TYPING 📲 FRI [08/01/23 08:30AM YUSRAH MUSA ABUBAKAR 💋🤟.  WHATSAPP NO. +234 816 098 3083. 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 SAFREEYYAH 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 (🏡 home of hospitality👐 and harmony). 👆Gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya🕊. (Yan annuri I really love you everything about you is so good but one thing is wrong that you are not mind wannan haka yake). Yusrah Musa Abubakar. DEDICATED TO MY MUM I LOVE YOU WITH ALL MY BODY AND HEART YOU ARE THE BLOOD THAT SCULATED IN MY HEART YOU ARE MY LIFE I LUV U💝 MAMANA. Some say hello some say hay but in islamically said:Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu. In the name of Allah the most benefits and the most merciful da sunan Allah buwayi gagara misali tsira da aminci su tabbata ga masoyin mu Muhammad rasulullah s a w we love our Nabeey we like him and peace be upon him AMEEN🙏👏. 🕌🕋🕌 Happy Juma'at Mubarak to all Muslims and it's Friday don't forget to recite suratul-Al khaf, I am so blessed to be a Muslim Alhamdulillah. (*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*) 📖Littafin 👉 Safreeyyah is a fiction 'kagaggen labari mai zaman kanshi sa annan banyi amfani da tunanin wani ba zallar basirar da Allah yaban ce please 'yar uwa ko d'an uwa marubuci ko marubuciya irina wanda taga littafin kuma taga wata kalma daidai da (A)👈 wanda tayi yanayi da wani littafin ta data taba rubutawa to tayi hakuri 🙏kuskuren basira aka samu tunanin mu yazo daya😜, na gode Yusrah ce👌. Ayi hakuri idan an samu typing error🚨. #YUSRAHMS# NO.01👉 02 Zaune take a kofar daki ta rafka tagumi naban tausayi da alama ko sanin hawaye sun jike mata fuska batai ba saboda irin tunanin datayi zurfi a cikin sa bangare guda kuma wutar data hura ce batasan ta mutu ba. Fitowar wata mata daga daki kenan ganin abinda ya faru da wutar ta yasa ta karaso a fusace tana sauke mata wani irin duka a bayan ta cikin tsawa tace"lallai Safara'u tunanin ubanki kike har kika bar min wuta ta mutu saboda baki gaji arziki ba shegiya dangin tsiya wallh ko kukan jini zaki wahala yanzu kika fara sha . A matukar zarane wannan kyakkyawar budurwar ta dago da manyan idon ta farare tas wanda a yanzu kukan da take sun koma ja tana kallon wacce ke tsaye a kanta batai zato ba ta sake jin saukar mari a fuskar ta wanda saida ta kifa kasa daga kan kujerar da take. Rai bace matar tayi kanta tana kara rufe ta da duka tace "shine zanyi miki mgn ki tsare ni da wadannan mayun idon naki masu kala dana mujiya bankadaddiya wallh na sake fitowa naga wutar nan ta mutu saina kusa kashe ki "ta karasa mgnr tana kai mata hauri da kafa ta kuwa same ta a ciki. Ba shiri ta saki kara tana rike cikin sbd azaba agurin ta kwanta tana murkususu tsallake ta matar tayi tana cewa"Allah yasa ki mutu kafin na fito da wallahi naji dadi na rabu da kaya me za'ai da rikon dan wani hakan ma dan kishiya aikin banza gayyar tsiya"daki ta wuce bata damu da yadda taga tana juya kanta alamar wani abu ya same ta ba. I Shigowar wani dattijo kenan ganin ta kwancce yasa ya saki ledar dake hannun shi kayan cefanan daya sayo suka tarwatse a kasa da saurin sa ya karaso yana daga ta ganin yadda jini ke fita a hancin ta cikin tashin hankali ya soma kwalla kira "ke Asabe ke Asabe kina ina ne me ya samu Safara'u jini yake fita daga hancin ta". Jin shiru ba'a amsa masa ba gashi ta fara amai harta bata masa kaya sai kawai ya mike yana daga ta Aisha ce ta shigo daidai zai fita a gidan rike da Safara'u. Hankali tashe tace "baffa lfy me ya same ta "bashi da bakin mgn kawai cewa yay taje gida maza tace yayan ta Murtala yazo zai kaisu chemist za a duba ta. Da gudu Aisha ta juya tana kuka yayin da baffa ya fita da ita kofar gida da yake makaranta ce dashi dukkan almajiran dake karatu acan dan nesa da gidan karkashin wata babbar bishiyan dorawa suka taso da saurin su suna cewa"malam lfy?"kai ya daga musu gabadaya ya kasa mgn. Suna haka saiga murtala da wani dan jitan dinsa na talakawa bayan sa kuma Aisha da babarta basu tsaya tambayar me ya faru ba kawai dora safara'un sukai a bayan mashin din babar Aisha ta hau domin ta rike ta Baffa da aisha suka bisu a baya. Jin mashin ya tashi yasa Asabe fitowa tana jan tsaki tai gurin wutar ta tana gyara itatuwan ta sun riga sun daina ci ita kadai sai tsine tsine take kuma tana fatan Allah yasa kada su dawo da Safah a raye saida ta maida wutar yadda take ta mike kenan ta gano kayan miya a barbaje alamar ya shigo rudewa tasa ya zubda bai kawo mata ba karasawa tay da kwano tana bi tana debewa tace"dole ka zubar mana tunda na taba 'yar gold mai ido da kwalli ta gaban jirgi ta gaban mota zaka dawo ka same ni indai na amsa suna na Indo. Tofa muje zuwa me hankali ya hau kura😂😜. Taku ce ta kullum Yusrah yar musa bin abubakar muhammad . Wata tsaleliyar tsadaddiyar mota ce wacce akafi sani da Mercedes-Benz take shara gudu akan wani kyakkyawan titi daya sha kwalliya ta ko'ina sosai motar ke gudu kamar sama zata tashi har wani tsalle take ita kadai. Motoci kuwa dama sun tsaya kowa ya parker a gefen titi dan sun san waye mai wannan motar bazai wuce yariman su ABDUL-JABBAR ba kuma hakan ya tabbatar musu da ya dawo yana gari . A wani irin kayataccen get ya tsaya yana horn da karfi kamar yadda yake da sauri aka bude masa tare da risnawa duk da basa ganin sa da gudu ya shiga masarautar wani titi ne shima mai kyau ya karya kwana ya shiga gurin tafiya mai nisa yai kafin ya iske inda motocin mahaifinsa suke yai parking da kyau wanda saida saurayin dake kusa dashi ya kusan bigewa da kujera. Fitowa sukai kusan kamar su daya saidai Abdul-jabbar yafi dayan fari kayan su irin daya sai sheki suke rike hannun juna sukai yayin da Amfal ya kalle shi yana cewa "kai gaskiya bros ka rage gudu a mota wallh banyi tunanin zamu zo gida lfy ba na dauka sai munbi ta asibiti nifa idan ba rudewa nayi ba ji nake motar kamar tsalle take". Murmushi yai yana kallon sa ba tare da yayi magana ba suka shiga fadar mahaifin nasu wanda masu tsaron kofar da sauri suka bude musu kana suka duka domin kwasar gaisuwa suna cire musu takalmin su. Mahaifin nasu na ganin su ya saki murmushin jin dadi yana mikewa tsaye ya bude musu hannu rungume shi suka wanda suna jin lokacin dayai ajiyan xuciya a rayuwa yana matukar son wadannan zaratan samarin kyawawan 'ya'yan nasa burinsa fatan sa addu'ar sa a kullum Allah ya kara hada kansu. Zama sukai suna sashi a tsakiya bayan sun gaida shi har lokacin murmushin sa na nan akan fuskar sa kayan marmarin dake gefe ya dauko apple guda daya yana kaiwa saitin bakin Abdul-jabbar rike hannun nasa Abdul-jabbar yay shima ya kai apple din saitin bakin Amfal karba Amfal yay daga nan shima Abdul-jabbar din ya karba sarki kuma yaci a karshe wajen saitin inda suka gucira kafin ya aje sauran. Yana kallon su yace "Allah yayi muku albarka 'ya'yana ya tsare min ku daga sharrin makiya ya baku mata na gari masu kyan hali kamar yadda kuke. "Ameen Abban mu mun gode Allah ya saka da alkhairi. Kai ya jinjina daidai shigowar wata mace ta kalle su sau daya kafin ta mayar da kallon ta kan Abdul-jabbar a ranta tace"ka dauke min da har tsawon kwana uku kun dawo amma bai nemi ya ganni ba wato kana son raba ni da shine sbd kai baka san dadin uwa ba to wallh baka isa ba". Ganin kallon da take masa yasa cikin muryarsa mai firgita mata dodan kunne a duk lokacin data jita yace",barka da shigowa Ammi fatan lfy a gare ki "kara kallon sa tay gira ya dage bai sake mgn ba ya dauke kanshi daga saitin ta . Dan tsaki taja kadan tana zama ta kalli sarki da shikam farin ciki ne tsantsa yake nunawa cikin yake tace"barka da hutawa ranka ya dade ashe yan lelen naka sun dawo amma basu ko leko ni ba"ta karasa maganar kamar zata zubda hawaye sbd bata san sanda maganar ta fito ba dan Allah ya tsari gatari da saran shuka tacewa Abdul-jabbar danta inaaa har abada. Emir(emiya sarki) bai tanka mata ba kamar yadda suma basuyi mgn ba taji haushi dan sarai ta dade da fahimtar idan tana gurin basa maganar arziki ta rasa dalili mikewa tayi bata sake cewa komai ba ta nufi fita. mikewa Amfal yai yana cewa"ammi kafin mu shigo kisa a hada mana abinci dan Allah banza tay masa zata fita taji Emir yana cewa"a'a ki barshi ga nawa ya ishe mu"aikam fuuuuu ta fice da sauri cikin bacin rai ita da danta yana masarautar amma sai tayi kwana nawa bata ganshi ba kamar bai damu da ita ba dole ta sake shiri tasan yadda zatai ta raba su ko ta wacce hanya ce. Alhmdllh Murtala yakai Safara'u chemist kamar yadda baffa yace kuma an duba ta dalilin fitar jini a hancin ta marin da Asabe ta mata ne da yake chemist ne ba asibiti ba kuma shima chemist din kusa da garin su yake a ranar suka koma gida yayin da Atine ta nemi Baffa ya kyale su tafi da Safara'u can gidan su. Amma yace a'a zai kula da ita insha Allahu badan sun so ba suka hakura yana rike da hannunta suka shiga gida Asabe dake kwance kan tabarmar kaba a kofar daki da yake lokacin zafi ne ganin sun shigo yasa ta tashi zaune tana gyara daurin kwali. Cikin salon munafinci tace"a'a ni 'yarnan daga ina tun safe ina ta zulumin ina kuka shiga na tambayi almajiran ka suka ce basu sani ba sunga dai murtala yazo da mashin ya dauke ta sun tafi wani guri ince dai lafiya dai ko"?. Kallon mamaki Baffa ke mata lallai matar nan ta raina masa hankali banza ya mata bai bata amsa ba ya zaunar da Safara'u yana shiga dakin da take kwana ya dauko wata karamar katifa ya fito da ita saida ya gama mata shimfida sannan yace ta zauna. Kofi ya dauko yana hada mata shayin daya sayo ya bata yana bare mata ayaba da lemo domin idan bai sani ba a yau bata ci komai ba saifa yanzu. Asabe dake kallon ikon Allah ta rike kugu tana cewa"kwarai malam wai a hakan kasan Allah amma baka da adalci wato ita da yake kaine ka haife ta saika sayo mata kayan dadi ni kuma dayake tsinto ni kai shine ina maka magana ka bawa iska ajiya ta". Kallon mmk Baffa ke mata "amma wallh Asabe baki da tunani ko kadan sbd shashanci yarinyar bata da lfy baki fada min kuma yanzu kice wai bani da adalci idan da kuma gawar ta na zo na samu fa shi kuma kice min me kinga Asabe ki fita idona idan kika kaini bango zan dau mataki a kanki karki manta yarinyar nan marainiya ce. Kuka Asabe tasa"wato abin harda zagi fada baizo ba gori yazo sbd ni ban taba haihuwa ba nagode da ci min fuska "daki ta shige yayin da baffa yaci gaba da kula da Safara'u saida ta koshi sannan ya daura mata gidan sauro ta kwanta shi kuma ya koma zauren gidan inda ya saba kwanciya. Bayan kwana biyu Safara'u ta dawo daidai saidai rashin mutuncin Asabe babu abinda ya canja saima gaba da yake dad'a yi kullum. Murtala na son safara'u amma ita kam a nata bangaren da sauki mutuwar bako a gari tafi son Adamu kuma kamar yadda tafi son Adamu Asabe haka take so dan murtala yana da dan abin hannu Adamu kuwa sai zaman majalisa kadai ya sani". Typing 📲 @¥$® ♏✔$^ ^%✅🅱^©^® 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 SAFREEYYAH 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 📚👌 Yusrah Musa Abubakar Gaisuwa gare ku yan Annuri masoya na kwarai ina matukar jinjina muku na gode da kauna Allah ya kara barin mu tare AMEEN.🙏 SAFEEYYAH ALIYU HAJARA ABLA'S INDO CE HAJARA B/KD MARYAM ALIYU AISHAT ABUBAKAR KEBBI ZARAH MUSA DAN ADAM NAJA'AT MUSA ABUBAKAR FATEEY MUSA ABUBAKAR. HAKIKA BANDA KAMAR KU KUNA RAINA IRIN SOSAI DIN NAN ONE LOVE 💞YAN UWA. #YUSRAHMS# NO.03👉 04 Zaune wata tsohuwa take wadda tadan manyanta a wani tsararran palor ita kadai take da radio a kusa da ita tana saurara. Sallama akai tare da cewa "mu shigo ko mu tsaya"?murmushi tayi dan ta gane mai muryar tace"wanda bai maganar ba ya shigo kai kuma aku mai bakin magana zuwa zakai ka dame ni dan haka koma ban gayyato kaba". Shigowa Amfal yai yana dariya bayan sa Abdul-jabbar zama sukai kusa da ita wanda kafin suyi mgn tace"wai dan Allah ku kuwa zakuiyi aure kalle ku gird'a gird'a amma babu mai zancen zaiyi mata to sai yaushe ko saina mutu"?. "Eh jira muke saikin wuce kabari tukuna kafin muyi dan muna yin aure saikin dorawa matan mu hawan jini shi yasa munfi son saikin gangara . Harararsa tay tana cewa"idan bakin ciki kake min yaro ba yanzu zan mutu ba saina ci lokacin yayan ku ma ran karfe gare ni ". "Taf waya fada miki aikam ran roba gare ki kuma bari kiga nagwada wani abu" sanda ya dauko kamar zai rima mata ba shiri yasa ta ihu tana kankame Abdul-jabbar wanda ke kallon su tun dazu suna burge shi saidai bazai iya surutu haka ba . Murmushi yayi yayin da Amfal ya aje sandan yana cewa"haba hajiya mai ran karfe da kin bari na gwada ashe dai da gaske kina tsohon mutuwa". Hararar sa tayi tana gyara zaman ta tace"kana jin mu ko Abdullahi daya rade ni kucewa uban ku me kun kashe masa uwa". Allah Amfala ka kiyaye ni ku tashi ku tafi ma na gode da ziyara sai anjima mikewa sukai hajiya ta bisu da kallo tana cewa miskili Allah ya baka mace mai surutu sai naga yadda zakai" Dan dakatawa yayi ba tare daya juyo ba yace"saina kawo miki ita kuje ku karata dan bazan taba auren mace mai surutu ba gadai wanda zaki wa fata madam " Dakuwa hajiya ta masa"kuma nice madam din "?Amfal zaiyi mgn hajiya tace"dan Allah kuje nagode ". "Allah bazan tafi ba saina fada hajiya ina sonki kuma bros dina ma yana sonki ma'ana dukkan mu muna sonki sai anjima ki huta lfy yau kisa a kawo miki abincin mutum uku dan anan za muci abincin dare". Murmushi tay "to naji sai anjima na gode" Fita sukai suka shiga sashin Ammi a palon suka same ta ganin su yasa ta hade rai tana cewa"me kuma ya kawo ku guri na ku koma inda kuka fito bana bukatar ganin ku". Da mmk Amfal yace"wai dan Allah Ammi me kike haka gaida ke fa muka zo yi sai kice bakya bukata". Harararsa tay"eh nace bana bukata idan kuma zaka sani dole sai naji babana"murmushi Amfal yai yana sakin hannun Abdul-jabbar ya karasa inda take yana zama tare da rike hannunta. Yace"yi hakuri Ammi yanzu zamu tafi basai kin kore muba dama haka ne idan mutum baida uwa saidai yay tabin rabi ana korar sa kamar wani kolo dan kawai mu marayu ne"ya karasa mgnr yana kallon yadda ta zaro ido jin abinda yace. Kara hade rai tayi tana cewa "a gidan uban wa ka zama maraya bayan ubanka na nan kuma nima mahaifiyar ka ina nan". kai ya girgiza "a'a Ammi mahaifi dai yana nan amma mahaifiya ta bata raye domin bani da bambanci da maraya kuma nida Abdul-jabbar abu daya ne mahaifiyar sa ta rasu bai san dadin uwa ba kamar yadda nima ban sani ba domin baki jani a jikin ki mun shaku ba ". Dafe kirji Ammi tay cikin tashin hankali tana kallon Amfal tace"na shiga uku ina mafarki ne ni kake fadawa wadannan maganganun Amfal ka fara hauka ne ko wannan mara mutuncin ne ya fara koya maka shaye shaye don labari yazo min cewa babu abinda baya sha a UK gaskiya ne". Mikewa Amfal yay yana cewa "eh ba haka bane mukam mun tafi dama sallama muka zo miki dan gobe gidan gona zamu wuce mu huta sai minyi sati zamu dawo ki huta lafiya"ya karasa maganar yana kissing hannunta karasowa Abdul-jabbar yai yana cewa"sorry Ammi kiyi hakuri"bata iya magana ba shima kiss ya bata mai matukar dumi da shiga rai kafin ya kalli Amfal alamar su tafi. Mikewa yay suna fita daga part dinta tafi mintuna goma da suman zaunen da tay daga baya ta sauke wani irin numfashi tana kallon inda yai kissing dina kafin ta goge tana mikewa ta fara zaga falon cikin juya maganar Amfal wato yana nufin ita photocopy ce bata da wani amfani lallai hakan ya matukar furgita mata lissafi dole tayi damara ta fara yaki domin ta kwato danta ya dawo gare ta yasan darajar ta. Tunawa tayi lokacin da Emir yace mata"Adama ina son Abdul-jabbar zai tafi karatu zan sashi a makarantar koyan aikin soja amma mene shawarar ki akan haka ya dace ko a'a". Murmushi Ammi tayi"eh to ranka ya dade ina ganin hakan zaifi domin Abdul-jabbar da soja ya dace kuma me zai hana ka saka su tare da Amfal gabadaya "kai Emir ya daga masha Allah hakan yayi nagode da shawara za'a saka su ". Murmushin samun nasara Ammy tay cikin jin dadi ta koma part dinta ta sani ba karamar wuya zata sa a ganawa Abdul-jabbar ba lallai akwai ta da kwakwalwa. Hanne ce ta shigo tare da cewa"ki gafarce ni ranki ya dade ance kina nema na"?. Kai Ammy ta daga eh ina neman ki hanne dama mai martaba ne ya kira ni dazu akan wai yana neman shawara ta zai tura Abdul-jabbar aikin soja nace masa eh sbd ina ganin wannan hanyar kadai zanbi na kuntata wa Abdul-jabbar nasa a gana masa azaba ya kasa jin dadin zaman duniya ya gwammace mutuwa da rayuwa". Kara dukawa hanne tay "haka ne ranki ya dade to amma indai kina son hakan saidai kar Amfal ya bishi domin idan suna tare burin ki bazai taba cika ba GAmfal da Abdul-jabbar akwai kauna da shakuwa mai karfi tsakinin su kuma zai wahala nan gaba ki samu kan Amfal domin Abdul-jabbar yana da shiga rai kamar yadda mahaifiyar sa take". Mikewa Ammi tay tana cewa"da kyau hanne tunani mai kyau zan koma gurin mai martaba na fada masa cewa Amfal bangaren likitanci zaiyi shine kadai hanyar raba su na gode sosai hanne tashi kije kuma kada ki bari kowa ya sani ni da ke ne idan maganar nan ta fita kinsan sauran". Jiki na rawa hanne tace"a min afuwa ba wanda zaiji hakan". "Ok yayi jeki". Bayan fitar hanne Ammi tay shiri ta koma gun Emir da salon jawo hankali saidai ta makaro baya magana biyu yace shawarar farko data bashi yafi so iya tashin hankali Ammi ta shiga har bacci ta daina yi amma hakan baisa ta juya ra'ayin Emir ba kuma tana ji tana gani suka tafi UK a tare yayi da har ramar bakin ciki tay kullum tana cikin saka da warwara". Sauke ajiyar zuciya Ammy tay bayan ta dawo daga dogon tunani ta kalli kofar da suka fita rai bace ta soma magana "laifi nane tun farko dana bawa mai martaba gurguwar shawara amma ba komai indai ana tare Abdul-jabbar nayi alkawari baza ka taba jin dadi ba duk hanyar da nasan zaka kuntata zan bita komai had'ari kuwa saina kaika kasa". Har kamar ni Adama wai dan dana haifa zaice bani da wani amfani a gunsa saboda da kai lallai Abdul-jabbar ka kira mutuwar ka saika gane kuren ka domin kai d'ana bai ganin daraja ta ". MRS AL'AMEEN AHMAD CE👌. ANA TARE INSHA ALLAH. Yaukam na gama typing sai idan Allah yaja kwanan mu zuwa gobe saimu dora inda muka tsaya.😜 Typing📲 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 SAFREEYYAH 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ANNURI WRITER'S ASSOCIATION🌌💫 📖🖊 Yusrah Musa Abubakar BARKAN MU DA KWANA 'YAN GROUP DINMU NA ANNURI AND VIP WOMEN24 TV DA GROUP DIN HAJARA @BLA & NI,'IMATULLAH FANS GROUP GA GAISUWA MAI TARIN YAWA DAGA YUSRAH .💞🍇💝. Start your day beautifully with fajr prayer and quran recitation. O Allah s w t make us among those who never miss salah🕌 AMEEN🙏👏. Yan uwa mu dage never stop learning because life never stop teaching. Yusrah Musa Abubakar #YUSRAH# NO.05👉 06 Shiru tayi sai kawai wani abu ya sake fado mata lokaci mai tsawo daya wuce ta riga maman Abdul-jabbar auren Emir kuma ta dade bata haihuwa bayan mutuwar uwar gidan sarki ya auri maman Abdul-jabbar ta wata hanyar ban mamaki da ba zata manta ba. Mai martaba yaje ziyara masarautar adamawa ya kuma yi kwanaki sakamakon dama can shida sarkin adamawa abokanai ne na hakika bayan yayi sati ya nemi komowa gida . Bayan sunyi ban kwana da sarkin adamawa kuma yayi masa rakiya mai dan nisa suka sake yin ban kwana barowar su adamawa kadan suka riske wani karamin kauye dake bakin titi a hanyar kuma dama suna bukatar ruwa zasu zubawa mota dan hakan sukai parking a bakin titin. Driver ya fita domin samo ruwa amma abin mmk garin kamar anyi yasa babu kowa a waje gashi ba halin ya shiga gidan mutane yana cikin tsaye wata kyakkyawar yar fulani tazo wucewa da korai da yawa a kanta kamar yadda fulani keyi idan zasuje tallen kindirmo(nono). Da sauri ya tare ta yana cewa "dan Allah idan kina da ruwa kidan bamu zamu saka a mota dakatawa tay tare da juyowa tana kallonsa tace"daga ina "amsa driver ya bata sarkin kano ne munzo ziyara masarautar ku ta adamawa zamu koma gida". Kai ta daga tana cewa"to jira ni anan bari na kawo muku "sauke kayan tay tana shiga wani gida sai gata ta fito da guga taje wata rijiya can nesa kadan ta debo masa cikin kwaryar ta daya tana kawo masa godiya yayi tare da karba yaje danya sawa mota tana tsaye tana jiransa duk abinda ke faruwa Emir na ganin su maganar ce dai bayaji. Mayar mata kokon driver yay zai juya ta ciro katuwar kwarya mai cike da kirdirmon tana bashi tace"wannan kyauta tace zuwa ga sarki ina mika gaisuwa amsa driver yay cikin mmk yace" kuma kwaryar taki fa,"?murmushi tay tana daukar kayan ta tace ba komai jeka da ita".gdy ya mata. Sannan cikin girmamawa ya koma mota yaiwa Emir bayani umarni ya bashi cewa yabi bayan ta yaga inda zata shiga yazo ya fada masa"kamar yadda yace haka ya rika binta a baya har ta shiga wani gida sa'an nan ya komo ya fadawa Emir daga haka yace su kama hanya". Abu kamar wani almara kullum Emir da ita yake kwana yake tashi ga yana yawan yin mafarkin ta tun abin baya damun sa har yazo yake hana shi gudanar da mulki yadda ya kamata karshe saida ya dangana gurin mahaifiyar sa hajiya ya mata bayani kuma ta gamsu har yadda baiyi tunani ba ya dauka zata masa fada cewa zai auri talaka yar kauye wacce ba jinin sarauta ba amma sai yaga sabanin haka yayi matukar farin ciki kuma yasa a shirya masa tafiya zuwa garin dan hajiya tace harda ita za'aje. Alhmdllh sunzo kauyen malam na Allah kamar yadda mutane sukaiwa garin lakabi domin wani babban malami ne da ake cewa baba na Allah ya fara kafa garin kuma shine mahaifin wannan yar fulanin. Da yake drivern yasan gidan sai basu sha wata wahala ba suka je a kofar gida suka samu malamin yana karatu yayi matukar mamakin ganin su da kalar hamshakan motocin da irin suturar jikin su dake nuni da cewa sudin yan gidan sarauta ne. Sallama suka masa ya amsa cikin aminci duk zaton sa hanya ce ta bace musu sai yaji labari sabanin haka cewa gurin sa suka zo . Cikin gida ya shiga yana sanar da matar sa cewa sunyi baki ta shinfida tabarma yadda yace haka tay sannan ya koma waje ya shigo dasu. Sosai sukai mamaki jin abinda ya kawo su da kuma silar hakan ita kanta fatima dake nesa dasu tana hura wuta saida gaban ta ya fadi jin sarkin kano ne data bashi ruwa yasa a mota kuma cewa wai yana sonta shine abinda yafi daga mata hankali su kansu iyayen ta sunyi mmk kuma basu amince ba dan sarkin ya fi karfin auren yarsu. Cikin nuna karamci malam na Allah yace"to alhmdllh masha Allah gaskiya naji dadi da nuna kaunar ka akan yata kuma na gode saidai ina mai baka hakuri bazan iya baka auren diya ta ba bawai dan wani abu ba a'a kawai dai kayi hakuri". A marairaice Emir yace"dan Allah na roki wannan alfarmar ka tausaya min ka bani auren Zarah ina sonta". Hadiza babar su Fatima dake gefe tace "hakurin dai shine yafi alkairi don yarmu ba sa'ar auren ka bace kafi karfin ta". Kafar malam Emir ya rike cikin magiya ya ce "dan girman Allah ka taimake ni wallh nayi alkawarin rike ta amana". Shiru malam yai domin Emir ya tokare dukkan hanzarin da yace dan girman Allah to saidai ya bayar dan Allah din. Sosai hajiya ke musu magiya domin tasan irin mugun halin da danta zai fada idan basu bashi auren yarta su ba dakyar suka amince a gurin suka yanke mgn da komai wanda hakan ba karamin farantawa Emir yay ba . Da suka tashi tafiya ya nemi a bashi damar ganin fatima amma saita gudu dole ya hakura suka tafi kamar yadda suka ce a wata uku za a tsaida maganar aure haka akai . Ganin ta shigo dakin su da gudu yasa Zainab tace"ya haka yar kauye kawai sai kace wanda suka ce zasu gudu da ke ni kinzo zaki balla min kafa ki cuci Abubakar dina ". Shiru Fatima tay Zainab taci gaba "kuma yanzu idan Saminu yaji me zaki ce masa gashi wani yayi masa shigar sauri". Kamar zatai kuka ta kalli zainab tana cewa"ni wallh ban sani ba har kunyar fita nake ji tun kafin ya sani ina ma nayi aure kafin mu hadu". Zainab tace"tab ai kuma duk dadewa ba zakiyi ba saikun hadu din tunda shine mijin idan Allah yayi zamu sha taushe". Harararta Fatima tay"wai nikam ba nike gaba dake ba yaushe na zama abin tsokana"? Dariya zainab tayi sai kuma ta rufe baki tana cewa"yi hakuri mantawa nayi". Mikewa Fatima tay tana cewa"eh mezai hana ki manta tunda kafadar ki ta taro tawa bari nabar miki dakin saiki cinye". Fita tayi tabar zainab na dariya da kuma tunanin abinda ya faru mai kama da tatsuniyar gizo da 'ko'ki. Nan gari ya dauka cewa malam na Allah ya koma na Allaro zai sayar da yarsa yaga kudi ya gigice idonsa sun rufe ya manta malinta sosai maganar tai maasa kuna amma ya shanye bai taba tankawa ba. Abun yana mugun damunsa har saida ya samu matar sa suka zauna yace"Hadiza kinji irin maganganun danake gudu ko gashi yanzu gari sai gulmar mu ake wai mun sayar da Fatima kiga fa gashi Zainaba almajiri na Abubakar zan bawa auren ta amma ban fita ba sai naji ana cewa wai dan kar ace na damu da duniya ne a zage ni me yasa mutane basu da adalci komai baza kai musu gwanin ta ba duk abinda kai a matsayin baka tsoron Allah kake". Hadiza tasan za'ai haka amma dole hakuri zasu dauka kuma su toshe kunnen su dan haka hakuri sosai ta bashi tare da kwantar masa hankali. Lokaci yayi kuma an daura auren dukkan su yayin da yan garin suka samu kyautuka a gurin sarkin kano wanda sunyi mamaki a ranar Fatima tay bankwana da iyayaen ta amma Emir yace ya dace suje suga mahallin yarsu malam yace a'a inda rai wata rana zasu zo haka kuwa aka wuce da ita tana gani ta koma sabuwar rayuwa. Yayin da ita ma yar uwar ta take kauyen su da mijin ta Abubakar kuma suna zaune lafiya. @Taskar Annuri writer's masu hankali da nutsuwa. MRS AL'AMEENAHMAD CE. TYPING📲 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 Godiya ga masoya sosai sosai godiya. 🕌🕋🕌 Friday may Allah accept your duas and protect you&your families from all calamities Ameen👏 May Allah open the door of success and happiness for all of you(Muslims)Ameen🙏. JUMA'AT MUBARAK🍇 🍎🍌🍉🍍🍐🍒🍏🍊🍇 #YUSRAH# NO.07👉 08 Lokaci mai tsaho ya wuce har Fatima nada ciki da Fatima taga gata sosai dan Emir ya auri mata da yawa basu haihu ba yayi zaton a shine sai kuma yanzu daya budi ido yaga Fatima da ciki abinda bai taba zato ba. Hankalin Adama(Ammi) ya tashi sanda ta bude ido taga Fatima da ciki ba hanyar da bata biba dan zubar dashi amma ta kasa sbd tsaron da Fatima take samu a dai dai wannan lokaci ne itama Ammi ta fahimci tana da cikin wanda hakan ba karamin sanya ta farin ciki yay ba dashi kansa Emir da kuma hajiya sosai ake tarairayar su Ammi ganin tana da ciki kuma nata mai mugun laulayi ne kullum tana cikin jinya saita dauke hankalin ta akan Fatima ta koma jida kanta. Sanda cikin Fatima ya isa haihuwa ita kuma Ammi yana wata hudu ranar juma'a ta tashi da nakuda sosai wanda ba shiri akai asibiti da ita kuma bata iya haihuwa da kanta ba sai cs akai mata aka fito da kyakkyawan baby boy fari tar kamar uwar sa. Fadar farin cikin da masarautar ta shiga bazai yuwu ba kawai dai sunyi farin ciki kuma ba'a bata sallama saida jikin ta ya warware kana suka dawo gida ranar da suka dawo kwanan babyn tara dan haka washe gari akai shagalin suna kuma baby yaci suna mahaifin Emir wato"ABDUL-JABBAR"yan uwan fatima sunzo kuma da suka tashi tafiya bayan suna suka nemi tafiya da ita Emir bai hana ba. Watan ta biyu akaje da tawaga aka dauko ta a dai dai wannan lokacin kuma itama ammi ta haihu namiji shima ranar suna yaci sunan kanin mahaifin Emir wato"AMFAL"hakan ba karamin farin ciki yasa sarki ba ganin Allah ya azurta shi da samari guda biyu lokaci daya. Wata rana kawai fatima ta tashi da wani irin zazzabi daya firgita Emir dan haka asibiti suka wuce a duba lafiyar ta abu kamar wasa duk iya kokarin likitoci ba suyi nasarar samo ranta ba domin lokacin rayuwar ta ya kare. Bazan iya fasalta muku irin tashin hankalin da kowa ya shiga ba dan Emir gado aka bashi a asibitin sbd tunda akace masa ta rasu ya fadi a gurin ya suma abin tausayi dole bada shi aka raka ta makwancinta ba daya farfado yayi kuka yayi bakin ciki ya dangana kuma dukkan soyyayyar sa ya tattare ta akan marayan dansa yana matukar tausaya masa da baisan komai ba. Ya nemi Ammi ta hada su ta shayar amma sai tayi masa wani kallon bazan yi ba tana cewa "gaskiya ranka ya dade bazan iya shayar da har yara biyu ba danni ban zama nanni ba dana ma daga dole nake shayar dashi kawai ka nema wacce zata kula maka da danka nima naji da nawa". Wannan magana ta bakantawa Emir rai cikin bacin rai yace"Adama ni kike kallon tsabar idona kina fada min mgn son ranki nagode ta inda Fatima ta fiki kenan a gurina har kwanan gobe da soyayyar tanake kwana itace jigon numfashi na da ana munsanye wallh dana zabi Fatima ta dawo gare ni itace matar data dace dani ba keba Adama". Kuka Ammi ta saki cikin shashsheka ta soma mgn"yanzu ranka ya dade ni kakewa fatan mutuwa sbd wata yar talakawa wallh bazan yarda ba". Sarki dake kallon ta da wani irin bacin rai dukawa yay yana daukar dan dake cinyar ta yace"hawainiya ma da take tashi taga ba uwa ba uba ba gatan kowa Allah ne ke kula da ita don haka wannan din ma ai dana ne shima basai kin shayar dashi ba zan kaisu gidan rainon tare sai ki zuba ruwa a kasa kisha". Cikin tashin hankali Ammi ta fara bashi hakuri yay banza da ita yana fita binsa tayi tana kuka har sashin hajiya a gaban hajiya ta zuba gwiwoyin ta tana kuka tace"dan Allah hajiya na roke ki kice ya bani dana wallh na tuba zan shayar da su dan Allah ranka ya dade kayi hakuri bazan sake ba". A tsawace Emir yace"ta fice daga nan din kafin ya tura ta gidan su jin haka tasan saki yake nufi ita kuma tana mutuwar son shi dan haka da gudu tabar inda suke tana fita ko kwali babu a kanta kamar sabuwar kamu. Tana ji tana gani aka kai su gurin raino da batasan ko ina bane kullum cikin magiya da bada hakuri take amma amsar daya ce ta gama bawa Amfal nono har abada. A kwana a tashi ba wuya har suka isa yaye sannan Emir ya karbo su ya dawowa da hajiya su ya hana Ammi Amfal haka suke ta girma agun hajiya har suka isa moro suka kai matsayin makaranta kuma aka saka su tare komai tare suke ba abinda yake rabasu duk zaton su hajiya ce babarsu. Emir yakan dauki Abdul-jabbar lokaci zuwa lokaci ya kaishi garin su fatima yayi kamar sati sa'an nan yaje ya dauko shi . Wani abin ban tsoro zainab kanwar Fatima itama ta haihu diya mace ansa mata suna SAFARA'U saidai ita daga kwanciya bacci ma aka tashi babu ita ta rasu lallai malam na Allah ya dau dangana yayin da kowa yake matukar tausaya masa a yanzu haka baida da ko daya dama iya sune kuma sun rasu. Bayan girman safara'u Abubakar yayi aure saidai baiyi dacen mace ta gari ba domin safah bata samun sassauci ko kadan a gurinta kullum cikin ukuba take amma da malam na Allah ya nemi karbarta sai abubakar yace yayi hakuri in sha Allah zaidau mataki. Haka gidan Emir ke rayuwa cikin aminci da kaunar yayan sa har suka dago samari sosai kuma a wannan lokacin ne sarki ya nemi shawarar Ammy kan yana so Abdul-jabbar zaije aikin soja tace hakan yayi ita a nata ganin mugunta tayi masa kuma sai hakan yafi masa alkhairi abunda ya faru kenan a baya kafin wannan lokacin. Tofa 🤔 hakan na nufin da mahaifiyar Abdul-jabbar da mahaifiyar Safara'u uwa daya ubah daya suke?😜 tab muje zuwa. Zama Ammi tay jagab akan kujera tare da zuba tagumi lallai tana bukatar shawara idan ta sake Amfal zai mata nisan da baza ta iya janyo shi gare ta ba yanzu mene abin yi ta ina zata fara?ta tambayi zuciyar ta shiru tay babu amsa dole ta hakura zuwa wani lokaci kafin hanne ta dawo. Bayan fitar su kallon Amfal Abdul-jabbar yay yana rike masa kunne yace"sai yaushe zakai hankali ne?kai kowa ma ka mayar dashi kakan ka Ammi fa mahaifiyar kace ya kamata taji dadi ka rungume ta kasan dadin uwa ina fada maka haka a matsayi na na dan uwan ka ba wai ina baka umarni bane ita uwa dadi ne da ita duk da ban sani ba amma ance kowa ya rasa ta yayi kuka shi yasa nake gargadin ka kai da ka samu taka a raye please ka shiga jikin ta ka samu wannan dadin da ake fada wanda a kullum ni ina kwadayin hakan amma na sani bazan samu ba har abada". Kallon sa Amfal yay jiki a sanyaye yana rungume shi cikin tausayawa muryar sa harya fara rawa yace"dan Allah ka daina cewa haka ka kaddara dukkan mu ni da kai marayu ne bamu da uwa ina tare da kai dan uwana iya rai da mutuwa komai namu daya ne ". Murmushi Abdul-jabbar yayi yana kallon shi yace"to naji lokacin magriba harya wuce ya kamata muje muyi sallah sai mu koma gurin hajiya kar kasa tayi ta jiran mu kuma bamu koma ba"wucewa sukai suna hira cikin jin dadin kasantuwar su tare a koda yaushe. Typing📲 ###################### #############=##=#### ################=## ####===#==##=####= #########====### ############# ###======== ####===# ##### ##= # Kuna ina yan group ku fito na shigo😜💃. Wannan page din naka ne dan uwa rabin jiki Cpt.SALEEM MUSA ABUBAKAR mai tambarin no going back . 🖊Yusrah Musa Abubakar💡 💫ANNURI W ASSOCIATION NAKU NE💫 Prophet Rasoolullahi s a w peace be upon him said:Be mindful of Allah and Allah will protect you ,be mindful of Allah and you will find him in front of you,if you ask then ask Allah(alone)☝,and if you seek help then seek help from Allah(alone) . #YUSRAH# NO.09👉 10 Tsaye Safah take bayan sallar isha kadan a kofar gidan su tare da Adamu suna zance murtala ya karaso gurin yaso ya kauda kai amma ya kasa sbd son da yake yiwa Safan ba dan karami bane yana matukar kishin ta. Dakatawa yay tare dayin sallama yana kallon ta a hasken farin watan daya haske ko ina yace"Safara'u ina son zamuyi mgn dan Allah ko minti biyar ne". Adamu dake hura hanci tunda yasan tafi sonshi ya tare maganar da zatayi da cewa "yaukan na riga ka malam sai a tari gobe "ya karasa maganar yana busawa murtala iskar bakin sa. Cikin bacin rai murtala ya danko wuyan sa nan fada ya kaure a tsakanin su wanda Baffa dake cikin gida harya jiyo ya fito salati Asabe keyi cikin son muzanta murtala tace"gaskiya yaron nan baka da tarbiya wato da bamu fito ba kashe shi kaso yi ko aiko kaima da an kashe ka jifa yadda ka shake masa wuya kamar wanda ka samu kayan goro". Murtala bai saurare taba ya fadawa Baffa komai sannan ya tafi shima Adamun tafiya yayi yana zage zage harda da ace su Baffa basu fito ba saiya bazar da murtala a kasa. Bayan sun shiga gida Baffa dake kallon Safah data zauna a gaban sa yace"Safara'u na sani kin girma tunda kinkai shekarun da za'a iya kiran su ashirin kinsan abinda yake fari da wanda ya kasance baki kafin nace wani abu ina son zan miki tambaya ki bani amsa"shin kina son aure ne waye kike so tsakanin murtala da Amadu"?. Shiru Safah tayi har saida Baffa ya sake mgn sannan muryar ta na rawa tace"Adamu nake so". Sosai Baffa yayi mamakin kuru irin nata duk zaton sa zataiwa murtala kara duba da cewa tun tana yarinya yake mata wahala kuma mahaifiyar sace ta raine ta bayan rasuwar zainab. Sauke ajiyar xuciya baffa yayi yana sake duban ta yace"Safara'u bazan miki dole ba tunda Adamu kike so Allah ya sanya albarka a cikin neman shi kuma murtala Allah ya bashi hakuri da dangana ya kuma bashi mace ta gari". Cikin jin dadi Asabe dake gefe tana jin kamar ta taka rawa dan murna tace "amin malam ashe mun kusa musha biki gaskiya a bari sai kaka sannan amfanin gona sunzo gida yadda zamu zubar da nera tunda ita kadai ce yarka dole kayi bajinta ta ban mamaki idan ba haka ba ayi yamudidi dakai a gari ace ka fiya son kudi ". Banza baffa yay mata yana mikewa cikin rashin jin dadin wanda Safah ta zaba baiko saurari Asabe ba yay waje dariya Asabe tay bayan fitar sa ta kalli safah dake shirin shiga daki tace"humm kinyi sa'a wallh da tsautsayi yasa kince murtala kike so da yau saina kusa kashe ki a gidan nan". Safara'u bata tanka mata ba ta shige daki yayin da Asabe keta jifan ta da maganganu marasa dadi tun tana jiyo ta har bacci ya dauke ta. Kamar yadda kullum ta saba ta share gidan tas ta hada kwanuka ta wanke sannan ta debo ruwa saida ta gama komai kafin tazo dorawa Asabe abincin sayarwarta ta fice dan ta kaiwa kakanun ta ziyara a hanya suka hadu da Aisha amma sai Aisha tay kamar bata ganta ba . Shan gaban ta safa tayi cikin mmk tana cewa"lfy Aisha me kuma nayi miki irin wannan shariya haka"?cikin bacin rai Aisha tace"aw bakisan me kika min ba haka ma zaki ce nagode " zata wuce Safah ta rike ta jikin ta duk yayi sanyi tace"dan Allah Aisha menene ki fada min wallh bansan abunda nai miki ba". Kallon uku saura sisi Aisha ta mata"dama taya zakasan abinda kika min wai dan Allah Safah meye abin ki a jiki yayan mu murtala da bakya sonshi"dan yatsina fuska safah tay"oh dama abinda yasa kike fushi dani kenan?to yanzun dai kiyi hakuri bani da amsar tambayar ki kila zan samu gaba". Fisge hannunta aisha tay tana wucewa Safah ta bita da kallo daga baya kuma ta kama dariya tana cewa"lallai Aisha ashe zaki dade kina fushi dani mai zanyi da murtala bayan ma na fishi tsayi idan zanyi masa mgn saina kalli kasa tab bazan iya ba ". Ita kadai take tafe tana surutu harta shiga gidan zaune akan tabarma ta same su da sallama ta karasa tana zama bayan sun gaisa malam na Allah ya dauko mata naman dake rufe a gefe yana mika mata. Karba tayi ganin abinda yake ciki yasa ta ce"gaskiya tsofin nan kuna jin dadi shi yasa bakwa tsufa ashe kullum tukunyar ku na sama nima yau nazo ayi dani. Dariya Hadiza tayi "dadin abin ma ba hana ki zuwa mukai ba balle kice mu marowata ne muna gari daya saiki shafe wata bamu ganki ba kin kyauta Safara'u kodan gara ke shi Abdul-jabbar na manta yaushe rabona dashi inaga ko muhammadun ya manta da mune nidai ba nace ba". Da mmk Safah tace"waye kuma Abdul-jabbar naji kina cewa kin dade baku hadu ba? dadina dake kalan dangi". Kafin hadiza tay mgn na Allah ya amshe da cewa"dan uwan kine sai rashin sanin juna tunda baku taba haduwa ba sai randa yazo sai kuga juna". Kallon sa safah keyi tace taya ya zama dan uwa na"?. Ta dalilin Fatima yayar mahaifiyar ki itace mahaifiyar sa saidai shi yana kano can ne gidan mahaifin sa mu kanmu mun dade bamu ganshi ba amma duk ranar daya zo zaku gabatar da juna saboda kulluwar zumunci ko bayan ranmu". Kallon sa sosai safah keyi tare da juya maganar a ranta lallai tana son ganin sa tana so su hadu dashi shine kadai jinin ta". Sauke ajiyan zuciya tay tana cewa "Allah ya kawo shi lfy tabbas ina so mu hadu naga dan uwa na". Zaku hadu in Allah ya yarda ki kwantar da hankalin ki kinji"kai ta daga alamar to kafin suka aje wanna zancen suka dauko wani dan debe mata kewa ganin tadan shiga damuwa. Typing📲 (*(*()*)*) {{}} (*(*()*)*) 🍇 SAFREEYYAH🍇 @YUSRAHMS ABUBAKAR AISHAT MUSA ABUBAKAR ABBAKAR MUSA ABUBAKAR I KNOW U LUV ME ALWAYS MAY ALLAH PROTECT YOU EVERYTHING ABOUT YOU IS SO GOOD BUT ONE THING IS WRONG THAT YOU ARE NOT MIND. MANZON ALLAH S A W Shafi'ul wara da kai aka bude kullalle rahmar ka ta isarwa wahalalle da makalalle ka sada bayi da Allah zuwan ka shalele badon da kai ba ba'a san azumi da zakka ba. #YUSRAHMS# NO.11👉 12 Fitowar Amfal daga wanka kenan ya kalli Abdul-jabbar dake tsaye jikin window yana karewa gidan gonar kallo yace"bros na fito shiga kada mu makara". Juyowa Abdul-jabbar yai yana kallon shi a hankali ya karaso yana dan dukan kafadar sji yace"wani lokacin idan kai wani abu kamar karamin yaro jifa a yadda ka fito babu towel ko bathrobe ne". Amfal dake kallon kanshi a mirror yace"akwai mana a haka dai na fito dan Allah shiga wankan nan kar mu makara yanzu karfe biyar fa kuma shida ya kamata muje". Abdul-jabbar bai sake mgn ba ya shige toilet yana jin Amfal na cewa "kila daga can na samo matar aure kaga idan na riga ka yin aure shikenan nan ka zama yaya na kofar gida". Duk abinda yake cewa Abdul-jabbar na jinshi bai tanka ba harya fito zama yay a gaban mirror kamar yadda suka saba Amfal ne ya taya shi shiri harya kammala sukai wankan kaya iri daya kamar yadda angon ya bukata domin abokin sune . Sun bata lokaci sosai wajen shiri amma da yake Abdul-jabbar ne matukin nan danan sai gasu tamkar ba gurin events ba babu wata hayaniya domin ba mutane da yawa aka gayyata ba biki ne na manya daga wane sai wani domin kusan duk 'ya'yan masu mukami ne a gun da yayan senatoci sai gwamna da honourable. Tarba sosai suka samu domin kowa a gurin yasan sudin su waye shi kanshi ango da ya kasance dan gidan minister yana jin ya raina kanshi balle fa saura jawabin akai na musamman akan zuwan su da nuna farin cikin ango da amaryar sa akan zuwan nasu. Humm yan mata kam anga samari masu aji sai kowacce ta fara dauko mudubi suna duba fuskar su masu gyara daurin kwali nayi ko zasu dace amma gabadaya hankalin ogannin ba a wurin yan matan yake ba yana ga abinda ya shafi rayuwar sune. Wata budurwa ce data kasa hakuri ta karaso gare su tare da cewa "zan iya zama"? No Amfal yace batare daya kalle taba da mmk ta bude ido a kansa kafin daga baya ta zauna akan daya daga cikin kujerun dake gunnn tana kallon Abdul-jabbar data kasa dauke idon ta a kanshi tace"barka dai suna na Bilkisa kuma ni yar gwanan jihar nan ce dan Allah idan bazaka damu ba kadan bani number wayan ka". Ko dagowa Abdul-jabbar bayyi ba balle yasa cewa dashi take hankalinta ta mayar kan Amfal tana cewa"please ban phone number shi gaskiya ba mgnr boye boye yayi min kar wata tamin shigar sauri da zafi zafi ake dukan karfe a bari ya wuce yana kawo fitar rabo. Amfal dake son yayi dariya ya dake yana cewa "ni bani da number shi kuma kin makara domin yana da mace harda yara uku yanzu aure na biyu ya sake ko wata ba'ayi ba ". Dafe kai bilkisa tay tana kallon Amfal tace to naga kaida shi duk daya ne Allah yasa ba'a riga niba"?zaro ido Amfal yay yana kallon ta yace"ni kuma ki rufa min asiri ban tashi yin aure ba ni yaro ne". Kai Bilkisa ta girgiza "gaskiya kaiba yaro bane dan haka nayi kamu"cikin jin haushi Amfal yace "da yake farauta kika fito ba ni kuma nayi miki kama da zomo🐇 ko gafiya saiki kama kikai gidan ku"😁. Murmushi tay "abin baikai haka ba kawai nidai ka amince min ina sonka"banza Amfal ya mata zata sake mgn aka neme ta cewa ta fito filin taro ta fadi wacce amarya da rayuwar ta mikewa tay tana cewa"minti biyu bari na dawo". Sauke ajiyan zuciya Amfal yay yana kallo Abdul-jabbar da shima shi yake kallo zayyi mgn ya mike yana cewa"malam na mamajo kana iya tasowa mu tafi kafin mayyar taka ta dawo "mikewa yai sunai wa ango alamar fatan akairi suka fita a wajen dan Abdul-jabbar ne dayaga abin Bilkisa bana, hankali ba yaiwa ango text cewa zasu tafi yayi kiran ta fili kafin ta farga su fece har dare yayi dan haka suna zuwa sallah sukai suka bi lafiyar gado. Sosai abinda Safara'u tayi ya taba xuciyar murtala bai taba kawowa a ransa xata 'kishi tadau Adamu ba saida yaga hakan ya faru. Saidai abin mmk da lallami ta hanya mafi sauki baba ya sauya akalar safah da addu'a sai son da takewa adamu ya koma kan murtala harma ana batun zuwa rokon arziki hankalin asabe ya tashi bata san safah ta samu inda zata huta tafi so koda yaushe ta kasance cikin wuya dan haka ta samu malam da shawara. Malam abinda kai baka kyauta ba yarinyar nan Adamu take so amma shine ka mata asiri ta koma son murtala idan kai haka ka ha'ince ta kuma sai Allah ya tambaye ka me yasa ka aikata haka". Malam dake sauraron ta yace"Asabe bansan shasanci barnan kafin ki tabo min bacin raina". Mikewa Asabe tay Allah ya bada hakuri malam dan kawai na fada maka gaskiya da kasan yadda ake zagin ka a gari ance kayiwa Adamu kyautar zobe da ka hana murtala Safara'u ka bashi". Sake cewa yai"nace kibar nan ko baki jini ba "kada kai, asabe tay cikin takaici tana cewa "ba laifin ka bane karatu ne ka dauka a gurin malamin ka malam Na Allah shine ya fara yi Saminun gidan kuka na san Fatima amma sbd kudi ya rude shi ya bawa sarki ita ya hana wanda yaiwa alkawari kaima hakan zakai kenan"?. Ai na sani murtala nada manyan shanu da awakai ga gonaki kuma ga shago kaima shiyasa idon ka ya rufe sbd za'a rika kawo maka madara ohni Indo amma fa anji kunya". Malam bai sake sauraron taba ya mike yana barin wurin Asabe data bishi da kallo tace"wallh malam indai ina raye safara'u bazata auri murtala ba idan kuwa ka taurare akan haka zansa kayi kukan bakin ciki da idon ka". Yau ya kama juma'a dan haka tun wuri Asabe ta dafa abincin sayarwar ta saidai ta rasa inda Safah ta shiga karshe gudun kar ayi mata kwashe ta dau hijabin ta tana bi duk inda tasan tana zuwa amma kowa yace bai ganta ba. Dole Asabe ta hakura tana dawowa gida tadau hayar wata yarinya a makotansu ta bata tallan abincin ta kuma dau kujera ta dake tana jiran komowar Safan. Safah na gidan su Na Allah acan ta wuni sai bayan anyi sallah a masallaci tayi musu saida safe tayo hanyar gida tana shiga Asabe ta mike tana cewa"ke yar iska daga gidan ubanwa kike dan raini shine kikai tafiyar ki yawo baki zo kinmin tallar abinci ba ko yau saina ci ubanki". Kanta tayo zata fara dukan ta cikin tsawa taji ance"idan kika kuskura hannun ki ya sauka a jikin ta na datse igiyar auren ki duk ukun"da sauri ta janye hannunta tare da juyowa ganin malam tay tsaye rike da tasbaha yana ja. Cikin bacin rai tace"yanzu malam a dakeni a hana ni kuka kawai gashi nan ta jawo min asara nayi kwashen abinci kudin mutane zai hau kaina wallh malam baka da adalci dan ba nice na haife ta ba shikenana ban isa da ita ba "ta karasa mgnr tana fashewa da kuka. Karasowa malam yay yana cewa"wallh Asabe lokacin da ake rabon hankali bacci kike to bari kiji daga yau doka tace Safara'u ba zata sake tallar abinci ba kinji na fada miki". Daki asabe ta wuce tana kuka yayin da malam ya kalli Safah dake tsaye yace"jeki kwanta"to tace tana shigewa daki shi kuma ya fita a gidan". Ina godiya da nuna yabawar ki ga littafin nan my sister Zarah Musa dan Adam hakika bani da kamar ki a kullum roko na ki kasance cikin farin ciki mai dorewa. Sauran yan uwa na nesa da kusa ina mika gaisuwa ta a gare ku tare da muku fatan alkhairin Allah a koda yaushe yakai muku inda kuke. Maman Khaleel Zaria Hajara Abla's Kano Indo ce Kano Rabi'at Bichi Hajara birnin kudu Zainab birnin kudu Aishat birnin kudu Ummi Salis kaduna Ambaby kwalli kano Walida kwalli kano Batila Abdllh Dutse Ruwaina Abdllh Dutse Asiya Haladu Dutse Badariyya Hassan Dutse Aishat Abubakar Kebbi Ameerah Hassan Dutse. Dama wadanda ban fada ba kuma badan na manta ba duk ina gaida ku na gode kuma da yabon ku gare ni. Bazan taba mantawa dake ba BASIRAH MUHAMMAD DUTSE INA MIKO TA'AZIYYAH TA GARE KI NA RASUWAR YARKI AISHATU BABY😢 KWANAN BAYA ALLAH YA MATA RAHMA YAKAI HASKE KABARIN TA MU KUMA IDAN TAMU TAZO UBANGIJI YA AMINTAR DAMU YA NUFE MU DA CIKAWA DA IMANI👏🙏. AMEEEEN. YUSRAH MUSA ABUBAKAR SEE YOU NEXT TOMORROW BE WITH ME AT ALWAYS MY LOVERS🤗💘. Daga Alkalamin hamshakin group din nan mai cike da baiwa wanda kuka fi sani da taken👉👉👉 ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 🌤HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI YAYAN TAFIYAR MU BABU RAGO A CIKIN TA BABU YAUDARA KO HA'INCI TSANTSAN GASKIYA MUKE NUNAWA☝👍👌. 📖🌫😘Mrs Al'ameen Ahmad ce. 😘😜LOVE FOR EVER😝😍 Typing📲 3:54pm monday February 2023 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 SAFREEYYAH 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 💡💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫👌🌌 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 🎀🎀🎀🎀🎀🎀 🎀🎀🎀🎀 🎀🎀 🎀 📖🖊 Yusrah M Abubakar DEDICATED TO MY MOTHER I LUV U AND I WILL BE WITH YOU ALWAYS YOU ARE THE BLOOD THAT IS SCULATED IN MY HEART. WANNAN PAGE DIN NA MALLAKA MAKA SHI KAI DAYA MY BROS ABDALLAH MUSA ABUBAKAR . On the authority of Anaass (RA)who say: I heard the messenger of Allah(peace be upon him)said: "Allah almighty has said:O son of Adam,as long you invoke me and ask of me,I shall forgive you for what you have done,and I shall not mind". It was related by Attirmidhi,who said that it was a hasan hadith. 'YAN UWA WANNAN PAGE DIN NA SADAUKAR DASHI GA DUK WANDA YA KARANTA LITTAFIN NAN DOMIN PAGE DIN YA TARA DUNBIN ABIM MAMAKI😜. #YUSRAHMS# NO.13👉 14 Cikin dare safah data kasance a dakin ta a kwance tana bacci kawai taji hayaniya a kanta ta dauka mafarki take saida taji abin bana 'kare bane ta bude idon ta Asabe ta gani tsaye a kanta gaa wasu samari biyu da bata san su waye su ba. Zaune ta tashi cikin mamaki tana kallon Asabe kafin tayi wani yunkuri taji Asaben na cewa"gata nan kuyi yadda kuke so da ita kuma bance ku tausaya mata ba zan kuma biya ku kudi mai dubun yawa idan kuka keta mata mutuncin ta kuka wulakanta ta". Jin abinda Asabe take cewa a matukar gigice Safah ta mike tsaye tare da nufar kofar fita tare ta garadan sukai suna finciko ta zuwa cikin dakin daya yace"ke dalla zonan gidan uban wa zaki fita"?ya fada yana fisge hijab din dake jikin ta kara ta saki tana fashewa da kuka ta soma kwalla kiran BAFFA BAFFA ka taimake ni zasu kashe ni. Dariya Asabe tayi tana cewa"ai yarinya ki daina bata bakin ki domin kin makaro baffan ki yasha maganin bacci bazai san me yake faruwa ba kuma zan baki gargadi idan har gari ya waye kika ce nice nasa a miki haka wallh kashe ki zanyi idan kunne yaji to jiki zai tsira". Saboda tsabar Safah bata cikin hankalin ta batasan me Asabe take cewa ba damuwar ta rikon da wannan katon ya mata burinta ta samu ta shammace su ta gudu juyawa Asabe tay tana fita a dakin". Yayin da dukka su biyun suka rufu a kanta kowa da inda ya nufa kuka Safah keyi mai taba zuciyar mai sauraron ta ganin fa idan ta sake da gaske zasu keta mata mutuncin da Asabe tace gashi danne tan da sukai ko motsin arziki ta kasa. Idon tane ya sauka akan kwalbar data dora maganin sauro akai baima daina ci ba hannunta ta mika da kyar ta samu ta dauko ta daidai dayan ya mike tsaye zai cire wandon sa wanda yake riken da ita ta saici goshin sa wajan saman kansa ta kuwa yi sa'a yayi aski malu ta sakar masa duka akai da wannan kwalbar sakin ta yayi ba arziki yana ihun neman agaji da kiran ta kashe ni. Da sauri dayan yayo kansa yana cewa"mu gani mai tayi maka"? ganin shima dayan ya maida hankalin sa gurin waccan yasa a zabure Safah ta mike tana fita a dakin cikin masifar tsinka gudu yayin da dayan ya ankara shima yabi bayan ta cikin mugun kakkarfan taku. Da yake kauyen baida girma nan da nan tayi nisa da shi ta shiga wani irin daji tana kuka gashi batasan inda take nufa ba tanajin yadda kafar ta ke taka 'kayoyi tana zafi amma haka ta daure taci gaba da shiga dajin. Tuntube ta kwasa ta fadi a kasa daidai wanda ke binta ya karaso kafin tayi yunkurin tashi ya bita ya danne da karfin tsiya tana ihu da neman agaji amma saida ya mata fayde kana ya tafi ya barta a gurin a kwance kamar matacciya. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a gigice cikin burkicewa Baffa ya farka daga wannan mummunan mafarkin da yay bala'in tada hankalinsa wanda tunda ya farka a firgice da gudu ya fito daga dakin sa ya shiga cikin gida yana salati jiki na rawa ya shiga dakin Safara'u. Kwance ya same ta tana shara bacci zama yay a gefen ta tare da zuba mata ido cikin tausayawa yana kuma share gumin daya jike masa fuska bai iya barin dakin ba dan gani yake kamar ba mafarki yay ba wadannan samarin zasu iya zuwa bai sake iya runtsawa ba sai salati da yake ta yi. Bai bar dakin ba saida akai kiran sallar asuba sannan ya mike da kyar duk jikin sa ya mutu ya fita a dakin alwala yay masallaci ma kasa zuwa yay sai a daki yay sallar sannan ya dukufa wajan addu'ar neman kariya zuwa ga 'yar Allah ya tsare ta a duk inda ta tsinci kanta. Saida gari ya waye sosai sannan ya shigo domin ya duba lafiyar ta a waje ya same ta tana karatu ganin sa yasa ta shafa fatiha tana cewa"Baffa ina kwana" lfy kalau safara'u fatan kin tashi lafiya ina fatan babu abinda ya sameki "?kaita daga yaci gaba da cewa"to kinji motsi ko kinga wani abu da daddare wanda ya tsorata ki ko kuma kinyi mafarki"? Nan ma kai ta girgiza masa"a'a Baffa banyi mafarkin komai ba kuma banji motsin kowa ba"sauke ajiyar zuciya yay yana hamdala zaiyi magana akai sallama. Duka juyawa sukai suna kallon hanyar kofar gida da mmk baffa yace "maryama kece yau a garin namu"?murmushi matar tay tana karasowa tace "eh wallh abubakar nan na kwana da yake shigowar dare nayi a gidan kawu Hakilu na kwana". Cikin fara'a baffa yace to sannu da zuwa maraba lale gaskiya naji dadi yaushe rabon da mu gana saiyau " Maryam tace"wallh dai ka ganni adamawa ta boye ni ina can yanzun ma dakyar suka barni na taho ina Asabe ne". Dan shiru Baffa yay tuna mafarkin da yayi kafi yace "tana daki kila ko wani abu take"safah ce ta gaishe da ita tana mikewa zata dau tsintsiya maryam tace"waini wannan ko itace yar taka ne ikon Allah abin ba wuya harta girma haka sai aure kenan". Murmushi baffa yay yana cewa"wallh ai lokaci ma muke jira yar gida za'ai da murtala dan wajan kani na". Maryam zatai mgn Asabe ta fito daga daki tana cewa sannu bakin sassafe "tun kafin maryam tay mgn asabe tace to nikam midille"zuwa ina kenan cewa baffa "tafiya Asabe ta fara tana cewa gidan mu"maryam ta tari numfashin baffa da cewa "haba Indo da wannan safiyar kamar me yaji"bata saurari maryam ba tay waje. Kai maryam ta jinjina gaskiya lamarin asabe sai a hankali maida kallonta tayi akan baffa tana cewa"idan har haka take taya wannan yarinyar take rayuwa gaskiya Abubakar akwai gyara a gidan ka nifa sai naji hankali na bai kwanta ba ". Sauke ajiyar zuciya baffa yay yana cewa"kullum ina kokari maryama bana so ace yata daya na kasa rike ta amma na sani cewa safara'u zaman wahala take a gidan nan babu wani jin dadi baba malam(Na Allah)ya nemi na bashi ita ta koma gurin sa da zama saidai inajin kunyar hakan mutane zasu ga kamar na kasa banfi karfin gida na ba ni kaina cikin damuwa nake". Wani mafarki ma da nayi ya mugun daga min hankali ji nake kamar naje na samu dan uwana a daurawa safara'u da murtala aure a yau ko hankali na zai kwanta da abinda na gani cikin mafarki". Kai maryam ta girgiza a'a Baffa idan bazaka damu ba zan tafi da safara'u adamawa domin nima nanda wata daya zan dawo kaga idan tabar nan din shikenan muna dawowa kawai sai ayi bikin ta ina ga hakan zaifi amma me kace ". Shiru baffa yai na dan lokaci kafin yace"na amince maryam ku tafi domin na yarda dake Allah yasa haka shine mafi alkairi". Cikin jin dadi maryam tace"amin ngd baffa bari na koma gidan Hamza jibi zan tafi sai tayi shiri zuwa gobe to baffa yace yayin da maryama ta mike tana masa sai anjima. Bayan tafiyar ta Baffa ya zaunar da safah yayi mata bayani kuma ta amince haka nan taji dadin barin garin da zatai bata san mene dalili ba ". Baffa da kansa yaje gidan malam na Allah ya sanar dashi abinda ke faruwa kar kwana biyu su jita shiru zata dan bi wata kanwar sune zuwa adaamawa suma addau'a sukai sannan safah taje musu sallama suka mata nasiha". Kamar yadda maryam tace bayan kwana biyu ranar da zata koma ta zo domin tafiya da safah nan fa bori ya hau Asabe tai ruwa tay tsaki ba inda safah zata je". Maryama dake rike da hannun safa tace"saiki hana tunda yarki ce"asabe na jijjiga tace"wallh babu inda zata salon kije ki koyo mata iskanci malam kana gani kamar wanda ta asirce ka zata tafi maka da yarinya wata uwa duniya". Ko sauraron ta baffa baiyi ba suka fita a gidan ya musu rakiya sannan ya sake bankwana da safah ya dawo gida" Da bala'i kwando kwando asabe ta tare shi yana shiga ta mike"sannu da dawowa wanda ya rako maza duniya saki tumaki ballo jakuna wallh anyi asara kai kana nan ka bude hanci da baki yarka ta tafi binni ita kuma ana can ana koya mata yadda ake iskanc............ Cikin tsawa baffa yace"Asabe ya isheki bana son hauka shashashar banza shashashar wofi kawai wacce bata san ciwon kanta ba".yana fadin haka ya fice a gidan tsaki asabe tayi tare da cewa "Allah yasa a dirko mata ciki daga can ta dawo maka da abin kunya da zanfi kowa jin dadi ". Sun sauka adamawa lfy a wani gida mai kyau inda anan maryam ke aiki ana biyan ta kudi mai tsoka wani bangare suka shiga a gidan har cikin dakin maryam tace ta huta kafin ta shiga cikin gidan ta dawo to tace mata. Bayan fitar maryam zama safah tayi tana tunani Baffanta sai yanzun taji da bata biyo ta ba gara zama gaban babanta akan nan dukda bata ga komai anan dinba. Tana cikin tunani maryam ta dawo da abinci a plate tana aje mata da pure water tace"Safara ga abinci kici saiki tashi kiyi wanka na fadawa hajiya tace na kaiki ta ganki kinsan me"?. Kai safah ta daga maryam taci gaba "zance ta baki aiki kamar yan gyare gyaren kitchen da, goge goge kafin mu tafi zaki dan tara abin kanki tunda kinga aure za'ai miki dole akwai yar sayayyar da zakiyi ko"?. Godiya safah tayi mata har taji yar damuwar ta taragu ta wannan hanyar tana bukatar wanda zai rika bata shawara haka amma batai dacen matar ubah ba. Abdul-jabbar ne zaune gaban mahaifinsa suna mgn Emir ya dube shi cikin murmushi yana cewa"ya kamata kayi shiri kaje ka gano kakanun ka kila ma ka fara mantawa dasu laifi nane dana dade banje ba kuma ban kaika ba". Dagowa Abdul-jabbar yay yana kallon shi yace"Abba ni kaina ina son maka tambaya akan haka domin ban manta suba kuma ina son naje na gansu". Kai emir ya jinjina daidai Amfal ya shigo yace "hakan nada kyau yaushe zaka je"?kafin yay mgn Amfal yace "Abba gobe zamuje dan nima ina son zuwa". To hakan nada kyau Allah ya tashe mu tafiya sai a fara shiri tun yanzu domin a tafi musu da abin arziki"Ammy dake labe ce ta shigo tana kallon Amfal tace "kaima naka kakanun zakaje ka gano yaushe rabon ka dacan harka manta amma yanzu kadau mazari da rawar kafa zakaje shishshigi". Dan hade rai Amfal yay yana cewa"kaji Abba muna zancen mu "Emir dake kallon Ammy yace"dan bamu guri muna magana ne zuwa jimawa kya dawo". "Dan bamu guri Ammy ta maimaita "eh haka nace yanzu lokacin ganawa da yaya nane naki lokacin sai anjima"juyawa Ammy tay tana fita cikin wani irin bacin rai ta koma part dinta". Cikin tsawa tace da bayin dake ayyuka su fice su bata guri bata bukatar ganin kowa jiki na rawa suka fita idan da sabo sun saba ko ba'a bata mata raiba idan tay ra'ayi haka take musu balle yau da aka tabo ta. Shigowar Hanne yasa ta mike tare da goya hannun ta a baya tana kaiwa da komowa dukawa hanne tay tana cewa"ran uwar gidana ya dade fatan ba wata matsala kamar naga kinadan cikin damuwa ". Dakatawa da zaga palon tayi tana komawa kan cushion din ta zauna muryar ta da fushi tace"ba kama bane lallai hanne ciwon xuciya na neman kama nI sbd rashi kauna da Amfal ke nuna min hakan yana mugun daga min hankali ace dan da na haifa baisan gani na balle yazo inda nake dole zan tashi tsaye zama bai kama ni ba yanzu ba lokacin kwanciyar hankali bane meye mafita"?mema zanyi wacce hanya zanbi ta ina zan fara ya za'ai na kwato dana". Kasa da murya hanne tayi tana cewa"ranki ya dade kar aji mu ya kamata mubi a huce zanje gida a cikin satin nan daga can zansan abinyi kafin na dawo zan taho miki da abinda zaki alfahari dani sai kinyi min kyauta mai tsoka tajin dadi". Zama ammy ta gyara "kamar ya ban gane ba me kike nufi". Hanne tace"ina nufin zanje gurin wani babban Malami ya yi mana duba akan mene dalilin da yasa danki bai damu dake ba kuma ya mana taimako yadda za'a raba kansu suji basa kaunar juna". Sauke ajiyar zuciya Ammy tay "shin kin tabbata aikin zaiyi nasara "?. Kwarai ranki ya dade ina da tabbaci aikin sa tamkar yankan wuka yake kuma yana ci sosai". To lallai ina son haka idan kin tashi tafiya zan baki kudi masu yawa wanda zasu isa ayi komai tashi kije"mikewa hanne tay tana gdy ta fita". Ammy taji matukar dadi gani take kamar ta faru ta kare bata son alakar shakuwar dake tsakanin Abdul-jabbar da Amfal ko kadan kuma ta daura niyya wannan karon sai tayi nasara . 🎀Mrs Al'ameen Ahmad ce,🎀 Mu kasance a koda yaushe one love kawaye da masoya. YUSRAH CE MAI TAMBARIN Y M A 👌. Typing📲 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 SAFREEYYAH 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫💫💫 »«»«»« «»«»«» «»«»«» »«»«»« 📖🖊¥u$®ah Musa ###==### ##### ### ## #. Banga abin ambata ga dukka wanin daha ba shi daya xa a so guda bawai gaibu ba,kafi kowa kyauta sannu gwarzo na Khadija kai muke wakewa we 💞 u manxon Allah peace be upon you. #Team Safreeyyah} #Team Abdul-jabbar}. #Nima nasa kaina team Yusrah 😁 Ku matso kusa ranar muce masoya ina gaisuwa da nuna kulawar ku gare ni na jina kwana biyu shiru da kukai kuma kuna ta aiko da text cewa, lafiya wallh kalau yan uwa jiya da shekaran jiya muna hidimar biki ne shi yasa kuka jini, shiru amma sakamakon nema na da kuke xan daure yau nayi page daya ko baida yawa ne na gode da kauna💕. To nima sai nayi nasara😠 Ammy muje zuwa maman khaleel tahau lilo 😜wayyo dadi🙆 . #YUSRAHMS# NO.15👉 16 Maryam ta samarwa Safah aiki a gidan kuma nan ba laifi mutane ne masu karamci domin babu wani kyama ko tsangwama da suke nuna mata domin yan matan gidan basuyi zaton aiki tazo ba duk zaton su ko yar wani mai kudin ce dan Safah ba baya ba kyan fulani farin fulani jinin fulani gaba da baya jawur take"' Tsaye take a kitchen tana wanke wanke Salmah ta shigo da jaka a hannunta alamar fita zatai kallon Safah tayi tana cewa"Na Allah(haka suke ce mata tunda tazo suka ji sunan kauyen su sai suke tsokanar ta) please kafin na dawo a school kimin crispy onion rings da irin lemon da ki kaiwa aunty Abida ranar da saurayin ta yazo nima anjima zanyi bako". Murmushi safah tay"anya salmah ban iya hadawa ba amma bari na tambayi umma maryam saita nuna min"ok dan Allah to dan Allah karki manta ki tsara min sosai"amsawa safah tayi yayi da salmah ta fice bayan ta gama wanke komai ta fita a kitchen a palor suka hadu da maryam fada mata abinda salmah keso tay dan haka kitchen din suka koma a hankali take nunawa safah yadda ake hadawa har suka gama kuma dukkan wani girki da zasuyi safah na kokari wajan ganin cewa ta haddace komai". Washe gari sosai Emir yasa akai shiri suka kama hanyar kauyan malam na Allah sosai Abdul-jabbar ke farin cikin zaiga ahlin mahaifiyar sa har jin dadin sa bai boyu ba. Alhmdllh sun sauka lfy yayin da suke kallon komai da kowa ba Abdul-jabbar daya dade baizo ba kuma ya manta garin hatta Emir da kansa mmk yake garin yayi mugun sauya masa kuma ya kara cika ba kamar da ba domin a da idan ka samu gida anan sai, kayi tafiya mai nisa ka samu wani yanzu kuwa garin a cike yake harda karamar kasuwa suke da ita. Sosai malam na Allah ya sauke su hannu biyu da farin cikin sa wanda bazai misaltu ba yana kuma kallon wadannan kyawawan samarin da a ransa yana ayyana akwai jikan sa a cikin su dan gidan yarsa Fatima. Shima Abdul-jabbar a nasa bangaren cewa yake wadannan suna suka haifi mahaifiya ta hakika ina matukar son su ina kuma burin kasancewa da su. Emir dake murmushi ya kalle malam na Allah yana cewa"Baba ayi min afuwa na rashin zuwa akan lokaci da banyi ba bawai na manta daku bane sai yanayin mulki da yake da takura amma ina mai baku hakuri gani yau nazo na kawo muku jikanku ku ganshi shima ya ganku kamar yadda baku manta dashi ba shima haka yace min bai manta daku ba saidai baisan hanyar zuwa garin ba gashinan kusa dakai wannan kuma dan uwansa ne kanin sa Amfal". Na Allah da tunda Emir ya fara mgn yake zubar da hawayen tuna yarsa ya zubawa Abdul-jabbar ido ya kasa mgn har saida Abdul-jabbar ya rike masa hannu sai kawai ya karasa fashewa da kuka . Yana cewa "Allah sarki Fatima Allah ya jikan ki Da rahma yakai haske makwancin ki Sannu yaro kaji Allah ya baka hakurin rashin mahaifiyar ka hakika ina sonka kamar yadda nake son mahaifiyar ka fatan kaima haka". Allah sarki rungume shi Abdul-jabbar yay ba tare da yayi mgn ba Hadiza ma na gefe tana sharar hawaye shi kanshi Emir jikin sa yayi sanyi sosai ganin yadda malam yake kuka da tsufan sa. Basu iya hana malam kuka ba saida yayi sosai sannan ya share hawaye da murmushi akan fuskar sa ya kalli Emir yana cewa"ngd sosai muhammadu Allah yayi maka albarka kwarai naji dadi sosai kuma na sani koda ace Fatima baku hada jini da ita ba baza ka manta damu ba bayan rasuwar ta". Cikin girmamawa Emir yace"Ai baba kunfi karfin haka a gurina badan ma yanayin da muke ciki na mulki ba da duk sati zan rika zuwa muku to amma babu hali". Malam yace"karka damu hakan ma nayi matukar jin dadin ganin ku kuma ina fatan ba yau zaku koma ba"?. Amsa Emir ya bashi"eh su ba yau zasu koma ba nine dai zan tafi domin zanyi baki da dare su daga baya zasu taho". Dadi sosai malam yaji domin ko ba komai zasu saba da jikan su . Lokacin da sarki ya tashi tafiya rakiya sukai masa kafin ya musu sallama da drivern sa suka wuce shi kuma malam suka dawo gida. Hidima suka hau yi musu ta saukar baki wanda malam ya yanka rago guda ya kawai mahauta suka yo masa tsiren sa ga kuma hadaddan kindirmo wanda already tun kafin suzo yake a dafe". Da dare bayan sunyo sallah malam ya raka su dakin da zasu kwana zaro ido waje Abdul-jabbar yayi yana kallon malam yace "haba dai katifar yayin shinkafa akai zamu kwana? Allah jiki na zaiyi ciwo ". Malam dake kallon sa yace"to aiko dai akai zaka kwana domin mu bamu da katifa mai soso irin taku ta yan binni". Gaskiya to ka nemo mana ko aro ce kafin gari ya waye wannan ai bazan iya bacci akai ba gashi ko filo babu Allah nan gaba idan zanzo da katifa zan rika zuwa". Malam daya bude baki yana kallon shi yace"kaga dan binni harda wani filo to mu bamu dashi idan ba nine zan kwanta kai matashin kan dani ba"?kwanciya malam yay yana kallon shi yace "kwanta kawai ba matsala zan iya daukar nauyin ka har zuwa asuba". Murmushi Abdul-jabbar yay yana dago shi yace"wanne kashi da ran jika fa kamar iska ta bushe dana dago ka idan kuma na kwanta a kanka ai gobe saidai mu kaika makabarta ". Malam yace"aida ka kwanta kawai ba komai bakon ka annabin ka dan nayi maka haka yanaa hakkin bakunta ka farantawa bakon ka kayi masa hidima har na tsawon kwana uku". "A'a to na yafe kawai zan kwanta a hakan saida safe"murmushi malam yay yana juyawa yace"Allah ya tashe mu lfy "daga haka ya fita zama Abdul-jabbar yay a gefen katifar yana kallon Amfal dake kallon sa tunda suka fara drama da malam yace"yadai zaka wani zuro min ido ko ban fadi gaskiya bane nasan yau har gari ya waye ba zamuyi baccin arziki ba". Kai Amfal ya girgiza yana mikewa yace"Allah bros wani sa'in idan kana mgn kamar ba kaiba ji yadda ka takurawa tsohon nan da tsokanar ka ai wannan katifar tafi dadin kwanciya akan wacce kake kwana akai". Inji uban wa ka taba ganin inda aka hada hanyar jirgi da mota"?Amfal yace"sosai ma kai baka taba gani ba kenan lallai ashe da sauran ka"rabuwa dashi Abdul-jabbar yay yana kwanciya. "Subahanallah"abinda yace kenan jin kamar wanda ya kwanta akan dutsi dariya Amfal yay yana kallon sa yace"yadai akwai laushi ko matsa min na kwanta nifa sai naji ma kamar tafi tamu dadin kwanciya inaga idan zamu tafi zan sayi daya naje na dora akan gadon mu". Da kuwa saidai ka kwana kai daya malam dan saimun raba dakin kwana". Kallon fitilar dake dakin yay irin yar wayarin dinnan ce mai batir biyu yana cewa "badan dare yayi ba da nayi abubuwa da yawa amma Allah ya tashe mu lafiya" matsawa kadan yay inda Amfal zai kwanta tuni hannun sa ya soki wani dan yayi aikam ba arziki ya mike yana cewa shikenan yatsa na ya fice Amfal hasko min". Mikewa Amfal yay hankali tashe yana kunna hasken waya sai ganin dan yayin sukai makale zare masa Amfal yay yana cewa "sannu ashe ma dan wannan abinne kamar ba soja ba"hade rai Abdul-jabbar yay yana kallon saa yace"idan soja ne dan abu ya cutar dani bazan fada ba sbd gamai jikin karfe ko". Dariya amfal yay "wallh harka tuna min da hajiya mai ran karfe Allah sarki masoyiya ta tana can kila ma ta dade dayin bacci ". Abdul-jabbar bai sake mgn ba shima Amfal haka kawai dai sun kwanta tare da kashe wutar dakin". Typing📲 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 SAFREEYYAH 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 💫🌌💡ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫🌌💡 @YUSRAH MUSA ABUBAKAR ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ ^^^^^^^^^^^^ ^^^^^^^ ^^^^ ^^ ^ MANXON ALLAH S A W Ya wanda halin sane tayar da mai rauni dabi'ar kace taimako ya nasiruddini a kujerar ka awwalun ne kai marar sani ya wanda bai taba hanawa masu nema ba". "Aminci ga miftahul jannatun na'ima Aminci ga 'kiblar bayi a ran kiyama Aminci ga mai shiryarwa cikin salama Aminci ga duk mai matsayi dakai ya samu Aminci ga duk mai girmaran dakai, ya samu Aminci ga duk mai daraja dakai ya samu Aminci ga fatuhul akbar aya imamu yusrah musa ce tare dani da gaisuwa ta". #YUSRAHMS# NO.17👉 18 Babu wanda yayi bacci a cikin su har gari ya waye dakyar kuwa sukaje masallaci sbd ciwon jiki. Karfe 12:00 suka dawo gidan daga masallacin dan a cewar Abdul-jabbar ya danfi akan gidan a kofar dakin suka zauna kan babbar tabarmar dake shinfide lokacin malam ya dawo daga kasuwa shima ya zauna bayan sun gaisa Hadiza ta kawo musu kayan karyawa hadaddan kunu da kyakkyawar waina mai kuli gefe guda kuma ga kwanan tuwo". Kallon ta Abdul-jabbar yayi"gaskiya nifa bazan ciba a nemo min abinci kawai naci dan yunwa nake ji"baki bude Hadiza tace"kuma bayan ga abinci nan har yafi kayan dadin da kake sha". Shiru yay yaa kallonta sugar ta zuba cikin kunun tasa ludayi ta gauraya sosai sannan ta dau kofi karami ta zuba tana bashi tace"akwai dadi kwada sha kaji"kai ya girgiza dan haka Hadiza ta mikawa Amfal tana cewa karbi jika na dan Allah rabu da wannan kai ci abinka". Karba Amfal yayi yana sha ya dago yana kallon Abdul-jabbar da shima shi yake kallo baiyi mgn ba yaci gaba da shan kunu sai gashi ya dire kofi yana cewa"kai gaskiya yayi sosai bari na kara"dariya Hadiza tayi wallh kara gashi nan kuma dan ma baka hada da wainar bane da sai kayi santi". Duk yadda Abdul-jabbar yaso mazewa saida ya tambayi Amfal"wai da dadi ne"aje kofin Amfal yay yana cewa"to maganar gaskiya nidai ba nace ba sbd a tare dani akwai koshi saidai kaida kake jin yunwa ka gwadaa kar nace da dadi kasha bai maka ba kace nayi karya". Harararsa Abdul-jabbar yay yana daukar kofin shima ya deba ya soma sha daga farko idan ka kalle shi zakai tunanin madaci yake sha sai daga baya suka ga ya dire kofi ya kuma deba dariya sukai amma ko kula su baiyi ba saida yasha kofi uku hatta wainar saida taki jiki". Malam yace"wato dan binni ya akai ne? naga ka ware sai shan kunu kake da alama ya burge ka da mu zakaiwa bagu waikai sai andoni da kwai". Dariya Amfal yay yana kallon yadda Abdul-jabbar ya tsume yace" ba andoni ake cewa ba indomie take acan dinma koko da kosai yake karyawa dasu kawai yaga ku tsofi ne shine yake son yi muku burga ". Malam yace "ai kuma saidai ya burge kansa gashinan ya dawo dai dai shine yake hade rai kar muce ya yaba da kunun da yasha kowa dai ya ganka yasan kai jinin fulani ne jauro". Hadiza tace"nima na gani kuma na shaida ta tafar sauke Abdul-jabbar baice ba saima mikewa da yay yana cewa a sama masa ruwan wanka tashi Hadiza tayi dan ta dafaa masa da yake ana dan yin sanyi ne . Tsaye Safah take tana gyara kayan abincin dake dinning a jere mk saurayin gidan shine babba ya shigo gano ta da yayi saiya fasa wuce wa ya karasa inda take yana kallon yadda kayan dake jikin ta sukai matukar yi mata kyau. Ba zato taji an dafa ta a razane ta dago ganin wanda ke tsaye yasa jikinta na rawa taja da baya kara matsowa yay yana murmushi yace"first lady ya kike"? Muryar ta na rawa tace"lafiya". Kai ya jinjina yana cewa"hakan nada kyau dama amm nace ba kinga lady ina jin yunwa please ki shiga kitchen ki samar min wani abu dazan ci kafin nayi wanka na fito"yana kaiwa nan yay gaba da kallo Safah ta bishi maganar Allah tunda saurayin nan ya dawo ta tsani gidan nan kuma zata samu baba maryam kawai tace ta mayar da ita gida hankalin ta zaifi kwanciya dan ta fuskanci mk kamar yana harkar mata. Sauke ajiyar zuciya tayi bayan wucewar sa kafin ta koma bangaren da suke ta dauko hijab tana fitowa ji tayi ance "Safah ina zuwa"? a gicece ta juya dan saboda firgici bata iya bambance cewa muryar mace bace. Ganin Alawiyah kanwar Salmah yasa ta sauke ajiyar zuciya tana cewa"wallh kitchen zan shiga wannan yayan naku ne yace na sama masa abinda zaici". Kara kallon ta Alawiyah tay"humm ai yaya nada takura balle wannan karon da yayi sa'a kina gidan yana son mace wacce ta iya girki shi yasa yake damun ki da abincin ki baya burge shi zuwan sa da Yanzu yasa an dauko wata saidai kita hakuri kafin ya gama kwanakin sa ya koma". Murmushin karfin hali safah tay batare da tayi mgn ba zata wuce Alawiyah tace"kinga raka ni anguwa har ma dawo dan wankan sa yakan ci lokaci" cikin jin dadi safah ta bita suka tafi dan dama fargabar komawa cikin gidan take tunda tasan hajiya bata nan taje gurin biki baba maryam kuma taje cikin yola ne dama iya itace a gidan suma yan matan duk suna makaranta batai tunanin Alawiyahn ta dawo ba". Kuyi hakuri🙇 typing yau baida yawa ina da uzurirrika ne😜. Mrs Al'ameen Ahmad ce ta kowa. ONE LOVE💕 Typing📲 🍇SAFREEYYAH🍇 ANNURI WRITER'S ASSOCIATION BY Y M A TA AL'AMEEN. 💫💡ANNURI WRITER'S ASSOCIATION🌌💡 🕌🕋🕌 📿It is FRIDAY DON'T FORGET TO RECITE SURATUL AL-KHAF,MAY ALLAH (S W T) OPEN THE DOOR OF SUCCESS AND HAPPINESS FOR ALL OF YOU (MUSLIM) AMEEEEEEN.🙏 ALLAHUMMA SALLI WA SALLIM ALA SAYYIDIINA MUHAMMADIN SAYYIDIL MURSALINA. 🎈🎈🎈🎈🎈 🎈🎈🎈🎈 🎈🎈🎈 🎈🎈 🎈 #YUSRAHMS# NO.19👉20 Kamar yadda Ammy ta umarci Hanne haka ne ya faru bayan taje wani kauye tayi tambayar waye babban malamin da yake cire aljanu aka fada mata batai kasa a gwiwa ba taje gurin sa ta masa bayanin komai na cewa tana son maganin raba tsakani . Bayan malam ya gama sauraron ta yace"to alhamdllh naji dukkan bayanan ki kuma na fahimta bani sunan su "kara dukawa hanne tay tace Abdul-jabbar da Amfal shine sunan samarin". Kai malam ya daga bayyi magana ya soma zana kasa yana gogewa yayi yafi sau ashirin, amma baiga komai ba wani irin farin abu ya tare abinda yake son gani dagowa yayi yana kallon Hanne yace "wannan aikin bazai yiwu ba banga komai ba saidai zanyi miki istihara na gani in yaso saiki dawo zuwa jibi na fada miki abinda na gani game da wadannan samari". Godiya Hanne tay tana ajewa malam kudi mai shegen yawa wanda kafin ta mike malam yace"a'a dauke kudin ki bani bukatar ko sisi"jiki na rawa Hanne ta dauki kudin da ta aje masa tayi waje tana mamakin zuhudin malamin batai tunanin zaiki karba ba. Batun su Abdul-jabbar kam shida Amfal cikin Adamawa suka shiga suka yo sayayya ta ban mamaki wanda da suka dawo saida malam yace sai sun mayar dakyar Abdul-jabbar ya lallame shi ya kyale suka shiga da kayan. Katifu ne da kayan abinci da generator ya kuma yowa Malam da Hadiza dinkuna da abubuwan ban sha'awa na zamani yan gari harda zuwa kallo ranar da aka tayar da generaton wai gidan malam ya zama gidan yan gayu . Mk bai kwana gida ba tun fitowar da yayi yaga ba Safah babu alamar ta ya duba ko'ina shiru yabar gidan domin wani program zaije . Ita kanta safah da taji cewa baya nan tayi matukar farin ciki kuma hankalin ta ya kwana tana fatan har ta tafi gida karya dawo". Hanne ce zaune tazo jin sakamako malam ya dube ta yana cewa"to kamar yadda na fada miki nayi istihara kuma abinda na gani shine baza su taba rabuwa ba kuma wani asiri ko magani da za ayi dan raba su bazai ci ba duk malamin daya karbi kudin ki da sunan zaiyi miki aiki a kansu to yaudarar ki kawai zaiyi danya ci kudin ki soyayya ce da shakuwa mai karfi tsakanin su shawarar dazan baki ki hakura ki kyale su suyi rayuwar su kema kya huta idan kinji amma idan baki yarda da abinda na fada miki ba zaki iya zuwa ki tambayi wani malamin da kike tunanin ya fini sani ki sake gwada sa'arki saidai ina da tabbacin ba zaki nasara ba zaki iya tafiya". Jiki a sanyaye tace "malam to bazai yiwu ko wani abu da zaisa su'ki juna? ba wallh idan na koma uwar gida na zatai fushi dajin wannan labarin". Shiru malam yay yana kallon ta yace"na fada miki babu wani abu daya isa raba su babu shi sai mutuwa kuma na gani duk wanda yay yinkurin cutar da dayan su to zaiga sakamakon da zai biyo baya ina sake jaddada miki da ki sanar da ita wacce ta aiko ki cewa injini malam nace ta zubar da makaman yaki ta kyale su suci gaba da rayuwa karta debowa kanta abinda yafi karfin ta domin akwai tsari sosai a jikin dukkan su biyun wanda mahaifiyar baban su ta yi musu tun suna kanana kuma har yanzu bata daina ba domin tana son su sosai". Gwiwoyin Hanne duk a sace tayiwa malam sallama ta tafi da zulumin yadda zata fara yiwa Ammy bayanin abinda malamin nan yace amma zata san yadda zatai idan ta koma". Sosai zaman kauyen malam na Allah ke yiwa Abdul-jabbar dadi dan har baya so su koma can gida duk da yana kewar Abban su. Dawowar su kenan daga zaga gari suka iske malam a waje kan wani itace wanda kana gani kasan ya dade a gurin zama sukai suna sashi a tsakiya domin suji dadin hirar,. Kallon su yake cikin murmushi yace"Abdullahi da rabon dai baza ku ga juna ba kaida yar kanwar taka domin sun tafi Adamawa ita da maryama tun watan jiya kuma bana tunanin zasu dawo kwana kusa bansan ranar da zaku hadu ba lokacin da kuka zo kaida Muhammadu a sanda zaku tafi aikin soja batai wayon da za'a ce mata kai din yayan ta bane shine ya hana haduwar ku amma ina rokon Allah yasa ku hadu a kwana kusa". Abdul-jabbar dake sauraron sa yace"naji kace kanwa ta a ina muka hadu wace ita"?. Kai Malam ya jinjina kwarai ita din yar uwar kace Abdullahi domin ta kasance yar gidan kanwar mahaifiyar ka Zainabu wanda ita ma Fatima bayan ta rasu da yan shekaru ta bita to yar data bari ce ita kadai ce kuka hada kakanni da ita domin ni dama Fatima da Zainab ne kawai na haifa a duniya su kuma suka haife ku hakika ina sonku ina alfahari da ku". Sosai Abdul-jabbar ke kallon shi yana juya maganar a ranshi lallai yana son ya ganta ita kadai ce jinin sa dazaiyi alfahari da ita a matsayin dangin sa na uwa bai daina duban Malam ba yace"me taje yi a Adamawa kuma yaushe zata dawo"?. "Bani da tabbaci Abdullahi domin ba muyi zancen da ita ba kawai dai tazo yI mana sallama ne da yake gidan mahaifin ta yana gaba da mu ne sosai idan ma dai baku hadu yanzu ba tunda idan ta dawo mahaifin nata yace zaiyi mata aure da yaron kanin sa inaga ma kun wuce ta majalisar su san wani shago in kazo bikin sai kuga juna". Cikin saurin da ba shiri Abdul-jabbar yace"aure kuma ?yanzu har tayi girman da za'ai mata aure? kodai irin auren kauyen da kuka saba za'ayi mata kodan ba nace ba bansani ba koda kadan na fita". Dariya na Allah yayi yana cewa"sannu dan binni aikam dai baza a kira ta da yarinya ba tunda a 'kalla zatai 18 nake tunani idan ba mantawa nayi ba saidai tana da tsayin kafa idan ka ganta zakai tunanin ta haura shekarun nata"'. "Ahhh kaji irin abin da nake fada tana tsayin kafa shiyasa za'ai auren taa lokacin ta baiyi ba tana yar karamar ta tafara tara yara duk subi su dora mata hawan jini wanda keda 18 ni a gurina yarinya sharaf wacce bata sansan ciwon kanta ba". Kallon sa Amfal yay"Allah malam gyabbo uban yan son girma kace za musha kallo idan ka tashi zaben macen aure sa'ar shekarun ka zaka dauka don na ramfo manufar ka tuntuni na fahimci inda ka dosa nan kusa". Aiko tukuicin harara ya samu cikin dakewa da tsokana Amfal yace"karya nayi maganar gaskiya malam bana son borin kunya kawai ka fito kace shirgegiyar mace kake so wanda ta kaika ba karamar yarinya ba kome kace mgn ta nakan daidai "?. "Ban sani ba domin ban sako dakai ba uban yan shishshigi" . Dariya Amfal yay "ni kuma nasa kaina wallh idan mutum ya zauna bros yadda kake da burga tsaf zaka sakaltar dashi dan kawai na fadi gaskiya". "Ka fadi gaskiya ko ka shararawa mutane karya malam dama idan baka fada ba ni a tsari na babu auren yarinya mai karamin shekaru sabod.......bai karasa ba Amfal yamai rada a kunne dan kada na Allah yaji. Yace cikin kasa da murya sosai"saboda idan ka auri karamar yarinya balla ta zakai baza ta iyaa da bukatunka ba tayi maka kadan a gado ko "?kallon sa Abdul-jabbar yay cikin xaro ido zaiyi mgn . Amfal yace"karka wani wayance nasan haka zaka ce shiyasa na riga fada"ya karasa maganar yana dage gira ga dariya fal cikin sa ganin yadda Abdul-jabbar din ke binsa da kallon ya kasa maida masa martani" "Nace ko nayi karya ne baa haka Kake nufi ba naga kana ta kallo na kodai ka shigaa shauki ne ban sani ba"?jin har lokacin bai tanka masa ba yace"gashi na hasbo jirgin ka lallai bros idan Kai aure zamu sha kallo saidai mu rufe kunnen mu da idanuwan mu dan kada mu makanc.........tashi yay da gudu ba tare daya karasa ba ganin Abdul-jabbar na shirin rike shi ya koma gefe yana dariya dan sarai dama so yake Abdul-jabbar din ya magantu. Na Allah na kallon su cikin jin dadin ganin yadda kansu yake a hade yayi farin cikin hakan kuma ya godewa Allah idan ba ka sani ba baza ka taba cewa uban su daya ba idan kuma aka fada maka sai kayi mmk,. Dawowa Amfal yay yana kallon sa yace"haba my bros ya muna mgnr arziki kuma ka wani kore ni dan Allah kaka malam jiye mana wannan maganar dan kawai na fadi......tarar numfashin sa Abdul-jabbar yay da fadin kasan Allah Amfal ni da kaine idan bakai shiru ba". Rufe baki Amfal yay cikin zolaya yace"na rufe ruf🙊 kar muje bacci ka mulmule min wuya sorry bros dina I am so sorry don't disturbing me ba da kai nake ba misali nayi ". "Kai ka sani I shall not mind" Rike baki malam yay "to naji kun fara sako turanci ni kuma bana ji abar maganar ku tashi na raka ku gidan mahaifin ta"mikewa sukai suna sashi a tsakiya yayin da duk inda suka gifta kallon su ake mutane na mamakin wai wannan yayan sarkin kano ne kuma babban dan gidan Fatima ne jikan malam na Allah". Mrs A Ahmad ce. We will meet again Thanks for loving me. Nafila bayan sallar magriba👇 Raka.a biyu ce Bayan ka idar da sallar magriba saika ta kayi niyyar nafila a raka.ar farko zaka karanta fatiha da 'kulya daya raka'a ta biyu kuma fatiha da 'kulhuwa daya kayi zaman tahiya kai sallama,idan kai haka Allah zai fidda kai a zunubin ka kamar yadda miciji yake fita daga cikin sa'bar sa. Allah ya bamu ikon yi Amin. "(Azeemu domin muntahal mukami (A kara hau dani makurar mukami (A karfafa mini a dade ni kaimi (Na bayyanar da sirri na zuciya ta). Ina godiya Safiyyah Aliyu Zaria (maman khaleel khairi da kuma khaleepha)ina matukar jin dadi da nuna kulawar kI gare ni Allah ya kara barin mu a tare may Allah help and bless you and your household anywhere you are. 💕 Mrs A Ahmad gnrl💕. Typing📲 🍇SAFREEYYAH🍇 🌌💡💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫💡🌌 Gidan haske da samar da farin ciki da karbar bakin ta ANNURI tana maraba marhabun lale lale da kowa ba cuta kuma babu cutarwa. 18@Yusin Al'ameen Ahmad »«»«»« «» »«»«»« Yusrahmusa65@gmail.com Whattpad. Mrs Al'ameen Ahmad ce. ADDU'AR NEMAN SAMUN SHIRIYA A WAJEN ALLAH (S W T) KAI DA IYALAN KA DA AL-UMMAR MUSULMI BAKI DAYA.👇 =====Rabbana waja'alna musullmaini laka wamin zurriyati na ummatan muslimatal laka wa'arina manasikana watub alaina innaka antat tauwabur raheem=====. »« »« «»«» »« »« 👏 Rabbana waba'asfihim rasulan minhum yatlu alaihim ayatika wa yu'allimuhumul kitaba walhikimata wa yuzakkihim innaka antal azizul hakim. Allahuma antas salam wa minkas salam tabarika ya zuljalalu wal ikram. #Astagfirillahal azimul lazi la'ilaha illah huwal hayyum 'kayyum wa'atubi ilaihi👉 idan ka fadi haka sau uku 3x bayan kowacce sallar farillah Allah zai gafarta maka zunubin ka na shekara dari hudu. YUSRAHMS ABUBAKAR 🙋Nifa I have no girman kai🙆😝 if you are fushi😠😎🙄 dani to wallh you are just batawa kan k lokaci😜😁😃 . #YUSRAHMS# NO.21👉 22 Yau mk ya dawo gari safara'u bata sani ba saida sukai abincin breakfast ita da baba maryam taje serving dinsu ta ganshi gaban ta ne yay mugun faduwa nan tahau maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Suna hada ido ya daga mata gira "alamar yadai"?saurin dauke kai tayi daga saitin inda yake da kyar hannun ta na rawa ta gama serving dinsu Allah Allah take tabar gurin sbd shi zata tafi kenan hajiya Binta data fahimci kamar safan bata cikin hankalin ta tace"meke damun kine Safara'u ko baki da lfy ne baki fada ba". Shiru tay har saida hajiya Binta ta sake tambayar ta dakyar jikin ta duk a sanyaye tace "eh hajiya bana jin dadi ne". "Ok kuma shine baza ki fada ba in banda abinki ai jinya ta koru komai jeki kwanta zansa a kira doctor ya duba ki"to safah tace zata tafi kenan taji mk na cewa"kawai mum bari na kaita a duba ta basai yazo ba" ba damuwa kadai hajiya binta tace"shi kuma ya mike cikin murmushi yana kallon safah da itama shi ta zubawa ido cikin tashin hankalin jin abinda yace tasan akwai wani kullalliyar da yake shiryawa. Har inda take ya tako cikin kasa da murya yace"big girl ina jiran ki a mota na zaki ganta black idan kin gama shiryawa kuma ki tabbata kinsa turare Mai matukar karfi da dadi saboda ina son haka". Yana fadin haka ya tafi ya barta a gurin ta daskare kamar Wata gunki cikin tarin kunar rai da fargaba salmah data lura da tsaiwar taa tace"safah kije mana ki dauko hijab dinki yaya baya son African time". Daga kafa safara'u tayi cikin tarin damuwa ta soma tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki har ta fita a part din ta shiga bangaren su kwanciya tayi akan katifa hawaye na zuba a idon ta lallai bata kaunar zaman Gidan nan sbd mk bari baba maryam ta shigo tace mata tana son taje taa gano baffan ta daga nan idan ta tafi baza taa sake dawowa ba har abada lamarin mk yana bata tsoro bargo taja tana lulluba kamar meyin bacci taci gaba da tunani kafin shigowar baba maryam din. Ba zato taji an yaye bargon data rufa kan tayi wani yunkuri ta sake jin ana jan zip din rigar ta a burkice ta wuntsula tana sauka daga kan katifar ta diro kasa wanda babu shiri ta saki kara sakamakon tankwashewar da kafar ta tayi durkusawa tay a gurin cikin azaba tana cewason "wash Allah kafa ta". Kanta mk ya nufo yana cewa sorry muga kafan mi tayi"ganin yayo kanta zai rike kafar yasa taa mike tana ja baya da sauri kara matso ta yayi. Cikin kuka tace"dan Allah ka bari bana so karka ka taba ni"dakatawa yay yana kallon ta yace"humyimm village girl wai ke me yasa bazaki waye ba ne gaki a haka beauty amma sai duhun kai look madam I love you ina sonki ne ki fahimta mana ki saki jikin ki dani zaki huta zan baki duk abinda kike so idan naji kina da dadin harka ma maybe na aure ki ladyna ko me kika ce ni da ke mun zama abokan harkalla". Zaro ido safah tay cikin tashin hankali tace"nidai dan Allah kayi hakuri ina da wanda zan aura"kallon sama da kasa ya mata yana cewa"yayi kyau Amma da alama shima da'ki'ki ne kamar ki dan yadda kike gidahuman nan zaki wuyar sha'ani shikenan kada Allah yasa kije ina ruwa na lafiyan waye yar kauye kawai". Fita yayi a dakin yayin da safah ta zauna cikin zulumi ga ciwon da Kafar ta ke mata batasan lokacin da kuka yazo mata ba kawai ta rufa cikin ta akan katifar ta soma rerawa dawowar mk gida ba karamar barazana ya zama a gare ta ba tun ranar dayai, four eye da ita bata sake jin dadin zaman gidan ba kullum a ankare take da shi dan shakka babu tana mai zargin iskanci tunda gashi kiri-kiri yana nuna mata halin sa ko shi waye yadda yake gwada mata abubuwa na rudanin duniya da dukiya daya same ta zilamammiya da yanzu ya cika burin sa a kanta saidai yayi kadan ta amince masa never history. Ganin har sha biyu tay amma babu alamar safara'u yasa maryam fitowa tana tambayar hajiya binta"hajiya ni kuwa ina safah tay"?amsa ta bata da cewa "a'a wai bata jin dadi ne shine mk ya tafi kaita a dubawa ta kuma kinga har Yanzu basu dawo ba". Baba maryam tace "to ko kuma sun dawo rashin jin dadin ya hana ta shigo ta sanar dake sun dawo ta wuce bangaren mu bari na dubo ta ". "Ok to shikenan kila tana can din jeki dubo ta"fita baba maryam tayi zuwa sashin su cikin mamaki ta tarar har lokacin Safah bata daina kuka ba zama tay tare da dago ta tana cewa"haba Safara'u me kike yi haka jinya ai dole ce zaki warke kinji ki daina kukan maza taso muje hajiya na neman ki taga baku dawo da wuri ba". Kai safah ta girgiza bazan iya ba kafa ta ciwo take min na bige yanzu"kafar baba maryam ta kalla ganin kama harta dan kumbura da alama targade ne zauna tay domin ta duba mata ta rike kafan tana Matsawa kara safah ta saka tana rike hannun baba maryam da hawayen ta wadanda dama basu tafi ta saki kuka tana cewa"dan Allah ki daina akwai ciwo". Cikin tausaywa baba maryam tace "na sani targade ne kikai bari na gyara miki zaki ji sauki yi hakuri ". Ci gaba tayi yayin da Safah har shidewa take dan azaba saida ta gama gyara Mata sannan ta saki kafar tana cewa "sannu kinji"Safah bata iya magana ba sai juya kai kawai take. Mikewa baba maryam tay tana cewa "bari naje na sanar da hajiya targade kikai ina zuwa"fita tay tabar Safah duk abin duniya ya dame ta lallai tana son komawa gida bata kuma marmarin dawowa idan ta samu ta kubuta zata ci gaba da damun baba maryam da rokon cewa, zata je gano baffan ta idan ta samu taje gida babu ita babu Adamawa. Komawar baba maryam cikin gidan ta sanar da hajiya Binta abinda ke faruwa hajiya da mamaki ya ishe ta taya Safah taji targade bayan taga lokacin da zata bar nan bayan ta gama serving dinsu tafiyar ta normal take. Kallon maryam tay da alamar tambaya tace"amma yaushe tayi targaden saidai bayan fitar ta anan domin banga wata alama a tafiyar ta dazai nuna taji ciwo ba"cikin kokwanto baba maryam tace"to ba'ace komai ba nidai kawai tace min bugewa tay saidai na sake tambayar ta idan na koma dame ta bige". Hajiya tace"eh gaskiya yana da kyau ki tambaye ta bai kamata a barta ba asibiti za'a kaita idan mutum na karkashin ka dole hakki ne a wuyan ka kula da duk wata damuwar sa". Mk da yana can gefe cikin daya daga kujerun palon kuma yana sauraron su jin hajiya tace a tambaye ta yaji tsoron kar tace shine dan haka cikin sauri ya shiga zancen nasu da cewa"mumy bayan mun dawo nefa ta fito a motar bata kula ba ta bige da murfin motar banyi tunanin targade bane shi yasa na kyale ta ". Cikin harara hajiya tace"ka kyauta da yake ciwon ba a jikin ka yake ba dole kace haka me laifin bayan Kun dawo kaa sanar dani sai kayi burus dan iskanci" Mk da tunda ta fara magana yake murmushi har takai aya sannan yace"sorry nayi laifi bada sona bane ni kaina na damu da yarinyar saboda akwai hankali da nutsuwa ga tarbiyya kawai matsalan ta kauyenci zaman ta anan yaci ta waye da komai amma har yanzu da sauran ta". "Allah ko wayayye to yayi kyau ka rufe min baki haka surutun ya ishe ni kasan dai banson hayaniya". Baba maryam kitchen ta koma domin yin ayyukan da safah keyi ganin haka yasa mk ya fahimci ta baro safah ita kadai mikewa yay cikin jin dadi zai je gurin ta kamar daga sama yaga ta shigo palon da dingishi tana tafiya a hankali. Da kallo ya bita lallai yana jin wani abu game da yarinyar nan kuma saiya binciko ko menene yana da yan mata da yawa amma fa yanzu maganar gaskiya duk ji yake sunyi expire a gunsa ita kawai yake iya kallo yasa gaba yake kwadayin samu da kasancewa a tare da ita ta hanyar halal ko akasin ta(haram) yana so ya dandani zakin ta kumaa lallai bazai janye wannan kudirin nasa ba saiya samu natsuwar da yake mafarkin samu daga gare ta a koda yaushe kuma duk rintsi yana nan akan bakan sa. Sauke ajiyar zuciya yayi mai masifar karfi jin wata iriyar sha'awar ta data taso masa lokaci guda ga joystick dinsa na neman tona masa asiri ta hanyar mikewa tsaye daa yayi". Dawowa daga zancen zucin daa yake yayi jin hajiya na cewa"ayya safah kin samu damar iya shigowa sannu kinji mk sai a hankali nasan halin sa maimmakon ya bude miki murfin motar ki fito yasan bakya jin dadI amma ya rabu dake kika bige ko yi hakuri kinji". Sosai safah mamaki ya kamata jin abinda hajiya tace dagowa tayi tana kallon mk wanda ke jifan ta da wani irin murmushi mai ma'anoni da yawa dan tsaki taja wanda tasan hajiya baza taji ba a ranta tace"ji munafiki mai siffa biyu wato karya kazo ka sharara musu cewa ka kaini asibiti mun dawo garin fitowa a cikin jakar wannan bakar motar taka nayi targade saboda gamai jikin roba alhali ba haka abin yake ba kaji kunya dai". Kamar yaji me tace ya matso kusa da inda take zaune yana cewa"ni kaina safah sai yanzu nasan naji kunya da ban tsaya na tambaye ki akan ko kinji ciwo ba yi hakuri kinji lady kitchiner Allah ya kiyaye gaba"banza safah ta masa tamkar ba'a halicce shi ba yasan dama bazata kula shi ba tunda da ba gaskiyar lamari ya fada ba. Alama ya mata da hannun sa cewa a tari gaba yana da babban uziri da ita sannan yasa kai ya fice daga palon da kallon tsantsan tsana mai karfi Safah ta raka shi tare da sauke wani numfashin kasantuwar sa a gun da yake neman hana ta shakar iska daidai sai bayan fitar sa taji dadian kuma taga palon yayi kyau yay haske mk tamkar mutuwa take kalloa shi. Fitar shi yayi daidai da shigowar Alawiyyah da Salam zama suka duka su biyun a matukar gajiye Alawiyyah tace"wash Allah baya na gaskiya mum idan dad namu ya dawo ki sanar dashi ya sauya mana school ta kusa da gida kullum idan na kwanta bacci dakyar nake tashi saboda gajiya ga drivern nan ya tsufa ya kamata ya huta haka a samo mana wani mai jini a jiki shi kadai yana tafe mota tana reverse akan titi nikam ina tsoro kar wata rana yaje ya danki tanki ya kashe mu". Kallon sama da kasa hajiya ke mata tace"sannu umma nice zanyi masa duk wannan bayanin ke me zai hana idan ya dawo ki same shi ki fada masa ba mahaifin ki bane saini zaki sa wannan aikin idan kika je da kanki zaifi fahimtar ki". Cikin shagwaba tace"Allah mum a'a dad nada fada ina tsoron zuwa ki taimaka min bana son fadan dadyna" "ok shiyasa ni kuma da bansan ciwon jikina ba kika min tura wawa a 'kaya kenan to bazan fada ba" dariya Alawiyyah tay "Allah mum ba haka bane nasan zaifi fahimtar ki akan ni tunda ke babba ce kuma mata ce saiya fi daukar maganar ki da muhimmanci akan tawa gani zayyi kamar ni shirme na fada masa idan kece kuwa da sauri zai amsa". Tab waye ya fada miki bakisan taurin dadin naku ba shiyasa kika ce haka amma ki gwada zuwa" kai Alawiyyah ta girgiza"kawai na hakura"ba tare data kalli inda Safah take ba tace"Safah dan kawo min wani abu man naci wallh yau yunwa nake ji"ko kafin Safah tay yunkurin tashi hajiya tace"a'a yau kowa saidai yayi da kansa targade ne a kafan ta bazata iya wannan zirga zirgar taku ba". Ba Alawiyyah ba hatta Salma da tunda suka shigo hankalin ta ke kan waya hankali tashe ta dago tana cewa "subahanallahi a ina taji ciwo kuma"? Hajiya dake kallon kafar tace"dazun nan nefa da bata jin dadi mk ya kaita an dubo ta sun dawo garin bude motar ta fito shine ta bige kinga dai gurin sai dada tashi yake kuma maryama tace min ta gyara mata amma dole inaga asibiti za'a kaita zaifi sauki kawai da barin ta a gida ba'asan ranar warkewar ta ba". Cikin tausayawa suka ce ayya sannu kinji Allah ya baki lafiya"amin Safah tace iyalan gidan nan suna burge ta amma mk ya bata musu gida dan basu sani bane"mikewa Alawiyyah tay tana cewa"bari naje kitchen bazan rasa abinda zanci ba wucewa tay Salmah ma ta mike tana shiga part dinsu aka bar iya hajiya da Safah a palon. Yaukam anan zan tsaya da typing don nayi matukar gajiya sorry fans typing akwai wuya😭😜😸. Mrs Al'ameen Ahmad ce,. Nagode da kulawa. ==///======///== #YUSRAHMS🙆. »«*»«*»« »«*»«*»« »«*»«*»« »«*»«*»«*» »«*»«*»« »«*»«*»« »«*»«*»«*» »«*»«*»« »«*»«*»«*» »«*»«*»«*» »«*»«*» »«*» «*» Typing📲 🍇 🍇 🍇SAFREEYYAH🍇 🍇 🍇 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 }{}{}{ }{}{}{ }{}{}{ }{}{}{ }{}{}{ ><>< ><>< ><>< ><>< ¥usrah Musa Abubakar Gimba ><>< ><>< ><>< ><>< 🙃 MRS AL'AMEEN AHMAD CE💞 Lalalalala!!!🙊 My bros anata shagalin ba kai shiyasa naji littafin baya tafiya yadda nake so ashe kaine na manta maza matso ga page dinka ya bayyana dan uwa na ABUBAKAR MUSA ABUBAKAR (AMEER) ina miko gaisuwa ta zuwa gareka wannan shafin da next page duk mallakin ka ne saika yarda sannan na bawa fans su karanta😜 idan kace a'a saimu tsallake😧 kawai babu wata matsala🙃😉. To yace karna baku dan haka yau da gobe ba typing😂. DEDICATED TO MY MOTHER MAY ALLAH FORGIVE YOU,MAY ALLAH HELP U MAMA NA I LUV U WITH ALL MY HEART AND MY LIFE AM ALL YOURS I LOVE U AGAIN AND AGAIN AND AGAIN. AYI HAKURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR. #YUSRAHMS# NO.23👉 24 Hanne ce durkushe gaban Ammy tana mata bayani dalla dalla kamar yadda malamin ya fada mata bata boye komai ba ta kara da cewa kuma ranki ya dade yace min ki zubar da makaman yakin ki dan bai gano miki nasara ba babu wanda ya isa raba su". Ammy dake zaune ta dora kafa daya kan daya tana sauraron hanne a matukar firgice ta mike tsaye cikin wani irin mugun yanayi kanta na juyawa ga wata hajijiya dake nema yada ita kasa a tsawace cikin daga murya tace"meeey kinsan abinda kike cewa kuwa Hanne kina cikin hankalin ki bazasu rabu ba fa har abada kike cewa kenan haka na nufin saidai na zuba ido kenan na hakura da d'ana malamin yake nufi kome inaaaaan hakan bamai yuwuwa bane bazan zuba idon ba bazan 'kyale ba lallai karya ne abinda yace Amfal dana ne kuma dole ya dawo gare ni kota halin kaka Hanne ina bukatar shawara mezanyi"? Mema zance wanne mataki zan taka? ta ina zan fara? eyeee na gaji nayi matukar zuwa bango shekara da shekaru ina cikin kunci ko bayin da basu da aiki sai bauta ai suna samun kansu cikin farin ciki balle ni gani fa Amfal tunda suka tafi da dan iskan yaron nan sunki dawowa har yanzu wai wannan wanne irin abune"ta karasa maganar muryarta kamar zai fashe har sarkewa take da yawu. Hanne dai ikon Allah take kallo saida Ammy ta gama sannan tace"ranki ya dade ki gafarce ni ai hakan ba yana nufin kuma shikenan ba zamu nemi wata hanyar da zamu bi baza mu sare ba duk mai nema fa yana tare da samu zan sake binciko miki wani malamin wanda yafi wancan mu sake gwada sa'ar mu nasan maluma da yawa wadanda suka kware ta kowanne fanni ranki ya dade zan sake kokarta miki". Wani burkitaccen kallo ammy kewa hanne tace"zancen banza kenan sanin da kikai musu na iska ne kuma ya tashi a wofi tunda ba amfana nayi dasu ba basu da wani tasiri a gurina". Hanne da kanta ke kasa bata iya dagowa ta kalli bacin ran dake tattare da Ammyn ba cikin son huce mata zuciya da kwantar mata da hankali tace"kiyi hakuri ranki ya dade nayi miki alkawarin zan sake duba wa na samo kwararre wanda aikin sa farat daya yakewa mutum". Zama Ammy tay tana huci ta nuna hanne da yatsa cikin nuna mulki da isa tace"wallh hanne ki shiga hankalin bansan shashanci na fuskanci kamar yawo kike min da tunani na ni abokiyar wasan kwaikwayon kice kome". 'Shiru Hanne tay cikin tsawa Ammy tace"ni zanyi magana ki manna min hauka kina matsayin baiwa ta mai yimin hidima hanne bari kiji wata magana badan Allah yasa kin kama ni ina kulla da tunanin yadda zan kawar da Abdul'jabbar ba da wallh ko kallo baki ishe niba ke kanki shaida ce ko jakadiya tayi kadan na kalle ta balle ke mai kula da lafiyar bayi ki shiga hankalin ki hanne kafin musa kafar wando daya dake idan kina bacci ne to ki farka ki wartsake ni matar sarki ce duk fadin masarautar nan bani da wacce zatai gugan kafada dani ina miki kashedi na karshe kafin ki kaini bango". Jikin Hanne yana matukar rawa ta kara dukawa tana bawa ammy hakuri"dan Allah ranki ya dade kimin afuwa bazan sake kuskure ba zan sake zuwa wani gurin wannan karon baza a samu sabani ba bazan sake kasa a gwiwa ba zan tashi tsaye na kokarta da dukkan karfi na kimin rai". Tsaki Ammy taja mai karfi tana sakar mata harara tace"ke kika sani kuma ke ya dama 'bace min da gani bana bukatar sake ganin ki kada ki kuskara ki sake nufo ni idan ba harda daddad'an labarin da kika san zai sani farin ciki ba 'bace min da gani zaman ki anan din babu abinda yake haddasa min banda bacin rai". Mikewa hanne tayi jiki a sanyaye tana cewa"tuba nake ranki ya dade kiyi min hakur.............bata karasa ba da saurinta ta fice har tana yin tuntube bata saurari zafin da kafar ke mata ba da gudu ta karasa fitowa daga sashin Ammyn tana komawa can yakin su na bayi sannan tsaya a saitin wata yar karamar shukekkiyar bishiya tana duba yatsan harya fashe jini ya fara fita tsaki tayi . Tana cewa"azzalumar mata kawai zata sa na cire yatsa na a banza kece dai shashashar mace wacce batasan abinda take ba amma badai niba dan wallh sau dubu na fiki hankali nasan kuma abinda nakeyi da wanda zanyi ya amfane ni domin idan nice a matsayin ki bazan takura kaina da wannan sokoncin kudirin naki ba kodan na samu soyayyar sarki aina rike masa wannan tilon dan nasa Abdul-jabbar amma da yake ke sha ka tafi ce bugun shaho kuma awon igiya gariya kika biyewa jakar zuciyar ki wacce bata saka miki komai sai gidadanci ina tausaya miki Adama kiyayyar da kikewa Abdul-jabbar ba gata ki kaiwa kanki ba kuma tunda kika zage ni kika cimin mutunci kika kaskanta ni dan kina gadara ke matar sarki ce ba matsala ta bace ba ruwa na da hakan zaki gane shayi ruwa ne bazan sake wahala akan cikar burin kiba kasuwanci zan farayi da tunani ki wacce ta rako mata asararriya kawai". Ta karasa maganar tana kallon gefe da gefe ko wani na jinta ganin babu alamar kowa yasa ta sauke ajiyar zuciya tana rufe idon ta taje tunanin lokacin data kama Ammy na maganar. Shekaru masu dan dama da suka wuce Hanne ce tafe rike da babban tray wanda ya kasance cike yake da kayan marmari ta shiga part din Ammy jin ana maganganu yasa taja ta tsaya tare da kashe kunne ji tayi yaro mai karamar murya na cewa"Ammy ki bani inibi da dabino yau Abbana baya nan kuma yanzu naje be dawo ba". Cikin tsawa Ammy tace"fita anan jimin munafikin yaro harda wani na baka inibi da dabino da yake Fatima ce taban ajiya kanta sheka lahira shiyasa zaka zo ka tambaye ni da kasan yadda na tsani ganin ka da baka iya doso niba kuma nice ajalin ka saina bakantawa rayuwar ka na kuntata ma baza ka taba jin dadi ba har ranar mutuwar ka". Tana kaiwa nan ta juya zata fara tafiya da gudu ya bita ba zato taji ya rike ta a fusace ta juyo tana fisge hannunta tare da tsika masa mari wanda saida ya kifa a gigice cikin azaba da dauriya ya mike wani irin dundu ta sakar masa tana cewa"hannu na yayi kama dana uwarka ne da zaka zo ka rike ni wallh yaron nan saina kashe k............... Kasa karasa maganar tay ganin hanne tsaye kuma da alama ta dade da zuwa zaro ido tayi tana kallon hanne tace"ke kuma uban me ya kawo ki nan din a wannan daren lallai zakisan kin ganni ina azabtar da wannan yaron kuma duk wanda kika kuskura kika fadawa hukuncin ki kisa ne a wajena dan duk wanda yasan sirri na bai kamata ya rayu ba mutuwa ce tafi dacewa dashi ko waye". Hankali a tashe hanne ta zuba gwiwoyinta a kasa jikin ta yana tsananta karkarwar tsoro dan sarai tasan Ammy zata aikata fiye da haka ta soma bata hakuri kallon ta ammi tay naji wannan kafirar magiyar taki ta ishe ni jira ni nan ina zuwa"tana fadin haka ta bude wata kofa ta shiga tare da rufowa da karfi wanda saida hanne ta toshe kunnen ta saboda kara. Shiru shiru ganin taki fitowa gashi dare yaja sai hanne tay tunanin ko ta manta ne wata zuciyar tace mata ko kuma tayi bacci ba ki tafi kawai gobe kya dawo"mikewa tay tana karasowa ta aje kayan marmarin har zata juya ta tuna yaron da ammi ta mara kallon gurin da yake tayi yana kife har lokaci tun sanda ta mare shi a firgice tayi gurinsa da sauri tana dago shi cikin tashin hankali ko duk zaton ta ya mutu ne amma sai taga akasin haka yadai hada gumi shakaf ya jike waige waige ta fara can ta hango wani karamin towel cikin hanzari ta dauko ta goge masa gumin sannan ta rike hannunsa cikin sanda ta bude kofa suka fita. Ko ina da haske saidai ba mutane duk an kwanta bacci sun danyi tafiya mai tsayi kafin su karasa sashin hajiya ta tsaya dashi a wani sako tana kallon shi murya kasa kasa tace"Abdul-jabbar me ya kaika gurin Adama tsautsayi ko? kaima kasan ba sonka take ba ka daina zuwa inda take kana zama gurin hajiya ko Abbanka baya nan kuma idan gari ya waye karka fadawa hajiya cewa ammi ta mare ka zaka jawo fitina da tashin hankali a masarautar nan wanda ba'ai zato ba akan haka sarki na iya sakin Adama dan haka kai shiru da bakinka Allah zai saka maka kaji"kai ya daga mata bayyi magana ba. "Yauwa dan albarka insha Allahu wata rana sai Adama taci arzikin ka kuma ta zauna a karkashin inuwar ka kuma nayi alkawari daga yau zan zama mai kula da dukkan wani motsin ka ta asirtacciyar hanya ba tare da kowa ya sani ba domin mahaifiyar ka Fatima ni tayi min komai a rayuwa itace ta kaini matsayin da nake yanzu kuma har abada bazan manta wannan alkhairin nata ba muje na raka ka" Hanne tace tana jansa suka karasa part din hajiya . Masu tsaron kofar tane suka tare hanne suna cewa"daga ina meya hada ki dashi kina matsayin baiwa kinsan idan sarki yaji labari sai an kaiki gurin horo an tambaye dan haka fadi gaskiyar inda kika ganshi"?. Hanne da duk ta rikice jin abinda suka fada kuma tasan ba karamin aikin su bane suce sun ganta dashi su jawo mata masifa dan haka saita yanke shawarar kawai ta musu karya donta kubuta daga zargi,kallon su tayi tana cewa"na fito ne zan rufe kofar sashin bayi kawai na ganshi a tsaye yana waige waige shine na tambaye shi ina zaije sai yace gurin hajiya shine fa na taho na kawo ba wani abu bane ku yarda dani gaskiya nake fada muku". Wanda ya karbi Abdul-jabbar ne yace"shikenan to yayi jeki"yana fadin haka ya budewa Abdul-jabbar din kofa ya shiga ita kuma hanne ta juya tana komawa yankin su na bayi cikin tausayawa yaron da ko mahaifiyar sa bai sani ba. Washe gari hanne na gurin aiki sako ya isketa daga uwar gidan sarki cewa tana son ganin yanzu kuma kada ta haura mintu guda bata jeba jikin hanne na rawa da gudunta ta isa part din Adama kishingide ta same ta cikin alkebba sai shan kamshi take tana juya kai cikin nuna mulki gefe guda kuma ga wata baiwa durkushe tana mata tausa a kafafunta gaban ta kuma mutum biyu daya na mata firfita da mafici dayar tana yanka tuffa da karamar wuka tana mika mata a baki sannan ga wani tsaye da wata irin murdaddiyar bulala sai zare ido yake yana muzurai🙊. Zubewa Hanne tay duk jikin ta na shaking saboda tsoro murya na rawa tace"ki gafarce ni ranki ya dade gani nazo bisa sawun wanda kika aika kira na tuba nake idan har nazo a makare ayi min afuwa". Tashi zaune Adama tay tanaiwa bayin alamar ya isa suje bata bukatar ganinsu mikewa sukai da sauri har suna hada hanya suka fita suna mamakin rashin kirkin wannan mace mai tunkaho da jida sarauta ga girman kai fal ciki,. Bayan fitar su Adama ta maida kallon ta kan wannan mutumin tana masa alama da ido kaiya jinjina sa'an nan ya karasa inda Hanne take babu zato taji saukar wannan zazzafar bulalar ta sauka a jikin ihu ta kurma cikin neman agaji wanda cikin tsawa Ammy tace ta rufewa mutane baki idan ta sake ko tari ne zata sa ayi mata hukuncin daya fi wannan sau dari. Hanne naji tana gani katon nan ya rika sharara mata bulala cikin mugunta da iya karfin sa saida ya sauke mata guda ashirin duk bayan ta ya kumbura wani gun ma ya fashe sannan Ammy ta kalle shi cikin murmushi tana tace"dakyau yayi kyau haka nake so babu sassauci ko wasa jeka ka gama aikin ka"dukawa yay cikin girmamawa ya kwashi godiya ya mike yana fita. Ammy dake tsaye ta zauna kan kujera tana kada kafa kuma tana kallon yadda Hanne ke juya kai saboda azaba murmushin jin dadin hakan tayi ta sani ko ba komai yanzu hankalin ta zai kwanta duk rintsi hanne bazata tona mata asiri ba dan duk fadin masarautar itace mutum ta farko data taba kamata tana azabtar da Abdul-jabbar kuma wannan ba shine karo na farko ba. Mikewa tayi ta tako har inda Hanne take ta fara zagaya ta tana tafa hunnu tace"yadai bulalan akwai dadi ko? humm kada ki damu wannan somin tabi kika gani indai har zan baki umarni ki karya min dokata ina matsayin shugabar ki to kuwa kina tare da wahala kuma zaki kasance cikin ukuba ta babu wanda ya isa jayayya dani ko waye shi dan haka ina mai gargadin ki da ki kiyaye gaba". Shin jiya raini ne yasa da na baki umarnin cewa ki jira ni ina zuwa kikai tafiyar ki saboda bankai matsayin ki bini ba kuma uban waye ya fidda Abdul-jabbar daga nan yakai shi sashin hajiya ko duk zakice min bake bace na sani dare ne bazai taba iya komawa da kansa ba fada min me yasa kika aikata haka!? A tsawace ta karasa maganar wanda Hanne saida tayi zaman dabas a kasa saboda firgici. Muryar ta na rawa ta soma magana"dan girma Allah ranki ya dade kiyi hakuri nayi zaton da naga baki fito ba ko kinyi bacci ne shiyasa na tafi da niyyar yau da safe na dawo ba ina nufin karya umarnin kiba ki gafarce ni uwar gidan mai martaba Abdul-jabbar kuma ba nice na kaishi gurin hajiya ba harna fice yana palon nan bansan komai akan haka ba ranki ya dade gaskiya nake fada miki". Huci Ammy ta fitar tana kallon hanne tace"naji zonan inason zamuyi magana dake ta sirri mene sunan ki"?da sauri hanne ta matso inda Ammin tace mata tana cewa "suna na HANNE" . Gyara zama tayi tana yin kasa da murya tace"yauwa hanne wata magana zan fada miki kinga duk fadin masarautar nan a yanzu babu wanda yasan sirrina da kudiri na da kuma shirina akan abinda nake kullawa akan Abdul-jabbar saike dan haka zan 'yanta ki na kuma baki babban mukami zaki zama amintacciya ta zan hada hannu dake domin na cimma buri na akan shafe Abdul-jabbar kuma bana bukatar kowa yasan haka, kin jini kin haddace abinda na fada miki"?. Hanne da har lokacin jikinta bai daina rawa ba tace"eh ranki ya dade zan iya kowanne irin aiki idan kika sani kuma baza a samu kuskure ba bazan taba saba lamba ba". Kai ammi ta rausaya hakan yayi tashi kije saina neme ki kuma koda wasa kada ki kuskura ki fadawa wani wata magana wannan tsakanin mune daga ni saike bana bukatar kowa". Godiya hanne tay tana mikewa ta fita tana komawa bangaren su na bayi ruwa mai zafi ta samu ta dumama jikinta tana tunanin maganar da sukai da ammi lallai tana tsoron ranar da asiri zai tonu ace harda ita a masu aikata muyagun laifuna amma dole tabi ammi ba yadda ta iya kodan tsira da rayuwar ta. Lokacin da hanne ta dawo daga tunanin ta kwafa tay cikin takaici tana cewa"wallh Adama duk abinda kikai min bashi kika ci akwai ranar biya tana nan zata zo bakisan nima ba kanwar lasa bace kowa yaci tuwo dani miya yasha miyar ma ban rage ba kwanon ya side muje zuwa ga fili kuma gamai doki saura sukuwa". Mrs Al'ameen Ahmad ce👍 ONE LOVE WE WILL MEET TOMORROW😜 YAN UWA. TYPING📲 🍇 🍇 SAFREEYYAH🍇 🍇 💫💫 ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫💫 STORY & WRITTEN BY YUSRAH MUSA ABUBAKAR »«Mrs Al'ameen Ahmad ce»« Dedicated to My mum i love u with all my life may Allah accept your du'ah and help you u anywhere u are mamana 👏. Abubuwan nasiha guda biyar masu tasiri ga rayuwar mai hankali. Duniyar da za'a barta😧 👉 meya kawo hadama? Rayuwar da zata kare😟 👉ina wani farin ciki? Ana sauraron mutuwa😭 👉ina wata walwala? Jikin da zai zama gawa😢 👉Me zaisa alfahar? Karshen da makomar sa kabari😭 👉me ya jawo girman kai? Duk wanda ya manta da wannan😠 👉to ina yabar hankalin sa?🤔. 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕋 🕋 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕋 🕋 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌🕋 🕋 🕌 🕌 🕌🕋 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌🕋 🕋 🕌 🕋 🕋 🕌🕋 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌🕋 🕋 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌 🕌🕋 🕌 ================================== 👏 May Allah open the door of success and happiness for all of you(Muslims) may Allah accept your du'as and protect you and your families from all calamities amin, start you day beautifully with fajr prayer and quran recitation, o Allah s w t make us among those who never miss salah Ameen ya Allah🙏. *JUMA'AT MUBARAK* 🍏🍇🍓🍍🍒🍐🍉🍎🍊. 🤗 Ina kuke 'knawayen asali ku fito ku taka rawa, 🎶🎹🎻🎷🎤 ga page dinku ya bayyana ku kadai naba dukkan sa as you wish kuyi yadda kuke so dashi mallakin kune har next page na baku just for remember"🌹😜💝. Hauwa'u Mu'awiyya Umar Kano (maman Al'ameen💕) Hafsat Haris (maman Aliyu) Fatima Idris (maman Usman) Suwaiba Yusuf (maman Auwal) Salmah Hayat (maman Afnan) Latifah Nura (maman boy) Asma'u Abdullah (maman mhmmd) Saudat Yusuf Dutse Khadijah A Yusuf Zainab Sunusi Dutse Khadijah Adams Dutse. 😘Mrs A Ahmad ce =""==""==""==""==""= #YUSRAHMS# NO.25👉 26 Da dare Safah da baba maryam na zaune a daki suna hira sukaji sallamar mk cikin mamaki baba tace"musaddiq kaine shigo mana ince dai lafiya ko hajiya ce ke nema na". Shigowa mk yay wanda gaba daya hankalin nakan Safah wacce ke kwance kan katifa da wata rigar bacci a jikinta mai kyau kanta ba kwali kuma a tsefe yake tayi donut dashi baki sitik mai santsi sai sheki yake wani irin abu yaji yana tsirga masa wanda ba shakka yau da ace babu baba maryam a dakin nan bayajin akwai wani abu dazai sa ya dagawa Safah kafa dole saiya kasance da ita. Baba maryam ce data lura dashi tace"musaddiq nace dai lafiya ko"?da sauri ya dauke kansa daga kallonta ya dawo kan baba maryam duk da hankalinsa da nutsuwar shi na wajen Safan dama saboda ita yazo bazai iya bacci ba har idan bai sakata a idonsa ba kallon baba maryam yay yana cewa"amm babu komai dama nazo na sake duba tane yaya kafan nata"?. Cikin fara'a baba maryam tace"ayya musaddiq da sauki gaskiya ka kyauta wallh yaro mai hankali nagode sosai da kulawa"kai ya daga tare da. kallon Safah cikin daga mata gira yace"ya jikin naki"? Dakyar Safah tace"da sauki tana sakar masa harara, murmushi yayi yana mikewa yace"ga tsaraba nan a bawa mai jinya saida safe"godiya baba maryam ta masa tana cewa"kuma harda abin arziki mun Allah ya kara budi" amin yace yana fita. Duba kayan baba maryam ta leda biyu daya babba daya karama babbar ta fara budawa dogayen riguna ne guda biyu masu tsada daidai tsayin Safah da takalmi abinda ya bawa safah haushi harda breziya😂 a ranta tace"jifa dan iska me zanyi da kayan ka". Dayar ledar kayan baba maryama ta bude sai gashi ta fito da katuwar kaza mai kamshi ga kuma robar ice-cream guda biyu baba maryam tace"kwarai wallh Safah kiga dan albarka ya kawo miki abin arziki gobe kiwa hajiya godiya kuma shima ki masa gaskiya mutanen gidan nan nada karamci". "Tashi kici" hade rai Safah tay "ni bazan ci kayan sa ba kawai daga ya kawo abu saina kama ci bansan meye a ciki ba duniya daba tabbas" kallo.n ta baba maryam "haba Safah amma kinsan bazaisa maganin mutuwa a ciki ba ko"?cikin shagwaba Safah tace"Allah baba nidai........katse ta baba maryam tay "Allah keme?karki rantse bansan shirmen banza tashi kici inda yana nan ai bazai ji dadi ba sai yaga kamar kina zargin sane". Tura baki Safah tay"to dama mene inba abin zargin ba" salati baba maryam tay"ke naci gidan ku rufe min baki bansan soko" dariya Safah tay "kin cinye gidan mu kenan Baffa na nacan yana kwana a waje Allah sarki"bude robar ice-cream din baba maryam tay tana sa karamin cokali ciki ta mika mata karba Safah tayi badon taso ba ta soma tana cewa"saidai yaci darajar ki nasha kayan sa saboda ke" baba maryam dake kallonta ta girgiza "kai Allah ya shirya minke Safah" murmushi tay ba tare da tayi magana ba naci gaba da shan ice-cream din. Washe gari Safah bata shiga gurin hajiya ba saida yamma ta tarar tayi bakuwar wata budurwa yar gidan kanin ta tazo mata ziyara daga mubi saidai Safah ta lura yar jin kaice sai wani shakar iska take a gadarance tana tauna chewingum ta soke daurin kwali a gaban goshi kana ganin ta ba sauki. Shigowar mk kenan ta mike cikin murnar ganin sa zata rungume shi ya dakatar da ita da hannunsa yana kallon Safah yace"big girl ya jikin naki fatan kafan ya warware"?shiru safah tay tamkar bada ita yake ba yayin da Abidah tay sak tana binta da wani irin kallon mamaki tace"naji kace mata big girl ba house girl dinku bace meya hada ta da wannan sunan kuma yaya mk"?. Zama mk yay cikin halin ko'in kula yana cewa"gashi nan kinyi tambaya kuma kin baiwa kanki amsa house girl ce sai akaiya"? kalle ta dakyau itadin babbar yarinya ce mai aji ma kuwa ta wuce rainin kowacce kucaka" yana fadin haka ya mike yabar palon cikin takaici Abidah ta bishi da kallo harya bacewa ganin ta kafin ta dawo da dubanta kan Safara'u kamar zatai magana sai kuma taja tsaki itama tabar palon. Dariya Safara'u tay tana cewa"lallai yarinya kina ruwa kasan bado wallh bamai cetoki indai mk ne zaki bayani domin saidai naba wani labarin sa". Y»*« »*« »*« »*« Watan su Abdul-jabbar guda a garin malam na Allah kuma ya kama yau zasu tafi bayan sun gama shiri malam ya zaunar dasu nasiha mai ratsa jiki yayi musu addu'a mai kyau da fatan alkhairi bayan sun shafa fatiha sukaiwa Hadiza sallama suna fita a gidan kasa hakuri tayi da sauri ta dauko mayafin ta har jikin motocin da suka zo daukar su itama tayi musu rakiya da kukan ta shi kanshi malam na Allah daurewa yake saboda ita mace ce mai rauni shiyasa nata ya fito fili amma shima yana kukan zuci. Murmushin karfin hali yay yana kallon ta yace"in banda abinki Hadiza ai rabuwa ba mutuwa bace hakan ba yana nufin baza mu sake ganinsa ba a'a inda rai ana tare zai sake dawowa gare mu kiyi hakuri kinji"kai Hadiza ta daga tana goge hawayen fuskarta ta kalli Abdul-jabbar tana cewa"Allah ya kiyaye hanya ya tsake ku daga sharrin dukkan abin 'ki a duk inda kuka tsinci kanku". Murmushi Abdul-jabbar yay yana kallonta yace"amin mun gode da addu'ar ku Allah ya saka da alkhairi sai wata rana"juyawa yayi gurin na Allah yace"mun tafi Allah ya kaddara saduwar mu" amin na Allah yace yayin da Abdul-jabbar ya juya yana shiga mota suna kallonsu suka tafi ba halin dakatar dasu tun suna ganin motocin har suka bacewa ganinsu sannan suka juya zuwa gida jiki a sanyaye. Fitowar safah daga kitchen kenan taji ance" hey kitchner dan kawo min abin sha mai sanyi sosai ki taho da cup hurry up and back quick" da mamaki Safah ke kallon Abidah a ranta tace"humm yau gata biyun mk lallai na tsane ku" Abidah ganin ta tsaya tana kallonta yasa cikin wulakanci tace"ke house girl baki ji abinda nace ba kika tsayar wannan mayun idon naki a kaina ?". Cikin bacin rai Safah ta juya zuwa kitchen ta dauko mata kamar yadda ta ajiye mata zata juya ta dakatar da ita da fadin"oh nice zan zuba da kaina waike me kika dau kanki kada ki manta matsayin ki yar aiki sunan ki tunda kuwa kika amshi wannan sunan ni a gurina kina tare da kaskanci aidama shi kwadayi mabudin wahala ne tunda kika zabi irin wannan rayuwar kuma mk yaki bani muhimmanci saboda ke to mu zuba ni da ke aga wanda zaiyi nasara wallahi kafin nabar gidan nan saina saita miki hanya da kafafun ki zaki gudu daga gidan nan". Ko dagowa safah batai ba balle Abidah tace taji zafin abinda ta fada mata ko tadau maganar ta da wani muhimmanci kawai hauka ta manna mata tana zubawa ta mike zata bar wurin Abidah tace"kuturun uban can harni zanyi magana ki mayar ni mahaukaciya yau sai naga uban daya goya miki baya a gidan nan". Kallonta safah tay babu wani alamar bacin rai a tare da ita tace"gashi kin baiwa kanki amsa jakar aji ki sani cewa ni nafi karfin cacar baki da irin ki baki isa kice zaki juya niba kedin banza kinyi tsararo baki kaiba ina alfaharin kasancewa ta diya mace ba asararriya sokuwa irinki ba"tana fadin haka ta juya cikin murmushi zata bar gurin. Finciko ta Abidah tay cike da masifa tace ni kike fadawa magana haka yaushe kika samu wannan mukamin"? Har lokacin Safah murmushin ta na nan akan fuskarta tana duban Abidah data gama burkicewa tace"karya na fada wallh har kin bani dariya ji yadda kika rike ni kamar wacce nai miki sata sake ni dalla malama na tafi uzuri na" "Ni kike cewa dalla malama dan uwar ki yau kuwa saina kusan kashe ki a gidan nan saikin fada min wanda yake zuga ki a gidan nan"hannu ta daga zata mari Safah taji an rike hannun da sauri ta juya ganin mk tsaye yasa tace"ka sake min hannu wallh yau saina balla yarinyar nan saina nuna mata isa ta da matsayi na zata ga kala ta harni zata tsaya tana fada ina fada matsayin ta na house girl". Murmushi mk yayi yana kallon Abidah yace"abinda tay shine daidai hukuncin daya dace dake kenan kinga gaba koba anan ba idan kika hadu da yar aikin da kika raina ma wayo sai kiji shakkar ta maganar saikin ga wanda ya goya mata baya a gidan nan gani nine sai akai ya"?. Kallonsa abidah keyi yaya mk da gaske kaine a gabana kake fada min son ranka akan wata yar aiki bare wacce baku hada jini ba ko mafarki nake dan Allah ka farkar dani"?. Kai mk ya girgiza yana kallonta yace" no you are not ba mafarki kike ba zahiri ne kalleni dakyau dan ki samu tabbacin haka"Abidah bata iya kallon sa ba sai kuka data fashe dashi da gudu tabar palon tana shiga part din su salmah. Dawo da kallon shi kan Safah yay yana cewa"big girl ashe kin kware a iya magana har haka amma ni bakya kula ni me yasa"?shiru Safah ta masa ganin ya matso inda take yasa da sauri ta matsa baya kara binta yayi cikin hanzari ta fice daga palon, zama yay yana sauke ajiyar zuciya tare da kallon kofar data bi a ransa yace"humm yarinya ki gama zille zillen ki rana ta dazan cimma buri na ta kusa zuwa kwanaki sun kusa cika" murmushi yay yana hango irin farin cikin da zai tsinci kansa a wannan rana. Mrs Al'ameen Ahmad Aliyu ce. Tnx for loving me Be with me at always my lovers We will meet next page. TNX. TYPING📲 🍇 SAFREEYAH🍇 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫🌌 💕Yusrah m Abbakar💕 Ku kara hakuri dai reader's naga kowa ya damu kan rashin haduwar Safah da Abdul-jabbar please🙇 ku dan kara hakuri lokaci nanan zuwa inda jirgin sama ✈ yaje to kunkuru 🐢 ma za'a ce masa barka da zuwa😜 lokacin haduwar tasu ne bai karaso ba amma ya kusa am so sorry my fans lovers. #YUSRAHMS# NO.27👉 28 Ammy na zaune kamar a mafarki taga Amfal ya shigo gurin ta a zabure ta mike tsaye tana fadada murmushin ta ganin ba tare da Abdul-jabbar suke ba sai tayi tunanin ko Hanne taje gurin wani malamin wanda ya fara aiki da kuwa tayi farin ciki. Karasowa yay har inda take yana zama yace"barka da hutawa Ammy fatan kin wuni lafiya"? Baki ammi ta washe cikin nuna tsantsan jin dadi lallai wannan malamin ya iya aiki za'aje dashi . Kallon sa tay da farin cikin ta wanda yaki boyuwa tace"yauwa dan albarka Amfal ko kaifa yanzu baka ji irin dadin da naji ba da kazo gaishe ni amma da ko kallon arziki ban samu a gurin ka haba Amfal me yasa nice fa na haife ka baka da uwar data wuce ni duk duniya amma meyasa saika shafe kwana uku kana gidan nan ina nan baka leko ni kaga lafiya ta kullum kana gurin Abban ka ko gurin hajiya ni kuma kona mutu ko nayi rai babu ruwan ka dani". Saukowa daga kujerar da Amfal yake yayi yana durkusawa a gabanta yace"kiyi hakuri ammina bazan sake ba daga yanzu kullum zaki rika gani na nasan cewa banda uwa saike kuma ina neman afuwan ki"ya karasa maganar yana rike hannunta,. Wai Ammi ji take kamar anyi mata bushara da aljannah anya da gaske ne Amfal ne yau suke zance haka cikin walwala lallai aikin malam ya fara ci dole ta sake zage dantse tunda hankalin sa ya fara juyowa kanta bari ya fita ta kira hanne ta mata albishir sa'an nan ta bata kyauta mai tsoka kara kallonsa tay zatai magana taji yace. Ammy kisa a yanka min fruits mana saboda an kusa kiran sallah domin shan ruwa"jiki na mazari Ammy tace"to Amfal bari na gyara maka da kaina ban yarda baiwa ta taba abinda ka bukata a gurina ba nice zan hada maka mai tsafta". Mikewa tayi tana karasawa inda tulin kayan marmarin suke ta soma gyara masa tana yankawa a karamin bowl Amfal na kallonta "yauwa ammi kuma ki hada min da lemo mara gas amma mai sanyi yau dukkan abin shan ruwan na part dinki ne nasan zaifi dadi". Kai ammy ta jinjina dan ta tabbatar da gaske aikin ya fara ci a ranta tace bari na gwada mu gani indai Amfal ya fara janye jikin sa daga gurin Abdul-jabbar idan ta masa maganar sa bari taga a yadda zai amsa, cikin fara'a tace" amma dai Amfal kai kadai zan hadawa banda Abdul-jabbar saboda yayi kadan na bata lokaci na akan sa". 'Yar dariya Amfal yay yana kallon yadda ta cika bowl din da kayan marmarin wanda ya sani idan itace zata sha tana daga kishingide za'a rika yankawa ana bata a baki amma ji yadda ta gyara a dan kankanin lokaci ta gama had............ Katse masa tunani tay da cewa" ina magana kayi dariya kawai baka ban amsa ba"?. Mikewa yay yana zuwa inda take yace" Ammy bafa nine zansha ruwan ba bros dina ne yayi azumin litinin shi zan kaiwa bari na tafi kinga an kusa kiran sallah kuma baisan nazo nan ba kar yayi ta nema na ya rasa ni bazai ji dadi ba zai shiga damuwa ni kuma bana son hakan". Wata irin ashar Ammy ta sakar masa jin abinda yake cewa cikin kunar rai da bakin ciki ta mike idon ya yayi ja ranta a mugun bace muryar ta a tsawace tace" Amfal yaushe na zama mahaukaciyar ka harni zakaiwa wasa da hankali kasa na bata lokaci na nayi maka wannan wahalar sannan kace bakai zaka sha ba wani banza can wofi zaka kaiwa amma yau badon kai dana bane kuma ina sonka wallh da saika gwammaci mutuwa akan ukubar dazan sa a dandana maka". Daukar fruit din Amfal yayi yana kallonta yace"kiyi hakuri ammi hakan bazai sake faruwa ba yanzun ma kuskure ne kuma zan kiyaye gaba". Juyawa yayi zai tafi Ammi tace"Amfal kodai kana shan wani abu"?murmushi yayi ba tare daya juyo ba yace" babu abinda nake sha Ammi sai coffee ki huta lafiya"tun kafin tayi magana ya fice wani irin yanke jiki tay ta fadi a gurin🙊. Amfal na shiga part din hajiya ya ganta zaune akan kujera gefen ta Abdul-jabbar ne shima yadan jingina kadan da kujerar daman yasan yana nan saidai da alama ba zance suke ba. Hajiya na ganin sa tace "aifa shikenan tunda kazo yanzu saika addabi kowa da surutun ka murmushi Amfal yay yana zama kusa da Abdul-jabbar yace" hajiya tawa nikwa na Allah naga Annabi kiga doron baya na". Kallon sa hajiya tay" dan ubanka doron bayan naka ka boye karna gani bana bukata". Dariya yayi yana ajewa Abdul-jabbar fruits din daya shigo dashi yana cewa"barka da shan ruwa bros Allah yasa ladan nida kai zamu samu". Hajiya dake kallon dukkan su biyun cikin jin dadin yadda suke tafiyar da rayuwar su tace" me kuwa zai hana ku raba ladan saboda ka kawo masa yayan itatuwa sannu gwani mai ido a tsakar ka". Gyara zama yay yadda zai fuskance ta da kyau yace" tofa yau nake ganin sa ido anan hajiya kodai kina kishi ne nasan dai kushewar badi sai badi dan bake na kawowa ba dan uwana na sani shine zan baiwa komai nawa ba kishiyar saura ba kuma nasan idan nazo gurin ki kina jin dadi taimakon kifa nake na debe miki kewa kuma da kika ce ina damun mutane saidai kisa munjaye kice muna damun mutane ni da ke kome kika ce"?. Oh ni 'yar gidan Sama'ila yau na gamu da gamo na anya Amfala kai kadai ne kuwa baka da mutan boye"?. "Ji hajiya da wani zance da duk zaman da muke dake dama bakisan ina da aljanu ba alhali kullum tare kuke kwana a gurin ki suna gadin ki sai yau kika sani tab kice duk wannan zantukan da suke miki cikin dare bakya ji lallai kuwa anayi babu ke kodan laifin bros ne dabai fada miki ba tun wuri amma yunzu saiki shiri tunda kin sani yau kar kiyi bacci sunce wasan kura zasu zo suyi miki". Hajiya da tunda ya fara magana bakin ta yake bude har yakai aya a firgice tace" na shiga uku ni hauwa'u da gaske kake"?. Kai Amfal ya daga "da gaske nake hajiya please kinga yau kece da kanki zaki tarbe su saiki shirya musu kayan cinye cinye da shaye shaye harda abincin india suka ce suna so nidai babu ruwa na dan na fita na fada miki idan kikai musu kuskure suka shanye miki hannu da kafa shikenan kina gani ba yadda zaki kin zama gurguwa komai saidai a maki kina zaune gaskiya hajiya ina tausaya miki dan kawai sunga kin zama tsohuwa shine suke so su shanye miki jini a kaiki makabarta kita tsugune a cikin kabari sai ranar da kwanan ki ya kare sannan ki bingire kasa ki fadi". Hannu hajiya ta dora a kai tana ihu"wayyo Allah shikenan ta faru ta kare la'ilaha illallahu yau zanyi mugun gani da idona a gidan nan shikenan ni 'yar sama'ila da mairo naga ta kaina" ganin yadda duk ta susuce yasa Abdul-jabbar rike mata hannu yace" hajiya Amfal bada gaske yake ba tsokanar ki kawai yake dan yaga yadda zaki yi dan Allah ki nutsu". Dan dakatawa hajiya tayi tace" iye Abdullahi me kake cewa😁"? yadda tayi maganar saida tasa Abdul-jabbar yay murmushin dabai niyya ba yace" cewa nayi Amfal wasa yake miki tsokanar ki yayi don yaga yadda zakiyi bashi da wasu aljanu shima da zai gansu kila ya suma dan kin fishi jarumta". Kallon Amfal hajiya tayi ganin yadda yake kallonta yana dariya tace" au dama karya kake ja'iri har kasa na bata hawaye na wallh zonan saika ci ubanka" da gudu ya tashi ganin ta dauko sanda yay hanyar fita yana cewa" wato hajiya yau bros ya hada mu fada harda dauko sanda to yi hakuri wasa nake miki haba masoyiyar kinsan fa nida ke bata baci". Binsa hajiya tay inji ubanwa bata baci bayan gashi kana neman dora min hawan jini Allah inna kama ka Amfala saika ci jakin uban ka"lekowa yay yana mata gwalo yace" ni Abbana baida jaki sai doki in marmarin ci kike zansa a yanka miki " . Hararar sa hajiya tay tana cewa "saboda ga mayya ko? Zan rike kane zakai bayani". Matsowa kusa da ita yay yace"zanyi bayani kam tunda yanzu har kuka ma nayi saboda ina tsoron mutuw,........rufe masa baki Abdul-jabbar yay yana cewa"saida safe hajiya ki hakuri da halin Amfal "batai magana ba yaja hannunsa suka fita daga part dinta sosai Amfal ke dariya daga baya kuma yayi shiru yana cewa"bros muje gurin Abba man ya sa mana albarka". Kallon you are not so kind Abdul-jabbar ya masa yana cewa" eh mezai hana muje gurinsa bayan ka gama burkita masa uwa saiya baka albarka malam babu inda zaka wuce muje "part dinsu suka wuce Amfal na kwaikwayon muryar hajiya inda tace"na shiga uku ni Hauwa'u da gaske kake". Misalin karfe goma na dare Safah ta fito daga bangaren su hajiya Binta zata tafi nasu tana cikin tafiya tazo saitin wasu fulawoyi masu yawa taji kamar motsin tafiya a bayanta dakatawa tay tare da cewa "waye anan? Jin shiru yasa cikin tsoro ta soma waige waige amma bata ga komai ba ta juya zata ci gaba da kenan taji an shaka mata abu a hanci wanda cikin sakan ta zube a gurin. Murmushi mk dake tsaye a kanta yayi cikin jin dadin ganin yau tarkonsa ya kama kurciya dukawa saitin fuskarta yay yana cewa" humm big girl yarinya mai wayo me kike tunani a kaina dama kawai na zuba miki ido ne ki gama zille zillen ki akwai ranar kama ki kuma gata tazo baza ki iya kwatar kanki ba a hannu na babu wanda ya isa ya cece ki yanzu lokaci na ne". Tofa me yake shirin faruwa ne reader's? Shin me mk yake nufi akan Safah? Zai cika burinsa kuwa,? Domin samun amsoshin wadannan tambayoyi mu hade a next page amma ba gobe sai jibi sai naga comment naku tukuna koda ma zanci gaba nagode da yabo taku har kullum YUSRAH MUSA ABUBAKAR GIMBA )()(Mrs Al'ameen Ahmad ce)()( till we meet"). ONE LOVE 👉👉 ☝ 💝 WRITTEN BY MRS AL'AMEEN AHMAD CE 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 (😘home of hospitality and harmony) 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 SAFREEYYAH 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Ayi hakuri idan an samu typing error🚨 matsalan ba daga ni bane daga keyboard ne😜. @Yusrahmusa ta kowa ce ASSALAM FANS MASOYA😜 AYYA KUYI HAKURI NAGA YAWAN KORAFE KORAFEN KU DA KUKE TURO MIN AKAN MK CEWA DON ALLAH KAR NACE FAYDE ZAIWA SAFAH INA BA HAKA ABIN YAKE BA IDAN HAKA TA FARU KUMA MENE RIBAR LITTAFIN TAYA MA HAKAN ZAI FARU BAYAN INA GURIN😜🙃 KU KWANTAR DA HANKALIN KU TAMKAR KUN HAU JIRGIN SAMA MAI YA KARE. "KORAFIN KU AKAN IRIN RASHIN JIN DADIN DA SAFAH KEYI TO AI DAMA HAKA ABIN YAKE A RAYUWA DOLE BAZA KA TABBATA KANA CIKIN FARIN CIKI BA DOLE WATA RANA KA SHIGA KUNCIN RAYUWA AMMA KU KARA HAKURI )(IT IS SAID THAT SUCCESS COMES AFTER TEARS😢)(KO A RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM IDAN KUKA DUBA ZAKU GA HAKA TAKE KUJI KU 'KI JI KU GANI KU 'KI GANI ZAMAN SAFAH A GIDAN SU MK NA DAN KARAMIN LOKACI NE KUNSAN ANCE {YOU MUST SUFFER😭 BEFORE YOU SUCCEED🙆😃}. "TO NASARA TANA GABA FARIN CIKIN SAFAH NA GABA KUDAI KU KASANCE DA BINTU MUSA ABUBAKAR KU KASHE KUNNEN👂 KU DOMIN JIN YADDA LABARIN ZAI KASANCE SAIKU BUDE IDANUWAN👀 KU DA KYAU KUSHA KARATU📖. Musamman Zarah dan Adam kinfi kowa to am sorry nima bada sona bane labarin ne yazo a haka nasan kin damu kuma kina nuna kaunar ki ga Littafin nan nagode da yabawa Allah ya barmu tare yar uwa, God bless you Ameeen. Na gode sosai masoya masu comment Allah ya saka da alkhairi gaskiya kuna matukar burge ni kuma ina jin dadin hakan da kuke min sharshin ku ga wannan littafin yana sake zaburar dani wajen ganin na nutsu na kawo muku duk wani abu da nasan inna rubata zai saku nishadi fata naa ku Amfana da kyawawan abubuwan da kukai karo dasu masu kyau ku zubar da wanda baiyi ba kamar dai halayyar mk da dabi'un ammy dana Asabe Allah ya bamu dacewa amin. #$hare #✅ote #¢omment And like 💝 ♈USRAH ♏USA 🅰BUBAKAR (Mrs Al'ameen ahmad ce) SAYYIDUL ISTIGFARI📿👇. 👏Allahuma anta rabbi la'ilaha illah anta kala'kata ni wa ana abduka wa ana ala ahdika wa wa'adika mastada'atu a'uzubika min sharril ma sana'atu abu'u laka bi ni'imatika alayyah wa abu'u bi zambi fagfilli fa innahu la yagfiriz zunubi illah anta🙏. {Ya Allah lallai kaine ubangiji na babu abin bautawa daa gaskiya saikai, ka halicce nI kuma nine/nice bawan ka kuma lallai ina kan alkawarin ka gwargwadon ikona ina ikrarin ni'imar ka aa kaina kuma ina ina ikrarin zunubi na ka gafarta mini domin ba mai gafartawa sai kai"}. "Ya hayyu ya kayyum bi rahmatika astagisu aslihli sha'ani kulluhu wala takilni ilah nafsi darfata aynun👏. #YUSRAHMS# NO.29👉 30 Fitowar Asabe kenan a daki ganin Baffa zaune ya zubawa guri daya ido yasa ta karaso tana cewa" a'a ni Indo malam irin wannan tagumi haka kodai kana tunanin inda 'yarka take ashe dama kanka zai gwaro da bango kaga dai yanzu ka gane gaskiya maryama ba mutuniyar arziki bace ta rude ka ta yaudare ka da dubu biyar ta gudu ma da 'ya tana can tana kasuwanci da ita nasan yanzu idan kididdigewa za'ai ta samu kudi da Safara'u yakai miliyan biyar kai kana nan kana hankara baki yarka tana binni". Ganin bai kula taba taci gaba" wai malam baka jina ne ko kuma suman zaune kai"? gara ka daina wahalar da kanka dan Safara'u dai yanzu ta maka nisa ba lallai ku hadu kwana kusa ba kuma ba fata nayi maka ba amma sai kayi kuka da idanunka kafin kaga safara'u idan ma zaka sake ganin ta kenan dan bana tunanin idan ta dawo zata kalle ka matsayin mahaifin ta tunda taje ta ga bariki idonta yaga manyan alhazai masu kudi da mukamai ta waye tasan takan duniya sai hakuri fa malam yanzu kaida yarka saidai kallo daga nesa" ta karasa maganar kamar zata sheke da dariya dan murna. Tunda ta fara magana Baffa ko motsawa baiyi ba saida ta gama ya dago yana kallonta cikin takaicin irin furucin data fada yanzun yace" aike Asabe na dade da sanin idan har ana maganar masu hankali bake a ciki idan banda shashanci ni kike iya tsayawa akai kina fadar dukkan abinda yazo bakin ki wanda ko mahaukacin da yake turu bazai aikata haka ba nagode basai kin nuna min a zahiri ba dama na dade da sanin ba kaunar Safara'u kike ba kuma in Allah yaso wata rana saikin ci arzikin ta nisa kuma da kika ambata zatai min wannan mummunar maganar taki ta koma kanki ke zataiwa nisa saboda babu wani hadin dangantaka tsakanin ku auren mahaifin ta kawai kike kuma yadda baki karbeta matsayin 'ya ba itama batayi miki kallon uwa ki rubuta ki aje nina fada miki safara'u mai kashin arziki ce kuma ina ji a jikina zata taka wani babban mataki wanda ke Asabe harki mutu a cikin zuriyar ku baza a samu kamar ta ba". Asabe datai tsuru tsuru tana kallon Baffa tace" abin kuma harda gori daga na fadi gaskiya sai cibi ya zama 'kari Allah ya bada hakuri masu 'ya mai 'kashin arziki taya kake tunanin wata rana zata daukaka tana yar talaka saidai idan asiri zakai idan ta dawo tace ta gano wani mai kudin sai kayi addu'ar kiranye ya biyo ta ya aura shikenan burinka ya cika kai kuma ka samu inuwar fakewa kayan abinci sutura da ragon sallarka duk shekara a sama aina gane nufin maganar ka kila wata rana ma kace zaka koma can gidan nata da zama idan kaga daula tayi yawa hummm gaskiya malam ka rage son zuciya duk wanda yahau motar kwadayi dai zai sauka tashar wulakanci kaima haka kake so kodan nasan kafin ya sakota ta taro maka dan wani abun sai a zo ayita fama ubah kwadayi 'ya son zuciya dangi ya lalace". Babu shakka maganar asabe tana mugun kona ran Baffa ji yake kamar yace ya saketa sanin zuciya bata da 'kashi kuma tabbas idan taci gaba da tsaiwa yana ganinta zai iya furta mata sakin sai kawai yace" Asabe bar gurin nan bacewa ganin na kafin na miki abinda zaki dana sani mutuniyar banza kin girma amma hankali har yanzu bai isheki ba". Jin abinda yake cewa Asabe tasan saki yake nufi da sauri tabar gurin tana yin inda murhu yake tace" yi hakuri malam bani nakar zomon ba rataya aka bani kuma ban karba ba laifin maryama ne data gudu maka da 'ya karka nemi hucewa a kaina da girma na ka tura ni gidan mu". Ganin bai kula taba ya mike zai fita tace" kadan turo min malu zai sayo min shinkafa a shagon murtala sirikin ka". Ba tare daya juyo ba ko ya daina tafiya ya bata amsa "babu wanda zan turo almajirai na ba yawace yawacen banza iyayensu suka turo su ba ki nemi wanda zaki rika aika daga yau da karatun su zasu ji koda aiken sana'ar ki"yana kaiwa ya wuce binsa Asabe tay da kallo tana dariyar jin dadi tace"oho dai ta haushi ta biyo Allah yasa daga can Adamawan su filla su kara gaba karsu dawo ko 'yan yankan kai su sace su ". =="="=="="== Yau su Abdul-jabbar zasu bar Nigeria zasu tafi UK bayan sun gama shiri part din hajiya suka shiga tana ganin su tace" tofa soja marmari daga nesa soja mazajen fama kune tuwon 'kaya miyar allura harkun shirya kenan? to Allah ya kiyaye ya kare mana ku" Amfal ta kalla "kai kuma wannan katon takalmi da kasa kamar bulo ai zafi ma ya isheka kafin kuje zai takura maka daka cire kasa wani". A'a barni dashi hajiya da kinsan irin dadin da yake dashi da yanzu kince a sayo miki kema kina sawa lokacin sanyi". "O'o ni bana bukata kaidin dai daya zame maka wajibi sai kaita fama" Abdul'jabbar ta kalla daya zuba mata ido tana cewa" miskili na yau ko yar maganar bazan samu ayimin ba kenan "?. Murmushi yayi amma baiyi magana ba ya mayar da kallonsa gurin Amfal yana masa alama su tafi juyawa sukai yayin da hajiya ta bisu da kallo tana musu kyakkyawar addu'a har suka fita. Basu jima a gurin Abban su ba suka fito rakiya ya musu har inda motar da zata kaisu airport take yana musu fatan alkhari zasu shiga mota Amfal ya tsaya yana matsawa kusa Emir cikin rada ya masa magana wanda ba shiri Emir ya kalle shi". A marairaice ganin irin kallon da Emir yake masa yace" dan Allah Abba ko bayan tafiyar mu kayi tunani akan abinda na fada maka karka kalli Ammy hakan da zakayi shine daidai". Kai Emir ya jinjina cikin murmushi yace" to na amince amma sai nayi tunani Allah ya kiyaye hanya" ran Amfal fari tar ya shiga mota suka hari airport ganin yadda yake farin ciki yasa Abdul-jabbar yace" waikai lafiyan ka kalau kuwa me kake fadawa Abba"? Dariya Amfal yay yana cewa "sorry bros idan na fada maka zaka bata min shiri kawai idan lokaci yayi zaka gane komai so nake wata ta fahimci rayuwa". Shikenan Allah yasa naga alkhairi dan nasan baka da sauki a iya abinda kaiwa hajiya" matsowa kusa dashi Amfal yay yana cewa" Allah alkhairin na fada masa kasan bazan yiwa Abba wasa ba" kai Abdul-jabbar ya daga baiyi magana ba har suka karasa airport din. Farkawar Safah kenan ta tsinci kanta kwance kan wani tafkeken gado da akaiwa ado da wasu irin jajaye da fararen flowers masu kyau a wani tsararran bedroom daya sha kwalliya ta ko'ina abubuwan 'kayatarwa ne kallonta takai jikin bangon dakin inda rubutu yake ta walwali ansa" I LOVE YOU SAFAH" PLEASE YOU LOVE ME, DON'T RUN AWAY FROM ME, DON'T LEAVE ME ALONE, I DON'T WANT MARRY SOMEONE BUT YOU,I DON'T WANT LOSING OF YOU, YOU'RE MY HEART MY DREAM YOU ARE SO SPECIAL THAT I LOVE, LIFE WITHOUT YOU LIKE A LIVE IN THE PRISON BE IN MY PART AND REMOVE MY TEARS". Abinda ta gani kenan yana haskawa da kaloli daban daban wanda yasa hankalinta yayi mugun tashi don ko shakka batai babu wanda zai iya yi mata haka sai mk to me yake nufi ita zata soshi kuma ta aure shi? Dora hannu tayi aka tace" na shiga uku ubangiji kaine gata na ka fidda ni daga tarkon mutumin nan ka zame min kariya daga sharrin sa". Mikewa tay tare da saukowa daga gadon tayi hanyar fita ta kuwa taki sa'a kofar ba'a rufe take ba da sauri amma cikin sanda ta soma tafiya tana waige-waige har tazo palor sauke ajiyar zuciya tay duk da bata san iya girman gidan su mk ba amma tasan nan ba gidan bane wani wurin ne dabam ya kawo ta meyasa zai mata haka? Wata zuciyar tace mata"Safah karki tsaya bata lokacin ki anan har yazo ya sameki ki tuna had'arin da kike ciki yanzu da inda kike kiyi kokarin ceton kanki ki kubuta shine mafita. Duba ko'ina tay koda mai kallon ta ganin babu kowa yasa a hanzarce da dukkan karfinta tay kofar fita a palon amma kofar tana rufe jijjigawa tay ko zata samu ta bude saidai tana nan kyam tsaye tayi a gurin cikin rudani da tunanin yadda zatay ta fita daga wannan kaddara data same ta kawai taji kara alamar an zura key za'a bude kofan da sauri taja baya cikin tashin hankali gaban ta na dukan dari💯 dari💯 . Shigowa mk yayi ganin Safah tsaye yasa ya sakar mata murmushi yana zama akan kujera tare da dora kafa daya kan daya yana mata wani irin kallon dake sake burkita mata lissafi yace" welcome to our home my pretty zauna mana bari na kawo miki abin sha tunda yau ke bakuwa tace ya kamata na karramaki". MRS AL'AMEEN AHMAD CE. WE WILL MEET AGAIN. TO READER'S NIMA BARI NA KARRAMA😜 KU NA TSAYA ANAN SAI IDAN ALLAH YA KAIMU ZUWA GOBE MU DORA INDA MUKA TSAYA TNX🤗 FOR UR SUPPORTS. Typing©¥$® SAFREEYYAH 💫AnNuRi WrItEr's AsSoCiAtIoN💫 (HoMe Of HoSpItAlItY AnD HaRmOnY) #YusrahMusa65@gmail.com "Wannan page din na bros dina ne Usman Ibrahim Usman da kuma Sulaiman Ibrahim Usman fatan Allah ya kara hada kan zumuncin mu🙏". YuSrAh MuSa AbUbAkAr mai tambarin YMA Dutse new world new life and new style. #YUSRAHMS# NO.31👉 32 Mikewa yayi yana shiga wata kofa ya dade sosai kafin ya fito rike da wasu kalar bottles Safah bata taba ganin irin su ba zama yay yana zubawa a cup sannan ya dago yace" big girl come and sit down mana kamar wata ba wayayyiya ba karki bani kunya kinga madam nutsu naga kinyi wani iri ba wani abu zanyi miki ba taimakon kai da kai ne ina so ki amince min ki bani kanki Safah ni kuma nayi miki alkawari zan baki duk abinda kike so kuma babu wanda zaisan hakan ta faru tsakanin mu amma me kika ce ". Wani kallon baka da hankali tayi masa cikin takaicin maganganun da suke fitowa daga bakin sa tace" Allah ya sauwake wallh Allah ya rufa asiri nice zan baka kaina nayi maka kala da irin banzayen karuwan da kake debowa kana abinda kaga dama dasu ka basu wani banzan kudin ka mara amfani toni ban kasance 'yar iska irin kaba ka rabu dani nayi rayuwa ta na tsane ka na tsani ganin ka domin baka cancanti a soka ba baza kuma ka samu abinda kake nema a guri na ba har abada nafi karfin wulakancin ka kadai nemi mai hali irin naka amma badai ni Safah ba". Zaro ido mk yayi yana kallon ta da mamakin yadda ta iya kallon kwayar idonsa babu tsoro ta fada masa son ranta, kara bude idonsa yayi sosai a kanta yace" ni kika cewa dan iska kike fadawa wadannan maganganun saboda na fada miki bukatar da nake so a gurin ki"?. Kanta tsaye tace" na fada mk kuma ka mayar dani inda ka dauko ni"?. "Idan kuma na 'kifa akwai abinda kika isa yi ne ko wani matakin da zaki dauka"?. Batare da wani jin d'ar ba tace" ba iya daya ba akwai matakai da yawa dazan taka kuma na tona maka asiri a gurin mahaifan ka daka zalunta kayi watsi da tarbiyyar da suka baka ka bata musu suna daga yanzu idan na sanar dasu dole ka datse alakar ka da kowacce ballagaza mara daraja kayi aure sai naga karshen iskanci". Dariya ya sheke da ita yana nuna Safah da yatsa alamar maganganun ta nishadi kawai suka sashi ya dade yana dariyar har Safah tayi tunanin ko ya zare ne sai da yayi mai isarsa daga baya ya tsagaita yana mikewa daga inda yake ya fara takawa yana nufar ta fuskarsa a hade sosai kamar ba yanzu ya gama dariya ba. Cikin tsoron abinda zai faru ganin yadda ya nufo ta yasa ta soma ja da baya idonta fal da hawaye bai daina binta ba saida ta kure bango kuka ta saki a daidai ya karaso inda take takurewa tayi tare da kankame jikinta guri daya bata bukatar mk ya taba ta. Idanuwan ta suna rufe amma tasan yaa karaso gaba daya ta saddakar yau bazata taba tsira a gurin sa ba ji tayi yace"big girl" kuma muryarsa is slowly a nutse kamar bashi ba. Hakan ne ya bata damar iya bude idonta da sukai ja tana kallon sa kneeldown yayi a gaban ta zai rike mata hannu ta goce bai sake kokarin rike ta ba ya soma magana "big girl ina sonki bada wasa ko yaudara ba da gaske nake na janye kudiri na a kanki yanzu son aure nake miki please try to understand karki watsi dani wallh har cikin zuciyata kece mace ta farko da naji zan iya rayuwar aure da ita ki amince min Safah ina sonki". Kai safah ta girgiza muryarta na rawa tace" kayi hakuri mk bazan iya auren kaba nima inaso ka fahimce ni bazan iya zama inuwa daya dakai ba". Cikin damuwa mk yace" but why"? "Saboda bana sonka dan Allah ka rabu dani". Sosai yaa zuba mata ido babu kyaftawa yana maimaita "saboda bana sonka ka rabu dani" mikewa tsaye yayi yana tafiya da baya da baya har ya koma kan kujerar daya tashi zama yay yana cira kwalba guda daya tare da runtse idonsa ya soma sha Safah na kallon shi wani irin jiifa yay da kwalbar yana huci ta daki bango ta ragargaje bude idonsa da sukai wani irin jawur kamar jini yayi numfashin yana fita da sauri ya kalli Safah da jikinta ke rawa yace" I love you" ya fada yana bude hannuwan sa alamar ta zo gareshi. Kuka Safah keyi don gabadaya mka ya gama tsorata daa lamarinsa ganin taki zuwa sai kuka da take kawai yadau waya tare dayin kira Safah batasan dawa yake waya ba kawai taji yace"Seeker kizo gidana yanzu ina jiranki"daga haka bai sake cewa komai ya aje wayar yana zamewa ya kwanta akan kujerar. Da kamar awa daya wata lady ta shigo da wata shara-sharar riga a jikinta da skirt iya gwiwa kanta babu ko kwalli tasha kitson attact kanana masu mugun tsayi har wajen cinyoyinta suka zo baisan ta shigo ba saboda kofar palon dama a bude take bata lura da safah dake tsaye can gefe ba gurinsa ta karasa ganin idonsa a rufe yasa ta duka tare da kissing din bakinsa wanda jin hakan da yay ya tabbatar masa cewa ta karaso bude idonsa yayi yana tashi zaune ya rungume ta"' Muryar ta a shagwabe tace" nayi kewarka sosai me yasa ka daina kirana idan na kiraka kaki dagawa ko naji kayi reject na shiga damuwa sosai yanzun ma ban tabbatar da gaske kaine ba saida nazo na ganka". Sakin ta yayi yana cewa "kwana zaki tayani fa ba surutu ba" Jin haka yasa Seeker ta fahimci abinda yake nufi mikewa tsaye tayi tana cire kayan jikinta wanda dama already shi 3quater ne kadai a jikinsa kansa tahau takwanta tana kuma dora bakinta a nasa shima zagaye hannuwansa yay a bayan ta. Safah dake tsaye ganin abinda suke yasa wasu irin zafafan hawaye suka soma zuba daga idon ta cikin sauri ta juya musu baya ga wata irin tsana da kiyayyar mk da suka sake mamaye ta lokaci guda". Tana jin yadda suke sambatu wanda hakan ya tabbatar mata da suna making sex ne yayin da hawaye ya cigaba da ambaliya a fuskarta wannan wacce irin bagidajiyar bahaguwar rayuwa mk ya zabarwa kansa . Tayi mugun gajiya da tsaiwar amma tunanin haram da zata juyo ta ganewa idonta yasa kawai ta daure taci gaba da tsaiwa har taji palon yay shiru zatonta ma sun bar palon ne amma me tana juyowa ta gansu kwance akan kujera. Murmushi mk ya mata yana cewa "big girl kinga wayayyiya ba irinki mai dod'ad'd'iyar kwakwalwa ba kin fahimta kema taho duk da nasan ke virgin ce amma babu matsala zan biki a sannu daga nan zuwa wayewar gari zan iya da dukkan ku biyun" kukan takaici ta fashe dashi tana dauke kanta daga saitinsu ganin kofar palon a bude yasa da gudu ta fice dukda dare yaja amma haka take tafiya a layi babu kowa gashi batama san hanyar da zata bi taje gida ba,. Haske ta gani yana tahowa ta bayan ta cikin tsoro ta waiga daidai isowar motar gabanta sauke glass din mk yay yana kallonta yace shigo man na mayar dake inda na dauko ki kamar yadda kika bukata ko idan na barki zaki iya komawa gidan da kanki"? Sanin bata da wata mafita sai hakan yasa dole ta shiga suka tafi saboda kada mai gadi ya gansu saiya tsayar da motar a nesa da gidan suka karaso a kafa ta wata kofar sirri suka shiga saida ya rakata har kofar bangaren su ba tare da yayi mata magana ba ya juya da harara ta rakashi tana bude kofa ta shiga dama tasan baba Maryam bata nan taje yola a matukar gajiye ta kwanta duk jikinta na mata ciwo gashi ta gagara yin bacci sai juyi take tana tunanin abinda mk yayi gani take kamar a mafarki akayi komai har sallar asuba bata iya runtsawa ba. Bayan tayi sallah gari yayi haske ganin da nepa yasa ta jona ruwan zafi a heater tayi wanka saida ta shirya sannan ta tafi part din hajiya ganin babu kowa a palor alamar basu fito ba yasa ta wuce kitchen Salmah ta gani da Alawiyyah a kitchen din suna hada kayan breakfast da mamaki tace sannunku harkun fara baku jirani nazo ba". Dukkan su juyowa sukai suna kallonta a tare cikin zaro ido suka ce" Safah kece yaushe kika dawo ina kika je munata nemanki kinsa hankalinmu ya tashi"? Safah dake kallonsu a ranta tace"taya suka san bana gida bayan tun a daren na dawo". Ganin batay magana ba yasa Alawiyyah fita da sauri ba'a jima ba sai gata ta dawo tana cewa" Safah mum na nemanki tana tace kije yanzu tunda mu kin 'ki bamu amsa" fita Safah tay jiki a sanyaye cikin fargabar abinda Hajiya Bintan zata tambayeta. Mrs A A Aliyu ce. TyPiNg📲 (*()*) Sunday 08:55pm 2023. 🍇SaFrEeYaH🍇 💫Annuri Writer's Association💫 )()(Home of hospitality and harmomy)()( YUSRAH MUSA ABUBAKAR. WHATSAPP NO: 09055273614 Dedicated to My mum I luv u with all my life may Allah accept your du'as mamana. 😘HAJARA TA AMINUN TA😝 'YAR B/KD KEMA FITO GA NAKI PAGE DIN YAZO READER'S KUCE YA BAYYANA INA MIKO GAISUWA TA DA FATAN ALKHAIRI GARE KI 'YAR UWA GUDAN JIKI ALLAH YABAR ZUMUNCIN MU🙏 KI GAIDA MIN BABATA ADAMA IDAN KUNYI WAYA KICE MATA 'YARTA YUSRAH NA GAISHE TA. Fatan Allah ya barmu tare ya hada kanmu da zumuncin mu ya Amintar da mu da rahmarsa🙏 ya giyasal mustagisina agisini,ya hayyu yaa 'kayyumu (👏 Allahumma salli wssallim ala sayyiduna Muhammadun sayyidil akramina sayyidil mubashshirina). 👉 Usman Ibrahim Usman 👉 Sulaiman Ibrahim Usman 👉 Abubakar Ibrahim Usman 👉 Khaleed Ibrahim Usman 👉 Husnah Ibrahim Usman 👉 Yusrah Musa Abubakar 👉 Salim Musa Abubakar 👉 Naja'at Musa Abubakar 👉 Fatima Musa Abubakar 👉 Aishat Musa Abubakar 👉 Abubakar Musa Abubakar 👉 Abdallah Musa Abubakar. #YUSRAHMS# NO.33👉 34 Hajiya na zaune Safah taje tare da gaisar da ita amsawa tay tana kallon Safan da mamaki kafin ta fara magana" Safara'u ina kika je ne tun ranar da maryam ta tafi yola yau tsawon kwana uku babu alamarki a gidan ko kuna da yan uwa ne a garin nan ban sani ba,? Amma da zaki tafi ya kamata ki fada min bakiga irin tashin hankalin dana shiga ba har na bayar da kudi ayi cikiyan ki ko bata kikai". Safah dake zaune tana sauraron hajiya aranta tace yau rabona da gidan nan kwana uku amma mk ya cuce ni duk zatona a jiya akai komai ashe har kwanaki na diba a gidan sa bana cikin hayyacina Allah ne ya soni baiyi min fayden ina halin suma ba tunda mummunan kudirin sa kenan a kaina hajiya baki dacen d'a ba dan da kinsan irin abinda yake aikatawa da kin shiga damuwa da bakin ciki kan halayyar mk. Ji tayi tace"Safah kinyi shiru meke damun kine wai koda wata matsala ne ki fada min"?. Da sauri Safah ta dawo daga zance zucin da take muryarta nadan rawa tace" dama ranar bayan nabar nan na koma part din da muke to danaga dare baiyi ba shine nasa hijab na fita inda na raka Alawiyyah tayo sayayya agarin dawowa da yake dare ne hanya ta bace min shine wata mata da taga inata kaiwa da komowa a layi tace min wa nake nema sai nace mata niba yar gari bace aiki ya kawo ni kuma yanzu na fito sayayya amma na kasa gane gidan shine tace idan har na yarda na bita da safe sai na nemi gidan da gari ya waye ta hana ni tahowa tace nadan kara hutawa sai jiya nayi mata sallama na taho da tambaya har nazo gidan itama matar gidan haya ne inda suke kuma jiya suka sauya anguwa ni kuma na taho wannan shine abinda ya faru hajiya kiyi hakuri na daga miki hankali". Kallonta hajiya tay" kin tabbata haka ne gaskiyar abinda ya faru "?. Kai Safah ta daga"eh hajiya haka ne kiyi hakuri nasan ban kyauta ba amma hakan bazai sake faruwa ba". "Shikenan Safah karki damu ai kuskure kowa nayi tunda dai lafiyar ki kalau ba wani abune ya sameki ba ni shine damuwa ta ba komai ki kwantar da hankalin ki kinji". Kai Safah ta daga cikin sauke ajiyar zuciya ganin shirin datai hajiyan ta yarda dashi ba tare da yi mata kwakkwarar bunkice ba, suna haka mk ya shigo ganin su yasa zuciyar sa tayi zargin magana sukeyi ji yay hankalinsa ya soma tashi karfa ace Safah hajiya ta matsa mata ta fadi gaskiyar cewa shine ya dauke ta daya shiga uku dan bamai raba shi da hajiyan kuma yasan da cast din sai yaje har gaban dad din su. Ganin irin kallon da hajiya take masa ya sake jin ya zargu kuma ga kunya data ishe shi kullum yana tunanin ranar da iyayen sa zasu gane yana harkar mata baisan yadda zaiyi ba kuma hakan yabi jininsa bazai iya dainawa ba bayajin ko aure yay zai iya rabuwa da yan matan sa. Tunani hajiya ta katse masa da fadin" mk ya kuma ka tsaya anan shigo man kaga fa Safan ta dawo ashe ba bata tayi ba tana gidan wata mata saika daina shan wahala gashi cikin kwana uku harka danyi rama". Safah ta kalla tana cewa" tun da kika bata bai huta ba shine yayi nan yayi can neman ki ya kasa sukuni duk ya damu". Cikin mamaki Safah da ta zubawa mk ido jin abinda hajiyan ta fada a ranta tace" ji munafiki mai siffa biyu wato ka sace ni sannan ka zagayo ka nuna bakasan komai ba harda tada hankalin ka waina bata bayan kaine sila wata rana saina tona asirin ka zakai bayani wannan abunda Kaimin bashi kaci kuma saika biya". Shima a nasa bangaren mamaki yake kenan bata fadawa hajiya cewa shine ya dauke taba a ranshi yace" good yarinya mai wayo kin hadu fa" kamar taji abinda yake cewa da sauri ta dago wanda akai sa'a daidai shima ya dago wata irin harara ta sakar masa mai nuni da cewa na tsane ka, zaro ido yayi cikin mamaki dan ya gane nufin hararar da ta masa amma saiya maze kamar baisan tanai ba da murmushin dake mata nuni da cewa ba hakura dake nayi ba saina cimma buri na a kanki yake kallonta muryarsa fes. Yace" dama wata karamar sayayyarki wacce bata fi 5k ba kika tafi ga kauyenci ya hana ki dawo gida da kanki kinga gaba ma saiki sake fita idan rabon 'yan yankan kaine suyi faten ki madam take care nan ba irin kauyen ku bane mai gidajen da basu fi ashirin da anguwa biyu ba nan gaba idan kika sake fita kika bata ba mai wahalar da kansa wajen nemo ki saiki kiyaye". Murmushi hajiya tay" haba mk baka girma mene abin tsorata ta da wasu 'yan yankan Kai kuma kinga Safah rabu dashi wasa yake miki bari na gano Salmah idan sun gama abinda na saka su ko shiririta kawai suke" hanyar kitchen din ta nufa ta barsu su biyu a palon. mk daya tattare dukkan hankalinsa gun Safah yace "me yasa kika boyewa mum nine na dauke ki saboda kinsan bazata yarda ba? ganin tayi masa shiru yaci gaba "lady kin taki sa'a tunda har kika gane hakan gaba idan kika shigo hannu na bazan daga miki kafa ba kika nemi tona min asiri ki asarar numfashin ki bazan kalli son da nake miki ba". Wani irin kallo🙄😠 tay masa tana cewa" duk abinda mutum zaiyi dai a rayuwa ya shuka alkhairi kodan goben sa kuma ya fadi gaskiya domin ranar mutuwar sa ni babu abinda Zance kayi komai lokacin kane da rayuwa da mutuwa duk suna tafiya ne waje daya sannan duniya tana da fadi kuma kowa linkaya yake baka da tabbacin ganin gobe maganar da kayi ban wani dauke ta da muhimmanci ba nafi tunanin baka cikin hayyacin ka yanzu don haka na maka uziri kaidin abin tausayin ne a wajena ina matukar tausaya maka domin dukiya da duniya sun rude ka baka tunanin mutuwa wata rana koda kudi kaso ganina bazaka ganni ba dan tayi ma wuya niba sa'ar yin bad'alar ka bace". Kai ya jinjina tare da mikewa ya karaso inda take saitin fuskarta ya duka yana cewa" taya kike tunanin zan barki kimin nisa kamar yadda kika ce da rayuwa da mutuwa Suna tafiya guri daya to ni dake ma haka ne bazan taba barin kiba duk inda kike muna tare zan kasance tamkar inuwar ki ke tawace kisa a ranki ke zan aura muyi rayuwa ki haifa min yarana kece uwar 'ya'yana Safah I love you ki gane mana kece komai nawa". "Karya ne wallhi karya ne mk abinda kake fada mata yaudarar ta kake babu abinda da zakai da yar talaka saidai ka auri sa'arka ka rasa inda girman kan naka zai kare sai akan 'yar aikin gidan ku tun wuri ka saita bakinka ka dawo hayyacinka idan ma bacci kake toka farka kaga wacce Ke Gaban ka kake kuma cewa kana sonta da aure ka dube ka kaiba sa'anta bane kalli daular gidan ku ita kuwa daga wani banzan 'kauye tazo cikin kargo da sabara haba mk kalleta da kyau itan ba kowa bace maid dinka ce savant dinka ce me muku hidimar gida ". Dukkan su kallon inda akai maganar sukai Abidah ce tsaye hawaye na zuba a idonta . Mikewa tsaye mk yay yana kallonta cikin tsawa yace" dan ubanki nine kike cewa ina karya me kike gadara dashi mum ko? To itama bazata hana na 'bab'balla kiba idan ban auri Safah da nake soba ki fada min gidan uban da zanje nayo auren mahaukaciyan yarinya kawai". Rike kugu tay"wallhi mk niba mahaukaciya bace nasan abinda nake soyayyar ka ce take neman hallaka min rayuwa dole in fada ko baka so kaine dai bakasan abinda kake ba tunda Idonka ya rufe akan wata banza yar aiki mara galihu kasan dai talauci ne yasa ta fito nema ta fake a inuwar ku tana samun abinda zata rike almajiran iyayenta amma sam ka kasa fahimta nice na dace da rayuwar ka ba wannan abar ba please mk ka soni kodan matsayina na kanwa a gare ka". Bude dukkan girman idonshi yay a kanta yana cewa" you see why you would never have sense matar tawa kike fadawa wadannan Maganganun a gabana saboda baki da kunya ba auntyn ki bace maimakon ki girmama ta matsayin ta na matar yayanki mk kamar yadda kike ikrari kodan you can do more then that saidai ki sani bazan taba sonki ba bazan bata lokaci na a kanki ba kalli kanki dakyau baki da wani tsari siffar tabarya😁 gare ki to idan na aureki mene riba ta? Maza ki saitawa kanki hanya". "Wallhi mk bazan barka ka huta ba saina aureka kuma zaka gani koni ko ka.......... Bata karasa ba da gudu tabar gurin ganin ya nufota ta shige part din su Alawiyyah bai fasa ba ya bi bayan ta cikin bacin rai dariya Safah tay "kai jama'a inda ranka kasha kallo dama da auren nata kayi tunda shashasha ce aikun dace da juna mahaukata biyu sai kuje ku karata". Da gudu cikin fargabar ganin ya biyota ta shiga bedroom zata rufe yaa hankada kofar baya taja numfashinta na fita da sauri tace" dan Allah kayi hakuri bazan sake ba". Ko sauraronta baiyi ba yaci gaba da binta gado ta fada wanda hakan ya bashi damar binta ya danne tare zura hannunsa a rigarta yana kama breast dinta kara tayi cikin muryar kuka tace" mk ka bari wannan fa haram kake aikatawa zan fadawa mum". "Kin dade baki fada mata ba uban waye yace ki kawo min raini koni sa'anki ne? yau saikin gane kuren ki" doguwar rigar dake jikinta ya cire yana dora hannunsa akan hips dinta yana shafa su babu yadda ta iya tana ji tana gani Saida ya gama latse mata ko'ina na jikinta sannan ya mike tsaye yana kallonta Cikin nuna gargadi. Yace" zanyi miki jan kunne na karshe kan sokon da kike min babu abin da za'a gani ayi sha'awa a jikinki bakya cikin matan da nake so wadanda ko kallonsu nayi sai naji hankalina ya tashi don haka kada ki kuskura na sake jin kin furta kalmar so a kaina wawiya kawai"yana fadin haka ya juya tare da barin dakin ya barta tana kuka duk jikinta zafi yake. Safah na zaune ya fita yana huci baiko kalli inda take ba tabe baki safah tay kaika sani kuma bai dame niba ko a jikina wannan matsalar kace tsakanin kune duk abinda kai mata. Da dare mk yana zaune a gidansa shi kadai a palor yana hutawa misalin sha biyun dare babu zato baiga shigowar kowa ba batare da karar bude kofa ba sai ganin mutum yay zaune a kujerar dake facing din tasa ya dora kafa daya kan daya cikin kwalliya kyakkyawa dashi yana sanye da kayan sarauta a jikinsa hannun sa rike da irin sandar da sarakai suke rikewa don kara armashin mulkin su da 'kwarjini. Tsalle mk yay a firgice ya koma bayan kujera muryar sa na rawa yace" waye kai"? daga ina kake"? me kake nema"? aljani ne kai ko mutum"? taya akai ka shigo nan din?. Wani irin kallo ya masa wanda yasa mk kusan sakin fitsari don tsoro. Cikin murya mai dadin sauti ya soma magana" sanin ni waye ko kai waye wannan ba shine abinda ya kawo ni gunka ba ka sani idan har wuta ta kama a rafin gas ba wanda zai iya kasheta idan kuma ka gwada to zakai asarar rayuwarka manya gaban ka 'karamin 'kwaro kura ba farkar kare bace kuma ko giwa🐘 a dawa tasan zaki🦁gurin farauta a tsari na bana magana biyu yau saida na shawo bala'i ina neman fitina sannan nazo maka sakarai zanyi maka gargadi dajan kunne na farko kuma na karshe akan Safah ka za'ke da yawa cikin gonar da ba taka ba kasani idan harna sake zuwa yi maka gargadi a kanta jikinka saiya fada maka saika gane ruwa basa'an kwando bane Safah tafi karfin ka da mummunan kudirinka idan ka kuskura ka sake mata kallon sha'awa zaka yabawa aya zakinta saika gwammace kida akan karatu zakaga irin matakin dazan dauka akanka 'karamin dan iska "yana kaiwa nan ya mike cikin tafiyar kasaita ya nufi kofar fita ba tare daya bude ba mk ya neme shi ya rasa wani irin zaman yan kaciya yay yana sauke numfashi yace" to shi kuma wannan daga ina mene alakarsa da Safah dazai zo yana min warning akan ta kodai aljanin tane👹 dan wannan ba mutum bane" kasa tashi yay a wajen don tsoro gani yake kamar zai dawo duk sanyin esin da yake palon amma shi gumi yake . Bai iya bacci ba gari na wayewa ya nufi gidan su direct kitchen ya wuce don yasan acan zai sameta yanzu yayi sa'a kuwa ita kadaice tana rage ayyuka kafin baba maryam ta karaso. Ganin bata san da zuwan saba yasa yay gyaran murya da sauri ta juyo cikin zaro ido zatai magana ya katse ta da fadin"ba wani abu ya kawo niba nazo ne na miki tambaya shin ke 'yar 'kungiyar shan jini ce jiya kika tura a kashe ni ko kuma kina da wani aljani basarake fada min gaskiya domin jiya yaje yayi min warning a kanki nasan saidai in kece kika sashi taya zaisan gida na idan bada hadin bakin kiba"?. Dafe kirji Safah tay ni kuma sharri zaka min🙄"?. Kai ya girgiza"ba wani sharri malama kawai ki yarda kin aikata domin ba mafarki nayi ba kuma ba'a rude nake ba a zahiri yazo min yana gargadi na saboda ke". Cikin haushi Safah tace" bansan akan me kake magana ba kwantar da hankalin ka na kusa bar muku gidan ku sai kaci karen ka da gishiri ba babbaka idan ma kana tunanin na tare maka jin dadi ne basai ka kulla min sharri ba lokaci kadan ya rage min". Kai ya jinjina bai sake magana ba ya juya yana fita a kitchen din da harara Safah ta raka shi tana jan tsuka" jimin mutum da tsohon sharri a'a ka manta ba 'yar 'kungiyar shan jini baca 'yar 'kungiyar shan bargo ce" cigaba tay da aikinta bata sake bi takan zancen ba dan sai yanzu take tunanin kila ko shawuwa yayi yazo yake karanta mata soko. Mrs Al'ameen Ahmad ce,😍 Typing📚📝 🍇SAFREEYYAH🍇 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 (*()*)👉 🏡home of hospitality👐 and harmony👫(*()*). 📝YUSRAH MUSA ABUBAKAR GIMBA. INA GAISHE DA DUKKANIN KU 'YAN UWANA NA JINI ALLAH YABAR MU TARE YA 'KARFAFA ZUMUNCIN MU🙏. Uwani mubi (maman nana,) Aishat Yakubu (maman Yusuf) Dumus Yusrah Sallau Musa kano Batula Adam Naseer kano, Musa Aliyu Mubi Yola Samira Ahmad (maman Zainab) Ummi Ahmad, (maman Nura) Nura Sani (Abban najasi) Umar Halifa kano Balaraba (maman Alhaji) kano Ibrahim lele Abubakar Usaina (maman Amatu) kano Maman Ahmad Dumus Sallau Sado Bauchi. 💞Mrs Al'ameen Ahmad ce💞 😘 When you are important🌿 to another person that person will always find a way to make time🕛 for you. 👉No excuses😎 👉No lies😉😝 And no broken promises💔. #YUSRAHMS# NO.35 👉 36 Ammi ce zaune ta kalli hanne tana cewa" Hanne meye labari kin dade bakya masarautar nan fatan kin dawo min da abin arziki wanda zanyi alfahari dake shin kin samo min wani kwararran malamin ne naga kin dawo fuskar ki fayau da annuri maza fadamin harna matso naji abinda yace miki fatan wannan karon anyi nasara . Murmushi hanne tay mai ma'ana tana cewa"ai ranki ya dade ki zuba ruwa kawai yau a kasa na farin ciki kisha don na samo miki wani malamin daya san abinda yake saidai yace min zai bincika daga baya na koma amma karna damu ya gano nasara a tattare da aikin kuma yace na miki albishir da cikar burinki a wannan karon zai share miki hawaye ki kwantar da hankalinki duk abinda kike so zaki samu zai miki komai". Numfashi Ammy ta sauke jin kamar anyi aikin ma tasamu abinda take so lallai kuwa da duk wata baiwa da take part dinta saita samu 'yanci kallon hanne tay tana cewa"da kuwa hanne na jinjina miki lallai za'aje dake kuma idan har nayi nasara zan kaiki zuwa babban matsayi sannan inaso idan kin koma gurin malam kice mas.......... Katse maganar Ammy tay jin an rafka sallama dan zaro ido tay tana kallon jakadiya dake dukushe can bakin kofa cikin bacin rai tace"bansan cewa ke jaka da'ki'kiya bace sai yau muna cikin magana zaki wani fado mana kamar wacce aka turo ki yaushe kika shigo kinji abinda muke tattaunawa kome sokuwar banza". Jakadiya dake durkushe tana sauraron ta wani irin takaicine ya lullubeta ta sani cewa ta girmi Ammy kodan wannan aita rika bata girma amma saboda itadin ba ahlil sarki bace tana sahun masu hidima yasa Ammy bata ganin darajar ta kuma koba haka ba tarasa metaywa Ammy dama can bata sonta. Cikin tsawa Ammy tace"ke wacce irin dabba ce jakadiya ba magana nake miki ba kikai banza dani saboda bani da daraja kome"?. Kai jakadiya ta girgiza tana cewa"kiyi hakuri ranki ya dade banji komai ba sannan mai martaba ne yake nemanki yanzu ki gafarce ni nayi kuskure"ta karasa maganar hawaye na zuba mata domin wannan bakin cikin ya isheta ace don kana karkashin mutum shikenan saiya dau girman kai ya rika wulakanta ka. Tsaki Ammy tay"naji bacewa ganina magulmaciyar banza harda kuka indai nice kuka ma yanzu kika soma don ni in mutum baiyi min ba bana ra'ayinsa to ya shiga uku bazai tabajin dadi ba ki bini a sannu jakadiya domin saura kiris nasa a tsige ki daga wannan mukamin naki a nada wata domin baki dace da matsayin ba". Hakuri jakadiya ke bata amma ko sauraronta batai ba tace tayi waje kafin ta nuna mata kalarta mikewa jakadiya tay jiki a sanyaye ta fice yayin da Ammy ta bita da kallon tsana tana yin kwafa tace"zanyi maganin kine bari dai hankalina ya kwanta zaki bayani Hanne ta kalla tana cewa"jeki kawai zan nemeki daga baya sai mu karasa maganar da muke yanzu ba lokaci zanje gurinki ran mai martaba ne". "To ranki ya dade fatan alkhairi a dawo lafiya"tashi Ammy tay tana wucewa daki donta shirya Hanne data mike itama zata tafi aranta tace"humm Adama gwana gimbiyar sarki zaki bayani sai na gama lalata miki tunanin gabadaya donni ba mahaukaciya ce irin ki ba dazan biye miki ki aikata mugun abu ba wata rana asirinki ya tonu a gane cewa dani kika hada baki zansan matakin dazan dauka a kanki muje zuwa". Fitowar Ammy kenan bayan ta gama shiryawa ganin har lokacin Hanne tana nan yasa tace"me kuma kike jira baki tafi ba nifa bana son rashin tunani dalla malama bana sallameki ba barnan". Baki bude Hanne take kallonta aranta tace"tofa ke baki da dama nice dalla malama lallai Adama kin cika amma zan nuna miki baki kaiba kinyi tsararo dani kike zance zan baki mamaki zanyi abinda baki taba tunani ba" a fili kuma sai tace "afuwan ranki ya dade na dauka zanyi miki rakiya ne shiyasa na tsaya". Cikin sakar mata harara Ammy " haka nace miki uwar yan shishshigi dama ke kike raka ni bansan hanya bane kome dalla ki barnan". Juyawa Hanne tay cikin jin zafin kalaman ta tafice zama Ammy tay tana huci ba'a jima ba wasu bayi su shidda da kaya iri daya a jikin su suka shigo mikewa Ammy tay tana wucewa gaba su kuma suka take mata baya har bangaren Emir . Tana shiga ta iske shi yasa waya gaba yana murmushi zama tay tana cewa"ranka ya dade barka da hutawa irin wannan murmushi da fara'a haka koda Amfal kukai waya ne"?. Murmushin sa bai gushe ba yake duban ta cikin muryar mulki yace" eh ba iya Amfal ba shida dan uwansa ne vidio call mukai dan nayi kewarsu sosai sunce min ma anyi musu karin girma baki ga yadda suka kara kyau da kiba ba kona baki ku gaisa da su dama suna tambayarki". Cikin jin haushi Ammi tace"ko shine dalilin da yasa ka kira ni na 'bata kafa ta"?. Kai Emir ya jinjina"eh ba haka bane wannan ma dabam tun dazu nake jiranki na aika a kiraki amma sai yanzu kika zo ko gimbiyar sarki mace daya kike kamar rai". Murmushi Ammy tay cikin jin dadin gimbiyar sarki daya kike mace guda daya ta rausayar dakai fuskarta bayyane da fara'a tace"wallhi ranka ya dade harna ji ka fasa min kai daka kirani muce guda daya a gareka nice sarauniyar ka kome kace". "Eh haka ne abinda kika ce gaskiyarki amma yanzu mu aje wannan maganar gefe kiran ki nayi don na sanar dake wani abu mai muhimmanci da zanyi Adama kin sani cewa duk namiji mijin mace hudu ne ko?balle kuma sarki wanda idan yana ra'ayi harda 'kwar'kwara inaso ki bude kunnenki ki saurare nida kyau kuma ki fahimta Adama ina mai baki bushara da cewa inason kara aure zan auri kanwar sarkin Adamawa abokina wacce mijinta ya rasu kwanan baya mene shawararki akan haka ki bani wani bayani dazai taimaka min domin kece makusanciya ta banda hajiya babu wanda yasan wannan zancen saike amma me kika ce"? Wata irin zabura Ammy tay wanda tasa Emir ya kusa yi mata dariya mikewa tsaye tay cikin tashin hankalin tana kallonsa tace"ranka ya dade da gaske kake mafarki nake kome banji abinda kace sosai ba dan maimaita min. "Dama nasan ba lallai ki gane kiji ko ki fahimce niba amma idan lokaci yazo kika ga komai azahiri cewa ba mafarki kike yiba daga nan zaki fahimta ki dawo daidai Adama bansan shashanci idan har Allah yasa anyi auren nan ki nutsu ki kama kanki kija girmanki banda hayaniya duk wata hanya da zaki bi kisan baku samu matsala ba matsayin kina babba kuma uwargida toki daure kibi wannan hanyar kar a samu sabani fatan yanzun kin gane"?. Cikin kuka Ammy tace"wallhi ban gane ba ban fahimta ba bazan yarda kamin kishiya ba mena tare meye bana yi maka ka fada in gyara kurena kishiya bata dace dani ba". "Haka dai kika ce a naki gajeran tunanin amma ni a wajena kin cancanti kishiya gaba da baya maganar bazaki yarda ba karyane don babu wani abu dazaki iyayi ko zaki wanda zai hana ni abinda naga dama ba aure kuma nan da sati za'a daura saiki kwana cikin shirin taryar sabuwar amaryar ki". Kasa magana Ammy tay saboda bakin ciki sai kawai ta juya tana barin fadar tasa hankalinta inyai million ya tashi ko ganin gabanta batayi da yake bata cikin nutsuwar da zata iya magana a wannan lokacin kawai kwanciya tayi tare da kara fashewa da sabon kuka gaba daya ta rasa inda zata sa kanta hatta kwakwalwar kanta zafi take saboda daukar caji😢. (Ayya Ammy sai hakuri fa mukan biki za musha mu gwangwaje💃💃). Kome kuka ce?😝. Wash😢 Allah fans typing akwai wuya😑 don haka gobe da jibi baza ku samu typing ba😝 zaku jini shiru zan huta sai ranar asabar in Allah ya bamu aron rai nagode yan whattpad ina yinku sosai ana tare👫💞. Mrs Al'ameen Ahmad ce,👌. 👍 Taku har a kullum, 😘🙈We will meet again 🤗 Tnk for your support. ONE☝ LOVE💝 YUSRAH MUSA ABUBAKAR CE.. BARKAN MU DA RANAR ASABAR YAN UWA FATAN KOWA YANA LAFIYA CIKIN FARIN CIKI DA KYAKKYAWAN YANAYI KAMAR YADDA NA MUKU ALKAWARI CEWA TYPING SAI RANAR ASABAR ALLAH YA KAWO MU SAI KU MATSO KUSA MU DORA INDA MUKA TSAYA DAN GANI NAZO KU FITO MU CASHE💃 YAU RANAR TAKU CE FANS WANNAN PAGE DIN NAKU NE MALLAKIN KUNE NA BADA SHI DUKA GARE KU KUN CANCANCI JINJINA👍 DA HANNU DUBU😝. 🌌💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION🌌💫 (🏡home of hospitality🤗 and harmony👌). 📝YUSRAH MUSA ABUBAKAR DEDICATED TO MY MOTHER I LOVE YOU MAY ALLAH ACCEPT YOUR DU'AS AMEEN MAMANA💞. #YUSRAHMS# NO.37👉 38 Hajiya Binta na zaune mk dake gefenta ta kalla tana cewa "bikin Salmah saura wata daya jiya dadin ku kafin ya tafi ya sameni akan na fada maka kafin lokacin bikin ka samo matar aure sai a hada ayi tare na isar da sakon sa yanzu ya rage naka kasan dai halinsa baisai na sake fada maka ba". Cikin wani irin yanayi mk yace"haba mum aure kuma nida ban shirya yi a kwana kusa ba taya cikin wata zan nemo matar dazan aura please na roke ki idan ya dawo kice masa ba yanzu zanyi ba yadan karamin lokaci". Wani kallo hajiya ta masa"Allah ko baba to baka isaba ni kaina na gaji da ganinka haka dandai ba yarda na iyane amma ga waraka tazo mk koba kaso dole ka nemo macen aure a wata dayan nan". Hade rai yay"nidai dan Allah mum ku kara min lokaci zan samo ba yanzu ba". "To ai ni kuma na dade da gano maka wacce ya kamata ka aura". Mk da duk yaji hankalinsa ya tashi yace" wa kenan mum"? . "Abidah mana mk ga mace a gida meye saika fita waje ka auro nice da kaina nayi tunanin hakan naga kuma ya dace mu hada zumunci mu kara karfafa shi". A firgice mk yake kallon hajiya Binta muryarsa harta sauya yace"Abidah fa kika ce mum? wai Abidah dai dana sani ta gidan nan ko kuma wata ce dabam a wani wurin"?. Dan harararsa hajiya tay"ji wani sokon banza Abidah tanan mana nake nufi 'yar gidan kawun ka 'Dayyabu zaka wani fuske kace wata ce dabam". Kai ya soma girgizawa"haba mum me zanyi da Abidah gaskiya batai min ba bata cikin tsarin kalar matan da nake son aura ki janye maganar nan mum hakan ba mai yiwuwa bane niba sa'anta bane". "Bazan janye ba mk inji ubanwa kaiba sa'anta bane meka fita fada min naji kaga fa banson shashancin banza". "Kiyi hakuri mum amma bana sonta dan Allah ki fahimta". "Bazan fahimta ba ni Abidah nake so ka aura idan kanada ra'ayi ko gaba kaga wacce kake so saika aura ban hana kaba"tana fadin haka ta mike zata bar gurin cikin magiya mk yace"ki saurari hanzari na wacce nake so ita kadai ce bata da sa'a tafi karfin zama da kishiya kuma gidana na ita kadai ce maishi banyi don nasa mata biyu ba saboda gudun hayaniya". Ba tare da hajiya Binta ta juyo ba tace" 'yar gidan uban waye ita data fi karfin zama da kishiya waye ubanta a ina take"? shiru mk yay ya kasa magana don yadda hajiya ta hauro kila idan tsautsayi yasa ya budi baki yace Safah ce may be ya jawo silar barin ta gidan shi kuma hakan ne baya so. Tsaki hajiya taja jin yayi shiru tace"maganar banza ma kenan kaika sani saika fara shirye shirye tun yanzu kayo lefe basai lokaci ya kure ba"gaba tai ta barshi a gurin cikin wani kalar bacin rai. Fitowa Abidah dake labe tayi tana dariya ta soma taka rawa a gaban sa tana cewa"gaskiya naji dadin wannan al'amari ya mk nan da wata na zama matarka kamar yadda nake mafarki kullum ashe dai tabarya zatai rana kai kuma ka zama turmi dama na fada maka bazan barka ka auri wata bani ba kuma dole ka koyi sona ka zauna dani iya raida mutuwa danna zame maka karfen kafa mai wuyar cirewa ni kujera ce dole ka zauna dani"ta karasa maganar tana sakin gud'a wacce ta sake tunzura mk a fusace ya mike ba tare data lura ba ta rike hanci tana faman 'kara kamar wata gyare😂. Ji tayi ya damki hannunta ya soma tafiya da ita ko damuwa batai ba dan tasan koma me zaiyi mata dole shine mai auren ta har part dinsa sukaje sakar mata hannu yay yana shiga bedroom zuwa jumawa ya fito rike da bel damkar ta yay cikin son huce haushin sa ya soma shimfida mata a jikinta ihu ta kurma tana bashi hakuri yay banza da ita saida ya zaneta tas sannan ya bude kofa yana turo ta waje ya mayar ya rufe. Cikin kuka ta daga murya tana kallon kofar tace" Allah ya isa azzalumi kuma hakan bazai hana na fadi abinda nay niyya ba dole kaso ni kuma ka aure ni bayan taimakon ka zanyi ganyar tsiya katon tuzuru kawai mai kwana rungume da filo"tana fadin haka da gudu tabar gurin saboda tsoron karya fito ya kama ta tasan saiya kusa kashe ta. Zaune suke a daki ranar da maryama ta dawo daga yola cikin damuwa Safah ta kalle ta tana cewa" waini baba sai yaushe zan tafi gida ne? ina so naje naga baffana dasu malam da Hadiza Allah zaman nan din ya ishe ni". Dariya baba maryam tay"kai Safah mene abin gajiya kuma dama nasan dole zaki kewar su wata biyar ba wasa ba amma ki kara hakuri so nake sai anyi bikin Salmah da Mk sai muje na raka ki kasuwa ki sayowa Baffanki d'an abin arziki ki kai masa dasu Hadizan kema kya sayi wasu yan abubuwan na aurenki da kudin aikin ki kamar kuloli da sauran su kinji ki 'kara hakuri saura yan kwanaki". Kai Safah ta daga cikin jin dadin lissafin da baba maryam ta mata tace"to Allah yakai mu baba nagode" murmushi baba maryam tay"yauwa ko kefa kin kusa ganin Baffa kwantar da hankali". * * * «»«»«» »«»«»« «»«»«» Kamar yadda Emir ya fadawa Ammy cewa zuwa sati amarya zata sauka hakan ne ya faru ankawo ta lafiya kuma part dinta yana kusa da part din Ammy a ranar dai Ammy ko iya runtsawa batayi ba tayi kuka tayi bakin ciki har bazai misaltu ba babban abinda yake daga mata hankali kuma yake bata tsoro taga amaryar ba wata babba bace dan batafi kanwarta ta biyu ba abin firgicin anan shine karfa nan da wani lokaci ta ganta da ciki ace itama zata haihu kila ba haihuwa daya bama yayanta suzo suyi yawa itama ya zama ta samu abin kirki a dukiyar sarki saidai ta dawo gefe ta zuba ido tay kallo wata banza tazo sama takai ta fita morewa ita data zauna dashi tsawon shekaru. Ammy dake zaune idonta a rufe tana wannan maganar a zuciyarta a firgice ta bude idonta gani take kamar har hakan ta faru muryarta har wani sauti take bayarwa mai amo cikin takaici tace" inaaanh karya ne wallahi ni za'a wulakanta hakan bamai yiwuwa bane bazan taba barinki haihu ba saidai koni koke idan ba neman a tozartani a idanun bayi ba meye da girmana za'ai min kishiya bazan taba yarda da wannan ba". Shiru tay tana huci daidai shigowar Hanne bayan ta gaishe da ita tun ba tace komai ba Ammy ta dube ta tana cewa"daga ina kike tun dazu ina jiranki"?. Gyara zama Hanne tay tana cewa"ki hakuri ranki ya dade sako ne ya iske mu daga mai martaba cewa yana bukatar dani da jakadiya da Gambo sannan da bayi masu take baya muje mu raka masa amaryarsa fadarsa amma ki gafarce ni tuba nake". Wani irin dafe kai Ammy tay jin hajijiya na diban ta da sauri ta nemi kujera ta zauna numfashinta na neman toshewa jin abinda Hanne ke cewa". Ta dauki dogon lokaci a haka kafin daga baya ta sauke zazzafar ajiyar zuciya tana kallon Hanne tace"dole zama bai kama kiba idan na bari na zuba ido na saki baki inaji ina gani mai martaba zaimin nisa don haka ina so yanzu ki shirya kibar masarautar nan zama bai kama kiba ki tafi gurin malam ki masa bayani cewa ya raba sosayyar dake tsakanin sarki da wannan mayyar matar idan ta kama harda kisa ne yayi indai burina zai cika ban damu ba komai ma ayi zan baki kudade masu yawa don yaji dadin yimin aiki mai kyau tashi kije ki shirya saiki dawo". "To ranki ya dade yanzu kuwa wannan abin bakin cikin har ina? barina dauko gyalena don babu wani shiri sai hankali yana kwance ake komai sauri zanyi na dauko" . Fita Hanne tay tabar Ammy ta kasa zaune ta kasa tsaye tana cikin haka sanarwa tazo mata daga wata baiwa mai mata hidima cewa sarki na kiran ta. cikin burkicewa bako shiri ta fita dama abinda take nema ne ya samu saboda saurin da take masu mata rakiya gudu gudu suke suna mamakin yau meya samu Ammyn ganin da sukai a hargitse take saidai baza'ace komai ba kishi yana saka mutum yayi fiye da hakama. Kamar an jefata akai haka ta fada musu suna zaune suna zance Emir harda dariyarsa data dade bata gani yayi irinta ba cikin takaici take kallon duk su biyun ga wani kishi dake taso mata ji take zuciyarta na tunzurata ta fadawa amaryar nan da duka ta ru'kur'kusheta🙊😁 ko ciwon dake damunta zai kauce. Kasa zama tay har saida Emir ya mata magana sannan ta zauna da 'kyar kamar me ciwon cinya sai cika take tana batsewa Emir yana lure da ita amma bai tanka mata ba yasan yanzu kishi ne yake ruda ta idan ta huce shikenan. Ammy dake kallon matar tun dazu aranta tace" humm zaki bayani muje zuwa da kafafun ki saikin gudu daga gidan nan babu wacce ta isa a yanzu nay hadan miji da ita ki jira na baki wata daya a kinyi zama mai nisa a gidan nan domin lahira zatai bakuw,.............. Katse mata tunani Emir yayi ganin kallon kurullar yayi yawa yace"am Adama ga amaryata matata Fatima Zarah nasan jiya sunbi ta gurin ki da ita kuma sun baki amanar ta rokona don Allah ayi zaman lafiya da gaskiya dukkanin ku daya ne a gurina kowa auren ta nake bana jin cewa daya tafi daya ina son ku hade kanku kinga kece babba kada wata matsala ta taso daga gareki inayi muku fatan alkhari". Ba zato Ammy tayi ta maimaita Fatima Fatima Fatima wanda da alama batasan tayi hakan ba sunan mahaifiyar Abdul-jabbar fa kenan a firgice ta kuma kallonta tana cewa"Fatima dai Fatima"?. Kai Emir ya jinjina "kwarai Fatima sunan ta kinga ikon Allah ko? Ya dawo min da Fatima na dana rasa yanzu itace zata maye min gurbinta sannan kuma ta zama mahaifiya ga Abdul-jabbar ta rika debe masa kewa nayi matukar farin ciki sosai da samun ta kodan d'ana daya kasance cikin maraici baisan dadin uwa ba yanzu zaiji abinda kowanne mai uwa yake ji fatan kin gane"?. Mai da kallon shi yayi kan amaryar yana cewa"Fatima ga mata ta Adama kuma mahaifiya a wajen d'ana Amfal". Murmushi Fatima tay tana kallon Ammy tace"barka da kwana uwar gidan mai martaba fatan na sameki lafiya? jiya ban samu mun gaisa ba anata hayaniya". Ammy datay wiki wiki ta daskare waje daya ta kasa magana saboda gani take kamar mahaifiyar Abdul-jabbar ce ta dawo da gaske,. Dan saita nutsuwar ta tayi cikin ya'ke tace"lafiya ya kike"? da'kyar ta karasa maganar tana maida hawayenta. Fatima da har lokacin fuskarta da annuri tace"Lafiya alhamdllh". Ganin Emir na shirin magana ita kuma ta gaji da takaicin da take kwasa ta riga ta gama kulewa tazo wuya saitay saurin tarar numfashin sa da fadin" ranka ya dade bari naje ana jirana ka huta lafiya"tun baiyi magana ba kamar guguwa na diban ta tafice binta yay da kallo tare da girgiza kai duk yana hankalce da ita kawai basarwa yayi tunda ga bakuwa a gurin bai kamata yayi wata magana data danganci abinda ya shafi 'barakarsu ba kodan gudun jawo fitinar abinda zai faru a gaba". Ammy na shiga part dinta ta tarar da Hanne zaune tana jiran ta dora hannuta tay aka🙆 ta zunduma wani uban ihu tana cewa" na shiga uku na lalace Hanne shikenan tawa tazo karshe Fatima ta dawo kodai dama rufe min akai ba mutuwa tay ba"?. Hanne data gama firgita jin maganar da Ammy take wacce hankali bazai dauka ba tace" ranki ya dade kamarya ganin ta kikayi ko kuma fada miki akai naga dai wanda ya mutu ya tafi kenan taya ta dawo to"🤔?. Ammy data rasa inda zata sa kanta tace" ni kaina bani da tabbacin hakan amma gashi nan mai martaba yana cewa shikenan Abdul-jabbar ya samu gurbin uwa shima saiya daina maraici kuma kice min Fatima bata dawo ba"?. Hanne data fahimci ammy bata cikin nutsuwar ta ganin amaryar mai martaba da tay kwakwalwarta ta hargitse yasa tace" ranki ya dade kodai a rude kike kallon tsoro ki kaiwa amaryar mai martaba amma babu hadin hanyar mota data jirgi wannan Fatiman dabam haka wacce ta mutu ma dabam ki kwantar da hankalin ki mubi abin a sannu babu ko dangantaka tsakanin su". Sauke ajiyar zuciya Ammy tay tana kallon Hanne tace"to yanzu yaya za'ai maganar zuwa gurin malamin ke nake saurara wacce hanya ya kamata mubi wanne mataki zan dauka"?. Hanne a ranta tace" tabdijan ana wata ga wata wa zaki zura a rijiya gaba dubu naji kina cewa wacce hanya zamubi zaki bidai ni meye nawa a ciki meya kaini shiga cikin wannan cakwakiyar babu ruwan 'yar Idi da jefa kanta a fitina tazo ta kwabe dani ke matarsa ce zai iyayi miki afuwa idan yasan gaskiya kodan darajar aure da d'an dake tsakanin ku ni kuwa asuwa mai ido ba d'an ciki wannan fadan kune na cikin gida babu abinda yay min zafi zan tsoma kaina abinda bai shafe niba asiri ya tonu ki barni dajan ido". Cikin tsawa Ammy tace" wannan wanne irin shashancin banza da wofi kika tsira Hanne kullum sai muna cikin magana ki kama wani sokon tunani ki rabu dani". Jiki na rawa Hanne tace" kiyi hakuri dama shirun da kika ga nayi ina tunanin gurin malamin daya kamata naje ne". "Ok yayi kyau to tuno ina sauraron ki". Cikin salon da Ammy baza ta ramfo taba tace" ai ranki ya dade na gama tunani zanje wajen malamin da kawai zai kashe ta idan kina da bukatar hakan amma me kika ce ya shugaba ta". Kai Ammy ta girgiza" a'a Hanne na fasa kasheta yanzu so nake ni da ita mu goga a haka batare da aikin malami ba da kissa ta zanyi amfani na 'kwace fada gurin mai martaba ya zama ni kadai yake gani a gaban sa". Cikin sauri Hanne tace"eh ranki ya dade hakama za'ai wannan shawarar tayi hanya mafi sauki itace tabi wacce kuma zata bulle tanan kadai zaki mata zarra ki bata tazara ta gane kedin bata yau bace kin zarcewa tunanin ta kisa ta raina kanta a duk lokacin da kuke gabansa bazai kalle taba ke yake duba hankalinsa yana gare ki". Cikin jin dan sassauci daga damuwar dake damunta ta dan ragu yasa ta kalli hanne tana cewa"Shikenan Hanne tashi kije zan jarraba wannan shawarar da kika bani saina sake neman ki idan naga tsarin dazan dauka akwai nasara da riba a cikin tafiyar". Mikewa Hanne tay tana cewa" to ranki ya dade ki huta lafiya" tana fadin haka ta fice cikin jin dadin wata rana zata zame kanta daga jikin Ammy kafin komai ya baiyana. MRS AL'AMEEN AHMAD CE👌. ()(*)() ()(*)() ()(*)() GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GARE KI KANWATA SARATU YAKUBU FATAN RAHMAR ALLAH DA GAFARAR SA A GARE KI. YUSRAH MS ABUBAKAR. ☝💝🍇🍉🍒🌹🍍🍑🌻🌼 TYPING📲 SATURDAY 08:03am 04/March/2023 🍇 🍇 SAFREEYYAH🍇 🍇 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 (🏡home of hospitality🤗 & harmony✨) STORY AND WRITTEN 📝Mrs Al'ameen Ahmad ce WANNAN PAGE DIN NAKU NE 'YA'YA NA ALLAH YA RAYA MANA KU ABISA TAFARKIN MANZON ALLAH(S A W)🙏 AMEEN. Aishat Mahraz Auwal Mahraz Hauwa Ahmad Aishat Ahmad Walida Abubakar Jamil Ahmad Muhammad Naseer Fatima Sadauki Adali Gali Amatu Gali. #YUSRAHMS# NO.39👉 40 Kwanaki nata tafiya har bikin su mk yazo anyi abubuwan kece raini sosai hajiya ta barnatar da kudi naban mamaki domin ba karya naira akwaita kamar kasa. Abidah kuwa tun ranar da mk ya daketa tsoron zagin datai masa yasa washe gari tana jin yadau mota ya fita agurguje tai wanka ta shirya ta gudu gida bata dawo ba sai ana gobe dinner taji haushi ganin har lokacin Safah na gidan batay tunanin zata dawo ta sameta ba ta dauka ta ware 'kauyen su amma bari a gama bikin nan saita fadawa hajiya ita mk yake so akan ta yake wulakanta ta. Washe gari tun safe ake shirin dinner har lokaci yay amma babu mk babu alamarsa Abidah ta kira wayarsa sakamakon angon Salmah yazo tun dazu suka wuce cikin damuwa harta soma bata kwalliyarta taje gurin hajiya. Cikin kuka tace" mum kinga mk har yanzu baizo mun tafi ba Salmah nasan sun dade da zuwa nakira wayarsa yaki daga min dan Allah ki gwada kozan samu ya daga idan yaga kece". Cikin bacin rai hajiya tace"kaji min iskancin banza to gidan uban wa ya tafi tun safe? Mk yana bata min rai da rashin jin maganar sa kinga daina bata kwalliyar ki bari na kira shi yanzu zaizo ku tafi". Ta karasa maganar tana danna masa kira ta shiga amma bai daga ba harta katse kara sa masa wani kiran tay. Mk na gidan sa rungume da seeker sunata aikata barna yana jin kiran yaki ko kallon wayar Seeker ce ta gaji tace" darling ana ta kiran ka please ka daga mana bakasan waye ba koda wata matsala ne". Basar da ita yay kamar baiji ba har wayar ta katse saida aka sake kira kamar baya so duk da yaga me kiran kuma yasan akan me ta kirashi. Yana dagawa maganar hajiya ce ta doki kunnen shi" kwarai mk yayi maka kyau ka tozartani ka nuna ban isa dakai ba a idon duniya yanzu dan ka wulakanta Abidah kowa yasan matar cushe ce kai haka? to amma ka sani ba ita ka wulakanta ba ni mahaifiyarka ka kunyata amma babu damuwa kayi duk abinda kaga dama lokacin kane"katse kiran tay tabar mk rike da waya yana kallo ya kasa magana. Murmushi Seeker tay tana dafa shi tace" sorry dear muje na shirya ka kada lokaci ya kure ni ina nan kaje ka dawo" mikewa mk yay tare da kiran Abidah muryar sa da fushi yace" ke wacce irin dabba ce wato ni zaki hada da mum dina ko? zaki gane kuren ki zan cire duk wani gigi da yake damun ki kuma bazan biyo tanan ba idan kinga dama mu hadu acan" cilli yay da wayar ko kashewa baiyi ba ya wuce toilet yayin da seeker tabi bayan shi. 'Yan dinner kam da basu san wainar da ake toyawa ba ganin kowa daban yazo sai mamaki ya kama su ko yanzu haka salon ya koma amarya tazo da kawayen ta ango ma yazo da abokanan sa babu wani nishadi😝. Tunda mk ya zauna hankalinsa kekan Safah wacce tasha kwalliya kamar ba ita ba tana zaune tare da Alawiyyah sai dariya suke suna tafawa. Kasa dauke idanunshi yay akan ta aranshi kuma fadi yake" haba big girl taya mazan barki ki auri wani bayan sonki ya zame min ciwo bazan iya rayuwa ba idan babu ke kece macen da kika dace da tsari na kuma nake sonki da dukkan zuciyata". 'Dan rufe ido yai cikin wani yanayi na shauki kamar kuma an tsikare shi ya bude idnosa maimakon ya sauke idon akan ta saiya sauke kan wani dake zaune kusa da kujerar ta da alama magana yake mata ita kuma tana shareshi mk jiyay jikinsa ya fara jijjiga kishin sa ya matso kusa mikewa yay yana nufar inda suke. Daidai ya karasa Safah da bata ma lura dashi ba ta mike zata sauya guri shi kuma mutumin ya rike mata gefen maya fi wohoho! Ai kamar an watsawa mk ruwan zafi a jikinsa haka ya zabura yana daka wani tsalle sai gashi ya dira a gun ba wata wata ko jira ayi magana ya fidda hannu ya dauke mutumin da mari kafin ya dago ya kara masa a daya 'barin fuskar. Cikin tsawa yace" sa'arka ce? ko tayi maka kama da irin yan iskan matan nan da zaka ja mata gyale dan uban waye kai? me ka taka saika fada min yau nace dan uban waye kai" ya karasa maganar yana damko wuyan rigar mutumin kowa a gurin rufe baki yay yana kallonsu yayin da Abidah ta lelayo ashar mai ruwa ta saki ganin akan wacce mk yake fadan. Da gudu Salmah ta karaso tana cewa" haba ya musaddiq ba girman ka bane kaifa abokin mijina ne amma ka shake masa wuya haka kayi hakuri abinda yay mata bai kyauta ba kuskure ne". "kuskuren uwar wa? dan yana abokin mijinki sai yazo yana ja mata mayafi shi dan iskan ina ne? baisan darajar mace ba sai uwars... Rufe masa baki Salmah tay cikin jin kunya tace" ya musaddiq ka bari mana dan Allah". Tsaki mk yaja mai karfi wanda yasa Salmah matsawa baya da sauri kafin ya juya yana fita a hall din a fusace Salmah batay tunanin don mk nason Safah ne yay haka ba ta dauka kawai ya kare mata mutunci ne sabanin Abidah da tasan komai kuka kawai ta kama ganin ya tafi babu abinda akai ga cake data sa akai musu da sunan su a jiki ta kashe kudi sosai kuma gashi ya tashi a banza wanda tay domin sa ko gani baiyi ba. Har suka dawo gida Abidah na kuka cewa tay saita fadawa hajiya komai Salmah ce ta hana ta. Washe gari aka daura aure wanda mk yaji tamkar da gaske igiya akasa aka daure shi saboda takaici dare nayi kuwa kowacce amarya akai hanyar gidan mijinta da ita babu wanda yakai Abidah zumudi yau zata kwana gidan mk matsayin matar sa. A gaijye Safah ta shigo bangaren su bayan sun dawo daga rakiyar Salmah ganin baba maryam zaune tana shirya kaya tana gyara su yasa Safah tay tunanin ko shirin tafiya take musu. Cikin farin ciki ta zauna tana cewa"baba maryam naga kina ta shirya kaya ko gobe zamu tafi nima na kwana a shirye? don sassafe zamu daga basai rana tayi ba don muje dawuri". Dariya baba maryam tay tana kallonta tace" in banda abinki Safah mene na gaggawa kawai daga kare biki yau ko ba'ki basu tafi munyi gyare gyaren gida ba saimu tafi? Idan kikai hakuri bazaki sake sati a gidan nan ba bayan idan kin tafi ma ba dawowa zaki ba". 'Dan yatsina fuska tay"umh mezai dawo dani kam gara aure na ya fiye min Allah yasa murtalan ma yanzu ya kara tsayi wani gajere daf da kasa ma dashi wallhi ni nafi son dogon namiji ba irin sa ba kamar tuntube". Rike baki baba maryam tay jin abinda Safan ke cewa tace" ke kinci gidan ku safah murtalan kike kira kamar tuntube saboda kin fishi tsayi? kila duk 'ya'yan da zaku haifa suma gajerun ne sai naga karshen ba'a kema kin samu iri". Dariya Safah tay tana rufe idonta baba maryam tace" ato abindai da kunya zagin suruki a gaban miji". 🌹Yusrah Musa Abubakar Gimba🌹 Till we meet tnk for your support. 💫ANNURIWRITER'SASSOCIATION💫 (Home of hospitality and harmony gidan🏡 karba hannu biyu🙌 da zaman lafiya💝). 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 SAFREEYYAH 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ########## ########## ######## ######## ##### ##### ### ### ## ## # # 👏 ALLAHUMA BIKA ASBAHNA WA BIKA AMSAINA WA BIKA NAHYA WA BIKA NA MUTU WA ILAIKAN NUSHUR. Sallim ala abban su nana binta mafi cika da girma a duk halitta ai nuru babullah mafi nagarta dashi halittu suka samu gata. #YUSRAHMS# NO.41👉 42 Abin mamaki hajiya na zaune a palor da safe washe garin daurin aure ba kowa ita kadaice baki na bangaren su Alawiyyah kuma bata tashi daga bacci ba. Da gudu Abidah ta shigo tana kuka ta fada cinyar hajiya jikinta sai kakkarwa yake. Cikin tashin hankali hajiya da take tunanin mk ko sakin Abidah yay ta soma tambayarta. "Abidah lafiya? meya faru? me akai miki? ina mk din? meya kawo ki kina kuka da wannan safiyar ko sakin ki yay"?. Kai Abidah ta girgiza murya na rawa kuma cikin kuka tace" mum bazan iya zama dashi ba kashe ni zaiyi Allah na fasa auren idan yazo kisa ya sake ni bazan koma gidan sa ba". Hajiya da duk Abidah ta gama dama mata lissafi ta gaza gane inda Abidan ta dosa tace" meya miki kike kuka ko dukan ki yay saboda rashin hankali"?. Kai Abidah ta girgiza" a'a mum tun jiya da aka kaini bayan tahowar su aunty Khadijah ya shigo dakin da nake yace min saina zabi mutuwa da zaman gidan sa idan ban sani ba to nasani tun wuri ni bai dauke ni komai ba ni sex machine dinsa ce domin bani da wani muhimmanci sai haka shine ya dace dani hukuncin da zanta karba kenan ba dare ba rana domin ba sona yake ba shine yamin fayde🙊 kuma ko tausayina baiji ba ya mammare ni yanzu kuma ya sake min wani fayden🙈 shine ya shiga wanka na samu na gudo don Allah hajiya ki taimake ni kisa shi ya sake ni bana son sake zama dashi". Sosai ran hajiya yay masifar baci jin abinda Abindan tace kallonta tay tana cewa" kinga kwantar da hankalin kiyi hakuri ki nutsu muyi magana na fahimci zancen ki yi shiru haka nan babu inda zaki zaizo ya samen......... Bata karasa ba taji ance" gani nazo mum ina kwana gaskiya nagode ashe gata kuka min da kuka min auren nan Allah ya saka da alkhairi cikin kwando kwando irin na tumatur😂 ina dadyn mu shima na jinjina masa da hannu biyu na kuma gode masa don kun iya zaben mace" ya karasa maganar kamar zai sheke da dariya ganin yadda hajiya tay. Mayar da kallon shi gun Abidah yay wacce ta gama shan jinin jikinta yace" ke kuma mara kunyar karya ni zaki zo kiwa sharri wai na miki fayde ko? ai kina fitowa na biyo bayan ki kuma naji duk abinda kika fada da iznin uban wa kika fito baki tambaya ba kina matar aure"?. Shiru Abidah tay ta kasa ko tari sai kallonsa da take" cikin tsawa yace" uban me kike kallo ba magana nake miki ba"?. A firgice Abidah ta sake kakkame hajiya cikin tsoro tana fashewa da kuka ganin yayo kanta. Cikin fada hajiya tace" kasan Allah mk ka fara kaini bango za kaci ubanka dama kai maka ita akai cewa gata nan ka kasheta kome? ka shiga hankalin ka fa mk kafin nadau mataki wannan ai shashanci ne". 'Dan hade rai mk yay yana cewa" haba mum wato nine mara gaskiya bayan taimakon ta nayi itafa ta nace tace saini tana sona kuma kika hana ni zabina kika aura min ita to meye lefina bayan jihadi nay". Kallon Abidah yay "ke kuma baki nasara ba saiki sake shiri don nafi karfin karyar ki taso mu tafi kwanan ki daya gidan miji har kika fito yawon muluguigui da munafinci saboda ke tantiriya ce zaki bayani". Jin abinda mk yace ta taso su koma yasa ta rike hajiya tana cewa" dan Allah hajiya ki cece ni karki bari ya tafi dani bazan koma gidansa ba ya sakeni". Kasa magana hajiya tay mk da yake dariyar mugunta cikin zare mata ido ya karaso yana 'bam'bare ta daga jikin hajiya ya mikar da ita tsaye kamar tsinke ya dauke ta tare da kallon hajiya yace" sorry mum ba laifina bane itace ta jawo komai amma kiyi hakuri kuma kada hakan ya dameki ki min fatan alkhari da addu'a mai kyau kinga ke mahaifiya tace don may be yanzu idan na koma kwallona ta shiga raga🏀 kinga kema kin samu jikalle". Ko bari ya karasa hajiya batai ba ta toshe kunnen ta dariya yayi yana juyawa ya fita a palon da Abidah na gunjin kuka". Tagumi hajiya tay domin mk yafi karfin ta bata da bakin magana saidai Abidah tayi ta hakuri dashi sauke ajiyar zuciya tay tana kallon kofar tace "Allah ya shiye ka mk gaskiya lamarin ka da gyara"ta karasa maganar tana girgiza kai dan saidai hakan". ++++++++++ Kamar yadda baba maryam ta cewa Safah bayan biki da kwana hudu suka je kasuwa sayayya duk abinda ya kamata ta sayowa safah ta sayo mata a gida ma hajiya ta hada mata abin arziki sosai saidai taji matukar rashin dadi da baba maryam tace mata Safah baza ta dawo ba aure za'ai mata kuma tadau alkawarin idan lokacin bikin yayi zata zo har kauyen su ayi da ita. Ranar da zasu tafi gida bayan sun gama shiryawa gurin hajiya suka shiga mata sallama cikin damuwa ta kalli baba maryarm tana cewa"harkun gama shirin yanzu sai tafiya shikenan". Baba maryam da itama duk jikin ta yay sanyi ganin yadda hajiyan ta damu da tafiyar Safan tace"eh hajiya duk kayan mu ma mun fita dasu suna harabar gidan so nake na fita na samo mana karamar mota wacce zata kaimu har kauyen sakamakon kayan Safah nada yawa". Kai hajiya ta daga tana cewa"basai kun nemo mota ba ga driver muje na masa magana saiya kaiku". "Hajiya kuma harda wahala haka dakin bari mun sami motar hidiman zatai yawa". "Haba maryam ai tunani na mun zama daya daku dan kawai an kaiku gida ba wani abu bane kyautatawa ma nada dadi". Mikewa baba maryam tay tana cewa"to hajiya mun gode Allah ya kara arziki mun tafi sai wata ran". Tashi hajiya tay suna fita tare har harabar gidan kallon safah data hakimce tay tana fadin"Safah da haka zaki tafi ko sallama ba muyi ba kuma ba dawowa zaki ba". Dan kallonta Safah tay cikin rashin jin dadi tana cewa"kiyi hakuri hajiya dama yanzu zan tashi na shiga sai kuma naga kun fito insha Allahu zan rika zuwa muku lokaci-lokaci". Driver hajiya taiwa magana tana cewa"to shikenan Safah Allah ya nuna mana lokacin saina zo bikin ki gaida gida". Dole da yake kayan da yawa sai babbar mota aka dauka musu hajiya na tsaye suka mata sallama suna shiga motar hajiyana kallo suka fita a gate suna dago mata hannu amma ba damar dakatar dasu haka ta juya cikin gida kamar mara lafiya duk jikinta ya saki. Safah kam suna fita daga gidan ta kifa kanta ta soma kuka kawai itama sai yaudin taji rashin dadin rabuwa dasu. Cikin rarrashi baba maryam tace"haba Safah kiyi hakuri mana rabuwa ba mutuwa bace ai a tunanina yanzu keda hajiya kun zama daya sai zumunci kuma kina jitace zata zo bikin kiko? ki kwantar da hankalin ki man bayan yanzu zaki ga Baffan ki dasu Hadiza ga kuma wadan mijin naki murtala da kika raina". Daina kukan Safah tay ta kama dariya baba maryam tace" ummh wato na soso miki inda yake miki kaikayi" dan rufe baki safah tay"Allah ba haka bane kawai ni baffa na nadamu na gani ba kowa ba". "Saurin me kike yanzu kuwa zaki ganshi". Kwatance baba maryam ta rika yiwa driver har suka shiga kauyen mota bata tsaya ko'ina ba sai kofar gidan malam Abubakar (baffa). Baffa na zaune a tsakar gida gurin wata ni'imtacciyar bishiyar zaitun daya dade da shuka ta domin har 'ya'yan ta anaci duk shekara idan lokacinsa yayi. Asabe na gefe tana gyaran shinkafar sayarwarta tace" ohni 'yasu duniya ina zaki damu mutum da girman sa a saye shi da dubu biyar" sai kuma tay dariya tana kallon baffa daya dago shima yana kallon ta don yasan dashi take zai magana tace" nifa zaka dade kana jin haushi na dan gaskiya nake fada maryam ta yaudare ka da dubu biyar ta gudu maka da 'ya tana can ana koya mata yadda ake bude ido da iya zaman bariki gashi kai kuma ka taho gangarar mutuwa saboda halin rayuwa kila gobe kaji ka a kabari shine zan baka wata shawara nace ko zaka bani wasiyya na ajewa safan taka dan kila sai bayan ranka sannan ta dawo kauyen nan idan ma zata dawo kenan". Ganin ya mata banza tace" yauwa ni kuwa malam dama inata so na tambaye ka wai kwanakin baya da dadewa naga wasu samari sun zo gidan nan su biyu su kuma daga ina? ahlin waye ko surukan kane daga Adamawan safan ta turo maka su ku gaisa"?. . har lokacin baffa bai kulata ba tabe baki tay tana maida hankalin takan aikin ta ga dariyar murna fal cikin ta kasa rikewa tay ta saki dariyar sosai tana cewa" Allah malam idan na kalle ka tausayi kake ban bawai dariya nake maka ba kuka nake taya ka na rashin diyar ka ayya yi hakuri ba dawowa zatai ba". Ba zato suka ji sallama wacce da sauri suka kalli hanyar kofar gidan Safah ce baba maryam na waje wajen debo kaya a mota mikewa tsaye Asabe tay a zabure tare dayin wani ihu tana murje idonta da kyau sannan ta sake bude su ganin ba mafarki take ba yasa tace" Safara'u kece nake gani ko gizo kike min"?. Kallon ta safah tay batare da tay magana ba ta karasa inda baffa yake shima ya saki allo yana mata kallon mamaki dan gani yake kamar bada gaske bane Safah ce a gaban saba yafi tunanin ko aljana ce taji isgilin da Asabe ke masa tazo a suffarta. Zama tay kusa dashi tana rike masa hannu cikin murmushi tace" baffa na barka da gida ina kwana fatan na same ka lafiya"?. Sauke ajiyar zuciya yay ganin dai itance a zahirance yace" Safara'u kece da gaske a gabana ba mafarki nake yiba ina maryaman take ko ke kadai kika taho"?. Kafin Safah ta bashi amsa baba maryam ta shigo rike da kaya a hannun ta bayan ta almajiran baffa ne suma kowa ya dauko ajiyewa sukai suna komawa don su kara debo wasu yayin da baba maryam ta karasa gurin baffa tana zama cikin fara'a tace" ina kwana Abubakar fatan na same ku lafiya"?. Cikin jin dadi baffa ya dubi baba maryam yana cewa"lafiya 'kalau maryama ya hanya sannun ku da zuwa". Zama baba maryam ta gyara tana kallon baffa tace" yauwa Abbakar sannun ka domin kaine ka cancanci awa sannu domin ban kyauta maka ba kuma ina mai baka hakuri na wuce ka'idar dana dauka a gurin ka wallahi yanayi na aikin ne a hakan ma yau da zamu taho ba kaga irin damuwar da hajiyan tay ba musamman da taji nace mata Safah ta taho kenan baza ta koma ba aure za'ai mata". Murmushi baffa yay" a'a maryama karki damu babu abinda na taba ji game da tafiyar ku kullum addu'a ta shine ku dawo lafiya cikin aminci kuma Allah ya amshi rokona na gode sosai ji yadda 'yata ta sake kyau da girma farkon shigowar ta badan sallama ta fara yi nadau muryarta ba da bazan gane taba inba tai magana ba ta canza sosai". 'Yar dariya baba maryam tay daidai almajiran sun gama shigowa da kayan ta soma budewa tana fito da dinkuna kala biyar duk shadda sun sha aikin wuta sai fitar da sheki suke tace" baffa wannan naka ne cikin dukiyar safah wacce tay aiki a gidan da mukaje ta dinko maka wadannan kuma sauran buhunan akwai kayan abinci data sayo nan ma da kudinta kuma ta sai wasu kayan na bagaren abinda ya shafi kayan daki da sauran su sannan hajiya tayi mata kyautar kudi dubu hamsim gashi tace a bata ga nata ragowar kudin aikin tane sannan ga wasu kayan data dinkowa kakanun ta su Hadiza ga kala biyu kuma shima ta yowa Asabe wannan shine bayanin baffa". Farin ciki sosai baffa ya nuna dajin dadin sa ga baba maryam ya kuma yi mata godiya da jinjinawa a gareta lallai tayi halacci kuma itadin mace ce wacce za'a dauki duk yarda a bata. Suna cikin zance suka ji Asabe ta fashe da kuka tana zaman yan bori a kasa dukka juyawa sukai kowa na mata kallon mamaki baba maryam data fahimci kamar kukan takaici take yasa cikin basarwa tace" subahanallahi Asabe me kike haka? kamar wata yarinya ko baki da lafiya naga kina hada zufa"? ta karasa maganar tana mata kallon bakin ciki saidai ya kashe ki. Kai Asabe ta girgiza tana share hawaye tace" a'a maryam ba jinya nakewa kuka ba kukan dadi ne ganin Safara'u ta dawo kullum muna cikin tunanin ta kinga malam har jinya da rashin lafiya mai tsanani yay saidai a kwantar saidai a tayar baya iya cin komai yana sambatu kodai yarsa baza ta dawo ba wani lokacin ma cewa yake Adamawa zaije ya taho daita nice mai rarrashin sa cewa ya kara hakuri zaku dawo shine tuna hakan ya sani kuka". Wani kallo baffa ya mata na zallar mamakin karyar datai masa kuma a gaban sa zaiyi magana baba maryam itama da tai watsi da zancen Asaben ta sashi a kwandon shara don tasan ba gaskiya bane tace" to yayi ai dama haka ake son mutum yana kula da tarbiyyar yaransa baiyi laifi ba yayi daidai balle nasan hakan bazai yuwu ba kawai zancen kine mara kan gado kin rasa abin fada kunya ta kama ki abu ga marar hali bera🐁 a kasuwa shine kika bullo ta nan". Sak Asabe tay kamar ruwa ya cinye ta tana zare ido maida hankalinta baba maryam tay kan baffa tana cewa"to Abbakar nizan tafi gidan Hamza sai gobe naje gidan kawu Hakilu kuma ina nan saina huta kafin na koma Adamawa yaushe ne bikin don hajiya tace min idan na tambaya na kirata a waya na fada mata itama zata zo". Kai baffa ya jinjina cikin fara'a yace" insha Allahu nan da kwana sha biyar tunda yau watan kwanan sa biyar sai ayi da ashirin"mikewa baba maryam tay to shikenan Allah ya nuna mana bari na karasa"godiya baffa ya mata yayin da Safah ta mike tana dauka mata jakarta don tayi mata rakiya suka fita a gidan. 🙆👍 Mrs Al'ameen Ahmad ce We will meet again lovers my everything is for you. Ana tare👭💝. TNK 4 💞 me. Typing📲 10:10pm sunday march 2023 🍇🍇 SAFREEYYAH🍇🍇 ✨ANNURI 📝WRITER'S 👪ASSOCIATION Gidan karba hannu biyu da zaman lafiya group din annuri na marhabun lale da ba'kinta🤗. YUSRAH MS ABUBAKAR GIMBA Ayya nagode da kulawa kwana biyu bakwa gani na online naga sakonni da yawa kuma nagode wallhi kwanakin nan bani da lafiya ne amma insha Allahu zan daure na rika yi muku typing ko baida yawa ne. GA NAKU PAGE DIN SISTERS DINA NA JINI ALLAH YA KARA HADA KANMU AMEEN. Naja'at Aminu Naja'at Ishaq Mariya Yakub Sarah Yakub Fatima Umar Nasiba Magaji Fadilah Saleh Aishat dan baba. DEDICATED TO. MY MOTHER MAY ALLAH HELP AND BLESS YOU MAMANA I LUV U WITH ALL MY LIFE MY EVERYTHING IS 4 U MAMA. 👏Allahumma bika amsaina wa bika asbahna wa bika nahya wa bika na mutu wa ilaikal masir. 💝 💝💝 💝💝💝 💝💝💝💝 💝💝💝💝💝 #YUSRAHMS# NO.43👉 44 Bayan sati biyu Fatima na zaune tare da bayin ta suna dan taya ta hira sakamakon Emir baya nan yayi tafiyar kwana biyu zuwa Germany suna cikin bata labari Ammy ta shiga cikin tsawa ta kalli bayin dake kewaye da Fatima tana cewa" ku dabbobi ku barnan kafin sakan daya bana bukatar kowa". Cikin mamaki Fatima ke kallonta ita kuma wannan lafiya kodai tabin hankali ya soma kamata zata shigowa mutane guri bako sallama kamar wacce ta shiga coci. Da gudu gudu bayin suka fita jikina rawa yayin da Ammy ta mayar da kallon ta kan Fatima tana cewa" ke kuma na dawo gareki wato har suna kika canza waike gimbiyar sarki ko saboda samun guri akuya🐐 da tukin tuwo to wallhi baki isa ba kinyi kadan ki sani wannan sunan nawa ne don haka kiyi gaggawar goge shi a bakin bayi kafin kiga irin matakin dazan dauka wanda bazai miki dadi ba". Kau dakai Fatima tay kamar bada ita take ba ta bawa iska ajiyarta cikin takaici Ammy tace" malama ba kiji abinda nace bane"?. Ba tare data kalleta ba tace" au sorry maman Amfal sannu da zuwa ga guri ki zauna bari insa a kawo miki abin sha mai dumi domin naga kamar sanyi ke damun ki". Ashar Ammy ta saki" nice zanyi magana kice sanyi na damuna wato ga mahaukaciya ko gargadi nazo nai miki daf da duka hawainiyar ki ta kiyayi rama ta wannan kinibibin da kisisina da kike a gaban mai martaba kamar wata tsohuwar karuwa ya ishe ki haka baki isa ki nuna min komai ba nina wuce inda kike zato na". Dariya Fatima tay tana kallon ta tace" tofa yauga hauka dangi dangi sannun ki da kokari tun dazu kina ta haushi saidai bana fahimtar abinda kike cewa magana kike ko bakin kine a haka dan na fahimci kamar bakya cikin hankalin ki kije a baki ruwa da abinci kici idan kin dawo daidai saiki zo muyi maganar domin ni a yanzu bani da lokacin shirmen ki dama waya zanyi da rabin raina dalilin bayi na taya ni fira yasa na hakura kinga yanzu kin taimaka min bari naje naji ya lafiyarsa idan kin gaji da tsaiwar ga guri nan ki zauna ko ki kwanta nina shiga daga ciki". Tana fadin haka ta mike rike da waya tana danna kiran Emir tare da karawa a kunne tace hello dear gaskiya nayi kewar ka yaushe zaka dawo na shiga maraici da yawa daidai ta bude kofar bedroom ta shiga zata rufe saida taywa Ammy gwalo😝 sannan ta rufe tana dariya domin da gaske da Emir suke wayar handfree tay don Ammy ma taji muryar sa. Wani irin bacin raine da takaici ya dabaibaye Ammy ita kadai ta rika waige waige kamar me neman wani abu ganin gurin cin abincin Fatiman an shirya shi kuma da alama bata ciba a fusace ta nufi gurin ta soma watsi da kayan tana tarwatsawa saida ta baje komai sannan ta koma kan kujerun palon tana hade su wasu kuma ta wuntsila su saida ta gata ta gama lalata mata palon tayi kaca kaca dashi sannan ta fice tana zage-zage. Bayan tahowar su safah daga Adamawa mk bai sani ba saida daga baya ya sani ba karamin tashin hankali ya shiga ba har rama yay kamar mara lafiya musamman daya ji hajiya tace baza ta dawo ba aure za'ai mata. Yau week end Alawiyyah na gidan mk gurin Abidah suna zance Alawiyyah ke cewa" nifa ba wuni nazo miki ba tafiya zanyi saboda taya mum aiki". Kallonta Abidah tay" wanne irin aiki kuma ina barorin gidan naku"? dariya Alawiyyah tay" kai dan Allah harkin sani dariyar daban shirya ba wai barori sun tafi gida mana ita Safah naji mum na cewa baza ta dawo ba aure ma za'ai mata". Mikewa Abidah tay cikin farin ciki tace" dan Allah da gaske kike Alawiyyah aure za'ai mata? wani tsalle ta daka kai amma naji dadi wallhi da baza ta dawo ba haba yarinya duk tabi ta tare gida kamar mayya". Kallonta Alawiyyah tay" ikon Allah ke kuma wannan matar farin ciki haka me ta tare miki"? Dariya sosai Abidah keyi tana juyi tace" ba ruwan ki kedai tunda kin min albishir zan baki kyauta" tabe baki Alawiyyah tay" a'a nagode rike abarki nina wuce" bata jira jin me Abidan zata ce ba tafice a palon tana mamakin ita kuma wannan murnan barin Safah gidan name take?. Safah ce zaune tare dasu hadiza taje musu ziyara sannan saura sati bikin ta malam ya kalleta yana cewa" Safara'u d'an uwanki Abdullahi yazo mana ziyara ya dade a nan bayan tafiyar ki Adamawa inaga dai ba rabon ku gana ko kuma sai bikin nan naki tunda yan kwanaki suka rage sai a sanar dashi kinga da zai tafi ma har wata salula ya barmin wai muna kiran sa niko bansan inda zan kunno maganarsa muji ta ba tana nan a ajiye Hadiza dauko mata wannan salular ta gani ko zata iya danno mana shi". To Hadiza tace tana mikewa ta shiga daki Safah kam zuba ido tay cikin mamaki taga meye na Allah yake nufi da salula sai taga hadiza ta kawo mata waya keypad a kwallinta tana cewa" gata duba mana tunda ke kinje binni kila kinga ana amfani da ita mude bata shigo mana nan ba". Dariya Safah tay tana karba tace" wai dama waya kuke cewa salula na dauka wata camera zan gani katuwa bari muga indai akwai kati na kira shi". Bude wayar tay tana shiga cikin contect ba number sai guda daya itama ba suna tunani tayi may be ko itace number tashi dan haka kawai ta danna kira tayi sa'a kuwa ta shiga saidai harta katse ba'a daga ba dan tsaki tay tana cewa" to ai gashi na kira ta shiga amma ba'a daga ba kodai kawai ya zura ku a kwalba ne"?. Dariya na Allah yay yana kallonta yace" eh ba'a kwalba zaki ce ba a bututun mai ko mizirari ya samu sake kunno shi mu gani" murmushi Safah tay wai sake kunno shi kamar gidan radio kara danna kiran tay wannan lokacin kuma sai aka kashe. Na Allah ta kalla tana fadin" to gashi yanzu ma ta shiga ya katse kiran dama dai kila ya baku ne dan kuyi ta kallonta matsayin photo decoration tunda bata da wani amfan........ Bata karasa ba wayar tahau ringtone dan zubawa number ido tay bata daga ba Hadiza tace" to ya kunno naji tana kara kuma banji maganar saba ko saita gama zamu jishi"?. Kai Safah ta girgiza dariya na cinta jin abinda Hadiza ke fada batai magana ba ta daga kiran tana sawa a handfree ta mika musu". Kallon ta na Allah yay" me zamuyi ko haka ne kunnowar"? Ba arziki Safah ta mike da gudu tana yin hanyar kofar gida sannan ta saki dariyar da take rikewa tana cewa"kasa a kunne kayi magana zaka ji shima yayi". "To na Allah yace yana karawa kamar yadda tace yayi yace" salama alekum Abdullahi kana jina"? daga can bangaren Abduljabbar dake zaune yana duba wani littafi yay murmushi yana cewa" wa alaika salam kakana na kaina ya kake" cikin mamaki na Allah yace" lah ikon Allah Hadiza kinji da gaske ta kunno shi". Karba hadiza tay tana kallon wayar tace" wai Abdullahi maganar ka nake jine" eh nine meyasa idan nakira wayar saina jita a kashe"? 'Yar dariya Hadiza tay tana cewa" ai bamusan yadda zamuyi mu kunno kaba yanzun ma Safara'u ce data dawo daga Adamawa muka ce ta dannoka". Dan shiru yay zuwa can yace" wace haka? ko yarinyar da kuke cewa sister nace" zaro ido Hadiza tay" tofa meye sister kuma"? dan rike kai Abdul-jabbar yay" ina nufin kanwa ta da kuke fada lokacin da nazo". Na Allah yace" eh fa Abdullahi ashe baka manta ba itace". "Ok bata wayan". Kallonta Hadiza tay" to gwana idan kin gama dariyar zo ki karba zaku gaisa da yayan naki" dawowa Safah tay tana karbar wayan tare da cewa" hello" dan janye wayar Abdul-jabbar yay yana kallon screen din kamar ita yake kallo dan lumshe ido yay tare da cewa subahanallah mene haka yake shirin faruwa dani"?. Jin anyi shiru yasa Safah ta kalli wayar ganin ba katse kiran yaiba tace" ina yini"? murya 'kar'kar yace" ya kike"? Dan jinjina kai Safah tay wannan akwai jan aji cikin mazewa tace" kalau yaya dama nace bamu taba haduwa ba gashi muna matsayin yan uwa amma dai zaka zo bikina daga nan sai muga juna ko"?. Cikin mamakin surutun ta Abdul-jabbar yace" eh zanzo saimu hadu" murmushi Safah tay wanda ya jishi tana cewa" to Allah ya kawoka yayana nagode sosai". "Ok ba damuwa bari na gama wani abu zan kira saimu karasa maganar" to tace yayin da ya kashe kiran yana rufe littafin tare da dan rufe ido. Ji yay Amfal na cewa" bros dawa kake waya ne naji muryar mace gashi naga ka shiga yanayi kodai aunty na samu you ban sani ba"? Bude ido Abdul-jabbar yay yana kallonsa yace" eh sai akai ya"? dariya Amfal yay" kai koda naji dama naga kwanakin nan kana yawan tunani ashe hubby ne ya shige ka lallai kace zamu sha bikin babban yaya". Ko kula shi Abdul-jabbar baiyi ba Amfal yaci gaba" Allah bros har naji dadi kaga nima ya kamata na nemo muyi auren nan tare kuma ba zama honey moon ba kama kafar yaro amma wai a ina ka samu lady ban sani ba kuma da yaushe yar wanne garin ce"?. Girgiza kai Abduljabbar yay yana kallon Amfal yace" oh kaga matsala ta dakai kenan please ka rabu dani karka dora min headache" dariya Amfal yay" ka huta sosai ango nikam na shiga wanka duk daren dadewa da kake boye min auntyn nawa zan ganta" wanka ya shiga yana cewa" wayyo Allah na dadi kashe hajiya bros zaiyi aure" Abdul-jabbar na jinsa bai tamka ba domin Amfal dan caza kaine ko ba nepa dole sai ana masa uziri. MRS AL'AMEEN AHMAD💝. TYPING📲 YUSRAH MUSA ABUBAKAR 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 Home of hospitality and harmony #YUSRAHMS# NO.45 👉 46 Na Allah dake kallon Safah yace" to yaudai kun gaisa saura haduwa itace mai wuya" mikewa Safah tay tana cewa" bari nadan ari wayar nan nayi kira ina dawowa" cikin tsokana Hadiza tace" a'a fa kodai-kodai" fasa tafiya Safah tay ta juyo tace" kodai-kodai me"? Karfa ku fassara ni na Allah yace" kodai-kodai kin kyasa shine zaki mana dan waken zagaye ki kira shi"?. Yatsina fuska tay" cafdi wa ya fada muku kunji ku da zargi to bashi zan kira ba nayi ya da murtalan"? na Allah yace" ba wani kedai fadi gaskiya karki yaudare mu muji labari ya canza" dariya Safah tay tana fita tace" yanzu zan dawo muku da salular ku". Tana fita tafiya tay maidan nisa inda tasan ba mutane kuma bamai jinta takarda ta buda tana saka number ta kira bugu daya kuwa ta shiga kuma tay sa'a aka daga mata. Dan daidaita murya tay tana cewa" hello hajiya ina yini ya gida ina Alawiyyah"? Daga can bangaren hajiya tace" lafiya dawa nake waya ban gane mai magana ba"? dariya Safah tay tana cewa" hajiya nice fa Safah dama kiran kinai mu gaisa a gurin baba maryam na karbi number". Murmushi hajiya tay" ayya Safah ashe kece ya gida fatan kun sauka lafiya yasu baffan ki? ki gaida min shi da kyau". Kai Safah ta daga" to hajiya insha Allahu zaiji". Shiru sukai na wajen minti biyu ba wanda yay magana sai daga baya hajiya tace" Safah ina fatan dai lafiya babu wata matsala naji kinyi shiru meya faru ne ko akwai wani abu"?. Zama Safah tay kan wata sararriyar bishiya cikin tunanin yadda zata fadawa hajiya abinda ke ranta tace" am dama wata magana nake son fada miki amma na kasa tun muna nan saboda tsoron yadda zaki fahimce ni amma yanzu ya zama dole na fada miki gaskiyar komai danki dau mataki tun wuri". "Ok Safah ina jinki fada min ko menene zan fahimce ki kar kiji komai ke tamkar 'yata haka na dauke ki". Sauke ajiyar zuciya Safah tay cikin rashin jin dadin abinda hajiyan zata ji daga bakin ta tace" dama magana ne akan mk lokacin dana bata tsawon kwana uku ba kowa ne ya sace niba sai shi bayan na fito daga part dinku ya shaka min wani abu a hanci daga nan bansan komai ba sai ganina nayi a gidan sa akan gado kuma da nayi yunkurin gudowa ya tare ni a palon sa yace saina amince masa na bashi kaina zai barni na taho hakan shine burin sa kawai a gare ni". Yayi iya juyin duniya da lallami naki amince masa a gaba na ya kira wata budurwa tazo gidan wai ta nuna min yadda ake wayewa" dan shiru tay sai kuma ta fashe da kuka tace hajiya kinsan abinda sukai a gaba na ya sadu da ita kuma yace wannan ba bakon abu bane a gurin sa yana da yan mata irin ta baza su kirgu ba da naga basa cikin hayyacin su shine na gudo daga gidan saiya biyo ni hanya ya dauko ni ya dawo dani gidan ku". Shine washe gari da kika tambaye ni ina naje tsawon kwana uku kunya da nauyin ki yasa na boye gaskiya na kasa fada miki kuma yanzun ma dan Allah hajiya ki fahimce ni kiwa mk fada da nasiha kina masa addu'a Allah ya shirye shi amma kwarai yana da hali mara kyau a boye ki yafe min nasan za kiji babu dadi amma nima ba yadda na iyane ya zama dole na fada miki gaskiya". Wani irin juyi kan hajiya yake jin abinda Safah ke fada mata wanda batai zato ba dakyar tace" na fahimce ki Safah kuma na gode da kika sanar dani wannan sirrin duk da bansan yawan shekarun da aka kwashe mk yana wannan abun ba ki gaishe min da kowa karki damu kuma kiyi hakuri abinda yay miki sai an jima". Tun kafin Safah tay magana hajiya ta kashe kiran, numfashi Safah ta fitar cikin razani tare da dafe kai gaban ta yay wani irin yankewa lokaci guda bugun zuciyarta ya karu cikin tashin hankali ta fara maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un sai yanzu take jin dama bata fadawa hajiya ba mema yasa ta aikata hakan wanne hali hajiya zata shiga wanne mataki zata dauka akan mk tana tsoron fitina ta biyo baya. Tunda suka gama waya hajiya ta kira mk cewa yazo yanzun nan tana neman sa kada ya kuskura ya bata mata lokaci gaba daya nutsuwa kaurace mata tayi zulumi bakin ciki sune tare da abinda mk yake aikatawa wanda bata sani ba su kawai take hangowa duk inda ta kalla mikewa tay ta soma zagaya falon ranta na mata suya akan halayyar mk wanda tana matsayin mahaifiya gareshi bata sani ba saidai taji daga wata majiyar amma tayi asara da bata fahimta tun farko ba ta sani cewa indai aka dauko yar aiki bata cin nisan wuta mk zaisa mata kahon zuka saiya kore ta amma bai taba nuna wani abu akan Safah ba saima yabon girkin ta da yake ta dauka gamon jini ne ashe akwai kullalliyar da yake kullawa a boye. Shigowar mk kenan ya nufi gurin hajiya dake ta zagaye palon tare da cewa" mum gani lafiya naji kin kira ni a waya muryarki wani iri meya ke faruwa"?. Juyowa hajiya tay idon jawur dashi tana kallon mk a fusace wanda baiyi zato ba yaji saukar wani 'kwak'kwaran mari a fuskarsa kafin ya dago ta kara wanka masa wani cikin kuka ta soma magana" musaddiq ka wulakanta mu ka tozarta mu kayi watsi da tarbiyyar da muka baka ka nuna kaiba d'a nagari bane yanzu dabi'a ce mai kyau wannan ka dauka kamar kaidai kayi asara ace mazinaci ne mai lalata yaran mutane baka tsoron gaba ya naka yayan zasu taso kila ma sannan ba ranka mk me ka rasa tun yaushe nake binka kai aure ka'ki sai kace min da lokaci ashe kasan irin mummunan aikin da kake aikatawa tun kafin lokaci ya kure maka ka tuba ka koma ga Allah ka daina abinda kake idan kaki akwai ranar mutuwa kuma ita kayi shirinta koda yaushe ba'a sa mata rana ka tuba mk ina gargadin ka". Jikin mk na rawa cikin tashin hankalin ya akai hajiya tasan yana harkar mata ya dago yana kallon ta yace" mum waye ya fada miki wannan maganar? bansan komai ba". Hajiya da hawaye ke fita a idonta tace" baka san komai ba kana nufin karya akai maka ba halin ka bane mk duk abinda zakai kasa tsoron Allah a lamarinka maimaikon dana fada maka jikinka yay laushi ka tuba zuwa ga wanda ya halicce ka saika nemi karyatawa kana zamewa harda baka san komai ba"?. Shiru mk yay cikin damuwa hajiya taci gaba" naji kaddara bakasan komai ba sharri akai maka amma Safah zatay maka karya ne baka aikata ba zata cemin kayi yanzun nan muka gama waya daita ta fada min duk abinda kai mata kaiko kunya baka jiba da kuma ace yarinyar bamai nisan hankali bace ta fadawa maryam me kake tunani kudin mu bashi zai ceto kaba da kuma itadin ta kasance mara kamun kai mai watsi da tarbiyyar iyayen ta kamarka saita biye maka kuyita aikata alfasha bamu sani ba harsai ranar tonon asiri randa cikin ya bayyana gareta kasa mu shiga uku". Cikin sanyin jiki mk ya durkusa gaban hajiya yana cewa" kiyi hakuri mum na bata miki rai". Cikin tsawa hajiya tace" ka yarda ka aikata kenan ka yarda halinka ne musaddiq bazan gaji da ce maka ka ji kunya ba kuma kayi asara shashashan yaro kawai kuma kada ka kuskura na ganka a palon nan idan na fito zamu neme ka sai dadyn ka ya dawo fita kaban guri karka sa na kama da wuta da zunubin ka". Cikin jin kunan kalaman hajiya mk ya mike yana fita a palon zuwa harabar gidan ya shiga motarsa tare da kifa kai a sitiyari ya runtse idonsa saiji yay hawaye masu zafi suna diga masa cikin mamaki ya bude idonsa yana kallon mirron jikin motar ganin tabbas shawayen ne da gaske wani irin dukan glass din motar yay tare da furzar da iska mai tsananin zafi yana jijjiga kansa ko tsoron ya masa ciwo ba yay. Lokaci guda kuma ya tsaya da komai ya nutsu da wani kalar murmushi wanda bamai gane ma'anarsa sai shi yace" hummm Safah! Safah!! Safah!!! Nine kika tonawa asiri kamar yadda kike fada kika sa ni a tsaka mai wuya na rantse da Allah saina nemo ki duk inda kike zan binciko ki saina dau matakin da zaki dana sani baki da wani amfani yanzu a gareni mutuwar ki na hannuna baza ki sake jin dadin zaman duniya ba musaddiq bamai hada kafada dani ki jira zuwana gareki yau-yau din nan basai gobe ba bana tunanin za kiga wayewar gari domin idona idonki saina kashe ki muje zuwa". Figar mota yay da mugun gudu ya fita a gidan yana tafiya wani gidan nasa da ban ba inda Abidah take ba waccan gidan sirrinsa ne ko iyayen sa basu san da gidan ba acan ya yada zango kafin ya gama shiri ya tafi neman ta. Safah na zaune har wannan lokacin akan itacen duk jikin ta a mace ta kasa tashi ga hawaye da yaki tsayawa a idonta jin ana kiran sallar magriba yasa ta mike ta soma tafiya zata koma gidan su Hadiza takai musu waya. Jitay ance" Safara'u daga ina dama ke nake nema tun safe na aiki Aisha gidan ku baffan ki yace kina gidan su na Allah". A firgice Safah ta juya ganin murtala yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da kakalo murmushin dole tace" au ashe kaine daga ina haka"?. Shima murmushin yay suna dan tafiya a hankali yace" na karbo mana ankon mune nida ke gashi naki kije dashi gida wannan ledar kuma cingam ne da zaki rabawa kawayen ki akwai kuma bakin lalle da ja yanzu dana sayo miki ki rangada min kunshi mai kyau sannan akwai kudi a ciki abinda kike bukata zaki iya fadawa Aisha saita sanar min sai anjima na wuce gida". To nagode Allah ya kara arziki" kai ya daga yana wucewa ita kuma ta shiga gidan su malam na Allah domin tay sallah sai bayan isha ta tafi gida. Misalin karfe goma na dare mk ya fito cikin shirin kaya bakake harda face mask yana saka wata hula wacce iya idonsa ne a waje zai fita kenan Abidah tace" wannan shigar kuma fa kamar wani shedan ina zaka je karfe goma na dare a haka"?. Juyowa yay yana kallonta da muryar shi data riga ta canza sakamakon magana da baiyi ba tun la'asar yace" gidan ubanki zanje idan kina da sako shegiyar yarinya na sako dake cikin al'amari nane balle kimin shishshigi". Jada baya Abidah tay da sauri tana cewa" Allah ya baka hakuri" tsaki yaja kamar zai shako ta sai kuma ya fasa yana fita daga palon mota ya shiga kawai yabar gidan tare da zaro wata wuka cikin gidan ta sai sheki take dariya yay yana cewa" kwantar da hankalin ki wuka zaki sha jini nan da yan awanni Safah gani nan gareki". Har kusan asuba mk na yawo amma babu wani haske akan abinda ya fito nema gashi baisan sunan garin ba balle ya tambaya ganin hasken rana ya fito yasa ya cire wannan bakaken kayan yasa riga da wando irin na mutane yaci gaba da tafiya har yazo wata bishiya ga yunwa na damunsa parking yay da motar yana fitowa ko zaiga wani mutum amma dai babu kowa tafiya ya farayi da kafa har yay nisa da motar jin ya gaji tunda bai saba ba ya tsaya a wata rijiya yana zama kan wani dan dutsi dake kusa da ita kafin ya samu wani yazo. Yana nan zaune wani almajiri yazo shan ruwa mk na kallon sa saida yasha zaitafi yace" kai danzo na tambaye ka mana". Cikin tsoro yaron yace" a'a malam ya hana mu yace indai mukaga bako ya kira mu ba dan garin nan ba kar muje" jin ya ambaci malam yasa mk yace" to naji basai kazo ba tsaya anan din nai maka tambayar waye babban malami a garin nan"?. Kai tsaye almajiri dake sidin robarsa ta bara yace" sunan sa malam na Allah" kai mk ya jinjina" yana da wata 'ya ana ce mata Safara'u ko aurenta ma zaiyi"?. Kai almajirin ya girgiza" a'a malam na Allah bashi da d'a ko daya saidai malamin mu shine yake da 'ya Safara'u ta dawo daga Adamawa ita da baba maryam gobe ma zaiyi aurenta a masallacin juma'a". Cikin farin ciki mk jin ya samu almajirin mahaifin ta yace" to gaka ma da har ina kiran ka kana kin zuwa dama gidan sa nake nema ni daga birni nake kuma ni malamin tsafta ne muje ka nuna min gidan sa daga nesa zan baka irin kayan dana kawo masa ka gani biscuit da coculate muje maza ka kaini". Da sauri almajirin ya wuce gaba mk ya bishi a baya da wani murmushin mugunta daga nesa da gidan suka tsaya almajirin yace" ga gidan can wancan malamin me rawani da yake zaune a tsakiya to shine baban ta gurinsa aka aiko ka" kai mk ya daga yana cewa" na gode kaji yaro toga caculate din taka" . Karba almajirin yay yana tafiyarsa mk kuma ya zubawa baffa ido ko ba'a fada ba wannan mahaifin Safah ne ga dogon hancin ta nan ya gani juyawa yay yana komawa wajen motar sa bai karasa gurin baffan ba. Mrs Al'ameen Ahmad ce,👍 Till we meet Thank for your support🌹. Typing 📝 Yusrah Musa Abubakar Gimba Ayi hakuri da typing error🚨 banjin dadi😢 kwana biyu. 💫ANNURI 📝WRITER'S 👪ASSOCIATION💫 🏡Home of 🤗Hospitality and 💚Harmony 🍇SAFREEYYAH🍇 💞👉 Zarah Musa dan adam 💞👉 Naja'at Musa Abubakar 💞👉 Kubrah Sani Muhammad. #YUSRAHMS# NO.47 👉 48 Safah kam na can tana shan lalle a gidan wata mata wacce itama yarta ta dawo daga birni gurin yan uwan su ta koyo acan tazo tana yi. Da gudu Aisha ta shigo gidan tana guda kamar hancinta zai cire cikin dariya tace" ahayye ayyuruyuri nanaye anayi muna jin dadi ana bari muna jin haushi ta yaya murtala ikon Allah bada kanki a sare kije gida kice ya fadi kai jama'a Safara'u irin wannan kyau haka lallai kice gobe ango zai shana jifa wani kamshi da kike kamar kin fada a rijiyar turare meye ne sirrin fada min naji kafin nawa yazo kinga na kware". Harararta Safah tay" idan kin gama shashancin zaki iya bani sakon dana aike ki" dariya Aisha tay" beban komai ba yace bashi da kudi kiyi hakuri" wani kallo Safah tay mata tana cewa" me kika ce"? Cikin tsokana Aisha tace" yace bashi da ko kwandala duk kin cinye masa kudi" Au haka ma yace dama in yana da kwandala ma me zatai mai sake min lallen nan Furera na dawo" jin haka yasa da sauri Aisha ta fito da dubu biyu tana mika mata tace" gashi nan ya bani kar kisa yanzu yazo ya zane ni da bulala kowa yana biki jikinsa a ware ni ina dingishi kamar gurguwa" Ke kika sani can da yawar ki debo min ruwa ni nayi wanka mu tafi gida" bokiti Aisha ta dauka tana cewa" yanzu ma kuwa amaryar mu bayan yayana za'a burge naki debowa bani minti daya ina dawowa ta shagonsa zanbi ya sako kwalbar turare guda daya a ruwan" tana fadin haka ta fita dan daga murya Safah tay yadda zata jita tace" banda lokacin shashancin ki nidai burina ki kawo min ruwa malama". Bayan sallar isha dukkan nin kawayen Safah sun hadu zasu taya ta cin tsire suna zaune a karkashin bishiyar zaitun din cikin gidan su sun taru yan kamun amarya su Asabe sai juyi ake ana gadara ansha sabon dinkin da Safah tayo mata a Adamawa gefe guda tukunya ce babba akan wuta ana dafa abincin yan kamu. Safah suna zaune a daki itada baffa cikin nasiha baffa yace" Safara'u tun yau base gobe ba zan fara miki nasiha ki rike darajar auren ki murtala yarone me hankali kuma kinga ke marainiya ce baki da uwa baki da me baki shawarra saini din dai dan Allah Safara'u idan Allah ya tashe mu lafiya gobe za'a daura miki aure kije dakin mijinki ki zama me hakuri da juriya ki rike Allah ki roke shi zai amsa miki ki tsaya a kofarsa zai karbeki ki nufe sa zai cire ki daga cikin kunci da damuwa ki dogara dashi ya isar miki ki kula sosai ke kadaice 'yata ina son ki amma dole aure shine zai raba mu inai miki fatan alkhari Allah yayi miki albarka ya tsare ki a duk inda kika tsinci kanki". Safah da hawaye ke zarya a kuncin ta da 'kyar muryarta na rawa tace" amin baffa nagode lallai kai ubah ne nagari wanda kowacce d'iya zatai alfahari da kai". Kai baffa ya jinjina zaiyi magana suka ji anyi sallama a kofar dakin wani yaro na cewa" wai ance Safara'u tazo a waje". Kallon juna sukai itada baffa kafin tace" kaje kace wai inji waye"? Dakatar da yaron baffa yay yana cewa" baki sani ba ko murtala ne kije ki gano mana amma karki dade kinga kin bar kawayen ki kuma na ji kina cewa a gurin maryama zaku kwana dasu" eh baffa acan zamu kwana bari na dawo" fita tay yayin da sukai karo da Aisha. Dan dafe goshi Aisha tay tan acewa" wash saurin me kike haka zaki lagarta ni"? tura ta gefe Safah tay tana cewa" ke matsa mana kin wani tare min hanya murtala ne yake kira na" dariya Aisha tay" oh wannan shine angon zumudi inace gobe iyanzu an raka ki amma yaudin ma bazai barki ki huta ba" kallonta Safah tay" kinga ban hanya kar yaga na dade" matsawa Aisha tay" inye cankadi kaga masu miji gaskiya kar yaga kin dade duk da komai kikai burgeshi yake ke amarya ce bakya lefi ko kin cinnawa shagon angon ki wuta zaice kuskure ne ki karbo kudin tsiren tare dani dan Allah" banza Safah ta mata tana fita a gidan. Ganin bata ga murtalan inda ya saba tsayawa ba idan yazo gurinta yasa ta cewa yaron" kai yana ina ne ban ganshi ba" dan tafiya sukai yaron yace mata" yana waccan bishiyar yace ki same shi" to tace yaron kuma ya juya abin sa. Cikin mamaki Safah ta nufi bishiyar domin ta gano shi a zaune amma me yasa yau sai nan bayan koda wasa bai taba yin hakan ba ita kadai take tunani a zuciyarta harta karasa gurin da sallama tace" haba murtala yau kuma shirar harnan bayan layin mu me yasa baza ka karasa ba"?. Mikewa tsaye mk yay yana cewa" wannan hamsim ne ba murtalan da kika sani bane barka da zuwa big girl nasan kinyi mamakin gani na amma ina tunanin kinsan abinda kika aikata min jiya kodan ba lallai ki tuna ba tunda karamar kwakwalwa gareki me kike tunani a kaina dama saboda rashin hankali da kike cemin wata rana zaki,tona min asiri gurin mahaifana da gaske kike? yayi kyau saidai karki manta abinda nace miki a waccan lokacin cewa idan tsautsayi yasa kika tona min asirina zan kashe ki kuma ban fasa ba yanzu ma abinda ya kawo ni kenan fatan kin shirya amsar hukuncinki big girl idan harkin shirya to nima a shirye nake". Duk jikin Safah rawa yake saboda tsoro dan ja da baya tay tana kallon sa tace" ban fadawa hajiya don tayi maka wani abuba nafada mata ne tayi maka fada kuma ka shiryu ka gane cewa abinda kake bashi dakyau amma tunda kaidin batacce ne sai ince Allah ya shiryar dakai kuma kayi hakuri abinda ya faru na roke ka mk ba wata alaka tsakani na dakai ka rabu dani nayi rayuwa gobe ne daurin aurena karka bata min shiri bani da wani hadi dakai ka dauka ban sanka ba ka manta da komai ka gyara halin ka kanemi yafiya a gurin wanda ya halicceka ka daina saba masa kai mutum ne baudadde mara kyan hali kayi kokarin gyara halinka tun lokaci bai kure maka ba". Kara bude idanuwan sa yay akanta jin abinda tace yana jijjiga kai yace" humm big girl kina ban dariya kuma kina bata lokacinki amfada miki wa'azi nazo kimin idai haka kike tunani to kinci kai babu abinda ya kawo ni wannan jakin sokon kauyen naku sai daukar fansa akan ki baki gane bane amma yanzu zan ganar dake ". Cikin dakewa Safah tace" me kake nufi"?. Fito da wuka yay yana kallonta yace "ga abinda zanyi kasheki zanyi na shafe tarihin ki a rayuwa shine babban burina". Matsawa Safah tay tana kallonshi tace" karya ne wallhi nafi karfin ka wulakanta ni kaidin banza". Jin abinda take cewa a fusace ya zare wukar daga cikin gidan ta ya nufo tada iya karfinsa ganin da gaske yake kashe ta zaiyi yasa a guje ta juya zuwa gida amma tayi rashin sa'a yasha gaban ta yana huci yace" ina kuma za kije ashe dai ina da zarra ki tsaya mana tunda kince kinfi karfina". Ganin ya sake tahowa gurin ta gadan-gadan yasa da mugun gudu ta juya yayin da yabi bayan ta da iya karfinsa............. Tofaaaaa muje zuwa..... ga mai son cigabansa sai a tuntu'be ni tanan. +234 816 098 3083 #400 Account no:2410673902 Yusrah Musa Zenith bank🏦. MINISTER ASHRAF #300 ME KAMAR SARKI #300 ROYALTY 500 Ga masu bu'katar siya Kuna iya kumin magana da wancan WhatsApp number Nawa ta sama. YMA DUTSE NEW WORLD🍎🌏. 🌹💓🌹💓🌹💓🌹💓🌹💓🌹💓🌹💓 🏵️🌹🌼.