*TKG* 01. "SADIYA.." Wannan karon a yanayin yadda ya kira sunana sai da na ji jikina ya amsa da ya sa kaina na ƙasa sai da na ɗago na kalle shi. Tabbas a cikin idanuwansa na hango kamar hawaye sun cika masa kwarmin idanuwa kuma na hango gajiya da haƙuri harda kunya a lokaci ɗaya. "Sadiya.." Ya sake furtawa cikin wani irin rauni. Raunin da har ina jin sautin fitar shi daga muryansa. "Sadiya.." "Ta.." Ya sake faɗa ararrabe daga gani ya kasa sarrafa kanshi halin da ya ke ciki na neman tona masa asiri. Ba na so ko ɗaya na nuna masa na san labarin abin da ke faruwa yadda bai faɗa mini ba nima ba zan nuna masa na sani ba. Tabbas na yi dauriya domin a lokaci ji na ke yi kamar na zube a kan kafafuwana tsabar yadda suke rawa. Ina jin wani irin nauyin jiki wanda na zuciyata ne ya sakar ma gangar jikina. Na yi iya ƙokarina kar ya fahimci nima a firgice na ke shi ya sa na gayyato mirmishi wanda ka na ganin shi gwara ma kuka a kan shi saboda ba daga ƙarƙashin zuciyata ya fito ba. Ina yin mirmishin ina kallon fuskar Yallaɓai amma sai na ga yau ba na ganin shi da haske a idanuwana sai ya yi mini wani baƙi kamar ba Yusuf ɗina ba. "Sadiya ta. Na dawo" Ya faɗa ya na kallona domin tun ɗazu idanuwanshi suna kaina ne. Ni kuma cikin rawan jiki da na zuciya na buɗe baki dakyar ina jin harshena na karkarwa a cikin bakina. "Na'am" Murya ta na rawa ina so na daidaita kaina amma wallahi na kasa. Kai jama'a kishi bala'i ne sai yau na sake samun tabbacin haka duk yadda na so a ro jarumta sai na ji na kasa ji na ke yi wani abu na min yawo a cikin jinin jikina. Kaina ya yi nauyi gabaɗaya ji na ke yi kamar zan faɗi saboda tsabar gigitar da na ke ciki saboda tashin hankali. "Na'am Yallaɓai n.." Sai sauran kalamai na suka maƙale a fatar bakina. Na kasa iya kiransa da yau ɗaya da Yallaɓai na. Yau ɗaya da na kalle shi ina jin dukan zuciya da cewa Yallaɓai yanzu ba nawa ba ne ni kaɗai ya tashi da ga mallakina ni ɗaya ya koma mallakinmu ni da wata. Ashe haka sauran mata da dama suke ji in an yi musu kishiya? Na ɗauka in Yallaɓai zai ƙara aure ba zan wani damu ba ashe ashe kishi ba a yi masa da wasa. Tabbas Ubangiji ne ya hallici mu mata shi kuma ya sanya mana kishi a zukatanmu shi kuma kaɗai ya san dalilin shi na haka.   Balle irin auran da Yallaɓai ya yi ban shirya ba. Lamarin ya zo min ne cikin bazata da tsamanin abin da ban taɓa tsammani ba. Ban taɓa zaton a wannan yanayin ne zan fara raba Yallaɓai da wata ba. Ban taɓa tunani ko hasashen haka ba. Takalmin da ke kafata har ya jiƙe da zufa haka wayar dake hannuna tana maiƙon zufan da ke fita daga jikina Yallaɓai ya fara taku ɗaya, biyu zuwa gare ni da sauri na yi baya a nufina na guje ma haɗuwar jikina da na shi domin yau kawai na ji ba na so Yallaɓai ya kusantoni. Ƙokarina na yi baya amma jikina ya ƙi ba ni haɗin kai saboda a firgice na ke. Bayan da na yi da sauri ya ja takalmin kafata ya turkuɗe na yi baya zan faɗi ban san lokacin da wayar hannuna ta faɗi ba, sai na ji Yallaɓai ya rike ni gam lokaci ɗaya yana kallona kafin ya ce. "Lafiyan ki kuwa? Ya faɗa ya na mai kallona cikin fitan hayyaci na kalle shi sai na ji in na cigaba da kallonsa zan iya fashewa da kuka har na tona asirin zuciyata. Ya ji jikina na rawa  ya kuma ya fahimci duk a firgice na ke ba na cikin hayyacina, shi ya na ƙoƙarin ya ta da ni tsaye ya raɓa ni da jikinsa ni kuma hannayen nashi na ke kallo domin sai na ga kamar sun zame min baƙi a cikin idanuwana yau ɗaya kawai sai na ji hannun Yallaɓai kamar baƙo a gare ni da ban san lokacin da na yi gefe ina mai kauce ma riƙonsa baa. Hannun kujera na dafe ina haki sama sama domin na ji tabbas numfashina na cijewa kamar ya na neman ya dawo wuyana. Yallaɓai ya kalleni a tsorace ya sake kallona kafin ya ce" Sadiya? Kina lafiya? Ya faɗa ya na ƙokarin ƙara matsowa kusa da ni da sauri na yi baya amma kuma ban saki hannun kujeran da ke gefena ba domin in har na yi gangancin saki ba zan iya riƙe kaina ba. Sadiya ki yi jarumta Sadiya ki daure. Haka na ji wata zuciyar na faɗa min da ya sa na yi saurin ƙwato numfashina da karfi na sauke ajiyar zuciya ina mai kallon wayata da ta faɗi a ƙasan Tayels. Yallaɓai ya bi in da na ke bi da kallo shi ya duka ya ɗauko min wayar ya riƙe ta a hannun shi. Kallona ya ke yi yana so ya yi mgana shima bakinsa ya yi masa nauyi kawai sai na miƙa masa hannu ya saka min wayar lokaci ɗaya yana faɗin" Kin tabbata kina lafiya? Ji na yi kamar in balla masa harara in ko na buɗe bakina na tabbata sai na danna masa ashar na katsinawa. Amma sai ban yi haka ba, na sake gayyato mirmishi ina mai ɗaga masa alamun lafiya ta ƙalau. Ajiyar zuciya na riƙa saukewa a jejjere ina huro iska daga bakina domin na samu natsuwa daga ƙasan raina ina ta mamaita Innalillahi domin Allah ya sake ba ni jarumta. Cikin ikon Allah na ji na samu natsuwa jikina ya daina rawa. Har na samu daman sakin hannun kujera na tsayu da kafafuwana.           Kallonsa na yi ya na tsaye ya harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ba ni kaɗai ba shi kan shi ma a firgicen ya ke sannan ba natsuwa a tare da shi. Ban tsaya sake kallon shi ba na yi karfin halin wucewa wajen ledojin da ya ijiye na duka na ɗauka ina faɗin" Su Jidda sun gaji da jira har sun yi barci." Na faɗa saboda gyara yanayina lokaci ɗaya ina ɗagowa da ledojin ta gabansa na wuce zuwa kan dining na ɗora ledojin amma ban buɗe su ba. Ina so na juyo amma ba na so mu sake haɗa ido da Yallaɓai. "Ki tashe su mana." Haka ya faɗa a sanyaye sai na juyo ina mirmishi kafin na ce" Sun riga sun yi barci fa? Ƙyale su kawai." Shi kuma kawai sai ya saki hannayenshi ya wuce kawai zuwa falo ya na mai faɗin"  Wannan babban rana ce a gare mu bai kamata mu yi murnan ba su a wajen ba." Ya ƙarishe faɗa ya na buɗe kofar falon ya shige ni ban bi bayan shi ba ina ta ƙoƙarin yaji da abin da ke taso min. Ina jin sa daga nan ya na kiran sunanayen su Jidda daman ba ta da nauyin barci. Baby ma ba ta dashi amma ba kamar Jidda ba. Tsayuwa na neman gagarata ya sa na samu ɗaya daga cikin kujerun falon na zauna ina sauke numfashi. A baya in yi ta ganin laifin matan da mazajensu ke ƙara aure su yi ta hauka sai da ya zo kaina na fahimci yanayin tabbas kishi ke haukata mata ya kuma sa ka kasa mallakan kanka, ina zaune a in da na zauna ya dawo falon tare da yaran dukkansu ya na riƙe da hannun su. Baby ce sarkin surutu sai faɗi ta ke yi. "Abba yaushe ka dawo? "Ban daɗe da dawowa ba Baby" Ya ba ta amsa dai dai suna zama kan kujera mai zaman mutum huɗu. "To ina ka je Abba? Baby ta faɗa tana mai hawa jikinsa ya na shafa kanta ya ce" Na je Rano ne." Ya ɗago kenan muka haɗa ido da shi sai na yi saurin kauda kai daman ina so na ji me zai ce? Tabbas can ya je kuma ya dawo da kyakyawan tsaraba na ce a raina a lokacin da na ji Baby na tambayan shi ya siyo mata tsaraba. Sai ya nuna mata ledojin kan Dining ya na faɗin ga tsaranbanta ca.   Daga shi sai Baby suke hiran su ni da Jidda kamar ba ma falon ita ta na gefe sai hamma ta ke yi daga gani barcine a idanuwanta ni kuma ina zaune ina fama da turirin zuciya. "Duk Umma ce ta haɗa wannan? Ya faɗa ya na nuna cake ɗin da ke gabansu. Da sauri Baby ta ce" Umma ce da Yaya Jidda. Abba ni ma zan ci Cake ɗin" Ta faɗa tana leƙa Cake ɗin . Na ji ya kalleni a cikin jikina ni kuma sai ban juya na kalle shi ba, ina kallon gefe ina ƙokarin sakin fuskata na nuna komai bai faru ba amma ina jin kamar ba zan iya nuna komai ɗin bai faru ba.   "Sorry Jidda barci ko? Na ji ya faɗa sai na ji ita kuma ta na faɗin" A'a Abba." "To Hammar kuma ta mane ne Jidda? Ya faɗa ta gefen ido na kalle su sai na ga ya na jan hancinta ita kuma tana mirmishi. Yana ɗago kansa zuwa gare ni na yi saurin ɗauke kaina kamar ban san suna wajen ba. Ƙila ya daɗe yana kallona domin falon ya yi shuru sai karakainan Baby kawai ke tashi a falon ni kuma na yi matukar ƙokarin sassauta fuskata. "Yaran nan fa na jin barci ta so su mu yi abin da ya kamata su je su kwanta." Ya faɗa a sanyaye. Ni kuma sai na yi kamar ban ji ba sai na maida kaina can gefe kamar ina kallon Tibi ahalin Tibin ma a kashe ta ke. "Sadiya" Shima yau ɗin ya raba ni da wata ni ai ba Sadiyarsa ba ce ni kaɗai ya na da gimbiya shi ya sa yau Yallabai ya ke kirana Sadiya gatsal ta sar ma ya kasa ma minibwannan karan. Ji na yi kamar na fashe da kuka saboda baƙin ciki. "Sadiya.' A wannan karon da ɗan karfi ya sake kiran sunana. A sanyaye na kalleshi kuma kallon bai yi yawa ba na yi saurin kauda kaina ina ƙoƙarin miƙewa sai na ji duk jikina ya saki. Amma hakanan na miƙe ina ƙokarin dai dai ta kaina ina gani ya na nuna min gefensa na yi kamar ban gani ba na zagaye shi na isa kujera mai zaman mutum biyu dake gefen su na zauna. Ban kalle shi ba sai na sadda kaina ƙasa ina wasa da zoben azurfan da ke hannuna. "Sadiya ta." Sai yanzu? Sai yanzu ne ya gane ni tasa ce kafin ya samu wata. Haka na faɗa a raina sai na ɗago idanuwana da na ji har nauyi sun yi min ina kallon shi, shima fa karfin hali ne amma kunya da nauyin Sadiya da ya ke ji sun hana shi sakewa. "Na tambaye ki meke damun ki, kin ce min bakomai." Ya faɗa ya na mai kureni da ido a cikin zuciyarsa kuma na san bugu ta ke yi saboda nima ƙura masa ido na ke yi ina hasashen shike nan yanzu wai kwana zan riƙa rabawa da wata a kan Yallaɓai ko? Shi kenan mun tashi daga Family of 4 mun koma Family of 5 ƙilama kafin a rufe shekara ta haihu za mu hauhawa. Sai na ji kuka na taho min amma na yi saurin kannewa. "Me ke damun ki?  Ko an faɗa miki wani abu ya faru ne? Shike nan ya fara kama kanshi da kanshi. An ce mara gaskiya ko a cikin ruwa ya ke gumi ya ke yi. Da gangan na kalle shi sai na ga ya daburce yana ƙokarin gyara mganarsa. "Nufina ko can Ɗorayi  su Alhajimmu duk lafiya ko? Mirmishin takaici ya kwace min. Yallabai ya na so ya raina ma kansa ma wayau. Ya na tunanin abin da ya rufe bai faɗa min ba ya na ji a ransa zai tabbata a rufe ne ni ban sani ba. Sai kawai na yi masa wani kallo kafin na ce" Ko ɗaya. Ba abin da ya faru kawai raina ne ya ɓaci ba ka dawo da wuri ba alhalin kasan tun karfe nawa muka shirya ni da yara muna zaman jiran ka? Na faɗa hawaye na ciko min a ƙwarmin idanuwana.  Ƙura masa ido na yi sai na ga ya sauke ajiyar zuciya irin na samun salama ya na neman ɗauko mgana na yi saurin tare shi da faɗin" Mu yanka cake ɗin ina jin barci.' Na faɗa ina mai kauda kaina saboda ƙokarina na maida hawayena sai ma na ga sun koma da kansu ba tare da na yi yinƙurin maida su ba. "Sadiya" Ya sake kiran sunana a zafafe na juya na kusa na ce ya daina kiran sunana haka tunda ba shi ya raɗa min ba amma sai ya yi sauri tare ni da cewa. "Ta so ki zo nan ki zauna kusa da ni." Ya faɗa ya na nuna min gefensa. Kamar na ce bar ni anan sai kuma ban ce ba na tashi na koma kusa da shi na zauna amma ban matso kusa da jikinsa ba sai shi ne ya sauke Baby da ke kan jikinsa gefen Jidda sai ya ƙara matsoni ba zato kawai na ji ya sunkuya ya sumbaci kuncina kallonsa na yi bai bani zarafin mgana ba ya yi mirmishi kafin ya ce. "Ki yi hakuri Sadiya." Kallonsa na ke yi amma na kasa mgana sai ya ƙara marairaicewa ya na ƙara matso ni a jikina. "Sorry ba na ce ki yi haƙuri ba? Kin ji ko? Ya faɗa ya na ƙoƙarin saka hannu ya ɗago haɓata da sauri na kauda kaina ina faɗin" Nima ai na ce komai ya wuce ko? Sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Yaushe kika ce! Yanzu dai ko? Ban iya ma yi masa mgana ba ya dame ni kamar na ce ya matsa baya amma na kasa. Shi bai san ni yanzu ba na so ma ina zuwa kusa dashi ba a raina na ke jin duk abin da na ke tunanin ni kaɗai ke da shi yanzu ya tashi a mallakina nawa ya koma mallakinmu kuma namu. Ya yi ƙokarin ba ni haƙuri amma kuma ya kasa bayyana uzurin da ya zaunar da shi tun safe sai dare, Me ya sa Yallaɓai ya boye min ? Zan hana shi aure ne? Ni a cikin zuciyata na fi jin zafin munafuntata da ya yi sama da auran shi. Har Ma'u ta na murna ta samu makamin da za ta ya ƙe da shi ni kuma na ce ƙaryanta ba zan taɓa bari ta samu wannan damar ba. Mun yanka Cake amma wannan shekaran Walimar tamu ba cike take da farinciki ba. A fuskata za ka fahimci ba na cikin farinciki shima kuma haka su Jidda ne kawai ke ta murn. Ko wajen yanka cake ɗin ma hannuna saman na Jidda na ɗora sai shi ne ya ɗau hannuna nawa ya ɗora saman wukar sannan ya kama sai ya ce yaran su ɗora saman na shi. A haka muka yanka cake ɗin kuma wajen ba da wa yarana na fara ba mawa sannan shi na karshe in da a ce zan yi masa kutumar uba wallahi ko kallo bai isheni ba amma hakanan na daure ma zuciyata. Shi ko ni ya fara yankawa ya saka min a baki wanda dakyar na buɗe bakin duk ma ya shafa min a gefem baki ya na ƙokarin ya saka hannu ya goge min na goge da kaina sai ya koma ya na ba ma su Jidda cake ɗin suma suna bashi suna ta dariyan farinciki ina kallonsu a cikin raina ina tunanin shike nan Yallaɓai ya yi sanadiyar lalatamin farincikina na wannan ranar. Daman ya ce zai ba ni suprise lalle na karɓi babban suprise da ba zan manta da shi ba a rayuwata ba. Na gaji so kawai na ke yi na keɓe ni kaɗai. Shi ya sa kawai na mike na isa ga ƙwalin agogon da na siya masa ban jira na bashi a hannunsa ba na ijiye masa a gabansa ina faɗin" Gift ɗin ka" Na ga ya yi shuru ya na kallona ni ko sai na yi saurin kallon su Jidda ina fadin" Oya tunda an gama ku je ku kwanta." Da sauri ya ce" Ba mu gama ba. Ba mu yi ciye ciye ba Madam."   Ina kallonsa ina shirin mgana da sauri ya ce" Kuma na siyo kaza gasashiya da tsire ba ki duba ba." Sai na fara hammar ƙarya ina faɗin" Ina jin barci Yallaɓai." Haka na faɗa kawai sai na ga ya miƙe ya na mai ɗaukan kwalin agogon ya bude ya na gani kafin ya kalleni ya na min mirmishin da ni yanzu ya daina yaudarata. Ban tammaci haka ba. Shammata ta ya yi ya kawo min rumguma lokaci ɗaya yana faɗin" Thank you so much. Happy marriage Anniversy MRS YUSUF INUWA." Haka ya faɗa ya na kamkame ni kamar sanda haka na tsaya masa, illa hannuna na dama da na saka kaɗan na dan rike shi kaɗan na ƙosa ya sake ni sai na fara mutsu mutsu shi ya sa ya sake ni amma sai ya sumbace ni a kumatuna sannan ya bi ni da kallo kafin ya ce" Thank you for coming in to my life Halima." Yaƙe kawai na yi domin ni kalamansa ba sa wani shiga ta. Su Jidda na kallah suna ta cin nama da cin cin ita da dai Baby duk ta yi dama dama da Cake jin na ce ina jin barci sai ya ce na je na kwanta shi in sun gama shi da yara zai gyara wajen sannan ya zo ya same ni kaina na gyaɗa masa kamar akan ƙaya na ke na yi saurin barin musu falo ina ji a jikina ya bini da kallo ni dai na fita na jawo musu kofa ba tare da na juyo ba.   Ƙaran ƙofar dai dai da sauke ajiyar zuciyarsa. Komawa ya yi ya zauna ya na jin zuciyarsa na rawa. Gabaɗaya yau sai ya ji ya kasa mallakan kansa. Ya kasa yin wata jarumta yau sai ya ke jin kamar ba Namiji ba duk da haramci ya yi ba amma yau ya fahimci abin da ake kira kunya da nauyin Sadiya sun gama lulluɓe rayuwarsa. Har ga Allah bai taɓa hango rayuwarsa ta yanzu a kusa ba. Ya ɗauka in zai ƙara aure da amincewar Sadiya da yardanta bai taɓa tunanin kaddara za ta juyo masa ta wannan fannin ba. Ya na tsoro ya na tsoro tsoron kar Sadiya ta ji labarin auransa a bakin wani ba abakin sa ba. Ya daɗe a kofar gida a cikin mota amma ya kasa shigowa ciki ya rasa jarunmta da karfin gwiwan da zai iya haɗa ido da Sadiya bayan kuma yau ya munafunceta ya yi aure ba tare da saninta  ba. NENE ce ita ce ta sha gabansa kuma ita ɗin Nene Uwa ce a gare shi da ba zai iya mata musu ko saɓa umarninta ba amma gabaɗaya yau yini ya yi jikinsa ya yi wani irin sanyin. Sanyin da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba. Ya na zaune su Jidda na ta bidirinsu amma ya kasa cewa komai. Har Naman da kazan su kaɗai suka ci shi ya kasa  in zai tuna tun abincin da ya ci jiya da daddare ne bai ƙara saka wani abu a cikinsa ba sai ɗan wannan cake ɗin kuma a yadda ya ke jin cikinsa ya toshe ba zai iya cin wani abu ba. Wayarsa ce da ke cikin aljihun gaban rigar shi ta yi ɗan kara alamun shigowar sako sai ya yi saurin ɗaukowa ya duba. Musbahu ne. "Yaya Tafida sun sallama Shagon nan fa. A kan dai yadda kuka yi mgana. Ga ma key din sun ba ni a hannuna." Daga jiya ne ya ke zumuɗi da fatan su sallama masa wannan shagon amma yanzu komai ya ƙare. Sai ya ji ma abin ya fita kansa. Abin da ya faru yau a Rano ya ɓata komai ɗin da ya shirya a matsayin zai ba ma Sadiya suprise. A cikin shagunan da ke ƙasan Office ɗin su ne wasu suka saki shi kuma ya yi mgana ya na so Saboda Sadiya su kuma masu wajen sun ce mai wajen ne zai yi amfani dashi amma ya na ce ya na so saboda kimarsa kuma akwai kyakyawan alaqa tsakaninsa da mai wajen ya sa suka sallama masa ya so ne ya ba ma Sadiya suprise da niyar in aka bashi kuɗin aikinsa na kaduna zai cika alkwari ya  ba ta kuɗi ta yi oder ɗin kayan da za a sanya a shagon a buɗe shi cikin ƙankani lokaci. Ya san a duniya Sadiya ba ta da wani buri sai na buɗe shagon Saloon da tun da suka yi aure ta ke da wannan burin kuma shi ya karbe mata duka kuɗaɗenta da alƙwarin zai tallafa mata domin cikar burinta. Amma a wannan lokacin sai ya ji ko ya nuna mata ma ba za ta yi murna ba in ya faɗa mata ya kara aure za ta fassara niyyarsa ta wani siga ne shi ya sa sai karsashinsa ya ragu.   "Ok." Kawai ya tura ma Musabahu daga nan ya maida wayar aljihu.  Kunya ce ko nauyi suka sa ya kasa ta shi ya bi Sadiya cikin ɗaki ya zauna tare da su Jidda har suka gama bidirinsu sannan ya ce su je su yi brush su sauya kaya su kwanta shi kuma suka bar shi da gyara in da suka ɓata sauran cake ɗin da komai ya kwaaso su ya kai kitchen ya tura a cikin fridge. Sai ya leƙa ɗakin su Jidda ya tabbatar da sun kwanta sannan ya rage musu hasken ɗakin ya rufe musu kofa ko'ina sai da ya duba ya rarrage hasken gidan gabaɗaya sannan ya wuce bederoom ɗin su. Na ji takun sa zai shigo da sauri na shigar da kaina cikin bargo na lafe kamar mai barci. Ahalin kuma ba barci na ke yi ba. Na ji shigowarsa kuma na ji tsayuwarsa a kaina na wani lokaci na ƙara lafewa ina nunfashi kamar mai barci sai kuma bai tashe ni ba can na ji ya buɗe kofa ya fita. Sai kuma na ji ya shiga tiolet leƙo da kaina na yi ina sauke numfashi tunda na shigo ɗakin nan tiolet kawai na shiga na kama ruwa na dawo na saka kayan barci na kwanta ina faman tunani na ɗauka in na keɓe ni kaɗai zan samu daman kuka sai kuma na kasa ashe ma kukan rahama ne suya kawai kirjina ke yi, wani tuƙuƙin abun da ya tokaremin a zuciyata tun a lokacin da Ma'u ta faɗa mini ya kasa wuce min. Na san Yallaɓai zai iya ƙara aure kuma na saka a raina zai iya auran Gimbiya amma ban ɗauka yau ba. Ban kuma kawo sa gobe ko jibi ko nan kusa ba. Lamarin ya shammace ni shammatan da ya firgitani matuƙa sai kuma yadda Yallaɓai ya munafunce ni? Zan hana shi kara aure ne? Ko zan hana shi yin abin da ubangiji ya ce ne? Takaicina ɗaya yadda na yarda dashi na ke yi masa kyakyawan zato daga karshe ya ci amanata ya yi aure ban sani ba. Ni kuma na yi ma kaina alƙwarin in dai bai buɗe baki shi da kanshi ya faɗamin ba zan ta ɓa nuna masa na sani ba zan jira na gani ina da sauran ƙima a wajensa da zai zaunar da ni ya faɗa min ya ƙara aure sannan ta yadda auran na shi ya zo bakatatan! Ko kuwa zai bar ni a rufe ne ya na yaudarata da kalaman bakinsa na ƙarya da munafunci. Ina jin zai buɗe kofar tiolet ɗin sa na koma da kaina cikin bargo na lafe. Wallahi ban iya barci ba duk ina jin kai da kawonsa har ya gama ya zo ya kwanta ina jin sa a kusa da ni ya na kiran sunana na ƙara lafewa domin a ji a raina yau ko nema Yallaɓai ya yi sai dai tsinuwan mala'ikun su hau kaina amma ba zan iya yi masa wani amfani ba. Ina jin sa sarai ya na ta kiran sunana na yi kamar mai barci har bargon ya ye min daga fuskata yana leƙani na yi bakam na ƙi motsi sai da dai ya ga kamar na yi barci. Sai ya gyara min kwanciya ya sake rufamin bargo amma bai rufe min fuska ba. Kamar ya san ba na buƙatar sa bai raɓu da ni ba sai ya koma gefe ya kwanta. Na daɗe ina jin karin maganar nan ta hausawa da sukan ce yadda na ga rana haka na ga dare a baya in ta tunanin kawai sai ka kwana ba ka yi barci ba? Sai yau na samu tabbacin hausawa fa sun yi gaskiya domin nima yau ɗin nan yadda na ga rana haka na ga daren. Barci ko na minti ɗaya bai ɗauke ni ba Yallaɓai ma ya kusa raba dare ya na juye juye amma daga baya ya samu barci ni ko a kunnena aka fara kiran sallar farko na asuba a kuma lokacin ne na yaƙi sheɗan na miƙe na sauko daga kan gadon ina mai kallon Yallaɓai sai na ji wani shashi na zuciyata na ji tausayinsa yadda ya kwanta ya takure jikinsa sannan ni ya bar ma blanket ɗin bai rufu da shi ba. An ce mata da miji sai Allah sai na ji a wani shashe na zuciyata na yi ma Yallaɓai uzuri. Wani shashen kuma na ce min Yusuf ne fa! Wanda ya fi kowa fahimtar ki. Kamar zan ƙyale shi sai kuma na fasa zuciyata mai imani da tausayi wacce ta gaza ganin baƙin Yallaɓai ta rinjaye ni na isa gare shi na ja bargon na lulluɓa masa sai na ga ya yi motsi ya ɗan gyara ya miƙe kafarsa. Ina tsaye ina kallon shi duk da akwai ɗan duhu amma hasken kwan lantarki haraban gida ya na shigo mana ta cikin bedroom ɗin mu. Juyawa na yi na fita daga bedroom din Tiolet na shiga na ɗauro alwala sai da na fito ne na duba agogon wayata 4:30am na asuba sai na shimfiɗa darduma na saka hijabi na tada sallah. Sai da na yi raka'a huɗu sannan na zauna ina salatin Annabi da istgifari a cikin raina rokon Allah kawai na ke yi ya ba ni juriya domin na ji kamar zan gaza na ji kamar ba zan iya ba kuma gashi ina so na iya ina so na daure. Bayan na yi addu'o'ina na neman sassauci wajen Ubangina yau rana farko da na yi addu'a ban yi ma Yallaɓai ba  kawai sai na ji gwara na yi ma kaina da ƴaƴana tunda yanzu Yallaɓai ya zama mallakinmu ba mallakina ba Na tashi na sake tada salla Yallaɓai ya farka da fitilan wayarsa ya haskoni sai ya ga ina salla, ni kuma ina ganin ya farka saboda ba na son mgana ya sa ina sallamewa na sake miƙewa na ƙara kabbarta wata sallar. Sai na ga ya sauko daga kan gadon shima ya fice ashe alwala ya ɗauro ya dawo ya saka jallabiya ya zo kusa da ni ya shimdiɗa sallaya dai dai ina sallame raka'a ta biyun da na faro. "Me ya sa ba ki tashe ni ba? Sai na ji na kasa mgana a da na saba in dai zan tashi sallar dare ina ta da Yallaɓai mu yi tare yau kuma ban tashe shi ba. Saboda kar na yi masa mgana sai na sake miƙewa na kabbarta salla da ƙarfi na ce." ALLAHU AKBAR." Ni na san Yallaɓai ya bi ni da kallo kuma ya na ɗan fara shan jinin jikinsa. Ban bi ta kansa ba sai da na sake yi raka'a huɗu sannan na zauna ina jan casbaha Yallaɓai ma raka'a shidda ya yi lokacin har an fara kiran sallah na biyu sai ya miƙe ya je ya ɗauko hula ya saka da casbahansa hasken ɗakin ya kunna ya na kallona kafin ya ce. "Na tafi masallaci." Kaina na gyaɗa masa ina ɗaga masa carbin hannuna alamun ina lazimi bai ce komai ba sai ya kaɗa kai ya fice daga bedroom ɗin ya ma mai rufo min ƙofar bedroom kamar an ƙwace ni haka na sauke ajiyar zuciya ina ta fitar da numfashi ta baki ina tunanin shi ya ta da yara bayan ya fita saboda ni ban fita ba sai bayan na idar da sallar asuba sai na leƙa su na ga sun tashi suna salla a ɗakin na zauna daman na zo da Qur'anina na fara karatuna so na ke yi zuciyata ta samu salaman da zan yi ma kaina tunani mai kyau kuma alhamdulillah na samu. Sai da na gama karatun nawa a cikin suratul Maryam sannan na yi ma Jidda na ta karatun tare da Baby ina cikin yi ma Baby ne Yallaɓai ya shigo ɗakin daman sun san na hana su tashi in muna karatu daga zaunen suka gaishe shi ya amsa ya na daga ƙofar ɗakin bai shigo ciki ba hankalina da idanuwana na kan Qur'anin da ke gaba na na ce. "Ina kwana." Ban san yanayin sa a lokacin ba ya dai amsa nuryansa a sanyaye. "Lafiya lau. Kin ta shi lafiya? Ban amsa shi ba na cigaba da biya ma Baby karatu gajiya ina ga ya yi da tsayuwa ya fice sai dai na ji ƙaran rufe kofarsa na raka shi da harara ƙasa ƙasa. Bayan na gama musu karatun sai muka yi azkar sannan na bar su na ce Jidda ta yi ma Baby wanka su shirya ni kuma na cire hijibina na ijiye anan ɗakin yara na shiga kitchen na dafa musu ruwan tea sai na soya musu kwai na ce su karya da shi sannan kuma su tafi dashi yadda na ke jin kaina ba zan iya firan dankali ba kai aiki mai wahala ba na son yi saboda duk jikina ya mutu. Yau tare da yarana na karya ban ko jira Yallaɓai ba. Ban kuma koma ɗakin ba sai da Salisu ya zo suka tafi sannan na koma ɗakin ni dai na ji sa ya na waya sanda na shiga a mganar da na tsinta na karshe ce ya sa fahimci da wanda ya ke wayar. Uncle Abba ne domin na ji ya na faɗa min" Na kasa. Na kasa zama jarumi a gaban Sadiya Abba" Daga nan na shigo ɗakin sai kuma ganina ya sa ya yi saurin cewa" In na fita za mu yi mgana" Da kuma sauri ya katse wayar ya na kallona. Ni ko sai na yi masa mirmishin ya ƙe kafin na ce" Wanka za ka fara yi ko sai ka karya? Cikin ƙaramin sauti ya ce" Mu dai fara karyawa amma zuwa anjuma ko? Kai tsaye na ce" To. Amma ni na riga na karya tare da yara.' Ban bashi zarafin mgana ba na yi fit na bar masa ɗakin na faɗa tiolet ruwan zafi ya ƙare a tiolet sai da na fita kitchen na jona a buta ya tafasa sannan na juye na yi wanka da shi lokacin da na fito zan shigo ɗakin saboda ƙofar ba ta rufu ba sosai na ji sa ya na mgana kuma again kamar a waya ce. "Haba Anty Bahijja ba na roƙe ku da kar ku bari  maganar auran nan ta fita ba tare da na faɗa ma Sadiya ba? Me ya sa kika yi status in ta gani fa? Ban san me ta ke ce masa ba amma dai na ji ya amsata da cewa" Ko da kin cire ta don Allah ki goge. In ita ba ta gani wani na ta ya gani ya faɗa mata fa? Da wani ido zan kalleta? Duk bayanin da zan mata ba zan iya wanke kaina ba don girma Allah ku bari ni na samu jarumtar da zan iya faɗa mata ku bari ni mijinta ta fara jin mganar nan daga bakina." Ban yi niyyar labe ba amma sai na ji ina so na ji har karshen mganar ta su. Kenan shima ya ga status ɗin da ta yi? Uhm wato ta cire ni amma ta manta ba ta cire yar'uwata Ma'u ba. Ko ta manta zan iya sani ta hanyarta ne? Jin ban ƙara jin mganarsa ba ne ya sa na san sun gama wayar kenan shi ya sa na yi gundubalan tura ƙofar na shigo ciki, ba shi da gaskiya shi ya sa ya wani firgita da ya ganni na shigo.   Ta gefen ido na kalle shi sai kuma na basar da shi na isa kan kujeran madubi na ja na zauna ina shafa mai ina hangensa ta madubi wayarsa ce a hannunsa amma kuma hankalinsa na kaina ya kasa iya buɗe hira a tsakaninmu ni kuma daman tun a jiya na ji kamar an shimfiɗa wata tazara mai yawa a tsakaninmu na yi shuru kawai ina shafa mai bayan na gama na warware gashina na gyara sannan na tashi na isa ga wardrope na dauko wata doguwar rigar atamfata na saka ina cikin ɗaura ɗankwali na ji mganarsa. "Yau sai aka karya a ka bar ni ko? Ban juyo ba na ce" Tea kawai na sha." Ya kasa mgana ni da na san Yallabai da hira amma yau kalaman bakinsa sun kare duk ya wani kama kanshi saboda na ƙure shi sai na juyo ina kallonsa kafin na ce" Lafiyan ka? Da sauri ya ce" Me kika gani? Cikin ido na kallesa kafin na ce" Bakomai." Daman na latsa sa ne sai kuma bai bani kunya ba.   "Ni? Bakomai ke ce ma na ga tun jiya kin yi wani sanyi sanyi kamar ba ki da lafiya." "Ko? Na faɗa ina masa wani kallon tara saura kwata. Sai ya amsa da min E. Kafin ya ɗora da fadin" Ko duk laifina ne na jiya ba a gama hucewa ba? Sai kawai na rausayar da kai kafin na ce" Ko ɗaya ni fa lafiyata kalau. Kai ne dai na ha kamar a firgice ka ke." "Ni? Ya faɗa ya na kallona sai na gyaɗa mai kai kafin na ce" E.  Ka na yin abu kamar mara gaskiya. Yallaɓai me ka je ka yi ne ban sani ba? Da gayya na tsare shi da ido ai sai Yallaban ka ya daburce yadda ya yi min kaɗan ya rage ban yi dariya ba. "Rashin gaskiya kuma? Me kuwa zan yi miki ni Sadiya.? A duburce ya ke mganar da ka ganshi za ka gane bashi da gaskiya sai na yi mirmishi kafin na ce" To na sani. Maza ai ba ku da gaskiya barin ma in kuka so ƙara auro." Wallahi na hango tashin hankali ƙarara a idanuwan Yallabai mganta ya kashe masa jiki da ya sa ma ya kasa mgana. Ni kuma saboda na kauda wannan firgicin ya sa na ce" Ranar Mandoy ina da komawa asibiti fa."   "Allah ya kaimu. An gama duka gwaje gwajen ne? Ina ɗaukan wayata dake gefen in da na kwanta na ce" Saura ɗaya." Ina jin ajiyar zuciyarsa kafin ya ce" Allah ya kaimu." Na amsa masa da Amin sai na fice ina faɗin" Ina falo." Ban jira cewarsa ba na fice ina danne leɓena na ƙasa a raina ina tunanin to wai daman akwai irin wannan hanyar na cin uban maza da zullumi mata ke hauka? Ai wannan bakam ɗin kaɗai ya ishe su ba sai ka wahalar da bakin ka wajen faɗa ba. Falon yara na koma na zauna sannan na kunna datar wayana. Duk da ina jin faɗuwar gaba ban fasa ba. Na kuma kasa iya sarrafa kaina sai da na je na ƙara duba sreenshoot ɗin da Ma'u ta turamin sannan na girgiza kaina na koma na duba status ɗin kaf yan gidansu Yallaɓai ban gani ba da gaske kenan sun ji roƙon sa? Ita kuma Anty Bahijja kamar yadda ta ce ne ta rufe ni ban gani ba. Saƙon Munnira ne ya ɗau hankalina da ya sa na fara zargin ta san abin da ya faru. "Matar Yallaɓai kina lafiya kuwa? Haka ta rubuta mini sai na sha jinin jikina. To ni na ji ballatana ita? Ko mijinta bai faɗa mata ƴan'uwansa mata za su iya kirnnta ta su faɗa mata tunda an san muna tare. Na shiga na ba ta amsa da ina nan lafiya sai na fita ga waya a hannuna amma na kasa yin wani abu da ita ji na nake yi kamar ba ni ba, sai na ke jin kamar ba wancan Sadiya ba wannan Sadiyan da Yallaɓai ya gama shayar da ita mamaki ne. Vibration ɗin wayar a hannuna ne ya sa na dawo hayyacina sai na ga Marwa ce ke kirana. Da sauri na ɗauka kamar a cikin wayar za a faɗa min abin da zai kwantar min da hankali. "Marwa." Na faɗa cikin sanyin murya. "Umma ina kwana." Nan muka gaisa na tambayi Yaya Aina da babanta ta ce duk suna lafiya. "Umma kin ji ni shuru ban dawo ba ko? Kafin na amsa mata ta cigaba da faɗin" Yau ne na je asibitin da zan yi pratical ne zaa kai report. Zan zo anjuma in sha Allahu." Sai na amsa mata  da toh kafin na ce" Allah ya sa ba kaya kika zo ɗauka ba? Tana dariya ta ce" Sai dai na zo Umma." Na ce Allah ya kawo ta lafiya sannan muka yi sallama. A cikin raina na ke jin da gaske yanzu zan so ɗaukan Marwa ta dawo hannuna ina bukatar wani a gefe tunda yanzu Yallaɓai ya zama namu ba nawa ba. Ban taɓa tunanin zan samu jarumtar iya faɗa ma wani Yallaɓai ya ƙara aure ba. Amma sai da na yi wani tunani sai na ga gwara ni a fara ji a bakina ina da tabbacin in na bari Ma'u ta yaɗa mganar nan kamar gazawata ce shi ya sa da hanzari na shiga group ɗin gidanmu na yi mgana. "Assalamu Alaikum fatan mun tashi lafiya? Ya iyalai ya yarorin mu? Daman zan sanar da ku jiya an ɗaura ma Yallaɓai aure da yar'uwan sa Gimbiya(Saudatu) a garin Rano." Na yi rubutu ya fi sau biyar ina gogewa kafin na yi dauriyan turawa ina gama turawa ya yi tickig ya ta fi na yi saurin kashe data na koma na jingina da jikin kujera ina maida numfashi.   Mintina goma tsakani kawai na ji wayata da ke hannuna ta na vibration ina dubawa sai na ga Yaya Balki amma har ta katse ban ɗauka ba ta na katsewa kiran Rahila na shigo min itama nata na gamawa sai na ga na Amina. Mirmishi kawai na yi na san suna so su ce min ne da gaske ne Sadiya? Da gaske ne Sadiya? Nima tambayar da na ke yi ma kaina kenan shin wai da gaske ne Yallaɓai ya ƙara aure Sadiya? Amma har yanzu na kasa samun zuciyar da za ta ƙaryata wannan auran na Yallaɓai. Wai daman haka kishi ya ke! In ko haka ya ke to tabbas Kishi ya na da ɗaci sannan na yi imani ga Allah ko ɗacin rashin wani makusancinka bai kai kishi ɗaci da maƙaƙi ba Na daɗe ina kwatanta yanayin zafin shi. A yadda na ke kwatatanshi ban taɓa hasso shi a yadda na ji sa ba. Tabbas kishi kummallon mata na ƙara jinjina ma duk wata mace da a ka yi mata kishiya saboda ƙishi akwai zafi akwai ƙuna akwai ɗaci da radaɗi. Raɗaɗin da in ba akan ka ya faru ba labari ba zai iya gamsar da kai ba. *Janafty* *04 Wed. December 2025* *TKD* 02. Haka suka yi ta kirana amma na kasa iya jarumtar ɗaukar wayarsu. Sai na ke jin kamar da na amsa wayarsu suka fara jefemin tambaya da cewa shin da gaske ne Yallaɓai ne ya ƙara aure ? Na tabbata rauni ne zai zo ya yi min rumfa ɗan jarumta da na samu ya ƙwace min na saka kuka shi ya sa na kasa iya ɗaga wayar ko ɗaya daga cikin su. Yaya Balki sau biyu ta kirani Rahila ce wajen sau huɗu da ta ga ban ɗauka ba sai ta haƙura amma ban da Amina da saboda na cin kiranta sai da na ɗaga wayarta. Tun kafin na yi mgana na ji karaɗinta a cikin kunnina sai da na runtse ido. "Ya Sadiya wai wani Yallaɓan kike nufi ya ƙara aure? Haka ta faɗa cikin sauri kamar ta na jira. Daman na san za a rina wai an saci zanin makauciya. Mirmishin yaƙe na yi kamar ta na gabana Amina ce ƴar'uwan da muka haɗa uwa ɗaya ita ce zan je gidanta na kwanta mata ina kuka ta lallasheni amma sai dai kash ta yi min nisa. "Wai dai Yallaɓan na ki babansu Jidda kike nufin jiya aka ɗaura ma aure? Haka ta sake faɗa jin na yi shuru. Cikin sanyin murya na ce" Shi fa Amina. Ai yanzu Yallaɓai ya zama namu mu biyu, ya tashi daga Yallaɓai na ni kaɗai" Na ƙarishe faɗa kamar zan fashe da kuka domin ina mganar ina jin wannan abun da ya tokaremin a kirjina ya na motsawa ina jin wani irin zafi a ƙasan zuciyata zafin da a kan jin in an yi maka wani gagarumin rashi mai zafi ko ka rasa wani abu naka mai muhimmaci. To irin wannan zafin da raɗaɗin na ke ji ya na taso min daga ƙasan zuciyata. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un na shiga uku ni Amina Yallaɓai dai ya ƙara aure Ya Sadiya" "E." Na bata amsa a takaice jin ta ƙara jero wani salatin ya sa na yi saurin cewa" Ke miye na wani salati! Shirka ne? Umarnin Allah ne fa." Daga can bangaren Amina ta sauke numfashi har ina jin hucin sa daga cikin wayar cikin ƙaramin sauti da wani abu a muryanta ta ce" Uhm ni mamaki ne ya ishe ni. Wallahi na kasa yarda" "Uhmm." Na samu kaina da cewa kawai. Nima ɗin in zan ji kamar karya ne sai kuma na ji wani shashi na zuciyata na gasgata lamarin. "To wai ya aka yi ne aure kwatsam ba sanarwa? Sai kawai mu ji an riga an ɗaura aure Ya Sadiya.? Takaici ya ƙara kamani sai kawai na gyaɗa kai kamar tana ganina kafin na ce" E nima kwatsam na ji Amina." "Kai jama'a har yanzu na kasa yarda Ya Sadiya." "Ki yarda Amina. Da gaske ne Yallaɓai kam ya ƙara aure." Sai ta yi shuru nima sai na yi shuru kafin can ta ce" Allah ya kyauta. To wacece ya aura ɗin? "Ƴar'uwansa ne. Ɗiyar marigayi Tafidan Rano ne. Mijinta ya rasu wattanin baya." Amina ta jinjina kafin ta yi fatan alheri daga karshe ta ce" Ki yi hakuri ya Sadiya ki kauda kai. Na tabbata duk wacce Yallaɓai zai auro wallahi a bayan ki ne." Uhm kawai na ce ban yi mgana ba. To wani baya kuma, ai an gama mgana tunda an raba mijin gabaɗaya shike nan kuma. Muna cikin waya Rahila na ta ƙara kirana ina katse na Amina na ɗauki wayarta itama tambayar ta farko shi ne wai wani Yallaɓan ne ya ƙara aure? Kai tsaye na ce mata" Wani Yallaɓan kika sani? Abban su Jidda ba." "Kai Sadiya fa." Sai kawai na yi mata dariya kafin na ce" Wai me ya sa kuke tamtama?wallahi tallahi da gaske na ke yi." Rahila ta jim kafin ta ce" Danƙari! Aure kuma bagatatan Sadiya? Yar wacece a Rano ya aura? Itama bayanin Gimbiya na yi mata da sauri ta ce" Gimbiya? Haba na gane ta ita ce ya aura ɗin? Sai na ɗaga mata kai kamar tana ganina fatan alheri ta yi kafin ta ce" Sadiya an shiga wata ƙwaryan sai kin ninka haƙurin ki. Duk da ta bangaren miji ba ni da haufi a kan ki in sha Allahu ba macen da za ta kama kafarki. Allah ya zaunar da ku lafiya." "Amin" Na amsa mata da Amin sai ta ce" Yaushe ne tariyan! Ko har an taren ne? Kai na fara girgizawa kafin na ce" A'a.." "To sai yaushe? "Ban sani ba Rahila." Haka na faɗa kai tsaye domin da gaske ɗin ban sani ba fahimtar yanayin da na ke ciki yasa ta yi min sallama kawai amma ni a muryanta sai na ji kamar tausayina ta ke yi. Tabbas ni abar tausayi ce domin ya kamata a riƙa sara ma duk wata macen da aka yo ma kishiya saboda zafin abin ba wanda zai iya kwatanta yanayin shi sai ya faru a kanka. Sannan duk macen da ta shanye ya ci a kira ta jaruma ko sarauniya kuma a yabe ta a jinjinta domin ta yi matukar namijin ƙoƙarin da ba kowa ne zai iya yi ba. Muna cikin waya da Yaya Balki ne Yallaɓai ya fito falon. Ganin shi ya sa sai na ce zan kirata zuwa anjuma a lokacin n nasiha kawai ta ke yi min tana nuna min na ƙara hakuri domin zan ci riban hakuri tunda ai ita an yi mata tana ta bani misali da kanta da ba ta da haƙki ga shi matar ma ta fita sun rabu da mijin kuma da ƴaƴa biyu a tsakaninsu. Kamar Yallabai ya fahimci wayar da na ke yi saboda sai da ya kalleni kafin ya ce" Wannan doguwar wayar fa? Ina mikewa na ce" Ya Balki ce muna wata mgana ne." "Ok. Na ga Tiolet ba ruwan zafi. Kin saka a heater ne.? Ban yi masa mgana ba na dai gyaɗa masa kai na yi wuce gaba ya biyo bayana a cikin tiolet ɗin daman na ke saka heater ɗin ni na je na jona masa sai ya ce na haɗa masa abin karya in ya yi wanka zai fita akwai mutanen da zai gani a office ne sai na amsa masa. Daga Tiolet na ja birki a kitchen ƙwai kawai na sake soya masa. Na kwasa na kai dining daman akwai ruwan tea a fulas sannan ga kayan tea ɗin da buredi. A niyyata na yi tafiyata falon yara na zauna amma sai na danne zuciyata na zauna a saman kujeran dining ina jiransa na tsawon lokaci ina zaune ne amma ina tunanin Mama. A raina na ce da uwata na raye yau da wajenta zan yini in sha kukana ta lallashe ni sai dai ina ba ta a raye. "Allah ya jadadda rahama a kabarin Mama da Hajiya." Na faɗa a fili ina jin ƙwalla na taruwa a ƙwarmin idanuwana sai dai na yi ƙoƙarin maida ƙwallar da ta taho min Ina nan zaune ƙamshin turaren Yallaɓai ya fara min maraba a ƙofifin hancina sai ga shi ya bayyana a cikin falon cikin shigar Shadda mai ruwan toka sabuwa ce sau ɗaya Yallaɓai ya taɓa sakata da wancan sallar azumin ya ɗinka ta ɗinki ba tazarce ba ne half jamba ce irin na matasan samarin zamani. A lokacin Yallaɓai masifa ya yi ta ma telan shi wai shi tazarce ya ce bai ce ya yi masa ƙaramar riga ba. Ni na yi ta tausan shi na ce ya yi haƙuri tunda an riga an ɗinka. Daƙyar ya haƙura amma bai ƙara saka kayan ba. Kuma kayan suna yi masa kyau matuƙa amma saboda ba haka ya so ɗinkin ba sai kayan su ka fita daga ranshi. Na sha ce masa ya saka kayan suna yi masa kyau sai ya ce min shi ba zai saka ba saboda ɗinkin su ɗan kama masa jiki shi dai kawai basu yi masa kyau ba. Da na gaji da yi masa magiyan ya saka nima sai na haƙura na ƙyaleshi har na manta da kayan a tunanina ma ya kyautar ne ashe suna nan sai yau ya ɗauko su ya saka saboda ya na ANGO.' "Ango.". Haka na maimaita a cikin raina ina jin kamar ƙirjina na ɗagowa saboda yanayin da na ke ciki. Kallonsa na ke yi da dukkan zuciyata. Haƙika duk macen da ta samun daman auren Yallaɓai ta gama dacewa domin shi ɗin mai kyau ne kuma ɗan gayu ne ɗan ƙwalisa da ya haɗa komai na matakin rayuwa. Ya yi min wani irin kyau a idona. Sai wata zuciyar ke faɗa min wannan adon duk ba na ki ba ne Sadiya tun yaushe kike son ya saka kayan yaƙi? Sai yau tun da zai je ya ga Gimbiya. Tuni na ji taɓon da ke zuciyata ya taso. na ma fara ganin hazo hazo ne saboda tuƙuƙin da ke muƙurƙusan zuciyata. Har gabana ya tako ya na wani tashin kamshi. Kafarsa na kallah sai na ga takalminsa da ya ke ji da shi a cikin jerin takalmansa ya saka sai na ɗago ina kallon hulan kansa itama mai tsadan ciki ne ya ɗauko ya saka. Lalle Yallaɓai kallonsa kawai na ke yi na ma kasa mgana ina ƙoƙarin danne abin da ke taso min daga ƙasan raina. "Kallon fa? Ya faɗa bayan ya ɗan buga min agogon hannun shi a saman kaina kaɗan. Sai na ƙara kallon shi a baya in Yallaɓai ya yi kwalliya ya yi kyau in zai fita har wani alfahari na ke yi amma yau kam sai na ga ina ganin duhun shi domin zuciyata na raya min ne wajen Gimbiya zai je kuma ina da tabbacin domin ita ya yi wannan gayun. "Ko na yi miki kyau ne Madam" Ya faɗa ya na mai miko min hannun shi lokaci ɗaya da agogon fatan da ke hannun shi. Na fahimci nufinshi kamar na ce ya je da shi sai Amaryansa Gimbiya ta ɗora masa sai kuma na fasa na saka hannu na karɓa ina saka masa lokaci ɗaya ina faɗin" Yau kuma kayan da ba a so ne aka saka? Na faɗa bayan na gama ɗaura masa agogon na mike ina ja masa kujeran zama. "Wallahi yau kawai na gansu ƙasan kaya. Na ɗauko su ne ban ma san za su shige ni ba ina ko sakawa sai na ga sun yi min kawai sai na bar su." Ya faɗa ya na mai zama a kan kujeran da na ja masa. "Uhmm." Na faɗa ina tura masa farantin ƙwai a gaban shi. Ruwan tea ɗin ma na zuba masa a wani Mug na tura masa gabanshi sannan na koma na zauna. "Kin siya wankan ne? Uhm! Ni fa kwata kwata kalamansa sun daina wani burgeni. Shi ya sa na yi masa ba kan,  ina kallonsa a ɗage bai sani ba ya fara karyawa ya na min hira sama sama ina amsa shi, sai da ya ce min ƙila gobe ya shiga kaduna. Sai kawai na gyaɗa kai kafin na ce" Allah ya kaimu." Ya amsa da Amin na ga alaman yau ya ɗan saki jikinsa ba kamar jiya ba. Ya na cikin karyawa na ji buga get na san Saude ne sai na mike na ce masa bari na je na buɗe ina jin Saude ce illau ko ita ce tare muka dawo falon ta rankwafa ta na gaishe da Yallaɓai ya amsa mata har ya na tambayan mamanta ta ce duk suna nan lafiya. "Sai yaushe za ku koma makaranta ne? Na faɗa ina komawa in da na tashi na zauna. "Ranar monday." Sai na gyaɗa kai ban yi magana ba ita kuma sai ta shige ciki ta bar ni da Yallaɓai ya na karyawa har sai da ya gama ana ta ma kiransa a waya ya ce min Musbahu ne, ni ya tura na koma bedroom na ɗauko masa key ɗin mota har ga Allah na so na duje ne na ki masa rakiya amma ya manne min dole na yi masa rakiya kamar yadda na saba amma na kasa iya ɗaga masa hannu kamar yadda na saba sai na ke ganin kamar in na ɗaga masa hannu na cucu kaina wata fa zai je gani? Watan ma wacce ya raba min kanshi da ita shi dai ya ɗaga min hannu na yi masa ya ƙe ya na fita da motar na shige ciki na rufo kofar, Ina jin sa ya rufe get ɗin sannan ya koma motarsa ya fice. Ina komawa cikin gida na ga Saude a kitchen ta fara haɗa wanke wanke kallonta na yi kafin na ce" Kin karya ne? Sai ta gyaɗa min kai ni kuma kawai sai na bi kofar da za ta maidani cikin bedroom ɗina wayata a hannuna ina faɗin" In dai kina jin yunwa akwai ruwan zafi ki sha tea kin ji ko? Sai ta gyaɗa min kai ni kuma na wuce ɗaki na koma kawai na kwanta waya a hannuna na kasa buɗe data saboda ba na son na ga wani abu da zai ɓata min rai shi yasa na ƙi taɓa wayar ma. Ina nan kwance a kan gado ina ta faman juye juye daga kudu zuwa arewa. Gabaɗaya zuciyata ba daɗi har hasaso Yallaɓai na ke yi ya na can shi da Gimbiya suna hira suna dariya. Kai kishi bala'i ne na kasa sukuni kamar zan haukace fa, in na runtse ido Yallabai na ke gani da Gimbiya sheɗan su kawai ya ke nuna min gabaɗaya na kasa sukuni kamar zan mutu haka na ji saboda zafin da zuciyata ke yi, ina cikin wannan halin Marwa ta zo zuwanta ne ya tsamo ni daga haukacewa na fara sumbatu saboda kishi. Marwa ta daɗe ita ta yi mini girki sai mangariba ta tafi Saude daman tun wajen azahar bayan ta gama aikinta ta tafi. Itama na ɗibar mata cake da yawa na ce ta je gida su ci da ƙannenta. Na yi na yi Marwa ta kwana ta ce min ba ta tambayi Babanta ba na ce zan kira waya ta ce a'a za ta dawo gobe in ta zo ɗaukan kayanta. Ina hararanta na ce" Marwa tawaye za ki yi min? Ta na dariya ta ce" Umma can gida ya fi kusa da asibitin da zan yi pratical ne amma zan dinga zuwa Allah kuwa." "Ki dawo nan mana sai Yallaɓai ya rika kai ki in zai fita office." Sai da na faɗa sai kuma na kwaɓi kaina daga jiya Yallabai ya tashi daga wannan wanda na sani yanzu namu ne ni da wata ba ni da wannan ikon a kan shi kamar baya. Hakanan na ba ta 1k muka yi sallama na ce ta gaida Ya Aina. Sannan na ɗibar mata na ta cake ɗin har da kazan jiya na ce na Anniversy ne. Ni daman kazan ko a bakina saboda gani na ke yi kamar kazar angwancin Yallaɓai ne  saboda ya ƙure ni. Sauran na bar ma su Jidda amma ni na haramta ma kaina cin kazan nan. Bayan tafiyarta na idar da sallar mangariba Ya Ainan ma ta kira wayata ta na faɗa min Ya Balki ta gaya mata wani labari wai Babansu jidda ya kara aure sai na tabbatar mata ita kanta ta jinjina har sai da ta ce min" Sadiya kishi akwai zafi sai kin daure." A raina na ce" Tabbas kishi akwai ɗaci ba ma zafi ba." "Yaushe ne tarewar? A ina za ta zauna ita matar Balki ta ce min wai  yar nan Rano ce ko? Sai na amsa mata kafin na ce" Ban san in da za ta zauna ba." "Ko nan gidan zai haɗe ku? A firgice na ce" Wani gidan Ya Aina? Ganin yadda na zabura ne ya sa ta yi dariya kafin ta ce" Nam ma Sadiya." Yaƙe na yi kafin na ce" Danƙari. Ai shi kan shi Yallabai ya san a nan gida ba Vacancy ɗin wata mace bayan ni ba ma zai fara ba." Yaya Aina na ta min dariya kafin mu yi sallama ta ce ina Marwa ko nan za ta kwana sai na ce ta taho ai tana hanya ma, daga nan muka yi sallama duk da ba na so haka nan na buɗe data saƙonni wasu na ture wasu. Ban duba na group ɗin mu ba domin na ga mgana har 50+ sai Ma'u da ta yi min mgana ta Pc ne ya ɗau hankalina da sauri na shiga na ga mgana ta yi a takaice. "Uhm Sadiya kenan. kin san ko za ki yi ma wasu wayau ban da ni ko? Haka kawai ta rubuta, na karanta na fita saboda ba ni da ta cewa sai wata lamba da ta min mgana ina shiga na ga an ce. "Sadiya Shema'u ce ashe kuma Yallaɓai an yi tsiyar irin ta su ta maza." Da uban emojin dariya kamar abin dariya ne ya faru wani malolon abu ya ƙara tokaremin zuciya daman ai ya na tokaren tasowa ya ke yi lokaci bayan lokaci in na tuna da abin. Da kamar zan yi mata banza sai kuma na fasa a raina na ce in na yi mata shuru za su ce sun yi nasara a kaina ni kuma in sha Allahu Nasaran ce a kaina ba zan taɓa bari su yi ba. Kawai sai na shiga na ba ta amsa dai dai da kalamanta. "Tsiyar me? Umarnin Allah ne fa kike kiran shi da tsiya kuma na gode ma Allah ni ya fara sani kafin wata ko banza ina da wannan darajan. Sannan da ka je ka iske ai gwara kai a kawo maka ya fi daraja." Daga ita har Ma'un na yi ma mganar a dunƙule ina kuma gamawa na yi blooking ɗin ta ba na son wata damuwa ta barni na ji da abin da ya ishe ni ma na shiga group na mu na gida ina ganin suna ta fatan alheri amma na kasa amsa su. Ya Murja dai sai da ta taɓa halin wai topha Yallaɓai dai ya ƙara aure? Ya Hamza ne ya yi mata mgana da cewa haramun ne! Ku fa mata kuna da matsala. Ma'u ta karanta saƙona amma ba ta yi mgana ba ina tunanin ba ta tsammaci haka daga gare ni ba ne. Ta so na yi ta hauka ita kuma ta samu abin yamaɗiɗi da ni a duniya to da ikon Allah sai dai sharrinta ya koma kanta in sha Allahu. Muniira ta sake turamin wani saƙo da ya ɓata min rai. "Kin tabbata kina lafiya ta Yallaɓai? Ta sani amma ta kasa faɗa min in da gasken ne ban ji labari haka daga su har Yallaɓai za su yi ta raina min wayau a fakaice. "Ban sani ba." Amsar da na maida mata kenan daga nan na rufe data na koma kawai na yi tagumi ina ganin lamarin kamar gaske kamar mafarki. Har to sai yaushe ne Yallaɓai zai gama wasa da hankalina ya faɗa min! ? Na ga kamar ba shi da niyya sai dai zan jira shi har zuwa tsawon lokacin da zai ta raina ma kansa wayau in da a baya ne kafin ya dawo ma yi waya sama da sau uku amma yanzu in na ma tuna shi raina sai ya ɓaci domin na daina tunashi shi kaɗai na koma in na tunanoshi sai tunanin Gimbiya ya gilmamin daga nan kuma sai na ji gabaɗaya Yallaɓan ya fita kaina gabaɗaya.    Bayan Sallar isha'i ina falo tare da yara bayan mun idar da salla wayar na hannun Baby ta na game kiran shi ya shigo sai ta wakilceni kafin ma ta kawo min sai ta ɗauka suka yi mgana ina ji kamar ya na tambayana ne sai ta ce gani can zaune ganin ta taso zuwa wajena ya sa na rarumo carbin da ke gefena na riƙe daman ina kan sallaya ne a lokacin ta na zuwa ta miƙo min wayar ta na faɗin. " Umma Abba ya ce a ba ki." Dai na gyaɗa kaina kafin na ɗaga carbin ina gyaran murya Uhm! uhm! Alamun ina uzuri ita kuma ba ta gane ba ta na ta ƙoƙarin kara min wayar a kunne Jidda da ke kan littafanta na makaranta na ture da kafata ita ta taso ta karbe wayar na ji tana faɗa masa Umma na jan casbaha ne Abba ban san me ya ce mata ta ce sai ya dawo sai da ya kashe wayar sannan ta kalleni ta na faɗin" Umma Abba ya ce a shigo da buredi ne? "Duba in da saura mu gani." Sai na ga ta kalleni bayan ta ga na yi mgana da sauri na ce" Na idar ne." Sai ta wuce zuwa kitchen ta duba ta dawo ta ce saura guda ɗaya ina daga zaunen na ce ta kira shi ta faɗa masa har da siga ma ya siyo mana ta mu wacce ta rage ta yi ƙasa da ya ke ta san password din wayar ta buɗe ta kira shi ta faɗa masa ya ce to zai taho da shi haka Jidda ta faɗa min bayan sun gama wayar sai na gyaɗa mata kaina. Ina nan zaune Baby ta kunna cartoon jifa jifa ina kalla sannan wani bangaren kuma ina can ina tunani. Sai da Jidda ta gama aikin makaranta sannan ta kwashe jakarta ta maida ɗaki bayan ta dawo falon na ce ta sako musu abinci akwai kaza a fridge ta ɗauko ta ta ɗumama su ci ta amsa da to bayan ta ɗumama kazan ta ɗibo abincin taliya ce jalop mai kifi tun wanda Marwa ta yi ne suka yi min ta yi na ce ba yanzu zan ci ba. Gabaɗaya na rasa ɗanɗanon bakina tun yinin yau daga ruwan tea na safe sai ruwa kawai na ke sha na kasa cin komai. Jna ji Jidda na ce min" Umma shima Abba taliya zai ci? Sai na kalleta yarinyar nan da iyayin tsiya wato har ta san babanta ba ya son cin taliya. A raina ko na ce ita zai ci in ya ga dama in kuma ya tsaya gidan amaryansa ya ƙoshi shike nan a fili kuma ban ta amsar ta ba shurun da na yi kawai ai ya faɗa mata E ne ita zai ci domin ni ba zan ƙara yin masa wani girki ba bala'in haushin shi na ke ji wallahi na rasa yadda zan yi da raina. Saboda ma kar ya dawo ina falon ya tare ni da mgana na ce musu zan je na kwanta Jidda ta kalleni kamar za ta yi mgana sai kuma ta fasa ina lura da ita sarai na san a ranta za ta ga abin da ba ta saba gani ba ne. Yallaɓai ko ƙarfe nawa zai kai bai dawo ba sai na jira ya dawo zan kwanta amma yau ɗin nan sai na ga in ma na tsaya jiransa ni ce sakara saboda ai wajen Amaryansa zai biya sai ya gama zamansa sannan ya dawo sai ni kuma da ban san ciwon kaina ba sai na zauna ina jiransa ai ko ya yi kaɗan. Shigewata ɗaki na yi, na yi shirin barci na koma na kwanta ina juye juye marata ce ta ɗan fara min ciwo ya sa ma na tashi na je kitchen na zuba ruwan lipto na sha saboda marata ta ɗaure ban tsammaci zuwan al'ada ba saboda ni family planing ya gama lalatamin al'ada ba na iya gane zuwansa sai dai kawai duk lokacin da ya ga dama ya ke zuwa wannan ciwon maran daman ina fama dashi lokaci bayan lokaci. Ɗaki na koma na kwanta kuma cikin ikon Allah sai ya lafamin, barci ne a idanuwana saboda akwai bashin sa a kaina a cikin raina na riƙa addu'ar Allah ya sa barci mai nauyi ya sace ni Allah ko ya amsa addu'ata barcin da na yi mai nauyi ne domin har dawowar Yallaɓai ban sani ba sai dai muka haɗu da asuba shi ne ya ke ce min ya dawo ya ga ina ta barci ya na fatan lafiya? A yatsine na ce masa marata ce ta ke ciwo a jiyan sai na sha mgani na kwanta. "Ayya Sorry.." Kaina na gyaɗa masa lokacin ya ɗauro alwala ne ya na saka riga ni kuma tashina kenan na fita zuwa Tiolet na duba Al'ada bai zo miin ba sai kawai na kama ruwa na ɗauro alwala sanda na fito baya nan ya fita masallaci sai da na yi raka'atul fajir sannan na gabatar da sallar asuba. Ko da na fita zuwa ɗakin su Jidda har sun tashi ina jin Yallaɓai ne kafin ya fita masallaci ya tashe su barci ne a idona suna cewa karatu na ce Jidda ta yi ma Baby su karanta azkar zan je na kwanta kuma ina komawa ɗaki na kwanta ga casbaha a hannuna sai barci kuma ya sake ɗaukana ban farka ba sai wajen tara saura na safe har su Jidda sun tafi makaranta Yallaɓai kuma na can falo yana aiki a kan system ɗin sa. Ina ganin haka sai kawai na fara yin wanka na shirya cikin riga da wando. Sai na leka kitchen ɗin na ga sun soya dankali da buredi da ƙwai, saboda kar in koma can falo mu haɗu da Yallabai ya sa na sake dafa wani ruwan tea lipto ne kawai da gnyen shayi ko siga ban saka ba na ɗibi dankalin anan kuma kitchen ɗin na zauna na ci kaɗan ba da yawa ba, ina tunanin ko Yallaɓai ya karya ko bai karya ba? Amma kuma na kasa zuwa falon na ga ni ko hakan ta faru ina wanke hannuna na koma tiolet na kuskure bakina sai na sake komawa bedroom ɗin mu na shige bargo ina jin sanyi sanyi na shigana kamar zazzaɓi zai kamani. Ina nan kwance sai ga Yallaɓai ya shigo ya riga ya kamani idanuwana biyu ba zan iya masa alaye da na saba masa kwana biyun nan ba. "Ina kwana." Na faɗa daga kwancen da na ke, sai da ya sauke kayan a hannunsa a saman dirowan gado sannan ya tako har gabana ya duka ya sumabci goshina lokaci ɗaya yana faɗin" Yaushe muka fara irin wannan gaisuwar Sadiya ta? Kallonsa na yi ba tare da na yi mgana ba sai na ga kawai ya ware min hannuwana alamun na taso wallahi wani turriri na ke ji a ƙasan raina ina tunanin yanzu fa yadda ya ke yi min nan tuni ya fara yi ma Gimbiya ko? Idanuwana suka ƙanƙance da kishi ina shirin na ce ni ya ƙyaleni ina jin barci ban samu dama ba ko ya fahimci niyyata ne ya sa kawai ya sunkuyo ya ɗago ni zaune yana faɗin"Oya ta so nan." Ba yadda na iya haka nan na miƙe a kasalance na faɗa jikinsa ya ƙamƙame na wani lokaci ya na sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Kwana biyu nan duk an daina min kirki Sadiya ta. Ko na yi miki laifin ne? A raina na ce babban laifi ma kuwa sai dai ban ce ba sai da na fara ture sa sannan ya sake ni ya na kallona hancina ya lakace kafin ya ce" Kwana biyu ba mu yi ɓarnan ruwa ba ko? Kafin na yi wani yunƙuro ya haɗo haɓata ya haɗe bakim mu waje ɗaya ban taɓa sanin akwai ranar da za ta zo Yallaɓai na taɓa ni ina jin ƙuna a cikin raina ba domin sheɗan ne ke haskomin su tare da Gimbiya ya na yi mata kwatankwacin irin abin da ya ke yi min tuni na ji wani ƙarfi ya shige ni da hannu na saka iya karfina na ture Yallaɓai baya ina mai ƙwace kaina daga gare shi. Cikin mamakin da na gani a saman fuskarsa ya kalleni. "Me kika yi hakan? Ya faɗa a ɗan zafafe amma cikin sanyin murya kai tsaye ina goge bakina kamar ya saka min cuta na ce" Ka ga Yallaɓai please." "Please mene? Ya katseni da sauri ya na kallona kirjinsa na ɗagawa sama da ƙasa alamun ranshi ya fara ɓaci. Ina yarfa hannu na ce" Ka ƙyaleni kwana biyu nan am not in the mood." Ina gama faɗin haka na koma kan gado na kwanta ina jan bargo kenan na ji ya fizge da karfi ya cilla dashi a kasa da gajiya a cikin idanuwana na kalle shi kafin na ce" Na ce ka yi hakuri ka ƙyale ni ko? Ban jin daɗi ne." "Ƙarya kike yi Sadiya." Ya faɗa ya na kallona sai na ware ido cikin mamaki ina kallonsa sai kawai ya yi wani mirmishi kafin ya ce" Kin ɗauka ban lura dake kwana biyu nan ba. Sam ba ki son ina taba ki in kuma na kusanto in da kike a fuskarki kike nuna ba ki son hakan sai na ɗaga miki kafa ina tunanin fushin da kike yi a kaina ne ba ki sauka ba! Amma Sadiya ji fa abin da kika yi yau ni ne na zo gare ki kika ture ni? Ture ni fa kika yi to me kike nufi? Ya ƙarishe faɗa a fusace kaina kawai na dafe saboda ni ba na son damuwa. "Na yi miki laifi ranar Anniversary ɗin mu na yi dare ban dawo ba. Yes na ji kuma na karɓi laifina sau nawa zan ce ki yi hakuri Sadiya? Ni kawai tsayawa na yi ina kallon ikon Allah don kawai ya ga ban buɗe baki na yi mgana ba shi ne zai wani tsaya a kaina ya na min masifa.   "Ki ba ni amsata ina miki mgana me hakan da kika yi ya ke nufi? Ya faɗa a fusace har ya na daka min tsawa na kai makura na ga ba zan iya ɗauka ba a fusace na sauko daga kan gado ina ƙokarin barin masa ɗakin da zafi ya riko ni ya yo baya da ni har ya na yaga min hannun rigar jikina saboda da ƙarfi ya jawo ni ta baya. "Kar ki sake ina mgana da ke kina barina a wajen zan saɓa miki Sadiya." Na ƙanƙance idanuwana ina kallonsa kafin na ce" Ni me zan ce? Na ce ka yi hakuri wannan faɗan ne kuma ban san dalilin shi ba" "Amsa tambaya za ki ba ni malama" Ido cikin ido yake kallona sai na fahimci ranshi ya ɓaci ya na ta sakin huci ni ko domin na ƙara kunsa masa takaici sai na ce" Me ka ke son sani? "Abin da kika yi yanzu? Me hakan ya ke nufi? Ya faɗa ya na wani taso min sai na ja baya ina faɗin" Me kuwa? Ni ba na nufin komai" "Na yi miki wani laifi ne bayan laifin ranar? Kawai saboda ya ga na yi shuru. Lalle nema Yallaɓai nima ko ina kallonsa na ce" Laifi! Sai ka tambayi kanka Yallaɓai." Na faɗa ina ƙoƙarin wucewa wannan karon da karfi ya jawo hannuna ya tamke har sai da na ji zafi ina kallon shi cikin mamaki kafin na samu zarafin mgana ya ce da ƙarfi" Ina tambayarki kina tambaya na Sadiya? Ihu Yallaɓai ke yi min a saman kaina saboda ina guje ma ɓacin raina kar nima na haukace masa. "Me na yi miki kike ba ni wasu attitude da ban gane musu ba ne? Ko akwai wani abu a zuciyan ki ne! Ki fada min na ji.!" Yadda yaƙarishe tsawan ne har ya na neman ɓallamin hannu ya sa a fusace na make hannunshi nima cikin ihu na ce" Sakar ni. Ban sani ba. " Na faɗa nima cikin hargowa ina mai ɓalla masa harara idanuwana har sun kaɗa sun yi jajir Wucewa na yi ina faɗin" Na ce ka yi haƙuri ka kyaleni amma ka ƙi so ka ke yi raina ya ɓaci na haukace maka? "To ki haukace mana. Ina dai dai da ke." Ya faɗa ya na wani sakin tsaki Yallaɓai na kallah wannan abun na ƙirjina na taso min har wani duhu duhu na ke gani wato wannan shi ne halin maza in sun ƙara aure yau wai ni Yallaɓai ke faɗa ma ya na dai dai da ni. Kallon shi na yi idanuwana sun cika da kwalla sai kawai na nuna kaina cikin sanyin murya ina faɗin" Yau ni ce Yallaɓai ka ke faɗin kana dai dai da ni ko? Sai na ga jikinsa ya yi sanyi saboda ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" To ya kike so na yi miki Sadiya. To taho ki ji." Ya faɗa ya na tahowa wajena da sauri na ɗaga masa hannu sai ya dakata kafin na kalleshi na jinjina kai ina faɗin" Ka guji haukacewan tawa domin na rantse da Allah kai ba za ka iya da ni ba sai ka yi gayya " Ina gama faɗin haka na fice daga ɗakin na bar shi nan. Ina jin kuka na taso min ɗakin su Jidda na shige na faɗa saman gadon Baby sai na ji kawai na fashe da kuka, sanin Yallaɓai zai iya biyo ni ya sa na tashi na rufe ƙofa ilai ya zo ya na ta kiran sunana na yi masa banza sai yau na samu damar yin kuka wato har na fara fuskantar wulakanci daga wajensa saboda ya ƙara aure ina kuka mai sauti amma kuma zafin da ke zuciyata ba ya raguwa sai ma ƙaruwa. Yallaɓai ya yi ta bugun kofa ban bude ba sai can kuma ya dawo ina jin sa ya na faɗin. "Sadiya ki yi hakuri raina ne ya ɓaci. Na shirya zan je kaduna in na dawo yau in sha Allahu za mu yi mgana" Ina jinsa ya gama mganganunsa ya fice ya bar gidan Ranar Saude ban san abin da ya hanata zuwa ba ni kuma kwance na yini ɗakin su Jidda salla kawai ke ta da ni ban komai ba hatta girki da suka dawo ne na ce Jidda ta dafa musu indomie ni kuma sai na sha ruwan zafi saboda cikina ya tanmke ga marata na matsannancin ciwo. Su kansu yaran sun san yau ba kanta Jidda ta ce" Umma ba ki da lafiya ne? Sai na amsa mata sannu ta yi min, yadda na yini kwance haka ma har dare ina kwance can bayan isha'i al'ada ta zo min sai na tashi na sake wanka na gyara jikina ranar ma da wuri na kwanta su Jidda ma na saka su barcin wuri. Wayata ko a yinin ranar ma kashe ta na yi saboda ba na so damu na fi son a bar ni na gama ji da abin da ke damuna wannan duka dukan da Yallaɓai ya yi mini ba. Ban ɗauka a daran ya dawo ba sai farkawa na yi cikin dare na ganshi kwance kusa da ni. Da safe kuma na dai gaishe shi na addinin da ya ce mace ta gaida mijinta ya amsa a daƙushe shima, muryata ta shaƙe da safe tunda kukan da na yi ta yi jiya ya saka min mura mai zai shi ne ma ya yi min mgana. "Sannu Mura kike yi? Ya faɗa lokacin da ya dawo daga kai su Jidda makaranta an saka su wata tahfiz can gaba damu kaɗan asabar da lahadi. Salisu na gida ba ya jin daɗi. Ya ji ni ina ta attishawa ne sai ya yi min sannu na amsa kuma shi da kanshi ya je ya dafo min shayin citta ya kawo min na sha sai na ɗan samu sauki sannan ya duba cikin box ɗin mu na mganguna ya samo min mganin mura ya ba ni na sha sai ya ce na kwanta na huta har yana gyara min kwanciya ya na rufamin bargo da ya ke kuma mganin kamar ya na saka barci sai barci ya ɗauke ni sai wajen sha ɗaya na farka na tashi ina mutsike ido wayata na kunna na ga 11 na safe ta gota gashi yau ɗin asabar. A kasalance na sauko daga kan gado ina hamma tiolet na shiga na kama ruwa yunwa na ji ina ji sai na tafi kitchen sai na ga Yallaɓai ya soya doya ya rage min ita na diɓa zuwa falon yara daga nan na ke jin tashin muryoyi kamar ba ta Yallaɓai shi kaɗai ba sai da na gama cin doya na kora da ruwan shayi sannan na kai kofin da filet kitchen ni kaina wajen duk ya yi min kazanta jiya Saude ba ta zo ba ni kuma ban yi ba. Bedroom na koma na sako hijabi da takalmi na yi sallama a falon Yallaɓai suka amsa min sannan na tura ƙofa na shiga. "Uncle Abba kai ne tafe ba labari." Na faɗa ina karisowa cikin falo, lokaci ɗaya ina ɗan tari kaɗan. "E. Na shigo duba wani fili sai na kira Yallaban ki ya ce yana gida na ƙariso. Ina zuwa ke na fara tambaya ya ce ba ki jin daɗi kin kwanta " Ina zama saman kujera mai zaman mutum ɗaya na ce" E wallahi sannu da zuwa." Na faɗa ina kallon Yallaɓai ta gefen ido ya na zaune a gefen Kawun na shi ya duƙar da kai ƙasa. "Sannu ya muran to? Sai na ce da sauƙi ina tambayan ya mutanen gida.  Mu ɗan yi hira saboda ni dai muna shiri da shi kuma har muka gama Yallaɓai bai saka mana baki ba, ban daɗe ba na tashi na koma falon su Jidda. Daga Yallaɓai har Uncle Abba sun bi bayan Sadiya da kallo har ta fice kafin Yallaɓai ya sauke ajiyar zuciya ya na faɗin" Ka ga abin da na ke faɗa maka ko? Kwata kwata na kasa gane kanta." "To daman ina za ka gane kanta ka yi mata kishiya.".. Yallaɓai ya ce" Ai ba ta sani ba." "Ko? Uncle Abba ya faɗa ya na kallon Yusuf. Shi kuma sai ya gyaɗa kai kafin ya ce" Yes. Domin na roƙe su kar su faɗa mata sai ta faraji daga bakina." Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce" Ni kuma sai na ke tunanin kamar ta sani Tafida." Ido Yusuf ya saka masa kafin ya ce" Ta sani? To wa ya faɗa mata? Abba ya zaƙuda kaffaɗa kafin ya ce"oho amma ka yi tunanin me ka yi mata da ta sauya maka haka? Ni kaina na ga duk ta yi wani iri kamar ba Sadiya ba." Yusuf ya yi shuru ya na tunanin kai bai yarda ta sani ba in ta sani me ya sa ba ta yi masa mganar ba. Sai dai ya fi yarda ƙila ta na ji dai a jikinta domin an ce mata in za a yi musu abokiyar zama suna ji a jikinsu. "Ba ta sani ba gaskiya rigimarta ce kawai ta tashi." Ya faɗa cikin jadaddawa. "To sai ka sanar da ita da wuri kafin ta sani a wani wajen." Sai ya jinjina kai kafin ya ce" In sha Allahu. Daga nan suka cigaba da tattaunawa duk a kan ba tun dai. *Janafty* *TKG* 03. FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622 Ni ko ina barin falo ɗaki na koma na ɗau wayata na kunna na kira Saude sai balaraba ta ɗauka tana faɗa mini Saude ba ta da lafiya zazzaɓi ya rufe ta. Amma ta ji sauƙi, fatan samun lafiya na yi mata sai ta ce min ko ina buƙatar ganin ta ne? Ai sai ta rarrafo ta zo tunda ta ji sauƙi. Da sauri na ce" A'a ta bar shi kawai in ta ƙara jin sauƙi sai ta zo." Sai muka yi sallama bayan na ce ta haɗa ni da Sauden na yi mata sannu sai ta ce mini ta shiga makewayi mun rabu akan zan sake kiranta in sha Allahu. Ajiyar zuciya na sauke ina mai riƙe ƙuguna aikin da ke gabana kawai na ke hasashe jiya ba a gyara gidan ba ga wanke wanke mai yawa ba a yi ba in dai ba ina so a zo gidana a tafi da ni a baki a bangaren kazanta ba ne. Dole na sauke son jiki na gyara gidana wayata na ɗauka zuwa kitchen na kunna karatun Qur'ni cikin suratul Maryam saboda ina son suran sosai ta na yi mini daɗi. Kaye kaye na fara yi a kitchen ɗin saboda ina so na fara gyara shi bayan na gama sai in yi wanke wanke na goge kitchen ɗin a lokacin da Yallaɓai ya shigo ina kwashe dattin da ke cikin filet ɗin wajen sink ina zubawa a cikin leda na ji shigowarsa ni kuma ina ta bin karatun na yi kamar ban gan shi ba na gama tara dattin na ɗau ledan zan fitar can waje sai ya saka hanny ya karɓa ban tsaya masa jayayya ba na sakar masa na koma  ina goge saman dirowers ɗin kitchen ɗin da wani ƙaramin towel saboda ma kar ya zo ya dame ni har ƙure volume ɗin wayata na yi da karatun na ji buɗe kofarsa da dawowarsa na kuma ji a jikina ni ya ke ta kallo amma ban juya ba ina cigaba da aikina lokaci ɗaya ina bin karatuna ga shi na tsuke cikin riga da wando amma jeans ɗin mai ɓudewa ta kasa ne sai wata ƙaramar riga amma na saka wani ƙaramin hijabi wanda ba zai dame ni ba saboda baƙon da muke dashi. Ni ban ji lokacin da ya taho ba kawai jin kansa na yi ya ɗoramin a saman kafaɗata. Na ɗan tsaya haka sai kuma kawai na basar na cigaba da aikina kuma ban dakata da jin karatun ba, leƙa fuskata ya ke yi har ya na shafa mini kumatu saboda dai na kula shi amman ban yi ba. Domin ni Yallaɓai duk wani abu da zai yi ko zai ƙara yi ya daina burgeni tunda abin na shi duk munafunci ne, gani na yi yana saka yatsa ya na latsa min gefen cikina kamar ya na so ya yi min cakulkuli da sauri na ƙwace jikina ina kallon shi. Marairaicewa ya yi ya na min wani kallo wanda a da kallon nan ya ke rikitani amma yau wallahi ko kaɗan ban ji wani abu ba, sai ma na koma na cigaba da aikina lokaci ɗaya ina faɗin. "Karatun Qur'ani ne fa." Na faɗa ina cigaba da bin karatun, shi kuma sai ya ƙara biyoni sai ji na yi ya rumgume ni ta baya ya sagalo kansa ta tsakanin wuyana sannan hannayensa ya sargafe su ta cikina ya matse ni, kiss ya yi ta min a wuyana da gefen bakina amma na ki bashi wata dama kawai sai ya zura hannunsa ya ɗauko wayar dake gefena ya tsaida karatun na ɗago a zafafe zan masa masifa da sauri ya haɗe bakin mu waje ɗaya duk iya ƙokarina yau na kasa kwatan kaina domin ya yi min bake bake ne ya rufe ni ruf ɗin da na kasa ƙwatar kaina amma har ya yi kiɗan shi ya yi rawan shi ban yi ƙwaƙwaran motsi ba, yau sai na ji kwata kwata bakin Yallaɓai kamar miyansa ya koma mini maɗaci domin wata zuciyar na faɗa mini  ya yi ma Gimbiya irin wannan shi ne kema ya zo yana yi miki tuni na ji kamar zan yi amai, na kasa haɗiye miyan bakina a gaban shi ya na kallona na saka hannu ina goge bakina kamar ya shafa min wani cuta. Hannuna ya riƙe caraf ya na wani tsare ido. "Cuta na saka miki da kike goge bakin Sadiya? Sai na kalle shi, tunda ya aure na zama ba tashi ba sai dai ya rika kirana da sunana Sadiya kawai gatsal. Tun daga nan na san na fara ganin iskancin namiji tun kafin ma su tare su fara zaman auren. "Sorry mana. " Ya faɗa ya na riƙe duka hannayena cikin shagwaɓa har ya na wani karya wuya. Na yi masa banza ban yi mgana ba sai kawai ya sake ni ya riƙe duka kunnuwansa yana faɗin" Sorry. Haba mana Sadiya ta." Ya faɗa lokaci ɗaya ya na ƙara marairaicewa na kalle shi na ƙara kallon shi wai yau ni ce Yallaɓai ya kalla ya ce ya na dai dai da ni, to ai shi ne zan gani in zai iya da ni ganin ya hana ni aikina sai bina ya ke yi ya na min magiya dole na ce na haƙura sai ya rumgumeni ya na mai sumbatar goshina kafin ya sake ni ya kuma bi ni da kallo ya na faɗin" Za mu samu abin karyawa ni da kawun na ki? Ya dai ci darajan Uncle Abba da ba zan yi ba amma saboda darajan mai daraja sai na amsa da toh duk zamansa a kitchen ya ga ina aiki bai tambayi ina Saude har sai da ya fita sannan ya ƙara dawowa. "Ina Saude? Ba za ta zo ba ne" "Ba ta da lafiya." Amsar da na bashi a takauce kenan sai ya juya yana mai faɗin Allah ya ba ta lafiya da harara na rakashi har ya fice sannan na yi ƙaramin tsaki ina mamakin halin maza na ƙara yarda da aka ce ba su da kunya tun daga ranar farko kunyar abin da Yallaɓai ya aikata min ya fita daga jikinsa ya daina nuna tsoro ko kunya ya yi aure ban sani ba, ban san tunanin shi ba, shi a tunanin shi ban sani ba sai ranar da ya ga dama sai ya faɗa mini ƙila ma bayan Gimbiyan ta tare, Ma'u ta cuceni da halin da na shiga cikin kwanakin gwara ma ban ji mganar ba sai a lokacin da ya ga damar faɗa min ga shi ta dalilinta sauran farincikina a kwanakin da ya kamata na yi shi ta yi silan ruguzamin shi, ni kam ai tsakani da Ma'u sai Allah ya isa kuma da ikon Allah duk wani sharrinta sai ya koma kanta. Ina aikina ina tunane tunane baƙin ciki na kara samun muhalli a cikin raina. Dankali na fere na soya musu da kwai sai na sake dafa musu ruwan tea na kai musu Uncle Abba na ta yi mini sannu. A falon na bar su suna karyawa ni kuma na koma na cigaba da aikina sai da na gama wanke wanke sannan na yi sharan ɗakunan gabaɗaya na wanke Tiolet ɗin mu da na su Jidda duka kuma na yi mopping gidan amma ban da falon Yallaɓai kirchen na gyara shi na goge shi tas ban zauna ba sai da na ɗora girki gwara na yi hutun gabaɗaya. Shi ma girkin saboda Uncle Abba ne domin ya na gidan bai tafi ba har bayan azahar sannan suka fita tare da Yallaɓai bayan ya ce mini daga masallaci zai raka Uncle Abba anguwa ba su  suka dawo ba sai bayan La'asar lokacin har na yi wanka tun ɗazu abinci kuma tuni na daɗe da gamawa Jalop ɗin shinkafa da Nama ɗan sauran da ya rage mana na saka a ciki. Sai kuma daman na haɗa zoɓo har ma ya yi sanyi shi na cika wani jug ɗina da shi kuma sai da suka shanye shi, Sai wajajen Biyar Uncle Abba ya yi mana sallama ya tafi bayan ya ba ni 10k ya ce na yara ne na karɓa ina godiya tare suka fita da Yallaɓai bayan tafiyar su ne na gyara falon na tattara abin da suka ɓata zuwa kitchen falon su Jidda na koma na kunna Mbc bollywood sai wani indian film da suke yi series ya ɗau hankalina mai suna Habibi da'im da kuma gargaliyan Labarci su ke mgana to ina ɗan tsinta sosai film ɗin ya ja hankalina tuni na fahimci a dai dai wannan lokacin suke saka cigaba film din sau shidda a sati ban da jumma'a da asabar a raina na saka cewa zan dinga bin shi dramar ta ɗau hankalina. Ƙarfe bakwai a ka gama film ɗin sai na ga sun fara shima wani ban tsaya ba na tashi yin salla su jidda tun wajen shidda da kwata suka shigo gidan a kafa suke dawowa tun da makarantar ba nisa har sun sauya kaya sun ci abinci. Tare da su muka yi salla sannan na ce su ɗauko Qur'ani mu yi karatu muna cikin karatun ne wayata da ke kan kujeran da na tashi a kai ta fara neman ɗauki alamun ana kirana Baby ce ta yi saurin ta shi ta ɗauko min ta na faɗa min Abba ne, har za ta ɗauka na fizge wayar ina faɗin. '"Ko ba Abba ba."   Na faɗa ina balla mata harara da sauri takoma kusa da ƴar'uwanta ta zauna ta na wani fiki fiki da ido. Na yi mamakin ganin Anty Zabba na kira a cikin raina na gane dalilin kiran kawai sai na mike sanye da hijabin da na yi sallah Jidda na kallah kafin na ce" Ku cigaba kafin na dawo." Sai ta amsa min ni kuma sai na bi ta ƙofar kitchen zuwa cikin ɗakin mu na barci. Wayar ta katse lokacin da na kai zaune gefen gado amma cikin lokaci sai ga wani kiran na ta ya sake shigomin, sai na ɗauka ina mai dai dai ta yanayina. Gaisawa muka yi da tambayan iyalan juna kamar yadda muka saba. Sai kuma muka yi shuru na wani lokaci saboda gaskiya mu ba abokan mgana da juna ba ne sosai. "Jiya ina ta kiran wayar ki a kashe." Ita ta fara kauda shurun, sai na ce" E. Wallahi." Daga nan sai na yi shuru ina jin sautin mirmishinta kafin ta ce" Sadiya ya muka ji da wannan jarabawar rayuwar! Na ji shima Tafidan na ki an ƙaƙaba masa wata matar." Gimbiya ce ko? Ban yi mamaki saboda ni na san kowa ya sani a tunanin Yallaɓai ni ce kaɗai ban sani ba tunda bai sanar min ba. "E. A ina kika ji labari hala? Na tambaya sai ta ce min Jamila ta faɗa mata jiya suka yi waya suna cikin wayar ma sai ta katse ba ta ma karisa ba ta labarin ba, ina ga shi ya sa ba ta ji an ce a yi shuru kar na ji ba." "Sadiya akwai zafi na sani. Ni kaina har yau ban fita daga wannan zafin da Usman ya haddasa mini ba." "Uhmm." Kawai na iya cewa zafi ai ba ma sai an faɗa ba. Ita kuma sai ta cigaba da faɗin" Kishi fa gaskiya ne Sadiya sai wanda aka yi mawa ya ke sanin haƙikanin zafin abin. In ka nuna damuwa a ce ka ɗaga hankalinka wane wane Alhalin ba wanda ya san irin zafin da kake ji acikin zuciyarka." "Kwarai." Na bata amsa sai ta cigaba da fadin" Ki daure Sadiya akwai zafi amma ki daure. Dangin mazajen mu suna neman ganin gazawarmu ce shi ya sa, shi na wajena ya auri yarinyar ogansa shi kuma na wajen ki ya auri yaruwansa duka fa domin a kaimu ƙasa ne kuma Allah ya fi su, ki daure zafin zai ta ƙaruwa barin ma in sun fara zama tare amma ki yi ta addu'a da ikon Allah za ki samu komai da sauƙi kin ji ko? '"Na ji. Kuma in sha Allahu ba damuwa." Mun dade muna mgana ta na ta bani shawarwari sai a lokacin ta ke faɗa min ashe a lokacin mganar auran ya Usman da ta dawo gida ba yaji ta yi ba ta ce kawai ta zo gida ne ta samu kwanciyar hankali amma dangin miji suka buga mata tambarin ta yi yaji, ni kaina na sha mamaki na ce mata mu ma haka aka ce mana wai kin yi tashin hankali har da su yin yaji. "Uhm wallahi ni ban yi yaji ba. Da amincewarsa na taho gida Sadiya. Gwara mu yi nesa da juna sai na samu damar rage jin zafinsa domin a zauna lafiya. Ba gashi an yi ba kuma muna zaune gida ɗaya da ita ba sai dai tana bangarenta ina nawa, ni dai ina zaman musulunci da ita, itama haka amma ba zan yi zaman daɗi da kishiya ba Sadiya shima ai na faɗa masa matarsa ta yi rayuwarta nima na yi tawa ni da ƴaƴana." "Shi ne alheri ma." Domin ban ga amfanin haɗa kai da kishiya yanzu ba kai ya waye ban da mutanen da wa ke maida kishiya yar'uwa wallahi gazarwar ki ta ke nema in kuma ta samu sai  ta yaƙe ki. Anty Zabba ta yi ta bani wasu labarai ta na faɗa min na zama jaruma. Shawarar da za ta bani kar na ce zan bibiye ta na ɗauke kaina a kanta sai na zauna lafiya amma kar na sakar mata kar kuma na ƙi ba ta dama a yi zaman musulunci wanda ba zai wuce jaje ko taya murna ba, ta yi na ta rayuwar nima na yi tawa a hankali a hankali zafin zai gushe har wata rana ma sai na manta ina da kishiya. Ina dariya na ce. "Daman ana mantawa? Itama ta na dariyan ta ce" Sosai ma. Barin ma in ba gida ɗaya za ku zauna ba" Sai na ce mata ban sanin masa ba nan na ke faɗa mata ni fa har yau bai faɗa min ba amma na ji yana waya ashe shi ne ya roke su kar su faɗa,min har sai bayan shi ya faɗa mini da kansa. Cikin dariya ta ce" Ya yi miki irin na Ɗan"uwansa nima ai bai faɗa min da farko a gari na ji. Ni ko na yi irin taki ban nuna masa na sani ba." Nima ina cigaba da ba ta labarin a wajen wata yar uwata na ji labarin. Anty Zabba ta ce na yi jarumta na cigaba da bin shi a haka na ga iya gudun ruwan shi. Hira ta ɗauke mana hankali har sai da aka kira sallar isha'i sannan muka yi sallama sai na ji zafin da ke taso min a saman ƙirjina ya na raguwa samun wanda mu ka yi hira ƙwatakwancin mai damuwa ko na ce gyambo irin nawa. Muna gama wayar ban koma falo ba sai da na yi sallar isha'i sannan na koma falo wajen su Jidda sai na iske ma suna salla bayan sun idar nace Jidda ta ɗibo min abinci tun da ɗazu da rana ban ci ba. Da gaske ne na ji sauƙi sauƙi a cikin raina tunda har ban ma yi barci da wuri ba sai da na jira dawowan Yallabai wajen tara na dare, ina ta kallonsa ina tunanin daga wajen Gimbiya ya ke amma sai na yi saurin kauda wannan tunanin kamar yadda Anty Zabba ta ba ni shawara. Shi kan shi na san ya ga chanji. Domin ni da kaina na haɗo masa ruwan lipto ya sha bai ci abincin ba ya ce cikinsa ya cika mun zauna da yara muna kallo har goma na dare sannan na ce su je su kwanta saboda makaranta gobe, mu kuma sai wajen sha ɗaya muka shiga kwanciya domin Yallabai ne ya ce sai ya ƙarisa kallon wani american film ɗin da muka fara kallo a MBC ACTION. Saboda ya ga na ɗan sake masa ya na ta ba ni labari ashe tun fitan shi suna tare da Uncle Abba sai daren nan suka je ya gaida Nene shi ya kawo shi gida sannan ya wuce. Ina gyara gashin kaina na ce" Allah ya kai shi lafiya " Su Yallaɓai an samu fuska ya na tarawan jiki duk da har ga Allah ba na cikin Mood ɗin haka nan na bashi dama, kuma daman al'adata kwana biyu ya yi ya ɗauke ni da na ke yi kwana biyar a baya. Yau ban san da me zan kare kaina ba. shi kan shi ya ɗan ga chanji domin ban yi masa wani rawan jiki ba, kar dai ya ce na yi masa kamar gunki ne ya sa na ɗan motsa masa kaɗan  na ga mamaki a saman fuskarsa amma bai furta min ba ni kuma ban bashi damar mgana ba, domin niki niki na yi da raina ina ta faman sha masa kamshi. Da asuba ma da na ga take taken shi na son ƙarawa sai na yi masa barcin ƙarya dole ya ƙyaleni. Bayan su Jidda sun tafi makaranta ni da shi ne kaɗai a gida, Marwa ta zo kwasan sauran kayanta ita na samu ta yi min gyaran gida muna ta hira da ita tana ma gidan sai ga Saude na ce ba na ce ta zauna a gida ta warke ba sai ta ce min ai ta ji sauƙi. Su suka ɗeɓemin kewa domin Marwa ta yi min abincin rana sai wajen ukun rana suka tafi. Yallaɓai kuma daman tun safe ya ce min yau da yamma ko da daddare ya na so zai yi mgana da ni, ina jin haka a raina na ce daga baya kenan. Sai na ji kamar ba na son jin ma abin da zai gaya min saboda ba zai zama wani sabon abu a wajena ba. Har na saka ma kaina dangana na ce zan tsaya na saurare shi ko domin na ji abin da zai ce min. Sannan ina son na san ta in da aka haihu a ragaya, to eh mana domin har yau ban ji labarin yadda wannan auran bazatan ta ya faru ba, shin daman can an shirya sa ne ko yaya abin ya ke! Bai ba ni wannan amsar ba mutum ɗaya ne ko zuwa biyu ko Yallaɓai ko kuma ita kanta Gimbiyar.   Wajajen ƙarfe biyar da wani abu na yamma muna falo tare da Yallaɓai shi ya na aiki a saman system ɗin sa ni kuma ina kallo a Mbc bollywood domin na fahimci suna series masu kyau da ma'ana. Jefi jefi muna hira duk da ƙarfin hiran na bakin Yallaɓai ne ya na ba ni labarin aikin su na kaduna da irin alherin da ya ke fatan samu kallonsa kawai na ke yi, a baya ne in ya na faɗa min haka na ke jin daɗi amma yau sai na ji ko kaɗan ban wani damu ba, in zai lura ma ni ina ta taɓe masa baki ne labarin duk ya gundure to Allah na tuba yanzu ai komai ya samu ba nawa ba ne ni da ƴaƴana ba, namu ne har da ita kanta Gimbiyar wa yasanin ma ko da kuɗin ya ke saka ran yi mata hidima da kuɗin ma ya kawo min kishiya. Fitsari ya tashe shi nan tiolet ɗin falo ya shiga ya kama ruwa. Ya tashi kenan ba daɗewa wayarsa da ke gefensa a in da ya tashi ta fara haske kaamar tana silet ne ina zaune amma na kasa tashi domin na daina saka ido akan wayar Yallaɓai domin tsira da kwanciyar hankalina. Duk da ina ankare da shi ni dai tun bayan faruwan auran na su ban taɓa ganin sun yi waya ba kamar ta ɗan rage kiran shi a bisa baya. Wata zuciyar ta ce min ke Sadiya in suna wayar ma za ki sani ne! Balle ma suna gari ɗaya ai suna ma haɗuwa su yi abin da a waya ma ba za su iya ba. Tunanin haka kawai ya sa na yi tsaki mai karfi na tashi da niyyar na bar masa falon. Amma sai zuciya ta rinjaye na ƙarisa wajen wayar ina ganin tana cigaba da hasken alamun mai kiran ya kasa haƙura. "Daughter." Gabana ya faɗi ya yi wani raga raga, kirjina ya amsa dum! Har sai da na dafe ƙirjinan nawa saboda na ji nauyin da ya yi min na neman rinjiya na. Dai dai lokacin Yallaɓai ya fito daga tiiolet ya na daura mazugin wandon shaddan da ke jikinsa. "Sadiya ta a taimaka a wanke min tiolet ɗin mana." Duk ƙokarina da nuna jarumta yau na kasa, me ya sa ta ke kiran shi? Ba kullum suna tare ba! Don kawai yau bai fita ba ta ganshi ba shi ne sai ta kasa sukuni sai ta neme shi! Ƙila ya fara ɗanɗana mata daɗin shi ne ba za ta iya hakura da shi ba, ina jin tahowar Yallaɓai ya na mgana amma turiri na ke ji na fitowa daga zuciyata har ina jin zafin a cikin bakina.   "Kawai kin yi ma tiolet ɗina tawaye shi sai a yi sati ba a kalle shi ba." Ya faɗa dai dai yana ƙarisowa wajen da na ke tsaye. "Na ga kina tsaye! Me ya faru? Na so ne na juya cikin lumana na bar masa falon amma kishi ya sarrafa zuciyata domin a fusace na juyo, ko kallon Yallaɓai ban yi ba da wani uban sauri na wuce sa har ina bangazan kafaɗansa. "Sadiya.." "Sadiya.." Haka ya riƙa kirana, amma ko juyowa ban yi ba, da wani irin zafi na buga masa ƙofar falon bam! Na kuma san sai da ƙaran ya shiga kansa ina tafe ne zuwa ɗaki amma ina ganin nisan shi a yau, ni dai kafata kawai ke tafe da ni ban san ya aka yi ba na ganni zaune saman cafet ina kuka bayan na shigo ɗakin barcin mu na rufe ƙofa duk ƙoƙarina na kar na yi kuka sai da na yi. A raina ina faɗin Yallaɓai ya cuce ni da ya yi auran nan a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba.   Ni dai tun da na shige ɗaki ban buɗe ba, ban kuma fito ba ina jin Yallaɓai ya gama bugun duniya da kiran sunana na yi masa banza. Sai da na ji fitarsa masallaci sallar mangariba na buɗe nima na shiga tiolet na yi alwala na zo na yi salla a lokacin su Jidda suka shigo sun dawo daga makaranta tun ɗazu wai Abba ya ce ba na jin daɗi, sai amsa musu da eh tunda ya ce ban jin daɗi ai shikenan zama na yi kan darduma ina ta salatin Annabi har sai da na samu natsuwa ana kuma kiran sallar isha'i na miƙe na yi ina idarwa na yi shirin barci na koma na kwanta. Ni yanzu ma waya ba ta gabana saboda na fahimci ita ke barazana da kwanciyar hankalina. Yallaɓai sai bayan isha'i ya dawo ya kuma shigo ɗakin sai na fara nishi kamar ban da lafiya. Sai ya ruɗe ya ƙariso gare ni yana tambayata meke damuna na dafe kaina na ce kaina ne, ya ce zai bani magani na ce ai nasha. Bawan Allah ya bani tausayi haka ya zauna a kusa dani ya na ta min sannu ni fa daman guje ma mganarsa ne a yau ya sa na yi haka ganin yaƙi tashi a kusa dani ya sa na fara barcin ƙarya, ganin haka yasa ya gyaramin kwanciya ganin ina zufa sai ya kunnamin fanka ya fice bayan ya rage min hasken ɗakin gabaɗaya. Yana fita na mike zaune ina mai harɗe hannayena a saman kirjina. Na daɗe ban yi barci ba ina ta tunanin wai yau Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai kai lamarin akwai girma. Tun ina jiyo ƙaran tibi daga falon yara har barci ya ɗauke ni sai asuba na tashi, da rawan jiki ya fara min sannu har ya na taɓa goshina. "Ya kan na ki? Ya yi sauƙi? Sai na gyaɗa kai ina faɗin ya yi sauƙi saboda na ji yana faɗin in ba zan iya ba na ɗaga zuwa asibiti sai wani sati da sauri na ce zan iya. Yallaɓai ranar ya yi ma yara da mu kan mu abin kari, doya ya soya mana sai abincin jiya da ya ɗumama duk tare za mu fita shima ya na da zuwa jana'iza baban wani yaron shi ne ya rasu a can sheƙa. Su Jidda suka fara tafiya mu kuma takwas da rabi muka fita ni da Yallaɓai sai da ya fara kaini asibiti sannan ya wuce jana'izan da za a yi ƙarfe tara na safe ya na ta ma sauri, ni kuma har muka rabu ban iya ce masa daga asibiti Ɗorayi zan wuce ba na bari sai na gama da asibitin sai na kira shi na faɗa masa.   Yau ban samun ganin Dr.Aisha Bukar da wuri ba, saboda ba ta zo da wuri ba , sai 12pm na rana na baro asibitin. Daman na je mata da Test ɗin da ta rubutamin a ƙarshen zuwana tun da yanzu bayan sati uku na ke dawowa. Yau ma ta ƙara rubuta mini wani amma tace shi ne na ƙarshe, daga shi za ta ɗora ni kan mganguna.   "Dr kina ganin zan ƙara samun ciki har na haihu? Na faɗa cikin karaya saboda ni dai na gama sarewa. Sai da ta kalleni kafin ta maida hankalinta kan fayel ɗina ta na rubutu. "E mana. Me zai hana? Likitoci ai ba Ubangiji ba ne, duk abin da muka faɗa hasashe amma ba gaibu ba ne. Balle ni ban ce miki kina da wata matsalan da ba za ki sake haihuwa ba. Za ki sake haihuwa haife haife ma in sha Allahu." Haka aka sha faɗa mini amma kuma kalaman Dr Aisha ya sa na samu sukuni, na yi mata godiya da ya ke mun saba sosai da ita. Sai da na fito bakin asibitin na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba sai na ƙara kirana har sau uku amma bai ɗauka ba.. gani a bakin hanya ina son hawa adaidaitan da za ta kaini Ɗorayi.   Dubaran tura masa saƙo ya shiga kaina. Da sauri na shiga bangaren saƙonni  na lalibo Yallaɓai tun saƙon Anniversty da na tura masa bai ko ba ni amsa ba, ban damu na shiga yi masa rubutu. "Ina so daga asibiti na je gida na gaida Alhajinmu." Na daɗe fa a bakin hanya raina har yafara ɓaci har na yanke shawaran ƙarisawa Office ɗin sa tunda ya ce min daga wajen jana'iza office zai zo, da ya ke ba nisa offishin na su na can gaba ne ko a ƙafa ma zan iya takawa. Ina wannan tunanin sai ga saƙon sa. "Ok." A takaiçe haushi ya kama ni na yi ja dogon tsaki na maida wayata jaka na samu adaidaita da za ta kaini ɗorayi.  Ina sauka a a bakin layi na tako zuwa cikin layi na haɗu da wasu matansa anguwa muka gaisa. Na shiga gida ana ta kiran sallar azahar na samu Gwaggo a tsakar gida ta na alwala gidan shuru. Ina sallama Gwaggo ta ɗago ta na amsawa. "Ah maraba Dubu ke ce tafe? Na amsa mata ina gaisheta ta amsa lokaci ɗaya tana tambayan Yallaɓai da yara, nace suna lafiya. Ɗakinta muka shiga ina tambayan Alhajinmu ta ce jiya ya je can yashe sai yau zai dawo. "Topha lafiya ko Gwaggo? 'Lafiya lau. Kan auran autan su Muntari ne kinsan bikin saura kwana goma." Gwaggo ta amsa min. Shaf na manta da bikin kuma daman na yi alƙwarin sai na je wannan karon. Nima sauke jakata na yi na tuɓe hijabi na fita na ɗauro alwala na zo na yi sallah bayan na idar Gwaggo ta ce ɗanwake ta yi na je na zuba na ci, ina son ɗanwake jikina na rawa na tashi na je na zubo na dawo ɗakin ina ci muna hira sai da na gama na sha ruwa sannan na ce mata daga asibiti na ke. "Allah sarki ina fatan dai ba matsala ko? Sai na amsa mata da " Muna saka ran haka Gwaggo." Sai ta yi min fatan Allah ya sa a dace ta ce min akwai na gargajiya a can gida ta yi mgana za ta karɓo min na ce to bari in na gama shan na asibitin tukkuna. Tun da Alhajinmu baya nan Gwaggo na faɗa ma ƙarin auren Yallaɓai itama ta sha mamaki har sai da ta furta.. "Topha aure haka bagatatan Sadiya? Ni kuma sai na ce mata an ɗaura ne amma ba a yi tariyan ba, duk da ban sani ba amma alamu sun nuna mini haka. Gwaggo ta yi fatan alheri nima kuma ta yi min nasiha ta ce sai na yi hakuri na kauda kai na ce mata in sha Allahu. Ina gida tare da Gwaggo muna ta hira sai gabda la'asar na yi ma Gwaggo sallama na ta fi gida bayan na ce a gaida Alhajinmu in ya dawo. Ina komawa gida na yi salla na shiga kitchen kuskus na dafa mai kayan lambu da hanta. Sai na yi lemun ginger na saka a fridge ya yi sanyi, Yallaɓai ya ba ni mamaki ko ya kirani? Har wayata na dinga dubawa amma bawan Allah bai kirani ba sai kuma abin ya dameni ai ya ga saƙo na ko? Wata zuciyar ta tunaar da ni yanzu fa ba ke kaɗai gare shi ba bai zama lalle sai ya damu da ke kamar baya ba. Ina ta so yakice tunanin haka a raina amman na kasa gaskiya kishi akwai wahala gabaɗaya har na fara rama a tsaye saboda zullumi da tunani ban sani ba. ****** Gwammaja. Wajajen takwas da wani abu na dare ya shigo anguwan gwammaja a motar shi. Ko a cikin gidan ma ya daɗe a mota ya kasa fitowa bayan ya kashe motar. Gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi ko na ce ya mutu. Ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak ya kasa ma wani tunani tun safe ya ce tun bayan barowansa wajen gaisuwan nan ya ji kamar zazzaɓi zai kama shi, ya je office ya yini amma ya kasa taɓuka komai kamar mara lafiya. Ya na gani Sadiya na kiran shi ya kasa ɗaga kiranta to me zai ce mata! Akwai wasu kalaman da zai iya kare kanshi ne da su ne? Ya ga saƙon ta ok ɗin ma da ya tura mata hannunsa na rawa ya tura mata, domin gani ya ke yi duk abin da ya ce ko zai ce a baya da yanzu Sadiya ba za ta daina masa kallon maƙyarci ba kuma ma ci Amana ba, duk da ba haramci ya aikata ba. Amma dai ba daɗi shi kan shi ya sani bai kyauta ma Sadiya ba Sai a lokacin lda suka haɗu da Yaya Abubakar a wajen jana'iza bayan sun gaisa ya yi masa murnan aure ya kuma ce Sadiya ce ta sanar dasu. Tun daga lokacin ya ji jikinsa ya mutu. Ashe ashe tuni Sadiya kallonsa kawai ta ke yi bai sani ba! Sai a lokacin ma ya riƙa tunano attitude ɗin da ta riƙa bashi tun ranar Anniversary ɗin su, bai taɓa kawo ma kansa labarin auran sa da Gimbiya ta ji ba, Bai taɓa tunanin roƙon da ya yi ma ƴan'uwan shi da alfarman da ya roƙa ba su yi masa ba. Ya a ka yi sadiya ta ji wannan mganar? Sai a lokacin ya tuna abin da ta yi jiya lokacin da ta ga Gimbiya na kiran wayarsa a she duk a lokacin ta na dannewa ne amma ta sani kawai kallon shi ta ke yi. Ya tuna a lokacin ya na hanya zai koma office daga wajen jana'iza ya kira Abba ya na faɗa masa Sadiya ta sani ba tare da shi ya faɗa mata ba. "Laifinka ne Tafida me ya sa ka yarda ma aka ɗaura auran ba ka koma gida ka faɗa mata ba? "Na so haka Abba amma Nene ta ce yanzu yanzu mu tafi Rano." Ya bashi amsa cikin karaya. Kalmar ɗaya Abba ya sake faɗa masa sai ya ji ya ƙara jin mutuwar jiki. "Kai ba ka jin shawara. Da tun tuni ka ji shawaranmu ni da Tariq da  a bakin ka Sadiya za ta ji wannan mganar gashi yanzu an ɓata komai sai dai ka yi hakuri ka zuanar da ita ka yi mata bayani " "Ba zan iya ba Abba. Ina jin kunya." Tafida ya faɗa  a marairaice. "To sai wa zai iya faɗa mata in ba kai ba? "Kai mana. Don Allah ka taimake ni ka zo ka yi magana da ita." "Mtseww. Ni na ce ka yi auran? Can ta matse maka " . Daga haka Abba ya katse wayarsa ya bar Tafida da tattaradi. Bayan tasowarsa daga office har gida ya koma amma wallahi ya kasa shiga ya kasa iya tattara kalaman da zai yi amfani da shi wajen kare kanshi a wajen Sadiya. Kawai sai kuma ga Kiran Nene da cewa ya zo gida tana son ganin shi, gaban shi ya faɗi domin a irin wannan kiran ne ya na zuwa a ranar bai yini ba sai da ya zama mijin Gimbiya abin da bai taɓa hasashe ba, ko ma yana hasashen bai kawo shi nan kusa ba. *Janafty* *TKG* 04. FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622 RANAR ƊAURIN AURAN GIMBIYA DA YUSUF. Ya ji tsoro da kiran Nene shi a tunanin shi kiran gaggawan da ta yi masa ko jikinta ne ya tashi, kuma ta ce ya zo gida da gaggawa tana neman shi sai ya firgita shi ya sa ya fita ko ƙaryawan da Sadiya ta matsa ya tsaya ya yi bai yi ba ya ce sai dai in ya dawo.   Bai taɓa kawo ma kansa hashashen ga in da kiran Nene ya dosa ba saboda a yana hanya ma kafin ya ƙariso gidan sai da ya kira lambar wayar Gimbiya amma ba ta ɗauka ba sai ya ƙara firgita a tunanin shi jikin Nenen ne ya yi tsanani. Hankalin shi bai ma kawo masa a muryanta bai ji alamun ciwo ko wani abu ba. Karfe takwas da rabi na safe ya shigo gidan, ya haɗu da Hajiya iya a ƙasa suka gaisa kuma ya ga ba ta ce masa komai ba, bai dai ji hankalinsa ya kwanta ba sai da ya shiga falon Nene ya ganta zaune a kan kujera ta yi wankanta tas da ita kuma cikin ƙoshin lafiya sannan ya iya sauke ajiyar zuciya na samun salama da natsuwa. Bayan ya zauna a gefenta ya shiga gaisheta cikin ladabi ta amsa masa cikin fara'a da soyayyar da ta ke yi masa wacce ba ta iya ɓoyuwa a cikin idanuwanta. "Ya wajen ita Sadiyan? Ina takwarata da Maimuna? Ina fatan duk kuna nan lafiya." Kansa na ƙasa ya ce"Duk lafiya lau Nene. Su Jidda kuma suna makaranta sun koma tun jiya." Kai ta gyaɗa kafin ta ce" Allah ya taimaka. Allah ya yi musu albarka gabaɗaya." Ya amsa da Amin Amin shuru na wani lokaci saboda ya ji falon shuru sai ya ɗan waiwaya ya kalli ɗakin da Gimbiya ta ke kwana ya gansa a kulle sannan ba alamun ta na ciki sai ya juya ya na kallon Nene lokaci ɗaya ya na faɗin" Ke kaɗai ce Nene? Daugther ta fita ne? "E. Ta fita yanzu ba daɗewa an kirata daga wajen aikinta." Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Ina hanyan zuwa nan ma na kira wayarta ba ta shiga. Ni fa hankalina ya tashi da kiran ki Nene na ɗauka ko jikin ne ya tashi." Sai da ta yi mirmishi kafin ta ce" Ko ɗaya lafiyata ƙalau Tafida." Sai kuma ta yi shuru shi kuma sai ya bi ta da Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon kwana Nene." Ta amsa masa da Amin Allah ya sa. Shuru ya sake biyo baya na tsawon mintina biyar. Ya na kallon Nene ya ji ko za ta ce wani abu. Amma ya ga ta yi shuru kuma ya san tun da ta kira shi akwai mgana. Sai ya gyara zama shi ya kauda shurun kafin ya ce" Nene akwai damuwa ne? Ko wani abu kike so na yi miki? Sai ta kalleshi, ko acikin ƴaƴanta Yusufa na dabam ne. Shi ne ya ɗibo kusan hallayar marigayi mahaifinsu. Shi ne kawai in ta yi shuru ya ke fahimtar ta na buƙatar wani abu amma ta na jin nauyin tambaya. "Nene ki yi mgana mana. Komai kike so nan duniya zan iya miki shi ko da ya gagareni zan nemi taimako a wajen wanda zai iya yi mini alfarma domin na faranta miki." Ya faɗa ya na matsowa kusa da ita. Sai ta ɗago ta kalleshi kafin ya ji ta saka hannayenta duka biyu ta kama duka hannayensa lokaci ɗaya ta na faɗin" Alfarma na ke so na roƙa a wajen ka Tafida. Amma kar ka ji a ranka ko na tursasa ka ne, ina so komai da zai faru ya zama da amincewarka da yardan ka ne." Cikin mamaki ya kalleta kafin ya ƙara jimƙe hannayenta ya na faɗin" Nene ni ne fa Tafida! Umarni kawai za ki ba ni na cika miki shi ai tsakanin mu ba alfarma Nene." "Akwai Tafida. Akwai alfarma a tsakanin uwa da ɗanta. Nima yau albarkacin wannan alfarman na ke so na ci a wajen ka Tafida." Da sauri ya ce" Faɗi ko miye Nene, ni ko zan cika mganarki da sunan umarni ba alfarma ba." Ta na mai kallonshi hannuwansu sarƙe cikin na juna ta ce" Tafida ka san a shekarun baya da ka kawo mganar auran Sadiya na goya maka baya a lokacin da ƴan'uwanka suka ƙi fahimtar ka ko? Sai ya gyaɗa mata kai amma gabanshi na faɗuwa domin bai gane in da mganar Nene zai dosa  yanzu kuma ba. "Har ga Allah tun  ganin farko da na fara yi ma Sadiya a cikin falon nan nawa a shekarun baya na yaba da hankalinta na kuma san ka yi dacen samun mata tagari. Sadiya ba ta gazamin ba kuma ba ta yi min komai ba wallahi sai ma tarin alherinta zuwa gareni." Ta ɗan dakata tana kallonshi kuma shi har ga Allah ya ƙosa ya ji in da mganganun Nene suka dosa.   Ajiyar zuciya Nene ta sauke kafin ta ce" Tun muna ƴan mata ni da Hajiyar Tafida muka yi alƙwarin da fatan in mun yi aure mun hayayyafa za mu yi haɗin auran zumunci a tsakanin y'aƴaƴyanmu domin ƙara karfafa zumuncin da ke tsakanimu, sai ga shi kuma mun auri mazaje abokai, sai amintan mu ya yi girman da mutane ma suna kwatance damu. Tafida tun da na haife ka na ji a raina kai ne za ka iya cika mini wannan alƙwarin. Zaman ka a Rano a gidansu Gimbiya da shaƙuwar da ke tsakaninku sai muka sakankance za ku dai dai ta kanku har burin mu ya cika kwatsam sai ka zo mini da mganar Sadiya." Zuwa yanzu kam jikinsa ya yi sanyi shi ai ba yaro ba ne tuni ya fara fahimtar in da maganganun Nene suka dosa amma bai katse ta ba, gwara ya ji ta har ƙarshe domin ya san a ina za ta dire mganganunta. Ita kuma kallon shi ta ke yi ta na ƙara nazarta yanayin sa. Amma ko a fuska bai nuna mata wata alama da za ta ce mganganunta ba sa yi masa daɗi ba. Sai kawai ta cigaba da faɗin. "Na so ka da Saudatu Tafida kamar yadda Hajiya itama ta so hakan sosai wanda har sai da ta furta mini tun a wancan lokacin. Amma saboda kai ka kawo Sadiya kuma ka nuna ita kake so a lokacin in na ce ka bari za ka bari kuma za ka yi min biyayya ka auri Gimbiya sai dai na yi tunanin na zama azzaluman uwa tunda na hana ka abin da kake so domin ni na wa cikar burin shi ya sa ban taɓa yi maka mganar ba na taka ma su Bahijja burki a kan ƙin auran ka na ce su yi maka fatan alheri, domin ko suma a lokacin da Gimbiyar suke hangenka. Amma suka danne saboda na ce su bar mganar matan mutum ai kabarinsa. A lokacin da mganar auranka ya samu Hajiya ko da ba ta furta ba, ni na san ba ta ji daɗi ba amma sai ta yi fatan alheri a gare ku gabaɗaya.   Na yi ta zura ido na ga ko za ka fahimci Gimbiya na sonka amma sai na ga ba ka nuna wata alama ba, wataƙila ka fahimta amma sai ba ka ba ma hakan muhimmanci ba. Gimbiya ta yi ta zaman jiranka ta na ture manemanta a yaƙininta cewa wata rana za ka iya fahimtar irin ƙaunar da ta ke yi maka. Amma sai ka kasa fahimtar ta, duk shekarun da ta ɓata ba ta yi aure ba ta kasa fidda yaƙini be a kanka ne, sai daga baya da ta fahimci ka fahimceta kawai dai ra'ayi ne a kanta ba ka dashi sai iyayenta da ƴan'uwanta suka yi mata faɗa har ta fidda wannam mijin ta aura sai ga shi cikin hukuncin Allah zaman bai yi tsawo  ba ya rasu ya barta. Ta dawo gida ta yi idda ta gama gashi yanzu ta dawo nan wajena da zama." Sai Nene ta dakata ta na sauke numfashi har kuma lokacin Hannayenta na hannun Tafida ya damƙe sanyin da jikinsa ya yi ya sa gabaɗaya ya kasa motsi ya na ji zufan hannun shi na jiƙa tafukan hannayen Nene da ke cikin na shi. "Yusufa." Yusufu wani suna ne da in Nene ta kira shi dashi ya san mgana ce mai muhimmanci. Ba ta kiran sunan shi sai dai ta kira shi da Tafida. Shi ya sa ya na jin haka ya ɗago da kansa ya na kallonta cikin dakiya ya amsa mata. "Na'am Nene" Ya amsa mata ya na tattaro dukan jarumtarsa a gabanta amma a ƙasan zuciyarsa ya yi rauni. Domin hasashen sa bai taɓa kawo sa ga wannan bingiren da Nene ta kawo shi yanzu ba. "Ka taɓa fahimtar har yanzu Gimbiya ba ta daina sonka ba? Ko ka taɓa lura da cewa har yanzu ba ta cire tsammani da yaƙini da cewa za ka iya zama na ta ba? Tambayoyin Nene sun yi masa tsauri da ya kasa cewa komai.. Sannan gashi ta ƙura masa ido ta na jiran amsarsa. In ya ce bai taɓa sanin Gimbiya na son shi ba ya yi ƙarya domin tun tana kunya har ta fito ma da alamomin da suke bayyana cewa ta na son shi, ba ma shi ba har mutanen da ke kusa da su sun fahimci irin soyayya da Gimbiya ta ke yi masa. Da farko shi ma ya ɗauka ya na sonta ne sai da ya haɗu da Sadiya anan ne ya fahimci ba so ba ne shakuwa ce kawai da haɗuwar jini. Sadiya ita ya ji ya na yi ma soyayyar da Ubangiji ya hallita tsakanin mace da namiji. Amma bai taɓa ƙin Gimbiya ba, sannan har gobe ta na daga cikin foverite ɗin mutane a wajensa amma bai taɓa tunanin ya saka tunanin auran ta a ran shi ba,  ba kuma domin ba zai iya auranta na ta ba sai domin tunanin hakan bai taɓa shiga ƙwaƙwalwarsa ba ne. "Shurun ka na nufin amsarka da E Tafida" Nene ta katse masa tunani, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Nene ba ni ba duk wanda ke tare da mu zai iya shaida akwai kyakyawan alaqa tsakanina da Gimbiya. Amma." Hannu ya ga Nene ta ɗaga mai tana kallonshi kafin ta je fa masa wata tambayar da ta ƙara rikita shi. "Kana son Saudatu!? "Za ka iya zaman aure da ita? Sai ya kasa mgana bakinsa na rawa ya na so ya yi mgana ya kasa. Tambayoyin suna da girma da tsauri in aka ce ya amsa su nan take kamar ana so ya yi gaggawa ne. A bari ya samu kamar sati ɗaya daga shi sai zuciyarsa ya gani ko za ta iya amsar tambayoyin Nene amma ina Nene ba ta bashi wannan damar ba yana ƙokarin mgana ta ƙara tare shi da faɗin" Ba buƙatar dogon lokaci ba ne Tafida ka faɗamin shin za ka iya auran Saudatu kuma ka yi zaman aure da ita? "E. Amma Nene.." "Ka gama min komai Tafida. Na gode da afarman ka. Na gode da biyyarka. Na gode da kyautatawarka a gareni. Allah ya saka maka da gidan aljannah. Allah ya shirya maka zuru'a ya yi ma rayuwarka da duk abin da ka saka hannu a kai albarka Na gode." Nene ta faɗa ta na zare hannayenta daga cikin na shi sai kuma ta fara sharan ƙwalla ganin haka sai bakin shi ya mutu Nene na share hawaye ta na ta saka masa albarka da addu'o'in gamawa da duniya lafiya su suka haɗu suka ƙara kashe masa baki da zuciya gabaɗaya. Ya ɗauka iya mamakin da Nene za ta gama bashi kenan ashe ba shike nan ba. Umarni ta bashi da cewa ya kira mata Zuwaira da Maimuna da Bahijja suma su taho gida yanzu tana son mgana da su. Ya ɗauka dai kan mganar da suka gama shi ya ke kiran su da wayarsa amma sai Nene ta karɓa ta yi musu mgana Zuwaira(Mimisco) ta fara zuwa tunda ita ce lokacin da aka kira ta ta na makaranta ta ce ma za su yi meeting ne amma ba ri ta saka a ɗaga zuwa anjuma sai ta taho. Sauran kuma suka ce yanzu za su shirya su taho suma dai hankalinsu ya tashi sun ɗauka jikin Nene ne sai da ta basu tabbacin ka da su damu ta na lafiya sannan hankalinsu ya kwanta suka ce ga su nan zuwa. Lokacin da Mimisco ta iso gidan ta ɗan yi mamakin ganin Tafida zaune, amma sai ba ta yi mgana ba ƙila dai ya shigo gidan ne amma dai tana tunanin da akwai dalili acikin kiran na Nene. Kalaman da Nene ta furta ma Mimisco ne ya sa ɗan sauran gudun jinin da ke tafiya a jikin Tafida ya tsaya cak! "Zuwaira Rano na ke so mu je a yau yau ɗin nan." "Rano kuma Nene! A yau kuma? Ta faɗa ta na kallon Tafida shima ita ya ke kallo amma ya kasa mgana sai ta maida hankalinta kan Nene ta na faɗin" To wani abu ya faru ne a can Nene? "Ba abin da ya faru sai Alheri. Aure na ke so yau a ɗaura a tsakanin Tafida da Saudatu." Shi dai sai da ya ji yam!  tsigogin jikinsa sun tashi. Numfashi ya yi sama sannan ya jawo shi ya dawo. Mimisco ko ido ta zaro ta na kallon Nene tana kuma kallon Tafida kafin ta ce"Wata Saudatun kuma Nene? Domin ita sai ta ji ma ta manta wacece Saudatun. "Gimbiya ta mu.".. "Topha yau shi Tafidan da kan shi ya ce ya na son ita Gimbiyan! Sannan ya ce a yau ya ke son a ɗaura auran? Mimisco ta faɗa cikin ƙarin mamaki, ta na kuma mai kallon Tafida da ya kasa mgana. Nene ce ta yi mata bayanin komai ta ƙara da cewa" Tunda har ya ce zai iya zaman aure da ita me za mu jira Zuwaira! A ɗaura kawai daga baya sai a yi mganar tariyan" Mimisco ta kasa mgana Tafida ta kalla sai taga itama ya kalleta yanayinsa kawai ta kalla ta fahimci a bazata mganar Nene ta zo masa in kiya ya yi mata ido itama sai ta yi masa alamun ya yi mgana mana.   Sai gani suka yi Nene ta miƙe tana faɗin" Bari na kira Hajiya na faɗa mata muna tafe." Ta faɗa cikin murna wanda har ya bayyana a muryanta. Mimisco ta yi saurin cewa"Nene dawo ki zauna." Sai ta juyo ta na kallonsu kafin ta dawo ta zauna ta na faɗin" Me ya faru ne? Mimisco ta kalli Tafida kafin ta ce" Ka yi mgana da Sadiya ne? Sai a lokacin ma ya fahimci ƙura ne turƙe a gaban shi bai sani ba, sai ya girgiza kansa kafin ya ce" Yanzu yanzu Nene ta yi min mganar kuma a yanzun ta yanke wannan hukuncin." Sai Mimicso ta kalli Nene kafin ta ce" Nene ki yi hakuri ki ba shi dama ya je gida ya yi mgana da matarsa zuwa gobe sai a yi yarda kike so." Amma Nene ta ce ba ta amince ba, ya kira Sadiya a waya ya faɗa mata kuma ai yana da sauran lokaci. "Waya kuma Nene? Gaskiya bai kyautu ya yi mata waya ba. Sai dai in haka kike so a je a ɗaura ɗin daga baya sai ya yi ma Sadiya bayani." Nene ta ce hakan za a yi kuma ta san Sadiya za ta fahimcesa. Ba yadda ya iya har Mimisco ba ta so gaggawan ba amma ba yarda ta iya Nene ta dake har ta Kira Hajiya ta ce suna nan tafe, Bahijja ta fara zuwa daga baya sai Maimuna suna jin ƙudurin Nene suka haɗa baki suna rangaɗa guɗa su lamarin ya yi musu daɗi matuka sannan Nene ta biya su. Da dai Tafida ya ga da gaske Nene ta ke sai ya roƙi su Bahijja da don Allah su yi shuru da wannan mganar kar Sadiya ta ji. Ya na so ne in ma za ta fara ji sai daga bakinsa har suka ɗan samu cacan baki da Bahijja domin ta ce bai isa ya hana su nuna farinciki ba. Sai da Mimisco ta shiga tsakani ta ce ya na da gaskiya. Za su tarwatsa masa gida ne ai ya na da gaskiya kuma mganar aure ai ba mganar wasa ba ne. Da haka dai suka yi alƙwarin ba za su fidda maganar ba. A lokacin ko awa ɗaya ba su ƙara a Kano ba suka ɗau hanyar Rano da shi da Nene da Mimisco da Bahijja Maimuna ta koma gidanta. Suna kuma zuwa Nene ta isar da kudurinta sai da Hajiya ta tashi ta rumgumeta ta na mai nuna farincikinta a gidan Tafidan Rano ƙanin baban Gimbiya aka ɗaura auren Yusuf da Saudatu kan Sadaki naira dubu 100k. Kuma ba a ɗaura ba sai da shi Waliyin nata ya kira ta a waya ya tambayi izininta tunda bazawara ce kuma addini ya ba ta wannan damar ita kanta a ba za ta ta ji mganar wai ta na son Yusuf? Domin ga waliyanshi sun iso domin nema masa auranta. Da rawan jiki da na zuciya ta amince, a cikin office ɗin ta bayan Anty Bahijja ta kira ta ta ce an ɗaura auran ta da Tafida sai da ta faɗi ta yi sujjudar shukur ta na hawayen farinciki atleast dai yau burinta ya cika tabbas kar bawa ya cire tsammani duk abin da ya ke rabon ka ne ko ya hau sama sai ya faɗo a kanka. Alhamdulillah. Bangaren Tafida Kawu Sa'adu ne da su Abba suka karɓa masa auran Sadakin kuma Nene ce ta biya da kuɗinta saboda yadda ta ke son Tafida da Saudatu. Bayan an gama ɗaura aure kuma acan gidan Hajiya aka fara ɗora girki na sadaka, bakinta har kunne ta kira sauran Ƴayanta a waya duk ta sanar da su kafin ka ce kwabo labari ya zaga Rano da kewayenta.  Abba shi kan shi ya yi mamakin auran nan cikin gaggawa da Mimisco ya yi mgana ita ce ke yi masa bayanin yadda lamarin ya fara. Amma Yusuf bai iya ba, domin lamarin kamar a mafarki ya ke gani. Duk roƙon da ya yi musu sai da Bahijja ta ɗora a status a tunaninta ta cire Sadiya ko ta manta da Ma'u ne?   Ko Tariq da ya ji yadda asalin lamarin ya faro ya ji wani iri. Duk da Gimbiya ƙanwarsa ce kuma ya na yi mata murna, amma bai ji daɗin yadda Tafida ya amince aka ɗaura aure ba tare da ya yi mgana da Sadiya ba shima Abba haka ya ce amma sun yi ta ba sa shawaran da ya koma gida ya sanar da ita gudun samun matsala, amma sai ya ji ya kasa ya na gani ta na tura masa saƙon Anniversary ɗin su sai a lokacin ma ya tuna muhimmancin ranar a gare su, sai dai ina ranar kuma sai ta rikice ta koma rana mara daɗi ga Sadiya ba zai iya kashe mata karsashinta wannan ranar ba, shi ya sa har ya gama nuku nukunsa ya koma gida ya kasa iya faɗa ma Sadiya wai shi ya ƙara aure ba tare da ta sani ba. Ya kusa shafe sama da awa ɗaya a waje ya kasa iya shigowa ga shi dai ba abin kunya ya aikata ba amma yana jin tsoro da kunyar haɗa ido da Sadiya a wannan yanayin. Lokacin da ya shigo gidan suka haɗa ido da Sadiya sai ya ji kunya kwataƙwacin kamar ya ci amanarta haka ya ji. Ya kasa iya sarrafa kansa a gabanta. Har aka wayi gari yana cikin wannan yanayin sai daga baya ne ya fara warwarewa. Bai taɓa tunanin Sadiya ta ji mganar auran shi ba, duk da dai mganar ta zagaya dangi tunda ana ta kiran shi ana masa fatan alheri. Ya yi ta mamakin duk labarin ya je ma kowa, a tunanin shi Sadiya ba za ta sani ba shi ya sa ya ke ta shirye shiryen yadda zai tunkare ta da maganar sai ga shi duka shirinsa ya rushe. Ga shi shagon da ya kama mata har ya biya kuɗin shekara key na hannun shi, kunya da nauyin sun saka ya kasa yi mata mgana, balle yanzu in ma ya nuna mata a zuciyarta za ta ce ba domin Allahya yi ba saboda ya yi mata kishiya ne shi ya sa ya kasa bata. Ya tuna jiya har sai da Musbahu ya yi masa mganar shagon. "Yaya Tafida wai ƙasa za mu koma ne? Sai ya girgiza masa kai a lokacin. Domin shi kan shi bai san mafitan shi a lokacin ba. Sanin da Sadiya ta yi ba tare da ya faɗa mata ba ya yi masa mumnunan duka, saboda yanayin da ya ke ciki tun da aka ɗaura auran sau biyu suka taɓa waya da Gimbiya gidan ma sau ɗaya ya je suka haɗu bayan kuma gaisuwa wata mgana mai tsawo ba ta shiga tsakaninsu ba, ya fi so sai ya gama da Sadiya sun samu daidaituwa kafin wata mgana ta biyo baya. Ya tsara a jiya zai yi mata mgana ya sanar da ita sai kuma Allah bai so ba ya yi tunanin yau ɗin in ya koma gida amma tun haɗuwarsa da Yaya Abubakar gabaɗaya tsarin sa ya ruguje mafita ya ke nema ya rasa mafitan. Shi ya sa ya kasa iya komawa gida da wuri ya kama hanyar gidan da dadaddren kenan kuma sai ga kiran Nene ya riskeshi. ****** Ya na cikin motan bai fito ba sama da mintina talatin. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. Wayar sa ya laluɓo a gaban Aljihunsa ya sake kiran Abba.   Yana ɗauka bai ko jira sun gaisa ba cikin roƙo ya fara faɗin" Don Allah Kawu ka taimaka min ka zo gida gobe ka ta ya ni fahimtar da Sadiya don Allah."    Daga can bangaren Abba ya ce" Sai kuma ka yi. Wallahi ba in da zan zo. Kai ba ka da baki ne? Ko kai ba Namiji ba ne? A sanyaye Tafida ya ce" Kunyar ta na ke ji fa." "To ai sai ka murje kunyar ka sanar da ita. Duk da dai bakin alƙalami ya riga ya bushe. Sai dai ka yi gyaran mgana daga baya."   "Kai yanzu don Allah ba za ka zo ka yi mgana da ita ba? "Wallahi ba zan zo ba. To ni me ye nawa! Ni ne mijinta? Kai ne mijinta kai ya dace ka zaunar da ita ka koyo kalaman haƙuri da kare kai har sai ta fahimceka. Kai fa namiji ne kuma ka fi ni sanin matarka sosai ka san kuma hanyoyin da za ka bi da ita har ta fahimceka. Amma ni dai na roƙe ka don Allah ka daina saka ni a cikin wannan mganar." Ko ma ya jira cewar Tafida ya kashe wayarsa ya bar sa cikin damuwa da tararradi Ya daɗe zaune yana tufka ya na warwara amma duk in da ya kamo ya fara tufka sai ya warware ya kasa samun mafita guda ɗaya da zai kama. Dole dai ya buɗe mota ya fito a kasalance kamar mara lafiya ya wuce cikin gida saboda dare ya yi kowa na cikin ɗakin shi, ɗakin Maman Farko ya leƙa suka gaisa daga nan ya wuce shashen Nene falon shuru har sun rage haske alamun sun kwanta da ya yi sallama ne ya ji muryan Nene daga ciki ta na amsa masa, sai ya cire takalminsa nan ƙofar falo ya shiga har cikin bedroom ɗin Nene Ya iske ta har ta kwanta ma ganin shi ya sa ta miƙe zaune bayan ta miƙe kafafunta ta na faɗin" Tafida sai yanzu? Ya na sosa kansa ya ce" Wallahi na tsaya gamawa da Office ne Nene" Ya faɗa dai dai ya na zama gefen kafafunta a gefen gadon. Gaisawa da tambayan iyalan shi ya ce suna lafiya kafafunta ya ɗauka ya ɗora a saman cinyarsa ya na matsawa. "Suna ciwo ne yanzu? Ya faɗa ya na kallonta lokaci ɗaya kuma yana ƙara matsa mata kafafun duka biyun. "Ba sosai ba. Saudatu na shafa min man zafi in zan kwanta." Kallonta ya yi kafin ya ce" Amma yau dai ba' a  shafa ba ko? Ban ji zafin sa ba " Ya faɗa ya na shinshina hannunsa. "E. Ba ta jin daɗi yau kanta ke ciwo ta ce min da wuri ma ta baro wajen aikinta." Cikin nuna jimami ya ce" Subhanallah ta sha mgani? "E. Ta sha da sauƙi ta ce bari ta kwanta ne. In ka tashi tafiya sai ka shiga ka duba ta." Sai ya amsa mata da toh sun ɗan fara taɓa hira ganin dare ya yi ya sa ta kalle shi kafin ta ce" Kan mganar Saudatu ne daman." Sai ya maida hankalinsa a kan Nene ganin haka ya sa sai ta cigaba da faɗin" Na ga an kusa yin sati da ɗaurin auran ku kuma ban ga kana zuwa ba, ballantana ma ku yi mganar yadda za ku tsara tarewar na ta." Shuru na wani lokacin kafin ta ƙarƙare da faɗin" Shi ne daman na kira ka na ce ka zo na ji ko lafiya? Shuru ya yi kafin ya sauke numfashi. "Nene." Ya kira ta amsa kafin ya ce" Daga ke har Gimbiya ku ɗan ƙaramin lokaci don Allah" "To shike nan" Nene ta faɗa ta na kallon shi a yanayinsa kawai ta gane akwai damuwa. "Akwai matsala ne Tafida? Sai ya gyaɗa kai  da sauri ta sauke kafafunta ƙasa ta zauna dakyau ta na faɗin" Sadiya ce? Sai ya ƙara gyaɗa mata kai ya ce" Ta ji labari Nene ta ji labari." Cikin mamaki ta ce" Ta ji labari? Ba ka gaya mata ba ne daman? Nan ma kai ya gyaɗa mata kafin ya ce" Na kasa faɗa mata ne. Ina ta riƙe mganar daman yau na ke shirin faɗa mata sai kuma na haɗu da yayanta wajen jana'iza sai gashi yana min murna kuma ya ce ita ta faɗa musu na ƙara aure." Ya karishe faɗa kamar zai yi kuka Nene ta dafa kanshi kafin ta ce" Ka kwantar da hankalinka. Kuna da fahimta kai da Sadiya. Yanzu ka tashi ka tafi gida ka zaunar da ita ka yi mata bayani na san za ta fahimta.' Sai ya gyaɗa kanshi kafin ya kalli Nene ya na faɗa min" Nene abin mamaki a ina ta ji! Kuma wa ya sanar da ita? Nene ta ce" Sanin wanda ya faɗa mata sai Allah. Amma ba abin mamaki ba ne domin ta ji labari. Magana in ka iya rufe bakin wani, ba za ka iya hana wani mgana ba. Ka yi kuskure da tun lokacin ba ka faɗa mata ba, amma yanzu ma baka makara ba ka tashi ka je gida ka zaunar da ita ka yi mgana da ita cikin Sigar da za ta fahimcen ka ka ji ko? Sai ya gyaɗa mata ɗan shafa kanshi ta yi kafin ta ce" Tashi ka je. In sha Allahu ba matsala." Da haka suka yi sallama bai fita ba sai da ya ga ta koma ta kwanta har ya ɗan rufa ma ƙafafunta bargo ya kashe mata fitilan ɗakin sannan ya fita. Har ya kai ƙofa zai fice sai ya tuna da Nene ta ce  ya shiga ya Duba Gimbiya sai ya fasa fitan ya dawo zuwa ɗakin da Gimbiyar ke ciki ya ƙwaƙwansa sau biyu daga ciki ta ce a shigo sai ga shi ya buɗe a hankali ya shiga da sallama. Ta amsa masa sallamansa tana zaune a gefen gado amma ta saka wani ƙaramin hijabi hasken ɗakin a kunne ya ke alamun ita ta kunna. Sun haɗa ido ita dashi sai ya yi mata mirmishi itama sai ta mayar masa. Tura ƙofar ya yi ta rufe kanta sannan shi kuma ya fara takowa zuwa gabanta da jikin wadrope ɗin da ke ɗakin ya Jingina wanda a baya babu shi a ɗakin ita Gimbiyar ne ta saka a ka yi mata anan garin. "Sannu ya jikin? Kan ya daina ciwo?   Ya kauda shurun da ke tsakaninsu tun bayan gaisuwan da ya shiga tsakaninsu. "Da sauƙi." Ta faɗa a hankali, cikin sanyin murya. Sai ya yi mata fatan samun sauƙi kafin ya ce" Kin sha mgani? Sai ta ɗago ta kalleshi kafin ta ce" E. Na sha." Shuru na wani lokaci ba tare da tsammani ba kanta na ƙasa ta ga ƙafafunsa a gabanta kafin ta ɗago kanta ta ji tattausan hannunsa bi sa goshinta sai da ta runtse ido cikin wani yanayi. "Uhm na ji kan na ki ba zafi sosai." Haka ya faɗa ya na yin baya kaɗan. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali saboda yanayin da ta ke ciki. Ya juya kamar zai fita daga ɗakin ya na faɗin. "Allah ya ƙara lafiya. Ki kwanta ki huta kin ji ko? A ƙasa ƙasa ta amsa da Amin. Har ya saka a hannu a jikin handel ɗin ƙofar sai kuma ya juyo daman itama kallon shi ta ke yi sai suka haɗa ido. "Daughter." Ya kira sunanta kamar yadda ya saba. "Na'am Daddy." Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce" Na faɗa ma Mamanki ke da ita ku ɗan ƙaramin lokaci kaɗan. Ina so na ɗan gama da wasu abubuwan ne first daga baya sai na zo mu yi mgamar tarewar ki ko? Ya faɗa ya na mai kallonta da sauri ta sunkuyar da kanta kafin ta ce" To." Ta na mirmishi, shima mirmishin ya yi mata sannan ya juya ya na faɗin" Sai da safe." "Gud night." Itama ta bashi amsa har ya fita ya rufe mata ƙofa ba ta daina mirmishi ba ya na fita ta faɗa gado ta na tsalle da kafafunta lokaci ɗaya ta na rufe bakinta. Ta ji shigowarsa falon Nene tun farko har leƙensa ta yi bai sani ba ta na ta Allah Allah ya shigo ta gan shi ko za ta ji daɗi sai ga shi Allah ya amsa roƙon ta. Wani irin rawa zuciyarta ya ke yi na soyayya da ƙauna har yanzu ba ta daina godema Allah ba domin ya gama yi mata komai. Ubangiji ya gama ba ta komai anan duniya tunda har ya mallaka mata Yusuf. Za ta iya jiransa ko nan da shekara ne ba dai an ɗaura ba ai an gama mai wahalan. ***** 10:50pm Goma da minti Hamsin Yallaɓai ya shigo cikin bedroom ɗin mu. Ina kwance da waya a hannuna ina dannawa shi ya sa ma na duba lokacin. Na so na yi barci kafin ya dawo barcin ne ya ƙi zuwa dole na ja wayata na kunna data ina ta shige shige. Mun yi chart da Amina sai Munnira. Sannan kuma mun yi waya da Sameena ƙanwar Gimbiya yadda ba ta min mganar auran Yallaɓai ba, nima ban yi mata ba na san ta sani kawai ba ta so ne ta fara ɗauko min mganar amma mun yi hira da ita sosai. Ni Munnira ke ba ni mamaki ta ƙi yi min mganar ni a tunanina ko wani zai ɓoye min su sai su ɓoye min amma ina jiran su wallahi sai na yi musu wankan soso da sabulu. Datti ma da daren nan ya kira ya na ce min ashe Yallaɓai ya yo amarya Amina ke faɗa masa shi bai damu ba dariyan shi ya ke yi  to daman su maza ina ruwan su ko uku Yallaɓai ya ƙaro min lokaci ɗaya na tabbata cewa za su yi ya yi dai dai. Ko a jikinsu tunda daman duk halinsu ɗaya na son kansu. Kafin ya dawo ba tunane tunanen da sheɗan bai gayyato min ba, in na runtse ido sai na riƙa hasko shi da Gimbiya a cikin yanayin da kan iya haifar min da hauhawan jinina sama. Lokacin da ya shigo da sallama na yi niyyar ne na ƙi amsswa amma sai na taushi zuciyata na amsa masa ta gefen ido ina kallon shi, domin ni kawai na saka a raina ya na wajen Gimbiya wato tun kafin ta tare ya fara raba ma na yini saura kwana kenan. Wanan malolon abun da ya ke cikin ƙirjina tun san da na ji labarin auran sa da bai wuce ba har yau shi ne ya taso min. Daƙyar na iya daurewa a shaƙe na yi masa sannu da zuwa sai na ga shima bai kalleni ba ya amsa kawai. "Ya gidan ne? Ya kika je kika samu su Alhajin? Ashe ya tuna in da na je. Ba ya kallona kayan jikinsa ya ke tuɓewa. Nima sai na kauda kai kafin na ce" Duk suna lafiya." Daga haka na cigaba da duba waya ta a IG har Volume na ƙure da gangan saboda haushi bai kalleni ba, kuma bai ƙara mgana ba bayan ya bar gajerun wando na ga ya fita sai na ji ƙaran ƙofa kenan ya shiga Tiolet wanka ya yo ya fito ina nan in da ya barni kwance, ina ta nazarinsa ta gefen ido, har ya gama shirin barcinsa na ga bai yi min mgana ba kuma ya na shirin kwanciya sai na daure na waiwaya ina kallon shi kafim na ce" Abinci fa na Dinner." Sai ya kwanta a can gefensa sannan ya ce" Ba na jin cin wani abu yanzu." Daga haka sai na ga ya juya min baya kawai ya yi kwanciyarsa. Mamaki ya kamani amma na kasa mgana sai nima ma juya masa bayan ina sakin ƙaramin tsaki kuma na tabbata ya ji ni. Amma bai yi wani motsi ba, da gayya na yi ta shiga Yuotube ina shiga waƙoƙi ina ji domin na dame shi amma har na gaji bai motsa ba, ba ni na kwanta ba sai 12pm sannan na ijiye waya da na ji barci, ina yin addu'an barci na runtse ido sai barci. Zai da ya tabbatar da ta yi barci sannan ya juya yana kallon bayanta. Dole ne ya sa ya yi avoiding ɗin Sadiya ya rasa da idanuwan da zai kalleta abin da ya yi shi ne dai dai. Bai ma ɗauka zai zo ya same ta idanuwanta biyu ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya yi kwanciyar rigingine ya na kallon rufin ɗakin na POP. Ya na kuma tunanin ta ina zai fara? Duk in da ya yi tunanin zai fara ta can sai ya ga hanyar ba mai ɓullewa ba ce, ya daɗe bai yi barci ba ya na faman juye juye amma har garin Allah ya waye bai samo mafita ba. **** Saboda rashin barcin da bai samu a daram jiya ba ya sa tun bayan da ya dawo sallar asuba ya ke kwance ya na barci sai kiran wayarsa ce ta tashe shi. Sai ya ga Nene ce ke kiran shi da sauri ya miƙe zaune ya na daidai ta yanayinsa. Sannan ya ɗaga kiran. "Tafida." Ta kira shi bayan ya yi mata sallama. "Na'am Nene ina kwana." "Lafiya lau. Kana gida ne? Sai ya amsata mata da E. "Ka yi mgana da Sadiya jiya! Cikin kasala da muryan barci ya ce" Ban yi ba Nene." "To ka jira ni. Kar ka yi mata mgana." Cikin mamaki ya ce" Me ya sa Nene? "Akwai dalili. Ka jira ni." Daga haka ta yanke wayarta sai ya bi wayar da kallo yana mamaki bai koma ya kwanta ba amma ya kishigiɗa da gado ya harɗe hannayensa a ƙirji ya na hasoso tunanin Nene na cewa ya jira ta. Bai taɓa tunanin shirin Nene na zuwa gidan shi ba ne sai bayam mintina talatin da wayarsu da Nene ya ji kamar ana buga get duk da ya san Sadiya na can cikin gida baya tunanin za ta ji, shima domin ya na cikin bedroom ne kuma  window ɗin su na haraban gidan ne. Sai ya miƙe daga shi sai bakin wando da singleti ya fita falo sai ya ga Sadiya kwance a falon yara kallo take yi ko kawai ta na kwance ne bai sani ba. Ina daga kwance na ga fitowarsa sai na yunƙura na miƙe zaune ina faɗin" Ina kwana." Sau ɗaya ya kalleni sai kawai ya yi gaba ya na faɗin" Lafiya lau.' Bari na je waje na ji ana buga get." Ya na gama faɗin haka ya buɗe kofa ya fice na rasa shi da kallon mamakim to wai har na fara masa baƙi a ido ne da ya sa Yallaɓai daga jiya zuwa yau ba ya son haɗa ido da ni? Zaune na ke ina mamakin shi, ni ko shigowar mota ma ban ji ba sai dai na ji kamar mgana daga falo sai na miƙe na kawo gabda ƙofa zan buɗe sai ya rigani turowa ya shigo sai muka haɗe ya kalleni na kalle shi. "Nene. Nene ce ta zo." Cikin mamaki na ce" Nene fa? Saboda ni dai tun da muka dawo gidan nan sau ɗaya ta taɓa zuwa shima rashin lafiya Baby ta yi shi ne ta zo duba ta. A wancan gidan kuwa har muka tashi ba ta taɓa zuwa ba. "E. Ta ce ta na son mgana da ke." Haka ya faɗa min kafin ya wuce. "Magana da ni? Na maimaita a cikin raina. "To wata mgana ce? "Ta wuce ta auran Yusuf da Gimbiya" Kamar wahayi haka na ji zuciyata na saƙa min magana. Uhm kawai nace a saman leɓena sannan na bi bayan shi domin na ɗauko hijabina ina shiga na ganshi ya saka riga zai fita ya raɓa ta gefena ya fice ni kuma na shigo ciki na ɗauko hijabin sallah na saka nima na bi bayan shi amma ni sai da na fara biyawa ta kitchen na dauko mata ruwa da lemu lokacin safe ne domin tara ma ba ta yi ba, bayan tafiyar yara makaranta ne ba daɗewa na kwanta a falon da Yallaɓai ya fito ya ganni kwance. *Janafty* *TKG* 05. Da sallama na shiga falon hannuna ɗauke da farantin da na ɗora ruwa da lemu tare da ƙananun kofunan glass a saman shi. Gabaɗayansu a tare suka amsa sallamata ashe Musbahu ne ya kawo ta ya na zaune gefen Yallaɓai a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ɗaya. Ita kuma Nene ta zauna akan mai zaman mutum huɗu ne. Sai da na ja center table ɗin da ke wajen na ɗora ruwan a kai sannan na durƙusa a gaban Nene ina gaisheta ta amsa cikin fara'a lokaci ɗaya ta na ba ni umarni na koma kan kujera na zauna sai na koma na zauna kan kujera mai zaman mutum biyu da ke gefen in da Nene ta ke zaune. "Anty Sadiya ina kwana." Musbahu ya gaisheni yana kallona na amsa ina faɗin kwana biyu idon sa kenan ya na yar dariya ya ce" Yallaɓan na ki ne har yau bai cire min ranar hutu ba shi ya sa bakya ganina" Mirmishi na yi amma ban yi magana ba, yadda Yallaɓai bai kalleni ba nima ban damu da na kalle shi ba domin tunda na shigo falon kansa na ƙasa ya yi shuru kamar wani mara gaskiya. Ko da ya ke ai mara gaskiyan ne tunda menene maraban dambe da faɗa? "Ina takwarata da Maimunatu? An tafi makaranta ko? Kaina na ƙasa na amsa ma da Nene da cewa" E Nene.' Sai ta rausayar dakai kafin ta ce" Allah ya ba da sa'a. Allah ya sa a samu karatu mai albarka." Muka amsa da Amin gabaɗayanmu. Shuru na wani lokaci domin shi Musabahu wayarsa yake ta latsawa ganin haka ya sa na gyara zama ina faɗin" Nene a kawo abun karyawa? Da sauri ta ce" A'a Alhamdulillah. Sai da na karya a gida na fito sai dai in Musbahu ga shi nan." Ta faɗa ta na kallon shi, sai da ya ɗan yi shuru kafin ya ce" Tea kawai matar Yallaɓai." Sai na miƙe ina faɗin bari na je na haɗo masa, har na fice daga falon ba wanda ya ce mini komai, daman already akwai ruwan lipton a cikin fulas, sai kawai na soya masa ƙwai guda uku ina cikin soyan ma ya leƙo ya ce gashi a falon su Jidda sai na ce to ina gama soya kwan na kai masa nan tare da mug da fulas ɗin ruwan zafi sannan na kwaso masa kayan tea ɗin har da buredi. "Sannu da aiki Anty Sadiya." "Yauwa." Na amsa masa ina ɗan mirmishi hannuna na wanke sannan na koma falon wajen Nene na koma na zauna kenan Nene ta kalli Yallaɓai da ke zaune jugum kamar wani marayan da ya zo neman abin sakawa a bakin salati. "Tafida." Ta kira sunan shi sai ya dago ya na kallonta lokaci ɗaya kafin ya ce" Na'am Nene." "Ba mu waje. Zan yi mgana da Sadiya daga ni sai ita." Da ni da shi gabaɗaya mun kalli juna sannan muka juya muna kallon Nene sai ta gyara zama kafin ta gyaɗa kanta lokaci ɗaya ta na ƙara jadadda mganarta. "E haka na ce. Ka ba mu wuri mu yi mgana Tafida." "To Nene." Haka ya faɗa sannan ya miƙe a hankali kamar wanda ƙwai ya fashe ma a ciki haka ya fice daga falon lokaci ɗaya ya na mai rufe mana ƙofar falon a sannu kar ta yi ƙara. Da ga ni har Nene da kallo muka bi shi ni kuma da ita kowa a cikin ranshi ya na da nashi tunani, ni dai ko tausayinshi ban ji ba domin a ganina wannan shi ake kira daga baya kenan an yi sadaka da bazawara. Shuru na ɗan wani lokaci kaina na ƙasa ina wasa da gefen hijabina na ji Nene ta kira sunana. "Sadiya." Sai da na ɗago na kalleta kafin na ce" Na'am Nene." "Na zo ne mu yi wata mgana da ke. Kuma kar ki yi tunanin ko mijinki ne ya turo ne" Na kalleta sai ta gyaɗamin kai kafin ta cigaba da faɗin" Ko ɗaya bai ma san zan zo ba. Bai kuma san da abin da na zo da shi ba, ni ce kawai na yi tunanin na ga lalle ya dace na zo na same ki mu yi mgana baki da baki." "Haba Nene don wannan shi ne sai kin zo da kanki? Ai da kirana kawai za ki yi a waya na je gida na same ki " Na faɗa cikin sanyin murya amma cike da biyayya. Ko ban ɗauketa a matsayin uwata ba na ɗauketa a matsayin uwar mijin da ta haifa min miji na aura sannan uwar mijin da ban taɓa samun matsala da ita ba. Tsakanina da ita akwai girmamawa da mutuntatawa mai yawan gaske. "A'a maganar ta ki ce, shi ya sa na ce gwara na zo da kaina." Ta faɗa ta na kallona, sai na jinjina kai ban yi mgana ba. "Sadiya kan mganar auren Tafida da Saudatu ne." Duk da na san maganar, kuma daman a cikin wani shashe na zuciyata na faɗa min ƙila dalilin zuwan Nenen kenan amma a yadda na ji maganar a bakinta ya sa sai da gabana ya amsa. Wannan abun da ya tokaremin a ƙirji na ji ya taso min amma sai na danne ban nuna komai ba illa kai da na gyaɗa mata amma na kasa iya furta wani abu. "Na san kin ji labari. Tun da jiya Tafida ya je cikin damuwa ya na sanar da ni kin ji labari ba tare da shi ya sanar dake da bakin sa ba." Kaina na sunkuyar domin na rasa ma abin da zan ce, Au ashe daman ya san na sani? Na rasa ma wani suna zan kira Yallaɓai da shi a dai dai wannan lokacin ba ma, kawai kai na rausayar ina jin kamar duk duniya ko marayu ba su kai ni zama a bar tausayi ba. "Ba ki  ce komai ba Sadiya." Nene ta ƙara katsemin tunani da maganarta na ɗago na kalleta itama ni ta ke kallo cikin karantar yanayina rasa abin da zence ne ya sa na gyaɗa mata kai kafin na ce" E. Na sani." "Tun yaushe kika san da labarin? "Tun a ranar da aka ɗaura auren." Na bama Nene amsa kai tsaye sai ta jinjina kai kafin ta ce" Ba zan yi mamaki ba. Domin mgana in ta wuce mutun ɗaya ta fara kirga uku to ba ka isa ka rufe bakin kowa ba, in ka rufe na wani, na wanin ba za ka iya dakatar da shi daga mgana ba. Ba kuma zan matsa sai na ji daga wajen da kika ji ba, zan je kai tsaye kan batun da ya kawo ni wajen ki Sadiya." Kaina dai na ƙasa ina ta wasa da gefen hijabina amma zuciyata zafi ta ke yi, kiran sunana ta sake yi na amsa sannan ta ce" Zan ba ki labarin yadda lamarin ya faru, ba domin ki yarda Tafida ba da gangan ya ƙi faɗa miki ba sai domin na ƙara samar da kyakyawan fahimtar juna a tsakanin ku." Ba tare da ta jira cewata ba ta fara gaya min yadda komai ya fara, ta in da aka hau da kuma ta in da aka sauka ta karishe da faɗin" Wallahi Allah ɗaya ne Tafida ya so na bashi ko kwana daya ne domin ya samu damar sanar da ke, ni kuma na ga duk ɗaya ne, ko ya sanar da ke kafin a ɗaura ko bayan an ɗaura tunda sai daga baya za a yi tariyan. A gabana kuma ya roƙi yan'uwansa da cewa su yi shuru da bakinsu ba ya so ki samu labari a bakin kowa sai daga bakin sa ba ki ga yadda ya ɗaga hankalinsa a jiyan da ya zo ya sameni ya na faɗa min ya haɗu da yayanki har ya yi masa murna sannan ya sanar masa ke kika faɗa masa. Ya damu ya ce ya na jin kunyar ki shi ya sa tun kwanaki ya kasa iya faɗa miki ba kuma domin don ya aikata haramci ba, a'a sai domin ke ɗin kina da daraja da ƙima a wajensa kina da mutumcin da ya ke tsoron ya sanar da ke labarin da zai ɗaga miki hankali, ya na jin kunya da nauyin faɗa miki ya yi aure ba tare da ya sanar da ke kafin auran ba. Yau da safe na kira shi ya sanar da ni bai faɗa miki ba sai na yi tunanin ya kasa shi ya sa ba tare da sanin kowa ba na ce Musbahu ya kawo ni domin ni na zaunar da ke na warware miki dukkan abin da ya faru na kuma ƙara tunatar da ke abubuwa ma su girman gaske da Ubangiji ya ba ki wanda nan gaba kar kishi ya rufe miki ido ki manta da su ko kuma ki kasa kallonsu a wani baiwa ko nasabar da Ubangiji ya ba ki Sadiya." Nene na magana amma idanuwana sun cika da ƙwalla ina ƙoƙarin hana su zubowa a saman fuskata. To bayanin na menene! Ba ta saka shi ya auri ɗiyar ƙawarta ba to ni kuma me ta ke so ta faɗa min? Wannan fa shi ne an cuceka amma ana so a hana ka yin ihu da kuka, har ga Allah na ga baƙin Nene me ya sa ba za ta bari Yallaɓai ya yi mgana da ni kafin a ɗaura auren ba? Sai na ji zuciya ta sosu kuma a ganina ta yi min rashin adalci da za ta ce a yi min kishiya kai tsaye ba ta re da shiri ko tsammani ba." Runtso idanuwana na yi, hawayen da na yi ta riƙewa suka zubomin shar! Duk Nene na kallona amma sai na kasa gefen hijabina ina sharewa a lokacin in za a tona zuciyata daga Uwar har ɗan duk haushin su na ke ji amma ina ƙoƙarin dannewa kuma a saman fuskata ina karyata abin da na ke ji a cikin zuciyata. "Ki yi hakuri Sadiya. Ki yi hakuri." Nene na bani haƙuri ina jin kamar ta na ƙara ma ciwo na barkonu ne, ina ta danne kuka na amma ina share hawaye ne wasu suna ƙara sauka kamar an buɗe famfo tun kuma da labarin auran nan ya zo min ko Yallaɓai ban taɓa zubar da hawayena a gabansa amma yau sai na ji na kasa iya wannan dauriyan ganin hawayen sun riga sun taho kai tsaye sai kawai na barsu suna ta zuba sharr, in suka kwaranya a saman fuskata har suna gangarowa a saman hijabin jikina, Idanuwana suna mai kallon zanen cafet ɗin da ke falon, ina jan hanci irin na masu kuka, so na ke yi na samu keɓewa ni kaɗai na fashe da kuka na yi birgima ko domin na ji sauƙi sauƙin abin da ke suka na acikin zuciyata.   "Ki yi haƙuri Sadiya. Daure na san kishi. Na san kishi ya na da zafi Sadiya amma in aka yi haƙuri za a ci riba wata rana." Kalamanta ya sa na kalleta, tabbas ta san kishi, ita da aka auro ma uku. Kenan itama ta san irin zafin da na ke ji a cikin zuciyata sai na ji na godema Allah a cikin raina ko banza za ta fahimci kwataƙwacin irin ɗacin da na ke ji a cikin zuciyata. Kaina na ƙara maidawa ƙasa lokaci ɗaya ina share hawayen saman fuskata da gefen hijabin jikina muryata har ta fara chanzawa na ce. "Bakomai Nene. Allah ya ba mu zaman lafiya da juna." Ta amsa da Amin Amin cikin mirmishi kafin ta ce" Sadiya wallahi ban yi ma Tafida ta yi auran Saudatu domin na ga kin gazamin ba. Ko na ga shi kin gaza masa ba, sai dai kamar yadda na faɗa miki tsohon kuduri ne a zuciyarmu ni da Hajiya ina kuma son na cika shi kafin na bar duniya shi ya sa auran ya zo bagata tan. Amma wallahi Allah ɗaya kenan ba ki taɓa min wani abu cikin sanin ki ba ko ma kin yi min a cikin rashin sani na yafe miki na sha faɗa a gaban idon ki a kuma bayan idon ki bakomai a tsakanina da Matar Tafida sai mutumtawa da Darajawa saboda haka kar ki saka a ranki ko kin gaza ne, ko kuma na ware ki,  da ke da Tafida da Saudatu ɗaya kuke a wajena, ba bu bambamci a tsakaninku kamar yadda Saudatu ta ke ƴa a wajena kema ƴa ce domin iyayenki ranar da kika zama ɗaya daga cikinmu ni suka ba ma amanarki suka kuma ce min ni uwa ce a gare ki na yi miki gyara in kin yi kuskure tamkar yadda zan yi ma ƴaƴana na cikina ko kin manta Sadiya? Kai na gyaɗa ai ba zan manta wannan ranar ba. Inna Mariya ce ta riƙa jadaddama Nene ƴa suka kawo mata ba suruka ba. Kai na ƙara jinjinawa kafin na ce" Haka ne Nene." Sai kuma na kalleta kafin na ce" Na gaza Nene. Na gaza wajen ba ki jikoki masu yawa daga tsatson Tafida kamar yadda kike so." "Kul kar ƙi ƙara wannan mganar Sadiya. Ba ki gaza ba kin kuma biya ni domin kin haifa min takwara kin kuma haifa min ƴa. Ni ko me na ke nema a duniya da Allah bai ba ni ba? Allah na tuba ni jika wanne ne ba a haifa min ba Sadiya! Ki godema Allah kina da biyu wata ɗayan ma ba ta samu ba shi ta ke nema. Ki kuma gode ma da Allah da ya baki har biyu sai ki yi ma Allah butulci da cewa gazawa ce? Maza ki nemi gafaran Allah domin ya yi miki kyauta ba ki gode masa ki nemi gafaran shi ki gode masa sai ki ga ya ƙara miki da ni'imar da ta fi irin Ni'imar da ya baki a baya." "Astagafurilla. Astagafrilla." Haka na shiga furtawa da sauti, domin sai na ji tsoro kar na batulce ma Allah ya ƙi ƙara min wata haihuwar domin nan duniya ba ni da wani buri sai na ganin Allah ya sake ba ni haihuwa ko da guda ɗaya ne. Zuciyata har rawa ta ke yi in na yi hasashen ƴaƴa biyun da Allah ya ba ni wata rana in ya so zai iya ɗauke kayansa sai na ji jikina har ƙwaƙwalwata ya na amsawa cikin wani yanayi wanda ba ki ba zai iya misaltawa ba. Nene ta ga yanayina ina ta rawan jiki sai ta ce na yi ta kiran sunan Allah har sai na samu natsuwa innalillahi na cigaba da maimaitawa a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai ga shi na dawo cikin natsuwa Nene ta durkusa da kanta ta buɗe ruwa ta zubamin a kofi ta ba ni ta ce na sha da bismillah. Ban yi musu ba na karɓa na sha da yawa na miƙa mata kofin ta karɓa ta maida shi saman farantin sannan ta koma ta zauna ta na kallona ina ta sauke numfashi. Sai da ta fahimci na samu natsuwa sannan ta shiga yi min nasiha mai ratsa jiki da cewa duk abin da na ga ya faru da bawa daga Ubangiji ne kuma duk abin da ya aikata dai dai ne shi ba ya kuskure, mu ƴan adam mu ke kuskure amma shi Ubangiji duk abin da ya yi a garemu mai kyau ne. Ta umarce da shawaran da daaina tunani na fauwalama Allah komai. Wataƙila jinkirin alheri ne nan gaba Ni'imar za ta fi ta baya yawa. Ina gyaɗa kaina cikin gamsuwa ina faɗin. "Allah ya sa. Allah ya sa. Na gode Nene Allah ya saka da alheri" Ta amsa da Amin kafin ta ce" Ina fatan kin fahimce ni. Sannan a mganganuna kin fahimci irin matsayin da kike da shi a zuciyar Tafida ko? Sai na kalleta alamun bangane ba sai ta gyara zama kafin ta fara da kiran sunana. "Sadiya ba ki fahimci irin martaban da ubangiji ya yi miki a acikin zuciyar mijin ki ba? To ko kin fahimta ba ki gane ba. Ni bari na warware miki irin taki baiwar da ubangiji ya yi miki ba ki sani ba." "Sadiya." Ta ƙara kiran sunana na amsa ina kallonta sai ta nuna kanta kafin ta ce" Kin san kishiyoyi uku Marigayi mahaifinsu su Tafida ya auro kafin rasuwarsa? Ba ta damu da mganata ba ta cigaba da faɗin" Zan faɗa miki wani sirrin da ban taɓa faɗa ma ko ƴaƴana ba. Ina yar yarinyata ya ƙara aure a lokacin cikin maimuna ƙarami ne a jikina. Maman farko da kike gani bashi ita a ka yi abokin mahaifinsa ne ya bashi ɗiyarsa. Da maganar da auren tsakani wattani huɗu ne, amma ya kasa faɗamin saboda ya na tsoron tashin hankalina gashi ina da ciki kar wani abu ya samu cikin jikina kar na ɗaga hankalina wani abu ya same ni ya sa bai iya faɗamin da kansa ba sai amininsa marigayi Tafidan Rano ne ya zo ya same ni ya sanar da ni a lokacin sai da ya kalleni kafin ya ce" Hauwa'u ki godema Allah kin yi dacen samun nagartatten mijin da ya ke gudun ɓacin ranki da tashin hankali. Yususa ya ƙi sanar da ke labarin  matar da aka bashi ne saboda ba ya so ya tashi hankalinki wani abu ya same ki, ya na jin kunyar ki matuƙa duk da ba haramci zai yi ba, a lokacin ya ce min Hauwa ba duka maza ne irin Yunusa ba, ba duka maza ke iya jin kunyar matansu kamar yadda Yunusa ke jin kunyarki ba ya sake sanar da ni cewa ba duka maza ke tsoron tashin hankalin matansu ba, saboda haka ki daure ki kuma yi haƙuri ki ba ma mijikin goyon baya kar ki ɗaga masa hankali, ki yi masa alfarman guje ma tashin hankalinsa kwatanƙwacin yadda ya guje ma na ki." Sadiya tun daga waɗanan kalaman da ya yi mini har ya bar duniya da gangan ban taɓa ɗaga masa hankali ba, in ma na ga hankalin shi ya ɗaga ni ce zan zama sillar kwantar masa da hankali, har ya yi duka aure aurensa ban taɓa ɗaga masa murya ba, na yi hakuri na danne saboda wannan nasabar da Ubangiji ya yi min a zuciyar mijina ba na so na bashi kunya. Na ci riban hakurina na zauna lafiya da shi da matansa tun yana rage ni ce giwarsa a cikin gida da waje har kuma ya koma ga Allah hakan bai sauya matsayina a wajensa ba sai ma ya ƙara hauhawa ninƙi ba ñinƙin, faruwan wannan lamarin ya sa kawai in na kalli Tafida sai na ga kamar na ga makwafin mahaifinsa ne a tare da shi, Sadiya ba wai ina faɗa miki wannan ne saboda tausan baki ba. A'a ina faɗa miki ke ma Allah ya yi miki wannan nasibin. Ba kowacce mace ba ce za ta samu miji na jin nauyinta ba, ba kuma kowace mace ba ce ke samun darajawa da mutumtawa a wajen mijin auranta ba. Ba kuma kowacce mace ke iya samun namijin da ke gudun tashin hankalinta da damuwarta ba. Ke Allah ya baki wannan nasibi na kawo miki wanman labarin ne saboda na ankar da ke wasu abubuwa guda biyu zuwa uku." Ta ƙarishe faɗa ta na kallona. Na kuma natsu na ba da duka hankalina a kanta ina sauraranta. "Sadiya." Na amsa da "Na'am Nene." Sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce" Kin ga duk sanyin halin Hauwa na sha yin shari'a tsakaninta da muttaƙa." Ido na zaro ina kallon Nene sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Ba tonon asiri ba ne Sadiya Nasabar da Ubangiji ya yi miki na ke son ƙara tunasar da ke. Sadiya tun auran ku da Tafida bai taɓa kawo min ƙaran ki ko da rana ɗaya ba. Bai taɓa zama ya kushe ki ba sai dai ya yabeki, ke ma haka ba ki taɓa kawo min ƙaran Tafida ba,duk da na san kuna samun matsala domin babu auran da  bashi da matsala sai dai ku binne shi ku kaɗai ba tare da sanin kowa ba. Sadiya wannan ma wata Nasaba ce da Ubangiji ya yi miki, kuma a cikin idanuwana ina karrama wannan ƙimar ta ki." Sai na ji kaina ya yi girma cikin alfahari Nene ba ta bani damar mgana ba ta cigaba da faɗin" To ba na so saboda wata ta zo ki sauya Sadiya. Kin zama turken gidan Tafida duk matar da ta zo daga bayanki sai dai ta ɗora igiyanta a kan wannan turken da kika riga kika kafa shi Sadiya. Kar ki sake da wannan matsayin da Allah ya ba ki na uwargida kan gida, kar ki yi sake da shi ya tashi a banza. Akwai zafi amma ki daure ki gani ƙi ƙi gani, ki ji kuma ki ƙi ji, a zo a gaya miki ki toshe kunnen ki in kika yi haka za ki zauna lafiya, ki ba ma mijinki dama damar da ya ke so daga wajen ki, ki yi ta addu'an zaman lafiya da salama Sadiya wallahi tallahi ba Saudatu ba ko Tafida bai isa wata rana ko halin su na maza ya motsa masa ya tozartaki ba saboda kin tsare mutumcin kan ki, na san Saudatu ke ma na san ki Sadiya in kuka yi hakuri za ku ba da shaidar kyakyawan zurua anan gaba. Ina roƙon ki  da ki riƙe wannan nasabobin da na sanar da ke Ubangiji ya yi miki, ko an yi miki wani abu in kika tuna su sai ki danne zuciyarki ki yi haƙuri in kika yi haka tabbas wata rana sai kin  ci riba in sha Allahu." Kamar hadda haka na haddace kalaman Nene a cikin kaina kuma cikin ikon Allah da kalamanta sai na ji zafin da ke cikin zuciyata ya na raguwa. Ina jin haushin ta da na fara ji ita da Yallaɓai ya na raguwa. Duk da an ce tsakanin miji da mata sai Allah gaskiya ne zan kalli Nasabar da na ke da shi a wajen Yallaɓai na lulluɓe duka sharrinsa a gareni kamar yadda shima ya ke kallon alherina ya lulluɓe sharrina ba kuma wai domin ba ni da shi ba, kowani ɗan adam ya na da na shi alherin kuma ya na da na shi sharrin. Sai kawai na kalli Nene ina murmishi kuma tabbas murmishi daga ƙasan zuciyata ya fito ba a iya saman leɓena ba ne. "Na gode Nene. Kuma na yi miki alkwarin ba za ki ji saɓanin tunanin da kike da shi a kaina ba in sha Allahu." Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Amin. In sha Allahu na gode nima da samu abin da nima na yi tsammani daga wajen ki. Na gode Allah ya yi muku albarka Allah kuma ya zaunar da ku lafiya ya kuma kaɗe fintintunu." Na amsa mata da Amin Amin sai ta ce za ta wuce amma kafin nan na yi ma Yallaɓai mgana kafin ta wuce, ni na tashi na leƙa falon da suke zaune shi da Musbahu na kira shi muka dawo tare wannan karon kasan cafet muka zauna ni da shi gabaɗaya ta kallemu kafin ta ce. " Na ƙara tunasar da Sadiya abin daman ta riga ta sani na auranka da Saudatu. Tafida sauran aikin na ka ne, ka zauna da matarka ku yi mgana ku fahimci juna ku tattauna rayuwarku tare. Dukkanku ina fatan tsamanin abin da na ke tsammani daga gare ku. Allah ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna. Dukkanku da ku da yayanku Allah ya yi muku albarka gabaɗaya." Muka yi ta amsa mata da Amin sannan ta yunƙura ta miƙe ta na faɗin" In ina da rai wata rana ina fatan alheri ya sake dawo dani gidan ku." Muka ƙara amsa mata da Amin. Yallaɓai ya shiga ƙwalama Musbahu kira ni kuma na je na kwaso mata takalmanta na jera mata ta zo ta saka ta na faɗin" Allah ya shi albarka. Allah ya ba ku zaman lafiya." Ni na buɗe mata kofa muka fita har haraba sannan sai ga Yallaɓai da Musbahu, sun fito na buɗe mata gaban mota ta shiga sannan na rufe ina ɗaga mata hannu Yallaɓai kuma ya tafi buɗe musu get har Musbahu ya fita da mota na ga ya tsaya Nene na mgana da Yallaɓai ta window na ga ya na gyaɗa mata kai sannan suka wuce shi kuma ya rufe get ɗin ina tsaye na harɗe hannu a kirji ina kallonsa sai yanzu da na ƙare masa kallo na fahimci ba ni kaɗai na yi raman tsaye ba Yallaɓai ma duk ya rame sai karan hanci kamar bashi ba. Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji yana shafa kumatuna sannan na fahimci ya ƙariso kusa da ni. "Ya dai? Ya faɗa ya na kallona sai kawai na sauke ajiyar zuciya. "Bakomai." Na sauke hannayena na juya zan tafi sai ya riƙo hannuna na dama, na juyo ina kallon shi. Sai kawai ya wuce gaba ya na riƙe da hannun nawa, nima ban kwace ba sai na bi bayan shi. Bai direni ko'ina ba sai a kan kujeran mai zaman mutum ɗaya shi kuma sai ya durkusa a gabana ya na mai riƙe duka hannayena biyu a hannayensa ina kallon shi ya na kallona sai na ji rauni ya na kama ni. Zan iya fashe masa da kuka sai na yi saurin kauda kai, shi kuma sai ya kai yatasun hannuna ɗaya bayan ɗaya a bakinsa ya na sumbata. Kallon sa na ke yi da duka zuciyata ina jin ta na sake buɗewa a karo na biyu na yarda da kaddara wataƙila zantu kan Nene ne suka farkar da ni, wataƙila ba za ta ga laifina ba domin itama ai ta san kishi ta kuma ce ya na da zafi sai an daure. "Sadiya ta."   Ya kira sunana cikin raunin murya sai na ɗaga ido na kalle shi kwarmin idanuwana suna mai cika kwallah. "Sadiya wallahi ban ɓoye miki wannan auran da wata manufa ba, sai domin na kasa.  Na Kasa jarumtar sanar da ke na ƙara aure. Ban san da wata kalma zan yi amfani da shi ba,ban kuma san ta yadda za ki karɓi mganar ba. Ba na so na faɗa miki wani abu da zai ɓata farincikin ki na wannan ranar. Ban san dalili ba sai na ji ina jin kunyarki. Ina jin kamar ban kyauta miki ba, har ma a cikin kwanakin nan Sadiya sai na riƙa ji a ƙasan zuciyata kamar na ci Amanarki ne, don Allah ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki ya fe min don Allah SADIYA TA." Ya ƙarishe faɗa ya na mai ɗora fuskarsa a saman tafukan hannayena ba kuka ya ke yi ba amma ina jin hucin numfashinsa lokaci ɗaya da bugawar zuciyarsa. Yau fa ban san me ya faru dani ba, kamar ruwa ruwa da an fara mgana sai na ji kamar na fi kowa rauni a duniya sai na fara kuka yanzu ma ɗin ma hawaye na ke yi, ina danne abin da ke taso min a cikin zuciya ta. Kai na ƙara yarda da cewa kishi cuta ne kishi masifa ne da bala'i domin a lokacin ji na ke yi ko na ce gani na ke yi yadda ya kwanta a jikina yana lallashina wata rana fa zai kwanta a jikin Gimbiya itama ya na lallashinta ko? Kawai sai na ji zuciyata na rufewa da kanta, ƙuncin da ya fara barina na ƙara ziyarta ta. Bai san ina kuka ba sai da ya ji ɗigan hawayena a saman hannunshi na dama da ya sauke shi a saman cinyata. Da sauri ya ɗago ya na kallona ai sai ya ga ina hawaye wasu na koran wasu da rawan jiki ya miƙe zaune ya samu hannun kujeran ya zauna ya mai sanya yatsun hannunsa  ya na share min hawaye amma kamar sun sani ya na share min wasu suna ƙara ɓulɓulowa. "In kina kuka Sadiya ta. Ni me kike so na yi? Haka ya faɗa ya na share min hawaye, kawai sai na fashe da kuka har da buɗe murya saboda ji na yi kamar in ban fittar da kukan ba zan iya mutuwa, tashi ya yi a ruɗe ya cicciɓeni shi ya koma ya zauna ya ɗora ni bisa jikinsa ya rumgume ya na ta share min hawaye, ya na kuma lallashina ni bai ma san ma lallashin na shi ke ƙara sakani kuka ba, ina shessheƙan kuka na ƙwaɓe hannun shi daga saman fuskata ya ƙara kawowa na ƙara kwaɓewa sai ya tsaya ya na leƙen fuskata da na ke boyeta a saman ƙirjinsa. Sai kawai ya daga hannayensa sama ya na faɗin" To na bari tunda ba ki son lallashin." Saki na ya yi sai gashi na zamiye kamar zan faɗi kasa kuma shi bai riƙe ni ba, gani zan sha ƙasa ya sa na ƙamƙame shi ina kallon shi ya na murmishi ya ce" Na kawo hannu ki ture ni? Ya faɗa ya na kallona wani abi ya soki zuciyata a raina na ce ai in Gimbiya ce ba zai bari ta kai ƙasa ba. Kawai sai sai na ƙara saka masa kuka lokaci ɗaya na saka duka hannayena ina dukkansa a ƙirji bai hanani ba sai da na yi har na gaji sannan na koma na lafe a saman kirjinsa ina maida numfashi hannayena suna zagaye a wuyansa. Sai da ya ga na yi laushi sannan ya saka hannuwansa ya tare ni sosai a saman jikinsa bai sake yi min mgana ba amma hannunsa guda ɗaya da ke bayana da shi ya ke ɗan bubbugamin bayan alamun lallashi, ina ta jan majina da jan numfashi cikin lokaci kuma sai kukan nawa ya ɗauke na koma ina ajiyar zuciya, har kuma na koma na yi lamo idanuwana suna lumshe amma ba barci na ke yi ba. Mun zauna a haka sama da awa ɗaya na san hannayensa da kafafunsa sun gama sandarewa da gangan na ƙi sauka a raina na ce gwara duk na gama more jikin ko ta zo sai dai ta samu saurana.   Kuma na samu natsuwa sosai fiye da tsammani na. Ba tare da ya nuna ya gaji ba na sake shi ya saka hannu zai riƙe ni na ce" Zan ta shi.' Sai ya taimaka min na miƙe hijabin jikina duk ya bushe da ruwan hawaye shima miƙewa ya yi ina gani yana juya wuya da hannayena. Sai da na yi dariyan mugunta a raina, ban ce masa komai ba ya ga na fara ta ku zan bar falon sai ya biyo bayana ya na faɗin" "Sadiya ba mu karya ba fa yau" Sai a lokacin sai kuma ya na mganar na ji cikina na juyawa sai na juyo muna fuskantar juna kafin na ce" In soya ƙwai mu sha tea."? Na tambaya cikin sarƙewa muryan. Ya ƙariso gabana ya kuma saka hannunshi ya riƙo hannayena lokaci ɗaya ya na faɗin" Za ki iya? Ko na kama miki? Kai kawai na gyaɗa masa alamin zan iya. Amma bai bar ni ba duk in da na bi yana bi na, hijabin jikina ma shi ya cire min tare muka soya ƙwanan ko na ce shi ya ma soya a falon yara muka karya dka da shima bai ja ni da hira ba amma zai kalleni da kulawa in ya ga na yi shuru na kasa kurɓan tea ɗin "Are you ok? Da kulawa ya ke tambayata amma ga ni na yi ni da ya yi ma kishiya sai na ga kamar tambayar ta renin wayau ne shi ya sa na bi na haɗe rai, duk da haka bai ƙyaleni ba bayan mun gama shi ya kwashe komai ya kai kitchen ya dawo ya iske ni dafe da kai ya na tambayata na ce kaina ne ya fara ciwo jikinsa na rawa ya je ya kawomin panadol ya ɓallo ya ba ni tare da ruwa na sha ya kuma riƙe ni har bedroom ɗin mu na kwanta na ya rufa ma ƙafafuna blanket. "Ki kwanta ki ɗan huta ina ga kukan da kika yi ne ya sa ka miki ciwon kai." Ya faɗa lokaci ɗaya ya duƙa ya sumbaci goshina. Ya juya zai fita sai na riƙe masa hannu sai ya juyo ya na faɗin" Me kike so uhm? Sai na ce"Ba za ka fita ba ne? "Ko zan fita sai zuwa anjuma." Sai na gyaɗa kai sannan na sakar masa hannu "Menene ko kina son wani abu ne? Sai na girgiza masa kai alamun babu, sai ya ƙara dawowa ya duƙa ya sumbaci bakina, har zai tashi na riƙe masa wuyan rigarsa da hannuna guda ɗaya na ɗago kaina nima na sumbaci bakinsa sannan na sake shi sai kuma da sauri na juya masa baya har ina runtse ido kamar na yi abin kunya na san ya na ta kallona sannan na ji sautin mirmishinsa kafin na ji takunsa da fitarsa lokaci ɗaya ya na faɗin. "Ina son ki Sadiya ta." "Ina sonka Yallaɓai na." Na faɗa a hankali tare da jin wasu tasowar wasu hawayen amma na danne. Ni fa sai yanzu da kishiya ta faɗo kaina na fahimci halin da waɗanda kishi ke saka su kashe miji ko su illata kishiya, a da in na ji labari in ta mamaki ina zaginsu a raina har ina ji ma a tunanina kawai saboda namiji sai mace ta haukace har da kisa. Wato daga ranar da na san Yallaɓai ya zama namu ba nawa ba na fara yi musu uzuri da gaske ba sa cikin hayyacinsu. Sheɗan na ƙawata zafin kishi, ka ji kamar ka yi hauka, ka koma kana ganin hotuna kala kala waɗanda in ba ka da imani tsab za su iya saka ka aikata abin da za ka dawo kana nadama. Ka koma kana ganin mutane dishi dishi tsabar kishi, zuciyata ta riƙa suya ta na kai ka in da in ka hasaso za ka ji kamar kowa ma na duniya ya mutu duk a huta. Ni kaina ba domin Allaah da addu'ar da na riƙa yi da dauriya da tuni an ji kanmu ni da Yallaɓai tsabar yadda na ke jin haushinsa sai sheɗan ya sarrafa tunanina na yi masa illa. "Astagafurillah." Na furta a fili saboda tunanin da ya giftamin a fili na furta" Ya Allah ka sassautamin wannan zafin kishi. Sannan ka  tsare ni da aikata abin da zai jawo min nadama a rayuwata." Na duba wayata ban gani ba sai na tuna na baro ta can falo sai na koma na kwanta na runtse ido ina karanto suratul Jumma'a tirya tiryan ina cikin yin karatun barci mai cike da natsuwa ya kwashe ni ban farka ba sai sha biyu da wani abu na rana. **** Ko da na tashi Yallaɓai ya gama komai na aikin gida. Girki ne kawai bai yi ba shima domin zai je office ne ya ce akwai aikin da zai yi, ya fita ya barni a falo yau har haraba na raka shi, ni kaina na yi mamakin ji na sakayau kamar ba ni ba.  Bayan fitansa ba daɗewa aka kawo naman rago kilo biyu duk da ma muna da sauran naman salla a cikin kakide, sannan ga dambun nama bai ƙare ba Musbahu ne ya kawo min tare da kayan miya da kayan lambu. Daga Yallaɓai ne, kawai sai na samu kaina da tambayan shi ina Yallaɓan ya ke.? "Ya na can office akwai mutanen da ya ke ganawa da su." Har ya bar gidan ina zaune ina tunanin dalilina na tambaya. Me na ke tsoro? Kar ya je wajen Gimbiya? Wata zuciyar ta ce kar ki manta ya aure ta wata rana tare za su kwana a ɗaki ɗaya. Sai na ji hankalina ya tashi amma sai na fara kiran sunan Allah har na samu natsuwa. A raina na saka jarumta sannan zan ɗauki shawaran Nene zan riƙe Allah domim shi kaɗai ne za ba ni ƙwarin gwiwan fuskantar wannan yaƙin da ke gabana. Wanka na fara yi sannan na shiga kitchen na soya naman nan gabaɗaya. Kayan miyan ma na yi blanding ɗin su, na tafasa na ɗiba na yi miya sauran na saka a fridge kafin wani lokaci na gama aikina na gyara kitchen ɗin wajen ƙarfe uku na rana ina falon yara lokacin mun gama waya da Balaraba kenan na ce Saude ta yi zamanta kawai sai gobe  sai ga kiran Hauwa a waya wai gobe ta na nan zuwa na ce Allah ya kawo ta a raina na kuduri niyyar sai na yi ma Hauwa tsinin baki domin ina jin haushin su ita da Munnira. Ina gida har yamma yara sun dawo daga makaranta har sun ci abinci. Mun yi waya da Yallaɓai ya na tambaya akwai kayan marmari? Na ce sun ƙare sai ya ce gashi nan zuwa zai taho dashi. To bayan mun yi mangariba muna azkar da yara ya sake kirana. "Sadiya ta." "Yallaɓai." Na amsa masa a sanyaye. "Ina Gwammaja yanzu haka bayan na tashi aiki sai na biyo zan duba Daughter daman ba ta jin daɗi da safen ma sai da Nene ta ce in na fito na zo na duba ta. To ina sauri ban biyo ba sai yanzu na kuma zo na iske ta ta na ta amai zan kaita asibiti a duba ta yanzu." Cikin danne abin da ke taso min na ce" Subhanallah. Ku je mana a duba ta ka yi mata sannu Allah ya ba ta lafiya." "Amin Sadiyata. Take care sai na dawo " Da haka muka yi sallama ban bari na saka tunanin komai ba muka cigaba da azkar din mu bayan mun gama ni na ɗora da karatun Qur'ani Allah ya cire min lamarin a cikin zuciyata. Kafin Yallaɓai ya dawo na sake wanka na yi masa kwalliya sai tara da rabi ya shigo gidan muna tare da su Jidda a falo muna kallon Cartoon ya shigo gidan suka tashi suna masa oyoyo ya tarbe su ni ma na miƙe ina masa sannu da zuwa ya amsa ya na kallona duk da bai furtamin ba amma na ga jin daɗi a fuakarsa da muryansa da ya ganni cikin kwalliyata kamar ko yaushe. Ledan hannunshi na karɓa zuwa kitchen na cire kayan marmari a leda na saka a frezer sauram kuma na wanke na yayyaka mana a Filet na kawo falon ya na zaune tare da su ya na yi musu hira. "Ya mai jikin? Na faɗa ina zaman gefen jidda, min jera da shi ya na gefen Jidda Baby kuma na kan jikin shi. "Ta ji sauƙi. Ulcer an saka mata drip da mganguna." "Ash. An ba ta gado ne? Na faɗa ina kallonshi sai ya kalleni kafin ya ce" No mun dawo gida. Sun ce dai ta riƙa cin abinci ta shan mganuna nan da sati ɗaya sai ta koma ta ga likita." "Allah ya ba ta lafiya." Ya amsa da Amin Baby sarkin mgana ta fara tambatyan waye ba lafiya? Shi kuma sai ya ce musu Anty Gimbiya ce da ya ke yaran suna son ta daga Jidda har Baby suka fara ma sa magiyan gobe ya kai su suke su duba ta sai ya fara cewa akwai makaranta su bari weekend su sai suje. Ina gefe na ce" Ya yi nisa. Ko da daddare gobe haka Yallaɓai? Na faɗa ina kallon shi, sai na ga ya kalleni kafin ya ce" To shike nan sai mu je ɗin." Suna jin haka suka fara murna. Nan muka bar su da shan su kankana ni da shi muka shiga ciki sai da ya yi wanka sannan na haɗa masa tea na kawo masa abinci tare muka ci tunda ni daman ban ci ba tuni su Jidda suna ɗaki sun kwanta muna ci muna ɗan taɓa hira ya ce min jibi Jumma'a zai shiga Kaduna domin ya duba aikin nan na ce Allah ya nuna mana. Bayan mun gama ya ta ya ni muka kwashe komai zuwa kitchen, muka kakkashe hasken ɗakunan da falo sannan muka koma ɗaki muka yi shirin kwanciya yau dai ban hana shi kaina ba na saki jiki mun farantama juna, muna riƙe da juna cikin yanayi na ma'aurata sai wayarsa ta yi ƙara alamun shigar saƙo sai bayan mun natsa har ma mun yi wankan tsarki ya duba ashe cikon kuɗin aikin da ya yi na gina tiolets da wasu azuzuwaa makaranttun gwammatin kano na tuntuni n a ka turo masa. Sai ya kamani ya rumgumeni ya na faɗa mini. Sai na riƙe shi nima ina mai ta ya sa farinciki. A zahirin gaskiya kuɗin nan ba su iya zuwa lokacin da ya dace ba. a can baya ne na yi zumuɗin zuwansu amma yanzu sai na ji ba na musu zumuɗi ko na so ko ban so wannan kuɗin da su za a yi shirye shiryen tariyan Gimbiya. Ana nufin kishiyar da za a kawo min wataƙila a nan wataƙila a wani gidan na dabam. *Janafty* *TKG* 06. FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622 Yallaɓai fa miliyoyi sun dira a cikin account ɗin sa na banki ba zama. Tun safe ya fita ya ma riga yara fita saboda sauri, bayan kuma tun asuban fari ya fara waye waye da mutane bakinsa ya kasa shuru. Ni fa tun a farkon auran mu tun ina mamakin halin Yallaɓai har ya zame min jiki, in ya yi wani abin na daina ganin sa a sabo a wajena. Tun da na san shi, shi ne mutun ƙwara ɗayan da zan ce na sani mai bayyana ya samu kuɗi a duniya. Kowa sai ya sani daman kuma tun kafin kuɗi su zo zai ta yi ma jama'a alƙwari da cewa in an biya shi kuɗin aikin sa na kaza zai baka kaza, a farkon auranmu na ga lamarin na shi wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara, tu ina yi masa mgana har na gaji na kama kaina domin na tabbatar da halin shi ne, ba zai iya dainawa ba.   Ni dai kafin ya fita sai da na yi masa maganar kar ya je ya yi ta facaka da kudaɗen nan ya rage sauran basukan mutane da suke kansa. Sai ya ce min zai rage daman na Kawu Abba ne mai yawa zai biya shi sai na Tariq da ya karɓa a wannan aikin na kaduna amma shi ba zai biya shi sai an biya shi na kadunan. Sai yaran shi da zai cika ma kuɗin aikin da suke yi rabi ya ba su, wasu ma bai ba su komai ba saboda ba kudaɗe a hannun shi. Ya fita da cewa office zai je amma tunda ya na da kuɗi sai in da mansa kuma ya ƙare ya bar ni ni kaɗai a gida tun da su Jidda sun tafi makaranta suma. Bayan fitan shi ba daɗewa ya kira wayata ya na faɗa min na rubuta list ɗin duk abin da muke buƙata a gida na kayan abinci da sauran kayan amfanin mu ni da yara, sai na amsa masa da to, bayan mun gama wayar na tashi na shiga Kitchen ina duba abin da babu. Sai da na gama gani sannan na koma ɗaki na rubuta a cikin wayata kayan amfanin mu kuma ni da yara sabulun wanka ne na su, sai nawa wanda na siya wajen Lame ya kawo gangara. Sai su man wanke kai da maclean sai izel da klin muna da komai su kaɗai ne suka yi ƙasa, sannan a raina na ce zan tuna masa da kuɗin makarantar yara domin wannan term ɗin ne ƙarshe, in suka yi hutu suka koma akwai biyan kuɗin makaranta. Test ma Jidda ta ce min suke yi sun kusa hutun kirisimet na ƙarshen shekara. Allah ya sa ma ya yi dubara lokacin da zai biya a second term ya biya gabaɗaya na season ɗin. Sanin Saude na makaranta sai in ta dawo ne in ta na da lokaci ma ta ke zuwa. A ranakun makaranta zuwanta ya koma sau huɗu ne kawai a sati. Alhamis da jumma'a sai weekend na san yau za ta zo amma sai wajen biyu na rana, kuma ga shi Hauwa ta ce min za ta zo sai ban kwanta ba na miƙe na yi aikin gidana da kaina ban bari wani tunani ya ziyarce ni ba, karatun Qur'ani na saka a wayata ina ta ji, kuma ina bi da bakina ko kafin goma na safe na gama komai gidana sai kamshin turaren wuta ya ke yi, haraban gidan ne na ga ya yi datti sai na bar shi da cewa in Saude ta zo sai ta share ta gyara wajen.  Wanka na yi na shirya cikin wani leshi na mai sauƙakƙan nauyi, ina falon yara ina hutawa wayata na hannuna ina danne danne, yanzu sai na yini na kwana ban buɗe data ba, ba na so na ga ma abin da zai ɓata min rai ko ya ɗaga min hankali shi ya sa na kama kaina. Ina nan zaune, ba kallo na ke yi ba saboda sun ɗauke wuta yau tun safe ba su dawo da shi ba. Ina ta mamakin ma rashin dawo da shin da ba su yi ba, saboda in suka ɗauke in ta daɗe ba su dawo dashi ba awa ɗaya amma yau sama da awanni uku ba wutar. Karatun Qur'anin na cigaba ji a wayata ina kuma zaune na kishigiɗa a saman kujera a sannu sannu ina bin karatun, idanuwana a lumshe suke sai na ji karatun ya tsaya wayar ta fara vibration alamun ana kirana, a kasalance na ɗan tashi daga saman kujeran da na ke zaune, ina mai buɗe idanuwana da suka yi min nauyi, domin sai na ji kamar barci barci ma na ke ji, hannu na saka na jawo wayar ina duba mai kiran nawa saboda kafin na ɗauki wayar kiran ya katse. "Yaya Aina ce." Da sauri na bi bayan kiran. Bayan ta ɗauka mun gaisa ta na min tsiya da cewa"Uwargida ran gida. Ko kina barci ne? Ina ɗan mirmishi kamar ta na ganina kafin na ce"Barci kuma Ya Aina? Na tashi tun safe." Yara ta tambaya na ce suna makaranta, Yallaɓai kuma da za ta tambaye shi sai da ta yi dariya kafin ta ce" Ina Yallaɓai Ango? Dariya na saka mai sauti kafin na ce" Ya na nan lafiya. Sai dai ya ɗan fita tun safe." Fatan dawowa lafiya ta yi masa sannan ta yi min mganar kan dalilin kiran na ta. "Kan maganar bikin Yashe ne. Yau fa saura kwana takwas. Na fara haɗa gudummuwar ne ina kira ina ƙara tunasar da ku, kema ina jiran na ki, gwara mu haɗa da wuri mu aika musu dashi kafin tafiyar tamu." Kai na gyaɗa mata kamar ta na kallona kafin na ce" Gaskiya ne. To kamar nawa nawa za mu ba da? Ya Aina ta ce" Ban yanke ma mu mata ba. Mazan dai na yanke ma nasu, mu kawai kowacce ta kimanta abin da ta ga za ta iya ba da wa sai kawai kowa ta ba da nata." Nan ma na ce hakan ya yi, mun rabu da cewa za ta ji saƙo tun da ina da acct lambarta sai ta ce min kar na tura a nata Atm ya yi expire sai dai na tura a na Marwa anan ta ke tara kuɗin, in ma sun gama haɗuwa ta na tunanin anan za mu yi siyayya wasu kaya duk da yadda suka ce a yi daga can haka ɗin za a yi. Mun gama waya kuma sai ta bar ni da tunanin nawa ya kamata na ba da, acct balance ɗina na duba kuɗin da ke ciki duka duka 35k ne, shima sun taru ne da kuɗin asibitin da Yallaɓai ke ba ni, wannan zuwan da na yi ma ko na adaidaita bai ba ni ba, ni kuma ban yi masa magana ba, tun da na san ya na yi sai na saka tsarin haka a raina na cewa a ranar ƙila bashi da kuɗin ne. Ga shi nima ina son zuwa bikin nan in na tura 30k gabaɗaya ni ba ni da kuɗin da zan riƙe a hannuna. Kuma a yanzu ba zan iya tambayan Yallaɓai kuɗi ba. Sai na ke ganin kamar komai ya tashi daga yadda na san shi zuwa wani abu na dabam. Na yi ta tunanin mafita ban samu ba sai kawai na ce zan tura 25k, ni sai na riƙe 10k a hannuna na tafiya in Yallaɓai ya ba ni kuɗin mai da sauran su na san zan samu wani abu a ciki ko da in mun je can zan iya ƙara ma mai bikin. Amina na kira muka yi mganar sai ta ce Ya Aina ta kira ta itama jiya da daddare. Ta ce min 20k mijinta ya ba ta ita kuma ta na da 10k za ta ƙara zama 30k kenan ni kuma sai na ce hakan ya yi ta yi ƙoƙari. "Yaya Sadiya ke hamsim za ki ba da ko? Matar Yallaɓai ce da kanta." Ta faɗa cikin zolaya, nima sai na biye mata har kuma muka gama waya ban iya faɗa mata ga abin da zan ba da ba. Yanzu fa ba da ba ne, gani na ke yi kamar an shata mana wani dogon layi tsakanina da Yallaɓai a raina na ji ba zan iya tambayar shi kuɗi ba, ba kuma domin in ya na dashi ba zai ba ni ba. Zan iya  karesa a gaban ko waye, in dai Yallaɓai na da kuɗi nima ina da shi, zai ɗauka ya bani kuɗi kawai na hidimata bayan na hidiman gida zai ba ni sama da adadin da na ce, in kuma na ce masa ina da buƙata jikinsa na rawa zai ba ni sai dai in dan bai  da shi ne gabaɗaya. Na kuma san in na faɗa masa muna da biki a Yashe an yanke mana kuɗi wallahi zai ba ni kawai ni ɗin ce ba zan iya yi masa mganar ba. Tun da yanzu ya zama ba nawa ni kaɗai ba. Na saka ma raina ya zama dole na miƙe na nemi sana'ar yi ko domin wata rana. Tunda in a baya ina tunanin daga ni sai shi sai ƴaƴanmu yanzu kiɗa ya sauya dole ma rawa ya sauya. Ya auro wata kuma in suka fara zama akwai yuyuwar su tara wasu zur'an to abubuwa da dama za su tashi daga yadda suke a baya su sauya wani muhalli yanzu. Nan take ban tsaya ma wani cewa ko zuwa anjuma ba na tura kuɗin, nan ta ke na tura ta acct ɗin Marwa na kira Yaya Aina na faɗa mata na tura 25k ta yi ta godiya da saka albarka sai ta ke faɗa min Ma'u 100k ta turo yanzu itama ita 50k mijinta 50k, na san wacece Ya Aina ba da munafunci ta faɗa ba da dai Ya Murja ce sai na ce da gayya ne, addu'an Allah ya saka musu da alheri na yi, mun rabu da ita cewa zuwa gobe in kuɗin sun haɗu za ta je gida ta gaya ma Alhajimu sai a san yadda za a yi. A bakin ta ma na ke ji Rahila tun ranar talata za ta wuce in ji Ya Muntari a raina na ji kamar nima na shirya na bi tun daga ranar ban taɓa jin ina yin nesa da Yallaɓai ba irin yanzu, kawai ina son na je can wani wajen da zan manta da ƙarin auran sa ma'ana dai zuciyata ta samu kyakyawan natsuwa. Duk da ban tambayi izininsa ba na yanke shawaran zan shirya ina tunanin tare za mu tafi da Rahila. Saboda ma jin haka ni da kaina na kira Rahilan a waya muka yi mgana. Ta ji daɗi da na ce mata ina ganin tare za mu wuce ranar talata ɗin. Bayan mun gama wayar da ita ina zaune ina tunanin wai ba mu da wasu ƴan'uwane daga nesa? Ko a wasu garuruwan? Ko dangin Mama ni dai na san duk suna kano ne, Alhajinmu kuma daga yan tumaki sai Yashe, ina zaune ina tunanin da a ce muna da dangi a can Lagos in na tafi sai an ganni. Sai Gimbiya ta tare Yallaɓai ya gama amarcinsa sannan zan dawo saboda ina jin kamar ba zan iya zama a gidan nan ina ji ina gani Yallaɓai na tafiya gidan wata ya na kwana ba. A cikin daren nan kishi zai iya saka ni na haɗiyi zuciya na mutu, ina zaunen nan ina faman tunane tunane Hauwa ta zo ta na ta buka get ban ji ba sai da ta kira wayana sannan na tashi na je na buɗe mata. Ita kaɗai ta zo yara duk suna makaranta.  A falon yara muka zauna na kawo mata ruwa da lemu sai soyayyen nama da dambun naman da ya yi mini saura. Sauran cincin da cake su Jidda duk sun cinye tare da Yallaɓai ni gabaɗaya ma komai ya fita kaina a bakina ma ina jin kamar na rasa ɗanɗano. Hira kawai muke yi da Hauwa yadda ba ta min maganar ba, nima a raina na kudiri niyyar ba zan yi mata ba, daga ita har Munniran muna nan har azahar sai da muka yi salla ne sannan na ɗora mana taliya fara tunda ina da Miya, na dawo falon kenan sai ta ke ce min da wuri za ta koma gida saboda yara yan makaranta za ta je ta yi musu girki, ni kuma sai na ce sai na da fa taliyan da yawa in ɗibar mata sai ta tafin musu da shi. Nepa sun maido wuta sai na kunna mana kallo a tashar Arewa24 suna haska wani Hausa Film, hiran duniya kawai mu ke yi da Hauwa ta ɗauko min wannan na hira mu bari mu kama wancan. Kuma na lura da magana a bakin ta amma ta kasa yi min kila tana tunanin ko har yanzu ban sani ba ne. Ni kuma daman na ce ba zan yi musu mgana ba in sun yi min sai mu yi ta kare in ba su yi min ba to sai dai a tafi a haka. Ruwan zafin da na saka a gas ya tafasa na je na karya taliya na saka sai na kuma dawowa falon na zauna. Hauwa ta kalleni ni kuma ina ɗan cire abin taliya da ya ɗan shigar min kumba. "Anty Sadiya." Hauwa ta kira sunana, na ɗago ina kallonta amma ban amsa ba, itama sai ta kasa ce min komai, sai na mai da kaina kan abin da na ke yi sai da na cire sannan na kalleta ina faɗin" Kin kirani kuma kin kasa cewa komai. Me ya faru ne? Kai tsaye ta ce min" Wai kina so ki ce min ba ki san wani abu ya faru ba? Sai da na juya baki sannan na ce" Ban sani ba  Hauwa. Wani abu ya faru ne? Na ƙarishe faɗa ina tsare ta da ido, mamakina ta ke yi, ko a har yanzu Yallaɓai bai sanar da ita ba? "Hauwa me ya faru ne? Na faɗa ina katse mata tunani sai ta yi saurin ɗaga hannu kafin ta ce" Ba ruwana. Tun da ba ki sani ba." Mirmishin takaici na yi ina kallon Hauwa kafin na ce" Me ye ban sani ba! Wai na auran Yallaɓai da Gimbiya? Hauwa ta zaro ido ta na kallona kafin ta ce" Daman kin sani? Haushinta ya kamani da sauri na ce" E da ba ku gaya min ba na sani a can duniya ba." Hauwa za ta kwaso rantsuwa na ɗaga mata hannu raina a ɓace ina faɗin" Daman ina jiran ki Hauwa daga ke har Munnira na yi ta tsumayin ku. Ai na ɗauka ni da ku ɗaya ne in kuka ji wani abu a kaina za ku yi saurin zuwa ku sanar da ni amma sai ga shi an yi min kishiya kowa ya rufeni ciki har da ku Hauwa. Kun bani mamaki kuma wallahi na riƙe ku a cikin raina Ubangiji ya gani na ji haushin ku ƙwarai kun kuma nuna min irin na ku zaman tare kenan." Na ƙarishe faɗa ina jin takaicin abin na taso min daga ƙasan zuciyata. Hauwa ta fara rawan bakin rantsuwan itama ba ta sani ba Muttaƙa bai faɗa mata ba daga can Rano ne ƙanwarta ta kira ta faɗa mata. Da ta kira Munnira ta faɗa mata sai ta ce itama ta ji Jamila ta kira ta faɗa mata amma an ce a yi shuru Tafidan bai sanar da ke ba tukunna." Hararan Hauwa kawai na ke yi ta na mgana ganin haka yasa ta ƙara kwaso rantsuwa ta na faɗin" Wallahi ki yarda da mu. Ta ya ya za mu fara sanar da ke wannan labarin mara daɗin ji? Munnira ta ce kar mu faɗa miki mu jira shi da ya kwanto kuran ya ɗaure ta da kansa." Ta ga dai in zaune ina karkaɗa kafa ban ce komai ba sai Hauwa ta yi mirmishi kafin ta ce" To ki yi hakuri tun da kin ji zafin mu." Kai tsaye na ce"Wallahi na ji zafin ku. Kuma waɗanan mganganun ba su saka na daina jin haushin ku ba. Haba a taren mu ya wuce wasa. To ai shi bai faɗa min ba a duniya na ji " Hauwa ta yi ta bani hakuri na ce ni fa ba zan haƙura ba sun ba ni haushi kuma na riƙe su a cikin raina na kuma ce mata wallahi in ita ce ko Munnira haka ya faru da su ba zan iya yin shuru ba saboda a tunani haɗuwar mu ta bangaren gidan aure ɗaya a shekarum da muka yi tare mun ƙulla kyakyawan alaqa a tsakaninmu da duk iskar ko guguwar da ta tunƙaro wani daga cikin mu sai in da karfin mu ya ƙare, ba su koma gefe su bari duniya na yi min dariya ba." "Mun ji mun yi laifi. Don Allah ki yi hakuri." "Ba fa zan haƙura ba. Ko na haƙura to ba zan ɓoye muku ba, na riƙe ku a cikin raina." Na faɗa kai tsaye ina kallon Hauwa da ta yi kalan Tausayi. Ni kuma na ƙara jadaddamata da cewa na riƙe su a raina ita da Munnira na hakura amma ba zan manta da abin da suka yi min ba, ta na jin haka ta ce to ba za ta iya da ni ita kaɗai ba nan ta ke ta ɗau waya ta kira Munnira ta ce ta zo gidana yanzu a she su suna can suna ɓoye min mganar kar na ji hankalina ya tashi ni kuma ina nan gida na ƙullace su. A cikin wayar ma Munnira ta ji ina mita ina faɗin kwarai Ubangiji ma ya sani na ƙullace ku a cikin raina. A she duk sun san abin da suka yi mini ba su kyauta ba muna cin abinci da Hauwa sai ga Munnira. Ni da kaina na je na buɗe mata gida ta na shigowa ta fara faɗin" Haba uwargidan Yallaɓai afuwan." Hararanta na yi kawai na wuce na barta ta biyo bayana itama da na ta mganganun, ni abincin ma duk ya fita kaina ita kanta Hauwa kaɗan ta ci Munnira daman da na yi mata ta yi sai cewa ta yi sai da ta ci abinci ta fito daga gida. "Haba Sadiya wa zai iya tunkaranki da mganar kishiya? Suna mafi muni a wajen mu mata. Tabbas na riga Hauwa jin mganar nan auran domin a daran Jamila ta kirani ta faɗa min ta kuma ce an ce a yi shuru saboda ba ki sani ba. Na shiga ruɗu da tashin hankali Sadiya lokacin da Hauwa ta kirani da niyyar wai mu shirya mu zo mu faɗa miki na ce a'a kar mu yi haka, ke ba za ki manta da mu a matsayin waɗanda suka sanar da ke labari mafi muni ba, sannan Tafida zai ta ganin baƙin mu. Mazajenmu kuma za su  ji haushin mu domin mun shiga hurumin da namu ba. Sadiya ki kalli dalilinmu ta fuskar fahimta ki yi mana uzuri, in kin ƙullace mu wannan ba laifi ba ne hali ne na ɗan adam saboda kina ganin har da mu aka munafunceki, amma kin ji dalilinmu ki yi duba da tsaka mai wuyar da muke ciki ki yi haƙuri zuciyarki ta yi sanyi a kan mu don Allah." Kallon Munnira kawai na ke yi har ta dire mganarta ban ce komai ba.  Ganin haka ya sa ta gyara zama a saman kujera mai zaman mtum ɗayan da ta ke fuskata ta, ta cigaba da faɗin" Ni fa sai dai ki yi ta ƙullatana Sadiya amma Allah ɗaya ne wallahi tallahi ba zan iya fara iya taran ki da labarin Yallaɓai ya ƙara aure ba. Hauwa ma ni na ƙwabeta. Gwara shi da kansa ya sanar da ke zai fi sauƙi." Kai na gyaɗa kafin na ce" Uhm to ai da ba ku sanar da ni ba shima bai faɗa min ba a daran aka kirani aka sanar da ni." "Waye don Allah.? Har Munnira da Hauwa suna haɗa baki wajen tambayata ko wace ce kai tsaye na ce musu Ma'u ce, ita Munnira ba za ta gane wace ce Ma'u a wajena ba Hauwa ta fi sanin ta ita ce ma ta yi mata bayanin matsayin Ma'un a wajena da ta in da suka haɗu da Anty Bahijja suke aminta. Munnira ta lailaya wata aashar kafin ta ce" Kai mutane ba su da kyau. Ita yanzu sai ta zaɓi bare a kan ki Sadiya? Ta na yar'uwanki ta kira ki ta na sanar da ke wannan baƙin labarin? Ina murmishin takaici na ce" E mana. Ita ai daɗi ta ke ji,da kuma gayya ta kirani ta sanar da ni hakan" "Amma wallahi ba ta kyauta  ba." In ji Hauwa. "Kai gaskiya ta yi asara." In ji Munnira.  Sai kawai na kalle su amma na kasa mgana saboda wannan tuƙiƙin dake zuciyata yanzu ke taso min da aka ta da mganar. "To wai shi Yallaɓai har yanzu bai sanar da ke ba? Munnira ta tamnayeni ta na kallona, jikina a sanyaye na ce" Bai sanar da ni da bakin sa ba sai bayan Nene ta zo gidan nan jiya ta sanar da ni da kanta." Gabaɗayansu suka waro min ido suna haɗa bakin faɗin" Ita Nenen? Sai suka ba ni dariya har sai da na dara kafin na gyara zama ina ba su labarin abin da ya faru tun ranar da aka ɗaura auran na dai ɓoye musu abubuwan da suka shafi siirun auran mu, amma na sanar da su duka mganganun Nene a kaina da shi kuma abin da Yallaɓan ya ce min a jiya na ƙarishe da cewa" Ni dai har yanzu bai ce min komai a kan Gimbiyar ba." "Tiƙashi.!" Munnira ta faɗa ta na sauƙowa ta yi zaman dirshan saman cafet. Ita daman Hauwa daman tuntuni a saman cafet ɗin ta ke zaune. "Wai daman ashe haka kishi ya ke? Kishi na da zafi da ƙuna. Wallahi ban taɓa sanin raɗaɗin kishi ya kai ƙunar haka ba sai yanzu da ya faru a kaina." Na faɗa ina jin numfashina na sarkewa. Hauwa da Munnira suka kalleni cikin tausayawa amma sun kasa mgana. "Ku yi ta fatan Allah ya bar ku da mazajenku har abada. In kuma kaddara ta saka sun ƙara ku fara addu'an salama da sanyin zuciya tun yanzu domin ban sam da abin da zan yi iya kwantanta muku zafin da ke cikin a yi maka kishiya ba. Ballatana kishiya irin tawa wacce ta zo min a cikin bazata. Wallahi ban taɓa tsammamin Yallaɓai zai ƙara aure a wannan gabar ba. Ban kawo hakan a raina ba kwata kwata ba." In na so na daure amma na kasa sai kuka, na dukar da kaina a cikin cinyoyina ina ta kuka Munnira ta taso zuwa kusa da ni ta zauna ta na lallashina. "Ki yi haƙuri Sadiya. Ki daure." "Ki daina kuka don Allah Anty Sadiya. ji na ke yi kamar na ta ya ki kukan wallahi" Hauwa ta faɗa a muryanta itama kamar ta yi kukan Lallashin su ma ƙara sakani kuka ya ke ganin na ƙi yin shuru ya sa Munnira ta ce Hauwa ta tashi su tafi tun da kuka suke sakani jin haka ya sa na haɗiye kukan da ke taso min. "Gaskiya Nene ba ta kyauta ba. In hae abin da ta faɗa gaskiya ne ba ta ɗauke ki a ƴa ba. In ke yarta ce sai ta saka a yi miki kishiya! Na fi ganin laifinta sama da laifin Yallaɓai, domin ita uwa ce umarninta sama ya ke da umarnin kowa." "Gaskiya ne. Nima dai haka na ce a raina. Ina laifin ta bari in ya zo ya faɗa miki sai a saka rana tun da ta matsa sai an ɗaura." Hauwa ta faɗa kai tsaye Munnira ta gyara zama ta na ƙara faɗin" Ni fa ban iya shuru ba, har Nasir sai da na yi ma ƙorafi namiji ne kuma ɗan'uwansa ne shi kan shi ya ce ba a kyauta miki ba, ya kamata a fara ba ma Tafida lokacin da zai yi miki mgana da ke haƙƙin ki ne mganar wai da ke da Gimbiya ɗaya ta ɗauke ku ta faɗa ne kawai amma Ke suruka ce a wajenta matar ɗan ta. Gimbiya kuma ƴa ce a wajenta kuma suruka gaskiyan mgana kenan, sauran mganganunta kuma gaskiya ta faɗa ko Nasir ya ce ya na da kyakyawan shaida a kan Yallaɓai na daraja ki, na yarda da duka Nasabobin da ta ce Ubangiji ya ba ki amma kar ki sake ki ji a ranki da cewa Nene da yayanta za su ɗauke ke da Gimbiya ɗaya. ba gaskiya ba ne Sadiya. Kawai dai a yi sha'ani an cuci na ƙauye." Duk fa abin da ta faɗa gaskiya ne. Ni daman ban isa na haɗa kaina da Gimbiya ba kuma ko Nene ta so ta ɓoye laifinta gaskiya ɗaya ce daga ƙin ta sai ɓataa ta yi son kai a wannan lamarin daga baya ne ta ji kunya ta zo ta na gyaran zence. Yadda Munnira ta tsani kishiya ina tunanin in ita ce aka yi ma irin auran Yallaɓai da Nasir da Duniya ta gama jin kansu. Faɗa min ta ke yi na saka a raina kawai ni girman ne Allah ya ba ni na kama kaina amma ba ta ce na zauna a takani ba duk da ta san halina. Hauwa dai ta na gefe yar cewa gaskiya ne, sun daɗe a gidana sai wajen biyar na yamma na raka su har bakin titi suka samu adaidaita sahu. Kafin tafiyar su har mganar tafiyata Yashe na yi musu Munnira ta ce wallahi gwara na je na huta ko na samu salama mganar tariya suka yi min na ce ban sani ba Munnira ta ce da an tsaida lokaci na sanar da su za su dawo mu ma shiri za mu yi duk da ta sanni ni ɗin a shirya na ke, sai dai kawai na ƙara sabon shirin. Na ji daɗin zuwan su kamar kar su tafi haka na dawo gida ni kaɗai duk sai na ji kewa, Allah ya taimake ni Khaleesat ta kirani a waya muka kusa awa muna hira. Kan dai maganar auran Yallaɓai ne itama faɗa min ta ke yi ta yi mamakin auran nan gaskiya. Duk daɗewar da muka yi muna waya shawarwari ta ke ba ni, na kama kaina na ƙi ji na ƙi gani, da sauran shawawarin masu girma ciki daman shi ne haƙuri sai na ninƙa haƙuri domin zan ta ganin abubuwa. Kowa fa maganarsa kenan akwai zafi sai na daure, kuma kowa kalmarsa kenan sai na yi hakuri wato an san cewa lamarin akwai zafi akwai ciwo an kuma san zan ta ganin abubuwa sai na yi haƙuri ni dai fata na Allah ya sa har Yallaɓai ya yi gangancin cewa a nan gidan za ta zauna domin a lokacin ne zan yi abin da ba a yi tsammani ba. Gidan nan gidan shi ne amma kuma ya zama gidana tun da domin ni ya gina shi, in ina ma tuna yadda a ka gama gidan har na tare a ciki sai dai kawai na kaina  wani abun gwara ka bar shi a rufe bayyana shi ba shi da amfani. Sai da su Jidda suka dawo makaranta gidan ya ɗan min daɗi. Yallaɓai tun safe da ya fita sai bayan isha'i ya shigo gidan da tarkacen su cakulate da ice crean ɗin da ya siyo ma Baby. Ya na dawowa ya yi wanka sannan ya ci abinci farar shinkafa na dafa masa tun da shi ba ya son taliya, ya na gama ci ya ce su Jidda su shirya za su je Gwammaja domin duba Gimbiya ni har na ma manta da maganar amma shi ya na nan sane. Yaran ko suna ta murna ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah. Yallaɓai ya sha shigan ƙananun kaya rigar fara ce haka wandon kuma baki ne har da saka rufaffen takalmi da daddaren kamar wanda zai je taɗi! A raina kuma sai na tuna ai ya na da Amarya shi ke da ko babban taɗi adon ma domin ita ya yi shi ya sa gabaɗaya na yi kici kicin da raina. Lokacin da za su fita na rakasu har bakin ƙofar falo, har Yallaɓai ya fita yaran sun yi gaba suna ɗaga min hannu har na ba ma Jidda Soyayyen nama na ce ta kai ma Nene ina tsaye riƙe da kofar falo na kasa tafiya sai na ji kamar an dasa ni. Kawai sai na ga Yallaɓai ya dawo sai ya ganni a tsaye riƙe da ƙofa sai muka tsaya muna kallo kallo. "Lafiya! Ko ka yi mantuwa ne? Na tambaye shi ganin ya na kallona. Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" E. Na manto waya ta a ɗaki." Sai na juya na ce bari na ɗauko masa a can bedroom ɗin mu ya barta ina ɗauko ma sa wayar hannuna tsautsayi ya sa na ta ɓata sai hasken ta ya kawo, idona ya hango min Daugther 3 missed call. Da sauri na danne gefe hasken wayar ta ɗauke, da sauri na koma na kai masa wayar ya karɓa ya na kallona kafin ya ce. "Thank you." Ya faɗa lokaci ɗaya ya na zura wayar cikin aljihun wandon shi sannan ya ɗago ya na kallona, idanuwana na ware masa ina kallonsa da sigar tambaya. "Ba damuwa in muka bar ki a gida ke kaɗai.? Sai kawai na tsaya ina kallon shi a fuskarsa na gama nazarin abin da ya ke nufi da maganarsa amma ban nuna masa na gane in da ya dosa ba. "Babu." Na bashi amsa a takaice, ya fita ni kuma na ja ƙofar zan rufe sai ya kira sunana. "Sadiya ta." Sai na dakata ina kallon shi har ina gyarawa tsayuwan yadda zan yi ma Yallaɓai tijara in har ya sake ya ce na shirya mu je gaida amaryansa sai Allah ya ƙwace sa bai ce ba. "Bar shi ma. In dai na dawo za mu yi mgana." Sai na gyaɗa kaina lokaci ɗaya ina faɗin" A dawo lafiya." Daga haka na maida kofa na rufe na koma can falon yara na zauna, ba na son damuwa ya sa na ɗau romot ina yawo a tsakanin tasha she, har dai na tsaya a Mbc2 suna haska wani american film mai kyau shi na tarrara ma hankalina gabaɗaya nan saboda kallon da ya ɗau hankalina ban ma ga daɗewarsu ba, sai da na ji kiran Yallaɓai a waya sannan na ga duba lokaci goman dare har ya gota. Yallaɓai na min ƴar murya wai ya siyo min tsire ko kaza? Ni ko na ce muna da sauran nama. "To ko fura ba za ki sha ba? Kar ya ga na ture ƙoƙarinsa sai kawai na ce ya siya min kawai furan, ba su shigo gidan ba sai goma da rabi na yi mamakin ganin har Baby ba ta yi barci ba na ɗauka acan ma za su fara barci,sai dai suna dawowa ta ce min Umma ina jin barci na ce ta shiga ciki mana ta kwanta. Jidda kuma na ce ta ta ya Baby ta cire kayan jikinta ta saka na barci, ni kuma da na yi ma kaina tsiya domin furan da Yallaɓai ya siyo min ita na sha na kwanta kuma na ji daɗin furan bakina ya yi min daɗi sosai. Kafin mu kwanta ya ce ina abin da ya ce na rubuta sai na nuna masa a wayata. "Kin tabbata su kenan muke buƙata? Ya faɗa ya na kallona lokacin dukkanmu muna saman gado amma ba mu kai ga kwanciya ba. "E yanzu dai su kenan gaskiya." "Bari da safe sai na tura can singer. Na ku kuma zan saka miki kuɗin in sha Allahu." Na amsa masa da Allah ya kaimu amin, har na juya zan kwanta na ji ya kira sunana. "Sadiya." Sai na juyo ina kallon shi kafin na amsa masa. "Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Yau Nene ta yi min mganar tariya. Ta ce in son samu ne zuwa karshen watan nan." Gabana ya faɗi amma ban nuna masa ba. Sai kawai na kalle shi kafin na ce" Allah ya nuna mana." "Amin. Ita ma Daughter na yi mgana da ita yau. Ta ce ba ta da matsala ko yaushe ne." Ya na mgana ne ina kallon shi kawai ina ganin kamar almara. Wai yau ni Yallaɓai ke maganar watar matar tasa da ni turƙashi! "Shi ne na ce a bari na zo gida na ji na ki tsarin? Lokacin ya yi miki? Sai kawai na yi mirmishin, mirmishin da iyakarsa saman leɓena. "Ni miye na wa a ciki? Tun da Nene ta amince da ita kanta Gimbiya ni me zan ce? Allah ya nuna mana." "Akwai na ki a ciki mana Sadiya." Ya katse ni, sai kawai na ƙura masa ido ba tare da na yi magana ba. "Saboda ke matata ce kuma kina da haƙƙin na sanar da ke abin ke faruwa kuma na ji ra'ayin ki" "Oh! Haka ne? Na faɗa ina kallonsa in zai lura kallon kar ka raina ma kanka wayau na yi masa ban sanin masa in ya gane. "E. " Ya faɗa ya na kallona saboda ba na son maganar ta yi tsayi ya sa na gyaɗa kaina kafin na ce" To na ce komai ya yi. Allah ya nuna mana." Ya amsa da Amin amma a sanyaye, juya masa baya na yi ina gyara kwanciyata. "Zuwa da safe za mu ƙarishe maganar." "Allah ya kaimu." Na amsa masa mganar, da ace bai matso kusa da ni ba, ko ta kanshi ba zan yi ba amma sai na ga ya rarrafo ya matso kusa da ni muka kwanta a jikin juna duk da ba mu yi komai ba amma mun kwanta tare mun kuma tashi tare, da sassafe ya  ta fi kaduna tea kawai ma ya iya tsayawa ya sha ko yara yau ba su riga shi fita ba. Tafiyar ta sa ba ta kwana ba ce amma da yamma ya kira ni ya ce ya yi dare kuma akwai abin da zai tsaya ya yi a goben shi ya sa zai kwana sai ranar asabar zai dawo na ce Allah ya kaimu. Ranar asabar ɗin ma sai yamma ya dawo ya na can kadunan aka kawo kayan abinci ni ma ya turamin kuɗi na abubuwwn da na ce masa ba mu da shi, ban je kasuwa ba ni dai na kira Aisha lame na siya lotion da shower gel, Marwa na kira ta zo na ba ta sauran saƙon bayan na rubuta mata, haka kurum na ji ba na son fita ko nan da kofar gida saboda ji na ke yi kamar ba ni ba. Duk yadda Yallaɓai ya so mu zauna mu yi mgana na ƙi ba shi fuskar hakan, cikin haka ne ma na faɗa masa maganar tafiyar mu Yashe biki bai hana ni ba daman na san ba zai hana ni ba, ranar lahadi da daddare na faɗa masa tafiyar na kuma ce talata ya ce Allah ya tsare sai washegari litini bayan yara sun tafi makaranta ya na tashi daga barci kamar da ni ya tashi a ranshi ina kitchen ya leƙo ya kirani sai na wanke hannuwana daman ina fere doya ne, itama ta ƙare jiya Yallaɓai ya aiko Musbahu da ita tare da dankalin turawa da na hausa.   Hannuna ya kama ina bin sa a baya har cikin bedroom ɗin mu ya zaunar da ni a kan gado shi kuma ya ja kujeren madubi ya zauna a gaba na ya na kallona. "Me ya faru? Na tambaye shi ina kallon shi cikin mamaki. "Me ya sa ki ke gujema mganar da na ce za mu yi? Ajiyar zuciya na sauke domin ya riga ya ritsani ba ni da mafita sai kawai na amshi laifina. "Ka yi haƙuri." "Na yi. Na yi Sadiya ta." Ya faɗa ya na min mirmishi. "Ina jin ka. Me zamu tattauna? Gabana na ta faɗi, saboda karshen wata saura kwanaki ne kaɗan. Sati biyu ma ba wani abu, ina tsoron na ji wata mganar da za ta tada min hankalina. "Kan mganar tariyan Daugther ne daman." Daugther. Daughter ƙaniya. Ai wani daughter da Daddy duk ta ƙare yanzu tun da an ɗaura auren. "Maganar gidan da za ta zauna ne daman." Ras! Haka na ji, fargaba na taso min sai kawai na kalle shi ban yi magana ba. "Na saka a nema min haya gida. Jiya dai an kirani an samu wani a can anguwan Taurani sai wani a sharaɗa yau na ke so mu je da ita ta ga gidan" Na ɗago ido ina kallon shi sai ma rasa me zan ce masa? To wai me ya rage ne? Ni fa duk wannan ga ya min fa Yallaɓai ya ke yi bai burgeni ba da ya sani da ma ya yi shuru da bakinsa ni a wajena da ya fi. Ko kaɗan ban ganin kirkinsa ta wannan fannin Amma dai na samu salama, tunda dai ba tare za mu zauna ba. Daɗin abin ma ta na can wata anguwar mai nisa da in da na ke, gwara hakan domin gwara kazantar da ba ka gani ba akan kazantar da agaban idanuwanka ya ke faruwa hausawa dai sun ce ƙazantar da ba ka gani ba sunanta Tsafta. *Janafty* *TKG* 07. Kamar a zahiri kallonsa na ke yi amma a baɗini ba shi na ke kallo ba. Hankalina da tunani ya yi nisan kiwo. Jikina gabaɗaya ya saki sai na ke jin kamar ba zan iya ba, kamar za'a ga gazawata in tafiya ta yi nisa. "Kin yi shuru ba ki ce komai ba Sadiya." Shi ya katse min tunani da ya sa na dawo hayyacina. Ajiyar zuciya na sauke kafin na maida hankalina zuwa ga kallon ƙasan cafet ɗin da ke gefen gadon. Ina so na yi magana amma sai na ji kamar an ɗaure min baki zuciyata ta yi wani irin nauyi sannan numfashina sai na ji kamar ya na sarƙewa sai na buɗe baki da niyyar magana sai na kasa sai da na ƙara sauke ajiyar zuciya na fitar da iska daga bakina sannan na fara jin ina dawowa cikin hayyacina. "Are u ok? Wani kallo na yi masa, tsabar ma Yallaɓai ya raina min wayau ya zaunar da ni yana min labarin kishiyan da ya yi min shi ne kuma ya ke tambayata ko ina lafiya? Kaɗan rage ban ce masa ban sani ba amma sai na danne zuciyata kamar yadda na saba amma ni kaina na san ina yi ma zuciyata gaddama sannan ina faɗin saɓanin abin da ta kitsa min. "To me zan ce? Haka na faɗa ina kallon sa, sai ya ƙure ni da ido, ni kuma sai na maida kaina ƙasa sai ma na kama wasa da zoben zurfan da ke hannuna. Ba tsammani kawai na ji ya riƙo hannayena cikin tafukan hannayensa sai na ɗago ina mai sake kallonsa a cikin kwarmin idanuwana akwai alamun taruwan ruwa, amma duk ƙoƙarina domin na hana su bayyana ne a gaban Yallaɓai a karo na biyu ne shi ya sa na ke ta ɗagagga ido na sama ina ƙokarin maida kukan da ke ƙoƙarin taso min. "Me za ki ce haka Sadiya ta? Ke ko ke da abin cewa? "Ko? Sai ya gyaɗa min kai ya na mai ƙara damke hannayena cikin na shi. "Saboda me? Haka na tambaye sa saboda sai na ga kamar Yallaɓai so ya ke ya kureni to in ba ƙurewa ba, ina ruwana da labarin hayan gidan da zai kama tun da ba ni zan zauna a gidan ba, abin da ya shafe shi, shi da Gimbiya ne. "Na faɗa miki ki daina cewa saboda mene Sadiya. Kar ki manta ke fa matata ce. Kuma uwar ƴaƴa na." "Sai me? Haka na faɗa, lokaci ɗaya ina ƙwace hannayena daga cikin na shi, sai ma na miƙe tsaye lokaci ɗaya ina faɗin" Don ina matarka sai me? Me ka ke so na ce? Duk abin da zan ce ai na gama cewa tun a baya Yallaɓai." Na ƙarishe faɗa ina mai kallon shi. Ya na shirin sake magana na yi saurin ƙara tare shi da cewa"Allah ya sanya alheri." "Amin" Na ji Yallaɓai ya faɗa, har na juya zan fita daga bedroom ɗin jin abin da ya ce ne, ya sa na juya ina yi masa wani irin kallo, ganin irin kallon da na ke yi masa ya sa wajen ya kwaso maganar da za ta kare sa sai ya ƙara yaɓa ma kansa ɗanyen kashi. "To ko za ki zo mu je Tare ne? "Mu je ina? Na faɗa a zabure saboda sai na ji kamar Yallaɓai na shirin dukana da bulalan kalamanshi ne. "Duba gidan mana." Ya faɗa ko kunya, sai na ƙara jin kamar ya watsa min ruwan sanyi sai da tsikar jikina suka ta shi yam! Kallon Yallaɓai na ke yi da dukkan zuciya wai daman wanna ne cin mutumcin irin na mazan irin sun ƙara aure! Wato ni tun kafin ma tafiya ta yi nisa Yallaɓai ya fara ƙokarin nuna min na shi halin, wata irin zuciya ce ta yunkuro min kawai sai na dawo gabansa na tsaya ina kallonsa ido cikin ido kafin na buɗe baki da na ke jin tsabar zafin da ke cikin zuciyata ina jin hucin sa daga cikin bakina. "Me ka ce? Sai ya yi shuru ya kasa maimaitawa ganin yadda na yi, mirmishi ya yi ya na ƙokarin ya mai da maganar ta sa wasa. "E. Ki shirya mu je mu duba gidajen tare ai ba wani abu ba ne ko? Ban san na ɗaga hannuna ba sai da na ga ina nuna sa da yatsa manuniya. Cikin kakkausan muryan da Yallaɓai ya ke daɗewa bai ji ni na yi masa magana da ita ba na buɗe baki na kira sunan shi. "Yusuf." Haka na faɗa ina masa gargaɗi da ido, shima jikinsa ya yi sanyi domin ya san duk ranar da na kira shi da sunan Yusuf ya san ba zaman lafiya a tsakanina da shi. Miƙewa tsaye ya yi cikin kwaso maganarsa. "Tsaya ki ji. Ni fa ba da wata manuf.." "Yusuf ko dai ni ce zan tashi daga wannan gidan Amaryanka ta zauna, ni kuma gidan hayan da za ka kama shi ne nawa? Na faɗa ina mai tsare shi da ido, ƙokarim riƙe ni ya ke na yi baya ina mai ɗaga masa hannu, faɗi ya ke yi cikin rawan murya wai shi ba haka ya ke nufi ba a fusace na ce" To in ba haka ka ke nufi ba! Me ka ke nufi da na shirya mu je duba gida tare? Ina ruwana da maaganar duba gida? Ko ya shafe ni ne? Na ƙarishe faɗa cikin tsawa ina mai zazzaro masa ido. Sai kawai ya sarke hannayensa duka biyu a saman ƙirjinsa ya na faɗin" Ba ki fahimce ni ba ne Sadiya. Ni fa ba da wata munafa na faɗi haka ba, saboda kar ki ji ba daɗi ne ya sa na ce haka amma tun da ranki ya ɓaci ki yi hakuri." Ya faɗa cikin ƙasa da murya shi kan shi jikinsa ya yi sanyi, sai da na yi masa mirmishin jin haushi sannan na yi baya ina mai riƙe kuguna kafin na ce" Ni na zama a bar zolayan ka ne Yusuf? Ko bashi daman mgana ban yi ba na cigaba da faɗin" Ina ruwana da abin da ya shafe ka kai da amaryan ka. Ni abin da ya shafe ka ne ya zame min dole na ji ba wanda ya shafeta ba, in ka na so mu zauna lafiya a gidan nan ni da kai to ka cire ni cikin wannan lissafin na ka. Mgana in ta shafe ka ba ni da yadda zan yi amma in ta shafi amaryaanka ne ka cire ni a ciki saboda babu ruwana a ciki na faɗa maka." Na faɗa ina mai sake nuna masa yatsa cikin gargaɗi. "Laifi ne domin na faɗa miki! ? Ba na so ki ji labari a waje ba za ki ji daɗi ba." "Na ji a wajen mana Sai me? Na tare shi cikin tsawa kafin na cigaba da faɗin" Sai me don na ƙarishe jin sauran labarin daga waje? Auran ma ai shi kanshi daga wajen na ji to saboda haka ma wannan ka daina zaunar da ni ka na ɓata min lokaci ka na gaya min, ka bar na ji daga wajen ya fi min da ka zaunar da ni kana tattauna abin bai shafe ni da ni ba." "Ni  al'amarina bai shafe ki ba Sadiya.? "Na ka ne ya shafe ni, amma na ta bai shafe ni ba. Saboda haka ka koya ma kanka ɗaura kowa a mizanin matsayin shi in har kana son zaman lafiya." Kallona ya ke yi, ni ma shi na ke, domin a lokacin ina jiran ya ƙara cewa tak ne a kan mganar Gimbiya ya ga hauka amma sai na ga kawai ya koma ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin" To shi kenan ki yi hakuri ba zan ƙara ba." "Better." Na faɗa ina mai juyawa zan bar masa bedroom ɗin, har na riƙe handle ɗin kofar sai na tuna da wani abu da sauri na juyo ina kallon shi, shi ma ni ya ke kallo sai kawai ya ga na dawo gabansa na tsaya kafin na kira sunan shi. "Yusuf" Kallona kawai ya ke ba tare da ya yi mgana ba. "Abin da ka ke yi ba shi zai goge taɓon ka yi min kishiya ban sani ba. Sannan ba shi zai goge taɓon ka yi min kishiya a lokacin da ban yi tsammani ba, ba kuma shi zai goge wannan taɓon da ka yi min a cikin zuciya ta ba. Ni dai na yi ma kaina alƙwarin ba za a ji  wani abu daga bangarena ba, amma ka sani duk abin da za ka yi ba zai taɓa goge taɓon ka shammace ni shammatan da ban taɓa tsammani daga gare ka ba, gwara ka yi harkan gaban ka kamar yadda ka saba, kar wajen ƙokarin kare kanka ka ɓata komai Yallaɓai. Gwara kawai mu tsaya a hakan ba na son wannan jaye jayen maganar naka domin ni ba burgeni ka ke yi ba sai ma haushin ka da na ke ji, gwara tun kafin rayuwankan mu su kai ga ɓaci gwara mu kiyaye ma juna." Na faɗa ina mai kallonsa cikin ido, ajiyar zuciya kafin ya ce" In sha Allahu." Ban tsaya bi ta kansa ba na fice har ina bango masa kofa kitchen na koma ina aikina ina masifa ni kaɗai ba ta yuyu kawai na zauna Yallaɓai na raina min hankali gwara na yi ma abin tufkan hanci ko zai gane duk kallonsa kawai na ke yi, ban kara komawa Bedroom ɗin nan ba har sai da ya yi wanka ya fita, na yi masa ta yi abin karyawa ya ce min ba zai ci ba, ko ta kan shi ban bi ba ya ce min zai fita ana jiran sa na ce Allah ya tsare. Sai da ya fita na koma bedroom ɗin na gyara sannan na wanke kaina saboda ina so na yi kitso sannan na yi wanka. Ban ko faɗa masa gobe ne tafiyarmu Yashe ni da Rahila ba sai in  ya dawo, sai yanzu ma na ƙara jin tafiyata ma ta zama dole ni ba zan zauna Yallaɓai na neman kashe ni da baƙin ciki da kalamansa ba. Mai kitsona na kira a waya na ce mata ta zo anjuma ta yi min kitso, su Jidda ko wancan satin ni na yi musu saboda na kira wayarta ban samu ba yau ɗin ma ta ce min ta na da yan kitso amma in za ta samu zuwa za ta gaya min. Mun yi waya da Rahila ni na kira ta kan tafiyar mu ta ce min goben za mu tafi, saboda Ya Aina ta shiga kasuwa yau da kuɗin da muka haɗa gabaɗaya za a ɗan tsinta kayan kitchen sai zanin gado da labulanya in kuɗin sun ragu sai a ƙara mata da wani abu sannan ta na faɗa min ɗinkunan Amaryan ma nan Kano aka kawo mata suma in an gama tare da su za mu wuce na ji daɗin haka domin ba na so ma a ɗaga tafiyar nan ta mu kamar fa a kan ƙaya na ka haka na ke jin kaina a gidan gabaɗaya. Na buɗe data ne na shiga group ɗin gidanmu na ga Ya Aina ta yi godiya ga kowa saboda kuɗin da a ka haɗa ba ta dai faɗi a dadi ba, ta ce ta je ta faɗa ma Alhajinmu ya na ta saka mana albarka anan ne na ji Ya Murja na maganar yan tafiya na ji ta na ceewa har da Ma'u a cikin masu zuwa ita da ta ce ba za ta samu zuwa ba amma Ma'u ta ce ta shirya ta na tunanin direba ne zai kai su, duk ina gani ban yi magana ba sannan an yi maganar cikin matar Ya Hamza ko ta Ya Auwal in wata za ta samu zuwa duka dai suka ce ba za su samu zuwa ba sai kawai a ka saka Zaitunan Yaya Abubakar a cikin masu tafiya. A raina na ce sai dai mu haɗu a can domin can anjuma da na sake hawa na ga Ya Murja na min mgana ni ba zan je ba ne? Kafin na ba ta amsa ma Amina ta faɗa mata gobe za mu tafi ni da Rahila saboda mun yi waya da ita da safe na faɗa mata.   Kawai sai Ya Murja ta yi tagging ɗina da cewa" Uwar gida yaushe ne tariyan Amaryan ta ki? Kamar zan amsa ta, sai na fasa kowa ya kirani a waya amma ban da ita, shi ya sa na yi kamar ban gani ba, amma ga mamaƙina Ma'u ce da ta zo ta ba ta amsa da cewa" Ƙarshen watan ne fa Ya Murja." Mamakinta ya ƙara kamani wato ita har ta sani kenan, ina gani Ya Murja na sake tambayan a ina amaryan za ta zauna? Ta ce ba ta sani ba tukunna amma dai haya a ka ce za a kama mata.   Ni dai kawai sai kallo na kasa magana Amina ce ta shiga hiran ta su ta na faɗin"Ya Ma'u ki bari Uwargida ta amsa mana mana" Sai ta tura emojin dariya kafin ta ce" Na wakilceta ne.' Yaya Murja ke ce ma Amina wai ta san akwai wata yayar mijina da suke aure a gida ɗaya da Ma'u suna shiri sosai a wajenta ƙila ta ke samun labari. Amina ta ce ikon Allah! Daga nan ba ta ƙara magana ba. Ta bar su suna ta mganganun su kamar ma da gayya suke yi ban ce komai ba na kashe data kawai na ijiye wayar saboda in na ma zauna ina gani sai raina ya yi ɓaci a banza. Kayana na shirya a cikin akwatina mai ɗan girma. Lame ta aiko min da mai da showel gel jiya. Kaya na diɓa sama da kala biyar domin sati zan yi a Yashe haka na yi niyya. Har wajen la'asar mai kitso ba ta zo ba sai da na ƙara kiranta sai ta ce min tana hanya. Ba na so na je da kaina a tsife domin na gaji da shi a haka gwara na kiteshi ga shi an fara sanyi ma kar ya karye min. Zuwan mai kitso ya sa na ɗan saki da ya ke ƴar zamfara ce ta na da hira muna ta fira muna dariya har su Jidda suka dawo makaranta ban yi girki ba daman sai na ce in sun cire kaya Jidda ta sulala musu ko indomie su ci, mai kitso na ta mamakin girman Jidda ina dariya na ce. "Kin dai daɗe ne ba ki ganta ba Maman Nana." Ta na jinjina kai ta ce" Ko! Amma duk da haka Jidda ta ƙara tsawo masha Allah. Mun kusa kaiwa ga suruki ga Baby ma masha Allah itama ta na ta girma." Ina ta dariya ban yi magana ba ina kallon Jiddan da ta cire unirform ta saka doguwar riga na atamfa sai nima na ga ta yi min girma, ba ta ma gama cika 14 ɗin ma sai watan gobe, sai dai nima na yarda ta ɗauko tsawon kafan babanta, Baby ce ke da jikin gaba gaɓan girma. Ni na ce Jidda ta dafa duka indomie ɗin tare da mu, Baby dai sai da tasha tea kafin a gama sai kuka ta ke yi wai ta na jin yunwa, sai da muka gama kitson sannan muka ci indomie Maman Nana ta ce ba za ta ci ba na ce sai dai na saka mata a cooler ta kai ma yara. Haka ko aka yi gabda mangariba ta tafi na ba ta kuɗin kitsonta da na adaidaita sai indomie ɗin da na saka mata a wata roba na ce ta kai ma su Nana daman haka na ke yi mata wani lokacin ko ma ta ci in za ta tafi in akwai na kan zuba mata na ce ta kai ma yara. Da a niyyata yau ba zan yi girki ba, sai kuma daga baya na ga bai kamata ba. Ya fita bai karya ba yanzu kuma ya dawo ba abinci? Duk da wata zuciyar tawa mara kirkin ciki na faɗa mib sun je duba gida da amaryansa kika sani ko sun biya gidan cin abinci sun ci? Amma ban biye mata ba na yaƙe ta, na miƙe na faɗa kitchen bayan na yi sallar mangariba na bar su Jidda a falo suna duba littafan makaranta domin ta ga ya min next week monday za su fara jarabawa shi ne na ce maza su ɗauko littafan su mu yi karatu, mun fara kenan tunanin dafa wani abu ya shige ni sai na tashi na bar su, suna yi su kaɗai. Ina shiga kitchen ɗin bayan tsayawa na tsawon mintina goma da nazari na ji kawai tuwo na ke son yi, to amma Yallaɓai bai cika son tuwo ba wani lokacin, na so na kira shi amma sai na fasa kar ya zo suna tare da Gimbiya sai na koma falon na ɗau wayata na tura mata saƙo. "Na yi mana Tuwo yau? Kamar ya na jira duka duka da turawan ko minti biyu ba a yi ba sai ga amarsa shi. "Da kin faranta mini zuciyata Madam." Sai da na yi mirmishi da na karanta sakon. Ni na san ya na can cikin damuwa bai yi tunanin buɗe masa mganar da na yi ba ɗazu ya fita cikin sanyin jiki ya na tunanin ina can ina fushi da shi, ni ko bai san abin da na faɗa ni tuni ya wuce daga wajena ba, na dai fitar da abin da ke raina ne saboda ba na so ya ƙara maimaita abin da ya yi yau, sannan kuma ya daina min kame kame ni da shi duk mu san gaskiya. Nan take na kunna gas na dora ruwan tuwo na deɓo shinkafar tuwo ina ɗan gyarawa, wanketa na yi na zuba na rufe sannan na dauko sauran man suyan salla da na saka kasusuwan da suke rage daman tuni tuni na ce miya zan yi da shi na yauƙi na ci tuwo da shi, to na duba kubewata ta kare sai kawai na ce ba ri na yi miyar zolagale, saboda dare ya yi sai na kunna wani gas ɗin na ɗora miya saboda ina so na gama a kan lokaci kafin Yallaɓai ya dawo. Allah ya taimake ni bayan isha'i na gama tuwon, har na ɗaure a leda, kuma daman bai da yawa saboda ma ɗumamen safe ne, miyan ne a kan wuta ba ta karisa ba sai tashin kamshi take yi sannan na saka mata man shanu tunda akwai sauran shi, Jidda na bar ma sallahu in miyan ta ƙarisa ta kashe gas ɗin duk da na ɗan rage ni kuma na je na yi wanka na ɗauro alwala na yi sallar isha'i sannan na sauya kaya na saka wasu riga da wando pakistan Mimisco ce ta taɓa kawo min tsaraba da ta je England. Kitson 2steps a ka yi min sai na zubo shi ta baya, saboda hulan da na saka tsakiyar kai ana gani shara shara ce ta na dai da tuntun love daga tsakiya, hulan mai adon pick irin adon jikin pakistan ɗin da ke jikina har da su jan baki na saka na sha gazal da mascara. Har taran dare Yallaɓai bai dawo ba, Baby ta yi barci ni da jidda kawai muka ci tuwon muna ta santi faɗi ta ke yi" Umma tuwon nan ya yi daɗi." Ina mirmishi na ce" Na gode ɗiyar Umma." Kallonta na ke yi ina mirmishi ni kaɗai bayan mun gama ci ita ta kwashe komai ta kai kitchen, nima bin bayanta na yi na wanko hannuna sai da muka dawo falo ta na tattara littafanta na kira sunan ta. "Jidda." "Na'am Umma." Ta amsa min ta na mai mayar da hankalinta a kaina. "Gobe za mu tafi biki Yashe ni da Ummar ku Rahila." Ina kallona sai na ga ta buɗe baki amma ba ta yi magana ba. "Kuma sati ɗaya zan yi in sha Allahu." Ido ta zaro kafin ta ce" Sati ɗaya Umma? Ina dariya na ce" E ko ya yi kaɗan ne? Sai ta dawo gefena ta zauna ta na faɗin" Umma zan biki don Allah ban taɓa zuwa ba." "A'a makaranta Jidda. Ki bari dai in an yi hutu in da mai zuwa sai na haɗa ku ku je tare." Ta na wani kwabe fuska ta ce" Umma to da wa za mu zauna a gida? "Da wa kuwa? Ga Abban ku.' Sai ta yi shuru ba ta yi magana ba amma ta ɓata rai, a raina na ce tafiya fa ba fashi  ko ya riƙa dawowa gida da wuri ko ya kwashe ku zuwa Gwammaja wannan duk ya rage na shi. Ina zaune Jidda ta kwashe duka littafab makarantar su ta kai ɗakin su, sannan ta zo ta ta da Baby suka shige ɗaki na bi su da cewa su yi fitsari kafin su kwanta kar kuma su manta addu'an barci shigan su ba daɗewa sai ga Yallaɓai ya shigo gidan, ya siyo min kwaakwa mai yawa saboda ya san ina so, akwai halin Yallaɓai da na ke matuƙar so shi ne ba ya shigowa gida hannu rabbana ko ba shi da kuɗi sai ya san abin da ya tsaya a siya a hanya ko saboda yara in ba su yi barci ba su ta so suna masa oyoyo sai ya ji nauyin in bai taho musu da wani abu ba, ni kaina in dai ya san abu ina so to ko a ina ya gan shi sai ya siyomin ya taho min dashi. Bai ma tsaya wanka ba ya  ce na zuba masa tuwon yana gaya min tun safe kankana ce kawai a cikinsa muna kan dining zaune lokacin ina zuba masa tuwon na ce"Kai. To me ya sa ba ka tsaya a gida ka karya ba.? Na faɗa ina tura masa filet ɗin gabansa, sai da ya saka cokali ya fara kai lomar farko ya haɗiye sannan ya kalleni ya na faɗin" Saboda kina jin haushina." Waro ido na yi kafin na ce" Ni? Sai ya gyaɗa min kai lokacin akwai tuwo a bakinsa sai da ya haɗiye sannan ya ce" E. Haka kika ce min da safe ko kin manta ne? Ya faɗa ya na mai kallona sai kawai na ce Uhm! Daga nan ban ƙara mgana ba shima sai da ya ci ya koshi ya haɗa da ruwa sannan ya yi hamdala, ni daman tun farko na ce masa na ƙoshi mun ci tare da Jidda. "Girki ya yi daɗi. Allah ya yi miki albarka amma a bi ni bashi zan biya tuƙwaici." CMirmishi kawai na yi ban yi mgana ba, hannun shi kawai na ji a wajen wuyana ya na jan jelan gashina lokaci ɗaya ya na faɗin" Kitso a ka yi ba a gaya min ba? Kai tsaye na ce" Kitson tafiya ne" "Tafiya kuma? "E. Ka manta za mu je can Yashe biki." Sai ya kaɗa kai kafin ya ce" Na sha'afa. Tafiyar ba sai jumma'a ba ne? Ina kallon shi na ce" Gobe ne." "Gobe fa? Ya maimaita cikin mamaki ni kuma sai na ƙara gyaɗa masa kai, bai ce komai ba kamar dai ya na mamaki ne ni kuma sai na shanye masa mamakin na miƙe ina tattara kwanukan da ya ɓata na ɗauka zuwa kitchen, lokacin da na dawo ba shi a falon ya shige ciki, ni kuma bayan na gama abin da na ke yi sai na kashe hasken falon na rufe ɗakin su Jidda na leƙa na duba su, bargo na gyara ma Jidda a kafafunta da ya janye Baby kuma kai ba ɗankwali sai da na binciko mata hula mai igiya na saka mata tana ta ture min hannu a cikin barci bayan na gama na rage musu hasken ɗakin na jawo musu kofa bayan na tofa musu addu'an barci. Har falon yara da kitchen sai da na rage hasken wuta na kashe komai sannan na wuce bedroom na iske Yallaɓai har ya yi wanka ya na saka kayan barci sai da na shigo na tuna da akwatina da na bari a kan gado sai na saka hannu na dago shi na sauke shi a gefe. "Kwana nawa za ki yi ne? Na ji Yallaɓai na tambaya, ban juyo na kalle shi ba na ce" Sati ɗaya in sha Allahu." Na kalle shi, ya na goge kansa da ƙaramin towel ne a lokacin amma sai da ya tsaya kawai ya na kallona ni ko na sha kuni na ƙarisa gaban wardrop na buɗe ina neman kayan barcin da zan saka. "To yara fa? "Su zauna anan ko Gwammaja."   Na faɗa ina mai tube rigar jikina bai ce komai ba, nima ban neme wata mgana ba har muka gama shirin barci mu ka kwanta gabaɗaya. Ina jin sa ya na ta juye juye ya na so ya yi magana amma ya kasa, ni ko da gangan na mulmula na haye jikinsa na sagalo hannayena ta wuyansa na yi lamo har na yi barci ina jin bugawar zuciyarsa sannan hannayensa da ya riƙe da su duk a sanyaye, ni dai ban san lokacin da barci ya kwashe shi ba, ni dai sai asuba na tashi saboda zan yi tafiya kuma har ga Allah ya ba ni tausayi shi ya sa ya na dawowa salla asuba na rumgumeshi ina faɗin" Mu yi ɓarnan ruwa ne Yallaɓai na? Ko na bankwana ba za ka nema ba? Kamar na yi masa sosa a in da ya ke masa ƙwaiƙayi tun da ya dafe ni sai da na gaya ma aya zaƙin ta kwanakinsa ya fanshe, sai bakwai fa muka yi wanka sannan na fita wajen yara, na sha dai sambatun Sadiyata ki yi hakuri ki yafe min wallahi ina son ki, da dai sauran su, har su Jidda suka tafi makaranta ban faɗa ma Baby zan yi tafiya ba saboda ba na son ta yi min rigima mun yi yar daɗi da Yallaɓai bayan tafiyan su Jidda ma ruwa muka koma shi dai kawai ya na faɗa min ya yi matuƙar kewata, ni kaina na yi kewarsa kuma na yi masa rawan jiki kamar yadda ya yi min.   Shi da kanshi ya ce yara Gwammaja za su koma har na dawo saboda gobe ma Kaduna zai tafi bai san kuma lokacin da zai dawo ba shi ya sa na shirya musu kayansu a cikin ƙaramar akwatin su, ni ban nuna masa komai a fuska ba amma a raina na san Gimbiya za ta yi rawan jiki da su tun a baya ma ta yi balle yanzu mai dalili. Ƙarfe goma muka fito daga gida na rufe gidan da key, Yallaɓai daman na da makullin shi, muna hanya zai kai ni Ɗorayi Rahila na can na jirana daga nan zai je Gwammaja ya kai kayan su Jidda daga nan na ya wuce Office, sai da muka je ƙofar gidanmu sannan ya turamin 20k na mota ya ce in na dawo za mu yi mgana. Tare muka shiga gidan dashi ya na riƙe da akwatina suka gaisa da Gwaggo da Alhajinmu. Gwaggo dai sai ta yi masa fatan alheri. Alhajinmu kuma ya ce shi dai bai ji daɗi ba da ba a gayyace shi wajen ɗaurin auran ba duk kunya ta kama Yallaɓai ina gani duk ya kasa natsuwa. Ni ko a raina na ce Alhajinmu da kalan dangi. Bai wani daɗe ba muka yi sallama ya wuce daman mun samu Rahila a gidan Ya Aina muke jira ta zo ta kawo mana kaya sai Ya Muntari da ya je karɓo ɗinkuna. Mu ne ba mu tafi ba sai azahar motar mu ta tashi, ta yantumaki muka hau daga can ne in mun sauka za mu hau na Yashe, Rahila ce ke da goyo ni dai daga ni sai kayana ina zan iya, ba mu muka isa Yashe ba sai biyar na yamma ko a yan tumaki mun daɗe ba mu samu mota ba sannan wacce muka hau daga kano ta samu matsala a hanya. Ni fa sai yau na ƙara yarda da cewa tafiya yankin azaba ce mun gaji ga kishi ga yunwa, yarinyar Rahila na ta rigima na ce kya yi yarinya mu kan mu iyayenki mun jiggata. Mun ga tarba a Yashe daman ahalin Alhajinmu Ahali ne masu karamci da son zumumci a ɗakin uwar Amarya muka sauka wato Marliya abokiyar zaman Mahaifiyarsu Muntari Jummai, gida ya sha fenti an gyara shi tsab yadda ƴan'uwa suka zagayemu ana ta hira ne ya sa na ji na manta da damuwata kamar na zo wata sabuwar duniya. Wayata na jaka sai da bayan isha'i na duba na ga Yallaɓai ya kikkirani ban gani ba sai daga baya na kira shi, ya ce min lokacin ya na Gwammaja ne zan yi mgana da Baby ta na ta rigima kuma shi yanzu ya dawo gida amma zai saka Gimbiya ta kirani sai na yi magana da ita. Kai tsaye na ce.   "Ƙyaleta kawai za ta ba ri ne." Domin ba na son magana da Gimbiyar ne gabaɗaya. Mun ɗan taba hira tunda daman da muka sauka na tura masa saƙo, tun da muna hanya ya na ta kirana, Yallaɓai fa ya na da kulawa matsalan kishiyan da ya yi min ne ya sa duk na daina ganin kirkin shi, a daran nan ba abin da ba'a kawo mana ba tuwo ni dai na ci miyar kuɓewa, na kuma sha fura har wajen sha ɗayan dare muna ta hira da su Baba Aminu haƙika ko ba su nuna ba sun yi farinciki da zuwan mu tun ballatana ma da muka ce musu har Gwaggo za ta taho su Alhajinmu kuma sai ranar ɗaurin aure. "Ma sha Allah. Gidan Yaya Sule gabaɗaya za su yi mana baƙunta kenan." In ji Baba Sani cikin murna da fara'a. Ni dai ina kwance a kan kafitar da aka sauke mu, Rahila ita na kan gado domin ta ce ba za ta kwana da ni ba kar na shure mata da ƴa da kafafuwata. Sai na buɗe baki ina kallonta ita kuma ta na dariya kai na jinjina kafin na ce" Rahila ki sani zan rama ne." Ta na dariya ta ce sai dai na rame, na daɗe ban yi barci ba ina jin wani iska na shiga jikina, ina ji in da ace ban zo ba da na yi kewar wannan yanayin na farinciki da na ke cioi mu ne har wajen biyun dare muna hira da Rahila, mu na tuna baya muna ta dariya ji na ke yi kamar baya ta dawo yanzu rayuwar ta fi daɗi.   Ko kafin ranar alhamis ɗin da su Ya Aina suka iso, mun riga mun zama yan gari domin mun sha yawo, mu ne gidajen yan'uwa da suke aure a kusa, sannan har gidan su Gwaggo mun je, sun zo sun iske mu mune ma ke yi musu maraba. Ya Aina sai Ma'u da Ya Murya, sai Zaitunan Ya Abubakar Gwaggo sai jibi za ta taho tare da su Alhajinmu. Mun sha biki sai wanda ya gani. Malunfashi a ka kai Amarya ni da Rahila da Ya Aina har da Ma'u mun je kai amarya Ya Murja ce ba ta je ba,  ranar lahadi muka dawo Yashe, litini su Ma'u suka koma kano da ya ke biki ne kuma ga jama'a har muka rabu dai ba mu raba hali ba. Ma'u dai ta je ta ga dangin babanta  kafin su koma. Baaba ba ta samu zuwa megidanta ba lafiya. Mu kuma muka ce sai mun cike sati gobe kenan talata, na ji daɗin zuwana Yashe domin ya sa na shafe tunanin auran Yallaɓai a cikin raina muna waya da shi lokaci bayan lokaci yara ma mun yi magana da su sau biyu Baby ce ke ta karaɗin ba ni labarin Anty Gimbiya ta yi musu kaza ta yi musu ita Jidda ba ta da surutu. Ranar litinin ɗin da yamma Munnira ta kirani a waya ta na faɗa min an kama ma Gimbiya hayan wani gida ita kaɗai a sharaɗa. Ni kuma dai Tauraini ya ce min da farƙo wataƙila wancan bai yi ba ne suka kama wani, ni kuma daman na ce ya daina zaunar da ni ya na faɗa min abin da bai shafe ni ba shi ya sa duk labarin da Munnira ke ba ni na ce mata ban san da labari ba. Ta na ga ya min anan Gwammaja za a yi taron biki, Hajiyar Tafida za ta yi nata acan Rano amma taro na gidan Nene, har da labarin Yallaɓai ya ba ma Gimbiya kuɗi masu yawa na lefe da na hidimar biki. Har Munnira na faɗin" To ke nawa ya baki? Gwara mu ji saboda mu ma mu shirya namu taron ko ya kika ce? Ina mirmishin ya ƙe na ce" Ni ba na gari ai na zo Yashe biki ƙila sai na koma za mu yi maganar da shi." Mun rabu da ita a kan in na koma zan yi musu waya ita da Hauwa da farko na ji a raina ba zan yi wani taro ba amma ɗazu da muka yi hiran da Rahila sai ta ce na yi domin kauda idon masu mgana gazawata a ke nema abu kaɗan zai zama abin magana nima na shirya taro ni da ahalina domin a zo a ɗebemin kewa sai kuma da ta faɗa na aminta da maganarta sannan mun yi chart da Ant Zabba itama ta nuna min fa'idar haka tace har kunshi da kitso duk na yi na gyara kaina yadda duk wanda ya ganni zan yi masa kwarjini, sai na ji duka na aminta da shawarwarin sa na ɗau damaran in na koma gida za mu yi mgana da Yallabai daman taron gidana ai nawa ne, na su na can Gwammaja. Na bari sai in na koma Kano sai na kira Inna Mariya na faɗa mata halin da a ke ciki kar su ji a wani waje, su ce ban faɗa musu ba. A daran na ga Yallaɓai ya turamin 1m miliyan ɗaya a acct ɗina, sai na kira wayarsa ba ta shiga ba sai na tura masa saƙo. "Na ga saƙo Yallaɓai na mene ne? Da ya saƙon ne ya kirani, ni kuma na gaji na kwanta da wuri sai da safe na ga kiran shi da saƙon shi. "Na ki ne. Yau dai za ku dawo ko? In kin dawo sai mu yi mgana." Ko bai faɗa min ba na san na faɗan kishiya ne, tun kana ji abin daga nesa ga shi yanzu har ya zo kaina wai Yallaɓai ya turamin kuɗi amma kuɗin na faɗan kishiya ne, duk dauriyata sai da na shige makewayi na ci kuka na ƙoshi, da zamu koma gida fitan safe muka yi Baba Aminu ya ba mu wake mai yawa ni da Rahila mu ne barkoni waken suya,daddawa kuɓewa zogale bushasshiya, da sauran su duk mun yo tsaraban shi ko da la'asar ta yi muna Ɗorayi sai yamma Yallaɓai shi da yara da ya biya Gwammaja ya ɗaukosu suka zo suka ɗauke ni zuwa gida. In ka yi tafiya duk sai ka ji gaɓɓanka sun saki, barci na yi ta yi kamar wata mattaciya kuma Alhamdulillah natsuwan da na je domin na samo kuma na samo ta, sosai na ji zuciyata ta samu sauƙi, bayan na huta da kwana biyu muka yi mgana da Yallaɓai shi ne ma ya ke faɗa min ya samu wasu kuɗi daga aikin su na Kaduna ne, na yi haƙuri da kuɗin hannuna na siya abin buƙata na kaya da sauran su , na yi ƙokarin nuna masa bakomai cikin raankwafa na yi masa godiya. "Na gode Yallaɓai. Allah ya ƙara buɗi" "Amin. Ki yi hakuri kin ji ko? Ya sake faɗa ya na mai kallona sai na girgiza masa kai kafin na ce" Kar ka damu bakomai." Na faɗa ina danne yanayinaa shi kuma ya yi shuru ne kawai rasa abin cewa tun da na dakatar da shi faɗa min halin da Gimbiya ke ciki, ni dai a falo na bar sa ya shiga zurfin tunani na koma ɗaki kawai na yi tagumi, in lissafina ya yi dai dai saura kwanaki kaɗan tariyan Gimbiya. Kenan ya dai tabbata Yallaɓai ya zama namu ya tashi daga nawa ni kaɗai. Na kai tunani zurfi na tuno lokacin da muka tare a wannan gidan. Lokacin da ya ya ma aka ƙarisa aikin gidan? Dakyar ne da soɗin goshi, sannan kuma lokacin ba ni da komai daga ni sai gado sai kujeru. Allah ya taimake ni yan'uwana suka tallafamin na fita kunya. Kayan ɗakina na siyar aka yi min sabon gado da kujeru, gadon shi ne a bedroom ɗin mu sai kuma kujerun a falon Yallaɓai, ɗakin yara kuma Ya Auwal ya taimaka min da kuɗi na yi musu gadajen ne, sai kuma na Ya Hamza shima da ya bani, na siya kayan kitchen ko na ce na ƙara sai cafet ɗin falo sauran kayan duk a hankali a hankali na riƙa siyan su, ko falon yara adashe na shiga na tara su kuɗi na yi kujerun nan da cafet sai dispanser abin da Yallaɓai ya siya daga Tv sai fridge duk ni na gama faɗi tashina kuɗaɗena duk suna kan shi, in na yi magana sai ya ce zai ba ni zai buɗe min shago in aka biya su, sai ga shi kuɗin aiki nawa a ka biya shi? Yanzu ba ta ni ya ke ba komai da ya samu kan maganar Tariyan nan ce a gabansa. Na ci kukana na share hawayena ni kaɗai ba wanda ya sani. Tariyan ya kama 28 ga wata ne, na kira Inna Maariya na faɗa mata ta ce za su zo in sha Allahu. Sannan ba tunanin auran nan da Yallaɓai ya yi ba ne zai saka ni gyara ba domin ni ɗin daman mai gyara ce na kira Surayya Halin yau na ce ina son haɗin uwargida, ta ce an gama sannan na sake siyan man gyaran jiki a wajen Aisha Lame, saboda ko Yallaɓai ya sha ce min fatata kamar ta Baby saboda taushi. To mayuka Aisha lame ni masu saka taushin fata da santsi, a can group din gida na sanar da tariyan Yallaɓai na kuma ce ina gayyatan kowa da kowa a ranar a gidana zan yi taro, Ya Auwal ya kirani ya ce Laila za ta zo garin daman suna da biki itama na ce na ji daɗin haka Amina ma da ban yi zato ba, sai gashi ta kirani ta na faɗa min a bar ta za ta zo, kuma haƙiƙa na ji dadin jin haka har Faridan Tariq ma ta ce za ta zo kuma ta ce min a gidana za ta sauka tabbas na yaba da wannan karamcin. Na kira Hauwa da Munnira sun zo mun yi shawara. Suka ce na siya kaya sabbi na ɗinka saboda in shiga in fita, haka ko aka yi na siya kala biyar atamfa uku leshi ɗaya, material ɗaya sai yara ma na yi musu duk da Yallaɓai ya yi mana shadda da ni da shi da yaran gabaɗaya. Ni ban ma san wa ya faɗa musu Abban su ya auri Anty Gimbiya ba sai da Jidda ta tambayeni na ce hakane ina tunanin lokacin da na je Yashe ne aka faɗa musu a Gwammaja ko baban na su ya faɗa musu da kanshi ban dai sani ba, maganar taron da zan yi kuma da kaina na samu Yallaɓai na faɗa masa ina so na yi taro ƴan'uwa ba su zo su taya ni zama da nuna masa farinciki. "Shi ne ba ki faɗa min da wuri ba? Ya faɗa cikin nuna mamakinsa ko bai yi tunanin zan yi taron ba ne. "Na ɗauka ka san uwargida na yin taro ko? "E. Amma ban ɗauka ke za ki yi ba." Hararan wasa na yi masa kafin na ce" Ban kai yadda ka ke tunanina ba." Mirmishi ya yi nima na ta ya shi, mun tsara za a yo cefane tunda muna da shinkafan tuwo za mu yi waina sai Nama da za a kawo da kayan Miya sannan shima ya ce min Kawu zai zo shi da Tariq suma suna son wainar na ce ba komai sai a yi da su gabaɗaya. Ko bai faɗa min ba na san ya ji daɗin yadda ya ga ina ta masa dariya ina ta kuma shirye shirye, tun yana sharewa har dai ya furtamin da kansa. "Na gode Sadiya ta. Ina ƙaunarki saboda Allah." "Nima ai saboda Allahn na ke sonka ko Yallaɓai? Na faɗa ina masa fari. Lokacin da daddare ne na fito wanka da sauri Yallaɓai ya ta so ya rumgume ni ya na shinshina min wuya, cakulckuli ya fara min na fara dariya ina ture sa. Allah sarki rayuwa. Yanzu fa nan da kwanaki sai dai Yallaɓai ya zo mu gaisa da safe in dai ya na gidan Amarya. Tabbas kishi ya na da zafi. Kuma zama Turken gida abu ne mai matuƙar wahala. *Janafty* *TKG* 08. Ranar alhamis su Jidda suka yi hutun makaranta. Jidda daman ita ce ta ke ɗaukan first postion a ajinsu Baby kuma Third, sun karɓo kyatuttuka tunda an yi speach and prize giving day ban je ba amma Yallaɓai ya je musu tare ma suka dawo. Ko da suka dawo mai kitso ta zo, da mai ƙunshi har an yi min ƙunshi saura kitso. Marwa daman ta na nan domin ni na ce ce ta tattaro, ta dawo wajena sai an gama biki, Amina ma ta iso tun azahar Hauwa da Munnira suna gidan suma tun safe sai zlZaitunan yaya Abubakar. Sameena ta kira ni ta ce suna nan tafe gobe ina mata tsiyan ita ko yar gidan amarya ce tana dariya ta ce. "Matar Baba akwai amana ni ai ina bayan uwargidan Yallaɓai." Haka dai muka gama wayar muna ta barkwanci, a bakin su Hauwa na ke jin mai gyaran jiki daga maiduguri Anty Bahijja ta ɗauko ma Gimbiya tun ana saura sati ɗaya ta sauka a gidan Nene. Taro ne Gimbiyar ta shirya sosai tun da ƙawayenta duk na Rano da Abuja da nan kano za su zo baban aminiyarta Naja dai daman suna tare ko da yaushe, tun da ba ɗaurin aure taron gabaɗaya na mata ne. Ƙannen Gimbiya da matan yayyenta duk Kano za su zo, can Rano sai dai manya dangi dai na can amma taron gabaɗaya ya na nan ne, a ranar alhamis ɗin ma aka je aka gyara gidan Amarya Halima ta biyo daga can zuwa gidana ta ke faɗe, ni dai ina gefo ban ce komai ba, Ban gayyaci kowa daga dangin Yallaɓai ba, sai wanda ya ga niyya ya zo. Amma ni dai na gayyato kaf ahalima har da Ma'u saboda na tusa mata haushi na ce ta gayyato min Shema'u. Na kuma san ita kanta ta yi mamaki, na kuma san za ta je can ɗin za kuma ta zo nan tunda Anty Bahijja kamar ita ce ma uwar Amarya saboda yadda ta ke rawan jiki kan auran nan, daman burinta ne da daɗewa na daina juyi a gidan ɗan'uwanta ni kaɗai gani ta ke yi kamar wata tsiyar Ɗan'uwan nata ya ke ba ni, ni fa shi ya sa har gwara Anty Maimuna a kan Anty Bahijja matar nan sam ba ta da hali mai kyau akwai baƙin ciki amma ita ta na can gidan wani a dangi wasu ta na abin da ta ga dama. Ni da ya ke ko a waya na rufe ta ba zan ga status ɗin ta saboda ina da tabbacin da gayya za ta yi ta ɗora abin da zan gani na ji haushi, ni kuma ba na so damuwa shi ya sa na kama kaina, ita kanta Gimbiyar ban san dalili ba ina jin ta aure min miji na goge lambarta a wayata cikin zafin ƙishi. Kamar na san haka za ta faru Ranar jumma'a sun gudanar da walima anan haraban gidansu Nene a Gwammaja duk sun sha abayoyi sun sha kyau, tsabar ma renin hankali Anty Bahijja ta ce ma Yallaɓai wai nima na zo wajen Waliman tunda malama ce za ta zo ta yi wa'azi a kan aure, shi kuma da ya ke ya san a yanzu ina kan tsini ne magana ma ta arziƙi ta tsiya na ke mayar da ita sai bai yi min magana ba ya ce ta rabu da ni kawai su yi abin su. Ni ban ma sani ba tunda Yallaɓai bai yi min maganar ba sai a safiyar jumma'an ta kirani a waya kuma daman na san da batun za su yi walima tunda Halima ta faɗa min, har ga Allah lokacin da na ga kiran Anty Bahijja a wayata sai da na ra ya a raina ba alheri a cikin kiran nata, amma ban ki ɗauka ba illau ko sai gashi ta na faɗa min wai ta aiko Tafida bai faɗa min saƙon ta ba ne? Kai tsaye na ce" Wani saƙo kenan? Domin ni dai ba mu yi maganar wani saƙo da shi ba." Lokacin ma bai jima da fita ba, ya tashi yau ɗin da cewar ba ya jin daɗin jikinsa na ɗauka munafuncin su na maza ne sai da na ji jikinsa ya ɗau zafi sannan na yarda. Ya dai sha paracetomol ya fita da cewar zai je a duba shi. "To na aiko shi ya sanar da ke yau akwai walima a Gwammaja" Mamakin ta ya kamani to in akwai walima ina ruwan Sadiya a ciki? "Bai sanar da ni ba, amma na ji a bakin mutane." Ba ba ta amsa a saukaƙe domin raina har ya fara ɓaci, ban yi ma ƙaninta bore don zai ƙara aure ba, amma ba shi zai ba ta damar ta zagayo ta na ƙokarin ci min mutumci ba, ba yayar mijina ba ko uwarsa ce zan nuna mata na san darajan kaina, sannan komai ya tsaya a muhallinsa zai fi alheri gare mu gabaɗaya. "Duk ɗaya. Ki shirya ki zo kema a yi walimar da ke. Karfe huɗu ce kuma wa'azi ne za a yi muku kan zaman aure da zamantakewa." "In shirya in zo kuma? "E." Ta ba ni amsa a takaici ina ta jin hayaniya ƙila ma ta na Gwammajan ne a gaban Gimbiyar da sauran su an saka ni a seaper za a ci min zarafi, cije leɓena na saka na yi, a ina tunani a cikin raina matar nan ba ta sanni ba ne, Ma'u ba ta ba ta cikakken labarin ni ni ba na barin ta kwana, kuma wanda ya ce da ni kule wallahi komai girman shi sai na ce da shi cas sai dai a yi wacce za a yi. "In ji wa.? Nima na tambaya a takaice, cikin fusata ina jin ta daga cikin wayar ta na faɗin" In ji ni, ko ban isa ba ne." Mirmishi na yi yadda zan kunnata kafin na ce"Ba maganar isa ba ce. Ko shi ƙanin na ki da na ke zaune domin shi ya ce na je zan ga ya masa ya yi hakuri ba zan je ba, ke ma kuma haƙurin zan ba ki ba zan samu zuwa ba, domin ni a lokacin aurena na yi walima kuma an yi min wa'azin aure da zamantakewa, bayan haka kuma Iyayena ba su kawo ni haka ba sun yi min shekara goma sha biyar da aurena kin san sai dai na zaunar na karantar da wani ba dai ni na zauna ana karanta min wani abu akan aure da zamantakewa ba wallahi." Na faɗa kai tsaye kuma ko a jikina. Ina ji ta yi shuru kafin ta ce"Me kike nufi Sadiya? "Abin da na ke nufi shi ne ba zan zo ba. In ina bukatar walima na shiryata a gidana mana? Sannan ni ba na bukatar walima da wa'azi ita dai wacce ta ke bukatar wa'azin ba ka ga shi kin kira za a yi mata? Me ya sa za ki gayyace ni cikin sha'anin da ni na riga na girme shi Anty Bahijja? Magana na yayyaɓa mata kuma na san sun yi mata zafi shi ya sa muka gama wayar kowa ran shi a ɓace. "Ba wani kin girma. Da ɗan abin da kika sani na cikin cokali kike cika ma mutane baki! Ke dai kawai malama zafin kishi ba zai bar ki ki zo ba ne. Kuma sai haƙuri Gimbiya zama daram a gidan Tafida in sha Allahu.' Ni kuma sai na maida mata da cewa" Nima ina fatan su zauna tare har mutuwa. Kuma kishi ai halas ne in ma ya hana ni zuwa na yi dai dai. Amma ga saƙo ki faɗa ma ita Gimbiyar ta ki, ta yi hakuri domin ni na ci na rage na ba ta saura kin ga kuwa komai na lalacewan giwa bai kai in ta mutu kiyashi ya ja ta ba, a macen ta ma tana da ƙima da daraja." Sai ta kama faɗa ta na faɗin wai na yi mata rashin kunya, wai sai ta faɗa ma Tafidan na ce me ya sa ba ta yi masa recording ba, na kashe wayata na barta ta na bambami ita kaɗai. Ina dalili mata ta bar ni da kishiyar da aka yi min kawai ta kirani za ta ɗaga min hankali, saboda yanayin da na ke ciki in na tuna gobe zan fara Raba Yallaɓai da wata macen duk sai na ji na rikice, ga jama'a a gidan shi ya sa na ke kannewa, saboda abu kaɗan za ka yi sai a tafi da kai a baki ace zafin kishi wance ba ku ga abin da ta ke yi ba shi ya sa da na ji abu ya taso min zan ta kiran sunan Allah. Balle ma Amina a nan gidana ta kwana kuma na ji daɗi kwarai da ita da Marwa muka raba dare muna hira, Yallaɓai ma jiyan ba da wuri ya shigo ba kuma ma bayan ya shigo abincinsa kawai na bashi ya ci ya shige ciki na dawo wajen su muna ta hira a ɗakin su Jidda. Amina ta zo mini da turarukan wuta masu ƙamshi ta ce a wajen ƙanwar mijinta ta siya a maiduguri ta ke aure an haɗo min har da kwallacha, fa humra ma su kyau da ƙamshi, shi ya sa saboda su na ke ɗauko mirmishi na aza a saman fuska, dalilin da ya sa ko da muka yi kaca kaca da Anty Bahijja a waya da na fito falo ban nuna musu ba tun safe suna ta ɗan ta ya ni gyara gidan ne, da goge goge ita da Marwa sannan ga Firdausin Yaya Balki da Amina ta kira ta a waya ta ce ta turo ta ta ya mu aiki, ni ba domin ita ba ba ma wanda na yi tunanin kira, sai Jidda da ke kama musu wani abun Baby kuma sai tsalle tsalle ita murna ma ta ke yi Anty Gimbiya Abba ya ce za ta dawo gidansu da zama Allah na tuba shi yaro ina ruwan shi. Can wajen azahar sai ga Munnira ta zo daman ita na ce kawai su je gidanta ita da Hauwa da Amina goben su soye waina ni kuma sai na yi miyar anan gida. To kayan waina ta zo na haɗa mata sai kuɗin icce na ba ta da na niƙa da sauran abin da za a bukata da wuri ta koma gida amma ta ce min za ta dawo anjuma na je rakata haraban gidan ta ke min maganar walima. "Ku na Walima a Gwammaja fa yau, ɗazu Anty Bahijja ta kirani wai duk mu zo saura mu ƙi zuwa tunda an ce tun satin nan gidan ki muka tare." Daman baƙin cikinta suna zuwa gidana ta so ne a bar ni kaɗai kamar mujiya na ko gyara tsayuwa na ba ta labarin nima yadda muka hau sama muka faɗo Munnira ta ba ni hannu muka ta fa ta na faɗin" Kin biya ni Sadiya. Kin biya ni fiye da zato na a kanki. Ki ji wulakanci ta na so ki kwashi jiki ki je ta wulakanta ki mana." "Ai ko sai dai ita ta wulaƙanta amma ni na fi ƙarfin ta wallahi." Haka na faɗa ina huci Munnira na dariya, mun rabu ta ce min wallahi itama ba za ta je ba sai dai Hauwa ta je, kai tsaye na ce" Hauwa za ta je mana. Kin san tsoron su ta ke ji." Kamar daman na sani tafiyan Munniran ba daɗewa sai ga Hauwa, da farko ba ta faɗa min ma za ta je wajen walima ba sai daga baya wai ta na faɗa min Anty Bahijja ta kira ta ta ce ta zo, ni ko mirmishi na yi kafin na ce" Bakomai Hauwa sai kin dawo." Saboda ni na san za ta je domin ta na jin tsoron kar ba ta je ba Anty Bahijja ta yi mata faɗa. Hauwa dai har yau ta kasa sama ma kanta ƴanci ni ko da na ke amarya a baya ban zauna wata shegiya da sunan yayar miji ko ƙanwarsa ta ta ka ni ba, kowa da matsayin shi, iya girmamawa ina ba su amma fa ba zan zauna ina jin tsoron su kamar na bauta musu ba, ba kuma su ke aurena ba ballatana su riƙa ba ni umarni ina bi cikin rawan jiki ba a baya ma ban yi haka ba ballantana yanzu da shekaru suka tura an riga an gogi jigida kowa ya san kowa. Zuwa bayan La'asar ba kowa a gidan daga ni sai Amina sai Marwa da Firdausi da Saude sai yara sai can ne Ya Balki ta zo, da yamma Yallaɓai ya aiko Musbahu da kayan miya da sauran cefane sai Ya Balki ta karɓi gyaran Miyan kafin ma ta fara sai ga Ya Aina ta zo sai suka haɗu gabaɗaya suna yi Amina kuma sai ta dau naman ta na tafasa gefe ɗaya kuma ni ina dafa zoɓo saboda na ce a yi saboda mutane duk da Yallaɓai ya saka an kawo mana lemun kwali da ruwa amma ni ina so ne shi ya sa na ce a yi, daman kuma daga Yashe an ba mu ganye zoɓo ni da Rahila itama sai mangariba ta shigo da ya ke ta sha tsiya a wajena na ce sai ta kwanan min da ko shirin kwananta ta zo tare da yaran, sai ɗan iface ifacen yaran ya ƙara ɗan raya gidan hayaniya da hada hada ya sa na ji zuciya ta yi sauƙi ina ta harkokina. Wajen bakwai da wani abu na yamma mai ɗinkinmu ya kawo mana kamar sun haɗa baki tare suka ƙwankwansa min gida da mai wanki, kayan Yallaɓai ne sai nawa, na yara daman kananun ni na ke wanke musu sai atamfofinsu ne da less na ke saka su a wanki ghana guda ne da kaya ya ce min Yallaɓai ne ya kira shi ya ce a kawo kayan, su Saude na kira suka kama min kayan zuwa cikin gida ina shigowa Amina ta kawo mini waya ta ce Yaya Auwal ne ya ce ya na ta kiran waya ta a ba na ɗauka sai a lokacin na tuna ta na cikin ɗaki na baro ta. Falon Yallaɓai na shige ina waya. Ya ce min Laila ta shigo gari amma sun yi mgana ita da yara sai gobe za ta zo gidana na ce bakomai ai itama biki gare su. Mun yi shuru na wani lokaci Ya Auwal ya san ni da hira da mgana amma yau gabaɗaya na yi sanyi. Tunani na ke ni ba uwa ba, ba kakanni baa dukan ya yi mini yawa. Aka ce ɗan uwa rabin jiki ko da ya ke namiji ya fahimci ina cikin damuwa sai na ji ya kira sunana a hankali. "Sadiya." Na amsa da Na'am ina ɗaga idanuwana sama domin sai na ji kamar zan fashe masa da kuka. "Ba ki bukatar wani abu? "Ba na bukatar komai Ya Auwal kiran ka mean alot to me. Na gode" Na faɗa muryata na rawa sai kawai ya ce" Ko Yallaɓan ya yi miki wani abu ne?. Da sauri na ce" A'a ba abin da ya yi min Ya Auwal." "Kin tabbata? Sai na gyaɗa masa kai kamar ya na ganina ina ta share kwalla da gefen rigana "E. Bakomai." Na amsa masa cikin muryan kuka. "To shike nan zan saka miki 50k ki kara wani abun kin ji ko? Kamar daman ina jira ne kawai sai na fashe da kuka cikin kukan na ke faɗa min" Na gode Ya Auwal. Allah ya kara ma nema albarka Allah ya ra ya maka zuru'a. Ita kuma Mama Allah ya jiƙan ta da Rahama." Kamar mutuwar ce ta dawo min sabuwa kawai sai na ƙara volume ɗin kukana ya na ma lallashina da min mgana ba na jinsa har ya kashe wayarsa ni kuma sai na sulale a ƙasan kujera ina ta kuka ina cikin kukan nan Jidda ta zo ta ganni hankali tashe ta je ta kira su Rahila suka taho da gudu ganin yadda na saka kaina acikin gwiyoyina ina ta kuka mai sauti sai tausayina ya kama su Rahila da Amina suka rumgumeni suna lallashina Ya Aina ta kori yaran can falo domin sun tsaya akan mu suna ta kallo Jidda duk ta damu sai faman faɗi ta ke yi. "Umma ko ba ki da lafiya ne? Baby ko har ta fara kuka da Rigima sai Marwa ta bi su can falon su ta na lallashin su, Ya Aina ta tsaya a kaina ta na faɗin"Me ye haka Sadiya? Har na saka miki suna jarumtar mata kuma sai ki ba ni kunya! Don Allah tashi ki bar kukan nan ki yi haƙuri ki ƙara daurewa da ikon Allah alheri ne za ki yi ta gani in sha Allahu." Amma na kasa iya yin wannan jarumtar kamar ana tunkuɗo kukan daga cikin zuciyata ya na zuwa ta bakina. Ya Balki kuma cewa ta yi" Ku bar ta don Allah ta yi kukan ta ko za ta samu sauƙin zuciya." Rahila da saurin kuka har ta fara tayani hawaye. Ni kuma ganin sun damu ya sa na ɗago ina faɗin" Ni fa ba kukan auren Yallaɓai na ke yi ba. Ina kuka ne na tuna da Mama ne." "Allah ya jikanta da Rahama." Suka haɗa baki gabaɗayansu wajen amsawa da Amin bayan kuma sun yi addu'a Amina sai ta fara kuka sai kawai ta tashi ta bar falon tana sharen ƙwalla ganin na ki daina kuka ya sa Yaya Aina ta kira Gwaggo a waya ta faɗa mata ba zato kawai Alhajinmu na gefe ya karɓe wayar ya kuma ce ma Ya Aina ta ba ni wayar zai yi mgana dashi. Sai na yi saurin tsaida kuka na ina gaishe da Alhajinmu. Cikin yanayin maganarsa ya ce" Dubu in na ce ki zo gida yanzu ina son ganin ki, za ki iya zuwa? Muryata a shake na ce masa in sha Allahu, shi kuma sai ya ce na taho yanzu ya na jirana, bayan na bama Ya Aina wayar sai ta ce ko ta rakoni ne, amma Alhajimu ya ce ni kaɗai ya ke son gani. Jin haka yasa na tashi na shiga ciki ina shiryawa ina cikin ne sai ga Faridan Tariq da Sameena da Hauwa sun shigo gidan ina ta jin hayaniya sai da na sako hijabi da takalmi bayan na dauko wayata da kuɗi na fito na gansu, muka rumgume da Sameena, Farida kuma muka gaisa cikin fara'a sai ta yi min mgana ko ban jin daɗi ne ta ga idona duk ya ta sa ga muryata a shake. "Mura na ke yi kaɗam." Na ba ma Farida amsa daga Walima suke domin ga kayan waliman nan sun taho da shi. Hauwa na kallah kafin na ce" Hauwa zan je Ɗorayi Alhajinmu na son ganina." Tare suka haɗa baki wajen tambayan lafiya na ce lafiya ƙalau, kafin na wuce sai da na gaya musu gidan Munnira za a yi waina gobe sai Hauwa ta ce Mutaƙƙa zai zo ya ɗauke ta da safe sai ta fara sauka a gidan Munnira in sun gama sai su taho da shi Sameena ma ta ce A Gwammaja za ta kwana amma da safen za ta je can gidan Munnira su yi aikin tare Farida dai nan za ta kwana ita zan dawo na same ta, Ya Balki da Ya Aina sun ce gida za su ta fi sai zuwa gobe, nan muka yi sallama Hauwa kuma har waje ta rako ni muka taka har bakin titi na samu abun hawa shi ne ta ke faɗa min ta ga yar uwata Ma'u da ƙawarta a wajen Walima su ne gaba gaba "Allah ya kyauta." Shi ne abin da na ce kawai saboda Ma'u daman ni na san duk in da za ta ga gazawata can ta ke sha'awa sai ta yi ta yi dadin abun ma itama kishiyar gare ta, kuma ba fata na ke yi mata ba Alhajin nan na ta sai ya ƙara aure ba kuma domin ina yi mata fata ba, na san zafin kishi ba zan taɓa fatan ko maƙiyina a yi masa kishiya ba. Sai da na kusa ma isa Ɗorayi sannan na tura ma Yallaɓai saƙon na taho Ɗorayi Alhajinmu na kirana ina gama tura masa saƙon na maida wayata cikin ƙaramar jakata. Ko da na shiga gida an ta salla isha'i a masallatai Alhajinmu ya tafi masallaci shi da Datti ashe ɗazu ya dawo garin. Nima alwalan na yi na gabatar da salla, Gwaggo ma haka bayan mun idar itama ta yi ta min nasiha ta fi jadaddamin na yi hakuri na zauna da abokiyar zama ta lafiya na kuma zauna da ita da zuciya ɗaya in ma ta na da wata manufan Allah zai maida mata kayanta. Ta na cikin yi min nasihan ne sai ga Alhajinmu ya shigo ya na jin mu a cikin ɗakin Gwaggo da kanshi ya shigo nan, ita kuma Gwaggo ta fita ta bamu wuri. Kalaman da Alhajinmu ya yi amfani da su wajen yi mini nasiha ko na ce tunatarwa su suka haɗe min da gyambon zuciyata na yi ta kuka ina shessheƙa. Alhajinmu ya hore ni da abubuwa masu yawa masu girman ciki shi ne na yi hakuri na yi haƙuri na yi hakuri wata rana zan ci riba. Alhajimmu ya kalleni ya kira sunana. "Dubu" Na ɗago fuskata ina kuka ga hawaye shaɓe shabe na amsa da "Na'am Alhajinmu." Sai kawai ya gyara zama ya na faɗin" Ki saka a ranki abokiyar zama alheri ce. Ba ri na ba ki misali da mahaifiyarki lokacin da na faɗa ma Maimuna ga ta nan Gwaggon ku zan ƙara aure, duk da zafin kishi irin na mata ba ta nuna min ba, nan ta ke ta yi addu'an Allah ya sa mu riba ci junan mu da alheri dukkan wani sharri Allah ya tsare mu matsayinta na babba ta yi haƙuri kuma ta ci riba kina gani a cikin gidan nan ba su taba faɗa ba, ba wai kuma ba sa kishi ba ne a'a suna yi amma cikin ilimi da tarbiya. Har Rukayya ta koma ga Allah Gwaggonku da ni kaina Alherin ta muke faɗa kuma har gobe ba za mu daina tuna ta muna kuka ba. Bayan ba ta a duniya Maimuna ita ce uwa a gare ku ta taɓa nuna muku bambamci da su Murjanatu? Ina kuka ina girgiza ma Alhajinmu kai, shi kuma sai ya cigaba da faɗin" To kin ga falalar alherin da ke cikin abokiyar zama. Ni ma ki saka misali a kaina Dubu. Mahaifiyarmu ta rasu ni da babarku Hasiya ta bar mu hannun Hajiya Allah ya jikanta itace ta zame mana uwar da har ta koma ga Allah muna alfahari da ita. Shin Hajiya kafin ta rasu ta taɓa nuna bambamci tsakanina da su Aminu? Ko ku ta taɓa nuna muku bambamci tsakanim ku da su Muntari? Duka ɗaya ne a wajenta to shima ya na daga cikin misalin alherin abokiyar zama saboda haka ya ke ƴa ta Halimatu mai babba suna ki yi gadom mai sunan ki yi rangwame ga haƙurin ki, ki danne zuciyarki ki yi fatan alheri a cikin wannan auran na mijinki, ko da rana ɗaya kar ki bari sheɗan ya saka miki sharri a kanta. Ki yi ƙoƙarin azaman da zai gudana a tsakaninku kar ki taɓa cutar da ita, in ita ta zo da niyar cuta Ubangiji da zuciya ya ke amfani sai ki ga ya yi miki sakayya. Ki daina kuka ina da kyakyawan yaƙini a kan Yusufa zai zama adalin namiji a gare ku, kuma zai yi muku adalci dai dai gwargwardo. Saboda haka ki rike girmanki ki yi ma Ubangiji godiya, in wani abu ya taso miki acikin zuciya ki kira sunan Allah, in kuma kin tuna da mahaifiyarki ki yi mata addu'a amma ki daina kuka, ki na damu kina da sauran ƴan'uwanki kina da mijinki da ƴaƴanki to ki ɗauka Ubangiji ya gama yi miki dukkan Ni'ima." Yallaɓai ya ɗauko ni a motarsa misalin tara na dare. Ina gidan gaba mai zaman banza amma kuka kawai na ke yi. Yallaɓai na ta kiran wayata ban ɗauka ba, wayar na cikin jaka sai ya kira ta Alhajinmu shi ya ce ya zo ya ɗauke ni, ni dai bayan Alhajimmu ya gama min nasiha ya sallame ni na fito Yallaɓai ya shiga ciki kuma ya ɗan daɗe sannan ya fito ni dai ina kuka na baro gidan Datti har bakin mota ya rakamu sai faɗi ya ke yi" Ya Sadiya kamar Alhajinmu ya saka miki duka? Ya faɗa ya na dariya Yallaɓai ne ya kula shi amma ni kuka kawai na ke yi, saboda ma kar Yallaɓai ya ji kansa ya yi girma ina kuka saboda auran shi mun kusa isa gida ina share hawayena na kalle shi ina faɗin" Mama na tuna. Mutuwar ta ce ta dawo mini kamar sabuwa." Bai ce komai ba sai ma kai da ya girgiza ya riƙe hannuna guda ɗaya da shima hannunsa ɗaya ya na faɗin" Na gane. Ki yi ta mata addu'a kin ji ko? Allah ya yi mata rahama." Na amsa da Amin ina jinjina kai, mun shiga gida tara da rabi da wani yara duk sun yi barci har da Faridan Tariq ma ta yi barci Rahila ce kawai da Amina zaune a falon yara suna kallo, sai ga mu mun dawo suka yi mana sannu da zuwa, Yallaɓai ya shige ciki ni kuma na zauna wajen su yadda ba su tambayi me ya faru a can ɗorayi ba, nima ban faɗa musu komai ba, zama muka yi muna ta hira ni tea ma na sha saboda cikina ya warware. Yallaɓai ma tea ɗin ya sha ya na dai can ɗaki mu kuma muna falo muna hira an tuna da ana ta dariya da shewa su suka ɗeɓe min kewa sai wajen ɗaya saura na dare muka je muka kwanta. Faridan Tariq daman ɗakin dake gefen namu ta sauka ita da Amina Rahila kuma sai ta ce ta kwana ɗakin su Marwa ina da katifa yara ta kasa sai Marwa da Saude daman sun shimfiɗa sun kwanta sauran yaran kuma sun kwanta tare da su Jidda. Ni kuma na shige ɗakin mu na kwanta gefen Yallaɓai da har ya yi barci ma. ***** Asabar. 28. Dec 2015. Ranar asabar mun tashi da taron biki, ni dai kamar muka tsara haka tsarin ya tafi. Su Munnira su ka yo waina su Amina kuma suka yi miya da zoɓo anan gida sai kuma Alele ba dai da yawa ba na ce su Saude su wanke wake a yi. Da safe dai Tea muka sha sai buredi sannan aka soya ƙosai. Da ya ke ba wasu jama'a na gayyata ba ƴan'uwana ne, dangin miji kuma suna can Gwammaja suna na su taron Tun 11am na safe muka yi wanka gabaɗaya gidan kowa ya shirya. Tun da tun safe an gama komai, zuwa sha ɗaya da rabi su Munnira sun iso da waina Yallaɓai kuma tun safe Kawu Abba da Tariq suka zo suka fita tare da shi, ashe Tariq tare suka zo da Farida anan garin ya kwana ni ban ma sani ba sai da safen da suka zo gidan ya ke faɗa min, anan ma suka karya sannan suka fita, Yallaɓai an sha wanka da fararen kaya har da babban riga, ni kaina na jinjina ma kaina kamar an ƙwara min ƙwarin gwiwa na yi mamakin yadda na tashi cikin kuzari da dakiya. Kawu Abba ya ce min na kwantar da hankali na su suna bayana kuma matukar Tafida ya yi min wani abu da ban gane ba kawai na kira shi zai yi min mganin shi, na ce an gama mgana zan ko kira shi suna ta dariya shi da Tariq. Abin mamaki Ya Murja da wuri ta zo ita da yaranta gabaɗaya Anti ce ba ta zo ba amma ta ce ta je makarantan hadda ne in sun ta so ta ce mata ta same ta a gidana abin da ya ƙara ba ni mamaki da ita shi ne har awara ta yo min mai yawa ta zo min da shi, har sai da idanuwana suka ciko da kwalla da Ya Balki ta ba ni kula cike da awara ta ce Ya Murja ta yo min ta zo da shi. Na kalleta cikin wani yanayi kafin na ce" Ya Murja ashe dai ba Ma'u kaɗai ki ke so ba. Nima kina so na." Na faɗa cikin wani yanayi a muryanta su Ya Aina suna ta mana dariya ita ko harata ta yi kafin ta ce" Ji wata magana mutun ya taɓa kin ɗan'uwansa ne Sadiya? Ni fitinarki ne ya ba ma shiri amma ki sani ke ɗin fa jinina ne, jinin da ke gudana a jikinki da jikina bai kai wanda ke gudana a jikin Ma'u ba Ki daina gasa da ita ni duka ɗaya na ɗauke ku." Sai kawai na rumgume Ya Murja ina ƙokarin maida ƙwallar da ta kawo min "Na gode Ya Murja. Allah ya bar zumunci." Ta amsa da Amin Amim ta na dariya su Rahila na ta ya mu, haƙiƙa ba abin da ya fi ka ga ɗan'uwanka ya zo ta ya ka farincikin ko aka sin shi, duk da dai ba ma shiri da Ya Murja yau sai ta nuna ma duniya ni ɗin jininta ne Ma'u ce bare domin da ake mganar jiya ba ta zo ba, Amina ta yi karaf ta ce an ce ta je can gidan dangin mijina Walima, kuma ni na faɗa mata yau da safe da na ji ta na cigiyar Ma'u. "Gaskiya ba ta kyauta ba. Duk zumuncin da ke tsakaninta da yayar mijin Sadiya ba kai kwatan alaqan da ke tsakaninta da Sadiya ba. Maganar gaskiya ba ta kyauta ba." In ji Ya Murja, Ya Aina ko cewa ta yi" To in ma an gayyaceta can ɗin me ya hana nan ɗin ma ta leƙo? Kome ke tsakaninsu Sadiya zumumci ya wuce wasa" Rahila ta karɓe da cewa" ballatana ita Sadiya ma tun da Alhaji ya yi sulhu shike nan ta daina faɗa da Ma'u. Ta kira ta a waya ta faɗa mata tana gayyatan ta ita da shema'u. Amina ta kaɗa kai kafin ta ce" To gulma ce ya kai ta amma in ba haka me ya sa sai ta je! Wannan ma fa kamar cin mutumci ne wallahi." Ya Balki kuma tace wallahi in ta zo sai ta yi mata mgana Ya Aina ta ce ta ƙyaleta ita da kanta za ta yi mata mgana, ni dai ina gefe sun tare min faɗa ban ce komai ba ina ta mirmishi. Daman muna cikin bedroom ɗina ne mun bar su Hauwa acan falon su Jidda suna hira tare da su Farida. Jama'an da na gayyata sun yi min kara sun zo min kaf iyalan Inna mariya da na yan gandun albasa sun zo min, har da matan su Kawu Tasi'u kuma da wuri suka zo, Sameena da wuri ta baro Gwammaja ta dawo gidana da kayanta ta ce nan za ta kwana sai gobe za ta je Rano daga can za ta koma gidan mijinta haƙika na yaba da karamcinta. Iya imu muka ci taron bikin mu, mun ci waina da alele da zoɓo sai son barka. Ma'u sai wajen uku na rana suka zo ita da Shema'u sun saka kaya iri ɗaya sun chaba kwalliya tare da kanwarta Zainab da Alhaji ƙarami. Ni da ya ke na daina saka sha'anin Ma'u a gabana da fara'a ta na tarbesu lokacin na sanya leshina riga da sikat kayan kuma sun zauna a jikina adon leshin ja ne, domin ni daman ina son jan abu, sai leshin ya yi min kyau na yi kwalliyata mai sauƙi na kashe ɗauri bayan na cire atamfar da na saka da safe na tabbata daga Gwammaja ta ke, kuma a yanayin da suka ganni cikin fara'a da gayu na ya yi musu baza ta sun ɗauka za su zo su ganni cikin kuka da baƙinciki ne, ina lura da su sai bi na suke yi da kallon mamaki ni kuma ina juyi da mazaune na domin akwai su Allah ya ba ni. Shema'u za ta min shaƙiyanci da cewa" Uwargida a gidan Yallaɓai wannan ba za kalan fa? Ina mata fari na kaɗa mata kugu sannan na juya wuyana gashina da ya sauka ya karkace na baza shi da gyara tsayuwata kafin na ce" Ke ma ba ki ji abin da kika faɗa ne. Uwargida a gidan Yallaɓai fa, kin kuma san cewa daman tun can matar Yallaɓai akwai kashe kala ba sabon abu ba ne wannan." Munnira na gefe ta ranguɗa ta na faɗin" Wannan gaskiya ne ta Yallaɓai ita belbela daman ai da farin gashin ta a ka gan ta." Sai ta mika ma Hauwa hannu suka tafa, Faridan Tariq na gefe ta miƙe ta yi juyi kafin ta riƙe hanci tana faɗin" Jama'a ku ta ya ni rangaɗa ma duk wata uwargida guɗa." Kafin kace me su Munnira sun rikita falon da guɗa, ni dai ina ta dariya ganin har da Ya Balki a masu guɗan. Ni dai na saka Amina ta zubo ma su Ma'u waina da alele, na ɗauka za ta ce sun ƙoshi sai na ga ta fara cin alalen. Amina ce ta yi mata tsiyan sai da yamma ta ke zuwa bikin gidn su? "Na ɗan je Gwammaja ne. Kin san ni duka tudun biyun nawa ne Uwargida da Amaryan." Ta fada ta na wani mirmishi, wanda na tabbata na yake ne, to ba nasara ta ga abin da ba ta yi tsammani n gani ba. Nan ta ke Ya Aina ta ce mata in ta gama cin abinci ta na so za ta yi magana da ita sai ta ce ti, sun yi dai hira da su Ya Murja ba wanda ya nuna mata ko a fuska, ni dai sai faman bina da kallo suke yi ita da Shema'u ganin yadda na ci kunshina baƙi da ja haka ma yara su Jidda su kansu sun sha gayu, suna falon sai ga su Suwaiba da Jamila sun leƙo min biki suna shigowa suka hau faɗin" Ina Uwargida a gidan Ya Tafidan ne! Ta fito mu tantance tun da mun gama gano gayun amarya saura na uwargida." Sai suka ci karo da ni ai sai suka ɗau shewa daman Jamila shaƙiya ce ta karshe zagaye ni ta fara yi ta na faɗin" Kai jama'a cancanɗi. Ni fa na kasa gane ki. Anty Sadiya kin gama cinye wannan gasar." Ta faɗa ta na buga shewa ta ba ni hannu muka kashe Suwaiba kuma sai zama ta yi kan kujera ta na faɗin" Ke ce ma Amaryan Ya Sadiya to ai ko Gimbiya sai dai ta nuna miki makeup ɗin da mai kwalliya ta yi mata. Amma tabbas Uwargida ta Yallaɓai wanka ya rusuna jama'a." Sai ta karkace hanci ta saki guɗa su Munnira na ta ya ta falon ya ɗau ihu, ina gefe ina ta dariya. Allah ya ɗauke min hamdala kawai na ke yi a cikin raina ashe da ban yi taro ba haka zan zauna baƙin ciki ya kashe ni kaɗai a gida. Suma nan suka zauna suka ci waina ana ta hira ana shewa yau dai gabaɗaya ranar ta uwargidaye ne, su Ma'u ana gefe duk an muzanta. Wannan muƙamin na manyan mata ne, sai mai nasibi ubangiji ke ba ma wannan sarautar in ji Ya Balki nan ko aka saka mata guɗa ana faɗin kwarai ma da gaske Yayarmu, ni dai ba na mgana sai dariya Suwaiba ke faɗin Yallabai na can Gwammaja ana ta hotuna ta na ma cikin faɗa ne wayata na hannun Marwa ta kawo min ta ce Yallaɓai na kira suna ko jin haka suka ɗau ihu suna faɗin. "Yallaɓai dai bai manta da matar Yallaɓai ba duk da ya ga Amarya." "Ita kanta Amarya in ta zo sai dai ta yi mana mubaya'a. " In ji Munnira sai suka ƙara saka shewa suna tafawa ita da Suwaiba daman mutuniyarta ne, Jamila ta mike ta na faɗin" Wai ya ne? Gidan Uwargida ba sauti? Ya Balki yar ta ya ɓera bari ta ce" Shi ne da ya kamata sa kar mana sauti mu yi takun uwar gida ran gida Yallaɓai ya na yi ma Sadiya rawa." Ni kaina wannan karon na kasa rike kaina sai da na fashe da dariya a jikin Tv falon yara akwai wajen saka flash Amina na da shi aka yo dowloading ɗin wakar Uwar gida suka kunna mana sauti, Suwaiba ta ce duk wacce ta san ita ɗin ba Uwargida ba ce ta koma gefe wannan filin na uwargidaye ne. Sai kawai suka miƙe suna takawa, ni dai na shige ɗakin su Jidda ina amsa wayar Yallaɓai tunda ya sake kira. "Yallabai na" Na faɗa har daga ƙarƙashin zuciyata kuma a cikin wayar ma har ya tona asirin halin da na ke ciki na farinciki. "Matar Yallaɓai." Ya faɗa daga can bangaren, ina jiyo hayani ya tabbata har lokacin ya na can Gwammaja ɗin. "Na'am mijin Sadiya." Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce" Me kika samu ne? Na ji ki cikin farinciki ne' Ina mirmishi na ce" Farinciki mana. Yan'uwana ke nan suna saka ni farinciki." "Alhamdulillah na ji daɗin jin haka." "Ya Hidima Yallaɓai? A amsa min da Alhamdulillah. "Sadiya ta yunwa na ke ji tun fitan mu fa ba mu ci wani abu ba." Da sauri na ce" Me ya sa ba ku ta ho gida ba! Tun ɗazu aka kawo waina alelen ma an gama fa." Da sauri ya ce" To in zo za ki ba ni? Ina dariya na ce" Ni na isa na hana Yallaɓai abinci? Sai kun taho zan shirya muku na ku in sha Allahu." Da haka muka yi sallama, ko da na fito falo waje ya cika da shewa ga kiɗa. Har da su Ya Balki ana cikin fili ana takawa da, ban ga Ma'u da Ya Aina kenan ta ja ta gefe suna mgana. Amina na yi ma mgana abinci su Yallabai daman an cire musu, tare muka shiga kitchen ɗin ina ganin abin da ta ke haɗawan, ina cikin kitchen ɗin Munnira ta zo ta ja ni ina faɗin ta bari ina zuwa amma ba ta saurareni ba, sai tsakiyar falo ta kuma riƙe hannuna ta na rawa da ni farida ta mike ta na min liki, Shema'u na ga ta na kallona sai kawai na sakin hannun Munnira na fara takawa, suna min shewa da guɗa hana ni saƙat suka yi har su Jidda fa sun shige rawan suma sun ce ba za a bar su a baya ba. Muna can muna bidiri ko shigowar su Yallaɓai ba mu ji ba, sai da ya leƙo da kansa ya na faɗin" Ku ce shasu kuke yi kenan" Ai su Suwaiba suna ganin shi suka rufe shi da guɗa, ya na kare fuskarshi ya ke faɗin" Wai guɗan nan ba ta ƙarewa ne Suwaiba? "Wanda muka yi maka a Gwammaja na Amarya ne. Wannan kuma ai sautin na uwargida ne." Suwaiba ta faɗa ta na ƙara sakin masa guɗaa akai, ya dafe kansa ya na dariya Jamila ma ta kama Munnira na ta ya ta, Sai ga Kawu da Tariq sun shigo. Kawu shi cewa ya yi" Danƙari Tafida ka ce ga in da ake biki." Tariq kuma ya ce" Shi fa Tafida duka amare gare shi." Ya faɗa ya na kallona ni kunya ma na ji na sauke kaima ƙasa, Suwaiba ta fara yi ma kawu shaƙiyanci wai shima Allah ya sa baɗi uwar haka suna Rano sun je suna ya zabga mata harara kafin ya ce" Sai dai in da cikin ta zo ko? Ni kaina sai da na yi dariya daman kawu akwai yanka mgana gaisuwa suka yi da su Ya Balki da su Inna Mariya ƙin barin shi suka yi suka ce sai an yi mana hotuna, haka nan suka tsaida mu suna ta ɗaukan mu hoto har da Tariq shima da wayarsa shi da Faridan sa, sai da na ce musu su yi haƙuri, Ango fa na jin yunwa a yi masa afuwa na bashi abinci ai sai su Suwaiba suka ƙara ɗaukan shewa suna dariya. "Allah ya shirye ki Suwaiba." Haka Tariq ya faɗa ya na girgiza kai. Dakyar Yallaɓai ya samu ya ƙwace suka koma falon shi sai na saka Marwa ta kai musu abincin da komai da komai a falon na Yallaɓai, bayan sun gama ci sun ƙoshi har suka bar ma gidan ban sani ba muna can ana ta hira da shewa, Ma'u dai tun da ta dawo falon ba ta ƙara dariya ba, ga ta nan dai zaune ta na bin kowa da kallo, muna nan tare da su Suwaiba har dare bayan mangariba na sauya kaya na saka material Ya Aina da Ya Balki har da Ya Murja da Zaituna da mutanen Gandun albasa sun koma gida sai aka bar su Rahila, Ma'u ma da kawarta ba su tafi ba, da daddaren Halima ta zo ita da ƙawarta ta ce daga nan gidan Amarya za su wuce domin an tafi da ita tun mangariba ta zo min ne kawai na ce mata na gode. Haka ma Lailan Ya Auwal a lokacin ta zo ita da ƙanwarta na yi mata uziri tun da suna da hidima. Sai wajen tara na dare gidan ya yi shuru, su Suwaiba sun koma Gwammaja su Ma'u sun tafi, Haka ma su Hauwa da Munnira daga ni sai Amina sai Rahila sai Sameena da ta yini ma kwance ba ta jin daɗi duk shewan da aka yi ta na ɗaki, sai Saude da Marwa sai su Jidda har maman Saude da mai yi mana kitso sun zo min biki. Su suka gyara gidan ma ya yi kintsi sai gidan ya koma ya yi shuru kamar ba shi ba ne ɗazu ya cika da hayaniyar mutane ana ta hidima sai kuma da ya yi shurun na fara jin wani iri a cikin ƙasan raina. Ranar da na ke gudu ce yau ta zo. Ranar da Yallaɓai zai je ya kwana da wata mace ba ni ba. Tirƙashi. *Janafty* *TKG* 09. *Assalamu alaikum!* *Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.* *Karku manta bamu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin faɗakarwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.* *Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.* *Ku biya kuɗinku ta wannan asusun Kamar haka👇🏻* For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account 👇🏻 7087809778 Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704. *Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin 08167768704.* Ƙarfe tara da rabi na dare sai ga Yallaɓai ya dawo shi kaɗai ya ce min ya ba ro su Tariq a gidan mai za su saka mai amotar shi kuma sai ya hau adai daita ya taho gida ya yi wanka ya shirya kafin lokacin sun taho sai su raka shi can gidan Gimbiyar.   Kamar ya sani bai ko neme ni na haɗa masa ruwan wanka ba, ba domin in ya ce na yi ba zan yi ba sai domin zuciyata a lokacin ba ta cikin sukuni, muna gama maganar nan da shi ya shiga wanka ni kuma sai na koma can falo wajen su Rahila ba na so na zauna ni kaɗai tunani da damuwa su taru su ƙara ruguza ɗan sauran kuzarina. Duk hiran da suke yi na kasa saka musu baki, zaune kawai na ke kamar mutum da mutumu ba na ma fahimtar hiran da suke yi, tun da ni nawa tunanin ya yi zurfin tunanin yau fa Yallaɓai ba anan zai kwana ba, yau ɗin wata rana ne da zai je ya kwana da wata mace ba ni ba, tuna haka kawai in na yi sai na ji numfashina ya sarƙe. Zuciyata na harbawa da sauri sauri ina dai zaune ne ina wasa da yatsun hannuna amma ni kaɗai na san halin da gangan jikina da zuciyata ke ciki, amma ban bari na shagala ba, sai na fara kiran sunan Allah a acikin raina domin na samu natsuwa.   Haka kawai na ji ba na son komawa cikin bedroom ɗin mu, tun da Yallaɓai a yanzu na san ya fito wanka ya na shiryawa. Tun da aka faro wannan al'amarin ban bari Yallaɓai ya ga gazawata ba. In ko na bari ya gani yanzu kamar na yi faɗuwar baƙar tasa ne, shi ya sa da na koma na gan shi raina ya sosa hankalina ya tashi gwara na yi zama na a nan cikin ƴan'uwana a ƙalla dai ko ba na da natsuwar fahimtar hiran su ina kallon fuskokinsu za su iya zame min garkuwa daga bayyana raunina a wannan daren. Ina nan zaune shuru sai ga Sameena ta fito daga ɗaki har sannu da su Amina suka yi ta mata wallahi ni ban ma ji ba, sai da ta zo kusa da ni ta na taɓa kafaɗata sannan na dawo duniyar da suke, kallona ta yi sai ta ga kamar ina firgice ne, sai ta zagayo kusa da ni ta zauna ta na faɗin" Matar Baba lafiya? "Ya jikin ki! Sannu" Na katse wancan tambayan na ta, sai ta amsa min da ta ji sauƙi, daga ni har ita sai muka rasa abin cewa, ni kam ba na rasa ba ne yanayin da na ke ciki ne ya sa kalaman bakina suka ƙare, Faridan Tariq daman ta na ɗakin su Jidda ta je kwantar da su Hassan sai ga ta fito ta na faɗin ga su Tariq can a waje ya ce suna kiran wayar Tafida ba ta shiga suna jiran shi a ƙofar gida.   Lokacin da ta faɗi haka sai gabaɗaya jikina ya fara rawa har Sameena da ke gefena sai da ta fahimci haka, da sauri ta saka hannu ta riƙe hannuna guda ɗaya sai na juya ina kallonta da idanuwana da na ji kamar sun juye, kai ta girgiza min kawai sai na bi ta da kallo domin kamar wata yarinya sai na kasa fahimtar ta, bakina na ji ya bushe na kasa ma haɗiye miyau, maƙogaro na kuma na wani irin zafi kamar wani abu ya karce ni ban sani ba. "Sadiya ki faɗa ma Yallaɓai suna jiran shi a ƙofar gida." Farida ta faɗa ta na kallona sai kawai na bi ta da kallo itama kamar irin ban fahimta ba, kuma dukkansu sai suka kasa gane yanayin da na ke ciki, illa Sameena da ke gefena da ta yi saurin cewa" Ta shi Matar Baba." Ta faɗa ta na kallona, lokaci ɗaya ta na ɗan bubbuga hannuna alamun lallashi da ban baki, ina ƙokarin ƙwato numfashina ne na ji muryan Yallaɓai ta korido ya na kiran sunana. "Sadiya." "Sadiya.." "To ai ga Yallaɓan ma can ya na kiran ki Ya Sadiya." Amina ta faɗa ta na kallona kamar an ja ni tsaye sai ganina na yi na miƙe kan kafafuna duk yadda na so na yi musu mirmishi na kasa illa kaina da na kaɗa ina faɗin" Ba. ba ri na yi masa mgana." Ina gama faɗin haka na juya zan wuce ban ko kallon gabana sai gashi na ci tuntuɓe da cafet na kusa faɗuwa gabaɗaya suka haɗa baki wajen faɗin" Subhanallah."   Na kusa kaiwa kasa na samu na riƙe kujera ban riga na kai ƙasan ba, jikina ba in da ba ya rawa sai kawai na wuce ina tafiya ina ji kamar ina jin sanyi zazzaɓi zai kamani domin ina ta matse jikina a waje ɗaya, da kallo suka bi ni, saboda sai a lokacin dukkansu suka kula da yanayina sai kuma jikinsu ya yi sanyi ina jin Farida daga bayana ta na faɗin" Ki yi a hankali Sadiya kar ki faɗi." Cikin muryan sanyi kamar na tausayi haka na ji a cikin maganarta. Ina gama shigewa koridon Sameena ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Allah ya ƙara ma Matar Baba haƙuri da juriya." Faridan Tariq sai ta koma ta zauna a gefen kujera ta na faɗin"Amin. Amma lamarin ba daɗi." Rahila dai da Amina ba su yi magana ba, amma jikin su duk ya yi sanyi sai falon ya koma ya yi shuru hiran ma sai ta tsaya kowa da tunanin da ya ke yi shi da zuciyarsa. Ni kuma ina fita daga koridon na buɗe kofa na tsaya a ƙofar bedroom ɗin na kasa shiga, dafe kirjina na yi jin kamar zuciya ta za ta faso ta fito saboda yanayin da na ke ciki, duƙawa na yi ina maida numfashi sama sama kamar wacce ta yi gudun tsere ji na ke yi kamar sheɗata na neman ɗaukewa na ma kasa iya dai daita yanayina ballatana har na tura ƙofa na shiga ɗakin, ina duƙen ban sani ba sai kawai na ji an buɗe kofa Yallaɓai ya bayyana a gabana. Kaina na dago ina duke kan gwiwoyiyina na ɗago ina kallon shi, na ga lokacin da ya ɗan buɗe ido cikin mamakin ganina a wajen, ni kuma kayan jikinsa na ke kallo wata shadda ce sabuwa ce mai ruwan sararin samaniya ɗinkin zamani ne, har saman kaina na ke jin ƙamshin turaran Yallaɓai har kafarsa sabon takalmi ne domin ni ban ma san ya siya takalmi sabo ba, kamar wani cuta ina ganin Yallaɓai sai na ji kawai ina haƙi, daga tsuggune kamar ina ganin hajijiya ne ma. "Sadiya lafiya? Me kike yi anan? Ya faɗa yana kallona yana ƙokarin shima ya duka shima da sauri na yi ƙoƙarin na miƙe kawai sai na ji juwwa ta ɗauke ni na yi baya zan faɗi da hanzari Yallaɓai ya taro ni, nima sai gani na ƙamƙame hannayensa ina cigaba da haki kamar mai cutar Asthma saboda na ɗauka zan faɗi ne, ni fa gabaɗaya ji na ke yi kamar wata cuta ta kamani, kuma irin cutar da ban taɓa samun kaina a cikin sa ba, ina tunanin cutar yau ce ta kamani. "Ba ki da lafiya ne? "Subhanallah." Na ji yo Yallaɓai na faɗa Sama sama ni dai ban dawo hayyacina ba sai da na ganni zaune a gefen gado, kitchen ya koma ya ɗauko min ruwa mai ɗan sanyi ya buɗe min ya kuma kafa min a baki ya ce na sha. Na ɗauka ban ji ƙishi sai ga shi na ɗaga roban ruwa na dire bakomai a ciki shi kan shi Yallaɓai da mamaki ya ke kallona Allah ya taimake ni sai na fara dawowa hayyacina na ji numfashina na daidaita sannan na daina hakin nan, kuma bakina bai bushe ba yanzu sannan ina jin maƙogwarona ya daina kartamin ɗin da ya ke yi ɗazu.   "Sadiya." Yallaɓai ya faɗa yana durƙushe a gabana lokaci ɗaya kuma ya na kallona sai na ɗago ina kallon shi, yadda kuka san na gaji haka na ke jin duk jikina ya yi sanyi kamar an yi min dukan tsiya. Fuskata ya saka hannu ya na shafawa har ya na ɗan tapping ɗin shi da hannun shi sai na ƙara buɗe idanuwana ina kallon shi amma ban yi magana ba. "Me ke damun ki? Haka ya faɗa cikin kulawa, a cikin zuciyata na ke maimaita Hasbunallahi wa'imal wakel. Sai kuma na ji nauyin jikina ya ragu sannan bakina ya saki numfashina ya dai daita, Yallaɓai ya tashi tsaye ya saka hannunsa guda biyu ya ɗago duka kafaɗuna tsaye lokaci ɗaya ya sakani a jikinsa ya rumgumeni ƙamƙam a cikin jikinsa nima ban san lokacin da na miƙa hannuwana na zagaye bayan shi na shige jikinsa sosai kamar zan tsaga jikinsa na koma ciki, shi kan shi ya ji yanayin riƙon da na yi masa duk yadda na so kar kuka ya zo min duk yadda na so kada yau ɗin nan na raunana sai da raunin zuciyata ya rinjayeni sai kawai ji na yi ina kuka har da shessheƙa, hawayena suna sauka a saman kafaɗan shi, ko bai faɗa min ba ni na san jikin Yallaɓai ya yi sanyi, domin kansa na saman kafaɗata kawai ya na riƙe da ni amma ya kasa iya mgana ni kuma ina ta kuka yi yi har da kamar zan shiɗe, kuma in za a kashe ne ba zan iya cewa ga dalilin kukana ba kawai ni dai a raina ji na ke yi kamar na fi kowa na duniya nan shiga matsala, kuma ina ji kamar Yallaɓai zai yi min nisan da tun da muka yi aure bai taɓa min irin shi ba. Bai hana ni kuka ba sai da muka yi kusan mintina goma a haka, daga ni har shi muna ji ana ta kiran wayarsa da ke saman side drower ɗin gadonmu. Amma bai sake ni ba har sai da na gaji da kukana na yi shuru ni ce ma na sake shi tuna cewa ana can ana jiran shi a waje sannan ita kanta Gimbiyar ta na can ta na jiran sa. Ban kalle shi ba da sauri na juya baya murya ta shaƙe ina faɗin. "Su Tariq na waje suna jiran ka." Na faɗa lokaci ɗaya ina goge hawayena da hannuna guda ɗaya. Ƙaramar jakarsa na gani a saman gado alamun ya gama haɗa kayan shi da zai bukata acan ina kallon jakar sai ga hawaye sharr, amma ina ƙokarin tare su, ya na ƙokarim sake riƙe ni na yi saurin kaucewa ina faɗin. " Yallaɓai ka je kawai sai da safe." Na faɗa ina ƙokarin maida kukana da ya taso min amma zuciyata sai da ta rinjayene na fashe masa da kuka na ma kasa iya kallon shi, sai kawai na juya da sauri zan fita amma bai bar ni ba da sauri ya riƙo ni amma ina ƙokarin zamewa daga riƙon shi cikin kuka kamar ina masa magiya na ke faɗin "Don Allah." Ina kuka maganar ta tsaya mini na kasa cigaba da magana sai ya sassauta riƙon da ya yi min ya na kallona wai ni Yallaɓai ke yi ma kallon tausayi saboda ya san ɗin abar tausayi ce. "Don Allah ka ƙyaleni." "Don Allah." Na faɗa ina masa magiya kuka na ke yi kamar raina zai fita, sai kawai ya sake ni na juya zan fita daga ɗakin sai ya kira sunana. "Sadiya." Sai na dakata amma ban juyo ba, sai dai na saka hanuna guda ɗaya na dafe bakina har sautin kukana ya fito. "Ki yi hakuri." "Kin ji." Wai haƙuri ya ke ba ni? In na ce ban hakura ba zai fasa tafiya ne? Ko kuwa  zai iya maida hannun agogo baya ne, ko juyawa ban yi ba na buɗe kofa na fice sai na rasa ina zani kawai sai na buɗe kofar tiolet na shige na rufe ƙofar da sakata na sulale sai ga ni na yi zaman dirshan a saman tayels ɗin Tiolet ina mai fashewa da kuka da karfin gaske, suya zuciyata ke yi, har hancina na ke jin ya na fitar da wani yaji yaji, idanuwana sun yi min mugun nauyin da na kasa iya juyawasu, kaina na wani irin saramin da ƙarfin gaske, kaina na kasa a cikin gwiyoyina ina cigaba da kukana mai sauti, roƙon da na yi masa ne ya sa ya ƙyaleni na ji fitowarsa daga bedroom sannan jikina ya ba ni ya daɗe a ƙofar tiolet ɗin kafin ya buɗe kofar korido ya fice, ba jimawa na ji buɗe get din sa tunda shima window ɗin makewayin na ta haraban gidan ne, ban san ko shi ya faɗa musu ga in da na ke ba domin can ba jimawa sai ga Farida ta zo har ƙofar tiolet ɗin ta na kiran sunana ban amsa ba, sai ga Sameena Amina da Rahila kar su yi tunanin wani abu ya sa daga ciki na yi musu gyaran murya. Ban san suna tsaye a ƙofar Tiolet ɗin ba, har sai da na wanke fuskata ina fitowa na gansu tsatsaye cikin damuwa sai kawai na yi mirmishi na fito ina rufe ƙofar Tiolet ɗin lokaci ɗaya ina faɗin" Lafiya ta kalau fa kar ku ɗaga hankalin ku." Na faɗa ina raɓawa ta gefen Rahila na buɗe kofar Bedroom ɗin mu na shiga sai na juyo ina rike da kofar ganin duk sun bi ni da kallon Tausayi sai na ƙara yin mirmishi da kumbararrun idanuwana kafin na ce. "Da gaske na ke yi lafiya ta ƙalau. Sai da safe ina so na zauna ni kaɗai ne." "Kin tabbata? In Farida ita kuma Amina sai cewa ta yi" Ko na zo na taya ki kwana ne Ya Sadiya? Sai na gyaɗa mata kai alamun toh, sai Sameena ta ce hakan ma ya yi, na juya na shiga cikin ɗakin Farida ce kaɗai ta biyo bayana sauran kuma suka koma a gefen gado na zauna ina yarfe ruwan fuskata. Ta na tsayen ba ta zauna ba ta ce" Ki yi ta kiran sunan Allah, in natsuwar ba ta samu ba ki kunna karatun Qur'ani in sha Allahu za ki samu salama da Aminci." Sai na amsa mata da toh, bayan na ce ta ɗauko mini wayar a can falo, sai ga shi ta fita ta kawo mini ta kuma fice bayan ta yi mini sai da safe, kayan jikina na sauya domin sun jiƙe, na saka riga da wando na barci da hula sai kuma na saka wani ƙaramin hijabi domin ina jin sanyi, sai da na kwanta na rufe kafafuna da bargo sannan na ɗauki wayar tawa sai na ga Yallaɓai ya tura mini saƙo yanzu ba daɗewa. "Ki yi haƙuri Sadiya ta. Ki sani auran da na ƙara ba shi ne zai cire ƙaunar da na ke yi miki a cikin zuciyata ba. Ki sani ke ce Yusuf haka Yusuf ne Sadiya mun zama Hanta da jini ɗaya ba zai iya rayuwa ba ɗaya ba. Kar ki ji a ranki cewa matsayin ki ya sauya ke ce a jiya kuma har da gobe ma ke ɗin ce. Ina ƙaunarki Sadiya ta ƙauna mara yankewa. Na gode da dukkan sadaukarwarki gare ni, na gode da karamci da mutumtawa, na gode da yaƙana da martabawa ba, na yi miki alƙwarin adalci mai yawan da zan kwantata a tsakanin ki da Saudatu. Ki yi barci cikin salama Amintattaciya ta." In a baya ne Yallaɓai ya turo mini waɗanan kalaman yini zan yi ko kwana cikin farinciki amma yau sam sai na ji ba su yi mini tasiri ba, ban goge saƙon ba amma na yi saurin fita daga kan sunan shi, domin sai na ji kamar zuciyata na zugani da na rubuta masa cewa in har ya na sona kuma adalci zai yi mini to ya saki Gimbiya ya dawo gareni, abin da ba zai taɓa faruwa ba kenan shi ya sa na yi saurin fita daga wajen na shiga cikin wayata na lalubo karatun Qur'ani baƙara na kunna na ɗan rage ƙara na saita shi dai dai kunnuwana sannan na koma na kwanta ga casbaha a hannuna ina ja, daman na rage hasken ɗakin sai duhu, ina kwance ina ta hailala da salati lokaci ɗaya karatun na shiga kaina duk yadda sheɗan ya so ya fassara tunanina na  kasa barcin ayoyin Allah sun fattake shi, haka na ji iskar natsuwa na shiga jikina da zuciyata sai ga ni na yi luf a kwance ina lumshe ido barci na son kamani barcin da ban taɓa tunanin zai iya ɗaukata a wannan daren ba. Sai ga shi kuma ya ɗauke ni, ba ni na farka ba sai uku na dare har lokacin karatun Qur'anin ya na ta yi, sai da na juya sai na ga Amina a gefena ta na barci da waya ta daman na duba lokaci uku ta gota sai kawai na sauko daga kan gadon na yaye bargo karatun na kashe sannan na yi amfani da wayar na haska tunda na ga sun ɗauke wuta Tiolet na shiga na ɗauro alwala na dawo ɗaki na shimfiɗa sallaya sannan na saka dogon hijabina na kabbarta salla sai da na yi raka'a takwas sannan na rufe da shafa'i da wuturi, bayan na idar na tashi na ɗauko Qur'ani na fara karatu daga suratul Tauba, a hankali na ke yi karatun saboda kar na ta da Amina, ba ni na tsaya da karatu ba sai da aka fara kiran salla na biyu daga msallatan kusa damu sannan na dakata na ɗaga hannayena sama na roƙi Ubangiji juriya da hakuri sannan na roƙe shi da ya iya yi min a dukkan lamarin da ni ba zan iya ba ya cire min kishi da kyashi ya ba ma zuciyata aminci da salama na daɗe ina kai ma Allah kukana sanman na shafa, na kuma koma ina neman gafaran Allah da casbahan hannuna lalle Ubangiji shi ne ke saukar da duk waraka sai ga ni zuciyata wasai sai ma wani iskar da na ke ji ya na shigata na salama da aminci. Ni na ta da Amina na ce lokacin sallah ya yi sai kawai ta juya ta ce min ba ta yi, fita na yi zuwa ɗakin kusa da ni sai na ga har sun ta shi ma Sameena ce kaɗai cikin bargo Farida ta ce min ta na hutu, na san da ga ita har Rahila sun yi mamakin ganina kamar ba ni ba, Farida ta kalleni lokacin da na ce ba ri na je na ta da su Marwa har na juya sai ta kira sunana na juyo ina kallonta. "Ina ta jiyo karatun ki ɗazu." Sai na mirmishi kafin na ce" Wai har kin jiyo? Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Nima da na kasa barci, fitan ki na ji ya sa bayan kin fito da ga tiolet ɗin nima na tashi na shiga na ɗauro alwala na yi nafiloli." Sai na jinjina mata kai ban yi mgana ba itama kuma sai ta ta da salla, Rahila daman sallar ta ke yi lokacin da na shigo. Fita na yi zuwa ɗakin su Jidda suma sun ta shi manyan sai yaran ne ke ta barci ni na ta da Baby ta na mutsike ido na ce ta shiga tiolet ta wanke ido ta yo alwala, na fita da cewa in na idar da salla zan dawo mu yi azkar, haka ko aka yi ina idar da salla na koma ɗakin  yaran na tattara su gabaɗaya baƙi da yan gida har da su Saude, na ce mu fara karanta azkar da karfi a tare, bayan mun gama na ce kowacce ta ɗauko Qur'ani mu yi karatu. Ni ce fa har wajen bakwai na safe a ɗakin yaran sai da na yi musu karatu gabaɗaya har Marwa sannan muka shiga kitchen tun da ta ce min yau za ta je asibiti, ta re da saude mu uku muka ɗan gyara kitchen din sannan na ce su fere doya a soya sai kunu da za a dama a yi ƙosai Rahila ce ta fara tasowa ita ta karɓe ni  daman kunin Saude na gyaran wake Marwa na fere doya.   Daga baya har Sameena da Farida sun fito sai aka kama gabaɗaya aikin, kafin lokaci an gama tunda hannun da yawa. Mai son shan kuni ya sha in tea ne ga shi nan in ƙosai ne ga shi nan, in kuma doya ne duk dai ga shi nan bayan an gama karyawa sai suka gyara min gidan su Rahila kenan yara kuma Saude ta yi musu wanka su Jidda kuma da suke manya suka yi ma kansu. Ni kaina tun safe na yi wanka na saka cikin sabbin atamfofina, zuwa azahar kowa ya yi wanka ya shirya har na fara kewa aka ce baƙo raba duk yau ɗin za su ta fi su bar ni  ni kaɗai daɗin abin ma yara sun samu hutun makaranta kaɗaicin ba zai yi min yawa ba. Da rana Tuwo aka yi miyar agushi ina da sauran manshanu sai aka juye shi sai ƙashin naman ragon ragowan na jiya aka yi amfani da shi, akwai ma ragowan waina da safe Rahila ta ɗumama ta saka masa siga ta sha da kuni da safe, alele daman ragowan balaraba na kwashe ma sauran da za ta wuce gida na ce ta kaima yara ban bari abinci ya kwanan min a gida ba. Sai da aka ci abincin rana sannan Farida ta yi shirin tafiya tun da ta ce Tariq ya kira ta ya ce ta je Gwammaja daga can za su wuce Sameena ma can Gwamnajan za ta je shi ya sa suka shirya za su tafi tare. Na yi musu godiya ƙwarai da karamci na yi musu rakiya har haraba gidan muka rumgume juna ɗaya bayan ɗaya. "Na gode sosai. Allah ya mai da ku gidajen ku lafiya." "Haba. Bakomai a yi ta dai hakuri a kauda kai Allah ya zaunar da ku lafiya ya kaɗe fitina." Farida ke faɗin haka ni kuma ina amsawa da Amin Amin, Sameena kuma hannuwana ta rike kafin ta ce" Matar Baba ni fa ba na jin ki, sannan Baba ma ya na sonki zuwan wata ba zai rage ki da komai ba in sha Allahu." Sai na yi mata mirmishi kafin na gyaɗa kai ina faɗin in sha Allahu. Ga su dai suna na kusa da Gimbiya amma ni sun nuna min ƙauna ƙwarai kuma na yi ta musu godiya na kuma yaba da karamcin su. Sun tafi ba daɗewa sai ga Hauwa da Munnira suka ce suma daga Gwammaja su ke, suka leƙo ni kafin su wuce gida har ina musu tsiyan ko daga gidan Amarya suke? Munnira na tabe baki ta ce min" Wani gidan Amaryan! Allah ya kyauta. Mu ba ma mu ce za mu je ba, masu zuwa dai sun je tun jiya yau ma da na ji wasu na mganar komawa Anty Bahijja ta hana ta ce a bar Amarya da ango su huta kar wanda ya je domin ya dame su." Cikin mamaki na ce" Topha. To su waye daman ke son zuwa? "Can dai ahalinsu na Rano ne. Naja ce kawai aka ce za ta je itama sako za ta kai mata. Wai kar a dame su ki ji fa." Munnira ta faɗa ta na kallona, muna zaune daman a falon yara ne sai kawai na jinjina kai kafin na ce" Ba shakka." Hauwa dai na gefe sai ta muskuta kafin ta ce" Su Ayshe tun safe suka koma ɗazu da muka yi waya ta ce min tun jiya Anty Bahijja ta ce duk wanda ke son ganin gidan Amarya ya je a jiya domin in Ango ya shiga ɗaki ba mai yi musu sintiri a dame su. Na ce kamar wata budurwa? Anty Bahijja akwai kambama abu wallahi." Ina ta dai kallonsu amma ban yi magana ba, Munnira ta ja tsaki kafin ta ce" Ita ce uwar Gimbiyar ba ki ga alama ba? Gani na yi hiran ta su za ta iya dawo min da damuwar zuciyata ya sa na katse hiran su da tambayan ko a zubo abinci? Sai suka ce sun ƙoshi amma ƙila kafin su tafi su ɗan taba tunda tuwo ne, muna tare da su har Yamma, suna ma gidan Ya Muntari ya zo ɗaukan Rahila da yara. Na matsa masa sai da ya shigo har falon Yallaɓai muka gaisa na kawo masa ruwa ya sha har su Jidda suka zo wajen sa suna masa hira ya na biye musu, shi daman akwai son yara in dai yara ne haka za ka gan shi da su ya na biye musu ba ruwan shi. "Ashe kuma kin samu abokiyar zama? Ya faɗa ya na kallona, kaina na ƙasa sai na gyaɗa masa kai. "To sai haƙuri Allah ya zaunar da ku lafiya ban da dai ɗaukan zuga." Na ce in sha Allahu, har ya na min tsiya wai Allah ya ƙara min haƙuri domin ya san halina ba ni da haƙuri. "Kai Ya Muntari." Na faɗa ina ƴar dariya, shima dariyan ya ke shi da Rahila ya na ce min ai ya san halina, kamar kar Rahila ta tafi amma ina ji ina gani ta wuce gida ita da yara ni da Amina har waje muka raka su, da Amina ta so ta je Ɗorayi ta kwana yau na marairaice na ce ta bari gobe da safe don Allah sannan ta yarda ta zauna na ce sai ma ta tafi tare da Saude kawai. Su ma su Hauwa suna yin sallar mangariba suka yi min sallama suka wuce mun rabu akan zan bi su  har gida na yi musu bangajiya sai gida ya rage daga ni sai Amina sai Saude sai yara. Nima sallar mangariban na yi sannan na natsu a ɗaki wayata tun safe ta na saman gado ban bi ta kanta ba sai da na gama azkar sannan na tube hijabin jikina na yi zaune gefen gado sannan na jawo wayar ina ganin an kirani, da ya ke a silent na saka wayar kuma ban bi ta kanta ba. 7 missed calls aka yi min Yallaɓai huɗu ya yi min sai Anty Zabba da ta yi min guda biyu sai wata lamba da ban san ko ta wacece ba sannan ga sako na an turamin tun kafin na buɗe jikina ya ba ni Yallaɓai ne shi ya sa ban yi ma rawan jikin buɗewa ba, sai da na kira Anty Zabba muka yi magana ita ke faɗa min ta ga hotunammu ni da Yallaɓai su Suwaiba sun ɗora a waya mun sha kyau. "Sadiya gaskiya kin burgeni ba domin kar a ce na so ki na ƙi amarya ba. Da na ce ko da ranar auranta ne amma kin fita kyau." Ina ta dariya na ce" Kin ko so ni Anty Zabba. Amma ina ni na fita kyau? "Allah da gaske na ke yi. Kun yi kyau sossi dukkan ku. Allah ya ba ku zaman lafiya da hakuri da juna." Ba mu jima muna mgana ba muka yi sallama, ni ban ma da hotunan ban ko hau online ɗin ba ballatana in gani, ba na ma som hawa domin na san sun ta ɗora na Gimbiya da Yallabai ni kuma ba na son ganin abin da zai ɓata min rai shi ya sa na haƙura da kunna data sai ƙura ta lafa. Sai da na kira lambar da aka kirani na ga ba a ɗauka ba sannan na duba saƙon Yallaɓai, saƙon har guda biyu ɗaya da safe ne ya turomin wajajen goma na safe ɗayan kuma da yamma nan ne, kamar yadda kiran na shi suke a jere. Biyu da safe biyu nan kuma da yamma nan ne ya sake kira. "Good morning My Darling Wife! Kun ta shi lafiya? Ina kewar ku. Ki gaida mini da Jidda da Baby." Sai Ɗayan kuma cewa ya yi. "Sadiya ta kuna lafiya ko? Gobe in zo na duba ku? Na kira ba ki ɗauka ba ko har yanzu akwai baƙi ne a gidan? Hmm! Kawai na ce a ƙasan maƙogwaaro na saboda na kasa ma mgana. Wai My Darling Wife Yallaɓai ne har da sauya min suna mai daɗi haka, wai munafunci irin na ɗa Namiji ya kwana da wata macen amma yana ce min wai ya yi kewar mu. Sannan tambayarsa ya zo ya duba mu sai da na ja mata tsaƙi, to yaushe namiji yaushe ya fara neman izinin in zai yi wani abu? Lokacin da ya yi auran ai bai gaya min ba. Sai na zuwa duba mu ne zai turo min wani munafunci, da na so na yi banza da saƙonni ne sai na fasa na rubuta masa gajeren saƙo ina yi ina hararan wayar kamar shi ne a cikin ta. "Muna nan lafiya. A'a ka yi zaman ka kawai ba gobe ba." Na yi mamakin yadda daga tura saƙo ko mintina goma ba a yi ba sai ga amsar shi kamar wayar ta na hannun shi ne. "To sai yaushe? Haka kawai ya ce, sai kawai na ga kamar so ya ke yi ya yi wasa da hankalina. Nan take na saka wayata a filght mode na dankwafar da wayar ina girgiza kafa, har da su kaɗa harshe takaici ya isheni ni kaɗai. Ina cikin wannan halin Amina ta shigo sai na ɗan saki, kamar ta san in na zauna ni kaɗai tunani zai iya yi mun kutse zaman ta a kusa da ni ya sa sai na maida hankalina kanta muna ta ɗan taɓa hira a kan dai yan gidanmu ne. "Ya Sadiya Ma'u ta ba ni mamaki. Ni fa in kika ce munafuka ce in yi ta mamakinta." Mirmishin takaici na yi kafin na ce" Uhm ai wanda bai san halinta ba zai taɓa yarda munafuka ba ce. Ta iya kissa fuska biyu gare ta shi ya sa." Amina ta jinjina kai kafin ta ce" Na gani kuwa. Ai da Ya Aina ta mata mgana sai ta fara kuka ta na cewa ita ba da wata manufa ta je Gwammaja ba. " Ina dariya na ce" To ko da wata manufar ne za ta nuna ne? Makira ce fa Ma'u ina faɗa muku ba ku yarda. Uhm! Shi ya sa ni ban taɓa son Ma'u ba halayyanta ba su da kyau sam" Sai Amina ta ja numfashi kafin ta ce" Uhm ai na gani yanzu. Ni dai fatana kar ta je ta rika bin Amaryan Yallaɓai ta rikita muku zama tunda ta shige ma yayar ta sa." "Za ta iya aikata komai domin ta ga ni na yi ƙasa. Amma kuma komai za ta yi na fi karfinta ni Allah na ce ita kuma tunda makirci ta saka ma gaba sai dai ya ƙare a kanta." "Amin wallahi kuwa ah." Amina ta faɗa har ta na riƙe baki ita fa Ma'u ce ke ba ta mamaki, ni ko na ce ta ma daina mamaki Ma'u ta wuce tunanin su wallahi nan na ke faɗa mata wasu sirrukan nawa ita ke faɗa ma Anty Bahijja in muka haɗu ta rika zagina ta yada min mgana na ƙarishe da cewa" Ina da ta cewa ne Amina? Ƴar'uwata ce ta ba da ni fa, shi ya sa na ke addu'an Allah ya shiga tsakanina da Ma'u duk mugun nufin ta ya koma kanta." "Amin in sha Allahu." Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na cigaba da faɗin" Ita fa abin da ya faru na rashin auran Ya Hamza ne ta riƙe a ranta shi ya sa ta ke jin haushin ki Ya Sadiya." "Sai dai ko ta mutu amma Ya Hamza ya yi mata nisa. Kuma wallahi tallahi ba na nadaman abin da na yi har nan da gaban Abada Amina" Na faɗa ina mai jadadda mganata sannan na ƙara da cewa" Ba ki lura ƙawarta Shema na ta ya ta ba. Ita kuma shegiya ta ki auru ai duk wanda ya ce tunkunyar wani ba za ta tafasa ba ina mai tabbatar miki da na shi ko ɗumi ba za ta yi ba. Kuma ko alaqarsu da Ma'u hali ne ya zo ɗaya amma in kin lura Ma'u ta fita wayau ita kuma har da kwaɗayi gani ta ke yi Ma'un na ba ta duniya ita kuma saboda mijinta na da kuɗi sai ta riƙa yi ma Shema'un abu kamar ita ce uwarta." Na ƙarishe faɗa ina mai kallon Amina wacce ta jinjina kai kafin ta ce" Kwarai kuwa. Kamar raƙumi da alaqarsa haka Ma'u ke jan Shema." Ƙwafa na yi kafin na ce" Gungun munafukai ai sai munafuncin su ya ci su in sha Allahu." Nan muka cigaba da hira har muka gangaro kan Ya Murja na ce ai ita wannan na daɗe da sanin yadda ta ɗauki Ma'u ba haka ta ɗauke mu ba, sannan kuma da ƙwaɗayin itama, wani cewa halina ne ba ta so duk mgana ce amma jiya ta ɗan samu muhallin afuwa acikin zuciyata a karon farko da ta gano Ma'u ba ta kyauta ba. Sannan Ya Abubakar ma sai a hankali. Shima raƙumin ne sai abin da ya ga an karkata acan ya ke. Har neman fitan hayyacinsa ya ke yi in dai akan lamarin Ma'u ne. Amina ta bushe da dariya kafin ta ce" Tsohuwar zuma ce Ya Sadiya " Nima ina taya ta dariyan na ce" Shi ya sa wani lokacin na ke yi masa uzuri." Mun daɗe muna hira har aka kira sallar isha'i sannan ta fita ta ce min za ta je falo ta yi kallo nima na ce in na idar da sallah zan fito. Una ko idarwa na fito na iske suna kallon wani indian Movie a Bolloywood Kuchi kuchi hota hae. Ina son film ɗin tuni na zauna muna kallo har da Saude da Jidda Baby ta kwanta ita da Sultana ɗiyar Amina ƙarama, muna cikin kallon Amina ta je ta ɗumamo mana Tuwo muna ci muna ƙona hannu sannan muna kallo bayan mun gama muka kora da lemu da ruwa, mune har 11pm har sai da aka gama film ɗin nan sannan muka tashi har Jidda ba ta yi barci ba sai da a ka gama sannan muka kora su ɗaki, ni na tsaya na rage hasken duka ɗakunan na duba ko'ina sannan na je na kwanta na iske Amina ta yi shirin barci ta na kwance suna waya da mijinta sai na ba su waje na shiga Tiolet na kama ruwa na yi brush, ko da na fito sun gama wayar sai nima na yi shirin kwanciya na saka kayan barci muka kwanta, mun ɗan fara hira ba daɗe barci ya ɗaukeni ban ƙara sanin kaina ba sai huɗun asuba sannan na tashi na ɗauro alwala na yi nafilfilu, sai da a ka fara kiran sallar farko sanman na fita na ta da su Jidda. Dakyar na idar da sallar asuba saboda barci na cin idona na haye gado ba ni na tashi ba sai tara na safe. Na iske gida ƙal an gyara ko'ina ya na tashin kamshi har sun karyawa Amina ta shirya sai tafiya Ɗorayi ita da Saude. Ina zama a saman kujera a falon su Jidda na ce" Ke Amina da sassafen nan? Kamar ana koran ki? Amina na gyara ɗaurin ɗankwalinta ta ce" Yau fa zan koma kaduna Ya Sadiya gwara na je na gaida su Alhaji na ɗan zauna zuwa azahar haka." "To tare da Dattin za ku koma? Sai ta gyaɗa min kai, ya na iya duk da ba na son tafiyarta haka nan na yi shuru ina laifi an yi min kwana uku. Ni da yara sai rakiya har bakin get muna ɗaga musu Hannu Saude dai gobe ma za ta dawo. Sai ga shi mun dawo cikin gida mun yi tsuru ni da su. Zama kawai na yi a falo ina nazarin rayuwa. Yanzu yau kwanan Yallaɓai biyu ya na cikin garin nan amma ba ya tare da mu sai na ji kwalla sun kawo min amma na yi saurin mayarwa. Tea na ce Jidda ta haɗo min na ci da Dankalin da Amina ta soya da safe. Su daman sum yi wankansu ni ce bayan na gama na tashi na yo wanka yau ma ɗin sabuwat atamfa ta na saka, ban zauna a ɗaki ba fito wajen su Jidda saboda su ɗeɓe min kewa. Baby ta ɗauke mana hankali da rawan drama ɗin da suka yi a makaranta ni da Jidda muna ta dariya. Haka muka yinin mu kaɗai a gida sai can bayan La'asar Musbahu ya zo ya ce min Yallaɓai ne ya ce ya zo ya duba mu ina mirmiahi na ce" To me zai same mu? Ai dole ma mu saba tunda haka tafiyar za ta miƙa." Ban tambaye shi ba da bakinsa ya ke faɗa min Yallaɓai bai fito Office ba kwana  biyu a raina na ce ya fito ya na can ya na cin amarcin sa, ya ɗan daɗe tunda har sai da ya tsaya ya ci abincin da na yi. Da zai tafi Baby sai ta fara rigiman wai ita sai ya kaita wajen Abba da Anty Gimbiya tun jiya ta fara min riginan Ina Abba na ce mata ya na gidan Anty Gimbiya ta ce sai ta je na ce ba yanzu ba, to jiyan ban biye mata ba sai yau ne bayan Tafiyan Musbahu yarinyar nan ta kafa min kuka da rigiman ita sai an kaita wajen Abba da Anty Gimbiya. Yarinyar nan har da zan shiga salla sai da na yi ma ta jan ido akan ta tashi a saman cafet ɗin ta je ta yi salla amma ba ta ji ba. Har na idar da sallah na fito ta na wajen ta na min kukan banza ba tare da na yi mata mgana ba na koma ɗaki na ɗauko bulalar injin ce wacce na ke dukansu ne, ƙarama ce ma wannan ɗayar babban Yallaɓai ya dauke ta wai ba ta dukan mutane ba ne kamar zan doke dabbobi. Ta na kwancen nan ta na rigima sai dai ta ji saukan bulala tuni ta fara ihu tun tana kiran Abba sai ta koma Umma ki yi hakuri Ya Jidda Ya jidda. Ta na kuka ta na majina karshenta dai Jiddan ta ƙwace ta, ta na ba ni hakuri. "Don Allah Umma ki yi haƙuri." Kwafa na yi kafin na ce"ka ji min yarinya mara mutumci kawai da mangariban nan ki ɗaga min hankali! A'a ba gidan Anty Gimbiya ba saura gidan Sarki." Raina a bace na koma ɗaki ina magana ni kaɗai. "Mata duk ta bi ta gama min da ƴaƴa. Ina dalili." Wayata da ta kwana ma a kashe ban san ko uban na su ma yau ya tuna da su ya neme ni ba. Sai ga shi can ajuma na koma na ganta har ta yi barci a raina na ce ashe ma iskanci ne irin na yara, Jidda ma da wuri ta kwanta ranar amma ni na ɗan dade ina kallo saboda ma kar na kwana ni kaɗai na yi tunani na ce Jidda ta zo ɗakina mu kwana ni kuma na ɗauki Baby na kaita bedroom ɗina na kwantar. Ranar tare da yara muka yi barcin mu har da su makara domin sai shidda na safe muka farka. Qur'ani na riƙe shi kuma ya kawo min salama da kwanciyar hankali a kwanakin da Yallaɓai ya yi a gidan wata mace ko na ce wata matar ta sa bayan ni, sai a ranar na kunna wayata na kikkira mutane na yi musu ban gajiya Amina ma ta ce jiyan da suka isa gida ta yi ta kirana a kashe haka ma Farida ta ce itama ni dai na ce su yi hakuri wayar ce ta mutu ba chaji ban sani ba. Ina lissafe da yau kwanan Yallaɓai uku kenan a gidan Gimbiya na ɗan ji ba daɗi da na kunna wayata ban ga saƙon shi ba amma dai ina ji a jikina ya kira ni wayar ce bai samu ba. Ko bai sanar da ni ba na san kwanakin bazawara kwana uku ne yau Yallaɓai zai dawo gidana shi ya sa da yamma na dumama sauran kazar da na siya wajen Hajiya Surayya Halin yau, na ci tare da tsumi karfe bakwai da wani abu na yamma Yallaɓai ya kira ni lokacin ma ina kan darduma ina lazimi ne bayan na idar da sallar mangariba. Ban ɗauka a lokacin ba sai da ta katse sannan ba daɗewa ya ƙara kira sannan na ɗauka cikin sanyin murya lokaci ɗaya da sallama a bakina. Sai ya amsa min daga can bangaren shima a sanyayen, tambayar ya kuke? Ya yara na ce lafiya lau daga nan shuru muka yi dukkanmu na wani lokaci. "Me ya faru jiya da yau wayarki a kashe." "Ta mutu ba chaji ne ban sani ba." Domin kar ma ya kawo tambayar ba wuta ne? Shi ya sa na ce ban san ta mutun ba. "Ok. Yanzu ba daɗewa za mu taho nan gida tare da Daugther" Haka na ji ya faɗa sai da na dan yi jim kafin na samu damar magana ya cigaba da faɗin" ina so zan yi magana da ku gabaɗaya." Sai da sauke ajiyar zuciya sanna na amsa masa da cewa. "Shike nan sai kun ƙariso." Da ga haka muka yi sallama ban tashi ba sai da na gama lazimina na yi salatin Annabi na shafa sannan na miƙe na ninke darduman na ɗora saman gado daman na yi wanka na saka riga da wando. Ban kuma jin zan iya sauya shigata turaren wuta na ɗauka na fita falo na  saka Jidda ta kunna Burner gidan ya dan yi kamshi Baby kuma na baje a falo ta ba je littafinta na drowing ta na ta zane zane kuma ta na bin shi da kala a baya in na gani sai na hana ta Yallabai ya ce na kyaleta na sani ko ita ce za ta ga je shi? Tun daga lokacin na saka mata ido daga karshe ma katon drawing ya siya mata mai kama da littafi da pensira na zane da clours ya na zane ni, in akwai makaranta ban barin ta yi amma yanzu da suka samu hutu ba na hana ta. Muna zaune a falon gabaɗayan mu mu ka ji shigowar Motar Yallabai gidan da ƙaran rufe get, tun da karfe ne dole in an buɗe ko an rufe sai mun ji kara. Jidda ta daka tsalle ta mike ta na faɗin" Baby Abba ne." Daga ita har Baby a guje suka fice baby ta yi falati da kayan zanen ta suka fice da gudu suna kiran oyoyo Abba, na ji buɗe kofar falon da yadda yaran suka naɗe shi da muryan shi ya na faɗin. "Oyoyo My princess. I miss u." Ina zaune a in da na ke na kasa tashi. Haka kurum sai na ji gabana na faɗuwa ras! Kamar kuma sai na ji kamar wani tsoro tsoro na shiga ta. Yau ne fa zan hada ido da kishiya? Kishiyar da mijina ya kwana da ita har uku. Ƙilama akwanakin nan ta samu ciki. "Auzubillahi minal sheɗanir rajim" Haka na faɗa da sauri domin koran sheɗan ɗin da ya ziyarce ni. *Janafty* *TKG* *Assalamu alaikum!* *Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.* *Karku manta bamu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin faɗakarwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.* *Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.* *Ku biya kuɗinku ta wannan asusun Kamar haka👇🏻* For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account 👇🏻 7087809778 Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704. *Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin 08167768704.* 10. Ina zaune ne amma na kasa tashi domin sai na ke jin gabaɗaya ilahirin jikina na rawa. To in ma na tashi wa zan je tarowa? Kishiya ko miji? Kawai sai na yi zama na amma fa zuciyata bugawa ta ke yi da sauri da sauri cikin lokaci ƙalilan hankalina ya tashi ina neman fita hayyacina saboda wani iri abu na ke ji yana ta so min daga ƙasan zuciyata. Kishi masifa ne, zai iya haifar ma da mata lalura mai karfin da nan ta ke za a iya kai su emergency a yi tunanin ciwon ya daɗe a jikinsu ne ba a sani ba alhalin kishi mai saka ma zuciya ciwo nan take ba tare da mutum ya sani ba. Idanuwana suna kallon ƙofar falon suka shigo, shi ya buɗe mata kofar ta fara shigowa hannunta na riƙe da na hannun Baby.  Sai shi ya biyo bayan su, shima hannunsa na riƙe da na Jidda. Gimbiya fara ce sosai doguwa domin har ta ɗan fini tsawo sannan tana da jikin murjewa kyakyawa ce domin hancin ta har baka. Sanye ta ke da atamfa mai kalan orange shi ya sa mayafin da ke jikinta ma kalan shi kenan, shi kuma Yallaɓai an cakare cikin ƙananun kaya har da zanzaro. Dukkansu fuskarsu tana fitar da wani annuri ne. Annurin da ka na ganin shi za ka san na farinciki ne wanda zuciya ke samu ta hanyar gangan jiki. Duk ina zaune ne na ƙare musu kallo, ina ganin za mu haɗa ido da su na yi saurin ɗauke kaina ina jin zuciyata na ƙara tsananta bugawa. Ina jinjina ma matan da ake yi musu kishiya sannan a haɗa su zama da su a gida ɗaya. Wallahi in ni ce ba zan iya ba, domin na tabbata wata rana zan iya haɗiyan zuciya na mutu saboda baƙin ciki.  Da na so na tashi na tarbe ta amma daga baya kawai sai na fasa sai ma gyara zaman da na yi daga in da na ke zaune na ce. "Sannun ku da zuwa." Na faɗa ina ƙara gayyato mirmishi a saman fuskata. Ita ta amsa amma a hankali shi ne na ji amsar ta shi da ƙarfi yaran na maƙale da su, shi ya nuna ma Gimbiya kujeran da za ta zauna na zaman mutum biyu, ta isa ta zauna Baby ta haye jikinta shi kuma sai ya durkusa a gabana lokaci ɗaya ya na mai riƙe duka hannayena cikin tafukan hannunsa so ya ke mu haɗa ido, ni kuma na ki bashi damar haka sai ma Juyawa da na yi ina kallon Jidda da ta zauna gefen Gimbiya sai mirmishi suke yi daga ita har Baby umh yara ai ba ku san dawan garin ba. "Jidda kawo ma Antyn ta ku ruwa da lemu mana." "To Umma." Ta faɗa da saurin ta sannan ta ta shi ta nufi kitchen ɗin. "Kalle ni mana Sadiya ta." Ya faɗa ya na leƙa fuskata sai na yi fuska ma maze na kalle shi ta ƙasan idanuwana. Haushi fa ya ke ba ni, hannayena ma da ya riƙe ji na ke yi kamar na ƙwace, domin haskowa na ke yi da waɗanan hannayen na shi fa ya riƙe Gimbiya da su, shi ne nima zai dawo ya na taɓa ni tuni na ji gabaɗaya hannayensa sun zame min kamar lantarki mai ja a cikin hannayena sai ƙokarin kwacewa na ke yi ya na ƙara riƙe ni, ita kuma Gimbiya ba ta kallon mu tana ta hiran ta ita da yara. "Yallaɓai. Ka bari mana." . Na faɗa bayan na ƙwace hannayena lokaci ɗaya ina kallon shi. "Ba ki yi mini sannu da zuwa ba." Ya sake faɗa yana mai ƙure ni da ido. "Shi wanda na yi maka fa? Kawai sai ya buɗe mini hannuwansa yana faɗin" Ba wannan ba irin wannan." Kaɗan ya rage ban danno masa na katsinawa ba amma dai na daure ban yi ba, sai ma hararan shi da na yi na matsa gefe ina kallon Gimbiya. "Ki sha ruwan mana." Ta na kallona ta ce" Zan sha." Muka yi shuru ni da ita, shi kuma sai ya zagayo ya zauna kusa da ni har kafaɗan shi na gogan nawa, a hankali na ƙara matsawa sai na ga ya ƙara matsoni, ina kuma ɗaga kaina sai na ga ta na kallon mu shi ya sa na barsa ban ƙara matsawa ba. "Na yi kewar ki sosai Sadiya ta." Haka ya yi min raɗa a kunne ya faɗa mini, ko kallon shi ban yi ba domin sai na ga kamar rawan jikin Yallaɓai ya ƙaru ne saboda a gaban matar shi ne, ni zai faɗa ma burauba a gaban matarsa. Kallo ma ni bai ishe ni ba sai ma na juya masa ƙeya ina ce ma Gimbiya ta sha ruwa mana. "Zan sha " Ta sake faɗa a hankali tana wasa da yatsun hannun Baby. "Anty Gimbiya ina ta kuka ina so na je wajen ku ke da Abba." Baby ta faɗa cikin shagwaɓa ita kuma sai ta shafa kanta ta na faɗin" Ban sani ba da kin kirani da gudu zan zo na tafi da ke My Baby." Sai Baby ta fara murna, ni ko gani zaune ina yaƙe ban yi mgana ba. "To ko Baby za ta ture gwamatin Jidda ne kawai sai ki tafi da ita ta ta ya ki kwana." Sai ta yi mirmishi ta na kallon shi kafin ta ce" Sai abin da ka ce Daddy" "Duk ɗaya ne ko Baby ko Jidda Daugther. Gwara Jidda ma ba za ta yi rigima ba amma Baby ba za ta yarda ki ta fi da Jidda ita ki bar ta ba." "Sai na tafi da su gabaɗaya mana Daddy." Ta faɗa cikin shagwaɓa ta na yi masa wani kallo. Kawai sai na ga ya yi wani mirmishi, mirnishin da na ɗauka bayan ni Yallaɓai ba zai sake yi ma wata mace irin shi ba sai gashi a gaba na a gaban yara Yallaɓai ke hira da wata mace ta na masa shagwaɓa ya na jin daɗi. "Daughter.." Ya faɗa ya na yar dariya sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujera ya na faɗin" Ke ma kin cika rigima. Su biyu ai sun yi miki yawa. Ita Madam sai a bar ta ita kaɗai ko su je kawai ni kaɗai na ishe ki ko Sadiya ta? Ya ƙarishe zencensa ya na kallona, ban ko kalle shi ba amma a cikin raina ina jinjina karfin halin irin na Yallaɓai wato ma har ya raba mini yayan nawa amma ni ban da darajan da zai faɗa min, ni fa a baya ne na ke da bakin cikawa a kan Yallaɓai amma a yanzu na shaida munafuki ne na gidi ma, ni fa yanzu ba duka ma mganganunsa ne abin yarda a wajena ba, na tabbata tunda ya ƙara aure zai kulla alaqa da ƙarya da munafunci. "Ya baƙun ta? Na katse shurun namu da mganata. Cikin wani karya murya ta ce" Baƙunta ya fara bin jiki." Ta faɗa ta na ƴar dariya, ni kuma sai na yi mirmishi ba tare da na sake yin magana ba amma da za a tona zuciyata baƙinƙirin ta ke, kiran sunan Allah kawai na ke yi domin saura kiris na fallasa a sirin zuciyata. Mun zauna shuru har na tsawom mintina ashirin ita dai sai hira ta ke yi da su Jidda Yallaɓai kuma ya na ta faman latsa waya ni kuma ina zaune abin tausayi E mana abar tausayi ni da gidana amma na kasa sakewa, sai satan kallon Gimbiya na ke yi sai da na ƙara lura dakyau na ga har da kwalliya ma ta yi, to wai ta manta yau mijin ma ya fita ɗakin ta ne? Sai da na lura sosai sai na ga jefi jefi suna kallon juna ita da Yallaɓai suna sakar ma juna mirmishi, ji na yi kamar na tashi na bar musu falon amma na ƙara dai haƙuri na zauna, ina so na duba lokaci amma wayata na baro ta a ɗaki kuma gashi ba na so na tambayi Yallaɓai kawai sai na yi shuru kamar in yi tagumi in fashe da kuka haka na ji, ban yi hakan ba amma acikin zuciyata Allah ya saka min kawai na ke faɗa domin Yallaɓai ya gama cutata. Kiran sa a ka yi a waya sai ya tashi ya koma falon shi, ba daɗewa ya dawo yadda ya bar mu haka ya dawo ya tadda mu, ita dai ta na ta hira da Baby mai shegen surutu in ta fara ba ta son ta tsayawa gwara Jidda ta fita Aji shi ya sa na ke son ta ba ta cika surutu haka barkatai ba. sai balla mata harara na ke yi ta gefe amma yarinyar nan ba ta ji ba sai zuba ta ke yi kamar ƴaƴan kanya. "Kun yi shuru abin ku." Ya faɗa yana mai sake zama gefena sai a lokacin na saci kallon Yallaɓai kwata kwata bai yi min kyau ba a raina ma faɗi na ke yi Yallaɓai an yi girman banza ka rufe arba'in kana wani cin zanzaro. A baya ne in yi ta masa nacin saka ƙananun kaya ya yi ta kuma cewa shi ba ya son sakawa amma sai ga shi yanzu ya saka har da zanzaro saboda ya burge wata tir! Tsaki na ja a hankali amma kuma sautin ya fita tun da shi ya ji har kuma sai ya kalleni na basar na haɗe rai kamar ba ni ba shi ya sa bai samu damar yi min wata mgana ba. "Jidda kama hannun Baby ku je falona ku kunna Tv ku yi kallo kafin na gama mgana da Ummomin na ku." Haka ya faɗa ya na kallon Jidda sai ta amsa masa da to. Amma Baby har da ƙin tashi ta makale ma Gimbiya. Shi ya tsaya ya na lallashinta shi da Gimbiyar ni ko tsawa na daka mata kafin na ce" Za ki tashi ko sai na zo nan na tattaka ki ? Na faɗa ina mata wani kallo ai kafin ma na yi wani matsi ta sauko daga jikin Gimbiyar ta na neman yi min kuka. "Kina ɓare min baki yanzu jikin ki zai gaya miki." Na faɗa ina kallonta jin haka yasa ta koma bayan Jidda ta raɓe, shi kuma Yallabai ni ya kallah kafin ya ce" Haba! Sai ki da ke ta? "Ta yi kukan sai ka gani." Na bashi amsa a takaice sai na ga kawai ya tsaya ya na kallona ni kuma na ɗaure fuska ina kallon jidda kafin na ce" Kama ta ku je mana." Sai ta riƙe hannun Baby suka wuce wacce ta yi narai narai kamar za ta yi kuka ga shi ba hali kuka Gimbiya na ɗaga mata hannu da alamun ta na nan ba tafiya za ta yi ba. Sai da suka shige da mintina sannan Yallaɓai ya gyara zama gyara murya ya yi irin na juyo na kalle shi sai ma na ƙara yamma da fuskata. "Wannan hijabin fa? Ki cire shi ki sha iska mana." Ya faɗa ya na kama gefen Hijabin kamar da gayya ya yi maganar ni zai ma mutumci gaban matarsa. Daman hijabin da na yi salla dashi ne ban cire ba, kawai sai na fizge hijabin daga hannun shi kafin na ce. "Ka bar min kayana. Tun da kuma ba zafi ake yi ba." Na faɗa ina jin kamar na rufe shi da duka ni fa na kosa ya gama maganarsa na shige ciki zuciyata ta kusa daina ɗaukan munafuncin Yallaɓai kar ta kai mu ga in ya faɗa na maida masa mara daɗi. "Halima." Ya kira sunana amsawa kawai na yi ban kalle shi ba saboda ni dai yanzu in Yallaɓai ya kirani da Halima ban wani rawan jiki saboda na san na yaudara ne shi ya sa na daina ma rawan jiki. "Daughter." "Na'am. Daddy". Ta amsa cikin sanyin sauti. Ina zaune ne amma ji na ke yi kamar ina yawo a sararin samaniya saboda hazo hazo na fara gani saboda wulaƙancin Yallaɓai, ni ya kira sunana sunan da ko ubana da ya yankamin rago ba ya kirana da wannan sunan ya na sakayawa saboda girmamawa haka sauran ahalina Sadiya suke kirana amma shi yau sabida cin mutumci ni ya kira ni da Halima ita kuma tunda sunan Nene gare ta ba zai iya kiran ta da sunanta na yanka ma sai ya sakaya kamar yadda ya saba. Wani iska na furzar daga bakina da ya sa sai da suka kalleni gabaɗayan su. "Lafiya? Ya faɗa ya na kallona, wani irin kallon sama da ƙasa na yi masa kawai na ɗauke kaina shima kuma ya ga yanayin kallon shi ya sa bai ƙara nema na da wata mgana ba ya kama kan shi. "Na san kun san dalilin da ya sa na tara ku anan ko? Daga ni har ita shuru muka yi masa, ni ko a raina na ce to kasan mun sani uban miye kuma za ka taramu? Amma dai ban yi magana ba sai ma na maida kaina ƙasa kawai ina wasa da gefen Hijabina. "Duk da kun sani amna tunatarwa tana daɗi. A matsayina na wanda kuke zaune domin shi akwai wasu mganganu da ya kamata na sake tunatar daku game da su." Uhm! A cikin raina na ja sheɗata na fesar ta baki, saboda yau wai ni ce zaune da wata matar a matsayin matar Yallaɓai bayan ni. Na kasa gasgatawa amma yanzu gasgatawa ya zama dole tunda ba mafarki ba ne a zahirin gaskiya ya ke faruwa. "Sadiya ga abokiyar zama nan na kawo miki. Aurena da Daugther Allah ne ya kaddaro shi, ke ma Daugther ga Yayanan na yi miki. Abun fatana na farko shine haɗin kan ku, ku sani wata ba ta fi wata a wajena ba dukkan ku mata ne da aure ya samar min da ku, ina fatan za ku haɗe kan ku ku zauna da juna lafiya domin samun zaman lafiya ta nima." "In sha Allahu." Ta faɗa cikin sanyin murya, ni ko ban ce komai ba sai daga baya da na ga ya yi shuru kenan ni ya je jira na ce wani abu. "Allah ya ba mu zaman lafiya." Suka amsa a tare da shi da Amin. "Sadiya ki sani ban aure Daughter domin kin taɓa gaza min ba. Ki kaddara zaɓin Allah ne sannan ikonsa ne. Ke ma ki sani ba ta rage ni da komai ba kar ki yi tunanin akwai ta bangaren da ta gaza min ne ko ɗaya. Ke ma ki ɗauka a kaddaran Allah ne aurena da ni da ke, ki yi mata biyayya domin wakiliyata ce, in ta yi miki gyara ki gyara in ta kwaɓa miki ki kwaɓu, in ta ba ki umarni ki bi wanda bai saɓa ma shari'a ba. Ba zan lamunci ki yi mata cin zarafi ko rashin kunya ba ba na so na ji wata baraka a tsakanin ku, Ku ba yara ba ne ballatana na ce komai sai na faɗa muku dukkanmu nan mun san komai saboda haka ina roƙon ku ku haɗe kan ku mu zauna da juna lafiya har mu zama abin kwantance a wajen su don Allah." "In sha Allahu." Ta sake faɗa ni kuma a yangance na ce" Allah ya sa." Sai kawai ya juyo kaina. "Sadiya." Sai na kalleshi sannan na amsa masa. "Na'am." "Na ɗora miki wani girma. Ki sani ki ce ni i don ba na nan ko da ma ina nan ke ce wakilyata. Kin fi ta sanina sosai fiye da ita. Ki riƙe girman ki, ni ma kuma ki riƙe min nawa girman. Don Allah ki yi zama da ita da zuciya ɗaya in wani saɓani ya haɗa ku ku zauna ku warware a tsakanin ku kar ki biye ma masu an ce ka ce domin ya na ɓata alaqa ba na fatan ku samu saɓanin da har ni sai na shiga ciki. Na fi son ku  yi zaman lafiya da har ni ba zan ji kan ku ba don Allah." Ajiyar zuciya na sauke domin na ga ya ƙura min ido sannan na ce" Allah ya ba ni ikon ɗaukan girman." Abin da kawai na ce kenan na yi shuru ita kuma sai ta ce" In sha Allahu ba za ka taɓa samun baraka daga bangarena ba" "Ma sha Allah na ji daɗin haka. Allah ya yi muku albarka ya kuma zaunar damu lafiya gabaɗaya." A cikina na amsa da Amin, ya ɗan sake yin shuru kafin ya ce" Sai maganar raba kwana. Wani tsari kuke ganin za ku yi? Ya fada ya na kallon mu, ni ko sai na yi kamar ban ji ba. "Duk yadda Maman Jidda ta tsara dai dai ne ni a wajena." Ta faɗa ta na kallona sai nima na kalleta kafin na ce" Ah ke ma kina daman ki tsara ɗin." Sai ta kalleshi kafin ta ce" To kai ka faɗa mana." Kai tsaye ya ce" Ni ba ruwana wannan ai maganar ku ne." Ya faɗa lokaci ɗaya ya na duba wayarsa. "Ni dai sai na ga gwara ita ta faɗa " Ta faɗa tana kallona, nima ko ina kallonta na ce" Ke ma kina damar ki faɗa duka ɗaya ne da ni da ke ɗin" Ganin mun fatra ja in ja ya sa ya kalleni kafin ya ce" Sadiya ki faɗa mana ke ce Babba." Zan yi magana ya dakatar da ni da cewa" Ke za ki tsara na ce ko? Sai na ga ya wani haɗe rai ya na kallona a raina na ce daga baya kenan. "To kamar kwana bibbiyu ya yi ko? Na faɗa ina kallon su sai ya kalli Gimbiya kafin ya ce" Ya yi ko? Da sauri ta ce" Ya yi." Sai ya juya ya na kallona kafin ya ce" Shikenan kwana biyu ya yi Madam." Ko kallon shi ban yi ba domin ni yaudaran Yallabai wanne ne ban sani ba. "In ba na gidan ɗaya to haƙƙi ne a kaina na je na duba yadda ta kwana. In kuma wani uzuri ya taso zan iya kiran waya. Kuma duk wacce ke son mgana da ni za ta iya kirana nima kuma a duk in da na ke zan iya kiran kowaccen ku, dukkaa ku mata na ne da Allah ya ba ni ku ta ƙarƙashin inuwar aure saboda haka ba bu shamaki a tsakaninku gabaɗaya ɗaya kuke a wajena." "Allah ya zaunar da mu lafiya. Madam ɗina yi mana addu'a.". Sai kawai na yi kamar ba da ni ya ke ba sai na kalli Gimbiya ganin ta na kallona shima sai na ga ya na kallona cikin basarwa na ce" Wai ni? Mirmishi ya yi kafin ya ce" Wace ce na ke kira Madam in ba ke ba? Sai na jinjina kai a raina na ce ai ka ce Madam tun da ka gama da ni ka yo sabuwa na zama cus ba ni da amfani dole na koma Madam ko burgeni sunan bai yi ba domin tabbas na ke da shi wulakanci ne na ɗa Namiji shi ya na kiran ta da Daughrt ni kuma Madam kamar wata inyamura. Ni na rufe zaman da addu'a sannan ya ce mu yi musabaha da juna, hakanan na mika mata hannu muka yi masabahan shi kuma ya duba lokaci ya ce goma har ta gota bari ya zo ya maida ta gida. Shi da kanshi ya leƙa falo ya ce Baby ta yi barci sai Jidda kaɗai a gaba na ya ce ta je ta haɗo kayanta na kwana biyu ta zo su tafi kamar zan yi magana amma sai na ce ba yanzu ba ba tare da ya yi magana da ni ba ina ji ina gani ya ta sa Jidda tare da Amaryansa da ba zai bari ta kwana ita kaɗai ba ya je maida su gida. Mun yi sallama da Gimbiya kadahan kadahan Jidda kuma na ce ta tafi da azkar ɗin ta da Qur'ani kar ta manta da koyarwa da na yi mata ta ce min in sha Allahu. Bayan tafiyarsu na kai Baby ɗaki na gyara mata kwanciya tare da yi mata addu'an barci. Sannan na rage mata hasken ɗakin na fito. Heater na kunna ya yi zafi sannan na yi wanka na saka kayan barci na duba agogo Yallaɓai ya fi mintina talatin da fita bai dawo ba, har na je kitchen na sha ruwan zafi daman da rana shinkafa na da fa Jallop. Ban damu da Yallaɓai ba tun da sai dare ya zo min gida ai ya cika cikinsa a can shi ya sa ko tunanin dafa wani abu ban yi ba. Bedroom na koma na kwanta amma na kasa barci tun ina mamakin Yallaɓai har na daina mamakinsa domin lamarinsa ya wuce tunanina da hasashena. Ba ni na ji karan buɗe get ɗin Yallaɓai ba sai sha ɗaya da mintina na dare, saboda akwai waya a gefe sai da na duba ajiyar zuciya kawai na saki a ƙasan raina ina tausan kaina kar Yallaɓai ya shigo na yi masa dibar albarka, saboda ma kar a samu matsala sai na yi lamo cikin bargo kamar mai barci ina jin sa ya shigowarsa cikin gida da zagayen da ya yi ya rarrage hasken ɗaku nan sannan ya shigo cikin bedroom ɗin ya zube key ɗin motarsa da laptop ɗin a saman madubi ta gefen ido na ke kallon shi shammata ta ya yi ya kamani ina kallon shi sai ya yi min mirmishi kafin ya ce. "Sorry kin ga na daɗe ko? "Akwai ruwan Zafi in za ka yi wanka ne." Na katse shi daga maganar saboda ba na son na ji. Karya ce da renin wayau ne kawai a cikin zencen sa. "Ok." Ya faɗa, ya na mai tuɓe kayan jikinsa ya rage daga shi sai gajerun wando sannan ya kalle ni kafin ya ce" Zan samu tea mai zafi Madam? Ya faɗa ya na min wani kallo, da kamar na ce a can ɗin da ka tsaya ba ta ba ka ka sha ba ne? Amma dai na danne zuciyata  na mike na zo zan fita ya ja min kumatuna lokaci ɗaya ya na faɗin" Na gode Matata ta kaina." Kai na fara tunanin ƙila dai Yallaɓai ya zauce ni domin ya na ta surutai marasa ma'ana. Kitchen na shiga na kunna gas na ɗora masa ruwan tea. Ina da shayin goriban da na siya wajen Aisha Lame saboda Yallaɓai shi na zazzaga masa na dafa masa bayan ya tafasa na tace masa a mug na kai masa ciki na iske har ya fito wanka ya na shafa mai, kan madubi na ijiye masa, kamar ina sauri na koma kan gado na kwanta sai ya juyo ya na kallona kafin ya ce. "Ko taya ni ma shiryawa ba za a yi ba? Ya faɗa ya na wani mini mirmishin da a baya ya san ya na kunna ni, amma a yanzu da zan fito na faɗa masa yadda na ke ganin baƙin sa in ya yi min wannan mirmishin da tuni ya kama kan shi. Sai da na shige cikin bargo sannan na leƙo kaina ina faɗin" shirin barcin ne sai an ta ya ka? Na faɗa ina masa wani kallo, shi wai ba shi da ganewa ne, ni fa da zai ƙyaleni da ya burgeni bai san bina ma da ya ke wani ƙara min takaicinsa ya ke yi ba. "Da ko barcin ne ai kina shirya ni ko? "Da ka ce yanzu kuma kiɗa ya sauya dole ma ruwa ya sauya." Na faɗa ina hararan shi ta gefen ido, tsabar ma Yallaɓai ya maida ni shashashan madina sai kawai ya kwashe da wata dariya kafin ya ce. "Me ya sauya? Uhm My Sady Baby? Bakina ne na yi masa limzani amma na kusa na yi masa wani gimgimeman tsaki, ganin in ma tsaya ina biye masa mahaukaciya zai maida ni nishaɗi ya ke yi shi fa amarcin ya karɓe sa matuƙa sai faman washe baki ya ke yi, baya na juya masa kawai ina ƙokarin ya ƙi da abin da ke taso min daga ƙasan zuciyata ina jin sa har ya gama shirin barcin sa ya kashe mana fitila ya zo ya kwanta na ɗauka zai yi gefen sa ne sai kawai na ga ya matso kusa da ni ya kwanto saman jikina ya na kiran sunana. "Saddy.." Wato saboda ya yi mini kishiya na zama abin dariyan shi kaɗan ya rage ban ture shi ba amma na yi masa bakam sai ya fara min cakulkuli tun ina kannewa har na kasa ina dariya na mirgina ina faɗin" Ka bari mana Yallaɓai." Amma bai ƙyale ni, sai da ya ga na kusa fita hayyacina har ina hawaye duk mun birkita gadon sannan ya ƙyaleni shi ma ɗin bi na ya yi ya danne ya na min wasu abubuwan, tun ina ture shi har dai ya fi ƙarfina dole na ba da kai bori ya hau, sai da muka samu natsuwa sannan muka yi wanka muka kwanta da asuba ma bayan ya dawo masallci sai da ya ƙara nema mana wani ɓarnan ruwan "Yallaɓai da sanyin nan kasan ɓarnan ruwa akwai wahala." Ya na shafa fuskata kafin ya ce" Ya fi daɗi ne. Kuma kin san cewa kin ƙara daɗi Madam? Ya faɗa ya na sumbatar goshina lokacin muna kwance a tare ne, saboda kalamansa sun yi kama da na yaudara yasa na yi masa banza. Wai kin ƙara daɗi! Duk da bai san na ƙara daɗi ba ne sai yanzu da ya je ya ɗanɗano wata? Ɗan renin wayau kawai. "So na ke yi na sake ajiyar mai sunan Alhajinmu ko Baban Gwammaja" Ya faɗa ya na shafa cikina zuwa saman marata, nima sai na ɗora hannuna saman hannun shi har na ji tahowar ƙwallah. "Allah ya sa haka Yallaɓai na." Ina so na sake haihuwa ni ko da guda ɗaya ne." Na faɗa ina jin sukan abin daga ƙasan raina. "In sha Allahu za ki ƙara haihuwa ba ma ɗaya ba dozin." Mirmishi kawai na yi amma ban yi mgana ba. "Ya ku ka yi da Likita zuwan ki na ƙarshe asibiti? Bayani na fara yi masa da cewa gwajin na ƙarshe ma ya na lap on 12 january zan koma in na karɓa sai na je na kai mata na ji me za ta ce tukunna. " In sha Allahu ba matsala." Na amsa da Allah ya sa. Bai kuma ƙyale nin ba sai da ya saka mu muka sake ɓarnan ruwa da safen nan. Ranar dai a gida ya yini bai fita ba saboda shi ma na ƙi dukan Baby domin tunda ta tashi barci ta ga ba Jidda ta fara rigima da Yallaɓai baya nan da tuni jikinta ya faɗa mata, shi ya zauna ya na lallashinta ni ko kallo ba su ishe ni ba. Sai washegari ya fita ya ce min zai biya ya duba Gimbiya daga nan zai shiga Office. Baby ta nace masa da ita ya tafi da cewa wai zai dawo da ita in zai dawo gida ni dai ban yi magana ba ina jiran na ga iya gudun ruwan shi. Sai ga shi tare da Gimbiyar suka kawo Jidda da Baby tun da yau ɗin ya na wajen ta ne. Ba su dade ba ni ma kuma ko fuska ban ba su ba muna gama gaisawa na bar su a falo na yi shigewata ciki sai da ya biyo ni muka yi sallama, hug ɗin ma na ƙi yarda na shige tiolet na bar shi nan dole ya wuce sai da na ji sun bar gidan na fito. Baby sun dawo da chaculte sai cincin da su alhaki suna ta budirinsu kallo ba su isheni ba suma ɗin haushin Ubansu ne duk ya shafe su. Tun ina ganin lamarin Yallaɓai in ya yi kwana biyu a gidana ya je can ya yi kwana biyu a wasa har na tabbatar da cewa gaskiya ne. Ba ni kaɗai ba ce matar Yallaɓai yanzu ba. Yana da wata matar shi ya sa ko cefane yanzu biyu ne Musbahu ya kawo min itama ya kai mata. Ya na kawo ta gidana su zo tare amma ni ban taɓa marmarin zuwa gidanta ba. Kuma in dai ya na gidana sai ya dauki Jidda ya kai mata in kuma ya ma can sai ya dawo da ita yadda bai taɓa min magana kan Jidda ba nima ban taɓa yi masa ba. Kwanaki can ya yi min maganar kan me ya haɗamu da Anty Bahijja.? a lokacin sai na tambaye sa. "Me ta ce maka hala? "Kawai ta na ta faɗa ne wai kin yi mata rashin kunya." Sai na jinjina kai kafin na ce" Ita ya ɗauke shi a rashin kunya amma ni ba haka na ke nufi ba" Sai ya tambaye ni mai ya haɗamu na ɗan faɗa masa da cewa" Na faɗa mata ko kai da na ke zaman ka, in ka matsa min da zuwa haƙuri zan ba ka. Ina ga shi ne ta ji haushi." A lokacin bai ce komai ba amma dai ya ce na kira ta na bata haƙuri ni ko dai na ce masa toh amma ban kira ba domin ban ga abin da na yi mata da zan kira ta na bata hakuri ba in ta so kar Allah ya sa ta haƙura in mun haɗu in na gaisheta kar ta amsa ita ta sani. Shi daman Yallaɓai ba mai damuwa da bin diddigi ba ne bai ma ƙara ta da mganar ba, ba ni ƙila ma tuni ya manta da batun in dai ba ita Anty Bahijjan ta sake masa mgana ba. Ga shi muna cikin sati na biyilu da tariyan Gimbiya tun ina tunanin zan iya sabawa da sallaman Yallaɓai in zai bar gidana har na fara tunanin har abada ba a sabawa kullum ne lamarin ni sabo na ke kallon shi a idanuwana. Ga shi tun bayan bikin ba wanda ya dawo gidana sai dai mu yi magana da su Hauwa ta waya Suwaiba ma sai da na kirata sannan ta turamin hotunan da ta ɗauke mu ni da Yallaɓai sun yi kyau amma ko status ban yi da su ba amma dai na ga Anty Maimuna ta sassaka hotunan su na bikin tariyan ƙila a lokacin ba ta samu sukunin sakawa ba, duk na kalla daga baya ne na yi ta daman kalla domin har da hoton Yallaɓai da Gimbiya su biyu, ta kwantar da kanta saman kafaɗansa ta na dariya shi kuma ya juya ya na kallonta kamar dai magana ya ke yi mata aka ɗau hoto. A ƙasan hoton ta saka caption. "Tafida da Gimbiyarsa. Alƙawarin Allah ya tabbata." Lalle fa Gimbiyarsa. Hoton nan da na gani ya daɗe yana gilmamin a cikin mafarkina da zahirina. Duk in da na zauna ko na kwanta da na runtse ido su na ke gani sai da na yi ta kiran sunan Allah sannan na samu sukuni da salama. Sai a yanzu na ke ganin cewa daman tun can Yallaɓai na son Gimbiya dama ne bai samu ba. Wannan rawan jikin kam ya na yi mata a gaba na kuma sai ya riƙa nuna ni ya ke yi ma rawan jiki, wai ni Yallaɓai zai maida ƙaramar yarinya Allah na tuba wani dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa. **** 20January 2016. Tuni na koma asibiti na ga Dr. Aisha Alhandulillah abin farincikina duka na tsallake matakin gwaje gwajen su kuma ta ba ni tabbacin ba wata matsala mai girma. Sai dai kawai side effect ya taɓa ni sannan kuma hormones ɗina sun ɗan yi rauni ne amma ta rubutamin manganganun da za su dai dai tamin al'ada da wanda za su ƙara taimaka min wajen samun ciki suna da tsada domin da na je phamarcy ma kuɗin da Yallaɓai ya ba ni ba su isa ba, na yi ta kiran wayar shi ban samu ba sai na kira na Musbahu shi ya faɗa masa sai shi kuma ya taho asibitin ya same ni, bayan ya biya kuɗin magunguna ya ɗauke ni ya maida ni gida. Duk da ina da kuɗi a cikin acct da gangan na ƙi taɓa su ni fa yanzu na fara jin ƙyashi yin hidimar da nawa ba, ba kamar da ba da shi kan shi ya san wani abun ma ba na jiran shi. Kan jiki kan karfi na dage na fara shan magunguna na saboda fata na da burina ni ma Allah ya sake ba ni wani cikin ko ɗaya ne na sake haifa. Kwana biyu tsakani na je gidan Hauwa daga can ni da ita muka je gidan Munnira muka haɗu muna ta hira. Sun tambayeni ya yanayin zaman na ce lafiya lau. To me zan ce? Zaman da yanzu aka fara ai sai tafiya ta tafi sannan halin kowa ma zai bayyana. Hauwa ita dai faɗi ta ke yi Yallaɓai ɗan halas ne, ni ko a raina na ce ai ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara da yatsa a hannun shi. Sai yamma muka rabu Hauwa ta hau adaidaita anguwarsu nima na hau ta anguwarmu na koma gida. Ina komawa ma na iske Marwa ta zo daga asibiti ta biyo ba na gida, daman Saude na bari a gida tare da su Jidda sai da dawo suka tafi gabaɗaya. Tun bayan tariyan Gimbiya sau ɗaya na je Gwammaja na gaishe da Alhajinmu daga nan na ɗauke kafa ina gida mai son ganina ya san in da na ke, iyakata in ina son mgana da mutun na yi masa waya. Ni yanzu ba ma Yallaɓai da Amaryansa ba ne a gabana sauran kudaɗen hannuna na ke son zama na yi tunanin sana'ar da zan fara, kar ma su ƙare a banza ban yi komai da su ba, tun dai na fahinci Yallaɓai zuma kawai ya ke lasamin a baƙi burina da ya ce zai zama sillar cikarsa na cire rai da su. Hankalina ya koma kan wani busineess ɗin da zan fara da zan dogara da kaina har Khaleesat na kira mun yi mgana saboda na ce ko nafara gwada hijabai ne? Sai ta ce wata Akwai ƙanwarta na siyarwa za ta tambaya min ta ji harkan in akwai fita sai ta haɗani da masu ɗinkin Hijaban anan sabon garin Zaria in muka saba ma ba sai na je ba ma. Kololin kawai zan faɗa su za su riƙa siya suna dinka min sai dai kawai a saka a mota a kawo min nan da nan na ce ta yi min ƙokari ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba da Amina kawai muka yi mgana ta ce wallahi na fara itama yanzu turaruka ta ke saidawa har ta ba ni shawaran na saro mayukan gyaran gashi tunda ina son bangaren na fara saidawa na ce shima zai zo daga baya mu fara da wannan ɗin dai mu gani. Ko a raina ban ji zan faɗa ma Yallaɓai ba sai dai in ya gani ya tambaya na amsa masa. Shima yanzu ai hankalinsa kashi biyu ne. Da ni kaina da ita amaryansa, ga su Jidda sun koma makaranta ta shiga Jss2 Ita kuma Baby primary 3, ya biya musu kuɗin makaranta daga nan na san Yallaɓai kuɗi gare shi, ba zan zage shi a yanzu ba  tunda iya adalci yana kwatantawa. Sai ɗan abin da ba a rasa ba na halin Ɗan adam. Zama ya yi zama an kwarari wata biyu da tariyan su sannan na fara lura da wani abu. Duk da Jidda ta koma makaranta ranar da ba ya gidan Gimbiya sai ya kaita. Ita kuma da safe sai in za ta wuce wajen aiki tunda ta na da mota sai ta kai Jidda makaranta in sun tashi ta je ta ɗaukota. Nan kuma Baby ita kaɗai Salisu kai kaiwa sai dai in har Yallaɓai na wajen Gimbiya ne ta ke gida duk da na ga ana ta min gantali da yarinya ban yi magana ba saboda ina ganin akwai sauran lokaci. Sai da na ga in dai zai zo gidan nan ranar da zai bar gidanta sai ta rako shi, kuma tana da mota amma a tashi za su zo bayan nan kuma shi zai maida ta gida ya ɓata lokaci kafin ya dawo duk na kauda kaina ban yi magana ba, sai abu na biyi in dai yana gidana to ta rika kiran waya kenan kamar wani ɗan kasuwan da ya ci mata bashi. Ni ko ba alfahari ba bana kiran shi in na san ya na gidanta. Sai dai in ma ya zama dole na yi masa saƙo in ya gani ya kira amma ita ba haka ba ne a wajenta in abu ne ta nema ba ta gani ba sai ta kira shi ta tambaye shi tun ina ba ta lokaci har dai na fahimci da gangan ta ke yi, ranar dai na ga abin na ta ya isheni da daddare har mun kwanta ta kira shi wai ta kasa kulle ƙofa, ina jin sa ya na faɗa mata key ɗin ne ya lalace gobe da safe zai saka Musbahu ya je da mai gyara sai a sauya key ɗin gabaɗaya. "Wai shekarun Gimbiya na wa ne? Sai ya kalleni kafin ya ce" 33 to 34 ina jin ko za ki girmeta da kaɗan ne" Sai na jinjina kai ban yi magana saboda na gama fahimtar renin wayau ne kawai kamar wata jaririya. "Me ya sa kika tambaya." "Na ga ta na yin abubuwa kamar Jidda ne" Ido ya zuramin alamun ƙarin bayani ni ko ina gyara gashina da tun da na yi tsifa ban kitse shi ba a gaban madubi na yi masa kamar bangane ba. "Me ya sa kika ce haka? Sai da na gama abin da na ke yi sannan na zo na kwanta lokaci ɗaya ina faɗin" Ka fi ni sanin dalilin." Da ga haka na yi kwanciyata na juya masa baya. Na san ya yi ta kallona ya kuma kasa mgana saboda ya san abin da na ke nufi. Mata kawai daga zuwanta za ta zo min da makirci a cikin gidana to ba ta isa ba zan taka ma ta burki daga ita har me biye mata. *Janafty* *TKG* 11. FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622 Yanzu Gimbiya tana cikin wata biyu ne da tarewa. Zaman su ya fara miƙawa tun ina ganin lamarin kamar wasa har dai daga karshe na saka a raina gaskiya ne sannan zan saba ɗabi'ar haka ta zame min jiki ko domin samun zaman lafiya ta. In na buɗe wardrope ɗina na ga cikin kayan Yallaɓai kashi uku babu kashi ɗaya a hankali a hankali ya na ta rage su, suna can gidan Gimbiya, bayan kaya ma hatta ma'ajiyar takalman mu sun yi rauni, wajen gudu huɗu duk babu su a wajen suna gidan Gimbiya bangaren unders ma sannu sannu dai suma ɗin suna ta raguwa, a raina na ce shi kenan duk ikon da na ke dashi a kan Yallaɓai da duk abin da ya mallaka yanzu wannan ikon ya fita daga hannuna saboda ba ni kaɗai ke da shi ba ya na da wata matar kuma itama ta na da iko akan shi da duk abin da ya mallaka. Iya kauda kai ina yi, saboda ni ce babba kuma na riƙe girmana duk da na san ina saurin fushi da zafin zuciya amma na danne ban bari kishi ya saka ni na yi abin da ba dai dai ba ne. Kwanaki na je na gaida Nene ta ƙara yi min nasiha da ƙara tunasar da ni girman da ake cewa ina da shi kar na ɗauka wani ne ya ba ni. Na saka a raina girma ne da Ubangiji ya ba ni. Na ji kuma na yi kamar ban ji ba sannan na gani na yi kamar ban gani ba. Duk da Gimbiyar ɗiya ta ke a wajenta ni Nene ba ta ƙi ni ba kuma ina ganin girmanta shi ya sa duk abin da ta faɗa min zan ji sannan ina ƙoƙarin yin amfani da shawarwarinta. Saboda haka ne ma na saka ma Yallaɓai ido ya gama mararin amarcinsa da rawan kafansa ƙala ban taɓa ce masa ba.   Na yi ta ƙoƙarin kauda kaina a kan al'amarin sa da Amaryansa shima kuma tun kafin auren nan da muka yi mganar ya daina mini labarinta ya tsaya iya matsayin shi. Iyakata dashi abin da ya shafe ni ko ya shafe shi ko ƴaƴana ni ma kuma bana tsallake hurumin da ba nawa ba domin samar ma kaina zaman lafiya da kwanciyar hankali.   Ko na sana'ar sai da Hijabai da aka kawo min daga Zariya guda Hamsin sai da  ɗan nuna rashin jin daɗin sa saboda ni dai ban faɗa masa sai dai kawai ya zo ya ga an kawo hijabai. Da farko ma ya ɗauka ko na saƙo ne bai tambaya ba sai da ya ji ina waya da Khaleesat anan ne ya fahimci nawa ne zan fara saida wa. Sai da ya bari har mun yi shirin kwanciya sannan ya yi min mgana. "Kasuwanci kika fara ban sani ba Sadiya? Sai na kalleshi kafin na ce" E. Ban fara ba zan dai fara in sha Allahu." Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Shi ne ba ki faɗa min? Yaushe kika fara yin wani abu ba tare da na sani ba? Sai ya ba ni mamaki ji karfin hali ɓarawo da sallama. "Ina ka samu lokacin zama ballatana na faɗa maka? "Ban gane ina na samu lokaci ba?  Ba nan na ke kwana ba in ban kwana ba, ba na zuwa da safe? Ban kiran ki a waya? Kai tsaye na ce" Ba wannan ba kai da ka ke cin amarci? Amma ina da niyyar in faɗa maka daman." Sai kawai ya kasa yi min mgana. Nima daga nan ban ƙara jan sa da wata mgana ba amma washegari na yi masa talla na ce ya siya ma yara tunda akwai na yara sai ya ce na ɗaukan musu guda biyu. Ba tare da ya sani ba na cire ma Nene da Gwaggo ɗaya ɗaya na saka albarka sai kuma bayan ya fita ya kirani a waya ya ce ya faɗa ma Gimbiya ta ce ta na so za ta zo ta duba nima na duba na ɗauka zai biya sannan na duba ma Nene itama. Ban ce masa na ɗaukan mata ba na yi masa godiya. Haka ko aka yi a daren ya kawo ta ta duba guda biyu ta ɗauka nima sai na ɗau biyun nan kuma ta ke ya turamin kuɗina Nene kuma biyu na ɗaukan mata sai na haɗa da na wajen nawa ya zama uku, ba shi ya kai mata ba Musbahu na kira ya zo ya karɓa ya kai mata daga baya na kira ta a waya na yi mata bayani ta ji daɗi ta yi ta saka min albarka. Kuma an ta siyan Hijaban duk da na ɗan yi kyattuka da wasu. Na ɗaukan ma Saude da Marwa. Sauran kuma na tallata ma su Ya Aina da su Ya Hamza kuma duk sun siya ma matansu. Sannan har group ɗin makarantarmu na shiga na yi musu talla har mutum uku sun aiko da kuɗi sun siya sun kuma aiko har gida an karɓan musu. Duk da mun ɗan samu saɓani da Anty Bahijja amma tuni na yi mata na ƴan duniya da kaina na kira ta na yi mata tallar Hijaban sai ta fara min faɗa wai na gama yi mata rashin kunya zan  neme ta yanzu. Ina dariya na wayance da cewa. "Haba Babbar Yaya. Wace ni Sadiya ai ban isa ba. Rashin fahimta ce. Ke ce ba ki fahimce ni ba." Sai kawai ta ce min" Ni Yar mijin ki ce ba ƙanwarsa ba Sadiya ya kamata ki riƙa tuna haka." Nan dai na samu na basar da mganar na tura mata tallar Hijabai kuma sai da ta siya ma ƴaƴanta haka itama Anty Maimuna ita sai gashi ta na gaya min Nene ma ta nuna mata wanda na bata da wanda Tafida ya siya mata. Itama ta siya ma kanta da yaranta, Mimisco babban harka ta yi min tambaya na kawai ta yi guda nawa suka rage? Na ce 15 suka rage na manya goma na yara guda biyar kawai ta ce na saka mata acct ɗina da farashin za ta saka min kuɗi sannan za ta aiko direba ya karɓa.  Da ina mata godiya sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce. "Haba Sadiya ku fa namu ne. Dole mu zama masu ƙarfafa muku gwiwa." "Na gode Mimisco Allah ya ƙara ma rayuwa albarka." Ta amsa min da Amin Amin sannan muka yi sallama kuma ba daɗewa Ina tura mata acct ɗin sai ga kuɗina ya shigo na daka tsalle ina murna. Tuni na kira Khaleesat na faɗa mata sai ta ce za ta tura min lambar ƙanwar na ta mu yi magana ita za ta haɗa ni da mai saida yadiddikan hijaban kawai da shi zan dinga magana da na siya kawai aiko min da shi direct ta hannuna kawai zai yi, sai na ce hakan ma ya yi. Ina ta murna na siyar da Hijabai na kuma ina fatan wannan sana'ar da na fara Allah ya sa ta ɗaure min ta kuma ta riƙe ni, na yi ma kowa talla amma ban da Ma'u domin ni ban ma faɗa mata ba, ba kuma na saka wani abu a raina ba ne a'a kawai dai ban faɗa mata ba ne amma a raina na saka cewa in aka ƙara saro wasu zan yi mata talla bakomai in ma ta na da wani aniya a cikin ranta ne Allah ya mayar mata da sharrinta. Khaleesat na tura min lambar ƙanwarta Madina na kira ta muka yi mgana ita ta haɗa ni da shamsu mai yadin hijabai na sabon garin zariya. Shi kuma ya haɗa ni da mai ɗinkin Hijaban anan kasuwar ya iya sosai domin shi ma ya ɗinka min na farko na biyun ma bayan duk na tura masa kololin da kuma adadin yadinka ya ce za a ɗinka nan da kwanaki biyu za su iso hannuna. Amina ma mun yi waya ta ce za ta tallata min in ana so anan Kaduna za ta yi min mgama sai na riƙa aiko mata da shi ta na siyar min aiko na ji daɗi har a cikin raina tuni na fara jin gwara na manta da rayuwar Yallaɓai da Amaryansa na kama sana'ata domin shi ne alherina. **** Alhamdulillah kawai zan ce domin har Hijaban da aka sake kawowa sun ƙare. Gimbiya ta sake min ciniki guda huɗu ta siya sannan ta ƙara siya ma su Jidda. Kuma ta yi min talla a can wajen aikinsu kusan ma rabin Hijaban daga ɓarayinta suka ƙare. Nima saboda jin daɗin haka har kyauta Hijabi na ba ta guda ɗaya na yi kuma mata godiya ta ce bakomai an zama ɗaya shima Yallaɓan na faɗa masa da cewa ya ta ya ni yi mata godiya sai jin daɗi ya ke yi an yabi Amaryansa tun ina mamakin Yallaɓai ni fa yanzu har ya zame min jiki ma.   Duk da ba wani sakar mata na ke yi ba. Ni dai ban taɓa takawa gidan ta ba amma ni tana yawan zuwa za mu gaisa a zauna ana hira sama sama na ke saka baki, saboda ni na kama girmana ban zaƙe ba ban kuma tusa kaina ina daga gefe gefe dai. Amma ita da yara kam ban isa na shiga tsakaninsu ba tun kafin auran ta da Yallaɓai daman ta shaƙu da su sannan komai ta samu su ne tun a baya ballatana yanzu da ta ke auren uban su. Komai ta samu su ne kuma na yarda ya na siyan mata daraja da ƙima a wajen Yallaɓai ya kuma saka ya ƙara sonta domin in dai ta kawo min wani ko ni ko yara haka zai ta washe baki, wani lokacin ma saƙon shi ya ke kawowa ya na faɗi ya na nuna farincikinsa. Ba ta zuwa hannu rabbana. Ko ta yo girki ko ta soyo nama ko kaza ko kayan fulawa haka dai. Su kuma su Jidda wani riborn da kayan kwalliya duk ta ɗauke min duk ita ke siya musu. Ni ban taɓa cewa komai ba sai godiya kayan wasa kam har suna yi musu yawa ta siya musu yan kanti ta kuma ɗinka musu duka dai, yadda ta ke kyautatamin da ƴaƴana in na fara wata mgana sai a ce baƙin ciki ne ko ba ni da haƙuri shi ya sa na koma gefe na yi bakam kawai ina lura da komai, in suka zo tare haka za ta yi ta wannan karera yan ita wai mai miji, ta na wani maƙale murya tana kiran Daddy shima ya na wani kiranta Daugther tun ina mamakin su har na koma na daina kawai ni dai sai ido domin ni ba wani munafuncin namiji da ban sani ba, sannan makircin mata ma ai mun gan shi kala kala so daga ita har shi ni sai dai kawai na kalle su. *** Yau Asabar Yallaɓai a gidana ya ke bayan ya dawo daga kaduna a ranar da daddare wanka kawai ya yi ko abinci bai tsaya ya ci ba ya ce Jidda ta zo ya kaita can gidan. Muna zaune a falo ni da ita da Baby, ban yi magana ba kuma ko ɗago kaina ban na kalle shi ba ina zaune ina yanke kumbana sai da na ji ya ce. "Ki haɗo kayan da ɗan yawa Jidda." Sai ta kalle shi, nima na ɗago ina kallon shi amma ban yi magana ba. "Abba can zan koma? Sai ya girgiza kai kafin ya ce" Ba daɗewa sosai ba. Umman ta ku ba ta jin daɗi ne kwana biyu shi ya sa." Yadda ba ni ya ke faɗa mawa ba nima ko sai na yi kamar ban ji ba amma kuma a ƙasan raina na ji kamar Yallaɓai ya wuce gona da iri. Ni fa na haifi Jidda amma sai ya riƙa nuna min kamar Gimbiya ce uwar ta ba ni ba. Ina zaune ina kallon ikon Allah, har Jidda ta haɗo kayanta da yawa a ƙaramar jakar ta. Baby kuma na wajen Yallaɓai ta riƙe mai hannu ta na faɗin itama za ta je, sai ya kalleni kafin ya ce" Zan ta fi da Baby in zan dawo sai mu dawo tare." "Sai kun dawo." Haka na faɗa ba tare da na ɗago na kalle shi ba, Jidda ta ce min Umma zan tafi? Itama ban kalle ta ba na ce sai ta dawo. Kuma bai saka Yallaɓai ya kalleni ya yi min wata mgana ba. Ina zaune har suka fice ya na riƙe da Baby da shi da kansa ya sanya mata hijabin jikinta suka fice suka bar ni, na yi ta ƙoƙarin na danne amma na kasa sannan ga shi tun wajen takwas da wani abu suka fita ba Yallaɓai ya dawo gidan ba sai goma da rabi kuma ya bar min abinci ya yi kwantai na yi masa ta yi ya ce min cikinsa ya cika tea kawai zai sha da haushi ya kamani na yi wucewata ɗaki a raina na ce sai dai ya koma can Gimbiyar ta baka ko kuma ka shiga kitchen ka haɗa da kanka. Bayan na kwantar da Baby a ɗaki na yi mata addu'an barci na koma ɗaki na yi shirin kwanciya na kuma yi kwanciyata shi ya na can falo ya na aiki a system ina ga ya na ta jiran Tea ne ya gaji ya ga ban kawo ba ya miƙe ya nema ma kansa mafita. Ni dai ko da ya dawo ɗaki na yi barci sai da asuba ne ya ke ce min wai jiya sai ya ji ni shuru? "Barci ne ya ɗauke ni." Haka na faɗa masa kai tsaye. Na kuma haɗe raina, kamar ya fahimta ne sai bai ƙara min mganar ba, ni fa bai faɗa min baki da baki Gimbiya ba ta da lafiya ba kuma ni ban tambaya ba, sai Munnira ce da ta kirani a waya ta na faɗa min wai ko ciki ne da ita? Sai da gabana ya faɗi amma ban nuna mata ba na ce ban sani ba gaskiya. Ni ban je ba saboda wanda ya ijiyeni bai faɗa min ba, bai kuma ce na je ba nima ban tusa kaina ba shi a tunanin shi ai na ji ya na faɗa lalle Yallaɓai ya manta halina ne shi ya sa. Har Hauwa ta je ta dubata ta biyo gidana ta na gaya min gida cike can ta bar su Anty Bahijja da Anty Maimuna. Ita ce ma na buɗe ma baki na tambayeta me ke damun Gimbiyar? "Ciwon kai. Sai maleria da ya saka jininta ya hau sosai." "Allah ya ba ta lafiya." Hauwa ke faɗa min Anty Bahijja ta ce ta ɗauka ciki ne Gimbiya ke da shi sai da a ka je asibiti sannan a ka ce ba ciki ba ne, ni dai na yi shuru ban ce komai ba ina nazari ni kaɗai. Sai da ta ce ta ga ai Jidda a can ta na tambayanta ko ta koma can ne gabaɗaya sai wai Anty Bahijja ta ce e ai jeka ka dawon bai da amfani gwara ta dawo wajen Gimbiyar gabaɗaya. "Haka ta ce miki? Na faɗa cikin mamaki ina kallon Hauwa. "E mana. Anty Maimuna ma na wajen ta kada ba ki ta ce ai daman Jidda ai yar gidan Gimbiyar ce shi ya sa Tafida ya ba ta ita." Kai kawai na jinjina a raina ina girmama tunanin Yallaɓai, ina ga ya manta da ni ce na haifi Jidda ba Gimbiya ba. Hauwa ta tafi ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ta dira a gidana da yamma domin ta na shigowa ana ta kiraye kirayen sallar mangariba ne. Na karɓe ta hannu bibbiyu kamar yadda na saba kamar ma ba zama ta zo yi ba. Sai da na ce ta zauna ita da Sulaihat ne, na tashi domin na kawo musu ruwa ta ce na bar shi kawai ta zo ne domin ta na son yin magana da ni sai na dawo na zauna ita kuma sai ta ce ma Sulaihat ta je ta zauna tare da Baby. Sai da ta fice ne sannan ta juyo ta na kallona kafin ta ce" Sadiya kin kyauta kenan? Cikin mamaki na kalleta kafin na ce" Me na yi kuma? "Laifi ki ka yi mana." "Laifin me? Na faɗa ina ƙara tambayanta domin ni dai ban san na aikata wani abu ba. "Kishi ne ya hana ki zuwa ki duba Gimbiya da jiki? Sai kawai na yi wani sansarai ina kallon Anty Bahijja. "E kalle ni dakyau. To in ba kishi ba menene? Ai ciwo ya wuce wasa ko da ba ki taɓa zuwa gidanta ba tunda yanzu rashin lafiya ne sai ki danne komai ki je ki duba ta ko bakomai a matsayinku ɗaya da ita kamar yadda kike matar Tafida itama haka take matarsa. Da auren shekaru da wanda aka ɗaura yau ai duk sunan su aure ko? "Haka ne." Na bata amsa ina shanye mamakina. "To ba ki kyauta ba. Da na ji an ce ba ki zo ba kin san halina yar gaskiya da gaskiya ce na ce sai na zo na faɗa miki ba ki kyauta ba, shima Tafida na kira shi a waya na yi masa faɗa ya ce ya sha'afa ne amma zai kawo ki domin ki duba ta." Sai kawai na zaune ni dai ban ce komai ba ina kallon Anty Bahijja. In tsaya ma yi mata wani bayani ma ɓata lokaci ne sai kawai na ce ta yi haƙuri zan je na duba ta in sha Allahu sai ta miƙe lokaci ɗaya ta na faɗin" Yakamata. Su kansu masu taya ki kishin su Hauwa duk sun je sun duba ta." "Zan je nima in sha Allahu." Ta ce Allah ya sa har da na rakasu haraba ta na min shaguɓe. "Sadiya kowa ya san mu mata muna da kishi amma ɓoyewa ake yi. Ki daina bayyanawa  gudun kar Gimbiya ta fahimta ta raina ki. Ga shi ta na son ki ta na son mijinki da ƴaƴanki ko domin haka ba za ki danne komai ki je ki gaishe ta ba? "Gaskiya ne. A yi haƙuri na yi kuskure." Sai ta wayance ta na min dariya wai ta na sona ina da fahimta wani lokacin in ban so rashin kunya ba. Ni Allah na tuba yaushe na taɓa mata rashin kunya! Iya biyayya fa ina yi musu da ba su girmansu su ne ba su iya kama girman na su ba haka na dawo cikin gidana ina ta juya maganganun Anty Bahijja a ƙasan raina ba kowa ya ja min wannan wulaƙancin ba sai Yallaɓai kuma wallahi ba zan ƙyale shi ba. A ranar daman zai koma gidan Gimbiya ba nan zai sauka ba, kuma na ce ba zan kira shi a waya ba sai ya zo za mu yi ta ƙare, ya kirani a daren mun yi sallama daman haka ya ke da safen litini bayan Baby ta tafi makaranta da wuri na shirya na riga shi fita kafin shi ya baro can zuwa gidana sai dai muka haɗu a can ni da shi bai ma san na zo ba sai ita Gimbiyar ne ta je ta kira shi. Ba kuma sanin gidan na yi ba, Hauwa na kira ta yi mini kwatan cen gidan Allah ya taimake ni gidan ma ya na bakin titi ne, sai da na sauka adaidaita na yi tambaya a ka nuna min ina buga get ɗin sai ga ta ta zo ta buɗe min. Ba ma shi ba, har ita na san ta yi mamakin ganina. Kuma ni dai yadda ake zuzuta rashin lafiyan na ta ban ga haka ba. Da bakinta ta ke faɗa min ta ji sauƙi, saboda na ganta cikin gayunta ne domin ai ba su yi tsamnanin ganina ba. Yallaɓai kuma ta ce yanzu ya dawo daga kai Jidda makaranta ina falo ta bar ni, ta je ciki ta kawo min lemu da ruwa ta ce abin karyawa na ce na karya daga gida duk da ina tunanin su kansu ba su karya ba. Gidanta itama ya yi kyau duk da iya falo na gani. Amma falon ya yi kyau ƙwarai kayanta duka yan waje ne forum, tare suka fito da Yallaɓan ya na sanye da Jallabiya da ya ganni zaune sai da ya nuna mamakin sa. "Shi ne kuma ba ki kirani na zo na kawo ki ba Madam? Ya faɗa ya na zama a gefena. Har ya na rumgumoni. "Gud morning" Ko amsa shi ban yi ba na juya ina kallon Gimbiya kafin na ce" Ki yi hakuri kar ki ga ban zo duba ki ba. Ni bai faɗa min ba ki da lafiya ba." Kanta na ƙasa ta na wasa da hijabin da bayan shiganta ta sako shi ta ce" Laa bakomai wallahi." Shi kuma ni ya ke kallo kafin ya ce" Ki ji tsoron Allah ban faɗa miki ba ta jin daɗi ba? Kallonsa na yi tare da balla masa harara kafin na ce" Ka dai yi magana da Jidda amma ni baka kalle ni ka ce Sadiya Gimbiya ba ta da lafiya ba. Ka ja ita ta ga laifina sannan yan'uwanka ma sun ga laifina tunda an biyo ni har gida an ce saboda kishi ne ya sa ban zo na duba ta ba, shi ya sa yau bayan Baby ta tafi makaranta na taho domin na wanke laifina. Ki yi hakuri ba kishi ne ya hana ni zuwa na duba ki ba." Daga ita har shi sun ɗan ji wanni iri, ni kuma ban damu ba sai na miƙe daman na tsaya a hanya na siya ayaba da kankana na ijiye mata saman center table ɗin dake tsakiyar falon lokaci ɗaya ina faɗin. "Amarya Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da Amin itama ta na miƙewa kafin ta ce" Ni fa ban ji wani abu ba. Ciwon ma ba sosai ba ne kawai su Anty Bahijja ne suka tambayeni kin zo na ce a'a amma ba da wata manufa na faɗa musu ba." Sai na juyo ina kallonta kafin na ce" Kar ki damu fa. Bakomai." Na faɗa ina mata murmishi shi kuma Gogan ya na zaune ya kasa mgana sai da na juya ina ce masa tafiya zan yi sannan ya ce na jira shi mana ya yi wanka sai mu fita tare. "A'a bari kawai na tafi kar Saude ta zo ba ta same ni ba."     Ganin na dage ba zan tsaya ba ne dole ya sa ya ce bari ya zo ya kaini gida sai ya dawo har zan ce ya bar shi daga baya kuma sai na yi shuru saboda ina so mu ƙare ta ni da shi. Ya ɗauko ni a mota muna hanya zai kai ni gida ya ga tun da muka ɗau hanya ban yi masa mgana ba sai ya kama kan shi. "Ki yi hakuri na ɗauka kin ji lokacin da na ke faɗa ma Jidda ne." "Oh.." Na faɗa ba tare da na kalle shi ba ina ma ƙoƙarin sassauta fushina ne. "Kin ji ko? Sai na kalle shi kafin na ce" Ni fa abu ɗaya ya ɓata min rai yadda ka ja zamin zagi wajen yan'uwanka? Ka faɗa min ne? Ko kuwa don kana magana da Jidda sai ya zama da ni ka ke? Ni ba za ka iya faɗa min baki da baki ba Yallaɓai? Na faɗa ina mai ƙuresa da ido sai ya gano kuskuren shi nan da nan ya fara ba ni haƙuri. "Ki yi hakuri don Allah. Na yi kuskure." Na haɗe rai ina faɗin" Burin ka daman yan'uwanka su ga laifina. Sannan matarka ta ji haushina ban zo na gaisheta ba. Ka kyauta Yallaɓai ka kyauta kawai zan ce maka." "Duk na ji kuma na amsa laifina. Na ce ki yi haƙuri." "Hakuri ai zama dole. Amma dai ba ka kyauta ba. Ko maganar zuwa gidanta da ban taɓa yi ba laifinka ne itama in za ta zo gidana ai kai ka ke kawo ta ba ta taɓa zuwa ita kaɗai ba sai dai ku zo tare da ita ko ka kawo ta ka maida ta. Ni ka taɓa ce min na zo mu je? Sai na yi tunanin ba ku gayyata ta shi ya sa ban tusa kaina ba amma kuma daga baya sai ni a ga laifina! Ko saboda ni ce Sadiya uwar laifi? Na faɗa ina kallon shi, saboda wallahi abin ya ɓata min rai matuƙa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Duk na amsa laifina. Ki yi hakuri haka ba zai ƙara faruwa ba." Shuru na yi masa ban yi mgana ba sai ya riƙe min hannu da hannun shi guda ɗaya, ɗayan kuma ya na tuki dashi. "Am Sorry kin ji" Na ƙara yi masa banza sai ya matse hannuna shi ya sa na kalle shi kafin ya marairaice ya na faɗin" Na ce fa a yi haƙuri ba shikenan sai a huce haka nan ba? "Na haƙura amma bayan wannan akwai wata mganar mu da ni kai." "Me kuma na yi? Ko kallon shi ban yi ba sai ma hannuna da na zare cikin na shi na yi gefe da fuskata ina kallon wucewar motoci fuskata a haɗe. "Sadiya ta." Sai na juya ina kallon shi. "Me kuma ya sake faruwa? Ya faɗa duk ya wani kama kanshi ba gaskiya. Sai ni kuma na ɗauke kaina kafin na ce" In mun je ai za ka ji." Sai ya yi shuru kamar ya na tunani kafin ya gyaɗa kai ya na mai faɗin" Shi ke nan ni sarkin laifi. Zan sake ba da haƙuri wannan karon ma." Ko ƙala ban ƙara ce masa ba har muka isa gida, a waje ya ijiye motar na ce masa ya shigo cikin gida mu yi magana kafin ya wuce. A falon farko muka tsaya ya na goye da hannayensa a bayan sa ya na kallona Ni kuma sai na sauke mayafin kaina ina faɗin. "Yallaɓai." "Na'am" "Na ce ko dai kai da Gimbiya ne kuka haifa min Jidda ne? Sai ya kalleni cikin mamaki kafin ya ce" Me ya kawo wannan mganar? Har ya na wani shan mur. Kai tsaye na ce" Abin da ya kawota shi ne. Labari na ji a gari an ce ka ba ma Gimbiya Jidda halak malak ni kuma da na ji labari sai na ce ba ka gaya min ba, ban san da wannan mganar ba." Na faɗa ina mai kallon shi sai ya wani rausayar dakai kafin ya ce" Ba har abada na ba ta ba. Daman ai yarta ce. Saboda ba ta jin daɗi ne kwana biyu nan ya sa na ce ta ɗan zauna da ita. Ina tunanin ai ba ki da matsala da hakan ko? "Ta ya ka san ba ni da matsalan da hakan tun da baka faɗa min ba? Sai ya yi kasaƙe ya na kallona ni kuma sai na ƙare ware masa ido kafin na ce" E. Ai ba ka yi magana da ni ballatana ka fahimci ko ina da matsala ko ba ni da shi? Sai ya yi shuru kawai ya na kallona, ni kuma na riƙe kugu ina cigaba da faɗin. "A matsayina na mahaifiyar Jidda ban da mutumcin da za ka yi mgana da ni Yallaɓai? Sai dai na ga kana aiwatar da duk abin da ranka ya so maka kai kaɗai? Ko a farkon tarewan Gimbiya da Jidda ta ke zuwa ta kwana da ita ka nemi shawara ta.? Duk da dai ba zan hana ba amma aƙalla dai ka daraja sunana na uwa ka yi magana da ni ba wai na riƙa jin maganar abin da ya shafi ƴaƴana a gari ni ban sani ba." "Sadiya ba ki da kara ne? Ba za ki yi ma Gimbiya kara ba? A fusace na ce" Ita na yi mata kara shi ya sa kaga ban yi magana ba sai yanzu. Kai ne ba ka yi min kara ba Yallaɓai. Sam ba ka yi min kara ba." "Laifi ne domin na zar tar da Umarni kan Jidda ban shawarce ki ba Sadiya? "Ba laifi ba ne amma a kalla dai ka daraja ni. Ai ba ci baya ba ne in ka ce min Sadiya Jidda za ta koma wajen Gimbiya na wani lokaci ai kasan ba zan ce komai ba amma dai zan ji daɗi a raina ka martabani ko? "To ki yi hakuri. Na ji ban kyauta ba shike nan ko? Sai na ɗan sassauta fushina ina mai juya fuska, mirmishi ya yi har ina jin sautin mirmishi kafin ya ce"Madam ki yi hakuri kin ji ko? "Ni fa ba rai na ne ya ɓaci ba kawai na faɗa maka ne domin ka kiyaye. Ba na so kar ka sake yi min haka ina gidan nan in abu ya shafe ni ko ƴaƴana ka daina abu ba tare da ka yi magana da ni ba." "An bari. Kuma za a yi mgana da ke in sha Allahu." Sai na sauke numfashi na koma na zauna ba ta re da na yi magana ba sai shima ya zo ya zauna a kusa da ni ya na faɗin" Shiken ko faɗan ya ƙare ko? Ya faɗa ya na rumgumoni zuwa jikinsa. "Ni ban yi faɗa ba." Na faɗa ina sunne kai a saman kirjinasa. Saman kaina ya sumbata kafin ya ce" To in ba faɗa ba me kenan kika yi? Tun a mota sai faɗa kike yi min mun zo gida ma ban tsira ba. Alhalin kuma nima kin yi min wani abu da ya sosa min rai kuma kema kin sani amma ban yi miki mgana ba, ko faɗa ma ban yi miki ba." Sai na yi saurin ɗagowa ina kallon shi kafin na ce" Ni? Me na yi maka kuma? "Kin sani fa Sadiya." "Ban sani ba fa." Na faɗa cikin shagwaɓa har ina kai masa duka a ƙirji, sai ya riƙe min hannu ya na kallona kafin ya ce. "Kin tsara za ki fara kasuwanci amma ba ki faɗa min ba har aka kawo kaya na yi miki mgana sai ce min kika yi wai kin bar ni na gama cin amarcina ne? Wannan mgana ne? Tsakaninki da Allah duk wani abu da zan yi ko za ki yi mun saba zama mu tattauna a tsakanimmu, amma sai ga shi yanzu kin sauya kin fara yin abubuwa kai tsaye ba tare da kin faɗa min ba ko dai ba zan ba da komai a kallah dai na saka albarka na ba da shawara ko? Ashe ya ji haushi, sai na ji daɗi ai ni haushin na ke son ya ji. "Kin kuma san na ji haushi amma ki ka share ni." Sai na yi mirmishi, kafin na ce" Afuwan Yallaɓai. Allah ya huci zuciyar Tafidan Rano." Kawai sai ya jinjina kai kafin ya ce" Na yi haƙuri fa. Kawai dai na faɗa miki ne domin kin san na ji haushin ki." "To a yi haƙuri Megida." Na faɗa ina shafa sajen shi zuwa gefen masa. "Laa la. Yallaɓai tafiya ta tafi. Furfura ka fara fa." Na faɗa ina masa dariya, ɗankwalin kaina ya cire ya na faɗin"Ke ma ai kin tafi. Ina dubawa zan ga ta ki furfuran." Ina dariya na kwaçe kaina ina faɗin" Ni yar yarinta? Yanzu na ke fa kai dai tsufa ya kama." "To ke kika tsufar da ni. Saurayi ɗan ƙwalisa kika aura amma ji yadda yanzu na dawo." Ya faɗa ya na wani kallon kanshi kafin ya ce" Sadiya ko yanzu na so zan auro biyu yan mata ƙwarara." Sai na balla masa harara kafin na ce" Kai yanzu a zuciyarka akwai wajen wata mace? "Ai ba ni na samar musu wajen ba Ubangiji ne." Sai na kasa mgana na tsaya ina kallinsa shi kuma ya na min dariya sai kawai na miƙe tsaya na ja hannun shi ina faɗin" Sai anjuma Yallaɓai." Ƙin tafiya ya yi sai da na riƙa tura shi sannan ya tafi ya na min dariya a raina na ce ni yanzu har wani aure za ka ƙara da zai ɗaga min hankali, ai sai dai Gimbiya itama ta ji yadda a ke ji na zafin kishi, yadda na samu na zazzage ma Yallaɓai abin da ke cikina sai na samu salama, kuma shima ai ya san bai kyauta ba shi ya sa ya ba da haƙuri. Tuni Gimbiya ta warware. Yallaɓai ya san na yi masa tsiya tsiya sai ga shi ya zo ya na faɗa min Jidda ta na so ta dawo gida amma ya ce ta ɗan zauna ta ƙara kwana biyu na ce bakomai. Ni daman saboda tahfez ɗin ta ya yi rauni ne amma acewarsa ita Gimbiyar na yi ma Jiddan karatu a can. Ko sati ba a yi da zuwana duba Gimbiya ba Nene ta faɗi a gida sai asibiti ana zuwa aka ba su gado. Jininta ya hau sosai ta samu jin jiri kuma ta ƙi mgana shi ne ranar kawai da safe ta faɗi Allah ne ma ya kyautata da ta samu shanyewar jiki, amma ko yanzu ɗin hannunta na dama da kafarta sun ɗan tabu bangaren hagu sun fi lafiya. Hankula sun tashi matuƙa ko ni na damu da ciwon Nene musamman saboda Yallaɓai ba ya son ganin ta cikin ciwo yanzu shina sai ya susuce. Shi ma ko in ba shi da lafiya ba ta da sukuni sai ta ji labarin ya samu lafiya shima ba ta yarda sai ta gan shi ya tako da kafafun shi ya zo duba ta. A wani asibitin kuɗi ne na cikin gari in da Mimisco ke kaita ta na ganin likita ne aka kwantar da Nene. Gabaɗayanmu can muke yini da ni da Hauwa da har da Munnira da su Halima,Hajiya iya da Maman farko, su Anty Bahijja daman suna gaba gaba su masu uwa. Gimbiya kuma ta bar bangaren surukai ita ta koma bangaren ɗiya. Ita ta ke kwana da Nene Hajiya iya aka ce ta riƙa kwana da ita Gimbiya ta yi tsaye ta ce ita za ta riƙa kwana da ita su Anty Bahijja kuma suka amsa, da ita Mimisco ta ce gwara Hajiya Iyan ita babba ce sannan ita Gimbiya ga jikinta ba daɗi amma ta yi tsaye ta ce ta warke Yallaɓai ma ya amince ta riƙa kwana da safe sai ta je gida ta yi wanka ta huta ta kuma dawo. An ga tururuwa har mutanen Rano duk sun zo, yan nesa kuma sun ta kiran waya. Kwana uku Nene jiki ya yi sauki ta na mgana ta na kuma motsa hannunta kaɗan kaɗan dai. Hajiya Tafida ma ta zo ta kwana ɗaya ta koma. Su Kawu Abba kuma kullum sai sun zo nima na kira Gida na faɗa Gwaggo sun zo ita da Alhajinmu da Ya Abubakar sannan su Rahila ma Ya Aina ta haɗo su gabaɗaya sun zo har asibiti sun duba Nene Ma'u kuma daman anan suka iske ta ma, ni fa har mamakinta na ke yi ko Nene ta haifi Alhaji mustapha sai haka shima ya na zuwa kuma ba sa zuwa hannu rabbana, kamar yadda muke dafo abinci ni da Hauwa haka itama ta ke zuwa da shi. Za mu haɗu da Gimbiya kullum amma tsakanina da ita gaisuwa ce, Jidda kuma ta koma gida saboda Gimbiya na asibiti, Yallaɓai kuma daman barci kawai ke kai shi gida da safe kafin ya wuce wajen aiki zai biya haka da yamma in ya dawo, wata rana har sai na fara gangyaɗi  ya ke cewa na tashi mu tafi gida yara fa Ɗorayi Salisu ke kai su in sun tashi makaranta sai za mu koma gida mu biya mu ɗauko su.   Kwanan Nene goma a asibiti sannan aka sallame ta ta dawo gida. Kuma ban taɓa fashin zuwa asibiti ba kullm safiyar Allah duk da zirga zirga ya sa duk na ji jikina na ciwo ga shi ina fama da ciwon mara kwana biyu nan ga ciwon kai da daddare na dai sha mgani amma ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba. Da Nene ta koma gida Gimbiya ma can ta tare, ta na kula da ita kowa kuma yabon ta ya ke yi da ƙoƙarinta ni kaina na yaba mata ni kuma da ba a yabe nin ba na yaba ma kaina domin ni don Allah na yi. A baya kafin Gimbiyar ta yi ni na yi ko a yanzu ɗin ma ina iya bakin ƙoƙarina. *Janafty* *TKG* 12. FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622 Gidana duk ya yi ƙura to ba na samun zama. Shi ya sa da aka sallami Nene sai na ɗan ɗaga kafa da zuwa Gwammaja in yau na je gobe ba zan je ba. Yallaɓai shima ya samu natsuwa tun da har Kaduna ya shiga ya kwana biyu. A ranar da zai dawo daga kadunan na je can Gwammaja da ya ke Jumma'a ne tare da su Jidda na ne tunda sai da na jira suka dawo muka taho tare. Na yo ma Nene ferfesun kayan ciki saboda na son ta na so, amma ina kawowa sai na ga Gimbiya ta yi mata amma duk da haka Nene ta karɓa ta ce za ta ci ko zuwa Gobe ne. A gabana Anty Bahijja ta ɗanɗana ferfesun kai tsaye ta ce wai Nene ba za ta ci ba na cika ya ji kuma ya yi gishiri. Kuma ni dai har ga Allah na ci kafin mu fito komai lafiya na kuma san laluranta me ya sa zan cika mata gishiri da ya ji? Duk da haka ban nuna wani abu na danne a gabana ta ce wanda Gimbiya ta yi mata za ta ci shi ne ba zai mata wani abun ba. "Wannan ko in kika ci sa ina ga sai kin koma Asibiti Nene." Sai Nenen ta ce to su ci mana, irin dai kar na ji ba daɗi. Ko a fuska ban nuna ba illa Nene da na kallah na ce" Ban san gishirin ya yi yawa haka ba Nene ki yi hakuri." Sai ta ce min haba bakomai ta gode da kyautatawa. Falo na koma ranar Hauwa ba ta zo ba, Munnira ma haka ba ni da abokin hira, ina gidan Naja'atu ta zo da Anty Maimuna Nene ta sha magani ta kwanta sai suka baro ciki suka dawo falo suna hira suna shewa ina zaune kamar da gayya suna jefa min mgana. Wai Naja'atu ke faɗin Gimbiya kar ta tsaya wasa ba wasa suka kaita ta yi ba. Haihuwa suke so. Ko kunya ta ma ba su ji ba kuma sun ganni domin har ita Naja'atun ma mun gaisa da ita. "Ahto faɗa mata dai. Ni fa ciwon da ta yi kwanaki har na buga murnan mun samu ƙaruwa ashe ba cikin ba ne." Ita kuma ta na mirmishi ta ce" Haka shima fa ya yi ta cewa ko ciki ne Daugther sai da muka je asibiti aka ce ba ciki ba ne sai da ya ba ni tausayi yadda na ga ya nuna damuwarsa." "Allah sarki bawan Allah. Hauhiwa ya ke so amma an katse mishi ita a gidan shi da karfi da ya ji." "To ai shi ya sa da Allah ya bashi dama ya mallaki gida biyu. Can ɗin da aka katse mishi nan kuma ba sai a buɗa masa ba." Anty Bahijja ta faɗa har suna tafawa da Anty Maimuna. Ni ko sai na yi kamar ban ji su ba wayata na ke latsawa amma a ƙasan raina baƙin ciki ne ya cika ni, nan suka ta yada min mgana amma ban tanka su ba shi ya sa tun kafin mangariba na yi shirin tafiya na shiga na yi ma Nene sallama. "Na gode Sadiya Allah ya saka da alheri." Na amsa mata da Amin na tasa kan Jidda da Baby, ko jiran Yallaɓai ma ban yi ba duk da na san in ya dawo nan zai biyo amma baƙin ciki ba zai bar ni na zauna. Ban kuma ƙi yi musu sallama ba na ce musu zan tafi har ita gimbiyan. "Ba za ki jira shi ya dawo ba? Gimbiyar ta ce min ni kuma sai na ce mata a'a ban san lokacin da zai dawo ba gwara na tafi kawai. "E ki tafi kawai shi in ya dawo ma ya na da wata matar a nan za ta kula dashi kafin ya ƙariso." Sai na yi mirmishi kafin na ce" Ai hakan ne ya kamata." Saboda kamar haka ɗin ne in ya zo sai wajen sha ɗaya ya ke komawa gida sannan ba duka ranakun ba ne in ya koma ya ke cin abincin da na dafa in na kawo masa sai ya ce ya ci abinci a Gwammaja. Shi ya sa abin da ta faɗa bai zame min wani baƙo ba Muna tafe a cikin adaidaita ina sharan ƙwalla saboda baƙin ciki, da Jidda ta gani ta yi magana sai na ce wani ƙwaro ne ya faɗa min a ido, haka na koma gida na ƙule a ɗaki na sha kukana na ƙoshi kuma da Yallaɓai ya dawo Gwammja ya sauka sai sha biyu saura ya shigo gidan nan ina zaune idanuwana biyu ban yi barci ba na yi masa sannu da zuwa ya amsa. "A haɗa abinci? Na faɗa lokacin da na ga ya na tuɓe shaddar da ke jikinsa. "No. Na ci abinci a gida" Haka kawai ya ce min ya tura kofa ya fice ina zaune na ji ƙaran buɗe ƙofa ya shiga tiolet sai na kaɗa kaina na koma na kwanta wasu hawaye masu zafi suka zubomin ban iya saka hannu na tare su ba. Domin saukar su ɗin wani ni'ima a cikin zuciyata. Ina kwancen na ji shigowarsa har kuma ya gama shirin kwanciya ya zo ya kwanta ina jin sa amma ban yi wani motsin da zai gane idanuwana biyu ba. Kwanciyarsa ba daɗewa na ji an kira wayarsa yanayin yadda ya ɗauki wayar ne da maganar sa ya sa na gane Gimbiya ce. A kan gadon aurena ina kwance daga gefe Yusuf ke faɗa ma wata macen ya na sonta. Har ya na ƙasa ƙasa da murya wajen furta mata. I LOVE U TOO DAUGHTER." Kukan zuciya na ke yi amma hawaye suna zuba daga saman ƙuncina a baya in aka ce hakan za ta faru sai na ƙaryata a tunanina Yallaɓai ba zai iya son wata mace sama da yadda ya so ni ba, amma tun daga lokacin da ya yi auren nan na fahimci cewa duk ƙarya ce, yarda da aminci da na ba ma Yallaɓai tuni na fahimci cewa na yi kuskure Namiji ne shi kuma zai iya sauya launi duk lokacin da ya so kamar yadda ya fara sauya min lokaci bayan lokaci. Ban san adadin lukutan da na ɗaukan barci bai iya ɗauka ta ba, na yi kuka kukan baƙin ciki wannan ƙololin abin da ya yi min sauƙi daga ƙasan zuciyata na ji ya na ta so min, ina ma kukan ne amma ina jin kamar ma ƙaruwa ya ke yi ba ya raguwa. Yallaɓai ko barci har da minshari na juya ina kallon shi ina jin wani kuka na ƙara taso min, yaushe a ka yi daren ballatana har garin ya waye? Har Yallaɓai na neman ya yi min nisa. Nisan da har abada ba zan iya dawo dashi kusa da ni ba, ganin kamar ya motsa ne ya sa ni kuma na tashi na faɗa tiolet a ciki na zauna na sha kukana sannan na tashi na kama ruwa nufina na ɗauro alwala amma sai na ga period ɗina ya zo. A lissafi daga watan jiya zuwa watan nan al'adan nawa ya ɗan dai dai ta sai dai ina fama da matsanacin ciwon mara ne a lokacin na kira Dr. Aisha ba ta ɗauka ba amma na bar mata saƙo ta wsop da niyyar in ta gani sai ta sanar da ni yadda zan yi. Ganin haka ya sa kawai sai na ɗauro alwala sai da na fito ne na duba lokaci a wayata na ga 2 saura ne na dare. Sai kawai na ɗau casbaha ta na koma na kwanta. A kwancen ina ta hailala da salatin Annabi a hankali a hankali kuma sai na samu sauƙin zuciya har barci ya kwashe ni ban sani ba. Kuma mai nauyi ne domin har sai da Yallaɓai ya tashe ni da asuba bayan ya dawo masallaci ya ga ban tashi ba, ban ce masa ina hutu ba sai kawai na tashi na shiga tiolet. Da safen nan da na gaishe shi a daƙune ya amsa kamar na yi masa wani abun nima ko ina ganin haka na kama kaina. Ina ma fama da kaina marata kamar za ta cire saboda yadda ta yi min nauyi sosai. Daƙyar na yi ma su Jidda breakfast suka tafi makaranta. Shima dai tea kawai ya sha ya yi wanka ya fita ya bar ni ina ta mutsu mutsun ciwon mara sai da Saude ta zo ne na saka ta dafa min ruwan zafi da Hulba na ɗan sha sai maran ya ɗan yi min sauƙi. Sake kiran Dr. Aisha na yi shima ɗin ba ta ɗauka ba, sai na yi mata uzuri tunda ita likita ce mai harka da jama'a ba lalle ta na da lokaci ba sai kawai na yi tunanin ya kamata gobe na shirya na je asibitin matsalan ba lalle ne ma in na je a goben na samu ganin Dr. Aishan ba. Haka na yini a gida kwance ban da lafiya. Ban kuma kira kowa ba yadda Yallaɓai ya fita bai iya tambayata me ke damuna ba saboda ai ya ganni sukuku shi ya sa nima ban neme na faɗa masa ba. Kuma tunda ya fita bai kirani ba nima ban kira shi ba, girki ma Saude na saka ta dafa kafin ta tafi ni a ɗaki na yini ina shan ruwan zafi domin na gasa marata. Sai can da yamma na ga saƙon Dr Asha ta ce bakomai na cigaba da shan mgani kaɗan kaɗan komai zai dai daita ciwon maran kuma da na ke yi sakamakon na kan ɗan daɗe ban yi al'ada ba ne kuma cuta ne a acikin jinin da ya ke fita shi ya sa zan ɗan riƙa fuskantan ciwon mara a farko farko amma ta ba ni tabbacin in na cigaba da yi duk wata zuwa nan gaba kaɗan ba zan riƙa fuskantan haka ba. Itama ta ce na riƙa shan ruwan zafi a kai a kai in sha Allahu zan samu sauƙi kuma na samu ɗin Alhamdulillah tunda har na samu na yi wanka a daren na sauya kaya sai dai fuskata duk ta kumbura har da ma kafafuna sai da na ɗan shafa mata man zafi. Yau ma Yallaɓai sai around 11 na dare ya shigo gidan. Yara har sun yi barci nima na fara barcin marata ne ya ƙulle sai na tashi na shiga tiiolet a lokacin ya shigo gidan. Yadda na iske shi zaune ya na duba wayarsa fuskar ba alamun rahama ya sa ban neme shi da wata mgana ba bayan sannu da zuwa. "Yauwa." Haka ya amsamin kamar na yaɓa masa wata mgana mara daɗi. Sai na yi shuru ina ƙoƙarin danne zuciyata. "Abinci fa? Bai kalleni ba hankalinshi na kan wayarsa ya ce" No am ok." Sai kawai na wuce na koma na kwanta na rufe ƙafafuwana zuwa cikina da bargo na juya masa baya ina ƙoƙarin danne tasowan wani ƙunci daga ƙasan zuciyata. "Ba ki je Gwamnaja ba yau? Ya tambayeni, ina daga kwancen na amsa masa da cewa E ban je ba. Sai na ji shuru sai ni ce na juya ina faɗin" Ai na ga Nenen ta ji sauƙi sosai." "Ta ji sauƙi Alhamdulillah." "Allah ya ƙara mata lafiya." Ya amsa min da Amin Amin daga nan ya tashi ya fice nima na juya na gyara kwanciyata ina ƙoƙarin danne komai na nuna komai ba komai ba ne daga saman fuskata amma a ƙarƙashin zuciyata kwata kwata ba daɗi.   Washegari da safiyar Talata ya na gida bai fita da wuri ba yana ta aiki a laptop ɗin sa ni kuma ina cikin ɗaki a kwance. Yadda bai tambayeni me ke damuna ba, nima ban faɗa masa komai ba ai ya na da hankali tun da ya ga ina kwanciya ai ya san ba lau ba, amma mutumin nan ko a jikinsa sai ma wanka da ya yi ya shirya cikin manyan kaya ya fice ya bar ni kwance cikin yanayi mara daɗi. Ban taɓa tunanin akwai wata rana da Yallaɓai zai ganni kwance bai fara rawan jikin tambayana lafiya na ke kwance? Me ke damuna? Amma yau sai ga shi kwana biyu ina kwance ban ji daɗi ya fice ya bar ni ko a jikinsa lalle na fara yarda ina da abokiyar zama. Ba ni kaɗai Yallaɓai ke da shi ba, shi ya sa yanzu ba zai cika damuwa da ni kamar a baya ba. Sannan na lura da wani abu tun kwanciya Nene asibiti bai neme ni ba sai ranar da ta dawo gida shima tun daga ranar har yau bai ƙara nema na ba, ni da na san Yallaɓai da bama ɓarnan ruwa muhimmaci amma yanzu kwata kwata ba ya nuna sha'awar haka, ko na daina burge shi ne ban sani ba? Wata zuciyar ne ta faɗa min cewa yanzu ba da ba ne ya na da wata matar, in ma ni bai neme ni ba ita ba zan ba da tabbacin bai samu natsuwa daga wajenta ba. Ina kwance ina tunanin nan sai ga kiran shi, ina ɗauka bayan mun gaisa shima gaisuwan ni na gaishe shi ya amsa sai ce min ya yi na shirya na je Gwammaja na sake duba Nene ni kuma ban ce masa komai ba na ce to. Na ɗauka zan ɗan rarrafa na je amma kuma sai na kasa gabaɗaya jin jikina na ke yi kamar ba nawa ba, sannan ni ba na so ma ina fita in ina cikin wannan yanayin ganin dai ba zan samu zuwa ba ya sa na yi ƙoƙarin neman wayar Yallaɓai na faɗa masa ban da lafiya amma ban samu wayarsa ba, ban yi tunanin rashin zuwan nawa zai iya zama matsala ba, ban kuma taɓa tunanin Yallaɓai zai iya min fahimtar a bai bai ba. Ranar Saude ma ba ta zo ba ta je makaranta Marwa na kira ta ce tana asibiti sai 2 na rana za ta dawo sai na ce ta biyo ta gidana ba na jin daɗi. Ita ta zo ta gyara min gida sannan ta yi ma su Jidda girki, ita da kira Ya Aina ta faɗa mata cewa ta na gidana ba na jin daɗi har ta ba ni ita ma muka gaisa ta na faɗan ban da lafiya amma ban faɗa ma kowa ba? Sai na ba ta haƙuri da cewa ba wani ciwo sosai ba ne shi ya sa ban ɗaga musu hankali ba, ita kuma Ya Aina ta kawo maganar cewa daman kwanan biyun nan duk kowa ya ji ni shuru na ce ina nan lafiya ba wani abu ba ne mai tsanani kar ta ɗaga hankalinta. Mun rabu da cewa Marwa ta kwana nan tun da ban ji daɗi na ji daɗin haka tun ballatana da Marwa ta ce Gobe ta na da hutu sai jibi ta ke da aikin dare sai na ji daɗi ko banza za ta ɗebemin kewan zaman gidan ni kaɗai. Yallaɓai da wuri ya dawo wajen tara na dare. Sai kuma ni da kaina na zauna ina nazarin wani abu. Kwana biyu ya ke yi in ya fita ya na kaiwa dare a Gwammaja kwana biyu kuma sai ya riƙa dawowa da wuri kuma har ya ci abinci sai zuciyata ta zargi kamar ya na raba mana kwana ne ni da Gimbiya duk da ta na can Gwammaja, saboda sai na ga kamar tsarin da ya ke bi kenan ban yi masa maganar rashin zuwana can Gwammaja ba nima kuma bai yi min ba kuma ko da ya ga Marwa a gidan bai damu da ya ji dalili ba sanin daman ai yar gidana ce ta na zuwa sosai shi ya sa hankalin shi bai kawo masa wani abu ba. Allah sai ya taimakeni washegari na tashi garas kamar ba ni ba, Marwa ta na nan sai yamma ta shirya ta tafi asibiti. Ranar dai mun yi azkar tare da su Jidda har na yi musu karatu ban dai ɗauki Qur'ani ba ne tunda ba ni da tsarki. Domin na ƙara samun tabbaci a kan sabuwar daɓi'ar Yallabai ya sa ban yi barci da wuri ba kuma illau ranar ma da wuri ya dawo na gabatar masa da abinci ya ci ya yi wanka, sannan sai ya jima ya na aiki a loptop har na yi barci na bar shi bai gama ba, washegari na sake zura masa ido sai ya maimaita abin da ya tsara bai shigo gidan ba sai sha ɗaya da rabi na dare ta ma gota ban yi barci ba a raina daman na kudri niyya sai na yi masa mgana saboda a daran na kira Nene na gaisheta na ba ta haƙuri na ce ban ji daɗi ne shi ya sa ba ta ganni ba sai ta yi min sannu ta ce ba ta sani ba domin ba su yi maganar da Tafida ba. A lokacin na ji maganarsa a ɗakin Nene da na wasu amma ban ɗauki muryan kowa ba sai na shi, kuma a lokacin ko tara bai yi ba kenan a can ne ya ke kwashe lokaci mai tsawo shi a dole mai Mata kawai sai na saka a raina sai na yi masa mgana. Gwara ya riƙa kwana a can duk ranar girkin Gimbiyar in Adalcin ya ke son ya kamanta dakyau, ni ba ma wani amfani ya ke yi min a gidan ba, gwara ya riƙa tsayawa can ya na kwanan shi zai fi sauƙi da wannan ciccin mganin da ya ke dawowa gida ya na yi min ba tare da na san laifin da na yi masa. Ina kwance a kan gado ya shigo na yi masa sannu da zuwa ya amsa ya na kallona. "Ba ki yi barci ba? Ya faɗa lokaci ɗaya ya na cire agogon hannun shi. "E." Na bashi amsa a gajarce sai ya jinjina kai kawai ya fice ya shiga tiolet ya ɗan daɗe sannan ya fito bai yi wanka ba na ga dai fuskar shi da ruwa, duk ina zaune ina kallon shi na yi masa ta yi abinci kamar yadda na yi zato sai ya ce min ya ƙoshi ya ci abinci a can Gwammaja. Sai da na bari ya yi shirin kwanciya ya na zaune gefen gado da wayarsa a hannunsa ya na dubawa ina kallon shi ya na ta mirmishi koma mene ne ya ke dubawa ya na jin daɗin haka. "Ya jikin Nenen? "Da sauƙi Alhandulillah." Ya ba ni amsa amma hankalinshi na kan wayarsa. "Allah ya ƙara mata lafiya." Ya amsa da Amin haka a gajarce, sai na ɗan yi shuru kafin kuma na yaye bargon jikina na sauko da kafafuna daga saman gado na sauke a saman cafet ɗin gefe da gefen gadon. "Yallaɓai." "Uhm." Ya amsa min a ciki hankalin shi har a lokacin na kan wayarsa. "Na ce ba." Sai ya ji na yi shuru sai ya juyo ya na kallona bayan ya ijiye wayar a gefen shi, ya na mai kallona kafin ya ce. "Ina jin ki. Kika ce me? Kai tsaye na ke kallon shi kafin na ce" Wata shawara na ke so ba ba ka Yallaɓai." "Ina sauraran ki." Ya faɗa ya na mai ƙureni da ido amma fa ya wani haɗe rai kamar ya san abin da zan faɗa "Me zai hana duk ranar girkin Gimbiya ka riƙa kwanan ka kawai a can Gwammaja." Giransa ya tattare waje ɗaya ya na min wani kallo amma ban fasa mgana ta ba. "Zai fi tunda akwai ɗakuna a can" "Me ya kawo wannan mganar kuma? "To ai na ga kana raba mana dare ne da ita. Da zuwan da kake yi kana raba dare barci kawai ke kawo ka nan shi ne na ce duk ranar girkinta ka riƙa kwanciyarka a can har ta koma gidan ta." Ya daɗe ya na kallona bai ce min komai ba, ni kuma ganin ya yi shuru ya sa na tashi zan fita zuwa tiolet har na ɗan gota shi zaune a gefen gado. "Kin gama mganarki? Sai na juyo ina kallon shi kafin na ce" E. Na gama." Sai kawai na ga ya miƙe ya wani harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ya fara takowa gabana cikin wani yanayi, sai na tsaya kawai ina kallon shi ba tare da na yi mgana. "Sadiya." Ya kira sunana a kausashe bai ma jira na amsa ba ya ce" Kishi ne ke rufe miki ido ko? Cikin mamaki na kalleshi ina shirin mgana kawai ya wani ɗaga min hannu a fusace ya ce" Ke kaɗai ce mai bakin magana!? Ko ke kaɗai ce ake yi ma ba dai dai ba? Ko ke kaɗai ce ake zalunta ehe? Ya ƙarishe faɗa ya na mai yi min tsawa, sai na yi baya kawai ina kallon Yallaɓai na kasa mgana. "Ko domin kin ga bana son ina yi miki faɗa? Ko kina tunanin ina tsoron ki ne? To bari ki ji na faɗa miki ba ki isa ba, ba ke kike aurena ba ni na ke auran ki Sadiya saboda haka ki shiga hankalinki tun kafin ki ɓata min rai na buɗe miki bakina ba za ki ji daɗi ba." Sai na fara mamakin sa? To wai ya na jira na ne, me na yi masa da zai wani fara balbaleni da masifa daga faɗin gaskiya ni ma ko a fusacen na kalle shi kafin na ce" To wai me aka yi maka? Daga faɗin gaskiya sai ka fara wasu mganganu da ban gane musu ba! Ni na ce ka yi laifi ne! Rayuwarka ce yadda ka so ai haka za ka tafiyar da ita. Kuma da kake maganar za ka buɗe bakin ka in ka bude ba zan ji daɗi ba, to don Allah Yallaɓai ka buɗe bakin naka ka yi mgana mana sai me? Na faɗa ina watsa hannayena daman raina a ɓace ya ke kuma a kusa na ke. "Kika ce sai me ko Sadiya? Na taso masa ina faɗin" E sai me in ka buɗe bakin? Me za ka faɗa min wanda ayyukan ka ba su nuna min ba. Koma za ka ce ka ce gaskiya na faɗa ina lura da kai kwana biyu nan kake cin abinci kuma ka dawo a kan lokaci kwana biyu kuma kana can Gwamnaja sai dare ka ke dawowa in na yi maka ta yi abinci ka ce ka ci a can, me ya sa ba zan yi tunanin ka raba ma kwanan ba ne kar a cuceta? Ni fa mafita na kawo maka domin kar ma ka yi tunanin alfarma ka ke yi min da kake kwana ranar girkinta a gidana shi ya sa na ce ka je can ka kwana ko ka riƙa tafiya can gidan nata kana kwana babu ruwana tunda in ba ka kwana a nan ɗin ba ba mutuwa zan yi ba, sannan kwanan ma da ka ke yi anan ɗin ba wani amfani kake tsinana min ba." Raina ne ya ɓaci na riƙa sakar masa mganganu na gama na juya zan bar masa ɗakin sai ya saka hannu ya fizogoni ya dawo dani cikin ɗakin da karfi har ya na hankaɗani na yi baya Allah ya sa ban faɗi ba. "Ina za ki je! Tun da kin gama fadin na ki sai ki jira nawa Malama." Ya faɗa ya na nuna min yatsa, sai kawai na koma na yi tsaye na harɗe hannuna a ƙirji ina girgiza jikina kafin na ce" Ai ban hana ka mgana ba." "Me ke damun ki? Me kuma kike taƙama dashi ne? Tun da na yi auran nan kike bi na da fitina ina ƙyaleki saboda ina ganin kamar ni ne ban yi miki dai dai ba, amma me ya sa haka! Me ya sa kike da ɓakin kishi ne Sadiya? Na buɗe baki na rufe ya fi sau uku ina rufewa na kasa mgana. "Ni ke kake kira da mai baƙin kishi Yusuf? "E mana baƙin kishi ke damun ki, kin ƙi ki kwantar da hankalinki ki yi ta zarge zarge. Kar ki manta itama Matatace kamar yadda kike matata kuma auren da na yi zunubi ne? Ko Allah ya hana ne? Ai sai kawai na rufe bakina na yi shuru, ganin idanuwan shi sun rufe ya na zaro maganganu. "To ba ri ki ji na faɗa miki ba ki isa ba. Ke in har kina da tunani za ki kawo wannan mganar? Gwammaja nan ne gidan Ubana kuma uwata ce ba lafiya ta ke jinya. Gimbiyar da kika saka ma ido kike kishi da ita ita ce ta bar komai na ta har da ni mijin da kike takama da ni ta je ta zauna ta na kula da mahaifiya ke ina kike? Ba kina gida akwance ba? Kin taɓa tunanin cewa bari ki je ki taimaka mata! Ko shekaranjiya da na kira ki na ce ki je kin je! Kin je? Na ce kin je? Ya ƙara daka min tsawa sai na saka hannuwana duka biyu na toshe kunnuwana saboda sosai ya yi min ihu a saman kaina. "Ki saki kunnuwan ki saurareni da kyau. Daughter ta yi min komai kuma komai za ki ce kin daɗe ba ki ce ba. Kwana kuma babu ruwanki ba ke za ki faɗa min abin da ya kamata in yi ba, in ina son kwana a can ke ba ki isa ki sani ko ki hana ni ba, shawara da zan ba ki ki riƙa saka alheri a cikin zuciyarki Sadiya saboda wata rana kar ki ji kunya." "Ba ni da alheri a zuciyata ka ke son ka ce mini Yusuf? Na faɗa muryata na rawa ina nuna kaina. "To ina alherin. Kin bi kin kwazzabi kan ki tunda na yi auren ba ki bar ni na huta ba daga kice na yi miki kaza sai kice ƴan'uwana sun yi miki kaza duk dai na biki da ki yi hakuri saboda a zauna lafiya. In ba zuciyarki ba ta saƙa miki alheri ba yanzu ya kamata a wannan halin ki tare ni da wannan mganar? Gimbiyar da kika tsana ita ce ke son ki tsakanina ga Allah ƴaƴanki kamar na ta ta ɗauke su amma ke ko sau ɗaya a zuciyarki ba za ki ɗan mutuntata ba? Ta na can ta na wahala da mahaifiyata ko sau ɗaya kin ji a ranki ya kamata ki gode mata! Ai ba ita kaɗai ba ce matata ke ma ɗin matatace kuma akwai haƙƙin mahaifiyata a kan ki Sadiya, kin je? Ba daina zuwa duba ta kika yi ba amma kullum anan gida na ke barin ki kwance amma saboda ba ki da kunya har kina tara ta da wata mganar banza saboda kin ga na yi miki shuru? To ki fita daga idanuwana ki kuma fita daga abin da ya shafe ni da matata babu ruwanki, kamar yadda kema kika ce na daina saka ki a lamarinta tun a baya to kema babu ruwanki da sha'aninta ko wani abu dake tsakanina da ita. Ni ne na ijiye ki, da ni za ki yi ba ita ba." Ko kafin ya gama mganganunsa na durƙushe a ƙasa ina kuka mai sauti lalle duniya juyi juyi wai ni yau Yallaɓai ke faɗa ma ba ni da alheri a zuciyata. Ina kuka na ɗago ina kallon shi hawaye wani na koran wani cikin shaƙewar murya na nuna kaina ina faɗin" Ni ka ke faɗa ma ba ni da alheri a cikin zuciyata Yusuf? Ni Sadiya? "E ke kika ja. Me ya sa zuciyarki ba ta ba ki damar ganin alherin mutanen da ke tare da ke? Kishi hauka ne Sadiya? Ya sake taso min babu nadama ma a cikin maganganun sa sai kawai na sake fashewa da kuka wani abu mai ɗaci na sukan zuciyata. kawai sai gani na na yi na miƙe ina faɗin" Yau ni kake yi ma gorin ban kula da Nene ba Yusuf? Ni kake yi ma gori? Sai ya yi shuru bai yi magana ba sai kawai na yi murmishin takaici ga hawaye wasu na korar wasu, sai kawai na kaɗa kaina kafin na ce" Zan faɗa ba domin ina so ka yarda da ni ba. Tunda Nene ta kwanta asibiti har ta dawo gida ban taɓa fashi ba, ko ban je na kwana da ita a yanzu a baya in ka manta na yi ƙila sama da abin da ka ke jijiyan wuya matarka ta yi. Mganar ban je Gwammaja ba ranar kuma ba ni da lafiya ne kwanciyar da ka ga ina yi ba ta lafiya ba ce, kuma na yi ta kiran wayar ka na faɗa ban samu ba ne, shi ne ka ke tunanin da gangan na ƙi zuwa? Kai iya naka zuciyar alherin kenan Yusuf? Na faɗa ina kallon shi, ina kuka saboda zuciyata ma zafi ta ke yi min ina numfashi sama sama kamar mai ciwon Asthama." "Wa kika faɗa ma ba ki da lafiya! Kin faɗa min? Ko ina da Allah musuru ne da zan san ba ki da lafiya.? Ya faɗa ya na kallona amma ya ɗan sassauta muryan shi. Kawai sai na kalle shi, sai ji na yi kamar juwwa za ta kwashe ni sai kawai na taka na fice daga ɗakin ina ji kuka na taso min daga ƙasan raina falon yara na koma na zauna na ci kukana kamar zan shiɗe, na tabbata in na cigaba da kuka nan zafin da zuciyata ta ke yi za ta iya bugawa na mutu Yusuf ba shi da asara. Ni wai yau Yallaɓai ya kalli tsabar idona ya na faɗa min Gimbiya ta yi masa komai wato ni kuma ban yi masa ba kenan ya manta tarin alherina a gareshi yau ni ce na zama mara zuciyar alheri, ina hawaye ina tuna baya, akwai wani lokaci a baya lokacin na haifi Jidda Nene ta yi wani ciwon kafafu mai zafin da ko bayi sai an kaita ni na koma Gwammaja da ga ni har Yusuf muna kwana acan ina kula da ita. Lokacin Mimisco ba su kasar ita da mijinta Anty Bahijja da Anty Maimuna kowacce na da iyalanta Halima ce lokacin kuma ta na makaranta ni ce na zauna da Nene har ta samu lafiya sannan na koma gidana a lokacin Yallaɓai ya ce na gama masa komai a duniya shi ne yau zai manta baya ya kalli tsabar idona yana faɗin Gimbiya ce ta yi masa komai ni kuma ban yi masa ba tunda zuciya ta ba alheri a cikinta, anan na kwana a falo a kan kujera ina kuka kukan baƙin ciki da takaici dare kuma mafi tsawo a wajena, ya ce wai daga na ce ya yi min kaza sai na ce ƴan'uwan sa sun yi min kaza ban da namiji mai manta alheri ni me na ce sun yi min? Ya manta yadda a baya na bauta musu na yi musu biyayya, amma yau duk ya manta sannan ya ce ni na tsani matarsa yaushe na ce na tsane ta? Kawai dai laifin nawa ne ya yi masa ƙaranci shi ya sa daga ya ce na yi kaza sai ya ce na yi kaza amma na kudira a cikin zuciya zan kiyaye ma komai na Yallaɓai yau ko korata ya yi a gidan shi ba zan buɗe baki na ce masa don me ba! Tunda ya iya kirana mara alheri na tabbata a gaba zai iya aikata komai. Har gabda asuba idona biyu sai a lokacin na samu barci sai sa na ji Jidda na tashina har sun yi salla, na tashi da karfin zuciyata amma idanuwana har sun kumbura saboda kuka. Tiolet din su na shiga na kama ruwa, sannan na zo muka yi azkar tare na shiga kitchen na ɗora musu abin breakfast ko ɗakin ban fatan komawa Yallaɓan ne ba na son gani saboda gabaɗaya baƙin sa na ke gani a cikin zuciyata shi ya sa ko hanyar ɗakin ma ban sake bi ba, a kan dining na jera masa abin karinsa na shige ɗakin su Jidda acan na yi wanka Allah ya sa na leƙa Yallaɓai ya shiga tiolet sai na lallaɓa na dauko kayana da abubuwan amfanina na fice na barsa ma ɗakin. Yadda na ɗau gaba dashi haka shima ya ɗau gaba da ni. Tun daga ranar ban ƙara kwana a ɗakin ba a ɗayan ɗakin na ke kwana, kuma kafin ya dawo mun shige ciki ban son na kwana da yara su fahimci wani abu, in kuma da safe ne kafin ya fito na gama masa komai na ijiye masa na koma cikin ɗaki. Wani lokacin ya ci wani lokacin kuma ya bar min kayana, ni kuma ban damu ba domin duk abin da Yallaɓai zai yi min ko zai ƙara min ba zai ba ni mamaki ba. Ranar junma'a Musbahu ya kawo min cefane duk da bai faɗamin ba a raina na ce ƙila Gimbiya za ta koma ne illau ko da yamma ya zo gidan ina jin shigowarsa na shige ciki sai can na ji tafiyarsa sai ga Jidda ta shigo ta kawo min man shanu da kuɗi 10k sannan ya ce a faɗa min Gimbiya ta koma gidanta ƙala ban ce ba na karɓi kuɗin na ijiye man shanun kuma na kai kitchen na ɗora tukunya na soya shi, a daran nan sai ga Ya Aina ta zo duba ni  Baban Marwa ya kawo ta ai na ce na ji sauƙi nan na roƙa na ce Marwa ta zo ta min weekend don Allah, baban ta ya ce ai Marwa ƴa ta ce umarni kawai zan ba da sai a faɗa mata sun ɗan jima kafin su tafi kuma na ji daɗi ɗan'uwana mai daɗi, a da ji na nake yi kamar a cikin kurkuku duk in da na yi tunanin zuwa sai na ga ba zan iya tambayan shi ba gwara na haƙura in ma shekara za mu yi a haka sai dai a yi. Washegari asabar su Jidda sun tafi Tahfez a ranar aka kawo min Hijabai daga zariya Musbahu daman ke karɓan min a nan Zaria road motar in ta shigo cikin gari sai ta tsaya nan ya karɓa min, shi ya kawo min har ya na ce min na ijiye masa guda biyu ni kuma na tasa shi da tsiyan ko ya samo mata ne. "Sai Yallaɓan ki ya sallame ni tukunna ko zan ɗauko maganar aure." Ina dariya na ce" Haba tun yaushe ya sallame me ka." "To ina ga ko Sabon Office ɗin nan na ƙasa in da muke na wa ne? Cikin zolaya ya faɗa, ni da ya ke ban ma san da shi ba amma ban nuna ba sai na ce ƙila na ka ɗin ne, mun yi ta hira har muka gangaro maganar gidan Bulo ya na faɗa min an fi wata biyu ba a aiki, Yallabai duk ya bari wajen na neman mutuwa. "Anty Sadiya ki yi masa mgana don Allah kar ya bari wajen ya mutu. Tun da ya na jin maganar ki." A raina na ce a da kenan, yanzu kam sai dai Gimbiya. Amma ban nuna masa ba sai kawai na ce zan masa mgana. Tuni na manta da takaicin Yallaɓai, na fara kiran mutane ina faɗa musu an kawo hijabai su siya na salla tunda babbar salla ke kusanto mu. Har Ma'u na kira na yi mata tallah sai ce min ta yi ai ta ji labarin ina sai da Hijabai ban yi mata tallah ba ne ya sa ba ta siya ba amma tunda yanzu na yi mata talla za ta zo gida ta duba ni dai a raina na ce kya ji da shi munafuka Ya Muntari ma na yi masa talla na ce ya siya ma Rahila da yara. Har Nasir da Mutaƙƙa sai da na ce su siya ma matan su da yara. Kuma duk sun ce matan za su zo gida su duba. Ranar dai ban yinin kunci ba cikin walwala na yini ranar Yallaɓai bai zo gidan ba sai can dare na ga saƙon shi saboda haushi na goge shi ma. "Ya kuke? Fatan kuna lafiya" Na gani amma sai na goge na kama harkan gaba na. Washegari Lahadi sai ga Kawu Abba ya zo ya ma ɗauka Yallaɓai na gidan ne na ce masa ba nan ya kwana ba ya na gidan Amarya shi kuma ya ce ya na ta kiran wayarsa ba ya samu ya shigo garin ne kuma ya na so su haɗu. A gidan ya karya ni na haɗo masa abin karyawa, muna ta hira da shi, kuma har lokacin bai samu wayar Yallaɓai ba sai daga baya ya ce ni na jara ba kiran shi a wayata mana ko zan same shi. "Ka yi haƙuri Kawu ka cigaba dai da gwadawa in baka same shi ba sai ka je gidan mana." Na faɗa ina kallon shi, sai kawai ya tsaya ya na kallona kafin ya ce" Me ya faru ne Sadiya? Tafida ya yi miki wani abu ne? Idanuwana suka cika da kwalla na yi saurin basarwa. "Bakomai." "A'a da komai fa." Ya faɗa ya na kallona lokaci ɗaya kuma ya na nazartan yanayina. *Janafty* *TKG* FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622 13. Kaina na mayar ƙasa ina wasa da gefen hijabina. Sai na sake ɗagowa ina kallon shi jin ya yi shuru sai muka haɗa ido dashi da sauri na ƙara sadda kaina ƙasa domin har ƙwalla sun cika min ƙwarmin idanuwana tuna irin cin mutumcin da Yallaɓai ya yi min. "Me ya faru? Ya sake tambayata sai na yi saurin shanye kukan da ke taso min har ina yin mirmishi wanda na aro shi na yafa a saman fuskata duk domin na kauda ma Kawu tunanin cewa wani abu ya faru. Sai dai kash ya riga ya fahimta sai dai na basar kawai. "Allah ba komai Kawu." Na faɗa ina masa mirmishi sai kawai ya gyara zama kafin ya ce" Na ji kin ce dai bakomai amma ban yarda ba komai ɗin ba Sadiya." Ina kallon shi na buɗe baki zan yi magana sai ya dakatar dani da hannu lokaci ɗaya ya kira sunana. "Sadiya." "Na'am." Kai tsaye ya kalleni kafin ya cigaba da faɗin" Kin san dai ni san ba zan taɓa yarda wani abu bai faru ba ko? To gwara ki yi shuru a tafi a wani abu ya faru ni ba zan matsa miki sai kin faɗa min ba amma kuma ba shi zai hana na ƙi baki haƙuri ba" Sai na kalleshi amma ban yi magana ba, ni ko a gida kowa ya sanni ba ni da daɓi'ar kai ƙaran miji duk abin da ya yi min a cikin gida za  mu yi ta ƙare shi ya sa a yanzu na ke jin nauyin furta cewa Yallaɓai ya yi min kaza, kamar yadda ya ce ne ina mgana tuni za a ce zafin kishi ne ya sa na ƙi kwantar da hankalina shi ya ma faɗa da bakin shi ballatana wani daga waje. "Sadiya." Ya katse min tunani sai na ɗago ina kallon shi. "Ki yi haƙuri." Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Bakomai Kawu." "Ban san me Tafida ya yi miki ba. Amma dai koma mene ne don Allah karki riƙe shi a cikin zuciyarki. Ba wai ina kare shi domin ya na nawa ba. Kema tawa ce wallahi. Sai dai ba shi zai hana na faɗa miki wata gaskiya ba." Na ɗago ina kallon shi, ba tare da na yi magana ba.. "Sadiya Tafida ya na sonki. Kuma duk macen da zai aura ko anan gaba sai dai su biyo bayan ki. Haƙuri za ki ƙara saboda kin san mu maza in muka ƙaro aure sai wasu canji canje su yi ta faruwa haka Allah ya hallicemu mu Maza wani lokacin muna da son kai da Matan alheri. Ki yi haƙuri ki yi masa uzuri na tabbatar miki da cewa ke ce giwar mata a wajen sa." Ina kallonsa ne amma ni kalamansa ba su wani kama zuciyata ba, shi kuma ganin kamar ban yarda da shi ba ya sa ya jinjina min kai. Sai kawai na yi mirmishin takaici kafin na ce" A da kenan amma yanzu Gimbiya ta sha gaba na." "Ba ta sha gaban ki ba Sadiya. Ai ke ba macen da ta isa ta sha gaban ki a wajen Tafida Allah."   Mirmishin na sake yi ba tare da na ƙara mgana ba. Ni kaɗai na san yanayin da na ke ji a cikin zuciyata kawai dai ina dannewa ne. "Ina da dalilina masu ƙarfi da ya sa na faɗi haka. Ba wai kuma don ki ji daɗi ba sai zallar gaskiya. Tafida fa kin san tare muka tashi dashi akwai wasu abubuwan da a mu'amala ne muka karanci juna ba ta hallaya ba. Ki amince da cewa ke Giwar mata ce a wajensa. Ki sani ke auran saurayi da budurwa kuka yi Tafida ya fara sonki tun zuciyarsa na da danƙo ya zauna dake zaman aure na shekaru zuciyarsa na buɗewa a kanki. Ki sani soyayyar da ya ke yi miki ba ya yi ma Amaryansa da ya aura. Bar ganin wai ko sun daɗe tare. Ba zan ce miki ba shaƙuwa tsakaninsu ba akwai amma ba so ba ne, ba kuma zan ce miki yanzu da suke zaman aure zuciyarsa ba za ta ribace shi za ta ja shi zuwa gare ta ba Amma ki sani ko ta ja shi ba za ta iya zurfin kai shi ta ki mazaunin ba. Shi ya sa na ce ki yi haƙuri ki yi masa uzuri wataƙila halin ɗan adam ne na ajizan ci kuma daman shi zaman aure zo mu saɓa ne kuma zo mu sulhunta." "Haka ne" Na faɗa ina jinjina masa kai. "To kin gani. Ki ƙara hakuri. Amma fa ba shi zai hana in ya yi miki ba dai dai a ci ubansa ba." Sai da na yi dariya shima dariyan ya yi kafin ya ce" E mana ai ba wu ce duka ba." Ya na mgana ya na danna wayarsa sai ya kalleni kafin ya ce" Kin ga sai yanzu na samu wayar ta shi." A speaker ya saka kiran har sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka murya a shaƙe daga ji barci ma ya ke yi. "Ya a ka yi ne." "Ban sani ba. Mallam watssake." "Me ya faru ne? "Ga ni a gidan ka." Cikin muryan barci Yusuf ya ce" Wani gidan kenan? "Wanda na fi sani." Kawu ya bashi amsa lokaci ɗaya. "Gidan Sadiya.? Kafim ma ya bashi amsa ya yi saurin cewa"Ka ƙariso nan mana ina nan ni." "In ƙariso ina? "Gidan Daughter mana. Daman ba ka taɓa zuwa ka ga gidan Amarya ba." "Wacece kuma wata Daughter." Sai da ya yi shuru kafin ya ce" To Saudatu." Tsaki kawu ya ja kafin ya ce" Tafida kana da sanabe wallahi. To ba zan ƙariso ba in za ka zo ina jiran ka kazo in kuma ba ka zo ba sai ka faɗa min na kama gaba na." "Kawu." "Na'am Tafida" "Gani nan zuwa." Daga haka shi daga can bangaren ya katse kiran duk ina zaune in jin su, Kawu sai masifa ya ke ya na faɗin" Wai ka auri mace amma kana kiran ta da wata ɗiyar ka? Tafida ba shi da hankali fa, kai suna ba na uwarka ba na ƙanwar uwarka ba." Ni dai ina ta dariya, mun ɗan cigaba da hira sama sama har ya ke faɗa min ya zo duba wani fili ne a nan cikin gari. "Ko dai auren ya tashi ne Kawu za a yi ma Amarya ginin gida." Na faɗa ina masa dariya da sigan zolaya. "Ko Aure na yi ai ban iya barin Rano Sadiya can a ka haife ni a can kuma nima zan gina nawa Ahalin in sha Allahu. Kawai dai ina siyan filaye ne anan cikin gari saboda Ajiya ne in ka bar kuɗin kuma za ka ksshe su ne a banza." Na ce haka ne, shi da kanshi ya ke faɗa min ya siya filaye anan garin huɗu kenan kuma takardun ma ai suna hannun Tafida na yi ta jinjina kai ina mamaki lalle Kawu Abba ya tara ko na ce ya na kan tarawa. "Kawu Allah ya sa ka samo mana mata wannan shekaran mu gwangwaje." Ya na mirmishi ya kalleni kafin ya ce" Amin Sadiya. In sha Allahu nima ba na so na wuce wannan shekaran addu'a za ki yi min Allah ya ba ni tagari matan ne na wannan zamanin duk sun zama sai a hankali." "Allah zai kawo ta gari in sha Allahu." Ya amsa da Amin kafin ya ce" Na ga ma wata iri a gidan ki kwanaki ina ta so na yi miki mgana ayyuka suka sha kaina.' Cikin mamaki na ce" Iri? Wani iri!? Sai ya kwashe da dariya kafin ya ba ni amsa an kira wayarsa sai kawai na tattara kwanukan da ya karya na fice na bar shi a falon ya na waya. Ina kitchen ina ta mamakin to wacece Kawu ya gani? Ko Saude ce? Wata zuciyar ta kira min sunan ta, sai kuma na tuna ai ya san Saude tunda ya na yawan zuwa gidana kuma ya na ganinta duk a iya tunanina na kasa gane wani iri ne wannan ya gani a gida kuma har ya yaba. A cikin raina ina fatan Allah ya sa ta gida ce, ina ganin mutumcin Kawu Abba ba domin ya na kawun Tafida ba sai domin ya na da kyakyawan halin da duk macen da ta  same shi ta more. Ban zauna ba na fara gyaran Kitchen domin Saude ma sai ta dawo daga allo za ta zo ni kuma ba na so na zauna in na zauna zai yi wahala na sake tashi, ina aikina gefe ɗaya kuma na haɗa tea ina kurɓa ko zuwan Yallaɓai ban ji ba, sai jin muryansa na yi a saman kaina lokaci ɗaya. "Madam ina kwana." Sai na juya na yi masa kallo ɗaya na ɗauke kaina na daɗe ban gan shi ba tun daren ranar da muka yi faɗa da shi. "Ina kwana." . Na mayar masa da gaisuwan shi kamar ba na so, na kuma cigaba da aikina na ma manta da wanzuwar shi a wajen ya gaji da tsayuwa ya ga ko kallo bai isheni ba sai shi ne da kan shi ya gaji ya ce." Madam ko zan samu shayin nan na mganin mura? Mura ta kamani tun jiya." Ya faɗa ya na jan hanci ko juyowa ban yi ba na ce" Za a kawo." Daga haka na isa gaban gas na kunna ina ɗora ƙaramar tukunya gajiya ya yi da tsayuwa ya kama gaban shi, ni kuma na raka shi da tsaki ni yanzu Yallaɓai ya fita kaina tunda ya gama ba ni mamaki ya yi min abin da ban taɓa tunani ba ko da ya ba ni haƙuri zai yi wahala na manta kalaman shi a kaina.   Ina cikin dafa masa shayin ne sai ga Marwa na kalleta ina faɗin" Sannu sai yau? Tun jiya ina ta jiran ki. Baban ki fa ya ce Umarni kawai zan ba da za ki zo " Tana dariya ta ce" Umma jiya aikin dare na yi sai yau da safe na dawo gida." "To kin ja ma kanki ba yau za ki tafi ba." "Daman sai gobe." Kallonta na yi kafin na ce" Sai dai jibi ko? "Umma jibi ina da aikin Safe ne." "Sai ki tafi daga nan ɗin ko? Sai ta yi shuru ta na dariya ni kuma ina hararanta. Kafin ta cire Hijabin da ta shigo da shi na ce tsaya na ta ce shayin nan ta miƙa ma Yallaɓai da ta wuto su a falo, ita na ba ma shayin ta kai masa sai ga shi ta dawo ta na ce min" Umma ɗayan baƙon fa ya ce shi ina na shi Shayin? Ina dariya na ce ta juye sauran a fulas ƙarami ta ɗau Mug ta kai musu falon daman akwai siga a can saman dining za su yi amfani da shi. Zuwan Marwa ya sa na koma na zauna ta karɓe ni daga aiki ina falo ina duba wayata ana ta siyan Hijabai tun da salla ta karato bai fi saura kwana goma ya rage ba, ina nan zaune Yallaɓai ya leƙo ya na cewa na zo mu yi sallama Kawu zai tafi, sai na rarumi Hijabin Marwa na zura tunda nawa na kai sa cikin ɗaki. Na ɗauka ma har ya miƙe ne sai kuma na je na gan shi zaune suna hira da Yallaɓai ina daga tsayen na ce" Kawu har an gama yi mana yinin? Ya na dariya ya ce" Taho ki zauna ai ban ga ta tafiya ba tun da ban yaɗa munafata ba." Cikin mamaki na zagayo na zauna kujeran zaman mutun ɗaya. Kawu na ke kallo duk da ina ganin mutumin nawa na ta kallona ni kuma sai na ba ma banza Ajiyar a cikin raina ma sai na ɗauka kamar bashi a wajen ba dai ni zai wulaƙanta ba wallahi sai ya ga ne bashi da wayau da ni ya ke zencen ba ya ce Gimbiya ta yi masa komai ba to zan bar shi da ita ta yi masa abin da ma ni ban taɓa yi masa ba. "Kawu me ya faru? Na faɗa ina kallon shi, wani lokacin in ce masa Uncle wani lokacin kuma Kawu. Amma dai Uncle ɗin ya fi kama bakina. "Ba nan muka fara magana na ce miki na ga wani iri a gidan nan ba? Da sauri na gyaɗa masa kai kawai sai ya cigaba da faɗin" Ga irin nan muna zaune a falon nan ta shigo. Ita ce wacce ki ka aiko ta kawo mana shayi." Ido na zaro ina kallon shi kafin na yi magana Yallaɓai ya tare ni. "Wai Marwa? Ya faɗa ya na kallon shi, shi ma kallon na shi ya yi kafin ya ce" Ina ruwanka? Da kai na ke magana." "Allah ya baka haƙuri." Yallaɓai ya faɗa ya na ɗauko wayarsa daga cikin aljuhu ya yi kamar hankalinsa na kan wayar amma ni na san hankalin shi na kanmu ne. "Sunan ta Marwa ne? Kawu ya tambayeni ya na kallona cikin mamaki da ya kasa ɓoyuwa a saman fuskata na gyaɗa masa kai kafin na ce" Sunan ta Marwa." "Ya kuke da ita? Ina mirmishi na ce" Ɗiya ta ce. Ɗiyar yayarmu ce Ya Aina uban mu ɗaya da mahaifiyarta." Sai kawai ya koma ya ɗora kafa kan ɗaya kafin ya ce" Alhamdulillah." Ina dariya amma ban yi magana ba amma ni kaina lamarin ya zo min a bazata Marwa fa? Yanzu duk ƴan matan duniya Kawu Marwa ya gani kuma ya yaba ikon Allah. "Wato haƙiƙa tun ranar bikin tariyan wannan yaron na ganta lokacin ta kawo mana abinci na yaba da natsuwarta to na ɗauka lamarin wasa ne shi ya sa ban yi magana ba. Sai kuma da na koma gida ina ta tunaninta ta na yawan faɗo min a cikin tunanina na so ma na kira ki a waya sai sabgogi suka sha kaina sai yanzu da na ƙara ganin ta sai na ji zuciyata ta ƙara yin wani nauyi a kanta." "Uncle.." Na faɗa ina ta dariya ina jin wani farinciki a ƙasan raina ba ni kaɗai ba hatta Yallaɓai fuskar shi ta cika da Annuri domin ni dai yau ce rana ta farko da Kawu ya zauna ya taɓa yabon wata mace duk wacce aka yi masa tayin ta sai ya kushe ta. Amma wai Marwa ce ta yi masa ikon Allah ya fi gaban wasa. "Kawu ka ce kawai ka faɗa tarkon so." DaKafarsa ya zungure shi  ya na faɗin" Wai ba na ce ba ruwanka ba! Ina mgana da surukata kar ka ƙara saka min baki malam." Yallaɓai na danne dariyan shi ya ce" Kawu" " Ka sake kiran sunana zan iya yi maka baki." Ya faɗa ya na hararan shi kafin ma ya ce" Kai tashi ma ka fita" "Allah ya huci zuciyar ka." Sai ya yi kyaci sannan ya dawo da hankalin shi kaina ya na gyara zama. "Kamar dai ina son ta ne fa." Ni kaina na kasa danne dariya ta sai da na sake ta jin kalaman Kawu har ya na wani gyaran murya, Yallabai ko har ya na duƙewa Kawu ya kai masa naushi sai ya kauce ya tashi ya sauya kujeran zama, sai ya koma ya na kallona kafin ya ce" Surukata dariya kuma kike yi? Ina danne dariya ta na ce" Na isa Kawu. Yanzu dai ya kake so a yi? Sai ya yi shuru kafin ya ce" To za ku iya aura mata tsoho kamar ni? Kai na gyaɗa kafin na ce" Me zai hana in dai ta na son ka? "To kina ganin za ta so ni? Kalle ni fa ba ma arba'in baya." "Me zai hana ta soka Kawu? Ai kawai nema za ka shiga yi har sai ciyo mana yaƙin a cikin zuciyarta." "Ko? Kina ganin zan iya? Ina mirmishi na ce" In sha Allah za ka yi." "To kina ganin in ta aminta da ni za ta iya zama a Rano.? "Me zai hana Kawu? A ko'ina aure ya kaita ai za ta zauna in sha Allahu." Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Haka ne. Shekaranta nawa ne? "Ashirin da uku." "Ta na makaranta ne? "E. Ta na makaranta koyon aikin jinya a garin tsafe amma yanzu ta dawo gida ne ta na pratical." "Ta kusa gamawa? Ji na ke yi kamar ba zan iya jiran wani dogon lokaci ba." Ina dariya na ce" Ina jin ta kusa gamawa gaskiya." Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Sadiya da gaske ina son ɗiyar ki tun ranar farko da na fara ganinta ban ƙara tabbatarwa ba sai yau da na ganta. Allah ya sa ku ba ni ita." "In sha Allahu za mu baka ita in rabon ka ne Kawu" Ina danne dariyata ganin duk ya susuce Yallaɓai ya kalla da ya kasaƙe da waya a hannun shi ya na jin mu. "Kai wai ba ka so ka yi albarka ne? "Me na yi kuma? Ya faɗa ya na danne dariya Kawu Abba ya jinjina kai kafin ya ce" Ka ce wani abu mana. Ko fatan alheri ba za ka iya yi min ba Tafida? Hannuwana ya ɗaga sama kafin ya ce" In ce me? Ni da ka ce ba ruwana in na ƙara saka maka baki a cikin maganar ka za ka yi min baki? "To na janye kalamaina saka bakin ka na ji." "Me zan ce? Sai kawai ya tsaya ya na kallon shi, shi kuma ya na dariya kafin ya ce" Allah ya ba da sa'a Kawu na." "Amin to in ma ba har zucci ba ne." Ni dai ina gefe ina ta faman mirmishi zuciyata kamar farar takarda. Kawai sai wayar Kawu ta fara ƙara alamun ana kira ya na duba sunan mai kiran ya kalleni sannan ya Kalli Yallaɓai kafin ya ce" Gaskiya Tafida ka cika tsurku" "Me na yi? "Me ka faɗa ma Tariq ya ke kirana? "Ni? Me na faɗa masa kuwa? Ya dai ji kana faɗa da bakin ka" "Au recording ka yi ka tura masa munafuki da matan ka biyu kana gulma? "Wani recording? Direct ya ji Soyayya ya fara zautaa ka." Kawu sai kawai ya tsaya ya na kallon shi har wayar ta katse bai ɗauka ba shi kuma Yallaɓai na yi masa dariya. "Ɗauki wayarka fatan alheri zai yi maka fa. Ko ba ka so? "Ina so mana. Ko da bai kai zuciyar ku ba." Ya faɗa lokaci ɗaya ya na ɗaga wayar amma ya sa ka a speaker. "Kawu ina kwana." Tariq ya faɗa daga can bangaren Kawu ya haɗe rai kamar ya na ganin shi kafin ya ce" kirani Abba na  ko Abdulmu'iz domin ni ba Kawun ka ba ne." Kaina na ƙasa ina danne dariya Yallaɓai ko har ya na ba ta sauti saboda dariya. "Mu ba ƴan'uwan juna ba ne? "Ni ban haɗa komai da kai ba Mallam." "To na ji ina yi ma Tafida kara ne." "Shima ai ni ƙanin uwarsa ne ba na Ubansa ba." Yallaɓai dariya har ya na ƙyaƙyawata ya na kallona da mun haɗa ido sai na haɗe rai na juyar da fuska. "Haka ne. To a bar mganar." "Yauwa yi fatan alherin ka ina mgana da Surukata ne ka katse ni." "Kawu ashe kuma an faɗa tarkon so? Ƴar yarinya ta susuta haka? "E ko ban kai ta susutanin ba ne? "Ni? Ban ce ba haba ai ka isa ma har ka gota. Kawu Allah Ubangiji ya sanya alheri ya sa a wannan shekaran za mu sallama ka." "To Amin." Ya faɗa ya na ɗan mirmishi kafin Tariq ya cigaba da faɗin" Mutumina kawai Tafida na kirana ina ɗauka ba sai na ji kana ruwan haruffan ƙauna ba. Wai wata yarinya ce ta susuta ka haka! Na san ta kuwa? "Ba ka san ta ba." "Tafida." Tariq ya ɗaga murya ya na kiran Yallaɓai shima ya amsa ya na faɗin" Ɗan'uwa nawa ka tara? Kasan mun yi alƙwarin biyan sadaki da kuɗin gaisuwa fa? Tariq ya ce" Ai asusu na yi. Shekaru sama da goma. Ka ce lokacin fasa asusu ya kama mu." "Tabbas. Domin da gaggawa ya ke so da wahala ma ya iya jira." "Allah. Ka ce Kawu dai ya faɗa da yawa." "Ba ma a mgana sai ma ka gan shi duk ya susuce." "Yo min Video ɗin shi mana." Kawu sai kawai ya kashe wayarsa Yallaɓai ya kalle shi ya na faɗin" Ya haka? Me ya sa ka kashe? "Ba ka da waya ne? Ya kira ka ta wayar ka. Ni ka ganni nan ba ni da lokaci ɓatawa a kan ku. Yauwa surukata yanzu ya za a yi ne? Kin ji dai matsaya ta." Ina mirmishi na ce" Na ji Kawu yanzu ya kake so a yi? Yadda kace haka za a yi." Sai ya yi shuru kamar ya na nazari ni kuma sai na ce" To ko zan kira ta ne sai mu ba ku waje? Da sauri ya ce" A'a sai na yi mgana da magabanta ta zan fara mgana da ita. Sai na jinjina kai kafin ya cigaba da faɗin" Za mu yi waya dai in na koma in sha Allahu." Ina mirmishi na ce" Allah ya sa. Kar ka ji komai Kawu kana da ni. Kuma Marwa yarinyar kirki ce ga natsuwa ba ina yabon ta ba ne fa." "Haba na sani. Ai na ga abubuwa da dama a tattare da ita." Ya faɗa ya na shafa sajen sa, Yallabai na gefe bai saka mana baki ba amma ya na sauraran mu. Tallar hijabai na yi masa sai ya ce" Hijabai kika fara saidawa kuma? Sai na gyaɗa masa Zaraf Yallaɓai ya ce" Ko za ka siya ma Marwatu ne? Hararansa ya juya ya yi kafin ya ce" Ina ruwanka? Ba hijabai ba, ka san dai ko kasuwar Hijaban ne zan iya siya mata  ita gabaɗaya ba ko? "Tabbas ko mai garin Rano Allah ya ja da zamanin ka." "To ka yi shuru. Ka jira lokaci kawai." "Allah ya nuna mana lokacin." Har da nima na amsa da Amin ɗin, cewa ya yi na ijiye masa guda goma na yayyensa da ƙannensa duk zai siya musu har da Innayi. Yallaɓai na gefe ya ce" Nene ta gode." "In kai uwarka ce ni yayata ce." Sai Yallaɓai ya koma kawai ya yi shuru ya na danne dariyan shi, nan ta ke na faɗa masa kuɗin ya saka min ya ce na ijiye masa in zai wuce zai dawo ya ɗauka ina ta masa godiya ya ce. "Haba bakomai an zama ɗaya.  Kin fara saidawa Hijaban ne ina shagon Saloon ɗin? Sai na yi shuru ban yi magana ba sai ya juya ya na kallon Yallaɓai kafin ya ce" Kai ya maganar shagon da ka ce min ka kama mata ƙasan offishin ka? Sai na ɗago ina kallon shi domin ni ban ma san da labarin ba. "Na saka Musbahu a ciki sannan ai na faɗa maka na ɗauki wani yaro Auwalu. Su na gyara ma ƙasa ni kuma ina sama saboda ina so na faɗaɗa kamfanina in sha Allahu." "Allah ya ba da sa'a. Ita kuma fa? "Zan buɗe mata in sha Allahu." Sai ya kalleni kafin ya koma ya na kallon shi lokaci ɗaya ya na faɗin" Mallam ba wani in sha Allahu. Tun yaushe ka ke alƙwari ba ka cika ba? Na san fa ba rashin kuɗi ba ne, Mallam ka samu kuɗi ka san na sani ko? Yallaɓai ba ya son kallona kai ya kauda kafin ya ce" Ba ni na yi alƙwari ba? To zan cika in sha Allahu." "Better domin yanzu ina bayan ta ne. Ba zan lamunci ka danne mata haƙƙi ba tsab za  ka iya ji sammaci daga hukumar kare haƙƙin ɗan adam." "Ba Shakka." Yallaɓai ya faɗa ya na kallon shi, shi kuma ya miƙe lokaci ɗaya ya na gyara zaman hulan kan shi kafin ya ce" E haka na ce. Sadiya ba ri mu je amma zan dawo kafin na wuce." Sai nima na miƙe ina musu fatan a dawo lafiya nan na bar su a falon suna ta halin su shi da Yallaɓai ni kuma na koma cikin gida saboda murna kamar na faɗa ma Marwa sai kuma na ce ba ri dai in yi shuru na jira ce shi kamar yadda ya ce kar na yi gaggawa amma ita kanta Marwa sai da ta ce Umma kina ta fara'a ina dariya na ce mata abin fara'an ne ya same ni. Ba su suka dawo ba sai bayan la'asar lokacin har Marwa ta gama shinkafa da miya da salak, ta kuma gyara gidan ya na ta kamshi, shi kuma Kawu tuni na haɗa masa Hijabansa waje ɗaya kololin daman ni ya ba ma zaɓi na zaɓar masu kyan ciki, ni kaina na ƙara ma na ni da yara har da Marwa na zuwa sallar idi. Bayan sun ci abinci tare da Yallaɓai ya ce zai wuce amma zai shiga Gwamnaja ya duba Nene tare suka sake fita da Yallaɓai ina jin su da na raka su Haraba Yallaɓai na faɗin ya kawo na Nene ya kai mata ya ce ai ya san hanyar gidan haka suka fita suna ta halin su da suka saba. Sai dare Yallaɓai ya dawo misalin tara da wani abu ashe ma a gidan ya ke ni na ma manta, ni dai ina ɗakin da yanzu ya zama wajen kwana na shi kuma bayan ya yi wanka Marwa daman na saka ta hada masa tea, a falon yara na ji su tare da su suna ta hira har na yi barci ban san lokacin da suka kwanta ba da safe Marwa ce ta yi hidiman gidan da yara har da shi kan shi Yallaɓai domin ina ciki na kulle ƙofa ko ma ya zo ba zai tarar da shi a bude ba sai da ya bar gidan sannan na fito. Haka a daran ma lokacin da ya dawo na shige ciki Marwa kawai ya gani da yara. Tun ya na ɗaukan lamarin wasa har dai ya fahimci na riga na hau dogin zuciya har ya bar gidan ya koma can ni ba na mgana da shi, ban ma yarda mun haɗu ba saboda ba na so ma na gaishe shi, Marwa ta koma gida ni kuma ina ta zaman jiran Kawu amma shuru sai dai na yi ta saka ma abin albarka na yi addu'an in da alheri Allah ya tabbatar tun da na gama al'adata har na yi wankan tsarki tun jiya. Hijabai sun ƙare na ci kasuwar salla,  na yi magana za a kawo min wasu amma sai bayan salla har Ma'u ta aiko Zainab ta karban musu guda biyar, har Baaba ta siya mawa kuma Alhamdulillah ina samu sosai ɗan riban da ba za ka raina ba. Har Yallaɓai ya sake dawowa gidana ba na masa mgana. Rana ta farko bai neme ni ba sai ana biyu shima na son saboda matsowan sallah ne, ina ɗakin da na mai da shi nawa da daddare Jidda ta shigo ta ce wai Abban su na kirana a falon shi, kamar na yi fuska na ƙi zuwa sai na fasa na tashi na saka mayafi na fita falin na same shi zaune ya na kallo amma ga wasu manyan lodoji a gabansa kamar na wani tambarin kamfani amma ban tsaya na duba ba. Sannu da zuwa na yi masa ya amsa yana kallona ni kuma sai na kauda kaina a tsaye na tsaya ban ko da niyar zama. "Madam ki zauna mana." In dai Yallaɓai ya san ya tafka rashin kirki ya iya kame kame, in ka ji ya na cewa Madam ya cuce ni ne zai yi min ƴar murya. Kamar ba zan zauna ba sai dai na dofana ɗuwawuna a saman kujeran da ke gefensa. Shuru na wani lokaci ya kasa mgana kunya duk ta kama shi. "Har na fara barci Jidda ta taso ni." Na faɗa ina kallon shi fuskata ba Annuri sai ya nuna min ledojin gaban shi kafin ya ce" Na ku ke da yara" Abin sai ya ba ni mamaki, amma ban yi magana ba na sunkunya na jawo ledojin ina dubawa na ga dai abaya guda biyu ta manya sai na yara sai takalma sai kuma pakiatan na yara na su Jidda kenan sai reborn da man kitso da ɗan kunnaye. Ban tambayi daga ina ba kawai na maida su leda ina faɗin" Mun gode Allah ya sa albarka." "Amin. Rigunan da takalman ni na siya muku Daughter ta yi oder din su daga Epgyt sai na ga sun yi mini kyau sai na ce a cire muku sauran kuma ita ta ce na kawo ma su Jidda su yi kwalliyan sallah." "Allah ya saka da alheri." Na faɗa kai tsaye sannan kuma na mike nan na bar masa kayan zan wuce sai ya kira sunana. "Sadiya." Sai na juya ina kallon shi, ni ya ke kallo kur kafin ya ce" Ki dawo ban gama mgana da ke ba." Sai na koma na zauna ina kallon gefe ina jin sa ya na mirmishi kafin ya ce" Uhm Halimatussadiya. Sadiya ta Yusuf shi kaɗai duk fushin ne ba a gama ba? Kamar ya na mgana da dutse ko motsi ban yi ba. "Ya mganar shirye shiryen salla? Me kika shirya ne? Sai na kalle shi kafin na ce" Shiri ai ya na hannun ka." "Ke fa? Ai  mun saba ke ce ke shirya komai." Kallonsa kawai na yi ban yi mgana ba da dai ya ga ba yi zan yi ba sai ya gyara zama ya na faɗin" Lokaci ya ƙure ku yi hakuri na so na ƙara muku kaya ko ɗaya ne." Ban ce masa komai ba sai ya cigaba da faɗin" Musbahu zai kawo cefane, sannan zan yi layya ke ma zan yi miki in sha Allahu." "Allah ya saka da alheri." "Amin My Sady." Ko kallon shi ban yi ba sai ma na ce" Ka gama mganar zan iya tafiya? Sai ya gyaɗa min kai na miƙe zan tafi ya sake kirana bayan na juyo sai ya ce" Ba ki ɗauki kayan ba to." Shi ya sa na koma na ɗauka na bar masa falon na kuma san ya bi ni da kallo, a ɗaki na je na zube kayan na yi kwanciyata da safe ma ranar shi ya kai yara makaranta suna ta murnan za a ba su hutun salla. Ban masa mgana ba na ga ya turamin kudi a acct ɗina sai ga kiran shi na ɗauka muka gaisa. "Na kitso ne da kunshi. Ke da yara." Nan ma na ce Allah ya saka da alheri. Ba shi ya faɗa mini Gimbiya za ta yi layya ba Musbahu ne da ya kawo mini cefanen kayan miya da naman miya ya ke faɗamin ita ma za ta yi layya sannan raguna uku Yallabai ya siya nawa da na shi sai zai yi ma Alhajinsu ita kuma Nene Mimisco ce za ta yi mata Ya Usman kuma zai yi ma Maman farko da Hajiya iya. Kuma za su yanka sa a cikin gidan gabaɗaya ragu nan ma suna can gidan. Yadda bai nemi na ji ba ni da ba ma mgana muke yi ban masa mgana ba. Mu ma gida Ya Hamza zai yi ma Alhajinmu da Gwaggo sannan Ya Auwal ma zai yi ma Mama da Baba Aminu, kuma sannan dukkansu a gida za su yi salla da iyalan su, wannan salla kuma ni ban yi komai ba cincin kaɗai na kira Saude da Marwa suka taya ni muka yi, ni ban yi kitso ba sai yara gyaran kai na je aka yi min a shagon Amesty. Amma mai lalle ana jibi salla  ta zo har gida ta yi mana ni da yara da Marwa tunda na ce a wajena za ta yi sallah Har ana jibi salla ba na ma Yallaɓai mgana amma ban fasa  sauƙe haƙkinsa dake kaina ba. Na aure ne dai kowa ya yi ta kanshi in ya na gidana ba na kwana a ɗakin mu sai bedroom ɗin baki, ranar dai a gidana ya ke sai gobe zai koma gidan Gimbiya. Yadda na watsar da shi ne na san ya dame shi, ranar da wuri ya dawo ya shammace ni ban rufe ƙofa ya shigo ɗakin kuma ga su Marwa ba su yi barci ba bana so na ɗaga murya ta. Ina zaune a gefen gado mun gama mgana da Amina kenan ya shigo ta na faɗa min itama ranar biyun salla ta na tafe. Sallamarsa kawai na amsa ban yi masa ko sannu da zuwa ba na maida kaina kan wayata. Zama ya yi a gefe na, ni kuma sai na yi saurin matsawa sai kawai ya kalleni kafin ya ce. "Sadiya wai gaba kike yi da mijin ki? Kai tsaye na ce" Ba na gaba dakai. Ko ina yi ne? Na faɗa ina tsare sa da idanuwana sai ya kasa mgana har ya na wani sauke ajiyar zuciya. "Ina yi maka mgana in mun haɗu. Kai ma in ka yi min magana ai ina amsawa." "Kina amsawa amma ba haka kika saba  ba Sadiya. Kina jin haushina tun faɗan da muka yi kwanaki ni kuma ya wuce awajena fa" "Nima ya wuce ai." "Bai wuce ba Sadiya." Sai na kalle shi amma ban yi magana ba. "Bai wuce ba. In da a ce ya wuce me ya sa kika raba mana ɗakin kwana? Ni na taɓa kaurace miki ne Sadiya? Me ya sa ni daga mgana za ki hau gaba da ni,kin daina kwana a kusa da ni, kin daina zama ki yi hira da ni kafin ma na dawo gidan kin shige ɗaki gabaɗaya kin watsar da ni tsakani ga Allah wannan shi ne kike cewa ya wuce? Sai na yi shuru ban yi magana amma kaina na ƙasa ba na so ma na yi mgana domin na yi alƙwarin daina yin sa'in sa da Yallabai kar wata rana na zage shi lamarin ya lalace." "Sadiya." Kallon shi na yi sai kawai ya sake matso ni ya na neman kama hannuna da sauri na matsa jikin gado Sai ya kaɗa kai kafin ya ce" You see ga shi nan ma kina guduna ne." Mirmishi na yi masa kafin na ce" Ba gudunka na ke yi ba. Ka ce ni ba ni da alheri ne sai na daina raɓar ka saboda kar na shafa maka rashin alherina." Baki ya buɗe kafin ya ce" Ki ji tsoron Allah Sadiya ni na ce haka? Ido cikin ido na kalle shi kafin na ce" E haka ka ce. Ka ce ma Gimbiya ta gama maka komai ni kuma shi yasa ni da ban taɓa maka komai ba na ja jikina daga gareka amma ni ba na gaba dakai." Na faɗa kai tsaye ina kallon shi sai ya dafe kan shi kafin ya ce"kash! Ni fa ba haka na ke nufi ba. Cewa na yi zuciyarki na saka miki abin da ba alheri ba amma ni wallahi tallahi ban ce ba ki da alheri ba." "Allah ko? Na faɗa ina kallon shi domin na ga kamar zai raina min wayau ne. "Da gaske ni ban ce miki ba ki da alheri. Kuma na da ce Daughter ta ga ma min komai na ce ne ke ba ki yi min? Abin da kika yi ita ai ba ta isa ta yi min shi ba Sadiya? Ke ce Yusuf fa in ba bu ke ai ba zan iya amsa sunana ba." "Ko'" Na sake faɗa ina kallon shi a raina ina auna cewa da gaske ne namiji bashi da kunya. Sai kawai ya matso ni ya matse ni ya shisshigemin ya na mai riƙo duka hannuwana ya na marairaicewa. "Kin riƙe ni a ranki ne! To don Allah ki yi hakuri kin ji ko? Ba haka na ke nufi ba." "Na haƙura" Na bashi amsa saboda ina so ya ƙyaleni amma bai ƙyaleni ba sai da ya rumgumeni ya na faɗin" Ki daina gaba da ni." "To." "Ki kuma daina ƙaurace min" "To " "Ki daina watsar da sha'anina ba na jin daɗi." "To" "Ina sonki. Ƙaunarki na ke yi Sadiya ta." "To." Sai ya ɗago ya na kallona kafin ya ce" Shima To ɗin ne? Sai kawai na kauda kaina ina mirmishi, shige min ya dinga yi ya na lallaɓa ni ban taɓa tunanin zan sake ba ma Yallaɓai wata dama ba sai ga shi na ba shi damar na yarda da maganar nan ta miji da mata sai Allah. Ni kaina na yi kewarsa sosai, haka na ke ƙamƙame shi ina maida numfashi sama sama, shi ma haka a kunnena ya ke min raɗa. "Na yi kewar gonar nan mai cike da ni'ima." A ƙasan maƙoshina na ce" Uhm" "Wajen ya ƙara sulɓi Madam me ye sirrin? Banza na yi masa sai kawai ya sumbaci baƙina kafin ya rumgumeni. "Da gaske na ke yi ina kaunarki Sadiya ta." A duhun ɗakin na ke kallon shi, ya na mai lumshe idanuwana barci na son ɗaukan shi bayan mun gama tsarkake jikin mu. Na ƙura ma fuskar shi ido ina kallon shi, na yarda yana sona amma kuma ya raba son gida biyu ɗayan ya ba ma Gimbiya. Itama haka ya ke yi mata in sun kaɗai ce? Innalilahi na fara kira a cikin raina domin tuni kirjina ya fara zafi kishi ya taso min da sauri na juya masa baya ƙwallah ne suka taho mini amma na kasa maida su sai da suka samu nasaran zubowa na yi saurin sharewa ji na yi ya motsa ya ƙara kamkameni ya na sauke min numfashinsa a saman wuyana ajiyar zuciya na sauke ina jin kamar numfashina na min gudun tsere sai da na buɗe bakina ina shaƙan numfashin ta baki domin sai na ji kamar iskar ɗakin ta yi min ƙaranci. *Janafty* *TKG* FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622 14. Tun a daran alhamis Yallaɓai ya kirani a waya saboda ranar ba a gidana ya ke ba. Ce min ya yi mu shirya ni da yara za su zo shi da Gimbiya su ɗauke mu domin zuwa sallar idi na ce masa to, domin ni yanzu tsakanina da Yallaɓai to ne domin na yi ma kaina alƙwarin kome zai yi ko ya ce ba zan ƙara yi masa mgana ba, ma'ana sai dai na gani na yi kamar ban gani ba na kuma ji na yi kamar ban ji ba domin a zauna lafiya.   Lokaci bayan lokaci ina tuna kalaman da ya jefe ni da su na cewa ba ni da alheri sannan Gimbiya ta yi masa komai ni kuma ban yi masa ba. Wani lokacin kallon shi kawai na ke yi domin ni a wajena ya gams shayar da ni dukkan mamakinsa shi ya sa yanzu komai zai yi ko a nan gaba ba na tunanin zai ɗaga min hankali ko kuma ya ba ni mamaki tunda a zaman auren mu na shekaru sha biyar ya iya buɗe baki ya ce ba ni da alheri sai wacce ya aura ko wata uku ba ta rufe a gidan shi ba ai ban tunanin kuma akwai sauran wani abu da Yallaɓai zai yi ko ya faɗa da zai sake ba ni mamaki.   Kamar yadda ya umarce mu, Ranar jumma'a da ta kama ranar idin babbar salla mun shirya har da Marwa ma da za ta yi salla tare da mu. Ko kafin su ƙariso mun jima da shiryawa domin tun huɗun asuba muka tashi ba mu koma barci ba har yaran ma gabaɗaya. Ba su shigo ba daga ƙofar gida ya tsaya da mota ya ce mu fito mu wuce mun makara lokacin wajen bakwai da arba'in na safe ne can masallacin cikin gari za mu je su su kan ta da salla takwas da rabi ne gwara ka je da wuri ka samu wajen parking da kuma wajen zama. Gabaɗaya muka fito ni na tsaya na rufe gidan su kuma su ka fara ƙarisawa. Na ƙariso lokacin Gimbiya a bakin motar ta ganta ta na rumgume yaran har ƙoƙarin ɗaga Baby ta ke yi. "Kar ki ba kanki wahala ba iya ɗaga ta za ki yi ba." Na faɗa dai dai ina ƙarisowa da ɗan sigan zolaya haka. Sai muka kalli juna sannan ta yi min mirmishi na maida mata. Ta na sanye da hijabi mai ruwan ƙasa kalan doguwar rigar da ke jikinta takalmin kafanta mai saukaƙƙen tudu ne sannan ta saka safa irin na su dai na ƴan gayu. Ni kuma daman atamfata na saka wata mai purple sai na yi amfani da kalan Hijabin, kafata nima flat shoe ne da safa su Jidda ma Atamfa na saka musu da hijaban da na siya musu har ƙasa haka ma Marwa. Gogan na kalla ya na cikin mota zaune sai dai ya na amsa waya ne shi ya sa bai fito ba. Hannu ta miƙa mini muka yi musabaha. "Barkanmu da salla Madam" "Barka da salla." Nima na maida mata martani Marwa ta gaiaheta sai ta amsa ta na yi mata kallon rashin sani. "Marwa. Ɗiyar yayata ce." Na faɗa ina dafa kafaɗan Marwa ɗin. Sai ta yi mirmishi kafin ta ce" Barkan mu da salla Marwa." Marwa ta amsa ta na mai ƙara gaisheta, daga cikin motan Yallaɓai ya ce ko a nan ne za mu yi sallar idi? Muna jin haka sai na buɗe gidan baya na ce Marwa su fara shiga ita da yara ni ban ma kawo ma kaina hawa gaban mota ba, saboda na ga Amarya a bakin wajen ta kame shi ya sa na shige baya abuna wata zuciya na ƙara tunatar da ni aka ma raba mijin gabaɗaya ballanta kuma gaban mota.   "Ina kwana Madam ɗina." Ya faɗa bayan yaran sun kuma gaishe shi ya juyo ya na musabaha da su. Nima hannun ya miƙa min sai na karɓa ina faɗin. "Barka da salla Yallaɓai." Sai ya jinjina min kai kafin ya ce" Barkan mu da salla Amintattaciya ta." Kallon shi na yi, amma ban yi mgana ba hannuna na zare cikin na shi kawai ina mai cema Baby ta koma ta zauna ko na dake ta saboda sai faman zillo ta ke yi ma mutane kamar za ta koma can gaban motan. Marwa ma ta gaishe shi ya amsa ya na faɗin" Marwatu barkanmu da salla." Ta amsa ta na ɗan mirmishi, sai ya juya ya na mai kallon Gimbiya sannan ya ƙara juyowa ya na sake kallona ni kuma tuni na maida hankalina wajen jan kabbarorin da Annabi(SWA). Ya koyar da mu a lokacin tafiya sallar idi. Allahu akbar. Allahu akbar. Allahu akbar. Walillahil hamdu. Har su Jidda ma na ce su yi ta maimaitawa. Har mun ɗan fara tafiya muna ta haɗuwa da mutane kowa ya ci sabbin kaya yau ta ke salla Yallaɓai na juya ina kallon keyarsa da yadda ya kafa hula ya na tashin kamshi wata wagambari ya saka mai ruwan ƙasa duk da bai sauko daga motar ba amma ya yi kyau matuƙa shi daman Yallaɓai mai kyau ne kuma ɗan gayu ne komai ya saka a jikin shi sai ya yi masa kyau ina daga gefe ne ta bayan kujeran Gimbiya ba na kallonta amma shi ina ganin shi sai ya ɗan kalleta yana mirmishi ƙila itama murmushin ta ke yi masa sai kuma in ya ɗago mun haɗa ido ta madubi sai ya wani kashe min ido, ai da na ga ya na nemen rena mini wayau tuni na juyar da kaina ina gani  gilmar motoci da waɗanda ke kasa ina jin farinciki a ƙasan raina na ganin hada hadan mutane, a cikin raina ina ta hasaso yanzu haka a gida su Alhajinmu suma sun kama hanyar zuwa sallar idi shi da su Ya Hamza tun jiya da muka yi waya da Gwaggo ta ce sun iso Ya Auwal ma daddaren ya ce min sun sauka shi da yara da Laila. Muna da ɗakuna a gidanmu ga na Mama ga na Hajiya duk kuma a gyare suke, can ƙofar shigowa kuma ɗaku nan su Ya Hamza tun na samartakansu ya na nan in sun zo gida nan sukan sauka har su gama kwanakin su koma sun gyara shi sun saka komai na morewa rayuwa a ciki. Har muka isa masallaci ban ƙara bi ta kan Yallaɓai da matar shi ba. Mun sauka a bakin hanya ya ce zai nemi wajen parking mu kuma mu karisa bangaren mata in an idar da salla zai kira mu. Daga nan muka ɗau darduman mu guda biyu itama Gimbiya ta zo da na ta, Marwa ta riƙe hannun Jidda ita kuma Gimbiya ta riƙe hannun Baby suna gaba ni kuma ina baya ina ta kabbarori. Mun samu wajen zama muka shimfiɗa sallaya muka zauna ba daɗewa aka ta da salla, bayan mun idar da salla aka fara hada hadan jama'a wasu na kafa sannan ga zirga zirgan ababen hawa waje ya cika makil ko'ina ga waiga jama'a ne kamar ba a mutuwa saboda cikowa. Mun samu mun fita can bakin titi da kafarmu ni wayata ma a gida na barta Gimbiya ce ta zo da ƙaramar jaka shi ya sa ta ɗauko wayarta ta nan Yallaɓai ya kira mu, ya na ta faɗan wai ya na ta kiran wayata ban ɗauka ba na ce ta faɗa masa ta na gida na baro ta. Mun haɗu da shi a can gaba kaɗan sannan muka shiga motar wannan karon ma Gimbiya a gaba ta kame ni kuma na shiga bayan kamar yadda na zo. "Ke haka ake yi sai ki bar waya a gida? Sai na kalle shi kafin na ce" Za ta zame min kaya ne shi ya sa ban ɗauko ta ba." Sai ya yi shuru bai yi mgana ba, sai kuma can ya kalli Gimbiyar kafin ya ce" Daugther ki koma baya ki zauna." Sai ta kalle shi kafin ta yi magana ya juyo ta baya ya na faɗin" Ke kuma Sadiya ki fito ki dawo gaba." Sai na ga ta ɗan yi wani tsam kafin ta ce Ok. Tana ƙokarin buɗe kofar motar ne na yi saurin cewa" Ki yi zaman ki ni fa nan ɗin ma ya isa. Ba duk mota ba ce da bayan da gaban ai duk ɗaya ne" Sai na ga kuma ta dakata da fitan kenan ta na son zaman gaban motan sai kawai na ga ya wani kalleni ya na wani haɗe rai. "Na ce ki fito ki dawo nan ki zauna ko? "Da dai ka bar ni anan ɗin." "Umarni ba jin ta baki ba. Ki fito ki dawo gaba ita kuma ta koma baya haka na ce." Ya faɗa har ya na wani tattarre naman goshinsa waje ɗaya na fitina ina jin haka sai na buɗe murfin mota na fito, itama ta fito  sai mu ka sauya wajen zama sai da muka zazzauna sannan ya ta da motar muna tafe a hankali saboda gowslow shi ya sa Yallaɓai tafe ya ke gaisawa da mutane har dai na ga ji na kalle shi ina faɗin. "Sannu. Wai kai kowa ka sani ne? Ya na dariya kafin ya ce" Ba kowa ba. Amma saboda aikina ina harka da mutane sosai." Ai ko na ga harka da mutane kafin mu fita wannan cunkosun Allah kaɗai ya san yawan jama'an da ya haɗu da su sai dai ki ji ana faɗin Injinjiya kai ne anan? Mutane ba su cika kiran shi da Yusuf ba sai Injiniya a gida kuma daman Tafida ne in ka ji Yusuf sai dai irin tsoffin abokan shi tun na makaranta. Har gida suka dawo damu kamar yadda suka ɗauke mu. Gimbiya dai fuskar nan ba Annuri ina ga ranta ya ɓaci ne da ya ce ta fito ta ba ni waje ni ko ban tsaya ma bi ta kanta ba a raina na ce kina da aiki. Mun rabu da Yallaɓai da cewa in ya maida Gimbiya gida  Gwammaja zai je ya yanka ragunan sallar nan sai anjuma zai leƙo. Yara ma suna ma Antynsu na su bye bye ba ta amsa ba muna dai tsaye suka juya kuma ta na bayan ba ta dawo gaban ba duk da na ga kamar ya juya ya na mata mgana kuma ina da tabbacin ce mata ya yi ta dawo gidan gaba ina ga za ta ce daga baya kenan, ni dai na buɗe gida muka shige a ƙasan raina ina ganin ƙokarinta Allah na tuba mene ne a zama gaban mota tare da miji. Ni Allah na tuba ina ga ita ce baƙuwa a harkan ni ba domin ya matsa min ba wallahi bai dame ni ba. To wai mijin kan shi fa raba shi kake yi da wata to mene ne a cikin zama a gaban mota? sai na ke ganin shi wannan ai ba wani abu ba ne. Muna dawowa muka sulala indomie muka ci, sai can da rana Musbahu ya kawo kayan ciki na Yallaɓai da nawa sai naman ragon da ya yi min layya daman duk shekara yana yi min in kuma bai da shi ya yi nashi shi kaɗai. Kuma in dai ya yi min to ni ake kawo ma Naman na diɓan ma gida sauran kuma mu yi amfani da shi a gida na Yallaɓai kai da kafa kawai ake gyarowa aka wo naman kaɗan ne ake kawowa duk sai ya ce ya yi sadaka da shi. Yau ma ɗin haka na yi na diɓar ma Gidanmu na ba ma Marwa na adaidaita ita da Jidda suka je suka kai musu muna gida ni da Baby muna jiran su yaran nan sai yamma suka dawo suna faɗa min gida cike da matan su ya Hamza ana ta hidima sai na ji kamar na yi tsuntsuwa na ganni a gida, Alhajinmu ya ba ma Jidda goron salla ya ce Baby ta nemi na ta mijin ya ba ta, Baby na jin haka ta fara rigima sai ta je  mu na yi mata dariya. Sai dare muka dafa shinkafa Jalop da nama, muna ma cikin ci ne sai ga Yallaɓai ya shigo gidan bai ma wani tsaya ba ko abincin da na yi masa ta yi bai ci ba ya dai sha ruwa sai nama ya ci, cincin kuma da na ɗibar masa a leda ya ce na saka masa ya tafi da shi, ina jin haka sai na ɗibar ma Gimbiya kar ta ga ya je da shi ita ban kai mata ba, tunda ni ma ta na kawo min abubuwa in dai ta yi har soyayyen naman ma na ɗibar mata ya ko karɓa ya na ta murna har ya na ce min. "Allah ya saka miki da alheri Sadiya ta." Na amsa masa da Amin to har ya tafi fa sai ga shi ya kirani a waya wai zai zo na zuba masa abinci Gimbiya ba ta yi girki ba saboda ba ta jin daɗi. Na ce to ya zo ba daɗewa sai ga shi, a raina na ce shi ma dai da gulman shi na fa yi masa ta yi da farko ya ce ba zai ci ba ya ɗauka ta dafa masa ne in ya koma kar ya ce mata ya ci a wajena ta ji haushi sai kuma ta ɓare da shi a babba kula na saka musu mai yawa ya na ta min godiya. "Godiyar nan ta yi yawa Yallaɓai sai ka ce na yi maka wani abu." "Wani abu ne mana. Ke dai kawai Allah ya yi miki albarka." Na amsa da Amin Amin sannan muka yi sallama ya tafi, ko washegari da ya ke gidana ma sai da ya karɓan mata tuwon shinkafar da na yi miyan agushi, ya na faɗa min ba ta yi girki ba ai ba ta son kamshin girki a raina na ce ko dai ciki ne? Amma ban furta masa ba amma dai na ce ya kamata su je asibiti ya ce za su je in sha Allahu.   Tuwon da ɗan yawa na yi na aika can Gwammaja sai Hauwa da Mutaƙƙa ya zo ya karɓan mata sannan Musbahu ya zo da wani abokin shi, suma sun ci na saka musu cincin da Nama, da daddare ma sai ga Adnan ya na gidan sai ga Datti ya zo Allah ya sa da sauran shi sai na saka musu da ya ke kuma sun san juna suna ta hira. Wannan salla ban samu wasu yan yawon salla ba da rana dai Firdausin Ya Balki ta yo min zuga ƙawayenta da ƴan'uwanta bayan sun ci abinci da za su tafi na ba su 2k goron sallah ina ta tsumayin ƙannen Marwa amma ba su zo ba ranar salla ta uku kuma Gwammaja muka yi ni ban tsaya dafa wani abinci ba tea muka sha da safe muka tafi suma can ɗin cike gidan ya ke can na iske Gimbiya ina ganinta na fahimci ba ta da lafiya ta yi zuru zuru sai kwanciya ni dai kamar shigar ciki na gani tare da ita amma ban yi mgana ba haka ma kowa ke faɗi in ya ganta su Anty Bahijja ne yan faɗin in sha Allahu ma cikine za ta faɗa ma Tafida ya kaita asibiti a tabbatar. Har su Hauwa sai da suka ce min kamar Amaryan ki na da shigar ciki na ce ban sani ba wallahi Munnira ta kalli Gimbiya ta sake kallonta kafin ta ce" Ke Sadiya na ba ki tabbacin Amaryan Tafida ciki ne da ita." Duk da acan ƙasan raina na ji wani iri amma ai tunda an yi dare ni na san garin zai waye komai daran daɗewa shi ya sa na yi mirmishi kafin na ce" Ina musu fatan haka" Saboda ni na san Yallaɓai na son haihuwa Allah ne kawai bai bashi masu yawa ba na tabbata zai fi kowa farinciki da hakan shi ya sa a ƙarƙashin zuciyata  na yi ta karfafama kaina Gwiwa in ma ta na da cikin. Cikin na Yallaɓai ne kuma ni da na sha yi ma kaina alƙwarin in Yallaɓai ya ƙara aure har ya samu ƙaruwa zan fi shi murna da farinciki sannan zan so duk wani abu da ya fito daga jininsa ko tsatson sa. Shi ya sa na yi ta kiran sunan Allah a raina har ya kawo min agaji na ji na samu salama. Muna Gwammaja har tara na dare da ɗaya da ɗaya kowacce mazajensu na ta zuwa ɗaukan su. Wannan karon dai Cincin kawai da nama na kawo ma Nene ta yi ta saka albarka, Hajiya Iya da Maman farko sai na kai musu cincin kawai suma suna ta godiya da faɗin" Sadiya ba kya gajiya? Ina zan gaji ina ganin su ne kamar iyayena mijina suma yadda zan kyautata ma Nene haka suma na ke yi musu kamar yadda suma na ga ƴaƴan gabaɗaya ba sa nuna bambamci a tsakaninsu. Gimbiya dai har da su Cake ta yi amma ina tunanin ba dawa ta yi aka yi mata an kawo min da yawa jiya har da dambun nama ga soyayye. Na gan shi na ma su Anty Bahijja suna ta ci da Naja'atu da ta zo daga baya. Wannan salla Yallabai bai siya mana kaji ba wai ya manta lokacin da na tuna masa kuma duk an siye sai dai bayan sallah ya ce mu bi shi bashi, ni kuma ban ji daɗi ba saboda ni dai na fi son naman kaza fiye da naman rago shi ya sa ban ma wani ci naman sosai ba kuma wannan sallar ban yi dambu ba na gaji Marwa ta ce za ta yi na ce ta bar shi kawai. Sai da Yallaɓai ya dawo sannan ya ɗauko mu gabaɗaya wannan karon ma a gidan gaban ya ce na zauna ita kuma a baya ita da yara. Sai dai muka fara kaita gida muka sauke su ita da Jidda sannan muka juya gida, muna hanyar komawa gida Yallaɓai ke faɗa min gobe zai kai  Rano Gombiya ta kwana biyu. "Gobe? Ita da ba ta da lafiya? Na faɗa ina mai kallon shi, sai ya kalleni shima kafin ya mai da hankalin kan tuƙin shi ya na cewa" Nima haka na ce mata amma ta matsa ita sai ta je. Sai na ce ta je ta kwana biyu ko? Kai na gyaɗa kafin na ce"Haka ne. Tunda kuma ai ba kwance take rigis ba." Daga haka na yi shuru ina jin shi ya na faɗa min wai ta matsu ne ta ta ji an ce duka yan'uwanta sun je can sallah. "Har da Tariq da Farida? "E mana. " Sai na jinjina kai kafin na ce" Ban ɗauka za su zo ba. Na ga ba su daɗe da komawa ba ne." Ya na dariya ya kalleni kafin ya karkato ya na min raɗa. "Maaganar Kawu da ɗiyarki ne musabbin zuwan shi." Sai na kalleshi ina faɗin" Da gaske? Sai ya koma ya gyara zama hankalinshi na wajen tuki ya na mai faɗin" Da gaske na ke faɗa miki. Gobe in na kai Gimbiya za mu haɗu mu kara tattaunawa yadda muka tsaida za ki ji " Sai na jinjina kai kafin na ce" Allah ya tabbatar mana da alheri." "Amin. Ai in sha Allahu Alheri ne tun da na ga Kawu ya susuce shi fa ya matsa mana sai mun haɗu akan mganar nan" Ina mirmishi na ce" Allah ya tabbatar Yallaɓai." Ya amsa da Amin muna tafe muna hira har gida, Marwa suka shige ciki da Baby ni da Yallaɓai muka zauna a falo muna kallo muna ta hira sai a lokacin ya ke faɗa min ya kama min shagon su na ƙasa sai kuma ga maganar auran shi da Gimbiya wai ya yi tunanin ya yi min mganar zan ce dannen kirji ne. Shi ya sa kawai ya buɗe ma su Musbahu da wani ma'aikaci da ya ɗauka suna zama a ƙasa shi kuma office ɗin shi na sama. "Bakomai. Allah ne bai yi lokacin ba. " "Zai yi lokacin in sha Allah soon." Na ce Allah ya sa amma ba wai domin na wani yarda da shi ba. "Wai shi Musbahu wani matsayi ka ba shi a wannan kamfanin naka ne Yallaɓai? "Manaja na ne shi. Wanda na ɗauka kuma mataimaki ne kafin dai mu ga abin da Allah zai yi kin san komai a sannu sannu ya ke tafiya." "Haka ne. Kai kuma fa? Ya na yar dariya ya ce" Ni? MD Managing derector." Hannu na ɗaga masa ina faɗin" Allah ya ƙaro dubban Nasarori mai girma MD" Ya amsa ya na shafa gashin kaina daman ina saman kirjinsa ne muna zaune a waje ɗaya muna hira muna kallon wani film a MBC action. Sai wajen sha biyun dare muka kwanta ni da Yallaɓai kafin mu kwanta sai da ya kira Gimbiya ta yi barci ba ta ɗauka ba sai da asuba ya same ta. Jikinta ya tambaya ta ce da sauƙi ina gefen shi ni ban ma ce ya ce mata ina gaisheta ba amma sai gashi ina jin sa ya na ce mata na ce ina mata sannu sai kawai na kalle shi ta gefen ido girgiza kawai na yi saboda Yallaɓai ya yi nisa ba ya jin kira lamarin na shi ya koma har da kage ni yaushe na ce ina mata sannu! Ai na yi mata sannun jiya da muka haɗu ba shiken nan ba. Daga ni har shi da wuri muka shirya ni duk da na tsaya na dafa shinkafa da miya da salat wanda zan tafi dashi ɗorayi. Yallaɓai sai da ya ci sannan ya fita ya ce zai je ya ɗauko su Gimbiya mu shirya in ya ijemu a Gwammaja za su wuce. Ban yi masa mgana ba sai da ya ɗaukota suka dawo gidan ta shigo na yi mata ta yin abinci ta ce ba za ta ci ba ganin kamar ta na wani zumɓuran baki da ya ce tare za mu fita gabaɗaya sai kawai na ce masa su tafi mu in mun tashi za mu hau adaidaita.   "Kin tabbata ba matsala? "Babu ku je kawai Allah ya kiyaye hanya." Na faɗa kai tsaye, saboda na ga sai wani cin magani ta ke yi ni dai ban ko bi ta kanta ba can su ƙarata yara ne suka raka su haraba ni dai daga ƙofar falo ban ƙara gaba ko'ina ba. Sun tafi ba daɗewa nima na tattara Iyalaina muka ya da zangon mu a Ɗorayi duk sammakona sai da su Rahila suka rigani zuwa Ma'u ce kawai na riga ta zuwa Amina daman tun jiya ta iso gida ya cika maƙil kwanmu da ƙwarkwatan mu Alhajinmu baki ya ƙi rufuwa. Ko su Ya Hamza ban da salla ba abin da ke fitar da su waje duk ana tare a falon Alhaji ana ta hiran yaushe gamo. Abinci daman kowwccen mu ta yo girkinta nan fa aka baje ana ta liyafa ana hira ana ta dariya cikin Annushuwa kowa kuma da ruƙunin da ya ke zaune ni dai ina zaune ne da Khaleesat da Amina sai Ya Hamza saboda daman tun muna yan mata Ya Hamza na cikin Fav  ɗina shi ma haka domin yadda ya ke kula da ni ko Rahila da suke uwa ɗaya albarka haka itama Rahila Ya Auwal ne na ta ko da matarsa ma sun fi ɗasawa ita kuma daman Ma'u tana rukunin Ya Murja ne Ya Aina kuma ita da Yaya Abubakar da Ya Balki ne in dai ya na gidan to tare suke zama Datti kuma ɗan gatan Alhaji ne ya na gefen shi. Saboda yau ta ke salla kuma an daɗe ba a haɗu ba sai ba a yi faɗa ba ana ta hiran zumumci ana ta shewa sai salla ke ta da mu.    Mun haɗu gabaɗaya mun yi ta hotunan tarihi da mu da ƴaƴanmu gabaɗaya. Mu ne har dare sannan Alhajinmu ya ce kowacce ta yi shirin tafiya gidan ta. Ni ban jira Yallaɓai ba domin ban san ko yaushe zai dawo ba, Ya Aina ta ce gobe Marwa ta koma gida sai na marairaice ina faɗin" Haba Ya Aina sai jibi dai. Kin ga gobe zan dawo za mu je can Gandun albasa ne" "To Allah ya kaimu." "To ke Ya Aina ku bar ma Sadiya Marwa ɗin gabaɗaya mana tun da dai ta na son ta." In ji Ya Hamza saboda shi ɗan ba ruwan shi ne, ba kuma shi da tsoron yin mgana in dai ita ce a zuciyarsa. "Sai ta haɗa da Jidda duk su aurar da su ita da Injiniya." Ya Auwal ya faɗa ya na dariya Gwaggo na wajen har ta saka baki da cewa" To ko a yanzu Sadiya ce uwar Marwa. Ita Aina Mama ce ita kuma Sadiya Umma ce ka ga ko Umma ce uwar amarya." Muna ta dariya gabaɗayanmu Ya Aina dai ba ta ce komai ba sai mirmishi. Tare muka fita da Ya Ainan Ya Auwal ya ɗau motar shi ya kai mu gida ni ya fara ijewa ni da yara ita kuma ya tafi kaita gida. Yallabai kuma sai wajen sha ɗayen dare ya dawo ni kuma na gaji domin har ma na fara barci sama sama na ji dawowar shi da mganar shi da safe kuma bai yi min wata mgana ba nima ina sauri za mu je gidan su Mama sai ban tambaye shi ba. Tare da yaran muka sake komawa can Gwammaja daga can muka haɗu gabaɗayanmu ban da dai Ma'u. Daman jiya ta ce za ta je kura wajen Baaba amma kaf ɗin mu ne muka je gandun albasa gidan su Mama. Inna Mariya daman ta na gida ne mijinta ya daɗe da rasuwa. Mun daɗe domin sai la'asar muka koma Gwammaja Ya Auwal da Ya Hamza sun yi musu alheri nima na kai musu nama da cincin da cake wanda na diɓa cikin wanda Gimbiya ta kawo min, suna ta mana godiya sun daɗe daman ba su ganmu mun haɗu gabaɗaya a lokaci ɗaya ba sai dai wani lokacin leƙowa dabam dabam. To wannan karon salla duk ya game mu waje ɗaya. Bayan mun dawo Gwammaja ne Yallaɓai ya kirani a waya ya ce na tura masa lambar Mijin Ya Aina Allah ya sa ina da shi na tura masa kuma ni ya ƙi faɗa min komai ya dai ce in na dawo za mu yi mgana saboda zumuɗi ana mangariba na tarkata su muka hau adai daita muka koma gida shi ko Yallaɓai sai wajen goma ya dawo min gida ina ta jiran shi in ji labari. Na yi ta naniƙe masa ina tambayansa ya ƙi faɗa min sai ja min rai ya ke yi daga ya ce bari ya yi wanka sai ya ce bari ya yi kaza har na gaji na ƙyale shi da muka zo kwanciya ma sai da ya ja muka yi ɓarnan ruwa bayan mun gama kuma ya ce ya na jin barci sai da safe da dai na fahimci da gangan ya ke wasa da hankalima sai na ƙyale shi. Da asuban fari wayar Ya Aina ta tashe ni daga barcin da na koma sai ga labarin da Yallaɓai ke min ƙwalele ta na faɗa min domin ina ɗaga wayar ta ko gaisawa ba mu yi ba ta ce. "Ke Sadiya jiya da daddare ba sai ga Baban su Jidda tare da baƙi ba." "Baƙi? Wasu baƙin? Ba maganarta ne ya ba ni mamaki  ba sai illa baƙin da ta ce ya zo da su. "E mana ko ba ki sani ba ne? "Ban san ko abin da na sani kike son ki sanar da ni ba Ya Aina." "To ke wani labari kika sani? Kai tsaye na ce" To ni dai na san Autan su Nene Kawu Abba ya zo gidana ya ga Marwa ya ce ya na so. Kuma Yallaɓai ya ce min sun haɗu jiya sun tattauna kuma shi Yallaɓai ya karɓi lambar Baban Marwa a wajena ban san kuma da mganar wasu baƙi ba." Cikin sauri ta ce" To ai mganar ne. Sun zo su uku da Baban jidda da wani sai shi mai son Marwa ɗin." "Ma sha Allah? Da me suka zo? "Sadiya wai neman izini suka zo suna so a ba su dama ya fara mgana da Marwa in sun dai daita ba su son ya ɗau lokaci." "Alhamdulillah. Ya Aina Allah ya sa an ba shi dama." "Babanta ya bashi dama Sadiya tun da dai daga bangaren ki da mijinki ne. Ba ki ga yadda ya ke jin daɗi yadda suka mutumtata shi ba ya ce tabbas ya ƙara ganin darajansu na yadda kafin su fara magana da Marwa sai da suka zo neman izini." Ina murmushi na ce" Ya Aina ai Kawu Abba mutum ne. Tare suka tashi da Yallaɓai fa tun suna ƙanana da wannan wanda suka zo tare Yayan Gimbiya ne Amaryan Yallaɓai. Kuma ina mai baki tabbacin ki bi lamarin da addu' a  in dai Marwa ta auri kawu ta gama yin miji." Ya Aina ta ce"Ikon Allah. Ni ban ma san shi ba. Amma ya faɗa ma Babanta tarihin shi ya ce an taɓa saka masa rana yarinyar ta rasu tun daga ranar bai ƙara neman wata ba sai yanzu akan Marwa. Sannan ya ce ya na noma ya na kiwo." Na karɓe da faɗin" Kwarai an yi masa tallar mata ba adadi ya ce ba ya so. Ke ce ba za ki san shi ba amma Rahila ta san su shi da Tariq tun Yallaɓai na neman aurena sun sha zuwa tare. Ya Aina gidan gona gare shi a Rano wai kin ga gidan da ya gina a can ne? Ba wai ina nuna ya na da kuɗi ba ne amma ina mai faɗa miki ya na da rufin asiri mata da yawa suna rubibin shi saboda in ba ya faɗa ba sai a ce saurayi ɗan shekaru talatin ne ba arba'in. Ke Ya Aina har Shema ƙawar Ma'u ta yaba da shi ya ce ba ya so, kin tuna na taɓa mata mgana har ya so ya zama faɗa kika ce na yi shuru? Ya Aina cikin mamaki ta ce" Na ko tuna ikon Allah." Ina dariya na ce" To kin ji fa. Ai mu sai godiya mun yi suruki ni uwar Amarya kuma surukar ango." Ya Aina ma dariyan ta ke yi kafin ta ce" Kin sani kika yi min shuru ko Sadiya.? "To ai na yi shuri ina ta addu'a kar na zo na faɗa kuma a ji shuru." "Haka ne kuma to Allah ya sa alheri. Yanzu a sanar da su Murja ko mu jira zuwa gaba kaɗan? Sai na ce" A'a su ba yanzu ba amma ki sanar da Alhajimmu da Gwaggo." Da haka muka yi sallama duk Yallaɓai na jin mu muna gama wayar na yi masa gwalo ina faɗin" Labarin ka ya yi kwantai Yallaɓai " Ya na dariya ya ce" Na ji bakomai. Kema ai kwantan kika samu" Nima na ji bakomai tun da bai faɗa min ba ya riƙe labarin shi, sai daga baya ya ke faɗa min yadda aka yi ya ce min na sanar da Marwa domin Kawu ya na so ya fara mgana da ita. Ina dariya na ce" To Kawu fa da gaske ya ke yi " "Ai Kawu ya susuce. In ba gani ya yi an yi auren ba to Kawu zai iya ba da mu." Ina ta dariya muna ma cikin mganar Ya Aina ta sake kirana ta ce ta manta ba ta ce na zaunar da Marwa na faɗa mata in ji Babanta na ce kar su damu zan sanar da ita. Yallabai bai fita da wuri ba sai azahar ya ce zai je Rano ya ɗauko Gimbiya na ce sai ya dawo nima ranar ban fita ba ina gida amma na yi waya da su Ya Hamza suma duk sun ɗau hanya domin komawa gida saboda aiki Amina ma ta bi Ya Auwal za su sauke ta a kaduna sai fatan Allah ya kai su lafiya. Ni na zaunar da Marwa na yi mata bayani ta na jin kunya ta rufe fuska ta na faɗin" Umma abokin Kawu fa kika ce? Ina dariya na ce" E to mi ye a ciki? Zan yi matukar farinciki in haka ta faru ina tunanin gobe ko jibi zai zo ya ganki. Marwa Kawu Abba ba shi da matsala ki ba shi dama kin ji ko? Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" To Umma in sha Allahu." Na ma ɗauka a ranar zai zo amma sai bai zo ba mun yi waya da Yallaɓai ya ɗauko Gimbiya sun dawo gida ya ce min ba ta da lafiya ta na fama da ciwon mara da safe za su je asibiti na ce Allah ya sauwaƙe. Washegari Kawu Abba da kanshi ya kirani ya ce zai zo. Marwan na gidana ne? Na ce ta na gidana da yau za ta koma gida amma tunda ya na tafe sai gobe a lokacin da muka yi wayar na faɗa masa ba ta nan ta je asibiti ta na da aikin safe sai biyu na rana za ta dawo sai ya ce min zai shigo da yamma in sha Allahu. Mun gama wayar da shi kenan Yallaɓai ya kirani. "Sadiya Albishirin ki " Ina ɗauka abin da ya fara ce min kenan duk da ban sani ba amma a raina na san abin da zai faɗa min ba na raba ɗayan biyu tun da na ji Yallaɓai farincikinsa ya ƙasa ɓoyuwa. "Goro fari ƙal. Me ya faru? "Daughter tana da ciki. Wata biyu Sadiya." Sai na danne abin da ke taso min na washe baki ina faɗin" Alhamdulillah Ma sha Allah barka da arziƙi Yallaɓai Allah ya raba su lafiya." Ya amsa min da Amin Amin sannan ya ce ni ya fara kira ya sanar ma wa, sai na ji daɗin haka ko bakomai ya karramani kuma na ji daɗi na yaba. Jin haka yasa na ce ya ba ni Gimbiyar na yi mata sannu sai ya ce ta na ciki tare da likita ya fito ne daman ya kirani sai na ce shikenan in sun koma gida zan kira shi sai ya ba ni ita na yi mata sannu. Duk yadda zuciyata ke son kaɗaicewa ta yi damuwa ban ba ta damar haka ba. Na taya Yallaɓai murna kwarai kusan shekaru bakwai ne ba a sake yi masa haihuwa ba dole ya yi farinciki amma na yi hawaye tare da fatan nima Allah ya sake ba ni ba domin ban gode masa ba a'a na gode masa ina kuma fatan ya ƙara min. Marwa ta na dawowa na faɗa mata ta shirya Kawu zai zo duk sai ta daburce daga karshe ni ce na taya ta shiryawa bayan na saka ta yi masa girki jalop ɗin shinkafa mai karas da gabeji. Ana idar da sallar la'asar sai ga shi ya iso ni na fara fita muka gaisa su Kawu an sha kwalliya za a burge Marwatu ta bakin Yallaɓai ba. "Yallaɓan kuma ba ya nan Kawu Abba." "E mun yi waya. Ya na can baki ya ƙi rufuwa Saudatu ta na da juna biyu." "E wallahi." "To Allah ya raba su lafiya. Mun yi mgana ya ce zai shigo kafin na tafi " Sai na amsa masa da toh na kuma ciki na turo Marwatu da farantin ruwa na ce in sun gama gaisawa ta koma ta ɗauko abinci Jidda dama ba sa nan yau suka koma makaranta sai shidda saura za su dawo gida. Bederoom na koma na ɗau wayata na kunna data. Ai na ga ruwan status. Anty Bahijja ta saka Ni'imar haihuwa za ta ƙara sauka a gidan Tafidan Nene Ubangiji Allah ya riƙa musu ya tsole idon maƙiya saboda na shaka mata haushi na tagging ɗin status ɗin na shiga na ce" Amin ya rabb mun gode. Ai ni Yallaɓai ya fara kira a wayar ya sanar min da cewa mun samu ƙaruwa." Ta gani amma ba ta yi mini mgana ba Anty Maimuna kuma har da saka hoton Gimbiya ta na cewa" A karon farko Hajiyar Tafida da Nene za su samu jika na farko da tsatson ahalinsu. Congratulatin Mutanen Rano da kewayenta gabaɗaya." Itama na shiga na ce mata Amin na ga har Naja'atu ta saka yadda kika san su Jidda ba ƴaƴa ba ne a bola aka tsinto su gajiya na yi da ganin takaici na kashe data ko na ce kiran Yallaɓai ya katse ni. Bayan mun gaisa sai ya haɗa ni da Gimbiya na yi mata sannu sun dawo gida kuma na ji hayaniya kenan gidan na cike da su Anty Bahijja domin ni na san ko kowa bai je ba ita sai ta je, mun yi sallama ya ce min zai shigo gidan anjuma. "Su Kawu ana can ana yaɗa manufa ko? Ina dariya na ce" Ban sani ba." "Su kaɗai kika bari a falo Sadiya? Kawu fa Tuzuru ne kin sani." Ina ƙara yin wata dariyar na ce" Ka zo sai ka saka ido " Ya ko ce ga shi nan zuwa sannan muka sallama ba daɗewa sai ga shi, sai da ya gama yi ma Kawu tsiya a falo sannan ya ƙariso ciki yunwa ya ke ji na saka mai abinci ya na ci ya na faɗa min tun shayin safe bai ci abinci ba a raina na ce na ga alama kam domin ya ci abinci sosai. "Ya mai jiki? "Ta ji sauƙi sun ce ta samu hutu ne. Shi ne na ke tunanin wa zai zauna da ita Jidda kin ga akwai makaranta." Sai na jinjina kai kafin na ce" Gaskiya ne. To kai ka koma can da kwana mana har ta ɗan samu ƙwarin jiki" "Ni kuma? Sai ya kalleni ya na mai nuna kan shi sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya ina faɗin" E.  Ka je bakomai ai lalura ce." Sai ga shi a gabana ya rumgumeni ya na faɗin" Na gode. Allah ya iya miki Sadiya ta." Na amsa da Amin sai hira ta buɗe ya na faɗa min yau duk abin da ta ci sai da ta amayar da shi sai da Anty Bahijja ta zo mata da kunin tsamiya daga gidanta shi ta sha ya zauna mata. Ya na ma faɗa min ta na can gidan ya baro ta shi ne ya samu sararin zuwa nan ni dai ina ta bin sa ne ka nuna wani abu a ce kana baƙin ciki.   Yana gidan har mangariba suka fita tare da Kawu. Marwa ta dawo min  da fara'an ta ta na gaya min ya ce ta ba shi lambarta ta ce wayarta ta lalace ya ce to zai kawo mata waya. "Umma to Baba zai bari na karɓa? Ina dariya na ce" Me zai hana! Ai ya je ya ga Baba. Kuma baban ne ya bashi izini Marwanatu." Sai ta dukar da kai ta na jin kunya ni kuma na daki kafaɗanta ina fadin" To ya ya a ke ciki? Kin san an ce ƙaramar uwa abokiyar shawara." Kanta na ƙasa ta ce" Ya na da ban dariya Umma." "To ina ruwan kawu. Balle ke da ya ke so ai za ki sha hira da barkwanci." Sai ta rufe fuska ni kuma na leƙa ina faɗin" To wai ya ya ne! A tsaida shi ko a sallame shi? Sai ta ki mgana sai ma tashi da ta yi za ta gudu na ko ce to shikenan tun da ba ta son shi zan faɗa masa. "Umma ni fa ban ce ba na so ba." "To kina so kenan? Sai ta gyɗa min kai kafin ta zura da gudu zuwa ɗakin su Jidda, har suna cin karo ma da Jiddan da ta fito ta na ce min" Umma me ya samu Ya Marwa? Ina dariya na ce" To Jidda ni me zan ce? Ki tambaye ta." Na faɗa ina dariya ita Jidda irin yaran nan ne marasa damuwa kawai sai ta wuce kitchen ta bar ni nan ina ta annuri. Washegari Marwa ta koma gida na faɗa mata zan tura ma Kawu lambar wayar Ya Aina zai riƙa samun ta ta can kafin ta tafi ta ke gaya min suna gama pratical suka koma makaranta semester ɗaya za su yi sai jarabawa ashe Diploma ce Kawu zai ji daɗin jin wannan labarin domin ya ce min ba ya so a ɗau lokaci sannan kuma ya ce shi bai faɗa ma kowa ba sai Innayi sai mu da muka sani ya na so ko maaganar za ta fita sai manya sun shiga ciiki shi ya sa na yi gum da bakina. Na je har gida na duba Gimbiya gaskiya ta na shan laulayi, duk ta rame sai ido ta ƙara fari kamar ba ta da jini Sulaihat ɗin Anty Bahijja kan je ta yinin mata suma kuma suna zuwa sannan kuma ga Yallaɓai. Sai dai ya yi kusan kwana goma a gidan Gimbiya sannan ya dawo nan lokacin ta ji sauƙi sosai ta na cin abinci kuma ta ɗan ayyukanta sai ɗan abin da ba a rasa ba.   A washegarin ranar da ya dawo gidana karfe huɗu na asuba wayar Gimbiya ta tashe mu ta na kuka wiwi da cewa cikinta a firgice Yallaɓai ya dau mota ya tafi can gida ni kuma ya bar ni a gida amma duk na damu ni na ma kira shi wajen shiddan safe na ji yadda ake ciki sai ya ce min ciwon mara ne ya turƙeta an ba ta gado kuma likita ya ce za a ba ta bed rest saboda cikin jikinta ya samu rauni zai iya zubewa a kowani lokaci yadda na ga hankalin Yallaɓai ya tashi ne ya sa na ɗan kwantar masa da hankali. Nima yara na tafiya makaranta na taho asibitin duk da dai ita Gimbiyar ba za ta ci komai ba yanzu amma na je da kayan tea da ruwan zafi ko da na je na iske Anty Bahijja da Maman farko a asibitin. *Janafty* *TKG015* Maman Farko ce kawai ta sakar min fuska to sai Yallaɓan amma Anty Bahijja ina gaishe ta ma kamar ina faɗa mata cuta a daƙune ta amsa ni. Na zo na iske an kai Gimbiya ɗakin hutu an yi mata kuma alluran barci amma ba su fara ba da izinin a shiga a ganta ba. Muna asibitin Anty Bahijja ta kira mutane ba adadi ta na faɗa musu Gimbiya na asibiti ina ga ko suna tambayan ta cikin ne? Sai ta ɗaga murya ta na faɗin. "Ciwon mara ne ya turƙeta. Cikin na nan ba abin da ya same shi amma sun ce za su ba ta bedrest ta huta sosai." Ni dai ina gefe zaune kusa da Maman farko Yallaɓai ya tafi gida ya je ya yi wanka ya dawo. Ita Nene da Maman farko suka yi waya ta na faɗa mata halin da ake ciki, bayan sun gama ne ta kalle ni zaune da kwandon da na sako kayan tea da ruwan zafi a gabana kamar wata marainiya sai ta kira sunana na ɗago ina amsawa. "Sannu da ƙokari Sadiya." Sai na amsa ina jinjina mata kai. Ai dole ta gaisheni na zo asibiti na yi zaman dabas saboda kishiya amma sai na duba Yallaɓai da ita kanta Gimbiya sai na saka a raina zan yi domin Allah domin kirkinta saboda ana ganin ban zo ba kafin kowa ya yi magana Anty Bahijja za ta fara yi da ni. Kafin kace kwabo an cika asibitin nan ni dai bayan azahar na koma gida tun da har lokacin ba ta farka ba kawai sai na yi musu sallama na koma gida Yallaɓai kuma ya dawo asibitin amma ya sake fita ya ce akwai mutane a office suna jiran shi sai da ya dawo da daddare ya ke faɗa min Gimbiya ta farka jikinta da sauƙi. "Allah ya ƙara mata lafiya." "Amin Amin." Sai na kalle shi ganin ya yi wani shuru haka ya na cin abinci sannu sannu. "To wa zai kwana da ita? "Maman farko aka bari da ita." Sai na jinjina kai ban yi magana ba amma a raina sai na ɗauka ai Anty Bahijja ce za ta tsaya ta kwana yadda ta ke nuna kamar ita ce ta haifi Gimbiyar ma. Washegari ma da safe yara na tafiya makaranta tare muka tafi asibitin da Yallaɓai ni na kai ma Maman farko abin karyawa har muka iske Gimbiyar ta na kwance amma idanunta biyu. "Sannu ya karfin jikin? Ta na ɗan mirmishi ta ce" Da sauƙi Madam ina su Jidda? Sai na ce suna makaranta amma sun ce a gaisheta ta amsa ta ɗan yamutsa fuska. Ni da Maman Farko waje muka fita muka ba su waje muna ta ma hira da ita. Ta ce min ai ta ji sauƙi matsalan ba ta son cin abincin Tea kawai ta sha jiya kuma a jiyan ta amayar dashi. "Topha. Subhanallah to yanzu me ta ke son ta ci? "Ban sani ba. komai a ka ce sai ta ce ba ta ci. Laulayin ta mai zafi ne sai dai fatan Allah ya sa a rabu lafiya." Na amsa da Amin Amin ban wani daɗe ba. Amma dai anan Yallaɓai ya bar ni ya tafi office ni kuma zuwan Anty Maimuna ya sa na yi musu sallama na koma gida da daddare ma na yi girki na ce Yallabai ya ɗauka ya kai ma Maman farko bayan ya je ya dawo shima ƙorafin da ya ke yi min kenan na rashin cin abincin Gimbiya sai na bashi shawaran ya samu likita da mganar. Ɗayan washegarin da safe ban koma ba shi kaɗai ya tafi da abin karyawa bayan ya dawo ne ya ce likitan ya ce masa ya tambayeta ko akwai wani abin da ta ke so ne in ta faɗa sai a dafo mata shi a kawo mata, ya na faɗa min ta ce ita faten tsaki ta ke so mai yakuwa. "Ikon Allah.." Na faɗa ina kallon shi. "Wallahi wai fanten yakuwa." Ina ƴar dariya na ce" Ina ko da bushasshiyar yakuwa da mai kitsona ta kawo min tsaki ma kamar ina dashi." Sai ya kalleni nima shi na kallah ban yi magana ba saboda na ga kamar ya na so ya yi magana. "Yallaɓai." "Uhm" Ya amsa a ƙasan maƙoshi ya na zaune a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ni kuma zaune na ke a hannun kujeran. "Mene ne? Ko kana son wani abu ne? Domin sai na ga kamar ya na so ya yi magana amma kuma ya kasa furta abin da ke zuciyarsa. "In roƙe ki alfarma? Sai na gyaɗa masa kai kafin na ce" Ba alfarma tsakaninmu Yallaɓai sai dai mutumtatawa da martabawa. Ka yi umarni kawai zan yi maka duk abin da kake so in dai bai saɓa ma shari'a ba." Kai ya jinjina kafin ya ce" Ina so in ce ki taimaka ki yi ma Daugther faten don Allah sai kuma na ji kamar ina jin kunyar ki " Ya faɗa ya na kallona nima shi na kallah amma ban yi magana ba. "Don Allah Sadiya ta." Sai na basar ina ƴar dariya kafin na ce" Haba miye na wani don Allah? Zan yi mata in sha Allahu." "Na gode. Allah ya yi miki albarka Abar ƙaunata." Na amsa da Amin shi kuma sai ya ja hannuna ya na sumbatata. Bai jima ba ya yi min sallama ya fita har a cikin zuciya ban ji kishi ko wani abu ba da zuciyata ɗaya na yi ma Gimbiya faten nan da yamma yara suna dawowa makaranta na ce su shirya tare da su za mu je asibitin su gaishe da Antyn su saboda in dai na je sai ta tambaye su. A waya na kira shi na ce ya dawo da wuri na gama sannan mu tafi da yara asibiti tun a cikin wayar na ji muryan shi cikin farinciki bayan kuma da ya dawo bakin sa ya ƙi rufuwa. Bini bi ni sai ya yi ta min godiya na ce kar ya damu ai mun zama ɗaya. A daran muka je asibitin ni da shi da yara na kai mata faten mun iske ma Maman farko da Nene wanda suka zo tare da Hajiya da Musbahu anan ne na ji suna hiran mutanen Rano sun zo amma ba wacce ta kwana sun ce komai Gimbiya ta ke bukata ta samu ba amfanin zaman su ni ko a raina na ce ba shakka ita da ta ke da uwa a gindin murhu ai ba ta da matsala. Gimbiya ta ji daɗin faten nan ta sha da yawa ta rage ta ce na safe ne har da Nene a masu yi min godiya saboda Yallaɓai ke ba da labarin ya na zuwa ya faɗa min Gimbiya na son fate sai na ce ina da tsakin da yakuwa na kuma ce zan yi. "Sannu Sadiya kin kyauta." In ji Mimisco. "Ai Sadiya ba ruwanta nima nan kullum safiya ita ke fara kawo min abin karyawa da daddare ma za ta ba ma Tafida ya kawo min kuma sannan kullum sai ta zo asibitin nan." "Gaskiya ta kyauta. Allah ya ƙara muku zaman lafiya." "Amin Amin." Aka amsa gabaɗaya. Nene ce sai daga baya ta yi magana bayan na yi mata gaisuwan ta na dabam ina tambayan jikin ta. "Jiki da sauƙi na gode Sadiya da kulawa." "Allah ya ƙara miki lafiya." Ta amsa da Amin kafin ta ce na sunkuyo sai na duka a gabanta abin da ya sa hankalin waɗanda ke ɗakin ya dawo kan mu kenan "Sadiya." "Na'am." Na amsa ina mai kallonta kawai sai ta bubbuga kafaɗata ta na faɗin" Na gode Sadiya. Daman na faɗa miki ina da kyakyawan tsammani a kan ki sai gashi ina ta ji da ganin abin da daman na yi tsammani daga gare ki." Mirmishi kawai na yi ba tare da na yi magana ba sai kawai ta ƙara dan buga kafaɗata kafin ta ce. "Allah ya yi muku albarka gabaɗaya." Na amsa Amin a hankali suma na ɗakin suka amsa da Amin Amin sannan na tashi. Ina ɗagowa muna haɗa ido da Yallaɓai sai ya yi min mirmishi nima na mayar masa. Gimbiya kuma ta na tare da Baby a saman gadon suna ta hira. "Ke Baby sauko kar ki danne Antyn ta ki mana." Na faɗa ina kallon su da sauri Gimbiyar ta ce" Ƙyaleta ai ba ta matse ni ba." Maman farko na dariya ta ce" Ina ruwan Maimunatu ba ruwanta dai ba irin Jidda ba ce ita akwai baki " Mimisco ta ce" Jidda Tafida ne in suka so hira suna yi in suka so miskilanci suna yi. Baby kuma ta wani bangaren Sadiya ne ta wani bangaren ta ɗauko hallayan mai suna domin Maimu ma akwai surutu." Gabaɗaya muka yi dariya kuma haka ɗin ne, domin Anty Maimuna akwai mgana ita Anty Bahijja shisshigi ne da saka ido, muna asibitin har wajen goma har su Nene ma sai da suka riga mu tafiya da za mu tafi Gimbiya ta kalleni ta na faɗin" Na gode Madam. Faten ya yi daɗi" Ina mirmishi na ce" Ko? To ko gobe a sake yo miki wani ne? Kanta na ƙasa ta ce" In ba zai zama takura ba ina so." "Wani takura. Bakomai zan yo miki in kuma akwai wani abun da kike so ne ki faɗa min ko shi sai ya faɗa min sai na dafo miki." "To na gode." Ta faɗa ta na mirmishi. Daga shi har Maman Farko suna jin mu amma ba su yi magana ba suna ta dai mirmishi sallama muka yi musu Baby Yallaɓai sai da ya ɗauketa daga zuwa dubiya ta haye gadon asibiti ta na sharan barci. Bayan mun koma gida Yallaɓai sai wani nan nan ya ke yi da ni a raina na ce Namiji. Namiji sai shi wai saboda ina ma matarsa kirki shi ne na zama fara yanzu a idon shi haka ya riƙa nanike min da daddare ya saka mu ɓarnan ruwa haka ma bayan salla asuba shi dai kawai na lura ya na cikin farinciki har wani suna ya sauya min ya na maƙale murya da kirana Abar ƙauna a raina na ce daga baya kenan an yi sadaka da bazawara. Kamar yadda na yi alƙwari na sake yi mata faten Yallaɓai ya kai mata ta kirani ta na ta min godiya na ce bakomai ranar ban je asibitin ba sai washegari na iske Naja'atu da wasu ƙawayen Gimbiya har da abokan aikinta haka na ji Najan na faɗa ma Maman farko na dai shiga mun gaisa na fito domin na ga ana ta nuna ni, ko ba a yi mgana ba na san sai na fita za a ce ita ce kishiyar ta ki? Ranar ma mun sake haɗewa da Anty Bahijja ina kuma asibitin sai ga Ma'u ta zo tun ina mamakim munafunci Ma'u har na zo na daina amma ta ba ni mamaki da na ganta sanin ni dai ban faɗa ma kowa ba sai Ya Aina ita ma Marwa ce da muka yi waya na faɗa mata sai ta sanar da ita shi ne ta kira ta ji, har ta ce ko za ta yi ma su Ya Balki mgana ne su zo asibitin su duba ta na ce su yi zaman su ai ta ji sauƙi haba abin sai ya yi yawa gani ni ina ta zarya sai kuma na gayyato dangina. Na san za ta sani tun da ta na tare da Anty Bahijja amma zuwan na ta ne ya fi ba ni mamaki kuma ita kanta ta ɗan yi wani iri da ta ganni. Mun gaisa da ita sama sama ina mai mamakinta Anty Bahijja ta yi mata jagora zuwa ciki ba daɗewa sai ga su sun fito har da ma wasu ƙawayen Gimbiyar da ita Naja'atun a gabansu Anty Bahijja ta kalleni ta na faɗin. "Sadiya ashe ba ki faɗa ma kowa a gidanku Gimbiya ba ta da lafiya ba? Sai na kalleta amma ban yi magana ba saboda na ga renin wayan ne ya yi yawa. To Gimbiyar uwata ce da zan yi she ɗan ciwonta a dangi ko Yallaɓai ne ai sai na ga daman na faɗa ballantana ita. "Sai da na kira Ma'u ina ta mata tsiyan ba ta zo ba shi ne ta ke min rantsuwan ba ta sani ba. Kai tsaye na ce to laifin Sadiya ne wannan ita ce ba ta sanar da ku ba." Ma'u na yi ma wani kallo kafin na sauke kallona kan Anty Bahijja kafin na ce" Ban faɗa ba amma tun da ita ta sani gashi har ta zo na wakiltata ta sanar da su." Daga haka na juya fuskata ina kallon wani bangaren raina kawai na ji yana tafasa ji na ke yi kamar na je na shake Ma'u. "Ai ko zan faɗa ma su Ya Murja. Don dai dubiya mene a ciki? In sha Allahu na san za su zo" Ni dai ƙala ban ƙara ce musu ba har suka gama mganan da ƙawayen Gimbiyar za su tafi kamar Anty Bahijja ta kwanta musu haka ta raka su ta na yi musu godiya ni fa matar nan har mamakinta na ke yi, ba ta da yadda za ta yi dani ne da tuni ta saka an koreni Gimbiya ta mamaye komai sai dai kuma ta Allah ba ta ta ba na riga na zame mata ciwon ido. Ma'u da za ta tafi har da ba da kuɗi ina zaune ina ganin ikon Allah da ta yi min sallama ina ji amma ban amsa mata ba na haɗe rai suka fice ita da Anty Bahijja na raka su da harara kafin na ja tsaki. Ranar kafin na bar asibitin nan sai da raina ya ɓaci Anty Bahijja daga ganin sauran fate da na yi ma Gimbiya jiya ta ce a bata ta shanye ta fara faɗa ba fa komai ne za ta riƙa sha ko ci ba kar ta manta ta na da juna biyu kuma ta na ƙarkashin kulawan likito ci ne. "Ke Bahijja to ai fanten ne ta ke samu ya zauna mata. Kuma Sadiya ce ke yo mata ta na aikowa dashi wani zubin ma da kanta ta ke kawowa." "Koma wace ce dai bai kamata a barta ta sha ba. Abu tun jiya duk ya yi sanyi sai kuma a bar ta tasha? Ai sai ya jawo mata wani illar Allah na tuba" Sai ta ɗanɗana faten da sauri ta furzar ta na faɗin" Tabɗijan wannan kaifin tsamin kawai ya isa ya zubar da ciki." Ina tsaye a ɗakin ina kallonta kuma ina jin ta amma matar nan ba ta fasa yada min mgana ba. "Anty Bahijja ni na ke son tsamin fa.' Gimbiya ta faɗa a hankali ita Maman farko shuru ta yi ba ta ƙara mgana ba. "Kuma Likitoci sun ce ba wata matsala ko Mama? Naja'atu ta faɗa ta na mai kallon Maman farko da ta yi kamar ba ta ji ba saboda abin ya ba ta haushi. Amma Anty Bahijja ƙiri ƙiri ta hana Gimbiya shan faten nan ta ce ba za ta sha ba. "To wanne zan sha? "Ba dai fate ba. Zan saka Suhailat ta yo miki ba shikenan ba" Har Gimbiya sai da ta kalleta amma ba ta yi mgana ba. Nima ban ce komai ba na tattara kololina na saka a kwando na yi musu sallama shi ne Anty Bahijjan ta ke ce min" Ba raina ƙokarin ki na yi ba. An gode amma ya yi tsami da yawa ne kin gane? "Kar ki damu. Ki cigaba da yi mata mara tsamin wanda ba zai zubar da ciki ba." Ina gama faɗin haka na fice ina yi ma Maman farko sai anjuma ta amsa min da cewa na gaida gida. Muna tafe acikin adaidaita ina jin ƙuna a raina na kuma ce tunda shi alheri ya koma sharri shike nan kuma an gama daman ni saboda Allah na yi da kuma Yallaɓai amma tunda lamarin ya zo da cin mutumci an gama mgana. Tun daga ranar ban ƙara dafa wani abu da sunan Gimbiya ba amma kuma ban fasa kai ma Maman farko. Gimbiyar da kanta ta kirani a waya ta na bani haƙuri na ce kar ta damu bakomai. Kawai ranar da Gimbiya ta cika sati a asibiti sai ga kiran Yallaɓai a waya wai don Allah na taimaka na yi ma Gimbiya faten wake kai tsaye ba kwana kwana na ce. "Gaskiya ba zan yi ba Yallaɓai. Amma ka kira Anty Bahijja ta yi mata daga gidan ta." "Saboda mene? Ya tambaya cikin mamaki kai tsaye na ce" Saboda ba na son ƙananun mganganu ka kuma sanni ba ni da haƙuri kamar zawo na ke yi in raina ya ɓaci" "Me ya faru? "Komai ma ya faru. Na yo fate Anty Bahijja ta hana Gimbiya sha ta ce ya yi tsami da yawa wannan zai iya zubar mata ciki ma." "Ita Anty Bahijjan ta ce? "Ya wuce wai." Na faɗa ina kaɗa kafa kamar ya na ganina. "To ina ruwanki da ita? Ai ba don ita kike yi ba." "Don Allah na ke yi amma ba shi zai saka na zauna ana ci mun mutumci ba. Daga alheri sai ya koma tsiya kuma? Na ƙarishe faɗa a fusace shi kuma ganin na fusata ya sa ya sassauta murya ya na faɗin" Na ji to ki yi hakuri kin ji ko? "Na yi haƙuri amma girkin ne ba zan yi ba." "To ni ne na ce ko Daughter? Bai kamata ki damu da mganar Anty Bahijja kin san halinta." "Dole fa na damu. In wani abu ya zo ya faru ba fata ake yi ba mganganu suka tashi fa? Kasan ba zan zauna a ci zarafi ba in kuma na yi magana a ce na cika ƙorafi daga na ce an yi min kaza sai na ce an yi min kaza." Da gayya na daba masa mgana kuma na san ya san dashi na ke yo ina dalili daga abin arziki ban da ma ina da zuciyar Imani ni har wata kishiya ne zan zauna ina ma girki ina zuwa kai mata asibiti duk wannan sadaukarwan da na yi ba ta gani ba ta na neman ci min mutumci to ba ta isa ba mganin ayi ma to kar ma a fara shi. "Ki yi hakuri na ce ko? "Na faɗa maka na haƙura." "To za ki yi ɗin? "A'a." "Me ya sa? "Ai na faɗa maka dalilina." Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Duk na ji kuma zam mata mgana amma dai yanzu ki yi hakuri saboda ni saboda Daugther ki yi mata don Allah." Sai na yi shuru ban yi magana ba amma ina ta ƙunƙuni. "Abar ƙaunata ki yi don Allah. Ni na yarda dake shi ya sa a komai nawa na ke sakawa a ciki. Da gaske na ke ke ɗin amintattaciya ta ce Sadiya." Nan ma na yi masa shuru har dai ya gaji ya ce" Kin ji ko? "Na ji." "Za ki yi ɗin? "Uhm." Ina jin sautin mirmishin shi kafin ya ce" Yauwa Abar ƙaunata. Allah ya yi albarka." "Amin." Na amsa da Amin aciki ciki shi kuma har da yo min kiss ta cikin waya kafin ya ce" Sai na dawo." Ko amshi ban yi ba na kashe wayata ina ƙunƙuni ina dalili Yallaɓai na neman ya maida ni yar aikin matarsa daga abin arziƙi ban so yi ba amma haka nan na tashi zan yi mata ban kalli kowa ba sai shi. Mijina ne a kowani hali zan cika Umarninsa, ko faɗa muka yi da Yallaɓai sai dai na yi gaba dashi da kaurace masa amma ba na hana shi abinci zan yi masa komai da na saba, ina bin Umarnin shi saboda na san haƙƙin mijina a kaina shi ya sa na danne komai na yi mata fanten wake ya aiko da hanta da allayahu na saka mata a ciki da ya dawo bayan isha'i ya yi wanka ya ci abinci ya je ya kai mata a wayar ma ya kira ni ta karɓa ta na ta min godiya na ce mata bakomai an zama ɗaya. Bayan mun gama wayar na daɗe zaune ina tunani sai na tuna mganar Alhajinmu da ya ce na yi mata alheri na kuma zauna da ita da alheri in ma ta na da wani sharri Allah zai mayar mata da kayanta. Kuma ni dai ba ta min komai ba. Laifinta ɗaya ta aure min miji amma ko bayan auran ta na girmamani ta na sona ta na son ƴaƴana ko da ya ke dole ta so ƴaƴana tun da ta na son ubansu sannan nima ta na girmamani sosai sai dai kishi na yau da gobe amma ba zan ce ga wani laifin da ta taɓa yi min ba, tunanin haka ya sa na watsar da mganar Anty Bahijja a cikin raina kuma Yallaɓai in dai bai manta ba sai ya yi mata mgana daman gashi ba shiri ita ta saki nono ya kama akwai faɗan saƙo da saƙo a tsakanin su. Kafin Yallaɓai ya dawo Marwa na kira da wayar Ya Aina ina tambayanta yadda suke ciki da Kawu nan ta ke faɗa min ma gobe ya ce zai zo ya kawo mata waya ina dariya na ce" To Madalla haka na ke son ji." Ita kunya ya hana ta mgana sai Ya Aina ta ba ma wayar muka gaisa. "Ya jikin abokiyar zaman ki? Ɗazu Murja ta kira ni wai Ma'u ta faɗa mata kishiyarki ba ta da lafiya ta na kwance a asibiti ya kamata mu leƙa." Ban yi mamakin abin da Ma'u ta ce ba kuma ban yi ma Ya Aina munafunci ba kai tsaye na ce" Ya Aina kar ku wani zo don Allah ta ji sauki kuma ga ni ina zuwa Ma'un ma ta je duk bai isa ba! Sai kun zo? "Kuma fa haka ne. To shikenan kya mata sannu. " Na amsa mata da zan faɗa mata. "Me ke damun ta hala? "Ciki gare ta sai ya ɗan samu rauni an dai ce ta samu cikakken hutu." Ya Aina ta ce Allah ya ingata ya raba lafiya. Daga nan muka yo sallama ba daɗewa Yallaɓai ya dawo ya na faɗa min na ga yadda Gimbiya ta sha fanten waken nan kuwa? "Ko? Na faɗa ina kallon shi, ya na zama saman kujera ya ke sake faɗin" Wallahi. Ta yi ta santi ta ce na ƙara gode miki." "Ayya ai bakomai." Na faɗa kai tsaye akwai sauran ragowan faten wake sai na kawo ma Yallaɓai ya sha kaɗan sai ya ɗan sha ruwan zafi ko da ya dawo su Jidda sun yi barci ni da shi ne muka yi ta kallo muna hira sai wajen sha biyun dare muka kwanta. Da safiyar asabar ba makaranta Tahfez kuma yara sun makara ya sa na ce su haƙura sai gobe kawai. Yallaɓai ya fita ba daɗewa sai ga shi ya dawo ina kitchen ina wanke wanke Saude ba ta nan sun je ƙauyen Gwarzo biki, Jidda na can ɗakin su na ce ta gyara Baby kuma na gaban Tibi ta na kallon Cartoon Ashe mantuwa ya yi ya dawo ɗauka a lokacin ne ya ke faɗa min suna saka rai yau ko gobe za a sallami Gimbiya na ce Allah ya sa domin ta fi sati a asibitin kuma ta ji sauƙi alhamdulillah. Ranar ban ma saka a raina zan je asibitin ba sai da Hauwa ta zo ta ce ba ta je ba, saboda ba ta nan taje Rano, jin haka ya sa na ce bari na shirya muje tare har ma Hauwa ta kira Munnira ita kuma sai ta ce shekarajiya Jamila ta biyo mata suka je amma tun da za mu je ba ri ta shirya mu jira ta sai mu tafi gabaɗaya. Haka ko aka yi sai da muka jira ta ta zo muka tafi tare na bar ma Jidda gidan ita da Baby. Mun je mun iske asibitin cike da mutane su Anty Bahijja ne da su Anty Maimuna. Halima Suwaiba, Nasara sai Jawaherr da ta ce jiya ta zo gida hutun semister, Maman farko ba ta nan ta koma gida ta yi wanka ta huta, mun gaggaisa da kowa da kowa cikin sakewa amma ita Anty Bahijja sai da ta saƙa mana mgana. "Uwargida da tawagan ta." Ta faɗa ta na dariya ni na san da sigan cin mutumci ne ta yi maaganar shi ya sa nima na mayar mata da martani. "Uhm Anty Bahijja yar tawagan Amarya kuma ba " To zan zauna ne ta na gaya min mgana me na yi mata? Da na faɗi haka sai ta wayance da dariya aka yi dariyan gabaɗaya kowa na ciki na ciki mun gaisa da Gimbiyar ta ji sauki itama ta sake faɗa min yau ko gobe likita ya ce za a sallameta na ce Allah ya ƙara lafiya. An cika ɗakin ana ta hira shi ne ma muka ji Anty Bahijja na waya da Hajiyar Tafida ana mganar wanda za a samo daga rano zai zauna tare da Gimbiya amma kamar ba a samu ba kowa na da iyalai da abin yi, bayan ta gama wayar ta kalli Anty Maimuna ta na faɗin" Kin ji ita kanta Baaba Asma'un da na hango ba ta da lafiya.' "Topha. Ba dai a samu mai zuwa ya zauna da itan ba kenan? "Ba a samu ba kam." "To ta koma wajen Nene kawai ta zauna ba shike nan ba." Anty Bahijja ta ce" Nima haka na ce da farko to kin san halin Tafida da taurin kai ya ce wai Nene na fama da kanta itama. Kuma na kawo hujjan ga su Maman farko ga iya ai duk za su kula da ita ya ce a'a a samo wacce za ta zauna da ita." "Wallahi kuwa. To da ya ce bai yarda ba yanzu da ba a samu mai zaman ba ya zai yi? "Shi dai ya sani. Abin haushin ma ita Mimisco ta goya masa baya. Shi fa shegen nuna iko ne da shi." Ni dai ina gefe in jin su ban tofa ba daga karshe ma ni da Hauwa muka fara tafiya salla tun da ana ta kiran sallar azahar Munnira ba ta yi ta na hutu shi ya sa ba ta biyo mu ba. Bayan ma mun idar da sallar mun zauna a wajen cikin asibitin muna ta hira da Hauwa. Ta na gaya min ba in da labarin cikin Gimbiya bai za ga ba na ce ai ya za ga tun da su Anty Bahijja na raye. "Ji fa suke yi kamar Tafida bai taɓa haihuwa ba sai yanzu." Ina murmishin takaici kafin na ce" Bai taɓa ba mana. Ni ai bare ce saboda haka ƴaƴana ma bare ne. Ita kuma ta su ce haka ma ƴaƴan da za ta haifa ma kin ga ai na su ne." Hauwa ta rike baki kafin ta ce" Lalle kam" Ban ƙara mgana ba amma ina ƙokarin danne wani abu dake ta so min a ƙasan zuciyata. Bayan mun koma ɗakin har dai lokacin Anty Bahijja na ta buge bugen waya amma ba a dace ba. To kowa na da abin yi wata mata ce za ta yarda a ɗaukota a zaunar da ita waje ɗaya sama da wata ɗaya tun da na ji Halima na faɗin likita ya ce bedrest za ta yi na sati biyar ko botiki ba a yarda ta ɗauka ba ai neman mai zaman akwai wahala Yallaɓai kuma ba mace ba ne ballatana su ce ya zauna ya kula da ita dole dai ƙanwar naƙi wata macen za su nema. Har muka baro asibitin gabda mangariba ba a dace ba ina jin Anty Maimuna har Nene ta kira ta na faɗa mata ba a samu mai zama ba kowa suka kira sai ya ce ga uzurin shi kila Nenen ta ce a dawo da Gimbiyar wajenta sai na ji ta na cewa. "To Nene Tafidan ya hana. Sai dai ki yi masa mgana ƙila ke ya saurare ki." Daga karshe na ji ta na cewa to shikenan. Mun rabu da su Hauwa a bakin asibiti na hau adaidaita zuwa gida ban san abin da ya faru ba, can bayan isha'i Yallaɓai ya na dawowa wanka kawai ya yi ko abinci bai ci ya ce mu je ɗaki zai yi magana da ni, ina falo ne ma ina koya ma Baby aikin da aka ba ta a makaranta da na ce ma ya bari mu gani sai gani na yi ya ƙariso ya kama hannuna ya mikar da ni tsaye ya kuma nufi har korido ya na faɗin. "Ƙarisa mata aikin Jidda." "To Abba." Ta faɗa cikin sanyin ta damam ta na gefe itama ta na yin nata. "Mene ne ya faru Yallaɓai? Na faɗa ina biye da shi a baya bai direni ko'ina ba sai da muka shiga cikin bedroom ɗin mu, kan gado ya zaunar da ni tun da na ga ya jawo stool ɗin madubi ya zauna na san akwai mgana ko wani abu ya faru. "Mene ne ya faru Yallaɓai? Ka fara ba ni tsoro." Na faɗa ina kallon shi ganin kamar ba ya cikin natsuwarsa. "Sadiya." "Na'am me ya faru? Na amsa shi a gaggauce sai ya sauke ajiyar zuciya ya riƙe hannayena duka biyu tun da na ga haka jikina ya ba ni cutavta Yallaɓai zai yi tun da na ga wannan ladabin na shi. "Me kake so? Na katse mishi tunani sai ya ɗago yana kallona kafin ya ce" Alfarma zan ƙara roƙa a wajen ki." "Ina jin ka" "Kin san ina sonki ko Sadiya ta? "Na san wannan ka tafi kai tsaye? Me kake son na yi maka? "Izinin ki na ke nema." "Izini kuma? Izinin me? Na faɗa cikin ƙanƙance ido ina kallon Yallaɓai. "Ina so Daughtet ta dawo gidan nan da zama" Sai na zaro ido ina kallon shi cikin mamakin kalaman shi. "Nufina na ɗan lokaci saboda kin san dai na faɗa miki dokar likita ko? To ba a samu wacce za ta je gidanta domin ta zauna da ita ba. An ce ta koma wajen Nene ni kuma na ce a'a Nene ma ba ta da lafiya sai na yi tunanin duk duniya bayan iyayena ba ni da kamarki. Za ki kula da Daugther a gaban idona haka kuma za ki kulata da ita a bayan ido na shi ya sa na yanke shawaran za ta dawo nan gidan ta zauna tare damu har ta fita daga dokar likitoci." Har ya gama mgana kallon shi na ke yi cikin mamaki. To yanzu kuma abin da ke shirin tunkaro ni kenab? Gimbiya a gidana? Ban taɓa tunanin haka ba shi ya sa na zama kawai ina kallon Yallaɓai na kasa mgana." "Ki yi magana mana Sadiya." Ya faɗa ya na matse hannayena cikin na shi. "Me kake so na ce? Ka na so na ce a'a ne? Na faɗa ina kallon shi sai ya yi saurin girgiza kai kafin ya samu zarafin mgana na tare shi da cewa" Na ce a'a mutane su je su ce kai da gidan ka na hana ka yin abin da kake so? "Ba haka ba ne. Haƙƙin ki ne na sanar da ke. Kuma muhimmanci ki ne ya sa na ce ta zo gidan ki ta zauna tare damu." Kallon shi kawai na ke yi na ma kasa mgana saboda mamaki. "Aiki zan riƙa yi ma matarka Yallaɓai? "Aiki kuma? Haba wani irin aiki kuma? Ko ni da na gina gidan nan da sunan ki na gina shi saboda haka duk wacce za ta zo ta zauna alfarman ki za ta ci. Ita Daugther rigar alfarman da kika yi min za ta shiga ciki amma in har kin ce a'a shike nan ba ni da zabi sai ta koma Rano kawai." "Ka san zan iya cewa a'a me ya sa ka kawo mini mganar? "Na san ma ba za ki ce Aa ɗin ba ne shi ya sa." Shuru kawai na yi ban yi mgana ba, uhm ni fa namiji ya daina mamaki ya zo ya na yaudarata da mgana yanzu na ce ban yarda ba magana ta fita a gari a ce na hana ta zama a gidan mijinta gida ba na uwata ba kuma ba na ubana ba. Gidan shi ne ya na da damar da ko kare ya kawo ya sauke ba zan yi magana ba. Abu ɗaya ne ba zan ɗauka cin zarafi da wulakanci. Sai na kalle shi na ga shima ni ya ke kallo ya na jiran ya ji me zan ce. "Shike nan bakomai ai gidan ka ne itama gidanta ne." Na faɗa ina danne wani abu daga ƙasan zuciya. Rumgumeni ya yi daga zaunan ya na faɗin" Na gode Abar ƙaunata" Kallon shi kawai na yi ba tare da na yi masa mgana ba. "Amma ina da mgana." Sai ya ɗago ya na kallona ni kuma sai na gyara zama ina faɗin" Ta zo ta zauna ban damu ko yau ko gobe ko sai ta shekara ko kuma anan ɗin ma zata zauna gabaɗaya ba. Ai gidan ka ne itama tana da iko da shi saboda haka ba ni da hurumin na ce wani abu akan haka, abu ɗaya ne ba zan ɗauka ba a zo har gidana a ce za a ci min mutumci, in hakan ya faru ba zan yi shuru ka san halina ba ni da hakuri matukar aka taɓa min mutumcina." "In sha Allahu ba abin da zai faru. Daughter tana girmamaki ina da tabbacin ba abin da zai faru." "To wai kar ma ya farun ne na yi mgana ka ce na cika cewa an yi min kaza." "Ba zai faru ba in sha Allahu.".. Ya faɗa ya na min mirmishi. Hannuna na zare a na shi kafin na miƙe ina faɗin" Wani ɗaki za mu sauke ta? "Wanda kika ce Madam" Sai na kalle shi kafin na ce" Ko ɗakin nan nawa na baƙi? Tun da kusa ne da namu." "Ba matsala? "Babu mana." "To shike nan a yi haka ɗin." Sai na jinJina kai kafin na ce bari in na gama da yara sai na shiga na dan ƙara gyara ɗakin Sai ya riƙo hannuna na juyo ina kallon shi. Shima ya na kallona har ya na wani sauke ido. "Na gode Abar ƙaunata" "Yallaɓai ni kuma yaushe na koma Abar ƙaunar ka kuma? Ya na mirmishi ya miƙe ya rumgumeni ya na faɗin" Tun a ranar farko da na fara ɗora idanuwana a kan na san cewa tabbas ke ɗin Abar ƙaunar Yusuf ne." Ni dai ina ta dariyan yaudaran Yallaɓai saboda na yarda da zaman matarshi a gidana shi ne zai zaunar da ni ya na min ruwan kalamai. Kai jama' a Maza na abin da suke so ranar kusan raba dare muka yi muna hira da Yallaɓai da na yi magana jikinsa na rawa saboda wata macen sai na ke tunanin in da na yi boren ban yarda ba ya na gaba gaba wajen ci min mutumci ko ba a yau ɗin nan ba nan gaba sai ya yi min gori kuma dangin sa su ji labari su tsine min. Da safe ya ke faɗa min sun yi waya da Gimbiyar an yi ma sallama saboda haka yanzu daga nan asibitin zai je ya ɗauko su. Na ce to ni kuma zan ɗan kara gyara ɗakin. Wanka ya yi muka karya tare su Jidda sun tafi Tahfeez da wuri tun da jiya ba su je ba. Ɗan gyara gidan na yi na saka turare daman ɗakin da Gimbiyar za ta zauna tun jiya na gama gyara shi daman kuma a gyare ya ke sai dai ƙura. Karfe sha ɗaya da wani abu na safe na ji ƙaran buɗe get da shigowar mota. Ban fita ba domin ba zan iya zuwa tarban kishiya ba ai na yi iya abin da zan iya yi. Ina falon yara suka shigo Gimbiya ne da Anty Bahijjja sai Maman farko Yallaɓai daga baya ya shigo ɗauke da kayan su. Na karɓe su faram faram kamar yadda na saba na yi musu kuma jagora har ɗakin da zata sauka Maman farko na ta yi min sannu da godiya ina amsawa na je na kawo musu ruwa suka ce sun ƙoshi fita na yi na ba su waje Yallaɓai bai zauna ba ya fice tare da Maman farko da zai maida ta gida ita dai na rakata har haraba sai bayan tafiyar su ne na dawo cikin gida na yi zamana a falo can ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ta fito ta kalleni daga sama har ƙasa kafin ta ce. "Wai ashe kin ji haushin hana Gimbiya shan faten nan da kika yo mata ranar a asibiti Sadiya ? Na kalleta ban yi mata mgana ba sai ta cigaba da faɗin" Ni ban san kin ji haushi ni fa har a zuciyata ba da wata munafa na yi ba kawai sai ga shi kin turo Tafida ya zo ya na min faɗa tun da an taba uwarsa ba." "Ni ban turo shi ba." Na faɗa ina kauda kaina gefe sai ta basar kafin ta ce" Koma da mene ne ni ban ce haka domin na ci zarafin ki. gwara ma ki daina jin haushina." Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba to me zan ce? In yi magana ta ce na zageta ko na yo mata rashin kunya.. Ta gama zagayen gidan ta koma ciki ba daɗewa sai ga Naja'atu ta zo kamar kayan Gimbiyar ta je ta kwaso mata. Wajen uku na rana suka tafi lokacin har na gama abinci amma ba su tsaya sun ci ba Anty Bahijja har ta na ƙara jadaddamin likita ya ce ko botiki kar Gimbiya ta ɗaga ta rika cin wake da abinci mai allayahu, hutu kawai ta ke bukata kuma shi za ta yi, na ji tsoron Allah tun da dai Tafida ya na ce sai an kawo ta gidana na kula da ita sosai Mamaki bar bar ni na yi mgana ba har suka fice daga gidan. Na saki a tsaki a fili na ce" Tun da ni na yi mata cikin ba.' ko kuma ni mahaifata ba ta taɓa ɗaukan cikin ba." Daman ni na san za a rina an saci zanin mahaukaciya ko ita Gimbiya ba ta munana min ba irin su Anty Bahijja yan kanzagi ai za su munana min. Zuciyata na kai nesa na riƙa shiga ina duba Gimbiya ba saboda Anty Bahijja ba sai saboda Allah da kuma Yallaɓai. Na samu bayan ta ci abiinci ta sha mgani sai ta kwanta barci sai bayan la'asar ta tashi ta yi salla. Saboda ita na yi mana Tuwon semo da miyar kuka mai naman rago tun da ta ce min ta na so. Da yamma da su Jidda suka dawo makaranta ya sa sai ga ta fito falo ma muna ta hira da ita. Sai dare Yallaɓai ya dawo yadda ya ganmu tare ya sa bakin sa ya ƙi rufuwa sai washe haƙora ya ke yi ina lura da shi. Kamar magungunanta akwai na barci ta na sha ta ce min za ta shiga ta kwanta sai na ce ma Yallaɓai ya je wajenta ya kwana saboda makirci har ya na ce min. "Ba matsala." "Babu." Na amsa masa a takaice saboda ni nasan can ya ke son ya ce zai kwana kunya ce ta hana shi mgana. Ina gidan a gaban idanuwana Yallaɓai ya shige da Gimbiya ɗaki suka sakayo ƙofa sai da na yi kuka karshenta dai Jidda da Baby na ɗauko zuwa ɗaki na suka taya ni kwana amma ji na ke yi kamar ba zan iya ba. Muna gida ɗaya kusa da ɗakin juna amma Yallaɓai ba ya tare da ni ya na tare da wata matar ba ni ba, lalle mata suna ƙokari matan da ake yi musu kishiya suna zama da su a gida ɗaya ya tabbata za a kira su Jarumai. *Janafty* *TKG016* Tun dawowar Gimbiya gidana na ke ta ganin ikon Allah a wajen Yallaɓai da dangin shi, su rawan ƙafa shima rawan ƙafa, ni dai ina gefe ina ganin komai kamar al'amara kamar mafarki. A ce yau wai a gaban idanuwana Yallaɓai ke ririta wata macen ba ni ba, kuma a cikin gidana ƴan'uwansa ke zarya saboda wata ba ni ba. Rayuwa kenan abin da ya baka dariya wata rana shi zai koma ya na ba ka tsoro. Anty Bahijja ku san kullum sai ta zo gidan nan sai ka ce ni ɗin zan cutar da Gimbiyar ne. Kuma in ta zo ta riƙa bibiya kenan me Gimbiya ta ci? Kar a riƙa ba ta abincin da ba ta so kar a riƙa tashin ta daga barci in ta kwanta daga ta ce wannan sai ta ce wannan, ni dai ba na wahalar da kaina wajen mgana, saboda duk abin da zan faɗa ba shi zai sa komai ya koma yadda ya ke a baya ba shi ya sa kawai na kawo ido na saka musu daga shi har ƴan'uwan na shi. Abu ɗaya na ke yi shi ne ina girki sannan in zan dafa na kan shiga na ji ra'ayinta in ma na dafa abin da ba ta so in har ta ce min ga abin da ta ke so ina dafa mata ba zai gagare ni ba. Don Allah na ke yi don kuma ita da Yallaɓai sannan in ya fita ina shiga na duba ta in na ji ta shuru saboda kar wani abu ya faru a ce ai ina gidan amma ban sani ba, ba ta cika fitowa falo da rana ba sai dare shima sai Yallaɓai ya matsa mata, yara kuma suna shiga wajenta suna ɗeɓe mata kewa ni dai tsakanina da ita sai mutumtatawa na kama girmana na riƙe gam ko da na gani ɗin ba na ma nuna na gani ɗin amma domin ba a yin abubuwa ba ana yin abubuwa, kawai dai ina kauda kaina ne, in na ga Yallaɓai na wani ɓare ɓare a kan Gimbiya kawai kai na ke girgizawa, sannan nima sai ki ga ya na wani min rawan baki ba saboda komai ba ne saboda matarsa ce ya ga ta na zaune damu ina kula da ita da zuciya ɗaya. Kallon shi kawai na ke yi amma ni a idanuwana kar na ke kallon shi ba wani abin da Yallaɓai zai yi da ban gane manufarsa ba Allah na tuba ai jiya ba yau ba. Kowa ya ji Gimbiya na gidana sai ya yi mamaki Munnira ta doka min kira ta na min kumfar bakin a gida ne zan sama ma kishiya wajen zama ta na kwance ina yi mata aiki? Ina dariya na ce" To miye a ciki Munnira? "Akwai mana. Kuma miji ya kwana da ita? "E" Na faɗa ina dariya wata ashar ta laulayo da sai da na ce"Ke Munnira ko ni da haɗa iri da katsina ban iya wannan ashar ɗin ba." "Abin ne na ji kamar ma na yi zage zage" "Me ye a ciki? To ai ta aure shi to gida kuma don ta zauna ai duk abu ɗaya ne Munnira. Ni dai fata na mu rabu lafiya kawai " Duk yadda ta so ta nuna min kar na yarda ta zauna ba ta aiki kuma ina bata miji ban nuna na gane ba, ni yanzu me zai dame ni? Abin da na ke ma gudu da kishi tuni ya faru to me ya yi saura? Ciki gare ta fa kuma cikin ba na kowa ba sai na Yallaɓai to me ya yi saura? Babu saboda haka mganar gida ko kwana ƙaramin abu ne a waje na tunda na iya hakuri na bari muka raba mijin da ita ai kuma an gama mgana. Daman ni a raina na yi niyyar na ce Yallaɓai ya yi sati a ɗakin Gimbiya ban dai riga na furta masa ba amma ina da niyyar haka har a cikin raina. Ranar da ya cika kwana uku a ɗakin Gimbiya ina shirin sai ya dawo da daddare na ce masa kawai ya yi mata sati kafin ya dawo wajena amma sai na ga da safiyar Allah Yallaɓai ya fito min da munafuci wai ni Yallabai zai mayar ƙaramar yarinya muna karyawa a saman dining ni da shi yara sun tafi makaranta. Gimbiya kuma ta na ciki ba ta tashi ba tukunna. Sai ya kalleni ya na min duniyan cin da ya koya tun da ya yi aure nan. "Abar ƙaunata." Sai na kalle shi amma ban yi magana ba. "Na gode." "Wannan godiyar fa? "Ta ki ce, ki karɓa da martabawa." Sai na yi mirmishii kafin na ce" To shike nan na karɓa." Tun da na ga yanayin shi na san cewa tabbas wani abu ya ke so, shi ya sa sai wani kashe murya ya ke yi ya na wani ja na da hira, sai faɗa min ya ke yi yanzu kwangila biyu ne a kan tuburin shi akwai na gina wani ƙaramin ma'aikata sannan akwai ma na Kaduna again faɗa min ya ke yi wattanin nan ya na ta samun aiki sai godiya. "Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ya kuma ba da sa'a." Ya amsa min da Amin ya na faɗa min zuwa gaba in komai ya dai dai ta, ya na so shima ya gina kamfanin shi ko ƙarami ne kafin zuwa gaba, ni kuma sai na ce ai hakan ya yi saboda komai na son cigaba, kuma babbar cigaba ne a gare shi tun da ya na samun manyan kwangiloli mun daɗe muna tattauna abin da ya shafi aiki sannan muka ganganro kan maganar Gimbiya wai ni Yallaɓai zai zaunar ya na kallo na ya na min bariki da munafuncin su na maza. "Ina faɗa miki jiya fa Daugther sai ciwon ciki cikin dare." "Subhanallah me ya faru? "Ni ma ban sani ba, ta ɗan yi kukan cikin ne amma ina ba ta mganinta sai kuma ya lafa sannan ta yi barci." "Allah ya ƙara lafiya. Ko dai za ku je asibiti ne? Sai ya girgiza min kai kafin ya ce" Na ce mu je asibiti ta ce min wai cikin ya bari." Sai na kalle shi amma ban yi mgana ba sai na ji ya cigaba da cewa" Ni tunani ma dare Sadiya. Amma dai na ce ga waya nan tun da muna tare in wani abu ya faru kawai sai ta kira ni ko? Ƙura masa ido na yi ina kallon shi sai ya ƙara cewa" Ko? Na ce ai ga waya ma da ta ji wani abu ta kirani ko ta kira ki." Har Yallaɓai ya gama lissafin kwanakin shi ya ƙare a ɗakin Gimbiya ba ya so ya ce min zai riƙa kwana a can saboda kar cikin dare wani abu ya faru kai tsaye shi ne zai shiryamin alaye kamar ni ɗin ƙaramar yarinya ce. "Ba ki ce komai ba? Ya faɗa ya na goge bakin shi da Tissue, sai na yi masa wani irin kallo kafin na yi mirmishi. "Me zan ce! Ai ba sai ta kai ga haka ba. Daman ina shirin na faɗa maka cewa ka yi zaman ka a ɗakin Gimbiya har ta samu lafiya ta koma gidan ta." "Saboda mene? Ya faɗa ya na kallona irin me ya sa kika min haka ɗin nan. "Saboda cikin dare mana? Ba fata mu ke yi ba in wani abu ya faru kiran waya zai yi wahala gwara dai ka na kusa ɗin zai fi." "Ban gane ba." Ya faɗa ya na kallona ni kuma sai na miƙe ina tattara kwanakun da muka yi amfani da su lokaci ɗaya ina faɗin" Shi ne na ce ka cigaba kawai da kwana tare da ita har ta samu lafiya ta koma gidan ta." Ina gama faɗin haka na kwashi kayan hannuna na bar masa falon, ni sai ma ya ba ni dariya daman wai Yallaɓai ya iya alayen magana haka? Ai ban taɓa sani ba sai yau ƙwalla suka cika min ƙwarmin idanuwana yau har an yi lokacin da Yallaɓai ba ya son kwana dani sai da wata macen. Har an zo gabar da zai ji gwara ya riƙa kwana da mataras sama da ni. Ni ce fa Sadiya. Sadiyar shi da ban taɓa tunanin wata rana da za ta so Yallaɓai ya ririta wata mace bayan ni ba, sai ga shi ya na faruwa a lokacin kusan ma da ban yi tunani ba. Ina kitchen din ya biyo ni ya na borin kunya. To borin kunya mana Yallaɓai ya kalli tsabar idanuwana ya na faɗin" ban gane na koma wajen ta gabaɗaya ba? Da wa kika yi shawara kafin ki yanke hukunci? Ni ko na ce ai maganar ba ta bukatar shawara shi ya sa ban faɗa masa ba. Sai ya fara kunyata kan shi ya na faɗin" To ni ban amince ba. Ki ma bar wannan mganar." Shuru na yi masa kawai saboda ba na so maganar ta yi nisa. Ya zo ya rumgumeni ya sumbace ni a goshi ya na faɗin" Sai na dawo." Na yi masa fatan dawowa lafiya ina ganin shi sai da ya shiga ciki ya duba Gimbiya sannan ya fice, ina aiki ina danne abin da ke ta so min a ƙasan raina ina ƙara karfafama kaina gwiwan da komai ma zai wuce in sha Allahu, duk rashin son aikina yanzu na zage Saude na makaranta sai al'hamis zuwa lahadi ta ke zuwa. Ko kafin Gimbiya ta tashi barci na gama duka aikina har na yi wanka sai da na fita falo na ganta zaune muka gaisa cikin faram faram ɗin da muka saba. Maaganar abin da za ta karya na yi mata sai ta ce. "Madam in da zan samu kunu da na so." "Ina da sauran garin kunun ai bai ƙare ba sai na dama miki." "Na gode Allah ya saka da alheri." "Amin. Bakomai." Na faɗa ina kallonta, sai na ga ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa sai na dawo ina faɗin" Na manta ya jikin? Yallaɓai ɗazu ya ke faɗa min jiya cikin dare ciwon ciki ya taso miki.? Sai ta kalleni kafin ta yi mirmishi ta na faɗin" Laa ba fa wani abu ba ne, wai sai da ya faɗa miki? Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Allah ya ƙara lafiya. Ina fatan dai ba matsala? "Babu matsala, kawai cikina ne ya ɗan lalace amma ba matsala " "Ayya sannu. Allah ya ƙara lafiya" Ta amsa da Amin sai na ce ta kunna Tv mana zaman shuru ba daɗi sai ta ce ba ta son hayaniya. Sai na ƙyaleta na tafi kitchen na ɗora mata ruwan zafin sannan na ɗauko garin kunin na dama, tsamiyar tawa ma kaɗan ta rage ita kenan na yi mata amfani da shi har garin kunin ma ya ƙare daman Maman Saude ce na aika ma gero ta daka min dole itama zan ƙara yi ma mgana ta sake daka min tun da Gimbiya kokon ta ke sha ai saboda ita ne gero har tiya goma Yallaɓai ya siyo ya ijemin ni dai ya san ban cika shan kuni ba in dai ba azumi ba, zai yi wahala na sha kuni sai dai kuma in ba ni da lafiya Yallaɓai ma sai irin shekara bayan shekara gaskiya tun da na ga an kawo gero na san saboda wacce aka kawo shi. Bayan na dama mata ban saka mata siga ba saboda ba ta so na kuma kawo mata har falo, ta karɓa ta na ta min godiya. Mun ɗan zauna ni da ita muna ɗan taɓa hira sama sama kafin ta gama shan kokon ta ce min za ta je ta sha mgani ta ɗan kwanta na ce mata to. Tun da ta shige ciki sai ni kaɗai a gida sai can da rana sai ga Naja'atu ta zo itama muna gaisawa ta shige ciki, daman haka suke yi da sun zo domin ita daman suka zo za su shige ciki. Ni daman muna ta waya da mai hijabai za a kawo min wasu sannan na saka a ɗinka ma Amina domin ta ce ta yi talla ana so. To shi ne za a aika mata kaduna ni ma za'a aiko min dashi, da daddare tuwon shinkafa na yi miyar ganye Naja'atu sai mangariba Direba ya zo ɗaukanta ashe ƙasar za su bari ita da mijinta shi ya sa ta zo yi ma ƙawar ta ta sallama nima da suka fito ne Gimbiyar ta rako ta ta ke faɗa min na ce Allah ya tsare hanya. Yallaɓai ya ɗauka na bar maganar sai ga shi ya na dawowa, bayan ya shiga ɗaki na ya yi wanka ya fito falo ya ni da shi da yara har da Gimbiyar muna cin abinci ita kaɗan ta ci tuwon miyan ne ta ɗan sha da yawa. Ni da Yallaɓai ne muke hira ita kuma daman yara ne abokan maganarta, ban sanin musu ba amma ba ta sakin jiki ta yi hira da shi in dai ina wajen gwara shi ma ya na ɗan janta da mgana ita ce za ka ga ta na wani sunne kai, amma na san in sun shiga ciki ba za su rasa yin hiran su ba. Ni da Yallaɓai mun daɗe a falo muna kallo daman in dai ya ga ana Horror film sai ya ja ni ya ce mu kalla tare. Yara tuni sun shige ciki Gimbiya ma ana fara ta tashi ta ce ba ta kallon fina finan tsoro har ya na zolayanta da cewa" Ke ba Jaruma ba ce Daugther amma zan koya miki kallo kamar yadda na koyar da Sadiya ta." Banza da shi ta yi ta shige ciki ta na yi min sai da safe ta bar ni da shi ya na ta takalata da hira ni ma da na gaji sai na fara yi masa hammar ƙarya, na kuma ce masa ina jin barci zan je na kwanta har na miƙe sai na kalle shi kafin na ce. "Sai da safe." "Sai na shigo dai ko? Ya faɗa hankalin shi na wajen kallo. "Ka manta! Ai a ɗakin Gimbiya za ka kwana." Sai ya ɗago ya na kallona kafin ya ce" Ba na ce a bar mganar ba." "Ba za a barta ba. Domin da gaske na ke yi." Kallona ya yi ni kuma sai na juya ina ƙara faɗin" Mu kwana lafiya." Na yi wuceta ciki Tiolet na shiga na kama ruwa sannan na koma ɗaki na sauya kaya zuwa na barci ina shirin kwanciya sai ga shi ya shigo sai na kalle shi kafin na ce" Ba mun yi sallama ba? Karisa shigowa ɗakin ya yi ya na faɗin" Sadiya me ya sa kika yi hakan? "Saboda hakan ne ya kamata. Ba ta da lafiya gwara ka riƙa kwana a kusa da ita." Sai ya yi shuru bai yi mgana ni kuma sai na zauna a gefen gado ina faɗin" Kar ka damu ba matsala ni na ce ai ka je." "Kin tabbata ba matsala? Sai na kalleshi ina jin takaici in Yallaɓai ya yi min tambayar nan daman zai yi min kishiya ne ya ce min kuma ba matsala. Ban nuna masa ba illa ƴar dariya da na yi kafin na ce" Na ce ba matsala ka je kawai." "Na je bakomai? Sai na gyaɗa masa kai sai na ga ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Na gode. Allah ya tashe mu lafiya." "Amin." Takowa ya yi zuwa gaba na ya duƙa ya na sumbatar goshina. "Sadiya." Ya kira sunana na ɗago ina kallon shi kafin na yi mgana ya ce. "Sai da safe." "Sai da safe." Na mayar masa da martanin mganarsa har ya juya zai tafi sai gashi ya ƙara juyowa ya na kallona kafin ya ce" Ko za ki ɗauko yara ne? "Bar su kawai yau ni kaɗai zan kwana." Sai na ga ya kalleni ni wannam makircin na Yallaɓai ya fara ba ni dariya wai yau ya saba tafiya ya bar ni? Da ya ke barin gidan ma gabaɗaya fa? Duk bai yi haka ba sai yau. "Ka je kawai Yallaɓai bakomai" "Kin tabbata? Sai kawai na kwashe da dariya kafin na ce" To ko da wani abun akwai abin da za a fasa ne? Sai ya ware min ido ya na kallona ni kuma sai na cigaba da faɗin" Ba abin da zai canza Yallaɓai, mene ne a cikin kwana? Tun da na yi sharing ɗin ka da ita an gama mgana. Kwana a ɗakin ta ba zai rage ni ba kuma ba zai kare ni ba saboda haka ka je kawai sai da safe." Ina gama faɗin haka na koma na kwanta ina mai rufe kafafuwana da bargo har ina lumshe ido, shima ganin haka ya sa ya ja siraran kafafun shi ya fice na bi shi da kallo daga wutsiyar ido na sai da ya fice ya jawo min kofa sannan na sauke ajiyar zuciya ina mai ƙara jinjina halin Maza in suka ƙara aure. Na daɗe ban yi barci ba sai can kuma barcin ya ɗauke ni har sai da na makara domin sai bayan da Yallaɓai ya dawo sallar asuba sannan ya tashe ni a cewarsa ya ɗauka na tashi ne. Da safen ne bayan Gimbiya ta fito mun gaisa sai take ce min wai Yallaɓai ya ce na ce ya riƙa kwana a wajenta har ta koma na ce haka ne, sai ta kalle ni kafin ta ce " Ba komai ai na ji sauƙi wallahi." "Duk da haka dai gwara ya na kusa da ke." Ina kallonta ta na ta mirmishi amma ba ta ce komai ba a raina na ce munafukai to daga ita har shi ɗin suna ji da munafuci da gulma. Ranar an yi baki daga Rano, Yayarta Mardiya da wasu ƙannen Hajiyar Tafida suka zo duba ta, ni na yi musu girki suna ta min godiya Yayar tata har ɗaki ta same ni ta yi min godiya a kan yadda na ke kula da Gimbiya na ce bakomai ai an zama ɗaya sai La'asar suka bar nan zuwa gidan Nene. Ranar asabar kuma Anty Maimuna ce ta zo da yaran ta nan suka yini a ɗakin Gimbiya ni dai iyakata na girki na ba su shi ne aiki na sun ƙule a cikin ɗaki ana hira ana shewa saboda can da Yamma ma Anty Bahijja ta zo gidan. Ranar lahadi ma an yi baƙi ƙawayen Gimbiyar su biyu sun zo duba ta suna ta min taɓe taben fuska ni kuma ban ba su fuskar da za su rena ni ba ni da gidan mijina ba matar da ta isa. Suma ciki suka bi ta ranar ma Dambu na yi kuma sun ci sai la'asar suka tafi a daran ranar aka kawo min hijabai na Amina ma mun yi waya a ranar aka tura mata na ta. Washegari litini kuma ina da komawa asibiti kuma magunguna sun kare shi ya sa na shirya na ce ma Yallaɓai zan koma asibiti amsar da ya ba ni lokacin ta ƙara sakani mamakinsa. "To dole sai kin koma yau ɗin ne? "E zan koma saboda magunguna sun ƙare gabaɗaya." Sai na ga ya yi jim bai ce komai ba sai na gyara tsayuwa ina faɗin" Me ya faru? Lokacin ma wanka na ke shirin shiga shi kuma ya na zaune a saman gado ya na aiki a system ɗin shi. "Ina tunanin in kika tafi wa zai zauna da Daugther? Sai na buɗe ido ina kallon shi, daman ai a rina an saci zanin mahaukaciya. Kamar ya ɗauke ni aiki na kula masa da mata har da cewa ya na tunanin in na fita wa zai zauna da ita? Kamar wata jaririya mata ta ji sauƙi in ta yi baƙi ta na dariya da shewa in a waya ne haka zan ji ta na ta rera hira rai rei amma ya na faɗa min in na tafi wa zai zauna da ita. "Ko za ki ɗaga tafiyar ne zuwa Next week? Kallon shi na yi irin kallon ba ka da adalci, wato na fasa zuwa asibiti na zauna a gida saboda matarsa da na ciki. Kawai sai na juya na hau tuɓe kaya ƙala ban ce ba, shima bai yi mgana ba na jawo towel ɗina na saka na fice na bar masa ɗakin, ina wanka ina jin takaicin Yallaɓai. Gaskiya wasu mazan ba su da adalci, haka kurum na fa sa zuwa ganin likita saboda matarsa? Duk mutumcin da na yi masa baya gani. To lalle ko yau zai sha mamakina daman da safen nan bayan ya dawo kai yara makaranta Salisu ya yi tafiya shi ne ya shigo ɗaki na ya zauna da na yi magana sai ya ce wai ta kwanta barci ne ba ya so ya dame ta, ni kuma tun da likita bai ba ni hutu ba sai ya zo ni ya dame ni shi ya sa na haɗe raina ban sakin masa fuska ba sai da na yi masa mganar zuwa asibiti shi ne zai tare ni da mganar banza. Ko da na fito wanka baya ɗakin na yi tsaki a raina na ce shirme kawai. Agurguje na shirya na saka hijabina sabo dogo har ƙasa, na ɗauki jakata a hannu da takalmina ina fiowa sai ga shi ya fito daga ɗakin Gimbiya sai muka haɗe. "Sai ina kuma? Ya faɗa ya na kallona nima ko ina kallon shi na ce" In da na ce maka zan je" "Asibitin? Sai na ɗaga masa kai, na duƙa ina saka takalmi kafata na saka safa gajera na zamani na mata. "Ba ki fasa ba kenan? "Na faɗa maka magunguna na sun ƙare ya kamata na je." Bai ce komai ba, nima ban ƙara mgana ba, na raɓa ta gefen shi na shiga ɗakin Gimbiyar sai na ganta zaune a gefen gado ta na duba wayarta alamu dai ta ɗan jima da tashi. Gaisawa muka yi ina tambayanta jikin ta, ta ce min ta warke ba ta jin komai. "Allah ya sauwaƙe." "Amin Anguwa za ki je ne? "E asibiti zan je." "Ba ki da lafiya ne? Ta faɗa ta na kallona sai na yi mirmishi kafin na ce" A'a kawai dai zan je ganin likita ne." "Allah ya dawo dake lafiya." Na amsa mata da Amin. Kafin na ce" Akwai ragowan shinkar jiya na ɗumama miki sai ruwan zafi in za ki sha ruwan lipto" Sai ta amsa min da to shike nan. "Za dai ki iya zama ke kaɗai ba matsala ko? "Ba matsala na fa ji sauƙi Madam yadda na ke jin kaina ko aiki ma zan iya yi." Sai na yi ƴar dariya kafin na ce" Ai haka muke so. Amma aikin nan ba yanzu ba sai kin fita daga dokar likita." "To na gaji da zama waje ɗaya.' "Lokaci ne. Kar ki damu. Sai na dawo." Ta rako ni har falo sai na ga Yallaɓai zaune ya na kallo dining na nuna mishi ina faɗin" Ga abin karyawan ka nan" "Wa zai zauna da ita? Tambayar da ya ƙara jefa min kenan ni ko kai tsaye na ce. "Ba ga ka fa? Me ka ke yi? Sai ya sake kallona kafin ya yi magana na ce" Sai ka zauna da ita har na dawo tun da kana tsoron kar wani abu ya faru ko? Kunya ya ji ko nauyi ban sanin masa ba. Bai yi dai mgana ba sai ita ce ta kare mganar da cewa ita fa bakomai za ta iya zama ita kaɗai. Ni dai na wuce na bar su nan har ya na wani mikewa wai bari ya zo ya kai ni, na ko daba masa mgana ina cewa" A'a ka zauna kar ka barta ita kaɗai." Sai ya yi shuru ya kasa mgana na fita haraba shi ne ya biyo ni ya ba ni 5k da cewa in an rubuta mangaguna, na kira shi a waya sai ya yi min transfer. Da a raina na saka da wuri zan dawo gida amma tun da Yallaɓai ya ne mi raina min wayau na ce sai ya ganni shi ya zauna mana ai shi ya yi cikin ɗan renin wayau kawai. Na samu ganin Dr. Aisha da na ce mata maganina ya ƙare sai ta ce ba matsala. Ta tambayeni al'adata ya daidai ta ko har yanzu ya na min tsallake? Sai na ce gaskiya wattani biyu kenan normal sai ciwo mara amma wannan watan ya zo min da sauƙi. "Zan sake rubuta miki mgani guda ɗaya shima dai na dai daita jinin al'adan ne kamar wan can" Sai na amsa ta mata da to. Abin da ke zuciyata na faɗa mata. "Dr kina ganin zan sake haihuwa? Ba ta kalleni ba ta na rubutu a saman takarda lokaci ɗaya ta na faɗin" In sha Allahu" "Dr ni ko ɗaya ne na ƙara." Na faɗa cikin rauni sai da ta ba ni takardan da ta rubutamin mganin sannan ta ce" Me ya sa kike son ki ƙara haihuwa? Ba kina da wasu ƴa'ƴan ba.? "Ina da shi Dr amma dai ina so na ƙara ne saboda mijina mai son yara ne." "Ko dai kina da kishiyoyi ne ana rigiman magaji? Ta faɗa da sigan zolaya sai kawai na yi mirmishi kafin na ce" Ko ɗaya. Ai shi ya na da wata matar ciki ma gare ta kila ta haifa masa namijin. Ni kawai ina son na sake haihuwan ne Dr namiji ko mace duka ina so." " Zai ba ki in sha Allahu fiye ma da ɗayan. Ai na faɗa miki ba ki da wata matsalan da zai hana ki haihuwa. Lokaci ne kawai." Nima na yarda da lokaci ne, kuma lokacin ne bai yi ba, in ya yi zan ƙara haihuwa nima. Na tsaya a phamarcy cikin asibitin na siya maganin kuma sai da na kira Yallaɓai ya turamin Kuɗi duk da guda ɗaya ne, ni fa na saka a raina duk wani abu na haƙkin Yallaɓai na daina masa kara a kan shi in biyar ne sai na kira shi ya tura, sai da na hau adaidaita sannan na kira shi na ce zan biya gidan Ya Aina sai da ya yi jim kafin ya ce sai na dawo na san ya na so ya ce min na dawo da wuri ne ba fuska, na kusa gidan Ya Aina sai na ga ya turo min saƙo. "Ni fa na fita, Daughter ita kaɗai ce a gida. Don Allah ki koma gida da wuri." "Ba zan koma ba." Na faɗa a fili saboda haushi har mai adaidaitan sai da ya juya ya na kallona tsaki na ja na maida wayata jaka, a bakin titi na sauka na taka zuwa gidan Ya Aina sai dai ta ganni kwatsam ko da na je Marwa ba ta nan tana asibiti mun sha hira duk dai akan Marwa da Kawu Abba Ya Aina na faɗa min cewa ba matsala Marwa dai na so ya kuma kawo mata waya faskekeya ban ga dai wayar ba amma na ga kwalin wayar. Zuwan shi biyu kuma da alamu dai sun fara dai daita kan su da Marwa. "Ma sha Allah na ji daɗin haka." Na faɗa ina jin daɗi har cikin zuciyata. "Ai ya ce ba ya so a ja lokaci suna gama fahintar juna zai turo manyan shi." "Haka ake so. Allah ya nuna mana " Ta amsa da Amin mun cigaba da hira a cikin hiran ne ta ke faɗa min Murja fa ta sani. Cikin mamaki na ce" Ke kika faɗa mata? Sai ta ce e, ranar ta zo gidan ta iske Kawu ya zo kuma ranar ya kawo ma Marwa shi ne da ta tambaya ta faɗa mata. "Murja har ta na jin haushina wai Marwa ta samu miji ban faɗa musu ba, ni dai na yi ta ba ta haƙuri " Cikin mamaki na ce" Ikon Allah. Kamar an saka ranar ne ba su sani ba? Ya Aina ta ce ai na san halin Murja ni fa a raina na ji ban so Ya Murja ta sani ba, sai ta kai mganar gaba kuma shi ya ce sai sun dai daita ne manya za su sani ko Nene Yallaɓai ya ce bai faɗa mata ba saboda Kawun ne ya ce su dakata tukunna ban dai nuna ma Ya Aina wani abu ba ban jira dawowar Marwa ba na tafi gida wajen uku na rana saboda yara ba kuma saboda Matar Yallaɓai ba, ina hanyar komawa gida Yallaɓai na ta kiran wayata na ƙi dagawa sai da na koma Gimbiya ke ce min Ya na ta kiranta ya na tambayar ta ko na dawo sai na ce zan kira shi, na gane daman gidan ya ke so na koma shi ya sa da matarsa ta faɗa masa na dawo bai ƙara nema ba. Saboda haushin shi da na ke ji da wuri na kwanta na ce kaina na ciwo, na bar shi da yara da matarsa ko da ya dawo ina ciki kwance ya dai shigo ya duba ni. "Kin sha mgani? Na ce masa na sha ya na wani taɓa goshina da wuyana ni ko burgeni bai yi ba na ce masa barci na ke so na yi, na san in na tashi kaina zai daina sara min sai ya fice ya na mai rufomin ƙofa na raka shi da harara, ko washegari a dakune na tashi daga shi matar tashi na riƙa yi musu yatsina ai shima sai ya sha jinin jikinsa ya san halina da na fara haka to ya san an ɓata min rai ne sai ya kiyaye ne da wata mgana sai da ni da kaina na ba ma kaina haƙuri na sauko gabaɗaya. **** Kimanin satin Gimbiya uku a tare damu. Ta warke garas ba wata matsala muna kuma zaune lafiya ba abin da ya taɓa faruwa tsakanimmu amma fa ina ganin bariki domin tun da ta ji sauƙi ta fara shan gayu ana ma miji kwalliya da karairaya, da daddare kuma su shige ciki suna shagalinsu ni kuma ina nan ina musu wahala, duk ina gani fa amma na nuna ban gani ba, ni abin da ya ke ba ni mamaki shi ne Yallaɓai har zai iya tsawon sati biyu bai neme ni ba amma kuma bai damu ba, ni fa a da na ɗauka Yallabai ba zai iya kwana biyu ba ni ba sai ga shi ya wuce tunanina ko a jikinsa. An ce ciki ya samu rauni bedrest ta ke yi amma suna ɓarnan ruwa ni na sani kuma suna sun sam ni ba yarinya ba ce ba su isa su yi min wayau ba. Na faɗa ma zuciyata Yallaɓai ma ya daina ba ni mamaki, domin ko ajikinsa ya na cin amarcin sa, tun da ga boyi boyi sun samu a gida na dai lallashi kaina tun da sati biyar ne in ya cika ta koma gidan ta, ban ji ba kuma ban gani ba saboda haka can su ƙarata. Yau ta kama laraba ne, Gimbiya da Yallaɓai sun je asibiti bayan sun dawo ya kawo ta gida shi ya fita muna falo muna hira ta tashi ta shiga ciki shigan ta ba dafewa sai na ji ana buga get ina zuwa na buɗe sai na ga Inna Mariya ce ban yi mamakin ganin ta ba saboda daman shekaranjiya mun yi waya za ta aiko min da wani mganin gargajiya na sanyi wanda ke wanko mahaifa. Aneesa ɗiyarta ta yi aure shekaru bakwai ba haihuwa shi ta karɓo mata ta yi amfani da shi ga shi yanzu ta haihu shi ne da na ji na ce ina so. Mun yi waya za ta karɓo min amma ban ɗauka za ta zo da kanta ta kawo min ba. Muka shigo cikin gida tare ina mata sannu da zuwa na kawo mata ruwa da lemo. Lokacin sha biyu ta gota anan falon yara muka zauna ta fito min da mgamin ta na nuna min. Akwai wanda zan sha da koko akwai kuma na ruwa har da na cin a abinci. Ta ɗauko ƙullin mganin ta na nuna min ta na kuma faɗa min magungunar arraɓi ne a ciki haɗe haɗen ganyeyyeki, shi zan rika sha a koko ta ɗauko ɗayan ta na faɗin. "Wannan kuma a ruwa za ki saka. Ina mai tabbatar miki in sha Allahu za a da ce." Ni ban san Gimbiya ta fito ba, da ya ke muna falon yara ne ashe ta daɗe a tsaye ta na kallon mu sai Inna Mariya ce ta ganta sai ta yi min mgana a hankali ta na cewa bakuwa na yi? Sai na juya na ga Gimbiya ganin na ganta ya sa ta ƙariso abin da ya ba ni mamaki ganin ta na ta kallon magunguna da Inna Mariya ta kawo min ni kuma har ga Allah ban kawo komai ba sai na gabatar musu da juna. "Inna ta ce ƙanwar Mama. " Na faɗa ina kallon Gimbiya nan da nan ta rankwafa ta na gaishe ta. "Abokiyar zama na ne, ba ta jin daɗi ne sai ta zo ta na zaune damu na wani lokaci." Na faɗa ma Inna Mariya itama cikin fara'a ta amsa mata gaisuwa ta yi mata ya jiki. "Bari na shiga ciki tunda kin yi da baƙuwa" Sai na amsa mata sai bayan wucewarta ne Inna Mariya ta ce min" Ke Sadiya na ga ta na ta mana wani kallo ne? "Ba ta da wata matsala Inna" Sai ta jinjina kai kafin ta ce Allah ya sa ba ta wani daɗe ba na yi na yi ma ta tsaya ta yi sallar azahar ta ce min daga wajen karɓo min mganin ta wuto gidana ba za ta zauna ba, har haraba na rakata na ba ta kuɗin mota da kuɗin mganin da ta karɓo min ta ce 5k ne gabaɗaya mun yi sallama na dawo cikin gida na tattara mganin nawa na kai kabinet ɗin kitchen na ajiye na daga nan tiolet na shiga zan kama ruwa sai na ga jini yanzo min yanzu in zan yi al'ada ko ciwon mara ba na ji sai dai na gan shi cikin salama ba kamar baya ba, da sai ya yi watanni bai zo ba kuma bayan ya zo ya yi ta min wasa. Kawai sai na wanke fuskata na fito. Ban san abin da ya faru ranar Gimbiya ba ta sakar min fuska ba da na ma shiga duba ta a daƙile ta amsa min tun da na ga haka na kama kaina. Abinci ma da na shiga na ce ko na zubo mata ne sai cewa ta yi ta ƙoshi. Ni dai na ga ban yi mata wani abu ba amma duk da haka na yi mata uziri saboda ta na da ciki daman a san yanayin masu ciki sai a hankali shi ya sa ban saka komai a cikin raina ba. Na cigaba da harkan gaba na. Kwana biyu tsakani ranar asabar kenan Jidda ce kaɗai ta je tahfez Baby na gida ba ta jin daɗi. Awara na saka aka yo mana daga gidan su Saude to ba a kawo mana ba sai na tambayi Gimbiya me za ta ci na dafa mata? Sai ta ce fanten wake haka na miƙe na dafa mata fentan waken nan na zuba na kai mata, Saude ma na gidan ta kawo min awarar ni da Baby tun ya na ɗanyen shi na mu ke ci na fara suyan kenan sai na ji ƙara daga ɗakin Gimbiya kamar ta na kiran sunana, saboda sauri har ina wurgar da ludayin hannuna mai ya na zubar min a kafa amma ban ji zafi ba ni da Saude da Baby muka iske Gimbiya a jigace a bakin tiolet ta na ce min maranta na ciwo sannan kuma ta ga jini hankalina ya tashi na koma ɗaki da gudu na kira Yallaɓai a waya bai ɗauka ba sai kawai na ce Saude ta fita ta taro mana adaidaita mu je asibiti. Ni na taimaka mata ta saka Hijabi da takalmi ni Baby ce ma ta rarumomin hijabin Jidda na saka kafata da silaf ɗin tsakar gida, muka tafi asibiti Saude ta rufe mana gidan gabaɗaya muka tafi asibitin da ta kwanta da farko na kaita ina zuwa aka amsheta suka shiga da ita saboda ruɗewa ban ɗauko waya ta ba sannan ban ɗauko kuɗi ba sai da na fita haraban asibitin na ari wayar wata Nurse na saka lambar Yallaɓai na kira shi sai lokacin ya ɗauka hankalina tashe na faɗa masa ga halin da ake ciki ya ce muna wani asibti ne na faɗa masa ya ce ga shi nan zuwa. Shi ya fara zuwa kuma har lokacin likitoci ba su ce komai ba, shi ya kira Anty Bahijja ya faɗa mata ita kuma ta yaɗa ma Dangi Yadda Yallaɓai ya ga na ɗaga hankalina sai na bashi tausayina shi ya koma ya na lallashina da cewa ba abin da zai faru, a gigice Anty Bahijja ta zo asibitin kuma ta na nan aka kira Yallaɓai ofishin likita sai ta bishi ni ban san me ya faru a ciki ba ta dai fito ta na ta faɗan mganganu. "Ni fa shi ya sa tun farko ban so Gimbiya ta je gidan Sadiya ta zauna ba. Saboda ba kamar gida wajen Nene ba. Yanzu to ga shi nan an ce ta ci wani abu da cikinta ba ya so ta kusa yin ɓarin cikin jikinta." "Duk fa ba wata matsala ba ce. Tunda dai cikin na lafiya itama tana lafiya ai shikenan ko? Amma ba ta bar mganar ba, an kira ta a waya ta ɗauka ta na surutu ni dai na yi zaune shuru kawai ban yi mgana ba. "Sadiya me kika ba ma Gimbiya ta ci ya kusa saka ta ɓarin cikin ta? Tambayar ta zo min a ba za ta na ma kasa mgana, sai kawai na kalleta ma juya ina kallon Yallaɓai cikin rawan baki na ce" Ni ko me zan ba ta? Awara na saka aka yi mana yau shi ne ita Gimbiyar ta ce na dafa mata fenten wake kuma ai na saba dafa mata ta ci kuma ba a taɓa samun matsala ba." "Uhm Allah ya iya faten waken ne? Sai na ji raina ya ɓaci a fusace na miƙe ina faɗin" Me kike nufi da mganar ki? Ta ta so ta yi min mgana Yallabai ya tare ta da cewa" Don Allah Bahijja ki bar wannan mganar. Yau Daugther ke zaune da Sadiya? Kuma duk a baya komai bai faru ba sai yau? Za ta yi mgana ya sake tare da cewa ba ya son wata mgana kuma kar ya ƙara jin ta ƙara min wata tambaya ganin ya harzuƙa sai ta yi shuru ni kuma na koma na zauna ina tunanin manufar Anty Bahijja ko ta na zargina da ni ce na ba ta wani abu ta ci da ya sa ta shiga wannan halin? Lalle ne ma matar nan, ganin Yallaɓai ya tare mgamar ya sa nima na yi shuru, sai Allah ya sa ma Gimbiya ta farka lafiya cikin ma bai fita ba amma dai likita ya ce ya na cikin risk sai an kiyaye. Yallaɓai ya maida ni gida ni da Baby da Saude saboda su Anty Maimuna duk sun zo, har a cikin zuciyata na yi murna da ba abin da ya faru. Da wani abu ya faru ai da na shiga uku ashe na gudu ban tsira ba ne, kwanan Gimbiya uku a asibiti aka sallameta nan ta ke aka wuce da ita wajen Nene. Ban yi magana ba amma a raina na ce gwara haka can ɗin in wani abu ya faru sai su ce uwar su ce sila. Ni dai na ga tun ana gobe za a sallami Gimbiya da na je asibitin duk ba wacce ta yi min wata mgana amma na ga suna yi mini wani kallo har da Halima da ita kanta Gimbiyar ta sauya min sai ban kawo komai a raina ba shi ya sa ana sallamota na shirya washegari da safe na je Gwammaja daman mun yi da su Hauwa suma za su je duba ta sai na ce kawai mu haɗu a can. Musamman na yi dambun shinkafa da zogale sanin Nene na so ya sa na diɓa na tafin mata da shi na je Ɗakin Nene cike da su Anty Bahijja kaf da ƴaƴanta Anty Maimuna Halima, Su Suwaiba ina gidan Hauwa ta ƙariso daman na iske Munnira. Na shiga har ɗaki na gaida Nene na kuma kai mata Dambun da na zo da shi, ta karɓa ta yi godiya Bayan na fito na shiga ɗakin da Gimbiya ke ciki, su Anty Bahijja na ciki da na yi sallama ba wacce ta amsa har ita Gimbiya sannan suna ganina suka yi shuru. Na gaishe su suka amsa min a daƙile, Gimbiya ina cewa ya jiki ko kallona ba ta yi ba a laɓanta ta amsa da. "Da sauƙi." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin." Ta faɗa kamar ba ta so, sai jikina ya yi sanyi wulaƙanci ƙiri ƙiri suka yi min a ciki sai na fito na koma falo wajen su Hauwa ina ƙirkiran mirmishi ban nuna musu ma wani abu ya faru ba. muna zaune Anty Bahijja ta zo ta wuce ɗakin Nene ba jimawa sai ga shi ta fito da kulan Dambun da na kawo ma Nene muna ji Nene na ƙwala mata kira har sai da ta fito da kanta. "Bahijja magana fa na ke yi miki." "Nene ba za ki ci dambun nan ba fa Kawai ke ma ta saka miki mgani ta kashe mana ke kamar yadda ta so kashe abin da ke cikin Gimbiya. Tun da daman ita ɗin dangin asiri ne an saba shige shige." "Bahijja ba na ce ki bar mganar nan ba ne? Har ta na wani jijiyan wuya wajen faɗin" Nene to sai a ƙyaleta bayan kowa ya san gaskiya? Ta faɗa ta na hararana ni fa da farko ban ma gane in da ta dosa ba ne sai da na ga ta na kallona sannan na fara dawo da abin da ya faru tun shigowata gidan nan, ban san lokacin da na miƙe ba haka ma su Hauwa saboda sai yanzu na gane in da Anty Bahijja ta dosa. "Ban ga ne ba? A kan wa kike mgana? Na faɗa ina kallonta sai kawai a gabana ta ɗaga kulan dambun ta sake shi ta a ƙasa murfin ya buɗe dambun ya Zube ƙasa idanuwana har sun ƙanƙance saboda ɓacin rai. "Me kenan kika yi? "Abin da idanuwanki suka gane miki." Ta faɗa ta na kallona ai sai na ƙarisa gabanta Hauwa na riƙe min hannu na fizge ita kuma Munnira na faɗin"Subhanallah zubar da abinci me ya yi zafi Anty Bahijja? Sai gabaɗaya har su Gimbiyar suka fffito Nene kuma faɗi ta ke yi" Sadiya ƙyaleta kin ji." "Ke dai za ki faɗa min abin da kike nufi da zubar da abinci da na kawo. Sannan da mganganun da kike a kaina?waye zai kashe muku uwa? Sannan waye ya so kashe abin da ke cikin gimbiya? Sannan waye dangin asiri? Kar dai ki ce da ni ki ke ? Na faɗa ina kallonta domin har duhu duhu na fara gani, ni za a yi ma tijara a bainar na si, ni za a ƙulla ma sheri a ci mutumcina da mutumcin dangina "Na ce ina fatan ba da ni kike ba ko? "Da ke ake ko kina da mgana ne? Sai kawai na ƙura mata ido ina kallonta. "Kika ce da ni kike? Ni ce mai yin asirin? "Ke ce mana. Kin so zubar da cikin Gimbiya Allah ya fiki. Ai duk mun san komai. Mun san cewa Yayar mamanki asiri ta yi ma abokiyar zamanta kaikayi ya koma kan masheƙiya ta mutu cikin hauka, kowa ya san wannan labarin saboda asirinta ya tonu." Mamaki ya hana ni mgana, idanuwana sun kawo ruwa cikin rawam murya na ce" A ina kika ji wannan labarin? "A bakin da ba zai yi min ƙarya ba. Ma'u ce ta faɗa min ko za ta yi miki ƙarya ne? "Ma'u." Na maaimata sunan a saman laɓɓana. Na kasa ma yin wani motai bakina na rawa na kasa mgana jikina ba in da baya rawa zuciyata ina jin kamar za ta faso ƙirjina ta fito saboda halin da na ke ciki. "Ma'u fa? Ma'u ƴar uwata da muka taso tare ita ce za ta zo dangin mijina ta yi min ƙazafi. Daman na san wannan bini binin na ta ba na lafiya ba ne. Sai ta ga na tozarta sannan hankalinta zai kwanta. Lalle ko akwai yaƙin duniya na uku tsakanina da Ma'u da duk wanda ke da hannu wajen yi min wannan mummunan ƙazafin. *Janafty* *TKG017* "Bahijja kina mata wani sanyi sanyi ke Sadiya har mganin asirin suke kawo miki har gida. Gimbiya ta gan ki lokacin da ƙanwar mamanki ta kawo miki su har gida ko shima za ki ƙarya ta ne? Kalaman Anty Maimuna suka buga min kai kamar an dake ni da ƙarfe sai da na ji kaina ya yi dum na ɗago ina kallonta ba bakina ba har idanuwana suna rawa ne a lokacin. "Haba Anty Maimuna me ya sa haka? Hauwa ta faɗa kamar ta yi kuka Munnira kuma sai ta hau tafa hannu ta na faɗin" Yanzu me Sadiya ta yi muku da za ku yi mata wannan mummunan ƙazafin? Ni kuma Gimbiya na ke kallo cikin mamakinta ina so na tabbatar da gaske ita ce ta faɗi ta ga ƙanwar Mamana ta kawo min asiri? sai na ga ta kauda kaita alamun kenan da gaske ne. Sai kawai na ji na fara jijjiga ni kaɗai saboda ɓacin rai ranar da Inna Mariya ta zo kawo min mganin na dawo min a cikin idanuwa. Oh shi ya sa daman ta ce min ta ga ta na ta kallon mu? Kenan zargin ta kawo min asiri ta ke yi min tun da gashi har ta kawo labarin gaba. Kuma tunda ina shige shige kuma ina baƙin ciki da cikin da ke jikinta tun da ni ban taɓa haihuwa ba shi ya sa na ba ta mgani ta ci a abinci cikinta ya zube sai Allah ya fini asirina ya tonu cikin bai zube ba. Shi ne aka zauna aka tattauna gwara a turke ni a ci min mutumci, duk a lokaci ɗaya na gama hango abin da ya faru shi ya sa ban san na yi wata dariya ba sai da na ga ina yin ta cikin mamaki suke kallona Anty Bahijja na nuna da yatsa na ina faɗin. "Ba a haifi wani ɗa namijin da zan kauce ma Allah saboda shi ba Bahijja" "Kuma kika kaucen? "Tunda kin yarda na kauce kuma na yi asirin tun da kin ce ni yar na gada ce, sannan ma ai an ce an ga tabbaci me kike jira Bahijja? Na kira sunanta cikin tsawa kafin ta samu zarafin magana na zare mayafin jikina na ɗaure a kuguna ina faɗin "Na ce tunda kin samu tabbaci me kike jira? Ba sai ki ɗau mataki ba Bahijja? Na faɗa ina nuna ta da yatsa, Itama ta so min tana faɗin zan ko ga matakin da za ta ɗauka Hauwa da Munnira na rike ni ina fizgewa, ita ma Bahijja su Maimuna na riƙe ta Nene ma ta mgana ba wanda ya ji ta, Hayaniya ya sa har su Hajiya Iya da Maman farko sai da suka shigo lokacin Anty Bahijja na faɗin zan ga abin da zai faru. "Ba abin da zan gani sai alheri me zan gani? Ya wuce ki saka ƙanin ki ya sake ni? To sai me? Kaina farau zawarci ke in ba ki saka shi ya yi min saki uku ba tabbas ke Bahijja ba ki haufu cikin uwarki da uban ki ba." "Ke Sadiya ki yi shuru" In ji Maman farko Suwaiba na ja na ita da su Hauwa ta na faɗin" Sadiya mu je mu je Sadiya." "Ni kike zagi don uban ki Sadiya. Ni sa'ar ki ce? "An zage ki ɗin ke uwata ce da ba za ki zagu ba? Har ni za ki yi ma kazafi na so zubar da ciki? To ni na zubar da cikin gimbiya na ci riban me? Ko haihuwa ce ban taɓa yi ba da za ta zame min baƙuwa? Amma ba laifin ki ba ne, laifin wacce ta faɗa miki ne. Amma ina so ki sani da ke da wacce ta faɗa miki na rantse da wanda raina ke hannun shi sai na yi ƙaran ku a wajen hukuma." Daƙyar su Suwaiba suka fita da ni daga ɗakin Nene tana zagina ina zaginta. Itama ana riƙe ta tana cewa a sake ta, ta doke ni "Na ce ku sake ta mana ta zo ta ga in zan bugun mata ko wanda na ke aure bai isa ya doke ba ballantana ke banza a banza." Itama ana riƙe ta tana fizgewa faɗi ta ke yi wai ai ba ƙarya aka yi min ba. Ina shige shige na wanke gaba na ba ma Tafida ya sha da ba ya ganin laifina, na shanye musu ɗan'uwa ko auran shi ma da Gimbiya Allah ne ya fi ƙarfina shi ya sa aka yi auren. Ni ko na ce ita mijinta da yan'uwansa da ta shanye su sai abin da ta ce itama kenan gaban na na ta ta wanke ta ba shi ya sha kenan.? Sai ta fara haƙilon faɗin" Ai mu kowa ya san zuru'ar mu ba mu da tambarin bin bokaye kuma ba a ji labarin wata cikin ahalin ta mutu cikin hauka ba." Har ta na cewa na yi shige shige na na haɗa Kawu Abba da ɗiyar yayata saboda shima a shanye shi sai yadda aka ga dama dashi to na rubuta na ijiye ko ta ce bokan mu ya yi ƙarya Abba ba zai auri dangin masu asiri ba har ta na faɗin me aurena ya tsinana ma Tafida? Ni kuma na ce in ba ta saka ya sake ni ba, to ba ta haifu ba. "Kuma dangin asirin su Kawu Abba ya gani ya ce ya na so in Allah ya haɗa ki raba in kin isa " "Mata kin bi kwazzaba ma rayuwata a gidan aurene? Me na tsare miki? Zaman ki na ke yi! Ke da kika miƙe kafa a gidan na ki mijin wa ya takura miki? Ko kema shige shigen kike yi? Ke ki ce kina son ki ji daɗi a gidan wani da zuru'an wani amma kuma ke ce wata ba za ta zo na ku zuru'an ta ji daɗi ba? Ashe haka kike da son kan ki? To wallahi kin kure ni akan matakin da ba zan ɗauka ba tun da kin fito ta haka to nima zan fito miki ta bangaren da kika fito min ni da ke shege ka fasa Bahijja" "Sadiya ba ki da kunya? Bahijja ba yayar mijin ki ba ce? Anty Maimuna ke tare ni da faɗin haka har ta na shan gaba na, idanuwana sun rufe yadda bacin rai ke sarrafa zuciyata a wajen ko mari na ta yi sai na rama. "Au ni ce ma ba ni da kunya daga ƙarshe kenan!? Ke ba ki ji duk mganganun da ta ke faɗa min ba ne! Me na yi mata? Kamar ta na jira. Ai ita ba ta kama girmanta na yayar mijina ba. Shi ya sa nima na bi girman nata na tattaka ni da ita wallahi sai mun cire renin da ke tsakanin juna." Nene hankalinta ya tashi ta yi ta yi Bahijja ta yi shuru ba ta yi ba sai ta Umarci Maman farko da ta ja ni zuwa ɗakin ta tun da ita ma Bahijjan ta ƙi sauraranta har da Halima a masu jan Anty Bahijja amma ta na wani zillo ai nima na haukace musu ta na zagina ina zaginta itama. Suwaiba da Maman farko da su Hauwa suka yi ta ja na Dakyar suka shiga dani ɗakin Maman farko na zame musu kamar mai aljanu sai da suka haɗa da rufe ƙofa Maman farko fadi ta ke yi" Innalillahi Sadiya ki yi shuru mana." "Ku kira Tafida mana." "Bari na kira shi" Cewar Suwaiba ta na wucewa cikin uwar ɗaki." "Ki yi hakuri Sadiya." In ji Munnira ta na kuka ganin na zaune saman cafet ɗin tsakar ɗakin Hajiya iya na rushe da kuka kamar wata yarinya. "Kazafin fa suka yi min? Sun ci mutumcina ni da zuru'ata? "Ki yi haƙuri amma tabbas an ci zarafin ki." In ji Maman farko Hauwa kuma faɗi ta ke yi" To daga ina wannan mganar ta fara fitowa? "Ko da ga ina ne ko waye wallahi ba zan bar wannan mganar ba sai hukuma ta ƙwatomin haƙƙin ƙazafin da suka yi min." Na faɗa ina jin ƙuna a ƙasan raina lokaci ya yi da zan tauna tsakuwa domin a ya ta ji tsoro. Ba Ma'u ba ko Baaba ce sai na yi kararta ba Bahijja ba ko Nene ce ta yi min wannan ƙazafin sai na ji dalilinta wallahi. Ina kuka zuciya ta na wani irin zafi ina ma jin turarin zafin daga maƙoshina. Duk alherin da na yi ma Gimbiya ni ce za ta saka ma da sharri. Lalle na yarda da maganar hausawa da suka ce mai kishiya ba ya mutuwar Allah. To an kawo gabar da komai zai ƙare, zan yi abin da hankalin kowa zai koma jikinsa. Jikina ba in da ba ya rawa kawai hasko kaina na ke yi na kama Ma'u na yi mata shaƙan da sai ta kusa zuwa lahira. Kawai sai gani na na yi na mike Munnira da Hauwa da suke ta jajanta lamarin suka mike suma, ganin na nufi hanyar barin falon na Maman farko ya sa Munnira ta ce. "Sadiya ina za ki je? Maganarta ya dawo da hankalin Maman farko a kan mu saboda itama wayarta ce a hannu ta na dannawa kamar neman wani ta ke yi a wayar. Kuma daga ma nan dakin muna jiyo hargagin Anty Bahijja da zage zagen da ta ke yi. "Ina kuma za ki je? Suwaiba ta faɗa ta na fitowa daga ciki. "Jakata zan ɗauko da mayafina " Na faɗa muryata a shaƙe sai Maman farko ta ce ba zan fita ba Hauwa ta je ta ɗauko min,sai na yi shuru amma ban zauna ba ina tsaye ina karkaɗa jikina in ba sumar da Ma'u a yau ba, ina jin ba zan huce haushina ba kafin na haɗa da jami'an tsaro sai na bar mata taɓon da za ta kiyaye ni har gaban abada. Ko raba ɗayan biyu ba zan yi ba Ya Murja ta faɗa ma Ma'u maganar Marwa da Kawu ita kuma ta zo ta fesa ma uwarta ai kuma komai ya zo karshe daga yau zan kawo karshen makircinta a kaina. Hauwa ta buɗe falon ta fita dai-dai lokacin da Maman farko ke faɗin" Kin samu Tafidan? "E ya ce ga shi nan a kan hanya. Ya ma ce Halima ta kira shi ta faɗa masa ba ki ji yadda hankalin shi ya tashi ba na ce ya taho a hankali Sadiya ta na ɗakin ki mun rufe ta." "Wayyo bawan Allah." Maman farko ta faɗa cikin wani yanayi ni dai ina tsaye kiƙam na kasa zama. Sai ga Hauwa da Hajiya jiya sun shigo, jakata kawai Hauwa ta dauko min da sauri na karɓa wayata na ciki da kuɗi lokacin biyu na rana har ta gota daman sai da na yi azahar na fito daga gida. "Sadiya ki yi hakuri. Kai wannan lamarin bai yi daɗi ba" In ji Hajiya Iya, Mama ko faɗi ta ke yi" Ni Bahijjan ce ta ba ni mamaki ko gaya mata abu aka yi ta yarda ba ta da shaida? Suwaiba ta karɓe da faɗin" Ita ko ke da shaida ba ku ji suna faɗin Gimbiya ta ce ta ga ƙanwar Maman Sadiya ta kawon mata magani ba! Itama ai ta haɗa fitina ita da wacce ta tari Bahijja da mganar wani tarihin wata ta mutu da hauka." "Ma'u ce tare suka tashi da Sadiya. Da babansu da ita mahaiyar Ma'u uban su ɗaya uwar su ɗaya' Hauwa ta faɗa sannan ta kora musu jawabin ta in da suka haɗu da Anty Bahijja. Hajiya iya na salati Maman farko na yi, Suwaiba ta ce" Na gane ta wata yar fara haka. Amma ko ta yi asara wallahi." Hankalinsu ya ɗauke da hiran su ba su san na zari mayafin da na gani a saman kujeran hanyar fita ba, na buɗe kofa na fice ko takalmi babu a kafata sai wani da na gani a ƙofar ɗakin na saka. Karan rufe kofa ta suka ji sannan suka far ga ga na fita sai suka biyo ni da gudu suna kiran sunana sun ɗauka ɗakin Nene zan koma sai su ka ga na fara sauka daga Bene Suwaiba da su Hauwa suka biyo bayana suna kiran sunana amma kamar wata hajijiya haka na rika sauri kamar zan kifa a haraba na ci karo da Mimisco ta iso itama ina ga kiranta aka yi. Har ta na tsayawa ta ɗauka zan yi mata mgana ne sai ta ga na wuce ta fuu kamar zan kifa. "Sadiya tsaya. Ki tsaya na ce Sadiya." Ko sauraranta ban yi ba mayafi a saman kafaɗa ina rike da ƙaramar jakata na fice da sauri kamar zan faɗi. Ba san ni ba ko sun biyo ni ni dai ina fita na fara sauri ina haɗa hanya har da gudu gudu ina hango bakin titi kawai na ga Motar Yallaɓai ta sha wo kwanar, yadda na dumfari in da zuciyata ke son zuwa ko waye ya tsaida ni ba zan tsaya ba ko da Alhajin mu ne kuwa. Ya wuce ni, ni ma na wuce shi da sauri sai ga shi ya na dawowa da baya da baya a motar ya na kiran sunana bayan ya sauke gilashi ko jin sa ban yi ba ganin ya tsaya da motar yasa na saka gudu ina zuwa bakin titi na saka hannu mai adaidaita na zuwa ba kowa a ciki ya tsaya na shiga ciki da sauri na ce. "Mu je Rijiyar zaki. Ka yi gudu da ni sosai." Haka na faɗa ina haki, sai na juya baya ina ganin Yallaɓai ya koma mota ya yi riverse kenan ni zai biyo ni kuma ina azalzal ma mai adaidata da cewa ya yi sauri kawai hango kaina na ke yi a gaban Ma'u yadda zan makure ta sai ta kusa mutuwa ji na ke yi kamar zan iya yin bindiga ni kaɗai tsabar halin da na ke ciki na bakin ciki da ɓacin rai, kafin na fara kai su ƙara sai na ci uban Ma'u saboda in hukuma ta shiga ciki da farko ba zan samu damar cin uban ta dakyau ba gwara na fara nuna mata ina nan a Sadiyar da ta sani ban sauya ba kuma wallahi ni da zumunci da Ma'u har abada. Bahijja da sauran masu ta ya ta a kaina Yallaɓai zai shiga tsakanina da su, da ita kanta matarsa munafuka mai maida alheri da alheri sai an tuhuman min ita a gidan uban wa ta ga Inna Mariya ta kawo min asiri? Wallahi ko sama da ƙasa ne za ta haɗe ba zan bar maganar nan ba. Wato maganin nan da Inna Mariya ta kawo min ranar shi ne ta ke magana akai kenan lalle kar ka raina mutum duk wannan abubuwan da suka faru Ma'u ce sila ita ta ba ma Anty Bahijja daman cin zarafina. Shin wai da aka je asibiti an ce ne magani Gimbiyar ta sha? Ba ɗaya fa kawai ta tsane ne shi ya sa ta ke neman hanyar ci min mutumci, ban da haka ai ta san Gimbiyar na ta matsalan raunin mahaifa ko acan Abuja ma ta yi ɓari kuma ni da bakin Anty Bahijja na ji lokacin rasuwar mijin Gimbiyar ta na faɗin ai an nema mata maganin gargajiya na matsalan ciwon maran da ta ke fama da shi ke sa ta yi ɓari in ta samu ciki, amma yanzu sun manta Ma'u ta zo ta ɓata ni su kuma daman kamar su na jira sun far min da cin mutumci to komai ya zo ƙarshe daga wannan ba za a ƙara ba. Muna tafe duk irin gudun da mai adaidaitan nan ya ke yi ni ba na gani, ji na ke yi kamar na karɓi tuƙin ƙila na isa in da na ke so a kan lokaci domin ji na ke yi kamar na yi tsuntsuwa na ganni a gaban Ma'u. Sai faman kiran wayata da ke cikin jaka ake yi amma ban bi ta kai ba, alokacin ni kaina ban san a yanayin da na ke ciki ba amma zan iya cewa tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin irin ɓacin ran da na ke ji a yanzu ba. Ban taɓa jin nauyin ƙirji da na zuciya irin na wannan ranar ba, ban taɓa tsintar kaina a yayin fusata da fushi mai tsanani irin na yau ba. Abu ɗaya ke ƙara tafasa min zuciya in na tuna yau duk cin mutumcin da Anty Bahijja ta yi min ba kowa ya ba ta dama ba sai Ma'u. Ma'u fa ƴar'uwata ce da za ta iya tsaya min da jikinta da aljihunta in ta ga wani zai cutar da ni wani ko zai ci zarafina, amma sai gashi yau ita da kanta ta ba da damar da aka taru aka ci zarafina a ka zagi dangin mahaifiyata da ta ke ƙasa ba ta san ma abin da ke faruwa ba. Ban san ina hawaye ba sai da na ji ɗigan su a saman hannuwana. Ban san ina kuka ba sai da na ji zuciyata na wani irin zafi, zafin kuma sosai kamar sheɗata za ta ɗauke min sai da na fara numfashi sama sama saboda halin da na ke ciki. Ina tuna labarin da ta je ta ba ma Anty Bahijja wani tsohon labari ne da mu muna yara ƙanana ma aka yi, da girman mu labari muka ji daga baya. Yayar Mama Inna Mandiya Allah ya jiƙanta mijinta ya auro wata bafullatana an yi auren ba daɗewa ta fara rashin lafiya aka yi ta yawon mgani anan ne aka ce wai asiri aka yi mata. Daga nan magana ta shiga gari aka yi ta cewa Inna Mandiya ce ta yi mata asiri ta kwanta jinya. Ƙwatsam kuma sai ta rasu bayan kuma mutuwarta ba daɗewa itama Inna Mandiya ta fara rashin lafiya na aljanu a yadda Mama ta faɗa ma na ana tunanin Gamo ta yi shi ne da wannan rashin lafiyan ta koma ga Allah. Magana ta za ga gari cewa ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙewa sama da shekaru amma mutane ba su bar maganar ba, an daɗe ana kiran gidan su Mama da gidan yan asiri, daga baya da mutane suka ga ji suka daina ni kaina na manta da labarin abin da ya faru sama da shekaru ashirin amma da ya ke ita Ma'u munafuka ce ta na tune da labarin shi ne ta zaunar da Anty Bahijja ta faɗa mata domin ni ta tozarta ni. Ban san ma na buɗe muryata ina kuka ba sai da mai Adaidaitan da na ke ciki ya juyo ya na faɗin" Hajiya lafiya? Na kalle shi amma na ƙasa mgana sai danne laɓena na ƙasa na ke yi kar na fashe da kuka tsabar yadda na ke ji na a rikice kamar na fita daga hayyacina. Wannan abin da aka yi min shi ne abu mafi munin da ya taɓa ɓata min rai tun aurena da Yusuf duk da an yi wasu a baya amma bai kai wanda ni za a tozarta ni sannan a yi min mummunan ƙazafi ba. "Ko rasuwa aka yi miki Hajiya? Sai haƙuri Allah ya jiƙan musulmi." Shi ya yi kiɗan shi ya yi rawan shi amma ni kallo bai ishe ni ba, ni kaɗai na san yanayin da na ke ciki. Ma'u daman suna farko farkon Rijiyar zaki ne gidanta na bakin titi da kin shiga layi kaɗan haka, gani na yi ma in na tsaya sai ya shiga dani zan ɓata lokaci ya sa na sauka a bakin titi na buɗe jakata na ɗauko masa 1k na bashi ya na mgana ban ji sa ba domin tuni na yi gaba. Hango kaina kawai na ke yi a gaban Ma'u na maƙureta ina dukanta ko zan ji kaɗan daga abin da ke taso min a ƙasan zuciyata ya ragu. Gudu gudu sauri sauri ina tafe a hanya na ga wani ƙaton dutse na ɗauka na riƙe a hannuna ina zuwa bakin get ɗin ban jira komai na saka dutsen nan na riƙa buga kofar da shi ina jin megadin gidan na tambayan waye na yi banza da shi, ya na buɗe get ɗin ta ƙaramar ƙofa bakin sa ya buɗe da shirin mgana na tura shi baya da ƙarfi na shigo gidan. Da idanuwana na ke kallon haraban gidan Allah ya ba ni sa'a na hango Ma'u tsaye a jikin mota da shirinta tsab na fita ta dukar da kai ta na duba wayarta. Ban jira komai ba da sassarfa na fara takawa zuwa gare ta megadi ya biyo ni ya na faɗin" Baiwar Allah lafiya? Bai sanni ba domin rabo na da gidan Ma'u tun haihuwan Alhaji ƙarami.. Hayaniyar Megadi ya sa hankalin Ma'u ya dawo kan mu yadda ta ke kallona na san ta yi mamakin ganina ne. Na dumfare ta da sauri dai dai ina fuskarta ƙofar shiga falonta. A kuma lokacin mijinta Alhaji Mustapha ya fito ya na saɓa babban riga da alama tare za su fita da Ma'u. Kafin ya ƙariso ni na riga shi ƙarisawa gaban Ma'u na saki jakar hannuna da mayafina lokacin da bakin ta ke motsi na ji ta ambaci sunana. "Sadiy.." Ban bari ta ƙarisa ba, saboda lokacin da na ganta ga ta a gabana sai na ji ɓacin ran da na yi kafin na zo gidanta ya ninka sama da sau saba'in ba tare da jira ba kawai na ɗaga hannuna da karfi na kwashe ta da wani mahaukacin mari ta bangaren damanta wanda sai da ta gicjiya gefe cikin razana da firgici. Adai dai lokacin da mijinta ya ƙariso ya na faɗin. "Sadiya ke ce ta fe? Ah Subhanallah." Sai maganarsa ta ƙare da kiran sunan Allah ganin na yi sauke ma matarsa marin diɓan mahaukaciya. Ganin ya na ƙokarin karisowa ya sa ta na ɗagowa cikin mamaki dafe da kunci na ƙara dagewa na sauke mata wani marin a bangaren dama da sai da wayar hannunta ta suɓuce a ƙasa ta ba da sautin ƙara kafin kuma ta yi wani motsi na saka hannuwana duka biyu na ɗago kafaɗunta na yo gaba da ita sai kuma da karfi na mai da ta baya gam! Na buga kanta da jikin motan da ta ke tsaye a gefenta, na ƙara ɗagota na ƙara maida ta gam sannan na saka duka hannuwana na shaƙe mata wuya kamar zan kasheta idanuwanta sun firfito waje ta na rike hannuwana domin ceton ranta amma a lokacin ni ba na ji ba na gani burina kawai na yi ma Ma'u dukan mutuwan da gaba ko sunana aka ambata sai ta razana. Alhaji Mustapha ya yo kaina cikin tashin hankali. "Ke ke Sadiya me ye haka? Ya ke faɗa ya na neman ɓambare hannayena daga wuyan Ma'u amma ina ya kasa domin sai na ji wani karfi na shiga ta, hankaɗe shi na yi gefe ya ta ga taga taga kamar zai faɗi. Sakin mata wuya na yi na jawo mayafin da ke jikinta na matse mata wuya da shi, na ƙara jawo ta ta dawo na sake maida ta ta ƙara buguwa da jikin mota gam! Ban tsaya ba na saka duka hannuwana dama da hauni na riƙa yarfa mata maruka kamar Allah ya aiko ni . Sai ga Alhaji Mustapha ya yo kaina shi da megadin shi suna neman raba ni da Ma'u. "Ke mahaukaciya ce! Yar'uwan ki ce fa? Ya faɗa lokacin da suka ƙwaci Ma'u daga hannuna ta na bayan shi duƙe ta na maida numfashi, Megadi na gefe ya na salati shi kuma Alhaji Mustpha ni ya ke kallo ganin yadda na ke huci kamar zakin da ya daɗe a dawa bai samu abinci ba. "Me ya same ki? Me ta yi miki za ki zo har cikin gidan ta kina dukan ta? Kin san me kika yi? Na yi tsaye ban yi masa mgana ba sai ya juya ya na duba Ma'u ya na yi mata sannu ya mikar da ita tsaye fuskarta ta yi ja da shatin hannayena idanuwanta sun yi ja sai kuka ni kuma ina kallonta ta na kuka ina ji a raina ba ta daku ba so na yi na yi mata dukan da ba za ta iya ma mgana ba. "Sadiya me na yi miki!l? Ni ce fa Ma'u yar'uwan ki? Sai na ji kamar ta jona min shoking a jikina a fusace na nuna ta da yatsa ina faɗin" Ke dai Ma'u ke dai Ma'u wallahi ke tsinanniya ce." Gabaɗayansu suka zuba min ido, ita ko sai ta fashe da kuka ta na nuna kanta. "Ni kike kira da tsinanniya Sadiya? "Kin wuce tsinanniya. Ke sheɗaniya ce." "Ya ishe ka haka fa Sadiya ina ganin girman ki" A fusace na ce" Ka daina gani daga yau. Ba ruwan ka a wannan mganar ka matsa gefe ba dai kai na ke yi ba." "Matata ce Asma'u ba ki da hurumin da za ki zo gidana kina tsine mata" Sai na kalleta ta na ta kuka kamar mutuniyar ƙwarai kafin na nuna da yatsa ina faɗin" Ma'u Allah ya tsine miki albarka munafuka mai fuska biyu." "Yar'uwan ki ce fa kike tsine mawa? Ya faɗa ya na mai daka min tsawa, ni ma a fusacen a tsawacen na ce" Ni ba yar'uwta ba ce domin na raba jinin da ke tsakanina da ita har abada. Domin abin da ta yi min jinina ba zai taɓa yi shi ba. Kuma ki sani wallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da ke Ma'u." Sai ya kasa mgana ya tsaya ya na kallona. "Me ya faru? "Ka tamnayi annamimiyar matar ka. Wacce ba ta ramin ta sai dai ramin wani." Sai kawai ya fara lalubo waya daga cikin aljihun rigan shi lokaci ɗaya ya na faɗin" Ni dai ban san me ya faru ba amma ba ri na kira Injiniya." Megadi kuma megidan ya ce ya tafi abin shi amma ya daga can gefe ya na kallon abin da ke faruwa hankalin shi ya tafi ga kiran waya na shammace shi na ƙara yin kan Ma'u wannan karon ta so kare kanta sai muka fara ƙoƙowa amma duk da haka sai da cire mata ɗankwalin kanta na damƙi shegen gashinta mai kama da hammatan ɗan iska na fara ja sai ta fara ihu da gudu ya rugo ya shiga tsakaninmu burina kawai na bar ma Ma'u taɓon da duk lokacin da ta kalle shi sai na faɗo mata a rai shi ya sa na riƙa waige waige ina neman dutse ko sanda na rotsa mata kai dashi ta haka ne ya samu damar saka ta cikin mota ya rufe na ɗauko dutse da na gan shi a can gefen na rika bugun gilashin motar da shi, shi kuma ba ya son riƙe ni sai dai ya na ƙare wa kuma ya na kiran sunana da faɗin na shiga hankalina. Ita kuma ta na cikin mota ta na kukan munafunci amma na ga lokacin da ta yi min wannan mirmishin nata ita a tunaninta ta yi nasara ne. Ƙarya ta ke yi ba ta yi nasara ba sai ma faɗuwa. "Wallahi yau dubin ki ya cika Ma'u daga yau karshen ki ya zo domin sai na tabbatar da kowa ya san wacece ke. " "Haƙuri koma me ya faru a zauna a tattauna? Na kalle shi da jajayen idanuwana kafin na ce" Shari'a ce za ta shiga tsakanina da matarka." Ina mgana ya na kiran waya sai ji na yi ya na cewa injiniya ga matarka a gida ta zo ta na jan Asma'u da faɗa ban san me ya ce masa ba na ji dai ya ce sai ya zo, ni kuma na kasa na tsare na ce ko ya fito da Ma'u ko na fasa gilashin motar ni na fito da ita. "Haba Sadiya ki natsu mana " "Yadda ta haifar min da rashin natsuwa. Nima wallahi sai na haifar mata da fiye da abin da ta yi min." Shi dai ya babbage bakin mota ya na ta ba ni haƙuri domin ya ga yadda na ke a rikice zan iya aikata duk abin da na ga dama. Ɗamara na ci da mayafin jikina ina girgiza kamar zan yi bi iska shi fa ya tsorata ya ɗauka ina da aljanu ne har Ma'u ma ta tsorata kuma ta bugu domin har fuskarta ta kumbura, da dai na tuna in Yallabai ya zo zai hana ni ƙarisawa ofishin yan sanda ya sa na karɓi jakata da Alhaji Mustpha ke miƙamin tun ɗazu ban karɓa ba. Sai da na karɓa sannan na ce. "Mu haɗu a gaban hukuma." Ya biyo ni ya na ce min injiniya na hanya na yi banza ds shi megadi tun kafin na ƙarisobya buɗe min kofa ina fita sai ga motar Yallaɓai na karisowa ina ganin shi sai na juya na nufi bangaren yamma shi kuma da sauri har da gudu ya fito ya taka ya na bina lokaci ɗaya ya na kiran sunana Allah ya sa layin ma ba jama'a da mun zama ƴan kallo. "Sadiya." "Sadiya magana fa na ke yi miki. Ki tsaya don Allah." Ban saurare shi ba sai da ya yi gudu ya sha gaba na, na kauce masa zan wuce ya riƙo ni da ƙarfi ya na kiran sunana. "Ka ba ni hanya na wuce ko? Na faɗa ina masa wani kallo da jajayen idanuwana da ina da tabbacin yanayin da ya ganni ya daɗe bai ganni a cikin sa ba. "Ina za ki je? Kin ga yadda kike kuwa? Sai da ya faɗa na kalli kaina da ɗamara. Kamar wata yar dambe sai na warware mayafin na yafa a kaina amma Yallaɓai ya ƙi sakina. "Ka sake ni na ce ko? Na faɗa a fusace ina kuma ƙokarin kwace kaina amma riƙon Yallaɓai ba na wasa ba ne na kasa. "In na sake ki ina za ki je? "Offishin yan sanda." Na bashi amsa ina huci kafin na cigaba da faɗin"Wallahi ba zan ƙyale duk wanda ya nemi ya tozartani ba. Sai hukuma ta bi min kadin kazafin da suka yi min ni da zuru'ata." Na karishe faɗa ina fashewa da kuka sai ya rike ni a jikinsa amma ina ta fizgewa ina faɗin ya sake ni domin ni ba zan bar wannan mganar ba. "Na ji nima ai ban ce ki barta ba. Mu je ki shiga mota sai mu je police station ɗin tare da ke." Sai na kalle shi sai ya gyaɗa min kai ya na ƙara rike duka hannuwana ya na jinjina min kai, ban san me ya sa na yarda da shi ba na bi shi zalau zalau har bakin mota ya buɗe ya sakani a ciki ya rufe sannan ya taka ya isa bakin get ɗin gidan Alhaji Mustapha bai shiga ba amma shi ya leƙo sun yi mgana ba daɗewa ya dawo ya buɗe mota ya shiga ya ta da ita ya yi riverse muka bar layin tun da muka fara tafiya na ke kuka kuma da karfi ina yi har da jiniya bai kuma hana ni kukan ba. "Ni Ma'u za ta tozarta? Ni yayarka za ta kalli idanuwana ta ce dangin uwata dangin asiri ne? "Ki yi hakuri" Yallabai ya faɗa a marairaice, ga shi sai kiran wayarsa ake yi bai ɗauka ba. "Yusuf lokacin da ka ce min matarka za ta zo ta zauna da mu me na faɗa maka? Ba sai da na ce ina tsoron wani abu kar ya faru daga baya ba! To yau ni matarka ta saka ma da sharri sakamakon alherin da na yi mata. Ita wai ta ce ta na gidan kanwar mamana ta kawo min asiri. Ita ce fa ta faɗi haka Yallaɓai" Na ƙarishe faɗa ina kallon shi ina kuka har da majina. "Ita Saudatun ne ta ce haka? Ya tambaya cikin mamaki. "Abin da ya fi min ciwo Anty Bahijja ta zubar da abincin da na kawo ma Nene ta ce ba zan kashe muku uwa kamar yadda na so na zubar ma da Gimbiya cikin jikinta? Yusuf a zama na da kai na taɓa kwatanta wani abu na cutarwa gareka ko yan'uwan ka? "Ba ki taɓa ba Sadiya" "Na taɓa zagin su! Na taba musu wani abu na rashin ɗa'a? Tsakaninmu sai girmamawa amma yau duk alherin zaman shekarun aurena da kai ya koma na sharri da ƙazafi? "Ki daina kuka don Allah Sadiya raina na ƙara ɓaci." Ya faɗa cikin wani yanayi ya na kuma gudu a mota sosai daga gani ran shi ya na ɓace ne. "Yusuf yau fa Anty Bahijja ta ce min ba ta ga abin da aurena da kai ya tsinana maka ba. Ta ce wai na wanke gaba na baka ka sha na mallake ka, shi ya sa na shiga na fita zan liƙa ma Kawu Abba ɗiyar yayata saboda shima a maida shi shanyayye kamar ka." "To ina ruwanta in kin shanye ni? Sannan uban wa ya faɗa musu labarin Kawu da Marwa." In kuka na ce" Munafuka Ma'u ce, shi yasa na ce maka sai na haɗa su da hukuma" "Ban ɗauka haka ta ke ba. Ma'u nan ta ba ni mamaki ". Ya faɗa cikin bacin rai kafin ya cigaba da faɗin" Me ya sa na ki kirani da abin ya faru ba? Kin san dai ba zan zura idi a ci miki mutumci ba. Duk wanda ya ci miki mutumci to tamkar nawa mutumci ya ci." . Na kasa mgana sai kuka kawai na ke yi ina faɗin ya kai ni offishin yan sanda. "Ki yi hakuri mu koma gida a zauna a yi mgana." A fusace na ce" Ba zan zauna da kowa ba Yusuf hukuma ce za ta tuhume su." "A'a." "To ka sauke ni na tari adaidaita" "Na ce a'a." Ya faɗa a fusace cikin tsawa, kamar zai dake ni daga gani ran maza ya ɓaci. "Babu wani hukuma. Ni nan zan tsaya miki sai na ji dalilin wannan kazafin da cin mutumci. Ki daina kuka ki bar min komai a hannuna kawai." "Ni dai a'a ka bari na kai su ƙara." "Na ce a'a ba za ki bi umarnina ba ne Sadiya? Ya yayyaƙomin kamar zai dake ni ai sai na yi shuru "Ko ba ki yarda da ni ba ne? Ko domin Anty Bahijja na yayata sai na zauna na zura ido a ci zarafin ki? Ba zan bar wannan mganar ba sai na ji dalilin wannan tozarcin. Na rantse da wanda raina ke hannun shi sai na tada ma duk wanda ya yi silan a taruwa a ci miki zarafi ki hankali shima" Ya faɗa a fusace har ya na dukan sitayari duk fusata ta sai da na koma na yi shuru saboda na ga Yallaɓai ya harzuka. Daman ya kan daɗe ran shi bai ɓaci ba in kuma ran shi ya ɓaci to ba shi da kyau. Sai na koma gefe ina maida numfashi ina jera ajiyar zuciya. "Na maida ke gida ko gidan Alhaji? "Mu je gidan Ya Aina." Na faɗa ba tare da wani tunani ba sai ya yi shuru bai yi mgana ba ana ta kuma cigaba da kiran wayarsa "Nene ina tare da Sadiya. Zan taho gidan yanzu in sha Allahu." Na ji ya na faɗa sai na ɗaga kai na kalle shi, ya na waya ne kuma Nenen da ya ambata ya sa na gane da ita ya ke waya. "Nene gidan Yayarta zan kai ta. Yanzu zan dawo gida, ki kuma sanar da Bahijja ba Sadiya ta tozarta ba ni ta tozarta na kuma gode mata." Sai na zo." Ya faɗa kafin ya kashe wayar haka muka yi tafiyar nan shuru ni ina ta sauke ajiyar zuciya shi kuma ya na ta tsula gudu ba daɗewa muka iso gidan Ya Aina ya sauke ni kuma bai ce min komai ba ya juya motar a fusace ya bar layin ni kuma na taka na shiga gidan Ya Aina da sallama cikin muryata da ke shaƙe saboda kukan da shaƙa kamar an yi min mutuwa. *Janafty* *TKG018* *Littafin TURKEN GIDA, 1k ne akan manhajar Telegram.* 09069067488 Na shiga gidan Ya Aina ko gani ba na yi saboda tashin hankali da damuwa. Tafe na ke ina jefa ƙafuwana ba tare da na san in da za su faɗa ba. Ya Aina na hanga a ɗan karamin madafinta dake tsakar gida sai ƙannen Marwa na gefen ɗakinta a kan tarbarma suna cin abinci. Ko sallama ma ban yi ba ni dai kawai na shigo kuma na dumfari ɗakin Ya Aina so na ke yi na samu waje ni kaɗai na fashe da kuka na yi kuka mai ƙara mai sauti ko zan ci ɗan sauƙi sauƙi abin da ke taso min daga ƙasan zuciyata. "Laa Mama ga Umma Sadiya." Na ji wani cikin yaran ya faɗa amma ba zan iya gane ko waye a cikin su ba. Ni dai ƙafafuwana na taka suka shigar da ni falon Ya Aina sannan lokaci ɗaya na zube a saman cafet ɗin ɗakin tare da fashewa da kuka mai sautin da har a tsakar gida ana jiyo kukana. Da gudu Ya Aina ta shigo ina jin salatinta. "Innalillahi me zan gani Sadiya? Ta faɗa lokaci ɗaya ta na zama kusa da ni ta saka hannu ta ɗago ni ta na mai kiran sunana. "Sadiya" "Ke Sadiya me ya faru? Ta ke faɗa cikin tashin hankali da damuwa. Ban buɗe idanuwana ba amma na ɗora kaina a saman cinyarta ina cigaba da rera kukana, sai na ji kamar jikina ya na wani irin yam tsikar jikina sun tashi yam! Zuciyata na ji ta buɗe ina so na yi kuka mai yawan da na daɗe ban yi irin shi ba. Sannan ji na a saman cinyar Ya Aina ya ƙara raunana raunina da ya sa na ji kamar tsawon shekaru ban samu kafaɗan da zai tallafeni ba, shi ya sa na daɗe ban yi kukan da na ke jin yau ya na tahowa daga ƙasan zuciyata ba. "Kai ku koma ku cigaba da cin abincin ku." Na ji ta na faɗa, sai na ɗan buɗe idanuwana da suka kumbura saboda kuka sai na gansu sun yi jere a bakin kofa suna kallon mu. Maganarta ya sa suka fara fita ɗaya bayan ɗaya amma fuskokinsu dañkare da mamakin ganina ina kuka.   Sai da suka fice sannan Ya Aina ta ƙara maida hankalinta a kaina. "Sadiya me ke faruwa ne?  Nan ma na yi mata shuru ina ta kuka hawaye da majina na zuba lokaci ɗaya. "Ko wani abu ya faru tsakanin ki da Baban su Jidda ne? Sai na ƙara ma kukana Volume amma na kasa mgana. "Sadiya ki bar kukan nan ki yi min bayani. Duk kin ɗaga min hankali." Ina shassheƙa na ce" Ki bar ni na yi kuka Ya Aina.. ki bar ni na yi kukan da zuciyata za ta samu natsuwa." Na ƙarishe faɗa ina mai ƙara fashewa da kuka sai ta ƙyaleni ina ta kukana amma ta saka hannunta guda ɗaya a bayana ta na bubbugawa alaman lallashi mun fi karfin sama da mintina ashirin sannan kukan ya fara ɗaukewa sai shessheƙa da kuma jan majina. "Sadiya me ke faruwa? Ta faɗa ta na kallona dai-dai lokacin da na tashi daga saman cinyarta ina faman goge hawayena da ɗankwalina da ya zame daga saman kaina. "Ya Aina Ma'u ta ba da gudummuwa an tozartani yau a dangin su Yusuf" "Ma'u kuma? Ya Aina ta maimaita sunan ta cikin mamaki. Kawai sai na ji sabon kuka ya taso min ina kukan ina labarta ma Ya Aina abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe. "Innalillahi wa'inna alaihirraju'un" "Anty Bahijja ta ci min mutumci ta kirani dangin bokaye  da asiri. Ta ce aurena da Yusuf ba ta ga amfanin shi ba, Ya Aina wai ni suke zargi da ƙoƙarin zubar da cikin Amaryan Yallaɓai? Duk ta dalilin Ma'u. Domin ita ce ta ba su damar duk abin da suka yi min Ya Aina." Na ƙarishe faɗa ina gunjin kuka da ƙarfi saboda sai na ji kamar a alokacin ma abin ya ke faruwa. "Innalillahi. Ita Ma'un ce ta aikata haka? Amma ta ba ni mamaki matuƙa ban taɓa tunanin haka daga gare ta ba." "Ba in ina cewa munafuka ba ce sai a riƙa ganin laifina ba? Yanzu dai kun yarda ko? to Ma'u ta daɗe ta na ci duduniyata a dangin Yallaɓai ta daɗe ta na son rana irin ta yau ta faru sai yau burinta ya cika." Na faɗa ina goge idanuwana da hannuna kamar wata yarinya. Ya Aina ta kasa mgana saboda lamerin ne ya zo mata cikin ba za tan da ba ta taɓa tunani ko tsammani ba. Salati kawai ta ke yi ta na ɗaukowa ta na direwa. "Ma'u ce ta je ta faɗa ma Anty Bahijja dangin mahaifiyata yan asiri ne, sannan ita kuma Amaryan Yallaɓai ta ƙara da cewa ta na gidan ma Inna Mariya ta kawo min asiri. Sannan kuma ta ce wai yadda na gama shanye Yallaɓai haka na ke so na tusa ma Kawu Marwa domin shima a shanye shi da asiri tun da mu ƴan na gada ne ba na haya ba." "Na shiga uku ni Aina. A ina suka ji labarim Marwan? Ko shi Abban ne ya faɗa? "Ma'u ce ta fasa maganar. Ita kuma Ya Murja ce ta faɗa mata. Ba ina faɗa muku munafuka ce kuna ganin kamar ban da haƙuri ba? Uhm ni kaɗai na san wace ce Ma'u da kaidin ta." Na faɗa ina mai ɗaura ɗankwali na rufe kaina kukan ya tsaya amma zafin da ke cikin zuciyata ya kasa raguwa. "Ma'u. Lalle ko Ma'u ta ba ni matuƙar mamaki." Ta fada ta na mai yin tagumi cikin ɗimuwa. "Shi ya sa na ce an zo ƙarshe wallahi tallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da su Ya Aina. Ba zan bar wannan kazafin da suka yi min ya tafi a banza ba." Sai ta kalleni kafin ta ce" Shi Babansu Jidda me ya ce? "Me kuwa? Ya ce shima zai ɗau mataki amma ba shi zai hana ni ɗau nawa matakin ba." "Alhajinmu ya sa ni? "Ke kaɗai kika san abin da ya faru." Na bata amsa ina kallonta sai kawai ta miƙe tana faɗin" Ya zama dole ya sani domin magana ce da ta shafi zumunci. Kuma ni kaina ba zan so a bar maganar ba gwara a ɗau mataki tun da ya shafi zuru'armu ya kuma shafi auran ki da mutumcin ki, ya zama wajibi a shiga wannan mganar domin a yi min lamarin tufkan hanci." "Wa za ki kira? Na tambayeta ganin ta na ɗaukan wayarta. "Hamza zan kira. Shi sai ya kira Alhajinmu." Sai na yi shuru saboda na san Ya Hamza zai ba ni dukkan goyon baya har sai ya ga an ƙwatamin haƙƙina. Da dai Ya Abubakar ne daman ba zan saka ran ya goyi bayana ya bar Ma'u ba amma kuma ya sani wannan karon ba gudu ba ja da baya ni da Ma'u har abada sannan sai hukuma ta shata mana layi a tsakaninmu. A gabana Ya Aina ta zauna ta labartama Ya Hamza duk abin da ya faru ta ƙarishe da cewa" Sadiya ta zo min ciki kuka na fitan hayyaci. Hamza Ma'u ba ta kyauta ba, kuma tun da ta taɓa auren Sadiya bai kamata a yi shuru ba. Ka kira Alhaji ka faɗa mishi sai a san yadda za a shiga mganar. Domin Sadiya ta ce ba za ta yarda ba sai ta kai ta ƙara hukuma." "Ta yi min dai-dai. " Ya Hamza ya faɗa kafin ya cigaba da faɗin" Ni ban yi mamakin abin da Ma'u ta aikata ba daman can halinta ne ta na wani muƙu muƙu na munafunci ba Sadiya ni nan Hamza Muhamamad Yashe jinin Sadiya ba zan bari cin zarafin da a ka yi mata ya tashi a banza ba. Sannan duk wanda ya taɓa zuru'an Mama kamar zuru'an Gwaggo ya taɓa. Sannan duk wanda ya nemi tozarta zuru'an Gwaggo kamar zuru'an Alhaji ya taɓa. Kuma taɓa waɗanan zuru'an dai-dai ya ke da ka taɓa mana mutumcin mu da darajan mu, kuma taɓa darajanmu dai-dai ya ke da ka nemi faɗa damu. Saboda haka wannan lamarin ba Sadiya kaɗai ya shafa, har damu gabaɗaya."   "Gaskiya ne wannan." "Sabo da haka, yanzu zan kira Alhaji a waya na faɗa masa abin da ke faruwa. Ya kamata ya sani saboda abu ne da ya shafi auren Sadiya. Sannan za a yi zama zan kira Auwalu jibi asabar mu shigo Kano. Ba Ma'u ba har Baaba sai an kira. Za ta ci ubanta sai mun ji in yayar Yusuf ita ce jininta ba Sadiya ba. Kuma daga wannan a yi mata iyaka da komai yadda za ta fahimci Sadiya ma ta na da gata." "Haka ne gaskiya ne. Haka yakamata a yi." Nan take ya ce ta ba ni wayar da ya ke a speaker ta saka wayar shi ya sa na ji komai. bayan na amsa mun gaisa ya ce" An ce kina ta kuka? To ki share hawayen ki, mu ƴan'uwanki za mu tsaya miki har sai gaskiya ta bayyana. Shi Yusuf ɗin me ya ce? Ko wani mataki ya ce zai ɗauka? "Ya ce zai ɗau mataki amma bai faɗa min matakin da zai ɗauka ba." "Ok. Daman ai na can gidan su matakin na hannun shi, mu kuma na mu na gida mu ne za mu gyara lamarin. Ki kwantar da hankalin ki, in ba za ki koma gida ki yi kwanciyar nan ki samu natsuwa har zuwa da safe. Amma shi kan shi Yusuf ɗin in bai wanke ki a wajen yan'uwansa da zargin da suka zarge ki ba, za mu saka baki mu mu ɗaukan miki mataki, ba ta yuyuwa a ɓata miki suna sannan a bar shi ya tafi a banza" Bai kashe wayarsa ba sai da ya jadaddamin na kwantar da hankalina wannan karon Ma'u ta ƙai ƙarshe kuma sai ya ga ƙarshenta. Sai na ji hankalina ya kwanta ba tabbaci gareni akan Ya Hamza ba. Ina da kyakyawan yaƙini a kan zai tsaya a kan wannan mganar har sai an ƙwatomin haƙƙina kamar yadda ya faɗa, sai na ji hankalina ya ɗan kwanta ko hukuma ba ta shiga ciki ba, hukumar ƴan'uwana za su tsaya min har sai gaskiya ta yi halinta. Har sai ainihin fuskar Ma'u ta bayyana a gaban kowa ya gane ta.   Ya Aina ta dafa min ruwa zafi na sha da bombita. Ta ce na kwanta na huta ciki na shiga na haye gadonta kuma cikin ikon Allah na ɗan samu barci amma zuwa huɗu da rabi na tashi lokacin Marwa ta dawo daga asibiti ba ta dameni da tambaya ba ƙila Ya Aina ta ce kar ta dame ni ne, amma dai mun gaisa har ina zolayanta da Amaryan kawu ta fita ta na faɗin" Kai Umma." Tsakar gida na fita na yo alwala na iske Ya Aina ta tankaɗen garin tuwo. Yaran duk ba sa nan sun tafi hadda yamma, ɗaki na koma na ta da salla, ina cikin sallar na ji muryan Rahila sai da na idar sai ga ta sun shigo ita da Ya Aina. "Ah Sadiyalle daman kina nan? Ta fada ta na ƙoƙarin zama a saman kujera. Sai da na ɗago ina faɗin" Ga ni ko kin gani Rahilatu." Sai lokacin muka haɗa ido ta ga yadda idanuwana suka kumbura saboda kuka. "Ciwon ido kike yi? Kafin na ba ta amsa Ya Aina ta ce" Kuka ta yi." Sai ta kara kallona kafin ta koma kuma ta na kallon Ya Aina. "Me ya faru? "Daga ina kike da yamman nan? Ya Aina ta katse mata tambaryarta. "Makociyata ce ƙanwarta ta haihu. Shi ne muka haɗu gabaɗaya muka taho barka muna zuwa na ga anguwarku ne sai na ce su wuce bari na shigo mu gaisa." "Me ya faru? Rahila ta tambaya bayan ta dire maganarta. "Lamarin ne abin mamaki da takaici." "Wai me ya faru don Allah? Nan Ya Aina ta labarta mata dukkan abin da ya faru sai Rahila ta saki Sahla da ke hannunta ta na shan nono kafin ta ce" Innalillahi kai Ma'u ta yi asara. Kai jama'a wannan wani irin cin zarafi ne da cin mutumci? Ta faɗa har idanuwanta ya na kawo ƙwalla Ni ta kalla ni ko na dukar da kaina ne kawai ban yi magana ba, saboda ana ƙara maganar abin ne ina jin ƙunar zuciyata na ƙara ƙamari. "Duk abin da ke faruwa tsakanin Ma'u da Sadiya ban taɓa ba ma Sadiya gaskiya ba sai dai na ba ma ita Ma'u saboda dai kar ta ji a ranta muna wareta saboda ita ba cikin mu ta ke ba. Amma ni kaina na san Ma'u da wani abu a ranta game da Sadiya. Sai dai har ga Allah ban taɓa tunanin ta yi nisa haka ba. Ban taɓa tunanin za ta iya ba da goyon baya a ci zarafin Sadiya ba. Ban taɓa tunanin za ta je ta kai mganganu masu muni haka ba, mene ne riban ta ? Me ta samu? Har wata can ta fi mata jininta? Mene ne riban abin da ta aikata? "Riban ta na tozarta. Ribanta a ci mutumcina na muzanta na wulaƙanta a idon duniya. Daman ta faɗa min a ranar da aka fasa auranta da Ya HamzaCds cewa sai ta yi sanadiyar muzgunama rayuwata kamar yadda na hana ta farincikinta nima sai ta hana ni nawa farincikin. Kuma ta daɗe ta na yi min bita da ƙulli wannan ne dai ya yi munin da ba zai ɓoyu ba." Na faɗa ina maida hawayen da suka cika min ƙwarmin idaanuwana. "Ba shakka." In ji Rahila kafin Ya Aina ta karɓe da faɗin" Shi ne daman ta ke riƙe da shi? To ai abin da kika yi ba laifi ba ne. Ta dalilinki aka samu masalaha sannan aka cece taɓarɓarewan zumuncin mu gabaɗaya." "Uhumm. Ni fa mamaki na ke yi wai Ma'u ce za ta yi ma Sadiya haka? Me ta tsare mata? Me ya sa ta yi haka? Har da zuwa ta na ba da labaran da ba su da tushe ballatana makama." Rahila ta faɗa ta na ƙara bayyana mamakinta. "To ai duk komai ya zo karshe. Domin Hamza ya ce ba za a bar mganar ba za a yi zama na musamman." "Sosai. Ko ni ban goyo bayan a bar mganar ba. Ita kanta Ya Murja hakan sai ya zame mata darasi da kwashe wasu labaarn ta na faɗa mata." Ya Aina ta ce" Kar ma ta yi hankali ita ta sani. Amma yaushe kana Babba ka riƙa bin yaro ƙarami kana gaya masa maganganu. Ni fa ban ɗauka za ta fita da mganar Marwa ba har sai da na ce mata ya ce ba ya so kowa ya ji sai sun gama dai-daitawa da ita Marwan sai ya je ya sanar da magabantan shi amman shi ne ta je ta faɗa ma Ma'u ita kuma ta je ta sanar ma ƙanwar uwarta." Ya Aina ta ƙarishe faɗa cikin bayyana zafin abin har a cikin zuciyarta. "Wata Marwan? Me ya samu ita Marwa ɗin? Ya Aina ce ta sanar da ita abin ake ciki. "Shi ne fa ta je ta kwashe ta faɗa ma Ma'u ita kuma ta sanar ma Yayar mijin Sadiya shi ne ta ke ce ma Sadiya yadda ta shanye Yusuf shi ne za ta haɗa shi da ɗiyar yayarta domin shima a shanye shi tun da mu yan dangin asiri ne." "La'ila. Ya Aina" Rahila ta faɗa ta na tafa hannuwana cikin al'ajabi da mamaki. "Gaskiya Ma'u ta yi asara. Ta zama jaka tunda ta iya zaɓan bare a kan jininta. Na ji ta fita daga zuciyata sam" "Wallahi nima. Ta fita daga raina kwata kwata. Ji wani tsohon labari da ko mu da aka yi shi muna da wayau, mun manta amma ita da ta ji labari ta iya riƙe shi a ranta har ta na kai shi gaba. Tir da ita. Tir da mai hali irin na ta." Haka suka haɗu suna ta tattaunawa ni dai ina gefe ina jin su su sai yau suka san Ma'u? Ai ni na daɗe da sanin hallayarta mara sa kyau. "Gwara da kika je gidanta kika yi mata hauka tun da ba ta da mutumcina." In ji Rahila. "Nima haka na ce." Ya Aina ta maida mata martani. Rahila ta daɗe sai gabda mangariba ta tafi, ni kuma ina gidan Yallaɓai bai kirani ba nima ban kira shi ba. Yau ko su Jidda ban tuna da su ba, sai na ji komai ma ni ya fita daga kaina, ba na son komai kuma ba na jin daɗin komai, har dare da Babansu Marwa ya dawo ya ganni a gidan Ya Aina ba ta buɗa masa ba sai dai ta ce yar matsala ce muka samu da Yallaɓai. Nan fa ya zauna ya na min nasihan haƙuri da rayuwa jin sa kawai na ke yi domin duk abin da zan faɗa masa ba zai yarda ba gwara kawai na yi masa shuru. Can dare Ya Auwal ya kira Ya Aina ya ce Ya Hamza duk ya yi masa bayani kuma jibi shima ya na ta fe. Har Gwaggo sai da ta kira Ya Aina ta ce labari ba daɗi suka ji Alhaji ma duk ya shiga damuwa. Ita ta yi mata ma wasu bayanan, Gwaggo sai salati ta ke ɗaukowa ta na direwa. "Asma'u ta ba ni kunyam ban taɓa tunanin sakara ba ce sai yau." Gwaggo ta ce min bayan ta ce a bani wayar ta yi ta lallashina ta ce Alhaji zai yi adalci kuma Ma'u ba ta kyauta ba kuma za a gaya mata. A kallah dai yanzu sun yarda da cewa Ma'u munafuka ce kuma fuska biyu gare ta. Gidan Ya Aina na kwana akan gadon ta ni da Marwa. Ita kuma a turakan megidan ta kwana tun da asuba Kawu Abba ya kira wayata lokacin ma ina zaune kan darduma ina azkar ne bayan mun gaisa ya ce min. "Sadiya na ji duk abubuwan da suka faru. Ban ji daɗi ba. Amma ina so ki sani Tafida ba zai ƙyale wannan mganar ba. Yanzu haka ya kira su Kawu Sa'adu yau muna tafe za a yi zama a gidan Nene ki yi haƙuri duk wanda ya haɗa maganar nan domin ya tozartaki sai dai shi ya tozarta ta in sha Allahu." "Allah ya sa." Na faɗa cikin sanyin murya. Ba mu wani daɗe muna mgana ba har ya na ce min ina gidan su Marwanatu ko? Na kuma san ita Marwan ta faɗa masa ina gidan su tun da ai na ji ta ƙasa ƙasa da daddare suna waya. Da safiyar jumma'a na wayi gari a gidan Ya Aina duk breakfast ɗin da ta haɗa min ban iya cin komai ba sai Tea kawai da na sha. Yara duk sun tafi makaranta Marwa ce kuma aikin rana gare ta yau, Ya Aina ta saka min ruwan zafi na yi wanka ta ba ni kayanta na saka tunda yawancin jikin mu duk ɗaya ne sai dai ma ta dan fi ni kiɓa. Munnira ta kirani a waya ta na faɗa min suma an kira su gidan Nene ita da Hauwa. "Ni ba wanda ya kirani ko Yallaɓan ma tun jiya da ya sauke ni gidan Ya Aina ban ƙara jin sa ba." Munnira ta ce" Hmm jiya bayan tafiyarki an yi abubuwa Sadiya. Daman ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Sadiya Allah ya wanke ki. Tafida ya tsaya miki jiya har ita Gimbiya sai da ta raina kanta." "Me ya faru? Na faɗa cikin sanyin murya. "Bayan fitan ki Mimisco ta zo itama ta yi ta faɗa da Anty Bahijja. Da ita kanta Gimbiya Nene kuma ta ce tunda Anty Bahijja ba ta jin maganarta ta je tun da ta isar da abin da ta so. Da ko Tafida ya dira a gidan sai da ya haukace musu. Shi da Anty Bahijja suka yi kaca kaca Mimisco kuma ta da su Maman farko suka goya masa baya. Har da Nene da ya ce ba zai ƙyale maganar ba ta ce itama ba ta ce ya ƙyale ba. Ita kuma Gimbiya a gaban mu ya kalleta ya ce" Ke kuma  kin ban mamaki Saudatu! Sadiyar ce za ki bari masu zuga ki zuga ki ki yi mata ƙazafi? Shin kin ji lokacin da likita ya ce wani mganin zubar da ciki ki ka sha? Da har za a zo a yi mgana ki amince har kina maida zencen! Kin ban kumya. Ta yi miki alheri kin saka mata da sharri. Ina so ki sani ba zan ƙyale ki ba ke ma sai kin maimaita abin da kika faɗa a gaban hukuma." Nan fa hankalinta ya tashi ta fara kuka ta na ba da haƙuri da cewa Anty Bahijja ce ta ce yar uwan Sadiya ta ce ta na shiga malamai ƙilama ta so zubar mata da ciki shi ne ta ce ai ta taɓa ganin ƙanwar mamaki ta kawo miki mgani ta na rantsuwan ita abin da ta faɗa kenan kawai." "Munafuka." Na faɗa ina jin zafin daga ƙasan zuciyata. "Wallahi ai duk kukanta Tafida bai saurareta ba. Kowa fa ya ba su rashin gaskiya shi ne a ka ce yau za a yi zamacda gabaɗaya waɗanda abin ya faru suna nan." "Allah ya kyauta." Na faɗa ina cije baki, na ce mata ina gidan Ya Aina anan na kwana. "Su Jidda fa? "Muna gidan har dare amma ba su zo ba." "Ina ga suna gida tare da Baban su." Da haka muka yi sallama. Ya Balki ta zo gidan itama da safe ashe Ya Aina ce ta kira ta ta faɗa mata, itama ta yi ta gunduma ma Ma'u ashar ta na faɗin" Yar asara kawai. sai ta je ga ta ga mutanen duniyan nan." Tana ma gidan Yallaɓai ya kirani ya ce ya na kofar gida na fito. Ina fita fuskarsa ba fara'a  ina gaishe shi ya amsa ya na kallona kafin ya ce. "Kin tashi lafiya.? Bai jira amsawata ba ya ce" Shigo mota mu je." "Ina? "Gwammaja." Sai na ce bari na koma na ɗauko jakata da wayata. Ina komawa cikin gida na faɗa ma su Ya Aina ya ce mu je can gidansu yanzu. "Gwara ku je kan a yi ma lamarin tufkar hanci." Na tafi da cewa duk yadda ake ciki zan kira Ya Aina a waya. Ya Balki ta rakani da cewa" Shi ya gama na shi mu ma za mu yi namu Allah sai mun taru mun ci uban Ma'u ƙila za ta shiga taitayinta daga yanzu." Ni dai na fice na bar su, tunda na shiga motar nan Yallaɓai bai ce min ba nima ban ce masa ba sai da na ji ya na waya ya na faɗin ga shi nan ya ɗauko ni. Sai da na bari ya gama wayar sannan na kalle shi ina faɗin. "Ina so na fara zuwa gida." "Me za ki ɗauka? "Wani abu ne." Sai ya kalleni amma bai yi magana ba. Gida ya maida ni, na shiga ciki shi kuma yana cikin mota. Kaya na sauya da hijabi sannan na sauya takalmi, na shiga kitchen na ɗibo magungunar da Inna Mariya ta kawo min na tusa a jaka ta, a yanayin kitchen ɗin na gane a gida yara suka kwana Yallaɓai ya yi musu girki shi ya sa na ga kitchen ɗin a hautsine. Ko kafin na fito sai da ya kira waya na lokacin ma ina bakin get, sai na fito na rufe get ɗin da makulli, ina komawa motar ya juya muka nufi Gwammaja. Tare da shi muka jera har falon Nene sai na ga ashe ma kowa ya hallara mu kaɗai ake jira. Ga Kawu Sa'adu da Kawu Abba sai Hajiyar Tafida da Nene a saman kujera sauran duk suna ƙasa hatta ko da Mimisco har da su Hauwa duk suna falon. Duk da zarafina da a ka ci jiya a gidan bai sa na fasa zuwa gaban Nene da Hajiya na gaishe su ba suka amsa min kamar ba abin da ya faru. Sai na koma can kusa da su Hauwa na zauna sannan na gaida su Kawu Sa'adu da Mimisco. Anty Bahijja da Anty Maimuna kallo ba su isheni ba, ballatana wata Gimbiya can. "Ma sha Allah. Tun da su sun iso. Ku yi ma su Maman Farko mgana su shigo." In ji Kawu Abba. Halima ce ta tashi ta je ta kira su sai ga shi sun shigo tare. Su kan na gaishe su tun da su kam ba su yi min komai ba,  suka amsa min suma kamar ba abin da ya faru. Yallaɓai dai kusa da Kawu Abba ya zauna a saman kujera. Mimisco ta buɗe taron da addu'a sannan Kawu Sa'adu ya fara jawabi. "Kowa anan wajen ya san dalilin taruwar mu a wannan falon jiya da yamma Tafida ya kira ni cikin damuwa ya na ba ni wani labari da ya ɗaga min hankali. Da cewa ke Bahijja kin ci zarafin mai ɗakin sa da yi mata kazafin ta na son zubar ma da ita amaryansa Saudatu juna biyu! Sannan har kina ikararin ita yar asiri ce kina ba da wani labarin da ba wanda ya san da ingancinsa. Abin na ki bai tsaya nan ba sai da kika bita da baƙaken maganganu mara sa daɗi waɗanda suka yi dai-dai da kin ci mata mutumci. Ta ce za ta kai hukuma shi ya hana ta da cewa shi ya kamata ya ɗau mataki shi kuma ya ga ya na da manya shi ya sa ya kira ni ya sanar da ni, ni kuma na taka na je na samu Hajiya na ce ta shirya mu je tare a yi komai a gabanta." Sai ya ɗan dakata falon ya yi shuru sai saukan numfashin mutane. "Ko ba haka a ka yi ba ke Bahijja? Ya faɗa ya na kallonta sai ta dago kanta ina kallonta ban ga alamun nadama a cikin idanuwanta ba. "Haka ne. Amma ai nima ba a ji zagina da.." "Ban tambaye ki ba." Ya daka mata tsawa sai ta yi shuru. Ni ya kallah kafin ya koma ya na kallon ita Anty Bahijjan ɗin "Ina jin ki yanzu ki faɗa min farkon abin da ya faru." Jin haka yasa ta gyara zama ta na rattabowa har da ƙarya wai na zazzageta. A cewarta mganar asiri ba ita ta faɗa ba yar'uwa Ma'u ce da ta zo gai da Gimbiya a asibiti ta ce sai an bi a sannu saboda zan iya zubar da cikin gimbiya. "A cewarta daman halin Sadiya ne shige shige. Tun da dangi mamanta su har shaidan bin bokaye aka yi musu. Ban san da labari ba sai ga shi ta na faɗa min ni kuma na ga yar'uwanta ne tare suka tashi ta fi kowa sanin Sadiya shi ya sa na yarda. Sannan da na zo ina mgana sai Gimbiya ta ce ai taɓa ganin Innarta ta kawo mata wasu maganguna ta na tunanin na asirin ne. Ni me na faɗa? Duk abin da ya faru ne na faɗa sai a ga laifina? Ta faɗa ta na hararata ni ko kallonta kawai na ke yi amma na kasa mgana saboda tsabar mamakinta. "Shi likitan ne ya ce wani abu ne ita Saudatun ta ci da cikin ya kusa zubewa? Ya katse mata mganarta sai ta fara kame kame. "Bai ce ba amma ya ce ta ci wani abu da cikin ta bai  karɓa ba." "Sai kuma ke kika ce  ita Sadiya ce ta yi sanadin hakan? "To Kawu a gidan ta take. Kuma ita ta dafa abincin da Gimbiya ta ci na ƙarshe ko kai ne Kawu wa za ka zarga? "shi ne hujjar ki? Sai ta yi shuru ta kasa mgana sai ya dawo da kallon shi kaina ya kira sunana na amsa cikin ladabi. "Kamar yadda Bahijja ta yi mana bayanin abin da ya faru kema za ki iya yi mana bayanin farkon abin da ya faru? "In sha Allahu Kawu." "Bismallah." Nima ko na gyara zama na fara mai da abin da ya faru tun zuwana gidan a jiya da zubar da abincin har zage zagen da muka yi ban ɓoye ba na faɗa na ƙarishe da faɗin" Kawu ni babban abin da ya fi ɓata min rai ƙazafin da suka yi min. Amma ta wani fannin ba ta da laifi tunda yar uwata ce ta ba da ni,   sai dai itama ba zan ƙyaleta ba mgana ta kai gaba za a ɗauki mataki. Saboda haka suma ina so a yi min adalci a bi min haƙƙin kazafin da suka yi min domin ba zan yafe ba " Na karishe faɗa ina mai rufe fuskata saboda kukan da ya ta so min "Kina da gaskiya. Tabbas wannan cim zarafi ne." In ji Kawu Sa'adu." "Ke Bahijja ni sa'an wasanki ne da za ki shiga gona ta don uban ki? Kawu Abba ya faɗa bayan ya daka mata tsaawa a fusace saboda har da mganganun da ta faɗa akan Marwa sai da na faɗa. Ai sai Anty Bahijja ta fara rantsuwa sharri na ƙulla mata ita ba ta ce  haka ba. "Kuma ko mganar Kawu Abba ɗin iita ƴar uwan Sadiya ta faɗa min." Ta faɗa ta na wani tura baki saboda Kawu ya zage ta. "To ina ruwan ki da Sha'anina! Ko uwarki gata nan zaune ba ta isa ta hana ni abin da na yi niyya ba. Sai dai ta ba ni shawara ballatana ke karan kaɗa miya? Kuma kina duniya zan auri ɗiyar yayar Sadiya sai dai ki mutu saboda baƙin ciki" "Kawu ni.." "Ba na son ji wata magana. Ke daman ina da labarinki kin cika saka ido. Ke wa ya je gidan mijin ki ya takura miki? Ok to ke da kike zaune lafiya ke ma asirin kike yi kenan ko? Kawu Abba ya ƙarishe faɗa a fusace, da ga ganin yadda ya ke mgana ran shi a ɓace ya ke. Tafida dai ƙala bai ce ba daga shi har Nene da Hajiyar Tafida. Sai Anty Bahijja ta fara kuka. Kawu Abba ya ce ta rufe ma mutane baki, kuma fa bai girmeta ba amma matsayin shi na Kawunta sannan kuma daman shi ba shi da wasa. "Kin takura mata ita da mijinta amma ke kina can kina zaune lafiya a gidan auran ki? Wanzami daman ai ba ya son jarfa ke ko an faɗa miki wata mgana ya kamata ki zo ki saki maganar kai tsaye? Shekaran Sadiya nawa tare da ku duk ba ki san haka ba sai yanzu? "Ni kaina sai da na ce ta bar mganar da ta faɗa min amma ba ta ji magana ta ba " Nene ta faɗa cikin bayyana ɓacin ranta. "Ni fa ba laifin kowa na ke gani ba sai na wannan yar'uwan Sadiyan duk ita ta ɓata komai. Ya kamata itama ta na wajen nan" Hajiyar Tafida ta faɗa itama. "Ba ruwammu da ita. Can tsakaninsu ne da Sadiya amma tabbas alaqar tun da ba ta alheri ba ce rabuwar shi ya fi." Kawu Sa'adu ya ce haka sai Anty Maimuna ta fara faɗin ai Ma'u ta na auran yaron yayar mijin Anty Bahijja ne. "To sai me? Za mu raba alaqar ko da ta fi karfin haka ballantana ba ta yi wani karfi ba." "Sosai. Tunda daga ita Bahijjan har ita dayan ba alheri a zukatan  su." In ji Mimisco da daman ita yar gaskiya da gaskiya ce. Duk kuma mganar da aka faɗa sai Anty Bahijja ta karyata Allah ya sa ga shaidu suka maida yadda na faɗa daki daki. Gimbiya ta sha kunya domin kai tsaye Kawu ya kalleta ya na faɗin" Ke Saudatu  ke ma kin ƙara hura fitina ke da kika zauna gidan Sadiya ta dafa abinci ta ba ki kina kwance sai ki saka mata da sharri? Kuma ke fa kika aure mata miji ita ba ta biki da sharri ba sai ke? Sai ta fara kuka tana faɗin a yi haƙuri kuskure ne ba za ta ƙara ba. "Ba tarbiyan da na yi ma Saudatu ba kenan ni kaina ta ba ni kunya." In ji Hajiyar Tafida. Ita kuma Nene sai ta ce koma me ya faru Anty Bahijja ce ta ja shi. Sai ta ƙara saka kuka ta na faɗin shike nan duk an maida laifi a kanta ba a duba nima cin mutumcin da na yi mata ba. "Ke kika fara ci mata mutumci. Kuma ta yi min dai-dai da ta rama kwatankwacin yadda kika yi mata." Tafida ya faɗa cikin fusata Kawu Abba ya taya shi da cewa" Kuma daman in babba bai ji kunyar hawa jaki ba. To shima jaki ba zai ci kunyar ka da shi ba. Ke kika zubar da girman ki, ban ga laifin duk wanda ya taka ki ba. Me ya sa ita Zuwaira ba a yi mata ba? Saboda ta kama kanta ba ta kuma zama ji da jiyarwan da kika zama ba." Sai ta ƙara fashewa da kuka ta kasa mgana ita da Gimbiya sai kunya. "Ba kuka za ki yi ba haƙuri zaki juya ki ba ta ki kuma janye kalaman da kika yi a kanta. In ba haka ba zan bar Tafida ya ɗau matakin da ya dace." Kawu Sa'adu ya faɗi haka Anty Bahijja da ta san akwai ranar da za ta zo ta ba ni haƙuri da ba ta aikata ba abin da aikata ba. Kowa kuma ita ya ba ma rashin gaskiya har su Maman farko dole ta juya ta ba ni haƙuri na ƙi mgana. "Sadiya ki yi hakuri kin ji ko? In sha Allahu ba za ta ƙara ba." In ji Nene sai na ga girmama maganar Nene shi ya sa na ce na yafe mata amma sai dai na ce"kin ci darajan Yusuf da Nene shi ya sa na yafe miki." Gimbiya ma aka ce ta ba ni haƙuri ta ba ni haƙuri Hajiyar Tafida ma ta ba ni haƙuri na yi shuru ban yi magana ba itama. "Ki yi hakuri kin ji ko? Yallaɓai ya faɗa a hankali ya na kallona. "Zan haƙura amma sai na cire mata kokwanto." Kafin ma ya yi mgana na zazzage jakata na fito da mgungunan a tsakiyar falon. "Ga mganin da ta ce Inna ta ta kawo min mganin sanyi na wanke mahaifa ne na ga ta karɓo ma yarta yana yi shi ne na ba da kuɗi ta kawo min. Wallahi tallahi ban taɓa karɓan wani abu da sunan na asiri domin na cutar da mijina ko makusantansa ba." Na karishe faɗa ciki son na yi kuka. "Ba ki yarda da ni ba ne? Yallaɓai ya katse ni, jin na ce zan Kira Inna Mariya ta yi mgana anan wajen. "Ba sai kin kirata ba Na yarda da ke duniya da lahira Sadiya." "Ba kai ba. Kowa ma saboda ya cire tantama a kaina." Kawu Sa'adu ya ce a bari na kira hakan da na kyau. Nan ta ke na kirata na saka ta a handfree bayan mun gaisa sai na ce. "Inna Mariya wai mganin da kika karɓo min mganin me ya ke yi wata ke tambaya ta? "Ya na wanke mara sannan ya na mganin sanyi sannan ya na wanke mahaifa ko mace ta daɗe ba ta haihu ba in dai ta yi amfani dashi ana dacewa. Ya na da kyau sosai kin fara amfani da shi ne? "Ban fara ba amma zan fara." "Ki fara Sadiya in sha Allahu za ki da ce" "Na amsa mata da Amin sannan muka yi sallama kai tsaye na kalli Gimbiya kafin na ce" Ina so ki sani ko ban taɓa haihuwa ba, ba zan yi shirka ba saboda ni na fito gidan tarbiya. Ballatana na haihu Saudatu ƴaƴana biyu ko a haka ubangiji ya bar ni ya gama min komai saboda haka ki sani ko duniya za ki tara abin da za ki haifa ba zai taɓa tsole min ido ba. Sannan duk da ban yi dogon zama da ke ba, ba zan yanke miki hukunci ba, zan yi miki kyakyawan shaida da uziri ina fatan ko anan gaba ki rika yi ma mutanen zaton alheri ba na sharri ba. Na yafe miki Allah ya kyauta na gaba." Na faɗa ina mai kauda kai, sai ga shi kunya ya gama lulluɓeta. Kawu Sa'adu ya ce" Gaskiya ne ya kamata mu riƙa kyautatama junan mu zato." Nima ya saka ni na ba ma Anty Bahijja haƙuri, na ba ta ba domin ina ji a raina na yi mata wani abun ba sai domin yi masa kara tun da shi babba ne kuma bai kamata na watsa masa ƙasa a ido ba. Sannan ya sha ta layi tsakanin Bahijja da Ma'u ya ce kar ta ƙara zuwa gidan nan bai hana su haɗu can dangin mijinta ba amma in aka sake jin wata mgana ta bullo ba za su hana ni na ɗau matakin da ya kamata ba. "Nima Kawu ka faɗa mata kar ta ƙara shiga harkan gidana da matana. Ba Saudatu ba Sadiya ba. Ta kama girmanta a matsayinta na yayata su kuma su girmamata a matsayinta na yayar mijinsu." In ji Yallaɓai. "Fakat" Kawu Abba ya faɗa, Kawu Sa'adu ya ce gaskiya kar ya ji kar ya ƙara gani. Har Anty Maimuna itama an ce kowacce ta ji da kanta ba ruwansu da matan ƙannensu. Mazan su ne dolen su su tsaya a kansu. Itama Gimbiya Yallaɓai ya ce ya yi mata tsakani da Anty Bahijja bai ce ya raba su ba amma ta sani su yi zumumcin su kawai in har wani munafunci ya sake fitowa sai ta raina kanta da sauri ta ce ba za a ƙara ba. Kafin a tashi Kaawu Abba ya gyara zama ya na faɗin" "Na so sai mun gama daidaitawa da Marwa kafin na kawo mganar amma tunda maganar ta yo kutse, shi kenan ni na ga ɗiyar Yayar Sadiya ina so ga Tafidan nan shi ya rakani gidansu na nemi izini ko Sadiyan ba ta sani ba, ina so kowa da ke nan ya shaida nan da lokaci kaɗan zan tura maganata domin a yi maganar aure. Wanda bai so abin ba  ya yi shurun sa kar ma ya saka albarka tunda da saka albarkarshi da rashin sakawan duk ɗaya ne ni a wajena." Kawu Sa'adu ya ce duk lamarin bai kai haka ba. Abu dai  ya riga ya faru a yi haƙuri a tari gaba tun da sun ba da haƙuri sun ce ba za su ƙara ba. To a yi musu afuwa. Da haka taron ya tashi, ban ko tsayawa ba na ce zan koma gida Yallaɓai ya ba ni kuɗin adai-daita muka fita tare da su Hauwa suna ta cewa Anty Bahijja ta sha kunya, da ga ita har Gimbiyar ni dai ban ce komai ba. Duk da na ɗan ji sanyi da Yallaɓai ya tsaya min amma ba a biyani ba tunda ba a bar ni na kai hukuma ba. Gidana na koma amma na kira Ya Aina na faɗa mata, na ce an yi muui mgana sun nemi gafara Amma sun shiga tsakanina da su gabaɗaya. "Hakan ma ya yi. Hamza ya ce min ya na hanya ma." Na ce Allah ya kawo shi lafiya. Tuɓewa na yi na fara gyaran gidana da ya yi datti. Bayan na gama ɗora girki, taliya na yi da miya, kayan miyan ma sai da na kira Yallaɓai ya aiko min da cefanen kayan miya shi na ya yi bilandin na yi miya da kifi. Da su Jidda suka dawo makaranta suka ganni suna ta murna na sha labari wajen Baby. Jidda na faɗin suna ta tambayana Abba ya ce wai na yi tafiya ne ni kaina na ji daɗi da na gansu ashe na yi kewarsu ban sani ba. Da su na yini a gidana suka ɗebe min kewa sai bayan isha'i Yallaɓai ya shigo da kayan marmari da yawa a leda. *Janafty* *TKG019019* Da yake na san Yallaɓai ba ya son cin taliya a cewarsa wai ba ta ƙosar dashi. Shi ya sa sai na dafa masa shinkafa mai karas da kabeji. Mu kuma sai muka ci sauran taliyan da ta rage ni da yara. Kayan marmarin da ya kawo rabi na ɗibar mana na wanke muka ci, rabi kuma na saka a cikin frizer. Sai da Yallaɓai ya yi wanka ya sauya kaya zuwa wasu sauƙaƙku na zaman gida sannan ya ci abinci ya na cin abincin ina gefen shi amma da ka ganni za ka fahimci sai a hankali saboda na zama wata shuru shuru kamar wata  mara lafiya. Duk da na saka kaya masu kyau amma ban yi kwalliya ba fuskata kawai in ka kalla za ka fahimci damuwa ƙara ƙara tun da har damuwar ta bayyana. Ya na gama cin abinci bayan na tattara komai na mai da kitchen yara kuma na ce su shiga ciki su kwanta. Nan na bar Yallaɓai a falo ya kunna kallo ni kuma sai na shiga ciki tiolet na fara shiga na kama ruwa sannan na fito na yi shirin kwanciya. Har na ma kwanta na rufe ƙafafuna zuwa saman cikina da bargo na kuma rage hasken ɗakin sannan can na ji shigowar Yallaɓai shima kayan jikinsa ya cire ya saka na barci sannan ya biyo ni kan gadon. A bayana ya kwanto ya na mai riƙo hannuwana da na harɗe ƙirjina da su, ya fara ɗan shafawa kaɗan kaɗan lokaci ɗaya ya na kiran sunana. "Sadiya ta." "Uhm" Na amsa a cikin maƙoshina, sai da ya ɗan yi jim kafin ya cigaba da faɗin" Ki yi haƙuri kin ji ko? Sai na gyaɗa masa kai ba tare da na yi magana ba. Haƙurin kam tabbas zan yi amma ba na jin zan iya mantawa da abin da suka yi min har gaban abada kuwa. "Ki yafe musu. Musamman ma Daughter ta yi nadama sosai kuma ta faɗa zugan Anty Bahijja ne sai sheɗan ya yi tasiri a kanta." Ita ce sheɗaniyar kanta na faɗa a cikin raina a fili ko numfashi kawai na fesar ba tare da na sake yin wata mgana ba. "Ki yi haƙuri ki manta komai don Allah" Nan ma shuru na yi sai ya leƙo fuskata lokaci ɗaya ya na faɗin" Kin ji ko? Sai na kaɗa kaina kafin na ce" Na ji. Ya wuce." "Ba irin wannan wucewan ba. Ina so ki yafe musu sannan ki manta da komai kar ki ce za ki riƙe su a cikin ranki. Sannan kar ki ce za ki daina zumunci da su. Sun zama dole a garemu Sadiya. Daugther matata ce Anty Bahijja kuma yayata ce ita ta saki nono na kama. Kin ga ke ma sun zama dolen ki, ina so ki cire abin a ranki in kun haɗu ki mu'amalance su kamar yadda kika saba." Kawai sai na yi shuru ina sauraran Yallaɓai. Haba ai maciji  sau ɗaya ya ke saran mumini ya yi hankali. Shi a tunanin shi zan ƙara sakar musu ne! Har abada ai sun yi min hankali sannan na yi karatun duniya na ƙara shiga taitayina. "Ba ki ce komai ba? Ya sake tambayata sai na gyara kwanciyata kaɗan duk da har lokacin bai bar jikina ba sannan bai sake ni ba. "Ban yi maka alƙwarin zan cigaba da mu'amala da su kamar baya ba. Sai dai na yi maka alƙwarin zan manta komai a hankali ba da gaggawa ba." "Me ya sa?   Sai da na ɗago na kalle shi ta hasken da ya ke shigowa ta window ɗin bedroom ɗin mu. Sannan na koma na kwantar da kaina a saman filo ina faɗin . "Saboda sun yi min hankali. A kan su na ƙara sanin karatun duniya. Ka yi haƙuri amma ba zan iya sake sakin jiki da su ba." Ya buɗe baki zai yi magana na yi saurin tare shi. "Kar ka matsa min Yallaɓai. Wataƙila a hankali in na manta na iya kallon su a matsayin kallon da na ke yi musu a baya. Shi ya sa na ce kar ka matsa min don Allah." Sai ya yi shuru bai ƙara magana ba. Sai dai ya karkato ni ina fuskantar shi, sumbatar goshina ya fara har ya gangaro saman bakina ya fara sumbatata. Duk da ba na cikin mood ɗin amma ban ture tayin shi ba. Sai nima na tallafe shi muka samar ma junanmu natsuwa ba mu wani daɗe  kamar yadda muka saba ba daga shi har ni ɗin ba mu da wani karsashi da baƙatuwa shi ya sa  lamarin bai yi  mana armashi kamar yadda muka saba ba. A daran muka tsarkake jikin mu, shi ya rigani barci ni kam na daɗe ban yi barci ba sai wajajen biyu saura na dare na samu barci ya kwashe ni.   Washegari kuma daman Asabar ne. Ina idar da sallar asuba na fara azkar kenan barci ya ɗauke ni a nan saman darduma Yallaɓai ne ma ya tashe ni ina layi na haye gado. Ba ni ta shi ba sai  da wayar Ya Hamza ta tashe ni. Sai bayan mun gama wayar ne na duba agogon wayata na ga har sha ɗaya saura na safe ai sai na diro daga kan gado na fita can falo yara na iske ba su nan  sun tafi hadda. Sai Yallaɓai kaɗai ne a gidan ya na aiki a system ɗin shi. "Ina kwana." Na faɗa lokacin da na shiga falon shi na gan shi zaune ya na aiki. "Kin tashi lafiya? Ya faɗa ya na mai ɗagowa ya na kallona. Sai na jinjina masa kai. Ban tambaye shi yara ba saboda na san sun tafi hadda ne. Na juya zan bar falon na ji shi ya na ce min." Tea suka sha sai ƙwai da Jidda ta soya musu suka ci suka tafi makaranta." Sai na gyaɗa kaina daga nan kitchen ɗin na shiga wato aikin na manya ne an yi kaca kaca da kitchen ɗin da jiya na gama wahalan gyarawa. Haushi duk ya kamani mu ma tea ɗin na sake dafa mana sai na fere mana doya muka sha dashi. Na so na ɗan gasa mana buredi sai kuma na fasa ganin rana ta yi, muna cikin karyawa na ce ma Yallaɓai ina son zan je Ɗorayi. "Ki shirya in zan fita sai na sauke ki kafin na wuce office" Yadda bai tambayeni me zan je ba, nima ban faɗa masa ba saboda na san ya san ba zai wuce maaganar Ma'u ba. Muna gamawa Yallaɓai ya fara yin wanka ni kuma sai na ɗan tsaya na gyara kitchen ga himilin wanke wanke. Saude ba ta nan fa ta tafi garin su ni kaina ban san ta tafi ba sai daga baya. Na yi ta faɗa da cewa ana tsakar makaranta ai ba a tafiya, ita kuma Balaraba sai ta ce wai auren ɗiyar ƙanin babansu ake yi Sauden ta matsa sai ta je. Ni dai fata na kar su je can su yi mata aure tun da can ƙauye sokoto ne garin  baban na su. Wanke wanke kawai na yi sauran ayyukan na ce in Jidda sun dawo ta ɗan gyara gidan. Yallaɓai na son tafiya tun da ana ta kiran shi ya yi baƙi. Mun bar gida wajen sha ɗaya da rabi na rana ya kai ni ɗorayi bai ko shiga ba ya wuce. Na je na iske Ya Hamza da Gwaggo a falon Alhajinmu ne suna hira nima sai na bi ayarin su. Bayan mun gaisa da Alhaji da Gwaggo ne na juya ina gaida Ya Hamza ina tambayan shi ya wajen su Khaleesat? "Duk suna nan lafiya. Sun ce a gaishe ku." Mun ɗan yi hira sama sama a kan sanyin da ake yi a can zaria. Sai ya kalleni kafin ya ce" Jiya an yi zama a can gidan Baban su Jiddan? Sai na gyaɗa masa kai kafin na fara bashi labarin abin da ya faru. Gwaggo na gefe ta na ji ita da Alhajinmu. "Ka ji ko Alhaji.? Ma'u sheɗaniya ce. Ta haɗa husuma ta na neman wargaza zaman lafiya a gidan auran Sadiya." Ya Hamza ya faɗa cikin ɓacin rai ganin haka ya sa na kalli Alhajinmu shi da Gwaggo da suka yi shuru sun kasa mgana na ce" To ita da ta ce ma Anty Bahijja a yi hankali da ni. Ina shige shigen malamai zan iya yin komai domin na ga bayan cikin Amaryan Yallaɓai." Gwaggo ta saka salati tana tafa hannu. "Kai Ma'u ta yi asara. Ta kuma ba ni mamaki. Wallahi tun da na ji abin da ya faru na kasa suƙuni kawai mamaki na ke yi me kika yi ma Asma'u da zafi haka da ta nemi tozarki haka Sadiya? "Me kuwa na yi mata Gwaggo? Na faɗa muku tun a baya kan fasa auranta da Ya Hamza ne daman ta ce na jira zan gani. Kuma ta daɗe ta na yi min shige da fice yanzu dai burinta ya cika akaina ta yi min sharri ta kuma yi sa'a na tozarta." "Za ta ko ci ubanta. Har Baaba sai an kira ta zo domin a kawo ƙarshen makircinta." Ya Hamza ya faɗa cikin jin haushi Gwaggo ta ce haka ya kamata a matseta sai ta faɗi dalilinta na aikata abin da ta aikata. Alhajinmu na zaune amma ƙala bai ce ba sai kaɗa kai kawai ya ke yi lamarin ya gama ba shi mamaki. Muna cikin magana da Ya Hamza Alhajinmu ya kira sunana na amsa ina mai kallon shi. "Ki faɗa min tun farko yadda lamarin ya faru." Na gyara zama na sake faɗa musu duk abin da ya faru har zuwa gidan Ma'u da na yi na ja ta da faɗa sai da na faɗa saboda ban ga abin ɓoyewa ba ni ai ban ma samu yadda na ke so ba, da na samu da tuni ta na gadon asibiti. " Daman ba tun yanzu ba. Na daɗe ina jin wasu labaraina a bakin Yayar mijina Alhajinmu. Ban taɓa ɗaga maganar ba saboda ko na ɗaga sai a ce ni ce ke da fitina tun da Alhaji ka ce in ban yi zumunci da Ma'u ba za ka yi fushi da ni ya sa na kauda komai ina zumunci da ita to ashe ita babban burinta na tozarta. Ta tozarta zuru'an Mama ni kuma ta yi min ƙazafin ina ƙokarin zubar da cikin Amaryan Yallaɓai. Alhaji ka yi haƙuri amma ina jin lokacin da zan datse zumuncin da ke tsakanina da Ma'u ya yi. Kuma na tabbata kaima ba za ka ce don me ba, domin matuƙar cin zarafi Ma'u ta gama yi min shi anan duniya." Gwaggo ta nisa amma  ba ta yi magana ba. Ya Hamza ko ya ce gaskiya ne babu amfanin yin zumunci da wanda ke neman ya tozarta ka. Ya kalli Alhajinmu ya na sake faɗin" Alhajinmu mataki za ka ɗauka domin bayan Sadiya har kai yar iskar yarinyar nan ta ci ma mutumci." Alhajinmu kai kawai ya girgiza ba taree da ya yi magana ba. "Ga ma labarin Marwa. Ƙanin Nene ya ganta gidana ya ce ya na so. Wallahi Babansu Jidda ya raka shi wajen Babansu Marwa ya neme ni izini ya na zuwa wajenta domin su dai-dai ta daman ya ce sai sun gama yarda da juna zai kai mganar ga manya. Amma Ya Murja na samun labari ta je ta faɗa ma Ma'u ita kuma munafuka ta kwashe ta faɗa ma Anty Bahijja. A ranar da abin ya faru har ta na ce min ban isa ba yadda na asirci Yallaɓai ne na ke so na tusa ma Kawun su ɗiyar Yayata shima a asirce shi sai yadda aka yi da shi tun da mu yan na gada ne ba haya ba." Gwaggo ta ƙara saka salati ta na faɗin" Na ga duniya ni Maimuna. Me Ma'u ta ke so ta zama ne! Ko na ce ta zama ma? Ya Hamza ya yi wani kayci kafin ya ce" Ni fa daman tuni na san za a rina. Tun a baya ta fi kowa kalkalin mgana da tsara zence. Ta ko gama ma kanta aiki sai ta gane ba ta da wayau" Alhajinmu ya jinjina kai kafin ya ce" Tabbas Ma'u ta yi kuskure. Kuma ya zama wajibi a nuna mata kuskurenta." "Tabbas." Gwaggo ta faɗa daga gani itama ranta duk ya gama ɓaci. "Hamza kira min Hasiya mu yi mgana." Alhajinmu ya faɗa ya na kallon Ya Hamza nan ta ke ko ya doka ma Baaba kira. A handfree Ya Hamza ya saka wayar bayan sun gaisa sai Alhajinmu ya ce ta zo gobe in da sarari ya na son ganinta kawai sai itama ta ce. "Daman ko ba ka kirani ba Ya Sule ni zan kira ka. Kana da labarin Sadiya ta je har gida ta daki Ma'u? Me ta yi mata? Ko na ce me Ma'u ta tsareta mata da ta tsane har haka? Ni da Ya Hamza muka kalli juna cikin mamaki. Ni fa ban yi wani mamaki ba domin yadda na san yunwar cikina a haka na san wacece Ma'u kuma ina da tabbacin ta san Ƙwanta ne ya fashe ya yi wari shi ne ta kira Baaba ta shirya mata mgana yadda in aka taso da maganar za ta samu mai tsaya mata. "Na samu labari. Kuma akan haka ne na ce ki zo." "To ai dai ya fi. Gwara ga Sadiya ga Ma'u sai na ji abin da ta yi mata da ta bi ta har gida ta dake ta" Ta na ta faɗa fa, ta na nuna daman ai tun zuwan Ma'u gidanmu ba ƙiyayyar da ban nuna mata ba, yanzu ma ta yi auren ban ƙyaleta ba to itama ta daina yin shuru wannan karon sai ta ji dalili. "Baaba ma ta na ƙara ɗaure ma yarinyar nan kugun yin wasu abubuwan" Ya Hamza ya faɗa cikin mamakin mganganun Baaba a waya. "Daman ai Hasiya ba ta son laifin Ma'u. Shi ya sa ta ke goyon bayan duk abin da ta faɗa mata." Ni dai mirmishi kawai na yi, to ko na yi mgana ban san me zan ce ba. In faɗa musu saboda Ma'u Baaba ta tsane ni ko na ce daman tun can ba ta so uwata ba shi ya sa nima ba ta sona. Ko na faɗi haka za a iya ƙaryatawa amma a cikin raina na kudiri niyyar gobe in aka zo zama wallahi ba zan raga mata ba, tunda ni ba ni da uwar da za ta kare laifina ai ina da bakin da ni zan iya ƙwatan kaina. "Bakomai. Allah ya kaimu goben zan kira Asma'u ta zo da megidanta kema goben ki taho tare da Yusufan kin ji? Alhajinmu ya faɗa ya na kallona sai na amsa da in sha Allahu. Ban daɗe ba bayan azahar na koma gida saboda na bar gidan ba shara. Bayan na tuɓe na share gidan na yi mopping na saka turaren wuta gidan ya ɗau kamshi. Mganin da Inna Mariya ta kawo min ko a raina ban ji ba na so na yi amfani da shi ba. Daman na asibitin sauran kaɗan na adana shi da cewa na asibitin na ƙarewa zan fara amfani da shi in gani ko za a dace. Duk da ko na asibitin ma ya yi min sosai. Ya dai-daita min lokacin al'adata  kwanakin nan yanzu lafiya lau na ke yi na gama sannan ba wannan azababben ciwon maran sai ɗan abin da ba rasa ba. Sai shidda su Jidda suka dawo daga hadda. Allah ya sa na gama abinci da wuri jalop ɗin kuskus na yi musu mai kayan lambu da hanta abinci ni kaina na san ya yi daɗi. Haka Jidda da Baby suka rika santi suna faɗin" Umma girkin ki ya yi daɗi sosai." Ina dariya na ce ko na saka musu waigi ne suna santi ne. Daman sun dawo a jigace tea kawai da buredi suka tafi dashi makaranta to daman ina tea zai riƙe su tun safe har yamma dole su ji kunya. Maimakon su dafa ko indomie ne, ko da ya ke na rasa me ya sa ba su son tafiya da indomie makaranta, barin ma Jidda sai ta ce wai indomie na yara ne, in dai ba ni ce na tashi na dafa musu taliya ko shinkafa suka tafi da shi ba ta gwammace su ɗura tea a goran su da buredi su tafi dashi akan su dafa indomie. Yallaɓai sai wajen tara na dare ya dawo ya zo da yara da rake mai yawa ya ce Nene ce ta ba shi ya kawo mana ni da yara. Na karɓa na ce mun gode daman ko bai faɗa ba na san zai biya ta can tun da matarsa na ca. Jidda ce ma ta tambaye shi ina Anty Gimbiya? Ya ce ta na  gidan Nene ta na gaishe su amma ni ko sunanta na ji an ambata sai raina ya ɓaci kuma a saman fuskata ma rashin jin daɗin ya na bayyana. Tun a daran na faɗa masa Alhajinmu na neman mu ni da shi a gida gobe, bai tamnbayi dalili ba ya ce Allah ya kaimu. Shi ya sa tun safe na tashi na dafa ma su Jidda Macaroni da Miya suka tafi da shi makaranta. Indomie kuma suka ci kafin su tafi, sai da na yi wanke wanke na gyara kitchen sannan na yi wanka shara daman na ce na gaji gaskiya sai gobe ina dalili har bayana na ciwo. Saude duk ta sangartani, mu kan mu da indomie da ƙwai muka karya sannan muka fita, muna hanya Ya Aina ta kira wayara wajen goma na safe tace kowa ya zo ni kaɗai ake jira na ce gamu nan a kan hanya. Ko da muka isa falon Alhajinmu cike, har Baaba ta iso matar nan ina gaisheta ba ta amsa ba, ni ko ban ƙara ba na wuce wajen Gwaggo na duka ina gaisheta ita da Alhajinmu. Shi kuma Yallaɓai ya fara gaisawa da Mazan har Ya Auwal na gani shi jiya da yamma ya sauka garin. Sai Ya Muntari da Ya Abubakar sai Alhaji Mustapha, matan kuma daga ni sai Ma'u sai Ya Aina sai Ya Balki sai kuma Ya Murja sai Gwaggo da Baaba. Dukkansu na yi musu magana ban da Ma'u. Saboda sai da na ganta na sake jin wani ƙuna ya taso min daga ƙasan zuciyata ta kalle ni nima na kalleta amma ba mu yi ma juna mgana ba. Sai dai na ɗan ji sanyi da na ga fuskarta gefe da gefe duk sun kumbura. A gefen Ya Aina na samu waje na zauna shi kuma Yallaɓai sai ya zauna a gefen da Ya Hamza ya ke zaune a ƙasan cafet ɗin da ke malale a falon Alhajinmu.   Ya Muntari Alhajinmu ya umarta shi ya buɗe mana taro da addu'a. Sannan ya ce dangane da sanin dalilin taruwarmu wasu sun sani wasu kuma ba su sani ba. Amma yanzu zan ƙara mamaita dalilin taruwarmu anan wajen yanzu nan kuma. Kiran sunana Alhajinmu ya yi na amsa sai ya ce na faɗi duk abin da ya faru daga farko har ƙarshe. Na ko gyara zama na fara maida zence kafin na gama Ma'u ta fara kukan makirci Baaba ko ina dire maganata ta nuna ni da yatsa kafin ta ce" Ƙarya kike masharranciya. Asma'un ne za ta faɗi haka? Ai ko ba ta san in da kika fito ba Sadiya Asma'u ba ta da wannan halin ki dai canza wata ƙarya wannan ba ta hau ba." "In karya ake yi mata ai ga ta nan sai ta ƙarya ta ko? Ya Hamza ya katse ta itama sai ta kalleshi kafin ta sake wata mgama ya kalli Ma'u ya na faɗin" Ba ga ta nan ba. Ta buɗe ta ce duk abin da aka faɗa sharri ne ba gaskiya ba." Sai Baaba ta kalli Ma'u ta na faɗin" Bar kuka buɗe baki ki karyata ta a gaban kowa da kowa" Na san daman Ma'u za ta iya karyata ni shi ya sa ma da ta buɗe ba ki ta ce ƙarya ne ita ba ta faɗa ba ban yi mamaki ba. "To kun ji dai ko? Ina fatan yanzu za ku yarda Sadiya na bin Asma'u da bi ta da ƙulli. Kuma magana kan dangin bokaye ba Mau ce ta faɗe shi ba tun tale tale haka ake kiran gidan su Ruƙayya da shi, su kan su ai ba su isa su hana ba. Wataƙila itama yayar mijin na Sadiya a can a gari ta ji labarin shi ne saboda kin tsani Asma'u za ƙi kulla mata sharrin ita ta faɗa ko? Ta ƙarishe faɗa ta na kallona sai ma na kasa mgana, ina tattaro abin da ya kamata na maida mata kar ace na yi rashin kunya. "Baban Jidda ko za ka taimaka ki kirana mana ita yayar naka? Kamar muna bukatar ta anan wajen" Ya Hamza ya faɗa fuskarshi a ɗaure. Shi ko Yallaɓai ya fito da waya a cikin aljihun ya na faɗin" Ba zai gagara ba, bari na kirata na ce ta taho yanzu." "Yauwa mun gode. Ke kuma yanzu ita wacce kika faɗa ma mganar za ta zo. A cikin su za mu gano mai son ya yi wasa da hankalim mu" Ya faɗa ya na mai kallon Ma'u Gwaggo na gefe ta ce gwara haka domin kar ma a ja mganar da nisa. Alhajinmu kuma na zaune amma bai yi mgana ba. Ina ga Ma'u ta ɗauka wasa ne ba za a kira Anty Bahijja ba. Sai da ta ga Yallaɓai ya kira wayarta ya kuma saka a speaker sai ta rage kukan makircinta ta na ƙifta idanuwana kamar wacce ta yi ƙarya. Allah na tuba ai ƙaryan ma ta yi. Ta na ɗaukan wayan da sallama Yallaɓai bai ma tsaya amsawa ba ya ce" Ina gidansu Sadiya. Ana maida mgana Ma'u ta ce ita ƙarya ake yi mata mganganin da kika ce ita ta faɗa ta ce ba ta ita ba ce. "In ji ita Ma'un? Anty Bahijja ta tambaya cikin mamaki. "E. Shi ne aka ce ko za ki iya zuwa nan gidan su Sadiyan? "Me zai hana? Ai sai na zo. Kuma in ba Ma'un ta ke faɗa min ba ina na ke jin wasu labaran? Ita ta san ita ta zo asibiti duba Gimbiya ta faɗa min mu yi hankali da Sadiya za ta iya sanadin cikin Gimbiya tunda sun yi gadon shiga bokaye ko a gabanta zan iya maimaita haka sai ta ƙaryatani na gani" "To shike nan in da buƙatar zuwan na ki zan sake kiran ki" Daga haka Yallaɓai ya katse kiran gabaɗaya sai kowa ya maida hankalin shi kan Ma'u da ta yi wani iri da ka ganta ba ta da gaskiya. Shi kan shi mijin na ta a cikin mamaki ya ke kallonta. "Da sake. Wannan sharri ne ban yarda da mganaganunsu ba." Baaba ta faɗa a fusace itama fa ta san gaakiya amma ta na neman take gaskiyan. "Za ki faɗa mana gaskiya ko sai ranki ya ɓaci? Ya Hamza ya faɗa cikin tsawa. Da ya sa Ma'u ta tsorata daman ko a baya ta na son shi amma kuma ta na shakkar shi. Sai kawai ta fara ɓarin jiki amma ta kasa mgana. "In faɗa ko ba ki faɗa ba? Ya sake maimaita tambayarsa cikin hargagi da ba ta san lokacin da ta ce e ita ta faɗa, Masu ƙoƙarin kare ta ma duk sai suka yi shuru jikinsu ya yi sanyi kuma ta ce ita ta faɗa amma ta koma ta na ta faman kuka. Ya Hamza sai sake mgana Alhajinmu ya ɗaga masa hannu. "Ƙyaleta Hamza. Yi mata a hankali mana." Ya faɗa cikin yanayinsa kafin ya mai da kallonsa kan Ma'u da ke kukan munafumci. "Asma'u" Ya kira sunanta ta amsa cikin kuka in ka ganta sai ka rantse da Allah an yi mata wani abu ne ko wani nata ne wani abu ya same shi ko an yi mata mutuwa. "Me ya sa kika aikata abin da kika aikata Asma'u? Me ya sa kika zaɓi ki tozarta yar'uwamki da ahalinta a idon duniya? Me ya sa kika aikata haka? Me ya sa kika zama haka? Ina ganin ki da girma a cikin idanuwana amma aikata abin da ban yi zato ba ya sa girmanki da ƙimarki da na ke gani ya ragu a cikin idanuwanan tabbas Asma'u kin yi ɓarna. Ɓarnan ma mai tarin yawan da kafin a yafe miki sai an ɗau lokaci. Kin ci amanar zumunci, kuma ba Dubu kika tozarta ba, ni kika tozarta kamar yadda itama in ta yi miki wani abu na tozarrci to itama ba ke ta yi ma wa ba. Ni ta yi mawa" Ya ƙarishe faɗa cikin kaushin murya ka na ji za ka san ran shi ya gama ɓaci. Ma'u sai kuka ba mgana saboda ba ta da tacewa. "Ina jin ki. Ki bar kuka ki faɗamin dalilin ki na yi ma zuru'an ki wannan tozarcin Asma'u. Ni fa da kaina na kira ki na kira Dubu na kira mazajenku na tara ku na yi muku sulhu. Na san Dubu da na fitina da riƙo amma ba ta tsallake mganata tun da na ce ta yi zumumci da ke ta ce za ta yi na san za ta yi ne. Kuma zan iya ba da shaidar ta ba ma ita ba kaf ɗin su ba za su yi miki ƙwataƙwacin abin da kika yi ba, sannan in suka ga wanda zai ci mutumcin ki sai in da ƙarfin su ya ƙare. Amma abin tir sai  ga ki da kan ki kike zuwa kina cin zarafin yar'uwanki domin ki ɓata mata suna ki kuma haddasa mata fitina a gidan aurenta? Shin me kika aikata? Kin san sunan abin da kika aikata! To sheɗanci ne. Kin zama sheɗaniya tun da kin zama silan haɗa fitina da dama. Kin ba ni kunya, ban taɓa zaton haka daga bangaren ki ba Asma'u." Ma'u sai kuka ba mgana, kowa jikinsa ya yi sanyi amma ban da ni domin ni na san wace ce Ma'u a kukanta ma ba Saduda a cikin shi. Alhajinmu ko a yadda ya ke mgana ranshi ya riga ya gama ɓaci, Baaba ce ganin Ma'un ta ƙi mgana sai kuka sai ta tare mganar da cewa. "Yaya Sule ba fa gaskiya ba ne Ma'u ba za ta yi ma Sadiya haka ba. Sai ma ita Sadiyar ce in aka ce ta yi hakan ba zan yi musu ba, saboda tun tuni ba ta ƙaunar Asma'u kowa kuma ya san haka. Shi ya sa na ce a yi.." "Ba ke na ke tambaya ba Hasiya. Ki bari Asma'u ta ba ni Amsa." Alhajinmu ya dakatar da ita a fusace da ya sa dole ta yi shuru ita kanta ta ji kunya ba za ta nuna ba ne, to ga suruki a wajen kuma ya gano munafuncin yarki dole kunya ta kamata amma da ya ke ba ta san kunya ba, ta na ƙoƙarin nuna a yi adalci yarta ce mai gaskiya ni ce mara gaskiya. "Muna sauraran ki. Ki faɗa mana dalilin ki na aikata abin da kika aikata." Alhajinmu ya sake tambayarta da ya sa cikin shessheƙan murya ta ce" Ban da wani dalili Alhaji sharri sheɗan ne don Allah ka yi haƙuri." Ta faɗa ta na kuka kamar za ta shiɗe Ya Hamza ya fara masifan ai mutum ba ya aikata laifi kuma ya ce ba dalili ita dai ta san dalilinta na aikata abin da ta aikata. "Wallahi ba ni da wani dalili kawai dai sharrin sheɗan ne" Ta sake faɗa ta na gunjin kuka. Sai kowa ya yi shuru ya ba sauraranta. "Alhajinmu ka yi haƙuri ka yafe min. Kuma zan karɓi duk hukuncin da ka yanke min" Ta sake faɗa tana kuka, sai na zama yar kallo kawai domin film kawai Ma'u ke yi ta na zuba acting. Kukan da ta ke yi domin a ji tausayinta ne amma ni na san wallahi ba kukan nadama ba ne. "To in sharrin sheɗan ne me ya sa shi sheɗan ɗin bai faɗa kan kowa ba sai kan Sadiya? Ki dai faɗi manufarki kawai." In ji Ya Auwalu Ya Hamza kuma ya karɓe da cewa" Nima shi na gani ba rami ba abin da zai kawo maganar rami." Karar Baaba ta karɓe da cewa" Ba ya wuce yar tsaman dake tsakanin su. Tunda kuma ta ba da haƙuri ai shikenan ko? "Ba shiken ba Baaba." Na faɗa a fusace saboda na ga tana son ture laifin yarta. "Ba shike nan ba, zarafina ta ci, ta yi min ƙazafi yau ko ƙararta na kai wallahi sai min yi sharia da ita." Baaba sai ta kasa mgana ni kuma sai na cigaba da faɗin"Me ya sa duk a cikin gidan nan ba ta son ganin bayan kowa sai ni? Me na yi mata? Abin tambayan kenan ni kuma na san abu ɗaya ne na yi mata tun a baya da na faɗi cewa Ya Abubakar na sonta har aka fasa auranta da Ya Hamza. Daman tun a baya ta faɗa min zan gani yadda na hana ta abin da ta ke so nima sai ta yi barazana da farinciki na ga shi  kuma ta ɗau hanya kuna gani." Na faɗa ina kallonta ta tsorata ba ta ɗauka zan kawo wannan mganar ba sai ta daburce tun da ga mijinta a wajen ta fara rantsuwan ba haka ba ne. "To in ba haka ba me na yi miki? Miji ɗaya muke aure ko facaloli ne mu da za ki bi ki addabi rayuwata? "Wallahi ba ki yi min komai ba Sadiya ko a baya da na faɗi haka yarinta ne. Amma tunda na auri Alhaji na cire komai a raina domin ya zame min garkuwan da na ke jjingina dai-dai da rana ɗaya ban taɓa nadaman auran shi ba." Sai ta ɗan dakata ta na kuka shi ta ke kallo, duk makircinta na fahimta ba ta so mganganuna su yi tasiri a zuciyarsa shi ya sa ta tsiro da wasu maganganu. Shi ta ke kallo ta na faɗin" Alhaji shin dai-dai da rana ɗaya ka taɓa ganin wani chanji daga wajena a kan ka? Sai ya girgiza kai kafin ya ce" Babu Ma'uta. Kuma kin ban labarin daman cewa Yayanki Hamza aka so ki aura sai Allah bai yi ba. Ni tsakanina da ke sai godiya da tarin alheri Asma'u." "Alhamdulillah ka gama mgana" Baaba ta faɗa da ƙarfi,kawai sai na ga Ma'u ta rarrafa zuwa gaban Alhaji ta faɗi ta na faɗin" Ka yi min gafara Alhaji in ba ka yafe min ba ina za ni Ba ni da wani uba kamar ka Sannan ba ni da wani gata sai gatan ka da gatan ƴan'uwana Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min sharrin sheɗan ne ba zan ƙara ba." Bai ce komai ba sai ta cigaba da kuka ta na masa magiya sai ya saka hannu ya ɗaga ta zaune ya na cewa ta share hawayenta. "Na yafe miki Asma'u. Uba ba zai taɓa riƙon yarsa a zuciyarsa ba. Sai dai ba shi zai hana ban faɗa miki cewa ba ki kyauta ba kin yi kuskure Babba. Ki yi juya ki nemi gafaran Dubu in kuma ta ce ba za ta yafe miki ta yi dai-dai ba zan matsa mata ba, na san ba zan ce ta cigaba da zumumci da ke ba, amma zan faɗa mata kar ta zama mai yanke zumumci da ke, ta yi miki kara sabo da ni da Mahaifiyarki. Amma tabbas ba ki kyauta ba ni kaina ban ji daɗin abin da kika aikata ba, ina jin kunyar kaina da waɗansu mganganun da aka ce daga bakin ki a ka ji su." Ta na kuka ta na faɗin za ta roƙe ni gafara ba ni ba dukkanmu za ta roƙi gafarammu. Ta fara da roƙon Gwaggo da cewa ta yafe mata ba za ta ƙara ba. "Bakomai Asma'u na yafe miki amma don Allah ki kiyaye. Dadiya fa ƴaruwanki ce bai kamata ki bari sheɗan ya yi tasiri a kanki saboda ita ba." Da ta je gaban Ya Aina ta na kuka ta na cewa ta yafe mata kai ta kauda kafin ta ce" Bakomai amma dai kin ba ni mamaki sannan ki yi haƙuri ina ji a raina ba zan ƙara yarda da ke ba." Ya Balki kam sai da ta kalleta ta ce" Kin dai ɓata wayon ki Ma'u ban zaci haka daga gare ki ba. Ki gyara domin ko a nan gaba ba munafunci da gulma ba shi da amfani." Ya Murja ba ta ce komai ta dai ce Allah ya yafe mana gabaɗaya amma ita kanta ai ta sha mamakin Ma'u. Ya Auwal ma yace shi in dai na yafe shima ya yafe. Yallaɓai ko da ta isa gaban shi tun kafin ta yi magana ya dakatar da ita da cewa. "Abin da kika aikata kin san bai chanchanci yafiya ba ko? Saboda kin haɗa fitina fitinar ba domin Allah ya taƙaita ba da yanzu lamarin ya wuce tunanin kowa. Sadiya matatace da muka yi aure tsawon shekaru goma sha biyar amma ni na san abin da za ta aikata da wanda ba za ta aikata ba, abu ɗaya zan faɗa miki shi ne ki daina biye ma zuciyarki ki kuma yi yaƙi da sheɗan da kika ce shi ya rinjaye ki. Mgana ta karshe shi ne alaaqar dake tsakanin ki da Yayata don Allah ta tsaya haka nan.  Ina son na zauna lafiya da matana da ƴan'uwana." Sai ta kasa mgana Ya Hamza ya ce daman alaqa in ba alheri a cikin ta rabuwan shi ya fi. Har Ya Abubakar da ya ke ɗan amshin shata sai da ya ce mata ba ta kyauta ba. "Ba Sadiya kika tozarta ba mu kika tozarta. Kuma ba zan ƙi faɗa miki kin ba ni kunya ba. Allah ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba." Shi ko Ya Hamza gyara zama ya yi ya na faɗin" Ke yanzu in Sadiya ta haɗa kai da abokiyar zaman ki ta ci duduniyarki za ki ji daɗi? Ta girgiza kanta sai ya cigaba da faɗin" To me ya sa kin san ba daɗi kika aikata abin da kika aikata? Sai ta ba shi amsa da sharrin sheɗan ne kamar zai deke ta ya ce" Ke ce sheɗaniyar kenan kuma in ba ki yaƙi da sheɗancin da ke tare da ke ba, ba za ki zauna lafiya ba. In wannan karom mun yi miki afuwa wallahi tallahi kika sake aikata makamacin haka sai dai ki je can gaban hukuma ki fitar da kan ki." Y Muntari kuwa hadisi ya jawo mata ya ce addini ya hore mu da mu so ma junanmu abin da muke so ma kan mu. Sannan ta shiga hankalinta kar ta koma ga Allah haƙƙin zumumci ya bibiyeta." Mijinta ko cewa ya yi ya yafe mata domin ya san sharrin sheɗan ne ba halinta ba ne har ya na share mata hawaye. Ni ce ta ƙarshe Ma'u ba ta ji kunya ba wai ta kalleni tana cewa na yafe mata sharrin sheɗan ne. "Ni da ke mun san gaskiya. Ba wani sheɗan daman kin shirya ma hakan. Ma'u abin da kika yi min mai zafi ne. Ina so ki sani ko na yafe miki ba zan iya cigaba da zumunci dake ba" Na faɗa kai tsaye saboda ba zan yi ƙarya ba zan yanke alaqata da Ma'u  domin ko ban yanke ba, ba na jin zan iya cigaba da mu'amala da ita. Sai kawai Baaba ta ce ai ni ce na ke da kafiya tunda ta roƙe ni gafara me zai saka ba zan yafe mata ba. "Na ce na yafe mata. Amma ba zan iya cigaba da zumumci da ita ba. Nan ɗin da ya haɗamu dole in mun haɗu mu gaisa domin  ni ba zan yi gaba da ita ba. Amma duk wani abu daya dangance ni na cire ta a ciki shi ne mgana." Kuma kowa ya goyo bayana har Alhajinmu wannan karon bai yi magana ba. Abu ɗaya ya ce min shi ne" Ki yi mata kara Dubu. Ki yi mata kara ko saboda ni. Ba yanzu ba in zuciyarki ta huce ki sada zumumci da Asma'u domin har abada ita ɗin jinin ki ce." Saboda Alhajinmu da kuma karan da ya ce in yi masa. Shi ya sa na gyaɗa masa kai ina mai faɗin" To Alhaji in sha Allahu zan yi yadda ka ce" "Na gode miki Dubu. In na faɗa kina ji, in na kuma ba ki unarni nan ta ke kike yi ba tare da jinkiri ba. Allah ya yi miki albarka." "Amin Alhajinmu." Sai ya kalleni kafin ya ce" In na ce kin yi kuskure a lokacin kike aminta da cewa kin yi kukure sannan ki ce za ki gyara. To yau ma zan ce kin yi wani kuskure guda ɗaya kacal Dubu." Ba ni kaɗai ba. Kowa da ke falon sai da ya kalli Alhajinmu cikin mamakin kalaman shi. "E kin yi kuskure guda ɗaya. Kuskure kuma shi ne me ya sa kika ta ka zuwa gidan Asma'u ki ka ja ta da faɗa? Me ya sa kika yi haka? "Raina ne ya ɓaci Alhaji. Raina ya ɓaci na ji baƙin cikin da ban taɓa ji ba, shi ya sa sai zuciyata ta ɗebeni har na je gidan ta amma ka yi haƙuri tun da na yi kuskure." "Na haƙura tun da kin ce na yi haƙuri. Kin amince ba ki kyauta ba? Sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya ina mai dukar da kaina ina mai kallon adon cafet ɗin falon. "To tun da kin amince ba ki kyauta ki juya ki ba ma Asma'u haƙuri." "Shi ne adalci kam" In ji Baaba. Ba domin Alhajinmu ba ne da ba wanda ya isa ya sa ni ba ma Ma'u haƙuri amma Alhajinmu ne shi isar kowa ne anan falon gabaɗaya. "Ki yi haƙuri." "Ba komai." Ma'u ta faɗa lokaci ɗaya ni da ita muna kallon juna. Kafin kuma kowa ya kauda kanshi gefe amma ni na gani sai da ta yi wannan shegen mirmishin na ta, a raina na ce wannan mirmishin yau na faɗuwa ba na nasararki ba ce Ma'u. Da haka taron ya tashi Ma'u ba ta yi gigin zama ba saboda ba ta ga fuska ta bi mijinta zuwa gida nima Yallaɓai na bi muka koma gida. Ya Murja ce ta kusa sakani dariya da ta na ce ma Ya Aina ta yarda da Ma'u ta ci amanarta da ka gaya mata mgana ta je ta kai shi gaba, sai dai ta ga haka ya faru ne ta ke faɗin Ma'u ta na da daman halin an ce ka ce musamman daman a kaina ta yi ta cewa na yi mata kaza na yi mata kaza. Ban yi magana ba amma dai na yi dariya, saboda da ko da  na yi mgana sai a ce ni ce mai fitina yanzu ai sun ga gaskiya Baaba dai duk baki ya mutu. Kuma ita ta so haka ta san gaskiya amma sai idanuwanta suka rufe daga  ƙarshe sai ta ji kunya gaban surukai. Ranar a gida muka yini ni da Yallaɓai bai fita ba. Muna tare ya na ɗan jana da hira har na saki jikina kaɗan. Tun daga ranar ban ƙara komawa ɗorayi ba, ballantana Gwammaja da na ji ma gidan ya fita daga kaina kwata kwata. Nene dai bayan lokaci ina kiran ta mu gaisa. Anty Bahijja kuma ban ƙara ganin ta ba, Gimbiyar ma haka tana can gidan Nene tun da an sake ba ta bedrest na sati biyar kuma ba a son zirga zirga. Harkan gabana kawai na ke yi tun da suka sha ni na warke shi kenan na koma tsoron duniya an fi sati biyu ban dawo dai-dai ba, har Tariq sai da ya kirani a waya ya na ba ni haƙuri haka ma Farida. Kawu Abba ko har gida ya dawo ya yi ta ba ni haƙuri na ce komai ya wuce. Mganar Marwa ko ya ce ba fashi manya ma suna shirin shiga cikin maganar tun da ba ya so shekara ta ƙare ba a yi auren ba. Maganar gaskiya na fi wata ban iya mantawa da abin da ya faru ba. Ni gabaɗaya ma kowa sai ya koma ba ni tsoro. Ba dangin nawa ba na Yallaɓai ba har Amina sai daga baya ta ji labari ta yi ta ashar ta na zage zage. Sai ga Ma'u ta na min mgana a chart na ban hakuri na yi block ɗinta har ta test massages ta ke turomin, amma na share ta. Ai an gama har abada ba zan ƙara yarda da ita ba. Nesa nesa kallon kura a tsakanina da ita shi ne zaman lafiyata Yallaɓai kuwa shi a ƙoƙarinsa na manta komai na sake rumgumar Yayarsa da Matarsa kamar baya. Ni ko na faɗa masa har abada. Za dai kawai a yi sha'ani, ni matar tashi ma ta fi ba ni mamaki yadda na sakankance da ita ta cutar da ni, itama ta turomin test mai tsawo na ban haƙuri ko karantawa ban yi ba na goge saboda ni gabaɗaya sun fita daga zuciyata ba na jin ko nan da shekara ɗaya ne zan iya sake sakin jiki da su. Ina ganin har abada ni da su. *Janafty* *TKG02020AA* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX *BAYAN WATANNI UKU* Watanni uku sun zo sun shuɗe kamar ƙiftawan ido. A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah da haka muke ta cinye kwanakin mu ba tare da mun farga ba.  A cikin watanni ukun da suka gabata, ba ƙoƙarin da ban yi domin na manta da abin da ya faru tsakanina da Gimbiya da su Anty Bahijja ba amma na kasa.  Duk lokacin da na tuna sai na ji gabaɗaya rayuwata ta yi ƙunci. Sai na ji zuciyata ta chunƙushe ga shi dai har a zuciyata na yafe musu amma kuma na kasa mantawa da abin da suka yi min. Barin ma in na ga ɗaya daga cikin su sai abin ya zo min shar a cikin raina. Bayan faruwan lamarin na daɗe ba na zuwa ko'ina ina gidana. Har sai da Nene ta kirani a waya ta na faɗin saboda Anty Bahijja itama na yi mata ya ji, dalilin haka ne ya sa na je Gwamnaja na gaishe da Nene Allah kuma ya taimake ni Gimbiya ba ta nan ta je ganin likita har kuma na baro gidan ba su dawo ba, Nene sai da ta ba ni tausayi yadda ta riƙa bani haƙuri kamar ita ta yi min laifi. Saboda ita na ji a raina wataƙila in muka haɗu da Anty Bahijja na iya gaisheta. Amma ba saboda darajan ta ba sai domin ta ci darajan Nene da Yallabai su ne kawai za su saka in muka haɗu na iya buɗe baki na gaisheta. Amma a cikin idanuwana ba na kallon ta da ƙima da girman da can baya na saba ganinta dashi.   Ilai ko mun haɗu da ita a gidan Nasara lokacin da ta haihu ranar suna. Sai ga ni ga Anty Bahijja da Anty Maimuna. Daƙyar na iya daurema zuciyata na gaishe su. Suka amsa suma cikin irin yanayin da na gaishe su. Kuma har na bar gidan sunan nan bamu ƙara mgana ba, ni ina tare da su Hauwa su kuma suna ciki tare da su Suwaiba. Gimbiya ba ta zo ba, ta na can Gwammaja ba ta fita tun da ta na ƙarƙashin dokan likita ne a bakin mijinta na ke jin kwanakin cikinta ya ɗan dawo baya, saboda raunin da ya samu amma ya tarkato ta ya kawo min ita har sau biyu gida na da sunan ta ƙara ba ni haƙuri amma bayan gaisuwa ban sake yarda wata mgana ta haɗamu ba sai ma na bar mata falon ita da yara da mijin gabaɗaya. A zuwan ta na farko bai yi magana ba sai da suka ƙara dawowa shi ɗin ma daddare ne ya ɗaukota ya sake kawo min ita da cewarsa ta ƙara sake ba ni haƙuri "Yallaɓai ka daina sa ta wahala ni fa na riga na ce na yafe tun a wancan lokacin" Haka na faɗa masa amma sai ya dake da cewa in na ce na yafe me ya sa ba zan saki jiki da ita mu dawo kamar da ba. "Yallaɓai da kamar wuya mu dawo kamar baya. Kawai ka bar ni tun da na ce komai ya wuce a bar shi a komai ya wucen mana." Ya ƙara nacewa da cewa wai ai shima ya na yi min laifi nima ina yi masa mu yi faɗa sosai daga baya kuma mu manta komai mu zo mu shirya me ya sa yanzu ba zan manta ba. "Kai Mijina ne. Kuma Ubangiji ne kaɗai ya san falalan da ke cikin aure. Wataƙila laifukan junanmu Allah ne ke umartan mala'iku suna shafe su daga cikin zukatan mu saboda martaba da daraja irin ta aure. Ita kuma matarka ce ita ɗin ba dole na ba ce, gaba ne ba zan yi da ita ba in muka haɗu za mu gaisa amma ka yi haƙuri ba zan ƙara sakin jikin da na yi a baya ba. Hausawa suka ce ruwa cikin cokali ya isa mai hankali wanka." Amsar da na bashi kenan a lokacin na samu ya shafa min lafiya da kawo matarsa tare da min magiya na saki jiki a koma kamar baya sai ka ce ba ni da tunani ko ban san ciwon kaina ba. Ma'u ma mun haɗe sau biyu da ita bayan abin da ya faru, na farko mun haɗu a Ɗorayi da Baaba Aminu ya zo Gwaggo ta kikkiramu ta ce mu zo mu gaishe shi. Ban fara yi mata magana ba ita ce ta gaishe ni na amsa kuma bayan nan har na koma gida magana ba ta ƙara haɗamu ba, amma su Ya Aina kam har sun manta sun sake sakin mata ni dai kan an gama sha ni kuma na warke. In aka yi maka laifi ka nuna an yi maka haka ma Annabi(SWA) Ya ce. In kuma a ka ba ka haƙuri to ka haƙura amma kar ka manta domin rashin mantawar shi ne zai ba ma mutum daman kar ya ƙara sakankacewa a sake cutar da shi.   Sai haɗuwa ta biyu a gidan Ya Balki da Firdausin ta ta yi sauka Qur'ani muka je walima a gidan ma ita ta fara min mgana muka gaisa shima kuma har muka rabu ba wanda ya ƙara tanka ɗan'uwansa ni fa da gaske na ke yi da na ce na yanke alaqa da ita. Kuma na ji daɗin yadda har Alhajinmu wannan karon bai tsamamin bq. Amma a raina na ce itama ba zan yi gaba da ita ba amma zumunci kamar ba ya ne dole ya ja baya a tsakaninmu. Dalilin haka ne ya sa har munafukan ƙawarta shema na daina ganin ta na ma na zarya a gida in wani abu ya faru. Ido ai da kunya ita kanta Ma'u ba ta san kunya ba ne shi ya sa ta iya gagicewa ta na shiga cikin jama'a bayan duk tsiyar da ta tafka. Maganar Marwa da Kawu Abba manya har sun shiga ciki amma ba'a saka rana ba. Cikin watan da zamu shiga Yallaɓai ya ce za a je a saka rana ita ma Marwa alokacin za ta koma makaranta ta ƙarishe semester ɗin ta. Koma da wani abu a zukatan su Anty Bahijja maganar da Kawu Abba ya yi ta rufe bakin kowa. Yan'uwan shi ko murna suke yi domin abin da suka daɗe suna jira ne sai yanzu ya tabbata. Shi ya sa ko kaɗan ba su damu ba su dai fatan alheri suke yi da fatan Allah ya sa albarka. Ta bakin Nene ta ce abin da muka daɗe muna jira ne mu dai ya furta ya na son wata zai aure ta kuma tun da har ya gani kuma ya na so za a nema masa kuma a aura masa. A cewar wasu ƴan'uwa daga can Rano wai Marwa ɗin an ce yarinya ce ta yi masa ƙanƙanta shi kuma ya ce tun da ita ba ta ce ya yi mata girma ba shima ko bai ga ƙanƙantarta ba. Da Yallaɓai ke faɗa min abin da ke faruwa sai da na yi dariya a fili na ce Marwa ai ta wuce yarinya shekarata ta ashirin da uku ta ke ba, waɗanda ma ba su kaita ba an yi musu aure sun zauna ballatana ita? Yallaɓai ya ce shima haka ya gani amma shi sai ya danganta haka da cewa haushi ne bai nemi ƴaƴan su na nan Rano ba ya tsallake sun kuma rasa abin kushe shi ya sa suka ɓullo da haka. Ba su san Abba na dai-dai da su ba. Muna ta dariya ni da shi ni kaina ina jinjina masa ya na da dakiya sannan kaifi ɗaya ne in ya ce A to ko ruwa da iska ba su isa su saka shi ya sauya ra'ayi ba. Shi ya sa na sha faɗa ma Ya Aina da Marwa za su yi alfahari da wannan auran watan wata rana in sha Allahu. Tuni na daina shan mganin asibiti. Na hannuna na ƙarewa na daina sha, ban kuma sake komawa asibitin ba. Gani na yi na daɗe ina amfani da na asibiti ba a samun abin da ake so ba sai dai sauƙi kam. Tun da al'adata na samu ya dai-dai ta. Sai kawai na watsar da na asibitin na fara shan wanda Inna Mariya ta kawo min kuma ina jin daɗin shi, ya na wanke mara kuma in na yi fitsari ko bayan gida ina ganin abin da na ke fitarwa da datti daga cikina. Na farko har ya ƙare na sake yi ma Inna Mariya mgana ta sake karɓo min har kuma a lokacin ban bari ta ji labarin abin da ya faru sanadin mganin ba, ko ba komai bai kamata ta ji ba, domin yadda zuciyata ta yi ɗaci na ta zuciyar sai ta fi tawa yin ɗaci shi ya sa ko da wasa ban taɓa gigin faɗa mata ba. Kuma na gargaɗi Amina itama na ce kar ta je wajen surutun ta ta kwashe ta faɗa mata ga abin da ya faru. Shi ya sa har lokacin ba ta sani ba kuma ba na fatan ta sani ɗin har abada. **** *Saturday* 29May. 2016. Yau asabar ɗin karshen maƙo ne. Jidda da Baby sun tafi Tahfez. Ni kaɗai ce a gida Yallaɓai ba anan ya kwana ba jiya ya na gidan Gimbiya tun da ta koma gidanta satin da ya kamata. A bakin mijinta na ke jin cikinta wata biyar har ya na faɗa min ya yi girma tun da har ya fito, ni  in Yallaɓai na surutansa ba na biye masa iyaka kawai na kalle shi in abin Allah ya sauwaƙe ne na ce in kuma na Allah ya kyauta na ce na kama kaina. Tun da na fahimci ya na jin daɗin yin hiran matar da ni sai ka ce ni ina da matsala da hakan ne. Yau akwai ranar iyaye daga makarantar su Jidda. Kuma Yallaɓai ya sani an aiko da takarda kuma head teacher na class ɗin su Jidda ta kira sa ta faɗa masa, kuma an tura a group na makaranta tun da ya na ciki. Nima clasa teacher ɗin su Baby ta faɗa min tun da ina da lambarta muna mgana in wani abu ya taso ta yi min mgana na ce za mu taho ni da Yallaɓai. Tun da duk shekara suna yi domin tattaunawa cigaban makaranta da yaranmu. Yallaɓai ya fi zuwa ni duka duka bai fi sau biyu na taɓa ba, ko a jiya da ya zo yi mana sallama yaran sun tuna masa nima na yi masa mgana ya ce daga can zai shirya sai ya biyo mu tafi tare. Amma Yallaɓai tun 10 na safe na shirya na zauna ina zaman jiran shi har Saude ta zo sha ɗaya da wani abu na rana Yallaɓai bai zo ba kuma in na kira shi sai ya ce min ga shi nan a saman hanya. Raina ya ɓaci na ga dai ba office ya je ba ya na gida amma kuma ya na ta raina min wayau. Ko daga Zaria ne a awa biyun da Yallaɓai ya kwashe ai kamata a ce ya sauka, har na yi zuciya na ɗauko jakata zan tafi saboda taron goma da rabi ne ga shi har an ci rabin lokaci kawai ina fita haraba gidan sai ga shi ya shigo ya na maiƙon wata farar shadda har da babban riga ta angon cin shi ce shi da Gimbiya. Baki na saki ina kallon shi domin ganin shi na yi ya na wani annuri kamar wanda aka yi ma albishir da kujeran makka sai da ya matso kusa da ni sannan na ji ƙamshin mai daɗi da sanyi dake tashi daga jikin shi. Ban ma san na saki baki ina kallon shi ba sai da na ji ya na faɗin. "Na yi miki kyau ne Madam? Ya faɗa ya na rufe min baki. Hannunsa na kaɓe daga fuskata ina jifansa da wata uwar harara. "Afuwan Abar ƙaunata." Ya faɗa har ya na ɗaga hannuwa sama. Kanar in yi tsaki sai kuma na fasa na wuce kawai na bar shi nan tsaye sai ya biyo bayana yana faɗin" Ba mu makara ba ki daina damuwa" "Haba Yallaɓai in ka san lokaci za ka ɓata me ya sa ba ka ce mu haɗu a can ba? "Mu haɗu can abin ai ya yi wani iri kuma? Gwara mu je tare zai fi ko? Ya faɗa ya na kallona lokaci ɗaya ya na ƴar dariya. Ni ko na sake maka masa wata harara na fice daga gidan, motarsa a waje ya barta ce min ya ke yi ba zan rufe gida ba ne sai na ce Saude na ciki sai kawai ya jawo kofar. Yallaɓai bai faɗa min ya ɗauko Amaryansa ba na je da ƙarfina na buɗe gidan gaba da niyar shiga kawai sai na gan ta a zaune ta kame ta ci uban gayu gyale a kafaɗa har da saka wani glass baƙi a fuskarta. Sannan kamar yadda mijinta ya faɗa ne ga cikinta ko har ya fito ta cikin doguwar rigar da ke jikinta kamar ma ado ta ke yi da cikin. Tiƙashi. Sai gani tsaye galala ina kallon ikon Allah. Ita ko da ta ganni ko a jikimta sai ma gilashin fuskarta da ta cire ta na faɗin"  ina kwana Madam" Na kasa amsawa sai Yallaɓai da na kalla lokacin da ya ƙariso yanayin kallon da na ke yi masa ne ya sa ya yi saurin cewa. "Tare zamu je saboda da ga can zan sauke ta gidan Naja" Kuma ya na gama faɗin haka ya buɗe bangaren direba ya shiga ni kuma ina tsaye kamar wata sakara. Dakyar na iya fusko numfashina sannan na iya matsawa baya ina matsawa ta saka hannu ta rufo ƙofar gaban da na buɗe. Duk sai na ji na muzanta har zan buɗe ƙofar gidan baya in shiga sai wata zuciyar ta hana ni. Wato su suna gidan gaba suna shan soyayya ni kuma ina gidan baya kamar almajira sai kawai na juya na zagaya ta can bangaren Yallaɓai ina zuwa sai ya sauke gilas ya na faɗin. "Ki shiga mana ba ke kike ta faɗan mum makara ba? Da idanuwana da suka kusa fallasa asirin da ke zuciyata na ce amma na danne ina faɗin" Ku je kawai" "Ban gane mu je kawai ba " Ya faɗa cikin mamaki. "To ai na ga ba sai mun je mu biyu ba tun da ga Gimbiya ku je kawai ni ba sai na je ba." Na ɗauka Yallaɓai zai matsa min sai na je amma ga mamakina sai kawai ya rausayar da kai ya na faɗin. "Kin tabbata mu tafi bakomai? Sai na gyada masa kai cikin ƙarin mamakin sa. "Ku je kawai. Itama kamar uwa ce a wajen su Jidda." "Gaskiya ne to mun gode da kara Maman Jidda." Ya faɗa ya na kallon matarsa har ya na kashe mata ido. Ni ko kaina na kauda ina faɗin" Sai kun dawo" Ina jin ta ta na faɗin" Allah ya sa" daga haka na wuce ko waigensu ban yi ba jakata na laluba na saka key na buɗe get ɗin domin in na na tsaya bugawa ɓata lokaci ne Saude na cikin gida kafin ta ji sai na daɗe. Haka na koma gida ina ƙara mamakin Yallaɓai ashe daman ni ya shanya ni ya na can ya na cin soyayyarsa bayan sun gama kuma ya tsaya jiranta ta shirya ni kuma ga ni shegiya ina ta zaman jiran shi kuma tsabar wulakancin namiji bai faɗa min tare suke ba sai dai kawai na je na ganta kuma ya na faɗin wani wuri za su wuce daga nan kenan sai dai na hau adaidaita na dawo gida. To ai Yallaɓai bai isa ya wulaƙantani ba in ma ya shirya na shiga gidan baya ne su suna gaba suna soyayyarsu sai dai duk abin da ya shirya ya koma masa. Tsabar ma daman ɗaukonin da za su yi kamar cikas ne gare su ina cewa su tafi gabaɗaya suka yi murna kamar daman ni ɗin lalura ce a wajen su. Yini na yi a gida ina kunci ni kaɗai. Da su Jidda suka dawo daga makaranta suna tambayan ko mun je makarantar su? Na ce Abban su ne ya je ni ban samu zuwa ba, shi kuma Abban na su sai dare ya zo gidan.  Ƙala ban ce masa ba nima bai yi min mgana ba yaran dai suka zagaye shi ya na faɗa musu yadda malaman su suka yaba musu  sosai. Baby dai ya ce teacher ɗin ta, ta ce ta fara saka wasa record ɗin ta ya fara ɗan jan baya. "Ki daina wasa kin ji ko My Baby? Ha faɗa ya na shafa kanta sai ta gyaɗa masa kai. Kwanto da da ita ya yi a saman jikinsa ya na faɗin" Anty Gimbiya ta ce ki ƙara dakewa za ta siya miki ipad na karatu." Baby na jin haka ta fara tsalle Yallaɓai ne fa ya yi zaune ya na faɗa musu tare da Antynsu Gimbiya su ka je makarantan na su, suna ta murna ni dai yadda bai ce Sadiya ji ba, nima ko ban nuna na ji ba. Bai jima ba ya yi musu sallama ya wuce ni ina ganin ma zai tafi sai na shige tiolet domin na gaji da ganin yaudaran Yallaɓai ya na ƙara ɓata min rai matuƙa. Washegari lahadi gidana Yallaɓai zai dawo da yamma. Bayan jiya sun yini tare yau ma tare suka yinin kawai da ya tashi dawowa sai ga shi ya ɗauko min matarsa ta sha gayu cikin wata doguwar rigar yadi mai baza a ƙasa. Ta yi rolling mayafi a saman kanta fuskar nan har tana maiƙo saboda hoda. Bakin nan ya na sheƙi saboda ƙyalin jan baki. Ta kawo ma yara cake ne da donut amma ni na san ba haka ya kawo ta ba, ta rako shi ne ko kuma shi ya ce ta rako shi ba su gaji da ganin juna ba. Tun kafin mangariba suka shigo gidan har ya fita salla ya bar mu. Ɗakin yara na bar ta tana salla nima na shiga ɗakina na yi, tuwon miyar allayu na yi mana. Har bayan isha'i tana gidan tare muka yi dinner har mamakin yadda Yallaɓai ke kafa kafa da ita na ke yi, ita ko sai wani iyayi ta ke wai ita mai ciki. Duk na gani na nuna ban gani ba, bayan mun gama cin abinci na ga dai Yallabai ya ce zai mai da ta gida har na ka ba shi da niyyar haka sai ma yara da ya kora falon su mu kuma sai ya kunna mana ya zauna saman kujera mai zaman mutum biyu ita kuma Gimbiyar ta na zaune a gefen shi ya na ba ta labarin wani American film da suke haskawa a MbAction. Ni ko ina kan kujeran Dining ban ta so ba ina kallon ikon Allah kamar ma fa ya manta da ni ne, sai can ne da ya juyo ya ganni sai ya ce" Kika zauna acan? Sai kawai sa ya sake juyawa ya na ce ma Gimbiya. "Kin san ita ba ta damu da kallo ba." Tsabar takaici sai kawai na miƙe ina tattara abubuwan da muka ɓata zuwa kitchen daga can ban dawo ba, falon su Jidda na tsaya na ce su kashe kallon in suna da sauran aikin makaramtan da ba su yi ba su ɗauko su duba gobe akwai makaranta suka ce min to. Daga nan na yi wuceta ɗaki domin ba dole aka yi min da sai na zauna ina kallon wulaƙanci da Yallaɓai ya shirya min a falona ba. Kai tsaye na shiga tiolet na kama ruwa na dawo na yi shirin kwanciya. Na kwanta kenan sai ga shi ya shigo. "Kin kwanta ne kuma? Dago kaina na yi ina kallon shi amma ban yi magana ba. Amma kaɗan ya rage ban amsa mishi da cewa" To kar na kwanta na zauna ina muku gadi." "Kin bar Daughter ita kaɗai ko? Kamar na yi masa tsaki sai na fasa kawai sai na mai da kaina saman filo ina faɗin" Ba ga ka ba? Sai ya yi dariya kafin ya ce" Haka ne. To zan mai da ta gida ko za ki zo ku yi sallama ne? "A'a na riga na kwanta. Ka faɗa mata mun gode mu kwana lafiya." Kamar zai yi magana sai ya fasa ya dai ce Amin ya fice. Ina jin fitar shi da mota wallahi sama da awa ɗaya sannan Yallaɓai ya dawo gidan kuma don ba shi da kunya ya dawo ya na ƙwaƙwumata sai ko na yi masa barcin ƙarya dole ya ƙyaleni, abin da ke ba ni mamaki matar nan ta na da mota amma duk in da za ta je shi zai kaita na rasa gane ita motarta amfanin da ta ke yi da ita. Ko aikinta da ta koma wata rana shi ya ke kaita kuma ya koma ya ɗaukota ranar dai na gaji na yi masa mganar ita motarta ba ta fita ba ce ta ado ce? "No kawai kin san yanayin da ta ke ciki ni na ce ta daina driving in dai ina kusa zan riƙa kai ta duk in da za ta je." "Ba shakka." Na bashi amsa cikin renin wayau ina taɓe baki amma sai ya basar da cewa. "E mana. Ke da ita kun maida ni direban ku da ƙarfi da ya ji." Kamar na ce ita dai ka ke yi ma aikin direban ci, ba ni ba sai kuma na fasa ban bashi amsa ba amma Allah na tuba tun ina amarya Yallabai da ko keke bai da shi adaidaita na rika yawo da ƙafata. Duka duka yaushe ya yi motar? Bayan tarewaan mu gidan nan ne fa, kuma ni dai a sananin ba ko'ina Yallaɓai ke samun damar kai ni ba, yawamci na fi yawo a cikin adaidaita. Duka kuma cikin Jidda da cikin Baby haka na riƙa zaryan asibiti a cikin adaidaita, duk bai duba condtion ɗina alokacin ba sai yanzu tun da yar gwal ta yi ciki ai ba zai bar ta ta riƙa tuƙi ba. Tsabar haushi ma ban ƙara tanka ma maganarsa ba na dai ɗauka da ya cigaba da maganganun sa zai  kuma gangaro kan cewa nima ya na jigila da ni a motar shi a baya ni ko na yi masa wankin babban bargo don na lura bai san ina masa kawaici ba. Yallaɓai bai daina kwaso mini matarsa duk ranar girkina ya na kawo min ba. Alhalin ranar girkinta ba na ganin shi sai dare in ya ta so daga wajen aiki ya biyo mu gaisa amma ita in ya na gidana tare suke yini. Na yi musu bakam ina auna tunaninsu na ga daga shi har ita sun maida ni shashasha. Ranar ko na yi niyyar taka musu burki ranar da aka kai sadakin Marwa da kayan saka rana aka saka wata takwas lokacin ta kamallah makaranta ta dawo gida. Ranar daman ya na gidan ta ne, da yamma zai dawo gidana kuma daman tare da Yallaɓai aka je aka yi komai tare da su Kawu Sa'adu. Bayan sun dawo ne shi ya tsaya gidan Gimbiya ya yi wanka kuma kawai ya ɗaukota suka taho tare. Ni daman ina gida amma suna tafiya Ya Aina ta kirani ta faɗa min an saka rana na riƙe hanci na rangaɗa guɗan farinciki ni kuma na shiga group ɗin gidanmu na sanar da su. Duk farincikin da na ke ciki da na ga Yallaɓai tare da Amaryansa sai da na ji raina ya ɓaci muna zaune afalon bayan ya dawo daga sallar isha'i har da yara gabaɗaya "Sai kika ji yau dai Finally Kawu ya fara taka matsayin girma." Yaƙe kawai na yi masa kafin na ce" Wallahi fa yanzu Ya Aina ta kirani ta na faɗa min." Ita ko ƴar iya sai buɗe baki ta yi ta na faɗin" Ma sha Allah. Allah ya sanya alheri." Ya amsa mata da Amin kafin ya ce" Lkacin kin haihu za a yi bikin ko? Ya faɗa ya na yi mata wani kallo sai ta kauda kai ta rufe fuska ta na yarfa masa hannu kafin ta ce" "Kunya na ke ji Daddy" Ta faɗa cikin shagwaɓa kawai sai Yallaɓai ya kalleni ya na faɗin" Sadiya kin ji ƙanwarki wai kunya ta ke ji in na yi maganar haihuwa." Kamar na ɗura ma shege ashar haka na ji, haka kurum Yallaɓai na neman ƙure haƙurina. Ai ban san lokacin da na basu amsa dai-dai da kalamansu ba, da ga shi har ita sai da suka kalleni. Amma sai da na ce Jidda da Baby su koma falon su suna ficewa na kalle su ina faɗin. "Kunyar me? Cikin? Ita ko ba ta ji kunyar yadda ta samu cikin ba ne sai fitowar cikin ne ta ke ji ma kunya? Sun kalle ni dukkansu kuma daga nan ba su ƙara mgana ba yan jakar uba ai sai ya sauya hira. Kan dai auran Kawu da Marwa ne ya na cewa kowa sai mamaki ya ke yi in ya ji an saka rana ana faɗin ashe dai Abba dai da gaske ya ke yi, tun ina amsa shi har na gaji na yi masa banza na bar ma ta hira saboda na ga sai tsoma baki ta ke yi cikin yanga da iyayi. Agogon bangon falon na kai ma duba tara har ta gota kawai sai na tashi ina faɗin. "Zo ka ji mana Yallaɓai." Ya ɗauka wata maganar arziƙi ne ya miƙe ya biyo bayana ya na faɗin" Mu je ta samu ne Sadiya ta? A raina na ce za ka ga samuwa har ɗakin barcin mu na kai shi na rufe ƙofa na tsaya ina kallon shi. "Me ya faru? Domin na san ya sha jinin jikin shi ya san mgana ce a bakina. "Yallaɓai ban ga ne sabon salon da matarka ta fito dashi ba. Ko na ce sabon salon da kai ka fito da shi ba." "Wani irin sabon salo? Ban ga ne ba? Ganin ya na neman raina min wayau ya sa na gyara tsayuwa ina faɗin" Duk ranar da za ka dawo gidana sai ka kwasomin matarka ta zo ta raba min dare a gida ina so na sake da mijina ta bi ta kankame ta hanani sakewa.  Sannan bayan duk haka bai ishe ta ba sai ta ƙara jan ka ka je mai da ta gida nan ma ka ƙara ɓata lokaci kafim ka dawo! Shin wai me hakan ke nufi ne? Ko wani tsari ne ka fito da shi ni ban sani ba? Tsabar ma shiga haƙki ko ƴaƴana ka ga ina tura mata ranar da kake gidanta ne? Ballanta ni na riƙa shiryawa ina bin ka? Na yi muku kara da kawaici masu yawa amma na ga daga kai har ita ba ku san zuru ba shi ya sa na ce bari in yi magana in ka manta in ƙara tunatar da kai wannan dai shiga haƙƙi ne." Na faɗa ina yarfa hannu da ya ke san ya san bai da gaskiya bai yi faɗa ba Sai kawai ya ce" To ki yi haƙuri ba za a ƙara ba. Ban ɗauka hakan zai ɓata miki rai ba ne" Tsabar takaici na kasa mgana sai kallon shi kawai na ke yi. "Ita ce ba ta son zaman ita kaɗai shi ya sa na ke ɗaukota mu zo nan ko za ta samu sakewa." "Ba ta son zama ita kaɗai ko kai ne ba ta son kana yi mata nisa? "To in ma haka ne laifi ne? Ya faɗa ya na sosa ƙeya har ya na min ƴar dariya. "Ba shakka. To ƙarshen soyayya dai ai mun ga Laila da Majnun" Kawai sai ya riƙo ni ya na faɗin" To ni ai ke ce Lailata ni kuma Majnun ɗin ki" Ture shi na yi ina hararanshi wai ni Yallaɓai zai yi ma wayau. "Oh ni dai na faɗa maka ba na so." "To ya kike son a yi yanzu? "Ka daina kwaso min ita ba na so. Ta tsaya iya matsayinta ban hana ta zuwa gaishe mu ba amma kar kuma a mai da zuwan ya zama na ibada mana." "To shike nan ba za a ƙara ba. Shi ke nan ko? Sai na gyaɗa masa kai saboda ya ga na ɗan zafafa sai ya rumgumeni ya na faɗin" Kai My Sady rigima." Tureshi na yi ina faɗin" ba rigima ba ce gaskiya ne." Ni ban san yadda suka ƙare ba fita ya yi ya bar ni a cikin ɗaki ban kuma san me ya faɗa mata ba amma tun daga ranar ta daina biyo min miji tana zuwa falona ta na min karairaya ba, shima ɗin ya daina kwaso min ita hakan ya fi kowa ya zauna in da Allah ya ajiye shi wannan dai da gida ɗaya muke da ta kashe ni da bariki ba ma gida ɗaya ba amma ba ta barni na huta ba Ni da Ya Aina ta tare da Ya Balki muka kafsa kayan saka Rana. Biyu muka raba. Kashi daya namu kashi ɗaya na dangin Babansu Marwa. Namu Gwammaja muka je dashi muka raba har da Ya Murja. An cire ma mutanen Yashe na su sai kuma can ƴan gandun albasa. Sannam mu ma muka cire namu. Na Amina lokacin Datti na gida shi aka ba ma da zai koma makaranta ya tafin mata dashi. Na Ya Auwal da Ya Hamza kuma an faɗa musu suka ce kawai a rabar ba sai an ijiye musu ba, shi Gwaggo ta ce za ta aika dashi maƙota ita kuma Ya Aina daman tun a can mun ɗibar mata na ta, ita da Marwa da maƙota tare da mutanenta. Kowa ya na ta fatan alheri ni na kira Marwa da kaina ta na makaranta muka yi magana ta ce min ya ce a Rano za ta zauna na ce daman ya faɗa ba shi da in da ya fi Rano gida shi a wajen shi, kuma can ne ya gina ƙaton gida da daɗewa. Ta dai ce suna waya lafiya lau ana ta shan soyayya na ce to ta dake ta kama shi gam a hannu ta shiga zuciyarsa sosai kafin ta ayi aurin wanda in aka yin auren kuma shi kenan. Yallaɓai na ji na ina wayar sai da na gama ya ce min wai ni uwar banza ce, na ce na ji bakomai ƙaramar uwa abokiyar wasa. "Kin kusa ijiye na ki surukin fa Sadiya" Ya faɗa ya na dariya nima ina taya shi na kuma ce masa ko Jidda ce haka zan zaunar da ita ina karanta mata. "Ba shakka uwar zamani." "Na gode Uban zamani." Yallaɓai ya yi fafur ya ce shi kam Dattijon zamani ne ba da shi da zama uban zamani ba. Bayan fitan shi na zauna ina tunani Jidda na cikin shekaru na sha biyar amma ba ta fara al'ada ba, sai dai ta fara ƙirgan dangi na gansu sun tsiro a ƙirjinta ban damu ba ƙila yanayin jikinta ne amma tabbas ta na gabda farawa  nan ba daɗewa ba, girma fa ya kama ni wasa wasa Jidda ta kusa kaiwa munzali. Ni kaɗai a ƙasan raina na ke musu add'an Allah ya tsare min su da dukkan tsarewansa wataƙila su kaɗai ne yayana anan gidan duniya. **** Friday. Munnira ce ta samu ɓari ni ban ma sani ba sai da Hauwa ta yi min waya ta na faɗa min tun da gaskiya mun kwana biyu ba mu haɗu da juna ba. Na dai san ta na da cikin tun da mun yi zencen da Hauwa kwanaki da ta zo gidana. Kuma kamar haɗin bakin itama Hauwan ta samu ciki ɗan wata ɗaya ta yi ɓarin shi amma da ta je ganin gida ne a Rano ta ce ma ba ta san dashi ba. To itama Munnira ta samu ɓari ta zame a banɗaki ta faɗi gefen cikin shikenan sai jini kwananta ɗaya a asibiti aka sallamota ta dawo gida. Ni da Hauwa mun je asibitin shi ne bayan ta koma gida muka tsara za mu je mu yini ranar jumma'a. Na kuma faɗa ma Yallaɓai ya ce sai mun dawo. Su Jidda a gida na ce zan bar su tare da Saude tun da na yi mata waya na ce in sun taso daga makaranta ta zo gida ina jiranta. Tun safe na gama ayyukana har da faten wake mai hanta na yi ma Munnira domin ta ce na taho mata da abin daɗi. Hauwa na zauna zaman jira tun da ita ce za ta biyo min, kawai ina zaune ina zaman jiranta sai ga wayar Yallaɓai bayan mun gaisa da ya ke yau ya bar gidana da yamma zai koma gidan Gimbiya. "Kun tafi ne? "A'a me ya faru? Na tambaya saboda na ji mamakin tambayarsa. "Daman zan ce ne ku jira Daugther ta taho yanzu da mota sai ta ɗauke ku, ku tafi tare gabaɗaya." Tuni na ji raina ya ɓaci Yallabai akwai sanabe da tsegemu. Yanzu haka ta ce za ta je ne zai ce ai mu ma za mu je ta biyo mu tafi tare. "Na faɗa mata ta biyo ta gida ku wuce." Har ya gama mganarsa ma, na so na danne ma zuciyata na amsa masa sai kuma na ga in na yi shuru ba amfani. "Yallaɓai yaushe muka fara fita anguwa da matarka? Sai ya yi shuru. "Ka bar mu tafi kawai. Ba ta san gidan ba ne? mu haɗu a can" "To ni na ce ta biyo ta nan ta ɗaukeku ku wuce ko ban isa ba ne? "Ka isa." "To tun da na isa a yi yadda na ce." Ya na gama faɗin haka ya katse kiran ya bar ni da ƙunƙuni. Da Hauwa ta zo na faɗa mata itama sai da ta ce topha sanabe daman kun saba fita tare ne? "Ina fa? Sanabe ne da gulma irin ta ɗa namiji ta na da mota mu kuma ba mu da ita ta zo ta yi mana lift mana." Hauwa na dariya ta ce ba shakka masu mota. Matar nan haka taɓata mana lokaci mu da muka ce yini za mu je mu yi sai 2 da wani abu na  rana sai ga ta zo. Har mamakin yadda ta ke cin kwalliya na ke yi in za ta fita. Allah ya sa nima da gayu na ta zo ta ganni ballantana ta ce ganin idone. Ita ta ɗauke mu a motar ta kamfanin toyota ce. Accord ina gidan gaba Hauwa na gidan baya har gidan Munnira itama da ta ganmu tare sai da ta yi min mgana. "Ke kuma wani ci baya ne ya same ki yawo da kishiya." Ina dariya na ce" Yallaɓai ne ya siyo min wannan wulaƙancin" Nan ba ta labarin yadda muka yi dashi Munnira ta buga shewa kafin ta ce" Ki yi zuciya ki yi mota Hajiya. Amma tabbas an nuna miki kafacinty mota yau ɗin nan" Ni kaina sai da na yi dariya na ce to ai ina sana'ata domin na kama sana'ar Hijabai hannu biyu kuma ina samu sosai yanzu har kaduna na ke aika ma Amina. "In sana'ata in da rai da rabo.." "Jariri za ya zamo ango." Hauwa ta karishe min muka tafa. Can falo muka bar Gimbiya a falo muna ciki muna hira muna shewa. Ba mu bar gidan ba sai shidda har gida muka kai Hauwa nima ta kawo ni gida nan ta yi sallar mangariba da ya ke ta san miji na ta ne sai ba ta tsaya ba ta tuka kanta zuwa gida ciki dai gashi nan ya bayyana daga gani ta na da girman ciki sosai. Mun je gidan Munnira da sati ɗaya Gimbiya ta je Rano ta yi sati Hajiyar Tafida kafa ta motsa ranar da za ta dawo gabaɗaya muka tafi ni da Yallabai da yara muka gaisheta sannan muka ɗauko Gimbiya muka dawo gida Kano. Rayuwa ta yi nisa kwanaki na ta gangarawa. Tuni Gimbiya har ya fara zuwa awo sannan suna ta siyayyan kayan haihuwa ta bakin mijinta.  Yadda Yallaɓai ke rawan jiki kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba, sai dai na yi masa uziri bayan tsawon shekaru bakwai ba a yi haihuwa a gidan shi ba abin mamaki ba ne domin ya nuna zumuɗi, bq shi ba hatta yan'uwan shi da nata suna ta ɗoki kowa fatan shi Gimbiya ta buɗe ido lafiya. Nima har acikin raina ina mata fatan haka. Kuma daman gashi Yallabai kuɗi ya ke samu kwangiloli ne ya yi ta yin su akai akai buɗi ko ta ko'ina tun cikin ta na wata takwas komai na haihuwa sun gama tanadar shi har ragunan da zai yanka firɗa firɗa suna can Rano. Hauwa ta ke faɗa min ita kuma kannenta ke kiranta suna kawo mata wani rahoton Ni dai na koma gefe na zama yar kallo abin jaje na yi abin murna ma na yi amma ni kaina na san duk abin da ke cikin Gimbiya in ya fito duniya zai ga gata. Duk da shi uban gayyar da kan shi ya ce min namiji ne aka gani a scan ɗin ta. Ban ji haushi ba domin nima ya nuna ma ƴaƴana gata da so shi da ƴan'uwan shi, shi ya sa na danne kishina ban taɓa nuna masa wani abu kan ɓare ɓaren da ya ke yi a kan cikin Gimbiya ba. *Janafty* *TKG02020B* Tun da cikin Gimbiya ya kai watan fitowarsa duniya Yallaɓai ya tattara gabaɗaya hankalin shi a kanta. Da a ce ya ga fuska zai ce ne na bashi dama ya koma can da zama har sai ta haihu tun da ga shi anguwan zoma. Sai dai bai samu wannan fuskar ba, ko da ya ke mene ne maraba da abin da ya ke yi. In ya na gidanta ba koda yaushe ya ke leƙomu ba sai dai ya kira waya in ko ya na gidana kwana kawai ke kawo shi tun safe zai fita ya je gidan Gimbiya daga nan sai ya wuce wajen aiki da daddare ma can ya ke raba dare sai sha ɗaya ya ke dawowa wata rana ma har sha biyun dare ya na kaiwa. Jiri ƙiri Yallaɓai ya san gaskiya kuma ya ke ta ke ta. E mana rashin aldaci ya ke nuna min kuma ai ya sani ba wai bai sani ba ni tun da ai kowa ya aikata mai kyau ya na sane. In ma mara kyau ɗin ne duk ya na sane. Ban dai taɓa magana ba saboda yanzu ina cewa uffan sai cibi ya zama ƙari tsab zai ce ni lokacin da na yi cikin bai kulani da ni ba ne? Ko ƴan'uwansa su ji labari su je hassada ne, shi ya sa ban taɓa ɗaga baki na yi masa mgana ba, kuma har a cikin zuciyata ina yi mata fatan ta sauka lafiya. Shi da kan shi ya zo ya na faɗa min ya yi ma Nene magana ta kira Hajiyar Tafida a samu wacce za ta zo ta zauna da Gimbiyar har ta haihu. Na ce hakan ya kamata kwana biyu tsakani kuma ya zo ya na faɗa min autar su Hajiyar ita ce Baaba Asma'u ta zo za ta zauna da ita har ta sauka lafiya. Amma zuwanta bai hana shi sintiri a gidan ba sai dai ya rage ba kamar lokacin da ba kowa ba. Cikin Gimbiya ya fita watan haihuwan shi har ya shiga wattani goma. In za a ƙirga ma ainihin wattanin cikin kafin ya koma baya kimanin watanni sha ɗaya kenan. Duk Yallaɓai ya tashi hankalinshi sun je asibiti an ce haihuwan ba ta taso ba, a cikin satin nan ma naguda ta ta so mata  gadan gadan kamar za ta haihun suna zuwa asibiti kuma komai ya tsaya nan suka kwana shuru aka dubata suka ce ba haihuwa ba ne dole suka koma gida da cewa nan da sati ɗaya in ba ta haihu da kanta ba za su yi mata C.S ne domin ceto abin da ke cikinta lafiya. Sati ɗaya bai cika ba wata ranar jumma'a da daddare 20 ga watan october 2016 misalin ƙarfe biyu da rabi na dare. Gimbiya ta fara zubar jini. Hankali tashe Baaba Asma'u ta kira wayar Yallaɓai ranar ya na gida na ne, barcin sa ma ya yi nauyi ni ce na tashi da vibration ya ishe ni. Ina ganin Baaba Asma'u na san mganar Gimbiya ce ni na ɗauki kiran ba ta bari na yi mgana ba cikin tashin hankali ta ce masa Gimbiyar na zubar da jini ni kaina na ruɗe saboda zubar jini ga mai naguda haɗari ne babba ban san lokacin da na ɗaka ma Yallabai uban duka a gadon baya ba ya tashi a firgice. Ina faɗa masa abin da ke faruwa ya sake firgicewa da haka zai fita daga shi sai gajeren wando da vest sai da na ce ya dawo na rarumo masa jallabiyansa ya saka na damƙa masa key ɗin motar shi, kamar zan bi shi sai kuma na fasa bai kamata na bar yara su kaɗai a gida kuma ga dare ba amma hankali ya tashi ko bayan tafiyar shi ban iya komawa barci ba ina zaune ina ta addu'an Allah ya sauwake ta lafiya duk da ba na salla ina hutu ban kwanta ba carbi na ɗauka ina ta hailala da yi ma Allah kirari ban san barci ya kwashe ni ba sai misalin ƙarfe  biyar saura na asuba kiran wayar Yallaɓai ya tashe ni da cewa an yi ma Gimbiya C.S. An samu nasaran ciro ɗa Namaji har a cikin zuciyata na yi farinciki na yi ta taya Yallaɓai murna muka rabu da shi da cewa shima ba daɗewa yanzu zai taho gida. Da asuban na faɗa ma su Jidda sun yi ƙani suna ta tsallen murna musamman ma Baby, Jidda dai sai dai ta yi mirmishi shine ƙololiyar nuna farincikinta Baby ce uwar tsalle tsalle ta na murna. Ta so ma ba za ta je Tahfez ba sai da na yi mata jan ido sannan ta bi Jidda suka tafi. Ni kuma na gyara gidan na yi ma Yallaɓai abun karyawa tun da ya ce min zai dawo gida, ina buɗe datan wayata na ga an yi saƙonni da yawa a group ɗin gidan su Yallaɓai ina shiga na ga Anty Bahijja ce ta sanar da an samu ƙaruwa a gidan Tafida Gimbiya ta haihu an samu Sadauki. Sai tagging ɗin sa ake yi ana masa murna ni ma na shiga na yi tagging ɗin sa na ce. "Alhamdulillah. Ina ta ya ka murna Yallaɓai. Allah ya raya ita kuma Maijego Allah ya ba ta lafiyar shayarwa." Mimisco ce kaɗai ta amsa da Amin sai Suwaiba da ta zolaye ni da cewa saura ke sai kawai na tura mata emojin mirmishi daga nan na kashe data na ijiye wayar. Yallaɓai sai wajen goma saura ya dawo gidan duk ya gaji ga barci a idanuwansa na tarbe shi cikin murna ya rumgumeni ya na ce min ya gaji sannan kuma ya na jin barci sai na ja shi tiolet na taimaka masa ya yi wanka ya so ya fara kwanciya sai na matsa masa a kan ya fara ƙaryawa sannan ya kwanta to muna saman dining ɗin ne ya ke ba ni labarin yadda komai ya faru. Ashe suna zuwa ne lokitoci suka ce a yi gaggawan saka hannu a yi mata C.S saboda cibiya ce ta sarƙe wuyan yaron. Nan ta ke ya saka hannu aka shiga da ita tiyata sai asuba suka fito da ita,   ta na can ɗakin hutu yanzu haka Baaba Asma'u ya baro tare da ita sai Nene da Anty Bahijja. "Ta farfaɗo kuwa? "E sai da ta farfaɗo sannan na taho ai." Sai na ce to alhamdulillah tun da ta farfaɗo na ce masa ina so na je asibitin sai ya ce na bari ya huta in ya tashi sai mu tafi tare. Haka ko a ka yi shi  na jira sai bayan azahar ya tashi daga barci ya sake yin wanka ni kuma lokacin na dafa kuskus mai karas da kabeji shi muka ci kafin mu tafi sannan kuma na ɗiba a kola wanda muka tafi da shi asibitin. A asibitin da ta ke zuwa dai anan ne ta haihu asibitin nan cike har da ƴan Rano sun zo mota guda su Anty Bahijja da su Anty Maimuna suna a gefen gado. Na gaishe su sama sama kamar yadda ke tsakaninmu tun faruwan abin da ya faru sannan na gaisa da Maijego an kuma ba ni yaro na ɗauka kamar Yallaɓai ya yi haki shi ya sa sai ya ɗauko fuskar Baby ban damu da mutanen da ke ɗakin ba na kalli Yallaɓai ina faɗin. "Yallaɓai kama su ke yi da Baby fa? Fuskarsa fuskar Baby kuma ai fuskar ta na ka ne ko? Sai ya leƙo ta kusa da ni shima ya na kallon shi kafin ya ce" Sai da kika faɗa na lura." Nasara na gefe ta ce itama ta ce ai wannan sak mai sunan Anty Maimuna ne. Buɗe bakin Anty Bahijja sai ta ce haba ai wannan ya fita kyau. Ita kuma Baaba Asma'u da ke gefe ta kada baki ta ce ai domin ya na jariri ne in ya ƙara girma zai iya ma riƙida ya sauya kammani. Ni dai na yi musu shuru kawai Yallaɓai ya koma wajen matarsa suna mgana ƙasa ƙasa. Likita ne ya shigo ya ce kowa ya fita Yallaɓai ne kawai muka bari a ciki mu kuma muka fito waje sai can ba daɗewa suka fito tare da likitan shi ne ya ke faɗin likitan ya ce ba sa son hayaniya, ya kamata kowa ya tafi gida a bar mutum ɗaya saboda maijego ta samu hutu. Ina jin haka Yallaɓai na tashi tafiya na bi sa bayan na ba ma Baaba Asma'u abincin da na taho dashi ta karɓa da godiya. Duk da ga manyan kololi nan na san ba su da matsalan abinci ni dai na yi don Allah ko ban yi niyar abu ba in na tuna da maganar Alhajinmu da ya ce duk abin da zan yi to na yi shi don Allah kuma na nufe ta da alheri shi ya sa ma har na ɗibi abincin na tafi da shi. Washegari ban koma ba, ko da Munnira da Hauwa suka kirani na ce ni jiya na je ba zan koma yau ba, na ce su je kawai ni ba zan je ba, ba su matsa min ba suka ce su za su je su yi barka, na faɗa ma duka yan gidanmu haihuwan ba saboda komai ba sai saboda Yallaɓai shima ya na yi min kara duk abin da ya samu ahalina sai in da ƙarfinsa ya ƙare. Sannan yanzu Ma'u munafuncin ta ya yi sanyi ko ma ta ji wajen Anty Bahijjan ba za ta nuna ta ji ba tun bayan faruwan lamarin ta kiyaye kanta, Ya Aina ta ce za su haɗu gabaɗaya su je asibitin su yi barka na ce ya kamata. Har Anty Zabba mun yi waya da ita ta ce ita ma Ya Usman ke faɗa mata da ya ke ba ta cikin group ɗin gidan su Yallaɓai tun lokacin auran Ya Usman ta fita daga ciki kuma ba a mai da ta ba, ta ce min za ta kira Yallaɓai ta yi masa barka. To sai da ya dawo da daddare ya ke faɗa min ta kira shi ta yi masa barka. Yallaɓai har wani jin daɗi ya ke yi in aka kira shi aka yi masa barka.  Kwanan Gimbiya Biyar a asibiti aka ba su sallama suka dawo gida. Su Ya Aina a na gobe za a yi sallama su ka je gabaɗayan su har da Zaitunan Ya Abubakar kuma Yallaɓai ya ji daɗi tun da shi ya ke sanar da ni zuwan na su. Ni daman sau biyu na je asibitin ban koma ba tun da daman asibitin cike ya ke da su Anty Bahijja.  Sai da ta koma gida na sake komawa sau ɗaya a ranar ne ma Yallaɓai ke fada min ya yi raɗin suna. Sunan jaririn Muhammad Inuwa. Sai da idanuwana suka kawo ƙwalla sunan da Yallaɓai ya so na sake haihu ya saka sai ga shi ni Allah bai ba ni ba amma shi ya ba shi a jinin wata matar Allah mai tsara komai a yadda ya so. Gwaggo ma kanta ta je har can Gwammaja ta yi ma Nene Barka ita da Ya Aina. Daga can kuma su ka wuce gidan Gimbiyar tare da Halima da ta zo za ta je gidan Nene ta ce su tafi tare su ka je suka yi ma Gimbiya barka. Sai bayan sun koma gida ne ma Ya Aina ta kirani ta na faɗa min. Shima Uban gayyar an faɗa masa sai ga shi ya zo ya na ce min ashe Gwaggo ta zo barka? Na ce eh sai ga Gogan na ta uban fara'a ban ga laifin shi ba ƙaruwa ya samu kuma ba zan ji haushi domin ya nuna murnansa ba. An ɗaga sunan sai da wani satin ya sake zagayowa sannan aka gudanar da taron suna a gidan Gimbiya da ke sharaɗa. Ranar sunan Yallaɓai baya nan tun safe ya tafi Dutse akwai kwangilan da ya samu a can ne. Raguna biyu aka yanka ma Muhammad Inuwa(Khalipa) shi ne alkunyar da za a riƙa kiran da shi. Taron suna aka shirya na gani na faɗa. Na je sunan tare da ni da Hauwa da Munnira, sannan ba tare da sanin Yallaɓai ba na siya ma maijego atamfa mai kyau sai rigan yaro da pampers. Su Hauwa ma duk sun je da abin suna, mutanen Rano sun zo da yawa Sameena ma ta zo har da Faridan Tariq ma. Can muka haɗe da su muka yi namu rukunin ana hira. Jidda da Baby daman tun jiya suna gidan sunan an yi abinci kala kala har da su tsire sannan an kira mai hoto an yi hotuna ni dai ban tusa kaina ba sai da ita kanta Gimbiyar ta kirani tare da ni da ita da su Jidda muka ɗau hoton Suwaiba na cewa hoton nan bai cika ba tun da ba ginƙishin buɗe bakin Anty Maimuna sai ta ce ai shi Tafidan za su yi na su shi da Gimbiya da Baby ni dai ban ce ƙala ba, to wani dare ne jemage bai gani ba? Ai sai dai daran na shi mutuwar. Muna gidan nan har yamma da ni aka gyara gidan bayan jama'a sun ragu daman aikin abinci ba a gidan aka yi ba kawo komai aka yi a dafen shi. Sai misalin tara na dare na koma gida na. Su Jidda nan na bar su duk da akwai makaranta ban isa na ce sai sun zo mun tafi gida ba domin na san ma ba za su zo ba gwara ma Jidda sai na bar su sai zuwa goben. Duk tare muka fita da su Hauwa kowa kuma ya hau adaidaitan da za ta kai sa gidan sa. Yallaɓai sai wajen sha biyu na dare ya dawo gidan a gajiye wanka kawai ya yi ya ci abinci ya kwanta. Washegari ban koma ba tun da ai ba hurumina ba ne sai yamma su Jidda suka dawo da nama mai yawa da su cake in ji Gimbiya na karɓa da godiya da fatan Allah ya raya mana Khalipa. Bayan suna da kwana uku Megidan ya ke ce min Gimbiya za ta koma Rano ta yi jegon ta na yi fatan alheri mota ya samo musu ta kwashe su, shi bai samu zuwa ba saboda sabon kwangilan da ya samu a Dutse ya sa ba ya samun zama yanzu. Gimbiya sai da ta fi kwana hamsin a Rano sannan ta dawo. Ta na dawowa na ce Yallaɓai ya je can ya yi mata sati sannan ya dawo wajena ya yi ta murna ranar da suka cika satin ne ya kawo min ita tare da Khalipa da ya yi wani ɓulɓul da shi ya ƙara wayau gwanin ban sha'awa har da za su tafi ya na hannuna sai daga baya ne da Baby ta saka rigima na goya mata shi. Yallaɓai na ta kafa kafa wai kar ta yar da shi, gabaɗaya ya kasa sukuni sai wani kafa kafa ya ke yi da Baby kar ta tula Khalipa a ƙasa abin da na lura da shi Yallaɓai na son wannan yaron har kuma soyayyar na shi ba ta ɓoyuwa a saman fuskarsa da ayyukansa. "Yallaɓai ka kwantar da hankalin ka. Ba za ta kada da shi ba, na ɗaure mata da kyau." "To duka duka Baby nawa ta ke da za ta goya wani? Haka ya ba ni amsa ganin haka ya sa na ce ma Baby ta zo na sauke mata shi, sai ta fara min kuka banza ai ba za a sauke shi ba, amma bai saka Yallaɓai ya haƙura ba shi a ganinsa kawai na yi masa kasada da ruhinsa ne, sai da Gimbiyar ta yi magana ta ce a bar mata shi ai za ta iya goyasa sannan ne ya yi shuru. Na kwana ina ta mamakin Yallaɓai ai ban gama mamaki ba sai da na ga a fuskar wayar shi ya cire hoton su Jidda da Baby da ya daɗe a wallpaper ɗin shi. Amma washegari da wayarsa ta faɗo hannuna na ga hoton shi ne tare da Gimbiya da Khalipa. Daman ai Anty Maimuna ta ce suma za su sha hoto aiko sun sha hoto shadda suka saka iri ɗaya mai ruwan sararin samaniya ni ban ma taɓa ganin Yallaɓai da kayan ba to tun da anko ne suka yi amaryan ƙarni da angon ƙarni daman ina zan gan shi da shi. Ta kwantar da kanta a saman kafaɗanshi suna dariya gabaɗaya suna kuma kallon Khalipa da ke hannunta. Ya shiga wanka ne daman ina gyaran gado wayar ta faɗo ban san a saman gadon ya ijiye ta ba. Karambani ya saka ni dannawa haske ya kawo shi ne na yi mummunan gani. Ba zan iya tuna yaushe ne Yallaɓai ya taɓa sakani a fuskar wayarsa ba. Ya na dai saka Jidda a farko kafin mu samu Baby. Bayan mun haifeta kuma sai ya koma sakata wata rana kuma in ya ga dama kawai sai ya saka hoton masallaci na taɓa yi masa zolaya da cewa sai ya yi ta saka hoton ƴaƴansa ni fa? Sai ya ce min wai ya za a yi ya saka hoto na? Ko wani kare da doki ya samu ganina na ɗauka a lokacin martabawa ne Yallaɓai ya yi min sai yanzu na fahimci ba ni ce na samu martabawansa ba Gimbiya ce ni matsayina  ne bai kai na zauna a kan fuskar wayarsa ba shi ya sa bai taɓa sakani ba. Idanuwana suka kawo ƙwalla na yi saurin share su jin motsin fitowarsa. A lokacin ban yi masa mgana ba sai na yi kamar ma ban gani ba sai da na zo fita daga ɗakin bayan na gama gyaran shi kuma ya na saka kaya. "Hoto fa ya yi kyau ƙwarai." "Wani hoto kuma? Ya faɗa da sauri ya na kallona ni kuma sai na yi kamar ban gani ba na yi masa mirmishi na fita. Ku san ai ya san abin da ya aikata sai ga shi muna ƙaryawa ya na yi min kame kamen su na maza in sun aikata wani abu na rashin gaskiya. "Wannan hoton wai kike mgana? Ya faɗa ya na nuna min wayarsa kallo ma bai isheni ba. Na cigaba da kurban tea ɗin da ke gabana. "Daugther ce ta matsa min sai mun yi hoton nan. Har walpaper ɗin ma ina tunanin ita ta saka shi na gani ina ta son na cire sai na sha'afa" Shi ya gama kiɗan shi sannan kuma ya yi rawan shi ban ce masa komai ba ganin haka yasa ya yi shuru shima bai ƙara mganar ba, ban sanin masa ba ko ya sauya sai can wata rana na ga ya saka hoton Khalipa da aka ɗauke shi ranar da ya zo duniya a raina na ce kai dai ka sani da munafuncin ka. Ko ya faɗa ko bai faɗa ba a irin soyayya da son da ya ke nuna ma Khalipa kowa ya shaida ya na matuƙar ƙaunar shi, ko ya na gidana ya dinga kallon hotunan Yaron da Video tare da yara suna nishaɗin su, wato ba zai iya ma kwana bai gan shi ba sai ya kalli hotunan shi ya ke jin daɗi. na san akwai abubuwa a gaba shi ya sa na roƙi Allah tun kafim zuwan lokacin ya ba ni haƙuri da juriya sannan ya ba ni wuyan ɗaukan koma mene ne zai faru anan gaba. ***** *BAYAN SHEKARA UKU.* KANO. LODGE ROAD. 20 September 2019. Lahadi. 11:30 na safiya. Kwance na ke a kan makeken sabon gadona na kamfanin royal. Na lulluɓe kafafuwana zuwa cikina da lallusan bargo mai ruwan madara. A cikin barcin ina can ina mafarkin wai gani a makka na je gaban ka'aba ina ta addu'a ina kuka, har ina jin danshin hawayen a saman fuskata. Ƙara narkewa na yi har ina ƙara motsawa sai dai me? Ina jin danshin ruwa a fuskata har zuwa wuyana a tunanina mafarkin ne ina kuka ashe ba mafarki ba ne zahiri ne sai da na ji ruwa tsii na ta sauka a saman fuskata zuwa saman wuyana ya ƙi tsayawa sannan na fara dawowa hayyacina.  Idanuwana na fara buɗewa a kasalance, ai da sauri na rufe saboda ruwan da ya yi min feshi a cikin idanuwana da sauri na kare fuskata ina ɗan yarfa hannuwana. Dariya na ji ana yi ta yara ƙasa ƙasa da hanzari na zuro kafafuwana ƙasa ina goge fuskata.  Khalipa na gani a tsaye a gaba na da bindigarsa ta wasa mai ruwa a jikinta wacce Yallaɓai ya siyo masa da ya je Saudiya wannan shekaran. Yaron ya na kallona ya na dariya wani takaici ya cika min zuciya kuma saboda bai da kunya har ya na ƙara saitani da bindigar ya na faɗi cikin muryan yara. "Umma faya faya." Wai Umma fire fire, ɗan mirmishi na ƙakaro kafin na miƙe tsaye na riƙe bindigar na duka a gaban shi ina kallon shi yaro ne ɗan kimanin shekaru uku da wattani, sai da Khalipa ya fara girma sannan mutane suka ƙara gasgata da Baby ya ke kama har ya na yin jikinsu na gaza gaza kamar na ƴaƴan hutu ko da ya ke ƴaƴan hutun ne tun da uban su yanzu ya samu duniya a tafin hannun shi sai juya ta ya ke yi a yadda ya so. "Khalipa ba ka ga Umma na barci ba ne? Na faɗa ina shafa sumar kansa, sai kawai ya fara min dariya. Ya na mgana amma ba a ganewa sosai amma ya na kiran sunan kowa kamar ni Umma da Abban su, sai Ya Jidda da Ya Baby sai sunan Mami wato Gimbiya a bakin shi da sunan su Nene ya san sunan kowa kuma ya iya kiran su, ina ƙokarin sake magana ya ƙwace bindigarsa ya fice da gudu daga ɗakin na bishi da kallo har ya fice sannan na miƙe ina hamma gefen gado na koma na zauna na ƙura ma window da ke cikin bedroom ɗina ido ina kallon rana da ta fara hudowa ta na shigowa ta tsakanin labulayen da ke cikin bedroom ɗina da ya sauya kamar ba shi ba sakamakon komai sabo ne a cikin ɗaki har ta fentin ma gabaɗaya. A cikin shekarun ukun da suka gabata abubuwa da dama sun faru masu daɗi da aka sin su. Masu daɗin sun fi yawa shi ya sa zan fara da su. Yallaɓai ya samu ƙaruwa ta arziƙi da dama a cikin wannan shekarun, karuwan kuma ba iya na dukiya ko arziƙi ba har na ƙara samun ƙaruwan ɗa namiji daga bangaren Gimbiya Khalipa da na shekara ɗaya da rabi ta sake samun ciki wannan karon ma aiki aka sake yi mata. Tun da ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda na farko ma ai an farka ta. Ta na nan yanzu haka ta na goyen Muhamamad Yusuf(Anwar) bayan haka kuma Yallaɓai ya yi ta shura ya na ta samun manyan kwangilolin gine ginen manyan makarantu da ma'aikatu da gidaje mafiyan shaharan ciki shi ne na gina makarantun aikin jinya la da gina makarantun manyan jamu'u  na gwammati da nayan kasuwa cikin shekarun ukun nan Yallaɓai ya samu ɗaukaka da shahara. Yanzu haka ya na nan ya na gina gma'aikatarsa ko na ce kamfaninda  anan zooa road ne ya siya wani tsohon ma'aikatan siyar da motoci ya buge shi ya na gina ƙaton kamfanin shi mai hawa uku amma dai suna nan suna aiki a tsohon offishin shi in da yanzu gabaɗaya sama da ƙasa ya zama duka mallakinsa sannan ya ɗau ma'aikata masu karatun abin da ya shafi fanni zane zane yanzu shi ba ya zane sai dai ya saka yaran shi su yi, sannan ya na da yara a bangaren masu leburan aikin gini sama da mutum ɗari uku a ƙarƙashin shi, ya na matuƙar taimaka ma matasa da aikin yi, yanzu haka gidajen bulo ɗin sa sama da guda biyar ne a garin Kano. A cikin shekaran nan ya biya ma kansa Makka shi da Nene suka je suka sauke farali suka dawo. Da ya dawo ne gabaɗaya rabin tsarabarsa kayan wasa ne na Khalipa da Anwar, Jidda da ta zama yan mata shekaranta sha bakwai tana kuma SS2 ne a babban sakandiri a yayin da Baby ke da shekaru goma sha ɗaya a duniya ta na ajin karshe a primary ne. Su kaya ya siya musu tun da sun girma sun wuce kayan wasa.   Yanzu haka gidan da Gimbiya ta ke ciki Yallaɓai ya siye shi ya zama mallakin shi sannan ya siya wani ƙaton fili a Aluvenue, kimanin sama da miliyan ashirin in da ya ce zai gina mana ƙaton gida da zai haɗe iyalan shi waje ɗaya. Sannan ni da ita gabaɗaya ya sauya mana fenti a gidajen mu sannan ya siya mana sabbin furtures, ni dai tsoffin nawa wasu na ba ma Inna Mariya wasu kuma na aika da su Yashe domin suna bukata kujerun babban falo na da gadona kuwa Rahila na ba ma wa tunda na yi sabbi masu kyau da tsada. Sauran tarkacen kayan kitchen kuma Maman Saude na ba ma wa. Katifa ma ta ɗayan ɗakin Maman Nana mai yi min kitso na ba ma wa.   Har gobe kuma ina nan da sana'ar sai da hijabaina kuma yanzu har sari ma na ke ba da wa.Maganar buɗe shagon saloon ta daɗe da shan ruwa. Yallaɓai bai sake min mganar ba nima ban ƙara yi masa ba. Ita dai Gimbiya kam yanzu shagon sai da abayoyi gare ta da takalma kuma Yallaɓan ne ya kama mata shagon da cewa ita ta kama da kanta da gadon ta na tsohon mijinta. kuma ta cigaba da oder kaya daga kasashen ƙetare. Akwai mai zama mata a shagon amma itama wani lokacin ta na zuwa ta zauna in ta na da lokaci. Kuma har gobe ta na cigaba da aikin ta na Gwammati. Cikin kuma ƙaruwan da aka samu shi ne na bukukuwan da muka sha kai da kai. Farko dai na Marwa da Kawu Abba muka fara yi ita yanzu haka ma  ta na nan da yaron ta mai suna Abdallah ta na garin Rano sannan ta na aiki a asibitin Gwammati na garin Rano, bayan ita kuma a wannan shekaran muka yi bikin Anti ƴar wajen ya Murja ta yi aure anan garin Kano. Bayan na ta kuma muka yi na Jawahir da Musbahu a rana ɗaya. Jawahir ta na kaduna Musbahu kuma a garin Kano ya ke zaune a kuma gidan kan shi tun da shi ne Manaja na kamfanin Yallaɓai sannan shi ke rike da gidajen bulo ɗin su gabaɗaya a ƙarkashinshi suke, Adnan kuma ya na nan BUK ya na master ɗin shi. Datti ma ya gama kasu ya na Abuja gidan Ya Auwal ya na aiki da wani kamfanin littafai bai yi aure ba. An yi rashe rashe tun da har Baaba sani mun rasa daga yashe. Bangaren Yallaɓai kuma sun rasa Innayi sai dai fatan Allah ya yi musu rahama.   A yanzu da na ke da matakin shekaru talatin da bakwai a duniya. Yallaɓai kam ya haura arba'in ya kama gidan Hamsin amma daga ni har shi in ba mun faɗi shekarun ba, ba mai sanin haka saboda mun mori jiki sannan ga jin daɗi musamman shi da ya ƙara zama babban mutum sosai. Ni kuma har gobe ban daina gyara jikina ba, har kuma zuwa lokacin ban ƙara samun ciki ba shekaru goma kenan tun ina mganin asibitin da na gargajiya har daga ƙarshe na haƙura na yi shekara ban ƙara shan wani mgani ba, daga na hausan har na gargajiya. Na fauwalama Allah duka lamuran shi duk kuma abin da ya yi min to dai-dai ne. Ba zan ce a shekarun ukun nan da suka gabata ba mu yi ta samun matsala da Yallaɓai ba mun samu sosai, sai dai wani abun kana barin shi ya wuce domin a zauna lafiya. Tsakanina da Gimbiya sama sama kamar baya ta na gidanta ina gidana amma duk da haka bai hana ta makirci da kissa ba. Tun haihuwan Khalipa na fahimci ta na da son kanta sannan makira ce. Ita ta ɗauka ni ban iya makircin ba ne shi ya sa ba na yi mata. Na iya kawai dai ni ina zaune da ita da zuciya ɗaya ne. Ina mamakin kishin da ta ke nunawa a kan Yallaɓai ta manta ni ce matar shi ta farko daga baya ya aureta amma yadda ta ke nunawa kamar ta fi ni kishi ne. Tun da khalipa ya isa fara tafiya ko na ce ya fara cin abinci duk in da Yallaɓai zai je tare su ke zuwa kamar ɗan gwal. Da ya zo ya fara tafiya kusan in dai Yallaɓai na gidana shima ya na gidan tare da uban. A cewar shi ya saba da shi ko ita Gimbiyar bai saba da ita kamar yadda ya saba da Yallaɓai ba shi ya sa ko yaye a gidana ya yi rabin yayen shi, da sunan ga su Jidda sannan kuma Khalipa ba ya kwana a kusa da kowa sai a jikin Baban shi. Kawai dai a takaice regular costumer ne shi a gidana. In Yallaɓai na gidana to shima ya na tare da shi in kuma ya na wajen Gimbiya to shima ya na can. Abin haushi ma da takaici sai a tsakiyarmu ya ke barci, ko an kai shi ɗaki su Jidda ya na barci da ya farka muna cikin barci za mu ji kukan shi dole sai a jikin uban ko a kusa da shi zai kwanta. Ni lokacin da na reni ƴaƴana ni kaɗai na sha wahalata amma ni gashi ta haifa ta bar ni ina shan wahala,  ga shi yaron ba ya jin mgana ga mugun wasa ga ƙarfin tsiya har Baby yanzu gagaranta ɗauka ya ke yi. Sai Jidda tun da ita kam ta zama ƴan mata kusan shekaru biyu da fara period ɗin ta. In na yi magana Yallaɓai ba ya bi ta kai sai ya ce yaro ne duk ranar da ya ke gidana tare da yaron nan muke kwana a kan gado ko ƴaƴana ba su yi min haka ba, sannan mgana kaɗan in na yi a kan Khalipa sai Yallaɓai ya juya min mgana ya ta so min shi ya sa na saka masa ido a yanzu haka a cikin yanayin da muke kenan na gaji matuƙa ba ni da lokacin sakewa da mijina Khalipa na naniƙe da shi wanka ne kaɗai ba ya bin sa amma ko masallaci tare su ke zuwa. A lokacin da ya dawo daga Saudiya na ga uwar tsaraban kayan wasan da ya kwaso musu sai da na yi magana da cewa Yallabai hala dai ba ibada ya kai ka saudiya ba. Siyan kayan wasa ka je yi ko? Ai daga wannan maganar ya fara min masifa wai ina mgana ba ta taunawa ko Baby ai ba za ta yi wannan mganar ba, sai da na yi nadamar yi masa mgana kwana biyu ya yi ya na gaba da ni. Daga faɗin gaskiya domin jaka ce shaƙe da kayan wasa ba dole na yi tunanin daman abin da ya kai sa ba kenan ni kaina gidana ga su nan da yawa ballantana gidansu da Jidda ta ce min ɗaki ne guda da kayan wasa na khalipa da Anwar. Na yi ta haƙuri ina kauda kaina yanzu haka Gimbiya sunan da su  Anty Bahijja ke kiranta da shi shi ne Uwar maza. Shekaranjiya ma mun haɗu gidan Naja suna ta haihu ana ta yi mata kirari da Giwar gidan Tafida uwar maza mace mai kashin arziƙi domin a cewarsu tun da Tafida ya aure ta ya ke ta ganin buɗi na arziƙi ni dai ban tanka ba tun da daman ai tun bayan faruwan lamarin nan sun sanni na san su, shi ya sa in suna abin su ba na biye musu suma kuma sai dai habaici da shakuɓe amma ba sa yi da ni kai tsaye. Munnira ce ma ta ce ita uwar mata ba uwa ba ce? Anty Maimuna ta ce uwa ce amma uwar maza ita ce da gida. Sai da muna adaidaita za mu tafi gida ni da Hauwa bayan mun rabu da Munnira ta ke min mgana wai kar na damu da mganganunsu ni ko sai na ce yau a ka fara? ai sun daɗe suna fadin haka ban taɓa nuna na damu ba, ita kuma Gimbiya ta na hura hamci ta na iyayi ita matar arziƙi ni ko na ce in ma tsiyar ce to Yallaɓai ne ya shafa min tun da ni kam da arziƙina ya aure ni ya tsiyata ni yanzu da ya samu duniya sai suka manta. Yanayin rayuwa ya sa na daina ma damuwa da wasu manganganun saboda ai jiya ba yau ba ne.  Kuma girma ya ƙara kamani da ya sa lamarin ya zame min jiki ba komai in na ji ko na gani na ke mgana ba amma tabbas an kusa kai ni bango akan lamarin Khalipa na zura ido na yi kara na yi kawaicin duk a banza ko ƴaƴana suna tasawa na ke daina kwana da su ballantana ɗan kishiya. A raina na ji ko me zai faru sai dai ya faru amma sai na yi ma Yallaɓai mgana. **** Tiolet na shiga na kama ruwa sannan na fita falo. Jidda ce kawai ke gida ba ta jin daɗi Baby kuma ta tafi Tahfeez. Falon su Khalipa duk ya kama kaca kaca da shi ya watso min fillows ɗin kujera a ƙasa. Jidda na falon ta na karatu a ipad ɗinta tun da Abbansu ya ce a wannan shekaran za ta yi jarabawar fita da Jamb. "Jidda kina zaune Khalipa ya hautsina min falo haka? Sai ta ɗago ta na kallona kafin ta yatsina fuska ta na faɗin" Na gaji da gyarawa ne Umma da na gyara sai ya ƙara watso su." Hararanta na yi kafin na ce" To ni ne kike so na kwashe? Ina mgana na ji ina taka ruwa na fara mata faɗan ta bari ya jiƙa min gida sai ta ce wai ita ba ta sani ba. "To ke za ki yi min gyara gidan  ko yarinya." Na faɗa ina shiga falon Yallaɓai nan ko sai da na kusa kuka ya watsa duka kujerun dining sannan na iske shi ya na feshe kujeru da ruwan bindigarsa ai saboda takaici ban san lokacin da na masa tsawa ba, kuma ga shi ba shi da tsoro, ke gizau Jidda na ƙwalama kira ta na zuwa na ce ta natsar da shi kuma ta gyara min gidana ko ranta ya ɓaci. "Umma wallahi na hana shi ya ƙi bari ne." Na wuce ina mai jan tsaki kafin na ce" Wannan ke ya shafa. Ni dai na fito na ga gidana ya yi tsab ya na tashin ƙamshi." Kitchen na shiga na haɗa tea daman akwai ruwa a fulas na dawo falon na zauna. Ina jin su ta na gyarawa ya na ƙara ɓatawa ita kuma ga shi ba ta da zafi shi ya sa ya ke ba ta wahala da Baby ce da yanzu an fara kokuwa. Da na ga ba zai bari ba sai na fito da bulalata na na nusa masa na ce ko ya natsu ko na zane shi, bai ko natsun ba sai da na chau la masa biyu sannan ya fara kuka daga nan sai barci shi ne fa Jidda ta samu ta yi min gyaran gidan. Ita ba ruwanta ta na son aiki ga wacce sai na yi da gaske ta ke aiki nan Baby in na yi magana sai Yallaɓai ya ce ai gado ta yi kuma daman an ce magaji ai mafiyi ina jin haka zan yi shuru. Allah sarki Saude ita na ke tunawa in su Jidda na makaranta aiki ya yi min yawa. Tuni an yi mata aure shekara ɗaya kenan a jigawa yanzu haka tsohon ciki gare ta. Duka masu zuwa su tayani aiki yanzu suma sun kama ɗaku nan kansu. Jidda dai ke ƙoƙari domin in dai ta na gida ba na aiki girki kam ba abin da ban koya mata ba. Yau Yallaɓai a gidana ya ke amma gobe zai koma gidan Gimbiya. Sai dare ya shigo gidan ya ce min ya ɗan tsaya a Gwammaja ne, da ya ke Nene yanzu ta samu lafiya sai dai ɗan ciwon kafa da ke matsa mata lokaci bayan lokaci haka. Ko da ya dawo Khalipa ya yi barci amma kamar ana masa wahayi da ya ji muryan ubab zai tashi nan fa ya maƙale masa har cikin gaurancinsa ya ke faɗa ma uban wai na dake shi, shi kuma ya ce ka yi ma Umma laifi kenan ko? "Ɓarna ya yi min bayan na saka Jidda na gyarawa ya ƙi barin ta ta yi aiki shi ne na yi masa bulala biyu." "Kai sarkin rigima ba za ka daina yi ma Umma ɓarna ba ko? Ya faɗa ya na shafa kumatunsa. Kallon Yallaɓai kawai na ke yi in ya na wani abun, faɗa ya ke yi itama Gimbiya haka ta ke fama da shi. A raina na ce muna fama dai ni fa sai dai na bar Yallaɓai da Khalipa domin a daran ma wasa suka fara yaron na bin shi da bindiga shi kuma ya na ɓoyewa shi da Baby saboda ita ce mai son wasa. Jidda kam ba ruwanta da wannan shanshanci shi ya sa na ke sonta ta na da aji sosai. Ɗaki na koma na yi kwanciya ta ban ma san shigowarsa ba, sai cikin dare na farka na gan shi maƙale da Khalipa wani abu ya kawo min wuya amma ban yi wani abu ba, ji na yi kamar na koma ɗayan ɗakin na kwana amma sai na fasa. Da safe muna karyawa bayan yara sun tafi makaranta. Yallaɓai ya siya sabuwar mota wata bakar benz tsohuwar tashi kuma ta na hannun salisu shi ke kai yara makaranta a ciki sai cefane. "Daughter ta ce a saka Khalipa a makaranta na ce laa ba yanzu baa" Kallon shi na yi lokacin ina tura dankalin a bakina. Ko a yanzun ma Khalipan na kan jikin shi ya na bashi dankalin a baki, ko fa fita Yallabai zai yi in ba da shi zai fita sai da dubara in kuma ya duba bai gan shi ba haka zai ta rigima to ya riga ya sabar masa. "Gaskiya kam a saka shi a Baby cllas ba." Na faɗa ina haɗiye abin da ke bakina. Amma sai Yallaɓai ya ce ba yanzu ba sai ya shekara biyar. "To me ya sa? Na ga dai  da bakin shi ko? Kuma ko Baby ta na da shekara huɗu ka saka ta a makaranta." "Da  Khalipa da Baby ba ɗaya suke ba. Shi fa ya shaƙu da ni kina tunanin zai zauna a makaranta? Wani kallo na wurga masa kafin na ce" Tabbas ba ɗaya suke ba na ga alama." Daga haka ban ƙara kula sa ba har ya gama mganganun sa. Tare suka fita da Khalipa ya ce zai kai shi gida a raina na ce a gayas daman na gaji ina so na kwanta. Bayan kwana biyu da ya dawo gidana bai zo da Khalipa fa a cewarsa uwar ce ta ce ba zai biyo shi ba. "Ta ce wai ana takura miki. Ni kuma na ce mata duk ɗaya ne da nan ɗin da can duk in da Khalipa ya ke so zai zauna." Kallon musulunci ma bai samu ba ya gama gyaran zencen sa ya yi shuru. Da safe kuma again muna ƙaryawa ya fara isa ta da labarin shagon Gimbiya na yi masa kasaƙe kawai ina jin sa kuma ina kallon shi. "Shagon ma fa ta ce ya yi kaɗan kaya ba sa wata suke ƙarewa yanzu fa har jiran oder ta ke yi " "Uhm Allah ya sa albarka." Na faɗa ina son kauda mganar amma ina shi a dole sai ya faɗa min. "Ina gaya miki ana siya kayan ta sosai duk abokaina da abokan kasuwancina wajenta suke ma matan su siyayya." "Ka kyauta Marketing manager." Na watsa masa mgana amma sai na ga ya yi dariya kafin ya ce" Haka Daugther ta ce ta naɗa ni markerting manager a shagon ta na iya talla." Kamar wani shashasha ya na ta dariya ji na yi kamar ina make sa da kofin hannuna amma sai na basar gani na yi ya dameni abu kaɗan ya ce Daugther daman ni sunan nan wallahi ya daɗe ya na ba ni haushi kawai yau na ce bari na yi masa mgana. "Yallaɓai kana da abin mamaki." "Na me fa? Ya tambaya ya na kallona. "Ka auri mace har ka yi mata ciki ta haihu sau biyu amma ka na ta wani kiranta da sunan Daugther don Allah miye ma'anar wannan sunan? Ƴa? To kai yarka daman ka aura ka ke yi ma ciki tana haihuwa? "Ban gane ba" Ya faɗa bayan ya rage fara'aran fuskar shi. "Ka duk gane abin da na ke nufi." "To sunan Daugther ɗin ke kuma ya tsaya miki a rai? Kike kishi da sunan? Ya faɗa ya na kallona kafin in samu zarafin mgana a fusace ya cigaba da faɗin" Kin ba ni mamaki me ya sa yanzu kwata kwata ba ki tauna mgana in za ki faɗa min ne? Ai kin san matsayin ta a wajena da matsayin sunan tun kafim mu yi aure haka na ke kiranta kuma ya kama bakina. Sai a ka ce kuma haramun ne don ta na matata kar na ce mata Daugther? "Ba haka na ke nufi ba." Na faɗa ina ƙoƙarin kare kaina ganin ya taso min "Haka kike nufi mana. Sai an yi magana ki ce ke kin girma kaza da kaza, kin girman ne kike yin abin da kike yi? Sunan mai sai kin yi masa wata fassaran? Ashe ita Allah ya jiƙanta ba domin ta mutu ba da sai ta haɗiye zuciya ta mutu. Wani irin suna ne ban kira ki da shi a gaban ta ba? Wallahi ba ta taɓa mgana ko ta nuna rashin jin daɗin ba, ban taɓa kiran ta da sunan soyayya ba ke fa! Ba sunan ƙaunar da ban kiraki da shi ba karshen ta dai to ke ɗin ce na ke kira abar ƙaunata a gaban ta, ba ta taɓa mgana ba sai ke? Don ina kiran ta Daugther? Ba ki son ji ne? To sai dai ki toshe kunnuwanki domin ba zan iya daina kiran ta da wannan sunan ba."   "Ka yi haƙuri." Na samu kaina da furtawa a cikin raina ina mai nadaman fara yi masa mganar. Daga mgana sai kawai cibi ya zama ƙari. "Ba maganar haƙuri ba ce. Ki gyara a matsayin ki na babba kar ki yi abin da za ta ji ko ta gani girman ki ya zube a wajen ta." Ya na gama faɗin haka ya miƙe a fusace ya shige ciki sai ga shi ya dawo da key ɗin mota daman a shirye ya ke ya fice ya na faɗin. "Sai na dawo." "A dawo lafiyan" Ko amsa ni bai yi ba ina jin tashin motarsa da ya dawo ma zai rufe get ɗin da ƙarfi ya tura shi har sai da ina daga falo na ji wani garam! Na riƙe baki ina faɗin ikon Allah! *Janafty* *TKG020C20c* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732 Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰 Sama da mintina goma da fitar Yallaɓai amma na kasa ko da motsa ɗan yatsa na saboda da al'ajabi daga mgana sai cibi ya zama ƙari.? Har ya na min wani gorin ya na kirana Abar ƙaunarsa ni na saka shi? Ban da ma gulma yaushe ne ya fara kirana da wannan sunan? Ba sai da ya yo min kishiya ba ne ya fara min sanaben kirana da sunaye kala kala. Sannan in zai kirani da wannan sunan sai in zai min yaudaran su na maza ko ya na so ya raina min wayau amma shi ne har ya na yi min gori. Abin fa ya tsaya min a zuciya cikin sanyin jiki na miƙe ina tattara tarkacen abubuwan da muka ɓata zuwa kitchen. Na gaji baya na har ciwo ya ke yi na saka anemin wata ƴar aiki, amma ba a samu ba can kwanaki na yi ma Inna Mariya mgana ta kawo min wata yar anguwan su amma ko sati ba ta yi da fara zuwa ba na ce ta bar shi kawai saboda ba ta iya aikin ba in ma ta yi sai na sake yi, in za ta yi shara bara da bana in mopping ne ta jiƙa min gida da ruwa. In kuma wanke wanke ne duk ta haɗe masu karni waje ɗaya kuma su yi ta warin omo ba ta wankewa da kyau ballantana ta ɗaureye su da kyau shi ya sa kawai na haƙura amma ni kaina na san zai yi wahala na samu mai aiki kamar Saude. Ɗaki na koma na zauna a gefen gado cikin sanyin jiki. Na rasa me ke min daɗi haka kurum zuciyata sai ta cunkushe, na zauna shuru kawai ina ta nazarin rayuwa ƙaran wayata da ke gefena ya dawo dani daga tunani mai zurfin da na faɗa ina dubawa sai na ga Munnira ce amma har wayar ta katse sai na kira ta daga baya. Duk da ban san dalilin kiran ba amma ina tunanin kan batun bikin autar su Hauwa ne Sakina da za a yi nan da sati biyu. Mun yi ankon can Rano sannan mu ma mun fitar da anko mu uku. Saboda duk duniya Hauwa ba ta da wasu ƙawaye makusanta ta a Kano irin ni da Munnira. Haka nima duk da dai ga su facololina amma kuma sun riga sun zama aminaina ma su taya ni kuka in dariya ne mu yi tare in kuma na baƙin ciki ne su ta ya ni su ne mutane na farko bayan iyayena da ƴan'uwana ma su zama kusa da ni a duk yanayin farinciki ko baƙin ciki. Nima shi ya sa in sha'anin su ne na ke ɗaukan shi da muhimmaci yanzu ma muna maganar gudummuwar da zamu haɗa ma Mamansu Hauwa mu aika da shi kafin lokacin bikin ne. Nima har wayar ta katse ba ta ɗauka ba sai na ƙyaleta na miƙe kenan zan bar ɗakin sai ga shi ta sake kirana sai na koma na zauna. Cikin fara'a na ɗaga kiran ina faɗin. " Mata a gidan Nasiru." "Uwargidan Alhaji Injiniya Tafida ba" Sai na ƙyalƙyace da dariya, itama ta na taya ni ina ji Samir na kuka yaron da ta ke goyo. Yanzu haka daga ita har Hauwa goyo su ke yi sun sake haihuwa. Ni ce dai Allah bai kawo karshen lamarin ba in kuma shi ne na ƙarshe to ina masa godiya domin ya yi min ni'ima ni'imar da ya tsame ni a cikin waɗanda ma bai taɓa ba ma haihuwan ba. Bayan mun gama gaisawa da tambayan yara sai muka gangara kan mganar mu. Mun tsaya akan cewa za mu haɗa ma Hauwa 50k Munnira za ta turo min sai na haɗa na tura ma Hauwan mu ce gudummuwar ce ba yawa. "Hakan ya yi. Zan tura miki zuwa anjuma. To mganar tafiyar mu fa? "Mu je ana gobe biki. Sai mu dawo ranar lahadi ko? Na ba ta amsa, sai ta ce hakan ma ya yi itama daman ta riga da tambaya ni ko na faɗa mata ba ma mu yi mganar ba. "To sai ki yi ƙokari ki yi masa magana duk da na san ba zai hana ki ba." "Uhm yanzu nan ya gama ƙare min tanadi Munnira." "Me ya faru? Munnira ta tambaya ban ɓoye mata komai ba na sanar da ita duk abin da ya faru na ƙarishe da faɗin" Kin ji yadda ya ta so min Munnira? Har ya na ce min wai ni wani irin suna ne ba ya kira na da shi a gabanta ita ba ta taɓa nuna damuwa ba sai ni. Har ya na ce min na kama girma na." Munnira ta bushe da dariya har da ƙyatatawa. Har sai da na ji haushin ta ina faɗin. "Ban son iskanci fa Munnira.".. Da ƙyar ta tsagaita da dariyarta ta na faɗin" Wallahi abin ne ya ba ni dariya. Lalle an nuna miki iya duniya Sadiya ke ma me ya kai ki? Ina ruwanki da sunan da ya ke kiranta? Ba Daugther ba Allah ya sa ruhinsa zai kira ta bai ma kamata ki nuna kin san yana yi ba, ballanta har ki nuna damuwar da zai samu damar faɗa miki mgana" "Ni fa haushi ya ke ba ni. Abu kaɗan ya ce Daugther." "To ina ruwan ki? Ke ma wallahi laifin ki ne, ke kika jawo duk maganganun da ya faɗa miki maganar gaskiya fa kenan" A daƙune na ce" To na ji ai shike nan" "Ba maganar shike nan. Gaskiya ce. Ke ma yadda na san ki da kama kanki me ya kaiki shiga abin da bai shafe ki ba wannan karon? "Ttsautsayi." "Allah ya raba mu da tsautsayi to." Munnira ta faɗa ta na min dariya sai na ji haushi na kashe wayata na bar ta ta na min dariya. Nima sai daga baya na yi ma kaina Allah ya ƙara da ban yi magana ba, da bai samu damar faɗa min maganganu son ran shi ba, da haka na yaƙice tunanin haka na shiga ayyukana amma a ƙarƙashin zuciyata ina ta auna maganganun Yallaɓai ba wasa ba ya faɗa min mganganu masu zafi amma tun da ni na shiga huruminsa duk ma abin da ya faɗa min ai ni na jawo shi. Ɗan wannan maganar ashe shi Yallaɓai ya ɗauka da zafi da ya dawo gidan ina masa sannu da zuwa, da ƙyar ya amsa ni kamar na faɗa masa cuta ina ganin haka na kama kaina domin nima ina da zafi ba zan bari ya ɓata min rai ba, in hakan ta faru to ni da shi ba za ta yi mana kyau ba. Abinci ma da na haɗa masa nan ya bar min kayana bai taɓa ba da safe ma tea kawai ya sha ya fice jira ya ke yi ƙila na sake bashi haƙuri bayan duk haƙurin da na bashi jiya ai ko sai da a yi zama a haka. Ranar daman ya bar gidana kuma har ya koma gidan Gimbiya ya gama kwanakinsa bai kirani ba, sau ɗaya ya zo gidan daddare shima wasu takardu ya zo ɗauka. Yadda ya basar da ni nima haka na basar da shi, tun da har na bashi haƙuri da farko ni kuma a raina na ƙudiri niyyar ba zan ƙara bashi haƙuri ba kuma. Kar ma ya haƙura shi ya sani. Ga shi ina son na tambaye shi maganar zuwa Rano amma ba fuska. Cefane ma Salisu ya kawo min kuma da in zai kawo Yallaɓai na kiran waya ta ya faɗa min amma ranar bai kirani ba, ni kuma da ya zo gidan ban yi masa mgana ba. Ranar da zai dawo wajena ranar Matar Musbahu ta zo min yini Mubeena mai kirki da ita. Yadda Musbahu ya ke ɗan gidana itama haka ta ke a wajena domin shi da kan shi ya nuna mata ta daraja ni shi ya sa ta ke girmanani. Ta na zuwa gidana sosai ta yi min yini. Ni ko bai fi sau biyu na taɓa zuwa gidanta ba da lokacin bikin su sai kuma da muka je tare da su Hauwa, na ji daɗn zuwanta da ya ke ta na da wayewa ta na ma karatu ne anan BUK Kano sai dai ta na shekaran karshe ne, ga ta ba ta son jiki in dai ta zo tare muke yin ayyukan mu, ita da bakinta ta ke faɗa min acikin hira Anty Bahijja har gida ta je ta na yi mata faɗan wai ta kama ni kamar ni ce yayar mijinta. Su za ta kama domin su ne dangin mijinta ni ma bare ce kamar ita. Da ta faɗa min dariya kawai na yi ni yanzu ai sun daina ba ni mamaki harkan gabana kawai na ke yi, tun da aka yi mana tsakani ba ta ƙara haɗo mu ba, duk da dai suna yi ta bayan fage. Yanzu har Halima na daina ganinta a gidana ta koma yar tsagin Gimbiya. Ƴaƴansu daman ba sa zuwa gidana amma gidan Gimbiya har truruwa suke yi mata ni wannan bai dame ni ba. Amma nima ƴaƴana sun daina zuwa musu hutu tun da abin na su ya koma wariyan lautin fata kowa ya riƙe na shi, ko da ya ke yanzu sun daina mararin su sun koma mararin su Khalipa yanzu su ne komai suka samu na su ne ni na manta rabon da su yi ma su Jidda ma wani abun ma ban damu duk da na san a baya sun yi daga baya da suka samu waɗanda suka maye musu gurbinsu sai suka manta da su. Ban lura da wannan domin babu abin da ƴaƴana suka nema suka rasa. Yallaɓai mai yi ma iyalan shi ne shi ya sa ban cika damuwa da wasu abubuwan su ba. Waina na yi ranar Mubeena ta ta yani muka yi aikin wainar. Har dare ta na gidana sai da Yallaɓai suka taho tare da Musbahu sannan suka koma gida tare bayan shima ya ci wainar a nan na kuma saka musu a kula su ka tafi dashi. Yallaɓai ya ɗan sake amma ba sosai ba har yanzu da sauran cin mgani a muryansa da ayyukansa ni kuma sai na nuna kamar ban ma san yana yi ba zuwa washegari sai ya saki ya dawo ya na min magana kamar ba shi ne ya ke ci min mgani ba. Fuskar da na gani ya sa na yi masa mganar bikin Rano nan ta ke ya amince ya kuma turamin 30k ya ce na yi na mota da guddumuwa. Da ya yi maganar yara na ce ga Jidda za ta iya kula da gida. Shi fa a ganin shi har yanzu Jidda yarinya ce ita kanta ta na bukatar kulawa sai na ce to ya kwashe su zuwa gidan Gimbiya kafin na dawo sai ya ce sai abin da ya gani. Ko Munnira ban kira na sanar mata an bar ni ba. Sai dai na faɗa ma Hauwa muna tafe ranar jumma'a ta na ta murna. Ita tun ranar litini ta na can, da na tura mata kuɗin da muka haɗa kamar ta yi kuka da ta kirani ta na min godiya na ce mata ai mun zama ɗaya. Marwa na kira ranar al'amis ana gobe tafiyarmu na ce mata muna tafe ta buga tsallen ihu ta na murna daman ai ta san da bikin tun da ni da kaina bayan bikin na su na je Rano na ɗauki Marwa na kai ta har gidan su Hauwa na yi ma ta uwar ɗaki da mamansu Hauwa da ƙannenta. Su ka kuma karɓeta hannu biyu suna zumunci yanzu bayan gidan iyayen mijinta ba ta da kamar gidan su Hauwa duk da har gidan su Gimbiya ta na zuwa amma sai wani abu ya faru na jaje ko na murna. Kawu Abba kulle gare shi ba ya son yawo ko Kano tun da Marwa ta yi aure sai da ta yi wata biyar sannan ta zo ganin gida daga nan kuma sai da ta dawo gida jego da ta koma ba ta dawo ba sai bikin Antin Ya Murja na su Jawahir ba su kwana ba a ranar suka zo tare da matan su Kawu Sa'adu a kuma ranar suka koma. Kafin safiyar jumma'a na shirya kayana tsab don ma telana ya ɓata min lokaci akwai kala ɗayan da bai gama min ba sai da na jira. Munnira ta biyo min, ba mu tafi ba sai da su Jidda suka dawo makaranta sannan muka ɗau hanyar Rano. Yallaɓai ba gidana ya kwana ba a waya muka yi sallama. Mun isa Rano da wuri shi ya sa ko su Anty Bahijja acan suka iske mu, mun baje ana komai damu a ka gaggaisa kusan ita Anty Bahijja ko yaya ne sai ta taɓa hali sai da ta ce ma Munnira wai ka ga Aminan yayar amarya har an hallara akan lokaci Munnira ta ce tabbas dole mu hallara akan lokaci domin ta Hauwa shirye shirye a matsayin mu na Amininta. Marwa nan gidan su Hauwa ta so muka haɗu da mangariba ta tafi za ta ce gida ta shirya ta na da aikin dare ne ranar. Mu kuma nan gidan su Hauwa muka kwana washegari aka tashi da yinin biki da ɗaurin aure, ni kwata kwata tun bayan saukan mu ba mu yi waya da Yallaɓai ba kuma bai faɗa min zai zo ba, duk da na san zai zo ɗin amma ban ɗauka tare da matarsa za su zo da yara ba sai ganin su Jidda kawai na yi wa ya kawo ku? Wai tare muke da Anty Gimbiya da Abba. Sai ga Khalipa da ita kanta Gimbiyar ɗauke da Anwar kenan shi ya tuko su alhalin ni bai nuna min ma za ta zo ba. Ban nuna mata wani abu ko a fuskata ba muka gaisa. Lokacin ni ban ma yi wanka ba sai daga baya ankon less ɗin da muka yi mu uku muka saka gabaɗayanmu wani marroon da baƙi yi yi mana kyau duk in da muka gifta sai an ce kai leshin nan ya yi kyau. Har cikin gida su Yallaɓai suka shigo Allah ya sanya alheri da shi da Kawu Abba da Tariq sai Musbahu sai Nasir da Muttaka. Sannan a ɗakin samarin gidan su Hauwa suka zauna aka kai musu abinci ni dai ban je ba domin na ga Gimbiya ce ke kai da kawo sai na bar mata amma dai mun je dukkan mu mun gaishe da mazajen namu. "Madam kin fa samu duniya" In ji Yallaɓai ya na kallona ni ko sai na kalle shi ina yi masa fari kafin na ce. "Allah ko! In ma duniyar ce ai kai ka ba ni ita a hannuna Yallaɓai." "Wannan gaskiya ne Uwargidan Alaji Tafida ba." Tariq ya faɗa ya na dariya Kawu kan cewa ya yi." Ba dole ya ba ta duniyar ba. Saboda ita ce ta san shi tun kafin duniyar ta same shi." "Tariq ya su Farida? Sai ban gan ta ba." Na faɗa ina kauda maganar Kawu Abba tun da na ga Gimbiya ta shigo lokacin Yallaɓai sai fama da yara ya ke yi, Khalipa ya manne masa ga Anwar a jikinsa duk sun ƙi bari ma ya ci abinci ni dai ina gefe a raina na ce can ku ƙarata. "Wallahi ba ta samu zuwa ba saboda makarantar yara." Tariq ya ba ni amsa, zan yi magana Munnira ta ja ni muka fita waje ta na min raɗa. "Ke na ga matar nan sai wani rawan kafa ta ke yi ne" Sai na kalleta ban ce komai ba na wuceta ina faɗin" Ta yi ta gama Munnira." Daga haka na koma cikin gida na bar su, can ma aka fara ƙidan ƙwarya muka je can muna chasewa da aka ce filin na yayyen amarya ne, muka shige fili ni da su Hauwa muna ta rawa ana yi mana liƙi sai can da yamma su Jidda suka ce za su tafi Gimbiyar ma ba ta min sallama ba a raina na ce a gayas, to uban gayyar bai min sallama ba ballanta ita. Amarya cikin garin Kano za a kaita a daran aka tafi da ita amma mu ba mu je ba. Tun da muna gari muka ce sai mu sa rana mu je daga baya. Ranar a gidan Marwa muka kwana washegari muka yi shirin dawowa gida. An ba mu kayan biki su cincin da dublan da kayan robobin da aka raba can muka bar Hauwa sai ranar talata za ta dawo. Amma tare muka taho da wasu dangin su kuma za su je gidan Amarya. Ko da na koma gida ba kowa, sai da na buɗe ashe suna can sharaɗa gidan Gimbiya. Yallaɓai bai kirani ba sai ni da kaina da na kira shi na ce na dawo. Shi ne da daddare sai gashi sun taho da yaran har da Khalipa da na ke murnan kwana biyu ya bar ni na huta ashe ba haka ba ne. Ranar ga gajiyan biki hayaniya ta yi yawa a can ba mu wani samun barci, amma yaron nan haka ya hana mu barci a ɗakin su Jidda na kai shi ya kwanta saboda ya fara barci a falo amma sha biyu saura muna kwance a ɗaki muka ji ihun shi dole Yallaɓai ya je ya ɗauko sa ya saka shi a tsakiyarmu kamar wani yaro haka ya tashi cikin dare daga ya ce zai sha ruwa sai ya ce zai ci abinci. Gabaɗaya ya hana ni barci, ni ƴaƴana ba su hana ni barci sai ɗan kishiya. Yaro kamar an haife shi da makirci da kissa a daran Yallaɓai ya tashi ya haɗa masa tea. Ban san yadda aka yi ya cire masa pampers ɗin jikinsa ba, kawai sai farkawa na yi da asuba na ga Khalipa ya kelayamin fitsari a sabuwar katifa ta. Tsabar baƙin ciki ma na kasa mgana. Wallahi ko su Jidda ba su yi zaman yi min fitsari a kan katifa ba domin tun zamanin napkin shi na ke yi musu in zamu kwanta. Kuma ba na bari su sha ruwa daddare ko su sha tea amma saboda iskanshi shi Yallaɓai cikin dare ma ya ke tashi ya na ɗura ma yaro ruwa ba dole ya yi fitsari ba da na ga kalli wajen har sai da ya yi shaida a zanin gado kawai sai na kalli Yallaɓai lokacin ya dawo daga sallar asuba Khalipa na can ɗakin su Jidda. "Yallaɓai cire ma Khalipa pampers ka yi? Ji fa yadda ya yi min fitsarin kwance." Kai tsaye ya ce" E jiya ne ya na ta rigima sai na cire masa sai na ga ma duk ya cika shi da fitsari." Ban sake magana ba sai shi ne ya ɗago ya kalleni kafin ya ce" Ba komai ai fitsarin yaro ne. Ki kuna fanka kawai ni bari na je can ɗakin na ɗan runtsa." Daga haka ya fice ya bar ni ina bin shi da kallon takaici. Sai da na cire zanin gadon sannan na saka ruwa da omo na goge wajen na saki fanka zanin gado kuma na fita waje na jiƙa shi ina ta ɓata rai da sassafe ya sakani wahala, ba fitsarin ne abin haushi ba na ga dai ba jariri ba ne, ba zan hana shi kwana a gidana ba amma ba a ɗakin da na ke kwana da mijina ba har kuma ya kwanta ya yi min fitsari. Shi ya sa ko su Jidda ba su ga fara'ata ba har shima ko da ya fito na haɗe rai na. Amma bai hana nai yi ma Khalipan wanka na sauya masa kaya ba. Ni kuma na je na wanke zanin gadon da ya yi min fitsari na shanya. Duk da Yallaɓai ya siya mana in ji min wanki amma da hannuna na wanke shi tun da guda ɗaya ne. Da Yallaɓai zai fita nan ya bar min shi wai maman shi ba ta nan za ta je asibiti Anwar ne ya kwana ya na ciwon ciiki. Ya fita ya bar ni ina ta aikin a kitchen ina can ina wanke wanke bayan na gama gyara duka ɗakunan na saka turaran wuta. Cartton na kunna ma Khalipa na yi masa jan ido da cewa in ya sake ya tashi sai na yi masa bulala ashe yaron nan bai ji ba ina can ina wanke wanke shi kuma ya samu dispanser ya danna ya yi min ta min ɓarin ruwa har ya gangaro ya jiƙa min cafet ruwa ne cike fa sai da ya yi rabi da shi kamar an ce na leƙa falon na ci karo da mummunan aikin da ya aika ta min Na ko kama shi na yi masa bulala biyar, saboda haushi ko ɗana ne ya yi min ɓarnan nan sai na dake shi sai kawai ya fashe da kuka ko tsayawa bi ta kan shi ban yi ba haka ya ja min aiki sai da na naɗe cafet ɗin nan na fita dashi na shanya. Sannan na koma na sake goge wajen yaro nan neman ya yi ya saka min hauka ranar ina can ina aiki amma ina fargaban abin da zan je na tarar na ƙudira a raina zan yi ma Yallabai magana sai dai duk abin da zai ce ya ce. Ga barcin gajiya a idanuwana amma ban isa na kwanta ba domin in na kwanta na san abin da zan ta shi na tarar shi ya sa bayan na gama aikin jikina da zuciyata na son na kwana na huta amma na kasa, tun da in dai na bar shi na kwanta sai ya jawo min gagurumin aiki shi kuma ga shi ba ya barcin rana ballantana mu kwanta tare. Ba ni na samu na huta ba sai da yamma shima ba barci ba tun da yamma ta yi. Dawowar su Jidda ya sa na shiga ciki na kwanta na dai samun natsuwa kawai. Allah ya sa in da ya yi fitsarin ya bushe sai na shimfiɗa wani sabon zanin gado, saboda gajiya ana sallar isha'i na kwanta tun kafin Yallaɓai ma ya shigo. Na dai haɗa masa abincin sa a dining, ni ban san yadda aka yi ba tun da da wuri na kwanta can cikin barci na ji kuka sannan da muryan Jidda ta na kiran sunan Abba sai na farka a firgice lokacin har Yallaɓai ya farka shima kuma ya kunna hasken ɗakin ma. Waya ta na jawo a gefen gado na duba lokaci ɗaya da rabi na dare. Hankalina ya tashi na ɗauka wani abu ne sai da na ga Yallaɓai ya buɗe ƙofa sai ga Jidda ta ɗauko Khalipa ya na kuka ya na ganin uban ya maƙale masa ya na kuka, shi kuma Yallabai sai ya rumgume shi ya na faɗin. "Shii ga Abba nan shii." "Abba ya tashi ne ya na ta kuka ya na cewa sai an kawo shi wajen ka." "To Jidda je ki kwanta. Sai da safe." "Sai da safe." Ta faɗa kafin ta juya, shi kuma sai ya rufo ƙofar ya ɗauko Khalipa, ina zaune sake da baki ina kallon abin mamaki yau ɗin ma wataƙila kamar kullum ya fara barci ne aka kai shi ɗakin su Jidda shi ne ya na farkawa ya ga bai ga Uban ba shi ne ya saka musu kuka. Na kasa magana ganin Yallaɓai ya kwantar dashi a tsakiyar mu, har ya na lulluɓe shi da bargo. Zuciyata ta ciwo ni yau ko ɗana ne sai na yi maganinsa ballanta ɗan kishiya. Ina iya ƙoƙarina amma yau kam an zo ƙarshe. A fusace na miƙe sanye na ke da doguwar rigar barci hulan kaina ma ta saɓule. Kitson kaina shiko ne har ya ɗan fara ma tsufa tun da ban yi kitson bikin nan na Rano ba. "Me hakan ke nufi Yallaɓai? Na faɗa ina kallon shi, ƙoƙarin kwanciya shima ya ke yi kafin ya ce" Zai kwana tare damu. Me ya sa kike tambaya? "Saboda ban gane ma'anar abin da kake yi min ba." Sai ya kalleni kafin ya ce" Me ye ba ki gane ba? Kwanan Khalipa tare da mu? "E." Na faɗa afusace saboda na fara harzuƙa ma da tambayoyin shi. "Miye a ciki? Ai ba yau aka fara ba ko? Kin san ai Khalipa ba ya iya barci sai tare da ni ko can gidan ne ita kanta Daugther ta san haka." Ya na gama faɗin haka ya koma ya kwanta ya na faɗin" Ki rage mana haske." Sai na ga yaron ya yi shuru Yallaɓai na kwanciya ya wani maƙale shi, baki na saki ina kallon shi, na ma kasa magana amma na ji a raina yau dai sai dai Yallaɓai ya zaɓa ko kwana da ni ko kwana da ɗansa. "Yallaɓai ni ce zan fita na bar maka ɗakin ko kai da ɗanka ne za ku fita ku bar min ɗakina? Na faɗa kai tsaye ina kallon shi, sai ya yi shuru bai motsa ba. Ina ganin haka a fusace na fizgi filo na kuma janye bargon da suka rufu da shi da ƙarfi ina faɗin" Zan bar muku ɗakin." Sai kawai na ga Yallaɓai ya miƙe a fusace ya riƙe bargon da na fizge ya na faɗin. "Sadiya me kike shirin aikatawa haka? "Abin da ka ji ka gani mana " Na bashi amsa a fusace saboda raina tuni ya gama ɓaci. Kawai sai ya fizge bargon ya shimfiɗa ma Khalipa. Yaron ya lumshe ido ban sani ba ko barci ya ke yi, har gabana ya tako ya na kallona kafin ya ce. " Sadiya yaushe kika koma haka? Yaushe kika zama haka? "Yaushe dai ka zama haka dai Haba ba ka yi min adalci. A ina ne aka ce dole sai da yaro zamu riƙa kwana? Ko ƴaƴana ka fi kowa sani suna shekara uku da wani muke raba shimfiɗa da su. Me ya sa shi ba za ku koya masa hakan ba? "Na faɗa miki a can ma haka ya ke. Ba ki ga yaro ba ne? Zuwa gaba zai daina." "To ni ina ruwana da can ma haka ya ke yi, ai can ɗin in ya yi wajen uwarsa ne, haba ni fa na gaji na yi kara na yi kawaicin amma ba ka gane ba. To daga yau ta kau in za ka kwana da ɗan ka, ka sauya ɗaki ko ni na bar maka daƙin gabaɗaya amma ba zan ƙara kwana da Khalipa ba." Har na gama faɗa na ya na kallona. Sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce" Ba sai kin bar mana ɗakin ba, tun da ɗakin ki ne mu za mu fita mu bar miki ɗakin." "Beter." Na amsa masa ina girgiza jikina. "Amma kin ban mamaki, ban taɓa tunanin haka kike ba Sadiya. Ashe gudan jinina ba jinin ki ba ne? Ashe Khalipa ba ɗaya ya ke da Jidda da Baby ba? "Ɗaya suke domin ko su ba ka ga ina kwana a gado ɗaya da su ba." Hannu ya ɗaga min ya na cigaba da faɗin" Sai yanzu na gano ki. Baƙin ciki kike yi a kan yara nan Sadiya ba tun yau ba, sai dai ban saka abin a raina ba saboda ina ƙaryata hakan sai ga shi yau kin tabbatar min.' Ya faɗa ya na kallona sai nima na kalle shi cikin mamakin kalamansa. "Baƙin ciki? Baƙin cikin me? A fusace ya ce" Baƙin ciki Daugther ta na haihuwa ke ba kya yi shi ya sa kike jin haushin su Khalipa ashe duk ƙarya ce da kike faɗin ƴaƴana ƴaƴan ki ne? Ashe duk yaudara ne? Tir wallahi kin ban kunya sannan kin ba ni mamaki " Na ma kasa magana sai nuna kaina na ke yi amma na kasa mgana. "A kan ƙaramin yaro kin kasa ɓoyo kishin ki da baƙim ciki Sadiya. Ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba amma ba zan ce miki komai ba sai na gode." Ya juya zai wuce bakin gadon na sha gaban shi da sauri ina nuna kaina kafin na ce" Ni ce yau ka ke kira ina baƙin ciki da ƴ'ayan ka Yallaɓai? "E baƙin ciki kike yi in ba baƙin ciki ba me kike yi! To ki sani ba ni na ce ki je ki yi planing ya ba ki matsala ba sannan ba Daugther ce ta kai ki ta baro ba, ke kika kai kan ki kika baro saboda haka ki daina zargin kowa sai kanki, haihuwa yanzu Daugther ta fara ƴaƴa kuma ba ki da hurumin tsanar su kuma ba ki da hurumin hana su zama gidan nan domin gidan na uban su ne ba na ki ba " Kafin Yallaɓai ya gama mgana ƙafafuwata sun kasa ɗaukata sai ga ni zuɓe a kasa. An ce kuka rahama ne sai yau na fahinci haka domin na kasa kuka, ina kallon Yallaɓai baki buɗe na ƙasa mgana amma kalamansa na shiga kaina suna kuma min amsa kuwwa! Ni yau Yallabai ke ma gorin haihuwa? Ni yau Yallaɓai ke cewa ni na kai kaina na ɓaro? A gaban idanuwana ina bin shi da kallo ya ɗau Khalipa suka bar min daki. Ni ce yau na zama yar baƙin ciki a wajen Yallaɓai ya kira ni da kowani suna sannan daga karshe ya ce nan ɗin ba gidan ubana ba ne gidan shi ne. Na so na yi kuka amma na kasa zuciyata na ƙuna. Baƙin ciki da takaici sun cika min zuciya anan wajen na haɗe kaina da gwiwa na saki kuka amma ba hawaye ina kuka amma kuma zafin da ke zuciyata sai ƙaruwa ya ke yi, har da ihu na yi na kwanta ina birgima amma ban ji ko ƙwatan abin da na ke ji a ƙasan zuciyata ya ragu ba. Barcin da ban koma ba kenan idanuwana biyu a ka yi asuba yadda zuciyata ta soye haka idanuwana suka soye suma. Ina jin fitan Yallaɓai masallaci da dawowar shi, duk ina zaune na kasa tashi domin sai na ji gabaɗaya jikina ya yi min wani irin nauyi kamar ba nawa ba na kasa tashi ballanta na shiga tiolet na kama ruwa na zo na yi sallah. Ban iya motsawa ba sai shidda saura na safe na iya miƙewa ina jin kaina ya yi min wani irin nauyi, ina riƙe da shi na shiga tiolet na kama ruwa sannan na yo alwala na zo na yi sallar asuba sai bayan da na yi sallar ne ina jan casbaha na ji hawaye na gangaro min saman kumatuna ban san adadin lokacin da na ɗauka ina kuka ba, Allah ya sa na sakaya ƙofar bedroom ɗin na ji Jidda ta zo ta na bugawa lokaci ɗaya da kiran sunana amma na kasa motsi ina zaune kamar status amma kuka na ke yi hawaye na sauka wasu na korar wasu. Ina jin gwara dai na yi kukan kar baƙin ciki ya kashe ni Yusuf Inuwa ba shi da asara. Ni yau Yusuf zai kalla ya kirani yar baƙin ciki kalmar ta fi baƙantamin rai amma lokacin da ya yi min gorin haihuwa sai na ji komai ya tsaya min cak. Lalle na yarda da kalmar nan da hausawa ke yawan faɗin namiji ƙanin Aljali, namiji ba ɗan goyo ba ne ni Sadiya Sulaiman Yashe ni Yusuf Inuwa zai kalla ya ce ina baƙin ciki da y'ayan shi kuma har ya na ce min haihuwa yanzu Gimbiya ta fara wato sai dai na mutu sannan har ya na min gorin gida. Kuka na yi ta yi kukan abubuwa da dama ne, na ji gabaɗaya gidan ya yi min wani irin ƙunci ji na ke yi ko numfashin da na ke shaƙa a gidan ma gurbattace ne. Na daɗe a cikin ɗaki, har wajen goman safe na ji fitan yara zuwa makaranta. Ina zaune a in da na yi salla ina kuka Yallaɓai ya yo wanka ya shigo ya sauya kaya bai ce min ba ni ban ma kalle shi ba amma na san ya ji yadda na ke jan hancina da macijana ya toshe min saboda kuka a haka ya sa kai ya fice shi da ɗansa. Ya jima da fita sannan na miƙe ina jin kamar kaina zai rabe gida biyu ga wani maƙaƙi da ke damuna a maƙoshina. Ko ta kan gidan ban bi ba na faɗa tiolet na yo wanka bayan na fito ko mai ban shafa ba na zura wata doguwar riga ta atamfa ƙaramin akwatina na jawo na fara haɗa kayana. Ban san ina zan je ba amma ji na yi zuciyata na tunkaɗani da tunanin na bar ma Yallaɓai gidan shi tun da ya ce ba gidan Uba ba ne, sannan me ye amfanin zaman nawa? Tun da duk sadaukarwar da na yi ta tsawon shekaru sha takwas da aure na da shi duk ya ta shi a banza to ai ban gama amfanin zama dashi ba. Duk wani abin da zan bukata sai da na haɗa shi a cikin akwatina sannan na ɗauki jakata na saka waya ta da Atm ɗina na duba kuma akwai kuɗi a ciki ya kai 10k. Hijabina dogo na zura na ɗau key din gidan ina jin cikina na jin yunwa amma bakina ya bushe ba na jin zan iya cin wani abu. Sai da na kulle gidan sai kuma ga ni ya bakin gidan ina tunanin to ni yanzu da na fito ina zani? Ɗorayi?. Wata zuciyar ta ce min a'a bai kamata na je gida yanzu ba. Aurena shekaru sha takwas ban taɓa zuwa da wata matsala ba bai kamata yanzu a ganni da ƙaton akwati da kaya ba. In kuma a ka tambaye ni me zan ce? Yallaɓai ya yi min wulaƙanci na dawo gida? Ya ji na yi ko mene ne? Hawayen baƙin cika suka zubo min a saman fuskata. Ba ni da in da zan je. Dangin Mama duk suna gandun albasa kuma bai kamata suma na je musu a wannan yanayin ba, duk in da na yi tunani sai na ji bai kamata na je ba. Har Ya Aina ta kawo min arai amma sai na ji iskar garin ma gabaɗaya ba na so na cigaba da shaƙa gwara na tafi wani waje nesa da in da na baro ko zan ba ma zuciyata damar da za ta samu natsuwar da za ta yi tunanin abin da ya kama ce ta. Sai kawai na sumgumi akwatina na fara tafiya zuwa titi na tari adaidaita na ce ya kai ni tasha. Muna zuwa tasha na ga motoci ana ta lodi na rasa in da za ni. Kawai sai ga wani ɗan union ya zo gabana ya na faɗin. "Kaduna. Kaduna. Kaduna za ki je Hajiya? Sai na bishi da kallo ban san bakina ya furta kaduna zan je ba ni dai kawai na ga an saka kayana a mota nima na shiga na zauna. Har motan ta cika muka ɗau hanya tunanin makomar sunan tafiya ta na ke yi? Ya ji na yi ko kuwa kashe aurena zan yi? Tun aurena da Yusuf yau shekara goma sha takwas. Ina da budurwa ƴa a gabana ban taɓa zuwa gida da sunan yaji ba, ban taɓa jin na gaji da auran Yallaɓai ba sai yau, ban taɓa jin in na yi yaji ban yi abu mara kyau ba, in har a shekarun da muka yi tare da Yusuf bai ji ko sau ɗaya na yi masa alfarma ba to bai kamata ni na yi masa wannan alfarman ba. Tun da muka yi aure ban taɓa kai ƙaran shi gidanmu ko gidan su ba amma yau abin da ya faru ya yi munin da ba zan yi zama a cikin gidansa ina tuna munanan kalamansa akaina ba. In na cigaba da zama baƙin ciki zai iya kashe ni. Mun fara nisa amma tunani kawai na ke yi, gabaɗaya ji na yi zuciyata na tashi, kaina ya yi wani girma ya na sara min. Kawai sai na fiddo wayata da ke cikin jakata kai tsaye lambar Yallaɓai na laluɓo na shiga bangaren tura masa saƙo ba tare da wani tunani ba na yi masa rubutu. "Ina so zan je Kaduna." Wayar na hannuna sama da mintina goma sannan ya dawo min da amsa. "A dawo lafiya." Kenan ya amince na tafi duk in da zan je bai damu ba. saboda ya gaji da ni yanzu ba ya buƙata ta a cikin rayuwarsa. Sai kawai na kashe wayata na mai da ta cikin jaka a kusa da window na zauna sai na jinginar da kaina ina kallon giftawan motoci hawaye masu zafi suna bin kumatuna, sai na saka hijabina a cikin rabin fuskata saboda kar hankalin mutane ya dawo kaina. Amma ni dai na san mun daɗe muna tafiya sannan har muka shiga kaduna kuka na ke yi. A tashar Kaduna na sauka ana ta kiraye kirayen sallar azahar. Ko da na sauka har jiri na ke gani, drop ɗin adaidaita na samu zuwa anguwan Rimi in da gidan Amina ya ke. Allah ya sa ban ɗauko wani kaya ba daga ƙaramin akwati sai ƙaramar jakata. Bayan na sallami mai adaidaita ina jan jikina da na ke ji kamar na faɗi jikina har ya na rawa rawa bakina ya bushe kamar yadda zuciyata ta bushe. Get ɗin na buga megadi ya buɗe ya na tambayana wajen wa na zo sai na ce masa matar gidan, bai sanni ba domin kamar an sauya megadin ne. Kafin ma ya tsaya min wani magana na ce masa ni yayar matar gidan ne ina ga kammani ya gani ya buɗe min ƙofa na shiga ina jan kafa har wani duhu duhu na ke gani. A ƙofar shiga falon na duƙe ina jin amai na taso min bayan na buga mata ƙofa. Amai na ke yi ruwa ruwa tun da bakomai a cikina. Na kasa tashi har na ji an buɗe ƙofar na ji muryan Amina ta na kiran sunana. "Ya Sadiya? "Ke ce? Ɗagowa na yi ina kallonta da idanuwana da suka yi laushi. Hannuna na miƙa mata ta kamani lokaci ɗaya ta na faɗin" Innalillahi Ya Sadiya me ya same ki? Ni dai ban bi ta kanta ba, nan na watsar da jakata da akwatin Amina ta kamani zuwa cikin falonta kan kujera na yi yarf kwance domin sai na ji kamar ruwan jikina ya ƙare da gudu ta koma ta ɗauko jakata sannan ta jawo akwatin zuwa tsakiyar falon. Ni kuma amai ya ƙara taso min sai na tashi ina tangaɗi na yi bedroom ɗin ta da gudu ina jin ta ta biyo bayana ta na faɗin. "Subhanallah Ya Sadiya." Sama sama na ke jin ta sai da na dangana da tiolet ɗin bedroom ɗin sai gani zaune a ƙasan tiolet domin ba zan iya tsayuwa ba, ji na ke yi kamar ba ni da ruwa ba ni da jini, ina amai amma ina ji kamar hanjin cikina za su yo waje, kakari kawai na ke yi ni dai na ji Amina ta buɗe ƙofar tiolet ta na ƙara kiran sunana amma ina kamar a wata duniyan na ke jin ta ,kaina da ya yi min nauyi na jingina da jikin garon Tiolet ɗin ina jin kamar fitsari na bin jikina. Ya illahi fiteari na ke yi a zaune saboda jikina ya yi mugun sakin da ba zan iya motsa koda ɗan yatsa na ba ne. "Innalillahi na shiga uku Ya Sadiya." Na ji ta kamani ta na ƙoƙarin miƙar da ni tsaye amma ina jikina gabaɗaya ya saki. Idanuwana suna lumshewa amma sai da suka gano min jan abu da na ga ya na zirarowa ta ƙasan kafafuwana. Kamar jini na gani. Ba kama ba ne jini ne ke bin ƙafafuwana ba fitsari ba ne. Sai na yi ƙoƙarin tashi ina mai dafe bango Amina na riƙe ni har ta fara murya kamar za ta yi kuka. "Mun shiga uku Ya Sadiya jini kike zubarwa." Na ƙara bin ƙafafuwana da kallo jini ne da gaske har ya gangaro ya ɓata farin tayels ɗin Tiolet ɗin. Ina ƙoƙarin na tsaya da kafafuwana amma na kasa. Kamar an ɗauke ni daga wannan duniyar haka na ji kamar ɗaukewar iska shuu.! Sai na tafi yaraf na faɗa a jikin Amina. Bakina na motsi ina so in yi magana a lokacin sai komai na duniyar ya tsaya mini cak kamar an zare rai daga gangan jikina. *Ƙarshen littafi na biyu.* *ZA MU TAFI HUTUN KWANA BIYU KAFIN MU ƊORA A LITTAFI NA UKU IN SHA ALLAHU. NA GODE DA JIMARIN BIBIYAR WANNAN LABARIN. *16. Jan 2025.* *Janafty* . .