[9/9, 7:37 AM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_* (```DiNaayah SafraAz```) _*BEtweEn two LoveRs*_ *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @MatarSayyadee01_ _Arewabook@Matarsayyadee0_ ~FROM THE WRITER OF;~ *ƘANWAR MATATA* *BA NI DA GATA* *ƊAN FAARI* *SAI A LAHIRA* *NI DA SHI ABU ƊAYA NE* *ZINA BABBAR BALA'I CE* *AUREN CIKIN GIDA* *GARWASHI* *ANYA UBANA NE* *MY DESTINY ( ~ƘADDARATA~)* _AND NOW_ *DINAAYAH SAFRAAZ (ƘANWAR MATATA RETURN)* _Godiya ta tabbata ga Allah Ubangiji (SWA) da ya ara min rai da lafiyar soma rubuta wannan littafin. Allah kai na ke roƙo ka ba ni ikon rubuta abunda zai zama hujja a gare ni ba hujja a kaina ba!_ 😍💖 *To my lovely and amazing fans, ga ni dai na sake dawo wa domin nishaɗantar da ku tare da ilimantarwa kamar yadda aka saba. Ina fatan ba za ku ba ni kunya ba kamar yadda ni ma ba zan ba ku kunya ba. I know, you guys trust me alot, ba zan cika ku da magana ba ku dai kawai ku yi supporting ɗina ta hanyar subscribing, liking da comment. I swear duk wacce ta bari a kai wannan tafiyar ba tare da ita ba she really miss alot. Duk wacce ta karanta ƘANWAR MATATA na san tabbas a ƙage ta ke da na fara ɗaura DINAAYAH SAFRAAZ kuma ba za ta yarda single page ya wuce ta ba.* _Greetings to you my earthly paradise (Sayyadee) thanks for the support & encouragement_💖💖 *_Special greeting to you my fansa; Queen Zarah, Rahamatou, Halimatu, Mrs Dimples, Maman Musa, Darma (really miss you), Maman Areef, Sa'adatu etc... You're not just my fans but sisters from another mother. I love your support and caring, love you irin lodi-lodi ɗinnan_* 😍💓 ```My comment section people, ina so ku sani idan fa babu ku babu matar Sayyadee. Da bazarku na ke taka rawa domin ku ke bani ƙwarin gwiwa. Ina yin ku irin totally ɗinnan.``` *_The book is dedicated to you my name sake (Sahibata Oum Mufeeda) and all my family members. Allah ya ƙara haɗa kawunanmu waje guda_* 👊🏼💪🏼 Chapter 001 "Mmm! Ƙamshi mai nake ji haka mai daɗi, Who's cooking mom?" Sauban ya faɗi yana shafa ɗamammen cikinsa bayan ya ajiye handout ɗin da ya shigo da shi a kan cuisine. Mummy da ke zaune a kan 1sitter riƙe da lemon juice tana sipping kaɗan-kaɗan ta ce, "Dinaayah ce ke girki daga dawowanta yanzu-yanzun nan ko hutawa ba ta yi ba. Hijjab kawai ta cire ta shiga kitchen daga na ce mata ina jin yunwa, kuma na yi-na yi da ita ta dawo ta zauna ni zan yi girkin amma ta ƙi." "Dinaayah ce fa, ke ma kin san ba za ta taɓa yarda ta zauna ba bayan kin furta kina jin yunwa. To wai yaushe ma ta tafi Abujan da har ta dawo? Ba ta ce sai hutu ya ƙare ba?" Sauban ya faɗi yana ɓalle maɓalli shirt ɗin jikinsa. "Dinaayah da mugun ƙulafucin kuma! Ni da ma na san ba lalle ta iya yin sati biyu ba balle har wata ɗaya da kwana biyar. Yarinyar da kullum tana manne da ni bacci kawai ke raba mu!" Mummy ta faɗi. "Hmm, ni dama don kar na yi magana ne aunty Zakiyya ta zage ni shiyasa na yi shuru. Don na san Dinaayah ba za ta iya zaman sati guda a Abuja ba balle wata guda har da ƙarin kwanaki biyar. Yarinyar da ɗakin hajiya ma ba ta iya zuwa ta kwana sai wani gari can daban." "Wai fa yarinyar nan kuka ta saka masu ba bu dare ba bu rana! Ai kuwa aunty Zakiyya ta duddungure ta sannan ta saka driver ya dawo da ita. Tun suna hanya ta kira ni sai balbala faɗa take yi wai kar ta ƙara ganin ƙafar Dinaayar a gidanta tun da ba ta da kirki." Dariya Sauban ya yi tare da faɗin, "Ai na san aunty Zakiyya ba ƙaramin shaƙa za ta yi ba. Bari na je kitchen ɗin na taimaka mata." Gyaɗa kai mummy ta yi ta cigaba da sipping lemon juice ɗin da Dinaayar ce ta haɗa mata shi wai ta soma sha kamun ta gama girki. Da sanɗa Sauban ya nufi ƙatoton kitchen ɗin da ke falon, sai dai yana zuwa baƙin ƙofar kitchen ɗin Dinaayah ta ce, "Welcome ya Sauban! Don Allah buɗe fridge ka kwaso min carrot manya guda biyar ka yanka min." "Ke! Wai yanzu ɗinma sai da kika gane na zo kitchen ɗin?" ya ƙarisa maganar yana dungurin kanta. Dariya ta yi kamun ta furta, "Idanuna ne kawai ba sa gani amma hancina yana jin ƙamshi, tun tsayuwarka na gane ka iso saboda ƙamshin jikinka da na ji." Yana wanke carrot ɗin da ya ɗauko daga fridge ya furta, "Wai kina nufin duk wanda ya zo kusa da ke kina iya gane ƙamshinsa ko bai yi magana ba?" Gyaɗa kai ta yi sannan ta ce, "Allah ya ba ni wannan baiwar na jin ƙamshin mutun ko da kuwa za ku saka turare iri ɗaya, kai ko da ma babu ƙamshin turaren kwata-kwata. Mutum na tsayawa kusa dani ko gittawa ta inda na ke zan san ko wanene in dai har na san shi saboda ina iya jiyo ƙamshin jikinsa. Ka san fa ba wai sai lallai da turare kaɗai ake iya gane ƙamshin mutun ba. Ko wani mutun akwai irin ƙamshin jiki da Allah ya yi masa." Jinjina kai Sauban ya yi yana mai faɗin, "Yau na fara jin hakan a wajanki, amma kuma da ki ka faɗa sai na fara hasaso wani abu. Akwai wani course mate ɗina da na haddace ƙamshin jikinsa. Ko ban ganshi ba da na shaƙo ƙamshi zan kira hakan ko wari oho! Zan gane yana wajen da na ke. Ke wallahi ko rigarsa aka kawo min wanda ban taɓa ganinsa da ita ba in har ya taɓa sakawa a jikinsa zan iya cinkar nasa ne rigar. Warin jikinsa har amai ya ke ƙoƙarin saka ni." Murmushi Dinaayah ta yi tare da kallon inda ya ke duk da kuwa ba gani ta ke yi ba amma sun haɗa idanu sabida fahimtar ainahin inda ya ke tsaye da ta yi sannan ta furta, "Wata ƙila yana ɗauke da wannan cutar ce ta body odour shiyasa ka ke jin haka. Ni kuma ba irin wannan warin na ke magana a kai ba. Ina fahimta da jin ƙamshin duk wanda ya ke kusa dani in har na san shi sosai. Misali, duka 'yan gidan nan na san ƙamshin su kuma ko cikin magagin bacci idan ɗaya daga cikin ku ya gitta ta kusa dani kai tsaye zan ce wane ne?" Dafa mata kafaɗa ya yi tare da faɗin, "Ban san mai yasa ba Dinaayah, ban taɓa kallon ki a matsayin makauniya mara idanu ba. Wani lokacin ma mance wa na ke yi wai bakya iya gani kamar kowa." "Oh, wai ne ma? Amma kuma ni ma ban taɓa kallon kaina a matsayin mai naƙasu ba, don na tabbatar Allah shi ya san dalilin da ya sa ya halicce ni a haka. Ni gode masa ma na ke yi domin bai bani damar ganin ƙazantar da ke cikin duniyar nan ba da na ke jin mutane da dama suna faɗi, kuma ranar tashin ƙiyama idanuna ba za su ba da shaida a kaina ba wajen amfani da su domin kallon haramun. Idan zan roƙi Allah akan ganin wani abu a duniyar nan to zan roƙi ya ara min idanun gani tamkar kowa sau ɗaya tak kawai, shi ma domin kallon littafin Allah mai girma tare da ɗaura hannu akan kowacce kalma ina karantawa sannan kuma in kalli fuskan Mom da Dad ɗinmu! Ina jin kewar idanu ne kawai duk lokacin da na shafa Alqur'ani ko kuma fuskokin iyayanmu." Dungure mata kai ya yi tare da faɗin, "Wato mu ba za ki roƙi ki ga fuskokin mu ba ko?" Dariya ta yi sosai ta tare da kai hannu saitin da ta san yana wajen ta shafo fuskansa sannan ta furta, "Na san kalar fuskanka mana! Ai kamanninmu ɗaya da kai sosai kai da ya Sam'an." Harararta ya yi tamar irin tana kallonsa ɗinnan. Ita kuma da ke juya stew ɗin da kan gas sai cewa ta yi, "Hararata ta ke yi ko?" Waro idanu ya yi tare da faɗin, "Ke! Ya aka yi ki ka san ina harararki?" Dariyar ta kuma yi kamun ta ce, "Idanuna ba sa iya ganinka, amma sanin halinka da na yi ne ya sa na ji a jikina kana hararata." Hannu ya kai ya tallabe ƙeyarta tare da faɗin, "Ke ɗin nan ko? Allah ya shirya mana ke! Wani lokacin sai ki riƙa abu kamar aljana wallahi. Kuma da ki ke wani cewa kin san kamanninmu ɗaya da ke ni da Sam'an ai don kin ji kowa yana faɗin haka ne." "Ba wani nan! Na riga na sani tun kan mutane su faɗa cewar ni da kai da ya Sauban tamkar an tsaga kara haka muke." Dinaayah ta faɗi tana mai kai hannu ta kashe gas sabida fahimtar da ta yi miyar ta soyu. Juyawa ta yi tare da nufa wajen dishes tamkar mai idanu ta ɗauko plate biyu. Da idanu kawai Sauban ya bi ta cike da matsanaicin ƙaunarta. Da sosai ta ke ba shi tausayi tun suna ƙanana amma daga baya da ya fahimci irin baiwar da Allah ya mata fiye da masu idanu sai ya ji sam bai kallonta a matsayin musaka wacce ta rasa wani ɓangare na ni'imar ubangiji da ya yi wa ɗan Adam. Dinaayah ba bu takun da bata haddace ba a cikin gidan, kama daga ɓangarensu kaf, ɓangare Hajiya har da ɗakin matar babansu aunty Habbooba kasancewar can ɗin ma dandalin firar su ce idan suka haɗu duka da sauran 'yan uwanta. Shara, wanke-wanke, girki da wanki duk babu wanda ba ta yi. Tun daddynsu na faɗa kamar ya ari baki har ya haƙura ya zuba idanu ganin Dinaayar ita ke ƙaunar haka, kuma duk abunda ta ke so yana mugun taya ta sonsa saboda matsanaicin tausayinta da ya ke ji. Ji ya ke da ana kyautar idanu da ya daɗe da cire nasa idanun ya mallaka mata. "Kawo plates ɗin na taya ki serving" Sauban ya faɗi yare da amsa ya nufi gaban tukunyar da ta sauke white basmati rice with peas and carrot ya zuba a plates ɗin sannan ya juye sauran a cikin kula ya wanke tukunyar tare da mayar da shi inda ya ke saboda Dinaayar, kasancewar ta san ma'ajin komai a kitchen da store, kuma dokar gidan ce da daddy da mummy su ka na na duk wanda ya yi amfani da wani abu a kitchen ya tabbatar ya mayar da shi inda ya ke. Da wuƙa da kayan wuta irin su blander, kettle, electric cooker da sauransu ne kawai ba ta amfani da su sabida dokar da daddy na kar wanda ya bari ta yi amfani da kayan wuta idan ya wuce maƙala cajin waya, shima charger ɗin na jikin socket sai dai kawai ta danna switch ta kunna tare da maƙala cable ɗin a jikin waya. Sai kuma kunna Braille Display ɗinta (Computer ɗin da makafi suke amfani da ita). Shi ma wani lokuta da dama mom, yaya Sauban ko shi kansa daddyn idan yana gida ke kunna mata. Duk da sau da dama ta fi amfani da Laptop sai ta yi using da keyboard ɗinsu na makafi. Wajen miyar da ke mugun ƙamshi ya nufa sannan ya zuba a ƙaramin bowl guda biyu sannan ya miƙa mata plate ɗaya ya furta, "Ga na mom ki kai mata sai in fito da na mu abinci." "Amma tare da kai za mu ci ko?" Dinaayah ta faɗi bayan ta amsa plate ɗin da ya kai saitin hannunta. "Ke ma kin san ai tare za mu ci. Ko da ma mun taɓa raba kwanon abinci ne idan ina gida?" Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Kawai na faɗa ne don in ji mai za ka ce." "To ai kin ji, kuma kin ji daɗin saka ni magana." "Ina miyar mummy?" ta faɗa kasancewar plate ɗin white rice ɗin kawai ya miƙa mata. "Na zuba mata a kai ai, ki wuce ki kai mata" ya faɗi hakane duk da bai yi hakan don jin abunda Dinaayar za ta ce. Dariya ta yi tare da faɗin, "Gwada ni wai ka ke yi? Babu miyan akan wannan abincin da ka ba ni, don da akwai zan ji kamshinsa." "To uwar 'yan jin ƙamshi! Ki je ki kai zan biyo ki da miyar." ya faɗi yana murmushi da yaba basirar da Allah ya mata. Shi ma bai iya ɗauko duka bawl ɗin miyar da na su plate of rice ɗin ba, bowl ɗin miyan ya fara kaiwa sannan ya dawo kitchen ɗin ya ɗauko na su ya dawo nan tsakiyar falon ya ajiye. "Sauko mu ci abincin ga na mu a nan, taku huɗu za kiyi." Sauban ya faɗi yana zuba miya a kan white rice ɗin. Zama Dinaayar ta yi daidai inda ya ke a gefensa, shi kuma sai ya miƙe ya koma yana facing ɗinta saboda abincin ya masu daɗin ci. Spoon ta ɗauka ta shiga ɗibar miyan tana sakawa a kan shinkafar kamun ta cakuɗa daidai inda ta saka sannan ta kai baki. Duk wanda ya shigo ɗakin ya ga yadda Dinaayah ke cin abinci cikin mutsuwa zai iya rantsewa da ubangijin halittu tana gani da idanunta in har bai santa ba. Sallama Aleesha ta yi a bakin ƙofa fuskanta ɓutu-ɓutu tamkar an aiko mata da saƙon mutuwa. Amma idanunta na sauka akan tagwainiyarta Dinaayah ta saki wani faɗaɗɗan murmushi tare da nufar Dinaayar da gudu ta rungume sannan ta ce, "I really miss you my twin sis wallahi. Ai har na fara shirin binki Abujan gobe, ashe ma kina tafe." ta ƙarisa maganar tana mai wurgar da labcoat ɗin da ke hannunta sannan ta zauna a gefen Dinaayar tare da amsar cokalin hannunta ta ɗebo shinkafa ta saka a baki. Ranƙwashi mai zafi Sauban ya sakar mata a tsakiyar ka tare da faɗin, "Dan gidanku ba ki iya gaisuwa da sannunku da gida ba? Kuma da ki ka zauna kina cin abincinmu, who gave you that permission?" Murguɗa baki Aleesha ta yi tare da faɗin, "Kai don Allah ya Sauban akwai zafi fa." ta faɗi maganar ne tana sosa inda ya kafa mata ranƙwashin. Mummy duk tana jin su amma ko kallon inda su ke ba ta yi ba don halinsu ne hakan, suna matuƙar-matuƙar ƙaunar junansu amma kuma duk suka haɗu sai sun yi faɗa. "Kun duba Benazir kuwa? Yau kwata-kwata ban gan gittawarta ba." mummy Sarah ta katse musu rigimar ta su. A tare Dinaayah da Aleesha suka juyo suka kalli mummy ɗin tare da faɗin, "Yau bata shigo nan part ɗin ba kwata-kwata?" "Bata shigo ba kam, kuma daddyn ku ya ce kamar a kwance ya ganta lulluɓe da bargo a falo. Ni ma na shiga duba ta ɗazu amma ban samu ganinta ba saboda tana ɗaki a kwance. Tsam Dinaayah ta miƙe tare da nufa ƙofar fita don kaf gidan idan aka cire ya Sauban da Aleesha, Benazir ɗin ita ce suka fi shaƙuwa sosai kamar ita ce ma twins sis ɗin tata ba Aleesha ba. Don ko Aleesha sai dai ta gwadawa Benazir ɗin mama ɗaya suka sha amma iya shaƙuwa sun shaƙu da juna fiye ma da Aleeshar ta wani ɓangaren. "Ki tsaya ki gama cin abinci mana! Mummy ke ma da kin bari ta gama cin abincin sai ki faɗa mata, yanzu gaba ɗaya duk ta tashi hankalinta kuma na san wannan abincin sai wani lokacin kuma," Sauban ya faɗa yana ɗan ɓata fuska. Dinaayah kuwa da sauri ta ƙarisa ficewa daga ɗakin gudun kar mom ɗin ta su ta dakatar da ita tare da tilasta mata cin abincin kamun zuwa dubo Benazir ɗinta. Gab! Suka ci karo ta yi saurin ja baya don sam ba ta ji tahowa da ƙamshin mutum ba saboda gaba ɗaya hankalinta ya koma wajen Benazir, "Sorry ya Sam'an ban ji tahowarka bane. Benazir ce ba lafiya shine na ke son zuwa dubo ta." Fuskan nan nasa a ɗaure kamar ko da yaushe wanda kullum mom sai ta yi ƙorafi a kan haka tare da goranta masa tana faɗin kaf danginta da na mahaifinsa babu mai fuskan shanu sai shi. Sam da mugun wuya mutum ya ga dariyar Sam'an, idan abu ya yi abu murmushi kawai ya ke yi wanda wannan dalilinne ma ya sa ake saurin bambamce su tsakaninsa da Sauban duk da kamanninsu da ya yi mugun ɓaci don hatta thumbprint ɗinsu iri ɗaya ne. Komai na su iri ɗaya sak, fara'ar fuska ce kawai ta bambamta su. "Kai don Allah ya Sam'an! ka riƙa ɗan dariya ko kaɗan ne idan ba haka ba babu budurwar da za ta soka" ta faɗi tamkar irin tana ganin fuskan nan nasa wanda sam ba haka bane, farin sanin da ta yi wa kaf 'yan gidan nasu ne kama daga iyayanta har ƙannenta da kuma yawan faɗin rashin fara'arsa da mutane da 'yan uwa suke yi. Kuma hakan ba wai yana nufin bai shiga cikin su bane, wani lokacin har abinci ana ci tare da shi. "Ke! Ina wasa da ke?" ya faɗi fuskan nan nasa a ɗaure amma a wajansa wai a hakan da sigar wasa ya faɗi maganar. Aleesha da ta biyo bayan Dinaayah ce ta ƙariso inda su ke tare da faɗin, "Mr Boss ka dawo?" Daƙuwa ya musu su duka sannan ya raɓe su ya shige ciki. Dariya suka kwashe da ita su duka sannan suka riƙe hannun juna suka nufi part ɗin amaryar babansu wato maman Benazir. Knocking su ka yi sannan suka murɗa handle ɗin ƙofar suka shiga, babu kowa a falon sai ƙamshin turaren kasko da ke tashi yana shiga ƙofofin hancinsu. Kai tsaye su ka wuce ɗakin Habbooba da ke upstairs, Aleesha ce ta murɗa handle ɗin za ta tura ta buɗe sai Dinaayah ta yi saurin kaɓe mata hannu tare da faɗin, "Knock first mana malama!" Turo baki ta yi sannan ta yi knocking ɗin tare da tura ƙofar lokaci guda. Lokaci guda ta zaro idanuwa akan Benazir da ke zaune dirshan a tsakiyar gado tana cin wafer biscuits da ke cikin wani ƙaton dogon kwali. Sai dai turo ƙofar da Aleesha ta yi ya yi daidai da wani irin zabura da Benazir ta yi har tana jifa da biscuits ɗin hannunta ta ja bargo har ka saboda a tsammaninta mahaifiyarta ce ta shigo ɗakin. "Munafuka!" Aleesha ta faɗi tare da nufa inda biscuits ɗin ya faɗi ta ɗauka, ita kuma Benazir ta yi saurin yaye bargon tare da sakin doguwar ajiyar zuciya. "Ashe yan ukuna ne! Wallahi na ɗauka aunty ce (ita ma auntyn ta ke cewa kamar yadda su Dinaayar da duk yaran gidan suke faɗa) ita na yi wa ƙaryar rashin lafiya ai. Ke kuma ban biscuits ɗina mayya kawai!" Benazir ta ƙarisa maganar tare da kai hannu za ta wafce biscuits ɗin amma sai Aleesha ta yi baya tana kai biscuits ɗin bakinta ta ɓalla. "Gaskiya kin ɗauki hakkina Benazir! Na ɗauka da gasken-gaske ba ki da lafiya har ina ƙin cin abinci." Dinaayah ce ta faɗi hakan tare da zama a bakin gado ta lalubi hannun Benazir ɗin ta riƙe domin jin temperature ɗinta. "I'm fine, sister. Aunty ce ke so na bi Sausan (cousin sister ɗinta 'yar wan mamanta) zuwa Maiduguri ni kuma Allah ba zan je ba, weather garin ba dai mahaukacin zafi ba!" Benazir ta faɗi tana yamutsa fuska. "Kawai saboda ba ki son zuwa Maiduguri sai ki fara ciwon ƙarya! Kuma Allah weather ɗin Maiduguri yana da kyau kuma yana gyara fata. To ki ma kwantar da hankalinki don Hajiya na nan tana shiri ƙarshen shekarar nan gaba ɗayanmu za mu tafi can auren yarinyar aunty Laure." Aleesha ta faɗi tana cin biscuits. "Ke don girman Allah! Ba dai Surayyar aunty Laure za ai wa aure ba? Yarinyar nan ta kai fifteen kuwa? Na shiga uku!" Benazir ta faɗi har da dafa ƙirji. "To wallahi ni ma dai na sha mamaki don a bakin da bai ƙarya na ji. Kin san dai Hajiya ba za ta faɗi ƙarya ba." Aleesha ta faɗa. Sai a lokacin Dinaayah ta saka baki wajen faɗin, "To ba ƙauye bane. Su ai ba su yarda yarinya ta haura sha huɗu ba a ɗakin miji ba tunda ba karatu suke ba. Kin manta labarin da hajiyar ta ba mu lokacin da dangin mahaifin aunty Laure su ka yi amfani da power su ka ɗauke ta a wajan ta su ka mata aure a ƙauye bayan har makaranta ta fara kuma ta yi nisa. Bayan rasuwar mijin ne fa hajiya ta sakawa idanunta kwalli ta kuma taho wa da aunty Lauren a wani ziyara da ta kai Maidugurin sai dai kuma dangin mahaifin yarinyar da ta haifa sun hana tafiya da ita 'yar aunty Lauren wai baza su ba da ba, haka nan hajiya ta haƙura don sun fi ƙarfinta tunda dangin uba ne. Suna dawowa Kaduna kuma hajiya ta jefa aunty Lauren a school, kuma ba gashi yanzu karatun ya taimaka mata ba tana aikinta a asibitin daddy." "Aikuwa dai! Hajiya na ƙaunar aunty Laure sosai kamar yarinyar da ta haifa a cikinta." Benazir ta faɗi. "To ai sun shaƙu ne, tun fa tana da eleven years hajiya ta ɗauko ta." Dinaayah ta faɗi. "Aunty Laure mutuniyar daddynmu!" Aleesha ta faɗi tana dariya tuna irin tsokakar junan da suke yi duk suka haɗu. "Ku tashi mu je side ɗin mummy mu ci abinci yanzu na gama." Dinaayah ta faɗi. "Kamar kuwa kin san baƙar yunwa na ke ji, pretending ne ya hana ni fita zuwa kitchen in nemi wani abu na ci." Benazir ta faɗi yayin da ta ke saukowa daga kan gado. Aleesha da idanu ta bi dogon gashin Benazir ɗin da ya kai kusan har tsakiyar bayanta ga cika da tsayi irin na asalin yaran shuwa arab. "Wai Bena bakya jin kanki na maki nauyin da wannan tulin gashin da kika tara." Hannu Benazir ta kai ta tattare gashin ta ɗaure da ribbon sannan ta saka hulan tare da faɗin, "Idan zai ƙaru fiye da haka ma ina so. Ni fa ban cikin matan da ke cewa wai basu san gashi saboda suna da shi, son abuna na ke yi sosai." ta ƙarisa maganar tana shafa jan baki a leɓenta. Taɓe baki Aleesha ta yi tare da faɗin, "Allah Bena idan ba ki rage kwalliya ba wata rana sai aljanun kwalliya sun shige ki. Part din mum fa za mu shine har da wani saka jan baki kamar wacce za ta fita anguwa." "Hausawa sun ce idan kana da kyau ka ƙara da wanka. Ku taso mu tafi." ta ƙarisa maganar tare da kamo hannun Dinaayah suka fice daga ɗakin Aleesha biye da su a baya. Tsaye ya ke a tsakiyar falon sanye cikin dark blue suit na company _brooks brothers_ yana gyara zaman tsadaddiyar baƙar cover shoe ɗin da ke sanye a ƙafarsa. Gaba ɗaya ƙamshin _Imperial majesty_ da ya game da _Caron Poivre_ ya bada wani fitinannan ƙamshi mai kwantar da zuciya. Aunty Habbooba a gefensa sanye cikin fari ƙal ɗin lifaya mai zanan ganye da jan kala, sai rigar da ke cikin lifayar kalar baƙi mai dogon hannu, yatsun hannunta ya sha lalle ja sai ɗaukar idanu ya ke, haka ma farar ƙafarta tasha lalle, sannan kyakkyawar fuskanta ya sha kyau. Magana ta ke masa wanda shi kaɗai ya ke jin abunda ta ke faɗi suna murmushi. "Daddy yana falo tabbas!" Dinaayah ta faɗi saboda shaƙo ƙamshin turaransa da ta yi. "Aiko dai gashi can shi da aunty tamkar za su gasar kyau." Aleesha ta faɗi tana murmushi don ba ƙaramin kyau dad da auntyn tasu su kai ba. Babu wanda zai kalli dad ɗin ya ce yana da manya 'ya'ya kamar su Sauban da su kai 26years of age ba. Idan suka jero shi da su Sam'an za ka rantse babban yaya ne tare da ƙannansa. Kamar yadda dad bai tsufa haka ma matan nasa mummy Sarah da aunty Habboba don dukkan su babu na banza wannan na wane wannan. Saukowarsu ta ja hankalin dad da aunty Habbooban suka zubawa stairs ɗin idanu fuska ɗauke da farincikin ganin 'ya'yan nasu. "The great daddy, Dr. Ibrahim Khalilullah Nurudden!" Benazir ta faɗi tana ƙoƙarin shiga camera a wayarta ƙirar iphone 14pro.... #DINAAYAH SAFRAAZ ##MATAR SAYYADEE #BETWEEN TWO LOVER'S #LOVE STORY #SADAUKARWA #CIN AMANA #ZAZZAFAR SOYAYYA #TAUSAYI #AFFECTION ##KHALILULLAH NURUDDEEN #KAISAAR #SAFRAAAZ THE KILLER 08128755583 no phone calls please, whatsapp only! Share fisabilillah [9/10, 2:31 PM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_* (```DiNaayah SafraAz```) _*BEtweEn two LoveRs*_ ☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them` ##Matar Sayyadee #Kaisaar #SAFRAAZ THE KILLER #DINAAYAH #Benazir #Aleesha Chapter 002 Hotuna ta riƙa ɗaukar su shi da aunty Habbooba kamun ta ƙarisa kusa da shi tare da su Dinaayah su kai salfie har da aunty Habbooban. "The beauty, the precious light and the caring one! 'Yan ukuna Allah ya muku albarka." faɗin Dr Khalilullah yana shafa kawunansu cike da jin daɗi. Gaba ɗaya 'ya'yansa akwai sunayan da ya saka masu ban da asalin na yanka da kowanne ke da shi. Sam'an shine the _Agelast_ (saboda rashin dariyarsa), Sauban (the Champion), Dinaayah yana kiranta da sunaye uku, (Precious Light, genius ko kuma ya ce Alayna Noor), Benazir (Beauty), Aleesha (The caring one), Ayraah (Lazy Queen), Amla (Silent soul), sai auta Afreen (Little Queen). Akwai wata irin mahaukaciyar soyayya da shaƙuwa tsakaninsa da 'ya'yansa. Bai haɗa 'ya'yansa da komai ba a duniya. Yana iyakacin bakin ƙoƙarinsa sosai ganin bai fifita ɗayansu akan ɗaya ba, sai dai a bayyane ya ke ga kowa irin ƙaunar da ya ke wa Dinaayah wanda bai rasa nasaba da nakasar da take da shi na rashin idanu. Sosai ya gina soyayya da ƙaunar juna a tsakanin kaf 'ya'yansa, bai yarda iyayan sun raine su akan 'yan ubanci ba. Ya nuna masu dukkansu ɗaya suke domin jini ɗaya ke yawo a jijiyoyin jikinsu, haka Hajiya mahaifiyarsa ita ma tana nata iyakacin bakin ƙoƙarin. Matan nasa ma sun basa haɗin kai sosai don idan kaga kan 'ya'ya sun rabu to tabbas daga iyaye mata ne saboda kishi. "Daddy, ka yi kyau sosai!" Dinaayah ta faɗi tana shafa suit ɗin da ke jikinsa, ɗaya hannuta kuma yana taɓa fuskansa har zuwa karan hancinsa saboda ɗan duƙowar da ya yi, don duk tsayinta daddyn ya fita tsawo. "Dagaske Dinaayah? Ki ce idan na fita zan yi kasuwa kenan?" ya faɗi yana satar kallon aunty Habbooba da gefen idanu. Hannu Dinaayah ta saka a baki ta toshe tare da faɗin, "Ba ruwana kai da aunty ne, kuma ai ka riga ka gama aure. Mum na matsayin mace biyu ne haka ma aunty, ko auntynmu?" ta ƙarisa maganar tana kallon inda ta ke kyautata zaton auntyn na tsaye a wajen saboda ƙamshinta da ta ke ji. "Faɗa masa dai Dinaayah!" aunty Habbooba ta faɗi tana hararar daddyn da ke murmushi. Benazir ce ta fashe da dariya kamun ta furta, "Dinaayah, Aleesha! Aunty Habbooba once says.....?" Dinaayah da Aleesha suka haɗa baki wajen faɗi, "Wallahi ka sha ƙarya daddynsu! Ai ka gama aure ka rufe ƙofa tuntuni. Kai da aure sai dai a aljanna idan ana yi wallahi tallahi." Gaba ɗaya har daddy dariyar suka saka banda aunty Habbooba da ta yi kicin-kicin tana kallon 'yarta Benazir tare da faɗin, "Sai kin ci gidan ku idan ni tsararki ce, au kwaikwayota ku ke yi? Ki gama laɓe-laɓen ciwon sai ki bi Sausan Maiduguri." Wani dariyar suka kuma fashewa da shi har da tafawa da daddy. Aunty Habbooba kuwa bin su ta yi ɗaya bayan ɗaya ta tattallabe masu ƙeya tare da kora su waje. "Kar ki takura mata tunda ba son zuwa take ba. Kin ga biki ma na matsowa na 'yar wajen Laure wanda za a yi ƙarshen shekaran nan, da an gama bikin sai ki ɗauke ta ku tafi zaga dangin," Dr Khalilullah ya faɗi bayan ya mayar da kallonsa izuwa gare ta. Taɓe baki ta yi tare da faɗin, "To ai shikenan. Dama ai kai ke ɗaure masu ƙafafu suna yin abunda suka ga dama a cikin gidan nan." Murmushi ya yi tare da faɗin, "Sai na dawo!" "Allah ya tsare ya kiyaye min kai daga sharrin matan zamani masu yi tamkar su ɗauke mijin wasu su gudu." aunty ta faɗa. Dariya ya yi mai faɗi kamun ya ce, "Kuma gashi ni sai na cike sauran ƙofofin da suke buɗe ba!" da sigar zolaya na ƙarisa zancen. "Wallahi ka sha ƙarya daddynsu! Ai ka gama aure ka rufe ƙofa tuntuni. Kai da aure sai dai a aljanna idan ana yi wallahi tallahi." aunty habboba ta faɗi har da tafa hannu. Dariya Dr ya yi sosai don dama abunda ya ke son ji ta faɗa kenan shiyasa ya zolaye ta. Aunty Habbooba akwai mahaukacin kishi na fitar hankali. Kowa na gidan ya san haka shiyasa 'ya'ya suke tsokalarta wani lokacin. Ko kuma hakanan idan duka suna zaune a falo sai ɗaya ta ɗau wayarsa, ɗaya kuma sai ta kira number ɗinsa, ɗaya kuma sa ta nufe sa da wayar tana faɗin, "Daddy ga wata number da ka yi saving da Sweetheart tana kira." tun kamun dr da ya san tsiya suke wa aunty Habbooba ya amsa wayar caraf aunty Habbooba ke karɓewa idanunta a waje tana kallon screen ɗin wayar, da zarar ta ci karo da sunan ɗaya daga cikin 'ya'yan sai ta yi kansu da gudu za ta make, gaba ɗaya sai su hau yi mata dariya har da dad da mummy Sarah. "To mai da wuƙar na janye zancena!" ya faɗi yana dariya tare da ficewa daga ɗakin. Kai tsaye part ɗin hajiya ya nufa. Knocking ya yi a ƙofa, 'yar aikin hajiya mai suna Lawisa ta zo ta buɗe masa ƙofar tare da ɗan rusunawa cike da girmama ta gaida shi, shima cikin sakin fuska ya amsa mata gaisuwar sannan ya wuce ciki yana faɗin, "Ina Hajiya?" "Tana ciki yanzu ta shiga domin ta kwanta ta huta. A kira ta ne?" Lawisa ta faɗa. "A a barta ta huta idan na dawo zan shigo." ya faɗi tare da juyawa ya bar ɗakin. Kiciɓis su kai da wansa ya Abdul-Hakeem shi ma za shiga duba hajiyar. "Dr fita za ka yi?" ya faɗa yana miƙa masa hannu su kai musabaha. "Eh zan je asibiti ne akwai wani patient da ke ƙarƙashin kulawata shi na ke son dubawa, daga nan kuma zan biya Maiduguri road." faɗin Dr Khalil. "Ma sha Allah, to Allah ya kiyaye sai ka dawo. Bari na duba hajiya." Abdul-Hakeem ya faɗi. "Ta kwanta fa, ni ma duba na zo yi sai Lawisa ta ce ta shiga ɗaki domin ta ɗan samu hutu shiyasa ma na juyo." "Ok to shikenan ni ma bari na wuce idan ta tashi na dawo." faɗin Abdul-Hakeem ɗin tare da jerawa da ƙaninsa Dr Khalil. Sai da suka zo inda za su rabu kowa ya yi hanyarsa, Abdul-Hakeem ya yi hanyar part ɗinsa da ke kusa da na Habbooba, shi kuma Dr Khalil ya yi hanyar part ɗin mummy Sarah. "Assalamu alaikum!" daddy ya faɗi tare da murɗa handle daidai lokacin da gaba ɗayansu suka amsa masa sallamar suna kallon ƙofar har da Dinaayar da bata gani. "The _Agelast_ and the _Champion_" ya faɗi yana kallon sashin da Sauban da Sam'an suke zaune waje ɗaya suna kallon abu a cikin laptop ɗin Sam'an ɗin. Nan da nan fuskan Sauban ya mamaye da fara'a yayin da Sam'an ya furta, "Welcome dad!" fuskan nan babu ko ɗigon fara'a. "Hmm! Wallahi ka riƙa fara'a ko za ka yi kyawun gani." daddy ya faɗi yana harararsa. Bai ce komai ba sai ma mayar da dubansa da ya yi kan screen ɗin laptop. Su Benazir sai dariya su ke ƙasa-ƙasa. "Daddy asibiti za ka tafi?" Benazir ta tambaya tana miƙewa tsaye. "Eh amma ba jimawa zan yi ba zan biya Maiduguri road. Wannan petient ɗin da ke fama da mouth cancer zan duba. Ina mummyn ku?" ya ƙarisa maganar da tambaya. "Tana sama, bari na yi sauri na shirya ni ma akwai abunda zan yi submitting sai na hau abun hawa na dawo ko kuma ka taya ni roƙon ya Sauban ya zo ya dawo dani gida." faɗin Benazir. "Kar ma ki kuskura ki fara, babu inda za ni yau a gidan nan!" ya Sauban ya faɗi yana shurinta da ƙafa kasancewar tana zaune a ƙasan kujeran da ya ke zaune ne. "Ku yanke shawarar ni bari na duba mom ɗin ku a sama iyayan rigima." Dr ya faɗa yana nufa hanyar stairs ɗin da zai kai shi zuwa ɗakin matarsa sanyin idaniyarsa. Tura ƙofar ya yi daidai lokacin da mummy Sarah ta juyo da fuskanta izuwa ƙofar, wani irin sanyayyiyar murmushi suka sakarwa junansu kamun nan ya ƙarisa shigowa ya maida ƙofar ya rufe sannan ya jingina da ƙofar ya ware hannayensa tare da faɗin, "Come here!" Kai tsaye ta nufe sa tare da shigewa jikinsa sannan ta furta, "I miss you soo much! Yau gaba ɗaya sau uku kawai na ganka." Kumatukanta ya ja tare da soma kallonta daga sama har ƙasa, sanye ta ke cikin atampa maroon colour da ya yi mata matuƙar kyau. Ɗinkin doguwar riga ce A shape ta ji beatwork kuma ba ƙaramin kyau ta yi mata ba, ɗaurin ɗankwalin zamani ta yi da ya ɗan bayyana gashinta ta can wajen ƙeya. "Ni ma na yi kewarki sosai! Kin yi kyau sosai bari na yi mana hoto" ya ƙarisa maganar tare da fiddo wayarsa ya yi masu hoto kusan kalaa biyar sannan ya soma ɗaukarta ita kaɗai tana masa styles kala-kala. "Na samu na kallo a office kamun attending petients ɗina." ya faɗi yana mayar da wayar cikin aljihu. "Ka turo min hotunan ta whatsapp ni ma na samu na kallo kamun ka dawo." "Sai kin biya tukun!" ya faɗi yana ɗage mata gira ɗaya. Magana ta raɗa masa a kunne da ya sa shi fashewa da dariya, ita kanta da ta yi maganar sai da ta yi dariyar. "Aikam kin biya, zan tura miki ina isa asibiti. Amma kuma sai kin cika alƙawarinki idan na dawo." "Baka da matsala a shirye na ke!" ta faɗi tana ba shi side hug shikuma ya jawota ya rungume gaba ɗaya tare da kissing kumatunta sannan ya furta, "Sai na dawo!" "Allah ya tsare ya kai ka lafiya kuma ya dawo min da kai lafiya." "Ba za ki addu'a Allah ya rufe min idanu akan kallon wata wacce za ta dage sai ta yi wuff da ni ba?" "Ai kai dai ka fi kowa sanin ban tsoron kishiya. Ta zo kowa ta iya allonta ta wanke." Dariya ya yi tare da faɗin, "I trust you! Amma dai ko yaya ne a riƙa nuna ana jin kishina zan ji daɗin haka." "Ana kishinka mana. Sosai ma! Kawai dai ban sakawa raina abunda na san zai iya yuwuwa har hakan ya jawo min wata matsala a zuciya da kuma tsakanina da happiness ɗina." "To ki kwantar da hankalinki ma don na rufe ƙofa, ta biyun ma da na ƙara don an fi ƙarfina ne babu yadda na iya." ya faɗi yana ɗage gira. Ƙofa ta nuna masa tare da faɗin, "Oya bye-bye Allah ya kiyaye hanya!" ta faɗi hakane sabida sam bata son suna magana yana kawo zancen Habbooba. "Au korata ki ke yi? Babu komai shikenan, zan tafi amma wallahi sai na dawo anjima kuma a nan zan kwana!" "Ina maraba da hakan tunda girkina ne!" ta faɗi tana dariya. Shima dariyar ya yi tare da juyawa ya fice daga ɗakin tana biye da shi a baya. Gaba ɗaya yaran kallon sama su ka yi yayin da iyayan nasu ke saukowa zuwa falon. Tafi suka fara yi raf-raf amma banda Sam'an da kallo ɗaya ya yiwa iyayan nasa ya mayar da kai kan laptop ɗinsa yana yaba kyau da soyayyarsu cikin zuciyarsa don ba ƙaramin burgesa su ke yi ba. "Wallahi kuma sai na maku hoto, ku tsaya cak kar ku ƙara ko taku ɗaya." Benazir ta faɗi tana ciro wayarta a cikin aljihun wandon da ke jikinta ta shiga ɗaukarsu hotuna. "Yauwa to yanzu ku sauko sai mu yi dukkan mu. Ya Sam'an don Allah ka tashi ka ɗauke mu" ta ƙarisa maganar tare da aje masa wayar a kan laptop ɗin sannan ta kamo hannun Dinaayah ta miƙar suka ƙarisa inda su mummyn suke tare da Aleesha da Sauban. Aje laptop ɗin ya yi a gefe sannan ya miƙe ya shiga ɗaukar su hoto fuskan nan babu fara'a tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa. Sai da ya masu kusan kala biyar sannan ya juya camera ya yi masu salfie har da shi sau ɗaya kawai shi ma don ya san dole mummy ta yi ƙorafi shiyasa. "Nonsense! Kana tunanin ka burge ni ne? Dama baka shigo ka ɓata mata hotonmu ba da wannan fuskan shanun naka. Ni dai kaf zuri'a ta babu mai irin wannan fuskan, haka ma gefen Dr na wajen uba don uwa duk mune." A kunnanta Dr ya raɗa mata, "Ina ki ka bar uncle Ameeru? Ai wallahi shi ma bai dariya." A hankali ta furta itama, "Wallahi yana ɗan sakin murmushin gefen baki wani lokacin, amma ɗanka ko ni ban ce na taɓa ganin murmushinsa ba tun da ya kai 14years, kai ni tun suna yara ma ta inda na ke bambamce su kenan, Sauban na dariya sosai shi kuma fuskan ɓutu-ɓutu ga uban kumatun da suke ƙara masa muni!" ta ƙarisa maganar tana zabgawa Sam'an ɗin harara. Wani zaro idanu ta yi don a bazata Sam'an ɗin ya sakar mata murmushin da shi kansa bai san lokacin da ya yi ba, kuma hakan ya faru ne cikin sakanni wanda ita kaɗai taga hakan don yana yi kuma ya mayar da fuska ya ɗinke. "Da ka san yadda ka yi mugun kyau da kayi murmushin nan da baza ka ƙara ɗaure fuska ba har abada. Don sai ka fito sak Dr wallahi." mummy ta faɗi. "Dagaske mummy ya yi murmushi!" gaba ɗaya suka haɗa baki har da Dinaayah. Shi kuma Sam'an tsam ya miƙe tare da laptop ɗinsa ya nufi hanyar ɗakinsu da ke nan ƙasa. "Wallahi murmushi ya yi!" mummy ta faɗi. Sauban sai ya yi karaf ya ce, "Ni ban yi wani mamaki ba don ya kan yi once in a while haka ko kuma idan yana hira da budurwarsa." "Budurwa! Dama akwai wacce za ta iya soyayya da ya Sam'an da wannan fuskan shanun nasa?" Aleesha ce ta faɗi hakan ya yin da Benazir ta ce, "Caɓ!" Dad da mummy kuma dariya kawai suka yi. "In jira ki ɗin ne kun gama yanke hukuncin?" daddy ya faɗa yana kallon Benazir kasancewar ita ce kaɗai cikin 'yayansa ta zaɓi irin aikinsa, sai dai ita Nurse cr (Pediatric nursing) ta karanta wato fannin cututtukan ƙananun yara. Housemanship ta ke yi a asibitin mahaifinta yanzu haka. "Na fasa zuwa sai gobe kawai, dama ba wani abu can zan yi ba. Amma daddy idan ka shiga ka cewa nurse Balaraba ta rubuta min attendance." ta ƙarisa maganar tana susa kai. Daƙuwa ya yi mata tare da faɗin, "Kina wasa da aikinki ko? Na san ai jiya ma baki je ba. Zan ɓata miki rai idan ban ganki a asibiti gobe ba!" "Ye sir!" Benazir ta faɗi har da sara masa da ya sa su Aleesha da mom dariya. "Sai na dawo." ya faɗi yana kallon Dinaayah da ke jira ya fita ta yi masa magana. Murmushi ya yi sannan ya juya ya fita Dinaayar ta bisa a baya, mom da ke son yi masa rakiya sai ta koma ta zauna saboda ba ta damar yin magana da mahaifin nata ganin kamar sirri ta ke son yi da shi. Don akwai mugun shaƙuwa sosai tsakaninsu. Ba ta ɓoye masa komai na ta. Sai da suka isa har wajen motarsa sannan ya jingina da mota tare da faɗin, "Ya aka yi Alayna Noor?" Sai da ta ɗan turo baki alamar shagwaɓa sannan ta ce, "Daddy wai KAISAAR ne ya ke ta damuwa zai zo nan gidan." Wani murmushi ne ya suɓucewa daddyn na farinciki kamun ya furta, "To ki bashi izini mana." Ɗagowa ta yi ta kalle sa tamkar tana gani kamun ta ce, "To ai baka ce komai ba tun wancen lokacin." "Shekaran jiya na gama bincike a kansa, kuma dama yau ɗin na ke shirin faɗa miki sakamakon. Yaron kirki ne ki ce masa na bashi izini ya zo ya fara neman soyayyarki kamun mu iyaye mu shiga ciki. Idan halayyansa da ɗabi'unsa sun miki sai ki faɗa min. Ko kina son sanin kamanninsa in faɗa miki?" Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Daddy in dai ya maka to ni ma ya min. Ba na wani son sanin kamanninsa." "To ko baki tambaya ba zan faɗa miki, yaro ne dogo fari kyakkyawa kuma mai ilimi both the two ga kunya da tarbiyya. Sannan iyayansa mutanan kirki ne kuma aiki ya ke yi a First bank matsayin manager." Rufe fuska da tafin hannu Dinaayah ta yi saboda kunyar da ta ji. Sai kuma ta ce, "To dad familynsa za su yarda ya aure ni duk da ban iya gani kamar kowa?" "Alayna, ke da kan ki kin sha faɗa baki taɓa kallon kanki a matsayin wacce ke da nakasa ba kuma ba wai don ina matsayin mahaifinki ba, duk namijin da ya same ki matsayin mata ya gama morewa." "Dagaske Daddy?" ta faɗi farinciki mamaye da fuskanta. "Ƙwarai kuwa! Ke dai ki je ki yi ta addu'a akan Allah ya zaɓa miki abunda ya fi alkhairi a rayuwarki, ni ma zan taya ki." "In sha Allah daddy. Sai ka dawo Allah ya tsare ka ya kiyaye hanya." "Ameen Alayna noor!" ya faɗi tare da buɗe motar ya shiga ya tada, ita kuma ta ja baya tare da yi masa bye-bye sannann ta juya. Yadda ta ke tafiya da confidence za ka rantse da Allah tana gani domin babu dibi-dibi ko lalubar hanya kasancewar ta haddace komai na gidan tsaf. Cak ta tsaya tana faɗaɗa murmushinta tare da faɗin, "Aunty Moon sannu da zuwa! Sunaya taho nan." Da mugun mamaki ƙawar Maimuna ɗiyar wan Dr Khalil ke kallon wacce Dinaayah ta kira da aunty moon tana mata magana da hannu da kuma idanu akan anya dagaske Dinaayah makauniya ce kuwa kamar yadda ta faɗa mata. Kamun ta dawo daga shan ruwan mamakin da ta yi sai ji ta yi Dinaayah ta ce, "Ina wuni?" kuma daidai inda ta ke tsaye ta ke kallo alamar dai ita ta ke gaisarwa. Wannan karan a bayyane ƙawar aunty Moon ɗin ta yi magana, "Mummyn Sunayaah gaskiya zolayata ki ke yi wannan ƙanwar ta ki ba makauniya bace." ta ƙarisa maganar ne tana waving a fuskan Dinaayar amma sai taga ko sau ɗaya bata kyafta idanu ba. Murmushi kawai Dinaayah ta yi tare da amsar Sunaayah da ke hannun aunty Moon don idan da sabo ta saba da irin su ƙawar aunty moon ɗin da ba sa yarda ita makauniya ce. "Ya akai ta san kina nan kuma ba ke ɗaya bace akwai Sunayaah da kuma ni?" a cikin gigitar mamaki ta yi maganar. "Ai Dinaayah da ƙamshi ta ke fahimtar mutun na kusa da ita, da ta san ki ma sunanki za ta kira. Ta ji ƙamshina da na Sanaayah ne shiyasa ta kira sunan mu, ke kuma ƙamshinki ta ji sai dai bata taɓa jin irinsa ba shiyasa ba ta iya kiran sunanki ba. Yanzu da za ki yi kwana huɗu zuwa bakwai a inda ta ke tsab za ta haddace ƙamshinka ta yadda ko a cikin mutane da yawa ki ke za ta kira sunanki." Maman Sanaayah ta faɗi tana murmushi. "Caɓ! Lallai Dinaayah ki godewa ubangiji da ya baki wannan baiwar. Ya hana ki idanun gani amma sai ya baki hancin jin ƙamshin gani." ƙawar aunty Moon ta faɗi. "Alhamdulillah!" Dinaayah ta faɗi tana murmushi. "Daga wajen aunty Sarah na ke sai na taras bakya ɗakin shine Bena (Benazir su ke cewa Bena in short) ta faɗa min kin bi Uncle Ibrahim waje za ku yi sirri." ta ƙarisa maganar cikin sigar zaulaya. Dariya kawai Dinayaah ta yi tare da faɗin "Bari na je ɗaki, ki bar min Sunaayah idan za ku wuce sai ki zo ki amshe ta." "Na bar maki, ai 'yarki ce!" faɗin aunty Moon tare da juyawa domin komawa ɗakin mahaifiyarta aunty Maryam matar wan Dr Khalil. Tsabar yanda Amina ƙawar aunty Moon ke kallon yadda Dinaayah ke tafiya ɗauke da Sunaayah a hannunta tamkar mai idanu har tuntuɓe sai da taci. Ba ta bar kallon su ba har sai da ta ga sun shige sannan ta juyo tana sauke ajiyar zuciya. "In dai Dinaayah ce baki fara ganin komai ba daga cikin baiwar da Allah ya mata. Don yarinyar nan da ki ke gani babu abunda ba ta yi kamaa daga girki, shara, wanke-wanke, mopping ke har kitso tana yiwa mahaifiyarta." aunty Moon ɗin ta faɗa. "Lallai yarinyar 'yar baiwa ce. Ina ma ina da ɗan uwa namiji wallahi da na ce masa ya zo ya samu matar aure. Ga kyau ga natsuwa, uwa uba ga baiwar da Allah ya mata." Amina ta faɗi. "Na faɗa miki babu abunda ki ka gani in dai Dinaayah ce." Dinaayah na shiga ɗaki Benazir ta furta, "Ahaf! Ba na faɗa maku ba. Ai babu abunda zai hana Dinayaah amso Sunaayah. Su Naayah sarkin 'yan son yara." "Allah ya kawo miji nagari ke ma dai ki mallaki na ki 'ya'yan." Aleesha ta faɗi tana dariya. "Har yanzu ba ku daidaita da KAISAAR ɗin bane?" Mummy Sarah ce ta yi maganar ba tare da ta ɗago ta kalli Dinaayar ba. Ita ko Dinaayah sauke Sunaayah ta yi a ƙasa tare da nufa wajen mummy Sarah ta rufe fuskanta a kan cinyarta tare da faɗin, "Kai mum don Allah, wa ya faɗa miki wannan maganaar?" Dariya mummy Sarah ta yi tare da faɗin, "Idan daddynki abokin sirri da shawararki ne, ni kuma ni ce abokiyar sirri da shawararsa!" "Wani KAISAAR ɗin wai?" Benazir ta faɗa da maɗaukakin mamakin yayin da Aleesha ta watsa hannu alamar bata sani ba........ #KAISAR #DINAAYAH #Mummy Sarah #Dr Khalil Ibrahim #Nassarawa (Wamba) #Between two lovers _Free pages fa basu da yawa, guda biyar ne kawai don haka ku hwara payment, sannan don girman Allah idan kin san za ki saya ne domin ki fitar kar ki zo na yafe naki cinikin_ `DINAAYAH SAFRAAZ ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVDENCE OF PAYMENT 08128755583` ```Ina ƙara baki shawara sister, kar ki bari ayi wannan tafiyar babu ke``` [9/12, 2:44 PM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_* (```DiNaayah SafraAz```) _*BEtweEn two LoveRs*_ ~Story and written~ *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @MatarSayyadee01_ _Arewabook@Matarsayyadee0_ ```In Islam, forgiveness is a vital aspect of our faith, and it's a reminder that we're not alone and that we're all connected in our humanity.``` _… verse of Holy Quran, Allah Almighty says: “The reward of the evil is the evil thereof, but whosoever forgives and makes amends, his reward is upon God!_ Chapter 003 Tsam Benazir ta tashi ta dawo side kusa da Dinaayah tare da faɗin, "Naayah (wani lokacin haka suke kiran sunan juna a gajarce) wanene KAISAAR don Allah? Ko KAISAAR ɗin dai da na sani?" Gyaɗa mata kai Dinaayah ta yi alamar eh tana ƙara cusa kanta tsakankanin cinyoyin mummy Sarah saboda kunyar da ya gama mamaye ta. Murmushi yaƙe Benazir ta yi tana zuciyarta na wani irin zillon tashin hankali don har ta soma ganin duhu-duhu a cikin idanunta. Sai kawai ta hau kan kujeran da mummy Sarah ke kai ta matsar da kan Dinaayah da ke kan cinyar mummy Sarah tare da ɗaura nata kan ta lumshe idanu tana jin tamkar ta fashe da kuka. Babu wanda ya lura da yanayinta a ɗakin sai ma ɓallewa da Aleesha da Sauban suka yi wajen tsokalar Dinaayah wanda ya saka Dinaayah tashi ta nufi sama domin gujewa tsokalar tasu. Da idanu mummy Sarah ta bita tana jin wani tsantsan ƙauna da tausayinta na huda gaba ɗaya tsokoki da jijiyoyin jikinta. Ƙwalla ne su ka taru a idanunsa, da sauri ta shanye su gudun kar su Sauban su gani. Sai kawai ta lumshe idanu tarr da kwantar da kai a jikin kujera tana jin wani relief kaɗan tuno da cewar babu wani mahaluƙi da ya isa ya gano ɓoyayyen sirri da suka daɗe da binnewa kusan shekaru ashirin da uku wanda ya yi daidai da haihuwar Aleesha da Dinaayah ɗin. Idanunta da su kai jazur ta buɗe sakamakon ringing da wayarta ta yi, hannu ta kai ta ɗauki wayar tare da kallon screen ɗin. Ganin sunan da ya bayyana a jiki bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba ta ɗauki wayar tare da karawa a kunne ta furta, "Ya Lukman sai yau ka tuna da ni?" yanayin da ta ji muryansa ne ya saka lokaci guda gabanta ya buga da ƙarfi tare da furta, "Lafiya, mai ke faruwa ya Lukman?" Daga can ɓangaren ya Lukman ya furta, "Sai haƙuri Saratu, Allah ya yiwa ba Nura rasuwa yanzun nan (wato wan mahaifinta)". "Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un!" mummy Sarah ta faɗi sau uku tare da fashewa da matsanaicin kuka da ya sa gaba Aleesha, Benazir da Sauban miƙewa tsaye, hatta Sam'an da ya shige ɗaki fitowa ya yi da saurin jin dogon salatin da mummynsa ke jerawa tare da kuka. "Mummy wa ye ya rasu?" Sauban da Sam'an suka haɗa baki suka faɗa. Aleesha da Benazir kuma jikinsu ne kawai ke rawa. "Allah ya yiwa ba Nura rasuwa yanzun nan, wan mahaifina da kullum na kallesa mahaifina na ke gani tsaye shima yau ya amsa kiran ubangiji. Kakanku ya rasu Sam'an." ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka sosai. Kama ta Sam'an ya yi tare da zaunar da ita ya shiga faɗin, "Hakika abin da Allah ya ɗauka nasa ne, kuma abin da ya bayar da shi ma nasa ne, kuma kowane abu a wurinsa yana da ajali. Allah ya girmama ladanki, ya kyautata haƙurinki a kan abin da kika rasa, ya gafarta wa mamacinki. Kar ki kururuwa mum, ki masa addu'a shi kaɗai ya ke buƙata a wajanki a halin yanzu. Allah ya jiƙansa da rahama ya bashi ikon amsa tambayoyi a cikin ƙabari kuma ya sa aljanna Firdaus ita ce makomarsa!" "Ameen!" Mummy ta faɗi da muryan kuka kamun ta kai hannu ta share hawayen da ke zubo mata sannan ta lalubo number ɗin Dr ta danna masa kira ringing biyu ya ɗaga kiran. "Har kin fara missing ɗin nawa kenan? Yanzun nan shigowa ta office kenan ko zama ban yi ba." "Dr......." kuka ya hana ta faɗin abunda take son faɗa masa. Shi kuma jin yanayinta duk sai ya ruɗe ya shiga faɗin, "Lafiya Sarah? Mai ke faruwa, mai ya sa kike kuka? Wani abu ne ya faru a gidan? Gani nan dawowa yanzun nan!" Kamun ya yanke wayar ta yi saurin faɗin, "Allah ya yiwa ba Nura rasuwa! Yanzu ya Lukman ya kira ya ke faɗa min." daƙyar ta iya controlling kanta bata fashe da matsanaicin kuka ba, amma hawaye ya jiƙa fuskanta shataf. "Inna lillah wa inna ilaihir raju'un! Allahu Akbar, Allah ya jiƙansa da rahama, My sincere condolence. Don Allah ki yi haƙuri ki saka dangana a zuciyarki. Bana son BP ɗinki ya hau, ba Nura addu'a kawai ya ke buƙata a wajanku. Gani nan zuwa yanzun nan, ku soma shiri da na zo sai mu wuce Nasarawan." Gyaɗa kai ta yi kamar yana kallonta sannan ta kashe wayar tare da miƙewa still tana hawaye ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin hajiya domin ta faɗa mata rasuwar. Ko da ta je ɗakin sai ta taras hajiya ta yi nisa a baccin da take yi sai kawai ta juya ta koma part ɗin aunty Habbooba ta sanar da ita, tare suka fito da Habbooba suka nufi part ɗin aunty Maryam tana ƙara kwantar mata da hankali. Ganin su kawai da aunty Maryam ta yi da yanayin fuskar mummy Sarah hankalinta ya yi mugun tashi don ta san tabbas babu lafiya. Uncle Abdul-Hakeem ma miƙewa ya yi tsaye daga kan kujera tare da faɗin, "Maman twince lafiya?" Danne kukan da ke yunƙuro mata ta yi tare da furta, "Allah ya yiwa ba Nura rasuwa, yanzu ya Lukman ya kira ni ya faɗa min." "Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un!" aunty Maryam da uncle Abdul-Hakeem suka haɗa baki su kai ta maimaitawa. "Allah ya jiƙansa da rahama ya kuma sa can ɗin da ya tafi ya fiye masa nan ɗin, kuma Allah ya baku haƙurin rashi. Kin faɗawa Doctor?" uncle Abdul-Hakeem ya faɗi. "Eh na kira shi, ya ce mu shirya gashi nan zuwa mu tafi Nasarawan." "To shikenan nima bari na shirya. Hajiya ta sani?" ya kuma faɗa. "Yanzun daga can nake sai naga har yanzun bata farka daga bacci ba shiyasa ba ƙyale ta ban tashe ta ba." Mummy Sarah ta furta tana share hawaye. "To kuje ku shirya, ni zan je na faɗa hajiyan yanzu." uncle Abdul-Hakeem ya faɗi ita da Habbooba suka juya suka fice daga ɗakin. "Daddyn Moon zan bi ku, in shirya?" aunty Maryam ta faɗi daidai lokacin da aunty Moon ta fito waya a kunnenta tana magana da mijinta. Ganin iyayanta cirko-cirko sai ta yi sallama da Amina ƙawarta da su ka gidan tare, bata jima da wucewa ba shine ta kira ta ta faɗa mata ta yi mantuwa a cikin jakarta. "Mom, dad lafiya?" ta yi maganar ne bayan ta iso inda su ke. "Wan mahaifin maman twince ne ta ya rasu yanzu a Nasarawa!" aunty Maryam ce ta bata amsa. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ba dai tagwainin babanta wanda suke mugun kama ɗinnan ba?" "Shi fa! Wanda za ki ga ba a haɗa cikakken watanni biyu bai zo ya duba su ba." aunty Maryam ta faɗi. "Allah sarki! Allah ya jiƙansa da rahama. Lallai kam anyi wa mummy Sarah rasuwa. Ta ce min duk ta kalle sa asalin mahaifinta ta ke gani a fuskansa, shi ke ɗebe mata kewar mahaifinta yau kuma gashi Allah ya amshi abunsa. Lokaci ya yi!" Moon ta faɗi. "Wallahi fa lokaci ya yi. Allah ya jiƙansa da rahama." Driver ne ya shigo da mota bayan gateman ya wangale masa ƙofa. Hankalinsa rabuwa biyu ya yi tun sanda ya ɗauko yaran a makaranta saboda faɗan da Ayraah da Amla su ke yi, Afreen kuma sai risgar kuka ta ke yi sabida watsa mata miyan stew da Ayraah ta yi a jikin gogaggen farar baby hijjab ɗinta wanda mahaɗine na sport wear ɗin da ke jikinta. Ayraah ɗin ta je watsawa Amla ne sai akai rashin sa a ta samu Afreen, ita kuma Afreen duk duniya ta tsani a saka mata datti, juice ko kuma miya a kaya. Wannan dalilin ya saka ta riƙa rusa kuka don duk ta kalli gaban hijab ɗin sai ta kuma fashewa da kuma. Ayraah ta bata haƙuri har ta gaji, sai ta dungure mata kai tare da faɗin ta yi ta kukan har a yi tashin ƙiyama. Hakan da Ayraah ta ce ba ƙaramin ƙara tunzurata ya yi ba ta kuma fashewa da kuka tana Allah-Allah su dawo gida ta tafi ta faɗawa mummy Sarah abunda Ayraah ɗin ta mata. Shi kansa Bala driver ya yi ban haƙurin shima har ya gaji. Ga Ayraah da Amla ɗin sai jife-jife suke a motar wanda shi kansa sai da aka same sa a ƙeya. Sun yi kaca-kaca da motar. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke bayan ya yi parking. Afreen ce ta soma fitowa ta ɓangaren dama ta kwasa da gudu ta yi part ɗin mummy Sarah tana kuka, ko tsayawa ɗaukar jakarta da lunch box ɗinta bata yi ba saboda ƙosawar da ta yi ta kai ƙarar Ayraah. Ƙwafa Ayraah ta yi bayan ta zabgawa Amla harara tare da faɗin, "Sai na ɓaɓɓala ki a cikin gidan nan, ni ba tsararki ba ce. Kuma bari daddy ya dawo sai na faɗa masa you disrespect me in the present of my friends don ki jawo min raini!" Wani wawan harara tamkar idanunta za su zazzago Amla ta watsa mata tare da faɗin, "Kika ce ni ba tsarki bace, to da me kwaɗo ya fi gaya? Mintuna biyar ne kacal ne kawai a tsakaninmu. Kina fitowa ni ma na fito. Shekara ɗaya, rana ɗaya, mintuna biyar ne kawai tsakaninmu! Kuma mummy ta faɗa min gaskiya ai, ni ce na soma yunƙuri fitowa ke kuma da yake dama kin iya mugunta sai kika taɗiye ni ƙafana ya harɗe da umbilical cord ɗina shine ki ka yi sauri ki ka riga ni fitowa." "Maƙaryaciyar banza! Wallahi mummy bata faɗi haka ba, kuma bari mu shiga ciki sai na faɗawa ya Sam'an abunda ki ka ce da kuma dizgani da ki ka yi a gaban ƙawayena." Ayraah ta faɗi. "To ki faɗa mana, tsoransa ake ji!" Amla ta faɗi har da wani gyatsine. Juyawa Ayraah ta yi ta kalli Bala Driver da ke tsaye yana kallon su yana murmushi don idan da sabo ya saba da rigimar 'yan biyun. "Baba Bala kana dai shaida na ko? In ce dai a kunnanka ta faɗi ba ta tsoran ya Sam'an ko?" Maganar bebaye Bala driver ya soma yi irin bai gane abunda ta ke cewa ba sannan kuma yana mata nuni da shi bai jin maganar da suke yi kwata-kwata. Turɓune fuska ta yi tare da faɗin, "Mun ɓata da kai baba Bala!" tana gama faɗin haka ta fizgi jakarta ta yi cikin gida ita kuma Amla sai dariya ta ke mata. Buɗe murya Bala driver ya yi tare da faɗin, "Ayraah ki yi haƙuri kar ki fushi da baba Bala. Ku ba a shiga tsakaninku ne shiyasa ban ce komai ba. Ina iya yin magana in dawo ina jin kunya." da dariya ya yi maganar. "Baram-baram!" Ayraah ta faɗi bayan ta juyo ta kallesa har da watsa hannu sannan ta juya ta cigaba da tafiya. "Rabu da ita baba Bala, ai da kanta za ta dawo ba sai ka kira ta ba." Amla ta faɗa tare da ɗaukar jakarta ita ma ta nufi part ɗin mummy Saran. Cak! Afreen ta tsaya daga bakin ƙofa tana kallon kowa da ke ɗakin jiki a sanyaye kamun ta mayar da kallonta kan mummy Sarah da ke zaune a kan kujera idanunta jazur. Da gudu ta nufe ta tare da faɗawa jikinta ta hau kuka itama duk da bata san mai ke faruwa ba. "Mummy mai aka miki kike kuka? Why are you crying?" Shafa kanta mummy Sarah ta shiga yi tare da faɗin, "It alright, na dena kukan ai. Rasuwa aka yi. Babana ne ya rasu yau shiyasa na yi kuka." Ɗagowa da sauri Afreen ta yi tare da faɗin, "Mom babanki da yake zuwa nan daga Nasarawa? Mai ya same shi?" Gyaɗa kai mummy Sarah ta yi tare da faɗin, "Eh shi! Lokacinsa ne ya yi." Rungumeta Afreen ta kuma yi tana fashewa da kuka sosai daidai nan Ayraah ta shigo ɗakin fuska a kumbure, amma ganin mummy na hawaye Afreen kuma na kuka sosai bata san ta yi wurgi da jakarta ba ta ƙarisa inda suke da gudu tana kuka. Itama Amla ta shigowa sai ta bi sahunsu. Dinaayah ce ta daka masu tsawa tare da faɗin, "Kuna hauka ne? Mummy na cikin damuwa ku kuma za ku zo kuna koke-koke domin ku ƙara mata. Bari na kira ya Sam'an ai yana gidan wanka ya shiga yi." Gaba ɗaya sai suka yi tsit amma kuma sun ƙi barin jikin mummy Saran har sai da ta kalli Afreen tare da faɗi, "Ki je wajen auntynku ki canzo kaya za mu je Nasarawa yanzu idan daddynku ya dawo." (tana nufin mahaifiyarta don da Afreen da Benazir mahaifiyarsu ɗaya {Habbooba}. Sauban, Sam'an, Dinaayah da Aleesha kuma duk Mummy Sarah ce ta haife su. Abunda ya sa Benazir da Afreen su ke cewa mahaifiyarsu aunty, saboda sun tashi sun ji Sauban da Sam'an suna faɗa, haka mummy da suke kiran Sarah duk a bakin su Sam'an ɗin suka ɗauka.) Da sauri Afreen ta tashi ta ɗauki jakarta ta fice daga ɗakin har tana buga ƙafarta, Benazir ɗin ma miƙewa ta yi ta fita domin canza kaya kasancewar wando da riga ne a jikinta. Hajiya ce ta shigo ɗakin a sanyaye tare da sallama a bakinta. A sanyaye Sarah ta amsa tana mai miƙewa tsaye domin bawa hajiya girma. "Uwata ashe abunda ya faru kenan, Nura sa'i ya yi! Allah ya jiƙansa da rahama ya baku haƙurin rashi. Yanzu mu kai waya da Ibrahim ta ce min ya kusa ƙarisowa gidan sai mu wuce Nasarawan. Aisha da Marmari daga nesa ma har sun hau hanya." ko gama rufe baki hajiya bata yi ba Dr ya yi sallama ya shigo. Mummy Sarah na haɗa idanu dashi sai hawaye sha kamar an buɗe fanfo. Kawas da idanu ya yi don kukanta ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ya ke yi ba. "My condolence, Sarah! Allah ya jiƙan ba Nura da rahama." Khalil ya faɗa yana wucewa sama domin canza kaya zuwa manya kasancewar na jikinsa suit ne. Ko da ya sauko gaba ɗaya kowa ya shirya shi kaɗai ake jira. Kamar haɗin baki kaya iri ɗaya suka saka saka shi da twince ɗinsa maza. Dub da dama su Sauban gabaa ɗaya kayansu iri ɗaya suke yi. Gaba ɗaya suka fito suka nufi wajen mota. Dr, hajiya, da sarah da Habbooba suka shiga sabuwar motarsa Rolls-Royce Sweptail. Hajiya, mummy Sarah da Afreen suka zauna a gidan baya Habbooba da dama duk za a fita ita ke yin maza ta shige gidan gaba, Sarah kuma bata taɓa damuwa da hakan ba, yau ma ɗin gaban ta shige ya kame yayin da Dr Khalil ya zauna mazaunin driver. Sauban da Sam'am Range Rover suka shiga shi da sauran ƙannansa Dinaayah, Benazir, Aleesha, Ayraah da Amla wanda Sam'an ɗin ne zai ja motar. Uncle Abdul-Hakeem shi ma a nasa motar shi da aunty Maryam, aunty Laure da tare suka dawo gidan da daddy daga asibiti, sai kuma Moon da ta kira mijinta ta sanar da shi sannan ya bata izinin tafiya ta'aziyar. Kasancewar ƙarfe uku da wani abu suka fita daga gida, sai ƙarfe bakwai da hamsin suka isa Nasarawa. Suna sauka bai fi mintuna talatin ba su ya Abdallah da aunty Aysha suka iso suma. Wani sabon babin kuka mummy Sarah suka buɗe ita da 'yan uwanta da suka haɗu a ɗakin ba Lukman. Na'ima yar mummy Sarah an ce suma ya riƙa yi saboda a kan cinyarta ba Nura Allah ya ɗauki rayuwarsa. Ciwo cikin kwana da wuni ya yi Allah ya ɗauki ransa. Kwata-kwata ba shi aka sakawa mutuwa ba saboda shi lafiyarsa ƙalau, ba Lukman da ke fama da ciwon hanta ne ma aka sakawa mutuwar sabida matsanaicin jinya da ya ke yi sai gashi ba Nuran da lafiyarsa ƙalau shine ya mutu sanadin ciwon cikin kwana ɗaya da wuni. Hajiya ce ta riƙa tausarsu da kalamai da nasiha sannan suka ɗan tsagaita da kukan suka koma yi masa addu'a wanda dama shi ya fi buƙata. Kyakkyawar masauki aka kai su ya Abdallah, ya Abdul-Hakeem da doctor. Su Sauban kuma a ɗakin 'yan uwansu gwaurayen gidan suka sauka. Sai da su kai isha'i sannan suka fita waje inda 'yan zaman makoki ke zaune suka ƙara yin gaisuwar sannan suka dawo cikin gida zuwa ɗakin marigayyiya Nenne su ka yiwa matan gaisuwa sannan suka koma waje. Mummy Sarah ta kasa saka komai a bakinta sabida jimamin mutuwar baban nata, sannan hawaye sun kasa tsayuwa a idanunta sai kallon makeken hoton ba Nuhu (mahaiifinta) da ba Nura da ya rasu a yau. Kamar ta kira su amsa haka take ji. Aunty Suhana yarinyar ba Lukman wacce ƙawa take a wajan mummy Sarah, ita ta tarkata kan su Dinaayah zuwa gidanta domin su fi sakewa. A nan suka haɗu da 'yar aunty Suhanan wanda sa'o'i suke da su Benazir sai dai sun ɗan girme mata. Hira suke ta yi saboda sun sake da Madina sosai. Sau biyu kawai ta Madinar ta taɓa ganinsu a zahiri, lokacin da aunty Hassan (yayar mummy Sarah) ta haihu da kuma mutuwar ƙanin Pastor Emmanuella Debora Daniel (Kakar mummy Sarah ta wajen uwa). Washa gari gaba ɗaya suka shirya domin dawowa gida ban da mummy Sarah, Benazir, Aleesha da Dinaayah, su sai anyi bakwai daddy zai dawo ya ɗauke su. Su Ayraah sai kuka suke suma za su zauna. Dakyar aunty Laure ta lallashe su sabida school da suke zuwa kuma makarantar bata son fashi kwata-kwata. Dr Khalil sai da ya ƙara kwantar mata da hankali tare da bata ATM card ɗinsa akan duk abunda ake buƙata kawai ta yi amfani da shi a saya sannan ya mata sallama bayan ya bada sadakan kuɗi masu yawa sannan ya wuce. Hajiya da su ya Abdallah su ma duk sai da suka ajiye kuɗi masu tsoka sannan suka wuce aka bar mummy Sarah da 'ya'ya kawai. Aunty Habbooba kuwa Allah-Allah ta ke su bar garin don a ƙage take don garin bai mata ba sam! Ba su tafi ba sai da suka biya gidan Pastor Emanuella Debora domin gaisawa duk da sun haɗu ma a daren don har sha ɗaya suna tare har da mahaifiyar sarah wato Lami. Baba Samueal ma ya zo sai dai shi waje kawai ya tsaya kuma bai jima ba ya tafi don har yau babu jituwa tsakaninsa da surukan nasa, haka ma tsakaninsa da tsohuwar matarsa Pastor Emmanuella Debora (Littafi Ƙanwar matata for more information about the saga. DM 08128755583). Washa garin ranar da akai ukun ba Nura su Dinaayah suka fara bin gidajen yayyin mummy Sarah domin ziyara. Gidan aunty Hassana suka fara zuwa. Tamkar za ta lashe su tsabar son da ta ke nuna masu su duka har Benazir bata cire ba sai nan-nan da su ta ke. Idan ta kalli Dinaayah sai ta hau sharar hawayen da ita kaɗai ta san dalili. Daga nan su ka tafi gidan Na'ima, ita ma dai kamaar Hassana haka ta yi masu, gidan Marfu'a da Nuratu duk sai da suka je. Duk inda suka je kowacce na wane wannan waje basu kulawa sannan babu wacce bata jawo Dinaayah a jiki ta rungume tare da fashewa da matsanaicin kuka. Su Benazir duk tunanunsu kukan rashin idanun gani da Dinaayah bata da shi suke yi. Daga nan gida aunty Nuratu suka wuto gidan Pastor Emanuella tare da rakiyar Madina. Su Aleesha ne ke ta kallon gidan ganinsa manne da hotunan Jesus ta ko ina har da ƙaton bana na hoto church ɗin pastor Emannuella ɗin. Dinaayah da ba ta ganin komai kai tsaye kawai ta ke tafiya bisa jagorancin Madina sabida bata san kan inda za su ɗin ba ƙafa kawai ta ke jefawa. Tun daga harabar gidan akai masu kyakkyawar tarba kasancewar an san da zuwansu. Ɗaya bayan ɗaya Lami ke bin su ta rungume lokacin da ta kai kan Dinaayah wani irin rusa kuka ta yi tare da rungumeta ƙaƙam. Tsawa Pastor Emmanuella ta buga mata tare faɗin, "Kar ki fara ki yi kuka a kan jikarki, yarinyar nan akwai albarka a jininta, haihuwarta kawai Aina'u ta yi amma nonon Sarah ta sha don haka albarka na yawo a jikinta. Sharrin mahaifiyarta a iya taɓa lafiyarta kawai ya tsaya shiyasa ta fito daga cikin Aina'u a matsayin makauniya. Yanzu zan shiga ciki da ita na yi mata addu'a tare da casting duk wani evil spirit da zai yi ƙoƙari zuwa kusa da ita balle ta yi irin halin Aina'u wacce yanzu haka na san tana wuta!" Da ƙarfi ta kuma faɗin, "I renounce and ask forgiveness for any negative inner vows made by me or by any of the people for whom I am praying. I ask that Jesus Christ release us from these negative inner vows and from any bondage they have caused us. I take the Sword of the Spirit and cut free myself and those for whom I am praying from all generational sins, weaknesses, character defects, and cellular and genetic disorders, in the name of Jesus Christ." Pastor Emmanuella ba gama faɗin haka ta kama hannu Dinaayah zuwa ciki yayin da Lamu da su Benazir suka bi bayanta hankalinsu a tashe don sam basu fahimci ko kalma ɗaya daga cikin abunda kakar mummy Saran ta ke faɗi akan Dinaayar ba. Dafe ƙirji Benazir ta yi tare da zazzaro idanu ganin Pastor Emmanuella ta gurfanar da Dinaayah da ke kuka a ƙasa sannan ta hau magana da mugun ƙarfi tana faɗin, "I bind satan, the spirits, powers and forces of darkness ... l bind any demonic assignments sent against any of the people and areas I am lifting up to the Lord. I bind all interaction, interplay or communication of spirits as it may affect any of the people and areas for which I am praying. I command in the name of Jesus Christ that all these satanic and demonic forces go to the feet of Jesus. I call forth and loose the Holy Spirit of God and the holy angels to come and cleanse every place where satan has had a foothold in the lives and situations of any of these people and areas, and to fill each cleansed area with the life and love of Our Lord Jesus Christ, in the name of Jesus Christ. In the name of Jesus Christ, I rebuke and break any curses, hexes, spells, demonic activity, or any other evil thing that has been sent against me or passed down through the generations to me or to any of the people or areas for whom I am praying." "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku yau ni Benazir mai nake gani haka? Dama Maman mummy Sarah da kakarta arna ne? Kuma wacece Aina'u da suke cewa ita ce maman Dinaayah? Wannan ma ai ƙarya ne da hauka irin ta aljihun baya!" ##Matar Sayyadee #Dinaayah #THE SECRET #BENAZIR #Mummy Sarah #KAISAAR #Between two lovers ##DINAAYAH SAFRAAZ _Free pages fa basu da yawa, guda biyar ne kawai don haka ku hwara payment, sannan don girman Allah idan kin san za ki saya ne domin ki fitar kar ki zo na yafe naki cinikin_ `DINAAYAH SAFRAAZ ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVDENCE OF PAYMENT 08128755583` ```Ina ƙara baki shawara sister, kar ki bari ayi wannan tafiyar babu ke``` [9/14, 5:56 PM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_* (```DiNaayah SafraAz```) _*BEtweEn two LoveRs*_ ~Story and written~ *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @MatarSayyadee01_ _Arewabook@Matarsayyadee0_ ```One notable hadith narrated by Abu Huraira states that one who does not show compassion to children or respect for their elders is not regarded as a Muslim. Another hadith relays the Prophet Muhammad's (PBUH) words that those who do not show compassion to humans will not receive compassion from Allah.``` _Allah says in the Quran, “And We have not sent you (O Muhammad) (PBUH) except as a mercy to the worlds” (21:107). This verse emphasizes the Prophet's role in showing mercy and empathy to all of Allah's creations, including humans, animals, and the environment._ Chapter 004 `NOT EDITED` "I did my best, it wasn't much I couldn't feel, so I tried to touch I've told the truth, I didn't come to fool you And even though it all went wrong I'll stand before the Lord of Song With nothing on my tongue but Hallelujah Hallelujah, Hallelujah Hallelujah, Hallelujah Hallelujah, Hallelujah Abunda Pastor Emmanuella ta riƙa faɗi kenan da ƙarfi tana bugun kan Dinaayah da ke duƙe jikinta na rawa don gaba kwarmaton da Pastor ke yi ya saka tane neman fita hayyacinta. Idanunta ne suka soma lumshe a hankali kamun ta yi wani irin zabura ta fasa ƙarar da ya gigita gaba ɗaya gida aka taru a kanta har da sauran 'yan uwan pastor da basu san da zuwan su Dinaayah ɗin ba. Ihu take yi da mahaukacin ƙarfi don har jijiyoyin wuyanta sun mimmiƙe. Pastor Emmanuella kuwa sai ta cigaba da karanto karatunsu na coci itama da bugun ƙarfi wai a cewarta Evil spirit ɗin da ke jikin Dinaayah ɗin ne suka motsa saboda addu'o'in da take yi. Lami da ke gefe tana kuka tare da ambaton Allah a zuciyarta, ganin tsayuwar ba zai mata ba ga jikarta a cikin mummunan hali wanda a cikin gidan mahaifiyarta komai ya faru, kitchen ta nufa da gudu ta ɗebo ruwa a cup ta shiga tofa addu'ar da duk ya zo mata a baki cikin cup ɗin. Benazir da Aleesha kuwa tun ihun farko da Dinaayah ta ƙwalla su ka yi kanta su ka rirriƙe ta suna kuka suna kiran sunanta don tunda su ke ba su taɓa ganin haka a tare da ita. Dinaayah da wannan lokacin ihu ta ke kwarara tamkar maƙoshinta zai yage kuma gashi muryanta gaba ɗaya ta canza tamkar na bunsurun akuya wani lokacin kuma kamar na rigalu wanda ke cikin balagar farko. Wani wawan shaƙa ta kai wa Benazir tare da jifa da ita sai da ta haɗu da kujera bayanta kuma ya bugu sosai, tsabar azabar da ta ji a bayan bata san lokaci da ta furta, "Wayyooo Allah bayana ya ƙarye!" Ko kamun Aleesha ta yi yunƙurin guduwa ita ma ta yi wurgi da ita sai da ganta ya bugu da gini wanda take ta sume a wajen. Yunƙurin da Dinaayah ta yi tamkar wata yar dambe ya sa su uncle John, uncle Uche da uncle Joshua riƙe amma wani yunƙuri ɗaya kawai ta yi ta watsar da su kuma kan pastor Emmanuella kawai ta ke ƙoƙarin nufa. Daidai nan Lami ta shigo falon hannunta ɗauke da cup ɗin da ta yi addu'a a ciki, sai ta riƙa tsoma hannunta tana bismillah tare da watsa wa Dinaayah a fuska. Wani gigitaccen ƙara Dinaayah ta kuma saki tare da yin tsalle ta shaƙi wuyan pastor Emmanuella ta haɗa jikin dogon fridge ɗin da ke falon tana buga kanta. Su uncle Joshua a gigice suka ƙarisa wajenta domin ceton mahaifiyarsu, sai dai mangari ɗaya take masu suke watsewa a ƙasa. Wuf Benazir ta miƙe tare da mancewa da raɗaɗin azabar da bayanta ke yi ta fita da gudu ko tsayawa saka takalma bata yi ba, Madina na ganin haka ta rufa mata baya. Gudu Benazir ta ke yi tana kuka sosai, jama'a sai kallonta suke suna tambayar Madina abunda ya faru amma ita ma ko kula su ba tai ba sai ma bin bayanBenazir ɗin da take yi itama da gudu. Kasancewar babu nisa sosai tsakanin gidan Pastor Emmanuella da gidan su iyayan mummy Sarah cikin ƙanƙanin lokacin Benazir ta isa tare da faɗawa gidan da wani irin rikitacciyar kukan da ya ɗaga duka gidan hankali suka rirriƙeta suna tambayar abunda ya faru amma Bena ta kasa magana sai nuna waje take yi da hannu. Mummy Sarah kuwa tsabar tashin hankali har zaninta na neman kufcewa sai da aunty Suhana ta yi saurin riƙo mata shi tare da tsayar da ita ta gyara ɗaurin da kyau. Tana isa kusa da Benazir ɗin ta rungumeta tare da faɗin, "Kwantar da hankalinki ki faɗa min mai ya faru. Ina 'yan uwanki, ina Dinaayah da Aleesha?" Nan ma kasa magana ta yi sai nuni ta ke da hannunta izuwa waje. Iyaye mazan gidan ne suka shigo har da Uncle Lukman (wan mummy Sarah). Mari ɗaya ya ɗaurawa fuskan Madina sannan ya ce, "Mai ya faru? Idan ita ta kasa magana ke ai da bakinki!" "Mun je gidan Pastor ne shine ta kama hannun Dinaayah ta yi ta mata wasu addu'o'i wai za ta raba da Evil spirit kada abunda wai wata Aina'u ta yi ya shafe ta. Kuma ga Dinaayah ɗin can kamar mai aljanu sai dukan mutane ta ke yi, Aleesha ma na can a sume a gidan!" da kuka Madina ta faɗi hakan. Mummy Sarah da jikinta ke wani irin rawa tamkar mazari da idanu ta yi ta bin bakin Madina har ta kammala magana. A kaf cikin maganganun inda maganar Aina'u ya shigo ne yafi tada mata da hankali har take neman fita daga hayyacinta. Kamun kowa ya ankara Mummy Sarah ta yi fitan bindiga a gidan tare da nufa gidan Pastor Emmanuella domin ɗauko 'ya'yanta. Tuni mutanan gidan suka rufa mata baya har da su ba Lukman da ransu ya ke a mugun ɓace da abunda pastor Emmanuella ta yi ɗin. Irin gudun da mummy Saratu ke yi ya matuƙar bawa kowa mamaki duk da dama ba wai ƙiba gare ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ta isa gate ɗin gidan kakar tata pastor Emmanuella tare da tura ƙofar da ƙarfi ta shige ciki ko sauraran gate man da ke mata magana bata yi ba don bai gane ba shi sam. Tana shiga su Lukman da ba Lukman suka iso suma suka shigo. Sunday mai gadi ya shiga ƙoƙarin hana su shiga can ciki, duka ɗaya ya Lukman ya masa ya faɗi ƙasa jini na zuba daga hancinsa. Isar mummy Sarah falon pastor ya yi daidai da wani mugun riƙo da su uncle Joshua su kai wa Dinaayah bayan sun cire hannunta a wuyar pastor dakyar ta koma gefe tana mai da numfashi don bata taɓa tunanin za ta ƙara kwana a duniya ba saboda shaƙar da ta ji tamkar hannun samudawan farko. "Dinaayah!" mummy Sarah ta ƙwalla kiran sunanta tare da nufa inda take ta riƙo hannunta amma sam su Uncle Joshua sun ƙi sakinta sai ihun addu'arsu suke mata. Ba Lukman na shigowa kallo ɗaya ya yiwa Dinaayah ya fahimci ba ita bace iskokai ne a kanta. "Ku kama mu je gida yanzun nan!" ba Lukman ɗin ya faɗi yana kallon 'ya'yansa maza. Da ƙyar su uku maza suka iya riƙeta suka fita mummy Sarah biye da su a baya tana kuka ko ta kan Aleesha da ke kafaɗan ya Lukman a sume bata yi ba. Lami ma hijjab ta ɗauko ta saka ta bi bayansu bayan ta gargaɗi mahaifiyarta pasto Emanuella kar ta saki ta ce za ta biyo bayansu. Kai tsaye ɗakin karatun ba Lukman aka yi da Dinaayah aka shimfiɗar a kan carpet don ta ɗan rage haukan da take yi. Aleesha kuma aka yi ɗakin mahaifiyar aunty Suhana da ita aka shafa mata ruwa a fuska ta farfaɗo sannan aka shiga goge jinin da ya ɓata goshinta don ta ji ciwo a wajen har ya yi ƙulu. Gaba ɗaya mazan gidan zobe suka yi wa Dinaayah sannan suka shiga karanto ayoyin ruqya, da wannan ya sauke wannan ke ɗauka har da ba Lukman da ke shaƙa mata wani turare a hanci da ke ƙara kiɗimata. Ihu ta shiga yi da buge-buge tamkat za ta mutu, can wata kakkaurar murya ta soma magana, "Ku bari! Ku daina ƙona ni. Ni masoyinta ne ba maƙiyi ba. Na zo na bata kariya ne. Ku bar ƙonani kar ku raba ni da matata uwar 'ya'yana!" Jinjina kai ba Lukman ya yi jin abunda aljanin da ke jikinta ya faɗi wanda ke nuni da shi ɗin jinnul ashique ne. "Ku cigaba da karatu kar ku tsaya!" ba Lukman ya faɗi yana ƙara shaƙa mata wannan turaren da ke hannunsa. "Miƙo min zare!" ba Lukman ɗin ya faɗi domin ƙulle babbar yatsar Dinaayah. Sai dai kamun Mansur ɗansa na uku ya yi wanu yunƙuri Dinaayah ta saki wasu mahaukatan atishawa a jere har uku wanda ke nuni da ya fice daga jikinta. Zurum Dinaayah ta miƙe zaune tana lalube da hannu tare da ƙwalla kiran sunan mummy da ƙarfi. "Ya fice kafirin!" ya Lukman ya faɗi ransa a ɓace. "Yana nan guduwa ya yi amma ba fita ya yi a jikinta ba. Jinnul ashique suna da matuƙar naci fiye da tunaninka, ba ƙaramin tashi tsaye za ayi a kan yarinyar nan ba idan ba haka sai ya hana ta aure." ba Lukman ya faɗi. Jinjina kai ya Lukman ya yi yana kallon Dinaayah da gaba ɗaya jikinta ya saki sai lalube ta ke yi. Tausayinta ne ya mamaye zuciyarsa ganin irin ƙaddarorin da ke kanta. Na farko tabon da ke bibiyarta, na biyu makanta ga kuma na uku ya ɓullo na jinnul ashique. "Ku kai ni wajen mummyna. Benazir! Benazir!! Kina ina? Aleeshaa!" ta yi ta ƙwala kiran sunansu tana lalube don ta kasa shaƙo ƙamshin wanda ta sani a wajen. Burum! Mummy Sarah ta shigo ɗakin. Zabura Dinaayah ta yi tana lalube tare da kiran sunan mummy ɗin sabida shaƙo ƙamshinta da ta yi. "Gani nan, kama hannuna Alyana noor ɗin daddy. Gani nan ba zan bari wani abu ya same ki ba. Taho mu tafi ɗaki." mummy Sarah ta faɗi. "Mummy mu tafi gida. Kar mu ƙara kwana a nan garin. Ki kira daddy don Allah!" Dinaayah ta faɗi tana riƙe hannun mummy Sarah da ƙarfi. "Kwantar da hankalinki Dinaayah, ai dama ɗazu daddyn naku ya kira ni ya ke ce min gobe zai zo ya ɗauke mu mu koma gida." Gyaɗa kai Dinaayah ta yi ta kuma ƙi bari su haɗa idanu ba Lukman da ya kafe ta da idanu yana zargin kamar har yanzu ba ita bace. "Mu fita daga ɗakin nan mummy yanzu don Allah!" Dinaayah ta faɗi tana miƙewa tsaye. Mummy Sarah ma miƙewa ta yi tare da kama hannunta, sai dai ko taku ɗaya basu yi ba ba Lukman ya dakatar da su wanda hakan ya saka Dinaayah cizon leɓen bakinta na ƙasa da ƙarfi sannan ta kuma damƙe hannun mummyn. "Bar ta anan ki yi tafiyarki, za ta dawo da ƙafafunta!" shine abunda ba Lukman ya faɗi yana nufa inda kaskon da ya ke saka turare ya ke. "Ki sake ta ki fita nace!" ba Lukman ya faɗi da ƙarfi yana zarowa mummy Sarah idanu wanda hakan ya saka ta saki hannun Dinaayah ta fice ba tare da ta shirya hakan ba. "Ni za ka kawo wa iskanci? To nan gidan da ka ke gani ba gidan da ake shigowa a yi wargi bane. Ubanka za ka ci don sai tabbatar na ƙone jikinta tass, mara tsoran Allah ja'iri!" Wani irin juyowa Dinaayah ta yi tare da nuna ba Lukman da hannu jikinta na rawa har laɓɓanta tare da faɗin, "Ka fita sabgata ko kuma na illataka. Kai ka san tsayin lokacin da na yi tare da ita da rana tsaka za ka zo ka fara ƙoƙarin raba mu? Ƙaryan ka ta sha ƙarya malam Lukman! Idan kana ji da ƙananan ƙwari to ka sani wannan babban ƙwaro ne a gabanka." Murmushin gefen baki ba Lukman ya yi sannan ya furta, "Ni kuma zan gwada maka ayoyin Allah na maganin ƙanana 'yan iska da kuma gaggan su. Mintuna biyu na baka ka tattara inaka-inaka ka bar jikin jikata ni kuma na maka alƙawarin barin ka da ranka, idan kuma ka ƙi, to baka ƙi gani ba!" "Kai ka isa! Ni da Dinaayah mutuwa ce za ta raba mu, kuma wallahi duk wanda ya yi ƙoƙari shiga tsakanina da halal ɗina ko waye shi sai na ga bayansa!" "Halal ɗinka?" ba Lukman ya faɗi yana kallon cikin ƙwayan idanun Dinaayah da ke wani irin maiƙo yana fitar da ruwan hawaye. "Eh! Halal ɗina ce don sai da na biya sadaki tukun na aure ta. Kuma yanzu haka 'ya'yanmu biyu tare. Ko so ka ke ni da 'ya'yana mu zama marayu? mara imani!" Ba Lukman gajiya ya yi da sa'insa da shi sai kawai ya kunna burner ya zuba turaren da ke matuƙar tayar da hankalin ko wani irin kafirin jinni mara tsoran Allah. Hayaƙin na fara sama Dinaayah ta hau wani irin buge-buge tana ihu tamkar gidan zai tsage. Kaf mutanan gida fitowa su kai tsakar gida su kai cirko-cirko suna sauraran ihunta. Aleesha, Benazir da mummy Sarah kuwa kuka kawai suke yi rungume a jikin mummyn. Sai da aka kwashi tsayin muntuna talatin kamun komai ya lafa daga ɗakin ba Lukman ɗin. Can sai ga ya Lukman saɓe da Dinaayah ɗin a kafaɗa ya wuce ɗakin matar ba Lukman ɗin ya shimfiɗar da ita tare da kunna ƙira'a sannan ya fito ya jawo ƙofar. "Kar kowa ya je inda ta ke har sai ta tashi da kanta, kuma kar a kashe ƙira'ar. Sarah ki je ba Lukman na kiran ki." Lukman ne ya yi maganar tare da ficewa daga gidan ya nufi nasa gidan don shima ya yi aure last 2years har da ɗansa ɗaya mai suna Nuhu suna kiransa (Ashraf). Jiki a sanyaye mummy Sarah ta shiga ɗakin ba Lukman ɗin tare da zama a ƙasa kasancewar shi yana kan kujera ne. "Tun yaushe ta ke fama da wannan matsalar?" ba Lukman ya faɗa ba tare da kalleta ba, idanunsa na kan wasu magungunan da ya ke haɗawa. "Gaskiya bata taɓa irin haka ba sai yau. Tun da na haifeta yau ne na fara ganin hakan a gare ta." Ɗan ɗagowa ya yi ya kalleta tare na kusan second biyar sannan ya mayar da kansa kan magungunar tare da faɗin, "Bata taɓa faɗa miki tana wani mafarkar haka wanda bata gane masu ba, ko kuma mafarkin wani na zuwa mata haka cikin bacci?" "Gaskiya bata taɓa faɗa min haka ba sai sau ɗaya da ta ce min ta yi mafarkin wani na binta da gudu amma bata san ko wanene ba, sannan gabanta ruwa ne wanda bai da iyaka kuma yana da mahaukacin zurfi, idan ta kawo wajen ruwan sai ta tsaya cak! Shikuma mai bin nata sai ya ce mata ya faɗa mata za ta yi gudu iya iyawarta amma ba zata taɓa tsere masa ba. Ni kuma sai na ce mata ta yi addu'a mafarki ne kawai babu abunda zai faru da ita." "To yarinyar nan tana fama da matsalar jinnul ashique! Kuma idan ba a tashi tsaye ba yarinyar nan za ta afka cikin babbar matsala fiye da wanda take ciki yanzu. Don ba lallai shi aljanin ya barta tai aure ba, idan ma ya barta to babu zaman lafiya tsakaninta da mijin." ba Lukman ya faɗi. Mummy Sarah tuni har ta soma kuka tana faɗin, "Baba menene kuma jinnul ashiq?" "Idan aka ce Jinnul Ashiq a na nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji. Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma kokarin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga kokarin kashe mata shi. Su na kuma kokarin hana mace samun ciki, ko kuma in ta samun cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa, ya zamo tun daga haifarsa za a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau’in Aljani shi muke kira JINNUL ASHIQ. Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne mutum yake yi da su." "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ba Lukman yanzu mecece mafita? Ya za ayi a rabaa da shi?" Ajiyar zuciya mai ƙarfi ba Lukman ya yi sannan ya furta, "Ga ayoyin da za a riƙa yi a cikin ruwa ana shafe duk jikinta da shi bayan la'asar ko kuma ta riƙa wanka da shi. Amma a waje mai tsarki ake wankan kamar cikin daki kuma ba da sabulu ba. Sannan sauran ruwan kada a zuba shi a kwata ko najasa, saidai a zubawa shuka ko a zuba a inda kasa za ta tsotse. Sai kuma a sake karanta wadannan jerin ayoyi a ruwa wanda ba azuba komai a ciki ba, sai mai lalurar ya dinga sha kullum, kuma kada ya sha wani ruwa sai wannan. Yanzu bari na yi addu'o'in cikin wancen tsaftataccen ruwan saman." Gyara zama mummy Sarah ta yi domin sauraransa. Sai da ya matso da bokitin kusa da shi sosai sannan ya zuba man _wardi_ a ciki tare da saka hannunsa na dama ya kuma matso da bakinsa gab da bokitin ya soma karatun. . – ﻓﺎﺗﺤﺔ ﺍﻟﻜـﺘﺎﺏ / ﺁﻳــﺔ ﺍﻟﻜﺮﺳــﻰ { ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍْ ﻣَﺎ ﺗَﺘْﻠُﻮﺍْ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦُ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﻠْﻚِ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ ﻭَﻣَﺎ ﻛَﻔَﺮَ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥُ ﻭَﻟَـﻜِﻦَّ ﺍﻟﺸَّﻴْﺎﻃِﻴﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍْ ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮَ ﻭَﻣَﺎ ﺃُﻧﺰِﻝَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤَﻠَﻜَﻴْﻦِ ﺑِﺒَﺎﺑِﻞَ ﻫَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎ ﻳُﻌَﻠِّﻤَﺎﻥِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﻘُﻮﻻَ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻧَﺤْﻦُ ﻓِﺘْﻨَﺔٌ ﻓَﻼَ ﺗَﻜْﻔُﺮْ ﻓَﻴَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣِﻨْﻬُﻤَﺎ ﻣَﺎ ﻳُﻔَﺮِّﻗُﻮﻥَ ﺑِﻪِ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟْﻤَﺮْﺀِ ﻭَﺯَﻭْﺟِﻪِ ﻭَﻣَﺎ ﻫُﻢ ﺑِﻀَﺂﺭِّﻳﻦَ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺇِﻻَّ ﺑِﺈِﺫْﻥِ ﺍﻟﻠّﻪِ ﻭَﻳَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﻳَﻀُﺮُّﻫُﻢْ ﻭَﻻَ ﻳَﻨﻔَﻌُﻬُﻢْ ﻭَﻟَﻘَﺪْ ﻋَﻠِﻤُﻮﺍْ ﻟَﻤَﻦِ ﺍﺷْﺘَﺮَﺍﻩُ ﻣَﺎ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺍﻵﺧِﺮَﺓِ ﻣِﻦْ ﺧَﻼَﻕٍ ﻭَﻟَﺒِﺌْﺲَ ﻣَﺎ ﺷَﺮَﻭْﺍْ ﺑِﻪِ ﺃَﻧﻔُﺴَﻬُﻢْ ﻟَﻮْ ﻛَﺎﻧُﻮﺍْ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ { ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 102 { ﻗَﺎﻟُﻮﺍْ ﻳَﺎ ﻣُﻮﺳَﻰ ﺇِﻣَّﺎ ﺃَﻥ ﺗُﻠْﻘِﻲَ ﻭَﺇِﻣَّﺎ ﺃَﻥ ﻧَّﻜُﻮﻥَ ﻧَﺤْﻦُ ﺍﻟْﻤُﻠْﻘِﻴﻦَ ‏( 115 ‏) ﻗَﺎﻝَ ﺃَﻟْﻘُﻮْﺍْ ﻓَﻠَﻤَّﺎ ﺃَﻟْﻘَﻮْﺍْ ﺳَﺤَﺮُﻭﺍْ ﺃَﻋْﻴُﻦَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﻭَﺍﺳْﺘَﺮْﻫَﺒُﻮﻩْﻡُ ﻭَﺟَﺎﺀﻭﺍ ﺑِﺴِﺤْﺮٍ ﻋَﻈِﻴﻢٍ ‏( 116 ‏) ﻭَﺃَﻭْﺣَﻴْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻰ ﻣُﻮﺳَﻰ ﺃَﻥْ ﺃَﻟْﻖِ ﻋَﺼَﺎﻙَ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻫِﻲَ ﺗَﻠْﻘَﻒُ ﻣَﺎ ﻳَﺄْﻓِﻜُﻮﻥَ ‏( 117 ‏) ﻓَﻮَﻗَﻊَ ﺍﻟْﺤَﻖُّ ﻭَﺑَﻄَﻞَ ﻣَﺎ ﻛَﺎﻧُﻮﺍْ ﻳَﻌْﻤَﻠُﻮﻥَ ‏( 118 ‏) ﻓَﻐُﻠِﺒُﻮﺍْ ﻫُﻨَﺎﻟِﻚَ ﻭَﺍﻧﻘَﻠَﺒُﻮﺍْ ﺻَﺎﻏِﺮِﻳﻦَ ‏( 119 ‏) ﻭَﺃُﻟْﻘِﻲَ ﺍﻟﺴَّﺤَﺮَﺓُ ﺳَﺎﺟِﺪِﻳﻦَ ‏( 120 ‏) ﻗَﺎﻟُﻮﺍْ ﺁﻣَﻨَّﺎ ﺑِﺮِﺏِّ ﺍﻟْﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ ‏( 121 ‏) ﺭَﺏِّ ﻣُﻮﺳَﻰ ﻭَﻫَﺎﺭُﻭﻥَ { ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ 115 : 122 } ﻓَﻠَﻤَّﺎ ﺃَﻟْﻘَﻮﺍْ ﻗَﺎﻝَ ﻣُﻮﺳَﻰ ﻣَﺎ ﺟِﺌْﺘُﻢ ﺑِﻪِ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﺳَﻴُﺒْﻄِﻠُﻪُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﻻَ ﻳُﺼْﻠِﺢُ ﻋَﻤَﻞَ ﺍﻟْﻤُﻔْﺴِﺪِﻳﻦَ ‏( 81 ‏) ﻭَﻳُﺤِﻖُّ ﺍﻟﻠّﻪُ ﺍﻟْﺤَﻖَّ ﺑِﻜَﻠِﻤَﺎﺗِﻪِ ﻭَﻟَﻮْ ﻛَﺮِﻩَ ﺍﻟْﻤُﺠْﺮِﻣُﻮﻥَ { ﻳﻮﻧﺲ 81 : 82 } ﻗَﺎﻝَ ﺑَﻞْ ﺃَﻟْﻘُﻮﺍ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﺣِﺒَﺎﻟُﻬُﻢْ ﻭَﻋِﺼِﻴُّﻬُﻢْ ﻳُﺨَﻴَّﻞُ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﻣِﻦ ﺳِﺤْﺮِﻫِﻢْ ﺃَﻧَّﻬَﺎ ﺗَﺴْﻌَﻰ ‏( 66 ‏) ﻓَﺄَﻭْﺟَﺲَ ﻓِﻲ ﻧَﻔْﺴِﻪِ ﺧِﻴﻔَﺔً ﻣُّﻮﺳَﻰ ‏( 67 ‏) ﻗُﻠْﻨَﺎ ﻟَﺎ ﺗَﺨَﻒْ ﺇِﻧَّﻚَ ﺃَﻧﺖَ ﺍﻟْﺄَﻋْﻠَﻰ ‏( 68 ‏) ﻭَﺃَﻟْﻖِ ﻣَﺎ ﻓِﻲ ﻳَﻤِﻴﻨِﻚَ ﺗَﻠْﻘَﻒْ ﻣَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ ﻛَﻴْﺪُ ﺳَﺎﺣِﺮٍ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﻔْﻠِﺢُ ﺍﻟﺴَّﺎﺣِﺮُ ﺣَﻴْﺚُ ﺃَﺗَﻰ { ﻃﻪ :66 69 } ﻭَﻗَﺪِﻣْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻰ ﻣَﺎ ﻋَﻤِﻠُﻮﺍ ﻣِﻦْ ﻋَﻤَﻞٍ ﻓَﺠَﻌَﻠْﻨَﺎﻩُ ﻫَﺒَﺎﺀ ﻣَّﻨﺜُﻮﺭًﺍ { ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ : 23 } ﺇِﻥَّ ﻫَـﺆُﻻﺀ ﻣُﺘَﺒَّﺮٌ ﻣَّﺎ ﻫُﻢْ ﻓِﻴﻪِ ﻭَﺑَﺎﻃِﻞٌ ﻣَّﺎ ﻛَﺎﻧُﻮﺍْ ﻳَﻌْﻤَﻠُﻮﻥَ { ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ : 139 } ﻭَﺇِﺫْ ﻳَﻌِﺪُﻛُﻢُ ﺍﻟﻠّﻪُ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﺍﻟﻄَّﺎﺋِﻔَﺘِﻴْﻦِ ﺃَﻧَّﻬَﺎ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﺗَﻮَﺩُّﻭﻥَ ﺃَﻥَّ ﻏَﻴْﺮَ ﺫَﺍﺕِ ﺍﻟﺸَّﻮْﻛَﺔِ ﺗَﻜُﻮﻥُ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﻠّﻪُ ﺃَﻥ ﻳُﺤِﻖَّ ﺍﻟﺤَﻖَّ ﺑِﻜَﻠِﻤَﺎﺗِﻪِ ﻭَﻳَﻘْﻄَﻊَ ﺩَﺍﺑِﺮَ ﺍﻟْﻜَﺎﻓِﺮِﻳﻦَ ‏( 7 ‏) ﻟِﻴُﺤِﻖَّ ﺍﻟْﺤَﻖَّ ﻭَﻳُﺒْﻄِﻞَ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞَ ﻭَﻟَﻮْ ﻛَﺮِﻩَ ﺍﻟْﻤُﺠْﺮِﻣُﻮﻥَ { ﺍﻷﻧﻔﺎﻝ : 7 8 } ﻭَﻗُﻞْ ﺟَﺎﺀ ﺍﻟْﺤَﻖُّ ﻭَﺯَﻫَﻖَ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞَ ﻛَﺎﻥَ ﺯَﻫُﻮﻗًﺎ { ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ : 81 } ﺑَﻞْ ﻧَﻘْﺬِﻑُ ﺑِﺎﻟْﺤَﻖِّ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞِ ﻓَﻴَﺪْﻣَﻐُﻪُ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻫُﻮَ ﺯَﺍﻫِﻖٌ ﻭَﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﻮَﻳْﻞُ ﻣِﻤَّﺎ ﺗَﺼِﻔُﻮﻥَ { ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ : 18 } ﻭَﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀ ﺫَﺍﺕِ ﺍﻟْﺒُﺮُﻭﺝِ ‏( 1 ‏) ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﻤَﻮْﻋُﻮﺩِ ‏( 2 ‏) ﻭَﺷَﺎﻫِﺪٍ ﻭَﻣَﺸْﻬُﻮﺩٍ ‏( 3 ‏) ﻗُﺘِﻞَ ﺃَﺻْﺤَﺎﺏُ ﺍﻟْﺄُﺧْﺪُﻭﺩِ ‏( 4 ‏) ﺍﻟﻨَّﺎﺭِ ﺫَﺍﺕِ ﺍﻟْﻮَﻗُﻮﺩِ ‏( 5 ‏) ﺇِﺫْ ﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﻗُﻌُﻮﺩٌ ‏( 6 ‏) ﻭَﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻳَﻔْﻌَﻠُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ﺷُﻬُﻮﺩٌ ‏( 7 ‏) ﻭَﻣَﺎ ﻧَﻘَﻤُﻮﺍ ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻥ ﻳُﺆْﻣِﻨُﻮﺍ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻌَﺰِﻳﺰِ ﺍﻟْﺤَﻤِﻴﺪِ ‏( 8 ‏) ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻟَﻪُ ﻣُﻠْﻚُ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻰ ﻛُﻞِّ ﺷَﻲْﺀٍ ﺷَﻬِﻴﺪٌ ‏( 9 ‏) ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻓَﺘَﻨُﻮﺍ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨَﺎﺕِ ﺛُﻢَّ ﻟَﻢْ ﻳَﺘُﻮﺑُﻮﺍ ﻓَﻠَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏُ ﺟَﻬَﻨَّﻢَ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏُ ﺍﻟْﺤَﺮِﻳﻖِ ‏( 10 ‏) ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻭَﻋَﻤِﻠُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﺎﻟِﺤَﺎﺕِ ﻟَﻬُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٌ ﺗَﺠْﺮِﻱ ﻣِﻦ ﺗَﺤْﺘِﻬَﺎ ﺍﻟْﺄَﻧْﻬَﺎﺭُ ﺫَﻟِﻚَ ﺍﻟْﻔَﻮْﺯُ ﺍﻟْﻜَﺒِﻴﺮُ ‏( 11 ‏) ﺇِﻥَّ ﺑَﻄْﺶَ ﺭَﺑِّﻚَ ﻟَﺸَﺪِﻳﺪٌ ‏( 12 ‏) ﺇِﻧَّﻪُ ﻫُﻮَ ﻳُﺒْﺪِﺉُ ﻭَﻳُﻌِﻴﺪُ ‏( 13 ‏) ﻭَﻫُﻮَ ﺍﻟْﻐَﻔُﻮﺭُ ﺍﻟْﻮَﺩُﻭﺩُ ‏( 14 ‏) ﺫُﻭ ﺍﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺍﻟْﻤَﺠِﻴﺪُ ‏( 15 ‏) ﻓَﻌَّﺎﻝٌ ﻟِّﻤَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ‏( 16 ‏) ﻫَﻞْ ﺃَﺗَﺎﻙَ ﺣَﺪِﻳﺚُ ﺍﻟْﺠُﻨُﻮﺩِ ‏( 17 ‏) ﻓِﺮْﻋَﻮْﻥَ ﻭَﺛَﻤُﻮﺩَ ‏( 18 ‏) ﺑَﻞِ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻓِﻲ ﺗَﻜْﺬِﻳﺐٍﻓِﺮْﻋَﻮْﻥَ ﻭَﺛَﻤُﻮﺩَ ‏( 18 ‏) ﺑَﻞِ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻓِﻲ ﺗَﻜْﺬِﻳﺐٍ ‏( 19 ‏) ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣِﻦ ﻭَﺭَﺍﺋِﻬِﻢ ﻣُّﺤِﻴﻂٌ ‏( 20 ‏) ﺑَﻞْ ﻫُﻮَ ﻗُﺮْﺁﻥٌ ﻣَّﺠِﻴﺪٌ ‏( 21 ‏) ﻓِﻲ ﻟَﻮْﺡٍ ﻣَّﺤْﻔُﻮﻅٍ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺒﺮﻭﺝ } ﺃَﻟَﻢْ ﻧَﺸْﺮَﺡْ ﻟَﻚَ ﺻَﺪْﺭَﻙَ ‏( 1 ‏) ﻭَﻭَﺿَﻌْﻨَﺎ ﻋَﻨﻚَ ﻭِﺯْﺭَﻙَ ‏( 2 ‏) ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺃَﻧﻘَﺾَ ﻇَﻬْﺮَﻙَ ‏( 3 ‏) ﻭَﺭَﻓَﻌْﻨَﺎ ﻟَﻚَ ﺫِﻛْﺮَﻙَ ‏( 4 ‏) ﻓَﺈِﻥَّ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮِ ﻳُﺴْﺮًﺍ ‏( 5 ‏) ﺇِﻥَّ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮِ ﻳُﺴْﺮًﺍ ‏( 6 ‏) ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻓَﺮَﻏْﺖَ ﻓَﺎﻧﺼَﺐْ ‏( 7 ‏) ﻭَﺇِﻟَﻰ ﺭَﺑِّﻚَ ﻓَﺎﺭْﻏَﺐْ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻹﻧﺸﺮﺍﺡ } ﺇِﺫَﺍ ﺯُﻟْﺰِﻟَﺖِ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽُ ﺯِﻟْﺰَﺍﻟَﻬَﺎ ‏( 1 ‏) ﻭَﺃَﺧْﺮَﺟَﺖِ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽُ ﺃَﺛْﻘَﺎﻟَﻬَﺎ ‏( 2 ‏) ﻭَﻗَﺎﻝَ ﺍﻟْﺈِﻧﺴَﺎﻥُ ﻣَﺎ ﻟَﻬَﺎ ‏( 3 ‏) ﻳَﻮْﻣَﺌِﺬٍ ﺗُﺤَﺪِّﺙُ ﺃَﺧْﺒَﺎﺭَﻫَﺎ ‏( 4 ‏) ﺑِﺄَﻥَّ ﺭَﺑَّﻚَ ﺃَﻭْﺣَﻰ ﻟَﻬَﺎ ‏( 5 ‏) ﻳَﻮْﻣَﺌِﺬٍ ﻳَﺼْﺪُﺭُ ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﺃَﺷْﺘَﺎﺗًﺎ ﻟِّﻴُﺮَﻭْﺍ ﺃَﻋْﻤَﺎﻟَﻬُﻢْ ‏( 6 ‏) ﻓَﻤَﻦ ﻳَﻌْﻤَﻞْ ﻣِﺜْﻘَﺎﻝَ ﺫَﺭَّﺓٍ ﺧَﻴْﺮًﺍ ﻳَﺮَﻩُ ‏( 7 ‏) ﻭَﻣَﻦ ﻳَﻌْﻤَﻞْ ﻣِﺜْﻘَﺎﻝَ ﺫَﺭَّﺓٍ ﺷَﺮًّﺍ ﻳَﺮَﻩُ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺰﻟﺰﻟﺔ } ﻭَﻳْﻞٌ ﻟِّﻜُﻞِّ ﻫُﻤَﺰَﺓٍ ﻟُّﻤَﺰَﺓٍ ‏( 1 ‏) ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻤَﻊَ ﻣَﺎﻟًﺎ ﻭَﻋَﺪَّﺩَﻩُ ‏( 2 ‏) ﻳَﺤْﺴَﺐُ ﺃَﻥَّ ﻣَﺎﻟَﻪُ ﺃَﺧْﻠَﺪَﻩُ ‏( 3 ‏) ﻛَﻠَّﺎ ﻟَﻴُﻨﺒَﺬَﻥَّ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺤُﻄَﻤَﺔِ ‏( 4 ‏) ﻭَﻣَﺎ ﺃَﺩْﺭَﺍﻙَ ﻣَﺎ ﺍﻟْﺤُﻄَﻤَﺔُ ‏( 5 ‏) ﻧَﺎﺭُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻤُﻮﻗَﺪَﺓُ ‏( 6 ‏) ﺍﻟَّﺘِﻲ ﺗَﻄَّﻠِﻊُ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺄَﻓْﺌِﺪَﺓِ ‏( 7 ‏) ﺇِﻧَّﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢ ﻣُّﺆْﺻَﺪَﺓٌ ‏( 8 ‏) ﻓِﻲ ﻋَﻤَﺪٍ ﻣُّﻤَﺪَّﺩَﺓٍ { } ﺃَﻟَﻢْ ﺗَﺮَ ﻛَﻴْﻒَ ﻓَﻌَﻞَ ﺭَﺑُّﻚَ ﺑِﺄَﺻْﺤَﺎﺏِ ﺍﻟْﻔِﻴﻞِ ‏( 1 ‏) ﺃَﻟَﻢْ ﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻛَﻴْﺪَﻫُﻢْ ﻓِﻲ ﺗَﻀْﻠِﻴﻞٍ ‏( 2 ‏) ﻭَﺃَﺭْﺳَﻞَ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢْ ﻃَﻴْﺮًﺍ ﺃَﺑَﺎﺑِﻴﻞَ ‏( 3 ‏) ﺗَﺮْﻣِﻴﻬِﻢ ﺑِﺤِﺠَﺎﺭَﺓٍ ﻣِّﻦ ﺳِﺠِّﻴﻞٍ ‏( 4 ‏) ﻓَﺠَﻌَﻠَﻬُﻢْ ﻛَﻌَﺼْﻒٍ ﻣَّﺄْﻛُﻮﻝٍ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻔﻴﻞ } ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪٌ ‏( 1 ‏) ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟﺼَّﻤَﺪُ ‏( 2 ‏) ﻟَﻢْ ﻳَﻠِﺪْ ﻭَﻟَﻢْ ﻳُﻮﻟَﺪْ ‏( 3 ‏) ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦ ﻟَّﻪُ ﻛُﻔُﻮًﺍ ﺃَﺣَﺪٌ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻹﺧﻼﺹ } ﻗُﻞْ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﺮَﺏِّ ﺍﻟْﻔَﻠَﻖِ ‏( 1 ‏) ﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﺧَﻠَﻖَ ‏( 2 ‏) ﻭَﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﻏَﺎﺳِﻖٍ ﺇِﺫَﺍ ﻭَﻗَﺐَ ‏( 3 ‏) ﻭَﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﺍﻟﻨَّﻔَّﺎﺛَﺎﺕِ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻌُﻘَﺪِ ‏( 4 ‏) ﻭَﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﺣَﺎﺳِﺪٍ ﺇِﺫَﺍ ﺣَﺴَﺪَ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻔﻠﻖ } ﻗُﻞْ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﺮَﺏِّ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ‏( 1 ‏) ﻣَﻠِﻚِ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ‏( 2 ‏) ﺇِﻟَﻪِ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ‏( 3 ‏) ﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﺍﻟْﻮَﺳْﻮَﺍﺱِ ﺍﻟْﺨَﻨَّﺎﺱِ ‏( 4 ‏) ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳُﻮَﺳْﻮِﺱُ ﻓِﻲ ﺻُﺪُﻭﺭِ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ‏( 5 ‏) ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺠِﻨَّﺔِ ﻭَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻨﺎﺱ } ﻭَﺍﻟﻠّﻪُ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﺄَﻋْﺪَﺍﺋِﻜُﻢْ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠّﻪِ ﻭَﻟِﻴًّﺎ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠّﻪِ ﻧَﺼِﻴﺮًﺍ{ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 45 } ﺫَﻟِﻚَ ﺍﻟْﻔَﻀْﻞُ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻠّﻪِ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠّﻪِ ﻋَﻠِﻴﻤًﺎ { ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 70 } ﻭَﺗَﻮَﻛَّﻞْ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻛِﻴﻠًﺎ { ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : 3 } ﻭَﺭَﺩَّ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﺑِﻐَﻴْﻈِﻬِﻢْ ﻟَﻢْ ﻳَﻨَﺎﻟُﻮﺍ ﺧَﻴْﺮًﺍ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ﺍﻟْﻘِﺘَﺎﻝَ ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻗَﻮِﻳًّﺎ ﻋَﺰِﻳﺰًﺍ { ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : 25 } ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﺒَﻠِّﻐُﻮﻥَ ﺭِﺳَﺎﻟَﺎﺕِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻳَﺨْﺸَﻮْﻧَﻪُ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺨْﺸَﻮْﻥَ ﺃَﺣَﺪًﺍ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﺣَﺴِﻴﺒًﺎ { ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : 39 } ﺇِﺫْ ﻳُﻮﺣِﻲ ﺭَﺑُّﻚَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﻤَﻶﺋِﻜَﺔِ ﺃَﻧِّﻲ ﻣَﻌَﻜُﻢْ ﻓَﺜَﺒِّﺘُﻮﺍْ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍْ ﺳَﺄُﻟْﻘِﻲ ﻓِﻲ ﻗُﻠُﻮﺏِ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍْ ﺍﻟﺮَّﻋْﺐَ ﻓَﺎﺿْﺮِﺑُﻮﺍْ ﻓَﻮْﻕَ ﺍﻷَﻋْﻨَﺎﻕِ ﻭَﺍﺿْﺮِﺑُﻮﺍْ ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﻛُﻞَّ ﺑَﻨَﺎﻥٍ ‏( 12 ‏) ﺫَﻟِﻚَ ﺑِﺄَﻧَّﻬُﻢْ ﺷَﺂﻗُّﻮﺍْ ﺍﻟﻠّﻪَ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟَﻪُ ﻭَﻣَﻦ ﻳُﺸَﺎﻗِﻖِ ﺍﻟﻠّﻪَ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟَﻪُ ﻓَﺈِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﺷَﺪِﻳﺪُ ﺍﻟْﻌِﻘَﺎﺏِ ‏( 13 ‏) ﺫَﻟِﻜُﻢْ ﻓَﺬُﻭﻗُﻮﻩُ ﻭَﺃَﻥَّ ﻟِﻠْﻜَﺎﻓِﺮِﻳﻦَ ﻋَﺬَﺍﺏَ ﺍﻟﻨَّﺎﺭِ { ﺍﻷﻧﻔﺎﻝ : 12 14 } ﻳَﻮْﻡَ ﺗُﺒَﺪَّﻝُ ﺍﻷَﺭْﺽُ ﻏَﻴْﺮَ ﺍﻷَﺭْﺽِ ﻭَﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕُ ﻭَﺑَﺮَﺯُﻭﺍْ ﻟﻠّﻪِ ﺍﻟْﻮَﺍﺣِﺪِ ﺍﻟْﻘَﻬَّﺎﺭِ ‏( 48 ‏) ﻭَﺗَﺮَﻯ ﺍﻟْﻤُﺠْﺮِﻣِﻴﻦَ ﻳَﻮْﻣَﺌِﺬٍ ﻣُّﻘَﺮَّﻧِﻴﻦَ ﻓِﻲ ﺍﻷَﺻْﻔَﺎﺩِ ‏( 49 ‏) ﺳَﺮَﺍﺑِﻴﻠُﻬُﻢ ﻣِّﻦ ﻗَﻄِﺮَﺍﻥٍ ﻭَﺗَﻐْﺸَﻰ ﻭُﺟُﻮﻫَﻬُﻢْ ﺍﻟﻨَّﺎﺭُ ‏( 50 ‏) ﻟِﻴَﺠْﺰِﻱ ﺍﻟﻠّﻪُ ﻛُﻞَّ ﻧَﻔْﺲٍ ﻣَّﺎ ﻛَﺴَﺒَﺖْ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﺳَﺮِﻳﻊُ ﺍﻟْﺤِﺴَﺎﺏِ { ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ 48 : 51 } ﻭَﻗُﻞِ ﺍﻟْﺤَﻖُّ ﻣِﻦ ﺭَّﺑِّﻜُﻢْ ﻓَﻤَﻦ ﺷَﺎﺀ ﻓَﻠْﻴُﺆْﻣِﻦ ﻭَﻣَﻦ ﺷَﺎﺀ ﻓَﻠْﻴَﻜْﻔُﺮْ ﺇِﻧَّﺎ ﺃَﻋْﺘَﺪْﻧَﺎ ﻟِﻠﻈَّﺎﻟِﻤِﻴﻦَ ﻧَﺎﺭًﺍ ﺃَﺣَﺎﻁَ ﺑِﻬِﻢْ ﺳُﺮَﺍﺩِﻗُﻬَﺎ ﻭَﺇِﻥ ﻳَﺴْﺘَﻐِﻴﺜُﻮﺍ ﻳُﻐَﺎﺛُﻮﺍ ﺑِﻤَﺎﺀ ﻛَﺎﻟْﻤُﻬْﻞِ ﻳَﺸْﻮِﻱ ﺍﻟْﻮُﺟُﻮﻩَ ﺑِﺌْﺲَ ﺍﻟﺸَّﺮَﺍﺏُ ﻭَﺳَﺎﺀﺕْ ﻣُﺮْﺗَﻔَﻘًﺎ { ﺍﻟﻜﻬﻒ : 29 } ﻫَﺬَﺍﻥِ ﺧَﺼْﻤَﺎﻥِ ﺍﺧْﺘَﺼَﻤُﻮﺍ ﻓِﻲ ﺭَﺑِّﻬِﻢْ ﻓَﺎﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻗُﻄِّﻌَﺖْ ﻟَﻬُﻢْ ﺛِﻴَﺎﺏٌ ﻣِّﻦ ﻧَّﺎﺭٍ ﻳُﺼَﺐُّ ﻣِﻦ ﻓَﻮْﻕِ ﺭُﺅُﻭﺳِﻬِﻢُ ﺍﻟْﺤَﻤِﻴﻢُ ‏( 19 ‏) ﻳُﺼْﻬَﺮُ ﺑِﻪِ ﻣَﺎ ﻓِﻲ ﺑُﻄُﻮﻧِﻬِﻢْ ﻭَﺍﻟْﺠُﻠُﻮﺩُ ‏( 20 ‏) ﻭَﻟَﻬُﻢ ﻣَّﻘَﺎﻣِﻊُ ﻣِﻦْ ﺣَﺪِﻳﺪٍ ‏( 21 ‏) ﻛُﻠَّﻤَﺎ ﺃَﺭَﺍﺩُﻭﺍ ﺃَﻥ ﻳَﺨْﺮُﺟُﻮﺍ ﻣِﻨْﻬَﺎ ﻣِﻦْ ﻏَﻢٍّ ﺃُﻋِﻴﺪُﻭﺍ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻭَﺫُﻭﻗُﻮﺍ ﻋَﺬَﺍﺏَ ﺍﻟْﺤَﺮِﻳﻖِ { ﺍﻟﺤﺞ 19 : 22 } ﻭَﺍﻟﺼَّﺎﻓَّﺎﺕِ ﺻَﻔًّﺎ ‏( 1 ‏) ﻓَﺎﻟﺰَّﺍﺟِﺮَﺍﺕِ ﺯَﺟْﺮًﺍ ‏( 2 ‏) ﻓَﺎﻟﺘَّﺎﻟِﻴَﺎﺕِ ﺫِﻛْﺮًﺍ ‏( 3 ‏) ﺇِﻥَّ ﺇِﻟَﻬَﻜُﻢْ ﻟَﻮَﺍﺣِﺪٌ ‏( 4 ‏) ﺭَﺏُّ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻭَﻣَﺎ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻤَﺎ ﻭَﺭَﺏُّ ﺍﻟْﻤَﺸَﺎﺭِﻕِ ‏( 5 ‏) ﺇِﻧَّﺎ ﺯَﻳَّﻨَّﺎ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀ ﺍﻟﺪُّﻧْﻴَﺎ ﺑِﺰِﻳﻨَﺔٍ ﺍﻟْﻜَﻮَﺍﻛِﺐِ ‏( 6 ‏) ﻭَﺣِﻔْﻈًﺎ ﻣِّﻦ ﻛُﻞِّ ﺷَﻴْﻄَﺎﻥٍ ﻣَّﺎﺭِﺩٍ ‏( 7 ‏) ﻟَﺎ ﻳَﺴَّﻤَّﻌُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﻤَﻠَﺈِ ﺍﻟْﺄَﻋْﻠَﻰ ﻭَﻳُﻘْﺬَﻓُﻮﻥَ ﻣِﻦ ﻛُﻞِّ ﺟَﺎﻧِﺐٍ ‏( 8 ‏) ﺩُﺣُﻮﺭًﺍ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏٌ ﻭَﺍﺻِﺐٌ ‏( 9 ‏) ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﻦْ ﺧَﻄِﻒَ ﺍﻟْﺨَﻄْﻔَﺔَ ﻓَﺄَﺗْﺒَﻌَﻪُ ﺷِﻬَﺎﺏٌ ﺛَﺎﻗِﺐٌ { ﺍﻟﺼﺎﻓﺎﺕ 1 : 10 } ﻭَﺳُﻘُﻮﺍ ﻣَﺎﺀ ﺣَﻤِﻴﻤًﺎ ﻓَﻘَﻄَّﻊَ ﺃَﻣْﻌَﺎﺀﻫُﻢْ { ﻣﺤﻤﺪ : 15 } ﺧُﺬُﻭﻩُ ﻓَﻐُﻠُّﻮﻩُ ‏( 30 ‏) ﺛُﻢَّ ﺍﻟْﺠَﺤِﻴﻢَ ﺻَﻠُّﻮﻩُ ‏( 31 ‏) ﺛُﻢَّ ﻓِﻲ ﺳِﻠْﺴِﻠَﺔٍ ﺫَﺭْﻋُﻬَﺎ ﺳَﺒْﻌُﻮﻥَ ﺫِﺭَﺍﻋًﺎ ﻓَﺎﺳْﻠُﻜُﻮﻩُ ‏( 32 ‏) ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻟَﺎ ﻳُﺆْﻣِﻦُ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢِ ‏( 33 ‏) ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺤُﺾُّ ﻋَﻠَﻰ ﻃَﻌَﺎﻡِ ﺍﻟْﻤِﺴْﻜِﻴﻦِ ‏( 34 ‏) ﻓَﻠَﻴْﺲَ ﻟَﻪُ ﺍﻟْﻴَﻮْﻡَ ﻫَﺎﻫُﻨَﺎ ﺣَﻤِﻴﻢٌ ‏( 35 ‏) ﻭَﻟَﺎ ﻃَﻌَﺎﻡٌ ﺇِﻟَّﺎ ﻣِﻦْ ﻏِﺴْﻠِﻴﻦٍ ‏( 36 ‏) ﻟَﺎ ﻳَﺄْﻛُﻠُﻪُ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟْﺨَﺎﻃِﺆُﻭﻥَ { ﺍﻟﺤﺎﻗﺔ 30 : 37 Sai da ya kai har ƙarshe sannan ya cire hannunsa a ruwan ya kulle tare da kallon mummy Sarah ya furta, "A yi kamar kwana uku ko biyar ko bakwai ana yin haka. Sai kuma ita mai lalurar ta kula wajen yawan karanta ( ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻳﺤﻴﻰ ﻭﻳﻤﻴﺖ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ kafa dari bayan sallar magriba da asuba. Ta kuma dinga karanta addu’ar Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ‏( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺏ ﺍﻟﺴﻤﻮﺍﺕ ﺍﻟﺴﺒﻊ ﻭﻣﺎ ﺃﻇﻠﺖ ، ﻭﺭﺏ ﺍﻷﺭﺿﻴﻦ ﻭﻣﺎ ﺃﻗﻠﺖ ، ﻭﺭﺏ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ﻭﻣﺎ ﺃﺿﻠﺖ ، ﻛﻦ ﻟﻰ ﺟﺎﺭﺍ ﻣﻦ ﺷﺮ ﺧﻠﻘﻚ ﻛﻠﻬﻢ ﺃﻥ ﻳﻔﺮﻁ ﻋﻠﻰّ ﺃﺣﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﺃﻭ ﺃﻥ ﻳﺒﻐﻰ ، ﻋﺰ ﺟﺎﺭﻙ ﻭﺟﻞ ﺛﻨﺎﺅﻙ ﻭﺗﻘﺪﺳﺖ ﺃﺳﻤﺎﺀﻙ ، ﻭﻻ ﺇﻟﻪ ﻏﻴﺮﻙ ). Kuma ta dinga karanta suratu Yaasiyn, ArRahmaan, Qaaf da Suratul Mulki bayan sallar La’asar. Shi tsawon kamar kwana uku ko biyar ko bakwai za ta yi" ##Matar Sayyadee #Dinaayah #THE SECRET #JINNUL ASHIQ #Mummy Sarah #KAISAAR #Benazir #Hatred #EteRnaL Love #Between two lovers ##DINAAYAH SAFRAAZ _Free pages fa basu da yawa, guda biyar ne kawai don haka ku hwara payment, sannan don girman Allah idan kin san za ki saya ne domin ki fitar kar ki zo na yafe naki cinikin_ `DINAAYAH SAFRAAZ ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVDENCE OF PAYMENT 08128755583` ```Ina ƙara baki shawara sister, kar ki bari ayi wannan tafiyar babu ke``` [9/16, 10:53 PM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_* (```DiNaayah SafraAz```) _*BEtweEn two LoveRs*_ ~Story and written~ *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @MatarSayyadee01_ _Arewabook@Matarsayyadee0_ ```Messenger of Allah (ﷺ) said, "There are three signs of a hypocrite: When he speaks, he lies; when he makes a promise, he breaks it; and when he is trusted, he betrays his trust."``` [ _Al-Bukhari and Muslim_]. *Another narration adds the words: 'Even if he observes fasts, performs Salat and asserts that he is a Muslim".* عن أبي هريرة ، رضي الله عنه ، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال‏:‏ “آية المنافق ثلاث‏:‏ إذا حدث كذب، وإذا وعد أخلف، وإذا أؤتمن خان‏"‏ ‏(‏‏(‏متفق عليه‏)‏‏)‏ ‏.‏ Chapter 005 `NOT EDITED` "Ba Lukman in sha Allah ba zan yi wasa da duk abunda ka ce ayi ba. Zan tashi tsaye kuma in rage bacci akan samuwar lafiyar 'yata. Idan wani abu ya samu Dinaayah haukacewa zan yi, Dr kuma zuciyarsa ce za ta buga." "Babu wani abunda zai same ku dukkan ku. In sha Allah zai rabu da jikinta in har kuka dage a kanta. Shi ma Ibrahim ɗin idan ya iso goben zan ƙara shaida masa komai da duk abunda ya kamata a yi mata. Yanzu idan ta farka wannan ruwan shi zai fara wucewa maƙoshinta. Sannan kuma ta yi wanka da ruwan a cikin baho sai ku kawo min ruwan domin zubar da shi a inda ya kamata." Ba Lukman ya faɗi yana cigaba da rarrabe magungunar da ke gabansa. "Allah ya ƙara girma ya kuma saka da alkhairi!" Mummy Sarah ta faɗi tana mai miƙewa tsaye ta fice daga ɗakin. A tsaye ƙofar ɗakin karatun ba Lukman mummy Sarah ta ga Lami mahaifiyarta tsaye tana kaiwa da komowa. Tana ganin Sarah ɗin ta nufo wajenta tare da kama hannunta suka nufi ƙofar gida. Sai da suka je inda babu idanun mutane sannan Lami ta kalli Sarah hankalinta a matuƙar tashe tare da faɗin, "Sarah mai ke faruwa? Mai ya samu Dinaayah?" Share hawayen da suka zubo mata a idanu mummy sarah ta yi sannan ta furta, "Ba Lukman ya ce aljani ne a jikinta kuma ya aure ta. Sai dai ya bayar da magani da addu'o'in da za a riƙa mata in sha Allah za rabu da ita har abada. Amma mama mai yasa grandma ta aikata wannan shirme? Abunda muka daɗe muna ɓoyewa shine ta yi ƙoƙarin bayyana shi a yau. Da wani irin ido da baki za mu kalli Dinaayah mu faɗa mata cewar ba mune iyayanta na asali ba? Haba mama! Yanzu pastor Emmanuella ta kyauta mana kenan?" Dafa kafaɗarta Lami ta yi tare da faɗin, "Ki kwantar da hankalinki, mama ba wai ta bayyana komai bane. Akwai yadda za ayi har yanzu a cigaba da ɓoye wannan sirrin. Idan Dinaayah, Aleesha ko Benazir sun tambaye ki akan abunda su ka ji mahaifiyata ta ce, ki faɗa masu depression ke damun pastor sabida rashin jikarta Aina'u da ta yi a wani hatsari shiyasa duk wanda ta gani sai ta riƙa tunanin Aina'un ce." Doguwar ajiyar zuciya mummy Sarah ta yi tare da jin wani relief don itama shawarar da Lamin ɗin ta bayar ya mata kuma da hakan take ganin za ta kawas da zargi a zukatan 'ya'yan nata. "Shikenan zan faɗa masu hakan. Ki koma gida mama gobe In sha Allah kamun mu wuce zan zo gidan amma ni kaɗai ko kuma tare da Dr, na san ma tare za mu zo, sai dai ba za mu zo da su Dinaayah ba gudun ƙara faruwar abunda ya faru a yau." "Babu komai Sarah, ni ma ba zan so ku zo ke da 'ya'yan ba duka. Tsufa sosai ya kama mom ɗina shiyasa ta ke yin wani abu kamar yarinya a yanzu, mu kanmu haƙuri muke yi da ita a yanzu." Lami ta faɗi. "To shikenan mama, amma babu matsalar komai ko?" mummy Sarah ta faɗi. "Babu komai Sarah. Allah ya muku albarka tare da zuri'arku gaba ɗaya. Ki koma wajen Dinaayah kar ta farka daga bacci." Lami ta faɗi. Sai da mummy Sarah ta rungume mahaifiyar tata tukun sannan ta rakata har waje don har yau dai taƙi karɓuwa a cikin gidan iyayan marigayi Nuhu wato mijinta. Ko da ta dawo ɗakin da Dinaayah ke kwance, su Benazir ta taras riƙe da Alqur'ani suna ta yi wa 'yar uwansu karatun duk da wanda ke tashi cikin MP sai dai volume ɗin a can ƙasa ya ke daidai wajen kunnenta. Gaba ɗayansu babu wacce bata tsiyayar da ruwan hawaye duk da karatun da ke fita daga bakunansu. Mummy Sarah ma sai ta nufi wajen da aka yi sa tamkar cupboard a falon wanda Ƙur'anai ne da mabanbamta littattafai da aka jera a wajan ta ɗauko izifi sittin ta buɗe ta shiga karatun itama. Sun kwashi fiye da awa guda suka karatun, duk wacce ta shigo ta ga abunda suke yi sai itama ta ɗauko nata Alƙur'anin ta bi sahunsu. Sallar la'asar ya tada su. Fitarsu bai fi da mintuna biyar ba itama Dinaayah ta farka wasai tamkar ba ita ce wacce aka yi fama da ita ɗazu ba. Sai dai ba komai ta iya tunawa ba idan aka cire maganganun da pastor Emmanuella ta faɗi lokacin da suka je gidan. Abunda ta tuna last shine lokacin da paston ta durƙusar da ita ƙasa tana mata ihun Halleluja a kunne. Wani irin durowa ta yi daga kan gadon tare da soma tafiya ba tare da sanin ainahin inda ta nufa ba. Guum! Ta buge da bango kasancewar ba hanyar falon tayi ba. Baya ya kuma yi ta canza hanya sai da wannan karon ma karo ta ci da keken ɗinkin da ke ɗakin gab da ƙofar da za ta sada mutun da falo. Bata haƙura ba ta cigaba da lalube har ta yi nasarar fitowa daga ɗakin daidai lokacin da mummy Sarah ke shirin tada sallah. Da sauri mummy Saran ta iso inda Dinaayah ta ke tare da riƙo hannunta ta zaunar da ita a kan kujera sannan ta ce, "Dinaayah mai yasa kika fito ke ɗaya? Ai da kin kwaɗa kiran sunana na zo na fito da ke da kaina." Murmushi Dinaayah ta yi tare da faɗin, "Mum yanzu kin fara min kallona makauniyar da kika ce baki taɓa ba kenan?" Da saurin mummy Sarah ta girgiza kai tare da faɗin, "Ba haka bane Naayah. Na san ke ɗin 'yar baiwa ce kuma mai tarin basira, na san za ki iya fitowa da kanki. Amma matsalar ita ce nan ɗin baƙon wajenki ne baki haddace komai na gidan ba. A gida na taɓa yi miki ƙorafi akan kin sauko daga upstairs zuwa downstairs?" Girgiza kai Dinaayah ta yi tare da furta, "Baki taɓa ba mom. Yanzu ma ko da kika ji na ce haka kawai na faɗa ne don inji mai za ki ce." "To kar ki sake!" mum Sarah ta faɗa tana mai kamo hannunDinaayah ta riƙe a hannunta tana kallon fuskanta. Babu inda ta baro mahaifinta, fara ce tass mai dogon hanci da matsaƙaitan idanu irin na mahaifinta dr Khalil. Tana da tsayi don duk gidan idan aka cire su Sauban tafi kowa tsayi. Abunda ya sa mutane da yawa basu yarda Dinaayah makauniya ce shine, idanunta farare ne ƙal, ƙwayar idanun kuma kalar blue mai ɗan duhu (tamkar na turawa), sa ɗigon ciki kuma ash haka yake. Idanunta ya fi komai kyawu a fuskanta. Da kallo ba za ka taɓa fahimtar ita ɗin makauniya bace. Saboda idanun tsaye suke waje ɗaya basu karkace ba kuma ƙwayar basa rawa. "In sha Allah mum ba zan sake ba. Amma mum ina son in tambaye ki, mai ya faru? Don the last thing da zan iya tunawa shine mun je gidan grandma ɗinki tana ta faɗi wasu maganganu da ban gane ba wai zata min addu'a saboda kar na biyo halin mamata Aina'u. Wai ba nononta na sha ba naki na sha don haka ba zan taɓa yin irin halinta ba. Sai kuma ta ja hannuna zuwa ciki ta shiga min karatunsu na 'yan coci to tun daga nan I can't remember anything that happen sai tashi na yi na ganni a kan gado." "Suma ki ka yi shiyasa baza ki iya tuna komai ba. Wannan maganar da grandma ɗina ta faɗa kuma ba komai bane sai shirme. Tana da wata jika sunanta Aina'u to ta yi hatsari ita da 'yarta suka mutu shine hankalinta ya tashi har ta samu depression a kan haka don ƙwaƙwalwarta ma sai da ta taɓu, shiyasa duk wacce ta gani in har cutar ta motsa sai ta fara wannan zancen banzan da ta miki. Shirme ne kawai irin na marasa hankali da tawakkali." "Ni ma dai haka nace wannan rashin hankaline. Ta yaya ma za a ce ba kece kika haife ni ba! Ba zan taɓa ganin wannan ranar ba a rayuwata in sha Allah. Ai mum duk yarinyar da ta fito a cikin wata macen ba ke ba I'm sorry for her! Ba zan ce ba tai sa'a ba, amma dai she miss don babu uwa tamkar ya ke a duniyar nan a yanzu. You're mummy like no other!" Rumgumeta Mummy Sarah ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sai dai wani irin tsoro da tausayine ya mamaye zuciyarta. Sosai ta ke tsoron ranar da tsautsayi zai saka Dinaayah ta gano ba ita ce asalin mahaifiyarta ba. Ba ma wannan ne asalin abunda ke tsoratata da ɗaga mata hankali ba, faɗawa Dinaayah irin abunda mahaifiya tata ta shuka a duniya kamun barinta duniyar shi yafi komai yagalgala natsuwarta tare da ninninka tashin hankalinta don ta tsani duk abunda zai ɗagawa 'yarta Dinaayah hankali. "Allah kai ne Allah, ubangijin sammai da ƙassai, ubangijin abunda ke ƙarƙashin ƙasa da cikin ruwa, ubangijin dukkan halittun duniya, kai na ke roƙo ka taya mu binne abunda muke ƙoƙarin bunnewa shekaru kusan ashirin da uku." A cikin zuciya mummy Sarah ta yi maganar. "Ungo wannan kofin ki shanye ruwan tass ki ban cup ɗin!" mummy sarah ta faɗi tana miƙa mata. Babu musu ta amshi cup ɗin ta shanye tass sannan ta miƙa mata. "Bari 'yan uwanki su shigo su raka ki kiyi alwala ki zo ki yi sallah. Ni bari na tada nawa." mummy Sarah ta faɗi tana miƙewa tsaye yayin da Dinaayah ta gyaɗa mata kai. Sai da ta yi raka'a biyu sannan su Benazir suka shigo ɗakin kasancewar ba a nan ɗakin su kai ta su sallar ba. Da sauri Benazir ta zo ta zauna kusa da Dinaayah, Aleesha ta zauna ɗaya ɓangaren. "Ya jikinki sister?" Benazir ce ta yi maganar tana riƙe hannun Dinaayah ɗin. "I'm very ok fa! Ku kwantar da hankalinku. Ban jin komai a jikina, yanzu dai ku kai ni in yi alwala in zo inyi sallah." Dinaayah ta faɗi. Miƙewa su ka yi suka kama hannunta su ka kai ta wajen da ake alwala bayan sun ciko mata ruwa a buta sun aje mata a gabanta. Kaf baƙin da su ke tsakar gidan babu wanda ya san cewa Dinaayah makauniya ce saboda yadda ta ke alwalar cikin natsuwa kamar tanda annabi (SAW) ya koyar. Bayan ta gama ta miƙe suka kama hannunta har ɗakin da suka baro lokacin mummy Sarah ta idar da sallah. Sai Dinaayah ta hau kan dardumar da ta sauka ta tada nata sallar. Benazir da Aleesha sai suka bi bayan mummy Sarah da ta shiga uwar ɗaka. A bakin gado suka same ta zaune ta buga tagumi, duk sai suka nemi waje suka zauna jiki a sanyaye suna kallon fuskanta da ke bayyanar da matsanaiciyar damuwa. "Mummy mai ya faru? Mai yasa kike cikin damuwa?" a tare su kai mata tambayar. "Dole na shiga damuwa, Dinaayah tana cikin wani hali. Baiwar Allah ga rashin idanu yanzu kuma wani bala'in ne ya ke bibiyarta. Ba Lukman ya ce jinnul ashiq ne ya shige ta kuma da alama ya jima a jikinta sai yau asirinsa bayyana." mummy ta faɗi. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Jinnul Ashiq fa? Caɓ! Wallahi mummy jinnul Ashiq ba sa taɓa bari mutum ya yi aure, idan ma ya yi sai sun kashe ko kuma su hana shi haihuwa da zaman lafiya." Aleesha ce ta yi maganar hankalinta na daɗa tashi. Benazir kuwa tsit ta yi tana kallon fuskan Aleesha da ke magana idanunta ba sa ƙiftawa har sai da ta ji tsoron yanayinta ta girgiza ta. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki tare da faɗin, "Mum to yanzu menene mafita? An samu yadda za a cire shi Ashiq ɗin a jikinta?" "In sha Allah an samu. Yanzu haka ma ruwan addu'ar yana ɗakin ba Lukman, idan mun tashi tafiya da su za mu tafi da kuma sauran magungunan da naga yana harhaɗawa." mummy Sarah ta faɗi. "To Alhamdulillah!" Benazir ta faɗa tana kuma sauke ajiyar zuciya. "Mum ina tunanin na san abunda ya saka aljanin nan ya hauro jikin Dinaayah yau." Aleesha ta faɗa. Da sauri mummy ta kalle ta tare da faɗin, "Menene shi?" "Kakarki ce ta za komai. Ita ta riƙa wasu maganganun da hankali ba zai ɗauka ba. Tana ta wasu maganganun da ke nuna kamar ba kece kika haife mu ni da Dinaayah ba. Dole in saka kaina a ciki tunda kowa dai ya san ni da Dinaayah 'yan biyu da muka fito ciki ɗaya kuma aka haife mu a rana ɗaya." "Wallahi Aleesha ni ma tambayar da nake so na yi wa mum kenan!" Benazir ta faɗi. Murmushi mom ta yi tare da faɗin, "Idan ban da rashin hankali da tunani wa zai kawo wannan zancen banza da hofin? Ai ko makaho ya shafa ya san ku ɗin 'ya'yan cikina ne. Ke da Dinaayah ba Identical twins bane, Dinaayah daddynku ta ke kama dashi sak ita da su Sauban, ke kuma da ni kike kama. Amma duk da haka duk inda kuka shiga har Benazir ana kallon ku za a san uba ɗaya ya haife ku saboda jini ɗaya da ke yawo a jikinku." "Tabbas!" Benazir da Dinaayah suka haɗa baki suka faɗa. "Gobe dai za mu koma gida in sha Allah. Daddyn ku shi zai zo da kansa ya ɗauke mu." mum ta faɗa. "Ni bari ma na ɗauko wayata na kira shi, tun da muka zo nan sau biyu kawai muka yi waya da shi" Benazir ta faɗi. "Shiyasa ya ke ji da Dinaayah, tun da muka zo kullum sai sun yi waya kamun ta kwanta bacci." mum ta faɗa. Benazir da Aleesha kallon juna su ka yi tare da faɗin, "Kai! Lallai ma Dinaayah shine ko ta faɗa mana. Miƙewa mummy ta yi tare da harararsu sannan ta ce, "Menene amfanin na ku wayar? Ta fi ku dumuwa da shi ne kawai." tana gama faɗin haka ta fice. Kiciɓis suka yi da Dinaayah za ta shigo ɗakin itama, "Mum ina wuni? Na idar da sallar." haka Dinaayah ta ke duk ta idar da kowacce sallah sai ta yi gaisuwa. "Lafiya ƙalau Dinaayah. Ki shiga ciki 'yan uwanki na ciki ku yi hira." tana gama faɗin haka ta gittata ta fice domin zuwa gidan babbar yayarsu Na'ima su yi shawara akan abunda ke cin zuciyarta game da halin da Dinaayah ta ke ciki. Kai tsaye Dinaayah ta nufe su saboda ƙamshinsu da ta ji wanda shine ya taimaka mata wajen isa inda suke ɗin. Su kuma matsa mata suka yi ta zauna a tsakiyarsu. Tana zama wayarta da ke hannun Benazir ya hau ringing. _KAISAAR IS CALLING NOW!_ Shine abunda computer ɗin wayar ta ce kamun ta soma ba da sautin waƙar _Ya dab-dab_ wanda shine ringing tone ɗin wayar. Ajiyar zuciya Benazir ta yi tare miƙa mata wayar sannan ta kwanta flat a kan gadon ta rumtse idanunta da ƙarfi tana jin wani abu mai ɗaci yana tokare maƙonshinta. "Amin wa'alaikassalam, ina wuni?" Dinaayah ta faɗi a sanyaye bayan ta kara wayar a kunnanta. Murmushi ta saki mai faɗi tare da kuma faɗin, "To ka yi haƙuri don Allah. Tafiyar gaggawa ce ta kama mu, baban mummynmu ne ya rasu shine muka tafi Nassarawa ta'aziya." Shuru ta yi tana sauraran abunda ya ke faɗi daga can wanda ya sakaa ta yin dariya har sauti ya fito sannan ta furta, "To shikena ai goben zamu dawo In sha Allah. I'm missing you too!" Ɗaga idanu Benazir ta yi ta kalli Dinaayah sannan ta mayar da kanta. Bata kuma ɗagowa ba har ta kammala wayar sannan ta kalleta tare da faɗin, "Naayah wai yaushe har ku ka yi sabo haka KAISAAR?" "It's a long story Bena, amma idan mun koma gida zan faɗa miki. Abunda kawai zan iya faɗa miki for now shine cousin sis ɗinsa Aliyaah ce sanadin haɗuwarmu." "Aliyaah?" Benazir ta faɗi da mamaki sosai a fuskanta. "Hmm! Sai ka ce baki san Dinaayah ba, ai daddy kawai ke sanin sirrinta. Tun ranar farko da KAISAAR ya faɗawa Naayah yana sonta sai da ta taɗa masa ya bata shawarar abunda za ta yi." Aleesha ta faɗi tana danna wayarta. "Hmm, lallai!" shine kawai abunda Benazir ɗin ta faɗi tare da lumshe idanu. Washa gari da wuri daddy ya iso Nassarawa hankali a tashe saboda mummy Sarah ta ɗan soma ƙwanƙwasawa masa abunda ya faru a jiyan. Daƙyar ya samu bacci, ana idar da asubahi ya tada mota ya ɗau hanya. Tsigar jikinsa mimmiƙewa suka riƙa yi lokacin da ba Lukman ke masa cikakkiyar bayani a kan jinnul ashiq ɗin da ke jikin Dinaayah. Har ƙwalla sai da daddy ya yi tare ɗaukar alƙawarin sai inda ƙarfinsa ya ƙare a kan nema mata magani ko da,kuwa hakan na nufin rasa tasa rayuwar. "Ku tashi tsaye sosai Ibrahim akan yarinyar nan. Don Jinnul Ashiq wani irin aljani ne azzalumi kuma mai matuƙar naci, don haka kuma sai ku yi naci sosai wajen yin magana da duk abubuwan da na umarce ku da ku yi. Allah ya bata lafiya." "To amma ba Lukman ya za a yi mutum ya iya gane wani na ɗauke da aljani a jikinsa?" Jinjina kai ba Lukman ya yi tare da soma magana. "YADDA ZA A GANE ALJANI YA SHAFI MUTUM:" a) Alamomin ɓoye (wanda shi mara lafiyar ne kawai ya sansu) b) Alamomin Sirri (wadanda yan uwan mara lafiyar ne suka san su) c) Alamomin Zahiri (waɗanda kana ganin mai shafar Aljanu za ka gane) _Ta ɓangaren namiji:-_ 1-rashin sha‘awar aure ko jima’i sam-sam. 2-‘kin miƙewar gaba lokacin da a kai nufin yin jima‘i, alhali kuma haka kawai ma yana tashi. 3-‘kin fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana iya zama a cikin marainan mutum. 4-saurin gajiya yayin jima‘i da rashin iya komawa 5-jin motsi kamar tafiyar wani abu a gaɓoɓin haihuwa yayin jima‘i. 6-rashin cimma buƙatar jima,i. 7- In ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya dauke ka. 8- Da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo tun kafin ka fara. 9- komawar gaba da maraina su shige ciki. 10- yawan ciwon kai, Ɓacin rai mara dalili, faduwar gaba, da dai sauran su. 11- haka kawai sai ka ji ka tsani matarka. 12- Yawan mafarki kana saduwa da wata matar. 13- Yawan samun matsaloli aduk inda ka je neman aure, sai maganar ta lalace. 14- Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai. 15- Matsananciyar sha’awa da tsoron mata da dai sauransu. YADDA MACE ZATA GANE ALJANI YA AURETA 1- yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi a cikin. 2- a duk lokacin da su kai nufin saduwa kawai sa ta ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al’adarta bane. 3- jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida. 4- suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar ta ba. 5- matsanancin ciwon baya ko kwankwaso. 6-ƙin yarda da jima‘i. 7- Za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban. 8- yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da taron suna. 9- ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannunsa a cikinki tare da fizgo wani abu, musamman idan kina da ciki. 10- yawan yin ɓarin ciki ba tare da wani sanannen dalili ba. 11- yawan mafarkin ana binki a guje ko ana kokawa da ke. 12- jin motsi a cikinki, wani lokaci ma har yana daɗa girma, amma in likitoci suka auna za su ce ba su ga komai ba. 13- rashin son yin magana da kowa da jin haushin mutane haka kawai. 14- tsanar mai gida haka kawai, alhali za ki ji kina sha’awar wasu mazan. 15- Jin wari mara dadi yana fito miki ko ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen gaba. 16- Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba. 17- Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi. 18- In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suyi mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fadar cewa wance kwarjini take musu. 19- Za ta dinga yawan zama a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane. 20- Idan yarinya tana zuwa makaranta za a ga kokarinta yana raguwa kuma tana ramewa. 21- Yawan ciwon kai da yin jiri. 22- Faduwar gaba, musamman idan magriba ta kusa. 25- da zaran mace ta fara barci sai ta ji an zungureta ta farka. Da dai alamomi da yawa." Wani hucin ajiyar zuciya daddy ya saki mai ƙarfi kamun ya kuma jefawa ba Lukman ɗin wani tambayar, "Shin baba aljani kala ɗaya ne kawai ko kuwa suna da yawa?" Girgiza kai ba Lukman ya yi tare da faɗin, "Aljanu sun kasu kashi-kashi, daga cikinsu akwai; Jinnut Ɗayyar ﺟﻦ ﺍﻟﻄﻴﺎﺭ Wato Aljani masu fika-fuki da suke tashi sama. b)Jinnul Ghauwas ﺟﻦ ﺍﻟﻐﻮﺍﺹ Wato Aljanin ruwa, me zama a cikin ruwa C)Jinnul Tabaddul ﺟﻦ ﺍﻟﺘﺒﺪﻝ Aljanu masu dawowa Yara bayan sun tsufa. d) Jinnul Atfal ﺟﻦ ﺍﻷﻃﻔﺎﻝ Aljanu masu shiga jikin kanan yara. e)Jinnul Bakam ko Jinnus Saqam ﺟﻦ ﺍﻟﺒﻜﻢ ﺃﻭ ﺟﻦ ﺍﻟﺴﻘﻢ Aljanu masu sa rashin lafiyar gaɓɓai. f)Jinnul jalab wattahdheer ﺟﻦ ﺍﻟﺠﻠﺐ ﻭﺍﻟﺘﺤﻀﻴﺮ Aljanu masu shiga jikin masu Rukiyyah da masu karance-karance akan Aljanu g)Jinnul Ghubar ﺟﻦ ﺍﻟﻐﺒﺎﺭ Aljanu masu yawo a cikin qura. h)Jinnul Hayyat Wal Aqarib ﺟﻦ ﺍﻟﺤﻴﺎﺕ ﻭﺍﻷﻗﺎﺭﺏ Aljanu masu siffar Macizai da kunami. i) Jinnul Sihr ko KhadimulMAGUNLUR السحر Aljanin da ke shiga jikin mutum ta hanyar tsafi ko sihiri j) Sakinul Maqabir ﺳﺎﻛﻦ ﺍﻟﻤﻘﺎﺑﺮ Aljanun Maƙabarta. k) Khadimul Hammam ﺧﺎﺩﻡ ﺍﻟﺤﻤﺎﻡ Wato Aljanun Bandaki ko Sarkin Ƙazamai. l)Amirul Baiti ﻋﺎﻣﺮ ﺍﻟﺒﻴﺖ Aljanin gida. Aljanun da suke zaune a gidajen mutane. m)Jinnul ƙariyn ﺟﻦ ﺍﻟﻘﺮﻳﻦ Nau’in Aljanin da kowa yana da shi. n)Ifriytun minal Jinni ﻋﻔﺮﻳﺖ ﻣﻦ ﺍﻟﺠﻦ Nau’in Aljanu masu Azababben ƙarfi. o) Shaiɗanun mariyd ﺷﻴﻄﺎﻥ ﻣﺮﻳﺪ ﺃﻭ ﻣﺎﺭﺩ Nau’in Aljanu masu bala’in taurin kai. p)Jinnul Katfah ﺟﻦ ﺍﻟﻜﺘﻔﺔ q)Sariqul Jinni ﺳﺎﺭﻕ ﺍﻟﺠﻦ Aljanu masu satar kayan mutane. r) Sariqus Sam’i ﺳﺎﺭﻕ ﺍﻟﺴﻤﻊ Aljanu masu sato maganar Mala’iku. s)Jinnul Shu’uwn ﺟﻦ ﺍﻟﺸﺆﻭﻥ Aljanu ‘yan rainin wayo, masu fitinar tsiya. t)Tabriyqul Jinni ﺗﺒﺮﻳﻖ ﺍﻟﺠﻦ u)Jinnul Was’was ﺟﻦ ﺍﻟﻮﺳﻮﺍﺱ Aljanu masu sa Wasu-wasi v) Jinnul Falsafiyy ﺟﻦ ﺍﻟﻔﻠﺴﻔﻲ Aljanu masu nazarin rayuwar mutane. w) Jinnul Ashiq ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ Wato Aljani mai aurar mace yana hana ta aure ko haihuwa. Dadai sauransu. x)Jinnuz Zulam ﺟﻦ ﺍﻟﻈﻼﻡ Aljanu masu zama a cikin duhu. Waɗannan da na lissafo sune rabe-raben aljanu." ##MATAR SAYYADEE #SAFRAAAZ THE KILLER #Aizaad #DINAAAYAH #Benazir #Aleesha #ALIYAAH #Ƙanwar Matata Return ##BETWEEN TWO LOVERS #DInaAYaH SaFrAAz ```This is just the short trailer of the story! Mutanena ban fa ɗauko kashi ɗaya daga cikin kaso ɗari na labarin ba fa. Dama kuma na faɗa free pages biyar kawai zan yi kuma Alhamdulillah na kammala. Mai son jin yadda labarin zai kaya sai yi payment in tsundumasa cikin paidgroup wanda in sha Allah a can cikakken labarin zai cigaba``` *_Free pages sun ƙare ki biya ɗarinki biyar idan kin karanta ƙanwar matata, idan kuma baki karanta ba 1k kacal za ki turo domin complete document na shi ƙanwar matatan sannan kuma in tsunduma ki cikin paidgroup na DINAAYAH SAFRAAZ wato KƘANWAR MATATA RETURN. Don girman Allah idan kin san za ki saya ne domin ki fitar kar ki zo na yafe naki cinikin!_* `DINAAYAH SAFRAAZ ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVDENCE OF PAYMENT 08128755583` _Ina ƙara baki shawara sister, kar ki bari ayi wannan tafiyar babu ke_