78 78 Gaban Nana ya faɗi, cikin tsoro da razani ta ce "Waye? Waye a nan?" Sai dai shiru ba a yi mata magana ba. Ta kunna fitilar kawai ta ga Imam Hammad a tsaye a cikin ɗakin. Ja da baya ta yi a razane tana toshe bakinta saboda ihun da take shirin kurmawa saboda razani da tsoro. "Idan ki ka yi ihun da Asal ta ji ki, za ki yi mata bayanin abin da ya kawo ni ɗakin nan, kuma duk hukuncin da ta zartar a kan ki sai an yi miki shi, komai tsaurin sa." Ta marairaice ido tana kallon sa cike da tsoro. Ya tako a hankali ya ƙaraso gabanta, ya zuba mata idanunsa da suka ƙara rikita ta, jikinta har tsuma yake yi. "Wace ce ke?" Ya yi maganar yana kafe ta da idanunsa. "Ni ba kowa ba ce" Ta furta jikinta na tsuma cike da tsoron ko yana hayyacinsa jiya da ta je turakarsa. "Ki gaya mini wace ce ke? Kuma da wace manufar ki ka zo gidan nan?" Ta rintse idanunta tana girgiza masa kai ta ce "Wallahi ni ba kowa ba ce ba, Matarka ce ma ta kawo ni nan" "Kin sanni a wani gurin kafin nan?" Ta ɗago kai ta kalle shi, ta girgiza masa kai a hankali, idanunta na cika da hawaye. "Kin hana ni cin ayaba, kin ci kin yi rashin lafiya, kin hana ni hawa kan taguwa, na hau na faɗo. Idan na ganki ina jin wasu abubuwa da ba na ganewa a jikina, tamkar ke ba ɗan Adam ba ce. Ɗanɗanon Abincinki na yi mini kama da wani Abinci da nake ci a wani guri da ba zan iya tunawa ba, idan ba Abincin da ki ka dafa ba, ba ya yi mini ɗanɗano a bakina. Ki na shafa irin turarena kin ba ni madara da habbatussauda, wani abu da ba kowa ya san ina sha ba. Ki gaya mini wace ce ke, kuma a ina ki ka sanni?" Ya yi maganar yana ƙara matsawa daf da ita yana ƙara ɗaga mata murya. "Ni ban sanka ba, ban taɓa zuwa Agadez ba sai a wannan karon, ni babu abin da na sani game da kai" Ta yi maganar hawaye na ta sintiri a kan fuskarta. Ya numfasa ya ce "Idan wani ne ma ya turo ki, ki ke yi mini wasa da hankali, ki ji tsoron Allah, jarrabawoyin da suka yi wa rayuwata ma ƙawaanya sun ishe ni. Kar ki bari na kama ki da kowane irin nau'i na rashin gaskiya" Ta yi shiru tana sunkuyar da kanta ƙasa. "Nana ko?" Ta jinjina masa kai cikin tsoro. "Ki yi haƙuri na tsorata ki, ba na son Asal ta gane wani abu, za ta ƙara tsanar ki ne." Daga haka ya juya ya bar ɗakin nata. Neman guri ta yi ta zauna tana mayar da numfashi, saboda yadda ta tsorata. ***** Sagir ne ya ɗauki Yusra suka tafi gidan su Shukura, domin ƙara jajantawa juna tare da su Hajiya Amina, ta kuma tabattar da iyayen Shukura ba sa zarginta da ɓatan Yusra kamar yadda take faɗa. A babban falon gidan suka zauna, Hajiya Amina duk ta rame saboda tashin hankali da kuma damuwa. Gefe ga Yusuf yayan Shukura, da shi ma fuskarsa take ɗauke da damuwa. Bayan sun gaisa Hajiya Amina ta ce "Sagir har yanzu babu wani labari game da ɓatan Shukura ko?" "Wallahi Mami babu, na yi sintirin gurin jami'an tsaro amma babu wani labari, kullum sai dai su ce mini a kan bincike. An kasa tracking ɗin in da wayarta take, abin dai sha'anin binciken na rasa gane wane iri ake yi" Hajiya Amina ta ce "Babu komai, akwai Allah mu ci gaba da gaya masa, in sha Allah za ta kuɓuta" Alhaji Zailani ne ya fito da shirin fita, Cikin girmamawa. Bai amsa ba ya ce "Yaya ake ciki da batun Shukura haryanzu babu wani labari?" "Eh Daddy, amma mu na ta addu'a in sha Allah za a gan ta" "Ka ga ni fa na gaji da wannan kwana-kwanar, ta ɓangarena zan ƙara saka wa a tsananta bincike, dan kai kan ka ban yarda da kai ba. Ta yaya za a ce rana tsaka a nemi yarinya a rasa ga tsohon ciki, kai me yasa ba a neme ka an rasa ba ko matarka sai ita?" Hajiya Amina ta ce "Haba Alhaji, ya za a yi Sagir ya sanya a sace Shukura a sace ya kai ta ina?" "Ni ki yi mini shiru, babu abin da ba zai iya faruwa ba" ya gama bambaminsa ya fita. Hajiya Amina ta ce "Ka yi haƙuri Sagir, kawai yana cikin tashin hankali da damuwar ɓatan Shukura ne. Dan Allah kar ka damu za a gan ta da yardar Allah" Yusra ta ce "Da ƙawata tana nan wataƙila da tuni ta gaya muku inda Shukura take". Gaba ɗaya suka kalli Yusra, ta ce "Eh Nana mana, ai kin tuna ta ko?" Ta yi maganar tana kallon Hajiya Amina. Ta jinjina kai. Amma Sagir ya ce "Mami bari mu tafi, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya ne" Mami ta ce "Allah sarki, amma ta yi gaskiya na san Nana, a ina ki ka santa?" Yusra sai ta yi shiru, saboda ba ta son ta ji an ce ba ta da cikakkiyar lafiya, amma tun da suka shigo gidan, ta ji ƙamshin Nana. ***** Nana kuwa bayan sallar asuba, ta kashingiɗa tana ta zancen zuci, tana tunanin mece ce mafitarta ta ƙarshe, ta fuskanci kullum al'amuran cikin ƙara rikice mata suke. Wayarta ta ɗaukko tana kallon hotunan Muhsin, kewarsa take yi sosai da sosai, har sai da hawaye ya cika mata ido. Sai ta yanke shawarar neman izini daga gurin Imam, ta je gida, dan ta ga ya fi Asal kan gado. Sai dai wani abu mai kama da bacci ya ɗauke ta, sai dai ta iya kiran shi da dannau, wato sleep paralysis, da wasu kan ce aljani ne yake danne mutum, ya yi iya ƙoƙarinsa gurin tashi amma ya kasa. Iya ƙoƙarinta take son ta yi addu'a, amma ta kasa. Inuwar mutum ta gani ya shigo ɗakin, amma ba ta iya tantance wane jinsin ba ne ba, mace ko namiji. Inuwar na zuwa aka zare wayar da ke hannunta, aka fice. Cikin razani da tsoro ta farka a galabaice tana ta haki tana rarraba ido, amma ba ta ga kowa a ɗakin ba, ta laluba ta nemi wayarya ta rasa. Hankalinta ya yi mummunan tashi, ta ɗaga fulon, ta zazzage inda take zaune, amma babu waya babu dalilinta. Ta tashi cikin azama ta hau buɗe kayanta, ko wayar tana ciki, amma wayam babu waya babu dalilinta. Ta fita da sauri ko za ta ga alamar wanda ya shigo sashen amma ba ta ga kowa ba. Hankalinta ya yi mummunan tashi, saboda rashin sanin wanda ya shigo ya ɗauke mata waya. Gudun masifar Asal idan ta makara gurin hattama abinci ya sanya ta shiga ɗakin girki. Ta fito jiki a sanyaye tana gyaran falon Asal ta fito, kamar Nana ta share ta sai kuma ta ce mata "Barka da wannan lokaci" "Yauwwa. Amm kar ki damu da ajiyewa Imam abinci, tun asuba baya nan, za su yi zaman majalisar Sultan." Nana ta jinjina kai. Idan haka ne ba shi ne ya sake shigar mata ɗaki ba kenan, to ko Asal ce? Da sauri ta ce "Amm ranki ya daɗe, na ce dan Allah.. sai kuma ta yi shiru kar ta tambaye ta, ta canza mata fassara. Asal ta ce "Ina sauraren ki" "Amm shikenan ba komai" Asal ta yi gaba ta yi waje abin ta. Gaba ɗaya hankalin Nana ya ƙi kwanciya, ba ta san a hannun wa wayar take ba, ba ta san ta ina balli zai tashi ba, tun da wayar babu security a kai. Ba kuma ta tunanin ma'aikatan gidan, saboda ba su da ikon shiga wannan sashen. ***** Gaba ɗaya su ke zaune cikin shiga ta alfarma ana tattaunawa, Sultan ya ce "Ina mai farincikin sanar da ku cewa kamfanin masarauta na zinari, zai shiga wata yarjejeniya da ƙasar faransa a kan zinari da kuma sindarin uranium da muke haƙowa. Dan haka ina ganin sai mu tura Imam Hammad da Omar, su je su karanta tsarin yarjejeniyar. Sai kuma a nan gida mu na da taro shi ma, a kan yadda zamu bunƙasa harkar safarar raƙuma da muke yi zuwa ƙasashen ƙetare. Akwai buƙatar fito da sabbin hanyoyi na ƙara faɗaɗa kiwon su da kuma shige da ficen su. Ina ga wannan da kaina zan je taron tare Imam Asad, Zahradeen" Tafawa Maleek ya ce "Wai dan Allah Jalaludeen ba ka jin nauyinmu da ka ke fito da son zuciyarka da son kan ka ƙarara a gaban jama'a?" Gaba ɗaya suka ɗaga kai su na kallon Tafawa. "Za ka tura ɗanka yarjejeniyar Zinari da sinadarin uranium, mu kuma ka haɗa ka 'ya'yanmu da harkar raƙuma" Abduou matawalle ya ce "Tafawa, yakamata ka san abin da ka ke faɗa fa, Sultan ka ke yi wa magana" "Ban saka da kai ba, da ɗan uwana nake magana" Tafawa ya yi maganar yana dakatar da Matawalle. Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba abin da ka ke zargi ba ne Tafawa. Hammad ai ɗanka ne, kuma ni duk matsayinsu ɗaya a gurina." "Ba matsayinsu ɗaya ba, me yasa ba ka tura Zahradeen ba sai shi, mutumin da ko cikakkiyar lafiya ba shi da ita?" Imam Zahradeen ya ce "Mai girma Tafawa, da ni da Imam Hammad ai duk ɗaya ne, ni dan ya je masarautar Agadez ya wakilta babu wani abu a ciki" "Yi mini shiru, kai har ka na da zarafin da ina magana da babanka ka din ga sanya baki? Ni na gaji da wannan bambanci da ka ke nunawa, sai ƙoƙari ka ke lallai sai ka tura ɗanka kan kujerar Sultan ta ƙarfin tsiya, bayan bai cancanta ba. Shi ba cikakkiyar lafiyar zuciya ba, ga rashin lafiyar ƙwaƙwalwa, kalli yatsunsa babu zobensa na tambari, ga shi tsawon shekaru da aure ba shi da magaji, ta yaya ka ke tunanin makaho ya jagoranci mai idanu? Ta yaya mutumi  da shi kansa ba zai iya tsayuwa da ƙafarsa ya yi rayuwa ba za a ce ya wakilci masarauta kamar Agadez a harkar kasuwanci" Cikin tsawa Sardaunan Agadez ya ce "Wane irin lafazi ne wannan ka ke yi Tafawa? Kar ka manta da wanda ka ke magana, babu ruwan masarauta da gaba ka ke da Sultan, zamu iya sanyawa a warware rawaninka a hukunta ka. Hammad ba ɗanka ba ne kai ma? 'yar ka fa yake aure, kuma ɗan ɗan uwanka ne, kai ba mai rufa masa asiri ba ne idan ma hakan ne? Batun zoben sa zamu yi bincike a kai, haihuwa kuma Allah ne yake bayar da ita, bai zama hujjar da za a ce an hana shi wata dama ba. Ko yana da ɗa ko babu idan Allah ya nufi ya yi mulkin Agadez wallahi sai ya yi" Gaba ɗaya gurin suka yi tsit. Ya mayar da idonsa ga Sultan cikin girmamawa ya ce "Ina neman afuwa ya shugabana bisa ɗaga murya da na yi a gaban sarki" Hammad ya dubi Sultan a tsanake ya ce "Ina neman a yi mini izini, zan ɗan fita" Da ka Sultan ya yi masa alama, ya yinƙura ya tashi ya fita. Zuciyar Sultan tamkar ta kama da wuta saboda damuwa da jin zafin kalaman ɗan uwansa ga ɗan nasa. Kai tsaye Imam Hammad ya koma gida, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi na maganganun da Tafawa ya faɗa a kansa. Ɗakin saukar baƙinsa ya wuce, da nufin ya zauna ya kaɗaice a ciki. Kawai ya tarar da Mahmoudu a ɗakin. Bai kula shi ba kawai ya nemi guri ya zauna idanun nan jawur. Mahmoudu ya tashi ya koma kusa da shi, ya kalli yadda idanunsa suka yi jawur ya ce "Imam, lafiya kuwa?" Yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Mahmoudu, ina son na roƙi Sultan ya cire ni daga duk wani abu da ya shafi harkar mulkin nan ba na so" Mahmoudu ya waro ido ya ce "Saboda me? Kai ma ka san abin da ba zai yiwu ba ne ai. Ka riga ka kai matsayin Imam kuma ka san me hakan yake nufi" "A cire ni a maye gurbina da wani, tun da akwa masu so. So nake na yi nesa da gidan nan, na samu nutsuwa na yi rayuwata cike da 'yanci yadda babu wanda zai dame ni ya takura mini. Gidan nan ji nake yi tamkar a kan wuta nake. A kan abin da bai taka kara ya karya ba an ci mini mutunci ana ce mini juya. Ni Tafawa yake ci wa mutunci saboda kawai Sultan ya ce na je faransa na wakilci masarauta? Wallahi wataran za su neme ni su rasa" "Mahmoudu a ransa ya ce wancan karon ma da ka gudu ni ka saka a bala'i' A zahiri ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri, duk inda ka je ma ba zaka iya zama ba sai ka dawo, dan Allah ka yi haƙuri" Ya yi wa Mahmoudu shiru, ya lumshe idanunsa. Yana kwance a kan cinyarta, ya zuba mata idanu yana kallonta. Sai shafa gashin kansa take yi tana yi masa murmushi mai ƙayatarwa. Bai yi mata magana ba, ita ma ba ta yi masa ba, amma yanayin ya yi masa daɗi sosai da sosai. Wata babbar mace ce a zaune, tana ta huci tamkar za ta fashe, cikin takaici da ƙunar rai take kallon matashin saurayin da yake gabanta. "Zahradeen wai kai wane irin mutum ne mara kishin zuci da bai san ciwon kansa ba? Ina nan na samu labarin ka na cewa Sultan wai a tura Hammad wakilci kai da shi duk abu ɗaya ne, a gidan uban wa ku ke abu ɗaya, ana ƙoƙarin nemo muku 'yanci, amma kai kana shirme da shiririta?. Ƙarara Sultan yake nuna bambanci a tsakaninku ammma kamar ya yi maka asiri ka zama nusari. To wallahi ni ba nusara ba ce, ban tsaya tsayin daka ka zama Imam ba, sai dan ka zama Sultan ɗin Agadez. Dan haka ba zan zuba ido shashancinka ya ɓata mini wahalata ba na gaya maka". Zahradeen ya yi shiru bai ce komai ba, shi sam bai ga wani abu da Sultan yake yi na nuna fifiko a kan Hammad ba, kawai yana ba shi kulawa ta musamman ne, saboda yanayin matsalar hawan jini da yake da ita, da kuma rashin mahaifiya. Aka ci gaba da dambarwa, a kan tafiyar sa Faransa. Ko da aka koma zaman tattaunawa, Mayan 'yan majalisar Sultan ra'ayinsu ya kasu biyu, wasu su na goyon bayan a tura Hammad, saboda nagartarsa da jajircewa ya cancanta mussaman da duk ya fi sauran Imam Imam ɗin ilmi da mu'amala, ga yarurruka da yake ji. Ya yinda wasu suka goyi bayan Tafawa a kan Hammad ba zai ce wakilci Agadez ba, sai sun ji ba'asin zobensa, sai kuma sun ji matakin lafiyar ƙwaƙwalwarsa. Da rahoton lafiyarsa na tsawon shekarun da ya yi a faransa. Wannan ƙa'idoji da suka shimfiɗa ƙa'idoji ne da sai an kwashe lokaci kafin cika su, wanda har lokacin taron ya zo ya wuce, ba a kammala cika su ba. Ganin gurin zai sake yamutsewa, ya sanya Imam Hammad yin gyaran murya. Cikin girmamawa ya ce "Ina godiya matuƙa da wannan dama da aka so ba ni, amma zaman lafiya da kwanciyar hankalin Agadez shi ne a gaba da komai. Ina roƙon a yi mini alfarmar yi mini afuwa, ba zan samu damar yin tafiya wakilcin nan ba, sakamakon hali na rashin lafiya da nake fama, ciwo zai iya kama ni a ko ina, dan haka Tafawa ya yi gaskiya, ina buƙatar hutu" Cikin tsawa Sardauna ya ce "Ba kai ka ke da wannan hurumin ba." "Mai girma Sardauna, gaskiya Tafawa ya faɗa, ban cancanci duk wannan abubuwan ba, shugabancin Imam ma zan sauka na nemi lafiyata" "Mun san ba ka da lafiya, amma ka ka na kan magani, dan haka larura ba za ta hana ka aiki ba" "Larurar ƙwaƙwalwa, mahaukaci ba zai wakilci masu hankali ba, ina neman afuwarku" Daga wannan maganar ya yi waje, saboda yadda idanunsa suka yi jawur, jikinsa ya fara tsuma. Tsit gurin ya yi aka hau kallon-kallo. Sardauna ya ce "Ka ga abin da ka janyo ko?" "Ai ba ƙarya na yi ba, shi ya faɗi cewa ƙarya nake yi ɗan sa ba mahaukaci ba ne?" Ya yi maganar yana kallon Sultan. AREWABOOKS Har wani duhu yake gani a idanunsa, saboda matsanancin ɓacin rai da tashin hankali. Mutumin da yake uba a gare shi, shi ne ya yi masa wannan kausasan laffuzan a gaban jama'a. Ya daɗe yana nuna masa ƙiyayya, amma lamarin bai fito ƙarara ba sai bayan da ya zama Imam.  Mussaman wannan dswowar da ya yi, dan ya matsa a kan lallai sai ya ji wani ciwon ne ya zaunar da shi a ƙasar waje har shekara biyu, kuma aka hana kowa zuwa duba shi? Ya kawo kai cikin falo, Nana tana ta aikace-aikacenta. Ɗan turus ta yi bayan da ta tuna Asal ta ce mata ba yanzu zai dawo ba. Fuuu ta ga ya nufi uwar ɗakinsa. Ta ɗan taɓe baki ta ci gaba da aikin gabanta. Sai dai zuciyarta na kan abin da ya sanya shi cikin fushi da tashin hankali haka. Duk da ba ta da wani kusanci da shi a wannan Duniyar tasa, amma mutum ne mara magana, amma yana da yawan fara'a. Asal ta fito daga wanka ta gan shi kwance a kan gado. Ta kalle shi ta ce "Amour ya na ga ka dawo kuma? Lafiya kuwa?" Muryar Asal kawai ta fusata shi, saboda abin da mahaifinta ya yi masa a fitarsa. Dan haka ya yi mata banza. Ta nufi gaban mudubi ta amsa wayar da take ta ringing, ta ajiye ta dawo ta dube shi ta ce "Sultan yana neman ka a sashen sa yanzun nan" Ya yi mata shiru, bai yi magana ba, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi, ta ɗora hannunta a kan kafaɗarsa. Ya tashi zaune a fusace ya ture hannun Asal, ya tashi ya fita. Sororo ta tsaya tana mamakin me yake damunsa haka? Gaba ɗaya ya fita ya bar sashen. **** Cikin matsananciyar damuwa Mama take kallon Jamila da ta yi wata irin rama mara fasali, duk ta bushe ta yi haske sai uban kai ɗauke da gashi. "Jamila ni fa na rasa gane kan ki gaba ɗaya, kalli yadda ki ka koma, dole ki shirya mu je gurin masu magani ko mayu ne suka kama ki, ki ke ta wannan wahalar duk kin ƙi lafiya" "Ni babu wasu mayu da suka kama ni" "To idan ba mayu ba wannan ciwon na mene ne haka? Fitar nan ma da ki ke yi gurin kasuwancin naku kin daina gaba ɗaya" "Ki ƙyale ni zan warke ne" Ta yi maganar cikin ƙosawa da maganganun Mama. Su na haka Yaya Atine ta yi sallama, Mama ta amsa tana yi mata maraba. Mama ta ce "Ke ki ke tafe a yammacin nan?" Ta ce "Wallahi kuwa, na ga kwana biyu ban leƙo ba, na ce bari na shigo, Isan ba ya nan ne?" "Eh ya fita baya nan" "Ita kuma wannan fa?" Cikin damuwa Mama ta ce "Ba ta da lafiya ne, nayi-nayi da ita, mu je gurin mai magani ta ƙi yarda, ga na Asibitin an yi ya ƙi jiki kullum ƙara rikicewa yake yi" "To me yake damunta ne har haka?" Mama ta ce "To gata nan dai, kullum zazzaɓi ba ta kuma son cin abinci ko fita ba ta yi, na Asibitin ya ƙi yi mata, mu koma na gargajiya ta ƙi" Yaya Atine ta ɗan zura wa Jamila ido, har sai da haushi ya kama Jamila, ta tashi ta bar gurin. Yaya Atine ta ce "Mhmm" Ta ɗaukko wata hirar daban. Ba ta wani jima ba ta yi wa Mama sallama ta tafi, sai dai cikin sa'a ta haɗu da Baba a ƙarshen layin, dan haka ta zauna suka dasa hira a hanya. Ta ce "Ashe Jamila babu lafiya?" "Eh wallahi ana ta fama, an kasa gane abin da yake damun ta" "Lallai, to gaskiya yakamata ku zurfafa bincike dan kuwa ɗan yau ka haife shi ne, amma ba ka haifi halinsa ba" Cikin rashin fahimta ya ce "Me ki ke nufi?" "Ni babu abin da nake nufi, balle a ce na ce, ni dai kawai na ce a zurfafa bincike ka ga tafiyata" Ya yi shiru yana nazarin maganganun 'yar uwattasa. **** Cikin fushi Sultan yake kallon Imam Hammad, ji yake yi tamkar ya kwaɗa masa mari ko ya huce. "Sai yanzu ka ga damar amsa kiran nawa?" Ya girgiza kai ya ce "A yi mini afuwa, jikina ne ya so motsa mini shi ya sanya ban samu fitowa ba" Sai kuma ya sassauta murya ya ce "Wani abin ne ya faru da kai bayan tafiyar taka?" Ya girgiza wa Sultan kai. Cikin rarrashi ya ce "Hammad, ba a cin nasara da karaya da kuma miƙa wuya farat ɗaya. Kuma Tafawa Maleeka bai yi ƙarya ba, ina son ka gaje kujerar Sultan ba dan komai ba sai domin ina buri da fatan ka gyara kura-kuran da na aikata a baya. Ni ba ina burin ka zama Sultan domin son zuciya ko wani abu ba, ko iya haka Allah ya yi maka mai kyau a duniya, ina yi maka fatan mai kyau a Lahira. Ka ma da ilimi, ka na da dukiya, ka na da mulki iko ka ke buƙata gurin aiwatar da wasu abubuwan. Kai kaɗai ne kujerata ba ta gabanka, kuma ka fi ni jajircewa da tsayawa a kan ra'ayinka da aƙidarka, burikanka a kan Agadez da ƙudure-ƙudirenka abubuwa ne da za su sauya rayuwar mutane da dama, saɓanin sauran da hawan kujerar ne kawai a gaban su, ba ƙalubale da abubuwan da suka kamata ba. Dan Allah ka yi haƙuri ka jure kar ka watsa mini ƙasa a ido. Wannan nagartar taka ya sanya manyan nan na majalissata suka ƙara tsanarka ba wani abu ba" Imam Hammad ya numfasa ya ce "Abie na ji duk bayananka. Amma ka yi haƙuri na riga na karaya, kalaman da ake jifa na da su sun yi tsauri da muni, su na taɓa zuciyata da yawa" "Na sani, ba na buƙatar ka musanta abin da na zo da shi, ka yi mini biyayya kawai. Kuma majalisa sun zartar da hukunci a kan Tafawa bisa abin da ya aikata" Hammad ya kalli Sultan ya ce "Ina fatan ba wani abin mai tsauri suka yanke a kansa ba, kar alaƙa tsakanina da shi ta ƙara yin tsami, ga 'yar sa ina aure. Ko ba komai uba ne a gare ni, kuma Asal ƙanwata ce kuma matata" Sultan ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu, hukuncin ba zai shafi nasaba da dangantaka ba, ka je ka samu ka huta" Ya risuna cikin girmamawa ya yi godiya ya fita. Bayan fitarsa Sultan ya zauna, zuciyarsa cunkushe da damuwa, tunani yake yi yaya aka yi Tafawa ya san batun larurar Hammad. Ya yi tunanin ko Asal ce ta gaya masa, amma ko Asal ba ta san taɓin hankali Hammad ya yi ba, kawai dai ciwo ne yake kama shi, gangar jikinsa ta sauya, ya din ga wannan jijjigar da kakarin. ***** Kaiwa da komowa Tafawa yake yi a cikin falonsa, zuciyarsa a cunkushe da baƙin ciki, bayan tuna yadda wasu daga cikin majalisar Sultan suka ƙaryata shi, bayan da ya faɗi cewa Hammad yana da taɓin hankali. Ya yi ƙwafa ya ce "Da ni ku ke zancen, sai na tabattar wa da Duniya ɗan ka mahaukaci ne, sai ya yi hauka tuburan Duniya ta gani ta shaida, kujerar da ka ke ƙoƙarin cusa shi ya hau, sai ta zama haramiyarsa ta har gaban Abada. Mulkin ai ba da shi aka haifoka ba, da za ka ce lallai ka yi shi ma sai ya yi ba. A wancan karon mu na ji mu na gani, aka ɗora ka aka ce bamu cancanta ba, a wannan karon dole sarauta ta bar gidanka ta dawo gidana, Asadullah sai ya hau kujerar Sultan, ko ka na raye ko ka mutu". ***** Tun da ya koma gida Asal ta share shi, shi ya manta ma abin da ya yi mata, ya ga tana basar da shi ga damuwa da yake ciki. "C'heri'" Ta ɗago ta kalle shi. "Me yake faruwa ne?" Ta girgiza masa kai alamar babu komai. "Idan na yi miki laifi ne, ki yi haƙuri, ina cikin damuwa ne kwanakin nan, ki din ga yi mini addu'a" Ya yi maganar yana hargitsa gashin kanta da ta gyara. Ya nemi guri ya kwanta ya lumshe idanunsa, yana fatan bacci ya ɗauke shi, ko ya samu sauƙin wannan damuwoyin. Yana jin ta ta kashe fitilar ɗakin, sai hasken fitila na gefen gado wanda ba mai takura ba ne. Ta hau kan gadon ta kwanta a bayansa, ta zura hannunta ƙirjinsa. A hankali ya juyo, ya rungumeta sosai a jikinsa yana shafa bayanta, duk da ta ji haushin abun da ya yi mata ɗazu, amma da yake ya ƙware a iya mantar da mutum laifin da ya aikata masa, dole ta ba da kai bori ya hau. A hankali ya ji jikinsa ya fara ɗaukar zafi. Ya raba Asal da jikinsa saboda yadda yake jin san tamkar an saka masa fetur an kunna wuta a jikinsa. Ya miƙe ya din ga kaiwa yana komawa a ɗakin, yana maimaita ya hayyu ya ƙayyum. Ya shiga banɗaki ya haɗa ruwan ɗumi ya yi wanka ya fito. Kasa jurewa ya yi jin yana neman ya fita daga hayyacinsa, ya fita falo. Yana fita ya ji wannan dadaɗan sanyin ya ratsa shi. Kan sa tsaye ya nufi inda yake jin sanyin na fitowa wanda hanyar ɗakin Nana ne. A corridor din gurin ya yada zango, ya samu guri ya zauna, ya jingina da jikin bango yana numfarfashi. ***** Kwanaki biyu a tsakani, aka kuma zama, sai dai a wannan karon ba da duka Imam ɗin aka zauna ba, Hammad ne kawai, sai manyan masu faɗa a ji na kusa da Sultan, wanda an yi zaman ne saboda abin ya shafi Hammad ɗin. Sardauna ya yi gyaran murya ya ce "Imam Hammad, kamar yadda Tafawa ya buƙata da shi da wasu daga cikin 'yan majalissar Sultan. Lallai mu na buƙatar jin gamsashshiyar amsar ina zobenka na tambarin Imam yake? Gamsashshiyar amsa mai cike da hujja muke so, na wai-wai ko kame-kame ba, dan ka san muhimmancin zoben idan babu shi dole za ka sauka daga kan muƙamin da ka ke kai. Abu na gaba, mu na buƙatar sakamakon rahoton lafiyarka, na tsawon lokacin da a ka ce ka shafe a faransa kana jinya. Kuma hakan baya nufin za a canza umarnin da Sultan ya yi? Zuwanka faransa wakiltar Agadez wajibi ne bisa ga sahalewar Sultan. Kai kuma Tafawa, duk da uba ne kai ga Imam Hammad, kuma uba a Agadez za a hukuntaka bisa ɗaga murya da yin jayayya da hukuncin da Sultan ya aiwatar, kamar yadda kwamitin ladabtarwa da sulhu ya yanke. Zaka kawo mana cikakkiyar shaida da hujja, ba wai-wai ko kame-kame ba, a kan Imam Hammad yana ɗauke da larurar ƙwaƙwalwa, akasin haka za'a yanka maka tara mai yawan gaske ka biya shi. Haka zalika an hukuntaka bisa amfani da kausasan laffuza a kan Imam Hammad, wanda yake shugaba ne da yake jagorantar Imam, da ake sanya ran zaman su sarakan gobe. Dan haka an dakatar da kai tsawon watanni shida, har sai ka gabatar da abin da aka nema daga gare ka" Cikin fusata ya miƙe ya ce "Ai dama na sani, wata maƙarƙashiyar da manaƙisar ake ƙulla mini, saboda ba a ƙaunata. Amma shi Jalaludeen ya musa cewar ɗansa mahaukaci ne mana. Ciwon hauka ya yi suka kai shi suka ɓoye amma aka ce jinya ya yi a ƙasar waje. Ba ku burge ni ba da ba sauke ni kuka yi daga muƙamina ba har abada ai. Kuma na faɗa na maimaita, Hammad ba zai taɓa zama Sultan a Agadez ba, ba shi da lafiyar zuciya, ba shi da ta ƙwaƙwalwa kuma ba shi da magaji juya ne, dan haka mai baƙin baya ba zai yi mulki a Agadez ba" Wani irin duka Hammad ya yi wa teburin gabansa da ya bayar da wani irin sauti. Ya kalli Tafawa ya ce "'yar ka zaka tuhuma ya aka yi ba ta haihuwa? Ni mahaukaci ne ka zagaye Agadez kana maimaita hakan, kuma ba ni da lafiyar zuciya shi ma ban damu ba, na yi sarauta ko kar na yi bai dame ni ba, duk abu dai ka san kujerar Sultan ta fi ƙarfinka. Duk abin da za ka faɗa a kaina ka faɗa amma kar ka sake kira na da Juya mai baƙin baya, Asal ita ce juya ita zaka bincika dan ni ina da ɗa, na haihu ba baƙin baya ne da ni ba! Zobe kuma ya ɓata ban san inda yake ba" Ɗif gurin ya yi, tamkar an yi ruwa an shanye, ko kuma babu mai sauran numfashi a gurin, saboda yadda maganganun nasa suke buƙatar fashin baƙi gwari-gwari. ***** Hajiya Amina cikin damuwa da nuna rashin jin daɗinta take duban Alhaji Zailani ta ce "Alhaji ban ji daɗin yadda ka yi wa yaron nan mijin Shukura ba. Tare da mu da shi ake ta faɗi tashin neman Shukura, bai kamata a ce gaya masa maganganun da suke nuni da cewar wai zarginsa ka ke yi da sace Shukura ba" Ya dube ta ya ce "To dan yana mijinta kar na zarge shi? Duniyar nan fa babu abin da ba zai iya faruwa ba, ni bincikena ba zai bar kowa ba, ya zama dole a binciki kowa, kuma ki rabu da ni da abin da yake damuna, ki ƙyale ni da maganar sani mijin Shukura" Ta ce "Shikenan, ni ina gudun kar daga baya a zo a ji kunya ne" Ya ɗan ɗago da sauri ya ce "Me ki ke nufi?" "Ahh a zo a ganta a gano ba shi da hannu a ciki, su ci gaba da zama da matarsa kai ka zo ka na jin kunya" Ya yi guntun tsaki, yana sake miƙe ƙafafuwansa a kan gadon. ***** Jamila ce a kwance dare ya tsala, amma ta yi ƙurii tana kallon roofing ɗakin. Tun da Abba ya koma ga Allah, bacci ya ƙaurace wa idanunta. Idan kuwa bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, to tabbas mafarkin Abba za ta yi ta yi, tana ganin sun yi aure ga yara ta haifa masa. Sannu a hankali ta tafi tunanin abin da ya faru. Bayan da Hajiya Sa'a ta yi mata bayanin yadda za ta sadaukar da ɗan gidan Alhaji Fatuhu ƙaninta. Abin ya dame ta, ga shi ta san idan ta je ta sanar wa su Alhaji Fatuhu, asiri ne zai tonu har ita, kuma ma mene ne shaidarta, dan ta san tsaf Hajiya Sa'a za ta zame ta bar ta a ciki. Ta yi tunanin ko ta sace 'yar tsanar, amma ta fasa, saboda yadda ta rabu da ta ta da ƙyar. Bayan fitar Hajiya Sa'a, Jamila na kwance a falo bacci ya ɗauke ta, ta yi mafarkin 'yar tsanar nan a ƙone ta yi baƙi ta biyo ta tana ƙoƙari shige mata cikin riga tana wani irin kuka tsiii-tsiii. Cikin ihu ta tashi a razane. Lokacin Abba ya shigo ɗakin, kawai ta cakume shi tana ihu. "Ƙanwata lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallonta, a hankali ta cika shi, ta nemi guri ta zauna ta ce masa tsorata ta yi a bacci. Ya zauna yana yi mata nasihar mafarki ba gaskiya ba ne, kuma ta din ga addu'a, idan ba haka shaiɗanu za su iya shiga jikinta saboda wannan tsoron da take ji. Sai dai har ta tafi gida, a tsorace take kuma tunani take yi, yaya za ta yi ta tseratar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga 'yar tsana ta sako ta a gaba a mafarki, yanzu bin ta take yi da sata sharɓeɓiyar wuƙa a mafarkin za ta kashe ta. Kawai ta yanke wata shawara a ranta, wajen ƙarfe sha ɗaya ta je gidan Hajiya Sa'a, lokacin bata nan ta fita gantalinta, cikin sa'a ta duba inda ta ajiye 'yar tsanar da tarkacen kayan tsafin ta ga su na nan. Ta kira Abba a waya, bayan sun gaisa ta tambaye shi yana ina, ya ce mata ya tafi kasuwa ta ce masa ya zo tana gidansu tana son ganinsa. Ba a yi awa ɗaya ba sai ga shi ya dawo, har da tsaraba ya sayo mata, cike da murnar ganinta, dan kwana biyu ta ɗauke ƙafa da zuwa gidan. Yanayin walwalar da ta gani a fuskarsa sai ta ji dana sanin kiransa da ta yi. Sai dai ya takura mata a kan lallai sai ta gaya masa abin da ya sanya ta kirawo shi. Ta ɗebo tarkacen nan na kayan tsafin Hajiya Sa'a, ta Zazzage masa a gabansa. Cikin mamaki ya dube ta ya ce "Mene ne wannan haka?" Ayshercool 08081012143 79 Tabbas ba ka san ko mene ne ba, kuma na san za ka yi mamakin mene ne wannan ɗin, amma ina mai baka haƙurin abin da zai fito daga bakina, ba ni da wani zaɓi ne nima, ina son yin ceton rai, na rasa wanda zan gayawa ya fahimce ni ya sama mini mafita ya rufa mini Asiri sai kai" Ta yi maganar cikin kuka. Cikin damuwa da ƙaguwa ya ce "Babu komai, ko mene ne gaya mini. Wallahi Jamila ina jin ki a raina fiye da yadda ki ke zato, ki gaya mini dan Allah" Ba ta tsallake masa komai ba, tun daga tariyar Maman Khairat a unguwar su, da fara zuwa gidanta zuwa haɗuwa da Hajiya Sa'a, ta gangaro har kan neman jinin Nana yadda suka saka ta a ƙungiyar asiri abin da aka yi mata, hatta labaran da Hajiya Sa'a ta ba ta na yadda ta shiga ƙungiyar sai da ta gaya masa. Jamila za ta iya cewa tun da take, ba ta taɓa ganin idanun ɗan Adam sun yi jan da na Abba suka yi ba. Ya ƙame a guri ɗaya tamkar babu rai a jikinsa. Cikin rikicewa ta ce "Dan Allah Yaya Abba ka yi haƙuri ka yafe mini, ban gaya maka dan na haɗa ka da mahaifiyarka ba ko makamancin haka, ceton rai nake fatan mu yi, bawan Allah nan da yake rashin lafiya kar ya kuma rasa ɗan sa. Kuma dama ni na san mutuwa zan yi, dan ba zan iya bayar da kowa ba ga barazana kuma da ake ta yi mini a mafarki. Dan Allah ka yafe mini ban faɗa dan na haɗa ka da mahaifiyarka ba. Idanunsa suka fara tsiyayar da hawaye, yayi kuka, ya yi kuka, Jamila kuma ta kasa rarrashinsa, can ya ce "Tabbas! Biri ya yi kama da mutum, yanayin facakar da Mummy take yi da kuɗi tamkar ba ta san zafin neman su ba abin yana ɗaure mini kai. Ina kula da harkokin kasuwancinta, amma na san abin da take kashewa ya ninka abin da muke samu. Kuma duk yadda zan bi na gano wani abu sai ta toshe. Jamila na ji daɗi sosai da sosai, da ba ki gaya wa wani abin da take aikatawa ba, kuma na ji daɗin ƙoƙarin kare kisan ɗan ɗan uwanta. Amma na yi mamakin yadda ta iya bayar da mahaifinmu saboda abin Duniya. Ita ma idan ba ta sadaukar da kowa ba mutuwa za ta yi ko?" Jamila ta jinjina masa kai tana kuka. Ya ce "Shikenan, babu komai, ki daina kuka, daga ke har ita ba zaku mutu ba, zan zama abin sadaukarwar ku, sai dai daga ni ina fatan duk yadda za ki yi ki fita daga cikin kungiyar nan. A razane Jamila ta ce "A'a ba zai yiwu ba, ban gaya maka dan ka ɗau wannan ɗanyen hukuncin ba, mafita zaka nemo" Abba ya ce "Wace mafitar Jamila? Na nuna wa Mummy na san abin da take yi? Ko na bari ke ko ita wani ya rasa ransa? Ko kuma ɗan Kawu Fatuhu da bai ji ba bai gani ba? Dan Allah Jamila duk yadda za ki yi kar ki yadda ki bayar da jinin wani, ki kuma bar kungiyar nan. Wallahi Jamila kuɗi ba su ne kwanciyar hankali da nutsuwar ɗan Adam ba." "Yaya Abba to me zaka yi?" "Ni zan zama abin sadaukarwar taku?" Ta girgiza kai ta ce "Ba zai yiwu ba gaskiya, na bayar da jininka kenan, ai gara ni na bayar da jinina ba zai yiwu ba" Ya ce "Ba ke za ki bayar ba, ni zan bayar da kaina, ina fatan hakan ya zame wa Mummy darasi, ya kuma yi silar fitarta daga abin da take aikatawa" Cikin kuka Jamila ta riƙe hannunsa ta ce "Idan ka yi haka ka kashe kanka fa kenan?" "Jamila wa zan tunkara ya lalata Wannan abun asirin Mahaifiyata ya tonu tana Kungiyar asiri? Wane kallo ɗan uwanta zai yi mata? Ke idan aka ce ki na kungiyar asiri wane kallo al'umma za su yi miki ko bayan kin tuba? Ina roƙonki dan Allah ki rufa mata asiri kar ki gaya wa kowa wannan maganar" Ya ƙarasa maganar yana tashi tsaye, ya hau tattare kayan. Rikicewa ta yi tana ƙoƙarin hana shi, amma ya ture ta ya ɗebe, ta riga ta yi masa bayanin duka yadda ake amfani da kayan. Dan haka ya buɗe alawoyin da ta yi niyyar zuwa ta ba wa Muhsin, ya saka a bakinsa. Ya nufi hanyar fita ya dakata ya ce "Idan na rayu shikenan, idan kuma an yi amfani da jinin nawa, ki tabattar wa Mummy ni ne sadaukarwata na shekara, kuma ki roƙa mini ita gafara, da kuma na zama ni ne mutum na ƙarshe da zai rasa ransa a dalilin nan duniyarta, ta tuna inda na tafi ita ma za ta tafi" Jamila ta yi kuka da dana sanin gaya wa Abba maganar nan. Yana zuwa ɗakinsa ya ɗau biro da takarda ya yi rubutu, ya caka alluran nan a jikin 'yar tsanar, kawai ya ga ta ɓace daga hannunsa. Bai razana ba, ya saka hankicin a ƙasan fulonsa. Bai yadda ya haɗu da Hajiya Sa'a ba, har dare ya yi yana ƙule a ɗaki, ya kwana a kan fulon da jan ƙyallen, wanda shi ma ya ɓace daga baya. Jamila ta yi kuka tamkar ranta zai fita, dan faɗiwar gaban da ta ji ce ta tabbatar mata da cewa Abba ya aikata abin da ya ce, kuma ƙungiya sun shanye masa jini. ***** Da ƙyar Abduou matawalle ya yi gyaran murya ya dubi Hammad ya ce "Yanzu Hammad har wuyanka ya yi kaurin da zaka din ga sa in sa da mu? Bamu san ka da haka ba, wannan ba halinka ba ne ba. Kuma ya zama dole a ladabtar da kai bisa nuna rashin ɗa'ar da ka nuna." "Da na ce mahaukaci ne ai ba a yarda ba, yanzu ga haukan nan yana yi " Tafawa ya yi maganar a harzuƙe. Cikin nutsuwa Imam ya ce "A cikin hayyacina nake, ina da ɗa, ka gaya wa ko a ciki da wajen Agadez " Sardauna ya dakatar da taron ya sallami kowa banda Imam Hammad, da Abdou matawalle sai kuma Sultan. Sardauna ya ce "Na san maganganun Tafawa ne suka yi maka zafi ka ke wannan iƙirarin, amma wannan soki burutsun naka, babu abin da zai haifar sai ƙarawa wuta fetur. Kaf faɗin Agadez Asal ce matarka, kuma tun da ku ka yi aure ba ku haihu ba, ko ka na da saɗaka ne bamu sani ba". "Allah ya taimaki Sardaunan Agadez, ni fa ba ƙarya nake yi ba, kuma ba soki burutsu nake yi ba. Ina da ɗa" Matawalle ya ce "Wai wani irin ɗa a na zaune ƙalau? Yaushe Asal ɗin ta haihu ba mu sani ba?" Ya girgiza kai ya ce "Asal ba ta haihu ba, ɗa na kuma ba shi da alaƙa da kowace mace a Agadez a ma Nijar gaba ɗaya" Sultan da ya fara harzuƙa ya ce "Kai ba na son shashanci fa, zan ci maka mutunci yanzun nan, wane irin shirme ne haka? Ko sai ka gazgata maganar Tafawa cewa baka da hankali" Cikin girmamawa ya ce "Tuba nake ranka ya daɗe, amma idan an bani dama zan yi bayanin komai". Abduou matawalle ya ce "Mu na sauraren ka". Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya daddana. "Ga Balaraba can tana jiran ki, ana neman ki a gidan Sultan" Nana ta ajiye tukunyar da take wankewa, ta kalli Asal ta ce ana nema na kuma a gidan Sultan? Laifi na yi?" "Idan kin je kya ji. Nima ban san me ki ka yi ba, Imam ne ya ce a kai ki" Gaba ɗaya sai jikin Nana ya yi sanyi, ta kammala abin da take yi a gurguje, ta shirya ta bi Balaraba. Su na tafe ta ce "Mama Balaraba, ko kin san abin da na yi ake nema na?" "A'a nifa Gimbiya ce kawai ta ce na raka ki? Amma idan kin san babu abin da ki ka yi, bai kamata ki ɗaga hankalinki ba, wataƙila Imam Hammad ne kawai yake neman ki" Cikin sanyin jiki Nana ta ce "Kuma a gidan Sultan?" "Eh wataƙila alkhairi ne, ko kuma girkin za ki yi" Duk da wannan kalaman na ƙwarin gwiwa, da Balaraba ta faɗa wa Nana, ita dai Nana ta ji ba ta gamsu da kiran ba. Tun daga nesa aka dakatar da Balaraba, aka turo wani ya shiga da Nana. Nana ta yi turus, bayan ganin manyan mutane har da Sultan a wajen, gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa, suka yi mata wani irin kwarjini ta ja ta tsaya a bakin ƙofar tana rarraba idanu. Su ma duk suka zura mata idanu, su na mamakin ita wannan da aka kirawo, me ya kawo ta nan. "Ƙaraso mana" Sayyid ya yi maganar yana kallonta. Sai ta diririce ta kasa gaba ta kasa baya. Da kansa ya fara takawa, yana tunkarar inda take, yana zuwa ya kamo hannunta, yana tafe tana bin sa a baya har zuwa tsakiyar gurin. Bai saki hannunta ba ya kalli idanunta ya ce "Ma Vie" Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faɗuwa, tsigar jikinta ta tashi, numfashinta ya fara fita sama-sama, jin abin da ya fito daga bakinsa tamkar almara. "Ki shaida musu ni ba juya ba ne, ina da yaro" Ƙoƙarin ja da baya ta fara yi, tare da son fizge hannunta tana girgiza masa kai. Sardauna ya ce "Imam, wace ce wannan ɗin? Me ka ke ƙoƙarin yi ne haka?" "Matata ce, ita ta haifa mini yaro" Ya ba shi amsar yana kallon Nana da idonta ya yi ja, ya cika da hawaye. Cikin rashin fahimta Matawalle ya ce "Ta yaya, wace ce wannan ɗin daga ina take?" Hammad ya yi shiru bai ce komai ba, shi kuwa Sultan tuni ya karaya, bayan ganin asirin Hammad ya tonu na taɓin hankali sa saboda soki burutsun da yake yi. Sardauna ya ce "Wai Imam kan ka ɗaya kuwa? Ita wannan ɗin daga ina ka samo ta, ta ina ta zama matarka?" Matawalle ya dubi Nana ya ce "Ke Baiwar Allah, daga ina? Kuma mene ne alaƙarki da shi?" Cikin ruɗewa da hawaye Nana ta ce "Ni babu wata alaƙa tsakanina da shi, aiki kawai Gimbiya Asal ta ɗaukko ni na yi mata, ni ban san shi ba" Hammad ya girgiza kai ya ce "A'a Husnah, kar ki ji tsoro, ina tare da ke. Kar ki yi mini haka dan Allah" "Dan Allah ka yi haƙuri ni ban san ka ba" Ta yi maganar kuka mai ƙarfi na ƙwace mata. "Cika ta tafi" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni. A hankali ya saki hannunta, ta juya da sauri ta fice. "Hammad, anya maganar Tafawa babu ƙamshin gaskiya a cikin ta, na ga baƙa ce kamar ma ba 'yar ƙasar nan ba ce? Meye haɗin ka da ita?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kai ya ƙi magana. Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Ina ga a bari zan yi magana da shi" Nana kuwa tun da ta fita take kuka, tana zuwa babu kowa a falon, ta wuce ɗakinta ta tattare kayanta cif ta yi waje. Sauri take zumbuɗawa tamkar za ta tashi sama, tana tafe tana fatan Allah ya bata nasarar ficewa daga gidan, ba tare da dakarun Asal sun ganta ba su hana ta fita, kamar yadda suka taɓa yi mata aka hana ta fita daga gidan. Sai dai ba ƙaramar tafiya ba ce ba, daga sashen da gidan Imam Hammad yake a cikin gidan zuwa shi kansa gidan. Ta sha doguwar tafiya kafin fita babban gate. Masu gadin ƙofar suka ƙare mata kallo ɗayan ya ce "Maraɗi za ki tafi ko? Ga mota can Imam ya ce a kai ki" Ta girgiza cikin mamaki ta ce "Ba zan hau ba, ni ba can zan je ba" "Idan ba za ki hau ba, ga wannan ya ce a baki" Aka miƙa mata envelope. Ba ta duba meye a ciki ba, ta karɓa suka buɗe mata ƙofa ta fice. Tana tafe tana waiwaye tana fatan kar a biyo ta a mayar da ita gidan nan. Ta ƙudurce a ranta, tana zuwa gidan Nene za ta ɗauke Muhsin ta yi Nigeria. Sai dai tana tafe tana kuka zuciyarta cike da takaici, yanzu dama duk tsawon wannan lokacin Sayyid ya gane ta. Amma ya bari take ta wahala saboda shi, ya ci amanarta bai yi mata adalci ba. Ba ƙaramin gudu motar da ta hau take yi ba, amma gani take kamar ba a sauri. Ta buɗe envelope ɗin da aka ba ta kuɗi sabbi kar a ciki. Sai wata takarda. "Dan Allah ki samu nutsuwa, za mu yi magana Asmy, kar ki yanke mini hukunci a yanayin da ki ke" Wani uban tsaki ta ja a fili. Tana furta "Ba ka yi mini adalci ba, ka cutar da ni" Ta yi maganar kaɗan-kaɗan. Sun sha tafiya ba kaɗan ba a hanya, kafin su isa Maraɗi. Daga nan Nana ta nemi abin hawa zuwa garin da suke da Nene. Sai dai tana zuwa ta tarar da gidan a rufe, ga babu waya a hannunta. Cikin matsananciyar damuwa ta shiga gidan su Ashura. Ashura na ganinta ta hau tsalle ta rungume ta, Nana ta maze suka gaisa cikin yaƙe. Suka din ga yi wa Nana maraba da zuwa, mutan gidan su na ta yaba yadda Nanan ta yi haske ta ƙara ƙiba. Nana da gabanta ke tsananta faɗuwa ta ce "Nene fa, ko ta tafi gurin sayar da Abinci?" "A'a Nene kusan kwana huɗu ba ta nan" Gaban Nana ya faɗi, ta ce "Ba ta nan ina ta tafi?" "Gaskiya ba na tunanin akwai wanda ta yi wa sallama, kawai dai gani muka yi ba ta nan" "Babar Ashura, dan Allah ku bani aron waya na kira ta" Ta yi maganar cikin tashin hankali, muryarta na rawa. Aka ba wa Nana waya, ta saka lambar Nene, wayar ta shiga, amma ba ta ɗauka ba. Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take yi tamkar ta kurma ihu, gaba ɗaya ta rikice, ta ji numfashinta yana fita sama-sama. Da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallolin da suke kanta. Su ka kawo mata abinci, amma ta ƙi ci, ta yi musu sallama ta ɗauki kayanta ta fice. Gidan Hajara ta nufa, inda suka kawo ta gidan Nene. Hajara ta din ga murna ganin Nana, suka rungume juna cikin farin ciki, duk da Nana cikin tashin hankali take. Hajara ta kawo mata Abinci, ta din ga jan ta da hira. Nana ta numfasa ta ce "Na je gida gurin Nene, na tarar ba ta nan, ga babu waya a hannuna, ko za ki kira mini ita a wayarki?" Hajara ta ce "Bari na kira ta" Sai da aka kira sau biyu, sannan Nene ta ɗaga. Cike da rawar jiki Nana ta ce "Nene" "Na'am Nana, ki na lafiya?" Nana ba ta amsa ba ta ce "Nene na zo ba kya nan, na kira wayarki ba kya ɗagawa ina ku ka tafi?" Nene ta numfasa ta ce "Nana ina mai baki haƙuri, baban ɗan ya zo ya karɓi ɗan sa" Cikin matsanancin tashin hankali Nana ta tashi tsaye ta ce "Nene waye baban ɗan? Nene wa ki ka ba wa ɗa na? Haka muka yi da ke Nene?" "Dan Allah Nana ki yi haƙuri, nima fin ƙarfina aka yi, babu yadda na iya, masu garin ne" "Nene ba ki kyauta mini ba, bamu yi haka da ke ba, dan zatin Allah Nene ki gaya mini inda ɗa na yake, dan Allah Nene, ki yi mini rai ki bani ɗa na" Nene ta ce "Nana da zan cutar da ke, da ban zauna da ke tsawon wannan lokacin ba, yadda muka yi a rubuce, haka ya karɓi ɗan sa a rubuce da hukuma, idan na hana su matsala zan shiga" Cikin rauni da hawaye Nana ta ce "Nene waye ya karɓe shi?" "Imam Hammad Jalaludeen Agadez " "Na shiga uku" Nana ta furta cikin matsanancin kuka da tashin hankali. AREWABOOKS Cikin tausayawa Hajara ta ce "Dan Allah Nana ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka? Kuma wai me yake faruwa ne?" Nana ba ta saurari Hajara ba, ta ci gaba da kuka, tare da lissafa yadda za ta ninka ta koma Agadez, ta ƙudurce a ranta gara ajalinta ya riske ta, a yi duk wadda za a yi ta karɓi ɗan ta, ko hakan zai yi silar tarwatsewar Agadez gaba ɗaya.', a kan ta tafi ta bar ɗan ta, a wannan gidan. Bugun ƙofar gidan aka din ga yi da ƙarfi ana sallama. Hajara ta tashi ta fita, ba a jima ba ta dawo, ta dubi Nana ta ce "Ki na da baƙi a waje" Nana ta ɗago jajayen idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce "Suwaye?" "Ki je ki gani, baƙinki ne dai" Nana ta yinƙura ta tashi ta fita, tana jan ƙafafuwanta, mutum biyu ta gani cikin kaaki, sai ɗaya da rawani, ya rufe fuskarsa sinkif, ba ta ganin komai sai idanunsa, duk da hakan bai hana ta yi masa kallon sani ba. Ba ta tsaya takura wa kanta ina ta san shi ba, saboda matsananciyar damuwa da tashin hankalin da take ciki. Cikin girmamawa ya ce mata "Barka da wannan lokaci" "Yauwwa sannu" Ta furta da dasashshiyar muryarta. "Imam Hammad ne ya aiko mu, ya ce mu tafi da ke" Ta yi wa mai maganar wani irin mugun kallo ta ce "Ya aiko ku ku tafi da ni ku kai ni ina? Ba zan bi ku ba, babu in da zan je" "Gurin yaronki za a kai ki" Sai kuma ta yi turus tana kallon su. "Tafiyar da ɗan nisa, ki ɗaukko kayanki, inda yaronki yake ya ce mu kai ki" Ba ta tsaya ta zurfafa tunani ba, ta shiga cikin gidan. Hajara ta ce "Nana yaya?" "Tafiya zan yi" "Ki je ina? Wai ni, me ya haɗa ki da Buzayen nan ma? An ce mini daga gidan Sultan ɗin Agadez aka zo gurinki, me yake faruwa ne?" "Zan yi miki bayani daga baya, bari na je tukuna" Ta ja jakarta, ta yi waje. Wata irin haɗaɗɗiyar mota ce, ta haɗu ga kyau ga wani daddaɗan sanyi da take fitarwa. Sai dai Nana ba ta tsaya tantance kyan motar ba, lissafinta kawai Muhsin ya zo hannunta, ta gudu. Dan ko me za a yi ba za ta bayar da ɗan ta ba, kuma ba za ta bar Nijar ba sai Sayyid ya sake ta. Sun sha tafiya, kafin su isa wani irin ƙaton gida, sai da ta ga an shiga gidan, ta waiwaya ta ga an rufe jibgegen gate ɗin gidan, sai kuma tsoro ya fara kama ta, dan ta san barin wannan gidan ba abu ne da zai yi sauƙi ba. Sai dai hanakalinta baki ɗaya ya fi karkata, ga ta yi tozali da ɗanta, ta san a halin da yake ciki. Ta sauka daga motar ta tsaya tana rarraba ido, mai rawanin ya yi mata jagora zuwa katafaren falon gidan. Ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Akwai banɗaki, da abinci, ki yi salla ki ci abinci kafin Imam ya zo" Wata irin muguwar razana Nana ta yi, ta ce "Sule? Kai ne dama? Me yasa..? Ta rasa wace tambayar ma yakamata ta ƙarasa. "Ki yi haƙuri, ba ni da damar ce miki komai, ki yi salla tukuna" Nana ta ƙara rikicewa kanta ya kulle. Da kyar ta samu ta yi sallolin. Jikinta sai ciwo yake yi saboda azabar zirga-zirgar tafiya ga cikinta babu komai. Gaba ɗaya rarraba ido kawai take yi, tana tunanin ta ina za ta ga Muhsin, ga fafur Sule ya ƙi tsayawa ya yi tafiyarsa ya bar ta sai itakaɗai, balle ya yi mata wani gamsashshen bayani. Jin ana turo ƙofar falon, ya sanya ta miƙe tana ƙara leƙawa ko za  ta ga Muhsin. Sai dai ba ta ga Muhsin ba sai baban Muhsin, yana sanye cikin baƙar jallabiya, ya yafa hirami a kansa, bayansa kuma Mahmoudu ne, wanda ta fi sani da Habu. Razana ta yi, ta tsaya ƙyam tamkar an dasa ta, ta haɗiye wani abu mai masaifar zafi tamkar wuta a maƙogwaronta zuwa ƙirjinta. Ya kalli idonta, yana ƙoƙarin tantance wane irin kallo take yi masa, ya rasa ta ina ma zai fara. "Ina ɗa na?" Ta jefa masa maganar a zafafe tana huci. Habu ya matso gaba ya ce "Nana, ki yi haƙuri ki ci abinci ki huta, ki samu nutsuwa, sai mu yi miki bayani" "Bayani? Wane bayanin nake buƙata bayan wanda na gani? Kun cuce ni, na ƙarar da lokacina ban tsinana wa rayuwata komai ba, na tsaya na yi biyayyar aure na rabauta, ashe mutumin da nake tausayawa azzalumi ne, kuma mugu ne. Kun zalunce ni kun yaudare ni, kun ɓoye mini abubuwa da dama, ba dan ba ni hakkinku ba Allah ya saka muka haɗu ba, da shikenan haia zan ci gaba da gararamba, ba ni da makoma. Ba zan yafe muku ba. Allah ba zai bar zaluncin da ku ka yi mini ba. Ka bani ɗa na dan ba ɗanka ba ne, baka da hurumi da shi Muhsin ba shi da uba na zaɓi ya tashi da wannan tambarin da ya san ubansa azzalumi ne da ya wofantar da rayuwar mahaifiyarsa". Wata irin suka maganganun Nana suke yi wa zuciyarsa, amma ya san koma Nanan ta faɗa a kansa, ba ta yi laifi ba, ya kuma cancanci hakan daga gare ta. Mahmoudu ya ce "Nana, kin san wa ki ke gaya wa haka? Mijinki ne fa?" Cikin kuka ta girgiza kai ta ce "Wannan ba mijina ba ne, mijina Buzu ne da bai san waye shi ba, babu kowa a duniyarsa sai matarsa da ta nuna masa ƙauna saboda Allah. Ba wannan mayaudarin da ya yaudare ni da cewa ni rayuwarsa ce ba, na yi asarar lokacina a kan nemansa ba. Ka bani ɗa na ka haɗa mini da takardar sakina na koma ƙasata na sama wa rayuwata mafita" Ta yi maganar tana riƙe rigarsa tana kuka mai fallasar da dubban damuwoyin da suke binne a ƙarƙashin zuciyarta tsawon lokaci. "Ma vie" ya furta a kasanlance idanunsa fal hawaye, yana kallon ƙwayar idonta. "Kar ka sake kira na da wannan sunan da na fi tsanar ji a rayuwata, Ni da nake mummuna, baƙa 'yar Nigeria da ba kowa ba hadima kuma baiwar da ake ci wa mutunci a gaban wanda yake yi mini iƙirarin ni rayuwarsa ce yana ji kuma yana gani. Wataƙila ma alhakin iyayena ne ya kama ni, da na baro su saboda wauta irin ta soyayya da ƙoƙarin sama wa ɗa na mafitar rayuwa. Ka bani ɗa na ka sake ni na koma inda na fito" Ta yi maganar tana zare masa ido tamkar numfashinta zai ɗauke. Ya saka hannunsa yana ƙoƙarin kamo ta jikinsa, amma ta yi baya tana kai masa duka ta ko ina, cikin kuka tana faɗin "Na tsane ka, na yi nadamar saninka, rayuwata da kai bai amfana mini komai ba, ban taɓa zaton za ku iya haɗa kai ku cutar da ni haka ba, ka bani ɗa na na gaya maka" Mahmoudu sai da ya tsure, ganin yadda kamaninta har canzawa suka yi saboda faɗa, idanunta tamkar ta tauna barkono saboda ja, ga ambaliyar da hawaye suke yi a fuskarta. A ɗan iya sanin da ya yi mata, tana da sanyin hali, banda tsiwa da ta kan yi wasu lokutan, bai taɓa tunanin za ta iya burkicewa haka ba. Shi kansa Imam Hammad sai da ya tsorata, yanayin da take ciki ya tabattar masa, sai ya yi aiki tuƙuru kan ma ya samu ta saurare shi. Ya shammace ta ya damƙe ta, ya nufi wata hanya da ita, ta din ga fizge-fizge, tana ci gaba da kuka da turjewa. "Ki nutsu, kar ki yi mini asarar cikin da yake jikinki" Wani irin burki ta ci, cike da rikicewa jikinta na tsuma, ji take tamkar ba ta ji daidai ba, sai dai kafin ta tantance, jikinta ya saki ta yi baya za ta faɗi ya riƙe ta. Jikinta ya yi sanyi ƙalau, sai hawaye da yake fita daga gefen idonta. Da haka ya yi nasarar shiga da ita ɗakin, ya kwantar da ita a kan gadon. Ya zare mata hijjabin jikinta. Ya zura mata idanunsa, a hankali yake lumshe su yana buɗewa a kan ta. Ya kamo hannayenta a cikin nasa, ya sumbaci hannayen, sannan ya ce "Duk abin da ki ka yi mini, kuma duk abin da ki ka kira ni da shi, na cancanta, ban kyauta miki ba, na sani ban kyauta ba, amma ki bani dama ko sau ɗaya ne ma viee, sau ɗaya tak, ki bani dama na ce wani abu. Na san ba halinki ba ne, wannan ba halin Husna ta ba ce, amma na karɓi laifina ki yi mini afuwa. Ban yi abin da na yi domin na zalunce ki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a ƙirjinta yana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin matsanancin sauri. ***** Asal ce take ta shiga tana fita cikin takaici, bayan jin Nana shiru ba ta kawo Abincin safe ba, ga babu alamar na rana, kuma ba  ta gyara sashen ba. Ita a tunaninta tuni ta dawo daga kiran da aka yi mata a can gidan Sultan. Takaici ya ishe ta, dan ta tsani zuwa ɗakin da Nana take a ganinta ƙasƙanci ne, amma jin shirun ya yi yawa, ta fara duba kitchen ba ta nan, ta wuce ɗakin Nana, saboda ya ci a ce ta dawo, duk da ba ta san kiran me Imam ya yi wa Nana ba. Sai dai tana zuwa ta ga wayam, hatta kayan Nana babu sai katifarta. Cikin tashin hankali ta fito ta tara su Balaraba da sauran ma'aikatan cikin gidan. Duk su ka taru "Wai gidan uban wa yarinyar nan, mai yi wa Imam girki ta tafi? Tun jiya ba ta gidan nan, hatta kayanta ta tattara ta tafi ta bar gidan nan." Cikin girmamawa Balaraba ta ce "Wallahi ranki ya daɗe, bamu ganta ba, kin san ta koma cikin sashenku, ba ganinta ma muke yi ba" "A ce kaf cikinku babu wanda ya ga fitarta?" Suka yi shiru, su na sauraren jarabar Asal. Ta ƙare musu rashin mutunci, ta sallame su. Kai komo ta din ga yi tana tunanin ina Nana ta tattara kayanta ta gudu? Haka kurum ta din ga jin kamar akwai abin da Nana take ƙullawa ta bar gidan. Tana komawa sashenta, ta tarar da tarin missed calls ɗin Tafawa. Cikin rawar jiki ta bi kiran wayar, aikuwa ya ɗaga hasale. "Wace irin wawuya ce ke, ina ta kiran wayarki amma kina can kina shashashanci ba ki ɗaga ba?" "Dan Allah ka yi haƙuri, ina can wani uzuri ne" "Uzurin banza uzurin wofi? Asal kin san me yake faruwa? Yau ni mijinki ya kalla ya ce mini na bincike ki, ke ce juya shi ba juya ba ne ya na da ɗa" Wani irin dumm maganar baban nata ta daki zuciyarta, ta ji wani banbarakwai, banda ba abokin wasanta ba ne, da ta ce ƙarya ya sharara mata, kuma da sai ta hukunta shi a kan hakan" "Na ji kin yi shiru?" "To ai na kasa ganewa ne, wai wane Imam ɗin ne yake da ɗan?" "Wanne ki ke aure? Kuma kaf cikinsu waye ba shi da ɗa ban da mijinki?" Cikin kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku na lalace. Abba ya zan yi, ni Hammad zai yi wa haka? A ina yake da ɗan?" "Ki nutsu ki kwantar da hankalinki, haryanzu ban tabattar ba tukuna, ina ga faɗa kawai ya yi dan ya huce takaicinsa, kuma saboda tsagwaron munafunci aka sallami kowa daga zaman, ba a bari na ji ƙarshen zancen ba, amma zan bincika na tabattar da gaskiyar maganar?" Ba ta iya tantance sauran abin da yake faɗa ba, ta kashe wayar jikinta yana rawa, ta hau kiran lambar Hammad, sai dai shiru wayarsa ba ta shiga, ta kira ya kusa sau hamsin, amma shiru ba ta shiga. Ta yi jifa da wayar tana huci. "Wallahi Hammad, zancen nan ko ba gaskiya ba ne ba, sai ka fuskanci mummunan tashin hankali da abin da ba ka taɓa zato ba. Wallahi ta tabatta ka haihu da wata mace, sai an mutu har Liman." Ta zauna Jikinta yana wata irin tsuma ta tashin hankali. Sultan kansa ya kasa zaune ya kasa tsaye, dan babu yadda ba su yi da shi ya yi magana ba, bayan tafiyar Nana ba amma ya ƙi. Hankalin Sultan ya yi mummunan tashi, Abduou matawalle ne ya din ga rarrashin sa yana kwantar masa da hankalin a kan su bi komai a hankali, har su samu Hammad ya yi musu bayani dalla-dalla. Sultan ya ce "Matawalle, a tsorace nake, Tafawa ya yi nasara, ya yi nasarar tabattar wa da Duniya cewar Hammad mahaukaci ne, idan ba haka ba ta yaya zai zo ya ce yana da ɗa, ɗan ma ba da buzuwa ba, 'yar wata ƙasar bayan ya san me hakan yake nufi. Tafawa ya ce "Kar ka yi mamaki, yanzu dole mu jira ya yi magana, mu ɗan ba shi lokaci ya nutsu, dan mu tabattar jikin ne, ko kuma da gaske yake. Kar ka manta tsawon lokacin da ya shafe ba tare da mu ba, bamu san me da me ya faru ba, kuma kar ka manta a Nigeria a ka gano mana shi" Sultan ya goge gumin da yake tsatstsafo masa ya ce "Matawalle, akwai gagarumar matsala, babu buƙatar mu ba shi wani lokaci na daban, dole ya warware mana zare da abawa mu ji yadda aka haihu a ragaya. Kira mini wayarsa, duk inda yake a nemo shi, kuma a kira mini yarinyar ma" Matawalle ya ce "Haka ne, kuma a nemo  wannan munufukin yaron Mahmoudu, domin tabbas ya san komai, ya san duk abin da ya faru" "Wai ni ita yarinyar ma, ni kamar na taɓa ganinta, a ina aka samo ta ne?" Matawalle ya ce "Eh, lokacin da Hammad ya dawo, tana cikin waɗanda suka yi girki, wai Gimbiya Asal ce ta kawo ta" "Asal kuma?" Sultan ya yi maganar yana nazari. Sai dai duk tarin kiran wayar da aka yi wa Imam Hammad, ko sau ɗaya wayar ba ta shiga ba. Hakan ya ƙara jefa su a tashin hankali. A hankali Nana ta yi miƙa, dan tamkar ta ci wani abu, haka ta yi wani irin nannauyan bacci. Cikinta ne yake wata irin ƙara, saboda azabar yunwar da take ji. Ta yinƙura da ƙyar, za ta tashi zaune, ta yi tozali da kyakykywar fuskarsa, yana kallonta. Ja da baya ta yi tamkar ta yi tozali da wanda ba muharraminta ba. Ta kalli jikinta babu hijjabi, rigar jikinta ma an canza mata wata. "Kin tashi?" "Ina ɗa na yake? Kuma waye ya ce ka taɓa ni ka canza mini riga, waye ya baka wannan damar?" "Sadakina" ya ba ta amsa kai tsaye. Ita tsantsar mamakin halayyarsa take yi ma a yanzu, gaba ɗaya ya canza mata. "Na haɗa ka da girman Allah, ka bani ɗa na, ka bani ɗa na, ni ban sanka ba, ɗana kuma ba ɗan ka ba ne, dan Allah ka bani yarona na tafi, dan Allah ka taimaka mini, na karɓi yarona na koma ƙasata" Ta yi maganar hawaye na bin fuskarta. Ya wani lumshe ido yana murmushi ya ce "To ni kuma ina za ki kai ni idan ki ka tafi?" "Ni ban sanka ba" "Haba?" Yayi maganar yana ƙanƙance idanunsa. Wani marurun takaici ne ya ƙule Nana. "Ki tsaya ki saurare ni, na yi miki bayani" "Ni ba zan ji wani bayaninka ba, duk abin da zai fito daga bakinka, ba zan taɓa yarda da shi ba. Ka bani ɗa na na tafi" Sayyid ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ki bari ki haifa mini abin da yake cikinki, ki bani abina, sai mu san abin yi" Daina ganewa Nana ta yi na wani ɗan lokaci, ta yi shiru ta tuna ya ce mata tana ɗauke da juna biyu ma ɗazu. Ta kalli cikinta, ta ɗago ta kalle shi, ya ɗage mata girarsa ɗaya. Ayshercool 08081012143 80 Gaba ɗaya kanta ya kulle, ta zuba masa idanunta da suka yi jawur. A mugun kasanlance ta ce "Ciki kuma?" Ya jinjina mata kai, ta rasa abin da za ta yi gaba ɗaya. Ciki yaushe? Yaushe wani abu ya shiga tsakaninsu da har za ta ɗauki ciki? Ta tambayi kanta, sai dai ta kasa tambayarsa. Sai tsare shi da ta yi da idanunta. Ya gyara zamansa sosai ya ce "Kina ji na?" "Babu abin da zan ji? Kar ka gaya mini komai, ba zan ji ba kuma ba na fatan ji. Abin da ka yi mini haka ma ya isa, ka bar ni na ji da kaina". Ta yi maganar a matuƙar zafafe. Ya ce "Shikenan na ji. Na rabu da ke. Amma ina so ki sani, muddin ba ki saki jikinki ba, ki din ga cin abinci ki rage wa kanki wannan damuwar ba, to fa ba zan ba ki Muhsin ba. Gwargwadon sakin jikinki, da cin abinci da zaki yi, shi zai sanya ki gan shi. Akasin haka kuma zan ci gaba da tsare ki a nan, na kai wa Asal shi ta riƙe shi, tun da dama ita Allah bai ba ta haihuwa ba. Wannan ma idan ki ka haifa ki bani abina tun da ba za ki saurare ni ba" Kallon ba ka da hankali ta yi masa. Ya yinƙura da kyar, jikinsa babu ƙwari, ya ɗauki hiraminsa ya rufe kansa ya fice ya bar ɗakin. A ɗaya falon ya tarar da Mahmoudu, cikin zaƙuwa ya ce masa "Yaya ta saurare ka kuwa?" Jiki a sanyaye ya girgiza kai tare da zama ya ce "Fafur ta ƙi saurar ta, duk wani rarrashi da ban baki da zan yi, taƙi saurarta kawai na ba ta ɗan ta na sake ta ta nanata mini, na rasa yadda zan yi ko na minti ɗaya ta saurare ni. Babban abin da yake ɗaga mini hankali gani nake kamar da gaske Husna ta daina so na" Mahmoudu ya girgiza kai ya ce "Ka yi haƙuri, ɓacin rai ne kawai ya sanya ta faɗar haka, amma a irin so da sadaukarwar da ta yi maka ba zai yiwu a ce ta daina sonka ba" Ya tashi zaune sosai yana kallon Mahmoudu ya ce "Kana ganin idan ta huce, za ta ci gaba da so na kuwa?" "Sosai ma, yanzun ma ɓacin rai ne kawai. Amma za ta ci gaba da sonka da zarar ta huce" Ya koma ya kashingiɗa yana kaɗa ƙafafuwansa. Mahmoudu ya numfasa ya ce "Yanzu Imam mene ne abin yi, na san fa yanzu ana can ana nemanmu, ta ina zaka fara Fuskantar wannan balahirar? Ta ina za a fahimce mu, akwai gagarumar matsala fa" Ya ɗan kwaɓe baki ya ce "Wannan balahairar ba ta kai fushin da Asmy take yi da ni ba. Ni duk yadda za su yi da ni sai dai su yi. Ko su bar ni a raye ko ma su yanka ni, burina da fatana na ga ta haƙura ta yafe mini ta saurare ni." "Yanzu soyayyarka gaba take da gagarumin tashin hankalin da yake gabanmu?" "Nesa ba kusa ba kuwa, idan aka kamanata shi da zunzurutun soyayya mara algus ɗin da na samu. Ko ka manta abu ne da nake nema ido rufe" Mahmoudu ya ce "Turƙashi, to yaya za ka yi da Gimbiya Asal?" Kawai ya saki murmushi, ya shafa sajensa. "Au dariya ma na baka?" "Eh mana, ni fa duk wannan masu sauƙi ne, ban ɗauke su matsaloli ba, zan gaya wa kowa gaskiya ko me za a yi mini sai dai a yi mini, ni fatana Asma'u ta yafe mini" Ya ƙarasa maganar cikin damuwa. "Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah za ta saurare ka, ta ɗauki zafi ne, amma tana hucewa za ta saurare ka" ***** Doctor Sharif ne yake kallon matarsa cikin tausayawa, cikinta ya tsufa, amma sai fama take da rashin lafiya, duk da haihuwa ta biyar za ta yi. A dole ya ba ta gado a Asibitin, cikin wata bakwai da sati ɗaya, amma tana ta zubar da ruwa, ga matsalar numfashi da suga da yake hawa yana sauka. Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Gida zaka tafi ka bar ni?" Ya ce "Eh mana, ba ga Yaya za ta kwana tare da ke ba? Kin ga yara su na gida, ga shi gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta, dole na koma gida. Da na kai su school zan taho nan, duk wani abu da za a yi miki, na yi shi a rubuce duk za a yi miki" Ta numfasa ta jinjina kai ta ce "To shikenan, sai da safe" "Yauwwa Madam, ki samu isasshen bacci dan Allah" "Idan na kwanta ne, baccin ko na fara sai na ji numfashina yana yi mini sama, kwanciyar babu daɗi sam" "Na sani, ki yi haƙuri sai ki kwanta a side ɗin hannunki na hagu ko na dama" Ta ce "To, sai da safe" Suka yi sallama ya tafi cike da tausayinta, wannan cikin tun yana ƙarami ya zo da tangarɗa yake wahalar da ita, ga shi ya tsufa ma amma ba ta daina wahala ba. Hankalin Alhaji Zailani ya yi mummunan tashi, ganin sauƙi sosai da sosai a tattare da Alhaji Fatuhu. Ga 'yan kasuwa sun yi masa caaa a ka, a kan lallai ba sa son shugabancinsa, sai dai ya sauka a canza wani. Ya tattara nutsuwarsa ya yi burusu da su, domin ba ya son ya rarraba hankalinsa, wani abin ya ƙwace masa. **** Nana kuwa ji ta yi da gaske yunwa na ƙoƙarin hana ta sukuni. Tashi ta yi ta fito, ta fara dube-dube. Yana daga inda yake tsaye yana kallon ta. "Me ki ke nema ne?" Firgita ta yi ta juyo tana kallon inda yake, ganin yadda yake ƙare mata kallo ne, ya sanya ta haɗe rai. "Ina fatan ba wani gurin ki ke shirin tafiya ba, babu hanyar da za ki bi ki je ko ina" "Ni ba guduwa zan yi ba, idan na ci Abincin yau za ka bari na gan shi?" Ya yi murmushi ya ce "Ki ci ɗin tukuna, Bismillah biyo ni" Jiki a sanyaye ta bi bayansa, cikin matsanancin tsoro, dan ganin shi take yi kamar wani mutum na daban. Haɗaɗen bedroom ya kai ta, ta tsaya saroro tana kallon ɗakin, ta ɗaga kai ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe ɗaya da rabi na dare. "Zauna ki jira ni a nan" Ta tsaya tana kallon sa. "Ki zauna mana" Ya yi maganar yana nuna mata bakin gado. Ta yi ƙyam tana kallonsa. Bai sake ce mata komai ba, ya fita ta tsaya tana zazzare ido, tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo. Ta gaji da tsayuwa, ta samu guri ta jingina da jikin bango, sanyin AC da yake ɗakin ya fara damunta. Falon ta koma, tana nan zaune sai ga shi ya shigo da leda a hannunsa. "Me yasa ki ka fito?" "Sanyi nake ji" Ta ba shi amsa a taƙaice. "Ohh yi haƙuri, mu je sai na kashe miki A.C" Ta girgiza masa kai tana sake haɗe rai. "Shikenan, zauna ga abincin na samo" Ya yi maganar yana riga ta zaman. Ta zuba wa ledar ido, bayan da ya fito da gasassun zabi guda biyu, babu abin da ya faɗo ranta, sai zaman su a gidan Hajiya Halima, lokacin da ya saka Habu ya kawo mata zabbi gasassu. Ya kalle ta ya ce "Ko na dafo miki shayi?" Ta girgiza kai ta tashi tsaye. "ina za ki je?" "Ɗakin da nake zan koma,a can zan ci" Ta ba shi amsa ciki-ciki. "To mu je can ɗin, nima ban ci komai ba, wataƙila idan muka ci tare, zan iya sakin jiki na ci Abincin" Nana ta ƙara haɗe rai ta ce "Ni fa ba zan ci wani abinci tare da kai ba, bana buƙatar duk wani abu da zai ƙara kusanta ni da kai. Ni a yanzu neman maraba nake yi da kai". "Neman maraba ki ke yi da ni?" Ya yi maganar yana murmushi mai ciwo, daga bisani ya ce "Shikenan, ɗauki abincin ki je ki ci, sai ki kwanta ki huta" Ya tashi ya bar mata falon. Ta tattare kan kayan abincin, ta tafi ɗakin da aka ajiye ta. Sosai ta fara ƙoƙarin cin abincin, saboda azabar yunwar da take ji, sai kuma ta tuna da gaske idan ba ta yi girki ba, ba ya cin abincin. Kenan tun da ta tafi bai ci cikakken abinci ba kenan ko yaya? Wata zuciyar ta tambaye ta. Har za ta yinƙura ta tashi, sai ta tuno batun cikin da ya ce tana da shi. A take wani malolon takaici ya ƙule ta, ta ƙuduri aniyar sai ta yi dalilin zubewar cikin nan. To tayaya ma za a yi a ce ina da ciki? Yaushe kuma ta yaya?" Ta tambayi kanta. Gaba ɗaya ta ji kanta yana juya mata, dan haka ta haƙura da tunanin, ta je ta wanke hannunta ta ta rufe abin da ta rage ta kwanta. Sai dai ta ƙi yadda ta yi bacci, saboda gudun kar ya biyo dare ya zo ya yi yinƙurin yi mata wani abin. Sai dai ko mintuna goma ba a yi ba, ta tsinci kanta a cikin Libraryn Ƙaisar. Ta gan shi a kwance a kan wani gado, ya lulluɓa da wani baƙin mayafi. Ya kalli fuskarta da ke ɗauke da damuwa ya ce "Ya dai?" Ta Numfasa ta ce "Ya na gan ka a kwance a nan?" "Eh to zan yi ta zama ba zan kwanta ba ne?" Ta ce "A'a, amma galibi sai ba ka da lafiya ka ke kwanciya a nan gurin" "Lafiyata ƙalau. Na ɗauka zan gan ki cikin murna da farin ciki, tun da mijinki ya dawo hayyacinsa ya gane ki, sai kuma na gan ki cikin damuwa?" Ta nemi guri ta zaune a gefen Ƙaisar ta ce "Ni fa ba na ƙaunar mutumin nan, fatana kawai ya bani ɗa na, na koma Nigeria Ubangiji Allah ya sanya su Baba su yafe mini, ina kyautata zaton alhakinsu ne ya kama ni" Ƙaisar ya ce "Waye ba kya ƙaunar yanzu?" "Sayyid" "Ƙarya ki ke yi" ta ce "Ƙarya kuma?" "Da dai ban san halinki ba ne" Cikin sanyin jiki ta ce "Da gaske nake, ba wasa nake yi maka ba. Ba na ko ƙaunar jin sunansa, ya yaudare ni, sun cutar da ni. Gaba ɗaya kimarsa da son da nake yi masa sun zube a idanuna" Ƙaisar ya yinƙura ya tashi zaune, yana ƙara rufe jikinsa ya ce "Tun da ya ce ki saurare shi, ki tsaya ki ji mai zai ce miki mana. Kar zuciyar da ki ka yi ta sanya ki yanke hukuncin da ba zai ɓulle muku ba" "Ni fa babu abin da zan ji daga bakinsa, ba na buƙatar sa a rayuwata gaba ɗaya" Ƙaisar ya yi murmushi yana gyara zamansa a hankali. Idon Nana ya sauka a kan Jakar Sarkin baka da ke gefen gadon da yake. "Ƙaisar, me ka ke yi da jakar Sarkin baka?" Ya yi mata shiru kamar bai ji ta ba. Miƙewa ta yi da sauri ta ce "Wani abu ya faru tsakaninka da Giyaz ko?" "A'a aron jakar na yi, wani aiki na yi da ita". Nana ta saka hannu ta ɗan ja mayafin da ya rufe jikinsa da shi, wani irin haske ne ya haske mata ido, daga bisani hasken ya ragu a hankali. Jikinsa ya yi wani irin kore-kore, wani gurin kuma ya yi baƙi ƙirin tamkar an ƙona shi. Nana ta ce "Meyafaru? Me ya same ka haka? Giyaz ya yi maka wani abu ne?" "Babu abin da ya faru, zan dawo miki da jakar ki kuma, ki je sai na sake neman ki" Nana ta farka daga baccin da take yi, fuskarta duk hawaye. Gaba ɗaya jikinta a sanyaye ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili, sannan ta gabatar da sallar asuba. Har gari ya yi haske, tana zaune a ƙasa. Shiru ta yi tana tuna yadda ta ga jikin Ƙaisar, sai ta ji abin ya dame ta sosai da sosai. "Mene ne makomar wannan sakankancewar da nake yi da Ƙaisar yanzu? Me yasa kuma yake taimakona a wasu guraren? Anya ba wani tarkon na yaudara ya yi mini ba, yake son na afka ya yi amfani da damar ba? Ko ma dai yaya ne, Ubangiji Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abin ƙi." Sosai take son mantawa da tunanin Ƙaisar, ta koma tunanin Muhsin, da wannan balahirar ta gabanta, amma abu ya ci tura, a jikinta take jin Ƙaisar, take jin ta damu da halin da ta gan shi a ciki. Sallamarsa ce ta katse mata tunani, ta amsa masa ciki-ciki. Ya je gabanta ya ajiye tray. Ya ɗan tsura mata ido ya ce "Barka da safiya Rayuwata" Wani mugun kallo ta yi masa, haɗi da uwar harara. Ya yi murmushi ya ce "Ga abin karyawa nan, kar ki manta sakin jikinki, da cin abincinki ne zai sanya ki ga ɗana" "Ka daina danganta mini ɗana da kanka, ba shi wata alaƙa da kai" Ta yi maganar cikin tsiwa. "Ba shi da alaƙa da ni, sai da Ƙaisar?" Ya yi maganar ya kallonta yana murmushi. Bai ba ta damar ba shi amsa ba ya ce "Yau zan koma gida, zan je na ji yadda za mu yi da su Sultan, amma ki nutsu ki kwantar da hankalinki dan Allah" "Ba ni da wata nutsuwa ko kwanciyar hankali, idan ba ɗa na na gani ya zo hannuna ba". Ya yi shiru yana tsare ta da idanunsa. Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ji gabanta ya faɗi, ta rasa gane wane irin kallo ne yake yi mata haka. Ta sunkuyar da kanta tana haɗe rai. Ta sake ɗaga ido ta suka haɗa ido, ya yi mata murmushi, ya ce "Ma vie, ban san daga ina nake jin ƙaunarki ba a rayuwata, kar ki hukunta ni da abin da ki ka gani kawai a zahiri. Ina sake roƙonki, ki bani dama ki ji ta bakina" "Ni babu abin da zan ji, na ce maka ɗana kawai nake buƙata" Ya shafi sajensa ya ce "Muhsin ai nawa ne ni da Asal. Idan ki ka haihu kuma nawa ni da ke, shi ma idan ba kya so sai ki bani abina" Wata irin ɗagowa ta yi, cike da takaici, ya shammace ta ya rungume ta ya haɗe bakinsu. Nana ta tattara nutsuwarta, da duk wata jarumta dan ganin ba ta biye wa Sayyid. Ta din ga ture shi iya ƙarfinta tana kai masa duka, amma tamkar dutse ba jikin ɗan Adam take duka ba. Sai da ta gaji ta ƙyale shi. A hankali ya zare bakinsa daga nata ya ɗago fuskarta yana kallonta. Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy, ko kin tafi kin bar ni, ba za ki taɓa samun nutuswa da kwanciyar hankali ba. Kamar yadda tun da muka rabu nawa ruhin ma bai samu nutsuwa ba. Ina ƙaunarki rayuwata" Duk yadda Nana ta so yi masa rashin kunya, ta gaggaya masa maganganu masu zafin gaske, amma ta kasa tamkar ya saka wani abu a cikin idanunsa da ya yi tasirin da ya hana ta maganar. "Ki yi mana addu'a rayuwata, akwai kaya a ɗakin da muka je jiya, idan kin yi wanka akwai kayan sakawa. Sai akwai kitchen shi ma, duk za ki iya shiga ki dafa mana duk abin da ki ke so. Sai na dawo" Ko tari Nana ba ta kuma yi ba, har ya tashi ya bar ɗakin, ta bi bayansa da harara. Nene ce rungume da Muhsin, ya sha ado cikin kayan buzaye, kayansa iri ɗaya da na jikin babansa, sai ƙoƙarin cire mayafin da aka rufe masa gashinsa da shi yake yi, sai ƙamshin turare yake yi. Hammad ya saka hannu ya karɓe shi fuskarsa ɗauke da murmushi har da wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Hammad ya ce "Mu je ko?" Nene jiki a sanyaye ta ce "Ina mai neman afuwarka, ni tsoron zuwa gidan nan nake yi. Kuma a wane hali Nana take ciki yanzu, na kasa nutsuwa gaba ɗaya, ina jin ban kyauta ba gaba ɗaya" "Ki kwantar da hankalinki, Nana tana tare da ni, kuma babu wanda zai yi miki komai a cikin gidan, ki taimaka mini dan Allah" AREWABOOKS Nene ta numfasa ta ce "Alfamarka ce kawai za ta sanya na yi maka abin da ka nema, dan na yi alƙawarin babu abin da zai sake haɗa ni da wannan gidan naku, saboda mummunan tabon da yake binne a zuciyata. Kuma da ko me za ka yi mini ba zan ba da ɗan nan ba, saboda ya saɓa alƙawarin da muka yi da Nana, ban kyauta mata ba za ta yi mini kallon mutuniyar banza mara alƙawari. Amma kai ma ɗa ne a gurina, ban da dalilin haka gaskiya ba zan iya ba" "Na sani, kuma na gode sosai da sosai, da wannan alfarma da ki ka yi mini" Ta risunar da kanta cikin girmamawa. Ya miƙa mata Muhsin ta karɓe shi, suka shiga mota. ***** A tsanake Tafawa ya kalli Asad ya ce "Asad, wai waye ka ce ya karɓi ayabar nan ya ci?" "Wata yarinya ce, ni ban santa ma a gidan nan ba gaba ɗaya" "Dole a nemo ko wacece, saboda an tabattar mini, da cin ayabar da ta yi, da gayya ta karɓa ta ci, dan aikin da aka yi ya ɓaci ya lalace." Asad ya yi shiru, ya ce "Gaskiya ban san ko wace ce ba, sai dai ko a tambayi Asal, ko ta santa abinci dai ya kawo mana. Ina kyautata zaton ko kuku ce ko dai makamancin hakan. Ban ma san yadda aka yi ta zo inda muke ba, dan kamar ba buzuwa ba ce gaskiya" Tafawa ya yi shiru yana nazari, ya ce "Babu yadda za a yi wadda ba buzuwa ba, ta tsallako ta shigo gidan sarautar Agadez, ta yi wannan abin, lallai zuwanta na manufa ne, dole a binciko wace ce." Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa. Asal duk ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankali, mussaman da Imam ya kwana uku ba ta san inda ya shiga ba, hakan ya sanya ta fara jin kamar akwai ƙamshin gaskiya a maganar da Tafawa ya gaya mata. Ta kasa jurewa ta je ta samu Sultan, tana yi masa kuka. Cikin damuwa ya ce "Yarinyar kirki lafiya kuwa?" "Sultan ji na yi an ce wai Imam yana da ɗa, dama aure ya yi ban sani ba? Kuma tun shekaranjiya ban sake ganinsa ba, kuma ba na samun sa a waya" Sultan ya ce "Waye ya gaya miki?" Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. Ya numfasa ya ce "Shikenan na fahimta, amma ki kwantar da hankalinki, na tabattar da Hammad ba zai aikata abin da zai zubar da kima da mutuncin gidan nan ba, dan haka ki yi haƙuri ki bani lokaci, ina kan bincike ne" "Amma Abie, to ina ya tafi, haryanzu ban san inda yake ba, kuma wayarsa ba ta shiga" Sultan ya ce "Na sani, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki. Zai dawo in sha Allah" Asal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi, sai dai zuciyarta ta gaza haƙuri da samun nutsuwa. Washegari, Sultan na tare da Sardauna da kuma Matawalle su na tattaunawa, aka zo neman iso cewar Imam Hammad yana neman izinin shigowa. Cikin takunsa mai burgewa, ya shiga. Gaba ɗaya suka zuba masa ido suna kallonsa. Hammad ya nemi guri ya zauna a ƙasa tare da gaishe su. Matawalle ya amasa masa. Sultan kuwa rasa abin cewa ma ya yi sai daga bisani ya numfasa ya ce "Ina ka tafi tsawon kwanaki uku haka, ka kashe wayoyinka ka tayar mana da hankali?" Hammad ya numfasa ya ce "Ina mai bayar da haƙuri, na laifin da na aikata, na yi hakan ne, domin tabattar muku da abin da na faɗa. Ina cikin hayyacina na faɗi abin da na faɗa, kuma da shaida a kan abin da na faɗa". Sardauna ya ce "Ka na da hankali kuwa? Ka na nufin da gaske ka haihu da matar da ba mu sani ba?" Ya jinjina kai daidai lokacin da Mahmoudu ya shigo ɗakin shima." Matawalle ya ce "Ga munafukin nan, ya san komai" Sardauna ya ce "Ni kun sani a duhu, shi kuma wannan waye ya kawo shi cikin wannan mas'alar?" Sultan ya ce "Bari mu ji ta bakinsa" Mahmoudu ya zauna ya gaishe su. Sannan ya numfasa ya ce "Da fari ina neman afuwar mai girma Sultan, da ahalinsa da 'yan majalissar sa, da ma duk wani wanda abin ya shafa. Na san na aikata laifin da na cancanci hukunci, kuma a shirye nake na karɓi hukuncin laifina, na aikata abin da ya saɓa wa dokar masarauta duk da girman matsayin Imam Hammad a ƙasar nan" Sardauna ya ce "Mu na jin ka, ka yi mana bayani, me ka aikata, kuma me a sani a kan lamarin?" Sultan ya numfasa ya ce "Wato Sardauna mun ɓoye wa mutane abubuwa da dama da suka faru. Magana ta gaskiya Imam Hammad ya samu matsala ya bar ƙasar nan bamu sani ba. Mun yi ta bibiyar inda zamu samo shi. Muka rufe muka ce yana faransa babu lafiya. Da muka rasa shi, aka rasa hadiminsa Mahmoudu, shi ne muka koma binciken Mahmoudu ta ƙarƙashin ƙasa, aka yi nasarar gano su a Nigeria. Sai dai da aka dawo da shi Agadez tamkar ya manta da mu baki ɗaya, baya cikin hayyacinsa. Bamu san haƙiƙanin abin da ya faru a Nigeria ba, sai dai idan sun yi mana bayani yanzu. Abin ya ɗaurewa Sardauna kai, gaba ɗaya bai san lamarin nan ba sai a yanzu, jin abin yake tamkar almara. Mahmoudu ya ce "Bayan na tafi da Shugabana Imam Hammad Nigeria, nema masa magani, bayan da na fuskanci ya manta duk wani abu da ya shafe shi. A can muka haɗu da yarinyar a gidan da muka zauna, mahaifinta ya ba shi aurenta. Shi da kansa ya ce a biya sadakin aurensa da ita. Tun da shugabana ne ba ni da 'yancin yi masa musu. Na yi ƙoƙarin tunatar da shi, amma ko na tuna masa, ba zai iya tuna komai da ya shafe shi ba" Matawalle ya ce "Wai wannan wace irin shiririta ce ku ke karanta mana? Wane irin abu ne haka? Ta yaya mutumin da ya manta komai ya san ya ce a biya masa sadaki ya yi aure?" Mahmoudu ya ce "Imam waye shi, da duk abin da ya shafi Agadez ya manta, amma duk wani abu na rayuwa na yau da kullum ya sani. Kuma ga shi a tambaye shi, tun da yanzu yana iya tuna abubuwan da suka faru a Nigeria" Sardauna ya ce "Shi tunanin nasa network ne kenan, ko zamani da idan wannan ya zo wannan zai wuce?" Kafin Mahmoudu ya bayar da amsa, Matawalle ya ce "Wato Mahmoudu ba ka ji kashedin da na yi maka ba a kan sanar da shi wani abu ba" Mahmoudu ya ce "Ba laifina ba ne ranka ya daɗe, shugabana ne duk abin da ya umarce ni, dole na yi ba ni da zaɓi" Hammad ya miƙe ya ce "Ina zuwa" Ko da Hammad ya fita, Mahmoudu suka ci gaba da yi wa tambayoyi, yana ta ƙoƙarin basu amsa da rufa wasu abubuwan. Tsit suka yi da suka ga Hammad ya dawo, Nene na bin sa a baya da ɗa a hannunta. Matawalle ya ce "Imam me ya kawo wannan matar gidan nan kuma?" Nene ta yi turus tana haɗe rai ta sunkuyar da kai. Kafin su ƙara magana, Muhsin ya jefo mayafin kansa ƙasa, tare da waiwayowa yana kallon mutanen gurin. A sukwane Sultan ya miƙe tsaye. Imam Hammad ya karɓi Muhsin daga hannun Nene, ya nufo Sultan da shi. Jikin Sultan ya hau tsuma, yana kallon yaron da ya jiye tamkar Hammad ɗin sa yana ƙarami. Shi kuwa Muhsin kallon babansa ya din ga yi yana kallon Sultan, ganinsu iri ɗaya. Ya miƙa hannu ya ɗauki Muhsin yana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah" Su kan su Sardauna da Matawalle, ƙura wa yaron ido suka yi, duk sharrin mai sharri ƙarya ne ya ce wannan ɗan ba na Hammad ba ne ba. Matawalle ya ce "Ikon Allah, da gaske dai Hammad yana da ɗa" Sultan ji yake yi tamkar ya haɗiye Muhsin, da a yake son ya sauke shi ya koma gurin Nene. Ya juya yana miƙawa Hammad hannu ya ɗauke shi. Sardauna ya miƙe ya ce "Yanzu ina uwar yaron take" "Tana nan" Imam ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa. Sardauna ya ce "Akwai rikita-rikita a lamarin nan. Dole a san yadda za a yi. Mu na buƙatar ka zo mana da uwar yaron nan, gobe in Allah ya kaimu. Ku kuma zamu tsare ku har sai komai ya daidaita mun gano komai." Nene ta ce "Ranka ya daɗe me zai sanya a tsare ni? Mahmoudu ne naku dama, ku ci gaba da tsare shi da duk abin da za ku yi masa, amma ni ina roƙon alfarma a ƙyale ni na tafi" Matawalle ya ce "Jayayya za ki yi da abin da muka ce kenan?" Nene ta sunkuyar da kai ta yi shiru. Hammad ya ce "Zan cika miki alƙawarin da na ɗauka, babu abin da zai faru in sha Allah, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu zan zo da ita" Nene ta yi shiru cikin sanyin jiki. Duk yadda Sultan ya so ƙanƙame Muhsin ya ƙi yadda, ya zamo ya sauka daga jikinsa, ya koma jikin Nene ya kwanta, ya saka hannunsa a baki. Gaba ɗaya Sultan ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda ganin Muhsin, bayan shafe lokaci yana fatan ɗan nasa ya samu haihuwa. Sardauna ya ce "To ita matar Mamman me ya kawo ta cikin wannan lamarin ne? Na ga kamar yaron ma ya santa?x Hammad ya ce "Eh, a gurinta yake ne" Haka aka killace Nene da Mahmoudu, aka hana su zuwa ko ina. ***** Ko da ya shiga sashensa babu kowa, Asal ba ta nan, ya yi mamakin inda ta tafi. Ya tafi kitchen ɗin da Nana take girki, ya shiga ya buɗe fridge ya samu sassanyar madarar raƙuma, ya tsiyaya ya fita. A ƙalla ya kai awanni biyu a zaune, sai ga Asal ta dawo, babu tsammani ta gan shi a falo a zaune. Ɗan turus ta yi tana kallon sa. Ya ce "Ƙaraso mana" Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi. "Ina ki ka je haka?" "Nemanka na je yi" ta furta jiki babu ƙwari. "To zan gudu ne? Ai gani na dawo" "Wancan karon ma ai ka tafi ka bar ni" Ya yi murmushi ya ce "Wannan na larura ne ai Cherié" Ya yi maganar yana miƙewa, har ya nufi bedroom ta ce "Hammad" tsayawa ya yi cak, jin ta kira shi da gundarin sunansa na yanka. "Da gaske ka haihu da wata a waje ban sani ba?" "Waye ya gaya miki?" Asal ta kalle shi ta ce "Kar ka amsa tambayata da tambaya, ka bani amsa ko na samu nutsuwar zuciya, babu abin da yake yi mini daɗi. An ce ka kira ni da juya, kuma ka ce ka na da ɗa, da gaske haka ne?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido. Sai ya fasa shiga ɗakin, ya nufi inda take zaune, ya tsura mata ido sannan ya ce "Ni da ke na taɓa gaya miki haka? Ta girgiza kai jiki a sanyaye. "Wanda ya gaya miki ya so cin mutuncinki ne, amma da bakina na taɓa faɗa?" Ta girgiza kai jikinta a sanyaye. "To ki toshe kunneki daga jin abin da za a zo a gaya miki wai wai, ki jira abin da zai fito daga bakina zuwa kunnuwanki" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, amma ba ka gaya mini inda ka je ba" "Wani aiki nake yi wa Sultan, ki kwantar da hankalinki" Ya miƙe ya tafi ya bar ta a gurin. Da magariba ta ga yana ta shiri, ta ce "Amour ina zaka je ne?" Ya ce "Eh yanzu zan yi miki bayani, zan je wani aiki da Sultan da ya saka ni ne, sai gobe in Allah ya kaimu zan dawo" "Aiki kuma sai da daddare?" Ya kalle ta ya ce "Asal, wai ki na zargina ne, yau na fara fita yin aiki da daddare, me yasa za ki tsare ni da tambayoyi kamar ba ki yarda da ni ba, shirya mu tafi tare" Yayi maganar yana haɗe rai. Ta risunar da kai cikin girmamawa ta ce "Tuba nake yi, zuciyata ce ta cika fargaba, amma ka yi haƙuri" Ya miƙe ya nufi hanyar fita, haka nan zuciyarta ta tsananta bugawa. Bayan fitarsa ya tsaya a harabar gidan, ya ɗauki wayarsa ya kira Tafawa. Tafawa ya ɗaga tare da yin sallama. Hammad ya amsa tare da cewa "Barka da dare ranka ya daɗe" "Barka dai" Ya amsa a taƙaice. "Yauwwa, dama na kira ka ne na sanar da kai, ka san abin da za ka din ga sanar da Asal, ka daina shiga cikin batun iyalina, idan ba haka ba za ka iya saka wa ta rasa ranta ko lafiyarta" "Hammad, ni ka ke gaya wa haka?" "Kai ka bani damar na gaya maka hakan ai. Abin da ba ka sani ba shi ne, Asal ta riga ta fara so na, tsawon lokacin da ya gabata, ci gaba da gaya mata magana kowace iri a kaina, ka iya haifar mata da matsala. Amma 'yarka ce duk abin da ka ke ganin shi ne daidai ka yi ba wani abu" Ya kashe wayarsa gaba ɗaya, ya shiga mota da kansa ya ja motar ya bar gidan. A zaune ya tarar da Nana a ɗakin da kayanta suke, ta sanya atamfa riga da skirt, kanta babu ɗan kwali. Ta yi parking ɗin black natural hair ɗin ta, da siririn band na yi wa yara kitso. Dan zabura ta yi, da ta ji motsinsa. Hannunsa riƙe da ledoji, ya ƙarasa ya zauna ya ajiye ledojin ya ce "Sannu da gida, na bar ki ke kaɗai ko?" "Dama can ai nikaɗai ɗin nake rayuwata" Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, amma dai kin rayu da ni ɗin ko?" Ta yi masa shiru tana kai hannunta ta ɗauki ɗan kwalin kayan, za ga ɗaure kanta. Ya janye ɗan kwalin ya ce "A haka nake son ganinki, kin yi mini kyau sosai da sosai" "Sayyid, duk wannan abubuwan da ka ke yi, ba za su taɓa tasiri a kaina ba, ka bani ɗana kawai na kama gabana" "Gaskiya ne maganganuna ba za su yi tasiri a kan ki ba, ciki har da kirana da Sayyid. Ga abinci na kawo miki, ki ci" Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Ai na ci Abincin kamar yadda ka ce, yaushe za ka ba ni ɗa na?" "Kin ci, amma ba kamar yadda nake buƙata ba, sonake ki ƙara ƙiba, alamu sun nuna ba kya nutsuwa ki ci abinci ki ƙoshi" Ta kawar da kanta gefe, dan kar ma ya ci gaba da jan hirar. Dan ba ta son duk wani abu da zai sanya a ranta ta ji za ta iya ci gaba da rayuwa da shi." Ya kwance rawaninsa, ya rage kayan jikinsa, ta kawar da kanta gefe, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri. Ya zauna a kusa da ita ta ɗago ta kalle shi, gashin nan a kwance ya sha gyara. Ya ɗago mata yatsunsa ya ce "Ina zobena ne? Kin saka an addabe ni a kan zoben nan da yawa" Yana nuna mata yatsunsa. Ta yamutsa fuska ta ce "Na yar da shi" "Kin yar da zobena, kin ajiye turarrukana da mayukan gashina, ki na kallo ki na jin daɗi. Soyayyar gaskiya mara algus. Gobe in Allah ya kaimu za mu je gaban Sultan, mu ji hukuncin da za a yanke mana. Saboda na aikata laifi mai girman da babu wanda ya taɓa aikata shi sai ni." Ayshercool. 08081012143 81 Nana ta taɓe baki ta ce "Wanda za a yanke maka dai, ni babu abin da ya haɗa ni da masarautarku, kawai a bani ɗa na na tafi" Ya zura mata ido, ya jinjina kai ya ce "Kin daina so na dai kenan ko?" "Eh" ta faɗa tana kawar da kanta gefe. "Shikenan, zan ƙara miki lokaci, zuwa lokacin da ki ka ga ya dace ki saurare ni, amma ki sani, ni shugaba ne, kuma wasu lokutan idan aka tashi kawo gyara, toshe kunne muke yi, mu farantawa wani mu ɓatawa wani, domin samar da gayar. Dan haka duk abin da ya kama zan banƙara na aikata, domin ganin ba ki suɓuce mini ba, ko da kuwa abin da zan aikata ɗin na nufin ƙara miki ƙiyayyata. Yanzu dai ga abinci ki samu ki ci, sai ki kwanta ki huta da wuri zamu tafi" Ta murguɗa baki ta sake kawar da kanta gefe. Duk wannan abubuwan da take yi masa, ko sau ɗaya bai ji haushinta ba, shi dai fatansa da roƙonsa ta saurare shi cikin nutsuwa, ya warware mata zare da abawa, saboda ya san ko shi ne haka ta faru a kansa, zai ce wulaƙanci ne aka yi masa. Ganin ya ƙi tashi ya bata guri, ya sanya ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya zuba mata ido, kamar zai lashe ta. Ta sake kai hannu ta ɗauki ɗankwalinta, amma ya jefa shi bayansa. Wannan kallon da yake ƙanƙance ido ya fara yi mata, ta ƙara tsuke fuska tana tattara nutsuwarta, amma ya kai hannunsa kan gashinta, ya fara shafawa a hankali. Bai sani ba ko dan ya saba ganin irin gashinsu Asal na buzaye nai laushi da santsi ya sanya na Nana yake burge shi. Baƙi ƙirin da shi natural, mai cika sosai da sosai. Ta hau ture hannunsa, amma yaƙi barin abin da yake yi, sai ma lumshe mata ido da ya hau yi. Duk wani abu da Nana za ta yi ta baƙanta masa rai, tana aikatawa domin gujewa barin nusarar zuciyarta ta sake yarda da shi, ta ba shi wata damar ya cutar da ita. Sai da ya bar ɗakin ta samu ta ci abinci, ta tura ƙofar ɗakin, sai dai babu mukulli yadda za ta datse ƙofar dan kar ya shigo mata. Tana kwanciya bacci, nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita. ***** Doctor Sharif ne ya tashi a razane, bayan mummunan mafarkin da ya yi da Shukura, ta biyo shi tana kuka jikinta duk jinin haihuwa, da wata sharɓeɓiyar wuƙa tana, ya ba ta jaririnta. Ya din ga gudu yana ihu, ya ɗan tsaya ya waiwaya kawai ya ganta a tsaye a kan matarsa, da wannan wuƙar a hannunta, tana kallon cikin tana kallonsa tana faɗin "Ka zo ka bani jaririna, ko na farka cikin matarka na ɗauke nata, ka ji abin da na ji" A daidai nan ya tashi cikin razani, ya haɗa uban gumi. Ya kalli agogon ɗakinsa ya ga ƙarfe biyu da kwata na dare, kawai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, so yake ya je ya ga halin da matarsa take ciki, amma ya tuna wa zai fita ya bar wa yaransa mata su biyu da suke bacci. Doctor Sharif bai samu haihuwa da wuri ba bayan ya yi aure, sai da suka shekara goma sannan ta haifi yara mata biyu, yanzu za ta yi na uku ciki yana ta wahalar da ita. Tun da ya haɗa kai da Alhaji Zailani ya ba shi jaririn Shukura abin yake damunsa, amma tun da Alhaji Zailani ya shaƙa masa kuɗi, sai ya manta sai kuma yau da ya yi wannan mummunan mafarkin. **** Yau ma Nana a kan gadon rannan ta hango Ƙaisar, lulluɓe da mayafi, hannunsa kawai ya ziro ta ƙasan mayafin yana rubutu a kan wani littafi. Ya ɗago kai ya kalle ta, ya ci gaba da rubutunsa. "Ƙaisar" "Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Wai dan Allah me ya same ka?" "A ina?" "Na ga yanzu kullum ka na kan gadon nan, kuma a lulluɓe. Giyaz ne ya yi maka wani abin ne?" Ya girgiza kai ya ce "A'a me ki ka gani?" "Na san shikaɗai ne yake iya cutar da kai" Ta yi maganar a sanyaye. "In ji wa? Akwai Aljanu masu ƙarfi da suka fi ni ƙarfi da za su iya cutar da ni. Kawai ni ba na shiga harkar kowa ne, ina gefe ina jin daɗin rayuwar kaɗaicina da litattafaina da haɗa magunguna na" Nana ta yi murmushi ta ce "Yaushe za ka yi aure ne kai?" "Sai na girma" "Au yanzu baka girma ba? Ina Haula ne?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Je ki ɗakin magungunana, akwai wata kwalba taswirarta kamar zanen Duniya, ki ɗaukko ki kawo mini" Nana ta ce "To" Ta nufi ɗakin da yake ajiye-ajiyen kayan maganinsa. Ta tsaya tana ta kallon kwalaben, da yadda wasu magungunan suke yawo a cikin kwalaben, tamkar abubuwa masu rai. Ta ga wanda ya ce ta ɗaukko ta waiwayo kawai ta ga Giyaz a tsaye a bayanta. "A'uzubikalimatillahi tammat" Ta furta cike da tsoro, a suffarsa ta tsoho tukuf ya bayyana a gabanta. Ya buɗe baki ya ce "Ban taɓa ganin halittar da na tsana a doron ƙasa ba sama da ke, sai na sabauta rayuwarki, sai na kashe ki na ƙarar da zuriyarku na huta da wannan bala'in. Ya ja da baya ya nuna ta da sandarsa, da take ci da wata irin wuta mai tartsatsi. Nana ta ja da baya, ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, tana jiran jin wutar ta fara ƙona ta, amma ta ji shiru. Ta buɗe idanunta a hankali ta ga Ƙaisar ya shiga tsakiyarsu, tartsatsin wutar ya ƙona shi, ya faɗi a gefe jikinsa yana hayaƙi. Nana ta saki kwalbar ta nufe shi da gudu. Cikin tashin hankali da tsoro ta ce "Ƙaisar, me ya same ka?" Sai a lokacin ta ga tarin raunukan da suke jikinsa, ga ƙonewar da ya yi yanzu. Giyaz ya ƙaraso kan Ƙaisar da sauri, ya saka hannunsa ya ɗago shi, amma ya ga jikinsa ya saki. "Wallahi muddin ɗa na ya mutu sai na kashe ki har lahira" Cikin dakiya da kawar da tsoro ta ce "Me ka yi masa? Kai wane irin azzalumar halitta ne wai, kowane abu yana alfahari da ɗansa da ƙoƙarin ba shi kariya, amma kai kullum cikin ƙoƙarin cutar da shi ka ke. Ƙaisar ka tashi dan Allah. Ta yi maganar cikin kuka tana ƙoƙarin taɓa shi, amma wani irin matsanancin sanyi ya ratsa ta. Ta buɗe idanunta a hankali cikin sheshsheƙar kuka, har da majina kawai ta ganta a jikin Sayyid ya riƙe ta gam yana kallonta cikin tausayawa. Ta yinƙura za ta tashi amma ya hana ta, ya ce "Ki bari ki ɗan nutsu. Me ya same shi ki ke wannan uban kukan haka? Idan komai ya lafa mini, dole na ɗauki mataki a kansa, dan ba zai yiwu ya din ga bibiyar matata ba, ina baƙin ciki da hakan" "Ba za ka yi masa komai ba, babu ruwanka da shi, tun da dai duk da tsana da abubuwan da nake yi masa, shi bai gudu ya bar ni ba, kamar yadda ka yi mini ba" Ya ɗan zura mata ido har zai yi magana sai kuma ya fasa. Ta zame daga jikinsa ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa da tashin hankali, tare da fatan Allah ya sanya ba wata mummunar illar Giyaz ya yi masa ba. Ya tashi ya bar mata ɗakin, dama kukanta da sheshsheƙarta ya jiyo, shi yasa ya fito ya je ɗakin nata. Washegari da safe, ya kawo mata kayan da za ta saka su tafi. Ya kalle ta cikin magiya ya ce "Ma vie, na san ni mai laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki tattara nutsuwarki guri guda, domin mu samu mafita. Duk abin da za su tambaye ki, ki sanar musu da komai, kar ki ɓoye musu komai saboda makomarmu" "Ni ba wata makomarmu, kawai ɗa na za a bani na tafi" Ya ce "To na ji, ga riga da za ki saka, ki je ki yi wanka ki shirya, ina jiran ki" Ta kalli rigar kamar ba zata karɓa ba, sai kuma ta karɓa ta ce "Na gode" Ya yi murmushi ya ce "Ko mu je ki yi wankan a ɗakina, akwai mayukan shafawa" "A'a ina da man da zan shafa" "To su ma nawan ne dai ki ke shafawa, saboda tsabar ƙauna" Ta murguɗa baki ta juya ta ajiye kayan, murmushi ya gaza barin fuskar sa. Ya ce "Kin san me na tuna? Lokacin da ki ke yi mini wanka mu na Nigeria, sauran ki yi mini wanka a Agadez". "Sai ka je gurin Gimbiya hamshaƙiya, farar fata da take biladama ta yi maka" Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba. Ko da ta yi yinƙurin juyowa, sai jikinsu ya haɗu, sam ba ta san ya ƙaraso bayanta ba, saboda cikin takunsa mai kama da hawainiya ya ƙaraso. Dan sam ba shi da hayaniya ko karakaina. Ya saka hannunsa ya zagaye ƙugunta, ƙirjinta ya tsananta bugawa tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarta. "Ma viee banda dalilin soyayyarki, ta sarƙe ni ta ko ina ta hana ni motsi, da sai na saka an sa bulala an zane mini ke. Imam Hammad ki ke yi wa magana a haka? Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina ɗaga mini murya" Ya yi maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai ta ta har su na jin numfashin juna. Yana murmushi ya ce "Na taɓa yi miki wannan kashedin, kin tuna?" Ya yi maganar yana kashe mata ido. "Dan haka ke za ki yi mini wanka a Agadez da ma" "Ni ka cika ni ba na son irin wannan abin" Ta yi maganar kamar numfashinta zai ɗauke. Ya cika ta ya bar ɗakin, ta zauna tana sauke numfashi. ***** "Jamila ki yi bayani, na kasa gane kan wannan ciwon naki, na fara jin tsoro ki gaya mini me yake faruwa?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai" "Wallahi sai kin gaya mini, damuwarki ta yi yawa, ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinyewa mene ne yake faruwa ki ke ɓoye mini" Mama ta yi maganar cikin tashin hankali tana zazzaro ido cikin fargabar abin da Jamilan za ta sanar da ita. Ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta ta ce "Dan Allah Mama ki yi haƙuri ki ƙyale ni, ni babu abin da yake damuna" "Wallahi Jamila sai kin gaya mini uban abin da yake damunki, mene ne yake damunki?" "Ni ma ban sani ba" Ta yi maganar tana kuka mai ƙona zuciya. "Wallahi kin sani sai kin gaya mini" Ta yi maganar tana ƙara zazzare wa Jamila ido. Kawai Jamila ta yi mata shiru, ta ci gaba da sheshsheƙar kuka. "Za ki gaya mini ko sai na shaƙe ki?" Jamila ta girgiza kai ta ce "Ciki ne da ni" Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Mama, ta ja da baya ta dafe ƙirjinta, tana wani irin haki, tare da kallon Jamila cike da tsoro. "Jaa..jam..jamilahh me ki ka ce? Ciki fa a ina? Kuma garin yaya?" Jamila ta ci gaba da sheshsheƙar kuka ba ta yi magana ba. Mama ta shaƙe Jamila ta ce "Ki gaya mini uban waye ya yi miki ciki kafin na take ki na kashe, da ki janyo mini abin kunya" "Ke Rabi, kina ina ne? Waye yake yi mini kuka, kuma maganar me na ji ana yi?" Muryar Baba ta katse ta. Da hanzari ta saki wuyan Jamila, ta ja da baya tana hararta cikin ƙunar rai. Ta yi ƙwafa ta fito daga ɗakin su Jamila. "Me yake faruwa ne?" "Babu komai, jikinta na shiga na duba" Baba ya ce "Kuma shi ne take ta kuka haka? Ni na gaji da larurar nan ta Jamila, wannan banke-banken hayaƙin da ki ke yi mata duk ba ne ba" Ta ce "To in sha Allah za mu je. Ka san mun je, mun kuma zuwa amma abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, amma za mu koma" ***** Nana ta tsaya tsuru da rigar nan a jikinta, ita kanta ta san ba dan albarkacin kaza ƙandagare kan sha ruwan kasko ba, ta san ba ta kai ta saka wannan rigar ba. Ta jikin mudubi ta hango shigowarsa, kayansa royal blue, kalar rigar jikinta. Ya ƙaraso gabanta, ya fesa mata turare, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro zobuna da abin hannu ya saka mata. Ta yi ƙuri da ido tana kallon hannun nata, rabon da ta sanya wani abu na ado, har ta manta. A tsorace ta ce "Ni dai zan cire wannan abin tsoro nake ji" Banza ya yi mata ya gyara zaman mayafin rigar a kanta. Ya din ga ƙare mata kallo yana mamakin yadda Asal take aibata Nana da muni, dan kawai baƙar fata ce. Idanunta manya sexy eyes, farare ƙal da su, gwanin ban sha'awa, ga shi rigar tamkar dan jikinta aka yi ta. Ya numfasa ya ce "Ina ƙara tuna miki, duk wani abu da za a tambaye ki, kar wanda ya baki tsoro, kar kuma ki rufa komai, muddin ki na son Muhsin ya dawo hannunki" "Meyasa kai ba za ka yi musu bayani ba kawai?" "Da bayanina ya wadatar, ba zan bari a zo wannan gaɓar ba". Ya ciro niƙab ya saka mata. Sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarta daga aljihun rigarsa. Nana ta waro ido ta ce "Wayata, ya aka yi ta zo hannunka? Dama kai ka ɗauka?" "Eh ni na ɗauka, kin ƙi saurarata, balle na yi miki bayanin komai, mu je" Ya yi maganar yana nuna mata hanya. Bakinta fal magana, amma ya yi mursisi, ya yi mata shiru. Ta tarar da takalma a falon gidan. Nana ta din ga ganin abin tamkar a mafarki. Su na zaune a baya ita da shi, ana jan su a motar. Ta yi shiru tana zabga addu'a Ubangiji Allah ya bata nasarar karɓar ɗanta, dan ko kaɗan ba ta sha'awar gidan nan, ɗan zamanta a gidan kawai ta fuskanci akwai kitimurmura a gidan. Tun da aka doshi gidan gaban Nana yake tsananta faɗuwa, haka kurum take jin ba ta ƙaunar gidan. Gefe guda kuma Nana tana ta tunanin halin da Ƙaisar yake ciki. Tun da aka yi parking suka fito, hadimai suke gaida Imam Hammad yana ɗaga musu hannu. Ya riƙe hannun Nana yana ratsa cikin gidan da ita. Gaba ɗaya aka zubo musu ido, ana son sanin wacece wannan ya riƙo hannunta, saboda kowa ya san ba Asal ba ce, saboda ba ta kai Asal tsawo ba, kuma Asal ba ma'abociyar niƙab ba ce, ko kanta ma ba ta damu da rufewa ba. Jikin Nana ya hau rawa, bayan da suka shiga ɗakin zama na musamman na cikin fadar Sultan. A can suka tarar da Sultan ɗin, ga Matawalle ga Sardauna, su na jiran isowarsu. Nana ta ja ta tsaya jikinta yana wata irin rawa, har ƙafafuwanta, gabanta ya din ga faɗuwa. Duk ta kowacwa kusurwar ɗakin, akaai na'urar sanyaya ɗaki, amma Nana ta kasa gane wane irin yanayi ma take ji. Ya kalli Nana ya ce "Ki nutsu mana, kar ki ji tsoro, dan Allah kar ki yi wani abu da zai rusa mana rayuwa, kar haushina da ki ke ji, ya sanya ki makance, ki yanke mana hukuncin da zai cutar da rayuwarmu" Nana dai ta gaza ko ƙwaƙƙwaran motsi. Ya ja hannun Nana, suka ƙarasa tsakiyar ɗakin suka zauna. Duk suka zubo musu ido. Sardauna ya yi wa Nana alama da ta cire niƙabinta. Ta saka hannu ta cire tana sunkuyar da kai. Abdou matawalle ya ce "Wannan kamar na taɓa ganinki ko?" Nana ta sunkuyar da kai. Sardauna ya dube ta ya ce "Ya sunanki?" "Nana Asma'u" Ta yi maganar kanta a sunkuye. "Daga ina ki ke?" Ta ce "Nigeria" "Kin san wannan?" Ya yi maganar yana nuna mata Imam,Nana ta ɗaga kai ta kalli Imam, ta kalli Sardauna, ta sunkuyar da kai. Matawalle ya ce "Ki yi magana mana, kin san shi?" AREWABOOKS Nana ta kalle shi, ya kalle ta, ya tsare ta da idanunsa, yana jiran ya ji me za ta ce. Abdou matawalle ya ce "Mu za ki kalla ki yi wa bayani. Ke ba ke muka gani cikin waɗanda suka kawo abinci ranar da aka yi taro ba?" Ta jinjina kai alamar eh. "To kin san shi ne dama?" Ya sake jefo mata tambayar. Ta jinjina kai. Sardauna ya ce "Ki buɗe baki ki yi magana mana, ki daina amsa mana da kai". "Eh na san shi" "Waye shi a gurinki?" Ta yi shiru tana nazarin amsar da za ta bayar, kar ta zama ta kwafsa su hana ta ɗan ta. Cike da karaya ya sake kallon Nana ya ce "Ma viee, talk ki yi magana mana" "Ni sai na ga Muhsin zan yi magana, dan Allah ka fara nuna mini ɗa na" Ya ce "To shikenan" Ya ce "Ina neman alfarma, zan saka a kawo mata Muhsin, za ta yi magana" Matawalle ya ce "Wane irin abu ne wannan? Ta san a gaban su wa take kuwa?" Sardaunan Agadez ya ce "Bari Matawalle, a saka a kawo shi, mu ji me za ta ce" Sardauna ya ciro wayarsa yana ɗan taɓawa, yana satar kallon Nana. Sultan kuwa rasa abin yi ya yi, ya tuna fuskarta a gurin taron cin abinci da aka yi, ya so ya bibiyi me ya kawo baƙuwa wannan gurin, amma abubuwa suka sha kansa. Wani irin gumi ne yake tsatstsafo masa bayan tuna irin taɓargazar da Hammad ya aikata, ka iya janyowa. Babban abin da ya ƙara sanya masa fargaba, shi ne abin da yake iya gani daga idanun Hammad a kan yarinyar. Ko a yanzu ya tattara hankalinsa a kanta, ta sunkuyar da kai sai zubar da hawaye take, da alama ma tamkar ya manta da zamansu a gurin. Wata hadima ce ta shigo, hannunta ɗauke da Muhsin. Yana ganin Nana, ya yi wani irin zillo daga jikin hadimar, yana wata irin ƙara yana cewa "Naaa" kamar yadda yake kiranta, Nene  kuma ya ce mata umma" Nana ta yi wata irin zabura ta nufe shi da gudu ta ɗauke shi, ta ƙanƙame shi a jikinta, tana zubar da hawaye cikin damuwa da kewar tilon ɗan nata. Shi na Muhsin ɗin, ƙanƙameta ya yi ya fashe da kuka. Jikin Sayyid ya yi sanyi sosai, ya din ga jin abin da ya aikata bai kyauta ba, kamar ya shiga hakkinsu da yawa, amma babu yadda ya iya ne, hakan ne kawai masalaha a garesu baki ɗaya. Sultan ya kalli Abdou matawalle suka haɗa ido, suka mayar kan Nana da ta durƙushe a gurin tana ta uban kuka. Matawalle ya yi gyaran murya ya ce "Wannan yaron wane ne shi a gurinki?" "Ɗa na ne" Ta faɗa cikin kuka. "Shi kuma wannan fa?" Ya nuna mata Hammad. "Mijina ne" Ta furta cikin sanyin jiki. "Waye baban yaron naki?" Ya sake tambayarta. Ta kalli Hammad ta ce "Shine" "Kin tabattar shi ne mahaifin yaron nan, kuma ke ki ka haifi yaron?" Ta jinjina kai ta ce "Na tabattar" "Ya aka yi ku ka haɗu ku ka yi aure?" Ta numfasa ta ce "A Nigeria muka haɗu, a can muka yi aure" "Waye shaidarki cewa mijinki ne shi?" Takaici ya fara kama Nana, wace shaida kuma bayan wannan ɗan wata shaida suke nema?. "Ni ba ni da wata shaida, Allah ne shaidata sai babana da ya ɗaura mana aure." Sardauna ya ce "Yaya aka yi mahaifin naki ya aura miki wanda bai san daga inda yake ba, ko ku ƙasarku ba ka bincike ku ke aure?" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ana yi, akwai 'yan uwansa da suke gadi tare, sun san aure muka yi, su Habu" Matawalle ya ce "Ban gane gadi ba, gadi kamar yaya?" Hammad ya ce "Ina neman alfarma dan Allah a tsagaita yi mata tambayoyin nan haka, duk a rikice take. Ga wannan wayar akwai video da hotuna a ciki, lokacin da muna rayuwa ne da ni da ita a Nigeria" Sulta ya ce "Hammad, ya zama dole ka yi mana shiru, a kammala binciken da yakamata, domin tabattar da gaskiyar lamarin nan" Sardauna ya sake kallon Nana ya ce "Ya aka yi ki ka zo gidan nan yin aiki?" Ta haɗiye yawu ta ce "Mu na Nigeria lokaci ɗaya na nemi 'yan uwansa na rasa, ya haɗu da larurar zuciya, ina tsaka da jinyarsa na neme shi na rasa. Kawai na yanke shawarar na zo Nijar ko zan haɗu da shi" Mamaki ya kama Hammad, yadda kai da fata taƙi bayanin ainihin ciwon da ya din ga yi bayan hawan jini. Matawalle ya ce "Ya aka yi da ku ka haɗu ba ki sanar da kowa mijinki ne ba? Kuma me yasa wacan karon da ya kira ki a nan, ki ka ce ba ki san shi ba? Anya akwai ƙamshin gaskiya a maganar nan?" Imam ya ce "Wancan karon laifina ne, kuma gaba ɗaya a ruɗe take" "Ba kai ake tambaya ba, ita muke tambaya" Matawalle ya katse Sayyid. Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ni ba na buƙatar na ci gaba da zama da shi, ku bani ɗa na kawai zan tafi na yi muku alƙawarin ba za ku sake ganina a inda yake ba" Suka yi tsit suna kallon Nana, daga bisani Sardauna ya ce "Haƙiƙa idan ta tabatta kin auri Imam Hammad, to kun tafka babban kuskure mussaman shi da ya san ƙa'ida da dokar masarauta. Sai dai uzuri ɗaya za a yi muku, shi ne shi ya haɗu da larura, ke kuma ba ki san wannan ƙa'idar ba. Babban mai laifi shi ne Mahmoudu kuma sai ya haɗu da tsatsauran hukunci. Babu buƙatar mu ci gaba da bincike da wani bin diddigi. Daga nan za a ɗauke ki a kai ki gidan baƙi na musamman, ki huta kwana biyu zamu haɗa miki sha tara ta arziki, za kuma mu sanya a mayar da ke har ƙasarku. Imam Hammad dole zamu san yadda zamu juya wannan lamarin, mu ɓoye gaskiyarsa, idan haryanzu da aurenka a kanta, zaka sauwwaƙe mata zamu karɓi ɗanmu a mayar da ita Nigeria" Wani irin mugun kallo Hammad ya yi wa Sardauna. Nana kuwa zabura ta yi tana ƙanƙame Muhsin ta ce "A'a Sayyid ne ɗanku, Muhsin kuma ɗa na ne, ba zan baku ɗa na ba, da shi zan tafi Nigeria" Matawalle ya ce "Ba zai yiwu ba, mu zamu karɓi Muhsin ki yi haƙuri. Abu ne da muka daɗe mu na nema daga Hammad. Ki yi haƙuri dole mu kare kimarsa da mutuncinsa a Agadez" Hammad ya miƙe a rikice, jin matakin da za a ɗauka, amma Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya. Da ido aka yi wa hadimar nan magana, ta nufi Nana gadan-gadan za ta ƙwace Muhsin. Nana ta ƙara ƙanƙame shi tana kuka cikin ɗaga murya ta ce "Ba zan baku ɗa na ba, ku ƙyale mini ɗa na, baku san baƙar azabar da na sha kan na haife shi ba. Zan bar muku naku ɗan har abada nima ku bar mini nawa" Matar ta fi ƙarfin Nana, Muhsin na zunduma ihu, Nana na kuka ta fizge shi. Nana ta bita da gudu tana janta "Ki bani ɗa na, wallahi ba zan bar muku shi ba. Ba za a kassara rayuwarsa kamar yadda aka kassara ta Sayyid ba". Wasu hadiman ne maza suka shigo, za su tasa Nana a gaba su fita da ita. Amma mugun kallon da Imam ya yi musu ya sanya suka tsaya. Ya ƙarasa inda Nana ta riƙe hadimar, ya saka hannu ya cire hannun Nana daga jikin hadimar da ta riƙe gam. "Ka ce su bani ɗa na, kuna ina lokacin da nake gantalin nemanka ba ni da ko muhallin zama da tsohon cikinsa? Ka damu da ɗan naka, ka tafi baka sake waiwayata ba? Ka bani ɗa na na tafi na barku" Idanunsa fal hawaye ya ce "Na sani, ki yi haƙuri Ma viee, ba a son raina ba komai ya faru ki yi haƙuri ki saurare ni" Sai dai tamkar yana ƙara ziga ta, ta ci gaba da cewa "Na yi dana sanin saninka a rayuwata, soyayya da tausayi ba su amfana wa rayuwata komai ba. Da na san abin da zan tarar kenan da na zauna inda Allah ya ajiye ni ban fito neman ka ba. A kan Muhsin zan iya karɓar Ƙaisar da abin da yake so na aikata sai dai masarautar taku ta tarwatse" muryarta tuni ta fara dashewa, saboda ɗaga murya da kukan da take yi mai tsuma zuciya. Matawalle ya ce "Imam wannan wace irin yarinya ce, mara ɗa'a da rashin tarbiyya? Kai ku fita da ita" "Kar wanda ya taɓa mini mata, zan fita da ita da kaina" Ya yi maganar yana ɗaga musu hannu alamar dakatarwa. Nana kuwa tuni ta silale jikinta ya saki, ya riƙe ta a jikinsa ba ta iya cewa uffan sai sauke numfashi da take yi kawai. Sultan ya yi shiru, yana ƙara jujjuya lamarin a cikin zuciyarsa. Imam da kansa ya saka Nana a cikin mota, ya babbake ya hana kowa ya taɓa ta. Ya rufe motar ya zagaya zai buɗe ɗaya ɓangaren ya shiga, amma wasu manyan hadimai suka tsare ƙofar. Ya kalle su ba tare da ya yi magana ba. Ɗayan ya ce "Tuba muke yi, umarni ne daga sama, cewar kar a kuskura a bari ka bar gidan nan" Cikin mamaki ya ce "Daga sama gurin wa?" "Daga sama gurina, kar wanda ya bar shi ya fita ko ina daga gidan nan, har sai mun bayar da umarnin hakan, ku kaita inda muka yi umarni, za mu sanya a mayar da ita Nigeria. Ina sake jaddada muku, kar wanda ya kuskura ya bar Imam Hammad ya fita daga gidan nan sai mun ba da damar hakan" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni, aka ji motar da Nana take ciki aka fita da ita daga gidan. Da ya san haka abubuwan nan za su kasance, da babu abin da zai hana ya ɗauki Nana da ɗansa ya bar musu ƙasar gaba ɗaya. Sai dai halin da Sultan zai shiga kawai yake tunani. Cike da baƙin ciki da takaici, ya koma ya iske Sultan, gabansa ya je ya tsaya cikin tashin hankali ya ce "Me yasa za ka yi haka? Idan ni ne a matsayin da take za ka so a yi mini haka? Ka kalli lamarin nan a matsayinka na uba, ba Sultan ba. Dokar masarauta  ba dokar addini ba ce ba. Me yasa 'yan majalissarka za su ziga ka ka yi haka? Babu wata hujja da ake buƙata domin tabattar da Asma'u matata ce, Mahmoudu su suka ɗaura mini aure. Shi ma kun ce a kulle shi ya yi laifi. Aure muka yi da Nana ga yarona ku na gani me yasa za a raba ta da ɗanta kuma a mayar da ita Nigeria haba Abie" "Hammad, ni ka zo gabana ka tsaya ka na gaya mini magana a haka saboda mace? Dole ne mu girmama tare da martaba al'adun masarautar nan, mu samu mu binne babban kuskuren da ku ka aikata ko dan tsira da mutuncinka. Hammad ya girgiza kai ya ce "Sultan, Asma'u ba mace ba ce kawai, ba zan binne laifukana saboda al'ada na je lahira ba ni da abin da zan gaya wa Allah ba. Zan ɗauki matata na bar ƙasar nan gaba ɗaya. Na bar muku sarautar da al'adar. Da na rayu babu su ma babu abin da ya same ni, ka gafarce ni" Mari Sultan ya kifa masa, ya janyo rigarsa yana kallon sa ya ce "Ko ka fara shan wani abu ne Hammad? Ni ka ke gaya wa ka bar mana sarautar za ka ɗauki wata bare ka bar ƙasar nan?" Jiki a sanyaye ya ce "Ba bare ba ce ba, matata ce kuma akwai ɗa a tsakaninmu. A halin yanzu a Duniya bayan kai ba na tunanin akwai wani wanda zai iya yi mini abun da ta yi mini. Gaskiyar da ba ka sona faɗa Abie ina tare da baƙin aljani, da yake burkita ni. Nana na iya ganinsa kuma itakaɗai take iya fahimtar halin da nake ci. Abie Nana ba mace ba ce kawai, waliyya ce a cikin mata, har shanyewar ɓarin jiki na yi, lokacin da ku ka gano su Mahmoudu aka ɗauke su, ba ta da wani mataimaki sai Allah kuma ba ta taɓa gajiya da ni ba. Asma'u har najasata ta wanke da hannunta. Da jikinta da lafiyarta da lokacikta da zuciyarta ta rayu da ni cikin kulawa da tausayawa. Idan na bari aka yi amfani da rashin gatanta saboda ni shafaffe da mai ne aka cutar da ita ban yi wa kaina adalci ba. Tsakanina da ita ba alaƙa ce gangar jiki ba kawai, akwai tasirin ruhika, da kuma tasirin alaƙar uba da ɗa. Wannan wani abu ne da ni da ita ne kawai muka sani. Abie ba za ku iya raba ni da Asma'u ba, idan ma ku ka raba mu, sai kun nemo ta da kanku" Ya ƙarasa maganar yana ja da baya ya fice ya bar ɗakin. Sultan ya dafe gaban goshinsa da yake yi masa wani irin raɗaɗi, ya nemi guri ya zauna. Duk yana jin maganganun Hammad a matsayin soki burutsun neman mafitar yadda zai samu ya zauna da Nana. Shi ma yana ganin ba a kyauta ba, a ƙwace mata yaro kuma a kore ta. Asal kuwa tana can ta gigice, bayan da ta samu labari cewar, an ga Hammad da wata mata ya riƙe hannunta sun shiga sashen Sultan. Ta rasa wa zata dosa domin ta ji gaskiyar lamarin. Tana cikin wannan gigitar, Tafawa ya kira ta, ta ɗaga jikinta yana ta tsuma. Ya ce "Asal, wace hadima ce a gidanki, ta kai abinci lokacin da su Asad suka zo?" Sai ta manta me ma ake nufi da hadima, sai da ya yi mata tsawa sannan ta farga ta ce "Wata hadima ce a gidan nan. Ce mini a ka yi an ga Imam Hammad da wata ya riƙo hannunta sun shiga sashen Sultan, ko ka na da labarin wace ce?" Ya ja tsaki ya ce "Sai me kuma? Ina tambayarki ki na tambayata wani abu daban." "Abbu dan Allah ka gaya mini idan ka san wani abu, ka ga ka ce mini ya ce yana da ɗa, a tsorace nake" Tafawa ya ce "Asal, kina nufin kina son Hammad ne?" Cikin kuka ta ce "Abbu mijina ne fa, ko ba na son sa ina duba makomata nima" Sai dai tana rufe bakinta, Hammad ya banko ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske. A razane ta saki wayar hannunta, ta waiwaya tana kallon sa. Da sauri ta tunkare shi tana faɗin "Hammad wace mata a ce an ganku kun shigo tare yau, har kana riƙe da hannunta kun shiga sashen Sultan? Kar dai maganar da aka gaya mini gaskiya ce?" Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan gadonsa ya faɗa kai. Ta nufe shi a hasale ta ce "Ka tashi ka yi mini bayani, wace matar a ganku tare? Kuma da gaske ka na da ɗa ko ba ka da shi? Yanzu da mutuncinka da kimarka ka zaɓi ka tozarta kanka ka kwanta da wata mace a waje dan ta haifa maka ɗa. Wallahi Hammad baka isa ba, ina yi maka rantsuwa da zatin Allah kowace matar ce sai na sanya an kashe ta, kuma an kashe mini banza dan duk cikin Agadez da kewayenta na san duk wata 'yar gata a bayana take. Ka tashi ka yi mini bayani" Wuyanta ya damƙa, jikinsa na wata irin tsuma, gani ta yi gaba ɗaya ya canza ya koma kamar wani horo, jikinsa ya koma jajawurr tamkar tumatir. Babu baƙar ƙwayar idanunsa sai farar nan tas, duk wata jijiya da taje jikinsa duk sun kumbura. ya faɗo daga kan gadon yana burgima, saboda yadda yake jin tamkar wuta na ci a ƙasan fatarsa. Tofa! Ayshercool 08081012143. Kar dai ku gaji da ni, ina yi muku tuni da cewar labarin Buzu ya shiga gasa a YouTube channel ɗin limamin tsakar gida, wanda da yawan likes na kashi goman farko za a yi amfani gurin alƙalanci. Ku taimaka ku je ku danna like a kashi goman farko na labarin BUZU na gode. 82 LITTAFIN KUƊI NE, KARKI RAINA GIRMAN HAKKI, 1K NE VIA 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Hankalin Sultan da muƙarrabansa ya dunguzuma nesa ba kusa ba. Suka gaza gane kan Imam Hammad ta ko ina. Ga Muhsin shi ma yana ta rikici, ba ya cin abinci sam, sai koke-koke ya ƙi saurar kowa saboda rashin sabo. Cikin tashin hankali Sultan yake kallon Hammad da yake wance kamar itace, ya dubi Matawalle ya ce "Anya Matawalle ba Asibiti zamu kai shi ba. Ina ga wannan ɓoye-ɓoyen da muke yi, lokaci ne ya yi da asirinmu zai tonu. Sai dai ina jin tsoron a san halin da muke ciki". Matawalle ya ce "Wannan ba abin da ya shafi Asibiti ba ne, ko ka manta haka ya yi ta yi a lokacin da aka dawo da shi daga Nigeria? Sai da muka fita faransa sannan ya daina wannan abin,har tunaninsa ya dawo?" Sultan ya ce "Haka ne, amma kamar wannan karon, abin ya ninka wancan da ya yi. Ba ya ci ba ya sha fa" Ya yi maganar cikin damuwa. Matawalle ya ce "Nima abin da ya tsorata ni gaskiya, amma dole mu nemo masu magani da za su duba shi. Amma ya zama dole mu samo waɗanda ba za su furta komai ba, idan ba haka ba nan ma akwai matsala" Sultan ya dafe kansa yana kallon Hammad, tamkar ya fashe da kuka. Asal ta shigo ɗakin da sallama, ta kalle su ta gaishe su cikin girmamawa suka amsa mata baki ɗaya. Cikin damuwa ta ce "Abie yau ma bai farka ba ko?" Sultan ya jinjina kai ya ce "Bai farka ba Asal" Daga nesa inda take tsaya take ɗan leƙa shi ta ce "Baccin dai yake yi?" Matawalle ya ce "Ƙaraso ki gan shi mana" Ta girgiza kai ta ce "A'a shaƙe ni yake yi ya kusa kashe ni, daga nan ma ina hango shi" Babu babban abin da yake sake ɗaga wa Sultan hankali, sama da wannan azababben zafin da jikinsa yake yi mai ban tsoro, kamar ba jikin ɗan Adam ba. Da yamma Sultan na cikin ɗakinsa, yana ta kai komo, ya rasa mene ne mafita, ya san muddin batun ciwon nan na Hammad ya fita, ba su da wata mafita. Aka sanar masa da isowar Imam Zahradeen. Ya bayar da iznin ya shiga. Bayan shigarsa suka gaisa. Ya dubi Sultan ya ce "Abie, wai ko ka aiki Imam Hammad wani gurin ne? Ya saka ni wani aiki, na je gidansa Gimbiya Asal ta ce "Baya nan, kuma a iya sanina ban san ya yi wata tafiya ba" Sultan ya ce "Haka ne, yana ƙarƙashin takunkumi na hana shi zuwa ko ina ne". Ya ce "Na sani, ina son ganinsa ne, a yi mini alfarmar nan, wani saƙo zan isar masa na aikin da ya sanya ni" Sultan ya dubi Zahradeen ya ce "Aikin me kenan?" Zahradeen ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Sultan ya ce "Shikenan na fahimta, amma a yanzu dai ka yi haƙuri ba zaka samu ganinsa ba, yana ƙarƙashin takunkumi " Imam Zahradeen ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Shikenan, godiya nake ranka ya daɗe" Daga haka ya tashi ya bar sashen. Ya san iya takunkumin hana fita aka ƙaƙaba masa, banda na killace shi a hana ganinsa gaba ɗaya, amma lokaci ɗaya an ce har ganinsa ma ba zai yiwu ba. ***** Nana ce zaune ta saka kwanon abinci a gaba ta yi shiru, Nene ta taɓa ta ta ce "Ki ci Abincin mana, kin bari yana ta shan iska" Nana ta numfasa ta ce "Nene wai zuwa yaushe zan je na karɓo ɗa na ne, ci gaba da zama fa bai kamace ni a garin nan ba, ni duk hankalina ya yi gida wallahi" "Nana na san duk abin da nake yi, ba na son ki faɗa komar mutanen nan, su ci moriyar ganga su yada kwaronta. Mutane ne masu bala'in son kansu fiye da yadda ki ke tunani, dan haka ki ɗan yi haƙuri. Sai dai Nene na rufe baki, wayarta ta fara ringing. Nene ta ɗauki wayar ta saka a kunnenta tare da yin sallama. "Barka da wannan lokaci Ummana" Ta amsa da "Barkanmu dai" "Umma dan Allah Nana tana tare da ke ne? Idan ke ki ka ɗauke ta ki taimaka ki sanar mini inda ki ka kaita, kan Imam Hammad ya farga ba ta nan, wallahi ban san me zan ce masa ba" Nene ta ce "Idan ya fargan me ya yi saura a tsakaninsu? Ba dai ɗanku ba ne kun ƙwace? Takardar sakinta kawai muke jira, zan mayar da ita Nigeria har gidansu" Mahmoudu ya ce "Ummana, wannan wani abu ne da ya shafi Nana da Imam da iyalinshi. Ni fa kamar ya san za a yi haka ya haɗa ni da Imam Zahradeen ya sanya aka killace ku a wannan gidan, kuma lokaci guda sai ki ɗauke ta ki tafi na neme ki na rasa. Dan girman Allah da buwayarsa ki taimaka ki gaya mini inda ku ke" "Kai ka kiyaye ni, ba zan faɗa ba ɗin, ba ku da wani haɗi da Nana, ka gaya wa ubangidanka ya aiko mini da takardar yarinyata, zan mayar da ita gaban iyayenta ta nemi gafararsu" Ta katse wayar. Nana ta ce "Nene to idan ya sake ni ba su bani Muhsin ɗin ba fa?" "Shi Muhsin ɗin da shi aka haife ki ne?" Idon Nana fal hawaye ta ce "Ni dai a bani ɗa na kan ya sake ni" Nene ta girgiza kai ta ce "Nana kina cikin jarrabawa, wannan ɗan shi zai sanya ki lalata komai ki kasa ƙwatarwa kanki 'yanci, ai sai ki yi" Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Amma Nene, ya aka yi aka saki Mahmoudu na ji sun ce wai sai sun hukunta shi, sun ɗora masa laifin aurenmu, sun sake shi kenan sun fasa hukunta shi?" Nene ta ce "Oho musu, su kashe shi ma kar su bar shi da rai." Nana ta waro ido ta ce "Nene wai ke ba kya son ɗan nan naki ne?" "To Nana idan ma ina son nasa, zan goya shi ne?" "To Nene dama mutum yana daina son ɗansa ne?" Nene kawai ta yi murmushi, ta tashi ta bar Nana da wasi-wasi. ***** Wasa-wasa aka shafe kwana uku curr ba a ga 'yar gidan Doctor Sharif ba, ga matarsa a Asibiti, hankalinsa ya tashi kamar zai haukace. Ga jikin matarsa kullum babu afuwa ga shi ta fara damuwa da ina Hafsa take. Sai dai ya ce mata tana gida ba ta da lafiya. Ya din ga yawo gurin 'yan sanda da gidajen radio, yana bayar da cigiya ko za a ganta. Ya din ga jin tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu. Gefe guda ga mummunan mafarkin da yake yi da Shukura babu ƙaƙƙautawa har fargabar kwanciya bacci yake yi. Saboda munanan mafarkai ne marasa daɗi. Ya shiga Asibiti ya tarar da wata katoɓara, an yi wa matarsa insulin allurar sauke sugar, fiye da kima suganta ya yi mummunan sauka, har ta shiga shock. Tare da sauran abokan aikinsa likitoci, suka yi ta fafutuka ƙoƙarin ganin sun ceto ranta. Yana tsaka da wannan tashin hankalin 'yan sanda suka kira shi, ya tafi cike da fatan 'yarsa Hafsa aka gani. Sai dai 'yan sanda suka ce masa Asibiti za su je ya ga wata yarinya da aka tsinta aka kaita domin a duba lafiyarta. Suka ɗauke shi a mota suka tafi. Sai dai suna zuwa aka tafi da shi ɗakin adana gawarwaki. Sam bai kawo komai a ransa ba, idonsa ya rufe kawai Hafsansa za a nuna masa. Sai dai aka fito da gawarwaki biyu. Ɗaya a kango a ka tsince ta, an fafe cikinta an kwashe wasu sassa na jikinta a can wata unguwa. Yarinyar sanye da Uniform ɗin makarantar da ya fasaltawa 'yan sanda. Tamkar ba Namiji ba, haka ya kurma uban ihu ya faɗi ƙasa sumamme, bayan ganin 'yarsa Hafsa a wannan mumman yanayi. Bangaren Sagir ma bai fitar da rai ba, yana ta addu'a, da ji a jikinsa Yusransa za ta dawo. Ga shi satin haihuwarta ya kama. Ya daure ya lallaɓa ya je duba Yusra. Wadda ita ma jiki yake a rikice. Sai dai da yaje ya tarar da jikinta da ɗan sauƙi, dan har suka ɗan fara hirar hankali. Ta ce "Haryanzu ba a ga matarka ba ko?" "Haryanzu Yusra, amma kina yi mata addu'a Allah ya bayyanata?" Ta ce "Ina yi mana, ina so Allah ya sanya a ganta, kuma fa a satin nan za ta haihu, dan ta ma fara naƙuda kaɗan-kaɗan" Ya ce "Yaya aka yi ki ka sani?" Ta ce "Mafarkinta na yi mana, tana kulle a wani ɗaki mai duhu, ta ce mini ba ta jin daɗin  zaman gurin, baka gani ba abin tausayi" Idonsa fal ƙwalla ya ce "Duk a mafarkin ki ka ga haka?" "Eh mana, tana ta kuka ma" Ya ce "Shikenan, ya isa haka. Ki ci gaba da yi mata addu'a bari na je gida. Amma yaushe za ki zo mu koma gida, ina fama da kaɗaici" Ta ce "Ko yau ka yi wa Anty magana sai na bika mu tafi" Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi" Shukura kuwa tana kwance a ƙasa, zama babu daɗi, kwanciya babu daɗi duk inda ta motsa cikin nan sai ya tokare ta. Ga ciwon baya da na ƙafafuwa da take yi da take kyautata zaton naƙuda ta fara a tsaitsaye. Sai dai tana yawan ganin Nana cikin mafarki, tana nanata mata ta yawaita addua babu ƙaƙƙautawa babu ji babu gani. Duk da tana yi ɗin amma ta ƙara ƙaimi gurin yi. ***** Ko da aka shiga kwana na biyar da shigar Hammad halin da yake ciki, Sultan ya gama tsurewa babban tashin hankalinsa rashin cin komai da ba ya yi ga abin kullum gaba yake yi. Tafawa ya samu Sultan a kan lallai a sake zaman majalissa, a ji bayanin Hammad a gaban kowa da kowa a kan yadda aka yi yake da ɗa kamar yadda ya faɗa." Matawalle ne ya amsa masa da cewar "A tunanina wannan maganar ai ta wuce ko?" "Ta wuce ta je ina? Kun san zata wuce ku ka dakatar da ni daga majalissa. Ya faɗi abin da dole sai ya fito ya kare maganar da ya yi. Ya ce yana da ɗa, ina ɗan yake? Kuma wacece uwar yaron? Idan kuma shaci faɗi ne to ta tabatta ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa da na faɗa ku ke ɓoyewa" Matawalle ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ka san abin da zaka din ga furtawa a kansa, ko babu alaƙar jini a tsakaninku shi shugaba ne." "Eh Hammad ɗa na ne, kuma shugaba ne, amma ba zai yiwu na zuba ido ina ganin ba daidai ba, a ce yana shugaba babu cikakkiyar lafiya ba kuma ku na dannewa ku ɓoyewa ba. Ita larura ai ba abin kunya ba ce, kuma abu ne da yakamata a sani domin a nemi lafiya" Cikin nutsuwa Sultan ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ban sna meyasa ka ke aibata shi da da wannan larurar ba" "Allah ya taimake ka, idan ba haka ba ne, mene ne gaskiyar batun ɗan da ya ce yana da shi?" Tafawa ya yi maganar yana tsare Sultan da ido. "Abu ne da muke kan bincike a kai, koma mene ne zaka ji daga baya" Ya ce "Shikenan na ji wannan, ina son zan yi magana da shi, magana ce a kan ɗiyata Asal" Sultan ya kalli Tafawa cike da takaici, ya san yana sane yake wannan bin ƙwaƙƙwafin da bin diddigin a kan lallai sai ya ga Hammad." Sultan ya ce "Za ka gan shi, amma nan da wani ɗan lokaci" Hakan ya sanya Tafawa sake tabattar da maganganun Asal. A ransa ya ce "Idan ka san wata baka san wata ba Jalaludeen" ***** Tun washegarin dawowar Nana daga gidan su Hammad, yanayin jikinta take jin babu daɗi, kamar akwai wani abu mara daɗi da yake faruwa. Sai dai ta danganta hakan da kewa da kuma tashin hankali da take ciki a kan Muhsin. Amma idan ta nutsu sai ta ji wannan damuwar daban ce, wannan a cikin jikinta da ruhinta take jin damuwar, sai dai ta yi iya ƙoƙarinta gurin danne damuwar, da duƙufa da addu'a Allah ya dawo mata da ɗanta. Yau da safe Nana ta fito ta tarar da Nana, ta ɗora tukkwane daban-daban har uku a kan murhu, tana ta harhaɗa wasu irin saiwoyi da sassaƙe-sassaƙe tana ta zubawa tana dafawa. Nana ta ce "Umman Muhsin, yau kuma baya aka tuna wa ake dafa wa magani" Nene ta yi murmushi ta ce "Ba kula ki zan yi ba ai ki ƙarata, daɗin abin ƙwaryar sama ce ke dukan ta ƙasa daga ni har ke" Nana ta yi dariya ta ce "Yasin ni ban bayar da magani ba" "A'a tuna dai, tuna dai yarinya" "To ai Sayyid kawai na yi wa" Nene ta ce "Kash, an zo gurin dan haka ki yi mini shiru" Ta ƙarasa maganar tana janyo wayarta da ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta tsuke fuska ta kira Mahmoudu a waya. Ya amsa tare da gaishe ta. Bayan ta amsa ta ce "Wannan uban kuɗin fa da ka sako mini?" "A'a ki yi haƙuri ai ba naki ba ne, na kula da Gimbiyar Imam ne" "Da can ku kuke bani abin kula da ita? Lokacin da take gararambar neman taimakon ba ku neme ta ba ba barin ta ku ka yi tana gantali a titi ba?" Ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ba zan iya gaya masa haka ba. Haryanzu fa ma ni ban sake ganinsa ba tun ranar da ya je tare da ita. Ba ya gidansa baya fitowa zaman majillisa, ko hawa ba ya fitowa. Duk da na san an saka masa takunkumi shige da fice amma an tsaurara masa sosai. Ki yi haƙuri har gida za mu zo ban haƙuri. Dan Allah ki taya mu rarrashinta dan ta ƙi saurararsa gaba ɗaya, kuma wallahi hankalinsa a tashe yake nesa ba kusa ba. Ga tarin magauta da yake da su a cikin gidan su ma da ba barinsa suka yi ba. Dan Allah ku yi haƙuri Umma ke kin san sha'anin gidan sarauta kin san komai" "Ni rabu da ni sai daɗin bakin tsiya, ai ko mutum zai danne ya yanka sai ka kare shi" Yayi dariya ya ce "Ai ɗanki ne, kin san ba zai aikata haka ba, tuba muke ranki ya daɗe. Wallahi ina ta faɗi tashin na gan shi ne ma, na san halin da yake ciki. Amma a ƙara ba wa Gimbiyar Imam haƙuri" "A'a babu ruwana, idan ku ka zo kwa bata da kanku" Suka yi sallama ta kashe wayar. Ta kalli Nana ta ce "Kafin ki yi wanka, fara ɗibar ruwan maganin nan, ki je ki yi wanka ki gama, sai ki yi wanka da shi. Ki fito ki sha wannan maganin sai ki karya. Nana ta ce "Shi kuma Nene na mene ne?" "Na tsarin jiki da kariya ne, saboda kariya ne" Ta yi maganar tana basarwa, tare da tsuke fuska dan kar Nana ta addabe ta da tambayoyi. Ganin hakan ya sanya Nana amsawa Nene, ba dan tana so ba. ***** Mahmoudu ne ya iske Sultan a gurin shan iskarsa da yamma. Kasancewar shi ma ba shi da iyaka a shiga da fita a gidan Sultan, saboda Hammad, dan haka ganinsa ba wahala yake yi masa ba. Sai dai yau kasancewar Sultan shikaɗai ne, ya fi sakin jiki da shi. "Barka da wannan yammaci Sultan" "Barkanmu dai Mahmoudu, kuna lafiya?" Ya amsa da "Alhamdillah. Alfarma nake nema daga gare ka Sultan" "Ina sauraren ka" "Dan Allah a yi mini izini na ga Imam Hammad ne. Sultan ya numfasa ya ce "Hammad babu lafiya. Ta so muje ka gani" Ya tashi cikin ladabi, ya bi bayan Sultan. Suka yi tafiya mai nisa a sashinsa, can cikin wani ɗaki suka je ya buɗe masa ɗakin. Cikin damuwa ya ce "Mahmoudu ya tabatta Hammad hauka yake yi, haukan ma irin wanda ban taɓa ganin kalarsa ba. Na ce ko a Nigeria da ku ka zauna ya yi irin wannan? Yanzu idan ka je kusa da shi zai iya shaƙe ka, tsawon wannan lokacin bai ci abinci ba, a haka kawai yake" Cikin tashin hankali ya ce "Yayi ciwo daban-daban, amma ban ga ya yi irin wannan ba, ina kyautata zaton mutum ɗaya ne ya san matsalolinsa ciki da waje, ya san bakin zaren wannan ciwon nasa" "Wane ne? Mahmoudu ba ma son asirinmu ya tonu fa" "Da asirinmu zai tonu da tuni ta tona, sai dai a zo da Mahaifiyar Muhsin" AREWABOOKS Cikin rashin fahimta Sultan ya ce "Ban gane me ka ke nufi ba?" Cikin girmamawa ya ce "Matarsa da ya zauna da ita a Nigeria, saboda ni kaina na fuskanci wasu abubuwa masu ban mamaki a tsakanin su, bayan sun yi aure." Ya yi maganar yana kallon inda Imam Hammad yake ta mimmiƙewa yana kakari, kamar ana yanka rago. Cikin damuwa ya ce "Yanzu tun wancan lokacin a haka yake?" Sultan ya jinjina masa kai ya ce "Ko ruwa bai sake sha ba, hankalina a tashe yake. Ga Tafawa ya sako ni gaba a kan Imam Hammad sosai da sosai; Yanzu dai mu je ka yi mini bayani gwari-gwari na fahimta" Bayan sun fito, suka zauna tare da Mahmoudu. Mahmoudu ya numfasa ya ce "Idan ban manta ba, bayan mun dawo daga bikin buɗe gidan cin abincin Imam na Maraɗi, mun dawo ka sanar masa da batun tafiya Damagaran ya wakilceka a taron sarakuna da za a yi a Zinder. Ba zan manta ba an kai ruwa rana sosai a kan tafiyar. A tsukin lokacin ya kan gaya mini cewa, shi gaba ɗaya ji yake yi baya ƙaunar zaman ƙasar nan, yana jin kamar a cikin wani bala'i da masifa yake. Da fari na zata da wasa yake yi, amma sai na fuskanci da gaske yake a lokacin. Na ce masa mu sanar maka ko ɗaga tafiyar za a yi, amma ya ce mini a'a kar na gaya wa kowa, baya son ya ɗaga wa kowa hankali. Tare muke kwana da shi a cikin gidan nan, muna shirin tafiya , kawai ya ce mini na same shi a ɗaya gidan nasa na kusa da gidan tarihi da yamma, mu yi tafiyar. Na ce masa mu tafi tare amma ya ce mini a'a. Haka kurum bayan tafiyarsa hankalina ya ƙi kwanciya. Kawai na kira shi na ce masa yana ina? Ya ce mini ya tafi zagaye can wajen gidan adana kayan tarihi na Agadez. Kawai na hau raƙumi na bi shi. Sai dai na je gidan adana kayan tarihi na tarar bayanan, aka kira ni da ɓoyayyiyar lamba, aka ce mini an san Imam Hammad nake nema, ya bi cikin sahara. Ba tunanin komai na kewaya bayan gidan inda Sahrar nan take. Na yi tafiya ta kai ta awa huɗu, saboda ina ganin sahun raƙumi a gurin. A tsakiyar sahara na ci karo da Imam Hammad cikin fita hayyaci a sume. Abin ya bani mamaki, na ciro shimfiɗa a jikin raƙumina, na yi na kwantar da shi na dudduba jikinsa na ga babu wata alama ta ciwo. Na jira ya farfaɗo ko na ɗauke shi mu koma gida. Cikin ikon Allah ya farfaɗo, na ce masa meyasa ya taho cikin sahara haka? Ko ba shi da lafiya ne?" Ya yi mini shiru. Na ba shi ruwa ya karɓa ya sha. Na ɗora shi a raƙumina ina mamakin yadda yanayinsa ya canza. Muka doshi dawowa, sai dai muna nufo Agadez ya din ga wani irin ihu, ya faɗi a cikin sahara daga kan raƙumin ya din ga burgima yana kururuwa. Na sauka na riƙe shi ina tambayar ko lafiya? Amma ba ya iya magana sai ihu kawai. Hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi da shi. Da mun nausa cikin sahara sosai sai ya yi shiru da mun nufo gida, sai ya rikice. Na rasa yadda zan yi ga yamma tana yi. Ba zai yiwu na ɗaukko shi na taho da shi yana wannan kururwar ba kowa yana ganinsa. Kawai aka kira ni da ɓoyayyiyar lambar nan aka ce, kar na dawo Niger da Imam, idan ba haka ba zai yi hauka tuburan ƙarshe ya rasa ransa gaba ɗaya. Na tambayi waye amma ba a bani amsa ba a ka kashe wayar. Na din ga mamakin waye wannan ya kira ni haka? Kasancewar na ga alamun gaskiya a abin da aka faɗa, da na juya da shi yake rikicewa, kawai sai na nufi Nigeria da shi cike da fargaba da zullumi. Akwai abokan hulaɗarmu na Nigeria, da muke kasuwancin asuwaki da dabino wanda da yawa ba su san waye ni ba, kuma ba su san Imam ba, kawai sai na neme su a waya. Aka ci gaba da kirana da wannan lambar ana gargaɗina kar na saka a masarauta a san da abin da ya samu Imam Hammad, saboda za a ce dole sai an dawo da shi, idan aka dawo da shi kuma zai rasa hankalinsa da rayuwar sa. Haka na ɓad da kamanni da ɓoye waye Imam, na shiga da shi Nigeria muka fara neman magani. Sai ya shafe sati bai yi magana ba, ya manta waye shi gaba ɗaya. Sai dai aka ɓoye lambar asusu, aka din ga turo mini kuɗi cikin asusuna, na ci gaba da harkar safarar dabino zuma da asuwaki tsakanin Nijar da Nigeria, ina tsoron taɓa kuɗin da ake turo mini saboda ban san na waye ba. Sai dai duk gurin masu magungunan da muka je, sai su ce mu yi haƙuri ba za su iya ba shi magani ba. Mun je gurin masu magunguna daban-daban amma bamu samu magani ba. Ya manta komai nasa da ya shafi Agadez. Na samu wani gida da abokan hulɗata suke gadi, muka shiga cikinsu. Zai yi wanka zai ci abinci zai yi salla, amma ba zai yi magana ba sai jefi-jefi. Idan kuma abin ya juyo ba ya ko cin abinci ba ya magana. Sai dai gaba ɗaya al'amuransa sun ƙara rikicewa, ya din ga abu kamar yana gane-gane. Kwatsam aka kawo mahaifiyar Muhsin, ita kuma za ta din ga aikin rainon yaro. Duk lokacin da ya ganta ya kan ƙure ta da idanunsa kamar yana ganin wani abu a tare da ita. Sai da na taɓa tambayarsa ko ya santa ya ce mini a'a amma tana da wani abu da yake nema domin ya tuna waye shi. Tsawon wannan lokacin ban taɓa gaya masa waye shi ba, saboda fatana ya tuna da kansa kuma kar na yi wani abu, da asirinmu zai tonu ko a cutar da shi. Kwatsam! Ban san abin da ya faru ba, muka tarar da ita a sume a cikin ɗakinmu, daga ita sai shi. Babu alamun ya yi mata wani abu na cutarwa, sai dai an ce abinci aka bata ta kawo mana ta suma a ɗakin. Mahafinta ya ce ba zai yadda ba ya ce sai ya aure ta. Ba zan ɓoye maka ba Sultan mahaifiyar Muhsin yar masu ƙaramin ƙarfi ce. Aka din ga dambarwa babanta ya ce sai dai Imama ya aure ta. Ina ta lallaɓawa ina bayar da haƙuri, amma ya ce na biya masa sadakin. Ba ni da ikon yin jayayya da shi, dole aka ɗaura musu auren. Sai dai mai kirna a wayar nan ya kira ni, ya sanar mini da ya san batun auren da aka yi wa Imam Hammad. Tun bayan aurensa da ita, ya fara samun sassauci, ya dawo yana magana, wasu daga halayensa suka canza. Yana kishinta fiye da kima, yana sakin jiki da ita ya yi hira da ita, ya yi wasa da ita abin da ba ya yi ma a rayuwarsa ta nan. Na sani akwai abin da ta din ga ɓoye mini game da zaman da take yi da shi, duk da nima ban bayyana mata waye shi ba. Amma na san ciwon nan yana motsa masa, duk da na yi mata bayanin ciwon nasa amma iya abin da na sani. Sai dai har aka je aka ɗauke mu daga Nigeria bata taɓa nuna mini yana yin wani abu na irin wannan rashin lafiyar ba. Dan haka ko dai tana da maganin ciwon sa, ko kuma rufa masa asiri ta yi." Sultan ya sauke wani irin nannauyan numfashi ya ce "Gaskiya na ji daɗi sosai da yadda ka rufa wasu abubuwan a gaban su Matawalle duk kusancina da su, akwai abin da ba zan so su sani ba. Amma ya aka yi ta san yana Agadez ta zo, nifa ina jin tsoron raɓa ɗa na da wanda zai cutar da shi" "Allah ya taimake ka, neman Imam ne ya sanya ta baro Nigeria babu wanda ya sani ta taho da tsohon ciki Nijar. A hannun mahaifiyata ta zauna. Duk da ba komai na sani ba, bayan na baro Nigeria, a bakinta za a ji komai. Amma Umma ta ce mini, ta gaya mata rashin lafiya ya yi sosai bayan an ɗauke mu daga Nigeria" Sultan ya jinjina kai ya ce "Kuma haryanzu baka san waye ya ɓoye lambar yake kiranka ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ban sani waye ba, lokacin da aka rufe ni an karɓi wayata, da aka dawo mini da ita ma, ba a sake kirana ba" Sultan ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Shikenan, amm zan yi magana da Matawalle, a je a taho da ita, idan ma an mayar da ita Nigeria ne, duk inda take a Nigeria a nemo ta. Amma ko waye yake kiran nan naka, yana da masaniya a kan abin da ya same shi. Amma shikenan" Mahmoudu ya ɗan yi Jimm, yana tsoron a gano Nene ta ɗauke ta, dan kuwa ba ya tunanin an sake waiwayar Nana tun da aka ce a je a killace ta, dan da tuni sun farga an baza nemanta, ko dan kar ta je ta faɗi cewa ita matar Hammad ce. Sultan ya sallame shi ya tashi ya tafi. Sultan ya dafe kansa ya yi shiru, saboda yadda al'amura suke ƙara rincaɓewa. Duk tarin yaransa babu wanda yake tausayi kamar Hammad. Kuma yana burin Hammad ɗin ya gaje shi, amma shi ne wanda jarrabawa kala-kala take bibiya. ***** "Nene, wai wannan naman da nake ta ci kashi-kashi na mene ne, ni gara ki bani hatsi kawai" Nene ta ce "To mijinki ne ya turo kuɗin ciyar da ke, kin ga kuwa dole na baki ingantaccen abinci." "Ni k ƙyale masa kuɗinsa, kawai lokaci nake jira idan ba ki yi wani abu ba, na je duk bala'in da za a yi, a yi a bani ɗa na, kan na basu mamaki wallahi. Dan ko zan mutu sai na raba su da shi" Nene ta ce "Ba ma za ki mutu ba. Za ki karɓi Muhsin, ki koma ɗakin mijinki Gimbiya, ina jinjina lamarin Ubangiji Nana, ashe duk wahalar da ki ka sha, duk zaman da muka yi Gimbiya ce ke Nana" Nana ta ɓata fuska ta ce "Dan Allah Nene ki daina, sai na ji wani banbarakwai, ni Sayyid nake so, ba Imam Hammad ba, ko kaɗan ba na sha'awar wannan gidan. Azabar tension ɗin da na sha a baya ma ta ishe ni, yanzu hutu nake buƙata" Nene kawai dariya tana girgiza kai, ta ce "Yaro man kaza, Nana na taɓa soyayyar nan fa nima, ba za ki yi mini wani alaye ba. Amma ni da ke mun sha banban. Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi ". Nana ta yi shiru, gaba ɗaya magungunan da Nene take bata, bata taɓa kawo na mene ne ba. Gaba ɗaya tana kwance ta kasa bacci, sai juye-juye take yi, a jikinta take jin yanayinta ya ƙara canzawa fiye da yadda take a baya. Dama lallaɓa rayuwarta take yi a hankali. Shiru ta yi tana tunanin ko wani hali Muhsin yake ciki?. Sai kuma ta tuna ta ji wayar da Nene ta yi da Mahmoudu a kan cewa, an sanya wa Hammad takunkumin fita. Ta tafi tunanin tun daga wane lokaci ya gane ta, amma ya share ya nuna kamar bai santa ba. Guntun tsaki ta ja, ta juya zata gyara kwanciyarta. Ta fara jin wannan ƙamshin na ɗakin nan da take ganinta tare da Sayyid yana ratsa hancinta. "Ina fatan ba da ni ake wannan tsakin ba?" Ba shiri ta buɗe idonta, kamar yadda ta yi tsammani a ɗakin ta gan su sai dai ya rame sosai da sosai. Tsiwa ta so yi masa, sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ce "Ba ka da lafiya ne?" "Lafiyata ƙalau, kewarki kawai nake yi, shi ya sanya rame" Ya tashi zaune ya matsa kusa da kta da ita ya rungumota jikinsa ya ce "Ma vie komai zai wuce in sha Allah, amma kar ki yanke hukuncin haƙura da ni, ba zan iya jurewa ba, ruhina da gangar jikina sun yi mugun sabo da ke, sabon da ba zan iya misalta miki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a kafaɗarta. Duk da wata zuciyar na azalzalarta da ta ture kan sa daga jikinta. Amma ya sake riƙo hannunta cikin sanyin jiki ya ce "Ki yi magana ko na ji daɗi mana" "Sayyid, ci gaba da rayuwa da kai ba zai haifar wa tawa rayuwar ɗa mai ido ba, zaren ba kalar yadin ba ne, kuma sama ta yi wa yaro nisa" "Ban ma gane me ki ke nufi ba, ni duk wata rayuwa da zan yi. Nutsuwata da kwanciyar hankalina na tattare da ke Ma vie" Ta yi masa shiru daga bisani ta ce "Ni fa gaskiya ka yi mini nauyi, ka ɗaga ni" Ya yi murmushi ya ce "Lokacin da ki ke so na, ba kya jin na yi miki nauyin, lallaɓa ni ki ke yi. Asmy" "Na'am" "Yanayin akwai zafi sosai, ina buƙatar sanyi" "Ko fifita ba zaka samu ba, balle wani sanyi" Sai dai tamkar a zahiri, haka ya ci gaba da lallaɓa Nana, da daɗaɗan kalaman da sai da ta manta da fushin da take yi, ta saki jikinta da shi. Babu tsammani Nana ta farka tana ta ajiyar zuciya. Ta tashi ta zauna ta jingina da bango. Jin yanayinta abin da ya faru ta yi tamkar a zahiri ba mafarki ba. Ta daɗe ba ta yi mafarki makamancin wannan ba. Tana son sanin ainihin abin da yake faruwa take ganinsu a wannan ɗakin. Mararta ta ƙulle ta kifa kanta a kan gwiwoyinta, ta tsorata da ramar da ta ga ya yi, jikinta ya ci gaba da bata yana cikin damuwa. Ga abubuwan da ta gani a cikin gidan game da shi. Ƙarshe dai kasa komawa bacci ta yi, ga tunanin Ƙaisar da shi ma ba ta san halin da yake ciki ba. Wayewar garin Allah, haka Nene ta sake zubowa Nana kajin nan da ɗuminsu sai ƙamshi suke yi. Nana tana ta lissafi da son yin gwajin ciki, domin tabattar da maganar Sayyid, dan sai da ta yi mafarkinsa jiya sannan ma ta tuna. Sai dai tana jin tsoro, ga shi tana jin Kunyar Nene balle ta gaya mata. Yaushe ma za ta fara bayanin ta na da ciki, cikin da ba ta san ya aka yi ya faru ba?. Tana cikin ɗaki tana cin naman nan, ta jiyo muryar Nene na waya. Mahmoudu ka kiyaye ni da batun Nanan nan fa" "Dan Allah Umma ki yi haƙuri, zamu shiga matsala sun farga Nana ba ta nan, yanzu haka nemanta ake yi" "Su neme ta, me ta yi musu?" "Babu abin da ta yi, Sultan ne yake son ganinta" "Sultan, ita ma za a yi mata abin da aka yi mini ɗin ne?" "A'a Umma dan Allah ki yi haƙuri dai, babu wanda ya san inda take. Ni na ce musu na san inda take, yanzu masalaha suke nema. Wallahi an kasa gane kansa gaba ɗaya. Yau kwana na tara kenan yana sume ko ruwa bai shiga cikinsa ba. Dan Allah ki gaya mini kuna ina?" Gaban Nana ya yi wata irin faɗuwa, ta miƙe tsaye tana sauraren me Nene za ta ce. "Zan neme ka zuwa anjima, sai na yi magana da ita, idan ta kama sai dai ku bi ta can Nigeria gurin iyayenta, ku roƙo alfarmarsu, ku ɗaukko ta" "Umma, Nigeria kuma ta koma? Shikenan mun kaɗe." Ta ce "Ka dai saurare ni na ce" Ta kashe wayar. Tana shiga ɗakin ta ga Nana a tsaye. Nene ta ce "Za ki je kenan?" Nana ta yi shiru tana kallon idon Nene. Nene ta yi murmushi ta ce "Ai ba zan hana ki ba. Ban sani ba ko daga nan ki karɓo takardar sakin naki. Ki haɗa abin da ki ke buƙata, zan kira shi na gaya masa su zo su ɗauke ki" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kina ganin idan na je, ban yi wauta ba ko kuma tarko suka yi mini ba?" Nene ta ce "Sam, ba na tunanin hakan, ba za a haɗa kai da Mahmoudu a yi miki haka ba. Ina yi miki fatan nasara." Nana ta ce "Nene mu tafi tare mana" Nene ta girgiza kai ta ce "A'a wace ni, ni da mijina bawa ne, ba sa ƙaunata ba sa son ganina. Ai ke ciwon ido ce, babu yadda suka iya da ke. Mussaman da yake Muhsin a tsakanin ku." Nene ta yi ba ta ƙwarin gwiwa, Nana kuwa addu'a take yi, da fatan Allah ya sanya ba Giyaz ne ya ci gaba da azabtar da shi ba. Bayan la'asar sai ga Mahmoudu a wata hamshaƙiyar mota zai ɗauki Nana. Nene ta yi masa kashedi sosai da sosai a kan ya ji tsoron Allah, kar a haɗa kai da shi, a cutar da Nana. Ya yi wa Nene alƙawarin hakan. Nana ta ɗauki kayanta Nene ta raka su har bakin ƙofa, tare da yi wa Nana fatan alkhairi. A motar Mahmoudu ya ci gaba da ba wa Nana haƙuri ya ce "Idan mun je, kar ki nuna musu fusata ko jin haushin sun ƙwace miki ɗa sun kore ki, bamu san abin da Allah zai yi ba idan mun je tare da ke. Wataƙila rashinki ne a kusa da shi da abin da aka yi miki ya sanya shi a wannan halin. Nana kwanan Hammad takwas ko ruwa bai shiga bakinsa ba, yana sume kawai. Ki yi haƙuri da abubuwan da suke faruwa mu je mu gani ko Allah zai sanya a dace." Nana ta jinjina masa kai, ƙasan zuciyarta tana addu'a. Ta wata hanya da bata taɓa sanin da ita ba, duk da gidan ba ƙaramin gida ba ne, suka bi. Ya yi parking gurin babu kowa an ƙawata shi da wasu irin dakakkun kujeru na gini da fulawoyi. Su na bin wata ƙofa suka shiga, sai ga su a sashen Sultan. Nana ta yi shiru ta ga yadda aka yi wa ƙasa ado da dukiya, kamar ba za a mutu a bar ta ba. Tsahirtawa ta yi da tunanin nata, bayan ganin mutanen da a yanzu ta tsani ganinsu, tun bayan yin ƙarfa-ƙarfar rabata da ɗanta. Sun kame a kan kujeru cikin manyan kayansu da rawani, sai dai sun sauke rawanin fuskarsu tana iya gane kowanne a cikin su. Tuna abin da Mahmoudu ya gaya mata, ya sanya ta daidaita nutsuwarta, ta tsuguna a gabansu ta ce "Ina wuninku" Suka yi shiru ba su amsa mata ba. Mahmoudu ya ce "Barka da yammaci za ki ce musu" Ta ce "Barkanku da yammaci, na same ku lafiya?" Matawalle ya ce "Alhamdillah, sai ki ka ji mun sake neman ki ko?" Ta ce "Eh, ina fatan ba wani laifin na sake yi ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ba ki yi laifi ba. Alfarma ma muke nema a gurinki" Ta risuna ta ce "To, Allah ya bani ikon yi" Ya ce "Kafin nan zan tambaye ki. Ke ce ki ka rayu da shi a Nigeria a matsayin matarsa bayan barinsa Agadez. Shin ko yana yin rashin lafiya mai kama da taɓin hankali, bayan larurar da ya yi na manta ko shi waye?" Nana ta ɗan ɗaga kai sannan ta mayar ta sunkuyar. Ta girgiza ta ce "A'a bai taɓa yi ba" Gaba ɗaya sai suka yi shiru su na kallon ta. Sardauna ya ce "Ki na nufin bai taɓa wani na larurar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa ba?" Nana ta ce "Eh sai matsalar zuciya da ya yi fama da ita" Sardauna ya ce "To idan haka ne, babu amfani kawo ta kenan, tun da babu wani haske da za ta iya bamu, ko wani abu da za ta iya yi" Nana ta risuna ta ce "Dan Allah ina son a bani dama, ko sau ɗaya na gan shi, dan Allah" Sardauna ya ce "A'a, babu buƙatar hakan" Sultan ya yi shiru yana nazarin fuskar Nana, daga bisani ya ce "Duk da haka, mu je ta gan shi, ko da wani abu da za ta iya yi a kai, ko abinci a samu ya ci" Matawalle ya ce "Gimbiya Asal ma ta gaza yin wani abu, balle ita?" Sultan ya miƙe sannan suka tashi. Su na gaba Nana da Mahmoudu su na baya. Ɗakin kansa an rage hasken fitilun cikinsa, hanyar da suka bi zuwa ɗakin ba zaka taɓa cewa akwai wani ɗaki a gurin ba. Daga nesa Nana ta hango shi, yana kwance a dunƙule guri ɗaya. Gashin kansa ya baje a ƙasa. Sardauna ya kunna fitilun ɗakin haske ya gauraye ɗakin. Ziiiiiiiiii ta fara jin wannan sautun, na turnuƙewar ƙurar sahara. Ta tattare nutsuwarta guri guda, ta din ga ambaton Allah. Kawai ta nufe shi. Sardauna zai yi magana Sultan ya hana shi, dan ba a yi wa Nana iznin zuwa inda yake ba. Ta durƙusa a kansa, ta ga an ɗaure masa hannayensa, jikinsa ya yi jawurr ga wannan hucin zafin da take iya ji, fiye da yadda sauran mutane idan sun raɓe shi suke ji. Ta hau kiciniyar kwance masa hannunsa. Wata irin miƙa ya yi tana gama kwance masa hannun. Ya miƙa hannunsa wuyanta, da wannan kalar idanun nasa mai ban tsoro. Cikin jarumta da dakiya, ta riƙe hannun nasa ta ce "Sayyid, nice. Ka saurari sautin muryar. Asmy ce ka ayyana addu'a a cikin ranka ko ba zaka iya furtawa ba." Bakinsa ne yake karkarwa yana son ya yi magana. Ta ce "Ka yi shiru, kar ka yi magana" Ya yi wani yinƙuri ya fizgota jikinsa da ƙarfi. Ayshercool 08081012143 84 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAN KI KARANTA. VIA 0069685771.AISHA ADAM STANBIC 08081012143 Gaba ɗaya suka yi cirko-cirko suna kallon ikon Allah. Tamkar matafiyin da ya shafe tsawon lokaci yana tafiya a sahara ba tare da ci ko sha ba, haka cacumar Nana da wani irin gigitaccen ƙarfi. Haka nan Nana ta ji jikinta babu ƙwari sosai. "Habu ku bamu guri" Nana ta furta cikin ƙarfin hali tana ƙoƙarin riƙe hannunsa. Mahmoudu ya ce "Amma kar ya shaƙe ki fa, ko ya yi miki illa" Ta ce "Ba zai yi mini ba, zai dawo daidai in sha Allah, idan ma ya shaƙenin zai dawo daidai in sha Allah, amma ku bani guri" Tamkar zai shige cikinta haka yake ƙoƙarin rungume ta. Gaba ɗaya Sultan ya ruɗe, Mahmoudu ya ce "Ranka ya daɗe, ta ce mu basu guri" Sardauna ya ce "Tayaya za mu tafi mu bar su, idan ta cutar da shi fa?" Mahmoudu ya ce "Ba za ta iya cutar da shi ba. Abin tsoron ma kar ya cutar da ita shi" Haka suka fita suka bar shi da Nana. Su na fita Nana ta sassauta murya ta ce "Sayyid, ka nutsu ka yi addu'a, kar ka yi ihu, ka yi addu'a ka ji" Sai dai sam yanayinsa bai nuna yana cikin hayyacinsa ba. Ta saka hannunta ta zuge rigarta ta cikin hijjabinta. Sai dai tana yi tana kokawa da shi. A hankali ta ba shi damar ƙanƙame ta kamar yadda yake ƙoƙarin yi. Wani irin nishi ya din ga saukewa mai sauti, jin sanyin jikin Nana. Sai dai sanyin bai kai wanda ya saba ji a jikinta ba. A hankali ya yi lamo a jikinta, da fari Nana ta fara ƙoƙarin karanta masa Alqur'ani, sai dai ta kasa jurewa ta fashe da kuka. Saboda wani irin gigitaccen zafi ne yake ratsa ta daga jikinsa kamar an kunna musu wuta. Ga shi yadda ya danne ta ba za ta iya matsawa ba, balle ta samu afuwa. "Ya hayyu ya ƙayyum Allah ka kawo mana ɗauki" Ta furta a lokacin da take jin yana ƙara matseta tamkar zai karya ƙasusuwanta. Sun ɗauki lokaci a haka, kafin ta ji jikinsa ya saki, ya sassauta riƙon da ya yi mata. Ta ture shi da kyar ta ɗaukko pillow ta tayar masa da kansa da shi. Sai dai idanunsa a lumshe kamar mai bacci, saɓanin da da idanun a buɗe tar sai dai babu ƙwayar idon sai farar. Ta koma gefe ta jingina da gadon da yake ɗakin, ko rigarta ba ta iya gyarawa ba, ta gyara hijjabinta ta jingina ta lumshe idanunta. Hawaye ne suka fara bin gefen idonta, wani irin azababben ciwo jikinta yake yi mata, kamar an yi mata dukan tsiya da kulki. Ga raɗaɗin da take ji a kan fatarta. A tsorace take waige-waige, ganin bugiren da Ƙaisar yake kwnaciya babu kowa. Ta duba gurin zamansa nan ma baya nan. Ta fita da sauri zuwa ɗakin magungunansa, nan ma baya nan ga inda Giyaz ya yi ɓarna ba a gyara ba, tabbacin bai da lafiya bai gyara ba. Ta din ga shiga tana fita a cikin Libraryn tana kiran sunansa amma ta ji shiru. Wata siririyar hanya ta bi, da haske ya ratso gurin. Ta bi hanyar sannu a hankali tana addu'a a cikin zuciyarta, da fatan Allah ya sanya ba wani abin ne ya samu Ƙaisar ɗin ba. Bayan Library ɗin ta ɓulla, ta hango shi a cikin tafkin da yake gurin a kwance, ya lumshe idonsa. Da sauri Nana ta ƙarasa tana faɗin "Ƙaisar, wannan ai sai ka tsorata ni, meyasa ka dawo nan ka kwanta, jikin ne dai?" Ya buɗe idanunsa ya kalle ta ya ce "A'a hutawa kawai nake yi" Nana ta samu guri ta zauna a gefe ta ce "A'a ai na san jikin ne, ba zaka faɗa mini ba ne" Ya ce "Ya jikin mijinki?" Ta ɗan yi shiru ta ce "Yana can Giyaz na ci gaba da azabtar da shi. Na rasa me ma zan yi gaba ɗaya, ni kaina a jikina nake jin na ƙone" Ƙaisar ya tashi zaune sosai a cikin ruwan ya ce "Ba Giyaz ba ne kawai, akwai tasirin asirin nan da ake yi masa da wuta. Sannan kuma ga Giyaz, shi Giyaz yana wasa da ƙwaƙwalwarsa ne, ya sanya ya tuna wannan ya manta wancan. Sai kuma ya kan shafe shi sai ya yi wannan suman. Amma wannan ƙonewar yana da alaƙa da wutar da ake hurawa wadda aka yi masa asirin da ita" Cikin damuwa Nana ta ce "To dan Allah waye ya yi masa asirin, kuma a ina aka yi masa?" Ya girgiza kai ya ce "Ki yi haƙuri, ba na shiga duk abin da bai shafe ni ba, saboda ni har kullum zaman lafiya nake fata. Sai dai na ga uwargijiyarki a dalilinki ta tuna gadon nasu gidan, da ke ki ka guji naki. Babu lallai sihiri ya yi tasiri mai ƙarfi a jikinki. Zai iya yiwuwa kina daf da inda aka yi masa sihirin. A wannan karon ne za ki yi faɗan ƙarshe, kar ki yi da wasa ki yi da gasken gaske. Ki buɗe idanunki, kibiyoyin da ki ka gani ana harbinsa da su mahaifinsa na karewa, yanzu ke za ki tare su. Ya fito daga cikin ruwan jikinsa yana ɗigar da ruwa, yana takawa da kyar, jikinsa duk wasu irin ramuka duk ya yi baƙi. Ya gyara zaman rigarsa ya rufe jikinsa sosai. Ya sake duban Nana ya ce "Kar ki yadda ki komawa iyayenki gida, babu wani kyakykywan sakamako. Za ki sake komawa farko dan sunanki zai ɓaci. Kar kuma ki yarda a raba ki da ɗanki, kar ki aminta da duk wani murmushi da za ki gani a fuskokin mutane, kuma kar ki sakankance da ƙiyayyar da za ki gani. Kowanne na iya taimaka miki ki samu haske. Kai da fata ki dage, duk rintsi kar ki kuskura a ci moriyar ganga a yada ke a gefe, saboda kin gama yi musu amfani. Ki kula sosai da sosai. Allah ya ba da sa'a" Cikin damuwa Matawalle ya ce "Shirun nan fa ya yi yawa. Anya ba za mu je mu sake dubawa ba" Sardauna ya ce "Abin da nake tunani kenan, kar abin da ba a so ya faru. Kai Mahmoudu tashi ka wuce gaba ka duba, idan lafiya mu shigo. Ni na kasa samun nutsuwa tun da na ji tana wai mu bata guri." Mahmoudu ne ya fara yin gaba, ya tura ƙofar ɗakin a hankali ya hango Nana a jingine shi kuma yana kwance a kusa da ita a kan fulo. Ya ƙarasa da sauri yana kiran sunan Nana, amma ba ta motsa ba, sai hawaye da yake ta fita daga idanunta da ta lumshe. Ƙarasowa suka yi su ma, suka rufu a kan Hammad. Sai suka ga jikinsa ya saki, idanunsa a rufe wannan jijiyoyin duk sun koma yadda suke. Sardauna ya ce "Ya aka yi ya koma daidai? Me ta yi masa?" Mahmoudu ya ce "Ban san me ta yi masa ba, Nana" Ya yi maganar yana kallonta. Sai dai shiru ba ta amsa ba. Sultan ya taɓa Hammd yana kiran sunansa, amma shi ma bai motsa ba. Kawai su ka ga Nana ta fara jijjiga, duk su ka ɗan ja da baya a tsorace su na kallonta. Mahmoudu ya rasa me zai yi. Sai bin su da kallo. A hankali kuma ta daina ta nemi guri ta kwanta a ƙasa. Matawalle ya ce "Wai ni na kasa fahimtar wannan abin, me ya same su haka?" Mahmoudu ya ce "Kamar akwai wani abu da bamu sani ba, ko za mu ɗan ƙara ba su lokaci?" Matawalle ya ce "Ni kaina duk ya kulle, ban taɓa ganin abu irin haka ba ai" Ƙarshe sai sake fita suka yi, suka bar Nana da Imam Hammad. Can jimawa Nana ta farka, ta yi miƙa tana salati, ta kalli agogon bangon dakin ta ga lokacin sallar magariba ya yi. Ɗakin ba kowa daga ita sai Sayyid da yake bacci. Ta yinƙura da kyar ta tashi tsaye, ta fara dudduba ɗakin, ta samo banɗak a cikin sa. Ta yo alwala ta ɗebo ruwan a wata container ta zo ta ajiye ta tayar da salla. Tana idarwa ta koma kansa, ta ɗauki ruwan da ta ɗebo a container ta yi shiru tana kallon ruwan, a hankali suratul Mulk ta zo kanta. Ta karanta Bismillah ta tofa, ta karanta suratul Mulk har ƙarshe. Wata addu'a ce da Malam Auwwal ya kan yi mata, musamman idan ba ta da lafiya ta faɗo mata, wanda tun da take bata taɓa kwatanta karanta ta ba, ba ma ta taɓa sanin ta iya ba sai yanzu da ta faɗo mata a ka. Da sauri ta yi Bismillah shashshafa masa ruwan da ta yi tofin. Ta dafa kansa ta fara karanto addu'ar "Bismillahi arƙik, min kulli shai'in yu'dika, wa min sharri kulli nafsin, au ainun hasid, Allahu yashfika, Bismillahi arƙik." Ta ɗan koma gefe ta yi shiru tana kallonsa, tana fatan Ubangiji Allah ya ba shi lafiya. Ta tattaɓa shi tana kiran sunansa a hankali "Sayyid ka na ji na?" A hankali ya motsa ya buɗe idanunsa da suka yi jaa ya kalle ta. Ƙara ware idon ya yi sosai domin ya tabattar ita ce ko kuma dai mafarki yake yi. Ya yinƙura gaba ɗaya zai tashi, ya ji wani irin jiri ya kama shi, ga cikinsa a ƙulle. "Alhamdillah" Ta furta tare da faɗin "Sannu yi a hankali" Ta sassauƙe fululluka, ta jingina su a jikin gadon, sannan ta ɗago shi da kyar, ya yinƙura ya zauna sosai ya jingina. Sai dai tamkar zai cinye ta, haka yake bin ta da kallo. Ya motsa baki yana son ya yi magana amma bakin ya din ga rawa. Ta girgiza masa kai ta ce "Kar ka yi magana". Ya yi shiru yana ci gaba da kallonta. Ta ce "Ka sanni ne?" Ya lumshe idanunsa ya buɗe. Ta yinƙura ta nufi wani jibgegen fridge da yake ɗakin, ta je ta buɗe. Ta ɗaukko ruwan roba ta zo ta zauna a kusa da shi. Ta cire masa rigarsa jikinsa. Ta ƙara shashasha masa ruwan nan. Ta lura da yadda jikinsa yake rawa, yake kallon ruwan hannunta da har raɓa yayi saboda sanyi. Ta kalli ruwan hannun nata ta kalle shi, kamar yadda ta gan shi a bacci, ya rame sosai fatarsa duk ta bushe saboda rashin ruwa. Leɓensa har tsagewa yayi. Ikon Allah ne kawai ya raya shi zuwa wannan lokaci ba ci ba sha. Ta ce "Buɗe bakinka" bakin yana rawa ya buɗe. Ta ɗaga jarkar za ta zuba masa ruwan su Matawalle suka sake shigowa. Sardauna ya ce "Ke, mene ne wannan za ki ba shi?" Nana ta ce "Ruwa ne, a fridge ɗin can na ɗaukko" Sultan kuwa sai da ya ɗan rikice ya ce "Matawalle ya tashi" Nana ta fara zuba masa ruwan a bakinsa, ya kai hannunsa biyu ya danƙe jarkar yana ɗaɗɗakar ruwan. Ƙoƙarin ƙwace ruwan Nana take yi, amma ya shanye. Yana shanyewa kuwa ya yi mata amai a jikinta har ta hancinsa haka ya din ga fitowa. Matawalle ya ce "To ko Asibiti za a tafi a kai shi?" Sultan ya ce "Ɗan jira mu gani" Yana gama aman ya kifa a kafaɗar Nana. A hankali ta ce "Ka gani, saboda kar ka yi amai ya sanya na so na baka a hankali. Sannu" Ya yi shiru yana ajiyar zuciya. Ta kalli Mahmoudu ta ce "Taimaka ka kuma ba ni wani ruwan" Da sauri Mahmoudu ya sake ɗaukko ruwa ya kawo mata. Ta ɗago shi ta ce "Yanzu a hankali za ka sha, kar ka kuma yin aman, za din ga zuba maka kana haɗiya" Haka aka yi, ta din ga zuba masa a hankali yana sha, yana yi yana ƙoƙarin kai hannu ya riƙe robar, tana riƙe hannunsa tamkar ƙaramin yaro. Nana tana son ta sake da shi, amma idonsu Sultan, ya sanya ta din ga komai a ɗarare gudun kar ta yi wani abu su yi mata wata fassarar ko sharrin. Ya jingina yana ta haki saboda duk ya galabaita. Mahmoudu ya ce "Kuma ke bai shaƙe kin ba da muka fita?" Nana ta yi murmushi ta ce "Ramin kura ai sai 'ya'yanta Habu. Ka samo mana ko kayan marmari ne da shayin Buzaye ya sha. Ai za ka sha ko?" Ta yi maganar tana kallonsa. Ya ci gaba da kallon ƙwayar idon Nana, maganganu ne fal a cikinsa, amma babu halin furta su" Su na ta jera masa sannu, amma babu wadda ya amsa a ciki. Matawalle ya ce "Bari na yi magana, a sanya hadimai su kawo kayan marmarin ya ci" Nana ta ce "A'a ranka ya daɗe, a saka Mahmoudu ya kawo" Duk suka tsaya suna kallon Nana, amma aka rasa mai magana. Nana ta nuna masa Sultan ta ce "Ka san wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Wannan fa? Ta nuna Mahmoudu nan ma ya jinjina kai. Ta ce "Ni fa?" Sai ya yi shiru, har ta fara karaya, da tunanin ko memory ɗin nasa ya sake ƙwacewa ya manta da ita. Kawai hawaye ya fara zirarowa daga idanunsa. AREWABOOKS Cikin damuwa Nana ta yi masa murmushi ta girgiza masa kai. Sultan ya ce "Hammad, me yake damun ka ne? Akwai wata matsala ne?" Ya yi shiru bai kula Sultan ba, Nana ta yinƙura ta ce "Bari na je na wanke aman da ya yi" Sardauna ya ce "Kar ki damu, za a kai ki inda za ki kwana, ba ma son kowa ya san kina nan. Za a baki wasu kayan ma sannan za a zo a gyara gurin. Kai kuma idan ka kawo Abincin sai a ba shi" Nana ta jinjina kai, ta yinƙura da niyyar ta tashi, amma ya damƙe hannunta cikin nasa gam. Ta dube shi ta ce "Mene ne?" Ya tsare ta da idanu. Ta ce "Kar ka damu, ba nisa zan yi ba, zan dawo in sha Allah" Ya damƙe hannunta ya ƙi saki, yana murzawa a hankali. Matawalle ya ce "Ka na ji Imam, zamu je a kai ta masauki ne, inda za ta zauna ta huta, kaima ka ci abinci kafin a san abin yi, an tafi samo mai magani da zai duba ka." Kamar sassaƙe, haka ya yi shiru ya riƙe hannun Nana. Sardauna ya ce "Ina ga mu bar ta tare da shi kawai, zuwa da safe sai mu san abin yi" Haka suka mimmiƙe, ƙiri-ƙiri suna ji suna gani, suka kama hanyar fita, su bar shi da Nana. Nana ta ce "Habu, dan Allah ɗan tsaya ka taimaka mini" Ya ce "To" Bayan fitar su Nana ta ce "Dan Allah ka kawo mini kayana, sannan ka kawo mini kayansa guda biyu. Ka kawo mini Alkur'ani. Sai kuma Abincin nan dan Allah duk yadda za a yi kai tsaye daga hannunka zai zo, kar ya biyo ta hannun kowa. Sai kuma ina son ka kawo mini habbatussauda da tazargade, da ganyen magarya sai almiski ja" Ya ce "In sha Allah ranki ya daɗe, yanzu kuwa. Sai dai su abin da ki ka lissafa ɗin nan, sai dai na shigo da su a ɓoye kar su ce wani abin za a yi masa" Nana ta ce "Idan da matsala ba sai ka kawo su ba, kawo mini Abincin da kayan kawai, kar na saka ka a cikin matsala. Amma lokacin da hakan tana faruwa da shi da muna Nigeria, idan na yi masa amfani da su yana samun sauƙi sosai" Mahmoudu ya ce "Kina nufin a Nigeria, yana irin haka?" Nana ta jinjina kai ta ce "Har ɓarin jikinsa sai da ya shanye, ka kawo mini Abincin da sauri na ba shi" Ya ce "To" Ya kalli Hammad ya ce "Sannu Imam, Ubangiji Allah ya sanya kaffara" Sai da Mahmoudu ya fita sannan ta kalle shi ta ce "Cika ni na je na wanke jikina, ka ga ka yi mini amai a jiki" A hankali ya saki hannunta, amma har ta shiga banɗakin nan kallonta yake yi. Ta wawwanke jikinta ta fito ta ƙara goge gurin da ya ɓata da aman. Matawalle ya ce "Anya abin nan ba shiri ne yaran nan suka yi ba, saboda ya ci gaba da zama da yarinyar nan ba?" Sardauna ya ce "Nima sai da na yi wannan tunanin" Sultan ya ce "Bana tunanin shiri ne, babu yadda za a yi ya kwana takwas babu ci babu sha, a kwance a guri ɗaya a ce shiri ne. Kai Matwalle ka manta abin da ya din ga yi, lokacin da aka gano shi a Nigeria aka dawo da shi. Ba magana ba cin abinci a sume kawai kuma aka rasa abin da yake damunsa sai da muka je faransa sannan ya dawo hayyacinsa?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin hana kansa, yi musu cikakken bayanin labarin da Mahmoudu ya ba shi, mussaman cewa da aka yi idan aka dawo da shi Nijar, zai iya haukacewa ko ma ya rasa ransa gaba ɗaya". Sardauna ya jinjina kai ya ce "To ai ita kanta yarinyar abar tsoro ce, ba ku ga abin da take yi ba? Ni abubuwan sun ɗaure mini kai sosai da sosai fa" Sultan ya ce "Tabbas lamarin akwai ɗaure kai, da ayar tambaya, dama Hammad ya gaya mini wani abu, amma dai bari mu ga abin da Allah zai yi, sannan mu jira zuwan mai maganin da aka tafi nema" ***** Mama ce take kallon Jamila cike da baƙin ciki da takaici. Kamar ta danne ta ta yanka ta ce "Jamila, so ki ke sai duniya ta san halin da muke ciki? Kin zaɓi mutuncinmu ya zube a rasa wanda zai aure ki saboda wannan abin kunyar. Tun kafin ya riƙa mu je a cire shi kin ƙi, Jamila kin fi son asirinmu ya tonu ko?" Ta yi maganar muryarta na rawa. Jamila ta girgiza kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Mama ba zan iya zubar da cikin nan ba wallahi, ni tsoro nake ji, kuma kar zunubin ya yi mini yawa ba ki san adadin tarin zunuban da suke kaina ba. Ki bari na ji da wasu dan Allah, ki ƙyale ni kawai" "Jamila ni ki ke cewa na ƙyale ki? Kin gwammaci ki durƙusa ki haife mana shege a gida, Duniya ta gani a shaida?" Mama "Na duniya daga baya ne, Allah ya riga ya shaida ya ga komai, ni yanzu addu'ata Ubangiji Allah ya yafe mini. Wataƙila haifar ɗan nan ne zai sanya na samu nutsuwa ni dai dan Allah ki ƙyale ni" Cikin takaici ta ce "Jamila kin san haihuwa kuwa? Kin san azabar haihuwar ɗan sunna balle shege, tsaf za ki mutuwa fa" Jamila ta goge hawayenta ta ce "Idan na mutu gurin haihuwa na yi shahada, wataƙila Allah ya yafe mini tarin kura-kuren da na aikata" Cikin tsawa ta ce "Uban waye ya ce miki mai cikin shege za ta yi shahada" Jamila ta ce "Mama ba ki san tarin zunuban da suke kaina ba, tuban da na yi sai Allah ya karɓi shahadata." Takaici ya sanya Mama fara rafka wa Jamila maficin hannunta ta ko ina. Jamila ta tashi da sauri, amma ta bi bayanta tana ci gaba da raɗa mata. Baba ya kawo kai cikin ɗaga murya ya ce "Rabi, wannan wane irin rashin imani ne haka? Yaya yarinya ba ta da cikakkiyar lafiya za ki biyo ta kina duka, me ta yi miki?" Mama ta tsaya tana mayar da numfashi cike da baƙin ciki da takaici. Suwaiba kuwa da take gefe, ta din ga tuntsura wata irin dariya mara daɗin ji, wadda ke bayyanar da rashin cikakken hankali ga mai yin ta. Mama ta rasa ihu za ta zunduma ta ji daɗi, ko kuma me yakamata yi ta ji sanyi. Hutu da fatan arzikin da take da shi a kan 'ya'yanta duk ba ta samu ba, ga mahaukaciya ga karuwa Nasiru shi ma ya fara 'yan ɗauke-ɗauke, dan sau biyu 'yan vigilant na kama shi, da laifin satar tukwanen mutane da kayan ƙarafa ya sayar da sunan gwangwan. Dan tun da Jamila ta cire tallafin da take ba su, ta daina zuwa gurin Hajiya Sa'a, suka koma ruwa. Baba ya ci gaba da yi mata faɗa a kan dukan da ta yi wa Jamila, ba tare da ya tsaya ya ji cikakken abin da Jamilar ta yi ba. Ji ta yi tamkar ta kama shi shima ta jibge shi, ko ta huce. Dan duk wannan masifar shi ne sila da ya tsaya ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da wataƙila ba su shiga wannan halin ba. Babban abin da ya ƙara ɓata mata rai, shi ne rashin zuwan Hajiya Sa'a ta duba Jamila, duk da taga kwana biyu ba ta zuwa maimakon ta neme su ta ji ko lafiya amma ba ta yi hakan ba. Ga Maman Khairat ta tashi daga unguwar da ta so zuwa a rakata gidan Hajiya Sa'a ta ji ko wani laifin Jamila ta yi wa Hajiya Sa'a haka?. Hajiya Sa'a kuwa tana can tana fama da kanta, dan tun mutuwar Abba ta shiga wani mawuyacin hali, duk lokacin da ta zauna babu abin da take yi sai tunanin ko yaya Abba ya ji da dodon ƙungiya ya zuƙi jininsa har ya mutu? Ta daina bibiyar duk wani abu da ya shafi kungiyar. Kasuwancin ma ta tattara ta ajiye a gefe ta koma guri ɗaya kawai. Daga kuka sai kwanciya da dana sani. Ga shi da ta fara tunanin wani irin mummunan ciwon kai yake yi mata dirar mikiya, har sai ta daina gani sosai. Wasu lokutan haka zata kulle kanta a ɗaki ta wuni, sai dai mai aikinta ta yi ta sabgoginta itakaɗai. Ta ce ko mutanenta sun zo, kar a bar kowa ya shiga inda take, kaɗaici kawai take so. **** Mahmoudu ya dawo, ya kai wa Nana shayi da kayan marmarin da ta ce . Sai kuma kayansu da Alƙur'ani. Ya haɗu da Sultan a hanyar da suke bi su shiga gurin. Domin wani sashi ne a can cikin sashensa da ba kowa ma ya san da shi ba. Hatta iyalansa sai da izninsa suke zuwa gurin. Wasu lokutan ya kan sanar da ya yi tafiya, ya tafi cikin gurin ya kulle kansa ya samu hutu da nutsuwa. Mahmoudu ya ƙarasa gabansa cikin girmamawa. Ya ce "Abincin ka kawo musu?" "Eh ranka ya daɗe" Sultan ya numfasa ya ce "Shikenan, amma ina fatan babu wata matsala barinsa tare da yarinyar nan, duk da na fuskanci tana da hankali akwai abubuwan da take ɓoyewa. Ni kaina ba komai nake son kowa ya sani ba" "In sha Allah Sultan, kare martaba, mutunci da kuma sirrikan Imam Hammad abu ne da ya zama wajibi a gare mu. Kuma tabbaci nake da shi ba yaƙini nake da shi, ba za ta taɓa aikata wani abu da zai cutar da shi ba" Ya jinjina kai ya ce "Na ga alamun haka, duk da na ga wasu abubuwa na ban mamaki a tattare da ita. Dama Hammad ya gaya mini sai mun neme ta, amma ban ɗauki zancen nasa da wani muhimmanci ba. Akwai wasu abubuwa da ya gaya mini da ban gama gane ma'anarsu ba, amma bari mu jira mu gani ya samu sauƙi" Mahmoudu ya risuna ya ce "Godiya muke ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana" Ya ɗaga wa Mahmoudu hannu. Nana na ganin Mahmoudu ta yi ajiyar zuciya, domin shi take ta jira ya kawo abin da za ta ba wa Hammad ya saka a cikinsa. Yana kwance a kan cinyarta tana shafa gashin kansa. Ya ajijiye mata kayan, Nana ta ce "Sannu da ƙoƙari, Ubangiji Allah ya biya ku da kai da mahaifiyarka, na fuskanci kirki da karamci a jininku yake, gado ka yi Nene akwai kirki" Ya ce "Allah ya taimake ki, ai kin ƙwace mini ita" Nana ita abin dariya yake bata, idan ta ji su na girmamata. Ta ce "Sayyid, ga abinci an kawo tashi ka ci" Mahmoudu ya taimaka mata, ta zaunar da shi. Ta zuba shayin a kofi, ta fara ba shi a hankali da cokali. Duk da wata irin yunwa da yake ji, tamkar ya haɗa da Nanan ya cinye, amma haka ya daure ya din ga karɓa a hankali. Ta ce wa Mahmoudu "Ka je ka samu ka huta, amma dan Allah ka zo da wuri, ka san ni da kai na saba, kuma kai kaɗai nake jin zan iya sakin jiki da kai. Sannan dan Allah abincinsa kar a bari ya biyo ta hannun kowa, ta gurinka kawai" Ya ce "In sha Allah, zan yi yadda ki ka ce, sai da safe" Sosai ya din ga cin kayan marmarin nan, yana sake shan shayin girfae da Habu ya kawo. Sai da Nana ta lura jikinsa ya daina rawa. Ya ɗan huta sannan ta tashi tsaye ta ce masa "Sayyid yinƙura a hankali ka tashi mu gani" Ya dafa gadon, ya tashi a hankali amma ya ji kamar kayan cikinsa zai zubo. Ta riƙe hannunsa yana durƙushe yana tafiya a hankali. Ƙofar banɗakin suka je, ta tsaya ta kalle shi ta ce "Mun yi wanka a Nigeria, yau za mu yi a Agadez ko?" Murmushi ya yi mata sai da haƙoransa suka bayyana. Suka shiga banɗakin. Sai dai wata irin kunyarsa da ba ta san daga ina ba, ta bujiro mata. Za ta iya cewa yau jiƙa-jiƙa kawai ta yi masa, saboda yadda ya ƙara yi mata kwarjini take ganin kamar wani aka canza mata. Babban abin da ya ƙara takura ta, shi ne kallon da yake ta bin ta da shi, kamar zai lashe ta. Da kanta ta yi masa brush, hakan ya din ga tuna mata da rayuwarsu ta Nigeria. Ta saka ya yi alwala, suka dawo ɗakin ta saka masa doguwar rigar jallabiya. Ta ce "To an ce kwananka takwas baka hayyacinka, yanzu zaka lissafa sallolin da suke kanka. Ka yi wanda zaka iya yanzu sauran sai ka ci gaba ko gobe in Allah ya kaimu ne" Ya jinjina kai, ya kalli gabas daga zauna ya tayar da salla, saboda ba zai iya tsayuwa ba. Nana ta din ga tunani ko ta roƙi alfarmar su nuna mata ɗanta ta gan shi, tun da nasu ɗan ya farfaɗo, amma wata zuciyar ta hana ta hakan, duk da tarin kewar Muhsin da take yi. Ta shiga banɗakin ita ma, ta yi wanka ta gama ta sako hijjabinta ta fito. Jakar kayanta ta buɗe, tana duddubawa, ta ga magungunan da Nene take bata na sha da wanka a ciki. Kawai ta yi murmushi ta shafa mayukanta, ta duba kaya masu sauƙin nauyi dan ta saka, dan duk da ba shi da lafiya ba za ta kwana shimfiɗa ɗaya da shi ba, da haryanzu ba ta san matsayinta ba, da matsayin kawo ta gurinsa ba, duk da da aka zo ita ta nema. Ga uwa uba rashin tabbacin da gaske tana da juna biyu ko kuwa?. Ta sakankance da salla yake yi, saboda a bayansa take zaune tana ƙoƙarin canza kaya. Kawai ta ji ya faɗo jikinta, suka faɗi ƙasa a gurin, hasken wutar ɗakin ya ɗauke baki ɗaya duhu ya mamaye ɗakin. Ayshercool 85 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA. VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC BANK 08081012143 Nana ta razana ta ce "Sayyid lafiya kuwa?" Ya rirriƙeta jikinsa na rawa. Nana ta yi shiru cike da damuwa, ga shi yanzu ta fara wahala da riƙon da yake yi mata, dan ya ninka wanda yake yi mata su na Nigeria. Haka ta haƙura ƙyale shi. Can bayan wani lokaci, hasken ɗakin ya dawo, a lokacin ya samu bacci, Nana ta yi shiru tana tunani daban-daban a kansa. Tabba! Tana da tarin tambayoyi da take buƙatar samun amsarsu, daga gare shi, dan akwai tarin abubuwan da suke faruwa, da suke ɗaure mata kai. Ta ture shi da kyar, ta tashi ta saka kayanta, ta kwanta a bayansa, tana jin yadda jikinta ya ƙara tsami da ciwo. Sai dai bayan bacci ya ɗauke ta, ta din ga munanan mafarkai marasa kyau da ban tsoro a cikin baccin. Abubuwan da ta din ga gani a gidan, sun tsorata ta. Har da yaƙe-yaƙen da aka din ga yi, kafin kafuwar masarautar, da irin azabar da bayi suka sha haka ta din ga gani. Ban da miyagun Aljanu masu ɗauke da siffofi daban-daban na ban tsoro a cikin baccin. Juyi ta din ga yi tana haɗa wani irin gumi, tana sauke numfashi saboda tsoro. Ga shi a baccin da fari a gefe take tana kallon abin da yake faruwa, kafin daga bisani ta ganta tsamo-tsamo a cikin rikicin da ake yi, daga bisani ma miyagun abubuwan suka din ga nufo ta. Cike da tashin hankali ta farka tana waige-waige. Amma ta yi ido huɗu da Hammad a zaune yana kallon ta, da alama ma sallolinsa ya yi. Mamaki ya kama ta, yaushe ya tashi har ya yi alawala ya zo yana rama sallolin. "Sannu ya jikin naka?" Ya jinjina kai yana kallonta. Ta sake cewa "Ka gama rama sallolin ne?" Ya girgiza mata kai, ta ce "To shikenan, bari na ƙara maka kayan marmarin, zuwa da safe sai ka fara gwada cin abinci" ya jinjina kai ta din ga ɓare masa ayaba yana ci, tana ba shi ruwa yana sha. Sai da ya yi mata nuni da ya ƙoshi. Ta tashi ta tafi banɗaki domin ta yi alwala ta ji mararta ta ƙulle. Ta tsuguna ta yi fitsari kawai ta ga fitsarin haɗe da jini. Ta shi ta yi cikin tsoro, ta gyara jikinta sai dai ta kasa gane jinin Al'ada ne, ko kuma na ɓari? Tun da dai ya ce mata tana da ciki. Ta kintsa jikinta ta fito, tun da ta fito idonsa a kanta, ta ƙaraso tana cewa "Sayyid, ka ce ina da ciki, yanzu kuma na ga jini ya zo mini, period ne ko ɓari?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido, cike da son tabbatar da abin da take zargi. Kawai ta ga yana murmushi. Cikin rashin fahimta ta ce "To ka yi mini bayani ko da hannu ne, zan gane. Dan Allah cikin ne da ni da gaske ɓari na yi? Ko kuma ba ni da komai dama?" Ya ci gaba da murmushi yana ƙanƙance idanunsa yana kallonta, kamar ba mara lafiya ba. Ji suka yi ana bubbuga ƙofa, ya tsuke fuska kamar ba shi ne yake murmushi ba. Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci. Mamaki ya kama Nana yadda ya iya zuwa da duku-dukun nan. Ya ƙaraso suka gaisa da Nana, ya kalli Hammad ya ce "Wai ya na ga daga jiya zuwa yau kamar ba kai ba. Ko dama rashin lafiyar ta ta ce?" Hammad ya ɗauki fulon hannunsa zai kai masa duka, amma ya kauce yana dariya. Sai mamaki ya kama Nana, dama yana wasa da Mahmoudu haka? Kodayake ko da suna Nigeria, su na hira amma ba sosai ba, a nan ma tun da ta fara ganinsu tare, duk maganar da zai yi masa cikin girmamawa yake yi masa. Amma kuma yanzu ta ga yana zolayarsa. Mahmoudu ya ce "Gimbiya ya jikin nasa, duk da daga haka ma Alhamdillah na ga alamun sauƙi a tattare da shi" Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Dan Allah ka daina ce mini gimbiyar nan." "Wallahi dole a ce da mijin Iya Baba Nana, babu wadda ta dace da wannan sunan a kaf Agadez idan ba ke ba. Ya jikin naka?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Imam Hammad. A sanyaye Nana ta ce "Ai maganar ba ta dawo ba tukuna sai a hankali" "Ikon Allah, kenan dai da gaske bayan tafiyata ya ci gaba da irin wannan ciwon, ni fa na zata tun da muka tafi bai sake yi ba. Amma Nana yaya abubuwa suka kasance ne bayan tafiyata, na san akwai tarin abubuwa marasa daɗi. Na san zuciyar musulunci ce ta sanya ki ke saurarenmu a yanzu ma, amma ki yi haƙuri. Har Nigeria aka je aka kama mu tare da su Sule. Sannan aka zo aka matsa ni da azabtarwa sai da na faɗi inda yake. Aka je gidan da ku ke gadi, ba kwa nan. Na raka su gidanku ina tsoron ya san yana da mata saboda gudun kar a cutar da ke. Ƙaninki ne ya gaya mini inda ku ke. Lokacin da aka je da ni shikaɗai muka tarar a gidan ba kya nan. Wallahi har aka ɗaukko shi sunanki kawai yake kira, yana ba zai tafi ya bar ki ba. Babu halin na faɗi cewa ya yi aure saboda na san hukuncin hakan a masarautar nan. Ga shi aka rufe ni a kurkuku da zargin ni ne na sace shi na kai shi Nigeria saboda ra'ayin kaina. Amma duk abubuwan da suka faru Nana ba su faru dan ni da Imam mu zalunce ki ba, dan Allah ki yi haƙuri" Tamkar ya sosowa Nana abin da yake yi mata ƙaiƙayi, da dannewa kawai take yi, ta fara hawaye. Ba Mahmoudu da ya ɗaukko maganar ba, shi kansa Imam Hammad sai ya rikice gaba ɗaya. Mahmoudu ya ce "Dan girman Allah ki yi haƙuri, da na san maganar nan, za ta ɓata miki rai da ban ɗaukko ta ba, ki yi haƙuri" Ta jinjina kai kawai, dan ita kanta ba ta san cikakken dalilin kukan ba, ta san dai tana buƙatar yin kukan ne ta samu afuwa a zuciyarta. Yau Sultan ne kaɗai ya zo duba Imam, sai dai ya ji daɗin yadda ya gan shi. Ya tarar har ya ci abinci ya yi wanka ya canza kaya, sai dai ba magana. Ya kalli Nana, ƙasan zuciyarsa yana yaba wa ƙoƙarinta da ƙarfin halinta. Ya ce "Kuma zai yi magana, na ga haryanzu bai ce komai ba" Nana ta sunkuyar da kai ta ce "Zai yi in sha Allah, sai dai wasu lokutan ya kan jima bai ce komai ba, kafin maganar ta dawo" Sultan ya jinjina kai cike da gamsuwa, ya ce "Muna godiya sosai da sosai. Ko akwai wani abu da ku ke buƙata?" Nana ta girgiza kai alamar a'a. "To shikenan, idan akwai wani abu, ki sanar da Mahmoudu ya gaya mini. An je za a taho da mai magani ya zo ya duba shi, idan kuma abin ba zai yiwu ba zamu kai shi Asibiti" Nana ta jinjina masa kai kawai. Inda Allah ya taimaki Nana, akwai pad a cikin kayanta, sai dai yanayin gurin babu gurin discarding pad ɗin. Cikin ikon Allah kuma ba ta zubar da jinin sosai. **** Sultan na zaune a sashensa, ya gama ganin wasu baƙinsa, aka yi wa Asal iso, ta shiga gurinsa. Bayan sun gaisa ta ce "Abie dama na zo ne ina son duba jikin Imam" Sultan ya gyara zamansa ya ce "Yarinyar kirki, Imam Hammad yana cikin yanayin da ba zai so a cika kawo masa ziyara ba. Dan haka mu na son ya samu hutu ne, kafin lokacin da za a samo mai maganin da zai duba shi" Cikin damuwa Asal ta ce "Ko sau ɗaya ne Sultan, jiya kwana na yi ina mafarkinsa, ina cikin damuwa ne" Ya ce "Na ga alamun hakan a tattare da ke, amma ki yi haƙuri ba za ki samu ganinsa ba, zuwa lokacin da zai samu afuwa sai ki gan shi har ma ku koma gida ma" Ba dan Asal ta so ba, haka ta haƙura ta tashi ta tafi. Tana kan hanya kiran Tafawa ya shigo wayarta. "Yaya ake ciki?" Ya tambayeta ba tare da amsa gaisuwar da ta yi masa ba. Ta ce "Yau ba a bani damar ganinsa ba, Sultan ya ce mini jikinsa ya yi zafi, dan haka ba zan samu ganinsa ba. Dole na jira zuwa lokacin da za a samo mai magani ya duba shi" "Ya dai tabatta haukan yake yi ko? Lokaci ya yi da zan bankaɗa abin nan, yadda Sultan zai kunyata daga shi har ɗan nasa" Asal ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ba hauka yake yi ba, rashin lafiya... "Ke yi mini shiru, abin da na yanke dole haka za a yi, kar ki sake ki sake yi mini musu" Ya katse ta yana yi mata tsawa da dole ta sanya ta yin shiru. ***** Alhaji Fatuhu ne ya kira wani abokinsa, ya ce ya zo ya kai shi gidan Yayarsa Hajiya Sa'a a motarsa, saboda yadda baya samun ta kwana biyu a waya. Ko da yaje gidan, mai aikinta ta sanar da shi cewa ta ce ko waye ya zo, kar a sake a dame ta. Ya kalli mai aikin ya ce "Ko wannan dokar za ta yi aiki a kan kowa, ba za ta yi a kaina ba, dan haka yi mini magana da ita" Mai aikin ta shiga ta fito, ta ce "Na yi mata magana ba ta kula ni ba" Ba shi da zaɓin da ya wuce ya shiga ɗakin nata da kansa. Ya tarar da ita a zaune, daga mutuwar Abba zuwa yanzu ta yi wani irin tsufa, jikinta duk ya saki. Fuskarta duk ta yi wani iri kamar ba ita ba. A hankali ya taka da sandarsa, sai ta ƙura masa ido tama fara tunanin a ina ma ta san shi? Gaba ɗaya sai kanta ya toshe ta kasa tuna waye shi. Sai da ya ce "Yaya Sa'a, lafiya kuwa?" Yana yin maganar, sai kuma ta tuna shi. Ta yi zuru tana tunanin ya aka yi ya samu lafiya haka har yake iya takawa? "Yaya Sa'a me yake damunki?" Ya yi maganar cikin damuwar halin da ya tarar da ita. Kawai ta fashe da kuka. Cikin damuwa ya ce "Haba ke kuwa, kamar ba musulma ba, yanzu da ke Allah ya jarabta da halin da nake ciki yaya za ki yi? Dan Allah ki yi haƙuri mu ci gaba da yi wa Abba addu'a, amma wannan hanyar da ki ka ɗaukko, ba mai ɓullewa ba ce ba" Ya yi ta rarrashinta da lafuzzan ƙwarin gwiwa. Ya sanya mai aikinta ta kawo Abinci, ya tabbatar ta ci sannan ya yi mata sallama ya tafi. Sai dai bayan tafiyarsa sai ta hau tunanin abin da ya faru gaske ne ya faru, ko kuwa dai mafarki ne. Gaba ɗaya. Haka ta zauna tana ta lissafin yanayin. ***** Bayan majalisar Sultan ta cika, domin ci gaba da gudanar da sha'anin mulki na Agadez. Akwai takardu da a kan turo domin gabatar da su a tattauna. Mai karanto takardun ya warwareta, ya zuba wa takardar ido sannan ya numfasa ya ce "Zuwa ga Sultan da 'yan Majalisar sa baki ɗaya. Sanin duk wanda ya kwana ya tashi a Agadez ne, babu wani abu da muke martabawa, bayan addininmu kamar al'adarmu. Mu na kira ga Sultan da 'yan majalissar sa, su gaggauta duba ga al'amarin Imam Hammad. Babu yadda za a yi ya ci gaba da jagorantar majalissar Imam, ba tare da zoben tambari ba, wanda kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kan inda zoben nasa yake. Sannan ya yi iƙirarin yana da ɗa, wanda haryanzu ba mu ji matsayar binciken da aka ce za a gudanar ba. A dan haka muke kira ga sauran 'yan uwanmu na majalissar Sultan, a gaggauta sanar da mutane sakamakon binciken da aka gudanar, sannan Imam Hammad ya fito gaban majalisar sarki, ya kare kansa, ko kuma ya sauka daga kan muƙaminsa na shugaban majalisar Imam, har zuwa lokacin da sakamakon binciken iƙirarin da ya yi na yana da ɗa zai fito. Idan kuma shaci faɗi ne abin da ya faɗa ta tabatta yana da matsalar ƙwaƙwalwa, kamar yadda jita-jita ta yi yawa. 86 A SAUKE HAKKI, A BIYA KUƊIN KARATU 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 08081012143 Gaba ɗaya tsit majalissar ta yi, aka rasa wanda zai sake cewa wani abu. Wani abu mai ɗaci ya tsirga wa Sultan a zuciyarsa, yana takaicin kasancewar Tafawa ɗan uwansa, yadda yake nuna son ganin bayan jininsa wato Hammad duk saboda mulki. Ya san ko ba a gaya masa ba, da saninsa aka rubuta wannan takardar aka kawo. Surutu 'yan majalissar suka fara yi ƙasa-ƙasa. Sardauna ya numfasa ya yi gyaran murya, duk aka yi shiru Sannan ya ce "Ina ga wannan maganar mun riga mun yi ta a baya. Ban ga amfanin sake dawo da ita ba, mu na nan ana kan bincike a kan al'amuran kuma za a zo da sakamakon binciken, sake dawo da maganar ba abu ne da zai taimake mu ba, duba da yadda muke da tarin abubu a gabamu, da yakamata a ce an mayar da hankali a kai" Ɗaya daga cikin mutanen majalisar ya ce "A'a Sardauna, ba na tunanin wannan ba maganar da za a tattauna ba ce ba. Kar ka manta goben Agadez ta ta'alaƙƙa da waɗannan Imam da aka naɗa, su ma suke jagorantar wasu al'amuran na sha'anin sarauta, muddin aka ce da tangarɗa kuma ba a ɗauki wani mataki ba, to yana nufin goben ƙasar nan yana cikin hakin da ba a sani ba" Matawalle ya ce "Turaki ai dama sanin gobe sai Allah. Mu muna bulayinmu ne kawai. Amma kamar yadda mai girma Sardauna ya ce, a jira sakamakon binciken ya fito tukuna. Sannan wani batun taɓin hankali da ake danganta Imam Hammad da shi, batu ne mara tushe balle makama, sannan duk wanda muka samu da yaɗa wannan zancen, za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansa." Haka aka so tayar da hatsaniya, sai da Sultan ya tsawatar, haka aka watse daga zaman babu wata ƙwaƙwƙwarar magana. Sultan ya san tabbas tun da  Tafawa ya samu magoya baya a Majalisa, al'amura za su sake dagulewa ne, kuma za su ci gaba da bibiya su ji ƙwal uwar daka. ***** Shukura ce a kwance a ƙasa, sai burgima take yi, wani irin matsanancin ciwo yana ratsa ta. Sai jujjuya kanta take yi a galabaice. Kamar kullum mai ba ta abinci ya buɗe ƙofar ya ziro abincin ya ajiye mata ya tafi. Sai dai a duk lokacin da aka kawo mata abincin, idan aka rufe ɗakin duhu ne yake gauraye ko ina, amma sai ga yau da sauran haske. Ta ɗaga kanta a mugun galabaice ta kalli ƙofar ta ga kamar ƙofar ce ba ta rufu ba. Ta lumshe idanunta cike da azabar ciwo, wata zuciyar na azalzalarta ta je ta buɗe ƙofar ko a buɗe take, wata zuciyar kuma ta ce mata wahalar ciwo ne kawai amma ƙofar a rufe take. Ta ji ciwon na ƙara tsananta, yayin da wani abu mai ɗumi da ba za ta iya tantance ko na mene ne ba, yake bin ƙafarta. Ta din ga jan jikinta a hankali, ta lalubi bango ta dafa, a durƙushe ta ƙarasa gaban ƙofar ta saka hannu ta ja, kawai ta ga ƙofar ta buɗe. Ta zura kanta ta lelleƙa ta ga babu kowa a harabar gurin, daji ne sosai aka yi ɗakin a cikinsa. Tana faɗin "La'ila ha illa Anta Subhanaka Inni Kuntu mina Zalumin" Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta tana takawa a hankali. Ko da ta duba jikinta sai ta ga alamun faya ce ta fashe, ga ruwanan mai haɗe da jini a jikin ƙafafuwanta da rigarta. Ba ta damu da yadda take gani dishi-dishi ba, saboda azabar galabaitar da ta yi, da kuma haske da ya cika mata ido, kawai ta saɓi hanyar da ba ta san ina ne ba, ta hau tafiya. Duk da duk taku ji take yi tamkar ɗan cikinta zai faɗo saboda nauyin cikin da azabar ciwo. Tafe take tana addu'a Allah ya kuɓutar da ita. Alhaji Fatuhu kuwa bayan komawarsa gida su na hira da Fadila ya ce "Fadila yakamata ku je ku duba Yaya Sa'a, saboda tana jin jiki nesa ba kusa ba, duk ta rame ta fita daga hayyacinta. Ta bani tausayi sosai da sosai haryanzu tana jin raɗaɗin mutuwar nan" Fadila ta ce "Allah sarki, har na tuna lokacin da na rasa Muhsin ɗina, da ta ce ba ni da tawakalli kamar a kaina a ka fara haihuwa, Allah sarki yanzu ta ji abin da na ji" Ya tsuke fuska ya ce "A taƙaice dai, gaya mini magana ki ke yi" Ta girgiza kai ta ce "Wace ni? Ai ban isa ba, kawai dai na tuna abin ne, kuma ya daɗe yana yi mini zafi" "To koma dai mene ne yanzu ya wuce, zan gaya wa Suwaiba, yakamata ku shirya ku je ku duba ta, a yi mata sannu, idan babu hali ma ina ga gara ta dawo gidan nan da zama, wataƙila kai komonmu zai rage mata damuwa da kaɗaici" Cikin sanyin ta ce "Ka manta ne? Ka manta mu ma a under notice muke, daga yanzu ko wani lokaci an ce mu fita mu bar gidan nan?" Ya yi shiru ya tafi zancen zuci. Ta ce "Dan Allah kar ka ɗaga hankalinka, mun samu Allah ya sanya ka farfaɗo da kyar. Ni da Maman su Janna za ta yarda da ɗan abin hannuna da nata, mu samu ko karamin gida ne a saya, ni ba na son hayar nan ko ɗaki uku ne mu koma" Ya waro ido ya ce "Ɗaki kuma? Ina ɗaki uku zai ishe mu rayuwa? Ko sashenki ɗakuna huɗu ne da falo biyu, ya yi mana kaɗan" Fadila ta ce "Daddy ka manta wacece Fadilan taka ne? Sai dai ku ya yi muku wahalar rayuwa ai ni na riga na saba, gidanmu ma na da daka auro ni ai ɗaki biyu ne ni da Umma" Ya ce "Ki daina tuna abin da ya wuce mana, ni ba ga shi kin zamo mana alkhairi ba. Da na tsaya duba wani shrime da ƙyale-ƙyale da daga ke har Suwaiba ba na tunanin za ku kasance da ni, duk da halin da muka tsinci kanmu. Ina ƙara yi muku godiya sosai da sosai" Fadila ta ce "Haba Daddy, ka cancanci fiye da haka daga gare mu, lokacin da ka ke da wadata ba mu ba, na kusa da mu ma ka yi musu, ka gatantamu ka kula da mu, sai Allah ya kawo mana jarrabawa kuma mu juya maka baya, da Allah bai barmu ba kuwa" Ya ce "Ke dai a yi sha'ani masoyiyya, idan Allah yana ƙaunar bawa, idan ya jarrabe shi ta nan, sai ya sassauta masa ta can, da yawa idan larura ta same su, iyalan nasu barin su suke yi. Kin san wani abu kuwa?" Ta ce "A'a sai ka faɗa Angona" Ya tuntsure da dariya ya ce "Ango ko?" Ta ɗaga masa gira tana murmushi. Ya ɗan ja kumatunta yana murmushi. Ya ce "Wannan rahar ma da nake yi da ke, ba tare da kin sauya mini ba saboda ba ni da lafiya, kuma ba ni da abin hannun yanzu ba, wallahi ba ƙaramin daɗi nake ji ba. Haƙiƙa larurar nan ta ƙara mini tsoron Allah da imani, ya ƙara kusantar da ni da Ubangijina, a duk lokacin da na motsa ambaton Allah kawai nake yi, gani nake rayuwata ce ta zo ƙarshe. Saɓanin lokacin da nake da dukiya da lafiya, ina ambaton Allah amma ba can sosai ba, ba kamar yadda na ƙara samun kusanci da Ubangiji ba lokacin da na rasa komai. Kuma a jikina nake jin wani tagomashin alkhairi yana kusanto mu in sha Allah" Ta ce "Haka ake so Daddy, ina fatan kuma ka canza tunaninka a kan magungunan gargajiya da na addini yanzu" Ya yi dariya ya ce "Na canza tuni, ke dai madalla da ke matar aljanna" Suka ci gaba da hira cike da nishaɗi. ***** Kwanakin Nana uku tare da Hammad, jikinsa ya yi ƙalau abin sa, sai dai magana ce babu. Nana ta yi iya ƙoƙarinta gurin tana kauce wa duk wani abu da zai sanya faruwar wata mu'amala tsakaninsu. A ƙasa suke kwana, ba ta taɓa kwanciya sai ya yi bacci, sai dai wasu lokutan ta ji ya ƙanƙameta idan ciwon ya motsa Sai dai tun da ya warware sosai, take ganin kamar ya canza mata, wani irin kwarjini yake yi mata yanzu, mussaman idan ya saka ta a gaba da kallo duk sai ta rikice. Ta kasa gane take-taken sa. Sai dai ta riƙi karatun Alkur'ani sosai da sosai. Sai dai tun wannan ganin na ƙarshe da ta yi wa Ƙaisar, ba ta sake ganinsa ba, ko a farke ko a cikin bacci ba. Duk ta damu shi ma ta na son sanin halin da yake ciki. Ga shi gaba ɗaya ta rikice, a kwana ɗayan da ta ga jinin nan, ba ta iya tantance wane jinin ta yi ba. Ɓari ko na haila. Tuni aka ƙara ƙawata ɗakin da kayan alatu, da kayan wanka da shafe-shafe na Imam Hammad, da duk wani abu da za su buƙata. Yana banɗaki yana wanka, ta gama cika cikinta da kayan marmari, dan ba ta fiye cin abincin da Mahmoudu yake kawowa ba, fruit take samu ta ci ta ƙoshi ta ci nama. Sai da ta fara tsorata kanta da tunanin anya ba cikin ne da gaske ba. Ta yi zurfi sosai da sosai a cikin tunani. Razana ta yi jin yadda ba ta ji alamun fitowarsa daga banɗakin ba, sai ji ta yi ya zagaya hannayensa a cikinta. Duk da ɗakin ƙato ne sosai da sosai amma duk ƙanƙantar motsi tana iya jinsa, amma sam ba ta ji motsinsa ba. Tsigar jikinta ta hau tashi, ta ji jikinta ya fara tsuma, tana neman ta rasa nutsuwarta. Ya ɗan yi murmushi ya cika ta, ya nuna mata gadon da yake ɗakin, alamar ta hau ta kwanta. Amma ta yi mursisi ta ƙame a gurin. Ya kama hannunta zai ja ta, amma ta ƙwace hannunta ta ja ta tsaya. Sai ya rabu da ita, yaje ya haye gadon ya kwanta. Ta tsaya a gurin tana rarraba ido, sai da ta ga ya jima da hawa gadon, ta lallaɓa ta ɗauki fulo ta ajiye a ƙasa ta kwanta. Kwanciyarta ke da wuya, ta fara jin sukuwar wasu halittu da ba ta san ko na mene ne ba, a cikin ɗakin. Hayaniyar  halittum ya ci gaba da yin amsa kuwwa a cikin kunnuwanta tamkar a filin yaƙi. Wani mutum ta gani ya shigo ta wata ƙofa, ba a iya tantance jinsinsa, ya rufe ko ina na jikinsa, yana shigowa ya nufi gadon da Sayyid yake kwance, ya ajiye wannan takardar, ya nufi wata ƙofa. Da azama Nana ta bi bayansa duk da yadda yake wani irin gudu kamar iska na kaɗa shi. Sai dai wannan sautin ƙarar ya hana ta ci gaba da bin sa. Rungume ta ya yi a jikinsa, jikinta na ta rawa, duk ta toshe kunnenta da hannayenta biyu. Saboda yadda take jin hayaniyar kamar zata tarwatsa mata kai. Ta ɗaga kai ta kalli Sayyid, ta kalli ƙofar ta ce "Akwai wani abu a nan?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya yi gaba, ya buɗe ƙofar. Ya riƙo hannunta suka ratsa hanyar da take baƙiƙirin mai ɗauke da duhu, kai ba ka ce a cikin wannan katafaren ɗakin mai ɗauke da hasken fitilu hanyar take ba. Babu tsammanni ta ga sun ɓullo wani guri kamar corridor. Shimfaɗaɗɗen yashin sahara ne a gurin, gurin ya bayar da wani ni'imtaccen sanyi, ga tsilla-tsillar bishiyu da suke a bushe a gurin hasken farin wata ya haske saharar. Ta waiwaya ɗaya gefen, ta hango wani irin gini, mai kama da tsaunin dutse, hasken wuta na ci na tashi ta wata kafa mai kama da taga a jikin ginin Dutsen. Bakinta na rawa ta kalle shi ta ce "Sayyid na san gurin nan, tun kafin na sanka nake mafarkin saharar nan, har na zo na sanka, ina mafarkinka a cikin saharar nan. Kuma a nan nake yawan ganin ka tare da Giyaz. A waccan bishiyar ku ke zama da su Habu ku sha shayi da wasu mutane ma da ban san su ba. Ina ne nan, kuma meyasa abubuwan da nake gani a bacci suke dawo mini a zahiri, haryanzu ina da ayoyin tambaya da dama a kanka" "Yanzu kin yarda da nake gaya miki ruhinmu a haɗe yake? Ɗaya ba zai iya rayuwa babu ɗaya ba" "Ba wannan nake son ji ba, haryanzu akwai wasu abubuwa ɓoyayyu da ban gama fahimta game da kai ba" "Komai zai warware a hankali, za ki fuskanci komai rayuwata, amma ba na nufin cutar da ke ta kowace fuska, amma sannu a hankali za ki fahimci abin da ki ke kokwanto a kai." Ta buɗe idanunta tana ƙarasa jin sautin muryarsa a cikin kunnuwanta. A kan gadon ta gansu tare, fuskarsa na kallon ta ta, yana ta yi mata numfashi a fuska a hankali, wanda hakan ya ƙara dagula mata lissafi dan kuwa ita ta san a zahiri abin ya faru, amma ya rikiɗe ya juye ya koma kamar mafarki. Ga shi yanzu Ƙaisar ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba, balle ta ce ko shi ne yake wujijjigata, hakan ya ƙara hargitsa mata tunaninta. Ta  tsura masa ido, kamar a fuskarsa za ta gano gaskiyar abin da take fata. "Meyafaru?" Sautin muryarsa ya doki dodon kunnuwanta. Ba ta ce masa komai ba, ta zame jikinta ta juya masa baya, tana ta tufka da warwara a zuciyarta. Sake matsawa ya yi kusa da ita, sai dai wannan karon bai yi magana ba, sai dai jin manufarsa, ya sanya ta zabura da sauri tana ƙanƙame jikinta. AREWABOOKS Ƙanƙance idanun ya yi, kasancewar fitilar ɗakin a kunne take, ya din ga bin Nana da kallo, yadda ta tsuke fuska ta sanya hannayenta tana kare jikinta. "Nana" Ya kira sunanta kamar yadda ake kiranta. Sai ta ji wani iri gaba ɗaya babu daɗi, ta kalle shi a tsorace. "Me yasa?" Ya furta a hankali. Ba ta ce komai ba ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin matsawa kaɗan. "Matata ce fa ke? Da gaske kin daina so na ko?" Ta ce "Ko ina sonka, ba zai yi mini wani amfani ba. Kuma a da ne nake da cikakken 'yanci a matsayin matarka, a Duniyar da nikaɗai ka ke kallo. Wannan duniyar kuma ka yi mini nisa, a yanzu ma na san da na gama amfani za a sallame ni, sake yadda da kai shi ne ganganci mafi muni da zan sake aikatawa" Ya ɗan fesar da wata iska daga bakinsa ya ce "Ki yi mini alfarma ki bani dama, na san tun da ki ka yadda ki ka sake dawowa kina so na, idan ba kya so na ba za ki yarda ki sake zuwa inda nake ba." Ya riƙo hannunta yana murzawa a hankali ya ce "Ba kya yi mini kwatankwacin son da nake yi miki. Kar ki hukunata ni da abubuwan da ki ke gani a zahiri kawai" A ɗan ƙufule ta ce "Ka ke son dai wadda ka ke so, ga matar so can kana da ita, wadda al'adarku ta amince ka so ka zauna da ita. Ai ni ina ga sai dai a saka ni a cikin bayi saboda baƙi da muni" Ta ƙarasa maganar tana tashi zaune. Shi ma tashi zaunen ya yi ya ce "A'a ai ni ban faɗi haka ba, ina da farar amma, nake ta bin ki ina lallaɓa ki. Dan Allah ni dai ki yi haƙuri, daga ni har ke mun yi kawar juna, wallahi ba ƙaramin kawaici nake yi ba kasancewata da ke a guri ɗaya" Baki buɗe take bin sa da kallon mamaki da rashin sanin abin yi. Cike da son tura masa takaici ta ce "Idan ba ka ce ba, amma ai a gabanka ta bautar da ni, ta wulaƙanta ni. Ba ƙaramin tozarta na yi ba da abubuwan da matarka ta yi mini ba. Ka je gurin halattacciyar matarka, da ahalinka suka san da zamanta, ba ni matar ɓoye ba" Ya ce "Haka ki ka ce?" "Eh" ta furta cikin tsiwa. Ya zuba mata ido yana kallonta, shi wani irin kyau mata ƙara masa, zuciyarsa har wani harbawa take yi da sauri kasancewarta a kusa da shi. Shi kansa ba zai iya cewa ga adadin abin da yake ji a kanta ba. A ransa ya ce "Ba komai ki yi yadda ki ke so, kin cancanta" A zahiri kuma sai ya sauka daga kan gadon, ya nufi hanyar fita. A ɗan ruɗe ta sauka daga kan gadon ita ma tana faɗin "Ina zaka je?" Bai yi magana ba ya ci gaba da tafiya, bayansa ta biyo da sauri tana faɗin "Sayyid ba ka da cikakkiyar lafiya fa, ina za ka je?" Ya rufa ta a cikin ɗakin, ya tafi. Ta jijjiga ƙofar amma ta ji ƙofar a rufe. Ta koma ta nemi guri ta zauna jikinta a sanyaye tana tunanin, kar wani abin ya same shi. ***** Tun da ɗan da ke cikin Shukura ya faɗo Duniya, ta fara ganin duhu, saboda wani irin bleeding da ta din ga yi. Matar da ta kawo ta Asibiti, gaba ɗaya a ruɗe take, saboda tun da ta haɗu da ita ba ta yi magana ba. Ga shi ta kawo ta Asibiti har ta haihu ba ta yi magana ba. Likitan ya ba ta shawarar ta kira jami'an tsaro ta sanar musu, saboda kar a je wani abu ya faru da ita. ***** Doctor Sharif kuwa tun da ya farfaɗo ya tashi da shanyewar ɓarin jiki, saboda tashin hankalin yadda ya ci karo da gawar 'yarsa cike da tozarci. Duk da maganarsa ba ta fita sosai, amma ƙoƙari yake yi ya tambayi ina matarsa, ya jikinta. Amma aka ce masa tana samun sauƙi, sai dai abin da bai sani ba shi ne, bayan tafiyarsa gurin 'yan sanda Allah ya yi mata cikawa. ***** Matawalle ne tare da Sultan suke tattaunawa, fuskar Sultan fal damuwa yake faɗin "Na rasa abin da na yi wa Tafawa a rayuwa, da yake nuna wa jinina wannan ƙiyayyar haka, abin da ba zan taɓa yi masa ba" Matawalle ya ce "Ai dama ba halinku ɗaya ba sam, ka kwantar da hankalinka mu bi a sannu, in sha Allah zamu samo mafita. Amma kwana biyu yaya ka ke ganin jikin Imam ɗin?" Ya ce "Jikinsa da sauƙi, ana samun ci gaba, sai dai ba ya magana sam. Jiya da yau nima ban shiga ba, ba na son yawan zarya da nake yi musu, kamar yarinyar a tsorace take da mu. Amma na yi mamakin yadda ta iya sarrafa shi ya dawo hayyacinsa." Matawalle ya ce "Allah ya baka nasara, ni fa ina jin tsoron a sake samun matsala" Sultan ya ce "Matsalar me fa?" "Kar a je wani abu ya faru, kana ganin yadda muke fama, ake tunanin yadda za mu ɓullo da lamarin bayyanawa Duniya ɗan gurin Imam Hammad da bayanin da za mu yi a gamsu. Yanzu kuma mun bar shi ya keɓe da ita idan aka kuma samun matsala fa?" Sultan ya ɗan yi murmushi ya ce "Sai mu karɓi ƙaddara, mu jira ta sake haihuwa. Amma ba na tunanin wani abu ma zai iya faruwa, tun da ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Kuma mai maganin da aka je ɗaukkowa ne ya ɗan yi balaguro, yana ƙarasa warwarewa za a raba su daga ɗakin, mu ga me ya kamata a yi mata" Matawalle ya ce "Haka ne, Ubangiji Allah ya ba shi ingantacciyar lafiya. Sultan ya amsa da "Amin" Hammad bai sake dawowa ba sai bayan sallar asuba. Da ya shigo ma bai kai ko kalli inda Nana take ba. "Ina kwana" Nana ta gaishe shi tana satar kallon sa, amma ya yi mata shiru bai amsa ba. Gaba ɗaya sai ta ji babu daɗi shirun da ya yi mata. Ya je gaban mudubi yana gyara gashinsa, ta ƙarasa gaban mudubin ta ce "Kawo na gyara maka?" Ya harare ta, ya share ta ya ci gaba da taje gashinsa. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, ya ajiye comb ɗin, ya kalli Nana ta je ta ɗaukki hijjabinta ta saka. Ya ƙarasa ya buɗe ƙofar. Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci. Ya gaida Hammad, ya ɗaga masa hannu. Nana ta gaishe shi ya ce "Ni yakamata na din ga gaishe ki, uwar gijiyarmu. Ya mai jiki?" Nana ta ce "Asma'un dai. Mai jiki da sauƙi Alhamdillah ina Nene?" "Tana nan ƙalau, ga saƙon ki nan in ji ta, ina ta lallaɓata ta dawo Agadez, na ajiye ta a gidana amma ta ƙi" Ya yi maganar yana nuna wa Nana flask. Nana ta ce "Dan Allah idan ka koma idan za a bari na ganta, ka ce dan Allah ta taimaka ta zo na ganta, Kodayake da an sallame ni daga nan, gurinta zan je ta ce za ta raka ni gid.. sai dai sauran maganar ba ta fito ba saboda harar da Sayyid ya yi mata. Mahmoudu ma ya kawar da maganar, ya koma yi wa Hammad magana da yarensu. Hammad ya yi shiru yana saurarensa. Ba ta san me suke tattaunawa ba, amma da alama abin da suke tattaunawar ya ɓata masa rai. Ya tashi ya ɗaukko biro da takarda ya fara rubutu. Sai gaban Nana ya faɗi, zuciyarta ta fara raya mata ko takardar saki yake rubuta mata. Ya gama rubutunsa ya miƙa wa Mahmoudu, suka fita tare. Ta yi ajiyar zuciya ta buɗe flask ɗin da Nene ta bayar a kawo mata. Nana ta yi murmushi ganin naman kaza cikin flask ɗin, ta ce "Nene so take sai na fashe saboda girma" Ba ta sake ganin Hammad ba, sai da daddare, da yaje ya yi wanka, ya canza kaya ya nufi hanyar fita. Nana ta ce "Sayyid wai yau ma nikaɗai zan kwana a ɗakin nan? Amma ka san ɗakin nan tsorata ni ake yi" Ya ce "Me zan zauna na yi miki, zan iya ɓata miki rai idan na ci gaba da zama a ɗakin nan, gurin matata zan tafi" Ya yi mata maganar a gadarance. Ƙifta ido kawai ta yi idanunta suka yi jawur. Sai a lokacin ya yi dana sanin abin da ya gaya mata, biyo bayan tuna matsanancin kishi da take da shi. Ji yayi kamar ya bata haƙuri, ya koma ya zauna, amma ya yi jarumta ya fice. Sai dai tun da ya fita abin duniya ya dame shi. Tausayin Nana ya mamaye shi, ya sa dole ta yi kishinda Asal kuma ta ji haushin sa, mussaman yadda Asal ɗin ta din ga yi mata isa da iko, da nuna mata ita ba komai ba ce ba. Tun da ya fita Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, wani abu mai raɗaɗin gaske, ya soke mata a ƙirjinta zuwa wuyanta. Duk da ta saba ganinsu guri ɗaya, tana kishin hakan amma na yau ya yi mata ciwo nesa ba kusa ba. Bacci ɓarawo ne ya ɗauke ta, sai dai wannan mummunan mafarkin, na halittun nan, suka din ga bin ta, gaba ɗaya baccin ya gaza yi mata daɗi. Kafin Asuba ta farka da wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon da kai. A inda ta yi salla ta kifa kanta ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa, ga jikinta babu daɗi. Ji ta yi an danne ta, ta buɗe idonta ta ga Muhsin ya ƙanƙame ta. Tashi ta yi zaune a rikice tana faɗin "Muhsin ɗina" Ya ƙanƙameta, ita ma ta rungume shi tana wani irin murmushi tamkar ta mayar da shi cikinta. Ta ɗaga kai ta ga Hammad a gefe, yana karyawa. Muhsin ya tashi daga jikinta, ya je gaban Imam ya ɗaukko dabino, ya dawo ya saka mata a baki, ya sake komawa ya ɗaukko ya kawo mata. Ta saka hannu ta karɓa tana jin wani irin tasirin alaƙa ta tsakanin uwa da ɗa. Sayyid ya ɗauki Muhsin, ya ajiye shi a kusa da shi, yana ba shi Abincin. Ya waiwaya ya kalli Nana ya ce "Naaa" ya din ga nuna mata kusa da shi, wai ta zo ta zauna ta ci. Sam Hammad bai nuna ya san tana gurin ba. Amma duk da haka yanayin ya yi mata daɗi mara misatuwa, yau ga mijinta ga ɗanta a guri ɗaya. Kuma alamu suka nuna mata, a zaman da Muhsin ya yi da su, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu. Dan duk ƙyuyar Muhsin ba ta ga alamar yana yi masa ba. Ƙarshe ta yi shiru tana kallonsu, ya shirya cikin jallabiya fara ƙal, ya shirya Muhsin da kansa, sai dai ga mamakinta ba ta ga ya naɗa rawani ba, ya saɓa ɗansa a kafaɗarsa ya yi waje. Ƙasan zuciyarsa kuwa raya masa ya din ga yi ya rungume ta, ya ji damuwarta, yana da abubuwan gaya mata da yawa, amma ya daure ya share ta. Sultan yana zaune, yana saka hannu a wasu takardu, tare da Tafawa da Sardauna. Aka shigo aka nema wa Tafawa iso. Gaba ɗaya suka shiga mamakin me ya kawo shi a daidai wannan lokacin. Bayan sun gaisa ya ce "Na samu takardar kiran da ka yi mini ne, shi ne na amsa kiran. Cikin mamaki Sultan ɗin ya ce "Ni ɗin kuma?" Tafawa ya ce "Amma saƙonna samu har gida aka kai mini takarda" Sultan ya ce "Ai ni ba zan aika maka da takarda dan ina neman ka ba, amma da mamaki" Tafawa ya ce "Ikon Allah, to waye ya aikata hakan?" "Ni ne" Imam Hammad ya amsa ya na ƙarasa shigowa gurin. Ayshercool 87 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAN KI KARANTA 08081012143 Ƙwalalo manyan idanunsa Tafawa ya yi, ganin Imam Hammad ya fito gashinsa a buɗe, saboda hakan abu ne mai girman gaske, mussaman ga shugaba kamarsa,hakan kuskure ne. Ba wannan ya fi kaɗa shi ba ma ɗan ƙaramin yaron da yake hannunsa ne ya fi tafiya da tunaninsa. Ya girgiza matuƙa gaya da ganin yaron. Su Sultan ma sak suka yi, su na mamakin yaushe ya Hammad ya samu sauƙi har haka, har bakinsa ya yi wannan buɗewar? Ga uwa uba wautar da ya yi na zuwa da Muhsin ba tare da an gama shirya yadda za a kare hakan ba. Imam Hammad ya nemi guri ya zauna, cikin girmamawa ya gaishe su, bai damu da jiran su amsa ba. Ya dubi Tafawa ya ce "Mai girma Tafawa, ina fatan ban yi laifi ba, kasancewar a ƙarshen wasiƙata, ban sanar da cewa ni nake nemanka ba, ba Sultan ba. Na zaɓi saka gurin haɗuwar ya zama nan ne, saboda sai ya fi dacewa da abubuwan da suke bakina. Kun aika da takarda Majalisar Sultan, sannan an aika da wata majalissar Imams. Duk da kwana biyu ba na samun sukunin zaman majalisar. Na gayyace ka nan ne domin warware maka duk wani abu da ka ke son sani, ba kai ba duk sauran wanda suke son sani ma. Ba sai mun ci gaba da wahalar da shari'a ba. Kamar yadda na gaya maka wannan shi ne ɗa na Muhsin, ina da ɗa, kamar yadda na din ga jaddada maka, ka din ga ganin kamar shaci faɗi ne, wanda nan gaba kaɗan zan bayyana wacece mahaifiyarsa ba na son mu zurfafa a kan wannan bangaren dan abu ne da ya shafe ni. Abu na gaba kuma ana cewa ba ni da cikakkiyar lafiya ba zan ci gaba da gudanar da shugabanci ba. Haka ne, yakamata na matsa gefe na samu cikakken hutu da nutsuwa kamar yadda ku ka buƙata. Sannan kuma babu zobena na tambari a hannuna. Ina mai farincikin sanar da kai cewa daga yau, na sauka daga kan muƙamina na shugabancin majalisar Imam. Ba iya wannan ba ina san a cire ni daga cikin Imam da ake sanya ran a cikinmu ne za mu gaji sarautar Sultan shi ya sanya na fito maka haka babu rawani. Ka na damar maye gurbina na Imam ko ma shugabancin majalisar Imam ɗin baki ɗaya, ko kuma ka ɗora Imam Asadullah na muddin hakan zai sama maka farinciki da kwanciyar hankali. Ka bar mu mu huta da ni da mahaifina. A ƙarshe ina ƙara gabatar maka da ma petit Hammad wato Imam Muhammad H.J Agadez wato Muhsin" Ya yi maganar yana murmushi tare da shafa kan Muhsin. Ya sake kallonsa ya ce "Idan babu sauran magana, za ka iya tafiya, ina muma fatan ka fahimci abubuwan da suka shige maka duhu game da ni" Tafawa mutuwar zaune ya yi, tare da bin Hammad da ido, jin sun Sardauna yi shiru kuma babu wanda ya musa, ko ƙaryata abin da Hammad ya faɗa  ya sanya shi tabattar da abubuwan da Hammad ya faɗa gaskiya ne. Sultan da tuni gumi ya jiƙe shi ya ce "Ina  fatan ka ji daɗi, da ka kai shi bangon da ka sanya ya fito ya tabattar maka da abin da ka ke son tabattarwa? Ina ga shikenan za ka iya tafiya." Tafawa bai iya furta uffan ba, jikinsa a matuƙar sanyaye, ya tashi yana jan ƙafarsa, da yake jin kamar ba a jikinsa take ba, da kyar ya fice. Gaba ɗaya suka yo kan Imam Hammad da faɗa kamar za su dake shi. Hammad ya ce "Ina neman afuwarku, a kan abin da na aikata ba tare da izninku ba. Amma har abada ƙarya fure take yi, ba ta 'ya'ya, ba zamu dauwwama ɓoye wa duniya abin da komai daren daɗewa sai ya bayyana ba. Ba zan iya ci gaba da jure kullum lokacinku ya tafi a kan bani kariya ba, duk na san na aikata laifi, zan tsaya a kan laifina na karɓi duk hukuncin da ya dace". Sardauna ya ce "Kuma saboda shirme sai ka ce ka sauka daga kan kujerar Imam? Dama kai ka ɗora kanka?" Suka din ga yi masa faɗa, shi kuwa ko a jikinsa, dan gara ya ɓallo duk abin da zai ɓallo a san abin yi, duk abin da za a yi masa a yi masa, ya san yadda zai da matarsa da ɗansa. ***** Kamar yadda Alhaji Fatuhu ya umarci Fadila,ta shirya tare da babbar 'yarsaJannat, suka tafi duba Hajiya Sa'a. Sai dai Hajiya Suwaiba ba ta je ba, saboda ba ta jin daɗi. Ko da suka je, ƙin fitowa falo ta yi, sai su ne suka shiga cikin bedroom ɗin ta, suka same ta. Sai dai kamar yadda Alhaji Fatuhu ya ba ta labari, haka ta ga tsufan Hajiya Sa'a ya fito. Kamar ba ita ce 'yar ƙwalisar nan mai ado da kwalliya ba. Suka gaishe ta, amma sai dai ta sake shiga halin ɗimuwa ta kasa gane su, kawai dai ta amsa musu. Fadila ta sauke Muhsin da yake bayanta, tana ba shi ruwa saboda daga bacci ya tashi. Hajiya Sa'a ta ƙura masa ido, har sai da ya lafe a jikin mahaifiyarsa yana kawar da kansa daga kallon Hajiya Sa'a. Hajiya Sa'a ta ce "Da tuni wannan tsinannen ɗan ne zai mutu, amma nawa ɗan ya mutu, Allah ya isa ban yafe ba, kuma shi ma in Allah ya yarda sai ya mutu" Cikin mamaki da rashin fahimta Fadila da Jannat suke kallonta. Fadila ta ce "Tsinanne kuma Yaya Sa'a, me ya yi miki? Ba ki gane shi ba ne? Muhsin ne ɗan gurin ƙaninki Alhaji Fatuhu" A fusace ta ce "Shi ɗin fa, Allah ya tsine masa Albarka, shi ma Fatuhun Allah ya tsine masa Allah ya sa ya mutu. Da tuni Abba yana raye, amma bai sha alawar ba sai Abba ya sha ya mutu. Ke ma Allah ya tsine miki shashasha" Waro ido suka yi gaba ɗaya, cike da tsoro. Jannah ta ce "Kin ga Anty, tashi mu tafi na fara jin tsoro, kar ta fara kai mana duka" Babu shiri suka miƙe, Fadila ta goya ɗanta suka bar gidan, sai tsine musu take yi, tana faɗar wasu abubuwa da ba su gane kan abin da take nufi ba. ***** Asal ta sha mamaki, ganin mahaifinta a gidanta wanda idan ba da wani dalili ba baya zuwa, sai dai yanayin fuskarsa ya sanya gabanta faɗuwa. Kan ta yi magana ya ce "Hammad da gaske yake yana da ɗa, domin na ga ɗan nasa yau ido da ido, aurenki da shi bai amfana mini komai ba gurin cikar muradina ba, kaiconki da gaza cika wa mahaifinki burinsa" A burkice ta ce "Wane Hammad ɗin, yana tsare babu lafiya bai san waye a kansa ba ma?" Cikin tsawa ya ce "Zan yi miki ƙarya ne? Daga cikin gidan Sultan nake, lafiyarsa ƙalau sai dai idan raina miki hankali suke yi, na yi magana da shi, kuma har ɗan nasa na gani da idanuna" Hannu Asal ta ɗora a ka, tana lissafa maganganun da mahaifinta yake gaya mata. Da ta rasa mene ne gaskiyarsu. Imam Hammad kuwa, tun da ya shiga ɗakin, ya hango Nana ta yi ruf da ciki a kan gadon, ga sautin sheshsheƙar kukanta na tashi. Ya rufe ƙofar ya ƙarasa gaban gadon da hanzari. Ya ɗora hannunsa a bayanta ya ce "Ma vie" Tashi ta yi zaune idanunta jawur, ta ce "Ina Muhsin ɗin?" "Na mayar da shi inda yake. Ya na ji kamar jikinki da zafi ne? Meyafaru ma ki ke kuka? Wani ya shigo ne, ko an yi miki wani abu ban sani ba?" "Ni ka mayar da ni gurin Nene, tun da ka samu lafiya" "Yaushe na samu lafiyar? Ni ban samu lafiya ba tukuna, ba ki san me nake ji a jikin nan nawa ba" Yayi maganar yana ci gaba da shafa ta a hankali. Cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya rayuwata, jikinki da zafi. Ga shi haushina ki ke ji kin ƙi yadda da ni, balle na ce ko Muhsin ne zai samu ƙani" Nana ta ci gaba da kuka, da ita kanta ta kasa tantance kukan me take yi. Ya yi murmushi ya ce "Yanzu kishin ne ya saka miki zazzaɓi ma viee?" Ture hannunsa ta yi tana kuka. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "Da wasa nake miki, ban je ko ina ba fa da na bar ɗakin nan, a ƙofar ɗakin nan nake kwana, saboda idan mu na tare guri ɗaya akwai matsala ne. Ba kuma na son ɓata miki rai" Kwanciya ta yi sosai a jikinsa, ta saka hannu ta zagaye bayansa ita ma, ta yi shiru tana mayar da numfashi. Ya din ga murmushi yana shafa bayanta ya ce "Ki yi haƙuri, ba na ƙaunar na din ga aikata duk wani abu da zai sanya mini ke fushi da damuwa. Je vous aime ina son ki rayuwata". Nana ta ɗago tana kallon ƙwayar idonsa, idanunta fal hawaye. Ya jinjina kai ya ce "Da gaske nake Asmy, ina yi miki so mai tsananin gaske. A jinina nake jinki ba iya zuciyata ba" "Sayyid" "Na'am rayuwata" "Kar na sakankance da kai, 'yan uwanka su ce ba zaka zauna da ni ba, ban san ya zan yi ba Sayyid. Ba gudunka nake dan na daina sonka ba, tsoro nake ji. Na azabtu ko a iya haka a tsaya, ina son na samu nutsuwar ƙwaƙwawa da zuciya. Na kasance da abubuwan da za su sanya ni farinciki" Ta yi maganar a raunane. "Ke jaruma ce Asmy, kar wani abu ya baki tsoro, kai da fata komai zai faru ina tare da ke, zan zaɓe ki da ɗana a kan komai, babu butulci tsakanina da ke, ai na san babu wani abu da zan yi miki da zai sanya na biya ki ko na kamanta abin da ki ka yi wa rayuwata ba. Kuma ina fatan a wannan karon za ki ba ni dama ki saurari uzurina, inda na yi miki kuskure kuma ki yafe mini. Ki bani dama mu ɗora ginin rayuwarmu rayuwa mai kyau da aminci" "Ni ba biyana za ka yi ba, ban yi dan ka biya ni ba, ni kawai su bar mini kai, kuma su dawo mini da Muhsin mu rayu tare" Ta yi maganar tana kuka. Ya yi murmushi idanunsa na cika da hawaye, ya ce "An bar miki ni, halak malak. Hammad naki ne rayuwata" Ya yi maganar yana haɗe bakinsa da Nana. Babu tsammani aka banko ƙofar ɗakin, Nana ta yi wata irin zabura, shi kuwa cikin nutsuwa ya waiwaya ya ga waye wannan ya shigo musu babu neman izni. Da Asal ya yi tozali, jikinta na wata irin tsuma take bin su da kallo. Ta nuna Nana da yatsanta bakinta yana wata irin rawa, jikinta ma karkarwa kawai yake yi, tamkar ana kaɗa mata gangi. Ba ta taɓa tsammanin abin da za ta gani ba kenan, ko a hasashe da tsammani ba ta taɓa hasko ganin Nana tare da mijinta ba. Kasamcewarta baƙar fata da ba ƙabilarsu ba. "Ham..Ha.ha...Hammad!" Ta faɗa cikin wani irin ƙaraji mai razanarwa. Bakin Asal ne ya ci gaba da rawa, dan da fari ma kanta gaba ɗaya kullewa ya yi, ta manta wace ce ma Nana. Ita da ta zo tambayarsa ba'asin ina ya samu ɗa, sai ta riski abin da ya fi maganar da ta zo da ita tashin hankali. Hankali kwance Nana ta gyara rigarta, ba tare da abin da ya faru ya ɗaga mata hankali ba. Ja da baya Asal ta fara yi, numfashinta na fita da kyar, jikinta na wata irin kyarma. A sukwane Imam Hammad ya diro daga kan gadon ya nufe ta, cikin tashin hankali bai so Asal ta san alaƙarsa da Nana ta wannan sigar ba. Amma ya san babanta shi ne ya lalata komai. "Kar ka taɓa ni, kar ka ƙaraso inda nake Hammad. Ka yaudare ni ka zalunce ni, dama rashin lafiyar da ka ke yi ƙarya ka ke yi? Ka haɗa kai da mahaifinka ne dan ku yaudare ni ku cutar da ni? Lalata da wannan ƙasƙantacciyar ƙazamar matar? Na zaɓo ta a matsayin kukunka dan kawar da kanka daga kalle-kallen wasu matan, ashe yaudarata ka ke yi? Tun tsawon lokacin da ta gudu na neme ta na rasa, a she a nan ka ɓoye ta ku ke lalata." Cikin azama Hammad, ya danƙo hannun Asal, da take ta fizge-fizge ya danna ƙofar ya datse ta. Ya kalli Asal ya ce "Ki nutsu cherié zan yi miki bayani, ni ba lalata nake yi da Asmy ba" Cike da baƙin ciki take kokowar fizgewa cikin ƙaraji ta ce "Idan ba lalata ku ke yi ba, me ku ke yi? Tsawon wannan lokacin da ba ta nan, ashe ku na tare ka ji kunya ba ka ji daɗin halinka ba. Ke kuma 'yar iska mazinaciya wallahi sai na ƙasaƙantar da ke, sai na saka an kashe mini ke a kashe banza" Nana ta ce "Point of correction my dear, ba da kukun mijinki ki ke magana ba a yanzu,  kuma ni ba mazinaciya ba ce ba. Ki dai nemi wani sunan ki kira ni da shi" Ya kalli Nana da ta tsuke fuska ya ce "Ma vie dan Allah ki yi shiru, mu warware matsalar nan a hankali" AREWABOOKS Daskarewa Asal ta yi jin sunan da ya kira Nana da shi, wanda shi gaba ɗaya ya manta, saboda yadda sunan ya shiga bakinsa ya zauna. "Hammad gaskiya ne abin kunnuwana suke jiye mini? A gabana? Hammad" Ta furta tana ajiyar zuciya mai ɗauke da nannauyan baƙin ciki da tashin hankali. Damƙar hannun Asal ya yi, ya buɗe ƙofar suka fita tare. Kokowa ya shiga yi da Asal, yadda take kai masa duka, tana fizge-fizge. "Asal, ki tsaya ki saurare ni, kar ki ji wa kan ki ciwo mana" "Ba zan saurare ka ba, ba na buƙatar duk wasu kalaman yaudara da ƙarya da za su fito daga bakinka. Me ya rage bayan abin da na gani? Da girmanka da mutuncinka ka ɓoye kukunka a sashen mahaifinka kana zina da ita, ba ka ji daɗin halinka ba" Kalaman Asal sun yi wa Hammad zafi nesa ba kusa ba, da kyar ya haɗiye wani yawu mai zafi ya ce "Ni ba zina nake yi ba, idan ba ki tsaya kin saurare ni ba, ki ka fita ki ka yayata abin da ba shikenan ba za ki cutar da ni dan kin yi mini ƙazafi" Kallonsa take yi, tana jinjina girman yadda ya ƙware a iya wasa da hankali, ta ci gaba da ƙoƙarin fizgewa, amma ya riƙe ta gam. "Hammad ka gama raina mini hankali, dama ga batun ɗa ana yi, an ce ka na da ɗa da a ƙalla ya shekara biyu, yanzu kuma na kama ka da wata, amma kana iƙrarin zan cutar da kai? Da ni da kai waye ya cutar da wani? Wadda ka yi wa ciki ba ta ishe ka ba, ka ɗauki kukunka ka sanya a sashen Sultan ka ke lalata da ita" "Ban taɓa cutar da ke ba Asal, a shekara goma sha biyu da muka yi da ke, idan zan iya aikata abin da ki ka faɗa kin sani, idan akasin hakan ne ma kin sani. Amma mu je gurin Sultan ɗin ki ji komai daga bakinsa. Nana kuwa guntun tsaki ta yi bayan fitarsu, ta tashi ta shiga banɗakin ta yi wanka, ta yi alwala. Ta ƙura wa kanta ido a mudubin banɗakin, tana tunanin yadda Asal ta din ga yi mata kallon ƙasƙanci, da bautar da ita ta ƙarfi da yaji, saboda tana da kuɗi da mulki, a matsayinta na kishiyarta, kuma ta daure ta haɗiye. Ta ci gaba da tunanin daga bisani ta fito da niyyar ta canza kaya, amma ta kasa, ta nemi guri ta zauna ta yi shiru. A zuciyarta take addu'a ta ce "Allah ga Nana, bakwarka ce ni mai raunin gaske, ga ɗan jaririn ɗa na da nake fatan ya samu kyakykywar rayuwa ya tashi a tsakanin uwa da uba. Ubangiji Allah ka na ji ka na gani, ka ga wahalar da na sha a baya, ga shi na zo wani bugire da nake sanya ran samun afuwa, sai dai alamu sun nuna an fi ƙarfina. Allah idan sun fi ƙarfina ba su fi ƙarfinka ba, da ni da su duk bayinka ne. Ubangiji Allah ka sassauta mini ka kawo mini ɗauki. Ubangiji Allah ka yaye mini wannan kishin da nake ji, ka sanya su bar ni na rayu da mijina da ɗa na. Ubangiji Allah ka ba wa mijina ingantacciyar lafiya ka yaye masa abin da yake damunsa, Allah ka ba kare mini ɗana daga dukkanin sharrin da ido ka iya gani, da wanda ma baya gani. Ƙaisar ma bawanka ne, Allah ka ba shi lafiya. Allah ka ga wahalar da na sha a baya, yanzu idan na koma suka raba ni da ɗa na, wata wahalar zan shiga, Allah ka kawo mini agaji" Sai kuma ta yi shiru tana nazari, duk abin da take faɗa ai Allahan yana ji yana gani. 'Idan ba ubangijina ba, wa nake da shi da zan kaiwa kukana kai tsaye ya share mini. Na san ya sani amma ƙara gaya masan, yana sama mini nutsuwa da kwanciyar hankali, ko da ina cikin damuwa. Ta ba wa kanta amsa. Asal ce a gaban Sultan, tana ta uban kuka, fuskar nan ta yi jawurr, idanunta sun kumbura sosai da sosai. Sultan ya yi shiru, saboda yadda abubuwan shi kansa suka kulle masa kai. Gaba ɗaya bai yi tunanin abubuwan za su damalmale har haka ba, ya ma rasa ta ina zai fara. Ya ce "Ki na ji na Asal. Wannan maganar abu ne mai faɗin gaske, da ko ba ki gano ba, dole za a yi miki bayani. Amma wannan bayanin ba ke kaɗai yakamata mu yi wa ba, a gaban mahafinki yakamata mu yi shi. Tabbas da gaske Imam Hammad ba shi da lafiya, kuma ke ma shaida ce, saboda kin zo kin gan shi a halin da yake ciki. Sai dai ita wannan yarinyar tana da alaƙa da samun sauƙinsa. Yanzu bayanin da zan yi miki ba za ki gane ba, ina son sai mun zauna gaba ɗaya za mu yi miki bayani. Amma ki samu nutsuwa ki kwantar da hankalinki. Gaba ɗaya Asal ba ta fahimci abin da Sultan yake gaya mata ba, gani take kawai yana ƙoƙarin goyon bayan ɗansa ne. Muryarsa ta sake tsinkayowa yana faɗin "Kar ki bari kowa ya ji maganar nan, sai mun zauna an yi miki bayani tukuna dan Allah." Ya dubi Imam Hammad ya ce masa ya kai Asal gida, ya rarrashe ta, ta samu nutsuwa kafin a yi mata bayanin komai. Nana kuwa kajin gurin Nene ta samu ta ci, saboda taga alamun idan ta biye ta kishin nan, yunwa ce za ta kar ta a banza, duk da yanzu naman duk ya ishe ta, abinci take so ta ci sosai. Ga shi ta yi zaton ko zai dawo mata da Muhsin, amma bai dawo mata da shi ba. Ba ta sake ganin Hammad ba, sai bayan sha ɗaya na dare. Idanunsa jawur da alama yana cikin damuwa kuma ko abinci ba ta tunanin ya ci. Sau ɗaya ta kalle shi ta basar, ba ta ko kula shi ba. Gani ta yi ya cire rigar jiknsa ya yar a ƙasa, ya hau kan gadon ya kwanta, ba ta motsa ba ta ci gaba da zamanta, dan haushinsa ne ma ya kama ta. Jin ya fara numfarfashi ya sanya ta tashi tsaye. Ta kalle shi ta ga ya fara komawa ja. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, abin da ta lura da shi kamar ciwon ya fi tsananta masa a Niger. Ta fara ƙoƙarin ninke masa rigar, kawai wannan takardar ta faɗo daga aljihun rigar. Ta ɗauki takardar ta yi shiru tana kallon takardar. Ta hau kan gadon ta juya shi da kyar, taga yana ta taune leɓensa yana jujjuya kansa. "Ki yi mini addu'a, zan mutu" ya furta da kyar kamar numfasihinsa zai ɗauke. Suratul Fatiha ta din ga karantawa da Bismillah tana tofa masa. Fizge-fizge ya fara yana girgiza kai ya ce "Tashi mu tafi" Cikin rashin fahimta ta ce "mu je Ina?" "Ki tashi nu tafi, kafin na rasa raina" Ya ƙarasa maganar yana dafe kansa da yake jin kamar zai yi bindiga. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi. Amma ba damar Nana ta tashi, saboda yadda ya rirriƙeta. Ga shi ta san ko ta ce a shigo babu lallai a jiyota daga waje. Mai bugun ne ya gaji da bugawa, ya turo ƙofar, Sultan ne tare da wata babbar mace fara solnda ita. Sai kuma Mahmoudu. A rikice suka ƙarasa gaban gadon, cikin tashin hankali Sultan ya ce "Jikin ne?" "Ki tashi mu tafi, zan rasa raina, ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Ki yi mini addu'a" Tuni Nana ta fara kuka, ta ce "Ina yi maka, kai ma ka din ga yi ko a zuciyarka ne. In sha Allah babu abin da zai same ka" Matar ta ce "Wannan ce matar tasa?" Sultan ya jinjina kai ya ce "Ita ce" Ta ce "Ikon Allah, lallai Allah gwani ne" Mahmoud kuwa jiki a sanyaye ya ce "Sannu Imam" "Hamud, dan Allah ka ɗauke ni ka sake tafiya da ni, ba na son zaman garin nan, ba ku san me nake ji ba." Mahmoudu ya kalli Sultan ya ce "Ranka ya daɗe, a irin wannan yanayin fiye ma da wannan, na bar Niger da shi a wancan lokacin. To kuma na ga alamar jikin na neman sake dawowa. A hankali ya fara fita hayyacinsa, ya fara lanƙwasa Nana, ta rintse idanunta Sultan ya ƙarasa da sauri yana faɗin "Kai kar ka yi wa 'yar mutane illa, Hammad" Mahmoudu rasa abin yi ya yi, dan ya san ganganci mafi girma da zai aikata shi ne ya taɓa jikin Nana garin ƙoƙarin ɓanɓare shi daga jikinta. Sai kuma Sultan ya ja ya tsaya shi ma ya rasa abin yi. "Ke kin san me nake ji ai" ya sake futawa cikin ƙarfin hali. "Na sani, shi ya sanya nake yi maka addu'a" Sultan ya ce "Hammad, kar ka ji mata ciwo fa" A hankali Nana ta ce "Ba zai ji mini ba in sha Allah" Addu'a ta ci gaba da yi masa, tana tofa masa. Sultan kam kasa jurewa ya yi, saboda ba ƙaramin tashin hankali yake shiga ba, idan ya ga ɗan nasa a cikin wannan yanayin. Sai kusan ƙarfe biyu na dare sannan ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya. Ya yinƙura ya tashi zaune yana kallon Nana. Ta ce "Sannu. Ka daina jin abin da ka ke ji ɗin?" Ba ta yi zaton zai iya magana ba ta ji ya yi, ya ce "Ina ji amma ya lafa mini" Ta ce "To Allah ya baka lafiya ingantacciya. Amm ka yi haƙuri kana cikin yanayin larura zan tambaye ka abu" ya yi shiru yana kallon ta. Ta ɗago masa wannan takardar ta ce "A cikin rigarka na ganta, waye ya saka maka ita?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba" Ta sake cewa "Shekaranjiya wani abu mai kama da mafarki ya faru, har muka fita ta wata ƙofa, gaske ne ko kuma mafarki nake yi?" "Gaske ne" Ya bata amsa kai tsaye. "Ina buƙatar fahimtar wasu abubuwan, dan ka na yin abubuwan da ba kowane ɗan Adam ne zai iya ba. Tun mu na Nigeria ka ke yin wasu abubuwan. Kuma ina buƙatar na ji abubuwan da suka faru wanda ban sani ba" Ya numfasa ya ce "Zo ki raka ni shan iska tukuna" Suka sauka daga kan gadon. Ya zira rigarsa ya buɗe ƙofar nan, suka ƙara ratsa duhu suka fita wannan corridor. Yau ma saharar ta gani, gurin ya ɗauki sanyi sosai da sosai. Ta kalli Wannan tsaunin dake gefen saharar ta ce. "Wai mene ne a cikin dutsen can, shi nake son sani" Ya kalli gurin ya ce "Nan ne ainihin inda kakanninmu suka fara mulki, dan haka duk wani kayan tarihi, a ciki a ke adana su" Nana ta ce "To ka gaya mini abin da na tambaye ka, kuma ina son ka kai ni na ga abubuwan tarihin garin naku" "Zan kai ki, kuma zan yi miki bayanin amma yanzu ba na jin daɗi" Ta ɗan shafa bayansa ta ce "Sannu" ya jinjina mata kai. Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta, sanyin gurin ya din ga ratsa su a tare. Ta ɗaga kai tana kallon wannan tsaunin, da ya ce mata gidan tarihi ne, tana jin kwaɗaituwa da son sanin abin da gidan ƙunsa. Tana jin kewar Ƙaisar, ta damu sosai ta san ya jikinsa, amma ko sama ko ƙasa ta daina ganinsa. Ta lumshe idanunta ta buɗe, kewar gida kuma na sake bijiro mata, tana cikin matuƙar fargaba a kan irin karɓar da za a yi mata idan ta koma. "Ma viee" "Na'am Shugabana" "Ina da wani kyakykywan albishir da zan baki, amma ba yanzu ba" Ta yi murmushi ta ce "Sai yaushe?" "Sai an wa Muhsin ƙani" Ta ce "Babu rana kenan" "Akwai mana nan kusa" yayi maganar yana ƙara ƙanƙameta. Asal kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan faɗa suka yi kaca-kaca da Hammad, duk da rarrashin da Sultan ya yi mata. Ta kira Hasna a waya, Hasna ta ɗaga tana "Faɗin Gimbiya Asal, kwana biyu" Cikin kuka ta ce "Hasna, kin san abin da Hammad ya yi mini kuwa?" Gaban Asal ya faɗi ta ce "Meyafaru?" "Hasna wai Hammad yana da ɗa" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ɗa kuma kamar yaya?" Cikin kuka ta ce"Ɗa dai ya haihu da wata, Tafawa kuma ya tabattar mini da hakan, kin san ba zai yi mini ƙarya ba. Kuma ba na ce miki yarinyar nan ta gudu ba, mai yi masa girki ba, har nake ce miki duk inda ta gudu zan saka a nemo ta" Hasna ta ce "Eh haka ne" "Na je na kama shi da ita, a can cikin sashen Sultan, duk tsawon lokacin da aka shafe ba ta nan, suna tare su na lalacewa, na shiga uku Hasna, ji nake kamar na kashe kaina na huta. Na tsani Hammad na tsane shi, ban taɓa cin karo da abin da ya gigita ni ba, kamar abin da na gani yau ba. Kuma Sultan goyon bayansa yake yi, wai in bari za a yi mini bayani, bayanin me za a yi mini an cuce ni Hasna" Ta yi maganar tana ƙara rushewa da kuka, kamar wadda aka nuna wa ranar mutuwarta. Hasna ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Asal, ki yi haƙuri ki nutsu, ki tattara hankalinki guri ɗaya kar ki yi ganganci da rayuwarki. Amma ni kwanaki na ji Al Hussain yana cewa ya kira shi ya ce ya yi masa bincike a kanta, a nemo kamfanin da suka kawo ta. To ni ban kawo komai a raina ba, na ɗauka da saninki, amma zan tambaye shi ko ya san wani abu. Amma dan Allah ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki" "Ba ki san me nake ji ba, hankalina ba zai taɓa kwnaciya ba" Haka Asal ta kwana ido biyu, babu abin da take hangowa sai abin da idanunta suka gane mata a tsakanin mijinta da wannan baƙar yarinyar. Bangaren su Nana da safe, da Mahmoudu ya kai musu abinci, ya sanar musu da cewa Sultan ya ce su zo gaba ɗayansu, mai maganin ya ƙaraso. Hammad ya ce "Waye mai maganin?" Ya ce "Ban san waye ba, kawai dai saƙon da ya bani kenan" "Ni fa ba na buƙatar wani mai magani, ga maganina nan a gefe na" Ya yi maganar yana kashewa Nana ido. Ta basar da shi, ta ɗan yi murmushi. Ya karya sannan suka rankaya suka fita tare. Tun da aka kawo Nana, sai a lokacin ta samu damar sake fitowa daga ɗakin da suke. Sai dai wani surƙuƙin ɗakin suka shiga. Abin har mamaki yake ba wa Nana, yadda ake ɗakuna a lunguna da saƙo na gidan, kamar marasa gaskiya, inda ba ka yi zato ba ma, sai ka ga ɗaki ne. Da Asal ta yi tozali a ɗakin, idanunta jawur, tana ganin Nana ta sake tsuke fuska, kamar ta tashi ta kashe ta ta huta. Suka je gaban Sultan suka gaishe shi, Nana ta basar ko kallon inda Asal take ba ta yi ba. Sultan ya ce "Asal, na saka an kira ki ne, saboda a yi komai a gaban idonki, a ji me mai maganin zai ce, saboda kina da hakki ki sani kar ki ga ana ci gaba da rufe ki a kan abubuwa, tun da mijinki ne" Ta yi shiru, saboda shi kansa Sultan ɗin haushin sa take ji. Sallamar da aka yi ne ya sanya Sultan yin shiru, Nana kuma ta miƙe tana faɗin "Kaii Sarki, dama ka na nan?" Ya yi dariya ya ce "Tuba nake uwar gijiyata, tuba nake uwar ɗakina" Bakin Nana ya ƙi rufuwa, tamkar ta ga wani ɗan uwanta na jini. Cikin murmushi ta sake cewa "Sarki mai baka mai aska, kai ne mai maganin da zaka duba Sayyid?" Ya ce "Ni ne uwar gijiyata, an yi mini lamuni, ko kuwa na koma ba a bani dama ba?. Ayshercool 08081012143 88 1K NE VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC IBTC BANK 08081012143 Nana ta kalli Sarkin baka ta yi murmushi ta ce "Wane mutum! Dama zan sake ganinka?" Ya yi murmushi, hadimin da ya rako Sarkin baka, ya ankarar da shi Sultan. Cikin girmamawa Sarkin baka ya risuna ya kwashi gaisuwa a gaban Sultan. Sultan ya ce "Na ga kamar ka santa ko?" Ya jinjina kai ya ce "Ƙwarai uwar gijiyata ce" Sai kuma ya sauke idanunsa a kan Sayyid, ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Kamar ba ka gane ni ba ko?" Mahmoudu ya ce "Ina dai yi maka kallon sani" Ya matsa gaban Hammad, ya zuba masa ido ya ce "Ka tuna ni?" Hammad ya yi shiru sannan daga bisani ya ce "Na tuna ka" "Waye ni?" "Ba zan iya cewa ga waye kai ba, amma mun je gurinka a Nigeria" Sarkin baka ya yi murmushi ya ce "Yanzu tunaninka kaf na zamanka a Nigeria ya dawo kana tuna komai?" Ya jinjina masa kai alamar eh. Ya dubi Nana ya ce "Kin ga batutuwan duk da na gaya miki sun dawo ko? Kin yarda ko haryanzu kina da ja?" Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ta sauya zani ba, ina nan a kan bakana" Ya ce "Babu laifi, amma an bani dama ko kuma na bar lamarin tun da na manya ne?" Matawalle ya ce "Bawan Allah, ina ganin ka yi abin da aka kawo ka ka yi mana. Idan ma wani abu ne a tsakaninku, kwa tattauna daga baya. Nan ba gurin wasa ba ne" Sarkin Baka ya tsuke fuska ya kalli Matawalle ya ce "Duk cikin aikina ne, kai ka san wacece wannan kuwa? Ku na da maganin matsalarku a tare da ku, amma ba ku sani ba" Gaba ɗaya suka kalli Nana, ita ma ta yi sororo cikin mamaki. Sarkin baka ya ce "Allah ne ya taƙaita masa, ba domin tana tare da shi ba, da sai ya zare ko ya mutu" Sultan da Mahmoudu suka haɗa ido. Sarkin Baka ya ce "Ni yanzu  abu ɗaya zuwa biyu zan ce, sauran magana ce tsakanina da ni da shi da Nana Asma'u Uwar ɗakina ba Allah ya taya miki" Ya yi maganar cikin girmamawa da jinjina wa Nana. Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi. Mahmoudu ya ce "Bawan Allah, nan fa a gaban Sarki ka ke, in yi maka da yaren da zaka fi ganewa" Sarkin Baka ya ce "Nima Sarki ne, dan haka a bari ni na gudanar da aikina. Kai ka manta Garba ga Baka ga Aska da ku ka kai mini wannan ɗan uwan naku can Nigeria" Mahmoudu ya yi sak ya ce "To ai na ga kamaninka sun canza?" "Eh, ba kamannina ne suka canza ba, dan baka ganni cikin kayan aikina ba ne ba." Sultan ya ce "Asal tashi ki je, duk abin da  aka tattauna za a gaya miki" Asal ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah ina roƙon alfarma, a yi komai a gabana, ina son sanin halin da yake ciki nima". Sardauna ya ce "Ke Asal! Ki nutsu ki saurara tukuna, ki tsaya mu ji kan rashin lafiyar tasa, sannan a yi miki bayani daga baya" Asal ta tashi jiki a sanyaye, tana kallon inda Nana take da kuma Hammad ta fice. Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Nana Asma'u, mene ne labari? Meyafaru bayan tafiyarki ne? Kuma yaya aka yi na ganki a birnin Agadez?" Nana ta yi murmushi ta ce "Komai ma ya faru Sarki, amma dogon labari ne, mai tsayin gaske" Ya murmusa, ya ƙare wa mutanen gurin kallo, sannan ya sake kallon Nana ya ce "Uwar ɗakina, me ya kawo ki Agadez ne?" Nana ta nuna masa Sayyid. Mahmoudu ya yi murmushi ganin abin da Nana ta yi. Ya ce "Uwar gijiyata, kina nan me yasa aka neme ni, kin karɓi aikin gurin uban duƙusa ne?". Nana ta girgiza kai. Ya ce "To bani labari meyafaru?" Sultan ya ce "Bawan Allah, ban fahimta ba me yake faruwa ne?" "Allah ya baka yawan rai, duk cikin aikina ne. Idan babu damuwa ina son na san matsayin kowa a nan" Mahmoudu ya ce "Ga Sultan kana gabansa, shi ne mahaifin Imam Hammad, sarkin Agadez, ga Matawalle da Sardauna, su ma iyaye ne a gare shi, kuma manya ne a Agadez. Sai Gimbiya Asal matarsa da ta fita. Sai kuma" Sai ya yi shiru yana bin su da kallo yana tsoron ya faɗi matsayin Nana ya yi laifi. Sarkin baka ya ce "Ba ka gaya mini matsayin uwar gijiyata ba" Sayyid ya ce "Matata ce" Sarkin baka ya sake yin murmushi ya ce "Na san a rina, an saci zanin mahaukaciya jikina ya bani tun a lokacin da na ganku. Allah ya baka yawan rai, in dai yana tare da Nana Asma'u zai samu sassaucin matsalarsa. Tana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya yake zaune lafiya a Agadez, bai sake ɓallewa ya bar ƙasar nan ba" Sarkin baka ya sake maimaita musu, Nana tana da alaƙa da maganin Hammad. Matawalle ya ce "Me ka ke nufi? Ko dai wani haɗin bakin ne, ku ke son ku yi mana" Sardauna ya yi maganar yana kallon Sarkin baka. Sarkin baka ya ce "Ɗan tsahirta mini tukuna, a kan aikina nake" Ya sake kallon Mahmoudu, ya ce "Ɗan uwana ko za ka iya tuna abin da na gaya muku, lokacin da ku ka je gurina?" Mahmoudu ya jinjina kai ya ce "Ka ce mana asiri aka yi masa, da baƙin aljani, ya manta duk abin da ya shafe shi, ya bar garinsu ba zai iya zama a garinsu ba. Kai kuma ba zaka iya ba shi magani ba, saboda ba aljani ne da za a iya sasantawa da shi ba, sai dai a je a karya asirin da aka yi masa. Na tambaye ka ko zaka iya karya asirin? Ka ce a'a shiga al'amuran aljanin nan akwai matsala, mu koma ƙasarmu a bincika inda aka yi masa sihiri a warware shi a can" Ya ce "Madalla" "Uwar gijiyata, ranar da aka kawo ki gidana neman magani, Meyafaru?" Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ka ce a je a kira buzayen da suka tafi. Aka ce maka sun tafi. Ka ce da an same su, wataƙila ga maganin nasa ciwon ko nawa" Sarkin baka ya ce "To Alhamdillah, an zo gaɓar da nake so a zo" "Allah ya baka nasara. Wannan ita ce rabin maganin abin da yake damunsa" Matawalle ya ce "Kai kalle mu da kyau, kar ka kuskura ka zo nan ku na gaya mana maganar banza. Idan ma haɗa kai ku ka yi, ku ka haɗa baki domin ku raina mana hankali, wallahi muka kama ka da rashin gaskiya, sai mun yi maka mummunan hukunci" Sarkin baka ya ce "Na san dai duk azabar da zaka yi mini ba zaka saka ni a jahannama ba ko? To bayan wuta da Ubangiji zai saka ni a ciki, azaba in dai ta Duniya ce babu wadda ban sha ba, duk wadda za ta biyo baya ɗazu ce. Ban sanku ba ban taɓa ganinku ba, dan me zan yi muku ƙarya? Wani abu ne ya faru da tun a baya, na yi hasashen faruwarsa. Zan yi wani bayani amma a gaban mara lafiya da shaƙiƙansa da ya yarda da su. Idan na faɗa ban ce lallai sai kun yadda ba, amma iya gaskiyata zan gaya muku. Wannan baiwar Allah da na nuna na santa, tabbas na santa amma ni babu wanda na haɗa kai da shi domin na zo nan gurin na yi cuta ba. Saboda duk wani abun duniya da nake fatan samu, Allah ya riga ya bani shi. Ranka ya daɗe zaɓi mutum biyu zamu yi magana. Duk suka yi zuru da ido, suna kallon Imam Hammad. Hammad ya kalli Sultan, Sarkin baka ya yi caraf ya ce "Ɗayar, na zaɓi uwar gijiyata mutum biyu kenan. Allah ya baka yawan rai, idan babu damuwa ina so mu keɓe tare da ku" Sultan ya ce "Babu laifi, Matawalle ko za ku bamu guri?" Sardauna ya ce "Mai girma Sultan, ka yi a hankali kar ka bari su yi maka wasa da hankali, su faɗa maka abin da ba shikenan ba" Sultan ya ce "Babu wani abu in sha Allah" Bayan fitarsu gaba ɗaya, Sarkin baka ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba dan ina tsoron hadisin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce Allah yana fushi da ɗan kasuwa mai rantsuwa a kan kasuwancinsa ba, da na yi maka rantsuwa domin nima bayar da magani kasuwancina ne, amma ina baka tabbacin duk abin da zai fito daga bakina gaskiya zan gaya maka. Na san duk alkhairin da zaka yi mini ba zaka yanke mini talauci ba, sai Allah ya yanke mini. Kuma ba zaka talauta ni ba sai Allah ya talauta ni. Babu ƙarya ko haɗin baki ko yaudara a cikin abubuwan da zan yi maka. Wannan bayin Allah biyu babu wanda ba a kawo mini shi gurina neman magani ba. Asma'u ko ba ta bayar da magani ba, tsantsar tauhidinta da yarda da Allah da ta yi, zai iya sanyawa yadda yake tare da ita ya samu lafiya ko dan albarkacin addu'a. Ai Allah shi ya ce a roƙe shi zai amsa. Kafin na ce maka komai, bari na yi maka wasu tambayi m ya ka ji lokacin da ka neme shi ka rasa a ƙasar nan?" Sultan ya ce "Na shiga tashin hankali, ba na iya cin abinci da cikakken bacci saboda rashin sanin inda yake." "Alhamdillah, yanzu da ya dawo ya ka ke ji?" "Murna nake yi mara misaltuwa, da jin cewa zan iya yin komai, dan na ga bai sake yin nesa da ni bax Sarkin baka ya ce "Alhamdillah, ka yi bayani dai-dai da abin da nake son ka faɗa. Wannan yarinyar da ɗanka ba za su rayu guri daban-daban ba. Idan haka ta kasance kuma ɗaya zai rayu cikin wahala. Saboda alaƙarsu akwai tasirin soyayyar uba da ɗa a tsakaninsu" Cikin rashin fahimta Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Me ka ke nufi?" "Aljanin da aka yi wa ɗanka asiri da shi, ɗansa ne a kanta yake ta ɗawainiya da ita saboda ta yarda ta yi masa wani aiki. Ya ɗauki tsawon shekaru ba sa tare, kwatsam da aka ba shi aiki a kan ɗanka, ya yo Nigeria da shi, suka haɗu da ita. Dan haka duk abin da zai faru, duk rashin jituwar da ke tsakaninsu, uban ba zai bari ɗansa ya ƙara nesa da shi ba. Saboda shi ne ɗa mafi soyuwa a gare shi" Sultan ya yi shiru cike da mamaki, yana bin Nana da Hammad da kallo. Ya ce "To yanzu babu yadda za ayi, a karya sihirin?" "Ni ba na ƙarya dan a so ni, ban san waye ya yi masa asiri ba, ban kuma san a daidai ina aka yi ba, balle na ce kai tsaye ga gurin a je a tona ba. Kuma ba zan yi karambani ba saboda aljanin shu'umi ne zai iya halaka ni. Amma ita tun da ɗansa yana tare da ita, ban sani ba ko ya samu sassauci ko makarin abin a dalilnta ba" Sultan ya yi shiru yana kallon su, lallai biri ya yi kama da mutum, duba da yadda lokaci guda take iya sarrafa shi, idan ciwon nan ya tashi. Sultan ya ce "Yanzu mene ne abin yi?" "Abin yi ɗaya, a ci gaba da addu'a, kuma ku ƙara taka tsantsan, sannan ban sani ba ko uwar gijiyata za ta nema mana alfarmar shugaba, ko akwai abin da zai iya yi a kan lamarin" Nana ta ɗan tsuke fuska tana mazewa. "Wa za ta roƙa mana " Sultan ya yi maganar cikin damuwa. "Ɗan nasa mana, ai hadiminta ne, kuma babu abin da za ta saka shi, ya kasa yi mata" Sultan ya kalli Nana ya ce "To ko za ki roƙa mana ɗin, duba da mawuyacin halin da yake shiga idan ciwon ya tashi" Nana ta yi shiru ta sunkuyar da kanta. Sarkin baka ya ce "Kar a yi gaggwa, a bi ta a sannu tukuna, ta yanke hukunci da kanta" Sultan ya ce "Shikenan, a mayar da kai masauki, kafin na kuma nemanka" Nana ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah zan yi magana da shi, idan babu matsala a hakan" Sultan ya ce "Babu damuwa" Hammad ya haɗe rai, amma Nana ta tashi ta bi shi waje. Ta ce "Sarkin baka, dama kana raye? Ƙaisar ya ce mini kashe ka zai yi" "Nana Asma'u, uban duƙusa bai kashe ni ba, sai dai na ji jiki kamar ba zan rayu ba. Shi ya kawo mini magani ma, sannan ya ƙara yi mini kashedi sosai a kanki. Daga nan ma har wasu magungunan ya sanar da ni" Ta ce "Ikon Allah, sarki ya magunguna ya marasa lafiya? Ina Salamatu da wannan aljanar taka" Ya yi dariya ya ce "Duk su na nan ƙalau" "To ya aka yi ka san cewa asiri aka yi wa Sayyid?" Ya harare ta ya ce "Halinki dai yana nan uwar ɗakina. Mutum mai hankali zai yi abin da mijinki yake yi ne? Abin da nake so da ke, ki ƙara addu'a kar ki yarda da kowa, kunnuwanki da idanunki su zama a buɗe komai na iya faruwa idan Allah ya taimake ki wataƙila ya samu lafiya ta hannunki" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ƙaisar ya nuna mini abubuwa da dama, sai dai ba na son gazgatawa ne, na shiga ruɗani, amma har yadda asirin yake na gani, to amma idan ya rabu da Giyaz iya samun lafiya duka?" "Ba na ce ba, tun da ban san a kan me da me aka ba shi aikin ba. Kuma ba shi da fuskar da zan tambaye shi. Amma ina jakar da na baki?" Kafin ta amsa, Sayyid ya fizgi hannunta da ƙarfi ya yi gaba da ita. Bai tsaya da ita ko ina ba, sai da suka je ɗakin da yake jinya. Idanunsa jawur ya ce "Dan wulaƙanci kawai ki je ki tsaya ki na surutun banza da mutumin da ba muharraminki ba" Ta marairaice ta ce "Haba Shugaba, wa nake da shi a nan daga ƙasarmu, yaushe rabon da na ga wani wanda na sani? Kuma Sarkin baka duk da yana wasu abubuwan da nake tantama a kansu, mutum ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba. Bayan tafiyarka daga gidansa, abubuwa da yawa sun faru, ni a gidan nasa a ka bar ni" "Ba na son jin koma mene ne ya faru" ya yi maganar yana tsuke fuska. Ta ce "Haba Shugaba, kar ka manta, maganinsa ya taka muhimmiyar rawa lokacin da ka yi rashin lafiya" Yayi mata shiru yana huci, tabbas a rayuwarsu da shi a Nigeria ta san shi da azabar kishi. Ta kwantar da murya, tana shafa bayansa ta ce "Haba Shugaba, dama mutum zai iya fushi da rayuwarsa, tuba nake ɗan manyan mutane, kuma babban mutum" Ɗan guntun murmushi ya saki, ita ma ta yi masa murmushin. Ya ce "Yauwwa, ki yi mini addu'a, in ajima za a sanar da Asal da iyayenta, matsayinki a gurina. Nana ta kwaɓe baki ta ce "Na yi maka addu'a, ta mutu mana, nima ban mutu ba da kishiyata ta mayar da ni baiwa saboda tana da kuɗi, ga kuma mijina ina kallonsu tare, amma ban isa na ce komai ba". Tsam ya miƙe, saboda ya san idan aka ci gaba da jan maganar faɗa za su yi. Ya ce "Ki shirya, idan na dawo yau komai dare, za mu je gurin kayan tarihi na Agadez, kuma zan baki labarin duk abubuwan da suka faru" Ta yi masa shiru ta cika ta yi fam, kamar za ta fashe. Ya tausasa murya ya ce "Na san kin yi haƙuri, amma ina sake baki haƙuri, dan Allah ki saki fuskarki" "Ni ka rabu da ni, ka je ku lallaɓa matar so, da al'adarku ta yarda da ita, ni kuma ka sake ni ku kora ni ƙasarmu" Ta yi maganar har da ƙwallar baƙin ciki. Ya yi murmushi ya ce "Duk wata matar so a bayanki take Gimbiya Ma vie. Kin ci Agadez kin ci Nigeria" ta murguɗa masa baki, ya shammace ta ya yi kissing ɗin bakinta. **** Asal ce a gaban Sultan, da Matawalle da Sardauna, ga kuma Tafawa sai Imam Asadullahi, da Imam Hammad sai Mahmoudu. Matawalle ya ce "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya, muka neme ku a yammacin nan, bayan sallar magariba haka. Mun san za ku ji abin wani banbarakwai, amma mu ma haka nan ya zo mana. Duk ana kan dambarwar ɗa da Imam Hammad yake da shi, wani abu ya sake faruwa da dole mu yi muku bayani, domin babu yadda muka iya mu ma, sai dai mu na kan tunanin matakin da za mu ɗauka." Tafawa ya ce "Mai girma Matwalle, wannan kwana-kwanar ta yi yawa, ka yi mana bayani kai tsaye." "Kamar yadda ka yi ta bin diddigi a baya, tabbas Hammad ya yi rashin lafiya, ya kuma je Nigeria jinya. Asal na san abin da ki ka gani ya ɗaga miki hankali kina ta wasi-wasi. Ɗan da Hammad yake da shi, ba ɗan kowa ba ne face ɗan matar da ki ka kawo a matsayin kukunsa. Wannan kukun tasa matarsa ce" AREWABOOKS Wani irin nannauyan numfashi Asal ta ja, tana jin kamar daga shi ba zata sake jan wani numfashin ba. Gaba ɗaya sai ta kasa gane me ma ake son a yi mata bayani. Wace ce ma kukun? Take tambayar kanta. Tafawa ma sak ya yi, yana murza yatsun hannunsa, ya tsare su da idanu ɗaya bayan ɗaya, sannan ya numfasa ya ce "Ku na nufin Imam Hammad ya auri wata wadda ba ƙabilarmu ba, daga Nigeria har ta haifa masa wannan yaron da na gani?" Sardauna ya ce "Haka ne" Ya sake rausayar da kai ya ce "To ina fatan a wannan karon, za ku yi adalci dokar masarauta ta yi aiki a kansa, a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata." Sardauna ya ce "Tukuna dai, sai mun ga abin da hali ya yi, saboda yanzu hankalinmu na kan samun lafiyarsa" "Lafiya, wace irin rashin lafiya kenan yake fama da ita? Kuma me ya kai shi Nigeria? Kuma a kan me ya karya dokar masarauta?" Matawalle ya ce "Wannan duk abu ne da za ka ji daga baya, amma yanzu a kan wannan gaɓar muke, zuwa gaba kaɗan za mu duba abin da ya dace a yi" Wani irin kuka Asal ta fashe da shi ta ce "Hammad, abin da za ka yi mini kenan, ka munafunce ni? Ka cutar da ni, ka ajiye ni hoto ban haihu ba ka je ka haihu da wata. Saboda ka tozarta ni ba ma ka auri Buzuwa daidai ni ba sai wannan ƙazama mummunar yarinyar?" Tafawa ya ce "Rufe mini baki, mutuniyar banza uban waye ya ce ki je ki kawo ta gidan sarauta, a matsayin kukun mijinki, alhalin kin san ba haka dokar masarauta take ba?" Hammad ya kalli Asal ya ce "Ki yi haƙuri, na san na yi miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki haƙuri yadda al'amuran suka kasance ba wai da gangan na yi ba. Kin san babu yadda za a yi ina zaune haka kurum na ɗau jiki na tafi Nigeria na... "Ka yi mini shiru, babu wata magana da zaka faɗa na yarda da kai, maƙaryaci... "Hattara!" Matawalle ya yi mata tsawa. "Ko me ya yi miki, dole ki ambace shi da girmamawa kar ki kuskura ki faɗi wani abu mummuna a kansa, ko me ya yi kuwa. Dan haka ki kiyaye harshenki" Cikin kuka take cewa "Wallahi sai ka sake ni, ba zan zauna da kai ba, kuma na bar ka da Allah sai ka sake ni" Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Yarinyar kirki, na san za ki ji abin wani iri, amma babu abin da zai raba aurenki da Imam. Haryanzu mu na kan tattauna matakin da za mu ɗauka amma sai kin bamu cikakken haɗin kai kin nutsu. Haryanzu ke ce halattacciyar matar Imam da kowa ya san da zamanta." A fusace Tafawa ya tashi ya kalli Asal, da gaba ɗaya ta rikice take kuka ya ce "Ke tashi mu tafi" Ta yinƙura ta tashi ta yanke jiki ta faɗi. Hammad ya taso da sauri ya nufo ta, amma Tafawa ya ce "Kar ka kuskura ka taɓa mini 'ya" Ya kalli Asadullah ya ce "Zo ka ɗauke ta mu tafi" Hammad ya ce "Ba zai yiwu ba, ba zai ɗauke ta ba. Kar ya fara taɓa mini mata" "Ni ka ke gayawa kar ya fara taɓa maka mata?" "Ni nake da hurumin ɗaukarta, ko na taɓa ta ban yarda ya taɓa mini mata ba" Ya yi maganar yana tsare Tafawa da ido. Sardauna ya ce "Tafawa ko da an samu rashin fahimta, bai kamata a ce ka hana shi taɓa matarsa ba, sai ka gama wannan ɓaɓatun ita kuma ta baka kunya, ai ba a shiga tsakanin mata da miji. Bari a kira barori mata su zo su ɗauke ta, a kai ta ɓangaren Gimbiya Bilkisu" Ya ce "Babu wanda ya isa, ba wanda zai taɓa mini 'ya" Sultan ya ce "Umarni ne, a kaita sashen Gimbiya Bilkisu, idan ta farfaɗo ta ɗan nutsu sai a kai ta gida" Tafawa ya tsaya cak yana kallon Sultan cikin ƙunar rai. Ƙaninsa yana ba shi umarni kuma dole ya bi. ***** Wata kyakykywar matashiya ce ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune tana bawa jaririn Nono. A rikice ta ƙarasa da sauri tana faɗin "Sister kin farfaɗo Alhamdillah, Alhamdillah, Alhamdillah ala kulli halin. Barka da arziki sannu" Ta ƙarasa gaban gadon tana rungume Shukura. Shukura ma ta rungume ta, tana faɗin "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Ta kalli Shukura ta ce "Babu komai, ni dai na gode wa Allah da ya sanya ki ka farfaɗo ki ka tashi. Sannu 'yar uwa" Ta sake maganar cikin iyayi da kulawa. Ta kalli likktar da ta take ta ɗawainiya da Shukura, ta ce "Sannu da ƙoƙari doctor, Allah ya biya ki kema" Doctor ta ce "Ba komai, yi wa kai ne." "Yanzu kawo lambar wani a kira miki" Shukura ta ɗan yi shiru sannan ta ce "To" Ta bayar da lambar Sagir, aka saka a wayar aka danna kiran wayar" Shukura ta miƙa hannu, ta karɓi wayar. Muryar Yusra ce ta yi mata sallama, ta tsuke fuska ta ce "Ina Baban Haidar" Wata irin rikicewa Yusra ta yi, ta ce "Shukura ke ce? Ina ki ka tafi muke ta neman bamu ganki ba? Kina ina?" Sai Shukura ta ɗan yi saroro, jin yadda Yusra ta rikice da murna. "Ina nan, idan yana kusa ba shi wayar" A rikice Yusra ta sake cewa "Baya nan, ki gaya mini kina ina na zo na ɗaukko ki?" "A'a ina nan lafiya kalau, idan ya dawo ki haɗa ni da shi" Yusra ta ce "Baya nan, layinsa ya saka a wayata, ni ban san lokacin da zai dawo ba, ki gaya mini kina ina?" Kamar Shukura ta share ta katse wayar, sai kuma ta gaya mata. Tana can wani Asibitin kuɗi, a can wata local government a wajen Kano. Sannan ta ɗora da cewa "Amma kar ki gaya wa kowa mun yi waya da ke" Yusra ta ce "Har mamanki? Tana can hankalinta a tashe fa ita ma" "Eh har ita, kar ki gaya wa kowa, idan ya dawo ki haɗa ni da shi, ina Haidar? Yana lafiya?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido, cike da fargabar ko shi ma ya salwanta. "Yana makaranta, to kina lafiya cikinki ma yana nan lafiya?" Shukura ta ce "Eh, lafiya kalau" "To dan Allah kar ki je ko ina daga nan gurin" "Tom" Ta faɗa a taƙaice. Matar ta kalli Shukura ta ce " 'Yar uwakki ce?" Ta girgiza kai ta ce "Abokiyar zamana ce" "Allah sarki, gaskiya daga ji tana sonki sosai ji yadda ta rikice" Shukura ta yi murmushi kawai. Sai dai ta tafi tunanin ta yadda za ta fuskanci Duniya ta sanar da cewa mahaifinta shi ke da alhakin sace ta, da salwantar mata da ɗa, da kuma mummunan zaluncin da ya yi wa mahaifiyarta da wadda yake tare da ita yanzu. Ita gaba ɗaya ma ba ta san ta ina zata fara bayanin miyagun ayyukansa a idon duniya ba a matsayinsa na mahaifinta. **** Nana tana son ta ga Sarkin Baka, akwai maganganu da dama a bakinta, amma ƙiri-ƙiri Sayyid ya hana. Ga shi ba ta da damar fita idan ba umarnin hakan a ka ba ta ba, tana son sake ganin Nene ma amma babu halin fita. Zaman Nana a guri ɗaya, ba fita daga ci sai sha da kwanciya, ya sanya ta ƙara yin kyau, ga lafiyayyen Abinci. Sai dai haryanzu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya ne ba ta da shi. Tana zaune tana zancen zuci, har bacci ya fara sace ta, ta ji an taɓa ta. Ta tashi da sauri tana kallonsa. "Har kin fara bacci ba ki jira ni ba?" "Eh, na zata a gurinta zaka kwana ai" "Idan ma na kwana a can ɗin, ai ke ki ka ja, kin daina damuwa da ni, ko tausayina ba kya ji" Ta kwaɓe baki ta ce "Garin tausayinka, na kwashi wani cikin na haihu ku kaɗa ni Nigeria" Ya ɗan marairaice murya ya ce "Haba Ma vie, Sayyid ɗinki ne fa, ke ba kya kewar ɗumin jikina ne" Nana ta kalle shi ta ce "Wane ɗumin, ai yanzu jikinka ba wani ɗumi idan ba azaba ba" Ya rausayar da kai ya ce "Da ɗin ma akwai, kuma kina jurewa" Ta girgiza kai ta ce "Amma bai kai na nan ba" "To ni ki bani Sanyin dan Allah" Ta tsuke fuska ta ce "Sayyid ka daina taɓa ni dan Allah, ni ba ƙin ka nake yi ba, amma ka tausaya mini inga yadda al'amuran za su kaya tukuna, ka san dambarwar da ake ta yi haryanzu ni tsoro nake ji kar a yi mini yadda aka yi wa Nene" Ya kwanta a gefenta ya numfasa ya ce "Ta baki labari kenan?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "In sha Allah a kanmu wannan muguwar al'adar za ta zama tarihi, dan ba zan yarda na rabu da rayuwata ba" Nana ta zumɓura baki tana kallonsa, ya ce "Da gaske nake Ma vie" Ya yi maganar sumbatar hannunta. Ta ɗan lumshe ido tana kallonsa. Ya ce "Tashi mu je" "Ina?" "Zo mu je ki gani mana, ko zan cinye ki ne" Ya yi maganar daga kwnace yana ci gaba da kallonta. Ta tashi zaune tana faɗin "Na sani, ko cinye nin zaka yi. To ka tashi mana kuma ka kwanta" Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga yana yi mata wannan kallon yana shafa bayanta. Ta ce "Yane? Ko in kwanciyata ne?" Ya ce "Allah sarki Hammad bawan Allah, kowa baya so na" Ya yi maganar yana tashi zaune. Nana ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa gashinsa ta ce "To dama wa zai so rigimamme" "Allah sarki, Ina kewar Ma vie ɗina ta da, mai so na da tausayina, ko motsi na yi hankalinta yana kai na, Allah sarki Asmyna ta Nigeria, soyayyarta ta daban ce a cikin zuciyata" Nana ta ce "Allah sarki Sayyid ɗina na Nigeria, da baya ganin kowa a duniyarsa sai Asmynsa kaɗai. Mai kallona da idon tausayi, wanda nake iya gano ƙaunata da tausayina a idanunsa, mai yaba duk wani motsina da ƙoƙarina. Ina kewar Sayyid ɗina na Nigeria" Ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Wannan Imam ɗin na Agadez fa?" Ta kalle shi ta ce "To ga shi nan dai, ban ma san inda ya dosa ba" Ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki. Ya yi dariya ya ce "Haka za ki ce ko? Ni ɗin ko? Sayyid ɗinki ne fa" "Sayyid nawa, Hammad na Asal" Ya ce "Wow, sake faɗar sunan na ji?" Ta noƙe masa kafaɗa. Ya ce "Shikenan ma, dama Asal ta fiki iya faɗar sunan" Ta harare shi, tare da sauka daga kan gadon. Shi ma saukkowar ya yi, ya wuce gaba ta bi shi a baya. Daga bisani ya jira ta, suka tafi tare. Ƙofar nan da suke bi su fita hanyar saharar nan, suka shiga, sai dai wannan karon canza akalar hanya, zuwa wata matattakala. Tsoro ya fara kama Nana, amma ta kasa magana, sai rarraba ido kawai da take yi. Wata ƙofa suka iso, ya ce "Kin san ina ne nan muka ɓullo?" Ta ce "A'a" "Gidan tarihi ne na masarautar Agadez" Nana ta ce"Wannan dutsen da nake hangowa?" Ya jinjina kai ya ce "Eh nan ne" Wani takurarren tsoho suka tarar a bakin ƙofar shiga gurin, yanayin ƙofar ya bayyanar da tsufan da ta yi a Duniya. Tsohon ya miƙe jikinsa na rawa, ya risuna yana gaida Imam Hammad. Hammad ya amsa cikin girmamawa. Nana ta ɗan tsaya ta yi shiru, tana nazarin ƙamshin turaren da ta ji a gurin, kamar ta taɓa jin sa a jikin wani, sai dai ba ta ga alamun a jikin wannan tsohon wannan ƙamshin yake tashi ba. Ya buɗe musu ƙofar, suka shiga. Ya kunna makunni, sai ga hasken fitilun ya haske gurin. Ya ci sunansa gidan tarihi, Nana ta faɗa a zuciyarta. Wani irin ƙaton guri ne mai kama da falo, da ƙofofi kashi-kashi a gurin. "Wannan gurin kamar Libraryn Ƙaisar saboda tsufa" Ta ɗaga kai tana kallon tsawon gurin, jikin dutse ne aka rarake aka yi wannan ginin da ƙofofi. Kanta ne ya sara ta yi shiru tana tunanin kamar ta san gurin nan, ta taɓa ganin gurin. A take ta fara jiyo wannan ƙamshin da take ji idan ta gan su a wannan ɗakin tare da Sayyid. Hammad ya kama hannunta ɗaya, ya buɗe ƙofa suka shiga, a take ta sske rikicewa, jikinta ya hau rawa ta kalle shi ta kalli ɗakin, ta sake kallonsa ta kalli ɗakin. "Sayyid wannan ɗakin" "Ɗakin da muke zuwa ko?" Ya yi maganar yana yi mata murmushi. Ta kalli gadon, da mudubin ɗakin, komai irin na da sosai da sosai, sai dai yanayin kayan ya nuna, wanda suka yi amfani da ɗakin masu faɗa a ji ne. Ta dafe kanta da take jin wata irin ƙara a ciki, ga ƙamshin turaren nan ya cika ilahirin gurin. "Sayyid wai ya aka yi haka ta faru a zahiri? Kar daga baya ka ce mini mafarki ne, ka fita da ni daga gurin nan kar na haukace Sayyid" "Ba za ki haukace ba, ki tsaya na yi miki bayani" Wani irin jiri ne ya din ga ɗibarta, ta din ga ganin wasu irin halittu na shawagi a ɗakin, ga hayaniya da suke yi cikin sauti mara daɗin ji. Jikin Nana na tsuma ta ce "Ka fita da ni daga gurin nan, wasu abubuwa nake gani ka fita da ni" "Babu wani abun tsoro fa a gurin nan, ki nutsu zan gaya miki komai daki-daki ciki har da abubuwan da suke shige miki duhu a kaina" Ayshercool 08081012143 89 LITTAFIN KUƊI NE 1K 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 A hankali Nana take ƙoƙarin buɗe idanunta, zuciyarta cike da matsanancin tsoron, da rabon da ta ji makamancinsa har ta manta, tare da fatan Allah ya sanya ta farka daga wannan mafarkin mara kan gado. A hankali take jin numfashin sa na sauke a fuskarta. Ta buɗe idonta sosai ta sauke a kan fuskarsa da ya tsare ta da idanunsa, sai dai kan ta yi wani yinƙuri, ƙamshin ɗakin ya mamaye mata hanci, hakan ya sake tabattar mata da ba mafarki ba ne ba zahiri ne. Ta zabura da sauri ta gansu a kan gadon tare ita da shi a cikin ɗakin dai. A gigice ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon cikin matsanancin tsoro, tana zazzaro masa ido. Sayyid ya riƙe ta ya ce "Dan Allah ki daina tsorata kanki, ki nutsu mana. Babu wani abin tsoro a gurin nan" "Ta yaya zan nutsu, kana caza mini ƙwaƙwalwa, na ma rasa me yake faruwa, kuma sannan ka ce babu abin tsoro a gurin" Ya ce "Zaki fahimci abin da yake faruwar, amma dole ki nutsu, kuma ki saurare ni"  Ya ɗago yatsunsa ya kalli zobunan hannunsa, da space ɗin guda ɗayan sannan ya dubi Nana ya ce "Abubuwan da ki ke gani a tare da ni, su na da alaƙa da wannan zobunan na hannuna. Nana ta kalle shi ta kalli zobunan cikin rashin fahimta. "Ina Zoben da na baki, mu na Nigeria?" Ba ta ba shi amsa ba, kawai ta hau ƙoƙarin tashi ta bar gurin. Ya din ga kokowa da Nana, amma idonta ya rufe, hanya kawai take nema ta gudu ta bar gurin. Dan gani take idan ta ci gaba da zama zaucewa za ta yi. Sai da ƙyar ya  lallaɓa ta ya ce "To shikenan, mu je na mayar da ke mu tafi, tun da ba za ki nutsu ba" Ya riƙo hannunta, sai dai duk a tsorace take, su na fita daga wannan ɗakin ya shiga da ita wani ɗakin. Gurin duk an yi wearing ɗin fitilu, sai dai da ya kunna fitilun gurin ya yi haske. Ta ƙara razana da ganin gurin. Komai na zamanin da ne sosai da sosai. Wasu zane-zanen mutane ne a manyan frames a kafe, har zuwa kan wasu hotunan da suke dishi-dishi na Black and white na da, zuwa kan hotunan da ake iya gane mutanen jiki sosai wanda ya nuna na baya-baya ne hotunan sai hoton Sultan da ya fita fes. Ɗaya bangon Hoton Sultan ne shi ma, da hotunan Imam Imam na Agadez a jere. Sai dai mutanen na jikin zanen da na hiton duk masu kyau ne, kuma yanayinsu ya nuna daga zuriya ɗaya suke. Sai kuma gefe  wasu ƙananan hotunan a wani ɓangare na ɗakin, da suke nuna yaƙe-yaƙe, da yanayi na zamanin bayi. Hammad ya ce "Wannan hotunan da ki ke gani, tun daga kan na zanen nan, hotunan wasu daga cikin sarakunan da suka yi gwagwarmaya gurin kafa masarautar Agadez ne. Waɗannan kuma, wasu daga cikin bayi ne, da suka yi wasu laifuka na rashin kyautawa, wanda tun daga zamanin har kawo yanzu, duk wanda aka haifa a zuriyarsu bawa ne, ciki har da wannan dattijon da yake gadin ƙofar gidan tarihi na Agadez. Idan ya mutu dole zuriyarsu za su bayar da wani wanda zai ci gaba da wannan aikin. SHEKARUN DA SUKA GABATA. Kamar yadda Nana ta fara karantawa, a cikin littafin Ƙaisar. An sha gwagwarmaya da yaƙe-yaƙe tsakanin 'yan uwa da suke ciki ɗaya domin samun damar ɗarewa karagar mulki. Kowane Sultan da ya zo karaga, akwai kalar mulkin da yake shimfiɗawa, wani al'ummarsa su samu sassauci, wasu kuma su shiga halin matsi. Sai dai hawa kan karagar ba shi ne aiki ba, ci gaba da ɗorewar mulkin, saboda a kowane lokaci ana iya samun masu kawo maka farmaki, a haɗa kai da na kusa da kai, a yi maka juyin mulki. Sannan tsugunno ba ta ƙarewa duk wanda ya zama Sultan ba, domin bayan kare kansa dole ya kare iyalinsa, idan ba haka ba 'ya'yansa tun da  ƙuruciya za a yi ta kashe su, ana gwara kansu da kwaɗaita musu kwaɗayin mulki, ta yadda idan ba su kashe junansu ba, za su iya kawar da uban dan su hau karagar mulkin. Ƙasar Agadez Allah ya albarkace ta zinari, wanda tun a wancan lokacin, shi ne babban dalilin da ya sanya kowa ke kwaɗayin ya hau mulki, aka yi ta yaƙe-yaƙe ana zubar da jini, tun da aka fuskanci zinaren abu ne mai matuƙar daraja a lokacin. Suka ci gaba da gudanar da yaƙe-yaƙe su na mamayar mutane su kafa Daular su. Ana tafe da wannan mulki, wanda mai ƙarfi ya kan kifar da na kan mulkin ya ƙwata, ya kashe na kan karagar, har aka zo kan mulkin Sultan Azhar. Zuwan Sulta Azhar ya sauya da yawa daga tarihin Agadez, kowane Sultan yana amfani da wani amintaccen boka, da yake yi masa ta'amalli da Aljanu, domin sanin abin da zai faru da ba shi wata kariya ta mussaman. Sarki Azhar ya gagari duk magautansa, yana da tarin mabiya. Azhar yana cikin manyan kwamandojin yaƙin sarkin wancan lokacin. Kakansa ya taɓa zama Sultan, aka yi masa juyin mulki aka rufe shi a kurkuku. Aka kame 'ya'yansa aka mayar da su fursinoni ciki har da mahaifinsa lokacin shi Azhar yana ƙarami Nono yake sha. Bayan da ya tasa bai fi shekara sha biyu ba, aka kame shi, aka sanya shi cikin sojojin yaƙi. Duk zuriyarsu aka mayar da su bayi, ya tashi da wannan ciwon a ransa, ya zama gawurtaccen Sadauki da ake ji da shi, saboda ƙarfinsa. Ashe yaƙin sunƙuru yake shiryawa Sultan ɗin lokacin ya shammace shi ya kifar da shi, ya ɗare karagar mulkin. Ya kame 'ya'yansa ya kashe su, ya kashe matan Sarkin, har ma da sauran 'yan uwansa da yake tunanin za su iya tasowa su nemi su karɓi sarauta. Ya din ga yaƙar sauran ƙasashen da ke kusa da Agadez, yana mayar da su ƙarƙashin ikonsa, ya kame baƙaƙen buzaye ya mayar da su bayi. waɗanda suka rage a 'yan uwansa wanda su ma sun tasa, yake ganin za su iya kawo masa tarnaƙi ya sanya aka gina wata irin kurku a ƙarƙashin ƙasa, duk aka zuba su a ciki. Wannan cikin dutsen da suke ciki, Bayin zamanin Sarki Azhar ne suka rarake shi, suka gina katafariyar fadarsa, kuma a cikinta aka gina kurkun da ya zuba 'yan uwansa. A cikin kurkukun nan, idan ka mutu a ciki zaka ruɓe ka lalace, a cikin rayayyu za ka gama ruɓewa babu mai fita da gawarka. Babu kalar azabar da ba a ganawa fursinoni a wannan kurkuku. Bayi kuma su na aikin ƙarfi gurin haƙo zinare, da aikinsa a kai wa Sarki Azhar a sarrafa a yi kayan more rayuwa ko a sayar ga maƙwabtan ƙasashen, ko kuma a yi musayarsu da wani abu mai muhimmanci. Ya kame bokayen ƙasar gaba ɗaya, aka haƙa rami aka cinna musu wuta, a cikin wannan fadar tasa. Boka ɗaya ya bari, wanda shi ne ya tallafa masa ya zama Sultan, wanda shi ma iyayensa na cikin amintattun kakan Azhar da ya yi sarauta, kan a yi juyin mulki a kashe su. Bokan nan ya mallaka wa Azhar gangan manyan Aljanu da suke taimaka masa gurin tafiyar da mulkinsa. Duk wata kafa da zai iya bari da za a iya amfani da ita gurin kawo ƙarshen mulkinsa ya toshe ta. Sai da ya fara manyanta, sannan ya auri wata kyakykywar matashiyar budurwa. Ta fara haifa masa 'ya'ya maza. Allah ya ɗora masa tsananin ƙaunar yaran nan kamar ransa. Sanin a kowani lokaci, ana iya amfani da wata dama a cutar da su, ya sanya ya killace su. Ya sanya bokansa sadaukar musu da wasu Aljanu da za su din ga yi musu hidima. Ya sanya doka a kan ko bayan ransa, babu wani wanda zai yi sarauta idan ba a cikin yaran nan ba. Duk dokar da ya kafa, babu mai iya yi masa musu. Babban abin da yake bawa al'ummarsa mamaki bai wuce yadda duk wanda ya fara ƙoƙarin ƙulla wani abu a kan ya kawar da sarkin nan ba, sai dai a wayi gari ya zama gawa. Sultan Azhar ya shimfiɗa mulki da dokoki yadda yake so, ya tara dukiya da haraji, da kuma arzikin zinarin da Agadez take da shi. Duk da haka ya kamanta kawo ci gaba a lokacin, a wani abin talakawa sun samu sassauci, an samu ci gaba a fannin cinikayya a lokacin, sai dai laifi ƙalilan sai a kai ka kurkukun Sultan Azhar wanda har abada babu wanda zai sake ganinka, idan kuma ya so sai a gadar wa zuriyarku da wata hidima ga fada da kai da iyalinka har abada. Sultan Azhar bai bar mulki ya mutu ba, sai da ya tsufa sosai da sosai, yaransa sun tasa sun zama matasa. Bayan ya mutu aka naɗa babban ɗansa a kan karagar mulki. Shi ma ya ɗora daga inda mahaifinsa ya tsaya, kuma shi bai samu tangarɗa da 'yan uwansa ba, saboda ya janyo su cikin harkar mulki. Sai dai mahaifiyarsu ce ta je ta samu bokan mijinta, ta gaya masa kokenta a kan ba ta son kan yaranta ya rarrabu, a kan mulki, ko wani ya kashe wani. Ya ba ta tabbacin hakan, ta hanyar yi mata surkulle daban-daban a kan yaran nata. Kasancewar komai nufin Allah ne, da wanda ya yi addu'a, da wanda ya bi hanyar da ba daidai ba ma, yana iya amsa wa kowa idan ya so, Allah ya taimake ta ba su kashe junansu a kan Mulki ba. Shi ma ya yi tsawon rai a kan karagar mulki, sai dai Aljanun nan sun ci gaba  da bibiyar zuriyar 'ya'yan sarakunan, su na ba su kariya. Bayan mutuwar wannan Sarkin da aka zo naɗa sabon Sarki, a nan aka samu dambarwa, sai da aka yi hatsaniya aka so yin ƙaramin yaƙi daga bisani aka ɗora ɗaya daga jikokin Azhar a kan Mulki wato Sultan Sadam. Har a lokacin matar Azhar tana raye haka Bokansa. Ba ta da wani abokin shawara da ya wuce wannan boka. Ta fuskanci kalubale sosai da sosai, saboda yadda magauta suka sako ta da 'ya'yanta gaba da son tarwatsa mata iyali, dan a banƙara Sarautar ta bar gidansu. Bayan hawan jikanta karagar mulki, a lokacin Bokan nan ya mutu, ɗansa ya gaje shi. Shi ma ya samu kyakykywan kusanci da Sultan Sadam a lokacin. Bokan ya ba shi shawarar mallakawa 'yan'yansa Aljanu, domin su ƙara samun tsaro daga duk wani farmaki. Sarki ya yi shawara da bokan, a kan yana son duk yadda za a yi, ya zamana kar sarauta ta bar gidansu, kar wani daga cikin 'yan'yan 'yan uwansa ko 'yan uwansa su yi sarauta. Sai ya fara da kafa dokar, duk wanda ya haura shekara talatin da biyar, babu shi babu sarauta a Agadez, sai dai ka na kan mulki ka kai wannan shekarun. Kamar yadda ya zo a tarihi da kakansa, da Sultan ɗin da ya gabace shi, duk ba su kai shekaru talatin da biyar ba suka hau kan karagar mulki. Bokan nan ya ƙera masa zobuna da azurfa kowanne yana da mallakin Aljani a jikinsa, da wannan zoben za su iya sarrafa aljanun nan yadda suke so. Tafi a hankali bayan shuɗewar zamaninsa, abubuwa suka ci gaba da juyawa, kowane Sarkin da zamaninsa da kuma yadda yake nasa mulkin. Sai dai Mallakar zoben nan ya zama sabon tashin hankali, dan daga bisani sai ya zamana wanda yake da zoben nan, shi ne kaɗai zai iya zama Sarki. Sai faɗa ya koma kan kowa na son ya mallaki zobe cikin 'ya'yan Sarakuna. Dan sai Zobunan suka zama gado na kowane gida, daga cikin 'ya'yan Sultan ɗin da ya sanya aka ba shi zobe. A hankali ya zama doka, duk wanda zai zama Sultan, sai ya zamana bai kai shekaru talatin da biyar ba, kuma sai ya zamana ya mallaki wannan zoben. Duk wanda ya mallaki zoben, yana da damar sarrafa aljanin da aka ɗora wa alhakin ɗawainiya da mamallakin wannan zobe, da dole sai ya zamana jinin zuriyar Sultan Azhar sannan zai yi masa hidima." Hammad ya numfasa ya fara nuna mata hotunan nan da bayaninsu ya ce "Kamar yadda yake a babban kundin adana tarihin masarautar Agadez, wannan shi ne Kakan Sarki Azhar, ga mahaifinsa, shi ma ga hotonsa, ga 'ya'yansa ga waɗanda suka yi sarauta a cikin 'ya'yansa. Wannan ita ce Gimbiya Saira, ita ce matar Sultan Azhar, da tun da ya mutu zuriyarsa ce kawai suke Mulkin Agadez ba a sake samun wanda ya ƙwaci mulki daga hannun zuriyarsa ba. Nana ta tsare shi da ido, har sai da ya tsargu ya ce "Lafiya kuwa?" "Sayyid, kana nufin ka na ta'amalli da Aljanu kenan, ta hanyar yin amfani da wannan zoben?" "Meyasa za ki yi tsalle ki tafi ƙarshen labarin? Ki jira na kai da kaina mana" AREWABOOKS Ta ɗan nutsu tana sunkuyar da kai. Sai dai ya yi shiru bai ci gaba ba. "Yaya ka yi shiru kuma?" "Ba na son na ci gaba ki yanke mini hukunci ne haka sama ta ka" "Ka yi haƙuri ba zan yi haka ba, in sha Allah na yi shiru har ka kammala" Ya kamo hannunta, suka fito daga cikin wannan ɗakin, ya nuna mata wani ɗakin ya ce "Wannan ɗakin, shi ne inda gawarwakin galibin tsofaffin sarakunan Agadez suke, na kusa da shi kuma ɗakin da a kan binne manyan masu faɗa a ji. Ba zan buɗe miki ba dan za ki iya tsorata. Ya buɗe wani ɗakin ya ce "Nan ɗakin kuma, shi ne ɗakin da ake sarrafa zinari, a cikin fadar Sultan yake. Duk nacin mutum bai isa ya saci zinare ya fita da shi ba, idan kuwa aka kama mutum a kurkukun nan zai mutu. Wannan ɗakin kuma, a ciki duk wani tarihin yaƙe-yaƙen da Agadez ta yi yake. A nan ake adana duk wani kayan Sultan muhimmai, irin su takalmi, kayan yaƙi takobi da sauransu. Shi kuma wancan ɗakin, wasu daga cikin sassan ƙashi. jikin manyan masu laifukan da aka kashe ne, da Sarakunan da aka yi wa juyin mulki aka kashe su. Zamani ya ci gaba da jujjuya, hasken addinin Musulunci ya fara bayyana, duk da nisan da Sarakunan ƙasar suka yi ba sa jin kira, dan hatta turawan mulkin mallaka ba su yadda sun kassara musu sarauta da tattalin arziki ba. Tasirin addinin musulunci ya sanya aka fara rage aikata wasu abubuwan, amma ba a daina wasu ba. Tsaface-tsaface da ta'amalli da Aljanu ba a daina su ba, ga su mutane masu tsatstsauran ra'ayi a kan al'adunsu, da tsafi. Domin ma'abota sarauta sun yarda da cewa, duk wanda ya zauna zai ga zama, mussaman yadda zuriya daban-daban suke farautar kujerar ko ta halin ƙaƙa duk da tushen ɗaya ne, amma kowa burinsa ya zamana Mulkin a gidansu yake. Sai dai dokar Sultan Sadam tana nan, ta sai wanda bai kai shekaru talatin da biyar ba ne zai yi mulki, sannan sai wanda yake da zoben nan shi ne zai yi mulki. Sai dai a baya-baya, aka samu ɓarkewar faɗa a tsakanin zuriyar Azhar, har aka yi ƙaramin yaƙi, suka zubar wa da juna jini, abin da ba a taɓa yi ba a tarihin masarautar. Abin a ya girgiza al'ummar ƙasar mussaman ma'abota sarauta, har suka fara tsoron ko ƙarshen masarautar ne ya zo, aka samu rikicin da ta kai ga 'yan uwan junan da tun zamanin iyaye da kakanni ba su taɓa samun rabuwar kai da ta kai ga amfani da makami ba sai a wannan karon. A lokacin zuwan ilimin addini da na zamani, da kuma wannan hatsaniya da ta faru, sai aka yi wa dokokin masarautar Agadez kwaskwarima. Domin samar da zaman lafiya da ƙara ƙarfafa masarautar sai aka ce sai wanda yake da wasu nagarta da wasu abubuwa masu muhimmanci shi ne zai zamana yana riƙe da zoben a kowanne gida da suka gaji zobunan. Sannan aka ƙara yawan zobunan suka zama uku, kowane gida su na da anihin zoben tambari wanda shi ne mai ɗauke da sihiri da aljanu sai kuma sauran biyu, sannan da abin hannun na tagulla. A zamanin Sultan Ansar, aka yi duk wannan sauye-sauyen, ya ƙirƙiro ƙaramar majalisar masu ɗauke da wannan zobunan, yadda za a din ga shigar da su cikin sha'anin mulki, da koya musu yadda mulki yake. Aka yi yarjejeniya a kan iya wannan masu zoben ne za su iya zama Sultan, sannan a cikin su duk wanda ya haura shekara talatin da biyar za a karɓi zoben daga hannunsa a nemi wanda ya cancanta a ba shi. A lokacin aka ce duk wanda zai mallaki zoben, domin zama ɗaya daga Imam, kamar yadda Sultan Ansar ya yi musu laƙabi da shi, dole ya zamana yana da ilimin addini, ya haddace kaso saba'in na tarihin Agadez, yana jin wasu yarurrukan bayan yaren su na uwa, da kuma hausa. Domin ya zamana mutanen Agadez su na jin Hausa sosai, saboda yanayin cinikayya da ke tsakaninsu. Sai dai har a lokacin akwai baƙaƙen al'adunsu da ba su canza ba, kuma ba a yi wa kwaskwarima ba, ba a daina azabtar da mutane a kurkukun nan ba. Sannan su na ƙyamar ɓakar fata, ta kowace fuska sun daƙile baƙaƙen buzaye, sun bautar da su, sun hana su motsi, dan kar su yi wani yinƙuri su yi musu juyin mulki. Ko a cikin kuyangi, ba a yarda basarake ya yi amfani da baƙar buzuwa ba, saboda kar su haɗa zuriya da su, su sanya ran za su samu 'yanci wataran. Kuma baƙaƙen bayi sun taka muhimmiyar rawa gurin gina daular Agadez, da haɓaka tattalin arzikinta, saboda juriyarsu da aiki tuƙuru. Sun daga lokacin da suka yi 'yanci, za su iya ajiue aikace-aikacen, kuma su na tsoron su ce za su rama bautar da su da aka yi tun zamanin iyaye da kakanni alhalin kakannin kakanninsu, da su aka kafa Daular kuma sun taɓa mulki. Hukunci na iya zama na kora, zaman kurkuku koma kisa, ga duk basaraken da aka kama, da aure ko mu'amala da baƙar buzuwa. Haka duk cinikayyar da suke yi da sauran ƙabilu, ba su yadda auratayya ta haɗa su mussaman da baƙar fata, nasu ma ba su aura ba balle na waje. Sannan yana daga sharuɗɗan da bokaye suka kafa musu, muddin suka yi auratayya da baƙaƙe, ana iya kawo ƙarshen mulkinsu, kuma baƙaƙe ka iya yin galaba a kansu, su ƙwace sarautar baki ɗaya. Zamanin Sultan Ansar bayan tabattar da waɗanann dokoki, shi ma yana da zobuna da abin hannun tagulla na waɗanda za su zama Imam. Lokacin da aka tabbatar da waɗannan dokokin, aka yi musu kwaskwarima, Sultan Ansar yana da tarin 'ya'ya, yana daga cikin dalilan da ya sanya shi ƙara inganta tare da gyara wasu dokokin saboda yana kwaɗayin ɗansa Jalaludeen ya zama Sultan a bayansa, saboda kusan duk abin da aka lissafo yana da su. Kuma ya lura akwai zalamar son Mulkin sosai a wasu daga cikin 'ya'yansa, mussaman babban ɗansa Saifuddeen. 'Ya'yan suka yi ta zuba ido, domin su ga wa zai ba wa zobunan nan, amma ya ƙi bawa kowa, sai daga bisani ya damƙa wa Jalaludeen, ya nemi sauran gidajen da suke da zobunan, su ba wa waɗanda suka zaɓa, a kafa majalisar Imam. Hankalin Saifuddeen da mahaifiyarsa da sauran 'yan uwansa ya yi mummunan tashi, ganin ya ɗauki zobunan tambari ya ba wa Jalaludeen, duk da ga yayyensa. Sai dai maimakon a samu Imam shida, sai aka samu biyar aka rasa inda sauran zobunan suke. Hankalin Saifudeen ya ƙi kwanciya, ya tashi hankalinsa da shi da mahaifiyarsa da wanda suke ɗaki ɗaya, a kan lallai su san yadda za su yi, ko dai a karɓe zoben nan daga hannun Jalaludeen, ko kuma a kashe shi. Sai dai suka fahimci karɓe zoben nan, ba abu ne da zai yiwu ba, saboda ya riga ya mallaki Aljanun da aka wakilta tasrifi da zoben. Duk wani Imam da yake Agadez, askin gashin kai ya haramta a gare shi, haka zalika barin gashin kansa ya haramta. Sannan babu su babu baƙaƙen bayi, a matsayin kuyangi. Sannan akwai nau'in abincin da ba za su ci ba. Bayan majalisar Imam ta kafu, da yawa sauran zuriyar, sun shiga taradaddin ina ɗaya zoben ya shiga?. A dole Saifudeen ya ɓoye hassadar da yake yi wa ɗan uwan nasa, ya ci gaba da ƙoƙarin ganin bayansa ta ƙarƙashin ƙasa. Ya din ga bin bokaye, har da na wata ƙasar a kan a haukata ɗan uwan nasa, ko ma a kashe shi, saboda shi ne ya fi dacewa da matsayin da yake kai, amma abu ya ci tura. Wataran Sultan Ansar ya kira Imam Jalaludeen ya ce masa "Ka Imam Jalaludeen, kana daga cikin manyan dilalan da ya sanya, na dage a kan canza wasu daga cikin dokokin Agadez, wanda za su iya taɓuwa. Iyaye da kakanninmu sun tafka kura-kurai, kura-kuran da yakamata a ce mun yi wasu sauye-sauyen da yakamata al'umma su samu sassauci. Sai dai kai nake ganin zaka iya kamantawa wataƙila ko bayan raina. Ragowar zoben da ake nema, yana gurina, idan Allah ya yi ka zama Sultan a Agadez kar ka  danƙa shi ga kowa, sai mafi cancanta. Na san da duk farmakin da ake kawo maka saboda damar da ka samu, amma ka yi haƙuri ka daure. Sannan zan ci gaba da sanya wa a yi maka duk wani abu na kariya da yakamata. Zan sanya a ƙara sadaukar maka da wasu daga cikin manyan hadiman aljanuna, domin ka samu cikakkiyar kariya. A lokacin an yi ginin zamani, na gidan Sultan, an baro tsohuwar fada ta cikin dutse da ake gudanar da mulki a cikinta. A zamanin Sultan Ansar, ya samu zaɓaɓɓu, aka gina ɗakuna-ɗakuna, a cikin sabuwar masarautar, da hanyoyin tserewa daga cikin gidan, idan an samu farmaki. Saifuddeen dai bai haƙura ba, ya haɗa kai da matarsa, ya aura wa ƙanin nasa ɗaya daga cikin ƙannen matarsa Gimbiya Bilkisu.  Saifuddeen ya din ga shiga yana fita, dan kar Jalaludeen ya zama Sultan, ya haɗa kai da wasu daga cikin Imam na majalisar lokacin, da ziga su kan cewar lallai su dage, su yi ƙoƙari su karɓi sauratarsu, mulki ya dawo hannunsu. Masu kwaɗayin mulki suka din ga yadda da zigarsa, wasu kuma suka din ga yi masa kallon ya za a yi ya nemi sarauta ta bar gidansu. Ya din ga ziga su ɗaya bayan ɗaya, ba tare da wani ya san yana ziga wani ba. Sannan ya koma ya din ga ziga sauran 'yan uwansa, a kan kar su kuskura su yarda su bari, Jalaludeen ya zama Sultan, alhalin duk ga su suna gaba da shi. A kwana a tashi, Sultan Ansar ya koma ga mahaliccinsa, babu ciwo ba komai, ya yi sallar magariba, ya yanke jiki ya faɗi sai gawa. An shiga cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, aka yi masa sutura, sai dai manyan 'yan majalisar Sultan na lokacin, ba su bari an wayi gari ba, suka damƙawa Imam Jalaludeen tagullar da kambun Sarautar Agadez, kamar yadda ya bar wasiyya. Sai dai a tsakaninsu ma 'yan majalissar sai da aka so a samu rarrabuwar kai, aka nemi a yi ƙaramin yaƙi a cikin daren. Babban na kusa da Sultan, ya sanya aka je aka ɗaukko masa Imam Jalaludeen, wanda ya san tun da Sultan ya mutu a kowane lokaci za a iya kashe shi. Abin da ba su sani ba shi ne, tun Sultan Ansar yana kan karagar mulki, suke tsara komai da shi da babban amininsa Matawallen Agadez, wanda shi ma duk zuriyar Azhar ne, sun haɗa kakanni. Aka yi ginin ta ƙarƙashin ƙasa, daga sabon gidan Saruta, zuwa tsohon gidan Sarauta, da aka mayar da shi gurin adana kayan tarihi na Agadez. An narka dukiya mai yawan gaske, gurin gina sabon gidan nan, saboda yanayin ƙasar sahara. Da haka ya saka aka ɗaukko masa Imam Jalaludeen, aka biyo da shi ta ƙarƙashin ƙasa, zuwa gidan tarihi, a gidan tarihin ma, cikin kurkukun ƙarƙashin ƙasa, a nan aka ba shi wannan kambun. Cikin kuka Sultan Jalaludeen ya ce "Yaya za a yi ina cikin jimami da alhinin rashin mahaifina, amma ku ta naɗin sarauta ku ke yi, ni ba zan iya karɓar wannan kayan ba" "Dole ka karɓa, ya kai Sultan Jalaludeen Ansar, wannan wasiyyar mahaifinka ce, da ya nemi muddin mu na numfashi a cika masa ita, tun kan a binne shi ya nemi a naɗa ka Sultan a Agadez. Ka zuba ido wayewar gari da an binne mahafinka, yaƙi zai nemi ya ɓarke a Agadez, abin da ba a son faruwarsa a zuriyarku. Dan haka muddin ka na son masaruta ta ci gaba da tsayawa da ƙafafuwanta dole ne ka yi haƙuri, sai dai a wayi gari da sabon Sultan." Haka su ka din ga tausar sa, da ba shi baki har ya yi haƙuri. Sannan suka ba shi wata ƙaramar jakar fata, wadda ta ɗara laya girma, amma ba ta kai girman a kirata jaka ba. Suka sanar masa tun Sultan yana raye, ya sanya bokansa ya yi masa ita, domin tsari da kariya daga miyagu. Kuma a matsayinsa na Sultan, zai iya amfani da ita, gurin sarrafa aljanun gidan Sarauta. Can gidansa kuwa tuni har an kame wasu daga cikin 'ya'yansa, ana ta nemansa ruwa a jallo, an tattare matansa an kame. Sai dai ko sama ko ƙasa aka neme shi a ka rasa. Washegari da sassafe tun kan a binne mahaifinsa aka wayi gari a kan ganshi an kan karagar Mulkin Agadez da duk wani abu da yake nuna shaidar shi ne Sultan a Agadez. Ayshercool 08081012143 90 1K NE A BIYA KUƊIN KARATU KAFIN A KARANTA. 0069685771 Aisha Adam stanbic bank 08081012143 Mutane sun sha mamakin abin da ya faru. Babu wanda ya isa ya ce dan me? Aka kame waɗanda suka yi yinƙurin nemansa su kashe shi. A ka yi jana'izar Sultan Ansar. Gaba ɗaya Jalaludeen baya murna, saboda raɗaɗin mutuwar mahaifinsu, ga kuma wannan nauyi da ya hau kansa da ƙanan shekaru da ba su wuce Ashirin da takwas ba. Sai dai duk zigar da Saifudden ya din ga yi wa Imam da 'yan uwansa, zamewa ya yi ya bar su, aka kama su sukaɗai. Mahaifiyar Jalaludeen ta yi masa nasiha sosai da sosai, a kan gudanar da sha'anin mulki. Duk da ya san tarin ƙiyayyar da Saifudden yake yi masa, da wasu daga cikin 'yan uwansa, amma haka ya janyo su a jikinsa, ya basu sarautu domin ya rage musu raɗaɗin abin da suke ji, kuma ya ƙara musu zaman lafiya da fahimtar juna. Ya yi wa Saifudeen Tafawan Agadez, wanda yana cikin manyan 'yan majalisar Sultan, da suke faɗa a ji. Ya yi wa ɗan uwansa Turakin Agadez, ɗan wan babansa ya yi masa Sardaunan Agadez. Bayan mutuwar Matawallen Agadez ya naɗa ɗansa Matawallen Agadez. Ya saka aka saki Imam Imam ɗin da suka yi zamani tare da su, suka yi yinƙurin halaka shi, sai dai gaba ɗaya ya sauke su daga kan muƙamin ya kuma yi amfani da ƙarfin mulki gurin ƙwace duk zobunansu, ya ce daga lokacin duk wanda zai zama Imam sai ya tantance shi, kuma sai da sahalewar sa. Aka yo caaa a kansa kamar za a cinye shi, su na ganin zai canza musu tsarin Al'ada. Duk gidajen da suke da gadon, suka bayar da wanda suka zaɓo. Hankalin Tafawa ya ƙara dugunzuma bayan da ya san cewa ba shi da makoma, ya san ba zai taɓa mulki a Agadez ba, haka 'ya'yansa, saboda rashin zoben, dan ya san Jalaludeen 'ya'yansa zai bawa. Wata rana Sultan Jalaludeen ya aika aka kira masa ɗan uwansa, ya zo ya same shi ya dube shi ya ce "Ya kai ɗan uwana, na san kai ne gaba da ni,  kuma ka so ka yi mulkin Agadez sosai da sosai, amma Allah bai nufa ba, ina mai sanar da kai cewa zobe ɗaya da aka neme shi aka rasa ya ɓace a tsakanin zuriyarmu, yana nan bai ɓata ba. Dan haka zan damƙa shi a gare ka, ka duba wanda ya dace a cikin 'ya'yanka ka bawa. Wataƙila a bayana a iya samun wani ya yi mulki daga gidanka" Cikin mamaki ya kalle shi ya ce "Amma yaya aka yi ka mallaki zoben da ake tunanin ya ɓace?" "Mahaifinmu ne ya bani shi, bayan nawa da yake hannuna, ya ce bayan ransa na damƙawa wanda ya cancanta" A take Saifudeen ya ji ya ƙara tsanar mahaifinsu, saboda irin wariyar launin fata da aka nuna musu, ya fifita ɗa ɗaya a kan su da ya haifa. Wannan abin da Jalaludeen ya yi bai sanya ya rage ƙiyayya da jin haushinsa da yake yi ba. Sai dai duk da haka majalisar Imam ba ta cika ba, ana ta zuba ido a ga wa Sultan zai bawa sauran zobuna biyun. A lokacin ya auri mahaifiyar Hammad, buzuwar ƙasar Algeriya da mahaifinta ya ba shi ita, bayan da yaje taron tattaunawa na bunƙasa tattalin arziki. Sai dai cikin ikon Allah, jininsu ya haɗu sosai da sosai ta shiga ransa. Imam Jalaludeen yana da kuyangi, da haihu da su, sai dai Gimbiya Bilkisu ta tsani Gimbiya 'yar Algeria Gimbiya Aafaf. Aurota babu daɗewa, ta haifi Hammad, dan watanninta tara cif ta haifo shi. Gimbiya Bilkisu tana da yara huɗu, uku mata sai guda ɗaya namiji Zahradeen, sai kuma 'ya'yan kuyanginsa mata guda biyu. Ba ta taɓa farga Gimbiya Aaafaf tana da juna biyu ba, saboda doguwar mace ce sosai, kuma su kan kwana biyu ba su haɗu ba, babu wanda yake shiga harkar wani. Haihuwar Hammad gaba ɗaya ya gigita Gimbiya Bilkisu, domin ta gama sakankankancewa ɗanta zai iya zama Sultan wataran kasancewar shikaɗai ne namiji. Sai dai ta shiga ɗar-ɗar da tunanin abin da ka iya zuwa ya dawo. Sultan Jalaludeen Amira yake kiran Aafaf da shi saboda ƙauna, ga wani irin so da yake yi Hammad, tamkar shikaɗai ne ɗansa. Sai dai ba Bilkisu ce kawai ta shiga ɗar-ɗar ba, har da sauran waɗanda suke sanya ran 'ya'yansu su zama sarakuna wataran. Bayan haihuwar Hammad, aka ci gaba da zuba ido a ga, ta ina sauran zobunan nan biyu za su ɓullo. Bilkisu a tsaye take sosai da sosai, gurin nema wa 'ya'yanta kariya mussaman Zahradeen, ba ta da yadda ko kaɗan a kansa abinci ma sai wanda ta tantance ta yarda da shi, sannan zai ci. Ba a daina ta'amalli da bokaye ba har a wannan lokacin. Hammad kuwa sai dai Sultan ya sanya a yi masa, dan sam Umminsa ba ta iya irin wannan abubuwan ba. Hammad ya tashi da hazaƙa da karsashi, sai dai ba ya son mutane. Kwatsam yana da shekaru shida, ya yi wata irin rashin lafiya da sai da aka fitar da rai da shi, da kyar da siɗin goshi sannan ya warke. Daga lokacin Sultan ya ƙara tsananta kulawarsa a kan Hammad. Sai dai a lokacin Mamman, mijin Nene, ya san wanda suka ba wa Hammad guba, kasancewar yana cikin manyan hadiman da yake shiri da Gimbiya Bilkisu. Shi yasa da ya aikata wannan laifin, manyan da suke majalisar kusa da Sultan, suka ƙara kambama abin aka yanke masa wannan hukuncin da babu sassauci a cikin sa. Shekarun Hammad bakwai a Duniya, ya haɗu da Mahmoudu, saboda yawan zuwa da Nene take yi da shi, ganin mahaifinsa a kurku, kuma ta kan je gaida Gimbiya Bilkisu. Sai dai sun ƙara shaƙuwa ne lokacin da Raƙuminsa ya taka Mahmoudu. Gimbiya Bilkisu ta so shiga lamarin Maganar mijin Nene, wato Mamman amma Sultan ya ce "Amira, kin ga ke baƙuwa ce a Agadez, kuma ni kaina na taka dokar ƙasar nan aurenki da na yi, dan dai babu yadda za a yi a hukunta ni ne. Idan na matsa aka saki Mamman matsala na iya faruwa. Dan wasu lokutan a kan al'adu babu abin da ba zai iya faruwa ba. Ina matuƙar gudun abin da ka iya biyo bayan sakin Mamman, duk da na san da girman dokar da na karya. Har ta rasu, ba ta daina yi masa magiya ba, da roƙonsa. Sai dai rayuwa ta yi wa Hammad tsanani, bayan rasuwar Umminsa. Al'amuran mulki sun yi wa mahaifinsa yawa, bai fiye samun cikakken lokacin saurarar Hammad ba. Ya ɗauke shi ya ba wa Gimbiya Bilkisu, duk da ya san ba shiri take yi da mahaifiyarsa ba, amma a zatonsa abin ba zai shafi Hammad ba. Mussaman da yake son a ƙara samun haɗin kai a tsakanin iyalinsa, baya son kwaɗayin mulki ya yi silar tarwatsewar kawunansu. Sai dai Gimbiya Bilkisu ta din ga samun shawarari daban-daban a kan Hammad. Ciki har da ta kawar da shi ta huta. Dangin Umminsa sun so a ba su shi, amma Sultan ya ce ko da wasa, kar su ƙara yi masa irin wannan zancen. Gimbiya Bilkisu kan kori Mahmoudu, ta rufe Hammad a ɗaki, tsawon kwanki a cikin sashinta, idan Sultan baya nan, ta hana shi Abinci ba tare da kowa ya sani ba. Ta san idan namansa za ta din ga sara tana zubarwa, ba zai faɗa ba. Sai ta ji Sultan zai dawo zata sake shi. Sai dai su haɗu su yi ta kuka da shi da Mahmoudu, wasu lokutan ma Mahmoudun ne yake kuka ban da shi. Wataran aka kira Mahmoudu, aka ba shi wani lemo ƙato jawur wanda ya ba shi ya ce  "Ka ga wannan lemon, ka je ka ba wa Hammad ya sha, idan ya sha, zan saka a saki babanka, ku tafi gida tare. Amma kar ka gaya wa kowa, kuma kar ka ce ni na baka" Mahmoudu ya karɓa, ya  tafi da murnarsa, ya kai wa Hammad lemon nan. Hammad ba ya tunanin komai idan Mahmoudu ya ba shi abu, ya karɓa ya ɓare har zai kai bakinsa, Mahmoudu ya ƙwace, ya gaya masa abin da ya faru. Hammad ya ce "In dai za a rabu da Abbanka, ka bani zan sha, amma Mahmoudu ya hana shi, cike da ƙuruciya Mahmoudu ya karɓi lemon ya shanye. Haka ya din ga zubar da jini ta hanci ta baki, har da kafofin jikinsa. Hankalin Sultan ya tashi, saboda ya san kusancin da ke tsakaninsa da ɗansa. Ya ɗauki nauyin maganinsa da ƙoƙarin zurfafa bincike a kan abin da ya faru amma ba a gano komai ba. Hammad ya tsallake abubuwa daban-daban na haɗari, na cutarwa a rayuwarsa, wani ya tsallake wani kuma ya rufta ya sha baƙar wahala ya warke. Mahmoudu kuma da yake tare da shi, kullum shi ma cikin farmaki yake da ƙoƙarin son a yi amfani da shi a cutar da Hammad. Duk wata makaranta da Hammad yake yi, tare suke yin ta da Mahmoudu. Saboda Sultan yana jin zafin abin da ya faru da mahaifinsa, ya san har abada Mahmoudu ba zai daina ganin baƙinsa ba. Ga gudunmuwar da kakansa, wato Baban Nene ya ba wa masarautar ta ɓangaren magunan da tsaface-tsaface. Shekarun Hammad sha takwas a duniya, Imam Sultan ya damƙa masa zoben tambari, sai dai ba a son ransa ba, ya kuma damƙawa Zahradeen ɗayan. Sannan ya shugabantar da Imam Hammad a Majalisar, duk da shi ne ƙarami a cikinsu, saboda ko a lokacin ya fisu ilimi sosai da sosai. Nan aka ɗauki surutun ya yi amfani da ƙarfin mulki gurin gwada mugunta, ta hanyar raba wasu gidajen da zobunan tambari, ya ba wa 'ya'yansa da ɗan ɗan uwansa. Sai dai hakan bai ishi Tafawa ba, musamman da ya ga an naɗa Hammad shugaban majalisar, ya ƙuduri aniyar duk yadda zai yi, ko hakan zai janyo yaƙi a Agadez masarautar ta rushe, sai ya yi duk yadda zai yi Asad ya hau karaga, ba zai bari abin da ya faru da su ya faru a kan 'ya'yansa ba, ya zuba ido Jalaludeen ya ɗora ɗansa a kan karaga ba. Tafawa ya je ya samu Sultan Jalaludeen, ya ce masa yadda nauyi ya hau kansa kamar haka, bai kamata a ce ba shi da aure ba, dan haka idan ba damuwa ga ƙanwarsa nan Asal ya ba shi ya aura. Sultan ya ce "Tafawa ai Hammad da Asal duk abu ɗaya ne, kuna duk hukuncin da ka yanke daidai ne. Zan sanar masa, sai dai ina so a bari ya ƙarasa karatunsa" Tafawa ya ce "A'a jinkirin ka iya kawo wani abu daban, a yi auren daga bisani sai ta tare idan ya kammala karatun" Bayan kwana biyu, Sultan ya kira Hammad, su na zaune su na shan shayi, Sultan ya sanar masa da abin da Tafawa ya zo da shi. A take annurin fuskar Hammad ya ɗauke, amma bai yi magana ba. "Na san wataƙila zaɓin bai yi maka ba, amma ka san yadda ake ta sururu a kan abubuwan da na aikata. Ka yi haƙuri ka karɓi auren nan. Hakan shi ne cikar kamala, kuma ka ga 'yar uwakka ce. Sannan na gaya maka, babban burina da fatana, bai wuce ka gaji karagata ba, ina fatan a samu canjin wasu miyagun al'adun a dalilinka" Hammad ya yi shiru, tun da ya zama Imam, ake ba shi kyautar mata duk da ƙarancin shekarunsa, amma Tafawa ya babbake ya hana, yanzu kuma ya zo da wannan maganar. Ya jinjina wa Sultan kai kawai bai ce komai ba. Sai dai da ya je sashensa, kamar ya yi wa Mahmoudu kuka, dan dama shikaɗai ne wanda yake sakin jiki da shi, ya gaya masa duka wata damuwarsa. Mahmoudu ya ce "To mene ne a ciki? Allah ya sanya albarka ya baku zaman lafiya, ai aure abin so ne" "Ba na son Asal Mahmoudu" Mahmoudu ya zaro ido ya ce "Ba ka sonta, 'yar uwakka ce fa" "Ba na sonta kwata-kwata, mahaifinta ba ya ƙaunata, muraran yake nuna mini, duk da yana ɓoye hakan a gaban Abie". "To ai ba ita ce take yi maka ba, bai kamata laifin mahaifinta ya shafe ta ba" Hammad ya ce "Amma ka san ba zai ɗauki 'yarsa ya aura mini haka kurum ba ko? Kamar yadda ya aura wa Abie Gimbiya Bilkisu na sha wahala a hannunta, haka zai aura mini Asal, su ci gaba da azabtar da ni, za kuma ka ce na gaya maka" "A'a kar ka yi wa auren baki mana tun kafin a yi, in sha Allah babu abin da zai faru sai alkhairi" Fuskar nan babu annuri ya kwanta, dan gani yake wannan auren kawai takura wa rayuwarsa za a yi, sai kuma ya numfasa ya kalli Mahmoudu ya ce "Ka san wani abu?" "A'a sai ka faɗa" "Ni wallahi baƙar mace ce take burge ni" AREWABOOKS Mahmoudu ya waro ido ya ce "Dan zatin Allah daga nan, kar ka kuma ɗaga maganar nan, ka san dai illar hakan, da abin da zai haifar" Ya gyaɗa kai ya ce "Ba ina nufin zan auri baƙar ba, amma ni dai su na yi mini kyau sosai da sosai. Da Umma ta yi maka ƙanwa sai na aura" "Dan Allah ka daina wannan maganar, in dai a Agadez ne, mu ba komai ba ne face masu yi muku hidima" Hammad ya ce "Babu aya babu hadisi a kan hakan, ina fatan wataran wannan dokar za ta kau, kowa ya auri wanda yake so, kowane kalar fata ya rayu cikin 'yanci ba tare da bauta ba. Har na koma ga Allah ina jin zafin abin da aka yi muku Mahmoudu. Kuma abin da ya faru da ku, yana daga dalilan da ya sanya nake matuƙar son baƙaƙen buzaye, da ma sauran baƙaƙen fata, duk farin nan namu fa, duk sunanmu 'yan Afrika kuma baƙaƙe to mene ne na ƙymar junan" Mahmoudu ya ce "Ai komai ya wuce ma, dan Allah ka daina wannan maganar kar ma ka sake ɗaga ta dan Allah" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Na so a ce zan iya ce wa Abie ba zan auri yarinyar nan ba, amma ba zan iya ba" "Dan Allah ko da wasa, kar ka gaya masa haka, ka yi haƙuri dan Allah. Kuma ni gara ka ce ba ka son ta, da dai ka yi waccan kataɓorar da ka faɗa da farko" Hamamd ya gyara kwanciyarsa, ya ce "Da wasa nake yi maka, kawai dai na gaya maka abin da yake raina ne. Fararen matan duk ba ga su nan ba, duk inda na kalla su ne ba. Amma ina son baƙa a ce matata ce, baƙa me kyau tubarkallah ka ga da ka na da ƙanwa, mai kama da Umma, na aure ta baƙaƙen mata su na yi mini kyau ma sha Allah" "Dan zatin Allah ka daina zancen baƙar nan" Yayi murmushi ganin yadda Mahmoudu da gaske baya son zancen, ya juya masa baya yana murmushi. Asal ce zaune a gaban Tafawa, yana zaune daga kan kujera. Ya ce "Ki na ji na ko? Na ba wa ɗan uwanki ke a matsayin matar da zai aura, Imam Hammad dan haka ki shirya a kowane lokaci za a iya ɗaura muku aure". Zabura Asal ta yi ta ce "Aure, kuma da Hammad?" "Eh da shi, mene ne?" Ta sunkuyar da kai tana girgizawa cikin matsananciyar damuwa. "Dan haka ki je zan sanar da mahaifiyarki a yi shiri" Tana barin turakarsa ta saka kuka, ta shiga sashen mahaifiyarta. Cikin damuwa ta ce "Kyakykywata Lafiya kuwa?" "Ammi, Abbu ne ya ce wai aure zai yi mini, dan Allah ban yi ƙarama da aure ba? Kuma wai Imam Hammad zai aura mini" Ta tsuke fuska ta ce "Ban gane ba saboda me? Dama haka ake yi" Asal ta ce "Dan Allah ni ki roƙe shi ya ƙyale ni, kar ya aura mini shi ba na son shi" "Ki kwantar da hankalinki, babu wanda zai yi miki auren dole ina raye". Mahaifiyar Asal ta tashi ta tafi turakar Tafawa, cikin takaici ta ce "Amma meyasa za ka yanke wannan hukuncin ba tare da amincewar yarinyar nan ba, ba ta ƙaunar auren nan fa" "Saboda 'ya ta ce na isa da ita" "Amma rayuwarta fa? Ta yaya za ta zauna da mutumin da ba ta so?" "Ta zauna da shi koma ta yaya ne" Asal ta din ga bori a kan ba ta son Hammad, ba za ta aure shi ba, dan sam ba ta shiryawa aure a lokacin ba, duk da tana da ƙarancin shekaru amma yadda take tsara wa kanta rayuwa sai ta ci Duniyarta da tsinke sannan za ta yi aure. Can kuma Sultan ya saka Hammad a gaba a kan lalai ya je su gaisa da Asal, duk da sun san juna akwai buƙatar su ƙara samun shaƙuwa a kuma tsara yadda biki zai gudana. Da to kawai Hammad yake amsa wa Sultan. Tare da Mahmoudu suka je gurin Asal, sai dai a ƙalla sun shafe awa ɗaya da rabi, Asal ba ta fito ba. Idan ya yi niyyar tafiya, sai Mahmoudu ya hana shi. Daga ƙarshe shi kansa Mahmoudu gajiya ya yi, suka tafi gaba ɗaya. Sai dai washegari, Sultan ya kira Hammad, ya ci masa mutunci abin da bai taɓa yi ba, wai girman kansa zai sanya ya lalata musu zumunci da ɗan uwansa. Yarinya ta gama shiri tana jiransa yana zuwa ya yi tafiyarsa. Abin ya yi wa Hammad ciwo, amma ya daure ya bawa Sultan haƙuri, ya tashi ya tafi. Sai da ya yi zuwa uku, sannan Asal ta zo. Kallo ɗaya ya yi mata ya tuna abin da Sultan ya yi masa saboda ita, ransa ya ƙara ɓaci ya ji wata irin tsanarta ta mamaye shi. Sam Asal ba ta da ɗa'a. Duk da kasancewarsa yaro ƙarami girman sarautarsa ya sanya yana da kamewa da son girma. Amma bai ga hakan a tattare da Asal ba, sai harare-harare da take yi. Ga shi a lokacin shi har cikin zuciyarsa yana son mace mai mamora, Asal kuwa ga yarinta ga babu alamar wani abin kirki a tattare da ita. Haka Tafawa ya din ga haɗa shi da Sultan a kan Asal. Tafawa ya lura idan bai yi a hankali ba, Asal za ta jiƙa masa aiki, ga mahaifiyarta sai bala'i take yi ba za a yi wa 'yarta auren dole ba. Ya same ta da daddare a ɗakinta, ya kifa mata wani uban mari, da sai da ta ga taurari ya ce "Ke kalle ni da kyau, idan ma babarki ce take ziga ki, to ki shiga hankalinki tun da wuri. Ban haɗa auren nan dan ki so ko kar ki so ba. Na haɗa auren nan ne domin cikar muradina. Za ki taimaka mini ne, ina son ɗan uwanki ya gaji karagar mulkin Sultan, dan ba zan bari sarauta ta dauwwama a gidansu ba. Dan haka dole ki haƙura da duk wani abu da ki ke so, domin cikar nawa muradin. Zan aura miki Hammad ne, na wani ɗan lokaci na samu cikar burina, daga nan ki yi duk abin da ki ka ga dama." Asal ta sha kuka sosai da sosai. Ita ta san Hammad ba shi da wata makusa ko kaɗan da za ta nuna a matsayin aibun da za ta ce ba ta son shi, kawai gani take auren kashe mata rayuwa ne. Mussaman yadda Allah ya yi mata kyakykywar halitta. Ko da ta gaya wa mahaifiyarta abin da Tafawa ya ce, zuwa ta yi ta same shi, tana faɗan ya za a yi ita ba da haifar ɗa ba, a tursasa wa 'yarta saboda cikar muradin wani, tun da yana da ƙanne mata a aura wa Hammad ɗin ƙannen Asadullah. Gudun kar ta ɓata masa aiki, ya sanya ya yi mata bayanin ai idan ya aura masa a ƙannen Asad, nan da nan za a gano shi, amma wanda suke ba ciki ɗaya ba, babu wanda zai kawo wani abu. Ya din ga kwaɗai mata abubuwan da za su samu idan Asad ya zama Sultan. Gimbiya Bilkisu ma har gida ta zo ta samu Tafawa, ta ce "Na ji labarin za ka aura wa Hammad ɗanka, duk da na san inda ka dosa, na san dalilinka na yin haka, amma kar ka manta da sauran rina a kaba, tun da Zahradeen ma Imam ne, kuma ɗan Sultan" Tafawa ya ce "Haba Gimbiya Bilkisu, ai ke 'yar uwata ce, ki zo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu yi nasarar ganin Hammad bai mulki Agadez ba. Kuma kema kanki kin san alamu sun nuna Hammad yake son ya damƙawa mulkin" Ta ce "Mu haɗa hannu, ka yi mini irin yadda ka yi wa wadancan mutanen da suka haɗa kai da kai. Kuma idan na haɗa kai da kai, waye zai haƙura ya bar wa wani tsakanin Asadullah da Zahradeen iya ruwa fid da kai kawai" Ta ƙarasa maganar tana dariya. Ta shiga gurin mahaifiyar Asal da niyyar su gaisa, amma ta ce mata "Ina fatan idanunki a buɗe suke,a kan auren nan da z a a yi wa 'yarki? Idan burinsa ya cika Asadullah ya zama Sultan Asal ba ta da wata makoma. Ita dai mace ce ba sarauta za ta yi ba. Ki bar ganin shi ya haife ta, buƙatarsa na biya zai ajiye ku gefe" Haka aka din ga ɗauki ba daɗi a kan auren nan, Hammad ya din ga fuskantar kalubale daga Sultan saboda yadda Tafawa yake haɗa su, har sai da Matawallen Agadez mahafin su Hasna da Al-Husssain ya ankarar da shi, Tafawa haɗa shi kawai yake yi da Hammad. Haka Sultan ya saka Hammad haɗawa Asal lefe, na ban mamaki, lefe na 'yar gata. Aka yi gagarumin biki da ya tara manyan mutane, ana ta jinjina yarintar amarya da ango, dan ma dai Hammad a nutse yake sosai. Bayan an yi aure, Hammad ya tsallaka ya tafi karatu tare da Mahmoudu, ba tare da ya sake bi ta kan Asal ba. Bayan ya zo hutu, Tafawa ya dage sai ta tare. Haka aka ginawa Hammad danƙareren gida a cikin gidan sarautar aka saka Asal a ciki. Tun da Asal ta tare, bai taɓa gigin zuwa inda take ba, ta din ga yi masa alwashin tun da ya aure ta, sai ya ga tashin hankali da bala'i. Ta din ga surfa masa rashin mutunci da tijara iri-iri, tun yana jurewa har ya fara gaya wa Mahmoudu zai ɗauki mataki, amma ya din ga rarrashin sa yana ba shi haƙuri. Bayan sun koma makaranta, ita ma Asal aka mayar da ita makaranta, sai dai aka kama mata gida, saboda makarantar nesa ce da Agadez. Idan ya tafi ko son tuna Asal baya yi. Saboda tashin hankali da rashin biyayya, ango na ƙiba shi kuwa ya yi uwar rama. Tafawa kuma ya din ga nanata mata, duk wani motsi na Hammad, ta din ga sanar da shi. A haka aka shafe shekaru uku da aure, ya mayar da hankali a kan karatunsa, da ginin katafaren gurin cin abincinsa a Agadez. Ita kuma mahaifiyar Asal ta fara saduda, tare da kwaɗaitawa Asal ta kwantar da hankalinta, idan Allah ya sanya ta haifi namiji, babu lallai Asadullah ya yi mulki. Ko da suka kammala degree na farko, suka dawo Niger, Asal babu abin da ya yi mata zafi da shi, shi ma bu kula ta yake yi ba, duk inda za ta fita yawonta babu ruwanta da neman izininsa. Wataran da daddare yana zaune a turakarsa, yana duba wasu litattafai ta yi sallama hannunta da tray. Ya amsa mata ta shiga ta ajiye masa ta ce "Ga shayi na dafa maka" Cikin mamaki ya din ga bin ta da kallo. Ya gyaɗa kai ya ce "To na gode" Ta na ɗan murmushi ta tashi ta fita. Bayan fitarta ya din ga kallon flask ɗin shayin, ya murza zoben hannunsa, sannan ya kalli kofin a take sai ga wani irin baƙin hayaƙi yana fitowa daga cikin kofin, shayin ya koma baƙi ƙirin mai kauri. Ya yi shiru yana mamakin yadda ƙiyayyar da take yi masa za ta sanya ta iya cutar da shi, dan tun da ya ga hakan ya san akwai wani abu a cikin shayin. Har ta fara shirin kwanciya, ya shiga ɗakin hannunsa riƙe da kofin. Bai ce mata komai ba ya zauna a kusa da ita ya miƙa mata kofin ya ce "Sha" ta dube shi ta ce "Ai na sha" "So nake ki sake sha ai". Ta girgiza masa kai tana kallon sa. Ya murza zoben hannunsa ya shafi saman kofin da yatsunsa, sai ga Asal ta ga abin da ya gani a cikin kofin. Ya sake kallon ta ya ce "Ki sha, ba za ki kashe ni nikaɗai ba" Ya yi maganar cikin tsawa. Ba ta taɓa tunanin zai yi mata kwarjini haka ba, gaba ɗaya ta rikice ta hau kuka. "Gaya mini wane ne? Waye ya baki wannan abin ki bani, kuma na mene ne?" Ta hau girgiza kai tana kuka. "Ki gaya mini kafin na ɗauki matakin da ya dace" Ta kasa magana ta ci gaba da girgiza kai. "Shikenan, tun da ba za ki faɗa ba, idan na kai ki gaban Sultan kya gaya masa meyasa ki ka yi yinƙurin cutar da ni" Ya fice ya bar ta a ɗakin, hankalinta ya yi mummunan tashi, ta kira lambar Abbanta amma ta ƙi shiga, ta karaya ajalinta ya zo a Agadez. Amma kwana uku shiru babu wanda ya kira ta, kuma ba ta sake ganinsa ba. Kwana na huɗu har ta kwanta, ta tashi ta shiga sashensa, ta gan shi a zaune yana cin dabino yana kallon labarai. Yana ganinta ya tsuke fuska ya tashi ya bar mata falon. Ta tsaya a falon tana wasi-wasi, sai dai ta shiga lissafin halin za za ga shiga idan ya tona mata asiri, ta san duk abin da za a yi mata ba za ta iya tona wa mahaifinta asiri ba. Ta daɗe tana tufka da warwara ta ga dai ba ta da sauran mafita. Dan haka kawai ta bi bayansa, gara duk wadda za a yi, a yi. Sai dai da ta shiga kawai ta tarar yana Video call da wata baturiya. Wani abu mai ɗaci ya tsirga mata ta tsaya tana kallon kyakykywar fuskarsa mai cike da ƙuruciya yana murmushi. Ayshercool 91 Bai daina wayar ba, kasancewar malamarsa ce a faransa. Sai dai bai bari ta fuskanci hakan ba. Ta ƙarasa gabansa cikin ƙunar rai da wani abu da ta kasan gano ma mene ne a ranta. Ta je ta tsaya masa a ka. Bai kula ta ba, ya ajiye system ɗin, ya fara ƙoƙarin kwanciya. Ta zauna a gefen gadon ya ce "Imam gurinka na zo" "An sake aiko kin ne?" Ta girgiza kai cikin sanyin jiki. "Faɗi abin da ya kawo ki zan kwanta" "Dan Allah ka yi haƙuri" shiakɗai ne abin da ta iya furtawa, ta fashe da kuka. "Na yi haƙuri da aka yi me?" "Abin da na yi maka, wallahi ba dan san raina ne ba" Hammad ya ce "Ba da son ranki ba? Bayan kin gaya mini ba kya so na, ba kya ƙaunar zama da ni, sai na yi dana sanin aurenki, ai ba abin mamaki ba ne ba dan an haɗa kai da ke an cutar da ni. Amma ko ba ki kalle ni a matsayin miji ba, yakamata ki kalle ni a ɗan uwanki ki yi haƙuri mu zauna lafiya. Koma waye ya saka ki, ku sani ba zan mutu ba sai wa'adin da Allah ya ɗibar mini ya yi " Asal ta din ga kuka tana ba shi haƙuri, dan ba ta yi zaton zai ma rufa mata asiri na kwanakin da ya yi ba. Daga ƙarshe ya ce "Tashi ki je babu wanda zan gayawa" "Dan Allah da gaske?" Ya tsare ta da ido, sai kuma ta nutsu ta ce "Na gode sosai da sosai, ba zan sake ba in sha Allah" "To ban guri zan kwanta" Ta ce "Dan Allah" sai kuma ta yi shiru. "Mene ne kuma?" "Dan Allah wace ce wadda ku ke waya da na shigo?" Kawai ya kwanta ya share ta. Yana jin yadda take kuka, ya hau baccinsa, saboda haryanzu yana jin ɗacinta, a kan yadda ya iya danne abin da yake ransa ya yi wa iyayensu biyayya, amma ita fuskarta a tasa ta gaya masa, ba ta son sa ba ta ƙaunarsa. Kasancewar ya saba baccinsa shikaɗai a ƙaton gadonsa, ya sanya shi ƙoƙarin yin juyi, amma ya ji kamar an yi masa dabaibayi. Asal ce a jikinsa tana ta bacci. Ya yinƙura zai ture ta saboda yadda ya ji shi wani iri saboda rashin sabo. Amma ta hana shi hakan."Ke ni fa kin matse ni, ki koma ɗakinki mana" Ta yi masa shiru duk da tana jin sa. Ƙarshe dai asancewar su 'yan Adam lafiyayyu, ba su bujirewa abin da gangar jikinsu ta buƙata ba. Tun daga lokacin Asal ta ɗan nutsu, musamman da take tsoron, kar wataran ya faɗi abin da ta yi masa. Duk da ba daina tsiyatakunta ta yi ba, idan ta bushi iska tana yi. Shi kuma baya son duk wani dalili da zai sanya a ga gazawarsa ko ya yi ƙorafi a kanta. Hankalin mahaifiyarta ya koma kan ganin Asal ta samu juna biyu, saboda zigar da Gimbiya Bilkisu take yi mata, a kan lallai ita ma ta yi ƙoƙarin ganin, 'yar ta ba ta zama abar morar Tafawa da ɗansa ba kawai. Dan ta san dole idan Asal ta haihu ta jiƙa musu aiki. Shi ma ɓangaren Hammad, sai Allah ya jarrabe shi da matsanancin son 'ya'ya. Gefe guda Tafawa bai fasa sanya Asal, yi wa Hammad binne-binne ba. Sai dai babban abin da yake ba shi mamaki shi ne yadda abubuwan ba su fiye tasiri a  kansa ba, har kiran Asal yake ya ƙare mata zagi, ya yi zaton ko ita ce ba ta yin aikin dai-dai, duk da wasu lokutan tana tsoron asirinta ya ƙara tonuwa. Aka tafi shekara ta shida da aure, a lokacin ne Hammad haƙurinsa ya fara ƙarewa, saboda haihuwa yake so, kuma ba dan komai ba shi kawai yaran yake so. Duk Imam ɗin ƙasar su na da aure da 'ya'ya amma shi shiru. Ya ce wa Asal su je Asibiti a duba ko lafiya, amma ta ce ba za ta je ba, ya kaɗa ya raya ta ce ba zata ba. Ya ce mata tun da haka ne, shi aure zai yi, ko ya mallaki kuyanga, dan saboda azabar kishinta ya sanya babu ruwansa da barorinsa. Tun da ya faɗi haka ta hau rashin lafiya, Sultan ya je duba ta, ta din ga yi masa kuka a kan ya roƙi Hammad kar ya yi aure, yayi haƙuri tana addu'a ta san za ta haihu wataran. Bata taɓa tunanin ta fara son Hammad har haka ba, sai da ya yi zancen aure, dan har iƙirarin kashe kanta ta yi. Tafawa ya samu Sultan har da kukan munafunci a kan ya saka baki, kar ya rasa Asal, ya rarrashi Hammad. Ganin yadda Asal ta gigice, ya sanya Sultan ya din ga rarrashinta, ya samu Hammad ya ce "Hammad, na san kana yi mini biyayya, kuma kai mutum ne mai haƙur da juriya, dan Allah ina son ka sanya a ranka, rashin haihuwa jarrabawarku ce. Kuma ba a san me Allah zai yi nan gaba ba, dan Allah ka yi haƙuri da batun auren nan, kuma ka daina yi mata zancen haihuwar nan, saboda a samu hankalinta ya kwanta." Karo na farko Hammad ya buɗe baki zai yi magana, amma Sultan ya dakatar da shi ya ce "Baka saba haka ba, kar ka fara a wannan karon, kai mai haƙuri ne, a wannan karon ma ina son ganin tasirin hakan a gare ka" Ya haɗiye yawu mai zafi, idanunsa suka yi jawur. Ya din ga zuwa Asibiti shikaɗai aka duba shi aka ce masa lafiyarsa ƙalau. Asal kuma ta ci gaba da yi masa kuka da magiya a kan ya yi haƙuri su ci gaba da addu'a, ta san wataran za ta haihu, amma ya bar maganar ƙara aure, dan da gaske idan ya yi aure sai ta kashe kanta. Ya so ya yi mata magana a kan to ta bari su je Asibiti, amma ya tuna abin da Sultan ya ce masa, dan haka a dole ya ja bakinsa ya yi shiru ya ci gaba da addu'a. Duk wanda ya yi alkhairi fatansa ya yi masa addu'a Allah ya ba shi haihuwa mai albarka, duk inda ya ji maganin haihuwa, da ya yadda da ingancinsa, sai ya karɓo ya kawowa Asal. Shi kansa Sultan abin ya dame shi, ba yau ba gobe cikin yi wa Hammad addu'a yake, ganin yadda yake ruɗewa idan ya ga 'ya'ya, duk wanda ya haihu a masarauta muddin ya ji labari, sai ya yi masa kyauta mai tsoka ya ce shi ma a yi masa addu'a. Matawalle ya samu Sultan ya ce "Anya ba ka ganin kamar an cutar da Imam Hammad da yawa, da an bari ya jarraba auren wata matar mu gani ko Allah zai sanya a dace" Sultan ya girgiza kai ya ce "In sha Allah zai ga daidai a rayuwarsa. Ina jin tausayin Asal ne, gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma a ɗan ƙara haƙuri a ci gaba da addu'a. Kuma ka san mahaifinta ba ya raina abin magana, yanzu sai abin ya zama na surutu. Ita kanta Asal abin ya dame ta, mussaman ganin yadda Hammad ɗin yake damuwa da lamarin 'ya'ya, sai dai baya yi mata maganar. Tun da ƙananan shekaru, Hammad ya haɗu da larurar hawan jini ake ta fama. Asal ta ƙara shiga tashin hankali, ganin yadda ake ƙara yi wa Hammad tayin matan aure, ga shi matan ma farmaki suke kawo masa, saboda yadda siffofin kamala da cikar zati ke bayyana a tattare da shi. Su kansu kuyangin gidan su na neman su zama mallakinsa. Sai dai a ransa ko zai yi kuyanga, baƙaƙen nan yake so ba farare ba. Duk ya kawar da kansa saboda Asal. Wataran ya fito zai fita, wata hadima ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi ya ce "Sa'ada na daina ganinki kwana biyu" "Allah ya taimake ka, na yi rashin lafiya ne" "Subhanallah, ai ban sani ba, kin rame sosai da sosai. Maza ki je a duba ki, kuma ki ci abinci sosai, kin fi kyau lokacin da ki ke da ƙiba, Allah ya sauwwaƙe" wasu lokutan Hammad akwai raha, saboda a cewarsa hakan zai ƙara masa kusanci da hadimansa, shi ba ya son wannan tsoron nasa da suke yi. Ta risuna cikin girmamawa tana murmushi ta yi masa godiya. Aikuwa ta sha bala'i a gurin Asal, ƙarshe ta kore ta daga sashen girke-girken gidan, zuwa wani abin daban. Asal ta saka masa kukan, dan me zai kula wannan hadimar, sannan ya yabi jikinta. Ya din ga rarrashinta ya ce shi ba da wani abu ya yi ba. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, ana tursasa Hammad jure abubuwa da dama Saboda Asal. Kwatsam Tafawa ya kira Asal, ya ce ta je ta same shi, sai da gabanta ya faɗi tana zaton ko wani laifin ta yi. Ya kira ta cikin turakarsa. Ya ɗaukko mata wata 'yar ƙaramar laya, ya ba ta ya ce ta je ta samu wani guri da ido ba zai kai kanta ba, inda Hammad yake zama ta saƙale ta. Ta yi shiru tana kallon layar, amma babu yadda ta iya haka ta karɓa ta tafi da ita. Ta din ga tunani ta saka ko kar ta saka. Saboda ba ta san ta mece ce ba. A iya zaman da suka yi tsawon shekaru tare, ba za ta iya cewa ga wani abu na cutarwa da Hammad ya yi mata ba, sai ma shi da yake shanye abubuwa da dama take yi masa, komai cutarwar hakan a gare shi. Cikin dare yana tsaka da barci, ya ji tamkar ana girgiza gadon da yake kai, ya din ga ganin wasu irin halittu marasa kyan gani da tsoratarwa. A haka ya wayi gari kansa na neman juyewa, tun gari ya waye ya daina magana. Asal kanta sai da ta tsorata. Sai da suka kwana biyu da kyar yake iya cin abinci, sai ya din ga abu kamar baya cikin hayyacinsa. Tafawa kuma ya din ga kiranta yana tambayarta duk halin da ake ciki. Sai da ta ga da gaske baya magana, ko majalisa baya fita, ta tsorata ta sanar da Sultan halin da ake ciki. Aka kai shi Asibiti amma aka kasa gane abin da yake damunsa. Sai dai jininsa da yake hawa fiye da kima. Ya yi jinya sosai da sosai. Da kyar ya warke, sai dai Tafawa bai haƙura ba, gefe babar Asal ta bazama neman maganin haihuwa tana ba wa Asal. Sai dai kwatsam! Ita ma ta haɗu da jinya, ciwon suga ba ta san tana da shi ba ya yi ajalinta. Asal ba ƙaramin kaɗuwa ta yi ba, da rasuwar mahaifiyarta tamkar za ta zare. Hammad ya yi ta rarrashinta yana ba ta baki. Tafawa bai samu zama ba, ya tashi nan ya faɗi can, duk domin ganin burinsa ya cika, gaba ɗaya rayuwarsa ba shi da cikakken sukuni, haka nan ya hana Asal ta zauna lafiya tare da mijinta. Ya zamana ku san kullum ba shi da cikakkiyar lafiya, yau da lafiya gobe babu. Tafawa ya fara magantuwa a kan yawan rashin lafiya da Hammad yake yi, yakamata ya sauka daga kan shugabancin Majilisar Imam, a bawa wani. A majalisar Sultan aka soke maganar da ya kawo. Hammad kawai yana tafiya ana ganinsa, amma a cikin jikinsa shikaɗai ya san abin yake ji. Ko Asal bai fiye sakin jiki da ita ya gaya mata damuwarsa ba, saboda sam ba ta da alƙibla, kuma tsawon shekaru da suka shafe tare, ba ta iya fahimtar damuwarsa rashin lafiya kai tsaye, sai idan tana da buƙatar wani abu a gurinsa. A haka ta sake neman komawa karatu, lokacin Hammad ya karaya da neman haihuwa. Idan yana salla har kuka yake yi, abin yana burge shi ya ga mutum da ɗan uwansa sun haɗa kai, shi kuma ba shi da wanda suke ciki ɗaya. Mahaifinsa kuma ayyuka sun yi masa yawa, matarsa kuma bai gama gane kanta ba. Dan haka duk wani rikicinsa, shi kuma ba ya gajiya. Wasu lokutan ya na jin daɗin ya bi Mahmoudu gurin Ummansa, su je su wuni, su ci abinci tare. Duk da yana matuƙar jin nauyinta, na abin da aka yi mata a masarautarsu, sai dai bai taɓa ganin hakan a fuskarta ba. Ya yi shiru yana kallon Nana, da ta yi shiru tana saurarensa. "Ya ka yi shiru kuma?" "Na gaji, kuma bacci nake ji" Ta ce "A'a wannan wayo ne na kar ka ƙarasa mini, dama ni ƙarsheƙarshen nan, ba jin daɗinsa na yi ba, gara ma farkon labarin tun da tarihi ne." "Saboda zancen Asal ne?" "Zan iya cewa eh ɗin ma, saboda mutane kaɗan na tsana a Duniya, kuma ta shiga cikinsu" Ta yi maganar tana tsuke fuska. "Amma meyasa?" Nana ta ce "Kawai ba ta yi mini ba" Hammad ya yi shiru ya ce "Ba na tunanin kishi ne kawai ya sanya ki ka faɗi haka, akwai wani dalili, ba kya faɗar magana haka kurum mara ma'ana" Ta ɗan gyaɗa kai ta ce "Ba mai ma'anar ba ce gaskiya, mu je a haka kawai, kishi ne ya sanya na faɗi haka. Yanzu dai ni ka tsallake nan, ka gaya mini yadda aka yi ka din ga wasa da hankalina, da yadda ka gane ni amma ka share ni, nake yi wa matarka aiki cikin ƙasƙanci da wulaƙanci. Kuma alhalin ka na iƙirarin ka na so na. Har kuka na yi mata, da ta ce za ta kawo ni Agadez na ce mata ina da jariri, amma buɗar bakin matar nan ta ce ni ta shafa, tun da talaka ce ni dole na yi abin da take so. Ba zan manta wasu abubuwan da ta yi mini ba na cin mutunci har abada" Ya ɗago da fuskar Nana tana kallonsa ya ce "Ba wannan ne dalilin da ya sanya ki ka ce ba kya sonta ba, akwai dalili. Wannan ba halinki ba ne, idan wannan dalili ne da abin da na yi miki ba za ki sake zuwa inda nake ba" AREWABOOKS Ta kawar da kanta gefe ta ce "Ka ƙarasa mini kawai, mu bar wannan maganar" "Asmy, Asal ko ba aure tsakanina da ita matata ce, ban kuma gaya miki halin da muke ciki, domin na tozartata ba, iya abin da na sani na sanar da ke game da zamantakewar mu, saboda shi ne mahaɗin labarin rayuwata da ke" "Ai dama ban ce kar ka so ta ba, ka je ka yi ta son nata" Ya ce "Ai ba zancen so muka yi da ke ba, ki yi shiru mu ƙarasa an kusa fara kiran Asuba" "Ba na son ji" Ta yi maganar tana kifa kanta tare da tsuke fuska. "Merci ma viee, ba na son ki din ga ɓata ranki, mun bar wannan maganar tun da ba kya so, yadda ba na son kowa ya raɓe ki, ke ma haka ne na sani, kuma na san kin yi ƙoƙari kin yi haƙuri sosai da sosai da juriyar da ki ka cancanci a sara miki, amma ki yi haƙuri mu ƙarasa maganar, daga ƙarshe duk hukuncin da ki ka yanke mini, zan karɓa" Ta ɗago kanta, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, azababben kishin Asal yana taso mata, babu abin da yake ƙara ɓata rai irin cin mutuncin da Asal ta din ga yi mata a matsayin kishiyarta. "Kin huce mu ci gaba?" Ta yi masa shiru. Ya ce "Matso na rungume ki, ki nutsu sai mu ci gaba" Ya ƙara matsawa kusa da ita, ya rungumota jikinsa, yana murmushi. Ta kwanta lamo a jikinsa yana shafa bayanta a hankali. A ransa ya ce "Asmy, ba za ki taɓa jin rabi a kwatankwacin abin da nake ji a kan ki ba, ina ƙaunarki ina kishinki, Allah ya bamu haƙurin zama da juna" Asal kuwa na can a tsaye, tamkar ta haɗiyi taɓarya, idanunta suka sauka a kan agogon bangon ɗakin. Idanunta sun bushe, zuciyarta ta ƙeƙashe sai raɗaɗi da idanun kawai suke yi mata. Haryanzu ta kasa yadda Hammad ne yake da wata matar, matar ma baƙar fata da a kyau ba ta kai ta komai ba. Babban abin da ya ƙara rikita ta bai wuce batun ɗa da Tafawa ya tabattar mata da Hammad yana da shi ba, har ɗan shekaru biyu ba. Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri da sauri, tsawon lokacin nan ba ta taɓa tunanin son da take yi wa Hammad ya kai haka ba, ashe duk abin da take yi bonono take rufe ƙofa da ɓarawo. Tana zaman zamanta ta janyo masifa da kanta jikinta. Ta din ga tunanin ko dai wata ƙulla-ƙullar ce ta daban aka yi. Sai kuma ta tuna babu yadda za a yi Nana ta samu zarafin shiga har sashen Sultan, su keɓe da Hammad idan ba matarsa ba ce ba. Kenan Sultan ya goyi bayan abin da Hammad ya yi na auren baƙar fata da ba ƙabilarsu ba?. Kawai ta ɗora hannu a ka ta rushe da kuka, hawaye ya ƙi zubo mata sai azabar zafi da zuciyarta take yi. Gimbiya Bilkisu ce ta shigo ɗakin tana faɗin "Asal lafiya kuwa?" "Na shiga uku na lalace Gimbiya, wallahi Hammad ya cuce ni ba zan yafe masa ba. Kuma wallahi sai ya rabu da ita, an cuce ni an cuci rayuwata" Ta rungume Asal tana rarrashinta, ta ce "Ki yi haƙuri, ki daina wannan kukan kar ki samu matsala, ki kwantar da hankalinki na san Sultan ba zai ƙyale shi ba, zai ɗauki mataki" Asal ta ci gaba da kuka da babu abin da yake ƙara mata sai nauyin zuciya. ***** Imam Hammad kuwa a hankali ya ɗan ɗago fuskar Nana ya ce "Bacci ki ke yi ne?" Ta girgiza kai alamar a'a. "To tashi mu ci gaba" Ta noƙe kafaɗa tana ƙara rungume shi. Ta ce "Imam ka ci gaba mu yi mu bar gurin nan, Aljanun gurin nan sun fara tsorata ni, kar a samu matsala" "Kina ganinsu ne?" "Su na bayyana a siffofi daban-daban, tsofaffi tukuf da matasa da wasu halittun daban, duk ina ganinsu addu'a kawai nake yi tun ɗazu" "Ni da ke duniyarm daban take, ƙalubale iri ɗaya, Ubangiji Allah ya bamu lafiya rayuwar Hammad". Ta sake lafewa a jikinsa ta ce "Ka ci gaba to" Ya numfasa. Rayuwa ta ci gaba da tafiya, Hammad na fuskantar suka da ƙalubale kala-kala. A kwana a tashi ya haɗu da larurar zafin jiki, idan jikinsa ya ɗauki zafi tamkar an hura wuta. Babu wanda ya sani sai Asal, dan ya fi kama shi cikin dare, ita ta ɗauka kawai normal zazzaɓi yake yi sai ta yi masa sannu kawai ta ci gaba da sabgoginta. Sultan ya mallaka masa wannan jakar fatar mai kama da laya, wadda ita ma a cewarsa ta tsari ce, kuma tana ɗauke da aljanun da suke yi wa mamallakanta hidima. Duk lokacin da ya murza zobensa, ya kan gansu a suffar tsuntsaye, irin wanda bai taɓa gani ba a duniya, ko suffar wani abun daban. Wasu lokutan ko be murza zoben ba, ya kan gansu, ko ya din ga ganinsu a barci. Duk da ba shiri suke yi da Yayansa Zahradeen ba, saboda Gimbiya Bilkisu ta shiga tsakaninsu, amma ya taɓa tambayarsa, ko yana ganin wannan tsuntsayen shi ma idan ya murza zobunansa. Zahradeen ya ce masa baya ganin komai, an ce duk mai zoben yana iya ta'amalli da aljanun jikin zoben, amma shi baya ganin komai. Ya tambayi Hammad ko yana gani shi. Ya ce masa aa saboda ya karanta tarihin zobunan a littafin Kundin Agadez ne ya sanya ya tambaye shi. Haka ya tambayi sauran Imam ɗin, su ma dai bai ji alamun akwai wanda yake ganin wani abu ba. Abin da bai sani ba, tun zamanin kakansa, aka canza zobunan, na hannunsa ne kawai na ƙwaran da babu wanda ya sani, sai mahaifinsa da kakansa, sai kuma marigayi Matawalle. Kwatsam tafiya ta kama Sultan, ga taron sarakuna da za a yi. Sai ya wakilta Hammad ya ce yaje ya wakilce shi. Nan da nan aka hau surutun da me bai wakilta kowa a majalisar sa ba, zai wakilta yaro ƙarami, maimakon ma a ce a cikin Imam ɗin a zaɓi wanda suka fi shi shekaru. A lokacin Hammad bai daɗe da buɗe sabon branch ɗin gidan abincinsa a Maraɗi ba, ya wakilta cousins ɗin sa Hasna da Al Hussain a matsayin masu kula da gidan cin abincin. Babban abin da yake ƙara ɗaga wa masu son ganin bayansa hankali, bai wuce yadda mutane suke son sa ba. Saboda ya iya shugabanci, shi wannan ƙyamar ma da ake nuna wa baƙaƙen buzaye ba ya yi. Yana damuwa da lamuran na ƙarƙashinsa sosai da sosai, wasu lokutan ma kamar ba basarake ba, saboda yadda yake alaƙa da su. Ga kuma girmama shi da suke yi tamkar Sarki. Hasali ya fi nuna saurata da izzarsa a lokacin da yake cikin 'yan uwansa masu Sarauta. Ga shi manyan mutane na son sa, su na son mu'amala da shi, saboda ladabinsa, da iya magana, fiye da sauran Imam, har ma da 'yan majalisar Sultan ɗin, mussaman da duk wanda ya ga Sultan ya ga Hammad, ya san jininsa ne. Yana ta shirye-shiryen tafiyar taron nan Niemey, a lokacin ga shi nan ne kawai, kansa kamar zai ɓare saboda ciwo. Yana kwance cikin dare tare da Asal su na bacci, ya yi mafarkin wani sanye da baƙaƙen kaya, yana soka masa allura a ka. Ya farka a razane, sai dai ya din ga jin raɗaɗin allurar nan a zahiri. Ya sanya hannayensa biyu ya dafe kansa, yana rintse idanunsa yana ambaton Allah, amma kan tamkar zai yi bindiga. Ya tashi zaune da kyar ya yaye bargon da ya rufe jikinsa kawai ya ga wata takarda. Ya ɗauki takardar ya duba sai ya ga hoton ƙwarangwal na ci da wuta, ga sunansa a jiki. Hakan ya yi daidai da sake jin kamar kwanyarsa za ta zazzago. Ya kifo daga kan gadon ya a rirriƙe kansa, ga jikinsa ya fara wannan zafin. Kawai ya din ga jin idan bai bar garin nan ba, mutuwa zai yi saboda wata irin azaba da yake ji mara misaltuwa. Ya yinƙura ya tashi da kyar, ya ga Asal a zaune a kan gadon tana kallonsa, ya nufi hanyar fita jikinsa na tsuma, amma kasancewar dishi-dishi yake gani, ya faɗi a gurin. Washegari ya tashi normal, sai dai jin da yake yi idan bai bar inda yake ba, kamar zai zauce. Ya yi tafiyarsa ɗaya gidan nasa, ko zai daina jin abin da yake ji, amma abu ya din ga jin cigaba, ya din ga jin kamar a cikin wata masifa yake. Ya yi waya da Mahmoudu a kan tafiyar su, ya ce masa su haɗu a ɗaya gidan nasa. Gaba ɗaya ya ji tashin hankalin na ƙara ƙaruwa, ga wata kururuwa da yake ji a cikin kunnuwansa, ganin wasu irin halittu su na yi masa shawagi a kansa. Su na ta watso masa takardun nan na zanen ƙwarangwal. Yana daga kwance ya din ga jin ana kiransa, ana ya tashi ya je gidan ajiye kayan tarihi ana nemansa. Ya toshe kunnunwansa, amma ya gaza daina jin hayaniyar. Jin da yayi yana neman ya haukace, kawai ya tashi ya fita ya hau tafiya. Duk da da ɗa  nisa daga gidansa na wajen masaruta, haka ya din ga tafiya har ya je gidan tarihin. Yana zuwa mai tsaron ƙofar ya buɗe masa. Da takardar nan mai hoton ƙwarangwal ya sake cin karo,  muraran a zahiri ya din ga ganin aljanun da ke cikin gidan tarihin nan, muraran a siffofi daban-daban. Su na ta fitowa daga cikin ɗakunan nan, wasu su na ratso bango su na fitowa, suka nufo shi su na yi masa wani irin ihu. Ya toshe kunnunwansa, sai ga waɗanda yake gani a suffar tsuntsaye, sun bayyana su na make masu nufo shin. Wata irin guguwa ta tashi a tsakiyar gurin, aka yi wata irin walƙiya mai ban tsoro sai ga Giyaz ya keto ta tsakiyar gidan tarihin ya bayyana a gabansa. Giyaz ya nufo shi, wannan tsuntsayen suka yi kansa, shi kuma Hammad ya tashi ya fice daga gurin, jiri yana ɗibarsa, ya san ya fito daga gidan tarihin sai dai bai san ina ya nufa ba, kawai ya buɗe ido ya gan shi a sahara tare da Mahmoudu. Ya yi shiru yana kallonsa, sai ga Giyaz ya kuma bayyana a cikin saharar, cikin tsofaffin kayan nan tamkar auduga saboda tsufa. Ga wani irin sauti da saharar take yi, tamkar iskar za ta taso. Wata irin dariya Giyaz yake yi mai ban tsoro. Ya ce "Ban sani ba, ko haɗuwa da kai ya sanya na ce na fi kowa sa'a a cikin sararin Duniyar nan, saboda aikin da aka bani a kanka, ya sanya na samu 'yanci. Ni ne Giyaz ibn Jaddul Jinn, ɗaya daga cikin aljanun da suka yi wa kakanninka hidima, daga ƙarshe aka kore shi daga fadar, saboda wani laifi da ya aikata da bai taka kara ya karya ba. Ya tattara iyalansa ya koma Nigeria da zama, ya cigaba da hayyayafa, can ma aka samu waɗanda suka ƙara cutar da shi. Duk da na shafe tsawon shekaru ashirin a tsare, yau wani boka ya bani 'yanci, sannan ya damƙa mini aiki a kanka. Dan haka ko zamu mutu tare sai na cika aikin nan da na karɓa a kan ka" Hammad bai gama gane me Giyaz yake faɗa ba, hankalinsa ya gushe. Bayan ya sake farfaɗowa, ya sake tozali da Habu, sai dai ya manta a inda ya san shi, ko ya taɓa ganinsa. Duk iya ƙoƙarinsa ya kasa tuna komai game da kansa. Shi dai ya san shi mutum ne, duk wani abu da ya shafi rayuwa yana iya tuna shi, amma duk wani abu da ya shafe shi, ya manta. Ko da Habu ya yi yinƙurin mayar da shi Agadez, bin sa kawai yake yi, amma bai san waye shi ba, sai dai su na dosar Agadez Giyaz yake bayyana, yana feso mu wata irin wuta mai ban tsoro, a take sai jikinsa ya ƙara rikicewa ya ji tamkar zai zauce kansa yana wani irin gigitaccen ciwo, bugun zuciyarsa ya ƙaru, ya din ga jin zafin wutar da Giyaz yake feso masa a jikinsa ta na ƙona shi. Gaba ɗaya ya rikicewa Habu. A dole suka bar Agadez suka nufi Nigeria. Su na tafe Hammad yana ganin abubuwan da ya lura abokin tafiyarsa wato Mahmoudu ba ya gani. Duk tambayar da ya yi masa a kan waye shi, ya sunansa ya tuna wani abu game da rayuwarsa amma ya kasa. Da suka shigo Nigeria, suka samu masauki, bai sake ganin Giyaz ba, sai dai lokaci zuwa lokaci wannan zafin jikin yana tayar masa. Tun da suka shigo Nigeria, yake mafarkin wata matashiyar budurwa, tare a cikin sahara. Sai ya kwaɗaitu da son saninta a zahiri. Idan ya kwanta bacci, ba abin da yake mafarki sai wannan yarinyar. A duk lokacin da ya farka, sai ya din ga jin akwai wani abu mai muhimmanci da yake son haɗuwa da shi, duk a duniyar da ya farka, babu wanda ya sani, banda iya mutanen da yake iya gani. Gurin mai magani na farko da suka fara zuwa da su Habu, wata yarinya ta gifta shi, ya ji wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, ya din ga jin tamkar ya koma ya bi inda ya ji sanyin nan. Haka da suka sake haɗuwa a gidan Sarkin baka, bai ga fuskarta ba, amma sanyin nan ya ƙara neman ya zauta shi. Sai dai ya sha mamaki, da ganin wani zanƙalelen mutum yana bin ta a baya, sai dai baya iya ganin iyakar tsawon mutumin. Gaba ɗaya ya lura, gane-gane da yake yi,  shikaɗai yake ganin abun sa. Lokaci lokaci ya kan yi mafarki da gidan tarihi, sai dai ya kasa tuna ina ne gurin. Duk lokacin da ya yi mafarkin yarinyar nan, ya kan tashi da matsanancin farin ciki mara misaltuwa, ya kan ji dama su dauwwama a cikin baccin nasa ba sai ya farka ba. Tun da suka fara aiki a gidan Alhaji Zailani, duk lokacin da zai gan shi, yana ganin jini yana bin sa, da wasu ƙanan yara, da wasu mutane su na kuka, amma Alhaji Zailani ba ya ganinsu, sauran mutane ma ba sa ganinsu, sai shikaɗai. Hakan ya jefa shi a cikin damuwa, da jin cewa shi wata halittar ne daban, da sauran mutane. Sai dai babu zato babu tsammani, ya yi ido huɗu da ita, da wani yammaci ta fito daga cikin gidan, wannan dogon mutumin yana biye da ita, sai dai ya ga wannan tsohon ne ya dawo matashi, bai bayyana a suffarsa ta tsohon da ya saba fitowa ba. Sanyin da ya ji ya ratsa shi ya sanya ya rikice, ya ƙudurce a ransa akwai wani abu da bai sani ba, ko yakamata ya sani, kuma wataƙila wannan da suke tare zai iya gaya masa waye shi, kuma daga ina yake!. Ayshercool. 08081012143 LITTAFIN KUƊI NE, VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 92 Kafin ya yinƙura ya fito daga ɗakin nasu, wanda yake gani ɗin ya ziro sanda ya hankaɗa shi ya faɗi sumamme. Ya fuskanci mutane kowa yana da ahali, uwa, uba, ɗan uwa, mata 'ya'ya ya san duk abu ne mai muhimmanci game da rayuwar mutum, amma shi ya kasa tuna komai a kan rayuwarsa. Su Habu da yake gani a tare da shi, ya san su na yi masa ƙoƙari amma ba ya jin su sosai da sosai a ransa, yadda za su iya zama wani ɓangare na rayuwarsa. Wasu lokutan idan maganar ba ta ɗauke ba, ya kan yi musu magana cikin iko da isa, ba tare da jin nauyin hakan ba, shi Mahmoudu sam baya damuwa da hakan, amma su Sule wasu lokutan abin yana sosa musu rai. Aka ci gaba da tura wa Habu kuɗaɗe cikin asusunsa. Yana ta tunanin yadda zai sanar da can gida Agadez cewa, ga fa halin da ake ciki, amma aka din ga tura masa saƙonni a kan muddin ya kuskura suka koma Agadez, Hammad zai iya rasa rayuwarsa. Ya tura wa Nene saƙon halin da ake ciki. Ya sanar mata ko an zo an tambayi yana ina ta ce ba ta sani ba kawai. Ya kashe wayarsa ya cire layin ya ajiye, ya samu na Nigeria ya saya ya saka. Sai bayan kwanaki biyu, aka farga ba a samun lambar Hammad, wayarsa na ajiye a ɗakinsa. Sultan ya ce wa Asal, kar ta kuskura ta gaya wa wani cewar Hammad ya ɓace ba a san inda yake ba, ana nan ana bincike a kan nemansa. Hammad kuwa sai ya kintaci lokacin da Nana za ta zo gidan Alhaji Zailani ko kuma ta tafi, sai ya fito harabar gidan ya zauna, ko kuma ya buɗe taga, ya san dole zai ji wannan sanyin. Sai dai duk lokacin da zai ganta, tare da wannan dogon mutumin ne da babu wanda yake ganinsa, sai dai ya fuskanci duk lokacin zai gan shi tare da Nana, ba ya cutar da shi, ko ya yi masa feshin wuta, amma duk lokacin da ya bayyanar masa a suffar tsoho sai ya cutar da shi. Duk lokacin da zai ga Nana yanayin fuskarta na nuna damuwa, dan haka sai ya din ga jin kamar ya je ya tambaye ta mene ne yake damunta fuskarta babu walwala. Wasu lokutan kuma Ƙaisar yake kallo, ita kuma sai ta din ga ganin tamkar yana addabarta da kallo. Ranar da Alhaji Zailani kuwa ya biyo ta, haka kurum ya din ga jin jikinsa babu daɗi, tamkar ya bita cikin gidan. Ko da ya ga Nana ta fito a sukwane kuwa, ya san akwai matsala, sai dai Giyaz ya bayyana a lokacin ya shaƙe Alhaji Zailani. A hankali ya fara lura da tsuntsayen da suke bayyana idan ya murza zoben hannunsa, ko kuma ya matsa jakar fatar da yake ratayawa a wuyansa. Ya kan tambayi tsuntsayen, ko sun san waye shi? Suwaye iyayensa? Da kuma 'yan uwansa? Tun da su na magana wasu lokutan. Ba sa ce masa komai sai dai su zana masa taswirar gidan tarihin Agadez a ƙasa. Idan ya kalla ya san gurin amma ya manta a ina ne. Sannu a hankali ya gane, akwai bambanci a tsakanin Giyaz da Ƙaisar ranar da faɗa ya haɗa su, Giyaz ya yi jifa da Ƙaisar sai da ya sha mamaki, ganin tsananin kammanin da ke tsakanin Giyaz da Ƙaisar. A ranar kuma ya fuskanci Nana ma tana gane-ganen abubuwan da ba kowa ne yake gani ba, hakan ya sanya ya ji a jikinsa ita daidai take da rayuwarsa, ita ce suke iri ɗaya. Amma ta yaya? Tun da yana jin Habu da Sule su na zancen Nigeria da Niger, shi da su irin su ɗaya, ga yarukan da yake iya yi, wanda alamu suka nuna inda suke ba duka yaren da suke yi mutanen gurin suke ji ba. Ɓangaren Ƙaisar ma, tun da ya ga Giyaz a tare da Sayyid ya rikice, domin bai taɓa tsammanin Giyaz zai dawo ba. Wataran bayan shafe kwanki biyar Sayyid yana fama da wannan zafin jikin da yake rikita shi. Ga babu magana abinci ma baya iya ci. Ya wayi gari ya ɗan samu sauƙi. Har ya ci abinci ya shiga ya yi wanka da la'asar. Kawai ya ji wannan sanyin yana kusanto shi. Babu tsammani ya ji muryarta, ta yi sallama sai dai ya yi shiru yana tunanin ko tsabar saka ta a ransa ne ya sanya ya ji muryarta. Yana tsaye cak da matajin hannunsa, ya ji muryar yaro a ɗakin bai ga yaro a ɗakin ba, kawai ya ga ta faɗo ɗakin. Su na haɗa ido ya ga ta yanke jiki ta faɗi. Ya ga Ƙaisar ya bayyana ya tsaya a kanta yana huci, shi dai ya tsaya yana kallonsa dan bai san abin da ya yi mata ba. Ya gama ya sanya kayansa Nana ta kwance, amma sanyin da yake tattare da ita na saukar masa da wata irin nutsuwa da daidaita zafin jikinsa. Tun daga lokacin aka fara dambarwar nan, har ta kai ga ɗaura masa aure da Nana, ya din ga jin amincewa da auren, shi ne hukunci mafi daɗi da zai yankewa wannan rayuwar tasa da yake yi mara kan gado. Ba ya jin ko ɗar sanya Habu ya yi masa duk wani abu da yake buƙata. Bayan aurensa da Nana a  jikinsa yake jin, samun nutsuwa a tattare da wannan duniyar da kuma kwanciyar hankali, idan ya matsa ya tuna wani abu da ya shafe shi game da ainihin waye shi, sai ya ji damuwa da baƙin ciki ya mamaye shi. Habu kuma bai taɓa gangancin gaya masa waye shi ba, kawai ya ƙyale shi a kan duk lokacin da ya tuna wani abin ya sanar da shi. Idan ya kwanta bacci baya mafarkin kowa, sai wannan dai gidan tarihin da yake gani, sai kuma ya din ga ganin wasu abubuwan da suka faru a ƙarnukan baya a wannan gidan sarautar, har ma da mutanen da suka yi rayuwa a gidan. Wasu lokutan har a zahiri yana ganinsa a gidan tarihin amma bai taɓa tuna a ina ya san gidan ba, sai dai bai manta abin da ya faru na ƙarshe a gidan ba, na firfitowar wannan halittun daga ɗakunan tarihin. Sai dai yana yawan ganin gidan, sakamakon aljanun da suke tattare da zobensa da kuma jakar fatarsa, ainihinsu mazauna gidan ne, kuma su ma su kan yi kewar gidan, tun da duk inda yake ya murza zoben sai sun zo. Lokacin da aka yi aurensu, aka kai Nana wannan aljanun na zobensa ne suka din ga rangaɗa guɗa. A duk lokacin da yake son ya yi wasa da hankalin Nana, sai ya murza zoben hannunsa, idan ya danne jijiyar da ke wajen ƙeyarta, sai ta yi bacci. Haka zalika yadda yake ganin gidan tarihin nan, haka ita ma take ganinsa. Da wannan aljanun yake amfani ya burkita mata lissafi, ya yi abu da ita a zahiri amma ta din ga ganin kamar a mafarki ne. Haka zalika Giyaz da yake taka rawa gurin addaba musu, tare da cutar da su, da abubuwa na ban tsoro. Ƙarfin ibadar Nana ne ya sanya suke samun sassauci a wasu abubuwan. Nana ba ta taɓa sanin amfanin zoben nan na hannunsa ba. Ya ɗauki zoben ya ba wa Nana kyautarsa, saboda abin da yake ji a zuciyarsa game da ita. Saboda a jikinsa yake jin zoben na da muhimmancin gaske, dan haka ya ɗauka ya bata. Ƙaisar ya yi ta gargaɗin Nana a kan Sayyid, saboda yana jiye mata tsoron Giyaz, da kuma kar Aljanun da yake ta'amalli da su, su cutar da ita. Duk da yadda Ƙaisar yake jin haushin Sayyid, da yadda Nana ta saki jiki da shi suke rayuwa, amma ya taka muhimmiyar rawa gurin ƙara jirkita hankalin Nana, da sauƙaƙawa Sayyid ɗin wasu abubuwan. A sakamakon yarjejeniya da suka yi da hadiman jikin zoben Sayyid, a kan za su ba shi wasu labarurruka da suka faru a wasu zamani da suka shuɗe, tun kafin a haife shi a cikin Duniya, bisa yarjejeniyar idan suka cutar da Nana ba za su taɓa zama lafiya ba. Duk da tsamin alaƙar da ke tsakanin Giyaz da Ƙaisar, amma yana jin daɗin ganin ɗan nasa, bayan shafe shekaru masu yawa bai gan shi ba. Ya na tsananta cutar da Nana da Sayyid, saboda ya muzgunawa Ƙaisar. Ko lokacin da ya bi Nana, har ya duba Baba, a zahiri ya ga ƙullin da Ƙaisar ya yi a ƙafar Baban, kuma da aljanun jikin zobensa, ya warware ƙullin. Rayuwarsa da Nana yana saka shi jin wata nutsuwa a tattare da shi, ga alaƙar Giyaz da ta Ƙaisar da ta shafi rayuwarsa da Nana. Sau ɗaya ya yi mafarkin Sultan, ya gan shi cikin damuwa da tashin hankali, ya farka a rikice da sunansa a bakinsa amma bai iya tuna ko waye shi ba. Can Agadez kuwa, bayan ɓatan Hammad, aka ankara da ɓacewar Mahmoudu, hakan ya sanya Sultan cewa duk inda Hammad yake yana tare da Mahmoudu. Sultan ba ya iya cin abinci, ba ya isasshen bacci saboda tashin hankalin rashin sanin inda Hammad yake. Ga shi ɓoyewa suke ta yi, duk da yadda Tafawa da muƙarrabansa ke ta ƙoƙarin bin diddigin gano abin da Sultan yake ɓoyewa. Lambar Mahmoudu da ta ƙi shiga, sai aka yi ta tracking lambar Mahmoudu, aka gano last inda ya yi amfani da ita a Nigeria ne. Aka din ga bin diddigi har gidan Alhaji Zailani, aka tafi da motoci gaba ɗaya aka kwaso Buzayen layin kaf. Sai da aka zo Agadez, sannan aka tantance su bayan da aka fahimci su ba su san komai ba, hasali ma wanda ake maganar a kansa ba su san waye shi ba. Aka ɗauke Mahmoudu daga cikinsu, aka din ga tuhumar sa, ina Hammad yake, amma ya ƙi magana saboda yana jin tsoron gargaɗin da aka din ga yi masa, a kan muddin Hammad ya dawo Agadez mutuwa zai yi. Mahmoudu ya sha azaba kala-kala, tamkar ba zai yi rai ba, sai da ya ji azaba sannan ya gaya musu cewar Hammad yana Nigeria. Aka saka shi a gaba zuwa Nigeria, aka taho da Hammad. Sai dai tunda aka taho da shi, sai ƙwaƙwalwar ta sak burkicewa, tunaninsa ya rikice. Bai gama tantance waye shi ba, hankalinsa ya dawo ba, sai da aka fitar da shi Faransa. Dama ƙwaƙwalwar a hargitse take, baya tantance komai, sai dai sannu a hankali tunaninsa na rayuwar da ya yi a Nigeria, ya shafe gaba ɗaya. Sai ainihin tunaninsa na waye shi ya dawo masa. Ganin ya dawo hayyacinsa ya daina iface-ifacen da yake yi, ya nuna ya gane Sultan da Matawalle, suka yi farin ciki sosai, suka tambaye shi ko ya tuna abin da ya faru da yaje Nigeria, sai ya rikice yake tambayar me ya kai shi Nigeria. Daga nan kawai sai suka ɓoye masa, suka ce jinya kawai ya yi mai tsawo a faransa. Likitoci suka din ga ba shi kulawa a kan matsalar zuciya da yake fama. Can a Agadez kuma, aka ci gaba da azabtar da Mahmoud a kan lallai sai ya faɗi dalilin da ya sanya, ya sace Hammad ya tafi da shi Nigeria. Ga Tafawa ya matsa a kan lallai sai an faɗi inda Hammad yake, tun da an doshi shekara biyu, babu wanda ya gan shi, ko kuma a ba su dama su je su duba shi, su gan shi ido da ido su tabattar yana raye babu wani abu da ya same shi. Sai dai Hammad ya kasa yarda da cewa, tsawon wannan lokacin, jinya yake yi. Tiryan-tiryan abin da ya faru na ƙarshe daga gidansa, zuwa gidan tarihi daga nan kuma sai ya rikice ya kasa tuna komai. Ya ce wa Sultan lallai a kawo masa Mahmoudu, Matawalle ya ce "Ko ka tuna wani abu ne? Me Mahmoudun zai yi maka?" Hammad ya ce "Babu komai, ni ba na jin daɗin zama nikaɗai ne, na saba duk inda nake mu na tare, ni dai a kawo mini shi" Matawalle ya ce "Ka yi haƙuri, Likitoci sun ce ba a buƙatar kowa ya zo inda ka ke ne" Ya yi shiru yana tunanin, ina Asal da ko sau ɗaya ba ta zo ba ita ma. Sai dai a jikinsa ya din ga jin kewar wani abu mai muhimmanci a tare da shi, kamar yana jin matsananciyar ƙishirwa. Sultan kuwa ya sanar da Asal batun ganin Hammad, amma ya ce mata rashin lafiya ce ta kama shi a Niemey, aka kai shi wani Asibiti a can, daga baya a ka kai shi faransa. Duk da ta yi mamakin yadda za a ce rashin lafiya ta kama mutum, a kai shi Asibiti amma ba a nemi ahalinsa an sanar da su ba tsawon shekaru. Sai dai hakan ma sai da ta gaya wa Tafawa. Ya ruɗe ya rikice dan ya so a ce wani mummunan abin ne ya samu Hammad. Tun da Asal ta ji labarin Hammad zai iya dawowa a kowane lokaci, take shirin karɓar sa, dan ba ƙaramin kewarsa ta yi ba. Dan ta shiga damuwa da tashin hankalin da sai da suka samun matsala da Tafawa bayan ɓacewar Hammad. Tun da Sultan ya ce a kowane lokaci zai iya dawowa, ta sanya aka yi gyaran gidan sosai. Sannan ta fara lissafin canza kuyangin da za su din ga yi masa hidima. Ga Tafawa ya yi mata alwashin idan ba za ta ci gaba da ba shi haɗin kai ba, zai nemi wani ya yi masa, ko da kuwa ta kama a salwantar da ran Hammad ɗin ne baki ɗaya. Sai dai duk da tunaninsa na Agadez ya dawo, bai fasa fama da wannan matsanancin zafin jikin ba, da yake jin tamkar ana ƙona shi ba. Sai dai ya rage tashi a kai a kai. Haɗuwar Asal da Nana, ya zame wa Asal tamkar tsintar dami a kala, ta ga idan ta kawo Nana gidan sauratar Agdez, kanta a tukunya yake game da sha'anin sarauta, ga girki ta iya, saboda Hammad na son daddaɗan Abinci, ga kuma Nana baƙa ce 'yar Nigeria, babu yadda za a yi ta ɗauki hankalin Hammad, saboda baƙar mace ta haramta a gare su, bisa ga Al'adar Agadez. Sai dai abin da Asal ba ta sani ba shi ne; a rashin sani kaza ta kwana a kan dami. AREWABOOKS Tun da Hammad ya sauka a filin tashi da sauukar jirage, gabansaa yake faɗuwa, ya kuma rasa dalilin hakan. Jin sa yake yi tamkar yana daf da maganin ƙishirwar da ta addabe shi. Bayan Nana ta yi amfani da ƙarfi, gurin tursasa wa Nana zuwa Agadez, ta sanya Nana cikin jerin waɗanda za su yi girkin karɓar Imam Hammad. Gabba ɗaya gida ya ɗauka Hammad zai dawo, bayan shafe dogon lokaci yana jinya. Su kansu wasu daga cikin Imam Imam ɗin, ba haka su ka so ba duk da abin jita-jita ake ta yi, Sultan bai tabattar da hakan ba, kuma a daren za a yi babban taro tare da 'yan majalisar Sarki, da kuma su Imam na shekara da ake gabatarwa. Sai dai babu tsammani, su ka ga Hammad ya bayyana a gurin. Tun da ya shiga gurin, ya ji wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, da kowace irin AC aka kunna, sanyin baya wadatar da shi har cikin ƙashinsa ya ji ya gamsar da shi. Ya ji wani irin jiri na neman ya ɗebe shi, amm ya daidaita nutsuwarsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa ya rabe ya je ya zauna. Bai ɗago kansa ba, ya ji Matawalle na tambayar me ya kawo wannan nan gurin. Aka sanar masa tana cikin masu girki ne. Bai dai ɗago ba sai murmushi da yake yi, saboda barka da zuwa da ake ta yi masa. Sai dai ƙirjinsa ya tsananta bugawa, da aka ce ta zo ta ɗanɗana Abincin, ta nufo inda suke. Ya kasa jurewa ya ɗaga kansa, sai ya ji kamar sanyin da yake ji yana ƙaruwa. Wani abu ya ji mara daɗi a ƙirjinsa ganin yadda ta ɗaura rigar girki a kan kayanta, ana ganin shape ɗin kyakykyawar surar da Allah ya yi mata ta bayyana. Kalar fatarta ya ɗauki hanklinsa, tsohon muradinsa na son baƙar mace ya motsa a zuciyarsa. A kallo ɗayan da ya yi mata duk ya nazarci wannan abubuwan ya sunkuyar da kansa. Amma ya nemi ya kasa jure bugun da zuciyarsa take yi babu ƙaƙƙautawa. Bai ji daɗin yadda Matawalle ya saka a ka fita da Nana ba, saboda yadda duk ta rikice a gurin. Sai dai ya yi ta mamakin yadda aka ta shiga cikin masu girki, alhalin tana baƙar fata 'yar Nigeria. Da suka tashi daga taron nan kuwa, da Asal ta gan shi, wani irin tsalle ta yi ta maƙalƙale shi, tana murna cikin matsanancin farin ciki har da hawayenta. Ya ɗago ta daga jikinsa yana murmushi yana kallon idanunta, da son gano ainihin abin da yake gani a idanun nata, dan abin da ya faru daren da ya bar Agadez fes yake dawo masa. Ya tsura wa idanun Asal ido, ya ce "Kin yi kewata har haka?" "Imam, kusan shekara biyu ba ma tare ka ce ko na yi kewar ka? tu me manques(Na yi kewar ka sosai) Ta yi maganar idanunta ɗauke da hawaye. Bai bari zuciyarsa ta ci gaba da raya masa abin da take raya masa ba. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "tu me manques. Na yi kewar ki sosai cherié. Ina fatan kina lafiya babu abin da ya same ki?" "Ba abin da ya same ni, sai damuwar rashin sanin inda ka ke, ina ka tafi aka neme ka aka rasa haka, ka tayar mini da hankali na shiga damuwa sosai" Ya yi shiru yana mamaki, Sultan ya ce masa faɗuwa ya yi, ya shiga coma na tsawon lokaci, yanzu kuma tana faɗin ya tafi ba a san inda yake ba, ga abin da ya faru na ƙarshe kan barinsa Agadez yana dawo masa. Sai ya kawar da tunanin komai daga cikin zuciyarsa. Duk rawar kan da Asal take yi, da murnar dawowarsa gaba ɗaya hankalinsa ba a kan hakan yake ba. Jin sa yake yi ba daidai ba. Ya yi iya ƙoƙarinsa ya sarrafa tunaninsa da nutsuwarsa gurin ba ta dukkanin kulawa da kuma lokacinsa, amma hankalinsa na kan abin da shi kansa bai san mene ne ba. Da dare ya yi kuwa, ya riga Asal kwanciya dan kar ma ta nemi wani abu a tare da shi, saboda fatansa ya gano takamaiman mene ne yake damunsa. Sannan ya yi mamaki rashin ganin Mahmoudu da bai yi ba. Yana kwanciya bacci surar Nana ta bijiro masa, a ƙasan zuciyarsa ya ji bai ji daɗin fitowarta a haka ba. Da sauri ya yi istigfari dan gudun kar shaiɗan ne yake ƙara ƙawata masa ita. Amma duk da haka bai daina ganin ta a idonsa ba, ds yadda ta zuba masa ido duk ta rikice ba. Ya yinƙura ya tashi zaune, ya ga Asal ta yi bacci, ya yi shiru yana tunanin wa zai tambaya wace ce ita. Ya gaji da zancen zucin ya matsa kusa da Asal ya kwanta tare da rungume ta a jikinsa. Sai ƙamshin turare take yi da alama ta shiryawa dawowarsa sosai. Ya shafa gashin kanta, tare da fatan Allah ya sanya Asal ɗin ta canza gaba ɗaya, tare da yi musu addu'ar samun rabo na alkhairi. Kamar ya tashe ta, sai kuma ya ƙyale ta kawai ya lumshe idanunsa yana addu'a a ƙasan zuciyarsa yana jiran bacci ya ɗauke shi. Yana tsaye a cikin sahara, ya riƙe akalar raƙuminsa, iskar sahara sai kaɗawa take yi, babbar rigar jikinsa na ɗagawa, ta cikin iskar yake jiyo sheshsheƙar kukan mace tana faɗin "Sayyid" ya waiwaya bai ga kowa ba. Shikaɗai ne a cikin saharar, sai dai bai daina jin sheshsheƙar kukan ba. A hankali ya buɗe idanunsa, wannan shi ne karo na bai san adadi ba, yana wannan mafarkin tun da ya buɗe ido a faransa. Jin kiran sallar Asuba ya sanya ya tashi ya tafi salla. Ranar farko da ya sake cin abinci bayan wanda ya ci da ya dawo, sai ya ji kamar ya san ɗanɗanon abincin, amma ya manta a ina ya san shi. Ranar da ya sake ganin Nana, Asal ta kira ta a kan ta zabga yaji a abinci ya kasa ci, sai da zuciyarsa ta kusa tsayawa, ya din ga jin kamar abu malaman haka ya taɓa faruwa, amma bai san a ina ba. Jikinsa ya din ga tsuma sakamakon jin sanyin da ya fara yi, ga kallon da take yi masa da ya sake burkita shi. Ya din ga matsa ƙwaƙwalwarsa, ko za ta ba shi wani abu, amma ya ji ya fara jin jiri. Bai tsaya kammala karin kumallon ba, ya tashi ya fita ya je ya samu Sultan, baya ya kammala zaman Majalissa, yake ce masa shi fa haryanzu bai ga Mahmoudu ba. Sultan ya ce masa ya yi tafiya ne, amma zai dawo. Haka kurum ya ji bai yadda da hakan ba, amma bai kuma cewa komai ba. Cikin hikima ya tambayi Asal inda ta samo Nana, ta sanar masa da a gidan Abincinsa na Maraɗi take aiki, ganin ta iya girki ya sanya ta kawo ta gidan, domin ta din ga dafa masa abinci. Sai dai a kullum abubuwan da Nana take yi, su na ƙara dagula masa lissafi nesa ba kusa ba. Matsin lamba da Hammad ya yi ya sanya aka sako Mahmoudu, kuma Matawalle ya jaddada masa lallai kar ya kuskura ya gaya wa Hammad komai a kan zuwan da suka yi Nigeria, kuma kar ya gaya masa ɗaure shi suka yi. Hammad bakinsa ya ƙi rufuwa, bayan ganin Mahmoudu da ya yi, saboda yadda yake jin Mahmoud a rayuwarsa ba ya jin Zahradeen yayansa da suke uba ɗaya haka. Sai ya yi ta yinƙurin ya yi wa Mahmoudu bayanin abubuwan ban mamakin da yake gani game da Nana, amma sai ya kasa. Babbn abin da ya sake ɗaure masa kai da ita, shi ne lokacin da ya hana ta cin ayaba. Ta karɓa ta ci, a lokacin ya ga Ƙisar a tare da ita. Ganin Ƙaisar ya ƙara hargitsa masa lissafi, saboda yana ganinsa hoton suffar Giyaz ya faɗo masa, amma ya manta a ina ma ya san fuskokin. Sai daga baya sannu a hankali ya tuna yadda Giyaz y fito masa a gidan tarihi, amma wanda ya gani tare da Nana bai kai wancan tsufa ba. Gefe guda kuma Ƙaisar da Giyaz su na ta dambarwa, Giyaz ya ce ba zai taɓa rabuwa da Nana ba, ya mantar da Hammad wace ce Nana da duk wata rayuwa da suka yi a Nigeria saboda ta ci gaba da shan wahala. Bokan da ya sanya Giyaz aikin ɓatar da Hammad kuwa, hankalinsa ya dugunzuma bayan da shi ma wands ya ba shi aikin, ya matsa masa lamba da masifar ya aka yi Hammad ya dawo Agadez bayan an ce har abada shi da Agadez. "Ya kai Giyaz, ina alƙawarin da muka yi da kai? Na baka 'yanci bisa sharaɗin za ka yi mini aiki, amma kwatsam sai na ga wanda na baka aikin a kansa ya dawo Agadez" Giyaz ya ce "A cikin aikin naka wanne ne ban yi ba? Na mantar da shi waye shi, na mantar da shi, ya bar Agadez ya yi nesa da ita, kuma ya yi. Ni da kai ba na tunanin akwai wanda yake bin wani bashi, na cika sharuɗɗanka kaf da muka yi yarjejeniya a kai" Bokan ya ce "Amma ai ga shi ya dawo Agadez cikin ƙoshin lafiya a hayyacinsa" "Eh, ai ba mu yi da kai zai bar Agadez har abada ba, na kuma yi iya abin da muka yi sharaɗi a kai" "Kar ka fusata ni, ka sanya na sake kama ka na rufe ka, ni bami yi haka da kai ba" Giyaz ya ce "Ƙarya ne, ni dai ka kama ni ka sake kulle ni, ba za ka iya wannan ba. Kuma duk abu dole na zauna inda zan iya ganin ɗa na. Kuma ina nan ina ci gaba da gudanar da aikin da ka bani bisa yarjejeniya, tun da haryanzu ina nan tare da shi ban bar shi ba" Bokan ya ce "Waye ɗan naka, kuma a ina yake?" "Babu wannan a cikin yarjejeniyar aikina da kai, ka bar zancen a yadda na bar shi kawai" Bokan nan ya san faɗa da Giyaz ba abu ne da zai haifar musu da ɗa mai ido ba, sai dai dawowar Hammad mayar musu da aiki baya ne. Mahmoudu tunanin Nana ya addabe shi, tare da ganin rashin dacewar abin da ya faru. Ga shi alamu sun nuna ƙiri-ƙiri Hammad bai san ya je ya yi wata rayuwa a Nigeria ba. Ya kuma san muddin ya ce zai je Nigeria sai Hammad ya bi ba'asi, kuma kwana ɗaya ko biyu ya yi kaɗan ya je ya nemi Nana, balle ya yi masa ƙaryar kasuwanci zai je. Ya sha tambayar Mahmoudu a kan ko akwai wani abu dayake damunsa, saboda yanayinsa ya nuna akwai damuwa. Amma ya kan ce masa babu komai. Hammad ya ce wa Asal baya buƙatar sake ganin Nana. Sai murna take saboda ta zata munin Nana yake gani, shi kuwa mafita yake nema, daga burkicewar da yake yi a duk lokacin da ya ganta. Sai dai kuma kwana biyu da ya daina ganinta sai ya shiga damuwa, ya zamana duk ranar da bai ganta ba, sai ya ji shi tamkar a kurku, wunin ranar bai yi masa daɗi ba sam. Yana zaune a ɗakinsa, yake kallon yatsunsa babu zobe guda ɗaya, wanda shi ya fi kowanne muhimmanci. Shi dai Matawalle ya ce masa duk wanda ya tambayi zoben ya ce an kai zoben gyara ya samu matsala. Ya kalli tagullar hannunsa, ya din ga murza ta a hankali yana zancen zuci. Saboda gaba ɗaya a rikice yake, kasancewar Nana ta kai masa abinci tana ƙamshin turarensa da yake amfani da shi. Shi dai ya san babu wanda ya bawa turaren, kuma mai aiki kamar Nana ba za ta iya sayen turaren ba, kuma babu yadda za a yi a ce satar turaren ta yi har ta samu ƙwarin gwiwar shafawa. Yadda take yi masa wasu abubuwan kai tsaye wasu lokutan abin yana ba shi mamaki sosai da sosai. Ganin ya yi hasken wutar ɗakin tana ɗaukewa tana kawowa, daga baya ta tsaya, sai ga wani ɗan gajeren abu a ya bayyana da tsawonsa bai fi 'yar tsana ba, kansa duk wasu ƙayoyi. Hammad ya zuba wa abin ido, ganin yana motsi. "Tuba nake shugabana na tsorata ka, ni ne aljanin da aka wakilta hidima ga duk wanda ya ɗauke da wannan tagullar, tun da ka ke ba ka taɓa nema na ba sai yanzu, me ka ke buƙata?" Hammad ya ce "Waye kai?" "Arun, bawan aljani ga Sultan Azhar, wannan tagullar mallakinsa ce, kuma ni mai hidima ne ga ma mallakin tagullar" Hammad ya zuba ido sosai, ya ga ɗan abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa gemunsa ƙasa yake ja. Ya ce "Amma da idan na murza zoben ba kai nake gani ba" Arun ya ce "Ai ba ni ka ke kira, hadiman wancan zoben daban, nima kuma daban" "To ina zoben nawa yake?" "Ka yi kyautarsa ga wanda ka ke matuƙar ƙauna a matsayin tukuicin soyayya" Hammad ya ce "Soyayya kuma? Ni ɗin? "Ƙwarai ya shugabana" "To wa na bawa, kuma yaushe na yi soyayyar, kuma mace ce ko namiji?" Arun ya sake cewa "Ba na son shiga hurumin da ba nawa ba, ina gudun sake rura wutar fitinar da ke tsakanin gangar jiki buyi, ruhika huɗu, alaƙa huɗu. Gangar jiki ta mutum biyu, ruhi huɗu, na mutum biyu da na aljan biyu, sai kuma alaƙar mata da miji da kuma uba da ɗa, sannu a hankali duk za ka fahimci abubuwan da nake nufi" Daga nan ya ɓace Hammad ya yi shiru yana juya maganganun da suka fi yi masa kama da shirme. Ya tashi ya fita falo, ya san lokacin kawo masa shayin dare ya yi, sai dai tun kafin ya ƙaraso cikin falon yake jiyo sautin muryarta tana waƙa. Daga nesa kaɗan ya tsaya yana kallonta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri. *_ina zana ganka_* *_saƙo zana baka*_ *Hotona da naka*_ *_Ko ina zana bika*_ *_Kowa tsane ka, ni na tsane shi sanya a ranka*_ *_Zuciyata na baka duk masu ƙin ka su daina shakka*_ *_Rayuwata na baka_* *_Ni ta ya zan guje ka*_ *_Ka dawo gare ni dan zuciya ta bar kewa*_ Gaba ɗaya sai ya daskare a gurin, gumi ya din ga tsatstsafo masa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga Kai komo, kansa kamar zai yi tsawa ya fashe. "Tabbas akwai wani abu, ya san wani abu mai kama da haka, amma yaushe? Kuma a ina?" Ya daɗe a tsaye a gurin, kafin ya saita nutsuwarsa ya shiga falon. Murmushi ta yi ta daina waƙar da ta ga ya fito ta risuna ta ce "Barka da dare" Ya jinjina mata kai. "Sayyid ga shayinka nan, ina fatan na kammala komai, zan iya tafiya?" Ya yi shiru yana jujjuya Sayyid da take kiransa da shi. Washegari da sassafe ya kira Mahmoudu a waya, ya sanar masa da yana son ganinsa za su yi magana. Amma Mahmoudu ya ce masa yana hanyar Maraɗi, zai kai wa Nene ziyara ne. Hammad ya yi ta mitar me yasa bai gaya masa su tafi tare, su je su gaishe ta, ya ba shi haƙuri. Sai dai tun da Mahmoudu ya je ya ga Muhsin ya rikice, ya din ga yi wa Nene tambayoyi a kan Muhsin, amma ta ƙi gaya masa haƙiƙanin gaskiyar waye Muhsin. Sai dai yanayin yadda ta ga Mahmoud ya rikice, ya sanya ta tabattar da ya ga abinda take tunani ita ma. Kwanansa ɗaya ya shirya ya nufo Agdez bayan ya faki idon Nene ya ɗauki hotunan Muhsin. Ya nufi Agadez da nufin komai zai faru sai dai ya faru. Hammad kuwa ya lallaɓa Asal ya yi mata wayo ya sanya ta dawo da Nana sashen su, ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Amma shi a jikinsa yana jin baƙin abubuwa game da 'yar Nigeria da jikinsa bai ba shi cutar da shi za ta yi ba, amma kasancewarta daf da inda yake yana samun nutsuwa da nishaɗin kallonta. Tun da Mahmoudu ya dawo, Hammad ya lura bakinsa akwai magana, amma ya ƙi ce masa komai. "Mahmoudu na lura bakinka akwai magana, amma ka ƙi gaya mini, duk da ba ma 'yar haka da ni da kai, amma bari ni na gaya maka tawa damuwar". Mahmoud ya ce "Ni babu wani abu da zan gaya maka, amma gaya mini mene ne yake damunka?" "Ina kukun da nake gaya maka Asal ta samo 'yar Nigeria?" Gaban Mahmoud ya faɗi amma ya dake ya ce "Eh meyafaru?" "Wasu abubuwa nake ji game da ita, da tun da nake ban taɓa ji game da wani mutum ba" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Ko santa ka ke yi ne?" "Anya kuwa, ban dai sani ba, amma ba normal mutum ba ce" "Ka na da mata fa a Nigeriar nan" Hammad ya kalle shi yana jiran ƙarin bayani. Mahmoudu ya ce "Da wasa nake yi, na dai ce zan aura maka 'yar maka 'yar Nigeria idan ka na so. Amma ina da wani abin al'ajabi da nake son nuna maka, amma tashi mu je ka shirya, ka ce mini za ku yi hawan raƙuma kar a yi ta jiran ka" Babu musu ya tashi suka fita. Kowanne a cikin su yana ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa. Sai dai bayan an yi hawan raƙuman, da Hammad ya faɗo tare da Mahmoudu aka dawo da Hammad gida. Sai dai ya yi mutuwar tsaye, da hango ta tana leƙen mutanen da suke kaiwa da komowa a falon fuskarta ɗauke da damuwa. A jere zuciyar Mahmoudu ta buga, addu'a ya fara yi, a kan Allah ya sanya ba mafarki yake yi ba, ko kuma tsabar saka abin a ransa ne ya sanya ta fara yi masa gizo ba. Ayshercool 08081012143 93 93 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA. 08081012143 Cikin hanzari Habu ya ja rawaninsa ya nufi barin falon, yana daf da fita Nana ta waiwaya ta ga wucewarsa, sosai ta tsaya tana kallon bayansa har ya fice tana yi masa kallon sani. Washegari da safe Bayan Tafawa ya zo duba shi, ya tafi zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, saboda kausasan kalaman da Tafawa ya yi amfani da su, har da ce masa ko shaye-shaye yake yi, shi ya sanya ya faɗo daga kan Taguwa. Wajen ƙarfe sha ɗaya, da ya ji sauƙi, ya lallaɓa ya fito, yana mamakin dalilin da ya sanya Nana hana shi hawa kan Taguwa, da ya hau kuma ya faɗo. Yana fitowa ya tarar da ita da Asal su na mujadala. Sai dai hangota kawai da ya yi, sai ya ji wani sanyi a ransa. Nana ce take kallon Asal cikin takaici, bayan da Asal ta ce mata ta din ga sanya da hadiman gidan suke sakawa. Nana ta rasa dalilin da ya sanya Asal ke son ƙasƙantar da ita ko ta halin ƙaƙa. Nana ta dube ta ta ce "A gaskiya ba zan iya sanya kayan da hadimai suke sanyawa ba, ko ki haƙura ki kalle ni da kayan jikina, ko kuma ki sallame ni. Tun da ni ba baiwarki ba ce ba, aiki kawai ki ka ɗaukko ni na yi miki" "Idan na so mayar da ke baiwar tawa ina da halin yin hakan, ke kin san ina da abin da ko nawa za a yi miki kuɗi zan iya bayarwa na saye ki" "Ko da Goma ta lalace a gaban biyar take har gaban Abada Gimbiya Asal. Kuma wani garin ya fi gaban kunu.  Ba ki da arzikin da za ki Asma'u a matsayin baiwarki" Nana ta ƙarasa maganar a zafafe. Hammad ya yi gyaran murya, suka tsaya Asal ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓawa Nana. "Cherié, ba zai yiwu ki ɗaukko wadda ba hadima ba a cikin gidan nan, alhalin kin san kin taka dokar gidan mulki ba, sannan ki ce ta din ga saka kayan hadimai a nan ta fiki gaskiya." Cikin mamaki Asal ta kalle shi za ta yi magana, amma ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa a dole ta yi shiru. Nana kuwa haɗa su ta yi, tai musu kallon banza ta wuce ta bar su a gurin. Sai dai kallon da ta yi musun, sai da ya kusa ɗimaucewa, ji ya yi tamkar ya bi bayanta. Wani murmushi ya saki ya nufi Asal yana lumshe ido ya ce "Ba girmanki ba ne, ki din ga sa'in sa da ma'aikatanki ai kin wuce nan". "Amma ka na kallo a yadda take yi mini magana, kuma ka hana ni magana?" Ta yi maganar kamar za ta yi kuka. Ya kamo hannunta ya ce "Yawan musayar yawu da na ƙasa da kai, raini yake janyowa, kuma kar ki yadda ki yi fin ƙarfi a abin da ba ki da gaskiya, nan ma raini zai din ga janyo miki" Ya ƙarasa maganar yana rungume Asal, amma a zahiri hanyar da Nana ta bi, ya bi da kallo ƙamshin turarensa da ta shafa ya ci gaba da karaɗa hancinsa. Mahmoudu kuwa bai yi bacci ba, so yake ya tabattar da abin da idanunsa suka gane masa, gaskiya ne ba gizo ba. Ya kira wayar Hammad, amma bai ɗauka ba, ga shi tsoron zuwa gidan yake domin kar su haɗu da Nana, ya san komai zai rikice ne. Ga yaron da ya gani a gurin Ummansa, ga kashedin su Matawalle, ga kuma wannan abu da ya tarar. "Anya yaron na ba ɗan Hammad ba ne?" Ya tambayi kansa. Wayewar garin Allah ya din ga kiran Hammad a waya amma bai ɗaga ba. Takaici ya ishe shi, sai can wajen Azahar sannan ya kira Mahmoudu. "Tun jiya nake kiran ka ka ƙi ɗaga wayata" Hammad ya ce "Ban jin daɗi ne, sai yanzu na duba wayar, ya ake ciki ne?" Mahmoudu ya ce "A ina zamu haɗu, ina da magana da kai" Hammad ya ce "Ina gurin Sultan, haryanzu bai sallame ni ba" "Idan ya sallame ka, mu haɗu a saharar gidan tarihi mu sha shayi, zan nuna maka wani abu" Hammad ya ce "To, saura na ga ba wani abin kirki ba ne, ba za ka yi mini ya jiki ba?" Mahmoudu ya ce "To ya jiki Allah ya kiyaye gaba sai mun haɗu" Hammad ya yi murmushi ya ajiye wayar. Da yamma suka haɗu a sahara, lokacin rana ta yi sanyi. Hammad ya ce "Sai wani nema na ka ke yi, me za ka bani?" Mahmoudu ya ce "Babu komai shayi kawai nake son mu sha tare." Hammad ya yi shiru yana kallon saharar, daga inda suke su na hango gidan tarihi, kuma suna hango wani sashe na gidan sarauta. Ya na shan shayin a hankali yana son ya tuna wani abu, amma ya kasa. Mahmoudu ya ce "Ya na ji ka yi shiru?" "Ina tunanin yarinyar nan ne" "Wacce?" "Wadda Asal ta kawo, a matsayin mai yi mini girki, abubu da dama su na faruwa da na kasa gane kansu" Nan ya sake gaya wa Mahmoudu yadda ta hana shi hawan taguwa, da abubuwan da yake ji game da ita" Mahmoudu ya ce "Kuma kai ba ka santa ba, baka taɓa ganinta ba ko a wani guri?" Ya ɗan yi shiru Sannan ya girgiza kai ya ce "A nan kawai na taɓa ganinta" "Baka tuna komai ba, da muka zo gurin nan?" Nan ma ya girgiza kai duk da yadda ya ji kansa ya fara ciwo. Mahmoudu ya ce "Gaskiya yakamata a ce duk yadda za mu yi, muyi bincike a kanta, mu san daga ina take, kar mu sakankance wani abin ya faru. Ka san ita kanta Gimbiya Asal ba ta yin abu babu dalili, kar mu je shirin Tafawa ne" Hammad ya ce "Gaskiya ne, amma ta ce mini daga gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ta a gurin su Al-Husssain" Mahmoudu ya ciro wayarsa ya daddana, ya miƙa masa ya ce "Ka ga wani ikon Allah" Hammd ya sanya hannu ya karɓa, ya yi shiru ya zuba wa wayar ido. Jiki a sanyaye ya ɗago ya kalli Mahmoudu ya ce "Ina ka samo wannan hoton?" "Samo shi na yi kawai na nuna maka" Ya damƙe wayar da ƙarfi, ƙirjinsa ya yi masa nauyi ya ce "Mahmoudu kuma ka tabatta wannan ba ɗana ba ne ba? Duk wanda ya kalli wannan hoton zai yi zaton ma nine" "Ka na da wata matar ne da zata haifa maka ɗa? Ko kuma Asal ta haihu ne bamu sani ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, amma wannan yaron buzu ne, duk inda iyayensa suke ka nemo mini su a faɗin ƙasar nan" "Me za ka yi musu?" "Zan yi musu alkhairi ne kawai. Amma Mahmoudu kawai ji nake kamar ina da alaƙa da shi, dan Allah ka tura mini hoton nan" Mahmoudu ya karɓi wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa shan shayin. Sule ne ya zo gurin a kan babur, ya kafe baburin, ya sauka ya gaida Hammad cikin girmamawa. Hammad dai ya amsa yana bin sa da kallo. Suka gaisa da Mahmoudu ma, ya ga sun sake sun fara hira. Mahmoudu yana ta satar kallon Hammad, ko zai ɗago ya tuna wani abin, amma ya ga babu alamar hakan. Bayan tafiyar Sule, yake gaya masa ai abokin kasuwancinsa ne na Nigeria. Kawai ya jinjina kai. Ƙaisar ne ya bayyana a gaban Giyaz, fuskarsa babu annuri ko kaɗan. Giyaz ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Ɗan samari ya dai?" "Zuwa yaushe zaka ci gaba da wannan mugun wasan da ka ke yi?" Giyaz ya ce "Wanne daga ciki?" "Kowanne ma? Ka dawowa da mutumin nan tunaninsa ya tuna da yarinyar nan, ga ɗa a tsakaninsu ko iya yanzu ka ɗauki fansar ai, ka ƙyale ta ta huta haka?" "Yaro yaro ne. Yarinyar da kakaninta suka cutar da mu, ta zo ta ƙona ni ta sanya ni jinya, ita ka ke tunanin na ɗagawa ƙafa ma sassauta mata?" "Ba na son alaƙata da kai ta ƙara tsami, amma zan yi abin da ba ka zato, ba zan zuba ido ka ci gaba da cutar da ita har haka ba" Ƙaisar ya yi maganar cikin ƙunar rai. Giyaz ya ce "To babu laifi, ka yi abin da duk za ka yi" Hammad kuwa da ya koma gida, ya kasa zaune ya kasa tsaye, hoton yaron nan ya din ga kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Yaya za a yi a ce a samu yaro yana irin wannan kamanin da shi, ba kamanni sama-sama ba, kamanni na zahiri nesa ba kusa ba. Bayan haka yaron ya yi masa kama da wani wanda ya sani ko ya taɓa gani, amma ya manta waye, ya din ga duba wayarsa ko Mahmoudu ya turo masa hoton yaron, amma wayam bai tuta masa ba. Gefe guda ya so haɗuwa da Nana, amma bai ganta ba. Sai washegari da ta kawo masa Abincin safe ta yi masa ya jiki. Ya ce "Sai yanzu za ki yi mini ya jikin?" Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, saboda wani irin kyau da ta yi masa. Ga ƙamshin da take yi, har wani ƙara nutsuwa ya yi yana kallonta. "Tuba nake ranka ya daɗe" Sayyid ɗin da take kiransa da shi, ya din ga kaiwa yana komowa a cikin kwanyarsa. Haka da rana da ta yi shigar Atamfa, kamar ya sace ta ya gudu. Ta karya ɗaurin ɗan kwali, ta yi kyau. Ya ce "Amm Asma'u ko?" Ta jinjina masa kai duk da yadda ta ji Asma'un banbarakwai a bakinsa. "Cherié ta ce mini a gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ki ko?" "Eh Sayyid" "Me ya kawo ki Niger ne? Ko takanas ki ka nemi aiki da mu, tun daga Nigeria?" Nana ta girgiza kai ta kalle shi ta ce "Abuna ne ya ɓata na zo Niger neman sa, ina son a yi mini izini, nan kusa na koma Nigeria" Ya jinjina kai kawai ba tare da ya gama fahimtar abin da take nufi ba. A daren ne kuma Nana ta jiyo kakarinsa, Asal ta fice ita kuma ta shiga ɗakin. Ƙara lafewa ya yi tamkar ya shige cikin ta, saboda daddaɗan sanyin da ya mamaye jikinsa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya ji yadda ta ƙanƙame shi tana kuka. Ya saurara ya yi shiru ya ji ba muryar Asal ba ce. "Allah ka duba mu, ka yaye masa wannan ciwo, Allah ka yi masa maganin abin da yake damunsa. Yana jin yadda take shafa gashinsa tana ci gaba da kuka tana faɗin "Da gaske ba ka gane ni ba Sayyid, ko kuma wasa ka ke yi mini da hankali kawai. Na fara sarewa Sayyid, idan wasa ne ka tausaya mini haka, wahalar da na sha ta isa, ka duba ni ka duba makomar abin da na haifa maka dan Allah" Ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana ci gaba da kuka. Gaba ɗaya sai ya rikice, bayan kukanta da maganganun da take yi da suka rikita masa lissafi, gangar jikinsa kuma wani saƙon take aika masa na daban, har wata tsuma ya fara yi. Sai dai Allah ya taimake shi, bai yi wani yinƙuri ba, ya ji tana magana da Ƙaisar, ta kwantar da shi a kan pillow ta koma gefe. Tunani ya din ga yi ina Asal ta tafi? Ya aka yi Nana ta shigo har turakarsa kai tsaye haka, kuma wasu irin maganganu take yi haka? Ya yi lamo kamar bacci yake yi, amma idonsa biyu. Sai gefin Asuba da ta bar ɗakin, ya tashi ya zauna, yana jin wani irin raɗaɗi a tsakiyar kansa, zuwa ƙirjinsa gaba ɗaya ji yake kamar zai fita hayyacinsa ƙwaƙwalwarsa na nema ta hargitse. Garau ya miƙe bayan sallar asuba, ya sake tuna yaron da Mahmoudu ya nuna masa, da maganganun da ya ji Nana tana yi. Ya kira Al Hussain a waya, ya ce masa lallai yana son cikakken bincike a kan Nana. Ga Sultan ya tura shi wakilicin wani ɗaurin aure, amma kusan baya cikin cikakken hayyacinsa, kansa cunkushe da lissafi kala-kala. Maganganun Nana suka din ga karafkiya a cikin kwanyarsa, da rungumar da ta yi masa ba tare da tsoron komai ba. Ko da ya dawo, har ya wuce ɗakinsa, amma kansa ya din ga wani irin ciwo, kawai ya yanke shawarar zuwa ya turke Nana, ta yi masa bayani dalla-dalla. Sai da ya bari Asal ta yi bacci, sannan ya tashi ya tafi ɗakin Nana. Sai dai da ya je ɗakin ya tarar ba ta ciki, sai wayarta da take kan katifarta a ajiye. Har zai juya ya fita, kawai ya nufi kan katifar ya sanya hannu ya ɗauki wayar. Ya jujjuya wayar, yanayin yadda screen ɗin wayar ya dusashe ya sanya ya gane wayar ta kwana biyu. Kawai ya danna madannin gefe a take hoton fuskar Nana da Muhsin ya bayyana a kan screen ɗin wayar. Mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta yi wani irin mummunan bugawa da ƙarfin gaske. Alamun tahowar Nana ya ji, babu shiri ya jefa wayar kan katifar ya yi sauri ya kashe fitilar ɗakin. AREWABOOKS Ko da Nana ta shigo ɗakin, jikinta ya bata akwai mutum a ciki. Da ta kunna fitilar ta yi arba da shi, ta rikice ta kusa kurma ihu, sai dai duk da a tsorace yake shi ma, amma  kasancewar sa Namiji ɗan gwagwarmaya ya sanya ya danne tsoronsa da tashin hankalin da yake ciki, ya yi mata duk tambayoyin da ya yi mata, sai dai bai tambaye ta haƙiƙanin abubuwan da yake son tambayarta ba. Duk amsoshin da ta ba shi, ba su gamshe shi ba, haka ya fice ya bar ta. Tun da ya bar ɗakin kusan kwanan tsaye ya yi, ya din ga kaiwa yana komowa a ɗakinsa ya dafe kansa, ya zauna ya tashi. Duk wani lissafi da ya yi sai ya ji babu mafita. Shi dai bai taɓa ganin Nana ba, amma meye haɗinta da yaron da Mahmoudu ya nuna masa? Sannan mene ne alaƙarta da shi da ta iya shiga turakarsa ta rungume shi take faɗar wannan maganganun da suke nuna da alaƙa a tsakaninsu. Har aka yi kiran sallar Asuba ko gyangyaɗi bai yi ba. Da Asuba da ya dawo daga masallaci, har zai wuce hanyar ɗakinta, ya koma ya nufi ɗakin nata. Ya jima a gurin yana kallon ƙofar. Ya buɗe ƙofar ɗakin a hankali. Ya tarar da ita tana bacci. Sai dai abin da bai sani ba, Ƙaisar ne ya ƙara wa Nana nauyin bacci, amma duk abin da yake faruwa tana gani, sai dai ba za ta iya motsi ba. Cikin sanɗa Hammad ya ɗauki wayar ya yi waje. Bai ko sake nufar ɗakinsa ba, ya fice. Gidan Mahmoudu ya tafi, ya je ya tarar da shi a zaune yana lazumi. Sai da Mahmoud ya tsorata ya ce "Lafiya na ganka da duku-dukun nan?" "Mahmoudu wane ne yaron nan da ka nuna mini? Kuma wace ce yarinyar da Asal ta kawo a matsayin mai yi mini girki?" Mahmoudu ya kalle shi ya kalli screen ɗin da yake nuna masa, tabbas Nana ce ba wata ba, amma zai so ya yi magana da Nana kafin gaya wa Hammad wani abu. "Ka yi magana ka tsaya ka na kallo na" Ya yi maganar cikin hasala. Mahmoudu ya ce "To ai Asal yakamata ka tambaya ba ni ba, ni fa cin karo kawai na yi da hoton na nuna maka" Zai yi magana kansa ya sara, ya saki wayar ya fara ja da baya yana dafe kansa, ya tafi zai faɗi Mahmoudu ya yi saurin tare shi, ya kwantar da shi a hankali. Ya ɗauki wayarsa ya kira Al-Husssain. Bayan sun gaisa Mahmoudu ya ce "Imam Hammad ya yi maka magana a kan yi masa bincike a kan yarinyar da Asal ta kawo Agadez ta din ga yi masa girki ko?" "Eh ya kira ni, ya yi mini maganar" "To yaya ake ciki, me aka gano a kanta?" Al Hussain ya ce "Eh ina kan yin binciken ne, amma dai wani kamfani ne, da suke samar wa mata, guraren aiki suka kawo ta. To na saka Hasna ta tuntuɓe su, dan ni gaskiya ban wani tantance ta ba, na ɗauke ta aiki, saboda ta ce daga Nigeria take. To gidan aikin sun ce, su ma wata mata ce jami'arsu ta kawo musu ita. Amma za a nemo matar yanzu haka su muke saurare" Mahmoudu ya ce "To shikenan, amma duk abin da aka ƙarasa bincikowa, ni zaka sanar, ka gaya masa tukuna" Sanin alaƙar da take tsakanin Hammad da Mahmoudu ya sanya kai tsaye ya ce masa to. Hammad kuwa yana kwnace, sai jujjuya kansa yake yi yana wani irin gumi. Giyaz yake gani yana yi masa wata irin dariya, da ƙara wadda ta cika masa kunne. Ya lallaɓa ya tashi zaune ya toshe kunnunwansa yana faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Mahmoudu ya durƙusa a gabansa yana kiran sunansa, amma bai amsa ba ya rintse idanunsa. "Sayyid, Sayyid dan Allah da gaske ba ka tuna ni ba?" Maganganun da Nana ta din ga yi masa ya din ga ji a cikin kunnensa. "Mahmoudu" ya kira sunansa a hankali. "Na'am Imam" "Mene ne alaƙata da yarinyar nan?" "Amm ban sani ba tukuna, ina jiran abin da Al Hussain zai ce ne tukuna" "Ka kirawo ta ka tambaye ta, wane ne yaron nan? Me yasa kuma yake kama da ni?" "Za a yi, amma ka yi shiru da bakin ka mu gano komai tukuna" Sai zuwa yamma Hammad ya ɗan samu nutsuwa, sai dai bai sake ganin Nana ba, abincinsa ma ajiye masa ta yi. Da daddare Asal ta ɗauki hankalinsa sosai, saboda yadda ta sha kwalliya cikin jajayen kayan bacci sai ɗaukar ido take yi. Yana ta ƙoƙarin kar ya shiga hakkinta, saboda damuwoyin da suka yi masa yawa. Sai dai bai iya taɓuka komai ba, hankalinsa ya fara gushewa. Wani irin haske ya din ga gani a cikin baccin nasa yana ɓullowa ta cikin wani mudubi, sama-sama ya din ga hango shi tare da Nana a ciki, cikin yanayin wata rayuwa da take nuna tsananin kusanci da kyakykywar alaƙa a tsakaninsu. Sai dai bai gama fahimtar abin cikin mudubin ba, Giyaz ya bayyana ya huro wata irin wuta a take mudubin ya tarwatse, ya ja da baya yana kare kansa. Giyaz ya gani tare da Ƙaisar, tsananin kamaninsu tsufan Giyaz ne kawai ya sanya shi ya banbance su. Farkawa ya yi jikinsa ya ɗauki wani irin zafi. Tashi ya yi yana zagaye ɗakin, amma ya ci gaba da jin zafin ya tsananta kawai ya fita ya je hanyar ɗakin Nana ya zauna. Zuciyarsa kuma sai azalzalarsa take yi a kan ya je ya samu Nana ya yi magana da ita, amma wata zuciyar ta hana shi hakan. Giyaz kuwa faɗa ne ya kacame tsakaninsa da Ƙaisar. "Ƙaisar muddin ka yi ƙoƙarin saka mutumin nan ya tuna yarinyar nan, zan iya hallakaka, ko kuma na saka shi ya haukace gaba ɗaya" Ƙaisar ya ce "Kafin ka halaka ni, ni zan halakka ka muddin za ka ci gaba da shiga abin da bai shafe ka ba" "Ni zaka hallaka, Giyaz bin Jaddul Jinn?" Ƙaisar ya ce "Ƙwarai kuwa, a kowane lokaci zan iya baka mamaki" Hammad kuwa da duku-duku ya sake tafiya gurin Mahmoudu. Yana ganinsa gabansa ya faɗi. Ya ce "Mahmoudu ka zauna mu yi magana" Mahmoudu ya zauna yana rarraba ido" "Ko dai ka gaya mini abin da ka ke ɓoye mini, ko kuma zan tari duk wanda nake ganin zan samu abin da nake nema, komai zai faru sai dai ya faru. Ka yi mini bayanin waye yaron nan, kuma wacece yarinyar nan" "Matarka ce" Ya ba shi amsa kai tsaye. Zabura ya yi ya ja da baya yana kallon Mahmoudu "Yaushe kuma ta yaya?" "An yi mini gargaɗi sosai da sosai, a kan kar na kuskura na gaya maka, duk da babu wanda ya san da wannan zancen ma. Amma ko zan rasa rayuwata na yi alƙawarin zan gaya maka iya gaskiyata. Nana matarka ce da ka aura a Nigeria. Bisa ga binciken da nake yi ta ƙarƙashin ƙasa kuma, kai ta fito nema ta zo Agadez" Jiki a sanyaye Ya ce " Mahmoudu ban fa gane me ka ke nufi ba, yaushe na je Nigeriar har na aure ta?" "Bayanan da Matawalle ya yi maka ba haka yake ba, ka manta da komai naka, na tafi da kai Nigeria. Yanzu duk bayanin da zan yi maka ba komai zaka fahimta ba, amma Nana Asma'u matarka ce" Hammad ya ce "Mahmoudu, anya ba haukacewa na yi ba kuwa? Ji nake yi kamar ba mutum ne ni ba. Gaskiya" Ya dafa kafaɗar Hammad ya ce "Mutum ne kai, wasu abubuwa ne dai kawai suke faruwa amma ka nutsu, ka yi addu'a. Dan muddin ba ka tuna komai ba, ba zamu iya tunkarar kowa da maganar nan ba. Mutumin da ya zo muna tare a sahara, tare aka kamo ni da su, tare muka yi aikin gadi da su a Nigeria. Hammad ban san yaya zan yi maka bayanin jajircewa da sadaukarwar da yarinyar nan ta yi saboda kai ba." Nan Mahmoudu ya din ga yi masa bayanin wasu abubuwan da ya sani. Ya yi shiru ya rasa gazgatawa zai yi ko ƙaryatawa, idan ya yi duba da wasu abubuwan sai ya ga yakamata ya gazgata batun, dan Mahmoudu ba zai masa ƙarya ba. Amma ya din ga jin sa kamar ba mutum ba, ko kuma a wata Duniyar yake ta daban. Da daddare yana tare da Asal, tana danna waya, Nana ta kawo Abincin dare. Kamar ya yi mata magana ya fasa, sai dai ƙasan zuciyarsa ya din ga fatan Allah ya sanya gaske ne, Nana matarsa ce, ta kowacce fuska ta yi masa. Tun kan ya ji kan wannan burkitaccen labarin yake jin wani abu na sukan zuciyarsa a game da ita. Babban abin da yake ƙara burge shi da ita, sanin mutuncin kanta da ba ta yadda Asal ta taka ta ba. Saɓanin waɗanda suke kwantar da kai Asal ɗin ta taka su saboda abin Duniya. Ya gaza manta rungumar da ta yi masa a turakarsa. Ta ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, amma bai sauke idanunsa ba ya ci gaba da kallon ta. A ɗan diririce ta ce "Na gama zan iya tafiya. Bai amsa mata ba ya tuna yadda take ba shi Nonon raƙumi da habbatussauda, ga abinciccikan da yake matuƙar da take gwangwaje shi da su. Asal ta ce "Za ki iya tafiya" Sai da Nana ta je tsakiyar falon sanan ya ce yana buƙatar lemon kankana da shayin citta da kanumfari kawai, ba zai sha na kimba ba. Nana ta yi shiru ta ci gaba da tafiya, Asal ta ce "Kin ji ai" A hankali Nana ta ce "Na ce miki ba ni da kunne ne, da ba zaki iya tsinana wa mijinki uban komai ba" "Ke ba magana nake yi miki ba" Nana ta waiwaya ta ce "Ai na amsa na ce to" Shi kuwa ya yi haka ne, dan ta sake dawowa ya ci gaba da kallon ta ko Allah zai sanya ya iya tuna wani abin. Amma har ta kawo masa shayin tayi tafiyarta bai tuna komai ba. Sosai faɗa ya ɓarke a tsakanin Giyaz da Ƙaisar a kan Nana, Giyaz ya din ga ɗaga Ƙaisar yana bu ga shi da ƙasa. Karfin Ƙaisar da na Giyaz ba ɗaya ba ne ba, duk da Giyaz ya kwana biyu a duniya amma yana da matuƙar ƙarfi. Ƙaisar ya baje a gurin, bayan buga shi da jikin dutsen gidan tarihin Agadez,da Giyaz ya yi, ga ƙona shi da ya din ga yi da wuta. Sai dai ganin Ƙaisar ya baje ko motsi ba ya yi, ya sanya ya nufe shi da sauri yana kiran sunansa, ya ɗago Ƙaisar, amma ya shammaci Giyaz, ya fito da jakar gurin Sarkin Baka daga cikin rigarsa, ya naɗe masa wuya da hannun jakar. Wata irin kururuwa Giyaz ya din ga yi, yana tumami a gurin yana burgima. Ihun nasa sai da ya razana da yawa daga cikin halittun da suke cikin gidan tarihin. Ƙaisar ya miƙe da kyar ya tunkari wani ɗaki, aljanun da suke ƙofar ɗakin su ka dare suka ba shi guri. Ya zura hannunsa a ya ɗaukko kwalbar da Giyaz ya ce tunanin Imam Hammad ne a cikinta. Ya ajiye ta a nesa kaɗan ya ja da baya ya din ga hura iskar bakinsa a jikin kwalbar. A take kwalbar ta yi wata irin ƙara ta tarwatse, a take ɗan hayaƙin da yake cikin kwalbar yana zagayawa a cikin wani ruwa ya bar cikin ta. Ƙaisar ya koma kan Giyaz da ya suma a gurin, ya ɗauke jakar da ya shaƙe shi da hannunta, ya ɓace daga gurin. A hankali yake juyi, ya buɗe bakinsa domin ya jarraba yin magana, ya ji ko maganar ta dawo ya ce "Ma vie" sai dai ya ji shiru. Shi ma shirun ya yi yana ji wani raɗaɗi tun daga cikin kansa har idanunsa. Ya yi juyi ya ji taushin abin da yake kai ya banbanta da nasu. Ya buɗe idanun da suke yi masa raɗaɗi da kyar yana kallon ɗakin. Asal ce ta shigo ya kalle ta, ta ce "Amour ta gama abinci, ka taso ka karya" Ya jinjina mata kansa da ya yi masa wani irin nauyi mara misaltuwa. Tabbas ya san Asal matarsa ce, amma ina Nana. Sai ya yi shiru sannu a hankali ƙwaƙwalwarsa ta tariyo masa yadda aka fita da shi daga gidansu na Buda yana fizge-fizge yana kiran matarsa Nana. Ya rintse idanunsa tare da damƙar gashin kansa yana girgiza kan, saboda yadda ƙwaƙwalwar tasa ta hargiste, tunanin ma ya rasa wanne zai yi. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya din ga maimaitawa babu ƙaƙƙautawa. Asal ta sake shigowa ta ce "Amour wai yane? Baccin ne bai ishe ka ba? Sha biyu saura fa na rana, ba ka ko karya ba" Ya yi mata nuni da hannunsa alamun yana zuwa. "Ok, ni zan je gida, Abbu yana jira na" Ya jinjina mata kai" Sannu a hankali ya fara samun nutsuwa, ya miƙe tsaye a hankali, ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, sai dai jiri ya din ga ɗibarsa. Ya fito ya zura rigarsa ya fita, ya hau kan doguwar kujera ya kwanta. Ya lumshe idanunsa, abubuwan da suka faru a Nigeria suka din ga dawo masa saɗara-saɗara, zuwa dawo da shi Niger da aka yi. To ya ya aka yi ya manta da ita komai nasa ya shafe da ya baro Nigeria, kuma yaya aka yi ya manta da komai nasa da yaje Nigeria. "Anya babu wata maƙarƙashiya ko wani abu da ban sani ba, game da rayuwata ba?" Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da kwandon kwanukan Abinci. Wata irin karaya ta ziyarce shi, zuciyarsa ta din ga azalzalarsa ya tashi ya rungume ta, Asmynsa ce, amma zuciyarsa ta din ga gargaɗinsa kar a samu matsala, dan ya san dokar Agadez. "Barka da wannan lokaci Sayyid, ga abincinka, na ga na safe ma baka ci ba, ko ba shi ka ke so ba ne?" Hannu kawai ya ɗaga mata, ya lumshe idanunsa, mamaki ya cika ta, ganin ba shi da niyyar magana, ya sanya ta tashi ta fita cike da damuwa. Tana fita ya haɗe tafukan hannayensa, ya dafe fuskarsa ya fashe da kuka, da wace fuskar zai kalle ta? Me zai ce mata? Ta ina za ta yarda da shi cewar ba yana sane ya ƙi kula ta ba. A hankali ya ci gaba da tuna tsantsar juriya da sadaukarwar da ta yi saboda shi. Ba ta haƙura ba ta taho nemansa, sun haɗu kuma bai gane ta ba. Ya so fita ya je ya samu Habu, amma ba zai iya ba, saboda ji yake yi tamkar an sauya masa gangar jikinsa. Wayarsa da ya bari tun daren jiya a falon tana caji, ya ɗauka ya duba ya ga Mahmudu ne yake kiransa. Ya ɗaga wayar bai yi magana ba, Mahmoudu ya ce "Hammad ina tunanin yaron nan fa ɗan gurin Nana ne, kuma.. "Nana matata ce, ina iya tuna komai yanzu" Mahmoudu a rikice ya ce "Ina fatan ba ka gaya mata ba?" "Babu wanda na gayawa" "Alhamdillah, kar ka ce mata komai, sai mun tabattar da abin da muke bincike, ka zo mu je Maraɗin gurin Umma, na san za ta saurareks fiye da ni. Amma ya aka yi ka tuna komai?" "Maganar ma da kyar nake yi Mahmoudu, ba zan iya fitowa ba. Mu yi magana anjima" Ya ajiye wayar hawaye na ci gaba da zuba daga idanunsa. Haka ya wuni ba tare da ya ci komai ba, jikinsa kuma gaba ɗaya babu ƙwari, kamar wanda aka zarewa laka. Babu abin da yake yi banda tuna rayuwar da suka yi da Nana, da girmama yadda aka yi ya manta da ita, ya kasa tuna ta. Sai dare sannan ya iya samu ya sha shayi kawai. Sai dai zuciyarsa babu daɗi a cunkushe. Ya lallaɓa jikinsa da yake a mace, ya nufi hanyar ɗakin Nana, sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana lissafin me zai ce mata? A hankali ya ɗago hannayensa, ya kalli yatsunsa, ya tuna yadda ya yi mata kyautar zoben, a lokacin da yake tsakiyar jin shauƙin ƙaunarta. A hankali ya murza tagullar hannunsa, sai ga Arun ya bayyana. Ya ce "Na amsa kira ya shugabana" "Ka duba mini; me yarinyar cikin ɗakin nan take yi?" Arun ya risuna ya ce "Tana ninkin kaya ne ya shugabana, amma alamu sun nuna a gajiye take sosai da sosai, kuma akwai damuwa a tare da ita, sai kuma bacci da take ji. Gajiyar da ta yi da damuwar da take ciki ya haifar mata da kasala sosai. Kuma ta yi kuka mai yawa awanni kaɗan da suka gabata". "Ya isa haka, ina son ta yi bacci yanzun nan" Arun ya ce "Shiga kanka tsaye mai gidana, an riga an gama." Hammad ya numfasa ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe. Ɗakin sai ƙamshin turaren wuta yake yi. Tana kwance a ƙasa ga kayan ninkin nata a gefe. Daga ita sai zani da ta ɗaura a ƙirjinta, saboda daga wanka ta fito ta zazzage kayan ta hau ninkewa ko za ta ga wayarta da ta nema ta rasa. Jikinsa har rawa yake yi, ya ƙarasa gabanta, bai yi wata-wata ba ya ɗago ta yana kallon kyakykyawar fuskarta. Wata irin karaya da matsanancin tausayinta ya ratsa zuciyarsa. Ya ƙanƙameta a jikinsa yana wani irin kuka zuciyarsa na yi masa zafi da ƙuna. "Ki yi haƙuri Asmyna, ki yi haƙuri ki yafe mini, ni kaina ban san abin da ya same ni ba, ban san yaya aka yi na gaza tunawa da ke ba. Ban yi miki adalci ba amma kk yi haƙuri rayuwata" Ya din ga yi mata surutai ba tare da ta san yana yi ba, saboda wani irin nannauyan bacci da take yi. Duk da yadda burki ya so ƙwace masa, kasancewarsa da Nana a wannan yanayi, da ya din ga tariyo masa irin rayuwar da suka yi ta tsantsar soyayya da ƙauna. Ya yi iya ƙoƙarinsa gurin sarrafa kansa da kyar gurin ganin bai aiwatar da wani abu ba. A ganinsa yin hakan tamkar rashin adalci ne kai tsaye a gare ta. Kamar wani zai ƙwace ta, haka ya matse ta a jikinsa, yana zubar da hawaye, yana sake jin wani abu na ratsa lungu da saƙo na gangar jiki da kuma ruhinsa a game da ita. A duniya ba ya jin yana da wani abu da zai iya aikata wa Nana ya yi ko kwatankwacin saka mata a kan abin da ta yi masa. Har gefin Asuba yana rungume da ita, hawaye kuma bai bar kwarara daga idanunsa ba, lissafi yake yi ko za ta yarda da shi, ta sake ba shi dama ta biyu. Ko kaɗan, tunaninsa da hankalinsa ba sa lissafa masa kalubalen da yake gabansa, na auren wata ƙabila baƙar fata da buzuwa ba. Da kyar ya iya raba jikinsa da ita, ya ɗan yafa mata zaninta, ya gyara mata kwanciyarta, ya durƙusa ya sumbace ta, ya ci gaba da kallonta, daga bisani ya tashi da kyar ya fice ya bar ɗakin. Ko da Nana ta farka ta sha mamakin yadda ta ga jikinta, ita dai ta san ta yi mafarkin tana tare da Sayyid, amma da ta farka ta ga alamun kamar an taɓa ta. Ga shi a iya saninta ninkin kaya take yi, amma ta farka ta ganta rabin tsirara, ta yi tunanin ko Ƙaisar ne, amma cikin hanzari ta kawar da wannan tunanin daga ranta da take jin tamkar saɓo ta aikata, dan ta san Ƙaisar bai taɓa yi mata yawo da hankali a abu makamancin wannan ba. Ta yi iya ƙoƙarinta ta kawar da tunanin komai daga ranta, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta yi alwala ta dawo ta yi sallar asuba tana ta istigfari saboda yadda ta makara. Gari yana yin haske, ya shirya ya tafi gidan Mahmoudu, duk da yadda jikinsa yake a mace. Kallo ɗaya Mahmoudu ya yi masa, ya gane a rikice uban gidan nasa yake. "Mahmoudu, wallahi na gane ta, na tuna ta Nana ce matata ce, to amma yaya aka yi komai ya shafe a cikin kaina na manta da ita?" Mahmoudu ya ce "Ka nutsu ka kwantar da hankalinka, yanzu aiki ne ya ganmu jawur, sai dai ba wannan ba dole mu tsananta bincike a kan abubuwan da suke faruwa da kai." "Ni kaina abubuwan sun ɗaure mini kai Mahmoudu, ji na nake yi wani iri, kamar an ƙwance wani nannauyan dutse daga kaina. Yanzu ta ina zamu fara, ni fa duk abin da za a yi ko Agadez za ta tashi, ba zan rabu da matata ba" Mahmoudu ya ce "Ban gane Agdez ta tashi ba, a'a gaskiya sai dai ku ku tashi kai da ita" Hammad ya ce "Mahmoudu ka daina wasa mana" "Na daina wasa shugabana, amma yanzu ka tuna su Sule?" "Na tuna shi, yanzu ina iya tuna komai fa a cikin ƙwaƙwalwata." "To ma sha Allah, albishirinka" "Mene ne?" "Wallahi sai ka saya, ba zan faɗa a sadaka ba" "Faɗi ko me ka ke so, wallahi zan baka" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Zan yi tunanin me nake so, amm yanzu yi sujudar godiya ga Allah tukuna" "Zan yi amma fara gaya mini" "Ta tabatta yaron nan, ɗan Nana ne, kuma a bincikena, da Gimbiya ta zo Niger, a hannun Ummana ta sauka. Al-Husssain ya turo mini komai nata, kamar yadda ka sanya shi bincike. A zahirin gaskiya da naje Maraɗi na gano yaron nan a gurin Ummana, shiyasa na damu da matsa bincike. Na kira Umma mun yi magana ta tabattar mini da ɗan Nana ne, kuma ɗanka ne yana daga dalilin da ya sanya ta turo ta Maraɗi aiki gidan cin abincinku, kuma ta ƙarfafeta ta taho Agadez ɗin" A rikice ya damƙi hannayen Mahmoudu a gigice ya ce "Dan Allah da gaske ɗana ne? Ina da ɗa? Mahmoudu? Mahmoudu dama zan haihu zan ga ɗana a Duniya. Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil Azim. Allahumma lakal hamdu wa laka shukur. Mahmoudu dan Allah da gaske ka ke?" Cikin tausayawa Hammad, mussaman sanin irin ƙalubalen da ya fuskanta na rashin haihuwa da jarabtar da Allah ya yi masa na son 'ya'ya, aka hana shi ƙara aure, kuma Tafawa ya din ga ƙalubalantarsa da hakan yana nemana a sauke shi. Mahmoudu ya dube shi ya ce "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ka san ka na da matsalar zuciya kar ciwonka ya tashi, amma ka san ba zan yi maka ƙarya da abin da ka daɗe kana nema ba. Ina da tabbaci a kan abin da na gaya maka, dan sai da na gama bincike na tabattar sannan na gaya maka. Hammad ya saki Mahmoudu, ya yi sujuda yana yi wa Allah godiya, sannan ya tashi fuskarsa sharkaf da hawaye ya ce "Yanzu mene ne abin yi? Ko ka zo mu je ka yi mata bayani, ban yi burus da ita ina sane ba" "A'a kar mu kuskura mu sanar mata komai yanzu, sai mun gama daidaita komai da shirya yadda zamu tunkari jama'ar Agadez da wannan babban al'amari" Ya share hawayensa ya ce "To tashi mu je Maraɗi na ga yarona" "Mu bari sai gobe in Allah ya kaimu" Hammad ya ce "Ba zan iya jira ba, kuma kar wani abu ya same shi, dole na dawo da shi kusa da ni, ko na ajiye su a wani guri keɓantacce, idan yana hannuna sai ta fi tsayawa ta saurare ni. Na san halinta akwai sauƙin kai amma akwai kafiya ba za ta saurare ni ta daɗin rai ba" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "To shikenan, amma ka jira kaɗan Sule ya zo, ku gaisa sai mu je Maraɗin tare da shi" Haka kuwa aka yi, ba a jima ba Sule ya shigo, ya risuna yana kwasar gaisuwa gurin Hammad. Ya rungume Sule tare da yi masa godiya, a kan ɗawainiya da kuma gudunmuwar da suka ba shi a lokacin yana Nigeria. Suka shirya suka tafi Maraɗi gidan Nene, ko da Hammad ya ga Muhsin, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rungume shi yana kuka, da gode wa Allah da ya sanya yana da rabon haihuwa a Duniya. Duk da sun kai ruwa rana da Nene, ta ce ba zata ba su Muhsin ba, dan ba su yi haka da Nana ba. Hammad ya ce ba ɗaukar Muhsin zai yi ba yana son ya nesanta su da gurin da suke na ɗan wani lokaci, kamar yadda Hammad ma ya yi tunani haka ita ma Nene ta tabattar masa da muddin ya jewa Nana kai tsaye babu abin da zai hana Nana zuwa ta ɗauki Muhsin ta gudu, dan ta san halinta dole ya bi komai a hankali. A hankali Hammad ya ɗago Nana daga jikinsa ya ce "Asmy bacci ki ka yi?". "Idona biyu" Ta ba shi amsa. "Kin yi shiru, Asmy ba da gangan na ganki na ƙi kula ki ba, kin san muddin ina cikin hayyacina babu yadda za a yi na share ki. A lokacin ina ta shirye-shiryen yadda zamu ɓullowa lamarin, Tafawa kuma ya sanya ni a gaba da da haƙilon ba zan yi mulki ba, ni juya ne, ga rashin lafiya ga hauka ga babu zobe. Ya daɗe yana jifana da kalmar juya, abin yana yi mini zafi da ciwo shiyasa na fallasa komai a lokacin da shirin duk abin da zai faru ya faru." Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yakamata mu tashi, an kira sallar Asuba". Hammad ya ce "Haka ne, amma ba ki ce komai ba" Ta ce "Zan ce ne, ina jin bacci ne sosai ka ga kwana muka yi ba mu yi bacci ba" Ya ce haka ne. Suka tashi suka koma ɗakin nan zai rufe amma ya tsaya ganin Nana na ƙara kallon ɗakin. Ya ce "Wannan ɗakin tun zamanin Sultan Azhar yake, duk Sultan ɗin da ya zo a nan ɗakin ne turakarsa. Kowane zamani akwai canji da kuma yadda ake ƙawata ɗakin. Kafin daga bisani a daina amfani da gidan gaba ɗaya." Nana ta jinjina kai ta ce "Ni yanzu abu ɗaya nake son ka gaya mini, ina da ciki ko ba ni da shi?" Ta yi maganar a ɗan shagwaɓa tana marairaice fuska. Ya yi murmushi ya ce "A cikin labarin kin ji inda wani abu ya faru ne?" "Eh mana, tun da kana zuwar mini ɗaki ba tare da sanina ba" Ya jinjina kai ya ce "Sosai kuwa, dan tun da na gano ke matata ce, kusan kullum tare muke kwana, ya yi maganar yana rufe ɗakin. Ya damƙi hannunta suka yi gaba, ja ta yi ta tsaya tayi shiru sannan ta ce "Sayyid ba ka nuna mini mene ne a cikin ɗakin can ba" Ya kalli ɗakin ya ce "Hanyar tsohuwar prison ce, inda daga baya ake aikin sarrafa gold a ciki, amma yanzu babu abin da ake yi da gurin" "Ina son ganin mene ne a ciki" Ya ce "To shikenan" Ya ja hannunta zuwa ƙofar gurin, amma suka tarar da ƙaton kwaɗo a jikin ƙofar. Ya ce "To ai gurin a rufe yake ma" "Ya aka yi sauran ƙofofin ba a saka mukulli ba sai wannan? A tambayi mai tsaron gidan ya buɗe mini zan gani" Hammad ya ce "To ai lokacin salla ya yi" Ta ce "Na sani gani kawai zan yi mu tafi" Ya tsaya yana kallon Nana da rikicin tsiya, ya ce "Zo mu je sai mu yi wa mai gadin magana, ya zo ya buɗe mana" ta bi shi a hankali jikinta cike da kasala ga kuma bacci da take ji. Ko da Hammad ya tambayi tsohon nan mai tsaron ƙofar, sai cewa ya yi "Allah ya taimake ka, ban san wanda ya rufe ɗakin nan ba, ya kwana biyu a rufe" Hammad ya ce "Wataƙila ko masu yawon buɗe ido su na ɓarna a gurin, shiyasa aka rufe" Nana ta ce "Waye yake da alhakin rufewar?". "Ma vie, wai lafiya kuwa?" "Hammd sai an buɗe gurin nan kafin na bar Agadez" "Shikenan na ji, za a buɗe amma muje mu yi salla tukuna" Da kyar ya lallaɓa ta suka bar gurin, saboda yadda take nema ta burkice masa gaba ɗaya. ***** Shukura na zaune a kan gadon Asibiti,  ta zuba ido tana kallon ɗan jaririnta, ƙato da shi mai matuƙar kama da Sagir, ta din ga tuno da jaririnta da aka ce ya mutu da haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da hakan. Ji ta yi an turo ƙofar ɗakin ta ɗago da sauri, gabanta ne ya faɗi ta yi turus tana kallon mai shigowar. Ayshercool 08081012143 94 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAFIN KI KARANTA. 0069685771 AISHA ADAM STANBIC Yusra ce ta shigo ɗakin, Shukura ta yi tsuru da ido tana kallonta. Yusra ta ƙarasa gaban gadon Shukura cikin damuwa ta ce "Meyasa ki ka taho nan, ki ka saka ake ta neman ki, duk hankalin mutane ya tashi?" Maimakon Shukura ta bata amsa sai cewa ta yi "Ke kaɗai, ki ka yi driving ki ka zo nan? Ina Baban Haidar ɗin?" "Wayarsa ce lalace, ya saka layin a wayata, yana can gurin meeting, kafin ya dawo kawai na ce bari na zo na ɗauke ki. Wannan ɗan da ki ka haifa ne?" Ta yi maganar tana karɓar jaririn hannun Shukura. Shukura ta jinjina kai jiki a sanyaye. Yausra ta ƙura wa jaririn ido tana kallonsa, tana ɗan murmushi ta mayar da hankali kan Shukura ta ce "Wai meyasa ki ka zo nan gurin ki ka zauna?" "Ba komai" "A'a da komai, kowa kin saka hankalinsa ya tashi sosai, ga ki da tsohon ciki, ki tashi mu tafi gida idan ya dawo kawai sai dai ya ganki. Abbanki har yana cewa zai ɗaure shi, shi ne ya saka ki ka ɓata, ai ba dan ya dawo da ni ki ka tafi ba ko?" Ta yi maganar jikinta a sanyaye tana kallon Shukura. Da mamaki Shukura ta ce "Daddyn ne ya ce zai ɗaure Sagir saboda ɓata na?" Yusra ta jinjina kai ta ce "Wallahi haka ya ce" Ta yi shiru tana zunzurutun ɓarna da zaluncin da ya gaya mata ya aikata. Ta numfasa ta ce "Amma ina fatan ba ki gaya wa kowa ina nan ba?" "Babu wanda na gayawa, ai kin ce kar na faɗa, ga abinci can ma na ɗaukko a mota, da 'yansanda zan gayawa amma na fasa" Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yauwwa gara da ba ki faɗa ba" Yusra ta ce "To ki taso mu tafi" "A'a ai sai an sallame ni tukuna, kuma yakamata ki koma gida saboda ki sanar masa inda nake" "Babu inda zan koma, salon in tafi ki sake guduwa" Ta yi maganar tana ƙara lulluɓe jaririn Shukura da yake hannunta. ***** Cikin damuwa Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, yadda take zubar da yawu tana wani irin ihu, da gurnani duk ta yi najasa a jikinta. Ga ƙafafuwanta sun shanye, ba ta gane kowa sai wannan gurnanin da take yi. Likitoci sai dai su ta mata allurar bacci. Ranar da Fadila ta je duba ta, duk da ba ta magana amma tana ganinta tare da Muhsin ta din ga ihu tana tsine masa tana faɗin "Da tuni wannan shegen ɗan ne zai mutu ba Abbana ba, Allah ya isa ba zan yafe ba" Alhaji Fatuhu yana gurin, ya yi mamakin jin irin wannan maganganun da take yi, amma sai ya bar hakan a sakamakon taɓuwa da aka ce ƙwaƙwalwarta ta yi. Likitan da ya kammala rubutu a kan takarda, ya miƙa wa Alhaji Fatuhu. Alhaji Fatuhu ya karɓa tare da kallon Likitan ya ce "Doctor haryanzu ba a gano takamaiman abin da yake damunta ba?" "To, duk wani abu da yakamata mu duba mun duba, jininta lafiya kalau ba ta da hawan jini. Babu alamar strock a tare da ita. Sai dai idan sakamakon gwaje-gwajenta ya kammala bamu ga komai ba, zamu tura ku ɓangaren ƙwaƙwalwa dama mu nan mun riƙe ta ne domin mu gano maƙasudin shanyewar limbs ɗinta, to haryanzu ba a gano komai ba, zuwa ranar Litinin zamu fara tura ku physiotherapy ko Allah zai sanya a dace" Alhaji Fatuhu ya jinjina kai cike da karaya, tabbas da lokacin da yake da kuɗinsa ne, da kansa zai fitar da ita waje a duba ta. Ko a yanzu ba ya jin daɗin yadda da kuɗinta ake nema mata magani. Haka ya tafi gida jikina a sanyaye. Alhamdillah jikinsa ya yi kyau sosai, duk da haryanzu da sanda yake yawo bai gama warewa ba, amma yana iya fita shikaɗai. 'yarsa Rauda ya samu a gida yake ta yi wa faɗan rashin zuwa duba Hajiya Sa'a da ba son yi. "A ƙa'ida kamata ya yi a ce ke ce a gurinta Raudah, kina kallo lokacin da nake kwance kullum tana tafe" Rauda ta ce "Daddy ni wallahi tsoron ganinta nake yi, kuma duk lokacin da muka je da Maman Muhsin, sai ta yi ta ihu tana tsine masa tana da tuni shi ya mutu ba ɗanta ba, ta yi ta ihu tsoro take bani" "To Raudah ai larura ce, ni da Allah ya jarabbe ni, ba har wari na din ga yi lokacin da nake kan fama da larura ba. Jarrabwa ce Allah ya jarabce mu, kuma ku da ku ke kusa da mu, ku ne zaku ƙarfafa mana gwiwa. Ku din ga haƙuri". Ta jinjina masa kai kawai ta ce "To" **** Nana bayan sun idar da sallar asuba, ta ɓungire ta hau bacci, saboda yadda suka kwana jiya babu bacci. Ya zauna a gabanta ya zuba mata idanunsa, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya din ga jinta a cikin jikinsa. Me zai yi wa wannan halitta domin nuna mata ɗumbin godiyarsa da farincikin kasancewa da ita. Ƙarshe ya ɓuge da sumbatarta yana shafa fuskarta, daga bisani ya tashi ya fita. Sashen Gimbiya Bilkisu ya wuce, ya tarar ba ta fito ba, ya wuce ɗakin da yake kyautata zaton Asal tana ciki. Aikuwa tana ciki ɗin fuskarta ta kumbura suntum ta yi jawur, idanunta sun yi wani irin kumburi mai ban tsoro. Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ta kawar da kanta gefe ta yi shiru, ji take kamar ta shaƙe shi ya mutu ta huta. "Asal" Ya kira sunanta. Ta ɗago ta kalle shi a ƙule. "Ina roƙon ki da kar ki ɗauki damuwa da tashin hankalin lamarin nan ki saka a cikin ranki. Duk abin da ya faru a cikin rayuwarmu abu ne da Allah ya riga ya ƙaddara" "Hammad ba na son jin komai daga gare ka, ka tashi ka tafi ka bani guri. Macuci ma ci amana, ba ka ji daɗin halinka ba" Ya ce "Na ji na kuma yadda, duk abin da za ki kira ni da shi na karɓa, na san kina cikin fushi ne, amma ina mai roƙonki kar wani ya ziga ki ko ya tayar miki da hankali aurenmu ya samu matsala" "Ka riga ka haifar da matsala a cikin aurenmu da kanka, matsalar da ba ta da magani. Har ka yi aure ka haihu ko Hammad, ba ruwanka da matsala ta kanka kawai ka sani. Ka tashi ta fita ka bani guri. Kuma wallahi ina mai yi mka rantsuwa da Allah, sai na yi mata mummunar illar da ba zata moru ba, sannan in saka a hallakata sai ta san ta jangwalo rigima mafi girman da ba zata iya tare ta ba a rayuwarta. Wallahi Hammad kai nawa ne nikaɗai ni Asal ba zan yi tarayya da ƙasƙantaciyar mace a koma mene ne ba" Ya yi murmushi ya ce "Ni dai ina roƙonki ki kwantar da hankalinki, kar ki biye wa zuciyarki dan kaf cika da batsewar Agadez ke Niger gaba ɗaya babu mahalukin da zai raba ni da matata da ɗana. Dan gara na bar muku Agadez ɗin da mulkinku na bi farin ciki da kwanciyar hankalina. Ba zan taɓa wulaƙantaki ko na yarda a wulaƙantaki ba, saboda matata ce ke kuma 'yar uwata. Amma wallahil azim duk abin da ya samu Asma'u ba zan ɗaga wa kowane mahaluki ƙafa ba, a kanta komai kusancina da shi kuwa, dan Asma'u rayuwata ce, dole kuwa na bawa rayuwata dukkan wata kariya dan babu gangar jikin da take fatan rabuwa da ruhi" Wani irin kukan kura ta yi, ta din ga kai masa duka ko ta ina, tana gaya masa maganganu masu zafi, amma ko gezau kawai ya tsaya yana kallonta. Gimbiya Bilkisu ce ta shigo da gudu tana tambayar ko lafiya saboda jin ihun Asal da ta yi. Ta ƙaraso ta rirriƙe Asal ta ce "Imam me ka yi mata?" Ya ce "Babu abin da na yi mata" Asal cikin gunjin kuka ta ce "Ammi ya cuce ni, ya bar gida tsawon lokaci ya je ya yi aurensa a ɓoye ya haihu ban sani ba, sai dai na ji zance sama taka, kuma yarinyar da na kawo a matsayin kukunsa. Wataƙila ma shirya komai suka yi, an cuce ni am zalunce ni, wallahi Ammi ba zan zauna da wata ba. Ya aka yi na fara son shi na bari son Hammad ya yi mini illa. Ni yake gaya wa kaf Agadez babu mai raba shi da waccan ƙasƙantaciyar halittar wallahi sai na kashe ta" Gimbiya Bilkisu ta rungume Asal ta ce "Yi shiru ki daina magana, ki daina faɗar wannan maganar. Ki kwantar da hankalinki" "Ammi zuciyata ciwo take yi mini, ko ganinsa ba na son yi, ya tashi ya tafi ya bani guri" Gimbiya Bilkisu ta numfasa ta ce "Imam, ina ga kamar yadda ta buƙata ka tashi ka tafi kawai, ka bata lokaci ta samu nutsuwa. Domin magna ta domin Allah ba ka kyautawa Asal ba, dole ta shiga damuwa da tashin hankali" Hammad ya ce "Allah ya taimake ki, kar ki zaɓi Asal saboda 'ya take a gurinki, a zamana da ita har zuwa abin da ya faru ban zalunce ta ba. Cikin ƙaraji Asal ta ce "Ammi kin ji ko? Kina jin abin da yake faɗa" "Imam ka tashi ka je kawai" Ya miƙe tsam ya fice daga ɗakin, Asal kuma ta ci gaba da kuka. Fita ya yi, ya nufi wani sashi na gidan, ya yi umarnin a je a zo masa da Sarkin baka. Yana nan zaune hadimai biyu suka shigo, tare da Sarkin baka, ya tarar da Hammad fuskar nan a ɗaure tamau babu annuri. Sarki ya ce "Barka da wannan lokaci" Hammad ya amsa da yauwwa barka. Ya ɗora da cewa "Ammm duk da zan iya cewa baƙon Sultan ne kai, amma saboda ni aka kawo ka gurin nan, kuma ina tunanin ina da damar yin magana da yanke wa kaina hukunci" Sarkin baka ya ce "Wannan gaskiya ne" "Ina ganin tun da babu wani abu da ya yi saura, ka ce ba zaka iya yi mini magani ba, yakamata ka yi magana da Sultan a sallame ka ka tafi" "Saboda ba ka son na kula matarka ko?" Hammad ya yi shiru yana kallon Sarkin baka. Sarki ya yi murmushi ya ce "Ai duk taka tsantsan ɗinka ina da yaƙinin Nana ta fika, kuma ko da take yi mini kallon ba a kan daidai nake ba, ta san ni ba mutumin banza ba ne. Wannan gidan naku ba zan taɓa tafiya na bar Nana a cikinsa ba saboda balahirar da na gani a gidan" Ya kalli Sarkin baka ya ce "A matsayinka na wa?" "A matsayina na ɗan uwanta, ba ka san ina da alaƙa da ita ba? Duk da na san zaka kalli alaƙar ba wata ta kusa ba, amma a yadda ba ta da kowa a cikinku daga ahalinta ina ga zan wakilci ahalinta a nan. Ina da dangantaka ta kakannin kakannin da ita. Ka kwantar da hankalinka ni ba zan cutar da kowa ba, ko na shiga tsakaninku ba amma dole zata buƙace ni, idan kuma ka bari na tafi wallahi ba zan dawo ba bar abada kuma hakan ka iya zame muku matsala. Kuma ya zama dole ka bata duk wata dama ta ganawa da ni a duk lokacin da ta buƙaci hakan, ta nan ne za a iya samun warwarar abubuwan da suka baibaye ka. Ba na son a ji daga bakina ne, kuma ina son ta fahimci akwai abin da idan yana cikin ƙaddararka ba ya nufin ka saɓa wa Allah, amma Allah na iya amfani da kai ya kawo wa wani bawan nasa mafita" Hammad ya yi shiru yana jujjuya maganganun Sarkin baka, duk da ba komai ya gane ba. Amma ya numfasa ya ce a mayar da Sarkin baka masaukinsa. Ya tashi ya fita, ya ɗauki mota ya bar gidan. Ya yi tafiya mai nisa aƙalla ta awa guda sannan ya iso wani makeken katafaren gida. Bayan ya shiga da motar ya ajiye, sai gaishe shi hadiman suke yi yana amsa musu cikin girmamawa. Ya shiga cikin gidan ya bi wata hanya ya hau kan bene. Ya ƙwanƙwasa wata ƙofa, sannan ya saka kansa ya shiga da sallama. Yana zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana cin inibi tare da wasu ƙanan yara su uku, jikin bangon ɗakin kuma ƙatuwar TV ce take yi, ana shirin cartoon. Cikin nishaɗi yaran ke ta cin inibin su na zubarwa, ɗaya daga cikinsu kuma yana jikin mutumin yana tana jagwalgwala nasa inibin cikin nutsuwa. Sallamar da ya yi ne ya sanya su waiwayawa, Muhsin ya jefar da inibin hannunsa, ya nufi Mahafinsa da gudu. Hammad ya ɗaga shi yana murmushi ya ƙarasa shiga cikin falon sauran yaran maza su ma suka nufi Hammad. Ya rungume su yana murmushi ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Kai ne ka ke wasan da su da sassafen nan?" Zahradeen ya yi murmushi ya ce "To ya na iya, su wannan biyun sun hana mamansu sakat da rigima, shi ma Muhsin sai kuka yake yi yau, yana kiran Umma, duk sun rikitata, shiyasa na kwaso su muka dawo nan" Hammad ya yi murmushi ya ce "Ina godiya sosai da sosai" Zahradeen ya tsuke fuska ya ce "Da aka yi me?" Hammad ya sake yin murmushi ya ce "Tuba nake baban Muhsin" Imam Zahradeen ya zauna sosai ya ce "Yaya ake ciki ne? Sultan bai kuma ce maka komai ba haryanzu?" Hammad ya girgiza kai ya ce "Ina dai jiran abin da zai ce, kawai dai yana yawan ce mini, sai abin da aka yanke na shawara" "Ka ga Imam, ka tsaya ka nutsu da kyau ka duba makomarka da makomar wannan jaririn yaron naka. Yaron nan na buƙatar mahaifiyarsa, kuma ina ganin ka dawo da mahaifiyar Mahmoudu gidan nan, su zauna kafin komai ya daidaita, na ga ya saba da ita sosai. Ka san ba abu ne mai sauƙi su bari ka fito da ita daga gidan nan ba. Saboda ina tsoron shawarwarin da Matawalle da kum Sardauna za su yanke a kan matsalar nan. Ba dan kar na yi musu ƙazafi ba, da na ce sun fi mutunta Al'adar Agadez sama da addininsu." Hammad ya ce "To ina nan dai ina sauraren su, na ji hukuncin da za su yanke ɗin" Imam Zahradeen ya ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi" Imam ya amsa da Amin. **** Jikin Shukura ne yake tsuma, tana kallon Yusra a inda suke ɓoye, ga ta rungume da jariri da yake ta ƙoƙarin farkawa ya tsala ihu. Yusra na riƙe da jaririn tana yi wa Shukura alama da ta kwantar da hankalinta. Ɗaya bayan ɗaya mutanen suka fita daga cikin ɗakin, ɗayan ya kira wayar Alhaji Zailani. Yana ɗagawa ya ce "Yaya kun same ta?" "Alhaji mun caje Asibitin nan kaf bamu ganta ba, ga shi sun yi mana barazanar kira mana jami'an tsaro kar su kama mu" "An bani tabbacin ta na cikin Asibitin nan, a yadda binciken nan ya nuna, dole ku nemo ta ba sai na ganta ba ku kashe ta kawai, dan ba za ta tona mini Asiri ba" Jaririn hannun Yusra ne ya tsala uban ihu, hankalin mutanen ya dawo kan ɗakin, ɗaya daga cikin su ya juya da sauri ya nufi ɗakin. ***** Nana tana tsaye a gaban mudubi, ta saka riga ta alfarma, gaba ɗaya jin ta take kamar a cikin tarko, ta gaji da zaman guri ɗayan nan, hankalinta na kan a ƙarƙare abin da za a yi, a bata ɗanta ta koma Nigeria. Gefe guda kuma zuciyarta na ci gaba da wasi-wasi da son lallai sai ta ga mene ne a rufe a wannan ɗakin na gidan tarihin Agadez. Asal ce ta bankaɗo ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske sai da Nana ta tsorata. Ta kalli Nana cikin doguwar riga mai maɗauri, ko 'yar uwatta mace zata sarawa kyawun dirin da Allah ya bata, balle ɗa namiji. Wani abu ɗacin gaske ya taso wa Asal, Gimbiya Bilkisu ce ta biyo bayan Asal. Nana dai ta tsaya ƙyam tana kallon su. AREWABOOKS Da sauri ya dawo, ya buɗe ɗakin jin kukan jariri, kawai ya tarar da Yusra a zaune a kan gado, tana jijjiga jariri. Cikin tsawa ya ce "Ke, me ki ke yi a nan wace ce ke?" Yusra ta ce "Kamar yaya? Nice a ɗakin nan, lafiya suwaye ku?" "Ya aka yi da muka shigo ɗakin nan bamu ganki ba?" Yusra ta ce "Ku na tsaye a bakin ƙofa na zo na wuce ku, na je na karɓo jaririna daga ɗakin jarirai ne, an sallamo shi daga can" Ɗayan ya ce "Ke ƙarya ki ke yi, mene ne sunanki?" Yusra ta ce "Ban gane mene ne sunana ba, suwaye ku tukuna me kuma ku ke nema a gurina ni ban sanku ba" Ɗayan ya dubi hoton cikin wayarsa, ya kalli Yusra ya ga sam babu haɗi. Ya tunkaro Yusra ya ce "Ki gaya mana mene ne sunanki?" "Yusra, sai kuma me?" "Na ke ce wata mata ta tsinto, ta kawo Asibitin nan ba?" "A ka tsinto kuma kamar wata kuɗi? Ni ban san zancen ba, mijina tare muka je na ɗaukko jaririna. Yanzun nan yayata kuma za ta dawo da take zaune tare da ni. Amma mene ne dalilinku na zuwa ku ritsa ni kuna tuhuma ta." Ta yi maganar cikin dakiya tana tsare mutumin da ido. Ƙasam zuciyarta fata take yi, Ubangiji Allah ya sa kar Shukura ta ce za ta fito ta tona musu asiri. Ɗayan ya ce "Ba fa ita ba ce ba, mu koma mu gaya masa ba ta Asibitin nan, ba a ba shi bayanin daidai ba" Suka ƙara ƙare wa Yusra kallo sannan suka fice. Abin da ya faru kuwa, Shukura babu yadda ba ta yi da Yusra ta tafi ba, amma ta ce babu inda za ta je ƙafarta ƙafarta, ba za ta tafi ta bar ta ba. Ga shi ta uzzura mata da tambayoyin yaya aka yi ta ɓata aka neme ta aka rasa. Alamu ya nuna mata haryanzu Yusra da saura kan babu daɗi dan haka ta ce mata sace ta aka yi, ta kuɓuta da ƙyar shi ne wata mata ta tsinto ta ta kawo ta Asibiti. Yusra ta ce "Lallai kin auna arziki tashi mu tafi to" Shukura ta ce "Ai ba a sallame ni ba, ba zai yiwu mu tafi ba, ba ni da cikakkiyar lafiya fa" "To ba sai mu koma Asibiti a can cikin gari ba, kin ga yadda mamanki ma hankalinta yake a tashe, idan muka je da Baban Haidar ta yi ta kuka" Wata Nurse ce ta yi sallama, suka gaisa da su Shukura, ta yi wa Shukura allurai. Wata ce ta sake shigowa da sauri, ta kalli Shukura ta ce "Ke ce Shukura ko?" Ta jinjina kai. "Wasu mutane ne suka zo, wai 'yar uwassu ce ke dubiya suka zo, amma yanayinsu kamar marasa gaskiya, mun ce babu mai wannan sunan, saboda mun san case ɗinki, amma ga shi can ana ta faɗa da su sun ce sai sun caje Asibitin nan, 'yar uwassu ce ke dole su ganki" Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskar Shukura. Nurse ɗin ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai an kore su ma, kar ki damu" Bayan sun fita a rikice ta kalli Yusra ta ce "Ina ga wanda suka sace ni ne suka biyo ni nan, dan Allah ki tashi mu tafi " Yusra ta ce "Ai da tuni mun tafi ki ka dage, yanzu bamu san suwaye ba, idan muka fita ai sai a samu matsala. Dole mu jira zuwa anjima sannan mu saci jiki mu gudu." Da ƙyar Shukura ta amince sai dai da aka jima suna tsaka da shirin guduwa, suka ji muryar mutanen a waje, Shukura ta rikice, Yusra ta yi dabarar janta su ɓuya. ***** Bin su da kallo Nana take yi , Asal ta ƙaraso gaban Nana cikin huci da zafin rai, tana kallonta kamar ta kai mata duka. "Munafuka, muguwa, na jawo ki jikina ashe haɗa baki aka yi da ke a cuce ni? Kin auri mijina kin haihu da shi ban sani ba, kuma da yake ke munafuka ce, ba ki taɓa gaya mini saboda ba kya tsoron Allah. Wallahi idan ba ki rabu da shi ba, sai na kashe ki, na kashe ɗan naki dole ki koma inda ki ka fito a yau ba sai gobe ba, 'yar matsaiyata ƙasƙantacciyar halitta" Nana ta dubi Asal ta ce "Subhanallah, ai Allah kaɗai ya san ƙasƙantaciyar halitta ba ke abar halitta ba. Kuma ɗan ja da baya, numfashinki yana takura mini a fuskata, sai na baki amsar maganganun" Asal ta rikice ta kalli Gimbiya Bilkisu ta kalli Nana, ita kanta Gimbiya ganin Nana da ta yi ta ɗauka sokuwa ce ba ta magana. Nana ba ta jira me za su yanke ba ta matsa daga gaban Asal ta ce "Wannan abubuwan da ki ke faɗa, duk ba ni za ki gaya wa ba, Sayyid za ki gaya wa domin igiyar aurena a hannunsa take. Sai ki ji amsar da zai baki. Kuma ni Allah ya bani haƙuri da na zauna ina kallonki da mijina ban nuna miki komai ba, na biki a yadda ki ke so zuwa lokacin da ya dawo hayyacinsa ya gane ni. Dan haka yanzu da ki ka san komai, ni ba baiwarki ba ce, kuma ba kukun mijinki ba ce, matarsa ce wato kishiyarki" Asal cikin ƙaraji ta hankaɗa Nana ta ce "Wallahi na fi ƙarfin na yi kishi da ke 'yar matsiyata ƙazama, baƙa mummuna. Wallahi sai na kashe ki na kashe abin da ki ka haifa." Gimbiya Bilkisu na ƙoƙarin riƙe ta, amma sai fizge-fizge take yi tana ihu. "To Bismillah Asal, ki kashe ni idan har hakan zai sanya ki huce. Ba za ki taɓa canzawa tuwo suna ba, Hammad mijina ne, wanda na fiki ƙaunarsa" "Ke ya ishe ki malama, dan kin ga na yi shiru saboda ba ki da kunya da mutunci sai ki tsaya kina gaya mata maganganun banza? To bari ki ji na gaya miki, sai kin bar gidan nan a yau ba sai gobe ba. Sai kin bar gidan nan buzayen jinin sarauta ba sa raɓar talaka, balle su aure su su rayu da su. Sai kin bar gidan a wulaƙance cikin ƙasƙanci kuma sai an hukunta Hammad kan laifn da ya aikata" Nana ta ƙare wa Gimbiya Bilkisu kallo ta ce "Haba Mama, ke da ba da ke nake kishin ba? Nifa kamata ya yi a sara mini akan haƙurin da na yi. Kuma ko ba komai, dole sunan 'yar matsiyata ya shiga kundin tarihin Agadez, mace ta farko da ta karya tarihi bayan ɗaruruwan shekaru. Ku daina zagina dan ban yi muku komai ba, abin da na sani kawai na fi Asal son Hammad har Duniya ta naɗe, haka zalika ba ni da tsara a zuciyarsa ki yi haƙuri" "Ƙarya ki ke yi, yadda na yi amfani da kuɗi na mallake ki ta ƙarfin tsiya, haka zan yi amfani da su na yi maganinki mummunan a bar ƙyanƙyami" Nana ta ji zafin maganganun Asal, amma ta yi murmushi ta ce "Ke kin ga alamar muni a tare da ni, kalli da kyau Gimbiya Asal. Kodayake ba wannan ba ma; kar ki manta kina magana da matar da ki kai gidan da ki ke kwana kina shaye-shaye da kaɗe-kaɗe da ƙawaye a lokacin da ba ta san halin da mijinta yake ciki ba, kar kuma ki manta matar da ki ke bawa magani ta zuba a shayin Imam Hammad, haka zalika matar da ta san kina ajiye masa takarda mai hoton ƙwarangwal da yake ci da wuta, wanda shi ne yake burkita masa hankali da lafiyar jiki; wannan matar ita ce matar mijinki kuma baƙa mummunar da ki ke ta kushewa ki ke iƙirarin kashewa" Dummm ƙirjin Asal ya buga da ƙarfi, ta ƙwalalo ido tana kallon Nana. Nana ta ci gaba da cewa "Ni ba karabutin mutanen da ki ka saba wulaƙanwatawa ba ne, kasancewar Hammad mijina ya sanya na bar idanuna a buɗe ta kowace kusurwa a kansa, tunda na haihu da shi, har abada ba zan bari wani abu mummuna ya same shi ba" Asal ta tattaro jarumta ta yi murmushin ƙarfin hali, bayan da mararata ta cika taf da uban fitsarin tsoro. "Ƙarya ki ke yi, ba ki da abin da za ki kawo ƙarshena a masarautar Agadez, saboda ba ki za hujja a kan wannan soki burutsun da ki ke yi" Ta yi maganar tana tsare Nana da ido. Nana ta ce "Kwantar da hankalinki, ba na buƙatar wata hujja ko wani abu, dan har gaban Abada ba zan taɓa tona miki asiri ba. Ai Hammad yana sonki kuma ko ba komai 'yar uwassa ce ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, amma daga yau da rana mai kamar irin ta yau, muddin ina tare da Hammad da ke da duk wani abu da yake kawowa rayuwarsa wani tarnaƙi" Gimbiya Bilkisu ba ta bari Asal ta sake magana ba, ta kama hannunta suka yi waje. Nana ta ja numfashi tana bin bayansu da kallo, kafin tsunduma tunani. Gimbiya Bilkisu ta kalli Asal ta ce "Ke, kina wani wawanci har ki ka bari ta san kina wannan abubuwan? Asal kina da hankali kuwa?" Cikin kuka ta ce "Ammi yaya zan yi, wallahi ban san da wata alaƙa a tsakaninsu ba, ban sani ba. Kuma ban san za ta kawo wani abu ba. Na shiga uku ba zan iya rayuwa babu Hammad ba wallahi Ammi ina son mijina, kuma ba zan iya buɗe ido na gan shi da wata ba ki taimake ni" "Nutsu ki kwantar da hankalinki, bari na yi wa babanki magana a san abin yi a yau ba sai gobe ba, dole a san yadda za a yi da yarinyar nan ki daina kuka" Da kyar ta din ga rarrashin Asal. Nana na zaune na zaman jiran dawowar Hammad,furucin Asal ya tsorata ta, ta fuskanci da gaske kowa na iya aikata duk abin da yake so, a wannan gidan domin cimma burinsa. Ita ba ta kanta take yi ba, ta ɗan jaririn ɗanta da ba ta san inda yake ba ta shi take yi. Ta ƙudurce a ranta, idan Hammad ya dawo, bori za ta yi masa sai ya fitar da ita daga gidansa komai zai faru, amma ƙasan zuciyarta yana ta azalzalarta a kan son a buɗe wannan dakin na gidan tarihin. Bayan azahar ya shigo, sai dai yanayinsa ya nuna mata a cikin damuwa yake. Ya nemi guri ya kwantar da kansa a kan cinyarta. Nana ta shafa kan a hankali ta ce "Lafiya kuwa?" Ya jinjina mata kai kawai. "Ka ci abinci ne?" "Na ci" ya amsa a hankali. "To meyafaru?" Ya ce "Babu komai" Nana ta numfasa ta ce "To dan Allah ina son ka dawo mini da Muhsin, kuma nifa na damu na koma gida, Sayyid hankalina a tashe yake wallahi, na san iyayena sun gaji da nema na" "Asmy kar ki ƙara mini damuwa dan Allah, ina sane da komai, a tsare nake yin komai in sha Allah zai wuce" Cikin damuwa ta ce "Zai wuce yaushe? Shekera ta uku nake shirin yi a ƙasar nan, nima ina da ahali bai kamata na tare a nan ba" Ya tashi zaune cikin damuwa, ya kalle ta zai yi magana, amma bai yi ba ya ciro wayarsa da take vibrating" Da to kawai ya amsa ya tashi ya fita. Nana ta koma ta nemi guri ta zauna cikin damuwa. Da sallama ya shiga ɗakin, ya tarar da Asal ga Sultan, ga Matawalle ga Tafawa da Sardauna sai Gimbiya Bilkisu da take ta ƙoƙarin rarrashin Asal. Gefe ga Imam Asadullahi ga kuma Imam Zahradeen rungume da Muhsin. Asal ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu ganin Muhsin, dan babu abin da ya banbanta shi da Hammad. Yayi mamakin yaushe aka yi masa wannan gangamin har haka? Bayan bai jima da barin gidan Imam Zahradeen ba ya tsaya a gurin Mahmoudu. Sardauna ya ce "Ka je ka zo da babar yaron nan" Babu kara ya karɓi ɗansa a hannun Yayansa Imam Zahradeen, ya tafi inda Nana take. Ya kai mintuna sha biyar, sannan suka dawo tare. Nana suka yi ido huɗu da Asal da idonta ya kumbura, Nana ta sakar mata murmushi ta kawar da kanta gefe. Guri ya tsit sai Muhsin da yake ta hawa jikin Nana yana yi mata surutunsa na yara. Zahradeen ya ce "Imam Muhsin, ka yi shiru" Sardauna ya yi murmushi ya ce "Har ya zama Imam shi ma?" Zahradeen ya ce "Eh mana Allah ya taimake ka. Ɗan Imam ai Imam ne" Suka yi murmushi. Tafawa ya ce "Yakamata mu yi abin da ya tara mu, ba tare da ɓata lokaci ba." Sardauna ya ce "Haka ne kam, Imam Hammad" Hammad ya ɗaga kai ya kalli Sardauna. "Duk da mun san aurenka da ita wannan 'yar Nigeria, ƙaddara ne daga Allah, Amma ina fatan ka sanar da ita matar taka, sharaɗin ƙasar Agadez na rashin auren bare?". Gaban Hammad ya faɗi, Nana kuma ta kalle shi suka yi ido huɗu. Sardauna ya dubi Nana ya ce "Ina fatan ya yi miki bayani?" Nana cikin girmamawa ta ce "Eh ranka ya daɗe. Ya yi mini na sani" Sororo ya bi Nana da kallo. Tafawa ya yi caraf da zancen, ganin ana neman a ɓata masa lokaci. "Amm dama na nemi a yi wannan zaman ne, domin na san mene ne makomar 'yata, sannan wane hukunci za a ɗauka a kan Hammad, bisa karya dokar Agadez" Hammad ya numfasa ya ce "Ai ni ba ni da wata matsala da Asal, ban sake ta ban kuma yi wani abu da... "Kai dalla rufe wa mutane baki, ai na san baka saketan ba, amma mene ne matsayinta? Zaka zauna da ita ne? Ka saki waccan yarinyar ko kuma mene ne?" Hammad ya tsuke fuska ya yi shiru. Matawalle ya ce "Amma mai girma Tafawa, bai kamata a je ga wannan maganar ba. Kana neman sanin matsayar Asal ne?" Tafawa ya ce "Ka bari mu yi magana da shi ka daina saka mini baki" Hammad ya ce "Makomar aurena da Asal, yana daga gare ta, idan tana son zama da ni, ba wani abu dama ni ban ce ba zan rayu da ita ba. Amma ina mai neman afuwarku ina shirye na ɗauki duk wani hukunci da za ku yi mini, amma sau ɗaya a rayuwata, nima ina neman ku yi mini alfarmar nan, ba zan iya sakin Nana ba, mussaman da rabo ya shiga tsakanina da ita. Ba zan iya sakinta ba". Sak suka yi su na bin Hammad da kallo. Sultan ya numfasa ya ce "Hammad, ba kai ka ke da ikon yanke wannan hukuncin ba, sai abin da muka yanke maka. Mai girma Tafawa muna mai baka haƙuri, Hammad ya tabattar da cewa aurensu yana nan daram, dan haka yakamata ta kwantar da hankalinta." "Babu batun kwanciyar hankali a nan, sai zuwa yaushe zamu san matsayarta, yarinyata tana wuni ta kwana babu bacci. Kuma da haka ku ke shashantar da duk wani laifi da zai aikata ba tare da an hukunta shi ba. A wannan karon dole a bar doka ta yi aiki a kansa, kuma a zartar da duk wani hukunci da yakamata a kansa. Ya saki matar nan a yanzu ya bata ɗanta ta tafi inda ta fito shi kuma a hukunta shi" Hammad ya girgiza kai ya ce "Zan karɓi kowane irin hukunci, amma ba zan rama sharri da alkhairi ba" Asal ta rushe da kuka tana rirriƙe Gimbiya Bilkisu. 95 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Tafawa a fusace ya ce "Kun gani ko? Abin har ya kai raini ya shiga tsakaninmu ya faɗi duk abin da ya ga dama. Kamar yaya ba za ka rama sharri da alkhairi ba, waye ya yi maka sharrin waye ya yi maka alkhairin?. Ya yi wa dokokinmu karan tsaye. Kuma dolensa ya yi murabus a gaban majalissa, a ba wa wani tun da ga taka mana doka, ga kuma rashin zobensa sannan wannan ɗan da yake tutiya da shi, babu wanda yake da yaƙinin na halal ne tun da babu waliyyinsa ko ɗaya a lokacin da aka ɗaura auren." "Zan jura komai amma ni ba mutumin banza ba ne ba, kuma kar ka sheganta mini ɗa, ban san da wace kalmar za a yi mana bayanin halin da na shiga har na auri Nana ka yarda ba. Tsawon shekaru ina yi muku biyayya, ko ina so ko ba na so, dokar Agadez ba dokar Allah ba ce ku bari na samu nutsuwar zuciya mana, idan ba so ku ke ku wayi gari ku ga na bar muku duniyar ba. Ta yaya zan yi wa Allah butulci akan abin da nake nema? Yarinyar da ta rayu da ni a lokaci mafi tsananin da babu wanda zai iya zama da ni ina hauka, na haɗu da larurar da hatta najasata ita take gyara mini da hannunta ba tare da ƙyama ta ba. Babu biyayya ga abokin halitta gurin saɓawa mahalicci, Asal na da zaɓin zama da ni ko ta ƙi na bata wannan damar, amma ba zan saki Nana ba ko zaku rataye ni" Sultan ya miƙe tsaye a fusace ya ce "Hammad!" Imam Zahradeen ya miƙe tsaye shi ma, ya dubi Sultan ya ce "Ya kai Abbanmu abin alfaharinmu, a duniya ba na tunanin ka taɓa son wani abu kamar yadda ka ke son Imam Hammad, kuma bana tunanin akwai wani wanda yake yi maka biyayyar da yake yi maka. Tun da ta kai shi ga yin sa in sa da ku, to tabbas ya kai bango. Amma ko sau ɗaya yakamata a ce mai girma Tafawa ya yi maka kara a kan Imam Hammad, amma duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninsa da Asal,  ƙarara yake goyon bayanta a turasasawa Hammad yin abu dan faranta mata, sau ɗaya ko dan saboda shi yakamata a yi wa dokar Agadez kwaskwarima. Gimbiya Bilkisu ta ce "Zahradeen kana da hankali kuwa? Waye ya sanya da kai?" "Ummi ki yi haƙuri, kina duba mafitar ɗan uwanki da 'yarsa, nima ta nawa ɗan uwan nake dubawa." "Ni ka ke gaya wa haka Zahradeen?" "Ina neman afuwarki, amma dan Allah kar ki yi mini mummunar fahimta Ummi." A fusace Sardauna ya ce "Ya isa haka, ya isa, kun manta a gaban wa ku ke ne? Ya za a yi kowa ya din ga magana yadda ya ga dama, babu ɗaa da girmamawa?" Kowa ya yi shiru. Nana cikin ladabi ta ce "Ina mai neman afuwarku, na san wannan hatsaniyar ta faru ne duk a dalilina. Amma da na san wannan al'amari zai faru, ko haka dokar ƙasar nan take, ba zan yi gangancin auren Sayyid ba. 'yan uwansa ba su yi mini wannan bayanin ba. Haka zalika ban faɗi haka dan a ga laifinsu ba, kamar yadda suka gaya mini shi ya nemi a biya sadakina ya aure ni. Amma kamar yadda wannan shugaban ya faɗa" Ta yi maganar tana kallon Tafawa. "Na amince zan ɗauki ɗana na koma Nigeria, idan ma kun ce ba ku da alaƙa da shi, na yarda zan zame masa uwa na zame masa uba.." "Babu inda za ki je mini da ɗa, kuma kema babu inda za ki je" Ya katse Nana yana maganar cikin ɗaga murya. Cikin kuka Nana ta ce "Sayyid babu abin da ya fi ahali daɗi da muhimmanci, sai da na baro nawa na fito nemanka na gane hakan, ni na baro nawa ahalin kai ga ka cikin gata, sun baibaye ka da soyayya da ƙauna. Dama gudun rasa ahalin ga Muhsin ne ya sanya na fito nemanka da tsohon cikinsa." Ta saka hannu a hijjabinta ta ciro zoben da ya bata ta ce "Wannan zoben ina kyautata zaton shi ne zoben da ake ta magana a kansa, tun mu na Nigeria Sayyid ya bani shi kyauta, domin jaddada soyayyarsa a gare ni. Muhsin kai wa Abbanka zobensa, kuma ina fatan ba za a ƙwace kujerarsa ta shugabanci ba, sanyin halinsa zai zamo ƙwarin gwiwa ga talakawan da ba su da ƙarfi. Na gode matuƙa da kulawa amma kar ku raba ni da ɗana dan Allah" Kuka Nana take yi sosai da sosai. Imam Zahradeen ya dubi Nana ya ce "Ɗauki yaronki ki koma, za a neme ki" Nana ta durƙusa ta ɗauki Hammad da ya riƙe zoben da Nana ta ba shi yana zura wa a baki. Ta karɓi zoben za ta ajiyewa Hammad shi, amma ya haɗa ya karɓe Muhsin. Asal kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka take jin yadda a gaban mutane ya nuna wa duniya ita zai iya rabuwa da ita, Nana ce ba zai rabu da ita ba. Tafawa bai yi shiru ba ya ci gaba da zazzaga bala'i kamar zai ari baki. Har sai da ran Sultan ya ɓaci. Ya yi wa Hammad umarnin ya tashi ya tafi kawai. Yana rumgume da Hammad ya ji muryar Asal a bayansa. Ya tsaya ya waiwaya yana kallonta, tamkar mahaukaciya sabon kamu ta ce "Hammad yau nika tozarta a gaban jama'a ka zaɓi bare baƙuwar haure a kaina, ka ƙasƙanta ni a gaban mutane, Hammad ni?" Ya girgiza kai ya ce "Asal ban ƙasƙanta ki ba, kuma har abada ba zan yi ba. Kamar yadda Nana ta faɗa daga ni har ke mu na cikin ahalinmu, muna da cikakkiyar ahali ita kuma fa? Sannan kuma harshenka alƙalinka Asal. Da raina da lafiyata da ƙuruciyata ki ka kalli tsabar idona ki ka din ga jifa na da kalaman ba kya sona ba kya ƙaunata. Duk da na yi miki uzurin ƙuruciya da yarinta a wancan lokacin, amma haryanzu ina ganin wani abu a cikin idaunki da ban tantance so ne ko ƙiyayya ba. Nana ta so ni a bata san waye ni ba, ta so ni a mutum mara asali da makoma auren shahada da kasada, ta rayu da ni da na ɓacewa duniyarta ta ci gaba da bulayin nema na, ba dan tana sanya ran na saka mata ba. Ki duba ratar za ke tsakanin misalan da na baki" Ya wuce rungume da yaronsa ya tafi. A ƙarshe dai Imam Zahradeen ne ya mayar da Sultan turakarsa sai jiri yake yi saboda ɓacin rai. Ya ɗebo ruwa ya ba shi ya karɓa ya sha yana mayar da numfashi. Sultan ya ce "Zahradeen" Ya amsa da "Na'am Abbie". "Na rasa ta ina zan ɓullowa lamarin nan gaba ɗaya" Zahradeen ya numfasa ya ce "Allah ya taimake ka, da Tafawa ne a matsayin da ka ke, komai za a yi ba zai taɓa ƙin goya wa ɗansa baya ba, dan ya faranta muku ba. Ka rintse idanunka ko toshe kunnenka. Ka kamanta yarinyar nan a matsayin 'yar cikin ka. Ana maganar shekara biyu zuwa ta uku rabonta da gidansu. Ka ga dai yadda yake zare idon nan, bai ƙi ya aikata duk wani abin kunya da zai zubar da mutuncin Agadez ba. Abie shin ba ka tunanin wata aya ce Ubangiji Allah ya saukar mana, domin ya nuna mana fari da baƙi halittarsa ce kuma duk yana kishi da son abin sa? Ka lissafa Allah ya hana shi haihuwa duk da ya yi aure da ƙanan shekaru, aka hana shi ƙara aure. Lokaci ɗaya Allah ya jarabce shi da ciwon da sai da ya keta ya bar Niger ya tafi Nigeria rabon wannan ɗan ya kai shi har can. Kuma duk da haka Allah ya jarabce shi da ciwon da sai tana kusa da shi yake samun afuwa. Yanzu idan muka rintse idanu daga hukuncin da Allah ya zartar dan mutunta al'ada muka tozarta baiwarsa kana tunanin Allah zai barmu? Ka duba ɗan jaririn yaron nan da yake kai komo a tsakanin su cikin farin ciki idan aka raba su, duk gatan da za a nuna masa bai kai ya tashi a tsakanin iyayensa ba. Abie Mai girma Tafawa ɗan uwanka ne, kuma ɗan uwan mahaifiyata ne, amma ina mai tabbatar maka ba zai taɓa ƙaunarka ba, har gara ni yana yi mini kara saboda ɗan 'yar uwassa ne, amma ba zai taɓa son Hammad ba. Kai kuma Hammad ɗanka ne komai za a yi ka banƙara shi ma ya samu abin da yake so" Sultan ya yi shiru cikin nazari, ya numfasa ya kalli Imam Zahradeen ya ce "To yanzu kai me ka ke tunani, kuma meyasa ba ka yi mini duk wannan bayanin tuntuni ba?" Zahradeen ya ƙara nutsuwa ya ce "Ina tsoron shiga lamarin ne a baya, amma Hammad da kansa ya same ni da maganar, kuma ya nuna mini yarda ta hanyar ajiye ɗansa a gidana. Yanzu ka bar wani batun Tafawa da wata majalissa kai ne Sultan, idan ka yi doka dole a bi ta. Ka bar Imam Hammad da matarsa, kuma ka soke wannan al'adar da aka ba wa wannan ƙarfin, ka yi musu fatan alkhairi" Sultan ya girgiza kai cikin jimami ya ce "Ba abu ne da zai yiwu cikin sauƙi ba" "Ka duba dai Abie, ka duba makomarsu baki ɗaya" "Shikenan, ka je zan yi tunanin abin yi" Imam Zahradeen ya ce "To shikenan Abie, amma dan Allah kar ka jira sai ka yi shawara da wani a cikin 'yan majalisarka" Sultan ya ce "To shikenan" Imam Zahradeen ya miƙe tsaye, ya ce "Bari na ƙarasa gurinsu, zan karɓi Muhsin na tafi da shi" Sultan ya jinjina kai kawai. Hammad ya shiga ɗakin da Nana take, cike da takaicin yadda ta ce, ita ta haƙura da shi, a bata ɗanta ta koma Nigeria, sai dai ya tarar da ita tana kuka. Ya kwantar da Muhsin da ya yi bacci, ya ƙarasa gabanta ya ce "Meyafaru kuma ki ke kuka?" Ta yi shiru ta ci gaba da kukan. "Mene ne?" Ya sake tambayarta. "Sayyid" Ta kira sunan shi a raunane. Ya zauna a kusa da ita ya ce "Mene ne?" Ya yi maganar yana ɗago ta cikin damuwa. Ta ƙanƙame shi tana kuka ta ce "Sayyid na faɗi haka ne dan su daina yi maka faɗa, amma ina sonka wallahi Sayyid, dan Allah kar su raba ni da kai" Ta yi maganar tana sheshsheƙar kuka. Shi ma rungumota ya yi sosai da sosai a jikinsa, yana wata irin ajiyar zuciya. Da kyar ya tattara nutsuwarsa, ya ce "Ki yi haƙuri Ma vie, Ubangijin da ya haɗa mu ne kaɗai zai raba mu. Ni da ke mutu ka raba in sha Allah" Zata yi magana suka ji ana bubbuga ƙofar ɗakin, Nana ta motsa za ta tashi, amma ya riƙe ta kuma ya yi umarnin a shigo. Imam Zahradeen ne ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, kunya duk ta kama Nana. Ya ɗan tsaya yana kallonsu ya ce "Kuka ku ke ne?" Nana ta yi saurin tashi tana share hawayenta ta ce "A'a". Imam Zahradeen ya ce "Ga idonki nan duk hawaye. Wai  me ki ke gaya masa ne, ya sanya duk ya rikice haka a kanki" Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi. Imam Hammad ya ce "Komai ma gaya mini take yi, shiyasa nake jin tamkar raba ni da ita, raba ni da rayuwata ne" Zahradeen ya jinjina kai ya ce "Na ga alama ai. Amma dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku ci gaba da addu'a, in Allah ya yarda a dalilinki za a sauya tsarin wasu dokokin na Agadez. Yanzu dai Muhsin zan ɗauka zamu tafi" Cikin marairaicewa Nana ta ce "Dan Allah ka bar mini shi a nan" Ta yi maganar tana kallon Imam Zahradeen. Ya girgiza kai ya ce "A'a barinsa a nan babu tsaro, tsawon lokacin nan yana tare da ni a can gidana, gobe in Allah ya kaimu za a kawo masa maman Mahmoudu. Idan kuma ba a yarda da ni ba, na bar ku abinku" Nana ta ce "A'a amma dan Allah ka tafi da ni, ina son na zauna tare da shi, kuma na ga Nene." "Wani irin mugun kallo Hammad ya yi mata" Zahradeen ya ce "Ai ko ba ki ce komai ba, dole za ki bar gidan nan, taso mu tafi" Hammad ya ce "Ya haka? Ku tafi ku je ina? Kuma yaya zaka tafi da ita Sultan bai sani ba?" Imam Zahradeen ya ce "Idan zaka biyo mu ne taso" Nana kuwa ta yinƙura ta tashi ta ɗauki jakar kayanta dama da hijjabi a jikinta. Hammad ya miƙe ya ce "Wai bin nasa za ki yi?" "Ni ba na son zama a nan, na gaji" Nana ta furta tana tura baki. Imam Zahradeen ya ɗauki Muhsin, ya kalli Imam Hammad ya ce "Ɗaukko mata jakarta" Zahradeen yana fita, Hammad ya riƙe ta ya ce "Dan me zaki ce za ki bi shi? Meye haka ki ke yi ne?" "Amma Sayyid na ga yayanka ne fa" "Ko ma wane ne, dan me za ki bi shi?" Ta girgiza kai idanunta na cika da hawaye "Ni na gaji da zaman gurin nan? Ni gaba ɗaya ma tsoro nake ji" Sayyid ya ce "Muje kar ki yi mini kuka" Ya saka Nana a gaba, suka bi ta baya, sai ga su a harabar gidan. Zahradeen har ya kwantar da Muhsin a cikin motar. Hammad ya buɗe wa Nana bayan motar, sai hararta yake yi, amma ta basar ta shige cikin motar ta kawar da kai. Haka nan take jin kamar ta fito daga kurku sai wani irin farinciki take ji da nishaɗi, a haka ya bar gidan da Nana a cikin motar. Tafawa kuwa ya ɗauki zafi, ya ci gaba da ziga 'yan majalisar Sultan a kan lallai su sanya ido a hukunta Hamma, sannan ya yi baƙin cikin fito da zoben nan da aka yi. Matar Imam Zahradeen ita ma haka take kyakykyawar gaske, fara sol da ita, yaransu huɗu, kyawawa su ma. Sai dai Nana ta ga matar ba ta ƙyamace ta ba, ta rungume Nana tana faɗin yau ga Umman Muhsin, baƙar Gimbiya ta farko a kaf faɗin Agadez. Nana dai ta kasa sakin jiki da matar, dan duk mutanen Agadez ɗin tsoro suke bata, kusan kowa ba abin yarda ba ne. Ganin Nana ba ta sake da ita ba, ya sanya ta bar ta a ɗakin da aka sauke ta. Washegari da sassafe Hammad ya tafi gidan Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce ba zai gansu ba sai bayan Azahar, tun da shi ba shi da kara. Nana tare da Muhsin suka kwana, kasa baccin kirki ta yi ta rungume shi, cikin farin ciki tana shafa shi. Aka kawo mata lafiyayyen Abinci, matar Imam Zahradeen ta kawo mata kaya masu kyau, ta ce ta saka. Hammad ya din ga yi wa Imam Zahradeen magiya. Zahradeen ya ce "Ka ga ba fa magana ake ta kai shugabana ne ba, yanzu muna magana ne a matsayin ya da ƙani, dan haka dole ka jira. Sai da aka yi azahar ɗin, suka yi salla, sai ga Mahmoudu tare da Nene. Hammad suka gaisa da Nene cikin girmamawa. Sai dai shigowar su Nene babu daɗewa, sai ga Sule shi ma ya zo, tare da wani matashin saurayi. Mamaki ya kama Mahmoudu, ganin Sule ya zo gidan, sai dai ya yi ta yi wa matashin kallon sani. Imam Zahradeen ya kalli Hammad ya ce "Ka san wannan?" Ya yi maganar yana nuna masa matashin. Ya yi shiru yana tsare shi da ido, ya ce "Na san shi, amma na manta a ina, na san dai na taɓa ganinsa" Imam Zahradeen ya kira wayar matarsa, ya ce ta zo da Nana. Wani irin kyau Nana ta yi, ɗinki ne na buzaye a jikinta, sai ƙamshin turare take yi ta shigo da sallama. Kasa riƙe farincikinta ta yi, ta nufi Nene da sauri. Sai dai ta yi wani irin wawan burki, bayan yin ido huɗu da matashin saurayin, da girma da kamala suka bayyana a tattare da shi bakinta na rawa ta ce "Imrana!!!" Wata irin sufa Nana ta yi, ta nufi Imrana a gigice, ta rirriƙe rigarsa tana zaro ido, tana son tabattarwa da gaske shi take gani, ko kuma gizo yake yi mata. Cikin rikicewa ta ce "Imrana, Imrana kai ne? Imrana dan Allah mafarki nake yi ko kuma kai ne?" Ya yi murmushi ya rungume ta idanunsa na cika da hawaye ya ce "Ni ne Nana, Imrananki ne" "Imrana ka tafi ba ka sake nema na ba, ka tafi ka bar ni nikaɗai, Imrana" Toshe mata baki ya yi, a hankali jikinta ya saki ya kuma yi sanyi ƙalau. Ƙaisar ta hango a bakin teku, yana kallon ruwan, ta ƙarasa inda yake da sauri, ta ce "Ƙaisar kai ne? Ya jikin naka? Ka warke?" Ta yi maganar tana riƙo hannunsa, sai dai maimakon ta ji ta kama tsoka sai ta ji tamkar ta taɓa ƙanƙara wani irin sanyi ƙalau. Ya dube ta ya ce "Ina taya ki murna" Ta ce "Murnar me?" Ya miƙe tsaye ya ce "Murnar komai ma, alamu sun nuna Ubangiji yana sonki, tsananin da ki ka din ga shiga, ya zame wa wasu silar alkhairi, kuma sannu a hankali Allah yana warware miki komai" Ta ɗan yi shiru ta ce "Ban fahimci me ka ke nufi ba" Ƙaisar ya ce "Ba sai kin fahimta ba. Ina taya ki murnar ganin ɗan uwanki, sai dai haryanzu da ɗan sauran rina a kaba. Shi wannan mijin naki, zuciyarsa da karsashinsa a kanki kawai yake. Amma bai damu da tsayuwa tsayin daka a kan abubuwa ba, ya kan karɓi abu duk yadda ya zo masa, ya tafi a haka komai zafi da raɗaɗin cutarwar da abin yake yi masa. Kar ki kuskura Sarkin baka ya tafi, baku bankaɗo abin da yake faruwa da shi ba, sannan Giyaz haryanzu yana tare da shi, sai dai a galabaice yake yana jinya. Kin san bamu fiye saɓa alƙawari ba, dan haka abu ne mawuyaci ya rabu da mijinki ta daɗin rai, saboda yarjejeniyar da suka yi da bokan nan. Kamar yadda na sanki, ki ci gaba da addu'a, zan iya cewa kusan komai ya zo ƙarshe, sai dai ban san abin da ka iya faruwa a gaba ba." "Ma vie" Ya yi maganar yana shafa fuskarta, a hankali ta buɗe ido ta kalli Sayyid, ta sake ɗaga kanta, ta ganta a jikin Imran. Kuka take sosai da sosai, da ita kanta ta kasa tantance ko na mene ne. Imrana da yake share hawayen ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka" "Kukan ne yake zuwa" Ta yi maganar wasu hawayen na ci gaba da zubowa. Ya kalli Muhsin da yake ta guje-guje a ɗakin, ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Wannan ne ɗan nata?" Ya yi murmushi ya jinjina masa kai. Nana ta sake cewa "Imrana ya aka yi ka san ina nan?" Ya yi murmushi ya ce "Bacci na kwanta, kawai na farka na ganni a nan" Kukan da take yi bai hana ta yin murmushi ba. Ta ce "Nene kin ga yayana, duk duniya shi ne kaɗai wanda muke ciki ɗaya da shi" Nene ta ce "Allah sarki, ga kammanni nan ku na yi da shi" Imam Zahradeen ya ce "Yakamata a fara ba wa baƙi" Nana ta ja jikinta ta zauna, ta ƙure Imrana da ido, gaba ɗaya ya nutsu, babu wannan hauma-haumar tasa. Shi kansa Imam Hammad kallon Imam Zahradeen yake cike da mamaki yana jiran jin bayani daga bakinsa. ***** Jamila ce a durƙushe tana wani irin kakari, ji take yi tamkar barin duniyar za ta yi saboda matsananciyar azabar da take ji. Ta ɗaga kai da kyar ta kalli Mama, a galabaice ta ce "Mama, me ki ka bani a cikin kukun nan na sha, Mama zan mutu zan rasa raina" Mama ya ce "Ai gara ki mutun na huta Jamila, gara ki tafi asirina ya rufu da wannan masifar da ki ka ɗaukko mini. Ba dai ke taurin kan tsiya ba, ai na san yadda zan yi da ke nima. Ƙwayar zubar da ciki na je na sayo a gurin Mariya Likita na zuba miki, dan ba za ki haife mini shege a gida ba". Jamila ta girgiza kai cikin matsananciyar azaba ta ce "Mama ba ki kyauta mini ba, zan iya rasa rayuwata Mama, kin san azabar da nake ji kuwa?" "Tun da ki ka iya jure miƙawa maza jikinki, dole ki jure azabar fitar cikin" "Wayyo Allahna" Ta faɗa a marairaice tana sake durƙushewa cikin azababben ciwo. ***** Fadila ce ta fito daga banɗain da ta shafe a ƙalla awa ɗaya da rabi a ciki, tana tufaka da warwara, sosai an matsa musu a kan su tashi su bar gidan. Har ta gaji da zuwan da wanda ya sai gidan yake yi yana ɗaga musu hankali kamar ba abokinsa ne ba. Ga shi haryanzu bai gama samun cikakkiyar lafiya ba, lallaɓawa kawai yake yi, shi kansa ya rasa inda zai sanya kansa saboda damuwa, ƙarfin hali kawai yake yi. Tana fitowa ta tarar da shi a tsaye da waya a hannunsa. Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?" A sanyaye ya ce "Coustom ne suke nema na a Lagos" Ta ɗan yi saroro ta ce "Suke neman ka kuma, lafiya dai?" Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi ban san mene ne ba, ga shi ko kuɗin motar tafiya ba ni da su. Allah ya sa ba wani abin ne mara daɗi ya sake tasowa ba" Fadila ta ce "Jikina ba ya bani wani mugun abin ne, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ne ya sanya suke neman ka. Bari na kira Umma idan da kuɗi a hannunta ta ara mini" Ya ce "A'a, kin san ba shi ne da ita ba, ba dan halin da Alhaji Zailani yake ciki na ɓatan 'yarsa ba, ai da shi zan cewa ya biya mana, ya raka ni muje mu ji ko mene ne" Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Dan Allah Daddy ka daina gayyato mutanen nan haka, mu din ga shiru tukuna idan alkhairi ne idan Allah ya tabattar sai kowa ma ya ji. Da za a samu kuɗin sai Umman su Raudha ta raka ka. Amma hakan nan za ka yi haƙuri mu nemo kuɗi ko ta mota ne ku tafi tare. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ka sanya alkhairi ne. Ya amsa da "Amin." **** Gaba ɗaya Shukura ta yi saranda da da ba zata tsira ba, daga ita har jaririnta, Yusra ta ce mata duk za ta yi ta nemi guri ta ɓuya, ba za ta iya fitar da ita da jaririn lokaci ɗaya ba, ta fuskanci mutanen nan, su na harabar inda Asibitin yake. Shukura na kuka ta ce "Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni?" Yusra ta ce "To yaya za mu yi, idan ba haka ba daga ke har jaririn za ku iya rasa ranku, ki bari na fita da jaririn, ki san duk yadda za ki yi ki ɓuya ko ki gudu. Amma Shukura suwaye wannan suke binki haka? Kuma me ki ka yi musu?" Shukura na kuka ta ce "Dogon zance ne, ke dai tafi da shi, idan ban rayu ba ma dan Allah ki kula mini da shi" Yausra ta bata mukullin motar da ta zo da ita ta ce "Idan kin samu dama, ki gudu ni zan san yadda zan yi" ta goya jaririn Shukura na kuka, Yusra ta fice daga ɗakin. **** Imran ya ci gaba da kallon Nana cikin zallar farin ciki da shauƙi, tare da kallon Muhsin dukkaninsu cikin shiga ta alfarma da kamala. Ya ce "Nana, ashe zan gan ki cikin farin ciki da kwanciyar hankali haka a rayuwata? Allah na gode maka da ban tursasa ki na kashe miki aure ba, ashe alkhairinki yana tattare da auren. Kasancewar daga Nana sai shi a ɗakin, ta ɗan jinjina kai ta ce "Amma an sha gwagwarmaya Imrana, duk da na gode wa Allah da ka bayyana yanzu, ka zo a gaɓar da na fi tsananin buƙatar ka, amma meyasa ka yi fushi da ni baka sake dawowa ba, dama akwai abin da zan yi maka ka yi irin wannan fushin da ni?" Ya girgiza kai ya ce "Babu shi, abin da za ki yi mini da zai sanya na guje ki. Amma ki yi haƙuri kaɗan za ki ji abin da ya faru. Na yi burin na samu wadata ki huta na gatanta ki Nana, amma Allah ya ƙaddara ke ce zan huta a dalilinki." "Ban gane ba, me ka ke nufi?" Imrana ya ce "Za ki gane ne" "Imrana ina Baba da su Jamila, na san ba zuwa gurin su Mama ka ke yi ba, da gurin su Ummi, ban san da wani idon zan tunkari gida ba, na tafka babban kuskure da bana tunanin za su iya yafe mini" "To kar Allah ya sa su yafe ɗin mana, ke dai ba kin riga kin yi gaba ba, su zauna da rashin yafiyar" Nana ta buɗe baki ta ce "Lallai hali zanen dutse, Imrana kar Allah ya sa su yafe, su Baban?" "Eh ɗin, ai ke yakamata a ce ma sun nemi yafiyarki, idan sun yafe shikenan, idan ma ba su yafe ba za ki ci gaba da rayuwa wataƙila ma babu wanda ya neme ki a cikin su" Hammad ya dubi Imam Zahradeen bakinsa fal tarin tambayoyi, amma yanayin fuskar Zahradeen ɗin babu alamar zai amsa masa tambayoyin nasa" Imam Zahradeen ya ce "Ya na ga ka ƙure ni da ido ne?" Hammad ya ce "Abubuwan da na gani suka ɗaure mini kai nake son ka yi mini bayani" Ya numfasa ya ce "Bayani ya zama dole Hammad, amma ina fatan zaka yi mini afuwa da duk abin da za ka ji a bayanin nawa" Imam Hammad ya ce "In sha Allah" Kamar yadda suka taru a falo ɗazu, haka suka sake taruwa bayan sallar la'asar. Imam Zahradeen ya ce "Ina yi wa kowa barka da zuwa wannan gida nawa. Wasu sun san da zuwan wasu, wasu ba su zan da zuwan wasu ba. Cikinmu akwai yan gidanmu na sarauta, akwai wanda ba su da alaƙa da gidan namu, amma a yanzu tilas mun zama abu guda, kuma zan warware wani abu da na san wasu za su gan shi wani iri, amma yi haƙuri da yadda komai zai zo, duk wanda yake gurin nan abin ya shafe shi ne. Imam Hammad, wannan bawan Allah da ku ke gani Sulei yarona ne, zamanku a tare da shi, da duk wani abu da ku ke ciki, wani abu ne na shiri da na yi shi" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon Sule tare da Imam Zahradeen. Bai damu da kallon da suke yi masa ba, ya ci gaba da cewa; wannan matashin saurayin da yake ɗan uwa ga matarka Hammad wato Imran, bayan da ya je ya same ku, ya yi yinƙurin tafiya da ƙanwarsa, hankalinka ya tashi sosai, ka kira Mahmoudu ka gaya masa, shi kuma sun yi maganar da Sulei, shi kuma Sulei ya gaya mini. Gudun kar ya kawo tangarɗa a rayuwar aurenku, ya sanya na saka aka bi diddigi aka nemo shi. Aka kawo mini shi har Agadez, na yi masa bayanin komai, da ko kai waye, da alfarmar da nake nema ya yi mini na yin shiru da bakinsa ya yi haƙuri ya bari ku rayu da ƙanwarsa, kai mutum ne mai asali da daraja, ƙaddara ce ta faɗa maka. Sai dai ya fututtuke yana ganin kamar rainin hankali ne kawai, idan kana da asali da daraja dan me zan barka a wulaƙance kana gadi. Da kyar ya fahimci abin da nake son ya fahimta, sai dai duk da haka gudun ya ƙara burkicewa saboda na ga rigimamme ne, na aika shi waje karatu. Sunansa yana cikin jerin waɗanda ka ke bawa tallafin karatu a Agadez, a cikinsu na saka shi aka kuma fitar da kuɗin dan kai ka biya masa ba ni ba. Fuskar Hammad ta yi wani irin ja, cikin kakkausar murya ya ce "Zahradeen" "Hammad" Ya miƙe tsaye ya ce "Labarin nan bai cika ba me ka ke ɓoyewa?" Imam Zahradeen ya yi murmushi ya ce "Wannan rigimar cikin gida ce, ka bar maganar a haka" "Ba zan bari ba, sai ka yi mini cikakken bayani" Mahmoudu shi kansa ɗaurewa ya yi, kenan duk wannan abin Sulei, kallon biri yake yi masa yake yi musu na ayaba, ya san komai, ya san waye Imam Hammad, amma ya zauna da su har da yi masa masifar kullum yana ɗawainiya da mutumin da bai san asalinsa ba?" Gaba ɗaya jikin Hammad ya hau tsuma, yana neman ya fita hayyacinsa. Hammad ya riƙe rigar Imam Zahradeen yana tsare shi da idanu cikin tuhuma. Zahradeen ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Ni ne nake tura maka saƙon cewar kar ka dawo da Hammad Agadez, lallai ka tafi Nigeria. Kuma ni na shirya yadda aka haɗa ku da Sule har ku ka yi aikin gadi tare. Sule ni yake yi wa aiki, duk wani abu da yake faruwa, da motsinku Sule yana sanar da ni. Kuma nine nake tura maka kuɗaɗe domin kula da Hammad da iyalin da ya aura, kuma aka sanar da ni kwanciyar hankalin da yake ciki. Sai dai bayan kame ku gaba ɗaya na kasa sanin halin da yake ciki, na tura Nigeria a bincika mini, aka tabattar mini da kama ku. Na ci gaba da bibiyar inda Nana take, amma binciken nawa bai cim mata ba, tayi ɓatan dabo, ga kuma alƙawarin da na yi wa ɗan uwanta, na zan tabattar da tana cikin ƙoshin lafiya. Sai dai da Allah ya dubi zuciyata sannu a hankali, komai ya din ga warwarewa, tun kafin ka gane ta, ni na gane ta saboda har hotonta ina da shi. Kuma aka yi sara a kan gaɓa ka zo ka same ni, da maganar cewa ka yi aure a Nigeria. Sai na bika muka tafi a haka, ban nuna maka komai ba, zuwa lokacin da nake ganin ya dace ka san komai!. 96 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Hammad bai iya cewa uffan ba, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita. Imam Zahradeen kuma bai motsa daga inda yake ba, ya zuba masa ido. Nana ta tashi a rikice ta ce "Sayyid ina zaka je ne? Kar ka yi fushi, ka tsaya ka saurare shi, kar ka yi wa al'amarin wata mummunar fassara. Bai tsaya ba kawai ya yi gaba, Mahmoudu ma tashi ya yi ya bi bayansa da sauri. Wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa. Ga farincikin ganin Imrana, amma alamu sun nuna Hammad ya ɗauki zafi da abin da Yayansa ya aikata, duk da ta wani fannin taimakonsa ya yi, amma ta wani fannin abin a saka masa ayar tambaya ne. ***** Sagir kuwa kamar zai haukace, saboda tashin hankali bai fita daga tashin hankalin ɓatan Shukura ba, ga Yusra ma ya neme ta ya rasa, tun safe ana maganar sha biyu saura na dare. Ga shi layin wayarsa yana cikin wayar Yusra, haka a dole yaje police station ya kai rahoton ɓacewar Yusra. Ya fara tunanin kar a fara zarginsa da ko shi ne yake aikata wani abu, matan nasa suke ɓacewa. Ƙarfe shida na safiya, suka ji ana bugun gate, bugu na tashin hankali kamar za a ɓall gate ɗin. Afujajan mai gadi ya buɗe gate ɗin, babu tsammani yaga Yusra a tsaye kamar korarriya. Ya zaro ido yana kallon ta cikin matsanancin mamaki. Gaba ɗaya gari ma bai gama waye ba, ya kalli hannunta ya ga jariri, bai yi magana ba ta banke shi ta wuce cikin gidan. A falo ta tarar da Antynta tare da mai gidanta, saboda bugun ƙofar da suka ji ana yi. Cikin mamaki Antyn ta ce "Yusra lafiya ki ka zo gidan nan da sassafen nan haka? Daga Kanon ki ka taho Abuja" Yusra ta yi shiru ba ta yi magana ba, kallon falon Yusra ta hau yi, tana tunanin yaya aka yi ma ta zo nan. Ita dai ta san ta ɗaukko jaririn ta fito titi, tama tafiya a hankali tana waige-waige, daga nan bata sake sanin abin da ya faru ba, ta ganta a ƙofar gidan Antynta da ta koma hannunta a Abuja. Mai gidan ya ƙarasa gaban Yusra, ya karɓi jaririn da ya fara kuka a hannunta. Yusra ta nemi guri ta zauna tana mayar da numfashi. "Yusra dan waye wannan, a ina ki ka samo shi?" Mai gidanta ya ce "Rabu da ita ta huta, wannan yaron a samo madara a bashi, sannan a kira mijinta mu ji ko da saninsa ta taho, kuma me yake faruwa" Antyn ta jinjina kai cikin damuwa, da fargabar a ina Yusra ta samo ɗa. ***** Jamila kuwa ta din ga zubar da jini babu ƙaƙƙautawa, ga azababben ciwon mara da ta din ga yi. Ta kwana ta wuni tana wata irin burgima da kuka mai ban tausayi. Baba ne ya dawo ya tarar da Jamila a cikin wannan yanayin. Baba ya ce "Rabi wai me yake damun Jamila haka ne, wannan wane irin ciwo ne tun jiya?" Mama ta ce "Ba fa wani abin ba ne ba, al'ada ce ta zo mata take shan wahala." "Haba, wahalar ta isa haka, wane irin ciwo ne haka, anya ba za a kaita Asibiti ba" Mama ta ce "Ba sai an kai ta ba, na bata magani za ta warke" Baba dai bai ji ya gamsu ba, amma ya ƙyale su kafin ta hayayyaƙo masa da masifa. ***** Asal duk ta fita hayyacinta, kullum cikin kuka, ta yi wata irin muguwar rama. Tana zaune a ɗakinta, Tafawa ya shigo ɗakin, ta ɗaga kai ta kalle shi. Ya ce "Dalilin me ne ne ya sanya ba kya cin abinci?" Ta yi shiru ba ta ce masa komai ba. "Kar ki saka damuwar abin da yake faruwar nan a cikin zuciyarki, duk yadda zan yi dole sai na tabattar da an hukunta Hammad, ba zai ci bulus ba abin da ya aikata." Asal ta yi shiru, wani irin baƙin ciki na taso mata a zuciyarta, ta din ga tuna yadda mahaifin nata ya din ga ingizata da tursasa ta aikata Wasu abubuwan. Ya yi wa rayuwarta illa duk a ƙoƙarin sa na ganin ya cimma wani burinsa da abu ne mai wahala ya samu cikarsa. Yana magana amma ta lula Duniyar tunani, ta tuna lokacin da aka kusa auren, ya kawo mata wani abu a ƙoƙo ya ce ta sha, sai bayan da ta sha sannan ya ce bai aura mata Hammad dan taje ta haihu da shi ba, domin har abada baya fatan ya haihu balle ya sanya ran samun magaji ya ƙara dagula masa lissafi gurin cim ma burinsa. Wasu irin zafafan hawaye suka zubo wa Asal, ta daɗe da gane rashin haihuwarta na da nasaba da wannan magani da mahaifinta ya bata, duk da a ɓoye ta je ganin likita a kan matsalar rashin haihuwar, aka ce mata hakan yana da alaƙa da ta'amalli da chemicals masu ƙarfi da ta yi. Da fari ta yi tunanin shaye-shaye da take yi, sai dai ko da shaye-shaye ta fi kyautata zaton maganin da Tafawa ya bata ne sila. Nana ta samu ta sake sosai da sosai da Imran ta din ga bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa, wasu guraren sai da ya yi hawaye. Haka kuma ya din ga yi wa Nene addu'a, a kan abin da ta yi wa Nana na taimako. Nene ta ce "Babu komai, ɗa na kowa ne. Kuma in sha Allah Nana daram zata zauna a ɗakin mijinta" Nana ta kalli Imrana ta ce "Imrana tsoro nake ji, ban san yaya su Baba za su kalle ni ba, ban san me zan ce musu ba, ga shu kai ma tun da ka tafi ba ka je gidan ba?" Imrana ya ce "Ba za ki daina wannan zancen ba, ba abin da za su yi miki. Nima ban je ɗin ba" Nene ta ce "Ai dole mu kafa mu tsare, daga nan Agadez a tashi tawaga, su je har gida a bawa iyayenku haƙuri, kaga yanzu kai ne waliyyinta, a tashi manya daga Agadez su je har Nigeria su ba wa iyayenku haƙuri a kan abin da ya faru, sannan kuma a yi. Sannan ya zama dole a yi wa Nana duk wani abu na dukiyar aure, a yi cikakken biki na 'yar gata duniya ta shaida auren yadda yakamata, dan gudun kar ma a zo a samu wata matsala a nan gaba." Imarana ya ce "Wannan gaskiya ne, amma kina ganin za su amince da hakan?" Nene ta ce "Dole za su amince, ko dan son da suke yi wa ɗan su. Tun da ɗansu yana son iyalinsa." Hammad kuwa gidansa ya koma, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ya din ga juyi yana tunani, tare da tambayar kansa, kenan duk abin da yake faruwa da sanin Zahradeen. Kasa jurewa ya yi ya tashi ya tafi gurin Sultan. Yana zaune Gimbiya Bilkisu ta sanya shi a gaba, tana ta maganganu a kan kar ya nuna son kai akan hukuncin da zai yanke, kuma ya duba Asal ita ma a yi mata adalci. Babu tsammani sai ga Hammad ya shigo, yanayin yadda fuskarsa ta yi jawur, ya sanya Sultan miƙewa yana tambayarsa ko lafiya? Amma Hammad ya yi shiru bai ce komai ba. Sultan ya kama hannunsa ya shiga da shi cikin ɗakinsa, ya zaunar da shi ya ce "Ka gaya mini mene ne?" Sai gumi da yake ta tsatstsafo masa amma bai yi magana ba. Mahmoudu kuwa daga fitowar Hammad ya biyo bayansa, ya neme shi ya rasa, yana son su yi magana, ya lallaɓa shi su bi abin a sannu su fahimci Zahradeen, dan ya ga alamar ya ɗau zafi lamarin ya ɗaure masa kai. Matar Imam Zahradeen ta yi sallama, suka amsa. Ta kalli Nana cikin sakin fuska ta ce "Gimbiyar Imam Hammad, Imam Zahradeen yana kira" Nana ta yi murmushi ta ce "Nana dai za ki ce" "Ina, wa ya isa faɗar sunan Gimbiya" Nana ta yinƙura ta tashi ta bi bayanta. Bayan sun shiga, matar Zahradeen ta koma, Nana ta zauna a ƙasan Carfet. Ya ce "Kin ga mijinki ya ɗauki zafi, yaƙi tsayawa ya saurare ni, balle ya fahimce ni, amma na ga ke kina cikin nutsuwarki, za ki fi fahimtata. Amma kafin nan kin ga ke ki ka zauna da shi, ko za ki iya gaya mini abin da ki ka sani, bayan haɗuwarku lokacin yana cikin rashin lafiya?" Ta jinjina masa kai, sannan ta yi masa bayanin, abin da take ganin ya dace ta gaya masa. Ya ce "Shikenan, Sultan ya kira ni a waya, ya ce yana nema na, na san wataƙila ya gaya masa ne, tare da ke za mu je gobe in Allah ya kaimu da safe" Nana ta amsa masa da "To" ***** Hajiya Halima ta kiɗime, tun bayan da Sagir ya kira wayarta yake tambayarta, ko Yusra ta je gidan. Har ta fara shirin tafiya Kano, Yayar Baban Yusra ta kira ta a waya, ta sanar mata ga Yusra ta zo tun ƙarfe shida na safiya tare da wani jariri da ba su san a ina ta samo shi ba. A kiɗime Hajiya Halima suka shirya, suka tafi gidan Antyn, su na zuwa suka tarar da ita cikin yanayin ɗimuwa, ba ta magana ga kuma wani ƙosashshen jariri da ba a san inda ta samo shi ba. Hajiya Halima ta ce "Ai ni mijinta ya kira ni cikin tashin hankali, yake tambayata wai ko Yusra ta zo, ya neme ta ya rasa. Hankalina a tashe na fara shirin tafiya Kano, kin san uwargidanta fa ita ma an neme ta an rasa. "Mami" Yausra ta faɗa da ƙarfi. "Na'am Yusra, sannu" "Ku gaya wa Daddyn Haidar yaje ya ɗaukko Shukura, za su kuma sace ta" Cikin rashin fahimta ta ce "Suwaye?" "Nima ban san su ba, amma sace ta za su yi, na baro ta a can" Duk yadda suka yi da Yusra ta yi musu bayanin yadda za su gane, ta kasa sai kukan aje a ɗaukko Shukura kar a kuma sace ta. Hajiya Halima ta kira Sagir da lambar da ya kira ta, ta sanar masa ga Yusra a Abuja tare da wani jariri da ba su san a inda a ta samo shi ba. Cikin kiɗima da tashin hankali, ya ɗauki mota ba tare da ya gaya wa kowa ba, ya kama hanyar Abuja. ***** Bayan su Nana sun hallara a gaban Sultan, ta yi tozali da Giyaz a tsaye da sandarsa a bayan Hammad, sai da jikinsa duk rauni ya ƙara tsufa ya yi wani iri. Jikinsa sai hayaƙi yake yi ya zubo mata ido. Sultan ya dubi Imam Zahradeen ya ce "Zahradeen me ka yi wa ɗan uwanka ne, ya ƙi magana, sunanka kawai ya furta ya yi shiru, a nan muka kwana tare da shi, ko sau ɗaya bai yi magana ba. Imam Zahradeen ya haɗiye wani abu mai ɗaci a wuyansa, yana tunanin ta ina zai fara bayani. Nana ta ce "A je a zo da Sarkin baka gurin nan, idan ba haka ba Giyaz zai iya haddasa matsala" Duk suka kalli Nana Imam Zahradeen ya ce "Waye hakan?" "Ku zo da shi dan Allah, kar a samu matsala wani abin yake son aikatawa" Ganin Nana na neman burkicewa, ya sanya Sultan ɗaukko wayarsa ya ɗan daddana, Hammad dai bai ce komai ba. Imam Zahradeen ya ce "Kafin na ce komai, ina mai neman afuwarku a kan abin da zan faɗa, kuma ina neman afuwa da ni da waɗanda zan faɗa a cikin maganata. Na ji daɗi sosai da sosai da ka neme mu a keɓantaccen guri kamar haka, ina roƙon ku rufa mana wannan asirin dan Allah" Sultan ya ce "Zahradeen, ka tafi kai tsaye ka yi mini bayani, kana ta zagaye-zagaye daga mu sai mu a gurin nan" Ya ƙarasa maganar yana kallon wayarsa, ya danna ya ce "Ku ba shi dama, shikaɗai ya shigo" Sarkin baka ya shigo da sallama, ya risuna a gaban Sultan ya kwashi gaisuwa, ya juya ya gaida Imam Zahradeen, amma ya yi shiru yana kallon Imam Hammad da kuma Nana. Sultan ya ce "Ga mai maganin an kira shi, ya aka yi?" Sarkin baka ya ce "Uwar gijiyata, meyafaru da Giyaz ne?" "Ƙaisar ya ce mini faɗa suka yi." Ta mayar da idonta kan Sultan ta ce "Allah ya baka nasara, ya ci gaba da maganar a gaban Sarkin baka, shi ma amintacce ne, idan ya fita Giyaz zai iya aikata masa wani abin" Sultan ya ce "Waye Giyaz ɗin ne?" Sarkin baka ya ce "Aljanin da aka yi masa asiri da shi ne ranka ya daɗe" Imam Zahradeen ya fara magana ya ce "Tabbas na san ni mai laifi ne, kuma duk hukuncin da za a yanke mini zan karɓa" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mahaifiyata, Gimbiya Bilkisu, sun haɗa baki da ɗan uwanta, mai girma Tafawa, suka yi masa sihiri, aka haɗa shi da aljanin da zai bar garin da shi gaba ɗaya. Wallahi ban san sun yi ba, sai daga baya take gaya mini, saboda su na son ko ni ko Asadullah wani ya gaji kujerar Hammad. Na nuna mata rashin jin daɗina, ta ce mini aikin gama ya riga ya gama, muddin Hammad ya dawo Agadez sai ya haukace, ko ma ya rasa rayuwarsa. Shi ne na ɓoye lamba, na nemi Mahmoudu, a lokacin bai riga ya bar ƙasar ba, abin dai ya fara taɓa shi ne. Yanzun ma ba ni da yadda zan yi ne, amma ban so na tona wa mahaifiyata asiri ba" Hammad ya sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunsa, Sultan ya rikice cikin tashin hankali da damuwa ya ce "Yanzu Zahradeen amma ka ɓoye mini wannan abin baka gaya mini ba? Yanzu ƙiyayyar da mahaifiyarka take yi wa Hammad har ya kai ga ta nemi ta zauta mini ɗa ya bar gida?" Zahradeen yana kuka ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri Abie, ban san komai a kai ba, sai daga baya. Kuma gudun kar idan ya dawo ya samu matsala, shiyasa na ce kar ya dawo Niger" Nana ta ce "Gidan tarihi, a gidan tarihin Agadez aka yi masa sihirin, kuma ba sihiri ɗaya ba ne, mutane daban-daban sun yi masa. Ranar da muka je cikin gidan tarihin tare da shi, na ji ƙamshin turaren Gimbiya Bilkisu a gurin. Sannan bayan ƙamshin turaren ta, na ji ƙamshin turaren wani ma. Gaba ɗaya suka ɗaga kai, su na kallon Nana. "Duk wanda yake ƙamshin nan, da alama yana ziyartar gurin, kuma wanda yake yi musu aikin sihirin a cikin gidan tarihin yake. Idan gidan tarihin nan babu kowa a cikin sa, to wannan mai gadin ne bokan da yake aikin, ko kuma ya san bokan da yake yi. A rikice Sultan ya ce "Wane gidan tarihin wai, waye mai gadin?" Sai kuma ya rufe bakinsa, suka dubi Hammad a rikice, yadda ya runtse idanunsa yana zubar da hawaye. Nana ta rikice ta tashi ta nufe shi, Sarkin baka ya ce "Kar ki taɓa shi, Giyaz ne yake zungurarsa, zai iya yi miki wani abin ya cutar da ke" Ya tafi gaban Hammad, ya kama goshinsa ya din ga karanta Bismillah da suratul Fatiha, yana tofa masa a tsakiyar kansa. Daga bisani ya ɗaga rigarsa ya ciro jakar nan da ya bawa Nana, ya ce "Idan baka tafi ka ƙyale shi ba, zan illataka da jakar nan kamar yadda Ƙaisar ya yi maka" Nana rikicewa ta yi, duk da ba yau ta saba ganin abin mamaki ba, jakar da take hannunta, ta neme ta ta rasa, ta ganta a gurin Ƙaisar, yanzu kuma ta koma hannun mai ita Sarkin baka. Ya kalli Nana ya ce "A gurin ƙamshin turaren wa ki ke ji?" Nana ta yi shiru tana satar kallon Sultan, tana kuma kallon Zahradeen. "Kar ki ji tsoron kowa, gaya mini" Ta ƙi magana tana jinjina yadda za su ɗauki abin. Ya ce "Muje ki nuna mini gurin, ai babu abin da zai gagara da ƙarfin ikon Allah" Sultan ya tashi a rikice jikinsa yana tsuma, idanunsa sun yi jawur saboda ya kaɗu da abubuwan da suka fito daga bakin Imam Zahradeen. Wani irin mugun tausayin Hammad ya mamaye masa zuciya. Ya kalli su Nana ya ce "Yanzu can gidan tarihin za mu je kenan?" N Sarkin baka ya ce "Eh Allah ya baka yawan rai" Imam Zahradeen ya ce "Ko a yi wa su Matawalle magana, a tafi da wani daga cikin su, ko hadimai" "Bana buƙata" Sultan ya faɗa fuskarsa babu annuri, ba tare da ya kalli inda Imam Zahradeen yake ba. Ya dubi Hammad da ya buɗe idanunsa, sai dai baya magana, dan tun da ya zo wa Sultan ya ce masa Zahradeen ne, bai sake yin magana ba. Ya shafa kansa ya ce "Hammad, ka na ji na?" Ya jinjina kai. "Ko zaka bi mu ne?" Ya girgiza kai. "Ka na nan mu je mu dawo?" Ya ɗaga masa kai alamar eh. Ya girgiza kai ya ce "Ina Mahmoudu ne, ban ganku tare da shi ba, a nemo shi ya zo ya zauna da shi tukuna sai mu tafi" Imam Zahradeen ya tafi ciro wayarsa, ya hau laluben lambar Mahmoudu. Sultan da ya kalli Imam Zahradeen sai ya ji ransa ya ɓaci, ya yi mamaki ya kaɗu matuƙa da jin abin da Gimbiya Bilkisu ta yi wa Hammad. Ga abubuwan da Tafawa ya din ga yi masa, da tursasa shi a kan yi masa abubuwan da yake so, da shi da 'yarsa amma hakan bai ishe su ba, suka nemi a ɓatar masa da ɗansa. Sai da Mahmoudu ya zo, Imam Zahradeen ya ce "Imam Hammad ba ya jin daɗi ne, ka zauna tare da shi, zamu je mu dawo" Tiryan-tiryan suka bi ta ɗakin da su Nana suke zaune, suka buɗe wannan ƙofar kamar yadda Nana ta yi musu bayanin ta nan suka bi, suka gangara har gidan tarihin. Mai gadin na ganin Sultan, jikinsa ya hau tsuma ya zube a ƙasa tamkar zai yi masa sujuda yana kwasar gaisuwa. Sai dai gaba ɗaya ya rikice da ganin Sarkin baka. Ko da suka shiga cikin gurin, kawai Sarkin baka ya bushe da dariya, duk suka tsaya suna kallonsa. Ya tsaya yana ƙare wa gurin kallo, yadda aka rarake dutse aka gina wannan gurin, mutanen zamanin da suka yi wannan aikin sun cancanci yabo. Sarkin baka ya sake bushewa da dariya ya ce "Sarki a dawa Sarki a gida, Ni mai Duna ni mai Salamatu, ni mai Mairo 'yar Fulani. Ni ake yi wa inkiya biyu, Garba ga Baka ga Aska, na yi gadon gidanmu, na ƙwaci wanda ban gada ba, na fi 'yan na gada iyawa. Ni Abubakar Garba mai taƙama da ikon Allah. Na ga mutum na ga Aljan, na ga cuta na bada maganinta, idan babu na ce ba ruwan Garba. Ya buga ƙafarsa ɗaya ya ce "Uwar gijiyata, ƙamshin turaren wa ki ka ce kina ji?" Nana ta sake kallon su Sultan, Sarkin Baka ya ce "Faɗi kanki tsaye, ba wanda zai yi miki abin da Allah bai yi miki ba" Ta ɗan sunkuyar da kai ta ce "Akwai wani Imam Omar, wanda ya kawo wa Imam Hammad ayaba tare da Yayan Asal" "Ƙamshin turarensa ne?" Imam Zahradeen ya tambaye ta cikin zaƙuwa. Ta ce "Ni tsoron faɗa nake, ba na son haɗa husuma ne" Sultan ya sassauta murya ya ce "Ki na ji na? Ba haɗa husuma ba ne ba, mijinki za ki taimaka tun da ke Allah ya yarje miki gano wasu abubuwan da mu ba mu gano ba" Bakinta na rawa ta ce "Wannan mai kama shi ɗin, da ku ke yawan zama ku uku, mai saka shuɗin rawani, bayan ƙamshin turaren Gimbiya Bilkisu, ranar da muka zo nan, ƙamshin turarensa ne yake tashi, alamar bai daɗe da tafiya ba" A rikice Imam Zahradeen ya ce "Sardaunan Agadez, ƙamshin turarensa ne" Buɗe baki Sultan ya yi, ya fara numfarfashi yana kallon Nana, ya ce "Me hakan yake nufi? Ina fatan ba dai wani abin ya yi ba?" Nana ta girgiza kai cikin tsoro ta ce "Ba ni da tabbas, tun da kowa yana da damae zuwa gurin nan, mussaman a cikin manyan Agadez kamar yadda Imam Hammad ya gaya mini. Amma me zai kawo shi nan cikin dare wajen ƙarfe sha biyu na dare. Kuma a mudubin Ƙaisar na ga wani abu da ya sanya ban ji na yarda da ɗakin can ba, amma ba ni da tabbas tun da maganar aljani ba abar yadda ba ce ba wasu lokutan" Sarkin baka kawai ya nufi ƙofar ɗakin, da Nana ta yi ta nacin a buɗe ta, yana zuwa ya jijjiga ƙofar, amma ya ga ƙaton mukulli a jiki. A nutse ya ƙare wa sauran ƙofofin kallo, ya saki mukullin ya nufi hanyar fita, yana zuwa ya janyo mai gadin nan har zuwa inda su Sultan suke. Ya kalle shi ido cikin ido Sarkin baka ya ce "Waye kai?" "Mai gadin gidan tarihin Agadez" Ya ba shi amsa. Sarkin baka ya ce "Kai, mugu shi ya san makwantar mugu. Kai da gani idanun nan nawa ka san babu abin da ban gani ba. Waye da waye suke zuwa gurin nan?" Mai gadin ya yi wa Sarkin baka wani irin kallo, ya ce "Kowa ma yana iya zuwa" "Ba kowan ba, muhimman mutanen da ka ke yi wa aiki" "Ni ba ni da wani aiki bayan buɗewa da rufewa, da kula da ababen tarihi" "Ka tabattar?" Ya ce "Eh" Sarkin baka ya numfasa ya fito da jakar nan tasa, ya nuna wa mai gadin nan,ya ce "Idan hatsabibancinka ya kai ya kawo, na san ka san wannan jakar, ko kuma ka ji labarinta, mussaman da Jaddul Jinn ya yi rayuwa a cikin Masarautar nan. Wannan jaka ce da uwar gijiyar Ƙaisar ta farko, Lanti ta haɗa, da gudunmawar uban duƙusa, ta hanyar yin amfani da wani sashi na gashin Jaddul Jinn. Da abubuwa daban-daban da baƙaƙen aljanu ba sa so. Ana iya yi wa aljani tarko da ita, ko ma halaka su baki ɗaya. Yanzu za ka yi mana bayani ne, ko kuma na gwada maka aikin jakar nan, na hallaka baƙin aljanin kanka, na haɗa ka faɗa da Giyaz, sannan na kashe ka?" Ya din ga kallon Sarkin baka, yaƙi magana. Nana ta ji sanyi ya fara ratsata. Mai gadin ya ɗan ja da baya yana kallonta. Ta waiwaya ta ga me yake kallo, kawai ta ga Ƙaisar a gurin. Jikinsa na rawa ya nufi ƙofar ɗakin, ya ciro wani mukulli ya buɗe, yana buɗewa wani irin wari ya daki hancinsu suka ja da baya. Jikin Nana ya hau tsuma, Shi kansa Sultan ja ya yi da baya cikin tsoro, yana kallon gurin. Sarkin baka ya tankaɗa ƙeyar mai gadin nan, suka shiga ɗakin. Ɗakin duhu kafin daga bisani kawai su ga haske ya gauraye ɗakin. Sarkin baka ya waiwaya ya cewa su Imam Zahradeen su shiga. Suka bi wata doguwar hanya, su na shiga suka wari yana ƙara cika musu hanci. Ɗakin tsohuwar kurkuku ce, da daga baya a ka mayar da ita gurin aikin zinaren da ake haƙowa. Wannan kurkukun da aka din ga azabtar da mutane a zamanin sarakunan baya. Gurin gwanin ban tsoro babu kyawun gani ko kaɗan. Nana ta kurma ihu ta ja ta tsaya jikinta yana tsuma, saboda razana da kuma firgicin abin da ta gani. Ƙwarangwal ne na cikakken mutum, an soke shi a jikin mashi, an kuma soke wani abu mai kama da takarda a jikin ƙwarangwal ɗin, da hotonsa a jiki yana ci da wuta, sai kuma sunan Imam Hammad Jalaludeen, a jikin abin mai kama da takarda an soke allurai a jiki. Sak abin da ta gani a cikin mudubin Ƙaisar. Jikinta ya din ga wata irin karkarwa, saboda razani da tsoro. Shi kansa Sultan daskarewa ya yi yana rarraba ido, saboda razani da tsoro. Sarkin baka ya ƙarasa gaban ramin, ramin ba mai zurfi ba ne ba, sai dai wasu irin manya-manyan itace ne a cikin ramin nan. Ya kalli jikin ƙwarangwal ɗin nan, ya yi baƙiƙirin saboda azabar wuta. "Ya ka yi wannan sihirin?" Sarkin baka ya yi maganar yana tsare shi da ido. Ya yi shiru. "Wallahi idan baka faɗa ba, sai na jefa ka a ramin nan na kunna wutar" Ya tsaya ya kalli ramin, ya rufe idanunsa ya faɗi wasu abubuwa, ya kalli ramin a take wata irin wuta ta tashi a cikin ramin. Wata irin ƙara ta din ga tashi a cikin ɗakin. Nana ta toshe kunnenta, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta toshe kunnenta, ta fashe da wani irin kuka na tashin hankali da gigicewa. Sarkin baka ya ce "waye ya saka ka wannan aikin, kuma yaya aka yi kana mai gadi ka ke bokanci?" Ya numfasa ya ce "Na koyi bokanci ne, domin na rama abubuwan da aka yi wa zuriyarmu. Na bautar da mu tun zamanin kakanni. Nana ta fara neman ta burkice musu gaba ɗaya, saboda sama-sama da numfashinta ya din ga yi. A rikice Sultan, ya ce Zahradeen ya fitar da Nana, kar wani abin ya same ta. Su na fita ta nemi guri ta zauna ta sauke numfashi cikin matsanancin tsoro da razani. ***** Mama ce a gaban Likita kamar ta yi kuka, ta yi ƙasa da murya sai magiya take yi masa. Ya kalle ta ya ce "Hajiya muddin ba ki gaya mini gaskiyar abin da ya faru ba, babu wani abu da zan iya yi a kan 'yarki" Cikin damuwa ta ce "Likita ka san ɗan yau ne, ka haife shi amma ba ka haifi halinsa ba, abin kunya ta kwaso mini, na yi na yi da ita a zubar ta ƙi, shi ne aka gaya mini wata ƙwaya na je na karɓo aka ce na saka mata guda goma a cikin kunu zai fita." Ya yi zuru da ido yana kallonta, ya ce "Amma baiwar Allah ba ki da imani, kin san abin da ki ka aikata kuwa?" "Dan Allah likita ka yi haƙuri,  ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka" Sai da ya yi mata faɗa kamar zai yi mata duka, sannan ya rubuta abin da za a yi wa Jamila. Hajiya Sa'a kuwa, ta daina magana gaba ɗaya, komai sai an yi mata. Ƙarshe Asibiti aka sallame ta, ta koma gida, gidan kuma babu mai jinyarta, abin duk ya damu Alhaji Fatuhu amma babu yadda ya iya. ***** Nana har wani irin jiri take yi, jikinta yana tsuma saboda tsoro da razanin da ta shiga. Sultan ya ƙi kallon inda Zahradeen yake, zai ɗauki Muhsin ya tafi da shi, amma ya yi masa tsawa ya ce kar ya taɓa shi. Gimbiya Bilkisu sam ba ta san me yake faruwa ba, da daddare ta shiryo ta zo sashen Sultan. Yana zaune a gefen gado ya yi shiru, ji yake yi tamkar kansa zai tarwatse. Muhsin yana kan makeken gadon Sultan yana bacci, gani yake yi idan ya kawar da ido daga kan yaron, shi ma cutar da shi za a yi, wani irin matsanancin tausayin Hammd ya hana shi sukuni. Da ya rufe idanunsa ya tuna abin da ya gani, sai tsigar jikinsa ta tashi. "Ranka ya daɗe, ko nan zan kawo maka abincin daren naka ne, barori sun shirya maka abinci tun ɗazu fa" Bai yi magana ba, ta mayar da idonta kan Muhsin ta ce "Wannan kuma a ina ka samo shi?" Ta yi maganar tana nufar gadon. Cikin tsawa ya ce "Kar ki kuskura ki taɓa shi" Ta razana ta ce "Sultan lafiya?" "Fita ki bani guri" Cikin rashin fahimta ta ce "Me yake faruwa ne?" "Na ce ki fita ki bani guri, ba na ko ƙaunar ganinki, ki fita kafin na ɗauki mummunan mataki a kanki" Babu shiri ta juya ta fice, ganin yadda jikinsa har rawa yake yi, saboda tsananin ɓacin rai. Ta din ga mamakin mene ne ya tayar masa da hankali ne har haka, yake wannan fushin?. ***** Nana kuwa tun da suka baro gidan tarihin, Sultan ya ce ta zauna a ɗakin nan da suke, ta samu nutsuwa. Da kyar ta samu ta iya yin salla. Tana zaune ta yi shiru, ta ga an buɗe ƙofar ɗakin, Hammad ta gani ya shigo, ba ta yi zaton ganinsa ba ko kaɗan. Ta miƙe tsaye ya ƙaraso fuskarsa ya zauna a kusa da ita, ya jingina da jikin gado. Sai kuma ya ɗago ya kwantar da kansa a jikinta. Nana ta ƙara janyo shi jikinta, ta ƙanƙame shi tana fashewa da kuka, wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta. "Ya aka yi ne rayuwata, kukan me ki ke yi" Ya furta a hankali yana ƙara shigewa jikinta. "Sonka kawai nake yi" Ta yi maganar tana kuma ƙanƙame shi. "Wannan kukan, ya fi kama da na wanda ake tausayawa, meyafaru ki gaya mini" "Ba komai Sayyid" "To idan dai kina so na sosai, ɗan bani sanyin mana" Yayi maganar yana ɗan shafa jikinta yana murmushi. Jin da gaske kukan take yi, ya sanya ya ɗago, shi ma idanunsa jawur, jikinsa babu ƙwari ya ce "Ki gaya mini, ko wani abin su Sultan suka ce miki?" "A'a" "Mene ne?" "Dan Allah Sayyid duk abin da za a ce maka Asal ta yi, ka yi haƙuri ka yafe mata" Ya yi murmushi mai ciwo, ya ce "Me Asal ɗin ta yi?" "Na san sai Sultan ya gaya maka, amma dan Allah ka yafe mata" Hammad ya ce "Ki na tunanin ban san komai ba ne? Lokaci ya yi da yakamata na huta" Nana ta ce "Wataƙila akwai abin da baka sani ba, dan Allah ko ka sani ka yi haƙuri ka yafe mata" Ya yi shiru ya sake kwanciya a jikin Nana, ta ƙara ƙanƙame shi, cikin matsanancin tausayawa. ***** Sultan na kashingiɗe, yana sauraren Tafawa, da sauran 'yan majalissa, sun kafe kai da fata a kan lallai a san matakin da za a ɗauka a kan Hammad, saboda yadda ya karya musu Al'adar masarauta. Sultan ya ɗago ya numfasa cikin ƙasaita, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Amm kamar yadda kowa ya sani, Agadez ta gaji Al'adu da ƙa'idoji daban-daban, wanda wasu an samar da su ne, tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci, ina ga lokaci ya yi da yakamata mu kama addininmu, mu yi watsi da duk al'adun da muke ganin su na kawo mana koma baya. Saboda haka a matsayina na Sultan mai ci na wannan lokaci, na soke wannan Al'ada a ƙasar Agadez. Baƙaƙen buzaye za su samu 'yanci, farin buzu ko buzuwa na da cikakken 'yancin auren duk wata ƙabila ko kalar fatar da yake son aure. Matar da Imam Hammad ya aura, bincikenmu ya tabattar da halattaccen aure suka yi, kuma mun karɓe ta. Hakazalika za mu bayyanawa duniya ɗan da ya haifa tare da matarsa ta Nigeria. 97 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Gaba ɗaya 'yan majalisar suka waiwayo suna kallon Sultan. Tafawa ya ce "Jalaludeen wannan wace irin maganar banza ce, dan me zamu bar gadon al'adun da muka gada daga iyaye da kakanninmu saboda son zuciyarka da ƙoƙarin bawa ɗanka kariya? Babu wanda zai lalata mana dokokinmu da al'adunmu. Dole a hukunta Hammad dai-dai da abin da ya aikata" "Mutanen farko ma, gadon iyaye da kakanni ne ya halakar da su. Daga lokacin da muka gaji al'adun, zuwa yanzu me al'adar ta haifar mana bayan tarin ɓarna kashi-kashi? Kuma ina bayar da wannan umarni ne a matsayina na Sultan, shugaba a Agadez ba magana nake yi ba a matsayin ɗan uwanku ko abokinku ba, duk wanda ya ɗaga murya ko kawo abin da ba shikenan ba, zan hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata" Matawalle ya ce "Amma Allah ya baka yawan rai, yanke wannan hukuncin haka kai tsaye, baka tunanin zai sanya wa talakawanka wasi-wasi da kawo tashin tashina a tsakanin masarauta da kuma jama'ar gari" Sultan ya numfasa ya ce "Lokuta da dama, gyara baya buƙatar lallai sai ka yi wa wani daidai, ko kuma sai kowa ya soka, ya yarda da kai mai gaskiya ne ko me kirki ne. Haka zalika zan sauke wasu daga cikin Imam Imam na ƙasar nan, zan yi wa dokokin Agadez garambawul da gudunmuwar dokokin ƙasar Niger, domin kowane ɗan Agadez ya samu cikakken 'yanci kamar sauran ɗan ƙasa ba tare da al'ada ta tauye wasu daga cikin 'yancin da suke da shi ba a ƙasar nan. Sai dai na san da yawa ba zai yi muku daɗi ba, za a ga kamar na yi rashin adalci saboda Hammad ɗana ne, amma kafin ku ce haka, bari mu yi komai a buɗe tare da ku". Ya kalli wani dogarinsa, ya ce "Ina da baƙo a mararrabar fada da hanyar cikin gida, ka ce ya iso" Duk suka yi tsuru-tsuru su na jira. Ba a jima ba, dogarin ya dawo tare da Sarkin baka sai kuma wannan mai gadi a ɗaɗɗaure da igiya tamau kamar ɓarawo. Wanda ba su san me ake ciki ba, suka yi ƙuri su na jiran jin ba'asi, wanda abin ya shafa kuma cikinsu ya ɗuri ruwa. Sarkin baka ya risuna ya yi gaisuwa a fada, cikin shigarsa ta hargi ya shigo hakan ya ƙara sanyawa duk aka zuba masa ido. Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Yi musu bayani" Sarkin baka ya kalle shi ya ce "Duk da na san, sun sanka amma ka yi musu bayanin waye kai" Ya sunkuyar da kai ya ce "Mai gadin gidan tarihin Agadez" Sarkin baka ya ce "Kuma me?" "Boka da nake yi wa wasu daga cikin manyan Agadez aiki" "Mene ne dalilinka na yin hakan?" Ya numfasa ya saci kallon Sultan ya ce "Na haka ne, saboda huce takaicin yadda ake bautar da mu tun daga kan kakana, wannan dalilin ya sanya lokacin boka Riyan, na koyi harkar bokanci a gurinsa" Sultan ya ce "Ina fatan kun ga ɗaya daga cikin illolin wannan al'adun da muke yi, marasa tsuhe balle makama? Mu na jinka ci gaba" Sarkin baka ya ce "Ba ka ji ka ci gaba mana" "An bani wasu ayyuka, duk da ba kowa ya san ina bokanci ba, sai dai akwai wani babba a masarautar nan da shi ya ƙarfafe ni na koyi harkar bokanci. Ni aka saka na yi wa Imam Hammad Asiri, da aljanin da ya sanya ya bar ƙasar nan, ya manta komai da ya shafe shi, ciki hadda tuna waye shi. Sannan aka bani aikin yi masa asiri da wani tsohon aljani a cikin gidan tarihin, da yake sanya masa wannan zafin jikin da yake gigita shi". Sarkin baka ya sake cewa "Yaya ka ke yi?" "Da fari na haƙa rami a cikin tsohuwar kurkuku, ana kawo mini itace cikin dare, ina tona tsofaffin kabarurruka na cikin gidan, na ɗauki ƙwarangwal ɗin, na saka shi a cikin wuta, da hatimai daban-daban da sunan Imam Hammad, duk lokacin da na babbaka wannan wutar yadda ƙwarangwal ɗin nan yake ƙonewa haka yake jin zafin a jikinsa. Idan ƙwarangwal ɗin ya murmushe saboda zafin wuta, sai na kuma tono wani. Daga baya kuma aka koma kawo mini sababbin gawarwaki na koma yin aikin da su, idan na saka musu wutar nan, haka yake jin wannan zafin a jikinsa" Gurin ya yi tsit, aka rasa wanda zai yi magana. Jikin Matawalle yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma suwaye haka?" Sultan ya ce "Ba sai an faɗe su ba, amma sun san kansu, kuma duk wanda yake da ja a kan maganar, yana iya zuwa gidan tarihin da kansa ya tabattar. Dan haka a yau na kawo ƙarshen zaman yau, dan haka zan zo da sauran bayani da abubuwan da zamu caccanza". Nan aka ci gaba da salallami, aka rasa mai sake cewa komai. Nana tana kwance tare da Hammad, kamar zai shige cikinta, sai shafa gashin sa take yi sannu a hankali. Ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru. Yadda bokan nan ya din ga yi musu bayanin, Imam Omar da mahaifinsa Sardauna, suke zuwa da yadda suka yi masa asirin nan na zafin jiki. Kuma da sanin Tafawa, kowa fafutukarsa ɗansa ya samu mulki. Haka zalika Asal ta yi soyayya da Omar, ita take ajiye wa Hammad takardun nan. Ko da auren Hammad sun yi soyayya tare, kafin daga bisani da ta ga babu amfani soyayyar tasu, ta fara son Hammad ta daina biye masa. Sai dai ya ci gaba da yi mata barazanar sai ya tona mata asiri, irin hirarrakin da suke yi. Sai dai babu wani abu na saɓon Allah da ya taɓa shiga tsakaninsu, sai dai duk wasu zantuttuka na banza har da wanda bai kamata ba, suna yi. Babu abin da bai sani ba a game da aurenta, da abubuwan da yake faruwa tsakaninta da Hammad ba. Hatta sirrin shimfiɗar aurensu, babu abin da Omar bai sani ba. Shi ya din ga ziga ta, tun daga lokacin da aka ce za a yi aurenta da Hammad, shi ya din ga ziga ta har bayan auren. Ya ci gaba da zuwa gurin bokan nan, yana karɓar wannan takardar, yana bawa Asal, wanda da ya yi tozali da takardar yake sake ruɗewa, jikinsa ya rikice ya yi ta jin ihun da alajanin nan yake yi a jikin ƙwarangwal ɗin nan, duk ya fita hayyacinsa. Babu yadda Omar bai yi da Bokan nan, ya yi masa abin da Asal za ta yarda shi, amma ya ce ba zai yi wannan cin amanar ba saboda Hammad yana yi masa alheri ta wasu ɓangarorin. Gaba ɗaya bokan ya gaya musu labarin, da abin da yake tsakanin Omar da Asal a baya. Babban abin da ya ɗaga wa Nana hankali, bai wuce yadda bokan ya ce, ko za su kashe shi, zai iya lalata sihirin da ya yi da aljanin jikin ƙwarangwal ɗin da yake amfani da shi, amma ba zai iya raba Hammad da Giyaz ba, saboda Giyaz baya saɓa alƙawari, kuma ga Nana tana tare da Hammad, yana ganin ɗansa a jikinta, idan ba kashe Giyaz za a yi har lahira ba, ba zai rabu da shi ba. Da ta zo nan a tunaninta, ta lumshe idanunta hawaye na zirarowa a hankali. Hammad ya yinƙura ya tashi zaune, ta maze ta goge hawayenta. Ya ƙare mata kallo ya yi wani irin tattausan murmushi, ya shafa gashin kansa ya ce "Ba ƙaramin kyau ki ka yi mini ba ma vie, ina kewa, ɗan yi mini waƙar mana abar ƙauna" Yayi maganar yana sumbatar hannunta, tare da matsawa kusa da ita. Ta ɗan matsa kaɗan ta ce "Ana ta kai ka na ta kaya" "To ni kayan ne suka fi damuna, fiye da kayan ai. Ki kwantar da hankalinki babu abin da zan yi miki, kuma ina roƙon Allah kar ya kama ki da laifin guduna da ki ke yi, saboda kin fi ni gaskiya ta kowace fuska. Amma har abada ni mai ƙaunar ki ne, kuma ba zan taɓa yarda a raba ni da rayuwata ba in sha Allah" Ya yi maganar yana sake rungume ta, wani abu mai sanya nutsuwa na fizagarsa game da ita. "Ka daina yi mini wannan kallon mana" Ta yi maganar tana hararasa cikin wasa. "Idan ban kalle ki ba wa zam kalla, kina nan a yadda ki ke ma vie, kamar baki haifi Muhsin ba" Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Da na canza daina sona za ka yi kenan?" Yayi murmushi ya ce "Haryanzu ba ki san waye Hammad ba, ke ɗin nake so ne Asmy, babu abin da zai canza a tattare da ke, na ji na daina sonki ko kaɗan. Ina son Husna" "Sake faɗa" Ta yi maganar tana tsare shi da ido. "Sai kin yi mini waƙa tukuna" Ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce "Sai ka biya ni tukuna." Ya ɗan yi shiru ya ce "Ina tuna mutane daban-daban da muka rayu da su a Nigeria, ko ina yayarki ɗin nan, da ta yi ta ɗawainiya da mu? Da 'yan gidanku, da mutumin nan da na tsana, wanda na yi wa gadi da farko. Sai kuma mutanen gidan da muka zauna, da muka yi aure" Nana ta ce "Gidansu budurwarka ko?" Ya ce "Eh nan" "To tashi daga jikina" Hammad ya ce "Ba zan tashi ba, ai ni ban ce budurwata ba, ke ki ka fara." Ta yi murmushi ta ce "Babu abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah, ni dai ina ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke a kanmu" Ya ce "Alkhairi in sha Allah, ni nama manta, yana nemanmu anjima, ban san me zai ce mana ba. Amma ina tsammanin alkhairi daga bakinsa" "Allah yasa ina fatan hakan nima, amma dan Allah ka sanya baki, na ga ya yi fushi sosai da sosai da ɗan uwanka, ko zaka saka baki?" "Ba ruwana" Ya bata amsa kai tsaye. Nana ta ce "Kar ka ce haka" Ya miƙe tsaye gaba ɗaya, sannan ya ce mata "Zan je na dawo, ki yi mana addu'a Allah ya sanya hukuncin da Sultan zai yanke, ya yi mana daɗi" Ya ƙarasa maganar yana sumbatar goshinta. Kamar zata tashi sama, haka Gimbiya Bilkisu ta faɗo turakar Sultan hankalinta a tashe, ko haɗiyar yawu ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi. A nutse ya juyo ya kalle ta, bayan ya gama warware rawanin kansa. Sai kuma ta tsaya ta kasa magana. Can kuma ta ce "Sultan, wai da gaske zaka sauke wasu daga cikin Imam? Meyasa? Kuma ina fatan babu Zahradeen a ciki?" "Idan da shi me za ki yi?" "Amma dai ka san bai kamata abin da ka yi, kuma a kan me zaka sauke Zahradeen yana ɗan cikinka? A wancan karon ka naɗa ƙaninsa a matsayin shugabansa, sannan ka zo ka sauke shi ai muzantawar tayi yawa. Zai ma zama abin surutu a Agadez" Cikin nutsuwarsa ya kalle ta ya ce "To shi ne me? Ai gara abin kunyar sauke shi daga Sultan, a kan tona muku asiri da ke da shi da ɗan uwanki Tafawa" Ya ƙarasa maganar cikin hasala. Sak ta yi tana ƙwalalo ido waje tana kallonsa. "Kar ki kalle ni kamar ba ki san abin da ki ka aikata ba, Bilkisu kin cutar da ni, kuma kin cutar da kanki. Kin yi yinƙurin kashe mini mata sau biyu, saboda gudun tonuwar asirinku, yayanki ya yi uwa ya yi makarɓiya ya sanya muka rufe Mamman, waya sani ko a ƙarshe ma ke dai ki ka yi sanadin rayuwar tata? Sannan tilon ɗan da ta bari a duniya ki ka sako a gaba da jaraba, ke kina yi yayanki yana yi, gaba ɗaya Hammad bai ji daɗin rayuwarsa ba, saboda azaba da masifar sihiri da makircinki. Kuma idan ki ka kuskura ki ka buɗe baki ki ka musa mini, sai na tona miki asiri sannan ki bar mini gida. Allah ne ya tona muku asiri a silar matarsa ta Nigeria da ya aura, kuma bokan naku yana hannunmu, ya tabattar da abin da ya aikata. Abu ɗaya zan duba na rabu da ke, 'ya'yan da na haifa tare da ke. Amma daga yau na haramtawa kaina ke har abada a matsayin matata, za ki yi zaman 'ya'yanki ne kawai. Kuma kar Zahradeen ya ƙara ayyana ni a matsayin mahaifinsa, kuma kar ya sake zuwa inda nake. Da ke da duk wanda ku ka aikata hakan, na bar ku da Allah. Faɗar abin da ku ka aikata tamkar tona wa zuriyarmu asiri ne" A rikice ta ce "Dan Allah Jalaludeen ka tsaya ka ji... "Ba zan ji komai ba, fice ki bani guri kafin na canza shawara" Yayi maganar yana yi mata wata irin gigitacciyar tsawa, babu shiri ta fice tana haɗa hanya. Tafawa ne ya shigo falon hankali a tashe, ya tarar da Asal tare da Asadullah. A fusace ya ce "Gidan uban wa ku ka tafi tun safe?" Da mamaki Asad ya ce "Kai ka kira ni a waya ai, ka ce na zo na kai Asal Asibiti, tun lokacin muna Asibiti, ba ta da lafiya sosai. Ya sharce gumin goshinsa ya ce "To, dara ta ci gida yau, Asirinmu ya tonu a fada" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suka kalle shi. "Eh, yau da bokan da yake yi mana aiki, na gidan tarihi aka zo fada, ya tona komai sunayenmu ne kawai bai kama ba. Kuma na san ya gaya wa Sultan komai, kuma duk a dalilin haukanki da dabbancinki Asal, haka kurum ki ka je ki ka jajubo masifa ki ka kawo ta har cikin gidan sarauta. Binciken da na yi, wannan yarinyar da ki ka kawo a matsayin kuku, ita ce ɗin dai ta yi sanadin tona asirinmu. Dan haka sai ku shirya baki ɗayanku, dan ban san wane irin hukunci za a ɗauka a kanmu ba. Asal ta ɗora hannu a ka ta ce "Wayyo Allah na shiga uku, Abbu sai da na ce muku mu daina wannan abin, amma kai ka saka ni, Imam Asad ya saka ni, Imam Omar ma ya saka ni da Sardauna, ku ka saka ni a tsakiya wallahi ina son Hammad, idan na rabu da shi ba zan taɓa samun miji kamarsa ba, wallahi ina sonsa" A fusace Asadullah ya ce "Ke rufe wa mutane baki, ke ta wani shashasha ma ki ke yi?" "Kai ne shashasha, dan duk saboda gobenka aka lalata tawa, an cuce ni, komai zan yi yanzu Hammad ba zai taɓa yafe mini ba, balle ya saurare ni" Tafawa ya dubi Asal ya ce "Asal kina da hankali kuwa? Kin san abin da ki ke faɗa kuwa?" "Abbu na san abin da nake faɗa, shikenan bani da makoma, matarsa ta shiga kundin tarihin baƙar mace ta farko da ta auri Imam a Agadez, ni kuma zan shiga kundin tarihin matar da ta sanya hannun gurin tarwatsa rayuwar mijinta"  Miƙewa tayi Tafawa yana kiranta, amma ko waiwayowa ba ta yi ba, ta fice daga ɗakin. **** Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falonsa, ga mamaki ya ga Fadila tare da uwargidansa Hajiya Suwaiba, suna zaune abin da bai taɓa gani ba. Suna ganin shi suka zuba masa ido, Hajiya Suwaiba ta ce "Ka ce sai gobe in Allah ya kaimi zaka dawo?" Ya ce "Eh, fasawa na yi na taho yau" Fadila ta ce "Amma Daddy lafiya dai ko, Rauda kawo masa ruwan sanyi" Suwaiba ta ce "Wai dan Allah Baban Rauda Meyafaru a Lagos ɗin ne?" Ya ce "Sai kun gaya mini, me ku ke tattaunawa ne, ganinku tare ya sanya ni farinciki" Hajiya Suwaiba ta ce "Abokin nan naka ne ya zo gidan nan, wanda ya sai gidan nan, shi ne muke tattaunawa mu tattara ɗan abin da ya yi saura, a nemo gida mu tashi, tun da mun ga alamar mutumin nan zai iya ci mana mutunci daga mu har kai." Ya yi murmushi tare da jinjina kai. Cikin damuwa Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka gaya mana, meyafaru muna fatan dai ba wani abin ne ya kuma kunno kai ba" Ya saki murmushi ya ce "Da baku ganni a haka ba, Alhamdillah an canza sabon controller na hukumar Coustom na ƙasa. An sakar mini kwantena Arba'i  da bakwai a cikin kwantenonina, da na mutane da na haɗa na yo order kaya" A rikice suka buɗe ido, suna jin abin kamar a mafarki. Hajiya Suwaiba baki na rawa ta ce "Daddy, kenan suna sane suka kama ka kayan naka, ba wani laifin ka yi ba, yanzu kana nufin an saki kayan?" Ya jinjina kai ya ce "An saki wasu daga cikin kayan, Allah ya karɓi addu'a" Gaba ɗaya suka rungume shi tare da yaransa, yana kuka su na kuka, babu abin da bakunansu ke furtawa sai tsantsar yabo da godiya ga Ubangiji Subhanahu wata'ala mai zaɓar wa kowane bawa abin da ya dace da rayuwarsa. Baban su Nana ji yayi tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu, bayan da likita ya sanar masa abin da yake damun Jamila. Duk da Mama ta roƙe si a kan su rufa musu asiri, amma ganin yadda Baban yake ta sintiri hankalinsa a tashe, an rasa takamaiman dalilin da ya sanya ake ta ƙara wa Jamila jini. Ya sanya ya yi wa Baba bayanin, cikin jikinta da ya zube ne, bai fita gaba ɗaya ba, ga jini ta zubar mai yawan gaske. A tsorace Baba ya kalli Mama ya ce "Rabi, wane cikin? A ina Jamila ta samu ciki?" Ta tsuru-tsuru tana jin kamar ta kama Likitan ta yi ta gwara kansa a gurin. "Rabi, dama abin da yake faruwa kenan ki ka ɓoye mini? Jamila da ciki? Kin cuce ni ba ki yi mini adalci ba, kuma ki ka ɓoye mini baki gaya mini ba ki ka nemi kashe ta da ƙwayoyi. Shikenan kanki ki ka yi wa, na fara zargin alhakin Nana ne duk yake bibiyarmu. Nana duk matsi da wahalar da ta sha a rayuwarta bata ɗaukko mini magana ba, ki ka yi mata sharri ki ka saka na amince na aura mata mutumin da ban san waye shi ba, an wayi gari shekara uku, babu ita babu ɗan uwanta, ke kuma naki 'ya'yan babu na mora daga mahaukaciya mai fama da aljanu sai lalattaciya. Abubuwan da ki ke yi wa Nana sharri da kuma yi mata gori a kai, duk sun kama ki a kan yarnki. Amma kanki ki ka yi wa Allah ya yi muku magani" Har ya gama maganar ya fita, ba ta sake iya cewa Uffan ba sai gursheƙen kuka da take yi. Jamila ma da ke kwance sai kukan da take faman yi. ***** Kasancewar Alhaji Fatuhu yana ɗakin Fadila ne, ta din ga gargaɗinsa a kan ya ja bakinsa ya yi shiru, kar yayi saurin gaya wa jama'a cewar an sakar masa kayansa. Ya ce "Haba masoyiyya, duk yawan jama'ar da suka taru suka jajanta mana, tsawon wannan lokacin, kusan shekara huɗu, kuma sai waraka ta zo mu yi shiru?" Fadila ta ce "Sa gani a hankali, baki yana yi wa abu illa, ka san waɗanda zaka janyo jikinka tukuna, ka lallaɓa ka ga abin da Allah zai yi sannu a hankali ka fara settling komai, amma dan Allah kar ka yi saurin gaya wa jama'a" Ya ce "To shikenan na ji, zan ɗan fita yanzu amma, sannan goben in Allah ya kaimu, gaskiya ki shirya mu je, zamu duba Yaya Sa'a, zan kuma mayar da ita Asibiti in sha Allah" Ta so musa masa zuwan, amma ta ga bai kamata ba, kawai ta haƙura ta shanyeta amsa masa da to. A gida Alhaji Fatuhu ya tarar da Alhaji Zailani, ya tarar da shi ya yi wata irin muguwar rama, bai matuƙar ban tsoro. Ya ce "Alhaji Zailani, lafiya kuwa me yake damunka haka? Ko duk tashin hankalin ɓatan Shukura ne?" Alhaji Zailani ya yi murmushi ya ce "Ba dole hankalina ya tashi ba, 'ya ta ɓace babu ita babu labarinta ba, gefe guda ga ciwon suga ya sako ni a gaba, yanzu an hana ni cin komai sai ganye, kusan ko ruwa na sha sai ya yi sama. Na rasa ma abin da yake yi mini daɗi" Cikin damuwa Alhaji Fatuhu ya ce "Haba kai kuwa, duk lokacin da muka yi waya ce mini ka ke yi kana nan lafiya, ayyuka sun yi maka yawa shiyasa na ce ni bari na zo da kaina, ko zan samu kana gida. Ni nawa jikin Alhamdillah ya yi kyau kai kuma babu lafiya haka. Ka kwantar da hankalinka in sha Allah zaka samu lafiya. Kuma za a ga Shukura da yardar Allah. Amma kai ma ka jarraba na gargajiya ko za a dace, ni na ga alfanun ire-iren magungunan nan wallahi" Alhaji Zailani ya ce "To shikenan, zan gwada da yardar Allah" A baɗini kuwa, Aljanin da yake bawa jini ne, ya fara burkita shi yake shan nasa jinin, saboda rashin bashi abin da ya nema a wannan shekarar. Ga shi ya yi ta mummunan mafarki da Shukura tana caka masa wuƙa tana kuka. Ga shi ya yi ta mafarkin ƙwarangwal ɗin jariri yana sha masa jini, ko yana fizgo kayan cikinsa yana ci. Idan ya tashi sai ya ji jikinsa kamar babu laka, ko hannunsa da kyar yake iya ɗagawa. Da yaje Asibiti aka ce ciwon sugar ne, yanzu ya hau in anjima ya yi ƙasa ko a ganshi normal. Ga shi ya fara surutai idan yana baccinn har Hajiya Amina ta fara tuhumar sa, da yi masa tambayoyi. **** Hammad na gaba, Nana na biye da shi, suka shiga turakar Sultan, karon farko Nana ta gan shi cikin riga da wando na shadda, babu rawani babu takunkumin yana shan shayi, Muhsin na kusa da shi, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya da nasa kofin shi ma yana sha. Ba zaka taɓa cewa Sultan ya haifi su Hammad ba, kamar yayansu ba mahaifinsu ba. Muhsin yana kallon su Nana ya hau murmushi, amma bai tashi daga kusa da Sultan ba. Sultan ya kalli Muhsin ya ce "Suwaye waɗancan? Ka san su?" Kawai ya ci gaba da murmushi yana shan shayinsa. Ita Nana a zatonta, Imam Zahradeen ne ya kuma tafiya da shi gidansa. Ta duƙa ta gaida Sultan, ya saki jiki sosai ya amsa mata, Hammad ma ya gaishe shi, shi ma ya amsa masa yana bin su da kallo, wata nustuwa da farin ciki na ratsa shi. Ya din da gode wa Allah, da bak biye wa su Sardauna ya kori Nana ba. "Ina fatan duk kuna cikin ƙoshin lafiya?" Hammad ya ce "Alhamdillah" "Ma sha Allah, Nana Asma'u" Nana ta ɗago da mamaki jin ya kira sunanta cikke. Ta ce "Na'am Abie" "Da farko ina mai baki haƙuri bisa ga abubuwa da suka faru, kar ki yi zaton ko dan muna sanya ran Hammd ya samu lafiya saboda ke ne, ya sanya na saukko. Ko kaɗan dama mun yi magana sosai da sosai da Mahmoudu ina ta tunanin yadda zan ɓullowa lamarin, ba tare da 'yan majalissata sun ga na nuna son kai ba, sai dai cikin ikon Allah a dalilinki, na fuskanci ingiza mai kantu ruwa suke yi mini. Kuma na koyo darussa daban-daban a dalilin faruwar wannan al'amura tabbas; idan bamu karɓi abin da ya faru a matsayin aya ba, to gaba Allah na iya jarabtarmu ta wani abin da ba zamu iya sa shi ba, a kan muguwar Al'adar da babu abin da ta haifar sai kawo mana koma baya. Yanzu dai ina baki haƙuri da abin da ya faru, wanda aka yi miki da gayya da wanda muka yi miki cikin kuskure. A duniya ko a gurina da na haifi Hammad bai samu nutsuwa da kwanciyar hankalin da ya samu a gurinki ba. Ga mu da kuɗi da wadata, amma Hammad bai tashi cikin kwanciyar hankali ba. Ko dan albarkacin wannan abokin nawa, dole na tabattar da kun ci gaba da rayuwa tare" Ya yi maganar yana shafa gashin Muhsin. Ya ce "Dan haka in sha Allah, muddin ina raye, babu wani abu da zai kawo muku cikas a rayuwar aurenku, Ubangiji Allah ya sanya muku albarka. Na ji duk tarihinki, har Nigeria na aika duk an yi mini binciken da yakamata, kuma na gamsu da abubuwan da na ji game da ke, da kuma rayuwar da ki ka yi da Hammad. Ina goyon bayan ku rayu tare, Hammad ba zai taɓa samun mace kamar ki ba Asma'u" Kawai Nana ta fara zirarar da hawayan farinciki. Hammad ya rikice gaba ɗaya ya ce "Abie, yanzu ka yarda na ci gaba da rayuwa da Nana? A matsayin matata duk da yadda al'adarmu ta hana?" Sultan ya yi murmushi ya ce "Na ma soke wannan dokar, daga yau babu ita a Agadez" Hammad ya tashi ya tafi gaban Sultan ya risuna, amma ya rasa abin da zai ce masa. Sultan ya rungume shi yana murmushi. Ya numfasa ya ce "Hammad, ban san iya adadin abin da ya rage maka na rayuwa ba, amma na baka damar ka yi duk abin da ka ke so wanda bai saɓa wa mahaliccinka ba, da zai sanya ka farinciki. Sannan ka sakar wa Tafawa 'yarsa, dan babu amfani ci gaba da zama da mutumin da yake ƙoƙarin ganin bayanka, yake cutar da kai tsawon lokaci. Ka yi haƙuri kuma ka yi biyayya, Ubangiji Allah ya baka ladan haƙuri da kuma biyayyar da ka yi. Sannan ina roƙon Allah ya baka lafiya ya kuma warware miyagun abubuwan da suka aikata maka."Ɗan uwanka kuma wannan ganin damarka ce ka ci gaba da mu'amala da shi, amma ni na yafe shi a matsayin ɗa na, na girgiza matuƙa da jin abin da suka aikata" Nana zata yi magana Hammad ya girgiza mata kai alamar ta yi shiru. "Ke ma in sha Allah, zamu tura wakilai, zamu je mu ba wa iyayenki haƙuri, kuma kamar yadda mahaifiyar Mahmoudu ta nema, kuma mun amince za mu yi hakan. Duk wata ɗawainiyar aure da ake yi wa mace, da za a aura a Agadez za mu yi miki ita, kuma zamu biki sosai kowa ya san da zamanki" Nana ta risuna ta ce "Na gode sosai da sosai Abie, Ubangiji Allah ya ƙara girma da sutura, ya kare ku daga dukkanin abin ƙi. Amma ni hukuncin da ka yanke mini bisa adalci da tausayi, da bani damar na rayu da Muhsin da mahaifinsa ya fi komai yi mini daɗi, ina ga ba sai an yi bikin nan ba, har dukiyar auren ma na yafe" Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba biyanki abin da ki ka yi mana zamu yi ba, kyautatawa ce daga gare mu, dan ƙara nuna martaba da daraja da duk wani ɗan Adam yake da shi, fari ko baƙi koma wani kalar launin fata ne. Ina ƙara amfani da wannan damar, gurin ƙara nuna ɗimbin godiyata a gare ki. Kin sadaukar kin jajirce, mun san bamu da abin biyan ki, amma ina kyautata miki zato da yi miki fatan alkhairi" Nana ta sunkuyar tana murmushi ta kasa magana ma. "Na ɗauki darussa daban-daban, a kan abubuwan da suka faru, komai sila ne, kuma wasu lokutan bawa baya samun ɗaukaka ko cimma nasara, sai an jarraba shi, wasu lokutan mai sauƙi, wasu lokutan kuma mai tsanani. Allah dai ya baku zaman lafiya na har abada. Shi kuma mai magani Sarkin baka ko? Ya ce yana nan tare da shi za a je Nigeria. Ɗan uwanki ma an ce mini yana Agadez yanzu haka, da Zahradeen ya kai shi karatu, zan saka a kawo mini shi nan, shi ma na yi masa godiya na ba shi haƙuri shi ma" Nana ta ce "Dan Allah Abie, ka duba girman abin da Imam Zahradeen ya yi, fiye da laifinsa ka yafe masa. " Yayi murmushi kawai ya ce "Za a duba" Hammad ma ya ci gaba da yi wa Sultan godiya, dan bai taɓa tsammanin zai yanke wannan hukuncin ba. Sultan ya ce Nana zata iya tafiya, bayan tafiyarta Hammad ya sake yi wa Sultan godiya sannan ya ce "Amma Abie hukuncin nan da ka yanke, ba zai janyo surutu da 'yan majalisar ka ba?" Sultan ya ce "Hammad, zan yi duk abin da nake ganin shi ne dai-dai, har abada na daina jiran wani ya sarrafa ni, duk abin da nake ganin shi ne daidai zan zartar da shi." Hammad ya jinjina kai yana sake gode wa Allah. Ya sake cewa "Amma Sultan meyasa ka ce na saki Asal?" "Me za ka yi da ita? Ko ba ka ji abin da ɗan uwanka ya faɗa sun haɗa kai da ubanta da Bilki suna neman ganin bayanka ba?" Hammad ya jinjina kai ya ce "Haka ne" "Amma idan kana son matarka, shikenan ba zan yi maka dole ba" Hammad ya ce "Ba na son aikata abin da za kalle ni a matsayin mara adalci, amma kamar ku ne ɓoye mini wani abu da kai da Maman Muhsin" Sultan ya sake yin murmushi ya ce "To idan ma mun ɓoye maka ai ba laifi muka yi ba, tashi ka yi tafiyarka" ***** Alhaji Fatuhu yaje dubiyar Doctor Sharif tare da Fadila da Suwaiba, sai dai ya tsorata da yanayin da ya gan shi a ciki, tun da ya ga Alhaji Fatuhu yake kuka, amma ya kasa magana, sai da kyar kamar an fizgo maganar ya ce "Ka yi hankali da Alhaji Zailani, kuma ka yafe mini dan Allah" Hakan ma ba komai ake ganewa ba, sai dai maganar ma bata fita da kyau, da kyar suka gane me yake cewa. Daga bisani suka tafi gidan Hajiya Sa'a, tana kwace a cikin najasa, Alhaji Fatuhu ya din ga yi wa masu aikinta faɗa, yana iƙirarin tun da komai ya fara daidaita, gidansa zai mayar da ita. Sai dai haka kurum ƙasan zuciyarsa ya din ga mamakin wani irin nau'in ciwo ne ake ta fama da shi haka. Maganar da Muhsin ya yi, yana ƙoƙarin karɓar wayar mamansa, ya sanya Hajiya Sa'a waiwayo wa da sauri ta kalli yaron. Ayshercool 08081012143 98 1K NE VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC BANK 08081012143 Cikin mamaki Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, saboda yadda ta ƙure Muhsin da ido. Ya ce "Yaya Sa'a, kin gane ni? Ko Muhsin ki ka gane?" "Ba dole na gane wannan tsinannen yaron da Allah ya tsine wa albarka ba? In sha Allah sai ya mutu kuma kun rasa. Da shi ne ya mutu da Abbana bai mutu ba, ɗan nawa guda ɗaya na rasa shi, ku ga naku nan yana rayuwa " Cikin rashin fahimta Alhaji Fatuhu ya ce "Yaya Sa'a kin san kuwa me ki ke cewa?" Cikin tsawa ta ce "Na sani mana, na sani, ina sane. Yanzu ga Abba ya mutu a banza, ni kuma dodon ƙungiya ya shanye mini wasu sassan jikina." Gaba ɗaya ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ganin maganganun da take yi, ba su yi tasiri a zuciyarsa ba. Ya dubi Fadila da ta takure a gefe, tana zare ido ya ce "Fadila, kar fa ku damu ko ku ɗaga hankalinku, kun san ba a hayyacinta take ba, tana fama da matsalar taɓin hankali." Hajiya Suwaiba ta ce "Duk da haka amma mutum ko ba shi da hankali, yana faɗar abin da yake aikatawa ne, amma babu rami mai ya kawo rami?" "Ƙaryata ni za ki yi kenan Suwaiba? Meye haɗin Yaya Sa'a da wani shan jini, kawai raɗaɗin mutuwar ɗanta ne yake damunta" Fafur ya hana su magana, tare da kare Sa'a, duk da ƙasan zuciyarsa maganar Hajiya Suwaiba ta kama zuciyarsa, da ta ce babu yadda za a yi Hajiya Sa'a ta yi wannan maganganu idan bata da alaƙa da su. ***** Imam Zahradeen ne zaune a gaban mahaifiyarsa Hajiya Bilkisu, cikin kuka take yi masa bala'i "Yanzu Zahradeen har zaka iya fifita bare a kaina mahaifiyarka, ka zaɓi ka tona mini asiri? Yanzu amfanin me hakan ya yi maka daga kai har ni. Duk fafutukar da na yi domin ka ne, amma a ƙarshe ka watsa mini ƙasa a idona. Ka lalata komai abin da nake harin ba zaka samu ba, saboda kai ne gwanin na iya da son burgewa, ka tona mana asiri ga shi kaima baka tsira ba" "Ban yi duk abin da na yi, domin tozarta ki ba Ammi, duk abin da na yi, na aikata ne domin kaucewa faɗa wa fushin Ubangiji. Bawa bai taɓa isa ya yi wa bawa abin da Allah bai yi masa ba. Duk ƙoƙarin ku Ammi idan Allah bai ƙaddara mu hau karagar nan ba ba zamu hau ba. A yanzu hakan ku nawa ne ku ke fafutuka, ko da an kawar da Hammad, kuma ba zaku samu zaman lafiya da fahimtar juna ba, kowa na sa yake son ya hau. Ammi Hammad fa shikaɗai ne ɗan uwana namiji... "Tashi ka bani guri, kafin baƙin ciki ya sanya na tsine maka, ka fita ka bani guri" Zuciyarsa cike da ƙuna ya tashi ya bar sashen ta. Murmushin fuskar Nana ya kasa ɓoyuwa, Ƙaisar shi ma murmushin ya yi, kamar koyaushe gyaran litattafansa yake yi. Ya ce "A karo na babu adadi, ina sake taya ki murna ma a wannan karon, tabbas ko a iya haka kin yi nasara. Kuma aya ce ke mai zaman kanta ga mutanen Agadez ba Agadez ba kawai ga duk wani mai hankali ma. Jaruma ce ke ta gaske uwar gijiyata" "Ƙaisar" "Na'am" "Ina yi maka kyakykywan fatan alkhairi na har abada " Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Har kin mantan Allah ya isan da ki ka yi mini a baya" Ta katse shi ta hanyar cewa "Duk wanda yake rinjayar da laifukan mutane, sama da alkhairinsu, to zai zama mara adalci" Ya ce "To ai ni ba mutum bane" Ta yi dariya ta ce "Ni a gurina kai mutum ne. Alkhairinka ya shafe laifukan ka Ƙaisar. Gaba ɗaya ji nake yi kamar ba ni ba, zan rayu da Hammad ɗina, da kuma Muhsin Allah abin godiya kamar komai ba zai wuce ba" Ya zauna yana faɗin "Babu abin da ba ya wucewa sai ikon Allah" Za ta yi magana ta farka daga baccin da ya ɗan ɗauke ta. Da Sayyid ta fara tozali ya ce "Amarya" "Ango" Ta amasa masa tana murmushi. "Nene ta ce sai na mayar mata da ke, wai shirya ki za a yi, ba dai yadda zan yi ne, na fi son ta bar mini ke in din ga jin ɗuminki. Ke ba kya buƙatar duk wani gyara, a gyarenki Allah ya yi ki" Nana ta tashi zaune ta ce "Allah ya shirya mini kai, Nenen zaka gaya wa haka ko? Ni sonake ma na gana da ɗan uwana na yi kewarsa" Hammad ya numfasa ya ce "Kin san Sultan sun samu matsala da Imam Zahradeen, ina ta girgiza miki kai ɗazu, ki bari sannu a hankali zai saukko zan san yadda zan yi na shirya su. Amma da farko ji na yi kamar ba zan yafe masa ba. Amma na duba girman abubuwan da ya yi na alkhairi a gare ni. Kuma ni duk mutumin da zai yi abin da zai kyautata miki to ni ya yi wa, dan haka na ji zan mayar da komai ba komai ba. Kin san wani abu ma vie" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Wallahi idan na kalle ki, na kalli Muhsin, sai in ji zan iya yafe wa kowa ma, Duniyar guda nawa take? Allah ya yi mini tagomashi da abin da na san ba dabara ta ba ce ba. Ba zan fasa gode wa Allah ba" Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya Sayyid. Amma ina da wani roƙo a gare ka; kamar yadda ku ka soke al'adar haramta auratayya tsakaninku da baƙaƙen fata, ina roƙon ku haramta duk wani nau'i na ta'amalli da Aljanu da shaiɗanu" Ta ɗan yi shiru tana satar kallonsa. Ya ce "Ina jinki" Ta ci gaba da faɗin "Ta'amalli da aljanu, da hana iliminku na addini tasiri a cikin rayuwarku, haɗi da riƙo da munanan al'adu su suka ƙara ta'azzara wasu abubuwan. Ga dai zobunanka masu ɗauke da hadiman aljanu, amma hakan bai hana a cutar da kai ba, cuta mai munin gaske. Su ba su baka kariya ba, su ba su hana a cutar da kai ba. Babu wata halitta da zata baka kariya ko ta hana faruwar wasu abubuwan a rayuwarka. Sai dai duk da wannan abin, ina girmama riƙo da ibadarka mussaman salla. Kai ma'abocin salla ne. Dan Allah Imam ka ƙara ƙoƙari gurin ganin an kakkaɓe al'adar amfani da aljanu a cikin harkar mulki. Ga saɓon Allah, ga gadar wa zuriya masifa da tashin hankali. Ni da kai ɗin nan mislai ne akan kanmu, ba zamu yi fatan ire-iren zuriyarmu su gaji wannan bala'in da muka shiga ba. Dan Allah Hammad ka yi ƙoƙari a yi yaƙi da ta'amalli da su, da kuma duk wani abu da ya shafe su. A ɗayanta Allah, a dogara da shi duk ba kwa buƙatar wannan abubuwan muddin kun riƙe Allah ". Ya numfasa ya ce "Maganganunki duk gaskiya ne Ma vie, kuma tuntuni na fara ƙoƙarin neman maraba da su, ni kaina na daɗe ba na son harkar da muke yi da su, amma in sha Allah zan ƙara ƙarfafa hakan, har abada za a daina amfani da duk wani nau'i na gurɓatacciyar al'ada a Agadez" Nana ta rungumo shi ta ce "Yauwwa farincikina, Ubangiji Allah ya saka maka da alkhairi, ya ƙara kare mini kai daga dukkanin wani sharrin. Allah ya ƙara ɗaukaka mini darajarka zuwa inda zato bai taɓa zato ba. Allah ya yi maka kyakykywan tsari daga sharrin duk wani abin ƙi komai ƙanƙantarsa." Ya tsurawa Nana ido, sannan ya ce "Ta yaya ake so na iya rayuwa babu wannan halittar? Halittar da harshenta kullum cikin yi mini addu'a da fatan Alkhairi take. Mai ɗauke da zuciyar da kullum take ƙoƙarin kusantar da ni ga Allah, baiwar Allah da kullum burinta ta sadaukar Saboda da komai saboda ni. In sha Allah mutuwa ce zata raba ni da ke rayuwata. Allah ya yi miki tukuci da gidan aljanna. Ina ƙaunrki Asma'u." Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, da ba ta san dalilin canzawarsu zuwa ja ba. "Nima ina ƙaunarka mijina, irin sosai da sosai, ban san ya zan misalta maka ba" "Ba sai kin misalita mini ba, na gani a zahiri" Ta sunkuyar da kanta tana ɗan murmushi. Ya ce "Yanzu me za ki shirya mana, na shirin bikin? Sultan ya ce sai an yi biki sosai a Agadez, me za ki shirya mana? Me da me ki ke so?" Ta girgiza kai ta ce "Kai kaɗai kawai nake so, kai kaɗai ka ishi Nana komai" Ya yi dariya ya ce "Zan kawo miki Imrana da Muhsin, har ma da Nene anjima su ɗebe miki kewa" Nana ta ce "Amma kuwa da ka kyauta, na gode sosai da sosai" Ya dungure mata kai yana murmushi. ***** Alhaji Fatuhu kuwa bacci ne ya gagare shi, kamar yadda dariya ta gagari kare, ya gagara yin bacci. Idan ya samu baccin ya fara ɗaukarsa, kawai sai ya ga Hajiya Sa'a, tana kuka tana sake maimaita abin da ta faɗa da suka je. Duk yadda ya din ga addu'a, da ƙoƙarin kawar da tunanin daga zuciyarsa, amma abu ya faskara. Sai dai ya danne ya ci gaba da addu'a. Sai kuma doctor Sharif ya faɗo masa, da shi ma yake cewa ya yafe masa, to ya yafe masa da ya yi masa me? Gaba ɗaya sai al'ajabi, ya hana shi yin farincikin dawowar kayansa. Ga shi ya zo gaya wa Alhaji Zailani,  tun da dama shi ne abokin kasuwancinsa, amma ya tuna yadda Fadila ta gargaɗe shi a kan haka. ***** Sagir kuwa tun da yaje Abuja gidansu Yusra, hankalinsa ya ƙara tashi. Jaririn da ya gani da shi yake kamanni, ya yarda jaririn nan ɗansa ne, amma babu yadda ba a yi da Yusra ta yi magana ba, ta faɗi a ina ta haɗu da Shukura ba. Sai dai ana ta ba wa jaririn madara. Sagir ya ce wa mamanta "Ina ga, zan koma Kano na samu iyayen Shukura na sanar da su cewar, an ga jaririn Shukura" Maman ta ce "A'a kar ka faɗa tukuna, kar a zargi Yusra da wani abu, a ci gaba da addu'a dai da bincike, haryanzu Yusra bata cikin nutsuwarta. Haka ya din ga sintiri tsakanin Abuja da Kano, ga shi ya kasa gaya wa kowa, saboda shi kansa ya san ayar tambaya za a saka wa Yusra. Sai dai al'amuran Yusran su na ba shi tsoro shi kansa, banda yana sonta kuma ya san halin da ta shiga, lokacin da Shukura ta ɓata, da babu abin da zai hana ya ce da sanya hannun Yusra a lamarin ɓatan Shukura, idan ba haka ba a ina ta samu jaririnta? **** Labari ya cika ciki da wajen Agadez, kan cewar Hammad yana da ɗa, ya auri 'yar Nigeria, haka zalika an soke Al'adar hana auren baƙar fata. Wasu daga cikin al'ummar garin hakan yayi musu daɗi, mussaman baƙaƙe, da suka din ga jin tamkar su zuba ruwa a ƙasa su sha. Ɓangaren fararen buzayen kuwa, gani suke yi tamkar rage musu kima ne, da kuma rage karsashin Masarautar. Cikin marasa gaskiya a fadar Sultan kuwa, cikinsu ya ɗuri ruwa cike da tashin hankali, saboda tsoron hukuncin da ka iya biyo bayan tonuwar asirinsu. Ga shi Sultan ya ƙi nuna musu ya san su ne, kuma tun daga ranar da aka kawo bokan nan fadar Sultan, ba a sake zaman majalissar ba. Waɗanda ba su san Nana ba, suka din ga sintirin gidan Sultan, su na son ga Nana, amma Nana na kauwwame a sashin Sultan. Tuni labari ya ishe Asal, wanda hakan ya sake gigitata,  tamkar za ta yi hauka. Wani irin so da matsanancin kishin Hammad ya din ga taso mata, ji take yi tamkar za ta yi hauka. Gani take yi ta ƙasaƙanta ta tozarta, a ce Nana ce kishiyarta, matar da ta ɗauka tamkar baiwar da ta saka kuɗi ta saya, amma yanzu ita ke da komai, ita kuma tana gefe ta zama 'yar kallo. Wasa-wasa Asal ta daina cin abinci sai kuka, ga Tafawa ba ta ita yake yi ba, ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke musu kawai yake yi. Duk matsanancin kishin Hammad, haka ya ƙyale Nana da Imarana, suka kasance tare suna ta hira irin ta 'yan uwantaka, tare bawa junansu labarin gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa. Ya ce "Bari na nuna miki wani abu" Imarana ya ɗan tashi ya fita, sannan ya dawo, ko da ya dawo ya miƙa wa Nana waya. Nana ta karɓi wayar tana kallonsa, ya yi mata alama da ta saka a kunnenta. Nana ta saka wayar a kunnenta, zuciyarta na ɗan bugawa da sauri. "Assalamu alaikum, Nana" Muryar Ummansu ce ta doki dodon kunnuwanta, a wani irin rikice Nana ta tashi tsaye, ta rasa ina zata dosa ta ce "Um..umma, muryarki ce ke ce?" "Nice Nana, kina nan lafiya?" Nana ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta ce "Umma, bani da bakin da zan yi miki magana, bani da idon da zan iya kallonki, ni mai tarin laifi ce" "Shhh, Babu abin da ki ka yi mini na ba dai-dai ba Nana. Sai dai tashin hankali da fargaba na shige shi, na rashin sanin inda ki ke, da kuma wani hali ki ke ciki, ga tsohon ciki kin tafi kin bar gida. Amma Imrana ya zo inda nake, tare da Yayan mijinki, sun yi mini bayanin komai. Nana na yi sujuda na gode wa Allah, ba wai domin daular da ki ke ciki ba, ko kina auren wani ba, sai domin murnar kina cikin ƙoshin lafiya tare da ke da yaronki. Sun ce kar na gaya wa kowa, babu wanda ya sani, amma sun zo sun yi mini alkhairi Imrana ya zama babban mutum ya nutsu, kema hankalinki yana kwance. Ni dai fatana su yi su kawo mini ke, ko na wanko ƙafata na taho,amma sun ce na yi haƙuri kaɗan" Cikin kuka Nana ta ce "Ni dai ki yafe mini dan Allah, tashin hankalin da na sanya ku a ciki, dan Allah ku yi haƙuri Umma" Imrana ya karɓe wayar ya ce "Umma sai anjima, da na sani ban haɗa ku ba, nema take ta rikice" **** Hajiya Amina tana zaune tare da Alhaji Zailani, tana ta lallaɓa shi a kan ya ci abinci, amma ya ƙi ci, saboda shikaɗai ya san bala'in da yake ciki. Tun da ya yi mafarkin an huda saitin zuciyarsa, dodon ƙungiya yana sha masa jini, ya farka ya ji saitin zuciyarsa ya yi masa wani irin nauyi. Ga jikinsa sai yi masa wani irin raɗaɗi yake yi, kamar ya yi wanka da yaji. Yana jin yadda wayarsa take ta ringing amma ya ƙi ɗagawa. Daga ƙarshe, Hajiya Amina ta saka hannu ta ɗauki wayar, ta saka a kunnenta tana sallama. Jin ta yi shiru ya sanya Alhaji Zailani ɗagowa ya kalle ta, sai dai ta tsare shi da idanunta ba ta ce masa uffan ba. Jiran Hajiya Amina yake yi ta yi magana, amma ta yi shiru ba ta yi magana ba. Jiki babu ƙwari ya ce "Ya dai? Meyafaru?" Jiki a sanyaye ta ce "Daga makarantar su Yusuf ne, wai yana kwance a Asibiti babu lafiya, yau kwana uku kenan" Ya waro ido ya ce "Yusuf ɗin?" Ta jinjina masa kai. "Ki kira su ki gaya musu, ni ba ni da lafiya, babu lallai na iya driving su dawo mini da ɗana gida" Hajiya Amin ta jinjina kai tare da mayar da hankalinta  kan wayar. ***** Gidan Baba ya zama tamkar maƙabarta, babu walwala ko kaɗan, ko ƙaunar tunkarar gidan baya son ya yi. Saboda matsananciyar damuwa, da takaicin abubuwan da suke faruwa a gidan. Jamila kuwa kullum tana ɗaki, dan ta sha baƙar azaba, sai da ta kwana tara a Asibiti, da kyar aka samo kanta kamar ba zata rayu ba. Ya daina shiga harkar Mama da yaranta gaba ɗaya, ko abincin gidan ya daina ci. Ga damuwa da kewar yaransa Nana da Imrana da suka addabi zuciyarsa. Ya fito daga cikin gida da buta a hannunsa, ya yi alwalar sallar Azahar sai ga wata danƙareriyar mota irin ta matafiya, sabuwa gal sai ƙyalli take yi ta shigo layin. Bai damu ba, ya idar da alwalarsa ya ɗaukko wayarsa, yana son kiran can Buda, saboda yaga kiran wayarsu, bai samu ya ɗaga ba. Sai ya ga motar nan an tsaya da ita a ƙofar gidan. Sai ya yi tsuru yana kallon motar. Sulei ne tare da Mahmoudu suka fito, suka nufo Baba. Ya tsaya saroro har suka ƙaraso inda yake. Suka durƙusa har ƙasa suka gaishe shi, ya amsa musu yana bin su da kallo, kasancewar sun rufe fuskokinsu da takunkumi. Bayan sun gaisa, Mahmoudu ya ce "Baba mu na tare da baƙi ne daga Agadez" Baba ya ɗan yi shiru, shi dai ya san babu wanda ya sani a Agadez, amma ya miƙe ya ce "To bari na kawo muku abin zama" Ya tashi ya shiga cikin gidan, ya ɗaukko tabarma ya shimfiɗa musu, ya koma ya aiki Nasiru ya sayo ruwa. Ya zata iya su Mahmoudu ne baƙin, kawai ya ga Sulei ya je ya buɗe motar, wani dogon mutum mai jiki ya fito da wani matashi, shi ma sanye da rawani suka fito, suka nufo shimfiɗar. Shi dai Baba duk abin ya ɗaure masa kai, tsoro ya shige shi. Ya yi musu barka da zuwa, suka zazzauna, Mahmoudu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Baba baka gane ni ba?" Baba ya yi shiru ya ce "Kamar dai na sanka, amma ban gane ka ba" Imam Zahradeen ya sauke rawaninsa shi ma, shi ma dai Baban ya yi masa kallon sani. Mahmoudu ya ce "Baba kamar baka gane mu ba ko?" Baba ya ce "Gaskiya dai" "Baƙi ka yi daga Agadez" "To bawan Allah, ni wa nake da shi Agadez, kuma ba ɓatan kai ku ka yi ba?" Mahmoudu ya ce "Ba mu yi ɓatan kai ba, na yi mamaki da ka ce ba ka gane ni ba, amma ai ka tuna buzun da ka aura wa 'yarka shekarun da suka gabata" A razane Baba ya ɗago ya kalli Mahmoudu, sai kuma ya riƙe rigarsa, ya ce "Dama ku ne? Ba ku yi mini adalci ba, ku ka tattara ku ka gudu, ku ka bar mini 'ya da jinyar ɗan uwanku, shi ma daga ƙarshe ya gudu ya bar ta, saboda wauta da rashin hankali wai ta tafi Niger neman shi, haryanzu shekara ta uku kenan, babu wanda ya san inda take, baku kyauta mini ba" Baba yayi maganar yana kuka kamar ƙaramin yaro. Imam Zahradeen ya ce "Baba, ka yi haƙuri abubuwan da suka faru ba a kyauta maka ba. Amma mu na da kyakyawan albishir ne" Baba ya ce "Kai ba kai ne mijin nata ba?" Yayi maganar yana nuna Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce "Baba ai na fi wancan tsufa, shi ya fi ni ƙuruciya, ya kuma fi ni kyau, ni yayansa ne. Zancen da nake yi maka, a kowane lokaci mahaifinmu zai iya aiko da mutanensa daga Agadez da kayan auren Nana za a sake gagarumin bikin aurensu" Baba ya ce "Ashsha! Yarinyar da nake gaya muku shekara uku babu wanda ya san inda take, kuma babu wanda ya waiwaye ta tunda ku ka gudu kuka bar ta. Kuma ni mene ne haɗina da Sarkin Agadez da zai kawo kayan aure? Ni dai na yi nadamar abin da na aikata na aurar da 'yata ga mutumin da ban san daga inda yake ba" Imam Zahradeen ya lura ran Baba a ɓace yake. Ya sassauta murya ya ce "Baba sunana Imam Zahradeen Jalaludeen Agadez, ni Yaya ne ga Imam Hammad Jalaludeen Agadez. Kuma 'ya'ya ga Sultan Jalaludeen Agadez, wato Sarkin Agadez na yanzu. Buzun da ka aura wa 'yarka, ɗan uwana ne, kuma  ɗa ne ga Sultan na Agadez." Baba ya kalli Imam Zahradeen kamar yana raina masa hankali. Ya ce "Ɗan sarki ne zai zo baro ƙasarsa ya zo Nigeria yana aikin gadi?" Mahmoudu ya ce "Baba, idan baka manta ba, ko lokacin da aka yi aurensu, a yanayi na rashin lafiya yake,  rashin lafiya ce ta kama shi" "To yaya za a yi a ce ɗan sarki ya zo Nigeria gadi, ni abin ya bani mamaki ne. Kuma na kasa yarda, ni kar ku sake dugunzuma mini hankali bayan halin da nake cikix Zahradeen ya ce "Baba ba dunguzuma maka hankali za mu yi ba. Mun zo mu sanar da kai batun zuwan baƙinka ne daga Agadez, kafin su zo ɗin." "To wai su zo, su yi mini me?" " 'yarka Nana, tana gurinmu tare da ɗanta Muhsin" Baba bai san ya aka yi ya tashi tsaye ba, yana zazzaro ido ya ce "Nana Asma'u dai 'ya ta? Yaya aka yi ku ka same ta? Tana ina? Kun taho mini da ita?" Mahmoudu ya miƙe tsaye ya ce "Baba shi ne bayanin da muke yi maka, Nana tana tare da mu, za a kawo dukiyar aurenta Nigeria za kuma a yi bikin aurensu sosai da sosai. Duk abin da za mu gaya maka yanzu ba za ka fahimce mu ba, saboda a cikin damuwa ka ke, kuma abubuwan da suka faru su na da tsawo da sarƙaƙiya akwai buƙatar a yi maka bayani daki-daki. Ba Nana ba hatta Imrana yana tare da mu a Agadez, akwai tarin bayanai da sai ka nutsu, an yi maka bayani zaka fahimce su" "Amm bawan Allah, ni ko yanzu a shirye nake, mu tafi Agadez ɗin na karɓi 'ya'yana. Bayan Nana kuma me ya haɗa ku da Imrana" Imam Zahradeen ya ce "Alkhairi ne, a cikin satin nan, zuwa mai kamawa in sha Allah; za a sake turo maka baƙi daga can. Kuma za a yi bikin su al'ada saɓanin yadda ya gudana, kuma za a yi maka bayani kamar yadda nake nanata maka. Amma kafin nan mu na son za a gyara maka gidan nan, ko kuma a canza maka wani" Baba ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar haka, muddin Nana yake so, babu amfani a raina inda ta fito, ni dai fatana na gansu cikin ƙoshin lafiya" Zahradeen ya ce "Ba raina maka aka yi ba, matsayinka da girmanka ne ya sanya za a yi maka." Fafur Baba ya ƙi yarda da hakan, da kyar suka rarrashe shi suka tafi, dan cewa ya yi ba za su bar ƙofar gidansa ba, ba tare da ya ga yaransa ba. Kasancewar duniya makarantar da ko babu malami, ta biya maka darasi dole ka ɗauka ce, ta karanta wa Baba darasin da duk son abin Duniyarsa, yanzu tsoro yake ji. Zuwansu Imam Zahradeen babu wanda ya sanarwa, saboda gani yake yi tamkar ƙarya Buzayen nan suka zo suka sharara masa. Ya kasa gaya wa kowa, sai Uwani ya kira ya sanar mata. Sai dai a ƙarshen maganar Baba ya ce "Amma Uwani ni ban ji na yarda ba, ji nake kamar ƙarya kawai suke yi ban ji na yarda ba" Uwani ta ce "Alhamdillah, ni dai na ji na yarda har cikin zuciyata. Ko ba hakan ba ne, ina fatan Allah ya tabattar da shi ya zama gaske. Wallahi zuciyata ta daɗe tana bani, mijin Nana ba ƙaramin mutum ba ne, to ita Nanan da gaske tana gurinsu, kuma har da Imrana sun haɗa ku ko a waya ne?" Ya ce "A'a, shiyasa na kasa yarda ma gaba ɗaya" "Isa, yarda ni dai na gama ta, zamu duƙufa mu ci gaba da addu'a in sha Allah Nana suna cikin kwanciyar hankali tare da ɗan uwanta" Kalaman Uwani suka ɗan ƙwarara wa Baba gwiwa. Bayan sallar isha'i ya shiga gida, yana zaune yana jin radio, Mama tana cikin ɗaki tare da Jamila da ta koma so silent, ko magana ba ta iya yi. Ihun da Jamila ta yi ne, ya sany Baba jifa da radio ya tashi tsaye yana rarraba ido. "Mama! Mama!! Dan Allah ki taimake ni, dodon ƙungiya zai shanye mini jini. Hajiya Sa'a kin cuce ni, kin cuci rayuwata, na kasa samun aminci da salama. Na baku Abba me kuma ku ke nama a gurina?" Cikin rashin fahimta duk suke kallon Jamila, Baba ya ce "Me yarinyar nan take faɗa ne haka?" Mama ta ce "Nima ban sani ba wallahi, ina ga jikin ne ya motsa." Baba ya ce "Jikinta ya motsa kuma take irin wannan maganganun?" Ba ta ko saurare su ba, ta ci gaba da surutanta. "Ni ban so shiga kungiyar nan ba, dole ki ka yi mini, ga shi kin sanya ni a bala'i, na rasa mutuncina, kin saka nayi kisan kai, yanzu kuma na kasa samun kwanciyar hankali, sai tsorata ni ake yi, nima ana nema na a kashe ni, kin cuce ni" Baba ya ce "Jamila, meyafaru ne? Me ki ke faɗa wai?" "Baba riƙe hannuna, Baba ku taimake ni" Ya ƙarasa ya riƙe hannun Jamila, cikin kuka ta ce "Baba na shiga uku, na aikata mummunar ɓarna, Baba hakki ne zai yi ajalina" Baba ya ce "Jamila, ki gaya mini, me ki ka aikata?" "Ƙungiyar asiri, Baba ƙungiyar asiri aka shigar da ni, saboda na kai jinin Nana" Kamar ta watsa wa Baba wuta, haka ya fizge hannunsa ya ja da baya, yana kallon Jamila da take ta uban kuka. Mama ta ce "A'a baban su Jamila, dan Allah kar ka yarda da abin da ta faɗa, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya, wataƙila zafin ciwo ne, amma wace irin magana ce wannan, a ina Jamila za ta ga wata kungiyar asiri ta shiga" Alhaji Zailani ne a durƙushe a gaban gawar ɗansa Yusuf, bayan an dawo da shi daga makaranta, dama babu rai aka dawo da shi. Ba shi ne abin da ya ɗaga masa hankali ba, sama da ganin busashshen jini a baki da kuma hancin Yusuf. Ba dan ya yi iya ƙoƙarinsa ba, da tuni ya aikata abin da zai fallasa kansa. Wani irin raɗaɗi da zafi ya din ga ji a zuciyarsa ya kasa magana, ya kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. Ba a jima ba, gidansa ya cika da jama'a, Hajiya Amina sai kuka take, ga Shukura ta ɓata, ga kuma mutuwar Yusuf. Ya hau neman lambobin yaransa, da ya sanya su kashe Shukura, a kan kar su kuskura su kashe ta, amma ya kasa samun su. Duk da daɗewar da yayi yana aikata zalunci kala-kala, mutuwar Yusuf ta dake shi, ta tsaya masa. Ya din ga jin tamkar ya yi ta kururuwa yana burgima, ko zai ji daɗi. Ko da aka yi jana'izar Yusuf, Alhaji Zailani tafiya ya yi ya kulle kansa a ɗaki. Kaf yaransa babu kowa sai Shukura yanzu, Shukuran ma ba a san inda take ba. Kuma ita ma baya tsammanin za ga tsallake sharrin dodon ƙungiya, tun da ya gaza bashi jinin shekara. Sosai ake ta shirye-shiryen gudanar da bikin auren Imam Hammad, da matarsa 'yar Nigeria. Ita Nana abin har mamaki yake bata. Tun da Sultan ya amince da auren Nana da Sultan, Nene take sintiri kawo wa Nana kayan gyaran jiki. Ban da matar da ake ware mussaman Nene take zuwa da ita, take yi wa Nana wani irin gyaran jiki na mussaman. Nana ta ce "Nene duk wannan abin fa ihu ne bayan hari" Nene ta ce "Ke, gyaran ne ba kya so?" "To Nene ya riga ya sanni a yadda nake, me kuma zan gyara?" Nene ta ce "To kar ki gyara, komai yana buƙatar gyara ai" Aka ajiye wa Nana kayan sakawa, da na ado irin na Buzaye. Nana ta ƙudurce a ranta, bayan ta tare, kayanta na 'yan Nigeria za ta saka Hammad ya ajiye mata, saboda ita ma tana son tata al'adar. Shi kansa Hammad ya so a ƙyale masa ita a haka, dan shi komai nata ya yi masa. Sai dai gyaran jikin da ake yi matan ba ƙaramin kyau take yi ba. Ga shi tare da Muhsin suke kwana da Nene, hakan ya ƙara sanya ta farin ciki. Hammad ya ce ta fita ta ɗan zagaya, amma ta sanya takunkumi ta rufe fuskarta. Har mamaki Nana take yi, yadda idan Muhsin ya ga raƙuma ko shayi, kamar zai tashi sama saboda murna. Sarkin baka ta hango, suka nufe inda yake. Cikin jinjina ya ce "Barka da tattaki uwar gijiyata" Nana ta yi dariya ta ce "Dan Allah ka daina kunya ka ke bani" Shi ma yana murmushin ya ɗago ya kalli Nene, ya ce "Ni kuwa dama ina ta son na yi miki magana, Allah bai yi ba" Nene ta ce "Ni ɗin ko? Ka sanni ne?" Ya ce "Eh, ai duk inda muka ga juna, muna gane kanmu" Ta yi dariya ta ce "Na ji, ai ban yi zaton haryanzu akawai abin da tattare da ni ba" Sarkin baka ya ce "Ni na ji na gane ai. Kuma ni ɗalibin marigayi Sa'adu Aska ne" Nene ta waro ido ta ce "Kana nufin Babana?" Sarkin baka ya ce "Ƙwarai da gaske, ya sanar da ni magunguna, sai muka kwana casa'in tare da shi, a mabanbantan dazuzzuka, daga bisani muka rabu, ban sake ganinsa ba. Mahaifinki mutumin kirki ne, ba zan manta da shi ba har abada" Nene ta ce "Ikon Allah" Nana ta ce "Sarki kai komai ma ka sani ne? Kuma kowa ya sa ka" Yayi murmushi ya ce "Na san dai abin da Allah ya sanar da ni, kowa ya sanni kuma na sha yawon duniya ne" Yayi maganar yana ɗaukar Muhsin. Nana ta ce "Sarki ka ga Nene ta daina harkar bayar da magani, kaima ina fatan zaka daina?" Ya ce "Meyasa zan daina? Ba a daɗe ba ni ba, ke kanki ki ka bayar da magani zan ce, ko ba ke ki ka tono inda aka yi wa mijinki asiri, meyasa Allah ya zaɓe ki ya nuna miki, duk yawan jama'ar da ke ƙasar nan. Abin da ki ke ta gudun sai da ya faru" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ba ina nufin ka daina bayar da magani ba, ka daina aiki da aljanu, shi ne ɓarnar. Sannan ka yi ilimi na zamani, cikakke domin ka inganta harkar maganin naka. Ya zamana maganunnanka da awo kar ka bayar da abin da zai cutar maimakon a samu lafiya" Yayi dariya, Nene ma ta yi, Ya ce "Yaro yaro ne. Nana a dalilinki wallahi na daina surkullen haɗa ayoyin Alkur'ani da wasu abubuwan na yi sihiri. Saboda uban gidana ma, Allah ya ja zamaninsa uban duƙusa ko in ce Ƙaisar, shi ma ya ce na daina wannan, na kuma daina. Na daina surkulle da sihiri na tuba, amma ba zan iya daina aiki da aljanu ba" Nana ta ce "Amma saboda me?" "Saboda ɗebo mini magani, wasu ayyukan kuma dole su ne nake aikawa su yi wani aikin." "Sarki, ta'amalli da aljanu da ka ke yi ba shi da wani alkhairi shirka ne, dan Allah ka daina. Kana cikin mutanen da nake son mu tsira Duniya da lahira." "Ni ba ni na nemi aljanu na fara aiki da su ba, aljanu su suka takura ni, kamar dai ke da kuma wannan baiwar Allah. Bana ta'amalli da aljanu, na bayar da kuɗi, ko na yi wa wasu sihiri, ko wani abu makamancin haka, ai kin je gurin maganin nawa kin gani" Nana ta ce "Sarki, kar mu shiga wani bugire da bai kamata mu shiga ba, mu kalli gaskiya kai tsaye kar mu yi mata wata kwaskwarima saboda son zuciyarmu" "Asma'u babu kwaskwarima domin ba wa ƙarya kariya a maganganuna. Su turawan da ku ke taƙama da su, su na amfani da ku, da daƙile magungunnku ne, saboda gina nasu kasuwancin. Kuma Nana magunguna na da awo nake bahar da su. Ban ƙi ba akwai masu bayar da magani, saboda neman abinci. Amma wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba, bai sani ba kawai. Kuma banda abin ki tun a zamanin baya magungunan 8su na da awo, wani a ce ka auna da ɓawon gyaɗa,ko farce, wani a ce ka sha safe da yamma, duk sharri ne wasu abubuwan da ake faɗa, da ƙoƙarin kashe mana magungunanmu. Sai a  ce ku daina shan magungunan gargajiya saboda ɗaci, hanta ba ta son ɗaci, amma Allah ya halicci maɗaciya a tsakiyar hanta. Idan hanta ba ta son ɗaci, Allah ba zai sanya matsarmama a cikin hanta ba. Kuma su magungunan baturen, ba ɗaci ne a cikin su ba. Ba zan kushe wa kowa ba, amma kar a kuskura a kushe mini nawa. Yakamata mu daina wannan musun haka,kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai " Nana ta ɗan yi jimm tana tunani, daga bisani ta ce "Wasu maganganun naka na kan dai-dai, amma kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai!" "To ki daina takura mini a kan lallai sai na yarda da abin da ki ke kai" 99 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Har Nana za ta sake magana, Nene ta riƙo hannunta, ta ce "Nana mu koma ciki, ai kin ɗan tattaka, kin san baya son a ganki, ko a gane ki a yanzu. Ɗan uwa idan muka kuma haɗuwa zamu tattauna sosai mu gaisa. Sosai shirye-shirye suka yi nisa, hankalin Sultan gaba ɗaya ya koma kan shirin zuwa Nigeria da bikin da za a gudanar. Sai dai yana ta fuskantar ƙalubalanta a kan hukuncin da ya zartar. Gimbiya Bilkisu ta rasa inda zata sanya kanta, ta tuntuɓi Tafawa ta sanar masa da matakin da Sultan ya ɗauka a kanta, amma ya ce mata shi ma ta kansa yake yi, hankalinsa a tashe yake. Duk yadda ta kai ga ƙoƙarin yin dabarun da Sultan zai saurare ta, fafur ya ƙi ko kallo ba ta ishe shi ba. Ranar ƙarshe ma da ta je ɗakinsa kamar zai dake ta ya ce "Bilkisu bana ƙaunarki bana ƙaunar ganinki, tun da har za ki yinƙurin sabauta mini rayuwar ɗa, idan ki ka sake zuwa inda nake, sai na yi miki abin da baki taɓa tsammani ba, fice ki bar mini ɗaki kafin na yi miki illa" Abin ya ɗaure mata kai, bata taɓa tunanin zai yi irin wannan fushin har haka ba. Jamila ta koma gata nan gata nan, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, kuma ita ba mara lafiya ba. Shi Baba gaba ɗaya ma yanzu tsoro suke ba shi. Ya riƙe istigfari ba dare babu rana, gaba ɗaya yaransa sun watse babu wani na kamawa. Gaddafi ya zo gida, ya tarar da gidan nasu duk wani iri. Yayi mamakin ganin yadda Jamila ta wani rakwakwkwaɓe, jiki babu ƙwari, ta yi wata irin muguwar rama ta fita daga hayyacinta kamar ba ita ba. Sun dawo daga sallar Asuba, tare da Baba, Baba ya numfasa ya ce "Gaddafi ka ga yadda Allah ya yi da gidanmu ko? Gaba ɗaya babu wani mai ɗan dama-dama" Gaddafi ya ce "Na gani Baba, ina son na yi magana dai na fasa, na ga Suwaiba ta daina magana gaba ɗaya, har da dalalen yawu take yi. Jamila kuma na kasa gane abin da yake damunta" Baba bai ɓoye masa komai ba, jikin Gaddafi ya din ga tsuma, ya dubi Baba ya ce "Baba, Jamila ta yi ciki, kuma tana maganar ƙungiyar asiri? Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Cikin matsananciyar damuwa Bab ya ce "Babarta ta ce zafin ciwo ne, amma na kasa yarda nima" Ya yi maganar yana zubar da hawaye. Gaddafi ya ce "Shiyasa Baba na din ga maganar kuɗin da ta din ga ta'amalli da su, amma mahaifiyarta ta nuna ba ta so, ta nuna baƙin ciki nake yi, da ci gaban Jamila ka ga irin abin ko? Shikenan sun lalata mana gida" Baba ya yi kuka ya ce "Ina kyautata zaton hakkin yaran nan ne, su Nana, dan sai daga bayan nan, nake duba wasu abubuwan da na aikata musu na ga sam babu adalci a cikinsa. Amma wasu mutane sun zo wai daga Agadez sun ce mini tana gurinsu" Nana Baba ya gaya wa Gaddafi abin da su Mahmoudu suka zo masa da shi. Gaddafi ya rikice ya ce "Baba kuma baka karɓi lambar wayarsu ba ko ka bi su ba?" Baba ya girgiza kai ya ce  "Ban karɓa ba, ni tsoro ma na ji, ji nake kamar ƙarya suke yi. Na bar wa Allah ikonsa" "Amma Baba akwai mamaki a cikin abubuwan da suka faɗa, masu sarƙaƙiyar gaske" Baba ya ce "To ai shiyasa ban ma gazgata ba, sai abin da hali yayi" Gaddafi ya ce "Ba wani abu, in sha Allah mu tsammaci alkhairi" Baba ya jinjina kai cike da gamsuwa. **** Nana ce a tsaye, tana kallon Ƙaisar, yana zuba wa wata tsuntsuwa abinci a cikin keji. Nana ta kalli tsuntuwar ta ce "Ƙaisar ita kuma wannan fa, a ina ka samo ta?" Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce tsinto ta na yi a daji, za ta mutu, ban zaci ma zata rayu ba, sai kuma na ga ta farfaɗo yanzu ta ware ma" Nana ta ƙarasa gaban kejin ta zauna, sannan ta ce "To kuma tsuntsuwa ce ita, ko kuma aljana ce?" Ya kalli Nana ya ce "Dama akwai tsuntsu mutum da aljan ne?" Nana ta ɗan yi shiru tana kallon tsuntsuwar. Ya ce "Mutum jinsinsa daban, aljani daban, haka ma tsuntsu daban. Babu Aljani tsuntsu sai dai Aljani ya shiga jikin tsuntsun, ina fatan kin gane?" Ta gyaɗa kai, ta ce "Haka ne, wai ni kuwa Ƙaisar ina Haulat? Ka fara son nata?" "Ban sani ba" Ya yi maganar yana hararta. Nana ta yi murmushi ta ce "To shikenan kai ba zaka yi aure ba kenan? To sonta ne baka yi ko kuma me ta yi maka?" Yayi mata shiru, yana rufe kejin tsuntsuwar nan. Nana ta numfasa ta ce "Ƙaisar ina kewar gida fiye da tunani, zuciyata kuma ta cika da fargabar rashin sanin abin da zan je na tarar. Ina jin kunyarsu ban san da wani idon zan kalle su ba. Duk da Imrana ya haɗa ni da Mama, ta yi mini Addu'a ta ce na kwantar da hankalina, amma kunyarsu nake ji ban kyauta ba abubuwan da na yi" Ya ce "Za ki tarar da alkhari in sha Allah, da abun da zai yi miki daɗi da wanda ba zai yi miki ba. Ni na din ga shagaltar da ke daga tunaninsu, da tunaninsu ya yi tasiri a zuciyarki, da ba ki cimma wannan nasarar ba, da kin rushe komai, dan idan ki ka koma gidan babu abin da zai canza" Cikin mamaki Nana ta kalle shi ta ce "Ban gane ba, kai ne ka sanya na daina jin damuwar da na din ga ji a baya, da son komawa gida?" "Sosai, saboda ruhi ne mu, mu na iya shiga ko ina a jikin ku, kuma muna iya hargitsa tunani da sanya muku rashin nutsuwa" Ta yi shiru tana nazari, ta sake cewa "Ƙaisar ka sanya ni a fargaba, abin da zan tarar a gida da gaske mara daɗi ne? Kodayake ko ka gaya mini ma idan na tashi na san mantawa zan yi sai abin da na je na tarar kawai" "Kin yi zaton da mugunta kawai nake nuna miki abu na mantar da ke ko?" Nana ta jinjina kai. "Ba haka ba ne, duk da ta wani fannin haka ɗin ne, muguntar ce da takaicin ƙin yarda da abin da na zo miki da su. Mafarki ya kasu kashi-kashi, duk da shi ma ina kan bincike a kansa. Akwai mafarkin da yake daga Allah ne, akwai mutanen da akan yi wa ishara a cikin bacci, na kusantowa ko kuma faruwar wani al'amari da bai faru ba kwata-kwata. Wasu kuma a nuna musu makamancin abin, wasu kuma su ga abu a duƙunƙune sai an fassara musu. Galibi waɗanda aljanu ke nuna wa mutum a mafarki, na haɗin faɗa ne. Abu ne da aka yi shi a bayan idon mutum bai san an yi ba, sai su nuna masa. Kuma ba su fiye nuna abin alkhairi ba sai akasin haka. Wasu idan sun gani su na iya shiru da bakinsu, wasu kuma basa iyawa sai sun faɗa. Sai su sanya a din ga yi wa mutanen wani kallo na daban, wasu a dole dalilin hakan kan sanya su fara bayar da magani. Ke na biyo miki ne ta hanya mai sauƙi, saboda bana son tilasta miki, na fi son ki amince da kanki. Sai na nuna miki abin da ya faru da baki sani ba, ko kuma wanda yake shirin faruwa, ko wanda nake hasashen abu ne mawuyaci bai faru ba. Akwai abin da idan na ƙyale ki, ki ka tashi da shi a ƙwaƙwalwarki, ba za ki iya yin shiru ba, za ki yi yinƙurin ɗaukar mataki, wanda hakan ka iya haifar da fitina, saboda idan ki ka haifar da matsalar ba ki da maganinta, tun da ba ki amince da bayar da magani ba. Ɗan Adam kuna da nau'in ciwo na gangar jiki, da kuma na ruhi, amma ba kwa damuwa da ciwon da yake damun ruhinku, kun fi damuwa da na gangar jiki. Mutum zai iya kashe maƙudan kuɗaɗe, a kan lafiyar gangar jikinsa, amma sam wani baya yadda ma ruhinsa yana rashin lafiya." Nana ta ce "Nima ban gane ba" Yayi murmushi ya gyara zamansa ya ce "Ruhi shi ne asalin rayuwa, da gangar jiki ta dogara a kai, wanda ba a iya ganinsa, ko taɓa shi, amma wanzuwarsa ce take sanya gangar jiki motsawa. Ruhi yana da alaƙa da hankali domin shi ne, ku 'yan Adam ku ke amfani da shi, gurin sarrafa duniyarku da gangar jiki. Lafiyayyen ruhi da tunani suke samar da nutsatsiyar gangar jiki mai cike da karsashi. Rashin lafiyar ruhi, ta fi ta gangar jiki hatsari. Idan ruhi yana rashin lafiya, yana kashe gangar jiki baki ɗaya. Sannan warkar da gangar jiki ya fi sauƙi a kan warkewar ruhi. Na san bayan nan nawa sun ɗan yi miki tsauri, amma bari na ɗan sauƙaƙa miki bayanan. Kamar yadda na ce miki ruhinku yana rashin lafiya, tabbas yana yi ciwukan da ido baya iya gani, sai dai ciwon na sanya hankalinku ya ƙwace, ku aikata abin da ba shi kenan ba. Misali Alhaji Zailani ruhinsa na fama da ciwon Hassada, amma bai taɓa tsayawa ya fahimta ba, saboda hankalinsa ya ƙwace har ya din ga aikata miyagun ayyuka. Wasu lokutan ku kan ji duniya ta yi muku zafi, kun tsani komai babu laifin tsaye babu na zaune, yana daga cikin alamomi na ruhinku na buƙatar kulawa ba shi da lafiya. Dan wasu lokutan shi ne yake taɓuwa sai hankali ya taɓu, nan da nan sai a ce ƙwaƙwalwa babu lafiya, idan ciwon ba shi da alaƙa da irin matsalolin da muke haddasa muku a ruhi. Hassada, ƙyashi, yawan ƙarya baƙin ciki babu dalili, burin gushewar ni'ima ga wani, yawan raya faruwar munan abubuwa. Yanke tsammani daga samun rahama, ko wani abu na alkhairi a rayuwa. da wasu cututtukan ma da ku kan danganta su damu, alamomi ne na rashin lafiyar ruhi, duk da mafi yawa wasu lokutan mu ne muke haddasa rashin lafiya a ruhinku. Idan ku ka ji alamu na ƙyashi ko hassada, ba ku fiye sakankankancewa ku roƙi Allah ya yaye muku ba, ko ku miƙe ku nemi maraba da hakan ba, ba ku fiye ɗaukarsa komai ba. Sai dai a hankali idan ya tsananta sai hankalinku ya gushe gangar jikinku ta aikata ɓarna. Kamar dai abubuwan da suka faru a masarautar su mijinki. Da abubuwan da aka yi masa. Ƙyashi, baƙin ciki hassada, son kai, da makamantansu duk larurar ruhi ce da ke kashe gangar jiki. Sai dai a zamana da ke na ƙara fahimtar wani abu, babu abin da ya kai addu'a kusanta mutum da Ubangiji, kuma duk ruhin da yake da kusanci da Allah zaka same shi cikin nutsuwa. Babu wanda ya san inda ruhin ɗan Adam yake sai Allah, amma galibi cututtukan da suke alaƙa da ƙwaƙwalwa da abubuwan da zuciya ka iya rayawa su na da alaƙa da ruhi. Lokuta da dama sai bawa ya yi ta addu'a, ya ga kamar bata karɓuwa, amma tasirin Addu'a da kusanci da Allah na sanya mutum a cikin nutsuwa, ta yadda zai ga wani da irin kaddararaa koma wadda ba ta kai tasa ba, amma ba shi da nutsuwa da kwanciyar hankali. Yanzu mu tsaya a nan, ma ci gaba wani lokacin, zan je ɗebo wani magani ne" Nana ba ta yi magana ba ta ji Muhsin yana kiran sunanta, yana kiran ruwa. Ba ta motsa ba, ta ji Nene ta tashi ta nemo ruwan ta ba shi. Abubuwan da suka tattauna da Ƙaisar kaf suka dawo kanta. Ya gaya mata wasu abubuwa da hannalinta bai taɓa kai wa kai ba. Tabbas ɗabi'ar zuciya ce jin ƙyashi ko hassada ko son kai wasu lokutan, hakan na nufin ruhin mutum babu lafiya kenan yana buƙatar attention?. ***** Babu kowa a gidan, Mama ta ritsa Jamila, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali take tambayarta "Jamila ki gaya mini gaskiya, da gaske ne abubuwan da ki ke faɗa cewar kin shiga ƙungiyar asiri, ko kema aljanun ne suka taɓa ki ki ke wannan soki burutsun?" Jamila ta sunkuyar da kai. Ta taƙarƙare ta dunƙule hannu ta ɗirka wa Jamila dundu ta ce "Za ki gaya mini ko sai na danne ki da fulo na kashe ki?" "Ki daina duka na, ba soki burutsu nake yi ba, da gaske nake Hajiya Sa'a ta saka ni a ƙungiyar asiri ba tare da sanina ba. Ta ƙulla alaƙa da ni ne, saboda na kawo mata jinin Nana ta ba wa ƙungiyarsu ta yi arziki, da ban kawo jinin Nana ba ta saka ni a ƙungiya. A can aka fara lalata mini rayuwa, sannan tsautsayi ya sake shiga tsakanina da ɗanta Abba, cikin jikina da ya fita nasa ne. Shi ya sadaukar da kansa saboda kar da na bayar da kowa a ƙungiya, amma haryanzu aljanun ƙungiyar bibiyata suke yi, suna nema su kashe ni nima, wannan ce gaskiyar da ki ke son ji Mama, wannan ce bayan ita babu wata kuma" Kafin Mama ta yi magana suka ji muryar Baba yana kuka ya ce "Jamila kin cuci kanki, ba ki kyautawa kanki ba, Jamila ƙungiyar asiri, kuma aka nemi jinin Nana" "Wallahi Baba ban bayar da jinin kowa ba, ba dan son raina na shiga ba, ban san ya aka yi na shiga ba." "Rufe mini baki, ni ta wani fannin na gode Allah da na yi wa Nanan aure ma, ta bar muku gidan. Kuma ki tattara yaranki ku bar mini gida Rabi, ko ƙaunar ganinki bana son yi. Ku je ku da Allah" Yayi maganar yana kuka. Mama ta rasa bakin magana, tabbas ita da din ga ƙara tunkuɗa Jamila jikin Hajiya Sa'a, ba tare da tunanin abin da ka iya faruwa ba. Daga cikin ɗaki Jamila na kuka take faɗin "Dan Allah Baba kar ka yi mini baki, ka yi haƙuri ka yafe mini dan Allah, ko iya haka na sha wahala, ina kan sha ma na san ba tsawon rai zan yi ba, ba za su bar ni haka ba nima kashe ni za su yi" "Gara su kashe ki, sai ya fi mini kwanciyar hankali" Ya goge hawayensa ya fice. Yana fita ya ci karo da Ummi, ta kalle shi ta ce "Baba fita zaka yi, ina ta sauri saboda na cim maka, ina ta kiran wayarka amma ba ta shiga" Ya ce "Eh, fita zan yi Allah ya sa dai lafiya?" "Lafiya ƙalau, mu shiga daga ciki" Ya girgiza kai ya ce "Ba na son sake shiga cikin gidan nan" Ummi ta ce "Amma Baba meyasa, magana ce mai muhimmanci" Ya ce "Ki yi ta a nan kawai" Jiki a sanyaye ta ce "Ranar da 'yan uwan mijin Nana suka zo gurinka sun je gidana" Sai Baba ya gyara tsayuwarsa, ya ce "Yaya aka yi suka san gidanki?" Ta ce "Nima ban sani ba, amma har magana na yi da mijin Nana, ka san lokacin da suka samu matsalar nan, da ba shi da lafiya sun zauna a unguwarmu" "Haka ne, amma nifa ban yarda da abin da suka gaya mini ba" Baba ya nuna wa Ummi guri suka zauna, ya ce "Ummi da gaske ke kin yadda?" Ummi ta ce "Baba ga zahiri nan kana gani, tun daga Nijar suka taho fa. Sun gaya mini ma an so gyara maka gidan nan ka ce ba ka so" Ya ce "Bar ni Ummi, ni yanzu na shiga hankalina da al'amuran rayuwa, babu abin da ya kai kwanciyar hankali da nutsuwa daɗi" Nan ya bata labarin halin da suke ciki da Jamila. Jikin Ummi ya yi sanyi sosai da sosai, ta ce "Baba idan ka kori Jamila ina za ta je yanzu? Ƙaddara ce Allah ya aiko dole a yi haƙuri da ita. Yanzu dai sirukanka za su ranar Lahadi idan Allah ya kaimu, sun kira ni a waya, an ce ba a samun lambarka. Mijin Nana ya sai duk wani abu da za a tarbi 'yan uwansa da za su zo. Kawowa kawai za a yi kafin su iso. Dan Allah ka kwantar da hankalinka ka bar batun Jamila mutanen nan su zo lafiya su tafi lafiya. ***** Asal na kwance a gadon Asibiti, Hasna na gefenta ta riƙe hannunta, sai uban kuka take yi. "Hasna wallahi ina son Hammad, ji nake mutuwa zan yi idan ya sake ni, ga shi haryanzu ban san a wani bugiren ya ajiye ni ba, bai sake ni ba, bai ce mini komai ba. Babanmu ne duk ya janyo mini da zigar Imam Omar." "Asal ki yi haƙuri mana, kar ki illata kanki a kan sa, shi fa yanzu ya samu wata ne da yake rawar ƙafa a kanta, ke sai ki kashe kanki fisabilillahi" "Hasna ba ki san me nake ji ba, wai ni ce nake da kishiya, wadda na ɗauka ƙasƙantacciya mara galihu na shiga uku" Hasna ta rungume ta, ta din ga rarrashinta tana yi mata nasiha. Kwanan Yusuf huɗu da mutuwa, tsufan Alhaji Zailani ya sake fitowa, duk ya fita hayyacinsa ya yi wani iri. Alhaji Zailani ya zo duba shi, yana ta rarrashinsa yana ba shi haƙuri. Mutane jefi-jefi na shigowa su na yin gaisuwa. Wani mutum ne ya yi sallama, suka amsa masa ya shiga, duk suka bi shi da kallo, dan babu wanda ya san shi a cikinsu. AREWABOOKS Sai da suka Shukura ta biyo bayan mutumin, sannan suka rikice gaba ɗaya suka miƙe, banda Alhaji Zailani. Hajiya Amina ta nufi Shukura da gudu har tana neman faɗuwa, ta rungume ta cikin tsananin tashin hankali da manakin ganinta ta ce "Shukura, ke ce? Ina ki ka shiga aka din ga neman ki, ina cikin jikin naki?" Wani irin tausayin Hajiya Amina ya shiga ran Shukura, ta rungume Hajiya Amina tana kuka. Alhaji Fatuhu ma cikin matsanancin mamaki yake faɗin "Ikon Allah, Allah da girma da iko yake. Sannu Shukura" Alhaji Zailani dai yana zaune yana kallon su, bai ko motsa ba. Idanun Shukura suka sauka a cikin nasa, ta ji tamkar ta yi tsalle ta shaƙe shi, saboda wani abu mai ɗaci da ya tsirga mata. Mutanen da ya sabauta rayuwarsu, duk ga su a tare da shi a zaune. Ta ce "Mummy wai na ga rumfa a harabar gidan nan, me yake faruwa ne?" Hajiya Amina ta ce "Ba wani abu bane ba, Shukura ina ki ka tafi?" Kan ta ba wa Hajiya Amina amsa ta durƙusa ta gaida Alhaji Zailani ya amsa mata cikin damuwa ya ce "Shukura kin sanya mu a tashin hankali, meyafaru wannan bawan Allah kuma waye?" Shukura ta numfasa ta ce "Garkuwa aka yi da ni, wannan mutumin Likita ne, shi ne wanda ya taimake ni, a gidansa na ƙarasa jinya" Suka gaisa da mutumin, Alhaji Fatuhu ya din ga yi masa godiya. Hajiya Amina ta ce "Daddy, ba ka ga Shukura ba, Shukura ce fa ta dawo" Ya sauke numfashi ya ce "Na ganta" Alhaji Fatuhu ya ce "Haba Zailani, amma atleast yakamata ka yi farincikin dawowarta ko, yarinyar da ake ta nema ba a gani ba, ta dawo kuma ka yi fuska" Alhaji Zailani ya ce "Ni yanzu ta mutuwar ɗana nake yi, dan Allah ku ƙyale ni" A burkice Shukura ta ce "Wane ɗan nasa?" Tsit suka yi aka rasa mai yi mata bayani, Alhaji Zailani da kansa ya gaya mata Yusuf ne ya mutu. Shukura ta gigice cikin matsanancin tashin hankali ta hau kuka, tana faɗin "Shi ma ka kashe shi ko? Da ni ba a kashe ni ba sai ka kashe mini ɗan uwa, wallahi ba zan yadda ba sai na tona maka asiri Duniya kowa ya san abin da ka ke yi" Likitan da ya rako ta, ya tashi tsam ya yi musu sallama, ya ce zai dawo. Duk yadda suka so Shukura ta nutsu amma ta ƙi, ta din ga surutan da ba su gane kansu ba, kuma Alhaji Zailani ya yi mursisi ya yi shiru. ***** Nana jikinta har wani sheƙi yake yi, ta yi kyau sosai da sosai, sai dai ganin Hammad ya yi mata wahala, saboda yana ta kai kawon shirin bikinsu. Yadda ta lura lamarin ba da wasa suka ɗauke shi ba, sai gayyatar mutane suke yi. Bangaren Sultan yana ta shan suka, da ƙorafe-ƙorafe, a kan ya ci mutuncin Al'adar da aka gada daga iyaye da kakanni. Bai tsaya a iya nan ba, ya ayyana rushe majalisar Imam da ake da ita. Ya sauke Tafawa, ya sauke Sardaunanda wasu daga cikin muƙarrabansa, tare da cewar za a ayyana waɗanda za su maye guraben su, a lokacin shagalin bikin Hammad da matarsa ta ɓoye da zai bayyana wa Duniya yanzu. Nana a ranta take ƙara jinjina ikon Allah, sai dai tana ganin lamarin bikin nasu, kamar a ƙasar turawa, sun yi aure sun haihu har da ɗa, sannan za a yi shagalin bikinsu. Gefe guda sannu a hankali take ƙara yi wa kanta fashin baƙin, bayanan da Ƙaisar ya yi mata a game da rashin lafiya da ya ce ruhin ɗan Adam yana yi. Kuma ga yadda ta fuskanta, babu wani magani tattare da hakan face ka yadda kana da ciwon, sannan ka tsananta addu'a Allah ya raba ka da shi. Tabbas ko a kankin kanta ta ga misali, ta ƙara samun nutsuwa da yarda da komai lokaci ne, lokacin da take addu'a Allah ya kawo mata ɗauki a kan matsalolinta, gani take kamar ba za su wuce ba, kamar waraka ba za ta zo ba. Ashe wannan addu'a da take yi, ke ƙara samar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali, tabbas banda haka, da irin azabar da ta ci da tuni ta amince da al'amarin bori, ko ma haukace saboda wahala da yadda ratuwarta ke tafiya kamar ba ta mutane ba. Ta kalli yadda a yanzu ba ta aikin fari bata na baƙi, sai dai kawai a kawo mata ta ci, ta yi ibada ta kwanta. Sai dai ta dage da roƙon Allah, kar Ni'ima ta sanya ta shagala da neman kusancinta da shi. **** Gidansu Nana, Mama ta yi mamaki, ganin Uwani ta zo ranar Asabar, wai zata kwana, da azahar ma sai ga Ummi da uban kayan cefane, har ma da Yaya Atine. Mama ta ce "Wai lafiya duk na ganku, meke faruwa ne?" Uwani ta ce "Kamar yaya meke faruwa? Karɓar kayan auren Nana muka zo ayi da mu mana" Ta yi saroro ta ce "Nana kuma, wace Nanan?" "Nana wacce da wacce ku ke da ita a gidan nan? Ba dangin mijinta ne za su zo daga Agadez ba?" Mama ta ce "Ban fa gane ba, yaushe aka ganta" Uwani ta ce "Ke Ummi, ba ku gaya mata ba ne?" Ummi ta ce "Ina ga Baba bai gaya mata ba, Nana tana Agadez can hannun dangin mijinta, gobe in Allah ya kaimu za su zo kawo kayan aurenta" "Shi ne kuma dan munafunci ba a gaya mini ba? Kuma wane irin kayan aure kuma bayan wanda aka yi" Ummi ta ce "Wallahi nima ban sani ba, sai dai sun zo za mu ji" Mamaki ya cika Mama, domin babu wanda ya tsaya ya yi mata cikakken bayani, kamar ma ba a son ta ji abin da yake faruwa. Washegari tun ƙarfe sha ɗaya na safe, gidan abincin da aka sai Abinci a hannunsu, suka kawo abinci mai rai da lafiya cikin kuloli na alfarma. Baba ya din ga shiga yana fita, shi fatansa kawai ya ga Nana ba wai abin da za a kawo na auren ba. Da azahar motoci biyu suka iso, ɗaya guda ɗaya ta alfarma ɗaya kuma ta matafiya. Ƙaton carfet dama aka shimfiɗa a tsakar gidan, aka shirya wannan uban kayan Abincin. Manyan mutane ne, farare sol Turaki da Matawallen Agadez, sai kum Tafida, sai kuma Imam Zahradeen, Mahmoudu Sulei, sai kuma Imrana. Kai tsaye Imarana ya nufi Baba, aikuwa Baban ya rungume shi yana fashewa da kuka. Yadda ya ga Imarana a nutse cikin kamala kawai ya sanya shi mantawa da tarin baƙin cikin da yake ciki, kuma sai a lokacin ya gazgata mutanen nan da gaske suke. Imrana ya ce "Baba kar ka yi magana, ka ga mu na tare da baƙi" Baba dai kai kawai ya iya jinjinawa yana sake riƙe shi, kamar zai sake guduwa. Ta taga Mama take ɗan leƙowa, ta saki baki tana kallon ikon Allah, suturar jikin buzayen kawai ya fallasa cewar a cikin rufin asiri suke, ba ƙananan mutane ba ne. Bayan Baba ya ɗan nutsu, duk sun nemi guri sun zauna, suka gaggaisa. Imam Zahradeen ya ce "To Baba mun sake dawowa, mun zo mu cika alƙawari da muka ɗauka, waɗanan 'yan uwan mahaifinmu ne, ga shi muka zo tare da su" Suka sake gaisawa Matawalle ya ce "Ɗan uwa, Sultan ne ya aiko mu wakilci mussaman, mu zo mu yi godiya, mu jinjina wa namijin ƙoƙarin da ka yi, na aura wa ɗanmu 'yarka ba tare da sanin waye shi ba. Haƙiƙa mu yarinyarka alkhairi ga ahalinmu da ƙasar Agadez baki ɗaya ma. A madadin Sultan Jalaludeen ya ce "Mu ce maka mun gode, mun sake gode wa. Mu na tafe da dukiyar aurenta, kamar yadda ake yi wa kowace 'ya da ake yi wa kabilar buzaye. Sannan ya ce ita wannan 'ya yanzu ta zama tasa, yana kuma gayyatarka da duk wani wanda yake sha'awar zuwa, gagarumin shagalin bikin yaran nasa. Hammad da kuma Gimbiya Asma'u." Baba ya numfasa yana ganin abin kamar a mafarki, ya ce "To ai tun da dai da aure a tsakaninsu, a ganina da an haƙura da bikin shagalin nan" Turaki ya ce "To ai ɗan gidan mulki ne, abu ne aka yi shi da babu wanda ya sani, kuma ya saɓa wa al'adarmu, wands a dalilinta an soke al'adar ma gaba ɗaya, dan haka dole a yi shagalin bikin domin nuna wa Duniya ita. Saboda gudun abin da ka iya biyo baya, saboda mutum ne mai mulki mai faɗa a ji a garin Agadez. Dan haka nan da mako guda za a yi bikin, duk adadin waɗanda za su je, za a ɗauki nauyinsu tun daga ƙasa Nigeria har can, domin yin wannan shagali" Daga cikin ɗakin Uwani ta rafsa wata irin guɗa mai ɗan karen sauti tana faɗin "Alhamdillah" har sai da hankalinsu ya koma kan inda sautin guɗar ya fito. Gaddafi dai daga baya ya shigo, suka yi ido huɗu da Imrana. Imarana ya tashi ya nufe shi, rungume juna suka yi. Gaddafi ya ce "Imrana, wannan karon nisan kiwon naka har ya kai tsawon wannan lokacin?" Imrana ya ce "Wani nisan kiwo, kame ni a kayi, a ka kai ni makarantar dole, abubuwa ne da yawa suka faru" Ai tuni suka manta da wani batun ba sa jituwa, saboda girman alaƙar jini, suka din ga murnar ganin junansu. Daga nan aka shiga shigo da kayan auren Nana, sai da Baba ya saki baki, a ransa ya fara tunanin anya mutanen nan su na da hankali kuwa. Saboda shi yanzu al'amuran abin duniya tsoro suke ba shi. Domin karrama abin da su Baba suke da shi, su Turaki suka ci abincin da aka kawo musu. Aka gabatar musu da 'yan uwan Nana, Yaya Atine sai rawar kai take, tana nanata musu ita yayar Baban Nana ce uwa ɗaya uba ɗaya, ita ta saki Nono ya kama. Haushi sai da ya kama Imran, Gaddafi ma ya tsuke fuska ya ce "Matar nan duk abin da aka haɗa da ita sai ta yi hauka" Imrana ya ce "Har da wani ita ta saki nono ya kama, kamar nonon akuya, ko kunya ba ta ji ba, kamar ba da ita aka dinga muzguna wa Nana ba" Ta din ga rawar ƙafa tana jan su da hira, sai da ta ba wa kowa haushi. Da suka tashi tafiya kuwa, Haka Ummi ta shiga maƙwabta ta karɓo kayan da aka shirya, na tukuci da za su tafi da shi, dan kar ma wani ya sanya zalama. Kaji, da kayan snacks masu yawan gaske, da dabino kusan kwano biyar da tasoshin turare. Turaki ya ce karramawar da aka yi musu ta isa, ba za su karɓi komai ba, ai Nana 'yar Sultan ce. Gaddafi ya ce idan ba su karɓa ba, ba za su ji daɗi ba. Baba ya ga za su tafi ya yi musu godiya sannan ya ce "To ba za a kawo mini Nanan ba, ita yaushe zan ganta?" Imam Zahradeen ya ce "Zaka ganta Baba, sai kun zo Agadez biki, za ku ganta in sha Allah, ga Imrana mun kawo maka har gida ai" Jiki a sanyaye ya ce "Nanan dai nake son gani, amma shikenan mun gode sosai da sosai" Imrana ya ce "Tun da ni baya son ganina, bari na biku mu koma" Cikin sauri Baba ya ce "A'a Imrana, kai ma na yi murna da ganinka" Suka yi murmushi baki ɗaya, su Mahmoudu ya ce "Duk wanda za su je, a kira a gaya mana adadin mutane, za a ɗauki nauyin zuwansu da dawowar su, sannan kuma idan an gama ganin kayan da su za a tafi. Daga nan suka hau mota suka tafi. Da suka koma gida, aka fara sauke kaya ana bubbuɗewa, Baba komawa ya yi gefe ya fashe da kuka, domin hatta shi akwati guda aka yi masa. Uwani ta ce "Isa meye haka kuma, ai abin farinciki ne, ka daina kukan nan dan Allah" Maƙwabta ma ba a bar su a baya ba, suka din ga shigowa, sun ɗauka ko kayan auren Jamila aka kawo ko na Suwaiba. Mama baƙin ciki ya cika mata ciki, ganin yadda nata 'ya'yan duk suka zama abin da suka zama, babu wani na kirki, ta din ga cizon yatsan ina ma nata 'ya'yan ta saka aka aura wa buzun ba Nana ba. Uwani ta ce "Allah ba azzalumin sarki ba ne, Nana ta sha wahala a rayuwa, ta yi ɗawainiya da yaron nan, da jikinta da ƙarfinta. Allah ya yi tana da rabon jin daɗi tun a Duniya" Ummi ta ce "Wallahi Uwani, Nana ta sha wahala, da shi sosai da sosai, Allah ya nuna ikonsa. Kuma shi ma ya yi halacci" Uwani ta ce "Ba kaɗan ba, Allah dai ya ba su zaman lafiya" Imran ya ce "Dan ma ba ku ji wahalar da ta sha a Niger ɗin nan ba, da yawon nemansa" Nan Imrana ya gaya musu abin da ya sani. Yaya Atine ta ja baki ta yi shiru. Uwani ta ce "To Isa, ina fatan ya zame maka izina, akan abubuwan da ka aikata wa yarinyar nan. Kuma ya zama dole a kira mahaifiyarta a sanar da ita komai, kuma a yi shirin tafiya da ita gurin bikin nan, dan ba za ka ci gaba da wannan jahilcin ba" Imrana ya ce "To ai a Bauchi muka kwana, an je har gida an kai wa Umma lefen ta gani, an yi mata godiya sannan muka taho nan yau" Uwani ta ce "Ikon Allah, haihuwa mai rana" Duk yadda Mama ta so ɓoye ɓakin cikinta abu ya ci tura. Can gidan Umman su Nana, ta yi sujuda babu adadi na tsantsar murna da farinciki. Iliyasu kansa bakinsa ya ƙi rufuwa, amma ko kallo bai ishe ta ba. Dan ta wani fannin guduwar Nana, sauƙi ya sama mata, dan tun da ya san ya yi sanadin ɓatan Nana, duk abin da take yi masa baya cewa uffan. "Mai Jidda kin ga ikon Allah ko? Ashe ta wani fannin gara da Nana ta je neman mijin nata, da tana zaune a nan babu lallai su haɗu. Allah sarki rayuwa" Maijidda ji ta yi kamar ta make shi, ya ga abin Duniya, jikinsa sai tsuma yake yi. ***** Asal na zaune ta damƙe wayarta iya ƙarfinta, saboda ganin hoton katin gayyatar bikin taron bikin Hammad da matarsa, da kuma naɗe-naɗen sarauta. Hasna ta ce "Asal, ki ajiye wayar nan ki samu ki saka wani abu a cikinki mana" Ta girgiza kai hawaye na gangarowa daga idanunta. Ji suka yi an buɗe ƙofar ɗakin, suka ɗaga baki ɗaya. Hammad ne ya shigo, jikinsa sanye da shiga ta alfarma. Ƙamshin turarensa ya mamaye ɗakin baki ɗaya. Hasna ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi. Asal kuwa ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na tsananta bugawa cike da tsoro da fargaba, saboda ba ta taɓa tsammanin ganinsa ba. Kuma ba ta san me yake tafe da shi ba. Da yatsunsa biyu ya yi wa Hasna alamar ta fita ta ba su guri. Ayshercool 08081012143 100 LITTAFIN KUƊI NE, A BIYA KUƊIN KARATU KAN A KARANTA. 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 08081012143 Asal ta sunkuyar da kanta ƙasa, ji take yi tamkar ƙasa ta tsage ta shige, saboda matsananciyar kunyarsa da take ji. Ya ƙarasa ya zauna a gefenta, ya ce "Me ya same ki haka?" Ba ta ɗago ba, ta girgiza masa kai. Shiru ya wanzu tsakanin su, babu wanda ya yi magana. Ya ce "Tun da ba za ki yi magana ba shikenan" Har ya yinƙura, ta riƙe rigarsa ta ce "Sakina ka zo ka yi ko?" "A'a, dama ai ni ban kore ki ba, na dai ba ki zaɓin zama da ni ne, amma na ga kamar ke da mahaifinki, kun fi gamsuwa da na sauwwaƙe miki." "Dan Allah Hammad ka yi haƙuri ka yafe mini, na san laifukana ba za su ƙirgu ba, sai a wannan karon Allah ya tona asirina" Yayi murmushi ya ce "Ba zan yi miki dole ki zauna da ni ba, muddin kin san zuciyarki haryanzu tana son Omar" Wata irin ɗagowa Asal ta yi a razane jin abin da ya ce. "Hmm Asal kenan, duk tsawon zaman da na yi da ke, babu abin da ban sani ba, kar ma ki yi zaton ko wani ne ya gaya mini. Saka mini magani da duk wani nau'i na ƙoƙarin illata ni da ki ke yi, duk na sani, kuma ina kallonki. Ba domin babu yadda zan yi da ke ba, sai domin ina jin tausayinki, kuma ke ƙanwata ce" Zamowa ta yi ƙasa cikin kuka ta riƙe rigarsa ta ce "Wallahi na yi nadama Hammad, na san ko ba ka ce mini komai ba, Hakkinka ba zai bar ni ba. Amma ba laifina ba ne ba, ka sani dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, kar ka sake ni. Wallahi ina sonka" "Dama ai ban ce zan sake ki ba, mahaifinki ne ya nemi hakan, kuma nima na so aikatawa amma na duba idan na yi haka, ba ki da wata kyakykywar makoma, bayan gama lalata rayuwarki da aka yi. Kuma ba na son asirinki ya ci gaba da tonuwa a idon Duniya. Uwa uba Nana tana ta yi mini magiyar kar na rabu da ke. Na so samarwa kaina cikakkiyar nutsuwa da rayuwa da wadda bata harin komai daga gare ni sai alkhairi, amma ban san me Allah zai yi mini a sanadin yafe miki ba. Asal zaki koma ɗakinki bisa sharaɗi, dan ta ni ko yanzu ki ci gaba da duk abin da ki ke yi mini, bai dame ni ba; amma muddin ki ka yi wani na yinƙurin cutar mini da matata ko ɗana, wallahi sai na ɗaure ki, ɗaurin rai da rai ma kuwa. Ba zan taɓa yin wasa da duk wani abu da ya shafe su ba, dan haka zaki amince da babu ruwanki da duk wani abu da ya shafe su, balle a zo ga batun cutarwa" Wani abu raɗaɗi ya tsirga wa Asal,  wai ita ake gindaya wa sharaɗi a kan Nana. Sai dai babu yadda ta iya ta jinjina masa kai ta ce "Na amince" Ya ce "Ki yi tunani da kyau, kar ki saɓa abin da ki ka ce daga baya, na ɗauki mataki ki ji haushina" "Na tabattar da na amince" Ya ce "To shikenan, tashi" Sai dai ƙafafuwanta suka yi mata nauyi, ta kasa tashi, saboda haryanzu tana jin nauyinsa, kenan har soyayyar da suka yi da Omar ya sani, amma ya ƙyale ta a gidansa. Babu tsammani ta ji ya saka hannu ya ɗago ta tsaye. Ya ce "Na saka an ɗan yi mana gyara a gida, zan canza miki komai. Har cikin zuciyata na yafe miki, na san wasu abubuwan ba laifinki ba ne, kuma ko dan kusanto da Nana gare ni da ki ke yi yakamata na yafe miki. Allah ya sanya kin yi tabbataccen tuba" A duk lokacin da ya ambaci Nana, sai ta ji baƙin ciki kamar ya halakka ta. Ya sumbaci goshinta, ya mayar da ita kan gadon ya zaunar da ita, ya ce "Allah ya baki lafiya" Daga haka ya juya ya fita. Wani irin kuka ta saka, gaba ɗaya alamu sun nuna, a yanzu baya ganin mutuncin komai idan ba na matarsa da ɗansa ba. Ƙarara a idonsa da mu'alarsa ake iya karanto tsagwaron son da yake yi wa Nana. Duk da yadda Sultan ya yi watsi da Imam Zahradeen, amma bai yi zuciya ba ya yi uwa ya yi makarɓiya a kan shirin gudanar da bikin ɗan uwansa. Tuni baƙi suka fara hallara, aka ɗauke Nana daga cikin gidan Sultan, zuwa estate ɗin da yake mallakin masarauta, da galibi ake saukar baƙi a can. Estate ɗin da sunan Hammad aka saka masa, wanda a nan ta fara zama tare da Asal da ƙawayenta a ɗaya daga cikin gidajen. Nana ba ta yi zato ba, ba ta yi tsammani ba, kawai ta tarar da mahaifiyarta da ƙannenta su Walida. Gaba ɗaya Nana ta yi wata irin rikicewa, jikinta ya hau tsuma. Maijidda da kanta ta tashi ta nufi Nana cikin farinciki. Nana ta faɗa jikinta ta rirriƙe ta, cikin dashewar murya ta ce "Um.umm.Umma! Umma ki yi haƙuri dan Allah" Maijidda ta ce "Shhh, kar ma ki kawo wannan zancen, ni yanzu lokacin farinciki ne da murna, dan haka kuka ya ƙare. Abin arziki da farinciki ne ya tara mu. Ni dai na gode wa Allah da ya sanya ina da rabon sake ganinku cikin kwanciyar hankali da kuma ƙoshin lafiya" "Umma idan ba ku yafe mini ba, hakkinku ba zai bar ni ba, na yi wauta na yi shirme, na bar ku da fargaba da kuma zullumi." "Duk ya wuce, ya zama tarihi, Alhamdillah tun da Allah ya amsa addu'armu ya haɗa mu cikin aminci da kwanciyar hankali." Tuni idanun Nana suka rine zuwa jawur, ta ƙanƙame Maijidda duk da babu wata shaƙuwar a zo a gani a tsakaninsu, amma wani irin abu ne mara misaltuwa Nana take jin sa a zuciyarta game da Umman nata. Ta ƙwaƙume ta, ta ƙi sakinta ta kwanta lamo a jikinta. Maijidda ta ce "Ai mijin naki ma ya zo mun gaisa, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Na ce a kawo mini jikin nawa na gan shi, aka ce mini yana ƙarƙashin kulawa ta musamman, zan gan shi amma ba yanzu ba" Nana dai babu baki, ba ta iya cewa komai ba. Sai yanzu take ƙara jinjina girman laifin da ta aikata. Ta tuna lokacin da aka raba ta da Muhsin na ɗan kwanaki tashin hankalin da ta shiga, ita kuma ta bar gida kusan shekara uku ba ta waiwaya ba, kuma still ana rarrashinta. Nene ce ta zo, tare da hadimai, da tarin kayan abinci, tare da su Anty Fati 'yan uwan Mai jidda da ta su motar isowarta kenan. Babu abin da Nana take yi sai gode wa Allah, sai murna suke yi da ganinta, tare da taya ta murnar matsayin da Allah ya ɗaukaka ta ya kai ta. Nana ta ce "Nene ga Ummana, Umma ga Mamana ta Niger ni yanzu a iyaye bayan ke, ba ni da wata uwa da ta wuce Nene. A hannunta na haifi Muhsin, ban san ya zan misalta miki riƙon da Nene ta yi mana ba Umma. Ki yi mata godiya." Nene ta ce "Dama idan uwa ta yi wa ɗanta abu, sai an yi mata godiya ai hakkinta ne ta yi" Ta miƙa wa Maijidda hannu suka gaisa, su Anty Fati suka hau yi mata godiya. Nene ta ce "Ni ina ƙaunar Nana saboda Allah, dan haka duk abin da na yi mata ina jin kamar na yi wa ɗan cikina ne" Sam ranar Nana bata rintsa ba, ji take yi tamkar mai Jidda ta mayar da ita cikinta, gani take idan ta yi bacci zai zamana abin da yake faruwa mafarki ne. Aka din ga ɗawainiya da su, Maijidda da ta taho da 'yan kayanta, na ƙara gyara Nana, yadda ta ga Nene na faɗi tashi a kan Nana, sai ta kasa komai. Washegari su Imrana suka iso, mota uku ta 'yan Kano, hatta Suwaiba da ba ta da cikakken hankali, da Jamila da babu cikakkiyar lafiya, haka Mama ta tarkata ta taho da su. Saboda a yi komai a kan idonta. Ana cewa ga motar su Baba can, Nana ta zabura za ta yi waje, Nene ta ce "Nana ya haka? Dole fa ki canza yadda ki ke gudanar da al'amuranki, da da kuma yanzu ba ɗaya ba ne ba. Ki bari za su shigo ai. Ummi ce ta fara shigowa, suka rumgume juna ita da Nana suka fashe da kuka. Su Uwani ma suka shigo gaba ɗaya sai falon ya kaure da koke-koke. Uwani da Ummi kamar su haɗiye Nana, Uwani ta ce "Ummi ke ce haka? Kin ga wani irin kyau da ki ka yi?" Nana ta yi murmushi. Ta riƙo hannun Jamila cike da farinciki, duk ƙasan zuciyarta cike yak da mamakin, yadda ta ga Jamila ta yi wata uwar rama mai ban tsoro. Duk da ba miji ɗaya suke aure ba yanzu sai da Mama ta yi turus ganin Mai Jidda, ba ta taɓa zaton za ta ganta gurin bikin Nana ba. Ta ganta tsaf da ita cikin nutsuwa. Uwani ta zauna kusa da Maijidda da su Anty Fati, suna hirar yaushe gamo. Nana dai kasa hirar ma tayi da su, gaba ɗaya kunyarsu ta hana ta cikakken sukunin haɗa ido da su. Bayan sallar isha'i, barori suka nemi da a yi shiru, Imam Hammad zai shigo. Aikuwa kamar ruwa ya cinye kowa aka yi shiru. Shi ne ya shigo tare da Mahmoudu, da hadaimai biyu, suka tsaya a bakin ƙofa shi kuma ya shiga. Yana ganin Uwani ya saki murmushi, ya tafi gabanta ya durƙusa. Ta ce "Ɗan nan, dama babban mutum ne kai? Ka gane ni?" Ya ce "Ɗa ba zai manta uwa ba ai, kuma ɗan halak baya manta alkhairi. Ba zan manta da ke ba, Allah ya saka da alkhairi" Ta ce "A'a ai ɗa baya yi wa uwa godiya, mun same ku lafiya?" Ya ce "Alhamdillah" Ya kalli Ummi da take ta murmushi ita ma, ya ce "Babbar Yaya, fatan kun sauka lafiya, kuma kun ji daɗin ƙasar tamu" Ummi ta ce "Alhamdillah, mun same ku lafiya?" Ya ce "Lafiya ƙalau, ina sake amfani da wannan damar, gurin sake baku haƙuri, da abin da Asmy ta yi, duk laifin a kaina yake, nine mai laifin amma ina bayar da haƙuri dan Allah a yafe mana. Sannan ina sake yi muku godiya sosai da sosai, Sultan ma ya ce a gaishe ku" Waɗanda ba su san shi ba, suka din ga yaba kyawu da kamalar Hammad. Daga nan ya nemi zai tafi da Nana, za ta je gurin su Baba inda suka sauka su gaisa, sannan a dawo da ita. Su na shiga mota, ya kwanta a jikin Nana yana sauke numfashi ya ce "Da na yi niyyar idan aka gama taron nan, ki yi kwana biyu ki huta, sannan ki tare amma gaskiya yanzu na fasa, ji nake kamar na gudu da ke" Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bari a kwana biyun" "Ba zan iya ba, ana tashi kawai a kai mini ke gida, gidanki ya kammala komai an saka mana, mukaɗai muka rage mu shiga" Yayi maganar yana sumbatar bakinta. "Ya naga jikinki ya yi sanyi ne, kamar wata amarya?" "Wallahi Sayyid tsoro nake ji, ban san da wani idon zan kalli Baba ba, ban kyauta ba abin da na yi ko kaɗan" "A'a ki kwantar da hankalinki, Baba fa tun kafin su zo, na tura an ba shi haƙuri, yau da suka zo an kai shi har gurin Sultan, ya ba shi haƙuri, nima na je na same shi, shi duk damuwarsa ma ya ganki ne. Babu wani abu in sha Allah" Haka suka ƙarasa jikin Nana a sanyaye duk a tsorace take. A wani sashi na gidan Sultan, aka sauki su Baba, tare da Imrana da Gaddafi. Nana ta tsaya cak, ta sanya hannayenta, ta toshe bakinta, wani irin kuka mai ƙarfin gaske yana kufce mata. Gaddafi ne ya taso ya riƙo hannunta, ya ƙarasa gaban Baba da ita. Sai da Sayyid ya ji wani iri, duk da kasancewar Gaddafin yayanta ne. Nana tun da ta buɗe ido, Baba bai taɓa rungume ta ba sai yau, tana kuka yana kuka. Da kyar maganarta take fita ta ce "Baba ka yi haƙuri, ka yi haƙuri dan Allah ka yafe mini. Baba na yi wauta da rashin hankali Baba ka yi haƙuri na san na sanya ku a tashin hankali" Sai da Baba ya yi kuka mai isar sa sannan ya iya furta "Babu komai Nana, ni dai na gode wa Allah tun da kina nan cikin ƙoshin lafiya, Alhamdillah, Alhamdillah na gode wa Allah". Haka ta rungume Nasiru ma tana kukan farinciki, ta ƙara tabattar da duk lalacewar naka naka ne, ta shiga farinciki mara misaltuwa da ganin ahalinta a tare da ita. Har Alhaji Fatuhu ya tafi ranar, Shukura ba ta yi musu bayanin komai ba, sai dai ta kaɗu ta shiga tashin hankali da mutuwar ɗan uwanta. Hajiya Amina ma babu rarrashin da ba ta yi mata ba, amma ba ta yi mata bayanin komai ba. Washegari da rana, sai ga Yusra tare da Sagir da Hajiya Halima da Siyama. Hajiya Amina ta karɓe su hannu bibbiyu. Ta ce "Sagir na zata zan ganka tun a jiya, na kira gidanku na sanar da Shukura ta dawo. Ya ce "Mummy bana gari ne, ina can Abuja fa, Yusra babu lafiya" "Wai Yusra haihuwa ki ka yi ne?" Mummy ta yi maganar tana kallon ta. Shukura ce ta fito, Yusra ta ajiye wa Sagir yaron, ta nufi Shukura ta ce "'yar uwa babu abin da ya same ki ko?" Shukura ta jinjina kai ta riƙe hannun Yusra ta ce "Yusra na gode sosai da sosai, na gode" Yusra ta rungume ta tana rarrashinta. Shukura ta ce "Mummy, ki kira Daddy a yi komai a kan idonsa, na kira Baban Rauda ma a wayarki" Cikin rashin fahimta ta ce "To wai meyafaru?" Shukura ta ce "Shi zan yi bayani" Tana rufe bakinta, Alhaji Zailani ya fito, ya tsaya yana kallon Yusra da kuma Shukura. Yayi murmushi ya ce "Har gangami ki ka yi na tona mini asiri Shukura? Shikenan, mu jira zuwan Fatuhun, ai tun da ki ka dawo na san za a yi hakan." Gaba ɗaya suka tsaya su na kallon Shukura. Hajiya Amina ta ce "Shukura mene wai? Alhaji ka yi mini bayani mana" Su na cikin maganar, Alhaji Fatuhu ya ƙaraso gidan, ya tarar da su a tsaye a falo. Ya ce "Hajiya Amina lafiya kuwa? Shukura ta kira ni a waya ta ce lallai na zo" Hajiya Amina ta ce "Wallahi nima ban san abin da yake faruwa ba, shi ma na ji yana zancen za a tona masa asiri na kasa ganewa" Ya kalli Shukura ya ce "Shukura, mene ne ki yi mana bayani" Shukura ta yi shiru tana kallon Alhaji Zailani, amma ta kasa magana, kawai ta fashe da kuka. Yusra ta ce "Ina gida wayar Baban Haidar ta lalace, ya saka layinsa a wayata, Shukura ta kira ta ce tana wani Asibiti a can wata ƙaramar hukuma a Kano. Wai garkuwa aka da ita ta kuɓuta, wata mata ta tsince ta, ta kaita Asibiti. Na ce ba zan tafi ba sai tare da ita, da magariba wasu suka zo Asibitin su na nemanta za su kashe ta. Shi ne na tafi da jaririn, ni ban ma san yadda aka yi ba na ganni a gidanmu na Abuja daga Asibitin. Amma babanta ne ya saka a sace ta" Gaba ɗaya suka kalli Yusra cike da mamaki. Alhaji Fatuhu ya ce "Kin san me ki ke faɗa kuwa?" Yusra ta ce "Na sani mana, ba fa ƙarya nake yi ba. Ai ita da kunya ta ce ga abin da ya yi, amma ni dai ku yi haƙuri na faɗa" Alhaji Fatuhu ya ce "Amma kamar an ce ai ba ta da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, wataƙila... Shukura cikin kuka ta ce "Yusra ba ƙarya take yi ba, Daddy ne ya sanya a sace ni, saboda ina bin diddigin yadda aka ce jaririna ya mutu, kuma saboda ya bayar da jaririna a matsayin sadaukarwarsa ta shekara a ƙungiyar asiri. Na so rufa masa asiri na yi shiru, amma ba zan iya ba, mussaman idan ina kallon mutanen da ya zalunta, da yadda yake ganin bayan rayuwarsu. Ni Yusuf ma ina kyautata zaton shi ne ya bayar da shi a kungiyar" Cikin tsawa Alhaji Fatuhu ya ce "Shut up Shukura, mahaifinki ne fa, ki ke yi masa wannan tonon sililin a gaban mutane. Kuma tayaya za ki haɗa kai da abokiyar zaman ki, ku yi masa wannan ƙazafin?" Shukura ta ce "Ko zan yi wa kowa ƙazafi yaya za a yi na yi masa? Bana jin komai ko a gaban waye zan tona masa asiri, iyaka dai a yi mini gori wataran hakan ba zai dame ni ba. Ɗana ya ɗauka ya bayar aka yi tsafi da shi aka yi maka asirin da ka rasa komai ka yi rashin lafiyar nan. Suka haɗa baki da Doctor Sharif aka yi mini tiyata aka ba su jaririna. Tayaya zan iya rufa wa mutumin da ya yi mini wannan zaluncin asiri?. Nan Shukura ta din ga faɗar miyagun ayyukan da Alhaji Zailani ya gaya mata ya yi da bakinsa. Wani irin bugu zuciyar Hajiya Amina ta yi, take ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, tamkar an zare mata lakar jikinta. Wani irin gumi ya fara tsatsafo mata ko ta ina. Alhaji Fatuhu bakinsa na rawa ya ce "Zailani, abin da yarinyar nan ta faɗa haka ne, ko kuma ɗimuwa ta shiga ne?" Yayi shiru bai yi magana ba, sai tsare su da idanu da ya yi. Sagir ya ɗan daddana wayarsa, mutumin nan da suka zo tare da Shukura ne ya shigo, tare da wasu ƙarti majiya ƙarfi su uku. Bayan ya yi musu sallama, ya yi musu bayanin shi jami'in tsaro ne, kuma Likita, shi ne ya haɗu da Shukura a lokacin da nutanen da Alhaji Zailani ya tura, suka gano ta, suka yi yinƙurin kashe ta, ya yi amfani da ƙwarewar aiki, ya kama mutum biyu daga ciki. Kuma sun tabattar da Alhaji Zailani ne ya saka su wannan aiki. Bakin Hajiya Amina na rawa, da kyar ta ce "Me na yi maka haka Zailani?" Daga nan ba ta sake cewa komai ba, ta silale ta faɗi ƙasa. Alhaji Fatuhu shi ma kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi ya yi, ji yayi tamkar numfashinsa zai ɗauke. Sai yanzu wasu abubuwan da suka faru suke dawo masa, amma bai taɓa zaton Alhaji Zailani zai iya aikata masa wannan mugun abun ba. Kafin a bar gidan da shi, ya tsaya ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Kar ka yi mamakin abin da ya faru, domin ban taɓa sonka ba, duba da yadda ka fini ta ko ina, kuma ban yi nadamar abin da na aikata maka ba. Duk abubuwan nan da na yi babu wata cikakkiyar shaida da za a iya kama ni da laifi da ita, balle a hukunta ni. Sai shaidar sace 'yata da na yi, wannan ma na san yadda zan fitar da kaina. Sai dai dole mu yi mutuwar kasko, domin ba ni kaɗai ba ne a ƙungiyar asirin, har da yayarka, da ta sadaukar naka da ɗanka da ya mutu, dan haka ko wani mataki zaka ɗauka a kaina, sai ka haɗa da ni da ita, gara ni abokinka ne kawai, ita kuma 'yar uwakka ce!". ***** Nana ta so sanya kayanta na Nigeria, a gurin bikin nan, Hammad ya ce shigar buzaye za a yi mata. Ta sha gyara ta yi kyau. Agadez ta ɗinke da tarin jama'a. Tun daga kan gashin kanta, lungu da saƙo na jikinta, babu inda bai ga gyara ba. Sai da ta tuna da lokacin bikinsu na farko, yadda aka kawo mata shadda ta alfarma. Yanzun ma haka ne, rigar ta sha aiki ita kanta shaddar ƙamshi take yi na musamman. Babu babban abin da ya razana Nana, irin sarƙar da aka saka mata ta gold da ta sauka har cikinta. Ta kalli mai kwalliyar ta ce "Ni gaskiya a cire mini wannan sarƙar ba zan iya saka wa ba, fariyar ta yi yawa" Matar ta ce "Ba fariya ba ce shugabata, ado ne na mutanen ƙasar nan, dan Allah kar ki ji wani abu, ai ana kammalawa dole za ki cire ne" Sai da aka yi ta fama da Nana sannan ta haƙura, gani take yi kamar ba ta hanyar da ya dace ta yi wa Allah godiya ba kenan, da wannan fariyar. Ta din ga istigfari, da fatan Allah ya sanya kar hakan ya sanya ta ji wani abu na girman kai ko tinƙaho. Ƙaton ɗakin taro ne, ta kowane ɓangare mutane ne, daban daban, 'ya'yan sarakuna da manyan mutane gurinsu daban, ɓangaren danginta daban, abin har ya fara bata tsoro ta ji kanta yana juyawa. Ba iya wannan ba, shi kansa Muhsin da kusan kwana biyar rabon ta da shi, an yi masa ado, kayansa iri ɗaya da na mahaifinsa. Aka buɗe taro da addu'a, da karanto jadawalin abin da za a gudanar a gurin. Aka fara da sake tabattar da rushe majalisar Imam, da zimmar duk wani ɗan sarki Imam ne, amma babu majalisarsu, da kuma cewar lallai su za su gaji sarauta. Aka sanar da sauke wasu daga manyan makusantan Sultan, ba tare da faɗar cikakken dalili ba, sai cewa saboda za a yi gyare-gyare ne a masarautar Agadez. Aka gabatar da roƙo ga gwamnatin tarayya, a kan ta bayar da tallafi su haɗu da masarautar Agadez, a gyara gidan tarihin nan, a faɗaɗa shi a ƙawata shi, ya zamana gurin buɗe idanu sosai ga baƙi. A kuma gina Hotel a ciki ko wajen gidan, saboda samar da masauki ga baƙin da za su din ga zuwa yawon buɗe ido. Daga nan aka sake jaddada dokar, halattawa ƙabilar buzaye auren duk matar da suke so, daga kowace ƙasa. Aka yi ta kaɗe-kaɗe ana shiga ana fita da abinci kala-kala. Daga bisani aka yi wa Imam Hammad naɗi aka ba shi sarautar Sardaunan Agadez, yayin da Imam Zahradeen aka ba shi sarautar Tafawa. Sai kuma abin da ba a taɓa tsammani ba, Sultan ya yi wa Mahmoudu Sarautar Tafeedan Agadez, tare da ba shi auren ɗaya daga cikin 'ya'yansa, wanda za a gudanar a nan take. Gigicewa Mahmoudu ya yi, Nana ma ta waro idanu saboda mamaki. Hammad kuwa ya sani, tare da Sultan suka shirya komai. Kuma ya tabattar ƙanwar tasa ta amince da auren Mahmoudu, ita ma tata mahaifiyar rasuwa ta yi, ita ce 'yar autarsu. Dama ba shi da matsala da Mahmoudu, kuma ya fuskanci su na shiri sosai, shiyasa ya nemi alfarmar Sultan ya yi wannan haɗin. Aka fito da Muhsin, aka gabatar da shi, a matsayin ɗan Hammad, da Duniya ba ta san da shi ba, kuma a ka yi masa naɗin Imam kuma Yariman Agadez mafi ƙarancin shekaru a tarihin Agadez, haka zalika kuma Imam da mahaifiyarsa ta sauya tarihin Agadez baki ɗaya. Nan manyan mutane suka din ga bajinta, da gwangwaje Muhsin da tsadaddun kyaututtuka na ban mamaki. Har sai da Nana ta kalli abin a matsayin Almubazzaranci. Daga bisani aka din ga koɗa Nana ana yi mata kirari, ita ma aka gabatar da ita, a matsayin matar sabon Sardaunan Agadez, kuma mahaifiyar Yarima. Nana gaba ɗaya sai ta rikice, kawai ta fashe da kuka. Aka bata mic a kan ta yi magana, amma ta kasa ƙarshe kawai ta yi sujudu shukur a gurin, jikinta na tsuma tana wani irin kuka. Hammad ne ya din ga rarrashin ta, yana ankarar da ita ranar farin ciki ce a gare su. Ba a bar uwar Yarima haka ba, sai da ta samu sarautar Garkuwar matan ƙasar Agadez. Haka matan manyan mutanen nan, suka din ga guɗa, suna yi mata kyaututtuka. Hammad ya yi godiya ga tarin al'ummar da suka halarci taron, tare da fatan ɗorewar Canjin da aka samu, na halatta auratayya da kuma tabattar da 'yancin kowane kalar fata. Ya yi godiya ga dangin Nana, tare da jinjina mata, da kamba mata a gaban tarin jama'ar nan. Duk bai fito ya bayyana wa mutanen abin da Nanan ta yi yake ta wasa ta ba, amma ya nuna wa Duniya yana ƙaunar Nana, kuma komai zai yi ba zai taɓa biyanta soyayyar da sadaukarwar da ta yi masa ba. "Haƙiƙa yau rana ce mai girima, da ɗumbin tarihi a gare ni, da ma al'ummar ƙasar nan, duk da akwai ranar da ta fi ta da ba zan manta da ita ba, ranar da na mallaki Gimbiya Asma'u a matsayin matata. Ba ni da kalaman da zan yi amfani gurin yi mata godiya, da nuna muku girma da matsayinta a rayuwata ba. Ni dai na san halitta ce mai girma, da ta cancanci na wasa ta, na yabe ta, na so ta na kambama ta ko a ina ne. Asma'u ke rayuwata ce" Ya ƙarasa maganar a raunane. "Allah ya yi miki mafificin tukuici. Haka zalika ba zan manta da ɗan uwana ba, ba sabon Tafawan Agadez ba, dama wannan yayana ne. Ina nufin Tafeedan Agadez. Ba ni da abin da zan iya faɗa, sai dai za ku dauwwama a cikin zuciyata da kuma addu'ata. Sai mai gayya mai aiki uba na gari mai girma Sultan uban ƙasa uban kowa da kowa. Mu na godiya da tarin karamci da dattakunka a gare mu. Iyayena na Nigeria, kafataninku muna ƙara sake miƙa godiya a gare ku" Nana kam kasa jurewa ta yi, ta rasa ma kukan me take yi, na murna ne ko kuma na damuwa. Ba Nana ba hatta iyayenta, sai da suka yi kukan murna, Baba bai taɓa tsammanin a zuriyarsa za a samu irin wannan tagomashin ba. Sai dai shi Allah, mai aikata abin da ya so ne a lokacin da ya so, ya kan ɗaga abu a lokacin da ya ga dama, zuwa ƙololuwar matsayin da zato bai taɓa zata ba. Taro ya watse lafiya, aka tashi cikin farin ciki, duk da zukatan maƙiya ba haka suka so ba. Ai kamar yadda Hammad ya ce, a ranar za ta tare, babu wani abu da ya yi saura da ake jira. Batun sabbin naɗe-naɗen da aka yi, ya sake cika gari, wasu suna ganin Sultan ya nuna son kai, gurin cire manyan mutane masu muƙamai, ya bawa 'ya'yansa. Nana ta so ta huta kafin ta tare, amma Maijidda ta ce a'a, tun da haka mijinta ya ce yana so. Baba duk abin sa, sai ga shi ga babar su Nana, a gurin bikin Nana. Abin mamaki Imrana ne ya sanya su a gaba ya din ga yi musu nasiha, da nuna musu illar gabar da suka din ga ya haifar musu. Nene ta riƙe hannun Nana ta ce "Gimbiyarmu, dan Allah a yi mana godiya, tabbas Hammad ya cika jagora, na ji daɗin abin da ya yi wa Mahmoudu, Ubangiji Allah ya saka da mafificin alkhairi" Gaba ɗaya Nana ta so ta sake sosai a cikin 'yan uwanta. Hammad yana ta shiri a ɗakinsa, Mahmoudu ya shigo, dan bai samu sukunin haɗuwa da Hammad ba, saboda karɓar baƙi. Hammad ya kalle shi ya ce "Ango ka sha ƙamshi" Ya buɗe baki zai yi magana, Hammd ya girgiza masa kai ya ce "Ɗan uwa kai ka ke bi na bashi, dan haka babu buƙatar wani dogon jawabi ko godiya a tsakaninmu, mai girma Tafeeda Allah ya taya riƙo" Ya yi maganar yana fesa masa turaren hannunsa. "Sardaunanmu, godiya ta zama dole a tsakaninmu ai, godiya dole na... Hammad ya tsuke fuska ya ce "To jeka waje ka yi godiyar" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Wallahi jin abin nake kamar a mafarki, bawa ya zama saraki ikon Allah, amma kana ganin Hanin ta amince da auren nan, tsakaninmu ba soyayya raha ce dai da girmama junanmu" Hammad ya ce "Ka na tsoro ne? Hanin na sonka, da amincewarta aka yi komai". "To kuma tana son baƙar fata" Hammad ya yi tsaki ya ce "Ka na da abin haushi wallahi. Kaf ƙabilar buzaye, ban taɓa ganin baƙi mai kyanka ba, har fararen ma, idan kuma duk baƙar fata gaba ɗaya matata ta fi kowane baƙar fata kyau" A tare suka yi dariya. Hammad ya ce "Kai mutumin kirki ne, mai nagarta na san na yi wa ƙanwata kyakykywan zaɓi ne, dan haka ba ni da fargaba" Suka ci gaba da tattaunawa cikin raha. Nana tamkar wadda za ta yi sabon aure, haka aka zaunar da ita aka din ga yi mata nasiha, Mai jidda ta nanata mata batun riƙe addu'a a duk inda take. Sai da aka kai ta har gurin Sultan nan ma ya yi musu nasiha sosai ita da Hammad. Daga bisani, Hammad ya ɗauke ta daga can gurin Sultan suka tafi, ya ce akwai walimar cin abincin dare tare da ita da danginta kaɗai, washegari kafin su wuce Nigeria. Asal kamar za ta mutu, haka take wani irin kuka tana rirriƙe Hasna. Tafawa ne yake ta bala'i ya ce "Wallahi ko za ki mutu sai ya sake ki, ban ga amfanin ki ci gaba da zama da mutane marasa mutunci ba, babu kunya babu tsoron Allah Jalaludeen ya sauke ni daga kujera ta, ya bawa 'ya'yansa, zai ga matakin da zan ɗauka a kansu." Asal ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, amma zan koma gidan Hammad, iya rufin asirin da ya yi mini ya isa, na yi maka biyayya iya yi na, amma ƙarshe na faɗa halaka, kuma buƙatar taka bata biya ba" "Wallahi Asal ki ka koma gidan Hammad babu ni babu ke, na gaya miki sai dai ki canza uba!" 101 Alhaji Sabo ya ce "Ya na ga ka tsaya cak haka?" Da kyar ya harhaɗo maganganun ya ce "Sabo, ce mini kai fa Amina ta mutu?" Ya ce "Eh mana, ranar da ta mutun mutane na ta tambayar ina ka ke, aka ce kana Asibiti, likitoci sun hana a zo gurin ka. Yanzu sai ka maze duk wanda ya yi maka gaisuwa ko ya zo dubiya kawai ka amsa. Ita kuma Shukura lallai ka san yadda za ka yi da ita, ka ɗauki mataki a kanta, ko kuma ka gaggauta bayar da jininta ga ƙungiya kawai" Ya yi shiru bai sake cewa komai ba, har suka isa gidansa, mutane na ganinsa suka din ga zuwa yi masa sannu, suna yi masa gaisuwa. Bai iya amsawa kowa ba, Alhaji Sabo ya ce su yi haƙuri ba ya iya magana, saboda yanayin jikinsa. Har sashensa Alhaji Sabo ya raka shi, suna zuwa ya tarar da hijjabin Hajiya Amina da sallayarta gurin da ta yi sallar walha, kafin ta fita ta bar ɗakin su Sagir su zo. Ya ɗauki hijjabin ya kalli Alhaji Sabo, ya ce "Kana nufin Amina ta mutu? Kalli hijjabinta fa inda ta yi salla" Alhaji Sabo ya ce "To shi ne me, kowa ma na haka ne ai. Kana ganin zaka iya zama a gidan nan kai kaɗai, ko a samo maka wanda zai tayaka zama?" Ya girgiza kai jiki a sanyaye, duk da mutuwar Yusf ta dake shi, amma bai taɓa jin mutuwar da ta daki zuciyarsa kamar mutuwar Hajiya Amina ba. Kan ƙiftawa da Bismillah. Ya ɗauka aljanin da ya bawa mahaifarta shikenan ya tseratar da ita daga ƙungiyar, abin da bai sani ba shi ne, bai isa ya tseratar da ita daga ajalinta ba. Ya nemi guri a gefen gado ya zauna, kawai ya din ga ganinta tana yi masa gizo. Duk izza da ƙafafa ta matan masu kuɗi, da ta'amalli da 'yan aiki, Hajiya Amina ba ta yadda mai aiki ta dafa masa abinci ba. Duk da son da yake yi mata, baya hana shi ya ci mata mutunci wasu lokutan. Amma ko ta yi fushi na lokacin ne ta ware. Ya yi mata wani irin so, mai wahalar mantawa. So yake yi ya samu damar zubar da hawaye, amma abu ya gagara. Vibrating wayarsa ta yi a kan gadon, ita ma yadda ya tafi ya bar ta, haka ya dawo ya tarar da ita. Ya ƙura mata ido daga bisani ya kai hannu ya ɗauka ya duba. Saƙo aka turo masa da lambar Doctor Sharif, ana sanar da shi Allah ya yi wa mai wayar rasuwar, za a yi jana'izarsa da yammacin ranar. Ya fito daga cikin saƙon, ya ga saƙon Yusuf na ƙarshe, da yake ce masa Daddy idan ka ga saƙona ka kira ni dan Allah na kasa samun ka a waya. Ya tuna yadda suka yi waya, Yusuf yana tsara masa yadda zai yi walimarsa na kammala master's da ya yi, suka da daɗe su na waya cikin raha da barkwanci. Ya tuna yanzu duk ba sa Duniya. "Saura kai, nan da anjima kai ne zaka mutu" Ya ji wata zuciyar ta raya masa. A take zuciyarsa ta tsinke ya buɗe idonsa a razane ya miƙe tsaye yana waige-waige. Wata irin fargaba ta shige shi, wani abu da bai san ko mene ne ba, ya tsirga masa tun daga cikin kansa har ƙafafuwansa. Da sauri ya fita daga ɗakin ya koma falonsa yana mayar da numfashi. **** Hammad ya kalli Asal da take ta kuka ya ce "Ko ki yi mini shiru, ko ki fita ki koma tun da ba dole na yi miki ba" Ba shiri ta hau goge hawayenta ta ce "Yi haƙuri, na daina" Ta yi maganar muryarta ƙasa-ƙasa. Gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi, har ga Allah ba ta son saɓa wa mahaifinta, amma ta san ba a kan gaskiya suke ba. Kuma idan ya kashe mata auren yaya yake son ta yi?. Ta yi shiru ta rakuɓe a gefen motar, kamar mai tsoron wani abu. Ya saka hannunsa ya janyo nata ya ɗora a kan cinyarsa yana murzawa a hankali hannu ɗaya kuma yana tuƙinsa. Ta ɗaga kanta ta kalle shi, ta ga ya mayar da hankali sosai a kan tuƙinsa. Ji ta yi kamar ta kwanta a jikinsa, amma ta tuna girman laifuffukan da yake kallonta da su yanzu, dan haka ta fasa. Ko da suka je gidan, ta tarar an yi wa gidan gyara sosai, an canza furnitures. Ta kalle shi za ta yi magana, amma sai ta fasa saboda gani take kamar fuskarsa a haɗe take. "Ina fatan canje-canjen da na yi ya yi miki, ban ɓata miki rai ba" Da sauri ta ce "A'a sun yi na gode sosai" "A'a faɗi gaskiya dai, na san ki da iyayi da ƙaƙale, idan bai yi ba a mayar da kayan a canzo wasu, tun da kamfanin wata uku suka bayar idan bai yi ba a mayar" Ta girgiza kai ta ce "Yayi sosai da sosai" Duk barorin gidan ba wani sonta suke yi ba, saboda fi'ilinta da wulaƙanci, amma da suka ga ta dawo sun yi murna, dan duk da wulaƙancinta akwai kyauta. Hannunta a buɗe yake sosai da sosai gurin ungo. Shi ya zo musu da abincin da ya saka aka kawo, daga gidan Abincinsa na Agadez. Ya ci kayansa kamar ya share ta, ganin ta ƙi sakin jiki ta ci, duk da ya ce ya yafe mata, amma wasu lokutan da ya kalle ta wasu abubuwan suke dawo masa. Duk da yafiya aba ce mai wahala wasu lokutan, amma mantawa da laifuka ya fi komai wahala. "Cherié, ba za ki ci abincin ba ne?" Ta ce "Na ci" "Ba ki ci da yawa ba ai, ke da na san ki da son abinci, matso na baki a baki" Haka ya yi ta ƙoƙarin danne komai, kamar yadda ya saba yi a baya. Da suka zo kwanciya ma, kasa sakin jiki ta yi, sai raɓe-raɓe take yi, tana satar kallonsa. Shi kuwa hankalinsa yana kan wayarsa, yana tsokanar Nana da roƙonta dan Allah kar ta kasa bacci, zai zo su haɗe ta mafarki. Emojin dariya ta tura masa, ta ce "Da kenan, ka ke yi mini wannan rufa idon, yanzu ina gane komai, ka yi addu'a ka kwanta sai da safe" Ya yi murmushi ya rufe data. Ya juya ya kalli Asal ya ce "Na canza kamanni ne?" Ta ɗan sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ya miƙa mata hannunsa ya ce  "Ƙaraso mana" A hankali ta ƙara, ya rungumo ta jikinsa, ya kwantar da ita sosai a kan gadon. Ya tashi ya je ya kashe fitilar ya dawo ya kwanta a kusa da ita. A ƙasan zuciyarsa ya din ga roƙon Allah ya sanya yafewa Asal da ya yi da sake karɓar ta a matsayin mata, kar ta sake yinƙurin cutar da shi. "Ya Allah da kyakkyawar niyya na yafe wa wannan baiwa taka, saboda ina tausayinta. Ubangiji Allah ka sanya ta gyara rayuwarta mu zauna lafiya" Sosai ya sake da ita, tamkar babu wani abu na rashin daɗi da ya faru. ***** Duk yadda Alhaji Zailani ya so kawar da komai a ransa a kasawa yayi. Ya din ga zagaya gidan yana kallon hanyar ɗakin Shukura, da har a yanzu idan ta zo gidan, a nan take kwana. Ya kalli inda Yusuf yake zama mussaman idan zai kalli ball. Suna kallon ƙwallo tare dukkanin su akwai team ɗin da suke supporting. Ya tuna kai komon Hajiya Amina a tsakaninsu, da ƙoƙarinta na ganin kowa ya samu abin da yake buƙata. Amma yanzu babu Yusuf babu Amina, Shukura kuma babu wani abu da ta tsana a yanzu sama da shi. Gidan ya yi masa wani irin zafi Duniya ta din ga juya masa. Dama salla ba wani damuwa ya yi da ita, domin rashin kiyaye ta na daga cikin dalilan da yake kawo musu rashin jituwa tsakaninsa da Amina. Ya din da ga jin sa tamkar a cikin wata Duniya yake, aka bar shi shikaɗai. Bugun ƙofar da ya yi yawa ne ya tashi ya je ya buɗe ƙofar main falon, ya tarar da mai delivery ya kawo masa abinci, kamar yadda Alhaji Sabo ya yi masa order, ya yi shiru yana tunanin ina mai gadi, da har mai delivery ya shigo haka. Ga harabar gidan babu kowa yan gaisuwa ma duk sun watse ya karɓa ya koma ya ajiye ya nemi guri ya kwanta. Rufe idanunsa ke da wuya, ya ga duhu ya yi, alhalin yamma ce da sauran haske. Ya buɗe idanunsa ya yinƙura zai tashi, amma ya ji tamkar an saka igiyoyi an ɗaɗɗaure shi, ya kasa motsa ko da yatsansa. Yana jin yadda zuciyarsa take bugawa ya sare cewa kan shi ma ya mutu ne, ya din ga rarraba idanu ya ga ta ina zai fara ganin mala'iku sun bayyana. Ya hango cewar shi ma yanzu likkafani za a saka masa a je a binne shi a rami a tafi a bar shi. Ya yi wani yinƙuri domin ya tashi amma abu ya gagara. Wata irin dariya ya ji ana yi mara daɗin ji, cikin sauti mai ƙarfi. "Abin da ka ke gudun sai ya faru, ba za ka tsere wa mutuwa ba, dole ka biya wa dodo buƙatar sa, ko kuma ya yi ajalinka. Ɗif ya daina jin muryar, sai kuma fuskar matarsa ta farko da ɗanta na fari, suka fara fitowa a ɗakin. Ya sake rikicewa sai dai bai iya kowane yinƙuri ba, Shukura ta bayyana jikinta duk jini, kamar ba ta daɗe da haihuwa ba, ta tunkaro shi gadan-gadan da wuƙa ta fara ƙoƙarin caka masa. Kamar wanda aka tasa daga bacci ya gan shi a tsakiyar titi, ƙafafuwansa ko takalmi ko babu. Ya kalli jikinsa babu suturar kirki, gari shiru ko ina duhu alamar dare ya tsala. Sai da ya yi da gaske sannna ya gano cam gaban unguarsu ya tafi. Rashin gurin zuwa ya sanya tilas ya sake koma wa gidan nasa, ya ci uwar tafiya da ƙafa ya koma. Sai dai ƙofar gidan a buɗe, babu masu gadi, abin da bai sani ba tuni zancen ya fara zagayawa, a kan abin da ake zarginsa da shi, kasancewar mai aikin gidan na laɓe ta ji maganganun da aka yi. Suna watsewa da aka tafi da Hajiya Amina Asibiti, aka tafi da Alhaji Zailani ta tattara kayanta ta gaya wa mai gadin abin da yake faruwa ta gudu. Alhaji Fatuhu ya ƙi sanar wa Iyalinsa abin da ya faru, sai dai gaba ɗaya ba shi da nutsuwa, ga kayansa ana ta saya babu ƙaƙƙautawa amma ba ya iya taɓuka komai, sai dai ya ɓuya ya yi kuka. Babu tsammani Fadila ta ritsa shi yana kuka, ya kasa cin abinci. Cikin damuwa ta ce "Daddy, ina gama ka da zatin Allah ka gaya mini abin da yake damunka, da ba haka ka ke yi ba fa. Gaba kamar ma a tsorace ka ke Duniyar, kuka fa ka ke yi dan Allah ka faɗa mini mene ne?" "Wallahi Fadila a tsorace nake da Duniyar, komai tsoro yake bani, ni dama rashin lafiyar da na yi na mutu, ban tashi ba da ban ji wannan abubuwan da damuwa da baƙin cikinsu zai halakka ni ba, bayan warkewr da na yi daga jinya ba" Ba ta san lokacin da ta fara kuka ba ta ce "Dan Allah Daddy mene ne?" "Fadila ba zan iya gaya miki ba, ku yi haƙuri kawai, Allah ya sanya mu dace" Haka ta gaji da rarrashin ta ƙyale shi. Shukura kuwa Sagir da Yusra ba abin da suke yi sai aikin rarrashinta, da bata haƙuri, Yusra ce take kula da Haidar da jaririn da ta haifa aka saka masa Ahmad Annur. Sai dai ta kasa yin lafiya, kusan kullum tana kwance, Alhaji Fatuhu duk kwana biyu sai yaje gidan ya rarrashe ta, ya bata haƙuri tare da kwantar mata da hankali. **** Da sassafe Asal ta nemi Hammad ta rasa, ta tashi ta fita falo, ta hango shi a kwnace a kan kujera yana video call da Nana. Ta tarar da shi yana cewa "Ba fa na ganin komai ma vie, dan Allah ki cire bargon nan" "A'a nifa bacci zan yi ka ke takura mini" "Zan rama ne Asmy, me za ki dafa zan shigo anjima in ganki in sha Allah" "Ba zan dafa komai ba, ai yau kana gurin matarka ta dafa ta baka" Ya marairaice ya ce "Ni ko? Shikenan tun da kin daina so na. Ɗan yi kissing goshina" Yayi maganar yana kara screen ɗin a fuskar sa. Da sauri Asal ta koma ɗaki, wani irin abu yana taso mata kamar za ta fita hayyacinta. Ji ta yi tana neman yin danasanin biyo shi ta dawo gidansa, amma ta tuna damarmakin da ya bata bayan da ya aure ta. Amma ta din ga muzguna masa, saboda hure mata kunne da Imam Omar ya din ga yi. Bai san daɗin aure ba sai da ta fara hankali ta fuskanci ba ya tanka duk rashin mutuncin da za ta yi masa. Idan zai yi magana a dankwafe shi. Sai a gaɓar da ta dawo hayyacinta ta gane shayi ruwa ne, take sonsa a lokacin ta fara karɓar sakamakon abin da ta aikata. Yanzu ba ta da wani abin cewa sai abin da ta gani kawai. Ta sha kukanta ta gode wa Allah. Nana an kai mata hadimai, duk da ba komai ta sakar musu ba. Har gida aka kawo mata dalleliyar motar da aka bata a gurin bikinsu, wanda Imam Zahradeen sabon Tafawan Agadez ne ya ba ta. Banda uban gwala-gwalai da ta samu. Ta fuskanci gold ne kyauta mafi tsada da muhimmanci da suke ba wa mutum mai muhimmanci mussaman ma mace. Lefenta kuwa, sai da ta din ga addu'a, saboda yadda mutane suka camfa duk auren da aka yi ɓarna a gurin yin sa ba ya ƙarko. Sai dai Hammad ya ce mata ai abin da aka yi mata kyautatawa ce, ba wai dukiyar aure ba. Kuma Allah ne ya tsamo ta ya bata rabonta ne. Ya kuma tuna mata a yadda aka yi auren su. Nana abin har kunya yake bata, yadda manyan mata wasu ma sun haife ta suke zuwa gidan, wai sun zo su gaishe ta, kuma in dai za su zo sai sun riƙo abin bata. Ta fara yi wa Nene ƙorafin ita wannan abin da ake yi mata ta gaji. Nene ta ce "Waye ya gaya miki ana shiga dawa dan ƙarya? Ai girma ne ya hau kanki, dan haka dole ki yi haƙuri. Ba kuma a yi wa masu mulki kyauta su mayar su ce a'a, dole ka karɓa. Kuma dole kema ki zama mai yawan kyauta. Sannan ki ƙirƙiro wani abu da zai amfani mata a ƙasar nan, saboda tabattar da za ki iya riƙe muƙamin da aka baki" Nana ta ce "To Allah ya bani iko, abinka da ba a saba ba" "Ke yi wa mutane shiru ke da ba a saba ɗin ba, dole a saba yanzu" Haka Nana ta din ga jin tamkar an ɗaɗɗaure ta saboda takura. Ranar da Hammad zai dawo, ya dawo tare da Muhsin, ta din ga murna dan har ta fara karaya Zahradeen ba zai bata ɗanta ba, ga shi tana jin nauyinsa, amma ta fara matsuwa da son ta yi magana. Nana ta ce "Sayyid amma ya dawo kenan ko?" Sayyid ya ce "To gamu nan dai, babansa sai masifa yake yi, sai da Sultan ya kira shi ya ce ya bamu ɗanmu. 'yan biyu sai kuka suke yi." Nana ta ce "Ina ma zan iya bar masa shi, amma raba ni da ɗayanku kamar raba ni da rayuwata ne" Hammad ya ce "Idan ma bayarwar ne, ba gara ki ba wa Asal ba?" Wani mugun kallo ta yi masa, da ya sanya shi yin shiru, ta saɓa ɗanta ta yi ɗaki. Baba gaba ɗaya ji ya yi kewar Nana ta dawo masa sabuwa fil, kamar a lokacin ta ɓata, daga ita har Imran, amma mussaman ma ita Nanan. Gaba ɗaya ganin da ya yi mata ya ji ɗanɗani haukaci ne. Kusan kullum sai sun yi waya ta what'sapp. Har yake gaya wa Nana an kai wa Gaddafi kuɗin aure. Ta din ga murna sosai. Ta ce "Baba Dan Allah ka yi wa Sarkin baka magana a kansu Suwaiba, dan Allah" "Wallahi Nana a kan yi mini maganar yaran nan, zan daina kira mu yi magana" Gaba ɗaya Nana ba ta jin daɗin hakan da Baba yake yi. Haka take kiran Ummanta ma, su yi waya da su Walida. Sai ga Iliyasu da karɓar waya, su gaisa da Nana yana neman yafiyarta a kan abubuwan da suka faru. Har ga Allah Nana ta tsani mutumin nan, ba zata manta abubuwan da ya yi mata ba, amma ta duba matsayin da Allah ya kaita a yanzu, dan haka ta ga ba girmanta ba ne ma zaman jin haushin wani ba. **** Kwanaki huɗu kenan, Alhaji Zailani kamar wanda aka yi wa asiri, ya kasa barin gidan, ga shi dare da rana tsorata shi kawai ake yi a gidan nan. Banda ihu marasa daɗin ji, a ɗauke shi a yi ta bugawa da ƙasa. Ko ya yi ta maƙabarta waɗanda ya bayar a ƙungiyar asiri, suna ta kokowa da shi za su danna shi a cikin kabari su rufe, yana ihu yana ƙoƙarin fitowa, ko kuma ya ga su na ƙoƙarin kashe shi. Duk yadda ya so sarrafa tunaninsa domin ya je gurin Malam Gambo neman mafita, amma ya kasa jin sa kawai yake yi a wata Duniyar daban. Tsawon kwanakin nan ya galabaita, ba ci ba sha, ba wanka ga kufcewar hankali. Yaje kitchen ya ɗaukko wuƙa ya riƙe yana zazzare ido, da nufin yana ganin sun fito masa ya caka musu. Sai dai Shukura ta bayyana, da wuƙar nan a hannunta, su na ta kokowa da shi, yana ƙoƙarin kar ya caka mata, saboda zuciyarsa na raya masa, itakaɗai ta rage masa yanzu. Kawai ya hango Alhaji Fatuhu na ƙyaƙayata masa dariya yana faɗin "Yanzu wa ya yi nasara? Ka rasa komai Zailani. Ba ka da kowa, ka kashe kowa naka, dukiyar kuma ba zata amfane ka ba. Ni kuma da ka yi niyyar hallakawa, komai nawa ya dawo, ga shi kuma dole mutuwa zaka yi" Ya saki Shukura ya nufi Alhaji Fatuhu yana faɗin "Na tsane ka, ba na ƙaunarka. Ba zan taɓa sonka ba kuma sai ka mutu, sai ka riga ni barin duniyar nan, na yi yadda nake so". Ya yi maganar yana cakawa Alhaji Fatuhu da yake gani wuƙar nan a cikin sa. Jini ne ya fara fitowa ta bakin Alhaji Fatuhu,  ya ce "Zailani wannan shi ne ƙarshen duk wanda ya gaza sarrafa ni. Ka kasa kula da ni a lokacin da na kamu da rashin lafiya. Ciwon ƙyashi ya kama ni, son duniya, hassada, mugunta, ƙeta na bushe na yi baƙi, har ka gaza sarrafa ni kullum burinka biya mini buƙatar duk da na bijiro maka, wanda ina bijiro maka buƙatuna ne, saboda samun sassaucin wannan ciwukan da suka kama ni, ka ƙi kulawa ka bani magani. Ga shi biyan buƙatuna ya sanya ka aikata abu mafi muni, ga ƙarshe mara kyau" Alhaji Fatuhu ya sake caka wa Alhaji Fatuhu da yake gani a gabansa. Wata irin zabura ya yi tare da kurma wani uban ihu, jin wani irin gigitacciyar azaba da raɗaɗi ya ratsa cikinsa. Abin da bai sani ba, da ya ɗauki wuƙar nan kansa y fara cakawa, ya fita waje yana tangaɗi, yana faɗin "Na kashe ku ɗin, na fi son duniya a kanku. A lahira rahamar Allah za ta saka na shiga aljanna a Duniya kuma ƙoƙarina ne zai tara mini abin duniya" Ya din ga surutu yana faɗar miyagun ayyukan da ya din ga aikatawa. Kafin a yi ƙoƙarin ƙwace wuƙar ya sake caka wa kansa a cikinsa, ya sulale ya faɗi ƙasa, jini yana zuba a jikinsa. Yana faɗuwa bakinsa a buɗe, Aljanin da ya mallaka ya bar gangar jikinsa. (Ya hayyu ya ƙayyum ya zuljalalu wal ikram Ubangiji Allah ka sanya mu yi kyakykywan ƙarshe, Allah ka raba mu da mummunan ƙarshe, Allah kar ka sanya mu cuci kowa🙏🙏🙏😭) Abin ka da zamani na amfani da social media, a lokacin da Alhaji Zailani yake wannan tamɓelen, aka samu masu ciro waya suka ɗauki abin da ya din ga yi, suka sanya a shafukan sada zumunta, duk wasu shafukan an sauke videos ɗin, saboda abin da yake ciki na tashin hankali. Tuni aka nemo jami'an tsaro, suka ɗauki gawar Alhaji Zailani. Sagir ne ya fara gani a social media ya tashi hankalinsa a dugunzume, ya tafi gidan Alhaji Fatuhu ya yi sallama da shi. Ya kalli Sagir ya ce "Lafiya kuwa? Ko Shukuran ce babu lafiya, na ganka kamar ba a nutse ba?" Ya ciro wayarsa ya nuna wa Alhaji Fatuhu abin da yake faruwa. Sai da ya jingina da bango sannan ya din ga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ya daɗe cikin mawuyacin hali, kafin ya daidaita nutsuwarsa ya dubi Sagir ya ce "Shukura ta gani?" Sagir ya ce "A'a, ai babu waya a hannunta ma" "To ka yi duk yadda za ka yi, kar waya ta shiga hannunta. Tun da Allah ya riga ya yi masa rasuwa, komai ya ƙare. Yanzu muje gurin 'yansanda mu roƙe su a taƙaita lamarin binciken nan, a yi masa sutura a binne shi" Sagir ya sara wa zuciya irin ta Alhaji Fatuhu, a irin abin da Alhaji Zailani ya yi masa, yake cewa su je su karɓi gawarsa a binne shi. Sun sha fama da 'yan sanda, dan hana gawarsa suka yi, sai da aka je gidansa, domin zurfafa bincike. Sai dai da bincike yayi bincike aka din ga gano, abubuwa na tsaface-tsaface da suke ɓoye a cikin gidan. Sannan aka buɗe wayarsa, yanayin tattaunawar sa da wasu daga cikin abokansa, ciki har da Malam Gambo, ya sanya jami'an tsaro kama su. ***** Sayyid a gurin Asal yake, amma yaje yana damunta. Sai da ya fara shirin tafiya, ta ce masa ya jira tana da baƙi su gaisa. "Suwaye baƙin kai a Agadez? Umma ce? (Da yake haka yake kiran Nene, kamar yadda Mahmoudu yake kiran ta)" "Ba ita ba ce" "To suwaye?" "Baƙi masu muhimmancin gaske ne, za ka gani" Ya ce "To bari na je masallaci, kafin su zo" Ya yi alwala ya fita falo, ya ga Nene tare da wata mata da namiji da alamu suka nuna mata da miji ne. Su na ganinsa suka ƙara nutsuwa, domin sukan ji zancensa a bakin Nene. Cikin girmamawa suka risuna su na gaishe shi. Ya amsa yana mamakin dalilin shigo masa da ƙato haka har cikin falo. Ya dake ya ce "Umma dama ke ce baƙuwar, ta dage kar na fita sai kin zo?" Ta yi murmushi ta ce "Ba ma nice baƙuwar ba, ga baƙin nata nan" Ta yi maganar tana nuna masa mata da mijin. Ya yi shiru yana kallonsu, ba su yi kama da 'yan Nigeria ba, sun fi kama da hausawan Niger, mussaman daga yanayin hausar su. Nana ce ta buɗe ƙofa ta fito, da gudu ta nufi Hajara ta rungume ta, Muhsin ya biyo bayanta ya ja ya tsaya a kusa da mahaifinsa. "Hajara, dama zan sake ganinki?" "Gani kuwa shugabata" Hajara ta yi maganar cikin girmamawa. Nana har ƙasa ta durƙusa ta gaida Auwwal, takaici ya kama Hammad, haryanzu Nana ta kasa gane mene ne matsayinta. Banda haka ya za a yi ta durƙusa har ƙasa tana gaida mutumin da shi kansa ya girme shi, da ma dattijo ne da sauƙi. Nene ta ce "Nana ba girmanki ba ne, ai shi yakamata ya gaishe ki" Shi ma a tsorace ya ce "Wallahi kuwa" "Kash, Nene ba ni da wani girma, ni na kasa jin girman nan. Meyasa ba zan girmama mutane mafiya karamci a gare ni ba?" Ta taso tana kallon Sayyid fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Wannan gidan su ne je, lokacin da na baro Agadez na nemi Nene na rasa, a can gidansu aka ɗaukko ni. Sayyid lokacin da na zo Niger na sauka a Maraɗi, ba ni da kowa sai Allah, Allah ya dubi zuciyata ya ji ƙaina ya haɗa ni da mutane masu karamci. Wannan su ne sanadin haɗuwa ta da Nene." Nan ta kwashe komai ta gaya masa. Sannan ta ɗora da cewa "Ina tambayar Nene su, ta ce mini sun tafi ci rani can ƙasar Mali. Sai yau Neme ta kira ni ta ce mini sun zo Niger, su na Agadez za ta kawo su mu gaisa. Ni na so mu je har inda suke amma ta hana" Kukan da Nana take yi kawai ya tabattar masa da ba ƙaramin karamci suka yi mata ba. Ya taka ya ƙarasa gaban Auwall da kansa yake ƙasa, ya miƙa masa hannu su yi musabaha. Da kyar ya iya miƙo masa hannu. Suka gaisa Hammad ya dafa kafaɗarsa ya ce "Na gode sosai da sosai. Mutane a zamanin nan abin tsoro ne, amma ka zama mutum na farko gurin bawa matar da baka sani ba taimako. Na gode sosai da sosai, dama Umma uwata ce, kai ne dai ban sani ba, tabbas tana bani labarinku. In sha Allah ba zaka sake zuwa Mali ci rani ba, da yardar Allah  na gode sosai da sosai Allah ya biya ka" Ya kalli matarsa ita ma ya yi mata godiya sosai. Tare suka je Salla da Auwwal, Hajara ta yi nufin ɗaukar Muhsin, amma ya ƙi saboda ƙyuya. Hadimai suka gabatar da Abinci, da abubuwan sha daban daban. Sayyid a dole yake ɗaga ƙafa a wasu abubuwan duk da azabar kishin Nana da yake yi. Ya yi iya ƙoƙarinsa a kan kar ya yi wani abu da ran su Auwwal zai sosu ko na Nene, ko dan albarkacin ɗawainiyar da suka yi da Nana. Har da kyautar kayan wasan Yara, suka kawowa Yarima Muhsin. A hirar ta su suke gaya wa Nana haryanzu Allah bai ba su haihuwa ba. Ta yi ta musu nasiha da basu misalai masu kwantar da hankali. Sai isha'i suka tashi tafiya, Hammad ya yi musu alkhairi, tare da jaddada musu godiya, ya kuma gaya wa Auwwal lokacin da zai zo Maraɗi, ya ba shi katinsa ya ce idan yaje ya nuna katin za a bari ya gan shi, zai ba shi abin yi. Bangaren Nana ma, kyaututtuka ta ba wa Hajara sosai, da ta ce ba zata karɓa ba, abin da suka yi wa Nana, dan Allah suka yi mata, Nene ta ce mata ba a mayar wa da masu mulki kyauta. Sai da Nana ta karɓi lambar wayar Hajara, ta din ga yi musu godiya kamar ta tsuguna musu. Hammad ya ɗauki Muhsin ya ce da kansa zai mayar da su har gidan da Nene take, kasancewar a gurinta suka sauka a Agadez. Daga can ya so wucewa gurin Asal da Muhsin dan yana kyautata zaton bata taɓa ganinsa ba, amma Nana ba ta sani ba, tsaf za su iya yin faɗa a kan hakan. Kuma da gaskiyar Nana kome nene Asal ce ta janyo, kuma duk abin da Nana za ta yi domin ta ba wa ɗanta kariya. Bugu da ƙari kuma ba ya son duk wani abu da zai kawo musu matsala, saboda wata irin kwanciyar hankali ya tsinci kansa a ciki. Ga taraiya da soyayya da yake samu daga gurinta. Duk da haryanzu Giyaz yana taɓa shi. Amma idan yana tare da ita, da ya gaya mata alamomin da yake ji, take yi masa addu'a ko ma muraran ta ga Giyaz ɗin tare da shi. Ya tattara hankalinsa a kan Nana da ta nufo shi, ta sanya doguwar riga ta cika ta, rigar ta zauna a jikinta. Ta ce "Wannan kallon sai ka saka na faɗi tukuna?" Yayi murmushi ya ce "Sai na riƙo ki kafin ki faɗin. Ta yi murmushi ta zauna a kusa da shi, ta kai kofin hannunta bakinsa ya buɗe baki yana sha. Ta ce "Amma ka yi sauri fa" "Eh, ina kai su na juyo ne, in sha Allah idan muka haɗu a Maraɗi, zan sama masa aikin yi" "Gaskiya ka kyauta, Allah ya saka maka da alkhairi" Ta ci gaba da ba shi labarin irin taimakon da suka yi mata. Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Lokacin mu na Nigeria, ba wuya kin samu rabo, Allah ya sa Niger ma haka ne, Allah ya sanya ƙani ko ƙanwar Muhsin sun samu a cikin nan" Nana ta tura baki ta ce "Sai Yarima ya shekara biyar" "Wace shekara biyar kuma? Kowa so yake sai ya karɓe shi, Zahradeen nata masifa, ga Sultan ya ce gobe na kai masa shi, amma idan Allah ya sa ki ka haihu, ko an ƙwace shi mu na da wani ko?" Kawai ta yi shiru tana murmushi, dan ji take gara ta haifi wasu a ƙwace da a ƙwace mata Muhsin. Su na hira ta ɗauki wayarta, za ta nuna masa abu, sai dai tana buɗe data videon Alhaji Zailani ta fara cin karo da shi a dandalin sada zumunta. Miƙewa ta yi tsaye jikinta na wata irin tsuma, kamar za ta zare. Ya karɓi wayar hannunta ya kalli videon. Ya ajiye wayar ya ce "Shiyasa wasu lokutan shafukan sada zumuntar nan duk ba su da wani amfani" "Sayyid ba ka gane waye ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ni ban san shi ba" "Ba ka tuna Alhaji Zailani ba?" Ya yi shiru ya tafi tunanin, kamar ya san sunan, can kuma ya ce "Na tuna, mutumin da muka fara gadi a gidansa da su Mahmoudu. To Allah ya kyauta ke mene ne naki na shiga tashin hankali haka?" "Dan Allah Sayyid ina son zuwa Nigeria" Ta yi maganar cikin tsoro da tashin hankali. "Sati uku da gama hidimar nan ki ce za ki Nigeria, a ƙalla nan da wata biyu nake son mu je tare" Sai ta rikice masa gaba ɗaya a kan ita fa dole Nigeria take son zuwa. Abu kamar wasa ya ɗauka da wasa take yi, sai da ya ga ta yanke jiki ta faɗi, jikinta ya yi sanyi ƙalau. A hankali ya ɗaga kai ya kalli tsuntsun da yake shawagi a saman ɗakin, da hakan ya tabattar masa da Ƙaisar ne ya zo mata. A ransa ya ƙudurce lallai a shirya tafiya Egypt ɗin nan, kafin su zo su ci gaba da samun matsala, su sake hana su zaman aure cikin kwanciyar hankali. Sai dai idan ya ce a yi mata passport a Niger, zai ɗan ɗauki lokaci, dan haka ya yanke shawarar za su je Nigeria a yi mata, sai su tafi. Har wajen ƙarfe goma na dare yana tare da Nana, sai dai ba ta dawo hayyacinta ba. Ya kira Asal ya gaya mata Nana babu lafiya, dan haka ta yi haƙuri ba zai samu damar dawowa a ranar ba. Asal kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, gani take kawai faɗa yayi, dan ya zauna ya kwana a gurin Nana, amma babu yadda ta iya. Shi kansa sai da ya raya za ta yi tunanin hakan, amma babu yadda za a yi ya tafi ya bar Nana a wannan yanayin. Duk yadda su Sagir suke yi wa Shukura ɓoye-ɓoye, sai da ta san Allah ya yi wa mahaifinta rasuwa. Hajiya Suwaiba ce ta fara ganin Videon nan, sai ba ta yi wa Alhaji Fatuhu magana ba, ta je gurin Fadila. Fadila ta ɗan yi mamakin ganin Hajiya Suwaiba a falon ta. Bayan sun gaisa ta ce "Fadila, ko Daddy ya gaya miki abin da yake damun sa?" Fadila ta ce "Wallahi bai gaya mini ba, na yi na yi ya ƙi ya gaya mini" "Kin ga wani video" Fadila ta karɓi videon tana kallo, jikinta ne ya hau karkarwa ta ce "Wannan ai Alhaji Zailani ne? Wai yana nufin Alhajinmu ya yi wa abin da yake faɗar nan?" "Nima abin da ya ɗaure mini kai kenan" Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama, ya ga duk sun zubo masa ido, kamar marasa gaskiya. "Lafiya kuwa?" Hajiya Suwaiba ce ta yi kokarin cewa "Daddy wani abu muka gani, shi ne dama abin da ka ke ɓoye mana?" "Me na ɓoye mukun?" Ta miƙa masa wayarta, yana kalla ya ajiya, ya zauna cikin damuwa, ya ce "Koma mene ne ya faru, ya riga ya faru, dan Allah a bar maganar nan ta wuce" Hajiya Suwaiba ta ce "Amma ya batun maganganun da ya din ga faɗa, yana cewa shi ya yi maka sihiri?" "Suwaiba a bar maganar nan dan Allah" "Amma ya zaka ce a bar ta, mutumin da ya tsugunar da mu, ya saka mu a wahala, to wallahi ni dai ban yafe ba." Fadila ta sha mamakin abubuwan da ta ji a videon nan, kuma ta tsorata imani ya ƙara shigarta, sai dai tun da ta ji Alhaji Fatuhu bai musa ba, to tabbas an yi hakan. ***** Nana Bakinta ya ƙi rufuwa, wani irin farinciki take ci, ganin sun kama hanyar Nigeria. Ta din ga tuna lokacin da ta yi balaguro, daga Nigeria zuwa Niger tsawon shekaru, ta tafi zuciya a cunkushe cike da rashin sanin makoma, sai dai kyakykywan yaƙini da dogaro ga Allah. Sai ga shi a wannan karon ta nufi zuwa gidan, cike da farinciki da kwanciyar hankali. Ta so tahowa da Muhsin, amma Hammad fafur ya hana, wai sai zo ɗaukarta zai taho da shi. Sai da suka samu saɓani kafin ta taho, dan cewa ta yi muddin Asal zai kai wa ɗanta gara ta haƙura da tafiyar. Ƙarshe sai da suka kai shi gidan Zahradeen, sannan ta hakura ta taho. A garin Bauchi ta fara yada zango, duk da nan ma abin da ya faru ba zai taɓa gogewa daga cikin ƙwaƙwalwarta ba. Mama tana ta kiranta a waya ta ji ko ta kusa ƙarasowa. Ko da Nana suka isa, Iliyasu ta fara gani a ƙofar gida, ya tsaya yana washe baki, ganin Nana ta fito daga danƙareriyar mota da aka kawo ta a ciki. "Maraba, sannunku da zuwa, sannu da zuwa" Ita Nana ma abun da yake yi matan, kunya ya din ga bata. Ta tarar da su Adda Maryam da Fati da wasu daga dangin Umman, duk sun cika gidan. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana. Suka din ga yi mata barka da zuwa. Nana ta sha karramawa, mijin umman sai nan nan yake yi da ita, yana washe mata baki har da yi mata raha. Baba ya din ga kiran Nana yana tambayarta sai yaushe zata ƙaraso. Ta ce masa ai ta sauka a Bauchi, sai ta kwana biyu za ta zo. Gaba ɗaya bai ji daɗin hakan ba, saboda yadda yake Alla-Alla ta zo ya sake ganinta. Sai da Nana ta kwana uku a Bauchi, Mama tana a kaita tasha a saka ta a mota, ta ce ai direbanta yana nan a Bauchin bai tafi ba. Suka sake ɗaukar hanyar Kano, jalla babbar Hausa yaro ko da me ka zo an fika. Nana ta yi kewar garinta na haihuwa ba kaɗan ba. Da sallama Nana ta shiga gidansu, Iya suturar jikinta, da yadda ta yi kyau mai ɗaukar ido ya sanya Mama yin saroro da kasa amsa mata sallamar. Nasiru ne ya fito da gudu yana faɗin Oyoyo ga masarautar Agadez da kanta. Masu arzikin zinare, masu kyauta da dama hagu ma ba ta san ana yi ba. Barka da zuwa Garkuwar matan Agadez ke ta Afrika ma gaba ɗaya." Kawai Nana ta tsaya tana murmushi, Jamila ta fito daga ɗakin, ta zo ta rungume Nana, sai Nana ta manta da batun wata Mama, ta hau murnar ganin 'yan uwanta. Nasiru ya je ya ɗaukko mata Akwatinta a mota. Nana ta dake ta ce "Mama ina wuni?" A dole bisa yaƙe Maman ta ce "Lafiya ƙalau Nana, ai kasa gane ki na yi, irin wannan gwala-gwalai haka. Ai na zata ba zaki sake saka su ba, dan kar ki yi almubazzaranci tun da da muka je fama aka yi ta yi da ke, ki ka ce ba kya so" Nana ta yi murmushi, tana tuna karatun da Ƙaisar ya yi mata, amma ta ce "To Mama yana iya, masu abu da abinsu, an ce mini haka suke adonsu, idan ka je gari ka ga 'yan gari da jela, aka ce kai ma ka nema ka maƙala. Gaba ɗaya Mama ba ta san baƙin cikinta ya fito muraran ba. Baba ma da ya dawo ya ga Nana, bakin nan a buɗe ya din ga murna yana yi mata maraba. Babu laifi sun yi nata karɓa mai kyau. Ta yi musu tsaraba mai yawa sosai kamar yadda ta yi wa mutanen Bauchi. Da daddare suna ɗaki suna ta hir da Jamila, take gaya wa Jamila abun da ta gani a waya, Jamila ta ƙara bata cikakken labarin abin da ya faru, da yadda Hajiya Sa'a take bayar da 'ya'yan Alhaji Fatuhu har ma da rashin lafiyar da Alhaji Fatuhun ya yi sai da ta bata labari. Jikin Nana ya din ga tsuma ta shiga tashin hankali, ta ƙudurce a ranta lallai a washegari za ta je gidan Alhaji Fatuhu, za ta je. Suwaiba ma ta dage ta din ga yi wa Nana hira, duk da galibin hirar tata shirme ce, tayi baƙi ƙirin duk ta bushe kamar wadda aka tsotse wa sinadaran jikinta. Gaddafi ma sun sha hira sosai da sosai da Nana. Da Safe da ta ce zata fita sai da Baba ya yi ta mitar daga zuwanta za ta fara yawo. Amma Nana ta nuna masa fitar ta dole ce, gidan Ummi za ta je. Tare da Jamila suka tafi gidan Alhaji Fatuhu. Sashen Fadila suka je, sai dai har suka gaisa ba ta gane su ba, har gara Jamila tana ta ƙoƙarin tuna ta. Yaronta Muhsin ne ya fito ya taso daga bacci, kamarsa ɗaya sak da wancan Muhsin ɗin. Nana na ganinsa ta miƙe tana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah. Banda na zo gaisuwar Muhsin, da cewa zan yi Muhsin ɗina ne nan". Ta yi maganar tana ɗaukar Muhsin tana shafa kansa. Fadila ta ce "Ya salam, Anty ai sai yanzu na gane ki, malamar Muhsin ko? Ai kin canza kamanni ne gaba ɗaya. Tun da ki ka yi aure bamu sake ganinki ba" Hawaye ya cika idanun Nana, ta ƙanƙame Muhsin, tana tuna wancan. Jamila ma cikin kuka ta ce "Na yi dana sanin Hajiya Sa'a, da tuni wannan ma ta bayar da shi kamar yadda ta bayar da wancan" A razane Fadila ta kalle ta ta ce "Me ki ke nufi?" Nana ta ce "Babu abin da take nufi" Fadila ta ce "A'a ga abu nan tana faɗa, kenan da gaske Hajiya Sa'a ita ta bayar mini da Muhsin ɗina? Ya aka yi ki ka sani" "Fadila na gaya miki wannan zancen ba haka yake ba, meyasa ki ke da gardama ne? Wannan ɗin suwaye su?" Ya kalli Jamila ya ce "Wannan ba ke ce nake gani a gidan Sa'a ba? Ya aka yi ki ka san wannan zancen?" Nana ta katse shi, ta hanyar gaishe shi, ya amsa sai dai tana magana ya gane ta. Ya ce "Nana ke ce?" Nana ta jinjina masa kai tana murmushi. "Baiwar Allah kin san tsawon lokacin da na ɗauka ina neman ki? Na din ga mafarkai daban-daban da ke. Jinya na haɗu da ita bayan kin yi aure" Fadila kasancewar ba wannan maganar take buƙata ba, cikin ɗimuwa ta ce wa Jamila ta gaya mata abin da Hajiya Sa'a ta yi wa ɗanta. Alhaji Fatuhu ya fara ƙoƙarin karewa ya hana, amma Jamila ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, na haddass muku fitina, amma gara na faɗa dan abu ne da yake ta damuna." Nan ta kwashe komai ta faɗa, har abin da Alhaji Fatuhu bai sani ba, da yadda ta shiga ƙungiyar asiri duk sai da ta faɗa, da yadda Abba ya mutu maimakon Muhsin. Cikin kiɗimewa Fadila ta riƙe Alhaji Fatuhu tana faɗin "Amma ka zalunce ni, saboda ka kare 'yar uwakka, ka din ga yi mini wasa da hankali ka ƙi yarda da abubuwan da take faɗa. Ɗana gudan jinina aka ba wa matsafa. Ɗana fa ɗan da na sha wahala na haifa." Nana ce ta sauke Muhsin, ta je ta kamo Fadila ta rungume ta cikin rarrashi ta ce "Yanzu wannan da ki ka haifa kin san Allah zai baki shi? Dan haka ko da ita ko babu ita, Allah ya ƙaddara ba rayayye bane ba. Kuma da na san Jamila zata faɗa ba zan yadda mu zo tare ba. Ki yi haƙuri ba zan ce sai kin yafe ba, amma kar ki ɗaga masa hankali, tashin hankalinki yake gudu ya sanya ya ɓoye miki. Kina kallo ya rasa ɗansa dalilin yar uwassa, abokinsa ya cutar da shi da mugun baƙin sihiri, kar ki ce za ki huce a kansa dan Allah" Ayshercool 08081012143 Littafin kuɗi ne, a biya 1k via 0069685771 Aisha Adam stanbic 103 Fadila ta saki rigar Alhaji Fatuhu, ta koma da baya tana zubar da hawaye cikin matsanancin tashin hankali da damuwa. Nana ta din ga yi mata nasiha mai shiga jiki tare da ba ta misali da kan kanta, irin faɗi tashin da ta din ga yi bayan auren ta. A hankali kuma sai Fadila ta din ga samun nutsuwa, tana jin damuwar ta ta, ta ragu ta kaɗu sosai da sosai da jin irin iftila'i da Nana ta din ga faɗawa ita ma. Alhaji Fatuhu ya ce "Sannu Nana" Nana ta yi murmushi ta ce "Yanzu ga shi komai ya wuce, amma soyayyar da nake yi wa marigayi Muhsin, ta sanya bayan na haihu na sanya wa yarona Muhammad Muhsin, shi ma sunan shi Muhsin, zai yi sa'an wannan Muhsin ɗin" Ta yi maganar tana kallon Muhsin da ya kwanta a jikin Alhaji Fatuhu. Fadila ta ce "Yanzu har sunan Muhsin ki ka saka wa yaronki?" Nana ta ce "Ƙwarai kuwa, Allah shaida ne na so Muhsin yaron nan ya shiga raina nesa ba kusa ba. Bayan shi sai Haidar ɗin Shukura jikan Alhaji Zailani, gaba ɗaya zuciyata ta tsinke ina tsoron a ce shi ma wani abin ya faru da shi" Alhaji Fatuhu ya ce "A'a yana nan cikin ƙoshin lafiya shi" Nana ta sake cewa "Dan Allah Maman Muhsin ina sake baki haƙuri, kar ki ga laifin 'yar uwata tun da har ta nemi yafiyarki ta bayyana duk abin da ya faru ba tare da tsoron abin da zai biyo baya. Yadda aka bi aka saka ta a ƙungiyar asiri ba da saninta ba, kuma a garin ta ceci wannan Muhsin ɗin, ɗan Hajiya Sa'a ya rasa ransa kuma ita ma haryanzu fama take yi da rashin lafiya" Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, dukkaninmu nan bamu wuce jarrabawa ba. Sai dai mun gode Allah, muna fatan ya zama kaffara a gare mu, domin ni jinya na sha, da sai da na din ga wari da raina, na yanke tsammani da rayuwa na rasa komai. Na ƙi yarda a yi mini maganin addini, ina tunanin ko na Asibiti ne. Wataƙila ma da Muhsin na amince an yi masa na addini da ko zai mutu zai samu afuwa. Ni kaina mafarki na din ga yi da ke kina ce mini sihiri aka yi mini, na nemi magani na yi mafarkin nan ya fi a ƙirga sannan na yarda na fara neman maganin addini. Wallahi rasa ɗana Muhsin bai yi mini zafin yadda nake tausaya wa Shukura da Zailani ya salwantar da rayuwarsa domin wai ya ga bayana ba. Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Yayi maganar yana fashewa da kuka, saboda dauriya kawai yake yi, amma abin yana mugun cin sa. Ya kasa sakin jiki ko Allah ya isa ya yi wa Zailani da 'yar uwassa gani yake iya bala'i da masifar da suka jefa kansi ma, ta ishe su a wajen Allah ba sai ya ƙara musu da Allah ya isa ba. Sai azahar su Nana suka bar gidan, sun yi hira sosai da Alhaji Fatuhu jin sa take yi kamar uba. Yake tsokanarta da zai din ga aika mata da kaya Niger tana sayarwa. Daga gidan Alhaji Fatuhu gidan Ummi suka wuce, jikin Nana duk a matuƙar sanyaye, sai abu ya faru ta yi ta tunanin a ina ta san abin, a ina ta taɓa gani, sai ta nutsu sai ta tuna Ƙaisar ne ya nuna mata. Ummi ta din ga yi wa su Nana masifar dan me za su zo da rana haka, bayan tun safe take saka ran ganinsu. Cikin jimami da damuwa, Nana ta kwashe komai ta gaya wa Ummi. Ummi ta kaɗu ta tsure da jin labarin da Nana ta bata, sai dai sam bata bayyana mata, wai Jamila har ƙungiyar asiri ta shiga ba, ita ma Ummin bata nuna mata Baba ya gaya mata ba. Ummi ta ce 'Ina ta saka ran ki zo mu sha hira, amma kin zo mini da abin tashin hankali. Suka watsar da wannan hirar, suka shiga wata. Hira tayi hira har take ba wa Nana labarin Saleh yana gidan yari, saboda sayen kayan sata da suka yi na gwangwan an kulle shi a Lagos. Ta tambaye ta su Barira, ta gaya mata auren Barira ya mutu, Sajida kuma tashi suka yi daga unguwar gaba ɗaya. Ta gaya wa Nana cewar sau biyu Hammad yana aiko mata da kuɗi masu tsoka, ya ce ta ɗauki nata ta tura wa Uwani sauran. Nana ta ce "Ni bai taɓa gaya mini ba ma, ha tsaraba kuma ya sake bani na kawo miki" Ummi ta ce "Allah sarki, Nana kin sha wahala ashe dai Allah ya yi kina da rabon jin daɗi a duniya" Nana ta ce "Ke dai bari, irin wanda ban taɓa tsammani ba. Amma wahalar da na sha sai da na yanke tsammani da samun afuwa. Sai kuma a hankali na lura da wani tsananin da na din ga shiga, shi ya din ga sadani da hanyoyin warwarewar matsalolin nawa. Na koma na din ga istigfari saboda na yi wa Ubangiji halin namu ɗan Adam, raki da kuma gaggawa Allah dai ya ƙara datar da mu" Jamila sai koma wa tayi gefe ta yi shiru, ba ta iya cewa komai. Da suka koma gida bayan magariba, Baba ya yi ta faɗan Nana ga ga da aure, amma taje ta yi dare a waje. Ta idar da sallar isha'i, tana ƙare wa ɗakinsu kallo, ɗakin da ta din ga shan azabar a Ƙaisar a cikin sa. Kawai ta tuna lokacin da ta ga bararoji na shan jinin Suwaiba. Ta kalli inda Suwaiban take, ta koma kamar wata mai shan inna, duk ta bushe ko abincin kirki ba ta ci, ƙwaƙwalwarta ta taɓu sosai da sosai. Ba shiri ta tashi ta aika Nasiru, ya nemo mata tazargade. Da kanta ta ɗauki Alqur'ani ta din ga karantawa tana busa wa a ruwa. Ta idar ta ba wa Suwaiba, ta shashashfa mata ruwan a jikinta, ta rungume ta tana ci gaba da yi mata karatun Alqur'ani ƙasan zuciyarta ta din ga yi mata addu'a da fatan Allah ya yaye mata wannan ciwon. Kullum sai Sayyid sun yi waya da Nana, aka fara processing yi mata passport, da kuma visa a Nigeria. Kwanan Nana uku, sai ga Suwaiba na iya cin abinci, Jamila ma tana cewa yanzu tana iya bacci sosai, ba tare da ana tsorata ta ba. Nana ta yi mata nasiha sosai da sosai a kan kula da ibada da kuma yin addu'a. Yaya Atine da kanta ta wanko ƙafa ta zo gidan, tana bala'in Nana ba ta je ta gidanta ba. Da ta ga Nana ba ta kula ta ba, sai kuma ta hau kame-kame tana faɗin "Haba ta gidana, a ce kin zo takanas bayan tsawon shekaru ba kya nan a ce, kuma ba ki taka kin je inda nake ba? Babu faɗa me ya kawo gaba Nana?" "To Yaya Atine kwata-kwata yaushe na zo garin, sai a hankali ai nake zagayawa amma kin zo kina ta faɗa" Nasiru ya ce "Ke ma dai Yaya Atine da fitina ki ke, ya za a yi ki zo ki rufe basarakiya da faɗa haka, kin ma ci sa'a da ta kula ki. Nanan yanzu fa ba wadda ki ka sani da ba ce" "Aikuwa na ga alama, maganar ma da kyar take yi, aishikenan" Nana duk gidansu ta rasa wanda ya ke da lambar Sarkin baka, kowa sai ya ce mata ba shi da ita. Nana ta kira lambar Sagir, kamar yadda ta karɓa a gurin Alhaji Fatuhu. Bayan sun gaisa ta ce masa kwatancen gidansa take nema, za ta zo gurin Shukura. Ya kwatanta mata ta yi masa godiya ta kashe wayar. Tana katse kiran, kiran Sayyid ya shigo wayarta. Ta yi murmushi ta ɗaga ta ce "Masoyi" Ya yi murmushi ya ce "Bayan kin tafi kin bar ni, kewa duk ta dame ni. Jina nake yi kamar maraya. Tabbas Nana ke rayuwata ce, ina roƙon Allah ya bamu jinkirin rayuwa mai amfani tare da ni da ke masoyiyya" "Amin ya hayyu ya ƙayyum. Ni kaina duk da ina farincikin ganin yan uwana, amma ina kewarka kai da Yarimana" Hammad ya kalli gefensa da larabci ya ce wa Muhsin "Zo ga Ammi, zo ka gaishe ta" Muhsin ya matsa kusa da Hammad ya kalli screen ɗin wayar, ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce "Ammi ki dawo" Jikinta ya yi sanyi ta ce "Haba yarimana, kar ka yi kuka ka ji, da wuri zan dawo ba zan iya jure ganin ka yi kuka ba" Ya jinjina mata kai. "Wai zuwa ka yi ka ɗaukko shi?" "Eh mana, karɓo shi na yi aro, muka taho gida, tun jiya ma yana gurina" Kamar ta yi magana sai ta fasa. Ya ce "Ki kwantar da hankalinki, ban kai mata ɗanki ba, amma dole zan kai shi ta gan shi, ko da kuwa ba ta ƙaunarsa, amma zan yi hakan ne idan ki na nan. Ki zama cikin shiri daga kowane lokaci wataƙila ta nan Nigeria za ki tafi Egypt mu haɗu a can" "To ai saura kwana uku na taho" "Eh, za a jinkirta tahowar ne, gara ki tafi ta Nigeria." Nana ta ɗan langaɓar da kai ta ce "To ai ni ban san ya ake abubuwan ba, kuma idan na zo ina zan yi?" Yayi dariya ya ce "Idan kin je ba ɓata za ki yi ba, ni zan je na taho da ke" Sun daɗe su na waya, sannan ta ajiye ta shirya. Tun da Nana ta zo gidan nan abinci mai rai da lafiya ake ci sau ukun nan, kuma duk abin da aka girka har maƙwabta ake kaiwa. Mama ga shi tana cin arzikin nata amma baƙin ciki kamar ya yi ajalinta, da ba 'ya'yanta ne a wannan daular ba. Gaddafi ma da yake ta shirin aure, shi ne yake kai komo gurin shirin tafiyar Nana Egypt. Ta gama shirinta, suka fita da Jamila, Baba har mamaki yake yi yadda Nana ta shiga cikin su take rayuwarta, domin shi Jamila tsoro ma take ba shi. Ita kuwa Nana abubuwan tashin hankalin da ta gani a rayuwarta, ba ta ɗauki wata ƙungiyar asiri da Jamila ta shiga da Muhammad ba. Su na ta sallama a falo babu kowa, can ƙasa-ƙasa suka ji an amsa. Nana ta yi shiru tana tunanin kamar ya san muryar. Yusra ce ta fito tana amsa sallamar. Tana ganin Nana ta ruɗe ta tafi ta rungume ta, "Ƙawata kece? Ina ki ka tafi ban sake ganinki ba, kowa na yi wa maganar ki, sai a ga kamar shirme nake faɗa". Cikin mamaki Nana ta ce "Ƙawata me ki ke yi a gidan nan kuma?" Cikin zaƙuwa ta ce "Ai Sagir ya dawo da ni tuntuni" "Ma sha Allah, Alhamdillah ya gida ina Hajiya da Siyama?" "Su na Abuja" "Ƙawata kin canza kamanni, kin yi kyau kin ƙara ƙiba tubarkallah, ina mijinki buzun nan?" "Yana Agadez. Ni gidan wata Shukura aka kwatanta mini kuma na zo na ganki" "To ai ita ma gidanta ne, ba Maman Haidar ba? Mijinmu ɗaya bari na kirawo miki ita, ba ta da lafiya ne ma" Ta juya ta nufi wata ƙofa, Nana ta din ga mamaki. Jamila ta ce "Ita wannan ɗin a ina ki ka santa?" "Gidan da muka yi gadi, a gidan suke" Mintuna kusan goma sha biyar, sannan Yusra ta fito, rungume da jariri a hannunta, ga Haidar ya zama saurayi Sagir kuma ya riƙo Shukura tana takowa a hankali. Nana ta miƙe tsaye, ganin Shukura ta rame sosai ta yi duhu, tana ganin Nana ta fashe da kuka. Cikin sanyin jiki Nana ta nufe ta tana "Faɗin Subhanallah" "Nana kin gani ko? Ki ka ce mini mafarki ba gaskiya ba ne ba, ni ga shi ya zama gaske Daddy ne ya yi amfani da ɗana ya yi tsafi, Mummyna ta mutu, ya kashe Yusuf ya kashe mahaifiyarmu da babban yayanmu. Nana ban yi dacen uba ba" Sagir ya ce "Shukura meye haka wai? Wannan ba sirrinki bane da yakamata ki ɓoye ba?" "Babu abin da zan ɓoye, Nana ta riga ta san komai" Nana ta rungume Shukura tana kuka ta ce "Kina nufin Yusuf da Hajiya Amina sun mutu? Tayaya mafarki ya zama gaske? Waye ya gaya miki da gaske ya bayar da jaririnki, ba gaskiya ba ne" Tamkar za ta shiɗe ta ce "Wallahi gaskiya ne, shi ya gaya mini da bakins, bayan ya saka an sace ni, da niyyar ya sake kashe mini jaririna" Jikin Nana ya yi wani irin sanyi, ta tuna Ƙaisar ya ce mata aljanu na iya nuna wa  mutum abu a mafarki saboda su haɗa faɗa. Sai dai ga shi abin ya tabatta. Ta rasa tausayin wa za ta fi ji ne? Fadila ko Shukura? Haka nan ma ta din ga rarrashinta tana ba ta haƙuri, tana tuna yadda ita ma Alhaji Zailani ya sako ta a gaba. Yanzu duk daɗewarsa a duniya, duk tara kuɗin da burin tara arzikin ya tara ya tafi ya bar shi a banza, ga tonon asiri da mummunan ƙarshe, waɗanda ya bari da za su iya yi masa addu'a duk ya bar musu mummunan tabo a zukatansu, da babu lallai su iya yafe masa balle ya samu addu'a. Ta kalli Haidar ta ce "Ka gane ni Haidar?" Ya yi murmushi ya ce "Eh Anty Nana ce" Sagir ya ce "Amma baka gaishe ta ba?" Ajiyar zuciya da Shukura ta yi, ya sanya Nana mayar da hankalinta kanta, Nana ina ji a jikina nan kusa zan mutu nima, nauyin da ƙirjina yake yi mini da numfashi da nake yi da kyar, na san nima nawa ajalin ya zo. Ki zama shaida idan na mutu kar a ba wa kowa ɗana sai Yusra. Da fari na ɗauki mugun kishi na saka a raina, amma daga bisani abin da Yusra ta yi mini na alkhairi na tabattar da ba kowace kishiya ce kishiya ba, Yusra tana da kyawun zuciya" AREWABOOKS Cikin tashin hankali Yusra ta ce "Ka ga zata ci gaba ko?" Sagir ya ce "Dan Allah Shukura ki daina maganar nan, kina ganin ba ta da cikakkiyar lafiya, tun da ba ta so ki daina dan Allah" Nana ta matsa kusa da Yusra da tuni manyan idanunta suka tara hawaye, ta kalli jaririn hannunta, ta ce "Wannan naki ne?" "Na Maman Haidar ne" "Ma sha Allah" Kawai Yausra ta miƙa wa Nana hannu tana murmushi. Nana ta kama hannun nata. A take ta ji jikinta ya yi sanyi. "Haula" Ta furta a hankali. "Ina yi miki barka da Gimbiyar Agadez, mai ɗauke da abin al'ajabi" Nana ta ce "Haryanzu ba ki rabu da ita ba dama?" "Ke kin sanmu akwai alƙawari, ina yi miki fatan alkhairi" Ta zare hannunta daga na Nana. Nana ta dubi Sagir ta ce "Kana nema mata magani kuwa? Ko kaima ka fi yarda da ciwon Asibiti ne yake damunta?" Ya ce "Haka suka ce mini a gidansu, Asibiti muke zuwa ganin likita" Nana ta ce "Gaskiya yakamata a yi mata na islamic ma" Nan ma Nana ta daɗe tare da su, sosai Shukura ta ji daɗin zuwan Nana, ita kanta Yusra ta ji daɗin zuwan nasu. Nana ta yi wa Shukura alkhairi, suka yi musayar lambar waya, ta tashi suka tafi. Daga gidan su Yusra, kasuwa suka je, Nana ta yi wa su Jamila sayayya sosai da sosai. Su na tafe a hanya Nana ta ce "Jamila, to kuma da gaske kin iya kasuwancin saye da sayarwar da Hajiya Sa'a take yi, ko kuma ba kasuwancin ku ke ba gaba ɗaya?" Jamila ta ce "A'a tana kasuwancin, na iya" "To jari nake son baki, ki je ki fara kema, na yi magana da Nasiru ma, da makaranta nake son ya koma, amma ya ce; shi gara na ba shi jari, zai fara sayar da omo da sabulai da ake yi a kasuwa. Dan Allah Jamila idan kin fara Allah ya sanya albarka, ki kula da iyayenmu. Kuma duk abin da ku ke buƙata muddin bai fi ƙarfina ba, ki yi mini waya tun da Alhamdillah inda nake babu abin da zan ce wa Allah sai godiya. Kuma na san ba wayona ko dabara ta ce, ta sanya Allah ya kai ni inda nake ba. Kuma Allah bai tsame ni ya yi mini wannan ni'imar dan ya fi sona ba. Kuma ina fatan a cikinmu Allah ya ƙara ɗaukaka wani, sama da inda nake ni a yanzu" Jamila har da kuka, tare da bawa Nana haƙurin abubuwan da babarsu da su suka yi mata a baya. "Jamila, idan Allah ya yi wa mutum ni'ima, idan ya yi gaba ba ya waiwayen baya, idan ba alkhairi zai kalla ba, ki manta komai ya wuce kamar ba a yi ba". Jamila ta yi ta nuna wa Mama kayan da Nana ta saya musu, da batun jarin da za ta bata, amma ta kwaɓe baki. Nana ba ta damu ba, ta yi wa Baba ɗinke-ɗinke. Gaddafi ya shigo, ya ce "Nana, mun yi waya da mijinki, ya ce bai same ki ba. Ki shirya jibi in Allah ya kaimu, jirgin ƙarfe goma za ki bi, zuwa can Egypt ɗin" Nana ta ce "Kai da wuri haka, na ɗauka za a kai irin kwanakin nan" Gaddafi ya ce "To ai abin da yake naku ne manya, kuna da alfarma a ko ina, ga shi nan har an yi an gama" Baba ne ya kalli yadda Mama ke yamutsa fuska, a hasale ya ce "Wallahi Rabi idan ba ki yi wasa ba, baƙin ciki ne zai kashe ki. Duk da abubuwan da ki ka din ga yi wa yarinyar nan, ga shi kina ta cin arzikinta da ke da 'ya'yanki, ba ta yi muku baƙin ciki ba, amma da ta motsa, ta yi wani abin alkhairi ko wani abin alkhairi ya same ta, sai ki kwaɓe baki ko ki kushe" "Ni kar ka yi mini sharri, me na yi wa Nanan, Allah na tuba me Nana take da shi, da zan yi mata baƙin ciki?" Baba ya ce "Eh batabda komai, sai abin da yake tukunyarki ki ke ci kika yatsins fuska saboda baƙin ciki" Takaici ya ishi Nana, ta tashi ta bar gurin. **** Nana tamkar idanunta su faɗo, saboda rarraba idon neman Sayyid. Sai kalle-kalle take yi kamar ma dai a tsorace take. Fararen fata da baƙaƙe, sai kai wa suke yi suna komowa. "Kamo ta nan" Yayi maganar yana rungumota, ta zabura a tsorace. Ya yi dariya ya ce "Matsaoraciya kawai, sai rarraba ido ki ke yi" "Shi ne zaka tsorata ni, da na yi ihu fa?" "Sai a yi miki dariya" Yayi maganar yana jan karan hancinta. Ya miƙa mata hannu suka gaisa, ya ce "Ya mutanen Nigeria su na lafiya?" Ya ce "Lafiya ƙalau Alhamdillah, su na gaishe ka" Ya ce "Ma sha Allah, in sha Allah da mun dawo, zamu sake zuwa tare, na gaishe su" Ya riƙe hannunta, suka shiga taxi suka tafi. Katafaren Hotel ne, suka sauka a ciki, gaba ɗaya Nana jin ta take yi, kamar ba ita ba, kamar mafarki take yi. Ya yi order Abinci, aka kawo mata, ta yi wanka tayi salla. Abinci kawai ya iya bari ta ci, ba tare da bata damar hutawa ba, ya ce sai ta biya shi kwanakin da ta yi a Nigeria ba ta nan. Nana dai da ya ishe ta, kawai ta hau kuka, ya lumshe idanu yana ƙare mata kallo. Ya yi murmushi ya ce "Ke yanzu dan Allah ba ki ji kunya ba abin da ki ke yi mini?" "Kai dai za ka ji kunya, haba daga zuwana?" Ta yi maganar tana hawaye. Ya tashi zaune yana leƙa fuskarta, fafur taƙi kallonsa, ƙoƙarin kare fuskarta take yi, amma yaƙi bata damar hakan. Ya ce "Ni fa zuwan nan namu da biyu, honeymoon muka zo" "Wane honeymoon, wanda ka yi a Agadez bai ishe ka ba, sai ka dame ni, daga zuwana ni dama ban zo ba" Hammad ya ce "Gaskiya na Agadez bai ishe ni ba, na fuskanci ƙanin Yarima da rigima ya zo, lokacin Yarima ai ni ake lallaɓawa ina jan aji. Idan kuma ba haka ba, mutum ya musa na tuno wa mutum abin da ya aikata" Murguɗa masa baki ta yi, tana goge hawayen fuskarta. Shi kuwa ya saka ta a gaba, ya din ga yi mata dariya. Sai da suka shafe kwana uku, da zuwa, har sai da Nana ta manta da abin da ya kawo su, sai dai ta ci abinci Hammad ya yi rigimarsa. Kwana na huɗu suka bar garin da suka sauka, suka tafi garin da malamin yake. Kafin su bar garin, sai da ya zagaya da ita ta ga gari sosai da sosai. A can garin ma da suka je, a Hotel suka sauka, sai dai a wannan karon ta tarar da Sultan da Matawalle su ma duk su na Hotel ɗin kowanne ɗakinsa daban amma. Sultan kamar ya ga 'yar cikinsa, ya din ga tambayarta ya ta baro 'yan uwanta da iyayenta. Washegari da safe suka hau mota, suka tafi gidan mutumin. Balarabe ne, sai dai yana jin turanci, tun da suka je gaban Nana ya tsananta faɗuwa. Ya yi musu kyakykyawar tarba, sai dai Nana ko buɗe bakinta ta kasa yi, balle ta gaishe shi. Ya kalli Nana cikin harshen turanci, ya ce "Sannu da zuwa" Ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ta ɓangaren Hammad ma, jikinsa sai tsuma yake yi. Da larabci suka din ga tattaunawa, Sultan da mutumin, tana iya fahimtar abin da suke faɗa amma ba duka ba. Ya miƙe tsaye ya kalli Hammad, ya ce ya biyo shi, da shi da Sultan. Nana ta koma gefe ta rakuɓe, ta din ga tunane-tunanen da ita kanta ba ta san daga ina take yin su ba. Gaba ɗaya ba ta cikin nustuwarta, ba ta kuma iya tantance abin da take ji. Wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, sannu a hankali ta din ga jin wani irin ihu mara daɗin ji. Ta saka hannu biyu ta toshe kunnuwanta, ta din ga jin tamkar ana ɓarar da kaya, ko ana kokowa da wani irin abu mai nauyi. Har azahar ta yi, Nana ba ta ga fitowar Hammad ba. Aka bata ruwa ta yi alwala ta yi salla, aka kawo mata abinci, amma ta kasa ci, hankalinta a tashe ba ta ga Hammad ba, ga kuma yanayin da take ji a jikinta mara daɗi. Sai wajen la'asar, sannan aka fito da Hammad, Sultan ya riƙo shi idanunsa a lumshe. Hankalin Nana ya tashi, ta miƙe tsaye tana faɗin "Lafiya meya same shi?" Sultan ya ce "Babu abin da ya faru, ki kwantar da hankalinki zai wartsake in sha Allah" Dattijon nan shi ne mai maganin, ya fito ya jagorance su har wani ɗaki. A ciki aka kwantar da Hammad, sai ajiyar zuciya yake yi, jikinsa yayi jawur hatta gashin kansa a hargiste, rawaninsa ma da babbar rigarsa a hannu Matawalle ya fito da ita. Ta din ga mamakin, yaya aka yi haka? Me aka yi masa ya fita daga hayyacinsa haka. Sai warin wasu mayuka yake yi, da ta gaza gane kowane iri ne. Su Sultan suka fita yin salla, Nana ta ƙarasa kusa da Hammad, ta taɓa shi, ta shafa gashin kansa ta ce "Sayyid, Sayyid ka na ji na kuwa?" "Mmm" ya amsa da kyar. "Mene ne, me ya yi maka?" Ya girgiza kai ba tare da ya buɗe idanunsa ba. Da su Sultan suka dawo, suka tarar da ita hankali a tashe. Matawalle ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zai wartsake a hankali in sha Allah. Ya ce sai dai mu kwana a nan, mu ga yanayin jikin nasa tukuna, sannan kema ya duba ki" Kasancewar mutumin babban malamin ruƙiyya ne, da magungunan musulunci yana da gurin saukar baƙi, saboda yadda ake zuwa daga garuruwa gurinsa. Sannu a hankali Hammad ya dawo hayyacinsa, har ya yi salla ya ci abinci, amma kana kallonsa zaka gane ba ya jin daɗi. Nana dai ba ta iya tambayarsa komai ba. Sultan ya tambaye ta, za ta iya kwana da shi, ko a bata wani ɗakin, ta ce zata iya zama tare da shi. Ba da wani shiri suka taho ba, kasancewar ba su san za su kwana a gidan ba. Gidan Sarkin baka ne ya faɗo mata, da irin gane-ganen da ta yi a gidan. Ta nemi guri ta kwanta a kusa da Hammad, ta ji ya matso da ita jikinsa, ya ƙanƙame ta. Kamar wadda ta farka daga bacci, haka ta ganta a Libraryn Ƙaisar. Sai dai gurin ya ɗan yi duhu, sheshsheƙa ta din ga jiyowa daga wani guri, ta tafi a hankali tana sanɗa. Tana buɗe ƙofar da take jiyo sautin ta ga wani irin ƙaton guri, Ƙaisar na durƙushe a kan gwiwoyinsa, ya saka wani abu dogo da ba ta san ko menene ba a gabansa, yana wani irin kuka. Da sauri ta ƙarasa gabansa, ta gefen mayafin take hango wani abu baƙi ƙirin kamar an ƙona itace. Sandar Giyaz ta gani kwance a gefen abin da yake gaban Ƙaisar ɗin, a razane Nana ta ce "Giyaz ne ya mutu?" Kawai Ƙaisar ya sake fashewa da kuka, yana yaye mayafin da ya rufe Giyaz. Ya yi wani irin baƙi kamar dutse yayi gobara. Ga wani irin tsawo mara misali da yayi, sai gemunsa da ya ƙara wani irin tsawo. Nana ta ja da baya a razane. Ƙaisar ya kifa a kansa yana wani irin kuka. Ji ta yi an girgiza ta, ta buɗe idonta, ta ga Hammad ya tsare ta da ido ya ce "Lafiya kuwa? Meyafaru?" Kasa magana ta yi, sai ajiyar zuciya da take yi kamar za ta shiɗe. Duk da jikinsa babu ƙwari haka ya din ga rarrashinta, yana tambayarta mene ne, amma taƙi magana. Da kyar ta tashi ta yi sallar asuba. Aka kawo musu abin karyawa, amma ta ƙi ko kallon abincin. Da ta tuno yadda Ƙaisar ya rungume Giyaz yana kuka, sai ta hawaye yana zubo mata. Hammad ya fita daga ɗakin, bayan mintuna kaɗan, ya dawo ya ce ta taso. Jikinta gaba ɗaya babu ƙwari, ta tashi ta bi bayansa. Ko su Sultan kasa gaisar da su ta yi, tana ganin Hammad ya nufi hanyar da aka bi da shi jiya, ta ja ta tsaya. Ya ce "Meya faru ne? Mu ƙarasa mana" Ta girgiza kai ta ce "Kai dai ka je, ni ba zani ba" "Saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba. "Ma viee, ki yi haƙuri babu abin da zai faru in sha Allah, magani za a yi mana mu rabu da wannan larurar, mu samu kwanciyar hankali mu zauna lafiya mu rayu kamar sauran mutane" Ta ce "Ni ba na so" Ta yi maganar tana kuka. Sultan ya ƙaraso ya ce "Meyafaru ne?" "Ni ba zan je ba, a ƙyale ni ba na so" Da gaske Nana ta kafe, ta ce ba za ta shiga ba, Matawalle ya shiga ya yi wa mutumin magana. Mutumin na fitowa ta juya zata arta da gudu. Hammad ya riƙo ta, ya ce "Amsy me yake damunki ne?" "Wallahi ba za a kashe Ƙaisar kamar yadda aka kashe Giyaz ba. Wallahi ba zan je ba. Da ya kashe shi gara ni ya kashe ni" "Asma'u, kin zaɓi aljani a kaina da rayuwar aurenmu kenan? Ki nutsu mana" Hammad ya yi mata magana cikin tsawa. Tana kuka ta ce "Wallahi ba zan tsaya ba, shi ma mai rai ne, kuma yana son rayuwarsa, ba zan tsaya a kashe ƙaisar ina gani ba" Mutumin ya tambayi Hammad, me take faɗa ne. Hammad ya yi masa bayani, cikin harshen turanci, yake gaya wa Nana, ba shi ya kashe Giyaz ba, taurin kai Giyaz yayi shi ya kashe kansa da kansa, amma ba shi ya kashe shi ba" "Ni dai ku ƙyale ni, zamu rabu a hankali, idan na bari aka kashe shi a dalilina ban yi masa adalci ba, ko ya cutar da ni ta wani bangaren bai cutar da ni ba. Ni dai kar a kashe shi dan Allah." Sultan ya sassauta murya ya ce "Kina ji, ba kashe shi za a yi ba, za yi miki tsakani da shi ne ya rabu da ke, amma ba kashe shi za a yi ba. Wancan ɗin ma ba shi ya kashe shi ba, shi ne ya kashe kansa dan kawai an nemi ya musulunta ko a ƙona shi" Nana ta girgiza kai ta ce "Ƙaisar kuka yake yi, an kashe babansa, ni ku bari zan yi magana da shi, yana cikin jimami dan Allah kar ku kashe shi" Ta ƙarasa maganar har da haɗa hannayenta biyu alamar magiya. Hammad ya rungume ta, ganin yadda take neman ta fita daga hayyacinta, ga shi yana kyautata zaton tana ɗauke da juna biyu. Nana tana da matuƙar raunin zuciya, da tausayi banda haka ya za a yi abin da ya wahalar da ita, ta din ga wannan kukan ta ce ba za a raba ta da shi ba. 104 Sosai Nana ta rikice musu, take ta uban kuka, babu irin ban haƙuri da rarrashin da Hammad bai yi mata ba, amma ta ƙi saurararsa tana cewa ita ba za a kashe Ƙaisar ba. Malamin ya ce su rabu da ita, su koma masaukinsu su kwana biyu ta samu nutsuwa, sai su dawo da ita. Har suka koma masauki, Hammad bai kula Nana ba, gani yake yi kawai kamar ta fifita zama da Aljani a kansa, ban da haka ita da kullum cikin taka tsantsan take da imaninta da rayuwarta, me za ta yi da zama da aljani, aljanin da babu abin da ya yi face wahalarwa da muma azabtar da rayuwarta. Ita ma ba ta kula shin ba, ba ta bi ta kansa ba, Sultan ya ja masa kunne sosai a kan kar ya yi mata faɗa, ko kuma ya ce zai takura ta. Kamar wasa Nana abu har da rashin lafiya, zazzaɓi sosai da sosai, ta ƙi cin abinci. Da ta tuna yadda ta ga Ƙaisar yana kuka, sai jikinta ya yi sanyi, shi ma halittar Allah ne, cutar da shi ba zai kawo masalaha ba, wataƙila sai ma ta'azzara wasu abubuwan. Tun bayan tariyarsu, ba su taɓa yin faɗa ba sai a wannan lokacin. Da daddare ma a ƙasa ya kwanta, ba ta ko saurare shi ba, ta haye gado duk da rashin cin abinci da ta yi, ya tsaye masa amma ya dake ya ƙi kula ta. Gefe guda ta hango Ƙaisar, yana zaune ya saka wata hanya a gaba ya takure yana kallon hanyar. Jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa gefensa ta zauna ta ce "Ƙaisar" Ya waiwayo a hankali ya kalli Nana ya ce "Na'am" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ina matuƙar jin nauyinka, da kuma kunyarka, ban ma san me zan ce ba, ina mai baka haƙurin rashin mahaifinka da ka yi". Ya ɗan jinjina kai ya ce "Haƙiƙa mahaifina ya so ni, so mai tsanani, duk mai sonsa to ya so ni. Sai dai bayan mun raba gari babu yadda ban yi ba ya gane gaskiya, amma abu ya gagara. Ban ji baƙin cikin mutuwar mahaifina kamar mutuwar da ya yi a matsayin kafiri babu ta inda zan yi masa addu'a na roƙa masa Allah gafara. Tabbas Giyaz shi ya kashe kansa bayan malamin nan ya takura masa a kan ya musulunta ko ya ƙona kansa." Ya yi maganar cikin matsananciyar damuwa. Nana ta rasa abin yi, a hankali ta ce "Ka yi haƙuri, babu wanda ya isa ya shirya wani, idan ba Allah ba, wannan ita ce taka ƙaddarar" Ya jinjina mata kai, sannan ya ce "Me yasa ba kya son a kashe ni? Ko a raba mu?" Nana ta ja numfashi sannan ta ce "A tarayyata da kai, duk da akwai ƙalubale mai tarin gaske, amma na koyi darrussa daban-daban, kuma na fahimci abubuwa da dama. Tabbas yadda muke da mutanen kirki da kuma ɓata gari, kuma ku na da na kirki da ɓata gari a cikin ku. Kamar yadda nake yawan faɗa, idan ka na son ka zama mafi alkhairin mutane, ka rinjayar da alkhairi a kan sharri. Kuma bayin Allah ne, ku na taku da rayuwar Allah ya sanya mu rayu da mu da ku a Duniya ɗaya, duk da mu na da banbancin halitta, bai kamata ɗayanmu ya zamana yana cutar da ɗaya ba, ko amfani da ɗaya gurin fin ƙarfi da mugunta ba. Ni dai a yanzu zan iya bugun ƙirji na ce a cikin halittar aljanu akwai bayin Allah, sai dai su ma ajizai ne su na aikata laifuka kamar yadda ɗan Adam yake yi" Ƙaisar ya jinjina kai kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Haƙiƙa nima tarayyata da ke na fuskanci abubuwa da dama game da rayuwa, kuma ina son baki wasu saƙonni da yakamata bil adam ku sani. Na ƙaru da abubuwa da dama ta ɓangarenki. Tabbas ba na cikin baƙaƙen aljanu, kuma ni musulmi ne, sai dai ban tsaya na fahimci addini yadda yakamata ba, gaba ɗaya na fi mayar da hankalina gurin burina, na sanin magunguna. Na ji daɗin samun ahalinki, gurin amfani da su, domin baje kolin baiwar da Allah ya yi mini, sai da kash, Duniya ɗaya muke rayuwa da ku, amma tsarin taku rayuwar ya banbanta da namu da cikin ƙiftawar idanu zamani yake canzawa. A lokacin da ki ka zo, nake farincikin samun cikakkiyar damar ci gaba da ayyukana, ashe lokacin ilimin addini ya daɗe da yawaita, duk da wasu sun rintse idanunsu daga kallon ilimin, su na aikata ɓarna fiye da ta sauran mutanen baya da suka rayu da jahilci. Rayuwa tare da ke, ya ƙara haska mini juriya a cikin ƙaddara, da taka tsantsan da tsananta imani da Allah. Duk tsanani da zafin ƙaddarar da ka ke ciki. Sannan kasancewaka mutumin kirki, ko mai tsoron Allah baya canza ɗabi'ar duniya ta zama mai adalci a gare ka, ko hakan ya hana Allah ya jarrabe ka. Wasu lokutan jarrabawa ta fi tsananta ma a lokacin da ka fi tsananta addu'a. Haka zalika idan Duniya za su taru domin su amfanar da kai wani abu, ba za su amfanar da kai komai ba, face abin da Allah ya rubuta maka, haka zalika idan za su taru domin su tauye ka da wani abu, ba za su tauye ka da komai ba face abin da Allah ya rubuta maka. Ban taɓa tsammanin tsakanin ke da mijinki wani ba zai mutu ba, saboda tasirin mugun tsafin da aka yi masa, ni kuma ga haushinki ina ji, ga burin Giyaz na ɗaukar fansa a kan ki. Haƙiƙa wanda ya dogara da Allah, Allah ya isar masa, ko ba a zo wannan gaɓar ba, ni da kaina zan tafi na bar ki, na yi nesa da ke da zuriyar ki. Zan yi ƙoƙarin shafe duk wani tarihin abin da ya faru a tsakaninmu da zuriyarku, kar a samu wani ya fito daga tsatsona ya nemi sake ɗaukar fansa. Ni kaina zan tafi inda ba a sanni ba, saboda kar wataran na ji na karaya na nemi sake dawowa gare ku, na kasa cika alƙawarin da na ɗauka. Zan ci gaba da neman ilimin addini, zan ci gaba da rubutu, da kuma bincike mai zurfi a kan ilimin sarrafa tsirrai. Sai dai na yi miki alƙawarin zan rubuta labarinki da girmamawa, da alfaharin kasancewarki uwar gijiyata, na fito da kyawawan halaye da kuma ɗabi'unki ababen koyi. Tauhidinki, juriya da kuma gudun Duniya. Zan yi iya yi na na kare wannan rubutu tsawon ƙarnuka, domin ya zama misali mai kyau ga duk wanda zai karanta. Domin zan yi ƙoƙarin nesanta kaina da duk wani abu da zai sanya na shiga harkar bil'adama. A ƙarshe ina fatan ki sanar da mutanenku, darussan da ki ka koya, a tsawon zaman da muka yi, sannan ki fahimtar da su aikata ayyukan jahilici da duk wani abu da kauce hanya, saboda kana iya shukar da ba za ta fito ba wataƙila sai shekaru masu yawa a gaba, a sanya wanda ba su ji ba, ba su gani ba girbe abin da ba su shuka ba, kamar dai yadda ya faru da ke. A ƙarshe ina yi miki kyakykywan fatan alkhairi, da fatan Ubangiji Allah ya sanya jarrabwoyin da ki ka shiga, su zame miki silar shiga aljanna, Allah ya raya miki yaronki da abin da za ki haifa a gaba ya shirya miki su. Ya baki zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada. Ina kuma fatan halittun Allah su gane cewa, jinkirin amsa addu'arsu a gurin Allah, baya nufin Allah ba ya son su, kuma zafin ƙaddara da jarrabawa baya nufin Ubangiji yana ƙin ka, sai ka yi duba ga rayuwar annabawa da salihan bayi. A ƙarshe ina roƙon dan Allah ki yafe mini,  dan na san muddin ba ki yafe mini ba, sai Allah ya saka miki cutar da ke da na yi, ba tare da wata halattacciyar hujja a kan shari'a ba." Nana na kuka ta ce "Ƙaisar na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana gaba ɗaya, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka ya sanya ka cikin salihan bayinsa. Ba zan taɓa mantawa da kai ba har abada" "Nima ba zan manta da ke ba Asma'u jikar Lanti. Ina fatan za ki yi ilimi mai zurfi ki karanci fannin ilimin magungunan musulunci da na gargajiya " Nana ta ce "Na yi maka alƙawarin haka. Amma daga nan ina zaka je?" "Can nesa da Duniyarki, zan nemi ilimi sosai " "Dan Allah ka tafi da Haula mana, tana matuƙar sonka da ƙaunar ka" Ya miƙe tsaye yana murmushi, ta ga ya zama wani irin dogo mara misali. Ta ja da baya tana kallonsa. Ta din ga jin muryarsa a sama ya ce "Yi haƙuri, kar na tsorata ki, duk suffar da ki ke ganinmu a cikinta da ni da Giyaz, ba suffofinmu ne na halitta ba, idan muka fito muku a siffofinmu na halitta zaku iya rasa rayukan ku, ko ku zauce. Mu kan suffantu da abubuwa ne da idanunku za su iya kalla. Na gode sosai da sosai uwar gijiyata ina yi miki fatan alkhairi." "Wayyo Allahana, shikenan ko ziyara ba zaka sake kawo mini ba. Tabbas a kan ka na yarda a sauran halittu akwai bayin Allah na ƙwarai, ba zan taɓa bari a raba ka da rayuwarka ba kai ma. Ina yi maka fatan alkhairi uban ɗakina, kuma ɗan uwana. Na san ba haka kurum Allah ya haɗa ni rayuwa da kai ba, duk da mu na da banbancin jinsi" Kuka take yi iya ƙarfinta, Hammad yana riƙe da ita gam a jikinsa, sai mimmiƙewa take yi tana ci gaba da kiran Ƙaisar. "Asmyna, ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka" Ta buɗe idanunta a hankali ta kalli Sayyid, ta kalli dattijon malamin nan, ga su Sultan a gefe duk a cikin wani ɗaki. Ta fashe da kuka ta ce "Shi ma an kashe shi ko?" Ya girgiza mata kai ya ce "A'a yarjejeniya kawai aka yi da shi, ya ce kun riga kun gama magana ma, ya yi miki alƙawarin ya tafi ya rabu da ke har abada" "Shikenan ba zan sake ganin Ƙaisar ba? Ya cutar da ni, amma... Sai ta kasa magana ta ci gaba da kuka. "Na sani, na san komai Asmy ki yi haƙuri, mu na da banbancin da ba zai yiwu ki ci gaba da rayuwa da shi" Haka suka din ga rarrashin Nana. Shi kansa malamin ruƙiyyar cewa yayi bai taɓa samun case mai rikitarwa kamar na Nana ba, domin shi kansa Ƙaisar sai da ya yi kuka ba kaɗan ba, kafin ya ƙara tabattar wa malamin ruƙiyyar nan cewar ya bar ta har abada. Kwana biyu suka ƙara a Egypt, Nana sam ba ta walwala kamar wadda aka raba da mahaifinta, gaba ɗaya memories ɗin abubuwan da suka din ga faruwa a rayuwarta a tsakaninta da Ƙaisar suka din ga dawo mata. Tabbas za ta kasance cikin biladama masu ban mamaki da suka yi rayuwa mai kusancin gaske tsakaninsu da Aljanu. Sai da suka ƙara kwana biyun. Haka Hammad ya haƙura ya din ga rarrashinta, saboda yadda duk ta danu, domin yana iya tuna wasu abubuwan da suka din ga faruwa tsakaninsa da Ƙaisar saboda Nana. Suka koma ta Nigeria, har da Sultan da Matawalle, suka gaisa da iyayen Nana, tare da sake jaddada musu godiyarsu, bisa ga abin da Nana ta yi wa yaransu na kulawa, tare da yi musu bangajiya na zuwa biki da suka yi Agadez. Tun da suka koma Agadez, hasashen Hammad ya tabatta, domin kuwa laulayi ne sosai ya kada Nana. Babban abin da yake damun Hammad, bai wuce duk yadda ya so, ya haɗa kan Nana da Asal ba, Nana ta ƙi yarda ta ce masa komai zai yi Asal ta riga ta furta mata ba ta ƙaunarta, kuma duk mutumin da zai nuna baya ƙaunarka ba ta ga abin mu'amala da shi ba. Sai dai ya ci gaba da matsa mata har ya yi fushi. Ta ce "Sayyid, bari na yi maka gwari-gwari tabbas ina jin zafin ƙiyayyar da Asal ta nuna mini, amma muddin za mu din ga haɗuwa, ko ka ce sai mun haɗa kai, ba zata taɓa sakewa ba, zan zame mata takura kasancewar na san sirrinta, za ta din ga ganina da abin. Bana fatan zame wa kowa matsala a rayuwata, ba na fatan Asal ta rayu a takure saboda ni. Dan haka ka yi haƙuri ka ƙyale ni" Ya gaji ya gaya wa Sultan halin da yake ciki da Nana, ya ce duk ya kai masa su can gida. Tun da Asal ta ga Nana, hankalinta ya ƙara tashi, ganin Nana da juna biyu a lokacin ya ɗago sosai, ga kuma Muhsin da tana ganinsa a wallpaper Hammad. Nana ta ƙara cika ta yi kyau sosai da sosai. Sultan ya yi musu nasiha sosai da sosai, tare da roƙonsu a kan komai ya wuce, idan ba haka ba muddin suka tafi a haka, to irin jahilcin da ya din ga faruwa a baya, na faɗan 'ya'yan sarakuna a baya, to kuma zai iya faruwa naku gidan, dan haka ku yi haƙuri ku tura komai baya. Nana sai da ta ɗan sha jinin jikinta, ko a lokacin yanayin yadda ta ga Asal kamar gaba ɗaya a tsorace take, duk ta kame jikinta babu izzar nan da jin kai da take yi a baya. Suka yi masa godiya, Nana ta tabattar masa da in Allah ya yarda komai zai canza. Asal ta lura da yadda shi kansa Sultan ta Nana yake yi, yanzu baya nuna mata kulawar da yake ba ta a baya. Ta lura Hammad ne kawai ya yafe mata yake yin ta. Duk yadda ta so share Muhsin, son da take yi wa Hammad, da kamanin da suke yi da Muhsin ɗin, sai da ya sanya ta tsaya kula shi. Babu inda ya bar Hammad a kamanni. Nana ba ta fasa jin kewar Ƙaisar ba, ita kanta har ƙoƙarin faɗa take yi wa kanta, amma sabo turken wawa, babu yadda ta iya, idan abin ya ishe ta har kuka take yi. Jamila ta riƙe istigfari da addu'a, da magungunan da Nana ta bata, cikin ikon Allah ta din ga samun afuwa, a kan lamarin larura da take fama. Lamarin Suwaiba ne dai ba arziki. A hankali tana juya kuɗin da Nana ta bata, idan jarin ya karye ta kira Nana, ta ƙara bata wani, gefe Nana tana lallaɓa Baba har ya haƙura yake shiga sabgar Jamila. Gaddafi ma ya yi aure, ya sha tagomashi daga gurin Nana. Nana ba iya gidansu ba, hatta maƙwabtansu sai da suka shiga rigar arzikinta. Tana samun kuɗi sosai a Agadez, ga allowance ɗin ta na sarautarta, ga na kasamcewarta matar Sardaunan Agadez. Ga shi Hammad yana sakar mata kuɗi sosai da sosai. Ban da tarin kyaututtuka da take samu. Nana ta ƙyale Hammad yake zuwar wa da Asal Muhsin, sai dai ta tsananta addu'a. Su Tafawa suka zama ba su da wata power ko ƙarfin faɗa a ji, dan hatta dogarai da jami'an tsaron da suke tare da su, sai da aka janye musu, aka yanke albashin da masarauta take biyansu. Hakazalika duk wani kasuwanci da masarauta ke gudanarwa, ake samun riba da Nana da Muhsin a ciki. Watan Nana tara da sati biyu cif ta sake haihuwa namiji. Hammad kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, kasancewar kaf Agadez Nana ba ta da uwar da ta wuce Nene, ita ce tsaye a kanta a kan komai. Nana ta yi mamakin ganin Asal ta zo yi mata barka. Ahmad aka sanya wa jaririn, ake kiransa da Hamdan. Har da kyaututtuka Asal ta bayar a ba wa jaririn. Sosai take jin tausayin Asal, a zuwa ukun da ta yi ganin jaririn, duk lokacin da ta zo, daga gaisuwa babu abin da yake haɗa su da Nana, amma idan ta karɓi jaririn tana daɗewa sosai da sosai tana kallon yaron. Iya ƙoƙari Hammad yayi, a kan mantawa da duk wani abu da Asal ta aikata, amma bakin alƙalami ya riga ya bushe, lokuta da dama abubuwan da ta aikata masa su na dawowa zuciyarsa. Ita kanta a dole, take ƙoƙari take rintse idanunta ta kawar da kanta daga wasu abubuwan da yake aikatawa, Nana ke da miji Nana ne da 'ya'ya, kuma take da goyon bayan uban miji, da masaurauta ma baki ɗaya. Gimbiya Bilkisu ta din ga ziga ta, a kan lallai ta haƙura da auren nan, amma Asal ta ce ba za ta haƙura ba. Wataran Mahmoudu ya kawo musu ziyara, tare da matarsa, ana falo suna ta hira, yake bawa Mahmoudu labarin, darun da aka sha da Nana a kan raba ta da Ƙaisar. Mahmoudu ya hau dariya ya ce "Wasa-wasa fa, Gimbiya akwai daru, banda ita wa yake fatan tarayya da Aljani?" Hammad ya yi dariya ya ce "Mahmoudu sabo turken wawa, ita idan ka lura da ita ne, gaba ɗaya rayuwarta ba ta da damuwa, kuma tana da matsanancin tausayi amma Aljanin nan ya azabtar da ita, ni kuma ga mahaifinsa na gana mini azaba, wallahi yarinyar nan Allah ne yake kare ta, da wata ce tsaf zata haukace. Saboda azaba har a zahiri muke ganinsu, na zo da muka koma Buda hannuna na dama ya shanye, bakina ya koma gefe nikaɗai na san azabar da nake sha. Ga laulayi tana yi ga jinyata. Idan na fita daga hankalina na yi yinƙurin kashe ta, sai na dawo hayyacina sai na ga abin kamar a mafarki. Duk yadda zan kwatanta maka azabar da muka sha mutum sai dai ya ji kamar labari. Saboda jarabar Ƙaisar da babansa aka tashe mu daga wani gida da muka zauna aka ce mayya ce. Amma sau ɗaya Asmy ba ta taɓa nuna mini a fuskarta za ta rabu da ni ba, saboda ta yi imanin idan ta rabu da ni wa zai kula da ni. Amma yarinyar nan ina lallaɓata ina tuna mata abubuwan da Ƙaisar ya yi mata na cutarwa sai cewa ta yi ina ruwana, lokacin da na gudu na bar ta na san me ya yi mata? Kuma ai ta yafe masa tun da ya yi mata abin alkhairi. An sha daru kan su rabu. Tana nan tana gaya mini sai ta rubuta littafi guda, a kan Aljanu saboda Ƙaisar. Tun ina kishi da aljanin nan na haƙura da na gane dai duk abu ba jinsinmu ɗaya ba" Suka din ga dariya, Asal dai ta yi shiru, ita zancen ma tsoro ya hau bata. Fadila kuwa ta din ga yi masa tambayoyi, a kan yadda aka yi ya zamana Nana ɗauke da ɗa a jikinta shi kuma Uba. Babban abin da ya bata tsoro da mamaki, cewar da ya yi, har ciwon ɓarin jiki yayi, da irin wahalar jinya da Nana ta yi. Ya din ga misalta musu irin yadda yake ji, idan ciwon nan ya tayar masa yadda yake jin kamar ya kashe kansa saboda azaba. Asal duk sai ta tsargu, ta kalli fuskarsa ta ga hirarsa kawai yake yi, hankali kwance, ba domin da alamar wata manufa a fuskarsa ba. 10YRS LATER Muhsin na da shekaru goma sha huɗu a Duniya, Nana ta kammala karatunta, na ilimin magungunan addinin musulunci. Hammad ya taimaka mata, ta gina katafariyar cibiyar koyar da addinin musulunci, wata a Agadez wata a Nigeria. A lokacin Nana yaranta huɗu duk maza, tana sanye da glass a fuskarta tana rubuce-rubuce, Hammad ya kira ta ya ce mata Asal ce ta kira shi ba ta da lafiya, ko za ta tura mata ko Yarima ne, idan da wani magani da za a bata kuma a bata. Nana ta ce "Ahh me Yarima zai iya yi, bari na je da kaina". Ko da ta je gidan kuwa, tuni Muhsin yana can, Nana ta ce "Amma maimakon ku kira ni ku gaya mini, me Muhsin zai iya yi miki?" Asal dai ta yi shiru, Muhsin yana kusa da ita ya ce "Kawai zuwa na yi nima, na tarar da ita bata da lafiya" Nana ta ce "Ina ganin kawai mu tafi Asibiti" Nana ta taimaka mata ta canza kaya, suka tafi Asibiti. Likitoci suka ce tiyata za a yi mata a cire abin da yake cikinta. Nana ta kira Hammad ta ce masa lallai ya dawo, tiyata za a yi wa Asal ana buƙatar a saka hannu. Ya ce "Ki saka, ba zan iya dawowa a yau ba, sai zuwa gobe in Allah ya kaimu" Nana ta ce "To ai ba zai yiwu ni na saka ba, ko a kira mahaifinta a waya?" Da sauri ya ce "A'a bari na kira Sultan, kuma ki tsaya ki bayar da order, kar wani ya zo a ba shi ɗana, idan ba ke ko Sultan ba, babu yadda zan yi na dawo ne" Haka aka yi, Sultan ya je Asibiti da kansa ba wakilici ba, ya sanya hannu aka ciro wa Asal jaririyarta. Nana aka fara ba wa yarinyar, ta yi wata irin ajiyar zuciya tare da gode wa Allah, sannan ta kai wa Sultan ita. Ya rungume yarinyar yana kallonta cike da ƙauna, ya ce "Kin ga ikon Allah, bayan shekaru kusan ashirin da aure, sai yanzu Allah ya yi ikonsa" Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya, Abin da na yi ta gaya wa Sayyid kenan, ba a cire rai da rahamar Allah. Asal na kwance a post up room, ta buɗe idanunta a hankali, ta kalli Nana da take ta shafa kan jaririyar. Tsawon wannan shekarun, babu wata jituwar arziki a tsakaninsu, sai dai tun kiran da Sultan ya yi musu, ya yi musu nasiha Nana ta daina hana yaranta zuwa inda Asal take. Aka sanar da haihuwar Asal, amma aka hana kowa zuwa Asibitin da take. 'ya'yan Nana haka suka kewaye Asal da jaririyar nan, wannan ya ɗauka wannan ya ɗauka. Da kyar suka tafi gida, saboda makaranta. Ƙarfe sha biyu da rabi Hammad ya iso Asibitin. Ya tarar da Nana tana shirya jaririyar a cikin kaya. Bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa mata hannu ta bashi, Nana ta ce "Ba tukuici babu komai" "Zan baki idan muka haɗu" Tana murmushi ta miƙa masa jaririyar, ta tashi ta basu guri. Ya ƙarasa kusa da Asal yana murmushi ys rungumota ya sumbaci goshinta. Ya ce "Kin ga ikon Allah ko Cherié?" Ta yi murmushi ta ce "Na gani, kalli kamar ta ɗaya da Yarima, duk kamar ka suke yi" Ya yi dariya ya ce "Ba dole su yi kama da ni ba, ni ɗin na wasa ne. Alhamdillah bayan samari da Allah ya bamu ga 'yar budurwa." Asal ta ce "A saka mata Asma'u" da sauri ya waiwayo ya kalle ta, ya ce "Ba na son wasa" "Da gaske nake, na ga kana sonta da yawa, ko ita ma za ta ci albarkacin son da ka ke yi wa rayuwarta, ka so ta sosai" Hammad ya ce "Kin ga ni ba na son rigima daga haihuwar ki, ke cewa na yi ba na sonki ne?" Ta girgiza kai ta ce "Ai ba ƙarya na yi ba, da na ce ka na sonta sosai, kuma ta cancanci ka so ta, na gane hakan bayan da na saurari yadda aka yi ka aure ta, da irin rayuwar da ku ka yi da kunnen basira. Duk a ajiye wannan a gefe, tsawon wannan lokacin na rayu da ci gaba da sanya ran samun haihuwa da kalamanta da suka bani ƙwarin gwiwa. Lokacin da na dawo gidanka, babu daɗewa, cikin dare na tashi fitsari saƙo ya shigo wayarka ƙarfe uku na dare. Na ɗau wayar na duba sai na ga saƙonta ne, ta ce ; Albishirinka yanzu na tashi daga barci, na yi mafarkin Asal ta haihu, ana ta shagali har na tashi ina jin abin a jikina da zuciyata, ko a kusa ko a nesa mafarkin nan zai zama gaske in sha Allah, ka samu maƙubaci ka bayar da nannauyar sadaka, Allah ya tabattar mana. Kuma idan mace ce sunana za ka saka" Duk da a lokacin da naga saƙon nan, na cire rai da samun haihuwa, amma a duk lokacin da na tuna saƙon nan, sai na ji ina ƙara sanya rai. Tsawon shekara goman nan, wannan saƙon nata yana cikin kaina, ina jin sa ina fatan Allah ya tabattar da shi. Babu wanda na taɓa gayawa sai yanzu da nake gaya maka. Bayan haka sanin sirrina, da abubuwan da na aikata bai taɓa sanyawa ko sau ɗaya ta kalle ni ta yi mini gori, da abubuwan da na aikata ba, banda barazanar da ta yi mini, lokacin da na gano matarka ce ita. Kuma bata taɓa yi mini wani abu, na gadara ko makamancin haka ba, saboda ta haihu da kai ni ban haihu ba. Ko na yi yunkurin sanya wa zuciyata irin wannan tunanin Hasna da Fadila su na ankarar da ni, mussaman da Fadila ta gaya mini Nana tana addu'ar ka da Allah ya sanya mata jin wani abu a ranta, dan ta haihu ni ban haihu ba, balle ta yi wani abu da zai sosa mini rai. A ƙarshe, na san maganin da ka kawo mini, ita ta sarrafa shi a kaina ta yi gwajin maganin haihuwa, kuma Allah ya amsa. Babu riba yin adawa da mutane irinta, rayuwarta take yi kai tsaye, ba tare da ƙyashi ko baƙin ciki ba. Kuma kasancewata tare da su Hasna, suna ƙara saita ni, saɓanin da da nake tare da miyagun ƙawaye. Na san ba zan taɓa kai wa ko rabinta a zuciyarka ba, kuma ba zan yi maka dole ba, iya wannan jihadin na zama da ni ka yi, ya isa a kira ka gwarzo, kuma hakan ne hukuncin da ya dace da ni, kana iya ƙoƙarinka a kaina, amma ni dai ka saka mini sunanta, ba kuma na yi hakan dan na burge ku ba ne, ko a ce tsirfa ba ce, a'a na yi hakan ne saboda jin wani sashin na damuwata da ta yi kamar tata." Gaba ɗaya jikin Hammad ya yi sanyi sosai da sosai. Ya rungumo Asal a jiknsa, yana sumbatar goshinta ya ce "Abubuwan da suka faru sun riga sun wuce, ki daina dawo da su. Kuma tun farko abubuwan ku ne na kishi da yake damunku, amma tabbas Nana tana da halaye da ɗabi'u na kirki, ina fatan Ubangiji Allah ya haɗa mini kanku gaba ɗaya ya shirya mini yarana". Nana ta ƙwanƙwasa ƙofar ta yi sallama, suka amsa, ta shigo da kwanukan Abinci. Hammad ya ce "Wai gida ki ka je?" "Eh na je na ɗaukko Abinci ne, mutane na ta son su zo su ga jaririya fa." "Ki ƙyale su, idan sun koma gida a ganta" Har ranar suna Nana ba ta san sunanta za a saka wa jaririyar ba, aka shirya gagarumin suna a Agadez. Nana ta yi wa jaririyar nan kaya na alfarma. Kawai ta ji Hammad yana gaya wa Zahradeen wai sunan jaririya Asma'u. Nana ta yi turus ta ce "Sayyid, amma da wasa ka ke yi ko?" "Kamar yaya wasa? Da gaske nake" Cikin damuwa ta ce "Dan zatin Allah ka yi haƙuri, wannan ai rigima ce, kawai salon ka ja mini magana a garin nan, shekara da shekaru tana neman abu, ta sha wahala ta haihu kuma a saka sunana?" "To ai ita ta nemi hakan ba ni ba" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi mata fin ƙarfi dai, Asal ba za ta yarda a saka wa yarinyarta sunana ba. Ni dai dan Allah ka canza" Kawai ya hau dariya, ya ce "To ni yaya zan yi muku? Idan kin je gurin sunan, ki tambaye ta" Nana ta ce "A'a ni dai na yafe, dan Allah ka canza mata suna, ya za a yi ka yi mata haka, salon kawai ka saka a ƙara tsana ta" "To ai ni ina sonki dan a tsane ki ba komai tun da ina sonki" Da gaske Nana ta fututtuke ta ce bata yarda ba, sai da ya ɗauke ta suka je gidan. Asal ta ce "Dan na ce a saka wa jaririyar ki sunanki shi ne za ki ce ba kya so? Kina jin haushina kenan tun abubuwan da suka faru tsawon shekaru goma" Nana ta ce "Wallahi ba haka ba ne ba, ba na son a yi miki fin ƙarfi ne, a takura miki abin da ba kya so" Asal ta ce "A'a ni na ce a saka mata, babu wanda ya takura mini" Nana ta yi wa Nana bayani kamar yadda ta yi wa Hammad, sannan ta ɗora da cewa "Nana ni da ke mu na da tabon juna, da ba zai taɓa yiwuwa na ce sai mun yi nu'amala da juna ba. Amma ina son yaranmu su tashi da haɗin kai, kamar yadda ki ka kawar da kai ki ka nuna mini yaranki nawa ne. Ba na fatan a sake samun matsala na rabuwar kawuna saboda mulki ko abin Duniya a tsakanin yaranmu. Ina fatan za ki saka mini takwarar ki a cikin su Yarima, ta samu kyakykywar kulawa. Kuma ina godiya da dukkanin wasu abubuwa na alkhairi da ki ka yi mini, da ɗaukar damuwa ta taki, duk da ba jituwa muke yi ba" Wani irin farinciki ya mamaye ta, ta ce "Tabbas takwarata kin haife ta ne, amma ni ki ka haifawa. Kuma na yi wannan alƙawarin na sanya ta cikin jerin 'ya'yana. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ya kawo biyar a bayan ta" Asal ta ce "Biyar sun yi yawa ai, yadda shekaruna su ka ja ɗin nan? Ita ɗin ma na gode Allah" Nana ta ce "Taskar Allah babu abin da babu, ko ba biyar ba Allah ya ƙaro mana wasu, shekara iyanzu a ce an kusa haifo mana wasu. Na gode sosai da sosai da karamcin nan da ki ka yi mini" Jin sunan da aka saka wa jaririya, ya janyo cecekuce sosai da sosai a garin. Da ganin kamar ba a yi wa Asal adalci. Kwanan Husna arba'in, Nana ta buɗe cibiyar magungunan musulunci. Manyan mutane duk sun halarta, har da 'yan uwan Nana na Nigeria. A daidai lokacin ta kammala rubutun littafinta, da ta yi bincike tsawon shekaru, a kan aljanu, da ilimin ruƙiyya da ladduban yin ta. A cikin sunayen mutane masu muhimmanci da ta lissafo a cikin littafin, sai da ta sanya sunan Ƙaisar Giyaz. Ko da aka nemi Asal ta tofa wani abu a gurin taron, Nana ba ta zaci za ta yi magana ba, amma ta karɓa ta taya ta murna, tare da shaidawa duniya, a kanta Nana ta fara gwajin maganin haihuwa kuma Allah ya amsa. Nene ta taimakawa Nana sosai a ɓangaren magungunan, haka Sarkin baka ya halarci taron, Hammad ne da kansa ya gayyace shi. Ya din ga yi wa Nana dariyar ba a guje wa ƙaddara. Nana ta yi murmushi ta ce "Na karɓe ta ta hanyar da ta dace ne" Nana ta yi shiru tana kallon gurin nata. A hankali ta furta "Na cika maka alƙawarinka uban ɗakina" "Nima na cika wanda na yi miki uwar gijiyata, na rubuta tarihinki da alƙalamin zinare a cikin kundi na mussaman da ba zai ɓace ba" Ta ji tamkar muryar Ƙaisar a gurin. Idonta ya sauka a kan award da ta yi da sunansa ta ajiye a gefe guda. Shukura wannan rashin lafiya da ta yi ta fama, da damuwar da take ciki ne yayi ajalinta, Yusra ta shiga damuwa da tashin hankali sosai, sai dai ta rungumi yaran Shukura da waɗanda ta haifa. Jamila ta samu wani jami'in ɗan sanda mai mata biyu ta aura, Allah ya taimake ta, ya ware mata gidanta sai dai tana shan azabar kishiyoyin duk da haka. Ta rungumi sana'arta sosai da sosai. Suwaiba kam ƙwaƙwalwa ta riga ta taɓu haka Mama ta ci gaba da wahala da ita. Allah Al-musawwiru, shekarar Husna ɗaya a duniya, ta sake samun juna biyu, a dole Nana ta ɗauke ta, ta yaye ta. Ta haifi yara biyu mace da namiji. Nana kuma sai a haihuwa ta ƙarshe, ta haifi 'ya mace, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma kan yaransu a haɗe yake sosai da sosai. Nana tsaye take a kan tarbiyya da kuma ilimin yaran mussaman na addini. Hatta garin Buda sai da suka amfana da Nana, dan ta sai filin da kukar Lanti take, filin da kukar da aka yi wa Lanti girka, aka buɗe islamiyya. Sannan duk shekara suna samun abin alkhairi na kayan masarufi mussaman da azumi. Ummanta duk ta aurar da ƙannenta mata, Imrana bayan ya kammala karatunsa, ya yi zamansa a faransa, sai da Nana ta matsa masa da batun aure, sannan ya ce ta samo masa duk wadda ta yi mata zai aura. Suka rayu cikin kwanciyar hankali, da son juna. Ta samu kulawa da tsantsar soyayya daga miji, yaransu gaba ɗaya suna matuƙar sonta da ƙaunarta. Husna kuwa tamkar babbar 'yar Nana. Yayin da Yarima yake ɗan gurin Asal. Ta shiga cikin mata da aka sanya sunansu a kundin tarihin Agadez. Ta rayu cikin aminci da nutsuwa, a rayuwar da sai ta so ta yanke tsammani saboda gwagwarmaya. Sai ɗan sauran ƙalubale da faɗi tashin rayuwa da ba a rasa bawa da shi. A hankali ya yi ajiyar zuciya, ya kalli matashin da yake zaune yana saurarensa, ya ce "Ka ji labarin Gimbiya Asma'u, to kai ma shigen abin da ya faru da su ne yake shirin faruwa da kai" Ɗaya matashin ya ce "Allah ya yi mini tsari, idan kuma ni ban taki irin wannan sa'ar da Nana ta taka ba fa? Lallaɓawa zan yi na bi dare na gudu na bar garin nan, sai ta koma bin wani. Haka kurum mahaukaciya ta liƙe mini ta din ga bi na" Ɗayan ya kwashe da dariya, ya ce "Dan Allah kar ka yi haka. Yau wuni ta yi a ƙofar gidan ku, an bata abinci ta ƙi ci, Yaya kawai take faɗa, dan Allah ka je ka bata Abinci kamar ma ba ta da lafiya" "Kai wallahi ba zan koma ba hauka ake yi, idan ta gaji ta ƙara gaba ta nemi wands za ta bi" *Tofa, ko su kuma wannan matasan suwaye? Waye wannan aka ba wa labarin BUZU da Nana, shi kuma wace mahaukaciyar ce take bin sa. Sai mu tara a gaba a cikin jerin littattafan da za su zo muku daga alƙalamina nan kusa ko a gaba* (Waɗanda suka gaza juriya, a farkon littafin da ganin na matsa rayuwar Nana a farko, ina fatan a ƙarshe kun fahimci abin da nake son ku fahimta. Ba kowace Addu'a Allah yake karɓa a take ba, ya kan jinkirtawa bawa, ya amsa masa lokacin da ya fi dacewa. Annabawan Allah misali ne a kanmu. Har kullum ina fatan zamu din ga kamanta wasu darussan da muke karantawa a littafi, da rayuwarmu ta zahiri, hakan ne zai sanya a ɗauki gyararrakin da yakamata.) TAMMAT BI HAMDILLAH. KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE. ALLAH YA KAWO MU ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN LAFIYA. DUKKAN YABO DA GODIYA DA JINJINA DA KIRARI SU TABATTA GA BUWAYIN SARKI GAGARA MISALI DA YA BANI ARON RAI DA LAFIYA, NA KAWO WANNAN LITTAFIN BAYAN SHAFE TSAWON SHEKARU BIYU INA BINCIKE A KANSA. INA ROƘON ALLAH ABIN DA NA YI NA KUSKURE YA YAFE MINI. GODIYA TA MUSAMMAN GA TEAM ƊIN BRIGHT PENS Aisha Adam Ayshercool Zainab shehu kumurya Na'ima Suleiman Nazeefa sabo Nashe. Ƙungiyar YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA. Godiya ta mussaman taki kekaɗai Amanar Cool Sai kuma gaisuwa ta mussaman da godiya, bisa taimakawa bincikena da ku ka yi. Maryam Muhammad Mum amnash Dr. Salihu Nura Adam (Salihan nur) Fatima A abdou Nijar Da ma kafatanin marubuta baki ɗaya. Hakazalika ina godiya, ga masu gyara, sharhi da shawara Ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi ya fi ni yabawa. Na gode sosai da sosai, da jimirin bibiyata, ina roƙon Allah duk wanda ya karanta littafin nan, ko ya ƙaru da wani abu, ko bai ƙaru ba Ubangiji Allah ya tabattar da zukatanmu ni da ku a kan Imani. Ina miƙa godiya sosai da sosai, ga waɗanda suka kasance tare da ni a tafiyar nan, tun daga telegram har AREWABOOKS. Waɗanda na yi wa kuskure, ina mai baku haƙuri, saboda ɗan Adam ce ni, mai ajizanci. Wanda ku ka sarrafa mini littafi, ta wasu hanyoyi ba da izinina ba, ba a yafiya ranar lahira. Wanda kuka karanta mini baku saya ba, ga account number na zan saka, ku bani hakkin wahalata na wata shida, akasin haka ina muku tuni da duk mai son ci gaba a nasa neman, baya yi wa wani mugunta. Kuma hakkin wani komai ƙanƙantarsa na iya kawo maka naƙasu a naka neman. A saka mini hakkina dan Allah, ko na bar mutum da Ubangijin Musa da Harun, ubangina ubangijinku. 0069685771 Aisha Adam stanbic bank. Sai mun haɗu a littafi na gaba, idan Allah ya bamu aron rai da lafiya. 08081012143 💃💃💃💃