*MU RAYU A TARE*                                 Zainab Habib (Mom Islam Book1 Page 1-2 Zaune take gaban mahaifiyar tata wacce ta kasance mahaukaciya, Iffat yarinyar ƴar shekara huɗu, tunda ta fara wayo ta gano basu da gidan daya wuce bola, inda taga mahaifiyarta take zama koda yaushe. Iffat yarinya ce mai wayon gaske, gata da surutu, tana gyarawa mahaifiyarta zani wanda ya buɗe ana ganin ilahirin cinyoyinta, taji ance "kee yarinyar mahaukaciya ungo" Kafin ta juya taji saukar abu a gabanta, a hankali takai dubanta tare da kunce baƙar ledar dake ɗauke da abinda mutumin ya jefo mata,  tana washe baki tace "Umma tuwo ne miyar kuka zakici?" Umman ta karɓe ledar tare da ajiyewa a gabanta, ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya, tunda Iffat taga Umma ta kusa cinye tuwon, ta janye ledar tare da rugawa da gudu, tana gudun tana cin tuwon. Umma ta miƙe tana wasu irin yaruka wanda Iffat ɗin ta gane me take faɗa amma sam taƙi kula Umman, UNGUWAR DALA, DAKE CIKIN GARIN KANO. "Haba Wasila tun ɗazu na kawo cefane amma naga ko tukunya baki ɗora ba?" Cikin yanayin rashin jin daɗin gane halin da take ciki na hura wutar tace "malam tun ɗazu nasa yara su kwasomin makamashi, wlhi har yanzu basu dawo ba gashi gawayin sam yaƙi kamawa, ko uffan bece ba ya juya yana tsaki, Juwairiyya ta fito riƙe da ƙugu tace "baba.." Har ya kusa kaiwa bakin ƙofa ya juyo, cike da nuna kulawa yace "ƴar baba ya akayi?" "Wlhi bacci tasha, har sai da naje na tashe ta , tasan yanzu ƙarfe ɗaya na rana ne, muna jin  yunwa amma taƙi ɗora abinci saboda mugunta, baba ni dai na fasa cin abincin" Malam Yusuf ya dawo da sauri tare da cewa "haba ƴar baba, idan kikace bazakici abinci ba, ki gayamin me zakici?" Cikin shagwaɓa Juwairiyya tace "baba Fate  nakeson sha" Malam Yusuf yace "ke  Hajara, sauke tukunyar shinkafar nan ki ɗora fate" Cikin ɓacin rai Hajara tace "haba malam gashi nayi sanwa har da kayan miyar, amma zaka ce in sauke?" Eh ki sauke ki auni masara mudu ɗaya akai ɓarji ga nera hamsin" "Juwairiyya zoki miƙa niƙan" "Taɓɓ wlhi nikam yunwa nakeji baba kai dai ka tafi kawai tunda ka faɗi abinda za'ayi" Malam Yusuf ya wuce yana cewa "ƴar baba kenan" Yana fita Hajara ta kalli Juwairiyya dake girgiza tana kallon Hajara, cikin tuhuma Hajara tace "idan alkairi kike ƙullawa zaki gani, idan sharri kike ƙullawa duk zaki gani" Kafin Hajara ta ƙara magana, Juwairiyya taje tai saurin zubar da sanwar abincin da Hajara tayi... Idan har naga ya samu karɓuwa posting kullum, idan naga akasin hakan to sai sati-sati, Cikin gadara Juwairiyya take cewa "kin kashe mahaifiyata kina neman mallakemin mahaifi, to ta Allah ba taki ba," Cikin tsananin ɓacin rai, Hajara taje ta wanke Juwairiyya da mari, zuciyarta na ƙuna tace "karkiga ina biye miki ba tsoranki nakeji ba, muddin kikace zaki dinga jifana da munanan kalamai wlhi sai nayi maganinki" Juwairiyya na tsaye riƙe da kumatu, tana bin Hajara da kallon raini, Kamar inda malam Yusuf ya bata umarnin aunar masara hakan tayi, a gajiye take tafiya har ta isa bakin ƙofar gidan hannunta riƙe da ƙwarwar da ta auno masara, kafin ta ƙwalawa ɗaya daga cikin yaran da suke wasa a ƙofar gidansu ta hango an ɗauke wutar nepa, cikin baƙin cikin hakan, Hajara tace "nepa basu da tabbas ya zanyi nikam?" Ta wuce gida tana riƙe da ƙwarya a hannunta. Ko sisi bata dashi bare ta ƙirƙiro dafa wani abun, ruwan sanwar da zata mayar dashi fate, Juwairiyya ta kifar, bata da zaɓin da ya wuce ta koma ta  zauna ta zubawa sarautar Allah ido, kana kuma ta jira hukuncin da malam Yusuf zeyi mata. HUDA zaune take a ɗan madai-daicin ɗakinsu wanda ya kasance ɗaƙi ɗaya ne suke amfani dashi, kasancewar gidan nasu babu wasu yawaitar ɗakuna,  a hankali Huda take bin kowanne sashe na fuskarta tana shafa jar hoda ƴar zazzage, Umma dake tsakar gida ta ƙwala mata kira tare da cewa "Huda yanzu fa muna ƙarfe goma ne na safiya, tun tuni kike kwalliya sai kace mai sauya fata, kin daɗe gurin wanka yanzu ma bakida niyar fitowa naga kamar?" Da ɗan ƙaramin bakinta na tsiwa tace "Umma gani nan, na gama kaya zansa" A gurguje Huda tasa doguwar riga ta material wanda yayi mata kyau, duk da ya tsufa, Tana sanya mayafi ta fito tana cewa "umma nagama ke nake jira" Umman ta gyara zaman kular data ajiye abincin da bokiti wanda yake ɗauke da robobi da cokula, kana da omo da soso, sai ɗan ƙaramin bokiti mai ɗauke da jar miya taji mangyaɗa, Huda tace "Umma wlhi kafin in ƙarasa bakin titi ina gajiya, kodai inje in taro me mashin ne?" Kafin Umman tayi magana, daga can waje sukaji ƙarar mashina, Umma tayi waje da gudu tana gyara ɗaurin zani, tana leƙawa ta ƙwala wa me mashin ɗin kira, me mashin yace "yana jira" Umma ta dawo cikin gida ta samu har Huda ta kwaso kayan, Umman ta tayata miƙo ragowar, kana ta kunto bakin zaninta ta miƙawa Huda nera ɗari tace "Allah ya kiyaye hanya, saura inji kin dawo kince wani yaci be baki kuɗi ba, wlhi sai na lahira yafiki jin daɗi, dan bazaki mai dani... Mai mashin yai saurin figarsu da gudu, sbda ya gaji dajin kalaman Umman, ya girgiza kai. Tana isowa gidan mai, kafin  takai ga sauka daga kan mashin samarin gurin suka taso suna shewa suna sauke mata kayan abincin, Huda ta miƙawa me mashin kuɗinsa ya wuce, ta kalli samarin tana murmishi tace "kodai kunci kun ƙoshi ne shiyasa kuketa yimin dariya?" Ɗaya daga cikinsu yace "mun isa ai bamu isa muci abincin wata yarinya anan ba, dole naki zamu jira, Huda tasa dariya, ta gyara zaman kayan a cikin wata ƴar rumfa, kana ta nemi gefen dogon benci ta zauna,  sha biyu na rana, mutane suka fara zuwa, tana zuba musu, harda samarin gurin,  wani saurayi yaci abinci be bata kuɗi ba, ta miƙe tsaye sbda taga ze tafi tace "malam baka bani kuɗina ba?" Cikin masifa da tsageranci saurayin yace "na ƙarfi ne naci kuma bazan bayarba" Huda tace "kaje kaci nacan wlhi sai Allah ya sakamin" Saurayin ya ɗaga hannu ze mareta, wani daga cikin wanda suke siyan abincinta ya taso yana cewa "amma baka da imani, kaci abincinta ka hanata kuɗi, har Kanada ikon dukanta?" "Eh ance baza'a bada ba ko Kanada abinda zakayi ne?" Mai kare Huda yace "eh yanzu ma kuwa" Kafin wanda ya shigarwa Huda ya zaro bel, saurayin ya gudu, Huda ta fashe da kuka gashi abinci ya ƙare, tsabar tunanin kuɗin hannun wannan saurayin ta cikawa mutane abinci, "Kiyi haƙuri Huda, nawa ne kuɗin wancan ɗan iskan gayen?" Huda tace "ɗari uku" Saurayin yace "ga ɗari biyar ki ajiye a gurinki, gobe zanci abinci" Huda tayi godiya, sai a lokacin taji mugun sanyi a ranta, ta tattara kayan abincin, harda robobin da bata wanke ba ta tari mashin ta wuce gida. IFFAT Yamma tayi sosai, ga wani gagarumin hadari ya haɗa, Iffat ta kamo hannun Umman ta tana cewa "Umma zomu samu gida, ruwa ze jiƙaki" Mahaukaciyar sai wasu irin abubuwa take, tana ta fizge-fizge, da soshe-soshe, Iffat ta tattaro ƙarfinta ta turo Umman nata, kafin ta kamo hannunta sunata tafiya, a barandar wani gida suka zauna, Iffat ta kalli sama, tace "Umma ruwan ya fara zubowa" Kasancewar ba magana mahaukaciyar takeyi ba, yasa ta ƙurawa Iffat ɗin ido kamar me shirin yin magana, me gidan ya fito yana ganinsu, ya haska fitila, kana yace "ke riƙe hannun mahaukaciya kuyi wani gurin, tsabar iskanci ku rasa inda zaku zauna se nan gurin?" Iffat tace "malam ka bawa Ummana abinci dan Allah yunwa takeji" Cike da masifa yaci gaba da cewa "dalla tashi anan yunwo" Iffat ta kamo hannun Umman ta suka bar gurin, suna cikin tafiya, wani mutumi ya kira Iffat, a tare suke tafiya da Umman nata har suka iso gurin Mutumin, ya miƙawa Iffat dubu ɗaya, kana yace "jeki cikin kasuwa ki siyo muku kayan shayi" Yasan suna cikin tsananin jin yunwa, sbda yana gani aka koresu. Iffat ta karɓi kuɗin kana ta ruga a guje tana fara'a, duk da ana shirin kiran sallahar magriba, A hankali wannan mutumin ya fara tunkaro mahaukaciyar yana wani irin murmishi, daga karshe ya cafke ta ya sanyata a motarsa wacce ya parkata can nesa dasu, motar babba ce irin Sharon ɗinnan, ya tura mahaukaciya a ciki yabar anguwar da ita, Tana ta buge- bugen gilashin motar da surutai, hakan besa yaji tsusayinta ya ajiyeta a kusa ba, sai da ya iso can bayan gari, gurin babu mutane sai gonaki, hanyar ma, ba kasafai mutane suke Bin ta ba, sai uzirinsu ya kawosu, bayan yayi parking ya kwantar da kujerar gaba tare da kallon baƙin tinted baƙi na gilashin motar, kana ya cire rigarsa ya kuma cire wandonsa, ya rage saura gajere. ALHAJI AUWAL Babban ɗan kasuwa a Bauchi, birni da ƙauye babu wanda be san sunansa ko labarinsa ba, ya shahara sosai yana uku daga cikin masu kuɗaɗen NIGERIA. Zaune take a katafaren parlonsu, wanda yake fidda ni'im taccen sanyi da sanyayyayen ƙamshi mai kwantar da hankalin wanda ya shaƙar, yarinyar ƴar shekara goma sha biyar ta fito hannunta riƙe da tsadaddiyar waya I phone 13pro, a yanayin inda tayi da fuskarta dole abin zai bawa mai karatu dariya, a hakan wai fushi takeyi, cikin girmamawa taɗan risina, sakamakon ganin fitowar Abban nata, "good morning Abba" "Morning how are you?" Cikin shagoɓa Amani tace "Abba ina lafiya sai dai akwai wata ƴar matsala" Cike da nuna kulawa Abban yake kallon ta kana yace "my lovely daughter meke faruwa?" "Abba inason kayi aure, tun bayan rasuwar Ummi ko maganar aure bakayi, ko jiya ma sai da mukayi shawara da bro Mahaboob da aunty Aseela da Inaya, sukace ya dace" Abba ya nemi guri ya zauna tare da zuba mata idanu, kafin yace "zanyi shawara amma kafin nan meyasa kikeson inyi aure?" Amani ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta, kafin ta buɗe tace "Abbana kodan ta dinga yi maka abinda kakeso, kaga duka abokanka sunada mata kaine kawai baka da ita" Abba yace "shi kenan naji, amman nikam dalilin da yasa naƙi aure, banason in auri matar da zata dinga takura muku" Amani tace "Abba karka damu" IFFAT Da gudu ta dawo tana cewa "Umma ga kayan shayin, kinga me shayin ma har a kofinsa ya zuba miki" Shirun da taji ne yasata sake leƙa inda suke kwana, wato gefen bola taga wayam babu Umman, cikin ɗaga murya, tana shirin yin kuka tace "Ummaaaa naaa mahaukaciyataaaa" Duk da haka babu wanda ya fito bare yasan ga halin da take ciki, hankali a tashe Iffat ta fara zagaye unguwa tana ƙwalawa Ummanta kira, sam ta gagara zama tasha shayin sai yawo takeyi dashi a hannu...! Page 3-4 Tana cikin tafiya tayi karo da ƙaton dutse wanda yai sanadiyar kai ta ƙasa, cikin kuka Iffat ta taɓi bakinta wanda yakeyi mata zugi, hannun nata ta kalla, ganin jini ya sanyata fashewa da kuka tana yarfe hannaye, daga can gefe shayin da bredin ya zube, bredin ne dai beyi komai ba, dan haka ta miƙe tana karkaɗe jikinta ta, kasancewar garin yayi duhu, yasa bata hango kofin ba, ta riƙe bradin taci gaba da tafiya tana kuka. A hankali mutumin ya raba mahaukaciya da zanin jikinta, idan mai karatu yaga mahaukaciyar nan, wlhi bazai fara tunkararta ba, duba da inda jikinta yake fitar da tiririn wari, marar daɗi, A haka ya faɗa mata ya dinga sukuwa a kanta, daga ƙarshe ya wani shigeta da ƙarfin bala'i har ƙafafuwansa na rawa, kafin ya ɗaura mata zaninta kamar inda ya ganta, shima ya mayar da kayansa, yasa tissue paper ya goge gurin ya fesa turare, kana ya bar gurin da motarsa, Suna tafe yana waya, sai cewa yake "ai nasamu na kwashi gara duk da mahaukaciyar ba wata babba bace amma wlhi tayi daɗi". Kafin mutumin yayi parking a inda ya ɗaukota, ya waiga ko ina baiga kowa ba, kana ya ajiyeta tana dukansa, harda cafke masa riga, yai saurin ƙwacewa ya ƙara da gudu, tare da shigewa mota. Iffat kuwa tayi nisa da anguwar sosai, saboda tsakaninta da inda aka dawo da mahaukaciya yakai nera ɗari, babu wanda ya ganta ya taimaka mata, haka ta dinga tafiya har, takai bakin titin anguwar da suke, wato ɗorayi, tana kuka ta nufi bakin titi ko waigawa batayi ba, sai ji kake ƙuuuuu...ƙiiii..., kafin kace me, wanda basu ga tsayuwar yarinyar ba duk suka hallara a gurin, sakamakon ƙugin motar da suka ji, Kowa sai ambatar "innalilahi wa inna ilaihir raji'un" yakeyi, a gigice mamallakin motar ya fito, hankalinsa a tashe yana cewa "ku taimaka ku samin ita a mota wani ya biyoni mu kaita asibiti" Wanda ya taya mai motar sa Iffat a mota, shine yabi mai motar suka wuce asibitin Murtala. Suna isa aka karɓesu cikin kulawa, sakamakon jinin da yake kokawar kwaranyowa jikinta, aka wuce da ita ɗakin gaggawa, Sosai suka fara bata kulawa ta musamman, kafin suka sanar musu da cewar "dole zata iya kaiwa gobe, bazai yiwu a sallameta a yau ba" Hakeem ya danna number Hajiya babba,  cikin wani irin yanayi na damuwa yace "Hajiya babba nayi hatsari a hanyar ɗorayi, nidai banji ciwo ba, amma yarinyar taci ciwo, bazan dawo gida yau ba sai zuwa gobe, dan Allah ki sanarwa da Hajiya ƙarama da Dady" Cike da nuna kulawa Hajiyar tace "Allah ya cigaba da karamin kai yarona" Hakeem ya amsa da "Amin" Kafin tace "muma goben zamu taho da izinin Ubangiji" Yace "Allah ya kawoku" Bayan an gama gyara Iffat, barci mai nauyi ya ɗauke ta, doctor ya kira Hakeem zuwa office, cikin azama Hakeem ɗin ya bishi, anan ne doctor yake tambayarsa "ina iyayen Iffat?" Hakeem ya sunkuyar da kansa ƙasa, kana yace, "sir a bakin titi na ganta, banma lura tana gurin ba, kawai ƙarar motata ne ya fargar dani, na tambayi wani mutumi wanda suka taimaka min gurin kawota da sanyata a mota, sunce basu santa ba" Likitan ya girgiza kai kana yace "gaskiya bazan ɓoye maka ba, yarinyar ta samu ciwon taɓuwar ƙwa-ƙwalwa, ba komai zata iya fahimta a yanzu ba, sai dai nan gaba insha Allah idan kuka kiyaye maganin da zamu ɗoraku akai, abubuwan zasu dinga warwarewa a hankali, sannan a kiyaye ɓata mata rai.. *💋MU RAYU A TARE💋* True life story Mom Islam Page 5-6 Hakeem yace "insha Allah doctor" Kafin doctor ɗin yace "zaka iya tafiya" Jikin Hakeem a sanyaye ya dawo harabar asibitin, ya samu jerin kujerun da suke ajiye a gurin ya zauna akai, hankali a tashe ya fara tunowa da illata rayuwar ƙaramar yarinya da yayi, besan iyayenta ba, bai ma san ta inda zai fara nemansu ba, a hankali wasu siraran hawaye suka zubo masa, yasa lallausan hannunsa ya share tare da ambaton "innalilahi wa inna ilaihir raji'un" kafin ya kalli mutumin da suka zo tare wanda, tunda Hakeem ɗin ya shigo yake kallonsa, a hankali mutumin ya ƙaraso jikinsa a sanyaye ya dafa kafaɗar Hakeem, kana yace "bawan Allah ni zan koma gida, iyalina zasu shiga tunani da fargaba tunda ba waya ne dani ba, ka kwantar da hankalinka, ko ban dawo ba idan an sallameku ka tafi da ita gidanku, duk da ban sanka ba, kuma ban taɓa ganinka ba, nasan kai mutumin ƙwarai ne ba mai cutarwa ba, zaka kula da ita inda ya kamata". Hakeem ya sake share hawayen da suka ƙara samun nasarar zubo masa, murya a disashe yace "Nagode Nagode Allah ya tashemu lafiya, ga numberta ko zaka buƙaci magana dani" Mutumin ya karɓa yana yiwa Hakeem godiya kana ya wuce. Duniya tayiwa Hakeem zafi, duk da zamu kirashi mai ƙarancin shekaru, dan tunda ya taso ko a tv bai taɓa ganin inda akayi hatsari ƙwa-ƙwalwa ta bugu tashi ɗaya ba, har ya fara zargin kodai likitan ƙarya yayi masa, Kamar wanda aka tsikara ya matsa jikin tagar asibitin, ya kafa idanunsa a gilashin tagar yana hango Iffat an naɗe mata kanta, sai wani irin numfashi take, A razane ya sake kai kallonsa gareta ya kuma fashewa da kuka, kafin daga baya ya fara tunanin ya za'ayi taci abinci?, Yanke shawarar komawa gurin likita yayi, cikin azama ya nufi ofishin likitan, yana zuwa kai tsaye ba tare da neman izinin shiga ba, ya shige, "Likita nace marar lafiyar zata iya cin abinci kuwa?" Hakeem ya faɗa yana tsaye a bakin ƙofa, "Babu buƙatar cin abinci sai zuwa gobe insha Allah" Jikin Hakeem a sanyaye ya koma ya zauna, a haka har gari ya waye ko runtsawa beyi ba, kafin a shiga sallar asuba yaje yayi alwala ya fara nafila har aka shiga sallah, bayan an idar ya ɗaga hannuwansa sama yana roƙawa Iffat lafiya a gurin Allah, har kowa ya fice aka barshi shi kaɗai, daga ƙarshe ya fito, tare da kallon harabar asibitin, duk da bawai gari yayi haske sosai bane. Sai yanzu ya tuna tun dare da ya kashe wayarsa be kunna ba, ya cirota kana ya kunna, kafin ya cire a security kiran dady ya shigo, Dady yace "suna mota Hakeem ya gaya musu sunan asibitin, bayan Hakeem ɗin ya sanar dasu suka kamo hanya, Shikuma Hakeem ɗin ya ƙarasa cikin asibitin, yana shiga ya doshi ɗakin Iffat, wani likita ya dakatar da Hakeem yana cewa "kaine ka kawo wata yarinya?" Jikin Hakeem na rawa yace "eh nine lafiya?" Likitan yace "akwai buƙatar a samo mata ruwan kunu ko shayi tasha" Hakeem yace "insha Allah" Jin Muryar su Hajiya babba yasa Hakeem juyawa yana yi musu sannu da zuwa, kafin ya nuna musu ɗakin da Iffat ke kwance har yanzu da oxygen a hancinta, jikin Hajiya ƙarama yayi sanyi matuƙa, sai kallon Iffat takeyi, wacce take ta rarraba idanu tana kallonsu kamar yau tazo duniya, "Dady yace "iyayenta fa?" Hakeem yace "dady kowa na tambaya cewa yakeyi be taɓa ganinta ba" Dadyn yace "amma ya yanayin jikin nata?" Hakeem yace "dady har yanzu dai banji tayi magana ba, duk da akwai abun numfashi a tare da ita, amma ance ƙwa-ƙwalwarta ta taɓu" Dukkansu suka kama salati Hajiya babba tace "yanzu aiki kenan zasuyi mata ?" Hakeem yace "wlhi nidai ban sani ba, gadai shi nan mun zuba musu ido" Dady yayi shiru, tausayin yarinyar ya kamashi, yana son gano inda yasan yarinyar amma ya kasa ganowa, haka dai ya haƙura, ya kawar da tunanin ta, suna zaune likita ya shigo da kayan aiki, ya cire mata abin numfashin kana ya sake yi mata wasu gwaje-gwaje, kana yace "sannunku, zaku iya bata abinci amma marar tauri, suka amsa da "to" BAUCHI Cikin shirin tafiya aiki Alhaji Auwal ya fito, hannunsa riƙe da ja ka irin wacce ma'aikata suke riƙewa, Amani ta fito riƙe da hular Alhaji Auwal a hannunta, ita kuma Aseela hannunta na riƙe da turare, Amani ta sanya wa Abba hula, Aseela ta fesa masa turare, Mahabob kuma yana riƙe da mukulin motar Abban, Inaya ta fito a shagwaɓe, kasancewar itace autarsu, Abba na ganinta yace "ƴar albarka lafiya?" "Abba aunty Aseela ce ta hanani wayarta, inyi Game" Abba yayi dariya, shi yama ɗauka wani babban abu ne, cikin sigar lallashi yace "karki damu zan siya miki sabuwa, Aseela ayi haƙuri a bata kafin in siyo mata nata" Aseela ta shagwaɓe fuska tace "Abba wlhi ta fiye shige-shige ne" Kana Aseela ta miƙa mata wayar, ta koma ciki da gudu su kuma suka fita raka Abba parking space, Suna tsaye ya shiga mota, Mahabob ya miƙawa driver key, suka yiwa Abba adu'ar Allah ya tsare, kana suka koma ciki. Tunda suka dawo, suka kafa meeting, akan auran da suke son Abban nasu yayi, sunata adu'ar Allah ya haɗashi da mata ta gari mai tausayinsa, A hankali drivern yayi tuƙi har suka iso ma'aikatar Alhaji Auwal ɗin ta ƙera kayayyaki, musamman atamfofi da rigunan sanyi, bayan drivern yayi parking an buɗewa Alhaji Auwal ya fito, idanunsa yai tozali da wata budurwa ta fito daga wani office, cikin nutsu yake kallonta har ta ƙaraso ta wucesu, ya ɗan tafi da sasarfa, kana ya tsaya ƙyam, yace "Ahmadu driver kiramin waccar yarinyar, cikin mamaki Ahmadu yace "to" har ta kusa fita daga get ɗin ya isar da saƙon Alhajin, jin ance mata Alhaji Auwal ne yake kiranta, sai ta fara rawar kai da rawar jiki, tunda ta sanshi tasan labarinsa, labarin gidansa ne bata sani ba, cikin nutsuwa ta iso gareshi, driver ya wuce, kana ta durƙusa ta gaishe shi, cikin farinciki da yabawa da hankalinta da yayi ya gyara tsayuwa, kana yace "sunana Alhaji Auwal" A hankali budurwar tace "masha Allah" kana yace ko zan iya sanin sunanki?" A kunyace budurwar tace "sunana Batool" Allhji Auwal yace "masha Allah, idan bazaki damu ba ina sonki, so bana wasa ba so na aure, kinsan dai ni ba yaro bane" Batool tace "to Alhaji yanzu zanje gida babana yanata kirana" Alhajin ya karɓi number wayarta tare da ciro kuɗi har kimanin 20k ya bata kana sukayi sallama, Tana tafe gabanta na ci gaba da faɗuwa, a zahiri bawai kiran nata akeyi ba, ƙafafuwan ta ne suka gaza ɗaukarta dan haka ta samo mafitar faɗan haka, Alhaji Auwal yayi murmishi, bai bar gurin ba har sai da Batool ta ɓace, kana ya shiga ciki, *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 7-8 Da sallama Huda ta shigo ita da wasu yara guda biyu, ɗaya yana riƙe da kular abincin siyarwarta, ɗaya yana riƙe da bokitin miya, ita kuma tana riƙe da robar soso da omo, Daga inda Umma take zaune ta amsa tare da cewa "oyoyo Huda ƴar albarka, an siyar da abincin duka ko?" Huda na murmishi tana kallon yaran da suka ajiye mata kaya tace "na gode" suka wuce. Kafin tace "Umma an siyar amma naga kuɗin bekai kamar na jiya ba" Cike da ruwan bala'i Umma tace "ni zaki mayar ƴar iska wacce batasan abinda takeyi ba, in tashi tun asuba in hana idona runtsawa kuma in hana jikina hutu, amma kicemin kuɗin be kai ba?" Kafin Umman ta kamo Huda ta cakumi wuyan rigarta tana cewa "gayamin wa kika bawa abinci bai baki kuɗi ba?" Huda ta zazzaro idanu waje cike da tsoro tace "wlhi Umma babu wanda na bawa daga zubin abincin ne haka" "Dan ubanki ce miki akayi nima a shago irin zubin abincin da sukeyi min kenan?" Huda ta girgiza kai cike da tsoro, Umma tace "gobe in Allah ya kaimu wlhi tallahi kinji na rantse idan baki dawo min da kuɗina cass ba sai na illataki tunda kin fara nunamin rashin gaskiya" Jikin Huda na rawa tace "nayi miki alƙawari Umma ki sakeni wlhi zan kawo miki gobe" Sannan Umman ta saketa tana mayar da numfashi kamar wacce tayi gudu, Tsabar tsoro da ya kama Huda, tunda ta miƙawa Umma kuɗin ta ɗauki buta ta yi alwalah, ta dawo ɗan ɗakinta ta shimfiɗa wani ɗan ƙyalle ta kabbara sallah, tare da rama sallolin azhar da la'asar, kana ta zauna jiran magriba. Har akayi isha'i bata fito ba, Umman ma bata nemeta ba, IFFAT A hankali Hajiya ƙarama ta dinga bata tea tana sha cikin nutsuwa, sai dai har yanzu babu wanda yaji sautin muryarta, ko kallon da take yiwa mutane ma wani iri, marar kyau, duk wanda yaga ƙwayar idanuwanta inda suke juyawa yasan Iffat na cikin wani hali. Haka suka wuni jiki a sanyaye babu wani kuzari, zuwa yamma Dady ya ɗauki Hajiya babba suka koma gida, ya rage saura Hakeem da Iffat ɗin da kuma Hajiya ƙarama, Hakeem ne ya fara fita yin sallahar magriba, bayan ya dawo Hajiya ƙarama taje tayi alwalah itama ta kabbara sallah, Hakeem na zaune yaga Iffat nata jijiga, alamun jikin ya tashi, cikin hanzarin da gudu yai ofishin likitan, ko sallama babu bare neman izini yace "doctor kazo yarinta zata mutu" A inda Hakeem ɗin yayi magana, doctor ya bawa wanda yake sallama haƙuri kana ya fice da gudu, abin al'ajabi, likitoci uku ne suka haɗu a kanta, amma sam har yanzu Iffat bata numfashi, a zahiri dai an fara kyautata zaton ko mutuwa tayi?, hankalin Hakeem yayi mummunan tashi, zufa babu ta inda bata karyo masa, rai a ɓace yace "aikin banza aikin wofi, likitoci kunkai ku huɗu amma kun kasa ceto rayuwar yarinyata kun kasa dawo mata da numfashinta?" Ɗaya daga cikin likitocin yayi murmishi ya girgiza kai, Ana fita da Hakeem yana ci gaba da gaggaya musu maganar da duk ta fito daga bakinsa. GIDAN MALAM YUSUF Har akayi kiran sallahar magriba Hajara na zaune akan kujera ƴar tsugunno ta rafka uban tagumi, tashin hankalinta baya wuce idan malam Yusuf ya shigo gidan ya fara surfa mata ruwan masifa, shine babbar damuwarta, jin an shiga sallah ya sanyata miƙewa ta ɗauki buta ta nufi banɗaki, tsaki tayi, sakamakon ganin tiƙeƙen kashi a bakin masai, kana ta samu tsinke ta tura tana Allah wadai da hali irin na Juwairiyya, kama ruwa tayi ta fito, kana ta tsugunna ta ɗaura alwalah ta nufi ɗakinta, tana shiga tasa ƙafa ɗaya ta faɗi tiimm, sakamakon santsi da ya kwashe ta wanda batasan ta ina yazo ba, cikin ɗaga murya tace "Juwairiyya bakya jina ne ?inata ihu dan Allah kizo ki taimaka min in tashi ƙafata ta gurɗe" Juwairiyya na daga ɗaki tace "kinga bani da lokacinki, kuma wlhi girki ne dole kiyi, idan baba ya kawo" Hajara tace "wlhi banga wanda ya isa ya sanyani girki a gidan an ba, musamman ma a wannan halin da nake ciki" Juwairiyya na daga ɗaki tace "idan baba ya dawo zaki mai-maita masa" Hajara ta fashe da kuka, mai ban tausayi, cikin ƙarfin hali ta kama bango da ƙofa ta miƙe, kana ta nemi guri akan kujera ta zauna, cikin ikon Allah aka kawo wutar nepa, Hajara ta kalli gurin da ta faɗi, ga zahiri nan sosai mangyaɗa aka zubar domin ta, tasan aikin na Juwairiyya ne, ba sai an gaya mata ba, Hajara ta girgiza kai, ta fara tunanin itakam me ta tarewa Juwairiyya a gidannan ne? Tana tsaka da tunani sai jin mutum tayi ya faɗi timmm..., cikin firgici tace "malam lafiya?" Ashe tun daga ɗakin Juwairiyya yake surfa masifa, yazo yiwa Hajara ya faɗi a bakin ƙofa, santsin man gyaɗan ya yar dashi, hajara ta rufe bakinta sakamakon dariya dake zuwar mata, malam Yusuf ya tattaro dukkan ƙarfinsa, yana cewa "ƴar baba zo kiyi temako babanki ya faɗi" Juwairiyya ta fito da gudu, ta bankaɗo labulen ɗakin Hajara, tana cewa "wlhi baba ina kallonta ta zuba maka miyar yauƙi a gurin kawai zata kashe mana kai ne" Tana maganar tana kamo hannun mahaifin nata, cikin ikon Allah ya miƙe amma har yanzu yana riƙe da Juwairiyya, Hajara ko ta zuba musu ido ba Um, ba um-um. Har zasu fice "Hajara tace "baba kasan dai ni marainiya ce, mahaifiyata ta rasu dan Allah baba ka rabu da Hajara, domin inada yaƙinin zuwa gaba zata iya kashemin kai" Cikin bin umarnin Juwairiyya yace "Hajara kije gida har sai na nemeki" A hassale Hajara ta miƙe, tama mance da zugin da ƙafarta keyi, cikin masifa tace "wlhi tallahi idan har baka sakeni yau ba, baka cika lusari me jin maganar fitsararriyar ƴarsa mai gurɓatacciyar tarbiyya" Sosai maganar tayiwa malam Yusuf zafi, zuciyarsa na raɗaɗi jikinsa na ɓari yace "Hajara yaushe kikayi baki da har kike jifana da munanan kalamai?" Kafin Hajara tayi magana, Juwairiyya ta saki baba ya faɗi ragwab, ta taho da sauri tare da ɗaga hannu zata mari Hajara, cikin azama Hajara ta riƙe hannun ta yar da Juwairiyya a ƙasa ta dinga duka kamar an aikota, malam Yusuf dake ƙoƙarin miƙewa ya kasa, gashi yaji Juwairiyya tana nishin mutuwa, cikin ɗaga murya yace "Hajara ki tattara duk abinda kika sani naki ki barmin gida, na sakeki saki uku na sake ƙara uku, kai idan anayin goma sha biyu yau nayi miki fice, karki kashemin yarinya ita kaɗai Allah ya bani, dan kinga ke bakya aihuwa shine zaki kashe ta, munafuka muguwa, Hajara tayi tafi tare da cewa "ayirii- yirrii, wlhi tafi nono fari, dama zaman gidanka ya zamemin dabaibayi ne, babu inda zanyi, yanzu kam Alhmdulilah" Ta fara tattara kaya, Juwairiyya ta miƙe jiki babu ƙwari, ta kamo baba suka fice, ita kuma Hajara ta fara tattara kayanta, takai kusan azhar sannan ta gama, ta fita ƙofar gida neman mota, cikin sa'a kuwa ta hango motar wani saurayi, wanda suke mutunci dashi, wato akori kura, ta ƙarasa tayi masa magana, ya amince zai kwashe mata kayan, amma zata nemi kuɗin fetur ta bashi, kan kace me, har sun kusa kwashe kayan, hatta tukwananta duk ta kwashe, babu abinda ta bari wanda ya kasance mallakinta. Bayan sun gama ta shiga gaban mota suka wuce anguwar su dake Rugan Julli, bayan drivern yayi parking a ƙofar gidansu, kasancewar ta nuna masa tun suna nesa, ta buɗe motar ta fito, shima haka, ta shige ciki, shi kuma ya fara firfito mata da kaya, tana shiga ta fashe da kuka, Goggo Dije na ganinta ta taso da sauri tana cewa "Hajara lafiya?" Hajara ta share hawaye, kana tace "mama baba yana ciki ne?" Goggo tace "ai ya tafi Kaduna neman kuɗi, ki sanar dani meke faruwa?". Kafin Hajara tayi magana, samarin anguwar sun fara shigowa da kayan gado, Goggo tayi shiru, domin ta fara zargin aikin gama ya gama, "Hajara kaso auran naki kikayi?" Hajara tace "wlhi Goggo duk hakurin da nakeyi bai gani ba, ya sakeni saki uku, Goggo tace "me kikayi masa?" sai ga wani saurayi nan ya shigo da takarda a hannunsa ya miƙawa Hajara, Hajara tayi masa godiya kana ta kalli takardar, kasancewar taɗan taɓa hausar boko tace "Goggo takardar saki ce" Goggo kam ta kasa furta koda kalma ɗaya, tunanin ta bai wuce baban Hajara idan yazo ya surfa musu masifa itada Hajara ba, dama sau tari yakan ce itace take hana Hajara zaman aure, tunda auran Hajara na biyu kenan, duk da ƙarancin shekarunta. HUDA Yau ma kamar kullum, taci kwalliyarta ta sanya riga da zani na atamfa, ɗinkin yayi mata kyau, kayan ma sababbi ne, kasancewar ɗinkin ƙaramar sallah ne da Umma tayi mata, rataye da jaka da hijab ta fito tsakar gida, Umman ta miƙa mata abinci a kwano tare da cewa "lokaci dai ba tsayawa jiranki zeyi ba" Cikin sauri-sauri, Huda take cin abincin, bata kai ga cinyewa ba ta miƙe tana cewa "Umma na ƙoshi" "Ai ke haka kike, daga ance miki kiyi sauri sai ki ajiye kwanon abinci, to wlhi kanki kika yiwa ba niba" Umman ta faɗa tana shiga ɗaki ta ɗauko mata takalmin sallahar ta, Huda na gani, ta zaro ido, kafin tace "umma wannan ai takalmin sallah ta ne" "Eh sai me, inace ni na siya miki?" Huda bata sake magana ba, tasa tare da ɗaukar bokiti tayi waje, Umman kuma ta ɗouko babbar kula, sukayo waje, cikin sava sai ga mai mashin ɗin da Umma ta samar mata, wanda sukayi dashi zai dinga zuwa yana ɗaukarta kullum, Cikin ikon Allah suka iso gurin sana'arta, bayan ta sauka ya sauke mata kayan abincin, tayi masa Allah ya tsare ta wuce, Yau kam anfi koda wane lokaci cika a gurin, dan harda baƙin ido wanda bata sansu ba, lokacin zuba abinci nayi ta fara zuzzuba musu, suna bata kuɗi, wasu sai sun gama ci sannan zasu miƙa mata kuɗi, wanda yake tare mata faɗa, ya miƙe tare da cewa "Huda dama ke nake jira kizo inyi miki sallama, babana yace in koma gida saboda aurena ya kusa" Idanun Huda sun ciko da hawaye, tace "Allah ya kiyaye hanya, shike nan bazaka sake dawowa ba?" Saurayin yace "gaskiya da kamar wuya, inayi miki fatan alkairi" Ya wuce shima zuciyarsa babu daɗi, An kammala cin abinci mutane biyu basu bata kuɗi ba, Huda ta miƙe tace "dan girman Allah ku bani kuɗi zan tafi gida", ɗayan ya ciro ɗari biyu ya miƙa mata, Huda tace "hamsin ɗin fa?" Saurayin yace "ki yafemin" Shiru tayi batace komai ba, shiko wanda bai bata kuɗin ba, ashe ya faki idonta ya gudu, gashi kowa ya tafi, Hankalin huda a tashe ta ɗora hannu a kai, kana ta fara hararo masu shagunan gurin, tare da shawarar "gurin wa zataje ya taimaka ya bata kuɗin abincin, gashi jiya tayiwa Umma alƙawarin yau zata ciko mata kuɗin daya ɓata" Ayi min afuwa kwana biyu banyi posting ba, Please a tayani share fisabilillah *💋MU RAYU A TARE💋*               Mom Islam Page 9-10 Jiki a sanyaye ta nufi shagon wani saurayi, yana siyarda manja da man gyaɗa da kuma kayan hatsi, cikin ladabin dole ta durƙusa a gabansa, kafin tace "ina wuni" "Lafiya lau ya kasuwa?" Me shagon yace mata, lokacin da yake fitowa daga cikin shagon sbda ya ganeta, yana yawan ganin an wuce da ita a mashin da kular abinci, "Malam dan Allah ka taimaka ka bani ɗari biyar, Ummana ce tace yau idan ban koma mata da kuɗi sun cika ba, sai tayimin duka" Mai shagon ya girgiza kai, tare da jin takaicin iyaye masu irin wannan halin, kafin ya ciro ɗari biyu, yace mata "nima ban daɗe da dawowa daga kasuwa ba, duk na kashe kuɗina" Da sauri ta karɓi kuɗin jikinta na karkarwa, ta miƙe tanayi masa godiya, A cikin zuciyarta kuwa bayan ta miƙe cewa takeyi "an kashe miciji ba'a sare kansa ba" Tana tafe tana kuka, ta ƙarasa shagon dake can bayan gidan mai, tana shiga shagon mai siyarda su drinks ɗin ta ƙarasa ciki, kasancewar bataga kowa ba, ido shaɓe-shaɓe da hawaye ta durƙusa a gaban mutumin da a ƙalla zeyi shekaru arba'in, kana tace "malam ka taimakeni ka bani ɗari uku, zan cikawa Ummana kuɗin abinci idan na koma gida duka zatayi min" Mutumin ya ce "meyasa zata dukeki?" Huda tayi shiru, sakamakon kukan da ya kuɓce mata, "Zan baki amma nima zaki bani wani abu" Jikin Huda na rawa tace "wlhi zan baka, saboda sam bata ma san abinda yake nufi ba, sbda kwata-kwata shekarunta basu wuce sha huɗu ba, amma Allah ya azurtata da cikar halitta, sbda ƙirjinta a cike yake, idan ka kalleta sai kace mai shekaru sha takwas ko ashirin. Mutumin ya ciro ɗari huɗu, kana ajiye su can kan dogon bencin dake shagonshi, kana yace "idan kika amince dani kinga harda nera ɗari na ƙara miki, yanzu Huda ta fara gano abinda mutumin yake nufi, Tunda ta tuna da dukan da Umman tace zatayi mata, sai taji zuciyarta ta tsinke, sbda idan Umman ta tashi yin duka bata raga mata, musamman ma akan dukiyarta, kamar wacce aka tsikara tace "na amince" Me shagon ya ce "bismillah" Yayi mata alamar ta shigo da hannunsa, ba musu tashigo, ya shiga da takalmanta ciki, kana ya rufe ƙofar shagon, kafin ya rufe sai da ya duba yaga babu kowa sannan ya rufe, kana ya ƙarasa ciki, ya samu huda tana tsaye a raɓe tana kuka, a hankali me shagon ya ƙarasa ya rungumota, tare da miƙa mata ragowar taliya wacce yaci, ya rage, Tana karɓa ta fara ci, kamar wacce ta kwana da yunwa, tana gamawa, ta ajiye robar, ya miƙa mata ruwan wanke hannu ta wanke, kana ya fara matsota tana matsawa baya, har ya ƙureta a jikin bango, Cikin ƙaramar murya yace "idan baki yarda na taɓa nonuwanki ba wlhi bazan baki kuɗin ba" Da sauri Huda ta yaye hijabinta, mai shago ya ɗorata akan cinyarsa ya dinga lugui guice mata nonuwa, yana sauke wani fitinannen nishi, jin bugun ƙofar da akeyi ne ya sanya shi sakinta da sauri, yana cewa "gaskiya idan ina taɓawa  kamar kar in dena, idan kuɗinki ya sake ɓata kullum ki dawo wlhi zan dinga baki, Huda tace "to" jikinta na ci gaba da rawa, Tana kuka ta sanya hijabi tare da riƙe takalmanta a hannu... Shin me zakucewa Huda itada mahaifiyarta??? Nace ba?  idan akayi shar'hi read more 6 zan dinga yi kuma kullum insha Allah Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋*               Mom Islam 11-12 Sai da ya leƙa ta window  yaga me buga ƙofar, kana ya dawo ya zauna, wanda idan ya buɗe masa komai zai iya faruwa, Gurin Huda ya dawo, ya miƙa mata kuɗin kana yace "bari wancan munafikin ya wuce sai ki fita" Huda tace "to" jikinta na ci gaba da rawa. Can anjima da ya tabbatar wanda yazo ya wuce, ya buɗe mata ƙofa ta fita, tare da ƙara jaddada mata idan tana neman cikon kuɗi ta dinga zuwa. Kayan abincin nata ta kwashe ta haɗasu a cikin kular, kasancewarta babba, kana ta tsare me mashin ta gaya masa anguwarsu ta hau, suka tafi. Suna isowa ta nuna masa ƙofar gidansu, ya ajiye, ta sauka ta miƙa masa kudin ya wuce, ita kuma ta shige gida, kanta ɗauke da kular abincin, Da sallama ta shiga, ta samu Umman nata tana kwashe shanya, sakamakon hadari daya haɗo, "sannu da gida Umma" Huda tace, lokacin da ta ƙarasa ciki, cikin dakin fuska Umman tace "yauwa Huda ƴar albarka sannu, da fatan dai anyi ciniki?" "Eh Umma, na dawo miki da bashin da kikebi" Umman na murmishi tace "jeki ɗauki abincinki kici ƴar albarka" Huda zuciyarta a sake ta ƙarasa bakin murhu ta buɗe kwanon abincin nata, ta washe baki, kafin tace "Umma kice mutumina kikayi Umma na washe baki, tace "ai kuwa idan ma zaki ƙara akwai" Huda ta ɗauka ta wuce ɗaki, Tunda ta shiga ta ajiye ɗan waken a gefe, ta fara tuno abubuwan da wannan mai shagon ya dinga yi mata, a zahiri tace "inhar zai dinga bani kuɗi in dawo in samu Ummana cikin farinciki zan dinga zuwa" Kafin ta ɗauki abincin ta fara ci hankali kwance. IFFAT Yau kwananta Uku a asibiti, Hajiya babba ce ta koma kula da ita, Hakeem kuwa ya jingine zuwa aiki, saboda koda wane lokaci ka gansa baya cikin nutsuwa, yau ake saka ran sallamarsu, tunda jikin Iffat ɗin ya sauka, an samu ƙwararrun likitoci wanda sukazo daga waje, duk da taimakon Dady da shugaban asibitin, kasancewarsu abokan juna tun suna makarantar sakandare, idan mutum yaga Iffat komai rashin tausayinka dole ka tausaya mata, duk da uwarta mahaukaciya ce, bai hana jikinta yin kyau ba, ga yalwar gashi, amma yanzu ta koma kamar tsinke tsabar sirantaka, gashin kanta kuwa yayi wani iri, duk da dama ba gyara yake samu ba tun asali. Iffat ɗin na zaune akan cinyar Hakeem wani baturen likita ya shigo, cikin nutsuwa ya kalli Iffat kana yace "insha Allah akwai alamar nasara, a binciken da mukayi mun gano ciwon beyi mata yawa sosai ba" Niko sai kallonsa nake, saboda inda yake magana kai kace wanda yayi rayuwa cikin hausawa. Kafin yaci gaba da cewa, akwai buƙatar ta dinga samun walwalah koda wane lokaci, a guji ɓata mata rai, sauran bayanan zamu rubutasu" Ya nuna Hakeem yace, ya biyoshi office, Kafin ya miƙe ya kamo hannun Iffat yace "tare dake zamu tafi" Iffat kawai kallonsa takeyi amma sam ta kasa magana, sosai takejin bakinta yana yi mata nauyi sosai, haka suka tafi tana ɗan ɗingishi, suka ƙarasa office, aka basu magunguna da sauran abubuwan da ya kamata a kiyaye kana ya miƙawa Iffat hannu, har yanzu kallonsa takeyi, Hakeem ya kamo hannunta yasa ana doctor, kana yace "Kyakkyawar yarinya inayi miki fatan samun lafiya" Hakeem yace "insha Allah" Lokacin da suka dawo ɗakin da aka kwantar da Iffat, dady yazo suka tattara kayan su suka wuce gida. ALHJ AUWAL Bayan ya gama binciken cigaban da aka samu da naƙasun da ya shigo, ya dawo gida da wuri kafin sallamar magriba, sbda lokacin ma ƙarfe biyar ne, tun da su Mahabob da Amani sukaji ƙarar tsayuwar motarsa suka fito da sauri, Amani ta buɗewa Alhaji murfin mota, bayan ya fito Mahabob ya ƙarɓi takardun hannunsa sukayi masa sannu da dawowa, Cike da farinciki Alhaji Auwal yake kallonsu, kafin yace "Aseela da  Inaya ?" Amani tace "Abba suna ciki" Suna tafe suna hira suka ƙarasa cikin gidan, a parlo dukkansu suka yada zango, su Aseela suka fito, ko wanne yana ƙoƙarin tambayar Abban "ya gajiyar aiki" Cike da nuna kulawa yace "Alhmdulilah albishirinku" Dukkansu suka amsa da "goro" suna son a gaya,   musu. "To yau dai burinku ya cika nayi budurwa, yanzu ma zan kirata, amma me kuke ganin zance mata?" Amani tace "Abba Gaskiya ayi bikin da wuri, Mahabob yace "Abba nidai inason kafin bikin dukkanmu har da antyn muje Makkah" Inaya tace "kai bro iyayen ita antyn basu da hankali ne, ba'a ɗaura aure ba zasu bayar da ita?" Aseela tace "nidai Abba kayi mana kaya iri ɗaya da antyn harda kai" Inaya tace "eyeeee Abba zai kawo mana anty" Abban ya ƙyalƙyale da dariya kana yace "Mahabob sai anyi aure, wannan alƙawari ne, harda sabuwar mota zan siya muku kai da Amani da Aseela, ita kuma Inaya zan siya mata kayan wasa" Dukkansu suka fara yi masa godiya, kana gurin yayi shiru, Abba yace "yau anje makaranta kuwa?" Dukkansu sukayi shiru, sbda basu da gaskiya. Mahabob yace "Abba ka kirata mu gaisa" Dukkansu suka matso kusa da Abban, Alh Auwal ya danna number Batool, ring ɗaya zuwa biyu ta ɗaga, cikin zazzaƙar muryarta, kafin tace "Aslamu alaikum Barka da yamma Alhji" Mahabob da Amani da Aseela da Inaya suka zaro ido. Alhji Auwal yace "Barka da fatan kin koma gida lafiya?" Batool tace "lafiya lau" Alhji Auwal yace "ga yarana zaku gaisa", Bata damu ba, tace "to" Cikin nuna ko ɗarr ya bawa Mahabob, ga mamakinta sai taji Muryar ƙato, bayan sun gaisa, aka bawa Amani itama bayan sun gaisa aka miƙawa Aseela, Aseela ta miƙawa Inaya, cikin shagwaɓa Inaya tace "anty ai zaki zamo Mamyn mu ko?" Batool tayi murmishi kafin tace "eh insha Allah, ya sunanki?" Inaya tace "sunana Inaya" Batool tace "masha Allah suna mai daɗi" Kafin Inaya ta miƙawa Abba, Yana dariya yace "kinji Inaya da rigima ko?" Batool tace "uhm" Kana ya sake cewa "ki sanarwa da iyayenki zan aiko magabata na" Nan da nan cikinta ya bada Ƙuuuuu, Sai kuma tace "toh" Sukayi sallama ya ajiye wayar. Acan ɓangaren Batool, suna gama waya da Alhji Auwal, ta fashe da matsanancin kuka, cike da nuna kulawa mahaifiyarta dake zaune akan carpet ta kalleta kafin tace "Batool lafiya naga kina kuka?" Cikin kuka Batool tace "Ummy wlhi wani Alhaji Auwal wanda yake da ma'aikatar sarrafa kayayyaki ne yace yana sona, dalilin haɗuwata dashi, naje Company ɗinsu gurin Sadeƙa, anan ya ganni, yanzu fa muka gaisa da yaransa, harda wani mai babbar murya, duk inda akayi ɗansa ma ya haifeni" Ummy tayi murmishi kafin tace "lallai Batool sai yanzu na tabbatar da ƙuruciya na damunki, kin dangwalo mana arziƙi kina neman yi mana haramiyarsa? kin kuwa san alkairin dake cikin auran wannan mutumin?" Batool tace "Ummy wataran zasu iya dukana fa" Ummy tace "wlhi basu isa ba, jefa baki da wayo, bakisan irinsu masu shekarunan sunfi nunawa yara kulawa ba, bazai taɓa bari a rainaki ba, duk da mahaifinki yanada ɗumbin dukiya amma ai kema kinsan be kamo ƙafar Auwalu ba, inhar na isa dake ki sanarwa da Alhaji kokuma ni in sanar masa" Cikin gamsuwa da maganar Ummynta tace "to Ummy ki sanar masa, nadena tsoro" Kiraye-kirayen sallahar magriba yasa suka bar parlo Ummy ta wuce ɗaki domin tayi alwalah, Batool ma ta wuce ɗakinta. Bayan anyi magriba, har lokacin sallah isha'i yayi, sannan Baban Batool ya dawo, Da sallama ya shigo, Ummy tayi masa sannu da dawowa, haka ma Batool ɗin kafin suka hallara a dining, tuwon shinkafa Ummyn tayi miyar kuɓewa ɗanya wace taji  soyayyen kifi, kana suka fara ci, sam Batool ta kasa zagewa taci abincin sakamakon tunani da yayiwa zuciyarta ƙawanya, 2 Baba yace "Mamana lafiya kuwa?" Kamar wacce ta razana tace "baba babu komai" "A'a ban yarda ba" Ummy ta ajiye cokali kafin tace "Alhji wai dan Alhaji Auwal yace yana sonta shine tabi ta damu mutane" Baba yace "wane Alhji Auwal?" Ummy tace "wanda dai ka sani to shi, ɗan kasuwa" Baba yace "Mamana ke kinyi arziƙi ai ke abin alfaharinki ne ma, ace sunanki ya kewaye duniya" Sunata ƙarfafa mata guwaiwa, har Ummy take gayawa baba cewar gobe zai turo da magabatansa, Baba yayi murna sosai, Acan ɓan garen Alhji Auwal bayan sunyi salloli harda isha'i, kafin suci abinci, Mahabob da Amani, sukace "Abba mu zamu siyo kayan lefe" Alhji Auwal yace "kamar nawa kuke ganin zai isa?" Sukace "sai dai munje gobe amma harda kai ko Abba?" Yana dariya yace "a'a kune zakuje, ai kunsan duk abinda ya dace" MALAM YUSUF. Da ƙyar Juwairiyya ta taimaka masa ya miƙe tsaye, ta ɗauko tabarma wacce take ɗakinta ta shimfiɗa masa,  tasa masa pillow kana ta kwantar dashi, sai wash-wash yakeyi, tanayi masa sannu. A wahalce yace "na rabu da Hajara na huta da ƙaya, Juwairiyya tace "ai kuwa wlhi Baba idan ka samu lafiya ka auro budurwa" Malam Yusuf yace "ina ni ina auran budurwa, ƴan mata yanzu idanuwansu sun buɗe kowacce budurwa zakaji tana cewa sai mai mota. Juwairiyya tace "nima baba ina fatan Allah ya bani mai mota" Tana cikin magana wani yaro ya shigo tare da sallama, Bayan ta amsa, akace wani mutumi yazo yace ayi masa sallama da Juwairiyya, Juwairiyya tace "kace ina zuwa" Ta miƙe tana cewa Allah yasa me mota ne. Ɗakinta ta koma ta feshe jikinta da turare, kana ta lulluɓa mayafi ta fito, A hankali ta kalli saurayin dake tsaye, kyakkyawa dashi son kowa ƙin wanda ya rasa, sai dai jikinsa wata koɗaɗɗiyar rigace wacce ta gaji da duniya, ƙafarsa kuwa tsohon silifas ne shima ba'a magana, a tsanake ta ƙare masa kallo kafin tace "a'uzubillahi wlhi nafi ƙarfin talaucinka, insha Allah sai me mota, ni zaka shafawa farar ƙafa, ma za wuce ka bani guri da jikinka kamar tsohon almajiri" Saurayin yayi murmishi kafin yace "haba ƴan mata, baki tsaya kinji abinda zan..." Kafin yakai ga idda maganar Juwairiyya ta shige ciki, Abokinsa Mubashir ya ƙaraso yana dariya ya taɓa kafaɗarsa kana yace "Prince Abdul ya kamata ka dena wannan basajar da ka ɗauko wa kanka, ka fitowa ƴan mata a kamanninka, nan ne zakaga rububi, mahaifinka sananne ne, kai kuwa kwanan nan ka dawo daga, Bangkok" Prince Abdul yayi murmishi, kana yace "nayi alƙawarin bazan taɓa auran matar da burinta ajiyemin yara da kuma burin mutuwata domin taci gado na, nafison matar da zataji tausayina kana ta soni tsakani da Allah, sannan kuma ta kula dani sannan ta haifamin yara masu tarbiyya, kasan kuwa zansha wahala, kuma yanzu na fara wannan shigar...! Waye shi ? Ya Rayuwar Iffat zata kasance? Ina mahaukaciya Juwairiyya fa? Hajara? Matar tsoho Batool? Idan akayi comments na gobe sai yafi nayau *💋MU RAYU A TARE??*               Mom Islam 13-14 Kai tsaye su Prince Abdul suka wuce mota. Mubashir ne a mazaunin driver, shikuma Prince Abdul yana kusa dashi, Mubashir ya harari Prince Abdul lokacin da yake tuƙi sun kusa fita a anguwar, dariya kawai Prince Abdul ɗin keyi, sbda haɗe fuska da Mubashir yayi, yasan faɗa zasuyi dole. IFFAT Yau kwanansu biyu da komowa gida, hankulan mutanen gidan duk ya tattara ga Iffat, saboda ta shiga ransu sosai, abin mamaki ko ruwa Iffat batasan ta inda zatasha ba, sai dai Allah bai mantar da ita sunansa ruwa ba, Hakeem kam koda wane lokaci yana ƙoƙari akanta da kuma abinda yake ganin zai gina mata jiki, washe gari, ta kama Lahadi, Dady yana gida, sbda tun asabar suke hutu, ya sanya Hakeem suzo shi da Iffat, yana riƙe da hannunta suka ƙaraso ɗakin dadyn yana zaune da tulin jaridu a gabansa, Hakeem yace "dady barka da rana" Dady yace "my son anyi la'asar sai dai muce Barka da yamma" Hakeem yayi murmishi kafin yace "hakane Dady, gamu" Iffat kuwa tana ta wasa da jaridun kasancewar komai ta gani abun wasa ne, sbda ta zamo mai juyaiyyar ƙwaƙwalwa, batasan abinda zai amfaneta ba, bata kuma san abinda zai zamo illa ga rayuwarta ba. Hakeem, wace shawara kake gani ya kamata mu yanke akan wannan ƙanwar taka?, ya kamata mu nemi iyayenta, Susan halin da take ciki, in yaso sai mu roƙi alfarma akan su bar mana ita muci gaba da kula da ita" Tunda Dady ya fara magana Hakeem ya fara sharar ƙwallah, gani yake za'a rabashi da farincikinshi, yanayi mata so na ƴan uwan taka, sbda ada Hajiya ƙarama ta haifi wata yarinya mai kama da Iffat, sai dai waccar da tana duniya da tuni ta kusa shekaru goma, ita kuma Iffat bata wuce huɗu ba, Dady yace "Hakeem bakace komai ba" Duk da dadyn ya lura da yanayinsa, bayason goyon bayansa akan abinda basu da ƙwaƙwarar hujja akai. Hakeem yaja numfashi "uhhhm" Kafin yace "dady nikam da zakaji shawarata da kaci gaba da riƙeta har abada" Dadyn ya girgiza kai, tare da faɗin "yaro-yaro ne tabbas bakasan komai akan duniya ba, dole daga yau zuwa ƙarshen satinnan mu fara bincikar iyayenta" Hakeem dai bai gamsu da shawarar dady ba, babu inda ya iya, ita kuma Iffat ɗin wasanta ma takeyi, sai dai taji suna kiranta da Eshat, wato sunan yarinyar Hajiya ƙarama wacce ta rasu. Dady yace "kuje" Hakeem ya kama hannun Iffat suka wuce. Suna komawa part ɗinsu, Hakeem ya kirayo Hajiya ƙarama da Hajiya babba, kana ya zaiyyana musu kaf abinda dady ya faɗa, ga mamakinsa sai yaji dukkansu sunce,"shawarar Alhji tayi dai-dai" Cikin fushi ya miƙe yabar gurin. ALHJI AUWAL Dukkansu ya sa a mota suka wuce kasuwa domin siyayyar kayan Abban nasu,  sai yamma liss sannan suka dawo, ko wanne yana kukan ya gaji, bayan anyi sallahar magriba da isha'i, basu samu damar ɗora komai ba, sai haɗa tea, kasancewar akawai ruwan zafi a flaks, sai da kowa ya ƙoshi, sannan nutsuwa tazo musu, ita kam Inaya har tayi barci tsabar gajiya, Alhji Auwal ya kirasu duka, kafin ya fara tambsyarsu meye babu? Amani da Mahabob sukace Abba saura kayan kwalliya, Aseela tace "Abba akwatuna har goma sha biyu?" Amani ta buge bakinta, Abban dai kallonsu ya koma yi, shima a gajiyen yake, ya miƙe yana ce musu sai da safe, sai a cigaba da lissafi. Anan ya barsu suna ƙirga tsadaddun zannuwan da suka siyo, kaf ciki babu ta 6k ko sama da haka, daga na 10k sai sama, shadoji kuwa ba'a magana, haka ma leshi da sauran mayafai da kayan barci,suma suja kuɗi. Aseela dama ta wuce ɗakinsu, Mahabob da Amani suka dinga jidar kayan suna kaiwa ɗaki suna dawowa, har sai da suka gama, tayiwa Mahabob sallama ta wuce ɗakinsu. BATOOL Kamar inda Alhji Auwal yayi mata alƙawarin washe garin ranar da suka haɗu zai turo magaba tansa, haka kuwa akayi, bai saɓa alƙawari ba sai gasu sun zo, da taimakon Batool ɗin. Baban Batool shi da yayunsa uku suka zauna da dangin Alhji Auwal suma su Uku, bayan tattaunawa da sanar da iyayen Batool ɗin da sukayi Alhajin yanada yara, kana suka ƙara da cewar tun Inaya na jaririya mahaifiyarsu ta rasu, wato gurin aihuwa, Iyayen Batool sukace Allah yayi mata rahama, ai duk ɗa na kowa ne, sunyi shedar Batool bata da matsala game da hakan, Daga nan suka buƙaci a yanke musu dukiyar aure, iyayen Batool sukace 200k, su kuma iyayen Alhji Auwal suka miƙa 500k, a matsayin sadakin Batool harda kuɗin gaisuwa a haɗe. Masha Allah kowa yakeyi, abu yayi Alhji Auwal ya haɗu da gidan karamci, dan an karrama su, daganan aka sanya rana sati biyu masu zuwa, sukayi sallama, koda suka bar gidan, suna hanya lokacin ƙarfe tara na dare 9:pm suka kira Alhji Auwal suka sanar masa da duk inda lamuran ya wakana, tare da sanar masa da cewar ansa biki kamar inda ya buƙaci a sanya masa, wato sati biyu" Yayi musu godiya sosai. HAJARA Tun da aka kwaso kayanta a gidan malam Yusuf, Goggo take cikin fargaba, da tsoron hukuncin da mahaifin Hajara zai yanke idan ya dawo, yau kwananta biyu da zuwa, yau ne kuma malam ɗin ya kira waya, a wayar mai shago dake ƙofar gidansu, dama idan yayi tafiya shi yake kira sai a bawa Goggo, bayan sun gaisa ya sanarwa da Goggo yana hanya, Hankalin Goggo a tashe tace "Allah ya kawoka lafiya, ta ajiye wayar saboda tunani wanda ta riga tayi nisa a kansa. Zuwa yamma sosai an kusa kiran sallah sai ga malam ya rangaɗo sallama, fuskarsa cike da murmishi, Goggo taje itama da fara'arta ta karɓi jakar hannunsa tanayi masa sannu da dawowa, yauwa yace tare da zama kan tabarmar da aka shimfiɗa a tskar gidan, sai ga Hajara nan ta fito daga nakewayi, a faɗace yace "ke kuma wane irin iskanci ne nan da nan sai kinzo kwana?" Hajara ta sunkuyar da kai, kafin tace "baba ya sakeni ne" "Ya me??" Wannan ƙarya ne, wlhi sai dai ki nemi gidan wani uban badai ni ba, bazan iya zama dake goɗai-goɗai da girmanki a gida ba, tamm abinda Goggo take gudu ya afku, Goggo ta share hawayen dake sintiri a fuskarta kafin tace "malam kayi haƙuri mu rungumi ƙaddara, kowane bawa da tasa ƙaddarar yake zuwa, kasan dai haƙurin da Hajara takeyi da Yusuf ba kowacce mace ce zata iya zama dashi da fitsararriyar yarinyarsa ba" "O' hoo kice harda sa hannunki ta nemi saki a gurin mijinta, nidai nace ta nemi wani gidan wallahi kinji na rantse ba gidana ba" Hajara na kuka, ta shiga ɗaki lokacin ana kiran sallahar magriba, ta ɗauko jakar kayanta, Goggo ta miƙe ta bi bayanta, kafin ta kamo hannun Hajara tace "ki wuce gidanmu kawai, gobe da safe ina nan zuwa.... Ayimin afuwa dan Allah *💋MU RAYU A TARE💋*             Mom Islam 15-16 Washe gari da wuri su Alhji Auwal suka koma kasuwa domin ƙarasa siyayya, Alhmdulilah yau kam sun gama, sun yiwa Batool siyayya ta gani ta faɗa,   har da ankon shaddar da Abban nasu yayi musu alƙawari duk sun siya, daga can ma suka miƙa ɗinki. Sai bayan sallahar azhar sannan suka dawo, wannan karon sun biya gurin sha ice cream, da su shawarma da pizza,  daganan suka dawo gida, Alhji Auwal ya wuce masallaci wanda yake jikin gidansu, su kuma suka shiga yin alwalah, bayan sun idar sun fito parlo, Mahabob ya shigo, kafin ya zauna, sukaji anata rangaɗo sallama, da sauri Aseela ta nufi bakin ƙofa tana cewa "waye?" Baba Amarya ita da Anty Saratu da Inna Binta suka ce, "kinci gidanku, zaki buɗe mana ko sai ranki ya ɓaci?" Amani ta miƙe da sauri, tana cewa "oyoyo su Inna amarya sannunku da zuwa" Bakinsu a washe suka shigo ciki, tare da kallon Mahabob dake ƙoƙarin zamewa ya gaishe su, sai da suka zauna sannan Mahabob ɗin ya gaishe su, suka amsa cike da nuna kulawa, kafin Inaya taje gurinsu tana dariya, da fara'arsu suka amsa, Inna Binta ta kamo hannunta, Kafin anty Saratu tace "ashe bikin Alhji ya kusa, shikam dangi sun isheshi baya neman kowa?" Amani tayi murmishi kafin tace "wlhi mun ɗauka su Kawu sun sanar muku ne, shiyasa kuyi haƙuri" Dukkansu suka amsa da "babu komai, dama munzo ne muji me yakeso a siya masa, kayan sa lalle kokuma kuɗi" Amani ta rufe baki, tare da cewa "bro Mahabob Please tayani mu kwaso kayan akwati kaga mun mance ashe harda wani abu ne?" Suka kwaso akwatunan, Anty Saratu ta riƙe baki, tare da cewa "wato har kun gama komai naku ba tare da neman shawara ba?" Ba su ce mata komai ba, sai cewa da Aseela tayi, ya kamata kayan sa lalle zaku siya, suka amsa da "toh" Lokacin sun buɗe akwatuna ko wanne sai riƙe baki yake, inna Binta tace "waɗannan kaya ma sunyi yawa a rage su" Amani tace "wlhi akwai wanda sukafi wannan, Ace kamar Abba zai kai kaya sai an nuna ƙaranta?" Anty Saratu tace "ke rufewa mutane baki" Ana cikin muhawara sai ga Abban ya shigo, Cikin fara'a yake yi musu sannu da zuwa, bayan sun gaisa suke shawartarsa  akan a rage kayan akwati, furr yace a'a idan da ƙari su kawo, suka tambaye shi kayan sa lalle, yace "eh suyi shikam besan ma anayi ba" Da suka tashi tafiya, Amani ta kawo musu drinks, sukayi musu sallama suka tafi. HUDA Yau ma kamar koda yaushe, Umman ta kammala dafa shinkafa da miya, ta zub  a kula, kana ta ƙwalawa Huda kira, Da sauri ta fito, yau kam tana sanye da riga irin ta gwanjo mai dogon hannu sai skel dogo wanda ya saukar mata ƙasa,  ta fito tana gyara mazaunin hijabinta, kafin tace "Umma sannu da aiki" "Yauwa" Umman tace, tare da ɗibo cokula tana ajiyewa, Ƙarar mashin ɗin da sukaji ne, yasa  Umma da Huda suka fara jidar kayan suna kaiwa gurin mai mashin ɗin, Umman na ajiyewa a zaure, Huda kuma na ƙarasawa dashi, Leƙowa Umman tayi ta bata kuɗin mashin kana tayi mata Allah ya kiyaye hanya, Huda na isa gurin siyar da abinci, mai mashin ya tsaya, ta sauke kayan tare da miƙa masa kuɗi ya wuce. Sai da ta gaishe da mutanen da suke gurin kafin ta nemi guri ta zauna, ko wanne na tsokanarta, Yau kam gidan mai ya cika da motoci, kasancewar ana lodin garuruwa anan, lokacin fara siyan abinci nayi,  mutanen gurin suka sisiya kana masu tafiya suka wuce. Wasu mata su biyar suka taho gurin huda, dukkansu sukace a sanya musu abinci na ɗari uku, ya kama duka ɗari bakwai da hamsin kenan, Huda ta sanya musu takai musu motar da suke, da mota ta tashi tafiya matan suka ajiyewa Huda robobin suka tafi, can anjima ta taho kafin takai ga gurin ragowar motocin taci karo da robobinta, hankali a tashe ta zaro ido tare da fashewa da kuka, tace "shikenan sun tafi, na shiga uku na lalace yau Umma zata kasheni" Tana kuka ta dawo gurin zamanta, mutanen da ta barsu a gurin suma sun tafi, sai da tayi kuka mai isarta, gashi abinci ya ƙare babu kuɗin robobi biyar, BATOOL Kwanci tashi asarar me rai, ikon Allah biki har ya rage saura kwana tara, Ummy kuwa sai ɗirkawa Batool magungunan mata takeyi a cewarta Alhajin ya daɗe babu aure baze yi mata da wasa ba, Shi kuma Baba duk abinda Ummy ta gaya masa sai ya biye mata, anyi mata haɗin turaruka da duk wasu kayayyaki na gyaran jiki, idan kaga Batool har wani walƙiya take, tsabar kyau, dama bazamu kirata da mummuna ba, Ƙawayenta kuwa tunda sukaji Alhji Auwal zata aura ko wacce sai shishige mata takeyi, har biki ya rage saura sati ɗaya, anata shirye shirye, ango kuwa kwata-kwata zuwansa befi sau biyu ba, yace kar a siyi kayan gado, iya kayan kitchen zasu siya, duk da yana dashi. A rana ta shida ne, Batool taje gurin dangin Ummynta, suma can ba'a barsu a baya ba, gurin ɗurka mata jiƙo na ƙarin ni'ima da neman zaman lafiya lolz, Kwananta biyu, ta dawo gida, sai da ta kwana ɗaya a gida kana taje ɗangin babanta, sukuma tayi musu kwana uku,biki ya rage saura kwana huɗu,  washe gari ta dawo gida, A ranar da ta dawo, a ranar aka kawo kayan akwati da na sa lalle daga ɓangaren Alhji Auwal, su Inna amarya da sauran dangi ne suka kawo. Dama sun san da zuwan kayan, suka shirya musu sha tara ta arziƙi,  kafin da suka tashi tafiya aka basu 30k a matsayin tukaici, sunyi murna sosai da karamci irin na gidan baban Batool, Washe gari akayi mata su dilka dama anayi mata, amma bai kai na wannan lokacin ba, koda yaushe anayi mata wankan turare, suma sun kashe kuɗaɗe masu yawa. HAJARA Bayan tayiwa su Inna wato mahaifiyar Goggo bayanin sakin ta da Yusuf yayi, Inna tace "ko wane bawa da tasa ƙaddarar, nidai kin ganni nan babu mai bani sai na fita tallar kayan koli sannan nake samun abinda zanci, idan ba damuwa, kiyi shawara da Goggonki ki siyar da kayan ga donki ki fara sarin kayan sawa ko gwajo ne, kina shiga dashi ƙauyika, Hajara tace "to insha Allah zan gaya mata" Washe gari, kwanan Hajara ɗaya da zuwa, basu suka karya ba sai wajen azhar babu abinci, a hakan ma sai da Inna ta aika Hajara karɓo mata bashi  sannan suka samu suka siyi lifton da bredi, Ƙarfe  uku dai-dai, inna ta ɗauki tallar kayan koli ta fice, Hajara ta zauna tayi jugum tana tunani iri-iri, can zuwa la'asar sai ga Inna ta dawo, hannunta riƙe da leda babba, Hajara da ta idar ta sallah taje ta karɓa, tanayi mata sannu da dawowa, Inna tace "wlhi biyan bashi akayi min da garin rogo shine na karɓo" Hajara tayi shiru, suna cikin magana, wata ana ce mata Hassan mai kyau ta shigo, Hajara na ganinta ta washe baki, saboda sun san juna tun ba yau ba, halin Hassana ne yasa Hajara rabuwa da ita, akwai ta da munafurci da cuta harma da cin gumin da ba nata ba, bayan hakan bata shakkar ta ciwa uban kowa mutunci, a hakan dai inda tazo kamar ta gyaru, dan akwai alamun nutsuwa a tare da ita. Hassana tace "Hajara ashe zamu sake haɗuwa?" Hajara tace "ai kuwa gashi Allah ya haɗamu" Goggo tace "banda mutuwa da auranta yayi ... Kuyi haƙuri bani da chaji Please a tayani share Banda chaji dan Allah *💋MU RAYU A TARE💋*            Mom Islam 17-18 "Mazan yanzu sun zamo abin tsoro wlhi aure ya zamo shige da fice yanzu, nikam tunda nayi wani aure shekaru uku da suka wuce, muka rabu tsiya-tsiya dashi, Allah yasa ma ban aihu dashi ba, tun daga nan na sallami aure" Inna tace "Uhm Hassana, babu macen da zata iya zure tozarci da wulaƙanci irin wanda Hajara ta jure a gidan auranta, nidai nace mata ta siyar da kayan ɗakinta ta kama sana'a, saboda babu inda zamuyi mu zauna babu sana'a, tunda bamu da kowa sai Allah" Hassana tace "idan babu damuwa Inna kuzo muje gidana sai muyi wata magana acan, zaku ganewa idonku ikon Allah" Hajara tace "to Inna zamuje ko?" Inna ta miƙe tare da janyo mayafi a jikin igiyar shanya tacewa Hajara "tashi muje" Hajara ta miƙe ta ɗauko hijabi a cikin ɗaki kana suka fita tare da Hassana, suna tafe suna hira, har suka iso anguwarsu Hassana, duk da ba wani nisa ne da anguwar ba, amma akwai tafiya. A bakin wani tangamemen get Hassana ta tsaya, hakan yasa suma suka tsaya, Hassana tasa key ta buɗe get ɗin tare da cewa "ku shigo" Duk cikinsu ko wanne tunaninsa be wuce yaji ina Hassana ta kawosu ba. Kamar inda ta umarcesu suka shiga ciki har parlon nata, ta nuna musu tsala-tsalan kujeru suka zauna, Hajara harda sauke gwauron numfashi, Hassana ta zauna a kujera mai kallon ta Inna kafin tace "Inna nasan zakuyi mamaki idan har nace muku nan ne gidana, anan nake rayuwa, ina aiki a ƙasar waje, Jikin Inna yana rawa tace "ikon Allah kice har kin leƙa waje kin barmu, to wane irin aiki kikeyi?" Hassana tace "wlhi aikin wanke-wanke a gidan larabawa, suna biyan mutum albashi mai kaurin gaske, shiyasa na dage, a cikin shekara ɗaya kinga inda na zamo" Tunda Hassana ta fara magana Hajara ta zuba mata ido, tana son cewarsu da ee de q, ya za'ayi nima inje, tana tsoron abinda Inna zatace, Kamar daga sama, taji Inna tace "to yanzu kamar Hajara zata iya zuwa kenan?" Free 3 se Waqqas Waqqas q ware se 3w welcome welcome 3 "Eh sosai ma, wlhi zata samu alkairi sosai, bayan haka kaf danginta sai sunyi alfahari da zuwanta" Inna tace "gaskiya bamu da kuɗi, koda an siyar da kayan ɗakinta bazasu isa taje can ƙasar ba" Hassana tayi dariya, kafin tace "haba Inna me kayan koli, nima mai iya yi muku jagora ne, ba tun yanzu nasan Hajara ba, wlhi tanada kirki, insha Allah zan taimaka muku, kawai ta fara shiri, koda tafiyar ta matso ya zamo a shirye take". Cikin amincewa tare da sanya albarka Inna tace "mungode, yanzu kuma ya rage tsakanina da iyayen ta, idan sun amince zaki ji ni". Daga nan sukayi sallama, a dawowa mashin su Inna suka hau ita da Hajara, ragowar kuɗin sukayi cefane, kasancewar kuɗin mashin biyu ta basu, sukuma suka hau mashin ɗaya. HUDA Tunda takawo shinkafa mutane suka fara miƙa mata kuɗi, sakamakon yau ba da wuri tazo ba, ana tsaka da siyan abinci ta ruɗe, har wani ya tafi mata da kuɗi bata sani ba, sai da tayi lissafi kafin ta zabga tagumi, gashi gurin mai shagon da ta saba zuwa baya nan, shawara ta yanke zuwa gurin masu yin lodi anan tashar, gurin babu mutane kasancewar sai an gangara duk tana kai abinci nan, idan sunada buƙata, "dan Allah malam ka taimakeni ka bani ɗari uku in cika kuɗin abinci wlhi wani yaci ya gudu" Wani dattijo wanda a ƙalla zeyi shekaru sittin ya kirawo ta, sakamakon wanda take yiwa magana ma waya yakeyi besan tayi masa ba, "biyoni ɗaki zan baki" Jikin Huda na rawa tace "to" Ba tare da jin ko mai b, ta shiga ɗakin da taga ya shiga, tunda idan ma bin nasa tayi bai wuce ya taɓa mata nonuwa ba ya bata kuɗi, cikin salo na wayo dattijon ya nemi wani buhu wanda yake a shimfiɗe a ɗakin ya zauna, tare da yi mata alama da hannu wato "kizo" Sai yanzu gabanta ya fara faɗuwa, duk da bayan haka batasan komai ba, ta gwammace yayi mata abinda zeyi mata ya bata kuɗin kodan kauce wa dukan Ummanta, Tana ƙarasowa kusa dashi ya ɗorata akan cinyarsa, tare da kunce mazugin wandonsa yana cewa "taɓa min nan, yanzu zan baki kuɗi" Huda ta tura hannu cikin tashin hankali, cikin rashin tsammani ta taɓo wani abu wanda ta kasa banbance meye... BATOOL Kwanci tashi asarar mai rai, gobe insha Allah Asabar ta kasance ranar ɗaurin auran Batol da Alhji Auwal, tun kafin ranar Batol tayi kyau har ta gaji, anyi rabon invitation card da sauran su, iya walimah zasuyi yau, cikin ikon Allah akayi komai aka kammala, Acan ɓangaren su Amani kuwa ansha party wanda shi kansa Abban nasu besan sunyi ba, tunda maza aka tara da mata aka dinga raye-raye, abinci ma basu wahalar da kansu ba ordersa akayi daga restaurants, a ranar aka sanya Mata lalle, bayan tayi na henna da ja, Washe gari dubban al'umma suka sheda d'aurin auran Alhji Auwal da Batool, ɗaurin auran da ya samu halartar manyan mutane wanda sukazo daga ƙasashe da dama, haka ma ƴan uwan Ummy da baban Batool suma ba'a barsu a baya ba, sunyo gudun mawar kayan ƙamshi na girki da kayan yaji da su kaninfari da sauransu, hatta can ƙaramar ma'aikata anyi wadaƙa da abinci da drinks da sauran abubuwan da aka dinga rabawa, Batool tasha faɗa agun dangi, musamman akan tayi biyayya ta kula da yaransa kar ta sake ta ɗauki zugar mutane ta cutar dasu Allah na ganinta, Hakan yasa ta dinga kuka, tunda taji mutane nata cewa nauyi ya hau ta ga na mijinta, ga na yara. Sai yamma liss sannan motoci guda biyar sharoon suka zo ɗaukar amarya, mutane kam harda maƙota babu wanda bai je ganin gidan Batool ba, kodan azo a bada labari, Alhmdulilah gida yayi kyau, ya tsaru, duk da dai anan ɗin yaransa suke, ɗakinta ne daban da parlonta amma duk a sashen suke kuma Babu inda zaka ce kafin kaje ka fita waje, Kowa sai yi mata fatan alkairi yakeyi, komai yayi, Ana kawosu zuwa magriba bayan anyi sallaha masu motoci suka aiko duk wanda zai koma gida yazo su tafi, sbda ba'a kwana, a gurguje aka sake jaddada mata nasiha tare da sake bata haƙu akan tayi zaman haƙuri tare da yi masa biyayya, kuma ta dinga jan yaran nasa a jiki. Batool tayi kuka sosai, gashi ita kaɗai a ɗaki, hakan yasa tayi alwalah tazo tayi sallar magriba da isha'i, wanda batayi ba, ta zauna akan sallahya bayan ta kammala adu'ointa, "Aslamu alaikum" "Wa'alaikumussalam" Batol ta amsa tare da jirin shigowar masu sallamar, Amani Alhji Auwal da Mahabob, sune suka shigo, hannun Mahabob riƙe da ledar kaji, ita kuma Amani hannunta riƙe da ledar Rufaida  Yoghurt.... Ayimin afuwa yarona ne babu lafiya shiyasa kuka jini shiru, Alhmdulilah yaji sauƙi, karku manta yawan shar'hi shike ƙarawa marubuci kuzarin yin typing.. Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 19-20 Kallo ɗaya Batol tayi musu kafin ta, sunkuyar da kanta, cikin sanyin murya tace "sannunku da shigowa" Amani tace "sannu Aunty Yaya Mahabob taso mu tafi" Alhji Auwal yayi murmishi kafin yace "bye Allah ya tashemu lafiya" Basu ƙarasa ɗakunan nasu ba, suka zube akan kujerun parlonsu, Mahabob akan 1 sitter Amani akan 3 ta miƙe ƙafa, sai ga su Inaya da Aseela sun fito suna cewa "kowa ya watse kenan?" Inaya ta fara kuka tana shure-shure da ƙafafu, Amani ta tambaye ta "lafiya kuwa?" "Nidai gurin dady zani" Aseela ta ɗauke ta, tare da ficewa da ita zuwa sashen Batool, da ƙarfi tayi nocking a bakin ƙofar, kasancewar kukan Inaya ya ƙaru sosai, Har sunyi sallar nunawa Allah godiya, Ya kamo hannun Batol kenan yaji nocking, da sauri yace "waye?" Aseela tace "Abba Inaya ce take kuka, tace gurinka zata zo" Abba ya mayar da babbar riga ya miƙe ya buɗe ƙofar kafin ya ƙarɓi inaya, har ya juyo Aseela tace "aunty ina wuni" Batool ta amsa da "lafiya lau ya karatu" Kafin Aseela ta bawa  Batool amsa, Abban yace "oya sai da safe" Bayan ta tafi, ya rufe ƙofar, tare da dawowa gurin Batool, ya kalli Inaya dake zaune akan cinyarta kafin yace "Auta kin gaishe da Auntyn baki kuwa?" Inaya ta kwaɓe fuska zatayi kuka, Har ƙarfe 12:am na dare suna zaune, da zarar Inaya taji ance za'a kwanta sai ta fashe da kuka, Batool kam sai gyangyaɗi takeyi, har Allah yasa Inaya tayi barci, Abba ya ɗorata akan gado, yazo ya ɗaga Batool itama ya kwantar, sosai yaci alwashin raya wannan dare tare da Batool amma hakan bai yiwu ba, dole ya haƙura, ya tashi ya yi alwalah, ya fara salloli tunda asbha dai tariga da tayi, sai dai a jira kiran sallah. IFFAT Washe gari, dady ya kira ƴan jaridu da masu aiki a gidan TV da duk masu yaɗa sanarwa a kafafen sada zumunta, tare da hotunan Iffat, Abin mamaki su Dadyn nata zuba ido suji an samu iyayen Iffat amma shiru. Hankalin kowa ya tashi, musamman ma su Hajiya babba da Hajiya ƙarama, Hakeem ya koma bakin aiki, a hakan ma sai da Dady yayi ta masa faɗa sannan, Iffat kuwa komai ta gani kallo ne, gashi bata cika magana ba, duk da suna yawan zuwa gidan Zoo ko zataga wani naman daji ko abun da zai sanya tayi magana, batayi sai dai kallo kawai. Bayan sati Uku. Hajiya babba da Hajiya ƙarama da Iffat suna zaune a parlo, hira sukeyi akan mugayen iyaye wanda suke jefar da ƴa'ƴansu a bola wasu tsinta suyi rainonsu, duk  maganar akan Iffat ake yinta, suna tsaka da hira Hajiya Fawziya tayi sallama, cikin fara'a dukkansu suka amsa, bayan sun gaisa ta kalli Iffat kafin tace "a ina kuka samo wannan yarinyar?" "Hajiya ƙarama tace "wlhi yarinyar sisterna ce" Hajiya Fawziya ta taɓe baki, duk Hajiya ƙarama na kallonta, kamar meyin wani abu Hajiya ƙarama ta miƙe, a sukwane tabar gurin. Parlon ya rage daga Hajiya babba sai Iffat da Fawziya, Fawziya ta taɓo Hajiya babba kafin tace "aunty wannan yarinyar waye?" "Ƴar tsintuwa ce, wlhi Hakeem ne ya bigeta shikenan ta samu juyewar ƙwaƙwalwa, kin ganta nan anyi cigiya har an gaji babu iyayenta" Hajiya Fawziya ta zaro ido, cike da tsegumi tace "shine kike zaune da ita?" Kinsan dai Hakeem befi shekaru 18yrs ba, bakya tunanin ya taso yace yana sonta?" Hajiya babba tace "wlhi kuwa, nima dai na fara tunani amma ai wannan Eshat ɗin ƙarama ce" "Mtsw aunty ina baki kina ƙin karɓa wlhi tallahi irinsu ne suke zamowa wanda ya riƙesu masifa, wata ƙil ma aljana ce baki sani ba, dubi idanuwanta, dubi gashinta har gadon baya" Hajiya babba tace "Ƙanwata yi a hankali, dan wannan me baƙin halin ta jiki wlhi sai tayiwa Alhji famfo... Ayi haƙuri babu yawa, insha Allah zan dinga yi da yawa, nidai burina aci gaba da comments, nikuma kullum in dingayin typing insha Allah mai yawa Ana wata ga wata muje zuwa... Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam *Wanda suke nema daga farko suyi min magana*👇 http://wa.me/08141799224 21-22 A gurguje suka gama shawar-warin inda za'akai Iffat ba tare da sanin kowa ba, cike da ƙwarin guwaiwa Hajiya Fawziya tabar gidan, Yau kam da wuri Hakeem ya dawo daga gurin aiki, duk da cewar ba wani aiki yakeyi ba, amman dai dady ya tsaya masa akan koda yaushe ya dinga zuwa yana ganin abinda sukeyi, Yana shigowa kai tsaye ɗakin Hajiya ƙarama ya wuce, murya ƙasa-ƙasa yace "Hajiya na dawo banga Iffat ba ko tayi barci ne?" Sai a lokacin ta dawo daga dogon tunanin da takeyi, kafin ta juyo tace "ka duba ɗakin hajiyarka tana nan, idan ka ganta ka kawomin ita" "Tom" Yana tafe yana waƙe-waƙensa har ya iso bedroom ɗin hajiyar tasa, kalaman da yaji Hajiyar tasa tana ambata ne yasa hankalin Hakeem mugun tashi, bai yi aune ba yaji tana ci gaba da cewa "nifa tunda na ganta a hospital nasan Alhji zai bata muƙami da daraja irin wanda zai bawa Hakeem, kinga kuwa ya kamata in ɗauki mataki tun yanzu, karki damu gobe insha Allah zanzo gidanki, domin muyi shawarar inda lamuran zasu kasance" Hankali a tashe Hakeem ya kalli ƙofar ɗakin hajiyarsa kafin ya waiga yaga babu kowa, a hankali ya juya tare da toshe bakinsa ya nufi ɗakinsa, yana shiga ya faɗa kan gado, tare da wurgar da ƴar ƙaramar leda wacce ke ɗauke da chocolate da biscuits a ciki, bai damu da zubowa kan tails da sukayi ba, ya tura hannu cikin gashin kansa wanda ya kasance baƙi wulik, irin mai kwanciya ne kamar anyi masa shampo. Tambayar da yakeyiwa kansa, shin dawa Hajiya take yin waya?" Bashi da mai bashi amsa, kana kuma baya fatan hajiyar tasan yaji duk wani ƙulli da take shirin yi akan Iffat, dole ya fara ƙoƙarin kawar da fushinsa, ta hanyar miƙewa ya sha banɗaki ya kulle kansa, a hankali ya ɗago hannunsa tare da kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, ƙarfe 5:20pm na yamma, kafin ya mayar da kallonsa ga mudubi yana ci gaba da tattaro sumar kansa. "Babana.! Babana..!" Hakeem naji hajiyar nayin nocking amma yai banza da ita kamar beji ba, sai da tayi sau uku sannan yace "ina toilet" "Okay zan duba girki a kitchen koda zaka nemeni" "Iffat ɗin fa?" Hakeem ya faɗa a hankali. Cikin sanɗa ya buɗe ƙofa tare da wucewa ɗakin hajiyar, sai da ya tabbatar da babu mai ganinsa, kafin ya tura ƙofar, ya samu babu Iffat sai wayar Hajiyar, cikin sauri ya cire code ɗin jiki, kasancewar sunansa ne a jiki, kafin ya duba gurin da tayi kira ɗazu,  number sister Fawziya  ya gani a farko, cikin hikima da dabara yayiwa Hajiya Fawziya Text massage, kamar haka, "Kiyi haƙuri ƙanwata yanzu Alhji ya shigo yacemin zamu fita anguwa gobe bazan samu zuwa ba" Hakeem ya tura saƙon, Saƙon yana tafiya sai ga kiran Hajiya Fawziya, Hakeem ya rage volume, tare da katse kiran, tabbas taji haushi sosai, saboda dama ba wani shiri suka cika yi da hajiyar ba, sai dai idan tanaso ta yagi wani abun, a jikinta, wanda ita hajiyar har yanzu ta kasa gane hakan. Kamar Wanda ya tuna wani abu, sai ya miƙe ya dawo ɗakinsa ya kwanta, duk da cewar yasan kwanciyar yamma bata da kyau hakan ya kwanta. Yana tsaka da tunani yaji ana nocking ɗin ƙofar ɗakinsa, cikin ɗaga murya yace "waye?" "Nice,  Hajiya ce take kiranka tana kicin" "Tom ina zuwa" Hakeem ya faɗa yana mita.. Tunda mutumin ya yasar da ita a gurin bola, take ta wani yage-yage, ga duhu yayi, a hakan duk wanda ya santa da yarinya zai iya gano damuwa akan fuskarta, wanda hakan yasa idonta ɗaya keta fitar da hawaye,  da sauri ta miƙe tare da rugawa da gudu tana surutai, babu wanda ya kulata, bare ya tausaya mata. Lokacin anyi sallahar magriba da isha'i duhu yayi sosai, sanyin iskar da akeyi ne, tare da gagarumin hadari kamar na ɗazu, ya sake haɗowa, ta rasa mafaka sbda idan ka lura da ita ba wani gani takeyi sosai ba, tunda babu haske a garin, sai ƙamƙame jikinta takeyi tana rawar sanyi haƙoranta na kaɗawa, a hankali ta tsagaita gudu tare da shiga irin ginin nan wanda ba'a rufa masa kwano ba, tashi ɗaya ruwa ya fara zubowa kamar da bakin ƙwarya, duk da ta rakuɓe a jikin ginin hakan bai hana ruwa dukanta ba, sosai ruwan ya jiƙata ga wani masifaffen zazzaɓi daya dirar mata tashi ɗaya, acan ƙasam zuciyarta tana kewar ƴarta Iffat, ba magana takeyi ba bare intayi a gane, koda tayi maganar ma babu mai fassara mata idan har ba Iffat ɗin ba, wani irin cakuɗin yare takeyi wanda kome tace "Allah yana sanar da Iffat, duk da ruwan ya jiƙata sosai hakan bai hana idonta na dama ci gaba da tsiyayar da ƙwalla ba, ga wani fizge-fizge da soshe-soshe da takeyi tare da rawar sanyi, har har ruwan ya ɗauke tana rakuɓe a gurin,  a hankali ta ɗaga kanta sama, taga haske ya gauraye ko ina, alamun an kawo wutar nepa, ta miƙe jikin nata na karkarwa ta fara zagaye ginin, can ta hango leda a ƙulle, da sauri ta isa gurin ledar tare da kuncewa, tsarsaman abinci ne wanda mutane suke wurgowa idan ya lalace, ta gyara bakin ledar har ji take kamar ta tura har da ledar tsabar yunwa, hannu baka hannu ƙwarya take cin abincin, tana gamawa ta suɗe hannunta tare dayin gyatsa, ta nemi  guri ta kwanta, ƙafarta ɗaure da gora. "Aslamu alaikum.. ina mutan gidan?" "Wa'alaikumussalam, oyoyo Inna sannu da zuwa" Goggo ta taso daga wanke-wanken da takeyi, tare da ɗauko tabarma dake jingine a bayan ƙofar ɗakinta ta shimfiɗa wa Inna, sanin innar bata shiga ɗakinta. Bayan sun gaisa tayiwa Goggo jajen mutuwar auren Hajara, Inna ta gyara zama, kafin tace "arziƙi yana binmu har gadon barcinmu" Cikin rashin fahimta Goggo tace "ban gane ba Inna wani abu ne ya faru?" "Eh to, wlhi wata yarinyar maƙotanmu ce, zata yiwa Hajara hanyar zuwa ƙasar waje aiki, shine nace bazanyi ƙasa a guwaiwa ba gurin zuwa sanar dake" Goggo ta jinjina kai, tare da cewa "Inna ke bakya tsoron wata matsala ta ɓullo nikam ina tsoro wlhi, Hajara ko Kano bata taɓa zuwa ba, bare ƙasar waje" Inna ta rufe Goggo da faɗa, harda cewa, da kinga alkairin da Hassana ke samowa wlhi bazaki kushe alkairin da na nufoki dashi ba, amma baki da hankali, mijin naki ya kori ƴarki kika barshi, bayan yanzu ga dama tazo miki, inda zaki nuna masa ruwa ba sa'an kwando bane, amma kin tsaya ni kina tijarani" Har ga Allah Goggo bataji daɗin shawarar da Inna ta kawo mata ba, "amma akwai Allah" Goggo ta faɗa a zuciyarta, tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. "Na'amince, amma a ina za'a samo kuɗin tafiyar, nikam sisi bana magani nasan koda kayan Hajara aka siyar duka kuɗin bazasu isa ba" "Habawa ai Hassana ƴar albarka ce, tace zatayi komai, inyaso idan aka samu abinda ake nema sai ta cire a ciki" Inna ta faɗa tana miƙewa tsaye. "To Allah ya shige mana gaba, yaushe ne tafiyar?" "Nan bada jimawa ba, ai hajaran ma zatazo" Daga nan sukayi sallama Inna ta wuce. Goggo ta dawo kan tabarma tare da jingina da bango tana tunanin tafiyar Hajara, tayi nisa a tunani sosai ta tuna da kayan miya dake ajiye a kicin, a hankali ta miƙe tare da nufar kicin ɗin tare da share hawaye, a fili tace "Akwai Allah" Cikin tsananin buƙatuwa tsohon ya runtse ido yana cewa "yauwa ƴar albarka, shafa ta a hankali inda saƙon zai isa inda ake so, Huda taci gaba da taɓa masa idanunta na zubar da hawaye, kan kace me har ya fara shirin yaye mata mayafin jikinta, tunda har ya kai hannunsa saman ƙirjinta, a hankali murya a sanyaye tace "sai ka bani kuɗi" Jikinsa na ɓari sbda ya gama rikicewa da abin da Huda takeyi masa, ya miƙo mata dubu ɗaya, kana yace "to ciremin mayafin, Huda tayi kamar zata cire mayafin ta miƙe ƙafa kamar me shirin yin wani abun, shikuma ya kwanta a rigingine, huda ta miƙe da sauri, tare da zubawa da gudu har tana faɗuwa, batasan ta fasa baki ba sai da takai ga gurin kayan abincinta, sannan ta shafo bakinta dake yi mata zogi, tama kasa kuka, farincikinta kuɗin da ta samu, tayi canji tasa kuɗin daya ɓata ragowar ta ƙulle a gefen zani, ta ƙarasa bakin titi ta tari mashin zuwa anguwarsu. Washe garin safiyar Litinin an tashi da sanyi mai shiga jiki, ƙarfe 8:pm, Hakeem ya shigo ɗakin Hajiya ƙarama da sallama, tana zaune hannunta riƙe da ɗan ƙaramin cup wanda yake ɗauke da zuma, ta amsa tare da cewa "Hakeem bismillah" Ƙarasowa yayi tare da risinawa ya gaishe da Hajiya, kafin ya leƙa fuskar Iffat dake barci cikin kwanciyar hankali, duk wanda yaga inda take barcin zai tabbatar da lafiya tana sake samuwa, "Hajiya Iffat har yanzu bata tashi ba?" "Ai Iffat tunda ta tashi cikin dare tasha tea ta koma barci" Hakeem yayi murmishi tare da sake leƙata yana ci gaba da murmishi. Hajiya ƙarama ta fice, sbda yau itace a kitchen, A hankali yaje ya shafi gefen fuskarta tare da kamo lallausan hannayenta yayi musu kiss kafin ya tallafo kanta yana wasa da jelar kitso na kalaba, yana wasa dashi, kamar wanda ya tuna wani abu, a hankali yayi baya yana ci gaba da ƙura mata ido, Sai kuma ya fice da sauri. Kai tsaye bedroom ɗin dady yaje, cikin sa'a ya samu dadyn a zaune da jarida a hannunsa, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga kafin dadyn ya amsa masa, yana cewa "banga ka shirya bane, ko yau kana hutu ne?" Kawar da zancen yayi ta hanyar cewa "Dady dan Allah ina roƙon alfarma a gurinka" Jikin dadyn a sanyaye ya kalli Hakeem, sbda Hakeem baya taɓa roƙonsa wani abun har sai dai in ya kasance mai muhimmanci sosai ba na wasa ba, "Ina jinka Hakeem, ka faɗi koma meye bakada matsala" "Dady ina ganin kamar idan aka fitar da Esha US zata iya samun lafiya" Dadyn ya nisa, tare da ƙurawa Hakeem ido kafin yace "insha Allah zan duba inga abinda ya dace sai ayi, abinda yake yimin ciwo shine har yanzu babu labarin danginta" Hakeem ya sunkuyar da kansa, sam ya kasa cewa komai Bayan kwana biyar da zuwan su Inna gidan Hassana, kasancewar koda yaushe Hassana tana tare da Hajara yasa, suka dinga zirga zirgar yin su hoto da duk wasu abubuwa da ake buƙata, kasancewar itama hassanar tana da na gaba da ita a harkar, Ana saura kwana biyu tafiyarsu, Hajara taje gidansu tun safe sai yamma ta dawo, duk zaman firar da sukayi ita da Goggo duk akan ta riƙe mutuncinta tayi abinda ya kaita, ta kiyaye cin abinda ba nata ba, kana ta kiyaye lokutan sallah kar neman abin duniya yasa ka mance da ibadarka, Da kuka suka rabu, Goggo kam tace ta yafe wa Hajara duniya da lahira, kana kuma tace "bazata iya zuwa suyi sallama ba, Allah ya tsare". Goggo taji daɗi da Baban Hajara baya nan bare yaji labari a gari, tunda shi ba waya ce dashi ba, sai yana son magana da ita, yaje gurin masu sana'ar kiran waya, ya kira su gaya masa minutes ɗin da yayi ya biya su. Washe gari, suka kammala shiri, Inna ma tayi mata faɗa sosai, jikin Hajara yayi sanyi dan har ta fara tunanin ko ta fasa ne, Inna sai ƙara mata ƙwarin guwaiwa takeyi....! Ayi haƙuri kwana biyu an jini shiru, wanda sukayi comments ban yi musu magana ba suyi hakuri abubuwanne sunyi yawa, masu nema daga farko suyi min magana Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam _Arewabook@momislam11_ 23-24 Cikin hukuncin ubangiji jirginsu ya sauka a Libiya, Taƙaitaccen bayani akan ƙasar Libiya. Mutunen Libya sun kai adadin 6000,000 a sahile a arewacin kasar kabilolin Libya su ne, larabawa, barbarawa, tubawa karaglawa ( hadin turkawa da larabawa ), Buzawa da 'yan tsurarun ( hausawa da bare-bari ). harshen larabci shi ne harshen kasar, larabcinsu yana da bambanci da sauran na kasashen larabawa kuma da akwai harsuna da yawa masu bambancin harshen ( Amazik, Buzanci tubanci da harshen Hausa ) shi ne harshen kasuwanci a birnin sabha da ke a kudancin kasar . katafaren gida  ne, wanda idan kaga gidan zaka ɗauka ba a duniyarmu yake ba, sbda tsayawa misalta kyawun gidan zai iya zamowa ɓata lokaci, gidan babba ne, kai kace gidan mutane da yawa, a cikin gidan ko muce parlon wanda anan Nigeria, muke kiransa da mu haɗu a parlo, Cikin isa da ƙasaita yake saukowa daga steps, daga yanayin fuskarsa idan ka kalla zaka tabbatar da koshi waye, shahazad kenan, da sauri ya ƙarasa saukowa kamar wanda ya tuna wani abu, kafin ya tako cikin taƙama ya zauna kusa da Mona, yana zama ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, kafin ya tallafo haɓarta, cikin cold voice ɗinsa wace ko yaushe yake using ɗinta a gurin Mona, yana ci gaba da  shafa haɓar tata yace "ƴan mata barka meyasa kika dawo parlo bayan kinsan ina tsananin buƙatarki a kusa dani?" Jikin Mona yana karkarwa, takai lallausar hannunta ta share hawaye tare da, ɗago kanta fararen idanuwanta suka sauka a nasa kyawawan idanun, bakinta ne ke motsi amma sam ta kasa furta koda ɗaya, "faɗi abinda ke bakinki" Murya na rawa tace "Please ka mayar dani gurin iyayena basu da kowa sai ni, a halin yanzu suna da buƙatata" Ta ƙarashe maganar tana tura yatsunta cikin sumar kanta, wacce ta kwanta har gadon bayanta, "Mona, kona mayar dake bazaki taɓa canzawa a matsayin mata ta ba, ko kin mance munyi aure kuma da yardarki da yardar iyayenki, kece zaɓina don haka ki kwantar da hankalinki" "Ni bazan iya zaman aure dakai ba, karatu zan koma" "Zan mayar dake makaranta tunda kinaso amma ki yarda keɗin mata ta ce" "Ya isaaaa.." "Karka sake kirana da matarka, mugu azzalumi" Da sauri shahazad ya dunkule hannu zai kai mata naushi, ko me ya tuna sai ya fasa ya dafe kansa, tare da miƙewa, Har ya yi taku biyu, wayarsa tayi ring, a hankali ya zaro wayar daga aljihu tare da karawa a kunnensa, "A zubasu a gidan hutawa ta" Mona ta runtse idanunta, tashi ɗaya hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa suka sake sulalowa, a hankali ta miƙe tare da juyowa ta kallashi, cike da nuna yanayi na sha'awarta yai saurin miƙewa ya kamo hannunta, a hankali ta faɗo jikinsa, cikin nuna masa ƙarfinta ta fara fizgewa tana tureshi, kai kace mai neman wani abu ya fara lalubarta yana kashe mata ido. LIBYA ANGUWAR (Sabha) Wata hamshaƙiyar mota mai numfashi ce tai parking a wani haɗaɗden gida, ga mamakina na tsaya ganin suwaye a cikinta, Hassana da Hajara na gani ko wanne hancinsa sanye da takum kumi, har shima balaraben dake driving ɗinsu, Duk da jar fatarsa hakan bai hanashi jin Hausa ba, kai kace bahaushe, "bismillah ku shiga gidan a buɗe yake" Hassana tayi gaba Hajara na Bin ta a baya suka ƙarasa cikin gidan, subhanallah kuzo kuga tsaruwar gidan, ni kaina tsayawa kallo nayi, ga mamakina sai naga an shigo dasu gidan su Shahazad, tambayar anan shine ƙofar guda biyu ce?" Dan ta baya aka shigo dasu, fentin kuma ba irin na gaban bane, Da farko driver ne ya shiga ya nema musu umarnin iso kafin ya dawo ya sanar musu zasu iya shiga. Shima Shahazad ɗin yaji Hausa sosai, Suka shigo bakunansu ɗauke da sallama, Mona tai ƙoƙarin kawar da fushinta ta hanyar amsa musu sallama, kafin ta dawo da baya ta nemi guri ta zauna, "barkanku da zuwa" Hajara ta ƙurawa Mona kallo a zuciyarta kuwa cewa take "ina mutanen gidan ko sunyi tafiya ne? dalilin tambayarta shine, taga Shahazad babban mutum sai dai kuɗi ya ɓoye duk wani girma da wani abu na ganin muni a tare dashi, sai dai ma kaga kyawunsa, ita kuma Mona a ƙalla batafi shekaru 12yrs ba, a duniya, Hassana ta taɓo Hajara tare da ƙifta mata ido alamar ta rage kallo, zasu iya samun Matsala, Shahazad ya ƙaraso cikin izza ya zauna kusa da Mona yana mai riƙe hannunta, kafin yace "masha Allah na gane ki, kece Haseena ko?" Shahazad ya nuna Hassana, cikin rawar jiki Hassana tace "ga sister na sunanta Hajara" "Masha Allah Hajar Barka da shugowa rayuwar Shahazad, ke Haseena mun riga da munyi magana da Abdul Alee akan can zakiyi masa aiki, ita kuma sabuwar zuwa zatayi mana aiki anan gidan" Hassana tace "Nagode sosai oga, alkairinka a gareni bani da bakin yi maka godiya" Mona kuwa tana zaune ta zuba musu idanu. Sun kai wajen ƙarfe 5:pm, kafin wata mota ta dinga horn a ƙofar gidan, bayan masu gadi sun buɗe mata motar ta shigo, mamalakin motar ya aika ɗaya daga cikin securityn gidan domin ya kira Hassana, cikin sa'a sai gasu sun fito har da hajara, kafin su ƙarasa can gurin motar, Hassana tace "Hajara wlhi idan kika kiyaye dokokin mutumin nan ba ƙaramin hutawa zakiyi ba, keda talauci sai dai kiga anayi, amma fa kiyi ƙoƙarin riƙe sirrukansa saboda mutum ne mai haɗarin gaske, wlhi tallahi ya kashe mutum ba wani abu bane a gurinsa, duk ƴan ta'addan da kikaji ana labarinsu a ƙasar Libya to da sa hannunsa a ciki, ɗan cocaine ne na bugawa a jarida, sai dai duk iskancin da yakeyi baya Wasa da sallah, wannan yarinyar da kika ganta matarsa ce, Kuma sirrinsa" Hajara ta dafe ƙirji, duba da inda taga Hassana tana maganar tana waiwayen bayanta. Sukayi sallama, yayin da suka iso gurin motar, dama sunyi musayar number waya, Hajara ta dawo jiki a sanyaye, sosai tsoron Shahazad ya fara shigarta, a zuciyarta tace "ashe suma suna yin auren wuri kenan, banda rashin tausayi ace ƙaramar yarinya ta auri wanda yake rikiɗewa saurayi da tsoho, wlhi wannan mutumin zaiyi shekaru 50yrs" Kafin ta ƙarasa ciki bakinta ɗauke da sallama. Har yanzu yana zaune a parlon banda Mona da ta gudu ta ƙulle ƙofarta, Yana ganin shigowar Hajara yace "zaki iya zama sbda in gabatar miki da dokoki da tsarukan gidan, sannan ki bani hankalinki duk abinda na faɗa yanzu bazan sake mai-maitawa ba, sai dai muje ga abubuwa na gaba, cox bani da isasshen time da zan tsaya surutu". Cikin ladabi da girmamawa Hajara tace "Nagode insha Allah zan kiyaye koma meye" Kafin ya fara magana ya cillo mata bandir-bandir na kuɗinsu nacan, sannan yace na farko bana son munafurci, idan har kika sake koda kuskure kika munafurceni komai yana iya faruwa, Mona matata ce, inaso ki zamo uwa a gareta bana son a dinga takura mata ko ɓata mata rai, karki sake ko wani guri kukaje tayi magana da wani koda wani abun take buƙata ayimin magana, babu inda babu mutane na, sannan kar ki sake in kamaki da lefin kina yiwa wani aiki bayanni, ko kina ɗibar sirrukan gidannan kina fitar mun dasu, Inaso ya zamo koda wane lokaci kina tare da ita kuma kina kula da ita, da zarar na shigo ki fice ki bamu guri lokacinmu ne, idan har kika cika waɗannan sharuɗan zamu zauna dake lafiya.." Kan Hajara a ƙasa tace "nayi maka alƙawarin hakan insha Allah" NIGERIA Prince Abdul laƙabi (Arshad) niko nace iko sai Allah, can na hango shi a kan wata haɗaɗɗiyar kujera leda sit baka jin ƙarar komai sai na AC da TV wanda ya mamaye ilahirin bangon ɗakin,  tashar MBC action ne yake ta aiki a TV ga mutane kamar ka zura hannu ka ciro su, Masha Allah gidan yayi babu makusa, hankalinsa yana kan faskekiyar wayarsa wacce yake ta lallatsawa, yana sanye da shadda getzner, mai ruwan ƙasa tasha aiki, duk da ba wani aiki mai yawa akayi mata ba, hakan kuma bai hana shaddar yi masa kyau ba, kansa kuwa hula ce, kalar kayansa zanna, yana danna wayar yana murmishi da alamu chart yakeyi, Wata farar Mata doguwa bawai tsayi sosai ba, tanada jiki shima ba sosai ba, ta fito hannunta riƙe da tray na kayan marmari, bayan ta zo gurin Prince, (Arshad) tace "ɗan Umma yau kuma me aka samu, naga bakazo fira bane?" Prince yayi murmishi wanda ya sake fito da ainihin kamar da sukeyi da matar, kafin yace Hajiya wlhi wata yarinya ce zata raina min hankali, kinga hotonta wai ta fini kyau, dan Allah Hajiya ki kalleni ki kalleta wa yafi wani kyau?" Hajiyar ta sake yin murmishi kafin tace "gaskiya nidai tayi min kyau" Prince ya kwaɓe fuska kamar ƙaramin yaro, kafin yace "Hajiya wato kina nufi ni mummuna ne?" "No ba haka bane, gani nayi nan bada jimawa ba, wata ƙila ta zamo surukata" Prince yayi dariya kafin yace "Hajiya ƴan matan yanzu babu abinda suke buri sama da auran mai kuɗi, babu duba nasaba hali ko wasu abubuwan da suka danganci hakan, sudai burinsu kenan, nikuma naɗau alwashin bazan taɓa auran matar da ta ganni cikin kyawawan kaya ba, Prince ya miƙe tare da ɗauko kayan da yake zuwa neman ƴan mata dasu, ya ajiye su a gaban Hajiya kafin yace "dasu nake zuwa neman aure, har yanzu Ban samu mai sona ba" "Meyasa haba babana, ba girmanka bane yawo da waɗannan kayan, duk da nasan babu wacce ta sanka a garinnan amma ya kamata ka dinga shiga ta mutunci" Prince ya miƙe tsaye ya kwashe kayan ko parlon bai dawo ba, ya wuce ɗakinsa ya kwanta. "Meyasa koda yaushe Hajiya bata fahimtarsa, batasan auran yanzu sai mutum ya dage zai samu mata mai biyayya ba, shikam yana neman matar da ko talauci ya shiga zata tsaya a tare dashi ta kula dashi bazata ƙyamaceshi ba, yana kuma sa ran insha Allah zai sameta" Kafin daga ƙarshe ya kashe data ya kalli agogo ƙarfe 12:pm ko breakfast beyi ba, haka ya kwanta, sbda barcin dake idonsa, jiya beyi barci da wuri ba. Idan kaga inda yayi kwanciyar dole abin zai baka dariya, pillow biyu ya ajiye a gabansa, ɗaya yana rungume dashi ɗaya kuma ya ɗora ƙafafunsa akai, koda yaushe haka yake barcinsa hankali kwance.... Hi fans kunsan meye? burina inga ana ruwan comments nikuma yanzu kullum zaku dinga ganin posting amma da ƙarfe 9:pm insha Allah, Nagode da soyayyarku a gareni much love Mom Islam ce.... *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 25-26 Washe gari ta kama lahadi, duk da yaɗau hutu a gurin aiki, amma yana son fita zuwa gurin aikin nasu, sbda wasu ƙananun maganganu da suka fara ɓullowa, lokacin da ya kammala wanka tare da sanya kaya, Batool ta fita zuwa kitchen, cike da so da ƙauna irin na uba da, ɗa ya kalli Inaya kafin ya matsa kusa da ita yace "yarinyar Abba me kikeso in siyo miki?" Cikin shagwaɓa Inaya tace "Abba zanje gurinsu Aunty Amani" "Okay ki bari kiyi brakfast sai momynki ta kaiki" Dole ta yarda da maganar Abban, har Abban ya miƙe yana ɗaura agogon hannu, Batool ta shigo tana sanye da doguwar rigar abaya milk color, ta yafa ɗankwalin a kanta, "Alhj na kammala brakfast amma sai kaci zaka wuce ko, sbda naga kamar kana shirin fita?" A shagwaɓe tayi maganar, hakan kuwa ya matuƙar burgeshi, sosai yake ƙara jin sonta na shigarsa, yama mance da Inaya a zaune ya kai hannunsa ƙugun Batool kafin yace "muje ki bani a baki" Abinka da yaro, Inaya ta zaro ido, itama Batool ɗin ta mance da Inaya saboda tana can bedroom, ita kuma Batool lokacin da ta shigo har ya kusa kawowa parlo, shine suka fito, suna fita, Inaya ta fice a sukwane sai gurin su Amani, my  baby ya akayi na ganki ko wanka bakiyi ba?" "Aunty Amani Abba ne ya rungume momy" Inaya ta zaro ido, a fili tace "Abban da kansa?" "Eh wai zasuje brakfast ko magana basuyi min ba" "A hassale Aseela tace "wato har tazo ta fara gwada mana iskanci ko, muda muka bada goyon bayan a aurota shine zata raina mana hankali a gidan mahaifinmu?" Amani tayi dariya mai sauti "Hhhh, wlhi waccar matar Abban dariya take bani, dan wlhi na tashi yi mata rashin mutunci kare ma baze ciba, ƙanwar tamu zata wulaƙanta?" °°°°°°°°°°°°°°°° "Alhji me kake so a fara zuba maka?" Sam hankalinsa baya ga maganar da takeyi, ya karkata ga murmishin da takeyi, da kuma kyawawan fararen idanunta da kuma mazaunanta da suka fi mazaunin kujerar girma, A hankali takai bakinta saitin fuskarsa ta hura masa iska, Yai ajiyar zuciya kafin yace "duk abinda zakici shi zanci" Dama abinci tayi kala uku, kuma ba wasu masu wuyar dahuwa ba, soyayyen dankali da miyar ƙwai sai yam balls sai indomie jollof sannan sai Black tea wanda yaji kayan ƙamshi, Cikin nutsuwa takai cokali ta ɗauko  dunƙulalliyar doyar da aka soya da ƙwai, kafin takai bakinsa, ya lumshe ido yayin da ya fara taunawa "gaskiya kin iya girki" Batool ta lumshe ido, shikam sai ci yakeyi, idan ta kuma ɗaukowa ya bata a bakinta, duk abinda sukeyi Amani na tsaye tana kallonsu, kasancewar duk sunyi nisa, babu wanda yasan da zuwanta, har ta gama yi musu Video ta koma part ɗinsu basu sani ba, Tana shiga ta kirasu ɗaya-bayan ɗaya tana cewa "kuzo kuga abinda Abba yakeyi" Aseela Amani Inaya Mahabob baya nan, dukkansu ukun suka fito, Amani ta nuna musu videon da tayiwa su Abba, cike da mamaki suka wangale baki, Amani tace "kunga tabbacin tanaso ta mallake mana Abbanmu, ko leƙowa dubamu beyi ba, bare yasan muna nan munyi kewarsa, Aseela tayi wani makirin murmishi kafin ta danna number Abba, har ring uku bai ɗaga ba, a zuciye tace "abu ya tabbata shikenan kashinmu ya bushe, ƙila ma da asiri tazo gidan" Amani ta gwada kiransa a wayarta, cikin sa'a ya ɗaga, yana rungume da Batool hannunsa na cikin rigarta, murya a kasalance yace "yarana kuna lafiya, kuyi min afuwa yau na tashi da ciwon kai ne" Amani tace "Abba Aseela ce a kwance babu lafiya har suma takeyi" Cikin sauri Abban ya janye Batool daga kan cinyarsa yana cewa "Aseela babu lafiya" Batool ta shige ɗaki da gudu ta sanyo hijabi tabi bayansa, Suna jin motsin shigowarsa, Aseela ta lulluɓa da bargo, dama an riga da an ajiye mata, ta hau rawar sanyi na ƙarya, Jikin Abba na rawa ya iso ɗakin hankali a tashe tun daga bakin ƙofar ya fara rangaɗawa Aseela kira, Amani tayi kalar tausayi kamar zatayi kuka, Batool na shigowa Inaya tace "Abba ko abinci ban ciba" Sai a lokacin Abba ya dafe kansa tare da matsawa ya kamo hannunta, "Amani jeki kicin ɗin momynku ki kawo abinci" Jikin Batool na rawa tace "dama nasa musu a kula, ina jira ka kammala ne sai in kawo musu, barin ɗauko musu" Abba ya kalli Aseela kafin yace "tashi muje asibiti" Aseela ta miƙe dafe da kai, tace "Abba naji sauƙi" "No bana son wata matsala ta sake faruwa ki tashi kawai muje asibiti" Amani tace "Abba na bata magani taji sauƙi" Da haka Abban ya  fara jan Amani da yaga fuskarta babu walwala da hira. Washe garin ranar mahaukaciya ta tashi da matsanancin jin sanyi mai shiga jiki, zazzaɓin da takeji ya zarce na ranar, Ta yayibo wata baƙar leda wacce ta ɗuri ruwan saman da akayi jiya, ta juye ruwan tare da farka ledar tayi riga da ita, a hakan tana nufin zeyi mata maganin sanyi, Da ƙyar ta miƙe tare da ficewa daga cikin ginin ta fara tafiya tana surutai, lokaci zuwa lokaci idonta na dama yana tsiyayar ƙwallah, har tayi nisa, wani saurayi ya ce "mahaukaciya gashi kici" Tasan sunanta kenan, ta waiga tare da ƙyalƙyale masa da dariya tana nunasa da yatsa, kana ta finciki ledar ta buɗe tana dariya, saurayin ya girgiza kai tare da Bin ta da gudu   ya ce "mahaukaciya ina son taimakonki zaki amince?" Kallonsa ta tsaya yi, daga bisani ta ruga da gudu har da gyara zaman ledar da tayi riga da ita, tana ci gaba da gudu, shima beyi ƙasa a guwaiwa ba ya bita, duk gudu da yakeyi  sam ya kasa cimmata, har yarfe zufa yake, tare da durƙusawa dan tayi masa nisa, kuma yana hangota. Kamar wanda aka ƙarawa ƙarfi ya cigaba da Bin ta, tana ganin ya sake biyota ta bi wani lungu shima ya bita, haka suka dinga kewaye anguwa kamar masu wasan tsere. Cike da tarin baƙinciki Juwairiyya ta dawo gida tana turo baki, Baba ya fito ya ganta a wannan yanayi, "ƴar baba lafiya kuwa na ganki haka?" Yana maganar ne yana miƙar da ƙafarsa da takeyi masa ciwo, "Baba wani yaro ne yazo gurina, wlhi idan kaga kayan jikinsa kamar mai yawo a bola" "Wlhi ƴar baba koni ban goyi da bayan ki auri wanda daga baya zamuzo muna nadama ba, banason in siyar da Akuya tazo tana ci min danga, da yardar Ubangiji sai kin auri mai faɗa aji a faɗin ƙasar nan, dole idan na samu lafiya zanje gurin malam mai Almajirai akan yayi mana istahara muga irin mijin da zaki aura, sannan kuma ya bamu maganin farinjini"         ************ Yankin MARZUK dake ƙasar LIBYA yanki ne wanda ya ƙunshi mutane da dama, a cikin ƙauyen akwai wani yanki da suke yi masa laƙabi da SHAHAZAD FOREST, haka suke yi wa anguwar laƙabi. Wasu irin mutane ne a yankin, Hausa sukeyi amma Hausar sai wanda yake da asalin fahimta ne zai gano mai suke cewa, yawancin ƴan matan garin haka suke rayuwarsu, inda ko wanne yake neman ɗan uwansa mace, duk namijin da aka haifa idan sukaji labari sai sun kashe shi, a cewarsu maza bala'i ne a tare da mutane, suma da suke rayuwa sunzo a sa'ar rayuwa kuma Ubangiji ya sanya musu albarka, Yau ma kamar ko wanne ƙarshen wata, Mutanen Shahazad sun shigo ƙauyen, tunda mazauna yankin suka fara jin jiniyar motoci, ko wanne ya fara guduwa, masu yara maza suna ɓoyesu a cikin ciyayi masu yara mata wanda suka kai ƴan mata iyayensu zasu dinga ɓoyesu, saboda gudun fyaɗe, Tunda motar ta yanko tsakiyar anguwar, suka hango wata mai ciki tana ta ihu, hannunta tallafe da mararta,  sosai hawaye ke kwaranya a fuskarta, kuma tashin hankalin ganin waɗannan mutane ne yasa tashi ɗaya naƙuda ya kamata, suna daga nesa da ita, suna shirya makirci da zalunci da zasuyi mata, kawai sukaji kukan jariri" Da sauri dukkansu suka sauko daga motar suka nufo gunta, Already da adda suka taho wasu Kuma hannunsu riƙe da wata kakkaifar wuƙa, cikin yanayi na rashin mutunci suka figota, ta runtse ido tare da buɗewa, ta fara magana da Hausar ta da bata fita "don Allah ka ƙyaleni karka cutar dani da abinda na haifa, wlhi ina sonshi babanshi ya kashe kansa saboda tsoronku".. "Keeee!!  banza marar hankali!!" Babu abinda kakeji sai ƙarar wuƙa da Adda, sun kashe ta sun kashe ɗan da ta haifa, sannan suka jata suka wurgata ruwan tsafinsu dake tsakiyar garin, cikin halin ko ina kula suka bar ƙauyen tare da ƙarewa ko ina kallo sukaga babu komai. Suna tafiya kowa ya fara fito da yaransa, duk iya kaf-kaf ɗinsu babu maza a ciki sai zallar mata, ƴan mata kuwa sunyi girma sosai amma dole suke rayuwar da suke tunanin itace ƙwarai, babu batun musulunci ko kwatankwacinsa, Bayan nan basusan mutunci ba, haka duk wasu kayan more rayuwa na alatu basu sanshi ba, abinda suka sani noma da aihuwa, wanka ba damuwarsu bane sai mutum yaso kaya kuwa, na jikinsu yayi wata basu sauya ba, wasu ma sai sun yage, maza suna ɗaura zani suyi shi kamar wando, mata kuma suna ɗaura zani a kwankwaso a samansu ma suna ɗaurawa su rufe nonuwansu, abinci basu damu su ci mai kyau ba, sunfi ga cin ganye wanda suke shukawa a ɗanyensa, idan kaga rayuwar mazauna yankin , abin tausayi ko ince abin tsoro. Hajara na tabbatarwa da Shahazad ya dawo ta koma ɗakin dake mazaunin nata a yanzu, kai tsaye ɗakin Mona ya wuce, cikin sa'a yana tura ƙofar ta buɗe, tana nan tana aikin nata wato tunani, kukanne kawai batayi ba, a hankali ya ƙarsa ya miƙar da ita ta zauna akan cinyarsa, tare da cewa "haba Mona, tunda mukayi aure babu abinda ya taɓa shiga tsakaninmu to meyasa?" Cikin gautsin baki tace "saboda baka cancanta ba, kai ba mijina bane, ka mayar dani gurin iyayena, bai saurareta ba, yaci gaba da shafa sumar kanta yana shinshina, da sauri ya miƙe sakamakon tura wasu muhimman abubuwa da zeyi, Ya shige bedroom ɗin ta, a hankali Mona ta ɗauki wayarta ta fara yi masa Video, wasu yanki na ƙasar yake neman mallakewa, ita kuma taɗau alwashin sai ta tona masa asiri sai tasa yayi nadamar abinda yake aikatawa, cikin sauri ya gama cike takardun tare da hotunan mutanen da za'a kashe, duk ta ɗauka, tare da bom da za'a jefa a gurin, bayan anyi kisan, a tsorace take ɗaukar, da sauri ya juyo sukayi ido huɗu dashi, hankalinta in yayi dubu ya tashi sbda bata taɓa tsinto ɓacin rai irin na yau ba a ƙwayar idonsa,  a tsanake yaci gaba da makawa wasu mutane jan biro, daga ƙarshe ya tattara takardun ya fice dasu, kai tsaye ya koma ɗakinsa...! Tofa gwarama? Comments da shar'hi shine burina idan anayi posting kullum insha Allah Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Masu nema daga farko ko masu son shiga group suyi min magana ranan👇 http://wa.me/08141799224 27-28 Mona ce ta faɗo masa rai, sai kuma yayi murmishi mai tarin ma'anoni da yawa, Kamar inda ya gindayawa Hajara sharuɗa da ayyukan da zata dinga yi musu, kallon ɗakin da take tayi, a fili ta furta "Aljannar duniya, ban taɓa tunanin zanzo wannan duniyar ba ko ince haɗaɗɗen gida wanda ya gaji da kyau" Kafin ta miƙe tsaye, Mona ce ta faɗo mata, ta fara tunanin ta ina zata ganta? Tana tsoron shige mata da yawa wannan mai kama da aljanin ya illata ta, tana tsaka da tunani taji Mona tana cewa "Hajarr" cikin ɗaga murya ta amsa, jiki na rawa ta fito, Mona tana zaune kan kujera mai zaman mutum ɗaya, hannunta riƙe da waya tana kallon video ɗin da tayiwa Shahazad ɗazu, jin ƙarasowar Hajara ya sanyata ajiye wayar tare da kashe hasken ta kalleta tace "uhm karki damu da wannan mugun ya fice, inaso ki rakani wani guri" A tsorace Hajara tace "Hajiya me gidan ya san "Eh" Mona tace a taƙaice, "Jeki shirya nima ina nan fitowa" Mona ta faɗa tare da miƙewa ta haye saman bene, Kamar daga sama taji ana bubbuga ƙofa, batayi tsammanin shiɗinne ba, tai sauri zuwa ta buɗe, Da sauri ta fara ja da baya, har sai da takai jikin gadonta, kafin ta tsaya cak, "Gudun me kikeyi bayan gani nazo gareki" Har yanzu Mona bata dena ci gaba da ja da bayan ba, yanzun ma sai da ta ƙure jikin bango kafin ta tsaya, shiko dariya ma ta bashi, har sai da ya dara, kafin ya tattaro ƙarfinsa ya fincikota ta faɗo jikinsa, cikin salo irin nasa yai kissing ɗin goshinta, kafin ya fincike ƴar yaloluwar rigarta, dama ba wasu na shanu ne da ita ba sosai, sai kuma ƙyalƙyale da dariya, kafin ya zuge zip ɗin sikel ɗinta ya zame ƙasa, ya cire mata pant. A taƙaice dai tsirara yayi mata, Mona kuwa tun tana kuka ƙasa-ƙasa ta koma yi da ƙarfi har sai da kunnen Hajara yaji, ita dake zaune a parlo tana jiran fitowar Mona su tafi, A tsorace Hajara ta miƙe jikinta babu inda baya rawa, tunda tayi ido biyu da Mona take jinta kamar ƴar cikinta da ta haifa, sbda idan da Allah ya bata aihuwa da tuni ta ajiye budurwar ƴa, A hankali ta hau steps ɗin, tana tafiya tana waigen bayanta gabanta na ci gaba da dukan  uku-uku, "Yau rana ce da nayiwa zuciyata Alƙawarin kasancewa dake, bakya ganin nayi ƙoƙari da auranmu wata ɗaya kenan ko rungumarki ban taɓa yiba, ai abin kizo ki tambayeni ne shin na dena sonki ne ko ya?" "Meyasa zan tambaye ka, ka ƙaddara nabar rayuwarka, wlhi Gara in kashe kaina da inci gaba da zama a gidanka" Abin mamaki, Shahazad bai damu da kakkausan kalaman da Mona take danƙara masa ba, sai dai yana kici-kicin cire mata hannu a ƙirji, Yana cire hannun yai saurin kai bakinsa  kan nipple ɗinta yana fizga  kamar wani kare, a zabure Mona ta ƙamƙameshi tana cewa "wayoo zai kasheni babu kowa ne?" Hajara da ta iso yanzu ta toshe bakinta a tunaninta shirin yankata yakeyi, Sai kuma taji Shahazad yana cewa "ai zasufi saurin fitowa, wahalar sha zasuyi min a haka" "Nikam bana so ka ƙyaleni mugu" Yana lakatar hancinta ya cire bakinsa, tare da zura hannunsa gabanta yana wani turawa sai kace wanda ya samu bebin roba, Mona ta zabura saboda zafin da ya ziyarceta tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kant, ƙoƙarin ƙwacewa takeyi amma sam ya tattara ƙarfinsa ya matseta yanata tura mata hannu a gaba,  ita kuma ko saurarawa ta kasayi sai ihu take, Yana riƙe da ita ya cire kayan jikinsa ya zamo tsirara, Mona ta runtse ido tare da  matse jikinta, tsoro firgici tunanin ta mutu an gama, duk da batasan abinda yake shirin yi ba, duk suka dirar mata, batayi aune ba taji ya shigeta da masifar ƙarfi wanda ko yanke wa tayi bata taɓa jin kwatankwacin zafin ba,  ihu iya ihu tayishi, Hajara kam ɗakinta ta koma ta rushe da kuka, a fili tana cewa "bazan iya zama a gidannan ba" Yanzu ne ma Mona take ihu mai tushe, saboda sam yaƙi ɗagata sai sukuwa yake a kanta, a take jini ya ɓalle sai kwarara yakeyi, Mona kuwa harta sume babu numfashi, hankalin Shahazad a tashe ya fara kiranta amma shiru, duk da hakan bai yarda babu numfashi a jikinta ba, sai da ya buɗe freezer ya ɗauko ruwan sanyi ya watsa mata yaji shiru, gashi har yanzu jini yaƙi tsayawa, da sauri ya buɗe ƙofa ya fito, kasancewar yasa gajeran wando, ya fito hankali a tashe "Hajarr.." Hajara ta amsa tare da fitowa da sauri, "Jeki gyara min Mona barin ɗauko key muje asibiti" Gaban Hajara ya faɗi, yana wucewa ɗakinsa ta wuce na Mona, ta dinga jijigata amma babu numfashi, ga jini yaƙi tsayawa,  da sauri ta wangale ƙafafun Mona ta hango aika-aikar da Shahazad yayi, cikin takaici ta girgiza kai tare da ɗaurayewa mona ɗin inda ya sauwwaƙa, kafin ta samu leda babba ta naɗeta a ciki, sbda kar jinin ya ɓata guri. Riga da wando yasa masu kamar Pakistan ya fito yana gyara sumar kansa, Sai da ya ɓata lokaci kafin ya fito suka riƙe Mona akasa a mota, Ma'aikatan gidan sai Allah ya kyauta sukeyi. A ɗari ya figi mota hajara na riƙe da  Mona suka wuce. Kai tsaye ya wuce da ita (Tripoli  international hospital healthcare Libya) Kasancewar assibitin ya samu ƙwararrun ma'aikata, suna isa aka wuce da ita ɗakin gaggawa, a gigice suka karɓeta, saboda a ido kawai zaka gane jini yayi ƙaranci gashi ko numfashi batayi, Tunda suka shigar da ita, sun hana Shahazad shiga, babban doctor na fito yaga Shahazad, har ƙasa ya durƙusa ya gaishe shi, kafin yace well come to  (TRIPOLI INTERNATIONAL HOSPITAL HEALTH CARE) Shahazad yayi murmishi kafin ya gyara tsayuwarsa yace "mata ta ce na kawo saboda sun rainani basu cemin komai ba" Doctor ya zaro ido, sbda yana cikin tsoro yai saurin zuwa ɗakin da aka kwantar da Mona, abu na farko da yayi ido huɗu dashi, gabanta ya wani daddage kamar wace aka faffasa, doctor yace "menene asalin damuwar ne?" Shahazad ya shigo a hassale ya cakumo wuyan mutum biyu kafin ya gwara kansu, a fusace yace "zaku kulamin da ita ne ko sai na kaiku lahira?" Tuni babban doctor ya saka kayan aiki ya fara ceto rayuwar Mona, tana aikin hankalinsa a tashe yana tunanin da wuya Mona zata rayu, gefe kuma ledar jini ne ake sanya mata, da yake sun siyo wanda zeyi dai-dai da nata a Lab, Dole Hajara ta nemi guri ta keɓe ta dinga kuka kamar wata ƙaramar yarinya, larabawan gurin sai kallonta sukeyi, wani farin Balarabe ya kamo hannunta tare da miƙa mata hanky ta share hawaye, ga mamakinta sai taji yana cewa "kiyi haƙuri, mutuwa dole ce sai dai idan lokacin mutum beyi ba" "Shikam musulmi ne" Hajara ta faɗa a zuciyarta. Shahazad ya fito hannunsa riƙe dana doctors biyu yana tafiya dasu yana gwara kansu, ya hango Hajara tsaye da wannan mutumi, kan Hajara yayi kamar wani mahaukacin zaki har wani kamar zai tashi sama yakeyi, kan kace me ya kamo Hajara ya shaƙo wuyanta, idanunsa sunyi jajir, sai cewa me kike  yakeyi gaya masa? Tunda balaraben yaga Shahazad ne yai saurin tattara iyalansa, harda matarsa da tazo a duba lafiyar babynta kasancewar ciki ne da ita, suka gudu. Shiko ya shaƙeta sai cewa yakeyi, me kike gaya masa sannan meye tsakaninki dashi?"     Sam ta kasa cewa komai, sbda iya shaƙewar da  yayi mata ko magana  bazata iya yi ba. NIGERIA*** Bayan kwana biyu da maganar da Hakeem yayiwa Dady ya kira Hajiya ƙarama da Hajiya babba, Hajiya ƙarama ce ta fara zuwa, ita da Iffat, bayan ta zauna ta zaunar da Iffat, Hajiya babba nacan ɗaki faɗa ya kaure a tsakaninta da Fawziya sam sun kasa fahimtar junansu, daga ƙarshe dai dole hajiyar ce ta kashe wayarta duka, tare da sake kumnawa tace "Ni yaushe na rubutawa Fawziya saƙo?" Daga ƙarshe ta miƙe zuwa ɗakin Dady. Tana shiga tahau rarraba idanu, "Badan komai na taraku ba sai dan in gaya muku zan fitar da Eshat waje sannan zan tafi da mutum ɗaya" Yana gama magana, Hajiya babba tace "dani za'aje ko?" Sanin halinta da son abin duniya yasa ko kallonta neyi ba, bare ya nunar mata da yaji maganar, "Gobe ki shirya zamu wuce Algeriya daga nan akwai wasu muhimman aiyuka da zan yi" Hajiya ƙarama tace "haba Alhji da kaje da Hajiya babba" "No banyi ra'ayi ba, idan kema kin fara canza hali ne ki sanar dani?" "Allah ya huci zuciyarsa, wlhi badan komai na faɗi haka ba" Hajiya babba ta miƙe cike da masifa tace "nuna banbanci da nuna kafin son wata shine damunka, nidai abinda na sani Allah sai ya saka min, sau nawa kake cewa ta shirya ku tafi, kodan kuci amana ta" Daga dadyn har hajiyar babu wanda yace mata komai. Aslamu alaikum saƙon godiyata ga masoyana, nayi farinciki da naga kun amshi littafin cikin aminci, dan Allah ina roƙon alfarma a tayani sharing ɗinsa, sannan masu yawa. Kawo ƙorafi akan lokacin yin posting yayi yawa, to ina tunanin ince kamar ƙarfe takwas zan koma posting, insha Allah sannan yawan comments yawan typing. Insha Allah daga gobe zamu fara fatan dai adinga shar'hi Nagode masoyana. Mom Islam taku ce💋 *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 29-30 Kafin ya basu umarnin tashi, Hajiya babba ta miƙe tana ci gaba da surutu har tabar gurin. Dady ya kalli Iffat kallo na tausayi kafin tace "Hajiya yarinyar nan tausayi take bani" Hajiya ƙarama ta janyo Iffat kusa da ita, kana tace "babban abinda yake damuna bai wuce, iyayenta da suka jita shiru ba, amma basu nemeta ba, bayan haka ga yarinyar kyakkyawa wlhi nikam tana burgeni, gashi ko sau ɗaya bamu taɓa jin muryarta ba" Dady bai ce komai ba, sai "kuje ku shirya tun da wuri ki bani passport ɗinki sauran abubuwan da za'a nema duk suna gurina" Hajiya ƙarama ta miƙe tare da kamo hannun Iffat, "kuna kula da cin abincinta kuwa?" "Eh Alhji" Kafin suka wuce. Wani wawan burki ya taka, tare da yin salari, jikinsa na ɓari yai parking mota, ya fito hankali a tashe yayi kanta  yana ambaton "Innalilahi wa inna ilaihir raji'un" Cikin ƙanƙanin lokaci mutane sukayi caaa a gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa, kafin Mahabob ya tallafo kanta yasa a mota, wani mutumi ya riƙe shi cikin masifa yace "wato dan kaga bata da gata shine zaka sanyata a mota ka gudu da ita ko? wlhi tallahi bazamu yarda ba sai munyi ƙararka" Mahabob ya dafe kansa, rai a ɓace yace "haba malam, duk rashin imanina bazanyi wasa da ran ɗan adam ba,  dan nasa ta a cikin mota shine zakuyi min mummunar fahimta, idan har kuka nemeni kuka rasa ku nemo Alhaji Auwal" "Alhaji Auwal dai, kake nufi wanda sunansa yayi shura?" Mahabob ya hararesu cikin sauri ya shige mota yaja sai hospital, Tare dashi aka shigar da ita emergency room, sosai zuciyarsa ke bugawa, a hankali yasa yakai hannunsa saitin zuciyarsa tare da lumshe ido, doctor ya kamo hannunsa ya fitar dashi zuwa Office ɗinsa, "Mara lafiyarka zata farka nan bada jimawa ba, Alhmdulilah batayi mummunan jin ciwo ba, sai dai rauni da taji a ƙafarta, karka damu" Mahabob yai murmishi kafin ya zaro wayarsa a aljihu, ya danna number mu lovely sisna, Amani ta ɗaga cikin yanayin damuwa tace "bro lafiya kuwa, tun asuba da ka fice har yanzu gashi ƙarfe biyar 5:pm?" Murya babu daɗin sauraro Mahabob yace "wlhi na bige wata yarinya tazo tsallaka titi, a halin yanzu dai muna asibiti" Cikin tashin hankali Amani tace "barin sanarwa da Abba, ko Kuma inzo" Cikin sauri Mahabob yace "ba sai kinzo ba zan dawo zuwa anjima" Yasan ba lallai ya dawo anjiman ba, kawai ya faɗi hakanne dan ya kwantar mata da hankali. Kiran sallahar magriba ne ya sashi miƙewa ya fito zuwa masallacin dake cikin asibitin, bayan yayi Sallah ya roƙawa mara lafiyarsa sauƙi a gurin Ubangiji, kana ya miƙe tare da sanya takalmin ya dawo cikin asibitin, haske ya gauraye ko'ina, idan kana ciki bazakayi zaton rana ba ce, office ɗin doctor ya koma, ya sameshi yana cike ƴan takardu, jin shigowar Mahabob yasa doctor ɗagowa yace "Barka da dawowa, yarinyar da ka kawo ta farka, zaka iya zuwa ganinta" Jikin Mahabob na rawa yace "Tom Nagode" Dama abinda yake sonji kenan. Fita yayi daga asibiti ya nufi shagunan da suke jere, ya kalli masu girke-girken gurin, duk mutanen gurin basuyi masa ba, saboda akwai shi da ƙyanƙyami, Madara ya siya ta gwangawani sai maltina da Apple juice kafin ya siyi sabon cup, yaje gurin masu siyarda kayan marmari, lemu abarba Apple kankana  gwanda da ayaba duk ya siya, aka sanya masa a leda ya kamo hanya hannunsa niƙi-niƙi da kaya, Kai tsaye room ɗin da aka kwantar da ita ya nufa, kafin ya ƙarasa ciki, tana jingine da pillo goshinta ɗaure da bandeji, "sannu" Mahabob yace cikin nuna kulawa, "Yauwa dan Allah ka mayar dani gurin Ummana" "Am sorry ki duba halin da kike ciki bakiga kinji rauni bane?" Kafin ya ɗauko cup ya haɗa madara da maltina guri ɗaya ya miƙo mata, sai yanzu ta tabbatar da rabonta da abinci tun safe, ta karɓa hannunta na ɓari, ta fara kurɓa ko cire kofin batayiba, har sai da ta shanye ta miƙa masa kofin, murmishin jin daɗi yayi, kafin ya buɗe babbar ledar tare da ɓare su Ayaba da lemu da duk sauran kasancewar an yanka lemun da gwanda, ya miƙa mata, aiko taci bana wasa ba, sbda sai da tayi gyatsa kai kace ba mara lafiya ba, kafin ta ture, Mahabob ya kalli screen ɗin wayarsa da yake ƙoƙarin rufe layin saboda Amani damunsa zatayi, A aljihu ya sanya wayar, kafin ya ɗago idanuwansa yasa anata kafin yace "kozan iya sanin sunanki?" "Sunana Huda" A ransa ya mai-maita "Huda" A fili yace "suna mai daɗi" Huda tayi murmishi sai kuma ta haɗe rai, tace "ina kular tallan shinkafa ta?" Mahabob ya dafe kai, kana yace "wlhi nidai banga kula ba, amma insha Allah idan aka sallameki zan siya miki duk abinda babu" "Kiyimin kwatancen inda kike?" Huda tace "Sabon layi" Mahabob yace "muna sa ran gobe insha Allah zasu sallameki sai dai ina tunanin mahaifiyarki da batasan abinda ya faru ba" Kiran sallahar isha'i ne ya sanya shi fita, yayo sallah ya dawo, Ya samu har tayi barci, Allah Sarki akan dogon bencin dake can nesa da gadon Huda ya kwanta, shima rabonsa da abinci tun na safe, kasancewar ba ma'abocin yawan cin abinci bane, barci mai nauyi ya ɗauke shi, Kasancewar alnyi mata allurar barci bata wani farka ba, sai gab asubha, lokacin shikam barcinsa yakeyi. Kiran sallahar asbha da akayi ne yasa Huda cewa "ɗan gaye an kira sallah" Sai da ta mai-maita sau uku sannan yaji, yayi salati kafin yasa takalmi ya shiga bayan gidan ɗakin yayi alwala ya tafi masallaci. Ita ko tunanin ummanta ya addabi rayuwarta, a inda take jin ƙarfi a jikinta ko yanzu akace ta tashi ta tafi, tafiya zatayi, Tana cikin wannan tunanin har ya shigo ya gaishe ta, ta amsa tana ɓoye fuska, kafin ya nemi guri ya zauna, yana tsoron ya ciro wayarsa ya kunna Amani ko Abba ko Aseela su tayar masa da hankali,  "Zaki iya miƙewa kiyi alwalah kiyi sallah?" "Eh zan iya" Huda ta zuro ƙafafunta ƙasa, tare da sanya takalmi ta sabo wanda ya siyo mata a daren jiya ta nufi banɗaki, ta ɗauro alwalah ta cire ɗankwalin kanta ta kabbara sallah, beyi yunƙurin hanata ba, tunda babu abinda zata shimfiɗa.                  °°°°°°°°°° "Ganin idanuwan Hajara sun fara kakkafewa ya sanya shi sake mata wuyan, da sauri ta faɗi ragwab ga wani irin tari daya sarƙeta, da sauri ya koma ɗakin da aka kwantar da Mona, cikin isa yace "ya ake ciki?" "Fyaɗe akayi mata, amma ya kamata kuɗauki mataki akan hakan" "Ubanka ne yace anyi mata fyaɗe?, to bari kaji she's my wife" Da sauri doctor ya kalli Shahazad, a zuciyarsa kuwa yana jinjina rashin Imani irin nasa, da har zai illata yarinya haka, Aiko Tasha ɗinki sosai, a razane ta farka tana cewa "shine zai kasheni ku taimakeni babu mutane a gidanne?" Cikin fusata Shahazad ya daka mata tsawa, kafin yace "idan matata ta samu matsala sai na kasheka" Kafin ya dawo waje inda yabar Hajara a zaune, cikin bada Umarni yace "wuce muje mota zaki tahowa da Mona ruwan zafi mai yawa" Wani doctor na bayansu yace "ai akwai gurin matsar ruwan zafi a ciki" to munafiki  jeka munji" Sai da ya gama ƙarewa Hajara kallo kafin ya sake komawa ciki, ya samu Mona ta barci, "Wuce muje" Ya sata a gaba suka wuce mota, Suna isowa gidan sai da ya bata umarnin fita kafin ta fice, kai tsaye kicin taje ta ɗora ruwan zafi kafin ta dawo ɗakinta, "Hajarrr" Shahazad ya ƙwala mata kira, da sauri ta fito parlo gurinsa ta durƙusa, jeki gyara ɗakin Mona.... Ayi haƙuri babu yawa *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 31-32 Jiki na rawa ta wuce ɗakin Mona, tana hawaye tana gyarawa, bayan ta kammala, ta fara neman turarukan da zasu kawar da ƙarni jin da ɗakin keyi, can ta hango room fresh mai ƙamshi sosai, tabi kowanne lungu da saƙo ta fesa, kamar ance ta waiga ta hango hotuna a ajiye kan mirror, Da sauri ta isa gurin ta dauki hotunan guda uku kafin ta kalli na farko, a fili tace "Mona, wannan kuma su waye?" Tsananin kamar da ta gani  a fuskar mata da mijin ne ya sata zargin ko sune iyayenta, A bayan hoton kuma akwai number waya, Batakai ga kallon ragowar hotunan ba ta ajiye su tare da ƙurawa number kallo a firgice ta fara tunanin kira, "Bani da sim card na ƙasar nan" Tunowa Ai Hassana ta ajiye mata a jakarta ta rataye  yasa tayi ajiyar zuciya, amma tana tunanin ta inda zata sato hoton ta fito dashi ba tare da mugun ya sani ba, Dabara ce ta faɗo mata ta kunce ɗaurin zaninta ta tura hoton ta cikin riga, kana ta ɗaura zanin akan rigar ta fito sai zufa takeyi, Da sauri take sauka daga steps ɗin sam taƙi su haɗa ido da Shahazad, cikin kakkausar murya yace "kawo hoton da kika ɗauka" "Innalilahi wa inna ilaihir raji'un" Ta ambata ƙirjinta na dukan uku-uku, tama kasa cewa dashi komai sai rawa da jikinta ya hau yi, zubewa tayi ƙasa jiki babu ƙwari ilahirin jikinta yai sanyi babu wani ƙwaƙwaran ƙarfi dake gareta, tace "ban ɗauki komai ba" "Ehh wato Shahazad Junaid Khan, zaki yiwa ƙarya bayan idona ya ganemin duk abinda kikayi?" Bata da wata mafita da ya wuce ta bashi hoton, haka kawai ta tsinci kanta da tura hannu ta saman ƙirjinta ta ciro hoton ta miƙa masa, "2Game over" Sam batasan me yake nufi ba, amma tasan wannan murmishin da yakeyi tsaf zai iya aikata mata koma meye tunda shikam baya shayin kowa, Kitchen ya wuce ya ɗauki ruwan zafin ba tare da yace "tazo su tafi ba, hankalinta yai mugun tashi, sbda taso su koma taga jikin Mona, amma babu inda ta iya dole ta zauna a gida, tambayarsa wani abun ma ba nata bane, tunda ta samu ya ƙyaleta da ranta beyi mata komai ba, ko kuma da wani shirin da yakeyi a kanta ne oho?" Tana so ta tsananta bincike akan halaiyyarsa yanzu kam guwaiwoyinta sunyi sanyi, ita ba kowa bace zai iya kasheta babu mai ɗaukar mata fansa. Da wannan tunanin ta koma ɗakinta ta ɗauki sim card na ƙasar tasa, kafin ta duba number Hassana, ring ɗaya ta ɗaga, kafin hassanar tace "Hajara inata kira sai acemin a kashe, kuma har kuɗi fa nasa miki" Hajara ta kawar da zancen ta hanyar cewa "Hassana dama kinsan wannan mutumin mugu ne kika kawoni gidansa?" "Haba Hajara ina ruwanki da halinsa, aiki ne ya kaiki ba sa'ido ba" Tunda Hassana tayiwa Hajara wannan maganar, tace "shikenan" Ta katse kiran. Ala-Uddin Samir. durƙushe take a gabansa tana mopping, hankalinsa a zahiri zaka ɗauka akan waya yake, alhalin kuwa rabin hankalinsa ya tattara ne ga ƙirjinta dake a buɗe ana ganin ilahirin nonuwanta, Sam batasan da hakan ba ita dai tanata aikinta, "Haseeinaaah" Ala-Uddin ya kira sunanta da cold voice ɗinsa, "Na'am" Hassana ta amsa tare da durƙusawa a gabansa, "Yau Lulu zata dawo da wuri ne?" "A'a tace min sai ƙarfe huɗu saboda yanzu karatun yayi yawa" "Okay kawomin Basmati" Hassana ta miƙe cikin girmamawa ta kawo masa, a ɗan matsakaicin faranti na tangaras me kyau, sai lemo na roba, wanda ya kasance shine ruwan shansa, Bayan ta ajiye masa, ya tsayar da ita kafin ya tsiyaya mata lemun a ɗan ƙaramin cup ya miƙa mata, Girgiza kai tayi alamar "a'a" Tsawar da ya daka mata ya sata saita nutsuwarta ta karɓa, Sai da ta shanye duka, kafin tabar gurin, koda yaushe hakan yake yi  mata, Tana komawa ɗakinta taji barci mai ɗaɗi yana shirin ɗaukarta, hankali kwance ta kwanta, tare da janyo abin rufa, lokacin ƙarfe 3:pm, Ala-Uddin ya leƙo cikin sanɗa tare da komawa parlo ya rufe ko ina kafin ya dawo ɗakin Hassana nan ma ya rufo ƙofa, lokacin da ya shigo har ta ɗago ido ta kallashi, sai dai kash bata isa ta banbance ko waye ba, idanunta sunyi kamar na mashayiya da tashi ɗaya, Cikin sauri ya cire gajeren wandon da ya kasance daga shi sai wata riga marar nauyi, Hassana kuwa riga da sikel ne irin na turawa Amma skel ɗin  ya saukar mata har ƙasa, duka kayan ya ciresu tare da ƙarewa tsaraicinta kallo, can kuma yai saurin afka mata, sbda tunowa da yayi, befi awa ɗaya ne dashi ba, haka ya yi mata rumfa tare da shigarta, har yanzu ta farka amma idanunta basa budewa sosai, sannan duk gaɓoɓin jikinta a sake suke, haka ya dinga kaiwa da kawowa yana sumbatunsa shi kaɗai, already maganin na minti 40 ne yanayi yana kallon waya... Afuwan Afuwan Please akuyi hakuri muna rashin nepa wlhi, insha Allah zuwa gobe idan na samu hali zanyi muku mai yawa . Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 33-34 3:45pm ya mirgina gefe, sai yanzu nutsuwa ta fara zuwar masa, ya miƙe da sauri, karo na farko kenan da sukayi ido biyu da Hassana, a razane ta miƙe tare da cewa "innalilahi wa inna ilaihir raji'un, dama yawan ganin jiƙewa da nakeyi kaine sila? Meyasa ka zaɓi kayi zina dani bayan Kanada matarka ta sunnah?" Da sauri Ala-Uddin Samir ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, ƙarfe 3:46pm alhalin tun ƙarfe 3:40pm da ya wuce ya kamata yayi nesa da ita "whay ya bari ta gansa,  yanzu zata tona masa asiri kenan kokuma zata rufa masa, runtse idanuwanta tayi, sbda kaucewa ganin tsaraicinsa, bayan ya kammala saka ƙananun kayansa, ya kalleta lokacin ta rufe jikinta da bargo a durƙushe yace "Haseeaina zanyi miki komai na rayuwa zan mayar dake ƴar gata zan fifitaki akan Lulu zan canza miki duniya ba wannan ba, inhar kin amince dani zan yi miki duka waɗannan abubuwan" Hassana ta kalli Ala-Uddin Samir cikin kallon bakada hankali tare da fassarori daban-daban ta kawar da kanta, 4:50pm na cika Ala-Uddin Samir ya miƙe jiki na rawa har zai fice sai kuma ya dawo yace "idan kinyi shawara any time ƙofa a buɗe take" Kana ya fice da sauri, miƙewa tayi ta faɗa toilet cikin dauriy, tayi wankan tsarki kafin tayo alwalahar la'asar, tana fitowa ta shimfiɗa sallahya ta kabbara Sallah, tana idarwa ta ɗaga hannu sama, tana kuka tana gayawa Allah halin da take ciki. Sallamar Lulu ne ya sanyata miƙewa da sauri ta fice, ko ninke sallahyar batayi ba, ta fito parlo. "Barka da dawowa shugabata" Cike da izza, Lulu tace "yauwa Barka, bani labari yau Ala-Uddin yayi waya da ƴan mata ne?" "A'a shugabata, nadaiji yana waya akan kasuwancinsa" Juyar da ido tayi farrr tare da juya mazaunai ta isa ɗakin Ala-Uddin, Ko jakar makarantar bata ajiye ba ta wuce ɗakinsa, yana zaune hannunsa riƙe da biro da takarda, wani irin zane yakeyi wanda ba kowane zai gane abinda yake zanawa ba, sbda sarƙaƙiyar rubutun. Tana tsantsar sonsa, hakan yasa idan suna tare take mancewa da komai, ta rungumoshi ta baya, tana cewa "nayi missing ɗinka Hubb" Ala-Uddin ya zagayo da ita kan cinyarsa tare da cewa "yau kinsha wahala a makaranta meyasa bazaki haƙura da karatunan ba?" Cikin siririyar murya tace "Hubb inaso in zamo cikakkiyar ƴar jarida domin mu yaƙi masu aikata yawaitar fyaɗe da kidnap da sauran ɓarayi" Ala-Uddin ya lumshe ido yana shafa gashin kanta, kafin yace "yanada kyau pretty sai dai Ina son rayuwarki kinsan wannan aikin salwantar da rai ne" Lulu tayi murmishi, kana tace "ai inada kai shiyasa bana damuwa jarumina". NIGERIA Ƙarfe 11:am aka sallami Huda daga asibiti, idan ka kalli fuskar Mahabob ya rame sosai, hannunsa riƙe dana Huda suka shiga office, hannunshi na hagu riƙe da takardar sallama, a rubuce likitan ya rubuta musu dokokin magungunan da allurai da zasuci gaba da karɓa na kwana uku, daga nan Mahabob ya biya ragowar kuɗin kana suka fito harabar asibitin, Kai tsaye gurin motarsa suka nufa, ya buɗe mata gaba shima ya shiga mazaunin direba, kafin ya tayar da motar suka fara tafiya. Har sunyi nisa a titi sai kuma yace "wace anguwa?" "Anguwar rimi" Suna shigowa anguwar, Umman Huda tana tahowa kanta ɗauke da buhu, cikin murna Huda tace "ga Ummana.." Da kallon tausayi ya bi Umman nata kafin yai parking a ƙofar gidan nasu, dan Umman nata har ta shige ciki. Sai da ya fara fitowa sannan ya buɗewa Huda itama ta fito, suka shiga ciki, tana gyara mazaunin hijabinta da ya yage, Da sallama ta shiga gidan, Umma ta fito daga ɗaki, tana salati, tare da cewa "au Huda ni na ɗauka kin fara yawon bariki ne?" Sai kuma ragowar zancen ya maƙale mata a saman laɓɓa sbda ganin kujewar da tayi a fuskarta, "Huda tukunna daga ina kika fito?" "Umma wani yana yi miki magana a waje wai zai shigo" Huda ta katse zancen. "Ce masa ya shigo Allah yasa samuwa mukayi" Tana fita ta sameshi a jikin mota a jingine, yana latsa waya, "Ɗan gaye ance ka shigo" Sai da Mahabob yayi murmishi kafin ya sanya keys a aljihu da wayarsa, kana ya shigo gidan. Da sallama ya ƙarasa tare da tsayawa cak, Can kwanuka nan tukwane ga tarin kayan wanke wanke marasa wanki a gefe, Daga bakin kofar ɗakin Umma, Huda tace "wai ka shigo" Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga ɗakin tare da durƙusawa ya gaishe da Umman, jiki na rawa fara'a sosai ta amsa tana yi masa godiyar kulawar da yabawa Huda, murmishi kawai yayi, kana yace ta godewa Allah, bai wani jima ba ya ciro kuɗi, ya ƙirga dubu goma, dama tunda ya ciro kuɗin Umma ke zaro ido, huda kuwa haushi ya gama kamata, "Umma ga shi a siya mata lemu" "Ah to harda ɗawainiya ne? to mun gode Allah yaji ƙan mahaifa" Kafin ya miƙe yana yi musu sallama, Umman kuwa sai cewa take "tashi ki bishi" Huda tabi bayansa, har gurin mota, har ya buɗe murfin motar ya juyo ya kalleta, kafin yace "Huda ni zan wuce sai na sake zuwa dubaki" Godiya tayi masa kana ya shiga motar ita kuma ta dawo gida. Tun fitar Huda umma take aiyyana "inhar wannan baƙon yace yana son yarinyar nan wlhi bazan amince da auran ba, domin guduwa zatayi ta barni". Tunda gari ya waye Hakeem yake rungume da Iffat, ita kuma sai shan yoghurt, takeyi hankalinta kwance, already Hajiya ƙarama ta riga da ta gama shiryata, dan har dady ya fito, Lokacin ma hajiyar ta fito, hannunta riƙe da babbar jaka ta matafiya, Hannun Iffat ta kamo kafin tace "Hakeem zaka bimu airport ne sai ku dawo tare da driver?" "Babu inda zeje, kamar inda ba'a buƙatar rakiyar mahaifiyarsa haka shima ba'a buƙatarsa, banda kinibi..." Dady ya tsayar da ita tare da cewa "nayi miki transfer na kuɗin cefane ki duba ko sun shigo?" "Oho kai ka sani kai ka damu dasu, mtsw" Dady yayi murmishi tare da cewa "Hakeem jeka duba wayar Hajiya ko kuɗin sun shiga" "To Dady" Yana zuwa ya ɗauki wayar, kasancewar tana parlon Hajiyar ita kuma hajiyar ta shige bedroom, tun daga nesa wayar tayi haske, sai da ya cire key sannan ya duba gurin ganin alert sannan ya dawo da gudu yana cewa "Dady 100k" Sannan dadyn yace "eh alhamdulilah tunda sun shiga, zomuje filin jirgi sai ku dawo tare da driver" Acan bedroom hankalin Hajiya babba ya tashi, tunani ta fara "Anya ba bin bokaye Hajiya ƙarama takeyi ba, shiyasa Alhji yake sata a gaban goshi, komai yace ita, komai ita" Da wannan tunanin ta miƙe ta fito parlo taga wayam babu Hakeem babu alamarsa, "Zai dawo ya sameni" Abinda ta faɗa kenan tana ci gaba da ruwan masifa. Hankalin Alhji Auwal ya mugun tashi, sakamakon rashin jin ɗuriyar Mahabob da yayi, duk inda yake sa ran zai ganshi, sai ace masa bezo ba, kwatsam anyi sallahar azhar bayan ya dawo daga masallaci yaji shewa da ihu a part ɗinsu Amani, yana rungume da Batool da har yanzu basu samu damar ganawa da junansu ba, ya miƙe tare da zuwa part ɗin, yana shiga yaga Mahabob a tsaye yana yi musu dariya, Aseela tace "wlhi na ɗauka ka ɓata ne, dama wannan shirin da nayi, nayine saboda mu tafi gidan rediyo a bada cigiyarka" Mahabob na dariya yace "haba sai kace ke, an gaya miki ni yaro ne?" Duk da Abban na tsaye yana jinsu, basu ganshi ba, yayi sallama, suka amsa cikin ɗokin ganin Mahabob, Abba ya zauna akan kujera tare da cewa, "yanzu Mahabob kana ganin kayi dai-dai kenan?Ai duk inda ka shiga yakamata ka buɗe wayarka tunda kira ya gagareka" Mahabob ya risina har ƙasa kafin yace "Abba dan Allah kayi haƙuri hatsari nayi na bige wata yarinya shine aka kwantar da ita, nikuma ina gudun ɗaga muku hankali shiyasa ban sanar ba" "To ai ba wayo bane, hankali kam ya tashi, amma ya jikin ita yarinyar?" "Taji sauƙi Abba, sai dai ina son a taimaka musu dan wlhi talauci yayi musu yawa suna buƙatar temako" "Mahabob duk wani taimako da kake ganin ya dace kayi musu, babu damuwa" Mahabob ya sake yiwa Abba godiya, Sai ga Batool nan ta shigo, tana sanye da hijabi har ƙasa, tun daga nesa Amani take watsa mata mugun kallo amma Batool ɗin bata lura ba, bayan tayi sallama ta nemi guri ta zauna, dukkansu suka gaishe ta, ta amsa cikin dakin fuska kafin ta tambayi Mahabob lafiya kuwa?" Abinda ya faru dashi ya sanar mata, kana yace "yana son dukkansu suke su gaishe da yarinyar da ya bige" Kafin Batool tace wani abu Amani tace "ai kuwa Abba ya kamata aje a dubota" Abban yace "insha Allah nima zani da izinin Ubangiji, sai ku shirya zuwa gobe ko?" Mahabob yaji daɗi sosai, yayiwa Abba godiya. Batool ta miƙe jiki babu ƙwari, sbda inhar tana guri da kuma ƴaƴansa a guri to sai dai tayi haƙuri dan a lokacin kamar ma mancewa yakeyi da ita, kuma kafin ta faɗi magana su sun riga da sun faɗa. Tana zuwa part ɗin ta, ta fashe da kukan nadama, tare da dana sani, itakam batasan meye ɗaɗin aure ba, komeye bashi da lokacin ta, gashi yaran gabaki ɗayansu sun dena girki, Allah yasa Inaya ana sanya mata pampas da haka zata jiƙe mata katifa, bata isa tayi magana ba, Bayan fitar Abban, Amani ta matso kusa da Mahabob kana tace "bro wlhi wannan matar Abban ƴar raunine hankali ce, wai brakfast idan ta gama, sai dai idan mune mukaje ɗauka ko Abba ya kiramu a waya wlhi bazata kiramu ba" Mahabob yace "kash Amani, meyasa baki da haƙuri ne?, idan tanada hali mai kyau zamu gani idan babu wlhi zamu gani" Yana gama magana tace "uhm ana gaya maka magana baka ganewa" Aseela tace "kunna mishi videon nan" Amani ta kunna ta miƙa masa, Mahabob yayi dariya, yayi dariya kana yace "amma ku Allah yayi munafukan yara da, bazaku bar Abbba ya huta ba, to meye amfanin yin auran idan bai kula da ita ba?" "Taɓɓ wlhi mallake mana Abba tayi, tun kafin ta shigo gidan, badan haka ba ai da bazasu dinga wannan iskancin ba" Amani da Aseela suka faɗa cikin haɗa baki. "Kunga wannan shine soyayyar aure, idan kukayi kuma mazanku zasuyi muku kudena sawa Abba ido, amma kafin ku karɓomin abinci" "To muma bamuci komai ba, tun abincin safe" Cikin daka tsawa, Mahabob yace "Amani karɓomin abinci" Amani ta fice tana cika tana batsewa ta nufi part ɗinsu Batool Kafin tayi magana, taga Abba na rungume da ita a ƙirjinsa, ko kukan me take oho,  itadai Amani taga yana share mata hawaye, Cikin sauri tace "Aslamu alaikum" Abba yai saurin sake Batool tare da cewa "Amani ƙalau?" "Bro Mahabob ne yace "in kawo masa abinci" "Batool har yanzu baki gama abincin bane?" Alhji ya kusa, "kasan shinkafa ba kamar indomie ba" "Please dafa masa indomie ɗin tunda shikam baya wasa da cikinsa" Babu musu ta wuce kitchen ta ɗora indomie a gas dama tanada ruwan zafi, Amani kuwa ƙin tafiya tayi sbda batasan Abba yaci gaba da iskanci...! Ayi haƙuri kwana biyu kunjini shiru Insha Allah zamu ci gaba Masu comments Nagode Allah yabar ƙauna *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 35-36 Har Abba ya koma ɗaki ya fito ya samu har yanzu Amani na zaune, "Zan fita sai na dawo" Abba yace tare da kallon Batool. Allah ya kiyaye hanya tayi masa, dan tarasa abinda zata sake cewa bayan haka, Amani na kallon yanayin fuskarta lokaci-lokaci,  Kitchen ɗin ta koma, ta duba indomien ta tsotse, ta zubo a faranti mai kyau, kana ta miƙawa Amani, Amani ta karɓa ta fice. Batool ta koma kitchen sauke abinci, ta ɗora miyar da dama tariga da ta gama tun ɗazu ɗumamawa zatayi, Inaya ta shigo idanunta sunyi rau-rau zatayi kuka, Batool tace "yarinyata keda waye?" "Aunty Amani ce ta hanani abinci" "Sorry na gama zo in zuba miki kici" Inaya na murna ta zauna, a parlon kan kujera tare da ƙurawa TV ido, Abincinta ta zuba, kana ta zuba nasu Amani a ƙatuwar kula da nama mai yawa, da miya daban sai cabeji da latas da cocumba a wata ƴar roba, kafin ta fita kai musu, Tana shiga da sallama, bayan sun amsa ta ƙarasa ta ajiye musu abincin, sannu sukayi mata kafin ta fice duk suka yo kan abincin harda Mahabob, itako tayo waje. Tana shigowa ta samu Inaya har tayi barci, dama tanason indan ta dawo ta kawo musu suci tare, ta zauna gefen Inaya cikin rashin jin daɗin barcin nata, Tasa abincin iya inda zata iya cinyewa, bayan ta kammala cin abincin ta sake shiga wanka, ta shirya cikin atamfa blue anyi mata adon zanen ganye da yellow sai ratsin ɓaki, sosai atamfar tayi mata kyau, tabi ko wane lungu na jikinta da turare, kana shimfiɗa sallahya sbda tayo alwalah, jiran kiran sallah take, ta fito parlo. Zuwa yamma liss gaf magriba Abba ya dawo, da gudu taje tayi masa oyoyo tare da rungume shi, lokacin Inaya ta farka, amma sai ta runtse idonta dan ace barci takeyi, Sai wani shafata Abban keyi kamar mage, yana kissing ɗin ta duk a idon inaya, "Dama ba nisa kayi ba?" "Eh wlhi naje ganin motar Mahabob ne da na sauya masa" "Masha Allah Ubangiji ya ƙara buɗi" "Amin ya rabbi, saura naki dana Amani" Batool ta zaro  tana ci gaba dayi masa godiya. SHAHAZAD FOREST. Yau sun tashi da ni'imar ruwan sama, yawancin matan murna sukeyi, sosai kowacce tana ƙoƙarin gyaran gonakinta, hankali kwance. Tunda mutanen Shahazad suka kwana biyu basu shigo yankin ba, wata mata wacce ta kasance itace shugabarsu ta fito hannunta riƙe da wani yaro wanda a ƙalla zeyi shekaru 10yrs a duniya, yaron fari ne tass ga dogon hanci, kowacce mace ta rufawa shugabarsu asiri, sbda suna sa ran samun ƴanci nan gaba, kuma suna saka ran yaron zai zame musu haske a rayuwarsu, shine zai yaƙi Shahazad. A cikinsu akwai mata wanda suka kasance mace da namiji kuma duk mata ne, wato Raniya da Salha, sunyi aure ne a bisa yarjewar shugabarsu, sbda su basusan abinda ya dace da wanda ma bai dace ba, Raniya itace matar, Salha kuma miji, inda mata da miji sukeyi haka suke rayuwa, tabbas koda shugabarsu bata yarda da wannan aure ba, sai sunyi tunda kaf ƙauyen su biyunan ƙwari ne kuma hatsabiban kansu, Zuwan bazata zuwan rashin tsammani, wani irin jiniya sukaji, yau ko sanarwar ma babu bare labari, kai tsaye cikin ƙauyen suka shigo, yau babu sauƙi hatta matan da sukayi gardama kashesu akeyi, Raniya ta fito domin tace Sahla ta gudu, wani daga cikin mota ya harbe ta da mota, jin harbin bindigar yasa Sahla guduwa dan tasan idan ta tsaya sai buzunta, tunda shugabarsu taga anata ɓarna ta kamo hannun Shukri suka ɓuya cikin ramin da mutanen basusan dashi ba, sai da sukaga sun rage yawan mutanen yankin kafin suka ɗaukesu a photo suka wuce. Jin tsit yasa ragowar mutanen fitowa wanda suka koma tsiraru, kai tsaye Sahla na zuwa ta wuce gurin Raniya tana kuka, Kuka takeyi wanda yake da ban tausayi, tabbas duk rashin imaninka dole zaka tausayawa Sahla, a fili tace "Raniya na rasaki har abada, ina amanar da mukayiwa junanmu ina sittin da muke yi tsakaninmu ina gwagwarmayar da muka sha kafin mu mallaki junanmu?" Wanda suka tattara ƴan uwansu suka dawo gareta suna bata haƙuri akan tayi haƙuri ta kauce a gurin, amma ina kamar ana sake tunzurata, Tana cikin kukan Shukri ya fito ba tare da sanin shugabarsu ba, cikin ɗaga murya yace "Sahla karki bari jinin Raniya ya tafi a banza ki shiga cikin garin Libya ki yaƙi shugaba Shahazad har sai inda ƙarfinki ya ƙare, zan taimaka miki idan shugabata ta yarda" Cikin kuka Sahla tace "an kashe min uwata an kashemin Ubana, tunda muka taso ake kashe mutane a gabanmu, babu wanda ya taɓa yunƙurin farmakarsu ko hanasu, an mayar mana da rai tamkar na dabbobi basu ɗaukemu da amfani ba,  nayi alƙawarin kawowa ƙauyenmu cigaba sannan nayi alƙawarin inhar nabar garinan bazan dawo ba, sai anyi abu biyu, ko ɗaya ya faru ko dukkansu, Ragowar matan suka taho gurin ta kowa ya bata goyon baya tare da ƙara mata ƙwarin guwaiwa. "Nima na goyi bayan ki sannan zan taimaka miki" Shugabarsu ta faɗa tana yiwa Sahla murmishi. Dole aka nemo ƙwararrun likitoci, tunda yace bai yarda da waɗancan ba, kwana uku da suka wuce babu wanda zai ce Mona zata gyaru, yanzu gashi har zama tana iya yi, bata wani cin abinci sai coffe shi kaɗai ne take iya jurar shansa, Burinta bai wuce Allah ya bata lafiya ta hukunta Shahazad ba, bayan haka ko a ranar ta mutu tayi arziƙi, Acan fannin Hajara, kowane motsi na lokaci baya wuce ta, sbda hankalinta gabaki ɗaya yana kan agogo, tausayin Mona takeji har cikin zuciyarta, tanaso ta ƙara shiga cikin cikin ragowar ɗakunan tana tunanin Shahazad anya bashi da wani abu wanda ake hango motsin mutum, itakam ta fara tsoro ko har numfashinta ya fara ƙirgawa ne, Gidan ya rage ita ɗaya, sai dai daga can gurin get akwai mutane sun kai 10 kowa da aikinsa harda jami'an tsaronsa, Parlo ta dawo ta kunna tv, domin ɗebe kewa, ina bazata iya kallon ba, ta kashe, a hankali tunanin su Inna da Goggo ya fara mata yawo a kanta, tana son kiransu tana tsoron gidan, sbda tana tunanin duk abinda ta faɗa akwai abinda yake baɗewa Shahazad na dawowa zai gaya masa, dole ta fasa kiran, amma zuciyarta nayi mata saƙa iri-iri. Cigaba yayi da zanen yayinda Lulu take shafa masa kwantaccen gashin da yayi luff a gemunsa, "Lulu Please kiɗan matsa inaso in gyara zaman masarautar nan" Da sauri Lulu ta zaro ido, cike da fargaba tace "haba Hubb kana nufin har yanzu baka haƙura da maganar masarautar ba? karka manta sarki ya mutu, karka manta Shakura tace ko bayan ranta bazaka..." "Stop..!!! Haba muku a maimakon ki kwantar min da hankali kunason famomin dafin dake sakaye a cikin zuciyata?" idan kin shirya gwagwarmaya dani zamu iya rayuwa tare, kamar inda kema kikeda burin aikin Jarida kikeson cika burinki ban hanki ba, dan haka karki sake ki dakatar dani akan ƙudurina, koshi Raza bai isa ya kaucewa makirci da sharri a ba, nasha yin mafarki akan nahau kujerar sarki Mazin, dan haka kiyi shawara da zuciyarki" Tsit Lulu tayi kamar ruwa ya cinyeta, kafin ta sake matsowa kusa dashi ta ɗora hannunta a nasa, murya a marai-raice tace "na shirya zama dakai" kana ta ɗora hannunta a nasa, Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungume ta ya lumshe ido. har ransa yanajin sonta amma sam ƙaunarta baya cikin zuciyarsa to meyesa? Lokacin da aka kira sallahar magriba gari ya fara duhu, amma anan gidan nasu haske kamar rana, lokacin ta gama musu irin abincin su, ta shiga ɗaki zatayi sallah sbda tayi alwalah, "Haseeaina.." Cikin ɗaga murya ta amsa da "na'am" "Kawo mana abinci ɗakin Hubb" Cikin Umarnin Lulu ta ɗibo abincin ta jere a babban trai mai kwalliya, tana tafe ƙirjinta na dukan uku-uku, har ta ƙarasa ɗakin da sallama, babu wanda ya amsa mata, a zuciyarta kuwa cewa take sai kace arna?" Lulu na manne da Ala-Uddin Samir, Hassana ta ajiye, Lulu ta kalli Ala-Uddin Samir kafin ta kalli Hassana sai kuma tace "lafiya kuwa Hubb?" Lafiya "Haseeaina tashi ki wuce" Ala-Uddin ya faɗa murya wata iri, Nan da nan kishi ya rufe Lulu cikin masifa tace "badai kallonta kakeyi ba?" "No kayan jikinta ne tadena sawa sunyi datta da yawa" Sannan Lulu tayi ajiyar zuciya, har zata miƙe Ala-Uddin ya riƙeta tare da cewa "ina buƙatarki a kusa dani a halin yanzu" Cikin jin dadi ta sake matseshi wanda a zahiri ba haka bane a zuciyarsa, Sai da sukaci abincin kafin sukayi sallah. NIGERIA Daƙyar saurayin ya shawo kan mahaukaciya tare da cafko kayan jikinta, wanda yana riƙe ta suka sake yagewa, dama a yage suke, Tunda yaga zatayi masa gardama ya ɗagata cak ya goyata, tare da yin tafiya da ita, sunyi tafiya sosai tanata fizge-fizge, A jikin wani gida suka tsaya, ya sauketa tare da kallon masallacin, yaga babu kowa, shiga da ita gidan yayi. Gidane babba, irin gidan yawannan matan gidan sunkai biyar, zamu iya kiran gidan da gidan gado, kowa yana gadara da gidan, akwai mama Lantana mahaifiyar saurayin wato Aliyu, sai mama Hajara bata da yara, sai mama Uwani sai Inna Hasiya, sai Ladi me tuwo, Ilahirin matan gidan suna zaune a tsakar gida, Suna ganin Aliyu da mahaukaciya suka riƙe baki, Mama Lantana tana ɗaki, Ladi me tuwo tace "ahayye faɗan da babu ruwan ka daɗin kallo gareshi" Mama Hajara ta zaro ido tanaso taga inda Aliyu zai shigar da mahaukaciya, Tunda sukaga ya shigar da ita ɗakin mamansa, suke jira suji malam yaro ya rufe shi da masifa, amma sukaji shiru, Bayan ya gaishe da mahaifinsa, ya kalli mahaifiyarsa kana yace "Ummi ki taimaka mata, Malam yaro yace "tabbas baiwar Allahan nan tana buƙatar taimako, amma Lantana sai kinsa baki" Mama Lantana tace "insha Allah, idan mune silar warkewarta zan tayata da adu'a, kaima sai kaci gaba dayi mata temako" "Da yardar Ubangiji a daren nan zamu gayawa Allah, insha Allah akwai alamun samun lafiya a tare da ita, yarinya ƙarama da ciwon HAUKA, kwata-kwata batafi shekaru21 ba amma jibeta" Aliyu ya sunkuyar da kansa, ƙasa, sbda tausayinta yana yawan kariyar masa da zuciya. Nan fa su Mama Hajara aka shiga gulma iri-iri. "Mama zan tafi gida, ko akwai abinda kuke buƙata?" Malam yaro yace "eh ka siyo mana ruwan zam-zam da dabino dan Allah kayi sauri" Cike da ladabi ya amsa ya fice. Bai jima ba sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da ƙatuwar leda, abinda ya bashi mamaki shine, ganin mahaukaciyar ta nutsu sosai sai kallon malam takeyi, Aliyu ya ajiye ledar tare da yi musu sallama, Mama na buɗe ledar taga madarar gari da milo da lifton harda ƙaton bredi da suga zam-zam ɗin da dabino, kamar inda malam ya buƙata....! Gobema akwai posting da yawa, amma fa idan naga comments ɗinku nayau Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 37-38 Zaku samu littafin tun daga farko har inda aka tsaya a gurare kamar haka👇 Arewabooks@ Momislam11 Wattpad@momislam2021 "Allah yayi maka albarka" Ummi ta faɗa lokacin da Aliyu yake yi musu sallama. Yana  fita ya tari mashin zuwa anguwar da yake,  duk da ba wani nisa ne dasu ba, amma yakan hau mashin wani sa'in, Suna tafe yana yiwa mai mashin ɗin kwatancen inda zai saukeshi, suna zuwa ya sauka kana yaba mai mashin kuɗinsa ya shiga gida. Gidane madai-daici, bashi da wani girma, amma koda yaushe suna cikin rufin asiri, sana'arsa shine, siyarda kayan abinci, tun yana da ƙaramin shago, yanzu Allah ya sake ɗaukakashi ya buɗe shago a kasuwa, Alhmdulilah anan yake samun duk wani abinda zeyiwa iyayensa hidima da gidansa, matarsa ɗaya Heedaya, bata taɓa aihuwa ba, a hakan suke cikin so da ƙauna. Da sallama ya shiga gidan yana ƙwala mata kira, "Hadeey.. Hadeey" Murmishi yayi sakamakon ganinta akan sallahya da yayi, ta ɗaga hannayenta sama tana roƙon Allah, shima ya ɗaga hannunsa, lokacin da tazo shafa adu'ar a tare suka shafa, tace "sannu da dawowa" "Yauwa sannu, ya kamata kiyimin oyoyo yau sai naji babu ɗaɗi" "Yi haƙuri yayah ka bini bashin na gobe idan Allah ya kaimu, ya ka baro su Ummi da malam?" "Sunan lafiya,  Hadeey na haɗu da wata mahaukaciya" Da sauri Heedaya ta miƙe tare da ninke sallahyar ta matso kusa dashi tare da cewa "Yayah a ina ka ganta?" "A can hanyar anguwarmu, wlhi daƙyar da nakamota, na kaita gidanmu gurin malam, kafin in kaita har na fara tunanin ko malam ɗin zai koremu ne, sai naga ya ƙyalemu ya amshets hannu biyu" Cikin tausayawa Heedaya tace "Yayah duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi, kaga idan ta sanadin ka Allah ze kawo mata lafiya, kaima kanada kaso mai tsoka a gurin Ubangiji" "Hakane Hadeey amma ina neman shawara a gurinki, nasan bazaki bani shawara marar kyau ba" "Tom Yayah ina jinka" "Inaso sati mai zuwa mu koma gidanmu tunda an gama saka tayis da winduna, kinga wannan gidan sai a barwa su Ummi" "Cikin farinciki Heedaya tace "wlhi da nafi kowa farinciki, nidai badan karkaji haushina ba sai ince, dama wannan gidan na tsaneshi, sbda babu inda zanyi ne yasa nake zuwa" Aliyu bai ce komai ba, sai ma rungumota da yayi yana mammatsa mata hannu a hankali, "Ga abinci can akan tabarma" "Me kika dafa mana?" "Shinkafa da miya ne sai kifi busashe" Aliyu ya shagwaɓa fuska kamar wani jariri, kafin yace "nikam ba yanzu zan ci ba, banfa yi sallah ba, sbda kamo matarnan wlhi yau ban samu sallah ba" "Yayah jekayi sallah idan ka dawo sai muci abinci" "Uhm kinsan alƙawarin mu na jiya, kince yau zakiyi tsarki ya kamata ki gyara wlhi ina dawowa sallah hamm" "Gimtse dariyar dake ƙoƙarin suɓuce mata tayi tare da ruƙo hannunsa, suka nufi inda butoci suke, butarsa ta miƙa masa kana koma ciki tana cewa "nifa nasan halin kayana" Yana daga tsakar gida shima dariyar yakeyi. Yana fita, ta ɗauko kwaɓaɓɓen haɗinta wanda yaji zuma ta lakata tayi matsi dashi, kafin ta ɗibo garin kaninfari ta zuba cokali biyu tare da madarar ruwa ta juye a ciki, ta nemi guri ta zauna tare da ɗaga kai ta shanye, Sai da akayi sallahar isha'i sannan ya dawo, lokacin haɗin ya fara bin jikinta, tanajin sallamarsa ta ɓoye a cikin labule, tasani tsabar zumuɗi abincin ma bazai ci ba, "Aslamu alaiku, Hadeey.." Jin shiru yasashi ƙarasawa cikin ɗakin yana cewa "wlhi ki fito kokuma idan na kamoki zaki gane shayi ruwa ne" Da sauri ta fito, sbda ya taɓa yi mata haka, bataji da daɗi ba. Daga bayansa ta tsaya, ta rungume shi ya goyata yanata zagaye ɗakin da ita, ciro soyayyar doya daƙawai sbda yasan tanaso, ya miƙa mata, godiya tayi masa kana ta kamo hannunsa suka wuce dakinta, sbda ɗakuna biyu ne a gidan, nata ciki da parlo sai kicin sai bayi, A kan gado suka zube, ya ƙura mata ido, ga mamakinta sai taga hawaye na zarya a idonsa, ko me ya tuna oho. Hankali a tashe take kallonsa, cikin tausasa murya tace "yayana ko nayi maka wani abunne?" "Babu abinda kikayi min sai ma wanda kikeyi min gurin kyautata min, ina ganin kaf duniya babu matar da zata ji tausayina ta kyautata min ta somin iyaye sannan kuma ta jure buƙatata sama dake" Sam tama kasa magana, cikin salo na kissa ta fara shafa masa baya kamar inda yake sanar mata yanaso, Lumshe ido yayi tare da sake rungumota yana sinsinar kanta dake fitar da ƙamshin man kitso, Sun daɗe suna wasa, daga ƙarshe suka faɗa duniyar luv. Daga airport aka dawo da Hakeem gida, lokacin duk sun shiga jirgi sai dai muyi musu fatan isa lafiya. ALGERIA Lokacin da jirginsu ya sauka Iffat tana barci, Kai tsaye masaukin da aka shiryawa dady suka wuce, Hajiya ƙarama tana rungume da Iffat, Gidane rantsatse mai kyau, tsayawa misalta kyau da tsarin gidan, ɓata lokaci ne, gidane da idan mai karatu ya gansa zai ga kamar duk gilashi akayi, sbda walwali da gidan keyi. Masu gadin gidan ma sunkai mutane biyar, sbda gidan babba ne, haɗe da jami'an tsaro, A parlo suka zube, Hajiya ƙarama har ta zauna ta miƙe domin kwantar da Iffat, tsarin gidan sai yayi mata wani iri, ɗakunan gado wanda ta leƙa sunkai huɗu, ɗakin da Allah ya bata iko ta shiga, ta kwantar da Iffat tare da yi mata adu'a, gurin dady ta dawo ta samu yanata waya, har ta daɗe a zaune bai gama wayar ba, Miƙewa tayi ta shiga neman bayangida sbda tayi alwalah, wayarta ta mutu batasan ko ƙarfe nawa bane yanzu. Cikin sa'a ta hango bayangida, ta shiga ta kunna pampo dan bataga buta ba, kallon numbobin dake jere tayi, kafin ta ɗaga kanta sama duk iya bokonta da sanin kayan zamani takasa kunnawa, sai da ta dawo ta kira dady, lokacin ya gama waya, ya danna wasu numbers sannan ruwan ya zubo Mai kyau ga daɗi. Kafin tayi alwalah ta buɗe jakar tafiyarsu ta ciro sallahya, ta dawo ɗakin da ta kwantar da Iffat ta fara Sallah. Kamar kullum da koyaushe, tana yawan saka Iffat a adu'a, bayan ta gama ta shafa. Jingina tayi da jikin gadon, kafin Hajiya babba ta faɗo mata, Hajiya ƙarama ta girgiza kai tare da miƙewa ta ninke sallahyar, Parlo ta dawo, ta samu dady baya nan ya fita, Ta koma gurin Iffat lokacin harta tashi, Little Eshat kin tashi?" Iffat ta zubawa Hajiya ƙarama ido kamar meson cewa wani abu. Dady ya shigo hannunsa riƙe da cajar Hajiya ƙarama yace "kisa wayarki sannan kuzo dining room abinci na can" "To" tace masa, tare da jona wayar Tata, sannan ta kamo hannun Iffat suka fito zuwa gurin cin abinci. Suna zuwa, Hajiya ƙarama ta zaunar da Iffat akan cinya tare da buɗe warmers ɗin dake ɗauke da abinci, Hannu Iffat takai kan farfesun kaji, Dady yace "masha Allah Iffat tanaso zataci" Saukowa ƙasa sukayi kan grass carpet mai taushi, Hajiya ƙarama ta fara bata a baki, dama ba ƙashi ne dashi ba. A daren yayi magana da babban likitan ƙwaƙwalwa, Washe gari, da sassafe aka shigar da Iffat ɗakin aiki. NIGERIA Zaune yake gaban malam mai Almajirai hannunsa riƙe da ɗari uku, bayan sun gaisa, malam Yusuf yace "nikam na warware, nazo ne akan yarinyata Juwairiyya" Malam mai Almajirai yace "masha Allah ai tunda na ganka nasan lafiya ta samu, to menene matsalar ita ƴar wajen naka?" Malam Yusuf yace "wlhi babu manena ne, babu wanda yake zuwa gurin ta, ni nafison samari su dinga yi mata layi, koma basuyi mata layi ba, inaso ta samu hamshaƙin mai kuɗi, wanda zata huta" Malam mai Almajirai yace "to yanzu dai wani hanzari ba gudu ba, akwai abubuwan da zamu siyawa aljanun kanta, sbda sune suke Kore mata samari, bayan haka zan bata wani kwalli da hoda, idan zata fita ta shafa, amma fa ta tabbatar anguwar masu hannu da shuni zataje, ko ba aikanta akayi ba ta dinga zagayawa" Malam Yusuf yace "to kamar nawa ne kuɗin turarukan?" "Dubu goma, nayi maka alƙawarin inhar kwalliya ta biya kuɗin sabulu sai kun ninka dubu goma sau miliyan kuma zakace munyi wannan zancen" Cike da jin daɗin alƙawarin da malamin yayi masa, yace "ina komawa gida zan taho maka dashi, ya miƙa masa ɗari uku yace "gashi asiyi goro" Godiya malam mai Almajirai yayi kana yace "yana tsumayinsa" Bayan tafiyar malam Yusuf malam mai Almajirai ya fara haɗo magunguna hardasu hayaƙi da turare na jiki da hoda da kwalli, Sai yamma liss lokacin ankusa shiga sallah, sannan malam Yusuf yazo, Bayan sun sake gaisawa ya miƙawa malam mai Almajirai kuɗin, shikuma ya miƙa masa magani, yayi masa godiya ya wuce. Washe gari, da wuri su Amani suka shirya, bayan sun gama karin kumallo sukayi wanka, suka haɗe cikin shadda mai ruwan sararin samaniya ita da Aseela, ita kuma Inaya doguwar riga ƴar kanti Batool ta sanya mata, Batool tasa Abaya milk color mai ratsin yellow ba sosai ba, sai adon duwatsu da rigar tasha, sam Abba ya hanata sanya mayafin dole sai dai tasa dogon hijabi, ta ɗauko handbag ɗinta ta fito part ɗinsu Amani, suma sun gama shiryawa, har suka gaisheta suka fito, sbda Mahabob yana parking space yana jiransu, Abba ma ya fito dukkansu suka wuce, Kasancewar sabuwar motar Mahabob ɗin mai ɗiban mutane kamar 8 ne yasa suka tafi a sake, kai tsaye anguwarsu huda suke shirin zuwa, a hanya Abba yace a siya musu kayan marmari, koda mai kayan ya zuba a leda ya miƙo Abba ya miƙa kuɗin sukaci gaba da tafiya. "Wlhi kinji sauƙi duk wani lamɓo da kikeyi saboda karkije tallah na rantse gobe sai kinje, ni zaki mayar shegiya marar galihu, in girka in baki kina daga zaune, gobe nayi zaki wuce tallah kinji na gaya miki karma kice bakisan da maganar ba" Sosai Umman take faɗa kamar zata ari baki, dama bawai taji sauƙi irin sosai ɗinnanne ba, jikin dai ya warware mata, tashi ɗaya ta fara rawar sanyi daga inda take zaune, Umman ta leƙo tana cewa "jibi abinda kikeyi sai kace bugun aljanu, wlhi abokin sharrinki yayi nisa, ni zaki gayawa ciwo, tun kafin kizo duniya nasan ana rashin lafiya, ke ciwon ma da yazo miki da gata harda asibiti sai kace ƴar gwamna, kina ganin idan zan kwanta ciwon mutuwa babu mai temakamin dole dai haka zan warke tunda jikin talaka ne" Idon Huda ta gefe na zubar hawaye tace "Umma sanyi nakeji Umma ki ɗagani anan Umma zan mutu" "Au..au ashe me mutuwa ma yanada kama? da ciwon gaskiya kikeyi zan ɗagaki amma tunda ciwon ƙarya kika rakitowa kanki nabar ɗagaki" Tun daga zauren gidan su Mahabob sukejin magana kamar ana faɗa, da gudu Mahabob yaje ya ɗago Huda, tare da kallon Umman da idanunta ya rufe, sbda har ta shiga ɗaki tana ci gaba da surfawa huda masifa, "Aslamu alaikum" Abba yayi sallama muryarsa wata iri, duk da sunyi ɗazu tun kafin su shigo Umman bataji ba, Da sauri ta fito tana amsa sallamar baki kamar gonar auduga, tace "ku shigo" Tunda suka shiga Mahabob ya fara shawarar inda zai nesanta Huda da gidan, a zuciyarsa yace "ta zamo ƴar aikinmu shine mafita.... Mom Islam ce... *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 39-40 Da kallon tausayi Amani ta bi Huda dashi, sakamakon kwanciyar da taga tayi. Cikin zumuɗi ta gaishe su, bayan sun gama gaisawa Abba yace "dama munzo duba jikin marar lafiya ne" "Lahh ai taji sauƙi iskanci takeji shiyasa kuka ganta haka" Abba yace "Ash shaa.. Allah ya shirya mana zuri'a" Bayan shiru da gurin yayi, Mahabob yayi gyaran murya kana yace "Abba ya kamata mu ɗauke ta aiki kodan su dinga rage zafin wani abun" Sai da Abban yayi nazari, kafin ya kalli Huda dake kwance har yanzu tana rawar sanyi, yace "eh hakane, idan ta samu lafiya muna neman alfarmar a bamu ita ta dinga yi mana wanke-wanke sai ki faɗi albashin da ya kamata a biyata" Abba ya faɗa yana kallon Umman Huda, tare da jiran amsar da zata bayar. "Toh Alhaji nidai bazance muku "eh ko a'a ba, sbda tana zuwarmin tallah, kuma dashi muke ci muke sha harma mu ɗinka tufafi" "Amani tace duk ba wannan ba, kuɗin kawai zaki gayawa Abba koma nawa ne zai baki" "Uhm gaskiya riba tsugugu nake samu a sana'ar shinkafa" Cikin ƙosawa da ƙaguwa Mahabob yace "am sorry kuɗin kawai zaki gaya mana" "Kullum idan na dafa shinkafa ina samun ribar dubu biyar" Huda ta ɗago jajayen idanuwa da suka rine tsabar zazzaɓi, tare kallon Umma, murya ƙasa-ƙasa, Huda tace "dubu ɗaya ne da ɗari uku" Umma tace "ke...ke kee gidanku, maƙaryaciya zaki mayar dani? cewa fa kikayi baki da lafiya, shiyasa nace ƙarya kikeyi" Abba yace "zan dinga biyanta dubu ɗari biyu da hamsin duk wata" Cikin sauri "Umma tace "to aiko mun gode amma tafiya da ita zakuyi ko anan zata zauna ta dinga sintirin tafiya kullum?, nikam bani da kuɗin mota" Mahabob yayi murmishi sbda umma dariya take bashi, kafin Abba yace wani abu, Mahabob ya riga shi yace "zamu tafi da ita Asabar da Lahadi zata dinga zuwa islamiyya duk ranar Lahadi sai ta dinga zuwa gaisheki. "Ah ai babu komai, koni in dinga zuwa gaisheta ba?" Babu wanda ya sake cewa da ita komai, sbda a maganganun nata sai kace na mai taɓuwar hankali, "Mahabob jeka mota ka duba gurin da nake ajiya akwai kuɗaɗe a ɗaure, kowanne dubu hamsin ne sai ka kwaso guda biyar" Cikin ladabi Mahabob yace "toh Abba" Umma kam hankalinta ya tashi, ashe Amani tanata yi mata magana bataji ba, sai da "Huda ta matso tace "umma anayi miki magana" Sannan tai firgit kamar me mafarki ta wayance da cewa "rikicin duniya, meye?" "Yaushe zamu tafi da ita?" Amani ta faɗa fuska a tamke. "Ko yanzu wlhi zaku iya tafiya" Batool ta girgiza kai. Mahabob na kawo kuɗin ya miƙawa Abba, tun kafin a miƙowa Umma take leƙe, duk suna kallonta. Sannan Abba ya miƙa mata kana yace "a shiryawa  yarinyar kayanta" "To..to Alhaji mungode dama munajin labarinka a gidajen talabijin ashe Allah zai haɗamu da irinku masu mutumci da sanin darajar ɗan adam" "Ke huda tashi ki shirya kayanki" Umma ta faɗa tana danne kuɗin da guwaiwar ƙafarta. Cikin dakiya, Abba yace "ayi mata uzuri a shirya mata" Duk wani kaya da Umma ta sani nata duk ta haɗa mata dashi harda takalmanta, da kayan kwaliyarta, ta ajiye musu gana masgo ɗin a gabansu, duk ta yage babu mamora, ta wani gefen duk kuɗin cizo" Abba yace "Batool ki juye kayan a mota, mu wuce" Kafin Abban ya miƙe dukkansu suka tashi, tare dayi mata sallama suka wuce, Tayi godiya kamar zata ari baki, Amani ce ta riƙe huda suka tafi gurin mota, sbda jikinta babu ƙwari.             __________ Tunda malam Yusuf ya kawowa Juwairiyya magani da turare taje tayi wanka, ta daɗe a wankan kamar zata sauya fata, ta fito hankali kwance, ƙasan zuciyarta fara'a ne a lulluɓe, ta nufi ɗakinta ta shafa mai, tayi kwalliya kai kace gurin ƙwararru taje, tasa shaddarta pink color tasha aikin wuta, har ƙasa, tayi kyau sosai, nima dai cewa nayi kumafa ba matar yara bace. Turaruka kala biyu ta fesa masu sauƙin kuɗi, kafin ta yafo farin mayafinta, ta ɗauko farin takalmi, kafin tazo ɗakin babanta ta ɗauki kwallin tasa,ta fesa turare, ragowar ƙullin maganin sai dare, ta fice bayan tayiwa baban sallama yace da ita "Allah ya bada sa'a" Amin tace masa ta fice tana karairaya, Can ƙasan anguwarsu ta nufa, tana tafe tana karairaya, cikin yauƙi ta ke kallon wata haɗaɗiyar mota dake tahowa, yana zuwa daf da ita ya rage gilashin motar, tare da cewa "ƴan mata idan bazaki damu ba, zan iya sanin sunanki, cikin sauri tace "sunana Juwairiyya" "Wow nice name suna mai daɗi, ko zan iya samun soyayyarki" Cikin zumuɗi tace "mezai hana?" "Okay Tom shiga mota in rage miki hanya" Motar ta shiga tare da nuna masa wani danƙareren gida tace "nan ne gidansu" Saurayin yace "sweety ni baki tambayi sunana ba?" Juwairiyya ta rufe fuska tare da cewa "yi haƙuri mantuwa nayi" Sunana Abdul-Alee cikin zumuɗi tace "wlhi sunan yamin daɗi" Suna isowa yace "zanzo anjima" "Ai nan gidan antyna ne gidanmu yana can ƙasa" "Okay Tom ki bani number waya" Ta karanto masa ya ɗauka, kana yayi mata flashing ta duba ta gani, sannan tace "ya shigo, sai da ta sauka taji kunyar ciro wayarta da wani gurin maɓɓallan duk sun cire babu. Da farinciki ta dawo gida ta gayawa babanta, shima yayiwa Allah godiya harda taka rawa. Kuyi haƙuri na fara gyangyaɗi 🤣 *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 41-42 Yau kwanan mahaukaciya ɗaya a gidan su Aliyu, alamomin waraka da sauƙi suna baiyyana, Tunda aka fara maganin malam ya hana Ummi ta barta fitowa waje, ko alwalah za'ayi mata, sai dai a kawo roba, har fitsari ma a po takeyi. A rana ta uku, da safe mahaukaciya na zaune, bayan sunyi sallah, ta kalli Ummi tace "sannu da aiki" Cikin jin daɗi da tsantsar farinciki Ummi tace "masha Allah ina ne yake yi miki ciwo?" Mahaukaciya tayi murmishi kafin tace "babu ko ina sai dai inajin ciwon kai amma ba sosai ba" "Insha Allah zeyi sauƙi shima a hankali" Suna cikin magana Malam ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, dukkansu suka amsa cikin haɗin baki, Cikin farinciki malam yace "masha Allah munayiwa Allah godiya Ubangiji ya ƙara lafiya" Suka amsa da Amin, "Ki cire kayan jikinki, tun jiya suke jikinki da nasa miki, sai kije kiyi wanka" "Eh ya kamata idan zaki fita ki dinga adu'a koda innalilahi wa inna ilaihir raji'un, ko li'ilafi quraish" Mahaukaciya tace "toh" Sabulu mai ƙamshi Ummi ta fito mata dashi, kana ta miƙa mata kwandon soso, da kuma zanin da zata ɗaura in zata fito, Ummin ta miƙe ta juye mata ruwan wankan ta kai mata, har yau babu wanda yace mata ya mai jikin da Aliyu ya kawo, hakan kuma bai damu su Ummin ba. "Malam mutane suna bani mamaki, wannan yarinya ce fa ƙarama, amma ina tunanin asiri akayi mata bawai haka kawai ciwon ya sameta ba?" "Malam ya kawar da kansa gefe, kana yace "tabbas asiri akayi mata, kuma ƴan uwanta ne kokuma tayi aurene tanada kishiya ban sani ba, amma wanda yayi mata yanada alaƙa da ita" Cikin tausayawa Ummi tace "Allah ya saka mata, Allah yasa zata iya tuna danginta" "Amin ya rabbi" Malam ya faɗa, ya ɗaukar kofin silba mai ɗauke da koko a ciki. Har malam ya fice mahaukaciya bata fito daga wanka ba, sai can anjima sai gashi ta fito, sabulu kam ya kusa ƙarewa tsabar durje jiki, "Wai-wai fans barinyi muku gulma wlhi mahaukaciya sai kace balarabiya, duk wanda ya santa da sunanta na mahaukaciya idan ya ganta ƙarya ne ya ganeta" Su Mama Lantana da suka kafa kujerar hira sai kallonta sukeyi,  suna cewa "kodai aljana ce kunga ta sauya fata" Mahaukaciya na jinsu ta ƙarasa ɗakin Ummi da sallama, Already Ummin ta fito da man shafawa da hoda tare da tozali, ta ajiye Mata, kana ta fito Mata da sabuwar atamfa wacce Aliyu yayi Mata tun sallah ɗinkin ya matseta sosai, Godiya mahaukaciya tayiwa Ummi, kana ta shafa man tayi kwalliya tasa kayan, duk da batasa bra ba tayi kyau sosai. Ummi ta kalleta, cike da farinciki tace "ammata na tayi kyau, kin kalli kanki a mudubi kuwa?" Mahaukaciya ta sunkuyar da kai. "Na gama aiyuka saura ɗora girki, shikuma sai anjima, so nakeyi ki bani labarinki tun daga lokacin da kikasan kanki har kawo yanzu" "Mahaukaciya tayi murmishi kafin tace "zan baki labari, amma da farko sunana Tasneem, amma ki kawo aikin girkin mu fara inayi ina baki labari" Ummi tace "karki damu, taliya zamu dafa, kuma ai akwai ruwan zafi a ajiye" Mahaukaciya tace "da farko dai asalin sunana Tasneem, ni bahaushiya ce, asalin ƴar garin Kano, iyayena sun rasu, a hatsarin mota, zasuje shiga jirgin tafiya Saudiya basu ma ƙarasa filin jirgin ba sukayi hatsari, lokacin banfi shekara goma sha uku ba, ranar da su Ummana sukayi kwana bakwai da rasuwa, danginta suka tafi dani gurinsu, a gurin ƙanwarta na girma, mahaifina babban ɗan kasuwa ne, Alhaji Sulaiman Bushasha, itama ƙanwar Umman tawa mai suna Karima, sunada kuɗi sosai, sai da nayi primary da secondary amma a jss na tsaya, dama tun ina k'arama aka sani a school, lokacin da na dawo gurin anty Karima naci gaba da secondary da Islamiya, inada shekaru goma sha shida, yaron aunty Karima ya fara neman aure na, mutane sunata cewa nayi ƙarama amma ita anty Karima bata ganin ƙan-ƙanta ta, haka ya dinga zuwa gurina hira yana zuwarmin da kayan ciye-ciye, har da kayan sawa, kwatsam wani mai suna Zahradden ya fito shima wai yana sona,yaron  hamshaƙin mai kuɗi ne, sbda mahaifinsa, yanada shaguna a kasuwa sunkai bakwai, sannan a wani garin ma yana dashi, banda ƙasar waje da sukasan da zamansa, dama anty Karima matar ƙanin Ummana ce, mijinta ne ƙanin Ummana, uwa ɗaya uba ɗaya suke da Ummana, shikuma mahaifin Zahradden abokin ƙanin Ummana ne, ina kiransa da Uncle, wata ranar Lahadi, da safe, ya kirani corridor sbda yana tsoron anty Karima, yacemin, kar in sake in karɓi soyayyar ƙanin Anty Karima, sunansa Haseem, Nace "Uncle mayasa kace haka?" Cikin kwantar min da hankali yace "wlhi yana shaye-shaye, nikuma maraicinki nake dubawa, duk da kinada gata ba na wasa ba, amma Allah da kansa yace "ki zaɓawa ƴaƴanki uba nagari, haka shima mijin, to kinga Haseem akwai gyara a lamuransa, tunda har neman mata yakeyi, kema kanki kin sani ba sai na gaya miki ba, zai fi ki auri wanda zai kula dake da ƴa'ƴanki, mahaifinsa mutumin kirki ne, kinga lokacin rasuwar iyayenmu, sai da yayi sati yana zarya wlhi naji daɗi, sannan iyayenki suma suka rasu, duk da bawai mun rasa bane, wlhi shi yake biya miki kuɗin makaranta". A lokacin kaina ya kulle, ina tsoron ɓata mu'amalarmu da Anty Karima sannan ina tsoron bijirewa Uncle, wata rana ta kirawoni akan in gaya mata tsakani da Allah nake son Haseem?, wlhi bansan lokacin da bakina ya suɓuta nace "ni Zahradden nakeso ba" Cikin sauri anty Karima ta kalleni kana tace min "au kina nufin bakyason ɗan uwana kenan?" "Ba haka bane anty nidai shi nakeso" Nan fa ta rufeni da masifa, tare da cemin "wlhi bazan ƙara tausaya miki ba, a matsakinki na marainiya, har nawa kike da zaki dinga nunawa mutane isa?, badan Haseem yace yana sonki ba, wlhi baza'ayi miki aure yanzu ba" Nidai ina jinta uffan ban ceba, taci gaba da cewa "karki sake neman wani abu a gurina, nima na cire hannu a lamuranki, kuma wlhi koda wasa kika sanarwa da yayanki maganar bakyason Haseem sai nayi maganinki" Ashe Uncle yana laɓe a bakin ƙofa yana jinta, Washe gari da ta fita anguwa ya kirani yacemin "in kwantar da hankalina anty Karima mutumce da inhar ta ƙwallafa rai a abu sai ta sameshi, shikuma bazai bari na auri Haseem ba, insha Allah gobe iyayen Zahradden zasu zo tambaya tare da dukiyar aure, in nuna bansan komai akai ba zeji da ita" "Toh" nace masa idanuna na tsiyayar ƙwallah, "Tasneem bawai kin isa aure bane, kawai ina son kuɓutar dake daga wannan gidanne nasan koda ina lura da wasu abubuwan bayan na dawo, idan na fita bansan abinda zatayi miki ba" "Daga nan ya miƙe yabarni a parlo inata kuka" Washe gari, ina ɗakina naji Uncle yana sanar mata da cewar "iyayen saurayina suna hanya tayi musu girki" Cikin rashin fahimta tace "bata fahimci abinda yake nufi ba, dama zugani yakeyi akan kar inso Haseem, shi kenan ta zuba mana ido, abinci ne bazatayi ba yayi abinda zeyi" Kasancewarsa mai haƙuri banji yace mata komai ba, sai ma ficewa da yayi, Can anjima na fito ina wanke-wanke, naga ya shigo da babbar leda, ashe abinci ya siyo a restaurant ya nemi kula ya juye ya Kai ɗakinsa, Dama yanada fridge ya ɗibo kayan sha ya ajiye musu. Ina kallonsa ta labule, tunda ba mai duhu bane, "Allah Sarki iyayena" Na faɗa lokacin da hawaye ke bin fuskata. Abinda zai baki mamaki, ta ƙofae baya suka shigo, har sukayi maganganu su suka gama babu wanda ya sani, ashe harda ƙanin kakarmu da abokin ƙanin kakarmu Uncle ya kirawo akayi maganar. Fitowar Uncle ya tabbatar min da sun tafi, Tun daga ranar na fara fuskantar matsaloli sosai, saboda wlhi ko abincin kirki bana samu, gashi kakannina duka sun rasu, sai dai ta wajen uwa, itace a raye, mahaifin Ummana ya rasu, Ranar da Anty Karima ta tafi anguwa na samu Uncle nace "masa, ya mayar dani gurin Hajiya, kakata mahaifiyarsu kenan, yacemin inyi haƙuri lokaci kaɗan ya rage" Kuka nasa masa, dole ya tausayamin washe gari, yasa na tattara komai nawa na koma can da zama, ranar nayi bacci sosai dan babu masifa, ita farinciki tadingayi da zuwana Dama Uncle ya sanar mata da maganar saka ranar biki da akayi sati Uku, Hajiya ta dingayi masa masifa akan ya gaji dani ne da ake shirin aurar dani yanzu ba a bari nayi karatu ba?" Haƙuri ya bata, daga nan bata sake cewa komai ba. "Allah Sarki Tasneem kice kinga uqubar rayuwa, bari mu ɗora girki naga har ƙarfe ɗaya saura 12:45pm" Back to story 🤞 Sosai tausayin Huda ya kama Amani, sosai taji zafin abinda Ummanta tayi Mata, amma ta fara tunanin Anya uwarta ce kuwa? Suna isowa gida, Aseela ta riƙewa Huda hannu suka wuce part ɗinsu, Amani kuma ta ɗauki jakar kayan, Mahabob yaji daɗin kulawar da suke nuna mata. Su kuma su Abba da Batool suka wuce nasu part ɗin, Inaya tana murnar ganin Huda tace "yau kam bazata kwana a gurinsu Abba ba" Lokacin da suka dawo ƙarfe 5:30pm tayi, Abba na zaune a parlo ya danna waya ya kira Amani, cikin bada umarni yace "Please ku dafa indomie ko kusha tea, na aiko Mahabob da bredi" Dayake suna zumuɗi babu wanda yace komai. Sosai Batool taji daɗin hutar da ita da Abba yayi, ta taho kusa dashi tare da zame ɗankwalin kanta, ƙananun kitsonta suka baiyyana, A hankali yakai hannu yana shafa su, cikin kasalalliyar murya yace "yau inaso in kasance da matata" Abinka da mai zumuɗi ko ince yarinta, sai cewa "tayi bakada matsala" ko wayewa ce oho. Rungume da juna suka wuce bedroom, kafin sai da ta tabbatar da ta kulle ko ina sannan, da sauri-sauri ya rabata da kayan jikinta, shima haka, tare da rage hasken glob ɗin ɗakin, sosai yake murza mata bre hankalinsa kwance, har wani mammatsasu yakeyi tana nishi ita Kuma, a kunne ta raɗa masa magana, "Inason yin magana dakai" "Haba hajiyata kome kikeso ƙofa a buɗe take" Cikin kissa da shagoɓa Batool tace "uhm dama inason in roƙi alfarma ne, naga Mahabob yarone mai biyayya, wlhi nayi masa sha'awar auren ƙanwata da ta gama karatu a Dubai, satinan har ta dawo gida" Cikin gamsuwa da maganar tata, Abba yace "haba ai kema momynsa ce, baki da matsala indai akan wannan ne an gama, nima ai samunki da nayi Mai tarbiya ga biyayya, wlhi ba k'aramin daɗi naji ba" Sosai Batool tayi murna saboda koba komai, kamar inda mamynta ta faɗa zasuci gado mai tsoka, inhar suka zamo su biyu a familyn Alhji Auwal. Naso yi muku sau biyu, wlhi hakan bata samu ba, masu comments Nagode wlhi kuna raina Kunyi yawa bare in lissafoku ɗaya-bayan ɗaya, wannan saƙo ne ga duk wani masoyina meyin comments. Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 43-44 Kwanansu biyar da zuwa Algeria, anyi aiki cikin sa'a, A Koda yaushe Hajiya ƙarama takan keɓe kanta ta dinga gayawa Allah halin da Iffat ɗin take ciki, duk da har yanzu bata fara magana ba, amma alamomin sauƙi sunata samuwa, su da kansu likitocin suka gayawa dady ya haɗa mata dana islamic. Kamar inda saurayin Juwairiyya Abdul-Alee yayi mata alƙawarin zuwa, sai gashi da daddare, zama yayi ƙofar gidansu kan dakali kafin ya kirata yace "ya iso gashi a ƙofar gidansu" Juwairiyya jiki na rawa ta fito, harda wani karairaya, kallon gefenta dataga mutum tayi kafin tace "malam lafiya kazo ka zauna mana anan kalan ka shafa mana talauci?" Abdul-Alee ya miƙe tare da cewa "haba Juwairiyya nine da muka haɗu dake ɗazu, dama motar abokina ne, na aro dan Allah karkice nayi miki ƙaryar arziki" Tunda ya fara magana Juwairiyya ta ke kallonsa cike da raini tace "mtsw asara ance maka ni ajinka ce?, ka tambayi kaf samarin anguwarnan sunana matar manya, kul karka sake zuwa gidannan dama kaso ka yaudareni ne?" Jiki a sanyaye ya miƙe har tana tofa masa miyau, Ta shige gida fuuu kamar zata tashi sama. Cikin takunsa na nutsuwa ya ƙarasa jikin mota tare da kallon Mubashir, suna haɗa ido, Mubashir ya galla masa harara tare da cewa "wlhi kai wawa ne, ina ganin wulaƙancin da yarinyar tayi maka amma bazaka fasa zuwa gurin ta ba?" Prince Abdul yace "wlhi tallahi Allah ya jarabceni da soyayyar wannan yarinyar, amma daga yau na haƙura insha Allah bazan sake zuwa ba" "Oho wlhi kaci gaba da zuwa" Daga nan suka shiga mota suka wuce. Niko nace Allah sarki kwalli da turare ya kamo miki Prince kin koreshi. Cikin ɓacin rai taje ta ɗibi gaushi tasa magani tayi hayaƙi, kana ta ɗauki turaren malam tasa tare da tozali, ta sauya kaya ta fice, a cewarta yau za'ayita ta ƙare. Kai tsaye wata anguwar ta masu kuɗi ta nufa, tana tafiya tana sauya salon tafiya, cikin sa'a wata danƙareriyar mota tayi parking a gefenta, Juwairiyya taci gaba da tafiya, bata saurari taga waye a ciki ba, Cikin ɗaga murya mutumin yace "ƴan mata dan Allah ki tsaya" Cike da jan aji ta juyo tare da kallon motar, sbda bata hango mamallakin motar Ba, tunda a gaba take shikuma yana baya. A hankali ta dawo gurin motar, da sauri ta sake kallonsa, a shekaru zeyi 40yrs amma sai kace ba wani babba ba, fuskarsa ce zata nuna maka yawan shekarunsa, "da farko dai sunana Alhji Al'amin, ina zaune a garin Abuja, bana zama a Nigeria nafi zama a Chad, bayan munyi aure zaki iya zaɓar ƙasar da kikeson ki zauna a cikinta Ni bamai takura bane" Mamallakin motar ya faɗa yana kashe mata ido, "Masha Allah ni kuma sunana Juwairiyya" "Am ina fatan zaki amshi soyayyata dan bada wasa nakeyi miki ba, inhar kin amince nanda sati biyu zamuyi aure" Cikin jin kunya Juwairiyya tace "babu damuwa Allah ya shige mana gaba" Tana shirin wucewa, ya ciro waya ƙirar I phone 13pro max ya miƙa mata a kwalinta, mamaki ya kamata hannunta har rawa yake, tace "duk wannan nawane?" Alhji Al'amin yayi murmishi yace "inhar kika zamo matata sai kin riƙe wacce tafi wannan, wlhi har cikin zuciyata nake sonki" Har ƙasa ta durƙusa tayi masa godiya, Yace "akwai sim card a ciki idan kika kunna zakiga kirana" Tace "toh" Zuciyarta nata rayo mata abubuwa da dama. "Yanzu ina sauri zanje airport ne wlhi, ga wannan babu yawa, kuɗi ya miƙo mata bandir na dubu ɗaya guda biyu, Hankalin Juwairiyya ya tashi, ta dinga yi masa godiya, Har ya yi mata sallama ya wuce bata dena leƙen motar tasa ba, cikin sauri ta nannaɗe kuɗin a mayafi tare da wayar, ta dinga gudu har ta kawo gida. Tana shigowa taga takalmin babanta, cikin ɗaga murya take cewa "baba ka fito wlhi abin arziƙi ya samu" Baba ya fito da sauri, sbda a tsakar gida ta zube ta kasa ƙarasawa gurinsa,  yana fitowa yayi ido biyu da kuɗaɗe, sbda waya kam besan kuɗinta ba, sai ita da ta sani, bakinsa har yana rawa yace "ƴar baba waye ya baki?" "Wlhi baba ina fita na haɗu dashi, yace baya zama a Nigeria a ƙasar waje yake zama, kuma yace idan na amince nanda sati biyu zamuyi aure" Jikin baba na rawa ya tattaro kuɗin yana rungume wa, tare da cewa "kice kin amince harda  waya ya baki?" "Eh wlhi baba bakasan tsadar wayar bane shiyasa baka ɗagata ba" Baba yayi tsaki yana cewa "yanzu dai tunda hidima yanzu ya fara, mu tafi hotal (Hotel) muci abinci, wlhi ƴan dirama (Drama) suna birgeni idan naga sunacin abinci acan" "Tabbas baya ka kawo shawara amma dole kasa kayanka na sallah saboda karsu rainamu" LIBYA Kamar inda babban likitan ya faɗa yau za'a sallami Mona, yau ɗin aka sallameta, kowa danginsa na zuwa, banda ita da maƙiyinta take gani koda wane lokaci, taji sauƙi sosai sbda tana tafiya amma tana ɗan ɗingishi, shima a hankali zata dena, cewar likitan. Maƙudan kuɗaɗe Shahazad ya cika sbda ayi masa aiki Urgent. Da yamma suka dawo gida, lokacin Hajara tana barci a ɗakinta, dan batayi zaton yau zasu dawo ba. Sai da yaje ɗakin Mona ya kwantar da ita, kafin ya dawo parlo ya nufi ɗakin Hajara "Hajarrr!!!" Ya faɗa da kakkausar murya, wacce ko a mafarki ta jita sai ta firgita. Da sauri ta miƙe zaune, tare da ware idanuwanta tana cewa "ya jikin Madam?" Kallon banza ya watsa mata kafin yace "ki ɗora abinci yanzu, Zarbiyan nake da buƙata akwai time table a sama ki duba da inda ake dafawa" Zata kuma magana ya fice. A hankali ta dafe kanta, tare da cewa "gobe insha Allah zan nemi alfarmar dena aiki a wannan gidan, wlhi bazan iya ba, gara in koma gurin Inna ko dusa zamu dingaci muci" Kafin ta share hawayen da suka kwaranyo mata ta miƙe zuwa kitchen. Allah ma ya taimaketa ta iya turanci duk da ba sosai bane, amma idan ta karanta tana gane wasu abubuwan. Yau da wuri, Lulu ta tafi, dan ko ƙarfe 8:am batayi ba, sam taƙi yin brakfast a gida, sbda tace "sauri takeyi, Gidan ya rage daga jami'an tsaro da ma'aikata sai Ala-Uddin da Hassana, tunda ta gaishe shi ya sanar mata da Black tea zatayi bata sake ganinsa ba, Bayan ta tafasa shayin ta juye a cup guda biyu, da nasa da nata, already yasan cup ɗinsa, tunda yafi nata kyau, sai da ya tabbatar da ta shiga ɗakinta sannan ya fito cikin sanɗa yaje kitchen tana kallonsa ta window, magani ya jefa a nata kana ya dawo ɗakinsa da gudu, Yanayin action ɗin da yayi yasa ta zargi akwai abinda yayi, tafito kamar batasan ya shiga ba...! Insha Allah zanyi muku wani 9:30 insha Allah Yau ansha hira naji daɗi sosai *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 45-46 Tana ganin ya koma ɗaki taje ta juye nata a gurin wanke-wanke, ta kunna pampo kana ta ɗauraye cup ɗin ta juyo ragowar na Kettle ɗin kana ta fito da cup biyu nata da nashi, shima ta window yake leƙenta har yana taka rawa, burinsa tasha shikuma ya iso gareta, a kan table na parlo ta ajiye coffe ɗin, kafin ta wuce da nashi ɗakinsa. Da sallama ta shiga, ta sameshi yana sanye da ƙananun kaya, ba kamar inda Lulu ta barshi ba, tare da hannunta ya haɗo cup ɗin da take miƙa masa, kana yace "Haseeaina" Cikin sanyin murya ta amsa da "na'am" Makirin murmishi yayi, kafin yace "kin amince da buƙata ta?" Jikinta na karkarwa tace "nidai kayi haƙuri ka barni in koma garinmu dan Allah na yafe maka duk abinda kayimin" "Never!!!" Yana saurin ajiye coffe ɗin, "Wlhi bazaki koma ƙasarku ba har sai kin amince da ƙudurina, nima inaso burina ya cika akan masarautar mu" Sam ta gaza fahimtar abinda yake nufi, dole ta zube a gurin tana roƙonsa, ganin yaƙi saurararta yasata cewa "shugabata tanada zafin kishi zata iya kasheni idan ta ganmu tare" "Sai me? ƙarya ne, ni bazan bari ta gano komai ba, sosai nake samun nutsuwa dake, tun kafin a bani umarnin kusantarki, dan haka ko kinaso ko bakyaso sai na dinga sex dake koda wane lokaci" A firgice Hassana ta miƙe tare da juyawa zata fice, da sauri ya fincikota ta faɗo jikinsa, cikin sauri ta kauce tare da sunkuyar dakai, hawaye na ambaliya a fuskarta, sam ta gaza haɗa ido dashi, sbda iya idanuwansa faɗar mata da gaba yakeyi, Yayi kisa a gaya mata zai sauya mata gida wanda yafi wannan, sai ga Lulu nan, ashe tanata sallama basuji ba, ganin Hassana a durƙushe gaban Ala-Uddin Samir yasata wurga jakar kan gado, tana gyara sumar kanta da ta rufe mata ido, tare da riƙe ƙugu tace "Hub lafiya?" "Mu Lulu wai dole sai ta tafi gida, naga kina buƙatar zamanta yasa nace "babu inda zata shine taketa kuka" "Kai Haseeaina, wannan karon bakizo da niyar yin aiki ba, wancan karon ai kinkai shekara ɗaya da rabi, meyafaru kikeson zuwa gida, idan kuɗi ne baki dashi ki bani number account zansa miki" Har Lulu tayi maganganunta ta gama Hassana ta kasa magana, Sai ma miƙewa da tayi ta fice da gudu, tayi kuka sosai da ta koma ɗakinta, sbda ta kasa ɗaukar coffe ɗinma ta sha. Hajara na kammala abincin tasa a faranti mai faɗi fari na tangaras, tare da saka cokula biyu, sbda haka Shahazad ya umarceta  tun farkon zuwanta, Tana haurawa steps gabanta na tsananta faɗuwa, Batasan takamaiman ɗakin da suke ba, dole ta fara nocking na Mona, cikin sa'a, yace "Yes" "Na kawo abinci ne" Hajara ta faɗa tana jiran abinda zece mata, "Okay" Ta shigo bakinta ɗauke da sallama, karfa idanunsu ya sarƙe ana juna, Hajara tai saurin sauke idanuwanta ƙasa, ashe Shahazad yana kallonsu, Bata jira an bata umarni ba, ta fice. Shahazad yayi wani irin makirin murmishi, Jikin Hajara na karkarwa ta ƙarasa ɗakinta, itakam gida take buƙatar zuwa, amma bataga fuskar magana ba, "gashi sai ya dinga yi mata mugun kallo ko meye dalili oho?" Mona na kwance, duk irin kallon da Shahazad yake yiwa Hajara tana kallonsa,  murya wata iri tace "shin Hajar tayi maka wani abunne?" "Ehhh, tana shiga gonar da ba Tata ba" Shahazad ya faɗa cikin kakkausar murya. "Dan Allah ka sassauta mata, tabani labarin batada iyaye, shiyasa ta zaɓi tayi aiki anan" Shahazad ya shafi gashin kanta, kafin yace "ki kwantar da hankalinki ki ci abinci zamuyi magana zuwa anjima" Mona ta fashe da kuka tana shure-shure tace "nidai kayi min alƙawari zaka riƙeta cikin aminci?" A gurinsa Alƙawari ba ƙaramin abu bane mai muhimmanci, idan yayi zaiyi wuya ya saɓa, Sam yaƙi cewa komai, Taci gaba da kuka tana ihu, Tunowa da dokokin asibiti da suka sanya masa, ya sashi saurin kamota ya ɗorata jikinsa kana yace "nayi miki alƙawari inhar kema kikayi min alƙawari" Batasan Alƙawarin meye yakeda buƙata ba, cikin sauri tace "nayi maka" Yana shafa gashin jikinta tare da mammatsa mata hannaye yace "Yakamata kisan ni masoyinki ne, inada burin baki farinciki sama da Ni kaina Amma kin kasa fahimtata" Sosai tayiwa Allah godiyar wannan tambayar da yayi mata, dan ta samu damar tuhumarta iyayenta. "Ka kawomin iyayena in gansu, nayi maka alƙawarin zan zauna dakai" Shahazad yai saurin ture ƙafafunta, kana yace "me kikeso ince miki?" "Dama kinsan zaki jawomin tashin hankali, su suka bani auranki, mahaifinki ne ya damƙamin ke a matsayin mata, nikuma na karɓa" Da sauri ta tare bakinta, a fili tace "ka kashesu" A nitse kamar ba kuka takeyi ba, yace "suna raye" "Yaushe zaka haɗani dasu" "Ranar Litinin saura kwana uku tunda yau muna Asabar" Sosai farinciki ya kamata, shiko a halin yanzu yana jin babu daɗi a zuciyarsa. Da sauri ya miƙe ya koma wani ɗaki can nesa da nata ya ɗaga wayar tafi da gidanka, wanda ya kira yana ɗagawa yace "kasan iyayen Mona?" "Eh na sansu sun jima da mutuwa" "Eh nasan da haka, inaso a samomin mutane biyu wanda suke da murya irin tasu, ka gaya musu ko nawa sukeda buƙata zan biya" Wanda ya kira yace "to angama me gida" Mona kuwa tanata farincikin zatayi magana da iyayenta. NIGERIA Yau kwanan Huda ɗaya a gidan Abba, bayan sun kammala cin abincin safe ta tattara kwanuka takai kitchen ta wanke, tana zama Inaya ta taho da gudu tana cewa "anty Huda wai kizo ki yiwa momy wanke-wanke" Amani ta taɓe baki, kana tace "zauna ki huta, ai ba ke aka kawowa ita ba" Huda tace "ai ba hutu nazoyi ba aiki aka ɗaukeni" Karaf a kunnen Mahabob, ya kamo hannunta ya zauna akan kujera ita ta zauna a ƙasa kan carpet kafin yace "ke ba ƴar aiki bace, dole a tausaya miki, shima Abban ba a ƴar aiki ya ɗaukoki ba, dan haka ki kwantar da hankalinki" Sam ta kasa kwantar da hankalin kamar inda suka faɗa, dan gani take kamar zata iya fuskantar hukunci a gurin momyn nasu, Yana fita Amani itama ta shige ciki, Huda ta fice da sauri. Lokacin Abba ya fita, Batool na ganinta tace "wato har kin fara samun gurin da zaki miƙe ƙafa a kirawoki kiyi burus kamar ba ke aka kirawo ba" Cikin tausasa murya, Huda tace "kiyi haƙuri Hajiya, na tsaya wanke nasu anty Amani ne" "Aikinsu yafi nawa kike nufi?" Kan Huda a ƙasa sam ta kasa ɗagowa, saboda cikowa da hawaye da sukayi, Kicin ta wuce, kasancewar Batool ɗin ta nuna mata tana ci gaba da masifa. Cikin sauri ta wanke kwanukan tunda ba yawa ne dasu ba, ta fito tasa hijabi ta koma part ɗinsu Amani, Batool ta bita da mugun kallo, Tana zuwa ta samu Aseela a zaune ta share hawaye, kana tace "ina anty Amani?" Aseela ta ƙwalawa Amani kira, Sai gata ta fito tana gyara dogon wandonta. "Ehee fita kikayi, sannan naga kamar kuka ma kikayi keda waye?" Sam huda bataso sanar musu da komai ba, amma ta kasa daurewa sai da ta gaya musu abinda Batool ta faɗa mata, Aseela tace "Anty Amani kira Abba kice matarsa tayiwa Huda duka"....! Kunsanni da barci da wuri😫 wato yau comments ɗin da nagani, wlhi naji daɗi sosai sbda kuna ƙaramin ƙarin guwaiwa sosai. Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 47-48 Sa'arsu ɗaya wayar Abban yaƙi shiga, dole suka haƙura. Bayan Tasneem da Ummi sun gama haɗa girki, tasa taliyar bayan ruwan ya tafasa, kana ta kalli agogo  1:pm, sukayi sallah sbda gudun katsewar labarin, lokacin da suka idar abincin ya dahu, babu maganar ci, aka juyeshi a kula, kana Ummi tace "Tasneem nikam ina jiran ci gaban labari" Murmishi Tasneem tayi, kafin taci gaba.. "Duk da na koma gidan Hajiya, Haseem bai dena bibiyata ba" Zuwansa biyu, Hajiya ta tareni tana tambayata meyasa nake kulashi tunda ba shi zan aura ba, sam na kasa gaya mata komai, sbda bata sanshi ba, bata ma san yanada dangantaka da Uncle ba, da ta matsamin nace, Hajiya sbda nace bana sonsa shine anty Karima ta fara tsangwamata shine Uncle ya dawo dani gidanki" "Ana auran dole ne yanzu?, har guda nawa kike da zasu aurar dake, nifa har yanzu hankalina bai kwanta da auranan da za'ayi miki ba, shiɗin yaron waye?" Hajiya ta tambayeni cikin fushi. "Yaron ƙanwar anty Karima ne, ya daɗe a gurinta dan haka take kiranshi yaronta kuma ɗan uwanta, dalilin da Uncle yace in dena kulashi, yana shaye-shaye" "Innalilahi wa inna ilaihir raji'un, wato ke kuma taƙi ƙaddarar kenan, shi wanda ya turo iyayensa me sunansa?" Kaina a ƙasa nace "Zahradden" "To Allah yasa idan anyi auran ya riƙeki tsakani da Allah" Nidai bance komai ba, na tashi na tattara kwanukan da nazo na samu, wanda hajiyar bata wanke ba, tass na wankesu na kife, na dawo ɗaki, Zuwa yamma, wayar Hajiya tayi ring, ina daga tsakar gida, naji Hajiya ta ƙwalamin kira, da sauri na shigo ɗakin na sameta ina cewa "Hajiya gani" Ta miƙo min wayar, tana cemin "Uncle ɗinki ne ya kira" Ƙara wayar nayi a kunne kana nace "Uncle ina yini" "Lafiya Tasneem ki shirya Zahradden zai zo yau Please ki nutsu karkiyi masa shirme" "To" nace cikin jin kunya. Sai da akayi sallahar magriba nayi, sannan na shiga wanka, ina fitowa na goge jikina da towel, na ɗauki mai na shafa, dama kwalliya bawai ta dameni bane, sai dai powder da na shafa, kana na buɗe akwatin kayana na ciro doguwar riga ta material, sai da na fesheta da turare, sannan nasa, kana na kalli kaina a mudubi,  na ɗauki hijabi nayi sallahar isha'i kasancewar ana kiran sallahar, na zauna adu'a dama tunda nayi wanka nayi alwalar sallar isha'i. Inajin ring ɗin wayar Hajiya gabana ya bada rass, sbda nikam ban taɓa hira da saurayi ba, wannan shine karon farko, "Tasneem zoki karɓi waya" Na fito da sauri, "Yazo ki fito" Bakina yayi nauyi, a zuciyata kuwa cewa nake "lallai ma ya raina Uncle shine ɗan aikensa" Cikin sauri na dawo ɗaki na ɗauki hijab wanda ya tsaya min iya guwaiwa fari nasa, kana na fita jikina na kyarma sbda fargabar inda zan sameshi. A hankali nake tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa, har na iso gurin da Hajiya tasa a ajiye fararen kujeru banga kowa ba, cikin sanyin murya naji ance "ji inda kike zaro ido kamar matsoraciya" Da sauri na waiga idanuwanmu suka sarƙe dana juna, Kunyarsa ta lulluɓeni, bansan lokacin dana durƙusa har ƙasa nace "ina wuni ba" "Lafiya" ya amsa yana dariya, "Wow na samu yarinya  har da durƙusamin" Da sauri na ɗago, tare da sanya tafin hannuna na rufe fuskata, Kafin ya sake wata magana nace "dan Allah kayi haƙuri zan koma gida cikina na ciwo" Lura da yayi na riƙe cikin ina yamutsa fuska yasashi, cewa "tom sai gobe, ga wannan zamudinga waya" Da sauri nace "a'a" Harna fara tafiya, naji yace "sai na gayawa Uncle" A zuciyata nace "yasan sunan da nake gayawa Uncle ɗin kenan?" Dole na karbi wayar, yacemin "harda sim card a ciki" nayi masa godiya na wuce. Ina shiga na miƙawa Hajiya wayar, na wuce toilet na dinga kashi, ƙarshe gudawa ne ya biyo baya, duk na tsure saboda tsoro, banyi zaton haka hirar take ba, Ina fitowa, na zube a gaban Hajiya. Kafin nayi magana, tacemin "masha Allah wayar tayi kyau" Wlhi na ɗauka zata yimin faɗa ne, Hajiya tayi-tayi dani inci abinci na kasa, na shige ɗakin da nake da wayar, na buɗe kwalin, infinix ce hot 10, ina kunnata kira na shigowa, Ikon Allah har yayi saving sunansa wai My life, Haka rayuwa ta dinga tafiya, koda yaushe muna waya, amma bana son inji yace zezo, shima da ya gane nafi sakewa a waya bai cika zuwa ba, Kwanci tashi asarar mai rai har bikinmu ya rage saura kwana biyar, zuwansa huɗu, duka bana wani sakewa dashi, an sanarwa dangi na kusa dana nesa, tunda bikin ya rage kwana uku, mutane suka fara zuwa,  irin gyaranan na fata da ake yiwa amare nikam babu wanda yayi min, ko meye dalili oho, amma fa naga gata sosai, ta fannin dangin mahaifina da mahaifiyata kuɗi da kaya har sai da aka nemi wani ɗakin, Uncle yayi ƙoƙari shima, ta fannin furnitures daga ƙasar waje aka kawosu, Ana biki saura kwana biyu, yayan Abbana yasa aka yankamin zabi manya aka soyesu akayi min miya, ranar da aka samin lalle nayi kuka sosai, sbda tunowa da mahaifiyata da nayi, duk da an nunamin gata amma wlh nayi kukan rashinta, ana gobe biki, Uncle ya kawomin ɗinkuna kala goma sha biyar, duk ciki babu na ƙaramin kuɗi, dama Ni ba ƙawaye ne dani ba, haka akayi taro ina ɗaki, anyita soya cincin da nakiya da dubulan, ranar da aka ɗaura aure, sabuwar gudawa ta dawo min, gani nakeyi  kamar a mafarki, ban gama tabbatarwa gaske bane sai da naji ance wai motocin tafiya da amarya sunzo" Lokacin anata yimin nasiha inata kuka, Hajiya ta riƙe hannuna muka shiga mota nida ita, Motarmu ce ta fara tafiya kafin ta sauran iyaye ta biyo baya. Gaskiya dangane da kyan gidan babu abinda zance, sbda ko gidan Abbana da ake labarin haɗuwarsa bekai na Zahradden ba, an narka nera, anan muka wuni da mutane, tunda gidan ya cika naji daɗi gani nake kamar baza'a watse ba, kasancewar lokacin ƙarfe 3:pm ne, sai da suka jira akayi la'asar sannan kowa ya fara haramar tafiya ciki harda Hajiya, har Hajiya tayimin sallama tayi gaba, ta dawo da baya tana cewa "kiyi haƙuri Tasneem antynki Karima batazo ba, bansan meye nufin ta ba" Duk da nasan ni take kwantarwa da hankali, nima nace "Hajiya yanzu haka tanayin nata taron ne acan" Sannan naga fuskar hajiyan taɗan sake, da kuka muka rabu, ashe haka aure yake. Zuwa dare, lokacin inata rama salolin da ake bina Zahradden ya shigo, na gaishe shi, kasancewar nayi sallama kuma na shafa adu'ar, amsa wa yayi cike da fara'a kafin ya kamo hannuna muka dawo parlo ya buɗe ledar dake ɗauke da gasassun kaji har uku da fresh milk kana ya cemin "bismillah" Shi ya dinga bani, duk da banci da yawa ba, nace barci nakeji, Sam yaƙi yarda, sai da yasa nayo alwalah dukkanmu mukayi sallah raka'a biyu, yayimin adu'a bayan ya dafa kaina, kana yazo fannin karɓar hakkinsa, Duk da nayi kuka sosai, amma ban wani yi masa gardama ba, sbda gargaɗin da Hajiya ta dingayi min. Tunda nayi wanka na dawo na kwanta, da asbha ya fice, aiki bayan ya dawo daga masallaci, lokacin da gari yayi haske wlhi na rasa nutsuwata, sam na kasa ban-bance halin da nake ciki, wani azababben ciwon kai ya ziyarceni, Nidai kawai naga Zahradden ya dawo, na cukumeshi ina cewa ka sakeni...! Please and Please nasan yayi kaɗan kuyi manage dan Allah idan na samu time zuwa dare zanyi muku wani. Mom Islam https://arewabooks.com/chapter?id=648b370d0b7269564606cc70 *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 49-50 Sam nakasa gane abinda yasa nakeyi masa rashin mutunci, washe gari, ya riko hannuna ya dawo dani gidan Hajiya, lokacin da muka shiga ɗakin Hajiya naji tana cewa "dama Uncle ɗinta yace yau zaku zo, da naji shiru wlhi har na fara tunanin ko ta gudu ne?" Zahradden ya fashe da matsanancin kuka ina kallonsa, Hajiya ta fara rarrashinsa tana ce masa "magani za ayi min idan na warke zan dawo ɗakina" Cikin kukan yake cewa "dan Allah karku rabani da matata wlhi ina sonta" Duk wani kalami da zai kwantar masa da hankali tayi amma ya kasa fahimtarta, dole Hajiya ta kirawo Uncle shima yazo ya dinga yiwa Zahradden nasiha, nidai naga Zahradden ɗin yayi waje, idanunsa shaɓe-shaɓe da hawaye, tun daga ranar naji soyayyarsa ta ficemin arai, idan yazo guduwa nake, idan naji muryarsa toshe kunne nakeyi. Na koma shiru-shiru bana fita ko'ina, hatta aiki Hajiya ta Dena bani, sbda na koma marar kunya tashi d'aya, Allah sarki duk da ciwon daya riskeni da rashin kunyar  da nakeyi musu da rashin magana, basu taɓa tsangwamata ko zagi ba, koda yaushe mutum biyu suna hanyar nema min magani, Ashe dukkansu biyu Uncle da Hajiya sun san inada ciki, kwanci tashi ina wannan hali cikina yakai wata bakwai, ciwo yanata gaba, lokacin cikina ya fito, Hajiya zata riƙemin hannu muje asibiti awo ko scanning, lokacin da cikina yakai wata tara da kwana tara, wlhi bansan inda kaina yake ba, washe gari nadai ganni a kwance riƙe da yarinya Hajiya ta sanya mata nono a baki, ina yawan ji ana cewa bada nono ga jariri akwai zafi, nikam banji ba, wlhi bansan ciwon komai ba, ranar suna yarinyar aka sanya mata Iffat. Ranar da Hajiya tace "idan mukayi arba'in, zamu koma gidan magani" Aiko ana i gobe zamu koma, naji kamar ana kiran sunana a waje, riƙe da Iffat na tashi, tun daga ranar bansan inda nake ba, sai yau.. Ummi ta dafa kafaɗar Tasneem kana tace "ki kwantar da hankalinki, idan zaki gane gida insha Allah zamu kaiki gidanku" Tasneem tace "nan wane gari ne?" Ummi tace "nan Kaduna ne" Tasneem ta zaro ido cike da mamaki amma ba tace komai ba. A ranar da yamma 4:pm Aliyu yazo gidan Ummi, sai da yabi kowane ɗaki ya gaishe su kafin ya dawo ɗakin Ummi, cike da murna Ummi tace "oyoyo ɗan albarka ga baƙuwarka ta warke" Aliyu yace "masha Allah godiya ta tabbata ga Allah tunda har akayi nasara, baiwar Allah sannu" Tasneem tace "Nagode Allah ya saka da alkairi Ummi ki tayani yi masa godiya" Kasancewar Ummi ta sanar mata da taimakon da Aliyun yayi mata. "Ummi malam yayi nisa ne?" "A'a yaje gaishe da abokinsa Hudu ne a can katsina road, na mance ban tambayeka Hadiya ba?" "Ummi tace in gaishi ki, gobe insha Allah tana nan zuwa" Cike da jin daɗi Ummin tace "Allah ya kaimu". Bayan an dawo da Hakeem gida, yana shigowa ya fashe da kuka, Hajiya babba ta dangware masa kai, tare da cewa "wlhi Hakeem dama inaso inyi maka magana tare da gargaɗi na ƙarshe, muddin kace bazaka fita a harkar waccar matacciyar yarinyar ba, wlhi sai nayi maganinka, har yaushe kayi girman dazan gaya maka kaƙi jin maganata, ko kana so kai da mahaifinka ku kasheni ne?" Cikin tausayawa Hajiya yace "Hajiya wlhi bazan sake ba, amma Eshat tana bani tausayi sosai" "Kai dalla can, wlhi idan da kasan asalin yarinyar nan, ko ance ka bibiyiyeta wlhi bazaka kulata ba" "Hajiya kinada labarin iyayenta ne?" "Eh mana tsintacciya ce a bola, anyi cikin shege ne aka yarda ita, shiyasa ka tsintota babu wanda yace ƴarsa ce, inaso ka cireta a cikin rayuwarka ka mance da ita, mahaifinka yana son haɗa matsayinku a guri ɗaya" Cikin sauri Hakeem yace "Hajiya kenan ƙazama ce na dena kulata wlhi" Tsabar murna da hajiyar ke ciki, ta janyosa ta rungume tana sanya masa albarka. ALGERIA Abin farinciki abin jin daɗi Iffat a zaune a ƙafar Hajiya ƙarama, Dady ya shigo, fuskarsa ɗauke da fara'a, naji yace "Hajiya gobe ne za'ayi sallamar nan, ya kamata in samu in cika musu kuɗinsu, Alhmdulilah" Cike da jin daɗi Hajiya ƙarama tace "wlhi na ɗauka zamuyi wata a asibitin nan sai naga kwananmu biyar, har an kammala komai, ragowar magungunan Islamic ɗin duk ta shanye" Dady yace "Eshat zo" Ta sauko daga jikin Hajiya ƙarama ta je gurin dady tana murmishi, Washe gari ya cika kuɗin asibitin aka sallamesu suka dawo gida. Kwanan Iffat shida da fitowa, suka tafi shopping, Iffat tayi kyau sosai, sbda duk kayan da Dady ya gani siyo Mata yakeyi komai tsadarsa, koda yaushe yanayi Mata kallon Eshat ɗinsa ne, suna zuwa ShopRite  dady ya haɗu da abokansa turawa, sai ɗaukar Iffat sukeyi suna cewa yarinyar tanada kyau, dady yana yi musu godiya, sbda Iffat yarinyace Mai shiga ran Wanda ya raɓu da ita. LIBYA Sosai Mona taji sauƙin jikinta, duk wani motsi nata yana tafin hannun Shahazad, Washe gari ta kama monday da misalin ƙarfe 5:am Shahazad ya fito cikin shirinsa na fita aiki, bata saba ganin ya fito cikin wannan lokacin ba, tana cikin barci, taji kamar a mafarki an turo ƙofarta, Firgit ta farka tare da miƙewa zaune, kallonsa kawai take ba tare da tace dashi komai ba, tako cikin isa tare da zama kan bed ya miƙo wuya kamar me neman wani abu, hannu ya tura cikin aljihun  suit  ɗinsa ya ciro biro kana ya buɗe tafin hannunta ya rubuta mata, idan har kika kwashe sirrin komai nawa kika bawa mutane sai na kasheki" Da sauri ta fara ja da baya, alamar tsoro, Yana wata makirar dariya yace "ai ban kashekin ba, gargaɗi dai nayi miki akan ki riƙe bakinki" Yana faɗar haka ya gyara gashin bakinsa, yayi Mata kiss a goshi ya fice, Da sauri ya ke sauka daga kan steps yana waya, har hajara ta fito, tana  hangoshi ta koma da gudu, Cikin wayartasa ne yake cewa "banason wasa, hannu na da naka gobe zamu shiga India, jirgin safe zanbi, ku zamo cikin shiri, duk Wanda yayi gardama ku harbeshi" Kafin yace "Hajarr.." Da sauri ta fito daga d'akinta tare da zubewa a ƙasa tace "Barka da fitowa me gida" "Yauwa ki kulamin da matata kar in ji mummunan labari a kanta idan har naji hakan' hhhh, ki ƙaddara kin mutu" Jikin Hajara na rawa tace "hakan ma bazata faru ba da yardar Ubangiji" Har yayi gaba, ya juyo yace "nasa 1 million a account ɗin da sisternki ta bani lokacin da kukazo" Hajara tace "godiya nake Allah ya saka da alkairi" "Amin yace kana yayi gaba" Jikin Mona a sanyaye ta miƙe tsaye, dan ita ba sallah takeyi ba, amman shi Shahazad yanayi shima ɗin dai sai a hankali, Cikin sauri ta sauko ta nufi ɗakin Hajara, ta samu tana sallah, Bayan Hajara ta idar da sallahar tace "Barka da safiya Madam" Barka "Hajar inason in baki labarina Please ki taimakeni, ina ganin kamar kece zaki iya miƙani ga iyayena" Gaban Hajara ya bada rass tare da tsoro, tace "idan inada halin hakan zan taimaka miki, amma karki manta muna cikin hatsari ni dake" Mona tace "karki damu Bama cikin hatsari, amma kin iya aiki da computer?" Mona ta tambayi Hajara. "Gaskiya ban taɓa amfani da ita ba, amma ina ganin abubuwa in karanta" "Akwai wata wacce Shahazad ya siyamin, sbda harkar kasuwancinsa da yakeso in temaka masa, nikuma bani da ra'ayin hakan" "Uhm nifa tsoro nakeji dan Allah karki ɗauko" Hajara ta faɗa tana runtse idanu. Cikin rashin tsoro Mona ta miƙe, tare da,  ficewa da gudu. Computer ta ɗauko ta fito hankalinta kwance, bazaka gane tsoro ya gushe a zuciyarta ba, har sai kunga inda ta zauna a parlo tana sarrafa computer hankali kwance, "Hajarr" Mona ta ƙwala mata kira. Cikin rawar ɗari ta fito, kamar me jin sanyi, ta zauna daga nesa. Kai tsaye Mona ta shiga searching ta rubuta Shahazad forest, Da sauri Hajara ta matso kusa da Mona tana cewa "mijinki yanada wani gari ne mallakinsa Kuma me sunansa?" "Eh yanada anan muke rayuwa" Gaban Hajara ya sake faɗuwa, ta fara jajantawa kanta mutuwarta, sbda har ta hango inda Shahazad zai kashesu babu tausayi, "Hajar kalla ki gani ga wani video" A tsorace Hajara ta sake matsowa, videon kashe-kashen da akeyi a yankin ta gani, tare da mutanen ƙauyen da suketa guduwa, gudun ceton rai. "Inaso inje jejin nan domin inga iyayena dangina da sauran ƙawaye na, zamana a ƙauye nan yafi min zaman ƙuncin da nakeyi a wannan gidan" Hajara tace "tabbas garinku-garinku ne, amma ni sai nake gani kamar zaman gidannan yafi karɓarki" Hajara tayi maganar domin kaucewa Maganar Mona. Gaskiya "Hajar kin yi kuskure sbda wannan gidan da kike gani kamar lahira yake, ina tsoron Shahazad, haka kawai yake zuwa ya kashe mutane ba tare da sunyi masa komai ba, shiɗin mugu ne" Hajara dai, idan ta tuno da gargaɗin Shahazad gareta sai cikinta yayi ƙugi, tsabar tsoro. Daga ƙarshe Hajara ta zame ta durƙusa gaban Mona kafin tace "dan Allah kiyi haƙuri ki gafarceni ki mayar da wannan abun, saboda wlhi tallahi zai iya haɗawa dake ya kashemu, ina ganinsa kamar me wankin idanu" Mona ta rufe computer tare da murmishi tace "komi daran, daɗewa wlhi sai na koma garinmu" Hajara tace "wlhi ni zaki shafawa dan bazai taɓa amincewa da abinda zance masa ba, nima kasheni zeyi, ki gafarceni" Mona ta miƙe tare da hayewa steps tana sheƙewa da dariya. Tunda Hassana ta koma ɗakinta tunanin Ala-Uddin Samir ya addabi rayuwarta, duk zuwanta gidansa da takeyi bata taɓa tsammanin haka yake ba, Acan ɓangarensa yanason Lulu tayi barci yaje ya dubo Hassana ya gani, shin maganin ya fara aiki. Sai shafata yakeyi yana cewa "my Lulu ya kamata ki kwanta ki huta, bakya samun enough time da zaki dinga barci da rana" "Hub idan ina tare dakai sam barci ƙauracemin yakeyi sbda tunaninka, amma yaushe ne zamu je masarautar ku" Ta faɗi maganar tana kashe masa idanu, "Ya kamata muje a cikin watannan sbda wasu shirye-shirye da nakeson gabatarwa a gidan, duk da bani da uwa uba duk sun mutu nine zan zamo mahaifin kaina, inaso in kawar da Nara a doron ƙasa, inaso Raza ya zamo maƙasƙanci a ƙarƙashina, inaso in tura ahalinsu wata duniyar, a halin yanzu na gama zana irin kujerar da zan sauya zanen taswirarta bayan nahau, ko bakyaso a kiraki da Princess Lulu?" Cikin farinciki tace "tabbas Nima na gano wani haske a tafiyar, sai dai kasan mutanen garinnan matsafa ne, meyasa bazamu shirya ba kafin muje" Ala-Uddin ya bubuga kafaɗarta a hankali, kafin yace "kamar kin mance waye Ala-Uddin Samir?" Ta tallafo haɓarsa  tare da sanya harshenta a cikin bakinsa, ta fara karkaɗawa... Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 51-52 Sun daɗe cikin wanan yanayin. Duk da haka zuciyarsa bata tare da ita, gangar jikinsa ne a tare da ita, hankalinsa ya tattara ga Hassana, itace burinsa da buƙatarsa, har waswasi yakeyi anya boka Namraj bai sanya masa soyayyar Haseeaina a zuciyarsa ba. Kamo joyst ɗinsa da tayi tana mulmulawa ne yasa ya firgit, lokaci ɗaya yanayinsa ya sauya, sha'awar da yake yiwa Hajara ta rikiɗe i zuwa gurin Lulu, Ganin ya zuba mata narkakkun idanuwansa, ya sanyata rungumeshi murya ƙasa-ƙasa tace "my Hub meyasa bakason saukemin haƙƙina alhalin kasan l love sexy Hub musamman da ƙirar jikinka take gwada jarumtarka" "Uhm Lulu nima inaso, sai dai some times tunanin kujerar da zan hau, take janyowa inji bana marmarin wata mace a kusa dani" "Haba my hub yakamata ka nutsu ka San Lulu zata taimakeka, kadena sanya damuwar da ta zamo ƙarshe a tarihin rayuwarmu, zanyi komai dominka, amma yanzu lokacin Hub da Lulu ne" Baya da zaɓi daya wuce ya biye mata, tunda bai samu ta ɓangaren Hassana ba, Da kanta ta cire masa komai tana wani shafeshi kamar mage, ko wane sashi na jikinsa da lungu lashewa takeyi, cikin salo na jan hankali, Acan ɓangaren Hassana, ta kammala haɗa kayanta a jaka, burinta taji muryarsu a parlo ta tambaye su zata koma gida mahaifiyarta babu lafiya, tayi kuka har ta gaji, idanunta sun kumbura, wannan zuwan bata zo a sa'a ba, ko tun da ɗin ma dai batasan yana amfani da ita bane oho?. Daga ƙarshe ta fito parlo ta zauna sanye da hijabi, da jakar kayanta a gabanta, takai kusan awa a zaune, sai da ƙarfe 1:20pm tayi, sannan suka fito rungume da juna, "Hassienna akwai matsala ne, na ganki da jakar kaya a gabanki?" "Babu inda zaki ai ba haka mukayi dake ba" Ala-Uddin ya faɗa yana juyar da kansa gefe. Cikin tausasa murya ta sauko kan carpet ta durƙusa kafin tace "dan Allah, kuyi haƙuri ku barni in tafi mahaifiyata babu lafiya" "Mahaifiyarki zata samu lafiya nawa kike da buƙata a tura mata?" Lulu ta tambayi Hassana cikin tausayawa. Dai-dai lokacin da zata buɗe bakinta tayi magana, hawaye suka zubo a tare tace "ina buƙatar ganinta dan Allah kuyimin rai" Lulu ta ciro wayarta a aljihu kana tace samin number, Sai da tayi jimm bata motsa ba, Ala-Uddin Samir yace "muna jiranki" Jikin Hassana na karkarwa tace "ba sai kun kirata ba, duk da kunajin Hausa  amma ita bataji" "Okay okay shi kenan ai ke kinajin Yaren da takeji ungo saka number ki kirata muyi magana" Bata da zaɓin daya wuce ta kirawo Inna, cikin rashin sa'a koda aka gwada number bata tafiya, Ala-Uddin Samir yace "bazakije ko ina ba, ance miki zuwa Nigeria kamar zuwa nan da cikin garinan ne?" Da sauri ta ɗauki jakar kayanta ta koma tana kuka, "Da girmanta amma bata da ikon yin komai, mtsw" Bayan tafiyarta, Lulu tace "Hub na rasa abinda ke damun Haseeaina" "Mance da maganar sakarci ne kawai" Washe gari, bayan sunyi brakfast, cikin sauri Lulu suka shirya fita, Ala-Uddin Samir zai ajiyeta a makaranta daga nan ya wuce gurin aiki, Hakan yasa Hassana ta samu damar sake fito da jakar kayanta ta fito da gudu, kamar haɗin baki duka masu tsaron gidan basa nan. Da gudu ta fice, anguwar shiru babu mutane, hakan yasa ta dinga gudu kamar bazata tsaya ba. Cikin sa'a wata mota ta fito tana tafiya a hankali, ganin Hassana yasa mai motar tsayawa yace "can I help you?" "Eh taimakeni dan Allah" Cikin sauri ya bud'e Mata ta shiga. Ya figi motar da uban gudu, Suna cikin tafiya tace "gidan Shahazad zaka kaini" Matuƙin motar ya jinjina kai kafin yace "no problem" Abin mamaki, a wani katafaren gida ya tsaya, tare da danna horn sai gashi an wangale get d'in, da masifar gudu ya ƙarasa shiga ciki. Cikin rashin fahimta Hassana tace "ina ne nan ka kawoni" "Your guest house welcome" Cikin sauri tace "me kake nufi, ka kawoni a kasheni ne?" Bai sake cewa komai ba, sai wata ƙofa daya nuna mata da hannu kafin ya juya ya shiga mota. Tana shirin sake cewa wani abu ya figi motar da gudu yabar gidan. Sam ta kasa sakewa da inda take tsaye, takai mintina a tsayen, wani saurayi yaji hausa yace "Oga yana magana" Ya miƙa mata wayar, A tsorace ta karɓa kana tace "waye?" "Hassienna" Cikin sauri tare da in-ina tace "mai...gi...gida...me.." "Ba sai kinyi doguwar magana ba, nine Ala-Uddin Samir, nan gidana ne, a yau kika samu ƴanci wanda yafi na Lulu, zanso ki saki jikinki, muyi harkarmu tare bake babu talauci" Rai a ɓace ba tare da jin tsoro ba tace "amma wlhi ka cuceni ka gama dani, dan Allah kasa a kasheni ka huta" Ala-Uddin yayi murmishi kamar tana ganinsa, kafin yace "ki ƙarasa ciki, kin shiga kenan" Ya katse kiran. Jiki babu ƙwari ta juya ta kalli wanda ya kawo mata wayar, kana tace "ina ne cikin gidan?" Ga ba ya shige, tana binsa a baya har suka isa, cikin gidan. Kawai zan iya ce muku gidan ya haɗu, ba ƙaramin kuɗi ya kashewa gidan ba, sbda muhimmancin masu zaman gidan. Sai da ya nuna mata ko ina sannan ya miƙa mata keys na gurin da kuɗaɗe suke ya fice. Takasa cewa saurayin komai, duk da tanayi masa kallon kamar mai sauƙin kai. Abin mamaki, gabaki ɗaya wayarta babu network ya ɗauke. Tunda Mona ta koma ɗakinta, mai makon ta ajiye computer kamar inda Hajara ta gaya mata, sai ta sake buɗewa tana searching manya-manyan ƴan ta'addan ƙasar Libya. Farko Shahazad ta gani a farko, sannan Ala-Uddin Samir, sai Karan Khan, su Uku a jerin wanda akayi cancel da jan biro. Hoton wani saurayi ta gani a gefe Mai suna Karan, kyakkyawan matashi mai ji da ƙarfi, da sauri ta bibiyi profile ɗinsa, kana ta shiga gurin chart tayi masa magana, da farko ta rubuta please I need your help don't forget to call me kana ta rubuta masa numberta, ta ajiye ta fita tare da kashe computer. Kafin ta zauna tana ci gaba da tsarawa zuciyarta da rayuwarta mafita, Hajara na zaune a parlo har yanzu ta kasa motsawa nan da can, ring ɗin wayar tafi da gidanka yasata saurin miƙewa ta ɗaga, "gobe ku shirya kuzo gurin bikin ƙanwata anan Ghat, nayiwa driver magana, sannan nasa a shirya komai, ki kularmin da Mona, na damƙa amanar Mona a hannunki, tabbas idan wani abu ya sameta sai na sheƙe ki.... Kuyi haƙuri wlhi ciwon kai tun jiya nake fama dashi Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 53-54 Bayan ta ajiye  ta haura sama tayiwa Mona nocking, bayan ta buɗe ta gaya mata saƙon da Shahazad ya sanar mata. Daga haka ta juya ba tare da Mona  tace komai ba. Kai tsaye computer ta ƙara janyowa kana ta kuma serching sunan Kharan, duk da shi wancan wanda aka haɗa hotonsu sunsa karan Khan, shikuma wannan karan sunansa, Cikin sa'a taga yasa mata, "a ina zamu haɗu insha Allah zan taimaka miki" Cikin sauri ta fara typing tace "gobe zamuje Ghat nida auntyna Please ka kawar dani daga gidan Shahazad, mugu ne" Da sauri ya turo mata, "idan da wannan number kikeyin whatsapp ki yimin magana, karki sake magana a system" Nan da nan tasa number tayi saving sai gashi ta ganshi a online. "Me ya kaiki gidan Shahazad?" Bata da amsar da ta wuce tace "ƙaddara" hakan ko ta rubuta masa. Yayi mata voice da cewar "a halin yanzu Shahazad ya fita a garin Libya jirginsu ya sauka a Bangkok, inaso kiyi taka tsantsan wajen kare kanki  da duk wata hanya da zatasa ya gano inda kike" "Eh zanyi ƙoƙari amma a ina zamu haɗu?" "Bani adreshin gidan bikin zanzo da kaina ba tare da kowa ya sani ba" "Mona tasa masa emoji na murmishi tare da yi masa godiya, ta tura masa bayanan komai akan anguwar da zasuje" Hajara nacan kitchen tana ɗora abinci, ga mamakinta sai taga Mona ta fito yau fuskarta wasai da farinciki, tace "Hajarr yau inason cin Kaji kabsa da Zabibi" Cike da kulawa Hajara tace "Madam yau kina cikin farinciki kodai oga yana hanya ne?" Hajara ta faɗa da alamar zolaya. "Haba Hajar, dan zai dawo yau kawai sai inyita farinciki nikam haka kawai nakejin shauƙi" Hajara ta cigaba da haɗa abubuwan da zata buƙata, ita kuma Mona ta koma ɗakinta tare da lodar kaya masu yawa.                   ********* Duk da kyawun gidan, bai hana Hassana jin tsanar gidan a ranta ba, sam gidan ya isheta, Abin takaici network ɗin wayarta bayayi, meke shirin faruwa da ita?,  gashi ɗazu yaron da Ala-Uddin ya kira, kiran ya shigo wayarsa amma ita kira baya tafiya, cikin fushi ta miƙe tsaye tana zagaye ɗakin, a ƙasan zuciyarta tana nadamar zuwa Libya aiki             Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 55-56 Washe gari da wuri suka shirya domin halartar taron bikin sistern Shahazad, sai da Mona ta tabbatar da ta gama shiryawa barin garin. Abin mamaki wanda Hajara ta daɗe bai wuce mata ba shine, fitowar da Mona tayi ko jinkiri babu, a parlo ta zauna tana jiran Hajara, har Hajara tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga irin ta larabawa ta fito rataye da jaka a kafaɗarta, Mona batace mata komai ba, duk da hankalinta ya raja'a akan waya, "Madam tun ɗazu shugaba ya kira yana tambayar mun tafi?" Zuciyar Mona wasai tace "mun gama komai ni dama ke nake jira, sai kaya da zan sauya" Hajara tayi murmishi sbda Sam ta kasa gane inda Mona ta dosa. Sanye da riga da wando Mona ta fito tare da  ɗaura siririn mayafi a kanta kana suka wuce gurin mota,  driver na ganinsu ya buɗe suka shiga, kana ya rufe, motoci biyi na biye dasu. Har sukayi nisa Mona  bata ɗago kai ta kalli titi ba, har sai da taji alamun mota ta daina tafiya sannan ta ɗago kai ta kalli Hajara, Hajara ko hankalinta na gurin masu wasa da ta hango a filin gurin. Driver ya buɗe musu mota tare da ɗaukar kayan Mona da jakar Hajara aka shigar ciki, tashi ɗaya hankulan mutanen gurin sukayo kan su Mona, dama bawai ta taɓa zuwa gidan bane, sbda Bama kowa ta sani ba, tunda wannan shine karo  na farko daya barta ta shiga cikin taron mutane. Suna tsaye wata budurwa tazo gurinsu, cikin farinciki da ɗaga      murya take cewa " matar yaya tazo" Hankulan mutanen gurin sukayo kansu, wata farar mata Balarabiya kamar su ɗaya da Shahazad ta  rungume Mona tana cewa "Hindu zoki shigar dasu ciki" Hajara sai murmishi takeyi, Sakamakon tattali da kula da taga mahaifiyar Shahazad take gwadawa Mona, riƙe da hannun Hajara aka shigar da Mona ciki, Bayan sun huta lokacin da aka kira sallahar azhar Hajara ta tashi ta shiga toilet ɗin ɗakin da suke ta ɗauro alwalah kana ta shimfiɗa ɗankwalinta ta kabbara sallah, ga dukkan alamu ba sallah mutanen gidan sukeyi ba, abin ya bawa Hajara mamaki sbda wasu lokutan tana ganin Shahazad yana Sallah, duk da  hakan shima bai mayar da ita farilla ba. Hajara na idarwa Mona tace "idan kin shirya gujewa wannan mugun zan tafi dake idan kuma zakici gaba da zama shikenan" Murya ƙasa-ƙasa Hajara tace "ban fahimci me kike nufi ba?" "Ina nufin zamana ya ƙare tare tare dashi, dama na daɗe ina neman mafita da muhimmiyar yanya yanzu ko na samu komai" Hajara tayi murmishi mai cike da tarin tambayoyi kana tace "bakya tsoron idan ya gano komai yasa a kashemu?" "Haba Hajar wanda zai tafi damu nan da mintuna talatin zai ƙaraso" Hajara tace "shikenan amma nayi farinciki" Suna zaune aka dinga jere abinci kala-kala a dining kana aka umarcesu da suje suci. Koda sukaje cin abincin kaɗan sukaji, a zahiri jikin kowacce daga cikinsu ya tsinke, Sannan ko wacce da tunanin da takeyi a cikin ranta. Wayar Mona tanayin ringing suka miƙe a tare, Mona ta kalli agogon dake manne a bango 6:30pm ga haske ta ko ina, tashi ɗaya duhu ya gauraye ko'ina na gidan, hakan yabawa Kharan damar ce mata ta fito ta ƙofar baya, yana jiransu, Cikin sanɗa suka fita riƙe da hannun juna, kana suka isa gurin motar, motarsu na tafiya haske ya baiyyana a gidan, kasancewar mutan gidan a gajiye suke, maman Shahazad tasa Hindu ta je ta nuna musu gurin kwana, cikin rashin sa'a Hindu na shiga taga wayam, babu su babu kayan su, ta duba toilet nan ma shiru kana ta zaune tana dogon nazari, sannan kuma ta fara tunanin me zataje ta cewa mama?. ALGERIYA Ikon Allah kenan yafi gaban wasa, yayinda lokuta suke tafiya kwanaki suke shuɗewa, yau kwanansu Hajiya ƙarama goma sha huɗu, 2weeks a Algeriya, inda sukayi nasarorin samun lafiyar Iffat tare da nasara akan aikinsa, gobe suke sa ran zasu koma gida, Iffat kam lafiya ta samu, sbda babu abinda bata ganewa na game da rayuwa, sai dai yawan surutunta ya ragu sosai. NIGERIA Tun ana saura kwana bakwai su dawo, dady ya sanarwa Hakeem da Hajiya babba, wani lokacin ma Iffat tana gaisawa da Hakeem idan dady ya kirashi, abinda Hajiya babba bata taɓa tsammani ba kenan, wato samun lafiyar Iffat, abin ya dagula mata lissafi, A ranar da suka sanar mata da lokacin dawowarsu, ta shirya zuwa gidansu, cike da mamaki mahaifiyar Hajiya babba take kallonta, kafin ta amsa sallamar tana cewa "yaushe rabon da inji muryarki ko a waya?" Hajiya babba ta fashe da kuka mai cike da makirci, kana tace "umma ina Fawziya?" "Fawziya tana ciki auren ma ya mutu" Hajiya babba ta dafe ƙirji kana tace "innalilahi wa inna ilaihir raji'un, wannan wane irin mummunan labari ne?" Umma tayi shiru tana kallon yanayin Hajiya babba. Koda ta shiga ɗakin tagumi tayi, Umma ta shigo kana ta zauna gefenta, cikin sigar lallashi tace "wai meke faruwa ne naga duk kin rame kin lalace tashi ɗaya Hajiya babba ta sake fashewa da kuka, a cikin kukan take cewa "yanzu alhaji baya Sona yafi son waccar shegiyar, ga wata y'ar tsintuwa da Hakeem ya samo aka kaita gidanmu, anyi cigiyar iyayenta har an gaji, dayake ciwon juyewar k'wakwalwa ne ya sameta, shine ya fitar da ita waje, har yanzu basu dawo ba". Hajiya babba ta k'arasa maganar tana sake fashewa da kuka, Umma ta matso kusa da ita kana tace "haba y'ata ki kwantar da hankalinki, wato yana nufin, har yar kwararo ta fiye masa na cikinsa, to wlh inaga akwai ayar tambaya akansa, kodai yarsa ce?" "A'a Umma wlhi ba yarsa bace, nidai so nakeyi a kaini gurin wani malamin yayimin temako dan waccar shegiyar ta lashe masa zuciya sai abinda tace shi yakeyi" "To ki kawantar da hankalinki idan har Ina raye saina share Miki kukanki, akwai dubu goma a gurina, Babanku baya gari, barin k'arasa aiki inzomuje gurin malam Mai turakar yasin wlhi idan kika amayar masa da duk matsalolin da suke damunki anyi an gama" Hajiya babba ta share hawaye, tare da rungumo Ummanta kafin tace "Umma wlhi Ina alfahari dake". Bayan Umma ta kammala aiyukanta ta d'auki hijabi da key motarta, Hajiya babba ta zauna mazaunin driver Umma ta zaro ido, tare da cewa "ni wlhi ban isa ba, kice lahira salamu alaikum, ace duk kudin mijinki har yanzu baki mallaki mota ba, ki duba ki gani motata ta uku kenan, ke ko d'aya baki ajiye ba" Hajiya babba ta fito tana cewa "umma ai yanzu nasan abinda yafi mota ma zan samu insha Allah... Ina mai  bawa ma masoyana hak'uri, musamman akan rashin ganin posting kuyi hak'uri dan Allah insha Allah yanzu zamuci gaba. Mom Islam 08141799224 *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 57-58 Kai tsaye suka wuce gurin boka, wani ƙasurgumin jeji suka dinga tafiya, bakajin kukan komai sai na, tsuntsaye, riƙe da hannun juna suke tafiya har Allah ya kawosu gindin wata ɗirkekeyiyar bishiyar kuka, cikin ƙaraji da murya marar daɗin sauraro sukaji ance "ku koma da baya, sannan kuma bama son sallama" Jikin Hajiya babba ya ɗauki kyarma, ta riƙe hannun umma gam tana cewa "Umma wlhi mu koma nikam bazan iya jure wari da tsawar nan ba" Shiru Umman tayi bata kulata ba, har suka  iso gurin bokan suna tafiya da baya, kana Umma taja hannunta suka zube a ƙasa. "An gaisheka boka an gaishe da madugu an gaishe da hatsabibi" Cikin jin daɗin kirarin yayi murmishi jajayen haƙoransa suka baiyyana, sai kuma ya turɓune fuska kafin yace "baku da matsala da maganina, duk wanda muka bawa sai ya dawo yayi mana godiya, dan haka ku kwantar da hankalinku, meke tafe daku?" Umma tace "wlhi kishiyar yarinyata ce ta mallake mijin bayajin maganar kowa sai Tata, sannan akwai wata maiyyar yarinya da aka tsinto, yana mugun sonta" A gaggauce boka yace "yanzu me kukeson ayi mata?" Hajiya babba da sai yanzu ta samu bakin magana tace "inaso ya zamo maganata kawai yakeji, sannan ya zamo danginsa suna sona sosai, ita kuma yarinyar inason a sanya ya mance da labarin ta, sannan ya dinga ji dani kamar tsoka ɗaya a miya" "Duk wannan zancen da kikayi, anyi an gama, ɗan gajere na jinki shine zeyi komai, amma kafin nan munason gashin kan ita kishiyar taki, sai kuma farcen Alhaji shima muna buƙata, sannan munason rigar yarinyar guda ɗaya" Jikin Hajiya babba na rawa tace "ni yanzu ina zan samu waɗannan abubuwan daka ambata?" Cikin daka tsawa yace "idan har kinason aiki dole kibi hanyoyin dana faɗa idan kuma bakyaso ku ɓacemin anan" Umma tayi murmishin yaƙe cikin sigar bada haƙuri da kwantar da muryar, "Dan Allah boka kayi mana rai, saboda inganci aiki irin naka shiyasa muka taho gurinka domin ka taimakemu" Boka ya sheƙe da dariya, kana yace "na gama magana idan an samu abubuwan dana ambata ko yanzu kuka kawo, yanzu aiki zai wakana" Umma ta riƙe hannun Hajiya babba kana ta fiddo kuɗaɗe dubu ashirin ta ajiye a gabansa, kana suka miƙe, suna tafiya da baya-da baya har suka iso gurin mota. Koda suka shiga mota, Hajiya babba ta rafka uban tagumi kana tace "Umma a ina zan samo waɗannan abubuwan da boka ya ambata?" Umma tace "haba kekuwa sai kace ba mace ba, idan har ke jinina ce wlhi zaki iya, kidena bani kunya" Hajiya babba tace "to shikenan Umma zan jaraba in gani" Sai bayan isha'i sannan ta koma gida,lokacin Hakeem ya daɗe dayin barci, sai da ta leƙashi sannan ta wuce ta kwanta babu batun Sallah, sai ma tunanin "ta yaya zata samo abinda boka ya umarceta?" Da wannan tunanin barci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Tun bayan tafiyar Huda daga gidan Ummanta, ta koma sarin kayan sawa takalmi da kayan koli hoda janbak da sauransu, sannan ana kawo mata kayan ɗaki irin kamar idan auren mutum ya mutu ta siya, sannan tana siyarda maganin mata sosai, dan yafi ƙarfi ma a sana'ar ta, Safiyar Asabar, bayan ta kammala gyara gida tayi abin karyawa, ta ɗaga waya ta kirawo ƙawarta, abin mamaki kuɗin da Alhji Auwal ya bata ba ƙaramin bunƙasa sukayi ba, Bayan ta ɗaga Umma tace "Maryamah ya zakiyi min haka, kawai jiya wani mutumi yazo hira gurina?" Wacce Umma ta kira da Maryamah ta tuntsure da dariya kana tace "wlhi gani nayi Kun dace shiyasa nayi masa hanya" Umma tace "to duk ma ba wannan ba, kinsan kuwa yace da wuri yakeson auren, nida nafi shekara goma ban waiwayi dangina ba, to yanzu me zance musu?" "Hhh Gaskiya ƙawata akwai ki da tsoro, a tunanina zaki fara nemo mana hanyar jin daɗi da huta kawai sai ki dinga wani tunani can, ko ance miki masu ɗaura miki aure babu su ne a garinnan? " "Gaskiya ne Maryamah Allah yasa mu dace, ya kamata kizo gobe ki rakani siyo kayan ɗaki tunda ya fara maganar bikin bayason ya wuce sati ɗaya" Maryam tace "ai komai zai tafi dai-dai insha Allah kedai kici gaba da tsuma kanki da magungunan nan naki masu rikita kwanyar mazaje" Umma tayi dariya kana tace "sai kinzo" Ta katse kiran. Jiga-jigan magunguna ta dinga ci gaba dasha, sbda ta gigita sabon ango. Washe gari, suka shiga kasuwa suka siyo gado da katifa da drowa da madubi, duk da na hannu ne, amma basu wani ji jiki ba, a ranar aka jera komai, da yamma sai ga Mahabob da Huda sun shigo da sallama, baki washe Umma take amsa wa, kana ta shigar dasu ɗakinta, bayan sun gaisa, Huda ta ajiye wa umma sabulai da omo tace Mahabob ne ya siya mata, Godiya Umman tayi masa kana ta sanya musu albarka, ta tambaye su ya iyayen nasu, Sukace l"afiya lau" Mahabob ya miƙe tare da cewa "Huda zan jira ki a waje" "To" tace masa  kana ta mayar da hankali kan kayan ɗakin da taga an sauya" "Umma masha Allah ɗaki yayi kyau" Umma ta washe baki kana tace "wlhi Huda aure zanyi nan da kwana shida, shiyasa naketa gyara gida" Huda tace "kai  Umma shine ko ki gayamin?" "Huda ba gashi kin sani ba" Daga nan suka ɗan taɓa hira, huda tayiwa Umma sallama suka wuce, da niyar sai ana biki saura kwana biyu zata zo ta kwana. Alhaji Lukman ɗan tijara, sunan wanda Umma zata aura kenan, Mutum ne mai arziƙin gaske, sai dai yanada wasu ɓoyayyun ɗabi'u, wanda ba kowa zai san da haka ba sai wanda ya zauna dashi, Zuwa dare har Umma ta kwanta rurin wayarta ya tasheta, murya irin ta mai barci tace "ranka shi daɗe Barka da dare" "Barka amaryar Lukman ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya" Umma ta amsa da "lafiya lau Alhmdulilah" "Dama inaso gobe idan Allah ya kaimu muje ki zaɓi irin gidan da kikeso ki zauna" Da sauri ta tashi zaune, tare da cewa "ni harna gyara gidana wlhi" "No ai bazai yiwu ba, dole a low cost zaki zauna G.R.A," Cikin farinciki tace "Allah ya kaimu goben" Ya amsa da "Amin" Alhaji Lukman ɗan tijara ya kalli abokansa dake zaune kusa dashi, kafin yace "mutuniyar ta faɗa" Suka sheƙe da dariya mai sauti, ɗaya daga cikin abokansa yace "ya kamata ka sanar mata da larurar dake tare da kai, kar sai Kunyi aure a dinga kai ruwa rana"...! Ayi  haƙuri da rashin posting da yawa Please Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 59-60 Sam baiji daɗin maganganun nasu ba, sannan ya alƙawartawa zuciyarsa bazai baiyyana mata ɓoyayyen sirrin dake lulluɓe a zuciyarsa ba. Washe gari, breakfast kawai tayi sai ga kiransa ya shigo wayarta, ring ɗaya ta ɗaga cikin salon bariki tace "amincin Allah ya tabbata a gare ka Alhajin Allah" Sai da ya lumshe ido, kana ya shafa tumbinsa, kasancewar daga shi sai gajeren wando yake zaune, kafin yace "tare dake, idan kin gama shiryawa zanzo mu tafi, kiga gidan da yayi miki" "Eh na gama" Ta faɗa tana miƙewa tare da ajiye wayar. Cikin sauri ta gyara ko'ina kana ta shirya cikin atamfa ɗinkin riga da zani sai mayafi data yafa, kalar adon atamfar wato pink color, kana ta maƙala ɗan kunne ta fito hannunta riƙe da key na gidan, kana ta fito waje, lokacin da take kulle gidan Alhji Lukman ɗan tijara ya iso, horn ya danna kana yayi murmishi, kallon Umma yakeyi kamar ƙaramar yarinya, sbda tashi ɗaya tayi haske tayi kyau, musamman ma da ta shiga shafe-shafe. Itama murmishin tayi kana ta buɗe gaba ta shiga. Suna cikin tafiya yace "zasu biya kasuwa domin suyi siyayyar kayan akwati" Cikin jin kunya tace "Tom" Kai tsaye suka wuce G.R.A dake ɓukur park, a bakin milk color ɗin get yayi parking kana suka fito, key ya ciro a aljihunsa sannan ya buɗe ƙofar suka kutsa kai ciki, "Masha Allah gida yayi kyau" Umma ta faɗa daga shigarsu, "Sai ma kin shiga ciki" Koda suka shiga cikin gidan, a kan ɗirkekiyar kujera mai numfashi Umma ta zube, tare da sauke ajiyar zuciya kana tace "Alhji bani da bakin yi maka godiya, sai dai ince Ubangiji ya ƙara arziki da wadatacciyar lafiya" "Amin ai kin wuce hakan, a gurina" Sai da ya zagaya da ita lungu da saƙo na gidan, kana ya tambaye ta idan akwai abinda beyi mata ba ta faɗa, "Yayi komai gunin sha'awa" Umma ta faɗa jiki na rawa. Daga nan suka wuce kasuwa, ya kashe mata kuɗi sosai musamman gurin siyan zannuwa da turaruka. Daga nan suka wuce Shan Rufaida yoghurt, koda sukaje Umma bata wani yi kauyanci ba, saima burgeshi da take dad'ayi, Daga nan ya dawo da ita gida, kaf kayan da suka siyo harda akwatunan yace ta wuce dasu gida. Bayan ya ajiyeta ya wuce. Tana shiga gida ta nemi guri ta zauna tare da ƙarewa kayan kallo. Jiki na kyarma ta ɗauki waya ta danna number Maryamah, kamar jira take, ring ɗaya ta ɗaga tare da cewa "sai kuma na jiki shiru" Umma ta kwashe da shewa kana tace "hamm Alhji ya kashemin kuɗi, da kinada halin zuwa da kinzo kin kashe ƙwarƙwatar ido" Maryamah ta gigice tare da cewa "wlhi ganinan zuwa ko zan sami wani abu" Lokacin da Maryamah tazo ana kiran sallahar azhar, ta samu umma na sallah, bayan ta idar ta shafa adu'a kana ta kalli Maryamah tayi murmishi kafin  tace."ƙawata kwaso kayan a kan gado" Jikin Maryamah na rawa ta kwaso kayan, tare da cewa "kai-kai ƙawata Allah ya yanke miki wahala, gaskiya irin waɗannan alhazan abin riritawa ne, gaskiya ki riƙe shi gam ƙawata" Umma tayi murmishi kafin tace "ya hutar damu maganar kayan ɗaki wlhi gida yayi kyau" Maryamah tace "haka akeso amma a shawarce ya kamata ki je garinku saboda kinsan aure ba abin wasa bane, dalilin...." Cikin daka tsawa, Umma tace "bakisan komai a kaina ba bakisan kowa nawa ba, dan haka bana buƙatar kowa ya sani" "Haba Umman Huda, ya ina baki muhimmiyar shawara kina kaucewa, bakya tunanin ta dalilin ƙaryar waliyai da zakiyi masa idan ya gano gaskiya abin bazaiyi kyau ba?" KANO•• Ƙauyen ƴan yakuba Garine wanda ya kasance ƙauye sosai, yawancin abinda sukeyi  shine noma da kiwo, kowanne magidanci taƙamarsa noma da kiwo, Gidan malam Ado, gidane mai ɗauke da mata biyu, koda yaushe basu da aiki sai masifa, duk da dukkansu babu wacce ta taɓa aihuwa, amma masifa taƙi ƙarewa a cikin gidan, Hansa'u itace babba sai  Saratu ita kuma itace amarya, hansa'u ta kasance mace mai haƙuri da kawaici, yayinda Saratu ta zamo gagararriya a cikin gidan, shekararsu biyar da auren Saratu, ya shawarcesu akan zai koma zuwa Jos cirani, dukkan su sunyi na'am, Wase Gari kuwa Saratu taje gidansu ta sanarwa mamanta maganar da malam Ado yayi, cikin rashin amincewa da tafiya da Saratu, tace "wlhi da ke zai tafi, ƙarya ne, tashi muje gurin baba insha a anyi an gama" Saratu ta miƙe tare da yafa zanin da ta luluɓa kana suka wuce gurin malam wato baban mamanta, suna zuwa maman nata ta isar masa da duk abubuwan da suke so, kana suka kwashe ƙarya da gaskiya suka gaya masa, Yayi musu alƙawarin kawar da hankalin jama'a akan tafiyarsu, sannan aka sanya masa tsanarta a zuciyarsa. "ammafa tanada juna biyu harna wata uku" Malam ya faɗa yana kallon Saratu, Saratu ta zaro ido tare da dafe ƙirji kana tace "wlhi sai na kashe abinda ke cikinta ko ta haisheshi" Daganan suka dawo da ƙulle-ƙullen magunguna, Saratu ta dawo gida, bayan sati ɗaya, abubuwa suka fara faruwa, kama daga kaf danginsa abokan arziƙinta da ƴan uwanta duka suka tsaneta, ko ina Hansa'u ta shiga sai dai a dinga kyararata tare da hantara, hakan yasa ta dena fita ko ina, sai alwalah da wanka ne yafe fito da ita, abinci kuwa sai dai idan almajiri ya shigo ne saratu zata zuba abincin ya miƙa mata, Sosai Saratu ta zamo tauraruwa mai haska ko ina, duk wannan gwagwarmayar da akeyi, mahaifiyar Hansa'u tayi tafiya garinsu sati Uku kenan bata gida, bayan ta dawo ta samu mummunan labari game da ƴarta Hansa'u, itakam asirin beyi tasiri a kanta ba, sbda tayi kuka kamar me, Kwanan mahaifiyarta biyu da dawowa su Saratu suka tafi Jos, Koda ta kawowa Hansa'u ziyara ta sameta tana kuka, ta tambaye ta lafiya ta sanar mata su malam Ado sun tafi sun barta, tana kuka take maganar, Maman ta dinga rarrashinta tare da  sanar mata, inhar Allah ya sauke ta lafiya, bayan ta yaye zata bashi yaronsa, idan namiji ne, idan kuma mace ce Tom" Da wannan shawarar suka koma gida, mamanta taci gaba da taimaka mata. Sun sauka lafiya a Anguwar Dogon agogo, dama ya riga da ya kama gida, kai tsaye shiga sukayi tunda mukulin gidan yana hannunsa, sukaci gaba da rayuwa cikin so da ƙauna, baya ganin lefinta sam ko me tayi masa, sannan ko aiki yaje ya dawo zai zazzage mata aljihu su raba kuɗin dai-dai...! Dan Allah ayi haƙuri zafa mu shiga typing da yawa🤣insha Allah amman yau anguwa naje, sannan ina jiran shar'i.. Ayi haƙuri da typing error Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 61-62 Acan ƙauye Hansa'u na aihuwa aka raɗawa yarinya suna Huda, wato sunan mahaifiyar malam Ado, shekarar Huda ɗaya a duniya Hansa'u ta rasu, sakamakon ciwon nono wanda ya zame mata cutar ajali, Sai da akayi kwana bakwai sannan malam Ado yazo gaisuwar rasuwa, mahaifiyar Hansa'u ta damƙa masa huda a hannunsa, yayi magiya akan su barta zai dinga aiko da kuɗi, ai mahaifiyar Hansa'u taƙi yarda, washe gari dole ya dawo da Huda Jos. Saratu na murna mijinta ya dawo, kawai ta hango yarinya a jikinsa, cikin yamutsa fuska tace "mezan gani ƴar wa ka kwaso mana?" A tunaninsa murna zatayi tunda bata taɓa aihuwa ba, sai yaga akasin hakan, ta murtuke fuska tana tuhumarsa, "Yarinyar Hansa'u ce da ta mutu ta bari" "Toni ina ruwana da mutuwarta wannan kai ta shafa, nidai kasan ba ƴar raino bace ko?" Cikin lallashi ya siye zuciyarta tare dayi mata alƙawarin siya mata kayan ɗaki, Haka huda ta taso cikin rayuwa marar daɗi ga tsangwama  da kyara da duka, har Allah yasa ta girm, tun tana da shekaru goma Saratu take ɗora mata tallah, Huda nada shekara goma sha daya malam Ado ya rasu, yafuta gurin aiki sai dawowa akayi da gawarsa, Saratu tayi kuka sosai, duk da bawai yana nunawa Huda kulawa bane, amma hakan bai hanata yin kuka ba. Bayan rasuwarsa, Saratu taci gaba da ɗorawa huda tallar shinkafa da miya, a haka har ta ƙara shekaru biyu, shine har kawo yanzu da Allah ya haɗata da Mahabob. Back to story Bayan kwana uku da yin maganar sistern Batool, Abba ya kira Mahabob a waya, kasancewar lokacin 12:pm yana barci bai ga kiran Abba, wayar sai ringing take, kasancewar a silent take. Sai 12:20pm ya farka, ya kunna haske wayarsa, ganin miss call ɗin Abba hankalinsa ya tashi, ɗaurayo baki kawai yayi ya fito zuwa part ɗin Batool. Da sallama ya shiga, suna parlo Abban na breakfast, Batool ta amsa fuska a sake, kana ya nemi guri ya zauna, cikin girmamawa yace "Abba kayi haƙuri lokacin da ka kirani ina barci" Sannan ya gaishe da Batool ya gaishe da Abban, "Babu damuwa, dama inason in sanar maka nayi maka mata ne, duba da yabawa da hankalinta da nayi sbda yarinyar nitsatsiyace, kuma nasan bazaka bani kunya ba" Sam zancen beyiwa Mahabob daɗi ba, kasancewarsa mai biyayya yasa ya kawar da damuwar da takeson lulluɓe masa fuska, yai ƙoƙarin aro murmishi kana yace "Abba godiya nake" Abba yace "wato Mahabob nidai babu abinda zance dakai sai godiya, sbda biyayya kam kanayi min, hakan yasa na baka kyautar Company ɗina na cikin gari" Batool ta zaro ido ba tare da kowa ya sani ba, sannan tace "godiya yake Alhaji" Abba ya ƙara da cewa "yarinyar ƙanwar Batool ce, sannan yau zatazo gidannan sai ku gana" "Toh Abba" Mahabob yace. Kafin Abba ya idda magana Batool ta haɗowa Mahabob shayi mai kauri da bredi da wainar kawai kana ta ajiye masa cokali mai yatsu, Ruwan shayin kawai ya iya kurɓa kana ya ajiye cup ɗin bai shanye duka ba, sannan ya miƙe yana cewa "Abba godiya nake" Cike da so da ƙaunarsa Abba yace "Nine da godiya Mahabob" Bayan fitar Mahabob Abba yace "idan har za'a dinga samun ƴa'ƴa irinki to wlhi kaf zuri'arku abin a aura ne" Batool tayi dariya tare da rufe fuska, Daga nan Abba ya miƙe, tare da kulle ƙofar part ɗin su ya dawo gurin Batool, Wani irin mayataccen kallo yake mata wanda yasa ta gane buƙatarsa, cikin sigar soyayya ta taho gurinsa tare da ɗaga rigarsa ta tura hannunta kan nipple ɗinsa ɗaya tana murzawa da hannu ɗaya kuma yana bakinta tana jujuyashi a hankali, ajiyar zuciya ya dinga saukewa mai cike da sha'awarta, daga ƙarshe dai ta cire masa rigar gaba ɗaya, shikuma ya rungumota ya tura hannu ƙasan mararta, nidai nace bari mu barsu su shaƙata muje gurinsu Amani muji ya ake ciki. Jiki a sanyaye Mahabob ya ƙarasa part ɗin su Amani, yana shiga ko sallama babu, Cikin yanayin damuwa ya zube akan kujera tare da dafe kansa, yana mai runtse idanuwansa. Babu kowa a parlon hakan ya bashi damar yin tunani. Yayi zurfi a cikin tunani sai ga Amani ta fito, Aseela ta fito Huda tabiyo bayansu, cikin yanayin damuwa Amani ta taho da sauri tare da cewa "bro lafiya kuwa?" "Babu lafiya sis" Hankali a tashe suka zube kan carpet tare da cewa "waye bro meke faruwa?" Aseela da Amani suka tambaye shi. "Abba ne yakeson yimin aure, wai harya zaɓamin mata ƴar uwar Momy" Amani ta zaro ido kafin tace "aure kuma? sannan ƴar uwar matarsa?" "Never wlhi karka amince" Huda da sai yanzu tayi magana tace "haba Aunty Amani duk wanda ya saɓawa iyayensa wuta zai shiga, ya kamata yayiwa Abba biyayya" Jiki a sanyaye Aseela tace "hakane bro kayi haƙuri kabi umarnin Abba" Kamar da wasa, sai ga wasu siraran hawaye sun kwaranyo ta fuskar Mahabob, ya share su da tafin hannunsa kana ya miƙa tsaye, yana ajiyar zuciya. Dukkansu jikinsu yayi sanyi matuƙa, idan ka cire Huda da take ganin gata Abban yayi masa, Sai da Abba ya samu nutsuwa kana ya je toilet yayi wanka, ya fito ɗaure da towel, kana ya goge jikinsa ya shafa mai, sannan ya zauna akan bed, gefensa ya kalla yayi murmishi, ya ɗauki kayan da Batool ta ciro masa ya ɗora kan cinya, tare da ajiye hular a gefe. Bayan ya gama shirinsa, lokacin har Batool ta fito daga wanka itama ta shirya cikin abaya dark blue tayi mata kyau sosai, ya ɗaura agogon hannu kana ya miƙe tare da rungumarta, a tare suka taho bakin ƙofa hannunta riƙe da hular Abba, tasa masa tana cewa "Allah ya kiyaye hanya, Allah ya bada sa'a" "Amin ya rabbi" Abba ya faɗa yana bin ta da kallo. Dalilin da yasa bata rakashi parking space ba , sbda ya hanata rakashi har can. Sai da ta tabbatar da ta kulle ko ina, kafin ta dawo ta ɗauki wayarta ta kira mamanta, maman na ɗagawa tace "mama Albishirinki" "Goro Mama tace tare da cewa Ƴar albarka sai gashi jiya an kawo mana kayan abinci cikin both" Batool tayi murmishi kafin tace "wlhi Alhji ne" Sannan tace "mama ina wanda nace miki inason a haɗa autarki dashi, wlhi Alhji ya bashi kyautar danƙareren Company wanda maƙudan kuɗaɗe suke shigowa" Mama ta miƙe tsaye tare da dafe ƙirji, cikin farinciki tace "wannan auren ya zame mana taki, gashi sai samun alkairai muketayi". Batool tace "wlhi kuwa sai ma ta aureshi, ki sata ta haɗo kayanta ta taho saboda suga juna, kinsan zafi ƙara jin sonta tunda kullum suna tare" "Eh kuma haka ne,insha Allah driver zai kawota ki kwantar da hankalinki" Batool ta katse kiran. Kwance take rungume da teddy, murya ƙasa-ƙasa take magana a waya, bugae ƙofar da mama tayi ne ya sata mirginawa tace "mtsw ba hali mutum ya kwanta sai an tasheshi, ni walhi nagaji da takura. Ta miƙe tana bubbuga ƙafa, ta buɗe ƙofar. Da murmishi Mama ta shigo tana cewa "Auta munyi samuwa Please ki tashi" Cikin sauri ta miƙe tare da cewa "mama nifa idan aikin wahala ne bazan iya ba" Mama ta rungumeta kana tace "wlhi iri aka samu, babban ɗan Alhaji Auwal wanda yake tashen nera" Naeema ta wurgar da teddy tana cewa "mama nifa sai dai muyi soyayya dan ban shirya aure ba, akwai wani baby na Wanda mukayi alƙawarin aure dashi" "Mtsw kaji irinta ai meyasa bazaki taɓa ganewa bane? arziƙi yana binki kina guduwa?" Daƙyar mama ta shawo kanta, harta amince amma da sharaɗin bazai hanata sakewa ba, Zuwa yamma Dady ya dawo, mama ta sanar masa ya amince shima yana murna, Naeema ta shirya, driver ya wuce da ita gidan Batool. LIBYA  (Ghat) Sosai hankulan mutanen gidan ya tashi, basuyi ƙasa a guwaiwa ba gurin kiran Shahazad suka sanar masa, hankali a tashe yace "karsu damu zaiyi wani abu" Cikin sauri ya kira babban ofishin jami'an tsaro, tare da sanar musu da su saka ido akan kowacce mota da take shige da fice, Abinka da masu faɗa aji, tunda da ɗaurin gindin manyan suke aikata komai, tashi ɗaya aka datse titinan shige da fice, da hanyar zirga-zirga. Gudu Kharan yakeyi dasu, babu tsayawa, suna zuwa checking point aka dakatar dasu, Kasancewar da layin motoci a gabansu yasa, Kharan ya samu damar umartar su Mona, da su kwanta ta ƙasan kujerun suyi kamar ba komai, kana ya mayar da carpet gurin. Koda layi yazo kansu, jami'an suka dinga haske-haske su biyu, har sun ɗagawa Kharan hannu, suka hango carpet na motsi, cikin sauri ɗaya daga cikinsu yace "stop!!" Karan ya figi mota da Uban gudu, suma suka bisu da motoci guda uku, Gudun da Kharan yakeyi har yafi na ɗazu, sbda a halin yanzu idan yayi sake komai yana iya faruwa. Da sauri yayi kwana da motar suka faɗa wani ƙasurgumin jeji, a tunaninsu sun tsira, ashe ana tracking number Mona, da Hajara, sam hankalin Kharan baya ga tunanin ta hakan yasa suke binsu, Cikin sauri da ɗaga murya Kharan yace "ku cire sim card ku yar wlhi tracking sukeyi" Hajara ta zaro ido sbda number mahaifiyarta dake jiki da number danginta, dole ta haƙura tunda basu da wani isasshen lokaci, duk wata hanya da ya gani kutswa yakeyi ta cikin jejin har Allah ya kawosu wani babban titi, Cikin azama ya sake sauya hanya, ga mamakinsu dukkansu a jirgi aka koma bibiyarsu. Yau kwanan Hassan bakwai a gidan Ala-Uddin Samir tun tana rashin sabo har ta saba, duk wani damuwa da take ciki da matsasti yanzu kam tana cin abinci tunda, taga babu larabar komawarta mahaifarta, Kamar kullum tayi sallahar azhar ta ɗaga hannayenta sama tana kaiwa Allah kukanta, kamar daga sama ya shigo hannunsa riƙe da babbar leda, Sallama bata cikin huruminsa dan haka ya nemi guri ya zauna, tare da wurga mata ledar dake hannunsa, bayan ta shafa adu'a ta kaleshi ta kalli ledar kana ta ajiye a gefe. "Haseeaina ki buɗe wannan ledar sannan ki fito da kayan cikinta, inaso yanzu kisa, zaki iya shiga toilet ko bedroom kokuma in baki guri duk wanda kika zaɓa" Jiki a sanyaye ta ciro kayan riga ce mai ruwan ƙwai yellow mai hannu ɗaya, iya ka nonuwanta kawai koda tasa zasu rufe mata, sai skel ɗin shima mai ruwan yellow da ratsin baƙi, shikuma mazaunanta zai rufe mata, gashi ko kauri babu, sai hula baƙa wacce ta kasance kamar ta sojoji mai adon tuta a gaba, cikin jin kunya Hassana ta kalli kayan tare da ƙare musu kallo, kafin tace, "Dan Allah shugabana kayi haƙuri bazan iya wannan shigar ba, a musulunce ma haramun ne, Allah ya haramta" "Okay haka kikace, idan baki saka kayannan ba sai na cire miki wanda ke jikinki in sanya miki waɗannan sai ki zaɓa..." Tofa ya kuke ganin lamarin zai kasance? # Mona # Shahazad # Ala-Uddin # Hassana # Mahabob Yawan comments yawan typing. Mom Islam 08141799224 *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 63-64 Book1 "Dan Allah kayi haƙuri, a musulunce haramun ne, ni kaina bazan iya shigar da zata fallasa tsaraicina ba" Tana shirin sake yi masa magana, taji ya kamota ya haɗe ta da jikinsa, kafin ya rabata da komai ya sanya mata wannan, Da sauri ta runtse idanunta hawaye na sauka, tare da ambaton "Innalilahi wa inna ilaihir raji'un, astagfirullah Allah kana gani bana da niyar zina ko saɓa maka Allah kayimin katanga daga sharrin wannan bawa naka" Cikin hukuncin Allah wayarsa ta fara ruri, rungume da hajaran ya ƙarasa ya ɗauko wayar, tare da karawa a kunnensa, "da sauri taga ya miƙe tare da ficewa bai ce da ita komai ba, Hakan ya bata damar cire kayan ta mayar da wanda ya cire mata tana hamdala. Yana fita ya daddanna waya ya kira lambar Lulu, Cikin tausayawa naji yana cewa "Lulu babu abinda ya sameki ko?" Muryarta bata fita sosai tace "Please Hub ka zo" Ya buɗe mota ya shiga, dole na kusa dashi ne yayi driving  har suka isa hospital. Ko rufe murfin motar beyi ba, ya shige, Dokar asibitin ne sai ka tabbatar musu da wanda kake nema, sannan kuma sun yarda dakai ba cutarwa zakayi ba, sai da Ala-Uddin ya cika sharuɗan sannan ya samu damar shiga dubata, Cikin murya irin ta nuna tausayawa yake cewa "Lulu ya ciwon cikin naki?" Idanunta a buɗe ta ɗora su ana Ala-Uddin kana tace "naji sauƙi" Ya kamo hannunta yana mammatsawa a hankali tare da shafa gashin kanta, Shigowar likita yasa Ala-Uddin cewa " yadai jikin nata babu wata matsala ko?" "Eh  juna biyu ta samu shine ya fita, befi na sati Uku ba" Ran Ala-Uddin fess ya ce "okay" Sbda a halin da ake ciki yanzu bayason Lulu ta samu ciki har ta aihu,  hakan yana iya zamowa matsala a gareshi. Sai gab magriba sannan aka sallemeta suka dawo gida. Sosai yake riritata saboda ya samu abinda yakeso, har wani lallaɓata yakeyi, Suna kawance yana rungume da ita, ya raɗa mata "my Lulu ya akayi kikayi mana ajiyar baby bani da labari" Lulu tayi murmishi kafin tace "naso nayi maka surprise  ne sai kuma komai ya baiyyana" Ala-Uddin ya sake rungumota kana yace "I love You so much my Lulu" Ta lumshe ido tare da manna masa kiss a kumatu. SHAHAZAD FOREST. Yau  SaLha ta kammala shirye-shiryen zuwa ɗaukar fansar mutuwar ƴar uwarta, Ba ƙaramin goyon baya Shugaba ta basu ba, Har ta fara tafiya, Raza ya ƙwala mata kira, cikin ɗaga murya yace "Salha karki kuskura ki ragawa mugu, zai iya dawowa ya kashemu gabaki ɗaya" Salha ta shafi kansa kana tace "bazan taɓa bari yayi nasara a kaina ba, har sai na aiwatar da duk abinda ya kaini, zan zamo masa ƴar leƙen asiri a lokacin da yake buƙatar taimako" Duka mutanen garin suka  goya mata baya,  bayan wasu daga cikinsu suka bata ma'adanansu wanda idan ta siyar zata samu maƙudan kuɗaɗe. Rataye da jaka a wuyanta ta tafi, ƙafarta babu takalmi, har ta kuma yin nisa a karo na biyu,  shugabarsu tace "Salha al'adar mutanen Libya sanya takalmi da kaya a jiki, kinga ke  bakiyi kama dasu ba, zaiyi wuya idan ba'a ganeki ba,  amma nasan Ubangiji bazai bari ki cutu ba, Yakamata ki fara da neman aiki ko a gurin makusantansa, sannan ki kame kanki da furta kalmomin da muke yawan furtawa bayan haka, karki yarda kici abinci da hannu yin hakan zai sa a gano daga inda kika fito" Slha tace "bazan bari su gane ba" Jiki a sanyaye tabar yankin nasu. Tunda su Kharan sukayi nasarar faɗawa ɗayan titin, suka dinga tafiya a hankali, duk da jirgin dake bibiyarsu, hakan besa ya dakata ba, Abin mamaki wanda baya ƙare wa bai wuce saukar jirgin a filin jejin da yayi ba, cikin tsoro Kharan ya yiwa motar key suka arce da gudu,  hakan ya bawa mutanen da suke cikin jirgi damar fitowa tare da kutsawa inda suke, sai waya da waya sukeyi, tare da harbe-harbe da bindiga. Sai da ya tabbatar da su ɓace musu sannan ya bar motar a gurin ya kamo hannun Hajara da Mona suka bar gurin, sbda gudu ƙafafunsu har ciwo sukayi, ga tsananin sanyi daya addabi Hajara, sai karkarwa takeyi. Daga nan sukaci gaba da shiga jeji wanda ya kasance ba mai ban tsoro sosai ba, dole suka yada zango a gindin wata bishiya, Kharan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, kafin yace "Shahazad mutum ne mai hatsarin gaske, zai iya bibiyarmu har a wannan jejin ma, da muke ciki, a shawarce ya kamata mu bar gurin an idan muka sake shiga ciki sai mu huta" Kamar inda ya umarcesu haka akayi suka dinga tafiya basusan inda suke shiga ba, suna cikin tafiya wani mutumi ya daka musu tsawa, wanda yasa Mona da Hajara shiga cikin firgici, Mutumin yace "Ɗan saurayi barkanku da shigowa jejin sarki Raja" Cikin salo na jin asalin labarinsu yace "meke tafe daku, dan naga kamar baku da gaskiya" Kharan yace  "munason  mu ga hanya zamuje Garin AL-KUFRA" Mutumin yace "nawa zaku biyani" Kharan yayi murmishi kafin yace "a halin yanzu babu kuɗi a gurina amma nayi maka alƙawarin idan muka sake haɗuwa zanyi maka alheri" "Ina bazan iya aikin wahala ba" Karan ya shaƙo wuyan rigarsa tare da cewa "zaka nuna mana ne ko sai na sheƙeka?" Jikinsa na rawa yace "kuzo muje" Sukaci gaba da tafiya  har suka ɓullo  titin da zai sadasu da garin   AL-KUFRA, sannan mutumin yace "amma kana kama da Kharan Khan wannan baban ɗan ta'addan" Kharan yace "tabbas muna kama amma komai namu bai kasance ɗaya ba, sannan mungode" Suna hawa titi, Kharan ya ciro waya ya danna number abokinsa Majid, ring ɗaya ya ɗaga tare da cewa abokina ina ka shiga su mama sunata tambayarka, nifa har na fara tsorata amma dai kana lafiya ko?" "Eh ina lafiya, Majid ka taho da mota zuwa titin sabon titin tafiya AL-KUFRA" "Mekuma ya kaika can, kai da ko yawo bakayi?" "Haba Majid tambayoyin sunyi yawa a halin yanzu ina cikin hatsari" Jikin Majid na rawa yai saurin ɗaukar key ya fito tare da yiwa motar key zuwa gurinda su Kharan suke, Yayi nisa sosai, yaga sojoji a hanya,  bai kawo komai ba ya ci gaba da tafiyarsa har Allah ya kawo shi gurin sojojin, abin mamaki wanda bazai taɓa wuce masa ba shine, hoton Kharan Khan mugun ɗan dabannan wanda suke kama da Kharan  suka nuna masa, tare da ɗora masa bindiga a kai, sukace yanayi mana basaja da sunan su biyu ne, a safiyar yau ya saci matar babban ɗan kasuwa Shahazad Khan munason ka gaya mana ka sanshi kokuma Kanada inda zakayi mu haɗu?"... More comments more typing Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam 65-66 Jikin Majid na cigaba da karkarwa yace "ban sanshi ba gaskiya" Sai da suka ɗauki number motar kafin suka barshi ya wuce. Duk da A C dake bada iska mai sanyi, amma gumi yake yi, sai da ya bari yayi nesa dasu kafin ya danna number Kharan, Dama jiran kiran Majid yake yi, ya ɗaga cikin yanayin damuwa kana yace "Majid kayi sauri" Daga can nesa Majid ya hango Kharan, hankali a tashe yake kallon matan dake tare dashi, kafin ya buɗe musu mota suka shiga, Allah ya taimake su a hanya babu jam'i hakan ya basu damar wucewa anguwarsu, Suna isa gida Majid yayi parking suka fito dukkansu, Kharan yayi musu umarni da su ƙarasa ciki, jikin mona da Hajara a matukar sanyaya suka shiga, Majid dake ƙare musu kallo yaje ya kulle get tare da rufe ƙofar da suka shigo ya dawo ya zauna kusa da Kharan dake mayarda numfashi. "Kharan waɗannan suwaye a ina ka samo su?" "Majid banason doguwar tambaya shi yasa ma na kawo su gidanka, tunda matarsa bata nan, idan na kuskura na kaisu gidanmu, tambayar Papa ma ta isheni" "Oky karka damu zan tayaka kula dasu" "Zanyi sallah Please " Hajara ta faɗa da siririyar Murya, "Bismillah" Kharan ya nuna mata toilet. KHARAN KHAN Tunda yaji labarin Kharan ya tsere dasu Mona, kuma yawancin mutane sun raja'a shine, hakan ya bashi damar farautar Kharan sbda wata manufa tasa, yasan idan har ya mallaki matar shahazad a sashin sa, babu shakka zai samu maƙudan kuɗaɗe, System ɗinsa ya ɗauko tare da searching sunan Kharan, tare da zooming na photonsa, Kharan Khan ya kalli fuskarsa a mirror kana ya kalli fuskar Kharan yayi makirin murmishi sbda kamar su ɗaya, abinda ya bambanta su idanun Kharan ruwan gold ne, shi kuma Kharan Khan idanunsa brown ne, boll's ɗin ciki, Murmishi ya sake yi a karo na biyu, kana ya cigaba da bibiyar sunan mahaifinsa da inda yake zama da inda yafi zama, Cikin Sa'a kuwa ya samu harda address na gidan Majid, hankali kwance ya ɗauki kwalbar giya dake gefensa ya kora, kafin yace "a shawarce, zanyi musu basaja, sannan nunar musu nine Kharan shi kuma idan ya shiga hannun jam'i nan ne zan samu damar buga wasa da shahazad, yana gama faɗar haka ya kashe system ɗin, tare da yin tafi. Bayan Hajara ta idar da sallah, ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah yayi musu kariya, Allah ya rufa musu asiri, daga zuwa aikatau ƙasar larabawa ta shiga rayuwar d bazata iya fassarawa ba, rayuwar da take gani a Film yau itace a ciki. Majid da Kharan, duka sun fice ya rage saura Mona da Hajara, Mona tace "Hajar kiyi haƙuri nasan zamu sha wahala amma wannan itace hanyar da zamu tserewa mugu" "Babu komai, kowane bawa da tasa ƙaddarar" Hajara ta faɗa tana miƙewa. Can anjima, Majid ya shigo hannunsa riƙe da leda, ya ajiye a gabansu, kana yace su buɗe suci" Mona ta kwaɓe fuska, tare da riƙe ƙirjinta alamar tashin zuciya tace "nikam bazanci ba, basmati nake nema" Majid ya zaro ido, sbda koda ya fita ana nan ana cigiyar inda Mona tayi, gabansa na tsananta faɗuwa yace "garin ya rikice ko ina babu daɗi" Kharan na bayansa yace "kai rago me yasa zaka bada maza, ya bigi kafaɗarsa kana yace "jeka siyo mata abinda take so" Majid ya fita jiki a sanyaye kana ya rufo ƙofar. Yana driving ya kusa zuwa gidan Abinci, Kharan Khan kuma na tsaye a bakin hanya, Sam Majid ya mance su biyu ne, sbda gigicewa da yayi, ganin Kharan Khan yasa yayi parking kana yace "Kharan har ka sauya kaya ne?" Murmishi kawai yayi, kana ya buɗe motar ya shiga, yanata danne-danne a waya, har Majid yayi parking ya siyo Basmati ya dawo cikin motar, sunyi nisa sosai yace "ɗazu nan fa ka gama zolayata amma yanzu naga kayi min shiru, iska cin naka ya motsa ne ko?" Kharan Khan yayi murmishi tare da cewa "uwum" ta cikin bakinsa, Suna isa gidan motoci biyu wanda suke binsu suka shigo tare da parking, Kharan Khan yasa aka kama Majid, kana ya ƙarasa ciki, cikin Sa'a yaci karo da Kharan yana shan coffee, hankali kwance ya toshe masa baki ya fita dashi ta baya, shima aka sanya shi a mota suka wuce dasu. Hannunsa riƙe da Basmati ya shigo tare da cewa "wacece a cikinku takeson Basmati?" Mona tace "nice" tare dayi masa godiya, Hajara tace "kanata ɗawainiya damu mungode" Kharan Khan yayi murmishi kafin yace "ai yiwa kaine, taimakawa mutane ya zamomin abokin rayuwa.... Kuyi hakuri wayata babu chaji, dan karkuyita zuba ido ne yasa nayi muku kaɗan anjima zamu ɗora Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam                      Book1 67-68  Inda Mona take cin Basmati ɗin sai yayi matuƙar burgeshi har wani murmishi yayi, kafin ya miƙe tsaye yace "amma ke ƴar Nigeria ce ko?" Ya kalli Hajara. "Eh amma ina fatan komawa nan bada jimawa ba" Murmishi ya sake yi a karo na biyu kafin yace "Mona matar shahazad Junaid Khan, ki ayyana a ranki kin tsere masa, abinda nakeso dake shine, ki rage tunani ni nan zan zamo muku gata ko wacce zata koma inda takeso" Ya faɗi maganar yana shafa sajen da yayi luff a gefen kumatunsa. "Bamu da isasshen lokaci, yanzu zamu bar nan zamu tafi India, sbda tserewa Shahazad, ya baza jam'i ta ko ina, mafitarmu shine mubar garin an, nariga na gama komai zamubi jirgin ƙasa" Inda yake maganar sai ka rantse da Allah har cikin zuciyarsa yakeyi, hankalin Mona a kwance tace "nifa ƙauyenmu nakeso ka mayar dani, ita kuma taimako take nema zuwa Nigeria" Kharan Khan yace "na fahimceku, Abinda nake nufi, duk wata hanya da zamubi za'a iya gano inda muke matsawar ba India muka tafi ba" Gabaki ɗaya kan Mona ya kulle a fili tace "idan har sai mun koma India a bar mu anan ai lokacin dana nemi taimakon ka bakace min haka ba" "Keee!!" Kharan Khan ya daka mata tsawa, tare da cewa "bawai sai abinda kikace zanyi ba, ko kubini India kokuma in barku anan" Tashi ɗaya suka fara kuka, Hajara kam sai ambaton sunayen Allah takeyi, gabanta na cigaba da faɗuwa. Kharan Khan zeyi magana kenan, sukaji jiniyar motar sojoji. Nigeria Abubuwa sun faru, haɗuwar Juwairiyya da Alhaji Al'amin, sati guda da haɗuwarsu Amma ya sauya musu gida, ya siyawa Malam Yusuf Mashin ita kuma ya mayar da ita ƴar gayu, a take malam Yusuf ya tara shedu aka sanya ranar auren Juwairiyya akan sadaki dubu ɗari bakwai, kuɗin gaisuwa dubu ɗari. Yanzu kam Alhaji Al'amin ya zamo ɗan gida, saboda daga yazo da mota zeyi sallama ya shigo, Kamar koda yaushe idan yana gari baya rabuwa da gidan nasu, yauma hakan take hannunsa riƙe da babbar leda ya shigo da sallama, kasancewar malam Yusuf ya fita sai Juwairiyya yasa taje ta karɓi ledar tana gaishe shi, amsa wa yayi kana yace "nama ne na kaji ki juye, jiki na rawa taje ta juye, ta dawo tsakar gida inda ta shimfiɗa masa tabarma, "Uhm kin kusa zamo wa mallakina ina jiran wannan ranar har mafarkinta nakeyi" Juwairiyya ta rufe ido tare da cewa "me kakeci na baka na zuba?" Yace "dambu" Ta kwashe da dariya, tare da cewa "uhm saura kwana shida ai" Murmishi yayi, kana ya miƙe tare da ajiye mata maƙudan kuɗaɗe ya fice ta miƙe ta rakashi, a hanya yake nuna mata photon gidan daya siya mata, kana yace kar su malam su siyi komai har kayan sawa. Kamar zata rungume shi tsabar Godiya. Malam Yusuf na dawowa ta sanar masa, yayi farin ciki harda ma ganin naman daya kawo musu. Abinda kowa bai sani ba, Alhaji Al'amin bai sanarwa da danginsa auren da zeyi ba, ko meye dalili oho. Acan ɓangarensu Dady yau suka sauka a garin su Bauchi, cikin kwanciyar hankali, tare da Iffat da Hajiya ƙarama, bayan sun gaisa a parlo, suka zube, Hakeem kam bakinsa yaƙi rufuwa, Hajiya babba kuwa ta shirya musu abincin tarba mai rai da lafiya, bata nuna musu komai ba, saboda cikar ƙudurinta, Har ɗaukar Iffat tayi ta ɗora a cinya, kana tace mata "ya jiki" "Da sauƙi" Iffat tace tana kallon Hakeem, Hakeem yace "wato kowa kinje gurinsa amma ni kinƙi kulani ko?" Iffat tayi dariya kana tace "yi haƙuri yaya gani nazo" Ta taho tanayi masa dariya, Washe gari, Dady ya koma ɗakin Hajiya babba, Iffat ta saba dashi, abinka da yaro ta bishi can, bayan sun gama breakfast ta hanyare cinyarsa tana cewa "Dady jiya da dare yaya yace zai sani a school idan ka yarda" Hajiya babba ta galla mata harara tare da kawar da kanta gefe, Dady yayi murmishi kafin yace "eh ni da kaina zan kaiki amma sai first an dawo hutu" Iffat ta hau  tsalle tana murna, Dady ya miƙe tare da cewa "nikam barin je in duba abubuwan da suka wakana bayan tafiyarmu kuyi hira ga Eshat nan" "Toh Alhaji a dawo lafiya" Yana fita ta kamo kunnen Iffat tace "wlhi idan kina shigo min sashe na sai na yankaki, kuma idan naji kin gayawa wani sai na ƙona bakinki" Iffat ta toshe baki, tare da miƙewa zata fice, Hajiya babba ta fincikota ta faɗi ƙasa, kana tace "munafuka ƴar zina" Iffat ta sunkiyar da kai, tare da fakar idon Hajiya babba ta ruga part ɗin Hajiya ƙarama da gudu. Cikin tuhuma Hajiya ƙarama tace "my Eshat lafiya?" "Babu kowa" Iffat ta faɗa tana zaro idanu. Har rana tayi Dady bai fita aiki ba, da yazo cin abinci yace "a kira masa Iffat" Sai da Hajiya babba tayi jimm kana ta miƙe taje sashen Hajiya ƙarama ta tsaya a bakin ƙofa kafin ta dawo, "Alhaji tayi barci" Dady yace "ikon Allah barcinta babu wuya, nazo wucewa naji firarsu ita da hajiya" Aran Hajiya babba kuwa, baƙinciki ne yayi kwance sam bata son taji Dady ya ambaci sunan iffat ko kaɗan. Hakeem ya mayar da hankalinsa ga jarabawar ƙarshe da suke yi na s.s.c.e, shi yasa bai cika zama a gida ba, sai dai idan ya dawo, yana cin abinci zai wuce gurin aiki, hakan yayiwa Hajiya babba daɗi, sbda batason taraiyyarsa da Iffat. Horn driver yayi a bakin get ɗin gidansu Amani, mai gadi ya taso da gudu ya buɗe get ɗin tare da yi musu sannu da zuwa, cike da isa da iko ta zuro ƙafafunta waje, kana ta fito da jikinta duka tana gyara mazaunin gilashinta, gyara zaman mayafinta tayi tare da fara takawa i zuwa cikin gidan, kamar mai tsoron taka ƙasa, cikin rashin sanin inda ta dosa ta murɗa handle ɗin ƙofar part ɗinsu Mona, Mahbob dake tsaye yana gyara zaman hular kansa suna magana da Amani, ta Kunno kai, a hankali ta jawo gilashinta tare da ƙaremusu kallo tace "Please nan ne gidan Alhaji Auwal?" Amani ta ture Mahbob ta ƙarasa fitowa gurinta kana tace "dallah banziya marar tarbiyya ki koma idan aka koya miki sallama da tarbiyya sai ki zo ki tambaya, nan gidan ya samu ingantaccen yabo kinji" Shikam Mahbob har ya riga ya fice, sbda baya son hayaniya, Naeema ta zaro ido kana tace "kee!!!, kinsan dawa kike magana kuwa?" "Ahh to dawa nake magana idan banda marar tarbiyya?" Naeema ta danna number Batool tana ɗauka, Naeema ta fashe da kukan ƙarya kana tace "tayi mistake ɗin shigowa yaran mijinta sunyi mata duka"....! Uhm nace kuyi haƙuri har yanzu banyi muku mai yawa ba. More comments more eheem Mom Islam *💋MURAYU A TARE 💋* Mom islam             Book1 page 69-70 Tuntsirewa da dariya Amani tayi, kana tace "shagali, sharri ga mai yinka" Ta shige ciki tare da bugo ƙofa. Naeema tayi ƙwafa tare da gyara zaman gilashinta, taci gaba da tafiya zuwa part ɗin su Batool,  cikin zafin rai, take bubuga ƙofar, Batool ta buɗe mata tare da rungumeta, Suna shiga ciki, kai tsaye suka wuce bedroom ɗin Batool, Naeema tace "wlhi anty Batool yaran mijinki basu da kunya harni zasu gaggayawa magana?" Batool ta tashe bakin Naeema da tafin hannunta, cikin rage murya tace "haba Naeema so kike yi mahaifinsu yaji kinsan fa yana gida?" "Mtsew ai yaran ne basu da tarbiyya wlhi" Naeema ta faɗa tana cire mayafin jikinta, "Yauwa ƙanwata, abinda nakeso dake, ki yi iya yinki gurin farauto zuciyar Mahbob, wlhi ba ƙaramin ji dake zai yi ba, kinga inda kika sake fresh ne ga kumatu kin ajiye" "Highe anty Batool duk ma ba wannan ba, shine kika zuga su Dady da mama dole sai na auri wannan yaron?, Bayan kinsan a tsarina babu batun aure har sai na cika muradi na?" Batool ta taɓo kafaɗar Naeema kafin tace "nasani amma dole ki kawar da ƙudirinki, tunda ga aljannar duniya zaki samu, ki wataya inda kike so ki taka wanda kikaga dama, duk da ke ba matar gwamna bace, amma dole da yawan mutane zasu biki, girkifa sai kinga damar yi har wanki wanke-wanke da guga, kinga kuwa rayuwar jin daɗi zakiyi" Duk da haka dai Naeema batace komai ba, Wayar Batool ta fara ruri, kallon screen ɗin wayar tayi, kana ta miƙe da sauri, tace "ki shirya zuwa gaishe da sirikinki" Naeema ta waro ido kafin tace "uhm nifa banason takura" Batool tace "nidai karki bani kunya" Batool na fita Naeema ta cire rigar ta ya rage daga ita sai bra da dogon wando, A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin Abba, tare kutsa kai ciki, ga mamakinta taga har ya shirya cikin shadda fara, tasha aikin wuta, Zama tayi a gefensa tare da kamo hannunsa tace "wlhi na ɗauka kana barci har yanzu shi yasa ban shigo ba" Cike da so da ƙauna ya janyota jikinsa, yana cewa "inason fita da wuri shi yasa" "Naeema tazo" Batool ta faɗa, tana rungume a jikinsa. "Masha Allah tazo lafiya?" "Lafiya lau" "Am na mance ban gaya miki ba, jiya yayana yakai dukiyar auren Mahbob gidanku" Batool tayi kamar zata shige jikinsa, a fili tace "Masha Allah, Ubangiji ya sanya alkairi" Abba ya amsa "da Amin". Ta ɗauko agogon hannu ta ɗaura masa, Kana ya miƙe tsaye, itama miƙewar tayi hannunta riƙe da hula, suka fito parlo. "Barin yiwa Naeema magana" Tana tura ƙofar ta ganta daga ita sai bra da dogon wando, murya ƙasa-ƙasa tace "dan Allah ki sanya kaya da hijabi ki fito ku gaisa" Naeema ta turo baki, tare da cewa "uhm ni wlhi kina takuramin da yawa" Hijabi ta saka kafin ta wuce parlo, zubewa tayi ta gaishe shi, ya tambaye ta yasu mama, tace masa "lafiya lau" Kana ta koma ɗaki, Batool tazo ta zauna kusa dashi, dama ta riga da tasa masa hular, Abba yace "gaskiya Naeema akwai hankali ga tarbiyya" Batool tace "kai Alhaji" Yace "da gaske gidanku ai babu wanda zai samu mata yayi buruss iri mai albarka" Batool ta kalli agogon dake manne a jikin bango, ƙarfe 12:30pm, Batool tace "Alhaji breakfast fa?" "Zanyi yanzu" Taje kitchen ta ɗauko flaks na ruwan zafi da gwangwanin madara da bonbita ta kawo, da cup kana da bredi, bayan ta haɗa masa shayin ta miƙa masa, ta kunce ledar bredi ta miƙa masa, Suna hada ido sukayi murmishi a tare. Yana kammala breakfast ɗin ya miƙe tare da cewa "sai na dawo" "Allah ya kiyaye hanya Allah ya tsare" Batool tayi masa kana ya fice. Kai tsaye part ɗinsu ya wuce, dukkansu suna zaune a parlo yai sallama ya shiga, "walaikumusalam" suka amsa, kowanensu ya gaishe shi, lokacin suma suke karyawa, Bayan ya amsa yace "ankai kuɗin auren Mahbob" Inaya ta taho da gudu ta rungumeshi, Cikin tsokana yace "auta maiyasa kwana biyu bakya zuwa part ɗin momynki?" "Babu komai" Inaya tace. Daga Batool har Aseela babu wanda yace komai, bare Huda, da bakowa ba. Da kallon mamaki yabi Amani, sbda ya santa farin sani, baya taɓa magana tayi masa banza, sannan duk abinda yake so shi takeso " "Amani lafiyarki kuwa?" Amani ta ƙirƙiro murmishin yaƙe kana tace "lafiya Abba" Abba yace "ba haka kike ba maiyasa kika sauya" Cikin ƙosawa da tambayoyin Abban tace "Allah ya sanya alkairi " Amin yace, jiki a sanyaye ya miƙe, tabbas gabaki ɗaya yaran sun sauya masa, har Inaya da batasan komai ba, "Ku shiga ku gaishe da budurwar Mahbob tazo ɗazu" "Toh" sukace cikin haɗin baki. Yana fita sukace babu inda zasu, Amani ta kalli Huda tace "wlhi idan kika sake zuwa sashen Batool sai na ɓata miki rai" Huda tace "Anty Amani, wlhi itace takeyi min masifa" "Ai ƙarewar masifa ta dukeki shine zata tabbatar da ita ba kowa bace fashe muguwa" Aseela tace "Abin mamaki aure daɗi, Abba baya shigowa ya duba tafiyarmu, ko yaga mun ci abinci ko bamuci ba, sannan ko fira ya dena yi damu" Amani tace "mtsew ke kika damu dasu ma" Huda tace "za'ayi bikin Ummana yau nakeson tafiya" Aseela tace "bari bro Mahbob yazo sai ya kaiki" Acan ɓangaren Umma kuwa, tayi sharr da ita, saboda harda shafe-shafen zamani akayi, tayi kyau, abokan malam Ado, wato mahaifin Huda, sunyi rawar gani, dan har karɓar auren sukayi, sai ranar ɗaurin auren Mahbob ya kawo Huda, a hakan ma yace "da yamma zai zo ya ɗauketa. Umma tayi kyau sosai, ta haɗe cikin atamfa ɗinkin riga da skirt, dama ba jiki ne da ita ba, sannan kuma bata da wasu yawaitar shekaru, sbda bata wuce 35yrs ba. Huda ƴar amarya, tare Umma tayi musu ɗinkin, yanzu kam ta rage yi mata kyara ko hantara, Zuwa la'asar motocin ɗaukar amarya suka zo guda uku, sharoon, yawancin mutanen anguwar sai da suka tafi, wasu sunje ganin ƙwaƙwaf, wasu sunje Allah ya sanya alkairi. Kasancewar Mahbob yazo lokacin da motocin zasu tafi, yace Huda ta shiga ya Kaita, bayan sun ga gida, suka yiwa Umma sallama ya koma da ita gida. Wannan gida shi ake kira da aljannar duniya, saboda gidan ya haɗɗu ya gaji da haɗuwa, mai kushe kyansa da tsaruwarsa sai maƙiyi. Wasu ma cewa suke yi ko sana'ar yankan kai mijin nata yakeyi, Lokacin da motocin suka dawo domin komawa da mutane, Maryamah na gurin Umma, sai gaya mata sirruka ake yi, daga ƙarshe suka yiwa Umma sallama suka tafi, Ita kuma ta buɗe toilet ta shiga, tsayawa kallonsa tayi, wasu abubuwan ma batasan inda ake amfani dasu ba, ta kunna famfo tayi alwalah, ta fito ta kabbara sallah. Bayan ta idar gami da yin addu'a, ta ninke sallahya ta hanye gado, Kiran sallahar isha'i ne da akayi, yasa ta sakko tayi sallah, lokacin Alhaji Lukman ya shigo, ita kuma tana ninke sallahya, Barka da shigowa tayi masa, kana ta zauna a bakin gado, Hannunsa riƙe da ledoji guda biyu, ya ajiye tare da cewa "kawo mana faranti" Da lalube taje kitchen ta ɗauko da cokali da cups ta dawo, umartar ta yayi da ta buɗe kajin da gasashen naman, ta zuba ko wanne kaɗan-kaɗan, ya zauna suka fara ci, ta tsiyaya musu 5alive mai sanyi, Ita ta fara cire hannu kana ta miƙe taje tayi brush ta sauya kaya zuwa na barci, Shima a nasa ɓangaren fridge yakai, kana ya koma ɗakinsa ya sauya kaya zuwa na barci. Ɗakinta ya dawo, lokacin ta kwanta, abin tambaya anan banga sunyi alwalar masu first night bane HHH, ya bi bayanta ya rungume, Kun sanfa Umma an tsumu sosai, sai wani turo masa ƙirjinta da yaci kuɗi tsabar gyara takeyi, shiko yanajin tudun nonuwan yayi burus ko meye dalili oho, shafo gashin kanta yayi, wanda yasha gyara, yace "maiyasa ba'ayi min kitso ba?" Murya ƙasa-ƙasa tace "uhm babu komai" Burinta bai wuce taji ya zura hannu a ƙasanta ba, sbda a halin yanzu duk ta fara tsiyaya, sai wani mammatse ƙafafu takeyi, harda dabara duk dan kar ya gane ta, Bakinsa yakai kan nipple ɗinta, hannunsa ɗaya yana murza ɗayan, Daga ƙarshe ta kai hannunta gabansa, taji wani babban Abu, Murya ƙasa-ƙasa tace "meye wannan?" "Robar fitsari ce" Umma ta zaro ido. Acan Garin Bauchi, Ummi da Aliyu sunata shirye-shiryen komawar Tasneem garin Kano, yau kwanan Haneefa biyu da zuwa, tazo ta gaishe da Tasneem da jiki, Jiya suka koma sabon gidansu, ita kuma Ummi gobe zasu koma, Washe gari, dama mota ta gama kwashe kayan, su Tasneem da matar Aliyu sunje sun gaya kayan, zuwa yamma Umma tayiwa mutan gidan sallama ita da malam suka tafi. Nanfa tsegumi ya tashi, kowanensu na tofa albarkacin bakinsa, Kwanansu biyu da komawa, Aliyu yace Tasneem ta shirya gobe zasu tafi Kano harda Malam. Washe gari, kuwa ta shirya, cikin baƙar abaya tasha ado, kasancewar Aliyu ya siyo mata kaya da ɗan yawa, da safe suka wuce tasha suka hau mota zuwa Kano,                      ***** Cikin hukuncin Allah sai gashi sun shigo Kano, bayan an saukesu a tasha, suka tari napepe zuwa anguwar Kurna, Ikon Allah duk haukar da Tasneem tayi bata mance da gidan Hajiya ba, suka ƙwanƙwasa ƙofa, wani ɗan ƙaramin yaro ya buɗe yana ta kallonsu, suka shiga, bayan sunyi sallama a ƙofar ɗakin hajiyan, bata ɗauki Muryar Tasneem ɗin ba, sai ganinsu tayi sun shigo, Hajiya ta mutsike idonta ta buɗe kana tace "Tasneem ashe kina raye?" Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi. Ummi da Aliyu sukace "Hajiya farin ciki zakiyi ba kuka ba" Tasneem tace "Hajiya ina uncle" Hajiya tace "ya lafiya ko jiya sai da yayi maganar ki, ina Iffat jaririyark?" Wasu zafafan hawaye suka kwaranyo a idanun Tasneem, zata yi magana kuka ya sarƙeta, Hajiya ta ɗaga waya, ta kira Uncle, yana ɗagawa tace "ga marainiyar Allah ta dawo gida, Tasneem" Jikin Uncle na karkarwa yace "gani nan zuwa Hajiya" Ba'a ɗau tsawon lokaci ba, sai gashi nan ya shigo, tsabar gigicewa a ƙasa ya zauna yana ƙarewa Tasneem kallo, "Ikon Allah ashe zamu sake haɗuwa, adu'armu bata faɗi ƙasa banza ba" Kana yace "Tasneem su waye waɗannan" "Sune suka taimakeni, Uncle wannan shine ya tsintoni, ta nuna Aliyu, kana tace "malam kuma mahaifin Aliyu ne shine yayimin magani, ga mahaifiyarsa itace ta kula dani.... Idan har naga comments sosai, zanyi wani, idan babu comment an jima  bazaku samu ba🤩 *💋MURAYU A TARE💋* Mom Islam         Book1 Page 71-72 Cikin jin daɗi Uncle yace "Masha Allah" tare da kallon Ummi da malam kana yace "muna godiya Ubangiji ya saka muku da mafificin alkairi" Hajiya tace "Aliyu haƙiƙa kayi namijin ƙoƙari, Ubangiji yasa a gama da duniya lafiya" Aliyu ya amsa da "Amen" Hajiya tace "Tasneem jeki kitchen ki ɗibo musu abinci" Tasneem ta miƙe tana murmishi kana ta wuce kitchen, Babbar foodflaks ta ɗauko taci ka musu shi da shinkafa, sannan ta ɗauko na miya tasa miya, ta zuba soyayyun nama kamar inda ta gani a ajiye, Sai da ta ɗauki cokula da farantai masu kyau, kana ta fito ta kawo parlon Hajiya. Har yanzu Uncle bai gaji da kallon Tasneem ba, shi a tunaninsa ma tariga da ta mutu, Ƙaramin yaron da suka samu a bakin get ne ya fito yana cewa "Hajiya na bige wayo Allah" Hajiya taje da sauri tana duba masa goshin da ya bige, "Babu abinda ya sameka kai dai raki irin naka" Tasneem kam kallon yaron takeyi babu ko ƙiftawa, sbda yayi mata kama da wani sashi na rayuwarta, sam bata bari kowa ya lura da hakan ba, amma kash Hajiya ta gane kallon da Tasneem take yiwa yaron, kawar da kai Tasneem tayi, tare da zuba musu abincin, Uncle ya fito waje tare da kiran Hajiya, Bayan Hajiya ta fito yace "Hajiya mutanen nan sunada kirkin da suka can canci ayi musu babbar kyauta, a ganinki meya kamata ayi musu dan nuna godiya?" Hajiya tace "sosai ma kuwa, kaga inda Tasneem tayi kyau kamar ba itace ta fita cikin wani yanayi ba, munyi cigiya har mun gaji, nidai a nawa ganin ka biya musu kuɗin Hajji dukkansu" Uncle yace "nima nayi tunanin hakan, amma sai nake ganin kamar zasufi buƙatar kuɗi" "A'a kayi hakan, zan basu dubu ɗari bayan sun dawo duk da nasan ba komai zatayi musu ba" "Allah ya shige mana gaba" Uncle ya faɗa cikin amincewa da shawarar Hajiya. "Malam dan Allah ka rage wannan masifar da kake yi, ita kanta Inna da tasan haka ne zai faru, Hajara ta tafi taƙi dawowa Wlhi bazata soma ba" Kamar ana ƙara masa faɗan, yace "shikenan ai talauci ba hauka bane, kinfi son a dinga nunani a layi kenan, babu wanda bashi da labarin inda Hajara taje, tsakanina daku Wlhi ba zan yafe ba" Ran goggo a ɓace ta gyara ɗaurin zaninta, a tunzure ta fara magana, "Karka yafe ɗin, yarinyar da auranta ya mutu ka tozartata, ai a tunanina abin ka jata a jikinka ne, shine zaka dinga wani surfewa mutane masifa, ni nan mahaifiyarta Wlhi na fika shiga damuwa, dan haka karka sake yimin maganar Hajara" "Anyi ɗin kiyi abinda zakiyi, ita mahaifiyar taki ai abin duniya tabi, shiyasa ta turata garin larabawa nemo kuɗi, dan haka ki ficemin a gida" Goggo ta taɓe baki, kafin tace "au ka mance gida ya zamo nawa, harda takardar sheda, kuɗina nasa na siya dan haka sai ka barmin gida" Jikin malam a sanyaye ya janyo kujera ƴar tsugunno ya zauna. Hausawa sukace rana bata ƙarya.. Yau kam mutuniyarku ta shiga daga ciki, a wani katafaren gida ilahirin motocin kawo amarya sukayi Horn, mai gadi ya buɗe, nan fa kallo ya koma sama, duk da kunsan garin Kano akawai tsararrun gidaje, to ga wani ma, wanda sai ka rantse a ƙasar Turai akayi ginin, yawancin murafen ƙofofin kai kace na zinare tsabar walwalin da yakeyi, Abin mamaki babu dangin Alhaji Al'amin sai iya dangin Juwairiya ta fannin babanta da mamanta, sai abokan arziƙi, ba wasu aiyuka sukayi ba, sbda gidan a gyare yake, anayin sallahar la'asr motocin komawa da mutane suka fara ɗibarsu, Gida ya rage iya Juwairiya, sosai take jin tsoron gidan, musamman ma da ya kasance tafkeke, a fili ta fara shawarar idan har sun zauna sun fahimci juna zata ce ya nemo mata ƴar aiki ta dinga ɗebe mata kewa. Har akayi sallahar magriba bai shigo ba, har akayi isha'i shiru, hankalin Juwairiya ya tashi sosai, ta ɗaga waya ta kira shi, ring ɗaya ya ɗaga tare da cewa "amarya bakya lefi, Wlhi tafiya ce ta kamani zuwa Dubai, bani da inda zanyi idan ba can na tafi ba" Jikin Juwairiya na ɓari tace "har ka tafinne?" A'a ban riga da na tafi ba, akwai wasu muhimman takardu da nake cikewa insha Allah ganinan zuwa" "Allah ya kawo ka lafiya" Juwairiya tace hankali a tashe. Har barci ya fara ɗaukarta taji alamun shigowarsa, da sauri ta murza idonta tare da tashi zaune, kana tace "baby Wlhi kasa na firgita" Al'amin yayi murmishi kafin ya ƙaraso gurinta, yace "matsoraciya" Tare da lakutar hancinta, Murmishi tayi kafin ta zauna kusa dashi a bakin gado, a shagwaɓe tace "uhm nikam Wlhi tafiyar nan bada son raina za'ayi ta ba, dan Allah karka tafi ka barni" Cikin kwantar da hankali yace "insha Allah, babu abinda zai sameki, nidai fatana koda yaushe mu kasance cikin so da ƙaunar junanmu, Kafin ya kamo hannunta suka wuce kitchen, nidai cewa nayi ko pillow aka miƙo min wallahi zanyi barcina a kitchen, yayi kyau sosai, ya buɗe gurin gasa cake ya ɗauko kaji a faranti mai kyau, kana ya miƙa mata ya rufe, Karɓa tayi tanayi masa murmishi tare da kallon farantin dake cike da gasashen naman kaji an yankasu, Riƙe da hannun juna suka taho parlo, da kansa ya buɗe fridge yace "wane irin lemo zakisha?" "Fanta" Juwairiya ta faɗa. Kawo mata yayi, ya ajiye akan table kana ya dawo ya zauna, Kamar wata jaririya ya ɗauko tare da miƙa mata baki, ta ƙarɓa tana yi masa murmishi. Bayan sun gama ci ta tattare kayan ta mayar dasu suka koma bedroom ɗinta, umartar ta yayi da tayi alwalah, already shima yayi, suka kabbara sallah raka'a biyu, kana ya dafa kanta yayi mata addu'a sannan ya riƙe mata hannu suka haye gado, sun raya daren cike da soyayya mai tsayawa a rai, musamman ma inda yake lallaɓata kamar wani ƙwai, a daren sai da ya mayar da ita cikakkiyar mace, tare da yi mata alƙawarin zasu tafi honeymoon ta zaɓi ƙasar da takeso, bayan ya dawo daga tafiya zasu wuce. Washe gari tun asbha Iffat ta tashi da zazzaɓi, wanda ya tayar wa da mutanen gidan hankali, banda Hajiya babba da take shirin ƙaɗata a gidan, Jikin Dady na rawa yace wa Hajiya ƙarama ya kamata mukai Eshat hospital sbda jikin nata ya tsananta" Ya ƙara da cewa "ba zanyiwa Hajiya babba magana sai ta kaita" Sam Hajiya ƙarama bataji daɗin abinda Dady yace ba, amma batasan ya fahimci akwai wasu matsaloli sai taja baki tayi shiru, dama ta riga da ta shirya Iffat ɗin, bayan gari yayi haske Dady ya tafi da Hajiya babba da Iffat Asibiti... Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE, Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700 Munkusa gama book1  abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding. Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Nagode *💋MURAYU A TARE 💋* Book2 coming soon 💃 Takensa *Wasa⛹️‍♀️farin girki🍵🔥* Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam        Book1 Page 73-74 Cikin ƙungurmin jejin garin Shahaza forest  Sahla take ci gaba da tafiya, a gajiye ta yada zango a gindin wata bishiya, Sai fitar da numfashi takeyi mai cike da alamomin gajiya, Ƙugin da cikinta yayi ne yasa ta buɗe jakarta ta ciro gurasa guda ɗaya ta dinga ci kamar wacce bata taɓa ido biyu da abinci ba, Acan saman bishiyar kuma wani ƙaton maciji ne yake saukowa yana harin gurin Sahla, kamar ance ta waiga, cikin sauri ta wurgar da ragowar gurasar hannunta kana ta ɗauki jakarta zata ruga da gudu, Cikin rashin tsammani ta zame a kan ganyayyakin dake shimfiɗe a ƙasa, ta kurma ihu tare da cewa "abar bauta ki taimakeni" Kafin takai ƙasa macijin ya shimfiɗe a ƙasa, ganin a kansa zata faɗo dole, yasa ta runtse idanun ta tare da gama saddaƙarwa ta mutu an gama, Duk da yanayin fatar jikin macijin ta ban banta da sauran majizai, hakan yasa ta sake razana, gata uwar tsoro, Shiko yabi ƙasa ya daɗa gyara mata kwanciya tayi luff a gadon bayansa, ashe sumewa tayi tsabar fargaba, Abin mamaki da al'ajabi macijin ya rikiɗe zuwa fatar larabawa harda yanayin fuskar ma, ya ɗauketa ya tsallake ruwa kai kace iska, sbda ni kaina bazance ga lokacin da suka tsallake katafaren kogin dake gabansu ba, cikin wasu lokuta ya kawo ta gidansu, ikon Allah kenan, gidan dai zamu iya cewa kamar gidan tarihi, sau da yawan turawan yankuna da dama, wannan gida ya mugun tsole musu ido, ansha kawo masa hari ta fannin tsafi, adu'ar musulmai akan galaba, duk Allah besa sun shiga ba, a taƙaice dai ginin kai kace bada ƙasa aka yi shi ba, sannan tambari da adon dake jikin ginin shine zai matuƙar firgita mai karatu, gini ne wanda ya amsa sunansa gini, sannan tambarin yawancin masu faɗa aji wanda suke da tarihin wannan guri sunada hoton tambarin, ada kenan zamu ce da kowa yake iya ganinsa, duk wanda kuka gansa a gurin zamu iya cewa yakai ƙwaro sosai, ma'ana Jarumi, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa shahazad Junaid Khan ya ƙirƙiri wannan jejin kenan, sukuma mazauna jejin tun kafin shahazad ya shirya wani tuggunsa suke zaune a ciki" A hankali ta buɗe ido, tare da kallon inda take, da sauri ta waiga taga babu kowa a ɗakin, hankali a tashe ta miƙe zaune tare da sake gyara zaman jakarta, kallon abubuwan da aka kewaye ɗakin, jikinta na karkarwa ta zuro ƙafafunta ƙasa, kana ta kalli fitillun da aka kunna sunkai guda goma, Shi kansa gadon da take kwance kyawunsa yafi gaban kwatance, Wata kyakkyawar mata ta fito daga cikin ɗakin dake kallon inda Sahla take, cikin zazzaƙar murya budurwar tace "sannu dame zan iya taimaka miki?" Sahla tace "inaso a mayar dani hanya, ni matafiya ce" Budurwar ta yi murmishi kafin tace "karki damu kafin nan ki bari Ludtfi yazo" Sahla ta ware ido, kana tace "waye shi?" Zaki gansa amma kafin ga wannan yace "ki tafi dashi, yanada labarin gurin shahazad zakije, sannan yace ki riƙe shi a matsayin kariya kuma dukiya, idan kinason dawowa nan ki ajiye diamond ɗin a gurin da rana take fitowa, sannan ki rufe idonki" Sahla tace "Nagode" Nocking ɗin ƙofar da akayi ne yasa Karan Khan firgita, murya ƙasa-ƙasa yace "ƴan sanda ne" Ya kamo hannun mona da na Hajara, a sukwane ya fice dasu ta ƙofar da jami'an Basu san  da ita ba, Suna tsaye suna shirya inda zasu yi su kama karan Khan ashe ya tsere musu, Kowanne da waya a hannunsa, suna magana a hankali tare da tafiya cikin sanɗa, A hankali suka faɗa cikin gidan, suka hau bankaɗe ko ina amma sukaga wayam, sawun takalmin Karan Khan da suka gani a hanyar da suka fice ne yasa suka fara shiga ta hanyar, amma sai dai kash sun tsere. Acan ɓangaren Shahazad kuwa, ya daɗa baza jami'an tsaro ta hanyar mota da jeji da jiragen ƙasa,  lokaci guda ko ina suka ji labarin an sace mona ita da ƴar aikinta,  ƴan jaridu suma ba'a barsu a baya ba gurin bincike da yaɗa sanarwa, Shi kansa yana binciken duk wani motsi na mutanen garin a na'ura.            💋 Wani irin juyi yayi akan kujerar da yake zaune, a fusace ya miƙe ya wankawa sojan dake tsaye a gabansa mari, "Get out of my office" Cikin ladabi sojan ya fice, Zancen banza zancen wofi, abin mamaki duk yawan mutanen garinnan ace sun kasa gano min inda mata take, Wlhi nan da kwana uku idan ba'a gano inda take ba, sai na sa an buɗewa ƴan garinnan wuta dukkansu, Da sauri Ministan harkokin kayayyakinsa da suke shige da fice, ya miƙe na kusa dashi ma suka miƙe cikin haɗin baki sukace "ayi mana sassauci mai girma shahazad, a fusace ya miƙe tare da cewa... Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE, Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700 Munkusa gama book1  abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding. Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Dan Allah kar ayi min Vtu Please👏  banda Vtu idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Nagode *💋MURAYU A TARE 💋* Book2 coming soon 💃 Takensa *Wasa⛹️‍♀️farin girki🍵🔥* Mom Islam *💋 MURAYU A TARE 💋* Mom Islam _Ina taya masoya barka da sallah, Allah Ubangiji ya biya mana buƙatunmu na alkairi, Allah yasa munada rabon ganin ta baɗi da rai da lafiya_ 💋 75-76 Sharce zufar dake sintiri a fuskarsa kana yace "na baku nan da kwana uku, bayan nan idan Mona bata dawo ba duk hukuncin da na yanke shine dai-dai da tsarina.." Dukkansu suka amsa da cewa "mai girma shahazad da yardar Ubangiji hakan ma bazai faru ba" Ko kallonsu beyi ba ya fice. Kai tsaye ya nufi gidansu, a nutse ya zauna akan kujera 3 sitter, kana ya shafin gashin da ya kewaye masa baki, a fili ya furta "never..!!" Rai a ɓace ya miƙe ya nufi upstairs, da sauri yake haye benen har yakai ƙofar ɗakinsa, hannu yakai kan handle ɗin ƙofar zai buɗe, kamar wanda ya tuna wani abu, sai ya fasa, ya koma ƙofar ɗakin Mona, jiki a sanyaye ya buɗe ƙofar tare wucewa bedroom ɗinta, kallonsa yakai kan kayan ɗakin tare da kallon madaidaiciyar hand bag ɗin dake ajiye akan gado yayi, kana ya buɗe jakar yaga babu komai, wurgi yayi da ita gefe tare da miƙewa ya kunna computer ɗin Mona, a farkon gurin searching yaga sunan Kharan, a tsorace ya shiga profile ɗinsa, kana ya hau binciken asalinsa duk da shiɗin ba ɓoyayye bane a gurinsa, Har chatting ɗinda sukayi da Mona duk ya gani, sbda har Whatsapp ɗinta ya duba, Cikin yanayin jarumta mai cike da tsantsar tunanin irin hukuncin daya dace ya miƙe, kana ya hau kewaye ɗakin yana bubuga hannu. Cikin sauri ya ɗauki number Kharan yayi saving a wayarsa, kana ya rufe computer ya koma ɗakinsa. "Hello Samir ga number wanda ya sace mona nan na turo maka" Samir yace "ai munada numbersa, a halin yanzu bata shiga, sannan mun bibiyi layin an dena amfani dashi" Shahazad ya cilla wayar kan gado tare da ture table ɗin dake kusa dashi, glass cup ɗin dake kai ya fashe, be bi ta kansa ba, ya dafe kansa. Sahla na tsaye ita da budurwar nan, sai ga wani kyakkyawan saurayi ya shigo, fari dogo kayan da yasa ba irin nasu wanda suke sawa bane, sbda ya banbanta da shigarsu, doguwar riga ce a jikinsa mai tambarin zanen dake jikin ƙofar shigowa, rigarsa har ƙasa baka iya ganin ƙafafunsa, sai da budurwar ta rusuna da kanta kafin tace "ya shugaba, baƙuwarmu tana son wucewa" Kansa a sama yace "an gama" Kana ya shige ɗakin da wannan budurwar ta fito, Shin Ludtfi mutum ne ko aljan? A hankali suka fito tare da budurwar ta nuna mata hanya kana ta koma cikin gidan, Sahla ta juyo ta kalli ginin, ya matuƙar bata tsoro da mamaki, sai dai wannan tambari da ta gani, bazai taɓa wuce mata ba, kamar ƙiftawar ido, ta tsallake kogin, kana taci gaba da tafiya, Tafiya takeyi kanta tsaye, tunda tasan wannan hanyar zata sadata da babban titin da zata je garin SABHA, wato garinsu Shahazad. Idan kaga inda take tafiyar kai kace bata sauri, sbda ƙafarta ko takalmi babu, Tashi ɗaya taga yamma tayi sosai, hankali a tashe ta fara tunanin inda zata yada zango, batayi yunƙurin tsayawa ba taci gaba da tafiya har Allah ya kawo ta kusa da bakin titi, Sahla tayi murmishi tanaci gaba da rungume jakarta, a gefen hanya ta zauna, tare da gyara zaman jakarta a kan cinyarta, cikin Sa'a wata mota ta hasko fitila, cikin sauri Sahla ta miƙe kana ta taho da gudu tana cewa "temako -temako" Drivern ya yi murmishi tare da kallon abokinsa dake kusa dashi a fili yace "sabuwar kamu" Dukkansu sukayi murmishi, Har ta cire rai zasu taimaka mata, sai gashi sun buɗe mata ƙofar baya, ta shiga tare da sake rungume jakarta. NIGERIA( Kano Sai washe gari Uncle ya kai su umma tasha, bayan albishir da yayi musu na zuwa Makkah dukkansu, tare da kyautar dubu ɗari uku, sosai Tasneem taji daɗin kyautar, sbda harda ita aka yi musu rakiyar, basu dawo gida ba sai da motar su ta tashi, a hanyarsu ta dawowa gidan Hajiya, Uncle ya hango Zahraddin yana cikin mota yana waya, duk da ance fuskar masoyi ko Muryar masoyi bata ɓacewa masoyin gaskiya, tabbas Tasneem ta mance da kamaninsa, amma tunda ta samu lafiya soyayyarsa take yawo a ko ina na jinin jikinta, Cikin ɗaga murya uncle yace "yarona..." Kunsan meye?" Wannan taɓa ka lashe ne, aiyuka ne sukayi min yawa shiyasa banyi muku typing da yawa ba, amma insha Allah komai yanzu yayi sauƙi alhmdulilah. Sannan albishir ɗin da zanyi muku shine, Kawo kunnenki kiji👂 Idan har kinason gano bakin zaren labarin, ki bibiyi book2&3 dake shirin zuwa nan bada jimawa ba, Shin kun shirya jin zazzafar cakwakiya🤷‍♀️ Mom islam💋08141799224 *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 77-78 Zahraddin ya kawar da wayar daga kunnensa, kafin ya ware ido, Da sauri ya fito daga mota, yana cewa "Uncle a ina kaga Tasneem?" Uncle yayi murmishi, su kuma idanun su suka sarƙe ana juna, a nutse yake ƙare mata kallo a zuciyarsa yana jin zafin nesa da juna da sukayi na wasu shekaru, tabbas soyayya abin so ce, musamman idan ka gamu da masoyin gaskiya, Uncle ya tsaya yana kallon irin yanayin da suke ciki, a fili ya furta "yaran zamani babu kunya, to zakizo mu tafi ne ko zaki bi mijinki?" Tasneem ta sunkiyar da kanta ƙasa, sosai kunya ta lulluɓeta, tarasa yanayin da takeji game da Zahraddin ɗin. A kunyace ta rufe murfin motar da bata san lokacin da ta buɗe ba, Zahraddin na tsaye Uncle yayiwa motar key suka wuce. "Ikon Allah ashe ina da rabon ganin mata, ashe zamu sake rayuwa cikin farin ciki kamar inda mukayi a gidana". Kana ya shiga mota ya wuce gidan Hajiya. A mota Tasneem sai sunkuyar da kanta ƙasa tayi, saboda kunyar Uncle da ta lulluɓeta, har suka iso gidan Hajiya kanta na ƙasa, shiko da ya lura da yanayin ta sai yayi murmishi, bayan yayi horn mai gadi ya buɗe masa ya shige, tare da parking motar, kafin ya fito ta riga shi fita da sauri ta shige ciki gurin Hajiya. Hajiya na ganinta ta washe baki, tana cewa "ikon Allah keda waye kiketa sauri har zaki murjemin ƙafa?" Tasneem tasa dariya tana cewa "Uncle ne Wlhi" Kafin Hajiya ta sake magana taji muryoyi biyu sunyi sallama, Hajiya da amsa da "wa'alaikumussalamu" Uncle ya shigo shi da Zahraddin, kasancewar Uncle ɗin na tsaye motar Zahraddin ta shigo shine suka shigo tare. Hajiya na washe baki tace "lale marhabun, angona sannu da zuwa" Zahraddin yayi murmishi kafin yace "ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe, shine ko ki kirani a waya kicemin Tasneem ta dawo ko?" Uncle yayi gyaran murya, wacce tasa Zahraddin gimtse dariyar da ta kufce masa, Hajiya tace "kaga tashi ka shiga ciki, yanzunnan ta wuce" Sum-sum ya miƙe ya shige, kai tsaye ɗakin da take, duk da besan inda ta shiga ba, cikin Sa'a ya hango ta zaune akan gado, da murmishi a fuskarsa ya ƙarasa, ita ko ta juya baya kamar mai tunanin wani abu, Ta baya ya rungumeta, har ta buɗe baki zatayi ihu ya rufe mata baki tare da ɗagota cak, duk da tanada ɗan ƙiba ba sosai ba, amma bai ji nauyin ɗagata ba, ya ɗorata akan gado, kana ya zauna a gefen ta, cikin Cold voice yace "Wlhi da kinsan irin missing ɗinki da nayi da baki dinga jamin aji ba, ace kin dawo garinnan amma bani da labari?" Kafin tayi magana sai da taɗau lokaci, kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "jiya na dawo" Ya kwaikwayi muryarta yace "jiya na dawo" Wannan abu nasa yana bata dariya, tana murmishi tace "har yanzu kana nan da halinka" Shima murmishi yayi kafin yace "yaushe zaki dawo gareni?" "Sai abinda su Hajiya sukace?" "Ke baki da abinda zaki ce musu? kawai ki sameta kice kinason komawa gidan mijinki" Tasneem ta zaro ido, kafin tace "ehhh, sokakeyi suce bani da kunya?" Zahraddin ya tallafo kumatunta, murya ƙasa-ƙasa yace "nayi missing ɗinki sosai, sai dai naga kamar ta ɓangarenki ba haka bane?" Dariya kawai tayi, cikin kuɓutar baki tace, "bazaka gane bane" Kamar wanda aka zabura ya rungumeta yana ce mata, "da gaske kema hakanne a zuciyarki?" Gyaɗa masa kai tayi, sbda rungumar da yayi mata, ta gamsu da kewarta da yayi, kamar Maraya ya kwantar da kansa a gadon bayanta yace "dan Allah ki dawo da wuri, my Tasneem kowacce mace na gani wlhi batayimin kyau, amma yanzu da nayi tozali da kyakkyawar fuskarki sai naji sanyi a raina, a kanki na fuskanci ƙalubale a gurin Dady, har cewa yayi zai haɗani aure da yarinyar abokinsa.." Cikin sauri tare da kishin da ya taso mata, ta kuma kasa tareshi tace "ai da ka aureta!!" Zahraddin na rungume da ita yace "ban riga da na amsa ba, bare aje babin aure, kinga amaryar Zahraddin mayar da wuƙar daga ke babu ƙari, na rufe ƙofa" Ajiyar zuciya ta sauke, lokaci ɗaya taji sonsa ya sake nunkuwa a cikin ranta, Uncle kuwa abin nasu yafi ƙarfinsa, yayiwa Hajiya sallama ya fice. Sun shafe awa ɗaya, Zahraddin yana ta nanata mata kewarta da yayi, da Hajiya ta gaji, tace "zoka fice ka barmin ƙawata ta huta haba" Zahraddin yayi murmishi kamar hajiyar na kallonsa, kana ya zare jikinsa ana Tasneem yayi mata kiss a goshi ya sauka daga kan gadon kana ya tsaya yana ƙare mata kallo, itama narkakkun idanuwansa take kallo, tashi ɗaya ya bata tausayi ta sauko da sauri ta rungumeshi tare da fashewa da kuka, hankali a tashe yake bubbuga bayanta, a hankali yace "Babyna lafiya?" Cikin Muryar kuka tace "sam banji ka ambaci jininka ba, banji ka kira sunanta ba, banji ka sanarmin da yadda kayi kewarta ba, zuciyata tana zafi idan na tuna na aihu amma bana tare da ƴata" Zahraddin ya cireta a jikinsa, tare da dafa kafaɗarta yace "tabbas ko barci nazo yi, ina tunanin ta, dan me zai sa in famo miki ciwo, nazo saki farin ciki in tafi kina kukan baƙinciki kenan?" Tasneem ta girgiza kai, shikuma yai saurin ficewa, Koda yazo parlo babu kowa, hakan ya bashi damar ficewa ko sallama bai yiwa hajiyar ba. UMMA House💋 Washe gari, da asbha ta farka, lokacin ma an jima da kiran sallah, duk mugamcinta bata ƙetare lokacin kiran sallah, amman Alhaji Lukman bai tashi ba, har ta shiga kitchen ta ɗora ruwan zafi tazo ta gyara gidan, duk da ba wani datti yayi ba, lokacin da ta ajiye ruwa a flaks a kan dining lokacin ya fito, yana waya, da alamu kiran da akayi masa ne ya rage masa jin daɗin barcin. Cikin rage murya tace "Alhaji Barka da fitowa anyi sallah tun ɗazu" "Toh" Kawai yace mata, kana ya wuce bedroom ɗinsa acan yayi sallahar. Kafin ta dawo ɗaki, ta dinga tunani kona meye oho, Ragowar ruwan ta juye ta shiga wanka, tana fitowa ta shafa mai tare da murza hoda tasa tozali kana ta buɗe drowa ta ciro, doguwar riga irin ƴar katinnan koda tasa ta matseta sosai, ana ganin shatin nonuwanta da mazaunanta, kasancewar rigar pink color ce, tasa hula pink, ta fito ta koma kitchen, acan Alhaji Lukman ya sameta, tun daga can nesa yake ƙare mata kallo, dama yazo sanar mata da cewar zai wuce gurin aiki, sai yayi ido biyu da abubuwan da sukafi burgeshi, A hankali yaje ya rungumeta tashi ɗaya, Umma taji ta dunguri robar fitsari, a ƙasan zuciyarta haushinsa ta kama ji, ga mutum har mutum amma bashi da lafiyar yin aiki, mtsew, shiko sai jifanta da murmishi yakeyi,.... Anjima akwai new update Amma fa idan kukayi comments, Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE, Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700 Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding. Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel Nagode Karkisake ayi book2 babu ke😂 domin kuwa hmmm *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 79-80 Rurin da wayarsa ta yi ne, yasa ya matsa gefe tare da amsa kiran, Bayan ya gama wayar, ya juyo gurin Umma, kafin yace "yau munada manyan baƙi ina tunanin koda sun zo bazasu sameni ba, ko shi kaɗai Alhaji Abdussalam ɗin yazo, sai ku gaisa". "Ai Gara ka bari su zo sai ka tafi" Alhaji Lukman ya kamo hannun umma tare da cewa "karki damu babban abokina ne, shida sauran abokanmu" "Toh" Umma tace, kafin ta narke ido tace "uhm ko abinci safe bakaci b" "No karki damu, kedai ki fara hidimar yi musu girki, yanzu zan fita" Cikin gamsuwa Umma ta juya kitchen taci gaba da hada hadar girki, Ƙarfe 7:30am ya wuce gurin aiki, Bayan Umma ta gama zuba sanwa a tukunya tare da sinadarin ɗanɗano, ta dawo parlo tana tunani, Tabbas duk wanda yaga Alhaji Lukman bazai yi tunanin yanada wata matsala ba, sbda yanayinsa da walwalarsa na, kamar bai damu da sharholiyar ba, Sosai tayi zurfi a tunani, daga ƙarshe ta tashi ta koma kitchen, cikin Sa'a ta samu ruwan ya tafasa, ta zuba shikafa da busashen kifi, bayan ta wankeshi da gishiri, kafin ta kawo hantar da dama ta riga da ta tafasata, ta yankata ƙana ƙanana, sannan ta motsa ta rufe, Duk da cewar ba wasu kalolin abinci ta iya ba, amma tanada yaƙinin wannan ɗin zeyi daɗi. Ɗakinta ta koma tana duba kayan da zata sauya, taji wayarta tayi ruri, rufe drowar tayi kana ta dawo kan gado ta zauna, Sai da ta daidaita nutsuwarta kafin ta ɗaga wayar, daga cikin wayar Maryamah tace "amarya an mance damu, ko kira babu?" Umma tayi murmishi na iya gefen baki kafin tace "haba Maryamah ni na isa in mance dake, ai da na zamo butulu" Maryamah tace "hmm zaki iya tabbas, sbda wannan tafkeken gidan da kika mallaka komai ze iya shige miki duhu" "Haba Maryamah ki dena wannan zancen, kinga zansa a tura miki da dubu goma yanzu, sai ki turo da lambar account" Jikin Maryamah na rawa tace "tabbas alamomi sun nuna baki mance dani ba" Cikin sauri ta turo mata da number account ɗin tare da sake kira tayi mata Godiya, Umma tace "kinga nikam ban iya tura kuɗin ba, zan bawa mai gadi ya kai a tura miki" Daga nan Umma ta katse kiran. Fasa ciro kayan tayi ta koma kitchen ta duba abinci, lokacin ta kusa tsotsewa ta dawo bedroom ta buɗe drowa ta ciro riga da zani wanda basu kamata ba, ta ciro ƙaramin hijab iya ƙirjinta tasa, kana ta dawo kitchen ta sake duba abincin ya dahu, ta sauke, ta rasa me zata sake dafa musu kawai ta kashe electric stove ɗin. Lokacin da ta kammala komai har 11:am tayi, Hakan yayi daidai da nocking ɗin ƙofa da taji, a tunaninta mutum biyu ne ko sama da haka, sai taga akasin hakan mutum ɗaya, Cikin sakin fuska tayi masa sannu da zuwa, tare da nuna masa gurin zama, ta janyo table gabansa, kasancewar yana da ɗan girma yasa ta ajiye tiran abincin akai, tare da ɗauko drinks na kwalba kala uku ta ajiye da duk wasu abubuwan da tasan ana buƙata, sam ta kasa sakewa, Allah -Allah takeyi ya fita kawai. Ringing ɗin da wayarta tayi ne ya sata miƙewa ta koma can dining ta ɗaga kiran, Daga can Alhaji Lukman yace "wannan wanda yazo shine ogana kuma masoyina, duk wasu lamura nawa shine dan Allah karkisa muji kunya" Umma ta leƙo ta kalli ogan nasa kafin ta koma da kanta ta katse kiran, bayan tayi masa alƙawarin baza'aji kunya ba, cikin rage sautin muryarta. Ga mamakinta sai taga yaci abincin sosai, yasha lemun kwalba, kafin ya ajiye cup ɗin, yace "sunana Alhaji Abdussalam, da fatan mai gidan yayi miki bayanin koni waye?" Fuskar Umma a sake tace "eh yace mai gidansa ne, muna godiya Allah ya saka da alkairi" "Amin Alhaji Abdussalam yace, kafin ya kalli agogon Hannunsa yace "sai dai wani hanzari ba gudu ba, kinada masaniyar mijinki bashi da lafiya?" "Eh" Umma ta gyaɗa kai. "Hakan baya damunki?, tabbas zai dameki, kamar ke mace mai aji mace mai kyan diri mace mai jini a jika mace mai zubin halitta irin taki, ace da auren Lukman kikayi tozali," Umma ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana nazarin maganarsa, Kafin ya sake cewa "yakai shekaru shida, yana fama da wannan cutar har ƙasar waje anje ba'a dace ba, sannan lokacin da ya fara maganin gargajiya, wani mutumi yace "Aljanu ne suka shafeshi, to gashi har yanzu beyi dacen magani ba" "Akwai shawarar da zan baki, nasan zatayi miki amfani" Duk da Umman batasan me yake shirin cewa ba, amma ƙirjinta ya fara lugude, sbda har zufa tafara yi. Ya ƙara da cewa, "idan har kin amince zan aureki, in baki sadaki a hannun ki, sannan inyi miki kayan lefe, sannan in baki kyautar gida bayan haka zan biya miki Makkah a matsayin nayiwa Lukman kyauta, Idan kikaƙi amin cewa da buƙata ta, tabbas zan kafa shedu in faɗawa kowa kin nemi nauyi lalata dake nikuma naƙi yarda, kinsan wane sakamako alhajin zai baki?, rabuwar wulaƙanci zakuyi nikuma inada ikon ajiye ki a gidana ko kinaso ko bakyaso". "Dan Allah Alhaji kayi haƙuri wlhi wannan haramune ne, ya haramta a musulunci" Da sauri ya dakatar da ita, tare da cewa "sati ɗaya na baki, zan aureki dole " Umma tace "aure kan aure?" Gyara zaman hularsa yayi, yana daga tsaye yace "nan da kwana uku zanyiwa Lukman transfern gurin aiki, zai koma ƙasar waje da aiki, zan ƙara masa matsayi ninki biyu sannan kema zai ƙara miki matsayi, "Ki rubuta ki ajiye sai wata rana" Yana faɗar haka ya fice. Umma ta rafka uban tagumi, tare da fashewa da kuka, ta ɗaga hannu sama tana cewa "Allah ka kawomin mafita na shiga uku" JUWAIRIYA House Yau kwananta biyu a gidan Alhaji Al'amin Soyayya yake gwada mata mai tsayawa a rai, kamar inda ya faɗa yau zeyi tafiya zuwa ƙasar da aka sauya masa a gurin aiki, London, Hankalin Juwairiya ya tashi sosai, tunda ta shirya masa kaya take kuka, shima jikinsa yayi sanyi, cak ya ɗagata ya ɗora kan kujera tare da mannata da jikinsa, ya haɗe goshinsu guri ɗaya sannan tayi shiru, da yaga haka, hankalinsa ya kwanta, tana kwance akan doguwar kujera har ya shiga ya fito da kayan bata biyo shi ba, Yana zuwa parlo yaga harda gyara kwanciya, tayi barci, da sauri ya ɗauki biro yayi rubutu ya ajiye mata ya fice, Yana zuwa parking space ya ƙwalawa driver kira, cikin sauri drivern ya shiga mota shikuma Al'amin ya shiga backside suka wuce.... Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE, Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700 Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding. Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 81-82 Duk da tashi ɗaya barci mai nauyi yayi nasarar ɗaukarta, hakan bai hanata farkawa ba, sakamakon wani mugun mafarki da tayi, da sauri ta sauko da ƙafafunta ƙasa, kafin ta miƙe tsaye tana yamutsa fuska, a tunaninta Al'amin yana bedroom ɗinsa, cikin rashin sa'a ta leƙa ko ina bata gansa ba, rai a ɓace ta ɗaga waya zata kirashi, sai ta fasa kamar wacce ta tuna wani abu, Parlo ta dawo ta zauna akan kujerar da ta kwanta, kana ta kalli agogon dake manne a jikin bango, ƙarfe 11:am, sauke idon da zatayi idonta ya sauka akan takarda, a tsorace ta jujuya takardar sbda ya ninketa, a fili ta furta, "gaskiya idan nace na buɗe wannan takardar akwai matsala, karfa azo ya rubuta abinda zai dameni ne, barin ɓoyeta. Jiki a sanyaye ta wuce kitchen domin samawa cikinta abinci. Bikin Naeema da Mahbob ya rage saura sati ɗaya, abin mamaki, ko sau ɗaya Mahbob bai taɓa furta wa abokansa maganar aurensa ba, har kawo yanzu da lokacin bikin ya matso, Da maraice Abba ya kirashi a waya, lokacin yana tare da Amani a wani gurin hutawa, suna tattauna abubuwan daya kamata su aiwatar a lokacin bikin, Cikin lallashi Amani tace "bro abinda nakeso dakai shine, ka kwantar da hankalinka, idan da zuciya ɗaya take sonka zaka gani..." "Please Amani ki rufe min baki, wace irin magana ne wannan, a halin da ake ciki ko maganar 5 minutes ban taɓa yarda munyi ba, sometimes wari ma take yimin, a hakan zamuyi zaman aure?" Amani ta sunkuyar da kansa ƙasa, hawaye na bin fuskarta, cikin shesheƙar kuka tace "a tunanina da Ammy na da rai Abba bazai fara wulaƙantamu ba" Mahbob ya kamo hannunta cikin marairaicewa yace "yanzu me kike ganin ya dace inyi?" "Kayi haƙuri insha Allah a hakan zamu samo mafita" Amani ta faɗa tana miƙewa tsaye, Suna tafe a hankali suna magana, har suka kawo gurin motar Mahbob, ya jingina a jikin motar kana yace "ki sani zanbi shawararki, duk abinda ya biyo baya kece sila" Cikin sauri ta dafe ƙirji tare da zagayawa mazaunin driver, shima ya shiga tayiwa motar key" Sosai Abban yaji haushin ƙin ɗaga wayarsa da Mahbob yaƙi yi, har ya hassala, Batool ta matso tana bashi haƙuri, sannan ya sake kiran number Mahbob ɗin, jiki a sanyaye yakai hannu ya ɗaga tare da sallama, kalmar data fara fitowa a bakin Abba itace.. "Kanada hankali kuwa, har da zan kiraka kaƙi ɗagamin waya?" Gaban Mahbob ya bada dumm cikin wani irin yanayi yace "Abba dan Allah kayi haƙuri" Sannan Abban yace "nasa an gyara ko ina na gidanka ka sanarwa da yarinyar Bama buƙatar komai" "Tom Abba" Mahbob ya faɗa hawaye cike da idanunsa, da sauri Amani tasa hannu ta goge masa tare da cewa "karka damu wllhi wataran sai labari, abinda yafi bani mamaki da Abba bai wuce, komai ya dinga fifita wannan yarinyar a kanmu ba, sam yanzu baya ambatarmu ko kiran waya ka gani to maganar aure zeyi maka" Har suka isa gida Amani na mita. Yau kwanan Naeema ɗaya da komawa, Dady yayi farin ciki da auran Naeema sosai, kaf abokansa kuwa babu wanda bashi da labari, sannan suka kira ƴar tashi da mai Sa'a, mama kuwa tun yanzu take ta kiraye-kirayen waya, akan danginta suzo su tayata aiki, Abinku da gidan da za'a huta, washe gari suka cika gida harda masu tambayo kwana goma a gurin miji. Ana biki saura kwana biyar, safiyar talata, Huda sam taƙi cin komai, Aseela ta damu sosai, suka dinga tambayarta meya faru, sai tace musu "babu komai" Sosai Amani ta tsorata da yanayin ta, da sauri ta ɗaga waya ta kira Mahbob, kan kace me sai gashi ya shigo, har yana mancewa da cire takalmi, cikin tausasa murya yace "Huda gayamin me akayi miki?" Kanta a ƙasa tace "Anty Batool ce ta kwaso kayan wanki da yawa kuma tace inzo inyi mata girkin dare, wai zasuje wankin kai" Mahbob ya riƙe ƙugu, a fusace yace "yaushe ta ganki?" "Tun su anty Amani suna barci ta aiko wata yarinya ta kirani" "Okay kice mata ni Mahbob nace bazakiyi ba, idan ta matsa miki kiyi mata jiƙa-jiƙa ina Worshing machine ɗin gidan?" Huda tace "tace min kar in kuskura inyi dashi" Amani ta dafe kumatu tana mamakin irin samun gurin da Batool tayi har takeyi musu iskanci haka. "Aslamu alaikum wai Huda tazo inji anty Batool" A hassale Mahbob yace "kice inji Mahbob bazata zo ba" Amani ta kamo hannun yarinyar tace "Karki faɗi haka kinji beautiful baby zan siya miki ice-cream" Yarinyar tayi murmishi kana tace "to me zance?" "Kice kawai tana zuwa" Yarinyar ta fice da gudu, "Bro nasan nayi maka lefi na tari numfashinka, karka manta, danginta sun cika gidannan so kakeyi su tafi damu a baki?" Shiru yayi bai ce da ita komai ba, sai ma shigewa ciki da yayi rai a ɓace, Yarinyar na zuwa tace "wai tana zuwa" Batool ta kalli ƙanwar mama da itace mahaifiyar yarinyar tace "wllhi Ummi kinga kisisinar da yarannan suke yi min?" Ƙanwar mahaifiyar Tata tace "hamm ai yaran miji ruƙonsu sai me haƙuri wllhi koni nayi banji daɗi ba, ki godewa Allah matane kuma sun girma nan bada jimawa ba auransu za'ayi, lokacin ne zaki miƙe ƙafa kiyi abinda kike so" Batool ta sauke ajiyar zuciya, Dawowar Abba ne yasa Ƙanwar maman nata tafiya, Abba ya ƙirgo 5k ya bawa yarinyar kana suka wuce sunayi masa godiya, A ƙofar shiga part ɗinsu Amani Batool ta haɗu da Huda zata wuce, Batool ta janyo mata wuyan hijab tare da cewa "ke har kinyi wayewar da zan aika a kiramin ke amma kiƙi zuwa?" "Kuyi haƙuri anty wllhi aikana akayi" "What!! Kar gidannan ki gayamin akwai wanda ya fini matsayi da har sai kin gama masa nasa aikan sannan zaki yimin nawa?" "Kafin in ƙirga uku ki wuce kiyi abinda na saki kuma Karki sake ki taɓamin Worshing machine" Sum-sum Huda ta wuce kai tsaye sashen Batool. A parlo ta samu Abba hannunsa riƙe da newspaper yana karatu, cikin ladabi ta durƙusa ta gaishe shi, amsa wa yayi fuskarsa ɗauke da murmishi kafin yace "ya kamata in baku kuɗin ankon yayanku" Kan Huda a sunkuye ta miƙe, Batool na shigowa taji maganar Abba na kuɗin anko, Sai da ta yatsina baki kafin ta wuce ɗakinta ta fara watsowa Huda kaya, abinda bata taɓa tsammani daga Abban ba ta jishi yau, cikin faɗa yake cewa "waye zeyi wannan wankin?" Kai tsaye Batool tace "Huda" "A'a Huda ba ƴar aiki bace, koda na kawota ban ajiye ta a matsayin ƴar aiki ba" Ko Uffan Batool batace ba, dan bata son alhajin ya fahimci inda ta dosa akan Huda, Cikin Muryar munafurci tace "ki tashi ki wuce" LIBYA*** Har yanzu suna cikin Libya, kasancewar rashin samun tikitin shiga ƙasar India, sakamakon tunani da Kharan Khan yakeyi akan kama mutane musamman ma matafiya tare da bincike a kansu, Yau kwanansu Hajara da Mona biyu a hannun Kharan, sam baya basu kyakkyawan abinci, sbda ƙuntatawa, zaune suke a wata tsohuwar ma'aikata wacce ta kasance ake lodin kayayyaki a jiragen ƙasa, duk da basa tunanin wani ze zo, amma yana tunanin makomarsu muddin jami'ai suka san da zamansu a gurin. Cikin sanɗa wani wanda bai saka kaki ba yake binsu, ga mamakina na hango jami'an sunkai goma, a bayan inda Kharan Khan suke zaune, cikin Sa'a kawai yaga an sanya masa bindiga a goshi, da sauri su Mona suka ɗaga hannu sama, tashi ɗaya suka fara kuka, duka aka tura su mota. Ala-uddin samir House** Tunda Hassana tabar gida Lulu ta kasa gane kan ala-uddin, sbda sam hankalinsa baya kanta, maganar yaƙi da yakeyi akan masarauta ma duk ya dena, hankalinta yayi matuƙar tashi, gashi suna jarabawar ƙarshe tana neman ta samu matsala. Washe gari ta kama Saturday tun da asbha aka tashi da ruwa, sanyi ya karaɗe ko ina, sosai Lulu take tsananin buƙatar Ala-uddin amma sam yaƙi ya nunar mata ya gane da hakan, Daga ƙarshe da ta matsu da yawa ta rungumeshi kai kace wani zai karɓe mata shi, sosai take ta goga jikinta da nashi, tare da manna masa tudun boobs ɗinta, a hankali take shafa gashin kansa tana yawo da ɗayan hannunta a tsakiyar bayansa, ga mamakinta yau sai taga ya juyo gareta, cikin zafin nama Yahau maida mata, daga ƙarshe ya rungumota ta gabansa, already shima ya cire komai, daga nan naga abinda yafi ƙarfina na rugo da gudu. Acan ɓangaren Hassana tabbas tasan kowane bawa da tasa ƙaddarar, duk da tana cikin wannan yanayin tafi tunanin halin da Hajara take ciki, sbda itace silar shigowarta ƙasar waje, sannan tana matuƙar tunanin halin da iyayen Hajara zasu shiga, a taƙaice ma dai bata da ikon zuwa wani guri bare tayi kira taji ya Hajaran take ciki, Ko ina na gidan a kulle yake, sannan mutum ɗaya ne a gidan wato me gadi, Sai sashen ta da koda yaushe yake a kulle keys ɗin kuma suna hannun ala-uddin, bata da ikon fita sai dai ta buɗe window shima akwai net a bayansa, Dole ta haƙura ta koma rayuwar kulle, duk da komai take buƙata zata samu amma hakan sam baya burgeta, ta gwammace da tayi irin wannan rayuwar gara tayi rayuwa a gidan da zatayi ta cin garin kwaki kullum, babban abinda yake mugun ɗaga mata hankali, bai wuce fushin da Ala-uddin yayi ba, lokacin da yazo ya so tilasta mata akan tasa waɗannan kaya tahau yi masa wa'azi, tun daga ranar bai sake waiwayarta ba, sati guda kenan. ****** Jikin Sahla sai rawa yake, koda wane lokaci tuno gargaɗin wannan matar da ta bata diamond takeyi, tana rungume da jaka har suka ƙarasa cikin garin SABHA, abin mamaki sukayi parking a gidan iyayen Shahazad, tare da umartarta da ta sakko, Kun san ƙasar waje ba kamar nan Nigeria ba, da bamu cika yarda da mutane ba, aradun Allah har murna suke suyi baƙi, Shakur ya kamo hannunta yana cewa "ƴar uwa ki saki jikinki" itadai burinta ta samu matsuguni sannan ta fara binciken abinda ya kawota, Kai tsaye suka shiga main parlo na Mama, Suna zaune a kan kujera harda ƙanwarsa, tana ganin Sahla ta taso da murmishinta kafin ta kamo hannunta suka zauna, cikin girmamawa Sahla ta miƙe ta gaishe da mama ta dubi Shakur tace "godiya nake" Kallon ta suka tsaya yi, ga dukkan alamu ba daga Libya take ba, amma a hankali zasu binciko labarinta.... Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE, Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700 Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding. Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 83-84 Shakur yace "mama a hanyar jeji na ganta tana neman agaji" Hindu dake ta zumuɗi tace "shikenan na samu ƙawa" Sam Sahla bata wani saki jiki dasu ba, duk da taga suna nan-nan da ita, a taƙaice ma batasan inda suka kawota ba, Tunda Shakur yaga bata saki jiki dasu ba, ya cewa mama "idan ta gama cin abinci zanzo mu tafi yawo" Cikin shagwaɓa Hindu tace "haba Shakur nayi baƙuwa shine zaka fice da ita?" Mama nayi musu dariya, Kawo abincin da kuku yayi ne yasa su katse maganar kowa na cewa ga abinda yake so, banda Sahla da ta gama aiyyanawa ranta ba cimarta bace, sannan dole zasu ganeta, "Yarana kuje kuci abinci sai ku kwanta" Mama ta faɗa tana kallon Shakur da ya turo baki da hindu da Sahla, "mama idan mun gama Karki manta zamu fita" Dubanta takai ga agogon bango kafin tace.. "No dare yayi kasan baƙuwace da alamu ba ƴar garinnan bace" Sahla tayi ajiyar zuciya, duk da tanason su fita kodan ta tambayi wasu abubuwan. Koda suka je gurin cin abinci, Sahla sam ta kasa cin abincin da su Hindu sukayi, sai dai coffee dake ajiye tadinga kurɓa har ta kusa shanyewa, NIGERIA Kamar inda Hajiya babba tayiwa Boka alƙawarin kawo masa gashi da farce da sauran abubuwan da ya buƙata, Washe gari ta shirya tsaf, cikin dakakken leshi mai ruwan malmo purple color yayi mata kyau sosai, kasancewar Alhaji ba a ɗakinta yake ba, ta ɗauko mayafinta kai tsaye ta wuce sashin Hajiya ƙarama, ɗakin Alhajin na farko shiyasa ta shige ba tare da ta ɗaga murya ba, bare Hajiya ƙarama tasan ta shigo, Cikin natsuwa wacce dadyn ya daɗe bai gani a tare da ita ba, ta shigo tare da durƙusawa ta gaishe shi, kana tace "Ummanta babu lafiya zata je yanzu a kaita asibiti" Da sauri Dady ya kalli agogo ƙarfe 7:am, kafin ya kalli fuskarta yace "Allah ya tsare" Har ta miƙe zata wuce sai kuma ta dawo tace "Alhaji zanyi abinda na saba, tunda daga nayi magana ace na cika kishi, da Hajiya ƙarama ce zata fita, kana rawar jiki zaka kaita kokuma ka miƙa mata kuɗi, amma ni hmm" Ta wuce kamar wacce aka tura. Yana magana ma bata tsaya saurararsa ba, ta wuce parking space ta yiwa driver magana suka wuce, Hakeem dake zaune a bedroom ɗin Hajiya babba a kan gado, ya zuba tagumi, yana mamakin hanashi bin ta da tayi, sbda tunda suke yawanci shike kaita gidan ƙawayenta, wannan karon tace ya huta, Suna isa anguwar, Hajiya babba tacewa driver "ajiyeni a bakin get" Abin yayi matuƙar bashi mamaki, hajiyar da ko parking kayi ba dai-dai ba sai ta dinga surfa masa masifa, Yanayin parking ta fito tare da cewa "ka koma gida kawai nagode" Har ya hau titin da zai sadashi da anguwarsu yana tunanin sauyawar da Hajiya babba tayi. Nocking tayi a get ɗin, mai gadi ya buɗe, tare da zubewa har ƙasa yana gaishe ta, Hajiya babba ta amsa cikin sakin fuska ta shige ciki, Tun daga nesa da bakin ƙofar take kwaɗa sallama, Abby dake zaune a babban Parlo ya amsa yana cewa "kamar Muryar Zainab?" "Eh itace zahiri" Umma ta faɗa. Hajiya babba ta turo ƙofae tare da sake yin sallama, Abby ya washe baki, kafin yace "yaushe rabon da in ga mamana?" Hajiya babba ta zube gaban Abby ta gaishe shi, kafin ta gaishe da Umma da ke ta yi mata murmishi, Abby ya tambaye ta mai gidan da abokiyar zamanta, Hajiya babba tace "duk suna lafiya" Abby ya miƙe tare da kallon agogon dake ɗaure a hannunsa yace " nakusa yin latti barin shirya in wuce" Hajiya babba tayi masa Allah ya tsare Umma tabi bayansa, Ganin haka yasa Hajiya babba shigewa ɗakin Fawziya, A kwance ta sameta ta lulluɓa da bargo tana barcinta cikin kwanciyar hankali, Hajiya ta bubbuga pillon da take kwance, Fawziya ta farka a tsorace, tana buɗe ido taga Hajiya tayi tsaki, mtsew kana tace "wllhi kin firgitani" "Ke dallah tashi ki bani shawara wane irin ciwo ya kamata a sawa Hajiya ƙarama?" Kamar dama Fawziyar na jira tace "wllhi warin jaɓa yafi komai a ganina, yarinyar kuma a mayar da ita wata dabba daban, da babu mai iya gano mutum ce akayi mata hakan" Hajiya Babba ta dafo kafaɗar Fawziya kana tace "gaskiya na yarinyar yayi mun wani iri" Fawziya ta tashi zaune tare da cewa "shikenan wllhi ko ciwon hauka aka saka mata sai an samu mai yi mata magani, kinga kamar ace a mayar da ita dabbar dake rayuwa a jeji sosai jejin da ba'a cika shigarsa ba, wllhi ke kanki hankalinki zai fi kwanciya" Suna tsaka da magana Umma ta shigo tana cewa "wace shawarar kuka yanke?" Wasa farin girki kuyi babu yawa, Nace ba😂 Anjima a gidan Umma zamuyi lunch *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 85-86 "Umma kawo kunnenki" Hajiya babba ta raɗa mata magana, umma tace "ya kamata ki tashi mu wuce sbda kinsan ba wani lokaci ne damu ba, ga gari na damina" Fawziya ta wuce toilet tana cewa "nima dani za'aje" Bayan sun gama kintsawa suka wuce a motar Umma, Fawziya tayi driving ɗinsu, har suka iso ƙungurmin jejin, kamar inda Umman tayi hakan sukayi yau ma, wato parking can nesa da jejin, sannan suka fara tafiya a ƙafa, Sunyi tafiya mai nisa sannan suka iso gurin boka, a halin yanzu Umma ta dena jin ɗarr game da boka sbda ko fargaba da tsoronsa bataji, burinta kawai taga aiki yayi kyau. Tun kafin ya basu Umarnin shigowa da baya, suka juya kana suka shigo kamar inda yake buƙata, cikin tausasa murya Umma tace "boka namu boka gatanmu mun zo da babban albishir duk abinda ka umarta yau an kawo su" Boka yayi murmishi kafin yace "buƙatarku ta biya" Hajiya babba ji takeyi kamar ta rungume bokan tsabar murna. Bayan ta miƙa masa ya karɓa, ya ɗaga ƙoƙo yana surkullensa a ciki, kana ya ajiye ƙoƙon da a halin yanzu yazo cike da magunguna da laya a ciki, Ƙullin magani ya ɗauko kana yace "wannan ki tabbatar kin sanya mata a cikin abinci" "Wannan laya ce, ya zamo koda yaushe tana kanki, kokuma kiyi kitso da ita, ma'ana ki binne ta a cikin gashinki, ga wannan maganin kin ganshi, ba a ko'ina zaki sameshi ba, shi wannan ko fesawa yarinyar kikayi ko kuma kisa mata abinci taci, shikenan kamar inda naji kunyi shawara zata zamo biri rayuwarta a jeji zata koma yi" Rai fess suka dinga yi masa godiya, Umma ta miƙa masa bandir ɗin ƴan dubu ɗaya guda huɗu kana ta sake yi masa godiya, Yasan Umma ko wacece a gurinsa baya ƙayyade mata kuɗi, sbda tana biyansa fiye da inda zai ambbata, kafin ya kalli Fawziya yace "kema ƴarinyar Hajiya ce?" Jikin Fawziya na rawa tace "eh" Boka ya miƙa mata wani icce dogo, kana yace "ki jiƙashi a kofi kidinga wanka dashi, kafin kiyi wankan ki ɗibi ruwan da hannuwanki biyu ki kira sunan mijinki, na baki mako guda zaki dawo kibawa Aljani ɗan gata labari" Fawziya ta dinga godiya kamar bazata dena ba, Hajiya ma taji daɗi sosai, Haka suka shigo mota ko wanne zuciyarsa wasai. Sam Hajiya babba taƙi amincewa Fawziya ta wuce da ita gidansu, sbda zumuɗin aiwatar da abinda boka ya bata, a bakin hanya suka sauketa ta tari mai mashin zuwa anguwarsu, Suna isowa ta bashi kuɗinsa kana ta ƙwanƙwasa get, mai gadi na buɗewa ta miƙa masa dubu ɗaya ta shige ciki, Yanta yi mata Godiya itakam tayi gaba. Idan kaga fuskar Hajiya babba kai kace ance mata gobe aljanna zaki shiga, Da sallama ta shiga babban parlonsu, tana shiga ta samu, Hakeem da Iffat da Hajiya ƙarama har da Dady suna kallo, Har zata balbalesu da masifa sai ta tuna kwana nawa ne ya rage?" Ta nemi guri ta zauna tayi musu sannu da gida, Dukkansu suka amsa da yauwa, Iffat tana ta kallonta tana murmishi, Dady yace "daga yanzu zan dawo shikenan har ƙarfe uku na rana" Hajiya ƙarama tace "Alhaji yace Umma babu lafiya, wllhi Ni ban san zaki tafi ba ai da na biki" Hajiya babba tace "ai taji sauƙi hawan jininta ne ya tashi yanzu alhmdulilah tana gida" A zuciyarta kuwa cewa take "idan da kin biyo NI ai da kin taƙai tani" Hakeem ya miƙe tare da wucewa ɗakinsa ya ɗauko key ɗin mota ya dawo zai wuce, Dady yace "Hakeem ina zuwa?" "Zanje duba Umma ne" Ko Uffan batace ba ya wuce. Hajiya ƙarama tace "a gaishe ta nima gobe zaka ka kaini" Hajiya babba ta miƙe tana cewa "washh" Ta shige ciki. A kan gado ta zauna tana tunanin yaushe ya kamata ta aiwatar da komai, A fili ta furta "insha Allah zuwa dare zan gama komai" UMMA House°° Kiran sallahar Azhar ne ya tashe ta a gurin, sbda jikinta yayi matuƙar sanyi har tunani takeyi da wane ido zata dinga kallon mijinta? Bata bar kan sallahya ba har sai da aka kira sallahar la'asr, Tana zaune jingine da jikin gado, taji sallamar Alhaji Lukman, jiki a sanyaye ta amsa, tare da kai dubanta gareshi, "Sannu da dawowa" Fuskarsa ɗauke da murmishi yace "yauwa Hajiyar Alhaji da fatan kin wuni lafiya ya baƙonmu" Sai da ƙirjinta ya bada rass!! Kafin tace "ai ya tafi" "Masha Allah ai ya kirani a waya yake sanar min da kayan tarba da aka shirya masa, wllhi har kyautar dubu ɗari biyar yamin, yace in baki dubu ɗari, ya ƙara da cewa wllhi Alhaji Abdussalam mutumin kirki ne ba ƙaramin kyauta ne dashi ba, yana yimin alkairi da yawa" Umma tace "Masha Allah mun gode" Kana ta miƙe dan kar ya gano tana cikin damuwa, hannunsa ta kamo suka dawo parlo, ta zubo masa ragowar abincin da ta dafa, dan a halin yanzu ƙarfin hali takeyi kawai, Yana ta zuba mata sumbatu yana cewa "abincin yayi daɗi kamar zai tsinke kunne" Bayan ya kammala cin abinci, ya miƙe ƙafarsa a kujerar da yake zaune, kafin ya kalli Umma yace "kuyi haƙuri wataran sai labari, nasan akan rashin lafiyata ne abun yake damunki insha Allah komai zezo ƙarshe, tunda yau munyi magana da Alhaji Abdussalam akan rashin lafiyata kwanannan zan tafi asibitin Egypt domin a sake dubani, kinsan sunada Islamic hospital acan" Umma ta kawar da kanta tare da runtse ido sai kuma ta buɗesu a hankali tana ambaton sunan Allah, Ya lura da yanayin ta, cikin kwantar da hankali yace "haba wannan aikin da za ayi domin mu ne gaba ɗaya, a tunanina farin ciki zakiyi ba ɓacin rai ba" "Ta wan gefen ina farin ciki ta wani gefen ina baƙincikin rabuwar da zamuyi na wasu lokutan da bansan yaushe zaka dawo ba" Ba jimawa zanyi ba, bai wuce wata ɗaya ba, sai dai kuma daga nan idan maganar transfer da za'ayi min ta taso zan wuce ko one week ne inyi" Tabbas duk wannan shirin yana daga cikin makircin Alhaji Abdussalam ya gaya mata komai game da hakan, ita kam ta kasa gano mafita, daga ƙarshe ta miƙawa Allah lamuranta, Haka suka dinga hira jifa-jifa sbda yana lura da yanayin ta, shiyasa yake janta hira. Har aka kira sallahar magriba suna zaune, daga ƙarshe ta miƙe zuwa sallah, shima alhajin ya miƙe ya wuce masallaci, Akan sallahya bayan ta idar da sallah adu'oi ta dinga kwararowa tana kuka.... Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE, Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700 Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding. Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 85-86 "Umma kawo kunnenki" Hajiya babba ta raɗa mata magana, umma tace "ya kamata ki tashi mu wuce sbda kinsan ba wani lokaci ne damu ba, ga gari na damina" Fawziya ta wuce toilet tana cewa "nima dani za'aje" Bayan sun gama kintsawa suka wuce a motar Umma, Fawziya tayi driving ɗinsu, har suka iso ƙungurmin jejin, kamar inda Umman tayi hakan sukayi yau ma, wato parking can nesa da jejin, sannan suka fara tafiya a ƙafa, Sunyi tafiya mai nisa sannan suka iso gurin boka, a halin yanzu Umma ta dena jin ɗarr game da boka sbda ko fargaba da tsoronsa bataji, burinta kawai taga aiki yayi kyau. Tun kafin ya basu Umarnin shigowa da baya, suka juya kana suka shigo kamar inda yake buƙata, cikin tausasa murya Umma tace "boka namu boka gatanmu mun zo da babban albishir duk abinda ka umarta yau an kawo su" Boka yayi murmishi kafin yace "buƙatarku ta biya" Hajiya babba ji takeyi kamar ta rungume bokan tsabar murna. Bayan ta miƙa masa ya karɓa, ya ɗaga ƙoƙo yana surkullensa a ciki, kana ya ajiye ƙoƙon da a halin yanzu yazo cike da magunguna da laya a ciki, Ƙullin magani ya ɗauko kana yace "wannan ki tabbatar kin sanya mata a cikin abinci" "Wannan laya ce, ya zamo koda yaushe tana kanki, kokuma kiyi kitso da ita, ma'ana ki binne ta a cikin gashinki, ga wannan maganin kin ganshi, ba a ko'ina zaki sameshi ba, shi wannan ko fesawa yarinyar kikayi ko kuma kisa mata abinci taci, shikenan kamar inda naji kunyi shawara zata zamo biri rayuwarta a jeji zata koma yi" Rai fess suka dinga yi masa godiya, Umma ta miƙa masa bandir ɗin ƴan dubu ɗaya guda huɗu kana ta sake yi masa godiya, Yasan Umma ko wacece a gurinsa baya ƙayyade mata kuɗi, sbda tana biyansa fiye da inda zai ambbata, kafin ya kalli Fawziya yace "kema ƴarinyar Hajiya ce?" Jikin Fawziya na rawa tace "eh" Boka ya miƙa mata wani icce dogo, kana yace "ki jiƙashi a kofi kidinga wanka dashi, kafin kiyi wankan ki ɗibi ruwan da hannuwanki biyu ki kira sunan mijinki, na baki mako guda zaki dawo kibawa Aljani ɗan gata labari" Fawziya ta dinga godiya kamar bazata dena ba, Hajiya ma taji daɗi sosai, Haka suka shigo mota ko wanne zuciyarsa wasai. Sam Hajiya babba taƙi amincewa Fawziya ta wuce da ita gidansu, sbda zumuɗin aiwatar da abinda boka ya bata, a bakin hanya suka sauketa ta tari mai mashin zuwa anguwarsu, Suna isowa ta bashi kuɗinsa kana ta ƙwanƙwasa get, mai gadi na buɗewa ta miƙa masa dubu ɗaya ta shige ciki, Yanta yi mata Godiya itakam tayi gaba. Idan kaga fuskar Hajiya babba kai kace ance mata gobe aljanna zaki shiga, Da sallama ta shiga babban parlonsu, tana shiga ta samu, Hakeem da Iffat da Hajiya ƙarama har da Dady suna kallo, Har zata balbalesu da masifa sai ta tuna kwana nawa ne ya rage?" Ta nemi guri ta zauna tayi musu sannu da gida, Dukkansu suka amsa da yauwa, Iffat tana ta kallonta tana murmishi, Dady yace "daga yanzu zan dawo shikenan har ƙarfe uku na rana" Hajiya ƙarama tace "Alhaji yace Umma babu lafiya, wllhi Ni ban san zaki tafi ba ai da na biki" Hajiya babba tace "ai taji sauƙi hawan jininta ne ya tashi yanzu alhmdulilah tana gida" A zuciyarta kuwa cewa take "idan da kin biyo NI ai da kin taƙai tani" Hakeem ya miƙe tare da wucewa ɗakinsa ya ɗauko key ɗin mota ya dawo zai wuce, Dady yace "Hakeem ina zuwa?" "Zanje duba Umma ne" Ko Uffan batace ba ya wuce. Hajiya ƙarama tace "a gaishe ta nima gobe zaka ka kaini" Hajiya babba ta miƙe tana cewa "washh" Ta shige ciki. A kan gado ta zauna tana tunanin yaushe ya kamata ta aiwatar da komai, A fili ta furta "insha Allah zuwa dare zan gama komai" UMMA House°° Kiran sallahar Azhar ne ya tashe ta a gurin, sbda jikinta yayi matuƙar sanyi har tunani takeyi da wane ido zata dinga kallon mijinta? Bata bar kan sallahya ba har sai da aka kira sallahar la'asr, Tana zaune jingine da jikin gado, taji sallamar Alhaji Lukman, jiki a sanyaye ta amsa, tare da kai dubanta gareshi, "Sannu da dawowa" Fuskarsa ɗauke da murmishi yace "yauwa Hajiyar Alhaji da fatan kin wuni lafiya ya baƙonmu" Sai da ƙirjinta ya bada rass!! Kafin tace "ai ya tafi" "Masha Allah ai ya kirani a waya yake sanar min da kayan tarba da aka shirya masa, wllhi har kyautar dubu ɗari biyar yamin, yace in baki dubu ɗari, ya ƙara da cewa wllhi Alhaji Abdussalam mutumin kirki ne ba ƙaramin kyauta ne dashi ba, yana yimin alkairi da yawa" Umma tace "Masha Allah mun gode" Kana ta miƙe dan kar ya gano tana cikin damuwa, hannunsa ta kamo suka dawo parlo, ta zubo masa ragowar abincin da ta dafa, dan a halin yanzu ƙarfin hali takeyi kawai, Yana ta zuba mata sumbatu yana cewa "abincin yayi daɗi kamar zai tsinke kunne" Bayan ya kammala cin abinci, ya miƙe ƙafarsa a kujerar da yake zaune, kafin ya kalli Umma yace "kuyi haƙuri wataran sai labari, nasan akan rashin lafiyata ne abun yake damunki insha Allah komai zezo ƙarshe, tunda yau munyi magana da Alhaji Abdussalam akan rashin lafiyata kwanannan zan tafi asibitin Egypt domin a sake dubani, kinsan sunada Islamic hospital acan" Umma ta kawar da kanta tare da runtse ido sai kuma ta buɗesu a hankali tana ambaton sunan Allah, Ya lura da yanayin ta, cikin kwantar da hankali yace "haba wannan aikin da za ayi domin mu ne gaba ɗaya, a tunanina farin ciki zakiyi ba ɓacin rai ba" "Ta wan gefen ina farin ciki ta wani gefen ina baƙincikin rabuwar da zamuyi na wasu lokutan da bansan yaushe zaka dawo ba" Ba jimawa zanyi ba, bai wuce wata ɗaya ba, sai dai kuma daga nan idan maganar transfer da za'ayi min ta taso zan wuce ko one week ne inyi" Tabbas duk wannan shirin yana daga cikin makircin Alhaji Abdussalam ya gaya mata komai game da hakan, ita kam ta kasa gano mafita, daga ƙarshe ta miƙawa Allah lamuranta, Haka suka dinga hira jifa-jifa sbda yana lura da yanayin ta, shiyasa yake janta hira. Har aka kira sallahar magriba suna zaune, daga ƙarshe ta miƙe zuwa sallah, shima alhajin ya miƙe ya wuce masallaci, Akan sallahya bayan ta idar da sallah adu'oi ta dinga kwararowa tana kuka.... Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE, Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700 Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding. Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 89-90 Da kallon mamaki Bappa Dattijo yabi Prince, kana ya nemi guri ya zauna yana kallon ƙwaryar furar da Prince besha ba, "Abdullahi meyasa bakasha fura ba, ko baƙunta kakeyi mana?" Prince ya sunkuyar da kansa ƙasa kafin yace "zansha Bappa wayata ce a hannun yarinyar da tazo dama wannan nonon har yanzu bata shigo ba" Bappa ya miƙe da sauri ya fice yana cewa "Ashsha Boɗɗo lamarinta sai ita" Koda ya fita waje bai ganta ba, ya tsaya a ƙofar gida tare da tunanin inda zai gano inda take. Ta ɗayar ƙofar Boɗɗo ta shigo da uban gudu, tare da sunkuyawa gaban akuyarta dake ɗauke da tsohon ciki, kurma ihu tayi tare da rungume akuyar tace "unguwar joma ta shusheni" Prince ya fito da gudun dan ganin me take yiwa ihu, ga mamakinsa sai ya ganta gaban akuya ta rungumeta idanun ta shaɓe-shaɓe da hawaye, "Dan Allah ki bani wayata, Noɗɗo kike ko Joɗɗo? nikam ki taimakeni Please" Boɗɗo ta zaro masa manyan idanun ta tare da cewa "kai mara taushayin ina ne, akuya ta jata aifu kana min jancen wani abun banja da wofi" Prince ya zaro ido, sbda yana maganar hankalinsa na gurin akuyar, ta wahala sosai, cikin sauri yace "kawo leda" Boɗɗo tace "bamu da leda me jakayi?" "Zan taimaka wa wannan akuyar ne" Da gudu ta miƙe ta kawo masa leda guda biyu, yasa ya ɗaure hannuwansa, cikin ikon Allah shi ya taimakawa akuyar har komai ya dai-daita, Tashi ɗaya ƙyanƙyami ya kama Prince, sai zubar da miyau yakeyi, ta kawo masa omo da ruwa ya wanke hannu, yana miƙewa sai ga Bappa ya shigo, "Ah Abdullahi me kakeyi anan?" Kafin yayi magana Boɗɗo tace "anguwar joma tayi mana" Bappa yace "Masha Allah ashe ka karanshi aikin anguwar joma?" Dariya ta kama Prince ya gimtse ya shige ɗakin yana cewa "eh" Bappa kam ya mance da maganar waya, tunda yaga akuyar Boɗɗo ta haifi yara uku, ya fice waje yana farin ciki, Bayan boɗɗo ta bawa akuyar abinci da ruwan sha, ta fice da gudu, ta tari ƙawayenta ta fara gaya musu akuyarta ta aihu sannan kuma anguwar joma tazo gidansu, Suka ɗunguma kan yashi, ashe anan ta binne wayar Prince ta zuba ƙasa akai, Wayar ta fara ring, ai dukkansu suka watse a gurin, tsabar tsoro, sai da akayi kira kusan goma suna nesa da wayar, daga ƙarshe wata a cikinsu tace "waƙa ce Kuzo muyi rawa, Idan wayar tayi ringing sai suyi ta rawa, idan kiran ya katse sai su tsaya, A haka har Prince ya zo gurin da suke, cikin sa'a yaji ringing ɗin wayarsa, sam ya rasa a ta ina take, cikin lallashi yace "dan Allah ku bani wayata" Boɗɗo ta matsar da yashi kana ta ciro masa tana cewa "kinshi darajar anguwar joma" Gaba ɗaya burin Prince bai wuce yaga wayar tasa batayi komai ba, amma fa ta cika da yashi, ya koma ciki yana gogewa. Sai da ya gama, ne ya samu damar shan nonon, sannan ya fara shawarar asubar fari zeyi sammako yabar garinnan sbda wannan yarinyar zata iya hallaka shi, ****. *** Tunda Tasneem ta dawo kullum sai Zahraddin ya zo, safe yamma, har abun ya fara damun Hajiya, ta kira Uncle a waya tace "itafa mijin Tasneem ya dameta da zarya dan Allah yazo ayi maganar mayar da ita, Uncle yace "insha Allah nan da kwana biyar zata koma" Amma Allah yayi wa yaron ƙanwar matarsa Rashida rasuwa, Tasneem na daga nesa da Hajiya tace "Allah ya gafarta masa" Hajiya ta amsa da Amen tare da cewa "kinga Allah ba azzalumin kowa bane, Tasneem marainiya zaki koma gidanki lafiyar Allah, dama ina ta tunanin wannan yaron wllhi" A ranar Hajiya ta kira wata ƙawarta ƴar mai duguri kasancewar ta zo gyaran amare wani gida anan cikin garin Kano, Sukayi alƙawarin gobe da wuri zatazo, Washe gari kafin matar tazo, Hajiya ta aika Tasneem kasuwa sbda idan an fara gyaran bazata dinga fita ba. Dawowar Tasneem kenan taga mai gyaran amarya tazo, bayan sun gaisa, sukayi sallah lokacin an kira Azhar aka fara. Yau kwana ɗaya da Zahraddin ya bata waya, ya kira yafi sau biyar kuma ko wanne sai sunyi magana, Kasancewar a keɓe suke da ita mai gyaran jikin, ta dinga gaya mata sirruka na zama da miji da inda zata zamo tauraruwa a gurin mijinta da sauransu. Yau kwanan Alhaji Al'amin biyu da tafiya, sam Juwairiya taƙi buɗe takarda, gashi ya kirata ya sanar mata da cewar sun kusa shigowa gari, Sosai ta shirya masa haɗaɗen girki mai rai da lafiya, tare da drinks na abarba da su kankana da madara, sai kunun zaƙi da tayi masa, ta shirya cikin leshi mai ruwan shuɗi, ɗinkin doguwar riga, tayi kyau sosai saboda a halin yanzu harda kumatu tayi. Ƙarfe 5:pm na yamma sai ga horn ɗin motar Alhaji Al'amin, kamar ta ruga da gudu ta tarboshi haka ta dinga, Tana zaune a parlo taji sallamarsa, kana ya tura ƙofar ya ƙaraso ciki, da gudu taje tayi hugging ɗinsa tana murnar dawowarsa, fuskarsa yalwace da murmishi yace "i miss You my Juwairiya da fatan kema kinyi kewata?" Tana kashe masa ido tace "eh man sosai ma" Suna rungume da juna suka zube akan kujera, Yaja kunnenta sai da tayi ƴar ƙara kafin yace "kin buɗe saƙon takardar nan baki cemin komai ba" Juwairiya ta waro ido kafin tace "wllhi na mance ne, ban ma karanta ba" "Oya jeki ɗauko" Taje ta ɗauko a sanyaye ta dawo ta zauna akan cinyarsa, ta buɗe ga abinda ta gani a rubuce" "Matata farincikina, haƙiƙa zanyi kewarki, kafin in dawo ki shirya zamuje ƙauyen iyayena domin su sanya mana albarka, ya zamo already ina dawowa tafiya zamuyi" Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya, ya sake rungumeta tsam, kana yace "yaushe kike ganin ya kamata mu tafi?" Juwairiya tayi sama da ido tare da cewa "ko jibi" Sosai yake shafa ta yana cewa "gaskiya ina tunanin bazan sake tafiya ba tare dake ba, wllhi har mafarki nakeyi, i miss You so much my wife" Hannunta tasa ta ratayo ƙugunsa kana tace "uhm ni da ka tafi ka barni na dinga kuka?" Dariya yasa yana lakace mata hanci. Tace "ka tashi muje kaci abinci" "Gaskiya na gaji, sosai inason ki rakani in watsa ruwa sannan sai inzo inci abincin" Ya miƙe tare da ɗagota, Rungume da juna suka wuce bedroom ɗinsa, sai da ta tayashi cire kaya kafin suka shiga toilet, aca n ɗin ma wasanni suka dinga yi daga ƙarshe akayi wankan suka fito, sam ya kasa haƙuri da ita, dole ya nuna buƙatarsa a fili, ko be gaya mata ba idanunsa sun nuna mata.... Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE, Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700 Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding. Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 91-92 Sosai ya nuna mata kewarta da yayi na wasu lokuta, daga ƙarshe ya dinga fito mata da tsaraba iri-iri, Washe gari, bayan anyi sallahar asbha, tare suka shiga kitchen suka ɗora breakfast, Juwairiya tana ta yi masa dariya harda riƙe kwankwaso kai kace mace, bayan sun kammala suka shiga wanka a tare, suna fitowa suka shafa mai, tare da sanya ankon bikinsu shadda mai ruwan sararin samaniya, sunyi kyau matuƙa, duk da simple makeup tayi, Bayan sunyi breakfast yace mata zasu fita yanzu, bata tambaye shi ina zasuje ba, bayan sun gama kintsawa ya kamo hannunta suka fito, tana sanye da ƙaton hijabi, suka shiga mota, da kansa yayi wa motar key suka fice, bayan an buɗe musu get, Kai tsaye kasuwa ya wuce, sukayi siyayya sosai mai yawa, har ta siyawa babanta shadda yadi goma da takalmi, siyayya sukayi na tafiya ƙauye, kaya na gani na faɗa. Daga nan suka dawo gida, a gajiye, ranar ko girki batayi ba sai tea suka sha suka kwanta, bayan sun rama sallolin da basuyi ba, Suka kwanta da niyar gobe in Allah ya kaimu da wuri zasu fita, Ikon Allah barci yayi daɗi har da makara, ko kiran sallahar asbha basuji ba, sai ƙarfe shida da rabi Al'amin ya fara farkawa, Kafin ya shiga toilet da sauri ya ɗauro alwalah yana mamakin barcin da sukayi mai yawa haka, Kana ya tashi Juwairiya, ganin gari ya fara haske yasa ta farka da sauri, tare da durowa ta wuce toilet, alwalar ta ɗauro kana ta shimfiɗa sallahya ta kabbara sallah, Bayan sun idar aka fara haramar wanka kasancewar da ruwa a flaks, Da safen ma tea suka sha kana ta janyo kayanta da ta riga ta shirya su, haɗe da nashi, duk wasu abubuwa wanda tasan zata buƙata sai da ta sanyasu, ƙarfe 10:am dai-dai suka kulle ko ina kana suka wuce parking space, drivern gidan na ganinsu ya je da gudu ya karɓi akwatin hannun Juwairiya kana yasa a Booth yana yi musu Allah ya kiyaye hanya, yau ma Al'amin ɗinne ya shiga mazaunin driver suka fice, ma'aikatan gidan sunayi musu adu'ar isa lafiya. Suna tafe tana ƙare masa kallo, duk da shiɗin ba yaro bane, amma tana jin sonsa a cikin jikinta, koda yaushe tunaninta bai wuce shi ba, jifa-jifa yakan kalleta su sakarwa junansu murmishi, sunyi nisa da inda suka baro, yace mata ƙauyen Kano zamuje Jibga, Juwairiya tace "ikon Allah wllhi ban taɓa jin sunan garin ba, Allah ya saukemu lafiya" Ya "furta Amen" Sannu a hankali Allah ya kawo su cikin garin Kano, ta ɗauka har sun iso ne, sai taga ina abin dai za'ace wasa farin girki, wasu ƙyauyaku ya dinga kutsawa, itadai Juwairiya shiru tayi, sbda tafiyar ta shallake tunaninta, sunyi tafiya mai nisan gaske, gashi ƙauyen da suke tunkara ko alamun pol waya na wuta babu, ƘAUYEN JIBGA Ƙarar shigowar mota da ilahirin yaran suka ji ne yasa ko wanne ya rugo da gudu, bayan Al'amin yayi parking, suka zo jikin motar suna shafawa, shiko sai washe baki yakeyi, sam ƙyanƙyamin garin takeyi bare ta zauna tare da mutanen cikinsa, ta tsani ƙuye ko ƴan ƙauye, musamman yanzu da ta sake komawa ƴar gayu, Ganin ta tsaya kallonsu yasa Al'amin kamo hannunta suka ƙarasa cikin gidan nasu, Wata mata da ta taho taga riƙe hannun da Al'amin yayi da Juwairiya, ta ruga da gudu har tana bigewa da bango, kai tsaye cikin gidansu ta shiga tare da faɗawa ɗakin Mari, cikin ƙasa da murya tace "wllhi tallahi yau idona idon Aminu ya dawo shida wata ƴar iska wllhi Karki ganta sai kace baturiya" Wacce aka kira da Mari ta miƙe tsaye cikin masifa tana sanye da rigar atamfa koɗaɗiya sai zani daban ko zanen jiki babu shima ya fita hayyacinsa, ga nono raɓeɓe har ciki, tana girgiza tace "wato da akayi masa asirin rabani da shi, aka kaɗashi binni shine yaje yayi kuɗi har ya mance dani da ƴa'ƴansa ko?" Wacce ta kawo gulmar tace "wllhi Karki sake a koma babu ke, ki tattara yaransa ku koma, sannan ki gayawa malam kinsan mahaifinsa da tausayi ki gaya masa a haɗaku kici uban shegiya, ubanme zata nuna miki a kula da miji.... 😔Wllhi rashin wuta yasa banyi muku typing ɗin da wuri ba, gashi babu yawa, akwai bidiri a ƙauye🤸 barci kuma nakeji.. A page 100 zamu ƙarƙare insha Allah, idan an gama biya da wuri muna gama book1 zamuci gaba da book2 idan ba'a biya da wuri ba, aradun Allah sai mun fi sati ɗaya ba'aci gaba da posting ba Nagode masoyana masu comments da shar'hi. Normal 300 Vip 700 08141799224 *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 93-94 "Ki ƙyaleni da su ai indai makirci ne irin na ƴan bariki babu abinda za'a nuna mana" Tun daga babban zauren gidan Al'amin ya fara cewa Juwairiya "dan Allah ki saki jikinki kwana uku zamuyi ki koma" A shagwaɓe tace "kai fa?" "Tare zamu koma ai ban isa in barki ki tafi ke kaɗai ba" Suka ƙarasa ciki bakunansu ɗauke da sallama, babban gida ne gidan a ƙalla mutanen ciki zasukai talatin, gidan ya haɗa da yara da jikoki harda surukai, Tunda mutan gidan suka hangosu aka fara gulmace-gulmace, shiko fuskarsa wasai sai gaishe su yakeyi, Juwairiya kam gaisuwar take amma sam bakajin abinda take cewa sai dai idan ka lura da bakinta na motsawa, kai tsaye suka wuce sashin su Al'amin, sashin ya kasance yana kewaye da ginin ƙasa amma da karar dawa suke girki ko kashin shanu, Baaba na ganin Al'amin ta washe baki, a fili tace "Aminu ashe rai kanga rai, zamu haɗu, dama kana raye?" Al'amin yayi murmishi kafin yace "Baaba ina raye, wllhi haka kawai naji hankalina ya tashi inason inga gida" Baaba ta kalli Juwairiya da ta sunkuyar da kanta ƙasa, kana tace "wannan kuma fa?" Sai da ya ɗan yi jimm kafin yace "Baaba mata ta ce, ko wata uku bamuyi ba" Cikin farin ciki tace "Masha Allah ga mari can ma ashe lokacin da ka tafi tanada ciki, yanzu shekarar yarinyar goma" Juwairiya ta zaro ido, tabbas taji kamar sunason cewa yanada mata, amma bazata yarda da tatsuniyar da kunnuwanta sukeyi mata ba, har sai ta ji daga bakinsa, Baaba na washe baki tace "ka shigar da ita can rumfa yanzunnan na kwashe dambu yaji zogale bari a siyo muku mangyaɗan ƙuli yanzu" Juwairiya ta yamutsa fuska, sai kuma ta yi murmishi sbda ganin yanayi mata murmishin, Hannunta ya kamo kana yace "muje can" Ga mamakinta ko tabarmar kirki babu, sannan gashi ɗakin duk warin daddawa, badan kar ta tashe hanci ya ganota ba, ai da ta toshe, kafin Baaba ta shigo, aka shigo masu da kayan dake cikin booth dukkansu, Nan fa mutane suka fara rubibin shigowa wasu su shigo wasu su fita, abinci kuwa sai da aka kawo kusan kala goma ko wanne da kwanonsa, Baaba ta shigo hannunta riƙe da dambu a kwanon Silva, sai mangyaɗa shima aɗan ƙaramin kwano da cokula biyu sai farantan Silva suma guda biyu, sannan ruwa a kofin Silva, tana cigaba dayi musu sannu, Al'amin ya kamo hannun baaba kana ya zaunar da ita, ya ce "Baaba duk waɗannan kayan naku ne keda malam" Baaba ta washe baki kana fara firfito dasu madarar gwangwanin da sauran kayan shayin, sannan sai kayan abinci buhun shinkafa buhun taliya irin ƴar buhunnan sai mangyaɗa da manja da sauransu, Baaba ta fashe da kuka tare da cewa "wllhi Aminu na ɗauka koda kaje binni ba a kintse kake ba" Al'amin ya miƙe tare da cewa "malam ya fita ne?" "Eh yana gona anjima nan zaka ganshi" Juwairiya dai sai kallonsu takeyi, gabaki ɗaya ƙauyen ya ishe ta ta gaji da zaman nan duk da yau sukazo, rabon ta da shan ruwan randa ko na leda tun kafin tayi aure ƙila ma yanzu ruwan rafi zatasha, Al'amin yace "Juwairiya kici abinci" Baaba tace "ashe ma uwata ce, Allah ya sanya muku albarka, idan bazata ci ba tunda ga kayan shayi sai a haɗa mata" Juwairiya tai saurin cewa "zanci mama" Shima yaji daɗi sosai sbda yaga alamun bata ƙyamaci ƙauyensu ba. Al'amin ya kamo hannun Baaba suka fice, can ɗakin awakai ko me suke tattaunawa oho, Juwairiya ta ciro wayarta taga network ya ɗauke, tayi tsakin da iya karsa laɓɓa kafin ta sanya cokali a cikin kwanon dambun bayan ta buɗe ta ɗibo takai baki, har zata kurma ihu sai kuma ta tuno da inda take, sannan ta haɗiye abincin daƙyar kamar zatayi amai, ta mayar da murfin ta rufe. Al'amin bai dawo ba har akayi sallahar la'asr, lokacin Baaba ta shigo, tare da cewa "Zuwaira kinci abincin kuwa?" "Juwairiya tace "eh naci mama" "To taso kiyi sallah yanzu malam ze shigo sai ku gaisa" Ta miƙe tare da ɗaukar butar tace "inane bayi?" Baaba ta nuna mata, daƙyar ta iya tsugunawa tayi fitsari, sbda dole nema yasa ta yi, dan ya matseta sosai, Ta fito tayi alwalah ta shigo ɗakin, ta samu Baaba ta shimfiɗa mata wata yaloluwar darduma, Juwairiya ta kawar da dardumar kana ta shimfiɗa ɗankwalinta, tayi sallahar akai, Allah yasa ma raka'a biyu zatayi. Bayan ta idar tai saurin naɗe ɗankwalin nata ta ninke dardumar ta koma ta zauna, Gyaran Muryar Malam da taji ne yasa ta gyara zama, har zata fito sai taji yayi sallama ya shigo, Cikin ladabi ta gaishe shi, bayan ya amsa yake tambayarta iyayenta, tace "suna lafiya" Kana ya sanya musu alkairi yace "Aminu ya sanar dashi kwana uku zasuyi su koma" Juwairiya sam bataji daɗin hakan ba, sbda a tunaninta gobe zasu koma, malam ɗin ya fara yi mata magana cikin sigar fahimta tare da sanar mata da yanada mata da yara guda biyar, anyi masa asiri ne yabar garin, har yakai shekaru goma bai dawo ba, sannan ya ƙara da cewa "matar ba ƙaramin dauriya da haƙuri tayi ba, idan sun cika kwanakin da zasu koma zai tafi dasu duka, kana ya ƙara da bata haƙuri akan cewa tayi haƙuri su zauna lafiya" Godiya Juwairiya tayiwa malam, a ƙasan zuciyarta kuwa gani take kamar an caka mata mashi, sbda har tafarfasa takeyi, malam ya fice yana farin cikin samun suruka ta gari. Sai da akayi magriba da isha'i, duk Juwairiya batayi alwalah ba, sbda batayi hutu ba, sannan tayi sallah, bayan ta idar ta ninke ɗankwalinta sai ga Al'amin nan ya shigo, Bata nunar masa da komai ba, ta ƙirƙiro murmishi ta maye gurbinsa da baƙincikin da take ciki, kafin tace "ina ka shiga na jika shiru har baba ya shigo?" Al'amin yayi murmishi kafin yace naje gaishe da ƴan uwa da abokan arziki, A zuciyarta tace "wllhi gobe bazanyi wunin ƙauyennan ba, bare ace zamu tafi wani gurin" Suna zaune Baaba ta kawo musu tuwo miyar kuɓewa bushashiya, Al'amin ya gyara zama kana ya ce a kawo masa cokali, bayan an kawo ya fara ci, sai da yayi mata magana kafin tasa hannu ta fara ci kamar mai tsoron abincin, shine ma yaci sosai, ya ƙudurtawa zuciyarsa baƙunta ne yake damunta, Zuwa dare ya wuce gurin kwana ita kuma Baaba tace "hau babban gado ki kwanta" Ta haye tare da kunna kallo a wayarta, Shiko ya samu yayi cajin wayarsa da power bank, asubha ta gari... Washe gari, kiran sallahar farko a kunnen Juwairiya, ta miƙe zaune tana ƙarewa ɗakin kallo, daga ƙarshe ta duro ƙasa tana kuka tana yarfe hannaye, daga ƙarshe ta dafe cikinta da kanta, Baaba ta sauko da sauri tana ce mata "maiya faru?" A wahalce take cewa "cikina kaina hannuwa na.... *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 95-96 Hankali a tashe ta fito tana bubuga ƙofar ɗakin malam, a firgice ya miƙe, kasancewar yana zaune kan darduma kana yace "lafiya?" "Babu lafiya matar Aminu ce take ciwon ciki" Malam yace "subahanallah ina zuwa" Bai jima ba ya fito hannunsa riƙe da allo yayi rubutu, ya miƙawa Baaba ta wanke ta bata tasha, tun daga nesa Juwairiya take jifan Baban da mugun kallo har ta iso, Allah sarki hankalin tsohuwa duk yabi ya tashi, Juwairiya kuwa sai ci gaba da juyi take, Baaba ta wanke ta miƙa mata tare da cewa "kiyi Bismillah Kisha" "To" baaban na ficewa ta buɗe zip ɗin jakarta ta ciro gorar fanta da tasha ɗazu, ta juye rubutun a ciki kana ta zuge zip ɗin, har taci gaba da ihun Baaba na waje tana haɗa wuta, bayan wutar ta kama tayi alwalah ta dawo ɗaki tana jerawa Juwairiya sannu, Irin ta jigatan nan har wani gyaɗa kai takeyi, alamar bakin ma yayi nauyi. Da ƙyar ta miƙe taje ta ɗauro alwalah ta dawo, burinta be wuce gari ya ƙara yin haske Al'amin ya shigo ya Kaita asibiti, daga ƙarshe ma su wuce gida. Tana zaune akan sallahya malam ya shigo lokacin an fito daga sallah, yayi mata ya jiki yace da sauƙi, A inda yaga yanayinta ya tsorata sosai, sbda sai juyi take tana riƙe da ciki, malam yace "bari mijinta yazo, ko asibitin bebeji su tafi" Kwatsam sai ga sallamar Al'amin, ya durƙusa ya gaishe da malam kana ya gaishe da Baaba ya kalli Juwairiya dake ta juye-juye, hankali a tashe yace "maiya sameta?" Baaba tace "wllhi tun asbha take haka, malam ma yayi rubutu an bata tasha Allah be kawo lafiyar ba tukuna" Al'amin yace "tashi muje asibiti" Tana kwance kamar wata wacce ta shekara tana ciwo, idan kaga inda take wani lanƙwashewa sai ka rantse ciwon gaske ne, gabaki ɗaya ta tashi hankulan mutane, Dole Baaba ta riƙeta suka shiga motar Al'amin aka wuce da ita asibitin bebeji, Bayan an shigar da ita ɗakin da ake kwantar da marar lafiya, da farko test akayi mata suka tabbatarwa Al'amin da tanada cikin sati biyu, sai maleria da typod dake damunta, suka sanya mata drip yana zuba kaɗan-kaɗan, Baaba ta koma gida domin ya dafo musu abinci, Al'amin ya zauna kusa da ita tare da gyara mata zaman hannu, sai sannan wayarsa tayi ringing alamun ana kiransa, da sauri ya ɗaga, harda ɗan ranƙwafawa alamar yana magana da wani mai muhimmanci, ji nayi yace "insha Allah megida gobe muna hanya" Kana ya ajiye wayar, sosai Juwairiya taji daɗi tare da fara ɗokin komawa gida. Zuwa yamma, dole aka sallame ta, suka koma gida, bayan Baaba ma ta dawo, ta kawo abinci sai komawa dashi sukayi, Bayan sun koma gida, Al'amin suka keɓe da malam, Acan bayan gari suka zauna, malam yace "Aminu bayan barin ka ƙauyennan wace irin rayuwa ka shiga?" Al'amin ya sunkuyar da kansa ƙasa kafin yace... Da farko daga nan na wuce garin Gombe, da sana'ar tura baro na fara, ina siyarda leda, kasancewar na tafi da dubu biyu ragowa bayan kuɗin mota, nakai shekara a haka, Allah ya haɗani da wani mutumi ya ɗaukeni gadi a gidansa, kwanci tashi ya dinga yabona akan wai inada gaskiya da riƙon amana, yasa aka koya min dreba, daga nan kuma ya buɗe min babban shago na siyar da turaruka, arziƙinsa nata hau hawa, har ya zamo na samu jari nawa na kaina, ya fara turani ƙasar waje sarin turaruka, nima ya zamo ya buɗemin babban shago, a halin yanzu shagunansa bakwai, nikuma inada shaguna uku a cikin garin Gombe ina da babban shago a ƙasar waje, a halin yanzu shikuma ya ƙara bunƙasa kasuwancinsa ta hanyar cigaba da sarin motoci yana siyarwa, wllhi har yanzu muna zaman arziƙi dashi, dama da muka zo inada niyar in siya muku gida acan sai ku koma kai da Baaba" Malam yace "Masha Allah haƙiƙa adu'ata bata faɗi ƙasa banza ba, sbda babu dare babu rana adu'oi nakeyi maka" "Sai dai bazan iya tashi in koma wani gari ba, idan ma haka kakeji ko fili ka siya sai kayi mana ginin zamani, amma inaso ka tafi da Mari da yaranka, kodan samun nutsuwa da kwanciyar hankali" Al'amin yace "eh nima inada niyar hakan, sbda jiya naje mun gaisa, na yi musu siyayya na sanar mata da ta shirya gobe zamu wuce insha Allah, sbda mai gidana ya kirani ɗazu akan zamuyi tafiya tare" Malam yace "to Masha Allah inayi muku fatan alkairi sai dai ka kula da matanka, karka dinga nuna musu bambanci a fili, duk da zuciya takan karkata ga ɓangaren da akafi yi mata biyayya" Al'amin yace "to" Daga nan ya dawo gida ya sanarwa da Baaba gobe zasu wuce, tare da alƙawarta mata zai turo da kuɗi su tashi anan su koma ginin da zeyi musu, Tun da yamma Juwairiya take shiri, bayan ta gama, taɗan kwanta, kasancewar Baaba ta haɗa mata tea da bredi, da tasha ta ɗanji dama dama, sbda iskancin nata harda yunwa a ciki, Can dare da dare kusan ƙarfe 9:pm sai ga Mari ita da yaran su uku, da wacce takai shekara goma sha biyar da mai shekaru goma sha uku, sai mai shekara goma, biyu mata ɗaya mai shekaru sha ɗayan shine namiji, Babbar Suwaiba, namijin Abubakar suna kiransa da Ɗan Bala, ƙaramar kuma Salma suna kiranta da Salamatu, Bayan sun gaishe da mama da Juwairiya, Mari ma ta gaishe su, daga nan take gayawa Baaba Aminu yace ta shirya gobe su wuce, Baaba tace "eh munyi maganar dashi, ga ƴar uwarki nan, ku zauna lafiya, kece babba dan Allah karku ɗauki zugar mutane" Cikin sanyin murya Juwairiya tace "insha Allah" Mari ma tace "in Allah ya yarda zamu zauna lafiya" Baaba tasa musu albarka, suka ɗan taɓa hira Juwairiya na jinsu, can anjima sukayi mata sallamar sai da safe, lokacin har Juwairiya tayi barci. Tun daga ranar da Alhaji Abdussalam yazo har washe gari, umma bata da walwalah, duk da Alhaji Lukman ya lura da hakan, sai ya bari, akan tafiyar da ya gaya mata ne, Bayan kwana uku da faruwar hakan. Alhaji Lukman ya fita aiki da wuri, sai ga wani saurayi yayi sallama, ƙarar bubuga ƙofar da Umma taji ne yasa ta ɗauko hijabi tasa, kana ta fito, bayan sun gaisa yace "saƙo ne daga Alhaji Abdussalam yace sunada taron saukar alƙur'ani na yaransu jibi insha Allah sanan yace a baki wannan" Karɓa tayi ta shige ciki ko uffan batace masa ba, hankali a tashe ta zube akan kujera tana tunanin mafita, Koda aka kira sallahar Azhar, ta miƙe taje tayo alwala tazo ta kabbara sallaha, kuka ta kamayi tana gayawa Allah damuwoyinta domin kuwa sunfi gaban tunaninta sheɗani ya shigo cikin rayuwarta yana neman ruguza mata farincikinta, duk da cewar Alhaji Lukman bashi da lafiya, amma bata taɓa tunanin rabuwa dashi ba, koda yaushe tayi masa adu'ar samun lafiya da nasara akan aikin da za'ayi mas *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 97-98 Jiki babu ƙwari ta janyo ledar da Alhaji Abdussalam ya bayar a kawo mata, kamar kar ta buɗe ledar, haka kawai ta tsinci kanta da buɗe ledar, kana ta ciro kayan ciki, doguwar riga ce abaya pink color sai mayafinta ɗan siriri gunin sha'awa, har zata mayar da rigar sai ta hango envelope, ta ɗauko ta buɗe taga kuɗaɗe masu yawa, bata da lokacin ƙirgasu ta mayar ta ajiye, tare da miƙewa da sauri ta haye saman drowa ta ɓoye kayan. Kana ta sakko tana tunanin idan har Lukman ya gano abinda ke shirin faruwa, tabbas bazai taɓa fahimtar ta ba, tanason ta sanar dashi tana tunanin gargaɗin da Alhaji Abdussalam yayi mata, akan cewar idan har ta sanarwa wani sai ya tozartata kuma sai yasa mijinta ya tsaneta, hawayen baƙinciki suka zubo mata, Ta rasa wa zata gayawa matsalarta, tana tunanin sanarwa da Maryamah tana shayin kar maryaman ta tona mata asiri, dole dai tabar abin a zuciyarta duk da zai zame mata dafi! Zuwa dare Alhaji Lukman ya dawo a gajiye, sai da yayi wanka ya sanya sleeping dress sannan dawo gurin Umma da sam taƙi zuwa ɗakinsa alhalin ba haka ta saba masa ba, koda ya shigo bedroom ɗinta ya samu tana kwance ta ƙudundune, da sauri ya ƙarasa inda take yakai hannu ya shafi fuskarta, hankali a tashe ya cire tare da ƙare mata kallo, ya fara kiranta a hankali, shanyayyun idanuwanta ta zuba masa haƙoranta suna karkarwa tace "sannu da dawowa" Cikin tausaya wa yace "haba uwar gida baki da lafiya shine kika kasa kirana, ai da duk abinda nakeyi zan bari inzo gareki, yanzu dai tashi muje asibiti" Duk da ciwon yaci ƙarfinta, amma gara ciwon da takeyi da ace taje walimar sauka tayi ido biyu da maƙiyinta gara ta wuni a asibiti, Ƙarfe 8:30pm tayi musu a asibitin Dr shugaba, bayan an bata gado anyi mata ƴan gwaje-gwaje, suka tabbatar masa da akwai abinda yake shirin faruwa musamman ciwon zuciya dan tana shikin firgici da tashin hankali, Kwananta ɗaya a asibitin, sai dai dinga yi musu take away na abinci, alhamduliy jikinta yayi sauƙi har ta samu tayi sallahar asbha, bayan ya dawo daga masallaci kiran Alhaji Abdussalam ya shigo wayarsa, jiki na rawa, gaishe shi yayi kana yace "ranka shi daɗe dafatan an wayi gari cikin ƙoshin lafiya?" "Lafiya lau dama inaso in gaya maka jiya har muka rabu ban sanar maka ba, akwai saukar alƙur'ani da yarana guda biyu zasuyi, idan matarka ta samu zuwa sai ka kawota" Alhaji Lukman yace "wllhi gamu a asibiti zazzaɓi anan muka kwana amma ina tunanin zasu sallamemu zuwa anjima" Alhaji Abdussalam yace "toh shikenan insha Allah zamuzo dubaku nida Hajiya Abida" Daganan sunayi sallama, Nidai nace Allah ya taimaka bataji zasu zo ɗinba, da ta sake firgita. Koda ya leƙo ya ganta akan sallahya tana zaune ya koma siyo mata tea da kayan shayi, cikin sauri ya dawo ya haɗa mata tasha shikam ya kasa sanya komai a bakinsa, Ƙarfe 10:am aka rubuta musu sallama tare da bashi takardar magani yaje pharmacy yasiya, ta biya kuɗi suka wuce a motarsa. Koda suka koma gida, a parlo ta kwanta sbda ji takeyi duniyar ta ishe ta, shikuma yanason ta samu sauƙi ya tambaye ta wace matsala ce take damunta? Ƙarfe 12:dai-dai wayar Alhaji Lukman tayi ringing, ya ɗaga yana cewa "Allah ya taimaki oga" Alhaji Abdussalam yace "gamunan mun kusa isowa" Jikin Alhaji Lukman na rawa yace "Allah ya kawo ku lafiya" Kafin ya matso kusa da Umma yace "oga fa suna hanya shi da matarsa" Aɗan firgice ta buɗe ido, tare da runtsesu kafin tace "Allah ya kawo su lafiya" Ya lura da ita kamar batayi murna da zuwan da zasuyi ba, amma sai yayi shiru tunda yaga ba isashiyar lafiya ne da ita ba. Har barci ya fara ɗaukarta suka ji nocking ɗin ƙofa, Alhaji Lukman yaje ya buɗe yanayi musu sannu da zuwa cikin fara'a, tare da yi musu umarnin su ƙaraso. Akan kujera mai zaman mutum uku suka zauna, Umma ta gaishesu ɗaya bayan ɗaya, sukayi mata ya jiki, tace da sauƙi, duk da ta ɗan rufe idanuwanta amma tana ƙarewa Hajiya Ubaidah kallo, farace tass babu abinda Umman zata nuna mata, duk da tafi Umman shekaru amma jin daɗi ya ɓoye hakan, ƴar gayu ce ajin farko, dan sai a ɗauki wata budurwar ma ba'a ɗauketa ba, kafin suka miƙe suna cewa zasu wuce gurin walimah, sai da suka fita masu gadi da driver suka fara shigo da kayan abinci harda na ƙwalama kamar bazai ƙare ba, sam kayan babu abinda ya burgeta a ciki, sannan ta lura da irin kallon da yake bin ta dashi, duk da Hajiya Abidah bata lura ba, da Alhajin. Suna can parking space Alhaji Abdussalam yake ce masa idan jikin yaƙi ya sauyawa Umma asibiti, Hajiya Ubaidah tace "kodai laulayi takeyi kake ɓoye mana?" Dariya yayi yanayi musu Allah ya kiyaye hanya tare da rufe musu murfin mota. Ita ko ta zurfafa cikin tunanin ga matarsa kyakkyawa me zeyi da ita mugu kawai. Alhaji Lukman ya dawo cikin fara'a yana cewa "Masha Allah Alhaji akwai halin kirki" "Mun gode" kawai Umma tace, kamar mai jin barci, hakan yasa shi wucewa ɗakinsa ya barta ta huta" Bayan kwana uku da rashin lafiyarta ta samu sauƙi sosai, dan idan ka ganta bazaka ce tayi ciwo ba, sai dai idanun ta da suka shishiga ciki, Kwana bakwai da samun lafiyarta kiran Alhaji Abdussalam ya shigo wayar Alhaji Lukman lokacin yana office, sai da gabansa ya faɗi, Alhajin ya sanar masa da maganar tafiyarsa da ta tashi, dama suna jira lokaci yayi ne tunda an rigada an shirya komai, Sam baiji daɗin hakan ba, amma yace "insha Allah," Ya fara tunanin halin da Umma zata shiga duk da ya tambaye ta abinda ke damunsa tace masa burinta ta ganshi ya zamo cikakken mutum kamar kowa, da wannan maganar ne yake samun ƙwarin guwaiwaar tafiya ƙasar waje. A ranar jiki a sanyaye ya dawo gida, ya sameta ta yi kwalliya cikin riga da skirt English wy tayi kyau sosai, a zuciyarsa kuwa ji yake da ace shi lafiyayyen namiji ne babu abinda zai hana shi shayar da ita a daren nan sai ya raba dare yana gamsar da ita, duk da kamar ya lura da ita mabuƙaciya ce, Kamar zata zauna a jikinsa yau kam sbda shagoɓa tadinga yi masa iri-iri, daga ƙarshe dai ya kasa ɓoye mata komai dole ya sanar mata, da sauri ta miƙe tabar gurin alamar tayi fushi, dole ya bita ya lallasheta tare da jaddada mata domin ta zeyi tafiya, Duk da tasan cewar akwai tuggu a A lamarin, ta aminta, ta zubo masa soyayyen dankalin turawa da gurasa wacce taji ƙuli da tumatur da albasa, sai kunun aya, sosai yake santi tare da ce mata zeyi missing girkinta idan yaje can, amma yanason yau ta taimaka tayi masa wani abun da zai dinga ci acan... Tom masoyana, saura pegi ɗaya mu kai 100 kowa yasan daga nan zamu shiga book2, wanda suka biya kuɗi suke yimin maganar dan Allah nayi adding ɗinsu a paid group na riga nayi sanarwa tun kafin mukai 80 nace idan har kunason daga mun gama book1 mu shiga book2 to tabbas ya kamata Ku biya kuɗinku, anjima zanyi posting posting page 99-100 daga nan zan rufe post section da comments section yau ɗinnan zan rufe insha Allah, 🤸Am sorry to say duk wanda yaga littafin MURAYU A TARE a waje wllhi littafin sata ne, idan kuma zaki siya dan ki fitarmin na yafe👏 Ga tsarin biyan kuɗin Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224 Normal group 300 Vip 700 Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel Mom Islam Book1 yana yi muku sai watarana😅wllhi inason duk wani masoyina ya karanta littafin nan sbda cakwakiyar cikinsa *💋MU RAYU A TARE💋* Mom Islam Book1 page 99-100 Finally book1 ya ƙare mu haɗu a book2 LIBYA Zaune yake hannunsa riƙe da waya, da alamu akwai abinda yake jira, rurin da wayarsa tayi ne ya sanya shi miƙewa da sauri tare da wucewa upstairs da sauri, abin mamaki bai ɗaga kiran wayar ba amma ya sauya kaya tare da sauya takalmin ƙafarsa, ya fice da gudu, Kai tsaye ya wuce parking space tare da buɗe mota zai shiga, cikin ladabi drivernsa yace "oga ayi haƙuri" kana ya nufo gurin shahazad ɗin, a inda drivern ya kalli yanayin fuskarsa, kamar an aiko masa da mala'ikan mutuwa, shahazad ɗin bai kulasa ba, dan ko arziƙin kallo bai samu ba, ya shigo mota, mai gadi na ganinsa ya wangale get yana miƙa gaisuwa, Acan station kuwa Mona da Hajara sunyi tsuru-tsuru, a tunaninsu hukuncin kisa za'a yanke musu, suna zaune a wani ɗaki wanda ya kasance bawai na tsanani bane, dan a gidan sama suke hawa na biyu, gabaki ɗaya Mona ta tayar da hankalinta sam ta gaza samun nutsuwa gani takeyi idan shahazad yazo sai ya yanke mata mummunan hukunci, tunda ita ce tayi musu silar komai, Hajara da ta lura da yanayinta tadinga yi mata faɗa akan ta kwantar da hankalinta sai taga beyi mata komai ba, tunda shiɗin wani lokacin yanada sanyi wani lokacin yanada zafi, Acan ɓangaren jami'an tsaro tunda suka gano Kharan da Kharan Khan su biyu ne, ana kama Kharan Khan aka saki Karan shi da Yazid, ranar da aka sake su aka buga jarida akan tarzomar dake faruwa, Kharan Khan kam sai inda hali ya yiwu, sbda yasha mugun duka, shahazad ya bada Umarnin ayi masa dukan da bazai gane wanda yake kansa ba, Kai tsaye su Kharan da Yazid suka wuce gida, yau kwanansu ashirin kenan rabon su da gidan inda suka bar gidan haka suka sameshi, har da abincin da Mona ta rage bata ƙarasa cinyewa ba, gashi duk tsutsa ta gama ci har ta bushe, tunda suka tafi aka karɓe wayoyinsu, ana sakinsu aka basu, dama shi karan ƙarama ce a hannunsa tunda ya riga da ya yarda babbar a hanya sbda tracking number da ake yi, duk da haka har yanzu yanajin done ya taimakawa Mona, sbda halin da take ciki, ya sani ita da wacce ya gansu tare suna tsananin halin neman taimako, amma yana tsoron daga fitowarsu ya tunkareta ai za'a iya samun matsala, Yazid yace "Kharan nikam wllhi gida zan koma bazan iya ci gaba da zama anan ba, sbda idan sojoji ko ƴan sanda suka zo neman wani bayani dole a tafi damu, zan koma ƙasarmu gaskiya" Kharan yace "tabbas haka ne, sbda a halin yanzu bamusan damuwar da iyayen mu da danginmu suka shiga ba, babbar damuwata kawu da bashi da lafiya ko a wane hali yake oho" A tare suka haɗa kaya, ragowar motar Yazid ce kaɗai a gidan, ya shiga inda ya ajiye key ya ɗauko, suka fito tare da garƙamawa gidan ƙaton kwaɗo suka shiga mota, cikin Sa'a sai gashi ta tashi suka wuce. Sunyi tafiya mai nisan gaske sannan suka iso garinsu *Ghadamis* gari ne mai yalwar kayan itatuwa ga tsari, abin mamaki ashe sunada kuɗi sosai, da Yazid da Kharan ɗan yaya da ƙani ne, mahaifin Kharan shine babba sannan sai mahaifin Yazid uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, kuma duk suna zaune a wannan babban gidan, parking ɗin da Yazid yayi ne yaja hankulan mutan gidan, Anty ta fito wato mahaifiyar Yazid sai Mama itace mahaifiyar Kharan, dukkansu da kuka suka ƙaraso dan basuyi tsammanin yaran nasu na raye ba, hakan yayi daidai da tsayuwar motar Leila, tunda Kharan ya hangota a cikin mota ya sauya fuska, Allah yasa yana rungume da mama har suka ƙarasa, Leila yarinyace ga Ministan Ghadamis, sam mahaifinta baya son lefin ta sannan duk abinda take nema bata rasashi ko ɗaukar rayuwar wani ne, yayi mata alƙawarin inhar yana raye sai ta samu duk abinda take so, ko zeyi yawo babu ko sisi, Sosai take son Kharan tun suna yara, tanada hali mai kyau, damuwarta idan har tana son abu to babu makawa sai ta sameshi, Tunda Kharan ya tafi, kullum sai tazo gidansu ta taya iyayenshi aiki, da haka ta sace zuciyarsu, kowanne su yaji yana matuƙar ƙaunarta, duk da sunada rufin asiri bai hana mahaifinta hidumta musu ba, musamman da ya tabbatar da zasu yarda ta auri Kharan ɗin, shima yayi iya bakin ƙokarinsa gurin ganin ya sa an nemo Kharan ɗin amma abin ya ci tura, Da sauri Leila take haura matatakalar da zaka taka ka haura babban parlonsu Kharan ɗin, cikin sakin fuska take cewa "Anty yaushe Kharan da Yazid suka dawo bani da labari?" Shiko yasha mur daga ƙarshe miƙewa yayi a sukwane ya wuce ɗakinsu, acan ya samu Yazid yana kiraye-kirayen waya, bayan ya gama ya kalli Kharan yace "mun dawo ko hutawa bamuyi ba, kana neman ɓata mana komai, haba Kharan yaushe zaka gane Leila sonka takeyi?" Bebi takan maganar Yazid ɗin ba yasa pillo ya toshe kunnuwansa. Shigowar anty da tiran abinci ne ya sashi saurin tashi ya karɓa yana cewa "sannu Anty" "Ya kamata Leila ta shigo ku gaisa tana tsananin sonka meyasa kake wulaƙantata karfa ya zamo tayi maka nisa a lokacin da kake buƙatarta a cikin rayuwarka" Yazid yace "wllhi Anty abinda nake gaya masa kenan, amma kice ta shigo Ni barin fita inga gari" "Zauna dai kaci abinci ai Leila ƴar gida ce, kunsha tafiya" Sam be bari ya zauna ɗin ba ya fice, daga shi sai dogon wando da farar bes, Kharan yakai Strawberry bakinsa kenan, Leila ta shigo fuskarta ɗauke da murmishi, Bai nuna yaji alamun shigowarta ba sai dai ga mamakinsa yaji ta rungumeshi, kyakkyawar rungumar da kowanne namiji zai buƙaci hakan daga gurin cikakkiyar mace kamar Leila, Ko in kula yayi mata, duk da har wani feeling yakeji game da hakan, ya rasa meyasa zata dinga takurawa rayuwarsa, shi san bai shirya dawowa ba, amma gashi ya dawo zata addabeshi da tsiyarta, sai da tayi masa kiss a gurare huɗu kafin ta ratayo hannunta a kafaɗarsa, cikin azama ya fara yunƙurin ture ta sai dai ina ta dage karfnta harda zagayo da hannuwanta a ƙugunsa, turo ƙofar da akayi ne yasa tai saurin zare hannayen, sai dai aikin gama ya gama dan Anty ta riga ta gansu, Cikin sauri ta juya fuskarta ɗauke da fara'a har take sanarwa da mama abinda ta gani, mama tace "dama yana sonta gulma ce, kinga a satinnan sai ayi biki kowa ma ya huta.. Shin za'ayi auran kuwa? idan sunyi auran wane irin zama zasuyi? amsar ku na cikin book2 Acan gidansu Shakur yau kwanan Sahla uku, mama ta gama ganota, abinda bata sani ba shine, yarinyar shahazad forest da kuma bincike akan shahazad ɗin da zatayi, sai dai jiya da suka keɓe ta tambayi Hindu labarinsa, ta kuma bata sbda hindu mace ce mai ruƙon gaskiya da Amana ta kasance mai ƙyamatar duk wani abun Ashsha da yake aikatawa, suna zaune a main parlo ya kira mama a waya, dama kamar jira take, ta ɗaga wayar jiki na rawa, "anga su Mona a halin yanzu ma zanje ɗaukosu ne" Mama tace "munayiwa Allah godiya gaskiya naji daɗi, gamunan sai mu haɗu acan" Ya katse kiran sbda isowa police station da yayi yaga mutane sun taru da uban yawa, hankali a tashe yayi parking mota tare da fitowa, abinda sam kwanyarsa bazata iya mantawa ba kenan, Mona ta faɗo tun daga gidan sama kanta ya fashe jini nata zuba babu rai a jikinta, ita kuma Hajara na kusa da ita a sume... Tofa😔idan Hajara ta farka wane irin hukunci kuke tunanin zai biyo baya? Muje zuwa Acan ɓangaren su Mama da Sahla da Hindu har da Shakur da Kawunsu aka shirya tafiyar, dan har sun isa gidan an buɗe musu tafkeken parlon mona, tun daga nan Sahla ta fara jin inama ace zata zamo ƴar aiki a wannan gidan, tabbas da sai ta mayar da shahazad mabaraci...! Kuna ganin hakan zata yiwu? NIGERIA Ƙauyen JIBGA Washe gari, bayan anyi sallahar asbha already dama sun gama shirya kayansu, tun kafin Mari ta fito Juwairiya ta shiga da kayanta mota, sbda tasan lokacin da za'a tafi, sannan ta shige gaban mota, dama sunyi sallama dasu malam da Baaba, dan har ta haɗa musu tsarabarsu an riga da ankai mota, acan ɓangaren Mari, masu zugata nayi masu yi mata nasiha sunayi, Daga nan suka fito tare da mutane da yawa, dan aƙalla zasukai fin talatin sai koke koke akayi, dole ma Mari ta shiga baya ita da ƴaƴanta, Kafin Al'amin ɗin yayi musu sallama suka wuce Abuja, Tun basu fita a cikin garin bebeji ba Mari ta kwarara Amai ta wanke motar, da sauri Al'amin yayi parking yana cewa "haba Mari, kinsan kina amai ai saiki ruƙo baƙar leda baki yimin amai a mota ba, wllhi duk motar ta ɗau tsami" Cike da masifa tace "kai Aminu wllhi kul ka kiyayeni dan ka auri ƴar binni mai kamada kasar Mayu hine zaka wani dinga himin togaciya wllhi bazan yarda a cimin mutunci ba, hegu munafukai" Ita dai Juwairiya ta toshe hancinta sannan ta sake yin ƙasa da gilashin gefen da take, Sunyi nisa sukaga mai rake, Mari tace "haka zamu dinga tafiya sai kace wasu waliyai ai dai ka saya mana abin sawa a bakin salati ko? Ga mai awara da miya can ma, sai da Juwairiya ta juyo ta kalleta, suka haɗa ido Mari ta galla mata harara... Wai kuna ganin anya idan aka isa gida babu matsala? RUGAR FULANI Sai yamma liss sannan Inna ta dawo Mahaifiyar Boɗɗo ta dinga bata labarin unguwar joma da Prince yayi, lokacin Bappa Dattijo ya shigo ya sanar mata da Prince ɗin koshi waye a gurinsu, Allah sarki jika ba wasa ba, Inna sai nan nan take dashi, dama ya sanar musu washe gari ze wuce, Washe gari, bayan anyi sallah ya shirya kayansa dan kwana uku yayi niyar yi, tunda yaga Boɗɗo zata kasheshi ya fasa, Bayan yayi wanka ya fito ya dawo ɗakin Bappa ya shirya cikin lallausan yadi mai ruwan ƙasa, sannan yasa hula yasa takalmi yayi kyau sosai, ya ɗaura agogo, ya fasa turare, dama an riga da an juye masa nono a robar fenti da lafiyayyar fura harda dambu, da man shanu shima a roba, tunda Boɗɗo taga ya fito ta fara buga ƙafa tana cewa "anguwar joma jan bika dan Allah ki tafi damu" Aikuwa Bappa yace ta kwaso kayanta tunda dai shanu yanzu basa gida, Gaban Prince ya bada rass idanunsa har fitar da ƙwalla suka fara... Tofa fans me kuke tunani, hamm idan ya sanyata a mota suka fara tafiya yaya kuke gani anya bazata aikata ɓarna ba kuwa?... Tabbas nayi mamakin makaranta littafin MURAYU A TARE, ashe haka yake da masoya, wllhi Nagode sosai ina sonku ina ƙaunarku, fatan shine mu haɗu a paid group domin aci gaba da gashi, karku mance littafin book1&2&3 ne zanyi kewarku😔 Allah ya bawa Kowa ikon biyan kudin littafin MURAYU A TARE, gwarama cakwakiya zallar ban dariya Wai Mona ta mutu ne kokuma dai ya akayi? Domin jin Ansar duk waɗannan sai mun haɗu a can HHH nace ba, wllhi littafin an ya wuce tunanin mom Islam Idan aka gama biyan kudi gobe ma zakuga posting, amma da kamar wuya duk da har yanzu mutane basu kai adadin inda nakeso ba, Karki siyi littafina ki fitarmin dan Allah na roƙeki Ga tsarin biyan kuɗin Normal group 300 Vip700 Dan Allah kar ayi min Vtu idan kuma ya zamo dole ayi min magana kafin ayi, Masu turo kati mtn zaku tura hoton katin ko numbobin jikin katin shedar biya ta nan 08141799224 Masu turawa ta account ga account number ta 3175689751 Zainab Habibu first Bank Shedar biya tanan 08141799224 Ƴan Niger kuma zasu tura karin Airtel Nagode Sai mun haɗu a paid group Inayiwa kowa fatan alkairi dan Allah wanda na ɓatawa ya yafe min nima na yafewa kowa.. *WATA MIYAR SAI A MAƘOTA KARKI BARI KIYI MISSING 🤸* Mom Islam takuce a koda yaushe fy