume da Nana a jikinsa. Cikin damuwa da tashin Ummi ta ce "Wai me ya faru ne?" Ya yi shiru yana kallon Ummi, sannan ya mayar da idonsa kan Nana. Ta ɗauki wayarta ta kira Baba. Tana jin ya ɗaga ta fashe da kuka. Baba ya ce "Ke meye haka lafiya?" "Baba babu lafiya, dan Allah ka zo gidan Nana, akwai matsala ne" "Gidan Nana kuma? Ina ne gidan Nanan, kuma matsalar mene?" "Baba mutanen unguwa sun taru, za su dake ta, kar su kashe ta ni ban ya zan yi ba" A sukwane Baba ya miƙe ya ce "Ƙarya ne. Nanan za su kashe mini, ai zan yarda kowa zai iya ɗaukko magana a cikin ku, amma ban da Nana. A can gidan gadin nata ne za su dake ta?" "Baba wane gidan gadi kuma, ai sun bar gidan tana nan kusa da ni, ka manta ne? Ka cewa Nasiru ya rako ka ya san gidan" "Gani nan zuwa" ya kashe wayar ya yi waje da sauri. Ummi ta tsaya a bakin ƙofar, tana ta ba su haƙuri. Amma sai nema suke yi su ture ta, su shiga ɗakin. "To ban da wulaƙanci ma, ta shige ɗaki taƙi fitowa, da yake ba ta da gaskiya. Maimakon mijinta ya fito ya bayar da haƙuri, shi ma ya yi zamansa saboda rashin tsoron Allah, da rashin gaskiya" Ummi ta ce "Mijinta ba shi da cikakkiyar lafiya, ita ma aljanu sun buge ta, dan Allah ku yi haƙuri" Sai dai abin ya fi ƙarfin Ummi, ƙoƙarin hankaɗe ta kawai suke yi, su cimma Nana. Ana haka sai ga maƙwabcin su Nana, tare da jami'an tsaro. A dole mutanen suka saurara. 'yan sanda suka ce, a tafi da Barira Asibiti, abin da likitoci suka ce, da shi za a yi amfani. Ana haka Baba ya ƙaraso, cikin tashin hankali. Ummi na ganin sa ta yi ajiyar zuciya. Ummi ta ce "Baba ka zo?" "Eh, ina Nanan take, kuma uban me ta yi za a dake ta da?" "Ai gama 'yan sanda sun zo, saɓani suka samu da wanda suke zaune gida ɗaya, shi ne suka ce mayya ce" Baba ya ce "Maita kuma? In ji uban wa?" Mijin Barira ya ce "Ga shaida Baba, kalli matata a baje a kwance" "Kuma sai ka ce 'yata mayya ce? To wallahi ƙarya ne, kaf danginmu babu mayu, ku dai nemo wani abun, ba maita ba wallahi" 'Yan sanda suka shiga maganar, aka tafi da Barira Asibiti. Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su, su na ta ƙara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba ɗaya zancen ya zagaya unguwa. Har sha ɗayan dare case bai ƙare ba, Nana ta farfaɗo ta ga Ummi a ɗakin su, ga duhun dare ya fara yi. "Ummi lafiya kuwa?" "Ina fa lafiya Nana, meya haɗa ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce". "Mayya kuma?" "Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faɗi sakamakon binciken su." Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan matsalar ta. Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi. Sajida ta haɗa kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba. Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken ƙwaƙwaf da suka yi, suka gano ta yi ɓari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaɓi na typhoid amma suka alaƙanta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faɗuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon ƙarya ne kawai aka gaya musu. Ga Barira ta farfaɗo, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana mayya ce. Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba ɗaya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa. Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuɗin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ƙara rikicewa. Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun ƙi dawowa gidan wai tsoro suke ji. Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga ɗakin. Hannunta riƙe kular Abinci. Ta kalli inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce "Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?" "Wallahi Ummi, gaba ɗaya hankalina a tashe yake" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata" Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce "Me ya faru?" Cike da karaya, da matsanancin tausayin ƙanwarta ta ce "Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuɗin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuɗinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ƙara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya ƙi wai wannan ɗin ma da ƙyar ya samo su ya kawo." Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" "Nana mene ne abin yi yanzu?" Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce "Ban sani ba Ummi" "To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na roƙi alfarmarsa?" Ta girgiza kai ta ce "A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan" "Bari na kira Baba na ji me zai ce" Nana ta ce "A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya ɓaci" "To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce" Ummi ta kira lambar Baba, yana ɗaga wayar muryarsa a sama ya ce "Ya kuma aka yi, ba an kashe case ɗin a gurin 'yan sanda ba?" Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce "Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi" "To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu wani?" "Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce ƙarama pressure ta yi mata yawa." "To Ummi ya ki ke so na yi? Ni dai nan gidan babu gurin da zan ajiye ta, ita da mijin nata, idan kuma ke ki na da guri ki taimaka ki ba su. Idan ba haka ba ta nemo 'yan uwansa su ɗauke shi, su rakata inda danginsa suke. Kin san dai nan gidan idan ta dawo, abin da za ta ci ma aiki ne. Nima yanzu sai abun da aka samo aka bani" Hawaye ya cika idon Ummi, cike da takaicin yadda Baba bai fiye damuwa da damuwarsu ba. Ta ce "Baba da ina da inda zan ajiye Nana da mijinta, wallahi ba zan kira ka ba" Nana ta ce "Ummi, dan Allah ki katse kiran nan, nima ba zan koma can gidan ba." Tarin Sayyid ta ji, ta mayar da hankalinta kan sa, ta nufe shi tana faɗin "Sannu Sayyid" "Ki ba ni ruwa" ta amsa da to. Ta ɗaukko ruwan leda, ta buɗe masa ya tashi zaune ta fara bashi. "Sannu Sayyid" Ummi ta faɗa cikin tausayawa, kallo ɗaya ta yi masa ta gane yana jin jiki. Da da ne, kome za a yi,ba zai bar gashin nan a buɗe ba. Amma yanzu ba ta gashin yake yi ba, ga fuskarsa duk ta kumbura. A zuciya irin ta Nana, ta san ko a titi ta tsince shi a wannan yanayin, ba za ta iya tafiya ta rabu da shi ba, balle mijinta. Ƙarar da wayarta ta yi ne, ya sanya ta dawo hayyacinta. Ta ɗaga wayar tare da yin sallama. "Ke Hansai, ina ta kiran wayar ki, amma ki ka ƙi ɗagawa?" Ummi ta ce "Eyya, ba haka ba ne Uwani,ba na kusa ne, ya gida ya mutanen garin?" "Lafiya ƙalau, ya na ji muryar ki ƙasa-ƙasa, laulayi ko rashin lafiya" Ummi ta yi yaƙe ta ce "Ba gara a ce laulayi nake ina kwance ba, da abin da yake faruwa" "Subhanallah, meyafaru?" Kasancewar Uwani kaka ce a gurin su Nana, ƙanwar kakarsu ce, da kakarsu wadda Nana ta ci sunanta da Uwani, uwa ɗaya uba ɗaya suke. Sai dai ita tana can Garko da iyalinta. Ummi ba ta ɓoye mata komai ba, ta gaya mata. Uwani ta rafka salati. Ta ce "Sai an yi magana ku nuna ku mutanen birni, kun fi mutanen karkara wayewa. Ina wayewar take. Aikuwa sai na kira Isa na ci ubansa mara mutunci. Tuntuni nake ganin take-takensa kamar har da ƙiyayyar uwar su, take shafar su a gurinsa. Ai Imrana yana zuwar mini nan. Ya hana kowa riƙe su kuma shi yana yi musu riƙon sakainar kashi. Yanzu ina duk sauran 'yan uwanki Ummi, ina 'ya'yan Atine, ina su Gaddafi da ba za ku iya taruwa ku rufa wa 'yar uwakku asiri ba?" AREWABOOKS "Wallahi Uwani mun yi iya yinmu ne.." "Rufe mini baki, ina wani iya yinku, kuma duk wanda ya ce mana mayu Allah ya isa bamu yafe ba. Mu bamu gaji maita ba, balle a saka yarinya a gaba a tsangwame ta. Na san babu lallai ta iya zaman ƙauye, amma mu nan akwai ɗakuna, har ma da gida da babu kowa, idan za su iya zama ta yi jinyarsa. Babu mai damun ta, kuma babu mai cewa ta tashi. Amma tabbas kun ji kunya, idan har ku ka bari Asma'u ta wulaƙanta, a ce an rasa inda za ta zauna, ta yi jinyar mijinta, yawan ku kun zama taron tsintsiya babu shara." Ummi ta yi shiru, Uwani akwai kirki da karamci, amma idan ta botsare tana faɗa, to duk gaskiyar ka, sai dai ka yi haƙuri. Ta gama faɗan ta, Ummi ta kashe wayar. Ta kalli Nana, ta ga yadda ta tattara hankalinta a kan mijinta, tana ba shi Abincin da ta kawo musu, sai lallaɓa shi take, da alamu abincin ma ba ya so. "Nana, kin ji abin da Uwani ta ce?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a. "Cewa ta yi idan za ki iya zama, ku tafi can Buda ki kula da shi, akwai inda za ku zauna. Kin ga nan tun Baba ya san maganar maitar nan, kamar Mama ta ji ne. Ita kuma kin san gishiri za ta ƙarawa abin ta yi ta bayar da labari. Amma ban sani ba ko ki na da wata shawarar?" "Ummi wace shawara? wanda yake ruwa ko takobi aka miƙa masa, ai karɓa zai yi. Sai dai shi nake tausayawa, amma ba ni da wata mafita da ta wuce wannan ɗin. Ni in dai zan samu inda zamu zaune na kula da shi, ba komai zan zauna ko a cikin dutse ne ba ƙauye ba" "Kin tabattar Nana? Da wayonki fa sau ɗaya Baba ya taɓa bari, muka je muka kwana biyu" Nana ta ce "Ba komai, zan zauna" Sayyid ya sanya hannunsa biyu, ya damƙe na Nana. Nana ta kalle shi ta ce "Sayyid, mene ne?" Idanunsa sun kaɗa sun yi jawur, wata jijiya a saman goshinsa ta ɗaga ta kumbura, fuskarsa ta yi jawur. Laɓɓansa sauka din ga karkarwa yana son ya yi magana, Nana ta girgiza kai ta ce "Ba sai ka yi magana ba Sayyid. In sha Allah duk rintsi ina tare da kai, har Allah Ubangiji ya baka lafiya" Ummi ta kasa jurewa ta fashe da kuka. Nana ta ce "Ummi idan ki ka yi kuka,ni ya zan yi? Kun saka ni a tsakiya, nama fi ku juriya, har da kai ma" ta yi maganar tana murmushi bayan saka idanunta cikin na Sayyid, duk da idon nata a cike da hawaye. "Ummi ki gaya wa Uwani na amince" Ummi ta share hawayenta ta ce "To shikenan, ya za a yi tafiyar to?" "Ina ga a sayar da kayan ɗakin nan, katifar ta ishemu, sai a sai ledar ɗaki, sai kayan sawarmu" "Nana, kina amarya amma a ce ɗakin ki babu kayan ɗaki, haka za ki je ki zauna? Kin san mutanen ƙauye ba sa raina abin surutu dai" "Ummi ai ba ado da kwalliya zan je ba. Kuɗin kayan ma riƙe saboda ɗawainiyar abinci da kuma magani" Ummi ta ɗan yi shiru ta ce "Kuma haka ne, yanzu zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan samo dillalai su saya" Cikin sauri Nana ta ce "A'a Ummi, ba na son ci gaba da zama a unguwar nan, ban san me za su yi mana ba. Idan da hali a nemo su yau kawai. Su saya gobe in Allah ya kaimu mu tafi" "To shikenan, bari na fita na gani" ***** Yana zaune a cikin office ɗin sa, ya ɗora ƙafafuwansa a kan tebur, yana juyi, ya din ga kiran lambar cike da fatan a ɗauka. Har ya yanke tsammani, kawai ya ji ta ɗauka, sai dai ta yi shiru. Da sauri ya sauke ƙafafuwansa ya ce "Hello" ta yi shiru ba ta amsa ba. "Hello ki na ji na?" "Eh" ta amsa a raunane. "To ba za ki yi mini magana ba?" "Ba cewa ka yi ba ka gane ni ba, ranar da na kira ka?" Ya ɗan yi guntun murmushi ya ce "Ki yi haƙuri, sai daga baya na ɗauki muryar ne. Ya ki ke ina fatan kina lafiya?" "Ai baka damu da ina lafiya ba, tun da ka sake ni baka ƙara nema na ba, saboda ka yi aure matarka ta haihu, dama ni haushina ka ke ji, ba na haihuwa" "A'a Yusra, kar mu fara haka da ke. Kin san ko bayan mun rabu, na yi ta neman lambarki, amma ba ta shiga har na haƙura. Ya jikin ki?" "Da sauƙi, amma ni ba mahaukaciya ba ce" Sagir ya ce "Ai dama ban ce ba" "Lokacin da muna tare ai ka ce" ya yi murmushi ya ce "Wannan ba ya wuce ba? Amma Mami ba ta san kin kira ni ba ko?" "Eh, ina gidan Mummy Zahra, da wata na haɗu sunanta Nana, ita ma ta san irin rashin lafiyata. Ita ma tana yi" Ya ce "Haba dai?" "Wallahi. Ita ta din ga ba ni shawara, ita ce ma ta ce na kira ka fa, na ma zata ba zaka ɗauka ba, ka ɗauka amma ka nuna ba ka gane ni ba" dariya ya yi ya sakankance sosai, yana sauraren Yusra. A yanayin surutun da take yi, ya fuskanci jikinta da saura, ba ta warke ba, amma ya tattara hankalinsa yana sauraren ta. Hirar ta din ga tuna masa da yadda suka zuba soyayya a baya kafin aure. Yana kallon kiran Shukura amma ya ƙi ɗagawa ya ba wa Yusra lokacin sa. "Ki na ji na" "Eh" "Yanzu ina gurin aiki, kuma lokacin salla ya yi, zan sake kiran ki, in sha Allah" "Tom sai anjima" "To 'yar farata, bye-bye" Kamar tana gabansa ta saki murmushi, cike da sanyin jiki, saboda ta yi kewar jin sunan. Shi ma murmushin ya yi, yana tuna wasu abubuwa da suka wuce. Ya kira Shukura, sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga. "Madam ya aka yi ne?" "Ina ta kiran ka, kana waya, har da rejecting kirana" "Sarkin ƙorafi, kin san da wa nake wayar ne?" "Ai ba sai ka gaya mini ba, na san 'yan matanka ne" "Ni ba da 'yan mata nake waya ba. Ya aka yi?" Shukura ta ce "Ba komai" "Madam Shukura, bakomai ɗin ki, na nufin akwai komai. Yanzu dai a yi mini afuwa da ni da 'yan matan nawa." "Ni shikenan kawai" ta kashe wayar. Ya girgiza kansa tare da ɗan lumshe idonsa. **** A ranar dillalai, suka saye wardrobe da mudubin Nana, da sauran kayan da take ganin za su zame musu shirgi. Ta tattare musu kayan su cikin bagcco, duk wani kayan amfaninsu ta tattare. Da safe ƙarfe goma, ita da Ummi suka je suka samo taxi. Har fargaba take yi kar mijin Ummi ya yi ƙorafi a kan yawon da take yi saboda ita. Duk da ba mazauni ba ne. Suka yi cinikin a nawa zai kai su Garko cikin ƙauyen Buda. Aka ɗaure katifa a saman taxi, aka loda kayan su a ciki. Ummi ta shiga gaban motar, ita da babbar 'yar ta Islam. Nana kuma suka shiga bayan motar, tare da Sayyid. Ya kwanta a jikin Nana ya yi shiru, ita kuma ta riƙe hannunsa tana matsa masa a hankali cike da kulawa. Awa ɗaya da rabi, suka isa har cikin garin Buda. Sai dai shigar su garin ke da wuya, Nana ta fara jin sanyi yana ratsa ta. Addu'a ta din ga yi, a kan Ubangiji Allah ya rufa mata asiri, ya kawo musu ɗauki, ya shiga tsakaninsu da su Ƙaisar. "Ma vie" ta ji ya yi magana. "Na'am Sayyid" Sai kuma ya yi shiru, bai sake cewa komai ba. Yara suka firfito suka tatstsaya bayan ganin mota ta tsaya a ƙofar gidan Uwani. Uwani da kanta ta fito tana tafa hannu, tana "Maraba da mutan birni. Ina yayar tawa take?" Nana ta buɗe motar ta fito tana murmushi. Ummi ta sallami mai motar, Uwani ta ce "Ina mai gidan?" Nana ta buɗe taxi ɗin, ya fito a hankali, kansa rufe da mayafi. Uwani bakinta fal magana, amma ta haɗiye ta yi musu maraba, zuwa cikin gidan. Babban gida ne mai ɗauke da ɓangarori. Ta kai su sashen ta, aka yi shimfiɗa Sayyid ya zauna ya jingina da bango. Abin da dai ba ya ƙauna, ya sake tararwa a garin, kallo. Ba ya son a zura masa ido, amma ya lura da yadda ake ta kallon sa. Uwani ta karrama su da ruwan pure water, da abinci shinkafa da wake. Ummi ta ce "Kafin cin abinci, Uwani a ina za su zauna, a gyara musu?" Sai da Uwani ta sake yi wa Ummi ta tas, tamkar ita ce Baban, sannan ta kalli Nana ta ce "Yayata, kin ga cikin gidan nan, akwai ɗakuna, idan ma ba zaku zauna a nan ba, nan baya tafiyar babu nisa, akwai gida da ɗakuna biyu da tsakar gida. Babu kowa a gidan idan za ku zauna". Nana ta ce "Gara su zauna a inda babu kowa" Ummi ta ce "Maimakon ku zauna a cikin mutane, yadda ko wani abin ne, a taimaka muku" Nana ta ce "Akwai dalili gara mu zauna inda babu kowan" Nana kuwa ta yi hakan ne, domin samun rufin asiri na larurar da suke fama daga ita har Sayyid. Ga uwa uba takura da Sayyid ba ya so. Uwani ta saka yara, su ka je su ka share gidan tas, aka wanke. Nana ta ce "Sayyid, bari mu je da Ummi, a gyara gidan, sai mu zo mu tafi da kai" Ya saka hannu ya riƙe nata, tare da girgiza mata kai alamar a'a. "Mu tafi tare za ka iya tafiya?" Ya jinjina mata kai alamar eh. "To ta so" Ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye. Uwani ta ce "Nana, ku bar shi a nan mana, tun da ba shi da lafiya, ke ku je, ku gyara gidan" Nana ta ce "Ai ba zai zauna ba, ya ce bin mu zai yi" "Ikon Allah, ni da bita zai-zai, to Allah ya taimaka" Nana ta yi murmushi kawai, tare da jin nauyin abin da Sayyid ɗin ya yi. Sauran yaran gidan Uwani, suka bi su Nana, su taya su shirya kaya. Wanda galibi Nana ba ta ma san su ba, saboda ba zuwa garin suke yi ba, domin ita rabonta da garin ma, har ta manta. Gidan ƙasa ne tsura, da zunzurutun turɓaya Ɗaki ɗaya ne gyararrre, sai aka yi masa siminti, da plasta, aka shafa farar ƙasa, da ƙofar langa-langa. Sai wani ɗakin kuma, si kuma ko rufi babu, sai banɗaki. Duk lalacewar gidan su Nana ya fi nan nesa ba kusa ba, Ummi jarumta kawai take yi, zuciyarta a cunkushe babu daɗi, biyo bayan tuna cewar a nan Nana za ta rayu. Sai dai ta ga tsantsar tawakkalli a fuskar Nana. Su ka gyara ɗakin aka shimfiɗa leda, sai katifar su. Sai kuma tarin kayan su, na girki sai na sakawa a cikin bagco. Uwani ta aiko musu da Abinci. Da la'asar bayan Ummi ta yi salla, ta ba wa Nana kuɗin barkononta da aka sayar, ta yi ta mata nasiha da kwantar mata da hankali, sannan ta yi musu sallama. Ɗan gidan Uwani ya ɗauke ta a kan babur, ya tafi da ita. Nana ta ƙarasa gaban Sayyid, da ya zuba mata idanu tamkar bai taɓa ganinta ba. Ta riƙo hannayen sa ta ce "Sayyid, duk da ban san wace irin rayuwa ka yi a baya ba. Amma wadda muka yi, mun yi ta ƙarƙashin kulawar su Habu, ba mu taɓa neman abu mun rasa ba. Amma Allah shi ne abin godiya. Wannan yanayin da muke ciki, ba zai dauwama ba in sha Allah. Ina fatan Allah ya baka lafiya, ya kuma baka haƙuri da juriyar a yanayin da muka tsinci kanmu a ciki". Ya sanya tafukan hannayen sa biyu, a fuskarta laɓɓansa na rawa, amma magana ta gagara. Ta girgiza masa kai tana murmushi, ta ce "Ruhinka yana cikin jikina, kar ka damu kanka lallai sai ka yi magana. A jikina ina jin abin da ka ke son faɗa" ɗan guntun murmushi ya yi, duk da yadda yake matuƙar son ya furta wani abu. Da daddare Uwani ta aiko musu da tuwon dawa, da miyar karkashi, ta sha daddawar kalwa har ɗaurin yajin daddawa. Ta san ba lallai ya iya ci ba, ta ba wa yaran da suka kawo kuɗi, ta ce su sayo mata buredi da shayi, na gurin masu sayarwa, da kuma maganin sauro, saboda azabar sauron da ke ɗakin. Sai dai ya ƙi shan shayin, buredi kawai ya ci ya kwanta. Nana jikinta na rawa ta ci tuwon, saboda yadda ranta ya biya, amma ƙarshe amai har ta hancinta sai da ta yi shi. Kan su kwanta, ta kunna maganin sauro, ta gyara masa shimfiɗa ya kwanta. Ita ma ta hau katifar ta tofa masa Addu'a, sannan ta kwanta a kusa da shi, tana yi masa fifita. Ta daɗe idonta biyu, kafin bacci ɓarawo ya sace ta. Sai dai kamar a zahiri, kuma kamar a mafarki ta fara jin hayaniya a kanta. Ba ta gama tantance hayaniyar mece ce ba, ta ji wani abu na wucewa ta saman roofin ɗakin. Idan abin ya daki kwanon ɗakin da abin da yake takawa, tamkar kwanon zai buɗe ya faɗo musu a ka. Ayshercool 08081012143 55 Wata irin yinƙurawa Nana ta yi, cikin azama da tashin hankali ta kifa a kan Sayyid, saboda kar abin da yake takun koma mene ne, ya faɗo masa a ka. "Ma vie" ya furta da ƙyar can ƙasan maƙoshinsa. Ta ɗago ta fara laluben fuskarsa a cikin duhu. "Sayyid, ba ka ji wani abu zai faɗo mana ba?" "A'a" Ta sake cewa maganar ta dawo "Maganar ta dawo?" "Eh" "To sannu" ta furta a hankali cikin tsoro, ta mayar da kanta kan ƙirjinsa a tsorace. Sai dai kamar dole, ta ƙarfin tsiya, wani baccin ya sake awon gaba da ita, tana cijewa da ƙoƙarin hana idonta sake yin bacci, amma abu ya ci tura, baccin ya kuma awon gaba da ita. Ganinta ta yi a tsaye a tsakiyar ɗakin, itakaɗai babu Sayyid. Ana ta cigaba da hayaniyar da ba ta gane me ake faɗa. Ta din ga waige-waige tana tunanin ina ya shiga haka? Sai dai ba ta gama tunanin ba ta ji muryoyi daban-daban suna faɗin "Lale da manyan baƙin garin Buda. Barka da zuwa." Sai kuma ta ji ana dariya tare da ci gaba da hayaniya. Idonsa biyu, yana jin yadda ta yi wa hannayensa wata irin muguwar damƙa, ta nutsa faratanta a jikin fatarsa, dan tuni ya karaya jini ne yake fita daga fatar tasa. Ta din ga juya kanta a kan ƙirjinsa tana kuka tana faɗin "A'a, mu ba baƙin ku ba ne ba, ba gurinku muka zo ba, mu ba baƙinku ba ne" jin ta fara ɗaga murya, ya sanya ya murginata gefensa, ya zame hular kanta yana shafa gashinta a hankali, tare da hura mata iskar bakinsa a kunnenta. Daga haka sai ta yi shiru, ta ci gaba da bacci. **** Barira sai da ta sha jini leda biyu a Asibiti da allurai da magunguna, amma tana komawa gida, abu ya ƙara rikicewa. Domin kuwa babu damar ta sanya haƙarƙarinta a ƙasa ta fara bacci, wannan jibgegiyar magen za ta bayyana, su hau kokowa da ita. Duk sai magen ta yayyage mata fuska da jikinta. Idan ta tashi sai ta ji jikinta na yi mata wani irin zugi da raɗaɗi. Ta cewa mijinta ita fa ba za ta koma wannan gidan ba. Ya sanar mata an tashi su Nana, daga su sai su Sajida a gidan kamar da, amma ta hau kujerar naƙi ta ce gidan ne ba za ta koma ba. Shi kuma ya ce sai dai ta yi ta zama a gidansu, dan ba shi da kuɗin kama wani gurin. Shukura ce tare da Hajiya Amina, suke hira. Ta je yi mata sannu da zuwa dawowar da ta yi daga umara. Alhaji Zailani ya yi sallama ya shigo falon. "Daddy sannu da zuwa" Ya ƙare mata kallo ya ce "Yauwwa, mara tawakalli da ba ta san ƙaddara ba" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai. Duk irin kashedin da nake yi miki, da rarrashin da na yi miki, ba ki ji ba abin har ya kai ki dizga bawan Allah nan, a gaban mutane kina cewa yana kashe mutane, idan ya yi ƙarar ki kina da shaida a kan haka?" Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. "Tambayarki nake yi" Ta girgiza kai alamar a'a. "Amma ki ke wannan iƙirarin, maimakon ki mayar da hankali a kan fatan Allah ya raya na gabanki, ya ba ki wani. Ba ki kyauta ba" Hajjya Amina ta yi ta kallon Shukura ko za ta ba shi haƙuri, amma ta yi mursisi. Ko da ya shiga ɗakinsa, babbar rigarsa ya cire saboda azabar gumin da yake yi. Dan tun da Doctor Sharif ya gaya masa ga yadda suka yi da Shukura hankalinsa ya yi mummunan tashi. Ya kuma sake jaddada wa Sharif, muddin wani abu ya fita to babu hannunsa a ciki. Kuma likitan ya yi masa bayanin process ɗin da ya bi, abu ne mai wahala a gano. Ya yakice gumi ya nemi guri ya zauna. Hajiya Amina ta ce "Me yasa ba ki ba shi haƙuri ba, kina kallon yadda ya yi fushi?" "Mummy, duk wannan abubuwan kamata ya yi a tsaya a saurare ni, a kuma fahimce ni. Da hankalina fa ta yaya zan din ga iƙirarin an kashe mini ɗa haka kurum. Mummy ranar da za a yi mini aiki, kina bacci cikin dare, na kasa bacci saboda damuwar da nake ciki, aka buɗe ƙofar ɗakin, aka zo aka kama hannuna aka laluba cannula, aka yi mini wata allura a cikin duhun nan. Tun da aka yi mini allurar nan. Na ji kaina ya fara juyawa, ina neman na fita hayyacina, duk iya ƙoƙarina na kasa, na ji jikina na ƙamewa kamar zan yi jijjiga. Saɓanin da da idan za a yi mini allura cikin dare, za a ƙwanƙwasa ɗakin, sai kin tashi kin ce a shigo tukuna, a kunna ftila a yi mini" Mummy ta ɗan yi shiru, cike da mamakin me yasa tuntuni ba ta faɗa ba, amma domin kawo ƙarshen maganar, sai kawai ta kawo gigin ciwo ne ya sanya ta ga haka a lokacin. Dan haka ta ce "Duk da haka wannan ma ba hujja ba ce, ke da ki ke fama da ciwo ina za ki tantance wani abu ma. Dan Allah ki bar zancen nan" Shukura ta yi murmushi ta ce "Shikenan, na bar shi" Sai kuma ta sake cewa "Mummy, Nana shiru, ni yakamata ki kwatanta mini gidan da suke na kai mata Haidar" "Gidan Alhaji Garba giwa ne fa, kuma fafur babanku ya hana ni zuwa ban san dalili ba" Dummm! Ƙirjin Shukura ya buga, ta ce "Saboda ne ya hana ki zuwan?" "Ban san dalili ba, za ki je ne? Sabon gidansa nan Kano" Shukura ta ce "Wace matar ce a gidan?" "Halima ce, uwar gidan sa" Shukura ta girgiza kai ta ce "Ba zani ba, gidansu tsohuwar matar Sagir ce" Mummy ta waro ido ta ce "Ke haba? Dama 'yar Halima ce matar Sagir ɗin?" "Eh mana" "Ikon Allah, da na ce wa Daddy, ya taimaka musu, a samo wa mijin Nana, gurin da zai yi gadi, su samu su zauna, shi ne aka samo gidan" Shukura ta ce "wai canza masu gadi ku ka yi ne?" "Ina fa, ina nan cikin gida, daga baya ma Yusuf yake gaya mini. Wai zuwa aka yi da motoci da alama daga ƙasar su ne ma, motocin duk rubutun fransanci aka kwashe su kaf, kuma babu wanda aka yi wa bayanin me yasa" "Ikon Allah, kuma ba laifi suka yi ba?" "To ina zan sani, ina nan cikin gida?" Suka ci gaba da tattaunawa da jajanta lamarin. Har wayar Nana suka jarraba kira, su ji ko ita nata mijin yana nan, ba a kama shi ba amma wayarta ba ta shiga sam. **** Da safe Nana ta tashi, ta fara alwala sannan ta zuba wa Sayyid ruwan da yara suka ɗebo musu jiya, dan gidan babu ruwa. Ya yi alwala a ƙofar ɗakin, sannan suka koma ciki ya yi salla. Sai dai bai ga alamun ta san abin da ta yi cikin daren jiya ba. Ƙarfe tara da rabi, Uwani ta aiko yara da kunu da 'yar tsala aka kawo wa su Nana. 'yar aiken ta ce "Uwani ta ce idan kin gama karayawa, wai ki je" Nana ta ce "To, zan zo a ce mata mun gode sosai da sosai, Allah ya biya ta" Ta koma ta zauna a gaban Sayyid ta ce "Sayyid, ka ga kunu ne da 'yar tsala za ka iya ci, ko na nemo maka wani abin?" Ya girgiza kai. "To za ka iya cin wannan ɗin?" Ya gyaɗa mata kai. Kunun tsamiya ne, na daka ba niƙa ba, ya sha kayan ƙamshi, sai dai babu suga ko kaɗan a ciki, ga tsamiyar nan cau har ka. Ƙuli-ƙulin 'yar tsalan, ya sha barkono, ta zuba masa a kofi ta ba shi. Ya saka hannu ya karɓa. Tun da ya yi kurɓa ɗaya, ya yi shiru. Nana ta ce "Za ka iya sha kuwa?" Ya jinjina kai ya ci gaba da sha, saboda Nana. Ya haɗa da 'yar tsalan nan, duk da ba son Abincin yake yi ba. "Sayyid, idan ba zaka iya cin Abincin nan ba, ka bari na nemo maka wani" Ya ɗaga kai ya kalle ta, sai dai ba baki, dan haka ya harare ta, ya ci gaba da cin abincin. Ta yi murmushi ta ce "Ni ka ke harara ko, aishikenan" Ya gama karyawa, ta saka ɗankwalinta, ta goge masa bakinsa da hannunsa. Ta ce "Bari na je kiran da Uwani take yi mini, daga nan na saka a raka ni, na ɗan yi mana sayayya, dan na san dole za ta daina bamu Abinci yau da gobe sai Allah" Bai ba ta amsa ba, ya jingina da bango, saboda yadda yake jin daɗin hakan, yana lumshe ido. "In je?" Ya yi mata shiru, kuma yaƙi yi mata wata alamar, da za ta gane ya amince ko a'a. Cikin shagwaɓa ta ce "Sayyid" ya kawar da kansa gefe, ya ƙi buɗe ido. "Duk da maganar nan ɗaukewa take yi, amma dai tun asalinka miskili ne, ina ta magana ka ƙi kula ni, ni ce fa rayuwartaka guda ka ke wa haka?" Murmushi ya yi, tare da saka hannunsa a cikinta, yana shafawa a hankali. "Wai ba za ka kalle ni ba?" Ta yi maganar tana juyo da fuskarsa. Ya ƙara rintse idanunsa, wai ba zai kalle ta ba. Nana ta din ga dariya. Ya ja jikinsa a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, ya zuba wa cikinta ido, tamkar zai gano abin da yake cikin. "Idan na haihu na ga yadda za a yi, da kai da jaririn wa zai bar wa wani cinyar nan" Ta yi maganar tana shafa gashin sa. ***** Hajiya Sa'a ce take cin abinci, tana kallon Jamila, da take ta cakala kaɗan-kaɗan. "Jamila ya ne? Ki saki jiki ki ci abinci mana" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba. "Ko dai haryanzu abin da ya faru ɗin ne yake damun ki? Tun wuri ki ajiye wannan abin, ki ci gaba da rayuwar ki cikin kwanciyar hankali. Ɗan ƙaramin abu ne fa, ranar da aka ce ki bayar da jini kuma ya zaki yi? Ki na gani Safiyya ta tafi Dubai ma sarin kaya, kuma duk harka ce ta ƙungiya ta ɗaukakata haka. Har gara ke ma da ba ki da aure, Safiyya da aurenta, amma kalli yadda ta kama ƙasa, mijin ma ita yake yi wa biyayya, ki saki jikinki dan Allah ki daina wannan damuwar. Ki ƙarasa cin abincin, Talatu ta gyara gidan, idan an zo ana son kaya, kin san gurin da suke, zan je sake duba Fatuhu ne, daga nan na je a gyara mini kaina" "To Mummy a dawo lafiya" "Yauwwa Daughter Allah ya sa" Ta gama abin da take yi ta fita, bayan fitar ta, Jamila ta tashi ta nufi harabar gidan, tana kallon flowers ɗin da aka ƙawata harabar da su. Jibga-jibgan motocin Hajiya Sa'a uku na hawa. Ga na ɗanta Abba biyu. Iya harabar gidan abar burgewa ce, ta yadda duk mai rai zai yi fatan ya samu wannan wadatar. Sai dai kash, hanyar da aka bi gurin tara dukiyar, duk wanda ya ji muddin yana da imani, sai ya gudu da ƙafafuwansa. Ji ta yi kamar wani abu yana bin wuyanta, ta juya a hankali ta ga Abba ne a tsaye, yana saka abin fulawa a wuya. Ta yi guntun murmushi ta ce "Yaya Abba" "Na'am ƙanwar Abba. Ya na ganki nan lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau, ba ka fita ba?" "Yau ba zan fita ba, ba na jin daɗi ne gaba ɗaya, dan da zazzaɓi ma na kwana wallahi" Cikin tausayawa ta ce "Kash, sannu Allah ya ba ka lafiya. Ka je Asibiti mana" Abba ya ɗan numfasa ya ce "Na sha magani already, dan haka ba sai na je ba, zo mu je mu zauna ki yi mini hira, na san zazzaɓin zai sauka gaba ɗaya" Dariya ta ɗan yi ta ce "Ai ni ban iya hira ba" "Ba wani nan, amma ki na yi da Mummy ai, gaskiya mu je sai kin yi mini" Tana dariya ya wuce gaba ta bi bayan sa. Sanyin halin Abba ya fara tasiri a zuciyar Jamila. ***** Alhaji Fatuhu na zaune, Hajiya Suwaiba ta gama gyara jikinsa, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya kalli uwar 'ya'yan nasa ya ce "Haryanzu Fadilan ba ta haihu ba?" Ta taɓe baki ta ce "Tana can ba ta haihun ba tukuna." "Allah ya sauke ta lafiya" ta yi shiru ba ta amsa ba. "Yakamata a sallame ni na koma gida haka, na gaji da zaman Asibitin nan gaba ɗaya" A hasale ta ce "To mu koma gida mu yi yaya ne? Nan ɗin ba dai magani ake baka ba ana kula da kai, komai sai ka nuna kai ba a kyauta maka ba, ba a iya ba haba dan Allah" Jiki a sanyaye ya ce "Yi haƙuri, Allah ya baki haƙuri" daga haka ya sunkuyar da kansa. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, ta zauna a kusa da shi, tana tunanin ta yi magana. Ta ga yana share hawaye. Cikin damuwa ta ce "Alhaji kuka ka ke yi? Dan Allah ka yi haƙuri raina ne a ɓace, amma dan Allah ka yi haƙuri" Ya yi mata shiru, gaba ɗaya ta rikice ta rasa abin da za ta ce. Raudah ce ta turo ƙofa hannunta da towel ta ce "Daddy guess what?" Ta miƙa masa narkeken jaririn da Fadila ta haifa. Hannunsa na karkarwa ya riƙe jaririn ya ce "Another Muhsin" ya yi maganar yana murmushi. Ya din ga yi wa jaririn kiss, yana shafa shi kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba. **** Fafur Sayyid ya hana Nana zuwa ko nan da can, har aka yi azahar.Uwani ta sake aiko musu da dambu, ta ce a cewa Nana ba za ta zo ba, sai ta zo da kanta. Cikin damuwa ta ce "Sayyid dan Allah ka bari na je, na ji kiran me take yi mini" fafur ya sha kunu ya tsuke fuska. Babu yadda Nana ta iya, ta zauna ta ƙi fita. Ta zazzage kayansu, tana ƙara gyara musu, ta fito da kayan wankin gashinsa, da turarrukansa da duk wata sai su Habu sun sayo sun kawo. Ta ɗaga kai ta ga ita yake kallo, ta ɗan yi murmushi ta haɗe su a guri ɗaya da combs ɗin sa na taje gashi. Sai yamma bayan sallar la'asar, ta yayyafawa tsakar gidan ruwa, ta share shi. Ta yi shimfiɗar tabarma a tsakar gidan, ta saka wa Sayyi fululluka ta kamo hannunsa zuwa waje. Ya zauna, ta ɗaukko mayafin rawaninsa ta yafa masa a kansa. Babu jimawa sai ga Uwani ta zo, tana faɗin "Tun da ba za ki zo ba, ni ga ni na zo da kaina" Nana ta ce "Ba ƙin zuwa na yi ba Uwani, yanayin jikinsa ne sai a hankali, shi yasa ban fito ba" "Koma dai mene ne gani na zo ai" Ta kalli Sayyid ta ce "Sannu ko" ya jinjina mata kawai. "Dama kiran ki nake yi, na ji idan akwai wani abu da ku ke buƙata?" "Eh, ina son yin sayayya ba mu da fitila sai ta waya, da kuma 'yan kayan buƙatu" "To da kin sanar, ai da na saka yara sun raka ki, dama zan ce miki kuma idan an kwana biyu, yakamata ki zo a ɗan zagaya da ke cikin dangi, su san kina garin nan, tun da dama ba zuwa ku ke yi ba, dui ba sanin ku aka yi ba" Nana ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah" "Wai ni Nana ina Mai jidda kuwa?" "Tana can Bauchi inda take aure" Uwani ta ce "Kuma tana zuwa?" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza kai. "Ai dama na san babu lallai ta zo, ko dan saboda baƙin halin Isa. Ai ya bamu mamaki. Ita ma tun da suka rabu ba ta sake zuwa garin nan ba. Kuma yakamata mu je na zagaya da ke, har inda danginta suke a nan" Cikin mamaki ta kalli Uwani ta ce "Danginta kuma?" "Ƙwarai da gaske, tushen Maijidda garin Buda ne. Kakanninta 'yan nan garin ne, can wajen unguwar Wanzamai, ƙarewa ma a nan garin suka haɗu da babanku. Ai kakarta aka raina a Bauchi, aka haifi babarta da ita a can. Har an saka mata rana, suka zo garin nan, ke ma Babanki ya zo gida, suka haɗu a dandali. Aka yi ta ɗauki ba daɗi suka ƙulla soyayya. Ga shi can garinsu an saka mata rana da wani, ina ga shi ne mijinta na yanzu da take aure. Asali tun kan ta auri babanku da shi aka fara saka mata rana. Kakarta ta ce sai an warware wancan baikon ta auri babanku, ko ba komai sa din ga zuwa gida a kai kai. Haka aka mayarwa da wancan kuɗinsa ta auri babanku. Ya Babanku ya  so ta sosai da sosai, kuma aka ƙulla auren nasu da tunanin hakan ya ƙara kawo zaman lafiya a tsakanin zuriyarmu da zuriyar wanzamai kin san a tarihin garin nan ba zaman lafiya ake ba. Kuma dai cikin ikon Allah sun fara zamansu lafiya gwanin sha'awa, amma Allah ya ƙaddara rabuwar su." Nana ta yi shiru tana tunanin, kamar ta san wani abu mai kama da wannan labarin da Uwani take ba ta, amma sam ta kasa tunawa. Gaba ɗaya hirar ta Uwani ta gundure ta, saboda ta san shi kansa Sayyid a takure yake, ba ya son mutane ko kaɗan, balle uwa uba dogon surutu. Ita kuwa Uwani tamkar an ƙona ta a ka ko gajiya ba ta yi. Babu wanda ya taɓa ba ta wannan labarin, sai yanzu babu wanda ya taɓa gaya mata cewar mahaifiyarsu tushenta a garin Buda yake, sai dai kamar ta san labarin da Uwanin ta bata. "Ga wata 'yar rama na zo muku da ita, sai ku ci kafin Abincin dare ya sauka. Wai shi mijin naki kurma ne?" "A'a ai kin ga ba shi da lafiya ne" "Eh gaskiya ne, Allah ya ba shi lafiya, amma a ina ki ka samo Buzu haka? Ni wai anya ma labarin da Rabi ta din ga bayar wa ranar bikinki nan gaskiya ne? Abin dai da mamaki. Allah ya ba shi lafiya bari na tafi, dan Allah idan ki ka samu lokaci kya zo a je a gaggaisa. "To in sha Allah zan zo" "Yauwwa, zan din ga turo miki yara, idan da aike kya din ga ba su, duk 'yan uwanki ne, 'ya'yan 'yan uwa ne. Kuma ki kwantar da hankalinki duk abin da ku ke buƙata ku sanar mini, da yardar Allah ba zai gagara ba" Nana ta ce "In sha Allah, mun gode sosai da sosai" "Ba komai, ki yi haƙuri ki riƙe mijinki ki kula da shi, sai ki ga kaf ayyukan ki, Allah bai karɓa ba, silar wannan jinyar ta sa ki shiga aljanna, a yi ta haƙuri yayata" Nana ta tashi ta raka ta, ta ce "In sha Allah" Ta yi ƙasa da murya ta cewa Nana "Dan ubanki, ki din ga ɓoye mijinki, kar ki bari 'yan mata su din ga zuwa su na kallon sa." Uwani ita iya rage muryarta kenan, amma Sayyid na jin ta. Nana ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, ya yi murmushi yana sunkuyar da kai. ***** Alhaji Fatuhu, farin cikinsa ya kasa ɓuya, duk da halin rashin lafiya da yake ciki, idan aka zo duba shi, sai ya yashe haƙoransa da sukaɗai suka rage farare a jikinsa. Alhaji Zailani ya ƙura wa jaririn ido, ya kalli Alhaji Fatuhu da yake ta yashe baki. Hajiya Sa'a ta ce "Kai Fatuhu. Sai ka ce ba a taɓa yi maka haihuwa ba, ji yadda ka ke washe baki, kana fama da kan ka" Hajiya Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce "Abin da na gani kenan" Alhaji Zailani ya ce "A'a ku bar shi ya yi, ɗan mutum fa, kyauta ce Allah ya ba shi, da duk Duniya babu mai ba shi. Ni ba gani ba 'ya'yan duk babu sai biyu ne suka tsaya." Ya yi maganar yana zuba wa jaririn ido, yana tuna na Shukura. Tun da yake harkar ƙungiya, bai taɓa bayar da jinin da ya tsaya masa ya kasa mantawa ba, sai na Shukura. Mussaman idan yana tuna irin baƙar wahalar da ta sha. Ya kalli Fadila, da take ɗakin a zaune, ga jego tana yi, amma ta tare a Asibiti da ɗanyen jaririn da ko suna ba a yi ba. Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Wane sunan za ka saka masa?" "Muhsin ɗina zan mayar" ya yi maganar muryarsa ɗauke da rauni. Hajiya Sa'a ta ce "Wai an din ga saka Muhsin ɗin kenan?" "Sunan mahaifin Fadila ne, shi za a mayar mu ci gaba da kiransa Muhsin, ni na yi mata alƙawari shi yasa. Na so Muhsin ɗina da ya rasu sosai da sosai. Na ji zafin rashin sa, sai dai ina tausayawa wannan Muhsin ɗin. Ya zo lokacin da mahaifinsa ba shi da komai, ba zan iya ɗaukar nauyinsa na kula da shi ba. Wataƙila ma kafin ya yi wayon sani na na rasu. Ga shi ko hakika ba zan iya yi masa ba" ya yi maganar hawaye na zubowa daga idanunsa. "Haba Fatuhu, ya haka? Dan dai Hakikar da za ayi wa jaririn nan, ka san ba za ta gagara ba, amma ya za ka zauna kana kuka kamar ƙaramin yaro, a gaban iyalinka da 'yan uwanka hakan bai kyautu ba ai". Alhaji Fatuhu ya ɗago idanunsa da suka yi jawur ya ce "Zailani. Ka san me nake ji kuwa? Gidaje da motocin hawa nake da, ina kyautar maƙudan kuɗaɗe ba tare da na ji komai ba, da abu ya dame ni, zan sai ticket na tafi umara. Ina da shaguna dukiya Allah ya yarje mini, bayan gwagwarmaya da na sha ta rayuwa. Astagfirillah ba ƙarar Allah nake kawowa ba, ko rashin imani da ƙaddara ba, ina jinjina girman lamarin Ubangiji, kuma ina jin babu daɗi ɗa na na cikina, ba zan iya saya masa ko wando ba" Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka yi haƙuri. Mu na murna sauƙi yana samuwa, ga shi ka na ta magana sosai da sosai, kukan nan karya mana zuciya yake yi. Kuma da ka yi mana a baya, yanzu kuma da Allah ya kawo jarrabawa shikenan sai a yi haƙuri" Su na nan zaune, sai ga ƙanin Baban Fadila, ya zo duba Alhaji Fatuhu ya kuma jaririn Fadila, wanda shi ne waliyyin Fadila. Sai dai shi ma ya tsorata da ganin Alhaji Fatuhu. "Alhaji haka jiki ya zama? Subhanallah Allah ya baka lafiya" "Amin kawu, amma jiki ya yi kyau Alhamdillah, tun da ina ta magana" "Haka ne, amma menene takamaiman abin da aka ce ya same ka ne?" Fadila ta ce "Haryanzu ba a gano takamaiman mene ne ba, yau a ce ƙodarsa ta kumbura, gobe a ce ko cancer ce, an yi gwaji ba ita ba ce. An yi gwajin zuciya shi ma lafiya ƙalau" Cikin damuwa ya ce "Amma Fatuhu ana haɗa maka da na addini kuwa? Ka san muna da ido ne ba na ganin gari ba. Mussaman ku da ku ke shahararrun mutane da Allah ya ba wa wadata. Yakamata a yi na sihiri da shaiɗanu" Alhaji Zailani ya ce "A'a ga likitoci su na kula da shi, ya za a yi a ce kuma a kawo wani abu daban? Magungunan gargajiyar nan kashe mutane suke yi ai, tun da ba auna su ake yi ba". Alhaji Fatuhu ma ya ce "A'a ba wannan ba ne, wa ya damu da ni da zai yi mini sihiri. Larura ce kawai kuma likitoci na kula da ni" "Kai, kalle ni da kyau. Duk bokon ka, nima ɗan boko ne, kuma na san ilimin addini, amma sihiri da shaiɗanu gaskiya ne. Tun da aka yi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam sihiri, duk duniya ban ga wanda ba za a yi wa ba. Ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinye wa ai akwai alamar tambaya, ga lalacewar dukiya lokaci guda. A dai tsananta addu'a. Ya gama bambaminsa ya fita. Alhaji Zailani ya din ga ziga Alhaji Fatuhu, tare da kushe magungunan gargajiya. Ba tare da jin nauyin Fadila da take gurin ba. Ya gama soki burutsunsa, ya tashi ya yi musu sallama, tare da cewa zai aiko da abin hakika. Har ya kusa ƙarasa wajen motarsa, ya waiwaya ya ga Hajiya Sa'a ta nufo shi, ya tsaya ta ƙarasa. Ya ce "Ya dai?" Ya yi maganar yana kallonta. "Zailani" "Na'am "An sauke ɗan uwana daga shugabancin 'yan kasuwa an ɗora ka, ka saka an dawo da shi Asibitin nan, ƙarƙashin kulawarka, an ce a yi masa maganin gargajiya ka haƙiƙance kana kushewa. Kar ka kuskura na tarar da sanya hannunka, a cikin wannan abubuwan da suke faruwa da ɗan uwana" Ya gyara tsayuwarsa ya yi murmushi ya ce "Babu sanya hannuna a ciki. Ina ƙoƙarin zama aboki mai halacci ne kawai. Sannan ki daina mazewa kamar ke ɗin mai ƙaunarsa ce, bayan sadaukar da 'ya'yansa maza da ki ke yi" "Duk da haka, munin abin da na yi bai kai wanda ka ke aikatawa ba, ka fi ni sanin kai da me da me ka sadaukar, dan haka ka kiyaye ni". Ta juya ta koma. Bin bayanta ya yi da kallo, ya ji wani abu ya tsirga masa, tabbas idan Hajiya Sa'a ta ci gaba da wannan gigin, zai ɗauki matakin da ya dace a kanta." ***** Cikin bacci, take jin hayaniya  a bayan ɗakin, tamkar ana cin kasuwa. Ga wata irin sukuwa da take ji a roofing ɗakin, tamkar ta dawakai. Tun da ta farka sai juyi take yi, bacci ya gagari idanunta, ayatul kursiyyu ce ta zo bakinta ta din ga maimaitawa, har ta samu nutsuwa daga razanin da take ciki. Ta ruge idanunta, sai dai a maimakon ta yi bacci, sai wata irin kewar Sayyid take addabar ta. Ta rasa dallin da ya sanya, ba ya kula ta yanzu. Duk da ba shi da lafiya tana yi masa wannan uzurin, amma duk da haka da ya kan yi attempting sai ya ƙyale ta, yanzu kuma gaba ɗaya ya daina yinƙurin aikata komai ma. Wanda da idan ya sako ta gaba, har takura take yi. Ta tashi zaune ta gyara maganin sauro, ta taka a hankali ta ɗaga labulen ɗakin, saboda zafi. Ta dawo ta ɗauki fitilar wayarta ta kunna. Ta haska shi ta ga idanunsa a lumshe, yana bacci. Ta zuba masa ido, ta fara tunanin ko ita ce mai matsala gaya mata ne bai yi ba, ko ma sharrin Ƙaisar ne?. Ta yi ajiyar zuciya, ta kashe fitilar, ta kwanta a gefen sa tana wasa da gashin ƙirjinsa. Zuwa na fuskarsa. Ta sake matsawa a hankali, tana sumbatar leɓansa, tamkar mara gaskiya. Gaba ɗaya a tunaninta bacci yake yi, sai da ta ji ya sanya hannayen sa, ya zagaye ta, tare da ba ta damar sumbatar bakin nasa. Nana za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa jin kunya irin ta yau ba, cikin sauri ta fara ƙoƙarin rabuwa da jikinsa ta matsa, amma ya mirgina ya rungume ta gam a jikinsa yana numfashi a hankali. Ayshercool 08081012143 56 Yana jin yadda jikinta yake tsuma, tamkar wadda aka kama tana aikata wani abin ashsha! Ko kuma wadda ake kaɗawa mazari. Magana yake son yi mata, amma abu ya gagara, duk ƙoƙarin da ya yi amma abu ya ci tura. Ya ƙara ƙanƙame ta tamkar wani zai ƙwace ta, ya din ga murza hannunta har ta fara jin zafin riƙon da ya yi mata. Yanayin ya ƙara ninka mata halin da take ciki, ta rintse idanunta. A hankali ta ji yana hura mata iska a cikin kunnenta, tamkar yana zuba mata wani sindari, haka ta ji wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Ƙamshin nan ta ji yana ratsa hancinta, ta buɗe idonta a hankali, kamar yadda ta yi tsammani, a wannan ɗakin ta gan su. Ta hau waige-waige. Ta wata ƙofa ta ga ya fito, ƙugunsa ɗaure da wani abu kamar zani, ya zauna a kusa da ita yana kashe mata ido. "Sayyid ka warke?" "Eh mana" "Ka daina jin duk abin da ka ke ji?" Ya jinjina kai yana murmushi. "To ka yi mini magana mana" "Ma vieee" ya faɗa yana ɗan jan maganar yana kwanciya a gefen ta. "Har na ji daɗi da ka samu lafiya, Allah ya ɗorar maka da sauƙin nan Sayyid" "Amin rayuwata, matso ki kwanta mu yi bacci" Ta noƙe kafaɗa ta ce "A'a"ya saki murmushi yana kama hannunta. Duhu ne ya gauraye ɗakin. Dariya ta fara jin Sayyid ɗin yana yi mata cakulkuli. Ta kasance da shi cikin wani yanayi mai tsayawa a zukata. Ba ta iya tantance a wani hali take, ta daina ganinta a ɗakin, sai a libraryn Ƙaisar. Ta tsaya tana kallon gurin, tana tunanin yaushe rabon da ta zo gurin nan. Ƙaisar ta hanga, a tsaye yana gyara litattafan sa. "Ƙaisar ka warke kenan?" Yayi shiru yana goge wani littafi, ya gama ya ajiye littafin sannan ya ce "Eh, na warke. Waye ya ce ki je ƙauyen nan?" "Ban gane waye ya ce na je ba? Zan kwana a titi ne? Ga mara lafiya ina da shi" "Gaskiya ne, bai kamata ki kwana a titi ba. Wannan dalilin ya sanya tun a farkon auren nan, na din ga haska miki matsalolin da za ki iya fuskanta, amma gani ki ke yi kamar ƙarya nake yi, to yanzu sai ki san yadda za ki yi, ki rayu da ke da wannan lanjararren mijin naki, da duk larurar duniya ta ƙare a kansa". A ƙule Nana ta ce "Larura Allah ne ya ɗora masa, kuma kun taka muhimmiyar rawa a larurarsa. Kuma ka daina ganin laifina. Zan tsallake shi ne a wannan yanayin da yake ciki, na bar shi? Mu bil adama mu na da bambanci da ku, mu na da tausayi da kuma nuna kulawa ga waɗanda muke ƙauna" "A'a kar ki tsallake ki bar shi, amma ki yi ɗamara fiye da ta baya, garin Buda ki ka zo za ki zauna, ban sani ba ko kin fahimci abin da nake faɗa ko ba ki fahimta ba. Idan ma ba ki fahimta ba, za ki gane daga baya. Bil adama ku na tausayi da nuna kulawa ga wanda ku ke ƙauna, ku ke iya ɗaukar jinin makusantanku ku bayar, a yi muku tsafi ko? Da kyau matsala kuma ki sani, ba ki ga komai ba" Daga haka ya ɓace ɓat. Ta buɗe idonta a hankali. Tana buɗe idonta, ta ji ana kaɗa kacakaura, da garaya a tsakar gidan su. Ana ta hayaniya tamkar ana cin kasuwa a tsakar gidan. Sanyi ta fara ji yana ratsa ta, bugun zuciyarta ya ƙaru, fiye da da, waiwaya ta yi tana son ganin ta inda za ta ga Ƙaisar, ko makamancin hakan amma ba ta ga kowa ba. Wata irin guɗa ta ji an rangaɗa da wata irin murya, mai sauti, sai kuma aka ce "Yeeee barka da zuwa wakilin rafi, ku matsa ku bayar da hanya ga ango mairamu ya iso" ta ji wata murya na faɗa, ana ci gaba da shewa da kaɗe-kaɗen garaya. "Ku kawo Nono da suga, a kirawo 'yar Mairo ga mijinta ya iso. Ga farin goro ƙwarya dubu biyu ta rafi ta ce a bawa mamman wakilin rafi, gaisuwar iyaye" sai kuma aka saka shewa. Ba yau Nana ta fara ire-iren wannan jiye-jiyen ba, amma ta tsorata da wannan sosai da sosai. Ta rirriƙe Sayyid, ga sanyin da take ji ya fara damunta. Cas cas cas, ta fara jin sautin kaɗawar wani abu mai kama da abin ado na mata. Ta kalli tsakar gidan ta hango wata irin zanƙaleliyar mata, mai tsawon gaske ƙafafuwanta duk sarƙoƙi, ta yi shigar Fulani, sai dai ita ma ba a iya ganin sawayenta tamkar a kan iska take tafiya. Ta ɗan ƙara buɗe idonta, ta ga rana ce tarwai a tsakar gidan, ga dandazon mutane ana ta hada-hada. Sai dai shigar mutanen irin na zamanin da ne can baya sosai, kamar dai taron wani abu ake yi. Wata mata ta hango sanye da kayan saƙi farare tas, ƙugunta sanye da wuri, kanta babu ɗan kwali duk ta yi wa tulin gashinta adon wurin, hannunta riƙe da sandar dargaza, tana kaɗa ta tana juyi. Wannan bafulatanar ce ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Nana ta ce "Baƙuwarmu, bikin girka ake yi, ko za ki taso ki ga yadda muke gudanar da al'adun bikin girka?" ta yi maganar tana zuro zanƙalelen hannunta cikin ɗakin Nana". "La'ilahaillalah, Sayyid, Sayyid wayyo Baba" ta tashi a gigice, rirriƙe ta ya yi, ya janyo wayarta, ya haska ta. Fuskar sa cike da mamaki yake kallon ta, yanayin fuskarsa ke bayyanar da alamar tambaya. "Sayyid wata mata ce, wata mata ce take ziro hannunta, tsoro nake ji, wasu mutane ne a tsakar gidan nan" ya haska ɗakin ta ga babu komai, haka tsakar gidan ma dare nesai hasken farin wata, babu komai. Sai a lokacin ta fahimci mafarki take yi. Ya ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma bai ga Ƙaisar a gurin ba, bai kuma ga wata alama da take nuna yana gurin ba. Gaba ɗaya ta nemi ko addu'a ɗaya, ta rasa a cikin kanta. Ta kaɗa ta raya amma babu abin da ya zo da kanta. Tana so ta karɓi wayarta ta kunna karatun Alƙur'ani, amma ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta son yi, saboda tsoron da take ji. Da ƙyar wani baccin ya ƙara sace ta. Babu babban abin da ya ba shi mamaki, irin yadda da safe take komawa normal, babu ma alamar akwai wani abu da yake ba ta tsoro cikin daren. Haka ta ci gaba da sabgoginta. Sai dai gaba ɗaya a kunyace take, ko idonsa ba ta iya kallo, saboda abin da ta aikata ya kama ta cikin dare. Shi ga tausayin kan su, ga kuma dariya ta ba shi. ***** Baba yana zaune yana shan koko da ƙosai a tsakar gida, sai ga kiran wayar Uwani. Ya kalli wayar tasa ya ce "Tofa! Wannan jarababbar tsohuwar ko me za ta ce mini, take kira na da safiyar nan oho. Ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa. Sai dai ba ya jin ta sosai saboda rashin network. Ba ta haƙura ba ta din ga kira har sai da ransa ya fara ɓaci. "Uwani ko a haƙura da wayar ne, kin ga babu network ne" "A'a ina jin ka yanzu. Amm dama kiran ka na yi, na tambaye ka ina Nana kuwa?" "Nana, tana gidan mijinta" "Gidan mijinta wanne?" "Mijinta dai na aure" Uwani ta ce "Eh a ina gidan yake?" "Amm can wajen gidan Ummi ne" "Rufe mini baki, mutumin banza da na wofi. Ai kwana uku kenan ina neman layinka, amma bana samu saboda garin nan bamu da natiyok ake cewa ko me?" "Uwani wai me ya faru ne?" "Ai ba za ka san meyafaru ba, tun da ka bar yarinya tana ragaita ita kaɗai ranta ga miji mai larura,an kore su daga gidan haya, ba su san ma inda za su je ba, kana zaune hankalinka kwance. Ai ko 'yar riƙo ce Nana ka duba lamarinta" Ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, ta wanke shi ta tas, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, ta ce kuma za ta kira Yaya Atine ma, sai ta ci ubanta. Ran Baba ya yi mummunan ɓaci, kenan Ummi da Nana haɗa kai suka yi, suka kai ƙararsa gurin Uwani. Ya kira Ummi ita ma ya fara sauke mata kwandon tijara. Ranta ya ɓaci ta ce "Ni fa Baba ban kai ƙarar ka gurin kowa ba, Uwani ce ta kira waya,  mu na tsaka da alhinin halin da Nana ne ciki, na gaya mata komai, kuma ni na faɗa ba Nana ba. Shi ne ta ce Nana su koma Ƙauye can gurin ta". Sai kuma Baba ya yi sak. "Ƙauye kuma? Ta yi me a ƙauye?" "To Baba zaman nan ɗin ya ƙi, kai kuma ka ƙi taimakawa, babu yadda muka iya Nana tana Buda" "Ke Ummi ki na ji na, duk yadda za ki yi, ki nemi kuɗin mota, ki je Buda ki taho mini da 'ya ta. Lallai ya sakar mini 'ya ku taho tare, ya je Allah ya ba shi lafiya" "Baba ya sake ta, 'yan uwansa ma ba a sa inda suke ba, wa za ta bar wa shi a can?" Yana cikin bambami kuɗin wayar suka ƙare. Dama Mama na tsaye tana jiran ya gama wayar, yana gamawa ta dube shi ta ce "Wato Nana ta kaso aurenta ta dawo ko? To wallahi ta dawo gidan nan ba ta da gurin zama, wai har ka manta irin zaman azabar da muka yi da yarinyar nan a cikin gidan nan? Babu bacci kullum bala'i da tashin hankalin iskokai, ba zai yiwu ba wallahi" Sai dai kafin Baba ya ba ta amsa, suka ji Suwaiba ta ƙyaƙyace da wata irin dariya mara daɗin ji tana faɗin "Asma'u a ƙauyen Buda, tushiya masomar dawa, kowa ya bar gida gida ya bar shi" ta yi maganar tana ci gaba da ƙyaƙyata dariya kamar ba mace ba. "Ke Suwaiba meye haka, wannan wace irin dariya ce? Ban hana ki irin wannan dariyar ba kamar ba mace ba?" Suwaiba ta ce "Ina ruwan ki da dariyata" Baba kawai ya gyaɗa kai, ya gyara hularsa ya fice ya bar gidan gaba ɗaya. **** Rashin maganar nan ta Sayyid, ba ƙaramin damun Nana take yi ba, abin ya yi yawa sosai. A wannan karon ta yi sa'a, ya bar ta ta je gurin Uwani, daga nan kuma ta je ta yo musu sayayya. Ta tafi ta bar shi da wayarta, domin ta ɗebe masa kewa. ***** Alhaji Zailani ya saka sabon layin da ya sayo a cikin waya, ya kira lambar Nana. Sayyid yana kwance yana jin yadda wayar take ta vibrating, amma ya yi banza. Saboda ko ya ɗaga ba iya magana zai yi ba. Jin mai kiran ba shi da niyyar daina kiran, ya sanya ya ɗauki wayar zai kashe. Sai dai ya fasa kawai ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa. "A tunanki dan kin yi blocking ɗin lambata, zai sanya na kasa cimma burina a kan ki ne? Yanzu hankalina ya dawo gare ki, na saka an kori mijinki daga gurin aiki. Kuma zan nemo ki duk inda ki ka shiga sai na cika burika a kanki" wani irin jiri Sayyid ya ji ya fara ɗibar sa. "Ba za ki yi magana ba?" Alhaji Zailani ya yi maganar yana kallon wayarsa. Wani irin haske ya ga wayar tana yi, tana fafar fafar za ta ɗauke. Mamaki ya kama shi, dan wayar ba ta taɓa yin haka ba. Fitilun ɗakin suka ɗauke, duhu ya gauraye ɗakin nasa. Sai ya rikice ya tashi tsaye yana waige-waige. "Karo na biyu, ka sake shigowa hanyata, duk da gargaɗin da na yi maka, cewar mallakina ce, ina sake yi maka gargaɗi, kafin na tona maka asiri." Alhaji Zailani ya toshe kunnensa, saboda wani irin sauti da yake ji mara daɗi, ga ɗakin yana ta jujjuya masa. Can ya ji shiru ya daina jin sautin, ya buɗe idanunsa a hankali. Sai dai ya ga Shukura a tsaye a gabansa, jini yana bin ƙafafuwanta, ga wuƙa a hannunta, tsirara ta. Ya miƙe cike da razani, ya fara ja da baya. "Daddy ina jaririna? Ka bani jaririna Daddy" Ya ci gaba da ja da baya. Da gudu ta bi shi, da wuƙar tsirararta. Ya fita da gudu yana ihu. "Alhaji lafiya kuwa? Anya hawan jinin nan bai fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ba, ya ya zaka din ga ihu haka?" Hajiya Amina ta yi maganar cikin mamaki tana kallonsa. Ya kalli gurin ya gan shi a kan gado, a ɗakinsa. Yana son yi wa Hajiya Amina tambayoyi, amma abu ya gagara saboda tsabar razani da tashin hankalin da yake ciki. AREWABOOKS ***** Uwani ta din ga yawo da Nana a cikin ƙauyen nan, tana nuna ta a dangi, tana gaya musu 'yar gurin Isa ce. Dan galibi ba su santa ba. Nana gaba ɗaya hankalinta yana kan Sayyid da ta baro a gida, shikaɗai tana gudun kar ta je yana buƙatar wani abin. Ganin gantalin ya yi yawa, ga duk inda suka je sai Uwani ta tsuguna ta surutu kamar babu gobe. Tun Nana tana jurewa, har ta gaji ta ce "Uwani, na bar mara lafiya a gida, ko za mu je inda zan yi sayayyar, na koma kar na je yana buƙatar wani abin. Uwani ta ce "Kuma fa haka ne, to mu je na raka ki. Na so ma sai ranar kasuwa za ki je sayayyar, an fi samun rahusa. Ai tun da Allah ya sa ki ka zo garin nan, za ki yi ta ganin 'yan uwa da dangi, za a yi ta zuwa duba mijin naki ma" Ita dai Nana ta yi shiru, dan duk surutunta, Uwani sai da ta saka ta gaji, ga azabar tafiyar ƙafa da suka sha. Ta rakata inda ta yo musu 'yan sayayyar kayan abinci, gaba ɗaya tsoron taɓa kuɗin take yi. Gani take yi kamar ƙarewa za su yi. Uwani ta raka ta har gida, sannan ita ma ta zagaya, ta koma nata gidan. Nana ta shiga ɗakin da Sallama, tana faɗin "Sayyid, ka ganni sai yanzu ko, ka yi haƙuri Uwani ce ta din ga ja na, ƙafafuwana kamar su karye" Sak dai ta yi shiru ganin wata irin kwanciya da ya yi a kife a kan cikinsa, hannunsa a lanƙwashe, kuma ba kamar mai ruf da ciki ba. Ga shi a tsakiyar ɗakin, ba inda ta tafi ta bar shi ba. Ta zube kayan ta nufe shi jikint a sanyaye, gabanta na bugawa saboda fargaba da tsoron ko mutuwa ya yi. Aikuwa tana juya shi ta ɗan ja da baya a tsorace tana sauke numfashi. Wayarta ta gani a ƙarƙashin inda ya kifa, idanunsa a kakkafe, babu baƙar ƙwayar idon, sai farar. Ga jikin zafi rauuu tamkar wuta. Ajiyar zuciya ta yi cike da damuwa, ta matsa kusa da shi ta yi Bismillah ta fara rage masa kayan jikinsa. Ta ɗebo ruwa ta din ga shashshafa masa tana sake nanata Bismillah. Ta je ta rufe ƙofar gidan, ta dawo ta cire rigar jikinta, ta kwanta a jikinsa, tana rintse idanunta saboda raɗaɗin da take ji a fatarta. Wani irin nishi yake, tamkar zai yi gurnani, yana miƙa jikinsa yana ƙara sandarewa. A hankali ta ji tamkar hankalinta yana gushewa, ita ba a farke be, kuma ita ba mai bacci ba. Ta ɗan ɗaga idonta, ta ga Ƙaisar tsaye a jikin ƙofar ɗakin yana kallon su. Ta yi shiru ba ta yi motsi ba, kuma ba ta yi magana ba, fatanta Sayyid ya samu sassauci daga azabar raɗaɗin da yake ji. "Ko dai ki bi a hankali, ko wannan ɗan tayin na cikinki ya yo waje saboda zafin jikinsa. Ko kuma Giyaz ya yi masa mummunar illa." Nana ta ɗaga kai ta kalli inda Ƙaisar yake, jikinta ya yi mata wani irin nauyi, ba ta ko iya motsa ɗan yatsanta. "Babu irin kashedin da ban yi miki ba tun da fari, ki ka yi burus da ni, gani ki ke kawai cutar da ke ne kaɗai abin da nake yi. Amma tun da jimirnki taurin kai, wahala sai ranar da Allah ya yanke miki, tukuna ma." A hankali ta lumshe idanunta har ta daina jin muryar Ƙaisar. **** Cikin damuwa Maijidda take kallon Saude ta ce "Yaya Saude haryanzu lambar Nanan ba ta shiga ko? Gaba ɗaya na kasa nutsuwa duk ji nake hankalina a tashe". Saude ta ce "Dan Allah ki daina damun kan ki, in sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya, kin san sharrin wayoyin nan, da rashin network, amma zan ci gaba da kiran ta, da na same ta zan sanar miki, kuma zan sake zuwa har gida na haɗa ki da ita." "To Allah ya sa dai lafiya, kin ga na yi, na yi, na kaɗa na raya, Baban su Walida ya ƙi ba ni wayata, tsawon wannan lokaci haka nake zaune babu waya. Kuma duk wasu dabaru da zan yi na samu dama na je Kano na samu na ga yaran nan, abu ya ci tura sai ka ce ba Muslimi ba, ba ya jin magiya ba ya jin rarrashi". "A'a kul Maijidda, uban 'ya'yan naki ki ke cewa kamar ba musulmi ba, kar ki sake. Ki rabu da shi da halinsa. Duk da Nana tana cewa za ta zo ita da mijinta, idan ma ba su zo ba, ni zan sake komawa na gano miki ita in Allah ya yarda. Iliyasu kuma ki rabu da shi ku lallaɓa kar ki fusata shi ya yi wani abin da ba a fata" Maijidda ta yi ajiyar zuciya, ta jinjina kai kawai, amma gaba ɗaya ba ta cikin nutsuwarta. **** Abu kamar wasa, aka shafe kwanaki biyar, Sayyid yana cikin wannan yanayin, sai dai Nana ta juya shi, ta goge masa jikinsa, ta yi masa ƙanin wanka a ɗaki, ta shafa masa turare ta saka masa kaya. Ga shi juya shi kawai aiki ne, saboda yadda ya yi mata nauyi, ga jikinta babu ƙwari saboda azabar laulayi. Juriyarta ce kawai ta sanya ba a gane mawuyacin halin da take ciki, dan ba ta taɓa yarda ta kwanta. Ga shi jikinsa duk ya kumbura, mussaman ƙafafuwansa. Tana zaune ta yi shiru tana kallonsa, kawai tamkar an yaye mata wani abu daga kanta, sarkin baka ya faɗo mata. Sai da ta ɗan zabura ta tafi tunanin ko yana wani hali yanzu?. "Ko dai can zan kai ka Sayyid?" Ta yi maganar tana kallonsa. "To ni da ban ma san a ina yake ba, ta yaya zan kai ka?" "Kul mene ne sahihancin magungunan da yake bayarwa? Mene ne halacci ko haramcin abin da yake yi, da za ki je neman magani gurinsa?" Wata zuciyar ta gargaɗe ta. Sai kuma ta yi shiru, tana tuna irin wahalhalun da ta sha, da faɗi tashin gurin masu magani, ita dai tana da yaƙinin har gurin bokaye da 'yan tsubbu an kai ta, domin a nema mata magani. Domin wasu ƙarara ayyukansu da abubuwan da suke faɗa, ne nuni da kaucewa hanyar gaskiya. "Allah na tuba, Allah ya sanya ba wannan ne dalilan da ya sanya nake ta shan wannan wahalar ba. Allah ka yafe mini, ba da son raina aka din ga kai ni wasu guraren ba. Allah ka bamu lafiya da ni da mijina, Ubangiji Allah ka yaye masa wannan larurar, ka dawo masa da tunaninsa. Allah ban yanke tsammanni da daga falalarka da ni'imamominka ba" Ta juyo a hankali ta dubi gurin da yake, ta ga idanunsa sun dawo daidai yana kallon ta. A rikice ta ce "Sayyid" "Ma vie" Cikin tsananin murna ta ce "Alhamdillah, ka tashi?" Ya jinjina kai yana lumshe idanunsa da suka yi masa nauyi. Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar. Sai dai jikin nan duk a kumbure,ga kuma haki da ya farfaɗo da shi. Haka yau ma ta taimaka masa ya yi wanka ya ci Abinci ya fara rama sallolinsa a zaune. Kallonsa take yi cikin damuwa, yakamata a ce sun koma Asibiti. Amma kafin a nemo mota a saka shi, su yi sammako su koma Asibiti, aiki ne. Mussaman da babu wadattacen kuɗi a hannun ta. A take ta tuna da maganin da sarkin baka yake haɗawa masu hawan jini, da wanda ɓarin jikinsu ya shanye a sakamakon hawan jini da matsalar zuciya. Ba ta jira ya idar ba, ta zari hijjabi ta yi waje. Ta din ga tuhumar kanta da yadda aka yi tuntuni ba ta tuna ba, sai yanzu. Tun da su magunguna ne da yake haɗa s da saiwoyi ba wani surkullen ya yi ba. Ta dawo ta tarar ya dawo bakin ƙofa ya zauna yana kallon hanya. Tafiya mai nisa ta yi sosai da ta fita, ta samo ɓawon kwakwa da sassaƙen zogale, sai kuma farin zoɓo. Ta hura wuta ta wanke su, duk ta zuba a tukunya ta zuba ruwa, ta kawo ɗan kanumfari ta zuba a ciki. Sai da ta kammala sannan ta koma gurinsa, ta ce "Ka yi haƙuri, magunguna na je samo maka, na fita ka na salla" "To na gode" "Allah ya baka lafiya shugabana, Allah ya sanya ya wuce kamar ba a yi ba" "Amin. Ke ma Allah ya baki lada, ya saka mini ke a aljanna. Ya sanya ki maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a aljanna" waro ido ta yi  ta gigice gaba ɗaya hawaye ya fara zirarowa daga idanunta ta ce "Sayyid ba ni da aikin da zai kai ni wannan matsayin. Amma ban san matsayinka a gurin Allah ba. Ban sani ba ko Allah ya karɓi addu'ar da ka yi mini. Amma a ce na maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa Innalillahi raji'un Sayyid na rasa me zan ce. Baiwa ce mai tarin zunubai kuma mai tarin rauni. Amma Allah kai mai yawan rahama ne da falala, Allah ka amsa wannan addu'a da ya yi mini shi ma ka ba shi abin da ya roƙa mini" Ya yi murmushi ya ce "Amin rayuwata" "Sayyid, anya an taɓa yi mini addu'a da ta tsuma ni kamar wannan? Subhanallah, subhanallah. Na ji daɗi wallahi" Shima idanunsa ne ya cika da hawayen, ya ci gaba da bin ta da idanunsa. Kawai sai Nana ta ji ta manta kaso mafi yawa na damuwarta. Da ta tuna Addu'ar da ya yi mata sai murmushi ya kasa barin fuskarta. Maganinta ya daɗe yana dahuwa, ta sauke ta mayar da ruwan girki. Ta tsiyaya masa a kofi, ta je ta zauna a gaban sa. "Sayyid ga magani na dafa maka, mu jarraba, bamu sani ba, ko Allah zai sanya a dace" ya kalli kofin ya kawar da kansa gefe, yana ɓata rai. Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka sha, babu ɗaci ko bauri fa" "Ba na son magungunan nan, babu yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi" "To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba" Da ƙyar ya yarda ya karɓa, ya ɗanɗana ya ji babu ɗaci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji ɗumin maganin ya yi masa daɗi. Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya ɗora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya haƙura da shan shayi. Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya sanya ya karɓe shi. Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banɗaki yana iya zuwa, ba tare da ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan. Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce "Ashe maganin Sarkin baka yana yi" Ya kalle ta, ta ce "Ka san Sarkin baka?" Ya ɗan yi shiru yana kallon ta. "Ranar da aka kai ni, kai na an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin na ji na fita daga hayyacina. Kai mun fa daɗe muna haɗuwa da kai." Ya yi murmushi ya ce "Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu" Ta ɓata fuska ta ce "Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni". Ya ɗan sake zuƙa shayin hannunsa ya ce "A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa" "Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena" Ya maze ya ce "Ai gani na yi kin liƙe mini, har cikin ɗakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice" "Ni ba ina sane na shiga ɗakinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin ɗakin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi" "A'a faɗi gaskiya dai, ni ki ka leƙo ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Mene ne?" Ta yi masa shiru. "Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi" ta yi masa shiru, tana matse ƙwalla. Ba wai wasan da yake yi mata ne ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faɗa da wanda Mama ta din ga yamaɗiɗi da ita, abin ne kawai ya dawo mata. Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya ce "Ba zan sake ba" Kwaɓe baki ta yi cikin shagwaɓa, wasu hawayen na ziraro mata. "Na ce na daina fa, ki bari ƙirjina ya fara nauyi" da sauri ta saka bayan hannunta, tana goge hawayen fuskarta. "Yauwwa dama ina so mu yi wata magana, mai muhimmanci da ke" Ta tattara hankalinta, gabanta na dukan uku-uku cike da wasi-wasin wace maganar zai yi da ita haka?. Ayshercool 08081012143 57 Ya yi mata alama da hannunsa, a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta. Ta jinjina masa kai, duk da gabanta na ci gaba da faɗuwa. "Amm na san kina haƙuri a kan abubuwan da suke faruwa, duk da kin ce mini ba kya so na din ga irin wannan maganganun, amma sun zama dole na yi. Ina ƙara yi miki godiya da nema miki yardar Allah, na san ba ni da abin da zan biya ki da shi a wannan Duniyar. Ke ce komai nawa da ki ka rage Asmy. Sannan ɓangaren abin da ya shafi auratayyarmu, shi ma na san... Ta katse sh6ta hanyar cewa "Amm ni dai a bar wannan zancen, bari na je na ɗora wakena" "A'a ki tsaya mu yi magana" "A'a ba sai mun yi ba" "To kar na sake jin kin bi dare ki na taɓa ni" Kamar ta yi tsuntuwa ta ɓace, saboda azabar kunya, ita a zatonta ma ya manta gaba ɗaya. Cikin azama ta miƙe ta ɗauki robar wakenta, ta nufi inda take girki. Tana tashi ya kashingiɗa yana dariya. Nana tana ta fifita wuta, yana daga zaune yana kallonta. Wani irin abu ne yake yi masa yawo a jikinsa, a game da ita. Yana jin zai iya yin komai, dan tabattar da ci gaba da zamanta mallakinsa, shikaɗai. Juriyarta, sadaukarwa da kuma tsananin tausayinta, ya sanya yake jin ina ma yana da wani abu da zai iya kamanta faranta mata rai, kamar yadda take ta wannan ɗawainiyar da shi. Ya san in dai a wannan Duniyar ne ba shi da abin da zai biya ta. Duk da matsananciyar damuwar da ya kan shiga, da jin cewa ya zama silar nakasta rayuwarta, ta zama tana rayuwa ba tare da tunanin wani abu da take so ta cimma ba. Kullum tunaninta a kan sa ne kawai. Tana ɗagowa suka haɗa ido, ta murguɗa masa baki, ta ci gaba da fifitar wutar gabanta. Ya tako zuwa gaban murhun ya tsuguna. "Dan Allah ka tashi, saboda numfashinka fa" "Kawo na yanka miki salak ɗin" "A'a kar ka yanke hannu" Ya ce "Ki kawo zan iya" Ta tsuke fuska ta kalle shi ta ce "Saboda sauƙi ya samu, kana iya fitowa da kanka yanzu, shi ne za ka din ga damuna ko?" Ya yi murmushi, ya zauna a gefe yana kallon ta, da ta ɗaga ido, sai su yi ido huɗu da shi, sai ya yi mata murmushi. Su na cikin cin abinci, ya ce "Ki na kiran Ummi?" "Ba na samun ta, ita ma ta kira ni wayar ba na ji. Uwani ta ce haka garin nan yake babu network, sai a yi kira fiye da sau goma ba ka samu mutum ba. "Idan na ƙara jin sauƙi, zamu je mu gaishe ta, mu yi mata godiya" Ta ce "Alhamdillah, lallai sauƙi ya samu." Ya ce "Eh, ina jin hakan a jikina nima. Mu je waje na ɗan tattaka na ga gari" Nana ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Allah abin godiya, wallahi Sayyid da har na fara fitar da rai da kai, na karaya sosai wallahi" Cikin murna ta saka hijjabinta, suka fita. Su na tafe a hankali ta kalle shi ta ce "Gaskiya na yi mamaki, ashe da gaske magungunan sarkin Baka yana yi" Ya tsuke fuska ya ce "Na gaji da jin zancen Sarkin Bakar nan" Nana ma ta yamutsa fuska ta ce "Sayyid ka yi haƙuri, amma na yi farin cikin yadda maganin da na gani a gurinsa ya yi maka aiki. Ina yi masa fatan idan a kan daidai yake, Ubangiji Allah ya ƙarfefe shi ya dafa masa, ko dan saboda yadda yake taimakon mutane. Idan kuma a kan kuskure yake Ubangiji Allah ya ganar da shi, ya ba shi ikon tuba kafin lokaci ya ƙure masa." Sayyid ya yi mata banza, suka ci gaba da takawa a hankali su na zagayawa. Wani irin sanyi ne ya fara ratsa Nana, ganin Sayyid ya durfafi wata hanya, ta kuma kasa ce masa uffan, balle ta hana shi. Su na tunkarar gurin, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri. Wata irin narkekiyar bishiyar kuka suka tarar a gurin mai ban tsoro. Yanayin yadda take ɗauke da wasu irin murɗaɗɗun rassa, da yadda murtuka-murtukan jijiyoyinta suka huda ƙasa suka mamaye gurin. Ga wani irin ƙaton kogo a jikinta, hakan ya nuna daɗewar da bishiyar ta yi da wanzuwa a gurin. "Asma'u" ya kira sunanta kai tsaye. Ta kalle shi cikin matsanancin mamakin yadda ya kira sunanta na yanka kai tsaye. "Ji nake yi kamar na san gurin nan" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Nima haka, amma ni dai na san ban taɓa zuwa gurin nan ba, amma ina jin kamar na san gurin, amma dai... Sai kuma ta yi shiru bayan da gurin ya gauraye da duhu aka yi wata irin walƙiyya, haske ya mamaye gurin. Tsohon nan ta gani a tsaye, riƙe da sandarsa ya zubo wa Nana idanunsa marasa kyan gani. Jikinta ne ya ɗau kyarma, ta ƙara rikicewa bayan ganin a hankali wasu halittu da take kyautata zaton ire-iren su Ƙaisar ne su na bayyana a bayansa. Tsohon ya kalle ta, ya buɗe baki ya fara magana. "Ina sake yi miki barka da zuwa, garin da kakanin kakaninki su ka durƙusa suka haifo matsalar da har abada ba za ta daina bibiyar zuriyar su ba. Zan ci gaba da azabtar da rayuwarki, za ki ci gaba da biyan bashin nan, ko bayan ranki, muddin aka ci gaba da samun haihuwar masu irin tauraronki." Yana rufe bakinsa, ɗaya daga cikinsu da Nana take kyautata zaton jininsin mace ce, saboda yanayin wani irin tsohon mayafi da ta yafa a kanta. Ta tunkaro Nana gadan-gadan. Tana zuwa matar, ta hankaɗa Nana ƙasa, sauran suka rufu a kan Nana, su na zira hannunsu a mararta, su na ciro gudan jini. "Ya hayyu ya ƙayyum ya Allah. Allah ka kawo mini ɗauki, Sayyid, Sayyid, Sayyid ka tashi"  Ta yi maganar tana jijjiga Sayyid da yake kwance a gefen ta yana bacci. Ya ja jikinsa ya tashi ya ce "Ma viee lafiya kuwa?" "Sayyid marata ciwo take yi. Sayyid marata. Sayyid babyna. Ba na son na rasa jaririna a wannan karon, Dan Allah ka taimake ni" Cikin rashin fahimta ya ce "Meyafaru ne?" "Marata ce take ciwo, Sayyid ba na son cikina ya zube, ina son jaririna Sayyid ciwo marata take yi sosai" Ta yi maganar tana zubar da hawaye. Ya saka hannunsa a mararta, ta saka hannayenta ya dafe hannunsa tamkar hakan ne zai hana cikin zubewa. Ya ce "Ki yi Addu'a" Kawai ta jinjina kai, amma Addu'a kam, ko ɗaya ba ta zo kanta ba, dan ta manta komai daga cikin kanta. Cikin rauni Nana ta ce "Sayyid fitsari nake ji, ya matse ni" Ya ce "To mu je ki yi" Ta girgiza kai ta ce "A'a ba na son na je na ga jini ya zubo, cikin ne zai zube" Ya ce "A'a ba za ki gani ba" . Ta miƙe ya kama hannunta, ya haska fitila har banɗaki, su na zuwa a tsorace ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta miƙe jikinta yana rawa. Ya rungume ta ya ce "Ki yi haƙuri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi ɓari, jinin da ki ke zubarwa ya fi wannan kin manta?" "A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube" Ya ce "A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba" Ya lallaɓa ta da ƙyar, ta gyara jikinta, ta ɗauraye jikinta, da banɗakin su ka koma ɗaki. Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro. Suka kwanta yana ɗan shafa ta, cikin sigar rarrashi. A hankali ta ce "Sayyid" "Na'am" "Da gaske mun fita ɗazu ko?" "Eh mun fita" "Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?" "Eh haka aka yi, mun je" Ta sake cewa "To daga nan meyafaru?" "Faɗuwa ki ka yi, na riƙe ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci" Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ƙara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa. Wannan bafulatanar matar ce, ta ƙara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ƙara rintse idanunta tare da ƙanƙame Sayyid. Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da ƙyar ta samu ya yi alwala ya yi salla. Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta ɗauke. Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko ɗaga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan gidan Uwani gona roron gyaɗa a gona. Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska. Ta ɗora musu Abinci, ta kammala ta fara dafa masa maganinsa, kawai ta ga ya fito daga cikin ɗakin. A zaton ta, ko banɗaki zai shiga, ta tashi da nufin kai masa ruwa, kawai ta ga ya nufi fita waje. Da sauri ta bi shi tana faɗin "Sayyid ina za ka je ne haka?" Ya yi mata shiru yana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Ta riƙo hannunsa, amma ya waiwayo fuskarsa a ɗaura kamar bai taɓa dariya ba, saka hannu ya hankaɗe ta, ta faɗi a gurin, ya saka kai ya fice daga gidan. Da gudu ta shiga ɗaki, ta ɗaukko hijjabi, ko takalmi ba ta saka ba, ta bi bayan sa. Ga yamma ta yi liƙis, hanya babu kowa, ta ga ya nufi hanyar inda wannan bishiyar ta kuka take. "Sayyid dan Allah, dan Allah kar ka koma gurin nan. Me za ka je ka yi?" Sai dai tamkar ba mara lafiya ba, saboda yadda yake sauri. Sai da ta ɗan haɗa da gudu, Saboda saurin da yake yi, amma ta ji gefen mararta ya ƙulle. Ta daure ta cim masa. Babu tsammani ta furta "Bismillah wa hifzan min kulli shaiɗanin marid." Aya ta bakwai cikin suratul saffat, kamar yadda Malam Auwal ya taɓa cewa ta yawaita nanata ayar. Gaba ɗaya ta shafe a cikin kanta, sai da ta faɗo mata yanzu. Tana karanta ayar, ta riƙe hannunsa ya ja ya tsaya ya yi shiru ya sunkuyar da kai. "Mu koma gida" ta yi maganar tana jan hannunsa, tamkar raƙumi da akala, ya bi ta suka koma gida. Allah ya taimake ta, babu wanda ya gan su har su ka isa gida. Ta rufe ƙofar. Su ka shiga ɗaki, ta kunna fitila ta kalli Sayyid cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ka fita? Me za ka je ka yi a wajen da?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kansa ƙasa fuskarsa babu annuri a ciki. Ba ta sake ce masa komai ba, ta fita banɗaki ta yi alwala, ta dawo ta yi salla, amma ta ga ba shi da niyyar tashi ya yi. "Sayyid, ba ka yi salla ba fa" Nan ma bai kula ta ba, dan haka ba ta sake magana ba, ta zubo masa Abinci ta zo gaban sa ta ajiye. Ta tashi ta ninke hijjabinta, tana waiwayowa, ta ga ya kifar da Abincin ya tarwatse a tsakar ɗakin, yana wani irin huci. "Sayyid wai meye haka ne? Idan ba ka cin abincin sai ka zubar mini a ƙasa?" Sai dai tana rufe baki, ya wulwula kwanon ya yi jifa da shi guri ɗaya. Ya miƙe ya fara fatali da kayan ɗakin. Take Nana ta fuskanci ba lafiya ba. Jiki a sanyaye ta rakuɓe tana kallon sa. Tana tunanin yanzu kuma abin har ya kai ga haka? Ba ta yi yinƙurin hana shi ba, ya yi kaca-kaca da ɗakin, ya fita tsakar gida ya nemi guri ya kwanta a dandaryar ƙasa. Inda ta yi wa Allah godiya ba su da maƙwabta, da kowa sai ya san abin da ya faru. Haka ta durƙusa ta hau aikin gyaran ɗakin, ta kintsa abin da za ta iya kintsawa. Ta dawo tsakar gida inda yake kwance. Ta durƙusa a kan sa, ta dafa shi ta ce "Tashi mu je ka kwanta a ɗaki, nan akwai sauro kuma ƙwari za su cije ka" Da ƙyar ya tashi, suka koma ɗaki, ya nemi guri ya kwanta a ƙasa. Kawai Nana ta zauna ta zura masa ido, cikin matsananciyar damuwa, duba da yadda take maganin ƙaba amma kai na daɗa kumbura. A haka dare ya tsala, ta gaji ta kwanta a gefen sa, zuciyarta fal da damuwa. Bacci na ƙoƙarin ɗaukar ta, ta ji tasowar guguwa ta buɗe idonta, ta gan su kwance a cikin sahara, ga yashin saharar na wani irin hanƙoro iska za ta mamaye su. Ta saka hannu ta rungume shi saboda guguwar saharar. Sautin tsohon nan ta ji yana wata irin dariya. Ji ta yi an hankaɗa ta, sai da ta wuntsula ɗakin gauraye da duhu, amma ta ga alamun Sayyid ne zaune a kan katifa shi ne ya hankaɗa ta. Ya tashi ya koma bakin ƙofa ya yi zamansa. Da kyar ta sake lallaɓa shi, ya koma ya kwanta. Ita ba ta sake komawa bacci ba, ta yi alwala ta zauna tana tasbihi har aka yi sallar asuba. Sai dai fafur ya yi salla ya ƙi yi. Ya nemi guri ya zauna ƙyam yana kallon ta. Ta dama masa kunu, ta soya fanke, ta zo ɗaki ta zauna a gaban sa. Ta ce "Ga kunu ka sha, amma dan Allah kar ka zubar Sayyid ka ji?" Ta yi maganar tana miƙa masa kofin kunun. Sai ya miƙo hannun hagu zai karɓa. Ta janye kofin ta ce "Hannun dama dai, wannan hannun za ka bani" Ta yi maganar tana nuna hannun damansa, amma bai miƙo mata ba, ya zura mata ido. Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta damƙa masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ƙame ƙam. Ta sake ƙoƙarin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace. Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi. Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!" Ta yi maganar tana kuma ƙoƙarin ganin ta miƙar da hannun nasa, amma hannun yana maƙale, kamar an tsotse shi. Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa ɗauke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta ɗebo kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buɗe bakinsa ba. "Buɗe baninka na baka" Ta yi maganar tana ƙoƙarin danne hawayen da ke ƙoƙarin ƙwace mata. A hankali ya buɗe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na ƙoƙarin zubowa. Kawai ya rufe bakin hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta. Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa. Ta fara ƙoƙarin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haɗiye wani kuma ya zubo. Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga hannu a maƙale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido. Ganin yana gyangyaɗi a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita. Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah malam, idan babu damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida" Ya kalle ta ya ce "A ina ne?" "Cikin Budu ne, nan unguwar maharba" "Taɓ gaskiya da nisa gurin nan ba kaɗan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa" "Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na roƙe ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah" Ya ce "Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu biyu" Nana ta ce "Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah" Ya rufe chemist ɗin ya bi Nana. Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce "Sayyid kar ka ga na fita ban gaya maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne, sai mu san abin yi." Bai ce komai ba, ta yi wa mai chemist magana, ya shigo ya gwada jininsa. Ya gwada ya kalli Nana ya ce "Jininsa bai wani hau sosai ba, 140/90 ne" Ajiyar zuciya Nana ta yi. Ta ce "A ganinka wannan hawan zai iya sanya masa shanyewar hannu?. Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba na tunanin haka, amma ban tabattar ba tun da ni ba likita ba ne ba. Amma a shekarunaa bana tunanin jinin 140 zai shanye masa wata gaɓa a jikinsa, amma dai ku je Asibiti a ƙara bincikawa" Nana ta ba shi kuɗin sa, ta yi tai masa godiya. Ta koma ɗaki ta zauna ta yi shiru, tana tunanin ko Uwani za ta tambaya, idan akwai wani mai magani, ta raka su, sai dai ta fasa saboda akwai sauran ɓurɓushin jahilci a tattare su, ba ta son surutu kuma tana tsoron a kai su gurin da ba shikenan ba. **** Alhaji Fatuhu kuwa kamar yadda ya matsa, sai da aka sallame shi ya koma gida. Gidan nasa ma wani abokin kasuwancinsa ne ya saya, ya bar shi a ciki ya zauna ya bar masa aro. Sagir yana kwance a kan gadonsa, yana kaɗa ƙafa ya ƙura wa screen ɗin wayarsa ido. Yusra ce zaune sanye da doguwar rigar material, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin kanta ya sha gyara. Tana ta zuba masa surutu. Har mamaki yake yi, yadda Yusra ta zama mai ɗan karen surutun tsiya, wanda da ba haka take ba. "Ya ka yi shiru ne?" Ya wani lumshe ido ya ce "Ina jin ki ai". "So talk, ka yi magana mana" ta yi maganar tana cika bakinta da guggurun hannunta. "Ina ga zan shigo Abuja mu haɗu very soon in sha Allah" wata irin zabura ta yi ta ce "Are You serious, dan Allah da gaske?" "Da gaske nake, zan zo na ganki, amma ki na ganin babu matsala a zuwan nawa? Kar a yi miki faɗa fa, ba zan ji daɗi hakan ba" Yusra ta ce "Babu wata matsala, ba za a yi mini faɗa ba, ai ba na tare da su Mami, ina gidan Anty Sumayya. Dan Allah ka zo" Sagir ya yi murmushi ya ce "Kin yi missing ɗina ne?" Ta gyaɗa masa kai tana murmushi. "Shikenan, i miss you too, ban taɓa tunanin ma za ki neme ni ba, na za ta ki na jin haushina haryanzu, amma in sha Allah zan shigo, zan sanar miki lokacin da zan shigo na zo na ganki" ya yi maganar yana kashe mata ido. Shukura ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a burkice ya kif wayar yana kallon ta. Ƙarara yanayinsa ya nuna alamun rashin gaskiya, amma ta share shi, ta haye kan gadon ta ja bargo ta lulluɓe jikinta. Ya matsa kusa da ita yana ɗan shafa ta ya ce "Sweetheart, ya na gan ki kamar a fusace ne? Lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau" ta amsa a taƙaice. Ɗan shiru ya yi yana tunanin ko dai ji wayar da yake yi ne? Amma a yadda ya santa da azababben kishi, da zargi da ta ji sai ta yi masa magana. Sai dai ya bar abin a haka bai matsa mata da tambayoyi ba gudun kar su yi faɗa. Tana ankare da take-taken Sagir, na rashin gaskiya. Sai dai ita yanzu ba wannan ne a gabanta ba, bin diddigin mutuwar ɗanta take son yi. Dan haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da natural mutuwa ya yi. Domin haryanzu tana mafarke-mafarke marasa  daɗi da mahaifinta da kuma Doctor Sharif. **** Aka shiga sati na biyu, Sayyid yana cikin wannan yanayi na rashin lafiya, kuma hannunsa bai saki ba, yana nan a maƙale. Ga hauka da yake yi tuburan wasu lokutan, wasu lokutan idan ya burkice sai ya shaƙe ta, ko ya hankaɗe ta ƙasa, sai dai ta yi ƙoƙarin kare cikinta. Ko kuma Ya ya ta watsi da duk abin da ya ci karo da shi, a ɗaki ko a tsakar gida. Wasu lokutan ma katangar ɗakin yake duka da kansa. Ya ƙi cin abinci ya ƙi shan magani, ba salla, komai sai dai ta yi masa cikin rarrashi da ban haƙuri. Tun tana jin tsoron ya yi mata wani abin, har ta daina ji, ta zuba wa sarautar Allah ido. Sannu a hankali ta rage yawan amai, sai dai zazzaɓi da rashin son cin abinci da take yi, hakan ya sanya ta tabattar da cikin jikinta bai fita ba haryanzu. Sai dai ba ma ta cikin nutsuwar da za ta nemi inda Asibiti yake ta je, ta tabattar da halin da suke ciki ita da jaririn saboda tashin hankalin da take ciki. Yanayin yadda uwani ta lura kamar Nana na ɓoye wani abu, ya sanya ta daina zuwa gidan,ta rage aika yara ma. Sai dai lokaci lokaci, ta kan aika mata da Abinci. Haka sauran 'yan uwansu na garin ma, su kan aiko mata da sha tara ta arziki saboda su na tausayin Nana, sun san mijinta a kwance yake babu lafiya. Yawon roro a gona kuwa yanzu Nana ta ƙware, ranar kasuwa ta je ta sayar da abin ta. Kasancewar ranar Asbar kasuwar garin take ci, sai ta tashi ta yi fanke da sassafe, jikan Uwani Haladu, ya kai mata kasuwa. Ko ta dafa masa zoɓo ta ƙuƙƙula ya tafi da shi. Idan ta gama komai kuma, ta bi yara gona roro. Dare ya tsala, amma Nana tana zaune tunkurkur, wuni Sayyid ya yi yana wani irin nishi, ga wannan azababben zafin jiki da yake fama da dhi. Tana zaune tana tunani, tana jin yadda mararta take motsi, cikin jikinta yake motsawa. Ba ta da sauran wanda za ta kai kukanta bayan Ubangiji. Ta fara tunanin ƙoƙarin tara musu kuɗin mota, su tafi Nijar, neman danginsa, sai dai idan sun je Nijar ɗin ina za su nufa? Babu tsammani ta ji Sayyid ɗin ya laluba cinyarta, ya kwantar da kansa. Ta shafa gashinsa ta ce "Sayyid" bai amsa ba, sai dai ya riƙe hannunta. Hakan ya tabattar mata da ya dawo hayyacinsa ne. Haka ta tashi a cikin daren ta tsiyayo ruwan zafi, ta ba shi shayi ta yi masa wanka suka kwanta, ta lulluɓe su da bargo. Sheshsheƙar kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daɗe yana dauriya, da son ɓoye gazawarsa, sai dai ta ga hakan a idanunsa. "Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina" ta yi maganar muryarta na rawa. Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya ɗauke shi. Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa ya daina damunta. Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi ɗakin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaɗan ne. Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ƙarfi. Jin yadda guguwar ta taso da ƙarfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya ta tashi da azama, ta fara ƙoƙarin rufe ƙofar katakon da take ɗakin. Sai dai tana danna ƙofar guguwar ma na danno ƙofar. A take ta fara karanto "A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha. Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha" take ta ji nauyin da ƙofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake. Da fari yana zaune a guri ɗaya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan ɗakin da hannu ɗaya, da sauri ta fara  bi tana tattarewa, cike da damuwa. Cikin siriryar muryarta ta ce "Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa" Ta ƙarasa maganar a raunane, duk yadda take ƙoƙarin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ƙi cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi duk rarrashin da ta yi a banza. Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce "Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa zafi da raɗaɗin da yake ji, ka saita masa tunani da ƙwaƙwalwarsa, ya yi rayuwa mai cike da nutsuwa da farin ciki irin na sauran mutane" sai kuma ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta. Ta ƙarasa gurinsa, ba tare da fargaba ba ta  riƙo hannunsa cikin nata jikinsa zafi sosai. Ta kalli cikin idanunsa sai taga yana birkice mata yana rikiɗewa kamar ba Sayyid ɗin ta ba, idanunsa har wani hayaƙi yake fitarwa, gaba ɗaya kaminsa sun sauya. Ta lallaɓa ta zaunar da shi, Ta yunƙura zata tashi, domin ta ɗaukko kununsa ta sake jarraba ba shi, ta ji ya cafko ta yana wani irin sambatu bakinsa na kumfa da dalalar da yawu, da alama magana yake son ya yi mata. Rashin ƙarfin jiki ya sanya ta faɗa jikinsa. Ya ƙanƙame ta sosai, saboda zafin da yake ji, ita kuma jikinta sanyi ƙalau. Ita ma jikinta ya ɗauki rawa, ta lafe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tsawon mintuna, jin ya ɗan nutsu jikinsa ya rage zafin ya sanya ta zare jikinta a hankali. Ta ɗaukko kofin kunun da cokali, sai wani ɗan ƙaramin tsumma, ta zauna a gabansa ta ɗebo kunun a cokali ta kai bakinsa, sai dai ya tsaya yana bin ta da ido, kamar ya ga baƙuwar halitta, ta buɗe nata bakin, ya kalleta shi ma ya buɗe nasa. Ta fara zuba kunun a bakinta ta haɗiye, sannan ta zuba masa a bakinsa shi ma. Ya haɗiye sai dai wani na biyo gefen bakinsa, bai haɗiye duka ba. Tana bashi tana goge masa wanda yake  zubowa. Sai da ta tabattar ya ƙoshi, sannan ta goge masa bakinsa. Ta ɗauki kofin ta nufi ƙofa ta buɗe a hankali ta ga an daina iskar, ta fita da kofin ta ajiye, ta tattara abin da guguwar ta watsa sannan ta dawo ɗakin. Jiki a sanyaye, ta zauna a gabansa tana ƙare wa kyakyawar fuskarsa kallo. Da ƙyar yake jan numfashi yana saukewa.  Ta sanya hannayenta biyu, ta gyara masa gashinsa, da ya rufe masa gefen idonsa, ta saka idonta a cikin nasa, cikin rauni da karaya, idanunta na zubar da hawaye ta motsa bakinta, ta fara magana "Sayyid, dan Allah ka yi magana ko na ji daɗi, wannan karon ka daɗe ba ka ce mini komai ba. Da na sanya ran ka fara samun  lafiya, amma kullum lamarin nan gaba yake yi. Ka gaya mini wane ne kai? Daga ina ka ke? Ina zan samu danginka da 'yan uwanka, wataƙila kai naka dangin ba za su guje mu ba, za su karɓe mu, tare da sarƙar da ta haɗa ƙaddarorinmu wuri guda, duk da ban kasance ɗaya daga cikinku ba, ni fatana a nema maka magani ka samu lafiya, ba na son ganin ka cikin wannan mummunan yanayin, idan na ci gaba da ganain ka a haka, zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ka yi magana" Ta yi maganar wasu hawayen na zirarowa daga cikin idanunta. Ayshercool 08081012143 58 Ya haɗiye wani irin yawu, da yake yi masa zafi a ƙirjinsa, yayi ƙoƙarin ɗago hannunsa na dama, sai ya tuna ya riga ya shanye, ba ya iya komai da shi. Ya buɗe baki da nufin ya kira sunanta, saboda tasiri da kuma ciwon da kukanta yake yi masa a zuciyarsa, amma ya gaza bakin ya karkace yawu ya fara zubowa daga bakin nasa, maimakon kiran sunanta da ya yi yinƙurin yi. Tana kuka, ta sanya tsumman da tayi amfani da shi wurin ba shi abinci, ta goge masa bakinsa. Ba shi da zaɓin da ya wuce, ba wa hawayen da yake maƙale a cikin idanunsa damar zubowa, ko shi ma ya samu sassauci abin da yake ji. A hankali ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta, a take ta silale ta faɗi a jikinsa. Ya sanya hannunsa mai lafiya, ya rungume ta, ya ci gaba da kuka. Jikinta gaba ɗaya ya saki. Ƙaisar ta gani a gurin haɗe-haɗen magungunan sa, yana ta haɗa wani abu a cikin kwalba. Zuciyarta ce take ta azalzalarta, da ƙoƙarin ingizata, sai dai ba ta yi magana ba. Babu tsammanni, ta ji ya fara magana "Zaɓi ɗaya ya rage miki, a halin yanzu, ko dai ki yadda da abin da na zo miki da shi, ki rungumi ƙaddararki, ko ki na kallo Buzun nan zai mutu, domin ba zai taɓa tuna waye shi ba har abada, muddin Giyaz yana tare da shi. Dan ba na tunanin akwai wanda zai iya raba shi da shi. Idan har bai iya tuna waye shi ba, shikenan kin ga ba ki da wata makoma. Abu ɗaya zai sanya a wannan karon na bar miki abin da yake cikinki, duk da ba ni da tabbacin zai zama mai cikakkiyar lafiya ko akasin haka, Giyaz da muƙarrabansa sun riga sun fara taɓa shi a cikin ki. Kin san meyasa ban ƙarasa lalata wannan cikin ba?" Bai jira ta ba shi amsa ba ya ce "Saboda zan so na ga yadda za ki yi, a lokacin da ɗan zai amsa sunan shege, kuma ba za ki iya hanawa ba, domin ba ki da hujjar kare kanki. Idan Buzun nan ya rayu bai san waye shi ba, ga kuma nakasa. Idan kuma ya mutu suwaye dangin baban ɗan ki? Daga ina yake? Suwaye ahalinsa? Kin san ku a jinsinku na bil'adam da uba ake ado ba riga ba. Babu wanda zai damu da wacece ta haifi mutum, amma za a damu da waye ubansa meye nasabarsa? Tun da ki ka zo garin nan, zuriyarmu suke alwashin yadda fansar su za ta kasance a kan ki. Kafin zuwa wannan ƙadamin babu abin da ban gaya miki ba, na gargaɗi. Dan haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya" Cikin kuka Nana ta hau girgiza kai ta ce "Ba zan yi bori ba Ƙaisar, ba zan yi shirka da Allah ba. Babu tsanani ko wahalar da za ta sanya na rabu da imanina. Amma na rasa gaba na rasa baya, ba dan ina neman taimakon ka ba, ko ka kawo mini ɗauki ba. Na san Ubangiji Allah shi zai taimake ni. Amma dan zatin Allah idan ka na da hannu a ciwon Sayyid, ka yi mini rai ka rabu da shi, shi ne kaɗai duniyata. Ina matuƙar tausayin sa, ban damu da jinya da nake yi ba, wahalar da yake sha ta isa haka. Idan kuma laifikan zuriyarmu ne suke shafar sa, dan Allah ku yi haƙuri ki ƙyale shi haka" Cikin sautin muryarsa mai ban tsoro, da ya kan yi amfani da ita, idan ya so razana ta, ko yi mata magana mai muhimmanci  ya ce "Na sha gaya miki na maimaita miki, daga lokacin da ki ka fara bani umarni, kin yadda kin amince da buƙata ta ne. Ba ni da hannu a ciwon mijinki, kuma bai ya cikin zuriyar ku, sai dai ƙaddara mai ƙarfin gaske, ta haɗa ku tarayya guri guda. Amma muddin ki na son ya warke daga wannan rashin lafiya, ba ma iya haka ba, ya tuna waye shi, sai kin karɓi ƙaddararki.". Nana ta sake marairaicewa ta ce "Ba zan iya shirka ba, ba zan iya zama 'yar bori ba. Zan jure jarrabawata komai zafinta amma ba zan yadda rasa imanina ba" Ƙaisar ya ce "A cikin biyu dole abu ɗaya ya faru, tunda kakaninki su suka ƙyanƙyashi wannan matsalar. Na yi iya ƙoƙarina gurin dakatar da ita a wancan lokacin, amma ta sake tasowa a wannan karon. Dole a cikinku ɗaya zai warke ya rayu ɗaya ya mutu a haka, dan babu alamar Giyaz zai sassauta wannan mummunan ƙudirin nasa a kan zuriyar ku. Gefe ga aikin da ya karɓa yake yi a akan mijinki, ko dai ki ci gaba da rayuwa da shi, laifukan ku na shafar sa, ko kuma ki yarda ki karɓe ni a matsayin hadiminki ki yi abin da nake so, ni kuma na san yadda zan yi da Giyaz, na baki maganin da mijinki zai warke" "Ta yaya? Me yasa sai ni? Me yasa ni zan biya zunubin da lokacin da aka aikata shi ba na nan, zunubin da zamanin da aka aikata shi, ya yi nisa da nawa zamanin? Me ya sa kakannina suka zaɓi zama 'yan bori? Suka gada mini wahala da masifa take ta bibiyar rayuwata. Na zama mujiya a cikin mutane, duk inda na tsuguna sai wata masifa ta afku, da za a jefa mini zargi, kasantuwata ni ba mutum ba ni ba wani jinsi daban ba? Me yasa zan girbe baƙar shukar da ban san a lokacin da aka dasa ta ba? Ina son mijina duk da daga ni har shi, ba mu san waye shi ba. Duk da Nijar ba ɗaki ɗaya bane ba, ba kuma ƙaramar alƙarya ba ce ba, ƙasa guda ce, na gwammace zagaye ta neman ahalinsa na damƙa shi a gare su, da na ci gaba da zama da shi, mummunar ƙaddarata tana shafarsa, ko kuma na zama 'yar bori na ci gaba da gadar da wahala da masifa ga zuriyarmu, gara ko ma mene ne ya ƙare a kaina." Ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, tana kuka mai bayyanar da tsantsar baƙin cikin da yake binne a cikin zuciyarta. ***** A hankali yake driving cikin nutsuwa, yana sauraren Jamila, da ke bin waƙar da ke tashi a cikin motar ƙasa-ƙasa, sai kuma ta yi shiru. "Ya ki ka yi shiru kuma?" Ta ce "Au wai ka na ji na?" Abba ya ce "Eh mana, har kin fi masu waƙar ma iyawa" Dariya ta yi ta ce "Ka ji ziga, muryar ta su da aka tace, aka goge tawa kuma a haka, ka ke cewa na fi su iyawa" "Au ba ki yarda ba? To shikenan ni dai na san kin fi iyawa" ya yi maganar yana parking ɗin motar a harabar gurin shan ice-cream ɗin. Abba bai taɓa soyayya ba, duk wannan abubuwan da yake yi wa Jamila, bai taɓa furta mata cewar yana sonta ba. Sai dai ita sarai ta gane sonta yake yi, so kuma ba na wasa ba. Sai dai tana mamakin yadda duk wannan abin da yake yi mata, ba ya iya nuna wa a gaban Hajiya Sa'a, hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai yana da wata manufa a kanta ne. Sai dai ta lura halaye da ɗabi'unsa, sun sha banban da na Hajiya Sa'a, shi Abba akwai tsantseni, da gudun saɓa wa Allah. Dan duk da son da yake yi mata, sai da ya yi mata faɗa a kan shigar banza da ta kan yi wasu lokutan. Ice cream su ka sha, yana ba ta labarin yadda ya yi karatu, da irin ƙalubalen da ya fuskanta na rayuwa. Su ka gama ya ɗauke ta ya mayar da ita gida. Bayan ta shiga gida, Mama ta ce "Yauwwa ke nake jira dama, gas ya ƙare na kira wayar ki kuma ba ki ɗaga ba" "Ina hanya ne, ga ATM ɗina, a bawa Nasiru ya je ya ɗuro. Har za ta shiga ɗaki sai ta fasa ta ce "Ni kuwa jama'a ina Nana ne? Wayarta ba ta shiga, shekaranjiya waccan ma na biya gidan da mijinta yake gadi, na ga kamar babu kowa a gidan" Mama ta taɓe baki ta ce "Au ke ba ki san abin da yake faruwa ba dama?" Ta tsaya tana kallon Mama ta ce "Mene ne yake faruwar?" "Ai tuni aka kore su daga wannan gida. Ke ba zama ki ke yi ba ne shi yasa, suka koma unguwar su Ummi, to kin santa duk inda ta zauna bala'i ne yake bibiyar gurin, hatsaniya ta haɗa ta da matan gidan da suke, suka ce mayya ce aka tashe su. Ai nan Babanku ya je aka yi ta fafatawa, da ta kwaso jiki ta taho nan, wai za ta dawo mijinta babu lafiya, na ce bani da gurin jinya a gidan nan. Allah ya raba ni da masifa, ba za ta dawo mini ba, to ƙarshe dai wai yanzu tana ƙauye, can gurin Uwani a can take jinyar mijin nata" Jamila ta yi sak, ta ce "Mama Nana tana ƙauye fa ki ka ce?" "Eh mana, to idan ba ƙauyen ba ina za ta je? Tana can" "To waye yake ba ta Abinci?" Mama ta ce "Oho ina na sani?" "Amma ya aka yi tsawon wannan lokacin ban sani ba? Yanzu ba kamar da ba ne, ban ji daɗin abin da ki ka yi ba Mama, bai kamata a kore ta ba a ce ta koma ƙauye da zama ba. Da ina nan ko na sani, da na kama musu wani gidan, gaskiya sai ta baro ƙauye" "To ke ina ruwanki? Mene ne naki a ciki uwar Iya? Kina kallon irin baƙar azabar da na sha, a kan zamana da ita a gidan nan. Na meye za ki kuma jajubo mana ita. Gara ki bani kuɗin da za ki kama mata hayar na bawa ɗanLadi, ɗan autanmu ya tafi kasuwa da zaman banzae da yake yi, na yi masa aure tun da Allah ya sanya kuttun arziki ya fashe mana, ba ki kai kuɗi inda babu amfani ba" Jamila ta dubi Mama ta ce "Wannan ɗan uwanki ne, sai ki nemi kuɗinki ki yi masa, nima 'yar uwata nake tunani. Haba Mama, ko wani Nana ta kashe miki ƙiyayyar ta isa haka ai. Ai yakamata a tausaya mata, miji babu lafiya ga zaman ƙauye, ita Uwanin za ta ɗauki nauyin Abincinsu ne? Tun da muka tashi a wahala muke a gidan nan, amma ita nata ya fi na kowa ma" Jamila ta ƙarasa maganar cikin damuwa, ta shige ɗaki, ta bar Mama da buɗaɗɗen baki. ***** Kallonsa Nana take yi, suna zaune sun yi juguum daga ita har shi. Bayan ta gama yi masa kitson zanen hannu guda takwas, ta yanke masa faratansa na hannu da na ƙafa. Kamar wadda aka mintsina ta tashi tsaye, ta kalle shi ta ce "Sayyid, bari na je na dawo" ya bi bayanta da kallo har ta fice. Sai dai a ƙalla ta kai awanni biyu kafin ta dawo, ko da ta dawo ta tarar da shi ya haɗe fuska, ta yi shiru ba ta kula shi ba, ta koma tsakar gida. Ta laluba kayanta, ta ɗaukko wata takarda mai ɗauke da ayoyin ruƙiyya da na karya sihiri, sannan ta hura wuta a cikin murhu. Ta dawo tsakar gida ta zauna, ta fara da Bismillah da karanta Suratul fatiha, sai Suratul falaƙi da nasi. Ta karanta ayoyi biyar ɗin farko na Suratul Baƙara, ta fara karanta Suratul mulk, a hankali sai ta fara gani dishi-dishi, ta fara daina ganewa. Ta busa ayoyin a cikin ruwan, Sai ta ajiye takardar. Ta ɗauki wata leda da ta zo da ita, ta fito da man habbatussauda da jan Almiski. Saboda wauta sai ta buɗe miskin, ta kai hancinta, da sauri ta dungurar da shi a gurin, ta ja da baya, dan tuni ta ji jikinta ya fara tsuma. Sai da ta ɗan samu nutsuwa, sannan ta zazzaga tazargaɗe a cikin bokitin, ta kawo ganyen magarya guda bakwai, ta saka a leda ta ɗan bubbuga musu muciya, ta haɗa a cikin ruwan. Ta yi shiru tana tunani a ranta ta ce "Allah ya sa ba mai magani na zama ba, Ƙaisar bai mayar da ni 'yar bori mai bayar da magani ba, larurar Sayyid ta saka na fara koyi da magungunan sarkin baka." "Amma ai ayoyin Alkur'ani ki ka karanta, shi ma kuma Sarkin Bakar yana amfani da Alkur'ani" wata zuciyar ta tunatar da ita. Haka dai ta ci gaba da wasi-wasi. Can yamma, bayan ta tabbatar da ganyen magarya da tazargaden sun tsumu, ta ɗumama ruwa ta tsiyayi ruwan tofin ta tace ta haɗa da ruwan ɗumin, ta kawo man habbatussauda ta tsiyaya a ciki, ta kawo jan miskin nan da ta saka kwalbar a ruwan ɗumi, ya narke ta tsiyaya a ciki, ta ɗebo garwashi a kasko ta shiga ɗakin. Yana ganin Nana ya tashi zaune yana kallon ta, ya ga ta samu ƙyalle ta ɗaure hancinta da bakinta. Ta nufo shi ya ga ta hau tuɓe masa kaya, ya din ga bin ta da ido, ta bar shi daga shi sai gajeren wando. Hannunsa da yake maƙale take kallo cikin damuwa, ta shafa hannun. Sai kuma ta yi Bismillah ta fara shafa masa wannan ruwan. Tun daga cikin kansa. Girgiza kai ya fara yi, yana ture ta da lafiyayyen hannunsa, yana toshe hancinsa. Ya din ga girgiza kai jikinsa yana karkarwa bakinsa yana rawa, ya din ga wani irin gunji yana miƙa. Amma sai da Nana ta jiƙe shi da ruwan nan tsaf. Ta kunna kiran salla a wayarta. Ta kawo tazargade, da habbatussauda da ganyen magarya ta zuba su a kan garwashin nan, hayaƙin ya turnuƙe ɗakin, ta ajiye shi a nesa da shi kaɗan. Ta fice daga ɗakin ta kulle shi a ciki. Ta tafi ta din ga wanke hannunta. Wani irin jiri ya din ga ɗaukar ta, ga matsanancin ciwon kai, ɓari ɗaya da ya sanya take jin, tamkar kan zai yi bindiga ya rabe. Ta samu guri ta zauna a tsakar gida, ta dafe saitin zuciyarta da yake ta bugawa da sauri. Bayan wasu mintuna, ta tashi ta je ta leƙa ta window, ta hango shi a kwance a ƙasa. A tsorace ta buɗe shi, ta nufe shi da sauri tana kiran sunansa. Gaba ɗaya ƙwayar idonsa baƙar ta ɗauke sai farar, ta durƙusa a kansa kawai ya miƙo hannu zai shaƙe ta, amma ta riƙe hannunsa. Hannun ya din ga rawa, ya sauke shi a hankali. "Sayyid" tana ambatar sunansa, ƙwayar idonsa ta dawo ya kalle ta. "Sannu Shugaba" hararta ya yi ya juya mata baya. Dariya ta fara yi ƙasa-ƙasa. Ta ce "Haba Shugaba, ya ka juya mini baya, juyo ka kalle ni" ya ƙi juyowa. Ta tashi ta buɗe labule saboda yadda warin ita ma ya fara damunta. Ta ɗaukko tsumma, ta hau goge masa jikinsa, saboda ya daina warin miskin nan ita ma ba ta so. Ya tashi zaune, tana goge masa. Ta ce "Ko a yi wanka?" Ya ɗaga idonsa yana hararta, jikinsa ya koma jawur kamar wanda ya ƙone. Ta din ga ɓoye dariyarta, ta yi masa wanka, ya din ga sinsuna jikinsa yana yamutsa fuska. Ya shafa fuskarsa ta ce "Ka yi haƙuri, magani ne, ina son ran Ubangiji Allah ya kawo mana afuwa" Ya ture ta daga jikinsa. Amma ta manne masa ta hau cinyarsa ta zauna tana dariya. Ta juyo da fuskarsa suna kallon juna, ta lumshe ido ta buɗe ta ce "Sannu shugaba" Ya jinjina mata kai. "In zubo Abinci ne?" Ya girgiza kai. "Sai an yi salla?" Ya gyaɗa mata kai. Ya yi sallar magariba da isha'i, ta zubo masa Abinci. Washegari ma da sassafe, ta kuma rutsa shi tana shafa masa ruwan nan. Yau ma ture ta ya din ga yi yana girgiza mata kai. Ta kunna masa hayaƙi, ta gudu ta rufe shi a ɗakin. Haka ta sake tarar da shi, ya koma ja ya haɗa uban gumi. Ta yi masa wanka. Ta ba shi Abinci ya karya. Allah ya dafa wa Nana, ba su taɓa rasa abin da za su ci ba. Kuma haka take ta jujjuya kuɗin. Sai da ta gama yi masa duk abin da zai buƙata, sannan ta tashi za ta yi wanka, tana tsaye daga ita sai bra da zani a ƙugunta, sai cika bakinta take da aya mai gishiri, ga cikinta ya ɗaga sosai. Ta waiwayo suka haɗa ido. "Ya ake kallona haka?" Ya yi mata alama da hannunsa mai lafiya ta zo. Ta ƙaraso gabansa ta durƙusa ta ce "Gani" ya nuna mata cinyarsa. Ta ce "Ina da nauyi fa, jiya ma dan na tsokane ka na zauna, ka ga baka da lafiya" ya saka hannu ya janyo ta, ta hau cinyar tasa tana dariya. Yatsansa ya saka ya ɗan latsa cikinta, ya kalle ta yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi ta ce "Kullum sai ya ce ko ta ce tana gaishe ka" Da hannunsa yake tambayarta yaushe za ta haihu? "Nima ban sani ba, amma dai bai fi wata  huɗu ba, saura wata biyar in Allah ya sa mu na raye. Idan ka samu lafiya sosai, za mu je mu ƙara dubawa idan su Habu sun dawo, idan ba su dawo ba sai mu tafi Nijar. Duk da na san da sun dawo zuwa yanzu za su neme mu" Ya yi shiru yana ci gaba da kallon cikinta, da lokaci lokaci yake dan harbawa. "Zan je na yi wanka" Da hannunsa ya yi mata alamar, su je ya yi mata. "Kana fama da kanka za ka yi mini wankan? Wato a ramawa kura aniyarta ko? To na yafe idan Allah ya baka lafiya sai ka yi mini Rayuwata" Cikin murmushi ya sunkuyo da kanta ya sumbaci goshinta ta da laɓɓanta. Hira yake so ya yi da ita, amma ya kasa sai dai ya kalle ta yana murmushi ko kuma ya din ga yi mata nuni da hannunsa. Ya ɗauki wayarta, ya kunna waƙar da take yi masa, yana yi mata nuni da ta yi masa. Ta ce "A'a karatu za mu ji ba waƙa ba, a wannan yanayin da muke ciki, ai ba mu ga ta waƙa ba Sayyid" Ya tsuke fuska yana hararta. Ta ce "To shikenan, bari a kashe waƙar, sai na raira maka da bakina ko?" Kawai ya tsare ta da ido yana wani lumshe ido. Tana dariya ta ce "Wai Sayyid ni fa ban gane maka ba kwana biyun nan, rigima ka ke ji, amma Alhamdillah alamun sauƙi ne da nasara. Aka shiga kwana na huɗu, tana shafa masa tofi tana kunna masa hayaƙi ta gudu ta bar shi a ɗaki. Yau sai dai ta gama shafa masa, za ta gudu ya riƙe ta gam. Duk yadda ta so guduwa ta kasa. Ya kalle ta yana murmushin mugunta. Aikuwa jikinta ya fara tsuma ta saka masa kuka, jin yadda gaba ɗaya duniyar take juya mata, tana shirin fita hayyacinta. Har dare ya yi suka kwanta, ba ta kula shi ba, dan gaba ɗaya jikinta ya mutu murus, babu abin da yake yi mata daɗi. Can cikin bacci ta ji ya yi magana"Ma viee" "Sayyid" "Na'am" "Magana ka yi?" "Eh, yanzu na ji ta zo" Ta tashi zaune cikin murna tana taɓa shi ta ce "Alhamdillah Sayyid, Allah ya ƙara lafiya" "Taɓa ni na ji, ko zan ji wani abu" Ta ce "Ga shi ina taɓa ka" Ya ce "Ba wannan ba" ya yi maganar yana rungumota da duk hannayen sa biyu. "Sayyid hannunka ya warke?" Ta tambaye shi a kiɗime cikin farin ciki. "Eh" ya amsa a taƙaice yana ƙoƙarin yin wani abin daban. "Bari na lalubo waya na haska ka na gani" "Kar ki haska ni" "Me yasa ganinka fa zan yi, hannun zan gani" "Kar ki haska ni" ya sake maimaitawa. A ɗan tsorace ta ce "Anya kai ne?" Ya yi dariya ya ce "A'a Ƙaisar ne. Idan ma ba ni ba ne, ai kina ganewa" Ta yi dariya ta ce "Wai Sayyid ya haka ne? Ka tsaya mu yi murnar ka samu sauƙi" Ruf ya rufe bakin Nana, bayan ya tabattar da lafiyarsa ta dawo. Duk da ya yi farin ciki da miƙewar da hannunsa ya yi, wanda farkawa ya yi daga bacci kawai ya ji hannun ya saki, duk da ya yi masa wani iri babu daɗi. Bayan wani lokaci, ya saka hannunsa ya ɗaukko fitila a gefen Nana, ya kunna ya haske ta. Rufe fuskar ta ta yi, ta juya bayan ta da sauri. Ya kwanta a jikinta yana yi mata raɗa a kunnenta. "To tashi ki haska ni ki ganni, kin ga hannun" Nana ta ƙare rufe fuskarta a fulo, ta ƙi ɗagowa. "Kin ga" ya yi maganar yana taɓa ta da hannun. Shi wannan abubuwan da take yi ma, ba ƙaramar dariya take ba shi ba. Da ƙyar ta tashi, tana kallon hannun nasa da take ganin, tamkar almara ya miƙe. Ta ja hannun ta ga ya miƙe, ta ce "Kuma ba ya ciwo?" Ya girgiza kai yana taɓa hannun ya ce "Ba ya yi" "Allah ya ƙara maka lafiya mai ɗorewa" "Amin. Na gode. Na gode" ta rufe bakinsa ta ce "Ya isa haka. Allah za mu godewa" "Alhamdillah. Amma ya zama dole na yi godiya, kuma na jinjina miki, saboda" bai ƙarasa maganar ba ta cije shi a kafaɗarsa, kamar yadda ya kan yi mata, idan yana jin raha. Kamar ba su ne cikin zullumi da damuwa ba, suka koma shagalinsu. Dare ya tsala amma tamkar rana a gare su, ƙarshe ma zaman hira suka zauna. Da anjima sai ta tattaɓa hannun nasa, dan ta tabattar lafiya kalau yake bai kuma maƙalewa ba. Haka suka kwana cikin nishaɗi, da kewar juna. Da safe ta gama abin da take yi, ta shigo da maganin da take shafa masa, ya kalle ta ya ce "Wallahi ki ka zo kaina da wannan abun, sai na yi miki wanka da shi, ke ma na kulle ki a ɗakin, ki ji abin da nake ji" Ganin yadda ya haɗe rai ya sanya ta rabu da shi. Wunin yau ma lafiya suka yi shi, babu damuwa, duk da jikinsa babu ƙarfi sosai. Ya ci Abincinsa ya yi sallolinsa babu wata matsala. Sai dai yau ma Nana ba ta samu rintsawa yadda yakamata ba, sai da ta san ya warke. Wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Wani mutum ta gani a tsaye a jikin bishiya, ya lulluɓe jikinsa da mayafi. Ta yi tsuru tana son ta ga waye haka. Yana ɗaga mayafin ta ga fuskarsa, ta ja da baya, ta tsorata. Tsohon nan ta gani, jikinsa yana ta fitar da wani irin baƙin abu, fuskarsa ta yi baƙi ƙirin, ga hayaƙi na fitowa daga cikin bakinsa da hancinsa gaba ɗaya siffarsa ta yi muni babu kyawun gani. Sai da Nana ta ja da baya, cikin tsoro da razani. "Kin tafka kuskure yarinya, kuma za ki san kin taɓa Giyaz bin Jaddul Jinn. Babu wanda ya taɓa karya alkadarina, abu ya yi tasiri sosai haka a jikina. Dan a duk lokacin da aka yi yinƙurin illata ni, barin guri nake yi. Sai dai kash kina ɗauke da abin da aka yi mini tarko da shi a wancan karon." Ya jefo mata wani littafi jikinta ya ce "Ga shi nan, littafin da ki ke ta bibiya sai kin ji ƙwaƙwaf, ki ƙarasa karantawa kafin na je na yi jinya na dawo. Amma ki sani dawowata ba za ta haifar miki da ɗa mai ido ba. Domin illar da ki ka yi mini sai na ninka wa mijinki, wahalar da ki ka sha ba ki ga komai ba." Kawai ya ɓacewa ganin Nana. Nana ta kalli littafin hannunta, na gurin Ƙaisar ne, da take ta bibiyar sai ta karanta hanata. Da kansa littafin ya buɗe, a daidai shafin da tsaya da karantawa wancan karon. Jiki na tsuma ta ci gaba da karantawa. Jama'ar da suke gurin girkar, wasu suka watse a dalilin gakin sarkin Aska ya bayyana a gurin, kar ya gansu ya hukunta su. Bayan musayar yawu a tsakanin Duna da uban duƙusa, Sarkin Baka ya yi girgiza ya ɓace. Uban duƙusa ya saka aka ɗauki kakan Lanti, a ka kai shi gida. Ita ma Lantin tana zuwa gida ta faɗi ƙasa. Ba ta sake farfaɗowa ba sai washegari. Sai dai bayan farfaɗowarta, ta tarar da kakanta cikin mawuyacin hali, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Cikin damuwa mijinta ya ce "Lanti sai da na gaya miki ina jin tsoron wannan abun, ki ka ce babu komai, ina tsoron kar rikici ya ɓarke a garin nan" "Babu rikicin da zai ɓarke, ka kwantar da hankalinka, ni dai kawai fatana na kawo ƙarshen Sarkin Aska." Kakan Lanti da ya yi tari, sai aman jini, dama ga jikin tsufa, ya zamana ko tashi baya iya yi saboda buguwar da ya yi. Kwanaki huɗu da faruwar lamarin, Lanti tana yi masa hayaƙi da ganyen ɓaure. Ya riƙo hannunta ya ce "Ya ke jikata, ki sani na yi miki Girka da babban Aminina, kuma ya ɗaukar mini alƙawarin ba ki duk wata kariya, da zama mai hidima a gare ki, kuma ya yi alƙawarin bawa zuriyarmu kariya daga cutarwar miyagun Aljanun cikin su. Dan haka a duk lokacin da ki ke buƙatar ganawa da shi, ki sanya kayan saƙin ki, ki ɗaura gurunki. Sai dai kar ki kira shi a guri mai ƙazanta, ba ya son zama a guri mai ƙazanta, kuma ba ya zama a guri mai najasa. Sannan 'yar ki Duna ne ya shafe ta, kuma ga wannan abu da ya faru, abu ne mawuyaci ta warke, sai dai idan uban duƙusa ne ya samo mata magani. Ni na san ba zan rayu ba, Duna ya riga ya yi mini illa, dan haka ki kula da mutanen Buda. Yana gama faɗin haka wuyansa ya karye. Lanti ta fashe da kuka, ya buɗe baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa, har ya daina motsi ya mutu. Nana ta yi kuka ba kaɗan ba, da mutuwar Kakanta. Ƙaisar ne a tsaye a kan wani dogon tsauni, gabansa kuma Giyaz ne, da yake kamannin da shi sak, tamkar ya yi kaki ya ajiye. "A kan me za ka je ka aikata wannan shirmen da ka yi? Ko har ka manta da cewar fansarmu za mu ɗauka a kan abin da mutanen nan suka yi mana?" "A'a Giyaz, mutanen nan ba su ne ainihin waɗanda suka fara rigimar nan ba, kuma ɓarnar da aka yi musu ta yi yawa. Babu amfani rashin zaman lafiya da tashin hankali. Kuma ka duba irin cutarwar da abokinka Duna ya haɗa kai da sarkin Aska yake yi wa mutanen garin nan. Yakamata a zauna lafiya, haɗa kai da bil'adama ana cutar da jinsinsu ba zai haifar da ɗa mai ido ba." "Rufe mini baki Ƙaisar" Ƙaisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da sunansa na yanka, saɓanin sunan da yake masa kara da shi, na uban duƙusa wanda da shi ake kiransa saboda kara ga mahaifinsa. Dan duk cikin bataliyar 'ya'yan da ya haifa, ya fi ƙaunar sa. Ya ɗora da cewa "Kar ka manta abin da suka yi wa Mahaifina Jaddul Jinn wanda yake kaka ga duk wani Aljani da yake nahiyar nan, da yadda ake girmama shi, sai mene ne dan a azabtar da su. Dan mene zaka hau kan bil'adama a matsayin bawa, duk da kasancewar ka ƙasaitaccen matashin aljani da ake ji da shi a jinsinmu" ya yi maganar cikin ɗaga murya, muryarsa na amsa kuwwa a ilahirin dajin. "Zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu rayu mu da su babu cuta babu cutarwa. Lalata musu amfanin gona, sanya musu rashin lafiya da makamantansu duk ba zai sanya ku huce ba, tun da waɗanda suka yi laifin na sun mutu basa nan" "Uban duƙusa yanzu ka fifita bil'adama a kan ni mahaifinka?" "Ko ɗaya, sai dai ka san muna mutunta yarjejeniya. Mun yi yarjejeniya da abokina, zan ci gaba da bawa zuriyarsa kariya, zan kula 'yar sa zan din ga kawo mata magunguna tana bayarwa. Kuma ya yarje mini ci gaba da yi wa zuriyarsa hidima, da bayar da magani ta hanyar waɗanda aka haifa da tauraron 'yar sa Lanti" "Ƙarya ka ke yi Ƙaisar. Ɗana ba zai zama bawa ga gajiyayyun halittu kamar bil'adama ba, ka sani yadda suke yi mana kallon halittu maƙaryata, haka su ma ba su da cika alƙawari. Ka tuna kai makaranci ne, manazarci kuma marubuci. Ka karanta litattafai da ni kaina ban san adadinsu ba. A ɗakin karatun ka akwai litattafan da aka rubuta dubbanin shekaru kafin zuwanka Duniya. Ka yi yawace-yawace a Duniya domin neman abubuwan rubutawa, kuma ina da tabbacin ka karanta tarin kashedin da magabantanmu suka yi mana a kan bil'adama. Dan haka ba zan bari iliminka da soyayyar da nake yi maka, su ƙare a kan yi wa biladama hidima ba, ba ma su su yi maka ba. Sai dai ka zaɓa, zama da mu ko kuma hidima ga bil'adama!" Ayshercool 08081012143 59 Ƙaisar ya ce "Haƙiƙa kai Babana ne, ka so ni mai sonka ma ya so ni. Kuma na san ni ne ruhi mafi soyuwa a gare ku. Ka tallafawa burikana da bani damarmaki a matsayina na ɗanka. Sai dai ka tuna, na kawo girman da zan iya yankewa rayuwata hukunci. Kamar yadda ka faɗa; na karanta kashedin da aka yi mana a litattafan magabata, na yi yawon neman labarai a duniya, amma babu inda na ga an ci riba da tashin hankali da yaƙar juna. Kuma Aljani bai taɓa nasara a kan bil'adama ba, komai tasirin cutarwar da ya yi masa. Na yi abota da bil'adama, na karanci wasu abubuwa masu muhimmanci dangane da zamantakewar su. Kuma ina son na yi amfani da ilimina na sanin magunguna, na sanar da wasusn su, domin samun waraka daga wasu cututtukan da mu ne muke haddasa musu su. Dan haka ina mai baka haƙuri, na riga na yi alƙawari ba zan iya warwarewa ba. Sannan ba a banza zan yi wa zuriyar sarkin baka wannan aiki ba. Kamar yadda na gaya maka, sun sadaukar mini da duk wani mai irin tauraron Lanti, domin gudanar da burina na son yaɗuwar ilimin bayar da magani" Cike da ƙunar rai Giyaz ya numfasa ya ce "Shikenan, ka yi abin da ka ke so, amma ka je, na sallama ka daga cikin zuriyaramu, kar ka sake danganta kanka da mu" daga haka Giyaz ya ɓace. Lanti ta damu da mutuwar kakanta, sai dai ba a rufa sati ba, 'yar ta ma mai larurar shan Inna ta mutu. Ta shiga tashin hankali sosai da sosai, tamkar za ta zauce. Hankalin Sarkin Aska kuwa ya yi mummunan tashi, bayan da Duna ya sanar da shi cewar, da Uban duƙusa aka yi wa Lanti girka. Kuma cutar da Uban duƙusa ka iya kawo fitina da tashin hankali a tsakanin su kan su Aljanun. Duk da zafin bil'adama da Giyaz yake ji a kan abin da suka yi wa mahaifinsa, amma ba zai lamunci kowane Aljani ya taɓa masa ɗa ba. Sarkin Aska ya ji baƙin ciki ba kaɗan ba,  da abin da Duna ya gaya masa, bayan tabattar da cewa ya samu abokiyar hamayya a garin. Ƙaisar ya fara bawa Lanti magunguna, ta fara aikin bayar da magani a garin. Babu nasiha da rarrashin da ahalin Ƙaisar ba su yi masa ba, a kan ya janye daga harkar taimakon biladama, amma fafur ya ƙi ya ce ba zai daina ba. Akwai kyakykywar fahimta a tsakanin Lanti da kuma Ƙaisar. Lanti ta kuma samun juna biyu, ta haihu sai dai ɗan da ta haifa, ba ta haife shi da irin taurarinta ba. Aka shiga zazzafan takun saƙa, a tsakanin Lanti da Sarkin Aska, dan mutane suna tururuwar karɓar magani a gurinta. Domin ita ba ta tsauwwala wa mutane, kuma ba ta neman su kawo wani abu da ya fi ƙarfinsu. Duk da Giyaz ya sallama Ƙaisar, amma hakan bai bayar da damar, 'yan uwansa su iya cutar da shi ba. A lokacin sai zuriyar Jaddul Jinn wasu suka goyi bayan zaman lafiya, kamar yadda Ƙaisar ya yi, wasu kuma suka zauna a kan bakar su na lallai sai an ci gaba da cutar da bil'adama da duk wanda ya fito daga wannan tushe na Buda. Sarkin Aska ya ci gaba da jan Aljanu, yana sadaukar musu da jini, yana amfani da su ta hanyar tsafi, da kuma alwashin taimaka musu a duk lokacin da suke buƙatar hakan. Cike da baƙin ciki, Giyaz ya zura wa Ƙaisar ido, babu yadda ya iya da shi. Ganin abin da Sarkin Aska yake ci gaba da yi, duk a ƙoƙarin sa na mamaye garin a ci gaba da tsoron sa, ya sanya Lanti ta ƙara zage damtse a kan harkar bayar da magani da laƙantar hanyoyin da za ta kawo ƙarshen Sarkin Aska. A haka ta haifi yara biyar maza, duk babu mai irin tauraronta, gaba ɗaya abin ya damu Ƙaisar, ganin babu wanda zai iya gadar ayyukan Lanti. Sai dai a jininsin mutane ma, 'yan uwan Sarkin Aska ba sa ƙaunar abin da yake aikatawa na zaluntar mutane. Wata jakar fatar damusa, Ƙaisar ya sanya Lanti ta fara haɗawa, wadda da ita take burin kawo ƙarshen Sarkin Aska, saboda babu irin mugun hari da yinƙurin da Sarkin Aska ba ya yi, dan ya kashe ta. Sai da ta shekara biyar, tana aikin jakar nan, tare da jiƙata da magunguna daban-daban. Ban da zanen hatimai kala-kala da yake cikin jakar. Ta haɗa kai da ɗan uwan Sarkin Aska, baya nan ya je ya ajiye masa jakar a ƙasan abin kwanciyar sa. Kuma ƙaisar ya ɓatar da sahun sa, ta yadda babu wanda ya gane a cikin aljanun da suke yi masa hidima. Tun da ya kwana a kan jakar, Aljanun da suke yi masa aiki, suka watse suka bar shi, ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da sai da ta yi ajalinsa. Yana mutuwa kuma aljanun suka fantsama kan 'ya'yansa da jikokinsa, sai dai aka rasa wanda zai gaje shi gurin ci gaba da aikin zaluntar al'ummar da yake yi. Sosai mutanen gari suka yi murna da mutuwar sa. Babban ɗan sa da suke bokancin tare ma, cewa ya yi ba zai iya ba. Ƙin samun wanda zai gaje shi, ya sanya aljanun fara sanya wa iyalansa cututtuka. Wasu kuturta wasu suka makance, har da waɗanda suka haukace. Aka din ga ɗauki ba daɗi da Lanti, a kan sai ta warkar da su. Ƙaisar ya gargaɗe ta a kan babu ruwanta ta rabu da su. Lanti ta shafe shekaru Ashirin da bakwai, tana aiki tare da Ƙaisar tana harkokinta na bori da bayar da magani, haka zalika ita ma ta yi wa mutane da dama girka, masu sha'awar harkar bori. Akwai bikin 'yan bori da ake gudanarwa da nuna bajinta duk shekara, wanda a nan ake yi wa masu so girka, ake bikin bajekolin abubuwan ban mamaki, na gidaje daban-daban. Maharba su yi na su, wanzamai, 'yan bori da dai sauran su. Domin bayan mutuwar Sarkin Aska an ɗan samu zaman lafiya, tun da dama shi yake assasa duk wata fitina da rashin zaman lafiya. Sai dai aljanu ba su fasa cutar da su da razana su ba, duk da Lanti tana iya kokarinta. Sai dai ita ma bayan wannan shekarun ta koma ga Allah. Sai dai kan ta mutu, a cikin jikokinta an samu guda ɗaya da take da irin tauraronta. Dan haka bayan mutuwar Lanti, aka ci gaba da ba ta kashi tsakanin mutanen garin, da Aljanun da sarkin Aska ya yi aiki da su, har ma da waɗanda ba 'yan asalin garin ba ne. Sai dai babu yadda Ƙaisar zai yi, a lokacin jikar Lanti ba ta kai lokacin da za ta iya bayar da magani ba. Kuma har a lokacin ba a fasa yi masa magiyar ya rabu da bil'adama ba. Gaba ɗaya ya nesan ta kansa da Ahalinsu. Bayan jikar Lanti ta fara tasawa, Ƙaisar ya fara bijiro mata, domin yin gadon kakarta, sai ta kasa ɗauka sai ma taɓin hankali da ta samu, duk da ta ɗan taɓa bayar da maganin amma ba sosai ba. A hakan ita ma ta yi aure ta hayayyafa. A cikin 'ya'yanta aka samu wadda ta gaje ta, duk da ba irin tauraronta ɗaya da Lanti ba. A lokacin Musulunci ya shigo cikin mutane, duk da bai yi ƙarfi a garin Buda ba. Asma'u ta bayar da magani ita ma, ta yi aiki tare da Ƙaisar, sai dai ba ta da ƙarfin zuciya da juriya irin ta Lanti. Gaba ɗaya ita ma ba wani daɗin aiki ya ji da ita ba. Ko yaya ya buɗe mata ido ta ga abu, sai ta kwanta ta hau jinya. Daga baya ma ta watsar ta tattara komatsan borin ta ajiya, ta ce ta tuba ta daina. Ganin ba a samun masu irin tauraron Lanti, ya sanya Ƙaisar fara sarewa, da haƙura da batun bayar da magani ta hanyar bil'adama. Sai dai yana iya yin sa gurin bawa zuriyar su Lanti kariya, daga cutarwar zuriyarsu. Duk abin da yake faruwa, Giyaz yana ankare da Ƙaisar, kuma yana murnar yadda ɗan sa ba zai ci gaba da zama bawa ga bil'adama ba. Aka din ga samun ci gaba a garin Buda, wasu suka din ga barin garin su na tafiya fatauci, wasu kuma tashin hankalin Aljanun da ya addabi garin ne ya sanya suka bar garin, ciki har da wasu daga cikin zuriyar Lanti. A can Bauchi aka haifi Maijidda, har ta girma, an saka mata rana saura watanni uku aurenta, su ka zo Buda, a nan suka haɗu da Isa, ya ƙallafa rai a kanta. Yayar kakarta ta ce sai an warware wancan baikon da aka yi da na can garin Bauchi, an yi da Isa, saboda ƙara danƙon zumunci, kuma hakan zai sanya su din ga kawo musu ziyara a kai a kai, da ƙara samun zaman lafiya a tsakanin zuriyar maharba da ta wanzamai. Aka mayar wa da wancan na Bauchi kuɗinsa, ita kuma ta auri Isa. Gidansa na Kano, inda yake harkokin kasuwancinsa, nan ya tafi da ita. Ya ajiye ta a gidansa da suke tare da matarsa babar Gaddafi. Ya ɗora wa Maijidda son duniya, kamar a kanta ya taɓa aure. Ba uwargidansa ba, hatta 'yan uwansa sai da suka fara jin haushin Maijidda saboda ba ya ɓoye son da yake yi mata, ga ta yarinya ƙarama amma su na ganin kamar ta mallake shi, dan shekarunta goma sha shida a lokacin. Kasancewar daga zuriyar Sarkin Aska Maijidda take, ta auri ɗan zuriyar Sarkin Baka, sai Aljanun da suka yi wa sarkin Aska hidima, suka shiga cikin lamarin auren, su ka fara haddasa musu matsala. Haka kurum sai ta ji ta tsani Isa, ba ta ƙaunar ganinsa ga yawan rashin lafiya. Kishiya da facaloli suka sako ta a gaba, ga jarabar dangin miji. Ana haka ya samu matsala da uwargidansa, da ta haifa masa Gaddafi da Ummi, ya sake ta. Nan ma aka ce Maijidda ce sila. Ya auri Rabi, suka zama ita da Maijidda. Yayarsa Atine ta ƙara haɗe kai da Rabi, su na cizguna mata. Maijidda ke riƙon su Gaddafi, tana iya kokarinta amma kullum cewa ake yi tana azabtar da su. Kasancewar Gaddafi ya fi Ummi wayo, ya tsani Maijidda cewa yake saboda ita aka saki babar su, kamar yadda Yaya Atine take faɗa. Ita kuma Ummi tana matuƙar ƙaunar Maijidda. Nan ma Rabi ta saka Maijidda a gaba, da kishi da ƙage kala-kala. Bayan haihuwar Imran sai da ya shekara uku da rabi, ta haifi Nana. A lokacin Isa ji yake kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba sai a kan Nana. Ya saka mata suna Asma'u, sunan kakarsa da ta riƙe shi take bala'in son sa. Hatta hakika biyu ya yi wa Nana, Ummi ma da ya saka mata sunan mahaifiyarsa bai yi mata abin da yake yi wa Nana ba. Isa kofur ne na 'yan sanda, abokan aikinsa suka yi masa ƙage, aka kore shi daga aiki har da prison. Ya koma harkar fawa, ya fara samun rufin asiri, harka ta buɗe masa yana samun rufin asiri sosai , sai dai kasancewar sa mutum ne da ba shi da sirri, duk samun sa sai ya bayar da labari, abokansa suka jefe shi sana'ar ta fita daga ransa ya daina zuwa ko ina, sai zaman gida. Tun da Allah ya sanya aka haifi Nana Ƙaisar ya ganta ya rikice, tamkar Lanti ta yi kaki ta ajiye saboda kamanin su. Ga irin tauraronta ɗaya da Lanti. Gaba ɗaya Ƙaisar ya tattara hankalinsa a kan Nana Asma'u yana ganin, ya samu uwar gijiya a zuriyar Lanti. Giyaz na fuskantar abin da ke shirin faruwa, ya fara ƙoƙarin raba Ƙaisar da Nana. Dan kullum yana tattare da ita. Wasu lokutan ya zungure ta tayi ta kuka. Manyan bokaye da ƙungiyon Asiri na zawarcin son yin aiki da Ƙaisar, saboda tarin baiwa da kuma ilimi da binciken ƙwaƙwaf da yake yi. Wanda za su aiki da shi ne, ya din ga taimaka musu, su kuma su din ga yi masa hidima, amma fafur ya ƙi. Saboda ba ya son duk wata alaƙa da jini. Ƙaisar ya yi tafiya zuwa wata ƙasa, ganawa da wani tsohon Aljani, a kan wani rubutu da yake yi, ya dawo ya tarar an saki Babar Nana, ita kuma Nana ta daina magana, ta daina tafiya ga Baba ya ƙwace ta, ya hana Maijidda ita. Ya fuskanci aikin mahaifinsa ne Giyaz. Ya je ya same shi yake tambayar sa me yasa ya yi wa Nana haka. Giyaz ya ce "Ka sani ba zan taɓa sake yadda, ka zama bawan bil'adama ba, da ka sake zama bawan bil'adama gara na kashe ta ko na kashe ka, kowa ma ya huta." Ƙaisar ya san Giyaz ba ya magana biyu, idan ya faɗi magana sai ya aikata. Dan haka Ƙaisar ya fara ƙoƙarin kare Nana, ya yi amfani da jakar da ya saka Lanti ta haɗa, ta yi amfani da ita gurin kashe Sarkin Aska. Ya ƙara yi mata aiki, da saiwoyi da wasu hatimai, ya yi wa Giyaz tarko da ita. Cikin matsananciyar sa'a, Giyaz ya faɗa tarkon Ƙaisar, saboda ya san muddin ya bar Giyaz, zai iya nakasta Nana nakasa ta har abada, ko ma ya kashe ta, kamar yadda ya furta. Ya ɗauki Giyaz, ya kai shi can nesa ya sadaukarwa wani boka shi, bisa musayar da za su yi, zai ba shi wani abu mai muhimmanci. Wanda ya yi hakan domin nesan ta shi da Nana da zuriyar Lanti. Duk da abin da ya yi ya dawo ya dame shi, yana matuƙar ƙaunar mahaifinsa, duk da saɓanin da suka samu, amma babu yadda iya, hakan ne kawai zai sanya ya nisanta shi da Nana. Sauran 'yan uwan Ƙaisar da tuntuni suke jin haushinsa, suka yo caaa a kan Ƙaisar, har suka nemi hallaka shi, saboda abin da ya yi wa mahaifinsu, amma sun san ko sun hallaka shi, idan Giyaz ya kuɓuta suma sai ya kashe su. Ɗan uwan Giyaz Duna, ya yi ta ƙoƙari gurin ganin ya kuɓutar da Giyaz, amma abu ya gagara. Nan suka din ga kai wa Nana hari, da yinƙurin hallaka ta. Maijidda kuwa bayan mutuwar aurenta, tana gama idda, Iliyasu tsohon saurayinta ya sake dawowa ya aure ta. Ko da Baban Nana ya samu labari, sai ya ce tana sane, ta ƙi zama da shi, saboda ta koma ta auri Iliyasu, dama son zama da shi take yi ba. Nana ta ga garari tun da ƙuruciya, babu cikakkiyar kulawa, kuma tun ba ta fi shekara uku ba take ganin Ƙaisar, da ma sauran 'yan uwansa da suke ta kokarin azabtar da ita. Maijidda ta so karɓar ko Nana ce, saboda rashin cikakkiyar lafiya, amma Isa ya hana fafur, ita ma can mijinta ko yaya ta motsa tana son ganin 'ya'yanta, sai ya hau bala'i wai za ta gurin tsohon mijinta. Tun Nana na ƙarama, take nuna alamun rashin lafiya, amma babu wanda ya kula. Ta kan wuni tana bacci tun safe, har dare babu wanda zai damu. Wasu lokutan ta daina magana ma ko tafiya gaba ɗaya. Idan kuma ta warware ta din ga fitinar da ta fi ƙarfin shekarunta nesa ba kusa ba. Ta kan ga Ƙaisar a zahiri, ko kuma a cikin bacci. Babu wanda ya damu da ta ci Abinci ko ba ta ci ba, mussaman da Baba ya daina sana'ar komai, sai dai Imran ya nema ya bata. Idan ta fita Ƙaisar ya kan zo a suffar mutum, ya ba ta abinci. Allah ya sanya masa matsananciyar ƙaunarta. Ya fara bayyana a jikinta ne, tun wani duka da Mama ta yi mata, bayan faɗa ya haɗa ta da Jamila. Sai da ta kwana biyu a sanƙame, tun daga nan suka gane halin da take ciki. Da ranta ya ɓaci sai hankalinta ya gushe. Ƙaisar ya sha ɗauke Nana, a neme ta a rasa kwana ɗaya ko biyu ya je ya ajiye ta gurin sa. Baba ya yi ƙoƙarin nema wa Nana magani, amma abu ya gagara. Labari ya iske Maijidda halin da Nana ne ciki, bayan da su Adda Saude suka zo ganin su Nana. Rabi ta haɗa tuggu a gurin Baba, ya ce kar su sake zuwar masa gida, kuma ba zai bayar da Nana ba. Wahala ta saka Imrana fara sace-sace saboda su ci Abinci, Rabi ta saka Baba ya kore shi daga gidan. Haka Nana ta tashi a cikin wahala, ga wanda bil'adama suke yi mata, ga wadda Ƙaisar yake yi mata da sunan kulawa. Ji ta yi tamkar an sanya hannu an shaƙe ta, a dole ta saki littafin ta ja da baya tana tari. Ta ɗaga kai ta kalli Ƙaisar, bai ce mata komai ba, ya ɗauki littafinsa ya juya ya tafi. Yana barin gurin Haula ta zagayo ta dafa Nana. Ta ɗaga kai ta kalle ta ta ce "Ƙawata, kwana biyu. Hadiminki ya ƙi saurarata balle na sanya ran zai karɓi buƙata ta, ki yi wani abu a kai dan Allah" Nana ta ce "Haula, gaba ɗaya jinsinku ba abin yadda ba ne, ki rabu da ni da wannan maganar ta ku" "Shikenan, na rabu da ke, amma kin yi ganganci abin da ki ka yi wa dattijo, Allah kaɗai ya san me zai yi miki idan ya gama jinya. Kuma har Ƙaisar ki ka janyowa shi ma ba zai bar shi ba" "Duk hukuncin da ya yi wa Ƙaisar yayi daidai, ɗa na gari ba zai taɓa yi wa babansa abin da ya yi wa nasa mahaifin ba" Haula ta ce "Kash! Nana kar ki zama butulu mana. Sai dai ina fatan kin fuskanci jakar gurin Sarkin baka da ya baki, wace jakar ce" Nana ba ta ba wa Haula amsa ba, Sayyid ya tashe ta. "Ma vie" yayi maganar yana matsawa jikinta sosai. Jiki a sanyaye ta amsa masa. Ya ce "Lafiya dai?" "Mmm" "Ko Ƙaisar ɗin ne?" "A'a" "To me yasa ki ka tsorata? Mene ne ya baki tsoro?" "Bakomai" "es-tu sûr? (Kin tabatta?)" Ta ce "Eh. Haryanzu hannunka lafiya ƙalau ko?" "Eh, amma akwai abin da ya tsorata ki, gaya mini mene ne?" Ji ta yi tamkar ta gaya masa, dan a wannan karon ba ta manta abin da Giyaz ya gaya mata ba, a kan idan ya warke zai sake waiwayar su. "Ma viee" "Sayyid" ta amsa a hankali. Ya yi maganar yana taɓa wuyanta "Sanyi ki ke ji Rayuwata" "Eh, amma ba sosai ba" "In baki ɗumi ne?" Yayi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa Dariya ta yi ta ce "A'a na yafe, ƙona ni za ka yi" Shi ma dariyar ya yi ya ce "To ni ki bani sanyin ina so" Ya yi maganar da sigar shawaɓa. "Wai kai ba ka jin bacci ne? Kawai ka farka cikin dare?" "Soyayya ce ta tashe ni" Sai da jikin Nana ya ɗan yi sanyi, ta ce "Soyayya kuma Sayyid?" "Eh, je t'aime ma femme" "To ai ban san me ka ce ba" Ya yi kissing ɗin goshinta ya ce "Ina sonki matata" wani abu ne ya tsirgawa Nana, tun daga tsakiyar kanta, har tafin ƙafarta. Shafa hannunsa ta yi, kamar mai tantamar abin da ya ce, ta ce "Sayyid" "A'a, kar ki yi tantama, ko ki yi kokwanto, shi yasa na baki sunan Rayuwata. Ko a wannan Duniyar, ko ma a wace Duniyar, kawai ina son matata, saboda ita ɗin Rayuwata ce. Babu abin da zai canza hakan." "Sayyid ina tsoron idan ka tuna waye kai, ka ji ba ka so na, zan cutu da yawa, zamana da kai na shaƙu da kai sosai zuciyata ba za ta iya ɗauka ba" Ta yi maganar cikin rauni da tsoro. Ya ɗaga kan Nana, ya sanya hannunsa a wuyanta, ta lumshe idanunta hawaye na bin gefen fuskarta. "Ƙa'idar ba za ta canza ba har abada, babu ruhin da zai samu nutsuwa a gangar jikin ɗayanmu muddin ba ma tare, ki saka haka a ranki. Sayyid yana son Rayuwarsa. Ko babu raina fatalwata za ta ci gaba da sonki" Nana ta yi ajiyar zuciya tare da dariya, ta shafa gashin kansa. "Allah ya sa haka. Ina son mijina sosai nima" murmushi ya yi yana kissing ɗin ta. Har garin Allah ya waye, maganganun Sayyid ne ke kai komo a cikin ƙwaƙwalwa, zuciya da kuma gangar jikin Nana. Wani irin shauƙi da farinciki ne yake kama ta, da tuna kalamansa. "Amarya" ya yi maganar yana kallon ƙwayar idonta. "Amarya da wannan ɗin?" Ta yi maganar tana nuna cikinta da ya fito sosai. Yayi murmushi yana shafa cikin ya ce "Duk da haka amarya ce ai, ko kin manta?" Ya yi maganar yana kashe mata ido. Ta yi murmushi tana ci gaba da ninkin kayan da ta wanke. "Sayyid, bari na je kasuwa na nemo kayan magungunan ka, na dafa maka, ka ci gaba da sha, kuɗin hannuna sun ɗan taru, zuwa ranar Monday in Allah ya kaimu, duk yadda za a yi, mu tafi Kano Asibiti. Na ji haryanzu zuciyarka ba ta bugawa sosai, na san ƙarfin hali kawai ka ke yi" "Gaskiya kin fiye saka ido, ya aka yi ki ka gane hakan, mai magani?" Ta jinjina kai ta ce "Au haka ma za ka ce ko? Hmm ai shikenan, za ka ga mai magani, yau sai na wanke ka da magani na kulle ka a ɗaki" "Eh saboda cin zali ba, kuma ke ki gudu, alhalin kamata ya yi ki yi mana tare" Ganin yadda yake rungumota ta ce "Sayyid na gama shiryawa, fita fa zan yi" Ya ce "Na sani" "Ka sani kuma ka ke son na ɓata lokaci? Dan Allah Sayyid jiya throughout the night mu na tare, yanzu kuma... "Shhhh... Ba ki ji jikina ya fara zafi ba" "Wallahi lafiyarka ƙalau, normal babu zafi a jikinka, wai wannan surutun duk daga ina?" Haka ya hana Nana fita, har bayan Azahar, kawai ta zuba wa Sarautar Allah ido. Kuma a fuskar sa take ganin tsantsar ƙarfin hali, amma ba shi da lafiya. Sai bayan la'asar ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bar ni na je na haɗo kayan nan Sayyid, ko haryanzu ba ka gama jin Sanyin ba?" Ya ɗaga mata gira. "To ga mafici, yi ta fifita, har na dawo" Dariya ya yi yana ɗan jan hancinsa. Ya kamo hannunta ya ɗora a wuyansa ya ce "Kin ji da zafi ko?" "Ba wani zafi. Waccan ranar ma wayo ka yi mini, wai na baka sanyin jikina" Dariya yake son yi sosai, amma sai ya yi kaɗan ya cije, ya ce "Ai ni Ƙaisar wasu lokutan taimakona yake yi" A sanyaye ta ce "Shi me yasa ba ka kishi da shi?" "In ji wa? Kawai abu ɗaya ne da babu yadda muka iya. Alaƙarsu ta ɗa da mahaifi tana tasiri a rayuwarmu ni da ke" Cikin mamaki Nana ta ce "Ta yaya? Kuma ya aka yi ka san Ƙaisar ɗan Giyaz ne?" "Yadda ki ke ganin Ƙaisar ku yi magana, haka nake ganin Giyaz, kuma na fuskanci waye shi a tattare da ni. Yanzu ki je ki dawo" "Kai amma na yi mamaki fa, kuma ba ka taɓa gaya mini ba. Bari na je na dawo, ina da tarin tambayoyin da zan yi maka" "Tom sai kin dawo" Ta saka hijjabinta, har za ta fita ya kirawo ta. Ya ce "Ba ki yi mini ba" Ta yi masa kiss a goshinsa, da bakinsa. "Allah ya yi miki albarka. Ki kula mini da kanki, kar wani ya kula mini ke, ki kular mini da babyna ki tafi a hankali ki je ki dawo" Ta kalli cikin ta ce "To Shugaba, in sha Allah" "To a dawo lafiya, I love you" Cikin murmushi ta ce "Inyee ɗan gayu, ka yi furansanci, ka yi turanci, ka yi hausa ga kuma yarenku. Zan koyo yaren da baka iya ba, na din ga tashin kanka da kalaman soyayya" Ya ce "Je ki dawo ki yi mini waƙa" "Sai dai na je na yi maka tsifa, na yi maka sabon kitso" ya tsuke fuska yana hararata. Ta fita tana waigensa tana murmushi. Tana fita ya jingina da jikin bango, yana dafe saitin zuciyarsa, yana haki sama-sama. Ya fito tsakar gida da kyar, ya zauna yana sake danne saitin zuciyarsa da yake jin wani irin abu kamar shocking daga zuciyarsa yana zagayawa bayansa har cikin kansa. Tsayuwar motoci ya ji a waje, sai dai hankalinsa ba ya kan hakan. Ya ji an daki ƙofar gidan da ƙarfi. Ya ɗaga kai ya ga wasu murɗaɗɗun ƙarti sun shigo cikin baƙaƙen kaya. Duk da mawuyacin halin da yake ciki, haka ya yinƙura ya tashi da ƙyar, ganin an shigo da Habu hannunsa da sarƙa. Ya din ga bin mutanen da kallo, Habu cikin matsananciyar damuwa ya zube a kan gwiwoyinsa ya ce "Ka yi mini Afuwa Imam, ba laifina ba ne ka yi haƙuri, na gaza baka kariyar da ta dace" Sayyid ya din ga bin sa da kallo, da alama ma ba ya gane me Habu yake nufi. Ƙartin nan biyu daga cikin su, suka yo kansa, suka riƙe shi. A rikice ya ce "A'a, ku rabu da ni. Me na yi muku?" Ƙoƙari suke su tasa shi su tafi da shi cikin salama, amma ya turje. Suka juya yare zuwa faransanci, su na rarrashin sa, ya wuce su tafi. "Ba zan je ko ina ba? Ina zan tafi na bar matata" Habu ya din ga girgiza masa kai da alamar ya daina faɗar maganar da yake yi. "Ku rabu da ni, ina zaku kai ni na tafi na bar Nana" maganar da yake yi cikin ɗaga murya, ga ƙoƙarin turjewa da yake yi, ya sanya zuciyarsa yin rauni, ya yi baya zai faɗi. Suka tare shi suka saɓa shi suka yi waje da shi. Aka saka Habu a cikin wata motar daban, Sayyid kuma aka saka shi a cikin wata baƙar Highlander mai tint glass, aka rufe suka tafi da shi. Nana tana tsaye ta bayar da kuɗi, za a bata kankana, dan daga ita har Sayyid, kawai ta ji gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa. Ta yi shiru, ta jiki gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Kawai ta juya ta tafi. Mai kayan yana ta yi mata magana, amma ba ta tsaya ba, ta nufi gida har da ɗan gudu saboda azabar sauri. Tana zuwa ƙofar gidan ta ga ƙofar gidan a ɓalle, da hanzari ta shiga gidan, tana kiran sunan Sayyid. Amma wayam ba ya nan, ta shiga ɗaki baya nan. Ta duba banɗaki nan ma ba ta gan shi ba. Ta fita waje da sauri, tana kalle-kalle, ta tafi hanyar inda bishiyar kukar nan take, tana tunanin ko jikinsa ne ya motsa, ya tafi can, sai dai can ma baya nan. Ta sake komawa gidan cikin tashin hankali, da wani yaro da yake zuwar mata aike ta haɗu a ƙofar gidanta ta ce "Ashiru, ko ka ga Sayyid ya fito daga gidan nan? Wannan mutumin na gidana farin nan?" "Wasu mutane ne suka shiga gidan suka tafi da shi, a mota suka zo" Sak Nana ta tsaya, tana ƙure Ashiru da ido, tamkar ma ba ta gane yaren da yaron yake yi. Ayshercool 08081012143 60 Cikin rawar murya Nana ta ce "Wace irin mota kuma Ashiru? Ka tabattar kuma Sayyid ne?" "Wallahi na tabattar, ina nan ina wasa suka zo, a motoci wannan farin na gidanki suka ɗaukko." Tamkar mahaukaciya ta bi sahun motar, ita ce har titi ko za ta ga motar da Ashiru ya ce, amma babu wata alama na za ta ga motar da aka daukar mata Sayyid aka saka a ciki. Gaba ɗaya ta kasa kuka, sai tsuma da jikinta yake yi tamkar mazari. Tuni rana ta faɗi, an fara kiran sallar magariba, ba ta san tafiyar da ta yi da nisa ba, sai da ta tashi dawowa. Gidan Uwani ta nufa, ta tarar da ita ta yi alwala, za ta yi sallar magariba. Uwani ta ce "Ke Nana, uban me ya fito da ke da magaribar nan, ga juna biyu kina da shi, duk da na san ba ki da ɗan aike amma koma mene ne, ai kya bari a idar da salla ko?" Nana ba ta yi magana ba, ta nemi guri ta zauna a ƙasa. "Ke lafiya kuwa?" Uwani ta yi maganar tana tattara hankalinta a kan Nana. Amma Nana ta kasa magana, sai murza zoben hannunta da take yi, tana ajiyar zuciya. "Ke ki yi mini magana, kar ki tayar mini da hankali mana". "Sayyid ne ya ɓata" "Kamar yaya sai ka ce wani zakara?" "Da gaske nake" "To ai ban gane ya ɓatan ba ne? Mutumin da yake jinyar ne ya iya tashi ya fita har ya ɓata?" "Ai kwana biyu jikin da ɗan sauƙi, dan har ya ce mu zo nu gaishe ki" Ta yi maganar ba tare da tana iya tantance me ma take faɗa ba. "A'a Nana, wataƙila dai wani wajen ya je zai dawo. Tashi ki yi sallar magariba, zuwa anjima a raka ki gidan ko ya dawo" Nana jin Uwani kawai take yi, ta tashi ta yi sallar magariba, aka yi isha'i. Uwani ta saka Nana a gaba zuwa gidanta, sai dai kamar yadda Nana ta bar gidan wayam babu Sayyid babu dalilinsa. Nana dai ba ta gaya wa Uwani abin da Ashiru ya gaya mata ba, na ya ga an zo da mota an tafi da shi ba. Sai wajen goma na dare, hankalin Uwani ya tashi. Ta sanar da samarin gidan halin da ake ciki. Nan suka bazama a cikin Buda yawon neman Sayyid, duk da galibi ma ba su san shi ba, kwatancensa Uwani ta yi musu, suka tafi yawon neman sa, har gurin jami'an tsaro aka kai rahoto. Sai dai har bayan sha biyun dare, babu wanda ya ji ko ɗuriyarsa. Uwani ta saka aka rufe gidan, ta ce Nana ta zauna a nan, ko zuwa dare zai dawo. Nana a ranta ta ce "Wane dare kuma bayan wannan" Daren ya zame wa Nana dare mafi tsawo a rayuwarta. Damuwa da tunani ya cika mata zuciya. Ba ta tunanin Sayyid zai iya tafiya ya bar ta. Idan kuma da gaske zuwa aka yi aka tafi da shi, to suwaye su ka tafi da shi? Ina suka kai shi, me ya yi musu? Ko dai wani laifin suke aikatawa ba ta sani ba? Amma shi da yake kwance babu lafiya, kullum tana tare da shi a gida, yaushe har yake aikata wani rashin gaskiya da ba ta sani ba. A haka har aka yi assalatu, a kan kunnenta. **** Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka. Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta. Gefe da gefen hanyat baki ɗaya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huɗu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado. Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi. Kallon sa ya yi, daga bisani ya ce "Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?" Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba" "Dans  quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)". "Bai fi awa ɗaya ya rage mana ba" "Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka. Ka ƙara sauri" Ya yi maganar yana haska fuskar Sayyid, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai  yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar. Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin Sayyid, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take bugawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito dummm!. Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ƙara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi. Kuma ka san idan ya mace mana mun shiga uku mun lalace" Lauwalli ya jinjina kai yana ƙara gudun motar. Ya ce "In sha Allah a raye za mu kai shi, ba za a samu matsala ba. Dan dai ka ƙi yarda ne, da na ce mu tsaya a Asibiti". "Kai dalla ka daina maganar tsayawa a wani Asibitin nan. Ka yi ka hanzarta mu cika umarnin nan, mukaɗai ake dako" "To shikenan, mun kusa in sha Allah" ya yi maganar yana ƙara gudun motar. **** Antin Yusra ce ta kalle ta, ta ce "Yusra duk wannan kwalliyar fa? Ta karɓar baƙon ce?" "Eh mana Mami, yana hanya ma ai" ta yi maganar tana tafiya ɗakinta, ta fesa turare. Wayarta ce ta fara ringing, ta ɗaga wayar tana murmushi ya ce "Gani a layin" "Duba lambar gidan, za su buɗe maka" Ya ce "Ok" Bayan mintuna goma sha biyar, ta fito ta ce "Mummy na tafi" "To a gaida baƙon, ya tabattar mana da alkhairi" Kawai ta fice tana murmushi. Tana zuwa ta gan shi a tsaye a cikin falon, yana kallon ƙaton frame na hoton mai gidan, da yake retired soja. Ganin abin take tamkar a mafarki, wai Sagir ɗin ta ne a gabanta. Jin ƙamshin turarenta ne ya sanya ya waiwaya. Da gudu ta ƙarasa inda yake ta faɗa jikinsa. Babu tunanin komai, Sagir ya ƙanƙame ta a jikinsa, bar siririn mayafin da ta yafa a kanta, yana zamewa gyararren gashin kanta, da yake ta ƙamshin mayuka ya bayyana. Ya din ga shafa bayanta yana murmushi, kawai ya ji tana sheshsheƙar kuka. A ɗan rikice ya ce "Lafiya, kuka kuma Yusra?" Ya zauna tare da ita a jikinsa, ya ce "Ina ta murna zan zo na gan ki, amma in zo ki din ga kuka, ko ba kya son ganina ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To mene ne" "Ka daina so na, tun da ka sake ni ba ka ƙara nema na ba" Ya ɗago fuskarta su na kallon juna yace "Da na daina son ki, ba zan zo nan ba Yusra, kin san yadda rabuwarmu ta kasance, ban daina sonki ba, ban kuma daina tunanin ki ba" "Almost three years, ba ka sake nema na ba" Sagir ya marairaice murya ya ce "To yanzu ba gani na zo har nan saboda ke ba? Haba wifey" ta zumɓura baki cikin ɗabi'arta ta shagwaɓa. Duk da ya zuciyarsa na tunatar da shi, tare da gargaɗin sa a kan Yusra ba muharramarsa ba ce, amma ya kasa yaƙar kansa, ya ƙyale ta a jikinsa yana jin yadda ya yi kewarta. "Talk mana, na zo kuma kin haɗe rai?" Tashi ta yi daga jikinsa, ta zauna a kusa da shi ta ce "Ya hanya?" "Alhamdillah, ki na lafiya ya jikin naki?" "Da sauƙi" "Kin warware?" Ta girgiza kai ta ce "Bayan ƙin yadda ku ka yi da gaske ba ni da lafiya. Sai ga shi na haɗu da wata Nana, ita ma tana irin ciwon da nake ji, ai ita ta san ba ƙarya nake yi ba." Ya ce "To yanzu dai duk ba wannan ba, i miss you Yusra, irin sosai da sosai ɗin nan fa" "Bayan ka yi aurenka, ba wani missing ɗina da ka yi" ta yi maganar tana tsiyaya masa lemo a cup ta miƙa masa. Ya karɓa ya kai bakinsa yana tsare ta da ido. Ta kalli screen ɗin wayarsa da ya kawo haske, hoton Haidar ya bayyana a kan screen ɗin. Ta ɗauki wayar tana kallon yaron ta ce "Waye wannan?" "Ɗanki ne Haidar, recently ma ta kuma haihuwa ɗan ya rasu" ta yi masa wani kallo, da bai tantance na mene ne ba ta ce "Da tuni nima wataƙila na haihu" Ya yi murmushi ya yi shiru, yana cin abincin da ta zuba masa. Cikin hikima ya karkatar da zancen suka ci gaba da hira. Wayarsa ce ta fara ringing, ta ajiye masa ganin hoton heart a kan sunan. Ya ɗaga wayar tare da yin sallama "Hello love" "Ka sauka lafiya?" "Alhamdillah am good dear" Shukura ta ce "To sai ka dawo, Allah ya tsare mana kai, take care" Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah dear" wani abu ne ya tokare wa Yusra a ƙirji, ta zuba masa ido. Ya ajiye wayar, bai kalle ta ba ya ce "Yusy, kin san na yi missing ɗin girkinki over?" Jin ta yi shiru ya sanya ya ɗaga kai ya kalle ta, ya ga tana hararsa. Ya yi murmushi ya ɗebo Abincin ya kai bakinta. Ta murguɗa masa baki ta tsuke fuska. "Smile, haba sweetheart" ta buɗe bakin ya saka mata Abincin. Haka ya ribace ta, suka ci gaba da hira. A nan ya yi sallar la'asar, sannan ta fito raka shi. A jikin motarsa suka tsaya, tana yi masa wani irin kallo mai ƙayatarwa. "Tom sai yaushe zan dawo?" "An jima kaɗan" Ya yi murmushi ya sake kallon ta ya ce "Yusra" Ta ce "Na'am" "Yaushe za ki dawo gidana, ji nake kamar na ɗauke ki, na tafi da ke Kano, ina kewar ki sosai da sosai. Yaushe za ki dawo gidana?" Ta girgiza masa kai ta ce "Ba zan dawo ba" Cikin mamaki ya ce "Saboda me?" "Ka auri wata, kuma Hajiyarka ba za ta bari na dawo ba, su Mami ma ba za su bar ni ba, kuma ma haryanzu ban gama warkewa ba" "Haryanzu ki na so na?" Ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Idan ba kya so na, me yasa ki ka nemi lambata, ki ka kira ni? Kuma har ki ka ba ni dama na zo?" Ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da murza yatsun hannunta. "Yusra Sagir ɗin ki ne fa, ɗago ido kalle ni" Kawai ya ga hawaye na bin fuskarta. "Sagir ɗina, da ya rabu da ni, saboda ba ni da lafiya ba" Ta yi maganar tana sheshsheƙa. Ganin babu kowa a gurin da suke, ya sanya ya janyo ta jikinsa, ya ɗago kanta yana kallon idonta ya ce "Yusra, ki na so na haryanzu?" Ta yi shiru hawaye na ci gaba da bin idanunta. "Ki na so na har yanzu, shi yasa ki ka neme ni. Dan haka batun ina da aure, Hajiyata ba za ta bari ba, 'yan uwana ba sa son ki, haryanzu ba ki da lafiya, duk ba ta taso ba. Za ki dawo gidana a karo na biyu in sha Allah. Haryanzu ina son ki Yusra" "Amma... "Babu amma tsakaninmu, believe me zan dawo da ke gidana in sha Allah" Jikinta ya yi sanyi. Ya cika ta a hankali, ya shiga motarsa. Ta tsaya ƙyam tana kallonsa, shi kansa da kyar ya tafi, tamkar ya ɗauki Yusra ya tafi da ita. Har ya kama hanyar Kano, zuciyarsa cike da tunanin ta ina zai fara. Dan shi har ga Allah yana son matarsa, ba a son ransa ya rabu da Yusra ba. Yanzu kuma da ya ganta, gaba ɗaya ya ƙara rikicewa ba abin da yake sai tuno soyayyar da suka yi, daga saurayi da budurwa zuwa auren su. Ko da ya je gida, Shukura ta karɓe shi tana yi masa sannu da zuwa. Amsa mata ya yi yana kallon ta, kafin ya ƙaraso ta kira shi ya fi sau biyu, yana zuwa hatta ruwan da zai yi wanka ta tanadar masa. Ya cire kayansa ya shiga wanka, kamar ta san ba zai iya salla ba, sai ya tsarkake jikinsa, saboda rungumar da ya yi wa Yusra. Tana cikin tattare kayansa, hancinta ya ji ƙamshin turaren da ba na sa ba a jikin kayansa. Turarensa ɗaya ne da ta san shi da shi. Jikinta ne ya yi sanyi, domin ta daɗe da karantar alamomin rashin gaskiya a tattare da shi. Wani abu ne ya soki zuciyarta amma ta yi ta maza ta haɗiye tare da ajiye kayan. **** Aka shiga kwana na biyar, ba tare da jin ko ɗuriyar Sayyid ba. Nana duk ta fita hayyacinta, ba ta iya cin abinci, ba ta bacci. Ga Uwani tun tana rarrashinta, ta koma yi mata faɗa tana ganin ta ƙi tawakalli ta ci gaba da addu'a. Ga shi ta hana ta komawa gidan nasu, a nan gurinta take zaune tare da ita. Yanzun ma Uwanin ce ta miƙo mata kofi da fura a ciki ta ce "Ungo ki samu ki sha furara nan Nana, ko ɗan cikinki ya samu wani abu shi ma. Rayuwa ba za ta yiwu a haka ba kina zaune babu Abinci, ga juna biyu ba. Idan wani gurin mutumin nan ya tafi, idan da rabo zai dawo ai" Nana ta karɓi kofin, tana ajiyar zuciya. "Maza ki shanye, kan na fito daga banɗaki" Nana ta jinjina kai tana kallon kofin. Uwani na shiga banɗaki, Nana ta ɗauki mukullin da aka kulle gidansu, ta tafi. Gani take kamar tana shiga za ta tarar da shi a inda ta bar shi. Ƙofar dama a lanjare take aka rufe ta. Ta shiga ɗakinsu, amma ta tarar wayam babu kowa a ciki. Ta kalli kan katifar su, ta ga abin hiraminsa na rawani a kai. Ta durƙusa a kan gwiwoyinta, ta damƙi hiramin nan, da yake ta ƙamshin turaren sa. Tamkar ta damƙi Sayyid ɗin. Cikin kuka ta ce "Haba Sayyid, daga cewa na je na dawo, sai ka tafi ka bar ni? Haba Sayyid yau kwananka biyar ba ka tare da ni. Da mutuwa ka yi na san wannan hukuncin Allah ne, dole na tawakalli, amma me yasa zaka tafi ban san halin da ka ke ciki ba. Haba Sayyid Haba Sayyid Nana ce fa" ta din ga soki burutsu tamkar zararriya. Wani irin kuka take yi mai haɗe da gunji da ƙunar zuciya. Ba ta san lokacin da Uwani ta shigo ba, tare da abokiyar zamanta Sabuwa ba, sai ji ta yi ta taɓa ta ta ce "Nana shi ne sai da ki ka fito ki ka zo ko? Ba na ce kar ki fito ba?" "Uwani. Sayyid ya tafi ya bar ni, na zata mafarki nake yi, me yasa zai tafi ya bar ni?" "Ke ki ji mini 'ya da rashin ta ido, yo ina zan san dalilin da ya sanya ya tafin ni? Ke ba za ki iya dakewa ki kama kanki ba, idan guduwa ya yi fa?" Sabuwa ta ce "A'a Yaya, su fa yaran birni su na nunawa junansu kulawa, ya za a yi mutum mara lafiya a neme shi a rasa, ki ce hankalinta ba zai tashi ba? Kina kallon yadda take tiri-tiri da shi take nula da abin ta ke kin san ba ƙaramin so take yi masa ba, ai da tausayi" Uwani ta ce "Kuma haka ne, amma tun da shi ya tafi nima jikata nake yi wa kar wani abu ya same ta, ga ciki. Ke Nana kuma ba garinsu ya tafi ba bai gaya miki ba? Ba kin ce ɗan Nijar ba ne?" "Ba shi da lafiya fa, ba zai iya wannan tafiyar ba" "A'a kar ki ce haka, idan ki ka bibiya ma, can ɗin ya tafi, amma yanzu ki yi haƙuri ki tashi mu tafi gida" "Uwani, dan Allah ki yi mini alfarma ki bar ni na kwana a nan" "To ya za ki kwana a gida ke kaɗai haka ake yi?" "Ni dai dan Allah ki bar ni a nan, wallahi da safe zan dawo na yi miki alƙawari" "A'a sai dai na turo yarinya ɗaya ta tayaki kwana" Nana ta amince da hakan, aka turo mata yarinya. Tuni yarinyar ta yi bacci, Nana kuma kwana ta yi aikin kuka. Lokaci Lokaci, sai ta yi tasbihi tare da ajiyar zuciya. Washegari da sassafe Uwani ta zo ta kawo mata abin karyawa. Yadda idanun Nana suka kumbura, ya sanya ta fahimci Nana ba ta yi bacci ba. "Wai ni Nana, babu wani wanda za ki kira, ki tambaye shi ko yaje? Ko kuma wani guri da za ki je a duba?" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza mata kai. "To shikenan sha kunun nan da ƙosai, kar su huce" Nana ta karɓi kunun tana kurɓa a hankali, ji take tamkar tana shan magani, saboda wani irin ɗaci da take ji kunun yake yi mata a bakinta. Amma saboda ba ta son faɗan Uwani, haka ta din ga shan kunun nan da ƙyar. Ta ɗan saci kallon Uwani ta ce "Uwani, ina ga gobe in Allah ya kaimu zan shirya na koma Kano" "Gurin wa?" Uwani ta jefe ta ta tambayar. Nana ta ɗan yi shiru, Uwani ta ce "Gurin wannan masoron Ubannaki da bai san ciwon kansa ba balle ya san naki? Ya kasa tallafa miki da larura ta samu mijinki, yanzu ne idan kin koma zai tsinana miki wani abu? Ga cikin fari ke ba sanin kan abubuwa ki ka yi ba, ga wannan shu'umar matar tasa, da ƙafa duk dama ba tsayawa za ta yi ta kula da ke ba?. Ban ƙi ba ki kira shi, ki sanar masa abin da yake faruwa a matsayin sa na ubanki ba, amma ba dai ki koma wannan gidan ba. Ki yi zaman ki a nan ki haihu, ki yi biƙinki idan mijin naki bai dawo ba, a san abin yi" Tabbas Uwani tana da gaskiya, idan ta koma gidansu rayuwarta ta sake komawa baya, ta san babu wani abin kirki ko kulawa da za ta samu a gidan, wataƙila ma a kore ta. Ummi kuma ta yi mata ɗawainiya da yawa, tana jin nauyin ta sake koma mata da matsala. Kuma ba ta ji a ranta za ta iya sake ko nufar hanyar gidan Alhaji Zailani ba, saboda yin hakan tamkar cin amanar Sayyid ne, kuma ita ba dolensu ba ce, da za ta je ta ɗora musu ɗawaniya. Dan haka Uwani na da gaskiya. Amma zamanta a nan ɗin ma, shi ma dai ɗawainiyar ce. Ta sake ɗago kai ta ce "To ina son na je Bauchi gurin Mamana" "Kai Nana ki na da gardama, gurin nawa ne dai ba za ki zauna ba, kin ƙallafa rai tun da mijinki ya bar garin nan kema sai kin bar shi?" "Ba haka ba ne Uwani, ina da dalili dan Allah ki bani damar hakan" "Shikenan Nana, ba zan matsa miki ba, Ubangiji Allah ya tabattar da alkhairi, amma ki bari kamar nan da sati ɗaya, ki ɗan ƙara samun nutsuwa. Nima na lalubi na mota na baki" "Ai ina da kuɗin mota" "Nima na san ki na da kuɗin motar, na ce zan baki ai" Nana ta ja bakinta ta tsuke. **** Jamila ta yi shirin fita, tana tsaye tana latsa wayarta ta ce "Baba har ya fita ne?" Mama ta ce "Tun da uwar kashinsa ta cika ya fita. Da dai bai ci ba da yanzu yana nan yana bin bango yana zabga hamma yana faɗa da ƙadangaru da bokitai" Jamila ta basar ta ce "Sonake ya bani cikakken kwatancen Buda, zan saka a kai ni, na je na ga Nana" "Wai ba za ki bar maganar Nanan na ba ko Jamila?" "Mama meye laifi idan na je na gan ta ne wai?" Nasiru ya ce "Laaa rannan kuwa wannan ɗan uwan mijin nata, da suka zo a ka kaita gidanta ranar biki, suka zo shi da wasu mutane, suka ce mini wai yanzu Nana a ina suke. Na dawo daga makarantar allo, na ce musu tana Buda can garin su Baba, shi ne ya ce na gaida Baba" Mama ta ce "Ikon Allah, amma yarinyar nan ta ce 'yan uwansa an neme su an rasa. Kai Nana muguwar makira ce ta ƙarshe" Jamila ta ce "Amm na tafi sai na dawo" "To Allah ya tsare, a gaida Hajiyar" " Za ta ji" ta amsa a taƙaice ta fita. Nana ta zauna ta haɗa kayan da za ta buƙata a cikin jaka guda ɗaya. Tattara sauran guri ɗaya, ta ɗauki jakar gurin Sarkin Baka, da kuɗin Nijar ɗin da suke ciki. Ta tattara sauran kuɗin da suke ɗakinta, tana tunanin ta tafi ko da Uwani ba ta sani ba. Ta tattara kayan kitchen ɗin ta, ta ce wa Uwani sayarwa za ta yi. "Me yasa za ki sayar da kayan ki Nana?" "Kawai kuɗin nake buƙata ne" "Gaskiya ba za ki sayar da kayan nan ba, ki bari ranar kasuwa, zan kai Tinkiyata kasuwa, na baki kuɗin amma ba za a sayar da kayan ba" Gaba ɗaya Nana ta ji ta damu yadda ta ɗorawa Uwani ɗawainiya. "Uwani kar ki sayar da Tinkiyarki dan Allah, gara a sayar... "Za ki rufe mini wannan dogon bakin naki, ko sai na kwaɗe ki? Ke ki ka sani na sayar? Ke dai akwai gardama" Babu yadda Nana ta iya, haka ta haƙura sai ranar kasuwa, aka sayar da Tinkiyar. Uwani ta ɗauki dubu talatin a kuɗin ta bawa Nana ta ce "Ban san iya adadin kuɗin da ki ke buƙata ba, amma ga wannan kya jalauta. Dan Allah ki kula da kan ki Nana, duk inda ki ka je idan kin ga akwai matsala, ki dawo mini nan ni zan riƙe ki na kula da ke" Nana ta din ga juya kuɗin, ta kalli Uwani idonta fal hawaye ta ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode" "Babu komai, Ubangiji Allah ya sauke ki lafiya, ya bayyana mijinki cikin aminci. Nan ma za mu ci gaba da jiran jami'an tsaro ko za a samu wani labari daga gurinsu. Allah ya bayyana shi" Nana ta amsa da Amin. Jin washegari Nana za ta bar garin, ya sanya 'yan uwa, suka din ga kawo mata abin alheri cikin mutunci da karramawa, tare da yi mata fatan alkhairi. Washegari da sassafe, Nana ta yi sallama da su Uwani, aka ɗauke ta a babur aka kai ta tashar ƙauyen. Aka kaita Garko, daga nan ta hau motar Kano. A Kano ta hau motar da za ta sada ta da garin Bauchi. Tsawon awanni huɗu da aka shafe, ana tafiya a motar, babu abin da Nana take yi, banda tunani ta saƙa wannan ta kwance wancan. Tunaninta a wani hali yake ciki, ya jikinsa? Su waye suka ɗauke shi? Mene ne makomarta idan bai dawo ba. Lokaci-lokaci ta kan shiga hijjabinta ta yi kuka, ta share hawayenta. Da ta sauka a tasha ƙarfe sha biyu na rana, ta samu abin hawa, har sunan unguwar da Mamanta take ta sani, sai dai ba ta san takamai ina ne gidan ba. Shi ma daga tashar zuwa garin da maman nata take, sai da aka yi tafiyar awa ɗaya da rabi. Ƙafafun Nana duk sun kumbura, da ƙyar take jan su. Ta ɗaukko wayarta ta kira lambar Anty Fati, ta ji ba ta shiga. Ta kira ta Adda Saude ba ta ɗaga ba. Ta nemi guri ta zauna, ta ci gaba da kiran wayar Adda Saude da ita kaɗai take shiga. Sai dai still ba a ɗaga wayar, ga shi ba ta san daga garin, ina ce unguwar da za ta nufa ba. Ta samu guri ta yi alwala, ta ciro sallaya a kayanta, ta shimfiɗa ta yi sallar azahar. Bayan Azahar sosai, Adda Saude ta kira wayar Nana. Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Ta amsa mata ta ce "Nana yi haƙuri, caji na kai wayar ne aka kunna mini, ya ki ke ya gida?" "Lafiya kalau Adda, kin ganni na zo Bauchi ne na sauka, sai dai ban san sunan unguwar da Mama take ba" "Ke haba dai, da gaske ki na Bauchi Nana?" "Eh Adda, na sauka ma tun ɗazu" "Subhanallah, ai ba ki gaya mini za ki zo ba, da tuni an shirya karɓar ki, ban sani ba an bar ki ki na jira, dan Allah ki yi haƙuri yanzu ki na daidai ina, na zo na tafi da ke?" Nana ta ce "Kar ki wahalar da kan ki dan Allah, ina garin ma, sunan Unguwar za ki gaya mini" Sai da Adda Saude ta ɗan ji dumm, amma ta maze ta cewa Nana ta samu abin hawa, ta haɗa ta da mai abin hawan ta yi mata kwatance. Nana ta ce "To" ta samu abin hawa, ta haɗa su ta kwatanta masa, sannan ta hau. Nana ba ta isa gidan da Mamanta take ba, sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar. Mama na tsakar gida tana ta fama da yara, kawai ta ji sallamar Nana. Ta ɗago da hanzari, sai dai ta kasa amsa sallamar ta nufi Nana da sauri suka rungume juna su na kuka. Ta ɗago Nana ta ce "Nana ba ki yi fushi da ni ba?" Nana ta girgiza kai ta ce "Ban yi ba" Ta ja hannun Nana zuwa ɗaki, ta saka yaran su shigo mata da ƙatuwar jakarta. "Sannu da zuwa, tare ku ke da mai gidan naki ne?" Nana ta sunkuyar da kai jikinta a sanyaye ta girgiza kai alamar a'a. "To yana ina shi?" Nana ta yi shiru. Cikin tashin hankali Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nana ba dai auren naki ne ya mutu ba?" Nan ma ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta. "Shikenan, yanzu nutsu. Bari na ɗora miki ruwa ki yi wanka, sai ki yi salla" Nana tana iya ganin tsantsar farinciki a kwance a fuskar mahaifiyarta. Ƙannenta suka kewaye ta, Nana ta din ga kallon su cike da so da ƙauna. Har gara Walida ta ɗan santa sauran kuwa duk ba su san Nana ba. Ruwa mai ɗumi ta haɗa wa Nana, ta yi wanka, ta yi sallar la'asar. Ta zubo wa Nana lafiyayyen Abinci, duk da yadda ranta ya biya a kan Abincin, amma ta kasa sakin jiki ta ci. Mama ta din ga kaiwa tana komowa, tana ta ɗawainiya da Nana tamkar ta goya ta, sai ta ji ina ma tuntuni ta samu irin wannan kulawar ta uwa. "Nana ina Imrana kuwa, ya daina zuwa gaba ɗaya" Nana ta ce "Lagos yake tafiya neman kuɗi" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ai shikenan, ya aka yi ina mijin naki ne? Me ya faru?" "Nemansa na yi na rasa" Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?" Nana tana kuka ta yi mata bayani. Cikin mamaki ta ce "To ina 'yan uwansa? A ina yake a Nijar ɗin?" Sai a lokacin ta fayyace wa Maman komai, game da auren zuwa ɓatan sa. "Nana, me yasa baki neme ni kin gaya mini ba? Yanzu duk wannan abin yake faruwa amma idan muka yi waya sai ki ce mini komai lafiya ƙalau? Ni kaina nan kina raina, ina ta fafutuka na ga yadda zan yi na zo na gan ki. Ba ki kyauta ba Nana, komai lalacewata, ni mahaifiyarki ce, yakamata a ce kin sanar da ni. Yanzu dai ki zauna a nan, mu ga abin da Allah zai yi, kafin ki haihu mu gani ko Allah zai sanya a ga mijin naki. Amma na yi mamaki matuƙa da mahaifinki ya aura miki wanda bai san usulinsa ba? Yanzu ƙiyayyar da yake yi minin har ta kai haka? Ko yana jin haushina amma ai ke 'yar sa ce, bai cancanci ya yi miki haka ba, amma babu komai. Nana abin da nake so da ke, daga yanzu duk abin da ya faru Nana, ko ba zan yi miki komai ba, ki sanar da ni, ki bani dama na taka rawa ta ta uwa a rayuwar ki ko yaya ne" Ta yi maganar tana riƙe hannun Nana. Sallamarsa ce ta tilastawa Nana haɗiye abin da take shirin furtawa, cike da tsoro. Ba ita ba hatta Maijidda, sai da zuciyarta ta buga da ƙarfi cike da tsoro. AYSHERCOOL 08081012143 61 Har zai gifta, zai shiga ɗaki ya hango Nana, cikin rawar baki, Nana ta gaishe shi, ya amsa mata sama-sama ya wuce, dan kallo ɗaya ya yi mata, ya gane ta. Jiki a sanyaye Maijidda ta tashi ta bi shi ɗaki, tana ɗan sinne kai, tana jiran ta ji me zai ce, amma bai ce komai ba. Ta kawo masa Abinci, tana jiran ta ji me zai ce, ga hankalinta a kan Nana, tana so ta je ta yi hira da 'yar ta, su yi hira ta ji ɗuminta, amma ta haƙura. Nana ma na ta gaban ne yake faɗuwa, tana tsoron abin da zai ce, saboda ba ta manta karan battarsu. Haka dai a ɗarare suke hira da yaran gidan. Maijidda na ta son yi masa magana, amma ta kasa. Ya gama cin abincin ya fita, ba tare da ya ce komai ba. Yana fita ta koma gurin Nana, suka ci gaba da hira, Nana ta kwanta a kan cinyar Mamanta, tana jin wani irin farinciki yana ratsa ta. "Kin fara zuwa awo ne Nana?" Wata irin kunya ta kama Nana, ta ɗan sinne kai ta girgiza mata kai. "Gaskiya yakamata, wata nawa ne cikin? Mu je a yi awo a duba, mu ga abin da zamu fara ajiyewa. Mu jira mu ga ikon Allah, idan an ga mijin naki shikenan, idan ba a gan shi ba kuma, ma san abin yi" Nana dai ta yi shiru, sai kuma ta ce "Mama ki yi mini addu'a, ki ce Allah ya bayyana shi cikin aminci" Mama ta yi dariya, ta ce "Lallai kam, to shikenan, Ubangiji Allah ya bayyana mini sirikina cikin aminci" Nana ta yi murmushi, dan kunya ce ta kama ta daga baya, da tuna katoɓarar da ta yi. Da daddare Mai Jidda ta yi wa Nana shimfiɗa, ta saka nata net. Sannan ta tafi nata ɗakin gurin mijinta, har za su kwanta, Mai Jidda ta dubi Iliyasu, jiki a sanyaye cikin ladabi ta ce "Baban Walida, na ga ka dawo ka ga Nana a gidan nan, ba ka ce komai ba" Ya dube ta ya ce "To me ki ke so na ce?" "Ahh dama kar ka ce ban gaya maka ba ne, dama ta ɗan zo ta zauna da ni ne, duba da yadda... "Kin ga dakata, na ɗaga miki ƙafa ne na yi shiru, na ga gudun ruwanki, kar ta wuce mini gobe a gida, ta wuce ta koma inda ta fito" "Dan Allah ka yi haƙuri Baban Walida, Nana ta samu matsala a aurenta ne, dan Allah ka yi haƙuri ba za ta daɗe ba, amma dan Allah kar ka ce ta tafi yanzu. Ni ko ruwan gidanka ka ce ba za ta sha ba, na amince dan Allah" "Ke Maijidda, bari ki ji na gaya miki, wallahi sai yarinyar nan ta bar gidan nan" Ya nemi guri ya yi kwanciyar sa, takaici ya ishi Maijidda. Nana kuwa tana jiyo hayaniyar su sama-sama, abin ya tsaye mata ta kasa bacci sam. Sai juye-juye, ga mararta ta ƙulle duk jikinta ma ciwo yake yi mata. **** Kwance yake a kan gadon Asibiti, jikinsa babu riga, sai dogon wando an rufe iya ƙafafuwansa da koren yadi. Ƙirjinsa kuma an manna masa abin ECG. Sai gashin sa a rufe da hular Asibiti. Na'urorin gefen gadonsa sai sauti suke fitarwa. Dattijo ne a tsaye a kansa, dogo fari tas, ya ɗaura hirami a iya kansa, ga gemunsa dogo duk farin gashin furfura a jiki. Ya kalli mutumin da yake tsaye ya ce "médecin (Likita) yanzu mene ne abin yi?" "Eh, gaskiya za a yi masa wannan allurar ne kamar yadda na yi maka bayani, idan kuma ba haka ba, gaskiya sai dai a saka masa na'ura a zuciyarsa wadda za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa" Na kusa da Dattijon mai sanye da shuɗiyar shadda, da babbar riga, kansa ya yi naɗi da baƙin rawani ya ce "Ka gani ko Sultan, Allah kaɗai ya san abin da suka yi masa a Nigeria. Dole yaron nan ya ɗanɗana kuɗarsa a ci gaba da tsare shi, har sai ya yi bayanin abin da ya yi masa a Nigeria, da aka neme shi aka rasa tsawon wannan lokacin. Su kan su sauran da aka kama su tare, dole a killace su a guri ɗaya, haryanzu ban bari an sake su ba, saboda idan maganar nan ta fasu akwai matsala" Sultan ya numfasa cikin damuwa ya ce "Ni wannan bai dame ni ba, na bar ragamar komai a hannunka, ni lafiyar sa ce a gabana yanzu. Likita ku yi duk abin da ya dace kawai. Lafiyarsa ce damuwata a halin yanzu" Likitan ya ce "In sha Allah" Dattijon ya saka hannunsa a cikin na mara lafiyan,yana kallonsa cikin matsananciyar damuwa. Kamar mafarki ya ga yana motsawa a hankali, sai ya ƙara tattara hankalinsa a kansa yana kiran sunansa. Wata irin miƙa ya yi, yana ƙoƙarin buɗe idanunsa, amma ya ji tamkar an cika masa idanun nasa da barkono. "Imam.. Hannunsa ya ɗora a ka yayi wata irin kururuwa, jin yadda naman jikinsa yake yi masa wata irin azaba, tamkar ana cizgar naman jikin nasa. Ga wani irin zafi da raɗaɗi da yake ji kamar yana cikin wuta. "Zafi! Wayyo wuta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wuta zafi jikina" Kansa suka yi gaba ɗaya cikin tashin hankali, su na ƙoƙarin rirriƙe shi, amma ya watsar da su ya diro daga kan gadon, yana girgiza kansa da yake yi masa wata irin azaba tamkar zai tarwatse. Tunaninsa ne ya hargitse gaba ɗaya, ƙwaƙwalwarsa na ta kokawar ƙwato wani abu daga cikin memories ɗin sa, amma abu ya kacame, gaba ɗaya tunaninsa ya hargitse, ya kasa tantance komai. Fizge-fizge ya din ga yi yana kururuwa jikinsa na rawa. Dattijon nan cikin jarumta da ƙarfin hali, ya bi shi da sauri ya damƙe shi iya ƙarfinsa. Kokawa suka din ga yi, a rikice likita da ɗaya mutumin suka yo kansu, likitan ya haɗa wata allura ya yi masa. Jikinsa ya saki a hankali bacci ya ɗauke shi. Kan gadon suka mayar da shi suka kwantar. Ɗaya mutumin ya kalli likitan ya ce "Ka na ji na?" Likitan ya jinjina kai cikin nutsuwa. "Ka san dai waye wannan, kuma ka san matsayinsa da girmansa ko?" Ya yi maganar yana nuna masa mara lafiyan. Ya jinjina kai ya ce "Na sani" "To muddin mu ka ji maganar abin nan da ya yi, ya fita waje, to ba wani ba ne ba kai ne, dole ka yi shiru da bakinka, kare sirrinsa wajibi ne a kan duk wani wanda yake yankin nan, idan kuma aka samu akasi ka furta wani abu, da rayuwarka za ka biya" Likitan yana tsuma ya ce "In sha Allah ba zan faɗa ba" **** Da safe mijin Maijidda ya shura takalmansa ya fice, bayan sun gama jayayya da ita, tana ta roƙonsa tana yi masa magiya. Gaba ɗaya Nana ta ji dana sanin zuwa Bauchi da ta yi. Babban abin da ya bata mamaki, ƙatuwar kaza Maman ta saka aka yanka, ta gyare ta tsaf, ta yi wa Nana farfesunta, aka sayo mata ƙaton buredi ta haɗa mata shayi. "Mama daga zuwana na ɗora miki ɗawainiya, ba ma na iya cin Abincin ni" "Ɗawainiyar ƙaniyarki, da can na yi miki ne Nana? Dan Allah ki daure ki mayar da hankali ki ci ki ƙoshi, idan kuma ki na son cin wani abin, ki gaya mini sai na dafa miki" "A'a ba na son cin komai, amma ki zo mu ci tare da su Walida" Maijidda ta ce "A'a, babu wanda zai ci, da rana ma ci Abincin tare, wannan dai na ki ne" Haka ta takura Nana, ta karya. Nana ta fito da nufin, ta kama musu ayyukan gida, amma Mama ta hana, ta dafa mata ruwa ta yi wanka. Ta fito ta tarar Mama tana wanke kayan da ta cire. "Haba Mama dan Allah ki bari na wanke da kaina, ya za ki din ga yi mini wanki?" "Tafi ɗaki ki je ki zauna ki huta, ga lemon fata can da rake, ki ɗan sha saboda ɗanɗanon bakinki. Akwai riɗi ma mai gishiri da mai suga, idan da wanda ki ke so" kawai Nana ta tsaya tana kallon ta, tana murmushi. Maijidda ta ce "Ya dai?" Ta girgiza kai ta ce "Ba komai Mama, na gode sosai" Nana ta shirya ta canza kaya, Khadija da take 'yar autar Mama, Nana ta kama ta tana tsefe mata kai. Ta ɗauki wayar Nana tana kallon hotuna. Sai ta buɗe wani video da Nana ta yi wa Sayyid,  ta yi masa kitso sai hararta yake yi tana cewa "Ka ga yadda ka yi kyau 'yan matana, yi murmushi mana" ya ɗago kansa ya hargitse idanunsa. Nana tana dariya. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, gani take kamar ta shiga cikin wayar ta ga Sayyid ɗin ta. "Anty Waye wannan?" "Mijina ne" ta ba ta amsa tana murmushi. "Ya na gan shi da kitso, kuma fari?" Nana ta yi dariya ta ce "Ni kuma baƙa ko?" "Eh, kuma ba kyau maza su yi kitso fa" "Wai in ji wa? Ba ki ga gashin nasa ne da yawa ba?" Khadijah ta ce "Eh, to yana ina yanzu?" "Ya je unguwa, zai dawo ya ɗauke ni mu tafi" "To ki nuna mini shi idan ya zo" Nana ta ce "To in sha Allah" Mama ta ce "Ke Khadijah, tashi ki bar ta ta huta, Nana kwanta ki huta, ki rabu da surutun yarinyar nan" Khadijah ta tashi tana zumɓura baki, Nana ta ɗan kashingiɗa kawai wani abu mai kama da bacci ya yi awon gaba da ita, kasa tantance ma me take yi ta yi, bacci ne ko kuma ido biyu. "Ma Vie" ta ji muryarsa a kunnenta. A razane ta waiwaya cikin damuwa. A tsakiyar sahara ta hange shi ta ce "Sayyid" Ganinsa ta yi a tsaye a kanta, kayan jikinsa duk a yayyage, ya yi baƙi kamar ya ƙone, gashin kansa a hargitse jikinsa sai fitar da hayaƙi yake, ya ce "Ma Vie sun mayar da ni inda za su kashe ni, dan Allah ki zo kar su kashe miki ni." Yayi maganar yana hawaye. Ta tashi cikin tashin hankali ta ce "Suwaye? Kuma a ina suke?" "Dan Allah ki zo, ni ban san su ba, amma na san mutuwa zan yi, dan Allah Husnah ki zo gurina, za su kashe ni. Idan kuma sun kashe ni, ki kular mini da ɗa na" "Sayyid, dan Allah kar ka tafi ka bar ni, dan Allah Sayyid ka dawo? Ka gaya mini kana ina, sai na zo na same ka na tafi da kai" Guguwar Sahara ce, ta taso ta turnuƙe gurin. Nana ta din ga tari, muryar Mama ta ji a kanta tana faɗin "Tari ki ke haka Nana?" Kawai ta ga Nana ta tashi, ta yi waje. Ta riƙe ta ta ce "Ina za ki ke?" Idanunta a rufe, fuskarta a murtuke ta ce "Ba ki ji Sayyid ne yake kirana ba?" "Waye hakan?" "Mijina mana" ta faɗa a fusace. "A'a babu wanda ya kira ki fa" Nana ta fara ƙoƙarin fizge hannunta ta ce "Yanzun nan fa ya fita daga ɗakin nan" "Nana babu kowa fa a gurin nan, daga mu sai ke" "Ni ki cika ni, na ji Muryar mijina gurinsa zan je yana kirana" Tsawa ta daka wa Nana ta ce "Ina magana ki na ɗaga mini murya? Wuce ki zauna babu wani wanda yake kiran ki" Nana ta buɗe idanunta, ta kalli Mamanta, sai dai ba ta yi magana ba, kawai ta ga Nana ta yi baya za ta faɗi. Ta riƙe ta ta kwantar da ita. Jikin Nana ya hau karkarwa, idanunta na fitar da hawaye. Cikin matsananciyar damuwa take kallon Nana, tana tunanin dama har zuwa yanzu, tana fama da larurar nan?. Ta rungume Nana a jikinta, ta kama goshinta, ta fara karanta mata Suratul Jinn, tana tofa mata a fuskarta. A hankali jikin Nana ya saki ta fara bacci. Ta yi shiru tana kallon fuskar Nana, tana tuna lokacin da take rungume da ita tana jaririya, cike da so da ƙauna.  Tare da tuno irin soyayya da rawar ƙafar da Isa ya din ga yi lokacin da aka haifi Nana, ba ta taɓa tunanin zai yi wannan riƙon sakainar kashin da rayuwar Nana ba. Adda Saude ce ta yi sallama, Mama ta amsa mata. Ta ɗan yi turus ta ce "Ya dai Nanan ba ta da lafiya ne, na ganta a kwance a jikinki haka?" "Wallahi kuwa, shigo daga ciki" ta zauna ta ajiye kayan da ta zo da su. Ta ce "Tun jiya na so zuwa, tun da muka yi waya da ita da ta ce mini tana garin nan, babansu ne baya nan bai dawo da wuri ba ga yara gidan babu kowa. Ikon Allah ciki ne ma da ita haka?" "Ga shi nan dai, har ya yi girma ma" "Ikon Allah, na yi mamaki da na ji zuwa ta yi babu sanarwa, tare da mijin suka zo?" Maijidda ta numfasa ta ce "A'a, matsala ma aka samu, ba a san inda mijin nata yake ba" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, garin yaya ina ya tafi?" "Wallahi ban sani ba, na dai ce ta zauna a nan, kafin nu ga abin da Allah zai yi. Ashe rashin lafiya ya sha, yarinyar nan ba ta taɓa gaya mini ba. Ga babanta bai karɓe ta ba, ƙarshe ma sai Buda ta koma ta yi jinyarsa, kuma dai ma ya tafi ba a san inda yake ba" Cikin jimami Saude ta ce "Kai subhanallah, abin nan bai yi daɗi ba, yanzu meya same ta haka?" "Iska ne ya buge ta, na ba ta abinci ta karya, ta fara bacci kawai ta tashi wai mijin ne yake kiranta. Ashe haryanzu tana fama da wannan matsalar. Wallahi Adda na yi dana sanin biye wa Iliyasu na watsar da yaran nan." Ta yi maganar hawaye na cika mata ido. "Ki yi haƙuri, amma yanzu ya ku ka yi da shi?" "Hmm mu na nan muna ta bugawa, wai sai ta bar gidan nan, ni kuma Nana ba za ta bar gidan nan ba, sai dai mu tafi tare" A ɗan tsorace Adda ta ce "A'a Maijidda, idan da matsala, a kaita gidan Fati tun da tana da yalwar guri, ko gurin Yakumbo,kar ku samu matsala" Ta girgiza kai ta ce "Ni na ke son kula da Nana da kaina. A cikin su ban san wanda zai ji ƙan wani ba, dukkaninsu su na buƙatata". Nana ta farka tana ɗan yin miƙa, ta cewa Maijidda fitsari za ta yi, ta raka Nana banɗaki ta je ta yi fitsari, ta saka ta ta yi alwala ta koma ta kwanta. Har zuwa yamma Adda na gidan, sai daf da magariba ta tafi, Nana kuma ta wartsake sai ciwon jiki da mararta da ke ɗan murɗawa. "Nana, ranar Litinin in sha Allah za mu je Asibiti, a fara yi miki awo, kuma zan duba gurin masu magungunan islamic ɗin nan, mu je a duba ki" Nana dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Da sallar Isha'i, Baban su Walida ya dawo, tun da ya hangi Nana a ɗaki, ya turnuƙe fuska ya kalli Mai Jidda ya ce "Me na ce miki a game da yarinyar nan?" "Baban Walida, ba a yi wa ɗa mugunta, dan Allah ka yi haƙuri ka bar Nana a gidan nan, ka ga 'yan uwanta ma duk ba su santa ba, ba su saba ba. Kuma ba a san me gobe za ta haifar ba. Wataƙila ita ce mai tallafar rayuwar ƙannen nata nan gaba." "Ni ba nusari ne kamar ubanta ba, ni zan tallafi rayuwar 'ya'yana. Ba na buƙatar ko sisinta a kan yarana. Ta koma gidan mijinta ko gidan ubanta, idan ba haka ba sai dai ki zaɓa, ko ta bar mini gida, ko kuma auren ki." Kafin ya rufe bakinsa ta tari numfashinsa ta ce "Na zaɓi 'ya ta, zan tafi tare da Nana, ko a daji ne na rayu da ita na kula da ita. Tun da ba dan wahala da bautarka da ta 'ya'yanka kawai Allah ya yi ni ba. Ba ka da kara Iliyasu. Nan har 'ya na riƙe maka na aurar da ita ban yi mata mugunta ba. Har 'ya'yan 'yan uwanka ka kawo mini na riƙe, ban taɓa muzguna musu ba, na riƙe maka, nawa 'ya'yan ne na banza kenan? Ƙiri-ƙiri ɗan da na durƙusa na haifa ya tsane ni, saboda yana ganin na kawo su Duniya amma ban damu da su ba. Su 'ya'yan da na riƙe maka haifar su na yi? Ko kuma dolena ne su, ni 'yar guda ɗaya ka gaza yi mini kara a kanta? To ka sani duka yau duka gobe shi ke sanya baƙin ba'auzine yin tawaye. Zan zube maka yaranka na ɗauki 'ya ta na tafi da ita, na kula da ita. Ka kwaɗa gidan ka cinye da kai da 'ya'yan naka" Cikin matsanancin mamaki ya ce "Maijidda, ni ki ke gaya wa wannan maganganun?" Cikin ƙunar rai ta ce "Na faɗa ɗin, shekara nawa na rayu da baƙin cikin rashin ganin 'ya'yana, kullum na motsa zargina ka ke da tsohon mijina. Ƙaddarar haihuwar yaran nan biyu ta sanya ban aure ka da fari ba na fara auren sa, amma a kan dalilinku marasa tushe balle makama kun azabtar da ni da nesan ta ni da yarana. Wallahi wannan karon na zaɓi 'ya ta" Kamar zubar wuta, haka Nana take jiyo cece kucen su. Dana sanin zuwa gidan ya cika mata zuciya. Tabbas ba za ta so mahaifiyarta ta kashe aurenta, da wannan gayyar 'ya'yan saboda ita kaɗai ba, idan ta bari hakan ya faru ba ta yi musu adalci ba baki ɗaya. Zurfin tunanin da ta tafi, bai bari ta gama jin yadda rigimar ta su ta kaya ba. A cikin daren bayan gari ya yi tsit, ta tashi ta haɗa kan kayanta cif. Ta laluba jakunkunan yaran na makarantar boko, ta samu biro da takarda ta yi rubutu, ta ninke ta ajiye a kan katifar ta. Da Asuba, Mama ta zo ta tashe ta, ta yi alawala ta yi sallar Asuba. Ganin yaran na ɗaya ɗakin su na salla, Mama ma tana bedroom ɗinta, tana salla, ya sanya ta lallaɓa ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan. Ta din ga zumbuɗa sauri, tamkar za ta tashi sama, ga faggon kaya. Tafiyar ƙafa ta ci sosai da sosai, har sai da gari ya yi haske, masu abin hawa suka fara fitowa, ta tari wani ta ce ya kai ta tasha. Yana kai ta tasha, ta yi sa'a an yi lodi saura gurin mutum biyu, tare da wata mata suka shiga tasha suka nufi babbar tashar Bauchi. Daga babbar tashar Bauchi, ta hau wata motar, duk da zuciyarta na raya mata kamar matakin da ta ɗauka ya yi tsauri, wata zuciyar kuma na raya mata shi ne mataki mafi cancanta da za ta ɗauka, mussaman idan ta tuna yanayin yadda ta yi mafarkin Sayyid. Wayarta ta ciro, ta shiga lambar Ummi, ta rubuta mata saƙo, sai da ta tabattar ya tafi, sannan ta kashe wayar, ta cire layinta daga cikin wayar. Gari ya ɗan fara haske, Baban su Walida ya fice, a matuƙar zuciye, ya yanke shawarar tafiya ya kai ƙarar ta, tun da dama ya san ya saba samun goyon baya, ba ga taɓa kai ƙararsa ba, amma shi ya kai ta ta, ya fi sau shurin masaƙi. Su Khadija har sun fara ƙiriniya a tsakar gida, a zuciye kasancewar da takaicin ubansu ta kwana ta daka musu tsawa, ta ce su koma ɗaki, kar su tashi Nana. A zaton ta Nana tana cikin ɗaki tana bacci. Jamila ce zaune a gidan Ummi, tana jajanta abubuwan da suka faru da Nana, ba tare da ta san ma hakan ya faru ba. "Wallahi Ummi da an sanar da ni zancen matar nan, da suka ce Nana mayya ce, wallahi da sai na saka an rufe ta, sai na ja shari'a da su har gaban Alƙali, sun san girman sharrin maita kuwa?" "Hmm ke dai a yi sha'ani, ga shi Nana ta bar gidan, amma an ce Haryanzu tana kwance babu lafiya matar, ni na fi tunanin ko Aljanun Nanan ne suka yi mata wani abin, tun da ta ce Nana take gani. Jamila wayar Nana fa ba ta shiga, ni kaina sai na shafe sati biyu ban yi magana da ita ba, saboda garin babu network. Haka nan za mu tafi kawai." Ummi ta shirya, da Jamila Abba ta so ya kai su, sai ta yi wani tunani ta fasa, dan ba ta san a yanayin da za su je su tarar da su Nana ba. Sai dai Ummi ta sha mamaki da suka isa garin, suka tarar da gidan Nana a garƙame. "Ikon Allah, ita kuwa Nana ina tafi haka? Ko sun je Asibiti ne?" Jamila ta ce "Asibiti yau Asabar?" "To maybe emergency suka je, kin san matsalar Zuciya yake fama. Mu ƙarasa gidan Uwani". Suka zagaya gurin Uwani, ta yi murna sosai da sosai da ganinsu, sai dai ta hau Jamila da faɗan ba sa zuwa sai yanzu, da yake Nana ce a garin. Ummi ta yi ta bata haƙuri, ta ce sun zo duba Nana ne, sun tarar da gidan a rufe. "Ohh abin tsiya, ba ma kwa bibiyar halin da take ciki, to Nana tun shekranjiya ta bar Buda, mijinta aka nema aka rasa ko sama ko ƙasa sama da sati biyu, ta ce mini gurin Babarta za ta tafi a Bauchi, babu yadda ban yi da ita mu yi zamanmu da ita a nan, amma fafur ta ce in ƙyale ta, tafiya za ta yi". Jamila ta ce "Danƙari" Ummi kuwa "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" kawai take maimaitawa. "Amma me yasa Nana ba ta dawo gida ba, sai ta tafi Bauchi, bayan ta san halin Baba" "Baban wofi, uban me zai tsinana mata, ko ta je gurin nasa" Suka gama jimamin da za su yi, suka tashi suka tafi. Jamila ta ce "Anya Ummi mu gaya wa Baba kuwa?" Ummi ta ce "Tun da shi ya haife mu, ba dole a gaya masa ba. Wallahi duk cikinmu babu wanda ya sha azabar ds Nana take sha a rayuwarta, da kin ga yadda take shan wahala da mutumin nan, sai kin tausaya mata, gaskiya idan guduwa ya yi ya bar ta, bai yi wa kansa adalci ba." Suka ci gaba da jajanta lamarin. Da suka shigo gari, Jamila ta tafi gida, Ummi ma ta tafi nata gidan. Mama na ganin Jamila ta dawo, ta fara yi mata tambayoyi, amma Jamila ta yi burus, ba ta gaya wa Mama komai ba. **** Tare da Kawun Mai jidda Iliyasu ya dawo, yana ta faman bambamin ta lalace, abin da ta ga dama shi take aikatawa. Sai kuma Adda Saude da suka taho tare, dama sai da ta yi tunanin a samu matsala saboda zuwan Nana. Suka tarar da Maijidda idanunta jawur, fuskarta babu annuri. Suka zazzauna a falonta, kawunta ya dube ta ya ce "Mai Jidda ban san ki da rashin ji ba, me yake faruwa ne?" Jiki a sanyaye ta miƙa masa takardar da Nana ta bari a kan shimfiɗarta. "Wannan ɗin na mene ne?" "Ku duba" ta yi maganar hawaye na zubo wa daga idonta. Adda Saude ta karɓa, ta buɗe takardar "Assalamu alaikum, na san lokacin da za ki ga takardata, na riga na yi nisa. Mama ina mai baki haƙuri da matakin da na ɗauka ban sanar da ke ba. Ba zan so a dadlilina nikaɗai ki bar ƙannena ba, dan Allah Mama ki yi haƙuri ki zauna da su. Na tafi neman mijina, a bawa baban su Walida haƙuri, amma kwana biyun nan da muka yi tare, ya fi kowane kwanaki yi mini daɗi a rayuwata na gode sosai Nana Asma'u" Shiru suka yi bayan da Adda Saude ta gama karanta rubutun, sai sautin kukan Maijidda da yake tashi. Cikin kuka ta ce "Shekara nawa ina yi masa kara, na riƙe nasa 'ya'yan? Amma ni sau ɗaya ya gaza yi mini kara, 'ya'yana sun tsane ni, a kan laifin da ba su suka yi ba, bai yadda su zo inda nake ba, nima kuma ba zan je ba. Idan na yi magana a ce na yi haƙuri, yarinyar nan ga tsohon ciki ina za ta tafi? Mijin da ita kanta ba ta san a ina yake ba" ta ƙarasa maganar tana ƙara rushewa da kuka. Kawu cikin sanyin jiki ya ce "To ita Nanan ya aka ta tafi babu sanarwa?" "Tun da ta zo yake masifar sai ta bar gidan nan, babu irin magiyar da ban yi masa ba, amma ya din ga ɗaga murya yana bala'i, gaskiya bayan Nana zan bi, ko zan ganta, ban san ina za ta je ba, da ta fita da tsohon cikin nan" "A'a ba za a yi haka ba, ki yi haƙuri Mai Jidda, rashin kyautawa Iliyasu ba ka kyauta ba, shi ɗa na kowa ne. Kuma tabbas mun daɗe mu na tausar ta, a kan ra'ayinka, ba tare da ba ta damar jin ta bakinta ba. Ka san raɗaɗin da yake cikin raba ɗa da uwa kuwa? Ba ka kyauta ba" Cikin kuka ta ce "Kawu dama ya bani zaɓi, na zaɓi 'ya ta, ya sauwwaƙe mini na fita na nemi yarinyata" Kawu ya ce "A'a ba za a yi haka ba, duk inda Nana take yanzu ta yi nisa, kuma idan aka ƙyale ki, ke kan ki ba ki san ina za ki nufa ki neme ta ba. Amma tun da ba yarinya ce ƙarama ba, na san duk inda take Allah zai kare ta, ki ci gaba da yi mata addu'a. Na san ina sha Allah, babu abin da zai same ta, amma batun ki ce ki kashe aure, ki bi ta ki zauna da ita ba mafita ba ce ba, haƙuri kin saba yin sa, a wannan karon ma shi ɗin dai zan baki, na san duk wanda aka ce wa ya yi haƙuri an zalunce shi ne, amma dai ki yi haƙuri. Kai kuma Iliyasu magana ta domin Allah, ba ka yi kara ba, ba ka kyauta ba ko kaɗan. Yaran nan saboda halinka sun daina zuwa inda take tsawon shekaru, amma daga zuwan yarinyar ka hau bala'i har ta ji, ta yanke wannan hukuncin. Ina kai auren ƙanwarka ne ya mutu, mijinta ya ƙi riƙe 'yar ka karɓo ka kawo mata ta riƙe maka? Har zama fa ta yi da ƙanwarka ta riƙe maka kan ta sake wani auren, amma kai ka kasa yi mata kara, a kan yarinya guda ɗaya tal". Iliyasu ya zata a wannan karon ma, za a goya masa baya, kamar yadda aka saba tsawon shekaru goma sha, sai dai ya ji wannan karon ba a goyi bayansa ba, sai ya yi tsuru-tsuru, dan haƙuri tabbas ya san Mai Jidda na da haƙuri da kawaici. Kawai ya tsani babansu Nana ne, saboda yadda aka fasa aurensa da ita, ta aure shi, shi yasa tsanar ta shafi su Nana. Haka aka din ga ba ta haƙuri, Kawunta ya yi ta rarrashinta. Nana tana zaune a cikin mota, daga jikin taga, tana kallon hanya, yadda ake ta kwarara gudu a motar, tamkar direban zai tashi sama. Gudun da motar take yi, bai dame ta ba, fatanta Allah ya sanya matakin da ta ɗauka, ya zama alkhairi a gare ta. Duk da ta san Nijar ba gida ne ba, ba unguwa ba ba kuma ɗan ƙaramin gari ba, ƙasa ce sukutum, mai ɗauke da garuruwa daban-daban da ƙabilu masu tarin yawa, balle kai tsaye tana zuwa ta doshi inda za ta gan shi. Duk ba abu ne mai sauƙi neman mutumin da ko ainihin sunansa ba ta sani ba a gari kamar wannan, amma tana jin a ranta motsi ya fi laɓewa, kuma rashin jini rashin tsagawa. Wannan shi ne mataki na ƙarshe da za ta iya ɗauka domin nemawa kanta mafita. Ta yarda da cewa Sarƙar, ƙaddara ce ta haɗa ta da Sayyid, ta yi wa rayuwarta dabaibayi, mussaman da ya tafi ya bar ta da ajiyarsa a tare da ita. Sai dai bayan wannan tana cike da zullumin halin da yake ciki, saboda ta san kaso mafi yawa na mafarkin ta ya kan zama gaske, a jikinta take jin duk a inda yake, yana buƙatarta a kusa da shi. Hankalinta ne ya dawo jikinta, bayan da ta ji ana cewa, an tsallaka boda sun shiga ƙasar Nijar!. AYSHERCOOL 08081012143 62 Jamila na ɗaki tana jiyo maganar Baba ya dawo, ba ta fito ba, sai da aka jima sannan ta fito tsakar gida. Ya ce"Jamila kun dawo ashe? Yaya ku ka baro Nanan?" Jamila ta yamutsa fuska ta ce "Bamu tarar da Nana ba, ta bar Buda ta tafi Bauchi gurin mamanta, kamar yadda Uwani ta gaya mana" A fusace ya ce "Bauchi gurin Maijidda? Lallai yarinyar nan ta riƙa ba ta ganin mutuncina, gidan ubanta ne a Bauchin da ta tafi? Uban me za ta yi a can?" Jamila ta ce "A'a Baba, kar ka ga laifinta fa, a lokacin da take buƙatar taimako, ba a duba ta ba. Na san ta bar Buda ne dan kar ta din ga ɗora wa Uwani ɗawainiya" Cikin kumfar baki ya ce "Wallahi ba zai yiwu ba, sai ta baro Bauchin nan, tun da dai ba gidan ubanta ba ne ba, kuma laifin Uwani ne ai da sai ta sako ta a gaba ta dawo da ita nan Kano, dan me za ta tafi wata Bauchi" Ummi ce ta yi sallama, suka amsa su na kallon ta. Jamila ta ce "Ummi ya dai? Ya na gan ki kuma?" "Ke Ummi, ke ce babbar algunguma, na san duk abin da Nana take yi kin sani, tun da da ke take shawara, ke ki ka bata shawarar ta tafi Bauchi ko?" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a, ba ni ba ce ba.  Dan hatta ɓatan mijinta ni ban sani ba, ba ta gaya mini ba sai yau da muka je Buda". Cikin rashin fahimta Baba ya ce "Ɓatan mijinta kamar yaya?" Ummi ta ce "Baba, duk ba wannan ba. Jamila bayan rabuwarmu ina shiga gida, saƙon Nana ya faɗo wayata, hankalina a tashe yake fa" "Ban gane ba, saƙon mene ne, ke Ummi ki yi mini bayani gwari-gwari sai wani kwalo-kwalo ki ke yi mini" "Baba, yau da muka je Buda, Uwani ta sanar mana, mijin Nana an neme shi an rasa kusan sati biyu. Har gurin 'yan sanda suka kai cigiya ba a san inda ya tafi ba. Bayan mun dawo ina shiga gida, saƙon tex message ɗin ta, ya shigo wayata. Ungo ka karanta message ne kusan kashi uku ga shi nan" Ya saka hannu ya karɓa, cike da fargabar abin da zai gani. "Assalamu alaikum, Ummi ya ki ke, ya su Islam. Ki yi haƙuri ban sanar miki ba, ba na son ɗaga miki hankali ne. Sayyid fa ya ɓata, daga na je sayo abu, na dawo na neme shi na rasa, ba na son ci gaba da ɗora miki ɗawainiya, ita ma Uwani yau da gobe sai Allah, ba ƙarfi ne da ita ba. Na je Bauchi Mama ta karɓe ni hannu bibbiyu, amma kamar zuwana zai zame mata matsala a gurin mijinta. Na san ko na koma gida, babu lallai Baba ya karɓe ni, na yanke shawarar na tafi Nijar, ko zan ga Sayyid ko danginsa. Kar ku ɗaga hankali gurin nema na, in sha Allah ba zan aikata abin da zai zame mana abin Allah wadai ba. Yanzu haka ina hanyar Niger, kar ku yi wahalar nema na, in sha Allah zan kasance cikin aminci, ku taya ni da addu'a. Nana Asma'u" A fili Baba ya karanta saƙon. Cikin fusata da tashin hankali ya ce "Wace irin mahaukaciyar yarinya ce Nana? Uban wa ye da ita a Nijar ɗin da ta wanke ƙafa  ta tafi can? Banda tsabar hauka da rashin hankali da wauta, a gidan uban wa za ta sauka? Ba nan ta ce mini ba ta san suwaye danginsa a can ɗin ba, to gidan uban wa ta tafi?" "To Allah dai ya kiyaye ya sa ba ɗaukar magana ta tafi ba" Mama ta yi maganar tana kwaɓe baki, wanda tun da aka fara magana da ba ta saka baki ba. Bai kula ta ba ya ce wa Ummi "Ke kira mini ita dan ubanta ta dawo gida, ko ƙasa nake ci ta zauna mu ci tare" Ummi ta ce "Baba wayarta fa ba ta shiga, tun kafin na zo gidan nan, nake ta gwadawa, amma ba ta shiga." "Ki sake kira ki ji dai" Ummi ta karɓi wayar ta kira Nana, amma aka ce wayar a kashe take. Baba ya dasa faɗa, Ummi a sanyaye ta ce "Dan Allah Baba kar ka yi mata baki, wallahi idan aka nustu Nana ba ta da laifi a cikin lamarin nan. Tin fil azal fa ba bincike aka yi ba, ba a san daga ina mutumin nan yake ba, ka aura mata shi, saboda kawai ka na tunanin su na aikata ɓarna, alhalin babu cikakkiyar hujja da ta nuna hakan. Ba ta bujire maka ba ta yi biyayya, duk dan kar ta dawo gidan nan, kamar yadda ka gindaya mata cewar babu zawarci, ya sanya ta dage kai da fata, ta yi aiki tuƙuru ta jure wahala da ƙalubale take jinyar mutumin nan. Ka san Nana da gudun magana, duk tsoron abin da ka iya biyo baya ya sanya ta yanke wannan hukuncin, ka yi haƙuri a yi mata addu'a kamar yadda ta buƙata " "Amma Ummi, Nana ko yayyanka Naman jikinta zan yi na cinye dan ba'i ba gara ta dawo mini nan ba! Dan me za ta kama hanya ta tafi Nijar? Gurin uban wa za ta je?" Jamila ma ta ce "Tun da dai ta riga ta tafi, dan Allah ka yi haƙuri" Baba ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ya shuri takalmansa ya yi waje. ***** Su na tafe a hanya, Nana tana addu'a, tana fatan Ubangiji Allah ya sauƙaƙa mata, ya taƙaita mata wahala. Ya haɗa ta da Sayyid cikin aminci, tare da fatan duk inda Sayyid yake, ya kasance cikin aminci. Ta maimaita Hsbunallahu wa ni'imal wakil, babu adadi, tare da tawasalli da ayoyin Alƙur'ani a kan Allah ya shiga lamarin ta, ya sauƙaƙa mata wahala. Ƙarfe shida saura, Nana suka sauka a  Maraɗi. Tun a Nigeria ta sai 'yan kayan ciye-ciye ta zuba a Jakarta. Ta yi sallar la'asar ƙasaru, sannan ta tsaya tana ƙarewa tashar motar kallo, tana tunanin ma ta ina za ta fara. Ta ji ƙafafuwanta kamar ba a jikinta suke ba, saboda nauyi, sun kumbura sun yi suntum, saboda azabar nauyi da gajiyar tafiya. Ga ɗan cikinta ya yi jingim ko motsi ta ji ya daina yi saboda azabar wahalar tafiya, Bayanta da mararta suka ƙulle mata, saboda azabar wahala. Ga jikinta tamkar an sassara ta, saboda gajiya babu isasshen gurin miƙe ƙafa. Masu babur na ta tambayarta ina za ta je, amma ta yi musu shiru, ta ɗauki bagcon kayanta, ta yi gaba. Tamkar ba ta jin jikinta, haka ta din ga jefa ƙafa tana tafiya. Ta yi nisa sosai da tasha, ta fara hango unguwanni da gidaje. Duhun magariba ya rufa, ta samu wani gida kawai ta shiga. Matar na tsugune tana tuƙa tuwo Nana ta yi sallama. Suka gaisa da Nana, matar ta tsaya tana kallon ta, ta ji abin da ya kawo ta. Nana ta ce "Dan Allah baiwar Allah, ni baƙuwa ce, hanya ce ta biyo da ni, dan Allah salla nake son na yi, idan babu damuwa zan kama ruwa ne na yi alwala". Matashiyar matar ta ce "To ba komai. Ga banɗaki nan da buta a ciki" Nana ta ajiye kayanta, ta shiga banɗakin ta zubar da uban fitsarin da ya cika mata mara dam. Ta yi miƙa saboda gaɓoɓinta da suke yi mata ciwo. Sannan ta yi alwala, bayan ta yi alwalar, ta tsaya ta ɗaga cikinta, tana ɗan tattaɓawa cike da damuwa, jin sa shiru bai dame ta da motsi ba. "Haba yaron kirki, ka motsa mana ko na ji daɗi, haba ɗan Baba. Nana na cikin damuwa dan Allah ka motsa" ta yi maganar a hankali cikin tsoro da damuwa, dan ta ji ana cewa idan ɗa ba ya motsi, to mutuwa ya yi. Har ta fitar da ran ɗan nan zai motsa, ta tsorata idonta ya fara cika da hawaye, kawai ta ji ya motsa a hankali, sai kuma ya ci gaba da motsawa. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta shafa cikin ta ce "Alhamdillah, Allah ya bayyana mana Sayyid ɗinmu cikin aminci" Gaba ɗaya ta manta a banɗaki take. Ta fito matar ta ba ta dadduma a ɗaki, ta shiga ta tayar da salla. Bayan ta idar da sallar, ta zauna a kan sallaya, ta din ga tasbihi tana gaya wa Allah damuwarta, har aka yi sallar isha'i. Nan ma ta tayar da salla ta yi, tana cikin addu'a matar ta shigo da kwanuka, ta ajiye. Nana ta shafa Addu'ar ta kalli matar ta ce "'yar uwa Na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode ƙwarai da gaske" "A'a babu komai, musulmi ai ɗan uwan musulmi ne, ki ci abinci kafin ki tafi dan Allah" Nana ta ce "A'a, na ƙoshi Alhamdillah, Allah ya saka da alkhairi, ya biya miki buƙatunki na alkhairi" Matar ta ce "A'a daga gani daga tafiya ki ke, ga juna biyu, ai sai wahala, dan Allah ki ci ko kaɗan ne kafin ki tafi" Nana ta dage matar ma ta dage. Da ƙyar Nana ta amince ta ɗan ci Abincin kaɗan sai dai babu abin da take tunani, sai yadda za ta yi da gurin kwana. Ta rufe sauran Abincin ta ce "Na gode sosai da sosai 'yar uwa, Allah ya saka da alkhairi" Matar ta amsa da "Amin, Allah ya kiyaye hanya" Nana ta amsa da Amin, ta ɗauki jakar kayanta ta yi waje. ***** Babar Nana wuni ta yi sukuku, gaba ɗaya hankalinta a tashe, sai koke-koke take yi. Baban su Walida kuma ya yi burus da ita. Ganin kuka da damuwa ba zai fishshe ta ba, ya sanya ta yi alwala ta hau kan sallaya, ta gabatar da salatul haja, sallar neman biyan buƙata a gurin Allah. Ta ɗaga hannayenta tana kuka, take yi wa Allah kirari da magiya. "Allah kai ne Allah, Allah kai ne ka halicce ni ka kuma halicci Nana, ka rayata ta girma cikin ikonka da kulawarka. Ya rabbil arshil azim duk inda yarinyar nan take, Ubangiji Allah ka kai mata ɗauki, da ita da abin da yake cikinta. Allah ka kare ta daga dukkanin sharrin abin ƙi, Allah ka zama gatanta ka tsare mini ita. Ya hayyu ya ƙayyum domin kyawawan sunayenka maɗaukaka masu girma, Ubangiji Allah ka kai wa Nana ɗauki, ta inda ba ta zata ba" ko abinci ba ta iya ci ranar ba, gaba ɗaya addu'ar wunin ranar, Nana kawai take yi wa. Can gida Baban su Nana ma, an ba shi Abincin dare, amma ya gagara ci sai uban tagumi da ya rafka. Lissafinsa kawai gidan uban wa za ta ga je a Nijar? Hannun wa za ta faɗa kuma a ina za ta kwana? Nasiru kuwa tun da ya samu labari shi ma abin duniya ya dame shi, kuma ya ɗora alhakin hakan a kan mahaifin su. Mama ta ce "Wai baban Jamila ba za ka ci Abincin ba sai ya sandare?" "Wai wane Abinci zan iya ci? Wanan shashashar yarinyar, tana can babu uban da ya san a yaya za ta kwana? Kai Nana muguwar sokuwa ce. Kin ga ɗauke Abincin nan, gurin Malamin Almajiran can zan je na gaya masa, ko kiranye ne a yi mata ta dawo gida dan ubanta". "Kiranye kuma?" "Eh mana, tun da dai shi mijin nata mutumin banza ne, bai san abin da ya dace ba, ya tafi ya bar ta, ai sai ta dawo gida, tun da ba ƙanin ubanta ba ne" Jamila ta ce "Kayya! Ba na tunanin wani kiranye zai yi wa Nana tasiri, ka san tana da haƙuri amma akwai taurin kai" "Aikuwa wannan karon, dole ya kama ta, duk gidan uban da ta tafi, sai ta dawo" ya yi maganar a fusace ya fice fuuuuu. Sagir yana tsaka da bacci, ya buɗe idonsa ya ga Shukura a zaune. "Sweetheart lafiya kuwa? Ya na gan ki a zaune?" Ji ta yi tamkar ta kifa masa mari, amma ta maze ta ce "Ba na jin daɗi ne" Ɗan rikicewa ya yi, ya tashi ya matsa kusa da ita. Da gaske jikinta da zafi. "Ya salam, bari na duba miki pcm" ya tashi ya kunna fitila, ya kawo mata ruwa da magani. A dole ta karɓa ta sha. Ya kashe fitilar ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta yana ɗan murzawa a hankali. "Sannu" "Yauwwa" ta amsa a taƙaice. "Beb anya ba wani cikin ba ne?" "Ahha haba dai, ba wani ciki maybe malaria ce" Sagir ya ce "Ban yadda ba, gobe in Allah ya kaimu zan kai ki Asibiti a sake duba mini ke. Ubangiji Allah ya sa cikin ne" shiru ta yi ba ta amsa masa ba, shi kum hakan bai dame shi ba. Duk haushin Sagir da take ji, yana da halayen da duk ƙiyayyarka da shi, muddin za ka yi masa adalci dole ka kira shi mutumin kirki. Yana da matuƙar tausayi, duk faɗan da za su yi, da ya ganta a yanayi na rashin lafiya, zai rikice gaba ɗaya. Haka ya lallaɓa ta ta kwanta, sai dai da ya fara bacci sai ya farka, ya taɓa goshinta da wuyanta. Ita kuma idonta biyu duk abin da yake yi tana jin sa. **** Sai da Nana ta tabattar da sawu ya ɗauke, sannan ta ɗauki jakarta, ta koma gidan da ta shiga ta yi salla. An kulle ƙofar gidan, amma ƙofar rilar gidan a buɗe. Ta shiga rilar, ta ciro daddumarta ta shimfiɗa, ta ɗaukko zani a kayanta ta yi kwanciyar ta. Har a wannan lokacin, da take shirin kwana a waje haka, ba ta ji ta yi nadamar tahowarta Nijar ba. Sai ma ji da take yi ta zo inda babu wanda ya santa, balle a din ga gudunta, a din ga ganin da ta rabu mutum sai wata masifar ta afka masa. Ta saka hannu ta tallafo cikinta, da ita ma take jin nauyinsa, ya wuce adadin watannin da take tunani. Tana jin yadda yake motsi, wanda motsin nasa kaɗai, wani irin farinciki da nishaɗi yake sanya ta. Sai kuma damuwa ta biyo bayan farincikin nata, bayan da ta tuno Sayyid, da kuma rashin sanin halin da yake ciki. Da haka bacci nannauya ya yi awon gaba da ita a gurin. Ko da dare yayi, Maijidda bacci gagarar idanunta ya yi, ta tattara Iliyasu ta watsa a gefe, addu'a kawai take yi Ubangiji Allah ya sanya Nana ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali. Tana zaune a kan gado, ta yi shiru abin duniya ya ishe ta. Ji ta yi yana lalubata, wani irin baƙin ciki ya turnuƙo zuciyarta. Ƙoƙarin janyo ta yake yi, ta buge hannunsa a fusace, saboda ko ƙaunar ganinsa ba ta son yi. Ya ce "Mai Jidda meye haka ne wai?" "Dan Allah ni ka rabu da ni, wallahi ko ƙaunar ganin ka ba na yi. Ni dan zatin Allah ka sake ni, gara na yi zaman 'ya'yana kawai, da na ci gaba da zama da mutumin da ba ya ƙaunata, na yi kuskure tun farko da na biye wa son zuciyarka na banzatar da 'ya'yana" Ta yi maganar tana kuka mai ƙunar zuciya. "Maijidda da ba na sonki, ke kin san ba za ki je ki yi wani auren ki fito na aure ki ba. Ni kishinki nake yi, kuma na gaya miki tsanar da na yi wa mijinki ne ya shafi 'ya'yansa" "Ka na ƙaunata, ina cikin wannan mawuyacin halin, da kai ne sila, za ka zo ka na naniƙata buƙatarka ce kawai a gabanka? Wallahi ba ka ƙauna ta. Kuma haƙurina ya riga ya ƙare, ka sauwwaƙe mini kawai, ni zan tafi neman 'ya ta. Allah kaɗai ya san a yaya za ta kwana a ƙasar da ba ta san kowa ba, ga tsohon ciki" Kasancewar buƙatarsa a gabansa, ya sanya ya kwantar da murya, kamar yadda ya saba ba ya tashi kalailaye ta, da kwantar da murya sai a irin wannan lokacin. "Wataƙila ma fa ba Niger ɗin ta tafi ba, ai ba yarinya ce ƙarama ba, na san gidan babanta ta koma, ki ke ta ɗaga hankalinki" "Da akwai damar zama a gurin Baban nata, ka na ganin za ta zo inda nake ne? Nana ba za ta ajiye mini wannan rubutun ta koma gidan babanta ba, ni ka riga ka cuce ni" Ta yi maganar tana sauka daga kan gadon. Ya bi bayan ta yana lallaɓa ta, amma ta wuce ko saurarasa ba ta yi ba ta bar ɗakin, abin da ba ta taɓa yi masa ba a tsawon zaman su. Baba ma abin Duniya ya dame shi, ya fito ƙofar gida yana takaicin abin da Nana ta yi, sai ga kiran Uwani. Kamar ya share sai kuma ya ɗaga, suka gaisa Uwani ta ce "Isa kiran ka na yi na ja maka kunne, tun jiya da su Ummi suka taho nake son na kira ka na ja maka kunne, kar ka kuskura ka kira yarinyar nan ka ce za yi mata faɗa, ko ka kira uwatta ka yi musu jaraba, saboda Nana ta tafi can, ita ma mafitarta take nema, tuntuni da ka kama 'yar ka ka riƙe, babu yadda za a yi ta tafi Bauchi gurin babarta. Kuma ga halin da take ciki an nemi miji an rasa, ba a san kowa nasa ba, yarinyar nan na cikin wani hali, dan haka kar ka ce za ka yi mata faɗa tun da kai ne ummul aba'isin duk wannan lamarin. Da ka binciki dangin mutumin nan kafin ka aura mata shi, da duk haka ba ta faru ba". "Uwani" "Na'am" "Nana fa ba ta Nigeria ma gaba ɗaya, mijin Babarta ya kore ta, ta rubuta wa Ummi saƙo ta tafi Niger neman mijinta" "Me? Ta tafi Nijar ta san a inda za ta gan shi ne?" "Oho ina san mata ma, na samu wani malami, na ba shi abin sadaka ya yi mata kiranye, gaba ɗaya yarinyar nan ba ta da lissafi" "A'a ai duk kai ka janyo, amma Nana ba ta yi dabara ba, wallahi da na san abin da zai faru kenan, da ban bari ta tafi ba" "Sai anjima bari na koma gurin malamin na gode " ya kashe wayar dan ita kanta Uwanin haushinta yake ji. Yana shirin yin gaba, sai ga wata mota ta tsaya a gaban Baba. Har Baba zai wuce, sai kuma ya tsaya. Wani matashin saurayi ne ya fito Baba ya din ga yi masa kallon sani. Matashin ya ƙaraso su ka gaisa. Matashin ya ce "Baba dama, Mamanmu ce ta aiko ni, can gidan da Nana ta yi aikin rainon yaro. To wai Hajiya ce kwana biyu suna ta kiran wayarta, ba ta shiga sam, kuma an je can gidan da suke gadi, amma ba sa nan, shi ne ta ce na zo gida na tambaya ko lafiya, ko kuma a bani lambarta da take shiga na kai mata" Baba ya kwaɓe fuska ya ce "Kai ne ta auri Buzun yaron nan a gidanku kenan?" "Eh ni ne Baba" "To ai 'yan uwansa ne suka fara guduwa, ya yi ta rashin lafiya, to yanzu dai shi ma ya gudu, ta tafi can Nijar neman sa". Yusuf ya yi sororo cikin rashin fahimta ya ce  "Ya gudu ta tafi nemansa kuma?" "Eh kamar dai yadda ka ji na gaya maka" Ganin kamar Baba a fusace yake, ya sanya Yusuf cewa "To shikenan Baba, Allah ya kyauta, ya bayyana su cikin aminci" Ya koma ya shiga motarsa ya tafi. ***** Sanyin iskar sahara ce ta din ga ratsa Nana, har ta fara karkarwa saboda sanyin. Ta ɗaga kai, ta ga sararin samaniya ta yi tarwai, sai hasken farin wata da ya haska cikin saharar. Wani irin ƙugi ta ji saharar tana yi, da alamun tasowar iska. Ta kalli gabas ta ga iskar sahara daga nesa, tana wani irin hanƙoro da alama iskar tana da ƙarfi. Sauke Numfashin Sayyid ta din ga ji a cikin saharar. Waige-waige ta fara tana neman ina za ta gan shi. "Sayyid, ka na ta ina ban ganka ba" "Ma viee" "Na'am Sayyid, ka na ina ne?" "Za su kashe ni, dan Allah ki zo mu koma gida, na fi son rayuwata da ke, na nufi nutsuwa" Cikin rauni ta ce "Sayyid ba na ganin ka, ka na gurin ina?" "Husna" ta sake jin muryarsa yana ajiyar zuciya. Gadan-gadan Nana ta nufi inda ƙurar Saharar nan take tasowa, saboda daga nan take jin sautin muryarsa. A ɗan razane ta farka, saboda taɓa ƙofar gidan da aka yi. Tana kwance a cikin duhu, ta hangi mai gidan ya fito, da alama masallaci ya tafi. Ta tashi da ƙyar, ta buɗe kayan ta, ta ɗauki ruwa pure water, ta kama ruwa ta yi alwala. Tana jin yadda magidanta suke buɗe gidaje, su na tafiya masallaci. Ita ma ta tayar da salla. Kusan mintuna Arba'in mai gidan ya dawo, sai da ya tsorata kasancewar gari ya fara haske. Ya ga mace tana salla a kan dadduma a cikin rilar gidan. Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar ta ci gaba da tasbihi. Sai dai duk iya ƙoƙarinsa a kan ya yi mata magana, ya kasa kamar an saka masa sakata a bakinsa. Ya lallaɓa ya buɗe ƙofa ya shiga gidansa, ya tarar da matarsa tana bacci, kasancewar Al'ada take yi, ba ta salla. Kamar ya tashe ta ya gaya mata batun matar da ya gani, amma ya kasa, ya haƙura ya ƙyale ta. **** Jamila bata taɓa sanin ta damu da Nana har haka ba, duk da takun saƙa da sukan yi wasu lokutan, saboda ƙuruciya da sakunta, wasu lokutan kuma saboda zigar Mama. Amma ta damu sosai da halin da Nanan ke ciki. Jikinta ya yi sanyi sosai da sosai, da Ummi ta ba ta labarin wahalar da ta yi ta faman yi, ga miji ga laulayin ciki. Yanzu mai ɗungurungun ta tafi inda babu mataimaki sai Allah. "Amm Jamila" "Na'am Mummy" "Kwana biyu na ɗaga miki ƙafa da batun Nana, saboda ki samu ki ƙara sakin jikinki, yanzu dai ki na ganin yadda al'amuran ƙungiya suke wakana, kuma na ga kin saki jikinki yanzu. Dole fa ki yi ƙoƙari a wannan karon, ki samo mana jinin Nana, saboda ba ƙaramin alkhairi ne a tattare da taurarinta ba. Tun da dai kin ga Uba ku ka haɗa kawai da ita." Jamila ta yi murmushi cike da takaici, amma a zahiri ta danne ta ce "To ai Nana mijinta ya ɗauke ta, ya tafi da ita can ƙasar su Nijar a can ma ina ga za ta haihu" "What? Jamila amma ya aka yi ba ki gaya mini ba, bayan kin san ƙudurina a kanta?" Jamila a ranta ta ce "Da yake ki ka halicce ta ba" A zahiri ta ce "To ai ni ban san haryanzu ana buƙatar jininta ba, da na ga ba ki kuma yi mini maganarta ba, na zata shikenan ya wuce" Kamar ta rufe Jamila da duka ta ce "Amma wallahi ba karamar shashasha ba ce, ɗaga miki ƙafa kawai na yi ki ƙara dawowa hayyacinki, aikuwa ko ki nemo Nana a samu jininta, ko kuma ƙungiya ta nemi jinin wani shaƙiƙinki, sai ki zaɓa". Jamila ta waro ido ta ce "Shaƙiƙina kuma Mummy, na shiga uku na lalace" "Ahh to dabara ta rage ga mai shiga rijiya ai, sai ki yi tunani, ni na haura sama zan yi bacci" Gaba ɗaya jikin Jamila ya yi sanyi, ta bi bayan Hajiya Sa'a da wani irin kallo. Har rana ta ɗaga gurin ƙarfe goma, Nana na zaune a rilar gidan nan, sai da rana ta tarar da ita, sannan ta yinƙura, ta ɗauki jakar kayanta, ta koma barandar da ke kallon gidan, ta zauna. Mai gidan da ta kwana ya fito zai tafi kasuwa, kawai ya sake ganin Nana, da hijjabinta da wannan bagcon kayan nata ya gane ta. Ƙarasa fitowa ya yi, da niyyar ya tambayi Nana me take nema ne? Amma su na haɗa ido da Nana ya kawar da kansa cikin sauri, saboda wata irin mummunar faɗuwar gaba da ta ziyarce shi. Sum-sum ya wuce ya tafi, ba tare da ya ce wa Nana komai ba. Rana ta fara zafi, ta sake ɗaukar jakarta ta yi gaba, ta din ga nanata lahaula wa la ƙuwwata illa billah. Hasbunallahu wa ni'imal wakil. ***** Alhaji Zailani yana zaune a falo, tare da Hajiya Amina, Yusuf ya shigo falon. Hajiya Amina ta kalle shi ta ce "Yusufa daga ina?" "Aiken ki na je Mami" Ta ce "Wanne daga ciki?" Ya zauna tare da faɗin "Ba shekaranjiya muka yi zancen Nana da ku ba? Gidansu na je, daga gidan nake na samu babanta a waje, ya gaya mini wai mijinta ne ya ɓata ta bi shi Nijar neman sa" Hajiya Amina ta dafe ƙirji ta ce "Ya ɓata kuma garin yaya? Ko shi ma ɗauke shi aka yi kamar yadda aka tafi da 'yan uwansa? Anya ba wani laifin suke aikatawa ba hakan ta faru? To ta san inda yake a Nijar ɗin ne?" Yusuf ya ce "Wallahi nima ban sani ba, haka dai ya ce mini" Alhaji Zailani da hantar cikinsa ta kaɗa ya ce "Wai maganar wa ku ke yi ne?" Cikin dakiya ta ce "Nana mana, yarinyar nan da ta kula da Haidar, wadda babanta ya aura wa Buzun nan" "To sai aka yi yaya?" Yayi maganar yana tsare ta da ido, yana tunanin ko Hajiya Amina ta ci gaba da bibiyarta, ta gaya mata abin da yake tsakaninsu. "A'a dama Shukura ce ta ce, kwana biyu shiru, kuma ba ta samun ta a waya, nima kuma ba na samun ta, shi ne na ce masa dan Allah idan ya biya ta hanyar gidanta, ya tsaya ya karɓo mini lambarta, to kuma wai sun tashi daga gidan. Shi ne ya je gidansu aka sanar masa da ta bi mijin Nijar" Ya yi wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya yi shiru bai kuma cewa komai ba. Hajiya Amina ta yi ta jajanta lamarin, tare da tausayawa Nana. Alhaji Zailani kuwa rikicewa ya yi, cike da kiɗima. Domin yana ta tsara yadda zai samu Nana ko ta halin ƙaƙa domin samun biyan buƙatar sa. Yaronsa da ya bawa ragamar bibiyarta, bai taɓa gaya masa ba, ce masa kawai ya yi ta koma Kurna. Wani irin gumi ya fara keto masa, ta ina za a fara neman ta yanzu har a gano ta, a Nijar. Sai ya ɗora wa kansa alhakin sakacinsa ne, da ya din ga bin al'amuran a sannu, duk da hakan ya faru a dalilin halin da yake shiga, a duk lokacin da ya yi yinƙurin aiwatar da wani abu a kan Nanan. **** Nana kuwa wuni ta yi tana gararanba a titi, daga wannan inuwa ta koma waccan, ga uban kaya ga kuma ciki. Dama Abinci ba damunta ya yi ba. Buredinta da ta yi guzuri ta ci abin ta, ta kora da ruwa. Tana son samun muhalli, tun da akwai kuɗi a hannunta, akwai na Nigeria akwai na Nijar, sai dai amana ta yi ƙaranci, ba ta san wa za ta tunkara ya taimake ta ba, tana tsoron a cutar da ita. Dare ya yi bayan sallar Isha'i, ta sake lallaɓawa ta koma gidan nan ta kwana a rila, da Asuba mijin matar ya sake ganin ta, hakan ya sanya hankalinsa fara tashi, ga shi ya kasa magana kamar wanda aka yi wa asiri. Yau bayan magariba da ya koma gida, sai ya sanya wa rilar sakata, ya kulle ta ciki. Sawu ya ɗauke, Nana ta lallaɓo ta zo ta kwana, kawai ta tarar da rilar a rufe, ta jijjiga ta ji an garƙame ta ciki. Jikinta ya yi sanyi, ga shi duk inda ta tafi ko ta yi niyyar ta yi gaba ta tafi wani gurin, sai hankalinta ya kasa kwanciya sai dai ta koma gidan nan. Ga yau wani irin bacci take ji, kamar ta kifa, ga shi tana son yin wanka, saboda yadda kayan jikinta suke mintsininta, tun da ta zo da su take yawo. Ta samu gefen gidan ta takure, tun tana hamma har bacci sosai ya yi awon gaba da ita. Da Asuba ta ciro jarkar ruwan da ta saka wasu yara suka zuba mata a cikin ƙaramar jarka, ta yi alwala ta yi raka'atanul fajr. Tana kallon mai gidan ya fito ya tafi masallaci yana haske-haske, amma bai gan ta ba, har ya tafi. Ya dawo daga masallaci kansa tsaye zai shiga gida, ya ga Nana a cikin rilar. Wata irin razana ya yi, ya kuma kasa magana sai kallonta da yake yi fuskarsa na bayyanar da tsoro ƙarara. Nana ta ce "Ka kulle rilar gidanka, jiya a waje na kwana, duk da ban ga laifin ka ba, amma da ka tambaye ni, me yasa nake kwana a nan" "Wa..wa.wace ce ke? Me ki ke yi a nan?" Ayshercool 08081012143 63 Nana ta ce "Dan Allah ka kwantar da hankalinka, kar ka tsorata wallahi ni mutum ce, ba abin da na isa na yi maka na cutarwa, ba kuma ni da nufin cutar da ku" "To me ki ke yi mini a gida?" "Wallahi baƙuwa ce ni, ranar da na sauka a garin nan, na shiga gidanka, matarka ta bani gurin salla, har da abinci, dan Allah taimakona za ku yi" Ya ce "Baiwar Allah wallahi mu ma talakawa ne, ba wani taimako da za mu iya yi miki" Ta ce "A'a amma ai ku musulmai ne, gudun zargi dan Allah idan babu damuwa, mu shiga ciki a yi maganar a gaban matarka, ku ji taimakon da nake buƙata idan za ku iya yi mini, idan kuma ba za ku iya yi mini ba, babu komai sai na nema a gaba" Kamar ya ce a'a, amma yanayin Nana sai ta ba shi tausayi, ya bata dama suka shiga gidan, yana gaba tana bin sa a baya. Nana ta tsaya a tsakar gida, ya shiga ya taso matarsa. Ta fito tana mustustuke ido, ya nuna mata Nana ya ce "Kin san wannan?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Kamar shekaranjiya ta zo, ta ce mini baƙuwa ce za ta yi salla" Ya ce "Yauwwa, sau uku ina ganinta a rilar gidan nan. Wai a nan take kwana, ta ce mini taimako take nema, amma a zo a gaban ki, sannan ta faɗi me take son mu yi mata". Matar ta kalli Nana,ta ce "Baiwar Allah, wane taimako za mu yi miki?" Nana ta ce "Ni baƙuwa ce daga Nigeria, dan Allah ku taimaka mini da inda zan zauna, ban san kowa a ƙasar nan ba. E" "Gaskiya baiwar Allah, ba bu gurin da za mu iya ajiye ki a gidan nan" matar ta tari numfashin Nana. Nana ta ce "A'a ba a nan za ku ba ni gurin zama ba, da kuɗi a gurina, sai dai ban san kan kuɗinku na ƙasar nan ba, ina da wasu ma na Nigeria, ban san yadda zan canza su ba. Kuma ina tsoron na faɗa hannun da ba na gari ba a cutar da ni. Haka kawai na ji na nutsu da nan tun lokacin da ki ka karrama ni, ko na tafi sai na dawo nan na kwana nake samun nutsuwa. So nake ku taimaka a sama mini gidan haya, ko ɗaki da zan kama dan Allah. Kuma wallahi ni ba macuciya ba ce ba zan cutar da ku ba. Ku yi wa Allah da ma'aiki ku taimaka mini, dan Allah" Ya kalli matar matar ta kalle shi, ta ɗan jinjina masa kai. Ya kalli Nana ya ce "Kin san harkar taimakon ce wuya ne da ita yanzu, sai ka taimaki mutum amma ya sanya ka a masifa. Nana ta ce "In dai kun yi niyyar taimakona, ko macuciya ce ni, Allah ba zai ba ni damar cutar da ku ba. Ku taimaka mini dan Allah, ko iya gidan hayar a sama mini" Ya kalli matarsa ya ce "Hajara, bata guri ta zauna, zuwa gari ya ƙarasa wayewa, sai mu san abin yi, mu duba girman Allah da ta haɗa mu da shi" Hajara ta ce "To shikenan babu damuwa" wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, ta risuna ta ce "Na gode, Ubangiji Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi, yadda ku ka taimaka mini Allah ya taimake ku haka" Suka amsa da Amin. Matar ta kai Nana wani ɗaki, ta ɗaukar mata kayanta ta shiga da su. Tana fita daga ɗakin, Nana ta zube ta yi sujjada tana gode wa Ubangiji buwayi gagara misali, ta san wannan ɗaukin kai tsaye daga gare shi ne, amma ba dan haka ba ta san ba ƙaramar wahala za ta sha ba. Sai yanzu da ta nustu, ta din ga jin ta a takure, saboda rashin wanka, ga cizonta da kayan jikinta suke yi. Gari ya yi haske matar ta shigo ta ce wa Nana "Ki na buƙatar wani abu ne?" Nana ta ce "Eh dan Allah zan yi wanka" "To shikenan babu damuwa, da kin sani tun ranar da ki ka zo, ki ka yi mini bayani, ga ki da juna biyu, amma a ce ki na kwana a waje bai dace ba" Nana ta ce "Larura ce, ba yadda zan yi, kuma babu daɗi ka ɗora wa mutane ɗawainiya sama ta ka" Ta ce "Haka ne" ta haɗa wa Nana ruwa, Nana ta duba kayanta ta ɗauki soso da sabulu, da brush. Ba ƙaramin daɗin wankan nan Nana ta ji ba. Ta koma ɗakin da suka sauke ta, ta fito koma ɗakin da aka sauke ta. Ta fito da mai ta shafa, ta saka kaya. Ta ji wata sassanyar iska na ratsa ta. Ta ɗaukko jakar kayan turarrukan Sayyid, da kayan gyaran gashin sa, ta yi zuru da ido, tana kallonsu. "In sha Allah za mu haɗu Sayyid, ina fatan Allah ya ƙaddara haɗuwarmu nan kusa" ta yi maganar a sanyaye. Sallamar Hajara ce ta sanya ta mayar da kayan cikin bagcconta, ta mayar da hankalinta kan ta. "Ko ki na buƙatar wani abun ne?" Nana ta girgiza kai fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "A'a ba na buƙatar komai, na gode sosai da sosai" "Ba komai, bari na kusa gama abin karyawa" Cikin murmushi Nana ta ce "Ba raina miki na yi ba, amma ni wannan taimakon da ku ka yi mini ya wadatar, ba sai kun ba ni Abinci ba, na gode sosai da sosai" Hajara ta ce "Haba dai, ya ma za ayi ki na baƙuwarmu a ce ba za mu ba ki Abinci ba, ai ba zai yiwu ba sam" "Ai kar ɗawainiyar ta yi yawa ne, abin da ku ka yi mini ma, na gode Allah ya biya ku" "A'a babu wata ɗawainiya" ta yi maganar tana fita waje. Ta so tambayar Nana me ya kawo ta Nijar, ga tsohon ciki, kuma ta ce ba ta da kowa, amma ta kasa saboda wani irin kwarjini da Nanan ta yi mata. Tun da ta bawa Nana abincin safe, da rana ta bata fura Nana take amai. Har sai da Hajara ta ji babu daɗi, ta yi zaton ko Abincinta ne ya saka Nana amai. A sanyaye ta ce "Ko Abincin nawa ne ya saka ki amai?" Nana ta yi murmushi ta ce "A'a kar ki damu, dama haka nake fama tun farkon cikin, ni na riga na saba ma" "Kayya ai ba a sabo da wahala, kin yi amai ya kusa goma, ko Asibiti zamu je?" "A'a zan daina in sha Allah" Gaba ɗaya Hajara ta damu, ganin yanayin da Nana take ciki. Nana ta ce "Ba ki taɓa haihuwa ba ne? In dai mutum ya haihu ya san irin wannan larurar ta ciki ai" Hajara ta ce "Ina fa? Watanmu takwas da aure, ban haihu ba". Nana ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo mai albarka" "To ai ni duk na tsorata ne, wannan aman ya yi yawa" "Ai ni na riga na saba ma, ba ya damuna yanzu" haka suka ɗan din ga taɓa hira. Mijin Hajara bai dawo ba sai isa'i, Nana na ɗaki tana shafa'i da wuturi. Ya ce wa Hajara "Ina baƙuwarmu?" "Tana nan sai dai ba ta da lafiya" "Me ya same ta?" "Wallahi tun da na ba ta Abinci take amai, haryanzu jikina duk ya yi sanyi" Ya ce "Subhanallah, kuma bai tsaya ba?" "Tana dai ta yi" Nana ta idar ta yi addu'a, sannan ta fito, ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata ya jiki. Ta ce "Jiki Alhamdillah" Ya ce "Baiwar Allah ba a samu gidan haya ba, duk inda na tambaya, sai masu tsada, kuma babu lallai a bayar, mussaman idan aka san ke kaɗai za ki zauna, kuma zaman ki ke kaɗai babu Namiji babu tsaro ko kaɗan. Amma na kuma bayar da cigiya ko za a samu wani, wanda yake da mutane a ciki sai a kama" Nana ta jinjina kai ta ce "Na saku ɗawainiya, Allah ya saka da alkhairi" Ya ce "Ba komai" ya kalli Hajara ya ce "Bari na je na dawo, ko za ku yi hira kar na takura muku" Nana ta ce "A'a ba komai, ka zauna ni sai na koma ɗaki" Ya ce "A'a dama zan fitan" Hajara ta raka shi soro, ta tsaya can su na hira Nana tana jiyo dariyar su. Sayyid ya faɗo mata a rai. Yana daga cikin manyan ni'imomi da nasarorin rayuwa, mutum ya auri wanda yake son sa, ya kuma dace da shi. Ta yi musu addu'a da fatan samun dauwamammen zaman lafiya da kuma zuriya ta gari masu albarka. Hajara ta dawo, ta zauna su ka ci gaba da ɗan taɓa hira da Nana. Ta cewa Nana "Ko sunanki ban sani ba" "Nana Asma'u, amma Nana ake ce mini" Ta ce "Allah sarki, amma ki na da aure ne?" Nana ta yi murmushi, ta ce "Kin yi mamakin yadda na taho inda ban san kowa ba ga tsohon ciki ko? Na san wataƙila, kina tunanin ina na samo ciki ne?" Hajara ta ce "Laaa a'a wallahi" Nana ta ce "Ai babu damuwa idan ma kin yi tunanin haka, ɗabi'ar zuciya ce. Matar aure ce ni, ko a yanzu haka ka ma ina da igiyoyin aure uku a kaina, wani dalili ne ya kawo ni ƙasar nan, kuma in sha Allah da na kammala, zan koma gida" "Allah sarki, Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya a samu abin da aka zo nema" Nana ta amsa da "Amin na gode sosai" ***** Su na zaune sun tattara hankalinsu a kan likitan, cikin matsananciyar girmamawa Likitan ya gaishe su. "Ya ya jikin Imam?" Ya amsa da "Jikinsa Alhamdillah, yana samun sauƙi sosai da sosai" "Ba yana samun sauƙi muke son ji ba, mene ne sakamakon binciken ku da aka gudanar?" Likitan ya ce "Eh sakamakon gwaje-gwaje, ya nuna babu abin da aka yi masa na cutarwa a jikinsa, gaba ɗaya babu wani abu na cutarwa a tare da shi" "Shi kuma matsalar zuciyar fa?" "Wannan yana da nasaba da hawan jini da yake da shi tuntuni, wataƙila ya daɗe ba a kan magani ba. Shi yasa ya shafi zuciyarsa. Sai dai matsala ɗaya" Cikin damuwa dattijon ya ce "Wace matsalar?" "Ƙwaƙwalwarsa, mun kasa gano abin da yake faruwa da ƙwaƙwalwarsa, haryanzu bai samu nutsuwar da zamu tattauna da shi ba, yana buƙatar kulawa ta musamman a bangaren ƙwaƙwalwa" Sultan ya dafe goshinsa, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, idanunsa suka yi jawur. Ya ɗago ya kalli Likitan ya ce "Ko gida za a mayar da shi, a saka duk abin da ake buƙata na kula da shi a ɗakin, ya zamana yana kusa da ni, hankalina ba ya kwanciya, yana nan ina can" Abduou ya ce "A'a Sultan, idan aka mayar da shi gida, za a iya gane halin da yake ciki, wanda ba ma fatan hakan, dole a ci gaba da toshe duk wata kafa da za a san halin da yake ciki, har zuwa lokacin da zai warware. Kuma za a ci gaba da matsa yaran can, har sai ya yi mana bayanin abin da suka yi masa a Nigeria. Kuma Asibitin nan akwai tsaro babu wanda ya san yana nan. A kula da shi har zuwa lokacin da za a yi tafiyar" Sultan ya yi ajiyar zuciya cike da gamsuwa, ya miƙe tsaye ya ce "Mu je na gan shi" Su ka miƙe gaba ɗaya, Likitan yana gaba su na biye da shi a baya. Cikin sauri suka ƙarasa gaban gadon. Idanunsa a rufe yana bacci. Sultan ya ƙarasa gaban gadon, fuskarsa ɗauke da damuwa. Ya din ga dudduba jikinsa, tamkar yana son gano wani abin. Ya kalli Likitan ya ce "Kun tabattar a jikinsa babu wani abu na illa ko cutarwa a tattare da shi?" "Babu ranka ya daɗe, lafiya kalau yake, ba a yi masa komai ba, sai wannan matsalar ta ƙwaƙwalwarsa. Ba na tunanin an tafi da shi Nigeria ne dan a cutar da shi, akwai dai wani abu... "Ya isa ba kai ke hurumin zartar da wannan hukuncin ba, sai abin da bincike ya tabattar" Babu shiri likitan ya ja bakinsa ya tsuke. Sultan ya ɗago hannun Imam na hagu, ya kalli yatsunsa ya ga yatsunsa biyu sanye da zobuna, ya ɗago hannun damansa, ya ga babu azurfa ɗaya sai ɗaya. Cikin tashin hankali ya ce "Abduou. Babu zoben Imam guda ɗaya" Cikin sauri Abdou ya ce "Wanne daga ciki?" Ya ɗago wa Abdou hannun Imam. A rikice Abduou ya kama hannunsa ya duba, ya kalli Sultan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga abin da nake gaya maka ko? Kai ne ka ke ƙoƙarin kare yaron can, ka ke cewa a bi shi a sannu ba ka tunanin zai iya cutar da shi, to ga shi nan ai ga irinta nan, tabbas ya san inda zoben nan yake, dole a matsa shi a fito da shi. Dalilin da ya sanya su ka sace shi kenan ma, su ka bar ƙasar nan da shi, su ka kai Nigeria. Zoben suke so su sace" Sultan ya dafe kansa, ya rasa abin da yake yi masa daɗi. "Sultan wannan ma wani sabon sirri ne, da yake buƙatar duk tsanani a rufa shi, a ci gaba da addu'a, amma dole a nemo zoben nan, idan ba haka ba zai fita daga sahun Imams" Sultan ya sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya yana kallon yadda yake bacci a kan gadon. **** Sai da Nana ta shafe kwanaki huɗu a gidan Hajara, ba a samu inda za ta zauna ba. Nana ma abin daya dame ta, sai ɗawaniya suke faman yi da ita, ga shi tana tsoron kar su ƙosa da ita, dan babu mai jurewa yau da kullum sai Ubangijin da ya halicci bawa. Ranar kwana na huɗu da yamma mai gidan ya dawo, Hajara ta kira Nana. Bayan sun sake gaisawa ya ce "Malama Nana, wallahi ba a samu gida ba, sai dai ina tafe a hanya wata shawara ta faɗo mini. Akwai wata 'yar uwar Babana a can wata unguwa, itakaɗai take zaune a gidanta, kuma akwai ɗakuna a gida, kuma ba mazauniya ba ce, tana fita sana'iinta. Sai dai fa mace mafaɗaciya, tana da yawan faɗa, ba wuya ta hasala. Ban sani ba ko za ki iya zama da ita?" Cikin farin ciki Nana ta ce "Zan iya zama da ita, in dai ta amince" "A'a dai ki yi tunani, mafaɗaciya ce sosai, idan kin amince zan tafi na je na same ta a daren nan, na yi mata bayani" Nana ta ce "Wallahi kar ka damu, zan iya zama da ita" Ya ce "To Allah ya sa, zan ne yi mata magana, idan ya so ko kuɗin hayar ne ita sai a bata" Nana ta yi ta masa godiya tana murna. Har Nana ta yi bacci bai dawo ba, sai washegari da safe, bayan ta karya,  Hajara ta cewa Nana ta shirya, za su tafi can gidan matar. Nana ta yi wanka ta shirya, suka fita suka hau abin hawa. Hajara ta ce "Nana kamar kar ki tafi, kwana biyun nan har na saba da ke" Nana ta yi murmushi ta ce "Nima haka, sai dai har Abada ba zan taɓa daina yi muku godiya da fatan Alkhairi, ba dan ba ƙaramin jihadi ku ka yi ba, ne ceton rayuwata" "Ba komai, mu ma bamu san ta inda Allah zai taimake mu ba". Sun yi tafiya mai ɗan nisa, kafin su je unguwar da matar take. Mijin Hajara ya sallami mai abin hawan, ya ɗauki kayan Nana su ka shiga layin gidan. A tsakar gida suka tarar da matar, ta cake ɗauri tana ta lissafin kuɗi. Ta amsa musu sallamar tana yi musu maraba. Suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunanta. Ta kawo musu ruwa da lemo ta ajiye. Cikin girmamawa Nana ta gaida matar. Ta kalli mijin Hajara ta ce "Wannan ce yarinyar?" Ya ce "Eh Nene" "To a haka dai ta yi zubin nutsuwa, dan dai ka matsa ne, amma ni ba na son yayime-yayime na je na ɗaukko wadda za ta hana ni sukuni, shi yasa duk girman gidan nake zamana nikaɗai abina. Sannan zan fara zama da ita na wata ɗaya, idan ba ta da matsala mu ci gaba da zama, idan akwai matsala na mayar mata da kuɗinta ta tashi ta bani guri. Kuma wallahi dan ma dai kai ne, da ba zan yadda ba". Nana cikin girmamawa ta ce "In sha Allah ba za ki same ni da matsala ba, in Allah ya yarda". Nene ta ce "To Allah ya sa, bari na buɗe ɗaya daga cikin ɗakunan ta zaɓa" Mijin Hajara ya ce "Ɗakunan a rufe, ai na san sun sha ƙura yanzu, ki yi haƙuri tun da akwai gyararru ki kwashe kayanki daga ɗaya ki ba ta. Kin ga ɗakin da ba komai, sai an nemi labule, da sauran abubuwa". Haka ya takure Nene, ta bawa ɗaki ɗaya, mai ɗauke da labulaye da carfet. Nana ta din ga godiya, ta ce  "Saura kuɗin hayar, nawa ne zan biya?" "Ai na biya ta, ba wani abu in sha Allah, ki zauna kawai" Nana ta ce "Ai da kuɗi a gurina" Hajara ta ce "Kar ki damu, ba wani abu ya biya, idan akwai wata matsala ko ba za ki iya zama ba, ki ce Nene ta kira mu a waya, in sha Allah babu wani abu" Nana sai da ta yi hawayen murna, ta raka su har waje sannan ta dawo. Ta tarar da Nene ta fito da wake fal za ta tsince. Nana ta lallaɓa ta zauna a kan tabarmar ta ce "Kawo na tsince miki" Nene ta ce "A'a ke da ki ke baƙuwa, yi zaman ki ki huta, kan Auwwalu ya dawo ya ce ina azabtar da ke, tun da ya ce ni masifaffiya ce". Ita Nana har ta gama zaman gidan ma, ba ta san sunansa ba. Ta yi murmushi ta ce "A'a ba komai, dan Allah ki bani na taya ki, ai na ga waken da yawa, kuma daga zaune zan taya ki" Ta dawo da robar waken tsakiyar su, ta kalli Nana ta ce "Nana ko?" Nana ta jinjina kai ta ce "Eh" "Ciki ne da ke haka ne?" Nana ta sunkuyar da kai tana tsince wake. "Ke kuwa me ya yi miki zafi, ki ka baro ƙasar ku da wannan tsohon ciki ki ka taho inda ba ki da kowa? Amma fa ki yi haƙuri da tambayoyina, kin san yanzu duniya babu gaskiya sosai" Nana ta ce "Haka ne. Mijina ɗan ƙasar nan ne, nice 'yar Nigeria. Na zo neman danginsa ne a nan" "Allah sarki, to a ina dangin nasa suke? Kuma shi yana ina" Nana ba ta son yayata halin da take ciki, ta fi son sai ta nutsu, ta ga kamun ludayin mutanen ƙasar tukuna, kafin ta saki jiki, amma ga Nene ta saka ta a gaba da tambayoyi. Kafin ta ba ta amsa, Allah ya taimake ta, aka kira Nene a waya, hakan ya sanya ba su ci gaba da zancen ba. **** Cikin tsananin tausayawa, yake bin matashin da kallo, saboda yadda duk ya fita daga hayyacinsa. Cikin damuwa ya kira sunansa a hankali ya ce "Mahmudu" ya ɗago idanunsa a galabaice, ya kalli wanda ya kira sunan nasa. "Ka yi musu bayanin duk abin da ya faru, ka faɗa musu iya gaskiyarka, ko Allah ya sanya su rabu da kai, wannan wahalar da ka ke yi ta isa haka?" Murya a cunkushe ya ce "Me zan gaya musu? Me zan ce da ka ke tunanin idan na faɗa za su yarda da ni?" "Iya abin da ka sani ɗin zaka faɗa" "A tunaninka tsawon wannan lokacin, ba iya abin da na sani ɗin ba nake gaya musu? Sai dai akwai abin da ko za a kashe ni, ba zan furta ba" "A'a Mahmudu, idan har za ka ci gaba da shiru da ɓoye wasu abubuwan, ba fa za a ƙyale ka ba, za su ci gaba da azabtar da kai ne kawai a banza. Ni dai zan faɗi abin da na sani" Mahmudu ya ce "Ka kwana da sanin, ka na furta wani abu, to tabbas kai ma za ka tsinci kanka, a halin da nake ciki yanzu. Ka yi shiru mu bar komai a yadda yake. Rufe sirrin Imam wajibi ne, akwai abin da idan na furta, zai iya janyo asarar rayuka ba ɗaya ba ba biyu ba, in dai wahala ce na san ɗayan biyu ne, ko na mutu ko ta wuce. Abu ɗaya nake so da kai, shi ne; dan Allah Ashiru, ka binciko a wani hali yake ciki? Tun da muka baro Nigeria, ba a haɗa mu a mota ɗaya ba ma, ban san ina aka yi da shi ba" Ashiru ya ce "Kai wannan fa babban aiki ne, tun ɓatansa fa, ba a bari labarin ma ya fita ba, balle a sanya ran jin halin da ake ciki yanzu, amma dai zai ɗan ƙyanƙyasa a ɓoye, na ga ko za a samu wani bayani. Sannan ina ƙara neman afuwarka a kan abin da ya faru" "Babu komai kar ka damu, an saki sauran ko? Su Sulei" "Eh an sake su, ai tun da suka fuskanci, ba su ma san a kan me ake binciken ba, an sake su amma fa an killace su" "Shikenan tashi ka je, kar a fahimci wani abu" Haka Ashiru ya tashi ya tafi yana waiwayen sa. ***** Sannu a hankali take tafiya, yana zaune a cikin mota yana hangen ta, ta tsallako titi, ta nufo motarsa tana murmushi. Ta buɗe motar ta shiga ta ce "Yaya Abba me ka ke jira a titin ne haka?" Ya lumshe idanunsa, jin yadda ƙamshin turaren jikinta, ya gauraye motar baki ɗaya. Ya ce "Wa zan jira ban da ƙanwata, kwana biyu ban gan ki ba, da gida zan bi ki ma, to sai na ji tsoron kar na je ko ki na da baƙo, ban sanar da ke zan zo ba. Kawai na tsaya a nan na ce bari na jira fitowar ki" Ta yi murmushi ta ce "Ko akwai baƙo, ba dolena na sallame shi na saurari yayana ba, kuma wani baƙi zan yi da safe haka?. To me ma zan samu ne?" Ta yi maganar tana laluba motar. Ya yi dariya ya ce "Laluba ki ɗauki duk abin da ki ke so" ta yi dariya ta ce "Dan ka san ba ka ajiye komai ba ko? Mu je kar Mummy ta yi ta jira na" Ya ce "Ok" ya fara tuƙa motar a hankali. Yana tuƙi yana satar kallon Jamila, wani irin kyau take ƙarawa a idanunsa kullum. Kullum ƙara shiga ransa take yi, ga shi ya kasa fitowa ya sanar mata da ainihin abin da yake cikin zuciyarsa. Duk wasu alamu da zai nuna mata sonta yake yi, ya yi amma ya kasa gaya mata baki da baki. Su na daf da shiga layin gidan ya tsaya ya ce "Ƙanwata" "Na'am Yaya Abba" "Ina son za mu yi wata magana da ke, amma maybe sai na dawo tukuna" Ta yi murmushi tare da gyara zaman mayafinta, ta ce "To shikenan babu laifi, a dawo lafiya" "Allah ya sa, ki kula mini da kan ki Please, zan kira ki idan na je kasuwa" Ta ce "To, ka sayo mini aya mai sukari a kasuwa" Yayi dariya ya ce "Aya kawai?" "Eh ita kawai" "To an gama ranki ya daɗe" ta fita daga motar tana ɗaga masa hannu" Da ta shiga cikin gida,ba ta tarar da Hajiya Sa'a a falo na, dan haka ta bi ta bedroom. Ta tarar tana wanka, ta nemi guri ta zauna tana danna wayarta. Can Hajiya Sa'a ta fito daga ita sai towel. Jamila ta kalle ta ta kawar da kai. "Jamila har na fitar da ran za ki zo ai" "Ba na jin daɗi ne, shi yasa da kamar ma ba zan zo ba fa" "Eyya sannu, bari na shirya ki raka ni mu je na duba Fatuhu" Jamila ta ce "Tom" Hajiya Sa'a ta zauna a kusa da Jamila, ta ɗan riƙo hannunta ta ce "Daughter wai ke haryanzu ba za ki waye ki faso gari ba? Ina ta saita ki a hanya kin ƙi yarda ki shiga layi" Jamila ta ɗan ɓata fuska tana zame hannunta ta ce "Gaskiya ni Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi" Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda ɗaukar ciki. Kuma... "Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi" Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda ɗaukar ciki. Kuma... "Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace za ta tsinana mini ba, ni bai ma yi mini tsari ba gaba ɗaya gaskiya. Ba gara na bi maza ba" Hajiya Sa'a ta kwashe da dariya, ta ce "Yaro man kaza, ai shikenan Daughter, bari na shirya mu fita". A gaban Jamila ta gama shirinta, ba tare da jin nauyin abin da ta tunkari Jamilan da shi ba, ta gama suka fita. Umman Fadila ce take kallonta a tsanake, bayan ta gama yi mata komai za ta tafi. "Fadila" "Na'am Umma" "Na san yanzu da da ba ɗaya ba ne ba, amma ko yaya ɗan abin da ki ke da shi idan ya samu, ko abinci ko kuɗi, ki din ga bayar da sadaka, da nufin Ubangiji Allah ya kawo muku ɗauki,ya sassauta muku wannan yanayin da ku ka tsinci kan ku a ciki" Fadila ta jinjina kai ta ce "In sha Allah" "Tun kwanank da kawunki, ya zo ya duba mijinki, ya kira ni yake mitar, kun tare ku na maganin Asibiti, kun ƙi mayar da hankali ku yi na gargajiya. Na ce masa mijin naki ne ɗan aƙida, kuma ke na haifa ba shi ba, balle na yi masa dole. Amma nima hankalina ya fara karkata ga a yi na hausan, mijinki mutumin kirki ne, ba zan manta halaccinsa a gare mu ba, dan haka na bayar da kuɗi a yi saukar Alqur'ani, da fatan Ubangiji Allah ya yaye masa koma mene ne, tun da shi Alqur'ani waraka ne. Ki yawaita karanta masa, ko ki kunna ya saurara, ko ki din ga busa wa a abincinsa ko abin shan sa. Ba mu san a inda za a dace ba, wannan abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, na Asibitin ba wani haske da ake gani, idan hagu ta ƙi ai sai a koma dama ko?" Fadila ta ce "Haka ne Umma, in sha Allah, zan yi duk abin da ki ka ce, kuma addu'a mu na yin ta sosai, ina yi masa. Sai dai kin san lamarin Ubangiji ba a yi masa dole, duk addu'arka sai lokacin yankewar abu ya yi tukuna". Umma ta ce "Haka ne, amma hakan ba ya nufin a sare, a ce an haƙura gaba ɗaya ba za a yi ba" Sosai Fadila take jin daɗin rarrashi da nasihar da Umma take yi mata a duk lokacin da ta zo gidan. Ko da su Hajiya Sa'a suka je gidan Alhaji Fatuhu, Alhaji Zailani yana gidan. Yana sashen Alhaji Fatuhu tare. Alhaji Zailani ya din ga kallon Jamila, yana ganin kamar ya santa, amma ya manta a inda ya san fuskarta. Suka gaisa Hajiya Sa'a ta kalli Fatuhu ta ce "Yaya ya jikin naka?" Ya jinjina kai ya ce "Alhamdillah" "Ka na samun sauƙi, ko dai haryanzu babu afuwa?" Ya yi murmushi ya ce "Da sauƙi" Daga haka suka koma hira da ita da Alhaji Zailani, tamkar ba dubiya su ka zo ba, bar sai da abin ya ba wa Jamila mamaki. Sun jima sannan su ka shiga suka gaisa da matansa suka tafi. Su na tafe a hanya Jamila ta ce "Mummy, mara lafiyar nan shi ne wanda ɗan sa ya mutu kwanaki ko? Yaran da Nana take koyarwa a makaranta" "Eh shi ne" "Allah sarki, to shi wannan Alhaji Zailanin, ko shi ne a can quaters ɗin bayan makarantar nan na ƙofar famfo?" Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Ya aka yi ki ka san shi?" "A'a na tambaya ne dai kawai, kenan shi ma Nana ta yi aiki a gidansa, yana da 'ya Shukura ko?" Hajiya Sa'a ta jinjina kai tana kallon Jamila. "To ai da Nanan gidanmu zai aura, ba a yi ba, aka yi aurenta da wannan Buzun, lokaci ɗaya kawai ya fito ya ce wai zai aure ta" Shiru Hajiya Sa'a ta yi tana kallon Jamila, ta san abu ne mawuyaci a ce haka kurum Alhaji Zailani ya ce zai auri yarinyar da ta fito daga gida kamar na su Nana, da ƙyar idan ba ya san sirrin da ke tattare da Nanan ba. A take gabanta ya faɗi, dan kuwa ko me za a yi ba za ta taɓa barin Alhaji Zailani ya riga ta amfani da jinin Nana ba" Jamila ta ce "Mummy ya na ji kin yi shiru ne?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai Jamila, dole mu nemo Nana ne duk inda ta shiga" Jamila ta ce "Saboda me?" "Saboda ƙungiya, za ta iya neman ki kawo jinin mafi kusanci da ke, a kowane lokaci! Ayshercool 08081012143 64 Jamila a ranta ta ce "Ni kuwa zan ga abin da ya ture wa Buzu naɗi, zan ga abin da zai faru idan na bijirewa buƙatar ƙungiyar" Jamila ta numfasa ta ce "Mummy, dan Allah tambayar ki zan yi" "Ina jin ki" "Wai dan Allah, ya aka yi ki ka shiga ƙungiyar nan?" Hajiya Sa'a ta kalli Jamila, sannan ta mayar da hankalinta kan tuƙin da take yi tana murmushi. Ta ce "Dogon labari ne Jamila, amma me yasa ki ka tambaye ni?" "Ina son na ji tarihin gwagwarmayar ki ne, ko nima zan daure na yi koyi da jarumtar ki, haryanzu wasu lokutan zuciyata tana rawa ne a kan lamarin" "Ai na ga alama kam. Jamila na sha gaya miki, muddin ki na son cimma abin da ki ke buri a rayuwa, babu ruwanki da kowa kan ki kawai za ki din ga dubawa. Na tashi a gidanmu bamu da komai, babata da babar Fatuhu, su ne ƙanana a matan gidan, kamar dai yanayin rayuwar gidanku, a haife ka, ba a damu da ɗawainiyarka ba. Manyan yayyenmu babu ruwansu da mu, saboda iyayen su mata sun cusa musu aƙidar ƙin iyayenmu. Babanmu ya mutu shi ma saboda bai bar komai ba, babu wanda ya damu da mu. Yayyenmu iyayensu kadai suke taimako da ƙannen su, mu kuma namu iyayen ke ta fafutuka da wahala. Fatuhu ya yi ta faɗi tashi da rayuwarsa, da ta mahaifiyarsa, sai dai yana tunawa da ni. Zailani tsohon saurayina ne, da rashin abin yi ya hana mu yin aure da shi. Ya shiga makaranta, bisa tallafin karatu, a can ya samo mana wannan ƙungiyar. Shi kuma lokacin Fatuhu ya fara zuwa kasuwa, ni kuma na riga na yi aure. Zailani ya gaza jan Fatuhu ƙungiya, saboda mutum ne mai tsantseni da ra'ayin riƙau. Ni kuma har a lokacin mijin da nake aure, ba shi da komai ba na samun irin rayuwar da nake so. Sannu a hankali na ci gaba da hulɗa da Zailani ya kai ni ƙungiya, ya zamana ba na rasa kuɗin kashewa dai. Fatuhu kuma ya ja Zailani kasuwa, suke kasuwanci tare, sai dai duk da tasirn ƙungiya, Zailani ya kasa tara abin da Fatuhu yake da shi. Kin san waye mutum na farko da na fara bayarwa?" Jamila ta girgiza kai alamar a'a. "Babban yayanmu, da iyayensu su ka mayar da mu saniyar ware a gida" Jamila ta jinjina kai a ɗan tsorace ta ce "Sai kuma ki ka ba da wa?" Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Zan ƙarasa miki nan gaba kaɗan, yanzu bari mu ƙarasa gida, akwai abin da nake son yi" Jamila ta jinjina kai tana satar kallon Hajiya Sa'a. Hajiya Sa'a ta ajiye Jamila, sannan ta ja motar ta tafi. Tana tafe ta kira layin Alhaji Zailani. Sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga tare da yin sallama. Ta ce "Ai na zata ba ka ɗaga ba ne" Ya ce "A'a ina tuƙi ne? Lafiya?" "Ƙalau, tambayarka abu zan yi" Ya ce "Ok, ina jin ki" "Ashe kwanaki da aure zaka yi?" Ya ce "Yaushe?" "Kwanakin baya mana, za ka auri wata yarinya Nana" Kamar tana gabansa ya tsuke fuska ya ce "Waye ya gaya miki" "A'a ba sai ka ji wanda ya gaya mini ba, zancen Duniya ba ya ɓuya ai, sai dai ka sani na san da abin da ka ke nema, ni ma shi nake farauta" "Sa'a ban fahimci abin da ki ke nufi ba fa, ki yi mini bayani gwari-gwari " "Za ka fahimta ne, ka je ka nutsu ka yi nazari" ta kashe wayar ta ajiye ta ci gaba da tuƙinta. ***** Yana zaune a takure a gurin, ya yi shiru tamkar mai jiran tsammannin wani abun, aka buɗe ƙofar ɗakin da yake . Wasu tiƙa-tiƙan murɗaɗɗun maza suka shigo. Ba su yi wata-wata ba, suka yi sama da shi, suka fito da shi daga gurin da yake zaune. Wani ɗakin aka sake kai shi, sai dai yana shiga ya yi turus, ganin mutumin da yake zaune a cikin ɗakin. Ƙartin suka juya suka fice, suka bar shi daga shi sai mutum biyu a ɗakin. "Bismillah ka zauna mana" cike da tsoro ya ƙarasa ya zauna yana rarraba ido, ya sunkuyar da kansa. "Mahmudu, ɗagowa za ka yi ka kalle ni ai" Ya ɗaga kai ya saci kallon mutumin, ya mayar da kansa ya sunkuyar. "Na san wannan zaman takurar ya ishe ka zuwa yanzu, kasancewarka mutum da ya saba da 'yanci a baya. Ina son ka buɗe kunne ka saurare ni da kyau, tambayoyi nake son na yi maka, muddin ka gaya mini gaskiya ka bani amsa, zaka iya samun sassauci, ko ma na yi umarnin a sake ka, ka yi tafiyarka gaba ɗaya" Ya jinjina kai ba tare da ya ɗago ba. Mutumin ya sauke rawnain fuskarsa ya ce "Na san an yi maka wannan tambayoyin an kum a baya, yanzu ma zan sake jaddada maka su, me yasa ka sace Imam ka kai shi Nigeria, da ka kai shi kuma me ka yi masa?" Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya girgiza kai ya ce "Ban sace shi ba, kuma ban yi masa komai na cutarwa a Nigeria ba" "To me yasa ka tafi da shi Nigeria ba ka sanar da kowa ba?" Mahmudu ya ce "Wannan wani sirri ne da ba zan iya tona shi ba, ko da za ku salwantar da rayuwata, wani abu wanda daga ni sai shi Imam" Abduou ya jinjina kai ya ce "Da amincewar sa ku ka tafi Nigeria kenan?" "A'a hasalima bai san komai ba, ba wani da zaɓi ne da ya rage, sai abin da na aikata ɗin" "Mahmudu, na fuskanci zama da maɗaukin kanwa ya sanya maka farin kai. Rayuwa da Imam ya sanya ka koyi baƙin taurin kai irin nasa. Amma ka snai, kama da wane ba ta wane, kuma  ina fatan ka san da tun da aka ɗaukko shi daga Nigeria har yau ba ya hayyacinsa, bai yi magana da kowa ba?" Mahmudu ya girgiza kai ya ce "A'a ranka ya daɗe. Rashin gane kowansa ba shi da nasaba da zuwansa Nigeria" "Saboda me?" "A can ɗin ma ba gane kowan yake yi ba" Abduou ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zoben Azurfarsa fa guda ɗaya da baya hannunsa, ina fatan ka san inda wannan yake?" A zabure Mahmudu ya kalli Abdou matawalle, jin abin da ya faɗa. "Ka daina zaro mini ido, kwanaki biyu kawai ka ke da su, ka faɗi inda zoben yake, ko kuma ka rasa rayuwar ka baki ɗaya, zaɓi ya rage naka" Abdou ya miƙe, ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa ya fice daga ɗakin. Cikin matsanancin tashin hankali, ya bi bayan matawalle da kallo. A Nigeria babu wanda ya san ma'anar zobunan da suke hannun Imam. Kuma ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ba shi dukkanin kariya, balle ya ce wani ya san muhimmancin su ne ya karɓa. Matuƙa ya ji yana son ya ga Imam, ya gana da shi, sai dai ya san ko mai zai yi babu mai ba shi wannan damar. Ga shi ya ji Abdou ya ce tun da aka dawo da shi, bai farfaɗo ba balle ya yi magana. Gefe guda kuma yana jin tsoron kar a koma a Nigeria a bibiyi Nana, saboda za ta shiga matsala ba kaɗan ba. Koma a wani hali take ciki yanzu? Ya tambayi kansa yana jin wata irin damuwa ta mamaye zuciyarsa, tare da ɗora wa kansa laifi amincewa da auren Imam da Nana, ya kuma ɓoye mata komai a kan Imam ɗin. Ya dafe kansa da yake jin tamkar zai tarwatse dan damuwa. **** Nana ta nutsu da zaman gidan Nene, duk Nenen akwai faɗa kamar yadda Hajara da mijinta suka din ga faɗa, amma sam hakan bai damu Nana ba, dan ba ta yi mata abin da za ta yi faɗan. Nana ta fuskanci Nene sana'ar Abinci take yi, wasu lokutan tun safe idan ta fita sai daf da magariba take dawowa. Ta kan dawo tar e da yaran da suke yi mata aiki, su fara rage aikin Abincin sayarwar da za a yi washegari. Nana tana jin yadda Nene take yi musu bala'i bisa kuskure kaɗan. Nene ta din ga gwada Nana, da ajiye kuɗi ko ina ta ga dama, ko ma ta fita ta bar ɗakunanta a buɗe, amma ko allura ba ta taɓa rasawa ba. Kullum sai ta ba wa Nana Abinci, na safe kan su fita na sayarwa ta ba ta na rana, idan sun dawo ta ba ta na dare, har da ma tsaraba ta masu ciki. Ma'aikatan Nene sun ɗauka ma, Nana 'yar uwatta ce. Idan sun dawo Nana kan fito ta ce za ta taya su aiki, Nene ta yi ta faɗa ta ce ba za ta yi ba. Sai dai hakan ba ya hana Nana kama musu wasu ayyukan. Nana ta shafe kusan wata guda a gidan Nene, ta ga kullum sai Nene ta ba ta Abincin nan sau uku, ba ta taɓa nuna mata ta gaji da ciyar da ita da take yi ba, wasu lokutan har tambayarta take yi, ko tana son cin wani abin ne daban. Da daddare ta kira Nana, Nana ta fito ta zauna a kusa da ita. Ta buɗe takarda fal kifi ta ce "Nana ga kifi ko za ki iya ci, idan ƙarnin ba zai dame ki ba". Nana ta dube ta ta ce "Nene, dama ina son mu yi magana ne" Nene ta ce "To ina jin ki" "Na ga kullum sai kin bani Abinci sau uku a rana, na ce ko za ki ba ni wani aikin na din ga yi miki, a maimakon Abincin da ki ke ba ni, ko gurin sayar da Abincin sai na din ga bin ki, ko wanke-wanke na din ga yi miki" Ta dubi Nana, sannan ta numfasa ta ce "Ni kuwa duk rashin imanina, da wannan tsohon cikin sai na saka ki aiki, dan dai abin da za ki ci sau uku ba zai gagara ba. Ban san takamaiman abin da ya kawo ki ƙasar nan ba, ban san kuma lokacin komawar ki ba, amma ba na tunanin abin da za mu ci ni da ke zai gagare ni. Ba zan ɓoye miki da fari ban so zamana da ke a gidan nan ba, saboda ba na son matsi da takura ko kaɗan, da su Auwwalu sun matsa ne, dan kora da hali na so yi miki. Amma yanayin ki ya nuna mini ki na ɗauke da damuwa mai nauyi a zuciyarki. Ba ƙaramin dalili ne zai sanya yarinyar mace, mai ƙanan shekaru kamar ki, ta baro gida ta taho uwa Duniya ba ga juna biyu. Kuma ki na yawan zama ki yi shiru, fuskar ki ɗauke da damuwa. Na kuma jarraba ki ta ɓangarori da dama, ban ga alamar rashin nutsuwa a tare da ke ba, shi yasa na ji zan iya zama da ke. Amma Nana tsakaninki da Allah wannan juna biyun na ki, na halal ne? Kuma da sanin iyayenki ki ka taho nan?" Tambayar Nene ta yi wa Nana mugun zafi a ƙirjinta, amma sam ba ta ji haushinta ba, dan kowaye dole ya yi irin wannan tambayar. Sai da ta ji hawaye ya cika mata ido, da tuna ire-iren waɗannan tambayoyin dole ta ci gaba da amsa su, a cikinta da abin da za ta haifa, muddin ba gano inda Sayyid yake ta yi ba. Ta haɗiye wani irin yawu mai zafi ta ce "Nene cikina na halal ne, ni matar aure ce, ban kuma gaya wa iyayena zan taho nan ba, sai da na riga na yo nisa da gida" "To saboda me, kuma ina mijinki?" Kawai Nana ta fashe da kuka, ta ce "Shi na fito nema, mijina da danginsa" Nene ta ce "Shikenan, ya isa haka ki kwantar da hankalinki, mu bar maganar ma yi wani lokacin. Amma sai dai ki yi haƙuri, dan dole sai mun ƙarasa wannan maganar Nana, saboda ni uwa ce, dole na mu'amalance ki na yi miki nuni da abin dai-dai da akasin haka. Ban ga alamar ki na magana da wani a can gida ba, ko ta tarhon hannunki ce ba. Mahaifiyarki tana raye?" Nana ta jinjina kai tana share hawayenta. Nene ta ce "Shikenan, share hawayenki mu ci kifin" Ta girgiza kai ta ce "Ƙarnin hawa kaina yake yi na ƙoshi" daga haka Nana ta tashi, ta koma ɗakinta. Sai dai ta din ga kuka, saboda ita kanta ba ta san ta ina al'amuran za su warware ta cimma abin da ta fito nema ba. Shukura ta rasa gane kanta da kanta, saboda rashin lafiya da take ta fama, ga Sagir ya rage ba ta kulawa, duk da yana ta ɓoye-ɓoye amma tuni ta daɗe da gano shi, sai dai ta maze ita ma ba ta nuna masa ba. Hajiya Amina ce ta je gidan, Shukura ta ji daɗin zuwanta sosai da sosai, a nan Hajiyar take gaya mata batun Nana. Cikin damuwa Shukura ta ce "Wallahi Mami, tun da aka yi auren nan, nake jin tausayinta, gaba ɗaya ban ga riba a abin da babanta ya yi mata ba. Babu bincike babu komai a ce an aura mata mutum, wasu lokutan na kan rasa ina tunanin mutanenmu yake tafiya" "Ke dai a yi sha'ani kawai, amma na jinjina batun ni kaina" "Shikenan an saka rayuwarta a gagari, ga ƙarancin shekaru" suka ci gaba da jajanta lamarin. Hajiya ta fuskanci yanayin Shukura kamar ba ta da cikakkiyar lafiya, ta kira Doctor Sharif ya zo ya duba ta. Shukura ba ta so ba sam, dan ko ƙaunar ganin Sharif ɗin ba ta yi, amma tuna ta yi wa Hajiya Alƙawarin komai ya wuce, ta yi tawakalli ta dangana ya sanya ta haƙura. Ya zo har gida ya yi mata gwaje-gwaje, ya kuma tabattar mata da tana da juna biyu. Hajiya Amina ta din ga murna, a duk lokacin da aka ce ga wata mace da ciki, sai ta yi ta murna, ta ji dama ita ce. Shukura ba ta wani yi murna ba, saboda ita gaba ɗaya haihuwar ma ta fita daga kanta. Da yamma Hajiya Amina ta koma gida, saboda tsabar zumuɗi, tana zuwa ta tarar da Alhaji Zailani a gida, ta hau ba shi labarin Shukura wani cikin ne da ita. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarce shi, yana tsoron a wannan karon ma, kar a nemi ya bayar da wani abu da ya danganci iyalinsa. Hajiya Amina ta din ga jin wani irin bacci, tana idar da sallar isha'i, ta ɓungire a gurin ta hau bacci. Ita da Nana ta gani a falo, a zaune suna hira, kamar yadda suka taɓa yi kwanaki lokacin Nanan, na zuwa gidan rainon Haidar. Ta ce "Hajiya, kin kuwa ci gaba da bibiyar Likitoci a kan matsalar rashin haihuwar ki?" Hajiya Amina ta ce "Nana ai ni na haƙura ma na bar wa Allah, yanzu shekaruna sun wuce na haihuwa" Nana ta ce "A gurinki ba, a gurin Allah yana bayar da falalarsa a inda ya so, da kuma lokacin da ya so ne. Ki daina biye wa wannan mijin naki, ya din ga sarrafa rayuwar ki yadda yake so. Ki nemi mafita a kan matsalolinki. Kuma Shukura ta dage da Addu'a, kar wannan ɗan ma ya sake raba ta da shi" Maganar Alhaji Zailani ce ta tashi Hajiya Amina daga mafarkin da take yi, tana kallonsa kawai ta ji gabanta ya faɗi" "Lafiya ki ke kwance a ƙasa haka ki ke bacci?" Ta ce "Bacci ne ya ɗan ɗauke ni ban sani ba" Ya ce "To ki tashi ki koma gado mana, kar wuyanki ya yi ciwo" Ta yinƙura ta tashi ta canza kaya ta hau gado ta kwanta, sai dai ta din ga jin mafarkin da ta yi da Nana a jikinta, tamkar a zahiri ya faru. Fadila ce zaune a kusa da Alhaji Fatuhu, gefenta kuma jaririnta ya yi wayo, yana ta bacci. Ta miƙa masa lemon da ta haɗa masa a kofi, ta zuba masa ido, yana sha a hankali. A ranta take faɗin "Ubangiji Allah ka bawa wannan bawa naka lafiya, albarkacin ayoyin Alkur'ani' Ta kalle shi tsaf, ya yi rama ta ban mamaki, dan ma yanzu ya ɗan ciko, ba kamar da ba" ya shanye ya miƙa mata kofin, ta karɓa ta ajiye a gefe. Ta matsa kusa da shi tana ɗan ƙara gyara masa filulluka. Ya ce "Na gode sosai, Allah ya yi miki albarka, ya raya miki Muhsin" Ta ce "Amin Daddy" "Da lafiyata ƙalau, da mun yi sauri, nan da wata wata taran, ki kuma haifo mana wani" Murmushi ta yi ta ce "Allah ya baka lafiya ya tashi kafaɗunka" ya amsa da Amin yana riƙe hannunta cikin nasa da ya yamuste kamar na tsoho. Hajiya Suwaiba ta ce ta shigo ɗakin, Fadila ta ɗan zabura ta ja da baya. Hajiyar ta ja tsaki ta ce "A hakan ma da kake wani abin ka ke ƙoƙarin yi, ai sai ku rufe ƙofa kar yara su faɗo, a lalata mini tarbiyyar yara" Fadila ta ce "Haba Hajiya, abu na ba shi ya riƙe hannuna, and laifi ne dan ya riƙe hannuna wani abin ki ka ga na yi?" "Kar ki yi mini rashin kunya dai? Idan ma yin ku ke, ku ƙarata ku da Allah" Ran Fadila ya yi mummunan ɓaci, ta yinƙura da niyyar, ta ɗauki ɗan ta ta bar ɗakin, amma ya riƙe hannunta, ya hana ta tafiya. Hajiya Suwaiba ta gama bala'inta ta tafi ta bar su. Idan ya ce Suwaiba ba ta ƙoƙari a kan rashin lafiyarsa ya yi ƙarya, tana iyakar ƙoƙarinta amma wasu lokutan tana da saurin ƙosawa gashi haryanzu azababben kishi na ɗawainiya da ita. **** Gidan Maijidda kuwa, Iliyasu bai taɓa tsammanin,    Maijidda na da taurin kai haka ba. Gaba ɗaya ta tarkata shi ta yi watsi da shi. Iyakarta da shi, ta girka Abinci ta ba shi, idan buƙatarsa ta tashi, ya yi kiɗansa ya yi rawarsa. Gaba ɗaya ta sanya damuwa a ranta, ta rame sosai da sosai, dan ko Abincin kirki ba ta iya ci, kusan kullum cikin kuka take, ko ta zauna ta yi shiru. Ga shi ya lura 'yan uwanta sun fara gajiya da sinturin kai ƙararta da yake yi, ba yau ba gobe. "Anya ka na ganin haka rayuwar Imam za ta ci gaba, duk lokacin da ya farka sai ihu da fizge-fizge, sai dai a yi ta yi masa allurar da zai yi bacci? Idan aka bar shi a haka rayuwarsa fa ta nakasa kenan har abada" Sultan ya ce "Abdou, ni kaina ala'amarin nan yana damuna, na rasa yadda zan yi. A ɓangaren ƙwaƙwalwar ma, babu wani gamsashshen bayanin abin da ya faru da shi. Ta ɓangarenka ma babu wani nagartaccen bayani daga bakin shi yaron, balle mu ji ko wani abin ɗin aka yi masa". "Sultan, ka ƙi bayar da dama a sanya 'yan doka, su maguza yaron nan, ya faɗi gaskiya ko ya ƙi Allah" Sultan ya girgiza kai ya ce "A'a, duk ranar da Imam ya samu lafiya, muddin ya ji labarin an cuzguna masa, zai yi fushi, kuma zai ji babu daɗi kai ka san irin alaƙar da take a tsakaninsu." "Amma yanzu ai yanzu a kan gaɓar bincike a ke Sultan. Amma tun da haka ka ce Shikenan, za a ci gaba da bin komai sannu a hankali" Sultan ya amsa da "Yauwwa" BAYAN WATA ƊAYA Sabo turken wawa, rashin ganin Ƙaisar da Nana ta daina yi, ya sanya ta din ga tunanin ko wani abin ne ya faru da shi. Sai dai yau kwatsam cikin barcinta, ta ganta a cikin Librarynsa. Sai dai ta gurin ƙwalam babu litatafai babu kayan rubutunsa sai mudubin da yake nuna mata abubuwa a cikinsa. Ta waiwaya ta lelleƙa, amma babu Ƙaisar babu alamunsa. Wani littafi guda ɗaya tal, ta hango a kan teburin rubutun Ƙaisar, ta ƙarasa ta nufi teburin ta ɗauki littafin. Bangon littafin na fatar wata dabba ne. Dan har da gashi-gashi a jiki. Yanayin bangon littafin ya sanya ta yi tunanin, ko mene ne a rubuce a littafin ba yanzu ya faru ba, ya kwana biyu da faruwa. Littafin ba wanda ta karanta tarihin su Lanti ne a ciki ba, wani ne daban. Hoton wata alƙarya ce, da ke tsakanin duwatsu, da aka rarake aka samar da katafariyar daula. Ta buɗe littafin shafin farko, ta fara karantawa. "Tushiya..." Shi ne abin da ke rubuce a shafin farko na littafin. "Ka sani,har abada da ɗan Gari a kan ci gari. Kuma ba a cimma buri da tausayi ko jin ƙai. Wannan mataki na farko kawai ka cimma, na sharar fagen cimma nasararka. Ka na buƙatar sanya wa mutane tsoronka, da shakkarka domin cimma burinka, kuma hakan ba zai taɓa yiwuwa ba sai ka zubar da jini, duk wanda ya biyo ta hanyarka ka datse rayuwarsa, kar ka damu da adadin rayukan da za a rasa, ka zubar da jini ba ƙaƙƙautawa har sai mutane sun fara jin fitsari a duk lokacin da aka ambaci sunanka. Ka kame mutanen gefen alƙaryar nan, ka mayar da su bayi, matansu ka mayar da su naka, mazansu su zama bayinka, ka yi amfani da ƙarfinsu da fikirarsu ka gina alƙaryar da babu wani mahaluki da zai iya ɗaga maka yatsa, kar ka gushe kana aikata hakan, har sai buƙata ta biya. Zaka kasance cikin sanyawar albarkar Aljanu, za su baka dukkanin goyon bayan da ka ke buƙata kar ka saurarwa kowa" Cikin damuwa mutumin ya kalli mai maganar ya ce "Ka sanya ni na kashe mahaifina da hannuna, yanzu ga wani abin ka sake zuwar mini da shi, kar ka manta ina da 'yan uwa maza, ba za su zuba mini ido, duk na yi wannan ba, na ɗauki abin da ba nawa ba, alhalin su na gaba da ni ba" Ji ta yi mudubin gurin yana wata irin ƙara tamkar zai tsage, a take ta ajiye littafin ta nufi mudubin tana kallonsa. Wata irin wuta ta gani tana ci a cikin mudubin. Wutar mai matuƙar ban tsoro saboda yadda take ci. Wani mashi ta gani a soke a jikin wani ƙwarangwal, ɗaya gefen mashin an yi rubutu a jikin wani abu mai kama da takarda. Ta ƙara matsawa domin karanta mene ne a jikin takardar amma ta ga mudubin yana hayaƙi yana baƙi yana washewa. A kusa da wutar ta ga wani abu mai kama da mutum, a lulluɓe da wani mayafi yana zuba wani abu a cikin wutar wanda yake ƙara sanya wutar ƙara balbala. Imam... ta iya gani a rubuce a jikin abin, mai kama da takarda, a gaban Imam ɗin akwai wani sunan, sai dai ba ta iya karanta sunan ba. A jikin wutar ta ga taswirar fuskar Sayyid yana jijjiga jikinsa na ƙonewa yana kururuwa yana kiran sunanta. Wata irin zabura ta yi ta kuma tunkarar mudubin gadan-gadan, mudubin ya yi wata irin tsawa ta ja da baya ta faɗi ƙasa. A gigice Nana ta farka, ta haɗa uban gumi ta yi sharkaf, ga wata irin ƙullewa da cikinta ya yi haɗi da mararta. Ta yinƙura da ƙyar ta tashi ta tafi banɗaki, a zatonta fitsari take ji, ko kuma bayan gida, amma ta ji ba bayan gida take ji ba, ta fitsarin amma still mararta kamar an saka wani abu an ɗaure mata. Ta yi alawala ta koma ɗakinta. A zaune take salla saboda yanayin girma da nauyin da cikin ya yi. Ta kasa tuna abin da ta gani, sai iya wutar nan da wannan tsawar da mudubin ya yi su kawai take iya tunawa. "Allahumma ajirni mina narr" Ta maimaita da tuno yadda ta ga wutar nan. Ta ji sam mafarkin nan bai yi mata daɗi ba, ko mene ne babu Alkhairi a tattare da shi sam. Sai da gari ya waye, sannan ta samu afuwa daga wannan ɗaurewar da mararta ta yi da bayanta. Jikinta babu daɗi, haka nan take lallaɓawa ta daure kar Nene ta fuskanci wani abu. Nana ta dama kunu da kanta, ta tashi tana tafe da kyar, Nene ta ce "Nana wai cikin nan naki wata nawa ne?" Ta ɗan yi shiru ta ce "Ina ga bakwai ne" "Anya kuwa Nana, kalli yadda ya cure guri ɗaya ya yi ƙasa sosai a ce cikin nan na watanni bakwai ne kawai? Amma ban sani ba ko biyu ne. Yakamata ma mu je Asibiti a duba ki, ni wallahi na ma manta shaf ana zuwa awo. Ko danmu lokacinmu ba awon ake yi ba oho" Nana dai ta yi murmushi kawai tana jin yadda ɗan yake ta motsi yana danno ta. Da ba rufe cikakken sati, mijin Hajara bai zo gidan ba, dama yana fargabar kar Nana ta kasa zama da Nene, saboda faɗanta, kuma cikin ikon Allah ya ga lafiya kalau suke zaune. Dan haka ya rage zuwa sosai. Tun da Nana ta je gidan, Neme ba ta barin ta ta fita, saboda ta ce mata tana da aure, kuma tana yawan gaya mata, ba a son mace mai ciki ta din ga yawo jama'a su na kallonta, saboda baki da ido. Ma'aikatan Nene duk sun saba da Nana, duk a tunaninsu 'yar uwatta ce, sai dai sukan tambayi Nana, ya aka yi hausarta ba irin tasu ba. Wasu lokutan sai Nene ta cewa Nana ta zauna a ɗaki kar ta fito, dan haka babu inda Nana ta sani a garin. Nana ta kwana huɗu, tana fama da wannan ciwon a tsaitsaye. Sai dai na yau ya fi na kullum, dan sam ba ta yi bacci ba, kuma ba ta gaya wa Nene ba. Da safe kan Nene ta fito, Nana ta yi shara ta wanke banɗaki, ta ɗora abin karin kumallo. Ta kuwa sha faɗa a gurin Nenen, sai dai ita ko a jikinta. Sun gama karyawa, Nene ta shiga ɗaki, ta ji Nana na kiran sunanta, cikin mawuyacin hali. Nene ta fito da sauri ta ce "Nana lafiya?" "Nene yoyon fitsari nake yi, ba na iya riƙe fitsari" gaban Nene ya faɗi ta ce "Kamar yaya?" "Ji na yi kawai fitsari yana bin ƙafata, kin ga" ta yi maganar tana ɗaga wa Nene doguwar rigarta, ruwa na ta bin ƙafafuwanta". "Nana wannan ai kamar naƙuda ki ke yi, anya ba ruwan mahaufa ba ne?" Duk da ƙoƙarin da ta yi, za ta yi magana, sai ta kasa saboda wani irin gigitaccen ciwo da ta ji. Har Nene ta fita suka samo abin hawa, Nana na cikin halin ciwo, ba ta iya gane komai. Nene ta ɗaukko wa Nana wasu kayan, su ka fita suka tafi Asibiti. A Asibitin ma, da aka tambayi Nana, cewa ta yi cikinta wata bakwai ne, sai dai da aka yi hoton cikin, ya nuna satin cikinta arba'in da biyu. Likitan ya yi mata tambayoyi, yaushe ta yi al'ada na ƙarshe, ta ce ita ba za ta iya ganewa ba, saboda ɓari kawai take yi a jere. Ya tabattar mata a cikin ɓarin da ta din ga yi, tun da ba Asibiti take zuwa a duba ba, akwai wanda bai fita ba ya ci gaba da girma, dan haka naƙuda take yi. Gaba ɗaya Nene ta rikice, kamar 'yar ta ce za ta haihu, sai a lokacin ta fita, ta sayo kayan jariri da ba ta san ma na wani jinsi ba ne, da ɗan abin da za a buƙata. Ma'aikata na tsaye a kan Nana, su na ƙoƙari, duk ta galabaita ma ta kasa nishin can ta ce "Ya hayyu ya ƙayyum" ta yi yinƙuri sai ga kan ɗan ya fito. Ita dai ba ta san yadda aka ƙarasa ba, ta ji kukan jariri ya cika ɗakin. Likita ta ɗago mata jaririn ta ce "Kalli me ki ka haifa?" Nana haushi ya kama ta, ta gama shan wannan uwar wahalar ga ɗan a hannunta, kuma a din ga tambayarta me ta haifa. Ta kalli yaron namiji ne, ta ga wani irin shirgegen ɗa, kamar ɗan wata biyu, sai ta hau mamakin yanzu wannan ɗan duk girmansa a jikinta ya rayu, kuma ta ɗan wannan gurin ya fito? Wata irin zabura ta yi ganin fuskar yaron, ta miƙa hannunta gaba ɗaya tana ƙoƙarin karɓe yaron daga hannun Likitar a kiɗime. Yana kan gadonsa na marasa lafiya a kwance, su ka ga ya yi wata jijjiga sai da gadon ya girgiza kamar an jona masa wani abu, kawai suka ga ya buɗe idonsa. A rikice suka kewaye shi, su na kiran sunansa, sai dai babu wanda ya amsawa sai bin su da yake da ido, kamar ya ga baƙin halittu. Sultan ya riƙo hannunsa ya ce "Imam ka gane mu kuwa?" Ya yi shiru yana bin Sultan da kallo. Abduou ya ce "Ikon Allah, ka ga wannan karon bai tashi da ihun ba, sannu Imam" Kawai ya yi shiru kamar saƙago, sai ƙwayar idonsa da yake juyawa. Ayshercool 08081012143 65 Nana kuwa da sauri wata ma'aikaciya ta mayar da ita ta kwantar, ta ce "Kar ki tashi, ai miƙo miki shi za a yi" Abin da ya razanata kuwa, bai wuce yadda ta ga fuskar Sayyid sak, a jikin ƙaton jaririn nata ba, ga sumar kansa a cike har goshinsa. Ga shi jariri amma hatta girar sa da gashi, haka jikinsa ma akwai gashi sosai. Aka ɗora mata shi a ƙirjinta, ta yi wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da furta Alhamdillah. Ta sanya hannayenta, ta zagaye shi, ta ɗora hannunta a kansa ta din ga karanto masa addu'oi. Ta din ga hasko irin murnar da Sayyid zai yi, da ya na nan aka haifi jaririn nan. Hawaye ya din ga gagangarowa ta gefen idonta. Tana jin Likitan tana tsokanarta da har da kukan daɗi, ba za ta bayar da jaririn ba sai an ba ta tukuici mai tsoka. Nana dai ta lumshe idanunta tana murmushi. Aka ɗauke jaririn aka gyara ta, aka yi mata ɗinki, sannan aka kai ta ɗakin hutu. Bakin Nene ya ƙi rufuwa, ta din ga kallon jaririn. Ta kira wayar su Hajara, ta gaya musu baƙuwar su Nana ta haihu. Nana ta din ga kallon Nene, da mamakin yadda take ta murnar haihuwar nan, tamkar ita ta haihu. Sai dai da Nana ta kalli fuskar jaririn sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, tana tsoron idan ba ta haɗu da Sayyid ko 'yan uwansa ba, yaya za ta yi mene ne makomar yaron kenan? Ga fargaba da tsoron kar su Ƙaisar su yi masa wani abu, kar shi ma ya yi mummunan gado kamar yadda ta yi. Haka dai ta ɗan saki fuska babu yabo ba fallasa. Bayan awanni shida aka sallame ta daga Asibitin suka koma gida. Aka bata magungunan da suka dace ta yi amfani da su, duk Nene ta biya komai. Nene ta shiga hidima da Nana sosai, ruwan wankanta da na jariri. Ga lafiyayyen Abinci, Hajara kanta idan za ta zo, sai ta yi girki. Kowa ya ɗauki jaririn Nana, sai ya burge shi. Ita kanta Nana tasirin Addu'a ne ya sanya Allah ya kawo mata wannan ɗaukin da gaggawa, mutanen da ta haɗu da su suke sonta. Kwana na biyar da haihuwarta, ta ɗebo kuɗi a cikin jakar gurin Sarkin baka, ta samu Nene ta ce "Nene kuɗin nan za su isa a sai wa yaron nan abin yanka?" Nene ta ce "Kar ki damu, mun yi magana da Auwwalu za a samo abin yanka in sha Allah" Nana ta ce "A'a Nene, ko ke ki ka haife ni, wahalar da za ku yi mini kenan, kuɗinki na sana'a ne. Ina son a saya masa kaya, a saya masa abin yanka, ko ba za su isa ba, a karɓa a ƙara irin kuɗin mahaifinsa ne, dan Allah kar ki ce a'a" Da ƙyar Nene ta karɓa. Dan kuɗin da yawa, aka sayo ƙaton rago, Nene har da ɗawainiyar yin girki, ta gayyaci maƙwabtanta suna. Muhammad Muhsin, shi ne sunan da Nana ta sanya wa jaririn, Muhsin saboda sunan ɗan gidan Alhaji Fatuhu da har abada ba za ta manta da mutuwarsa ba. Maƙwabtan Nene da ma'aikatanta sun yi wa Nene kara, sosai suka tara mata abin alheri na kuɗi, da kayan sakawa kasancewar Nene duk masifarta akwai kyauta, shi yasa take shiri da mutane. Da daddare Nene ta yi wa Muhsin wanka, Nana ma ta yi ta ba ta jaririn ta shayar da shi. Ta fita tsakar gida ta ƙarasa aikace-aikacenta. Kukan jaririn ta din ga ji, Nene ta ce "Nana ya ne, ki kula da shi mana" Amma Nana ba ta amsa ba, sai kukan jaririn da ta ci gaba da ji. Ta koma ɗakin ta ɗaga labule, kawai ta tarar da Nana, ta saka jaririn a gaba tana ta uban kuka. Hankali tashe ta shiga ɗakin cikin damuwa ta ce "Ke lafiya, kukan me ki ke yi?" Nana ta kasa magana, ta ci gaba da kuka, ga jaririn a kan cinyarta amma ta kasa riƙe shi. Nene ta ƙarasa ta ɗauke jaririn ta ce "Ba za ki illata ɗan mutane ba, maza yi ta kukan, idan kin gama kya kula da shi" Nene ta goye shi a bayan ta, ta ci gaba da sabgoginta ta ƙyale Nana. Ba ta sake kula Nana ba, sai da ta yi kuka mai isarta ta gaji. Nene ta gyara shimfiɗarta, ta kwantar da Muhsin da ya yi bacci. Ta koma gurin Nana, ta zauna. "Nana" ta kira sunanta. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta. "Ki gaya mini tsakaninki da Allah, yaron nan ta hanyar aure ki ka haife shi ko kuwa? Na san tambayar nan tana baƙanta miki rai, amma haƙuri za ki yi da ni" Nana ta share hawayenta ta ce "Nene ni ba ƙarya na yi miki ba, ina da aure wallahi ɗan sunna ne" "To Alhamdillah, dama jira nake Allah ya sauke ki lafiya, idan ta kama da kaina sai na je Nigeria, na mayar da ke gaban iyayenki Nana, wannan zaman naki kina yarinyar mace, ba kamace ki ba" "A'a ba zan koma ba Nene" "To saboda me?" Hawaye na ambaliya a fuskar Nana ta ce "Sai na haɗu da Babansa, ko danginsa. Ai sun san na taho neman sa" Nene ta ce "To a wane garin baban nasa yake?" Ta girgiza kai ta ce "Nima ban sani ba" "Kamar yaya? Meye sunansa da garin da yake ko hotonsa, sai a taya ki cigiyarsa" Nana ta sake girgiza kanta ta ce "Ban sani ba" "Wacce daga cikin tambayar ce ba ki sani ba?" "Nene ban san garin su ba, ban san sunansa ba, kuma ba ni da hotonsa" Nene ta ce "Ke kar ki raina mini wayo mana, na kwaɗe ki, ta yaya za ki auri mutum ba ki san sunansa ba, ba ki san sunan garinsu ba kawai ki ka kamo hanya ki ka taho? Me ki ke ɓoye mini ne?" Nana ta ɗan yi shiru ta numfasa ta ce "Ƙaddara ce ta haɗa ni da shi muka yi aure, ban san sunansa na gaskiya ba, ni ba shi sunan Sayyid. Ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa kuma." Nan Nana ta warware mata komai da ya danganci aurenta da shi, duk da ba komai ta gaya mata ba. Nene ta yi shiru sannan ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, dama shi ne Sayyid ɗin da ki ke ambata idan kina bacci? Amma Nana iyayenki sun yi ganganci. Ke yanzu ko hotonsa ba ki da shi. Kawai Nana ta ɗaga mata kai alamar eh. "To ai Nana zama guri ɗaya a haka, ba zai sanya a gano shi ba, dole sai an taɓuka wani abin, wane ƙabilar ne ko shi ma ba ki sani ba?" Nana ta yi shiru ta rasa ma me za ta cewa Nene. Nene ta ce "To shikenan, amma ba kya ganin yakamata gidanku su san kin haihu?" "Nene babu buƙata goben jaririn nan nake hange" "Haka ne, to Ubangiji Allah ya kyauta, amma wannan lamarin naki akwai sarƙaƙiya Nana. Amma ba komai Allah ya taƙaita" Nana ta amsa da Amin. **** Baba yana tsakar gida yana shan kunu, sai ga Suwaiba ta fito, gaba ɗaya ta zama wata iri kamar shiri-shiri. Ta kalli Baba ta cake a ƙofar ɗaki ta ce "Nana fa ta haihu" ba shiri ya ajiye ludayin kunun ya kalli Suwaiba ya ce "In ji wa? Waye ya gaya miki?" "Nanan ce ta gaya mini" "Ke a ina ki ka ganta?" "Ina bacci a ɗaki, na ganta da jaririn, ta ce mini haihuwa ta yi" Wani uban tsaki Baba ya ja, saboda jin shiritar da Suwaiban take faɗa. Dan da fari ya zata ma da gaske take yi. Alhaji Zailani ne tare da Malam Gambo, su na zaune fuskarsa ɗauke da damuwa. Malam Gambo ya ce "Wai duk me yasa ka damu ne har haka? Ka na tsoron ƙungiya ta sake cewa ka kawo jininka ne?" Alhaji Zailani ya numfsa ya ce "Abu na farko burukana biyu, ɗaya ya cika na durƙusar da Fatuhu. Amma samun yarinyar nan ya zame mini bala'i, ƙarewa ma da yake azzaluma ce mai baƙin hali, wai ta tafi Nijar. Ban kuma san ta yadda zan yi na same ta ba. Babu yadda ban yi na samu yarinyar nan ba, amma duk lokacin da na yi wani yinƙuri a kanta, sai hankalina ya gushe. Yanzu babban tashin hankalina wannan jarababbiyar Sa'a, ashe ita ma ƙoƙari take yi, ta mallaki jinin yarinyar nan. Ga shi na rasa dalilin da ya sanya Shukura take ta zargin likitan da yake yi mini aiki, da kisan jaririnta." Malam Gambo ya numfasa ya ce "Ka tattara nutsuwarka guri guda, nasara na buƙatar kasada a kowane lokaci. Ita waccan yarinyar ka jingine batunta a yanzu tukuna, tun a wancan lokacin ai na gaya maka tana ɗauke da wani shu'umin aljani ne mai taurin kai a kanta ba zai taɓa barin burinka ya cika ta daɗin rai a kanta ba. Ba kai kaɗai ba koma waye kuwa. Sannan ƙungiya idan ta sake buƙatar jini, sai ka bayar da na ɗaya daga 'ya'yanka ko namijin, ko kuma ita yarinyar taka a bar jaririn nata ba shikenan ba. Kawai ya zuba wa Malam Gambo ido, idanunsa suka yi jawur sai dai bai ce komai ba ya tashi ya fita. **** Ɓangaren Sagir kuwa, sosai yake sintiri tsakanin Kano da Abuja, saboda Yusra, saboda soyayyar da suke yi ma a yanzu, ba su yi ta a lokacin da suke saurayi da budurwa ba. Wata irin muguwar shaƙuwa suka yi, da shaiɗan ke barazanar shiga cikin lamarin nasu, ga shi ya rasa ta inda zai tunkari Hajiyarsa da batun, domin ba son Yusra suke yi ba. Shukura tuni ta daɗe da gano inda ya dosa, amma ta zuba masa ido ta ga ina ne ƙarshen alewar zai kasance. **** Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta yi wata guda da haihuwa, Nene ta tattara ta daina fita gurin sana'arta. Sai aikin kula da Nana, ga shi kullum da sassafe kan ta ci komai, ake kawo nonon raƙumi fresh Nana ta sha, sannan ta ci Abinci. Nana tana kwance tana bacci da azahar, saboda yadda Muhsin ba ya barin su bacci da daddare, saboda ba ya ɗaga wa Nana ƙafa da tsotso, ga kuka sai dai Nene ta taya ta riƙonsa. Yana gabanta yana bacci, ita ma ya ɗauke ta, ta ɗaga kai ta ga ya shigo ta ƙofar ɗakin. Tana kwance ba ta motsa ba ta ga ya ƙaraso ya zuba musu ido, daga ita har Muhsin, ya sanya hannunsa ya shafa gashin jaririn, ya durƙusa ya sumbaci gishin yaron. Sannan ya kalli Nana idanunsa cike da hawaye. "Sayyid, yaushe za ka zo ka ganmu? Mu na buƙatar ka a kusa da mu, dan Allah kar ka tafi ka bar mu" Ya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa, sai dai bai yi magana ba. Sai da aka jima sosai yana murza yatsun ta a hankali sannan ya ce "Ma vie" "Na'am" "Gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, rayukanmu su na kewar juna, ki kula mini da rayuwata da ke jikin ki, da jikin ɗa na, ina ƙaunarku Nana" Riƙe Sayyid ta yi, tana kuka tana "Dan Allah Sayyid kar ka tafi ka bar mu, mu na buƙatar ka a rayuwarmu, dan Allah Sayyid, dan Allah" Nene ta yi shiru tana kallon yadda Nana ta riƙe ta tana kuka. Da yake sheshsheƙar Nanan ta jiyo, ta taho ɗakin tana zuwa ta tarar da Nana tana nema ta danne jaririn. Bayan ta ɗauke shi ne, Nana ta riƙe mata riga. Nene ta zuba wa Sarautar Allah ido, Nana ta buɗe idanunta a hankali ta ga yadda ta riƙe Nene gam. A hankali ta cika ta tana sunkuyar da kai. Sai dai ta ɗaga kanta tana kallon ɗakin, tana jin ƙamshin turaren Sayyid a hancinta. Nene ba ta ce mata komai ba, ta goya Muhsin ta fice da shi daga ɗakin. Nana ta lallaɓa, ta tafi gurin da kayanta suke, ta bubbuɗe jakar kayan shafe-shafensa, da take ta adanawa tana kallon su tana jin daɗi. Sai dai a wannan karon hawaye take yi, tare da jin zuciyarta tamkar za ta buga. Ta zazzage kayan ta din ga bin su da kallo, ta ɗago Azurfarsa da ya ba ta, ta ce ya yi mata yawa, ya ce ta ɗaure da zare ta yi sarƙa da shi. A hankali ta furta "Da mutuwa ka yi na san Allah ne ya karɓe ka babu yadda na iya, da aurenmu ne ya ƙare shi ma na san wannan ƙaddara ce, ba a kaina a ka fara ba. Amma ban san a wani hali ma ka ke ba, duk a inda ka ke ina fatan Ubangiji Allah ya sanya ka na cikin aminci da kwanciyar hankali Sayyid. **** Yana zaune a kujerar da ke cikin ɗakin, da abu a cikin kofin yana sha a hankali. Murmushi ya gaza barin fuskar Sultan, ya zauna a kusa da shi yana murmushi ya ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa Imam, ya jikin naka?" Ya kalli Sultan ya mayar da hankali ya ci gaba da shan shayin da ke cikin kofin hannunsa ba tare da ya furta komai ba. Cikin damuwa Sultan ya ce "Har yanzu ba ka gane ni ba Imam?" Har yanzun dai bai yi magana ba, bai kuma fasa shan shayinsa ba. Sultan ya riƙo hannunsa guda ɗaya cikin nasa, ya ce "Imam ka kalli Abbanka mana, ka yi magana ko hankalina zai kwanta" Ya waiwaya ya kalli dattijon. Cikin murna Sultan ya ce "Ka na jin abin da nake faɗa?" Ya yi shiru yana ci gaba da kallonsa, bai yi magana ba. "Ka yi mini magana ka ce wani abu mana" A hankali ya zame hannunsa daga na dattijon, ya tashi daga kan kujerar ya koma gadonsa na marasa lafiya ya kwanta. Sultan ya yi shiru yana kallonsa, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Kar a ce ƙwaƙwalwar ɗan sa ta taɓu. A yadda alaƙarsa da ɗan sa take, ba ƙaramin abu ne zai sanya ya yi masa haka ba. Kwanciyarsa ke da wuya, ya fara jijjiga, a rikice Sultan ya nufe shi. Sai dai ya fara kururuwa yana faɗin "Wuta zafi" Matawalle ne ya shigo ɗakin da sauri, suka rufu a kansa, Sultan ya din ga tofa masa Addu'a. Har ya daina jijjigar. Abdou ya kalli Sultan ya ce "Abubuwa fa kamar ƙara rikicewa suke yi, mene ne abin yi yanzu. Ina tsoron a bi diddigi a gano halin da yake ciki fa" "A fita da shi waje kawai, wataƙila a dace a can, ni na kasa gane kan abubuwan da ake yi masa a nan" "A wannan yanayin, da ihun da yake yi" "Abduou" Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya. Abduou ya risunar da kai ya ce "Za a shirya duk abin da yakamata, za a yi abin da ka ce". Jamila ce take ta juyi a kan katifarta, tana jiran reply ɗin Abba, saboda chatting suke yi. Sai dai shiru bai yi reply ba har ta gaji ta yi bacci. Da safe sai gurin sha ɗaya ta tashi daga bacci, da yake tana fashin salla. Ta duba wayar, ta tarar da tarin messages ɗin sa da kiran waya, ta share ta je ta yi wanka ta shirya. Daga tsakar gida ta ce "Mama ni na wuce" "Ba za ki tsaya ki karya kumallo ba?" "Zan ci a can, sai na dawo" Suwaiba na tsakar gida, tana goge kaushi, ta ce "Jamila" "Yes" Jamila ta amsa. "Nana fa na gaishe ki, ba ki ga jaririnta ba" Jamila ta ce "Ai dama ke da Nanan, kan ku ba ƙalau ba, shi yasa ke kaɗai take kawowa ziyara a mafarki." Sai kuma ta ɗan yi shiru cikin damuwa ta ce "Allah sarki Nana, ko ta na wani halin yanzu oho" ta ɗan ja numfashi ta sauke ta fita, tana ci gaba da tunanin Nana. A falon Hajiya Sa'a ta tarar da Abba yana zaune yana Video game. Tana shigowa ya yi murmushi ya tashi zaune ya ce "Sannu da zuwa" Ta murguɗa masa baki ta nufi bedroom ɗin Hajiya Sa'a. "To ai ba ta nan" ya yi maganar yana miƙewa ya bi bayanta. "Me na yi miki ne ki ke hararata? Na tura miki saƙo duk ba reply" Ta kalle shi ta ce "Ba jiya na yi ta jiranka da daddare ba, ka ƙi kula ni" "Eyya, bacci ne ya kwashe ni, ki yi haƙuri" "Ba wani nan, da budurwarka ka ke chatting ka share ni" Ya waro ido ya ce "Wallahi ba ni da wata budurwa bayan ke, kema kin san ba na iya kula 'yan mata kema da ƙyar ai na gaya miki ina son ki" sai kuma ta tuntsure da dariya ya taya ta shi ma. Za ta yi magana kawai Hajiya Sa'a ta shigo falon, ta gan su a zaune a kan dining suna hira har da dariya, alhalin a gabanta basar da juna suke yi. Ɗan saroro Hajiya Sa'a ta yi tana kallon su, Jamila cike da bariki ta ce "Mummy sannu da zuwa" "Yauwwa" ta amsa a taƙaice. Abba ma kam kasa magana ya yi gaba ɗaya. Ya yi wa Jamila sallama ya fita, sai dai Hajiya Sa'a ta yi kicin-kicin ta ƙi sakar wa Jamila fuska gaba ɗaya. Jamila kuwa ta din ga ƙissimawa a ranta, muddin abin da take zargi ya zama gaskiya game da Hajiya Sa'a za ta ba ta mamaki ba kaɗan ba. ***** Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta kwana arba'in cif da haihuwa. Sai da Nene ta kwana goma sha biyar, ba ta fita gurin sana'arta, saboda jegon Nana sai dai yaranta su je, sai bayan kwana sati biyun sannan ta fara fita, shi ma da wuri take dawowa. Ranar da Nana ta kwana arba'in, ta saka Nana ta shirya suka je gidan su Hajara. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana, duk da ta rame, amma yanayin ta akwai nutsuwa a tattare da ita. Auwwalu ya ɗauki Muhsin ya ce "Ohh Allah ka bamu mu ma ɗan kyakykywan jariri, ka ga ɗa kamar na larabawa" Hajara ta amsa da "Amin dai" Nene ta ce "Ka ga fitsararru, babu ko kunyar idona?" Auwwalu ya ce "To ai addu'a muka yi. Ban da rashin kara ma, a ƙa'ida fa ɗan nan, sunana na ya kamata a saka masa" Nene ta ce "Saboda kai ɗin waye?" Nana ta yi murmushi ta ce "Yaya Auwwal, ai sunanka ne da shi, laƙanin ne kawai ba ɗaya ba" Ya yi murmushi ya ce "Kuma fa haka ne" sosai suka karrama su Nana. Da suka tashi tafiya ma, sai da suka kuma bawa Jaririn kyautar kuɗi da kaya, a so samu Nana ba ta so suka karɓa ba, amma Nene ta amshe. Da suka dawo kuma ta zagaya da Nana gidajen maƙwabta, suka gaggaisa. Tun da suka doshi wani gida, Nana ta din ga jin gabanta na faɗuwa, kamar ta cewa Nene ba za ta shiga ba, amma ta kasa. Ta din ga addu'a tare da fatan Allah ya rufa mata asiri ya sanya ba wani abin ne zai faru da ita ba, ko Ƙaisar ne zai dawo ya hana ta sukuni a ƙasar da ba ta da kowa ba. Ko da su ka shiga cikin gidan, sai Nana ta fara jin sanyi, yana ratsa ta a hankali. Aka shimfiɗa su tabarma, da ƙyar Nana suka gaisa da mutanen gidan, ta nemi guri ta zauna. Sai ta daina gane abin da Nene suke faɗa ma. Ta din ga jiyo muryar su Nene can nesa da ita, hakan ya tabattar mata da gidan akwai wani abu. Wani irin sauti ta din ga ji, a cikin kunnunwanta, kamar gurnani kamar nishi. Ta daina ganin su Nene gaba ɗaya, sai wata mata da ta fito ta tunkaro ta. Ga matar babba da ita amma jikinta ɗauke da zaren mahaifa daga cibiyarta dogon zaren har kan wani baƙin ƙwarangwal da yake bin ta, hannun ƙwarangwal ɗin kuma mahaifa ce yake lasa da jini da komai a jiki. Jikin Nana ya hau tsuma, ta din ga kallon matar da ƙwarangwal ɗin, tana son yin addu'a ta kasa. "Nana" ta ji muryar Nene ta kira sunanta. Sai ta buɗe ido ta kalli Nene. "Tashi mu tafi yamma ta yi" Nana ba ta motsa ba, ta ga matar da ta gani yanzu tare da ƙwarangwal ta nufo ta. Matar gidan ta ce "Kar ki kuskura ki taɓa ta, yi haƙuri dan Allah ba ta da cikakkiyar lafiya ne" ta yi maganar tana kallon Nana. Sai dai matar ba ta tsaya ba, ta yi kan Nana gadan-gadan. Wani irin azababben ƙarf ya zo wa da Nana, ta ji zuciyarta na tafasa jira take matar kawai ta ƙaraso gare ta, ta illata ta. Amma Nene ta danƙi hannun Nana, ta hana matar ƙarasawa gurin Nana ta ce "Ke Ashura, meye haka ne? Ba ki ga baƙuwa ba ce?" Matar cikin wata irin harɗaɗiyar magana da zubar da yawu ta ce "Magana zan yi mata, ta saka wannan ƙwarangwal ɗin ya daina bina" gaba ɗaya suka kalli Nana. Ɗaya matar ta ce "Wani ƙwarangwal ɗin, rabonta da magana ma fa ta fi sati biyu" Kawai matar ta saka kuka, lallai sai ta je gurin Nana, ta cewa ƙwarangwal ya daina bin ta. Nene ta ja hannun Nana suka yi waje. Sai dai ta ji jikin Nana tamkar gawa saboda sanyin da ya yi. Su na zuwa gidan Nana ta nemi guri ta zauna, ba ta cewa Nene uffan ba. Can bayan magariba, sai ga matar da su ka je gidanta ta zo, Nene ta ce "Gaji lafiya kuwa?" "Dan Allah Nene ki taimaka mini, ko 'yar nan taki za ta zo mu je gurin Ashura, sai ihu take tana burgima tun da ku ka tafi" "Ta zo ta yi mata me?" Gaji ta ce "A'a ban sani ba ko akwai wani taimako... "Taimakon me?" Nene ta katse ta. "Kin san dai Ashura ba hankali ne da ita ba, wataƙila almatsutsan haukanta ne kawai ya tashi take wannan abubuwan, ki tafi babu inda Nana za ta zo" Gaji ta fita jiki a sanyaye, dan idan ta matsa sai Nene ta balbale ta da masifa. Nene ta ajiyewa Nana nonon raƙumi, da abincin dare, amma ta ƙi ci saboda sanyin da take ji. Nana ta haɗa kanta gwiwa, tana jin yadda jikinta yake tsuma ta ce "Sayyid sanyi nake ji" "Ke Nana" Nana ta ɗago ido ta kalli Nene. "Ba za ki ci abincin ba ne?" "Na ƙoshi, amma dan Allah Nene mara lafiyar can ta can gidan, ta faɗi wani abu a kaina ne?" Nene ta ce "Za ki ba ta magani ne?" Sai Nana ta yi turus tana kallon Nene, gabanta yana tsananta faɗuwa. "Ba ta ce komai a kan ki ba, amma idan kin amince za ki yi magana da aljanin nata, ko ki bata magani kamar yadda ake so ki yi, sai mu je" Gaban Nana ya faɗi, ta bi Nene da kallo cike da mamakin, yaya aka yi Nene ta san wannan maganar, alhalin ko da wasa ba ta taɓa gaya mata ba. "Nana mamaki ki ke yi? Ai ba a banza na yarda na karɓe ki muke zaune a cikin gidan nan ba da ni da ke. Tun zuwanku na ga abubuwan da na gani a tattare da ke. Na ga inuwar rauhanin aljani a tattare da ke, kuma da alama ko dai kin gamu da baƙin aljani a hanya, ko kuma kin yi rayuwa da shi, saboda akwai warinsa a tattare da ke, saboda yana ta'amalli da jini, har ma warin nasa yana ƙoƙarin danne, ƙamshin rauhanin da yake tattare da ke. Sannan akwai alamu na alaƙa mai ƙarfi a tsakanin wannan rauhani da Aljanin da yake tattare da ke. Jiri ne ya fara ɗibar Nana, cikin wani yanayi mai kama da fitar hayyaci ta ce "Nene, wace ce ke? Ya aka yi ki ka san abin da ban gaya miki ba? Ki gaya mini ke wace ce?" "Nana, masu iya magana suka ce mugu shi ya san makwantar mugu. Ni na yi harkar bori da bayar da magani, ni baƙin aljani ma na gada daga gurin mahaifina. Ya azabtar da ni ya hana ni aure, na ƙi bayar da magani ya shanye mini ƙafafuwa, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na gaji na ce zan ajiye, saboda kullum cikin larura nake, ga shi ya sanya na saka a yi ta zubar masa da jini. Ya sake burkita ni, ya hana ni aure, na koma ciwon hauka yau na kuturce gobe na daina gani, anjima na kasa tafiya. Ya buɗe mini ido nake ganinsu muraran a siffofi na ban tsoro, nake jin maganganun su a cikin kunnuwana. Ya ɗauke ni ya kai ni can wata uwa duniya ya yasar da ni, na yi ta gararamba sannan ya gaji ya dawo da ni. Ko ya saka na yi ta zubar da jini babu ƙaƙƙautawa. Duk inda muka je neman magani, sai a ce sai dai na haƙura na ci gaba da bayar da magani. Da ƙyar wani mai magani ya raba ni da shi, ta hanyar yin amfani da wani aljanin. Ya kafa sharuɗɗa sai da aka yi masa yanka, da sauran abubuwa dai na sharuɗɗa sannan Allah ya raba ni da shi. Bayan mun rabun ma, da ƙyar na samu na yi aure, shi ma dai kusan kullum cikin rigima da miji, na zo babu haihuwa, sai rigima sai dai ya dage ya ƙi rabuwa da ni. Sai daga baya Allah ya bani haihuwar ɗa namiji, daga nan ban sake haihuwa ba. Yarona yana can ƙasarku Nigeria. Mijina kuma Allah ya yi masa rasuwa, ni kuma na ci gaba da sabgogina ban sake wani auren ba, duk da wasu lokutan haryanzu abubuwan na taɓa ni." Nana tana Libraryn Ƙaisar, daga can nesa take jiyo maganar Nene. Kai tsaye gurin mudubin nan ta nufa, cike da fatan ta sake ganin ko fuskar Sayyid ne, amma ta tarar da mudubin wayam, sai ma baƙi ƙirin da ya yi. Ta daɗe a tsaye ta zura wa mudubin idanun amma babu alamar wani abu zai bayyana a mudubin ta gani. Ta hango littafin da ta fara karantawa a yashe a ƙasa, inda ta yasar da shi, hakan ya tabattar mata da Ƙaisar ba ya cikin ɗakin karatun nasa na wani lokaci. Ta sanya hannu ta ɗauki littafin, ta nutsu ta ci gaba da karantawa. "Idan ka bari tsoro ya ɗarsu a cikin zuciyarka, to tabbas ba za ka iya cimma abin da ka ke hari ba. Tun da kawar da mahaifinka bai yi maka wahala ba, wannan ma ba zai gagare ka ba, ka kashe su ɗaya bayan ɗaya, ka yi mulki cike da izza ka tara sojoji da runduna da za ta razana duniya". Ire-iren waɗannan kalamai na ziga da kambamawa, ya sanya matashin saurayin jin kansa na daɗa kumbura, tare da ji a ransa zai aikata komai domin cimma burinsa. Ana tsaka da jimamin mutuwar shugaba a garin, ya ci gaba da tattara sojojin sa na ƙarƙashin ƙasa, da shirya hanyoyin da zai bi gurin kawar da dukkanin wanda ka iya kawo masa tangarɗa. Ganin babu abin da ake yi a farkon littafin, ban da tsagwaron zalunci, zubar da jini da rashin tausayi ko imani, tsananin ƙiyayya da kisan kai a tsakanin 'yan uwa, duk don kowa yana kwaɗayin ɗarewa gadon mulki. Ga bautarwa ta fitar hankali ga na ƙasa ba tare da afuwa ko sassauci ba, sai Nana ta ji gaba ɗaya littafin ya ishe ta, ba ya yi mata daɗin karantawa, har ma gara na tarihin Buda a kan wannan. A hankali ta buɗe idonta, da ya yi mata nauyi, ta ga gari ya yi haske, ta shafa gefenta ta ji babu Muhsin, kawai ta yi zaton ko Nene ce ta goya shi, dan idan Nene na nan, tsakaninta da Muhsin shayarwa ne kawai, ita take yi masa komai kamar ita ta haife shi. Tana ɗaga kai ta ga wannan mahaukaciyar, riƙe da Muhsin a hannunta, gefenta ga wannan ƙwarangwal ɗin baƙi ƙirin da shi kamar an gasa shi da wuta. Ihu Nana ta saka a cike da matuƙar razana, ba wai dan ta ga ƙwarangwal ɗin ba, sai ganin ɗan ta a hannun mahaukaciya ga aljani a bayanta yana ta lasar jinin jikin mahaifar da ke ɗauke da zaren cibi. Ayshercool 08081012143 66 Nece ce ta fito hankali a tashe, ta shiga ɗakin da Nana take ciki, ta tarar da Ashura a tsaye rungume da jaririn Nana. A matuƙar fusace ta ƙarasa ta karɓe Muhsin, ta ajiye shi a kan katifa, ta ce  "Uban me ya shigo da ke ki ka ɗauke shi?" Cikin tsoro ta girgiza kai ta ce "Babu komai" "Uban me ki ka yi masa?" "Wallahi ban yi masa komai ba" Nene ta shaƙe ta, ta ce "Ki gaya mini me ki ka yi masa?" Cikin kuka ta ce "Wallahi ba abin da na yi masa" "To me yasa ki ka shigo?" "Wallahi son shi kawai nake yi" "Ɗan ki ne da za ki ce son shi ki ke yi, wani abin za ki yi masa kenan" cikin kuka ta ce "A'a Nene" Nene ta ce "Wallahi na sake ganinki a gidan nan, sai na yi miki shegen duka, babu ke babu jaririn nan" Nana ta saka hannu ta ture Nene, ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ki daina dukanta, ai ta ce babu abin da ta yi masa" Nene ta ce "Ba dan kin farka ba fa? idan ta yi masa wani abin, ni ina banɗaki ke ki na bacci fa?" Nana ta ce "In sha Allah babu abin da za ta yi masa. Zo mu je na raka ki gida" Nene ta ce "Nana ki rabu da ita ta tafi gidan" Nana ta ce "Nene zan raka ta, ni duk inda na ga mai irin larurar nan, tausayi yake bani" Nene ta ce "Can ta matse muku ke da ita, ku je can ku ƙarata, ni dai na sake ganinta a gidan nan, ta taɓa yaron nan, sai na yi mata shegen duka da itace" Nana ta kama hannun Ashura da ke ta rarraba ido, suka fita daga gidan. ***** Hajiya Sa'a ta tattara hankalinta a kan Abba da yake zaune a gabanta a bedroom ɗin ta. "Magana nake yi maka, ka ɗago ka kalle ni, mene ne a tsakaninka da yarinyar nan Jamila?" Ya ce "Ba komai" "To ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, na sanya katanga a tsakaninka da ita, babu kai babu ita, kar ka kuskura na ji wata magana a tsakaninka da ita, kuma matar aure na samo maka ita, zan baka lambarta ka kira ta ku gaisa. Ka je ku gana, kuma nan kurkusa za a yi komai a gama. Ka fita daga harkar Jamila, ka fita daga harkar ta na gaya maka na kuma nanata maka, idan ba haka ba daga kai har ita ba za ku ji daɗin abin da zai biyo baya" Ya jinjina kai jiki a sanyaye ya ce "To in sha Allah zan kiyaye" "Tashi ka bani guri" ya yinƙura ya tashi jiki a sanyaye, ya fice daga ɗakin,  zuciyarsa na wani irin zafi. Bai taɓa zaton za ta nuna adawarta da maganar haka ba, ganin yadda take da Jamila. Ko da ya tafi ɗakinsa, kiran Jamila ya shigo wayarsa, jiki a sanyaye ya ɗaga wayar ya ce "Hello Jamila" "Jamila kuma, yau ba ƙanwartaka?" "Afuwan a yi mini afuwa" Cikin damuwa Jamila ta ce "Yaya lafiya kuwa?" "Lafiya ƙalau, ina fatan kin je gida lafiya, ba ki bari na dawo na mayar da ke ba" "Ina sauri ne, kuma ba na son wahalar da kai gaba ɗaya. Ko dai Mummy ta yi maka magana a kan ka daina kula ni ne?" Da sauri ya ce "A'a ai kin san ba za ta hana ba ko kaɗan" Jamila ta ce "To shikenan, amma dan Allah in anjima ka zo na ganka" Ya yi murmushi ya ce "Ni ki ke son gani?" "Eh mana, ko na haƙura?" "Ina ni na isa, ina yin sallar isha'i za ki ganni a bar ƙaunar Abba" "To abin ƙaunar ƙanwarsa, sai ka zo" ya sauke wayar yana murmushi, sai dai yana sauke wayar ya ɗan yi shiru cikin damuwa, bayan tuna abin da Mummyn ta gaya masa na kashedi. **** Muhsin ɗin Nana tamkar ana hura shi, saboda girma ya cika ya yi fam. Ga shi fafur Nana ta ƙi bari a yi masa aski, ta cewa Nene babansa ma ba ya aski, dan haka a bar masa sumarsa. Nene ta fara jinginar da shi, a tsakanin fululluka tana koya masa zama. Nene ta ce "Nana bari na hanzarta na fita, ki kula da yaron nan dan Allah, ban da shiririta, ko ki ƙyale shi yana kuka ki yi masa banza" Nana ta ce "To Nene ki goya abinki ki tafi da shi mana, tun da kullum ba na yi muku abin arziki" "Kya dai ji da shi, ni dai na gaya miki, kuma wallahi mahaukaciyar can ta shigo, ki ka ɗauki yaron nan ki ka bata, sai na ɓata muku rai daga ke har ita" Nana ta ce "Ni dai ba wannan ba, Nene so nake na fara bin ki gurin sana'ar nan, zaman gidan nan yana damuna, ba akin fari babu na baƙi" Nene ta ce "Nima na yi wannan tunanin Nana, amma bai kamata a ce kina matar aure mu din ga fita bakin titi babu iznin mijinki ba, kin san halin maza wasu ba kirki ne da su ba, mussaman ke ga ƙuruciya ma. Sam ba mutuncinki ba ne ba, dama jira nake yi Muhsin ya ƙara ƙwari, na nema miki ko gurin ɗinki ne ko makamancin haka, ki din ga zuwa sannan mu ga ta ina za mu fara laluben mijinki, amma tun da Muhsin ya yi ƙwari, mu fara lalubawa zaman haka ba zai yiwu ba, motsi ya fi laɓewa ai" Ta jinjina kai ta ce "To shikenan Nene, duk yadda ki ce Shikenan, na gode sosai da sosai Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi" Nene ta ce "Amin yarinyar kirki" Fitar Nene babu jimawa sosai, sai ga Ashura ta faɗo gidan. Nana ta ba ta ce mata ta shigo ɗakin, amma ta ƙi. Nana ta tashi ta fita ta shimfiɗa mata tabarma, sannan ta ɗaukko Muhsin, ta zo ta zauna ta ba wa Ashura shi. Ta karɓe shi tana buɗe baki cikin murna, ta kalli Nana ta ce "Ina son yaron nan" Nana ta ce "Da gaske?" Ta jinjina wa Nana kai, ya jima a hannun Ashura, sannan ta ba wa Nana shi, Nana ta mayar da shi ɗaki ta kwantar. Sai dai tana dawowa ta tarar da Ashura a tsaye tana kuka, gefenta ga ƙwarangwal ɗin nan. Nana ta ce "Me ka ke buƙata ne?" "Ki na ganina kenan?" "Eh ina ganin ka, sannan wannan mahaifar da ka ke lasa mene ne ma'anar hakan? Tun da ƙazanta ce" Ya ce "Lokacin da aka haife ta ne, da za su dawo daga Asibiti, aka manta mahaifar, shi kuma mai motar ya yar a bola, ni kuma na tsinta na biyo ta." Cikin damuwa Nana ta ce "Amma baka kyauta ba, tun da babu wanda ya yi maka wani laifi ka ke yi mata abin da ka ke yi mata". Ya ce "Ai mu ba sai an yi mana abu ba, idan mu na son mutum. Kin ga ke ma da ki ke addu'a wasu lokutan, ba dan tasirin Addu'a da ki ke yi, da kuma tsoron uban duƙusa da ake yi ba, da bataliyar da za su shiga jikinki da yawa. Saboda da guda ɗaya ya yi hanya, wasu ma suke samun kafar shiga jikin mutum. Kuma Allah ya taimake ki, Sarkin baka ya rage tasirin uban duƙusa a tare da ke, da duk inda muke sai kin din ga ganinmu, kuma muraran za ki din ga ganin cututtuka da sihiri a zahiri, sai kin kusa haukacewa idan ba ki bayar da magani ba. Kawai dai shi yana lallaɓa ki ne" Nana ta ce "Yaya aka yi ka san Ƙaisar, kuma ka san Sarkin baka?" Ya ce "Jaddul Jinn babu wanda bai san shi a nahiyar nan ba, dan haka sanin jikansa uban duƙusa ba abin mamaki ba ne. Sarkin baka kuma shi ne ya mayar da ni ƙwarangwal, mun taɓa artabu da shi da na shiga jikin sata mesa, ya ƙona ni. Kuma na ga kin haɗa jini da shi, ba yadda na iya da ke ne kawai, da sai na ɗauki fansar abin da aka yi mini a kan ki" Nana ta yi shiru jikinta ya yi sanyi, su na gama maganar Ashura ta juya ta fita ya bi ta a baya. Nana ta din ga jinjina azabar naci da riƙo irin na halittun nan. **** BAYAN WANI LOKACI. Girman ɗan mutum babu wuya, in ji masu iya magana, Muhsin ya cika watanni bakwai, Nana na zaune tare da Nene. Nene ta kai ta gurin koyon girke-girke, yanzu kuma tana zuwa koyon ɗinki. Nana har mamakin yadda Nene take yi mata take. Sai dai ta fara karaya da yanke tsammannin haɗuwa da Sayyid. Nene ce ta shigo gidan, bayanta goye da Muhsin, yana ta mamular cukui. Nene ta sauke shi ta zaunar da shi ta ce "Wannan ɗan naki, idan bai nuna mini halinsa ba, ai ba za a ce ɗan buzaye ne ba, mun taho hanya ya ga raƙuma, wai sai dai mu tsaya ya kalli raƙumi, sai zillo yake a bayana yana ihu, sai da na tsaya na ɓata lokaci yana kallon raƙuma yana miƙa musu hannu. Ya cire hular kansa ya yar, kowa ya ga kansa da wannan kitson sai an tambayi mace ce ko namiji. Ke ma da taurin kan tsiya, kin ƙi bari a yi masa aski, kuma kina yi masa kitso kamar wani mace." Nana ta yi murmushi ta ce "Ni babu ruwana, ba shiga faɗanku zan yi ba, balle na ji kunya ku gwale ni" Shi kuwa cukun hannunsa kawai yake mamulawa a bakinsa, Nene ta juya za ta fita tsakar gida ya rarrafa ya bi ta yana kukan ta ɗauke shi. Nana ta sake yin murmushi ta ce "Na haifa wa Nene ɗa" Tana jiyo rigimarsa da Nene, ya hana ta aiki, idan ta hana shi wannan ya koma wancan. Nana ta din ga dariya daga ɗaki, aka jima kuma Nene ta zuba masa shayi sai kuma ya nutsu, guri ɗaya, yana sha yana wasa da gashinsa. Ashura tana son zuwa gidan Nene gurin Nana, amma tana tsoron Nene, ga Muhsin da ya ganta yake sanya ihu, tsoronta yake ji. Ɓangare guda kuma, zuciyar Nana na saƙa mata ya kamata ta gusa ta bar gidan Nene, saboda ta ja lokaci a gidan. Amma tana tuna tijarar Nene, da rashin sanin ina za ta dosa. Ba ta san wani irin mutum ne Sayyid ba, mutumin da za a yi alfahari da haɗa nasaba da shi ne ko akasin haka, duk da tana kyautata masa zato. Shi yasa take ɓoye wasu abubuwan, dan kare mutuncin sa da rashin sanin a yaya za ta haɗu da shi. Washegari da safe Nana ta tashi, ta jiyo hirar Muhsin a tsakar gida. Ta tashi ta fita kar ya yi wata ɓarnar, sai ta gan shi a lungun kitchen ɗin Nene, ya juyo bayansa, kamar dai wani abun ya samu yana wasa da shi. "Kai babyn Sayyid, me ka yi a gurin nan, taho ka sha" bai waiwayo ba ya ci gaba da abin da yake yi. Nana ta nufe inda yake. Wata irin narkekiyar mesa ta gani a cikin lungun, shi kuma yana ta duƙunƙuna kanta da hannu bibbiyu yana hira. Ji ta yi tamkar an ɗaure ta tamau, ta kasa gaba ta kasa baya, kuma ta kasa magana. Mesar ta miƙe sai ga Ƙaisar ya bayyana a gurin. Muhsin ya ɗaga kai yana dariya yana kallon Ƙaisar. Ƙaisar ya ciro wani abu a kwalba, ya buɗe bakin Muhsin ya zuba masa, Nana ta rikice amma ta kasa motsa kowace gaɓa ta jikinta. Muhsin ya kama rigar Ƙaisar yana wasa da ita, yana yi yana kallon Ƙaisar ɗin. Ƙaisar ya saka hannu ya shafa kitson kan sa, ya miƙe tsaye ya ɓace. Sai da ya ɓace Nana ta iya motsawa, amma duk da haka ta kasa zuwa inda Muhsin yake, sai shi ne ya rarrafo ya nufo inda take. Ta saka hannu da ƙyar tana dudduba jikinsa, ko wani abin ya yi masa amma jikinsa lafiya ƙalau. Ta shiga fargaba da tsoron me ya ba shi ya sha?. Ta ja jikinta ta koma jikin bango, ta fara shayar da shi, tana roƙon Ubangiji Allah ya kare mata yaronta daga sharrin su Ƙaisar da kowane irin nau'i na shaiɗani. Nene na fitowa, ya cika Nana ya tafi gurinta, sai da ya gama wasansa, ya sake komawa gurin Nana. Tana shayar da shi, tana ganin fuskar Sayyid a tattare da shi, dan hatta idan ya ɓata rai, tamkar mahaifinsa. Sai dai tunani da tsoron abin da ka iya samun sa, ya gaza barin zuciyarta, tun daga ganin da ta yi wa Ƙaisar da shi. Ta so gaya wa Nene, amma ta ja bakinta ta yi shiru ba ta gaya mata ba. Sai dai tun gabatowar magariba, take jin sanyi. Ta shige ɗakin ta ƙudundune, ta bar su Nene. Tana tsaye a sahara, sai dai a wannan karon babu ƙurar Saharar, ta hangi Sayyid a zaune yana shan shayi, shikaɗai. Ta taka sannu a hankali ta ƙarasa inda yake, ya ɗago ya kalle ta yana murmushi. Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ka warke ne?" "Da sauƙi, na yi nesa da inda nake jin ciwon, kuma na yi nisa da gurin waɗanda za su kashe ni" Cikin damuwa ta ce "Ni fa?" Ya ajiye kofin hannunsa, ya rungumota jikinsa yana kallon fuskarta, idanunsa cike da hawaye ya ce "Yadda ruhinki da gangar jikinki, suka gaza samun nutsuwa, tun bayan rabuwarmu haka nima nawa suka gaza samun nutsuwa. Ina kewarku gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, ina buƙatar ki a kusa da ni" Ita Nana gaza riƙe nata hawayen ta yi, tuni ta ba su dama suke zuba. Ya girgiza mata kai tare da cewa "Kar ki manta, muddin kina raye kuma ina raye a doron duniya, gangar jikinmu ba za ta samu nutsuwa ba, sai mun haɗu. Ina kewar ki ma vie." Ya yi maganar yana ƙanƙame ta a jikinsa. Ta buɗe idonta tana ji yadda hawaye ya jiƙa mata fuska. Ta tashi zaune da ƙyar, ta yi shiru ta tafi tunani. "Nana ba a bori da sanyin jiki, ci gaba da zaman ki a gidan nan, tamkar ki na matsawa dattijuwar nan ne da take ɗawainiya da ke, kuma ba za ki taɓa haɗuwa da Sayyid ki na zaune guri ɗaya ba, yakamata ki motsa". Ta tashi ta yi alwala, ta yi sallar magariba da isha'i, ta idar ta shiga ɗakin Nene ta ɗaukko Muhsin, ta dawo da shi ɗakinta saboda ko zai farka cikin dare. Nana ji ta yi tamkar ta fice daga gidan a cikin daren nan, amma ta kasa saboda ba ta san ina za ta nufa ba, a wannan uban daren. Ta haƙura da niyyar da Asubar fari, ta tashi ta fice, amma bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita, sai da aka kusa idar da salla, Nene ta tashe ta yi sallar Asuba. Tana idar da sallar kuma, Muhsin ya tashi ya saka rigima, Nene ta ɗauke shi suka tafi ɗakinta. Tun da wuri yaran Nene suka zo, suka ɗauki kayan Abinci, amma Nene ta ƙi fita ranar ta wuni a gida, yaranta ne suka je suka sayar da Abincin. Abu kamar wasa a jere kwanaki huɗu Nana tana yinƙurin guduwa, amma Nene ta kasa ta tsare tamkar ta san abin da Nana take shiryawa. ***** Jamila ta nuna wa Hajiya Sa'a tamkar ba ta san ita ta taka wa ɗan ta Abba burki a kanta ba, Hajiya Sa'a sai shirin bikin Abba take yi, yayin da gefe guda kuma Jamila ta yi blocking ɗin sa, ta daina ɗaga wayarsa gaba ɗaya. Dama idan Hajiya Sa'a na nan, ba ya iya yi mata magana, da zarar ta fita kuma sai Jamila ta kulle ƙofar sashen. Ya rasa abin da yake yi masa daɗi, har layi ya canza ya kira Jamila, amma tana ɗagawa ta ji muryarsa ta kashe. Ga shi tun da Hajiya Sa'a ta fuskanci abin da yake tsakanin su, ta daina yawan fita ta bar Jamila a gidan, idan ma fita za ta yi sai dai su fita tare. Sai dai yau Jamila ba ta jin daɗi, dan haka Hajiya Sa'a ta fita ita kaɗai, saboda ta sakankance Abba yana can kasuwa. Awa guda da tafiyarta, Jamila na kan doguwar kujera tana bacci, ta ji tsayuwar mutum a kan ta. Ta buɗe idonta a hankali ta ga Abba a tsugune a gabanta yana kallonta. Tashi ta yi zaune tana tsuke fuska tare da gyara zaman rigarta za ta tashi. Cikin zafin nama da tsoron rashin sabo, ya riƙe hannunta ya ce "Dan Allah Jamila ki tsaya ki saurare ni" ya yi maganar cikin marairaicewa kamar zai yi kuka. "In saurare ka ka ce mini me Yaya Abba? Dan Allah ka rabu da ni." Ta yi maganar itama idanunta fal hawaye, saboda ba ta taɓa sanin ta kamu da matsananciyar soyayyar Abba ba, sai yanzu da Hajiya Sa'a take ƙoƙarin farraƙa su. "Jamila dan Allah ki fahimce ni, kin san a son raina ba zan auri wata ke ga ki na bar ki ba, wallahi Jamila ina son ki, ban taɓa son wata 'ya ba sai ke" Ta kalle shi hawaye na zuba daga idonta ta ce "Ko ma mene ne, ai yanzu aure za ka yi, ka rabu da ni dan Allah" Girgiza kai ya yi cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ganin yadda take zubar da hawaye, zai yi magana ta fizge hannunta ta shiga ɗaya falon, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake bin ta yana ƙoƙarin rarrashinta. Sai dai kash, garin ya rarrashi Jamila, sai shaiɗan ya buga musu ganga su ka taka rawa, duk da Jamila ta fuskanci cin zarafi da keta haddi a ƙungiyarsu ta asiri, a wannan karon ma tsoro da rashin sabo suka yi tasiri a a gare ta, duk da a nasa ɓangaren ma haka ne. Daga shi har ita suka saka kuka mai cike da nadama da dana sanin abin da suka aikata. Maganganun Nana suka din ga dawo mata daki-daki, na nasihar da ta din ga yi mata a baya. Duk da babu wanda ya san halin da Nana ne ciki, a tsawon wannan lokacin kusan shekara guda, amma gara Nana da ita, Ko ba komai Nana aure ta yi, ita kuwa fa da fari bokaye da aljanu sun kwanta da ita, a wannan karon kuma ruɗin soyayya da sharrin shaiɗan. "Jamila, dan Allah ki yi haƙuri, ki kuma rufa mini asiri, ke ma kin sa hakan ba halina ba ne ba, amma duk yadda zan yi, zan aure ki, ni na fara aikata ɓarnar nan, kuma zan gyara ta in sha Allah" Jamila ta kalle shi ta kawar da kai, tana jinjina lallai Abba bai san komai ba, tun da bai iya gane ba budurwa ba ce ba, duk da bayan abin da Hajiya Sa'a ta kai ta aka yi mata, bazama ta yi neman magungunan gyara. Ya lallaɓata ta gyara jikinta, ta nemi guri ta kwanta, ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Ya koma part ɗin sa ya rufe ƙofa, kawai ya fashe da kuka. Bai taɓa tunanin aikata zina a rayuwarsa ba, ba ta taɓa burge shi ba, bai kuma taɓa kawo ta a ransa ba. Sai dai yau ya wayi gari da aikata ta dumu-dumu. Sai dai wani abin mamaki duk da abin da ya faru a tsakanin su, bai daina jin matsananciyar ƙaunar Jamila ba. Ya rasa dalilin da ya sanya Mummy ba ta son alaƙar su, duk da irin kusancin da yake tsakaninta da Jamilar. A kwance Hajiya Sa'a ta dawo ta tarar da Jamila. Ta ce "Daughter haryanzu jikin ne? Ko Asibiti za mu je ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a Mummy na sha magani ai" "Yakamata ki warke, mun kusa zuwa taron ƙungiya fa na shekara, lokaci ya kusa" Kawai Jamila ta gyaɗa kai. "Ga shi kuma haryanzu babu wani labari da ki ka samo, a kan 'yar uwakki, dan haka sai ki shirya sadaukar da jini" Jamila dai ta yi shiru, tana jin kamar ta kashe tsinnaniyar matar ta huta. ***** Nana na zaune tana shayar da Muhsin, Nene tana gefe tana lissafa kuɗin da aka kawo mata daga gurin sayar da Abincinta. Nana ta numfasa ta ce "Nene wai me yasa kwana biyu ba kya fita gurin Abinci ne?" Nene ta kalle ta ta ce "Na fita ki samu damar guduwa ko?" Nana ta yi turus tana kallon Nene. Nene ta yi murmushi ta ce "Yarinyar nan ki na wasa da ni, tuni na gane duk wani take-taken ki ai, jira nake yi na ga iya gudun ruwanki. Ke yanzu idan ki ka fita gidan uban wa za ki je? Ki na da tabbacin za ki iya sake haɗuwa da mutanen da za su kula da ke ne? Ko an gaya miki kowa ne zai iya yin taimako? Kin tattara kayanki gaba ɗaya, kina ɗauke ɗanki daga ɗakina, jira ki ke yi ki samu dama ki gudu, to ki tafi duk inda za ki tafi, amma ba za ki tafi da jaririn nan kina gararanba a gari ba, tun da duk ƙoƙarin da nake yi a kan ki ba kya gani. Kina zaune a nan na saka ana ta yi mini cigiyar masu gadi da suke zuwa Nigeria, ko akwai wanda ya san mai suna Habu ko Sayyid ki ka ce sunansa ko wa? Anma ba kya gani, to ki fita ki tafi duk inda ki ka ga dama, tun da ba ki da kan gado, kuma ba ki san darajar igiyoyi ukun da ke kan ki ba" Nana ta sha jinin jikinta, da faɗan da Nene take yi mata. Ta ce "Dan Allah Nene ki yi haƙuri, na ga na ɗora miki ɗawainiya ne ga shi haryanzu ina zaune babu wani labari a kan sa". "Ni na ce kin ɗaura mini ɗawainiya ne uwar iya? Ki yi duk abin da ki ka ga dama" Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba" Nene ta yi mata shiru, daidai lokacin kuma Muhsin ya gantsarawa Nana cizo, da 'yan haƙoran da suka fara leƙowa. A fusace ta dake shi a kan pampers ɗin jikinsa, ta cire shi daga jikin Nonon, ta zaunar da shi tana ƙara tsuke fuska tare da hararsa. Sexy eyes ɗin sa irin na mahaifinsa ya zuba mata, yana kallonta ko ƙiftawa ba ya yi, gaba ɗaya ya rikiɗe fuskarsa ta koma ta Sayyid sak, farar fatarsa ta yi jawur. Nene ta ce "Yaka yaron kirki, ka ƙyale ta da halin ta, shi ne za ki huce a kansa, ai ni na yi miki ba shi ba" Ya rarrafa ya koma jikin Nene ya kwanta yana ci gaba da kallon Nana. Sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi da abin da ta aikata, ba tare da duba ƙanƙantar ɗan yaron nata ba. Ta shige ɗakinta ta mayar da kayanta da ta haɗe guri ɗaya inda suke. Wayarta ta ɗaukko da babu layi a cikinta, ta duba jakarta ta ɗaukko memorynta ta mayar kan wayar, ta fara duba hotunan Sayyid da ke ciki. Har da hotunan  Haidar ɗan gurin Shukura a cikin wayar, da hotunanta na aure da aka yi mata da wayar. Gaba ɗaya ta ji tana kewar ƙasa Nigeria, amma hakan bai sanya ta ji za ta iya komawa a yanzu ba. Tunaninta ya katse bayan da ta ji muryar wata ƙawar Nene a tsakar gida, wadda ita ta yi hanyar kai Nana gurin koyon girke-girke. Amma Nana ta ƙi fitowa. Hira suke yi da Nene, take ba ta labarin ma'aikata ake nema, wanda suka iya girki sosai a wani restaurant, na wata Hajiya a can cikin birnin Maraɗi. Nene ta ce "Ba na yi wa Nana irin wannan harkar ne, saboda mutanen banza, ba dan haka ba ai da na ce ta je, tun da ta iya girki sosai" Matar ta ce "To ai a ɓangaren girki kawai za ta zauna, su na buƙatar kuku amma mai tsafta wadda ta iya girki, kuma tana biya sosai kin san buzayen nan kamar ba su san ciwon kuɗi ba, buzuwa ce mai gurin" Nene ta ce "Ai kin ga tana da yaro, shayarwa take yi, ai da na ce a kaita, amma idan za su ɗauke ta da yaron shikenan". "Anya kuwa, gaskiya ba na tunanin haka, ba ma za su yadda ba. Idan ta tafi a ƙalla za ta iya yin wata, ba ta zo gida ba, za a ba ta komai a can. bari na tashi na tafi dama tsayawa na yi mu gaisa sai anjima" Suka yi sallama matar ta tafi. Nana ta fito da sauri ta ce "Nene, ina son zuwa gurin abincin buzayen nan" Nene ta ce "Kin yarda mijin naki buzu ne kenan? Daga an ce gurin buzuwa kin rikice za ki je, bayan da kin ce mini ba ki san ƙabilarsa ba, Allah dai ya shirye ki." Nana ta yi shiru, tana mamakin yadda aka yi Nene take iya gano ta idan ta yi mata ƙarya. Nana tun dukan da ta yi wa Muhsin, juyin duniya har la'asar bai ƙara waiwayarta da sunan ta shayar da shi ba. Sai da ta ji sun cika, sun fara damunta, sannan ta ɗauke shi ta ba shi, amma fafur ya ƙi karɓa, ta kaɗa ta raya ya ƙi sha. Nene tana kallon su, ta ƙi magana, ta dama masa kunu ta haɗa da nono ta zaunar da shi ta ba shi ya sha, ya ci gaba da wasan sa. Nana ta ga sun mayar da ita saniyar ware ma. Har garin Allah ya waye, bai saurari Nana ba. Ta sake ɗaukarsa, saboda yadda nonon ya cika, yake yi mata ciwo, amma fafur yaron nan ya ƙi sha. "Dan Allah yaron kirki ka yi haƙuri ka sha, ba zan sake dukan ka ba, dan Allah ka sha ba ka isa yaye ba" Nana ta yi maganar cikin damuwa. Nene ta kwashe da dariya, ta ce "Kin ga ki ƙyale yaron nan, ina ga fa ya yi zuciya ya yaye kansa, sai dai yi haƙuri" Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas sai ya yaye kansa? Ya yi wuri ai" "To ba ke ki ka janyo koma mene ne ba?, tun da kin ce da babansa yake kama komai da komai, wataƙila har halayensa ya ɗaukko, kuma wataƙila wannan abin da ya yi akwai abin da yake nunawa bamu gane ba. Tun da yana shan kununsa, yana rarrafensa, ki rabu da shi kawai. A haɗa sabaya da sauran saiwoyi, ki yi ta sha saboda kar su lalace". Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas fa" "To ai ga ki nan ga shi. Sai ki ba shi ya sha ai" Da Nana ta ɗauke shi da nufin, ta shayar da shi, sai ya hau zunduma ihu,yana turjewa sai dai ta ƙyale shi. Nana ta din ga jinjina yadda aka yi, ɗan wata takwas ya san ya yi zuciya da abu. Sai da aka kwana huɗu, Nana ta ga da gaske ya yaye kansa, iyaka ya zo jikinta ya yi wasan sa ya tafi. Nene ta ce "Nana ki daina damuwa fa, girmansa tubarkallah da ƙiriniyarsa kamar ta ɗan shekara guda ce, ki rabu da shi kawai, daga yanzu idan za ki yi magana ki din ga yi masa da girmamawa, ki daina yi masa tsawa, manya ba sa son wargi. Kuma ki din ga duba darajar sunan da ki ka sanya masa" ta yi maganar tana yi wa Muhsin rawa. "To Nene sai na bari ya lalace ba zan ce masa bari ba?" "A'a ban ce kar ki ce masa bari ba, amma a wannan yanayin shi sarki ne, abin da yake so haka za ki yi haƙuri ki yi masa. Da kin tsaya a zare masa ido kawai da haɗe rai, amma saboda na yi miki faɗa, ki ka haɗa masa da duka, kuma ki ka ƙwace ki ka dungurar da shi, dole ya bar miki abin ki ai". Nana kalle shi yana ta wasa da kofi, yana bugawa a ƙasa, shi ma ya ɗago ya kalle ta. Sayyid ta tuna lokacin da ya ritsa ta yana yi mata kashedin a kan daina yi masa tsawa ko ɗaga masa murya. Wani guntun murmushi ya suɓuce mata. Nene ta ce "Ni kuwa Nana ga shawara" Ta ce "To Nene" "Kamar yadda ki ke faɗa motsi ya fi laɓewa, na ce ko dai za a jarraba ki je gurin aikin nan, na harkar dafe-dafen ko Allah zai sanya a dace. Duk da ba na jin a jikina, masu kuɗi a cikin buzaye masu katafaren gurin abinci, za su iya tafiya aikin gadi, amma bamu san ina rana za ta faɗi ba" Nana ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Ban san ya zan yi ba ne, tun da kin ga ga Muhsin. Ko za su din ga bari na je na dawo kullum?". Nene ta ce "Ki na ji fa ta ce sai ki yi wata ba ki zo gida ba, kuma akwai tazara a tsakaninmu sosai, kuma ba zai yiwu ki tafi da Muhsin ba, ba za su yarda ba. Amma ga shawara idan kin ga kin yarda da ni, ki bar mini Muhsin a nan, ki je ko ai kin na wata uku ki yi, ko Allah zai sanya a dace, sai ki ci gaba da cigiyarsa a gurin." Ayshercool 08081012143 67 Nana ta yi turus, tana kallon Nene. Nene ta ce "Ba zan yi miki dole ba, dan kuwa wannan magana ce da kowacce uwa sai ta jinjina girmanta da nauyinta. Sai dai ni ba zan takura miki ba kuma ban ce sai kin yadda da ni ba, ko mene ne za mu yi shi ne a gaban hukuma, mu je mu yi yarjejeniya mu saka hannu sannan ki tafi. Ban san dalilin da Allah ya sanya ya haɗa ni da ke ba, duk rashin son mutane na, ki ka shiga raina ba nake tausayinki ke da yaronki. Har ga Allah ina fatan ki haɗu da mijinki ko danginsa, ki samu ki koma gida ki nutsu ki kula da yaronki. Kamar yadda na gaya miki ne, ba zan yi miki dole ba, ki je ki yi shawara idan kin amince shikenan, idan ba ki amince ba babu wani abu, ni dai fatana Ubangiji Allah ya bayyana abin da ki ka fito nema". Nana ta yi shiru, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta ɗauki caji da tunani daban-daban. **** Jamila kuwa tun da ta je gida, Mama take tambayarta ko lafiya ta ganta wani iri, amma ta ce mata babu komai. Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta kwanta, sallolinta kawai ta yi na magariba da isha'i ta sake kwanciya. Gaba ɗaya abin Duniya ya gama damunta, dana sani da takaici duk ya cunkushe mata zuciya. Wayarta ce ta fara ringing, ta duba ta ga baƙuwar lamba ce, jikinta ya ba ta Abba ne, ta ɗaga kiran ta saka a kunnenta. Muryarsa ƙasa-ƙasa ya kira sunanta ya ce "Ya jikin naki?" "Da sauƙi" ta amsa a hankali hawaye na ci gaba da gangarowa kan kumatunta. "Dan Allah Jamila ina ƙara ba ki haƙuri, kuma ki dubi girman Allah ki rufa mini Asiri, ke ma kin san hakan ba halina ba ne ba. Wallahi na rasa inda zan sanya zuciyata na rasa abin da yake yi mini daɗi. Yanzu haka zazzaɓi ne a jikina. Dan Allah ki yafe mini Jamila, na san koma mene ne duk laifina ne. Amma in sha Allah kamar yadda na yi miki alƙawari zan aure ki Jamila, wallahi ina son ki, duk abin nan laifin Mummy ne amma ki yi haƙuri ki yafe mini" Jamila ta ci gaba da kuka, ta kasa ce masa komai, ya ƙara ruɗewa ya ce "Dan Allah ki yi mini magana, dan Allah ki yafe mini idan ba ki yafe mini ba na san har na koma ga Allah, ba zan samu nutsuwa ba" Ya yi maganar yana kuka mai cike da nadama tamkar ƙaramin yaro. Duk yadda Jamila ta so jin haushinsa sai ta kasa, tabbas ita shaida ce wannan ba halin Abba ba ne, dan da halinsa ne da ba zai din ga wannan kukan ba, zai ga ya ci bulus ne kawai. "Yaya Abba na yafe maka, mu haɗu mu nemi yafiyar Allah, sannan ka daina kukan nan dan Allah, ka sha magani ka kwanta. Kuma Asiri idan na tona kaina na tonawa ba kai ba, Ubangiji Allah ya yafe mana" Ya tashi zaune a kan gadonsa, cikin damuwa ya ce "Da gaske kin yafe mini Jamila?" "Eh Yaya Abba, sai da safe, kaina yana ciwo sosai" "To na zo na kai ki Asibiti ne?" Jamila ta ce "A'a, na sha magani ina jin bacci ma, sai da safe" ta katse kiran tana ƙara duƙunƙunewa a cikin bargo. Wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, ya nemi guri shi ma ya kwanta, zuciyarsa fal tunani daban-daban. ***** Nana hankalinta ya rabu kashi-kashi, a jikinta ba ta jin Nene za ta cutar da ita, duba da yadda take ɗawainiya da ita da ɗanta, tamkar ita ta haife ta. Sai dai ta yaya za ta iya ta tafi ta bar ɗan ta, da matar da babu dangin iya babu na Baba a tsakanin su. Sai dai tabbas akwai buƙatar ta gusa, ta yi wani yinƙuri, domin ci gaba da ƙoƙarin haɗuwa da mijin nata, amma ba ta ji ta gamsu da wannan shawarar ba. Sai dai tun da suka yi maganar nan, da ta kwanta take mafarki ga ta a gurin girke-girken, tana cikin gurin girkin, ta waje sai ga din ga jiyo muryar Sayyid yana magana. Idan ta fita sai ta neme shi ta rasa, sai dai ta ci gaba da jin muryar ta sa, nesa da ita kaɗan, sai dai ba ta san daga wane ɓangaren muryar tasa take ba. Sai ta yi irin wannan mafarkin sai ta farka. Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, kawai sai ta ci gaba da addu'a a kan lamarin, ta juya ta ci gaba da bacci, sai dai babu tsammani sai ga ta a ɗakin karatun Ƙaisar, an yi mata gyara sosai, an ƙara yawan litattafan da suke ciki. Ya saka mudubinsa a gaba, yana ta zuba masa wani ruwa yana wanke shi. Bai ce wa Nana komai ba, har ta gaji da tsayuwa, ta ɗan yi gyaran murya. Ya ɗaga kai ya kalle ta. Ta ce "Sannu da aiki" "Yauwwa" ya amsa yana tashi tsaye. Ta ce "Kwana biyu ina ka shiga ne?" Ya ɗaga kai ya kalle ta ya mayar ya sunkuyar yana ɗaukar wani littafi. "Amm dama ina ta son na ganka, na tambaye ka, sannan na roƙe ka alfarma. Dan da kai da Giyaz da duk wani mai son ɗaukar fansa a kan zuriyarmu, ya ɗauka a kaina, dan Allah ku ƙyale mini yarona. Na ga rannan ka ba shi wani abu da ban san ko mene ne ba, dan Allah kar ku yi masa komai" Bai ko motsa ba, balle ta sanya ran zai yi mata magana. "Ƙaisar ka yi magana ma dan Allah" "Na ce miki ne? Ko har kin manta abin da ki ka faɗa a kaina, saboda abin da na yi wa mahaifina a kan na kare ki?" Sai kuma Nana ta yi shiru, ta sha jinin jikinta. Ya wurgo mata littafin nan da ta fara karantawa, ya ce "Ga wannan ki ci gaba da karantawa, wataƙila zai yi miki amfani a gaba" Ta kalli littafin ta kalle shi, ta ce "Me yasa ka amince na karanta wannan littafin, wancan kuma ka hana ni karantawa? Ni ba zan iya ci gaba da karantawa ba, babu komai a ciki sai tashin hankali da zubar da jini na tsagwaron rashin tausayi da adalci, ni bai burge ni ba, ba zan karanta ba" "Ko? Amma idan an yi magana sai ki nuna kamar babu wata halitta da ta kai ɗan Adam tsarki da tsoron Allah. Allah ya karrama ɗan Adam a kan dukkanin halittunsa. Amma ba duk ɗan Adam ne mai tsarkin zuciya ba. Wannan zubar da jinin da kashe-kashen da yake rubuce a cikin littafin nan, da gaske an yi su, domin cimma buƙatar Duniya, kuma haryanzu ana kan yi ma. Abu ne da ya faru wani ƙarni a baya, kuma abin yake ta bibiyar zuriyar har wannan zamanin. Na ce ki karanta kin ƙi, kin ce ba kya so shikenan ba zan yi miki dole ba, amma bari ki ga wani abu. Ya ɗauki littafin ya buɗe cikin wani feji, ɓangare ɗaya na bangon littafin zane ne, ɓangare ɗaya kuma bayanin yadda taswirar zanen take ne. Ya haska littafin a jikin mudubin. A nan take hoton ya bayyana a jikin mudubin, wannan ɗakin da take ganinta a ciki ita da Sayyid shi ne ya bayyana a jikin mudubin, ba iya haka ba har ƙamshin da gurin yake yi ta fara ji a hancinta. A rikice ta ce "Nan gurin? Dama ina son sanin ina ne, yaya aka yi muke zuwa gurin nan ni da Sayyid, kuma idan abu ya faru a gurin kamar gaske." Ƙaisar ya rufe littafin ya ce "Ai kuma kin yi wa kan ki, ba zan bayar ba. Ya jefa littafin sama ya ɓace ɓat ita kuma ta tashi daga baccin. **** Kwana biyu Jamila ba ta je gidan Hajiya Sa'a ba, saboda jikinta da ya matsa, idan Abba ya kira wayarta a kashe, ga shi ba ta zuwa gidansu, shi ba abin ya tambayi Mummy ba. Yana kwance a ɗakinsa, ya tura mata saƙo. "Hankalina a tashe yake ƙanwata, dan Allah ki yi mini ko flashing ne, hankalina na matuƙar tashe dan Allah ki ɗaga wayata" Ya tura mata saƙon, tare da ajiye wayar. Hajjya Sa'a ce ta shiga ɗakin nasa, ta iske shi a kan kujera. Yana ganinta ya tashi zaune. Daga tsaye ta ce "Abba ba zaka fita bane? Baka fito ka karya ba, kuma baka fita kasuwa ba meyafaru ne?" Ya girgiza mata kai ya ce "Babu komai fa" "A'a akwai wani abu, na kasa gane kan ka 'yan kwanakin nan, hatta shirin bikinka nikaɗai nake abina, me yake damunka? Duk saboda Jamila ne?" Ya girgiza kai ya ce "Ba kin ce ba kya son alaƙarmu ba, ni kawai ba ni da lafiya ne" ta yi shiru tana nazartarsa, kawai ta yi ƙwafa ta fice daga ɗakin. Ya koma ya jingina, ya lumshe idanunsa, sai kiran Jamila. Ya ɗauka ya katse kiran ya kira ta cikin azarɓaɓi ya ce "Ƙanwata lafiya kuwa? Ba kya ɗaga wayata ko haryanzu kina fushin ne?" Cikin numfarfashi ta ce "A'a Yaya Abba, ba ni da lafiya ne haryanzu" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya aka yi ba ki gaya mini ba? Kina gida ne?" "Eh" ta amsa muryarta ƙasa-ƙasa. "To shirya gani nan, bari na zo mu je Asibiti" "To Yaya Abba, na gode" ta ajiye wayar da ƙyar. Hankalinsa ya yi mummunan tashi, a zatonsa aika-aikar da ya yi ce, ta sanya mata rashin lafiya har haka. Da sauri ya zura kaya, ya ɗauki mukullin motarsa ya yi waje ya tafi gidansu Jamila. Yanayin yadda Jamila ta fito, tamkar ya je ya ɗaukko ta, fuskarta duk ta kumbura, da alama tana jin jiki sosai da sosai. Ya buɗe mata gaban motar ta shiga. Cikin tausayawa ya ce "Sannu ƙanwata, haka jikin naki ya yi ba ki gaya mini ba?" "Ba na son tayar maka da hankali ne, kai ma ba ka da lafiya, amma Mama fa ta kai ni Asibiti" Gabansa ya faɗi ya ce "Allah ya sa ba ta gane komai ba" Ta girgiza kai ta ce "Babu abin da ta gane, zazzaɓi ne fa kawai" A tsorace ya ce "Jamila ko ciki ne?" Ta kalle shi, sai da ta ji kamar ta yi dariya, duk da halin da take ciki. "Tun kan hakan ta faru ai nake rashin lafiya, ba wannan ba ne ba, ba wani ciki". Ya sake cewa "Amma duk da haka kamar ya assasa miki ciwon, amma bari mu je Asibitin" haka ya ja motarsa su ka bar layin. Safiyya ce ta tarar da Hajiya Sa'a ta cika ta yi fam, tana zaune a falonta. Da kyar Hajiya Sa'a ta iya amsa mata sallamarta. Ta zauna a kusa da Hajiya Sa'a ta ce "Mummynmu maganin kukanmu, lafiya kuwa na ga ranki a ɓace?" "Ba dole ki ganni a haka ba? Da gaske fa Abba son Jamila yake yi, nema yake ya bujire mini, kin ga yadda duk ya damu saboda na raba su. Ga bikinsa na ƙaratowa da Yasmin. Maman Khairat ta tuntsure da dariya ta ce "To meye a ciki, idan tana son sa ki bar su mana" Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Amma ba ki da hankali, yarinyar da shugaban ƙungiya suka kwanta da ita, sai Abba ya auri ragowa? Ba ma wannan ba, kar ki manta idan ƙungiya ta buƙaci ta bayar da jininsa fa, shikenan ta bayar da jinin tilon ɗan nawa?" Maman Khairat ta ce "Na fahimce ki Mummy, da wasa nake yi miki, amma maganar gaskiya yanzu haka kan na taho ma, na ga motar Abba a unguwarmu, kuma na san ba ku da kowa a unguwar, dan haka gurin Jamila ya je" Cikin matsanancin ɓacin rai ta ce "Gurin Jamila kuma? Yarinyar nan ta zame mini masifa da bala'i ko? Maganinta zan yi, wallahi sai ta rabu da Abba, ko ita ta haifar mini shi" Maman Khairat ta ce "Ki yi dai a hankali, kin san halin yaran zamanin nan" Hajiya Sa'a ta ci gaba da huci, tamkar macijiya saboda takaici. Maman Khairat ta ce "Ina dai ƙara gaya miki, ki bi komai a sannu, kin san halin yaran zamanin nan, sai su baki mamaki. Shi kansa Abban duk yadda yake yi miki biyayya, idan ba ki yi wasa ba, a wannan karon tsaf zai bujire miki". "Ai ga alamu nan ina gani, amma ni zan sanya wa Abba doka, na hana shi abu, amma ya zagaye ya je ya aikata? Shikenan, na san matakin da zan ɗauka. Da ni suke zancen. Alhaji Fatuhu ne zaune a harabar gidan sa, a kan kujera, ya kan ɗan iya dogara sanda ya tashi tsaye yanzu. Idan aka taimaka masa har harabar gidan yake iya fitowa, duk da idan jikin ya tashi kuma, sai ba ya iya hakan ko kaɗan. Yana zaune a harabar gidan, yana kallon ƙaramin ɗan sa na gurin Fadila, yana ta wasa da Ball, yana jin yadda ƙaunar ɗan ke ratsa masa zuciya. Gefe guda yana tausayin yaron nasa, dan bai taɓa iya saya masa abin naira biyar ba da kuɗinsa. Hatta abincin da suke ci, 'yan uwa da abokan arziki ne suke kawo musu, ga shi wanda ya sai gidansa ya ba du aronsa suke zaune a ciki, ya fara ƙishin-ƙishin ɗin yana buƙatar gidan. Fadila ce ta ƙaraso tana murmushi ta ce "Daddy kallon Ball ka ke yi?" Ya yi murmushi ya ce "Eh mana, yana ta in tashi mu yi tare, ina ma zan iya da ko sau ɗaya mun yi tare, no na saka shi farinciki" Ta zauna a ɗaya daga cikin fararen kujerun, ta ce "A hakan ma, ka na sanya shi farin ciki ai" "Fadila" Ta tattara masa nutsuwarta ta ce "Na'am Daddy" "Kin san wani abu?" Ta ce "A'a sai ka faɗa" "Ina yarinyar nan Nana?" "Wace Nanan?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Malamar Muhsin, da yake faɗa" Ta ce "Ohh Allah sarki, na tuna ta" "Mafarkinta nake yi" Ta ɗan yi saroro ta ce "Mafarki kuma?" "Eh Fadila, har aikawa na yi gidansu, a yi mini alfarmar a faɗa mini inda gidanta yake, wani abu nake gani da ya fara damuna" Ta danne kishinta ta ce "To ka yi mini bayani mana" "Kin dai san ni ba ma'abocin, biye-biye ba ne ba, da yarda da harkokin shirme da zai sanya na ji wani zai iya cutar da ni ba, amma a jere sau kusan biyar ina mafarki da ita". Cikin ƙosawa ta ce "Daddy ka yi mini bayani, ka na ta kwana-kwana da ni" "Ganinta nake yi a mafarki, tana ce mini an yi mini sihiri, karo kusan biyar fa" Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kuma ka yarda?" "Ba ma son na yarda na gazgata hakan, amma na ji kamar na fara amincewa, saboda yadda nake ganinta abin ya yi yawa, ya wuce a ce shirmen mafarki ne kawai." Fadila ta numfasa ta ce "Ai ni tuntuni na zargi hakan, amma sanin halinka na rashin son irin wannan abubuwan, ya sanya ba na yi maka maganar. Ko wannan sauƙin da ka ke samu, na san tasirin addu'a ne. Dan kuwa Umma kuɗi take bayarwa ana sauke karatun Alqur'ani." Cikin mamaki ya ce "Amma ke kina ganin, akwai wanda zai damu da ni, har ya iya yi mini sihiri? Ina azkar ɗina da addu'oina, gani nake sun wadace ni, babu wanda zai damu da ni ya yi mini wani sihiri." Ta gyara zamanta sosai ta ce "A duk Duniya waye ya koyar da mu azkar ɗin? Na san za ka ce manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, amma an yi wa fiyayyen halitta sihiri, kuma ya kama shi. Daddy ka yi haƙuri da abin da zan faɗa maka. Kana ibadarka ta farilla daidai gwargwado, amma ba ka damu da nafilfili ba, da tsananta addu'a. Kana ganin Allah ya baka duk abin da ka ke buƙata, ba ka fiye tsananta addu'a da neman kariyar Allah ba. Sannan azkar da ka ke yi, kuma a yi shiri ya kama ka, ba ya nufin Allah baya kare ka, amma wataƙila jarrabawa ce daga gare shi, kamar yadda ya ce zai jarrabe mu, ba a fasa jarraba mai imani, kuma jarrabawa alama ce ta soyayyar Ubangiji. Allah ya jarrabe ka da cuta, ka nemi magani shi ma a cikin jarrabawa ne, amma Daddy ka naɗe ka dage, kai sai na Asibiti kawai, bayan akwai magungunan musulunci da suke na halal babu kauce hanya, idan an jarraba ba a san inda za a dace ba, amma ka ƙi ka ce kai sai na bature, na baturen kuma ba a gano komai ba, kame-kame kawai ake yi." Ya yi shiru yana nazarin kalaman Fadila, ya numfasa ya ce "To yanzu mene ne abin yi? Kin ga yanzu bani da kuɗi, kuma irin wannan abubuwan sai da kuɗi". "Kar ka damu, zan yi wa Kawu magana, shi ma ranar da ya zo duba ka, ai ya ce a yi na islamic, Alhaji Zailani ya ce ba za a yi ba. Da haka za tuntuɓe shi, in sha Allah ba zai gagara ba" Alhaji Fatuhu ya ce "Allah ya sa, dama duk ina tsoron, kar a aikata abin da zai kauce wa hanya ne, amma na amince yanzu a yi ɗin" Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, yaya ita yarinyar an gano ta ɗin?" Ya girgiza kai ya ce "Ina fa, an ce wai ba ma ta ƙasar nan, amma ina ta mamakin dalilin da ya sanya nake mafarinta, kuma idan na farka sai na ji kamar a zahiri, shi ya sanya ma na fara yarda" Fadila ta ce "To Allah ya sanya a dace" ya amsa da "Amin" ***** Ɓangaren Nana kuwa, gaba ɗaya kanta ya kulle a kan lamarin nan, kawai sai ta dasa addu'a, a kan idan da alkhairi a tafiyarta, Ubangiji Allah ya sanya mata son tafiyar, ya tsare mata Muhsin, idan kuma babu, Allah ya cire mata abin daga zuciyarta. Kamar yadda ta saba ji haka ma wannan karon, ta ji muryarsa, da gudu ta ajiye abin da take yi, ta nufi taga ta leƙa sai ta hango giftwarsa da doguwar riga baƙa a jikinsa. Da gudu ta fita daga gurin, ta nufe shi tana ƙwala masa kira, amma ya ɓace mata. Cike da takaici ta yi juyi, tare da jan guntun tsaki, kawai ta ji hancinta ya fara shinshino mata, ƙamshin wannan ɗakin na cikin dutse, da take ganinsi tare da Sayyid. Ta buɗe idonta a hankali, ta ji ana shafar cikinta a hankali, tare da yi mata numfashi a wuyanta. "Sayyid" ta furta a ɗan tsorace. "Asmyna, ina kewarki da yawa, gangar jikina na ta kewarki. Idan ina jin zafi babu mai bani sanyin da ki ke bani, babu wanda yake iya fahimtar kurman baƙin rayuwata, ki ƙaraso gare ni Please" ya yi maganar yana shafa wuyanta, tare da yin maganar ƙasa-ƙasa. Ta saka hannu ta shafa gashinsa ta ce "Ina ta gaya wa Allah Sayyid, ya san lokacin da ya dace ya haɗa mu, amma jikina yana ba ni, ina daf da kai in sha Allah" "Ki ƙaraso da wuri Asmyna, ina cikin matsananciyar buƙatarki" "Ina ta ƙoƙari Sayyid, kuma ina gaya wa Allah, na san zai haɗa mu a nan kusa, kuma ina roƙonsa ya kare mini kai a duk inda ka ke, na san kuma yana ji ya kuma amsa in sha Allah" "Nana, wai ba kya salla ne, gari ya fara haske fa" ta ji muryar Nene. Ta tashi tana mustustuke idonta, hancinta na ci gaba da jiyo mata sauran ƙamshin turaren nan. Da ta yi salla ta idar, ta je ta samu Nene a ɗakinta, suka gaisa. Ta ce "Nene na amince" "Da me?" "Zan tafi gurin yin girkin nan" Nene ta ce "Ina fatan ba wani ne ya matsa miki ba? Ko kuma kunyata ki ka ji ba ki ka ce za ki je?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a, wa ma na sani na saba da shi, da zai ziga ni na ɗauka? Babu wanda ya ziga ni" Nene ta ce "To shikenan, zan kira ta a waya na ji, idan ba a samu wata ba, sai ki je. Sai mu je gurin jami'an tsaro mu yi yarjejeniya mu yi rubutu, mu je a yi a gaban su Auwwalu ma da Hajara" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a Nene, na yarda da ke, abin duk bai kai haka ba ai" Nene ta ce "A'a, haka kurum wani irin ki ka yarda da ni, ɗan mutum fa zan riƙe miki, a'a, mu je mu yi a rubuce, yadda jami'an tsaro ma za su din ga sanya ido, kar wani abu ya faru ma. Sai dai abin da Allah ya aiko na ƙaddara wannan ba yadda muka iya, kuma na san za ki yi mini uzuri a wannan. Amma idan aka yi haka kema sai kin fi sakewa, hankalinki ya kwanta. Nana ta jinjina kai ta ce "Ni dai, bakin da zan yi miki godiya ba ni da shi, amma ina fatan Allah ya yi miki tukuici da abu mafi dacewa da abin da ki ka yi mini na alkhairi, a duniya da kuma Lahira" "Amin Nana, ai ɗa na kowa ne, Allah ya tabattar mana da alkhairinsa, ya kuma bayyana miki mijinki da ahalinsa cikin aminci". "Amin uwata ta kaina" ta yi maganar tana murmushi. Sai dai tun da Nana ta amince za ta bar wa Nene Muhsin, ta fara jin kewar ɗan nata, ta din ga jin kamar ta ce ta fasa. Saboda kallonsa kawai na sanya mata matsanancin farinciki da nishaɗi, idan ta tuna mallakinta ne shi ɗin. Tana jin ko ba ta ga Sayyid ba tana da ƙaramin Sayyid, duk da tana fatan ta gan shi ɗin, ko ba komai al'umma sa kalli ɗan nata da kima da daraja. Ko da Nene ta kira matar, Matar ta tabbatar wa Nene, akwai sauran space ɗin da Nana, za ta yi musu aiki, sai dai a saka ranar da za su tafi ta kai ta. Haka nan fargabar Nana ta ƙaru, ta rasa murna take ko tsoro, duk da abu mafi rinjaye kewar ɗan jaririn ɗanta ne, da yanzu take ƙara shaƙuwa da shi,ƙaunarsa take ƙara shiga ranta. Tana jin tamkar ta fasa tafiyar nan, amma ƙasan zuciyarta tana jin tafiyar ta ta alkhairi ne. ***** Ɓangaren Abba kuwa, sai da aka yi wa Jamila ƙarin ruwa, typhoid ne ya yi mata mummunan kamu. Sai kuma damuwa da take ciki, jininta ya ɗan hau. Abba ya biya duk bills ɗin, ya janyo kujerar ɗakin, ya zauna a gaban gadonta, ruwan da aka saka yana shiga jikinta. "Ko a kira Mama a waya a sanar mata ne?" Ya yi maganar cikin kulawa. Ta ce "A'a, na gaya mata Asibiti zan je, ana gamawa sai ka mayar da ni gida" Ya ce "To shikenan, mai zan sayo miki ki samu ki ci?" "Ba na son cin komai, kawai kar ka matsa daga kusa da ni, ka zauna a nan" ta yi maganar tana riƙe hannunsa a cikin nata. Ji ya yi zuciyarsa ta narke, da matsanancin tausayin kan su, ya ce "Ina tare da ke matata, har abada in sha Allah" ta yi murmushi tana ƙara riƙe hannunsa. A hankali kuma ta saki hannun nasa, da tuna rashin dacewar hakan, sai dai wani irin abu mai wuyar fassara take ji, game da Abban. Yana kallon kiran Hajiya Sa'a, amma ya ƙi ɗagawa, kawai ya din ga jin zafinta. Har azahar sannan ruwan da ake saka mata ya ƙare, ya ɗauke ta a motarsa, ya yi mata sayayya sannan ya mayar da ita gida. Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya kira Mummy. "Sai yanzu ka ga damar ɗaga wayar tawa?" "A'a caji take yi ne, ki yi haƙuri?" "Kana ina ne?" Ya ce "Na ɗan je wani uzuri ne, na zo ne?" "A'a shikenan" ta ƙyale shi, bayan tuna shawarar da Safiyya ta bata, wato maman Khairat. ***** Kamar yadda Nene ta buƙata, sai da suka je gurin jami'an tsaro, suka yi yarjejeniya, aka rubuta da yaren hausa, French da kuma turanci, duk suka sanya hannu, a gaban su Auwwalu da jami'an tsaro. Daga nan suka dawo gida Nene ta ba wa Nana wata 'yar madaidaiciyar Jaka, da za ta haɗa kayanta da za ta buƙata a ciki. Ta kalli Nana ta ce "Nana dan Allah ki kula da kan ki, duk da na san ke kamammiyar yarinya ce, ba mutuniyar banza ba, amma tunatar da mumini abu ne mai kyau, ki riƙe mutuncinki, ki kiyaye hakkin aurenki. Idan ki ka ga wani abu na ba dai-dai ba, ko wanda ya saɓawa addininki, a haƙura da sabgar nan. Kuma cikin hikima za ki din ga bincikawar,ba sai kowa ya fuskanci ainihin abin da ya nai ki gurin bax Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Nene zan kula da kaina, ba zan ba ki kunya ba, ki taya ni da addu'a, Ubangiji Allah ya sanya zuwana ya zame mana alkhairi baki ɗaya" "In sha Allah, addu'a ina nan zan ci gaba da yi miki ita da yardar Allah." Nana ta haɗa kayanta, amma ji take kamar ta fasa tafiyar, amma ta ƙarfafi zuciyarta, ta hana hakan yin tasiri a ranta. Ranar Asabar, da safe matar ta zo domin tafiya tare da Nana. Nene ta ce mata "Dan Allah gata nan amana, Hansatu, kar ki kai ta idan za a cutar da ita, kin ga yaro ne da ita ƙarami, dan Allah idan akwai matsala a gurin nan, gara ki saka a sallamo ta ta dawo gida." Hansatu ta ce "Haba Nene, ya ki ke haka kamar ba ki yarda da ni ba ne?" "A'a ba rashin yarda ba ne ba, 'yar amana ce shi yasa nake jadda da miki, ga kuma ƙaramin yaro da take da shi" "Ba ki da matsala fa, ki kwantar da hankalinki" Nana ta kalli Muhsin, da yake jikin Nene, yana wasansa, idanun Nana fal hawaye ta ce "My little Sayyid, zo ka yi sallama da Umminka" ya taso daga jikin Nene ya nufo Nana. Hatta dogayen gaɓoɓin jikinsa, irin na Sayyid ne sak. Ta rungume shi a jikinta, hawaye na zuba daga idanunta "Allah ka kula mini da ɗa na, Allah kar ka saka wani abin cutarwa ya same shi, Ubangiji Allah ka sanya na je na dawo na tarar da shi lafiya" ta furta a hankali ƙasa-ƙasa. Ta ɗago ta kalle shi ta ga yana yi mata murmushi, ta sumbaci goshinsa, ta miƙe ta ɗauki jakar kayan nata, Nene ta rako su har bakin ƙofa, suka hau abin hawan da Hansatu ta zo da shi, suka tafi. 08081012143 68 Nana ta din ga waige, tana hango su Nene tare da Muhsin, har suka ɓacewa ganinta gaba ɗaya. Hansatu su na tafe su na ta  hira da direban motar, aka biya gidanta, aka ɗauki wasu matasan matan sannan suka ɗauki hanyar tafiya. Tana jin yadda suke ta hirarrakinsu a cikin motar, amma ta kasa tofa komai, da ta rufe ido, ɗan jaririnta take hangowa, gefe guda kuma zuciyarta cike da fatan Allah ya sa tafiyar nan, ta yi mata rana. A ƙalla sun yi tafiyar awanni biyu da rabi a mota, sannan suka isa wani gida. Hansatu ta yi musu bayanin, a nan za su sauka su huta, washegari ta kai kowacce inda ta ɗaukko ta za ta kai ta. Nana ta din ga addu'a da fatan Allah ya sanya ba mugun hannu ta faɗo ba, duk da kafin ta taho Nene ta bata layi ta saka a wayarta, ta ce mata duk abin da ta ga ba ta yarda da shi ba, ta kira ta ta sanar mata. A duk lokacin da Nana ta ɗaga wayar ta kalla, sai ta tuna Hajiya Amina, Haidar da kuma sauran jama'arta na Nigeria. A gidan nan suka yi salla, aka ba su abinci suka ci, sai dai Nana ta yi mamaki ganin mata da yawa a gidan. Duk da ƙabilu ne daban-daban matan, akwai Zabarmawa, akwai Bugaje, da hausawa da sauran ƙabilun ma da ba ta sani ba a Nijar. Wai gidan kamar kamfani ne, wannan matan aiki ake nema musu, duk ciki Nana ce kawai 'Nigeria a cikinsu. Gaba ɗaya ta takure kanta ta kasa jikinta da su. Gaba ɗaya daren ranar, Nana ta kasa bacci, ta din ga tunanin Muhsin, da tunanin ko zai yi kukan rashin ganinta. Washegari Hansatu ta ce wa Nana ta shirya, ta ɗauki kayanta su tafi. Haka kuwa aka yi ta sake ɗaukarta su ka fita. Nana ta sha mamaki, ganin haɗuwar da gurin cin abincin ya yi, kuma babban abin da ya ƙara bata mamaki, gurin cin abincin tamkar hotel. Suka shiga cikin gurin, Hansatu ta kai Nana wani katafaren ofishi, da yak3 gurin mai kula da ɗaukar ma'aikatan, da yake namiji ne. Rawaninsa ne ya tabattar mata da buzu ne, ganinsa kawai sai Nana ta ji wani irin sanyi, tamkar ta ga Sayyid. Nana ta gaishe shi, ya amsa sama-sama yana ɗan basarwa. Hansatu ta ce masa "Wannan ita ce ma'aikaciyar, na kawo ta a yi mata gwajin, a gani idan za ku ɗauke ta" Ya ɗaga kai ya  sake kallon Nana ya ce "Sannu ko" Nana cikin girmamawa ta ce "Yauwwa sannu da aiki" Ya miƙo mata ƙunshin wasu takardu ya ce "Ga wannan duba, ki ga yadda tsarin aikin namu yake, ki gani idan sun yi miki, kafin mu je inda za a yi miki gwajin, idan kin ci sai ki sanya hannu a takardun, ki fara aiki da mu" Nana ta saka hannu ta karɓi takardun, amma ta ga rubutun French, ta kalli Hansatu, ta kalle shi ta ce "Ai ban iya fransanci ba" Ya kalli Nana ya ce "Ba ki yi makaranta ba?" Ta ce "Na yi, amma ni ban iya French ba, turanci na iya sai Hausa" Hansatu ta ce "A yi haƙuri Yallaɓai, 'yar Nigeria ce, daga Nigeria take" Sai kuma ya kalli Nana ya faɗaɗa murmushinsa ya ce "Daga Nigeria ki ke? Ki ka baro babbar ƙasa kamar Nigeria ki ka zo jamhuriyar Nijar ki yi aiki da mu?" Nana ta ɗan risunar da kai tana murmushin dole, ganin yana murmushi shi ma. Ya ce "Ahh to ai 'yan Nigeria ƙawayenmu ne, ba ma ƙawaye ba 'yan uwanmu ne. Dan haka zan ba ki aiki amma da sharaɗin za ki koya mini turanci, idan kin yarda na baki aiki" Nana ta yi murmushi, saboda yanayin yadda ya yi maganar cikin zolaya. Ya yi 'yar dariya ya ce "Ai duk wanda ya zo Nijar, mussaman daga Nigeria baƙonmu ne, akwai buƙatar mu karrama shi sosai da sosai, ko dan ƙara zumuncinmu da mutanen Nigeria. Dan haka babu wani abu, wannan wani ci gaba ne ma zan iya cewa gurin Abincinmu ya samu, kin ga girke-girken da ba a yi a nan, na can ƙasar kya din ga yi mana. Mu na da gurin kwana na ma'aikatanmu, awa ashirin da huɗu muke yi mu na aiki. Kamar yadda ki ka gani babban gurin cin abinci ne da manyan mutane ke zuwa cin abinci. Masu sayar da abinci daban, masu girki daban, ke za ki kasance a ɓangaren masu girki ne. Mu je mu zagaya ku ga gurin sosai da sosai. Ya jagoranci su Nana, ya nuna musu gurin, tsarin ya yi wa Nana sosai, duk da abin da ba ta ji daɗi ba, maganar zuwa hutun sati ɗaya ne kacal, duk ƙarshen wata. Su Hansatu za a din ga tura wa albashinta, su cire nasu kason su bawa Nana sauran. Ita Nana duk hakan bai dame ta ba, babban fatanta buƙatarta ta biya kawai. Suka kammala duk cike-ciken da za su yi, aka sallami Hansatu, Nana kuma aka kaita gurin kwanan ma'aikata. Ɗakin da aka kai Nana, su uku ne a ciki, da banɗaki a ciki. Ta ajiye jakar kayanta, Hansatu ta kalle ta ta ce "To Nana, kamar dai yadda ya gaya miki, mu kamfani ne, kuma a ƙarƙashinmu ki ka zo nan, dan haka gurinmu albashinki zai din ga tafiya, mu zamu din ga sallamar ki" Nana hakan ko a jikinta, dan ita ko ba za su ba ta komai ba, indai akwai gurin kwana da abinci, kuma kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, hakan ba damuwarta ba ne ba. A fili ta ce "Babu damuwa, hakan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da mafificin Alkhairi". "Amin, a hakan ma gaskiya kina da sa'a sosai da sosai, sai da muka kawo musu mata uku, da ƙyar suka ɗauki ɗaya, wai duk ba su yi musu ba, wasu kuma sai an zo yi musu gwaji sai su faɗi. Amma ke ya ce ba zai yi miki ma gwaji ba, kawai an ɗauke ki aikin. Abin da zan gaya miki kawai shi ne ki kula, ki kula da kanki sosai da sosai, banda ƙazanta banda son jiki. Sannan kar ki ga kin tsallake wannan matakin, ya ɗauke ki aiki a haka cikin sauƙi, ki zata miƙe ƙafa za ki yi, mace ce mai gurin nan, kuskure kaɗan za ki ta ci mutuncinki ta kore ki. Su kan su ma'aikatan kwantar da kai suke yi, su na yi mata biyayya, duk wata tijara da bala'inta kawai ki toshe kunnenki ki yi haƙuri." Nana ta yi shiru, sai da Hansatu ta gama gaba ɗaya sannan ta numfasa ta ce "To Ubangiji Allah ya iya mana" Hansatu ta amsa da "Yauwwa Amin" Hakanan Nana ta ji a jikinta, ba za ta ɗauki wulaƙanci da cin zarafi ba, duk da kuwa abin da take son cimma. Ko Nene da ake kambama faɗanta da masifarta, ba ta cin mutunci, kuma duk abin da za ta yi faɗa a kai, to a kan gaskiya ne. Amm yanayin yadda Hansatu take yi mata bayanin mai gurin nan, a kaikaice dai ba ta san darajar mutane ba. Ɗakin da Nana take, ita da wasu Zabarmawa ne guda biyu. Ta yi alwala ta yi sallar Azahar. Ta daɗe a kan abin salla, tana gaya wa Allah, cikin magiya a kan ya sanya ta samu abin da ta fito nema, ya kuma raba ta da duk wani sharri da abin ƙi. Bayan ta idar, ɗaya daga cikin 'yan ɗakin, ta ce mata ta zo su je ta zagaya da ita. Can ɓangaren da ake girke-girken ta kai Nana, suka zagaya daga nan ta kaita cikin gurin da ake sayar da abincin. Nana ta yi mamakin girman gurin, da yadda gurin Abincin yake da tarin kwastomomi. Sai dai da gani ka san na manya ne, dan duk waɗanda suke zuwa gurin cin abinci akwai alamun abin hannu a tattare da su. ***** Ɓangaren su  Shukura cikin jikinta ya tsufa sosai, sai dai a wannan karon ta dage fafur ta ƙi yin awo a Asibitin su Doctor Sharif. Gefe Sagir ya jewa mahaifiyarsa, da maganar son dawo da Yusra, amma ta ce ba ta lamunta ba, ba ta buƙatar ya sake rayuwa da Yusra, gara yaje ya auro wata can daban, amma ba Yusra ba. Gaba ɗaya ya shiga damuwa, saboda mugun sabo da shaƙuwar da ya kuma yi da Yusra. Ita ma Hajiya Halima tun da ta samu labarin, Sagir ne tsohon mijin Yusra yake zuwa gurinta, ta din ga bala'i ta ce ko shi ne autan maza, Yusra ba za ta koma hannunsa ba, balle a sake ci mata mutunci a sako ta. Ga shi daga shi har ita su na son junansu. Dan haka ya yanke shawarar tafiya gurin ƙanin mahaifinsa ya yi masa magana. Shi kuma ya kira Hajiya Halima ya din ga yi mata faɗan dan me za ta hana shi mayar da matarsa alhalin sulhu alkhairi ne, wancan karon da auren ya mutu ma, gutsuri tsomarsu ce ta kashe Auren. Mussaman ta kira Sagir gida, ds ya je ya same ta, ta dirarar masa da bala'i. "Wato ƙarata ka je ka kai wa ƙanin ubanka saboda mace ko Sagir?" Ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya ba ƙararki na kai ba" "Rufen baki ko na make ka, ba ƙarata ka kai ba ya kira ni yana faɗa? Tun da abin da ka zaɓa kenan, ka je ka yi duk abin da ka ga dama" Kalaman na Hajiya, tamkar ɗsure shi ne da jijiyoyin jikinsa, gaba ɗaya ya rasa abin da yake yi masa daɗi ba ya son ya yi abin da daga baya zai zo yana dana sani, saboda rashin amincewar Hajiyarsa. **** Daren yau sam Nana ba ta samu isasshen bacci ba, da yake sai washegari aka ce za ta fara aikin, ba ta yi aikin komai ba ranar. Raba dare ta yi tana nafilfili addu'oi, saboda a jikinta tana jin wani abu game da gurin, wanda ta kasa tantance ko mene ne. Washegari da safe, suka shirya ita da 'yan ɗakinsu, suka tafi gurin aikin Abincin. Kayan girki ne ga su nan a zube, kamar abin banza, yanayin yadda aka jibge kayan a gurin, Nana ta sha jinin jikinta, ta san aiki ne tuƙuru za a yi shi gurin. Aka ba su jadawalin abinccicikan da za a girka a ranar, Nana ta san wasu, wasu kuma ba ta san su ba. Su na nan tsaye shugabar ɓangaren na ƙara yi wa Nana bayani, da gurɓatacciyar hausarta, sai ga mutumin jiya shigo. Gaba ɗaya suka wani ruɗe, masu gyara tsayuwa na yi, masu kama aiki suna yi, Nana dai ta ƙame a gurin da take. Ba yabo ba fallasa ya din ga amsa gaisuwar da ake yi masa, sai da ya zo kan Nana ya saki murmushi ya ce "Baƙuwarmu, ya ki ka ga gurin namu, ba dai wata matsala ko?" Nana ta girgiza kai ta ce "Babu matsala" Ya ce "Yauwwa, ki saki jiki ki yi aikinki da mu, kamar kina Nigeria, duk abin da ba ki gane ba, ga shugabar sashin nan, idan kuma ba haka ba ni ki zo ki same ni ki yi mini magana" Ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah, na gode sosai da sosai" Ya kalli matar ya ce "Dan Allah kar a ce za a sakar mata aiki lokaci ɗaya, a koya mata abin da ta sani ba a hankali, kafin a sakar mata aiki" Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?" "Kin ji na ambaci hakan ne, a maganata?" Ta girgiza kai ta ce "Tuba nake" Ya ce "'Yar Nigeria, a yi aiki lafiya" "Na gode sosai" Nana ta yi maganar cikin girmamawa. Ya wuce ya fita. Bayan ya fita suka juya yare, suka ɗan yi maganganu, sai dai duk da Nana ba ta jin yaren nasu, ta san gulmarta suke yi. Suna aiki amma gaba ɗaya hankalin Nana ba a kan aikin yake ba, yana kan halin da Sabir yake ciki. Tana ta tunani yaya yake? Yana rigima ko kuwa bai damu ba ya kwantar hankalinsa, haka ta yi ta wasi-wasi a zuciyarta. ***** Hajiya Amina ce ta yi shirin tafiya Umara, ta tsaya a Egypt za ta kwana biyu, ta tsaya a ɗan binciki lafiyarta. Sai dai ta din ga ji a ranta, yakamata a ƙara bincika mata matsalarta ta rashin haihuwa, mussaman da take tuna maganganun Nana. Sai dai gefe guda tana tuna yadda Alhaji Zailani yake gargaɗinta a kan shi ya fauwwala wa Allah, bai damu lallai sai ta haihu ba, tun da an nemi magani ba a dace ba. Sai dai a wannan karon, ta sake jin tana son jarraba da bibiyar lafiyarta, da ganin likita, ko za a dace, tun da ba ta daina al'ada ba ma. Da harshen turanci suka tattauna da Likitan, ta yi masa bayani, ya rubuta mata gwaje-gwaje ya ce ta je ta yi, ciki har da hoto. Kasancewar komai na su ba kamar na ƙasarmu ba, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi duk gwaje-gwajen, aka tura wa Likitan sakamakon. Bayan ta koma gurin Likitan ya duba na'ura mai ƙwaƙwalwarsa, ya kalli Hajiya Halima ya ce mata "Sakamakon hoton da aka yi mata, ya nuna babu mahaifa a jikinta gaba ɗaya" wata irin ƙara cikinta yayi, zuciyarta ta buga a jejjere da ƙarfin gaske, sai ta hau kame-kame tana tunanin, ko kunnuwanta ba su ji daidai ba? Ko kuma turancin nata ne ya ƙwace. Cikin rawar murya ta ce "Ka tabattar da abin da ka gaya mini, ko kuma nice ban fahimta ba?" Ya ce "Na tabattar, shi ne sakamakon gwajin da aka turo mini, amma idan ba ki yadda da sakamakon ba, kina iya zuwa wani Asibitin a sake duba ki!. Yammm ta ji kanta yana yi, ta daina gane komai, hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, tana son yi wa likitan tarin tambayoyi amma kanta ya kulle. Shin da gaske ana iya samun mace babu mahaifa, ko kuma wani abin ne daban? Ya aka yi duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana bulayin neman haihuwa ba a taɓa gaya mata ba ta da mahaifa ba sai yanzu?. Gaba ɗaya Hajiya Amina, ta rasa kalmomin da za ta tattaro ta sake furta wani abu. Jikinta rawa kawai yake yi, wani irin gumi yana tsatstsafowa ta kowace kafa ta gashin jikinta. Likitan ya ci gaba da yi mata bayani, amma ta kasa fahimta. Ba ta san ma da ya aka yi ta bar Asibitin ba, ta koma masaukinta saboda tsabar ɗimuwa. Ta kuma rasa wa za ta kira ta sanarwa wannan maganar. Gaba ɗaya kanta ya juye, dan ba ta ma iya tuna yadda su ka ƙarƙare da Likitan ba. Tana so ta zubar da hawaye, ta ji sanyi a ranta, amma abu ya gagara idanunta suka bushe zuciyarta ta yi nauyi. Babbar tambayarta ita ce, dama ana iya samun macen da ba ta da mahaifa? Ko kuwa ta ta ce ta yi ɓatan dabo?. Tambayar da ta rasa wa za ta yi wa, balle a ba ta amsa. ***** Nana kuwa gurin nan aiki ake yi tamkar babu gobe, duk da ba ta da son jiki, amma aikin yana da yawa ga babu isasshen hutu, sai aikin ɗorawa da saukewa. Ga shi ta kasa sakin jiki da ma'aikatan gurin, saboda yadda suke tsangwamarta, da nuna mata ƙabilanci, saboda ita ba 'yar ƙasar su ba ce ba. Sam ba sa gaban Nana, duk da tana ɗan saka ido ta ga, ko akwai wata mai hankali da za ta ji ta yarda da ita, a kaikaice ta ɗan fara ƙwanƙwasa cigiyar Sayyid. Sai dai gaba ɗaya ba su yi mata ba ma'aikatan gurin, gaba ɗaya ba ta ji ta aminta da ko mutum ɗaya daga cikin su ba. Kullum da safe Al hussain, mutumin da ya ɗauke ta aiki, sai ya zagaya su ya ga yadda suke gudanar da aikin safe da yamma. Da ya zo ma'aikatan suke nutsuwa, kowa ce ta kame kanta, marasa kamun kai kuma su fara ɗan karairaya. Shi kuma ya tsuke fuska yana basarwa. Sai dai da ya ga Nana sai ya saki fuska, ko ba ta kula shi ba, shi sai ya yi mata magana. "'yar Nigeria ya alƙawarinmu ne?" Nana ta ɗan saki fuska ta ce "Wanne?" "Au har kin manta?" Ta yi murmushi ta ce "Duk lokacin da ka shirya, sai mu fara" Ya ce "Kin san akwai wani abokina, sonake kafin na haɗu da shi, ko gaisuwa na iya da turanci, saboda ya iya turanci ni ban iya ba, ya juya yare ya yi ta magana ba na gane me yake cewa, to kin ga yakamata na ba shi mamaki nima" Nana ta ce "Gaskiya ne, shi ma Buzu ne kamar ka?" Al Hussain ya ce "Ya aka yi ki ka san ni Buzu ne?" "Ga rawani nan ka na yi" ya yi dariya ya ce "Kash, to shikenan tun da kin gane, shi ma buzu ne, mun kwana biyu ma bamu haɗu ba, ban je Agadez ba" "Duk Buzaye a Agadez ku ke?" Ya girgiza kai ya ce "A'a, sai dai mun fi yawa a can, ko kina son zuwa ne? Mu na da wani gurin Abincin ma a can, babban wannan sai a mayar da ke can" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a tamabaya dai kawai na yi" Ya jinjina kan ya ce "To yaya aikin?" "Alhamdillah" "To ma sha Allah, Allah ya taimaka" Tun da suka fara hirar nan, Nana ta lura da irin kallon da ake yi mata, saboda ya tsaya sun yi hira. Sai dai ita ba kallon ne ya dame ta ba, a jikinta take jin sam ba ta kyauta ba, tsayawa da ta yi tana magana da Al Hussain har take yi masa murmushi ba, saboda ta san da Sayyid yana gurin, ko da makamancin wasa ba za ta taɓa aikata hakan ba, saboda yadda yake tsananin kishinta. A hankali ta ce "Ka yi haƙuri Sayyid, babu yadda na iya ne, duk a ƙoƙarina na son zuwa gare ka ne, ka yi mini afuwa" ta furta a hankali kamar mai raɗa. "Nana wai a ina ki ka san Al Hussain ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalli Shugabar gurin nasu, da take yi mata tamabaya cike da tuhuma. Kamar Nana ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce "Waye hakan?" Matar ta ce "Kamar yaya?" Nana ta ce "Wanda ki ke tambayata" Gaba ɗaya suka kalli Nana, jin yadda take bawa Adama, shugabar ɗakin girki. Ita kuwa Nana ko a jikinta da irin amsar da ta bawa Adaman. Cike da takaici Adama ta ce"Mutumin da ya fita yanzu" Nana ta ce "Au sunansa kenan dama? A nan Nijar na san shi, meyafaru?" Ta yi maganar tana tsare Adama da ido, tana jiran abin da za ta sake cewa. Sai dai ta yi shiru ba ta kuma magana ba, su kuma suka hau mamakin irin amsar da Nana ta bata, kuma ba ta iya ce mata komai ba. Gaba ɗaya Nana hankalinta ya koma kan sauran kwanaki nawa ta koma gida, duk da kullum sai ta yi waya da Nene. Amma ta ga kamar kwanakin ba sa matsawa sam. **** Hajiya Amina revers ta yi, ta dawo gida Nigeria, saboda kiɗima da tashin hankali da take ciki, ta rasa wanda za ta fara tunkara da maganar. Ta so samun mijin Alhaji Zailani a waya, ta fara yi masa bayani, amma ba ta same shi a waya ba. Ta koma gida a kiɗime, amma ta tarar da saƙon ya yi balaguro zuwa Abuja. Jikinta na rawa ta kira Doctor Sharif, ya ɗaga yana faɗin "Hajjaju barka da yamma" "Sharif abu zan tambaye ka dan Allah" Gabansa ya faɗi, saboda yadda ya ji muryarta cike da tsoro da kuma damuwa. "Hajiya lafiya dai?" "Lafiya ƙalau, tambaya zan yi maka dan Allah" "To Allah ya sa na sani" "Dan Allah Sharif ana iya samun matar da ba ta da mahaifa dama?" Ya yi shiru sanann ya ce "Me yasa ki ka tamabaya?" "Ka bani amsa kawai" Nutsuwa ya yi ya tattara hankalinsa, kar ya ba ta amsar da zai fallasa wani ɓoyayyen abin da bai kamata ba. Duk da bai san dalilin da ya sanya ta yi tambayar ba. "Eh ana samu Hajiya, sosai ana samu wani abu ne ya faru?" "A'a shikenan na gode sosai" ta kashe wayar, sai a lokacin hawaye ya fara gangaro mata, da ta ƙara tabattar da har abada ba za ta samu haihuwa ba. "Amina butulci za ki yi wa Ubangiji? Sauran ni'imomin da ya yi miki fa?" Wata zuciyar ta tunatar da ita. Sai dai kasancewarta biladama mai ɗauke da zuciya irin ta ɗan adam, sai ta kasa jurewa ta bi nasihar da zuciyarta take yi mata, ta fashe da matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Duk da ta daɗe tana yin sa a ɓoye, amma ba ta yanke tsammani ba ta ci gaba da addu'a, amma a wannan karon da ta san ba ta da rabo baki ɗaya, sai ta sare. ***** Shirye-shiryen bikin Abba yayi nisa, dan bai fi saura sati biyu bikin ba, ta ƙara saka masa ido da shi da Jamila. Jamila sam ba ta nuna mata cewar ta san abin da take yi ba, ta rabu da ita. Ya kasance taronsu na ƙungiya lokaci yayi, dan haka suka shirya tafiya a wannan karon har da maman Khairat. Da suka je masaukinsu ma a garin Abuja, Jamila ba ta shiga sabgarsu ba, harkokinta kawai take yi. Maman Khairat ta ce "Wai Jamsy ya ne? Duk kin zama so silenta, babu wannan rawar kan" Jamila ta ɗan taɓe baki kawai. Hajiya Sa'a ta ce "Jamila haushina take ji, ban san me na yi mata ba" Jamila ta ce "Mummy kenan" "A'a ba wani Mummy kenan, magana za ki yi" "To Mummy, ki na ta daughter daughter, amma ƙarara ki ka nuna ba kya ƙaunata, daga ganina tare da Abba, ki ka haɗe rai ki ka yi kicin-kicin, ki ka tashi nema masa aure. Abin ya bani mamaki" Hajiya Sa'a suka haɗa idi da maman Khairat, ta ce "Haba daughter, ya za a yi na ƙi ki da Abba, ke me ma za ki yi da aure? Na daɗe ina gaya miki za ki iya rayuwa ki da kuɗinki, ba tare da kin yi aure ba. Za ki huta ki yi duk abin da ki ke so." "Amma Abba ma ai yana da kuɗi, shi me yasa ba ki ce ya yi rayuwa da kuɗi kawai ba, ki ke shirin yi masa aure? Duk wata ƙasaita, kuɗi da wadatar mace, inuwar aure ginshiƙi ce kuma sutura ce ga 'ya mace. Amma na san saboda ni rayuwata ta gama lalacewa, ke kuma kina son ɗan ki ya yi kyakykywar rayuwa, ki ka yi ƙoƙarin raba ni da shi. Sai dai tun ran gini tun ran zane. Ban ji haushinki ba ko kaɗan Mummy, abin da ki ka yi shi kowacce uwa za ta yi. Ina yi mana fatan dacewa da ƙarshe mai kyau" Tana gama maganar ta yinƙura ta tashi, ta bar ɗakin. Safiyya ta ce "Kin ga Hajiya, ki bi yarinyar nan a hankali, alamu sun nuna hankali ya fara shigarta, ta san ciwon kanta, kuma abin da aka yi mata duk da ta samu kuɗi ya yi mata ciwo. Kar ki bi ta da ƙarfin tsiya ta yi tawaye" Hajiya Sa'a ta numfasa ta ce "Na ga alama, amma ba zan taɓa rainon ɗan kwiykwiyo, ya girma ya fara yi mini haushi ba. Ina son samun jinin 'yar uwatta na riga Zailani samu ko ta halin ƙaƙa, daga nan zan yi maganinta" Safiyya ta jinjina kai. Doctor Sharif ya din ga kiran Alhaji Zailani, ya sanar da shi kiran da Hajiya Amina ta yi masa, amma ya kasa samunsa a waya, saboda su shinga taron manyan ƙungiya da suke yi, wanda sai sun kwana uku suke fitowa, sannan ayi babban taro na kowa da kowa da ke cikin ƙungiya. Ganin kiran Hajiya Amina ya bawa Shukura mamaki, dan idan tana Saudiyya sai dai su yi video call. Ta ɗaga ta ce "Mami, yaya ba ki samu tafiyar ba ne?" "Shukura za ki iya zuwa gida, ban takura miki ba" Cikin tashin hankali Shukura ta ce "Lafiya kuwa, ya na ji muryarki a haka?" "Dan Allah idan da hali ki zo gida" "Shikenan, gani nan zan kira baban Haidar na gaya masa, gani nan Allah ya sa lafiya" Hankali a tashe, ga tsohon ciki haka ta ɗauki mota ta tafi gida. Tana matuƙar jin Hajiya Amina a zuciyarta, saboda bayan rasuwar mahaifiyarsu, tun su na ƙanana babu yadda ba ta so cuzguna mata ba, amma Hajiya Amina babu ruwanta. Ba ta damu da abin da mutane za su ce ba, ta riƙe ta da halin ta, sai da ta ƙara wayo sannan ta gane ba ta da wata uwa da ta wuce ta. Shi yasa take matuƙar jin damuwarta a ranta tamkar uwar da ta haife ta. A bedroom ta tarar da ita, idanunta jawur sun kumbura. Cikin tashin hankali ta ƙarasa ta zauna ta ce "Lafiya kuwa? Ko ba ki da lafiya ne?" Ta girgiza kai ta ce "Yi haƙuri Shukura, na taso ki ga tsohon ciki, na rasa da wanda zan yi zancen nan na ji daɗi a raina." Cikin damuwa ta ce "To meyafaru?" "Shukura wai ba ni da mahaifa" Shukura ta yi saroro, ta ce "Kamar yaya?" Ta share hawayenta ta gaya mata duk abin da ya faru. A ƙarshe ta ce "Na kira Doctor Sharif ya ce mini eh ana iya samun mata da basu da mahaifa, amma na yi mamakin yadda duk yawon Asibiti da na yi a nan, ba a taɓa gaya mini ba" Shukura ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Anya kuwa? Kin san fa kin daɗe da daina zuwa Asibiti a kan matsalar nan, Daddy ba ya so. Sannan ku ne ku ke yarda da maganar Sharif ɗin nan, ki rabu da shi mu je wani Asibitin daban, a sake duba ki a tabattar da abin da yake faruwa. Duk da ba na tunanin za a samu matsala a abin da can Egypt ɗin suka gaya miki." Ta girgiza kai ta ce "A'a Shukura, babu inda zan sake zuwa, na yi maganar ne da ke dama na samu sanyi a raina, na kira babanki ba ta shiga" Shukura ta yi shiru, kawai dai ta ji ita abin kamar akwai lauje cikin naɗi. ***** Nana ta shafe sati na biyu, tana aiki a wannan gidan Abinci. Sai dai ita kanta tana mamakin irin yadda Al Hussain yake kyautata mata. Hakan ya sanya gaba ɗaya suka ƙara saka mata ido suka tsangwame ta, mussaman Adama da 'yar ta Raliya, da alamu suka nuna Al Hussain take so. Idan aiki ya ɗan yi sauƙi, Nana kan fita ta shiga cikin gurin cin abincin, ta zagaya ko za ta ga ko mai da Sayyid ne, amma ba ta ga kowa ba. Sai dai gabanta ya kan faɗi a duk lokacin da ta ga masu rawani sun zo gurin cin abinci, sai ta ga kamar za ta gan shi a cikin su. Ta gama zagayenta, ta koma cikin gurin girkin, Adama ta kalle ta ta tsuke fuska ta ce "Daga ina ki ke, ana tsaka da aiki?" "Na ɗan je wani uzuri ne" "Na me, kuma a ina?" Nana ta ce "Uzuri dai na ɗan Adam, na yau da gobe, ai rayuwa na buƙatar sirri ko?" "Ni fa na fuskanci take-takenki na rashin kunya baki da kunya ko kaɗan, saboda kin ga Al Hussain yana tsaya miki, wallahi idan ba ki yi wasa ba sai na kawo ƙarshen aikinki a nan, sai na saka an kore ki daga gurin nan" Kallonta kawai Nana ta yi ta kawar da kai, ta ci gaba da abin da take yi. Har ta gama bala'inta, 'yan korenta suka taya ta, Nana ba ta tanka mata ba. Washegari da sassafe, Nana ta baro ɗakinsu, ta tafi kitchen ta fara aikinta, duk da wasu lokutan suna yi mata mugunta, su din ga sakar mata aiki. "Ina sauran ma'aikatan gurin nan?" Ta ji wata murya ta daki kunnenta, da ba ta san mai ita ba. Ta ɗaga kai ta kalli matashiyar matar, doguwa fara jawur, mai kama da Al Hussain. Kawai ta mayar da kanta ta ci gaba da aikin gabanta. "Ke ba kya ji ina magana ne?" Nana ta ɗago kai ta ce "Su na zuwa" Nana na rufe bakinta, sai ga Adama ta shigo, ita da sauran ma'aikatan. Wata irin rikicewa suka yi, suka hau tsuma su na gaida matar. "Wace ce wannan? Da ba ta da mutunci ba ta da ɗa'a, nake magana tana bani amsa a wulaƙance" ta yi maganar tana nuna Nana. Nana a ranta ta hau mamakin wane wulaƙancin ta yi mata, ita da ta zo guri babu sallama babu gabatar da kai, koma wace ce ba zai wuce ita ce mai gurin da ake faɗa ba. Nana a ranta ta ce "Koma wace ce ke, Allah ya fi ki" sai dai ba ta sake ɗaga kai ta kalle su ba, ta ci gaba da yankan kabejin hannunta. Ayshercool 08081012143. 69 Adama ta risunar da kai ta ce  "Ki yi haƙuri ranki ya daɗe, mu ma haka muke ta fama da ita mu ma, amma ki yi haƙuri baƙuwa ce" "Baƙuwa kuma ba ta iya magana ba, baƙuwa daga ina?" Raliya ta ce "'yar Nigeria ce" " 'yar Nigeria, waye ya saka Al-Husssain ɗaukar wata 'yar Nigeria, dama haka 'yan Nigerian ku ke, ba ku da mutunci ba ku san me ku ke yi ba?" Maganganun matar sun soki zuciyar Nana, tamkar ta mayar mata da martani ta ce "Ku a Nijar ba ku san muhimmancin sallama, da girmama na ƙasa da kai ba" Sai dai ta yi shiru ta ci gaba da aikin gabanta. Haka ya ƙara tunzura matar ta fita fuuuu tana bala'i tana sai Nana ta bar aiki a gurin. Matar na barin gurin Raliya ta kalli Nana ta ce "Allah ya ƙara, idan kina cin ƙasa ai ki kiyayi ta shuri, yau kin taɓo abin da ya fi ƙarfinki, kin yi a bakin aikinki" Babban abin da ya ɗaure musu kai, bai wuce yadda Nana ta ƙara yin burus, ta ci gaba da aikin gabanta. Adama ta ce "Anya yarinyar nan ba mahaukaciya ba ce kuwa?" Ɗayar ta ce "Ko ta mayar da mu mahaukata ba. Amma idan haukan take ji, ai Hasna babarta ce" Wata matashiyar mata ce ta shigo, sanye da uniform a jikinta. Ta yi sallama suka amsa. Ta ce "Ina Nana?" Nana ta ce "Ga ni" "Ki zo ana neman ki a ofishin Al Hussain" Ta ce "To gani nan" ta yi maganar tana ajiye wuƙar hannunta, ta wanke hannunta ta bi bayan matar. Sai dai har matar ta yi gaba ta bar Nana, da ƙyar Nana take iya ɗaga ƙafafuwanta, saboda matsanancin nauyin da ta ji sun yi mata, ga sanyi da ya fara ratsa ta ta ko ina. "Ya hayyu ya ƙayyum. Allah ka taimake ni, Ƙaisar kar ka yi mini haka mana"  Ta furta a hankali zuciyarta na bugawa. Ta saka hannu ta tura ƙofar ofishin. A tsaye ta tarar da matar ɗazu, tana zazzaga masifa, Al Hussain yana zaune yana kallon ta. Sai dai Nana ta yi turus, ganin Ƙaisar a zaune a jikin na'urar sanyaya guri, da ke cikin ɗakin. "Nana ƙaraso mana" muryarsa ta dawo da Nana hayyacinta. A hankali ta ƙarasa ya ce ta zauna a kan kujera. "Al Hussain ka na da lafiya kuwa? Yarinyar ta yi mini rashin mutunci, ka ce ta zauna a kan kujera?" Ya ce "A'a Hasna, na fa san halinki, kuma a aikin da Nana ta yi da mu na ɗan lokaci, ba ta da matsala sam. Nana meyafaru ne?" Nana ta buɗe baki za ta yi magana, Hasna ta tari numfashinta ta ci gaba da masifa. Al-Husssain ya daki tebur ya kalli Hasna, hakan ya sanya ta yin shiru tana harar Nana. Nana ta ce "Ban san wace ce ba ne, ta yi haƙuri" Hasna ta daki tebur ta ce "Ka gani ko, garin kwashe-kwashe ka kwaso mara mutunci, to wallahi sai ta bar gurin nan, tun da ba na ubanta ba ne" Al-Husssain ya ce "Tsakani da Allah, Nana mutuniyar kirki ce mai girmama mutane, ba na tunanin za ta yi miki wani abu na rashin mutunci. Nana ki je ki ci gaba da aikinki" Ta jinjina masa ta kalli Hasna ta ce "Ki yi haƙuri, ban san wace ce ke ba, ba ki gaya mini ba, na zata a cikin abokan aikina ne kaw... "Ke, na yi miki kama da wadda za ta zama abokiyar aikinki?. Za ta ci gaba da magana Nana ta tsare ta da ido, sai ta rikice gaba ɗaya ta rasa abin da za ta ce. Al-Husssain ya ce "Maza jeki ki ci gaba da aikinki" Nana ta miƙe tsaye, kawai ta ji jiri ya ɗebe ta, ta yi saurin riƙe kujerar. Al Hussain ya miƙe da sauri ya ce "Ba ki da lafiya ne?" A sanyaye ta ce "A'a jiri nake ji ne" "Idan ba za ki iya aikin ba, ki je ki kwanta ki samu hutu" Nana ta ce "A'a zan iya ma, in sha Allah" Ta lallaɓa ta fita daga ofishin, sai dai tana jiyo Al Hussain yana ce mata, ki yi a hankali kin san mu na da baƙi, idan kuma ki ka ci gaba da hayayaga mutuncinki ne zai zube, wannan halin naki babu abin da zai janyo miki sai raini. Gaba Nana ta yi, tana bin bango, sai dai sosai ta ji Duniyar na juya mata. Ta lallaɓa ta koma ɗakinsu da ƙyar, sai dai a ɗakin ta din ga jin wani irin sauti mara daɗi, ga sanyi tana ji amma numfashinta tamkar zai ɗauke. Ta buɗe tagogin ɗakin, kasancewar saman bene ne, ta hango wasu irin manyan motoci a harabar gurin. Naɗin kan mutanen ya sanya ta tabattar da Buzaye ne, sai dai suna sanye cikin kaya na alfarma. Nana ta zuba musu ido, tana son ganin fuskar ɗaya daga cikin mutanen da aka buɗewa wata danƙareriyar mota. Wanda haka kurum ta din ga jin kamar akwai wani abu mai matuƙar muhimmanci da yakamata ta sani game da mutumin, da ba ta san ko wane ne ba, duk da yanayin ƙirar jikinsa ba irin na Sayyid ba ne. Wata irin ƙara ta din ga ji cika mata kunne. Ta dafe kunnenta, ta durƙusa hawaye na bin fuskarta. Yanayin gaba ɗaya mara daɗi ne, rashin daɗin da ba za ta iya misaltawa ba sam. Dariyar Giyaz ta din ga ji sama-sama, a hankali dariyar ta cika ilahirin ɗakin. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, wa hifzan min kulli shaiɗanin marid" shi ne abin da ta furta a hankali. "Asmy" ta ji muryarsa cikin karkarwa, yayin da ƙarar iskar sahara take kaɗawa. A galabaice ta ce "Sayyid" "Ma vie" Ta sake cewa "Na'am Sayyid, na fara sarewa, ina jin kamar ba zan yi nasara ba, ba zan ganka ba, na fara karaya." Ta yi maganar tana kuka. "A'a kar ki karaya, kar ki yi mini haka, ina buƙatar ki dan Allah" A hankali take sauke numfashi, idanunta a lumshe ƙirjinta ya yi nauyi kamar numfasihinta zai ɗauke. ***** Daren da Jamila ba za ta taɓa mantawa da shi ba, ya sake maimaita kansa. Daren da ta zama ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar asiri, daren da aka lalata rayuwarta a matsayin maraba da shiga ƙungiyar. Kamar yadda yake ɗabi'ar ƙungiyar, suna sanye da jajayen kaya. Sai dai a wannan karon Jamila ta gusa daga matakin farko na shiga ƙungiyar. Babban abin da ya bawa Jamila mamaki, bai wuce yadda aka fesa wani abu a gurin, sai ganinsu ta yi a dokar daji ba. Wani irin daji mai ban tsoro, mai ɗauke da manyan dogwayen bishiyu, ga shi baƙiƙirin ɗauke da duhu. A wani fili suke a gaban wani dutse, babu tsammanni ta ga wuta takama a tsakiya tana ci bal-bal. Daga bisani dajin ya din ga amsa kuwwa da wata irin ƙara mara daɗin ji. Aka din ga karanto abubuwan da Jamila ba ta iya fahimta. Aka jefowa kowa ƙyalle da abin da zai sadaukar na shekara, kafin zagayowar wani taron. Jamila ta kalli ƙyallen da yake gabanta, jawur da shi. Hannunta na rawa ta ɗauka ta fara ƙoƙarin warwarewa. Da hasken da wutar ta bayar Jamila ta karanta abin da yake rubuce a jiki, da aka rubuta da jini. Ta din ga kallon ƙyallen tare da rubutun. Ta duƙunƙune ƙyallen ta jefa a wuta, kamar yadda kowa ya yi. Sai dai jikinta a sanyaye, gabanta kuma ya tsananta faɗuwa. A wannan karon har da wasu irin dogayen mutane, da ta kasa gane mutanen ne ko kuwa wani jinsin ne, saboda yadda suka shallake kowa tsawo a gurin kuma suna sanye da baƙaƙen kaya har kansu a rufe yake. A wannan karon abubuwan da Jamila ta gani sai da ta tsorata, ashe wancan karon babu abin da ta gani. Ƙungiyar mataki-mataki ce. Su matakin su Alhaji Zailani ma, kowannensu yana da aljanin da kusan bauta masa yake yi. Sun ba wa aljanun jini babu adadi, na makusantansu, da wanda ma ba makusnatansu ba. Aljanun na iya shiga kowane irin hatsari, dan ganin buƙatar irin su ta biya komai wahalarta. Haka suma su Alhaji Zailani, duk abin da Aljanun suka buƙata suna yi musu, domin ɗorewar biyan buƙatunsu. Alhaji Zailani ya kan karɓi saƙonnin nasa Aljanin ta hannun Malam Gambo, wanda su ne manyan malaman da suke gudanar da sihiri a cikin ƙungiyar bayan ɓangaren neman Duniya da samun kuɗi da suke yi. Su kan kira aljanu daban-daban da sanya su aikace-aikace na sihiri. Aljanin Alhaji Zailani ya buƙaci aiki da jinin Nana, da kuma mu'amala da mai irin tauraronta dan biyan buƙatun Alhaji Zailani, sai dai abu ya gagara kamar yadda dariya ta gagari kare. Hakan ya sanya a wannan karon ma ya sake buƙatar jinin Alhaji Zailani, wanda idan ba Shukura ko Yusuf ba, sai dai abin da Shukura za ta haifa. Ɓangaren Hajiya Sa'a ma hakan ne, bayan sanin fa'idar jinin irin na masu tauraron Nana, da yadda bayan haɗuwarta da Nana karon farko, Aljanin ya yi mata bayanin irin tagomashin da za ta samu, idan ya sha jinin Nana, da kuma bautar da zai yi mata idan ya sha jinin ko kuma ta kawo Nana ƙungiya, ta hanyar na ta bokan na cikin ƙungiyar, kuma bokan ya kwaɗai mata damarmakin da za ta iya samu idan ta mallaki Aljanin kan Nana kamar yadda aka gaya wa Alhaji Zailani ma. Ita ma a wannan karon, an sake buƙatar jinin makusancinta, wanda ko dai Abba, ko Alhaji Fatuhu ko kuma dai ɗansa Muhsin, su ne shaƙiƙanta. Jamila a firgice ta farka, a tunaninta ko duk mafarki ne, ta farka da wani irin matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ƙoƙon kanta tamkar zai tarwatse saboda azabar ciwo. Maman Khairat ta taso tana yi mata sannu. Ta ce "Wai ke Jamila wace irin raguwa ce ne haka? Ai yakamata a ce zuwa yanzu kin riga kin saba fa" Hajiya Sa'a ta ce "Dole za ta razana dama, yanzu ta shiga mataki na biyu sai a hankali" Jamila ta ɗan yi shiru tana so ta fuskanci ko a wannan karon ma an yi lalata da ita, amma ba ta ji hakan ba. Sai kanta da yake ta wata irin azaba, ga jikinta tamkar ana ƙona ta saboda zafin zazzaɓi. ***** Shukura ta je awo, likitan da yake duba ta doctor Sabo, ya na ta ƙara kwantar mata da hankali, saboda a wannan karon ma akwai hawan jini a tattare da ita. Har za ta tashi ta tafi ta ce "Doctor dan Allah wata tambaya ce da ni" Ya ce "To Allah ya sanya na sani" "Wai dan Allah ana iya samun mace wadda ba ta da mahaifa?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Eh ana samu, amma a mafi ƙanƙantar lokuta sosai, saboda a cikin mata dubu biyar da ƙyar ake samun mace guda ɗaya da irin wannan case ɗin" Ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "To Doctor kai ka taɓa haɗuwa da irin waɗanda ba su da mahaifar?" Ya girgiza kai ya ce "A'a. Amma me yasa ki ke tambaya?" "Mamana ce ba ta taɓa haihuwa ba, da tana zuwa ganin Likita amma ta daina, sai last week ta je Egypt, aka duba ta ska ce ba ta da mahaifa" Ya waro ido ya ce "Ba ta da mahaifa, kuma ta taɓa haihuwa?" "A'a ba ta taɓa haihuwa ba, step mum ɗina ce" Ya ce "Ikon Allah, kuma ba a taɓa yi mata aiki ba ko makamancin haka?" Ta yi shiru ta girgiza kai ta ce "Bana tunanin haka, amma bari na kira maka ita" Shukura ta kira lambar Hajiya Amina ta ɗaga. Suka gaisa ta ce "Mami, ina Asibiti ne na yi wa likitan da nake awo a hannunsa magana, ya ce na haɗa ku" "Shukura, ba na ce a bar maganar nan ba kawai?" "A'a ki yi haƙuri, na riga na yi magana da shi ai" ta ba wa Doctor Sabo waya. Suka gaisa ya ce "Hajiya garin yaya aka ce ba ki da mahaifa ne?" "Wallahi nima ban sani ba, abin da dai suka ce mini kenan" "A Nigeria an taɓa duba ki a baya an gaya miki hakan?" Ta ce "A'a" "An taɓa yi miki tiyata?" "A'a Likita ba a taɓa yi mini ba" Doctor Sabo ya ce "Ikon Allah, kuma yaushe rabon ki da Al'ada?" Ta ce "Ai dama ba regular nake yi ba, wasu lokutan sai na yi wata shida ma ban yi ba, idan ya zo kuma ba ya fin kwana biyu wataran ma wuni ɗaya ne shikenan" "To dama tun kina budurwa haka ki ke yi?" "A'a gaskiya, da lafiya ƙalau nake al'ada daga baya ne ya koma haka". "Bayan ya koma hakan kin taɓa zuwa an ƙara bincikawa, kuma a baya ba a taɓa gaya miki mene ne ya hana ki haihuwa ba?" Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce "Ko a baya komai lafiya ƙalau ake ce mini, daga baya kuma da ya koma haka, mijina ya ce na haƙura da yawon Asibitin nan, dan haka ban sake zuwa a kan issue ɗin haihuwa ba. Amma ina fuskantar matsalolin gynea sai dai akwai likita da nake gaya wa ya rubuta mini magani kawai". Doctor Sabo ya ce "Idan babu damuwa, akwai buƙatar ki zo Asibiti mu ƙara bincikawa sosai da sosai, wannan serious issue ne" "Doctor na gode sosai da sosai, amma ba na tunanin zan iya zuwa, na haƙura dama buri ne irin na ɗan Adam amma shekaruna sun ja, na bar wa Allah ikonsa." "A'a kar ki ce haka baiwar Allah, akwai Abubuwan da farwuarsu daga Allah ne mun sani, wasu kuma akwai sababi. Wataƙila akwai wani abu na musamman a tattare da ke da ya dace a bankaɗo. Ina doubting a ce Egypt su bayar da result ɗin da ba shi ba ne ba. Amma dai za mu ƙara bincikawa." Hajiya Amina ta amsa masa da to, ta yi masa godiya amma sam ba ta ji za ta iya zuwa a wani bibiya ba, kamar tana tsoron wani abu. Doctor Sabo ya ce lallai Shukura ta lallaɓo ta, su zo Asibiti yakamata a yi ƙwƙƙwaran bincike a kan lamarin. Alhaji Zailani yana kashingiɗe ya kira Doctor Sharif. Bayan sun gaisa ya ce "Ina cikin uzuri ne kwana biyun nan, shi yasa ban ɗaga wayarka ba, ya ake ciki?" "Dama zan gaya maka ne, Hajiya ce ta kira ni tana tambayata wai ko ana iya samun mace wadda ba ta da mahaifa, to ban san dai mene ne ba, amma na ce maya eh." Wata irin zabura Alhaji Zailani ya yi ya ce "Daga nan me ta ce maka?" "Ba ta ce mini komai ba ta kashe wayar" "Shikenan na gode" ya kashe wayar ya dafe goshinsa, "Amina kin fiye taurin kai, dama kaza garin tone-tonenta take tono wuƙar yanka kanta!" Sannu a hankali Nana take bin doguwar barandar, tana hangen masu shigowa da masu fita daga cikin gurin cin abincin. Tun safe motoci suke shiga su na fita. Sai dai ta jima a tsaye a gurin, ba ta ga wani abu da za ta iya riƙa, ko wani wanda za ta tunkara ta yi wa magana ba. Duk manyan mutane ne na alfarma ba ta tunanin akwai wanda ma zai tsaya saurarta, su kuma ma'aikatan gurin da take sanya ran za ta iya tambaya wani abu, ba zaman lafiya suke yi ba. Jiki a sanyaye ta juya, ta kama hanyar komawa gurin girke-girken, Al Hassan yana hango ta, ta ofishin sa. A kan hanyarta ta komawa, suka yi kiciɓis da Hasna. Nana ta ɗan raɓe gefe ta ce mata "Ina kwana" "Lafiya" ta amsa har za ta wuce Nana, sai ta dawo da baya ta ƙara kallon ta ta ce "Au ashe ke ce fitsararriyar nan ko?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a rashin fahimta ne, yanzu da na san wacece ce ke ai ga shi na gaishe ki" Ta so ta yi wani abu da za ta yarfa Nana da za ta saka ta ji zafi a ranta, amma sai ta kasa. Gaba ɗaya ma sai ta ga Nanan kalar abin tausayi a yau, kamar ba ta da kuzari ko kaɗan fuskarta ɗauke da damuwa. "Amm ki kawo mini shayi ofishina, shayin girfa, kar kuma a cika sugar ba na son sugar da yawa" "To ina ne ofishin" "Ki tambaya" ta amsawa Nana tana yin gaba abin ta. Nana ta koma gurin girkin, ta fara ƙoƙarin dafa shayin girfa, saboda babu shi, Adama ta saka ta wani aikin. Wasu lokutan har rasa yadda za ta yi take yi, sai dai ta kan jure dan kar ta gaza ta sare, dan jikinta yana bata zamanta a gurin nan ka iya sanyawa ta yi nasara. Sai dai abinka da ɗan Adam, wasu lokutan ta kan bujire. Ta kammala ta tambayi ofishin Hasna, aka nuna mata ta kai mata shayin har can. Tana tare da Al Hussain  ta tarar da ita, da wasu manyan mutane guda uku a office ɗin. Cikin girmamawa Nana ta gaishe su, cikin gurɓatacciyar hausa suka amsawa Nana. Hasna ta sake mayar da Nana, wai ta kawowa baƙinsu shayi. Haka Nana ta koma, ta sake kai musu wani shayin, duk da hakan ba aikinta ba ne ba. Ta fito daga ofishin, Al Hussain ya biyo ta yana kiran sunanta. Ta tsaya ta waiwayo ta jira ya ƙaraso. "Nana ko haryanzu jikin ne ba ki warke ba?" Cikin ƙarfin hali ta girgiza kai ta ce "A'a jiki na warke" "A'a idan ba ki warke ba, na saka a kai ki Asibiti, sai a baki hutu" Ta girgiza kai cike da ƙwarin gwiwa ta ce "A'a na ji sauƙi fa, zan ci gaba da aiki in sha Allah, na gode sosai da sosai" Ta juya ta ci gaba da tafiya. Shi dai haka kurum Nana tana ba shi tausayi, sai dai babu wata dama da ta bari, da za a iya zama da ita a ji matsalar ta, ko za a iya taimaka mata. Ya lura ko a cikin ma'aikatan ba ta da sukuni, ba ta sakin jiki da su. Kuma yanayin ta ƙarara yake bayyanar da damuwa duk da tana da ƙoƙarin dakiya. ***** Alhaji Zailani ya din ga kiran lambar Hajiya Amina. Gaba ɗaya ya rikice hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, yana tsoron kar ta aikata wani abin da zai kawo matsala. Ga jirginsa sai washegari zai koma Kano, ga shi yana da manyan uzururrukan da yake son yi a Abuja, da ba zai iya tsallakewa ya bar su ba. Shukura ta je har gida, ta sake samun Hajiya Amina ta lallaɓa ta a kan ta amince su je gurin Doctor Sabo, amma ta ce babu inda za ta je. Da ƙyar ta amince ta ce ba za ta je a ranar ba sai washegari. Shukura ta ɗan numfasa ta ce "Mami ba na son yi miki maganar nan ki na cikin damuwa, sai dai nima ba a son raina ba, na rasa abin da yake yi mini daɗi" Cikin damuwa Hajiya Amina ta ce "Dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar wannan cikin ma ya sake samun matsala mene ne?" Ta numfasa ta ce "Sagir ne fa yake ta ƙoƙarin dawo da tsohuwar matarsa" Hajiya Amina ta ce "To shi ne ki ka damu haka? Dan Allah ki rabu da shi ya ƙarata, ki lallaɓa ki haihu lafiya kalau, kin ga ga hawan jini ki na fama fa" "Wallahi Mami zuba masa idon na yi, takaicina bai gaya mini ba, su na ta ƙwarbai da Hajiya, ta ce ba zai dawo da ita, a bakin ƙannensa nake ji". "To babu ruwanki, su sha'anin dangin mijin nan ba a zaƙalƙale musu, idan ta dawo ɗin ma wataƙila su tattara su haɗe kai, babu ruwan ki ki kula da kan ki, ki sauka lafiya" Shukura ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, sannan dan Allah Mami ke ma ki kwantar da hankalinki, nutsuwarki ita ce ta wa, dan Allah Mami ki kwantar da hankalinki kema" "Wallahi Shukura ƙarfin addu'a ya sanya mini nutsuwa da tawakalli, yadda ku ke yi mini biyayya da ke da Yusuf ko ni na haife ku, Alhamdillah na san iya abin da za ku yi mini kenan. Kuma na san ko yau na bar Duniya za ku tuna da ni ku yi mini addu'a" Idon Shukura fal hawaye ta ce "Mami ke uwa ce abar alfahari, har Duniya ta naɗe ke uwa ce a gare mu, kuma muna alfahari da samun ki" Suka rungume juna da ita da Shukura, Hajiya Amina ta ci gaba da gode wa Allah, tana jin da natan ta haifa wataƙila ma ba lallai su yi mata biyayya haka ba. Sai bayan tafiyar Shukura, sannan ta shiga ɗaki, ta tarar da kiran wayar Alhaji Zailani rututu. Yana ganin kiranta ya ɗaga, bai tsaya amsa gaisuwar ta ba, ya hau tambayarta abin da ya hana ta tafiya. Ta ce "Matsala aka samu, kuma na yi ta kiran ka a waya, ba ka ɗaga wa" "Matsalar me?" "Ba komai, idan ka dawo ma yi magana" Ya ce "Yanzu nake son ki gaya mini koma mene ne, meye dalilinki na kiran Sharif kina tambayarsa ana haifar mace babu mahaifa?" Ta ce "Amma laifin me na yi haka? Na tsaya a Egypt su duba lafiyata ne, tun ina can nake neman ka, ban same ka ba, sakamakon gwajinsu ne ya tabattar da ba na ɗauke da mahaifa" "To uban waye ya ce ki je? Ba sai da na ce miki ki bar batun yawon neman haihuwar nan ba, da yake ban isa na saka miki doka ki bi ba, kin raina ni bani da mutunci a idonki?" Duk bayanin da ta so ta yi masa, yaƙi saurararta, ya din ga zazzaga mata bala'i. Ranta ya ɓaci, ta ga Sharif bai kyauta mata ba, ya za a yi daga tambayarsa abu ya ɗau waya ya kira shi ya gaya masa, ai gara ta gaya masa da kanta, duk da ba wani abin ta ce masa ba, tambaya ce kawai ta yi masa. ***** Ɓamgaren Alhaji Fatuhu, Hajiya Suwaiba kamar ta yi bindiga, ganin ya amince ana yi masa maganin gargajiya, a ganinta dan Fadila ta saka baki ne, ta lallaɓa shi yake yi. Yanzun ma Fadila tana ta ƙoƙarin kunna garwashin da za ta yi masa turare, gefe ta kunna mp sautin ayoyin ruƙiyya su na tashi a hankali. Ya kalli Fadila ya ce "Baby, ina fatan dai magungunan nan, babu wani abu na kauce hanya a cikin su?" Ta girgiza kai ta ce "Haba Daddy, kai ma ka san ba zan yi duk wani abu da zai taɓa imaninmu ba in sha Allah, Kawu ne duk ya bayar da su, kuma ka san shi ma masanin Addini ne sosai. Babu wani na shirka a ciki." Ya ce "To ki yi haƙuri, kawai da na tambaya ne, kin san yanayin abin, kar garin magani mu kauce hanya na je na mutu a mummunan tafarki, ya zamana na kasa jure ƙaddarata na kauce hanya" Fadila ta ce "In sha Allah ba zaka mutu yanzu ba, za ka samu lafiya" "To ki yi haƙuri, na ga kin ji haushix Ta girgiza kai ta na ɗan murmushi ta ce "A'a ban ji ba" "Kin ji mana, kin tura baki gaban ne ba ki ji haushi ba?" Sai kuma suka yi dariya a tare. Ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake magana ba, na yarda da ke, ba zaki cutar da mu ba" Hajiya Suwaiba ta shigo ɗakin, tana basarwa jin yadda ɗakin ya ɗume da ƙamshin jan almiski, da ƙaurin hayaƙi. Ta ɗan taɓa baki a ranta ta ce watakila ma a cikin wannan tsiyatakun take mallake ka. Ta ajiye masa kwanukan Abinci, ta juya za ta fice. Ya ce "Ba magana ne?" "Sannu ya jiki?" Ta faɗa a daƙile. "Jiki Alhamdillah, a hankali ji nake jikina ya yi daɗi, na ɗan samu sassauci daga abin da nake ji kamar an ɗaure ni, ba na iya motsi sai da ƙyar da dabara, da ƙirjina da yake yi mini nauyi nake jin kamar an toshe mini baki da hanci da kokowa nake numfashi" Duk da tana jin haushinsa sai kuma ta saki fuska ta ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa kenan? Ubangiji Allah ya ɗorar da sauƙi, dama komai nufi ne na Allah" Ta kalli Muhsin da yake ta tattaɓa kwanon abincin da ta kawo. Ta ce "Kai ɗan lukuti acici, ka zubar mini da Abinci sai ka biya ni. Ki zuba masa abincin ko ci zai yi" Ta yi maganar sama-sama tana ɗan kallon Fadila. Duk da matsanancin kishin da Hajiya Suwaiba take yi da ita, yanayin yadda take yi wa Muhsin wasu lokutan ya sanya Fadila ba ta fiye jin haushinta ba. ***** Hasna kuwa ta sako Nana a gaba, bayan aikin da take yi, ta din ga sanya ta wasu ayyukan daban da ba sa cikin jadawalin wanda aka ɗauke ta yi. Wasu lokutan sai ta gama aiki, ta koma ɗakinsu, sai ta saka a taso ta, ta saka ta aiki. Abin ya ishi Nana amma ta danne. A wannan karon ma, har ta yi shirin kwanciyar, aka zo aka kira ta. Kawai ta ji a ranta, ko Hasna za ta kashe ta yau, sai dai ta kashe ta, dan ba za ta yi mata kowane aiki ba, sai dai ta kore ta. Ƙarafe goma sha ɗaya na dare, amma tana ofishinta ba ta tashi ba. Ko da Nana ta je, tsayawa ta yi ƙyam tana jiran ta ji me Hasnan za ta ce. Sai dai ta ci gaba da aikin gabanta, sai da Nana ta fara ƙosawa, sannan ta kalle ta ta ce "Amma an ce 'yar Nigeria ce ke ko?" "Eh" Nana ta amsa a ƙufule. Ta ɗan ƙura wa Nana ido sannan ta ce "Ina da wasu baƙi ne gobe in Allah ya kaimu " Nana ta ɗago tana kallonta, ta ji ina ne ƙarshen zancen, dan kullum cikin baƙi suke kamar gurin boka. "Dan haka ba aikin gurin cin abincin nan za ki yi ba gobe in Allah ya kaimu, aikina za ki yi. Zan saka a sanar musu ma. Ina son ki yi Abinci mai kyau da daɗi na Nigeria. Ina son na sauke su da shi. Wajen la'asar za su zo, dan haka za ki dafa abin karayawa, da abincin rana da na dare, za a zo a ɗauka" Nana ta yi ajiyar zuciya jin ba wani aikin rainin hankalin Hasna ta saka ta ba. "Allah ya kaimu, zan iya tafiya?" Hasna ta ce "Saurin me ki ke yi ne?" "Na gaji ne sosai, bacci nake ji ina son na samu na tashi da wuri" Ta jinjina kai ta ce "Ya yi je ki" Nana ta fice ta tafi ɗakinsu. Sai dai duk gajiyar da ta yi, bacci ya gagari idanunta. Tun bayan sallar Asuba, ta tafi kitchen ɗin ta fara aikin da Hasna ta saka ta. Sai bayan Azahar ta kammala komai, Hasna ta aiko aka ta ɗauki Abincin. Nana ta fara shirin tafiya ta je ta yi wanka ta huta. Adama ta ce "Ina za ki je kuma ga ayyukan kitchen fal?" Nana ta numfasa ta ce "Ki yi haƙuri, Hasna ce ta saka ni aiki, ta ce idan na gama, na je na huta" "A'a ba zai yiwu ba, ni ce mini a aka yi kawai za ki yi mata aiki, dan hakan idan kin gama ki saka hannu ku ci gaba da aikinmu, wa za ki bar wa wannan aikin?" "To ki yi haƙuri, na gaji gaskiya ba na jin daɗi" kawai ta fice, tattaunawa suka shiga yi a tsakanin su, yadda za su kawo ƙarshen Nana a gurin baki ɗaya. A ƙarshe suka yanke shawarar, su ƙara ƙaimi su ɓata ta a gurin Hasna, ganin yadda ita ma ta sako Nana a gaba da tsangwama. Bayan sallar isha'i, Nana ta daɗe a zaune tana tasbihi, tunanin gidansu da 'yan uwanta ya addabi zuciyarta, ga shi abin da ta fito neman har yau babu labari. Ta daɗe tana addu'a kafin ta nemi guri ta kwanta. Washegari ma su na ta aiki tun safe har Yamma, sai ga Hasna ta shigo. Duk yadda Hasna take da kyau, ita da Al Hussain, wannan da suka shigo ta fita kyau, tamkar balarabiya, jawur da doguwa sai dai siririya ce sosai. Fuskarta ta sha make up, sai zuba ƙamshi take yi. Ta yafa ɗan siririn mayafin abayarta a kanta. Sai kallonsu take ɗaya bayan ɗaya tana yatsuna fuska su na yare ita da Hasna. Duk suka gaishe su, Nana kuma ta yi burus. Hasna ta nuna mata Nana ta ce "Kin ganta nan" Asal ta yamutsa fuska ta ce "Ya na ganta baƙa ƙirin haka, ina fatan ba na ƙazanta ba ne?" Nana ta yi mamakin jin Hausa raɗau a bakinta. "Ke ina ruwanki da baƙinta, ba dai Abinci ya yi ba?" "Eh kin san ba na son ƙazanta ne" Hasna ta ce "Sauran ma'aikatan namu ma ai akwai baƙaƙe, kuma kema kin san da ba ta da tsafta, ba zan saka ta yi miki girki ba.Ke Nana ba ki ganni da baƙuwa ba ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle su, ta yi shiru tana wasa da wuƙar hannunta, saboda ciwon da maganganun da suke yi ya yi mata, na cin zarafin baƙar fatarta da danganta ta da ƙazanta, duk ba wai duhu ne da ita sosai ba. Shiru Hasna ta yi ta kamo wata hirar, ganin alamun idan ta matsa Nana za ta yarfa ta ne a gaban baƙuwarta. Ba a taɓa ma'aikacin da ba ya shakkar ta ba sai Nana. Duk abin da ta saka ta na aiki za ta yi, amma ba ta son rainin hankali. Bayan sun fito Asal ta tsaya ta kalli Hasna ta ce "Hasna" "Na'am" "Ina ga yarinyar nan ta yi dai-dai da abin da nake nema" "Wace yarinyar?" Asal ta ce "Wannan 'yar Nigeriar, ina buƙatar za ki ba ni ita" Ayshercool 08081012143 70 Sai da Nene ta tabattar Nana ta ɗan nutsu, sannan suka kwanta. Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta ɗan sai abubuwan da za ta buƙata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can ɗin yake ba. Nana ta ce "Ni babu abin da nake buƙata, ki bani wani abin na riƙe a hannuna, sauran kuɗin kuma ki riƙe saboda kula da Muhsin na s... "Biyana za ki yi kenan dan na riƙe miki Muhsin?" Nene ta katse ta. "Allah ya baki haƙuri, ba haka nake nufi na, na ga dole ɗan abubuwan buƙatunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuɗi sun" "Kuɗinki ba su isa su saka na riƙe miki ɗa ba ko?" Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi haƙuri. Nene ta ce "Ba zan yi haƙurin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faɗa ki hau bani haƙuri, wato in ci kaina to sai na idar" Nana ta yi mata shiru ta yi faɗanta ta gama. Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na ɗan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta ɗauki wani abin ta ce ba za ta ɗauka na. Nana ta haɗe rai ta ce "Eh dama ba ki ɗauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karɓa" "Ni za ki yi wa wayo, na ji ban ɗauke ki 'yar ba, ni ga ɗana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ƙyar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karɓi abin da Nana ta saya mata. Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da ɗa, amma ban taɓa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?" Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?" "A'a kawai dai tambaya na yi " "Yana can Nigeria" "To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?" "Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki" Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haɗu ba". Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta ɗauke ɗanta ta tafi da shi. Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta ɗiɗɗinka kayan da ta sayo, ta sake haɗa jakarta ta ɗauki muhimman abubuwa a kayanta. Duk da a ɗaki Nene take rufe mata su, ba ta taɓa ganin alamar Nenen tana yi  bincike a cikin kayan ba. ***** Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini. Gaba ɗaya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaɓi ya ƙaru. Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faɗin za ta sake bayar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan ɗan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba ɗaya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron. A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ƙura mata ido ta yi tana bin ta da kallo. Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiɗe. Jamila ta yi tsaki ta shige ɗakinsu. Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba. ***** Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa. Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga saƙo" Sharif ya yinƙura ya tashi ya tafi. Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaɓar da ki ka ƙetare layin da bai kamata ki ƙetare ba, kina ƙoƙarin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi haƙuri da duk matakin da zan ɗauka a kan ki. ***** Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar. Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan raƙumi yana biye da su a cikin saharar. Kamar an taɓa ta ta ɗan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ƙirjinta. Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ƙashinta, ta ɗaga ido tana ɗan waige-waige ta ga ta ina za ta gano Ƙaisar ko wata baƙuwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba. Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai. Nana na son karanta Symbols ɗin da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai ɗauke da ƙaton gate ta ciki suka wuce. Ba ƙaramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ƙarasa ba sai bayan magariba. Kewar ɗan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da Maraɗi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege. Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ƙasaita a cikin gurin. A ƙofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko ƙafafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya. Ya buɗe bayan motar ya ɗaukko ƙatuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwaƙa. Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ƙawatu ya yi kyau sosai da sosai. A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan" Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan ɗin, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba" "Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai" Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice. Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla. Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido. Can ta ji ƙarar mota, aka buɗe ƙofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buɗe gate ɗin, aka shigo da wata haɗaɗɗiyar mota aka yi parking ɗin ta. Aka buɗe ƙofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta ɗaura mayafin a wuyanta, kanta babu ɗankwali. Har bakin ƙofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matuƙa, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa. Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ƙasar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki ɗaya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira. Ba ta san iya adadin lokacin da ta ɗauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta. "Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ƙauyen ki ke ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta. "Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?" "Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?" Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ƙarfin hali. Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ƙasa ta miƙe ta kwanta. Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci" Daga haka ta tashi ta bar falon. Nana ta tashi ta shiga kitchen ɗin, ta tarar da Abinci, ta ɗauka ta ci sannan ta ɗan dawo hayyacinta. A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla. Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal. Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana. Nana tana nan zaune, aka zo aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, ta tashi a ɗan tsorace ta buɗe, wani mutum ya miƙo mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi. Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ƙawayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaɗe-kaɗe har kusan ɗaya na dare su na abu ɗaya, suka hana Nana bacci. Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa? Sai washegari sannan ta saukko ƙasa, a lokacin ƙawayen nata duk sun tafi. Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ƙara kwanar mini a falo, ga ɗaki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba ɗaya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da ƙawayena, da sauran aikace-aikacen gida. Abu na farko dalilin da ya sanya na ɗaukko ki, ke ba ƙabilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaɗai za ki yi mini" Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch ɗin za a kai ta aiki ba, wannan zuƙaƙƙiyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuɗi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaɓi kowa ba sai ita?. "Ba kya ji na ne?" "Na ji" "Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so". Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faɗin ƙasar nan ki rasa wanda za ki ɗaukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba" "Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki buƙata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ƙulewa. ***** Gaba ɗaya Shukura ta burkicewa Sagir, ba ɗaga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja ɗaya take harkokinta, da gaske take ƙoƙarin gano abin da mahaifinta yake ɓoyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta. Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar. Ɓangarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ƙara gyara shi, aka haɗa gidan gaba ɗaya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya ɗau harama. Duk yadda ya so ya lallaɓa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi. Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ƙawayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ƙoƙarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta. Tana tsaka da nazarin yadda za ta ɓullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati ɗaya zamu bar nan, zamu je asalin inda na ɗauke ki ki yi mini aiki a gurin" Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me? "Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taƙaice. ***** Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu. Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ƙorafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita. Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka. Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai. "Ƙanwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da ɓarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi" Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi haƙuri ka yi aurenka kawai, ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin" "A'a ki daina faɗa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ƙarfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta. Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ƙuro mata ido tamkar ba ta taɓa ganinta ba. "Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Jamila ta ja tsaki, tana ƙoƙarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila" "Na'am mene ne?" "Ki ɗauki saƙonki mana" Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saƙon?" "Na cikin jakarki" "Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?" "A'a ni tuni kawai nake yi miki da saƙonki na cikin jakar" Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saƙon? Miƙo mini jakar dai na gani" Suwaiba ta ce "A'a ba zan taɓa miki jaka ba" Jamila ta janyo jakar ta fara buɗewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura ƙiris ta kurma ihu, ta rikice gaba ɗaya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita. Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana ƙyaƙyatawa tana kallon Jamila. Gaba ɗaya Jamila ta kiɗime ta rasa abin da yake yi mata daɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta. ***** Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan ƙafafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan. Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan baƙin ciki. Da ƙyar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?" Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa ɗaya daga kujerun da ke ajiye a gurin. Alhaji Zailani ya zauna suka ƙara gaisawa "Bani labari, ya aka yi sauƙi ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?" Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan ɗaurewa da nake ji a jikina ya yi mini sauƙi, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daɗewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux "Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?" "A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba" Alhaji Zailani ya miƙe ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi" "Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?" "Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin ƙunar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taɓa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba. ***** Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faɗa cikin matsanancin ɓacin rai. "A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba ɗaukar ta aiki muka yi saboda buƙatar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haɗa kai ku yi mata haka wannan wulaƙanci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar ƙasarmu ba" "Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da ɗa ma" "Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da ƙarfi da kuɗi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba" "Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba taƙi yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba" "Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku" Ta kwaɓe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya ɓata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?" "Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi ƙoƙarin hana Asal ɗaukar Nana. ***** Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan. Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai. Ta sha aiki ta gama, ta ɗan zauna a falo tana hutawa, sai ga ɗaya daga gayyar ƙawayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi" Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka" "Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa" "Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu" "Ke, kin san wace ce ni ki ke gaya mini haka?" "Ban san wace ce ke ba, kuma ba na buƙatar sani" Asal ta saukko tana tambayar lafiya. Ta gaya mata abin da ya faru, ta kalli Nana ta ce "Wai ke me yasa ba ki da mutunci, ban gaya miki dole ki girmama baƙina ba, mene ne a cikin dafa shayi mintinan nawa ne kin yi kin gama?" Ta kalli Asal ta ce "Ki yi haƙuri, wallahi ko cokali ba zan iya sake ɗauka ba, yau na bautu a gidan nan ke kin sani, kuma ban taɓa yi miki ƙorafi ba, amma yanzu dai na gaji gaskiya" Suka juya yare suka yi magana, ba ta san me suka ce ba, ta ga sun koma kan bene. Washegari da wuri suka ɗau hanya, sai dai ga mammakin Nana, har da rakiyar jami'an tsaro, kuma a wannan karon shigar Shadda Asal ta yi, an yi wa shaddar aiki tun daga sama har ƙasa. Mota ɗaya suka hau, ta ce Nana ta hau gaba, ita kuma ta hau baya. Sai da aka kuma wata tafiyar mai nisa, sannan ta ga sun tunkari wani  irin ginin ƙasa tamkar ginin ganuwar Kano. Ginin ya ƙayatar da Nana sosai da sosai. Jami'an tsaro ne suke gadin ƙatuwar ƙofar gurin, da wasu Buzaye farare tas sanye da rawani. Nana kamar ta ce a tsaya, ta duba buzayen nan ɗaya bayan ɗaya ko za ta ga Sayyid ɗin ta cikinsu. Sai da motar su ta tsaya, suka sauke glass ɗin motar. Da Hausa suka gaisa, suka yi mata sannu da zuwa, ɗaya daga cikin su ya kalli Nana ya ce "Wannan fa?" "Baƙuwata ce" ta ba shi amsa, ya jinjina kai motar ta shige. Su na shiga Nana ta ga ai gari ne guda a cikin ganuwar nan. Sun ɗan yi tafiya kafin su shiga wani ƙaton gida. Nana ta tsaya tana ganin yadda aka yi wa ginin ƙasa wani irin ado mai ƙayatarwa. Tun da suka doshi shiga gidan, ake gaida Asal cikin girmamawa, ita kuma ta yi fuska sai taku take cike da ƙasaita, kamar ba ita ce suke rashin hankali da ƙawayenta a wancan gidan ba. Wannan gidan saɓanin wancan da mutane a ciki, kuma da alama duk a ƙarƙashin Asal suke. "Wace ce ita?" Nana ta tambayi kanta. Sai da suka ƙarasa wani falo, sannan ta yi wa wata dattijuwar magana da yaren su. Matar ta kalli Nana ta ce "Bahaushiya ce ke ko? Zo mu je na kai ki masauki" Babu musu Nana ta bi ta, matar ta kai ta wani daki ta ce nan ne ɗakinta. Sai da Nana ta kwana biyu a gidan, ba ta sake ganin Asal ba, ba kuma ta aikin fari ba ta na baƙi kawai tana zaune, sai dai za a kawo mata Abincin safe, rana da dare sau uku a rana. Sai dai babban abin da ya dame ta, tun da ta shigo gidan, network ɗin wayar ya sauka gaba daya, ko ta kira Nene ba ta shiga sam. A kwana na huɗu, da daddare dattijuwar matar nan ta zo ta kira Nana. Babu musu Nana ta tashi ta bi bayanta. Sun yi 'yar tafiya su na ratsa faluka masu kyau da ado, sannan suka bi wata ƙofa. Sanyin A.C ya daki Nana, ga wani irin haɗaɗɗan ƙamshi. Asal ta hahakimce a kan kujera kaɗa ƙafa. Ta kalli dattijuwar ta ce ta jira a waje. Daga ƙasa wata matar ce a zauna a kan carfet, ta gurfana kamar tana jiran Asal ɗin ta gafarta mata. Nana ta yi turus tana tunanin a ina za ta zauna, sama ko ƙasa. Matar ta kalli Nana cikin zare ido ta ce "Ke ki rage tsawon ki, kin tsaya mata a ka" Nana ta ja guri ta zauna a kan carfet ɗin ita ma. Asal kamar ba za ta yi magana ba, sai da ta gama iyayinta ta sauke ƙafarta ƙasa ta dubi Nana ta ce "Amm na saka an kirawo mini ke, saboda ki san abin da na kawo ki gidan nan ki yi. Ke dai da ganin gidan nan kin san ba gurin da za a yi wasa ne ko shirirta ba, babban gida ne na mulki. Saboda dalilin girki da kuma wani dalili na ƙashin kaina, ya sanya na kawo ki gidan nan. Ba a ɗaukko bare wanda yake ba jinin gidan nan ba, ko ƙabilarmu ba ya yi mana aiki, amma na ga wasu abubuwa a tattare da ke da ya sanya na kawo ki cikin gidan nan. Kamar yadda na gaya miki, ina ƙara jaddada miki, zaman ki a gidan nan dole ki yi taka tsantsan, babu ruwanki da shishshigi, saka ido, gulma ko kuma shiga abin da babu ruwanki. Sannan kar ki kuskura wani ya ce zai haɗa kai da ke a yi wani abu, rayuwarki za ta iya salwanta ba tare da kowa ma ya sani ba, dan haka sai ki san irin zaman da za ki yi." Nana ta yi shiru ta gama sauraren ta, sai dai har a lokacin ba ta ji dalilin da ya sanya Asal kawo ta gidan ba, dafa abinci kowa ma zai iya mai yasa sai ita. Wannan matar da ta tarar a zaune, ta tafi da ita, ta kai ta gurin da ake girke-girken abinci, da gaya mata yadda jadawalin girke-girken gidan yake. Ta ɗaukko kayan ds Asal ta bayar a ba ta, na kayan shafe-shafe da mayukan wanka zuwa kayan sakawa. Da Nana ta koma ɗakinta, ta kalli kayan ta fara tunanin Allah ya sa ba kwance Asal ba ne, dan gara ta saka kwancen Ashura da ta saka na Asal, da ba ta da mutunci. A washegari Nana ta fara aiki a wannan madafa, sai dai madafar daban-daban ce. Akwai wadda ake girkin da ma'aikatan gidan ne suke ci, akwai wadda na baƙin da suke zuwa ne, sai kuma masu girka wa Asal abinci daban, dan haka Nana na cikin masu yi wa Asal girki. Sosai matar nan ta ƙara jan kunnen Nana, a kan ta kula da kanta, dan muddin aka samu matsala ba za ta sha ba. Nana a ranta ta ce "Ji wata jaraba, da wannan wahalar mutum ya girka abin da zai ci mana da kansa." Kwana huɗu da fara aikinta, ranar Alhamis da daddare, tana shirin kwanciya, aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta. Ta tashi ta buɗe, ta ga shugabar girke-girke ta gidan, kamar yadda aka gabatar mata da ita a baya. "Ki sako hijjabinki, ki biyo ni" Nana ta saka hijjabinta ta fito tana tunanin ko lafiya. Harabar gidan matar ta yi, Nana ta bi bayanta, ta nuna mata mota. Nana ta kalli dare ya yi kuma an zo da mota an ce a tafi da ita. Cike da mamaki Nana ta shiga motar, sai ta ga mutum uku, da su ma duk tare suke aikin girkin a gidan a cikin motar. Ta shiga ta zauna, ita ma shugabar ta su ta shiga. Nana ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah ina za mu je ne?" "Za ki gani" "Eh amma na ga dare ne fa" "Idan mun je za ki ji dalilin fitar" Nana ta yi shiru tana tunani, ita ba ma wannan ba, hankalinta ya koma kan rashin samun damar kiran waya da ba ta iya yi, kuma ba a kiranta ya shigo. Dan sai da ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin, ko matsalar daga wayarta ne, ta ce mata kar ta kuskura ta bari ma a san tana da waya, dan sai an ƙwace ta. Tana ta zancen zuci, har suka isa inda aka tsaya suka sauka, aka shiga da su. Asal ce a tsaye, tare da dattijuwar matar da ta saka ta raka Nana masauki. Suna tsaye a cikin ɗakin Nanan. Asal ta ce "Zazzage mini kayanta, ki ɗaga mini komai ɗaya bayan ɗaya" Ayshercool 71 Ɗaya bayan ɗaya, aka din ga zazzage kayan Nana. Aka zazzage su tsaf aka Azzage jakar da ta zuba kayan turarukanta da mayukan shafawa, duk ba ta ga wani abu ba, sai jakar gurin sarkin baka. Ta nuna jakar ta ce "Mene wannan?" Ta ɗago jakar ta ce "Jaka ce" "Buɗe ta ki zazzage na gani" Ta fara kokowar buɗe jaka, amma babu gurin da zata buɗe ta. Kawai ta ce "Shikenan" ta fice ta bar ɗakin. Can gurin kuma Nana tara su aka yi, su shida. "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya aka kawo ku nan, to zaɓo ku aka yi saboda an yarda da amanarku, ana daf da yin taro da Sultan da kuma dukkanin Imams na gidan nan. Dan haka ku aka zaɓo za ku yi girki na musamman. Amma ku sani kamar yadda wasu sani wasu ba su sani ba, muddin aka samu wata matsala ko ƙware wani ya yi, a sanadin abincin da ku ka dafa, to ku tabattar da rayuwarku za ku biya. Dole ku yi taka tsantsan ku kula." Matar ta yi maganar daki-daki. "In sha Allah" suka amsa mata. Ta ce su bi bayanta, suka je wani ƙaton guri, ɗauke da nau'oin kayan masarufi kala-kala. Ta yi musu bayanin da su ne za su yi amfani su yi girkin, sannan ya zama dole su sanya wa bakinsu sakata su yi aiki cikin amana, kuma kada wanda ya san su aka zaɓa da za su yi wannan girki. Nan ma suka amsa, ita dai Nana sai kallo da ido, dan abubuwan sun daina ba ta mamaki, wannan maganar ce ta sanya aka taso ta a daren nan, sai ka ce wanda za su girkawa wasu waliyyai abinci. Ko da aka mayar da su Nana gida, ta sha mamakin ganin kayanta a hargitse a cikin ɗaki. Da mamaki ta ƙarasa kan kayan nata, ta ɗaɗɗaga. Cikin takaici Nana ta tashi ta fita, sai dai kowa ya tafi makwancinsa ya kwanta. Kawai ta ji taku a bayanta. Ta waiwaya ta ga Asal na fitowa. "Har kun dawo kenan?" "Eh, sai dai na shiga ɗakina na tarar da an caje mini kayana an zubar da su a ƙasa, ban sani ba ko kina da masaniya a kan haka?" Asal ta ce "Me yasa ki ka zarge ni?" "Saboda na ga ba a gudanar da komai a gidan nan sai da izninki" Asal ta yi murmushi ta ce "Haka ne, kina da kaifin ƙwaƙwalwa kamar yadda na yi tsammani, ni na saka aka caje kayanki saboda na san da wa nake zaune" "Me yasa ba ki tambaye ni abin da ki ke buƙatar sani ba, za a caje mini kaya" "Saboda a ƙarƙashina ki ke, a gidana ki ke zaune dole na sani idan da wani abu da ki ke tattare da shi na cutarwa" Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ƙarƙshinki, ina da personal life ɗina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ƙulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?" "Yi ƙasa da muryarki, kar ki kuskura ki ɗaga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi" "Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini ɗaki ki taɓa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba." Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haɗiye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru" Nana ta yi mata banza, ta koma ɗakin nata, ta gyara kayanta tsaf. Ta kulle ɗakin ta koma ta ɗaga katifar ɗakin, ta ɗaukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta ɓoye su. Haka kurum take jin kayan na buƙatar sirri. Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata. ***** Shukura na zaune a ɗakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buɗe ƙofa ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ƙamshin turare take zubawa. Ya sha manyan kayansa, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji. "Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haɗiye maganar da ya yi niyyar yi. "Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa. Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba. Ya matsa kusa da ita, ya riƙo hannunta, ta fizge hannunta ta haye kan gadon ta kwanta. Bai ji haushin abin da ta yi masa ba ko kaɗan, ya san idan ba ta son sa ba za ta yi kishinsa ba, sai dai ita ma Yusra tana buƙatarsa tun da tun farko bai kamata ya sake ta saboda larurarta ba. Ya tashi ya kashe mata fitila, har zai fita ya koma gaban gadon, ya durƙusa daidai fuskarta ya ce "Ki yi mini afuwa Shukura, ban yi haka domin na cutar da ke ba, ko na muzguna miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki saboda lafiyarki da abin da yake cikinki" Daga haka ya tashi ya fice. Sai da ya fita sannan ta ba wa hawayen da suka maƙale a ƙirjinta damar zirarowa, zuciyarta ta din ga yi mata ƙuna, tamkar ta tashi ta bar gidan. Duk da ya fita da damuwar halin da Shukura take ciki, amma bayan wani ɗan lokaci tuni ya manta, suka ci suka ƙoshi da shi da Yusra. Bayan sun gabatar da salla, sun yi addu'oi, suka yi zamansu kawai su na hira. Sai gurin ɗaya saura sannan suka tashi suka kwanta. Yadda Sagir yake murna da kasancewa da Yusra, ko aurensu na fari bai yi haka ba, tuni wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su, daga shi har ita. Shukura kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, ga wani irin zafi da ya addabe ta duk da na'urar sanyaya ɗaki da ke cikin ɗakin. Washegari sai ƙarfe sha ɗaya na safe ya shiga ɗakin Shukura. Idonta kawai ya kalla ya ga alamun rashin bacci a tattare da idanunta, sun yi jawur sun kumbura. "Oum Haidar" ya kira sunanta, yana zama a kan gadon, tana shan tea. "Ina kwana" ta faɗa a taƙaice. Idanunsa ya sauka a kan ledar da ya kawo mata, babu alamar ko taɓa ledar ta yi. "Shukura me yake damunki ne haka? Na kawo abu ko taɓawa ba ki yi ba, kin yi bacci makuwa" "Sagir, dan Allah ka tashi ka bani guri, ni bana buƙatarka a kusa da ni, kaɗaici nake so" "Ni ki ke cewa na fita na baki guri?" Ya yi maganar yana nuna kansa. Ƙoƙarin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata take yi, amma abu ya gagara kawai ya fara zubowa ba tare da ta shirya hakan ba. Jikinsa ya yi sanyi, ganin yadda take kuka sosai da sosai. Cikin kwantar da murya, yake ƙoƙarin rarrashinta, amma ta tashi ta shige banɗaki ta bar shi a gurin. Ya yi shiru ya rasa abin da yake yi masa daɗi, shi babbar damuwarsa ma cikin da take ɗauke da shi, ga matsalarta ta hawan jini. ***** Tamkar bayi haka su Nana suke aiki, kullum za a ɗaukkosu daga wancan gidan da Asal take, a kawo su nan su wuni su na aiki. Har mamaki take yi wannan mutanen su kuwa har su nawa ne, dan kamar har da almubazzaranci a cikin lamarin. Sai dai kowa cikin kaffa-kaffa yake aikin tare da fatan kar wani abu ya biyo baya da za a kama su da laifi. Kwana na uku, wanda ranar suka dafa normal Abinci, sauran kwanakin kayan snacks ne suka din ga yi. Duk cikin su Nana ce 'yar Nigeria, sauran duk 'yan Nijar ne, sai dai galibinsu baƙaƙen buzaye ne. Sai da suka kammala aikin, aka ba su wasu kaya fararen dogwayen riguna, da rigar girki, aka saka su kai Abincin wani ɗaki. Katafaren ɗakina da dogon tebur, an gyara shi sai tashin ƙamshi yake yi. Sai dai gabanta ya yi mummunan faɗuwa da jin irin ƙamshin da yake tashi a ɗakin. Take jikinta ya hau rawa, har ta nemi ta kifar da abin da ta ɗaukko. Ta ɗaga kanta a hankali ta kalli jerin manyan frames ɗin da ke ɗakin, sai dai mutanen jikin hotunan, dukkaninsu fuskokinsu a rufe yake, ba ta iya gane kowa daga cikin su ba. "Ke Nana ki kai mana kin ja kin tsaya" Nana ta jinjina kai jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban teburin. Ta ajiye kayan, ta ɗaga kai ta kalli yadda ginin ɗakin yake da matuƙar tsayi. Jiki a sanyaye ta ci gaba da kai komo, su na shirya abincin. Bayan sun shaƙe teburin da uban kayan Abinci, aka ba su umarnin su tsaya kar wanda ya fita. Su na tsaye Nana ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe goma na dare. Wani ƙaton mutum ya shigo, ya kalli gurin da yadda aka shirya teburin, ya kalli su Nana ya ce "Waɗanan ne suka yi girkin?" Balaraba wadda ita ce ta jagoranci su Nana gurin girke-girken ta risuna ta ce "Eh su ne ranka ya daɗe" "Wace ce wannan? Na ga kamar ba tamu ba ce" Ya yi maganar yana nuna Nana, da gaba ɗaya rabin hankalinta ba ya jikinta. Balaraba ta ce "Gimbiya Asal ce ta zaɓo ta, ta saka ta a cikin masu girkin" Ya yi shiru yana kallon Nana, daga bisani ya jinjina kai ya kalli Balaraba ya ce "Ki je, su su tsaya" Ta jinjina kai ta fice. Wata ƙofa aka buɗe, wani matashi ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, dogo ne sanye da farar jallabiya ya ɗaura hirami a kansa, ba dan ta yi wa Sayyid kyakykywan sani ba, za ta iya cewa shi ne. Ƙirjinta ya tsananta bugawa, sai dai kafin ta daidaita nutsuwarta, wani ma ya biyo bayansa, shi ma dai kamarsa ɗaya da Sayyid ɗin. Tunani ta fara yi ko Giyaz da Ƙaisar ne suka fara yi mata gizo suke yi mata wasa da tunani. Ɗaya bayan ɗaya suka din ga shigowa, sai da ta ƙirga mutum biyar cif, biyu kamar su ɗaya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai. Ɗaya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna ɗaya daga kujerun da babu kowa a kai. "Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar" "Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke ɓoyewa" Nana ji ta yi ana busar sarewa a ƙofar bayan su, gaba ɗaya suka ja gefe domin bayar da hanya. Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa baƙa, ya lulluɓe kansa da hiraminsa. Gaba ɗaya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu ƙasa, Nana kuma ta yi masa ƙuri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya ɗauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da Ƙaisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?. Gaba ɗaya matasan suka miƙe tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon. Tamkar yana tausayin ƙasar haka yake taka ta, yana ɗan yin rangaji kaɗan, sassanyan ƙamshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaɗe ilahirin gurin, fiye da ƙamshin turarukan da ke tashi a gurin. Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da ƙarfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko ƙiftawa ba ta yi. Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, ɗaya bayan ɗaya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo. Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?" Ɗaya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne" Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta ƙarshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku" Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez. Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol ɗin unguwar kenan. H.J Agadez. Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ƙame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai daga bisani ya saka hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode) Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba. Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin ɗazu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta ɗanɗana Abincin nan" Mutumin ya ƙare musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci. Nana ba ta san a yadda take iya ɗaga ƙafafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta ƙarasa gaban teburin. Ɗayar ta din ga bubbuɗe Abincin, ta fara ɗanɗanawa. "Ke kina da gaskiya kuwa? Ki ɗanɗana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa. Rikicewa ta yi gaba ɗaya, ya ɗaga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huɗu, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruɗe. Ta ɗebo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi. Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wataƙila mun yi mata kwarjini ne" Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin. Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, haƙoranta na haɗuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta. Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango. Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wataƙila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba ɗaya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta. ***** A hankali Nana ta yi juyi, ta buɗe idonta ta ganta a ɗakin da take kwana. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da mafarki ta yi ba gaskiya ba ne abin da ya faru. Hamdala ta yi ta ce "Ni dai na san mafarki ne da ma, dan babu yadda za ayi Sayyid ya ganni ya kasa kula ni, ya nuna kamar bai sanni ba. To wannan idan gaskiya ne ma, ta ina zan fara bayanin ni matarsa ce a yarda da ni? Mutumin da na ji ana batun ya daɗe a faransa yana jinya, anya ma Sayyid ɗina ne? Tun da dai mafarki ne duk da sauƙi. Sallama aka yi a ɗakin, ta ga Balaraba ta shigo ɗakin. Ta ce "Kin tashi?" Nana ta yi shiru tana kallonta. "Ina ga aiki da ki ka sha a kwanakin nan ne, ya sanya ki ka gaji zazzaɓi ya kama ki, Likita ya ce a bari ki huta sosai da sosai. Gimbiya Asal ta ce a baki hutu na kwana uku ki warware kan ki koma bakin aiki." Nana ta jinjina kai kawai, tana kokawa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tabattar gaske ne, ko kuwa dai mafarkin ne? Ta tashi ta yi alwala ta yi salla, sai dai gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga matsanancin ciwon kai da jiri da take ji, dan haka ta nemi guri ta sake kwanciya. ***** Jamila ta ɗauki jakarta ɗauke da wannan tarkacen da take kira da tarkacen jaraba, ta fita waje, ta samu ta sayo fetur a 'yar jarka, ta samu guri ta zuba musu fetur ɗin ta kunna musu ashana ta ƙone su. Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin. Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a. Hajiyar ta yi iya ƙoƙarinta gurin ɓoye jin haushin Jamila da take yi, ta karɓe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuɗin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a ƙasa. Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ƙungiya wa za ki bayar ne?" Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba" "Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?" "A'a na rage ji" "To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da ɗan Fatuhu" Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan. Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?" Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki ƙi bin umarnin ƙungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ƙara bayan tuna ta ƙona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu. A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar. ***** Fafur Nana ta ƙi yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da Ƙaisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki. Su na ɗakin girki su na ta ɗorawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki" Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina buƙata ki zo gurina ki karɓi wayar ki kira" Nana ta ɗan yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode" "Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?" "Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne" Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga saƙo can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki" Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal ɗin ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita. Dogwayen riguna na alfarma Nana ta samu, guda uku da kuɗi. Ta yi murna sosai da kayan, saboda rigunan na alfarma ne. Katafaren ɗakin bacci ne, mai ɗauke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki. Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun ɗakin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba. Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ƙara yi maka gargaɗi da jan kunne a kan ka ƙara kula da kan ka. Kar ka ɗauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faɗi wani abu da zai rusa shirinmu, mun ɓoye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya buƙaci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin. "Abii" "Na'am abin ƙaunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke ɓoye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na ɗauka ina jinya ba a hayyacina ba?" "Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na buƙatar hutu mussaman a ƙwaƙwalwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaɗawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai ƙasar nan, a shaida dai kana raye, cikin ƙoshin lafiya" "Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya ƙare ba" Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daɗi babu ƙari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai". "Amma Sultan ko zaka saka na ɓoye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata... "Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan ɗin. ***** Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faɗuwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta ɗaura alwala take ta addu'a. Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tuƙuru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake. Ko ta ina ƙamshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma. Ɓangaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani baƙo ne mai muhimmanci zai sauka a gidan. Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, baƙo ɗaya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba. Ta fito kenan ta ci karo da Asal, ta sanya zani da doguwar riga na shadda baƙar shadda, kanta babu ɗan kwali, hannayenta da yatsunta duk zobunan gwal ne, uwa uba wata irin sarƙa da ta saka ta zinari tun daga wuyanta har cikinta. Gashinta ya sha ado, ta sake shi har kafaɗarta, shi ma ta sanya masa wata siririyar sarƙa da ta kwanto har goshinta. Duk hassadar mai hassada babu yadda za a yi ka kalle ta ka kushe ta, jawur da ita a cikin baƙar shaddar sai ta haska shaddar. Ita dai Nana tun da ta zo gidan, ba ta taɓa ganin Asal da miji ko 'yan uwa ba, sai tarkacen ƙawayenta, su ma a wancan gidan ne, wannan gidan ba sa biyo ta su zo. Kuma duk abin nan Nana ba ta taɓa bin diddigi ta ji wace ce Asal ba, me yasa kuma take rayuwa a gidan daga ita sai masu yi mata hidima ba. Da daddare Nana ta ji su Balaraba su na yare, su na faɗin sunan Imam, lokaci lokaci su na haɗa wa da Hausa, sai dai ta manta a inda ta taɓa jin Imam ɗin. Babban abin da ya ɗaurewa Imam kai, bai wuce yadda a faransa yake jin sa garau, ba shi da wata damuwa ko wani ciwo da yake ji ba. Amma tun da ya sanya ƙafarsa a Agadez tsawon kwanaki huɗu, ko sau ɗaya zuciyarsa ba ta saurara da bugun da take yi cikin sauri babu ƙaƙƙautawa ba. Nana na ta kai komo a kitchen, ta kammala duk wani aiki da ya shafe ta, tana shirin tafiya ta je ta kwanta. Balaraba ta ce "Saurin me ki ke yi ne Nana?" "Ina son na je na yi wanka na kwanta ne" "Ki je ki yi wankan, nan da mintuna talatin za ki kai wa Gimbiya Asal bunu da madara sashinta" Har Nana za ta yi magana, dan ba ta shiga sashin Asal sai sau ɗaya, ta taɓa zuwa idan sun yi girki akwai waɗanda suke kaɗai suke iya zuwa sashen su kai. Ta fasa maganar ta ce "To" A gurguje Nana ta kintsa, ta koma ta ɗauki kayan za ta yi gaba, Balaraba ta ce "Ai ba sashinta za a kai ba, Ramata raka ta" Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta ɗan kwaɓe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta. Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta ɗaga kai ta din ga kallon ƙawataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ƙware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci. Tana saka ƙafarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai ɓare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai. Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet ɗin ɗakin. Bayan ta ajiye ta yi taku huɗu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ƙara yawa. Ta sauke idanunta a kan ƙaton frame da hotonsa a jiki. Danƙarewa ta yi a guri ɗaya, ta kasa motsa ko da ƙafarta. Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaɓa. Ɗan ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza. "Lafiya dai ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh. "Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?" Ramata ta ce "Abinci muka kawo" "Waye ya yi?" Ta nuna Nana da ba ta juyo ba. "Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ƙame ba ta juyo ba. A wulaƙance Ramata ta taɓa ta ta ce "Ana yi miki magana" "Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini" Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa. Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiɗimata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jan ƙafafuwanta a hankali. "Me ya same ki ne?" Ta girgiza kai alamar ba komai. "Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai" "Ba ni da lafiya" Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki ɓata mini rai" Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya ɗauka a hankali ya kai bakinsa yana sha. Nana kuwa a ɗakinta, gaba ɗaya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaɗina a kai kenan Ƙaisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya alƙawari ya ce haka? Na haƙura zan ɗauki ɗa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wataƙila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da alaƙa da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana ɗauke da ruhin ɗan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta. Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa. Wani irin zafi yake ji a cikin ƙwaƙwalwarsa, tamkar kansa zai tarwatse. Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza. Ya yi wankan ya lulluɓo jikinsa da towel. Asal ta sha kwalliya cikin baƙaƙen kaya na bacci. Ta nufo shi tana rangwaɗa, ta cire towel ɗin da ya lulluɓa da shi. Ya ɗan lumshe idanunsa saboda ƙamshin turaren da Asal take yi mai jan hankali. Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam" "Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi" "Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?" "A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba" Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haɗiye ya fasa. Ya fara ƙoƙarin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daɗin ji a cikin sa. "Imam jikin ne dai?" Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa. Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaɗan. Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba. Bayan mintuna talatin sai ga Asal a ɗakin, ta kalli Nana a wulaƙance cikin isa da gadara ta ce "Ki ka ce ba za ki yi aiki ba yau? Saboda gidanki ne ko zaman kan ki ki ke yi a gidan? An kai wa Imam shayi ya ƙi sha ya ce ba irin na jiya ba ne" "Eh ba zan yi girki ba, kuma barin gidan nan zan yi, na gaji da wannan aikin, zan je na ga yarona" Asal ta yi dariya ta ce "Ai kuma ƙarya ki ke yi. Na ɗaukko ki gidan nan saboda nesanta mijin da waɗanann munafukan hadiman, na kawo bare da baki san komai a kan harkar gidan mulki ba. Kuma ba kya cikin kalar matan da za su iya ɗaukar hankalinsa. Dan haka na kawo ki ne dan ki din ga kula da abin da Imam zai ci aikin da ki ka zo yi gidan nan kenan. Nana ta yi wa Asal wani irin kallo mai cike da tsana, ji take tamkar ta kama Asal ta yi ta jibgarta har sai ta ji ta huce. "Gimbiya Asal, ai an bar kari tun ran tubani. Ba zan yi girki ba sai dai yunwa ta kashe Imam ɗin, ke da yake aure idan ba za ki girka masa ba, to kar Allah ya sa ci, sai na bar gidan nan ba zan zauna ba" Ta yi maganar cikin ɗaga murya da zazzaro ido. Asal ta yi taku biyu, ta hankaɗa Nana baya ta ce "Ki kiyaye harshenki a kan abin da zai din ga fitowa daga bakinki, a kan mijina. Biyan buƙatata ce kawai ta sanya nake ƙyale ki, ki daina ƙoƙarin ƙetare iyaka. Tafiya kuma ga hanya nan maza ki tafi mu gani, idan kina tunanin da ka na kawo ki gidan nan na ajiye" Ayshercool 08081012143 Littafin kuɗi ne, 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic bank ku tura mini hakkina kan ku karanta. 72 Sai da Nene ta tabattar Nana ta ɗan nutsu, sannan suka kwanta. Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta ɗan sai abubuwan da za ta buƙata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can ɗin yake ba. Nana ta ce "Ni babu abin da nake buƙata, ki bani wani abin na riƙe a hannuna, sauran kuɗin kuma ki riƙe saboda kula da Muhsin na s... "Biyana za ki yi kenan dan na riƙe miki Muhsin?" Nene ta katse ta. "Allah ya baki haƙuri, ba haka nake nufi na, na ga dole ɗan abubuwan buƙatunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuɗi sun" "Kuɗinki ba su isa su saka na riƙe miki ɗa ba ko?" Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi haƙuri. Nene ta ce "Ba zan yi haƙurin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faɗa ki hau bani haƙuri, wato in ci kaina to sai na idar" Nana ta yi mata shiru ta yi faɗanta ta gama. Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na ɗan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta ɗauki wani abin ta ce ba za ta ɗauka na. Nana ta haɗe rai ta ce "Eh dama ba ki ɗauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karɓa" "Ni za ki yi wa wayo, na ji ban ɗauke ki 'yar ba, ni ga ɗana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ƙyar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karɓi abin da Nana ta saya mata. Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da ɗa, amma ban taɓa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?" Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?" "A'a kawai dai tambaya na yi " "Yana can Nigeria" "To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?" "Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki" Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haɗu ba". Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta ɗauke ɗanta ta tafi da shi. Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta ɗiɗɗinka kayan da ta sayo, ta sake haɗa jakarta ta ɗauki muhimman abubuwa a kayanta. Duk da a ɗaki Nene take rufe mata su, ba ta taɓa ganin alamar Nenen tana yi  bincike a cikin kayan ba. ***** Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini. Gaba ɗaya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaɓi ya ƙaru. Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faɗin za ta sake bayar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan ɗan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba ɗaya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron. A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ƙura mata ido ta yi tana bin ta da kallo. Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiɗe. Jamila ta yi tsaki ta shige ɗakinsu. Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba. ***** Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa. Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga saƙo" Sharif ya yinƙura ya tashi ya tafi. Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaɓar da ki ka ƙetare layin da bai kamata ki ƙetare ba, kina ƙoƙarin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi haƙuri da duk matakin da zan ɗauka a kan ki. ***** Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar. Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan raƙumi yana biye da su a cikin saharar. Kamar an taɓa ta ta ɗan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ƙirjinta. Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ƙashinta, ta ɗaga ido tana ɗan waige-waige ta ga ta ina za ta gano Ƙaisar ko wata baƙuwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba. Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai. Nana na son karanta Symbols ɗin da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai ɗauke da ƙaton gate ta ciki suka wuce. Ba ƙaramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ƙarasa ba sai bayan magariba. Kewar ɗan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da Maraɗi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege. Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ƙasaita a cikin gurin. A ƙofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko ƙafafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya. Ya buɗe bayan motar ya ɗaukko ƙatuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwaƙa. Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ƙawatu ya yi kyau sosai da sosai. A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan" Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan ɗin, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba" "Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai" Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice. Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla. Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido. Can ta ji ƙarar mota, aka buɗe ƙofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buɗe gate ɗin, aka shigo da wata haɗaɗɗiyar mota aka yi parking ɗin ta. Aka buɗe ƙofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta ɗaura mayafin a wuyanta, kanta babu ɗankwali. Har bakin ƙofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matuƙa, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa. Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ƙasar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki ɗaya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira. Ba ta san iya adadin lokacin da ta ɗauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta. "Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ƙauyen ki ke ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta. "Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?" "Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?" Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ƙarfin hali. Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ƙasa ta miƙe ta kwanta. Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci" Daga haka ta tashi ta bar falon. Nana ta tashi ta shiga kitchen ɗin, ta tarar da Abinci, ta ɗauka ta ci sannan ta ɗan dawo hayyacinta. A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla. Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal. Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana. Nana tana nan zaune, aka zo aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, ta tashi a ɗan tsorace ta buɗe, wani mutum ya miƙo mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi. Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ƙawayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaɗe-kaɗe har kusan ɗaya na dare su na abu ɗaya, suka hana Nana bacci. Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa? Sai washegari sannan ta saukko ƙasa, a lokacin ƙawayen nata duk sun tafi. Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ƙara kwanar mini a falo, ga ɗaki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba ɗaya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da ƙawayena, da sauran aikace-aikacen gida. Abu na farko dalilin da ya sanya na ɗaukko ki, ke ba ƙabilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaɗai za ki yi mini" Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch ɗin za a kai ta aiki ba, wannan zuƙaƙƙiyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuɗi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaɓi kowa ba sai ita?. "Ba kya ji na ne?" "Na ji" "Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so". Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faɗin ƙasar nan ki rasa wanda za ki ɗaukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba" "Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki buƙata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ƙulewa. ***** Gaba ɗaya Shukura ta burkicewa Sagir, ba ɗaga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja ɗaya take harkokinta, da gaske take ƙoƙarin gano abin da mahaifinta yake ɓoyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta. Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar. Ɓangarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ƙara gyara shi, aka haɗa gidan gaba ɗaya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya ɗau harama. Duk yadda ya so ya lallaɓa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi. Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ƙawayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ƙoƙarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta. Tana tsaka da nazarin yadda za ta ɓullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati ɗaya zamu bar nan, zamu je asalin inda na ɗauke ki ki yi mini aiki a gurin" Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me? "Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taƙaice. ***** Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu. Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ƙorafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita. Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka. Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai. "Ƙanwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da ɓarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi" Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi haƙuri ka yi aurenka kawai, ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin" "A'a ki daina faɗa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ƙarfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta. Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ƙuro mata ido tamkar ba ta taɓa ganinta ba. "Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Jamila ta ja tsaki, tana ƙoƙarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila" "Na'am mene ne?" "Ki ɗauki saƙonki mana" Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saƙon?" "Na cikin jakarki" "Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?" "A'a ni tuni kawai nake yi miki da saƙonki na cikin jakar" Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saƙon? Miƙo mini jakar dai na gani" Suwaiba ta ce "A'a ba zan taɓa miki jaka ba" Jamila ta janyo jakar ta fara buɗewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura ƙiris ta kurma ihu, ta rikice gaba ɗaya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita. Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana ƙyaƙyatawa tana kallon Jamila. Gaba ɗaya Jamila ta kiɗime ta rasa abin da yake yi mata daɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta. ***** Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan ƙafafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan. Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan baƙin ciki. Da ƙyar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?" Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa ɗaya daga kujerun da ke ajiye a gurin. Alhaji Zailani ya zauna suka ƙara gaisawa "Bani labari, ya aka yi sauƙi ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?" Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan ɗaurewa da nake ji a jikina ya yi mini sauƙi, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daɗewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux "Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?" "A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba" Alhaji Zailani ya miƙe ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi" "Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?" "Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin ƙunar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taɓa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba. ***** Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faɗa cikin matsanancin ɓacin rai. "A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba ɗaukar ta aiki muka yi saboda buƙatar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haɗa kai ku yi mata haka wannan wulaƙanci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar ƙasarmu ba" "Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da ɗa ma" "Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da ƙarfi da kuɗi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba" "Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba taƙi yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba" "Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku" Ta kwaɓe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya ɓata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?" "Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi ƙoƙarin hana Asal ɗaukar Nana. ***** Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan. Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai. Ta sha aiki ta gama, ta ɗan zauna a falo tana hutawa, sai ga ɗaya daga gayyar ƙawayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi" Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka" "Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa" "Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu" "Ke, kin san wace ce ni ki ke gaya mini haka?" "Ban san wace ce ke ba, kuma ba na buƙatar sani" Asal ta saukko tana tambayar lafiya. Ta gaya mata abin da ya faru, ta kalli Nana ta ce "Wai ke me yasa ba ki da mutunci, ban gaya miki dole ki girmama baƙina ba, mene ne a cikin dafa shayi mintinan nawa ne kin yi kin gama?" Ta kalli Asal ta ce "Ki yi haƙuri, wallahi ko cokali ba zan iya sake ɗauka ba, yau na bautu a gidan nan ke kin sani, kuma ban taɓa yi miki ƙorafi ba, amma yanzu dai na gaji gaskiya" Suka juya yare suka yi magana, ba ta san me suka ce ba, ta ga sun koma kan bene. Washegari da wuri suka ɗau hanya, sai dai ga mammakin Nana, har da rakiyar jami'an tsaro, kuma a wannan karon shigar Shadda Asal ta yi, an yi wa shaddar aiki tun daga sama har ƙasa. Mota ɗaya suka hau, ta ce Nana ta hau gaba, ita kuma ta hau baya. Sai da aka kuma wata tafiyar mai nisa, sannan ta ga sun tunkari wani  irin ginin ƙasa tamkar ginin ganuwar Kano. Ginin ya ƙayatar da Nana sosai da sosai. Jami'an tsaro ne suke gadin ƙatuwar ƙofar gurin, da wasu Buzaye farare tas sanye da rawani. Nana kamar ta ce a tsaya, ta duba buzayen nan ɗaya bayan ɗaya ko za ta ga Sayyid ɗin ta cikinsu. Sai da motar su ta tsaya, suka sauke glass ɗin motar. Da Hausa suka gaisa, suka yi mata sannu da zuwa, ɗaya daga cikin su ya kalli Nana ya ce "Wannan fa?" "Baƙuwata ce" ta ba shi amsa, ya jinjina kai motar ta shige. Su na shiga Nana ta ga ai gari ne guda a cikin ganuwar nan. Sun ɗan yi tafiya kafin su shiga wani ƙaton gida. Nana ta tsaya tana ganin yadda aka yi wa ginin ƙasa wani irin ado mai ƙayatarwa. Tun da suka doshi shiga gidan, ake gaida Asal cikin girmamawa, ita kuma ta yi fuska sai taku take cike da ƙasaita, kamar ba ita ce suke rashin hankali da ƙawayenta a wancan gidan ba. Wannan gidan saɓanin wancan da mutane a ciki, kuma da alama duk a ƙarƙashin Asal suke. "Wace ce ita?" Nana ta tambayi kanta. Sai da suka ƙarasa wani falo, sannan ta yi wa wata dattijuwar magana da yaren su. Matar ta kalli Nana ta ce "Bahaushiya ce ke ko? Zo mu je na kai ki masauki" Babu musu Nana ta bi ta, matar ta kai ta wani daki ta ce nan ne ɗakinta. Sai da Nana ta kwana biyu a gidan, ba ta sake ganin Asal ba, ba kuma ta aikin fari ba ta na baƙi kawai tana zaune, sai dai za a kawo mata Abincin safe, rana da dare sau uku a rana. Sai dai babban abin da ya dame ta, tun da ta shigo gidan, network ɗin wayar ya sauka gaba daya, ko ta kira Nene ba ta shiga sam. A kwana na huɗu, da daddare dattijuwar matar nan ta zo ta kira Nana. Babu musu Nana ta tashi ta bi bayanta. Sun yi 'yar tafiya su na ratsa faluka masu kyau da ado, sannan suka bi wata ƙofa. Sanyin A.C ya daki Nana, ga wani irin haɗaɗɗan ƙamshi. Asal ta hahakimce a kan kujera kaɗa ƙafa. Ta kalli dattijuwar ta ce ta jira a waje. Daga ƙasa wata matar ce a zauna a kan carfet, ta gurfana kamar tana jiran Asal ɗin ta gafarta mata. Nana ta yi turus tana tunanin a ina za ta zauna, sama ko ƙasa. Matar ta kalli Nana cikin zare ido ta ce "Ke ki rage tsawon ki, kin tsaya mata a ka" Nana ta ja guri ta zauna a kan carfet ɗin ita ma. Asal kamar ba za ta yi magana ba, sai da ta gama iyayinta ta sauke ƙafarta ƙasa ta dubi Nana ta ce "Amm na saka an kirawo mini ke, saboda ki san abin da na kawo ki gidan nan ki yi. Ke dai da ganin gidan nan kin san ba gurin da za a yi wasa ne ko shirirta ba, babban gida ne na mulki. Saboda dalilin girki da kuma wani dalili na ƙashin kaina, ya sanya na kawo ki gidan nan. Ba a ɗaukko bare wanda yake ba jinin gidan nan ba, ko ƙabilarmu ba ya yi mana aiki, amma na ga wasu abubuwa a tattare da ke da ya sanya na kawo ki cikin gidan nan. Kamar yadda na gaya miki, ina ƙara jaddada miki, zaman ki a gidan nan dole ki yi taka tsantsan, babu ruwanki da shishshigi, saka ido, gulma ko kuma shiga abin da babu ruwanki. Sannan kar ki kuskura wani ya ce zai haɗa kai da ke a yi wani abu, rayuwarki za ta iya salwanta ba tare da kowa ma ya sani ba, dan haka sai ki san irin zaman da za ki yi." Nana ta yi shiru ta gama sauraren ta, sai dai har a lokacin ba ta ji dalilin da ya sanya Asal kawo ta gidan ba, dafa abinci kowa ma zai iya mai yasa sai ita. Wannan matar da ta tarar a zaune, ta tafi da ita, ta kai ta gurin da ake girke-girken abinci, da gaya mata yadda jadawalin girke-girken gidan yake. Ta ɗaukko kayan ds Asal ta bayar a ba ta, na kayan shafe-shafe da mayukan wanka zuwa kayan sakawa. Da Nana ta koma ɗakinta, ta kalli kayan ta fara tunanin Allah ya sa ba kwance Asal ba ne, dan gara ta saka kwancen Ashura da ta saka na Asal, da ba ta da mutunci. A washegari Nana ta fara aiki a wannan madafa, sai dai madafar daban-daban ce. Akwai wadda ake girkin da ma'aikatan gidan ne suke ci, akwai wadda na baƙin da suke zuwa ne, sai kuma masu girka wa Asal abinci daban, dan haka Nana na cikin masu yi wa Asal girki. Sosai matar nan ta ƙara jan kunnen Nana, a kan ta kula da kanta, dan muddin aka samu matsala ba za ta sha ba. Nana a ranta ta ce "Ji wata jaraba, da wannan wahalar mutum ya girka abin da zai ci mana da kansa." Kwana huɗu da fara aikinta, ranar Alhamis da daddare, tana shirin kwanciya, aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta. Ta tashi ta buɗe, ta ga shugabar girke-girke ta gidan, kamar yadda aka gabatar mata da ita a baya. "Ki sako hijjabinki, ki biyo ni" Nana ta saka hijjabinta ta fito tana tunanin ko lafiya. Harabar gidan matar ta yi, Nana ta bi bayanta, ta nuna mata mota. Nana ta kalli dare ya yi kuma an zo da mota an ce a tafi da ita. Cike da mamaki Nana ta shiga motar, sai ta ga mutum uku, da su ma duk tare suke aikin girkin a gidan a cikin motar. Ta shiga ta zauna, ita ma shugabar ta su ta shiga. Nana ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah ina za mu je ne?" "Za ki gani" "Eh amma na ga dare ne fa" "Idan mun je za ki ji dalilin fitar" Nana ta yi shiru tana tunani, ita ba ma wannan ba, hankalinta ya koma kan rashin samun damar kiran waya da ba ta iya yi, kuma ba a kiranta ya shigo. Dan sai da ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin, ko matsalar daga wayarta ne, ta ce mata kar ta kuskura ta bari ma a san tana da waya, dan sai an ƙwace ta. Tana ta zancen zuci, har suka isa inda aka tsaya suka sauka, aka shiga da su. Asal ce a tsaye, tare da dattijuwar matar da ta saka ta raka Nana masauki. Suna tsaye a cikin ɗakin Nanan. Asal ta ce "Zazzage mini kayanta, ki ɗaga mini komai ɗaya bayan ɗaya" Ayshercool Ku tura mini hakkina kan ku karanta 0069685771 Aisha Adam stanbic. 73 Ɗaya bayan ɗaya, aka din ga zazzage kayan Nana. Aka zazzage su tsaf aka Azzage jakar da ta zuba kayan turarukanta da mayukan shafawa, duk ba ta ga wani abu ba, sai jakar gurin sarkin baka. Ta nuna jakar ta ce "Mene wannan?" Ta ɗago jakar ta ce "Jaka ce" "Buɗe ta ki zazzage na gani" Ta fara kokowar buɗe jaka, amma babu gurin da zata buɗe ta. Kawai ta ce "Shikenan" ta fice ta bar ɗakin. Can gurin kuma Nana tara su aka yi, su shida. "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya aka kawo ku nan, to zaɓo ku aka yi saboda an yarda da amanarku, ana daf da yin taro da Sultan da kuma dukkanin Imams na gidan nan. Dan haka ku aka zaɓo za ku yi girki na musamman. Amma ku sani kamar yadda wasu sani wasu ba su sani ba, muddin aka samu wata matsala ko ƙware wani ya yi, a sanadin abincin da ku ka dafa, to ku tabattar da rayuwarku za ku biya. Dole ku yi taka tsantsan ku kula." Matar ta yi maganar daki-daki. "In sha Allah" suka amsa mata. Ta ce su bi bayanta, suka je wani ƙaton guri, ɗauke da nau'oin kayan masarufi kala-kala. Ta yi musu bayanin da su ne za su yi amfani su yi girkin, sannan ya zama dole su sanya wa bakinsu sakata su yi aiki cikin amana, kuma kada wanda ya san su aka zaɓa da za su yi wannan girki. Nan ma suka amsa, ita dai Nana sai kallo da ido, dan abubuwan sun daina ba ta mamaki, wannan maganar ce ta sanya aka taso ta a daren nan, sai ka ce wanda za su girkawa wasu waliyyai abinci. Ko da aka mayar da su Nana gida, ta sha mamakin ganin kayanta a hargitse a cikin ɗaki. Da mamaki ta ƙarasa kan kayan nata, ta ɗaɗɗaga. Cikin takaici Nana ta tashi ta fita, sai dai kowa ya tafi makwancinsa ya kwanta. Kawai ta ji taku a bayanta. Ta waiwaya ta ga Asal na fitowa. "Har kun dawo kenan?" "Eh, sai dai na shiga ɗakina na tarar da an caje mini kayana an zubar da su a ƙasa, ban sani ba ko kina da masaniya a kan haka?" Asal ta ce "Me yasa ki ka zarge ni?" "Saboda na ga ba a gudanar da komai a gidan nan sai da izninki" Asal ta yi murmushi ta ce "Haka ne, kina da kaifin ƙwaƙwalwa kamar yadda na yi tsammani, ni na saka aka caje kayanki saboda na san da wa nake zaune" "Me yasa ba ki tambaye ni abin da ki ke buƙatar sani ba, za a caje mini kaya" "Saboda a ƙarƙashina ki ke, a gidana ki ke zaune dole na sani idan da wani abu da ki ke tattare da shi na cutarwa" Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ƙarƙshinki, ina da personal life ɗina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ƙulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?" "Yi ƙasa da muryarki, kar ki kuskura ki ɗaga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi" "Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini ɗaki ki taɓa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba." Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haɗiye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru" Nana ta yi mata banza, ta koma ɗakin nata, ta gyara kayanta tsaf. Ta kulle ɗakin ta koma ta ɗaga katifar ɗakin, ta ɗaukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta ɓoye su. Haka kurum take jin kayan na buƙatar sirri. Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata. ***** Shukura na zaune a ɗakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buɗe ƙofa ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ƙamshin turare take zubawa. Ya sha manyan kayansa, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji. "Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haɗiye maganar da ya yi niyyar yi. "Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa. Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba. Ya matsa kusa da ita, ya riƙo hannunta, ta fizge hannunta ta haye kan gadon ta kwanta. Bai ji haushin abin da ta yi masa ba ko kaɗan, ya san idan ba ta son sa ba za ta yi kishinsa ba, sai dai ita ma Yusra tana buƙatarsa tun da tun farko bai kamata ya sake ta saboda larurarta ba. Ya tashi ya kashe mata fitila, har zai fita ya koma gaban gadon, ya durƙusa daidai fuskarta ya ce "Ki yi mini afuwa Shukura, ban yi haka domin na cutar da ke ba, ko na muzguna miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki saboda lafiyarki da abin da yake cikinki" Daga haka ya tashi ya fice. Sai da ya fita sannan ta ba wa hawayen da suka maƙale a ƙirjinta damar zirarowa, zuciyarta ta din ga yi mata ƙuna, tamkar ta tashi ta bar gidan. Duk da ya fita da damuwar halin da Shukura take ciki, amma bayan wani ɗan lokaci tuni ya manta, suka ci suka ƙoshi da shi da Yusra. Bayan sun gabatar da salla, sun yi addu'oi, suka yi zamansu kawai su na hira. Sai gurin ɗaya saura sannan suka tashi suka kwanta. Yadda Sagir yake murna da kasancewa da Yusra, ko aurensu na fari bai yi haka ba, tuni wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su, daga shi har ita. Shukura kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, ga wani irin zafi da ya addabe ta duk da na'urar sanyaya ɗaki da ke cikin ɗakin. Washegari sai ƙarfe sha ɗaya na safe ya shiga ɗakin Shukura. Idonta kawai ya kalla ya ga alamun rashin bacci a tattare da idanunta, sun yi jawur sun kumbura. "Oum Haidar" ya kira sunanta, yana zama a kan gadon, tana shan tea. "Ina kwana" ta faɗa a taƙaice. Idanunsa ya sauka a kan ledar da ya kawo mata, babu alamar ko taɓa ledar ta yi. "Shukura me yake damunki ne haka? Na kawo abu ko taɓawa ba ki yi ba, kin yi bacci makuwa" "Sagir, dan Allah ka tashi ka bani guri, ni bana buƙatarka a kusa da ni, kaɗaici nake so" "Ni ki ke cewa na fita na baki guri?" Ya yi maganar yana nuna kansa. Ƙoƙarin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata take yi, amma abu ya gagara kawai ya fara zubowa ba tare da ta shirya hakan ba. Jikinsa ya yi sanyi, ganin yadda take kuka sosai da sosai. Cikin kwantar da murya, yake ƙoƙarin rarrashinta, amma ta tashi ta shige banɗaki ta bar shi a gurin. Ya yi shiru ya rasa abin da yake yi masa daɗi, shi babbar damuwarsa ma cikin da take ɗauke da shi, ga matsalarta ta hawan jini. ***** Tamkar bayi haka su Nana suke aiki, kullum za a ɗaukkosu daga wancan gidan da Asal take, a kawo su nan su wuni su na aiki. Har mamaki take yi wannan mutanen su kuwa har su nawa ne, dan kamar har da almubazzaranci a cikin lamarin. Sai dai kowa cikin kaffa-kaffa yake aikin tare da fatan kar wani abu ya biyo baya da za a kama su da laifi. Kwana na uku, wanda ranar suka dafa normal Abinci, sauran kwanakin kayan snacks ne suka din ga yi. Duk cikin su Nana ce 'yar Nigeria, sauran duk 'yan Nijar ne, sai dai galibinsu baƙaƙen buzaye ne. Sai da suka kammala aikin, aka ba su wasu kaya fararen dogwayen riguna, da rigar girki, aka saka su kai Abincin wani ɗaki. Katafaren ɗakina da dogon tebur, an gyara shi sai tashin ƙamshi yake yi. Sai dai gabanta ya yi mummunan faɗuwa da jin irin ƙamshin da yake tashi a ɗakin. Take jikinta ya hau rawa, har ta nemi ta kifar da abin da ta ɗaukko. Ta ɗaga kanta a hankali ta kalli jerin manyan frames ɗin da ke ɗakin, sai dai mutanen jikin hotunan, dukkaninsu fuskokinsu a rufe yake, ba ta iya gane kowa daga cikin su ba. "Ke Nana ki kai mana kin ja kin tsaya" Nana ta jinjina kai jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban teburin. Ta ajiye kayan, ta ɗaga kai ta kalli yadda ginin ɗakin yake da matuƙar tsayi. Jiki a sanyaye ta ci gaba da kai komo, su na shirya abincin. Bayan sun shaƙe teburin da uban kayan Abinci, aka ba su umarnin su tsaya kar wanda ya fita. Su na tsaye Nana ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe goma na dare. Wani ƙaton mutum ya shigo, ya kalli gurin da yadda aka shirya teburin, ya kalli su Nana ya ce "Waɗanan ne suka yi girkin?" Balaraba wadda ita ce ta jagoranci su Nana gurin girke-girken ta risuna ta ce "Eh su ne ranka ya daɗe" "Wace ce wannan? Na ga kamar ba tamu ba ce" Ya yi maganar yana nuna Nana, da gaba ɗaya rabin hankalinta ba ya jikinta. Balaraba ta ce "Gimbiya Asal ce ta zaɓo ta, ta saka ta a cikin masu girkin" Ya yi shiru yana kallon Nana, daga bisani ya jinjina kai ya kalli Balaraba ya ce "Ki je, su su tsaya" Ta jinjina kai ta fice. Wata ƙofa aka buɗe, wani matashi ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, dogo ne sanye da farar jallabiya ya ɗaura hirami a kansa, ba dan ta yi wa Sayyid kyakykywan sani ba, za ta iya cewa shi ne. Ƙirjinta ya tsananta bugawa, sai dai kafin ta daidaita nutsuwarta, wani ma ya biyo bayansa, shi ma dai kamarsa ɗaya da Sayyid ɗin. Tunani ta fara yi ko Giyaz da Ƙaisar ne suka fara yi mata gizo suke yi mata wasa da tunani. Ɗaya bayan ɗaya suka din ga shigowa, sai da ta ƙirga mutum biyar cif, biyu kamar su ɗaya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai. Ɗaya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna ɗaya daga kujerun da babu kowa a kai. "Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar" "Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke ɓoyewa" Nana ji ta yi ana busar sarewa a ƙofar bayan su, gaba ɗaya suka ja gefe domin bayar da hanya. Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa baƙa, ya lulluɓe kansa da hiraminsa. Gaba ɗaya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu ƙasa, Nana kuma ta yi masa ƙuri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya ɗauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da Ƙaisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?. Gaba ɗaya matasan suka miƙe tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon. Tamkar yana tausayin ƙasar haka yake taka ta, yana ɗan yin rangaji kaɗan, sassanyan ƙamshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaɗe ilahirin gurin, fiye da ƙamshin turarukan da ke tashi a gurin. Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da ƙarfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko ƙiftawa ba ta yi. Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, ɗaya bayan ɗaya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo. Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?" Ɗaya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne" Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta ƙarshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku" Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez. Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol ɗin unguwar kenan. H.J Agadez. Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ƙame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai daga bisani ya saka hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode) Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba. Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin ɗazu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta ɗanɗana Abincin nan" Mutumin ya ƙare musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci. Nana ba ta san a yadda take iya ɗaga ƙafafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta ƙarasa gaban teburin. Ɗayar ta din ga bubbuɗe Abincin, ta fara ɗanɗanawa. "Ke kina da gaskiya kuwa? Ki ɗanɗana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa. Rikicewa ta yi gaba ɗaya, ya ɗaga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huɗu, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruɗe. Ta ɗebo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi. Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wataƙila mun yi mata kwarjini ne" Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin. Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, haƙoranta na haɗuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta. Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango. Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wataƙila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba ɗaya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta. ***** A hankali Nana ta yi juyi, ta buɗe idonta ta ganta a ɗakin da take kwana. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da mafarki ta yi ba gaskiya ba ne abin da ya faru. Hamdala ta yi ta ce "Ni dai na san mafarki ne da ma, dan babu yadda za ayi Sayyid ya ganni ya kasa kula ni, ya nuna kamar bai sanni ba. To wannan idan gaskiya ne ma, ta ina zan fara bayanin ni matarsa ce a yarda da ni? Mutumin da na ji ana batun ya daɗe a faransa yana jinya, anya ma Sayyid ɗina ne? Tun da dai mafarki ne duk da sauƙi. Sallama aka yi a ɗakin, ta ga Balaraba ta shigo ɗakin. Ta ce "Kin tashi?" Nana ta yi shiru tana kallonta. "Ina ga aiki da ki ka sha a kwanakin nan ne, ya sanya ki ka gaji zazzaɓi ya kama ki, Likita ya ce a bari ki huta sosai da sosai. Gimbiya Asal ta ce a baki hutu na kwana uku ki warware kan ki koma bakin aiki." Nana ta jinjina kai kawai, tana kokawa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tabattar gaske ne, ko kuwa dai mafarkin ne? Ta tashi ta yi alwala ta yi salla, sai dai gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga matsanancin ciwon kai da jiri da take ji, dan haka ta nemi guri ta sake kwanciya. ***** Jamila ta ɗauki jakarta ɗauke da wannan tarkacen da take kira da tarkacen jaraba, ta fita waje, ta samu ta sayo fetur a 'yar jarka, ta samu guri ta zuba musu fetur ɗin ta kunna musu ashana ta ƙone su. Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin. Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a. Hajiyar ta yi iya ƙoƙarinta gurin ɓoye jin haushin Jamila da take yi, ta karɓe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuɗin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a ƙasa. Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ƙungiya wa za ki bayar ne?" Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba" "Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?" "A'a na rage ji" "To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da ɗan Fatuhu" Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan. Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?" Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki ƙi bin umarnin ƙungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ƙara bayan tuna ta ƙona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu. A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar. ***** Fafur Nana ta ƙi yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da Ƙaisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki. Nana suna ɗakin girki su na ta ɗorawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki" Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina buƙata ki zo gurina ki karɓi wayar ki kira" Nana ta ɗan yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode" "Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?" "Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne" Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga saƙo can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki" Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal ɗin ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita. Katafaren ɗakin bacci ne, mai ɗauke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki. Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun ɗakin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba. Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ƙara yi maka gargaɗi da jan kunne a kan ka ƙara kula da kan ka. Kar ka ɗauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faɗi wani abu da zai rusa shirinmu, mun ɓoye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya buƙaci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin. "Abii" "Na'am abin ƙaunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke ɓoye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na ɗauka ina jinya ba a hayyacina ba?" "Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na buƙatar hutu mussaman a ƙwaƙwalwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaɗawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai ƙasar nan, a shaida dai kana raye, cikin ƙoshin lafiya" "Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya ƙare ba" Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daɗi babu ƙari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai". "Amma Sultan ko zaka saka na ɓoye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata... "Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan ɗin. ***** Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faɗuwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta ɗaura alwala take ta addu'a. Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tuƙuru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake. Ko ta ina ƙamshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma. Ɓangaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani baƙo ne mai muhimmanci zai sauka a gidan. Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, baƙo ɗaya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba. Ta fito kenan ta ci karo da Asal, ta sanya zani da doguwar riga na shadda baƙar shadda, kanta babu ɗan kwali, hannayenta da yatsunta duk zobunan gwal ne, uwa uba wata irin sarƙa da ta saka ta zinari tun daga wuyanta har cikinta. Gashinta ya sha ado, ta sake shi har kafaɗarta, shi ma ta sanya masa wata siririyar sarƙa da ta kwanto har goshinta. Duk hassadar mai hassada babu yadda za a yi ka kalle ta ka kushe ta, jawur da ita a cikin baƙar shaddar sai ta haska shaddar. Ita dai Nana tun da ta zo gidan, ba ta taɓa ganin Asal da miji ko 'yan uwa ba, sai tarkacen ƙawayenta, su ma a wancan gidan ne, wannan gidan ba sa biyo ta su zo. Kuma duk abin nan Nana ba ta taɓa bin diddigi ta ji wace ce Asal ba, me yasa kuma take rayuwa a gidan daga ita sai masu yi mata hidima ba. Da daddare Nana ta ji su Balaraba su na yare, su na faɗin sunan Imam, lokaci lokaci su na haɗa wa da Hausa, sai dai ta manta a inda ta taɓa jin Imam ɗin. Babban abin da ya ɗaurewa Imam kai, bai wuce yadda a faransa yake jin sa garau, ba shi da wata damuwa ko wani ciwo da yake ji ba. Amma tun da ya sanya ƙafarsa a Agadez tsawon kwanaki huɗu, ko sau ɗaya zuciyarsa ba ta saurara da bugun da take yi cikin sauri babu ƙaƙƙautawa ba. Nana na ta kai komo a kitchen, ta kammala duk wani aiki da ya shafe ta, tana shirin tafiya ta je ta kwanta. Balaraba ta ce "Saurin me ki ke yi ne Nana?" "Ina son na je na yi wanka na kwanta ne" "Ki je ki yi wankan, nan da mintuna talatin za ki kai wa Gimbiya Asal bunu da madara sashinta" Har Nana za ta yi magana, dan ba ta shiga sashin Asal sai sau ɗaya, ta taɓa zuwa idan sun yi girki akwai waɗanda suke kaɗai suke iya zuwa sashen su kai. Ta fasa maganar ta ce "To" A gurguje Nana ta kintsa, ta koma ta ɗauki kayan za ta yi gaba, Balaraba ta ce "Ai ba sashinta za a kai ba, Ramata raka ta" Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta ɗan kwaɓe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta. Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta ɗaga kai ta din ga kallon ƙawataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ƙware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci. Tana saka ƙafarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai ɓare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai. Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet ɗin ɗakin. Bayan ta ajiye ta yi taku huɗu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ƙara yawa. Ta sauke idanunta a kan ƙaton frame da hotonsa a jiki. Danƙarewa ta yi a guri ɗaya, ta kasa motsa ko da ƙafarta. Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaɓa. Ɗan ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza. "Lafiya dai ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh. "Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?" Ramata ta ce "Abinci muka kawo" "Waye ya yi?" Ta nuna Nana da ba ta juyo ba. "Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ƙame ba ta juyo ba. A wulaƙance Ramata ta taɓa ta ta ce "Ana yi miki magana" "Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini" Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa. Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiɗimata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jan ƙafafuwanta a hankali. "Me ya same ki ne?" Ta girgiza kai alamar ba komai. "Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai" "Ba ni da lafiya" Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki ɓata mini rai" Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya ɗauka a hankali ya kai bakinsa yana sha. Nana kuwa a ɗakinta, gaba ɗaya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaɗina a kai kenan Ƙaisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya alƙawari ya ce haka? Na haƙura zan ɗauki ɗa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wataƙila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da alaƙa da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana ɗauke da ruhin ɗan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta. Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa. Wani irin zafi yake ji a cikin ƙwaƙwalwarsa, tamkar kansa zai tarwatse. Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza. Ya yi wankan ya lulluɓo jikinsa da towel. Asal ta sha kwalliya cikin baƙaƙen kaya na bacci. Ta nufo shi tana rangwaɗa, ta cire towel ɗin da ya lulluɓa da shi. Ya ɗan lumshe idanunsa saboda ƙamshin turaren da Asal take yi mai jan hankali. Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam" "Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi" "Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?" "A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba" Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haɗiye ya fasa. Ya fara ƙoƙarin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daɗin ji a cikin sa. "Imam jikin ne dai?" Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa. Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaɗan. Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba. Bayan mintuna talatin sai ga Asal a ɗakin, ta kalli Nana a wulaƙance cikin isa da gadara ta ce "Ki ka ce ba za ki yi aiki ba yau? Saboda gidanki ne ko zaman kan ki ki ke yi a gidan? An kai wa Imam shayi ya ƙi sha ya ce ba irin na jiya ba ne" "Eh ba zan yi girki ba, kuma barin gidan nan zan yi, na gaji da wannan aikin, zan je na ga yarona" Asal ta yi dariya ta ce "Ai kuma ƙarya ki ke yi. Na ɗaukko ki gidan nan saboda nesanta mijin da waɗanann munafukan hadiman, na kawo bare da baki san komai a kan harkar gidan mulki ba. Kuma ba kya cikin kalar matan da za su iya ɗaukar hankalinsa. Dan haka na kawo ki ne dan ki din ga kula da abin da Imam zai ci aikin da ki ka zo yi gidan nan kenan. Nana ta yi wa Asal wani irin kallo mai cike da tsana, ji take tamkar ta kama Asal ta yi ta jibgarta har sai ta ji ta huce. "Gimbiya Asal, ai an bar kari tun ran tubani. Ba zan yi girki ba sai dai yunwa ta kashe Imam ɗin, ke da yake aure idan ba za ki girka masa ba, to kar Allah ya sa ci, sai na bar gidan nan ba zan zauna ba" Ta yi maganar cikin ɗaga murya da zazzaro ido. Asal ta yi taku biyu, ta hankaɗa Nana baya ta ce "Ki kiyaye harshenki a kan abin da zai din ga fitowa daga bakinki, a kan mijina. Biyan buƙatata ce kawai ta sanya nake ƙyale ki, ki daina ƙoƙarin ƙetare iyaka. Tafiya kuma ga hanya nan maza ki tafi mu gani, idan kina tunanin da ka na kawo ki gidan nan na ajiye" Ayshercool 08081012143 74 Wata irin tafasa zuciyar Nana ta din ga yi, ta din ga jin tamkar za ta tsaga ƙirjinta ta fito. Asal ta yi wani shu'umin murmushi ta ce "Ko za ki dake ni ne? Na ga kina ta huci tamkar macijiya. Sannan ina mai ƙara jaddada miki, muddin mijina ya ci wani abu da ya samar masa da matsala a dalilin abincinki da rayuwarki za ki biya. Babu tsautsayi babu ƙaddara a gidan nan. Dan haka sai ki tattara dukkanin nutsuwarki ki san abin da ya kamace ki. Sannan babu ruwanki da yi masa magana, ko yi masa shishshigi, ki dafa abinci ki kai sashensa kawai, babu wanda yake da damar zuwa sashen kai tsaye, ke kawai ki ke da wannan damar a cikin bayin gidan nan, dan haka ina ƙara gargaɗinki a kan ki iya kan ki a zaman gidan nan" Kalmar Bayin da Asal ta faɗa, sai da Nana ta ji kamar ta fashe. A gidan uban wa ta zama baiwarta. Za ta yi magana ta ji tamkar an saka abu a danne mata maƙogwaronta, ta kasa magana. Tana ji tana gani Asal ta gama caɓa mata baƙaƙen maganganu, ta fice. Nana ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta rasa wani tunani ma za ta yi, kanta ya kulle ta zauna tana ci gaba da kuka mai sauti da ratsa zuciya. Ta kasa samun sukunin da za ta yi tunanin mafita ma. Asal na komawa sashen Imam, ta tarar da shi ya shirya tsaf da alamar fita zai yi. "Imam, fita kuma zaka yi?" Ya jinjina mata kai. "To ai ba ka karya ba, kuma mu ɗauki tsawon wannan lokacin ba ma tare baka nan, kuma yanzu ka ce fita za ka yi?" Ya ci gaba da ƙoƙarin fita, amma ta tare shi. "Haba Imam, ko kewata ba ka yi ba? Ba ka yi farin ciki da ganina ba ne? ka ke shirin ficewa ka bar ni?" Ya tsaya yana ƙarewa fuskarta kallo ya yi murmushin gefen baki ya ce "Abincin ne ban ji daɗin sa kamar na jiya ba. Sannan Gimbiya Bilkisu zan je na gaisar". Noƙe masa kafa ta yi tana riƙe rigarsa. Ya ajiye agogonsa ya nemi guri ya zauna, hakan ya sanya ita ma ta zauna tana murmushi. Nana kuwa tana tsaka da kuka ta ji an dafa ta, ta ɗaga kanta a hankali ta ganta a ɗakin karatun Ƙaisar. Sai dai wannan karon tsawonsa daidai da ita, ya zauna sosai ya fuskance ta. Ta sunkuyar da kanta hawaye na ci gaba da kwararowa daga cikin idanunta. "Uwar gijiyata" Nana ta ɗaga idanunta a hankali ta dube shi, ta mayar da kanta ta sunkuyar. "Bai kamata ki nuna karaya a wannan gaɓar ba, duk da ina jin zafin yadda ki ka yi burus da ni, da buƙatata da gargaɗin da na din ga yi miki a baya, amma wannan kamar ita ce gaɓa ta ƙarshe mai kuma matuƙar wahala, idan ki ka sare a yanzu wahalar da ki ka yi tuƙuru a baya za ta tashi a banza kenan. Ba ki da tabbacin ya gane ki? Ko kuma bai gane ki ba, sai dai komai ya zo da sauƙi. Ita wannan matar sauƙaƙa miki aiki ta yi, tun da ta kawo ki kusa da shi, ta kawo ki har inda yake, godiya ma yakamata ki yi mata. Ki kawar da kai daga kan duk wani abu na wulaƙanci da za ta yi miki a yanzu, a ƙarshe ke ce da riba, ki fara tantance halin da yake ciki, kafin ki ɗauki mataki na ƙarshe" Cikin kuka Nana ta ce "Ƙaisar na karaya, na sare ba zan iya ba, wa zai yarda da ni matarsa ce, banbancim da ke tsakanina da shi tazara ce mai nisan gaske. Ba na buƙatar ya gane ni, gida zan koma na nemi gafarar iyayena na kula da yarona" "Ba za ki koma gida yanzu ba, yaronki yana hannu na gari a yanzu duk ban san gaba ba. Na daɗe ban ga bil'adama mai juriya sadaukarwa da tsantsar juriya kamar ki ba. Imaninki da Allah ina da tabbacin ba zaki wulaƙanta ba kamar yadda ki ke yawan faɗa mini. Kar ki karaya ki tsaya ki karɓi abin da yake naki ne, idan ki ka karaya ki ka tafi kin yi biyu babu, wahalarki kuma ta tashi a banza" Da wannan maganganun ta buɗe idonta, tana sauke numfashi a hankali. Daki-daki ta din ga jin maganganun Ƙaisar na dawo mata. Ta yi shiru tana nazari, ta tashi zaune a hankali. "Abin da yake nawa? Eh Ƙaisar, Sayyid nawa ne, bai kamata na karaya a wannan gaɓar ba" ta furta idanunta na sake cika da hawaye bayan tuna Asal matarsa ce. Ta din ga tunanin suwaye suka tafi da shi lokacin suna Buda? Ko dai da kansa ya gudu ya bar ta? Ina su Habu, ta gan shi shikaɗai? Da gaske taɓin hankali ya yi a baya ya manta wace ce ita, ko kuwa dai raina mata hankali ya yi, ko kuwa dai duk wannan abin ba Sayyid ɗin ta ba ne?" Wata zuciyar ta ce "Haba dai, ko na makance na shafa na san Sayyid, ko za a ajiye irin sa dubu zan fitar da Sayyid a cikin su. Ina zan samu amsoshin tambayoyina ne?" Ta yi maganar tana dafe kanta da yake yi mata wani irin ciwo. Ƙaisar kuwa yana sakin Nana, ɗakin karatunsa ya gauraye da sautin dariyar Giyaz, dariya ta rashin imani mara daɗin ji. Ƙaisar ya waiwaya, yana kallon inda Giyaz yake shawagi a sama yana ƙyaƙyata dariyar, hakan ya tabattar masa da Giyaz ya gama jinyar abin da Nana ta yi masa. Ya yi wata irin girgiza ya bayyana a gaban Ƙaisar, ya din ga zagaye Ƙaisar yana ci gaba da dariyar cike da mugunta, daga bisani ya tsahirta da dariyar ya ce "'yan samari, yaushe imaninka ya ƙaru haka, har ka ke yi wa uwar gijiyar da ba ta ɗauke a bakin komai ba, nasiha da ba ta shawara?" Ƙaisar ya tsuke fuska ya ce "Ban yi maka iyaka da zuwa inda nake ba?" Giyaz ya ce "Daɗin abin har gori ta yi maka a kan butulcin ka yi mini, amma da yake ba zuciya ce da kai ba, ka na liƙe da ita. To bari na gaya maka abin da ba ka sani ba, ni ne na sake juye tunaninsa na shafe masa wancan tunanin, yadda abin zai yi mata ciwo, dama na gaya mata dawowata ba za ta yi mata daɗi ba, tun da na tashi daga jinya nake tunanin yadda zan ƙuntata mata na ƙuntata maka. Ya ɗagowa Ƙaisar wata kwalba, da wani farin haske yana yawo a cikin ruwan da ke cikin kwalbar. "Ka ga wannan, tunaninsa ne a ciki na duk wani abu da ya shafe ta na rufe shi ba zai taɓa tuna ta ba har abada. Sai dai ta dauwwama gararamba babu makoma. Na ga ka yi wa ɗanta riga-kafi, dan ka hana ni cutar da shi, sai dai ka riga ka makar... Ƙaisar ya ce "Kai ne ka makara, dan cutarwar da ka yi masa a ciki ma bai yi tasiri ba. Kar ka manta Bil'adama ce. Kar ka manta aiki aka baka ka shafe wancan tunanin nasa, ba ka taɓa tunanin zai tuna waye shi ba, sai ga shi yanzu ya tuna waye shi, dan haka wannan ma baka da tabbacin zai manta rayuwarsu har abada" Giyaz ya ce "Za ka gani, ka zuba ido zaka ce na gaya maka, duk wata hanya da zan bi na tsohe farincikin yarinyar nan na ƙuntata mata sai na yi" "Kana tunanin akwai sauran wahalar da ta rage wadda ba ta sha ba a baya? Haryanzu ba ka san suwaye biladama ba, waɗanda ka ke ta'amalli da su miyagun cikinsu ne, hatsabibancinsu kawai ka ke gani. Amma wannan karon ne za mu yi fito na fito na gasken gaske tsakanin ni da kai a kan yarinyar nan. Kar ka manta ka fi ni shekaru da daɗewa a duniya, hasali ma kai ka haife ni, amma ni marubuci ne, kuma manazarci sannan masanin magunguna kar ka ƙetare iyaka, zan iya baka mamaki." Giyaz ya sake kecewa da dariya ya ce "Gaskiya ne marubuci, kuma masanin magani, ka buɗe wannan kwalbar idan ka isa ya tuna waye shi saboda ka taimaki uwar gijiyar ka, ka faranta mata. Ƙaisar ya ce "Kai ka yi imani da cewa ka rufe tunaninsa a kwalba, amma kai zan cewa ka zuba ido ka ga ikon Allah" Giyaz ya ce "Shikenan ina zuba ido" daga haka ya ɓace ɓat daga libraryn. Har bayan azahar Imam yana tare da Asal, sai dai da aka kawo abincin rana, ba Nana ce ta kawo ba, Asal ta yi ta bala'i a kan kar wanda ta sake gani a sashen, idan ba a nemi izini ba ko kuma idan Nana ce ta kawo ba. Ta kira Imam da nufin ya ci abincin rana, sai dai ya yi loma biyu ya  kalli Asal ya yi shiru, ya tsiyayo shayi daga cikin haɗaɗiyar butar shayin, ya kai bakinsa, ya ɗan sha kaɗan ya ajiye, ya ɗauki robar madara ya buɗe yana sha. "Amour" ta furta a shagwaɓe ya ɗaga idanunsa ya kalle ta. "Ba ka ci abincin ba fa" Ya girgiza kai ya ce "Ba irin na jiya ba ne" "To wai meye a cikin na jiyan ne da ya sanya shi daban?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba, kawai dai wannan ɗin ban ji ɗanɗanonsa ba, kin san haryanzu jikin nawa sai a hankali, ba na cin abinci sai da na dawo ɗin nan" "Kuku fa na samo maka mussaman daga Nigeria, ta iya girki ita ta yi maka na jiyan ma, sai dai muguwar kidahuma ce, kuma ba ta da kirki amma ina da tabbacin ba za ta cutar da mu ba, a can gidan cin abinci na Maraɗi na ɗaukko ta mussaman saboda kai" Ya jinjina mata kai tare da yi mata alamar jinjina. Sai dai a baɗini cikin ƙwaƙwalwarsa, Nigeria da ta ambata sai da tsigar jikinsa ta tashi, gabansa kuma ya faɗi. Duk dabarun da Asal yakamata ta yi ta saka ya ci abincin nan ya ƙo ci, ya sha madarar raƙumi ya ce ta ishe shi ba sai ya ci abincin ba. Asal ta ɗanɗana Abincin, sai dai ba ta ji wani rashin ɗanɗano ba, abincin ya yi daɗi amma shi ya ce babu ɗanɗano. Da daddare Asal ta tafi ta yi wanka, ta je ta samu Nana, idan ba ta yi girkin daren ba, za ta gwada mata mene ne matsayinta a gidan. Sai dai ɓangaren Nana, tun da ta ji su Ramata duk sun ruɗe, wai an yi girki Imam ya ƙi ci, Asal sai bala'i take yi, kuma ta ce kar su sake dafa wani abu a kai masa muddin ba Nana ba ce ba. Yana zaune yana kallon labarai, shikaɗai a falon ya ji yanayinsa ya fara canzawa. Ya yi shiru yana tunanin me yake shirin faruwa da shi ne haka. Ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama, tana shigowa idanunsa suka haɗe lokaci guda. A zahiri ya ga shocking ɗin da jikin Nana ya yi, dan sai da farantin hannunta ya yi rawa. Sai dai shi ma na sa jikin ya yi, amma da sauri ta sunkuyar da kanta. Gabanta ya yi mummunan faɗuwa bayan ganin Giyaz da ta yi a tsaye a gefen Sayyid yana kallon ta yana dariya. Ya ƙura mata ido yana son gane wani abu da shi kansa bai san mene ne ba. "Ita ce 'yar Nigeria da Asal ta samo?" Ya tambayi kansa a zuciyarsa. Zaucewa ya kusa yi, bayan da Nana ta ƙaraso daf da shi ta ajiye farantin, ya ji ƙamshin turaren sa na tashi a jikinta. Ko da Nana ta ɗago ta saci kallonsa, ta gan shi a nutse yana kallon talabijin ɗin sa yana kaɗa ƙafafuwansa, kamar ma bai san ɗan Adam ya wanzu a gurin ba. Tuni hawaye ya cika mata ido, ganin mutumin da ta yi rayuwa mai cike da so da ƙauna tare da shi, abokin wasanta abokin hirarta, ya zame mata wani na daban a yanzu. Ba ta kai ƙofa ba Asal ta ƙwala mata kira. Ta yi maza ta goge hawayenta ta juyo. Wani abu ya caki zuciyar Nana, ganin Asal da wata 'yar riga a da guntun wando, babu kunya ko makamancin ganin idon Nana ta ce "Zo zan gabatar wa da amour ke" Ta zauna a kusa da shi tamkar za ta shige cikinsa,  ta ce "Imam, ga wadda nake gaya maka, kukun da na samo maka 'yar Nigeria" Sayyid ya yi wa Asal wani kallo yana ɗan lumshe ido, Nana tamkar ta zunduma ihu, sassaucin da ta samu ɗaya shi ne ganin ƙirjin Asal  babu wani abin kirki na jan hankali, duk da yadda ta taƙarƙare tana banƙarewa. Guntun tsaki ya kusa ƙwacewa Nana. A hankali cikin magana daki-daki ya ce "Babu masu girki a Niger, har sai an tsallaka Nigeria?" "Eh mana, duk dan saboda na burgeka ne" ta yi maganar cikin shagwaɓa tana shafa sajensa. "Idan ba ki burgenin ba fa?" "Haba Imam, me yasa haka dan Allah?" "Na ji, amma idan ta girka a samu mai kawowa ba na son ta din ga shigo mini nan" Nana ta kalle shi, zuciyarta ta tsananta bugawa. "Gaskiya Imam ba na son barorin nan su din ga shigowa sashenka, mugwayen munafukai ne duk nan yadda da su ba,  ba kuma zai yiwu maza su din ga shigo mini" Ya buɗe baki zai yi magana, Nana ta tsare shi da ido. Asal ta kalle ta ta ce "Je ki kawai sai da safe, rigima yake ji" Nana gani take kamar da gayya Asal take wannan abubuwan. Ba ta san lokacin da ta furta "Shegiya" ba a hankali. Bayan fitar ta, Asal ta ce "Imam me yasa baka son ta din ga shigowa ne?" Ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Tsoro take bani, idan na ganta gabana faɗuwa yake yi." A zaton Asal, Nanan muni ta yi masa, shi yasa baya ƙaunar ganinta, dan haka wani irin farinciki ya kama ta, ta ci gaba da lallaɓa shi a kan ya yi haƙuri Nana ta din ga shigowa sashen tana kawo masa abincin. Shiru ya yi mata ganin ba ta fahimci mai yake nufi ba, dan da suka yi ido huɗu da Nanan gani ya yi tamkar ta na yi masa kallon tuhuma, shi da bai taɓa ganinta ba, da zai iya zai so ya samu dama ya tambaye ta, ya ji ko laifi ya yi mata. Ko kuma ma ba mutum ba ce ba, da yake jin jikinsa ya canza a duk lokacin da ya ganta. Sai dai ya ci Abincin da ta kawo, da daddaren. Nana kuwa rabi da kwata kwanan tsaye ta yi, tayi kukan har ta gaji. Ita yanzu kawai ta zuba wa sarautar Allah ido. Furucin Sayyid ya rusa duk wani ƙwarin gwiwa da take da shi. Da safe kuwa da ta yi girkin,  da wuri ta kai cikin ikon Allah, ba kowa a falon. Kusan awa ɗaya da rabi da kai Abincin aka aiko kiran Nana, ta san za a rina, saboda abin da ta aikata, ta san dole a neme ta. Kanta tsaye ta shiga falon Imam, ta tarar da fuskarsa jawur hatta idonsa ma ya yi ja. Asal cikin bala'i ta hau Nana da faɗa. "Kashe mini miji za ki yi? Na ɗaukko ki ina tunanin za ki yi abin arziki, amma ki yi yinƙurin kashe shi, ban gaya miki sharaɗin wani abu ya samu mijina a dalilin abincinki ba?" AREWABOOKS Nana ta zuba wa Asal ido, sannan ta kalle shi ta mayar da idonta ga Asal ta ce "To ai ni ba ki gaya mini me na yi ba" "A kan me za ki cika yaji a cikin abinci ki cika tafarnuwa? Bayan ba ya son abinci mai yaji da yawa" "Ki daina yi mini faɗa, tun da ba ki gaya mini baya cin abinci mai yaji ba, kuskure ne bai kamata ki yi mini faɗa ba dan yau ɗaya na yi kuskure ba, amma bari na ɗanɗana Abincin na ji, sai na ga me zan gyara a gaba" Ta nufe shi gadan-gadan ta kalli fuskarsa, yadda ta koma sak lokacin suna tare, tana ba shi abinci mai yaji, ba zai yi magana ba sai dai ta gani a fuskarsa. Ta durƙusa ta ɗauki cokalin da ya ci abinci da shi, ta ɗiba ta kai bakinta, ta ɗago suka yi ido huɗu da shi, ya sunkuyar da kansa da sauri. Ta risunar da kai ta ce "Tuba nake Shugaba, na yi kuskure in sha Allah zan kiyaye hakan ba zan sake ba. Ba a gaya mini ba ka cin yaji da yawa ba ne, amma zan kiyaye" Ya sake ɗaga ido suka yi ido huɗu. Ya rintse idanunsa yana tunanin wace ce wannan? Meye haɗinsa da ita jikinsa yake rikicewa a duk lokacin da ya ganta? Sai dai duk da wannan tambayoyin da yake da su, kalmar shugaba da ta kira shi da ita, ta din ga yawo a cikin kansa. Nana ta miƙe tsaye ta kalli Asal da tsaya tamkar ta fashe, ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri zan sake kiyayewa, ba zan sake maimaita kuskuren da na yi ba". Kawai Asal ta janyo Nana, cikin mamaki take kallon Asal. "Nana ina ki ka samu wannan turaren?" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wane turaren?" "Wanda yake tashi a jikinki, Imam ba ka ji ba?" Shi dai ya yi shiru bai ce komai ba. Nana ta ɗage hijjabin jikinta, doguwar rigar da aka ba ta ta bayyana a jikinta da tamkar sai da aka aunata aka ba ta ta ce "Rigar da aka ba ni ce take ƙamshin, nima a haka aka bani ita" Ta tsaya tana yi wa Nana kallon tuhuma da rashin gamsuwa da abin da ta faɗa, sannan babban abin da ya ƙara ɗaure mata kai, yadda Nanan yau take ɗauke da ƙwarin gwiwa yau. "Cherie, ki sallame ta kawai ya wuce" Asal ta saki Nana tana bin ta da kallo. Ta ce "Na tafi da Abincin na dafo wani ne?" Asal za ta yi magana ya ce "A'a" Nana ta ɗauki farantin Abincin nata ta yi waje tana murmushin nasara, dan ta fuskanci ta fara dagula wa Asal lissafi. ***** "Ba wai-wai nake ki ji ba, gaskiya ne Hammad ya dawo Agadez kuma cikin hayyacinsa ba hauka ba, ya aka yi haka ta faru, kuma har Sultan yana iƙirarin ya yi jinya ne a faransa, yanzu ya warke zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa, yaya aka yi aka haihu a ragaya?" "Waye ya ce ya warke ɗin ne? Babu waraka a tattare da Imam Hammad" "Amma kai ka ce zai haukace ya bar ƙasar nan baki ɗaya, amma ya dawo cikin ƙoshin lafiya, an ce ma wai jinya ya yi a faransa" "Imam Hammad bai warke ba, kuma ba jinya ya yi a faransa ba, ya bar ƙasar nan ya yi nisa ya je ya yi rayuwar ƙasƙanci ba tare da tuna waye shi ba ma. Sai dai an samu mushkila inda ya tafi ɗin, wanda a can nake tunanin an ɓata mana fiye da rabin aikin ma, akwai dai yadda aka yi aka gano inda yake, amma tabbas ya yi nisa da gida ba tare da sanin waye shi ba. Amma warkewa kam bai warke ba, an samu matsala ne wani ya shiga cikin aikin ya ɓata wani abu , amma wannan ce gaɓar da ta fi cancanta mu sake hargitsa shi, za a ƙara ƙaimi a kan aikin, komai zai tafi yadda yakamata, a ƙaryata Sultan ya kunyata a idon duniya, a lokacin da ɗan nasa abin ƙaunarsa zai yi hauka tuburan duniya ta sani" "To shikenan, ina nan ina zuba ido, ina kuma jiran ji daga gare ka, da kuma abin da zai faru." ***** Nana ta girka Abincin rana, ta shirya shi a kan tray, ta je ta ajiye a falon Imam. Ta ja ta tsaya ta ƙi tafiya. Ta daɗe a tsaye, kafin su fito tare da Asal. Ganinsu taren ba ƙaramin dukan Nana ya yi ba, amma ta danne ta koma gefe ta sunkuyar da kai. Ja ya yi ya tsaya, saboda yana kusanto Nana, yana jin tamkar zuciyarsa za ta tsaga ƙirjinsa ta fito, ya din ga jin tamkar zai fita hayyacinsa. Asal ta kalle shi ta ce "Yaya dai?" Ya ɗaga kai ya kalli inda Nana take, kawai ya juya ya koma ɗaki. Ta ƙaraso gaban Nana ta ce "Ke ya aka yi ne? Ba cewa na yi miki, ki din ga ajiye abincin ki tafi ba?" Nana ta haɗiye wani abu mai ɗaci ta ce "Ki yi haƙuri, dama wata alfarma zan nema na a gurinki" "Ta me?" "Kin ce dole na kula da abin da mijinki zai din ga ci na yi taka tsantsan, to kuma gurin girkin yana can waje, duk da idan ina girki tsayawa nake yi a gurin girkin, amma ina jin tsoron kar wani ya shiga ya yi wani abu na ba dai-dai ba a yi zaton ko nice, shi ne na ce ko za a yi wa ɗakin girki mukulli a bani?" Asal ta ɗan yi shiru, sannan ta ce "Kuma kin yi magana mai kyau, zan san abin yi in sha Allah, za ki iya tafiya" Bayan Nana ta fita, ta koma da bayata shiga ɗakin, ta tarar da shi a kan gado ya takure jikinsa ya yi shiru, jin motsinta ya sanya ya waiwayo. "Imam, meyafaru ne wai?" "Na ce miki yarinyar nan ta daina shigowa, bana jin daɗin jikina idan na ganta, ina kyautata zaton ma ba mutum ba ce ba" Asal ta tuntsure da dariya ta ce "Mutum ce fa, dan dai kawai ba ka son hayaniya ne, kuma ba hankali ta cika ba. Amma ai Abincinta yana yi maka daɗi, shi ka ke ci fa, kuma idan ba ita ta yi ba baka ci" Ya numfasa ya ce "Ni dai kar ki ɗaukko abin da zai zame mana matsala" Ta karairaye murya ta ce "Imam ba zan taɓa kawo abin da zai cutar da mu ba, ka kwantar da hankalinka za ka daina ji, ka san ita ba ƙabilarmu ba ce, ba kuma 'yar ƙasarmu ba ce ba, shi yasa ka ke jin haka, amma ka kwantar da hankalinka" Ya jinjina mata kai kawai bai ce komai ba, ya san ba za ta taɓa fuskantar halin da yake shiga ba. ***** Yusra da Sagir su na zaune a falonsa, yana ta kallon agogon hannunsa, Shukura yake ta jira ta fito yana so ya haɗa su, ya yi musu nasiha, amma kusan awa guda da yi mata magana, amma shiru ba ta fito ba. Ransa ya ɓaci da irin wannan wulaƙanci da take ta yi, ya rarrashe ta, ya ba ta haƙuri amma ta ƙi sauraren sa, sai wulaƙanci take yi masa yadda ranta ya ga dama. Ga shi yana tausayinta saboda tsohon ciki da yake jikinta, ga hawan jini, amma ko a jikinta tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai, bayan wannan idan zai shekara yana magana, ba za ta kula shi ba, sai dai ya gaji ya tashi. Yanzun ma har ya fusata zai je ya same ta, sai ga shi ta fito, fuskar nan babu annuri da alama ma fita za ta yi. Ta zo ta nemi guri ta zauna, ta yi shiru ba ta ce komai ba. Yusra ma ta kalle ta ta basar, ba ta kula ta ba. "Mu na nan mu na ta jiran ki tun ɗazu, amma baki fito ba" Fuska a ɗan tsuke ta ce "Shiryawa na tsaya yi ne" "Ina za ki je ne?" Ta kwaɓe fuska ta ce "Awo" Ta ba shi amsa a taƙaice. Ya numfasa dan ba ya son biye mata, dan ya ga a kusa take, ko alamar ganin Yusra ba ta yi ba. "Amm dama ba wani dalili ya sanya na tara ku a nan gaba ɗaya ba, ina son in gabatar muku da juna, sannan kuma na yi muku nasiha a kan haɗin kai da zaman lafiya. Shukura kamar yadda ki ka sani tun da farko, kafin na aure ki, na auri Yusra sai dai ƙaddara ta gifta mun rabu. Ke ma kuma Yusra na sanar da ke bayan rabuwarmu na auri Shukura. Dan haka ina mai roƙonku a kan zaman lafiya da haƙuri da juna, domin na samu nutsuwa na yi muku adalci. Yusra ga Shukura, Shukura ga 'yar uwakki Yusra" Da ƙyar Yusra ta ce "Sannu" Haushi ya kama Shukura, wai sanni sai ka ce wadda take ciwo, da ya san zai dawo da Yusra dan me zai sake ta ya aure ta. Sagir ya ce "Shukura tana yi miki magana fa" Shukura ta ce "Hankalina na yana kan tafiyata Asibiti ne, ba na jin daɗin jikina. Amarya ina yi miki barka da zuwa, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya" Ta ƙarasa maganar tare da miƙewa da ƙyar. "Shukura ki tsaya mana mu gama sai ki tafi" Cikin fushi ta ce "Na ce maka fa bani da lafiya, kwana na yi ba na jin daɗin jikina" Sai kuma ya tuna takaicin abin da take yi masa ya sanya bai je ya ganta da daddare ba, ya wuce gurin Yusra. Shukura kuwa tuni ta nufi ƙofa, ya bi bayanta yana "Ki tsaya na sauke ki a Asibitin" Ta girgiza kai ta ce "A'a ka koma gurin amaryarka, kar ka bar ta itakaɗai" Jiki a sanyaye ya kira sunanta, ta ɗaga ido ta kalle shi. Idanunta sun yi jawur sun cika da hawaye. Hannu ya sanya yana share mata hawayen da ya fara gangarowa kan kuncinta, ya ce "Dan Allah Shukura ki daina, ban dawo da Yusra dan na ɓata miki rai, ko na cutar da ke ba, wallahi kukan nan da ki ke yi da rashin walwalar ki yana damuna ba kaɗan ba, dan Allah ki daina" Ta ce "Tom, bari na tafi kar na makara" Ya ce "Bari na canzo kaya na zo na kai ki" Ta ce "Kar ka damu, zan iya driving ai, yanzu zan dawo in sha Allah" "To me za ki sayo mini idan kin tashi dawowa?" Murmushin yaƙe ta yi ta ce "Me ka ke so?" "Abin daɗi, sai kuma uwa uba ki ƙara yi mini murmushin nan dan Allah" Murmushin ta sake yi tana taɓa jakarta. Ya dafa cikinta ya ce "A dawo lafiya Allah ya tsare, ki kular mini da kan ku sosai. Dan Allah ki daina fushin nan da ni Shukura, kin ga yau zan dawo gurinki, kuma ina son zuwa inda ki ke amma yadda ki ke yi mini ne ba na jin daɗi, har fargabar zuwa inda ki ke nake yi. Dan Allah idan na zo kar ki haɗe mini rai dan Allah sweetheart" "Tom" "Tom ɗin nan kuwa ta kai zuci?" Shukura ta ce "Ta kai mana" "Yauwwa babyna, ina jiranki, ki dawo da wuri dan Allah" "To in sha Allah" Ya buɗe mata motar, yana jin daɗin yadda ta sakar masa fuska, tsayawa ya yi janta da hira, yana tsaye a bakin ƙofar motar, ita kuma tana ciki a zaune. Abin mata da miji sai ga Shukura tana dariya, da haka suka yi sallama ta fita. Yusra kuwa sai da haushi ya kama ta, yadda ya yi ficewarsa ya je ya shantake a gurin Shukura, kamar ma ya manta da wanzuwarta a gurin. ***** Duk yadda Asal take ɗokin Imam, gaba ɗaya gani take kamar ba a cikin nutsuwarsa yake ba, kamar wani abu yana damunsa, babu yadda ba ta yi ba a kan ya gaya mata mene ne yake damunsa ba, amma ya ce mata shi babu abin da yake damunsa. A hankali ta yi juyi a kan gadon, ta zuba masa ido yadda yake ta uban gumi, tare da yin haki, har sai da ta ɗan tsorata. Sai dai ta ga ya yi juyi ya ci gaba da baccinsa. Kwana biyu Nana ta daina yadda su haɗu, kamar yadda ya buƙata, sai dai yau da ta shiga ta tarar yana nan. Babu tsammani ya ga Nana, hakan ya sanya ya ɗan zabura, har sai da ta gani. "Sayyid ina kwana" Shiru ya yi yana tunani, sai kuma ya maze bai motsa ba. "Ban san laifin da na yi da ya sanya, ka nemi na daina zuwa inda ka ke ba, amma idan laifi na yi maka, ina neman afuwarka Sayyid" Sannu a hankali kalmomin da ta yi amfani da su, suka din ga shigarsa ɗaya bayan ɗaya, yana jin kalaman na da wata fassara da yakamata ya sani, amma ya kasa gano fassarar, duk da yana jin yaren na hausa, kuma da shi ta yi maganar. Ƙamshin turaren sa da Asal take faɗa, yanzu ma shi yake ji yana tashi a jikinta. Ta miƙe ta yi waje cikin sanyin jiki, kawai ya tashi ya yinƙura, ya bi bayanta. Sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana tunanin to idan ya bi bayanta ina zai je, ko kuma me zai ce mata?. Kawai ya koma da baya ya nemi guri ya zauna. ***** Satin bikin Abba ya kama, Hajiya Sa'a duk ta yi busy, Jamila kuma ta rage zuwa gidan gaba ɗaya. Hajiya Sa'a tana ta jiran Abba za ta aike shi, amma shiru har sha ɗaya na safe bai fito ba, haushi ya kama ta dan muraran yake adawa da auren nan da zai yi. Bala'i take ta yi, tare da alwashin ɗaukar mummunan mataki a kan Jamila. Dan a cewarta ita take ziga shi. Ta shiga ɗakinsa tana bala'i, kawai ta gan shi a kwance yana bacci. "Abba wannan wane irin bacci ne har haka? Kai da muke da hidima a gaba, dan ka nuna mini ban isa ba, shi ne za ka nemi guri ka yi ta baccin asara" Sai dai ya yi shiru bai tashi ba. Ta ƙarasa ta ɗala masa duka a ƙafafuwansa, amma shiru bai tashi ba. A iya saninta, Abba ba shi da nauyin bacci, amma yau dai abin ya yi yawa. Ta jirkita shi, ga mamakinta kawai ta gan jini a hancinsa, da bakinsa ga fatarsa ta yamutse jikinsa ya yi fari ƙwal. Sai dai yanayin jikin nasa ya nuna akwai nutsuwa a tattare da shi. Wani irin magigicin ihu Hajiya Sa'a ta yi, ta hau kururuwa tana jijjiga gawar Abba, tana kiran sunansa da wata irin murya ta tashin hankali, girgiza shi take yi tana ihu da kururuwa a kan gawar, amma Abba rai ya riga ya yi halinsa. Hajiya Sa'a ta tashi da gudu ta nufi cikin gidan, tana ihu tana kururuwa tana "Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ku zo ku taya ni duba ɗana me ya samu Abba, dan Allah ku taimake ni kar Abba ya mutu ya bar ni na shiga uku na lalace" Tuni mutanen da ke gidan, suka fito aka je aka dudduba aka tabattar da mutuwar Abba. Ɗaya daga cikin ƙawayenta ta ce "Kuma ba guba ya sha ba, ko wani abu ko ba shi da lafiya?" Hajiya Sa'a babu baki sai kuka kawai da take yi. Safiyya ta ja ta tayi waje da ita, ba su tsaya a ko ina ba sai bedroom ɗin ta. "Hajiya me ki ka fahimta game da gawar Abba?" Cikin kuka da tashin hankali ta ce "Ni ban fahimci komai ba" "Duk wanda muka bayar a ƙungiya, yana zubar da jini ne ta hancinsa da bakinsa, kuma fatarsu haka take komawa, wani ya bayar da Abba a ƙungiyar Asiri, ko tamu ko wata ƙungiyar". Wani irin ihu Hajiya Sa'a ta zunduma, Safiyya ta toshe mata baki tana faɗin "Hajiya ki rufa mana asiri kar ki tona mana asiri a gano mu" Wayar Safiyya da ke aljihunta ce ta fara ringing, ta ciro ta sai ta ga Jamila ce take kiran wayar. Ta kalli Hajiya Sa'a da ke zunduma ihu sannan ta ɗaga. "Na san zuwa yanzu Hajiya tana cikin mawuyacin hali. Ba za ta iya ɗaga waya ba, amma ina taya mu jaje da ni da ita, Abba ya zama sadaukarwarmu na shekara da ni da ita. Ina fatan zuwa yanzu ta ji abin da ake ji, a duk lokacin da ta bayar da jinin wani ga ƙungiya, ina fatan Allah ya gafarta wa Abba sadaukarwar da ya yi, ya ceci masoyiyyarsa da kuma tseratar da ɗan ƙanin mahaifiyarsa, kuma Abba bai mutu ba, sai da ya san abin da muke aikatawa. Sannan ina taya mu murna, ina ɗauke da cikin Abba a jikina. Ba zan gushe ba ina yi wa Abba a addu'a, da yi masa fatan rahama. Abba mutumin kirki ne, kuma rayayye da ya fita daga cikin matacciya Allah ya sa ya huta" 75 Jamila ta katse wayarta, wani irin kuka ya ƙwace mata, ta din ga wani irin kuka mai gunji. Mama ce ta faɗo ɗakin cikin damuwa ta kalli Jamila, ta ce "Jamila lafiya kuwa, nake jin kukanki tun daga tsakar gida?" Jamila ta yi shiru tana ci gaba da gunjin kuka. Cikin damuwa Mama ta ce "Jamila, ni fa na kasa gane miki a 'yan kwanakin nan, wai mene ne yake damunki ne? Gaba ɗaya ba ki da sukuni, ga koke-koke ko Hajiyar ce ta kore ki ne?" Ta girgiza mata kai alamar a'a. "To mene ne?" "Dan Allah ki ƙyale ni na ji da abin da ya dame ni, Wayyo Allahna" Duk yadda Mama ta kaɗa ta raya, ta yi rarrashin amma fafur Jamila ta ƙi magana, taƙi gaya mata halin da take ciki, haka ta gaji ta bar ta a ɗakin. Tana fita Jamila ta ƙara rushewa da kuka, wani irin zafi take ji a ƙirjinta, soyayyar Abba ta din ga ji sabuwa fil a cikin ranta, ba ta taɓa tunanin al'amura za su kasance kamar yadda suka kasance a yanzu ba. Ji take tamkar ta kashe kanta ta huta, ko ita ma tattara ta shiga uwa duniya kamar yadda yayarta Nana ta yi. ***** "Imam Asad, haba ba kar manta sunan naka, kai jarumi ne, ina mai tabbatar maka da cewa Hammad ba zai zama Sultan a Agadez ba, duk wannan abubuwan da Sultan yake yi da rawar ƙafar da yake yi, mun san abin da yake nufi, dan mun san inda baki ya karkata ta nan yawu yake zuba. Amma Hammad akwai abubuwan da ya rasa, da ƙa'idojin da bai cika ba, dan haka burin Sultan na Hammad ya maye gurbinsa ba zai taɓa yiwuwa ba har abada" Imam Asad ya gyara zamansa, fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Anya kuwa? Duk abin da Sultan yake so, dole shi muƙarrabansa za su yi su mara masa baya, ina jin tsoron ya furta Hammad ya maye gurbinsa, muddin ya furta ko yana raye ko ba ya raye, sai an zartar da shi, sai dai idan Hammad ne ya bar Duniya" Mutumin ya ce "Kar ka yi la'akari da haka, ko me zai ɗauke mu zamu aikata, ko mene ne, babu wanda zai gaji Sultan sai Imam Asadullahi Jalal, dan haka ka ci gaba da ƙoƙari, burinmu dole ne ya cika" Imam Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa. ***** Cikin damuwa Sagir yake kallon agogon hannunsa, yana sake kiran lambar Shukura, ƙarfe biyar da rabi na yamma amma shiru ba ta dawo ba. Duk da Yusra sai da suka yi rigima da shi, a kan yadda ya tafi ya bar ta ɗazu, sai dai ta damu ganin fuskarsa babu walwala yana ta kallon waya. "Baby wai wa ka ke ta kira haka ne?" "Shukura nake kira, ta ce mini 9zata daɗe ba, tun safe da ta fita haryanzu ba ta dawo ba" Yusra ta basar ba ta kuma cewa komai ba, sai dai abin ita ma sai ta ji hankalinta ya tashi, ganin har ya fita masallaci sallar magariba Shukura ba ta dawo ba. Yana dawowa ya dubi Yusar ya ce "Ba ta dawo ba ko?" "Eh ba ta dawo ba, ko ta biya wani gurin ne?" Jiki a sanyaye ya ce "Ba na tunanin hakan, ko za ta biya wani gurin, duk faɗan da muka yi tana gaya mini, ba ma ta da yawan yawo, ba ta fiye son fita ba, idan ba gidansu za ta je ba. Bari na je gidansu, na kuma je Asibitin na ji" "To Allah ya sa tana lafiya, to ko haihuwa ta yi a Asibitin suka riƙe ta, na ga cikin nata ma sha Allah ya tsufa sosai" Ya girgiza kai ya ce "Da haihuwa za ta yi, da tuni an kira ni an sanar mini, bari na je na gani" Yusra ta ce "To Allah ya sa tana nan lafiya dai" Ya amsa da Amin, ya fita. Gaba ɗaya sai Yusra ta ji hankalinta ya tashi. Gidansu ya fara zuwa, ya shiga suka gaisa da Hajiya Amina, sai dai bai ga alamar Shukura ta je gidan ba, ya wayance da nufin zai tafi da Haidar, amma Haidar ɗin ya ƙi bin sa. Hankali a tashe ya tafi Asibitin doctor Sabo, aka ce masa tun safe ta je awo, sha ɗaya da rabi kuma ta bar Asibitin, kamar yadda har a cc camera ya nuna. Nan hankalin Sagir ya dunguzuma, ya ƙara ruɗewa ya burkice, duk inda yake tunanin Shukura za ta je, ya je bai same ta ba. Wayoyinta da su na shiga, amma suka daina. Ya tafi gurin 'yan sanda ya kai report ɗin ɓatan Shukura, bai koma gida ba sai sha biyun dare. Yusra na ganinsa ta tashi tana tambayarsa "Yaya an ganta?" Jiki a sanyaye ya girgiza mata, take gabanta ya faɗi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba saboda ka dawo da ni ne ta tafi ba, Ubangiji Allah ya sa ta dawo, ni zan iya tafiya ma na bar muku gidan, idan zamana ne ba ta so ta bar gidan" "Shukura ba za ta bar gidan nan saboda na dawo da ke ba. Dan kan ta fita mun yi magana ta fahimta da ita, mun daɗe mu na magana, ba saboda ke ne ta bar gidan nan ba" Gaba ɗaya Sagir ya kasa rintsawa, sai damuwa da tashin hankali, haka ita ma Yusra, ƙarshe ma kuka ta saka tana cewa saboda ita ne Shukura ta fita ba ta dawo ba. ***** Yau da Nana ta bushi iska, harabar gidan ta fita tana zagayawa, sai dai zuciyarta a cunkushe take, gaba ɗaya tunaninta yana kan Muhsin, kewar ɗanta take yi sosai da sosai, ga wannan azzalumar matar ta hana ta tafiya, sai dai ita kanta hankalinta ya rabu kashi-kashi ne, ga tunanin Muhsin ga kuma Sayyid da take ganin samu a lokaci guda take ganin rashi. Sai a yau ta ƙara tabattar da girma da ƙasaitar gidan, ba ta taɓa ganin raƙumi da ake faɗa ba, sai yau a cikin gidan. Ban da dawakai, da wasu dabbobin ma da ba ta san sunansu ba, ba kuma ta taɓa ganinsu ba. Asal ta hango hannunta a cikin na Sayyid, an fito da wata danƙareriyar mota, sun shiga an ja sun fice. Nana ta tsaya ta yi shiru cikin damuwa. Cikin matuƙar farin ciki dattijuwar matar fara ƙal, ta miƙe ta rungume Imam Hammad. Cikin girmamawa ya durƙusa zai gaishe ta, amma ta hana shi ta ce "Ai ni yakamata na kwashi gaisuwa shugabana. Ina ta yi wa Sultan ciwon bakin ban gan ka ba, ya ce a bari ka huta kar wanda ya je gida aka dame ka, har sai ka fito dan kan ka" Ya yi murmushi ya ce "Na same ku lafiya?" Ta ce "Alhamdillah, sannu Imam Hammad, an sha jinya Ubangiji Allah ya sanya kaffara" Asal ta ce "Wai ni ba za ki yi mini sanun ba, kin maze kamar ba ki ganni ba" Matar ta ce "Wa yake ta taki, ga mara lafiya" Gimbiya Bilkisu ta yi musu kyakykywar tarba, aka karrama su da Abinci kala-kala, amma ya ƙi ci. Hirar ma idan ta yi sai dai ya yi murmushi kawai, bai fiye tofawa ba. Bayan sun gama da sashen Gimbiya, suka nufi sashen Sultan. Imam Hammad na shiga falon Sultan, Sultan ya miƙe cikin farin ciki fuskarsa ɗauke da murmushi. Abdou ma murmushin ya saki, cikin girmamawa suka gaisa. Imam Nuradden, da Imam Asad duk su na tare da Sultan. Cikin girmamawa suka gaida Hammad, fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa musu. Sun taɓa hira kafin Sultan ya ce "Imam Hammad, zo muje ka raka ni tattaki mana, na miƙe ƙafafuwana" Imam Asad ya ce "Sultan, mu ma mu yi maka rakiyar ne?" "A'a ku da kullum muna tare ga baƙona da muka yi shekaru ba ma tare" Yayi maganar yana riƙe hannun Hammad, suka fita ta wata ƙofa. Imam ya din ga kallon gidan tamkar baƙonsa, kamar ba a ciki yake rayuwa ba a baya. "Hammad" "Na'am Abi" "Kamar wani abu yana damunka, ka gaya mini mene ne" Imam ya yi murmushi ya ce "Babu abin da yake damuna, idan ma akwai ban san mene ne ba" Sultan ya ƙara tattara hankalinsa a kan Hammad ya ce "Ka tabattar? ba ka fa da wanda zaka gaya wa dauwarka idan ba ni ba, ka daina wannan zurfin cikin Imam ba na so ka gaya mini" "Babu abin da yake damun Hammad ɗinka fa" Sultan ya yi murmushi yana dafa kafaɗar Hammad. "Ka san haryanzu miskilin ɗan yaron nan, mai guje-guje a harabar nan nake gani, ya yi guje-gujensa ya faɗi ya ji ciwo, ya zo ya yi ta yi wa Abinsa kuka, ya ce sai na ce ciwon ya daina yi masa zafi, kuma na daki rama masa na daki ƙasar na rama masa" Hammad ya yi dariya sai da haƙoransa suka bayyana ya ce "Duk da wannan gemun na fuskata haryanzu wannan ɗan yaron naka ka ke gani?" "Eh mana, gani nake kamar jiya Sarah ta haifa mini kai. Allah ya jaddada rahama ga Umminka" Ya amsa da Amin cikin sanyin jiki. Sultan ya sake numfasawa ya ce "Hammad, haryanzu babu wani abu da ka iya tunawa bayan fara rashin lafiyarka?" "Ban tuna komai ba" Ya ɗago hannun Hammad ya ce "Bamu san fa inda zobenka yake ba haryanzu, abin ya dame ni, ina tsoron a farga da babu zoben nan, ina tsoron abin da ka iya biyo baya, idan aka gano babu zoben nan" Ya kalli yatsun nasa ya ce "Abiena, duk abin da Allah ya ƙaddara zai faru dole zai faru ka daina damuwa. Ni yanzu ina mamakin Mamudu bai san ina Agadez ba ne?" Sultan ya ɗan ji dumm, sai kuma ya ce "Ni na hana a sanar da dawowarka, sonake ka samu lafiya sosai, amma dole za a sanar masa da dawowarka" Imam ya ce "Ni zan je na same shi, ya ganni a bazata" Sultan ya ce "A'a zan saka a sanar masa, zai zo har gida ya same ka" Ya ji daɗin kasancewa da mahaifinsa, sai dare sannan suka tafi gida tare da Asal. Duk wunin da suka yi bai ci komai ba, har suka koma gida. Nana ta kammala aikinta na yau, ta yi wanka tana zaune a ɗakinta, tana karatun Alkur'ani. Kawai ta din ga jin kamar akwai wani abu da ba daidai ba. Ta ajiye Alqur'anin ta tashi ta tafi ɗakin girkin Abincin Imam. Wata mata ta gani ta kawo kai za ta fita daga kitchen ɗin, alahalin babu wanda yake shiga sai ita sai Balaraba ko Asal. Nana ta ce "Baiwar Allah lafiya kuwa?" "Saƙo ne aka bayar, ke ce mai girkin Imam, dan haka ke za ki kai masa" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce ke? Kuma waye waye ya bayar da saƙon, kuma saƙon mene ne?" "Ba ni da lokacin amsa tambayoyinki, babu ruwanki da kuma saƙon na mene ne, ga shi can na ajiye miki a cikin kitchen ɗin, kaiwa ne kawai naki" Nana da mamaki ta bi matar ta kallo dan ba ta taɓa ganinta a gidan ba. Ta shiga kitchen ɗin da sauri, ta fara kalle-kalle tana tsoron kar ta je wani abin cutarwa ne. Wani ɗan kwando ta gani ƙarami, an nannaɗe shi ba za ta iya ganin mene ne a ciki ba. Wata zuciyar ta raya mata, ta kwance ta ga mene ne a ciki, wata kuma ta hana ta,sai dai har ta gama grkin dare tana kallon kwandon tana tunanin mene ne a ciki? Waye zai bayar da saƙo babu suna, kuma me yasa sai ita za ta kai? yanayin saƙon dai kamar babu gaskiya a lamarin. Da fargaba ta haɗa da ɗan kwandon ta nufi sashinsa gabanta yana faɗuwa. Yau shikaɗai ne a zaune, babu Asal. Duk da ruɗewar da yake yi idan ya ganta, amma ya ji daɗin ganin ta kawo masa Abinci, dan tun safe bai sake cin komai ba. Sai dai yau ba iya faɗuwar gaban yake ji ba, har da wata ƙara, mara daɗin ji makamanciyar wadda ya din ga ji daren da zai fara ciwo. Ta ajiye kwanukan ta ce "Barka da yammaci Sayyid, fatan ka na lafiya." "Alhamdillah" ya furta ba tare da ya shirya hakan ba, yana mamakin daga ina wannan sautin yake. Ita kanta Nana ba ta zata zai amsa mata gaisuwar da ta yi masa ba. Ganin babu Asal a gurin, ya sanya Nana zuba masa Abinci da shayi. Ta kalle shi duk da yadda yake yi mata wani irin kwarjini da a baya bata taɓa zaton yana da shi ba ta ce "Ko yanzu ma sai na ɗanɗana?" Ya girgiza kai alamar a'a. Ya sauka daga kan kujerar, yana jin ƙarar nan na ci gaba da addabar kunnuwansa. Cike da son basar da abin da yake ji, dan gujewaa sake faruwar abin da ya faru a wancan karon, ya yi Bismillah ya fara cin abincin. Duk da a takure yake da yadda take kallonsa, kuma ba zai taɓa iya cin abinci a gaban wanda bai kamata ya ci ba, amma ya kasa yi mata magana, kuma bai ji hakan da ya yi a matsayin wani laifi ba a matsayin sa na ɗan gidan mulki ba, wanda hakan yana cikin kamewa da suke da ita, musamman ma shi da hakan ya haɗu da ɗabi'unsa. "Sayyid, ina jin yadda mutanen gidan nan suke yabon ka, sosai da sosai da yabon karamcinka. Duk da a baya ban so zuwa gidan nan aiki ba, amma sai dai na ji babu daɗi da yadda ni ban samu wannan karamcin daga gare ka ba, sai ma ƙyama da ka ke nuna mini, da ƙabilanci ban sani ba ko dan ni ba ƙabilarku ba ce, kuma ba 'yar ƙasarku ba ce ba, shi ya sanya ka ke yi mini haka. Amma ina neman afuwa idan na faɗi wani abu ba daidai ba ko ya ɓata maka rai, bana nufin hakan shugabana" Gaba ɗaya babu tsoro ko fargabar Asal ta fito ta tarar da ita a ranta, daɗi ma ta ji na ko ba komai yau ta keɓe tare da shi. A wannan karon ma, jin maganganun nata ya din ga yi da matuƙar muhimmanci. Yaya zai yi mata bayanin ba tsanarta ya yi ba, baya iya tantance abin da ruhinsa da gangar jikinsa ke nufi a kanta ne. Shirun da ta ga ya yi, da yadda yake jujjuya cokalin ya sanya ta yin ajiyar zuciya, ganin alamun saƙonninta na isa kai tsaye inda take so. Ta nuna masa kwandon da aka bayar aka ce a ba shi, ta tashi ta fita. Kitchen ta koma tana ƙarasa goge-goge, kawai. Sai dai ta ji alamun mutum a bayanta. Ta waiwaya ta gan shi a tsaye a ƙofar kitchen ɗin, idanunsa jawur, ga Giyaz a gefensa, cikin suffarsa ta tsohon nan mara kyan gani. Ya fara takowa cikin kitchen ɗin, yana kusanto ta, gabanta yana faɗuwa ta zuba masa ido. Ya ɗago mata wata takarda ɗauke da hoton ƙwarangwal yana ci da wuta, an rubuta Imam Hammad Jalaludeen a jiki. "Waye ya bayar da wannan saƙon?" Kan Nana ya sara mafarkin da ta taɓa yi, ya fara ƙoƙarin zuwar mata kanta. "Waye na ce waye ya bayar da wannan saƙon?" Ya yi maganar cikin wata irin murya da ba ta taɓa jin sa da ita ba a rayuwar da suka yi!!! Cikin rawar murya ta ce "Nima ban sani ba, saƙo ne kawai aka ba ni aka ce na baka" "Waye? Waye ya bayar da saƙon? Ki gaya mini?" Ta kame jikinta cikin tsoro ta ce "Ban santa ba wata ce?" Launin idonsa ne ya fara canzawa, baƙar ƙwayar idon ta ɗauke, sai farin kawai. "Giyaz" Nana ta furta a hankali. AREWABOOKS. Jikinsa ne ya fara ƙamewa, fitilun kitchen ɗin suka ɗauke gaba ɗaya, ta ce "A wannan karon me ka ke buƙata kuma?" Muryar Giyaz ta din ga ji, yana wata irin dariya. "Ai dama na gaya miki, ki jira dawowata". "Na fi ƙarfinka, a waccan rayuwar da ya yi, da wannan ɗin ma, na fi ƙarfinka har abada". "Kar 'yar ƙaramar ƙwarin gwiwar da wancan yaron ya baki, ya sanya ki yi tunanin za ki iya yi mini wani abu, mu zuba mu gani". Nana ji ta yi abu ya faɗo jikinta mai nauyi, suka faɗi ƙasa tare. Wal hasken fitilar kitchen ɗin ya dawo. Imam ta gani a kwance a gefenta. Da sauri Nana ta nufe shi, jikinta na rawa za ta taɓa shi. Amma ta ganta itakaɗai a ɗakin karatun Ƙaisar, cikin azama ta tashi tana waige-waige, ta ga Ƙaisar a tsaya a bayanta. "Yana ina?" Ta faɗa a sanyaye. "Na san abin da ki ke ji, amma ya yi wuri, kuskure kaɗan za ki aikata ki lalata komai. Kar ki yi mamakin a din ga bibiyarki, saboda zaɓar ki da matar nan ta yi a matsayin mai dafa abincinsa, kuskure kaɗan ki na iya kwana a ciki ki shiga matsala. Kuma Giyaz zai yi ta tunzura ki, har ki yi wani abin da za ki saka kan ki a zargi. Ki din ga bin komai a hankali" Nana ta yi ajiyar zuciya, itakaɗai ta san abin da take ji, a kan Sayyid. Dan a gare ta gara lokacin da ya ɓata ba ganinsa take yi ba, amma yanzu ga ta ga shi, amma ya yi mata nisa. ***** Sagir kuwa ya zama tamkar zararre, aka kwana uku babu Shukura babu labarinta, sai a kwana na uku ya sanar da gidansu Shukura halin da ake ciki. Hajiya Amina ta gigice ta rasa inda za ta tsoma ranta. Hankalinta ya yi mummunan tashi. Alhaji Zailani ya din ga yi wa Sagir bala'i, a kan me tun ɓatan Shukura bai gaya musu ba sai yanzu. Aka ƙara sanar da jami'an tsaro, aka kuma baza komar neman Shukura. **** Ummi ce ta kawowa Baba ziyara, sai dai yanzu Baba duk ya zama abin tausayi, duk inda ya zauna sai da ya ja uban tagumi ya yi shiru, da ya samu dama kuma sai ya hau zancen Nana. Yanzun ma hirar da yake ta yi wa Ummi kenan. "Ummi kin ga Nana haryanzu shiru ko? Babu ita babu ɗan uwanta, shi ma tun wannan zuwan da ya yi bai sake zuwa gidan nan ba. Gara shi namiji ne ita kuwa ban san halin da take ciki ba. Nan gida kuma ita Suwaiba yanzu ba ta da maraba da mahaukaciya, na ce a kaita Asibiti babarta ta ƙi yarda. Ita ma Jamila 'yan kwanakin nan, gaba ɗaya ba na gane kanta, dama kuma babarta ta nuna mini in daina shiga sabgarsu 'yarta ce, saboda abin Duniya" Ummi ta ce "Gaskiya ne Baba, abin duk babu daɗi kam, amma Baba wani abun an bar gini tun ran zane ne, wannan abubuwan tun daga tushe yakamata a ce an yi wani abu na kaucewa farwuarsu, yanzu sai dai a yi ta haƙuri ana gaya wa Allah. Ta dai ɗan ba shi baki sannan ta tashi ta shiga cikin gidan. Suka gaisa da Mama a tsakar gida, suka hau hira. "Wai ina Jamila ne?" Mama ta ce "Tana ɗaki" "Amma tana ji na zo, ta yi burus?" Ta yi maganar tana leƙa ɗakin. Ta tarar da Jamila a kwance ta yi rigingine. "Jamila yau 'yar shariya ce babu magana ma?" Jamila ta yinƙura ta tashi zaune, suka gaisa sama-sama. "Wai ba ki da lafiya ne?" Ta jinjina kai alamar eh. "Jamila kin fiye yawan rashin lafiya, Allah ya kawo mana siriki mu sha biki. Ta ga dai mutanen gidan nasu duk sai a hankali, ta yi musu sallama ta tafi. Hajiya Sa'a tamkar za ta haukace, kwana uku amma sai an yi da gaske take cin abinci kaɗan. Ta rame ta zabge kamar ta shekara tana larura. Ko gaisuwar aka yi mata ba ta iya amsawa, idanunta suka koɗe suka yi jawur. Mutane da dama sun ji mutuwar Abba, saboda mutuwar fuju'a ga matashi, tana taɓa zukata, mussaman Abban da yake mutumin kirki ne, ga girmama mutane. Ranar da Abba ya kwana uku da rasuwa, Safiyya ta samu Hajiya Sa'a a ɗaki, ta ce "Hajiya yanzu mene ne abin yi, wani matakin ki ke ganin za ki ɗauka a kan wannan lamarin?" Hajiya Sa'a ta sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Duk matakin da zan ɗauka, kafin mutuwarsa yakamata na ɗauke shi, dana sani nake mara amfani na janyo yarinyar nan jikina, sannan idan na matsa, tsaf za ta tona mana asiri, dan haka ba zan saurare ta a yanzu ba, ina cikin matsanancin kewa da alhinin rashin tilon ɗana. Sai dai wallahi sai ta tafi inda Abba ya tafi, ko da kuwa nima zan rasa raina na" Jiki a sanyaye ta ce "Hajiya ki bi a hankali, kar garin neman gira a rasa idanu" "Ki zuba ido kawai" ta faɗa a taƙaice tana share hawaye. Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya sanya Nana farkawa, ta ganta a ɗakinta a kwance, ba ta iya tuna abun da ya faru ba tun daga biyo ta da Sayyid ya yi. Ta kalli ƙwan fitilar ɗakin a kunne, ta yinƙura za ta tashi, kawai ta takardar nan, da ya nuna mata yake tambayarta waye ya aiko da ita. A tsorace ta ja gefe, tana kallon takardar. Jikinta na rawa bakinta ɗauke da addu'a, ta ɗauki takardar ta sake ƙare mata kallo. Ta ninke ta ta saka a cikin kayanta, ta shiga banɗaki. ***** Nana na tsaka da aiki a kitchen, ta ji motsi a kitchen ɗin. Ta waiwaya ta kalli inda take jin motsin, ta ga Asal. Cike da takaicin babu yadda ta iya, ta ce mata "Barka da safiya" "Barka, amm na ce akwai abin da ya faru ne? Imam ya ce lallai a tsananta tsaro a gurin girkin nan, ki gaya mini idan da wani abu da ya faru?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a babu wani abu da ya faru fa" Asal ta ce "Kar na kama ki da aikata rashin gaskiya, hukuncin da zan yi miki sai kin gwammace kiɗa da karatu" Nana ta yi mata shiru, a ranta ta ce "Kya ji da shi" Asal ta juya ta fita, Nana ta raka ta da harara. Mahmudu ne durƙushe a kan gwiwoyinsa, a gaban Abdou matawalle. Ya numfasa ya dube shi ya ce "Imam Hammad ya samu lafiya, ya dawo Nijar" Mahmudu ya ɗago kai a zabure, yana kallon Matawalle. "Ka sani, koma me ka ke yi masa da ka ke mallake shi, mu na sane mun zaba maka ido,mun yi maka talala ne mu ga gudun ruwanka. Tun da ya sako ƙafarsa a ƙasar nan, tun ma yana can, yake zancenka yana cewa kana ina?. To ka tsaya da kyau ka saurare ni, zamu sake ka amma hakan ba ya nufin ka yi 'yanci ne, ko kuma mun daina zarginka, mu na nan mu na saka maka ido a ƙarƙashin takunkumi za mu sake ka. Sannan kar ka kuskura ka gaya wa Imam batun sace shi da ka yi da rayuwar da ya yi a Nigeria. Dan babu yadda ba a yi ya tuna wani abu ba, amma abu ya gagara. Dan haka ba a buƙatar ya san ya yi wata rayuwa a Nigeria, balle maganar nan ta fita, idan kuwa ka bari a ka ji maganar nan a waje, hukuncin da zai biyo baya ba zai yi maka daɗi ba. Wannan saƙo ne daga Sultan, ba a buƙatar ya san ya yi wata rayuwar daban, dole ka ja bakinka ka tsuke. Dan ka san hukuncin kisa shi ya dace da kai, an ɗaga maka ƙafa ne, saboda son da Imam yake yi maka, ba a buƙatar abin da zai taɓa masa zuciya" Mahmudu ya saci kallon Matawalle, yana jin zafin yadda mutumin nan yake ɗora masa sace Imam. Haka nan ya risuna ya yi wa Matwalle godiya. ***** Asal ce zaune a gaban Sultan, yake yi mata magana cikin nutsuwa da dattaku. "Yarinyar kirki, na san za ki yi mamakin sake kiran ki da na yi, duk da jiya kun zo gidan nan, to ina da baƙi ne ban samu mun yi magana ba a jiya, shi ya sanya na ce ki zo yau ina son ganinki" Asal ta jinjina kai, tana saurarensa cikin nutsuwa. "Na san kin ɗauki dogon lokaci mijinki baya kusa da ke, wasu faɗi tashin duk da ke aka yi kin san komai. To ga shi Ubangiji Allah ya yi masa dawowa cikin aminci. Sai dai duk da haka haryanzu bai gama samun lafiya ba. Dan Allah dan Annabi ina roƙon ki, ki zama mai haƙuri da juriya da kuma rufa masa asiri. Kin san yadda yake da magauta ta kowacce kusurwa, dan Allah ina sake roƙon ki, ki zama rufin asiri ga Imam, duk abin da ki ka gani wanda ba ki yadda da shi ba, ki zo ki sanar mini ban yarda ki gaya wa kowa ba. Dan Allah ki yi haƙuri da shi ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali daga gare ki" Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Abie, ba zaka same ni da wata matsala ba, zan zama mai rufa wa mijina asiri" "Na gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya yi muku albarka, ya baku zuriya ta gari masu jin ƙai" "Amin Abbie, muna godiya sosai da sosai" Sosai Imam Hammad yake son ya ci gaba da gudanar da al'amuransa da ayyukansa da yake yi, kamar a baya, amma abu ya gagara gaba ɗaya ji yake komai ya fita daga ransa. Jin jikinsa yake yi kamar a ɗaɗɗaure duniyar sam ba ta yi masa daɗi, ga shi takamaima bai san abin da yake damunsa ba. Sultan ne ya aika da mota aka ɗauke shi, bai san ina za a kai shi ba, bai kuma tambaya ba. Gidan da ake sauke baƙin Sultan nan aka kai shi. Sai ya fara mamakin ko wata ganawar zai yi da baƙin, amma Sultan bai gaya masa ba?. Sai dai babu zato babu tsammani ya ga Mahmudu. Cikin matsanancin farin ciki suka nufi juna, Imam ya ce "Mahmudu" Ya rungume shi cikin farin ciki. Sai dai wata irin karaya ta shiga zuciyar Mahmoud. Imam ya ce "Tun da na dawo nake cigiyarka, na ce ko ba ka san na dawo ba, a Faransa ma sai da na roƙi a kawo mini kai, mu zauna tare na yi jinyar, amma ba a bani dama ba" sai dai jin sheshsheƙar kukan Mahmoud ya ɗaga masa hankali, ya ɗago shi cikin damuwa ya ce "Mahmoud, ko na yi maka wani abu ne?" Ya girgiza kai yana share hawayensa ya ce "Ai ba ka yi mini laifi, ko me za ka yi mini a duniya kuwa. Murna ce da kewa ta sanya ni kuka" Jiki a sanyaye ya ce "Dan Allah ka bari, zuciyata ta karaya nima" Sai dai maimakon ya yi shirun, tamkar tunzura shi ya yi, ya sake fashewa da kuka. Hawaye ne ya cika idanun Imam, ya ce "Dan Allah ka gaya mini idan wani abin ne ya faru, duk ka sanya jikina ya yi sanyi, kamar ban taɓa ganin kana kuka ba" Ya share hawayensa ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na ce maka murna ce kawai nake da ganinka ya shugabana, ina fatan ka dawo cikin ƙoshin lafiya" Ya yi tsaki ya ce "Za ka fara ko? Waye shugaban naka?" "Kai mana Allah ya baka nasara" Kawai ya yi wata dariya ya ce '"Ka ci gaba, zan rama ne" Mahmudu ya yi dariyar shi ma ya ce "Ba zan iya fasalta adadin yadda na yi kewar ka ba, da farincikin da nake ciki, a sanadin dawowarka ba" Imam ya ce "Na fika murna da ganinka" Duk da yau suka haɗu tun dawowarsa, amma ji yake kamar ya gaya wa Mahmudu abubuwan da yake ji, amma sai ya fasa ya ga kamar ya yi wuri. Shi kuma Mahmudu zuciyarsa cike take da karaya, da kuma tunanin tayaya zai gaya wa Imam Hammad cewa ya yi aure a Nigeria, alhalin ga kashedin da aka yi masa. Ita Nana da suka baro a Nigeria mene ne matsayinta. Ya tuna irin ɗawainiyar da ta din ga yi da shi, da rayuwar da suka yi, amma alamu ya nuna sam Hammad bai san an yi hakan na, dan da ya tuna zai yi masa maganar. A ransa ya yanke dole ya shirya da kansa ya tafi Nigeria neman Nana, kuma ko me za a yi masa idan ya gano ta, dole ya kawo ta ya gabatar da abin da ya faru, ko da hakan yana nufin a yanke masa hukuncin kisa ne, gara ya yi da ya mutu da hakkin Nana a kansa. Ya din ga mamaki da tambayar kansa, yaya aka yi a wannan karon, Imam ya dawo hayyacinsa ya sake mantawa da rayuwarsa da Nana, bakinsa fal tambayoyi amma babu halin furta su, saboda kashedin da aka riga aka yi masa. Tare da Mahmoud suka zauna suka sha hira sai dai abincin da aka shirya musu, Imam ya ƙi ci. "Imam, wai ya na ga ba ka cin abincin ne?" "Abincin da ya fito daga hannu ɗaya ne tal yake yi mini ɗanɗano a bakina yanzu, idan ba shi ba duk wanda na ci salam nake ji" Cikin mamaki ya ce "Abincin wani hannu kenan?" Ya ɗan yi shiru ya ce "Asal ce ta kawo wata mai yin girki daga Nigeria, idan ba ita ta dafa ba, ba na gane kan Abincin" Ƙwarewa Mahmud ya yi, Hammad ya miƙa masa ruwa yana yi masa sannu, ya yi shiru ya ce "Daga Nigeria kuma?" "Eh" "Lallai Imam ka na da rigima, amma duk Nijar sai da aka tsallaka Nigeria aka samo ta?" Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Ka san rigimar Asal, wai a gurin cin abincin Maraɗi ta gano ta, ta kawo ta nan. Zan saka ta yi girki ka zo ka ci" Mahmoud ya jinjina kai, daga bisani ya kawar da zancen, yana ci gaba da lissafa yadda za je Nigeria ya taho da Nana, dan ya san tun da Hammad ya dawo, yanzu duk inda za shi su na tare. Da ƙwarin gwiwa yanzu Nana take girki, kasancewar ta sa wanda take yi wa girkin. Bayan da Nana ta kammala girkin rana tana shirin, kai wa sashen Imam, Asal ta same ta ta ce "Ba sai kin kai wa Imam Abinci ba, baya nan sai dare zai dawo, ki shirya masa abincin dare kawai" Nana ta amsa mata da to. Tun da Imam ya dawo, yake kaiwa yana komowa yana jiran ya ga ta ina za a kawo Abinci, saboda yunwar da yake ji. Ga shi dududu ƙarfe goma ya dawo, amma Asal har ta kwanta bacci. Ya yi hamma bai san adadinta ba, saboda yunwar da yake ji. Sallamar Nana ta saka ya kalli hanyar shigowa, wannan karon a kwando ta zubo kayan Abincin. Sai dai yau saɓanin hijjabi, doguwar riga ce a jikinta milk, da mayafin rigar. Tun da ta yi sallama ya amsa a ƙasan maƙoshinsa ya sunkuyar da kansa ƙasa bai kuma magana ba. Ta ƙarasa ta ajiye kwamdon, ta sauke kwanukan, har za ta yi masa zancen saƙon nan da aka bayar, sai ta fasa dan kar ta wargaza shirinta. Da wani na iya ganin halin da zuciyar wani ke ciki, da Imam ya daɗe da jin kunya, saboda bugun zuciyarsa, ga wani irin azalzalarsa da take yi, ya sake kallon Nana, dan ba ya tunanin ya taɓa ganin wanda doguwar riga ta yi kyau kamar baƙar kukunsa 'yar Nigeria. Ta zuzzuba masa abincin, ga kayan marmari ga kuma shayi na musamman. Da ta zuzzuba masa. Ta numfasa ta ce "Ɗazu na yi girkin rana, aka sanar mini da baka nan, na ce duk lokacin da ba zaka kasance a gida ba, ina son a yi mini izini na dafa maka ka fita da shi, ba zan so shugabana ya kasance da yunwa ba, tun da alhakina ne girka maka Abinci" Ta yi maganar cikin girmamawa tana sunkuyar da kai. Jin ya yi shiru ya sanya ta ɗaga kanta, ta ga tuni ya ɗauki shayi ya kai bakinsa yana sha. Kawai ta ɗan juya ƙwayar idonta, tare da yin murmushi. Sai da ya kusa ƙwarewa, saboda tabbas ya san irin wannan kallon, amma a ina? Yana matuƙar son ya yi mata magana, amma ba ya iya wa. Nana ba ta ba shi damar ɗaukar wani mataki ba, ta tashi ta nufi hanyar fita. Tun da ta tashi ya bi ta da ido har ta fice. Abin duniya duk ya dame shi, Nana kuwa ta cika da murna, ganin saƙonninta na isa yadda take so, sai dai tana buƙatar ƙara samun kusanci da shi. Cikin marairaicewa yake kallonta, fuskarsa ɗauke da damuwa ganin yadda take kuka tamkar ranta zai fita, ga shi ta yi duhu ta rame, ba kamar yadda ya santa ba a baya. "Ma vie, ki yi mini afuwa, ba laifina ba ne, ina jin yadda ruhinki yake motsi a cikin jikina, dan Allah kar ki yi fushi da ni ki yi mini uzuri " Ya yi maganar yana ƙoƙarin rungume ta ya rarrashe ta. Ja da baya ta yi tana girgiza masa kai tana kuka ta ce "Ba ka so na Sayyid, ka yada alƙawari ka tafi ka bar ni, ka manta da ni, ka bar ni da dakon ruhinka, da ya hanani sukuni sai da na fito nemanka, ba ka yi mini adalci ba Sayyid" "Ma vie, ban ya da alƙawari ba, gangar jikina ce a Nijar, amma ruhina yana Nigeria dan Allah ma vie" Asal ta yi ƙuri da ido tana kallon yadda ya haɗa gumi a cikin bacci, sai numfarfashi yake yi da kyar yana faɗin "Ma vie, ke rayuwata ce, ban yi miki butulci ba" AYSHERCOOL 1K NE VIA 0069685771 Aisha Adam stanbic bank 08081012143 76 Asal ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah. Shiru ta yi jikinta ya yi sanyi tana kallonsa, sai dai ta yi shiru ta ci gaba da kallonsa. A razane ya farka, sai dai ya juya ya ci gaba da  baccinsa. Da safe ya lura da Asal ba ta walwala, ta ƙi sakin jiki da shi ma gaba ɗaya. Har ya share ta sai kuma ya tambaye ta ko lafiya? "Lafiya kalau" ta amsa masa a taƙaice. Ya fita ɗan tattaki, yana jin mafarkin da ya yi a jikinsa, amma ya kasa tuna mafarkin abin da ya yi. Cikin girmamawa ma'aikatan ke ta risunawa su na gaishe shi. Babu yabo babu fallasa ya din ga amsa musu. Zuwa ƙarfe goma Nana ta kammala girki. Sai dai yau ba su haɗu ba kwata-kwata. Har lumshe idanunsa yake yi bayan da ya sha kunun gyaɗar da ta yi, ga lafiyayyen ƙosai mai zafi. Ya karya tsaf ya gama, Asal ta fito daga ɗaki ta cika ta batse. Kallo ɗaya ya yi mata ya maze, ganin ya basar da ita ya sanya ta ƙura masa ido ya kalle ta, yana mamakin dalilin da ya sanya ta ke yi masa wannan kallon. "Imam ina fatan inda ka tafi, ba cin amanata ka yi ba" Kallon rashin fahimta ya yi mata ya ce "Me ki ke nufi?" "Ni kaina ban kai ga tantance abin da nake nufi ba, amma na fara ganin wasu abubuwa me da ban gane musu ba, abin ya tsaro ta ni ne" Ya ce "Yi mini bayani" "Ka na kiran wata da rayuwarka a cikin baccinka" Ya yi mata ƙuri da ido, sannan ya ce "Kin tabattaa?" "Ba ka yarda ba ƙarya nake yi maka kenan?" "A'a ban ce haka ba, amma kin ce bacci nake yi, kin ga mai bacci kuma bai san abin da yake aikatawa ba. Wataƙila shirmen mafarki ne kawai, wataƙila ma ke na gani a cikin baccin nake kira da rayuwata" Sai kuma ta yi murmushi ta ce "Kuma haka ne, wallahi har na ji zuciyata ta yi sanyi, ka yi haƙuri da abin da na yi " Ya yi murmushi yana kashingiɗa ya ce "Ban haƙura ba tukuna" Ta ce "Ai ba zan sake ba, ina kishinka ne sosai. Da ina da hali ko fita sai ka daina yi. Ina sane da duk masu ƙoƙarin yi maka kyautar 'ya'aynsu su na so ka aura. Imam kai nawa ne nikaɗai Imam Hammad, babu wata mace da za ta iya samun kafar da za ta shiga zuciyarka. Inda na gode wa Allah, ka yi daban Imam, ba ka da rawar kai, da kule-kulen nan, da ko a cikin barorin nan, da suke rawar ƙafa ka yi saɗaka da su, sai ka saurare su. Shi yasa nake ƙara ƙoƙarin na kare gidana ina fatan ba ka ga laifina ba" Ya sanya hannunsa yana shafa gashin kanta, ya ƙanƙance idanunsa yana kallonta, daga bisani ya saki murmushi ya ce "Gimbiya Asal, sarauniyar mata masu kishi ta duk faɗin Agadez" Ta zumɓura baki ta ce "Ta duk Duniya dai, ni in dai a kan ka ne. Da ina da yadda zan yi ma sai ka daina kallon kowace mace, sai maza kawai" Ta yi maganar har cikin zuciyarta. Kawai ya kama dariya, dan shi gaba ɗaya dariya ma ta ba shi. "Ya ka ke dariya kuma?" Hammad ya ce "To ya ba zan yi dariya ba, ina ji ina gani an bani kyautar mata na mayar da hannun kyauta" Fuskarta ɗauke da damuwa ta ce "Dama ka na so kenan?" "To waye ba ya son mace? Ina so mana. Amma tawa kawai" "So ka ke sai ka saka ni kuka" Ta yi maganar idanunta na cika da hawaye. Lumshe idanunsa ya yi yana buɗewa, yana kallonta. "Ga abinci ki karya" Ta noƙe kafaɗa. Nana ce ta yi sallama, Asal ta kalli inda ta shigo, ta tsuke fuska haka kurum yau ta ji haushin Nana ya ninku a zuciyarta. Nana ta yi saurin sunkuyar da kanta, dan Asal a zaune take a kan cinyar Sayyid. "Zan kwashe kwanuka" ta yi maganar muryarta har harɗewa take yi, saboda abin da ya taso mata. "To ni dai yanzu ka kira ni da rayuwarka a zahiri, tun da ka ce ni ka ke kira a mafarki" Ta yi maganar kamar ba ta san Nana ta shigo ba. Ras gaban Nana ya faɗi, ya lumshe idanunsa yana murmushi ya ƙi magana. Kawai Nana ta fusata ta tattare kwanukan za ta yi waje. "Malama ki ajiye ban karya ba, ki fita kya dawo ki kwashe" Ko waiwayowa Nana ba ta yi ba, wata irin zabura ta yi cikin matsanancin fushi, amma ya riƙe ta ya ce "Cherie na sha gaya miki, irin wannan halayen naki ga na ƙasa da ke, babu abin da za su janyo miki sai tsana da raini. Ita kuma rayuwa a na son ko kana guzurin maƙiyi ka yi na masoyi" "Amma Amour kana kallon abin da ta yi mini, ko sau ɗaya sai na sanya a ladabtar da yarinyar nan ta san matsayina a gidan nan" Ya ce "A'a, ke ce baki kyauta ba abin da ki ka yi. Ita ba ta tashi cikin jerin hadimanki ba, kawai dai kin ɗaukko ta ta yi miki aiki ne, dan haka sai kin din ga yi mata uzuri" "Wane uzuri ne ba na yi mata, abin da ta yi mini wulaƙanci ne tana sane, ban da yadda take kula da abincinka na aminta da ita a kan hakan, da sai na hora ta sannan na kore ta ta bar gidan nan" "Shikenan ki yi yadda ki ke so, tun da ba zan faɗa ki ji ba" Ya yi maganar yana ture ta daga jikinsa. "Imam fushi ka yi da ni a kan wannan mummunar yarinyar?" "Ba a kanta na yi fushi ba, yadda ba kya jin magana ne ya ɓata mini rai, idan ki ka ci gaba da sanya wa ma'aikatanki ƙiyayyarki, babu abin da ba za a iya haɗa kai da su a yi miki ba. Idan na isa a bar maganar nan. Ba na son yadda ki ke tafiyar da ma'aikatanki wasu lokutan, ba na son yawan shiga maganar ne, amma raina ki za su yi" Asal ta yi shiru ta tsuke fuska, ta sauka daga kan cinyarsa baki ɗaya. **** Alhaji Fatuhu ma duk da yadda yake fama da kansa, sai da ya je gurin jana'izar Abba, kuma da shi aka yi zaman makoki. Ya ji mutuwar nan sosai da sosai, saboda Abba mutuminsa ne. Ko da yake jinya a sati ya kan je sau biyu ko uku duba shi. Ya kan zauna su yi hira sosai mussaman idan ya tarar jikin nasa da sauƙi. Kusan kullum Hajiya Sa'a gani take mafarki take yi, idan aka wayi gari za ta ga Abba bai mutu ba, amma ta ga babu alamun hakan. Ba ta ƙara kiɗimewa ba sai ma da aka yi kwana bakwai da mutuwar, kowa ya watse ya bar gidan. Ɗakin Abba ta tafi da daddare, ta buɗe ɗakin tana rintse idanunta tana jin tamkar za ta gan shi ya ɗago, da wannan murmushin nasa irin na fuskar mahifinsa. Amma ta ga ɗakin nasa wayam, babu komai. Wasu irin zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kumatunta, ba ta taɓa dana sanin shiga ƙungiyar asiri da duk wasu miyagun laifuka da take aikatawa ba, sai da ta rasa tilon ɗan da Allah ya ba ta a rayuwa. Wanda babu irin ƙoƙarin da ba ta yi, domin ganin ta kare shi da sadaukarwar ƙungiya. Ashe bonono ta yi rufe da ɓarawo bayan janyo Jamila cikin harkar ƙungiya, wanda ta yi hakan ne, domin janyo Jamila kusa da ita yadda za ta samu mallakar jinin Nana. Ta zauna a gaban ƙatuwar katifarsa, ta din ga wani irin kuka mai sauti, da sai da ƙirjinta ya fara yi mata zafi. ***** Asal ce zaune a kan carfet, saman kujerar da take kai kuma wani babban mutum ne, cikin shigar buzaye, kansa ɗauke da rawani. "Ki na ji na da kyau ko?" Ta jinjina kai cikin nutsuwa, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta yi. "Ina fatan haryanzu ba ki manta dalilin da ya sanya ki ka auri Hammad ba" Ta amsa da "Eh ban manta ba" "To barka, yanzu ya dawo, kuma babu abin da zai canza, za ki ci gaba da gudanar da aiki, kamar yadda yake a baya. Ba na buƙatar kuskure ko kuma wani uzuri. Duk wani motsinsa da duk abin da yakamata mu sani mai muhimmanci ki sanar da ni, idan kuma ki ka bari ni na gano ba ki sanar da ni ba, ranki zai yi mummunan ɓaci" Jiki a sanyaye ta jinjina kai. "Dole a ci gaba da aiki tuƙuru, domin nesanta shi da kujerar Sultan, da mahaifinsa ke ta ƙoƙarin kusantar da shi da ita, mu na buƙatar kujerar nan ko ta halin ƙaƙa, dan haka ina nan ina saka miki ido da kuma sauraren ki" Asal ta sake jinjina kai, jikinta babu ƙwari ta tashi ta fice. Da ƙyar take ɗaga ƙafafuwanta, damuwa duk ta cika mata kai, ta ma rasa wane tunanin yakamata ta yi. Da ta koma gida, ta tarar da hadimai na gyara ɓangaren Imam, ga ƙamshin turaren sa, da alama bai daɗe da fita ba. Cikin tsawa ta kore su gaba ɗaya, ta ce su ajiye aikin su fita daga sashen, sannan su kira mata Nana. Jiki na rawa suka ajiye suka fita. Nana tana tsaka da karatun Alkur'ani saƙon Asal ya iske ta, sai ta hau tunanin kiran me take yi mata. Duk da ta san abin da ta yi mata da safe. Nana ta tashi cike da ƙwarin gwiwa, dan ji take yi daidai take da Asal, tun da duk abu dai ba za ta raba ta da ranta ba. Nana ta shiga fuskarta a haɗe ita ma, ta shiga ɗakin ta tsaya, tana ta huci tana son ta balbale Nana da faɗa, sai kuma ta kasa ganin yadda Nanan ta tsuke fuska ita ma, ta yi mata wani irin kwarjini. Amma duk da haka ta maze cikin dakiya da ƙarfin hali ta ce "Amm tambaya nake son yi miki, ban sani ba ko nice a ƙarƙashinki, da zan din ga yi miki magana kina ji na ki yi mini banza" Nana ta ɗaga kai tana kallonta. "Ko ba ki gane me nake nufi ba ne? Abin da ki ka aikata da safe" Nana ta ce "Na gane, gani na yi bai kamata na tsaya ina kallon ku a yanayin da ku ke ba, ko na din ga sauraren maganganunku ba. Hakan zai zama kamar munafunci ne, shi ya sanya na tafi, amma ki yi haƙuri" Asal ta watsa mata wani banzan kallo cike da tsana ta yi ƙwafa sannan ta ce "Daga yanzu aikinki ba iya girkin Imam ba ne ba, har da gyaran sashen sa, ba na buƙatar kowa ya din ga raɓar inda yake." "Amma ɗaukko ni ki ka yi na din ga girki kawai, ya za ki haɗa mini da aikin shara da goge-goge. Kuma masu yin aikin su uku ne, ni kuma nikaɗai ce, aikin bai yi mini yawa ba kuwa?" "Kin san a kan kuɗi nawa na biya na ɗaukko ki? Ko a Nigeria ba na tunanin ko za a sayar da kaf danginku, za ku iya biyan kuɗin da na biya na karɓo ki ba. Dan haka ina da hurumin sanya ki duk abin da na ga dama" "To Gimbiya Asal, babu damuwa zan yi abin da ki ke so. Duk da dangina ba za su iya biyan kuɗin da ki ka biya ba. Amma na san wataƙila mijina zai iya biya ya fanshe ni" Nana ta yi maganar tana murmushin da Asal ba ta gama gane kansa ba. Nana ce ta ƙarasa aikin gyaran falon nan, ta yi goge-goge. Haƙurƙurtar da kanta ta din ga yi, da ta tuna mijinta take yi wa wannan aikin. Duk da ayyukan sun yi mata yawa. Ita dai fatanta Ubangiji Allah ya sanya Sayyid ya tuna ta domin ta san matsayinta. Tana kammalawa ta koma kitchen, ta ɗora girkin rana. Ta kammala ta kai ajiye. Ta ƙara goge ɗakin saboda ta san halin Asal sai ta tafi za ta huta, za ta sanya a kirawo ta, ta hau yi mata kinibibi da sanabe kala-kala. Ta gama aikin goge-gogen kenan, ta gano wani photo album. Ta ɗauka ta nutsu tana dubawa, duk rubutun French ne a jiki. Shafin Farko hoton Sultan ne, wanda ba dan yanayin shekaru da fuskarsa ta nuna ba, sai ka ce Imam Hammad ne, wanda tsananin kamannin har Muhsin da ta baro a gurin Nene. Ta buɗe ɗaya shafin ta ga hoton wani, shi ma fari tas mai kama da su Sayyid sai dai shi ma babba ne. Kowanne a ƙasa da sunan sarautarsa. Sai kuma ta shiga wani shafi mai ɗauke da hoton Sayyid a ƙasa an rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. Wani murmushi ya suɓuce mata ta ce "Ka fi kowa kyau a cikin album ɗin nan Shugabana." Ta furta cikin murmushi. Hotunan wannan matasan da suka yi wa girki a gidan Sultan su ma kowanne da sunansa a ƙasa. Amma a farkon sunan kowanne da Imam. Nana ta din ga mamakin to kowa ma Imam ne kenan?. Muryar Asal ta jiyo sun nufo cikin falon, ta hanyar da take kyautata zaton a nan turakar Imam take, kuma tana tunanin ɗaya hanyar sashen Asal za ta mayar da kai, kai tsaye. "Imam, wai ina zobenka ne?" Ta yi maganar tana ɗago hannunsa, Nana kuma tana hango su daga inda take zaune. "Ya karye yana gurin gyara" "Gurin gyara kuma Imam? Ya za a yi dakakkiyar azurfa kamar wannan a ce ta karye? Ka san fa muhimmancin da zoben nan yake da shi a gurinka, ya za a yi ya karye?" Daidai lokacin suka ƙaraso tsakiyar falon, ya ce "Zobe ya ɓata ban san inda yake ba, ina fatan kin gamsu yanzu. Kar ki sake yi mini maganarsa. Yanzu zan fita, kar ki manta da saƙona" Sai a lokacin suka ga Nana da ke zaune a cikin falon. "Me ki ke yi a nan?" Asal ta tambaye ta. "Babu komai, gyra ɗakin na yi" "Kuma sai ki nemi guri ki zauna sai ka ce ɗakinki? Imam yana da baƙi anjima, za ki sake dafa wani abin, kuma za su sha shayi, ba na son wauta ko makamancin haka" Nana ta jinjina kai ta kalle shi ta ce "Barka da yammaci Sayyid, in sha Allah zan yi" Asal ta ɗan yi shiru tana nazari jin ta kira shi Sayyid ba Imam ba. A ɗan corridor ɗin ta tsaya tana zancen zuci, jin ana maganar zobe. Wane zoben kenan? Ko dai zoben da ya ɗauka ya ba ta ne? A'a ba ta tunanin haka wataƙila dai wani abin ne daban. Gyaran murya da ya yi da ƙamshin turaren da ya cika gurin ne ya sanya ta farga ta waiwaya, sai ta ga a kan hanya ta tsaya. Ta yi taku biyu ta ba shi guri, ya saci kallonta, zuciyarsa ta din ga raya masa son sanin wace ce ita, sanin na sosai ya yi mata tambayoyi game da wasu abubuwa. Ya haɗiye yawu ya zo zai gifta ta, wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, sanyin da zai yi fatan dauwwama a cikin sa, saboda yadda ya saba da zafin jikinsa, wanda duk sanyin da yake guri, a cikin jikinsa yake jin wannan zafin. Sai dai wannan sanyin da ya ratsa shi, har cikin ƙashinsa ya ji sanyin. Ya sake waiwayawa ya kalli Nana, amma ya ga shi take kallo. Ji yake tamkar ya koma da baya ya ƙara samun kusanci da ita, sai ya fi jin sanyin sosai da sosai. Tun da Allah ya jarrabe shi da ciwon nan, bai taɓa jin sanyi mai daɗin wannan ya ratsa shi ba, kuma ya yi imani da Allah daga jikinta wannan sanyin yake, saboda sun samu kusanci sosai da sosai da zai gifta ta. "Allah ya sa ba wani abin ake kuma shirya mini ko wani tarkon ake shirin yi mini da ke ba" Ya yi maganar a zuciyarsa. Nana ta yi mamakin dalilin da ya sanya shi tsayawa haka. Zuciyarsa ta din ga raya masa ya koma da baya, daf da Nana, ko zai fi kin sanyin yadda yake so. AREWABOOKS Nana ta ce "Sayyid ko wani abu ka ke buƙata ne?" Sai da ta yi maganar sannan ya farga, bai ce mata komai ba kawai ya fice ya bar gurin. **** Shukura ce a zaune ta takure jikinta, tana kallon kwanon abincin da aka kawo mata, Abinci mai rai da lafiya sai dai ko sha'awar kai wa bakinta ba ta yi ba, duk da uwar yunwar da take ji, tamkar ta ci babu. Shiru ta yi tana tuna yadda bayan fitowarta daga Asibiti suka yi karo da wani mai adaidaita sahu. Ya fito yana jarabar sai ta biya shi, duk da shi ne da laifi, amma ta kasa fitowa daga motar, ta sauke gilas ta ce ya gaya mata dammage ɗin nawa ta yi masa ta biya shi. Daga sauke glass ɗin nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi ta ganta a wannan ɗakin, da sai dai a zuro mata abinci kawai. Ba ta iya banbance adadin lokacin da ta kwashe a gurin ba, sai dai ta kintaci lokacin salla ta yi. Babu tsammani ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, hakan ya sanya ta kalli ƙofar da sauri. Sai dai hasken fitilar mai wayarya haske mata ido, ba ta iya gane waye ba. Sannu a hankali ya jingine wayar hannunsa ya zura mata ido. Duk da ta ɗan razana amma abin bai wani ba ta mamaki sosai ba. Ya zuba mata ido sannan ya ce "Kin yi mamaki ko?" Ta girgiza kai ta ce "Ba sosai ba" "Ko me yasa?" "Saboda jikina ya daɗe da bani hakan" "Ta yaya kenan?" "Na daɗe ina zarginka ne, sai dai ana ta dankwafe ni, an hanani" "Gaskiya ne, ban so ki zurfafa ki takura da son sanin abin da bai kamata ki yi ta bibiya sai kin gano ba, amma ban san me ki ka gani ki ka dage kina bin diddigina ba" "Zarginka nake yi da kai da doctor Sharif na kasa yadda ɗa na mutuwa ya yi, saboda har yau ina ji a jikina, mafarkin da na yi gaskiya ne" Alhaji Zailani ya ce "Haka ne, lokuta da dama mafarki ishara ne, duk da ban san abin da ki ka gani ba, amma zarginki gaskiya ne duk da na yi iya yi na a kan na ɓoye komai, sai dai kashi kin zaƙe Shukura, soyayyar da nake yi miki ba za ta hana ni ɗaukar matakin da ya dace a kan ki ba" Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Da gaske ka na da masaniya a kan batun mahaifar Mami?" "Ina da ita, haka zalika ina da masaniya a kan jaririnki ma da ki ke ta zargina da Sharif a kai, duk da ban san me ki ka gani a mafarkin ba" Shukura ta yi masa wani irin kallo, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. "Tabbas mafarkinki ishara ne. Amma kafin na yi miki wannan bayanin ina son ki sani, talauci bala'i ne Shukura, babu yadda ban yi a kan na yi yaƙi da shi ba, amma abu ya gagara. Na faɗi na tashi na yi iya yi na amma na kasa nasara a rayuwata. Burina ya gaza cika na mallakar manyan motoci da gidaje da tara manyan kuɗaɗe yadda zan yi nesa da talauci. 'yar makarantar da nake taƙama da ita, abubuwa suka nemi ƙwace mini, bayan faɗuwa a jarrabbawa. A taƙaice dai a makaranta na samu ƙungiyar asiri na shiga, cike da burin na gama makaranta cikin sa'a da fatan cikar burikana na yin arziki mai yawan gaske ta hanya mai matuƙar sauƙi. Bayan na auri mahaifiyarku, ta haifi Sadik, ƙungiya ta fara neman jini a gurina. Na bayar da babban ɗa na Sadik, na kaɗu na shiga tashin hankali, sai dai hakan ne zai ba ni damar taka babban matsayi a ƙungiyar, duk da na bayar da waɗanda ba jinina ba a ƙungiyar amma na ji zafin bayar da Sadik. Aka haifi Yusuf, aka haife ki, ba a sake neman kowa ba, sai da wata buƙata ta sake taso mini, wadda biyan buƙatar na buƙatar na ƙara taka wani matsayi a ƙungiyar. Haka na bayar da matata ta fari, Hafsat da tsohon ciki, na saka mata ƙyallen jini a ƙasan shimfiɗarta ta tashi da ciwon naƙuda ta mutu a gurin haihuwa. Hakan ya sanya dukiyata ƙara haɓaka, na yi kuɗi na yi suna. Duk fafutukar kasuwanci da muke yi tare da Fatuhu, shikaɗai yake abin sa, ni fakewa kawai nake yi da kasuwanci amma ta ƙungiyar asiri nake samun kuɗina. Duk da ina samu ta kasuwancin ma, amma ga mamakina Fatuhu da baya ƙungiyar asiri, ya fi ni samun kuɗi, kuma duk inda muka je an fi son sa. Bayan na auri Amina, aka buƙaci duk wani ɗa da za ta haifa, zan din ga ba wa dodon ƙungiya. Lamarin ya yi mini nauyi, saboda ina jin ɗacin rabuwa da iyalina. Na nemi sassauci, sai aka dasa wa Amina wani jaririn aljani a cikin mahaifarta, duk cikin da ta samu ba ma ta sani yake cinyewa. Sai dai kawai ta wayi gari tana zubar da jini, babu ƙaƙƙautawa. Karo shida na shidan saura ƙiris ta rasa ranta, saboda jini take zubarwa ba kaɗan ba, sai dai a yi ta saka mata jini. Ba a taɓa gane ɓari take yi ba, an zata larura ce kawai,  Asibiti aka kasa gane abin da yake damunta, na kuma hana a yi mata na hausa, tana zaune lafiya kawai sai ta hau zubar da jini babu ƙaƙƙautawa. Ta damu ta damu da matsalar rashin haihuwa, amma na hana ta zuwa Asibiti ta ci gaba da bibiyar lafiyarta. Ni kaina na damu da wahalar da take sha, sai aka nemi na sadaukar da mahaifarta gaba ɗaya ga wannan jaririn aljani, yadda ba sai ta ci gaba da samun ciki ba, cinyewar da yake tana azabtar da ita ba. Haka na amince, cikin dare ta farka tana ihu da buge-bige, ina kunna fitila na haska, na ganmu a cikin jini male-male. Na rirriƙe ta, amma ta fita daga hayyacinta, ihu kawai take tana riƙe mararta, a dole  na ɗauke ta muka yi Asibiti, ganin za ta rasa ranta saboda zubar jinin nan. Ta fi kwana uku ba ta hayyacinta, jini kawai ake saka mata. Aka tura mu scanic, domin a gano musababbin zubar jinin. Na takurawa mai scanic ɗin ya gaya mini me ya gani. Ya sanar da ni babu mahaifa ma a jikinta gaba ɗaya, dan haka bai ma gano daga inda bleeding ɗin yake ba a scanic ɗin, sai dai a ci gaba da bincike. Abin ya bani mamaki, duk da a cikin ƙungiyar asiri nake, ban taɓa tunanin za a ga abin a zahiri a yi scan a ga babu mahaifa ba. Na biya mai scannnic kuɗi, ya rubuta sakamakon da ba daidai ba. Muka koma gurin likita, aka din ga bincike ba a gane komai ba. Ita kuwa sai da ta shafe kwana goma ba ta tantance wanda yake kanta, har an fitar da rai da ita sai kuma ta warke. Na daɗe ina tunanin abin da na yi mata saboda son da nake yi mata. Muka tattauna da malamina, da mamakin yadda a scanic ɗin aka gane bata da mahaifa ma zata a zahiri bs a za a gane ba. Sai ya ce mini idan na ce haka na ƙaryata kungiyar asiri gaskiya ce kenan, amma ya aka yi na yadda da kuɗin da nake samu a cikinta, har nake kashe su a zahiri? Ya ce mini dole na san duk yadda zan yi na ci gaba da rufe mata ba ta da mahaifa, dan kar ta ce za ta bi diddigi duk da ko ta bi diddigin babu abin da za ta iya ganowa. Wannan aljani haryanzu yana rayuwa a cikin Amina, gurbin da mahaifarta take, kan addabe ta da ciwo wasu lokutan, sannan wannan aljani shi ne yake saka ta zubar da jini lokaci zuwa lokaci da take tunanin Al'ada take yi. Wasu lokutan ta zubar da jini fiye da kima wanda take tunanin duk su ne dalilin rashin haihuwarta." Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba. Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba. Da ƙyar ta harhaɗo kalmomin da ta ce "Kai ka kashe Mummy, kuma ka bayar da mahaifar Mami? Da..da.dama aljani duk zai iya yin irin wannan abin?" Yayi dariya ya ce "Ki na mamaki ne? Kodayake mutane duk abin da ba a kanmu ya faru ba, bamu fiye yarda ba, nima da fari kasa yarda na yi, abin ya ɗaure mini kai. Sai dai idan ki ka duba, ba a taɓa yi wa Amina aiki ba, kuma babu alamar tabo na tiyata a jikinta, dan haka ta yaya za ta rasa mahaifarta? Aljani muddin za ka yi masa biyayya, ka yi abin da yake so, to zai zama mai biya maka dukkanin buƙatunka. Da su ake sihiri, da su ake jifa, neman shugabanci, ɗaukaka kungiyoyin asiri da makamantansu. Duk wani siddabaru da za a ce miki sun yi ba abin mamaki ba ne ba" Ya yi maganar yana wata 'yar guntuwar dariya. Shukura ta ƙara rikicewa ta kiɗime. Ta ce "Yanzu Daddy, duk son da mahaifiyarmu ta yi maka kai ka kashe ta? Ga amanarmu da Mami ta riƙe ta kula da mu, ashe dama rashin haihuwarta da ciwon nan na zubar da jini da take yi babu gaira babu dalili, kai ne sila? Kai ka haddassa mata? Yanzu tayaya zaka nemi yafiyar su? Ka rasa imaninka saboda abin Duniya? Kai fa ka kashe su" Ya ce "No in ji wa? Ai ban rasa imanina ba, ai annabi ya ce duk wanda ya ce La'ila ha illalahu zai shiga aljanna" Cikin kuka ta ce "La'ila ha illalahu ba ta fatar baki ba Daddy, tayaya za ka shiga aljanna bayan ka kai buƙatarka gurin wanin Allah da ya buƙaci ka saɓa wa mahaliccinka dan ya biya maka buƙata. Me yasa ka ga buƙatar ka ta yi girman da ta gagari Ubangijinka ka dangana ga waninsa" "Wannan wa'azin naki kin riga kin makara Shukura. Ina da yaƙinin zan tuba kan na mutu, kuma Allah zai yafe mini" "Wa ya baka garantin ganin nan da awa ɗaya ma?" Ta yi maganar tana kuka mai tsuma zuciya. "Ina da shi, dan ko ciwon kai sai na shekara ban yi ba" Ya miƙe tsaye yana faɗin "Ki mayar da hankali ki din ga cin abinci, saboda ke da abin cikinki nake sanya ran ku zama sadsukarwar ƙarshe da zan yi a ƙungiya. Sai dai kafin nan, ina roƙon afuwarki ko ba komai ke ma kin ci albarkacin dukiyata. Ɗanki da ki ka rasa ni na yi amfani da shi" Daga nan ya ɗauki wayarsa ya yi gaba abin sa hankalinsa a kwance, kamar bai aikata komai ba. Wani irin gunji Shukura ta din ga yi tana kuka mai tsuma zuciya, ta din ga fatan ina ma mafarki ne ba gaske ba. Tabbas wannan babbar jarrabawa ce, a ce mutum irin mahaifinta shi ne mahaifinka, gara a ce an haife ka ba ta hanyar aure ba, ko makamancin haka. Amma uba irin Alhaji Zailani ba shi da wani amfani. Duk wata gwagwarmayar sa da faɗi tashinsa a kan iyalinsa ya zama na banza, a dalilin wannan mummunar hanyar mara ɓullewa. Abubuwan da ya gaya mata sun shallake tunaninta, yanzu yadda ya tafi haka zai je ya ci gaba da rayuwa da Hajiya Amina duk da zaluncin da ya yi mata. Ta ji dama ta ba wa Sagir damar kai ta Asibiti wataƙila da ba a samu damar sace ta ba. Cikin kuka take roƙon Ubangiji Allah ya tona wa mahaifinta asiri, saboda a yadda zuciyarsa ta ƙeƙashe ɗin nan, babu wani abu na rashin imani da zalunci da ba zai iya aikatawa ba. Can gida Sagir ko abinci ba ya iya ci. Yusra kuwa abin ka da ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, sai ta kwanta rashin lafiya, saboda yadda ta addabi kanta da ɗorawa kanta alhakin ɓatan Shukura, dan cewa take saboda ta dawo gidan Sagir Shukura ta tafi. Haka Hajiya Amina ma, Addu'a kawai take yi a kan Ubangiji Allah ya bayyana Shukura a duk inda take. Sosai take jin tamkar 'yar cikinta ce ta ɓata, tun tana daurewa har ta kasa ta fara zubar da hawaye, kasancewar babu wani labari mai daɗin ji da zai nuna an kusa gano inda Shukura take. **** Asal ta na tsaye a banɗakin cikin ɗakinta, bayan tabattar da Imam baya ɗakin, ta danna wata lamba ta kira. Can aka ɗauka mutumin ya ce "Na'am ina jin ki" "Ina da labari ne" "Ina sauraren ki" Ta numfasa ta ce "Hannun Imam babu zobensa na tambari, na tambaye shi ya ce mini karyewa ya yi ya kai gyara, daga bisani kuma ya ce mini bai san inda yake ba" "Kin tabattar da hakan, ba kuma ɓoye shi ya yi a wani gurin ba?" Asal ta ce "Eh na tabattar ai zobe ne da ba ya cire shi, tun da ya dawo babu zoben a tare da shi" Mutumin ya numfasa ya ce "Madalla, ki ci gaba da sanya ido da sanar da ni duk wani abu da yakamata na sani" Ta jinjina kai tamkar yana ganinta ta kashe wayar ta fita. Jikin Nana tamkar an yi mata duka, saboda azabar gajiya da ta yi. Ta kammala aikinta tana ta gyaran kitchen, sai ga Balaraba ta shigo da ƙatuwar jarka. Ta ajiye ta ta ce "Gashi nan madarar raƙumi ce da Imam yake sha" "To sannu da ƙoƙari Mama Balaraba" Ta ce "Yauwwa kukun Imam, Allah ya taimake ki" Nana ta yi murmushi ta ce "Kar ki ba ni kunya mana" "Ba kunya zan ba ki ba, ai ke yanzu duk wata kuku a gidan nan a ƙarƙashinki take, ke kaɗai ki ke dafa abincin da zai ci, dole mu girmama ki saboda kema shugabarmu ce" "A'a ni ba shugabarku ba ce ba, ni da nake bare ma a cikinku. Amma dan Allah Mama Balaraba wai su wa ake cewa Imam ɗin nan ne? Dan na ga wanda ake kira da hakan da yawa" "Eh su Biyar ne, galibinsu jikoki ne na gidan sarauta, su na cikin jerin waɗanda za su iya gadon kujerar Sultan. Shi Imam Hammad a gidansu su biyu ne  da shi da Imam Abdallah, sai Imam Zahradeen shi ma jikan marigayi Sultan ne, akwai Imam Asadullah yayan Asal, sai Imam Omar, waɗannan su ne jerin waɗanda ake sanya ran za su gaji kujerar Sultan. Duk da su na ganin cewa Sultan na yanzu nuna son kai ƙarara na son Imam Hammad ya gaje shi a cikin yaransa. Imam Hammad yana da 'yan uwa da suke uba ɗaya amma su biyu ne suka cika ƙa'idojin zama Imam. A ƙasar nan ana girmama duk wani Imam fiye da zatonki, mu na ƙasa mu na son Imam Hammad sosai mussaman baƙaƙen buzaye da fararen ke  yi mana kallon kamar ba 'yan uwansu ne mu ba, bayinsu ne kawai. Idan kin lura galibi hadiman gidan nan baƙaƙen buzaye ne, fararen kaɗan ne ƙarara yake ƙoƙarin yaƙi da kyamar da fararen buzaye suke yi mana, yana ta fafutukar nema mana 'yanci, da ƙoƙarin mu ma a din ga bamu dama a cikin shugabanci, bai kamata iyayenmu sun ƙare a bauta mu ma mu ƙare a haka ba. Amma manyan nan ba sa son shi sam, gani suke yana ƙoƙarin hana su rawar gaban hantsi. Ni tun da ya dawo ma duk ya canza mutum ne mai sanyin hali, amma kaifi ɗaya ne, ba sani babu sabo. Shi ne shugaban majalisar duk Imam ɗin ƙasar nan. Duk da a cikin su akwai wanda suka girme masa, amma a haka dole su girmama shi kamar yadda yake a dokar ƙasar nan. Tarihin masarautar Agadez yana da yawa da kuma faɗi Nana, bari na tafi na je na ci gaba da aikina. Nana ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai da sosai" Bayan fitar Balaraba Nana ta naɗe hannunta a ƙirjinta, tana nazari da tunani. Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, ta duba kayanta ta lalubo takardar nan da aka kawo saƙon aka ce a ba wa Sayyid. Ta ƙare wa takardar kallo. "Ko a cikin Imams ɗin nan ne wani ya aiko da wannan takardar?" Ta yi maganar tana tuna maganganun da ta ji suna yi ranar da aka kai su yin girki a gidan Sultan. Ta koma ta lalubo zoben gurin Sayyid ta din ga jujjuya zoben ta ce "Ko kai a ke nema ne? Idan kai ne ta yaya zan ba shi abin sa, tun da ban san iya adadin muhimmancin sa a gare ka ba, idan na baka ka manta ni ta yaya zan yi bayani a yarda da ni?" Ta din ga surutai ita kaɗai ta gaji ta nannaɗe kayan ta buɗe jakar sarkin baka ta watsa takardar da zoben ta rufe ta ajiye a cikin kayanta. Bayan sallar magariba aka sanar mata baƙin Imam sun iso, su na can sashin karɓar baƙin sa wanda ɗaki ne a can wajen lambun gidan. A kwanduna ta shirya kulolin Abincin, ɗaya daga ma'aikatan gidan, ta taya ta kai wa. Su na zazzaune a ɗakin, gaban su shaƙe da kayan marmari da uban soyayyen nama. Duk wannan Imam Imam ɗin ne, gaba ɗaya zaune a gurin. Ayabar hannun Sayyid ta kalla, da ya kai bakinsa ya gutsura fuskarsa ɗauke da murmushi. A take ta ga jini yana bin bakinsa, ayabar ta koma baƙa ƙirin, wasu abubuwa masu tsini tamkar ƙayoyi suka tsiro a jikinta. Ayshercool 08081012143 77 Rikicewa ta yi, amma ta fara ƙoƙarin daidaita nutsuwarta dan ta san idan ta yi wani gangancin a gurin, babu lallai ta sha ta daɗin rai duba da girman mutanen da suke gurin a zaune. Ganin ta tsaya ta zuba masa ido, ya sanya ya sauke hannunsa a hankali yana kallon ta shi ma. Ta ƙarasa shigowa a hankali ta ajiye musu kwanukan abincin. Zuba mata ido suka yi, gaba ɗaya suka yi shiru daga hirar da suke yi. Ta ce "Shugabana, ga abincin ko zan jira ku duba idan da abin da bai yi ba?" Ya girgiza kai ya ce "Za ki iya tafiya" Sai dai ta kasa tashi, ta ci gaba da rarraba ido. Ya sake cewa "Za ki iya tafiya" "Dan Allah ka taimaka mini da ayabar hannunka, yunwa nake ji" Imam Omar ya ce "Imam Hammad, wai wace ce wannan ɗin? Ta san waye kai kuwa abin hannunka za ka ba ta?" Ya kalli ayabar ya kalle ta, bai kai ga yin magana ba, ta saka hannayenta biyu ta miƙa masa. Tamkar soko haka ya miƙa mata ayabar, ba tare da musun komai ba. Ya ce "Ga wata nan ki ɗauki yadda za ta ishe ki" Ta girgiza kai ta ce "Wannan kawai ta ishe ni, na gode sosai da sosai" Duk su ka bi Nana da ido, wasu cike da takaici, wasu kuma mamakin tsaurin idonta, duk da ba abin mamaki ba ne sosai, tun da ba ta san irin girmansu da matsayinsu ba, kasancewarta bare ba ƙabilarsu ba, kuma ba 'yar ƙasarsu ba. A hankali ta saci kallon hannayensu, sai ta gan su sanye da zobunan nan irin na hannun Sayyid da ya ɗauka ya bata. A take ta koma gefe ta cinye ayabar, sannan ta yinƙura ta tashi. Imam Asad ya fara masifar wace mahaukaciyar haka, da za ta zo ta yi musu wannan rashin hankalin, su zuba ido su na kallonta. Hammad ya ce "Ina mai baku haƙuri, baƙuwa ce a cikin lamarin gidan mulki, ku yi mata afuwa" Nana tuni ta fice daga ɗakin, aikuwa fitarta ke da wuya, jiri ya fara ɗibanta, bango ta dafa tana bi a hankali, sai dai kan ta kai inda take so ta yanke jiki ta faɗi. Faɗan Ƙaisar ne ya sanya ta buɗe ido, a matuƙar galabaice. "Waye ya ce da ki ka karɓa ki ci? Kin san abin da aka yi a jikin ayabar? Ban da na riga na buɗe miki ido ki na ganin abubuwa, da ba zan sake bari ki ga komai a kansa. Sai kin kashe kan ki a banza a kan mutumin nan, gaba ɗaya kin ƙarar da ƙarfinsa a kan ki, wanda ko tabbacin idan ya tuna ki zai miki irin wannan son ba ki da shi" Nana dai kasa magana ta yi, saboda yadda jikinta yake a mace, duniyar take juya mata. Ɗaga bakinta ya yi ya zuba mata wani abu mai kama da turiri, ta yi wani yinƙuri ta hau amai ta hanci da bakinta. Ba ƙaramin galabaita ta yi ba, jin yadda ƙayoyin da suka tsiro a jikin ayabar su na sukar ƙirjinta gurin yinƙurin aman da ta yi. Cikin fusata mutumin yake magana, "Wane irin wawanci ne haka da shirme da rashin hankali, ta yaya zamu shirya abu ka je ka bari ya ɓaci?" Cikin damuwa matashin ya ce "Wallahi Tafawa ba laifina ba ne ba, dan har ya fara ci wata yarinya ce ta hana shi ci, wai ya ba ta yunwa take ji" "Wace yarinyar ce a kaf faɗin Agadez za ta je tsakiyar ku, har Imam zai ci abu ta ce ya bata? Ɗaya daga cikin mugwayen ɗabi'unsa kenan da ya sanya yake zubar da kimar ku a idon mutane maƙasƙanta, har su samu zarafin raina ku. Ban da raini da wulaƙanci har baiwa ta ga abu a hannun Imam na ƙasar Agadez ta ce za ta ci." Ya buɗe baki zai yi magana ya ce "Ka ga tashi ka bani guri ni kafin na mangare ka" Haka ya ja bakinsa ya tashi ya fice jikinsa a sanyaye. ***** Alhaji Zailani ne a zaune a falon Hajiya Sa'a, ya je yi mata ta'aziyyar mutuwar Abba. Ya numfasa ya ce "Wai dama Abban ba shi da lafiya ne?" Ta girgiza kai ta wassafa masa dukkanin abin da ya faru. Cikin kaɗuwa yake jin bayanin nata. Ya ce "Ban da ke Hajiya Sa'a, ina ke ina gayyato yarinya da rana tsaka ki janyo ta jikinki, ga shi ta zame miki masifa, haba Sa'a. Ke kin san ba kowa a ke fallasawa sirrin ƙungiya ba, Allah ya kyauta, ya yi mata gaisuwa ya tafi. ***** Hammad tun bayan tafiyar sauran 'yan uwansa yake tunani daban-daban a ransa. Tuni aka saita masa wayarsa, ya ci gaba da amfaninsa da ita. Wayewar gari yana ta jiran Abinci amma shiru, ya gaji da jira saboda yana jin yunwa, ya tafi ya tashi Asal da take ta bacci. "Imam lafiya kuwa?" "Ba a kawo mini Abinci ba, ina jin yunwa zan fita" Kamar ta yi tsaki, saboda ta ji daɗin baccin, haushi ya kama ta, tare da tunanin uban abin da ya hana Nana tashi ta yi masa girki ko ta makara haka. Ga shi duk hadiman sashen ta kore su, dan haka ta tashi da kanta, ta fita. A zaune ta tarar da Nana ta jingina da bango, idanunta duk sun faɗa kamar ta kwana tana amai da gudawa. "Wani wulaƙancin ne ya sanya ba ki tashi kin yi wa Imam girki ba, har ki ka saka na biyo ki nan?" Nana ta numfasa ta ce "Ba ni da lafiya ne" "Ba ki da lafiya kuma Imam ba zai ci abinci ba? Kin san ba kowane Abinci yake ci ba" Wani malulun takaici ya ƙule Nana, wato lafiyarta ba abin da yake gabanta ba ne, kawai fatanta ta yi wa mijinta girki tun da ga baiwa. "Magana nake yi miki kin yi mini shiru" "To me zan ce miki, ba ni da lafiya, ai ban taɓa ƙin yin girki ba. Ko wani abu da ki ka saka ni ba, amma yau ba ni da lafiya babu abin da zan iya yi. Idan ke ba za ki yi mini uzuri ba, ki gaya masa kukunsa babu lafiya na san, shi zai iya yi mini uzuri" A hasale Asal ta buɗe baki za ta yi magana, Nana ta yi mata wani irin kallo, da a dole ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓa wa Nana. Ta haƙura ta juya ta fita, tana tunanin me ta ji ne ko ta gani, ta kasa yi wa Nana rashin mutunci. Tana komawa ya kalle ta ya ce "Ina Abincin?" "Wai ba ta da lafiya" "Me ya same ta?" Ta girgiza kai jiki a mace ta ce "Nima ban sani ba" Ya so sake wata tambayar, amma sanin halin Asal ya sanya shi ta shi, zai fita. Ta ce "To ina za ka je ba ka karya ba?" "Zan samu abin da zan ci, zan je na ga Mahmoud ne" Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fita. Bakin Imam Hammad fal maganganu kamar yadda bakin Mahmudu yake fal maganganu, amma kowanne ya kasa furta wa kowa. Hammad ne ya numfasa ya ce "Mahmud ina son na koma kan ayyukana, amma Sultan ya ce mini na dakata, akwai abubuwan da nake son yi da yawa." Mahmoudu ya ce "To ka yi haƙuri, wataƙila akwai dalilin da ya sanya ya ce ka dakata tukuna" Ya numfasa ya ce "Haka ne, wai yaushe za ka shigo gida ne?" Ya girgiza kai ya ce "Ba na son shiga gidan nan naku" "Saboda me?" "Kai ma ka sani ai" Imam ya ce "Ban san komai ba. Jiya Imams sun kawo mini ziyara. Ranar Lahadi za mu yi zagayen raƙuma da shan shayi, ka zo mu je tare" "Imam, ka na manta waye ni, da ƙoƙarin kai ni matsayin da Allah bai kai ni ba, ni dai dan Allah ka yi haƙuri" "Mahmoudu, idan ba kai ba wa ka ke so na janyo jikina? Ka san komai fa? Shikenan haka ni zan zauna?" Yayi maganar muryarsa ɗauke da rauni. "Haba jarumin shugabana, ka na fa da wanda ku ka shaƙu, ku ke da kusanci tsakaninku sosai da sosai" "Waye?" Ya yi maganar yana kallonsa. "Zan haɗa ku kwanan nan, aure zan ƙara yi maka kwanan nan, ka na son 'yar Nigeria?" Ƙanƙance idanunsa ya yi yana kallon Mahmoudu. Ya ce "Ga ka nan ga Asal ai" "Ahh yi haƙuri, kar ka gaya mata sai ta saka a fille mini kai" Hammad ya yi murmushi yana gyara zamansa. Sai da Nana ta shafe kwana uku ba ta aikin komai, haka kurum Imam ya ji abin ya tsaye masa ya dame shi, ko ya yi ƙoƙarin mantawa sai ya kasa. Kwanakin nan uku kame-kame kawai yake yi gurin cin abinci, duk abin da zai ci sai ya ga kamar abin zai cutar da shi. Ga uwa uba rashin ɗanɗanon abinci da ba ya ji gaba ɗaya. Yau da Nana ta lallaɓa ta fito, ta ji ana ta zancen hawan zagayen da za a yi a kan raƙuma. Har ya yi shirinsa zai fita, ya tarar da Abinci a falo. Cikin zaƙuwa ya ƙarasa ya buɗe, tabbas ƙamshin girkinta ne. Wani murmushi ya suɓuce masa cike da farin ciki. Sai dai sam ba su haɗu ba. Har yau jikinta babu ƙwari sosai, bayan fitarsa ta shiga ta gyara abin da za ta gyara, kawai ta nemi guri ta zauna, tana hutawa wani irin bacci ne ya ɗauke ta a gurin. Ba ta jima da fara baccin ba, sai ga ta a Libraryn Ƙaisar. Waiwaye ta fara yi taga ta ina za ta gan shi, sai dai ba ta gan shin ba, sai wata guguwa da ta taso, ta watso mata littafin nan da ta ce ba za ta karanta ba. Ta kalli littafin a gabanta amma ba ta motsa ba, ba kuma ta ɗauka ba. Kawai littafin ya buɗe kansa da kansa, sai mudubin nan ya haska inda ya buɗe ɗin. Sayyid ta gani a tsaye a cikin sahara ana ta harbo masa kibiya ta ko ina, Sultan ta ta gani yana ƙoƙarin tare masa, shi ana samun sa da kibiyar. Har ya fara gazawa aka fara samun Sayyid. Ya na tsaka da tarewar aka janyo shi aka nufi wata wuta da shi, da cin ta yake gwanin ban tsoro. Ba ta iya ganin fuskar wanda yake jan na shi, saboda ya rufe fuskarsa da rawani. Gaba ɗaya Nana ta gigice ta rintse idanunta tana addu'a kar Allah ya ba wa mutumin nasara, can jin shiru sai ta buɗe idonta a hankali. Sai ta daina ganin wancan lamarin, sai wata taguwa da ake ta ɗurawa wasu abubuwa. Sayyid na zuwa ya kama taguwar ya hau, yana hawa ta din ga walagigi da shi, ta nufi kan wani rami da shi. Zumbur Nana ta tashi, tare da miƙewa tsaye a falon. Zuciyarta sai bugawa take yi da sauri. Waje ta yi da wani irin hanzari, ta nufi inda ake shirya raƙuman da za a yi hawan da su. Raƙuman duk jajaye ne, an yi musu wani irin ado, ga su ƙosassu. Gaba ɗaya ta ji ba ta yarda da lamarin ba, ta juya ta sake kwasar hanya ta koma sashen su. Tana zuwa ta ci karo da shi ya fito, sanye da makamanciyar shigar da ya shigo ɗakinta bayan auren su. Takobinsa na soke a gefen ƙugunsa, babbar rigar jikinsa ta sha aiki. Kallon Nana ya yi, fuskarta ta nuna rama sosai da sosai. Nana so take ta yi masa magana amma yana tare da Asal da ta sha kwalliya ita ma, sai hura hanci take yi. Gaba ɗaya yanayinta ya nuna masa a rikice take, kuma magana ce a bakinta. Har za su gifta inda Nana take ya ce "Sayyid excuse me" Asal ta waiwayo ta kalli Nana jin ta ce masa Sayyid maimakon Imam. Ya kalli Asal ya kalli Nana, sai kuma ya yi taku biyu ya matsa daf da Nana, ya sunkuyo daidai tsawonta. Gaba ɗaya sauran barorin da suke gurin ma zubo musu ido suka yi. "Dan Allah kar ka hau Taguwar nan" Ta yi maganar cikin tsoro muryarta har tana rawa. Ya ɗaga idonsa ya saka a nata, wanda hakan ya rikita ta, tamkar ba ta taɓa saninsa ba. Bai ce mata komai ba, ya miƙe ya yi gaba. Asal ta bi shi cikin fushi tana tambayarsa "Wai me ta ce maka?" Ya numfasa ya ce "Da tana son ki ji, ba za ta zaɓi ta gaya mini ba". "Imam ban gane ba, mene ne abin da ba za ta faɗa kowa ya ji ba?" "Ai kin san duk wanda yake ƙarƙashina, ina ba shi lokacina na saurare shi. Kar ki manta mutumin da yake da Asal doka ba ta ba shi dama a kan wata wadda ba ƙabilarsa ba, mussaman baƙar fata, kin fi kowa sani na, ki daina saka wani abu a ranki dan Allah" Ya yi maganar daidai lokacin da suka ƙarasa gurin. Daga nesa Nana take hango an ba shi shayi a kofi, ya karɓa ya shanye, an sake zuba masa ya karɓa ya sha. Aka cika gurin da kaɗe-kaɗe, juyi suka din ga yi tare da sauran 'yan uwansa Imam, su na wasa da takubbansu, gwanin burgewa. Duk da tashin hankalin da Nana take ciki, sai da abin ya ƙayatar da ita. Aka jero raƙuman nan, suka din ga kama su su na hawa. Nana gabanta ya tsananta faɗuwa, cike da ƙwarewa ya kama raƙumin nan ya haye. Idonsa suka sauka a cikin na Nana, fuskarta ɗauke da damuwa, ya lumshe idanunsa ya saita akalar raƙumin nasa, ya wuce gaba sauran suka bi bayansa. Mutane suka rufa musu baya, suka kama hanyar barin gidan. Jiki a sanyaye Nana ta koma. A tsaye ta jingina a gurin girki, tana tunanin abin da ka iya biyo bayan hawan Raƙumar nan da ya yi. But Asal ta faɗo cikin huci, Nana ko motsawa ba ta yi ba sai bin ta da kallo kawai da ta yi. Har gabanta Asal ta zo tana huci "Uban me ki ka gaya wa Imam, kuma saboda me za ki din ga kiransa da Sayyid? Ban yi miki gargaɗi a kan sa ba?" Nana ta kalle ta, ta ga kar ta yi wani abun da zai sanya ta kore ta a yanzu, dan haka ta sassauta murya ta ce "Haba ya shugabata, Sayyid da Imam duk abu ɗaya ne ai, yana nufin shugaba, mu a Nigeria Sayyid muke cewa, kema idan ki na so sai na kira ki Sayyada. Kuma me Sayyid zai yi da baƙar mace 'yar Nigeria, ai ramin kura sai 'ya'yanta. Kawai ne nemi afuwarsa ne a kan rashin samun gudanar da aikina da na yi, a kwanaki da suka gabata, saboda shi ne ƙa'idar gidan sarauta. Ki yi haƙuri iya matsayina da aikina nake tsayawa." Asal ta numfasa tana huci, duk da hankalinta ya ɗan kwanta. "Shikenan na ji, daga yanzu za ki bar ɗakin da ki ke, za ki koma ɗakin hadimai da ke tsakanin sashen Imam da nawa. Sannan akwai gurin girki a gurin girki a gurin, yadda za a din ga sauƙaƙa miki, sai dai babu ke babu fitowa a duk lokacin da yake nan, muddin ba abinci ki ka kawo masa ba, kuma ba gyaran sashen za ki yi ba. An dawo da ke sashen nan ne, domin ƙara tabattar da tsaron abincin da Imam zai ci" Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, na gode sosai da sosai" "Ki hanzarta, ki kwaso kayanki ki mayar can, a yau ba sai gobe ba, ku yi magana da Balaraba ta kai ki" Nana ta risuna ta yi wa Asal godiya, haka aka yi, a ranar ta kwashe kayanta ta mayar can ɓangaren, barorin gidan na ta ƙara mamakin, yadda a ke ɗaga likkafar Nana baƙuwar haure sama da su. Nana kuwa murna ta din ga yi, ganin tana ƙara samun kusanci da Imam, ta san addu'a da take yi ce Allah yake taimakonta, kuma tana fatan Allah zai yanke mata wannan wahalar nan kusa. Fita ta yi da nufin ta kwaso kayan wancan ɗakin girkin ta dawo da su nan, ta ga mutane na kaiwa da komowa a sashen. Wani ta gani a cikin mutanen fuskarsa rufe da rawani, amma ta ga kamar ta san shi ta taɓa ganinsa, kamar ta bi bayan mutumin, sai ta ji ana faɗin Imam ne ya faɗo daga kan Taguwarsa.! AREWABOOKS Nana ta rasa wa za ta nufa ta samu cikakken bayanin abin da ya faru. Ta san za a rina, tun da ta ga abin nan kuma ta din ga ji a jikinta, ta san wani abun sai ya faru. A can ɗaki kuma, sannu Asal ta din ga jera masa, ya jinjina mata kai kawai. Ya lumshe idanunsa yana tuna yadda Nana ta roƙe shi kar ya hau Taguwar. "Wace ce ke?" Ya furta a hankali. Asal ta ce "Magana ka ke yi ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Tun da ya hau kan Taguwar nan yake jiri, duk yadda ya ƙwarara jikinsa, da ƙoƙarin sarrafata ya kasa, dan daina gani ya yi gaba ɗaya sai jin sa ya yi ya zamo ƙasa. Ya yi ajiyar zuciya yana sauke numfashi. "Imam na saka ta dawo ɗakin Hadaimai kamar yadda ka buƙata, ko za ka ci wani abun a kawo maka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. "Ina ne yake yi maka ciwo to?" Ya yinƙura ya tashi ya ce "Babu ko ina salla zan yi" Yana tangaɗi haka ya shiga ya yi salla, ya sake kwanciya. Nana na ta kai komo falon babu kowa, tana son ta san halin da yake ciki amma babu wanda za ta tambaya. Wata tawaga ta ga sun shigo sashen, kallo ɗaya ta yi masa ta gane Sultan, tana son fita tana jin tsoron kar ta yi laifi, haka ta tsaya tana hangen abin da yake faruwa. Asal ta fito cikin hijjabi suka gaisa, ta yi wa Sultan jagora zuwa cikin ɗakin. Da hanzari ya nufe shi yana faɗin "Hammad, tashi maza a tafi Asibiti" Ya buɗe idonsa ya kalle shi ya ce "Babu abin da yake damuna Sultan, ba sai na je Asibiti ba" Cikin damuwa ya ce "Me yasa ka yi hawan bayan ka san ba cikakkiyar Lafiya ce da kai ba? Kuma da ka ji ba za ka iya ba ai sai ka haƙura" "Lokacin da na yi ba na jin komai a jikina, amma tuba nake ba zan sake ba" Sultan ya ce "Ka tabattar ba ka jin komai a jikinka ba sai mun je Asibiti ba?" "Ba na jin komai Abie, ka kwantar da hankalinka" Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, Allah ya tsare gaba ka kwanta ka huta sosai" Ya jinjina masa kai, suka yi sallama ya tafi. Duk yadda Nana ta so sanin halin da yake ciki, haka ta haƙura, sai dai bacci mai daɗi ya gagara ɗaukan ta. Da sassafe ta fita ta hau gyaran sashen, tana jira ko za ta ji motsin Asal, duk yadda za a yi ta tambaye ta, ya jikinsa sai dai ta ji shiru, haka ta ajiye Abincin kari ta koma ɗakin da aka ba ta. Sai wajen sha daya da rabi, ta ji motsi a falon, ta fito ta leƙa. Shiru ta yi tana kallon mutumin da ya zo, kamar shi ta taɓa gani a gidan cin abincin su Al Hussain. Yana tare da Imam Asad. Sayyid yana zaune a ƙasan Carfet, shi kuma yana saman kujera. Allah ya taimaki Nana da Hausa suke magana, ba yarensu ba. "Kai ya aka yi ka faɗo daga kan taguwa, ko ka fara shan wani abu ne ba mu sani ba?" Asal ta ce "A'a Imam ba ya shan komai, dama ba shi da cikakkiyar lafiya ai" "Ina magana kina sanya baki?" Asal ta ja bakinta ta tsuke. Ya mayar da idanunsa kan Hammad ya ci gaba da cewa "Allah ya sauwwaƙe ya kuma kiyaye gaba. Amma ka din ga kulawa dai" Bai ko ɗaga kansa ba, balle ya tanka masa, sai dai jikin Asal ya yi sanyi. Ba ta ji daɗin yadda Tafawa ya zarge shi da shaye-shaye ba. Wuni aka yi zuwa duba Imam Hammad, sai dai ds Yamma Nana na tsaka da gyaran falon ta ga wannan takardar, mai ƙwarangwal ɗin nan yana ci da wuta. Gaban Nana ya faɗi, ta yi shiru tana kallon takardar. Jikinta ya ba ta kowaye yake yi masa wannan aika-aika yana cikin waɗanda suka zo dubiya yau. Nana tana aiki a kitchen, Asal ta same ta, ta miƙa mata wani ƙulli ta ce "Ga shi nan, ki dafa wa Imam a shayi, maganinsa ne" Nana ta karɓa ta amsa da to. Ba ta yi tunanin komai ba, ta dafa shayin ta je ta ajiye a falo. Asal tana zaune tana jiranta a falo. Ta tashi ta karɓa, Nana ta ce "A yi wa shugaba sannu, ina fatan Allah ya ba shi lafiya ya kiyaye gaba" Asal ta amsa da Amin a ciki, ta nufi ɗakin baccinsu. Yau Nana kamar ta fasa ihu, ta cika wata guda a gidan Asal, yau gaba ɗaya hankalinta yana kan ɗan jaririnta. Ga shi tun da ta zo ba su yi waya ba ko sau ɗaya ba. Haka kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, kwana uku Asal na ba wa Nana maganin Sayyid tana dafa masa. Sai a na ukun yake fitowa ya zauna a falon, amma ba ya fita. A kai Abincin safiyar kwana na uku, Nana ta haɗu da shi. Cikin girmamawa ta ce "Barka da safiya Sayyid, ashe tsautsayin da ya faru kenan, Ubangiji Allah ya kiyaye gaba." "Ba ki yi mini sannu ba sai yanzu?" Ta ɗaga kai ta kalle shi, duk ta ji abin wani banbarakwai, amma har cikin ranta ta ji dadin maganar da ya yi mata. Ta ɗan juya idanunta ta risunar da kanta ta ce "Tuba nake Shugabana, ban samu damar ganinka ba ne, duk da na yi ƙoƙarin hakan, ba na son uwar gijiyata ta ce na zaƙe ne, amma tuba nake Ubangiji Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani " "Amin na gode sosai. Ina ganin ƙoƙarin da ki ke ta yi, ina yabawa, ki yi haƙuri da Asal kar ki tsane ta, duk da na san tana takura miki wasu lokutan" "Babu takura a ciki, matuƙar hidima taka ce shugabana" Ya ce "Madalla na gode sosai" Ta tashi ta bar falon, a ranta tana cewa ina Asal ta ga kirki, shi da yake hangenta daga nesa ma, ya san tana ƙoƙari, ita kuwa ban da jaraba da uwar hantara da nuna mata ƙyama babu abin da take yi. Asal ta shirya ta fita tun safe, dan haka Imam ne kawai a sashen. Da Nana ta tashi kai masa abincin rana, ta sha kwalliya cikin doguwar rigar Atamfa. Duk yadda yake jin jikinsa babu daɗi, yana motsa shi da kyar, amma bai hana shi satar kallon Nana ba. Ba ƙaramin kyau ta yi ba, ga ƙamshin turaren sa da yake tashi a jikinta. Ta kalli idanunsa da suka yi jawur, tamkar jini zai zubo daga cikin su. "Sayyid lafiya kuwa?" Kai kawai ya jinjina ya mayar da idonsa ya lumshe, yana jin wannan ƙarar mara daɗin ji a kunnensa. Haka Nana ta tashi ta bar shi a gurin, saboda tsoron abin da ka iya biyo baya. Sai dare Asal ta dawo, kuma itakaɗai Nana ta ga ta ci Abincin dare. Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, Nana ta gabatar da sallolinta na dare. Ta zauna tana karanta Alqur'ani, a hankali sai ta daina ganewa. Ziiiiiiiiii ta fara jin ƙarar guguwar iskar sahara tana tasowa. Ta rufe Alqur'anin a hankali ta ajiye, sannu a hankali sanyi ya fara ratsa ta. Ji ta yi tamkar an buga wani abu da ƙarfi, ta zabura ta miƙe tsaye. Cikin hanzari ta buɗe ƙofar ɗakin da take ciki ta fito corridor da ɗakinta yake ta tsaya. "Imam mene ne haka? Meye haka ka ke yi wai?" Sautin kakarinsa ya daki kunnuwan Nana. Gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye. Asal ta gani ta fito da gudu daga ɗakin, ta yi waje ta fice daga falon, ta ja ƙofar falon da karfi ta rufe. Gaba ɗaya sai kan Nana ya kulle ta rasa abin yi, ta bi bayan Asal, amma ta ji ƙofar a rufe gam. Ta juya a hankali ta kalli hanyar bedroom ɗin da sautin kakarinsa yake ta fitowa. A hankali ta fara takawa tana tunkarar hanyar ɗakin, duk da ba ta taɓa zuwa ko daf da gurin ba. Zuciyarta na bugawa cike da tsoro ta buɗe ƙofar ɗakin. Wani irin sanyin na'urar sanyaya ɗaki ta dake ta, hakan ya ƙara ninka sanyin da take ji. Wani ni'imtaccen ƙamshi ya ziyarci hancinta. Girman ɗakin baccin har tsoro ya ba wa Nana, ita dai tana mamakin yadda suke abubuwan su kamar babu lissafi, ɗakin kwana kawai an yi shi gari guda. Idanunta ya sauka a kan Sayyid da yake shirin faɗowa daga kan gadon yana jijjiga. Ta ƙarasa da sauri daidai lokacin ya faɗo ƙasa. Ta ɗaukko pillow za ta saka masa, kawai ta ga wannan hoton a ƙasan fulonsa. Cikin mamaki take kallon hoton, tare da mamakin yaya aka yi ya zo kan shimfiɗarsa. Ta durƙusa a kansa, ta kalli jikinsa duk wata jijiya da take jikinsa ta miƙe ta kumbura. Ƙwayar idonsa ta koma fara ƙal, gashin kansa ya hargitse, gaba ɗaya ya koma abin tsoro tamkar wani dodo. Ta yi Bismillah ta zauna, tare da jin sai dai komai zai faru ya faru, ko a mutu ko a yi rai, ko da za a zo a kama ta gara balli ya tashi ko za su ƙaryatata gara duk abin da zai faru ya faru, da bar shi a wannan yanayin da bayan shi kansa babu wanda ya kai ta sanin mawuyacin halin da yake shiga. Tamkar mayen ƙarfe haka ya riƙe ta gam, bakinsa yana karkarwa yana furta "Wuta! Zafi!" Ya danneta a ƙasa ya ƙanƙameta, bakinsa na fitar za kumfa. A hankali ta fara karanto suratul Saffat, ta sanya hannunta a cikin gashin kansa tana shafawa a hankali. Sannu a hankali ya daina wannan gurnanin da yake yi ya yi shiru, sanyin jikinta ya fara ɗibarsa. Ya yin da ita kuma take jin tamkar ana gasa ta a tukuba saboda zafin Jikinsa. Sosai Nana ta ƙanƙame shi ita ma, cike da matsananciyar kewarsa, wasu hawaye da ita kanta ba ta san na mene ne ba, suka din ga sintiri a kan fuskarta. "Sai ki tashi ki tafi tun da ya samu bacci, tun da ke dai a rayuwarki ba kya tsoron matsala, tarar aradu kawai ki ke yi da ka. Maimakon ki bari mutumin nan ya gane ki, a yi duk wadda za a yi, amma sai ƙoƙarin kunno wa kan ki matsala ki ke yi" Ƙaisar ya yi maganar cike da takaici yana harar ta. Nana ta ce "Wasu lokutan nasara ns buƙatar sadsukarwa, da kuma tarar aradu da ka. Mu da ku ba irin zubin halittarmu ɗaya ba, ba zan iya jure ganinsa a wannan mawuyacin halin ba. Ina tausaya masa a yanzu fiye da a lokacin da na san shi bai kan sa ba, yake ce mini yana ji a jikinsa rayuwar da yake da ni ya fi wadda ya manta aminci da kwanciyar hankali, ga shi kuma yanzu ina gani. Sai na ƙyale shi a haka?" Ƙaisar ya yi tsaki ya ce "Allah ya sa shi zai iya yin abin da ki ke yi a kan sa" Nana ta numfasa ta ce "Dama ba dan ya rama mini nake yi ba" Sai gefen asuba jikinsa ya saki, ya ci gaba da nannauyan bacci. Ta saka masa filo ta tashi, sai dai jikinta tamkar ana karyata haka take ji, saboda azabar riƙon da ya yi mata. Bayan ta idar da sallar asuba, ta yi adduo'inta ta shiga kitchen. Kafin ƙarfe tara har ta kammala komai, ciki har da gyaran katafaren falon Imam Hammad. Tana son sanin halin da yake ciki, ya farfaɗo ko kuwa bai farfaɗo ba. Tana can tana tunani, shi kuwa tuni ya fito ras da shi, ya hau buɗe-buɗen kwanuka. Har wani murmushi ya yi ganin ƙosai a cikin kayan karyawarsa. Shiru ya yi yana kallon kofin madarar raƙumin da ke gabansa, bayan da ya buɗe ya ga 'ya'yan habbatussauda a kan madarar. Ya ciro wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa. "Al Hussain" "Allah ya taimaki Imam Hammad adalin shugaba abin koyi" "Barka da wannan lokaci ya aiki?" "Alhamdillah, ina nan tafe cikin Agadez a wannan satin, tun da an ce mini yanzu ana ganin ka" Imam ya ce "Eh, ammm tambayarka nake son yi" "Ok Imam, Allah ya sanya ba wani abun aka ce na yi ba" "Akwai yarinya da Asal ta zo da ita, ta ce a nan gurin cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ta, wata 'yar Nigeria" Al Hussain ya ce "Haka ne, sai dai ba na nan suka tursasata Gimbiya Asal ta tafi da ita, na ɗauka ma nan  gidan cin abinci na Agadez za ta dawo da ita" "A ina ku ka samo ta?" Al Hussain ya ji gabansa ya faɗi cike da tsoron, ko wani abin ne ya faru. "Wani kamfani ne suka kawo ta, da muke neman ma'aikata masu ƙwarewa a fannin girki" "A nemo kamfanin, da shugaban kamfanin" "To in sha Allah, amma ina fatan ba wani abin ne ya faru ba?" Imam ya ce "Sarkin ruɗewa, babu abin da ya faru, ina sauraren ka" Daga haka ya ajiye wayar daidai lokacin da Asal ta shigo. Ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce "Ke ina ki ka tafi ne? Na yi zaton ma ko ki na sashenki ne?" Ba ta ba shi amsa ba, Sultan ya shigo a rikice. Da mamaki yake kallon su. Sultan ya ƙaraso cikin hanzari ya ce "Hammad ka na lafiya ya jikin naka?" Imam ya ce "Ai ni lafiyata ƙalau, tun ranar da na faɗo fa babu abin da ya same ni" Sultan ya kalli Asal, a rikice ta ce "Wallahi Sultan ba shi da lafiya, ba ka ga riƙon da ya yi mini jiya ba, wasu abubuwa ya din ga yi masu ban tsoro". Imam ya ɗaga kai ya yi mata wani irin kallo, da sai da hantar cikinta ta kaɗa. Ya gyaɗa kai ya ce "Ni ban san me take magana a kai ba, lafiya ƙalau na kwanta kawai dai ba na jin daɗi kaina yana yi mini ciwo, ban sani ba ko ciwon haukan ne ya motsa mini ba" Sultan ya ce "A'a ba ka da wani ciwon hauka, kawai dai rashin fahimta ne, ka san ba ka da cikakkiyar lafiya" Hammad ya miƙe riƙe da kofin madararsa, yana sha a hankali ya ce "Abie zan je na shirya, zan ɗan fita ne" Ya nufi ɗakin sa. Asal ta kalli Sultan ta ce "Wallahi Sultan ba ƙarya nake yi ba" "Na sani, na san ba ƙarya ki ke yi ba, ki yi haƙuri. Dan Allah ki yi shiru da bakinki kar ki gaya wa kowa. Zan san abin da zan yi a kai" Nana kuwa burgima ta din ga yi a ɗaki, saboda azabar ciwon da jikinta yake yi mata, kamar ta saka ihu haka take ji. Tun da ta jiyo muryar sa sama-sama a falo, hankalinta ya kwanta ta san jikinsa da sauƙi. Sai dai wunin yau ma ba su haɗu ba, Asal ta ce mata ta ajiye masa Abincin, za a ɗauka a kai masa inda yake. Ruwan zafi Nana ta dafa, ta shiga ta ya wanka da shi, ko za ta samu afuwa, ta gyara jikinta ta fita. Gidan ya yi shiru saboda dare ne, kowa ya kwanta. Ta shiga kitchen ɗin ta tabbatar komai lafiya ƙalau, sannan ta koma ɗakinta. Tana shiga ɗakin ta ga duhu an kashe fitila, ta nufi gurin kunna fitilar ta ji an mayar da ƙofar ɗakin an rufe. Ayshercool 08081012143 1K NE VIA 0069685771 Aisha Adam stanbic bank 💃💃💃