*TKGB30A1* *Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.* Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732 A hankali na riƙa buɗe idanuwana da suka yi mini wani nauyi. Da farin POP da a ka yi rufin ɗakin na fara cin karo, a hankali na juya dama da haunina amma na rasa fahimtar a in da nake, kamar dai ƙaramin ɗaki ne sai da idanuwana suka sake washewa sannan na soma fahimtar in da na tsinci kaina. Da ƙyar na miƙe zaune, ina sake bin ɗakin da kallo in har idanuwana sun ganin min daidai in kuma ba mafarki na ke yi ba tabbas ina asibiti kuma a gadon asibiti. Sakamakon ɓarayin hannun damana da na kalla sai na ga hannuna saƙale da abin ƙarin ruwa da na ɗaga idanuwana sama kuma sai na ga ruwa ake ƙara mini. Ɗis! Ɗis haka na ƙura ma saukan ruwa ta cikin ma zubar sa zuwa cikin jikina idanuwana jikina na bi da kallo sai na ga ba kayan da na baro gida da su ba ne jikina ba. Wata doguwar riga ce a jikina wanda in dai ban yi kuskure ba kayan Amina ne a jikina. "Me ya faru da ni? Na faɗa a sarari saboda na kasa tuna komai. Na kasa tuna lokacin da na tsinci kaina a gadon asibiti. Ɗakin ba kowa sai ni kaɗai kamar irin daƙunan ne na VIP. Kaina na dafe da hannuna na hagu jin ya ɗan saramai ina tunanin lokaci na ƙarshe kafin a hankalina ya gushe. Tabbas a gidan Amina na tuna ina cikin Toilet ɗin ta ina amai daga nan sai na ga jini. E tabbas na ga jini daga nan ne na fita hayyacina ban ƙara sanin in da kaina ya ke ba sai yanzu da na tsinci kaina a gadon asibiti. "Innalillahi." Na faɗa Daidai lokacin da na shafa kasan marata na ji kunzugu. Da gaske ne na yi zubar jini amma me ya kawo mini zubar da jini? Damuwa ce da firgici suka kawo min zuwan period ba tare da lokacin sa ya yi ba. Haka na faɗa ma kaina a cikin zuciyata.  Yanayin lokaci nake so na fahimta amma na kasa ganewa. Sakamakon ɗakin akwai wutar lantarki sannan window ɗin ɗakin ya na nesa da ni. Sai dai duk da haka na ɗan fahimci akwai haske daga waje kenan duk abin da ma ya same ni bai daɗe ba tun da har yanzu dare bai yi ba akwai sauran rana. Na muskuta kenan na gyara zama daidai lokacin aka buɗe ƙofar ɗakin a ka shigo. Na bi wacce ta shigo da kallo Nurse ce domin fararen kaya ne a jikinta wata yar mai ƙiba da ita. "Sannu ya jikin na ki? Ta faɗa bayan ta ƙariso gaban gadon da na ke zaune. "Yauwa. Da sauƙi" Na bata amsa a hankali ita kuma sai ta saka hannu ta dauƙo wani fayel da ke saman ɗan teburin da ke gefen gadona ta buɗe ta na dubawa. "Don Allah wa ya kawo ni nan? Sai da ta kalleni kafin ta cigaba da duba fayel ɗina na ma ɗauka ba ta ji ba ne. "Dr Ibrahim Aliyu." Sai na kalleta amma na kasa mgana saboda na kasa tuna waye na sani mai wannan sunan. "Jiya tare da wata mata suka kawo ki." "Jiya? Na faɗa cikin mamaki har ina waro ido. Ijiye fayel ɗina ta yi lokaci ɗaya ta na cire min ƙarin ruwan da ke hannuna kafin ta cigaba da faɗin. "Yes. Sun kawo ba kya cikin hayyacin ki. Kin farfaɗo amma muka sake mai dake da alluran barci." Kallonta kawai na ke yi na kasa magana. Tun jiya na ke asibiti ban sani ba? Me ya same ni haka? "Na cire miki ki ɗan huta. Zuwa an juma sai a mayar miki da shi" Har ta juya za ta tafi na kasa haƙuri. "Sister don Allah me ya same ni? Sai ta juyo ta na kallona kafin ta kaɗa kai ta na faɗin. "Miscarriage "Miss cra gge." Na maimaita a rarrabe. "Yes. Kin samu ɓarin ciki ne a jiyan." Ta na gama faɗin haka ta juya ta na faɗin" Matar da suka kawo ki jiya ita ta kwana da ke. Ta je gida ta dawo nan ba daɗewa ba." Tana gama faɗin haka ta fice lokaci ɗaya ta na jawo min ƙofar ɗakin har sai da ta ɗan ba ta sauti. "Ɓari? Wani irin ɓari kuma? Domin sai na ji tunani ya tsaya cak na kasa fassaran ma'anar maganar Nurse ɗin. "Daman ana ɓari ba a samu ciki ba? Tambayar da na yi ma kaina a fili kenan kafin na samu amsar ta an sake buɗe ƙofar ɗakin an shigo. Da rinannun idanuwana da suka yi min nauyi da na ɗaga ina kallon mai shigowa. Amina ce a kan gaba sai megidanta biye da ita ɗauke da kwando a hannunsa ita kuma riƙe da ledoji guda biyu suka shigo ɗakin sai da na gan su ne sannan na tuna da sunan da Nurse ta faɗa min. Tabbas mijin Amina ne Dr Ibrahim Aliyu malami ne a jami'ar Kaduna. Da ya ke kuma sai da ya haura arba'in san da ya auri Amina shi ya sa duk wanda ya gan sa zai san ba yaro ƙarami ba ne. "Ya Sadiya kin tashi? Amina ta katse mini tunanina sai na kalleta ta zauna a gefen gadon ta na mai riƙo hannuna mara kanular. "Ya jikin na ki? Jiya kin ba ni tsaro wallahi." Ta faɗa ta na yar dariya lokaci ɗaya ta na kallon mijinta. Kallonta kawai na ke yi na kasa mgana domin sai na ji bakina ya yi min wani irin nauyin da na kasa furta harafi ɗaya daga bakina. "Maman Jidda ya ƙarfin jikin na ki? Sai a lokacin na ji na yi magana bayan na kalle shi. "Da sauƙi Dr. " "Ma sha Allah. Allah ya ƙara lafiya." Na amsa da Amin a saman leɓe na. Ita kuma Amina sai ta miƙe ta nufi kwandon da suka shigo da shi ta na tambayana me zan ci? Dr na gefe ya ce ta fara haɗa min tea ne ya warware min ciki tun da tun jiya ban ci wani abu ba. "Kenan da gaske ne tun jiya na ke asibtin cikin rashin hayyaci? Tambayar da na yi ma kaina kenan ban samu amsarta ba Amina ta haɗo min tea ta kawo min na karɓa hannuna na ɗan rawa sai Amina ta taya ni riƙewa da hannayenta ta na faɗin. "Har yanzu jikin na ta ba ƙarfi." "Kin san daman sai a hankali." Dr ya amsa mata lokaci ɗaya yana duba wayarsa da ke hannunsa. Ina ta taimakamin ina shan tea ɗin da cokali, Dr ba daɗe ba ya ce zai shiga cikin makaranta Amina ta sakar min kofin ganin saura kaɗan ta miƙe domin yi masa rakiya. "Allah ya ƙara lafiya Maman Jidda." "Amin Dr. Na gode da ɗawainiya da ga zuwa baƙun ta na zo muku da hidima." "Haba bakomai. Ai lalura ce Allah ya ƙara afuwa." "Amin" . Na amsa a hankali, sun fice ina mai bin su da kallo kawai sai ina hakaito kaina ni da Yallaɓai. Yanzu itama Amina watan wata rana Dr zai iya nuna mata halin su na Maza ranar da ya yi aure. Wata ƙila shi kuma ba irin Yallaɓai ba ne, wataƙila shi ya san me ake kira hallaci. Duka na shanye tea ɗin domin ina jin jikina fayeu kamar takarda kuma ina jin yunwa kaɗan amma ba da yawa ba sai dai kuma ruwan zafin ya taimaka wajen farfaɗo da bushewar da cikina ya yi tare da maƙogwaro na har da saman labɓana. Ji na yi marata kamar ta ƙulle ina jin fitsari sai na yi ƙoƙarin miƙewa tsaye a hankali, sannan na ijiye kofin saman drewer ɗin gefen gadon da na ke kwance. Sai a lokacin na fahimci ko hijabi ma babu a jikina daga ni sai rigar nan sai ɗankwali Allah ya sa bai saɓule ba tsabar halin da na kr ci na manta da rufe jikina a gaban suruki. To su da suka kawo ni asibiti cikin rai ƙwakwa mutuwa me ye ya yi saura kuma? Da ƙyar na iya taka kafafuwana zuwa tiolet ɗin cikin ɗakin ji na yi kamar in faɗi jikina kamar fallen takarda saboda rashin ƙwarin jiki. Tabbas jini ke zubar min tun da ga shi a jikin pad ɗin da ke jikina. To ko dai maganar Nurse ɗin gaskiya ne na samu ɓari?  Amma abin tambaya anan daman ina da ciki ne? Dawowar Amina ɗakin ne da ta ga ba ta ganni ba sai ta ƙwala min kira shi ya sa na yi tsarki na fito ina faɗin. "Gani nan Amina." Da sauri ta zo ta kamani ganin ina faman da fa bango ta maida ni har saman gado na zauna sannan ta koma gefe na kamar ɗazu ta zauna. "Ya Sadiya jiya kin ba ni tsoro" "Me ya faru? Na kasa tuna komai" Na faɗa ina kallon ta. "Suma fa kika yi a cikin tiolet ga shi kina ta zubar da jini. Na ƙwalla ƙara ina ta ihu ba mai jina. Ƙwatsam sai ga shi Allah ya aiko min da Baban Yunma shi ya taimaka min muka kawo ki asibitin nan, ko da muka zo kin fita hayyacin ki tun jiya sai yau kika farfaɗo " Ina kallonta amma na kasa mgana, sai ta cigaba da faɗin" Jiyan kin farfaɗo da daddare amma sai kika koma bayan sun yi miki alluran barci." "Da gaske ne tun jiya na ke kwance a nan? Amina ta ɗaga min kai kafin ta ce" E nan kika kwana tare da ni da safen nan ne na koma gida na yo abin karyawa sannan na taho miki da wasu kaya." Ta mike ta na nuna min kayan sawan ta da ta zo min da shi ganin pant da pad a cikin kayan ya sa na gasgata zargina. "Me ya same ni? Me ya sa na ke zubar da jini? Sai ta dawo kusa da ni again ta sake zama ta na faɗin" Ya Sadiya ɓari kika yi fa? Ƙura mata ido na yi ba tare da na yi mgana ba sai ta riƙe hannuna guda ɗaya ta na faɗin. " Wallahi Ya Sadiya. Na ce ashe ciki gare ki ban sani ba? "Nima ban san da shi ba Amina." Na faɗa wasu hawaye masu zafin da ban da taruwan su ba suka kece mini. Hawayen baƙin ciki. Hawayen takaici, hawayen nadama da dana sanin da na biye ma Yallaɓai ya yi sanadiyar na rasa wani abu mai muhimmaci da na daɗe ina neman tsawon shekaru goma na cikin rayuwar da ubangiji ya ba ni. "Wallahi Ya Sadiya kin zubar da jini shi ya sa likitan ya ce ki riƙa shan ko cin a baben ƙarin jini." "Wata nawa ne cikin? Na faɗa ina kallonta cikin kuka. Sai a lokacin ita ta farga ma kuka na ke yi da sauri ta dafa kafaɗata lokaci ɗaya ta na faɗin. "Ƙarami ne likitan ya ce sati huɗu bai ma gama cika ba ƙila shi ya sa ma ba ki san da shi ba " Wasu hawayen ne suka ƙara ke ce min ban sani ba. Ban taɓa kawo ma kaina ciki gare ni ba, ko da period ɗina ya tsallake min wata ban yi tunanin haka ba, sanin daman ya na yi min haka sai dai ban saka lissafin da cewa tun da na sha mganin lokacin al'ada ya gyaru ba kawai sai na yi tunanin ya dawo da yi min wasan da ya fara min a baya ne. Ashe ashe ciki ne Allah ya ba ni bayan na fidda rai da yaƙinin zan sake haihuwa. Ban san ina kuka har da shessheƙa ba sai da na ji Amina na bubbuga bayana ta na mai faɗin. "Ki daina kuka Ya Sadiya. In sha Allahu Allah zai kawo wani da gaggawa. Allah kuma ma ya taimaka cikin ya fita duka ba su yi miki ma wankin ciki ba." Amina na kallah itama ni ta ke kallo kawai sai na fashe da kuka mai sauti na kwantar da kaina a saman cinyarta ina kuka ina ma tana lallashina amma har muryanta ta fara rawa. "Ni kaina Ya Sadiya sai da na yi ƙwalla da aka ce ciki ne da ke amma kin samu ɓari. Na ce Allah sarki Ya Sadiya abin da ta daɗe ta na nema ga shi ta samu amma Ubangiji ya yi ikon shi. Ki yi haƙuri za ki samu wani da ikon Allah." Ba wani Ubangiji da ya yi ikon shi. Yallabai ne ya yi sanadiyar da na rasa ɗana gudun jinina. Domin shi ne ya saka ni cikin cikin baƙin cikin da har ya yi sanadiyar ɓarin cikina. Cikin da na shafe tsawon shekaru goma ina fafutukan samun sa sai ga shi ya samu ɗin amma tun kafin na ma san da wanzuwar shi ya bi rariya. Kuka na ke yi da ƙarfi da dukkan zuciya ta. Kukan rasa gudan jinina. Kukan baƙin ciki da wani kullutun abu da ya tokre min a ƙirji na jin wani irin haushin Yallaɓai da ban taɓa jin irin shi ba sai yau. Na yi kuka sosai kukan rasa gudan jinina. Lallashin Amina bai sa zuciya ta ta yi sanyi, sai da na yi kuka sannan na ɗan ji sanyi sanyi amma wannan taɓon da Yallabai ya saka min ba na jin zan iya mantawa. Idanuwana sun yi jajir sun tasa saboda kuka Amina faɗi ta ke yi Allah zai ba ni wani na daina kuka jin ta kawai na ke yo. Ko na samu wani ba shi zai goge taɓon na samu kafin shi kuma ya zuɓe ba, kuma ba shi zai taɓa goge taɓon sanadiyar baƙin ciki Yallabai na rasa abu mafi soyuwa gare ni a karon farko ba. Da ƙyar Amina ta lallasheni na ci abinci fanten doya da hanta na ci na ɗora da maltina sai na ji na fara samun ƙarfin jiki na komawa na yi na kwanta ina kukan zucci sai ga Likita ya shigo duba ni ya yi min tambayoyi na amsa masa cikin raunin zuciya. Ledan ruwa ya sake rubutamin sannan ya umarci Nurse ɗin da suke tare ta mai da ruwan da ya rage da aka cire da safe ya ida sa shiga jikina. "Madam kin samu misscarrge so za mu riƙe ki a nan kwana uku  saboda jikin ki ya samu karfi. Hop za ki bamu haɗin kai ki riƙa cin abinci saboda kina bukatar jini sosai." Sai na gyaɗa masa kai, sai ya jinjina min kai shima kafin ya ce. "Good. Allah ya ƙara lafiya." Daga nan ya fice tare da zugan Nurse ɗin da ke bayan shi takardan da ya rubuta Amina ta karɓa itama ta bi bayan su da cewa bari ta je ta siyo. Ba daɗewa ga shi ta dawo da kwali a hannunta a jikin kwalin ne na ga sunan asibitin GARKUWA HOSPITAL. Amina ta daɗe a tare da ni sannan ta ce min za ta koma gida ta yi girki sannan ta taho min da ruwan zafin da zan yi wanka. "To." Na amsa mata da farko sannan na ce" Ina su Yumna? "Suna makaranta. Jiya da babansu suka kwana da safe ma shi ya yi musu shirin makaranta." Sai na yi mirmishi ban yi mgana ba. Ta haɗa kayan da za ta koma da su sannan ta yi min sallama ta ce sai anjuma za ta dawo. "To sai an juma ɗin." Ta faɗa ta na rike hannuna mara ƙanula. "Sai anjuma." Na faɗa a hankali ina jin kamar barci na son ɗauka ta. Har ta kama hanyar fita sai ta dawo da sauri ta na faɗin. "Laa kin ga na manta ga wayarki " Ta faɗa lokaci ɗaya ta na fiddo wayata daga jakarta ta miƙa min na saka hannuna mai lafiya na karɓa ina juyata cikin mamaki sannan ina kallon Amina. "A cikin jakar ki na gani shi ne na saka miki ita chaji. In kina bukatar wani abu ki kirani shi ya sa na taho miki da ita. Ko in za ki kira Baban su Jidda ki faɗa mai halin da ake ciki." "Ba zan faɗa masa ba." Na bata amsa da sauri sai ta tsaya ta na kallona cikin nazari. "Ba shi ba, har can mutanen gidan kar ki sake ki faɗa ma kowa ko da sun kira ki." "To me ya sa? "Haka nan kawai ai na ji sauƙi ba buƙatar a tashi hankali kowa." Na faɗa ina kallonta. "To ko Yallaɓai ba za ki kira ba? Wannan karon kai na girgiza mata alamun a'a sai ta zakuɗa kafaɗa kafin ta ce shikenan kayan hannunta ta duka ta ɗauka sannan ta yi min sallama ta fice daga ɗakin na bi ta da kallo sai da ta ficen sannan na danna gefen wayar haske ta kawo. 12:30pm na rana ne agogon wayar ya nuna ita Amina ta ɗauka rashin chaji ne ya sa wayar ta mutu ba ta san ni na kashe ta da kaina ba tun jiya ɗin nan ba wanda ya kirani. Wanda na ke tunanin ya kiran kuma ni na san ba zai kira din ba kamar zan sake kashe wayar sai kuma na fasa na bar ta a kunne bayan na tura ta ƙasan filon da na ke kwance. Kamar a jikin ƙarin ruwan an yi min allura barci ban daɗe ba barci ya tafi da ni mai nauyi sosai wanda har ina jin nauyin sa a yadda jikina ya saki gabaɗaya ko ɗan ya tsana na kasa ɗagawa saboda nauyin barcin da ya kwasheni. ***** Kwana huɗu na yi a asibiti sannan a ka sallame ni. Kuma duka abin da a ka kashe na asibitin nan Dr ya biya ga shi asibitin na kuɗi ne amma haka suka yi ta ɗawainiya da ni. Na ji sauƙi kuma na samu ƙarfin jiki amma dai na ɗan yi rama, sannan likita ya yi ta jadaddamin na riƙa cin abincin da zai ƙara min jini, sannan na riƙa cin abinci da ganye da wake sannan na yi ta shan maltina da madara. Sannan suka rubutamin mugungunar da zan rika sha na wanke mara ko da sauran wani jini ko datti sannan na ɗan yi complain ɗin ciwon mara shima sun rubuta min mgani. Kuma a nan asibitin muka siya mganin kafin mu koma gida. Gidan Amina na sake komawa ina ta jin nauyin ma Dr cikin ikon Allah kwana biyu da sallamoni daga asibiti ya tafi Seminar lagos sai na ɗan samu sakewa duk da ni ina ɗakin Amina ne tare da  Yunma ita kuma ta na ɗakin Megidan tare da Sumayya da Yasir. Tafiyar Dr ya sa sai na ɗan saki jikina har ina fitowa falo. Sati ɗaya jini ya ɗauke min na yi wankan tsarki na fara ibada ta,  kuma duk wannan tsawon lokaci Yallaɓai bai neme ni ba nima kuma ban neme sa ba sannan da gayya na bar waya ta a kunne domin na fahimci zurfin yadda na zama mara amfani a rayuwar Yusuf gabaɗaya sai ga shi na gani. Sama da kwana takwas na bar gida bai taɓa kirana dai-dai da rana ɗaya ya ji ya lafiyata ba. Har Musbahu ya kirani domin Mubeena ya tura gidana ta dawo ta ce ba na nan sai da ya kirani ne na ce masa ina kaduna, kai tsaye ya ce ba su maganar da Tafida ba a raina na ce daman ai ba zai yi ba. Ina da kwana goma a Kaduna Munnira ta kira wayata da yamma ta ce ga ta a kofar gidana ta na bugawa kamar ba kowa. "Ina Kaduna Munnira." Ina jin yadda ta maimaita kadunan cikin mamaki kafin ta ce. "Topha. Me ya faru? Aminar ba ta da lafiya ne? "Lafiyanta ƙalau na zo ganinta ne kawai." "Ki ce zumumcin ganin Amina ya motsa. To yara fa? Ko suna Gwamnaja? "Ban sani ba. Gida na bar su tare da babansu." "Wata ƙila suna gidan Gimbiya." Da haka muka bar mganar hira muka ɗan yi sama sama kafin mu yi sallama sai da ta ce yaushe zan dawo? "Ban saka rana ba." "Eyye. Kin ji ki tsaya ki ɗan huta" Ina mata dariya daga nan muka yi sallama.  Ita ta faɗa ma Hauwa ina kaduna sai gashi ta kirani, su har sun damu da ni amma wanda ya ijiye ni na koma ni da banza duk ɗaya a wajensa. Ban taɓa tunanin zan kai tsawon kwanakin ba tare da Yallaɓai ya neme ba amma ganin har na kwarari sati biyu bai kirani ba sai na daina mamakinsa na kuma ɗauka da gasken na gama yi ma Yusuf amfani a rayuwarsa. Duk na yi waya da su Ya Aina amma ban nuna musu ba na gida ba har Ya Balki mun yi magana wasu maƙotan ta na son Hijabai na ce na hannuna sun ƙare sai an sake kawowa. Ban faɗa ma Amina komai ba, itama ba ta dame ni da mgana ba. Amma tabbas a raina na san cewa ta yi shuru ita kanta ta san lafiya lafiya ba zan zo gidan ta na shantake ba. Ashe ma duk ta na lura da motsi na ban sani ba sai ranar da na ke da sati biyu muna zaune a falo ni da su Yunma in na kallon su tuna wa na ke yi da nawa yaran da suka yi min nisa ina cikin kewarsu sai na yi kamar in kira Yallaɓai ba sabo da shi ba sai saboda yarana amma sai na ji na kasa domin wani irin haushin shi na ke ji haushin da ban taɓa ji ba shi ya sa na ke danne komai amma Allah kaɗai ya san damuwar da na ke ciki. Duk dare sai na yi kukan ɓarin cikina kuma sai na ji na ƙara jin haushin Yallabai daga ƙasan zuciyata.   "Ya Sadiya" Amina ta kirani sai na bar kallon yaran da ke wasa a tsakar falon na koma ina kallonta. Tsaye ta ke a gefen kujeran da na ke zaune daman muna tare ne muna hira sai ta tashi ta shiga ciki. "Mu je ɗaki na mu yi mgana." Ban kawo cewa mganar Yusuf ba ne da ba zan yi saurin tashi na bi ta ciki ba Gefen gadonta muka zauna gabaɗaya. "Me ya faru? Na faɗa ina kallonta ganin ta yi shuru ta ƙi mgana. "Ya Sadiya kun samu matsala da Baban su Jidda ne ko? Sai na kalleta kafin na ce" Me kika gani? "Abubuwa da yawa. Ba ya kiran ki ke ma haka. Infact ma ni ban taɓa ganin ya kiran ki ba tun dawowar mu daga asibiti." Sai na yi shuru na kasa mgana saboda ba ni da amsarta a lokacin "Ko bai san kin taho nan ba ne? "Ya sani" Na amsa mata da sauri ina ƙokarin mai da kwallar da suka cika min ƙwarmin idanuwana. "Ya sani fa kika ce? "Ya sani Amina." Wannan karon na faɗa cikin kwarin gwiwa. Sai kuma hawaye suka ke ce min  wasu na korar wasu sai ta ruɗe ta riƙo hannayena ta na faɗin. "Na shiga uku ba dai sakin ki ya yi ba ko? "Bai sake ni ba." Na amsa mata ina kallonta ina ganinta ta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta ce" Alhamdulillah da sauƙi." Sai kuma ta koma ta na kallona kafin ta ce" Me ya faru? Na kasa mgana kawai sai kuka ya kece min, na riƙe hannayena Amina a saman fuskata ina kuka har da shessheƙa. "Amina wai ni Yallaɓai ya kalli idanuwana ya ce ina yi ma baƙin ciki da  Matarsa da ƴaƴansa saboda ban ƙara haihuwa ba." Amina ta ƙwalalo idanuwana ta na kallona. Hannayenta na jinƙe cikin nawa ina jin kamar za ta iya cire min ƙuncin da ke zuciyata in na faɗa mata halin da na ke ciki. "Amina bai tsaya anan ba sai da ya yi min gorin haihuwa. Ya ce ina baƙin ciki da yayansa kuma sai dai na mutu. Sannan ya ce gida gidan shi ba gidan ubana ba ne." "Shi Yallaɓan ya ce miki haka? Amina ta katse ni cikin mamaki da alja'abi na gyaɗa mata ina kuka ina ba ta labarin duk abin da ya faru daga farko har ƙarshe na ƙarishe da faɗin" Amina na taho gidan ki cikin damuwa da kuka. Tsawon kwanaki nan Yallaɓai bai nemi ba? Me ya ke nufi? Hakan da ya yi ba ya nuni da abin da ya faɗa har zuciyarsa ba ne? Amina yau Yallaɓai ya nuna min ba ni da sauran amfani a wajensa Gimbiya ce matar arziƙi uwar yaya maza ita ce mai amfani yanzu a wajen shi da ƴan'uwan shi." Na faɗa ina kuka. Kukan baƙin ciki kukan kishi da kukan nadaman yadda na yarda da Yallaɓai daga ƙarshe ya tozartani na baro gidanshi na zo gidan ƙanwata ina zaune. Me ya fi wannan tozarci da cin zarafi? Amina ma kamar ta yi kuka mamaki ma ya hana ta mgana. "Shi Yallaɓai nan duk ya aika miki haka Ya Sadiya? "Ya wuce wai Amina. Ni yanzu na rasa ya zan yi? In na kashe aurena ina za ni Amina? Shekara sha takwas da aurena jidda ta isa minzali amma ban wuce tozarcin Namiji ba." Sai a yanzu na ke jin sauƙi sauƙi da na ke fada ma Amina damuwata. Amma a kasan raina danƙare ya ke da nadama. Nadamar yadda na yarda da duka kalaman Yusuf Inuwa tun a ranar farko na da fara ganin shi da ace ban bari ya ruɗe ni da kalamansa ba da wata ƙila wannan ranar ba ta zo ba. "Gaskiya ya ba ni mamaki. Ƙiri ƙiri ya yi miki rashin adalci ki yi mgana kuma ya nemi tozarki? Tsskani ga Allah ya dace ya ce da yaro zaku riƙa kwana? Ba ya tunanin in kina buƙatar sa fa? "Shi ba ya buƙatata domin ina tunanin rabo na da Yallaɓai na ƙarshe ranar da na samu cikin da ya zube ne Amina. Sai ya zo gida na har ya koma can wani abu ba ya shiga tsakanina da shi." Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso min. "Bai kyauta ba. Kuma wallahi zai gane kuren shi." Kai kawai na girgiza na kasa mgana saboda in na zauna ina faɗin wani abun ma sai a ce na yi masa sharri ne. "Amina ki yi fatan ki mutu tare da mijinki da ƴaƴan ku. In kuma ƙarin aure na cikin kaddaran shi ki yi ta fatan Allah ya ba ki haƙuri da juriya sannan ya ba ki wuyan ɗauka. Domin kishi na da zafi sannan masifa ne kuma bala'i ne" Amina sai ta yi shuru ta kasa mgana. Ni kuma ina share hawayena na cigaba da faɗin" Domin duk zaman lafiyan da ke tsakanin ki da mijin ki in ya auro ta sai ta shiga tsakanin wannan zaman lafiya. Sannan duk amincin da ke tsakanin ki da shi sai ta zo ta raba shi haka ma duk yardan da ke tsakanin ku wata rana sai ya ce ke ba abin amincewa ba ce. Duk faɗan da za ku yi da mijin ki ke kaɗai ba zai kai girman faɗan da za ku yi  in ya karo aure ba ki sani duk haƙurin ki da kawaicin ki wara rana sai an ƙure ki. Ki sani kishiya ƙalubale mai zaman kanta a gidan aure wanda ba a yi mawa ba ko za a bashi labari ba zai taɓa ganewa ba sai wanda ya tsinci kan shi a yanayin kaɗai zai iya sanin raɗaɗi tare da ƙalubalen." "To in haka ne Allah ya raba mu da kishiya." "In ta alherin ce fa ? "Ko ta alherin ce Allah ya yi mana tsari da ita." Sai Amina ta ba ni dariya sai da na murmusa. Ita manaki ta ke yi a tunanin Yallaɓai ba zai taɓa juya min baya ba na manta namiji mai manta alheri wasu mazan da yawa batulai ne, an yi musu alheri su manta su nemi saka ma mutumin da ya yi musu alheri da sharri. Amina ta ce ita ma ta na goyon baya kar na sake na neme shi har mahadi ko ya bayyana tun da bai san mutumci ba. Maganar da muka yi da Amina sai ya fama min da mikin da ke cikin zuciyata. Ranar sukuku na yini sannan na daɗe ban yi barci ba ina tunanin mafitar da zan nema ma kaina ba zan zauna takaicin wani namiji ya kashe ni ba, in ma bai kashe ni ba ya saka min zuciyan da zan rayuwa sunan mattaciya. Ya zama dole na koyi jajircewa na kuma koyi tsayuwa da ƙafafuwana. Na yi tunanin ba zan cigaba da fakewa a gidan Amina ba in mijin ta ya dawo lamarin zai zama wani iri. Ba kuma zan koma Kano ba saboda duk da in da na je ba za a fars duba masalahata ba. Ni kuma a yanzu na shirya ma Yallaɓai da duk abin da ya ke takama da shi. In koma gida Alhajinmu ba zai zauna ina zauna a gida kuma ya yi shuru ba. Gwara kawai daga nan na wuce Yashe wajen Baaba Aminu na fashe masa da kuka ya na tausayi na tabbata zai fara duba masalahata kafin wani abu ya biyo baya. Haka na tsai da shawara da ni da zuciyata ko Amina ba ta sani ba. Washegarin da muka yi maganar da ita Gwaggo ta kira waya ta har gabana ya faɗi na ɗauka ma ko maganar ba na gida ta je musu ne amma sai na ji ta ce kwana biyu ta ji ni shuru ne ya sa ta kira ni. Ga ma Alhajinmu nan ya na ta cigiya har ta ba ni Alhajin mu ka gaisa ya na min zolayan shi da ya saba na Hajiya Dubu kwana biyu. Sai na yi ƙaryan ba na ɗan jin daɗi ne shi ya sa har muka gama waya ina ɗari dari saboda ba na so su ji wani abu yanzu na fi so komai mai zai faru ya zama na tsakanina da Yallaɓai ne kamar yadda aka saba. A ranar har Marwa ma mun yi waya da ita amma itama ban faɗa mata ba saboda da ta ji Kawu Abba ya ji shi kuma in ya ji zai yi shuru ba faruwan haka sai Yallaɓai ya dauka shi ɗin ya isa ne shi ya sa na kai ƙaran shi wajen abokinsa kuma ɗan'uwan shim shi ya sa ban bari ma ta fahimci wani abu ba. Ranar da na ke da kwana ashirin  a gidan Amina da daddare Gimbiya ta kira wayata. Har sau biyu ban ɗauka ba saboda ban san me ya haɗa ni da ita da za ta kirani ba sai da na ga kiran ya ƙi ƙarewa sannan na ɗaga kiran amma maimakon na ji muryanta sai na ji muryan Jidda. "Jidda." Na faɗa ina mai tashi zaune saboda mamakin jin muryan ta ban za ta ba. "Na'am Umma mun yi kewar ki yaushe za ki dawo? Ta faɗa cikin sanyin ta a koda yaushe. " Ina nan dawowa Jidda. Kuna lafiya? Ina Baby? "Ta na can falo ita da Abba da Anty Gimbiya." Wani abu ya tsaya min a ƙasan maƙoshi da ƙyar na ce" Wa ya ba ki waya? "Ɗauka na yi Umma ba ta sani ba. Ina ta tambayan Abba yaushe za ki dawo ya ce kin je Kaduna gidan Umma Amina." Ashe dai bai manta da in da na je ba. Lallashin Jidda na yi da cewa zan dawo kwanan nan, na ce ta gaishe min da Baby ina nan dawowa muna magana wayar sai na fara hawaye a ƙasan zuciyata ina ta tsine ma Yallaɓai domin shi ne ya yi sanadiyar da na yi nesa da ƴaƴana. A ƙasan raina ina jin daɗi in na tuna yau ni na samu ciki duk da ya zube amma dai na samu sassaucin cewa wataƙila mahaifata za ta iya ɗaukan ciki ba shike nan ba kamar yadda na ke tunani a baya. Ke nan gidan Gimbiya ya tarkata yaran ya kai mata? Oh itama ta ji in da daɗi godiyar ta ma ɗaya daga Jidda har Baby ba yara ba ne ban da girki ba ɗawainiyar da za ta yi musu girkin ma Jidda ta iya makaranta ne kaɗai cikas ɗin ta. Da safe na tashi fuska a kumbure. Sai kuma Amina ta ke faɗa min Dr gobe zai dawo sai hankalina ya tashi. "Amina zan zo na tafi ba zan bari Dr ya dawo ya same ni ba." "Me ya sa? "Da kunya Amina. To zaman me na ke yi a gidan sama da sati biyu? Itama sai ta yi shuru domin ta hasaso abin da ni na na hasaso. "Abin kunya ne fa Amina. Ke ƙanwata ba yayata ba." "To Ya Sadiya ba sai na faɗa masa matsala kuka samu da Baban Jidda ba? Hararanta na yi kafin na ce" Ban saka ki ba. Ba ki da hankali yarinyar nan." Ina tunanin wucewa Yashe ya kamani gwara na fara shiri yau na wuce. "To ina za ki je? Ko gida za ki koma? "Ba zan koma ba Amina. Zan dai nemi wani wajen na je kawai" "Ina to za ki je? Sai na kalleta amma ban yi mgana ba na wuce cikin ɗaki sai ta biyo bayana ta na na cin sai na fada mata in da zan je. " Ke ki ƙyale ni " Na faɗa ina jawo akwatina sai ta riƙe ta na faɗin" Don Allah ya Sadiya ki zauna Allah ba na son ki tafi." Ta faɗa cikin shagwaɓa sai ta warce shi daga hannunta ina faɗin. " Na ki wasa ne yarinya" "Abuja za ki je? Sai na kalleta shuru ina wani nazari ni ban kawo gidan Ya Auwal a raina ba saboda in dai na je sai ya ji ba a si ba kuma zai kira Yallaɓai. Dama dai Ya Hamza ne shi ne ɗan goya min baya amma shima ba zan je gidan shi ba saboda shima zai iya kiran Yallaɓai ni kuma ba na so ya ji a ran shi na damu da shi ne shi ya sa na je na kai karan shi yadda ya zaɓa nima haka na zaɓar ma kaina. "A'a ba zan je can ba." Amina sai ta kasa mgana, ni kuma na fara haɗa kayana kenan wayata da ke gefen gado ta fara kuka alamun ana kira Amina ta fi kusa da wayar ba tare da na kalleta ba na ce. "Wa ye ke kira hala? "Yallaɓai na." Amina ta faɗa a hankali da sauri na kalleta cikin mamaki a kallo nawa ganin haka yasa sai ta miƙa min wayar na karɓa cikin san yin jiki. A hannuna wayar ta yanke kuma ba daɗewa ya sake kira. Sai da ya yi min kira biyae bi da bi ban ɗauka ba sannab shuɗewar mintina huɗu tsakani saƙon shi ya shigo. "Yaushe za ki dawo ne? Yara sun damu da tambarki."   Yara ne suka damu ba shi ba, to tun da shi da ya ijiye ni bai dami ba shike nan yara kuma shi ne uban su tsaki na yi na dankwar da wayar gefe na cigaba da haɗa kayana Amina ta ɗau wayar ta na dubawa kafin ta ce. "Ka ji wani kutumar uba wai yara sun damu? Shi ne fa ya damu ya rasa abin da zai ce shi ne ya fake da yara." "Mtsewww.!" Muka ja wani dogon tsaki a tare ni da ita sannan muka kalli juna muka yi dariya. *Janafty**TKGB30B2* *Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.* Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732 Itama Amina sai ta samu gefen gadon da nake zaune ta zauna lokaci ɗaya tana saka hannu ta na taya ni nin ke kayan da na zube kan gado muna kuma sakawa a cikin ƙaramar akwatina. Allah ya sa ma sauran kayan Amina ta haɗa cikin wankin su mai wankin su ya zo ya karɓa an wanke su tas an kuma goge. Waɗanan da muke ninkewa zannuwa na sakawa a gida ne sai rigunan barci da wanduna sai unders su ne jiya da na samu sauƙin jiki na wanke su da kaina Amina ma ta yi ta yi na bari ta wanke mini na ce ta bar su zan iya yi da kaina. "Ina za ki je daga nan Ya Sadiya? Amina ta ƙara tambaya na ni kuma sai na yi mata shuru har muka gama ninke kayan gabaɗaya na ja akwatin na rufe daman sauran kayan na ciki na ja ta can gefen wardrope in da take a jingine sannan na koma in da na tashi na sake zama. "Na ƙi ba zan faɗa miki ba." "Don Allah fa na ce." Ta sake marairaicewa kamar wata ƙaramar yarinya. "To Yashe zan wuce." Sai ta ƙwalalo ido ta na kallona kafin ta ce"Yashe fa Ya Sadiya? Sai na gyaɗa mata kai kafin na ce" To ina zan je in ba can ba? Sai Amina ta gyara zama har da matsowa kusa da ni ta na faɗin" in ba ki shawara Ya Sadiya? Ina kallonta sai na gyaɗa mata kai kafin na ce" Me zai hana? Ina sauraran ki." Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Gaskiya in dai za ki ji shawarata kar ki je ko'ina. In dai ba za ki zauna  anan ba sannan ba za ki je Abuja gidan Ya Auwal ba, ko gidan Ya Hamza ba to shawarata ita ce da dai ki je wani wajen gwara ki koma gida kawai Ya Sadiya." Ta gama faɗa har tana ɗaga mini hannu ni kuma daman kallonta nake yi kafin na daƙuna fuska ina faɗin. "Wani gidan kenan? "Gidan auran ki mana Ya Sadiya." Wata uwar harara na jefa mata kafin na yi ƙaramin tsaki ina faɗin" Ai ni da ke  na faɗa miki megidan har gorin gidan ya yi mini ko? "To ai bai kore ki ba Ya Sadiya ɓacin rai ne." "Oh kina nufin na koma duk cin kashin da ya yi mini ya tafi a banza kenan ko? Da sauri ta ce" Ni ban ce ki ƙyale shi ya tafi a banza ba." "To me kike nufi Amina? Na faɗa a ƙufule. "Ba ki ba ni dama na gama maganata ba ne shi ya sa." "In jin ki." Na faɗa a tsume har ina kauda kaina domin ita kanta Aminar sai na ji ta fara ba ni haushi so ta ke yi ni ta kwaye min baya ta goyo bayan Yallaɓai? "Nufina yanzu duk in da za ki je Ya Sadiya wani ƙarin tonon asiri ne. Abin da ba ki taɓa yi ba kar ma ki fara. Har gwara ma ki koma gida wajen Gwaggo da ki je Yashe can fa ƙauye ne in wani ya yi shuru wallahi wani ba zai yi shuru ba. Gwara ki koma gidan ki amma shi ma Yallaɓai ki gasa mai aya a hannu yadda zai fahimci shayi ruwa ne madara ake saka masa ya yi kauri." Ta gama faɗa ta na kallona ganin na ƙi mgana kuma na ƙi sakin fuska sai ta marairaice ta na sake faɗin" Ko ba haka ba? Ki duba magana ta da idon basira Ya Sadiya." Yadda ta ce idon basira ne ya sa sai da na yi dariya, itama sai ta hau dariyan Kafin na jinjina kai ina fadin" Haka ne kin yi gaskiya." "Yauwa Ya Sadiya ki koma ko saboda su Jidda." Sai na jinjina kai a karo na biyu kafin na ce" To shi ke nan zan koma Amina." Sai ta murmusa kafin ta rumgumoni tana faɗin" Ko ke fa My Ya Sadiya." Mirmishi kawai na yi ba tare da na yi mgana ba. Duk in da ɗan uwa ya ke daɗi gare shi ni kaina sai na ji kamar kar na tafi, sai dai kuma gaskiya ta faɗa minj duk in da zan je yanzu kamar na soka wuƙa a cinyata ne na yi kururuwa na yi kirari gwara na koma amma ni da Yallabai zaman yan marina za mu yi tsakanin ni da shi. Falo na kuma wajen yara Amina na kitchen ta na girkin Yamma. Yasir ne da Sumayya a gidan Afra ta tafi islamiya daga baya barin su na yi a falon na shiga kitchen wajen Amina ina ta ya ta aiki jefi jefi muna hira har muka gangaro kan mganar Ma'u. "Wai Ma'u shuru kamar ba ta nan" "Ta na nan, ai tun da aka yi wannan turken ni da ita sai ta shafa mini lafiya." Amina ta ƙyalƙyace da dariya ta na faɗin" Ni kaina sai mu daɗe ba mu yi waya ba, ko a group na gida ta daina mgana kamar baya." "Ni kaina na ga ta yi sanyi kamar ba ita ba." Na faɗa ina yanka albasa. "Rabon da mu yi waya tun lokacin da ta kirani ta na faɗa  mini auren shema'u na ce mata ba zan samu zuwa ba." "Ni dai bayan nan mun ɗan hadu a ɗorayi " Na ba ma Amina amsa, an yi bikin Shema'u ko wata biyar ba a yi ba ta yi aure a gombe. Wani tsohon chairman ta aura matansa huɗu ɗaya ce ta rasu ya cike da ita dukkan mu mun je bikin amma ba mu je can Gombe ba Ma'un ce ta je su Shema an gama yawon duniya an gaji dai an yi aure can kwanaki da na je gida Gwaggo ke faɗa mini ta zo ganin gida har ta shigo gaishe su har ta ba ma Alhaji dubu biyar a raina na ce su shema an samu duniya kenan. Mun cigaba da hiran Ma'u ni da Amina har muka gangaro kan Anty Bahijja nan na ke ba ta labarin irin sunayen da suke kiran Gimbiya da cewa ita ce mai ƙashin arziƙi. "Allah na tuba Amina ai ni da arziƙina Yusuf ya aure ni. In ma tsiyar ne sai dai in shi ne ya goga mini" Me Amina za ta yi in ba dariya ba har ta na rike ciki na kusa buga mata ƙasan wuƙan hannuna ina faɗin" Ban son iskanci fa Amina" "To ke ce Ya Sadiya da wata magana." "Allah kuwa. To har ni za a yi ma gorin ƙashin arziƙi." Ni da ita muna ta dariya cikin annushuwa da hira muka gama girkin nan ana ta kiran sallar mangariba ni da ita muka je muka yi salla, Afra ta dawo ta isko ni daki tana mini hira akwai surutu kamar Baby ce daman kuma tsaran juna ne. Bayan sallar isha'i muna falo muna cin abinci Yallaɓai na ta kiran wayata bai haƙura ba. "Ya Sadiya ki ɗauka ki faɗa masa gobe za ki dawo" "Wallahi ba zan ɗauka ba." Na faɗa ina hararanta sai ta sunne kai tana yar dariya. Kira uku ya yi mini bayan na ɗazu da na shiga sallar asuba na ga huɗu, ni kuma na ce wallahi ba zan taɓa daga kiran shi ba sai yau? Sai yau ne ya tuna da ni matarsa ce? Sai yau? Ai ya makara wataƙila da ya kira kafin yau ɗin da wata ƙila na saurare shi. Mun gama cin abinci mun dawo falo Amina ta kunna mana kallo ni ba na ma kallon hankalina na wajen Afra ina koya mata aikin makarantan da a ka ba su a english Yasir da sumyyah na ta wasannin su a tsakiyar falon Na ji ana kiran wayar Amina amma ban dai bi ta kai ba sai da na ji tana faɗin" Ya Hamza ke kirana." Ban kawo komai a raina ba na ce" To ki ɗaga mana." Na ji ta ɗauka da sallama suna gaisawa daga nan sai na ji tana faɗin" Ya Sadiya wai? E ga ta nan ina ga wayar tana ɗaki ne shi ya sa ba ta ga kiran ba." Sai na dawo da hankalina kanta har ina miƙewa. A ina Ya Hamza ya san ina gidan Amina.? "Ga Ya Sadiyar" Na ji Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na ta isowa in da nake ta miƙa mini wayar na karɓa ina mata inkiya da ido a ina ya san inan nan?  Sai ta rika min nuni na yi mgana Ya Hamza na jin mu. "Salamu Alaikum Ya Hamza." "Sadiya kina lafiya? Ya faɗa daga bangarensa. "Lafiya lau. Ya su Anty Khaleesat da yara? "Duk suna nan lafiya." Shuru na wani lokaci na kasa mgana amma gaba na ya faɗi ina tunanin a ina ya san ba na gida ina kaduna ko dai Yallaɓai ne ya kai masa ƙarana? Dam! Na ji ƙirjina ya amsa ban samu sararin mgana ba na ji Ya Hamza na faɗin "Ashe kina kaduna? Ina shirin na amsa masa sai kawai ya cigaba da faɗin. "Ke haka ake yi ehe da ga zuwa ziyara sai ki shantake a gidan ƙanwarki sama da kwana goma ba ki da ranar ƙomawa gidan mijin ki? Mamaki ma ya hana ni mgana. Mamakin Yallaɓai da zai tashi wasa da ni. "Dama daman gobe nake shirin komawa." "To ya dai kamata. Shi ya kirani yanzu yana faɗa mini ba ki a gida sama da sati ya na ta kuma kiran wayarki ba ki ɗauka ba." "Wayar ta na silent ne ban ji kiran na shi ba." Na samu kaina da furtawa. "To sai ki kira shi yanzu ku yi magana. Sannan gobe ki koma gidan ki Sadiya. Shi kan shi Dr sai ya ga rashin hankalin mu gandan gandan dake, ke ba suna kika zo ba sannan ba biki ba daga kun ɗan samu matsala da miji sai ki kama hanya ki tafi gidan ƙanwarki? In ma yajin za ki yi kuma tun da ba ki je ɗorayi ba me ya hana ba ki taho gidana ko gidan Auwal ba? "Ka yi haƙuri Ya Hamza." "Ba maganar haƙuri ba ne. Ba a haka kin ji ko? Amina ƙanwarki ce bai kamata ki je gidan ta in wani abu ya faru ba. Mu ya kamata ki fara nema." "To Ya Hamza." Na furta ina ƙokarin mai da ƙwalla da suka cika mini ƙwarmin idanuwana. "Ki yi haƙuri ki koma giden ki ki rumgumi mijin ki da ƴaƴanki. Ya faɗa mini da kan shi ranshi ne ya ɓaci ya ɗan faɗa miki wasu mganganu ma su zafi sai kika ji haushi kika ce za ki taho kaduna. Ya ce ya bar ki taho ne saboda ke da shi ku samu zukatan ku su huta sai kuma ya ga kin shantake kin ƙi dawowa yana ta kiran wayarki kuma ba ki ɗauka ba." Shuru na yi domin kalaman bakina sun gama ƙarewa. Yallaɓai ya shirya wasan ƙwaikwayon shi ya nemi yan wasa kuma har an yi wasa an tashi karshe dai shi ke da nasara akaina bayan tarin tozarcin da ya yi mini "Ki yi haƙuri kin ji ko? Haba Sadiya da girman ki ai yaji bai kamace ki ba, ki yi hakuri ki koma gidan ki, ke yanzu uwa ce sai dai ma ki yi ma wasu faɗa." "To Ya Hamza in sha Allahu gobe da safe zan koma." "Yauwa. To mu kwana lafiya amma ki kira shi yanzu." Da haka muka yi sallama da shi muna gama wayar Amina ta zauna gefena tana faɗin" Wai me Babansu Jidda ya kira Ya Hamza ya faɗa ma sa? Na ji ya na miki faɗa ne? Sai na kalleta, lokaci ɗaya hawayen da na ke ta riƙewa suka kece mini amma sai na yi saurin saka hannu na goge hawayen ina faɗin. "Ya kira shi ya faɗa mai mun ɗan samu sabani ranshi ya ɓaci ya ɗan faɗa mini mganganu ni kuma sai na ji haushi na ce zan taho Kaduna a cewarsa ya bar ni na taho saboda ni da shi mu samu zuciyarmu ta yi sanyi amma sai ya ga na daɗe ban dawo ba kuma yana ta kirana a waya ban ɗauka ba" "Lalle ne ma. " Amina ta faɗa ta na riƙe haba kafin ta cigaba da faɗin" Yallaɓan nan na ki ya Saduiya sai ke" Ta faɗa tana dariya na kalleta amma ban yi mgana ba. Na fahimci manufarsa ya yi saurin kiran Ya Hamza ne ya faɗa masa saboda ni ya rigani wanda ko daga baya na faɗi wata mgana ba za a goya mink baya. Yallabai ya san ni sarai kamar yadda na san shi ciki da bai. Ya san ba zan taɓa zuwa na kai ƙaran shi ba ya kuma san ba zan taɓa fasa mganar faɗan mu ba amma ya san ina da kafiya zan iya ƙin dawowa a lokacin da ya so ya kuma san in ba Ya Hamza ko Ya Auwal ba, ba wanda zai matsa mini na koma shi ya sa sai ya yi saurin kiran Ya Hamza. Ya san da gangam na ƙi ɗaga wayarsa ya kuma sha jinin jikinsa ko kunya ne zencen ban sanin masa ba. Sai yanzu ne ya tuna da ina da amfani a rayuwarsa? Wallahi tallahi sai ya raina kansa kuma bashin gorin da ya yi mini na gida da na haihuwa watan tara na zai biya su. Sannan ya yi sanadiyar na rasa gudan jinina bana jin ko da na yafe masa laifinsa to ba na jin zan iya yafe masa wannan kasadar da ya ja mini na rasa wani abu mai muhimmaci a rayuwata. Zan koma ba domin Ya Hamza ya yi min mgana ba sai domin ina da niyyar komawar. Amma kuma kiɗa ya sauya dole rawa shima ya sauya. Na daɗe ban yi barci ba ina tunanin mafitan da zan nema ma kaina in na koma gida. Na yi tunanin zan koma makaranta na yi masters ɗina sannan zan inganta sana'ata ta hijabai har ma da ƙarin wani sana'o'in na daina dogara da Yallaɓai na kuma daina dogara da duk abin da ya ke takaman ya mallaka. Daga ni sai ƴaƴana domin nan duniya su ne kaɗai na aminta da ɗari bisa ɗari ba za su taɓa juya min baya ba. Da safiyar talata na yi shirin komawa Kano. Tare muka fita da Amina za ta je saloon ita da Yasir ne Afra da Sumaiyya na makaranta Amina sai sha'awata take ba ni ta iya driving ba in da ba ta zuwa a garin Kaduna da yar motar ta da Dr ya siya mata. Ni ma a raina na kudiri niyyar zan dukufa da sana'a har nima na mallaki mota ta kaina da gumina. Ita ta kai ni tasha na samu mota sannan muka yi sallama sai da motar ta tashi na bar ta a tasha. Kuma har kuɗin motar ita ta biya mini da cewa Dr ne ya ce ta ba ni na ƙara riƙewa a hannuna. Mun rabu ina ɗaga mata hanmu tana ɗaga mini nima. Motar mu ta tashi goma saura ba mu isa Kano ba sai biyu na rana. Daga tasha na hau adaidaita zuwa gidana. Ba kowa a gidan sai da na saka makulli na buɗe gidan na shiga ko'ina ya yi ƙura. Na shiga cikin bedroom ɗina na ijiye akwatin hannuna da jaka sannan na zare mayafi na shiga tiolet na kama ruwa na yo alwala na taho na yi salla ina idarwa na tashi na shiga kitchen, shima dai duk ya yi ƙura amma dai ba a yi amfani da komai ba. Gas na kunna na dafa ruwan zafi na sha tea, sai ƙwai da na soya guda uku bayan na gama na koma ɗaki na ɗauko wayata kamar in kira shi sai na fasa. Domin ban bi umarnin Ya Hamza, jiya ban neme shi ba shima bai sake nema ba ina da tabbacin wata ƙila ya sake kiran Ya Hamzan ne shi kuma ya faɗa masa na ce yau zan koma gida. Ganin ba zan iya kiran shi ba sai kawai na tura masa saƙo. "Na dawo gida." Ina gama tura masa sai na kira wayar Salisu direba bayan mun gaisa na ce masa yau in ya dauko su Jidda ya kawo mini su gida na dawo. Yana ta min sannu da zuwa na gama waya dashi kenan Balaraba ta kira ni ta na faɗa mini  Saude ta sauka duk sai na ji ɓacin raina ya tafi ina mata barka ta samu megida tun da namiji ta haifa. A Lokacin na kira wayar sai mijinta ya ɗauka ya ce ta na wankan da yake ba a asibiti ta haihu ba a gida ne amma sun kira anguwan zoma. Mun rabu a kan cewa in ta fito zai faɗa mata za ta kirani. Sai ko gashi ta na fitowa ta kira ni muka yi magana abin hamdalar shi ne ta haihu lafiya ba wata matsala na yi mata mganar za ta dawo gida ne ko anan za ta zauna sai ta ce min ita ba ta sani ba, ni ko kai tsaye na ce mata gwara dai ta dawo gida a kula da ita ko bayan suna ne sai ta ce mini za ta yi magana da megidanta na ce ya kamata. Na ɗan kwanta sai la'asar sannan na tashi na yi salla sannan na fara gyaran gidan na share ko'ina na goge na saka turaren wuta gidan ya fara ƙamshi duk da na gaji ban zauna ba na fara tunanin abin da zan dafa na duba friza na sai na ci karo da miyar da na yi ana gobe tafiyata tana nan ba ta yi komai ba kuma ina da sauran kayan miya da kayan lambu sai dai duk sun bushe sai na kwashe su kawai na zubar har da ma su kankana suma duk ƙanƙara ya sa sun yi wani nakwa nakwa saboda daɗewa sai kawai duk na kwashe na zubar a bola na goge firizan. Miyan na sake gyarawa na dafa mana farar shinkafa na gama shidda saura na yamma na goge kitchen ɗin sannan na je na yi wanka na fito kenan ina saka kaya na ji ana buga get a raina na ce to yan makaranta sun dawo. Wani riga da wando na saka pakistan ne rigar ja ne da baƙi ba ta da hannu sai daga kasa an ɗan zoɓa ta, sai wando sakakke ne bai kama min jiki ba sai na saka hula baƙa mai kwalliya ta sama, kaina akwai kitso a can Kaduna Amina ta yi min shi duk da ba ta wani iya kitson ba amma na gaji da kan ya tsufa sai na tsife na ce ta yi min ko kalaba ne shi ne ta zarga min shi haka, kuma gashi ba ta kama shi da kyau ba duk ya fara sukurkucewa har kunya na ke ji na buɗe kan a gaban mutane. Silafas ɗin cikin gida na saka sannan na saka mayafi na fita zuwa haraban gidan na buɗe ma yara ƙofa suna ganina har Jidda sai da suka faɗa jikina suna min oyoyo na tarbe su cikin farinciki. Da gaske na yi kewar su sosai musamman ma surutun Baby. Salisu bai tafi ba daman in ya kawo su sai ya tabbatar da an buɗe gida sun shiga ya ke tafiya mun gaisa da shi ya yi min barka da dawowa ni kuma na ce ya gaida iyalan na shi, na rufe gida muka dawo cikin gida ni da ƴaƴana. "Baby ciwo kika yi? Na ga kin rame ne? Na faɗa ina tattaɓa wuyan ta lokacin da muka dawo cikin gida. "Ta yi zazzaɓi na kwana biyu a gidan Anty Gimbiya." Jidda ta ba ni amsa sai na zauna saman kujera na jawo Baby ta zauna saman cinyata ina shafa fuskarta na ke faɗin. "Ayya sorry My princess Umma ta tafi ta bar ki ko? Sai Baby ta fara tura baki tana faɗin" Umma ni dai kar ki ƙara tafiya ba ki tafi da ni ba ina ta kuka Abba sai ya yi ta cewa za ki dawo ba ki dawo ba sai da aka daɗe." Dariya na yi ina mai rumgumeta kafin na ce" Ba zan ƙara tafiya na bar My princess ba in sha Allahu " Jin haka ya sa ta fara tsallen murna ita dai Jidda na zaune ta na mirmishi. Ranar ni na ta ya Baby cire kayan makaranta ta saka na gida Jidda ma ta sauya ta fito na zubo mana abinci a filet muka ci tare. Na sha labarai wajen Baby duk abin da ya faru da ba na nan sai da ta faɗa mini Jidda na gefe ta na cin abincinta tak ba ta ce ba, ashe ranar da na tafi ranar daga makaranta ya ce salisu ya kai su sharaɗa ba su ma kwana a gidan ba kenan. Bayan mun gama Jidda ta tattara komai ta kai kitchen ta kuma share in da muka ɓata. An kira mangariba muka yi alwala muka yi salla a falo, muka yi azkar sannan na ce mun dade ba mu yi karatun Qur'ani su ɗauko mu yi karatu.  Ba mu muka tsagaita da karatun ba sai da a ka kira sallar isha'i sannan muka dakata muka yi salla, muna idarwa na ce su yi aikin makaranta ni kuma sai na shiga ciki na ɗauki wayata ina dubawa sai na ga Yallaɓai ya yi min saƙo. "Ya yi kyau." Abin da ya ce kenan a saƙon na shi ƙaramin tsaki na ja na danna delete saƙon ya goge daga wayata. Data na kunna ina ganin saƙonni nata shigo mini ma su tambaya hijabai ne daga yan makarantar mu ta BUK daman suna siya tun da duk na yi musu tallah. Na amsa na yi ta ba su da cewa cikin satin nan za a kawo tun da ina Kaduna ma mun yi mgana da mai ɗinkin Hijaban lissafi kawai za mu yi na tura masa kuɗin shi, sannan na fara tunanin yadda zan in ganta kasuwancina  shi ya sa a I.G na yi ta following ɗin masu ƙananun kasuwanci domin na ga yadda suke marketing ɗin kayan su sai na fahimci ina bukatar suna da ledan da zan rika saka ma kowa hijabin shi in ya siya shima duk inganta kasuwanci ne, sannan ina bukatar ɗinka hijaban in diffirent styles ma'ana kowani yanayin ɗinki ya kasance ana samu bambamci sosai da ganin abu unique a hijaban da na ke siyarwa sannan akwai bukatar na ƙara da wani abu. Ni kaɗai na zauna ina ta tunanin da me zan kara? Na fi son abin da ni kaɗai na ke siyarwa ba ko ba ma ni kaɗai ba to ya kasance bai yi yawa ba. Lamarin ya kai har littafi da biro na ɗauko na fara rubutu har takalma na saka da atamfofi amma sai na ji hankalina bai kwanta da su ba sai kawai na saka under wears irin su pant, bra, sikat gajerun wanduna da dogaye tare da sleeping drees sai na ji na fi karkata anan sai na fara tunanin sunan da zan saka a jikin logon kasuwancina daga jarshe da na ga na matsa ma kaina da yawa sai na ijiye zuwa da safe amma waya na hannuna ina ta shige-shige ina ganin sunayen da mata ke sanya ma kasuwancin su very interesting. Ina cikin shige- shige na sai ga kiran Surayya Dee Bojuwa herbel, da na ga kiran ta sai da na ji kunya na daɗe ban nema ta ba daman ina shirin neman ta ne muka samu matsala da Yallaɓai.  Ta ce kwana biyu ba ta ji motsina ba  shi ya sa ta kira ta ji ko lafiya Ina dariya na ce" Lafiya ƙalau wallahi kwanaki can ne na kwanta asibiti da yake na samu ɓari." "Subhanallahi Sannu. Allah ya kawo wani mai albarka." Na amsa mata da Amin sai ta fara min mganar tun da na yi ɓari ai ya kamata na yi gyara sai na ce mata zan yi in sha Allahu amma ba ni da kuɗi a hannu in na samu zan yi mata mgana. "Haba Matar injiniya. Ni dake ai ba haka tsakanin mu kawai ki yi lissafin abin da kike so mai delivery da safe sai ya kawo miki" Sai na kasa ce mata komai tabbas mun saba ko ba ni da kuɗi a hannu ta na ba ni kaya in na samu sai na tura mata. In na ce zan yi mata wani bayani ba za ta taɓa ganewa ba sai kawai na ce zan tura mata whatsApp abubuwan da nake so da haka muka yi sallama. Sai na yi zuru ina tunani to gyaran me zan yi? Na gyara ma wanda ya gaji da ni! Ko na ce na fara tsufa na rage daɗi shi ya sa yanzu Yallaɓai ya daina marmarina. Na so na sha kayan lambu ne su kankana da rake da za su ɗan ta da min ni'ima saboda amfanin kaina ba domin shi ba, amma ban yi niyyar siyan wani mgani na sha ba shi ya sa ma na share Surayya kawai ban tura mata ba, na dai kira Aisha lame na ce ta aiko min da lotion sai shower gel saboda na wajena saura kaɗan ya ƙare mun rabu da ita kan cewa da safe zan san ya mata kuɗin. Hankalina ya yi kan wayata shi ya sa ko shigowar motar Yallaɓai ban ji ba sannan ban ji maganar yaran ba, ina kwance ruf da ciki a saman gado ya shigo ɗakin ba domin ban san shigowarsa gidan da ba da a ce na sani da ba zan taɓa ɗaga idanuwana na kalle shi ba amma tun da cikin rashin sani ne ina ɗagowa muka haɗa ido huɗu da shi, da sauri na mai da kaina kan wayata. Saboda sai da na gan shi sai na ji wani irin ƙunci na mamaye min zuciya. Na so na daure ma zuciyata ko sannu da zuwa na yi masa amma na kasa shi ya sa na yi kamar ban san da shigowarsa ɗakin ba shima ina ga ya na jiran ne na fara yi masa mgana shi ya sa har ya ijiye ƙaramar jakar hannunsa saman side drower ɗin gadon tare da agogon fatan da ya cire daga hannun shi ya fita bai ce min sannu ba nima ban ce masa ba ina kwance in da nake  ya dawo ya tuɓe kayan jikinsa daga shi sai gajerun wando ya koma tiolet duk ina kallon shi ta wutsiyar ido sannan na raka shi da hararan da bai san ina yi ba har kuma ya yi wankan shi ya fto ban ta shi ba, ya shafa mai sannan ya saka saukaƙkun kayan zaman gida ya fita can wajen su Jidda. Ni kuma na daɗe kan wayata sai wajen goma da rabi na kashe data nima na miƙe na faɗa tiolet na kama ruwa, sannan na zo na saka kayan barci na shafa ma wuyana da hannuna humra sannan na kwanta har ina kashe wutar bedroom ɗin kuma cikin ikon Allah barci ya ɗauke ni ban ta shi ba sai huɗu da rabi na asuba, na je na kama ruwa na yo alwala na zo na shimfiɗa sallaya na ta da salla, ina kan darduman Yallaɓai ya tashi lokacin an fara kiran sallar farko ni kuma na gama nafilfiluna ina ta jan casbaha ko kallo bai isheni ba kamar yadda shima bai nuna ma ya san ina gidan ba. Ina idar da sallar asuba na tafi ɗakin su Jidda muka yi azkar da karatu bayan mun gama muka shiga kitchen ni da Jidda muka yi abin karyawa. Kuni na ji ina son sha tun jiya daman na jika geron sai na wanke na niƙa shi a blander Jidda kuma wanke wake shima na niƙa shi a blander, ni na dama kunin da tsamiya Jidda kuma ta fara tuyan ƙosan daga baya na karɓa na ce ta je ta shirya kar ta makara. Ni da ƴaƴana muka karya lokaci na yi Salisu ya zo ɗaukan su suka wuce ni ko daman na ci na ƙoshi sai na kishigiɗa a kan kujeran falon su Jidda tibin a kunne sai na ɗauki remot na sauya tasha zuwa arewa24 suna maimacin shirin daɗin kowa. Ina nan zaune ina kallo sai na ji motsin fitowar Yallaɓai ta wutsiyar ido na kalle shi, ya fito daga shi sai dogon wando da farar singlet Yallaɓai har wani kiba ya narka to in ba idona ƙarya ya yi min ba har da timbi ya fara ijiyewa ya samu duniya. Yau ɗin ma na so na daure na gaishe shi amma sai na ka sa ma na ƙara sautin talabijin ɗin a zuwan ko ya yi mini magana ma ba zan ji sa ba. Ina zaune nan ya zo ya wuce ni zuwa kitchen ai ban gama mamaki ba sai ga shi ya fito da Mug cike da kunu sai filet shaƙe da ƙosai, daman ni ban shirya masa na sa a saman dining ba, a kitchen na bar komai shi ne ya shiga ya gani ya nema ma kansa mafita. Baki na saki ina kallon shi ya zo ya zauna saman kujeran dake fuskanta ta, har ya na haɗe kafafunwabaa ya kuma jawo center table ɗin da ke tsakiyar falon zuwa gaban shi ya ijiye mug ɗin kunun da filet ɗin da ya shaƙo kosan a ciki. Remot na gefe na ya ta so ya zo ya ɗauka, ya sauya ta sha zuwa MbcAction. Ina ga ya so na yi magana ne sai kuma ya ga na mike tsam na wuce ciki na bar sa anan. Ban san yadda ya ƙare ba ina shiga ciki na kwanta sai barci tashi kawai na yi na ga bashi a gidan ya fita a raina na ce ɗan renin wayau ranar da yamma Salisu ya kawo min cefane shi na ba ma kuɗi ya je ya siyo mini kayan marmari na yi fruit salat na sha sannan na faɗa masa da safe direba zai kira shi za a kawo min hijabai daga Zariya zai karɓo daman tun da Musbahu ya yi aure sai na koma Salisu ke karɓan kayan a tasha. Haka muka yi ta zaman doya da manja tsakanina da Yallaɓai in ya na gidana. In kuma ya na gidan Gimbiya ya kan zo duba mu da daddare. Har kuma ya gama zaman shi ya tafi ko ma ya ganni ba ma mgana. Ya san halina sarai na iya gaba shi kuma ina ga jirana yake na je na bashi haƙuri tun da ni na yi masa ba dai-dai ba ni kuma a raina na ce wallahi ya yi kaɗan ina yin abinci na ijiye masa na shi saman dining kuma ba kunya yake zama ya narka ma cikin sa. Na san har Jidda ta fahimci tsakanina da Abban na su ba zaman lafiya domin tun tasowarta ba haka ta ga muna gudanar da rayuwar mu ba, shi ya sa ta tsiri in ya shigo gidan ta biyo ni ɗaki ta na faɗa mini ga Abba ni kuma sai na ce ta je ga ni nan zuwa kuma haka zan yi ƙeme ƙeme na ƙi fita sai dai su in yana son wani abu ya ce su yi masa tun yarinyar bata fahimta ba har na fara fahimtar ba jituwa a tsakaninmu yanzu. Ranar da yana gidan Gimbiya ya zo mana sallama da daddare ina ɗaki ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ba su ba ni kuɗi ta shigo tana faɗa mini ga Abba ya zo ya na falo. Sai da na yi mata wani kallo sannan na ce" Ke in kika ƙara zuwa min ikina wani iyayin ga Abba ya zo sai na yi fata fata dake wallahi." Sai Jidda ta kasa mgana ta tsaya ta na kallona kafin ta ce" Amma Umm." "Fita ki ba ni waje. Shi bai san in da nake ba ne? Ko sai kin zo kina damuna? Ki sake dawo ki gani in ban yi miki bugun tsiya ba." Ai Jidda da sauri ta fice tana mai rufomin ƙofa na bi ta da ƙwafa ina faɗin" Ka ji min munasiran yarinya." Sai da yi kyafci sannan na cigaba da rubutuna amma a kasan raina ina jin zafi shi ai ya san in da nake, tun da bai neme ni ba ni kuma me ya sa zan nuna na san da zuwan shi? Jira ya ke yi har yanzu na zo ina bashi haƙuri lalle ko bai san taurin kaina ba ne shi ya sa. Wallahi ba zan ba shi haƙuri ba, domin ni ban ga laifin da na yi masa ba. Sai ma shi ne ya yi min laifi da yake buƙatar ya ba ni haƙuri amma ya yi fuska yana jiran ne na fara ba shi haƙuri ai ko sai da ya bushe. Da safe Amina ta kirani bayan mun gaisa tana mini tambayar banza wai na faɗa ma Yallaɓai na yi ɓari kuwa? Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" Ban faɗa masa ba. Wani abu ne? "Kai Ya Sadiya ai kamata ya sani ko? "To ke sai ki faɗa masa tun da ya kamata ya sani ɗin" Sai ta fara dariya ƙasa ƙasa ta na faɗin Allah ya ba ni haƙuri sai na fara masifa ina faɗin. "Ai bai nemi ya sani ba, tun da na dawo ba ya mini mgana bai ma san ina rayuwa ba sai ni ce zan bishi ina faɗa masa na yi ɓari? A she ma yana gaba na kenan" Sai Amina ta kashe wayarta ta bar ni ina ta masifa ni kaɗai. Haushin kowa na ke ji yanzu ina shiri zan je Ɗorayi, saboda Balaraba ta kirani kan zuwa Jigawa gobe sunan Saude daman na ce zan je, da safen ba a gidana ya kwana ba saƙo na tura masa kuma har na gama shirina na fita bai dawo mini da amsa ba. Sai da na fara biyawa gida na gaida Gwaggo Alhaji ba ya nan ya tafi Yashe duba gonakinsa. An kusa fara noma damina ta fara mana sallama na ɗan jima a gidan sannan na shiga gidan su Saude. Ma su zuwa sunan ƙannenta ne guda biyu sai ƙannen Saude da maƙota haka gobe za mu tafi sai jibi mu dawo tare da Sauden gabaɗaya tun da mijin ya amince ta dawo gida ta yi jegon ta.  Sai azahar na baro ɗorayi bayan na yi salla a gida shagon Amesty na biya na yi tsifa sannan na yi Saloon yau ma sai da ta yi mini mganar ya mganar buɗe shagona na ce mata ya na nan soon in sha Allahu. Ban ji a raina zan haƙura da burina ba so kawai nake yi na tsaya da kafafuna amma sai na cika burina na buɗe shagon saloon in sha Allahu. Daga nan na dawo gida sai ma da na dawo gida ne na duba wayata na ga saƙon Yallaɓai na adawo lafiya a raina na ce aikin ɓur in ji tusa, na fara shirin tafiya jigawa suna. Daman tuni na siya Atamfa wajen Dija collection da pampers tare da rigan yaro sai na haɗa mata da setin mayukan jarirai, ina da ƴan kuɗaɗena da su na yi amfani da daddare daman Yallaɓai zai dawo gidana shi ya sa sai da na bari ya shigo gidan yana falo tare da su Jidda sai na fito na kira Jidda ta na zuwa na ce ta je ta faɗa ma Babanta gobe zan je Jigawa Saude ta haihu. Na ga ta tsaya ta na kallona amma yadda na haɗe rai ne ya sa ba ta samu damar mgana ba ta wuce ta koma falon ni kuma na koma bedroom na zauna ina jiran ta. Can ba daɗewa sai ga shi ta dawo da kuɗi a hannunta sabbi yan dubu ta miƙa mini tana na faɗin" Abba ya ce Allah ya kiyaye hanya." Ban karɓa ba na bi kuɗin da kallo kafin na ce" Wannan kuɗin fa? "Shi ya ce na ba ki." Karɓa na yi na kirga 10k ne cif kamar wata almajira ai ko siyayyan da na yi ma Saude ta fi karfin 10k ballanta a zo maganar kuɗin mota. Mai da ma Jidda kuɗin na yi sai ta ƙi karɓa ta tsaya tana kallona. "Ki mayar masa. Na gode." Kuma yarinya sai ta ƙi karɓa wani kallo na yi mata kafin na ce" Ki karɓa mana." Sai ta noƙe hannu tana faɗin" Umma kar ki yi haka" Bai kamata Abba ya ba ki kuɗi kuma ki ce ba za ki karɓa ba." Baki na saki kawai ina kallon Jidda. Wai ta na faɗa mini abin da ya kamace ni. "Kuma Umma ni dai ba zan iya mayar masa ba sai dai ki mayar masa da kan ki" Kafin ta rufe baki na watsa mata kuɗin a fusace na miƙe ina faɗin" Ke da kuɗin kar ki bari na buɗe idanuwana na gan ku a ɗakin nan. Ki kwashe su salim alim ki fice ki ba ni waje Jidda." Amma sai ta tsaya za ta mini mgana ai ko na da ka mata tsawa ina faɗin. "Ki fita na ce ko? Sai ta duka ta tattara kudin ta fice cikin san yi jiki na dafe kaina ina tsaki, Jidda ma laifina ta ke gani, uban ta na yi min wulakanci tana ƙoƙarin kare masa saboda ba ta da tunani sakarya ce. Ni kaɗai a ɗaki ina ta masifa sai ma na tattara kayana da duk abin da zan buƙata na kai ɗayan ɗakin na can na kwana da asuba ma kuma mun haɗu na fito daga cikin ɗakin shi kuma ya fito daga tiolet muka kusa cin karo, ya yi baya nima na yi baya. Ya kuma kalleni ni ma na kalle shi amma kowannen mu sai ya kauda kan shi, ya shiga ɗakin barcin mu ni kuma na shiga tiolet. Tun safe na shirya takwas da wani na safe aka kirani an samu mota ana jirana. Kuma ga Yallaɓai bai fita ba. Ba domin yana falon shi ba da ba abin da bai hana ni tafiyata ban yi masa sallama ba. Amma ganin shi a falo ya sa da na fito na yi masa sallama na ce na tafi amma mutumin nan ya na ta duba abu a system ɗin shi bai ko ɗago ba ya ce min Allah ya kiyaye hanya. Kamar zan ce masa zan yi kwana ɗaya amma yadda ya nuna mini halin ko in kula, ya sa na yi tafiya ta ba tare da na yi masa wata mgana ba amma har na kai ɗorayi raina na ƙuna. Na fara shiga gida na gai da Gwaggo na iske ƴaƴan Ya Abubakar wai zaituna ta tafi Funtua biki, na ce sai su ɗebe miki kewan Alhaji Gwaggo. Ƙarfe tara da rabi muka kama hanya a golf da aka yo mana tasha. Balaraba 5k na ba ta sannan na nuna mata abin da na siya ma Saude ta yi ta mini godiya. Ni ko na ce haba ai Saude ƙanwata ce ballantana ta yi min alheri ƙwarai kuma sakamakon alheri to ya zama alheri ne. Mun isa da azahar lafiya mun iske ana ta suna dangin miji da makota sun cika gida Saude ta ji daɗin ganina sosai ta nuna murnan ta mun sha suna Rahila ta kirani ta ce ta zo gida Gwaggo ta ce ina Jigawa na je suna. Na ce mata wallahi ga shi sai ma gobe zan dawo mun daɗe muna waya da ita kafin mu yi sallama. Da daddare mu muka gyara gidan da aka ɓata sannan muka shirya ma Saude kayan ta na tafiya. Ta samu kayan suna ba laifi, sai godiya shima mijin na ta ya iya bakin ƙoƙarin shi, bayan duk mun gama ayyukan ina kwance a kan kafitar da aka shimfiɗa mana ni da kanwar maman su Saude Yallabai ya kira waya ta sai na fita falo ina duba agogon bangon da ke ɗaki goma har ta gota amma abin mamaki me ya sa ya ke kirana? "Assalamu alaikum" "Kina ina ne? Ko amsa sallama ta bai yi ba ya tare ni da mganar ko ina ina ne ? "Ina gidan Saude a jigawa." "Can za ki kwana ne? Sai na haɗiye wani abu a maƙoshina saboda na ji kamar a zafafa ya ke mgana. "E sai gobe za mu dawo tare da ita." "Da izinin wa za ki kwana? Kin faɗa min kwana za ki yi Sadiya? Sai na kasa magana tun da dai ba ni da gaskiya. "Sadiya don kina gaba da ni ba shi zai hana tasirin ni mijin ki ba ne ya yi aiki a kan ki ba. Ki na yin abubuwa gaban kan ki ina ta kauda kai amma wallahi kin fara ƙure ni kar ki bari na faɗo kan ki" Ban yi mamaki ba. To daman ni da ya ke ji ra bai samu dama ba sai yanzu. "Kin aiko min Jidda da cewa za ki je suna na ce sai kin dawo na aika miki da kuɗi kin dawo min da su Sadiya me kike nufi da ni? A she ba zan ci albarkacin Jidda ki karɓi kuɗin nan ba? Dole sai kin nuna mata ni da ke babu jituwa ko! To kin kyauta kuma ya yi miki kyau." Ashe dai ya ji haushin dawo masa da kuɗin da na yi. Na ko ji daɗi a cikin zuciyata da ya ji shima haushin da na daɗe ina ji. "Allah ya kai mu goben ki dawo. Za mu zauna sai ki faɗa min duk abin da na yi miki da zafi da ya sa kika maidani  ni da banza duk ɗaya Sadiya." "Ka yi haƙuri." Na faɗa saboda ina so ya ƙyale ni barci nake ji na gaji. " Bakomai kawai ban ji daɗin da ba ki faɗa mini zaki kwana ba ne." Baki na buɗe na sake rufewa ya wani sassauta murya jin na bashi haƙuri sai ma abin na shi ya ba ni dariya sai da na murmusa shima ina jin sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce. "Na yi kewar mirmishin ki Sadiya ta. " "Uhm!" Na faɗa a ƙasan maƙoshi. "Sai kin dawo goben a matsayina na Babba zan ba ki haƙuri a duka laifukan  da kike tunanin na yi miki su Sadiya." Ban yi magana ba amma na yi shuru ina jin sa. Ban yi mamaki ba daman na san ya na neman hanyar da za mu shirya ne. "Na gaji. Na gaji da wannan horon da muka yi ma juna. Ki dawo mu zauna mu warware komai a tsakanin mu kin ji ko? Ya faɗa cikin sanyin murya sai na gyaɗa kai kamar ya na ganina kafin na ce. " Sai da safe.'" "Sai da safe Madam." Daga haka na katse wayata. Na daɗe zaune ina tunani daman ai yanzu duk zai ce na yi haƙuri shi ba da gayya ya faɗin duk mganar da ya faɗa ba. In ma na haƙura amma ba shi zai saka na manta da abin da ya yi mini ba. *Janafty*.*TKGB30C3* *Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.* Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732 Washe gari tun safe muka tashi da aikin nama muka soye shi a ka raba a ka ɗibar ma dangin mijin Saude kafin mu haɗa kayan tafiya. Tashar mota ya samo mana tun daga ƙofar gidan Saude a garin Jigawa har zuwa ƙofar gidan su a anguwan Ɗorayi da ke Kano, zuwa la'asar duk muna Kano ni daman muna isowa na shige gidan Gwaggo na yi salla na iske har lokacin Alhajinmu bai dawo ba. "Gaskiya Alhajinmu ya ga wuri. Yashe ta yi masa daɗi wannan karon." Na faɗa ina dariya Gwaggo ta ce ai ko wannan karon dai ya daɗe, ni kaina ban samu kiran shi ba sai a lokacin har ya ba ni Baba Aminu muka gaisa da shi yana ta saka mana albarka. Ina shirin tafiya sai ga saƙon naman suna da yawa daga gidan su Saude har da omo da sabulu na Gwaggo. Da zan tafi tare da Gwaggo muka shiga gidan ta yi ma Saude barka a nan na bar ta na wuce gida na shiga gida ba daɗewa domin ruwan zafi kawai na ɗora ban ma san me zan dafa ba su Jidda suka dawo daga makaranta kawai sai na sulala mana indomie na haɗa da ƙwai na dafa mana muka ci, tun da yamma ta yi sannan yau Yallaɓai na gidan Gimbiya ba ni da wata matsala. Saboda yana neman shiri bayan mangariba sai ga kiran shi, tambayarsa ita ce na dawo? Na ce masa na dawo tun ɗazu sai ya ce mini zai shigo gidan in ya dawo. Ban ma san ashe tafiya ya yi ba sai da ya zo gidan wajajen taran dare, ina ɗakina saboda yana son shirin da gaske har ciki ya biyo ni, muka gaisa shi ne fa ya ke faɗa mini Dutse ya je akwai wani gidan radio da za a gina kuma shi a ka ba ma kwangilar wajen shi ya sa ba ya samun zama ni dai nawa fatan alheri kawai. Tare da shi muka fito falo ina ba ma su Jidda naman sunan da a ka bani na gidan su Saude. Tsoka bibbiyu na ba su ni kuma sai na saka sauran tsoka ɗayan a bakina akwai kuma saura biyu a hannuna da ƙashi. " Umma Sadiya. Ni ina nawa naman sunan? Ba zato kawai na ji maganarsa ban tsaya nuna masa mamakina ba na miƙa masa sauran na hannuna. Sai dai na shanye mamakin nawa da na ga ya saka hannu ya karɓa har kuma ya ɗauki tsokan da ta rage ya saka a baki ya na taunawa. "Lah Abba kai ma kana cin naman suna? Baby ta faɗa tana yi masa dariya duƙawa ya yi daga in da muke tsaye a bayan kujerun falon ya lakace mata hanci yana  faɗin" E mana. Ai har na ki naman sunan na ci." "Na Ya Jidda fa? Ta faɗa ta na dariya. "Har na ta ma na ci." "To na Umma fa? Sai na kalle shi, nima ni ya kallah kafin ya yi dariya ni kuma sai na kauda kaina na zagaya na zauna saman kujeran da Jidda ke zaune ta na ta duba wani littafin Chemistry ba ta shiga maganar Baby da Abban na ta ba. Na ga dai ya yi mata raɗa a kunne tana kallona tana dariya amma ban san me ya faɗa mata ba. Bai zauna ba ya yi mana sallama ya tafi. Saboda gulma har yana zuwa yana sumbatar goshina. Yaushe rabon duniya da ayyarahe? Amma dai ban kushe sa ba, na yi masa yaƙe Baby ce ta raka shi har haraban gida amma daga ni har Jidda muna daga in da muke ko motsawa ba mu yi ba.   Washegari da safe bai zo ba amma ya kira ni a waya yana tambayan yadda na tashi ni da yara. Na ce masa muna lafiya sai ya ce zai ta fi Dutse sai zuwa anjuma in ya dawo na ce a dawo lafiya. Ranar a gida na yini ina warware gajiya mun yi waya da Anty Laila maƙotan ta na son hijabai sun gani a wajenta da yake ta siya kuma shima Ya Auwal ya siya mata wasu. Nan da nan na ji ciniki na ce ta tura mini colours da simple ɗin irin wanda suke so sai na tura a ɗin ka musu daga can za a tura musu Abujan ba sai an ma an kawo mini shi nan ba. Datti ma mun yi waya amma ni na kira shi ina masa tsiyan tun da ya fara zaman kansa ya daina neman mutane. "Kai Ya Sadiya ko kwanaki ba na kira ki ban same ki ba " "Uhm kai Datti fita idanuwana na rufe. " Sai ya fara dariya yana faɗin" To na ji na amsa laifina a yi min afuwa" Sannan na yarda muka gaisa yana tambayan ya yara na ce suna lafiya. "Ko jiya sai da Jidda ta yi zencen ka da cewa Uncle Datti shuru kwana biyu" "Allah sarki Jiddodi ta na lafiya ko? Ya mganar jarabawarta? "Yallaɓai ya ce a wannan shekaran za ta yi har Jamb ma." "Za ta iya ai ta na da ƙwanya mu ta yi gado" Dariya na yi shima yana ta ya ni, mun sha hira da shi ya ce ma ƙarshen wata zai shigo garin ba sa samun hutu ne mai tsawo ni ko na ce daman aikin kamfani ai sai mai haƙuri. Ina jin zumunci har Ya Aina na kira da Ya Balki muka gaisa Ya Murja ce da na kira ba ta gida yara suka  ɗau wayar Rahila kuma Ya Muntari ya ɗauka ya ce min wayar na hannunsa tun jiya wutar layin su ta lalace wayar ta kwana ba chaji sai ya fita da ita yau ɗin domin ya sa mata chaji bai ma daɗe da kunna wayar ba sai ga kirana. Na dai ce ya gaisheta in ya koma gida ya ce in sha Allahu zai faɗa mata. Amina ce kaɗai da ban kira ba saboda ita ko kafin tafiya ta Jigawa ai mun yi waya. Ma'u kuma daman na yanke alaqa da ita, ba ta kirana ba na kiranta sai dai in mun haɗu a gidajen ƴan'uwa amma dai ban goge lambarta ba kamar yadda nima na ke da yaƙinin ba ta share tawa ba. Daga nan na yi ta shige shige na a I. G. Ni kaɗai ban taɓa jin ina jin haushin halina ba sai kwanakin nan ba ni da wata ƙawa Aminiya shaƙiƙiyan da yau in na shiga matsala zan je mata da mgana ta saurareni kuma ta ba ni shawara kamar yadda na ga wasu suna dashi, ni ko ni ɗaya tal ban taɓa ƙawa ba bare ba sai su Munnira su kuma aure ne ya haɗa ni da su duk da mun shaƙu amma akwai wani matsalan nawa da ba na iya faɗa musu saboda shi aure ai sirri ne, kuma cikin kowani aure da zamantakewa akwai matsaloli kowa kuma da irin na shi matsalan. Ba komai ba ne za ka zo kana faɗa akwai wani abun da ya ke buƙatar sakaya. Yau da a ce bani da shigen halin rashin sakin jiki da mutane da yanzu ina da ƙawaye na tuna tun muna makaranta ƙawayen da suka yi ta shige mini ina ba sar da su. Har na zo matakin jami'a yan set ɗin mu sun yi ta shige mini amma na ƙi ba ma kowa fuska har Maijidda ma ta layin mu ta so ni har muka haɗu a jami'a da ta ga dai ba na yi da ita sai ta kama kanta. Ta yi aure a cikin garin Kano nan amma ban taɓa zuwa gidan ta ba na dai je bikin da Rahila ta matsa mii  kuma har gida Maijiddan ta kawo min IV da mintin gayyata. Kaf waɗanda muka yi karatun jami'a da su ba na zumunci da kowa. Wasu ina ɗan kiran su a waya jaje ko murna shima na zo na daina daga baya nima tun suna bina har kowa ya rabu da ni ina dai cikin group ɗin kuma ina ganin ana ta abubuwa in sha'ani ya tashi na ɗayan mu a haɗa kudi kuma a je, ni dai na kan ba da wani lokaci amma zuwa ban taɓa yi ba. Sai dai in ga ana turo hotuna suna zumunci su amma ni na ware kaina kamar saniyar ware. Ban taɓa jin abin ya dame ni ba sai yanzu amma a ƙasan zuciya na ƙudiri a raina nima yanzu zan nemi jama'a domin na fahimci jama'a rahama ne. Ranar ma sai dare Yallaɓai ya zo gidan kuma again a ɗakin barcin mu ya sameni ina ta rubutu. "Madam wai labarai kika fara rubutawa ne? "Me ka gani? Na ɗago ina kallon shi bayan na dakata da rubutun da nake yi. Gyara zama na yi a gefen gadon lokaci ɗaya ina gyara zaman doguwar rigar  material ɗin dake jikina. "To gani na yi kwanan nan kina ta faman rubuce rubuce." Kallonsa na yi ina tuna yaushe ne ya ganni ina rubutu? Ni dai ina tunanin wannan ne na biyu amma zai ce wai kwanan nan ya na ganina ina rubuce rubuce. "Kawai abin kasuwanci ne. Ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ne." "Da kyau Hajiyar Business" "Ya Hanya? Sai na kau da maganar ganin duk ya gaji daga yanayin ma yadda ya ke mgana. "Lafiya lau. Amma na gaji sosai" "To ka zauna mana." Na faɗa ina nuna masa gefen gado saboda na ga yana tsaye kuma ga shi ya ce ya gaji." "Bari kawai na ƙarisa gida na yi wanka na huta gabaɗaya." "Kuma fa haka ne." Na faɗa ina kau da tunanin ya ƙi amsar ta yi na ne. Ni fa taimakon sa na yi ganin ya ce ya gaji kuma yana tsaye kamar wani dakaren soja. "Maganar mu fa Sadiya? "Wacce magana? Na tambaya ina kallon shi. Sai ya gyara tsayuwa yana mai harɗe hannayensa a ƙirji kafin ya ce. "Mganar da na ce in kika dawo za mu yi. Domin mu warware rashin jituwan dake tsakanin mu." Sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Muna gabar ne har yanzu? Ai ina jin kamar mun warware komai." "A'a. "To me ya yi saura? "Komai ma." Ya katseni ya na mai tsareni da idanuwansa. "Kin daina gaba da ni amma kuma kin ƙi komawa kamar yadda kike a baya Sadiya." "Mun daina gaba da juna za ka ce ko? Ya na kallona na cigaba da faɗin" Tun da kaima ba ka yi mini magana Yallaɓai." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Duk na ji na amsa laifina shi ya sa na ce mu zauna mu yi magana domin mu fahimci juna." "Na ji za mu yi in sha Alkahu." Na faɗa ina ƙokarin komawa in cigaba da rubutuna. "To yaushe? Sai da na ɗago na kalle shi ido na cikin ido sannan na ce. "Sai ranar da na karɓi girki." Murmishi ya yi kafin ya ƙariso gaba na ban yi aune ba kawai ya ɗan rankwafa ya sumbaci laɓɓana kafin ya miƙe ya fice yana faɗin. "Sai da safe Sadiya ta." "Sai da safe." Na amsa masa a saman laɓɓana bayan fitan shi har ina shafa wajen. Yaushe rabon da a yi haka! Tun kafin faɗan mu da shi a kan Khalipa. Yaron na raina ina son tambayan shi amma na fasa tun da ya nuna min iyakata ya je amma ƙaunar da nake yi ma jininsa ba zan fasa saboda shi ba, ko faɗan mu ne ya sa kwana biyu tun da na dawo bai tarkatomun Khalipan ba, amma na ƙudiri niyyar in na ga ba a kawo shi ba zan kira Gumbiyar na ce ta kawo shi ya yi mini kwana biyu na saba da shi duk da ɓarnar shi, shi kuma na san ya yi sabo da gidana sosai kawai dai kwana ɗaki ɗayan da Yallaɓai ya tsiro da shi na ga ana cutata shi ya sa na yi magana amma ba da niyyar Khalipa ya daina zuwa ba tun a baya ban hana shi zuwa ba sai yanzu?. ****** Tun da yau Yallaɓai zai dawo gida na na kira Maman Nana na ce in ta samu lokaci ta zo ta yi mini kitso. Da safen ko ta zo ta yi min 2step ƙananu. Kuma kitson ya yi kyau tun da na duba a cameran waya ta na gani. Sai azahar ta tafi bayan na yi mana girki duk dai macaroni na dafa mana muka ci da ranar. Bayan tafiyan ta na gyara gidan na yi shara na saka turare ɗan kwanciya na yi na ɗan huta zuwa la'asar na tashi bayan na yi sallar la'asar Sannan na ɗora ma su Jidda girki da man macaronin guda ɗaya na dafa. Cous-cous na dafa mai kayan lambu daman kuma Yallaɓai na so shi ya sa na yi. Sai zoɓon da na haɗa daman tun safe na riga na dafa genyen zoɓon haɗawan kawai na yi. Sai sauran kayan marmarin da suka rage mana na yanka na yi mana fruit salad ni da Yallaɓai. Shidda saura su Jidda suka dawo makaranta ajaran majaran saboda yunwa ko uniform ba su cire ba suka fara cin abinci. Baby na faɗa min Umma cikina kamar an kwashe min kayan cikina ina gefe ina ta yi mata dariya ganin tana cin abinci hannu baka hannu ƙwarya. "Baby ki ci a sannu kar ki shaƙe.' "Umma ba ki san yunwan da na ke ji ba ne" Ina ta mata dariya ni na je na kawo musu da zoɓon ya yi sanyi na saka a firiza. "Ya Jidda ke ma duk yunwar ba baka sai kunne? Sunne kai ta yi ta na faɗin. "Umma ni kin ji na yi magana ne? "Ba ki ce komai ba. Ke dai ci abinci kawai." Na faɗa ina yar dariya. Yarinya na jin yunwa tana noƙewa. Bayan sun gama cin abincin sun ƙoshi, suka sauya kaya zuwa na gida lokacin an kira salla sai muka yi alwala muka yi salla yau ba mu yi karatu ba saboda wankin uniform muka fita  ta baya muka wanke su tare da yan riganunan barcin Baby da ƙananun wandunan ta daman Jidda ke wanke musu tare da na ta. Muna gamawa ana kiran sallar isha'i muka sake ɗauro alwala muka yi sallar isha'i. Muna idarwa ni kuma na faɗa wanka bayan na fito na yi gayu na cikin riga da zani na wata atamfata hollond ta na cikin kayan da na siya lokacin auran Yallaɓai da Gimbiya. Na kashe ɗauri na ture ka ga tsiya na ba za gashina ya sauko har kafaɗuna. Har da su jan baki na saka na kuma zirara gazal a girana, na fita falo wajen yara da dai na ga shuru Yallaɓai bai shigo ba sai na diɓi abincina na ci na kora da zoɓo da fruit salat. Bai kuma shigo ba sai goma har ta ma gota. Tuni har na kaɗa su Jidda ɗakin su na ce su yi shirin kwanciya so ni kaɗai ya iske zaune a falon ina kallo duk da hankalina ba akan kallon yake ba. Miƙewa na yi ina kallon shi, nufar sa na yi ganinsa da ledoji a hannunsa. "Sannu da zuwa." Na faɗa ina karɓan ledojin hannunasa. "Yauwa Madam ya gidan? Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakar min ledojin a hannuna. Na amsa da lafiya lau lokacin da na nufi kitchen na duba ledojin tsire ne sai fura mai sanyi an dama ta a leda. Na san ni ya siyo mawa da yake ya san ina son fura duk da cikina ya cika amma ta ba ni sha'awa zan sha zuwa anjuma in cikina ya sassaɓe. Naman dai a firiza na saka shi  da safe sai mu ci na san na mu ne Yallaɓai ba ya son tsire ya fi son gashi na naman rago. Sai ya ce wai tsire duk ƙuli ne ba nama ba. Ko da na fito ba shi a falon ya na ciki sai na koma kitchen ɗin na hada masa abinci na kai dining sai da na gama shirya masa duk abin da zai buƙata sannan na koma bedroom ɗin na iske Yallaɓai ya fito daga wanka ya na saka sauƙaƙƙun kayan zama cikin gida riga da wata ƙaramar riga mara hannu. Sai ma yau na ƙare ma Yallaɓai kallo da gaske kam Yallaɓai ya fara ijiye tumbi da na ƙura ma gashin kansa ido har na hango ƙyali ƙyalin furfura a saman kan shi har ma da sajen shi. A raina na ce su Yallaɓai tafiya ta fara miƙawa. "Tunanin me Sadiya ta take yi ne ahalin ga ni a kusa? Ya faɗa ya na mai sagalo hannun shi a kafaɗana sai na tattaro murmushi na kalle shi na yi masa. "Abinci.? Na faɗa ina kallon shi sai ya shafa cikin sa yana faɗin daman yunwar yake ji. Ya ƙi sakina ya na dafe da ni muka fita can falo sai da zai zauna saman kujeran dinning ne ya sake ni. Nima gefen sa na zauna na zuba masa cous-cous ɗin da zoɓo sai fruit salaf ɗin sai ya ce na zuba masa leda ɗaya na fura yana so zai sha sai na koma kitchen na juyo masa a wani ƙaramin mug. Ina gefen shi har ya gama cin abinci kuma daga yanayin sa na fahimci ya ji daɗin haka. Barin ma yadda na ga ya ci abincin sosai da alamu dai yau Yallaɓai ya yi ta su Baby ta babuwa ta addabi cikin sa. "Girki ya yi daɗi. Haka ma mai girkin ta yi kyau." Ya faɗa ya na kallona sai na yi murmushi k amma ban ce komai ba. Bayan na tattara abubuwan da ya ɓata na mai da kitchen ina dawowa ya ce wai kallo za mu yi, kujera mai zaman mutum biyu na samu na zauna amma Yallaɓai sai da ya biyo ni ya nane minI, ina basarwa ina komai karshenta dai sai gani a saman jikinsa kamar yadda muke yi a baya in muna kallo. Ɗankwalin kaina ya zame min yama ta wasa da gashin kaina shi ke kallon ni kuma na kwantar da kaina kawai a saman ƙirjinsa ina tunanin rayuwa juyi juyi. Yanzu fa yadda nake yi da Yallabai haka itama Gimbiya take yi da shi gabaɗaya sai na ji ƙuncin zuciyata ya dawo. Har wani gishiri gishiri na ji miyan bakina na yi saboda takaici ina jin sa yana ta ɓabatun magana amma ban biye masa ba. "Ƙitson nan ya yi kyau. Yaushe a ka yi shi? "Yau." Na bashi amsa kai tsaye. "Lalle ko za ki karɓi tuƙwaici domin kitson ya yi kyau sosai." Ya gama faɗa sannan ya sumbaci kaina. Ni ko mgana ban yi ba ganin haka ya sa ya leƙo fuskata yana faɗin" Kin yi shuru? "Me zan ce? "Komai ma ki ce Sadiya ta." Sai kawai na yi masa shuru saboda ni ai ya gama shanye ruwan kaina ba wani sauran abin da zai yi mini da zai kankare mganganunsa a wajena suna nan damfare a ƙasan zuciyata sun yi min tsataa. Ganin kamar ba ya jin barci ya sa na fara yi masa hamman ƙarya na ce ina jin barci dole ya kashe kallon muka koma bedroon ɗin mu amma ni na fara yin gaba shi kuma ya tsaya duba yara sannan ya kashe wutar duka ɗakunan kafin ya shigo har na yi shirin kwanciya amma ban kwanta ba. Na saka wata doguwar rigar barcina mai taushi. Ina shafa humra a wuyana da hannayena ya shigo. Shima dai tiolet ya shiga ya kama ruwa ya wanke baki sannan ya dawo ya tuɓe riga ya kuma tuɓe wando da ga shi sai gajerun wando ya hau gadon a gefena maimakon ya yi nashi ɓarayin sai ya mirgino har kan filona ya tsoma na shi kan Muka yi shuru ni da shi, muna kallon rufin dakin da hasken wutar tun da bai riga ya kashe ba. Juyowa ya yi ya na kallona ni kuma da sauri na ce" Ka rage mana hasken wutar mana." "Ba yanzu ba." Sai na ƙura masa ido kafin na samu sararin magana ya cigaba da faɗin. "Sai mun yi maganar mu." Na kalle shi amma ban yi magana ba sai na ga ya miƙe zaune nima ya umarce ni da na tashi ba ni da mafita dole na mike zaune a saman gadon muna kallon juna. "Sadiya" "Na'am." Na amsa mishi kamar yadda ya kira sunana. Sai kawai na ga ya kama duka hannuwana ya jimƙe cikin tafukan hannayen shi. "Ki faɗa mini duka abin da na yi miki da ya ɓata miki rai ni kuma na yi miki alƙwarin zan ba ki haƙuri." Ya faɗa yana murza hannayena sannan kuma yana mai tsareni da ido. "Ni fa ba komai. Komai ya wuce." "Bai wuce ba." "Allah na ce maka ba komai ba sai ka ba ni haƙuri ba.'" "Me ya sa kike haka ne? Ya faɗa ya na tsareni da idanuwansa a kaushashe ya cigaba da faɗin. "Fahimtar juna nake so mu yi Sadiya. Ni dake ba shekaranjiya muka faro rayuwar nan ba, ba kuma jiya ba ne, ba kuma yau ba ne. Sabo da haka maganar komai ya wuce ni dake mun san ba haka ba ne ko? Ya gama faɗa ya na mai tsare ni da idanuwansa kuma ya kama hannayena ya riƙe ba halin na ƙwaci kaina. "Haka ne" "To ki yi magana domin mu fahimci juna." "Na ce ba komai fa" Na faɗa ina kauda kaina sai ga shi ya saka hannu ya dawo da fuskata zuwa in da yake. "Ni na san akwai komai fa" "To mene ne? Komai ya wuce tun da na haƙura ga shi ni da kai muna zaune a waje ɗaya." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Komai bai wuce ba. Saboda na yi miki mganganu ranar marasa daɗi kuma na san har ga Allah ke ma ranki ba zai yi miki daɗi ba.' Ashe ya san abin da ya yi? Shima ya san bai kyauta ba! A lokacin ya sani ko sai yanzu daga baya." "Raina ne ya ɓaci a ranar har na kasa fahimtar ki sai daga baya da na zauna na yi tunani sai na fahimci ni ne ban kyauta ba sannan na yi miki rashin adalci." Ƙura masa ido na yi, hawaye suna taruwa a ƙwarmin idanuwana. Maganganunsa na baya suna mini amsa kuwwa kamar a lokacin yake faɗa mini. "Na yi kuskure. Kuma na gane kuskure na don Allah ki yi haƙuri ki manta komai." "In manta komai fa ka ce? Na katse shi cikin rawan murya. "E ki manta na ce. Ki ɗauka na faɗa ne a fatar baki amma ba har cikin zuciya ta ba." "Har gorin haihuwan da ka yi mini Yusuf? Har cewan da ka yi ina baƙin ciki da Gimbiya da ƴaƴanta? Har goran ta mini da ka yi na cewa ba kai ka ce na je na yi planning ba ni na saka kai na? Har shi na manta har shi kake so na manta kamar komai bai faru ba? Sai ya kasa mgana na ƙura masa ido, amma ya dukar da kaina ya na faɗin "Ki yi haƙuri ɓacin rai ne." "Sai ɓacin rai ya sa ka yi mini gorin gida Yallaɓai? Na faɗa ina mai kecewa da kuka. Kukan da ke taso mini daga ƙasan zuciyata. Kukan sanadin rasa gudan jinina kukan ɓacin rai da baƙin ciki da mganganun Yallaɓai suka dasa min a cikin zuciyata. "Ka rufe idanuwan ka. Ka manta da ko planning ɗin da na yi da amincewar ka na yi. Kuma in da na tara sanin haka zai faru da ni zan yi har jawo mini matsala ne? Kuma ka sani ko ban yi ba in Allah ya ce Jidda da Baby kaɗai ne rabona na ƴaƴana a nan duniya ba ni da yadda zan yi kokawa da kaddara ta. Kuma ka ce ina baƙin ciki da Gimbiya da ƴaƴan ka, wannan kam sai na ce ba ka yi mini adalci ba ban taɓa zama da matarka da wata zuciyar ba sai zuciyar musulunci su Khalipa kuwa ɗaya suke da su Jidda a wajena. Amma rana ɗaya kuskure kaɗan da kai ne ka yi amma ka rufe idanuwanka ka ce ba na son jininka. Sannan daga ƙarshe ka yi mini gori. Gorin nan gidan uban su khalipa ne ni kuma ba gidan ubana ba ne.'" Na dakata ina shessheƙan kuka ina ji ya na damƙe hannayena da ke cikin na shi alamun rarrashi amma bai hana ni kuka ba. Na nuna saitin zuciyata ina cigaba da faɗin. "A nan mganganun ka suka yi min illa. Ban taɓa tunanin irin ta ka martabawan ba kenan Yusuf. Na ɗauka ni ina da ƙima da karamcin da za ka guji faɗa mini kalaman da za su sosa mini rai in har kana yi min karan shekarun da muka shafe ni da kai muna zaman aure. Ni da kai mun wuce karnin soyyayya mun koma abu ɗaya. Abu ɗaya Yallaɓai." Na ƙarishe ina mai cigaba da kukana sai na ji kamar lokacin ne ma lamarin yake faruwa. "Ki yi haƙuri. Sharrin sheɗan ne."   Ina jin sa amma ban yi magana ba ina cigaba da kukana, sai ga shi ya matso kusa da ni ya rumgumeni ya na faman lallashina. "Am sorry." "Ki yi haƙuri don Allah ki yafe mini Sadiya ta." Sai kawai na ƙara karfin kukana ina ƙokarin ƙwace kaina daga riƙon sa amma shi bai sake ni ba. "Wallahi ni kaina na azabtu da kalaman da na faɗa miki. Sharrin zuciya ne." Hannayena na saka duka biyu ina dukan shi a ƙirji lokaci ɗaya ina kuka har da sheshesheƙa. "Sharrin zuciya ne ya sa ka yi min goron haihuwa? Ƴaƴana biyu fa, ko a haka Allah ya bar ni na gode masa kuma ko garke Gimbiya za ta haifa maka wallahi ni mai farinciki da haka, ban taɓa jin zan yi baƙin ciki saboda ka samu ƙaruwa da wata matar ba ni ba. Illa ni mai farinciki be ina cewa jinin ka jinina ne, duk ɗaya na ɗauke su da su Jidda. Amma kai zuciyarka ta saka maka bambamci Yusuf." Na faɗa ina ta dukansa ta ko'ina kuma bai hana ni ba sai da na gaji don kaina sannan na lafe a jikinsa na yi laushi. "Ki yi haƙuri ina mai neman afuwarki." Ya yi ta nanata na yi haƙuri har sai da muryansa ta dishashe nima nawa ya daɗe da disashewa saboda kuka. Ɗago kaina ya yi ya na share mini hawaye. "Ba zan ƙara ba. Kin ji ko? Ya faɗa ya na matse mini fuska sannan ya sumbaci goshina. Sai kuma ya gangaro wajen laɓbana ya na sumbatata. Ban buɗe masa bakin ba sai na datse shi kuma sai ya kalleni ya na faɗin" Ba ki maraba da ni ne? Ko ba ki haƙura ba ne? Ina kallon shi saboda akwai hasken a ɗakin shima ni yake kallo na tsawon wani lokaci. "Na tsufa Yallaɓai me za ka ji in ka maraban ce ni? Ya buɗe baki da sauri zai yi magana na yi saurin rufe masa baki da hannuna guda ɗaya. "Yaushe rabon da ka neme ni mu yi ɓarnan ruwa? Na tsufa ko? Ko na ƙafe ne yanzu babu danshin ruwa? Na faɗa ina zubar ƙwalla da sauri ya fizge bakin shi, yana kallona na buɗe baki na yi magana ya damƙe bakina ya shiga sumbata na da karfi da karfi lokaci ɗaya yana sabule min rigar barcin da ke jikina. Sumbatata yake yi da zafi zafi tun ina tamke bakina har dai na saki na ba da kai bori ya hau. Bai saki bakina ba sai da ya kai ni kwance bayan ya raba ni da rigar jikina. Ina haki ya na haki, ya dakata ya na kallona. Ya yi wurgi da gajeren wandon da ya cire daga jikinsa. Ni da shi naked muna kallon duka jikin mu abin da ba mu taɓa yi ba in za mu ribaci juna sai a cikin duhu ba mu taɓa kaɗaicewa da juna cikin haske irin na yau ba. "Ni za ki faɗa ma kin tsufa Sadiya? Ni na ɓare ki a leda kina  ƴ'ar yarinyar ki. Ni ma ke kika ɓare ni a leda ina saurayina. Sadiya ko wajen babu danshin ruwa ni Yusuf zan da dasasa shi har sai na ɓulɓulo da wannan danshin" Ina shirin mgana ya saka nauyin ƙirjinsa ya danne ni. Lokaci ɗaya ya na haɗe nipples ɗin sa da nonuwana. Har tsakiyar kaina na ji abin ban dawo hayyacina ba na ji ya ƙara kama bakina, komai da zafi zafi yake yi mini alamun yau in na shiga hannu sai na gane ba ni da wayau. Ai ko na gane domin da gaske ya ke ko ba danshi sai da ya ɓulɓulo da wannan danshi na yi ta zubar ruwa. Ranar ba in da Yallabai ba lashe a jikina ba hauka ne kawai ban yi ba amma har ihu sai da ya sakani, kusan fa famshe duk kwanakin sa ya yi, da ya sauka muna gama sauke numfashi sai ya sake damƙo ni da na fara masa magiya sai ya ce ai na ce wajen babu danshi to danshi ya ke so ya ɓulɓulo mini da shi. Da hasken wutar lantarki muka yi komai yana kallona ina kallon shi ni da na ji nauyi sai na runtse idanuwana muka daina haɗa ido da shi bai ƙyale ni ba sai da ya ce na yarda ban tsufa ba? Na yarda ko mun tsufa za mu iya samo wannan danshin ruwan na ce masa na amince sannan ya sarara mini sai da na yi gashi. Dukkan mu sai da muka tsarkake jikinmu muka saka wasu kayan barcin muka koma muka kwanta maƙale da juna. Zuciya ta yi sanyi duk haushin da nake ji a kan Yallabai ya tafi ban ma san in da fushin na wa ya je ba, amma na danganta haka da yadda ya fahimci ya yi laifi kuma ya ba ni dama na yi magana ya ba ni haƙuri. Barci muka yi cikin salama makale da juna wanda mun daɗe rabon mu da wannan yanayin. Ko bayan sallar asuba sai da Yallaɓai ya sake biyo danshin nan ta bakin shi, bayan mun gama ne muna sauke numfashi ba mu ma tsarkake jikin mu ba a lokacin kaina na saman hannunsa na hagu da ya rumgumo ni da shi. "Yallaɓai." "Uhm" "Ranar da na je kaduna." "Uhm" Ya sake faɗa kamar mai jin barci. "Na samu miscarriage" "Uhm" Sai kuma na ga da sauri ya mike zaune har ya na wancalar da kaina sai kuma ya saka hannu ya ta da ni zaune ina mai danne kafaɗuna da duka hannayen shi guda biyu. "Me kika ce"? Ina murmushi na ce" Na ce na samu ɓari a kaduna. Cikin wata ɗaya ne ni kaina ban san dashi ba sai da ya fita." Ƙura minI ido ya yi kafin ya ce" Da gaske kike yi Sadiya? Ya faɗa da wani irin murna a muryansa. Sai na gyaɗa masa kai alamun haka ne sai kawai ya rumgumeni ƙamƙam yana faɗin. "Alhamdulillah." "Ka ji abin da na ce da kyau Yallabai? Na faɗa ina tantama in ya fahimci na ce ɓari na yi. Sai da ya saki rumgumar da ya yi mini ya na kallona sannan ya riƙe hannayena yana dariya ya ce" Na ji da kyau. Kin yi barin ciki ko Sadiya? Sai na gyaɗa masa kai sai kawai ya ce" Ina farincikine ne a ƙalla dai ina da yaƙinin za ki sake haihuwa zan sake ganin ki ɗauke da cikina Sadiya" Murnan da ya yi ta ba ni mamaki ban taɓa tunanin zai yi murnan in na ƙara samun ciki ba. "Na yi kewar laulayin ki. Fushin ki in kina da ciki na yi kewar ganin kumbararun kafafuwanki. Na yi kewar ganin cikin ki ya turo Sadiya. Ina kewar ganin kina shayar da Baby everything da kika sani ina kewar shi a tare da ke" Hawaye suka cika min ƙwarmin idanuwana. "A ƙalla yanzu zan ta saka hop. Sannan zan ƙara dakewa ko?  Ya ƙarishe faɗa yana mai shafa jikina. Shi murna kawai yake yi. "Kai ba ka jimamin rashin cikin da muka yi? Sai sannan ya ɗan sauya fuska kafin ya ce" Na yi jimami sosai amma me ya fitar da shi? Wannan tafiyar da kika yi ranki a ɓace ko? Ban ba shi amsa ya saka hannuna ya ɗan mari kan shi yana faɗin" Ni ne ko ? Ni ne ko? Sai kuma ya koma ya kwanta a kan cinyata ta wajen cibiyata ya na faɗin" Ni ne na ɓata ma Umma rai, laifina ne da ya sa muka rasa gudan jinnin mu. Sadiya ki yafe mini" Ya faɗa lokaci ɗaya ya na rungumo cikina zuwa kuguna. Sai na shafa kan shi cikin tattausan lafazi na ce" Ba laifinka ba ne daman can Allah ya yi ba mai zama ba ne." "Kuma Allah zai ba mu wani ka ji ko? Sai ya ɗago ya na kallona kafin na gyaɗa masa ina faɗin" In sha Allahu.  Kar ka damu.' Sai ya sake komawa ya kwantar da kansa a cinyata yana faɗin" In sha Allahu ma ya bi cikin danshin ya shige. "Me? Na tambaya ina kallon shi. Cikina ya shafa kafin ma ya yi magana na samu amsana sai na samu kaina da amsa wa da Allah ya sa.  Duƙawa na yi da kaina na sumbaci goshin sa. "Ina ƙaunarki Sadiya ta." "Nima haka." "Kema me? "Ina sonka Yallaɓai na." Na faɗa ina yi masa murmishi, shima kallona ya ke yi cike da so da ƙauna. Muna wannan kwanciyar ta soyayya na zayyane masa abin da ya faru a Kaduna da kwanakin da na yi a gadon asibiti. "Ban ji daɗi da ba ni na wahala da ke ba." "Haka Allah ya so." "Allah ya saka ma Amina da mijinta da alheri." "Amin Amin." ***** Shike nan faɗa ya ƙare tsakanina da Yallaɓai ni da na ce ko na yafe masa ba zan manta ba sai gashi tuni na manta na kama mijina gam mun fi ma baya ɗinkewa da nuna ma juna soyayya. Jidda kam ta na lura da mun shirya ranar har tsiya ta yi mini  da ta ga na kira mai ƙunshi har gida ta na yi mini buɗe bakin yarinyar sai ce mini ta yi. "Su Umma manya an gama fushi da Abba kuma yanzu an dawo ana yi masa kwalliya." Da na balla mata harara sannan na rakata da daƙuwa sai ta shige ɗaki tana mini dariya. Da Yallaɓai ya dawo sai da na faɗa masa shima dariyan ya yi ta yi kafin ya ce" Ahto da gaskiyan uwata an gama min yanga da jan Aji an ga dai ba wani sai ni an dawo mini." Da ya faɗi haka sai da na maka masa filon da ke hannuna ina kunƙuni ina cewa zan dai yi maneji da shi,  shi ko ya ce ko yanzu ya tashi ƙara aure zai samu budurwa ni kuma in na samu tsoho ma na gode Allah domin duk ya gama suɗe danshin haka na yi ta maka masa filo amma bai yi shuru ba sai da ya ƙarisa ai ko ya daku da filon kujera. Amina ma sai da ta yi mini shaƙiyanci daga ta kira muna waya ina faɗin Yallaɓai ma ya ce a yi musu godiya ita da Dr. Sai cewa ta yi" Ya Sadiya wai kin yafe ma Yallaɓan ne da har kika bashi labarin kin samu ɓari? "To ya na iya Amina. Ya yi ta bani haƙuri sannan ya ce sharrin sheɗan ne shi ya sa na haƙura." Sai kawai Amina ta fara mini dariya. "Nan fa kika ce har abada ba za ki manta da abin da ya yi miki ba." Cikin masifa na ce" Ai ban ce na manta ba na dai ce na yafe masa. Kuma kowa ai yana kuskure ko? Ganin ta mai da ni mahaukaciya ya sa na kashe wayata ina masifa. Ni kaina ina mamakin yadda duk yadda na kai ga ƙullatan Yallaɓai da ya zo ya lallasheni ya ba ni haƙuri shike nan sai na ji na haƙura sannan na manta da komai mun cigaba da rayuwarmu kamar komai bai faru ba. Ganin mun shirya ya sa na ce ya dawo mini da ɗana Khalipa. Ya na jin haka washe gari sai ga Gimbiyar ya kwaso mini ita da yaran gabaɗaya. Nan suka yi mini yini, har dare muna tare ranar kuma Yallabai ya na gidana ne daddare muna falon Yallaɓai yaran kuma suna falon su sai ga Baby ta zo kawo min ƙaran Khalipa wai yana mini tsalle saman kujera. "Ƙyale shi Baby shima gidan su ne ki bar shi ya shaƙata" Yallabai ya gano mgana na tusa masa ita kums sai ta miƙe tana faɗin don ya na gidan su ai ba za a bar shi ya yi ɓarna ba. Da motar ta  ta zo bayan isha'i ta tuka kanta da yara suka koma gida Khalipa da na ce a bar mini shi ta ce jibi za su tafi Rano ganin kamar ba ta son barin na shi ya sa sai na ƙyaleta Yallaɓai kuma na ji amma bai yi mgana ba. Sai da muka yi shirin kwanciya sannan Yallabai ya yi maganar akan maganar da na yi ɗazu a kan Khalipa. "Laa Allah ni ba da wata munafa na yi mganar ba." "Uhm to shike nan tun da kin ce haka." Da haka a ka bar maganar amma na ji sanyi a raina tun da ya fahimci in da magana ya dosa. Ni dai ban san ya abin ya ke ba amma ranar da Khalipa ya zo gidana zai kwana da ya yi barcin uban ya kai shi ɗakin su Jidda ya kuma ce ko zai yi kukan jini su bar shi in ya gaji zai kwanta. Sai ga shi ranar barcin mu ka sha, sai da safe Jidda ke faɗin ya tashi yana rigima ya na kiran sunan Abba da ya ga an yi banza da shi ne ya koma ya kwanta. Tun daga lokacin na samu lafiyan Khalipa a raina na ce daman iskanci ne da na yi shuru da yanzu an daɗe ana cuta ta. Ganin mun samu jituwa da Yallaɓai a wani dare da yana gida na bayan mun gama samun natsuwa sai na ce masa ina so zan koma makaranta. "Makaranta? Wata makarantar? Islamiya? Yallaɓai ya tambaya cikin mamaki. "A'a boko dai. Masters nake so na koma na yi." Kawai ba sai Yallaɓai ya fara mini dariya ba sai ka ce ya ga mahaukaciya sabon kamu nan da nan na harzuƙa. "Mene abin dariya a mgana ta? Sai ya dakata yana faɗin" Ki yi haƙuri amma mganar ce ta ba ni dariya ke yanzu gotai gotai da ke da budurwan ƴ'a ki ce za ki koma makaranta? "To ana girma da karatu ne? "A'a kawai dai." Sai kawai ya cigaba da dariyan shi. Na cika na yi fam ina shirin fashewa. "Kin ga yi haƙuri." "Izinin ka na ke nema shekaran da za mu shiga nake so na koma." "To ai ni ba zan hana ki ba amma da zan ba ki wata shawara." Sai na kalle shi ta wutsiyar ido duk da akwai duhu a ɗakin amma muna kallon juna ta hasken dake shigowa ta jikin labulan window ɗin bedroom ɗin.   "Kina so? "Ina jin ka" Na faɗa a daƙune. "Ki haƙura da karatun nan Sadiya. Digree gare ki fa yanzu mata ne nawa ne ke neman kwalin karatun ki ba su samu ba? Komawa makaranta abu ne mai kyau amma wahala kawai za ki ƙara ma kan ki a yanzu. Saboda ƙwaƙwalwar ba za ki haɗa ta da lokacin baya da na yanzu ba? "Wannan ne shawaran? Na faɗa ina kallon shi domin so na yi ma na juya masa baya. "Shawaran ita ce ki bari kawai na ƙara miki jari ki cigaba da kasuwancin sai da hijaban ki kawai " Ya gama faɗa har yana wata dariya. Raina ya ɓaci na ƙufula. "Ka ba ni izinin na cigaba da karatun? "Why not in kina sha'awa? Sai na ce Allah ya ba da sa'a." "Amin" Na fada azafafe sannan na juya masa baya sai ya biyo ni ya na faɗin" To jarin fa? "Ba na buƙata" "To shike ko kuɗina sun huta" Ya faɗa yana mini dariya kara shige min ya yi yana tsokanata da Sadiya ta masu mastars ke dole sai kin kamo kwalin karatuna ina jin sa na yi masa banza domin haushi ya ba ni ya ina mganar cigaba na kuma yana mini dariya. Tun daga lokacin ya samu sara da na yi magan sai ya ce su Sadiyallle masu degree da Masters ni ko na ce da ikon Allah, na gane in ina fushi ma ya fi jin daɗin tsokana ta sai na daina nuna na ji haushin shi, Maganar jari kuma tun da na ce ba na so bai ƙara mini mgana ba, ni kuma da gasken ba na so shi ya sa ma har su Ya Hamza na faɗa ma zan koma makaranta da na ce Yallabai ya amince fatan alheri kawai suka yi mini.  Na gama shirina tsab saboda muna tunkaran sabuwar shekara da cewa ko Yallaɓai bai taimaka mini da sisin shi ba zan kwashe jarin hijabai na koma makaranta da shi. **** *2020* Da gaske na ke yi na nemi gurbin Masters a BUK Kano, kuma har na samu, har na yi cuku cuku, kuma ilai dai bangarena na farko na sake ɗauka na kula da tattalin arziki wato Economics Sannan Jidda na son ta biya Jamb tun da sai bayan sun rubuta Jam ɗin za su fara jarabawar su ta WAEC.  Ko lokacin da Jidda za ta cike Jamb tare da Musbahu suka je ni ban san ina ta cike ba sai da ta dawo take faɗa minI a first chioce ABU Zariya ta cike. "Ni dai ba ruwana kin san dai Abban ku ya ce a garin nan za ki yi karatu ba ya son nesa." "To ni Umma ina son ABU ne kuma ai ba ga Kawu Hamza a zaria ba" Kallonta na yi kafin na ce" Ya san da shi ɗin ya ce ba za ki je ba" Za ta fara mini magiya na katse ta faɗin" Ba ruwana na ma faɗa miki." Ai ko da ya dawo ta faɗa masa ta sha faɗa ya kuma ce mata ta ma cire rai ba anan za ta yi ba BUK za ta yi domin ba ya so ta yi nesa.   Jidda na ji ta na gani dole ta cire rai tun da Ya ce ba za ta je ba to mgana ta ƙare. A she ya je sun yi mgana da Gimbiya itama ta roƙe shi, amma ya ce ya gama mganar sa. Ni daman ban saka baki ba sabo da tun da ya kafe da wahala ya sauya ra'ayi infact nima shirin nawa karatun nake  yi Yallaɓai tun ya na ɗauka wasa ne har dai ya ga na miƙe ga kaina. Wasu abubuwan duk ta online Datti ya yi mini su sauran kuma na shiga cikin makaranta na ƙarisa. Da dai Yallaɓai ya ga tabbas na samu addmission har ya na zuga ni wai na yi part-time. Ni ko na ce full-time zan yi. Ɗa gare ni ko jika da zan yi part-time sai ya yi shuru. Ina shirin yin rigistration ne Yallaɓai ma ya ba ni kuɗi ya ce na hidimar makaranta ban tambaye shi ba kuma da bai ba ni ba, ba zan tambaya ba. Kwatsam kawai aka fara cutar corona a Negeria, daman tun december 2019 cutar ta fara ɓulla a na mganar ta a kafafen sada zumunta. Kafin a motsa ta fara yaɗuwa a Nigeria kafin ka ce me an shiga lockdown wannan hutun na corona shi ya ruguza burina na komawa makaranta Yallaɓai sai ya koma yana mini dariya har wani suna ya saka mini wai mai kwalin masters zaman gida dole. Sai ga shi da ga ni har yara mun koma mun dafe a gida. Jidda ke ba ni tausayi su da ke da shirin zana jarabawar fita an yi musu tsiya. *Janafty**TKG0B30D4* *Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.* Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732 Ban ji daɗin ɓullowar cutar corona ba, sannan ban ji daɗin lockdown ɗin da a ka san ya mana ba gabaɗaya ƙasa ta tsaya waje ɗaya cak. Ba makarantu ba zuwa aiki komai ya tsaya, in fita ta kama ka dole sai ka saka takumkumi kamar wani ɓarawo kana tsaka tsan tsan. Shikenan Burina na son komawa makaranta ya tsaya cak shima amma duk da haka ban karaya ba faɗa ma kaina nake yi na san na ɗan lokaci ne kasa za ta daidai ta na cika burina na komawa makaranta. Kowa na cikin takura da wannan lockdown ɗin amma sai na ga kamar Yallaɓai shi murna ma yake yi, ko don ba aikin gwammati yake yi ba ne wataƙila domin ya ga na shi ayukan ba su tsaya ba ne shi ya sa. Sai daga baya na fahimci har da zama na a gida ban samu tafiya makaranta ba kamar yadda na ci buri saboda ba shi da aiki sai tsokana ta har wani suna ya saka mini yanzu Hajiya Saadiya mai kwalin mastes. In kuma ya tashi tsokana ta da cewa masu masters dai an koma zaman gida tun ina nuna jin haushina shi kuma ya yi ta dariya har wani jin daɗin tsokana ta yake yi ranar dai na gaji na ƙufulu na ƙudirta a raina in ya sake tsokana ta sai na mayar masa da martani kamar ya ko san ina jiran shi sai ga shi ranar ya kwana a gidan Gimbiya sai ya biyo nan gidan da safe mu gaisa sai ya iske ni na ci gayu na cikin riga da wando ina zaune a saman kujeran falon ina danna waya ta lokaci ɗaya kuma ina ɗan kallon talabijin ɗin da Baby ta kunna cartoon a ke yi a MBC3. Da Surraya Dee mai kyan ɗa'a muke chart na tura mata ciko kuɗin ta domin satin da ya wuce na siya mganin sanyi da haɗin kaza. Tana ta mini tsiya saboda sai da ta ƙara kirana ta ce ta ji shuru ba ta ji ni ba, ni kuma na ce mata lokacin muna ɗan hatsaniya ne da megidan da ya ke ta san yanayin tun da itama matar aure ce. Ta ce Mazan ne sai a hankali su yi tutsu in sun so a yi daɗi ana yi in suka so tsiya ma sun san ta kan shi. Shi ne fa muke ta hira da ita a kan matsalolin rayuwa na yau da gobe. Jidda na ɗaki tun da suka daina zuwa makaranta in dai ba aiki za ta yi ba tana cikin ɗaki tana karantu Baby ce yar falo mu yi ta hidiman mu, itama ɗin yau ta na can falon Abban na su ta na zane zane a takardu ta bar ni, ni kaɗai ina ta danna waya ta. To tun da an kulle mu a gida sai kafafen sada zumunta suka zama ababen debe mana kewa. Na ji shigowarsa suna mgana da Baby a falo ban tashi daga zaunen da nake ba sai ga shi ya shigo cikin shigar ƙananun kaya ni Yallaɓai har mamaki ya ke ba ni shi bai son ya girma ba ne? Ko don jikinsa ba ya nuna shekarun sa? Ya kama kafar wajen shekaru arba'in da bakwai amma kuma yana jin kansa kamar ɗan shekaru talatin. "Wannan kallon fa Madam? Ya faɗa lokaci ɗaya yana jan hancina. Ashe ya ƙariso har gaba na ban sani ba. "Ko na yi miki kyau ne? Ya sake faɗa yana mini murmushi har yana kashe mini ido ɗaya. Sai na yi dariya kafin na ce" Wani kyau? Ina kallon ka ne, a raina ina cewa Yallaɓai na ya fara tsufa" Yana zama gefena yana faɗin" Ko? Ke dai ce da mganarki amma ni har yanzu ji na, na ke yi kamar ɗan saurayi mai shekaru talatin." Sai na buge kafaɗansa ina dariya kafin na ce" Jidda fa ƴ'ar ka ce? Ko ka manta ne? Sai ya jawo kafaɗata saman tashi ya saka hannunsa guda ɗaya ya zagayo ƙuguna da shi. "To sai me! Ke in ba fa na faɗa ba ɗan Saurayi a ke kallona. Kuma tsab in na tsai da budurwa yar sha za ta tsaya mini" Hararan sa na yi kafin na ce" Wai ko dai ƙara aure da za ka yi da yarinya ƙarama ne Yallaɓai? "Me kika gani? Ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa. "To na ga da an fara mgana sai ka ce ko yanzu za ka iya auro yarinya yar sha sa'ar Jidda." "To in ma da gaske ne Haramun ne? Ai sai na buɗe baki ina kallon Yallaɓai. Ganin na kasa mgana ne ya sa ya rufe mini baki yana mini dariya sai na ture shi gefe ina hararan shi. Shi kuma ya na ƙara naniƙe ni ina ture shi yana minidariya. "My Sady kishi" "Ina ruwana ai ba a kaina za ta zauna ba kuma ai ni ka gama mini kishiya. Gimbiya ce a kan layi " Dariyan nishaɗi ya yi kafin ya ce" Ka ji ta kamar gaske" Na yi masa banza saboda na ga alamun ya na so maganar ya yi dariya ya na jin nishaɗi. Da gaske nake yi ai ni ya gama mini kishiya ko wata zai aura sai dai Gimbiya ta ji ƙwatan ƙwancin yadda na ji a lokacin da ya auro ta. Kallon sa nake yi yana tambaya ta Jidda na ce ta na ɗaki sai ya tashi ya shiga dakin na bi shi da kallo. Yallaɓai bai taɓa ce mini yana sha'awan tara mata ba amma ni a ƙasan raina na ke jin giyar kuɗi za ta iya ɗibar sa ya ji mun yi masa kaɗan kuma wannan wargajenjen filin da na ji labarin ya siya ba, ba iya ni da Gimbiya ba ne. Wataƙila shashen mata huɗu ne zai gina a hasashena tun da bai taɓa furta mini haka ba. Ya ce sai an gama ginin kamfanin shi an buɗe shi sannan zai fara ginin gida can kwanaki ma da muka bi ta hanyar na ga Kamfani ya yi nisa kaɗan ya rage a ƙarisa. In ana misalin maza jajirtattu masu jajircewa da juriya to sunan Yallaɓai zan fara kamawa a shekarun da na san shi sama da shekaru goma sha takwas ya jajirce domin mafarkinsa ya tabbata na gina kamfanin shi, domin ya taimaki matasan da aikin yi to ko a haka ya tsaya wallahi ya cigaba domin matasan da suke aiki a ƙarkashin shi shi kan shi bai san iyakar su ba. Da masu ilimin da ma waɗanda ba su da ilimin duk na shi ne, masu ilimin suna aiki a bangaren ma'aikatan shi mara sa ilimin kuma suna aiki a bangaren kwangilan gine ginen shi. Kuma ya na da tausayi da kyautatawa ga kuma mu yadda ya ke kyautatama mu da iyayen shi, shi ya sa Allah ba zai bar shi ya taɓe ba. "Ke wai me ke damun ki kike yawan shiga tunani ne? Na ji yana faɗa lokaci ɗaya ya na mai zama a gefe na. Har ya na wani jawo ni jikinsa yana shafa bayana zuwa kuguna sannan ya cigaba da faɗin. "Uhm mene ne. Faɗa mini damuwarki yanzu na yi miki mganin ta." Kamar abun arziƙi na ɗago ina kallon shi kafin na marairai ce ina faɗin" Yallaɓai wai yaushe za a buɗe gari ne? Tsakani ga Allah ba a kyauta mana ba da yanzu fa mun yi nisa da lectures" Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba, har ya na ƙyaƙyatawa. Ni kuma sai na haɗe rai na koma gefe na yi bakam. Ina jiran ya taɓo ni sauke masa jin haushin shi da nake ji. "Ai in za ki shirya zaman gida ki shirya. Domin cutar ma ƙara yaɗuwa ta ke yi ba ma maganar a buɗe gari." Kallona ya ke yi fa yana tsintsira min dariya. "Hajiyar Masters. Ki yi wannan master ɗin ki a gidan auren ki, taho mu je ciki ni ma ai malamin ne sai na baki karatu" Ya ma miƙo hannu ya kamani na bige hannun shi ina hararan shi amma bai saka ya daina dariya ba. "Yallaɓai." Na kira sunan shi a tsume. "Na'am My Sady masu kwalin masters" "Ni dai ko murna kake yi da faruwan wannan abin ne? Ko daman can da ka ce ka bar ni na koma makaranta ba har zuciyar ka ba ne? Na ƙarishe ina mai kura masa ido. Ya na danne dariyarsa ya ce" Wallahi har raina na amince miki. Ya za a yi na yi murna da haka? Ya ƙarishe faɗa yana daga hannu sama amma bai daina mini dariya ba. "Na ga kamar murna kake yi. Wato gara da a ka yi haka ko? "Murna kuma! Da girmana Sadiya? Ya faɗa yana sosa sajensa amma bai daina dariya ba kawai sai na miƙe fuu da wayata ina faɗin"Ohon in ma ka na murnan gwara da a ka yi ne gwara ka daina saboda ba ni kaɗai ba ce a gidan har da ƴaƴan ka" "Kuma haka ne fa." Ya faɗa yana kuma cigaba da dariya. "Kuma in sha Allahu, za a buɗe gari kuma zan shiga makaranta Ehe." Na faɗa ina mai barin masa falon sai ya biyo ni yana faɗa mini. "In sha Allahu wa ya isa ya hana ki zama mai kwalin masters" Gabaɗaya Yallabai ya mai da ni abar nishaɗinsa na so ina shige ɗaki na rufe ne sai ya shammace ni ya biyo ni yana faɗin shi fa ba dariya yake yi mini "Wallahi in na tuna yadda kika ci burin karatun nan sai na ji duk ba daɗi. Sorry My Sady in sha Allahu zaman gidan ba zai yi tsawo ba." Wani kallo na yi masa saboda yana faɗa ne amma yana danne dariyan shi kawai sai na fusata na jawo filo na wurga masa ina faɗin. " Ka fita Yallaɓai" "Na je ina? Har tsayawa yake yi yana tambaya ta, sai na ƙara rarumo ɗayan ina ƙokarin jifan sa da shi sai ya mamayeni ya rumgumeni yana mini dariya ni kuma ina fizge fizge sai ya fara min cakulcakuli a dole sai na yi dariya. Yallaɓai akwai mugunta wallahi sai da na yi hawaye, har fa sai da na ce masa zan yi fitsari a wando in bai daina ba sannan ya ƙyaleni. Bai bar gidan ba sai da na dai na fushi na dawo ina dariya ni ce har haraba na raka shi muna soyewar mu. ***** Tun ina saka ran za a buɗe gari na yi registration ɗin makaranta har na cire rai ganin har mun shiga wata biyu muna kwararan na uku, sai na ce gwara na zauna na yi ma kaina tunanin mafita. Tun da karatu dai ba zai yuyu ba gwara na mai da hankalina kan sana'ar hijabai na da yadda zan ƙara ingata shi, sai na fara tunanin sunan da sanya ma kasuwancina. Da ƙwaƙwalwar ta ƙi sai na nemo Jidda na ce ta sama min suna. Haka muka zauna muna ta zaɓe har sunana ta haɗa ni da Yallaɓai SADYUF na ce ba na so da a baya ne zan iya haɗawa dashi amma tun da ya yo mini kishiya na fahimci Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai. Ta haɗa da haruffan sunanta da na Baby na ce ba na so sunan ya yi kama da na ma'aikatan Yallaɓai ne. HM TAFIDA AND SON'S LIMITED. Sai na ce a samu dai wani ganin zai yi wahala na ce kawai ta haɗa min da sunana, mun yi kwanaki ba a samu wanda ya yi min ba sai da na ce mata ina so na saro inears wear sai ta ce to bari a haɗa gabaɗaya. Da ƙyar dai Jidda ta samo min SADY S YASHE HIJABS AND MORE. Sai na ji sunan ya kwanta min arai nan take na ce bari mu tafi da wannan sunan kawai. Musbahu na nema tun da shi ne ɗan gida ne kuma idon gari ne kusan ya san ko'ina. In da Allah ya taimake ni kuɗin da Yallaɓai ya tura mini na hidimam makaranta da na ce zan mai da masa sai ya ce na riƙe na ƙara jari ya bar mini, da su na yi amfani domin ƙara bunƙasa kasuwancina. Musbahu ya shige mini gaba a ka buga mini ledojin da tambarin logona na SADY S YASHE HIJABS AND MORE. An yi manya da ƙanana sannan an yi na kwali su na manya costumer ne Sannan an yi min sticker na mannawa a jikin kaya bayan na siya ledoji farare da zan riƙa saka hijaban da kayan in an siya. Tun dai an samu zaman gida bari mu kama sana'a zama bai ganmu ba. Musbahu ya saka cikin masu zanen su na kamfani ya zana min logo mai kyau na saka shi a duka handle ɗina na kafafen sada zumunta. Kuma kowa ya gani sai ya ce sunan ya yi kyau. Ya Hamza sai da ya ce bai ga sunan Yallaɓai ba ina dariya ban ce komai ba har Ma'u da muka daɗe ba mu yi mgana ba da na ɗora a status a ƙasa na yi caption da cewa. "SADY HIJABS AND MORE. Muna siyar da nau'in hijaban da kuke so sannan za mu fara kawo muku inners wears, kamar su pants, bra, sikat, mini trouser and more. Please potonorize your Sister. Sadiya Sulaiman Yashe C.E.O" A nan Yallaɓai ya gani ya yi tagging ya turo mini dariya. Na shaka na auna masa naushin hannu na sticket kawai sai ya yo mini Vn ranar ma ba a gidana ya kwana ba yana gidan Gimbiya amma a daran zai dawo gidana. "Daman shawaran nan na kawo miki tun farko kiƙa ƙi karɓa. Duk wanda ya tuba don wuya ba lada." Haka ya ce min fa sannan ya ƙarishe da dariya. Ina masa Typing sai ga shi ya sake turomin mgana. "Congratulation My Sady. Duk abin da kika saka ma suna ko hannu sunan shi Nasara. I wish you the best" Kalamansa suka wanke mini zuciya na fasa tura masa abin da na yi niyya. "Thank you Mijin Sadiya." Kamar ya ijiye wayar amma dai ya tafi bai kashe data ba. Mutane sai fatan alheri suke yi mini har Anty Maimuna sai da ta ce yana da kyau kam na ƙara da wani abun Anty Zuwaira kuma ta yi tagging da zamu siya in sha Allahu. Daman ita ai ba ta da matsala Anty Bahijja ne ta gani ba ta yi mgana ba. Amma har Gimbiya ta yi mini murna sannan ta ce za ta yi mini talla a status ɗin mutanenta su gani ko za su siya na ce Na gode. Daga nan na kashe data na sauka sai zuwa can an juma Sameena ta kira ta ce ta na son hijabai da na pant da bra shi ne take faɗa min a status ɗin Yallaɓai ta gani ya ɗora sai da muka gama waya sannan na buɗe data na gani. Ya saka ne amma bai yi wani rubutu ba. Na ga kara domin sun ta sakawa a status suna yi mini tallah. Marwa ma ta saka Hauwa ma da ta yi waya Munnira ma haka yan gidanmu Ya Balki sai Amina har da Datti Ya Auwal dai da Ya Hamza ba a saka su a lissafi su waɗanan ba su damu da saka statua ba irin Yallaɓai ne. Ya Abubakar kuma shi wannan ɗan buga buga ne bai ma cika hawa online ɗin ba. Gidan su Yallabai su Musbahu ne da su Adnan sai Jawahir da su Suwaiba sune daman nawa. Duk kuma wanda ya ga logon zai ce zane ne, ma su abu da abin su kura da kallabin kitse. Kamar wasa na yi ta samun odar masu siyan hijabai da inners barin ma da azumi ya ke tunkaro mu. Da ya ke a mota kawai ake saka mun ina tura masa bayanan da kololin na Hijabai inners kuma sara na yi da yawa na yara da manya na tura kuɗi a ka kawo minI har na cin kasuwar salla. hijaban dai sai na ƙaro tun da guda 50 na ce a akawo mini. Da suka iso duk wanda ya siya ni da Jidda muka yi zaman saka su. A leda muna manna sticker sai lamarin ya burgeni ni kaina komai da tsari kan ya fi burgewa Jidda ta yi Vadeo muna saka sticker ta kuma ɗora mini a status ta ce kaya sun iso. Nan da nan cikin sati ɗaya kaya suka ƙare sai na sake tura kudi ɓarin ma Inners ɗin sun tafi yadda ma ban yi zato ba daman su Hijabai ana siyan su sosai. Wannan karon sai na ce a sako mini da mayafai da kayan barci suma dai ba laifin ana ta siye da na gida da na waje. Sana'ata na riƙe gadan gadan. In dai ka ganni da waya to ina can ina marketing. Yallabai har suna ya sauya min wai hajiyar Hijabai ni dai na ce ka ji da iyayin ka tun da karatun dai bai zo hannuna ba gwara na kama abin da ya zo hannuna. Ana cikin haka a ka kawo mana kayan saka ranar Suhailat ɗin Anty Bahijja bayan sallar azumi za a yi bikin kuma Kaduna za a kai Amarya. Ni da kaina na kira ta a waya na yi mata Allah ya sanya alheri. Ni ba na gaba da ita muna gaisawa in mun haɗu amma daga wannan gaisuwan kowa sabgan gaban shi yake yi tun da aka yi mana tsakani ni da ita. Cikin ikon Ubangiji muka riski watan ramadana cikin lockdow abubuwa duk sai a hankali saboda yanayin zirgan zirgan gari duk da ba kamar lokacin gari na sake ba wannan karon ma Yallaɓai ya siya buhun gero da siga sai wake buhu ɗaya na alale da ƙosai na kai ma Maman Saude yin kunin ita kuma Maman Nana mai yi min kitso a ka ba ta yin ƙosai da alalen. Sannan ya rarraba ma matansa da ke aiki a ƙarkashin sa kayan abinci wasu kuma ya ba su kuɗi, daga can Rano Kawu Abba ya aiko mana da su ƙwai da dankalin turawa. Nima Yallabai ya ba ni kayan abinci har da kuɗi na kai gida duk da na san itama Gimbiya ya ba ta ta kai can Rano amma ni bai gaya mini ba, ban nemi da sai na ji ba kuma Azumi ashirin da tara muka yi kuma ban sha ko ɗaya ba ko da ban ga period ɗina ban damu ba, ko watan da ya wuce ma bai zo ba saboda an sha yin azumi ni ban sha ba sai ban saka tunanin komai a raina ba. Yallaɓai ya yi mana kayan alfarma ni da yara har salla ta wuce muna saka sabbin kaya sannan ya yi ma iyayena har Inna Mariya ya yi ma turmin atamfa wannan shekaran. Ni kuma na caɓa da cinikin hijabai da inears wannan sallar kaf su Ya Hamza wajena suka yi ma iyalansu siyayya kuma na ji daɗi a dangin Yallaɓai kuma su Musbahu ne da su Anty Zuwaira har Anty Maimuna ta siya ma yara. Gimbiya ma ta siya kuma ta kawo mini costumer kuma na ji daɗi na gode mata. Yallaɓai ma kuɗi ya ba ni na yara sai kawai na cire musu a ciki da ni kaina na saka kuɗin a ciki. Kuma ba abin zan ce ma Allah sai godiya ina samu ina yi ma kaina hidima sannan abu na ƴan uwa ya ta so ina ɗauka na yi ba sai na je ina yi ma Yallaɓai yar murya ba. An ɗaga bikin ɗiyar Anty Bahijja sai gab da babbar sallah a bakin Munnira nake jin wai uban mijin ne ya biya ma Sulaihait ɗin kujeran makka tare da mijin ana ɗaura auren za su tafi tare na ce Allah ya sa su je lafiya su dawo lafiya. **** Kamar kar a yi salla sai na fara rashin lafiya. Kuma rashin lafiya irin a tsatsaye haka. Kasala ya riƙa damuna na dai na cin abinci komai ba ya mini daɗi ban da kunin tsamiya mai zafi ba abin da ke shiga cikina. Sannan ba na iya shan kowani ruwa. Ba ni da aiki sai kwanciya tun ina ganin abin wasa har dai na fara tunanin watakila ina da ciki. Tun da in dai na ci abinci sai na yi amai ga Yallaɓai ba ya nan ya je Dutse wajen kwanan su huɗu a can, karyata kaina nake yi da ba ciki gare ni ba saboda ko wancan da na yi ɓarin shi ban ga alamomin shi ba sai kawai na fi amimta da maleria ke damuna na saka a ka siya mini mganin maleria na fara sha. Ai duk ranar da na sha sai na yi amai sannan sai na fara miyau ba na iya haɗiye miyau. Sannan na yi ta kwana da zazzaɓi gari na wayewa sai na ji sauki. Jidda ta ce za ta rakani asibiti na ce ba zan je ba har waya ta sata ta yi ma Yallaɓai waya ta faɗa mai halin da na ke ciki sai ya ce ta ba ni wayar haka ya riƙa mini faɗa ya kuma ce umarni ne maza maza na tashi na shirya Jidda ta rakani asibiti na ga likita. Ba yadda na iya haka na shirya. Sai a lokacin na fahimci na rame sannan na ƙara haske, wani asibitin kuɗi muka je muna zuwa suka yi mini tambayoyi na faɗa musu wajen wata uku kenan ban ga al'adata ba sun ɗibi jinina da kuma fitsari muka zauna jiran sakamako Yallaɓai kuma sai kira ya ke yi Jidda ce ke ɗaga kiran ni ina ta kaina sai kwanciya nake yi a kujerun asibiti. Lokacin da sakamako ya fito likita ya ba ni farar takarda sannan ya faɗa mini ina da shigar ciki ɗan kimanin wattani biyu da kwanaki. Duk da alomomin masu ciki sun bayyana a tare da ni ban saka ma kaina yaƙini ba. Hawaye suka zubo minibsai na sharce su a cikin raina na yi ma Allah godiya sannan na yi masa kirari. Jidda na wajen domin ita ta riƙe ni muka shiga da muka fito ina riƙe da takardan muka samu adaidaita da zai mai da mu gida. Amma sai da Jidda ta biya Pharmacy ta siya mini magungunar da ya rubutamin na ƙarin jini da na cin abinci. Da farko da Yallaɓai ya ce zai kira Salisu ya kai mu tun da motar na hannun shi in fita haka ta kama ina kiran shi ni na ce ya ƙyale shi mu fita mu hau adaidaita sahu. Har a cikin adaidaita kwanciya na yi da leda a hannuna ina tara miyau duk cikina da na yi da ga na Jidda har na Baby ban yi miyau ba, kai ban ma yi wannan laulayin mai wahalar wa ba. Tun kafin mu kai gida Jidda ta kira Yallaɓai tana murna tana faɗa mai likita ya ce Umma na da ciki. "Jidda da gaske kike yi? Ina ji saboda wayar an ƙure mata kara. A yanayin muryan Yallaɓai za ka san akwai zaƙuwa da zamuɗi. "Na rantse da Allah Abba Umma za ta sake haihuwa." Ta faɗa cikin har sai da mai adaidaitan ya juyo yana kallonta ina ganin shi sai da ya yi murmishi ya juya kai ya na faɗin" Hajiya yanzu daman wannan budurwan ƴar ki ce? Wallahi na dauka ƙanwarki ce ni dai dariya kawai na yi ba tare da na yi magana ba. "Ma sha Allah. Allah ya inganta.'" Na ce Amin ita Jidda ba ta ma jin sa ta na can ta na waya, ban yi mamakin kalamansa ba saboda ba shi kaɗai ya taɓa faɗan haka ba sau tari mutanen da ba su sani ba in suka ganni da Jidda sai su yi tunanin ƙanwata ce. Saboda na haifi Jidda da ƙananun shekaru shi ya sa muka ta so kamar ƴa da ƙanwa sannan na mori ƙaramin jiki. Ji kawai na yi Jidda ta manna min waya a kunne ta ce ga Abba na mgana. Sai da na cire facemark na tofar da miyau a ledan da ke hannuna sannan na karɓi wayar " Yallaɓai." "Congratulations My Sady. " "Congratulations Yallaɓai na." Na faɗa a hankali ina murmushi. "Alhamdulillah Allah abin godiya. Kin gani ko? Daman ni a jiki na na ke jin ba ki gama haifa min ƴaƴa ba Sadiya. Yanzu kin aminta da magana ta? "Na aminta Yallaɓai." Na faɗa a hankali saboda jikina gabaɗaya ba ƙarfi, faɗi yake yi yana cikin farinciki mai tsanani sai na katse shi da cewa. "Yallaɓai ban da lafiya. Jikina ba ƙarfi ba na iya cin abinci ba na shan ruwa." Na ce kamar zan yi masa kuka shi kuma sai ya ruɗe. "Sannu. Me likitan ya ce! Me ya sa ba su riƙe ki a can ba? Sai na kasa mgana domin maganar ma wahala take yi mini sai kawai na ce ya bari mu koma gida sai mu yi magana. Dalilin da ya sa ya katse wayar kenan muna ko komawa gida ya sake kira ya na tambayana yadda nake ji. "Yallaɓai miyau ya yi ta taruwa a bakina. Ni komai ma baya mini daɗi ban iya zama fa sai kwanciya ban taɓa laulayi mai zafi irin wannan ba." Yallaɓai duk ya damu sai lallashina ya ke yi, daga ƙarshe ya ce zuwa gobe zai dawo na kula da kaina. Sai da ya kashe wayar na ji taruwan kwalla ina tausayin kaina ina tausayin shi ban ɗauka bayan tsawon shekaru goma zan sake samun ciki ba. Amma na yi yaƙini da ubangiji mai bayarwa a lokacin da ya so da kuma wanda ya so. Na saka a raina in ina da rabo Allah zai sake ba ni sai ga shi kuma ashe ina cikin waɗanda Ubangiji ke yi ma Ni'ima in sun yi haƙuri ya ƙara musu a lokacin da ba su yi tssammani ba. Ban taɓa tunanin Yallaɓai zai yi mini rawan jiki in na samu ciki ba sai ga shi yana yi min bawan Allah ya na son haihuwa. Na ɗauka tun da Gimbiya ta haifa masa biyu duka maza yanzu ba ya zumuɗinta amma sai ya kore mini shakku. Lokacin da na faɗa masaa na yi ɓari da ya nuna da yakinin wata rana zan sake samun ciki na haihu bai ɗadani da ƙasa ba kamar yadda bayan samun cikin ya nuna farincikin sa. Kwana ya yi ya na kirana yana jin jiki. Jidda kam ya yi mata kashedin ta kula da ni ban san adadi ba. Baby da Jidda ta faɗa mata Umma za ta haifa musu wata Baby yini ta yi tsalle da ihu ni dai ina kwance zama ma ba na so ina yi. Washegari da rana Yallaɓai ya dawo duk da ba gidana zai sauka ba, yana gidan Gimbiya ne tun da ni ranar da zai bar gidana ya yi tafiyar. Amma duk da haka gidana ya fara sauka ya duba ni ya iske ni kwance da gwangwani miyau da a ka cika min da ƙasa. Ya rumgumeni nima na lafe a jikimsa shi ina sauke numfashi. Yallaɓai ya yi ta shafa marata kamar ya buɗe ya ga abin da ke ciki. Shi kan shi ya ce na rame bakina ya bushe ya yi ɓawo to ko ruwa fa ba na sha sannan ban iya cin komai sai kunin tsamiya. Duk bakina da surutu na bakina ya mutu. Allah ya sa Jidda na gida ita ke kula da gidan da yin abinci. Yallaɓai ya faɗa ma Gimbiya ina da ciki ya kuma kawo ta ta duba ni ita da su Khalipa, ina kwance ne ina fama da kaina a saman kujeran falon su Jidda. Ina kallon Gimbiyar tun da muka gaisa ta koma gefe ta tsume. Duk da ban da lafiya amma na fahimci kamar ranar ranta na bace ne, sai na danganta haka da ƙila ita da Mijinta ne. Ko jiran shi da ya ce ta yi ma ba ta yi ba, la'asar na yi ta ce min za ta ta fi wai za ta biya ta shago. Su Khalipa ma da Jidda ta ce ta bar su sai ta ce wai daga Shago Gwammaja za ta biya shi ya sa ba za ta bar su ba. Ni dai ina kwance amma sai da na tofa na ce ta bar su mana in Yallaɓai ya dawo sai ya mai da su amma sai ta ce kar wai su dame ni ba ni da lafiya. Ina jin haka ban takura ma kaina ba na ce su gaida Nene in sun je. Tun kuma daga ranar sama da sati ba ta dawo ba na tuna lokacin cikin Khalipa da kwanciyar da ta yi ta yi a asiniti ina jigila da ita. A raina na ce da ban haihu ba da na ji haushin duniya. Munnira ce ta kira ni a waya tana faɗa mini haihuwar Salma Yayar Jawahir C.S a ka yi mata, a ranar da ta kira ni ta ce jiya da daddare ne ta haihun shi ne ta kira ni ta ji yaushe za mu je! Tun da anan Kano ne a Dala. Shi ne na ce mata ba ni da lafiya ma ina gida. A ranar ta zo duba ni kafin in faɗa mata ina da ciki ita ta fara cewa matar injinya ciki ne da ke na ce mata e sai ta buga shewa ta riƙe hanci ta rangaɗa guda ta kuma kira Hauwa tana faɗa mata sai Hauwa ta fara faɗa min an ware ta ba a faɗa mata ba. Ni ko na ce ba wanda na sanar ma wa, nan Munnira ta yini har da lissafin sai ta ɗauko DJ ranar sunan na yi dariya kawai a raina na ce Allah ya sa na rabu dai lafiya. Washegari sai ga Hauwa ta zo duba ni. To su ne da aka haɗu ca gidan Salma ranar suna duk wanda ya ga bai ganni ba sai su ce ina gida ina fama da laulayi. Anan ne wasu suka ji, su Anty Bahijja kuma ina da tabbacin Gimbiya ta faɗa mata gwara ma Anty Maimuna in ta ce ba ta sani ba amma zai yi wahala Anty Bahijja ta ji abu ita ba ta ji ba musamman za ta kira ta a waya ta faɗa mata. Anty Zuwaira har gida ta zo ta duba ni ta ba ni dubu ashirin ta ce na siya gero tun da na ce kunu kawai nake sha ina son ta saboda wallahi tana da matukar kirki shi ya sa nake girmamata. Ita ta ce mini Nene ce ta faɗa mata ba ni da lafiya ta zo ta duba ni, Nenen kuma na san Yallaɓai ne ya sanar da ita. Mubeena na zuwa duba ni akai akai har Marwa ma ta zo ita kuma Kawu ne ya faɗa mata ita kuma ta yaɗa ma Ya Aina ta nan maganar cikina ya faso a dangin mu kowa ya ji sai ya ce ikon Allah lalle bayan wuya sai dai daɗi sannan ba a cire ma Ubangiji yaƙini in ka yi hakuri za ka ci riba. Sun zo dukkansu sun duba ni har da Ma'u Gwaggo ma ta zo har gida kuma na ji daɗi su Ya Hamza a waya suka gaishe ni da matan su. Zainatun Ya Abubakar ta zo yi min yini, ta yi mini wanki da girki ranar. Ranar da Nene ta zo ita da Hajiya iya da Maman farko a raina na ce duk abin dake cikina ɗan gata ne. Tun da har su Nene suka zo duniya. Nene ko faɗi ta ke yi Allah ya raba lafiya. Amma ko su kan su sun yi ta ƙorafin rama ta da rashin cin abinci na ce komai na ci sai na yi amai kuni kawai ke zama a cikina shima mai zafi. Ruwa ko rabon da in sha har na manta. Yallaɓai tsausayina ya ke yi sai ya ce ya za a yi ɗan adam ya rayu ba ruwa na ce to ga shi dai ka gani. Gimbiya sau ɗaya ta dawo shima ba ta daɗe ba ta tafi sai na ga kamar ba ta murna da samun cikina. Amma sai na yi saurin cire tunanin haka a raina sai na yi mata uzuri na kuma saka mata kyakyawan yaƙini. Inna Mariya ni da kaina na kira ta na faɗa mata ta yi ta murna ta kuma zo har gida ta duba ni. Ko da nake kwance in ana son Hijabai ko kaya Jidda ke mgana da mai ɗinka min daga Zaria a kawo kuma ta zauna duk ta saka musu sticker ta kuma saka su a ledojinsu shi ya sa ba ni da damuwa. Na shafe wata ɗaya da wani abu ina wannan zazzafan laulayi sannan na ɗan fara samuwa. Na fara cin abinci tuwo haka sai ɗanwake sai awara sai dambu, amma ban da su shinkafa da taliya. Duk sona da fura da kayan marmari na daina son su yanzu, ruwa kuma na fara sha amma sai mai sanyi ko na ce mai ƙanƙara ya na narkewa ina sha. Yallabai ya yi ta faɗa wai sanyi zai kamani amma shi kan shi da ya ga shi ne ruwan da na ke sha sai ya ƙyale ni. Na ɗan fara samuwa tun da na daina kwanciya kasalar sai dare ya yi yanzu ta ke nika min jiki, sannan tun da na fara laulayin nan ban yadda mun yi ɓarnan ruwa da Yallaɓai ba to ina ta kaina. Shima kuma bai matsa mini ba, kuma bai sani ba kwata kwata abin ne na ji ba na ma son shi. Na ɗan fara dan kiɓan kumatu amma fa kaya na duk sun yi mini yawa. Na faɗa a raina na faɗa asarari da cewa wannan cikin ɗan gata ne shi ya sa ya ke wahalar da ni. Amma dai na ji sauƙi sosai ba kamar kwanakin baya ba. Cikina na wata uku cikin na huɗu aka fara hidiman bikin Sulaihat ɗin Anty Bahijja. Matar nan ba ta zo ta duba ni ba duk da ta san ba ni da lafiya. Amma dai Anty Maimuna ranar ta biyo Nasara sun taho tare. Da Anty Bahijja da Halima ba su zo ba daman ita Halima tuni ta koma bangaren Gimbiya. Yarinyar nan mun sha haɗuwa a Gwammaja ko sha'anin su ta yi kamar ba ta ganni ba. Wai ni ce Halima ta ke gani ta wulaƙanta, lalle na yarda rayuwa ta na cike da mutane masu abin mamaki. Yadda ba a saka ni a shirye shirye ba, ban tusa kaina ba an dai fidda ankon mother eve da na yinin biki. Yallaɓai ya siya mini tun da matarsa ce ta ɗauko Gimbiya. Jidda kuma Anty Zuwaira ta yi mata tare da sauran sa'aninta su Farhan Anty Maimuna Baby ma su suka yi mata, ni ina fama da kaina ba ma ta kan bikin na ke yi ba, bikin zai kama babbar salla saura kwana tara ne. Na dai san Kaduna za a kai ta. Bikin kuma zai yi jama'a tun da har Anty Zabba da muka yi waya ta ce za su zo gabaɗaya har da yara tun da ba makaranta. Sannan kaf su mazan gidan da ke zaune ne sa za su taho da matan su. Matar Jafar ce kawai ba za ta zo ba ita za ta tarbi bakin nan in ji Anty Bahijja, nima duk a bakin Munnira na ke jin wasu labaran a bakin ta na ji su Gimbiya su ne ƙirjin biki sannan har list an yi na mutanen da za a tafi da su a kaduna. A dalilin ina fama da kaina ban ji a raina zan je kai Amarya kaduna ba, ko da ma ina lafiya ba zan tusa kaina ba. Ban je gidan bikin ba ma sai ranar laraba da a ka yi mothers eve ɗin. Yallaɓai ma cewa ya yi in ba zan iya ba na yi zama na su Jidda su tafi sai na ce zan iya. Tare da su Hauwa muka tafi can muka iske matar Muhammad Kabir Nafisa har Faridan Tariq ta zo Marwa ma ta zo muna tare da ita tun da gidana ta sauka. Anty Bahijja ta sha gayu ka ce ita ma Amarya ce da ƙawayenta suma yan gayu su Gimbiya ana ta shiga da fita har makeup ta yi su Khalipa ma an sha gayu. Anwar ne ma na gan shi a hannun Baby ta na fama dashi, Ni dai na je na gaishe da uwar biki na yi mata fatan alheri shi ne ta ke ce mini an ce ba ni da lafiya na warke kenan na ce mata Alhamdulillah. Kowa ya ganni sai ya ce na rame amma fa na yi shar da ni. Suwaiba kam har sai da ta ishe ni wai ban ga kyan da na yi ba ne ko Tafida ya ganni kafin na fito na ce ban sani ba. Mun haɗu da Gimbiya amma ba ta minI mgana ba da cewa ita ta na fama da jama'a ba ta ganni ba ni ko na ce ba zan bi ta domin mu gaisa ba. Ita da Najan Anty Zuwaira ne akan komai kuma suma sun ui gayyar ƙawayen su irin su yan gayu kirari kawai suke yi mata tun da kusa damu suka zauna a haraban gidan in da aka saka kanofi da kujeru. Su Ma'u ana gefe ba karsashi to ta ga iyayenta a kinibibi dole ta koma baya. Gimbiya suke ta raba takeaway da snack a ciki da naman kaza sai ruwa da lemu. Da ta zo wajen ƙawayen na su sai shewa ya hau ta shi ana yi mata kirari. "Ka ga Saudatu sa'ar mata. Gimbiya kike sunan ki ne. Kuma kin cika Gimbiya a zuciyar Injiniya Yusuf Tafida. Takawarki lafiya giwar Tafida. Takawarki lafiya Amaryan Tafida. Takawarki lafiya uwar maza a gida ko da kika je an haihu amma ke da kika tashi sai kika yi irin haihuwan da ba a taɓa yi ba. Ka ga uwar maza a gidan Alhaji Yusuf Tafida. Ko gobe aka sake masa haihuwa ba za a kwantata irin ta ki ba" Sai suka buga shewa ta miƙa hannu suka tafa ta jiya musu kugu kafin ta ce" Wallahi ko gobe aka sake masa haihuwa ba za ta kama kafar irin tawa haihuwar ba faɗi ki ƙara." Ta faɗa ta na wani fari da ƙara juyawa. "Takawar ki lafiya ki juyi dai Gimbiya a girman ki ne. Kin ci lokacin kuma za ki ci na wasu in sha Allahu kuma daga kanki ba ƙari kin cika duka gurbaben mata huɗun nan" Sai kawai ta ɓalle jaka ta fara zazzaga ma mai yi mata wannan kirarin kudi suna ta ihu da shewa sai hankula duk ya koma kan su. Duk da Maganar suke yi amma ko waye ya ji ya san magana ce mai harshe damo ko na ce habaici. Hauwa ta kalleni ganin na yi shuru kawai ina zaune. "Kamar fa da ke suke. Wai ko da ta zo an haihu amma ba a yi kamar irin ta ta ba" "Kuma wai ko da an sake haihuwan ba za a sake irin ta ta ba" Munnira ta amshe itama. "Da Sadiya fa suke yi. Shi ya sa na tsani Gimbiyar nan munafuka ce baƙn ciki take yi kin samu ciki ta so ne ita ta yi ta haihuwa ke kuma ki zama yar kallo." Hauwa ta saki tsski kafin ta ce" Wallahi haka ne ma. Sai kin ji mganganun da take zuwa gida ta na yi. Ta yi ma Tafidan da Dangin sa haihuwan da ba a taɓa yi masa ba. Tun da ta haifi maza har ji fa na yi wai ta ce yadda ya ke son su Khalipa ko su Jidda albarka." "Ka ji sakarya. Ya fara samun su Jidda? Ai wallahi ƙarya ta ke yi.' Baƙin ciki suka hana ni mgana amma na daure jin Munnira ta ce wallahi za ta tashi ta je ta yi musu mgana sai na riƙe ta ina faɗin" Rabu da su so suke a tanka a yi wani abu kuma ace ba mu da gaskiya ku ƙyaleta. In za ta je ta faɗa ma duniya cewa Yallabai ma ya fi son ta a kaina ni bai dame ni ba. Fatana na sauka lafiya." "Allah ya sa ki haifi namiji na ga ta tsiya." Sai na yi mirmishi ina tuna wayar da na yi da Dr. Aisha AKTH. da na faɗa mata ina da ciki ta yi murna karshe ta ce Allah ya kawo boy ni kuma na ce mata ko boy ko girl duk wanda ya Allah ya bani ina iso. Yanzu ɗin ma cewa na yi. "Ko namiji ko mace duk wanda Allah ya ba ni iso." Suna kallona sai na kaɗa kai kafin na ce" Ni ba ruwana da jinsi Ni ko duka mata zan tara ina so. Ita haihuwan maza ke gabanta." Daga nan na kashe maganar. Amma har Suwaiba sai da ta zo wajen mu ta na zagin Gimbiya a cewarta ni ban yi kishi da ita ba ita da ta aure mini miji sai ita. Ant Zabba ba ta wajen da ya ke so sun iso har da Amaryan Usman ɗin itama da tsohon ciki za ta yi haihuwa na uku kenan itama kamar Gimbiyar gwarne take yi. Da ta zo wajen mu ta ji ana mai da zence ta yi ta mini masifa ta na faɗin ina da sanyi na daina sanyi da kishiya za ta rika cin kasuwarta a kaina na yi dariya kawai ban ce komai ba. Sun yi fa abubuwa Gimbiya da gayya ta ke komai amma ni ban biye mata, sai mangariba a ka tashi sai a lokacin Ant Zuwaira ta zo tana zuwa kuma ta nemo ni ni da Munnira da Anty Zabba ta ce mu shirya da mu za a je Kaduna kai Amarya. "Anty Zuwaira ina fama da kaina'" "Ai kin ji sauƙi ko ba za ki iya zuwa ba ne? Sai na kasa musa mata sai ta buga kafaɗata da cewa" Ku ne matan kawunne manya saboda haka da ku za a je." Sai na ce to Allah ya kai mu Hauwa a ka ce ba za ta je su sai daga baya ba a son a je da yawa ne. Anty Zuwaira ta ce ba da ita ba Anty Maimuna ce da Nasara sai Suwaiba da Halima a yayyen uwa iyaye kenan sai Maman farko da Hajiyar Tafida da ƙanwar baban Sulaihat ɗin a kakkanin Amarya. Sai ƴaƴan yayyen baban ta guda biyu ƙawayenta. Sai a nan aka zaɓo ɗiyar Anty Maimuna sai yar makarantar su guda ɗaya ƙawarta. A Rano kuma an saka yayar Gimbiya amma ita ban ji an saka ta ba sannan har da Faridan Tariq Marwa ma an saka ta ita kaɗai a ce a matan kawun ne. Ana so a yi lamarin da tsari ne kamar da angon ya bukata ba su son cikowa abun ka ga masu kuɗi. An ce matukin jirgin kasa ne Captain akwai kuɗi a hannun shi sannan zuru'an su suna da kuɗi nima duk a bakin Munnira nake ji tsuliyan gari. Da na koma gida ni kaɗai yara duk suna can na baro su za su kwana. Sai ga Yallaɓai ba a gidana yake ba sai ya ce Gimbiya da yara can za su kwana sai washegari jumma'a ranar walima muna karyawa ya ce. "Za ki iya zuwa kaduna kuwa? Ya Zuwaira ta matsa mini sai ke dai kin je." "Nima haka ta faɗa mini jiya. Ni da Munnira da Anty Zabba." Yana kurɓa tea ɗin dake hannun shi a mug ya ce" Na ce ga Daughter tun da ita ce ta ce minibza ta je kai Amarya amma sai ta ce a a dole sai ke tun da ke ce Babba." Ban yi magana ba amma ni kaina na san Gimbiya za ta ce sai ta je kaduna kai amarya yadda ta ke rawan jiki da bikin nan. "Shike nan tun da za ki iya zuwa sai ki shirya. Amma please ki kular mini da kanki da Baby na." Ya faɗa ya na mini murmishi. Nima sai na yi masa murmushi kafin na ce" Da na ce ko ita Gimbiyar ta je? "A'a gaskiya Ya Zuwaira ta faɗa ke ce Babba kuma ke ɗin ce wakiliyata so ke ɗin ya kamata ki je tun da kin ji sauƙi." Sai na gyaɗa kaina ban saka aka ba wallahi. Ranar mun je walima ban san me ya faru ba mun haɗu da Gimbiya a ƙofar shiga falon Anty Bahijja ina washe mata baki ta yi kamar ba ta ganni ba ta ɗauke kanta. Har ta na ture kafaɗanta sai da muka shiga ciki ne Suwaiba ke faɗa mini kan tafiya kaduna ne an ce su bari sau ranar lahadi sai su je tare da wasu kayan ita da Naja shi ne ta ce ita tuni su yi mgana da Tafida kuma ya ce za ta je Kaduna. Ita kuma Anty Zuwaira ta ce ni ce zamu tafi da Amarya gobe shi ne ta fita tana ƙunƙuni "Topha." Na faɗa a fili a raina na ce ni ban ga abin ɓacin rai ba. Munnira ta ce ta raina wayon ta akan kai amarya sai kace zuwa madina? Ni dai Allah ya kyauta kawai na ce kuma a ranar sai da Anty Zuwaira ta tabbatar mini da na shirya da ni za a je. Ranar ma ba ta yi mini mgana ba sai fushi take yi tana cika ta na batsewa. Ma'u ta ba ni tausayi da bikin nan kamar ba a santa ba, ita kanta Anty Bahijja ta na fama da mutane ba ta bi ta kanta ba, sai dai tana raɓe wajen dangin mijinta da a ce muna zaman amana ne ni da ita za mu haɗe to da yake ba ta da hali sai ta zama kamar mujiya ga shi Shema ta yi aure da a da ne tare za su zo. An sha wa'azi malamai uku aka gayyato mata suka yi ma amarya wa'azin zaman aure da zamantakewa sai mangariba a ka tashi. Yallaɓai ya zo ya ɗauke ni wajen taran dare kuma ko gidan bai shiga ba. Bayan mun koma na ga ya na ta waya abin da ya sa na fahimci da Gimbiya yake mgana saboda maganar da ya yi mata. "Me ya sa kike da taurin kai ne Saudatu? Na ce miki ba za ki je ba Sadiya ce babba ita za ta je kuma hakan ne ya kamata." "Ok to ki yi yadda kike so" Ya faɗa a fusace ya kashe wayar. Ban taɓa jin ya kira sunanta ba sai ranar, ta kwaɓe musu saboda zuwana Kaduna ni ko da karambani bayan mun kwanta na ga har lokacin bai huce ba sai na ce masa na hakura ya bar ta ta je kawai. "Wallahi ba za ta je ba. Ke ma in ba za ki je ba fine amma na riga na rantse ba za ta je ba kuma kin san ba macen da isa ta saka ni na yi kaffaran kan aikin banza da wofi." Ai ina jin haka sai na koma na lafe a kan filo na ji shuru. Shi da kan shi da ya hucen ya matso ni jikinsa lokacin na ma ɗan fara barci ina ƙoƙarin motsawa na ji yana mini raɗa a kunni. "Sai da safe" Ban amsa mishi ba saboda barcin ya fara fizgata. Na dai ƙara shiga jikinsa sosai na lafe shi kuma ina jin sa yana rufe mana jiki da bargo. *Janafty**TKGB30E05* Washegari asabar muka tashi da shagalin biki. Sha ɗaya na safe a ka ɗaura aure kuma sun ce a lokacin za su tafi da amarya. Shi ya sa duk nuƙu nuƙun da a ka tsaya yi ɗaya da rabi motacin ɗaukan Amarya suka miƙa hanya. Ni mota ɗaya muka shiga da Munnira da Anty Zabba sai Marwa. Faridan Tariq tana motar Amarya a gidan gaba.   Da yake motocin sabbi ne sannan kuma masu lafiya ne a na gudu ma sai ka ji kamar ma ba a yi. Zuwa huɗu da rabi biyar saura mun sauka a gidan Amarya. Mun iske matar Jafar Nauwara, sai ƙawayen Anty Bahijja ina ga su ƴan Kaduna nan ne da wasu dangin angon su suka tarbe mu. Ma sha Allah gida ya yi kyau ƙwarai. kuma iyayenta sun kashe mata kuɗi kayan ta kaf ba na Nigeria ba ne a ƙasar waje a ka siyo su kuma ba a sauke su ko'ina ba sai Kaduna. Kuma da ya ke akwai ma'aikata maza su suka gyara komai, mu kan mu kayan kitchen ne muka zo da shi sai su cafet da labulanya sai ɗan abin da ba a rasa ba. A nan muka yi sallar la'asar muka ci abinci sannan muka kama a ka ƙarisa gyaran daƙun nan. Muna gidan har dare dangin mijin na ta zuwa a nan ne ma mu ke jin jibi jibin nan za su bi jirgin yawo zuwa Madina, mai son ganin ɗakin Amarya sai dai ya jira bayan salla kuma in sun dawo daga Hajji. Ba a gidan Amarya muka kwana ba. Ni da Munnira da Anty Zabba har da Marwa gidan Faridan Tariq muka kwana. Ita ma Nauwaran Jafar ta diɓi wasu ƴan'uwa. Daga ƙawayenta sai kakkaninta a ka bar Amarya da su ta kwana. Kuma bayan mun kwana can muka hantse sai wajen sha ɗaya muka dawo gidan Amarya da ke anguwan malali. Da yake abin na yan gayu ne ba wani cikowa sannan an gyara ko'ina tsab. Muna komawa ba daɗewa sai ga Naja ta zo ita da Suwaiba da Halima sai Anty Maimuna jiya ba su samu tafiya ba. Ni dai ban ga Gimbiya ba, ban kuma Tambaya ba amma Munnira sai da ta tambayi Suwaiba ita kuma ta ce Gimbiyar ce ta mata musu lokacin a na ta jiran ta daga baya ta ce su ta fi ba za ta je ba. Zuwa kai Amarya kamar wani kayan gabas ni Sadiya? Sai da muka yi azahar muka ci abinci sannan a ka kawo mota muka ɗau Amarya da su turamen atamfa da shadda sai kayan abinci da su cincin ɗin da su Naja suka taho da shi. Gidan Iyayen mijin muka je da ke NDA.  Muka kai musu Amarya sannan da kayan da muka ta ho da shi. Amarya ta samu tarba da kuɗaɗe sosai. Da ya ke suna da kumbar susa ko su gidan iyayen na shi ma a abin kallo ne. Sai a lokacin suke  faɗa mana tafiyar su Madina  jibi in sha Allahu a ka yi ta fatan alheri. Muna gidan har wajen uku saura sannan muka yi shirin tafiya daman kowacce da shirin ta tun da sun faɗa mana daga nan Kano za a wuce da mu. Nan muka bar Nauwaran Jafar da Farida sai Hajiyar Tafida da Tariq ya riƙe ta wai ta jira shi zuwa gobe zai saka a mai da ita gida. Mu kan mu an ba mu turamen Atamfa kowaccen mu sannan da kuɗi cash 10k sannan a ka ɗauke mu zuwa Kano cikin motocin alfarma kamar yadda a ka ɗauko mu. Ba mu isa gida ba sai bayan Mangariba kuma suna ijiye mu suka juya zuwa Kaduna. A gidan Anty Bahijja muka sauka tun da ita ce uwar biki ya kamata ta ga dawowar mu, amma ba domin haka ba gidana zan wuce na gaji sannan kasala duk ya rufe ni, tun da muka je ban ci wani abincin kirki ba. Na yi amai duk na galabaita barin ma yau ɗin amma ban ƙi sauka ba. A na ta yi ma na maraba da dawowa muna zaune dukkan mu a falon Anty Bahijja a na ta mai da yadda a ka yi a can Kaduna. Maman Farko na ta faɗin Sulaihait ta yi dacen surukai masu dattako sai fatan zaman lafiya sannan ga labarin kyautar ban girman da a ka yi ma na Anty Bahijja sai faman washe baki take yi. A raina na ce wato kowa na son na shi ya je ya ji daɗi. Amma ta na takura ma wasu in ta ga suna jin daɗi lalle wanzami daman a ka ce ba ya son jarfa. Tun da muka sauka kowa na ta zuwa mana sannu da zuwa. Tun da akwai sauran jama'a a gidan har Hauwa a gidan muka same ta. Ni ban ma san Gimbiya tana gidan ba sai da na fara ganin Khalipa. Ban ga Jidda ba sai Baby ita ke faɗa mini Jidda na gidan Gwaggon su Zuwaira. Bedroom ɗin da ke falon Anty Bahijja na shiga domin na kama ruwa na yi salla ina shiga na ga Gimbiya ta fito daga cikin tiolet ɗin cikin ɗakin ɗauke da Anwar kamar ta wanke masa kashi ne tun da na gan shi ba pampers. Ina ganinta na washe mata baki ina faɗin. "Maman Khalipa ashe kina gidan? Amma sai matar nan ta yi kamar ba ta ji ni ba, gani ni da ita a cikin ɗaki ban dandara ba na sake faɗin. "Mun dawo yanzu ba daɗewa a na ta hira a falo ban gan ki ba." Na saki baki kawai ina bin ta da kallo domin zuwa ta yi ta raɓa ta gefe na ta fice daga ɗakin kamar ba ta san Allah ya yi ni a tsaye a wajen ba. Har ta na banko ƙofar a saman fuskata  bam! Jikina ya yi sanyi ban san adadin sakannin da bakina ya yi a buɗe kafin na rufe shi ba. Jikina a sanyaye na shiga tiolet na yo alwala na zo na yi salla da hijabin da na samu a cikin wardrope ɗin ɗakin ina jin na Suhailait ne domin ɗakin nata ne kafin aure ya tashe ta. Ina idarwa na fito da niyar na ce ma su Munnira ni zan ta fi gida. Sai kawai na ga Gimbiya suna mgana da Naja. Kamar zan wuce na ƙyaleta sai kuma wata zuciyar ta ce na yi mata mgana na ji ko na yi mata wani abu ne da zan yi ta mata mgana tana mini wulaƙanci. "Anty Sadiya ba dai tafiya ba? Naja ta faɗa ganin na taho in da suke tsaye a gefen falon suna mgaana. Tana ganina ta wani haɗe rai kamar ta ga mutuwarta. "E yanzu na ke son tafiya ba na jin daɗin jikina ne." "Gaskiya sannu. " Ta faɗa sai kuma ta juya tana ce ma Gimbiya."Amai ta yi ta yi a can wallahi." Ban san ko maganar ta suɓuce mata ba ne, ko kuma daman da niyya ta faɗa ban sani ba sai ji kawai muka ji ta ja wani ubn tsaki kafin ta ce. " Mtswww to ina ruwana ni dai mu cigaba da zencen mu. " Ba ni kaɗai ba hatta Naja sai da ta ji wani iri ina kallonta ta na ma Gimbiyar mgana da ido. Ni ko da farkon da na zo wajen har na sauya shawara na wuce kawai ba tare da na yi mata mgana ba tun da na ga da ta ƙara ganina ta haɗe rai amma kalamanta na yanzu su suka ɓata mini rai ya sa na ce sai na yi mata mgana. "Amma ko dai ba ruwan ki ai mgana mai daɗi ma Sadaka ne in ji Annabi(SAW)" Na ma yar mata da martani ina kallonta sai ta wani ɗauke kanta sama jikinta na jijjiga irin ƙiris take jira ɗin. "Don Allah ki yi haƙuri Anty Sadiya." Naja ta faɗa ta na kallona na so na danne zuciyata na yi haƙurin amma sai Gimbiya ta ɓata komai. "Mi ye na wani ba ta haƙuri an yi mata wani laifi ne? Ta faɗa tana mini yatsina. Na ga rainin hankali a lamarin Gimbiya fa ya fara yawa tun ina hakuri tana ƙure ni daman kuma tun da na samu cikin nan a wuya na ke abu kaɗan ke ɓata mini rai ina kiyaye mata sabo ni ba sa'ar yin ta ba ce wanda ya ijiye mu ni shi ne daidai da ni tun abun na mu na mu uku ta ja sai da mutane su ka far ga da abin da ke faruwa domin ni dai ba zan yi shuru ina kallonta ta na so ta ci kasuwa a kaina ba. "Ba ko a yi mini laifi ba. Amma ina tunanin wata ƙila ni na yi miki laifi tun da tun shekaranjiya in muka haɗu a gidan nan in na yi miki magana sai ki yi kamar ba ki jini ba yau ma ban dandara ba ina ganin ki na yi miki mgana kika yi banza da ni. Ni ko Gimbiya me na yi miki da zafi haka? Me na yi miki da ya sa kike jin haushina? Kawai sai matar nan ta fara ɗaga murya tana faɗin" A a malama ɗan dakata ba na son sharri ni yaushe kika yi mini mgana ban amsa ki ba? Ai ko sai dai in ban ji ki ba. Ni dai ki tsaya da mganar nan a nan ahto domin kar ta je gaba. Yanzu sai  ki ji magana a gaba ana ƙokarin ɗora min jarkar tsaba." Naja na yi mata mgana amma tana mini rashin kunya har ta na wani ƙara yarfa hannu tana cigaba da faɗin" To Naja haka kurum ina cikin zaman lafiyana ta jawo mini wani masifan. Yanzu nan sai ki ji mgana ta kai kunnen Daddy shi kuma da yake ba ta laifi a wajensa ya hau ni da faɗa. To ba na so mganar ta tsaya iya nan, maganar kin yi maganar na yi banza da ke ban san an yi haka ba wataƙila lokacin da kika yi mini maganar ban ji ba ne." Ai sai na ma kasa mgana sabida mamaki lokacin har su Munnira sun zagaye mu suna tambayan ba'asi ita kuma Gimbiya Naja na janye ta tana ba ni haƙuri tana ce ma su Suwaiba ba wani abin faɗa ba ne na ce ne na yi ma Gimbiya mgana ta yi banza da ni sai ita kuma Gimbiyar ta ce ba ta ji ba ne. Amma ba faɗa ba ne. "Ba faɗa ba ne ta ke faɗa minI kar na kai mganar gaba? Wato ga munafuka ko me? Kin taɓa jin wani abu ya faru Yallaɓai ya ce daga bakina ya ji? Ina ruwana da sha'aninki da za ki tsaya a gaba na balle na riƙa hirar ki da miji? Kina gidan ki ina gidana me ye haɗina da ke! Ni ma sha'anin gabana ya isheni ba ni da lokacin wannan sannan ban gane kin ce wai ni daman ba na laifi a wajen shi ba? Me kike nufi? Sannan kina nufin ni zan yi miki ƙarya ne Gimbiya? Na ci riban me? Ke ma kan ki kin san ba ki isa na yi miki ƙarya ba domin isar ki ba ta kai har haka a wajena ba" "Sadiya me ya faru? Maman farko da tambayeni lokacin da ta ƙariso wajen ina ƙoƙarin magana kawai sai Gimbiya ta buga shewa tana faɗin" Ahayye. Shi ya sa na ga kin yi ƙutun ƙutun kin tafi Kaduna. To ina fatan kin je kin ciwo abin da ba ki taɓa ci ba ko? "Ke Gimbiya me ye haka? Anty Maimuna ta faɗa tana shiga tsakanin mu. "Ba dai rashin kunya za ki yi ma Sadiyar ba ko? Anty Zabba ta faɗa. Hauwa ko rike ni ta yi tana cewa kar na ce komai Munnira ko faɗi take yi" Jaruba wallahi kika ce za ki yi ma Sadiya rashin za ki daku a falon nan wallahi." Wata shewar ta buga kafin ta ce" Ko ita ba zan da kun mata ba. Ballatana ku yan koren ta." "Haba Saudatu" Maman Farko ta faɗa kamar ranta ya ƙara ɓaci Anty Bahijja ba ta wajen daga baya a ka kirata ta zo dai dai lokacin da Munnira ke sa'in sa da Gimbiya. "Ni kaina ba kai isar da zan yi sa'in sa dake ba. Ballanata Sadiya ta fi ƙarfin ki. Kuma Kaduna ta je ke ma ya sa ba ki je ba? Kin ga kenan isar ki ce ba ta kai ba ita kuma da na ta isar ya kai miji ya sahale mata ta je duk shi ne haushin na ki? Sorry ki yarinya mijin wata kika aura dole ki zamo ta baya ko kina so ko bakya so. Kuma na san duk wannan kumfar bakin da kike yi ba a kan tafiyar mu Kaduna ba ce, haushi ne baƙin ciki kin ji labarin Sadiya na da ciki sannan Tafida na ririta ta shike nan sai hassadarki ta motsa wato kin so ne ke da kika  zo kika aure mata miji sannan kuma ki zama ke ce ke ta haihuwa ita kuma ko oho ko? Sai ga shi ba ke kaɗai ke da Allah ba. Ubangiji na kowa da kowa ne. Ta samu ciki kin kasa ɓoye hassdarki shi ya sa kika zo za ki yi ma mutane rashin kunya. To ba sa'an ki anan kuma duk tsiya dai a baya kika zo sai da aura ta rage sannan kika samu." "Ke Munnira" In ji Anty Bahijja. Maman Farko ba ta yi magana ba Anty Maimuna ce ta ce" Munnira ke ba za ki ba da haƙuri ba sai hura wuta! Wallahi kar na ƙara jin bakin ki" "Ta yi magana dole fa a mayar mata da martani domin rashin kunya ce za ta yi ma mutane." Munnira ta faɗa a fusace. Anty Zabba sai ta yi aikin hankali ta kama hannuna tana faɗin" Ta ho mu je Sadiya kin ga ba ke kaɗai ba ne. Ɓaçin rai kaɗan zai iya shafar abin da ke cikin ki. Munnira ai ta gama mgana taho mu je." Har na bi ta, saboda raina ya ɓaci har wani duhu duhu na ke gani amma tabbas Munnira ta faɗa masu zafi shi ya sa ta kasa magana amma Gimbiya ba ta so mganar ta tsaya nan ba sai ta fara masifa har tana fizge hannunta a cikin na Naja da ke riƙe ta, tana faɗin kar ta tanka mgana ta mutu har Maman Farko sai da ta roƙe ta da kar ta ce komai a bar mganan hakanan "Ahayye. Nanaye baƙin cikin me zan yi niSaudatu! Ai duk haihuwan da za a sake yi ma Daddy sai dai ta biyo bayan haihuwar da na yi masa. Biyu ne amma kamar da goma ne. Irin kuma haihuwar da ba a taɓa masa ba sai da ya auro ni sannan na haifa masa.'" "Ke Saudatu me ya sa ke b a ki jin mgana ne? Maman Farko ta faɗa a fusace tana cigaba da faɗin" A na cewa a bar mganar kina ƙara magana? "Kyaleta Mama ba riba za ta ci ba domin kowa a nan wajen ya san ba ta da gaskiya." In ji Suwaiba saboda kowa ran shi ya ɓaci da mganganun Gimbiya. Har na ci burki da zan juya na bata amsa Munnira ta ƙara fansana "Wallahi ƙarya kike yi. Ai am gama yi ma Tafida farar haihuwa tun haihuwan Jidda. Kin san soyayyar a haifa ma ɗa kana tashen samartaka! Kin san girman soyayya auran saurayi da budurwa? Wallahi ko goma za ki ta haifa maza sai dai ki biyo baya amma ba dai ki zo a gaba ba. Kuma in Sadiya ta haihu ki rubuta ki ijiye sai kin gane cewa ke dai kin yi irin na ki haihuwan amma ba dai ki yi irin na Sadiya ba." Na so na yi shuru amma sai na kasa saboda na biyu kenan ta na faɗin ta yi haihuwan da ba a taɓa yi ma Tafida ba saboda ta haifi maza ni kuma ban iya haihuwan namiji ba shi ne ban iya farar haihuwa ba. kawai sai na juya na fizge hannuna daga na Anty Zabba na isa gaban Gimbiya ina kallonta kafin na ce. " Sau biyu kenan ina jin kina nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. Ban yi miki magana a farko ba amma yau na kasa haƙuri sai na tanka. Gimbiya ni fa Yusuf kaɗai na aura kuma soyayyace ta sa na yarda da shi har ma iyayena suka aminta da shi muka zama a ƙarƙashin inuwar aure. Yau ko mata dubu zan haifa da ɗigon jinin Yusuf wallahi ni Allah ya gama mini komai Gimbiya. Ya tsamoni cikin duba ya yi mini ni'imar da ba kowa ya yi ma wa ba. Haihuwan namiji ko mace ni ban ɗauke shi a wani abu ba. Ɗaya na ɗauke shi. Mata suna da matuƙar tasiri a rayuwar mu da addininmu. Kin manta cewa mace ce ta fara karɓan addinin musulunci a mata? Kin manta da tarihin matar Firauna? Hasiya da irin gwagwarmayan da ta yi domin addinin Allah. Ko kina da labarin Allah ya gina mata gida a Aljannah? To kamar yadda Maza suke da tarihi a cikin addininmu haka ma Mata ke da wannan tarihin. Saboda haka ni in mata Allah zai ba ni ina so in ta haihuwarsu ina roƙon Allah ya shirya mini su. Ya kuma sa su yi ma addininsu hidima. Ke kuma da kike son Mazan saboda tunanin su ne ke da gidan Allah ya yi ta baki ko dubu za ki haifa wallahi tallahi ba zai tsole mini gefen ganina ba Gimbiya. Gargaɗin da zan yi miki shi ne ki daina ƙoƙarin mayar da ƴa'ƴana a baya. Suma ƴa'ƴa ne dai-dai da irin haihuwan da kike tunanin kin yi a kan su Khalipa." Ina gama faɗin haka na wuce. Maman farko ta jinjina kai tana na faɗin" Shi kenan Sadiya kin gama mgana." Kowa sai ya yi shuru ya yi sanyi ita ko Gimbiya sai ta fashe da kuka jin yadda har Hajiya iya da ba ta san farkon faɗan ba ta na salla sai da ta ce Gimbiya ce ba ta da gaskiya. "Ko ba ta girme ki ba ai tana gaba da ke a aure." "Balle ma wallahi Sadiya ta girme ta. Sai dai ta yi sa'ar ƙanwar ta Amina." In ji Munnira,  Suwaiba ta karɓe da cewa" Tsaya tsaya ma ko da ma a ce ba ta girme ta a shekaru ba a gidan aure ita ce babba. Kuma bai kamata ta girmama ta ba? Ai kowa ya ji wannan abin da ya faru a san ba ki ta ki gaskiya ba Gimbiyan" Ni dai ban tsaya ba na ce zan tafi gida. Yau ma tun safe rabon da mu yi waya da Yallaɓai. Anty Maimuna ta ba ni mamaki har da ita a masu ba ni haƙuri Anty Bahijja kuma ta rufe Gimbiya ta faɗa tana kukan munafunci. Tare da Marwa da Munnira muka fita Hauwa ta ce Muttaƙa zai zo ya ɗauke ta. Anty Zabba kuma gidan su ta ce za ta je ta kwana. Amaryan ta ma tun da suka sauka daman gidansu ta sauka bikin ma daga can ta zo. Muna cikin adaidaita Munnira sai jaraba take yi tana ce mini wai ina yi ma Gimbiya sanyi sanyi shi ya sa ta raina ni. "Wallahi ta ba ni mamaki ko kunya ba ta ji ba." Marwa ta faɗa cikin mamaki. Munnira ta ce"To daman tana da kunyar ne! Wallah ba ta da kunya ta daɗe tana neman da man da za ta ci kasuwa a kan Sadiya." "Sai me? Don Allah ku bar mganar ni wallahi raina ma ƙara ɓaci yake yi " Na faɗa ni a ƙokarina su bar mganar amma Munnira ba ta bar ta ba sai masifa take yi tana cewa na faɗa ma Yallaɓai domin ya dauƙi mataki. "Ni ba ruwana ba ki ji ta ce kar na kai ta gaba ba." "Ki kaita ɗin domin ta san kin isa." Shuru na yi ban yi magana ba. Saboda ni ba halina ba ne wannan surutun, abubuwa da dama sai dai ya ji su can a bakin ƴan gidan su. Ni bar ni da mgana in na ga za a cuce ni ko magana kan lamarin da ya shafe ni amma ba ruwana da mganar kishiya. Ko kafin ma ya yi aure ko hatsiyar mu da yayyen shi ban taɓa faɗa masa sai dai in ya ji labari ya zo ya tambaye ni amma ba dai ni na kwashi jiki na je ina ce masa an yi kaza an yi kaza ba. Shi ya sa yau ɗin ma na yi shuru amma har a ƙasan raina ba zan faɗa masa ko da kuma ba zai ji labari ba amma dai ina da yaƙinin tabbas zai iya sani. Mu mai adaidaita ya fara saukewa sannan ya wuce da Munnira. Allah ya so ni ga Marwa ina komawa gida na kwanta sai zazzaɓi ita ce na samu ta dama min kuni na sha ya zauna a cikina. Ni saboda bacin rai ko Baby ban nema ba da zamu taho. Sai kawai na ce gobe sai su dawo tare da Jidda.  Haka Yallaɓai ya zo ya same ni a kwance ya yi ta faɗan sai da ya ce ba ya son na je Anty Zuwaaira ta matsa sai an je da ni gashi nan na dawo ba ni da lafiya sai da na ce masa ba fa komai ba ne aman da na yi a can sai ɗan zazzaɓi kuma ya san ina yin zazzaɓi haka daddare sannan ya ɗan sarara da faɗan da ya fara Paracetamol ya ba ni na sha na yi sallah na kwanta sai na ji daɗin jiki na zuwa safe kuma sai na ji ya sake ni. Marwa ta gyara minI gida ta yi mana abin kari itama da safen ta wuce Ɗorayi za ta gai da su Gwaggo. Daga can ta wuce gidan su ta kwana da safe ta wuce Rano. Iya kwanakin da Kawu ya ba ta kenan. Ni kaɗai a gida domin Yallaɓai da hantsi shima ya fita, sai can bayan la'asar dai ga shi an kawo su Jidda. Ita na samu ta yi girki ni kuma na ce ta dama mini kuni domin wanda Marwa ta dama min tas na shanye shi kuma shi kaɗai na ke samu ya na zama a cikina sai ganye haka irin su Kabeji, latas da allayahu. In a ka sanya su a cikin abinci ina samu na ci sosai. Amma wani kifi wani nama ko warin shi ba na so balle su ƙwai da sauran nau'ikan abincin da ba na so ma na ji warin su in ana dafawa. Ni warin ma maggi mai star ne kwata kwata ba na so shi ya sa na daina ma giftawa ta Kitchen ɗin na bar ma Jidda ne ban san yadda yake ciki ba, domin na daɗe ban shiga cikin sa ba. Har a ka kwarari kwana huɗu da dawowata gida ban ji Yallaɓai ya yi mini wata mgana ba. Sai ranar jumma'a ranar ma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne. Yau Mubeenan Musbahu ta zo ta yinin mini ita ta yi girki da gyaran gida. Tun da ya ga ba ni da lafiya yana yawan turo ta gidana kuma ina jin daɗin haka. Sai dare Musbahu ya zo ya ɗauke ta shi ya sa na koma ɗaki na kwanta saboda na ji na fara jin sanyi sanyi. Ina cikin bargo ina shafa kasan marata cikina ya shiga wata na huɗu kuma har ya fara turowa. Ina jin ƙaunar abin da ke cikina sosai wata ƙila don irin wahalan laulayin da na ke sha ne na tuna kafin bikin Suhailat maganar da muka yi da Yallaɓai. "Yallaɓai in na mace na haifa sunan Mama za mu saka mata." "In kuma Namiji ne to sunan Alhajin Ɗorayi za mu saka masa ko? Ya ƙarishe mini yana dariya. Nima dariyan na yi kafin na ce" Ka yi gaskiya. Tabbas haka ne a raina." A lokacin jawo ni jikinsa ya yi yana faɗin" Kar ki damu fata na ki sauka lafiya duk sunan da kike so shi za mu sanya kin ji ko? Sai na ji daɗi har ina ba shi sumba. Vibration ɗin waya ta ne ya dawo da ni daga tunanin da na faɗa. Ta na gefen in da na ke kwance ne na saka hannu na ɗauko ta sai na ga Yallaɓai ke kirana. Ban kawo komai a raina a tunanina sallama zai yi mini kamar yadda ya ke yi in bai samu zuwa ba. "Zan taho da Daughter yanzu ina so mu yi mgana gabaɗaya." Abin da ya ce minI kenan bayan mun gaisa. Sai na ce masa sai sun taho. Har muka gama wayar tunanina bai hasaso  mini kan abin da ya faru ba ne sai daga baya na fara tunanin wataƙila kan haka ne amma kuma a ina ya ji? Ko wa ya faɗa masa? Watsar da tunanin na yi saboda ba ni da mai ba ni amsar su. Sai da suka zo gidan sannan na fito daga ɗakin na saka hijabi amma duk wanda ya gani ya san ina fama da azaban laulayi duk na yi fari na lashe na kuma rame. kullum ina fama da bushewar baki da maƙogwaro. Ina ganin Gimbiya sai na tuna da faɗan da ya shiga tsakanin mu da ita shi ya sa na yi kamar ban gan ta ba kamar yadda itama na ga ta yi, sai wani cin magani take yi tana wani hura hanci. Shima gogan ransa a ɓace na gan shi da ga gani sun yi ta ne kafin su ƙariso. Jidda ya haɗa da yaran gabaɗaya da cewa su koma falon su za mu yi mganam ita ta tattara su suka bar mana falon. Shi yana saman kujera mai zaman mutun uku ni kuma ina zaune a mai zaman mutum biyu a gefen sa ita kuma sai ta zauna kan mai zaman mutum ɗaya muna fuskatan juna ni da ita. Ai ni tun da ta yi mini wannan wulakancin na yi alƙwarin duk in da za mu haɗu in ba ta ce sannu ba ba zan tanka ta ba. Da mutumcina ba zan zauna wacce ba ta isa ta zubar mini da ƙima ba. "Ba ku gaisa ba? Ya faɗa bayan ya kore shurun namu gabaɗaya. "Tsakanin ni da ita wa ya zo ya samu wani? Na tambaye shi ina mai kallon shi da idananuwa da suka ƙanƙance. "Ita ce " Ya faɗa yana kaɗa kai, ni ban yi magana ba sai shi ne ya kalleta kafin ya ce" Ki gaishe ta mana." Ta yi shuru taƙi mgana ni dai kaina na ƙasa ina wasa da gefeb hijabina da ya sani bai ɗauko mini ita ba. Ta zo har falo na tana yi mini Taƙama. "Ba da ke nake mgana ba." Na ji ya da ka mata tsawa. "Ina yini." Ta faɗa kamar dole. Ko da ya ke ai dolen ce ya saka ta. "Ke kuma ki amsa tun da ta gaishe ki." Ya faɗa muryansa a sama daga gani yau an taɓo zuciyar ƴan maza. "Lafiya lau." Nima na faɗa a tsume saboda ni ba gan amfanin wannan zaman  ba tun da wacce ta yi laifin ba ta ji a karan kanta ta yi nadamar abin da ta yi ba. "Hakan da kuka nuna shi ne ya ƙara tabbatar mini akwai wani abu da ya faru a tsakanin  ku wanda kuka rufe ni ba ku gaya mini ba. Ban sani ba ba domin Kawu Abba ya kirani ya faɗa mini ba, sannan Maman Farko ma ta kira ni ta ce na tara ku kun samu yar hatsaniya ranar a gidan Bahijja amma cikin ku a ka rasa me faɗa mini wani abu ya faru? Me ya sa haka? Dukkan mu muka yi shuru. Ni sai da ya faɗa sannan na gano in da ya fara samun labari. Wato Marwa ce ta sanar ma da mijinta shi kuma ya kira Yallaɓai ya faɗa masa. Sai Maman farko da ta yi masa mgana ashe ita ma mara kunyar ba ta faɗa masa ba. "Daku fa na ke mgana? "Me ya sa ba ku faɗa mini ba? Ya faɗa yana ɗan sausaauta fushinsa saboda ya yi ƙasa da muryan sa. "Kasan daman ni ba halina ba ne na tare ka da mganar an yi kaza an yi kaza. Ballatana matarka daman ta ce ni ce ke kai ta gaba a wajen ka." "Wannan ba Hujja ba ne. Ke ce babba bai kamata ki same ni ki faɗa mini wani abu ya faru ba? Ba na so mganar ta yi tsayi ya sa na ce" Ka yi haƙuri na yi kuskure." "Gaskiya ban ji daɗi ba. A ce sama da kwanaki ban san wani abu ya faru da matana ba sai wasu ne za su kirani suna faɗa mini ? Kun yi mini adalci kenan? "Ka yi haƙuri." Na sake faɗa ita hajiyar tana zaune tana karkaɗa kafa ba ta yi mgana ba. "Ya wuce. Amma kar a ƙara irin haka ba na so. Duk abin da zai faru da ya wuce ku biyu wasu suka sani to nima ya kamata na sani ɗin" "In sha Allahu." Na faɗa ina muskutawa domin na gaji da zama duk na takura. "Me ya faru ne a tsakanin ku da a ka ce kun yi sa'in sa a gaban mutane? Yaushe kuka fara sa'in sa a tsakanin ku ni ban sani ba? Tambayar gabaɗayan mu ya yi mana. Amma ni ban ce komai ba ita kuma sai ta fara faɗin" Ai na ɗauka ka san duk abin da ya faru." "Na sani zan zo in tara ku ina tambayar ku? Ya faɗa a ɗan fusace ganin ya harzuƙa ya sa ta fara mgana a ƙoƙarinta na ta juya mganar tun da ta fara faɗin wai na ce na yi mata mgana ta yi banza da ita. Ita ba ta ji ba ne amma shi kenan na fara faɗa ina faɗin ta ji da gangan ne. "Sadiya" Ya katseta da kiran sunana sai na ɗago kaina ina amsawa. "Na'am" "Ki yi mini bayanin abin da ya faru daga farko." Na buɗe baki zan yi mgana ta tare ni da cewa" Ni ba ka yarda da ni ba sai ita kenan? "E. Ai ita na fara sanin kafin ke. Saboda haka ita zan fara ba ma Amincina kafin na baki " Sai ta yi shuru bayan ta koma ta haɗe rai tana faɗin. "To ai shike nan." Ni dai ban bi ta kanta ba na yi masa bayanin duk abin da ya faru tun daga farko. Ban ɓoye masa komai ba har mganganun da na gaya mata da wanda su Munnira suka faɗa mata duka na faɗa masa na ƙarishe da cewa" Na yi ƙoƙarin na danne zuciyata amma na kasa. Saboda na ga ta na ta nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. In su ta ce farar haihuwa ne su kuma su Jidda ɓakar haihuwa take son ta kira su? Ta fada mganar nan ba sau ɗaya ba kuma sau biyu ba. Shi ya sa na tanka mata har ta kai mu ga sa'in sa" Sai ta taso mini tana faɗin" Ni yaushe na ce su baƙar haihuwan? Ni fa ba haka nake nufi ba. Munnira ce ta ce wai ina bakin ciki da kin samu ciki ni ko na ce me zai dame ni,? Ni da na yi farar haihuwa.." "Shutup." Ya katse ta bayan ya da ka mata tsawa. Sai ta yi shuru ta na wani nuƙufarci. "Har kina sake maimaitawa? "To ai na ga ba." "Ki  rufe mini baki na ce ko? Ya sake mata tsawa har ya na miƙewa kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin" Ni shikenan ba za a bar ni na yi mgana ba. To da yake ita kake so ai ka bar ta ta yi mgana ni kuma da a ka tsana ina mgana kana mini tsawa." "An hana ki ɗin. Kuma ba a son ki ɗin, an tsane ki, ki yi abin da za ki yi wawuya kawai " Kamar famfio sai ta ƙara ma kukanta volume. "Ki yi mini shuru na ce ko? Ya sake faɗa a fusace dole ta kama bakinta ta koma tana haɗiyan zuciya. Shima sai ya koma ya zauna yana sauke numfashi kafin ya kalleni yana faɗin" kin yi mini laifi Sadiya. Me ya sa da kika yi ta mata mgana tana miki wulaƙanci ba ki faɗa mini ba! Da tun lokacin zan faɗa mata ko ni da nake aurrn ki ba ki taɓa mini mgana na yi miki haka ba ballatana ita ? Sannan mganar tun da kika samu ciki ba kya laifi a wajena sai ki faɗa mata tun kafin ki samu ciki ke ɗin daman ba kya laifina a wajena ko za ta ɗau mataki ne? Wallahi da kin faɗa mini da na ci mata mutumci da ba ta isa ta tare ki da wata mgana ba." "Ka yi hakuri." "Kar ƙi kara ganinta ki ce za ki yi mata mgana. Umarni ne daga ni na ce duk in da kuka haɗu ita ce za ta fara gaishe ki " "Tabɗijam" "Ko ba za ki bi Umarnina ba ne? Ya katse ta a fusace kamar zai kai mata duka. "Na ji." "Wallahi tallahi kika kuskura na sake jin kin yi sa'in sa da Sadiya sai na nuna miki kalata. Haba. Ke ba ki jin lallashi ne? Wani irin haƙuri ne ban baki ba ? In Sadiya ce wallahi umarni ɗaya nake ba ta ta bishi amma ke sai yanzu za ki fiddomin sabbin hallaya? Haka kike daman? Ko zuga ki a ke yi! To in ma zugi ne ba ki isa ki ce ni za ki juya ni ba. Ni ba batulu ba ne kafin na same ki da Sadiya kika ganni. Kin san faɗin tashin da muka sha tare kafin mu kawo a lokacin da kika aure ni? Kin san gwagwarmayan  da muka faro ta da ni da ita kafin zuwan ki? Ni ban raina ta ba sai ke? Ki raina mini mata sannan ki na neman ɓata mini ƴa'ƴana? Har kina dukan ƙirji da kin yi mini farar haihuwa? Na taɓa faɗa miki na bambamce tsakanin su Khalipa da su Jidda ne? Ban da ba ki da tunanin ba su Jidda na fara samu kafin su Khalipan ba? Dukkansu ƴa'ƴana ne kuma ina son  su amma mace ko namiji ba wanda ya fi wani a wajena. Na rantse da wanda raina ke hannun shi Saudatu in na ƙara samun labarin kin ce ke farar haihuwa kika yi sai na saɓa miki. Saɓawa mafi munin da ba ki taɓa sanin haka nake ba " Ya dakata ya na sauke numfashi ita kuma tana ta kuka. "Ki bata haƙuri. Kuma wallahi in kuka ƙara haɗuwa ko kallon banza kika yi mata in na ji labari ni da ke ne." Ba ta da yadda ta iya ne ya sa ta ba ni haƙuri tana kuka. "In ba ɗan adam da manta alheri ba wani wahala da kara ne Sadiya ba ta yi miki lokacin da kike da cikin Khalipa ba? Har kin manta yanzu ba ki da abin ciwa mutumci sai ita? To bari ki ji ki sani in kika tozarta Sadiya kamar ni kika tozarta. Tozartani kuma da-dai yake da kin tozarta auran ki. Ita da zuciya ɗaya take zaune da ke amma ke ki zo ki auran mata miji kuma ki hana ta zaman lafiya? To ba ki isa ba ki shiga taitayin ki da ni wallahi in ba haka ba ki kasa gane kaina" Sai kuka take yi ta kasa mgana ina ga ba ta yi tunanin lamarin zai ɓare da ita kamar haka ɗin ba. Yallaɓai ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba har sai da ta koma tana ba ni tausayi. "Ka yi haƙuri ma na Yallaɓai." Na faɗa ina so ya bar mganar amma bai bari ba sai da ya gaji don kan shi sannan ya koma yana sauke numfashi. "Itama ta yi haƙuri kan mganganun da ta ce Munnira ta faɗa mata." "Ai ba mganar haƙuri duk mganar da ta faɗa gaskiya ta faɗa mata. Saboda haka ba wani mganar a bata ma haƙuri." "A'a ka saka ta ba ni haƙuri nima ba laifin in na ba ta haƙuri." Sai ya yi shuru ni kuma sai na juya ina kallonta kafin na ce" Ki yi haƙuri kan mganganun da na faɗa miki har da wanda ma su Munnira suka yi. Hakan ba za ta ƙara faruwa ba." Ba ta yi mgana ba sai jan zuciya kawai take yi. Yallabai ya yi mgana ta ƙarshe shi ne kar ya sake jin labari makamcin wannan ya sake faruwa in hakan ya sake faruwa kowacce cikin mu ke da laifi zai haɗa mu ne gabaɗaya ya hukuntamu. "In sha Allahu hakan ba zai ƙara faruwa ba. Ka yi haƙuri." "Na gode Sadiya ta." Haka ya ɗauke ta suka koma. Ni na san za su kwana ba zaman lafiya domin a fusace ta fita haraba yaran ma shi ya tsaya ya taho da su. Ni dai a raina na ce ku ƙarata faɗan da ba ruwan ai daɗin kallo ne da shi. Sannan daman in har ka rike gaskiya a je dai a dawo wata rana kai ke da nasara. Tun da ya yi mana wannan sulhun ban ƙara bi ta kanta ba har aka zo a yi sallar babbar salla ba mu ƙara haɗuwa ba sai a Gwammaja a falon Nene da ya ke ba a sallar idi saboda corona yadda ta gaisheni ba fara'a nima haka na amsa mata cikin yanayin da ta gaisheni. Nene ta ji labari ta sake kiran mu har cikin ɗakin ta ni da Gimbiyar ta sake yi mana faɗa, ni dai na ce mata na yi mata alƙwarin hakan ba zai ƙara faruwa ba. Itama ta ce ta bari ba za ta ƙara ba. Amma har muka bar gidan nan ba mu ƙara ma zama a inuwa ɗaya ba. Kowa na harkan gaban shi, Munnira ta dame ni sai da na faɗa musu tara  mu da Yallaɓai ya yi amma ban faɗa musu masifan da ya yi ta mata ba amma dai na sanar da su ya ce in muka ƙara haduwa ita ce za ta riƙa gaishe ni. "Da kyau. Tafida daman ai Namiji ne." Ni dai ban ce komai ba. Saboda namiji ne mai canza launi baƙin cikin sa kuma amarya da uwargida duk sun kurɓe sa. Shi ya sa don ya yi wannan faɗan zuwa Gimbiya bai saka na ji daɗin haka ba wata rana ni kaina zai iya yi mini haka kuma a gabanta. Abu ɗaya na ji daɗin shi yadda ya nuna mata shi a wajen shi daga mace har namiji duk ɗaya suke kuma ya nuna mata ina da daraja ta nan kawai ya burgeni. ***** Haka lokaci ya ci gaba da tafiya tun ina sa ran za a buɗe gari har na fidda raina. To ko an buɗe gari ina mganar komawa makaranta ina fama da kaina. Jdda ma nake ji itama daga farko ne ta damu daga karshe sai ta saki jikinta kawai zaman gida dole. Ko Tahfiz ɗin su babu duk wata makaranta an daina yin ta in dai za ta haifar da cunkosun jama'a. Ni kuma gefe ɗaya ina cigaba da renon cikina da ya shiga watani shidda har na fara zuwa awo a nan asibitin Aminu Kano AKTH. Cikina ya fito daga gani cikin zai yi girma wannan karon. Allah ya taimake ni lokacin da ya shiga watani biyar sai na dawo da cin abinci kamar gara shi ya sa cikin wata ɗaya na mai da jikina har na fara haɗa wata kiɓa. Kumatuna sun yi luhu luhu wuyana har ya na neman haɗewa saboda kiba. Abincin na ke ci kamar hauka a rana sama da sau huɗu har cikin dare, yanzu tea na saka ma ƙahon zuƙa madara ba ta sati ta ƙare har Yallabai sai da ya ce wato abincin da ban ci ba ne a baya na ke famshewa. Kowa ya ganni sai ya ce Sadiya cikin nan ya buɗa ki? Shi ya sa hancina da bakina suka yi girma saboda yadda fuskata ta ciko sosai. *** Lahadi. August, 2020. Lahadin ƙarshe mako ne Yallaɓai a gidana yake tun ranar jumma'a ya je Abuja sao jiya da daddare ya dawo.  Can ma aiki ya samu na gina ma'aikatan sarrafa leda ba ya samun hutu sai a yi ƙarshen mako sama da biyar bai kwanta a gida ya huta ba. Jiya ma ya dawo da daddare mun daɗe muna hira saboda ni tun da cikina ya shiga wattanin sa na shidda na daina barcin dare sosai amma ina yi na rana hani'an. Faɗa mini yake ba shi da kuɗi ya kwashe ya saka a ginin ma'aikatan shi, ga wannan aikin sai da ya ɗan ci bashi daɗin sa ma sun ce za su ba da rabin aiki rabi kuma sai an gama. Ga na Dutse bai kamallah ba amma an kusa sai ya raba yaran na shi uku. Biyu ya kai su Abuja. Kaɗan kuma suka zauna a Dutse suna ƙarisawa. Wasu kuma suna na ma'aikatan shi duk sauran aikin kaɗan ne. Kofofi ne suka rage sai fanti da sauran ɗan abin da ba a rasa ba a gama. Shi damuwar shi in an gama aiki furnitures ɗin da za a sanya a a wajen ne tunanin shi ya so ya yi oder ɗin ko da rabi ne amma bai samu ba sai na bashi shawaran ya bi komai a hankali in an gama aikin Dutse an gama biya sai ya yi oder ɗin ko rabi ne Allah bar shi daga  ya siya saura. A yadda ya faɗa mini yana so a farkon shekaran 2021 kamfanin shi ya fara aiki a sabon gini. Ni na yi ta kwantar masa da hamkali har wajen biyu na dare sannan muka kwanta da asuba kuma bayan mun idar da salla ya ce sai ya yi barnan ruwa. Ni dai ina tura baki aka yi a ka gama maganar gaskiya cikin nan ba ya son ɓarnan ruwan nan shi ya sa ya ce bai ji daɗin da ba irin cikin Baby na ƙara samu ba ina hararan shi na ce wato ya so ne ya ƙara samun damar da zai ta shagalin sa ya ce kamar na sani. Tun da ya kwanta ya ke barci har azahar. Ganin azahar ta yi ya sa na tashe shi wajen ɗaya da rabi. Da ƙyar ya tashi ya yi sallah ya so ya koma barci na ce masa don Allah ya bari ya yi wanka ya karya. Wanka ma ni na taya shi na gaggasamai jiki saboda ya ce ko'ina ciwo suke yi masa. '"Wai ni hala ƙankare nan kake ɗauka a saman kai ne? "Ba na ɗauka amma in ta kama ina ɗauka. Kamar yadda suke yini a tsaye suna aiki nima a matsayina na Injiniya mai kula da aikin kamar haka ne a tsayen na ke yini." Cikin tausayawa na ce" Sannu.  Allah ya tsare mana kai mijin mu." Na faɗa ina danna masa kafaɗunsa lokacin ina sha masa vesiline ne. Ya amsa da Amin yana dariya. "Ko in shafa ma ka man zafi ne? "Yauwa shafa mini Allah ya yi miki albarka." Dirowan gado na jawo na ɗauko na fara sha fa masa kafaɗunsa zuwa bayansa ya na tambayana in da na samu man zafi na ce Gwaggo ta ba ni ta ce na riƙa shafawa a kafafuna da suke kumbura. "Ba kumburi ba ne tsabar cin abinci ne ko? Ya faɗa yana dariya sai na lakato na shafa masa a fuska ya ji zafinn yajin  ya sa ya kare fuskarsa yana faɗin" Makanta ni kike son yi Sadiya? Ni kuma ina ta dariya ina faɗin" Ka kara cewa ina da cin abinci. Wai ba ɗanka ba ne ke saka ni cin ba? "Shi ne." Ya faɗa yana danne dariyan shi. Haka na gama shafa masa muna hira nima har sha fa mini ya yi a ƙafafun nawa sannan ya saka kaya. Yau a bedroon na kawo masa abin ƙarin bayan ya gama na kwashe na mai da kitchen su Jidda ma sai da suka biyo sa suka gaishe shi a ciki. Nan na bar shi na je falo muna duba hijabai ni da Jidda. Jiya suka iso na ce ta ɗauko list mu cire ma waɗanda suka saka oder. Can na ɓata lokaci ko da na koma ɗaki na ɗauka zan gan shi ya na barci amma sai na iske shi zaune yana waya ina shigowa ma ya gama wayar. "Yallaɓai ba ka kwanta ba? "Yanzu waya ta tashe ni." Sai na zauna kusa da shi ina matsa masa kafaɗanshi. "Sun daina ciwo? "Sun yi sauƙi." Ya faɗa yana kallona. Sai na sake shi ina faɗin" Yallaɓai ni fa ina son ka fara koya mini mota." Daga maganar arziƙi sai kawai na ga Yallaɓai ya kalleni ya wani kwashe dariya. "Mota? A hakan ne za ki koyi mota? Ya faɗa ya na kallon cikina. Sai na fusata a kuma fusacen na ce" E a hakan ko ba za ka koya mini ba ne? Na fada ina haɗe fuskata ganin yana ta mini dariya sai ka ce na faɗin abin dariya. "Ko ba za ka koya mini ba ne. Na je wajen da ake biya na koya? "E to gaskiya domin ni ina na ga lokacin koya miki mota fisabilillahi Sadiya? Wai ma to ke kina da motar ne da kike son koya? "Ba ni da shi amma ina da niyar siya ne" "Da wani kuɗin? Yallaɓai ya faɗa har yana tagumi. "Da kuɗina mana" "Kina da kuɗi ne da man? Tambayoyinsa sun fara ƙular da ni ya sa a ɗan tsume na ce. "Ai ba zaman banza nake yi ba kasan ina da sana'ata." "Wai da riban hijaban ne za ki siya mota da man? Sai kawai na kalle shi na kasa mgana. Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba har ya na duƙawa rike da ciki. "Ke yanzu daman kin san riba ake samu haka tsagwa gwa shi ne ba ki faɗa mini na saka hannun jarina ba? To wai kamar nawa yanzu kika tara na siyan motan? "Ban sani ba." Na faɗa a fusace ina mikewa da cikina gaba. Har na bar ɗakin Yallaɓai na tintsira mini dariya abin ya yi mini ciwo. Kuma wallahi zan bashi mamaki da ni yake zencen. *Janafty**TKG0B3F06* Duk da na bar ma Yallaɓai ɗakin sai da ya ƙara biyo ni falon. Ina zaune ina cin dankalin hausa ɗanye kitchen na shiga na ga Jidda na ferewa wai shi ta ke sha'awa za ta soya ta ci nima nan take na ji ya shiga raina sai na ce kawai ta fere da ɗan yawa sai mu ci gabaɗaya. Shi ne kafin na taho na ɗauki wanda ta feren ƙarami na wanke na taho da shi falon Yallaɓai na zauna ina gutsira a hankali ina jin daɗin sa a bakina da cikina gabaɗaya. "Aa Hajiyar mota nan kuma a ka dawo? Wani kallo na yi masa amma ban yi magana ba. Yana dariya ya zagayo ya zauna a gefena yana faɗin. "San mini dankalin" Ya faɗa ya na kamo hannuna na yi saurin fizgewa ina ƙara haɗe rai. "Ba za ki ba ni ba? Nan ma na yi masa shuru. Saboda ganin har lokacin bai dai na yi mini dariya ba. Maganata ta zama a bar dariya a wajen shi shi ya fi ƙular da ni kuma ni har a cikin zuciyata da gaske nake yi zan koyi mota saboda nima ina son wata rana na ganni ina tuƙa mota da sunan tawa ce. "To fushin duk na mene ne Madam? "Ko duk  fushin na ce ba ni da lokacin koya miki mota ne? Sai a lokacin na kalle shi ta gefen ido kafin na ce" Na me! Abu na kuɗi zan je na biya a koya mini kasha zaman ka." "To ni me ya sa zan bari wani ƙaton banza ya koya ma matata mota? "Haka ka so." Na faɗa a tsume kuma cikin gatse sai ya gimtse dariyan sa lokaci ɗaya yana faɗin" Ba za a yi haka ba. Yanzu dai ki bari in na samu dama zuwa ki haihu sai na koya miki." Na yi masa shuru ban ƙara magana ba amma ina ta gutsiran dankali da ƙarfi yana ƙara saboda haushi. "Kan lokacin ma ƙila abubuwa sun warware na sauya mota sai kawai na bar miki nawa Hajiya ta." "Ba na son wannan motar." Na faɗa da sauri ina kallon shi fuskata ba fara'a saboda ni fa gani na ke yi kawai Yallaɓai zama ya yi ya na ci mini fuska. "Sabo da mene ne? "Ba na sonta ne. Mota kamar za ka hau foo? "Foo kuuma? Yallaɓai ya maimaita cikin alamun tambaya. Sai na gyaɗa masa kai kafin na ce" E. Ni zan siya mota ta mai kyau irin ta mata." Yallaɓai sai dariya yake yi yana kallona. "Wai miye? Na zama abin dariya ne? Na faɗa a tsume fuskata a murtike ba ko fara'a. "Ke yanzu motar tawa ce kamar za a hau foo? Lalle kin ma raina mini wayau. Motar nan ma a gan ki a ciki duniya ne hajiya amma tun da kin raina shi kenan. Zan siya miki ta mata ko irin ta Daughter satin da ya wuce ta sauya mota wata Vibe mai kyau ta mata kina son irin ta na siya miki? Bai ba ni zarafin mgana ba na ga ya ɗauko wayarsa ya latsa sai ga hoton motar yana nuna mini tana da kyau. Sai da na gama gani sannan na ture hannun shi ina faɗin" Ba na son irin ta. In ta shi siya ai ni na san irin wacce nake so" Kawai sai ya riƙe baki cikin mamaki ni kuma sai na juya masa ƙeya ina faɗin" Kuma saura ka ce wai saboda matarka na da mota ne, nake son siya. Ni kawai ina so ne saboda nima na faso gari na dai na garari a cikin Adaidaita sahu." "Yaushe ne kike garari a cikin adaidaita sahu Sadiya? "Ba na yi ne? Na juya a fusace ina tambayarsa. "Fisabillahi fa Sadiya" Gani na yi magana da shi ma ƙara ɓata minu rai yake yi ya sa kawai na tashi na sauya kujeran zama na bar shi yana mini dariya. Tunani nake yi wata ƙila shi da matarsa sun shirya ne can kwanaki bai ko zencen ta in ma zencen ya zama dole sunanta ya ke kira kai tsaye. Yau ko tun da ya kira ta da sunan da ya ke kiran ta dashi na san sun shirya. Saurin kauda tunanin na yi ina mai faɗin miji da mata sai Allah tuni zai lallasheta su shirya har yana wani ɗaukan hoton mota ya na nuna mini saboda iyayi. Ina ta hararan shi ta gefen ido lokacin yana amsa waya ne. Bayan ya gama kawai sai ya ɗau remot ya chanza tasha. Daga MBCBOLLYWOOD suna haska wani indian film mai suna Khabi kushi kabhi gham. Tsohon film ne mun kalle shi tun muna da ɗan wayau ina son film ɗin kawai ina cikin kallo Yallaɓai ya sauya mini tasha ya kai can wani tashar turawa a na rawa. "Haba Yallaɓai ya za ka sauya mini tasha? Na faɗa a ƙufule sai kawai ya kalle ni bai yi magana ba ni kuma na mike a fusace na je na karɓe romot ɗin hannun shi na mayar tashar da nake sannan na koma na zauna ina girgiza ƙafafuwana saboda yadda na ke jin ɓacin raina nw hauhawa. "Allah ya ba ki haƙuri ban san kallo kike yi ba." "Kallo na ke yi mana. Ko da ka shigo ba shi ka iske ni ina yi ba? Na faɗa ina mai ƙure sa da ido fahintar da ya yi a fusace nake da shi ya sa koma ya jingina a jikin kushin ɗin kujeran ya na mai dannne dariyan shi. "To miye abin faɗa anan? Na ce ki yi haƙuri ban sani ba ne? Ɗauke kai na yi na mai da hankalina wajen kallon. Shi kuma ina ganin shi yana ta dariya ƙasa ƙasa. "Na gode Yallaɓai na zama abin dariya a wajen ka " "Kai na shiga uku. Wai dariyan ma ba zan yi ba? "E in dai a gaba na ne to zan ce ni kake yi ma dariya? Na ƙarishe faɗa ina zaro masa ido sai kawai ya koma ya kwanta a saman kujeran har yana miƙe kafa kafin ya ce" Ke dai ke ce yanzu kin koma rigimmaniya abu kaɗan sai ki yi zuciya ki hau faɗa. Allah ya baki haƙuri ni kin ga ma barci na ke ji" "Ka je ɗaki mana. Nan ai ba wajen barci ba ne" "Ni da gidana sai an zaɓa mini in da zan kwanta? Ina ƙoƙarin mgana ya yi saurin dakatar da ni yana daga kwancen bai taso ba ya ce. "Ki ƙyale ni na yi barci Sadiya. Ba zan iya da rigimar ki ba." Jin haka ya sa na yi shuru ban ƙara masa mgana ba. Zuwa can sai na ga kamar da gasken barcin ne ke fizgan sa, sai na rage ƙaran talabijin ɗin domin kamar ya dame shi. Daga baya ma da na ya fara barcin hani'an sai na kashe kallon a nan falo na koma falon su Jidda na kunna na cigaba. Har ta gama soya dankalin mu ka ci ni da ita. Baby na ɗakin su daga wasa ta bingire da barci sai la'asar na saka Jidda ta tashe su. Yallaɓai ma sai da na tashe shi sannan ya iya tashi da gaske yake yi yana da gajiya a jikinsa. Duk sai ya ba ni tausayi yana da ƙoƙari sannan ni kaina zan iya ba da shaidar mijina jajirtattace ne. Sai na ce masa ya bari da daddare ya sake wanka da ruwan zafi na ƙara shafe masa jikinsa da man zafi in sha Allahu zuwa gobe ƙasusuwan na shi da suka rirriƙe za su sake shi ya ce da ko ya yi ta saka mini albarka. Haka ko na yi masa zuwa washe gari tun asuba da muka tashi salla ya ce minI ya ji daɗin jikinsa. Ni kuma sai na mayar masa da martanin ya riƙa siyan man zafi ko ya na can gidan Gimbiya ne in ya ji kasusuwansa sun riƙe sai ya gasa jikinsa ta shafa masa. Nan ta ke ya ce ai tun da ya ji daɗin sa shi zai riƙa siya. Haka rayuwar dai ta cigaba da gangarawa yau a ji daɗi gobe a damu akasin sa. Gefe ɗaya ina cigaba da renon cikina da ya yi wani irin girma na ban mamaki ni ma ya mai da ni wata ƙatuwa. Shi ya sa ba na son fita sai ya zama dole. Daga asibiti sai gida ko Ɗorayi na daɗe ban je ba. Tun wani zuwa da na yi daga asibiti na biya na gai da  su Gwaggo ban koma ba amma dai ina mgana da su Ya Aina ta waya muna gaisawa. Siyayya kayan haihuwa kuɗi Yallaɓai ya ba ni muka je kasuwa ni da Jidda muka siyo komai da komai sai abin da ba a rasa ba. Da ya ke tun scan ɗin da na yi ya nuna mace zan haifa kuma ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba. A raina na ji ko da macen na samu tabbas zan yi ma Allah godiya. Tun da ya yi min ni',ima a farko a yanzu ma ya sake zaɓo ni cikin dubu ya sake ba ni wannan ni'imar. Itama Jidda zencen ta kenan Umma ki hai fa mana baby mai kyau mu yi ta renon ta ni da Baby. Itama Babyn macen ta ke so Yallaɓai kuma daman bai da zaɓi duk abin da na haifa ya na maraba dashi. Cikina na shiga wata na bakwai sai ya fara yin ƙasa. Mutane da dama sai su yi ta cewa namiji zan haifa saboda yanayin girma cikin. Ni kaina ina mamakin girman shi, ban taɓa yin ciki mai girman shi ba, ko na Jidda da ya ke na farko ne, jikina ya bi gwara ma na Baby ya ɗan yi girma. Amma shi wannan girman shi na dabam ne. Ban taɓa saka ma zuciyata ina son sai na haifi namiji ba. Abin da nake addu'a a duka khamsul salawati ɗina shi ne Allah ya sauke ni lafiya. Jinsin namiji ko macen duk wanda Allah ya ba ni, ni mai gode ma ni'imarsa ne. Kuma ni ban taɓa lura da cikin nan muni ya saka ni ba. Ban cika kallon madubi ba ta kaina na ke yi. Sai da za mu je gai da Mimisco ta yi fama da zazzabi ni da Yallaɓai da yara. Su sun rigani fita ni kuma na tsaya ɗauko makullin gida da hijabina har ƙasa na tsaya rufe gida tuni na ce ma Yallaɓai ya samo mana megadi ya ƙi. Wai a wannan a kurkin gidan ne sai ya wani saka megadi? Na bari in ya gina wancan babban gida sai ya ɗauki megadi amma ba a nan ba. Na fara takawa sannu a hankali zuwa wajen mota. Sai da na ƙariso na ji Yallaɓai na dariya shi da ƴa'ƴan shi. Ban ɗauka da ni suke ba na ɗauka labari ya ke ba su na abin dariya shi ya sa ban damu ba na buɗe mota da ƙyar na shiga na zauna a bangaren mai zaman banza na gidan gaba sai da na gyara zama sannan na ce. "Na ce motar na kama da za a hau foo ka ji haushina Yallaɓai. Yanzu don Allah ga irin mu masu lalura ai sai yaro ya jirgice a ciki saboda wannan motar ta ka." Sai na ji sun ƙara kwashe minI da dariya har da Jidda da nake gani saliha ba ruwanta. Sai na waiwaya ina kallon su nima ina ta ya su dariyan. A tunanina maganar da na yi ta saka su dariya ashe  ni ce suke yi ma dariya kamar sun samu cortoon. "Yallaɓai." Na kira sunan shi cikin mamaki ganin yadda yake dariya har ya na kwantar da kan shi saman sitiyari. Na fara zargin da ni yake saboda na ga sai ya kalle ni sai ya ƙara tsintsirewa da dariya. "Me kika gani? Ya faɗa ya na kuma cigaba da dariyan. Sai na ɗan tsume kawai na juya ina kallon gefen window ni kam ai na daina biye ma Yallaɓai tun da ya ce mini wai nishaɗi na ke bashi. Haka kurum zai ta sa ni yana mini dariya ko ya yi ta ja na da mgana ko faɗa sai na fara masifa sai ya koma gefe yana mini dariya. Tun da na fahimci mahaukaciya ya ke son mai da ni na fita sha'anin sa. In ya na dariyan shi ba na bi ta kansa. "Wai uban wa kuke yi ma dariya? Na faɗa cikin ƙufula. Ganin har su Jidda ban daina jin tashin dariyan su ƙasa ƙasa ba. Sai suka yi tsit kamar ruwa ya ci su. Yallaɓai kuma ba ni da yadda zan yi dashi shi ya sa na kallon shi a ɗage sannan na ɗauke kaina sama ina hura hanci. "Me suka yi miki? Ba su suka kai zomon ba." "To dariyan me kuke yi? Haka kurum ku ta sani kuna yi mini dariya? Na faɗa har ina yarfa hannu. Zaune kawai na yi ina kallon Yallaɓai na kallona ya na cigaba da dariyan sa. Tuni na harzuƙa na cika saura kiris na fashe. "Me ye abin dariya a jikina? Na faɗa ina kallon shi ganin da ya yi a fusace na yi maganar ya san yanzu nan zan birkice musu. Ya kuma san halina ba ni da sauƙi. "Wai. Sannu Hajiya Dubu." Ya faɗa ya na kallona har ya na ƙwarewa saboda dariya. A raina na ce Allah ya ƙara. Saboda ai dariyan ta mugunta ce. "Ban taɓa tunanin sunan da Alhaji ke kiran ki dashi ya dace da ke ba sai yau." Sai kawai na koma ina bin kaina da kallo. Rarrashin kaina na ke kar na kai ma Yallaɓai duka. Sunan nan ban da Alhajinmu da Gwaggo na haramta ma kowa ya kira ni da sunan nan saboda ba na so. In wanda na ke jin kunya ne ba na mgana amma in har ba na jin kunyar nan ta ke zan maka in karin da cewa ni ba sunana Dubu ba. Yallaɓai bai cika tsokana da sunan ba sabo da ya san yadda na fi tsanar sunan gwara ma a kira ni da Sadiya ƴar laushi. Amma yau Saboda cin mutumci yana kirana da shi a gaban ƴa'ƴa na bayan ya tara su suna yi  mini dariya. Da dai na fahimci yadda ciki ya mai da ni suke yi ma dariya sai ban ƙara magana ba. Ya gama dariyan shi ya na tsokanata da mgana na yi masa banza. Su jidda kan sun yi tsit sun san halina wallahi yarinya ta ƙara mgana sai na yi mata bugun tsiya. Tun da uban su ba zai dakun mini ba to ai su ni na haife su zan yi iya hawa ruwan cikin yarinya na yi mata lilis ba mai ce mini me ya sa? Baby ta fi shan dukana  domin da cikin nan ban san a dadin dundu da rankwashi nawa ta sha ba. Ita Jidda ba ta cika laifi ba ina son yarinyar ta na da gudun zuciyar iyayenta. Bar muka isa gidan Mimisco a tsume nake. Ita kanta sai da ta yi maganar ta ga raina a ɓace me aka yi mini. Cikin jin haushi na ce" Wai Yallaɓai ke mini dariya saboda ciki ya sa duk na zama cus. Har yana tara su Jidda suna kallona suna mini dariya. Tsabar yadda abin ya tsaya min a rai sai da na ji hawaye sun kawo minI. Ita ko da yake ta san irin yanayin nan da nan ta fara masa faɗa. "Kai shike nan haka ake yi? Sai ka yi ta mata dariya? Waye silan da ta koma haka in ba kai ba? Ka daina tun da ta ce ba ta so don Allah Tafida ka daina. Ka san yanayin masu ciki sai a hankali in suka ce ba su so abu gwara a bar shi zai fi alheri." "To na bari shi kenan? Ya faɗa ya na kallona kuma ya na ƙara mini dariyan yadda zuciyata ta kawo a lokacin duk da a gaban yayarsa ne sai da na shammace sa na kai masa bugu a gadon bayan sa lokaci ɗaya kuma na fashe da kuka domin ji na yi in ban yi kuka ba kamar zan mutu saboda haushi. "Kin gan ta ko Mimisco? To kuma ta dake ni, ni ban yi kuka ba sai ita? "Tashi ka fita ka ba mu wuri." Da haka ta fattake shi,ya fita can falon mijinta ni kuma sai ta koma ta ba ni haƙuri. "Ki yi haƙuri Sadiya. Kin ji ko? "Mimisco na gaji da abin da Yallaɓai ya ke yi mini a cikin gidan nan.  Abu kaɗan sai ya ta sa ni a gaba ya na mini dariya." Na gama faɗa bilhaƙki da gaskiya ina sharen ƙwalla sai ta taso ta zo gefena ta zauna ta na bubbuga bayana alamun lallashi. "Ƙyale shi. Tsokanar ki yake yi kuma jin daɗi yake yi fa. Ki daina biye masa kin ji ko? Ina sharan ƙwalla na ce" Da man nima ai ba na biye masa " Ita ta yi ta lallashina ta ba ni haƙuri, mun yi awa ɗaya da wani abu sannan muka yi shirin tafiya ita da megidanta da yara suka rakomu har bakin mota suna ɗaga mana hannu "Allah ya huci zuciyar gimbiyar Tafida." Ya faɗa bayan mun fara tafiya. Ganin na yi masa fuska ina hura hanci ba annuri a fuskata kwata kwata. Kaina na mai da barayin window ina kallon giftawan motoci na yi kamar ban ji sa ba sai ya ƙyale ni ya koma suna mgana da Jidda kan mganar buɗe gari sai na karkata kunnina ina jin su. "Cutar ta fara sauƙi. Tun da an nemi kariya ina tunanin ba zai wuce wata biyu ba za a buɗe gari ku koma makaranta." "Allah ya sa Abba. Amma har na gaji da zaman gida. Da yanzu ina level 1 fa Abba." Ta faɗa cikin ƴar shagwaɓa. Sai Yallaɓai ya yi dariya kafin ya ce" Allah ya tsara Nene ta. Kar ki damu za ki shiga makaranta a shekara mai zuwa in sha Allahu." Ina jin su amma tun da ina jin haushin shi ban nuna ma na ji ba. Ban yi wani murna ba da na kalli cikina sai ƙarsashina ya ragu ina zan je da wannan cikin? In ma na haihu ba hutu ba ne har sai na yi yaye. Wataƙila Yallaɓai ya yi ta addu'a ne shi ya sa ba ni da rabon komawa makaranta. Muna cikin motar kafin mu kai gida na ji Baby na tambayan shi ina su Khalipa sai a lokacin Gimbiyar ta faɗo mini a rai. Kwana biyu ba mu haɗu ba sai na ji ya na cewa ba sa gari sun tafi Rano da yara jiya. Har Jidda ke faɗin yaushe za a saka Khalipa a makaranta? Ya ce da zaran an buɗe makarantu. Har muka kai gida ina tunanin wani abu. Tuni Gimbiya ta janye ƴaƴanta daga zuwa gidana. Wato na gama cin wahala da su musamman ma Khalipa shi ne yanzu za ta nuna min ita ƴaƴanta ne. Shi kan shi Yallaɓai ya daina tarkato mun su. Wata ƙila ta nuna ba ta so ne sai ya bar ta da ƴaƴanta haka nake tunani. Su Jidda ma ta daina neman su nima ba na cewa su je gidanta. Gwara Baby ma da Jidda. Ita ba ta son zuwa ma kwata kwata. Yallabai ma ba ya matsa musu abin da na fahimta kowa ya zauna in da yake kawai. Kuma Gimbiya yadda take kishi da ni ina da tabbacin ni da ta aure mini miji bana yi da ita. Ta so ni ta riƙa juya ni ta ba ni umarni ta zama ita ke tafiyar da rayuwar Yallaɓai gabaɗaya sai kuma ba ta samu wannan damar ba. Baƙin cikinta Yallaɓai ya nuna ina da daraja. Sai ta ke ganin ya fi sona a kanta nima kuma ina ganin ya na son ta. Daga baya sai na fahimci maza in suna da mace fiye da ɗaya to zargin an fi wata a kaina ba zai bar zukatan mu. Duk yadda ya so ya yi adalci sai wata ta ce ya cuceta. Haka rayuwar namiji mai mace fiye da ɗaya yake. Ni dai na riƙe maganar da Alhajin mu ya yi mini na zama da ita da zuciya ɗaya. Ruwan ta ne ta zauna da ni da wani manufa ni dai na riƙe Allah kuma shi ne ke yi mini jagoranci a duka lamurana. Har muka koma gida ina cin mgani ina ta hura hanci. Ban ɗauka zan haƙura da wuri ba sai gashi a daran ya lallasheni na haƙura amma da sharaɗin ba zai ƙara mini dariya ba in ya ƙara duk matakin da na ɗauka ya amince. Sai ya fara cewa zan hana shi dariya ne? Na ce ba zan hana shi ba amma in dai a kaina ne na haramta masa. Da ya ga na tubure sai ya amince tun daga lokacin na samu lafiyan shi in ma zai yi dariyan to a bayan idanuwana yake yi. Tun kuma daga lokacin nake kallon kaina a madubi ina ganin duk na yi baƙi na lalace na yi muni. Sai na daina ganin laifin Yallaɓai in ya yi mini dariya. Tabbas halitta ta jirkice. Komai na fuskata ya yi girma ni kaina ina na ga hancina a madubi na shafa na ji ya buɗe fafa sai na yi ma kaina dariya. Ina ciki mai sauya halitta amma fa shi wannan cikin komai na shi wani sabon salon ya zo da shi. **** *September* A ƙarshen watan september lokacin cikina ya shiga wata na takwas kenan. Muka yi wayi gari a safiyar talata da rasuwar yaron Ya Abubakar na farko mai sunan Ya Hamza. Ciwon ciki daga dare zuwa safe, sun ɗauko shi da asuba zuwa asibiti suna hanya ma ya rasu. Yaro ne ɗan shekaru goma sa'an Baby ne ta ma ɗan girme shi da kaɗan. Ya Aina ta kira ni ta faɗa mini ƙarfe shidda na safe ta ce na zo gida a nan za a yi masa wanka da sallah. Yallaɓai ba ya gidana ya na can gidan Gimbiya sai na kira shi a waya amma bai ɗauka ba a na farko sai da na sake kiran shi Gimbiya ta ɗauka ba gaisuwa ba komai ta ce mini wai yana wanka. Duk da na ji wani motsi a cikin zuciya ta ban nuna mata ba sai na ce in ya fito ta faɗa masa yaron Ya Abubakar ya rasu za mu tafi Ɗorayi ni da yara sai ta ce to za ta faɗa masa sai a lokacin ta ce Allah ya jiƙan sa na ce Amin. Bayan na kashe wayar sai da na duba lokaci shidda na safe ta gota da mintina ashirin. Na san kuma dalili ɗaya ke saka Yallaɓai wankan safe. Wani abu ya ƙara sukan raina daman da gayya ta ɗaga wayar domin ta faɗa minI ta yi sunna da Yallaɓai. Ganin ni da a ka yi ma rashi tuna kishiya ba nawa ba ne sai na watsar da maganar Gimbiya na fita na je ba yi ma su Jidda mgana na ce su shirya mu je ɗorayi. Hamzan Ya Abubakar ya rasu Baby sai ta fara kuka Allah sarki abokin wasanta ne in dai suka haɗu Jidda ma ta yi shuru jikinta duk ya yi sanyi. Ba mu tsaya wanka ba muka saka hijabai na kulle gida muka samu adaidaita zuwa can Ɗorayi. Gida cike da mutane har Ma'u a can na ganta. Sai dai ina zuwa Rahila na zuwa har Zaitunan da ƴan'uwanta suna gidan Allah Sarki ta na ta kuka gwanin ban tausayi. Gwaggo ce ta yi ma yaron wanka su Ya Abubakar da Alhajinmu da su Ya Muntari duk suna waje a ƙofar gida. Bayan Gwaggo ta gama yi masa wanka a ce iyayen shi suje su gan shi su yi masa addu'a. Shi dai Ya Abubakar ya yi dakiya amman Zaituna sai da a ka riƙe tana ta kuka kamar za ta shiɗe. A ƙofar gida a ka yi masa salla sannan a ka tafi kai shi gidan sa na gaskiya. Allah ya ba mu sa'a. Su Jidda duk sun yi tsuru tsuru jikin su ya yi sanyi. Rayuwa kenan Allah ka kyautata ta mu bayan ta su Amin. Sai da a ka dawo daga kai shi can wajen sha biyu Zaituna da ƴan'uwanta suka koma can gidan ta saboda masu zuwa mata gaisuwa mu kuma sai muka zauna a nan saboda makota. Amma Ya Balki ta bi su can gidan, su Amina duk sun kira sun yi gaisuwa Ya Hamza da Ya Auwal sun kira kuma matan su sun kira. Sun ce za su shigo gaisuwa weekend saboda yanayin aikin su. Sai can rana Yallaɓai ya kira ni ya ce mini gashi ya zo ya ba ni mamaki tun safe sai yanzu? Sai da ya shigo cikin gida muka keɓe muna mgana ne ya ce mini Gimbiya ba ta faɗa masa ba har sai da ya tashi barci. Kasa mgana na yi kawai na tsaya ina kallonta. "Lalle." Kawai na iya furtawa saboda mamaki ya hana ni ma mgana. "Sai da na yi mata faɗa. Wai ta manta ne ba ta faɗa mini ba lokacin da ta tuna kuma na kwanta. Na ce da tashe ni ai mutuwa ta wuce komai." Ni dai kawai na kalle shi amma ban yi magana ba. To me zan ce? Ai da yaron yayanta be ya rasu ba barci ba ko me yake yi za ta tashe shi ta  faɗa masa amma tun da bai shafe ta ba ba za ta damu da ta faɗa masa a kan lokaci ba. "Ki yi haƙuri. Allah ya jiƙan sa." "Amin" Na amsa masa kafin na ce" Ka zo kuma Zaitunan ta koma gidan ta ɗazu." "Ayya to mu je ki rakani na yi mata gaisuwa daga can sai na wuce office." Sai na ce masa to daman muna korido ne a tsaye muna mgana cikin gida na koma na ɗauko Hijabi ina faɗa ma Gwaggo zan raka Baban su Jidda gidan su Zaituna. Rahila na zaune ta miƙe ta ce za ta je. Ma'u na kalla tana zaune ta yi tagumi tun da safe na lura da ita ba ta da kuzari ta yi firgai firgai kuma ni dai a yadda na san Ma'u ba haka ta ke ba. In ma idanuwana sun gano min dai-dai ta rame ta yi baki sannan ba gayun nan ba surutu. Kuma ba za a ce mutuwar da a ka yi ba ce ta mai da ita haka ba ai Baaba na raye ban ga abin da zai saka Ma'u ta susuce haka ba. Ko a lokacin suna zaune kugu da kugu ita da Ya Murja. Wataƙila koma me ke damunta ita za ta fi kowa sani tun da suna tare. Ni dai ban samu na furta ma kowa yanayin da na ga Ma'u ba har muka kai Yallabai gidan Zaintuna ya yi mata gaisuwa mu can ya bar mu ya wuce. Da ya ke ba nisa. Ya Abubakar ya siya wani ƙaramin gida a can ƙasan layin gidanmu shi ya sa sai suka dawo kusa. Mu na gidan sai bayan la'asar muka koma gidanmu. Nan ma ana ta shigowa maƙota da abokan arzuka duk wanda ya zo sai a yi masa kwatancen gidan Zaituna. Ya Murja da Ya Aina su suka yi abincin rana tun da akwai mutane. Muna gidan har dare ni dai da wuri na tafi bayan mangariba Yallaɓai ba gidana yake ba, sai da muka koma ya kira ni ya ce zai zo ya ɗauke mu na ce mu kan muna gida. Washegari ma ban jira shi ba. Tun safe na ta da Jidda ta taya ni muka dafa abinci shinkafa da wake muka saka a babban kula ƙarama da babba.  Babban a ɗakin Gwaggo karamar kuma na ba ma su Jidda su ka kai gidan Zaituna. Ƴan'uwan Yallaɓai duk sun kira sun yi mini gaisuwa da ya ke Yallabai in wani abu ya faru na jaje ko na murna ya kan saka a group ɗin su. Ranar biyu Hauwa da Munnira suka zo mini gaisuwa. Sai ranar da a ka yi uku Gimbiya ta zo lokacin ma ta iske su Suwaiba da Jamila sun leƙo mun gaisuwa. Shi ya sa ba ta wani daɗe ba daga ita sai Anwar Suwaiba ce ma ta tambayi  Khalipa sai ta ce ta baro shi a can Rano. Ni dai ban ko tambaye shi ba tun da ba ta ma wani daɗe ba ta ce za ta tafi na yi mata rakiya har waje. Ta zo da mota har ta rage ma su Suwaiba hanya zuwa Gwamnaja. Na ko ga sabuwar motar ta a fili ma ɗaukan ido take yi. Bayan an yi uku ne ban sake komawa ba sai ranar da biyar. Ranar lahadi kenan da su Ya Hamza suka zo ba su kwana ba a ranar suka koma. Shi daman Ya Auwal ya ɗan zo yin wani abu ne a reshen su na nan Kano kuma ba shi kaɗai ya zo ba shi ya sa bai jima ba ya tafi da cewa daga can kawai za su koma Abuja ne. Kuma tun daga ranar ban koma ba sai ranar bakwai a gidan Zaituna, muka zauna a ranar su Inna Mariya suka zo gaisuwa an manta da su sai da Amina da ke kaduna ta kira wayar Inna ta faɗa mata. Da suka zo tana ta faɗa ni dai na ba ta haƙuri na ce wallahi an sha'afa ne. Matar Kawu Tasi'u ta zo da fanke da yawa na sadaka sai bayan la'asar suka tafi. Dukkan mu muna gidan har Ma'u da ranar ba da wuri ta zo ba ashe ba ni kaɗai na fahimci Ma'u ta susuce ba sai da Rahila ta yi mini mgana. "Sadiya wai Ma'u ciwo ta yi ne? Ta ke tambayata sai na kalleta kafin na ce" Ni ko ta ina zan sani? Nima dai haka na ganta duk a firgice tun ranar da a ka yi rasuwar na." Rahila ta jinjina kai kafin ta ce" Nima wallahi na tun ranar na lura. Kamar wacce ta yi jinya duk ta firgice." Sai na jinjina kai ina ƙara kallon Ma'u. Wallahi har idanuwanta sun zumar ma. Sannan na daina ganin Zainab ƙanwarta da ke wajenta ko ta koma gida ne oho? Sannan ba ta ma zo da yara ba tun da a ka yi rasuwar ita kaɗai take zuwa ba. Kuma ban ga Alhaji Mustapha ba na ji dai a bakin Ya Aina ranar da a ka yi rasuwar da shi a ka yi jana'iza. Duk da ba na shiri da Ma'u na ji na damu da ganin yanayin ta. Na tuna a shekaran da ta wuce na taɓa zuwa gida Alhajinmu ya kirani yana mai tambaya ta. "Kina zumunci da ƴar'uwan ki Asma'u kuwa Dubu? A lokacin ban ɓoye ma Alhajimmu komai ba gaskiya ta na faɗa masa. "Ina dai yi maka kara Alhajimmu. Ina gaisheta in mun haɗu sannan in abu ya kama na jaje ko na murna ina yi mata." "Kin kyauta Dubu. Kin yi mini kara sannan kin yi ma zumunci kara." Daga lokacin bai ƙara matsa mini ba. Tun da dai ya samu tabbacin ba ma gaba da juna. Nima hakan ya fi mini tun da yanzu na samu sauƙin ta. Sai yanzu da na gan ta sai na fahimci itama ta na can tana fama da kanta ne. Ko da ga ganin yanayin ta wani al'amari ne mai girma ya gigita tunaninta Ma'u  fa macen da ba komai yake razanata ba. Ba a cika ganin gazarta ba amma yau na ga kasawa a yanayinta da idanuwanta. Ashe ba ni da Rahila duk muka fahimci Ma'u ba ta hayyacinta ba har da Ya Aina da Ya Balki. Ita dai Ya Balki Zainab ta fara tambaya da yara sai Ya Murja ta amsa da cewa Zainab ta je ganin gida. Su Alhaji ƙarami kuma suna gidan iyayen Alhaji mustpha sun je hutu. "Oh shi ne na ga Ma'un duk ta yi wani sanyi haka? Kewar yaran ce? Ya Aina ta faɗa cikin zolaya. Ma'u yaƙe kawai ta yi ta kasa mgana. Ina lura da Ya Murja ta na son mgana amma kuma sai ta fasa yi shuru. "Wai ni kam ina labarin Shema'u? Na daɗe ban ganta ba ina jin tun auren ta." Sai Ma'u ta rausayar da kai kafin ta ce" Tana can Gombe. Mijinta kulle yake yi mata." "Kuma ba ta da ciki? In ji Rahila. "Ba ta da ciki gaskiya." Ta faɗa a sanyaye ni dai kallonta kawai nake yi. Maganar Allah Ma'u ta rame ko ni kaɗai ke ganin ramar na ta? Na faɗa a cikin raina. "Shi ya sa ba ta yawan zuwa kenan." To Allah ya zaunar da ita lafiya da man wasu mazan akwai kulle. Kuma itama Shema'u sai da haka in da ya bar ta da duk sati za ta iya zuwa Kano a shirmen ta." Sun cigaba da tattauna mganar Shema'u. Ma'u na gefe ta yi tagumi ta yi shuru da ga gani ta shiga zurfin tunani kamar ba zan yi mgana ba sai na muskuta da cikina a gaba. Wata doguwar riga ce a jikina da na saka a ka ɗinka min su bubu tun da duka kayana sun yi mini kaɗan. Sai na siya yaduka da ƙananun atamfofi na ba da a ka mini ɗunkunan masu ciki su na ke sawa ina jin daɗin su. "Wai ni kaɗai na lura da Ma'u duk ta rame? Na faɗa ina kallon su Ya Aina sai suma suka kalle ni sannan suka koma suna kallonta duk sai ta tsargu. "Nima wallahi na lura. Ba har na yi magana ba ranar." Rahila ta faɗa, Ya Aina ko sai ta yi shuru kafin ta ce" Ni kaina na ga haka tun kwanaki da na ganta. To na yanzu ma abin ya ƙara lalacewa idanuwanta duk sun zurma" "To ko ciki ne da ke Ma'u? In ji Ya Balki. Sai Ma'u ta kasa mgana ta dukar da kai tana wasa da kwalliyar material ɗin rigar da ke jikinta. "Ma'u me ke faruwa da ke ne? Mu ƴan'uwan ki ne. Kina ganin bai kamata mu san matsalar ki ba? Kawai sai Ma'u ta saka kuka. Ni fa har ina buɗe baki saboda mamaki. Na daɗe ban ga kukan Ma'u na haƙika ba sai ranar. Duk sauran kukan  da na saba gani na makirci ne amma na yau na gaske ne fitowa yake da sauti daga ƙarkashin zuciyanta. "Subhanallah me ya faru Ma'u? Ya Balki ta faɗa. Ni da Rahila ma mun kasa magana. Ganin yanayin Ya Murja ya sa na san ta san abin da ke faruwa. "Ya Murja fa ina ganin ta san wani abu." Na faɗa ina kallon su Ya Aina duk suka mai da kallon su kan Ya Murja. "Murja me ke faruwa? Sai ta kalli Ma'u kafin ta ce"Uhm aure Alhaji Mustapha zai ƙara. An kusa karshen shekaran nan." Yadda na zaro ido kamar na ga wani abun tsoro Kowa sai jikin sa ya yi sanyi. Duk da ba na son Ma'u itama ba ta so na amma jini ya yi aiki a kaina wallahi na tausaya mata matuka. Kishi bala'i ne ba wanda ke gane yanayin sai wanda ya faru a kan shi. Ni da ya ke Victim ce ai na san irin yanayin da take ciki. Na ji na ƙara tausayinta da Ya Murja ke faɗin karamar yarinya ce yar sha takwas zai aura kuma sai da a ka saka ranar ta ke ji bakin Uwargidan shi. Matsaloli da dama yanzu ya daina ma rawan jiki a kanta da ta yi masa mgana bai faɗa mata sai da suka yi tsiya har ya ce in ba za ta iya zama ba ta tafi shi bai hana ta ba ashe  gurmu a ka yi har sai da Baaba ta zo garin nan amma Alhajinmu bai sani ba. Itama Ya Murja ta ce faɗan su na biyu ne Ma'un ta zo gidan ta, ta na kuka shi ne ta san abin da ke faruwa ita da mijinta suka mai da ita. Yadda ta ke faɗa yadda Alhaji Mustapha ya ɗauko auren nan to uwarsa ce kawai za ta ce kar a yi ya saduda. Amma ba Ma'u ba ya ce ko za ta mutu sai ya yi auren ita ba a aure ya aure ta. Yadda Ya Murja ta ce Ma'un ta faɗa mata ita uwargidan sai daɗi ta ke ji tana ƙara zunguran Alhajin da maganar auren. "To daman me zai dame ta tun da ba ita za a yo ma wa ba? Na faɗa ina jin wani motsa daga ƙasan zuciyata. ta ba ni tausayi kishi ai masifa ce. "Haka ne. Amma ita ma Ma'u ta kwazzaɓi kanta tun da ta san ba zai fasa wannan auren ba, me ya sa ba za ta kwantar da hankalin ta ba? "Ya Aina Alhaji ba ya sona yanzu. Magana kaɗan sai ya rufe ni da faɗa. Hajiya Zainab ce ke juya shi ta na gaba gaba wajen zuga shi ya yi auren kuma yarinya ƙarama fa zai auro." Ta faɗa ta na ƙara rushewa da kuka. Da gaskiyanta haka a ke ji fa in za a yi ma mutum kishiya. Balle ita da ta haɗu da kai din kishiya ita ai daman za ta so a yi mana amma kuma ba ta kyauta bai kamata in ba ya kamata in ba za ta iya hana shi ba to kar ta ingiza shi. "Duk da haka Ma'u da kin kwantar da hankalin ki. Kin ta rama ki kashe kan ki a banza shi fa ba fasawa zai yi ba" "Wallahi kuwa. Ki yi hakuri ki kauda kan ki. Ki yi koyi da Sadiya mana. Lokacin auran Baban su Jidda jarumtar da ta nuna wallahi sai da ta burge kowa."   In ji Ya Balki. "Gaskiya. Haƙuri a ke yi tun da su Maza in suka yunƙuri da maganar aure ba mai iya hana su. In ka matsa ma sai su ce ka yi gaba." Cewar Rahila. "Wallahi nima haka na yi ta faɗa mata ta yi haƙuri da kwantar da hankali ta ki jin mgana ta." Ya Murja ta faɗa, duk suka haɗu suna ta mata faɗa ta kwantar da hankalinta ta yi hakuri da na so na yi shuru tun da ai kamar alhakina ne yakama ta, lokacin da za a yi mini kishiya ta biye ma su Anty Bahijja ana mini dariya ta manta ita mace ce zai iya faɗowa kanta. Ita ai kishiya yanzu ta zama ruwan dare in ba a yi miki ita a kusa ba. A gaba kaɗan za a iya miki ita. "Ma'u kalle ni nan in ba ki wata shawara in har zaki iya ɗauka." Na faɗa ina kallonta itama sai ta bar goge hawayen tana kallona. "Kukan ki da wani fushin ki da ramar da kike yi duk a banza ne a wajen namiji. In dai suka tashi ƙara aure in ke ta gida ba ki haƙuri ba wallahi sunan ki sorry. A gari a kalle ki a wacce za a yi ma kishiya ta ki kwantar da hankali. Shi kuma yana miki kallon mai son kanta. Dangin sa suna yi miki kallon ba a aure a ka aure ki? Mafita ɗaya ce a gare ki, ki kwantar da hankali ki dogara ga Allah. Ki kaima Allah kukan ki shi Ubangijin kowa ne mai share ma kowa kukan shi. Ki roƙe sa ya cire miki damuwa ya ba ki dangana. Ya ba ki juriya da haƙurin ɗauka. Sannan ki sani dole sai kin toshe kunnuwan ki, abin da kika ji ki nuna baki ji ba, wanda kika gani to ki nuna ba ki ji ba. Ki tsaya a matsayin ki magana in ba ta shafe ki ba ki zare kan ki ciki. Magana in dai ba ta tsallake hurumin da kika ga za a tozarki ba kar ki sake ki tanka. Yanzu gazawar ki a ke nema domin a samu damar ya ƙar ki, in ki ka yi sakaci kaɗan in ya auro ta za ki zama a bar takawarta amma in kika rumgumi haƙuri wallahi za ki ci riba. Ki zauna da ita saboda Allah sai ki ga ubangiji ya yi miki nasibin da har shi mijin na ki zai dawo yana daraja ki. Ki yi duba da ni ba irin abin da ban gani ba. Amma na yi hakuri na jure, Gimbiya kishi ta ke da ni muraran amma ban nuna mata na san tana yi ba. Kwanaki har sa'in mun yi da ita amma ban faɗa ma kowa ba. Saboda Yallaɓai ya yi mini kara ya kuma darajani ya nuna mata in ta ce za ta mini rashin ɗa'a to kamar shi ta yi mawa! Me ya jawo mini wannan darajan? Haƙurina da nuna komai ba komai ba. Na san kishi da zafi na san kishi na da raɗaɗi amma don Allah ki daure ki yi addu'a  in sha Allahu za ki samu sauƙi samun sauƙin ki kuma shi zai ba ki damar da za ki zauna ki yi ma kan ki tunanin mafita. Mafitan kuma shi ne haƙuri da kauda kai. Wata rana sai labari Ma'u. Haka  duk wata macen da aka yi ma abokiyar zama ta ke ji da farko amma in ta yi haƙuri wata rana sai dai ta tuna." "Wannan gaskiya ne." In Ya Aina. Ya Balki ma ta ce shawara mai kyau. Har Ya Murja sai da ta ce na gama ba ta dukkan shawaran da za su ba ta. Ma'u sai sharan ƙwalla tana mini godiya na ce yiwa kai ne amma na jadadda mata faɗa da miji ba na ta ba ne. Itama uwargidan nata na yi ne saboda ta ga ta ɗaga hankalin ta in ta ga ta kwantar da hankalinta da kanta za ta daina. Daman ai kulawa yabawa ta ga ana yabawan ne shi ya sa. Har na koma gida auren mijin Ma'u ya tsaya mini a rai. Na tausaya mata matuka. Ba ita kaɗai duk macen da za a yi ma abokiyar zama tausayi take ba ni. Mace ba ta sanin gwagwarmayan zamantakewa har sai an yi mata abokiyar zama. In shekaru dubu za ki kwashe da mijin ki in dai bai ƙara aure ba, to ba ki san zamantakewa mai cike da fafutuka ba. Mu da a ka yi mawa muke zaune da su mu kadai ne za mu iya faɗin irin fafutukan da muke yi a zamantakewar mu na yau da kullum. Na daɗe ban cire abin a raina ba. Kuma kusan ɗan'uwa rabin jiki duk yadda na ke jin haushin Ma'u tausayinta ya danne haushin nata bayan kwana biyu na kira ta a waya na ƙara tausarta ta, da ba ta shawarwarin da za ta riƙe su amfane ta. Tana kuka tana faɗa  mini. "Na gode Sadiya. Na gode Allah ya saka da alheri." "Bakomai yiwa kai ne Ma'u" "Duk da haka dai zan yi miki godiya. Duk da tarin abubuwan ƙin da na yi miki ba ki riƙe ni ba. Matsala ta tunkaro ni kin nuna mini ke ɗin ɗin yar'uwata ce. Ba ki yi mini dariya kamar yadda na ke yi miki ba in kin shiga matsala. Sai ki ka zabi ki jawo ni a jiki ki saboda mu gudu tare mu yi tsiran tare. Na gode Sadiya kin ƙara haska mini rayuwa. Na gode ina fatan ki yafe mini duka laifukan da na yi miki." Sai ta ba ni tausayi har sai da ruwa ya cika kwarmin idanuwana "Na yafe miki Ma'u. Allah ya yafe mana gabaɗaya." Muka yi sallama kamar ta yi min sujjada. Rayuwa kenan ban taɓa tunanin Ma'u za ta yi laushi haka ba sai ga shi a cikin lokaci ƙalilan Namiji ya birkita mata tunani. Hmm namiji. Namiji buhun ƙaya ne. Mai sauya launi gabansa fari bayan sa baƙi. *Janafty**TKGB30G07* Lokaci bayan lokaci ina kiran Ma'u na ji yadda a ke ciki. Zamantakewarta da Alhajin nata dai sai a hankali, tun da ya yi niyyar auren nan sai ya yi ita kuma Ma'u rashin haƙurin ta ya sa duk ta zube a wajen shi. Shi fa daman Namiji haka yake. In suka tashi ƙara aure to ba sa ji ba sa gani ne in ba ka yi haƙuri ba to za ka yi nadama ko kuma ka ga a na yi. Kuma a yadda na lura ita Uwargidan Ma'u ta na yin komai da gayya ne saboda tura ma Ma'u haushi. Ko ramuwa ta ke yi wa ya sanin mata. Domin Ma'u ta yi lokacin ta yanzu ne alƙadarinta ya ƙarye take girban a bin da ta shuƙa. Ni dai haƙuri nake ba ta domin babu kamar haƙuri. Ba a yanzu za ta ga riban hakurin ba sai nan gaba. In dai za mu yi waya da Ma'u sai na ji ta cikin kuka Allah sarki wallahi tausayinta nake ji. Saboda ni na san zafin ƙishi, ga kuma ita abu ya haɗe mata biyu ga kishi ga ba zaman lafiya da miji. dole ta yi kuka, abin da ya ba ni mamaki cikin lokaci ƙankani wannan rashin jituwar dake tsakanina da Ma'u ya gushe. Har mantawa na ke yi da ba ma jituwa, ko ban kira ta abu kaɗan za ta kirani ta na faɗa mini ni kuma na yi ta ba ta hakuri domin shi ne kaɗai abin da zan iya faɗa mata. Sannan shawaran haƙuri na da zafi sai dai tana da riba a nan gaba. Tana kawo mini ƙorafin cewa ranar da ya ke gidanta kusan raba dare ya ke yi waya ko chart in ta yi magana sai ya ce ba ta isa ta hana shi yin waya ba. Na yi ta ce mata ta yi haƙuri ta ƙyale shi ta riƙa shigewa cikin ɗakin ta, ba ta ji ba ballanta hankalinta ya tashi tun da ta faɗa mini ba a ɗakinta ya ke wayar ba ko falo ko cikin Bedroom ɗin shi. Sannan ta ce ba ya mgana da ita ko gaishe shi ta yi da ƙyar ya ke amsawa. Ya kuma je can Kura ya karɓo yaran ya kai su gidan Uwargidan, da ita kawai ya ke shawara yanzu ita ce ke kitsa masa komai a kanta duk na ce ta kauda kanta daman yana yi ne saboda ta yi mgana to ta yi kamar ba ta ji ba kuma ba ta gani ba. Ni ko Yallaɓai ban taɓa masa mganar ba sai ranar ya na gida na ya ji muna waya duk da tashi na yi daga falon saboda sirrina bai kamata na yi wayar yana wajen ba. Sai da na dawo falon ne jin bai tambaye ni ba, na san halin shi Yallaɓai bai cika bin diddigi ba. Ni ce ma na faɗa masa Alhaji Mustapha zai ƙara aure. Kawai sai ya fashe da dariya ya na faɗin."Ma sha Allah. Ta uku fa zai yi ko? Ya faɗa ya na kallona sai kawai na gyaɗa masa kai ban samu zarafin mgana ba. "Kai ya yi ƙoƙari da kyau. Gwara in kana da shi ka cike sunnar gabaɗaya." Kawai sai na yi jagale ina kallon Yallaɓai har wani dariyan nishaɗi yake yi. "Yaushe ne bikin? "Ban sani ba." Na faɗa ina tsumewa, sai ya sake kallona yana mini dariya. Haɗe rai na yi ina kauda kai kafin na ce" Yallaɓai ko kai ma kana shirin yo ta ukun ne? Sai ya kalleni kafin ya ce" To in Allah ya kaddara min zan ce ba na so ne? Har sai da na buɗe baki saboda mamakin sa. Ni fa daman tuni na sha jinin jikina Yallaɓai zai iya ƙara aure in ma bai cike ƙofa ba. "Kishi kike yi? Ba ki so na ƙara aure? Tsaki na so na ja amma sai na yi shi a ƙasan raina. "Ai ni ka gama mini kishiya Yallaɓai. Duk wacce za ta zo daga baya ba za ta ɗaga mini hankali ba." "Ki ce wallahi." Ya faɗa ya na mini dariya sai na ga ya mai da ni kamar wata shashasha. Hararan sa na yi, ban sake mgana ba. "Ki rantse in yanzu na ce zan ƙara aure ba za ki ji komai a ranki ba? "Ba zan ji ba. Ba kuma sai na rantse ba." Kawai sai Yallaɓai ya ta so ya zo gabana ya durƙusa. "Ki ce wallahi ba za ki yi kishi ba." Sai kawai na kalle shi, lura na yi maganar ma nishaɗi take saka shi. "Ba sai na rantse ba." "To ƙarya ne. Ke ɗin ce ba za ki ki kishi ba? Ya faɗa har ya na jan mini kumatu, na ture hannunshi kafin na ce" Me ya sa zan yi kishi! Na faɗa maka ni ka ga mini kishiya. Yanzu ai tsakanin ka da Gimbiyar ka ne." "Saboda kina sona Sadiya. Shi ya sa za ki ji kishi na." Kamar zan yi mgana sai na fasa ganin ko na tanka ba zai bar maganar ba zai ta tsokana ne yana mini dariya sai kawai na kauda kaina ban yi magana ba. Cikina ya shafa kafin ya ce. "Bomboy fito ka ga mamanka sarkin kishi." Da dai ya ga ban kula shi ba sai ya koma wajen zaman shi daman aiki ya ke yi a cikin system ɗin shi ya baro ya zo jin ta baki ganin kuma na ɗaure fuska ya sa dole ya ƙyaleni a cewar s na zama jagwam magana ma masifa ce da faɗa a wajena. Saboda ma yadda ya yi ban samu faɗa masa matsalan Ma'u ba na kama kaina sanin ina ma faɗa masa sai ya ce laifinta ne tun da Namiji ne, ba zai ga laifin ɗan'uwansa ba. Mun yi waya da Ma'u kwana biyu ranar wata laraba Yallaɓai ma ba gidana yake ba, misalin tara na dare sai ga Ma'u a gidana afujajan cikin kuka sai da na ji gabaɗaya hankalina ya ɗaga, Yallaɓai ya fita kenan ya zo yi mana sallama ina tunanin ko gida bai kai ba lokacin da ta zo. Ɗaki na ja ta cikin tashin hankalin ina tambayan ta ko lafiya na girgiza da take faɗa mini Alhaji Mustapha ne ya ce ta bar masa gidansa ya sake ta saki ɗaya. Sannan lamarin bai tsaya a nan ba sai da ya haɗa mata da mari gabaɗaya farar fuskarta gefen hagu ya ta sa da shatin hannunsa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un har da mari? Na faɗa ina cikin matsanancin tashin hankali. Ma'u ko kuka kawai take yi ta ma kasa mgana gabaɗaya sai na ji ƙafafuwana sun yi sanyi. Cikin jikina sai da na ji ya cire waje ɗaya ya motsa saboda tashin hankali. "Me kika yi masa da zafi haka Ma'u? Na faɗa ina mai dafa kafaɗanta cikin yanayina na damuwa. Da ƙyar na samu ta tsaigata da kukan nata ta yi mini bayani da cewa yau a gidanta ya ke yi jiya ma haka to a cewarta jiya sai wajen sha ɗaya ya shigo gidan kuma ya yi shigewarsa ɗakin sa ko da ta shiga yana ta waya haushi ya sa ta fita ta bar masa ɗakin shi ne yau da ya dawo ya shiga ɗakinta a kan gadon ta yana waya da budurwansa ita kuma ranta ya ɓaci ta fizge wayar ta haɗa da bango ta fashe shi ne ya kifa mata mari, ita kuma ranta ya ɓaci ta yi ta faɗin mganganu shima yana faɗa daga ƙarshe ya ce ta bar masa gida ya saketa saki ɗaya. "Innalillahi Ma'u me ya aike ki? Me ya sa kika biye masa? "Haba Sadiya a kan gadona na sunna zai kwanta yama yi mini waya da budurwa na yi magana yana ce mini ai ba budurwa ba ce matarsa ce tun da saura wata ɗaya auren su. Ni kuma raina ya ɓaci na fasa wayar shi ne ya mare ni. Sadiya bai ishe shi ba har sai da ya ce ya sake ni, ni fa wai Alhaji ya saka ni fa Ma'u" Ta faɗa cikin gunjin kuka gabaɗaya sai na ji kaina ya sara. Ba ni a ka saka ba amma na ji sakin nan a raina. A raina ina tunanin yadda Alhaji Mustapa ke son Ma'u ya na ririta yau ita ce ya sake ta saboda wata mace. Macen ma da bai aure ta ba. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya. Lallashinta nake yi amma ni kaina na rasa kalaman bakina, lamarin ya dake ni, na ji abun a cikin raina na rasa yadda zan yi da Ma'u kuka kawai take lamarin akwai cin rai da baƙin ciki namiji ya sake ka saboda wata mace macen ma ba ta ma shigo gidan ba, to in ta shigo kenan sai abin da ya yi gaba. Ni kaina kamar in yi kuka idanuwana har sun kaɗa hawaye sun tarun mini a ƙwarmin idanuwana, abin da Alhaji Mustapha ya yi zalinci ne kuma rashin adalci ne a kan gadon aurenta? Tsakani ga Allah ya kyauta kenan, sai na fahimci so kawai yake yi daman ya ga yadda Ma'un za ta yi ne. Duk yadda na ke cewa ta yi hakuri sai na ji hakan da ta yi ta ni a wajena dai-dai ta yi ta kuma san mutumcinta amma marin ne da ta bari a ka yi shi ne kuskurenta sannan me ya sa ta fasa ma sa waya? Da da ta yi masa magana bai ji ba sai ta bar masa ɗakin duk tsiya dai ba kwana zai yi ai ya na wayar ba. Kai gabaɗaya na girgiza da lamarin nan jikina ya yi sanyi matuƙa har na gaza wajen lallashin Ma'u. Na bar Ma'u a ciki na fito falo Baby ta yi barci Jidda ce kaɗai ba ta yi barci ba. Amma na kora ta ɗaki daman tana falon su tana karatu ne. Jidda fa ba ta yarda ta yi zaman gida a banza ba ko da yaushe cikin duba littafanta na makaranta take yi. Na zauna na rasa mafita wa zan kira a daran nan? Har na yi tunanin kiran Ya Aina sai na fasa in na yi tunanin Ɗorayi sai na ji gwiwata ta yi sanyi. Duk wanda zan kira yanzu wataƙila ma sun kai ga kwanciya kar na ɗaga musu hankali, Yallaɓai na ji shawaran na kira shi ya kwanta mini a zuciyata har na ciro wayar a chaji zan kira shi sai na fasa tuna yana gidan Gimbiya bai da ce na kira shi ba, ko ba domin komai ba akwai sirrin da ba na so ta ji, shawaran na tsayar ni da zuciyata a kan da safe sai na kira shi, da haka na koma ciki na samu Ma'u har lokacin na dirjan kuka nan fa na zauna ina ta ba ta haƙuri na san lamarin akwai ciwo amma ta yi hakuri zuwa da safe sai mu ga yadda za mu yi ta koma gidan mijinta. "Ba zan koma ba Sadiya. Allah na gama zama da shi tun da har ni zai wulaƙanta a kan wata macen da bai aura ba." "A'a Ma'u ba za a yi haka ba. Za ki koma gidan ki. In ba ki koma ba ta vi riba kenan kin bari wata macen da ba ta ma shigo ba ta kore ki daga gidan mijin ki da ƴaƴanki." Na gama faɗa ina bubbuga bayanta alamun lallashi. "Duk ma abin da ya faru ai shi ya so haka Sadiya. Tun da ya ɗauko maganar auren nan ba irin cin kashin da Alhaji bai yi mini ina ta kauda kai ba saboda kin ce na yi haƙuri amma yau ya kureni har da mari fa? Sannan ya ce mini ya sake ni na bar masa gida. Ni Ma'u ni ce wai namiji ya sake ni kuma ya yi mini koran wulaƙanci? Sai ta sake fashewa da kuka tabbas an yi mata tozarci duk da dai shima ina tunanin cikin ɓacin rai ya yi saki amma dai abin da ya yi bai kyautu ba, a yadda na ke jin zuciyata in ni ce ka yi ma wannan tozarci wallahi ba ma zan tsaya a kusa ba tafiya zan yi in da sai ka fara kuka kafin na dawo. Ni a tunanina ko na ce a hange na saki shi ne ƙarshen tozarcin da namiji zai yi ma mace saboda zai ƙara aure. Amma ba zan ce Ma'u kar ta koma gidan ta ba, sulhu a ke nema, gidan ta daban nawa gidan dabam haka zalika, zuciyarmu ba iri ɗaya ba ne amma ni kam ba zan zauna ka mare ni ka mari banza ba, duk da haka tun da ta zo wajena da kukanta sai na tabbatar da an ƙwatar mata yancin ta. Tuni Alhajin ya zube min a idona ina ganinsa da ɗan kima a baya amma a daran na ji gabaɗaya na daina mutumtata shi. Mun kai har wajen misalin biyun dare ina ba ma Ma'u baki a ɗakina mu ka kwana ni da ita saboda na ga ba ta ma cikin natsuwarta. Tana fashin salla ai da na saka ta mun yi tsayuwar dare a kan Alhaji Mustapha amma ni sai da na yi raka'a biyu sannan na kwanta. Duk da nauyin cikina amma ina ƙoƙarin yin salololin dare tun da na riga na saba. Ina da tabbacin Ma'u ba ta samu barci a daren ba duk lokacin da zan farka idanuwanta biyu. Baiwar Allah ta ba ni tausayi ni ma ai na shiga haka a baya kuma na san yadda mutun ke ji a zuciyarsa. Na so na zauna nima ban yi barci ba na ta ya ta jimami da ban baki amma ina barci ɓarawo sai da ya sace ni sai asuba na farka har ma mun kusa makara. Ina idar da salla na fita zuwa ɗakin su Jidda ganin Ma'u ta samu barci can na je muka yi azkar da karatun Qur'ani sai bakwai saura na baro ɗakin na bar su su ɗan ƙara runtsawa tun da ba zuwa makaranta yanzu mun kan kai sha ɗaya ma ba mu tashi ba in ba Yallabai na gidan ba ne in zai fita da wuri. Falo na dawo na cire waya ta a chaji ta daɗe da cika tun jiya amma na manta ban cire ba. Yallabai na kira sai da ta shiga ma na ga kamar ya yi safe da yawa ina ma wannan tunanin na ji ya ɗaga wayar a muryansa na fahimci kamar ya na barci ne na tashe shi. "Sadiya me ya faru? Ya faɗa da sauri Allah sarki bawan Allah shi ma hankalin shi ya tashi ganin kirana a wannan lokacin. Ina da ciki fargabansa kar ya zo wani abu ne ya faru mara daɗi. "Ka kwantar da hankalin ka bakomai." Na faɗa cikin kwantar da murya ina jin ajiyar zuciyarsa. "To ina kwana? Wallahi na tsorata da na ga kiran ki, " Saboda ya san ni ba mai damun sa da waya ba ne in har ya na can gidan, in kuma ya ga na kira to ba lafiya. "Kai kaɗai ne a in da kake? Na tambaye shi sai ya ce shi kaɗai Gimbiya ta can ɗakin yara. "Me ya faru ne? Ya sake tambaya kamar bai yarda da cewa wani abu bai faru ba." "Jiya ne bayan fitan ka sai ga Ma'u ta zo mini cikin kuka Alhaji Mustapha ya sake ta." "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un wani irin saki kuma? "To ai har da marin ta ma ya yi Yallaɓai" "Mari? Ya maimaita cikin sigan tambaya. "Ƙwarai kuma ya ce ta bar masa gidan sa a daran" "Subhanallah me ya faru a tsakanin su haka? "Ka taho gida in ba damuwa yanzu sai mu yi mganar." Nan da nan ya ce min gashi nan zuwa. Bayan mun kashe wayar na zauna kawai ina tunani rayuwa kenan Yau wai ni ce Ma'u ta zo mini da matsalanta, yau ina su Ya Murja ina su Anty Bahijjan ina su Shema'u? Yau duk ba za su yi mata amfani ba dole dolenta dai jininta ne zai yi mata wani anfanin da a da take ganin ni ban isa ba, kuma yadda ta zo ta faɗa mini wallahi sai Alhaji Mustapha ya roƙi gafaran Ma'u a kan wannan cin zarafin da ya yi mata. Zuciya ta sai ta fara zafi ina cin wani raɗadi daga ƙasan zuciyata kamar ni a ka yi mawa, na yadda akwai jinin Ma'u a jinina shi ya sa yake motsawa a kan ta in wani abu ya same ta. Ina nan zaune a falon su Jidda sama da mintina arba'in har Yallaɓai ya shigo gidan. Shima dai ya nuna damuwarsa a saman fuskarsa na zauna na zayyana masa duk abin da ya faru na ƙarishe da faɗin" Tun jiya da ta zo ta ke kuka. Ta ce ba za ta koma ba tun da ya tozarta ta, ba ta yi barci sai da safen nan ba ka ganta ba gwanin ban tausayi." "Gaskiya bai kyauta ba. Haba da hankalin shi me ya sa zai yi haka? Yallaɓai ya faɗa kai tsaye, shi ma ai ya san gaskiya kowa kuma ya ji wannan mganar sai ya ce bai kyauta ba. "Kuma a kan gaskiyanta ta yi mgana. A kan gadon ta fa ya je yana yin waya shi ne ta yi mgana ya yi mata wannan wulaƙanci." Na faɗa cikin bayyana jin haushina. "Shi ya sa na ce miki bai kyauta ba. Ya kuma nuna ko auren ya yi ba zai yi adalci ba. In ba wawanci ba me ya sa za ka zo cikin gida kan gadon ku na sunna kana waya da wata macen da ba ka riga ka aura ba, kenan itama ka nuna mata matar ka ba ta da daraja a wajen ka in ta shigo gidan za ta iya taka ta yadda ta ga dama tun da kai ka ba ta damar haka.' "Gaskiyan mgana kenan" Na faɗa ina kallon Yallaɓai ina mirmishi. Shi ya sa na ke son Yallaɓai ta wanni fanni akwai shi da faɗin gaskiya komai ɗacin ta. "Ita kuma rashin kyautawarta ɗaya ne me ya sa ta fasa masa waya? Da ta yi masa magana bai ji ba da ta ƙyale shi ta bar masa ɗaki in ta yi haƙuri zai wuce har kuma wata rana ya dawo ya na jin kunya. " Duk abin da Yallaɓai ya faɗa gaskiya ne, nan na zauna ina faɗa masa wasu abubuwan da suka faru a baya ya jinjina kai yana faɗin" Duk laifin shi ne a matsayin shi na magidanci bai zama adali ba, ai ba a ce in za ka ƙara aure ka tozarta matarka ta gida ba. Ita kuma in ta nuna damuwarta ba ta yi laifi ba mijinta ne zai ƙara aure kuma tana dai-dai da ta nuna kishinta afili sai dai kuskurenta ɗaya me ya sa ba ta yi kishin cikin ilimi ba? Ta yi kishin da ta ta yar ma da mijinta hankalinshi kuma ganin tana kishin ne ya sa ya ke yi duk abin da ya yi, in da a ce ta yi masa kamar ba ta san yana yi ba da tuni ba ta kai su ga haka ba. Ta yi koyi da ke mana? Na san kina kishi na amma kishin mummuƙe kika yi mini sai da na dawo ina jin kuyar ki cikin ruwan sanyi kika saka na gane ba ni da wayau" Ya ƙarishe faɗa yana kallona yadda na ga bai yi dariya ba ne na ga ne ba wasa yake yi ba. Sai da na harare shi sannan ya yi mini mirmishi yana faɗin ai gaskiya ne kishin mata masu Aji kenan a gasa namiji ta ruwan sanyi da zai zo ya na ba da haƙuri da kan shi, shuru na yi ban yi magana ba domin ni kaina ai ya gasa min aya a hannu kawai dai ana kauda kai ne a zamantakewa. Mun tattauna dashi sosai daga karshe ya ce mu karya sai mu tafi tare da shi har da Ma'un nan kuma take ya kira Alhajin Mutspha ya ce za mu taho gidan Ma'u nan ba daɗewa ba ko kunya ya na faɗa ma Yallabai sun samu matsala jiya ba ta kwana a gidan ba Yallaɓai ya ce ya sani gidan sa ta kwana tare ma za mu taho ya ce yana gidan Hajiya Zainab amma zai taho nan gidan Ma'u yanzu. "Ka ji min munafuki wato saboda ita Hajiyar ta san Ma'u ba ta nan shi ya sa ya je can ya kwana." Na fada cikin jin haushi tun da duk na ji wayar na su a speaker ya saka wayar lokacin da ya kira shi. "To mi ye laifin shi? Matan ahi biyu bai kamata ya yi kwanan gauro ba." Wata uwar harara na jefi Yallaɓai dashi sai ya fara mini dariya ya na faɗin" Daga magana? Yi hakuri ba ni na kai zomin ba rataya kawai a ka ba ni." Saboda haushi ban tanka shi ba yanzu yanzu ya na maganar kamar zai yi gaskiya a lamarin shin amma kuma yanzu ya na so ya yi son kai a lamarin shi. Tare da shi muka dafa ruwan zafi shi ya ma soya ƙwai, ba buredi sai ya fita ya siyo, kafin ya dawo Ma'u ta tashi na saka ma ruwan a hiter ya yi zafi na ce ta yi wanka mu karya Yallaɓai ya zo za mu tafi can gidan na ta gabaɗaya. Sai da ta yi wanka nima na yi, kaya na bata ta saka nima na zurma doguwar rigata mai kama da buhu ta bakin Yallaɓai bujun bujun ga cikina gaba ina tafiya a tale, Yallaɓai na falo can na je na same shi muka karya ita Ma'u ciki na kai mata na ta saboda ta samu sakewa. Sai da za mu tafi na ta da su Jidda suna ta barci na ce mata za mu fita ta yi musu wani abu su karya dashi ita da Baby in kuma za su sha Tea ne dai ga su ga gidan nan mu mun fita zuwa gidan Umman su Ma'u. Yallaɓai ya ɗauke mu a motar shi, sai da muka ɗau hanya ne suka ƙara gaisawa da Ma'u ya na ba ta haƙuri sai ta fashe da kuka ta na faɗin" Baban su Jidda sakina fa ya yi a kan wata macen? "Ki yi haƙuri ya yi kuskure kuma zan faɗa masa." "Kuma wallahi sai ya biya ta marin ta da ya yi." Na faɗa a fusace, sai Yallabai ya kalleni kafin ya ce"To ya biya ta, ko rama marin na ta za ta yi? "In ta kama ba" Sai Yallaɓai ya girgiza kai hankalin shi na wajen tuƙi ya ce" Ma'u kar ki biye ma wannan ƴar'uwan ta ki, a kusa ta ke kin dai gane" "Ba wani a kusa na ke sai gaskiya ai ba zai mari banza ba." "To na ji bai mari banza ba, daman ai ya san bai kyauta ba kuma ina da tabbacin yanzu haka ya yi nadama." "Daga baya kenan an yi sadaka da bazawara." Har Ma'u sai da ta yi dariya shi ko Yallaɓai kallona kawai ya ke yi yaa girgiza kai ganin yadda na haƙiƙance. "To ni dai ki yi haƙuri kar mu je sulhu ki ɓata ma lamarin." Na harari Yallaɓai ina faɗin" In dai har ina wajen sai na yi magana in kuma ba ka son hakan ta faru sai dai ka sauke ni na koma gida tun da ba ka son na faɗi gaskiya." Na faɗa ina murguɗa masa baki ai sai ya yi shuru bai ƙara mgana ba, ko da muka isa gidan Alhajin na Ma'u bai iso ba sai da muka shiga muka jira shi. Lokacin da ya zo har ya yi wanka ya ba za shadda na maiƙo har da babban riga a raina na ce kuɗi masu gidan rana duk su suke saka shi wani jin kai da ganin zai iya yin komai. Da ƙyar na gaishe shi saboda ina jin haushin shi a nan falon Ma'u muka zauna shi Yallaɓai ya fara ba ma dama ya maimaita magana sai kame kame yake yi, wai ta raina shi tun da ya ce zai ƙara aure taƙi kwantar da hankalinta ta sauya ta na abubuwa waɗanda ba halinta ba har ya na cewa wai haƙuri ya ke yi da ita sai jiya ta ƙure shi, shi kuma ran shi ya ɓaci har ya mare ta kuma ya furta sakin amma a jiyan bayan ta fita har bayan ta ya bi bai ganta ba kuma a jiyan ya janye sakin ya mai da ɗakin ta Kallonsa nake yi a ƙasa ƙasa ina taɓe baki, ita ma Ma'u ta faɗi na ta a zencen gaskiya duka laifin shi ne. Duk shi ya rikita Ma'u ta koma haka a zaman nan ya ya bi Hajiya Zainab ban san sau adadin nawa ba ne, yana alfahari da cewa ita ba ruwanta ba ta ɗaga masa hankali lokacin da zai auri Ma'u ba yanzu ma ba ta ɗaga masa ba, sai yanzu ne ita za ta ɗaga masa hankali. Ya yi ta maganganu Yallaɓai ya ba ni haushi bai wani nuna masa kuskurensa ba yana wani lallaɓa sa, ni yadda ya nuna mini a gida ban ɗauka zai yi masa wannan lakwa lakwan ba. Daga ƙarshe an samu masalaha ya ba ta haƙuri itama ta bashi, kuma ya yi alƙwarin ba zai sake yin waya a gidanta ba in ma zai yi to ya kauce ma jin ta da ganinta. Ni ko ganin ba a yi maganar mari ba na gyara zama da cikina tulale a gaba na ce. "To marin da ka yi mata fa? Tsakani ga Allah ba ka kyauta me ya sa za ka mare ta a kan wata? Na faɗa ina kauda kaina cikin jin hauahi. Yallaɓai na yi mini abin da ba na so mutumin nan ya wani tattare wai an gama mgana ina dawo da su baya. "To ka gama mgana ba ka yi maganar mari ba? Na faɗa ina kure sa da ido, kawai ya wani bi ya tattare ni ai gwara a nuna masa bai mari banza ba. "Ahto ka sani cewa Ma'u tana da gata duk abin da zai shiga tsakanin ku kar ka sake kai hannunka jikinta. In kuma ka sake to za mu kai mganar gaba, tun da Alhajin mu mata ya ba ka ba jaka ba" Yadda na fiffitike ne ya sa har shi Alhaji Mustapha sai da ya yi dariya. "Alhaji ka rabu da ita. Kasan masu ciki suna da saurin harzuƙa." Na ma kasa mgana saboda Yallaɓai ya kai ni bango. "Haba ba komai gaskiya ta faɗa na yi nadama kuma ni da ita zan rarrasheta. A yi mini afuwa Ya Sadiya." Ya ce mini yana kallona Yallaɓai ma yana dariya dukkansu a ɗage nake kallon su a cikin zuciyata na ce ai duk kanwar ja ce. "Yau na sake yadda da maganan nan ta hausawa da suke cewa jini jini ne. Ga shi yau Sadiya na mini faɗa saboda na taɓa mata Ma'u." Sai da ya yi maganar sai na ji kunya na tashi ina mirmishi na ja Ma'u muka shiga ciki muka bar su nan a falo. A ciki ba shawaran da ban ba ma Ma'u ba, ganin tana cikin damuwa ya sa na ce ta je ko Kura wajen Baaba ta bar Kano za ta samu natsuwa na kwana biyu sai ta dawo. "Ina zan je Sadiya? Baaba fa cikin kishiyoyi take ba na so na je na bar mata abin faɗe" "Ai ba dawo mata kika yi ba. Zuwa za ki yi da niyar za ki yi sati ɗaya daga nan in kika huta zuciyarki ta yi sanyi sai ki dawo ba tare da ita ko ita Baaban ta san wani abu ya faru ba." Sai ta kalleni kafin ta jinjina kai ni kuma sai na ƙara da cewa" Saboda zuciyarki ta yi sanyi. Kuma Baaba uwa ce in kina ganinta hankalin ki zai kwanta ga su Zainab za ki samu yar natsuwa. In ma za ki dawo sai ku dawo tare saboda ta ɗebe miki kewa. Yara kuma kar ki yi mgana lokacin da ya ga dama ya dawo da su duk ɗaya ne da can da nan ɗin. Kar ki sake ki sake yi masa mgana kin ji ko? Sai ta gyaɗa min kai alamun ta ji, hannuna ta riƙe tana faɗin" Na gode Sadiya. Allah ya bar ki da Yallaɓai har abada ya ba ku zaman lafiya." Na amsa da amin amin nima ina mata ƙwatanƙwacin addu'ar da ta yi mini. Ba mu baro gidan ba sai da muka sulhuta komai sai gashi tare suka rakomu har haraban gida muna fita bayan mun ɗau hanya Yallaɓai ya kalleni yana faɗin. "Kin ga ni ko? Shi ya sa na ce miki kar ki zaƙe mata da miji sai Allah." "Uhm" Kawai na ce ina kallon Yallaɓai da na so kar na yi magana amma na ga dai ba zan iya haƙuri ba. "Yallaɓai ni dai ka daina mini irin haka. Kawai ina so na ƙwatar ma y'ar uwata yancin ta kana dakatar da ni" Ya kalleni ya sake kallona kafin ya ce" Me na yi kuma? Daga mgana. To ai na bar miki kin karɓan mata Umma Sadiya" Ya faɗa yana mini dariya na yi kamar na kai masa duka saboda haushi amma ban yi ba saboda dai ya wuce duka in dai a wajena ne. Yallaɓai ai sha kumdum ne maƙura ne. Muna hanya wayar sa na tsakiyar mu Gimbiya na ta kiran shi ya ɗauka ban ji dai me ta ce ba amma na ji shi ya na ce mata gashi nan zuwa. Ina zaune a gefe ko kala ban ce ba, ita wai nan ya fita da safe ranar girkinta shi ne take ta jaraban kiran shi. Kafin mu isa gida na sake masa maganar koyon mota kawai sai Yallaɓai ya ce" Ke da wannan abin a gaban ki ne za ki je koyon mota? Kya bari dai ki haihu." "Za ka koya mini in na haihun! In ba za ka koya mini ba na nemo ko Adnan ko Musbahu" Sai ya fara dariya kafin ya ce" Ba za a yi haka ba Uwargida sarautar mata. Ke ce Alhaji Alhaji ya zama ke. Dole na ijiye duka harkokina na cika umarnnin ki." Ko gatse dai ya yi na biye mishi na ce ƙwarai kuwa. Yana kawo ni gida ko shiga bai yi ba Amarya na ta kira kai Gimbiya ba ta da haƙuri a rayuwarta ni dai na sauka na shige gida shi kuma ya wuce ban san yadda suka ƙare ba domin ni ban sake ganin shi ba sai washegari da yamma da zai dawo gidana. Labarin abin da ya faru da Ma'u da mijinta daga ni sai Yallaɓai ko su Ya Aina ban taɓa faɗa mata ba duk ko yadda muke da ita. Na aminta da wani abu ɗaya ka riƙe sirrin wanda ya aminta dakai. Ba daɗi ta ji wannan mganar a bakin su sai ta ji ta raina ni, yadda nima ban faɗa ba itama kuma ba ta fidda mganar ba. Haba ai ba abin faɗe ba ne tun da ba abin daɗi ba ne muka rufe maganar a tsakanin mu tun da dai an samu sulhu. Kuma ko sati ba a yi ba mun haɗu a gida mun je duba Gwaggo da take zazzaɓi har ƙarin ruwa a ka yi mata a gida. Ta ga har mun zo mun taru gabaɗaya mun kuma rabu ba ta ji na yi maganar ba tana komawa gida sai da ta kira ni tana mini godiya har tana cewa na nuna mata na fita. Da ita ne ko domin a yi mini dariya za ta faɗa amma ni na nuna mata na yi ma zumumci kara kamar Yadda Alhajinmu ya roƙe ni. "Ai ba mganar daɗi ba ne Ma'u. Sirrin ki kuma ai sirrina ne in na je na faɗa to ni za a yi ma dariya." Ko Ya Aina sai da ta yi mini mgana. Ta ga ni da Ma'u gwanin sha'awa har Rahila ma sai da ta yi magana na yi dariya kawai na ce duniyar ma nawa take? Ya Aina ta ce haka ne kuma na burgeta. Rahila kuma har tana mini shaƙiyancin da cewa ko na kusa mutuwa ne na zama saliha, na ce mata ai ba yanzu zan mutu sai ta rigani mutuwa muna ta dariya ni da ita. Ba su san irin masifan da Yallaɓai da su Jidda ke karɓa ba, sun ga masifa da cikin nan kala kala. A ƙarshen watan aktober a ka ba da sanarwa lafawar cutar corona. Farkon watan November kuma a ka buɗe gari har da makarantu gabaɗaya. Su Jidda a na ta murna an koma makaranta ta ɗauka da sun koma za su fara jarabawa ne amma sai a ka ce sai sabuwar shekara saboda calander ya birkice Jamb sai sun sake rigister. Wato abubuwa da dama a hutun nan na corona ya dagula shi, komai ya koma baya sai dai kuma a hankali komai zai dai- dai ta ni dai ban yi maganar komawa makaranta ba, in ma na yi Yallaɓai dariya kawai zai yi mini na ji ma kamar ba ni da rabon karatun ne daman haka Yallaɓai yake so. Ko da na koma bayan na haihu renon fa ai aiki ne mai zaman kan shi kafin sai kawai na cire karatun a raina na ce wata ƙila ba alheri ba ne. Na mai da hankalina kan sana'ata na hijabai da inears. Kuma Alhamdulillah ina samun alheri matuƙa. Ga shi cikina ya yi ƙasa na shiga watan haihuwana. EDD dina 17 November ne. Har ina ce ma Yallaɓai in na haihu zan haɗa mana da Wedding Annivesary na cikar auren mu shekara 20 wanda tun June muka cika shekarun lokacin ina ta kaina laulayi ya saka ni gaba ya sa ko maganar ma ban yi ba Yallaɓai daman ni nake tuna masa tun a baya ballantana yanzu da harkokinsa suka yi yawa. ***** 10. November 2020. Tuesday. Talata. Lafiya lau na tashi ko ciwon bayan da kwana biyu na kan tashi dashi yau ban ji sa ba. Yara duk sun tafi makaranta daga ni sai Yallaɓai a gida kwanan su uku a Abuja sai jiya ya dawo da daddare ya sauka a gidana daman daga can gidan Gimbiya tafiyar ta kama shi. Lafiya lau muka karya, ya ce ba da wuri zai fita ba sai bayan azahar muna cikin bedroom Yallaɓai na kwance ni kuma ina zaune a gefen gado ina ware kayana da na yara sai na Yallabai da safen mai wanki ya kawo su. hira muke yi sama sama sai na ji shuru ashe barci ne ya ɗauke shi. Sai na cigaba da aikina. Na kwashe kayana na jere cikin kwaba haka ma na Yallabai na su Jidda ne na ce bari na kai musu ɗakin su, sai dai ina in mikewa ne ya gagara. Ƙafafuwana sun riƙe, bayana ya ƙage, daman kafafun sun kumbura cikin ya sunkunya ya yi kasa ba ni ma da riga a jikina da ga ni sai zani zafi kawai na ji ina yawan ji tun da cikina ya shiga watan haihuwan shi. Na yi ƙoƙarin dafa jikin gado na miƙe ai ban san lokacin na saki ƙara ba, wanda ya ta da Yallaɓai a firgce. Tuni har na duƙe a kasa ina riƙe bayana da na ji kamar ya tsage. "Me ya faru? Yallaɓai ya faɗa yana dirowa gabana. "Baya na. Wayyo Yallaɓai bayana ya tsage." Na faɗa cikin tsananin azaba har ina cije bakina. Yallaɓai na duba bayan nawa ne ni kuma ina ta wash wash kawai na ji ruwa na bin kafafuna ina dubawa sai na ga har faya ta fashe ai sai na zaro ido cikin ƙaraji nake faɗin. "Haihuwa ce Yallaɓai. Haihuwa ce faya ta fashe." Na faɗa ina makarƙyata jin yadda marata ke wani irin juyawa. Kusan fa na manta yadda haihuwa take shekaru goma ba wasa ba. Ji nake yi kamar ban taɓa haihuwa ba azaban da nake ji kamar ban taɓa jin irin shi ba. "Innaliillahi haihuwa? To mu tafi asibiti ko? Ya faɗa cikin ɗimuwa shi ma ya ruɗe kamar ni. Kawai sai na yi zaune kawai tuni zanin da ke jikina ya yi ta kanshi nima ina ta kaina na fahimci gajeruwar naguda zan yi. Haihuwa ce gadan gadan ta taho mini ban shirya ba. "Ba lokaci Yallaɓai. Ba lokaci ka zo ka zoo.." Na faɗa da ƙaraji jin abu na turowa ta gaba na. Kan ɗa ne ya turo, Yallaɓai ya ruɗe bai taɓa ganin haihuwa ba sai ranar shima da ya matso kusa na riƙe shi gam ina nishi amma bakina bai mutu ba. "Zai fito. Zai fiiiiii.. too.." Na faɗa ina karta kumbuna na a jikin fatar hannun Yallaɓai saboda nishin da nake yi, ga kan ɗa na ƙoƙarin fitowa da Yallaɓai ya leƙa ya gani sai ya ruɗe faɗi yake yi" Ga shi nan fa zai fito na shiga uku.". Ya faɗa cikin fitan hayyaci.. Ni dai bam san yadda a ka yi ba domin kamar na shiɗe ne da na yi wani irin ƙarfafan nishi ina ƙara damke hannun Yallaɓai ihun har sai da muryata ta dishe. Sama sama na ji abu sulumf sulumf har sau biyu ya faɗo lokaci ɗaya da kukan jaririya "Inyainya. Inya." Sai na koma na kwanta a ƙasan tayels ɗin dake bedroom ɗin domin cafet ɗin yana da ga wajen ƙuguna ne, wajen kaina kuma tayels ne haka na ji jikina ya saki yaraf na kwanta kawai ina maida numfashi ina jin Yallaɓai cikin fitan hayyaci yana faɗin. "Sadiya kin haihu. Wallahi kin haihu." Muryansa cikin farinciki da wani irin ɗimuwa mara misali. Ni kuma ina ta sauke ajiyar zuciya a jere ga zufa da ya wanke minu jiki kamar an kwarara mini ruwa. Haihuwa na yi cikin abin da bai gaza da mintina goma ba. Allahu akbar Allah shi ne Ubangiji mai yin yadda ya so a lokacin da ya so. "Alhamdulillah." Alhamdulillah' Na ke faɗa a zucci da sarari saboda Ubangiji ya yi mini sutura na haihu a cikin ɗakina tare da mijina cikin lafiya da ƙarfina. Allah ne abin godiya. *Janafty**TKGB3H08* *Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.* Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732 Ganin da na yi Yallaɓai a ruɗe yake, ni kuma jikina duk ya saki ina kwance itama jaririyan na kwance cikin ƙazanta tana ta callara kuka, tun lokacin da ta faɗo ta callara kuka na san cewa da gaske ƴa mace na sake haifa. Sai na kira sunan Yallaɓai ya taho wajena sai na ce ya kamani cikin rawan jiki ya kamani na tashi zaune. Sai a lokacin  na fahimci jaririyar tare da uwa mahaifa ta faɗo shi ya sa na ji fitowar abu sau biyu daga ƙasana. Zanin da ke jikina da ya yi gefe na ce ya ɗauko jiki na rawa ya tashi ya ɗauko sannan na ce ya buɗe dirowan gadon mu ya ɗauko kit ɗin mu na magunguna akwai reza a ciki, bayan ya kawo mini na karɓa na rike jaririyan shi kuma na ce ya riƙe zanin na saka ta a cikin zanin tana hannun shi sannan na daidai ta na yanke cibiyar na ce ya matsa daga wajen tun da gabaɗaya mun yi dama dama daga ni har shi cikin kazantar haihuwa. "Ya zan yi mata Sadiya? Ya faɗa yana kallona ya na kuma riƙe da jaririyar. "Ka naɗe ta a cikin zanin ka kwantar da ita a kan gado ka zo ka kama ni na tashi." Haka ko a ka yi bayan ya kwantar da ita sai callara kukan jarirai take yi ya zo ya kamani na tashi tsaye. Na saka shi ya buɗe karamar akwatina in da na tara kayan haihuwa na ce ya ba ni na ɗaura. Bayan na ɗaura na ce ya je ya saka min ruwa a hiter tiolet da gudu ya fita ni kuma na tattaka ina ware ƙafa domin sai ina jin kamar na ƙaru ta ƙasana na isa in da yarinyar ke kwance na ƙura mata ido ina kallonta lalle dole ta ci sunan uwata. Domin a kammanni ma ni ta ɗauko. Yallabai ya dawo ɗakin ya ganni tsaye ina kallon ta yana zuwa na kalle shi da mirmishi kafin na ce. "Alhamdulillah mace na haifa Yallaɓai. Mace Allah ya sake ba mu" Sai kawai ya rumgumeni bai damu da yanayin da nake ciki ba. Cikin tsananin farinciki ya ke faɗin. "Alhamdulillah. Allah na gode maka da ya sake nuna mini wannan ranar" Wai a haka don ƙarfin hali Yallaɓai sai da ya sumbaci bakina na ture shi ina faɗin" Ko minti goma ban yi da haihuwa ba Yallaɓai? Sai ya yi mini dariya kawai bai ce komai ba. Shi na saka ya kwashe kayan su Jidda dake zube akan gado ya saka musu cikin wardrope kar su ɓaci. Ba ni da tsummokarai sai kawai na ce ya kwaso doguwayen rigunan da na ɗinka na yi amfani da su lokacin ina da ciki waɗanda shi da kan shi ya saka musu suna da buhu in naɗe kazantar da su kawai a kai su bola bayan an wanke tun da sun gama amfani. Jaririyar kuma na goge mata jiki da dotel, tare muka goge kazantar ni da Yallaɓai ina cewa ya bar shi yana mini faɗa  wai na mayar da shi mara tausayi ta ya ina cikin wannan halin zan ce ya koma ya zauna yana kallona ai sai na yi shuru. Tas muka gyara wajen duk da ba sosai ba amma mun goge kazantar haihuwar. Ita kuma uwa mahaifa na ce ya je ya haƙa rami a haraba ya rufe. Ya ɗauka cikin wani zani ya fita dashi ya je ya rufe bayan ya dawo ya sake fita da cafet tun da a kan shi na haihu na ce ma Yallaɓai kawai a wurgar da shi ya ce  a'a sai an wanke in zan yi kyauta da shi ne sai na yi amma ba zai bari a wurgar da shi ba. A baho babba da ya ɗauko muka tara kayan da muka yi gogen-gogen na ce ya fita dashi can ta ƙotar kitchen. "Kar ka ce kuma za ka wanke ka bari su Ya Aina su zo don Allah.' Sai ya ce minI to, sai da ya dawo ne na ce ya miko mini wayata, tana falon su Jidda ya je ya ɗauko ya kawo mini jikin sa na rawa. Jaririyar na jikinsa ya nace sai da  na ba shi ita. "Kar ta ɓata ma ka jiki. Kasan gogewa kawai na yi ba a yi mata wanka ba.' "To ai jikin nawa ya riga da ya ɓaci ba matsala in ta ƙara ɓatawa" Sai da ya yi magana na lura shima  dogon wandon da ke jikinsa duk ya ɓaci da jini har farar vest ɗin jikinshi wa ya ga maza yau sun yi aiki. Ya Aina na kira na ce mata ta zo gida na haihu. "Ke Sadiya" "Wallahi da gaske Ya Aina. Na samu ƙaruwan mace." Sai ta yi kabbara kafin ta ce min gata nan zuwa domin na ce ta yi sauri ko yarinyar ma ba a wanke ba Sai da na gama wayar na duba lokaci sha biyu ne da wani abu zai iya zama gab da sha biyun na haihu ko kafin ma. Saboda na kira Ya Aina ya sa na matsa Yallaɓai ya je ya yi wanka jikin sa ya ɓaci. "To ke da ita fa? "Za mu yi in Ya Aina ta zo.' "Amma za mu je asibiti a duba mini ku ko? Sai na yi dariya kawai ganin yadda ya kama jaririyar ya rumgume. "Za mu je asibiti mana. Ka je ka yi wanka kafin ta zo" Da kyar ya ba ni jaririyar nan ya tafi ya yi wanka nima ya bar ni rumgume da ita har lokacin ina yi ma Allah kirari. Ina jin jini na zuba ta ƙasa na Allah ya sa na samu wani zani na tara a ƙasa na kafin na yi wanka.  Na yi ta ma Allah kirari ina riƙe da kyautar da Ubangiji ya sake yi mini bayan na fidda rai. Ina ta hailala da kabarbari a cikin zuciyata domin Allah shi kaɗai ne wanda kum fa ya kum ne a lokacin da ya so a lokacin komai yake faruwa. Ina nan zaune Yallaɓai ya fito wanka, yana ma saka kaya ne Ya Aina ta kira wayata da cewa ga ta nan a bakin get shi ya sa a gurguje Yallaɓai ya shirya ya fita ya je ya buɗe mata suka taho ciki a tare yana gaba tana bin shi a baya har cikin bedroom ɗina sai ga shi ta ganni a zaune gefen gado riƙe da jaririya ai sai ta riƙe haɓa kafin ta ce. "Ikon Allah da gaske dai kin haihu? Sai kawai na yi mata dariya ba tare da na yi magana ba. "Wallahi Ya Aina ni kaina na yi mamakin haihuwar nan, abin da bai gaza mintina goma ba har ta haihu." "Sannu Dubu. Sannu Dubu na ce barkan mu da arziƙi." Ta faɗa lokaci ɗaya tana karɓan jaririyar da ke hannuna ni kuma sai na sakar mata ina faɗin" Yauwa Ya Aina." Na faɗa ina mata mirmishi, gefena ta zauna a kan gadon ta na kallon jaririyar kafin ta ce" Ma sha Allah. Ga ta nan ko kamaanninki ta ɗauko Sadiya" "Shi ya sa na ce ta gama cin sunan Mama." "In sha Allahu." Yallaɓai ya ba ni amsa lokaci ɗaya yana kallona nima shi na kallah ina mai jadadda masa godiyata ta idanuwana. Ya Aina ko sai washe baki take yi cikin hamdala. Yallaɓai ne ya yi maganar tafiyar mu asibiti ya sa ta tashi ta ce bari ta saka ruwan zafi ta fara yi ma jinjirar wanka sai na ce akwai ma ruwan zafi a hiter ta tiolet Sai ta ce to bari ta yi amfani dashi bam damu ba sanin duk abin da ya kamata za ta yi kamar yadda ta yi mini a haihuwan Baby ita ta yi jinyata a asibiti har muka dawo gida shi ya sa nake ganin ƙimar Yaya Aina ta na yi ma zumunci kara da jikinta da aljihunta. Nan ta bar ni da Yallaɓai zaune mun ta sa jinjira muna kallo bakin mu ya ƙi rufuwa sai da ta ɗebo ruwan a baho sannan ta karɓe ta. Tas ta yi mata wanka bayan ta yi ta sauya ruwan Yallaɓai na faman kai da kawo, ta saba saboda in dai na haihu kaf dangina da dangin Yallaɓai sun san shi ba mai zama ba ne, da shi za a yi ta shiga da fita in na kamawa ne ya kama sai ya ga jama'a sun taru ne yake haƙura ya fice daga gidan. Na taɓa jin Anty Maimuna na yi masa tsiya a haihuwan Anwar wai yadda suka san shi da hidima a kaina in na haihu amma Gimbiya an mata aiki a asibiti ya bar gida kaca kaca bai iya gyara komai ba. A gabana ne ranar na je giden bayan an sallamota kai tsaye ya ce Sadiya kika ce, ba lalle abin da na ke yi a can na yi shi a nan ba. Sannan bai zama dole shima abin da na ke yi anan na je can na yi ba. Tana jin haka sai ta yi shuru ni ko a fili ma sai da na murmusa ban ji wani mamaki ba saboda sai da a ka yi mini kishiya na fahimci abu kaɗan ma da bai kai ya kawo ba in ba ka kai zuciyarka nesa ba sai kishi ya turniƙe ka. Shi ya jawo mata akwatin da na haɗa kayan haihuwan ta shirya jaririyan cikin kayan sanyi masu kyau bayan ta shafe mata da man zaitun ta kuma gasa cibiyar sosai ta saka mata mgani saboda ta yi saurin faɗi, ta nannaɗeta cikin towel ta miƙa ma Yallaɓai da yake jira daman. Faɗa mini yake yi yanayin jikinta irin na Baby ne ƙatuwa ce mai kiɓa haka na haifi Baby kuma har gobe ta na nan da ɗan jikinta kuma wannan jikin na su Anty Bahijja ne ko na ce na Nene domin har yanzu da shekaru suka tura akwai jiki a tare da ita. Nan muka bar Yallaɓai Ya Aina ta iza ƙeyata tiolet ta kama mini na gasa jikina kuma sosai na ji daɗi a ciki ta bar ni ta fita zuwa kitchen ashe tea ta haɗo mini mai kauri da ƙwai sannan ta kawo min saban buredi ta bincika ta ga ma ina da garin kunu amma ba shi da yawa sai ta yi ma Yallaɓai maaganar gero sai ya ce in ya fita zai yi magana za a kawo. Ko da na fito shi yake faɗa mino ya yi ma ta huɗuba da suna Rukayya bayan ya lasa mata dabino a bakinta. "Allah ya raya mana Ruƙyyaatu Yallaɓai na." "Na gode. Na gode. Na gode da wannan martabawan na ka. Ubangiji ya yi maka sakamako da wannan karan da ka yi mini." Kafin ya yi magana Ya Aina ta dawo ɗakin tana tambaya ta omo sai na ce ta duba a dirowan kitchen duk da bai da yawa sai Yallaɓai ya ce in rubuta duk wani abu da ake bukata za a kawo anjuma. Ta juya da nufin fita sai na kira ta ina faɗa mata Yallaɓai ya yi mata huɗuba da sunan Mama. "Ma sha Allah. Allah ya raya mai sunan Mama. Allah ya sa ki biyo halin mai sunan." Dukkanmh muka amsa mata da Amin Amin nan ta fice ta bar mu. Yallaɓai na riƙe da ita na shirya na saka wata doguwar rigana sai gashi ta shige ni, na ɗan ragu amma ciki na nan kamar ban haihu ba sai da Yallaɓai ya ce ko akwai twin ɗin Rukayya ne a ciki ba mu sani ba ina dariya na ce wani twin jini ne a ciki a hankali a hankali zai ta sauka amma zan ɗan riƙa ɗaure shi saboda koyarwa iyayen mu na da kenan ka riƙa ɗaure ciki a cewarsu in ka sake shi haka shi kenan zai bi jikin ka.  Pamper na saka na tare ƙasana da shi sannan na zauna ina zaman ƙaryawa na biyu domin sai na ke jin kamar na shekara ne ban saka komai a cikina ba saboda yunwar da na ke ji ina tusa buredi a bakina ina kallon Yallaɓai na yi mata hoto. "Yallaɓai ba ka sanar da kowa haihuwan nan ba fa." "Zan sanar yanzu." Ya faɗa yana ƙara yi mata wani hoton har yana wani karkacewa sai da na yi dariya. Ni dai ai na sha mamakin yadda na iya ta da jug guda da tea na kuma haɗa da ƙaton saban buredi na cinye ga ƙwai manya faifai biyu lalle a gaida Haihuwa domin wani abu sai haihuwa in ba haihuwa ba da cikin jego ba ina ni ina ta da wannan uban ruwan shayin? Haka na faɗa ma Yallaɓai da na ga yana kallona sai ya yi dariya kafin ya ce. " Ni wallahi hankalina baya kan ki. Ban ma lura da aikin da kika yi ba. Na ce to sannu da aiki Umma Sadiya." Sai na fashe da dariya yana ta ya ni, a gurguje na shirya muka yi ma Ya Aina sallama muka fita muka barta tana ta wankin kayan haihuwa. Wayata ma a gida na bar ta, muna hanya ne, na ce ma Yallaɓai alkunyar Ruƙayya za mu riƙa kiran ta YUMNA. Ya ce abin da na ke so ai shi za a yi tun da Yallaɓai ya zama ni, nima na zama shi muna ta hiran mu har muka isa asibitin Aminu kano shashen masu awo suma sun yi mamakin haihuwanta da nake faɗa musu yadda lamarin ya faru, suka karɓi Yumna suna ta santi barin ma da suka ganni ras da ni kamar ban haihu ba. Ita dai Yumna an yi mata alluran su na jarirai ne domin rigafi aka ce ranar da ta yi kwana bakwai za mu dawo a yi wasu, ni kuma suka duba ni a tunanina ma na samu ƙari sosai sai suka ce na samu ƙari amma ba sosai ba. Amma dole ne suka rike ni sai sun yi mini ɗinki shi ya sa na kira Yallaɓai na faɗa masa sai ya ce ba damuwa sai ya jira ni daman muna zuwa sai da ya je ya yi sallar azahar da ta suɓuce masa. Ni ban sani ba ashe Yallaɓai ya ɗora hoton Yumna a status ya yi magana sannan ya tura a family group ɗin su na gida da cewa na sauka lafiya. Ana ta kiran waya ta, mu kuma muna asibiti sai wajen gab da la'asar muka koma gida bayan an yi min ɗinki da dokokin na yi ta shiga ruwan ɗumi,tare da wasu magungunar da likita ya rubuta mini. Tun muna asibitin ruwan Nono ya fara zuwa har na ma bata ta sha, saboda tana ta rigiman alluran da a ka yi mata. Mu na mota a hanyar komawa gida sai da na ƙara ba ta, tana ta rigima ni kaina azaban nake ji daga ƙasana, saboda ɗinki kana ganina duk na jigata shi kuma Yallaɓai sai kiran shi a ke yi a waya a na masa barka yana amsawa a muryan shi cikin farinciki da Annushuwa. Ko da muka koma gida, jama'a cike. Rahila ta zo ita da Ma'u da Ya Murja. Ya Balki ce ba ta nan ta je suna a dangin mijinta Jigawa amma ta ce gobe za ta dawo. Nan na iske Hauwa mun dawo ba daɗewa sai ga Munnira da Mubeenan Musbahu sun iso suma, suna ta mamaki wai kamar ban haihu ba, ita kuma Munnira ta kama min masifa wai ace na haihu tun sha biyun rana amma na kasa kiran su sai dai kawai ta ga Mimisco ta poster jaririya a status ina dariya na ce ta yi haƙuri wayar a gida ma na bar ta mun tafi asibiti amma ba ta haƙura ba tana ta mita yadda suka shirya ma haihuwan nan ai kamata ya yi a ji haihuwan daga bakin su da ƙyar na samu ta haƙura amma in dai Munnira ce akwai ta da na cin magana. Nan na bar musu jaririyan Ya Murja ta saka mini ruwan ɗumi na shiga na gasa ƙasa na sannan na sake yin wanka ina fitowa suka kawo abinci mai rai da lafiya shinkafa da miya da nama suka ce cefane a ka kawo bayan fitan mu na san Yallaɓai ne ya tura kuɗi a ka kawo mana cefane, sai da na natsa sannan na ɗau wayata na ga tarin kira ba adadi. Har Gwaggo ta kira ni sai da na sake dubawa ne sannan na ga har Alhajin mu ya kira ni. Ya Auwal da Ya Hamza dukkansu tare da matayen su sun kira wayata. Sameena ma ta kirani ita da Nafeesa, ina ga lokacin da suka ji labarin haihuwan ne suka yi ta kirana sai dai na riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya ina kiran su muna gaisawa da ƙarfin gwiwata na ke faɗin sunan Mamana ta ci Rukayya amma za mu yi mata alkunya da Yumna. Sameena ta ce ai sun sa ni Yallaɓai ya saka a status ɗin shi lamarin ya ba ni mamaki na san ya kan saka hoto wani lokacin amma bai cika yin rubutu a ƙasa ba. Ban da Haihuwan Jidda lokacin a na cikin samartaka wannan ya ɗora ta ya yi ta ma Allah godiya amma Haihuwan Baby bai saka hoto ba ya dai yi rubutun ya samu ƙaruwa. Haka ma na su Anwar da Khalipa amma ita Yumna ta zo a sa a tun da har ya ɗora ta ya yi rubutu nan da nan na buɗe data na shiga na gani. Ta yi kyau ƙwarai a hoton wato wanda ya ɗauke ta ina zaune ne a ɗazu ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton shi ne. "Alhamdulillah. Allah na gode maka. Ubangiji ya sake azurtani da samun ƙaruwa daga Sadiyata. Na yi ta jira ban fidda rai ba, na yi ta ji a jikina Ubangiji bai yanke mini samun zuru'a daga tsatson Sadiya ba. Na yi haƙurin jira. Na shekara ɗaya,biyu, uku har zuwa shekaru goma ban cire tsammani ba. Kwatsam sai ga Ruƙayyatu(Yumna) kyautar da Ubangiji ya yi mana ita da misalin ƙarfe 12pm na rana. Ku yi mata addu'ar Allah ya raya mana ita tare da sauran ƴan'uwanta." Ni kaɗai ina ta faman mirmishi, hoton na ɗauka nima na ɗora a status ɗina. "It's Baby girl. Name Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna)" Nan na ga ruwan comments ana ta Allah ya raya. Har Hauwa Jamilu sai da ta buga ihu ta  yo mini VN tana ce mini ikon Allah ba ta taɓa tunanin zan ƙara haihuwa ba. Maijidda Bala yar anguwan mu kuwa ta ce mini ita ko in sha Allahu sai ta zo suna sai na ji daɗi na ce mata ina gayyatar duka yan set ɗin mu in sha Allahu gagarumin suna zan haɗa saboda murnan samun Rukayyatu da na yi a lokacin da na fidda tsammani. Nan ta ke Maijidda ta tura mganar haihuwan tawa a cikin group ɗin mu na makaranta sai tagging ɗina a ke yi ana mini barka wanda bai gane ni ba ma su Hauwa na ta yi masu kwatance, a zuciyata sai na ji wani iri lokaci ya yi da zan gyara mu'amalata da ƙawayena ana  yi da kai ai ya fi a ce ba a yi da kai. Ranar yini na yi amsa waya da zirga zirgan mutane. Da yamma su Jidda suka dawo daga makaranta ai sai buga ihun murna da suka ganni da jaririya na haihu, Baby ta haye gadon ta ɗauke ta ta ƙamƙame tana faɗin na bar mata ina ta mata dariya Hauwa ta ce ta ɗauka ai daman na ta ne. Jidda kuma ni take kallo kafin ta ce" Wai da gaske kin haihu ne Umma? Ina hararanta na ce" A a ban haihu ba jaririyar roba ce." Munnira da Hauwa na ta mata dariya sai ta ji kunya ta kauda kanta. Baiwar Allah sai ta matso kusa da ni a hankali ta na ce min" Umma amma ba abin da ya same ki ko? Sai na dafa kafaɗanta ina faɗin. "Ba abin da ya same ni Hauwa'u. Na gode da kulawa Allah ya yi miki albarka." Sai ta yi mirmishi ta amsa da Amin a hankali. Da ƙyar Baby ta bari ta ɗauki jaririyar nan sai da Munnira ta zare mata ido tana faɗin" Ke ba fa taki ce ke kaɗai ba." Sai Baby ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka Hauwa ta rumgumeta tana  lallashinta ni dai ina gefe ina mirmishi su da iyayen su. .Su Rahila da Ma'u da su Ya Aina suna can tare da su Mubeena suna aiki Tuwo suke yi Ya Murja kuma ta koma gida sai da safe za ta dawo da yamma nan sai ga Zabba'un Ya Abubakar fakam fakam da cewa daga gidan Gwaggo take ita ke faɗa mata na haihu sai a lokacin na tuna ban kira su  ita da Alhajin mu  ba sai na bari sai da a ka idar da sallar mangariba sannan na fara kiran Gwaggo. Ita ce bayan ta min barka na faɗa mata sunan Mama jaririyar ta ci. "Haka Aina'u ta ce. Allah ya raya mana ita cikin addinin musulunci" Na amsa mata da Amin Amin sai ta miƙa ma Alhajin wayar ni na fara gaishe shi cikin girmamawa. "Lafiya lau Dubu an buɗe ido lafiya! Na amsa masa da lafiya lau. "Kin tabbatar da ba abin da ke damun ki? Ina mirmishin jin daɗi na amsa masa da cewa ba na jin komai alhamdulillah. "To Allah ya ba ki lafiya. Gwaggon ku ta faɗa mini sunan jmRukayya kika ma yar  ko? Na ce E Alhajin mu nan take ya fara kwarara mata addu'o'i. "Allah ya albarkaci rayuwarta Allah ya raya ta. Allah ya tsare ta daga sharrin zamani. Allah ya ba ku ikon yi mata tarbiya. Allah ya yi musu albarka ita da sauran yan'uwanta gabaɗaya. Shi kuma mahaifin su Allah ya yalwata masa arziƙinsa yadda ba zai gajiya ba wajen hidimar ku gabaɗaya." Na yi ta amsa da Amin Amin ni dai sai da na kashe wayata ina jin tahowar ƙwalla a cikin ƙwarmin idanuwana. Allah sarki iyaye ma su daɗi a fili sai da na ce" Allah ya jiƙan ki Mama " Na faɗa ina mai kallon jaririyar da ta ci sunan ta, ta na kwance tana sharan barcin ta, duk ba su tafi ba sai bayan isha'i bayan har wanka Ya Aina ta sake yi ma Yumna ni ma na sake yi na shiga ruwan ɗumi sannan na take cikina da tuwo miyar agushi da kuni dukkansu sun tafi da cewa sai gobe za su dawo suka bar sai ni kaɗai sai yara can zuwa ƙarfe tara sai ga Yallaɓai ya dawo gidan ya taho mini da fura da kayan marmari da yawa na ce Jidda ta karɓa ta ɗaurayo ma na sauran kuma bayan sun ɗiba ta saka shi cikin frizer. Yallaɓai na gidan Mimisco ta kira ni ta yi minI barka bayan ita sai Anty Bahijja ita Anty Maimuna daman tun ɗazu ta kira ni, abin mamaki Gimbiya ba ta kira ni ba sannan ta ga status ɗina amma ba ta mini magana ba. Na so na yi ma Yallaɓai magana sai ban yi ba yana gidan har wajen sha ɗaya saura na dare nan ya ci tuwo ya zauna riƙe da Yumna muna ta hira da ni da shi da yara. Amma Gimbiya da ta kafa kira sai da ya yi mana sallama ya tafi, yau girkinta ne a fargabanta kar ya kwana a wajena tun da na haihu. Dama muna mganar abubuwan da babu ne na ce masa akwai komai sai dai kayan abinci in zai ƙaro sai omo da sabulun wanka da na wanki sai geron da Ya Aina ta yi masa mgana sai ya ce mini na rubuta na aika masa da shi gobe da safe Musbahu zai kawo min. Haka ko a kayi kafin na kwanta na rubuta na tura masa, tare da yara muka kwana Yumna ta tashi da kukan dare bayan na ba ta nono na sakar ma Jidda ita tana lallashinta ban ma san yauahe suka kwanta ba ni dai kamar ƴar maye haka na kwanta ina barci. Washegari tun safe Ya Murja ta fara dira ko da ta zo ma har Jidda sun yi wanka ta gama ɗumama sauran tuwon jiya. Baby ce har da rigiman ita ba za ta je makaranta ba na ce lalle ta na da aiki  ni masifa na fara mata za ta fara mini kuka na ce zan mata bugun tsiya ƙarshen ta dai Ya Murja ta lallaɓata sannan ta amince suka tafi. Yau Ya Murja ta yi ma Yumna wanka nima ta taimaka mini na gasa jikina bayan na shiga ruwan ɗumi saboda ɗinkin dake jikina. Sannan ta fara gyaran gidan ba daɗewa sai ga Gwaggo ita da Balaraba Maman Saude sun zo mini barka kamar haɗin baki sai ga Nene da Hajiya Iya sai Maman farko Adnan ya kawo su sai da na faɗa musu Yunma ta zama mai sa'a kishiyoyinta na ta kara kaina a kanta suna ta dariya. Sun ji daɗin ganin mu tas lafiya lau kamar ban haihu ba. Ba su wani jima ba suka tafi amma Balaraba sai ta tsaya tana kama ma Ya Murja aiki. Bayan fitan su ba daɗewa sai ga jama'ar Gandun albasa ni da kaina na kira Inna Mariya na sanar da ita na haihu, tare ta ke da matan su Kawu Tasi'u dukkansu dai suka yi mini barka ba daɗewa suka tafi. Da safen Musbahu ya kawo buhun gero sai rabin buhun siga sai kwalin omo guda biyu, tissue sai kayan tea da yawa saboda daman na ce masa sun kusa ƙarewa. Kayan abinci kuma ya ce sai anjuma za a kawo daga kasuwa. Ranar ma kamar jiya ne, yini gidan ya yi a cike da yan barka Amina ta kira ni a waya tana faɗin tun ana jibi suna za ta taho na ce daman ban ɗauke ma kowa ba har su Ya Hamza na faɗa musu in su na yafe musu to ban yafe ma matan su ba. Tun da na haihu kullun gidana Munnira da Hauwa suke yini da Mubeena , Su Ya Aina ma kullum sai sun leƙo Ma'u da Rahila suma kullun sai sun taho kamar haihuwar farko. Yadda na daɗe ban haihu ba , ba shakka na faɗa ma Yallaɓai taro zan yi ba ni da taro ba domin na yo gayya. Har Tariq da ya kira ni ya yi mini barka sai da na ce ban ɗauke ma Farida ba. Haka ma Kawu da ya kawo Marwa shi da ita na ce to ya sani tun ana gobe suna domin suna zan shirya sunan da ban taɓa yi ba yana dariya ya ce ya amince mini domin ya cancanci na yi taro na gani da za a ba da labari. Amma Yallaɓai na neman ya kawo minI yawa wai shi ba shi da kuɗi ya faɗa mini an gama ginin kamfamin shi yanzu oder kayan amfani ke gaban shi zuwa farkon shekaran 2021 yake son su fara aiki. A takaice dai yana faɗa mini ba shi da kuɗi na ce na ji ya ba ni iya abin da ya yi niyya. 100k ya tura mini na shgalin suna, 100k kuma ya ce na siya kayan fitar suna ni da yara. Daman ni bai san ina da kala uku a ɗinke ba cikin kuɗin da ya ba ni na hidimar haihuwa na siya ma kaina. Da kuɗin da ya ba ni sai na siya mana wani swiss lece mai kyau blue ni da yara daman suma na yi musu kala ɗaya na Atamfa super kowaccen su na yi mata riga da zani. Nima na ɗinka super wax ɗin amma kalata na dabam ne. Sannan su Munnira sun fitar da ankon suna wata vatik mai kyau da yarari, suka kuma ce ba su ɗauke ma kowa ba. Kaf yayyena sun siya tun da Munnira ce ta saro ankon haka Farida ta ce a ɗaukan mata in kai mata ɗinki ita da Amina Marwa ma an nan kano a ka kai mata ɗinki har Saude da ke dutse ta siya itama za ta zo matan su Ya Hamza a mota a ka sanya musu na su a cewar su ba su yarda a ɗinka musu a nan ba. A dangin Yallaɓai daga Sameena sai Jamila da Suwaiba suka yi, Mimiaco ba ta yi ba amma ta yi ma yaranta ƙananun Mubeena daman yar gidana ce, Munnira duk ta nuna ma su Anty Bahijja amma take faɗa mini Anty Maimuna sai da ta ce wai na cika tsirfa haihuwa ta ukun ne sai na fidda anko ita kuma ta ce su suka fidda. Ba dai wacce ta yi mu ma ba mu damu  da su yi ɗin ba domin ba saboda da su muka fidda ba. Na tura su Hauwa Jamilu da su samira duk sun siya an akai musu har gida sun yi mini alƙwarin zuwa mini suna. Gimbiya ma ba ta siya ba ni da sai da na kwana biyu da haihuwa sannan ta zo mini barka da borin kunya wai ba ta samun zama ne ga aiki ga shago ni dai tak ban ce mata ba. Da Munnira ta nuna mata ankon sai ta ce ba a nuna mata da wuri ba ba lalle ta samu ɗinki ba har tana cewa ai irin wannan in an san za a yi sai a fiddo shi tun kafin in haihun. Munnira na ba ni labarin amsar da ta ba ta sai da na yi dariya wai su yanzu suka ga damar fiddawa kuma ba dole a ka ce sai ta yi ba daman fita haƙƙi ne. Na yi dariya sanin halin Munnira da ba ta barin ta kwana. Har Naja tana ta ya ƙawarta kishi ba ta yi ankon nan ba, ba domin ya gagare ta ba Anty Zabba ba za ta samu zuwa ba amma ta ce mini zan ga saƙo in sha Allahu. Su a tunanin su sunan da zan yi duk na salon na saka ɗan'uwan su kashe kuɗi ne domin Anty Bahijja ma ta furta a can gidan Nene a na jibi suna Suwaiba da ta zo ta ke faɗa mini, ni ko na ce ya ba ni kuɗi da kayan abinci amma sauran hidima  tawa ce ba hannun Yallaɓai a cikin shi. Ni Halima ce ma ta ke ƙara ba ni mamaki sau ɗaya ta zo mini barka shima ba ta wani daɗe bs ta yi tafiyarta. Na tuna lokacin da nake zuwa gidanta na ci uwar aiki amma yau ni ce banza a idanuwanta Gimbiya ce gwana. Na yi kyafci a cikin zuciyata domin na saka ma raina akwai ranar da in ta mu ta haɗo mu sai na yi mata wankan tsarki da za ta gane ba ta da wayau. Tun ranar litini da ya kama ana goben sunan Yumna gidana ya ɗinke da baƙi. Daman tun da na haihu na ce Yallaɓai ya koma wajen Gimbiya ya ce bai ga dama ba sai jiya ne ya tafi can amma ban sanin masa ko zai dawo bayan suna ba amma ni dai na ce masa ya koma gidanta har sai na yi arba'in ya ce ban isa ba. Amina tun safe suka sauka ita da Farida tare suka haɗa tafiyar Marwa ma da azahar ta iso. Rahila da Ma'u da kayan su suka taho tare da yaransu daman na faɗa musu in suka zo sai an gama suna can kuma sai ga Sameena sai da muka rumgume ga shi dai ƙanwar Gimbiya ce amma tana ƙaunata saboda da Allah. Daga Rano ta ke sannan ta sauka a gidana. Su Munnira daman ai suna nan sai suna ya tashi. A ranar mai ƙunshi ta zo ta yi mini saloon kuma tun safe na je shagon Amesty ta yi mini. Har su Munnira sun ce za su yi ƙunshin. Can sai ga Saude ta iso itama sai na ji daɗi su Khaleesat ne sai gobe amma Laila Ya Auwal ya ce mini ta na hanya. Gida ya kacame da ayuuka. Da yake za su yi waina sai sinasir da aikatau muka kai sannam za su yi alale da shinkafa jalop mai kaza. tun da akwai naman miya da Yallaɓai ya aiko da shi. Raguna kuma uku Yallaɓai zai yan ka ma Rukayy suma ragunan su Suwaiba na faɗa mini su Anty Bahijja suna ta surutu ni a bakin ta ma nake jin raguna biyu Ya Usman ya siya masa ɗayan kuma Mimisco ce kuma ya ce tun da da sunan Rukayya a ka ba da su to duka za a yanka mata su. Sannan nima na ba da a yi mini tsire sannan na saka mai yin ledojin kayana na hijabai ya buga mini na suna da jakar nan mai ɗauke da sunan Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna) name on 17 November 2020. Cut-ceey: Hauwa'u Yusuf Muhammad(Jidda) and Maimunatu Yusuf Muhammad(Baby) Lemuka da ruwan roba katan katan Yallaɓai ya saka a ka sauke mini sanman ni kuma za mu yi zoɓo da kunin aya duk za mu saka a robobin ma su ɗauke da sunan Rukayyatu. Wanda a ledan za a saka mutum da jalof ɗin shinkafa mai kaza sai tsire da zoɓo wannan na in zai tafi gida ne. Da yamma kwandon tumatir da solon tattasai da attarugu mai yawa Musbahu ya zo da shi tare da gyararrun kaji guda ashirin a buhu, lokacin su Anty Bahijja da su Gimbiya duk suna gidan ba aikin da suke yi sun kame a gefe suna tsegumi tare da taɓe baki ni ko kallo ba su ishe ni ba, da suka ga an kawo wannan kayan nan kamar su mutu sun ɗauka Yallaɓai ne ke ta kashe mini kuɗi tun da nima yar matsiyata ne ba ni da kuɗi. Ya Hamza da Ya Auwal sai suka suka haɗa mini 150k na kuɗi saboda na ce musu zan yi suna kuma Yallaɓai ba shi da kuɗi, abin da ya ba ni ba za su ishe ni ba, Shi ya sa suka tura mini kuɗi har Datti sai da ya tura mini 30k ya ce na ƙara. Kawu Abba 50k ya tura mini bayan Marwa ta zo mini da atamfofi masu tsada guda uuku da kayan jarirai. Amina ma turamen ta kawo mini da kayan jarirai Farida ita ma turminta huɗu da kayan jarirai sama da guda biyar, tun kafin goben ta yi gefen gadona ya fara cika da kaya sannan wasu ma hidiman  su Munnira ke yi ba sa faɗa mini. Suma ita da Hauwa turame uku suka yi min da su pampers da kayan sanyi sannan sun ba da an yi mini yajin jego mai yawa mai daddawa. Ina can cikin ɗaki ban sani ba Hauwa ta zo tana faɗa mini wai ashe sai da Anty Bahijja ta kira Musbahu tana tambayan shi ko Tafida ne ya ba da saƙo ya kawo? Shi kuma ya ce ni na tura masa kuɗi ba Yallaɓai ba ni tana faɗa minibsai da na bushe da dariya. Matar nan ba za ta bar ni na huta ba na yi alƙwarin in ta sake magana a gabana sai na mayar mata da martani ana cikin gida a na aiki su kuma suna zaunes sai ji da jiyarwa. Bayan mangariba mai ɗinkin mu ya kawo mini sauran nawa  da na yara sai na Farida da Amina. Ni na fita har haraban gida na karɓa muka yi maganar ƙarishen kuɗin ɗinki na dawo kenan falon Baby ta tare ni tana faɗin wai Anty Gimbiya ba ta zo da su Khalipa ba. Kayan ɗinkin da ke hannuna na miƙa ma Amina da ta zo ta tare ni da mgana na ce ta bari in zo. Ina sanye da doguwar riga tsaraban makka ne cikin tsaraban Yallaɓai., rigar ba takai mini har ƙasa  sosai ba tana da mayafinta shi ne ma jiki na, na yi kyau ɓulɓul da ni domin ga ruwan zafi daman sannan kuma na saka Aisha lame ta kawo mini mai da shower gel, kuma ina kula da jikina ina cin mai kyau ina shan mai kyau ni kaina na san na yi kyau da haihuwan Yumna sannan cikina ya fara komawa jikina ya yi cif sai na zama wata yar dumduma gwanin sha'awa kowa ya zo ya ganni sai ya ce mini na ƙara kyau da na haihu mene ne sirrin? Na ce Yallaɓai ne sirrina muna ta dariya. A tsakiyar falon Yallaɓai na tsaya tun da nan suke zaune har da su Halima. Anty Maimuna ba ta zo ba itama Anty Bahijja gulma ne ya kawo ta. Yau ga shi Anty Bahijja na zaune amma bayan gaisuwa ba abin da ya ƙara haɗa su da Ma'u duniya juyi juyi. Gimbiya ta ƙura mini ido tana kallona ita kuma Naja da gayya take ce  mini" Ka ga uwar gida a gidan Uncle Tafida" Na yi mata fari ina faɗin" Faɗi ki ƙara Uwargida mai babban muƙami a wajen megida " Sai ta yi shuru ai ba zan bari ta saƙa mini magana ba Gimbiya na kalla ina faɗin" Baby ta kawo min ƙaran ki." Sai ta yi wani luu da ido kafin ta ce" Ni fa? Me ta ce miki na yi? "Ta ce ba ki zo da Khalipa ba" Anwar ma da za ta zo da shi ya na wajen Halima. "Ayya ai Khalipa na Rano Anty Marliya da ta zo ya saka rigima sai ya bita sai kawai na ce su ta fi dashi." Sai na jinjina kai kafin na ce" Amma ai da kin ce su zo da shi saboda suna ko? Kawai karaf  Halima ta saka bakinta. "Don dai suna me ya sa zai dawo? Suna dai ba biki ba fisabilillahi." "To nima shi na gani." In ji Naja. Anty Bahijja dai ba ta yi mgana ba, ni ko sai na juya ina kallon Halima kafin na ce" Aa. fa ba suna kawai ba wannan sunan ya sha bambam da sunan da kika saba zuwa ko gani Halima. Suna ne garurumin da baki taɓa ganin irin shi ba." "Allah ko? Ta faɗa cikin mamaki ni kuma sai na gyaɗa mata kai, muna cikin haka ne sai ga su baby da murna da akwati Laaila ta iso mutanen Abuja. Muka rumgume juna ina yi mata maraba ta gaggaisa da su Anty Bahijja. Yara wajen ɗaukan wata leda suka yagata kayan ciki ya zube kayan fulawa ne ta yo mini cincin da donot sai cake, ina ta faɗa sai ta ce ai namu ne ta zo mini da shi saboda gobe. Ta ce mini ma ta saka ƙanwarta ta yi mini meatpie gobe za ta kawo. Su Amina duk sun taho falon da suka ji tahowar Laila. Munnira ta daddage ta rangaɗa guɗa Amina na ta ya ta. Ina ta dariyan farinciki na ce"Na gode Anty Laila." "Ba komai an zama ɗaya. Kin ga yadda yayanki ya ruɗe. Ki yi ki gama aikin nan ki tafi kayan fulawan nan ma duk tare da shi muka shiga kasuwa muka siyo komai ina cewa ya bari na siya da kuɗina ya hana shi dai faɗi yake Sadiya ce ta haihu ta yi ma Mama takwara saboda haka muma za mu yi ma wannan haihuwan na ta kara." A gaban su Anty Bahijja ta fiddo mini kayan suna. Atamfa biyu leshi ɗaya sai kayan jaririya guda bakwai bayan su pampers da mayuka da rigunan sanyi. Har su Aina sun ƙariso suna ta ɗaga kaya suna gani da farinciki. Amina ta ranguɗa guɗa tana faɗin" wannan yarinya ta ga gata. Ta shaida ita ɗin yar dangi ce gaba da baya." "Tabbas yar dangi ce. Ya Hamza ya nuna bajintarsa ga Ya Auwal ma ya nuna na shi Ubangiji Allah ya bar zumumci." Aka amsa da Amin gabaɗaya  da gayya ba na ce" Kuma duk sun tura mini kuɗi duk da su na yi wasu hidiman." Mu mun man ta da su Gimbiya a falon ma ballanta su ce da gayya mu ke yi sai da daga baya ne da muka haɗa ido da Gimbiyar sannan na ce bari nima na ɗan ɗana. "Na daɗe da sanin ni yar dangi ce amma na ƙara ganin kara a haihuwan Rukayyatu. Na ga karamci a wajen ku yan uwana na gode. Alhajin mu ma buhun shinkafa cir shanshera ya ba ni saboda Rukayya" Su Rahila har da kabbara Ni kuma na cigaba da faɗin "Mijina ya yi mini dukkan gata na gode masa. Sannan ƙawayena da ku dangina gabaɗaya kun rufa mini asiri kuma ina mai gode maku uUbangiji ya ruɓanya muku." Munnira da Amina sun fi kowa zaƙin murya wajen amsawa da Amin Munnira har ta na faɗin wani abun ma sai gobe. Ta ba ni hannu muka tafa ni da ita. Gabaɗaya su Gimbiya sun gama muzanta Anty Bahijja ma ba san tafiyarta ba na ji daɗin haka saboda ta fahimci ba Yallaɓai kaɗai ya yi mini hidima ba, Gimbiyar ma sai wajen tara na dare suka fita tare da Naja da Halima sai bayan tafiyar su ne da muka zauna da Sameena nake jin wasu manganganu. Ni da ita ba mu taɓa zama mun yi maganar zama na da Gimbiya ba sai ranar. Kusan raba dare muka yi muna hira na faɗa mata wasu rigingimun da suka faru tsakanina da Gimbiya. Itama tana ba ni wasu labaran da ban san da su ba. Ashe Gimbiya kishi take yi da ni da tana da iko da tuni ta koreni. A bakin Sameena nake jin ko maganar haihuwan ta ce Tafida sai rawam jiki yake yi a kaina kuɗin shi duk a kaina da yayana ya ke ƙarewa to daɗin abin ma dai ban yi irin haihuwanta ba mace na haifa. Haka ƙannenta suke ta faɗa da masu goya mata baya. Kuma wai a haihuwan nan da na yi sai da ta nemi ya ranta mata kuɗi ta biya kuɗin shipping, amma ya ce mata ba shi da kuɗi aamma ni ga shi nan ya ba ni kuɗi ina ta wadaƙa har suna na shirya mai kama da biki. Har cewa ta yi yadda Yallaɓai ke jin maganata ko Nene albarka. Na yi dariya kafin na ce ma Sameena." Duk maganganun su Anty Bahijja a kaina ne itama ta ɗauka. Ni gaskiya na riƙe kuma shi ke riƙe da ni har gobe. Maganar hidimar suna kuma wallahi  kayan abinci da kayan sawa kawai Yallaɓai ya yi mini. Sai sauran abin da ba a raasa ba. Maganar gaskiya nima na yi hidima da kuɗina sannan ku ma da muke tare kun yi mini amma ba kuɗin Yallaɓai ba ne balle hankalinsu ya tashi kar na karar da kuɗin ɗan'uwan su." Sameena ta ce wallahi ita ta sani ita ko magana ta ji a kaina ba ta yarda. Lamarin Gimbiya ya daina ba ni mamaki tun da kishin take so a yi to za a yi. Sannan suna kuma za a yi sai dai ta mutu. Ni Allah ya ji ƙaina da ban yi haƙuri a lokaci haihuwar Gimbiya ba, da tuni an buga mini tambari amma yau da na yi haƙuri ga shi komai ya wuce abin da Yallaɓai ya yi mata ko rabin shi bai yi mini a haihuwan Rukayya ba amma Na tsaya mata a ƙahon zuciya saboda kishi da baƙin ciki. *Janafty**TKGB3I09* RANAR SUNA. Talata. 17,November. 2020. A safiyar talata muka tashi da hidiman sunan Rukayyatu(Yumna). Da yake duka nan suka kwana tun asuba suka tashi da aikace aikace kafin ka ce kwabo an gama komai. Alele ne ma ƙarshen gamawa amma waina tun asuba suka fara suya tun da tun a daran jiya suka haɗa ƙullun wainar miya kuma da safen nan wuta kawai suka ta da mata tun jiya sun gama haɗa komai. Kafin azahar komai ya kammallah gida ya fes sannan duk mun yi wanka amma ba mu saka anko ba sai bayan ƙarfe biyu amma ni da yara da ba su je makaranta mun saka sabbin kaya muna walwali. Yunma ma tun safe a ka yi mata wanka a ka saka mata kyakyawan kayan jarirai masu kyau da safa da takalminta na yara mai kyau da hula cikin kayan da Yallaɓai ya ba ni kuɗi na siya mata ne. Da safen nan ya zo ya gan mu har Amina ta matsa masa sai da ya tsaya muka yi hoto. Shima ya sha farar shadda har da babban riga har sai da na ce masa " Yallabai hala kai ma walima za ka haɗa mana? "A'a kawai na yi shigar fararen kaya ne domin nuna murnata a wannan ranar" Abin da ya faɗa mini kenan na yi shuru kawai ina kallon shi ya yi kyau sosai. Sajen sa na shafo in da tsillin furfura suka fara fito masa, Yallaɓai fa yanzu shekarunsa wajen arba'in da takwas ne yana ƙoƙarin shiga gidan hamsin Allahu akbar jiya ba yau ba, ni ina ta kallon shi a matsayin ɗan saurayin da na aura ɗan shekaru ashirin da bakwai da takwas a duniya. "Kallon fa Madam? Shi kan shi ya gaji da kallon sa da nake yi sai da ya yi mini magana sai na yi mirmishi. Na isa gare shi na rumgume shi, shima sai ya kama ƙuguna ta baya yana faɗin" Wata Sadiya ta yi kewar Yusuf ɗin ta ko? Ya faɗa yana sumbatar wuyana. Sai na noƙe ina ɗan mirmishi mun daɗe a haka muna shaƙan turaran juna sannan muka saki juna lokaci ɗaya muna masu kallon juna. Mun raja'a a kallon juna sai da shigowar Amina da kukan Yunma ya fargar da mu sannan muka saki juna na karɓeta na zauna gefen gado shima biyo ni ya yi shi ya zage min zip ɗin gaban riga ta na fito da nono ina ba ma Yunma. Yana zaune gefena muna hira yana faɗa mini Tariq da Kawu sun tura mai kuɗi wai ya ƙara na hidimar suna. "Allah ya saka musu da alheri. To sai ka ƙara mini wani abu don Allah Yallaɓai." Na faɗa har langwaɓe kaina sai ya wani kalle ni kafin ya ce" Da ga jin na ce an ba ni kuɗi sai ki ce na ba ki? Ke yanzu me ya rage ba ki yi ba ko ba ki siya ba? "Yallaɓai ban ɗauko mai DJ da mai hoto ba fa" Na ƙarishe faɗa cikin shagwaɓa har ina tura masa baki. Yallaɓai sakin baki ya yi hakan bai ishe shi ba sai da ya riƙe haɓa yana faɗin" Kika ce me? "Na ce DJ da mai hoto. Domin kasan Haihuwan Yumna na dabam ne za a sha shagali." "To ni ba da ni ba." "Acikin gida ne fa Yallaɓai ba matsala tun da duka taron na mata ne." "Ba amince ba." "Yallaɓai." "Sadiya na ce ban amince ba ko? Ya faɗa yana mai kallona a fuskarsa da maganarsa na fahimci ba wasa yake yi ba. "To shike nan." Na so na yi fushi ne amma sai na ga bai damu ba kawai ya miƙe yana saɓa babbar rigan shi. Duƙawa ya yi ya sumbaci goshin Yunma kafin ya dago nima ya sumbaci kumatuna lokaci ɗaya yana faɗin" Na tafi. Take care a yi suna lafiya." Da dai na ga zai tafin sai na ce to ya taimaka mini da kuɗin zan kira ko mai hoton ne. "Wani irin mai hoto kuma Sadiya? In hoto kike so ba ga wayoyi nan ba? Sai kin gaji da hotuna yau." "Ni fa ba irin shi ba. Na camera nake so" "Lalle." Yallaɓai ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin" Ni ba ni da kuɗi kin cika tsarabe tsarabe Sadiya. Suna ba dai a ci a sha ba ne? Kuma na tanadi abinci miye wani hoto? Hoton ma da a ka ce haramun ne? Ni dai ai sai na kasa mgana ina ji ina gani Yallaɓai ya fice ya bar ni zaune bai ba ni ko sisi ba, to ya za a yi ya ba ni shi da ya ce hoto ma haramun ne. Dj dai tun da ya hana amma mai hoto kam zai zo daman mun yi magana da Samira class mate ɗina ita ce na taɓa zuwa sunan yaronta na ga an kira shi sai ta ce mini ƙanin mijinta ne. Na ɗauka zan samu wani abu a wajen Yallaɓai ne sai na ƙara tun da ban samu ba sai na ɗauka cikin kuɗina na tura mata rabi, anjuma da yamma zai zo, na samu kuɗi sosai ko Anty Zabba 20k ta tura mini ta ce ba yawa ni ko na ce mai yawan kenan, ina ta mata godiya. Har mai makeup na samu ita kuma ƙawar Anty Khaleesat ce tare suka yi makaranta ta yi mata mgana itama anjuma za ta zo ta yi mini kafin baƙi su fara suwa. Kaf yan uwan Mama na gandun albasa sun taho mini suna. Kuma na ji daɗi sai na sauke su a ɗakin su Jidda. Falon Yallaɓai kuma na ce a bar ma dangin Yallaɓai saboda ba na son ƙananun mganganun falon su Jidda kuma yan gidanmu da sauran mutane ciki kuma ga bedroom ɗina na zauna ni da ƙawayena da mutanen arziƙi. An kawo sinasir da tsiren sannan tun jiya a ka haɗa da kunin aya suka ɗuɗɗura a gorinan suka saka sticker a fridge ma suka kwana ina ganin haka sai na kira su Ya Aina na ce su raba komai kashi uku, ɗaya namu ne da ƴan'uwan mu ɗaya kuma na yan uwan Yallaɓai ɗaya kuma ni da ƙawayena da yara tun da Baby ta ce mini yan ajin su za su zo Jidda dai na san hali ba gayya za ta yi ba. Bayan na saka an diɓar ma su Gwaggo na ba da a ka kai musu sannan na saka Hauwa ta ɗibar ma Gwammaja suma suka aika da shi can wajen su Nene. Na saka suka ɗibar ma Yallaɓai na ce zam kira shi in yana office ne zan kira Musbahu da Adnan matan kuma na ce su ɗibar ma yaran su da mazajen su a yi komai cikin tsari. Na bangaren mu ragamar na hannun Amina na bangaren su Yallaɓai kuma Munnira ce ni dai na gama jan kunnenta kar ta yi faɗa da kowa a yi suna a tashi lafiya. Ta ce mini ba za ta yi ba amma ni na san sai ta yi mgana ni da na san halin Munnira. Karfe biyu na rana mai kwalliya ta iso kusan ma lokaci ɗaya suka iso tare da Khaleesat wai mota ta lalace musu a hanya. Itama ta kawo mini turamin atamfa da riga tare da kayan sanyi na karɓa ina ta godiya. Swiss lece na saka cikin wanda na siya na ɗinka sannan a ka tsantsara min kyakyawan kwalliya wanda tun kafin a gama kowa ya shigo sai ya yi santin kyan da na yi kyau ma sai da a ka gama ta yi mini wani irin ɗauri mai kyau da na duba madubi na ɗauka jidda ce tsabar yadda na dawo kamar budurwa. Na yi amfani da takalmi baki mai tudu kaɗan da mayafi baƙi da jaka, Na saka ɗan kunnaye na masu kyau da tsada, ba ni da zinare ko na zobe sai da na yi hawayen takaici na tuna wanda a ka siya mini da Sadaki na, Yallaɓai ya saka na siyar da shi muka cinye kuɗin, da cewa in ya samu zai siya mini wani har yau lokacin bai yi ba ina jin ma ya manta da abin da ya faru. Ni kaina na san na yi wani irin kyau duk kuma in da na gifta Ƙamshi ke tashi, oil ne mai bala'in, wajen wata mai siyar da turaruka a faceebook na san ta Maryam kitty. Tun da na fara siyan turarenta ban taɓa saka shi ba a yi santin kamshin ba Yallaɓai ya daɗe da sanar da ni yana son ƙamshina. Har na ce in na samu kuɗi zan ce ta haɗa masa na maza daga baya da ya ɓata mini rai na fasa. Yumna ma an sauya mata kaya ta yi kyau daman ta sha kunshi a hannu da kafa da Ya Murja ta sake kun sa mata yau da safe yau ma mun so komawa asibiti amma sai Yallaɓai ya ce mu bari gobe da safe kar mu je a yi mata allura ta dawo da rigima amma dai tun kwana uku da haihuwanta wanzami ya zo ya cire mata belu sannan ya yi mata askin gashin kanta kamar yadda ya zo a cikin sunna. Zuwa biyu da rabi shagalin suna ya kamkama, baki suna ta zuwa ban yi tunanin zan tara mutane haka ba ni da ban damu da zuwa suna ba, duk sun saka ankon su sai suka yi kyau sosai. Maijidda Bala daman ta zo garin lokacin da na haihu da ya ke mijinta ya samu aiki a Dutse sun koma can da zama ita ce ta yo mini gayyar su Samira da Hauwa jamilu sai da na yi ƙwalla da suka kawo min pampers da mayukan jiki da hoda na jarirai sai safa da huluna suka ce kuɗin da a ka haɗa mini ne suka siya mini da shi, duk da ina ba da wa in na gani amma ba kowanne na ke yi ba, amma dai tabbas na ji daɗi na kuma martaba wannan karan da suka yi mini, sun kuma saka ankon su gwanin ban sha'awa. Muna cikin bedroom ɗina tare da su muna hiran yaushe gamo. A nan Rahila ta kawo musu abinci sinasir da waina sai alale da ruwa da drinks can cikin gida kuma su Munnira na ta ji da baƙi. Suwaiba da Jamila sun zo mini suna da wuri amma ko Gimbiya sai wajen uku na rana ta zo tare da Halima da Naja. Mimisco daman ta ce mini tana Abuja amma yaranta ƙananun suna nan, Anty Maimuna ba ta zo ba sai can wajen la'asar suka zo ita da Anty Bahijja. Su Nasara da suke kusa duk sun zo mini suna kuma an ba su abinci kamar na kowa ba nuna bambamci ko da suka zo na sauya kaya na saka anko da suka shigo suka ganni sai da mamakinsu ya nuna tun ballantana da suka ga gefen gado na cike da kayan arziƙin da a ke kawo mini. Gimbiya ta ta ba ni saƙo a leda Anty Bahijja ma ta ba ni leda Babba cike ta ce na su ne gabaɗaya daman haka suke yi bai ɗaya suke mini hidima in har na haihu. Naja ce kawai ta ɗauki Yunma amma bayan ita haka suka fita ba su ɗauke ta ba sun fita fuska ba daɗi domin ba haka suka so su ganni ba. Ga shi sun tarar da ɗaki cike da mutane su da ba su yi anko ba sai suka ga su ne ma dabam a wajen domin kowa ya yi ban da su. Ba abin da zan ce ma mutane sai godiya domin sun yi mini karam kaya sai da na koma jefa su a ƙasa saboda gadon nawa ya cika kowa ba ya zuwa hannu rabbana in ba a bani saƙo a leda ba za a ba ni kuɗi hatta Ya Abubakar da Ya Muntari sun tura mini kuɗi sannan matan su ma sun zo sun kawo mini turame, sai da a ka yi sallar la'asar sannan mai hoto ya zo a haraban gidan shi da yaran shi suka yi decration na ɗaukan hoton. Mamaki kawai na ke ba ma su Anty Bahijja sun kasa magana na fito da tawagata mun sha hotuna zafafa na shiga na fita da kaya sama da kala biyar ni da Yumna, na kuma gayyaci su Anty Bahijja zuwa hoton sun shiga amma a cunkushe Gimbiya ma mun yi ni da ita sannan mun yi da yara. Muna cikin hoton ne sai ga ƴa'ƴan su Anty Bahijja da na Anty Maimuna waɗanda ke gida wasu sun yi aure wasu kuma suna makaranta. Ana gamawa da hoto suka saka kiɗa a speaker suka yi connecting da waya daman Munnira na da home thearter ita ta zo da su daga gida saboda ta ce chasu za su yi ni dai na sulale na koma cikin gida na kira Musbahu na tambaye shi Yallabai ya ce yana office tare da Kawu sai na ce ya zo gida ya karban musu abinci ba daɗewa sai ga shi ya zo na saka Mubeena ta je ta kai mishi har da na shi gabaɗaya. Sun ta saka kiɗa su suna ruwa ni dai ban shiga ba, ina da ɗinki a ƙasana duk da ya kusa warkewa amma gwara na kiyaye amma da Munnira da Hauwa da Amina suna rawa na shiga na yi musu manni, Yumna ta na hannun Sameena itama ta shiga tana juyawa, har su Suwaiba duk sun shige daman su ai ba ruwan su ana cikin shagali ana ta farinciki suma Gimbiya da tawagarta suna wajen Anty Maimuna dai da Anty Bahijja sun yi mini sallama za su tafi na saka Munnira ta salleme su da ledan su ta ce mini sai da Anty Bahijja ta taɓe baki kafin ta ce"Lalle Tafida ya riƙe ma Sadiya kan macijin har da wani leda ne in mutum zai tafi? Duk abincin da aka ci bai isa ba? Ni dai a yadda ta faɗa mini ta ce ba ta tanka ba amma ni na san ƙarya take yi sai ta ba ta amsa. Sun tafi sun bar su Gimbiya da yaran su ina ga sai daga baya suma za su tafi. Ana cikin shan wakar ado gwanja na kujeran tsarkar gida, Munnira ta sauya zuwa kirarin uwargida. Kirari ne da wani mawaƙi ya yi ga uwargida je, kuma tabbas kirarin ya yi sosai ni dai ina ta dariya da farinciki su ka ja ni cikin fili suna kuma bin kirarim suna nuna ni. "Uwar gida ran gida in babu ke gida ya ɓaci. Haka zalika kowa ya zo ke ya tarar. Ke ce Amarya kuma ke ce uwargida, ke kika fara kafa gida saboda haka kowa ya zo ke ya tarar. Ke ɗin dai ce Uwargida haka za su gan ki kuma haka za su bar ki, hassadansu sai dai ta koma kansu. Allah Ya barki da Alhaji Tafida ya kuma kashe ki a ɗakin Tafida. Takalmin kaza mutu ka raba." Ina ta dariya saboda duk in da a ka ce Megida sai su sauya suna su kira sunan Yallaɓai. Jin daɗin kirarin ya saka na fiddo kuɗi a jaka ta sabbin yan ɗari bibbiyu da Khaleesat ta ba ni na riƙa manna musu. Daga baya ma Jamila kashe speaker ɗin ta yi ta ɗaga muryanta ta na rausayawa a gabana ta fara faɗin. "Yau taken naki ne Uwargida a gidan Tafida. Uwar gida ran gida shalele a wajen Tafida. Kowa ya zo ke za ya tarar. A buga a bar ki sai ta Allah ta yi Uwargida sai gaban ki in da kike so. Wallahi ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya. Mun sani mun kuma tabbata da tsohuwar zuma ake mgani. In ka ji ana a wasa a wasa ba kaifi, ke ce wakiliyar Tafida kowa ya zo arziƙin ki ya ke ci, kin zama Tafida Tafida ya zama ke, maganarki a ke yi wa ke batun yan karere. A matsa a matsa ga Uwargida Sadiya a gidan Tafida ta hallara na ce a matsa a matsa." Kaina na ji ya fashe,na ji na yi girim girim nan da nan na zazzage musu kuɗaɗen dake jakata sai shewa da ihu ya ta shi Amina da Munnira suka ɗora da guɗa. Har da Sameena a wajen ni ban ma lura da Gimbiya ba, ballantana na ji cewa ina yi da gayya ne sai bayan mun baro haraba zuwa cikin gida Hauwa ke tsegunta min ga Sameena can naja na yi mata faɗa wai ba ta kishin ƴar'uwanta ta biye mana a na yi ma yaruwanta habaici. Na riƙe haba cikin mamaki ina faɗin habaici kuma? Hauwa ta ce wallahi su haka suka ɗauka sai kawai na ce to Allah ya kyauta ni dai fata na mu rabu da kowa lafiya. Ai ko na gan su da Sameena a can haraba bayan mangariba lokacin da na fito zan raka su Samira. Su ko salla ma ba su yi ba suna nan suna mganganu har da Halima a wajen, suna ganina suka yi shuru Sameena ko daga gani ranta ya gama ɓaci domin juyawa ta yi ta shige ciki a fusace kamar za ta tashi sama ni dai ban ce komai ba iyaka dai na ce musu ya kuka tsaya a nan? Sai Halima ta ce minI wai tafiya za su yi sai na ce su je su karbi saƙo a wajen Munnira sai ta amsa mini da to. Ni na dawo cikin gida ban san me ya faru ba Sameena ɗayan ɗakin ta shige nima ban neme ta ba kawai muna cikin ɗaki ni da su Ya Aina suna ta ƙwashe min kayan da na samu nawa da na Yumna sai ga Khaleesat ta shigo tana faɗin wai ga Amina can suna hayaniya da ƙanwar mijina mamaki ya kamani ina tambayan kaina me ya haɗa su? Gabaɗayan mu muka fita can falon Yallaɓai muka iske Amina da Halima suna cacan baki ga su Gimbiya zaune Munnira ce me ke jan Amina da cewa ta yi shuru amma Halima da rashin kunya ina falon ta ce ma Amina. "An zo an samu banza an tattare, za a kai gida. Saboda babu a house ɗin tsoho sannan a house ɗin miji ma babu." "Ke Amina me ke faruwa! Me ya haɗa ki da ita? Na faɗa ina shiga tsakiyar su saboda Amina ta ta so tana faɗin" Wallahi ƙarya kike yi. Kin san ko daga yanayin mu za ki san mun fi ƙarfin wannan abun da kike haƙilo a kan shi. Ni mijina ba mai kuɗi ba ne amma yana da rufin asiri kuma a gidan ubana mun fi ƙarfin abincin shekara. Kaf yayyena suna gidan mazajensu cikin rufin asirin mazan kuma akwai ma'aikacin banki da ma'aikacin bankin kuɗin duniya wato CVN kin ga ko tsakanin ni da ke sai a nemi wanda ke rigima kan tsire. Tsiren da dubu biyat ɗin ki ta gama biya miki bukata amma kin tsaya kina ta da jijiyan wuya. An daɗe ba a gamu ba miyau ya tsinke ƙwadayi ya tashi ba." "Amina." Haka na ke kiran sunanta amma ce min take yi" Ya Sadiya don Allah bar ni na ga karshen rashin kunyar yarinyar nan." "Ni ba mara kunya ba ce. Sannan yarinya na bayan uwarta." "Ke Halima." Na daka matsa tsawa domin raina ya gama baci na ga tana shirin zagar mini uwa ne a gaba na kuma a gidana. "Ni da gidan yayana ke ɗin banza? "Ƙwarai kin fita iko da shi. Abin da a ka hana ki ma ai yayan na ki ya siya ko? Naja ta shigar mata, Amina na ja ina mata faɗa. "Me ya haɗa ki sa'in sa da ita? "Ya Sadiya ni fa ban shiga harkan ta ba, ba kin ce na riƙe na bakin mu a hannuna ba, kawai ta na ganina da shi ta ce sai na ba ta leda ɗaya ni kuma sai na ga ai ga shi nan a hannunta Munnira ta ba ta, amma matar nan ta na ce sai na sake bata sai na ce ita ta samu wasu ba su samu ba ta bari a sallami waɗanda ba su samu shike nan ta fara zagina ta na gaya mini mangaganu duk yadda na kai ga haƙurina sai da ta ƙure ni." "Nima na zo ina yi ma Haliman magana tana neman yi mini rashin kunya." Munnira ta faɗa tana kallona sai na kaɗa kai ina faɗin" Amina dauka ki ba ta. Ko ba yayanta ya siya ba matar yayanta ce ta siya. Ko guda goma take so ki ba ta ai arziƙi ne a zo wajen ka har kana da abin da za ka ba da." Ina faɗin haka sai Amina ta miƙa mata leda ukun da ke hannunta, su Ya Aina ma suka ce shikenan ko rigima ta ƙare. Amma sai Halima ta ƙi karɓa sai ma falati da ta yi da ledan daga hannun Amina. Suka watse mini a tsakiyar falon na yi jagale ina kallon Halima na ɗauka iya nan za ta tsaya amma ba ta tsaya ba kamar ta na jirana. "Ai ni nafi ƙarfin wannan abun. Ke dai ki kara akai gida." "Kin fi ƙarfin shi kike rigima don an hana ki? Munnira ta katse Halima. Ya Balki ta saka baki da cewa kowa ya yi hakuri ta duka ta na kwashe wanda Halima ta zubar Hauwa ta amshe ta. Amina za ta sake mgana Ya Aina ta tare ta ni ko daman ina ta danne zuciyata ne amma ba domin haka ba wallahi Halima ba ta isa ba. Gimbiyar ta su na zaune ta haɗa kafafu tana kaɗawa "Na gode Halima. Tun da masalahan da na nema da ke baki yarda ba, ba na son tashin hankali zo ki fice ki bar mini gidana." Na faɗa ina nuna mata hanya. Yadda ta kalle ni cikin mamaki ne ya sa na ƙara haɗa rai na. "E ki fita ki bar mini gidana na gode da sunan da kika zo amma ni ba na son rigima" "In fita fa ba kika ce? "E ki fita na ce" Na ina ƙara jadadda mata sai ta juya tana kallon su Naja suma da mamakina a fuskokinsu. "Sadiya ƙyaleta kawai. Ai Aminar an shiga da ita ciki maganar ta ƙare." In ji Ma'u sai na juya ina kallonta kafin na ce" Wallahi sai ta bar mini gida. Ta zo ta fita kawai." Na faɗa cikin ɓacin rai, ina sake nuna mata hanyar fita. "To ba zan fita ba." Ta faɗa tana ƙara cijewa har da riƙe kugu. "Ba zan fita ba, tun da nan ɗin ai ba gidan ki ba ne." "Ok to ke gidan ki ne? Na katsete cikin ina saita kaina domin wallahi in na harzuƙa zan iya jawo ta na yi mata bugun tsiya ba ruwana da aurenta ballanta ya'yan ta. "Ba gidana ba ne amma gidan yayana ne na fi ki iko da shi. Kuma ai nan ɗin ba gidan ubanki ba ne" A bazata na ji maganar duk lalacewata a idanuwan Halima ban ɗauka za ta iya zagin ubana ba. "Ke Halima Sadiya kika zaga? In ji Suwaiba da ta shigo falon yanzu daman na bar ta a ɗakina tana salla. "Ita wace ce da ba za a zage ta ba. Na ga za ta nuna mini iko ne da gidan Yayana. Alhalin ba ta isa ba ita ɗin banza abanza k" "Tas! Sai ƙaran saukan mari suka ji na sharara ma Halima mari sai ga ta dafe da ƙuunci. "Ko giwa ta mutu ba ta yi lalacewar da kiyashi zai ja ta ba. Ba ki isa ki zo har gidana ki ci kasuwa a kaina ba ƙaryan ki yarinya gwara tun wuri ki shiga hankalin ki, ki kuma kwashi jikinki ki fice mini a gida kafin raina ya ɓaci wallahi na yi miki dukan tsiya" "Ni kika mara? "In ba ki fice mini a gida ba duka zan yi miki wallahi." Na faɗa ina nuna mata zan iya ya ɗin. Munnira ta kwashe da dariya Suwaiba da Jamila suka ce da kyau. "Me ya sa kika mare ta a kan gaskiyan ta? Naja ta miƙe tana challanging ɗina. "Na mare ta ko za ki rama mata ne? Na faɗa ina kallonta domin kaɗan na ke jira yanzu sai na saka a yi musu dukan tsiya su bar mini gida amma sai na ga Gimbiyar ba ta yi magana ba. Kuma ba ta tsawarta ba. "In nan gidan Yayanta ne ni kuma matar yayanta ne da gidan da shi kan shi yayan nata a ƙarƙashin ikona suke. Kuma ko shi bai isa ya zo yana mini wulaƙanci ba, ballanta ita ɗin banza. Duk wacce ba lafiya ya kawo ta ba, ta zo ta fice mini a gida kafin na haukace muku." Kawai sai na fara masifa ina faɗin ni da gidana ba shege ko shegiyar da ta isa wallahi. Amma suka ƙi fita na ce zan yi ma Halima duka Ya Murja da su Rahila suka rike ni ashe tun fara faɗan Gimbiya ta kira Yallabai ana cikin haka sai ga su shi da Kawu ashe ma suna hanyar zuwa ne ta kira shi wai gani nan na kori Halima har ina marinta. Lokacin da suka shigo na gama harzuƙa yana tambayan ba'asi ni ban bi ta kan shi ba Suwaiba ce da su Munnira ke ma yar musu da zence. "Wallahi sai Halima ta bar minI gida in kuma ba ta fita ba ni zan fita na bar mata gidan." Na faɗa ina numfarfashi Kawu ne ke ba ni haƙuri har yana cewa" Gwara da kika mare ta. Kuma kina dai-dai da ki kore ta tun da, ba ta da kunya." Yallabai da suka yi tunanin zai goyi bayan su sai ya kware musu faɗa ya yi mata kaca kaca ya kuma ce ta fita ta bar gidan tun da ba alheri ya kawo ta ba. "Amma Uncle." Naja ta tare shi za ta kare ma Halima. "Rufe min baki kawun me? Me ya sa ba ki tsawarta mata ba? Ta yi shuru ta kasa mgana Gimbiya ma tas ya yi mata ya ce ta iya kiran shi ta faɗa masa na mari Halima amma a gabanta Haliman na yi mini rashin kunya ba ta iya mata mgana ba. "Ni miye nawa a ciki? Na saka baki sai a ce kishi ne. Ba ruwana kar ka sakani a ciki " Ta faɗa tana wani tura baki ni saboda haushi ciki na koma ban san yadda suka ƙare ba amma na so wallahi na yi mata dukan tsiya. Kuma ta ƙara dawo mini gida ta gani sai ta raina kanta. Sameena ke faɗa mini daman suna jirana ne sunq ta zagina wai na yi albuzurranci da kuɗin Tafida na ce bakomai na isa ne. A nan ta ke faɗa mini yadda suka yi mata wai ta shige mini saboda munafunci ita kuma ta ce tana tare da ni tuntuni saboda Gimbiya ba za ta ja baya da ni ba. Ranar raina ɓace na kwana da safe a hanyar mu ta zuwa asibiti ya ke sake ba ni haƙuri na ce bakomai. Mun je an duba ɗinkina suka ce ya kusa warkewa sannan an sake yi ma Yumna allura. Mun dawo gida na iske suna ta suyan ragunan da aka kawo su a yanke yau da safe. Daman na san magana za ta je ta dawo sai da Anty Bahijja ta kirani wai me Halima ta yi mini na mare ta? Na ce rashin kunya ta yi mini buɗe bakin ta sai ce mini ta yi ashe ba daɗi ni ba na yin rashin kunyar ne? Ni kuma na ce ni ban bi kowa gidan shi na yi masa rashin kunya ba itama gidana ta zo kuma ko yau ta dawo wallahi ta ƙara mini rashin kunya duka zan mata ba ma mari ba. Ai sai ta ce to kar na fasa mu ka kashe waya zukata na ƙuna. Ranar yini na yi zuciyata ba daɗi da wuri suka gama suya suka ɗibar mini nawa. Sai na su na can Gwammaja. Na saka su Ya Aina suka ɗiba na su har da y'an can gandun albasa. Nima na ɗibar ma su Hauwa a ka raba da yaji kafin yamma gida ya watse har su Laila suna koma Ɗorayi za su kwana washegari su ɗau hanya. Ina ta musu godiya na su Samira Rahila na ba mawa na ce ta aika ma Maijidda za ta kai ma su Samira. An yi taron suna an ta shi lafiya gyaran gidan washegari Saude da Marwa da Mubeena suka gyara mini tun da sai ranar da Yamma Kawu ya zo ya ɗauke ta suka koma rano. Tun da a ka yi suna a ka gama na mai da hankalina wajen renon Yumna. Ta tsiri rigiman dare ba ta barina na yi barci ɗan kumarin da na yi duk na fara sakewa. Ga shi Yallaɓai can gidan Gimbiya yake kwana nan ya gama cika mini baki shi bai amince ya koma can ba amma sai ga shi an gama taron suna gida ya watse amma bai dawo ba ni kuma ban yi masa magana ba daman na san can munafumcin ne irin na su na maza. Sai dai ya zo duba mu safe da yamma. Daga ni sai yara suma suna zuwa makaranta sai yamma asabar da lahadi kuma Tahfez Jidda har ta kusa sauka izifinta hamsin da biyar Baby kuma ta na cikin izifinta na ashirin. Ni kaɗai a gida ga fama da aiki ga fama da Yumna wacce ta cika rigima ga tsotso mintina kaɗan ta fara rigiman nono shi ya sa ta zama wata burkuta da ita. Muna da kwana goma sha biyar da haihuwa na ga Yallaɓai ya dawo kwana a gida na kamar zan yi masa magana sai dai ban yi ba. Kwana biyu tsakani kuma sai ya ɗauke kafa ya koma can ni sai na koma kawai na zura masa ido saboda na ga jeka ka dawon da ya ke yi, na kasa gane nufin sa. Sai a tsakanin Munnira ta sake leko ni a bakinta nake jin rigima ce suka yi shi da Gimbiyar ta sa har sai da Nene ta shiga ciki. A kan dai maganar kuɗin da ta ce ya ara mata na shipping ɗin kayanta ya ce ba shi da kuɗi amma ni ya ba ni kuɗi na yi suna har ina kiran mai hoto. Ita ko abin ya tsaya mata a rai ta ce mini ranar ta na gidan a ka yi har da su Maman farko a shigar maganar shi kuma ya rantse ba shi ya ba ni kuɗin wasu abubuwan ba da kuɗina na yi, amma ba ta yarda ba ita a dole ya yi rashin adalci. Wato dalilin dawowan shi gidana kenan sannan kuma ya koma bayan sun shirya. Ni dai na ce ma Munnira Allah ya kyauta can su ƙarata. Sai da ma muka yi maganar hotuna da Munnira sannan na tuna na tura ma mai hoto ragowan kuɗin sa ya turo mini hotuna. Washegari ko carbi na yi a status ɗina hotuna ne ba adadi na saka. Na farko nawa da Yallaɓai na saka da yara wanda Amina ta ɗauke mu ranar suna da safe. Na yi caption da cewa" Shekaru ashirin da albarka ƴaƴa uku. Alhamdulillah." Sai na saka wanda muke mu uku ni da shi da Yumna. Shi ke riƙe da ita ni kuma sai na shafa sajen sa. A ƙasan hoton na saka sticker ɗaga hannu na za a saman kai sannan na ce" Jama'a na ba ni Yallaɓai na ne na ga ya fara furfura" Ai ko na sha comments har Ya Hamza sai da ya yi mini mgana da cewa. Ke kina nufin ya dauwama a saurayin da kika aura ne? Sorry yarinya." Maijidda Bala ta yi dariya ta ce" Sadiya rayuwar auranki da Yallaɓai a bar sha'awa ce Allah ya bar ku tare." Na amsa mata da Amin ba ta san tarin ƙalubalen da na fuskanta ba ne. Ba su san ma an yi mini kishiya ba sai a sunan Yumna na faɗa musu suna ta mamaki ai ni yanzu na yi hankali na kama jama'a. Ni dai ban ɗora hoton Gimbiya ba amma ma tura mata wanda ta ke ciki haka ma su Anty Bahijjs. Yan gidanmu duk na tura musu sun ɗora mu. A gidan su Yallaɓai da ga Mimisco sai su Suwaiba su Munnira daman nawa ne, mazan kuma daman Musbahu da Adnan suka yi ta ɗora mu suna addu'a. Yallaɓai ma turamai na yi wajen guda hamsin sai turo mini emojin mamaki ya yi ni kuma na ce masa miye? Da alaman tambaya sai ce mini ya yi wai wa ya ba ni kuɗin waɗanan hotunan? Na ce tun da bai bai ba ina ruwan shi sai ya turamin na emojin baki da zip kuma ina tunanin bai buɗe hotunan ba, shi ya sa ko a status bai saka ba. Ban damu ba sanin halin Yallaɓai wani lokacin ba ya yin abin da a ke zaton shi da shi sai saɓanin haka Har Shemau Ma'un ta kirani ta mini barka saboda ma yafe ma Ma'u shi ya sa itama na ji na yafe mata. Ta ce mini in ta shigo garin za ta shigo ta ga Baby na ce sai ta zo so. Kara an yi mini shi sosai kuma na gode ni ce na tara turamen atamfa kaɗan ne babu a hamsin bayan kayan jarirai da sabulai da sauran su da masu tura mini kuɗi. Da na nuna ma Yallaɓai sai da ya jinjina kai kafin ya ce wai ni da kaya sai nan da shekaru biyar na ce bai isa ba. Ya saka albarka yana dariya a ciki na nemi shawaran shi na ce zan ba ma Gwaggo ɗaya Nene ɗaya sabulai kuma na ba su Maman farko da su Inna Mariya ya ce duk yadda na yi dai-dai ne tun da kayana ne. Ban damu ba sanin halin shi, shi ya sa na yi gaban kaina na ware musu da niyyar in na yi arba'in in na je gaishe su na kai musu. Mun shigo watan december ƙarshen shekara. Ina ta jego na ina kula da kaina gefe ɗaya bikin Alhaji Mustapha na ta ƙaratowa. Ma'u duk ta damu ni ce ma ƙarfin gwiwanta. Sai ma Allah ya sa a ka ɗaga bikin sai Jan ƙarshe. 27 ga watan december na yi arba'In a ranar da na yi arba'in Gwammaja na yini na kai ma su Nene saƙon su suna ta godiya tun da na je Yumna na tsakanin ɗakunan su Maman farko da Hajiya iya sai da zamu fita. Washegari kuma na yini a ɗorayi na kai ma Alhajinmu matarsa nan da nan ya ce shi kan ya saki jidda ya samu sabuwa Gwaggo na dariya ta ce da tsohuwar zuma dai a ke mgani. Ranar ma a wajen Alhajinmu ta yini kuma ikon Allah ba ta yi rigima ba, a jere na haɗa fitan na je gidajen su Ya Aina na je har can gandun albasa wajen su Inna Mariya. Na je gidan Munnira da Hauwa na yi musu yini da ban gajiya wajen kwana goma har Yallaɓai ya ce ba zan sake fita ba duk gari an gama gani na kullum sai na fita sannan na samu natsuwa a gida na fara gyara kaina. Surayya dee ce mai kayan ɗa'a ta gyara ni da haɗin kazar sababi na masu jego. Daman kuma bayan haihuwata na dage da cin kayan marmari da ganye da kuma kifi domin ƙarin ni'ima. Sannan Amina ma ta aiko mini da Gumba na sha da madara Yallaɓai na ta rara gefe na hana shi sai da na ji na yi tsab sannan na gayyace shi. Ranar na sha sambatu amma na gane ba ni da wayau, domin Yallaɓai kaca kaca ya yi wajen ɓarnan ruwa sai da ya famshe kwanakinsa har yana haɗa wanka ma. *Janafty**TKGB3J010* Washegari ma bai bar ni na huta ba, ko falo bai bar ni na fita ba sai wajen sha ɗaya na safe su Jidda ma shi dai ya fita suka gan shi suka gaishe shi. Daman ba sa jira na yanzu sun girma komai na buƙatunsu, su suke yi ma kan su. Sai alokacin na samu damar yi ma Yumna wanka sannan nima na shiga wankan kuma na bar mishi Yunma kwance a gefen shi shi kuma yana duba abu a cikin laptop ɗin shi. Ina fitowa ɗaure da Towel a ƙuguna na iske sa har ya gama abin da yake yi ya ture laptop ɗin gefe. Tambayarsa nake yi Yumna ta yi barci ne? Sai ya leƙata yana faɗin ta soma barci. "Ai gwara ta yi barcin nan kowa ya huta." Na faɗa ina mai zama saman stool ɗin madubin dake bedroom ɗin namu. Ban san tahowar shi ba sai kawai jin sa na yi yana shafa min wuya a lokacin ne na ci karo da fuskarsa ta jikin madubin dake gabana. "Me ya faru Yallaɓai? Na faɗa ina mai kallon shi ta madubin, bai amsa ba sai ma sunkuyowa da ya yi ya na mai sumbatar wuyana. Tun da na ga haka na sha jikin jikina da sauri na ture shi ina faɗin" Na yi wanka fa Yallaɓai." "Me ya sa kika yi wankan? Mamaki ya sa sai da na ɗago ina kallon shi. "E. Ai ban sallameki ba hajiya." Ya faɗa har yana wani ƙara tsumewa irin shi fa da gaske yake yi. "Yallaɓai tun daran jiya kake abu ɗaya. Yau da safe ma don Allah kai baka gajiya ne? Na faɗa ina cigaba da shafa ma jikina man shafawar da na lakuto a hannuna. "To ni ban gaji ba." "Ba ka gaji ba? "E" Ya amsa mini har yana wani haɗe rai sai na kalle shi kafin na ce" To ai sai dai ka yi haƙuri zuwa anjuma ka ga na riga na yi wanka." Amma Yallaɓai ya ce bai san wannan ba sai ma jikina da ya matso da ƙarfi ya ta da ni tsaye ya rumgumeni yana faɗin. "Ke ce kin ƙara sugar. Wato ta bakin ki haihuwan Yumna na dabam ne." Ya faɗa ya na shafa cikina, hannunsa na bige sai ya kai shi saman ƙirjina yana matsawa da ɗan ƙarfi har sai da na yi yar ƙara yadda na haɗe rai ne ya sa ya fara mini dariya yana faɗin" Ki gama shan kunun ki sai na ƙara horan ki kenan. Me ya sa kika yi wanka ni ban ba ki izini ba? Kasa magana na yi, kuma abin da ya faɗa sai da ya cika shi. Lalata mini wanka ya yi kuma bayan mun gama ina shirin sauka daga gadon ya riƙo ni wai bai ba ni izini tashi ba haka nan na koma na kwanta ya cigaba da jagwalgwala ni son ran shi sai da ya nishaɗi don kansa ya ce mu je mu yi wanka sai tura mishi baki na ke yi amma ko a jikinsa. Ban samu lafiya ba sai da ya fita sallar azahar ma ta suɓuce masa sai dai ya yi ta a gidaa bayan mun karya a lokacin sannan ya yi mini sallama ya fita. Yana fita nima bayan na yi sallar na koma barci. Daman Yumna tun da ta ji ruwan zafi take barci. Ba mu muka tashi ba sai gab da la'asar shima ɗin kukan Yumna ne ya tashe ni. Sai da na ba ta Nono sannan na tashi na ɗauro alwala na yi salla sanin Yumna ba za ta kwanta ita kaɗai a ɗaki ba ya sa na goyata sannan na shiga kitchen domin neman abin da zan dafa ma su Jidda kafin su dawo daga makaranta. Da yake Yallaɓai ya yo mana cefane cikin satin nan sai kawai na yi mana cous-cous mai kayan lambu. Da yake ba shi da wahala nan da nan na kamalla shi. Ko da suka dawo ina falon su ina cin nawa Yunma na hannuna tana ƙiriniyar su na yara. Suna dawowa Baby ta fara damuƙarta daman in dai tana gida ba ni da haufin yar reno tun tana kuka in ta ɗauke ta har ta saba in ma ta ganta ta dinga kallonta alamun tana nuna mata sani. Sai da na karɓe ta sannan Baby ta samu daman cin abinci. Bayan sun gama na goya mata ita, Jidda kuma ta je ɗaureye musu kayan makaranta. Ranar da wuri Yallaɓai ya dawo gidan ko kafin tara mun shige ciki ni da shi da Yumna Baby ta yi barci Jidda ce ke karatu tun da mun shiga sabuwar shekaran 2021 akawai jarabawowi a gabanta. Ni dai kwana biyun da Yallaɓai ya yi a gidana da wayyo Allah na ƙarishe shi duk cinyoyina ciwo suke yi da gaɓɓaina saboda bai sarara mini ba, in na yi ƙorafi sai ya ce wai ai ya yi ƙoƙari wajen kwana hamsin sai na ce ba yana da wata matar ba sai ya harare ni ya ce ita sunanta Saudatu ke kuma Sadiya kin ga kowacce na da nata tarim bambamcin da ya bambamta ta da ƴa'ruwata tun da na ji haka ban ƙara yi masa magana ba. Da ba ya gidana barci na yi ta sha ina hutawa ina zan iya. Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya. Shekaran 2021 ta zo ma da Yallaɓai da babban buɗi na alheri domin ya dace da samun wani babban kwangilan gina jami'ar kuɗi a nan garin Abuja. Yadda Yallaɓai ke murna ne ya sa na san cewa ba ƙaramin alheri zai samu ba abin farincikin ma sun bashi 70% na kuɗin aikin shi satin kaf yini ya yi cikin farinciki shi ya sa ba tare da sanya ba ya saka Khalipa a makarantar su Jidda. Amma shi Gimbiya ke kai shi da kanta su Jidda kuma Salisu ne. Samuwar kuɗin hannun shi ya sa ya tsayar da lokacin buɗe kamfanin shi ƙarshen watan Feb. Tun da ya ce yana tunanin kayan da ya yi oder su sauka a tsakiyar wata mai kamawa. A cikin haka ne aka fara shagalin bikin mijin Ma'u. Mu ne gaba gaba masu dannen ƙirji, na ba ma Ma'u gudummuwa sosai a wajen auren nan, a ka yi taro lafiya aka tashi lafiya ba tare da na bari an ga gazawarta ba. Ta ji daɗi ta kirani tana ta yi mini godiya har shi Alhajin ya yi ma Yallaɓai maaganar daidaitarwar mu ba ƙaramin canji yake gani a tattare da Ma'u. Ni daman haƙuri na ce ta yi gashi da ta yi haƙurin har an yi auren komai ya wuce. Har Baaba da ke adawa da ni yanzu ta ɗan sakar mini,nima sama sama tunda daman can ni da ita jininmu bai haɗu ba. Jidda ta sake sabunta rigister ɗin ta na Jamb. Da ƙyar da saka bakin Kawu Abba Yallaɓai ya bari ta cike ABU zaria a first chioce ɗin ta. Shi dai wai baya so ta yi nesa da gida ni kuma na ce ai duk in da take addu'armu na tare da ita kuma ai zaria gida ce. Hmm kawai ya ce shi fa daman ya amince ne domin an fi ƙarfin shi ba domin yana ra'ayin haka ba. Ita dai Jidda tun da ya amince sai murna ta ke yi sai bayan salla za su yi jamb ɗin da sun zana ta, za su fara rubuta jarabawar fita babban sakandiri. Shi ya sa ba ta zama yanzu ita ce jamb class da lesson har asabar da lahadi yanzu ba ta zama Jidda na ci gare ta kamar mahaifinta in suka saka kansu a abu agaba sai sun ga sun cin ma nasara. Ranar kawai Yallaɓai  ya ce mu shirya da ni da yara gabaɗaya har da Gimbiya mu je mu ga ma'aikata sannan mu ƙarisa mu ga filin da ya siya tuntuni wanda zai gina ma gida da zai haɗe mu gabaɗaya. Ranar lahadi ne kuma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne. Jidda ma ya hana ta zuwa lesson ɗin ta da ake yi musu a makaranta saboda fitan da za mu yi, mun cakaree gabaɗayan mu har Yumna na yi mata gayu, shi muka rika jira tun da yana can gidan ne sai ya kwaso su sai ya zo mu wuce ta gidana. Sai da suka ɓata mana lokaci sannan suka zo. Gimbiya an ci gayu abaya ta saka ta yane mayafin a saman kanta ta saka wani takalmi mai rufi har da uban gilashi su Khalipa ma sun ci gayu cikin riga da wando yan kanti. Ni daman doguwar rigar atamfa na saka ɗinkin kaftan na saka mayafi kalan kayan sai na saka takalmina baki mai saukakken tudu. Jidda ma haka ita dai Baby pakistan ne riga da wando a jikinta da breziya Hijab. Tana kuma riƙe da Yumna ni ce ke ɗauke da jaka da na sako mata ruwa da ƙyallen goge tumbulunta tun da tumbuli take yi shi ya sa take yi kiba kamar ana hurata. Mun gaisa sama sama da ta so ta shige gidan gaba ne sai kuma ta fasa ta shiga baya da yara. Ni ko ba ta san mota ba ta dame ni ba, mijin ma gabaɗaya na raba shi ballantana wata motar banza. Muna tafe ni da shi muna hira shi ne ma yake sako ta a cikin maganarmu shima ɗin a daƙune take amsa mishi ban san me aka yi mata ba, ko Yumna ba ta ɗauka ba nima ban tura mata ba. Na fahimci bata kaunar fita ta haɗamu ni da mijina ta aure mini shi, ni ban yi kishi ba sai ita? Mamaki take ba ni in dai fita ta haɗamu gabaɗaya ta riƙa cin mgani kenan. Ni ba na ta ita in muka gaisa ban ƙara jan ta da magana sai dai in har ita ce ta sake yi minI magana. Ina da aji ba zan zauna ina bin kishiya ba. Har muka isa hira muke yi da Yallaɓai yana faɗa mini yanzu ƙasa za su fara amfani da shi sama sai zuwa gaba. Wancan kuma wajen tun da ya siye shi tuntuni yanzu yana matsayin mallakin shi ne. Zai ba da hayan saman ƙasan kuma yana tunanin abin da zai saka a wajen. "Yallaɓai to ka buɗe shagon sai da kayan gine gine mana " Yana tuki ne amma sai da ya juyo yana kallona. "E mana. Na ga kai ma in ka buɗe amfaninka ne tun da in kwangila ta samu suma kayan ginin siyansu kake yi." Sai ya jinjina kai alamun gamsuwa kafin ya ɗan waiwaya baya yana faɗin" Ke fa Daughter ba ki ce komai ba? "Me zan ce? "Ke ma ki ba ni shawara. Kin ga Sadiya ta. Kusan komai da zan yi in na nemi shawaranta tana kawo mini shawarwari masu kyau kuma in na yi amfani da su ina ganin alfanu sosai." "To ba gashi ta baka ba" Ta faɗa har a muryanta haushin ta bai boyu ba. "Duk da haka kema ina son jin na ki shawaran" Shuru ta yi kamar ba za ta yi magana ba sai da ya sake yi mata magana sannan ta ce" Ni a ganina me zai hana ka buɗe shagon provision tun da wajen a bakin titi ne." Jinjina kai ya yi kafin ya ce" Good. Ke ma kin kawo point amma na Sadiya ya fi muhummanci. Bari mu fara da na ta, daga baya in komai ya tafi daidai sai a buɗe shagon provision ɗin" "Ka san shawaran ta za ka ɗauka me ya sa ka na ce sai na yi magana? Ta faɗa a zafafe. "Saboda kema kina da haƙƙi a kan haka." "Uhm" Kawai ta ce ba ta ƙara magana ba, ni ko ina zaune kamar zan yi magana sai na kwaɓi kaina. Yara ma ba sa jin abin da muke tattaunawa suna ta wasannin su. Gwara ma Jidda amma ita hankalinta na kan Tab ɗin da ke hannunta. Na yi na yi  da Yallaɓai ya siya mata waya ya ce sai ta shiga Jami'a. Tab ɗin daman shi saboda karatu ya siya mata. Ko rigister ɗin jam da sim ɗin Yallaɓai ta yi amfani wani lokacin yana da tsauri wani lokacin kuma yana da sauƙin kai. Har muka isa ma'aikata ba ta ƙara magana ba sai ma amsa wayarta da ta riƙa yi lokaci bayan lokaci. Ƙwarai waje ya yi kyau fiye da labari da gani a hoto. Kafin shiga ma'aikatan akwai babban get in da masu gadi ke tsaro har mutum biyu saboda sace sacen kayan aiki. Sannan daga gefe an makala wani allo da aka yi ma rubutu kamar na zaiba mai ɗauke da sunan ma'aikatan HM TAFIDA AND SON'S LIMITED" Ma'aikatan na nan a kan titiN zaria road gaba kaɗan da in da office ɗin su yake na yanzu. Kuma wajen babba ne akwai fili a haraba da zai ci kimanin motoci sama da goma. Sannan an yi shuke-shuke daman Yallaɓai na son shuke-shuke. Ko'ina sai da Yallaɓai ya zagaya damu an gama komai fenti ne ma ake ƙarisawa a wani wajen. Office ɗin Yallaɓai babban yana benen sama ne amma tun da ba yanzu za su fara amfani da can ɗin ba sai ya samu wani a ƙasa da aka saka masa suna da zane kamar na zaiba wato Managin Director Md. Har office ɗin Musbahu na gani  shima makeke na ce tabbas ya cancanta har sama mun haura shi dai ba a ƙarisa ba amma ma'aikata suna kan aiki. Akwai ɗakin hutawa da sauran su ba abin da dai ma'aikatan ba ta mallaka ba sai godiya. Ina kallon Yallaɓai ina tuna a farkon auren mu in ya ce mini shi ba ya son aiki a ƙarƙashin wani ya fi son aiki na ƙashin kanshi. In ya ce mini ya na son gina kamfanin shi na zane zane da abin da ya shafi kwangilan gine-gine a shaci faɗi nake ɗaukan duka mganganunsa. Ban taɓa tunanin bayan shekaru ashirin Yallaɓai zai cimma burin sa ba. Sai ga shi ya cimma burin sa da nasara tabbas ya yi aiki taƙuri sannan ya jajirce wahala da rashin kuɗi bai sa ya nuna gazawarsa ba. A gaban yara a gaban Gimbiya na rumgume shi sannan na bashi sumbata a gefen kumatun shi, ina mai faɗin. "Congratulation Yallaɓaina. Im so proud of you." Na faɗa ina yi masa wani irin ƙayattacen mirmishi. Sai ya sake riƙo ni gefen kafaɗansa na dama yana mai kallona ya ce. " Amin. Nima ina alfari dake Sadiya ta. Duk matakin da wannan kamfanin zai kai ke ce a gaba. Kin ba ni dukkan gudummuwar da macen ƙwarai ke ba ma mijinta. Thank you so much haƙika da ban haɗu da ke a shekaru ashirin a baya ba da na tafka babban asara rasa mace kamar ki." Sai na ji wani farin ciki ya lulluɓe ni har ina ƙara narkewa a jikin shi, Jidda na gefe sai ji muka yi ƙyars ta yi mana hoto. Baby da su Khalipa ba su san ma me ake yi ba suna can suna wasa. "Jidda Allah ya sa hoton ya yi kyau." Na faɗa ina dariya. Yallaɓai ko sai faɗin yake yi  ta ƙara yi mana wani. "Kun yi kyau sosai Umma da Abba." "Mun gode yar albarka ta wajen Abban ta" Yallaɓai ya faɗa har yana ɗaga mata babban yatsan shi alamun jinjina. Jidda na ta ɗaukan mu hoto kwata kwata na sha'afa da Gimbiya sai da ta yi tsaki na ji sannan na juya muka haɗa ido, wallahi na gan ta harara ta, ta yi sannan ta yi motsi da bakinta ta ɓata rai, duk da na ga abin da ta yi mini ban riƙe shi a wani abu ba sai na juya ina kallon Yallaɓai kafin na ce "Mun manta da Amarya. Kira ta a yi mana hoton tare mana." Saboda ba lallai in ni na yi mata magana ta saurare ni ba. Wataƙila za ta iya ganin hakan a matsayin cin fuska. "Haka ne. Daughter taho mu yo hoto in an gama sai mu yi da yaran gabaɗaya." Amma sai ta yi kamar ba ta ji ba, sai ma ta juya yana kiran ta ta yi banza dashi ta fita daga office ɗin na shi, da muke ciki Jidda na ɗaukan mu hoto. "Ka je ka yo lallashi Yallaɓai." Na faɗa ina kallon sa. Ni kaina yaƙe nake yi amma a ƙasan zuciyata ina jin wani abu kamar kishi na motsa mini. "Me a ka yi mata? Ƙyaleta." Ya faɗa ne kawai amma sai na ga hankalinshi ya tafi a kallon ƙofa ko za ta dawo sai na ƙara roƙon sa da ya je ya ba ta hakuri ta zo a yi musu hoton. "Ƙyale ta kawai." Jin abin da ya sake faɗa ya sa sai na kama kaina ban ƙara yi masa magana ba. Ina lura dashi saboda fushin da ta yi ya sa sama sama muka yi hotuna da sauran yaran sai ya ce a bar shi haka ya na so mu je filin can mu gani ya mai da mu gida yana da wajen zuwa. Ko da muka fito tana cikin mota kila da ace da motarta ta zo sai dai su haɗu a gida. Ya yi sallama da masu gadin sannan muka tafi a cikin motan ma Khalipa sai da ya sha mari wai ya ta ka mata kafa. "Kawai saboda ya taka ki sai ki yi masa irin wannan marin haka? Yallabai ya faɗa cikin mamaki, ni kaina ban yi maagana ba ne amma marin da ta yi masa ya yi tsauri a bi sa dai laifin da ya yi. Yaron sai ya fashe da kuka Baby ce ke lallashin sa. "Sorry. Khalipa sorry." Amma sai ƙara ɓare ma mutane baki yake yi, ni dai na sake tallafan Yumna dake hannuna da ta yi barci faɗan da ba ruwanka daɗin kallo ne dashi. "Kar ki sake yi masa irin wannan marin." "Ya yi laifi kar a hukunta shi? Ta faɗa a zafafe ni a tunanina ko dai daman suna faɗa ne kafin su fito? Domin na ga a zafafe take kamar za ta kai duka. "Ni dai na faɗa miki kar ki sake. Ba a hana ki yi masa hukunci ba amma ba mari irin haka ba." "Na ji." Ta ce a ƙasa ƙasa, shima sai na ga ya yi wani ƙyaci na ɓacin rai a raina na ce can ta matse muku. Tafe tafe sai ga mu a anguwar Alu veneu in da Yallaɓai ya siya wawaken fili. Mun sauka daga mota dukkan mu muka shiga filin babba ne Yallaɓai ke nuna mana yadda fasalin ginin zai kama. Ya tabbatar mana da kan shi zai yi zanen gidan shi, ya yi masa irin fasalin da ya ke so a cewarsa yanzu ginin ne a gaban shi bayan taron lunching na buɗe kamfanin shi za a fara yin katanga a saka get sai kuma a fara gini. "Flat huɗu zan yi a cikin filin nan in sha Allahu." "Kuma duk a gida ɗaya nufina a haɗe? Na faɗa ina kallon filin, babba ne amma flat huɗu na su waye? "E mana. Naki ɗaya na Daughter ɗaya. Ɗaya nawa ɗayan kuma ko saboda baƙi." Ina shirin sake magana Gimbiya ta yi zaraf ta ce. " Me ye amfanin yin shashen baƙi tun da ga shashen ka? Infact ma mu kan mu na san akwai spare room a bangarorin mu." Sai na zama ƴar kallo, domin kai tsaye Yallaɓai ya ce" Duk da haka flat huɗu zan yi." "Babu amfanin yin haka." Ta bashi amsa sai ya share ta bai yi magana ba. Ni kuma da ƙarin bayani sai na ce" Yana da amfani ko saboda su Khalipa in sun tasa zai musu amfani. "To kin ji ma." Ya faɗa cike da ƙarfin gwiwa. Amma ita duk ba ta gamsu ba na san fargabanta kar Yallaɓai ya ce zai ƙara aure amma saboda na ƙara samun tabbacin sai na tsaƙalo maganar. "Yallaɓai ko dai shashen ɗin Amarya ne." Yadda ta yi saurin kallona da razana a yanayin ta shi bai yi haka ba sai ma dariya da ya yi kafin ya ce" Wannan kuma lamari ne na Ubangiji. In ya kaddaro mini zan gode masa." "Yallaɓai dai zai yi ginin mata huɗu ne. Wata ƙila shashen naka ma in ka ji ra'ayin aure zai tashi a naka ya koma nata." Ni na faɗa amma yana ta dariyan nishaɗi. "Ke ko? Ya faɗa ya na nuna ni da hannu. Nima dariyan nake yi ina faɗin" To ai gaskiya ne." Gimbiya na tsaye amma ta kasa magana sai dai ina kallonta ta gefen ido ta ƙara kumbura. Har tana wani kifta idanuwana kamar na yi dariya sai na kanne. Yaran suna can gefe Khalipa da Baby suna ta wasan ƙasa Jidda na tsawarta musu  har da Anwar da shima yana tafiyan shi ko'ina. Ban ɗauka za ta yi magana ba tun da har muka baro wajen muka shiga mota. Muna hanya zai fara sauke mu gida Gimbiya ta kira sunana daga bayan mota. "Madam" Da man haka take kira na ko ta ce Maman jidda. "Na'am" Na amsa mata ina ɗan waiwayawa  bayan in da take zaune ita da yara. "Kina ta wani dariya yana faɗa miki in aure na cikin kaddaransa zai ƙara." Sai na saki dariyan nishaɗi kafin na ce" To kuka kike so na yi? "Amma bai kamata ki yi masa dariya ba." "Ikon Allah." Ni da shi muka haɗa baki wajen faɗa. "Ka gama aure Daddy. Ni da Madam mun ishe ka in sha Allahu." "Gaskiya ne." Na biye mata ina ƴar dariya. "Ba ku isa ba. Ku ji minI ƙarfin hali ni na ce kun ishe ni ne? "Ko ba ka ce ba mu mun ce ko Madam? Ta faɗa tana sako ni a ciki. "Tabbas. Yallaɓai mun rufe ƙofa. Gimbiya ce a madadin biyu nima a madadin biyu shike nan mun cike maka ƙofa." Na ƙarishe faɗa ina dariya. "Shi kenan ko." Ta faɗa cikin jadadadawa. "To ba ku isa ba." Ya faɗa yana wani haɗe rai irin da gaske nake yi ɗin. "Mun isa har ma mun yi yawa." "Haka kuka ce? "E haka muka ce." Ta mayar masa da martanin cikin nuna da gaske take yi. "Ok we shall see." "See me?ba abin da za mu gani sai alheri wallahi ko ɗauko auro ka yi ni da Madam sai mun ruguza shi. Mu ai ka gama auro wata mace kuma a duniya tun da ka aure mu." A yadda take magana kaɗai ya isa a fahimci da gaske take yi. Har suka sauke mu a gida ina jinjina zafin kishin Gimbiya. Wato wata rana in har Yallaɓai ya ɗauko auro akwai yaƙin duniya na uku ita da Yallaɓai kanbu! Da abin na kwana a zuciyata gari na wayewa na kira Munnira na tsegunta mata yadda muka kwashe da Gimbiya jiya. Matar nan da ta laulayo ashar sai da na ce. " Ke Munnira ki ji tsoron Allah wannan ashar ɗin fa?" Na faɗa ina dariya saboda na ga ta  ma fini kambama lamarin. "To ba dole na  danno ashar ba. Ba a aure ita aka auro ta! Ba a yin kishiya ke kika bari aka yo miki da ita? Ba na son iskancin banza." Ina ƙyatata dariya na ce" Ita ai za ta zo a matsayin kishiyar wata amma ita ba za ta bari a kawo mata wata a matsayin kishiya ba." Munnira ta ce" Taɗijam! Tana da aiki ni tun da har aka yi miki da ita fata na yanzu itama ayo mata ta ji in da daɗi." Ina dariya na ce" To waya sanin ko zai ƙara." "To ke ba ki ga alamu ba? "Ban gani ba amma in dai ana maganar za ki gan shi cikin nishaɗi ba ya ƙoran maganar gaskiya." "An gama magana. Tafida in ya ga wata yar shila zai yi tunanin ƙara aure." "Zai iya yuyuwa tun da ya iya yi mini kishiya itama ba abin mamaki ba ne don ya yo mata." "Namijin kenen. Uhm Maza mutanen mu." Muna ta dariya ni da ita, har ina tsokanarta in Nasir ya gano wata yar jan fata haka. "Ta zo ai ba a kaina za ta zauna ba." Na yi mamaki jin haka Munnira ta yi sanyi. "Ke kuma yau? Kin saduda ne yanzu ta shigo." "To na ga ko ka yi haukan ma in suka yi niyya sai sun yi." Na kwashe da dariya ina faɗin" In dai ji maza kawai matar nan bana son sadudan ƙarya" Itama dariyan take yi mun daɗe muna mgana kafin mu yi sallama. Da Yallaɓai ya dawo gidana sai da na yi masa taɗin da cewa" Kai Gimbiyar taka ba ta son kishiya. Sai ka shirya in dai za ka ƙara aure za ta yi maka daru." "Za ma ta yi ta gama ne. Tun da har na iya yi miki kishiya ita nata mai sauƙi ne." Amsar da ya ba ni kenan, sai na kalle shi kawai ina dariya. Ban sani ba amma haka kurun na ke ji a jikina watan wata rana Yallaɓai zai iya ƙara aure ko bai cike gurbin ba. Wata ƙila kuma ya yi gadon marigayi mahaifin su. Tun da jajirtattace ne, sannan yanzu ya samu buɗin da riƙe mata sama da biyu ba zai zama wahala a gare shi ba. Maganar lunching ɗin kamfanin Yallaɓai ya ta so. Ya ce ya na so a yi komai a gama kafin azumi. Shi ya sa ya ke ta shirin sa muma muna taya shi. Sanin rana ce babba a gare shi, ya yi katin gayyata kuma ya gayyaci mutane sosai abokan karatun shi, abokan harkokin shi, ƴan uwan shi na nesa da na kusa. Ya gayyaci yan siyasa amma ba sosai ba, Kawu Abba da Tariq sun yi gayya suma daga bangaren su. Tun da shi Tariq a matsayin shi na lauyan kamfani shima ya gayyato ƴan uwan shi lauyoyi. Kaf ƴan uwan shi maza za su hallarta hatta Ya Usman da ke nesa. A hankali yake ta shirin sa mun yi shawara da shi, akan za a yi abincin na sadaka sannan zai ba da a yi masa saukan Qur'ani acan ma'aikatan kafin a fara amfani da shi ya ce mini To. Abincin da lunching kuma Mimisco ta ce za ta ɗauki nauyin komai da komai har da ruwan da za a sha da lemu a wajen.  Kayan da ya yi oder suka iso kamar su kujerun ofishoshi da I.C, cafet da sauran su a ƙarshen watan Febuary kayan suka sauka daman kuma ranar lunching goma ga watan March ne. Ranar lahadi za a fara taron goma na safe zuwa ƙarfe ɗaya na rana. Ya ɗauki Nene da su Maman Farko ya kai su wajen sun gani sun yi murna da addu'o'i. Alhajinmu da Gwaggo da na je na faɗa musu sun kira shi sun yi masa fatan alheri yana ta jin daɗi. Shi dai ya ce walimarsa ta maza ne amma in za mu yi gayya a gida ƴan uwa a zo a yi murna bai hana ba, shi ya sa duk na faɗa ma yan gidanmu. Sai su Munnira sauran tawagan gidan su Yallaɓai yan bangaren Gimbiya ne. Ni Jamila da Suwaiba ne daman na sa ka ran in ma za su fito ranar kenan. Da bakin shi ya ke faɗa mini Gimbiya kayan snaks ta yi mishi har da ƙananun kofunan mug da sunan kamfani, ni kuma lokacin ba ni da kuɗi. Duk na ci ubansu da sunan Yumna hijaban ma tun da na haihu sau ɗaya aka kawo mini. Ba domin Gimbiya ta yi ba a'a sai domin nima matarsa ce kuma ya kamata nima na nuna nawa bajintar. Da na yi tunanin memo amma sai Adnan ya faɗa mini su Anty Bahijja sun yi masa Memo, sai na ce tun da har an yi memo da mug ni bari na yi jaka wacce za a saka gift ɗin a ciki ba ni da kuɗi amma haka na yi ƙarma ƙarma sai da Ya Auwal ya cika mini wajen 30k sannan na ba da a ka yi masa guda hamsin ta hannun Adnan. Jakar ta kwali ce an saka sunan kamfanin ne. Congratulaton Md Yusuf Muhammad Inuwa on your opening ceremoney of your company. Hm Tafida and son's Limited. Cut ceey. "Miss Sadiya Yusuf Muhammad, Hauwa'u Yusuf Muhammad, Maimunatu Yusuf Muhammad and Rukyyatu Yusuf Muhammad. Bai sani ba, kuma na ce kar Adnan ya faɗa masa sai ranar kawai sai dai ya gani. Bangaren abincin sadaka ni ya bar ma ragama buhun shinkafa za a dafa da wake, sai na raba biyu rabi na ba ma Maman Saude aikin rabin kuma sai na ba ma Maman Naana mai yi mana kitso. Na ce in sun yi su raba shi ga almajirai sadaka ce. Bangaren kayan da zai saka kuma ranar ya zo ya na cw mini da ya saka suit ko manyan kaya wanne ya fi? Ni kuma na ce ya saka manyan kaya zai fi ƙwarjini. Sai ya ce shima haka ya ce amma Gimbiya ta ce suit zai saka har ta siya masa ma ni kuma jin haka ya sa na ce duk wanda ya yi masa ya saka zai yi kyau tun da da man shi ɗin mai kyau ne. Sai ya ce kawai shi dai zai saka manyan kaya. Ya nuna min wata dakakkiyar gezner fara da ya siya ya ba da ɗinki har da babban riga. Sannan ya siya cover shoe baki mai kyau da hula dara sai agogon fata mai tsada. Ranar dai Yallaɓai sai wanda ya gan shi kawai amma kyau ne zai yi har sai ya gaji da kyau. Tuni status ya ɗauka yan gidan su kaf sun ɗora katin gayyatan suna ta ya shi murna. Nima na dora har Samira ta yi min magana ko mata na zuwa na ce mata e amma mata gida ne, nan take ta ce mini za ta yi ma Hauwa magana wata ƙila su shigo fatan alheri. Su Ya Hamza  duk na tura musu sai aka ci sa'a a satin zai shigo Kano ya ba ni tabbacin zai je Ya Auwal dai a waya ya kira Yallaɓai ya yi masa murna. Amma Ya Muntari da Ya Abubakar da Datti duk sun ce za su je. Sai jin daɗi nake yi domin ni kaɗai na san dararen da Yallaɓai ya ɓata bai samu barci ba saboda zuwan wannan ranar mai ɗimɓin tarihi. ****. . RANAR TARO. 10 March. 2021. Lahadi. Ko da ba a gidana Yallaɓai ya kwana ba amma ya biyo ta gidana ya yi mini sallama ni da yara muka rumgume shi domin ta ya shi murna a wannan rana mai matukar muhimmamci a gare shi. Kun ga Yallaɓai? Cancaɗi ni kaina sai da na saki baki da hanci ina kallon shi. Domin ya dawo min wani ɗan saurayi ɗan shekara talatin. Da man ya na son fararen kaya ko don ya san suna yi masa kyau ne oho? Har da wani farin gilashi su Yallaɓai manya an fito sharr. Tare da Kawu Abba shima ya sha Babban riga. Ya kuma kyauta domin da Marwa ya taho mini duk da tana ta fama da laulayin ciki. Tariq na hanya bai riga ya iso ba. Hadda su Khalipa su kan yan kanti suka saka da su za a je ni kam ni da ƴa'ƴana ko ba mu je ba mun cakare a gida har ko da Yumna na mata gayu kuma itama sai da Yallaɓai ya ɗauke ta na ce murna ta ke taya shi tun da tana jin muryansa ta fara harba ƙafafu. Sun fita gidana tara da wani abu ba a fara taron ba sai sha ɗaya na safe. Har sarkin Rano ya zo da Tafidan Rano kanin mahaifin Gimbiya. Ta waya muke ganin komai live Adnan ke yi da wayarsa ya na turawa a group ɗin gidan su. Irin su Musbahu suna ta hotuna suna ɗorawa. Sun gayyaci yan jaridu da masu Video da hotuna. Muna gida amma kamar mu yi tsuntsuwa mu gan mu a wajen Baby sai tsallen murna take yi, su Ma'u da Rahila ne suka zo mini sai su Munnir. Hauwa ta ma dafa shinkafar jalop mai nama muka ci muka sha da lemu. Suma duka mazajensu na can wajen taron Kafin a fara Yallaɓai ya turo min saƙo. Saƙon da na maimaita shi sama da sau goma saboda daɗin kalaman na shi.  saƙon da ya samu wajem zama na musamman a ƙasan zuciyata. "Sadiya ta ki sani kome yau na zama Nene ce sila tun da ita ce ta haife ni. Amma ina so ki sani bayan ita ke ce mace ta farko da kika bani ƙwarin gwiwa. Na gode Sadiya ta. Adnan ya nuna min abin da kika yi mini. Ina rubuta miki wannan saƙon cike da godiya a bakina. Zuciyata cike da ƙaunarki. Hawayen farincikin kasancewarki matata sun tarun mini a ƙwarmin idanuwana." Nima sai na ji taruwan ƙwalla kafin na fita daga shauƙin da na shiga wani saƙon na shi ya sake shigo mini. "A yau a wannan rana mai muhimmaci nake so na faɗa miki ni ke ce abu mafi muhimmanci da na mallaka a rayuwata. Na gode Abar ƙaunata. Yusuf na ƙaunarki. Ki tuna haka Halimatussadiya." Sai kawai na samu kaina da ƙwalla, har sai da na saka hannu na share Allah ya sa ni kaɗai ne a ciki daga ni sai Yumna. Ita na ja na rungume ni ina jin wani irin shauƙi na motsawa daga ƙasan zuciyata. An fara taro cikin nasara bayan an nuno hoton Yallaɓai ya yanka igiyar nan da almaka shi, tare da addu'oi.  Sannan a ka shiga ciki da a ka ƙawata shi da kujeru da kanofi. Manyan baki sun yi jawabai sosai na godiya da jinjina da burgewa. Kawu ya ba da labarin Yallaɓai. Tariq ya ƙara da irin gwagwarmayan da ya sha kafin ya kawo yau. Sannan ya yi amfani da haka wajen zaburar da matasa domin su nemi na kansu. Ya faɗi har tarin alherin da Yallaɓai ya cimma  a shekaru ashirin da wani abu . Mafi rinjayen ciki samar da matasa aiki daga karƙashinsa sannan da gina wannan ma'aikatan bayan ya fara da kama hayan ƙaramin shago sai gashi yau ya mallaki ƙaton waje da sunan mallakin shi. Ya Usman ya yi jawabi a matsayin babba Yaya. "Yusuf ƙanina ne amma zan iya cewa ya fini jajircewa.  Ni gidan soja kawai na sani amma shi ya san gwagwamarya. Ya san zane ya san gine gine, ya san ya ɗau kankare akan sa. Sanadin shi matasa da dama sun samu aikin yi. Ciki har da ƙanin mu dake aiki a ƙarkashin sa. Abin da zan ce shi ne Yusuf is a good Exmples ga matansa mu. Ku tashi ku nema. Ku jajirce in kuka gwada kuka faɗi ku sake miƙewa ku cigaba da tafiya. Watan wata rana za mu iya samun kamar Yusuf ko ma waɗanda suka zarta shi da samun ɗaukaka sanadin jajircewarsa. Congratulations My Bro. Allah Ubangiji ya sa nan da shekaru goma duka arewa kowacce state kana da reshe Amin." Sai tafi raf! Mu kan mu mun zagaye waya muna kallo kamar mu yi hawaye. Mimisco ce ta ɗora jawabin a status har mijinta ma ya je shima ya yi jawabi, daga ƙarshe ne Yallaɓai ya yi jawabinsa. Da farko ya yi sallama sannan ya yi salati ga Annabi(SAW) sannan ya gangaro wajen gode ma iyayen shi. Tare da addu'an Allah ya jiƙan Marigayi Muhammad Inuwa. Mace ta farko bayan Nene ni ce wacce Yallaɓai ya gode mawa. Wallahi ina kallo ina hawaye ban sani ba su Munnira na ta minI sowa amma ni ina hawayen farinciki. "Zan miƙa sakon godiyata zuwa ga Matata Uwargidana. Sadiya Sulaiman Yashe(Mrs Yusuf Muhamma Inuwa) bayan iyayena da ƴan uwana. Ita ce macen da ta yi gwagwamaryan rayuwa da ni cikin samu da rashi. Sadiya ta kasance wata mace mai hikima da baiwa. Wannan sunan kamfanin idea ɗin ta ne, duk da burina ne amma da shawaranta yau na kai ga gaci. Sunan da ke jikin wannan kamfanin ma nata ne. Ita ta samar da shi. HM TAFIDA ba mallakina ba ne ni kaɗai. Namu ne ni da ita da ƴaƴanmu. Ni zan kasance Md a idanuwanku amma asalin mai juya kujeran tana gida. Miss Sadiya Yusuf Muhammad ina miki jinjina ina kuma ta ya ki murna. Da girmamawa ina mai sanar dake MUN YI NASARA" Ya faɗa sannan ya ɗaga hannu sai ihu da tafi. Daga nan Vedio ya yanke tuni na ɗauka na saka a status ɗina na ma kasa magana sai emojin kuka na saka. Munnira faɗi take yi" Wallahi gaskiya ya fada. Da bai ambace ki ba da ya yi butulci." Ni dai ina ta sharan ƙwallar farinciki. Sauran jawabin na shi godiya ne ga amininsa guda biyu Tariq da kawu sai ƴan uwan shi gabaɗaya sannan ya jinjina ma Musabahu domin da jajircewan shi suka samu nasara. Daga ƙarshe ya yi godiya ga matasan da ke aiki a ƙarkashinsa domin ya ce ba domin su ba, da bai yi nasara a yau ba a ƙarshen ƙarshen dai ya kira sunanayen su Jidda da su Khalipa da Gimbiya ya gode musu a cewarsa suma suna cikin labarin nasarar shi a wannan ranar. Kafin taron ya tashi sai da matasan da yake aiki da su bangaren gine gine suka bashi award na takarda da gilashi sannan aka tashi taron za a ci abinci a raba gift shike nan taro ya tashi. Ni Yallaɓai ya gama mini komai. Na maimaita kallon jawabin sa ban san iyaka ba. Ya Hamza sai da ya kira ni ina ɗauka ya ce" To Miss Sadiya yau ta sha godiya wajen Mr. Yusuf. Ya dai ce ke ce Md shi acting Md ne." Sai kawai na hau dariya shima ya na taya ni. Nan ya fara mini nasiha ya na fadin" Kin yi abu mai kyau ko Alhajinmu in ya ji zai ya ba miki kin tsaya ma mijinki. Da daɗi ba daɗi yau kun yi nasara. Congratulatons" Saƙonni sai da suka yi mini yawa nima murna ake taya ni. Tabbas ni ma na samu nasara. Datti daga wajen taro gidana ya taho ya na ta sake ba ni labari. Shima ya taho da jakarsa na gift faɗi yake yi" Ya Sadiya Yallaɓai ya gama tashin kaina da jawabin sa. Danƙari." Kowa sai ya ce abin ya burgeshi ba kamar wasu mazan butulu masu manta alheri ba. Ni kam Yallaɓai bai manta da ni ba ranar ba a  gidana yake ba amma da daddare bayan sun sallami baki sai da ya zo gidana lokacin duk an watse daga ni sai yara. Marwa ma tun dazu Kawu ya zo ya ɗauketa. Baby ta yi barci Jidda ce ta ce sai ta jira Abban ta. Ai ko muna jin buɗe get ni da ita muka fita. Ni saboda zumuɗi da sauri a falo na baro Yunma. Sai ga ni, ni da Jidda muna rige rigen faɗa ma Yallaɓai. Ture Jidda ya yi yana faɗin" Jidda ya za ki ture mini mata kuma" Tana dariyan farinciki ta ce" Congratulations Abba. You make us proud Today." Sai ya sake ni ya rugumeta sannan ya ɗago ya dafa kafaɗunta yana faɗin. "Thank you Fav Daughter." Ni ko sai da na sumbaci gefe kumatunsa sannan na ce" Da ikon Allah ka fara hawa matakin nasara kenan." "Amin My Sady." Ya faɗa ya na mini mirmishi, ya shiga gidan amma ruwa kawai ya sha ya tafi bayan na ce gobe ni zan ba shi na wa gift ɗin. "Mai daɗi ko Sadiya ta? "Sosai ma. Ya fi mazan ƙwaila." "Ina godiya Hajiya ta." Muka raka shi har haraba muna ɗaga masa hannu. Na cika alƙwari domin washe gari da ya dawo gidana ban nuna masa gajiyawa ta ba sosai na saki jiki muka yi ma ruwa tas. Ƙarshen shi ne kawai ba mu gani ba. Tabbas kwans biyun da ya yi a gidana na saka su a cikin tarihin rayuwar auran mu. Ni ban sani ba ashe kalaman da Yallaɓai ya yi a kaina Gimbiya kishi ya kusa kashe ta a cewarta ita bai ambaceta ba sai daga ƙarshe. Nima Sameena ta kira ni tana mini tsegumi ta ce a group ɗin su na gida Gimbiyar ta yi maganar da aka turo jawabin ta ce ai ita saboda haushi ba ta ma gama saurara ba. Na yi dariya na ce to me ta ke tsammani? Ya ya yabe ta sama da ni? To ta jira tukunna da sauran lokaci. Nima na samu gift ɗin tun da ya yi saura kaf yan gidanmu sai da na ba su, na ba ma Hauwa da Munnira da Mubeena har Ya Auwal na ba ma Datti na shi ya kai mishi. Amina kuma ta kira ni a waya ta ce sai na ijiye mata mug ɗin da Memo na ce an gama. Na ɗaga akwatina na saka mata. Sauran kuma na ba ma su Jidda nima na ijiye ko domin tarihi. Hankula sun kwanta. Tun da an yi taro lafiya an gama lafiya. Ni kan sai da na hi sati ina saka jawabin Yallaɓai a status ɗina, da hotuna kar ku ga laifina yaɓo na aka yi, dole na yi ta sakawa ina jin dadi. Na kuma san na tura ma Gimbiya haushi. Ya Auwal har sai da ya gaji ya ce sun gaji da gani har sun haddace. Na ce su cigaba da gani suna haddacewa sai an yi wata zan dai na sakawa. Kuma haka aka yi ko bai kai wata ba an kusa. Tuni aiki ya kamkama a sabon kamfani sai hamdala kuma kamar an buɗe a sa'a kwangololi suna ta zuwa saman tuberin Yallaɓai. Abin sai godiya kawai. Fara aikin babban kamfanin Yallaɓai da wattani biyu muka fara azumin watan ramadana. Kafin azumin Gimbiya ta yaye Anwar a ka kai shi can Rano. Yallaɓai na ji ya na faɗa a nan na ji tun da ba ta faɗa mini ba. Mun yi azumi ashirin da tara mun yi salla a satin salla Jidda suka zana Jamb kuma cikin ikon Allah ta samu 220. Ta cancanta domin ba ta da wasa. Ba daɗewa kuma suka fara WAEC su Jidda an zama yan mata za ta yi graduation zai zama tana da shekara sha takwas cikin na sha tara. Baby kuma za ta shiga Jss2 tana da shekara sha biyu kenan. Na roki Yallaɓai da cewa ya bari na haɗa ma Jidda Waliman gama makaranta har yanzu dai bai ce komai ba. Ya ce sai ya yi tunani. Na lura tun da Yallabai ya koma babban ma'aikata ba ya son kashe kuɗi. Kuma sai ya kashe domin walima zan shirya ma Jidda in ta gama jarabawa kuma da kudinsa za a yi komai in sha Allahu. *Janafty**TKGB3K011* Ganin hankula sun kwanta ya sa ranar wata laraba Yallaɓai na gidana muna falon shi bayan mun gama ƙaryawa. Yumna na hannun shi yana yi mata wasa tana ta bangala masa dariyan su na yara. "Yallaɓai." "Uhm" Ya amsa mini hankalin shi na wajen Yumna ɗaga ta sama yake yi yana cillata tana dariya. Yallaɓai ba ya ba ni mamaki in dai akan yara ne, haka yake zai iya ɓata lokacin sa mai tsawo shi da yaran shi ba shi da wannan damuwan in dai yana gidan to Yumna na hannun shi su yi ta kara kaina a kanta shi da Baby. "Ya maganar koya mini mota? Kyan dai alƙwari cikawa. Yanzu na haihu ba ni da ciki" Na faɗa ina kallon shi ina daga kujera mai zaman mutum ɗaya shi kuma yana zaune a saman mai zaman mutum uku ne shi da Yumna. Kallona ya yi kafin ya ce" Ko ba ki da ciki ai kina da goyo ko? "Goyo kuma? Yumna ce za ta hana ni koyon mota Yallaɓai? Na faɗa ina cikin mamakin sa, har ina ɗan haɗe rai domin sai na ga kamar ba ya so kwata kwata ya koya mini motar nan to bai isa ba in ba zai koya mini ba ya ba ni dama na yi ma Musbahu ko Adnan magana su koya mini. "Ki bari ta ƙara wayau zuwa ki yaye ta mana. Amma ai yanzu ba ki da natsuwar koyon tuki ko Yumna? Ya faɗa yana kallonta sannan ya nuno mata ni yana faɗin"ki yi ma Umman ki bore wai za ta koyi tuki ba ki yi wayau ba! Ki ce baki yarda ba." Kamar tana ji sai ko ta fara wuntsila kafafunta tana wani abu irin na su na jarirai da suke cikin wattanin haihuwa ba su shekara ba. "Yauwa. Yumna ma ta ce ba ta amince ba sai ta girma." "Tabɗijam! Ai lokacin ma na ƙware a tuki har Zaria ma ina tuƙa kaina in sha Allahu." Na faɗa cikin gatse har ina mele baki. Kallona ya yi ganin na haɗe rai ne ya sa ya fara ma yar da maganar wasa da dariya. "Har garuruwa ma za ki riƙa zuwa kenan a motar kan ki? "Ƙwarai da gaske. In sha Allahu." "To Allah Ya tabbatar. " Ya faɗa yana yi mini dariya sai na shaka ina hura hanci na sake kallon shi ina faɗin" Za ka cika alƙwari ne ko kuwa ka ba ni izinin na nemo wanda zai koya mini a mutumce? "Au ni kenan ba a mutumce zan koya miki ba kenan? "Ni dai ban ce ba" "Kin ce mana." Ya faɗa yana mai tsare ni da ido. "To na ga sai kokarin yi mini wulaƙanci kake yi da na yi maka zencen koyon mota." Sai ya yi murmishi kafin ya ta so daga in da yake zaune ya zo kusa da ni ya zauna Yunma kuma ya ɗora mini ita a saman cinyata shi kuma sai ya saka hannunsa na dama ya sagalo kafaɗata. "Uhm to mene kuma na fushi? Ni na isa na ce ba zan yi miki abin da kike so ba? Ina tura baki na ce" To gashi sai againsing ɗin maganar kake yi duk lokacin da na ta da maganar." "Ni har na isa? Ke ba ki san wasa ba ne. Ko shike nan ni ba zan yi wasa da matata ba? Ya faɗa ya na jan kumatuna. Gyara ma Yumna zama na yi a kan cinyata lokaci ɗaya ina fadin" To yaushe za mu fara? "Mu bari weekend ko? "Allah Ya kaimu da rai da lafiya." Na amsa ina masa mirmishi. Shima martanin mirmishi ya mayar mini, sannan ya ɗan ramƙwafa ya sumbaci ƙuncina lokaci ɗaya ya miƙe yana faɗin" Tukwaici me zan samu? Ina dariya na ce" Me kake so? "Abin daɗi mana." Ya faɗa yana kashe mini ido ɗaya na san manufar shi ya sa na miƙe ina saɓa Yumna a saman kafaɗata lokaci ɗaya ina faɗin"To ka bari anjuma zan yi maka kyakyawan Tanadi" "Uhm ni yanzu na ke so." "Yanzu kuma? Na faɗa cikin mamaki sabo da ko yau da asuba bai bar ni na huta ba. Amma wai yanzu ya na ƙoƙarin komawa ruwa. Matsowa ya yi kusa da ni ya rumgumo ƙuguna ya na faɗin" Muje ki ba ni, ina son na fita ne yau ina da baƙin da zan gani da ƙarfe sha ɗaya na safe." "To ka je mana. In ka dawo ai abin daɗin ba zai gudu ba" Ƙirjina ya taɓa har yana ɗan matsaawa har sai da na kalle shi, lumshe ido ya yi sannan ya buɗe yana yi mini wani kallon ƙasa ƙasa. "Wai ba ka gajiya ne Yallaɓai? Har ya na wani miƙa yana ta da power hannun shi kafin ya ce" Gajiya? Taɓ ni ai yanzu na ke jin kaina ma." Taɓe baki na yi bai ƙyale ni ba sai turani gaba da ya hau yi da hannayensa a saman kafaɗuna. Bai kuma ƙyaleni ba sai da ya sake ɓaro mana wani ɓarnan ruwa sai bayan mun gama ne ya yi wanka da zai fita har yana faɗa mini saura na anjuma in ya dawo. "Wani anjuman? Malam tuƙwaicin  har guda nawa ne? Da hannushi ya ƙirga mini guda uku, hararan shi na yi kafin na ce" Kai dai Yallaɓai sam yanzu ba ka yi mini abu don Allah sai ka dawo ka fanshe ko? Maganata ta saka shi dariya har yana ƙyaƙyatawa. "Na ji ba komai.  Duk cikin cika sunnar ma'aiki ne(SAW)" Ni da Yunma muna haraba mun rakosa ya karɓeta ya yi mata wasa ya sumbaceta sannan ya miko mini ita bayan ya haɗamu duka ya rumgume. "Ki kular mini da kan ki Abar ƙaunata." Ya faɗa yana kai mini sumba a gefen bakina. Nima na mayar masa da martani kafin na ce. "A dawo lafiya Allah Ya ba da sa'a." "Amin My Sady." Muna tsaye ya shiga mota ya ta da. Daman ya buɗe get ya fita sannan ya dawo ya rufe get ɗin duk muna tsaye ina ɗaga masa hannu shima yana ɗaga mini sai da na ji ƙara tashin motarsa sannan na koma cikin gida ni da Yumna. Haka ko aka yi weekend na shiga Yallaɓai ya ce na shirya. Ranar farko ba da Yunma muka je ba wajen Baby na bar ta. jidda ba ta nan ta ta fi Tahfezz suna ta ƙoƙarin haɗa haddarsu ne gabaɗaya ba ta samun zama sosai. Ranar farko haka na yi ta rawan jiki da na hannu ban yi wani abun arziƙi ba da ya ke wani fili ne can gabanmu Yallaɓai ke koya mini anan, haka rana ta biyu tare da Yumna tun da Baby ta je Hadda itama Yallabai ke rike da ita ni kuma yana nuna mini yadda ake fara kunna mota da sauran su sai na yi kamar na gane in ya sakar mini sai na yi shirme kuma motar Auto ce shi ya sa za ta yi mini wahala amma ya ce wani sati zai saka Salisu ya kawo ta hannun shi tun da ita Munual ce za ta fi mini saukin koya. A satin dai haka muka gama ban gane komai ba Yallaɓai na ta yi mini dariya amma daga baya da ya ga na damu sai ya bar dariyan ya koma ya na lallashina da ban baki. Ni har cewa na yi an ya ina da rabon tuka motar kaina kuwa! Tun da gashi nan ma motar ta gagare ni iyawa. Shi kuma yana lallashina da cewa zan iya in sha Allahu. To satin na biyu motar hannun Salisu ya karba ita dai kan an ga sauyi tun da ranar lahadi har ya sakar mini sitiyari amma fa da na fara tafiya sai na ruɗe na kasa yin kwana na saki kan mota Allah ya sa Yallaɓai na gefe riƙe da Yumna ya yi saurin rike kan motar da na halakamu, duk na ruɗe sai da kuma koma gida ya yi mini faɗan na daina ruɗewa na riƙa natsuwa ne in ba haka ba zan daɗe ban koyi abin da ke da sauƙi ba, kuma ya fahimci ina da tsoro to na fara cire wannan tsoron in ba haka ba, to ba zan iya ba. Haka dai haka dai duk sati muna ta lallaɓawa kuma cikin ikon Allah na fara iya mota. Yallaɓai na sakar mini har na dawo damu gida ma. Ina ta murna da farimciki na iya mota na faɗa ma su Jidda suna ta mini ihun murna suma kar da Baby ta ji labari yan gidanmu kuma na ce mamaki zan ba su sai na yi mota na tuka kaina zuwa gidajen su su sha kallo. Sama da wata biyu Yallaɓai na koya mini mota kuma Alhamdulillah hannuna ya faɗa soaai fiye ma da tunanin shi tun da har cikin gari muna shiga na tuƙa mu, kuma na mayar da mu gida. Sannan har motarsa ma ina iya tukata yanzu lafiya lau. Ranar wata  lahadi ni kaɗai na fito, tun da motar yara saboda ina amfani da ita ya sa tun ranar Jumma'a in Salisu ya ɗauko su daga makaranta sai ya ba ni key sai kuma Monday zai dawo ya karɓa. To in dai Yallaɓai ba gidana yake ba kafin ya ƙariso in na gama ayyuka gida zan ɗauko Yumna mu fita a motar ina ɗan zagaya anguwa daga can sama zuwa kasa saboda dai hannuna ya ƙarawa faɗawa. To ranar ma ni kaɗai na fita kuma a gida na bar wayata sai da ina kan hanyar dawowa na haɗu da Yallaɓai a kasa yana tahowa lokaci ɗaya yana waya sai magana yake yi yana ɗaga hannu bai ma ganni ba ni ce na hango shi yana sanye da jallabiya da dogon baƙin wando. Jallabiyan mai kalan ruwan kasa ne har da wata hula ya saka rabin kai na rasa a ina Yallaɓai ya samo wannan hulan tun kwanakin nan na ga yana saka ta lokaci bayan lokaci. Daga nesa na ke kallon shi, tun da na ɗan rage gudu. Yumna na kalla daga kwance a kan kujeran mai zaman banza. Sai na yi mirmishi kafin na ce" Yunma ga baban ki can" Na faɗa ina mai ƙara kallon shi ta cikin gilashin mota tumbin da ya fara tarawa yake shafawa ya na faman magana a waya lura da yi bai ganni ba, kuma ni ya fito nema tun da ya je gidan ba na nan ya san na fito ne. Hon na yi masa lokacin da na kawo kusa da shi, sai da ya juyo sannan na ɗaga masa hannu ina dariya. Sai ya rike baki yana kallona kafin ya yanke wayar. Tsaya wa na yi lokaci ɗaya ina sauke gilashin gefen da Yumna ke kwance. "Hy ɗan saurayi ji mana " Na faɗa ina kashe masa ido ɗaya. Sanye na ke da wando baki plazo da riga ƙarama amma na saka after dress a saman kayana na saka brieziya hijab na Baby ne ma na maƙalashi da zan fito. Yumna ma ta sha gayu abin ta sai tashin ƙamshi take yi. "Eye Yan matana irin wannan cakarewa haka? Ya faɗa yana yi mini mirmishi, lokaci ɗaya yana rike hannuwan Yumna itama ta rike shi gam ganin shi ya sa har ta fara wuntsila kafa tana masa gaurancin su na yara. Wai ita nan ta san me yi mata wasa haka take yi musu ita da Baby ta riga ta gane su in dai wajen yi mata wasa ne. "Ya son ranka Ɗan saurayi." "Raina fesa. Da kyau Hajiya ta." Ya faɗa yana nuna mini babban yatsa alamun jinjina. "Shigo na rage maka hanya." Na faɗa ina masa dariya shima yana ta ya ni, buɗe masa motar na yi shi kuma ya shigo bayan ya ɗauki Yunma a saman jikinsa sai da muka fara tafiya na ji yana yi ma Yunma cakulckuli tana ta dariyan su na ihu irin na yara sannan na kalle shi ina faɗin" Yunma har ta gane ka kai da Baby in dai wajen wasa ne, in ba kwa kusa ta yi mini zillo tana son wasa ni ko na ce ba zan iya ba yarinya ki ji babanki ya zo." Yana dariya ya ce" Me ya sa ba za ki yi mata wasa ba? "Ban iya ba" "Kin iya. Ke dai ba ki san yi mata ne, Yumna Umman ki ta iya wasa ba ta son yi miki ne kawai saboda haka kisan zaman da za ki yi da ita yauwa." Kamar ta na jin sa ta yi zuru tana kallon shi, ni da shi muka kwashe da dariya ganin yadda ta wani yi nakwa nakwa da fuska kamar za ta yi kuka. "Kar ka haɗa ni da uwata." "To ki riƙa yi mata wasa. Irin wannan" Ya faɗa yana shilla ta sama ya kuma caɓeta sai ga ta, tana bangala masa dariya. "Aikin kenan daman shi ya sa in ta ganka ta yi ta zillo duk ka koya mata mugun wasa Yallaɓai." "Dai dai kenan ma" Muna tafe muna taɓa hira, ta kofar gida muka wuce mun kai farkon layi na sake kwana muka dawo sai a lokacin na lura ban ga motarsa ba. "Ka shiga da motar ka cikin gida ne? "A'a ba da ita na zo ba. Tun jiya tana gareji bakin mai ke zuba sai na kai ta aduba mini. Adaidaita na hayo." Sai na gyaɗa kaina ban yi magana ba muna tafe sai ya kalleni kafin ya ce" Ehe Madam hannu fa ya faɗa." Ina masa fari da ido na ce" To ya ka gani? "Lafiya lau. Yanzu kam ba in da ba za iya tukamu ba." "To Alhamdulillah saura motar kaina in sha Allahu." "Akwai kuɗin siyan motan ne har yanzu? Ya faɗa yana yi mini dariya ban ba shi amsa ba sai da muka isa gindin wata bishiya na yi parking na kashe motar sannan na kalle shi ina faɗin" Babu kam. Duk na ruguza jarina. Ina tunanin na riƙe wannan ko kai yara makaranta ne sai na rika kai su ina zuwa ina dawowa da su, tun da ina gida ba abin da na ke yi." Bai yi magana ba amma dai ya kalleni, sai kuma ya ma yar da hankalin shi kan yi ma Yumna wasa. "Ko Yallaɓai? Kafin na samu kudin siyan motar ko? "A'a ba zai a yi haka ba" "Me ya sa to? Na tare shi ina mai kallon shi, sai ya dawo da hankalin shi kaina lokaci ɗaya yana faɗin" Saboda tuntuni motar nan tana hannun Salisu kuma kin ga ya tambayi izini tun a shekarun baya ya na ɗan haya da ita nan ƙauyakun kusa damu yana ɗan samun na cefane kawai sai rana tsaka na ce zan karɓa motata kin ga hakan ya dace? Sai na yi shuru ina kallon shi ban yi magana ba amma dai gaskiya ya faɗa bai kyautu a karɓa ba. "Shi ya sa ba zan karɓa ba. Kuma kin ga ya daɗe yana aiki tare da ni tun mashin ɗin sa har ya zo ya rasa mashin ɗin bayan na sauya mota sai na bar mishi wannan a hannun shi ba saboda kai su Jidda makaranta ba ne, saboda shima ya taimaki kan shi ne kin ga ne? Sai na gyaɗa masa kai kafin na ce" Haka ne." "To kin gani. Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu abubuwa suna ƙara warware mini zan siya miki mota in sha Allahu." Kallon sa na ke yi domin ni na san alƙwarin Yallaɓai haka ya yi mini na buɗe shago har yau bai iya cika alƙawarin da ya ɗaukar mini ba. "Kin yi shuru? Sai na sauke ajiyar zuciya kafin na ce" Uhm Allah Ya sa." "Amin ko ba ki yarda da abin da na ce ba ne? Wallahi zan siya miki ba ni na ce ba." Ƙureni da ido ya yi ganin ina kallon shi ban ce komai ba. "Ki yi mini magana mana ba na son wannan shurun fa" "Yallaɓai ni dai ka daina yi mini alƙwari in dai ka san ba za ka iya cika mini ba" Sai ya zura mini ido kawai bai yi magana ba. "Ka daina lasa mini zuma a baki kuma ka tafi da sauran zumarka ban ƙara ganin ta." "Wani alƙawari na yi miki ban cika ba Sadiya? Ya faɗa a muryansa a natse ba maaganar wasa nima ko na gyara zama ina faɗin" Suna da yawa amma babban ciki ne na buɗe mini shagon Saloon. Ka samu damarmar maki da yawa a baya Yallaɓai amma ba ka cika mini alƙawarin da ka yi mini ba, duk da ba kyauta za ka buɗe mini ba da kuɗaɗena a hannunka amma abu ya gagara ko da yaushe sai dai ka ce kai ka yi alƙawari za ka  buɗe mini amma shuru. Duba fa ka gani Gimbiya a bayana ta zo gashi yanzu har ta buɗe shago business ɗin ta na ta bunƙasa amma ni sai dai ka yi ta lasa mini zuma a baki. Ba domin na ɗan kama ma businness ɗin hijaban nan ba da har yau ina nan ina zaman jiran warrabuka." Na gama faɗa a tsume, ban so na yi magana ba amma yau ne ya kai ni bango. Na gaji sai ya zauna ya yi ta cewa zai yi mini kaza zai yi mini kaza amma ya kusa cika alƙwari ko ɗaya da ya yi mini sai maganaa a fatar baki. Shuru ya yi ya kasa mgana har yana dukar dakai. "Ka yi haƙuri ban so na yi maganar nan ba. Ta kama ne." "Kallon maƙaryaci ashe kike yi mini Sadiya ban sani ba? Ya faɗa yana mai kallona. "Ni dai ban ce ba." "Haka ne mana. Kina mini kallon makaryaci sannan mara adalci ke ban buɗe miki shago ba amma na je na buɗe ma Daughter ko? "Ni fa ba haka na ke nufi ba." "Haka ne mana. Ga shi kin faɗa mini da ba ki fara ma sana'ar sai da hibajai ba da har yanzu kina nan kina zaman jiran warrabuka ko? Ko ba haka kika ce ba? Shuru kawai na yi ganin yana neman sauya mini mgana ta. "Muje gida sai mu yi maganar a can" Na faɗa ina kokarin ta da motar tsawa ya daka mini sai da Yumna ta firgirta ta fashe da kuka. "Ba in da za mu je, anan kika fara ta kuma anan za mu ƙarƙare ta." Ya faɗa da karfi har ya na buga kujeran mota ni gani na yi ma yana neman sakar mini da yarinya da ya sa da sauri na saka hannu na karɓeta ina rumgumeta ganin ta firgita tana ta kuka. Rigata na ɗaga ina zaro mata Mama saboda in ba shi na ba ta ba, ba za ta daina kuka ba. Ina ba ta Nono Yallaɓai ya ta sani a cikin motar nan yana ta yi mini masifa saboda ba ya son gaskiya. Eh mana rashin gaskiya in ba haka ba ai bai cika alƙawarin ba. Kawai yana kunfar baki ba shi da abin faɗa ko da zai kare kan shi da shi. "Ni kike yi ma kallon maƙaryaci sannan macuci tun da kin ce abu ba kyauta ba tun da na cinye kuɗin ki kuma ban buɗe miki shago ba." "Ni fa ban ce ka cinye mini kuɗi ba Yallabai ka tsaya ka fahimci maganar nan don Allah" "Me zan fahimta! Bayan wanda na gama fahimta. Wato ke dai yanzu ma kina tunanin na zalunce na cinye miki kuɗi ban cika miki alƙawari ba ko? Ya faɗa yana mai tsareni da ido. "Haba mana Yallaɓai." "Haba ko gaskiya" Ya faɗa a fusace ni kawai sai na yi masa shuru ganin ya harzuƙa. "To na gode ban taɓa tunanin irin kallon da kike yi mini ba kenan amma yanzu tun da kin furta mini kuma na ji zan yi lamarin tufkan hanci. Ki faɗa mini nawa ne kuɗin ki da kike tunanin na cinye, zan biya ki kuma ba na son ki yafe mini ko naira biyar a ciki in kuma kika yafe mini to ni wallahi ban yafe miki ba" "Yallaɓai." Na faɗa ina buɗe baki cikin mamakin kalaman shi. Daga magana sai ciɓi ya zama ƙari duk tsawon wannan shekarun da ban taɓa masa magana duk bai ga hallacin da na yi masa sai yau ne zai ce ni ce butulu saboda kawai na faɗa masa gaskiya. "Kuma maganar buɗe shago kuma ni na yi niyya alƙawari ne kuma zan cika in sha Allahu. Na yi kuma ranstuwa da Wallahi tallahi zan buɗe miki shagon Saloon na muka mallaka miki shi halak malak in sha Allahu Sadiya." Sai kawai na gyaɗa kai ban ce komai ba, na mai da kaina da hankalina wajen ba ma Yumna, saboda na fahimci ko magana na sake yi ba zai taɓa fahimta ta ba. "Nawa ne duka kudin ki da ke hannuna? Ko kallon shi ban yi ba saboda haushi. "Ki rubuta ki tura mini cikin satin nan zan tura miki kuɗin ki ba na so ki sake yi mini kallon wanda bai yi miki adalci ba." Tsaki na so na ja masa sai na fasa ni na ɗauka ma zai ce ne yau yau ɗin nan zai tura mini kudin ganin yadda ya yi zuciya. "Sai maganar Daughter kin ce wai ita da ta zo a bayan ki ga ta nan na buɗe mata shago businness ɗin ta na ta haɓbaka. To ina so na faɗa miki ko na ce tunasarwa ce tun da kin sani sai dai in kin runtse ido ne saboda wata munufarki, ko da na auri Daughter da kuɗin ta na ganta mijinta ya mutu ya bar mata gado. Da kuɗin ta da buɗe shago, ni dai na taimaka mata wajen neman shago da sauran su amma wallahi tallahi ba sisi na a cikin kasuwamcin ta ban rantse miki domin ina jin tsoron ki ba sai domin na fita daga zargin da kike yi mini na rashin adalci." Ban san tsakin da na ke riƙewa ya fito ba sai da na ga ya kalleni cikin mamaki kafin ya ce" Ni kike yi ma Tsaki Sadiya? Ni Yusuf? Da zan ce ya yi haƙuri sai na fasa na yi masa banza. Na gama ba ma Yunma Nono na rufe rigata na ɗora ta a saman jikina na ja key zan ta da mota Yallaɓai ya make mini hannu yana yi mini ihu a saman kaina. "Ni kike yiwa Tsaki Sadiya? Rashin kunya za ki yi mini? Sai kawai na koma na jingina da kujeran mota ina sauke numfashi, sai tsorata mini yarinya yake yi da ihun shi. "Na gode kin ji ko? Tun kina yarinyarki ba ki yi mini rashin kunya sai yanzu da girma ya kama ki ko Sadiya? Ya faɗa har ya na nuna ni sai ma ya ba ni dariya har sai da na ɗan dara shi kuma sai ya jijjiga kansa kawai bai ƙara maagana ba sai ma ficewarsa da ya yi a motar ban kira shi ba na ta da mota na zo na wuce sa, na koma gida ina ta jiran shi duk da wata zuciyar na faɗa mini ba zai dawo ba tun da ya yi fushi haka ko aka yi bai shigo gidan ba daga can ya yi gaba da man a gidan Gimbiya yake, sai washegari ne zai dawo gidana kuma har sai washegarin da dare na gan shi, haka ya shigo mini gida a daƙune ina gaishe shi da kyar ya amsa kamar na faɗa masa cuta. Daga shi sai yaran shi ya riƙa mgana. Shi da Jidda sun kai har wajen sha biyun dare yana mata solving Quention paper na Neco wancan shekaran. Tun da sun kusa gama WEAC bai wuce paper biyu su gama ba za su fara Neco kafin babban salla shi ya sa ba ta samun natsuwa ko da yaushe cikin karatu suke yi. Ni dai ganin ba a yi da ni ya sa na kama kaina na ja jikina ni da Yumna muka shiga ciki muka kwanta sai cikin dare da na farka ne na gan shi rumgume da Yumna ni uwar Yumna tun da ana fushi da ni, ni kaina kamar jikina ya sani duk mugun barci yau ban ganganra jikinsa ba. Da safe ma haka ya yi mini wani nuku nuku da fuska ni dai ina ganin ikon Allah har ya koma gidan Gimbiya ba ma yar daɗi da shi, da farko na so na biye masa a yi zaman doya da manjan sai daga baya na zauna na yi tunanin ban kyauta ko domin tsakin da na yi masa shi zai fi tsaya masa a rai. Shi ya sa ranar da zai dawo gidana na ci kwalliya saboda ina son sulhu. Ba ƙaramin kai zuciyata nesa na yi ba ina bashi haƙuri yana yi mini cin mgani. Kallona ya yi kafin ya ce" Uhm ni yau na ke magana Sadiya ki kalle ni ki yi mini tsaki? Haka na lalace daman a idanuwan ki? "Ka yi haƙuri tsakin ya suɓuce mini ne." Duk da haƙurin da na yi ta bashi bai saka ya hakura duka ba amma dai ya ɗan sassauta tun da har a daran ma ya neme ni mun yi ɓarnan ruwan da safe kuka ya tashi ya na sake yi mini cin magani ni dai na ce ai na ga ta kaina. Bai saki ba sai da ya fi sati yana yi mini isa isa daga ƙarshe dai ya haƙura don kan shi ya sauko amma ko yaya abin ya faɗo masa a rai sai ya yi ƙyafci a cewarsa ba abin da ya kai tsaki reni. Ya tsani ko wanda ya girme shi ne ya yi masa tsaƙi ballanta ni da nake ƙarƙashinsa ni dai nawa cewar ai ban haƙuri ne, ya dawo yana yi mini burga na yi lissafin kuɗina ya biya ni na yi banza da shi, daman can jin ta baki ne muna shiryawa sai shuru kuma bai ƙara ta da maganar ba. Shike nan na samu faɗan mu ya wuce sannan maganar biyan bashi dai ya sha ruwa daga lokacin da man can ba biya na zai yi ba, barazana ne kawai. Sallar babban salla ne ke ta matsowa muna ta shiri. Daman da sallar ne muke haɗuwa gabaɗayanmu a gida wannan ma salla hakan ce ta faru an hadu gabaɗaya an yi hiran zuumci an yi wasa an yi dariya an yi faɗa an kuma shirya. In ka ganni ni da Ma'u ba za ka taɓa cewa mun taɓa samun matsala ba a baya. Ma'u ta na faɗa mini Amarya da Hajiya Zainab sun haɗa mata kai, na ce ta yi haƙuri duk ta kau da kai haɗuwa in ba ta Allah ba ce tana zaune za ta ji kan su. Duk da ta fara kwantar da hankalinta amma har yanzu Ma'u ba ta mai da jikinta ba, sannan Alhajin ya daina rawan jikin da ya ke yi a kanta a da duk in da Ma'u za ta je in bai kai ta direba zai kaita amma yanzi har ta saba yawo a cikin adaidaita. Ni da na ga ta yi fari ma na ɗauka tana da ciki ne sai da na tambayeta ta rantse mini ba ta da ciki a lokacin ma jini take yi. Marwan Ya Aina ce cikinta har ya fito ita ke gaba sai Rahila ta kunsa ƙarami. Sai a Gwammaja muka haɗu da Gimbiya rabo na da ita tun wani zuwa da na yi gai da Nene bayan sunan Yunma muka haɗu sai da salla kuma muka sake haɗuwa. Ta yi fari ta ƙara zama wata katuwa ni dai sai na ga kamar ciki gare ta ban dai furta ma kowa ba. Da man ai ta yaye Anwar yana yawon shi ko'ina suna ganina da ga shi har Khalipa suka rumgumeni suna kiran Umma daman haka Khalipa ke kirana saboda ya ji a bakin su Jidda. Shi ya sa sai Anwar shima ya kama sunan. Nan muka yini gabaɗaya ni ban bi ta kanta ba tun bayan da muka gaisa muna ɗakin Maman farko ni da su Munnira muna ta hiran mu sai dare Yallaɓai ya zo ya ɗauke mu daman gidanta yake, mu aka fara saukewa sannan suka yi mana sai da safe suka wuce gidan su. Nun yi babbar salla a watan june ne. Lokacin Yunma na cikin watan ta na bakwai ne har ta fara wayau tun yaushe har ina koya mata zama. Tana wayau tana ƙara zama burtuka yanzu Baby da nishi take iya ɗaukanta. Jidda tuni har sun fara Neco Baby ce kawai ke zuwa makaranta kullun ita in ba su da paper tana gida. Ta ɗauke mini komai ita ke aikin gida gabaɗaya ni sai dai kawai na ci na kwanta, Yallaɓai ya yi ta mini tsiya wai daman abin da na ke so kenan na ce to sai dai ya yi haƙuri tun da raina ya kai kuma na haifa. Ni bai faɗa mini Gimbiya na da ciki ba amma tun ganin da na yi mata da salla na zargi haka. Sai da Jamila ta shigo anguwar mu wani gaisuwa gidan abokin mijinta ta shigo gidana ta ke faɗa mini ashe kuma Gimbiya ciki gareta? Na ce ban sani ba wallahi. "Tab ciki ko gashi nan har ya fito ba ki gan shi a jikinta da salla ba ne da kuka haɗu? "Ban lura ba" Na faɗa ba tare da na sake yin wata magana. "Ai ko ciki gare ta. Da Suwaiba ta yi magana ta ce ba an ce likita ya ce ta huta ba Anty Bahijja ta ce likita ai ba Allah ba ne. Lafiyan ta ƙalau kuma za ta iya haihuwa da kanta gwara ta yi ta haihuwa tun da Mijinta mai son ƴaƴa ne" "Ba shakka" Na faɗa ina jinjina kai, na rasa me zan ce ma. Ita dai Gimbiya haihuwa ce a gabanta ita a dole sai ta fini yawan ƴaƴa a raina na ce ta yi ta haihuwa ko duniya za ta haifa ba ta gaba na. Na tuna ko bayan haihuwan Anwar ni da Yallaɓai mun yi magana ya ce za ta yi planning ko na shekara biyu saboda dokar likita ban sani ba ko ba su yi tsarin iyalin ba ne. Shuru na yi da bakina na yi kamar ban ji ba ko Yallaɓan da bai faɗa mini ba nima ban nuna masa na ji ba, kowa kuma ban yi maganar da shi hatta ko da su Munnira. Sai ma Hauwa ce ta kira ni a waya ta na faɗa mini  a Rano ta ji labarin Gimbiya na da ciki na ce mata e da gaske ne. "Ba likita ya ce ta huta ba? "Ba ta son hutun ne Hauwa. Ki barta ta yi haihuwanta." "Allah ya sauwake." Haka muka rufe maganar muka shiga wata, mun ɗan jima muna magana kafim mu yi sallama Munnira ma da ta ji ba ta yi mini maagana ba sai da na je gidanta ranar daga asibiti na kai Yumna tana da fama da ciwon ciki, shi ne muke maganar da ita. "Ai kishiyar nan taki munasura ce Sadiya. Ta ce ita haihuwa yanzu ta fara a gidan Tafida ba ta ma yi komai ba tukunna." "Allah haka ta ce? Munnira ta ce"Haka ta ce, ta ke faɗa a gidan su nima Hauwa ce ke faɗa mini da ta je gidan su ta ji maganar." "To Allah ya ba ta masu albarka" "Addu'a za ki yi mata? "To zan ce ne kar Allah Ya ba ta masu albarka ne Munnira? Allah ya ba ta masu albarka ko ba komai ai ai ƴa'ƴan Yallaɓai ne. Kuma duk saurin ta sai dai a kira su ƙannen su Jidda ba dai yayyen su ba" "Wannan gaskiya ne." "To kin gani. Ku bar ta lokaci ne wata rana sai labari." Har na baro gidan Munnira ba mu ƙara ma ta da hiran Gimbiya ba, ni ma da na dawo na cire abin a raina na watsar nima na gode ma Ubangiji tun da har ya ba ni biyu ya kuma ƙara mini a lokacin da na cire tsammani, ita takamar tana da ya'ya maza ita ce ta haihu ni tun da mata ne yarana ban haihu ba ko alama ba ta gabana harkan rayuwata kawai na ke yi. Kuma yadda shima ya yi shuru bai taɓa mini maganar nima ban yi masa ba sai ranar da ya ke gidanta har dare bai zo ya duba mu kamar yadda ya saba sai a washegari da safe ya zo yana faɗa mini a jiyan Gimbiya ce ba lafiya a asibiti suka yini, amma an sallamota tana gida in na samu lokaci na shirya mu je ni da yara mu duba ta a gida. Kamar zan je sai mun samu lokacin sabo da ban manta wulaƙancin da ta yi mini da cikin Yumna ba ni ko ba zan ƙara rawan jiki a kanta ba. Na ce masa za mu je ranar da su Jidda ke gida na masa Allah ya ƙara lafiya amma ko gaisheta ban ce ya yi ba. Kwana biyu tsakani ranar lahadi Jidda na gida ta je Hadda ba ta dafe ba ta dawo tun da sun gama haɗa Qur'anin su suna bita ne kafin a yi musu waliman sauka. Daman a gidan ya kwana yana ganin su dukkansu a gida sai ya ce mu shirya  mu je mu duba ta daman na kudira a raina ba zan je ba. Sai kawai na nemi waje na kwanta na ce ba na jin dadi wai to bari a fasa sai gobe in na samu sauƙi. "A'a ku tafi kawai ku gaishe ta." Na faɗa ina daga kwance a saman gado Sai ya ce to bari su tafi amma har da Yunma Baby ta ɗauka suka tafi, tun bayan la'asar sai dare suka dawo sai ga su da yara niki niki Anwar da Khalepa da kayan su, sannan ba su dawo da Jidda ba wai tana can za ta kwana saboda Gimbiyar ita kadai ce yaran ma tace a kawo mini su sun dame ta da hayaniya ga shi ba ta da lafiya. "Topha. Ai nima ba ni da lafiyan kuma daman Jidda ce ƙarfin aikin gidan yanzu." Na faɗa a tsume bayan duk ya gama rattabo mini bayaninsa. Wato ga jaka dole ta ce a kawo mini yara. "Ga Baby za ta taimaka miki da wani abun. Ita ma Jidda zuwa jibi za ta dawo tun da ranar laraba suna da jarabawa." Takaici ma ya hana ni mgana, tun da yaran nan suka zo hutu na ya ƙare tun da Jidda ba ta nan dole na ke tashi da safe na yi musu shirin makaranta. Har Anwar da ke ɗan shekara biyu an saka shi makaranta ajin yara ban sani ba da man a can uwar su ke kai su yanzu kuma tun da suna gidana Salisu ne. Ko Yallaɓai in bai fita da wuri ba, sai da Jidda ta kwana uku ta dawo da na ke tambayanta Antyn ta su a kwance take? Sai ta ce mini. "Wani kwance Umma? Ta ji sauki fa ta yi ta chart da waye wayenta abinci ne ma in ta ci wani lokacin ta ke Amai." Jinjina kai kawai na yi, a raina na ce ban ga laifinta ba wanda ya samu rana ga igiya ai sai ya yi ta shanya. Yallabai ne ya ɗaure mata gindin yara kuma na yi magana ya ga ɓakina. Amma me ya sa bai kai su gidan Naja ko Anty Bahijja ba? Sai ni ko wacce suka raina to ai ya yi kyau ni kaɗai ranar na rika masifa a cikin gida kuma har lokacin bai faɗa mini ciki gare ta ba, nima ban tambaya ba sai ranar da ya ke gidana har mun yi shirun kwanciya ya fita ɗakin yara sai ga shi ni kuma ina kwance ina ba ma Yumna Nono ta farka ta fara mini jananun kuka. "Meke damun Gimbiya ne haka da take ta rashin lafiya? Da gayya na yi masa tambayan ya na sauya kayan jikinsa zuwa na barci yake amsa mini. "Laulayi ne." "Laulayi? Na maimaita cikin sigan tambaya. "E ciki gare ta. Ba ki sani ba? Sai da na balla masa wata uwar harara kafin na ce" Na sani mana tun da ka sanar da ni." Sai ya yi dariya lokaci ɗaya yana hayo gadom har kusa da ni, hannunsa ya sa ya ɗan shafa fuskar Yumna zuwa jikinta. "Kar ka ja ta da wasan ka. Ka ja mana tsayuwar daren dole." . Dariya ya fara yi ni kuma na kanne ina fadin" Ahto domin kai zan haɗa da ita na yi kwanciya ta wallahi." "Na ji ba komai. Ai na iya reno nima." "Ka iya fa." Na faɗa cikin gatse,shi kuma yana ta mini dariya. Ganin na gimtse fuska ne ya sa ya saussauta murya ya na faɗin" Da gaske ba ki san Daughter na da ciki ba? "Na sani na ce ba ka faɗa mini ba? Na faɗa ina masa wani kallo. "Yi hakuri ma yar da wuƙar wallahi na ɗauka fa kin sani shi ya sa ba mu yi maganar da ke ba." Uhm" Na faɗa kafin na ce" Allah Ya raba lafiya.' "Amin ai da sauƙi ma bai wahalar da ita kamar cikin Anwar ba." Na yi masa banza na cigaba da ba ma Yunma Nono. "Kin san likita ya ce ta huta. To da na yi mata mganar ko za ta yi tsarin iyali ne ai kin san mun ma yi maganar da ke ko? Ya faɗa yana kallona sai na gyaɗa masa sai ya cigaba da faɗin" Sai ta ce ita ba za ta yi ba. Wai ba ta son yi saboda ba ta so ta yi itama ta samu matsala irin na ki." "Jar Uba! Ban san na yi ashar ba sai da na ji ya fito. Yallabai ya yi ƙasake yana kallona. Cire Yumna na yi daga nono na kwantar da ita gefe ina kallon Yallaɓai. "Zagi kuma Sadiya? "Dole na yi ashar na ga matarka na neman rena mini wayau ne." "Na me fa? Ya faɗa shima ya ɗan sauya yanayin shi. "Saboda ta raina ni sai ta yi kwantance da ni ni kaɗai ce macen da ta taɓa tsarin iyali ya sakar mata matsala? Ko tsarin jikin mu da jinin mu ɗaya ne. Wata ƙila ita in ta yi sai ta wanye lafiya ai komai na Allah ne amma don tsabar renin wayau sai ta fake da ni? Ina ruwanta to da rayuwata" "Ki tsaya ki fahimci ne ita fa ba haka take nufi ba." "Ya take nufi? Kar ka wani kare mata. To ni ba ni da wata matsala ba kuma zan gani ba in sha Allahu sako na baka ka sanar da ita ni Sadiya ba ni da matsala ban kuma tare da ita wanda ke ƙababa mini ita ma ya je Aniyarsa ta bisa wallahi." Na ƙarishe faɗa a fusace saboda raina ya gama baci ina gidana amma ta na can tana raina mini wayau. "Topha ni ce Aniyata ta bi ni ko Daughter? "Oho ni dai na ce ba ni da matsala mai neman kuma goga mini ita sai ta faɗa kan shi Ehe." Na fada ina sauka daga gadon gadon bi na ya yi da kallo ya yi kafin ya ce" Yi hakuri kar ki dake ni." "Ban isa ba kuma." "Kin isa ma tun da gashi kin rufe ni da faɗa daga mgana. Na gaji fa wallahi zan daina raga muku daga ke har ita ba daman in yi magana a kan ku da ɗaya daga cikin su sai cibi ya zama kari daga mai cewa ba na yi mata adalci sai yi mini tsaki, sai mai cewa in an cuceta Allah ya isa. Yau dai mai kankat kin ce ni din nan wai Aniyata ta bini, daga magana ko barina ma na ƙarisa maganata ba ki yi ba kin rufe ni da faɗa kamar wani ɗan ki." Ya faɗa a fusace, jijiyoyin sa na sake miƙewa kamar daman yana jira na ne. "Kai ba ka ga laifin matarka ba? "E ban ga laifin ta ba. Na faɗa miki daga yau ba zan ƙara raga muku ba. Ba ta yuyuwa ina mijinku kuna ƙarƙashina amma kuna ƙokarin rika sarrafa ni, saboda kawai ina muku kawaici? Kaina a ka fara auran mata biyu? Na gaji wallahi ku fita hanyata kafin wata rana ku harzuƙa ni na yi muku abin da ba ku yi tunani ba." Ganin yadda ya fusata ya sa sai na yi shuru, salaf salf na fice zuwa tiolet ina kunshe dariyata ashe itama can rufe shi take yi da faɗa a kaina. Ina ga ita ce ta yi masa Allah ya isa ni dai ba ni ba ce, kama ruwa na yi na fito ina saita kaina ko da na dawo ya ja Yumna ya rumgume yau sai dai na ci kaina kenan mirmishi na yi, na shafa ma hannayena da wuyana turare sannan na kashe fitilar ɗakin na kwanta muka saka Yumna a tsakiya na ja hannun shi ina so na sarke tare da hannuna ya ƙi ya damƙe hannun shi, na tsugule shi a hannun amma ya damƙe sai ma ya rike hannun Yumna cikin na shi na ya jimƙe. Ni da na ke son rigima sai na taso daga in da na ke na haura tsakiya na raba shi da Yumna na shige jikinsa mamaki ya hana shi magana ina kallon shi ta ɗan hasken dake shigowa ta waje ya ɗan murmusa. Ya rumgumeni, na kwanta a saman kirjinsa muna kallon Dama ni da shi dukkanmu mun sarƙe hannayen mu waje ɗaya mun rumgumo Yunma ina jin sa ya yi mana addu'an barci ya tofa mana. Ba mu daɗe ba ni da shi barci ya ɗauke mu, Yumna daman ta rigamu komawa tun da ta sha Nono ta koma barcinta. Asuba ta gari. YUFSAD. *Janafty**TKGB30L12* *Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.* Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732 Washe-gari haka Yallaɓai ya tashi yana mini cin magani ina masa magana da ƙyar yake amsa ni, sai ya koma ma ya na ba ni dariya. Sai da na sallami yara zuwa makaranta sannan na yi ma Yumna wanka na shiryata na bashi ita ya riƙe ta na koma kitchen ina duba dankalin turawan da na saka amai kar ya ƙone. Har Jidda yau suna da paper ta tafi daga ni sai Yallaɓai a gida sai Yumna ina daga Kitchen ina jiyo dariyan ta yana yi mata wasa. Mirmishi kawai na yi, in dai Yumna ne yanzu har ta waye da wasannin Yallaɓai ƙiyuwa ta fara yi ma Jidda saboda ita ba ta yi mata wasa amma da Baby ne ko su Khalipa da ba ma ganin su take yi koda yaushe ba har tana zillo in ta gan su. Yallaɓai ko ta riƙa harba ƙafafuwa kenan in ta gan shi in ko tana zaune ne sai ta tsintsira tun ina mamaki har na daina. Yallaɓai da wuri ya ce mini zai fita, zai fara biyawa ta Gwammaja ya duba Nene kafin ya wuce office. Shi ya sa da wuri ya yi wanka ya shirya nima wankan na yi sannan muka zauna a kan dining muna karyawa sai kiran shi ake yi a waya harkokinsa can dai. "Yallaɓai ka ce harkokin sun buɗe? "Alhamdulillah." Ya faɗa fuskarsa ba walwala lokaci ɗaya yana tusa dankalin a bakin shi sannan ya bi da ruwan tea ɗin dake cikin ƙaramin mug a gaban shi. "To duk fushin na mene ne mijin Sadiya? Kallona ya yi sai kawai ya ɗauke kan shi ya cigaba da cin dankalin shi da tea. "Mene ne uhm? Ni ce? To yi hakuri ka ji Yallaɓai na. Ba na son ina ganin ɓacin ranka" "A baya ne ba ki san ganin ɓacin raina amma ban da yanzu." Ya faɗa ba tare da ya kalleni ba, sai na yi mirmishi kafin na ce" To na ji yi haƙuri ka ji? "Uhn" Ya faɗa kawai yana cigaba da tura dankali bakin sa. "To ka ce ka haƙura mana? "Me kika yi mini? Ba ki yi mini laifin komai ba so ki daina ba ni haƙuri" "Na yi mana. Maganar jiya ko? Na faɗa ina kallon sa, ni dai na san ran shi ya ɓaci kuma ya na jin haushina ko don ganin yadda yake magana yana cin magani. "Ka yi haƙuri ni ba da kai nake ba" "To da wa kike? Ya faɗa yana kallona sai na kasa magana saboda ya zura mini idanuwansa cikin wani yanayi yana kallona. Kai kawai ya girgiza sannan ya mai da kansa ƙasa ya cigaba da shan tea ɗin sa ba tare da ya ƙara wata magana ba ni kuma sai jikina ya yi sanyi sosai nima sai na debo dankali ina mai turawa a bakina cikin sanyin jiki da na zuciya. Bai wani ci da yawa ba ya share bakin sa da tissue ɗin da ke saman dining sannan ya ɗago yana kallona nima shi na ke kallo. "Har ka ƙoshi? "Alhamdulillah" Ya faɗa yana mai miƙewa sai kuma na ga ya koma ya zauna yana mai duba agogon fatan da ke tsitsiyan hannun shi na hagu, sannan ya sake ɗagowa yana kallona kafin ya kira sunana a kausashe. "Sadiya" "Na'am" Na amsa ina kallonsa cikin natsuwa ganin kamar magana zai yi ganin yadda ya kira sunana. "Kin yi mini laifi jiya kuma har na ji haushin ki. Amma sai na yafe miki kafin na kwanta saboda ba na so ki kwana da fushin Mala'iku a kan ki." Sai na kasa mgana na yi jagale ina kallon shi. "Ba zan hana yin magana ba saboda bakin ki ne. Amma ina so ki sani ni mijin ki ne, ki san irin kalaman da za ki riƙa amfani da su wajen mgana da ni, mijin ki ne ni ba kanin ki ko ɗan ki ba, bai kamata ina fara magana ki rufe ni da faɗa ba kina ta faɗin mganganu son ranki, daga karshe ma har zagina kika yi." "Zagi kuma? Ni? Na faɗa ina nuna kaina cikin zaro ido. "E zagi ko ƙarya zan yi miki? Ya faɗa yana kallona, sai na kasa magana na dukar da kaina ina fadin" Ni fa ba da kai na ke yi ba. Kawai na" "Kawai me! Ai ni ne na ke yi miki maganana. Ya kamata ina magana ki ce mini jar uba!? Ya faɗa yana mai kafe ni da ido sai ya karya lagona. Saboda na san ban kyauta ba amma na kasa magana ba. "Kar ki sake, ba na so in kuma kina so ki ƙure hakurina ne to shike nan ki ciga ba. " Ɗagowa na yi ina kallonsa ganin ya mike tsaye alamun zai fita. "Ka yi haƙuri." "Na haƙura na faɗa miki ne saboda ki kiyaye." "In sha Allahu." Na faɗa cikin sanyin murya kamar ba shi ba sai na ga ya yi mirmishi ya matso ya ɗan ramkwafa ya sumbaci goshinaa. "Sai na dawo." Na miƙe ina shirin masa rakiya da sauri ya saka hannuwan shi ya ma yar da ni zaune ya na faɗin" Ki gama ba sai kin yi mini rakiya ba." "To sai ka dawo. Allah Ya ba da sa'a." "Amin ki kular mini da kanki. Ke da Yumna." Sai na gyaɗa masa kai, ina kallonsa har ya fice daga falo ya bar mini ƙamshin turaren shi, ina zaune a wajen na ji tashin motarsa da fitarsa sannan na ji karan jan get an ma yar an rufe, ajiyar zuciya na sauke sannan na cigaba da tura dankalin gabana nima sai na ji cikina ya tushe sai kawai na tattara na rufe ma su Baby in sun dawo makaranta su ci, da yake da safen ma ba su tsaya ci ba amma sun tafi da shi. Khalipa da Anwar amma Jidda tuni ta daina ɗaukan abinci ta ce na yara ne. Baby ce ba ta girma ita wannan uwar acicin ma ranar da ba ta je da abinci makaranta haka za ta dawo kamar ta ci babu.   Bedroom na koma saboda na baro Yumna tana barci, wayata na ɗauka ina latsawa bayan na zauna a gefen gado Data na buɗe na shiga yanar gizo-gizo ina ganin abin da ke faruwa, waɗanda suka yi mini magana duk na amsa su yawancin duk masu oder hijabai ne da yake na kwana biyu ban kawo su amma ina haɗa kan kudaɗen hannuna ne, ko na salla babba ban saro hijabai ba, na dai saro su inners ɗin saboda ba ishashun kudaɗe a hannuna. Daga nan I. G na shiga ina ta kalle-kalle na sai da na gaji jin na fara jin barci sannan na ijiye wayar na kwanta ban tashi ba sai bayan azahar Allah ya taimake ni yau Yunma barci take sha ko tashi ba ta yi ba amma na san za ta taɓa kukan dare tun da ta yi barcin rana sosai haka. Barcin da na yi duk sai ya sakar mini kasala shi ya sa ko girki ban yi ba. Gidan ma ko sharan shi ban yi ba, yini na yi kwanciya sai danna waya sai da Yumna ta tashi ne na haƙura ma da kwanciyar da suka dawo daga makaranta sauran dankali suka sha tare da Tea, Jidda kuma na ce ta ɗora mana girki har da ni da Babansu tun da yau ba zan iya yin wani girki ba. Shinkafa da miya ta yi sai na kira Musbabu na ce in ba damuwa ina son kayan lambu, sai ya ce mini ba sa nan sun fita shi da Yallaɓai sai na ce to ya bar shi kawai daga karshe Adnan na kira shi ya siyo mana su kabeji da cocumber sai da ya kawo na bashi kudin nan ma ya yi isha'i ya ci abincin yana ta santin har yana ba ma Jidda Tuƙwaicin dubu biyar na girkin da ta yi. Bai jira dawowar Yallaɓai ba ya ta fi saboda Yallabai sai after 10 ya dawo a gajiye ya ce mini na haɗa masa kayan tafiya kala uku Jigawa zai je gobe kuma akwai yuyuwar ya yi kwana uku a can. Tafiyar Yallaɓai ya sa su Khalipa ba su koma gidan su ba, ni kuma ban ji na duba ta ba na dai kira ta a waya na yi mata sannu ta ce mini ai ta ma samu lafiya, har tana ce mini ya su Khalipa an kawo mini hayaniya na ce ai ba komai. Yallaɓai sai da ya yi kwana shidda sannan ya dawo. Washe gari kuma ko hutawa bai yi ba ya wuce Kaduna daga can ya je Abuja kwangiloli ne yake samu ga su nan akai akai shi ya sa yanzu ba ya samun zama dalilin haka ne ya sa su Khalipa suka share wajen sati uku a gidana ba su koma ba sai a satin da suke da uku ne Yallaɓai ya samu zama a weekend ranar kuma sai ya faɗo yana gidana ne. Safiyar lahadi, ranar Yallabai zai koma gidan Gimbiya kuma ya ce a shirya kayan su Khalipa za su koma gida tun da Gimbiyar ta samu lafiya. Wankin kayan su daman mai wanki na haɗa mawa sai na kira shi na ce ya kawo sauran kananun kuma tare da Uniform na saka Jidda ta ɗan wanke musu, ni da Baby kuma muka gyara gidan bayan mun gama na ce ta gyara Kitchen ta yi mini wanke-wanke sai Baby ta fara tura baki tana cewa ita kanta ke ciwo. "Ai ko kan naki zai cire ne sai kin gyara mini Kitchen kin kuma yi mini wanke-wanke yarinya." Na faɗa ina zare mata ido. Ta san halina tana yi mini wata magana za ta ji dundu shi ya sa bakin ta alaikun ta wuce, Jidda ke yi to yau tana wanki in ta gama ma za ta yi mu su Khalipa wanka. Yumna na goye a baya tun da na yi mata wanka take barci. Yallaɓai na ciki yana ta barci tun bayan da ya dawo sallar asuba ya koma bai tashi ba har muka karya sai ban tashe su ba sanin ya fi sati biyu bai samu lokaci ya huta ba bawan Allah ya na ta fadi tashi duk an kan mu, jiya ma Gwammaja muka yini ni da yara sai dare muka dawo da yake Nene ta ɗan yi zazzabi kwana biyu. Baby na tura baki da komai ta gama aikin da na saka ta ban bari ta zauna ba na ce ta ɗora musu abinci Jidda tana gama ayyukata ta saka hijabi ƙawayenta sun biyo mata sun tafi tahfez suna ta mura'ju'a domin an kusa yin musu walimar saukar su, jarabawa kuma sauran ta paper ɗaya su gama shi ya sa nake ta tunanin tun da abin ya zo a tare zan ɗan jinkirta na haɗe graduation ɗin ta tare da Walimar saukar su gabaɗaya. Yallaɓai sai biyu saura ya tashi, ya yi salla sannan ya sha tea ya hau kuma aiki a cikin laptop ɗin sa na wani lokaci ni kuma a lokacin na gaji sai kawai na kwanta Yunma ma a wajensa na bar ta, na daɗe ina barci sai bayan la'sar na tashi shima ɗin hayaniyan yaran ne ya tashe ni, na duba agogon wayata hudu da rabi har ta gota sai ban fita ba, na shiga Tiolet na ɗauro alwala na zo na yi salla sannan na fita falo. Abin da na gani ne ya sa ban san na riƙe kugu daga korido na ƙame ina kallon ikon Allah ba. An yi mini kaca kaca da falo ba ma wannan ne abin mamakin ba. Illa Yallaɓai da na gani daga shi sai bakin wando sai singlet haka su Khalipa ba riguna sai kananun wanduna har da Baby itama ta ci zanzaro da kayan tekwando ɗin su na makaranta suna wasan doke ni in doke ka su da Yallaɓai gabaɗaya sun haɗa zufa. Jidda ce kaɗai ba ta shiga ba tana zauna ɗauke da Yumna da ke zillo kamar ta je a yi da ita. Baki na saki da hanci ina kallon ikon Allah. Yallabai na ware hannu yana faɗin su zo su zo, suna zuwa suna kai masa duka yana tarewa suma yana kai musu suna tarewa, Baby ce ta ba ni mamaki yadda na ga ta ware ƙafa ta na kai ma Yallaɓai bugu yana ƙarewa itama yana kai mata tana karewa da sunan wasa. Na ma kasa magana saboda haushi da mamaki Jidda ce ta fara ganina tana dariya ta ce. " Umma ko zaki shiga a yi chinese din da ke ne? Hararan da na wurga mata ne ya sa ta rufe bakinta tana dariya ƙarisowa na yi falon ina fadin" Na shige su ni Halima. Yallaɓai me zan gani haka? Sai a lokacin ya lura da ni ya na wani tsalle na ga kamar zai yo kaina na kwace ina faɗin" Yallaɓai.'" Na ma kasa magana saboda mamaki Baby ta kalleni tana faɗin" Umma akwai dadi ki shigo mu yi da ke' "E Umma ki shigo" In ji Khalipa. Hararansu na yi kafin na ce" Ni? Ai ba ni da irin ƙarfin ku Allah ya ba da sa'a." Buɗe bakin Yallaɓai sai cewa ya yi wai na zo ko na rage kitse na ce na ji, amma ni ba zan shiga ba na tuna lokacin ina amarya Yallaɓai ya yi ta ja na da irin wannan wasan tuni na nuna masa bana so saboda shi ya iya kai duka ni kuma ban iya ba daga wasa sai a cuceka. "Ke me ya sa ba ki shiga ba? Na faɗa ina zama gefen Jidda. Yumna na ganina ta fara zillo tana miƙo mini hannu sai na karbeta. "Ban iya ba Umma." Ta faɗa a hankali ni da man na san ba za ta shiga ba. Ina son Jidda saboda kamewarta da Ajin ta. "Kin taimaki kanki. Ita wancan da ba ta san ciwon kanta ba ai ga ta can ta na ware kafa kamar wata namiji." Jidda ta fara dariya ni kuma haushi ya kume ni ganin yaran sun danne Yallaɓai suna kai masa naushin  wasa gabaɗaya sun cika mana kunnuwana da iface ifacen su hauahi ya kama ni na yi ma Baby tsawa na ce ta baro wajen nan. "Me ya sa? Ki ƙyale ta mana." In ji Yallaɓai ganin ta yi mini wani nakwa nakwa  da fuska kamar za ta yi kuka. "Haba Yallaɓai ita fa mace ce. Ka dai yi can da su Khalipa su da suke maza amma ita bai da ce ba." "A wajen ba shi ne bai dace ba, amma ni a wajena Normal ne. Domin ta na mace shikenan ba za ta yi wasa da babanta ba? Ko su mata ba ƴaƴa ba ne? Sai na yi shuru saboda Yallabai tun da ya tare maganar ba zam iya ja da shi ba, ita ko jin ban yi magana ba sai ta koma cikin murna shi kuma sai ya zo ya ja hannun Jidda yana faɗin" Come on Daughter mana." Sai ta maƙe kafaɗa tana faɗin" Abba karatu zan yi" "Ba za ki yi wasa da Abba ba? Sai ta noke kanta ba ta yi magana sai kawai ya ƙyaleta yana fadin" Kar ki zama raguwa irin mamanki mana Jidda." Hararan shi na yi kafin na yi magana ya tare ni da fadin" Ƙarya na yi ai ragganta ke hana ki yi, wannan fa koya ma yarana nake yi faɗan kare kai domin wata rana." Ni da Jidda muka kalli juna na tsintsire da dariya itama tana ta ya ni, ganin muna yi masa dariya ya sa ya ce" Au dariya ma kuke yi mini ko? Shi ke nan." "Yallaɓai baka da aikin yi ne yau? "Kin san dai ba zaman banza na ke yi ba ko? "To na ga ne yau kana ji da karfi." Yana ɗaga power ɗin hannun shi kafin ya ce" Sosai. Amma yau din rana ce ta musamman domin iyalaina da yarana." Ina dariya na ce" Ka ce yau Happy Family day ce Yallaɓai" Banza ya yi dani ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Jidda ya ce ta ɗauko masa ruwa mai sanyi a fridge su Baby na kalla har suna kusa ɓaro mini da Tv ƙasa cikin ɗaga murya na ce" Duk barnan da aka yi mini baby ke ce za ki ɗauki asara domin bugun tsiya zan yi miki. Kuma ki sani ku gama ke za ki gyara mini falo na ma faɗa miki." "Ubanta dai kike so ki ce ya gyara ba ita ba." Ina dariya na kalli Yallaɓai kafin na ce" Ni dai ban ce ba" "In ma kika ce ai kin san ba zai gagare ni ba malama." "Na sani." Na amsa ina masa dariya Jidda ta kawo masa ruwan gora da kofi bai ma zuba a kofin ba ya buɗe ya kafa kai kaɗan ya rage ina kallon shi na ce. "Lalle Yallaɓai ka gajiyar da kanka." "Ni ai ba malalacin namiji ba ne. Lebura ne ni mai aikin ƙarfi." "Allah ya taimaki Md Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana." Na faɗa ina masa dariya har ina aika masa da jinjina. Miƙewa ya yi bayan Jidda ta koma kitchen mai da kofin da ruwan, Yunma ke zillo za ta wajen shi sai ya ƙarbeta yana faɗin" Ke kuma za ki shiga wasan ne? Ina jin haka da sauri na ce" Yallaɓai don Allah kar ku wahalar mini da ƴa'" Amma ki saurarena bai yi ba sai ma ya juya yana ce ma su Baby" Mun samu ƙarin patner.' Suka fara ihi kafin in ce me ina zaune an dadumar mini yarinya na miƙe ina kiran sunan Yallaɓai amma ya yi biris da ni shilla sama yake yi yana caɓewa maimakon ta yi kuka sai dariya kwantar da ita ya yi a ƙasan cafet yaran suka rufu kanta suma mata wasa suna kai mata hannu itama jaira tana kamawa. Ihu na yi musu ina faɗin" Wallahi Yallabai kada kai da yaranka kun halaka mini yarinya to." Ko sauarara na ma ba su yi ba da na ga za su ma yar da ni mahaukaciya sai na bar musu falon amma ina cike da fargaba kar su naushe mini yarinya. Kitchen na shiga na ɗibo abinci na koma ɗakina na ci na koshi, har lokacin ba su bar wasan ba har daga ɗaki ina jin iface ifacen su Yunma ina jiyo dariyanta na ɗauka za ta ga ji ta fara kuka sai ta ba ni kunya ko kukanta ban ji ba. Sai da aka kira mangariba Yallaɓai ya hakura da wasan nan ya zo ya yi wanka ya tara su Khalipa zuwa masallaci Yunma kuma an kawo mini ita ina ba ta nono na cire mata pampers na sake yi mata wanka da ruwan zafi sai barci ina ta masifa ni kaɗai. "Ai dole ki yi barci kin sha wuya." Falo ma da na fita bayan na yi salla kaca kaca Baby ba ta gyara ba ai da muryan ɓacin rai na fara kiran sunanta sai ga shi ta fito da hijabi alamun salla ta idar. "Ke ubanki kika bar ma falon ya gyara ko ni? Sai ta fara sosa kai kafin ta ce" Umma na gaji ki bari da safe sai na gyara." "Ko mutuwa za ki yi yau sai kin gyara mini falo na aike ki ki yi mugun wasa har ki gaji? Sai ta girgiza mini kai shammatanta na yi na ƙarisa gabanta tana shirin guduwa na damki kunnenta ɗaya na matse ina faɗin" ba ki da hankali ashe ban sani ba Maimuna? Sai ta fara kukan shagwaɓa tana faɗin" Umma zafi kunnena." "Ke namiji ce da za ki je kina wasan maza? "Umma Abba ne ya ce na shiga." "Abban ne ya ce ki shiga ko? Ya ce ki shiga dole ne? Ba ga ƴar uwan ki nan ba kin ga ita ta shiga ne? "A'a" Ta faɗa cikin kuka har ta fara hawaye, ƙara jan kunnen na yi ina faɗin" Wallahi in na sake ganin kin shiga irin wannan wasan sai na yi fata fata da ke a cikin gidan nan" "Kin ji ko ba ki ji ba? Na faɗa cikin tsawa da sauri ta ce" Allah ba zan ƙara shiga ba Umma." Dundu mai lafiya na yi mata a baya sannan na sake ta ina faɗin" Ki ma ƙara ki gani ɗin. Maza ki gyara mini falo wawiya kawai kin girma amma kina cin ƙasa." Sai ta yi gefe tana sosa kunnenta lokaci ɗaya tana faman hawaye daidai shigowar su Yallaɓai ganin tana kuka ya sa ya kalleni yana faɗin" Me ta yi miki kika da ke ta? Na yi masa banza na wuce, ina jin sa yana faɗin" Sadiya ki daina duka mini yarinya fa. Na faɗa miki ba na so amma kin ƙi jin magana ta." Na yi shigewata Bedroom ina masifa ni kaɗai yarinya na mace amma tana yin abubuwa irin na maza shi kuma Yallaɓai ba zai fahimci illa abun ba sai nan gaba ni ko ina uwa ba zan zauna in yi shuru ba. Daga yaran har Yallaɓan ban ƙara ganin su ba sai bayan sallar isha'i da ya zo ya shirya ya ce mini za su ta fi saboda su Khalipa na fito ina da jakar lilipop na ɗauko na ba su shi da Anwar na Yumna ne da Suwaiba ta kawo mata tun da ta shan zaƙi, abinci ma na fara ba ta mai ruwa ruwa kamar tea kwai da sauran su ruwa daman tun haihuwanta na ce zan yi exclusive Yallaɓai ya ce ya bi Exclusive da gudu ba takalmi in har na yi ma yarinyar sa mugunta na hana ta ruwa bai yafe mini ba, shi ya sa ba mu yi ba sannan ga shi ta sha madaran yara sosai shi ya sa kullum ƙara ƙiba kawai Yumna ke yi tana ba ma masu ɗaukanta wahala ni kaina sai ina nishi in zan ɗaga ta. Saboda Baby ba ta da hankali ta yi ɗamara za ta bi su, kallo ɗata kawai na yi mata ta shiga taitayin ta Yallaɓai na cewa ta ɗauko kayan makarantar ta, ta je can ta kwana cikin masifa na ce" Ba za ta je ba. "Saboda mene? "To me za ta je ta yi? Su Khalipa ne kuma ba ga su nan sati uku tare damu yau ne za su koma ba? "To ina ruwanki tana son ta je. Ba ta gaji da ganin su ba." "Sai dai ko ta mutu amma ba yau ba. Ba za ta je ba." Yallaɓai zai yi magana na tare shi da faɗin" Wallahi ba za ta je ba, ka ji ma na rantse." Yallabai ya kasa mgana ya kira sunana na yi kamar ban ji ba, na shafa kan Anwar ina faɗin su gaida mamannsu. "Bye Umma." "Bye Khalipa." Na faɗa ina ɗaga musu hannu, na yi shigewata ɗaki ina jin idanuwan Yallaɓai a kaina na ki yarda ma mu haɗa ido. Ai suna fita na sake fita falo suna ɗakin su Jidda na ninke ƙananun kayanta da ta wanke Baby na kan gado tana kuka saboda na hana ta zuwa. Ban yi wata ba ta ɗaka mata duka a baya sai ta banƙare tana ganina ta yi tsalle ta yi ƙarshen gado tana matse kukanta. "Kuka kike yi mini saboda wannan mganar? Sai ta fara girgiza kai cikin kuka kafin ta yi magana na tare ta da cewa" To kukan me kika hau gado kina yi mana a cikin gida? "Ba komai." Ta faɗa  tana hadiye kukan ta. Kallonta na yi kafin na wata dariya ina nuna ta da yatsa kafin na ce" Kin ga Jidda na yin haka? Ke ce mara jin magana ko? ke Yarinya ce? Nan ma ta girgiza mini kai zare mata ido na yi kafin na ce' Wallahi ya zama na ƙarshe in sake yi magana a gaban babanki ki ce za ki yi mini gaddama kika ga yadda zan yi ƙulin kubura dake a cikin gidan nan." "Ki yi hakuri Umma" Ta faɗa cikin kuka sai ta ba ni tausayi amma ban nuna mata ba. "Ki yi haƙuri Umma ba za ta ƙara ba." Jidda ta faɗa cikin sanyin ta sai na yi ƙyafci na fita daga ɗakin fuu har ina bango musu ƙofar na koma ɗaki ina masifa ni kaɗai daga baya sai na koma ina dariyan kaina. Na rasa haushin wa na ke ji? Yallaɓai ko yayan shi? Tun daga cikin Yumna na samu wannan ɗabi'ar abu kaɗan yake harzuƙa ni in ta faɗa kan abin da bai kai ya kawo ba. ****** Jidda ta gama jarabawarta gabaɗaya sannan Walimar saukar su kuma za a yi a farkon watan August ne, sai kawai na ce za mu haɗe shi da waliman gradution ɗinta da birthday ɗin ta na cika shekara  sha tara a duniya duk da ta ɗan gota amma zan haɗa mata kayattaciyar Walima. Yallaɓai ne wani lokacin ko na ce za mu yi sai ya ce a'a na dai yi musu tun suna yara amma suna kawo girma sai ya riƙa hanawa iya fa mu kaɗai a gida amma sai Yallaɓai ya ce wai birthday haramun ne. Wannan karon dai na ci karfin sa ya amince. Tun da har da Waliman saukar su sannan Amarya ta saka baki Gimbiya ba. Shi ya sa ya bari sannan ya saki kuɗi aka yi ta shirye-Shirye kuma dai daman Jidda is his fav Daugther. Ba wani gayya muka yi ba iya yan makarantan su na boko sai ƙawayenta na Tahfez su goma ne mata za su yi sauka sai maza huɗu. Sun yi ankon Hijabai masu ruwan ƙasa da dogayen baƙaƙen riguna sannan sun haɗa kudi kowa 20k amma Yallaɓai 50k ya ba ma makarantar suna ta godiya. Ni dai daga gida na yi mata memo da yar jaka ƙarama, ita kuma Gimbiya ta yi mata kayan su Snacks, Mimisco ta yi mata sabbin kaya kala huɗu har da jallabiyoyi da takalma sannan ta yi mata jaka na takarda babba a ka saka hoton ta. Ai na ci dariya domin ni da na ce zan yi na hoto Yallaɓai ya tuma ya ce bai amince ba sai ga shi Mimisco ta yi da ya gani sai ya kasa magana. Anty Maimuna ta siya maltina katan goma da ruwan gora. Anty Bahijja ta yo abinci mai rai da lafiya, Suwaiba ta kawo mata sabon alqur'ani da casbaha. Naja ta kawo mata darduma na Makka da hijabi, sauka ne Jidda za ta yi da walimar Graduation amma ta samu kyatttuka sai da na yi mamaki kaf dangin Babanta sun nuna mata bajinta. Hatta Babanta Usman ya aiko mata da 50k. Ya Auwal Laptop sabuwa ya aiko mata da shi Ya Hamza kuma ya gwangwaje da kayan su chaculte kala kala sama da guda biyar. Musbahu kuma ya gwangwaje ta da sabuwar waya. Jidda sai da ta yi kuka da ta ga irin kayan da a ka haɗa mata Baby na ta tura bakin ba a kawo mata ba ta ce sai ta yi ƙoƙari itama ta sauke Qur'ani sai a yi mata abin da ma ya fi haka. Kaf yan gidanmu suma sun yi bajinta matan da Mazan. Alhajimmu ya saka aka yanka mata tinkiya cikin dabobbinsa na ƙauye Baba Aminu ya taho da ita tare da kaji da zabbi shi ya sa Yallaɓai bai siya komai ba yana gefe iyayenta sun gama mata komai. Ranar saukar lahadi ce tun tara muna haraban tahfezz ɗin su Jidda. Kaf ɗin su Ya Aina sun taho Rahila ce kaɗai ba ta zo ba laulayi, Kawu Abba shi da Marwa da tsohon ciki Gimbiya tare da su Khalipa da Naja, su Maman farko da Hajiya Iya. Su Munnira da Hauwa hatta Mimisco ta zo ita da Anty Bahijja da Anty Maimuna. Kaf din su Musbahu da Adnan Muttaƙa da su Suwaiba suna wajen taro sosai Jidda ta gani sai hamdala. Yallabai na da ganawa da wasu mutanen sai daga baya yazo lokacin ma Jidda aka kira tana karatu. Sai da na yi ƙwalla da Jidda ke karatu, y'an uwanta na ta ɗaukan ta Video cikin burgewa. Bayan sun gama karatu aka kaddamar da su sha huɗu masu sauka aka ba su allon sauka. Mun yi hotuna tun da Adnan ya kira mai hoto, ta samu kyattuka, wajen malamai Kawu a envilop ya saka mata sabbin yan 1k A wajen a matsayin shi na Uba ta rumgume shi tana masa godiya. Duk mun zo da abinci da lemuka da ruwa da abun rabo. Tantin da muka zauna ba fariya ba sai muka zama abun kallo Jidda haka ta yi ta rabon jaka da Memo da abinci ruwa da maltina haka suke rabo. Baby kaf yan ajinsu ta gayyato suka ci suka sha, daga makaranta muka dawo gida muka ya da zango muka cigaba da walimar a gida. Mazan daman daga makarantan muka rabu da su. Mimisco har gida ta biyo ni ta ci abinci sannan ta tafi. Su Anty Bahijja sai la'asar suka tafi har Gimbiya ranar sai dare. Na aika da abincin walimar da naman da kayan Snacks da abin rabo na aika da shi Gwammaja da Ɗorayi suma su shaida. Sauran kuma duk wanda zai fita jakan sa cike da kayan walima. Rahila ma na ba da saƙo akai mata Halima ce ba ta zo ba a cewar Gimbiya ba ta da lafiya ne, amma ni ban damu ba ta kanta na ke yi ba. Ranar gidana cike da jama'a har dare ranar ba gidana Yallaɓai yake yi ba sai washegari ya dawo gidan, sannan ya ga kayattukan da Jidda ta samu sai da ya shafa kanta kafin ya ce. "Good girl. Am so proud of you Daughter." Ga waya ga laptop, shi Yallaɓai Tab ya siya mata sabuwa, tsohuwar ya ce ta bar ma Baby, da take ta tura baki ita ba a siya mata komai ba ya ce ta ƙara ƙoƙari itama za a siya mata. Hotuna sun yi kyau na yi ta carbi a status mutane nata saka albarka bayan kwana biyu na saka ta , ta shirya ta je Gwammaja ta kai ma Nene allon saukar ta, daga can ta wuce Ɗorayi ta kai ma su Alhajinmu suka gani suka saka albarka. Kuɗin da Jidda ta samu na tattara su na siya mata ɗan kunnen gold na ba ta ta maƙala a kunnen ta. Sai da na yi shawara da Yallaɓai shi kuma ya ce kudi na Jidda ne in ta amince sai na siya mata. Da na tambayeta  tace mini tana so shi ne muka je tare kasuwa na siya mata. Amma na cire 30k a ciki na ƙara jarin hijabai da na ce ma na ara sai ta ce ba aro ba na baki Umma, na yi ta saka mata albarka. Adanan ya kai ta ta yi register ɗin layi tun da ta yi waya. Ta sha dokoki wajen Yallaɓai ban da shige shige WhatsApp kawai ta buɗe lambobi daga na mu sai na kawunta sai na yan ajinsu sai na y'anuwanta su kenan a cikin wayar. Ganin za ta fara zaman gidan kafin cuku cukun makaranta sai ta ce mini tana son ta koyi kayan su Snack haka sannan tana son koyon kwalliya na aminta da shawaranta sai na yi ma Yallaɓai magana shima sai ya yi na'am da mganar ya ce ta nemi in da ake yi sai ya ba ta kudi ta shiga.. Gimbiya na yi ma mgana saboda na ga ita duk ta iya su, ni kuma ba su dame ni ba, ita ta yi ma wata da ta sani mai yin snack sosai ta buɗe online class aka saka Jidda sannan ta na yin na gida sau biyu a sati alhamis da jummaa wata uku 20k Yallaɓai ya biya mata ta fara zuwa. Sannan na kwalliya ni kuma da na ke yi followimg ɗin su a I.G na yi ma wata Zahrajj magana da bayanin kuma ita a sharaɗa take amma tana da shago a nan zoo road wajen kamfanin Yallaɓai. Da na yi ma Jidda rigister ita sau uku ne a sati jumma da asabar da lahadi da safe. Shi kuma na Snack daman da yamma ne. Jidda tana da naciya da dakiya in dai ta sa kanta za ta yi abu. Ko sati biyu ba ta yi da fara zuwa ba ta fara iyawa. In ta dawo gida sai ta gwada Yallaɓai kuma ya ɗaure mata kugu ya sa aka kawo mata fulawa da siga sauran kayan kuma ya ba ta kuɗi ta siya kwalliya kuma Tariq ya aiko mata da babban kit na ƙwalliya, Baby ta yi jin haushi ta ce an fi son Jidda a kanta in ta yi mata dariya. Maganar gaskiya Jidda na da farinjinin jama'a sosai saboda yanayinta na sanyi da rashin hayaniya. A tsukin Marwa ta haihu an samu mace ta ci sunan Innayi ana kiran ta Afiya muka tafi Rano suna har Gimbiya ta je, itama cikinta har ya turo gaba. Kwana uku muka yi a gidan Marwa ni da Munnira da Hauwa da su Ma'u da Rahila sai Ya Balki. Su Anty Bahijja sun zo suna amma ba su ko kwana ba, dangin Baban Marwa ma sun zo amma washe-gari suka koma mu kaɗai aka bari muka yi soye muka natsa. Ana gobe za mu koma gida ne muka yawata garin mun je gidan su Kawu gidan su Nene kenan daga nan muka je gidan su Hauwa. Na karshe shi ne gidan su Gimbiya. Hajiyar Tafida na nan da ƙannen Gimbiya da suka zo gida. Ƙiri-ƙiri suka yi mana wulaƙanci ita dai Hajiyar ta karbe mu faram faram amma ƙannen Gimbiya saboda ni a wulakance suka amsa gaisuwar mu. Shashen Mamansu Sameena me kawai aka karrama mu. Bayan mun fito daga gidan Munnira na ta kumduma zagi ni da Hauwa muna yi mata dariya. Na ɗan ji haushi amma ban damu ba daga baya na watsar da abin. Washegari muka koma gida Kano kuma ko a labari ban taba faɗa ma Yallaɓai ba. ***** Yallaɓai tuni ya zagaye filin shi an saka get har an fara gini gadan-gadan domin yanzu Yallaɓai kuɗi yake samu mahaukata. Kwangiloli sama da biyar yake yi a lokaci ɗaya. Ba zato ba tsammani ban ma saka rai ba Yallaɓai ya siya mini mota a watan November ranar goma ga wata ranar da Yunma ta cika shekara ɗaya. Har na shirya mata party a gida Jidda ta yi mata cake tun da yanzu ta ƙware, sai ga Yallabai da maƙullin mota ya siya mini vibe fara, amma ba sabuwa ba ce sai dai ba ta sha miya ba. Na daka tsalle na ruƙumƙume Yallaɓai ina faman ihu da murna ni da yara shima farinciki yake yi ganin yadda gabaɗaya na rikice saboda murna. "Mota ka siya mini Yallaɓai? Innalillahi." Na ke faɗa na ma kasa mgana saboda murna da farimciki. "Mu je ki ganta tana haraba. Ita na tuƙo, tawa na ce Musbahu ya taho mini da ita daga baya." Ai sai gani ni da yara muna rige-rigen fita har da Yumna dake tafiya itama har ana neman ture ta Yallaɓai ya sunkuto ta ya biyo bayana. Da na ga motata sai na dafa ta kawai na fashe da kuka. "Yallaɓai wannan mota ta ce? Shi da yara suna ta mini dariya ganin ina kuka sai ya ƙariso ya rumgumeni shi da Yumna yana bubbuga bayana lokaci ɗaya yana faɗin" Kin yi mota saura ki je ki sauke farali My Sady." "Yallaɓai har saudiya za ka biya mini? "In sha Allahu Sadiya ta." Ai sai na ƙara fashewa da kuka na rumgume Yallaɓai na ƙamƙame shi ina ɗaga murya cikin kuka amma na kasa magana. "Shii. Bar kuka yau ranar farimciki ne ok? Ya faɗa yana ɗago fuskata ya fara share mini hawaye. Yumna na ta ya shi. "Kin ga har Yumna ma ba ta son ganin Umman ta na kuka." "Yallaɓai kukan farinciki ne" Na faɗa wasu hawaye, na gangaro mini na farinciki. "To za ki karar da hawayen na ki ne a yau? Ki adana su saboda ba ki ga komai ba. Tun da Ubangiji ya wadata ni ni kuma zan yi ta saka ki farinciki har ƙarshen rayuwar mu Sadiya ta." A gaban yara na yi ɗage na sumbaci bakin Yallaɓai sannan na sake shi ina kallon shi kafin na ce. "Na gode Yallaɓai. Ubangiji ya yi ma dukiyarka albarka. Na gode." Na faɗa ina ƙara gocewa da kuka Yunma ma sai ta fara. Baby da Jidda na can suna santin mota, ko ta kan mu ba su bi ba, "Bar kuka nan kin ga Yunma ta fara." Ya faɗa yana bubbuga bayana. Amma na kasa tsaida hawayena. Sai da ya share mini sannan ya saka ni na shiga motar na yi bismilla da addu'a.. "Allah ya tsare Hanya Madam me" Yallabai ya faɗa yana lekowa ta window Yunma ta ya fito ni, na karɓeta ina fadin" Amin Sadaukina " Babby har ta kame a gaba Jidda dai baya ta buɗe ta shiga tana faɗin. "Umma tubuli Allah ya sa ki kashe ta lafiya." "Amin Amin Jidda. Yallaɓai saura Jidda ka siya mata ta ta motar" "Da a ce nan garin za ta yi makaranta da na siya mata amma tun da zariya ne sai dai in ta gama in sha Allahu." "Allah ya amimce Yallaɓai na." Jidda ta kalli Babanta kafin ta ce" Mun gode Yallabai Allah ya karo buɗi." Baby ta ƙyalƙyace da dariya kafin ta ce" Abba Yallaɓai " Ni da shi muka yi dariya gabaɗaya. Daran nan da kyar na iya barci gani na ke yi kamar mafarki waahegari ni na kai Baby makaranta a mota ta, daga can ɗorayi na dira Yallaɓai na bari a gida shi da Jidda daman na ce sai in da mai ya ƙare. Sai da su Gwaggo su ka ganni da mota na ce su fita ita da Alhajinmu suna ta murna da saka albarka. Daga nan sai gidan Ya Abubakar shima na kai masa ya gani. Na je har gidan Ya Aina na nuna mata sannan na koma gida na ɗauki hoton motar na yi status da ita sannan na yi caption a kasa da cewa. "Alhamdulillah. Yallaɓaina ya gwangwaje ni da mota jiya. Matar Yallaɓai ta yi mota jama'a ku ta ya ni murna." Nan da nan aka yi mini caa Sadiya kin yi mota! Congratulaton Mimiaco ta ce kin chanchanta ta Yallabai. Ita ce kaɗai ta yi mini murna sai su suwaiba da Nasara da Jamila. Gimbiya ta gani amma ko Allah ya tsare ba ta ce ba, Ya Hamza ya turo mini rawa kafin ya ce" Lalle Yallaɓai ya iya gwangwaja danƙari. Allah ya tsare " Adanan kuwa faɗi yake yi" Ya Sadiya kin rigani yin mota? Na ce to ka zauna ni ai na yi gaba. Su Maijidda da Samira suna ta mini fatan alheri. Munnira da Hauwa gida suka zo yi mini murna, da za su tafi na tuka su na kai kowacce gidan ta. Ni fa tun da na yi mota na dai na zaman gidan ni ce can ni ce nan, har Jidda ni ke kai ta wajen koyon kwalliyarta tun da sun gama na snacks, sati mai zuwa ma zata je zariya yin POS UME. Ni ce har Gwammaja na kai ma su Nene mota suka saka albarka. Lokacin Jawahir da Umma Salma sun zo ganin gida suma sun saka albarka suka ce ai na caancanci mota na kuma chanchanci na shiga na fita. Yallaɓai ai nawa ne an sha gwagwamarya. Wajen sati biyu ban zauna a gida ba, Yallaɓai ya gaji ya ce na zauna na huta har abada fa motar nan tawa ce sannan na hakura gani nake yi kamar zai ce na kawo key ɗin an fasa za a mayar ma da masu shi. Faridan Tariq ta ce itama a satin Tariq ya siya mata na ce mun yi amarya a tare. Anty Zabba da muka yi waya ta ce ta yi mini murna yayan shi da ya ji sai ya ce ya kyauta muka yi ɗan tsegumi har tana ce mini yanzu sai Gimbiya ta daina yi mini gani gani anan ne ma na ke faɗa mata ita da su Anty Bahijja ba su yi mini murna ba. Ta ce na raba su hassada ne da bakin ciki na ce sai dai ya koma musu kuwa. Ba sa gabana ta ce ya fi haka. Ni ina gida ban san wainar da ake toyawa ba. A satin da Jidda ta tafi Zariya gidan Ya Hamza ta sauka bayan ta gama jarabawar ba ta dawo Ya Hamza ya ce sai sakamako ya fito za ta dawo. A Safiyar litin Ni kaɗai a gida Baby na makaranta daga ni  sai Yumna da ta koyi shegen ɓarna tana tafiya turba turɓa da ƙyar, Yallaɓai ba gidana ya kwana ba bai kuma shigo da safe ba sai na yi tunanin fitan gaggawa ce ta kama shi, da man wani lokacin in bai samu dama ba sai dai mu yi gaisuwar ta waya. Wajen sha ɗaya na safe Sameena ta kira waya muka gaisa tana yi mini murna. Har ina mata tsiyan ta makara ta ce mini wallahi ba ta ji labari ba sai satin nan da ta je gida ta ji ana ta rigima kan motar.  Ashe har yaji Gimbiya ta yi akan Yallaɓai ya siya mini mota. Saboda ta yi masa maganar siyayyan kayan haihuwa ya ce ta jira sai ya siya mini mota sannan zai dawo kanta shi ne ta suka yi tsiya fata fata har ta yi yaji. Kwananta hudu a gida amma ta dawo shekaranjiya yara ma can Gwamnaja aka kai su wajen Nene. Na yi ta mamaki domin Yallaɓai bai ba ni wata alama ba, tun da ni dai bai zo gidana ya kwana ba ashe shi kaɗai ya riƙa kwana don kar na fahimci wani abu. Sameena ta ce tana gidan shekaranjiya asabar Yallabai ya je can Rano tare da Kawu aka zauna ana ma yar da magana Gimbiya tana ta kuka tana faɗin ba ya yi mata adalci komai ni komai kamar na shanye sa shi ne ya ce e na shanye sa ne, itama za ta iya shanye sai bai hana ta ba mota ne ya siya mini haihuwa kuma tun da ba gobe ba ne ta jira ta gani in bai ba ta kudin siyayyan ba sai ta yi magana. Sai da Tafidan Rano ya shiga maganar sannan ta biyo sa suka dawo gida tare. Na jinjina lamarin Gimbiya a raina sosai. Hasashena ya kasa hasaso mini tsanar da matar nan ta yi mini ta zo ta same ni da mijina amma tana neman ta hana ni zaman lafiya! Kwana na yi ina auna abin a kasan raina wai ta yi ya ji saboda an siya mini mota. A bakin Sameena na ke ji tana cewa itama ai ta yi ta yi ya sauya mata mota ya ƙi. Amma ni ya siya mini shi kuma ya ce ita tana da shi, ni kuma ban da shi shi ya sa ya fara siya mini tun da ni ce uwargida. Ta jira in ya samu kuɗi sai ya sauya mana gabaɗaya ta ce Hajiyarsu na ta yi mata faɗan ita ba ta ga ƙoƙarin da ya ke yi ba miye don ya siya ma matarsa mota shekara nawa suna tare bai siya mata ba sai yanzu? Ita na za ta gode ma Allah da ni'imar da ya yi mata sai ta bari sheɗan na yi mata susa a kunne. Ta bakin Sameena ta ce bakin ciki ƙiri kiri Gimbiya ta nuna akan an siya mini mota. Ni ko da gayya na ce ta ko fara gani in sha Allahu sai dai ta mutu in ba za ta iya ba ta fi ta bar ni gidana da mijina daman a ciki ta zo ta ganni na matsa mata amma shi ne za ta yi mini butulci. Kamar in yi ma Yallaɓai magana sai na fasa ganin shi bai faɗa mini amma na riƙe ta a raina, a satin da na ji maganar muka haɗu a Gwamnaja Maman farko ce ta zame daga bene ta samu gocewa shi ne na je dubata kuma da motar na je  a ɗakin Nene a gaban Anty Bahijja da ita kanta Nenen na kalli Gimbiya na ce mata. "Gimbiya Yallaɓai ya siya mini mota kowa ya yi mini murna ban da ke ko ba ki sani ba ne? Da gayya na faɗi haka, ai sai ta ji kunya ta fara kame kamen wai kwana biyun nan ba ta ji daɗi ba ne ta so ma ta zo har gida ne ta yi mini murna. Kallonta kawai na ke yi ni sai na raina wayan ta. Matar da ke da shago guda amma ɗan abin da Yallaɓai yake yi mini ya hana ta sukuni. "Allah Ya sanya alheri." Na amsa da Amin ina kaɗa key ɗin hannuna. "Kema Anty Bahijja ba ki yi mini murna ba." Duk na kunyata su, ita da yake akwai isa kai tsaye ta ce" Kin kawo mini ita har gida ne kika ga ban yi miki murna ba? Sai na nuna mata na fita iya bariki kai tsaye na ce" Ban kai miki gida ba amma yau ga ta can a haraba na zo da ita. In za ki fita ki duba ta, ki saka albarka Anty Bahijja." Sai ta kasa magana Nene na wajen ta saka baki ta ce ba su kyauta. Abin alheri ne ya same ni yana da kyau su yi mini murna sai ga shi jiki an sanyaye da zan tafi suka fita ganin motar suna saka albarka na ciki na ciki. Halima ina haraba ta shigo yadda ba ta gaisheni ba, nima ban nuna na ganta ba, na shige mota ta ni da Yumna na yi tafiyata suka bini da kallo har na fice a raina na ce ku yi ku gama. Babu yadda kuka iya da ni nan gani nan bari ɗumammen Manya. *Janafty**TKGB3M013* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732 Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰 Shuru na yi da bakina kamar yadda Yallaɓai ya yi shuru bai faɗa mini ko ya nuna mini sun samu matsala da matarsa saboda ya siya mini mota. Nima sai na yi kamar ban ji wata magana ba na cigaba da sabgogin gabana. Addu'a kawai nake yi ma Jidda akan Allah ya ba ta sa'a ta samu gurɓin karatu a jami'ar bayero saboda ta ƙwallafa rai sosai akan makarantar. Cikin ikon Allah satin ta ɗaya a Zaria Khaleesat ta kira ni tana faɗa mini Jidda ta ci Jarabawar da ta yi, na yi ta murna da farinciki Yallaɓai na dawowa na faɗa masa sai ya ce mini Jiddan ta kira shi ta faɗa masa, har yana cika baki da cewa shi da man ya san abin da ya haifa he is sure za ta tsallake, baki na saki ina kallon Yallaɓai yana yaɓon ƴar sa, har yana kallona yana ce mini ƙwakwalwarsa ta biyo shi ya sa take da hazaƙa. "Me kake nufi Yallaɓai? "Ni ai ban ce komai ba na dai ce Jidda ƙoƙarina ta ɗauko. Shi ya sa duk abin da ta yi ma himma take samun nasara da taimakon Ubangiji." Ya faɗa yana ƴ'ar dariya. "Allah Ya ba mu sa'a." Na faɗa kawai saboda ba na so maganar ta yi tsayi amma Yallaɓai bai so haka ba kawai sai ya kalleni yana sake faɗin" Amma kin ga Baby ina jin kanki ta ɗauko sam ba ta kai Jidda ƙoƙari" "Au ni daƙikiya ce kake so ka ce ko Yallaɓai? Na faɗa ina masa wani kallo sai ya fara dariya yana faɗin" Ni yaushe na ce miki daƙiƙiya? Ban bari ya cigaba da magana ba na yi wucewata ina faɗin" Sai kuma ka yi. Na gode da cin mutumci Yallaɓai. Ka ji na ce Na gode." Jin yadda na yi maganar ya san na yi fushi sai ya biyo ni ciki yana rage mini murya, da ƙyar na haƙura sai da ya yi mini rantsuwa da cewa da wasa yake yi sannan na aminta da shi har na saki fuska muka cigaba da hira. Daman da daddare ne ya zo yi mana sallama tun da gidan Gimbiya zai kwana yau da gobe. Ranar jumma'a Jidda ta dawo, gidan Khaleesat na saka aka aika mini da saƙon hijabai ta taho mini da shi, ta dawo a jigace ta sha wuya motarsu ta yi ta lalacewa a hanya sai mangariba ta iso. Yallaɓai ya kirani ya fi sau biyar yana yi mini masifan ya zan haɗa yarinya da kaya na san ba ta taɓa tafiya waje mai nisa ba, ko da za ta tafin ma da kyar ya bari da ace baya da wani abin da zai yi shi zai kaita. Amma sai da ya kaita  tasha yana jadadda mata ta kula da kanta, kafin ta kai ko ban san sau nawa ya kira ta a waya ba, to yau ma za ta dawo ya yi ta kiranta daga baya sai ya daina samun ta a waya shi ne zai sauke faɗan shi a kaina, tun ballatana da Jiddan ba ta taso da wuri ba saboda jiran sakona. Ai ni sai shuru da ba da haƙuri tun da dai ba ni da gaskiya. Sai da ta shigo gidan nan na samu sauke numfashin salama na kira Yallaɓai na faɗa masa duk da haka bai fasa faɗin abin da ke ran shi ba. "Sai yanzu ta iso? Sadiya ba ki kyauta mini ba, kawai ki haɗa yarinya da kaya ki wahalar da ita fisabillahi kin kyauta kenan? "Na ce ka yi haƙuri Yallaɓai ganin za ta dawo ne ya sa na ce ta karɓa ta taho mini da shi." "Ni dai ba na so. Kar ƙi kara yin haka. Ba ta fa taɓa tafiya ta yi ita kaɗai ba" Mamakinsa ya kama ni, Jidda kamar wata ƙaramar yarinya ni dai shuru na yi har ya gama bambamin sa ya kashe wayar ban ƙara ce masa komai ba, tun da tun ɗazu nake ba shi haƙuri amma kamar ya haƙura sai kuma da ya ji ba ta dawo ba sai ya fara mini masifan wai ni na ja. Ni fa daman na sani Jidda a wajen Yallaɓai ta musamman ce, in dai lamarin da ya shafe ta ba ya zaune ba ya tsaye, ya yi ta wani kafa kafa da ita kamar wata ƙaramar yarinya. Ai ban ma ga kafa kafa ba sai da ya dawo gidan haka ya zaunar da ita yana tambayanta ta sha wahala? Ta gaji ne ba dai ta samu wata matsala ba ko? Tana dariya tana faɗa masa ita lafiyanta ƙalau, ba ta samu wata matsala ba kawai lalacewar motar ne, har yana tattaɓa wuyanta, ya ji ko tana da zazzaɓi, ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah na kasa mgana. Na ɗauka Yallaɓai ya gama faɗan shi amma ina yana ganin hilimin saƙon da Jidda ta taho da shi faɗan shi ya dawo farko wai da gangan na yi kamar Jidda ne zan saka ta ɗauko uban kaya haka? Wai har Yallaɓai na faɗin an ya ina da tausayi kuwa? Baki na saki kafin na rufe ina faɗin" To wai duk wannan faɗan na mene kuma Yallaɓai? Ina ce ba ga Jiddan ta dawo ba? Kuma ita Jiddan yarinya ce kar ka manta she is 19yrs kuma jami'a za ta shiga so Jidda ba yarinya ba ce, ka ma daina jijiyan wuya ko Baby ta wuce yarinya ballantana Jidda." Na faɗa cikin jin haushin sa, to ya dame ni magana ta ƙi ta ƙare kamar cin kwan makauniya, maimakon ya yi shuru sai ya ma ya harzuƙa ya fara faɗin duk haƙurin da na ba shi na ƙarya ne tun da ban yi nadaman abin da na yi ba ina cewa wai Jidda ba yarinya ba ce. "Za ki haɗa da kanki ne? Kin ga ko har yanzu yarinya ce." "Jaririya ce Nono take sha Yallaɓai" Sai ya yi shuru bai ƙara mgana ba ni kuma a lokacin na hau sama na miƙe ina faɗin" Kayan fa ba akanta ta ɗauko su ba. Yadda kake wanman faɗan ko dakon su ta yi daga Zaria zuwa nan sai haka" Ina gama faɗin haka na ɗauki Yunma muka bar musu falon haba ba ta yuyuwa kamar wata Jiddan gwal ne, ai ganin yadda na yi cuɗuncuɗun da fuska na haɗe rai ya san halina shi ya sa sai ya bar maganar amma da ban yi masa haka ba abin mamaki ba har ya gama kwana biyun shi kullum sai ya ta da maganar ina dalili. Waɗanan Hijabai ai ban siyar da su cikin daɗin rai ba domin na tuna da bambamin faɗan da Yallaɓai ya yi ta mini raina sai ya sosu, in ta yi ƙyafci ni kaɗai saboda takaici. Zan ga yadda zai yi in ta samu admission za ta tafi makaranta sai na ga ƙarewar so da ƙauna. Kuma ba daɗewa suka ba ta Admission, da kuma Course ɗin da ta zaba wato Phamarcy, nan da Yallaɓai ya fara yi mata shirin makaranta privision kamar za a buɗe shago komai Jidda ta ce tana so ya siya mata har da ma wanda ba ta ce ba, tare suka je kasuwan shi da Jiddan da Baby ni ina gida ko gayyata ta bai yi ba kuma na so ya ba ni ragama ni na samu riba a ciki amma Yallaɓai ya yi fuska ni kuma ban yi masa mgana ba saboda kar ya ranfo ni, na zura masa ido kawai ina ganin ikon Allah wajen uban da yar gabaɗaya. Da yake sai January  sabuwar shekara za ta yi rigistration ta koma sannan su fara karatu. Shi ya sa shekaran na kamawa na 2022 ana buɗe portal ɗin biyan kuɗin makaranta ya ɗauke ta suka tafi. Ranar cikin ikon Allah zai je Kaduna sai ya biya ya sauke ta a cikin makaranta da in ta gama abin da za ta yi ta wuce gidan Uncle Hamza. To kwanan ta biyu tun da har hostel sai da ta tsaya ta yi clicking ta samu Queen Amina Room of 12 ta ce su huɗu ne a ɗakin ta samu loka da gadon ƙasa, a gida daman Babanta ya siya mata katifa mai kyau, ranar da Yallaɓai zai dawo ya biya ya ɗauko ta suka dawo tare bakin shi ya huta nima kunnuwana suka huta. Washegari kuma ya saka Adnan ya rakata firstbank ta buɗe, banki saboda makaranta. Jidda duk ta zagaya gidajen yan'uwan Babanta ta yi musu sallama. Mimisco ta ce na ba ta hijabai guda biyar za ta biya kuɗin. Su Anty Bahijja kuɗi duk suka ba ta, har Gwammaja ta je da Ɗorayi ta yi musu sallama su Ya Aina a waya na faɗa musu suka yi fatan Allah ya sa a fara cikin nasara. Ta je har gidan Gimbiya ta yi mata sallama sai ta ba ta takalmi cover shoe guda biyu sai abaya guda ɗaya da kayan kwalliya. Kawu kuma ya aiko mata da dankalin turawa da kwai da yawa, dankalin ma kaɗan na ɗibar mata kwan kuma Yallaɓai ya ce sai ta je can ta siya saboda zai jigata a hanya kafin su kai. Ranar lahadi 28january Jidda za ta tafi makaranta za ta bar mu da kewa. Duk da Yallaɓai bai ce da ni za a je ba amma na yi shiri ni da Baby da Yumna na ce zamu raka Jidda har makaranta itama na ta murna ashe Yallabai ya shirya da wacce zai je, sai ana gobe tafiya ranar asabar kenan ya ga ina ta shiri, na yi mata dambun nama ita kuma ta yi ma kanta su Snacks cokes, donut, cincin cake kaɗan ta yi saboda lalacewa sai miya da ta yi mai naman rago, sai ƙuli da na siya mata mai yawa yaji kuma Munnira ta dako mata mai daɗi ya ji tafarnuwa, Hauwa ta aiko mata da garin rogo mai kyau, da kansu suka zo suka kawo mata tare da yi mata yan nasihohin ta yi abin da ya kaita ba ruwanta da rayuwar makaranta ta tuna da tarbiyan da iyayenta suka ba ta. Sai bayan tafiyar su na zaunar da ita na yi mata nawa. Karatun Qur'ani salla da azkar kar ta yi wasa da su ta dake da karatu ban da shagala da ƙawayen banza duk abin da ya shige miki duhu ga gidan Uncle ɗin ki ne, in kina jin kewan gida ki je ki yi musu Weekend na yi mata fada sosai tana kuka ta ce in sha Allahu ba za ta saɓa magana ta ba. Ni daman ba na jin ta Jidda ba ta da rawan kai, da man dai Baby ce uwar rawan kai. Ina cikin yi mata nasihan sai ga Yallaɓai ya shigo jiya da yau duk a gidan Gimbiya yake. Ganin mu zaune a falo ga su Jidda duk a ƙasan cafet sun natsu ya sa ya ƙariso yana faɗin. "Me ake tattaunawa na ga har Yumna ta yi ladabi" Sai da ya faɗa na kalleta can gefen Baby ta yi zuru tana kallona kamar tana jin abin da na ke faɗi, sai na hau dariya ita kuma ganin babanta yasa ta mike da gudu tana faɗin" Aba Aba." Da yake ta fara mgana tana kiran Aba Uma, Ya Jido da Baby ita dai na yi na yi amma Yumna bakin ta ya saba da Baby ba ta kiran ta Yaya. Ɗagata sama ya yi yana faɗin" My chubby Daugther." Saboda har yanzu Yumna da kibanta. Tana ganin ta a hannun babanta sai ta fara zillo tana kamo habarsa, ita a dole sai ya yi mata wasan da ya saba mata. Ɗaga ta sama ya yi ya dawo da ita haka ya riƙa yi mata sai ka ji ta fara bangala dariya. Yumna daman ai yar son mugun wasa ne ko jiya sai da na cauleta da bulala Baby kuma ta ci dundu saboda sun ɓata mini falo, wai da sunan wasa, bai zauna ba sai da ya ga ta kusa siƙewa saboda dariya sannan ya zauna ya zaro chaculate a aljihun wandon jikinsa ya ba ta ɗaya, ɗaya ya ba ma Baby ɗayan kuma ya ba ma Jidda amma ni ina zaune bai ba ni ba. "Ina nawa abin daɗin Yallaɓai? "Kin yi girma da yawa abin yara ne." "Lalle na ga son kai." Na faɗa ina girgiza kaina kai tsaye ya ce mini nima na so kaina bai hana ni ba. Na ce ya ci bashi ne wallahi zan rama ya ce sai dai na rame. Kiran sunan Jidda ya yi ganin ta yi shuru tana ɗagowa ya gane ta yi kuka. "Jidda me ya faru? Kukan kewan gida kike yi? Sai ta gyaɗa kanta da hannuna ya nuna mata kusa dashi yana faɗin" Taho nan Mamana." Sumu sumu ta tashi ta ƙarisa kusa da shi ta zauna Yumna na kan jikinsa ya buɗe mata chaculte ɗin ta fara sha duk ta yi dama dama da shi a bakinta. "Kar ki damu kin ji ko? Zariya ai gida ce ba wata matsala ki dai ki ma yar da hankalinki a wajen karatu. Make us proud Jiddan Abban ta." Sai ta gyaɗa mai kafin ta ce" In Allahu Abba." Kanta ya shafa kafin ya ce" Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki sa'a a dukkan karatun ki." Ni da shi da ita muka amsa da Amin sai ya cigaba da ce mata in ta ji ganin gida kawai ta hayo mota ta taho, in kuma ba dama ta kira shi a waya shi sai ya je ya ganta. Sannan ga Uncle ɗin ta Hamza ga Abban ta Tariq. Duk wandr ta ke son gani ko take bukatar wani in ta yi musu mgana za su yi mata ta ce to Abba. Ina daga gefe na ce" Tariq ai ya yi nisa Ya Hamza dai da suke kusa. Da na kira shi ina fada masa ga Jiddan nan za ta zo makaramta a kular mana da ita. Kañiyarki Dubu ya ce mini wai ni ce na ke masa kashedin ya kula da Jidda? Na ƙarishe faɗa ina dariya. Yallabai ya ce shima sun yi waya kusan abin da ya ce mishi shima haka ya ce masa amma shi bai zage shi ba, amma dai ya ce masa daga shi har ni kar mu ƙara kiran shi a kan Jidda tun da mu ba mu da kara. "Kai Ya Hamza ba dama." Na faɗa ina dariya. Yallabai na taya ni dariyan Ina maaganar ko Weekend bayan sati ta ji kewan mutane sai ta je ta yi musu acan. "Bai yi nisa ba? "Ba wani nisa. Ina samaru ina pizzet? Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Ya yi nisa mana. Karatu Jidda za ta yi so in dai ba hutu suka samu ba ba zan so ta rika barin cikim makaranta ba." Sai na yi shuru kawai ina kallon Yallaɓai da mamaki ba ya so ta je gidan Yayan nawa ne me ya ke nufi da maganarsa? "Akwai wata ƙawar Daughter da suka yi karatu tare a BUK. Tana auren wani H.O.D na department ɗin Computer Science kuma acikin Abu samaru suke zaune. So Daughter ta ce ta yi mata mgana nake ga zai fi in ta ji kewan gida ta je wajenta tun da duk cikin makarantar ne." "Ba shakka." Na faɗa ina kallon Yallaɓai yadda ya dage yana bayani. "Ai kin ga ba za ki haɗa cikin makaranta da wajen makaranta ba ko? "Ba zan haɗa ba. Amma ai ba garin za ta bari ba, duka duka mintina nawa ne tsakanin makarantar da Gidan Ya Hamza? Kenan kana so ka ce ƴa ta tana karatu a garin da Yayana ke zaune kenan ba za ta je ba ko? Sai gidan wata bare ka amince ta je kenan? Na faɗa ina yi masa wani kallo, kallona ya yi kamar zai yi magana kawai sai ya ja tsaki ya kauda kai yana gyara ma Yumna bakin ta. Na ji zafin tsakin da ya yi mini, amma ban nuna ba sai na yi shuru ban ƙara mgana ba a ƙasan zuciyata na ce na ga mai hana ta zuwa gidan Yayana. Ko shi Yallaban bai isa ba ballanta wata matarsa. Gajiya na yi da zaman na ga sai magana yake yi da yayan sa. Sai kawai na mike na miƙa hannu na ƙarɓi Yumna ina kallon Jidda da Baby kafin na ce" Ku kwanta da wuri kun san muna da tafiya gobe" "Ina za ku je? Yallaɓai ya tare ni lokaci ɗaya yana mai kallona. "Za mu yi ma Ya Jidda Rakiya makaranta ne Abba.". Baby ta famshe ni, ga mamakina kawai sai na ji Yallaɓai na faɗin" Ke da wa kenan? "Ni da Umma da Yumna" Na juya zan bar falon saboda nu na gaji da wannan shan ƙamshin na Yallaɓai kawai sai na ji yana faɗin" Ke dai da su Khalipa. Ni Umman ki ba ta faɗa mini za ta je ba. Tare da Daughter na shirya ita da ta ce mini za ta je." Kan uba.! Na faɗa a fatar bakina, na juyo ina son kallon fuskar Yallaɓai amma ya ƙi bari mu haɗa ido. "To Umma fa Abba? Jidda ta tambaya cikin ƴar damuwa. "Ba ta ce za ta je ba an riga ta." Haka ya faɗa ko a jikin shi, saboda bakin ciki ya sa na juya kawai na shige ta kitchen zuwa ɗakin barcin mu. Ni Yallaɓai ke nuna ma iyakata akan y'ar da na haifa, wai ni ina uwar Jidda yana faɗa ma yayan shi cewa ban tambaya da wuri ba an rigani. To in sai na tambaya sai dai kar na je in har ya ga bam chanchanta ba, to ya je da wacce ya ke ganin ta cancanta. Na kasa sukuni maganar Yallaɓai ya tafasa mini zuciya shi ya sa da ya shigo mini sallama zai tafi ina saka ma Yumna Pampers lokacin da ya ce mini zai tafi sai da safe ko amsa shi ban yi ba shima ya san tsiyar da ya yi sai bai damu da ya tsaya ba ya fice na raka shi da uwar harara. Ni fa akan iyakata da Yallaɓai ke nuna mini akan matarsa haƙurina ya kusa ƙarewa. Ni ina yi mata kara amma ni ba ta yi mini kuma yana gani bai taɓa magana ba, sai a kaina ne sai ya riƙa cin kasuwarsa yadda ya ga dama to bai isa ba. Kwana na yi da takaicin Yallaɓai tun asuba da muka tashi ba mu kwanta ba saboda tafiyar Jidda. Ban shirya ba mutumin da ya ce wata ta rigani ai in na shirya sai ya tozartani a gabanta shi ya sa sai na kama kaina amma fa bai ci bulus ba wallahi. Ƙarfe tara da wani abu suka shigo gidana shi da Gimbiya da su Khalipa da suka sha gayu, Gimbiya ce ta ba ni mamaki cikinta fa ina jin ya kusa shiga wata na takwas amma ita ya zaɓe ta taje tun da ita yake so, ni kuma banza a banza ba zan je ba. Ko daga ganin yanayin dressing ɗin da ta yi na san ta shirya ma tafiyar. Ta ci wani leshi doguwar riga ta ɗora ɗauri ta zubo kitson ta na baya da ta yi, fuska ta sha kwalliya har da jan baki mayafi a saman kafaɗa tana wani cin cimghm ita yar iska. Ban ji haushin ta ba kowa ya jawo mini wannan renin ba sai Yallaɓai shi ya sa ni ko kallo bai ishe ni ba. Har da abinci na ga sun zo da shi, shi ma shadda ya saka mai kalan sararim samaniya shi da su Khalipa suka yi anko. Yallaɓai har da babban riga an ci uban gayu sai na fahimci kawai ya fake da guzuma ne zai harbi karsara. Amma wannan tafiyar ba ta Jidda ba ne ta su ce shi da matarsa ne. Saboda ma ta ƙure ni tana ganina ban shirya ba sai da take ce mini. "Madam ya na ga ba ki shirya ba? Ko ba za ki je ba ne? "Ba zan je ba, haba mun yi yawa ga ki? Ke ma ai uwar Jidda ce in kika rakata kamar ni ce na rakata duk ɗaya ne.' Yallaɓai na wajen na yarfa musu magana shi da ita. Ni zai yi ma tozarci, shi ya sa ko gaishe shi ban yi, shima bai yi mini magana ba kamar da man can yana jin haushina. Shi da ya fiffita da kayan suka loda a booth wasu ma sai da aka sanya su a baya. Baby na ta murna, Yumna ganin haka sai ta fara kuka na saka zani na goya ta domin ba na son ma ta fara yi mini rigima. Ban yi fushi ba haraba na yi musu rakiya Amarya an kame a gaban mota yaran na baya Jidda da ba ta shiga ba ta rumgumeni sai kuka nima har ta sakani hawaye duk dauriyana sai da na yi kuka. "Ki yi hakuri Jidda kin ji? Karatu ne za ki je, za mu rika mgana ta waya ba matsala." "Umma" Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka cikin dauriya na rabata da jikina ina share mata hawaye ina mai faɗin" Ki daina kuka kin ji ko? Ki  riƙe manganganun da na yi miki kin ji ko? Ki kula da kan ki ban da kula maza. Ban amince ba in dai ba mgana ce ta karatu ba? Ki riƙe azkar da karatun Qur'ani domin daga Allah sai kan ki kike da shi a can kuma mganar zuwa gidan Ya Hamza za ki je weekend bayan sati uku huɗu haka ki je ki gansu ki huta kin ji ko? Sai ta sake rumgume ni tana kuka, nima na riƙe ta ina bubbuga bayanta alamun lallashi sai ga Yallaɓai ya fito daga mota yana faɗin" Ki sake ta don Allah, ba na so mu yi dare a hanya" Ko kallon shi ban yi ba na sake ta na raka ta har mota ba ta shiga ba sai ta sumbaci kumatun Yumna da ta fara barci tana faɗin za ta yi kewar mu. "Mu ma za mu yi kewarki Jidda. Allah ya ba ki sa'a." Na tura mota na rufe ina ɗaga mata hannu, hawaye suka taho mini sai kawai na juya na shige cikin gida, ga baƙin cikin Wulakancin Yallaɓai ga kewar Jidda. Sun tafi amma Yallaɓai bai yi mini sallama ba haka na faɗa a raina da na ji fitan mota da rufe get sai kawai na kifa kaina a saman dining na fashe da kuka. Ban san shigowar sa ba sai ji kawai na yi an dafa ni a firgice na ɗago sai na ci karo da Yallaɓai yana kallona kawai sai na mai da kaina ƙasa ina cigaba da tsiyayan ƙwalla. "Sorry ko za ki shirya mu tafi ne? Ko kallon shi ma ban yi ba saboda takaici. "Ga Jidda can tana ta kuka itana kema kina nan kina kuka. Shi ne Daughter ta ce ko kawai ki shirya mu tafi gabaɗaya " Wani irin kallon da na yi ma Yallaɓai shi ya sa da sauri ya ce" Me kuma na yi? Yi haƙuri." Kawai sai na ture hannunsa daga kafaɗata kafin na miƙe ina faɗin" Ka gama magana ka ce wata ta rigani. Saboda haka ku je kawai Allah ya tsare." "Ni fa wasa nake yi da wannan mganar" Yallaɓai ya raina mini wayau. Wai wasa yake yi? Ya kirani ya ce na shirya ko da ya ga ban shirya ba. Bai damu ba ko mgana ma bai yi mini ba sai yanzu da matar shi ta yi magana. Ƙokarin riƙe ni yake yi na fizge jikina na bar masa falon ban san lokacin da ya ƙara gaba ba. Na yi ta tafasa ni kaɗai a gida saboda da zaran na tuna wulakancin Yallaɓai sai na ji ina tafasa ni kaɗai. Haka na yini a gida daga ni sai Yunma sai can da azahar sai ga Mubeena da Musbahu shi yake faɗa mini daman Yallabai ya ce da Anty Gimbiya za su tafi ba da ni ba amma saboda munafunci ya zo yana ce mini wai wasa yake yi mini. Zuwan su ne ya sa na ɗan saki Mubeena ce ta yi mana girki, Yallaɓai ya kira ni da kan shi ya ce sun sauka suna ma cikin makarantar, sai na kira Khaleesat na faɗa mata da man ta ce za su leka su ga wajen ita da Ya Hamza. Mun yi waya da Jiddan itama can da gabda la'asar da su Ya Hamza suka je, ita ke faɗa mini Yallabai da Antynsu sun tafi gidan kawar Anty ina jin haka na ce gidan wannan ne da Yallaɓai ya yi maganarta ranar. Wani abu ya taso mini daga kasan zuciyata amma dai na daure. Daga baya da muka yi waya da Khaleesat ta ke faɗa mini sai da suka jira su Yallaɓai suka dawo a bakin ta na ke jin sun yi dare nan za su kwana amma yara kawai za su bar musu Yallabai da Amaryansa Hotel za su kama. Ni fa daman na faɗa, ni na san da wata a ƙasa. Namiji uhm ni Yallaɓai zai yi ma haka? To ai shike nan, shi gogan sai dare ya kira ni ina ga bayan ya sun gama natsawa a hotel ɗin da suka kama sannan ya kirani yana daidaiciyar mgana. "Sadiya mun yi dare za mu tsaya mu kwana zuwa da safe.' "Allah ya nuna mana goben lafiya." Na faɗa a yatsine, na yi kums shuru jin ya yi shuru har ina jiyo maganar Gimbiya amma ban san abin da ta ke faɗa ba. Ina shirin kashe wayar ne na ji yana faɗin" Yara suna gidan Ya Hamza" "Anty Khaleesat ta faɗa mini." Na faɗa da gayya domin ya san na sani. Jin na ji labarin a in da suke yasa bai ja mganar ba ya yi mini sallama saboda bariki har yana rage murya yana faɗin" Na yi kewar Sadiya ta " Ashar ne kawai a bakina shi ya sa na yi shuru domin in na yi magana zan zage shi ne shi ya sa na yi kamar ban ji ba. "Ina Yumna ta? I miss her." "Ta yi barci." Na faɗa a gajiye ban bari ya sake magana ba na yi saurin cewa" Zan kwanta sai da safe." Ban jira cewarsa ba, na kashe wayata ina jan uban tsaki wayar na hannuna ina jin wani abu na taso mini. Ina tuna me na yi ma Yallaɓai da zai shirya mini wulakanci haka. Shigowar sako daga  waya ta, ya sa na duba Yallaɓai ne. "Ki yi haƙuri My Sady kin ji? "I love you." "Munafuki" Na faɗa a fili kafin na dankwafar da wayar. Barcina ranar rabi da rabi ne, da na farka sai takaicin Yallaɓai ya taso mini da safe ina ganin kiran shi ba ƙi dagawa. Sai can da muka yi waya da Jidda ta ce sun ta so ba su haɗu ba saboda yau ta fara attending ɗin lactures na yi mata fatan alheri sannan muka yi sallama cike da kewa. Na san za su sauka a gidana shi ya sa ki girki ban yi ba suka dawo ga yunwa ba abinci sai fita Yallaɓai ya yi ya siyo abincin ai yadda ya ganni ina cika ina batsewa ya san in ya yi mini magana to zan fa fashe na fara masifa shi ya sa bakin sa alaikun ya fita ya je ya siyo kuma har ni ɗin ya siyo mawa na karba kuma na ci. Sai da yamma ya tara matarsa da yaran su ya mai da su gida da wuri ya dawo yana mini yar murya da labarin Jidda. Kallo ni bai ishe ni ba, ya yi ya gama yaga ban tanka shi ba sai ya koma ban haƙuri. "Kin ga ta ce mini za ta je bai kyautu na ce mataa a'a ba. Ni kuma ganin ba ki ce mini za ki je ba shi ya sa ban kawo da ke ba. Ki yi hakuri na san kina da kara kamar yadda kika ce ke da ita kun zama ɗaya." Ni kallon shi kawai na ke yi, domin ni ba zan ɓata ma bakina akan shi ba tun da na san duk yaudara ce ta maza. Da na ga zai dame ni sai na ce masa ni ba haushi na ji ba amma da zai ƙyale ni da maganar nan da ya samu zaman lafiya. Shi ya sa sai ya yi shuru da mganar, ranar dai ba mu yi kwanan daɗi ba sai washegari na ɗan saki muka shirya amma na daɗe ina kallon Yallaɓai da wulaƙancin da ya yi mini amma tun da ya karyata kansa sai na ƙyale shi ɓan kara ta yar da mganar ba.. Na  ɗauki girman na yi hakuri na share, Jidda ana can an kwarari sati uku a makaranta ko da yaushe ina kiran ta na ji halin da take ciki. Yallabai ma ko da yaushe satin ma ya shiga Kaduna sai da ya biya ya ganta. Mu dai ta bar mana kewa koda yaushe Baby zencenta kenan Ya Jidda, ni kaina ina kewarta da sanyin halinta gida ya rage daga ni sai Baby sai Yumna. ***** Cikin Gimbiya ya shiga watan haihuwan shi a bakin Yallaɓai na ji, hankalin shi duk ba a kwance yake ba, ni dai in yana magana ina yi masa fatan Allah ya sa ta sauka lafiya. EDD dinta ma bai cika domin karshen watan march ya ce mini za ta haihu amma a ba ta kai ba ranar wata laraba yana gidana da safe ta kira shi ba ta da lafiya ya fita. Tun da ya fita bai dawo ba kuma bai kirani ba sai ni ce can na kira shi , a lokacin ya ke faɗamini suna asibiti haihuwa ce amma har lokacin ba ta haihu ba. "Aikin za a sake yi mata? "A'a sun ce a dakata a gani za ta iya haihuwa da kanta." Fatan sauka lafiya na yi masa na kashe wayata. Da a baya ne tsab zan shirya mu je, ni kan ai Gimbiya ta gama yi mini hankali ban ko a raina zan iya zuwa ba. Har dare da Yallaɓai ya dawo ba ta haihu ba, haka muka kwana da shi bai yi barci ba ni dai barcina na sha to ina ruwana, ai ni na gama hana kaina zaman lafiya a kan Gimbiya. Washegari tun safe ya tafi asibitin har yana jirana ko zan je na duba ta na ce ya je zan yi ma Hauwa ko Munnira waya mu je tare nan ko ba zuwa zan yi ba kuma ban kira kowa ba. Ba ta haihu ba sai bayan la'asar kafin ya kirani a status ɗin Anty Bahijja namiji Gimbiya ta sake haifa. Anty Bahijjan ma a ƙasan hoton ta rubutu mai farar haihuwa ta sake yo wata farar ƙal ma kuwa. Na yi taging na yi Allah ya raya domin ni ba na baƙin ciki. Sai daga baya angon karnin ya kirani ya faɗa mini ta haihu da kanta. Amma za su riƙe ta zuwa gobe ta zubar da jini sosai." "Ayya. Allah ya raya ya kuma ba ta lafiya" Ya amsa da Amin Amin. "Kin fito ne? Sai da ya yi magana na tuna da karyan da na yi masa. Da sauri na ce" Ban fito ba. Na kira su Hauwa sun ce mu bari gobe da safe kawai." Bai ce komai ba ya ce Allah ya kaimu. Ni ban kira su Hauwa da na yi ƙarya da su ba, washegari da safe da ya bar gidana asibitin ya fara biyawa sai ya iske Hauwa ni ina na sani ba sai da Hauwa ta kirani tana cewa. "Sadiya me kika faɗa ma Tafida? Mun haɗu a asibiti yana ce mini ya na taho na bar ki alhalin kin ce masa tare zamu zo.' "To sai kika ce masa me? "Na kasa mgana. To ni me zan ce? Na ciji yatsa kafin na ce" Kash! Kin kwafsa mini. Nan na ba ta labarin abin da ya faru. "Ni fa ban yi niyyar zuwa ba ne" "Ki tura mata Aniyarta ki zo ko saboda Yallaɓan." "To bari dai mu gani. Zan je na yi barka amma ba zuwan da na saba yi a da ba." Da muka gama waya da Hauwa na yi niyyar na je amma sai na kama ciwon ciki sai zawo, zan fita ne ina zawo na yi zama na a gida da daddare da Yallabai ya dawo sai da ya ce mini Hauwa ta je asibiti yau "E. Ni na ce ta tafi kawai. Ban ji dadi cikina ke ta ciwo sai kuma na fara gudawa." "Sannu ya bari ko sai mun je asibiti? Ya faɗa da kulawa sai na ce ya yi sauki, ni bai nuna mini komai ba shi ya sa nima ban damu ba. Ban kuma samu zuwa ba sai washegari da yamma bayan an sallamo Gimbiyar da safe, Munnira na kira a waya na biya gida na ɗauke ta. Sanda muka je yan Rano sun zo Mota guda su Naja da Anty Bahijja suna gidan ana ta shewa Anty Bahijja da ba ta gani ta ƙyale sai da ta ce mana. "Jiya ɗayar ta ku ta zo ku sai yau ake ganin ku? Wai Hauwa ce ɗayar mu. Munnira ce ta tsaya mata mgana ni gaisheta kawai na yi na wuce ciki wajen  Gimbiya. Mun gaisa da yan uwanta na Rano sannan na karisa gefen gado na zauna muka gaisa na ɗauki Jaririn sak Khalipa yana jariri, na yi masa addu'a na bata shi ba wani jima ba muka tafi, daga nan na mai da Munnira gida da motata na koma gida ban faɗa ma kowa haihuwan Gimbiya hatta su Ya Aina Jidda ta kira ni tana cewa Abban su ya kirata yana murna yana faɗa mata sun yi ƙani na ce ai fa. Ta ce har hotuna ya tura mata. To ba abin mamaki ba ne tun da farar haihuwa ce aka sake yi masa. Tun da na je barka ban ƙara komawa ba. Ga mamakina ana jibi suna Yallaɓai da zai fita sai ya ce mini na shirya na je na duba mai jego. "Na je ai na duba ta." "Na sani. Ya kamata ki sake komawa kafin suna." Kamar zan yi magana sai ban yi ba, na ce to yana fita ko na ce ba in da zan je. Ranar yini na yi barci ma da ya dawo bai tambayeni amma na san ai ya fara biyawa ta gidan ta. Tun da Baaba Asma'u ta zo wacce ta zauna mata da haihuwan Anwar shi ya sa yake kwana a gidana. Ni ce da kaina na faɗa masa ban je ba ba na jin daɗi. Na ga ya kalle ni amma ganin bai sauya fuska ba ya san ban damu ba. "Allah ya sauwaƙe." Na amsa masa da Amin Amin Kuma ko washegari ban je ba na yi zamana a gida. Munnira dai da Hauwa sun leka aikin suna ni dai sun kirani na ce musu ba in da zan je. Ranar suna na yi niyyar lekawa shima ba da safe ba. Danan na cire mata atamfa ɗaya da pampers sai mayukan yara cikin saura na Yumna na saka a leda na ce in na leka goben zan kai mata. *Janafty**TKGB3N014* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732 Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰 A daran da Yallaɓai ya dawo yake faɗa mini sunan yaro Muhammad. Na ce Allah ya raya mana Muhammad cikin addinin islama ya ce Amin Amin. Tare muka kwana cikin farinciki, da wuri ya fita saboda ya ce akwai mutanen da ke jiran shi a can office amma ya sha wankan shi ya ci gayu cikin shadda dark blue amma ba mai babban riga ba. Sai ya fito a angon ƙarninsa ina zolayansa kafin ya fita. Bayan na dawo raka shi na yi ma Yumna wanka na goya ta na fara ayyuka Baby daman ita ta fara fita kafin Yallaɓai. Jiya da daddare na ji ta fara faɗin yau sunan Anty Gimbiya ba za ta je makaranta ba tun kafin Yallaɓai ya ji labari ya ɗaure mata kugu na ja mata kunne shi ya sa yau da safe ba ta yi rigiman ba za ta je ba. Shara na yi sannan na yi mopping gidan duk ya yi ƙura kwana biyu ban yi ba,  da man Jidda ne ta sangartani yanzu kuma tana makaranta Baby kuma ga makaranta ranar weekend kuma tana Tahfez in ma ta dawo wanke-wanke kawai ya isa ta fara tura baki tana faɗin ita duk ta gaji shi ya sa ban ma dogara da ita domin na fahinci ko a zamanin baya Baby ta fi ni lalaci. Har ga Allah ban yi niyyar zuwa sunan da wuri ba. Wajen sha ɗaya na safe sai ga wayar Hauwa tana faɗa mini na shirya na ce mata ni fa ba yanzu zan je ba sai anjuma. "Don Allah ki shirya mu taho gidan ki mu wuce tare." "Ke da wa? Na faɗa ina tura baki kamar tana ganina. "Ni da Munnira mana. Mutanen Rano ma suna kan hanya yanzu muka gama waya da Ashen mu." Cikin mamaki na ce" Ikon Allah suma duk za su taho ne? "E tare da yan gidan su Gimbiyar ne. Hajiyarsu ta aika ma Mama shi ne ta ce ashe ta shirya ta bi su." Ni dai sun takura mini ba ni da yadda zan yi sai na ce bari na shirya. Mun gama wayar da ita kenan Marwa ta kirani ashe har da ita a masu tahowa suna kuma a can gidan sunan za su sauka jin haka ya sa sai na ce bari na shirya kawai mu wuce tare da su Munnira. Ni daman yan gidanmu ban faɗan ma kowa ba Ma'u ce kawai ta sani kuma na san ba a bakina ta ji ba, ta yi mini maaganar ashe Gimbiya ta haihu na ce e ta yi fatan alheri ba ta zo ba kuma. Domin gabaɗaya alaqar su da Anty Bahijja ya ja baya. Ni yadda ma Ma'un take faɗa mini Amaryan Alhaji Mustpaha yanzu ita dangin shi suka rike ita da Hajiya Zainab ina jin har Anty Bahijjan ta yi ma Ma'u batulci. Na san ta sarai za ta aikata tun da ita daman ba ta da alkibla. Kafin na shiga wanka na kira Hauwa a waya na ce na chanza shawara su biyo mun sai na ɗauke su a motata mu tafi tare sai ta ce mini to. Sai da na yi wanka na shirya cikin wani leshina sabo ne yana daga cikin kayan da na samu da sunan Yumna ɗinkin bubu doguwar riga. Leshin mai kalan maroon ne sai na yi amfani da mayafi kalan shi takalmi ma da jaka ina da maroon da su na yi amfani. Yumna kuma na yi mata gayu cikin kaya yan kanti jajaye harta takalmin kafanta da safa ja ne, haka hulan da ke kanta na gyara mata gashin kanta. Ta biyo a sumar kai amma Yallaɓai ba ya bari a yi mata kitso sau ɗaya Maman Nana da ta zo yi mana kitso ni da Baby  na ɗan ce ta yi mata kalaba aka sanya mata band kitson ya yi kyau amma ta yi ta kuka saboda ba ta saba ba. A daran Yallaɓai da ya dawo ya gani ya ce sai na kwace mata wai an ci zalin yarinya don an ga ba ta mgana tun ballanta da take ta kuka shi a tafau zafin kan ne ya saka ta kuka tun kuma daga ranar ya ce ba za a ƙara mata kitso ba sai ta girma an yaye ko sai kanta ya yi ƙwari. Sanin halin Yallaɓai da naci wani lokacin in har aka sake kuma ya gani ni ce zan sha mgana sai kawai na ƙyaleta ban ƙara yi mata ba, amma kowa ya ganta sai ya ce ga ta da gashi amma ba a yi mata kitso sai na ce babanta ne ba ya so. Daga karshe ma sai na sissiya mata huluna kananun size kamar nata, na ke saka mata in zamu fita yau ma kalan ja mai maroon, na saka mata na rufe mata kan ta da shi, sannan na je ɗakin su Baby na ɗauko mata kaya a cikin dirowanta. Shadda na ɗauko mata doguwar riga da ƙaramin mayafi. Hauwa na tsaya ina ta jira sai wajen azahar ta shigo gidana shi ya sa sai da muka tsaya a gida muka yi salla sannan muka fito na rufe gida na tuƙa mu a mota ta, sai da muka tsaya a kan hanya na sha mai da safe Yallaɓai ya saka mini 5k ya ce na saka mai a mota, wani lokacin ma Adnan zai turo ya ɗau motar ya je ya saka mini wata rana ma da kan shi zai tura ya je ya ciko mini da tankina ya kawo mini. In ba lokaci kuma sai kawai ya ba ni kuɗin amma ba ko yaushe ba wani lokacin ina sakawa da kudina. Ai ya gama yi mini mai wuyar tun da ya siya mini motar. Na man da zan yi zirga-zirga na a cikin gari ba zai gagare ni ba.   A gidan man kafin layi ya zo kanmu na kira wayar Salisu na sanar da shi in ya ɗauko Baby daga makaranta gidan Maman su Khalipa zai kawo ta. Sai ya ce mini to, a bakin shi na ke jin ashe su Khalipa ba su je makaranta yau ba. Hauwa na ke faɗa mawa ta yi dariya kafin ta ce" To da man ai ba za su je ba. Suna fa ake yi sunan ma na gidan su." Ban ce komai ba, illa Yumna da nake kallo wacce ke hannun suna ta wasa da yaron Hauwa. Ita har ta yaye shi ma yana neman shekara uku ne ma. Munnira na tuna shi ya sa na kalli Hauwa kafin na ce" Wai kina ganin zuwan Hadiza ba zai hana Munnira zuwa gidan sunan nan ba kuwa? Na faɗa ina kallon Hauwa. Domin na kira wayar Munnira da niyyar na ce mata mu haɗu a gidana sai mu wuce gabaɗaya. Sai ce mini ta yi mu tafi kawai ƙanwarta Hadiza ta zo daman mun yi ta ɗin da ita tace mini ta zo garin da yake a garin Minna take aure. A yau ɗin ne ta kai ma Munniran ziyara. "To wa ya sani. Ina jin kamar fa Hadizan nan gidan Munniran za ta kwana " Hauwa ta amsa mini daidai lokacin layi na zuwa kan mu sai ban ba ta amsa ba sai da na yi mgana da mai zuba man na faɗa masa na adadin da zai zuba mini ina da kuɗi a jaka ta, sai na bashi sai da muka bar gidan man muka ɗau hanyar sharaɗa sannan na kalli Hauwa kafin na ce" Wataƙila nan za ta kwana. Kila su zo tare in ta yi niyya ba." "Ai fa. Ta bakin ki in ta yi ra'ayi za ta jawo ta su taho tare" Muna tafe muna hira ni da Hauwa har gidan Gimbiya. A waje na yi parking ɗin motata tun da ga na wasu nan duk a wajen, har da na Anty Bahijja na gani da man na san ai tana gidan tun safe. Gimbiya ce fa ballantana tana dukan ƙirjin cewa an sake yi musu farar haihuwa. Mun shiga gidan ina ɗauke da Yumna da jakata da key ɗin motata. sai Hauwa itama riƙe da goyonta ita ta ɗauko ledan kayan Baby da saƙon Gimbiya tun da ita ba ta ɗauko jaka ba. Gida fa cike da baki, ashe har anko sun yi ba mu sani ba, ba wanda ya nuna mana. Ni da Hauwa muka kalli juna amma ba mu yi magana ba. Marwa ne da Ashe suka tare mu shi ya sa ma muka saki fuska sun sauka tun ɗazu. Ashe har tana yi mini tsiya. "Anty Sadiya sunan na ku har da anko kuka fitar amma ba labari " "Nima yadda kika gan shi haka na gan shi." Na faɗa ina dariya da yake tana da barkwanci ne ita Aisha. Ashe su Hauwa ke kiranta, lokacin sunan Yumna ba ta da lafiya ne shi ya sa ba ta zo ba, karɓan Yumna ta yi, ta fara ƙoƙarin yi mata kuka da sauri ta ce" Ke ƙaniyarki nima uwarki ce." Ni da Hauwa muna ta dariya. Mun gaisa da Marwa na dauƙi Afra ina faɗin ta yi mini girma a ido sosai ba kamar ganin ƙarshe da na yi mata ba. "Umma ta kusa wattani shidda fa? Sai na buɗe baki ina faɗin" Lokaci ba wuya. Allah ya sa mu da ce." Ta amsa da Amin tana dariya, Baby ta tambaya na ce tana makaranta amma in sun dawo nan za a kawo ta na ma taho mata kayan da za ta sauya. "Su Jidda ana can makaranta ko? "Wallahi tana can. Yau ma dai ba mu yi waya ba." "Allah ya ba da sa'a." Duk suna falon ne, tare da sauran dangin Gimbiya na Rano. Ban ware su ba na bisu muka gaisa cikin sakewa. Su Anty Bahijja da Naja ana ta kai da kawo su leshi ne a jikinsu iri ɗaya ina tunanin anko suka yi. "Barka da aiki Anty Bahijja an yi suna lafiya? Na faɗa lokacin da ta zo wucewa. Waigowa ta yi sai ta nuna kamar yanzu ta gani alhalin ni na san tun shigowata ta gan ni har ido ma mun haɗa da ita. "Sadiya ce! Sai yanzu za ki zo mana Suna? Ina mirmishi na tashi na isa wajenta ina faɗin" To ka ga ku Anty Bahijja ai ba sai mun yi samakko ba, kuma dai kin ga na tsaya na shirya angon ƙarni a gida ne kafin na fito " "Gaskiya ne. Ina Yumna? "Tana hannun Marwa" Na bata amsa sai ta ce na shiga ciki mana, ta waiga ba ta ga Munnira ba sai Hauwa tun da har sun gaisa. "Ina ɗayar yar tawagan na ki? Sai da na yi dariya kafin na ce" Ta yi baƙuwa ƙanwar ta, ta zo kila anjuma ta leƙo " Sai ta wani jinjina kai kafin ta ce" Kina dariya karya na yi ba yan tawagan ki ba ne? Duk wanda ya ce miki kule sai sun ce masa caass." Ni dai ina ta dariya ban yi magana ba, na tuna can kwanaki Mubeena ta taɓa faɗa mini Anty Maimuna ta ce wai tsoro na su Hauwa ke ji, sai abin da na ce shi suke yi shi ya sa duk in da nake suna bina a baya. Ni kuma na san haushi suke ji saboda suna tare da ni. Sai na jujjuya ina neman Mubeenan ban gan ta ba, wata kila ba ta zo ba ne, Anty Bahijja ta ce na shiga ciki Gimbiyar na ciki tare da ƙawayenta.     Na kama hanyar Bedroom ɗin da Gimbiya ke ciki muka haɗu da Naja, ta gaisheni na amsa ina tambayan ta ya hidima ta ce sun gode Allah. Daga nan na shiga ɗakin Gimbiya dake cike da kawayenta da ƙannenta har da yayyenta. Da fara'ata na shiga aka gaggaisa nan na ga autar su Gimbiya Maryama da ke aure a can Lagos ba ts cika zuwa ba na dai ji labarinta amma ban taba ganin ta ba sai yau, ni na fara yi mata mgana amma sai na ga tana amsa ni a fuzge ban bi ta kanta ba na isa gefen gado kusa da Gimbiya na zauna muna gaisawa ta ci shadda pink ta ji aiki an yi mata makeup ta yi ras da ita. Suma ƙawayenta sun sha kwalliya sun sha anko. Gaisawa muka yi ta ba ni Muhammad na ɗauka shima an yi masa gayun su na yara da kaya masu kyau da tsada. "Allah Ya raya mana Muhammad" Na faɗa sai ta amsa da Amin Amin. "Ina Baby? Ko ta je makaranta ne? "E ta tafi. Amma na kira Salisu zai kawo ta nan, tun da na zo mata da kayam da za ta saka." "Ayya. Su Jidda ana can makaranta. Ta kirani da safe muka gaisa ta ce Anty wani suna za mu riƙa kiran Muhamnad na ce ta saka masa suna cikin sanyin ta ta ce Anty Ammar ya yi? Ina dariya na ce" Ta ko iya zaɓan suna. Allah ya raya Muhammad(Anwar)" Aka amsa da Amin gabaɗaya da waɗanda ke gefen mu suna jin mu. Ina nan zaune sai ga Hauwa ta shigo sai na matsa mata gefena tazauna ta mika mata Muhammad, sannan na karɓi ledan sakonta na mika mata ta karɓa tana faɗin. "Ba kya gajiya Madam! To na gode Ammar na godiya Allah ya saka da alheri " "Haba ba yawa fa. Amin" Yumna ta tambaya na ce tana wajen Marwa, yarinya Marwa ɗin ma ta yi barci nan saman gadom Gimbiya na kwantar da ita. Har ita Gimbiyar sai da ta tambayi Munnira wai ya ta gan mu mu biyu daga ni sai Hauwa na yi dariya na ce ta yi baƙuwa ne amma za ta taho daga baya. Mun saba in dai wani abu ne a dangin mazajen mu to mu uku suke ganin mu. Kowa ya san ni da su Hauwa mun zama aminai ne ba facaloli ba. Abinci ta ce a kawo mana sai na ce a kai mana falo can za mu koma, ba mu ma kai ga barin dakin ba sai ga Suwaiba ta iso tare da ita muka fita falo ana ta hira. An kawo mana abinci tuwon shinkafa mai naman rago. Sai dambun zogale sai alale, sai muka haɗu da ni da Suwaiba da Hauwa muna cin abincin ina tambayan Jamila ta ce itama yau ƙanwar mijinta ake suna ta haihu sai anjauma za ta leƙo. Muna cin abinci muna hira su Marwa suka dawo in da muke suka zauna a cikin hiran ne Hauwa ke maganar me ya sa ba ta ga Suwaiba da ankon sunan ba? "Wa? Mu a suwa. Naja ta tura mini na ce ba ni da halin yi." "Au da man ankon ma sai wanda ya isa ake nuna ma wa? Hauwa ta faɗa tana riƙe baki. Suwaiba na dariya ta ce" Ku ba a nuna muku ba? Wataƙila saboda Sadiya ne domin na ga ana kishi da ita ko sunan ma in kun lura yanayin na Yumna aka kwaikwaya. Duk haihuwar su Khalipa ba ta yi anko ba sai wannan? "Uhm' Kawai na iya cewa kafin na yi magana Ashe ta karɓe da cewa" Wai ba a nuna muku ankon ba da gaske? "Wallahi ba mu sani ba." Na rantse mata sai ta yi kasake kafin ta ce" To har Rano wannan akon bari mu ku ji." "Zai kai can mana. Kun manta gidan su na can ne." In ji Suwaiba, Marwa ta ce itama Anty Bahijja ta tura ma Kawu Abba ya ce ba zai siya ba sunan ne sai an yi anko. Shi ne ta ce ai nima da na haihu na yi anko kuma ya siya mata a lokacin shi ko ya ce ba shi ya siya ba da kuɗinta ta siya a wancan lokacin. Yanzu ma shine ya nuna mata in tana da kuɗi ta siya Marwa ta ce ita kam ba ta da kuɗi ba ta siya ba. "Ikon Allah.! Suwaiba ta sake faɗa tana mai mamaki, Hauwa ta ce da man ko na Yumna ba su yi ba gwara ma da ba su nuna mana ba muma ba za mu yi ba. "Da sun sanar damu za mu yi ko don mu tura musu Aniyar su." Na faɗa ina mirmishi. "Wallahi kuwa." In ji Marwa. Muna ta hiran mu, Naja ta zo ta ga ba a kawo mana ruwa ba da kunin Aya ba. "Wa ya kawo muku abincin? Ta tambaya tana kallon mu. "Maryama ce ta kawo musu abinci ba ruwa ba lemu." Ashe ta faɗa cikin gatse sai Naja ta yi dariya ta ce Ashe ta biyo ta karɓo mana. Ita ta bita sai ga shi ta dawo da ruwan gora da fanta sai kunin Aya da zobo cikin wani roba. Tana ta masifa wai an ce Maryama ta ba da zobo da kunin aya tana wani daga kai. "Har tana ce mini ba kin sha ba ke Ashe? Na ce na sha in zan ƙara za ki hana ni ne? Na kwashe da dariya ganin yadda Ashe ta yi da baki tana kwantata mana yadda suka kwashe da Autar su Gimbiya. "Sai ta ce me? In ji Suwaiba itama tana dariya. "Me kuwa? Ta yi shuru ai ta san ni yadda ba ta taɓuwa nima haka. Naja ta ce na ku ne sai ta wuce ta buɗe dakin ta ba ni." Hauwa na dariya ta ce"Da man Maryama ba ta da dama. Ga rashin kunya da ta yi auran nan ne ma ta yi sauƙi." "Rashin kunya ai duk tare muka yi muna yan mata. Ni yanzu ai sai dai ta nuna mini zaman agolege ni kuma na gwada mata na Sulaja." Ni dai dariya har ina kwarewa, Yunma na zaman jikina ina ba ta alale har tana sulmiyowa. "Ke da man ba cikin garin Lagos ɗin take aure ba? "In ji wa! Ko dai ake raina ma wayau. Tana cikin garin Agege can mijinta yake kasuwanci. Shine da ta zo garin ta yi ta buɗa hanci wai ita a dole tana auran miji mai kuɗi suna zaune a garin lagos. Allah na tuba wallahi ko ni da mijina ke aikin gwammati a kallon farko mai hankali in ya yi mana ya san na fita jin daɗi " Ni da Suwaiba muna tsintsira dariya ina faɗin Munnura ta yi missing na so tana wajen nan da an ji muryanta a sama. Abin da ya ɗan tsagaita hiran ma Faridan Tariq ne ta kira ni a waya ta ce ita ba ta samu zuwa ba suna sai sallar azumi take tunanin za su shigo garin. Sai na ke faɗa mata ina gidan sunan gamu nan ana ta hira ana dariya ta ce na gaida kowa da kowa. Muna zaune a falon sai ga Mubeena ashe tana makaranta suna da test duk ta sha wuya Naja na yi ma magana na ce a kawo ma Mubeena abinci daga makaranta take. An kawo mata itama irin na mu, muna nan muna ta hira sallar la'asar ne ya tada mu bayan mun yi salla mun idar muka fito an kira mai hoto kamar dai lokacin sunan Yumna. Mun fiffito, sai ga Munnira yar halas ita da Hadiza ƙanwarta tana ko ganin mai hoto sai da ta riƙe baki kafin ta ce" To pha sabon salo tusa a lasifika." "To za ki fara ko? Hauwa ta tare ta, tana dariya. "To ai na ga ana ta so a kwaikwayo mu ne." "Ai komai ma irin naku ne. Ba ki ga har da su anko ba.? Suwaiba ta fada mata tana dariya Munnira ta waiga ta sake waigawa kafin ta saki shewa da ƙarfi tana faɗin" Ahayye nanaye. Yau ina ganin abin da yafi karfina ni haihuwar mutun biyu" "Kishin ne har da na suna? Hadiza ta faɗa tana dariya Ashe ta ce" To miye ma ba a yi ma kishi yanzu? Kishi ya zama ɗan gata yanzu." Ni dai ganin hankula sun fara dawowa kanmu na ce Munnira ta yi wa Allah ta yi shuru "Zan yi shuru amma in na ga abun da zan magantu wallahi sai na mangantu." "Nima ina bayan ki." In ji Ashe har suna tafawa sai na lura hatta Hadiza irin su Munnira ne,  har tana cewa tun da dai a dake ba za mu dakun ma kowa ba ai da sauƙi. "Ni dai ku rufa mana asiri mu bar gidan sunan nan lafiya kafin a yi mana rubuti." "Ai wallahi ba wacce ta isa tab.!" Munnira ta faɗa har tana ɗaga murya na balla mata harara. Munnira ba ta shiga ciki ba sai da aka gama hotuna yadda ba a gayyace mu, mu ma ba mu tura kan mu ba, ni ko a sunan Yumna na kirata mun yi amma ni ko kallona ba wanda ya yi. Su Naja ne da su Anty Bahijja sai ƙawayenta da dangin ta ba ma kamar Maryama ɗin nan na yadda ta cika kauɗin tsiya. Bayan an gama hotunan muka dawo cikin gida muka zazzauna a falo muna hira. Munnira ina kwabarta sai da ta yi ma Naja magana wai an fidda anko an nuna ma waɗanda aka so. "Haba. Ban tura muku ba? To wallahi na manta ne" Ta faɗa daga ji ma karya ne, Suwaiba ko ta ce" Sadiya ai ba a waya ya kamata a nuna mata har gida ya kamata a kai mata ta gani." "Anty Suwaiba abubuwan sun yi mini yawa. Jibi za mu bar kasar ni da Honey. Ankon ma Gimbiya ba ta so a fitar ba ni ce na matsa. Mantuwa ne duk wanda ban turamawa ba ya yi hakuri." "Ai ba komai. Kun hutattashe mu da kuɗin mu " In ji Munnira. "Afuwan Anty Sadiya." Naja ta faɗa, tana kallona ni ko sai na yi mirmishi na ce ba komai. Nan dai ta wuce tana juya mazaunai. "Ƙarya take yi wallahi kunya ce, da man domin ta ji kunyar na yi magana " "Allah ya shirye ki Munnira " Hauwa ta faɗa tana dariya ni kuma sai na ce" Kuma da ba haka take ba. Da ni ce mai bakin amma yanzu Munnira ta taka ni." Na faɗa ina dariya kai tsaye ta ce" Wallahi da bakina kawai dai na ɗan yi lamɓo ne. Sai da na gama ganin takun kowa sannan na bayyana kalata." Muka kwashe da dariya gabaɗaya muna nan zaune aka mai do nepa falon ya yi haske Suwaiba ke tsokanan Anty Bahijja da ba chasu ne ta ce ita ina ruwanta da chasu yanzu ma gida za ta tafi, ba ta kuma daɗe da maganar ba muka ga tafiyarta ta fita ba daɗewa Maryama ta zo ta kunna waya da wakar Amarya ki haɗa kayan ki na Nura. Inuwa tana wani takawa yan gidansu na yi mata ihu Ba zato kawai Munnira ta ce" wannan ai tsohuwar waka ce. Kuma ƙauyanci ne mu taka rawa da ita." Kallon Munnira kawai na ke yi kallon ina ruwan ki. "Gaskiya ba. Kuma sautin waya ai ba sauti ba ne. A nemo speaker." Hadiza kanwarta ta amsa mata, daman duk zamu ce ta iske mu je mu. Suka yi kamar ba su ji ba, Maryam ɗin ta cigaba da rawan ta suna yi mata tafi. Ita ke fadin a je ta fito mata da Gimbiya ta zo ta yi rawa. Sai kawai ta saka wakar uwar gida ran gida har Gimbiyan ta fito lokacin ta sauya kaya ma Maryam ɗin ta kamo hannunta tana bin wakar. "Uwar gida ran gida Tafida yana yi miki rawa." In da aka ce shaba sai ta kira sunan Yallabai Ni da su Munnira muka kalli juna kafin mu yi dariya cikin mu ba wacce ta yi tunanin Munnira za ta mike sai ganin ta kawai mu ka yi a cikin su tana juyi tana faɗin" A fagen na mu ne mu Uwagidaye ne bai kamata amayar ta shigo ba." Sadiya, Hauwa wannan fagen namu ne." Ni dai ban tashi ba Ashe da Hadiza suka mike suka mara mata baya Suwaiba na zuga su da tabbas filin naku ne. Sai kawai a ka bar musu filin Maryama ta saki baki ita da su Gimbiya. Ita Gimbiyar ba ta yi magana ba sai ita Maryam ɗin ta ce"Miye haka? Ai ko fili na Anty Gimbiya ne. Domin ita ce Uwargida ita ce Amarya." "Ina kika baro Uwargida Sadiya? Kirarinta ta Yallaɓai. Ta zama Tafida Tafida ya zama ita." Munnira tafaɗa cikin sigan wasa. Sai kawai  Maryama ta yi ja tsaki kafin ta ce" In ana babbakan giwa wake ta kiyashi? Uwargidan banza da wofi. Ai ko Amarya ita ke da Gida. Ita ta yi farar haihuwa zaranta maza har guda uku ta haifa. Kin ga ita ce gidan ma gabaɗaya." "Ai kuma ba a nan take ba ai an take bodari ta kai." Ashe ta mayar mata da martani Hadiza ta karɓa da cewa" Ko goma Amarya za ta zo ta haifa sai sun jira domin za su kira wasu yaya da Anty suma za a kira su yanzu kafin baya." Tun muna ganin abin cikin wasa har aka koma jefa ma juna mganganu cikin zafi. Sai na mike ina yi ma Munnira magana akan ta yi shuru. "In yi shuru! Daga magana na ga yarinyar nan za ta yi mini rashin kunya. Ba ta sanni ba ne ko? "Da aurena da yayana ki kirani yarinya dan sake tunani dai baiwar Allah." Maryama ta faɗa har tana tafawa hannuwa Gimbiyar na yi mata magana ta fara masifa tana faɗin" Ina ruwan su damu daga saka waka sai su shigo suna neman gaya mana mgana! Wa ke tsoron su? "Na ce dai ki yi shuru ko? Ta tsawarta mata. "To abun na su ne kamar da gayya Anty Gimbiya." In ji Halima ni wallahi ban ma ganta ba sai yanzu ina tunanin ko yanzu ta zo, ko kuma ta zo da safe ta je gida ta dawo. "E mana da gayya ne. Tawagan uwargida ne ta bakin su, to wallahi mata ba ta isa ta watsa mana taro ba sai dai mu watse ta" "Ke ai kin yi kaɗan ki watse mu Maryama sai dai ke mu watse ki wallahi. " Ashe ta shige tsakanin Munnira da Maryama tana faɗin haka. "Anty Munnira bar mini wannan faɗan koma gefe ki yi kallo" Ta matsar da Munnira gefe tana nuna Maryama da yatsa kafin ta ce" Maryama karyan iskanci kike yi. Ni ce nan daidai da kugun ki wallahi " Kawai sai ta saka hannu ta kabar da hannun Ashe tana faɗin" Ke Ashe kin sanni na san ki. Faɗan nan ba naki ba ne amma tun da kin shiga saboda yayarki Hauwa na ƙawar matar can mu zuba da ni da ke shege ka fasa." Ta faɗa tana shan gaban Ashe har tana ture ta baya. Abu kamar wasa wasa ashe na gaske ne ni ina gefe rike da Yumna ina ta ma Munnira mganar su bari domin har da ita maryama na magana tana ma yar mata ita da Ashe har da Halima. Hauwa ma da wasu yan Rano suka je suna jan Ashe amma ta ce tun da rigima Maryama take so to ta tare shi ta same shi a wajen ta. Gimbiya ma da ƴan'uwanta suna ta yi ma Maryam ɗin magana amma ba su ji ba. Irin su Halima yan kan zagi suna faɗin daman da gayya ne. Ga shi ba wasu manya Anty Bahijja ta tafi Anty Maimuna daman ba ta zo ba. Naja ce ta shiga tsakiyar su ta raba domin kaɗan ya rage afara kai ma juna duka. "Miye haka? Daga suna na farinciki sai kuma ku ma yar mana da taro na tsiya.? Ta faɗa cikin bacin rai kafin ta kalli Munnira tana faɗin" Anty Munni wannan ba girman ki ba ne don Allah ki ja tawagarki ku koma gefe domin a samu zaman lafiya." Munnira kuma ta ce sun yi kaɗan daga abin arziki sai a nemi a ce sune suka zo da fitina. Karaf wata ƙawar Gimbiya ta ce" Kune mana. Ina ruwan ki da waƙar da aka saka na uwargida ko na Amarya. Maganar gaskiya ku ne ba kwa son zaman lafiya. Ko kuma daman domin ku lalata mana suna kuka zo." Munnira ta yi shewa ta dire da cewa an lalata su yi wani abun mana. Suwaiba na yi ma magana ita na samu ta jawo hannun Munnira amma sai Maryama ta ja tsiyar da cewa" Abin da ya kawo su kenan mana. Ga munafukar can ita ce ta turo su ita kuma ta koma gefe ta bakam kamar ba ta san me ke faruwa ba. Anty Gimbiya ki faɗa ma Kishiyarki ta ja tawagarta ta bar gidan nan kafin raina ya ɓaci a yi ɓaattaciya" Maganar ta ba ni mamaki, sai kallo ya koma kaina duk sai na ji na muzanta. Naja ta zo gabana tana faɗin" Don Allah Anty Sadiya ki yi musu mgana su daina." "Na yi musu magana mana Naja ko ba ki gani ba ne? Ni zan ce su zo suna ne su yi rigima da wata? Ku yi mini adalci mana" "Ba wani adalci, ke ce munafukar da man tun da kika zo kika ga abubuwa sun tafi daidai kishin ki ya motsa ba haka aka so wai ƙanin miji yafi miji kyau." Maryama ta faɗa tana wani girgiza jiki, sannan ta nuna Munnira da su Hauwa tana faɗin" Saboda baƙinciki sai ki ka yi amfani da waɗanan yan koren naki domin su wargazamana taro. To daga ke har su ba ku isa ba. Sai dai mu mu wargazaku mu kore ku tun da ba zaman lafiya ya kawo ku ba." Baki na saki ina kallonta kafin in nuna kaina ina faɗin" Da ni kike? "Akwai wata munnafukar ce bayan ke. Kin ga Anty Gimbiya na ta farar haihuwa. Bakin cikin ki ya kasa boyuwa sai da kika bayyana. To sai dai ki mutu aamma gida ya zama namu haka ma Yaya Tafidan shima namu ne sai mun ga dama mu ba da aron shi." Maryama ta ba ni amsa ba tsoro ko tunanin wani. Kafafuwata suka fara rawa saboda ɓacin rai har ni na yi lalacewan da ƙanwar Gimbiya za ta ci zarafina. Yarinyar da ko Amina ta girme meta. Marwa ke rike ni tana cewa na yi haƙuri kar na tanka Suwaiba kuma tana yi ma Gimbiya mgana ta ja ma ƙanwarta kunne manganganunta suna tsauri da yawa. "Me zan ce Anty Suwaiba? Ni ba zan hana ta ba domin duk abin da ta faɗa gsskiya. Taro na suka zo su watsa kuma sun ji daɗi.' Kawai sai ta fashe da kuka munafunci, Munnira kuma ta fashe kawai sai ta dira kan ƙanwar Gimbiya ta shaƙo tana faɗin karya take yi, ai sune ma za su ce kishi ne ke damun yayarta domin duk wani abun da ta yi a wannan taron Sadiya ta kwaikwaya mu ba mu ce tana baƙin ciki ba sai mu ne za ki ce muna bakin ciki? To mun watse taron in ta isa sai ta yi wani abu ko ta ɗau mataki. Ni ban san me ta buɗe baki ta faɗa ba, sai ji kawai na yi kaya kaya an fara kai duka Munnira ta fara kai ma Maryama Mari, ita kuma ta rama kawai sai suka fara dambe na ruɗe ina kiran sunan Munnira. "Haba Munnira ba girman ki ba ne faɗa da wannan yarinyar." Hauwa ta fada har da ni a masu rabo Yumna wajen Marwa na bar ta,ƴan'uwansu na Rano suna ta faɗa suka ce ga mota can ta dawo ɗaukan su za su wuce ba za su iya da masifa ba, da man yau za su koma, ita kuma Hadiza ganin ana faɗa da yayarta sai ta shiga suka yi ma Maryanma taron dangi suka kaita kasa. Gimbiya da Naja ganin haka suka shiga tsakani, wajen ƙokarin raba su Munnira idanuwanta ya rufe ta ture Gimbiya sai da ta faɗi gefe kusa da kujera hannunta ya bugu sai da ta yi ƙara. Kukanta ne ma ya raba faɗan sai kowa ya koma kanta Naja ta ɗaga ta irin kukan da Gimbiya ke yi ko dukanta aka yi sai kuka. "Innalillahi shike nan sun karya ta burin su ya cika." In ji wata cikin kawayen Gimbiyar. "A kira Yaya Tafida mana shi sai ya zo ya ganin ma idanuwansa matarsa da Tawaganta za su nakasa masa mata." In ji Halima, ni gabaɗaya kaina ya kulle ma, amma sai da na yi na Munnira masifa. "Da wannan yarinyar ne zaki zo kina faɗa Munnira! Gaskiya wannan rashin sanin kimar kai ne " Har ga Allah in na san abin da zai faru kenan da ban zo ba. Na ce su tattara mu tafi na je da niyyar na ba ma Gimbiya haƙuri ta juyar mini da kai tana faɗin" burin ki ya cika kin samu abin da kike so. Amma ki sani wallahi ba zan bar maganar nan haka ba." Sai na ga ma tsayawa magana kamar ɓata bakina zan yi kawai sai na wuce. Har Ashe da Halima sai da na yi ma faɗa. Muka rankayo gabaɗaya zuwa waje muna fitowa Salisu na sauke Baby sai na ce kawai su juya. Motar na ce Munnira da Hadiza su shiga ya kai su gida ni kuma na ɗauko Hauwa da Ashe, tun da tace can za ta kwana sai Marwa da nima a gidana ta ce za ta kwana. Suwaiba na cikin gidan mun bar,ta tana ban haƙuri. "Munnira ta goga mini baƙin fanti a dangin Yallabai. Yanzu ko rantsuwa na yi ba za a yarda ba ni na saka Munnira dambe da ƙanwar Gimbiya ba " Na faɗa cikin damuwa. Ni na san abin da na ke hange da man yaya lafiyan kura ballantana ta yi zawo. An ce ina baƙin ciki saboda ban haifi namiji ba kalaman sun yi mini dafi a zuciyata. "Gaskiya ba ta kyauta ba. Haba ke kuma Ashe wallahi sai na faɗa ma Mama. Yanzu Sadiya kuka bar ma abin mgana." Hauwa ta faɗa tana dungurar kan Ƙanwarta Ashe. Tura baki ta yi kafin ta ce" Ni fa ban yi nadama ba. Ni Anty Munnira ma shigan sauri ta yi mini. Ni ce na so na yi ma Maryama bugun tsiya wallahi" "Kuma bakin ki bai mutu ba ko? Hauwa ta sake faɗa sai ta yi shuru ni kuma na ma kasa mgana hankalina ya tashi. Ba wai domin za a kira Yallaɓai ba sai domin ni ban je sunan nan da wata zuciya ba. Amma gashi abubuwa marasa daɗi sun faru Allah kaɗai ya san a yanayin da labarin nan zai fita. Fuskata ba walwala na sauke su Hauwa a gida tana faɗa mini wai na kwantar da hankalina ko Yallaɓai ya zo zai fahimceni in na yi masa bayani kallonta kawai na yi. In har an so ya fahimcenin ba. Mun koma gida muka iske Baby a ƙofar gida tana jiran mu ita da Salisun. Shi ya bude mini get na shiga da motata ciki. "Umma me ya sa muka dawo! Ni ba zan je sunan Anty Gimbiyar ba ne? Baby ta fara tare ni da mgana bayan na fito daga mota. "Ni matsa ki ban waje kafin na gwabje ki." Na faɗa a fusace saboda ta ba ni haushi. Marwa ce ta ja ta gefe tana yi mata mgana ni kuma na wuce cikin gida. A falon Yallaɓai na samu matsugunni ina mai da numfashi, gabaɗaya sai na tsargu kaina, wallahi ban ji daɗi ba ba kuma a son raina abin da ya faru ya faru ba. Ina zaune su Marwa suka shigo ko kallon su ban yi ba na tashi jaka da mayafi a hannu na shige ciki ina ji Yunma na kuka tana Uma na yi banza da ita. Kwanciya na yi a kan gado kawai na rasa mafita. Tunanin maganar da zan harhaɗa na kare kaima a wajen Yallaɓai na ke yi amma da kamar wuya. Tun da a san tare nake da Munnira Allah ne kaɗai zai iya fitar da ni, na kasa haƙuri sai na ɗauki waya na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba har sau uku a raina na ce shike nan wayar na hannuna sai ga kiran Suwaiba da sauri na ɗaga kiran "Suwaiba sun kira Yallaɓan ne? "E ya ce gashi nan a hanya zai zo. Ni dai na gaji da ba ma Gimbiya hakuri na baro gidan gani ni da Mubeena za mu samu adaidaita." Ta amsa mini, sai na furzar da iskar bakina kafin na ce" Wallahi Suwaiba na kasa sukuni Allah ne kaɗai zai fidda ni a wannan sabgar." "Gaskiya. Domin Gimbiya sai kuka take yi shima jaririn na kuka. Ina jin hannun nan da ta bugu ta yi gocewa ko targaɗe. Allah kaɗai ya san mganganun da za su faɗa masa in ya zo. Halima can na barta tana ta faɗin duk abin da ya faru da gayya ne ke ce kika shirya komai." "Uhm" Kawai na iya faɗa na kashe wayar. Daman ai ba ta kaunata tun marin da na yi mata na kore ta a gidana ni na san tana neman ranar ɗaukan fansa a wajena sai yau ta samu dama ai sai ta yi amfani da damarta da kyau da kyau. Ina nan zaune Yallaɓai bai kirani ba har aka fara kiran sallar mangariba. Daga Marwa har Baby ba su neme ni ba nima ban nemi kowa ba. Tiolet na faɗa na yo alwala na so na ta yar da salla. Ina cikin yin salla na ji shigowar motar Yallaɓai da ƙaran buɗe get sai da gabana ya faɗi. Ya shigo falon farko ina tahiyar ƙarshe ina jin sa yana kirana suna da karfi daga ji ran shi a ɓace ya ke. "Sadiya" "Sadiya" Ban zan iya sanin ko na ƙarishe salatin Annabi ba, na sallame salla, da hijabin jikina na fito daga bedroom na buɗe kofa na fito korido shima ya buɗe ta falo ya fito sai muka haɗe. "Na'am. Ina salla ne lokacin da ka shigo." "Me Daughter ta yi miki da za ki kwashi mutane ku je ku dake ta ita da ƙanwarta? Baki na buɗe ina kallon Yallabai yadda ya yi mini tambayar a kausaahe alamun tabbaci ma gare shi ba hasashe ba. Sai na ma kasa mgana har na buɗe bakina sai kuma na yi shuru kawai. "Ba da ke nake magana ba kin yi mini shuru kamar wani ɗan iska? Ya faɗa yana mai yi mini ihu a saman kaina. Kawai sai na ɗaga ido ina mai ƙara kallonsa kafin na ce" Ni ban kwashi mutane su je su dake ta ba. Wa ya ce maka an dake ta? Ni dai na san Munnira sun yi faɗa da kanwarta ta shigo rabo ba ta sani ba ta ture ta shike nan abin da na sani. Kuma ni har ga Allah ba da yawuna Munnira ta yi abin da ta yi ba. Ni da hankalina zan kwashi mutane aje a yi tashin hankali? Me matarka ta yi mini da zafi da zan yi mata haka? "Wa ya sanin miki. Duk abin da ya faru kina sane saboda ai su Munniran da Hauwa tare da ke suke. In kika tsawarta musu ai za su bari amma da ya ke kema akwai mugun nufi a ranki. Shi ya sa kika yi shuru sai da abu ya faru za ki zo kina faɗamini wai mai matata ta yi miki da zafi? Kika san abin da ta yi miki domin ni ba makaho ba ne tun haihuwan nan na ga take-taken ki, ko barka sai da na yi ta miki magana kika je, asibiti ma ba ki je kin duba ta ba sai da ta koma gida da na yi magana sai ki ce ba ki da lafiya. To duk na gama gano ki. Kin kuma kyauta da abin da kika yi. Saboda ke an targaɗa mini mata a banza a wofi na gode Sadiya kin ji ko? Na ce Na gode." Ya faɗa cikin hargagi har yana yarfa hannu. Marwa da Baby suka fito da sauri daga dakin su Jidda suka gan mu cirko cirko ni da Yallabai. "Ni ce mai mugun nufi a raina?. Ni Yusuf? Na faɗa ina nuna kaina cikin tarim mamakinsa. "E ke ce fa, kuma kin aiwatar da nufin ki, kin kyauta. Amma ki sani ba ita kika yi ma wannan tozarcin ba illa ni. In ma kin ji hauahi tana ta haihuwan Maza ni ba ki yi mini adalci ba. Domin na shafa faɗa miki da mazan da matan duk ɗaya ne a wajena me ya sa ba za ki yi mini kara Sadiya ki boye kishin ki ba? Abin da kika yi dai dai ne? Abin da kika yi sunan shi ne zubar da ƙima. Watarana in Saudatu ta gan ki   ba ta darajaki ba. Juzt bleme your self domin ke kika zubar da girmanki, ta bi kuma ta tattaka shi." Wai Yallaɓai har yana nuna mini hannu yana gaggaya mini magana ina kallon shi kwarmin idanuwana suna cika da kwallah. "Na ɗauka in ina da wani mugun nufi tun a shekaran baya zaka sani ba yanzu ba." "Da ba ki da shi. Yanzu kika ɓullo da sabbin hallaya marasa kyau. Kin bari sheɗan na zugaki. Tare da su waɗanda kika rike a naki. Na daɗe da sanin saboda ke su Hauwa ba sa zumumci da Daughter amma ban taɓa magana ba. Kuma a adalci ai dake da ita duk ɗaya ne yadda za su yi miki haka za su yi mata. Duk na share wannan ban taba magana ba sai abu ya zo har da duka har gidan ta? To ba ki isa ba yadda kema ban kyaleki ba suma ba zan ƙyale su ba na kira Nasir da Mutaƙƙa kowannen su zai ja ma matarsa kunne. In dai ba za su dauke ki ɗaya da Matata ba to sai dai a raba wannan alaqar taku gabaɗaya tun da ba ta alheri ba ce sai ta sharri." Ai ban san na kwashe da dariya ba, sai da na ga na yi ta cikin takaici da bakin ciki hawayen da suka zubo mini na share ina kallon Yallaɓai ido cikin ido kafin na ce"Wannan kuma wallahi ta yi kaɗan. Lokacin da tazo tare ta ganmu kuma wallahi tare za ta bar mu. Zama daram in ji mai naguda." Na faɗa ina mai riƙe kuguna. Domin na lura an gama shiryaa mai mganganu ni zai zo ya tara mini gajiya to wallahi bai isa ba. "Ni kike faɗa ma haka Sadiya? "An faɗa maka sai me? Kai waye? Mijina! Na yi wata bazawar dariya kafin na nuna shi ina faɗin" Mijina ne kai da muka yi zaman aure na shekari sama da ashirin ashe kai ba za ka iya sanin abin da zan iyawa aikatawa da wanda ba zan iya aikatawa ba? Wato duk abin da matarka da danginta suka faɗa akaina shi ne gaskiya a wajenka ko? To bari ka ji na faɗa maka ko na ce na ƙara tunasar dakai ko garke Gimbiya za ta haifa maka na Maza wallahi ko a gefen gyalena da yau ban haihu ba da bakin ciki ya kashe ni. Maganar zuwa barka ban yi niyya zuwa ba ne, duk ita a nata haihuwan ka fahimci ni ban je ba amma a lokacin da na haifi Yunma ba ka fahimci sai da ta ga dama ta zo ba? Ita ka same ta ka yi mata mgana kamar yadda ka yi mini? Wato sai ni ce marainiyar ka dole ka zo ka same ni ka sauke mini magana. To bari ka ji na rantse da wanda raina ke hanun shi ina dai dai dakai daga kai har munafukar matar taka." "Sadiya." "Yusuf" Yadda ya kira sunana cikin tsawa nima haka na buɗe murya na kira sunan shi yana huci ina huci. Sai kukan Yumna muka ji, can sai na Baby ko ni juyawa ban yi ba shine ya juya yana kallon su yara sun ga abin da ba su taba gani ba. "Marwa ki ja yaran nan ku koma ciiki." Ya faɗa yana sassauta muryan shi, "A shiga da su ciki kuma? Daga baya kenan wai an yi sadaka da bazaawara. Ai sun gama ganin ka, kana ci ma uwarsu zarafi a kan wata banza a banza.' Na faɗa ina haki saboda ɓacin rai. "Kar ƙi kara ce mata Banza." "Na ce banza a banza Yusuf don Allah ka dauki mataki in ka isa." Na faɗa ina isa gaban shi na tsaya ina riƙe kuguna. "Da gaske banza ce tun da ba ta iya ramin kanta sai dai na wani. Kuma wallahi tallahi ba ta isa na amsa laifin da ban aikata ba. Rashin kunya ba irin wacce ƙanwarta ba ta yi mini ba shi ba a faɗa maka ba sai gulma da munafunci? Na faɗa ina zare masa ido. "Ki matsa daga gabana kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba ki yi tunani ba Sadiya." Ya ɗan fara saukowa tun da ya daina ɗaga murya ko saboda yara ne oho. Marwa ta ja su sun koma ciki amma har lokacin ana jiyo kukan su. "Me zaka yi! Na ce Yusuf me za ka yi? Na faɗa ina ƙara ɗaga murya ni fa tun da ya jawo wannan faɗan to gwara a yi shi kawai kowa ya san matsayin shi. "Ƙina so ki ga abin da zan yi ne ? "E. Ina so na gani. " Sai ya wani nuna kanshi kafin ya ce" Ni kike tsarewa cikin gadara kina faɗin na ɗau mataki akan sadiya? "E sai me? Tsoron me zan ji? Ƙarshen mataki kenan ka ce ka sake ni ko Yusuf? To ai ba ƙarewar rayuwata ba ce ta zo in na rabu dakai ba sai me.' Kawai sai ya tsaya yana kallona nima ko ina kallon shi ido cikin ido. "Yau yanzu ka ce na fice maka a gida zan fita. Tun da daman ka ce ba gidan Ubana ba ne." "To ki tafin ma who stop you? Na hana ki tafiya? The door is open Sadiya. A sauka lafiya." Ya faɗa yana nuna mini ƙofar falo. Na razana da kalamansa amma ina zuciyata ta ƙekashi ban nuna masa na razana ba, kawai sai na yi mirmishi kafin na ce" Da a ce yau Sulaiman Yashe bai da gida da na sha wulaƙanci."   Ba ni da kuɗi a jikina daga ni sai hijabin salla na amma ina ganin in na koma ciki zai ga kamar na gaza ne. Sai kawai na wuce har na isa kofa falon sai na juya ina kallonsa dafe da kai a kausshe na ce. "Ni Sadiya ni yau Yusuf ka kora a gidan ka ko? "Kin ce za ki tafi kina tunanin zan tsayar da ke ne? Ki sauka lafiya na ce Halimaaa.! Ya ja sunan shima a kausaahe yana kallona ina kallon shi. Idanuwanshi sun kala nima nawa ya kala ya yi jajir sai kawai na buɗe kofar falon na fice ina jin Marwa ta biyo ni tana Umma Umma. Sai a lokacin na tuna da ita a fusace na waiga ina faɗin" Ki dauki mayafinki mu bar masa gidan shi Marwa." "Umma..amm" "Wallahi zan mare ki za ki taho mu tafi ne ko na yi tafiyata." "Zan zo." Ta fada tana zakuɗa goyon ta dake bayanta har ta fara hawaye. Baby ta fito ita da Yumna ina jin Yallabai ya rike su yana mgana da su kasa kasa. Marwa ta dauko mayafi ta fito na ji ta tsaya tana mgana da Yallaɓai a fusace na ce" Wai ke ubanki ne da za ki tsaya kina masa mgana? Ki jira har sai ya kai ga haɗa ki da jami'an tsaro sannan sai ki bar masa gidan sa." Na ga ya buɗe kofar falon ya fito Yumna na hannun shi tana ganina ta fara Uma tana miƙan hannuna na juya zan fita Marwa dake bayana ta ce" Umma ko Yumna ba za ki tsaya ki karba ba! "Ba da ita na zo ba. Saboda haka ba da ita zan koma ba." Baby ta rigo tana Umma Umma cikin kuka na tsayar da ita da hannu ina faɗin" Kar ma ki ƙariso ki koma nan ne gidan Ubanki nima gidan nawa Uban zan koma ya tattaraku ya kai ma Matar so ta haɗa da farar haihuwa duk ta riƙe " "Sadiya." Ya kira ni a tsawa ce, ko kallon shi ban yi ba na fice daga falon ina jin kukan Baby da yadda Yumna ta yanka ihu. Ni kaina duk dauriyata sai da na ji hawaye sun kece mini. Wani abu ya tsaya mini kahon zuciya, wai ni ce yau Yallabai ya kora daga gidan shi. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya. *Janafty**TKBB3N15* Lokacin da na fito daga gida na san ba ni da kuɗi a tare da ni amma hankalina bai tashi ba sai da muka kai titi. Sannan na fahimci daga ni sai kayan jikina da hijabi na fito. Takalmin kafata na silafas ɗin cikin gida ne, tsabar a yanayin da na fito ba mai daɗi ba ne. Marwa na kalla da ke biye da ni, ga Afra sai ƙananun kuka take yi tana faman jijjigata. "Marwa kin fito da ƙudi? Na tambaya ina jan majina. Saboda tun fitowarmu har bakin titi hawayena bai  tsagaita ba. "E na ɗauko ƙaramar jaka ta" Ta faɗa tana nuna mini jakar sai na sake jan hanci irin na masu kukan nan, mun ɗan jima kafin mu samu Adaidaita muka shiga na ce Ɗorayi zai kai mu. Muna tafe shuru sai kukan Afra ni dai ina ta goge hawaye lokaci bayan lokaci ina jin nono na yana zuba kenan har yanzu Yumna ba ta daina kuka ba. Sai na ji tausayinta kamar in koma in ɗaukota amma kuma gwara da na barta shima ya ji in da daɗi. "Umma." Marwa ta kira sunana tana kallona, nima da rinanun idanuwana na kalleta. "Me ya faru? Ganin ta ƙura mini ido amma ta kasa mgana. "Umma me ya sa kika taho? Da kin tsaya kun fahimci juna da Kawu " Wata uwar harara na jefa mata sai ta yi saurin kama bakinta ta yi shuru. "Kika sake yi mini maganar shi zan kwasa miki mari Marwa." Na faɗa ina huci ni kaɗai har ya yi mini wannan tozarcin kuma take tunanin na zauna mu fahimci juna? Mutumin da ya ce na bar masa gida ai ya gama magana. "Ke ko a ranki ba ki ji haushin tozarcin da ya yi mini ba. Amma kina maganar wai da ban taho ba na zauna mu fahimci juna. Tun da ke a yanayin da kika gan shi kin ga alama yana buƙatar hakan." "Ki yi haƙuri Umma " Ta faɗa a sanyaye amma ni sai na ji kamar ana hura ma ɓaçin raina wuta ma na cigaba da faɗa ta in da nake shiga ba ta nan nake fita ba, saboda ni gani nake yi goyon bayan Yallaɓai take yi ni kuma tana ganin laifina domin na bar masa gidan sa kamar yadda ya buƙata. "Umma da kin taho da ko Yumna ne? "Ba zan taho da ita ba ɗin. Lokacin da ya auro ni ai ba da ita Alhajinmu ya haɗo masa ba. Su zauna gidan ubansu nima gidan nawa uban za koma." "Umma tana ta kuka fa" "Ke zan ci ubanki fa Marwa in ba ki ƙyale ni da waɗanan mganganun naki ba. Kina ƙara tunzarani." "Allah Ya ba ki haƙuri" Ta faɗa tana sunkuyar da kai kamar munafukar tsabar yadda ta ba ni haushi kamar na kai mata duka. "Namiji ya yi maka irin wannan wulakancin kuma don ba ka da zuciya sai ka cigaba da zama? To ko ke Kawu ya yi ma haka ni uwarki na ba ki Umarnin ki baro mishi gidan shi ki dawo gida domin ya san ubanki na da gida ba a daji ya auro ki ba." Ba ita kaɗai har mai Adaidaitan sai da ya juyo yana kallona na haɗe rai ina harare harare. "Hajiya a dai yi haƙuri. Rayuwar auran yanzu duk ɗan hakuri ne." Hararan bayan shi na yi, domin ni yanzu duk wani namiji na gama sallama shi wallahi. Duka halin su ɗaya ba su da adalci sannan butulai ne. In za ka yanki naman jikinka kana ba su suna ci wata rana sai sun nuna ma duniya kai ne mara amfani a wajen su. Ni yau Yallaɓai ya kalla ido cikin ido ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa wai har yana faɗin an targaɗa masa mata a sanadina. Ai na ɗauka yadda ya zo yana cika yana batsewa zai rama mata ne, sai wataƙila ya ji huce daga raɗaɗin taba matar so da aka yi. Ban ga laifin su ba duk mganganun da suka shirya masa in har ya yi amfani da hankalin shi da tunanin shi bai kamata ya fara da haka ba, da sai ya fara yin bincike kafin ya zartar da wata mgana. Har muka sauka a Dorayi ni kadai na ke cika ina batsewa ina karkaɗa kafa. A bakin titi muka sauka Marwa ta biya shi kuɗin shi da taka da kafarmu muka ta ka zuwa gida. Lokacin ana ta kiraye kirayen sallar isha'i a wasu masallatan anguwan. Ai ban ji wani kukan baƙin ciki ya taho mini ba sai da na ji kafafuwana sun taka zauren gidanmu. Bayan shekaru ashirin da wani abu yau Yallaɓai ya bar mini tarihi. Tarihin ma mai nauyin da na ke jin sa har a cikin zuciyata. Ni ce a gaba Marwa na bin bayana. Ba wutar nepa amma akwai hasken tocila a tsakar gida sai da muka ƙariso tsakar gida sannan na ga Alhajinmu duke yana alwala. Gwaggo ce ke tsaye tana haskamai da fitila. Ni na yi sallama amma muryata ta shaƙe da farko, sai da na sake yi kamar a tare ni da Marwa. Gwaggo ta amsa lokaci ɗaya ta nai mai hasko fitila cikin mamaki. "Sadiya.'; Gwaggo ta faɗa cikin mamaki da har ya bayyana a muryanta Alhajinmu kuma sai da ya idar da alwala sannan ya miƙe yana mai kiran sunana. "Dubu" Kamar yana tantama ɗin ce ko ba ni ɗin ba ce. "Na'am Alhaji." Na faɗa cikin karyewan sauti kafin lokaci ɗaya na fashe da kuka. Gwaggo ta ce" Subhanallah ke da waye haka? Alhajinmu kuma duk ya ruɗe faɗi yake yi. "Maimuna kama ta ku shiga ciki. Ba lafiya" Kamar haɗin baki sai ga nepa sun kawo wuta tsakar gidan ya yi haske ɗau. "Marwanatu." Alhaji da Gwaggo suka haɗa baki wajem ambaton sunan ta. "Na'am." Ta amsa itama a sanyaye. Ai sai Alhajimmu ya kalli Gwaggo itama ta kalle shi Allah kaɗai ya san mai suke sakawa a zuciyarsu amma in zan iya karantar fuskokin su, sun bayyana damuwa tare da mamakin ganin mu a tare a wannan daren. "Dubu lafiya? Me ke faruwa ne? Me Marwanatu ke yi tare da ke? "Alhaji ƙafafuwana sun fara rawa. Allah ya sa dai lafiya.' Gwaggo ta faɗa cikin damuwa. "Ina fa lafiya. Ba lafiya Maimuna " Alhajinmu ya faɗa shima a muryansa har ta bayyana damuwa. Muna tsaye ni da Marwa mun kasa mgana, gwara ita ba kuka take yi ba ni kuka na ke yi har yana ba da sauti. "Shin ba ku faɗa mana abin da ke faruwa ko sai kun sarƙe mana Numfashi da zullumi? Gwaggo ta faɗa tana ɗan karisowa in da muke tsaye. "Ke Sadiya bar kuka. Taho mu je abin da ke faruwa.' Ta faɗa tana riko ni, ina jin ta taba ni sai na faɗa jikinta na ƙara fashewa da kuka ina faɗin" Gwaggo Yallaɓai ne ya ce wai na bar masa gidan sa" "Innalillahi wa'inna ilaihirraju"un. Gwaggo ta yi salati. "La'ilahaillalahu." Alhajinmu ya karɓa. "Muhamadan rasulillahi." Gwaggo ta ƙarishe cikin wani yanayi "Da kika yi masa me zai kore ki da girman ki da kuma daren nan? Gwaggo ta tambaya daga jin muryan ta za ka san hankalinta ya tashi. "Ban yi masa komai Gwaggo a kan matar shi ne ya ke son ya wulaƙanta ni." . Na fada ina shessheƙa. Gwaggo ta na bubbuga bayana alamun lallashi ta ce"Kai jama'a. Me ya sa Yusuf zai haka? Da girmansa? To ita Marwanatu ba  na gan ku tare a wannan daren? "Suna ta zo. Gimbiya ce ta haihu yau suna suka taho daga Rano ɗazu da rana" Ina jin Gwaggo ta sauke numfashi kafin ta ce" To da sauƙi ai na ɗauka itama wata matsalar ce." "Umma ce ta ce na taho mu tafi. Mun baro Baby da Yumna na ta kuka." Marwa ta faɗa kafin Gwaggo ta yi magana Alhajinmu ya ɗan murmusa yana so ya yi magana sai kuma ya yi shuru. "Alhaji ya ka murmusa? Ka na ji surukin naka da ɗazun nan ka gama yabon sa ya baka kunya ya koro maka y'a kusan shekaru ashirin da aure cikin dare." "Ho Mata kenan ku dai ba a rabaku da son kai. Ni daman na san ai ta tsuniyar gizo ai ba ta wuce ta ƙoƙi ko? "Ban ga ne ba Alhaji. Kuka fa Sadiya ke yi? "Duk na ji. Kamata ku shiga ciki bari na je masallaci na dawo sai mu zauna mu yi magana. Allah ya rufa mana asiri.". Ta amsa da amin ya fice ni kuma Gwaggo ta rike ni zuwa falon Alhaji Marwa ta bi bayan mu. Zama muka yi a saman kujera mai zaman mutum biyu ni da Gwaggo. "Wai shi Yusuf din ya ce ki bar masa gidan shi! "Wallahi shi ya ce Gwaggo " Na faɗa ina jan hanci irin na masu kuka. "Me kika yi masa da zafi haka? Gaskiya ya ba ni mamaki ai ko mai kika yi masa bai kamata ya yi miki haka ba " Ina goge hanci ina zayyana ma Gwaggo abin da ya faru ina hawaye ina faɗin" Abin takaici Gwaggo wai ni Yallabai ke kallona ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa saboda tana haihuwan yaya maza ni kuma mata shine ina bakin kishi da ita na kasa hakuri na saka an dakar masa mata shi ne ya zo yana ta faɗa mini mganganu son ran shi daga ƙarshe ya ce na bar masa gidan shi" Gwaggo ta yi salati ta dire kafin ta ce"oH ni Maimuna. Ashe yarinyar makira ce? Ina ganinta shuru shuru kamar ta Allah. Su suka shirya masa komai, shi kuma laifin sa ɗaya rashin bincike sannan na ga ɓakin sa da ya iya buɗe baki ya ce ki bar masa gida Haba. Ai ba ki cancanci wannan tozarcin ba.' Uhm" Kawai na iya cewa saboda zuciyata suya take yi. In ina tuna abin da ya faru. "Umma ba cewa fa ya yi ki tafi ba. Ke kika ce mai za ki tafi ya ce shi ba zai hana ki ba " Marwa na ƙura ma ido cikin takaicinta da bakin ciki. Na ma kasa mgana saboda na rasa abin da zan ce mata. Ina tunanin ba ni ce ƙanwar uwarta ba Yusuf Muhammad Inuwa ne. "Af to me ya rage? Ai duk ɗaya. Mata ai mu haka Allah ya hallice mu, wata ƙila ta fadi haka ne ta gwada zurfin matsayinta shi kuma sai bai ba ta kunya ba, ya nuna mata iya na shi tattalin a kanta ya ce ta tafi ba zai hana ta ba. To ai shike nan bari Alhaji ya dawo sai ya ji shi ne da an tashi hira sai ya ce mijin Dubu  dabam ne ina ganin ƙimarsa. To ai yau ga ƙarshen ƙima nan ya kore masa ƴ'a gabanin mangariba da isha'a da girmanta da komai, bai yi miki haka kina da kuruciya ba sai da shekaru suka fara gangarawa." Gwaggo sai faɗa take yi ni sai na ga ma ta fini ɗaukan zafi. Har a ƙasan raina ban ji daɗin da ma zo gida na buɗe cikina ba amma kuma ai shi ya ja. Da bai yi abin magana ba da ba a yi magana ba. Alwala muka yi ni da Marwa muka yi salla muna cikin sallar Alhajinmu ya dawo shi ya sa muna idarwa Gwaggo ta zo ta kira ni, da man a ɗakin Mama muka yi sallar. falon Alhajinmu na koma yana zaune ga kwamukan abinci Gwaggo ta jera masa amma bai taɓa komai ba. Duk da ya nuna kamar bai damu ba amma na san ya damu ya kasa yin wani abu ba tare da ya ji damuwata ba. Allah sarki Alhajinmu ina son shi saboda in dai matsala ta tunkaro iylanshi shi baya samun natsuwa sai ya ga ya yi maganin matsalan nan. Dattijo ne mai juriya da jajircewa. Sai a lokacin na ji nadama da tunanin me ya sa na taho gida na ɗaga musu hankali? Da man ban zo ba, ssi wata zuciya ta ce gwara da kika zo a karon farko yau dai Yusuf zai fahimci ba da gidan shi kaɗai kika dogara ba. "Dubu." Alhaji ya kira ni kamar yadda ya saba. Ina mai zama gaban shi na tankwashe kafa na amsa masa. "Na'am ina yini Alhajinmu." "Lafiya lau. Sai kika baro mini mata can tana kuka? Kaina na kasa na kasa mgana. "Bai kamata laifin wani ya shafi wani ba Dubu. Rukayyatu nawa take da za ta fara karban hukuncin da ba na ta ba? Ba mama take sha ba har yanzu? "E Alhajinmu." "Kin ji ko? Me ya sa kika yi haka Dubu? Koda na sanki da fushi ai ban san ki da rashin tausayi ba ko? "Ka yi hakuri Alhaji na yi kuskure." "Kin yi kuskure babba. Domin kin ɗauki alhakin ran da bai ji ba, sannan bai gani ba, kar ki ƙara irin haka komai zai faru kar ki yi hukunci a in da bai dace ba. Ina ruwanta? Ta sam ne babanta ya yi miki? To ko domin wata rana ki yi aikin hankali kin ji ko? "Na ji. In sha Allahu ba za a sake ba." Na faɗa ina wasa da gefen hijabina. "Yauwa. In kin baro ita Mai sunan Gwaggon ta ku ita babba ce. Amma Rukayyatu kin ɗauki haƙƙin ta." Ni dai na yi shuru, saboda sai a yanzu da Alhaji ya sake jadadda mini sannan na sake fahintar ban kyauta ba. Ina jin nonuwana suna cika na san tana can tana rigima. "Allah ya kyauta na gaba." Na amsa da Amin shuru na wani lokaci kafin Alhajinmu ya sske kiran sunana. "Halima." Tun da na ji haka na san mganar mai girma ce. "Na'am" "Me ya haɗa ki da Yusufa har ya ce ki taho gida a daran nan? Nan da nan na gyara zama cikin natsuwa na warware ma Alhajinmu komai tun daga farko na haihuwan da ta yi ban je barka da wuri da abin da ya faru yau. Har mganganun da muka yaba ma juna na fada masa, ni fa duk a tunanina Alhajinmu zai goya mini baya in ji ɗibar albarkar da Yallabai ya yi mini saboda matarsa. "An faɗa masa ƙarya da gaskiya daga can Alhajinmu kawai yana zuwa gida ba bincike bai ji ta bakina ba kawai ya fara mini masifa da faɗa kamar zai dage ni." Na ƙarishe faɗa ina goge ƙwalla da gefen hijabina. Domin ina mai da yadda aka yi hawaye suka kece mini. Alhajinmu ya yi shuru ni na ma ɗauka ko wani abu ne sai da na dago kaina na ga kallona yake yi na wani lokaci sannan ya gyaɗa kai ya yi wani mirmishin su na manya kafin ya ce. "Dubu ba dai kina so ki faɗa mini rashin kunya kika yi ma mijin naki ba? "A'a. Kawai dai raina ne ya baci nima na ma yar masa da martani Alhajimmu." Sai ya yi dariya wannan karon mai sauti kafin ya ce" Hohoho hausawa suka ce ko shekara ɗari ka yi baka haɗu da mutum ba. In ka fara ganin shi tambayi halin shi, domin hali zanen dutse ko zai iya sauya komai to ba zai iya sauya wannan halin na shi ba." Na yi kasaƙe saboda ina so na fahinci in da maganar Alhajinmu ta dosa. "Dubu na san ki sarai bakin ki ba ya iya shuru. Kina da saurin hasala da faɗa. Kina so na ce kinyi daidai da abin da kika yi ne? To ba zan ce kin yi daidai ba sai ma na kira sunan ki ki amsa na sanar da ke da kaushin murya da cewa ba ki kyauta ba." Baki na buɗe ina kallon Alhajinmu. Duk da na san halin shi amma ban tsammaci zai iya cewa wai ban kyauta ba? Me na yi na rashin kyautawar? "Na san a cikin zuciyarki kina ta tamtaman me kika yi na rashin kyautawa ko? Duk buɗe kunnuwanki da kyau Dubu. Kin yi rashin kyautawa da yawa a cikin duka abin da ya faru. Kuma hukuncin da Yusuf ya so yankewa yana kan daidai ne shima. Tun da ba a gaban shi komai ya faru ba shima faɗa masa aka yi, kuma da bakin ki kika ce daga can gidan abokiyar zaman taki an faɗa masa ƙarya da gaskiya. To ke me ya sa da ya zo gare ki, ba ki zaunar da shi kin faɗa masa gaskiyan abin da ya faru ba? "Alhajinmu bai ba ni da mar haka ba faɗa kawai yake yi ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba." "Shi ne kuma yana faɗa kina fada. Har kika yi masa rashin ɗaa da gatsen ko yanzu ya ce ki bar masa gida za ki ta fi ko? To menene abin kuka don ya yi miki abin da kika bukata Dubu? Ai sai na kasa mgana na dukar da kaina kasa. In Alhajinmu ya saka a ɗaki tun kana jin kana da gaskiya sai ka sare ka fahimci kai ne ba ka da gaskiya saboda irin kalaman da yake amfani da su wajen jawo hankalin mutum "Ni da ke nan da Yusufa zai ƙara aure na kira ki, a wannan falon kika zauma kamar haka na yi miki nasiha? A cikin duka nasihin da na yi miki wata kalma na yi ta jadadda miki da in kika rike ta zaki rabauta? "Haƙuri. Ka ce na je na yi ta hakuri wata rana ni ce zan zama mai riba." "To ashe ba ki manta ba? To me ya sa yanzu kika kasa haƙurin kika kuma kasa rabauta da sakamakon masu hakuri? Sai kawai na sake fashewa da kuka ina fadin" Alhajinmu na yi ta haƙru wallahi ba ka san hakurin da na ke yi ba ne. Ko wani abu ne suka yi mini da na tuna da nasiharka na ke ma yar da komai ba komai ba. Yau ma ɗin ya ƙure ni ne shi ya sa na tanka masa." Na gama faɗa ina ta jan hanci saboda kuka. "Du ka na ji kin yi haƙurin a baya amma abin da kika aikata yau duk ya kore wancan haƙurin na ki na baya " Na ma kasa mgana na buɗe baki zan yi sai na ma yar na rufe. Ni fa na manta ne in dai Alhajinmu ne ba zai taɓa bani goyon baya ba da gaskiyan Gwaggo Alhajinmu na ganin ƙimar Yallaɓai a duk cikin surukansa ya sha faɗa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. "Kina maganar ke ma da kika haihu ba ta zo ba kaza da kaza ina ruwan ki da wannan? Ke dai ba ki yi don Allah ba ai bai kamata,ki duba ita abin da ta yi miki ba. Ke kin yi mata domin Allah da zaman tare. Ruwanta ne ta ma yar miki da martanin Alheri ko sharri. Ke dai Ubangiji ya yi amfani da zuciyarki kuma ladan ki na wajen Allah. Ba hujja ba ce mijinki ya ba ki umarnin ki je asibiti ki dubata ki yi zaman ki, ki ƙi zuwa kin ga kenan kin saba umarninsa kuma mala'iku sun yi fushi dake matuƙar ba ki nemi gafaran shi ba. Sannan kuma abin da ya faru yau sanadin ki ne, ko da ruwan zam zam ba za ki iya wamke kanki ba tun da kin je wajen sannan waɗanda ke tare da ke ne suka yi hatsiyani ni da ke mun san ke ba ki saka su ba amma ba za mu ƙi gaskiyan cewa a sanadinki suka yi komai." "Wallahi ni Alhajinmu ban ce kowa ya yi faɗa saboda ni ba." Na fada ina ƙara rantse masa da Allah. "Na ce miki ni da ke mun san ba ki saka su ba. Amma shi da sauran mutane in suka ji labarin za su yarda ba bakin ki a ciki! Ki yi tunani ki gani. A wannan gabar Yusufa ba shi da laifi abin da ya ji da shi zai yi amfani." Ina sharan ƙwallah na ce" Amma me ya sa ba zai yi bincike ba sai ya rufe ni da faɗa har yana ce mini ina da mugun nufi a raina? Dariya na ga Alhajinmu ya yi kafin ya ce" Dubu ke kika jawo duk zargin da ya yi miki. Me ya sa kika bashi kofar ya fahimci kamar kina jin haushi da haihuwar da aka yi mass? Ki tuna  shi ma fa ɗan adam ne yana da zuciya kamar yadda kike da ita. Sheɗan ne ya kawata masa a zuciyarsa amma ina da tabbacin ba haka yake nufi da gaske ba. Ai in da kima da mugun nufi akan matarsa da tun a farkon auran shi zai fahinci haka." Ni sai na ga kamar kawai ina zaune Alhajinmu na ta faman boye laifukan Yallaɓai yana bayyana nawa. "Har fa ce mini ya yi wai ina kishi da tana haihuwan Maza ni kuma Allah bai ba ni ba " Na faɗa hawaye na kece mini saboda takaicin kalamansa. "Haka zai yi tunani haka ma kowa zai yi tunani. Haihuwa kuma na Ubangiji ne daman Allah ya faɗa mana wasu zai ba su maza da mata, wasu mata kaɗai wasu mazan kaɗai wasu ma har su koma ga Allah ba zai ba su haihuwan ba ki godema Allah kina cikin zabaɓɓun Ubangiji. Maganar ita tana yin farar haihuwa ki bar ta da tunaninta, tun da ai shi mijin na ku bai ce ba ya son matan ba duka yana so kuma duka ƴaƴan shi ne. Sai ki roƙi Ubangiji ya baki mai albarka daga Mazan ko daga matan." Kawai sai na cigaba da sharan ƙwalla domin ni dai Alhajinmu ya gama ƙure duka mganganuna. "Ki yi haƙuri ki daina kuka ba wai ina goyon bayan shi ba ne a'a ina faɗa miki gaskiya ne a matsayina na adalin Uba. Ba wai don kina ƴ'ata na goyo bayan ki ba, a'a ni ke da shi duka ƴaƴana ne zan yi miki adalci kamar yadda zan yi masa. Ki daina kuka ya isa haka nan ba wani abu ba ne. Kawai sheɗan ne ya shiga tsakani ganin kun kasa samun fahimtar juna." "Alhajinmu ta ya ya zai fahimce ni? "Ta hanyar amfani  da kalamai na kwantar da hankali kar ki ɗaga sautin ki sama da na shi, na tabbata da kin yi haka da kun fahimci juna.' "Uhm" Na sha numfashi saboda na fahimci Alhajinmu ba zai gane karatun kurma ba. Murmishi ya yi ganin na yi shuru yana kaɗa kai ya ce" Kukan ya isa kin ji share hawayen ki." Ban yi musu ba share hawayena. "Yau kike so ki koma gidanki ko sai gobe da safe? Na kalli Alhajinmu baki buɗe kafin na ce" To kore ni fa ya yi me ya sa zan koma? "Ashe ba yanzu na gama yi miki nasiha na ganar da ke kuskuran ki ba? To za ki koma gidan auran ki in sha Allahu. Shima ai na san yana can cikin damuwa in bai zo a daran nan zai da safe ina da tabbacin haka" Kallon Alhajimmu na ke yi na kasa mgana yadda kawai yake da confident a kan Yallaɓai ke ba ni mamaki. Don ba warware masa komai ba! Ai wallahi da ya san wani abu da tuni zai daina wani cika baki a kan shi. "Har gobe ina ganin sa da ƙima. Tun bayan shekaru ashirin da doriya na ba shi amanarki dai dai da rana ɗaya bai taɓa kawo mini ƙaran ki ba. Ko da yaushe ya zo gaisheni godiya yake yi mini yana yaba miki. Duk da na san kina saɓa masa shina haka amma bai taba fada mini saɓanin alherin ki ba. Ya zauna dake cikin daɗi da rashin sa. Kema ai ba ki taba kawo mini ƙaran sa ba sai yau. To na yau ɗin ma duk kishi ne shi ya sa ban ɗauke sa wani abu mai girma ba. Ki koma gidanki ki daidaita da mijinki domin yana yi miki kara ba domin komai sai domin yana son ki. Ki je ki ba shi haƙuri ki kara haƙuri  Mai hakuri in ya yi ta shan haƙuri ba ya kiɓa lokaci ɗaya amma watan wata rana zai zama giwa in har ya koshi da hakuri" "Ki yi hakurin kin ji ko? Ki koma ki cigaba da Biyayya aure. Domin Aljannarki tana a karƙashin diga digin mijin ki ne Dubu. In kin yi masa biyayya ki rabauta. In kin saɓa masa ki taɓe. Ni ba ruwana na riga na sauke haƙƙin Ubangiji na in kin bauɗe na faɗa miki gaskiya." Na yi shuru ban yi magana ba kaina na ƙasa amma na daina kuka. "Kin ji ko? Ya sake faɗa yana kallona sai na gyaɗakaina kafin na ce" In sha Allahu Alhajinmu na gode Allah ya ƙara girma." Ya amsa da Amin kafin ya cigaba da faɗin" Da dake da Rahila ne na ke yawan kafa misali da ku. Na kan ce tun da na aurar da ku ba ku taɓa tada mini hankali da korafin mzajen ku ba. Sannan suma ba su taɓa kawo mini maganar sharrin ku ba sai alheri. Amma sai ga shi a wancan satin nan in da kike zaune Muntari ya zauna yana karanta mini wani abu daga cikin na ƙuntata da Rahila ta ke yi masa ya kasa haƙuri ya kasa tanƙwasata sai da ya karya kaurin nan ya zo gabana yana faɗa mini na kira ta na yi mata faɗa. To kema ko sati ba a yi ga ki nan zaune kina kawo mini suka akan mijin ki, ke da Rahila kuna so ku ba ma misalina kunya ne? Da sauri na ce" Ba za mu ba ka kunya ba in sha Allahu Alhajinmu." "To na ji daɗin haka. Allah ya sa. Allah ya yi muku albarka addu'ata a koda yaushe ya zaunar da ku lafiya sannan ya yalwata ma mazajen ku samun su yadda za su riƙe ku bisa gaskiya da amana." . Na amsa da Amin kafin na yi tambayar da ke sosa mini rai. "Alhaji me Rahilan ta yi ma Ya Muntari? "Ina ruwan ki? Wannan tsakanina da ɗana ne. Ya faɗa mini kuma na sauke haƙƙi na kirata a wannan falon na yi mata faɗa ta yi mini kuma alƙawarin ta daina. Kamar yadda kema ba zan yi taɗin nan da kowa ba itama ba zan zo ina faɗin rashin kyautatarwarta ba. Ni kamar alƙali ne shi kuma alƙali ana son shi da gaskiya da rike sirri " "Ai ni za ta faɗa mini Alhaji" Na faɗa ina mirmishi shima mirmishin ya yi kafin ya ce" Wannan shima dai duk tsakanimku ne. In ta faɗa miki ba ta yi laifi ba. Domin tare kuka tashi kuka girma, akwai sirrukan masu yawan da zaku tattauna a tsakaninku na yan uwa." "Haka ne Alhaji." "To kin gani. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya. Tashi ki je ki samu wani abu ki ci sannan ki kwanta da safe ki koma ɗakin mijinki ki tallafi yayanki. Ke da kika kusa kai ga suruki Dubu amaryata da na saka ana can jami'a ana ta karatu ko? Ina dariya na amsa masa" E Alhaji amma ai ta ce ba ta ssku ba auranku na zoɓe ne." "Manta da ita, ga matata ta gaskiya me zan yi da ta roba? Amma dai ina nan ina jiran ta a falon nan ta kawo mini suruki na ga ko na fishi dogon hanci." Me zan yi in ba dariya ba, da man shi Alhaji dariyan ya ke so na yi.  Ya sallame bayan ya ce na ce Marwanatu ta zo su gaisa ita da wannan yarinyar na ta mai kukan tsiya duk ta cika masa kunni. Na fita ina dariya na koma ɗakin Gwaggo na iske su suna ta hira na faɗa mata saƙon Alhaji sai ta sunkunci yarta ta fuce tana faɗin" Shi ta ke jira ya lallasheta." Bayan fttan ta Gwaggo ba ta matsa mini sai ta ji yadda muka yi da Alhaji ba amma dai na faɗa mata zan koma saboda Yumna. "E gaskiya ya kamata baiwar Allah na san za ta sha kuka." "Wallahi  Gwaggo Nonuwana har sun fara tasawa." "Wayyo sannu. Ko za ki sha panadol ne in kin ci abinci." "To Gwaggio" Ita ta kawo mini abincin Tuwo ne miyar kubewa bushasshiya. Na ci da yawa muna hira ban gama ba Marwa ta dawo ta ce ma Gwaggo ta je ta ba ma Alhaji Tuwo kafin ya suma saboda Yunwa. "Ai  da man ke ce kika tsayar da shi, amma shi uwarhaka ai ya koshi ya kwanta." Muna ta dariya ta fice ta bar mu, Marwa ta zauna muka ƙarishe cin tuwo da ita ta fita da kwamukan ta ɗibo mana ruwa na sha mgani da shi. Akwai katifa a ɗakin Gwaggo ita Marwa ta shimfiɗa za ta kwanta ni kuma na ce ina gado Na yi mata sai da safe ganin waya a hannunta sai na yi tunanin mijinta za ta kira. Har na juya ta kirani. "Umma." Na juyo ina kallonta. "Za ki koma ko? Sai da na yatsina fuska kafin na ce" Alhaji ya matsa. Zan koma gobe in sha Allahu." Sai ta kama murna. Na yi shigewata na bar ta. Kayan jikina na cire, na samu wata rigar Gwaggo ta makka ce Ma'u ta kawo mata ita da daɗewa lokacin da mijinta ya koma. Gwaggo a lokacin ta ce ba ta so wai na yara ne muka matsa mata ta karba. Ashe za ta yi mini amfani ita na zuba mai taushi har kasa na ɗaure kaina dakallabi na haye gadon Gwaggo. Na daɗe ban yi barci ba kewan gidana kewar 'ƴayana da mijina. Su suka taru suka yi mini rufdugu na yi ta juye juye sai can barci ya kwashe ni har ina makara sai da na ji Gwaggo na kiran sunana. Sannan na iya tashi na je na ɗauro alwala na yi salla nonuwana sun yi mini nauyi sun kwana a ba tsotsa ina jin kamar zazzaɓi zai kama ni amma haka na fita na share tsakar gidan nan tas na haɗa wamke-wanke Marwa ta karba sannan na je na gaida Alhajinmu ƙara jadadda mini yake yi da na ƙarya na shirya na koma gidana. Ni dai ba ni da ta cewa daman ai dole na koma ko domin Yumna amma a kasan zuciya ina cewa ba don halin Yallaɓai ba shima. Ɗumamamman tuwon jiya muka ci da safe, na ƙara shan panadol na kwanta da niyar na dan runtsa barci ya sarkeni, tun wajen tara na kwanta ni ce sai wajen sha ɗaya na tashi. Shima ɗin tada ni Marwa ta yi wai tana faɗa mini ga su Kawu nan. "Wani kawun? Na faɗa ina mitsike idanuwana masu cike da barci Kafin ta samu zarafin magana na ji kukan Yumna ai da sauri da diro daga saman gadon Gwaggo a ƙofar falo muka ci karo da Baby ɗauke da Yumna tana ganina ta rumgumeni tare da Yumma tana faɗin" Umma mun yi kewarki jiya. Yumna ta kwana kuka Abba ne ya yi ta lallashinta yana ta ba ta tea" A zuciyata na ce da kyau na ji daɗi da ya ɗanɗana. Ture Baby na yi baya kaɗan ina karɓan Yumna wacce ke ta miƙo mini hannu tana faɗin Uma. Da sauri na karɓeta na rumgumeta ni da ita muka sauke ajiyar zuciya kamar mun shekara ba mu ga juna ba..zama na yi a saman kujera na fara ba ta nono. Allah sarki baiwar Allah ta karɓe da sauri tana sauke numfashi. Ina shafa kanta ina mai jin tausayinta. Sai na ga an yi mata wanka itama Baby ta yi wankanta. "Ba ki je makaranta ba? "Umma mun fa makara. Abba bai yi barci da wuri ba sai 7:30am muka tashi fa." Ta faɗa tana kirga mini da hannunta. "Uhm wa ya yi ma Yumna wanka? "Abba mana. Ni kuma na yi da kai na shi ya soya mana doya da kwai Umma." "Ya kyauta." Na faɗa ina jinjina kai Marwa na kalla ganin tana ta shiri alamun kamar ta yi wanka ne. "Gida za ki leƙa? "A'a tafiya za mu yi" "Ke da wa? "Ni da Kawu mana. " Sai ta ga na yi shuru ina kallonta sai ta yi dariya kafin ta ce" Umma ni da Baban Abadallah." Sai na ware ido kafin na ce" Ya zo ne? "Ya zo tun dazu tare muka zo da shi da Abba." Baby ta fanshe ta sai na fara tunanin ko wa ya faɗa ma Kawu ko kuma dai ya zo ɗaukan Marwa ne bai san abin da ya faru ba sai yau. "Ni ba ruwana. Nima da safen nan ya ce mini zai zo Abban Jidda ya yi masa waya akan kum samu matsala." "Uhm" Kawai na ce na cigaba da ba ma Baby Nono Jidda na ta yi mini surutu na yi kamar ban jiba. Wayata na gida ban san adadin waɗanda suka kira ni ba. Ba daɗewa muka ji muryan su a tsakar gida sai ga Gwaggo ta shigo da hijabinta tana faɗin" "Ki ta so ta..'" Ganina a zaune sai ta ce" Au ashe kin tashi? To maza ki shirya ga mijinki can na jiran ki." Baki na tura kafin na ce" To ban yi wanka ba zan tafi Gwaggo " "Ba gidan ki za ki koma ba? In kin je can sai ki yi. Maza tashi kafin Alhaji ya ji ya leƙo da kansa kin san halin shi." Ba ni da yadda zan yi haka nan na yanke ba ma Yumna Nono Gwaggo ta karɓeta tana yi mata wasa. Kayana na je na saka na ɗauko hijabina na saka. Baby tuni ta fita wajen babanta Marwa na yi ma magana ko yanzu za su wuce ta ce zai kaita gida ta gai da Ya Aina. Amma kafin su wuce za ta biyo gidan tun da akwai kayanta a can na ce mata toh. Na karɓi Yumna hannun Gwaggo na shiga yi ma Alhajin mu sallama. "Allah ya yi miki albarka. Mijinki ya yi ta bani haƙuri sharrin shedan ne Allah ya tsare na gaba.' Na ce Amin sannan ya yi ma Yumna wasa, har yana ba ta 500 ya ce kuɗin zance ne. Na karɓan mata ina masa godiya. Koda na fita kofar gida suna jikin motar Yallaɓai shi da Kawu suna mgana amma kowannen su da motar shi ya zo. Baby na cikin mota da alamu ni suke jira. Ba domin Kawu ba wallahi shigewata mota zan yi amma saboda shi na tsaya ina gaishe shi. "Lafiya lau Surukata. Ashe kuma abin da wannann mara mutumcin ya yi miki kenan? Sai na kasa magana amma na kauda kaina bana son ma mu haɗa ido da Yallaɓai. "Ai da kin kirani wallahi sai na shigar miki. Amma ko yanzu na yi mata faɗa na ce kuma ya gode ma Allah ma ya samu surukai na gari in wani ne Alhaji ai ko kallon sa ba zai yi ba. Maimakon haka ma sai ya karrama mu, muna bashi haƙuri muma yana ba mu." Nan ma na yi shuru kaina na kasa, Yumna ce ma ke miƙa ma Yallabai hannu tana faɗin Aba da sauri na janyeta ina ƙara haɗe raina. "Ki yi haƙuri kin ji ko? Fushi ne da shedan suka yi tasri a kan shi amma ya tuba ya ce ba zai ƙara ba." Sai na ɗan kalle shi ta gefen ido kansa na ƙasa yana ɗan mirmishi kamar ba shi ne ya yi mini wulakanci ba jiya. "Ba komai. Allah ya kyauta na gaba.' Suka amsa da Amin gabaɗaya. Shi ya buɗe mini gaban mota na ƙi shiga na faɗa baya kusa da Baby. Mun tafi muka bar Kawu anan amma ya ce za su biyo kafin su wuce. Muna tafe a hanya yana ta kallona ta madubin gaban mota ni ko na yi cuɗun ciɗun da fuska bai ga fuskar ma wata mgana ba. Haka muka isa gida ni ko jiran shi ban yi ba na yi wuce wata cikin gida. Ya biyo ni har ɗaki yana so ya yi mini magana na bar masa yarsa nan saman gado na faɗa tiolet na banko masa ƙofa ai ban fito ba sai da na ji ƙaran jan get alamin ya fita sannan na fito ina jan tsaki. Sai da na yi wanka sannan na duba gidan. Kitchen dai ya sha kyau Baby na saka ta gyara shi ta goge da falon su. Falon Yallaɓai ko ta kan shi ban bi ba girki ma doya na ce Baby ta fre mana ta sulala mu ci da mai da yaji sai bayan azhar na duba wayata. Hauwa da Munnira sun kikkirani da Rahila sai Suwaiba. Munnira na fara kira ba ta ɗauka ba sai na kira Hauwa. Ita ke faɗa mini Mutaƙka ya yi fata fata jiya akan abin da ya faru, ni tsabar haushi ban san lokacin da na ce. "Ku fita hanyata ku fara aminta da Gimbiya shine faɗan na su." "Wani irin magaana ne wannan? Ai ba su isa ba. Shima ai na faɗa masa ba zai yuyu ba sai ya ce wai shi bai ne na rabu dake ba amma na daina wulakanta Gimbiya saboda ke Ya Tafida ya ce ba ya jin daɗin haka." "Kar Allah ya sa ya ji daɗin mana.' Na faɗa cikin ɓacin rai, ban faɗa mata na je gida har na kwana ba amma na faɗa mun hau ramar da ba ta da ganye mun fado a jiya da daddare ni da Yallaɓai. "Kai Gimbiya ba ta ji daɗi ba. Ta haɗa karya da gaskiya.' "Daga shi har ita in sun fasa sun raina Ubangijin su.' Sai da na faɗa sannan na rufe baki ina waige-waige ni kaɗai sai da na yi dariya Hauwa ma sai da ta dara." "Haushi take ji kuna tare da ni, ba ma ita ba har su Anty Bahijja ma. Kuma sai dai su mutu wallahi.' Hauwa ta ce kwarai mun daɗe muna mgana kiran wayar Munnira ne ya katse mu. Ta ce mini Ashe ta koma tun safe,Marwa fa? Na ce mijinta ya zo ɗaukanta ta je gida ta dawo. Munnira zage-zage ta dinga yi tana faɗa mimi hauka hauka ta yi ma Nasir jiya ya zo yana ce mata ita ke hassada fitina tsakanin matan Yaya Tafida." "Ai ko jiya ya ga tijara. Na fashe kamar tayagas faaa faaa. Haka nake yi ta in da na ke shiga ba ta nan nake fita ba. Ai daga karshe sai ya dawo yana bani haƙuri." Ina dariya na ce" Duk haka suke suna da son kan su. Amma ba su da laifi abin da Yallaɓai ya faɗa musu. Za a ce ke ce ke da fitina ya ja miki kunne." "To ai ba shi kaɗai ba hadda su Anty Bahijja, a group ɗin gidan su je ki gani sai abin da suka manta ba su fada mana ba, na fara ma yar da martani Mimisco ta kira ni ta ce kar na sake magama shi ya sa na yi shuru." "Au kuma? "Wallahi kunna data ki sha kallo." Ba musu na yanke wayar na kunna data. Sai da na bari saƙonnin duk sun gama shigowa a group din gidan su Yallabai Iyalan Marigayi Muhammad Inuwa02. Mata ne kaɗao sai mi surukai a ciki mazan suna can na farkon. An yi ta cin kasuwa akan mu har Yayar Gimbiya da ba ta zo ma sunan ba, tana ta mganar cewa ba za su yarda da duka ba ko su Anty Bahijja su ɗau mataki ko su su ɗauka da kan su. Ita ko yar kanzagi Anty Bahijja ta ce ai Tafida tuni ya ɗauka mataki dukkanmu an ja mana kunne. Anty Maimuna ta fito ta ce ba lafin kowa ba ne sai ni Munnira ta ce ko gobe yarinya ta sake mata rashin kunya sai ta mata dukan tsiya. Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya Nasir zai ji, group ya koma faɗi in faɗa har sun jj labarin abin da ya faru. A cewar Jamila ta ce Gimbiya da bakinta tafaɗa mata ni da su Munnira taron dangin muka yi mata ita da yan uwanta Suwaiba ta yi taggin ta ce ƙarya ne tana wajen ta yi Vn wajen mimtina sha tana bayanin abin da ya faru ni ina fara ji ma haushi ya sa na kashe gabaɗaya. An yi manganganu har Ant Zabba ta tanka ta ce in dai har gida muka je muka dake su ba mu kyauta ba.. amma ya kamata a yi bincike domim a samu sulhu. Mimisco ta tawatar ganin abin na nemen ya zama rigima ta ce kar wanda ya ƙara mgana. Ba ni da damar ma yar da martani shi ya sa na yi shuru. Kafin ma na kashe datan sai ga kiran Mimisco na ɗauka muka gaisa sannan ta tambayeni abin da ya faru duk na zayyane mata, ta ce gaskiya suma ba su kyauta amma Munmira ma ba ta kyauta da tun farko ba ta tanka su ba. Ta yi mini faɗa sosai ta ce bai kamata ina barin ƙananun abubuwa suna shan gabana ba. Na yi gaba fa sai dai a biyo bayana. Na ji daɗin magana da ita shi ya sa duk cikin yayyen Yallaɓai Mimisco na dabam ce a wajena. Ta ce ko an buɗe gidan kar na tanka ma kowa na yi shuru kawai itama amsa ce. Nan take na yi mata alƙawarin ba zan yi magana ba ta yi mini godiya muka yi sallama. Mun gama wayar kenan ina shirin ajiyeta bayan na kashe data Jidda ta kira ni kwana biyu ba mu gaisa. Bayan gaisuwa da tambayan makaranta ta kira sunana. "Umma." "Na'am Jidda." "Me ya faru tsakanin ki da Abba ne? Cikin mamaki na ce" Me kika gani? "To ya kira ni yanzu ba daɗewa yana faɗa mini ya yi miki laifi kina fushi da shi na kira ki na baki haƙuri" "In ji baban na ki? "E Umma. Don Allah ki yi masa haƙuri ba ki ji muryan Abba ba duk ya damu." Sai na yi mirmishi kafin na ce" Bayan nan bai faɗa miki komai ba? Bai faɗa miki laifin da ya yi ba? Tana dariya ta ce."Umma ba sai ya faɗa mini ni dai kawai ya ce kina fushi da shi na kira ki na ce ki yafe masa ki kula shi." "To." "Don Allah Umma." "Na ce to ko? Na faɗa a ɗan hasale. "To ai Umma na san halin ki ne yanzu sai ki fara gaba da shi, yana mgana kina yin banza da shi. Allah Abba abin tausayi ne fa Umma in dai a kan ki ne." "Ƙaniyarki Jidda." Na fada ina danne dariyata itama dariyan ta ke yi. "Ke har kin san abin tausayi a kaina? Zan ci mutimcin ki fa" "Wallahi Umma in ba ki yi masa mgana da ya ganki duk sai ya ruɗe" "Sai anjuma Jidda" Na faɗa mirmishi, jin tana yi mini shaƙiyanci. "Umma a duba mini my Abbana don Allah." Kawai sai na yi tsaki na kashe wayar, har ta saka ni mirmishi wai Yallabai ne da kiran Jidda yana cewa ta ba ni haƙuri, ba ma wannan ba yaran mu fa yanzu duk motsin mu suna ankare damu  ji dai Jidda da na ke ganinta shuru shuru ashe tana ankare da komai. Wayar da muka yi da ita sai na ji zuciyata ya ɗan sauka Ina cikin ɗaki Marwa ta zo, ba ta wani daɗe ba amma ssi da na zuba mata doya ta tafin ma Kawu da shi tun da yana so amma ya ce ba za su tsaya ba akwatinta ta ɗauka na raka ta har haraba na ba ma Afra 1k na ce ita 500 Abadalla ma haka tana ta mini godiya. Kawu daman a can waje ya yi parking ɗin motar shi. Yallaɓai na neman shiri da wuri ya dawo ana yin sallar mangariba ya siyo mini fura da kayan marmari ban sake masa gwiwa ba amma dai na karɓa kadahan kadahan. Lokacin na yi wanka abinci kuma daman farar shinkafa na dafa da daddaren ina da sauran miya, saboda na san muna faɗa sai na ji gayu na tsuke cikin riga da wando ina tafe mazaunena suna kaɗawa. Ai da ƙyar ya fita sallar isha'i yana dawowa ina ciki Yumna na wajen Baby ya ritsani yakulle kofa. "Sadiya so kike yi na haukace a kan ki ko? Ina tssye lokaci ɗaya ina ninke darduman da na idar da salla a kanta na ce" Sai dai in matarka ce za ta haukata ka. Amma ni Sadiya ai ban kai wannan matsayin ba.' Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji ya ruƙumƙume ni daga tsayen yana mai faɗin" Ki yi haƙuri ki yafe mini na yi kuskuren da na zo na yi miki magana cikin fushi. Am sorry please." Na yi banza da shi, amma dai ban yi ƙoƙarin kwace jikina ba. Ya juyo da ni muna kallon juna ya saka hannu ya zare mini hijabin jikina yana bina da wani kallo duk ban yi masa mgana ba. "Kike cewa ba ki isa ba Sadiya ta? To wai wata kuma isar kike so na nuna miki da za ki san ni a wajena kin isa kin iss. Ke ɗin isa ce kafin ma isar ta iso." A tsume na kalle shi kafin na ce" ai ka gama nuna mini isata tun da jiya ka ce na bar maka gida.' Sai kawai ya riƙo hannuna duka buyin cikin na shi ya matse yan faɗin" Na rantse da wanda raina ke hannun shi. Lokacin da kika ce in na ce ki tafi za ki tafi na faɗa ne domin na ga zaki iya tafiya ki bar ni Sadiya? Sai na ga wai kin tafi? Lokacin da kika fita wallahi ji na yi kaina ya yi wani girimgirim Sadiya na shiga tashin hankali. Me ya sa za ki yi mini irin wannan gatsen fisabillahi"? "Gatsen me? Kai ka ce na tafi ba za ka hana ni ba." "Na gwada ne, na gwada ki na ɗauka kema a wasa kika faɗa " Kallon sa na yi ina wata dariya kafin na ce" Wasa? Ni ka ga wasa a magana ne." "Wallahi ban gani ba. Kin ba ni tabbaci jiya. Ni dai kar ki ƙara yi mini irin haka bana so. Sai ki saka ai zuciyata ta buga." Na buɗe baki zan yi magana ya haɗe bakin mu waje ɗaya yana tallafo kaina na yi masa tsaye ƙiƙam shi ya sa sumbatar ba ta yi armashi ba. "Ki tallafe ni ma Sadiya ta." Ya faɗa cikin karyewan sauti a yanayin shi kaɗai da na kalla na san tallafan yake so. "Me zan maka? Yara na falo fa? Ƙamƙameni ya yi yana faɗin" Na kulle ɗakin ba za su shigo ba " Ganin ina kallon shi ya sa kamar zai yi kuka ya marairaice mini yana faɗin" Don Allah I need you sosai." Sai na kasa musa massa ya ja na ya yi zuwa kan gado yana mai ƙamkame hannuwana. Duk yadda na so na basar da shi na kasa Yusuf ne fa?  Yusuf ɗin da na sani tun yana matashin sa. Sai kawai nima na tallabe shi, na saki jiki na ba shi abin da yake so. Bayam mun natsa tun kafin mu kai ga wanka ina saman ƙirjinsa ya rumgumeni yana faɗin" Ki yi haƙurin kin ji ko? Ke mai hakuri ce ki ƙara akan na baya. Mimisco ta kira ni , Suwaiba ma duk sun sake yi mini bayani na gamsu. Itama Daughter zan yi mata faɗa kowa ya yi hakuri domin a zauna lafiya kin ji" Na yi kamar ban ji ba sai da ya ƙara faɗn" Kin ji ko? "Na ji." "Ba ki yafe mini ba ko? "Uhm" Sai ya sumbaci goshina kafin ya ce. " Ina kaunar ki." "Ina sonka Yusuf ɗina." Na faɗa ina sake rumgumoshi kamar na saka shi a aljanma haka ya ƙamƙameni yana faɗin "Na gode Abar ƙaunata Ubangiji ya bar mu tare har mutuwa. Mutuwan ma ta ɗauke mu rana ɗaya" Ina mirmishi na amsa da Amin. Mun so mu shagala sai muka ji kukan Yumna a kofar ɗaki tana kiran sunana. Uma "Uma. Ni da Yallaɓai muka kalli juna muka kwashe da dariyan nishaɗi. *Janafty**TKGB3016* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732 Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰 Shike nan faɗan mu ya ƙare ni da Yallaɓai amma lokaci bayan lokacin in muna zaune da ya yi magana zan kalle shi na ce" Ni ai Yallaɓai ka ga ƙarar mini da ruwan kaina. Ni da ka kalla ido cikin ido ka ce mini ina da mugun nufi akan matarka. Wallahi na kasa mantawa da wannan maganar" In na faɗi haka sai ya marairaice yana lallashina shi a dole sai na manta duk kalaman da ya yi amfani da su a kaina. "Me ya sa ba ki mantuwa ne Sadiya? Maganganun da na faɗa cikin fushi kema kin san ba a son raina ba ne. In ma na ce kina da mugun nufi ai kaina na yi mawa. Tun da tsawon shekarun da muke tare da ke ban amfana da komai ba sai alheri. Ki yi haƙuri don Allah ki daina dawo da maganar da ta wuce." In ya faɗi haka sai na tura masa baki na ce" Uhm, ai ka san da haka ka manta ka yi ta manganganu." "Ki yi mini afuwa ki yafe mini. Halin ɗan adam ne na ajizanci."   Haka ya kan faɗi in na ta da maganar kuma ba wai ban yafe ba ne na yafe amma na kasa mantawa in na ga yana yi mini rawam ƙafa sai na kalle shi na tuna masa maganar. Tun yana lallashi da sake ban hakuri watarana ma shuru yake yi mini amma ya kan ce Allah na sama yana gani kuskure ne ya yi kuma ba wanda ya wuce ya yi kuskure. Har cewa ya yi sharrin sheɗan ne ranar ina ta tsintsira dariya shi kuma sai ya yi fuska yana hararata.   Kwana biyu kamar na manta da maganar kawai ranar yana gidana da daddare muna falon muna kallo, Yumna ta yi barci tana ɗakin su Baby, sai za mu kwanta zan je na ɗaukota. Wani American film muke kallo daman sune fina finan Yallaɓai ni kwata kwata ba sa burgeni sabo da shi ne ma na ke kallo, in ya ga na yi shuru sai ya yi ta mini bayani iyakata Umh da Hmm to ni bai san ba na son wannan bayanin ba, da zai ƙyale ni da na ji daɗi amma ba zai gane ba ni kuma ba na son na kushe ƙokarinsa. Yana cikin ba ni labarin film din ne ya gangaro kan karatu shi ne ma yake faɗa mini ya nemi gurbin PHD a Universty of Ibadan har ya samu. Baki na buɗe kafin na kalle shi ina faɗin" Lalle Yallaɓai can Ibadan ɗin za ka koma? "A'a ai online ne karatun sai in za a yi jarabawa zan je." "Allah ya ba da sa'a." Ya amsa da Amin Amin. "Saura ni Yallaɓai maganar komawata master" "Ina za ki je da Yumna? Ki bari ki yayeta sai ki koma." Na kalli Yallabai shima ya kalleni, ai yadda ya ga ina kallon shi ne ya sa ya yi dariya kafin ya ce" Wallahi da gaske na ke yi. Zan hana ki komawa makaranta ne? Ko Daughter na faɗa mata in har za ta koma ni ba ni da damuwa." Shuru kawai na yi masa na ma kasa mgana ina zencen makarantana yana kawo mini zencen wata matar shi, tsaki na so na yi sai na fasa kar ya ce na raina shi yana magana ina yi masa tsaki. "Kina yayeta in sha Allahu sai ki koma. In kuma lokacin na sake yin ajiya shike nan sai ki jira ki sake haihu ki yaye sai ki koma." Ai ban san na kai ma kafaɗan Yallabai duka ba ya kauce yana dariya. "Me na faɗa? Ba ki son haihuwan ne yanzu? "Ban sani ba." Na faɗa ina tsumewa, Rumgumoni ya yi yana faɗin"Sorry tsokanarki fa nake yi, ke ba ki san wasa ba? "Ni ka ƙyale ni, ni ai na gama haihuwa da kai, ni da ka ce ina da mugun nufi a raina game da kai da matarka." Na faɗa ina kallon shi, da sauri ya sake ni, ni na faɗa ne a wasa amma sai na ga ya wani daure fuska. "Yi haƙ.." "Sadiya." Ya katse ni da kiran sunana a fusace kafin na amsa ya nuna mini yatsa yana faɗin" Ba na ce ki bar tado da wannan mganar ba? Me ya sa ba kya jin magana ne, ko so kike yi ki ɓata mini rai hankalin ki ya kwanta ko? To shike nan kin ɓata mini rai kin ji daɗi." Ya faɗa yana ture hannuna da na ɗora a kan cinyarsa. Ya mike na yi saurin kama hannun shi guda ɗaya. "Sorry" Na faɗa ina leƙen fuskarsa, tun da ya kauda kai ne ya ki dariya sai na jawo shi ya faɗo gefena na sumbaci ƙuncinsa ina ƙara faɗin" Am sorry Yallaɓai na." Lumshe ido ya yi ya buɗe kafin ya kalleni har muryan shi ta sauya." "Me ya sa kike haka ne Sadiya? "Ba zan ƙara ba" "Shike nan ni ba zan yi kuskure kuma na zo na gyara daga baya ba? Na ba ki hakuri kin ce kin hakura to dawo da maganar kuma duk na mene ne? Ni fa mijinki ne, ke matata ce da soyayya ce ta kawo mu a wannan karnin, kina yi mini laufuka, kafin ma ki roƙe ni nake yafe miki saboda ba na son mala'iku su yi fushi da ke. Amma ke me ya sa in saɓani ya shiga tsakaninmu magana kaɗan bisa kuskure sai ki ma yar da shi makami a kaina? Ko don kin ga ina lalacewa a kanki da ban baki shi ya sa kike yi mini yanga? Sai na kasa mgana saboda maganganun shi sun sanyaya mini jiki. "Ka yi haƙuri wasa nake yi." "Wannan maganar ba abar wasa ba ce. Ki bari kar ki ƙara ta yar da ita raina ba ya so. In kika ƙara zan kai karan ki wajen Alhajinmu." Da sauri na kalle shi gira ya ɗaga mini kafin ya ce" Da gaske na ke yi. Kin fara kular da ni da mganganun ki." "Yi haƙuri ni dai. So kake yi ka sa Alhajinmu ya daina misali da mu.? "Tun yaushe? Ai kin gama karya mini wannan record ɗin a gaban Alhaji. Fisabillahi abin da kika yi  ba ki kyauta mini ba." Na tura baki kafin na ce" To ba kai ka ja ba. Cewa ka yi na fita ba za ka hana ni ba." "Kuma kika juya kika tafin ko kunya? Ya faɗa yana kallona ni kuma sai na juya masa baki, caraf ya kama bakin nawa ya ja, na yi ɗan ƙara ina buge hannun shi. "To kar na tafin? Na nuna maka muna da gidan uba muma" "To ai kin makara. Domin Alhajinmu ya fi sona a kan ki." "Na ga alama." Na faɗa ina rike baki shi kuma yana yi mini dariya. "Haka fa Alhajinmu ya zaunar da ni ina faɗa masa abin da ka yi mini ina kuka amma shi yana koro mini jawabin laifina ne a fakaice yana yabon ka." Na karishe faɗa cikin mamaki, Yallabai ya kwashe da dariya yana mai rumgumoni cikin nishaɗi, muka yi baya shi ya jinginar da kansa a jikin kujera mai zaman mutun huɗun da muke zaune ni kuma ya yi ma kaina da jikina masauƙi a saman kirjinsa. "Wallahi na yarda Yallaɓai Alhajinmu ya daɗe yana yin ka." "Tun a ranar farko da na fara ganin shi nima na ji kamar mahaifina. Ba ƙarya ba ne yana ƙaunata nima ina ƙaunarsa sosai na ke ganin girmansa saboda shi ɗin adalin Uba ne sannan dattijo ne." Ina ta mirmishi jin yana ta yaɓon mahaifina. "Na je gabansa ina mai neman afuwa na yi miki laifi. Amma ni yake sake ba ma haƙuri da Amana. Ya ce Yusufa ka yi hakuri da Duhu ka cigaba da hakuri da ita akan wanda kake yi a baya. In ta yi maka laifi ka yi mata hukunci cikin natsuwa bayan ka yi bincike. Saboda shi yanke hukunci cikin fushi yana kawo dana sani. Kin ga dai afakaice ya yi mini nasihan na daina saurin yanke hukunci cikin fushi ba tare da bincike ba." Ya faɗa yana wasa da gashin kaina da na yi tsifa ban yi ri ga na yi kitso ba. "Kawu ya yi ta kambama dattakon Alhaji. Na ce ai bai ga komai ba ni ne zan bashi labarin Dattakon sa." Sai na ɗago ina kallon shi, sumbatar lebensa na yi kafin na ce. " Na gode." "See your mouth kin gode mene! Nima Alhaji mahaifina ne so ki daina yi mini godiya kuma duk abin da na faɗa akan shi kyakyawan hallayan shi ne." Na gyaɗa kaina ina faɗin" Gaskiya ne. Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon kwana." "Amin ya yi tsawon ran da zai ga takwaran shi in sha Allahu." Sai na kalle shi kafin na yi magana ya rigani da cewa. "Ina so na yi ma Alhajinmu Takwara Sadiya." "Uhm me ya sa ba ka yi masa a wannan haihuwan na Gimbiya ba? Mirmushi ya yi har ina jin sautin mirmushin. Kafin ya ce" Zan iya yi masa ba wanda ya isa ya ce don me. Amma na fi so takwaran Alhajinmu ya kasance Dubu da Yusufa ne iyayen sa. Sai ya fi soyuwa a wajen ki da wajen Alhajinmu." Girgiza kaina na yi kafin na ce" ba ka san Alhajin mu ba ne. Ko ni ko Gimbiya duka ba zai bambata mu ba." "Duk da haka dai. Hausawa suka ce abin cikin ƙwan ai ya fi ƙwan daɗi." Dariya na yi shima yana taya ni,na ƙara rumgume shi ina faɗin. "I love you Yallaɓai na." "I really like you Sadiya ta " Na ɗago ba zato kawai ya haɗe bakin mu, yana sumbata na. Sai nima na rumƙumƙume shi da hannayena na zagaye da su zuwa maransa ina shafawa. Hannu ɗayan kuma na saman kirjinsa ina masa wasa. Ban ɗauka za mu zarce ba sai da na ga Yallabai na sabule mini ƙaramar rigar da jikina da sauri na riƙe masa hannu ina kallon shi. "Ina so. "Mu yi a falo." Ya faɗa ararrabe saboda a lokacin ya ɗan kai sama can yana buƙatar matallafiya. "Yara fa? Kar su shigo." Sai ya tashi yana layi, ya je ya rufe mana ƙofar falo ya kashe wutar amma bai kashe kallon ba. Tun yana tafe gare ni ya cire farar vest ɗin jikinsa ya yi kuma fatali da dogon wandon dake jikinsa, kaina ya ƙariso ya jawo ni a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ya zaunar da ni a saman jikinsa muna masu kallon juna. Ƙura mini ido ya yi da ɗan hasken Tibin da ke falon idanuwansa sun juye sun yi ja sannan sun ƙanƙance. "Sadiya ta." "Uhm" Na faɗa a ƙasan makoshi. "Ki agaza miniiiii" Ya faɗa cikin wani yanayi sai da tsikar jikina ya tashi da gudu na haɗe bakin mu waje ɗaya shi kuma hannayen shi na kara kaina wajen raba ni da yar ƙaramar shimin dake jikina. Ba ka jin komai sai tashin nunfashin mu sama sama. Gaskiya Yesterday was cool. Na faɗa a cikin raina jiya nan mun yi nishaɗi da ni da Yallabai mun gamsu da juna fiye da tunanin mai tunani. Yallabai na ƙarshe ne wajen sarrafa ma mace da jan ragamar tunaninta in ta shiga hannun sa. A jiya nan haka ya ruka juyi da ni kamar waina ni ma ba a bar ni a baya ba na yi ƙoƙari sosai wajen faranta masa rai. Sai wajen ɗayan dare muka koma ɗakin mu bayan na je na ɗauko Yumna. Da asuba kuma a tiolet ya yi ɓarnan ruwan shi,  ina ya bari ya bari amma bai ji ba sai ya ɗaga ni sama sai ji na yi kawai ya baƙunce shi, ban ɗauka har a tiolet lamarin zai ba da armashi ba sai da ya nuna mini hanya. Kai jama'a ni dai na faɗa muku Yallaɓai duniya ne wallahi." Ni dai tun da faɗan mu ya kare da Yallaɓai na manta da maganar Rahila sai da ta zo gidana na tuna na yi mata zencen me ya haɗa ta da Ya Muntari? Magana ta kawo magana na ba ta labarin artabuna da Yallaɓai, har dalilin da ya sa na ji batun su ita da Ya Muntari Shi ne take faɗa mini kan wata budurwansa ce da ya ke kashe ma kuɗi, tana ɗauke masa hankali, ai ni na yi suman zaune kar ka raina namiji. Ya Muntari da nake gani sumu sumu kamar na Allah ashe kwallo ne.. Rahila na hawaye tana faɗa mini irin tashin hankalin da watsttatsiyar yarinyar nan ta saka ta a ciki. Ta hargitsa mata gida ba zaman lafiya ita da Ya Muntari, ta daina wanka ta daina mgana ta daina girki shine da ya gaji da magiya ya kawo ƙaranta wajen Alhaji. "Tabdijam amma dai Ya Muntari bai da kunya." Rahila ta jinjina kai kafin tace" Dakyar na samu ya rabu da ita .Kuma ba shi da ƙudin auranta amma tana cinye masa kuɗi daga waje." Ni dai har Rahila ta tafi ina ta kambama lamarin a ƙasan raina. Wai Ya Muntari tabdijam! Ban taɓa tunanin haka daga gare shi ba. Ai daga nan na daina raina wayan namiji. Yana fama da rayuwarsa amma yana ɗebe ma kansa aiki. Allah dai ya kyauta. Yadda ni kaɗai na sani sai ban furta ma kowa ba amma na yi ƙoƙari sosai wajen taimakon yar uwata ta dawo cikin hayyacinta da shawarwari da jikina kuma da Aljihuna. Lokaci kaɗan kuma ta manta ta dawo kamar ba ita ba. Maza maza mutanen mu. *** Tun bayan abin da ya faru ba mu ƙara haɗuwa da Gimbiya ba sai da ta yi arba'in ta zo gidana kuma ina da tabbacin Yallabai ne ya matsa mata tun da shi ya kawo ta da kan shi. Da sunan an kawo mini Ammar na gan shi. Ban nuna komai ba na yi musu kyakyawan tarba, gidana ta yi yini tun safe har dare har yara da suka dawo makaranta nan Salisu ya kawo su tun da mamansu ta na gidana. Da farko ta ɗan yi ɗari ɗari, amma daga baya da ta ga na nuna kamar ma wani abu bai faru ba sai ta saki jikinta. Amma ban ƙyaleta ba sai da na yi mata maganar da man kuma na yi alƙwarin ko ba jima in dai muka haɗu sai na fada mata gaskiya. Ce mata na yi a duk abin da za ta yi to ta riƙe gaskiya da amana. Ta sani Allah na sama yana ganin ta, in har ta nufi wani da sharri to ta sani ƙaiƙayi na iya komawa kan masheƙiya. Sai ta fara kame-kame da cewa wai ba ita ce ta faɗa masa abin da ya faru ba kawai dai ya zo ya ganta tana kuka ga targaɗe a hannu shi ne ya fusata tana ta dai ƙoƙarin kare kanta na ƙarya ahalin ni da ita mun san ba gaskiya ta ke faɗa ba. "Magana ai ta wuce. Da man na ce sai na faɗa miki gaskiya. Ki sani ni tsakani da Allah na ke zaune da ke ban taɓa nufin ki da wani sharhi ba. Ruwanki ne ki gyara alaqata da ke a zuciyarki ruwanki ne ki cigaba da ɗaukata tun farko. Amma ni dai ba zan fasa zama da ke tsakani da Allah ba sannan ba zan fasa mutumtataki a matsayin  ki na matar mijina kuma uwar yayansa ba." "Na gode in sha Allahu zan gyara. Don Allah ki yi haƙuri " "Ba komai. Ban riƙe ki ba, koma na ƙullaceki a baya na yafe miki. Ni da ke ba mu isa mu hana kan mu jin kishin juna ba tunda kishi gaskiya ne. Amma in ya taso mana mu koyi yadda za mu sarrafa shi akan mu. Allah ya ba mu zaman lafiya." Ta amsa Amin duk ta ji kunya ni kuma abin da ke zuciyata na faɗa mata. Tare muka yi ma tuwon shinkafar da na yi mana da daddare muna yi muna ɗan hira jefe-jefi a bakinta ma na ke jin Nene ta yi zazzabi kwana biyu na ce ban sani ba ai da na je na duba ta. Da Yallaɓai ya dawo da daddaee ya ji daɗin ganin mu tare gwanin ban sha'awa. Ranar girkina ne saboda haka na yi kwalliya yar caras da ni ina tashin ƙamshi. Tare muka yi dinner gabaɗaya har yaran cikin farinciki abin da ba mu taɓa yi ba. Ni ban faɗa masa wani abu ba shi ne muna falon shi tare ya kallemu ni da ita yana faɗin" Na ga chanji daga gare ku na ji daɗi kwarai." Sai ta ce masa ai ni ce na yi mata nasiha kuma ta ji za ta gyara in sha Allahu. Ya yi ta washe baki yana jin daɗi ya taso ya rumgumeni yana sumbatana a ƙuncina na ture shi ina hararan shi. "Ke ce jagoran mata na ko a gidan Aljanna Sadiya ta. Ni da duk abin da na mallaka duka na ki ne." "Har wannan gidan? Na faɗa ina dariya. Sai ya gyara zama a hannun kujeran da nake zaune ya ce" Wannan gidan da abin da ke cikin shi ai ya zama na ki, yau ba fata nake yi ko mutuwa ko rabuwa ba wanda ya isa ya fidda ke daga cikin sa. Sai dai ni ki kore ni ma domin kin cancanta." Ina dariya na ture shi ina faɗin"Bana son daɗin baki." "Wallahi da gaske na ke yi " Ya faɗa yana ƙoƙarin ya dawo ya zauna kusa da ni sai na tashi na koma kusa da Gimbiya na zauna. " Ni za ku haɗe ma kai? Ya faɗa yana kama baki ni da ita muka haɗa baki wajen fadin" E ɗin." Muka faɗa a tare muna dariya sai ya koma ya zauna akan kujeran da na tashi yana faɗin" Za ku neme ni yara " "Yara? Na faɗa ina kallon shi sai ya zare mini ido yana faɗin" E yara ko kun girme ni ne? Sai na yi shuru tun da na fahimci yana jin magana ne. Saboda jin daɗi sai wajen goma ya tafi kai su gida da ya dawo bayan mun kwanta sai da ya yi mini maganar. "Na gode Sadiyata. Don Allah ki cigaba da haƙuri. Ba ki ji farincikin da na ji ba lokacin da na gan ku tare da Daughter ba" "Uhm" Kawai na iya cewa domin sai na ga kamar Yallaɓai na sane a duk wasu iskancin da Gimbiya ke yi. Me ya sa ba zai mata faɗa ba? Sai ni ce zai yi ta nanata ma in yi haƙuri da ita, ita ba zai ce ta yi haƙurin ba. Ni dai na yi masa yaƙe kawai ban nuna komai ba, sabo da kauda maganar sai na yi masa maganar zazzabin da aka ce Nene ta yi kwana biyu. Sai ya ce mini ta ji sauƙi ne shi ya sa bai faɗa mini ba amma na bari weekend sai na shirya mu je da yara mu gaishe ta na amsa masa. Haka ko aka yi ranar lahadi muka je Gwammaja tun safe muka yini. Da man su Baby sun yi hutun Tahfez saboda gabatowar azumi, Nene ta ji sauki amma jikinta ba karfi ina gidan sai ga Halima wataƙila saboda idanuwan Nene ne ya sa ta gaishe ni, nima saboda mahaifiyarta na amsa. Ni saboda ita a bangaren Maman farko na yi yini na, sabo da ba na son abin da zai haɗa ni da yarinya. In ta neme kawo mini wargi ba zan ɗauka ba. Muna gidan har dare tun da Yallabai ne ya kawo mu sannan shi ya ce zai biyo ya ɗauke mu. Motata a gida na barta. Tun la'asar Halima ta tafi gida shi ya sa na koma ɗakin Nene, duk da ba ta fito fili ta furta mini ta ji maganar hatsniyar da muka yi a gidan sunan Ammar ba a maganganunta na san jirwaye take yi mini mai kama da wanka. Hausawa suka ce ruwa cikin cokali, ya ishi mai hankali wanka. Ta yi ta ba ni haƙuri ne, tare da nuna mini na cigaba da haƙuri ina kauda kai. Sannan ta gangaro kan maganar Halima ta na nuna mini na yi hakuri da ita akwai yarinta a tare da ita, da ta ji labari ta yi mata faɗa sosai tun rashin kunyar da ta yi mini na farko. Ni dai ban ce komai ba illa to, amma ina ganin beken Nene, Haliman ce yarinya? Mata da mijinta da yayanta ai ta san abin da take yi. Na dai nuna ma Nene komai ya wuce amma a ƙasan raina na kudiri niyyar ba zan bi ƙanwar miji ta samu damar cin kasuwa a kaina ba. Ni ko yayar miji na ga tana tozartani kama kaina nake yi ballanta ita ƙaramar alhaki. Mune sai goman dare Yallaɓai ya biyo muka tafi gida. Mu dai mun tsaya mun ci tuwo shi kuma sai da na dafa masa Tea da Indomie ya ci kafin ya kwanta. Sabgogin gaba na kawai na cigaba da yi ga matsowar azumi, shi ya sa na saro inears da yaawa wannan sallar har da mayafai da takalma na yara da manya. Yallabai ya ba ni 100k rance a cewarsa zan biya shi in na haɗa ribata na ce na ji na karba da shi na samu na ganganɗa na ɗinko hijabai diffirent ɗinki kala kala sama da hamsi suna gida sai dai da an saka oder na saka a leda na naɗe Baby na taya ni muna sawa a jaka ko a leda. Tun da Jidda na makaranta sai Baby ke taimakona yanzu. Kuma Alhamdulillah, ana siya sosai ina samu ga Jidda ma tana saka mini a status tana yi mini talla har yan makarantan su sun ce suna so. Irin mata yan dapertment din su, akwai wata ma course ɗin  ɗaya sannan ɗakin su ɗaya Ummu Salma Hamza ɗiyar Iyan zazzau ne na garin zaria itama akwai ƙoƙari kamar Jidda shi ya sa suka fara ƙawance shima ɗin sai da Jidda ta neme shawarata ni kuma na faɗa ma Yallaɓai na ce ya saka a yi masa bincike kan yarinyar kar ya zo ta shiga jikin ɗiyarmu ta cutar damu. Shi ya bincika kuma ya ce yarinyar ta fito babban gida masu tarbiya. Jin haka ya sa muka ba ma Jidda izini ta saki jiki da ita, to ita ce ta siya hijabai sama da kala ashirin kaloli dabam-dabam. Ni kuma sai na ba ta kyautar ɗaya da dogon wando da sikat da pant saboda kyautatawa mai son ɗiyata. Cikin saƙon Khaleesat na saka musu sakon su can gidan suka je suka karɓa. A lokacin suka fara test ni dai addu'ata ko da yaushe Allah ya tsare mini yarana Jidda kuma ina yi mata fatan sa'a da nasara. Yallabai kuma yaƙini gare shi a kan Jidda da cewa in sha Allahu za ta saka shi alfahari wata rana. Cikin haka muka shiga watan Ramadana, Jidda sai kusan salla ta dawo gida hutun na su ma na sati ɗaya ne ana fice salla ta koma saboda suna shirye-shiryen fara jarabawar farkon zangon karatu. Mu dai muna gida muna bin su da addu'a sai da suka gama jarabawa suka samu hutu ta dawo gida, duk ra rame sai ɗan wuya da tsawo. Yallabai ya yi ta faɗa wai kar ta saka ma ranta karatu ta mutu saboda naci. Ta riƙa hutawa tana cin abinci, dawowar Jidda na sake saka mata ido ko zan ga wani canji ban ga komai ba sai ma girma da hankali da natsuwa da Jidda ta kara. In ina kallonta sai na cika da alfahari na ce Ubangiji ka gama yi mini komai tun da ka ba ni Jidda. Baby ce dai wannan ko aure ta yi na tabbata sai na rika yi ina kwaɓa mata. Shegen rawan kai ne da surutu gare ta. Kafin su koma Ummu salma Hamza ta kawo mata ziyara takanas ta zaria. Direba ya kawo ta a ranar kuma suka koma, ni kaina har da ni a masu yi ma Ƙawar Jidda Hidima. Itama na ganta mai kyau da ita age mate ɗin Jidda ce, ita ta fi Jidda haske da kiɓa amma tsawon su ɗaya. Itama a zuwan da ta yi na fahimci tana da natsuwa sosai.  Har Yallabai sai da Jidda ta kira shi ya dawo gida ya ga Ummu Salma suka gaaisa ni kuma ta ba ni mahaifiyarta muka yi waya. Ta ce mini tana shigowa Kano, za ta neme ni wata rana na ce in sha Allahu. Amma ta ce na karɓi lambarta a wajen Ummu sai na kirata na ce in sha Allahu. Ta kawo ma Jidda Atamfa da mayafi, sai Baby ta kawo mata doguwar riga har Yumna an kawo kayan wasa tun da ta san sunansu a baki. Nima da za ta tafi na ba ta hijabai biyu na ce ta kai ma mamanta. Sai turaren wuta da na jiki sauran nawa ne na kwashe na ba ta, Jidda daman ta yi cincin da donut ta kwashe mata aka yi raffing. Yallabai kuma 20k ya ba ta tace karɓa ya zare mata da cewa shi mahaifin Jidda ne. Kuma duk wanda yake aminta da Jidda ya tabbata shi din uba ne gare shi, shi ya sa ta karba ta duka har kasa tana godiya. Muka rakata har waje, direban daman da ya kawo ta, tafiya ya yi sai da za su tafi ya dawo. Ni da kaina na yi ma Jidda alƙwarin itama za ta je har gida wajen Ummu salma. An ce tuwon girma miyan shi nama. Kafin babbar salla suka koma makaranta. A lokacin na yaye Yumna, da na biye ma Yallaɓai to ba zan yaye ta ba. A cewarsa wai ba ta gama yin ƙwari ba yarinya bukekiya tana yawon ta ko'ina, tuni na cire ta a nono tana da wattani sha bakwai cikin na sha takwas. Da wajen Ma'u zan kai ta yayen, tun da ita ta yi mini magana. Har Marwa itama ta yi nacin na kai mata Yumna yaye. Ma'un da muke kusa na yi niyyar na kai mata ita ta yayeta kwatsam sai muka wayi gari da rasuwar mijin Baaba. Ma'u na can Kura mu ma mun je mun kwana ɗaya mun dawo har Amina dake Kaduna ta taho. To Allah ya sa dai ita ce uwar yayen Yumna ita tafi da ita Kaduna a can ta yi babbar salla. Tun tana rigiman Umma Abba Baby har ta gaji ta haƙura tun da akwai yara a gida. Yallabai ya gaji da korafi na ɗauki hakkin yarinya ya haƙura shima. Sai da ta yi wajen wata biyu sannan Amina ta dawo da ita. Yumna ta ɗan rame sannan ta kara girma sun kawo ta da sha tara na arziki ita da mijinta Yallabai na ta fadan wai na tura musu ɗawaniya.  Na ce na ji ba komai ai ƙanwata ce in ta yi mata ba ta faɗi ba. Rayuwa dai alhamdulillah tana tafiya cikin farinciki. Yallabai yanzu fa na neman ya sha kwana. Kuɗi kawai yake facaka har mota ya sauya wata jeep ce itama mai tsada. Adnan ya faɗa mini da muke hira da shi za ta kai miliyan huɗu daga nan na yi shuru. Sannan ya bude shagunan sai da kayan gini, komai na na'uin gini akwai, kofifi, interlock, simnti, kayan aikin tiolet, kwano, ba abin da babu a wajen ƙasan wajen kuma ya saki shagunan masu aski da wasu yan kasuwan sun kama sannan ginin gidan shi ya yi nisa har an yi linfter an saka kankare tuni yanzu ma rufe yace mini ake yi, an ma kusa gamawa da ya nuna mini a hoto. Sai ina ta mamakin gaggawan da yake yi a kan ginin nan sai da na yi masa mgana. "Ina so ne ko ba ku tare ƙarshen shekaran nan ba to a farkon shekaran 2023 mu tare a sabon gida in sha Allahu." "Allah ya amince mai girma Md." Na faɗa ina dariya har ina jinjina, saboda maganar gaskiya Allah ya buɗa ma Yallabai kwangolili ne wasu na jiran wasu malam. Kuma in dai aka bashi kwangila ya yi shike nan duk wanda ya gani sai ya yaba yace a haɗa shi da shi sillar gasikiya da amana da aiki ba ha'in ci. Mu kan mu mun shaida Mijin mu na da kuɗi yanzu, abinci sai dai mu yi kyautarsa. Duk wani abu na daɗi muna ci, suturu kuwa na kece raini muke sawa mu da yayanmu. Ba mu ba har iyayen shi ma yana yi musu nima ba abinda zan ce masa sai godiya. Ya ba ni kuɗi na kai gida ya kai kayan abinci komai fa sai godiya. Da shi da Kawu sun yi ma Tariq fintikau shi duk cikin su ba shi da ƙarfi tun da aikin Gwammati yake yi. Su kuma yan buga buga ne da man. **** BAYAN WATTANI HUƊU. A watan october 2022 Baaba ta gama idda sai ga shi karshen ta dai gidanmu ta dawo da zama ita da sauran ƙannen Ma'u su Zainab. A ɗakin Hajiya Dubu su Ya Hamza suka gyara mata daman tarkace ake sawa a ciki. Baaba duk ta yi laushi kamar ba ita ba, ni ce wai za mu zauna muna hira da ita har muna dariya abin da ban taɓa tunanin fatuwarsa ba. Datti ya samu aiki a NNPC reshen jihar kaduna har an saka masa rana zai yi aure zai auri wata abokiyar karatunsa tun suna KAsu ba ta yi aure ba har ta yi masters tana aiki itama. Duk kuma a kusan lokaci ɗaya aka saka musu ranar aure tare da Adnan, wanda shima ya fara aiki a ma'aikatan Yallabai a matsayin Engeanaring na karatu. Tuni ginin gidanmu ya yi nisa ko na ce cikin kashi uku an yi biyu saura ɗaya. Tun da ko wancan satin da hanya ta bi da mu ni da Ma'u da su Ya Aina na ɗauko su a motata mun je gaba da in da gidanmu na mu yake, gaisuwa yayar Zaitunan Ya Abubakar ne ta rasu muka je mata gaisuwa. Na bi da su ta gidan har sauka ma muka yi suka gani, Mun shiga ciki ma'aikata ne sama da ashirin suna aiki, wasu sun sanni suna ta faman gaisheni waɗanda ba su sanni ba suna faɗa musu matar injiniya ce. Mun iske suna ta saka inteelock na tsakar gida. Wasu na ciki ɗakunan suna yin filista, wasu na ma an gama ana saka kofofi daman POP da wearing din wuta ana gama rafta Yallabai ya ce an yi su. Na ga har fulawoyi aka shushuka a gidan har sun girma daman Yallaɓai akwai son shuke-shuke a gida. Ya Aina da Ya Balki suna santin girman gidan da kyan shi, Ma'u ko har da guzarin kasar wajen da yake tana da ƙaramin ciki sha take yi wai ta yi mata daɗi. Muna tafe a hanyar komawarmu Ɗorayi Ya Murja ta ce"Gidan nan da girma yake. Amma na ga shashi huɗu ko aure Baban Jiddan zai ƙara? Ya Balki tace" Ni ma abin da zan ce kenan bayan shashin Sadiya da na abokiyar zamanta nata ga biyu nan kusa da juna." "Nima fa ina ta mamaki." In ji Ma'u dake gidan Gaba su suna can baya ne. Ina dariya na ce" To Allah masani. Mu ma dai haka muka gani da na yi magana ya ce ɗaya na shi ne ɗaya na baki. Daga karshe yace ga shi da yara maza ya yi awadace ne." "Uhm ya dai ce muku ne amma da wahala bai ƙara ko dayan ba ne ballanta yanzu da giyar kudi ke ɗiban shi " In ji Ya Aina ni ko na saka dariya ina ba su labarin diramasu da Gimbiya. "In Yau Yallaɓai ya ce zai yi aure ai akwai yaƙin duniya na uku shi da matarsa." "Ta yi ta gama. In dai ya yi niyya sai ya yi." In ji Ma'u ita da ta ga zahiri, ga amarya har ta haihu, itama an zama daya da ita. Ni dai ina ta dariya har muka kariso gida, Rahila ba ta je ba, ba ta da lafiya ta ce sai gobe za ta leko, muna gidan har bayan la'asar muna ta hira da  Baaba da Gwaggo. Har a raina ban kawo ma Yallaɓai aure yanzu ba, ba kuma don ban ji a raina zai ƙara ba amma sai don ina ganin wataƙila akwai sauran lokaci. Sai dai me? Sai na fara ganin canje-canje daga wajen shi, yana yawan kafa-kafa da wayarsa a kwanakin nan. Abin da a baya bai dame shi ba in ba aiki zai yi a ciki ba ko an kira shi ta yini a in da take bai taɓa ba ya fi amfani da laptop ɗinsa a kan wayarsa Amma a kwaanakin nan Yallaɓai na kan wayarsa har murmishi zan ga yana yi wani lokacin, na rasa me ya ke dubawa ko kuma me ya ke karantawa? Sannan wata rana in yana gidana zai dawo ya yi wanka ya ci uban gayu ya fita in na yi magana sai yace akwai mutanen da zai gani ne. Ni kuma samin shi da jama'a da hulɗodi sai ban damu da fitan na shi ba amma a kwanankin na fara zargin Yallaɓai yana yin wani sabon abun da bai saba yin shi ba, sannan ranar ma Yumna na wasa da wayarsa da ya ijiye a saman kujeran falon sa ya shiga tiolet, sai na karɓa abin mamaki na san code ɗin buɗe wayarsa date ɗin aurenmu ne, amma sai  na gwada ya ƙi buɗewa kenan ya canza. Da ya fito ya ga wayar a hannuna ya ɗan yi wani iri, da sauri kuma ya karɓe wayarsa ni kuma sai na ce masa Yumna ce za ta yi masa wasa da shi na karɓa Tambayarsa na yi ashe kuma ya sauya code ɗin buɗe wayarsa.   "E na sauya." Bai kuma faɗa mini abin da ya sauya da shi ba sai da na tambaye shi. "Date ɗin ranar da na buɗe ma'aikatana ne." Haka kawai ya faɗa daga nan kuma ya koma ya zauna ya cigaba da duba wayar tashi. Har yana wani mirmishi na yi kasake kaawai ina bin sa da kallon mamaki amma na kasa magana. Na ɗauka ni kadai ce na fahimci Yallaɓai na yin wasu baƙin abubuwa. Sai da Gimbiya ta yi mini magana a chart, da man tun bayan faɗan da na yi mata muke yar daɗi da ita in ma wani abu ne ya shige mata duhu akan mijinmu za ta kira ni mu tattauna. "Maman Jidda." Na amsa mata lokacin Allah ya sa ina online itama haka. "Kin fahimci Daddy na yin wani abu a boye wanda ba ya so mu sani!? Sai na ce mata ban fahimta ba, saboda ko na ce na fahimta ba ni da hujja tun da ban ji ba, kuma ban gani ba. "Me kika gani? Me ya sa kuma kika ce haka? Sai na rubuta mata tambayoyin na tura mata sai na ga tana yi mini Vn Yana shigowa da sauri na buɗe. "Maman Jidda Daddy na yin wani abu gaskiya. Yanzu fa kafa kafa yake yi da wayar sa kuma a da ba haka yake yi ba. Maman Jidda Daddy fa yanzu sai ya kai 1 na dare yana online sai ka rasa da wa yake yin charting da na yi magana sai ya ce wai da abokan hulɗarsa ne. Sannan sai ya rika yin wanka ya ci gayu ya ɗau mota ya fita sai dare yake dawowa ni fa gaskiya na fara ji a jikina anya anya kina ganin ba wata ce can a waje ta fara ɗauke masa hankali muna nan zaune ba mu sani ba." "Hmmm." Kawai na tura mata na ma kasa magana. Ashe dai ba ni kaɗai na lura da wani abu na ɗaukan hankalin Yallabai a kwanakin nan ba. "Ki yi magana. Ke ma kin fahimci haka,? "Nima na fahimta amma na kasa gane me ya jawo haka." Na amsa mata "Kin ji ko. Wallahi mu tashi tsaye da bincike kar muna zaune wata shegiya ta ɗauke masa hankali.' Sai kawai na ce mata to zan bincika itama a ɓarayinta ta bi komai a sannu sai ta amsa ni da to, wai har da cewa ta sanni da sanyi wani lokacin wannan karon ba abin yin sanyi ba ne sai kawai na tura mata dariya. A ranar da muka yi magana yana gidan Gimbiya ne sai washegari da zai dawo gidana ya saba dawowa da wuri, amma yau har goman dare bai shigo ba na gaji da jiran shi kuma na kira shi bai ɗauka ba. Kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tun da ni ban saba kiran ta haka ba. Baby ce daman ke jiran shi kan maganar JSSCE ɗin ta na makaranta ta ƙi yin barci daga ƙarshe da ta gaji da jira dole ta kwanta. Ba Yallabai ya shigo ba sai sha ɗaya saura. A yanayin da ya shigo mini ba na lafiya ba ne. Toilet ya faɗa yana faɗa mini cikinsa ya lalace. Wayarsa da babban rigan sa ni ya bari da su tunda ni ce na tarbe shi. Na shiga bedroom ɗin mu da niyyar na ijiye masa wayar da key ɗin mota sai rigan shi. Ina shirin ijiye masa wayar a saman gado kira ya shigo. Gabana ya faɗi ras! Ganin sunan mai kiran RABI'ATU BUK." Har ta katse na kasa daina kallon wayar. Kaf a tunanina ban tunano wata yar uwan Yallaɓai mai wannan sunan ba. Ban gama mamaki ba gur! Saƙonta ya shigo wayar daga sama na ja na fara ganin abin da ta rubuto. "Yallaɓai na ka isa gida lafiya? Mun gode...! Daga nan sai saƙon ya yanke, jiki na rawa na watsar da rigar hannuna ina ƙoƙarin gwada buɗe wayar amma na kasa. Wata zuciyar ta ce Sadiya ki natsu ki yi aiki da hankali. Sai kawai na ijiye ma sa wayarsa nan saman gadon na zauna a gefe na ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya ina girgizawa. Mintina biyar sai ga shi ya buɗe kofar bedroom ɗin ya fito yana nishi sama sama. "Cikina kawai ina hanya ya karta. Ina zuwa sai gudawa kina da ko pulajin ne Sadiya? Ya faɗa yana dafe cikinsa. Lokaci ɗaya yana ƙarisowa gabana yana kuma ƙoƙarin cire rigar jikinsa. "An kira wayarka. " Ya kalleni a ɗan tsume yana cire rigan daga shi sai farar vest. "Ta kuma turo saƙo." Sai kawai ya tsaya yana ksllona. Nima ina kallon fuskar shi yanayin shi ya nuna tsoro amma sai ya yi dakiya irin ta maza. "Rabi'atu ce ko? Ya faɗa yana kallona. "E ita ce" Na faɗa ina kallon shi, shima yana mai kallona sai kawai na ga ya yi murmishi. Mirmishin da na ji ya soke ni a ƙasan zuciyata. *Janafty**TKGB3017* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732 Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰 "Da man na san za ta kira." Ya sake faɗa lokaci ɗaya da ƙwatanƙwacin irin mirmishin da ya yi a farko lokacin da na ce an kira wayarsa. Gabana ya sake faɗi ras! Ba tunanin komai na kawo ba sai tunanin Yallaɓai ko dai ya fara bin mata ne? To ni dai ban san wannan yarinyar ba sai yau amma shi a yanayin da ya nuna kamar ya jima da sanin ta. Sannan fuskarsa ta bayyana asirin zuciyarsa na yadda take da muhimmaci a wajen shi koda bai furta da fatar baki ba. "Yallaɓai." Na faɗa jikina na rawa tare da zuciyata ban san ma na sauke kafafuwana daga harɗe sun da na yi ba sai da na ji suna karkawa, tare da dukan junansu saboda tsoron tunanin da ya shige ni yanzu nan. "Na'am." Ya faɗa yana mai kallona fuskarsa ba alamun wani firgici ko nadama. "Me ya faru? Ya faɗa yana mai sake kure ni da ido, sai na ga kamar yana neman raina mini wayau bayan ya san abin da ya faru amma kuma yana sake kallona yana tambayata me ya faru? "Wa ce ce Rabi' atu? Na fada da sigar tambaya amma a rarrabe saboda fargaban amsan da zan ji ya faɗa mini. Ni fa cikina har curewa ya yi waje ɗaya nima ina jin kamar in na yi motsi zan iya barkewa da zawo saboda zullumi. "Wata ce ba ki san ta ba." Ya faɗa yana sauke rigar hannunsa a saman gado. Sai kuma ya saka hannu ya ɗauki wayarsa yana dubawa. Mirmishi yake yi alamun yana karanta saƙon nata ne. Ban san ina da wannan ƙarfin ba sai da na ganni tsaye kan ƙafafuwana lokaci ɗaya kuma na saka hannuna da ƙarfi na fizge wayar daga hannun shi. "Wace ce Rabi'atu Yusuf ina tambayan ka kana faɗa mini wai ban santa ba. Wace ce wannan yarinyar ehe? Na faɗa ina mai ɓoye wayar a bayana sannan cikin ɗaga murya nake maganar. Ni fa na gama tunanin kaf na haɗe shi waje ɗaya Yallaɓai ya fara neman mata a waje shi ya sa yanzu ba shi da lokacin mu. Innalillahi Wa'inna alaihirraju'un. Nake nanatawa a cikin zuciyata lokacin da na ga kawai ya kalle ni amma bai yi magana ba. "Yusuf wace ce Rabi'atu? Kar dai a ce abin da zuciyata take zargi akan ka gaskiya ne? Na faɗa ina jin zufa na taruwa a saman hancina tsabar tashin hankalin da nake ciki. "Me zuciyarki ke tunani na a kaina Sadiya? Ya faɗa hankalin shi a kwance har yana karya hannayensa a saman kirjinsa alamun bai damu da yanayin da na shiga ba. "Yusuf neman mata ka fara yi? Mu har ka gama moran mu ka fara hango matan bariki? "Subhanallah wannan mganar bai da ce ba Sadiya. Allah ya tsare ni da aikata ɓarna. Ban yi da ƙananun shekaru ba sai da girma ya kama ni Sadiya? Ya faɗa a yanayin muryansa da ɗan bacin rai kaɗan. Domin har yana sauke hannuwan shi ya nufe ni da su yana faɗin. "Taho mu zauna na yi miki bayani." Da sauri na ja baya domin ni kawai idanuwana suna hango mini Yallaɓai wasa yake son yi da tunanina shi ya sa. "Na saurare ka? Me za ka faɗa mini? Tun farko me ya sa da na tambayeka wace ce ita ba ka faɗa mini ba? "To mun bar ɗakin nan ne kika ga ban faɗa miki ba? Da man ko ba ki gani ba ina da shirin sanar dake a kwanakin nam." Sai kawai na saki baki ina kallon shi, a gefen gado ya zauna hankalin shi kwance. "Na ce ki taho dai ki zauna mu yi magana." Ya faɗa yana nuna mini gefen sa, sai na ɗauke kaina kafin na jijjiga jikina ina faɗin" In ba ka yi lalacewa kana matashin ka ba, yanzu da ka haɗu da yar iska yar bari.." "Ya isa haka Sadiya." Ya ɗaga mini murya sannan ya ƙara da ɗaga mini hannu abin da ya hana ni ƙarisa maganar da na ɗauko. "Me ya sa kika kasa shaida na ne Sadiya? Ashe ba za ki iya rantsuwan a kan bayan ku da kuke gonakin da Ubangiji ya hallata mini ba, ba zan iya shinshinar gonar da ba mallakina ba ne? A she ni ba za ki iya mini wannan shaidar ba? "Ɗan Adam mai sauyawa. Tun ballanta jinsin Namiji. Me ye kake ɓoye-ɓoyewa in ba wata yar bariki ka samu a waje tana ɗauke maka hankali ba? Na katse shi nima ina taso masa sai kawai ya yi shuru amma ya kalleni yadda na firgice da zargina shi ya sa sai ya gyaɗa kai kafin ya ce" Ko dai mu jinsin maza muna sauyawa amma ba sauyawa ta wannan bangaren ba Sadiya. Ba maganar yar bariki kuma ki daina faɗa, ba ki san wace ce Rabi'atu ba, sabo da haka ki daina danganta da sunayen banza." "Ƙarya na yi. Wace ce ita in ba yar bariki me bin mazan wasu a titi ba? "Ba ita ce ke bi ni ba. Ni ne  ke bin ta Sadiya." Ya faɗa yana kallona. Kamar an iska ya wuce ta gefen kunnuwana haka na ji kamar sautin wani abu ya wuce. Shuru na yi ina kallon shi, shima ni yake kallo. ."Me ha kan ke nufi? Na faɗa ina mai raba bakina saboda rawan da ya fara yi mini. "Sadiya Rabi'atu ba karuwa ba ce sannan ba ƴar bariki ba. Yarinya ce da ta fito daga gidan tarbiya da dattako." Ni fa duk ba nan na ke so ya je ba. Matsayinta a rayuwarsa na ke son sani. "Ni na ganta na ce ina son ta." Sai na yi ma Yallaɓai zuro kamar na warke makanta. "Kuma AURANTA zan yi in sha Allahu " Shike nan ƙurungus kan kusa. Ni gabaɗaya na sha'afa idanuwana sun rufe na manta cewa bayan biyu. Ubangiji ya ce su cike huɗu in har za su yi adalci, na sha'afa da cewa bayan mu akwai guraben mata biyu, tunanina da zuciyata kawai suna hasko mini Yallaɓai ya fara neman matan bariki saboda yana da kuɗi. Su kuma matan bariki da man in har kana da kuɗi shike nam za su tallata maka ƙofar lalacewa. Na manta yadda ya aure ni ya kuma auri Gimbiya. To watan wata rana in ya yi ra'ayi zai iya auro wata ko wasu ma biyu bayan mu. Na manta ko na ce ban ɗauka yanzu ba ne. Kamar yadda auran shi da Gimbiya ya shammace ni haka labarin wannan auren ma ya sake shammata na. Na kasa motsi daga in da nake tsaye. Zuru kawai na yi ina bin Yallaɓai da kallo shi kuma ganin haka sai ya taso ya zo ya kamani ya zauna da ni a gefen gado sannan ya kuma ya zauna a gefen har yana dafa kafaɗata hannunsa na rito a wajen kirjina. "Bayanin da nake so ki zauna na yi miki ne tun farko kika kasa zama ballanta ki fahimce ni." Ya faɗa yana mai kallon fuskata. Nima shi nake kallo, na tuna ni ce nan na sha cika bakin cewa in Yallaɓai ya tashi kara aure ba zan damu ba domin ni ya gama yi mini kishiya, Gimbiya ce ke da wannan ƙuncin ba ni ba, ban tabbatar ma da kaina kishi sunan shi Kishi ba sai yau, domin sai na ji wannan ƙullutun abin da ya taɓa tsaya mini a ƙahon zuciya a daran da na samu labarin Yallaɓai ya auri Gimbiya. Irin shi ne na ji ya tokare mini zuciya. Ya yi sanadiyar rufe bakina da kassara sauran kuzarina. "Ba ki ji komai ba Sadiya ta? Ya faɗa yana leƙen fuskata. Kamar an ƙwato numfashina haka na ji na saki ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan na kalli Yallabai. Sai ga ni jiki a sanyaye ina mai mikar masa wayar sa, ya saka hannu ya karɓa. "Ka yi haƙuri ban san haka maganar take ba." Na faɗa cikin sanyin murya. Sai na ji kwarmin idanuwana suna cika da kwallah. Sai ya fara dariya yana faɗin" Me ya faru? Ni ba ki yi mini laifin ba ni haƙuri ba na ji daɗi da kika zama mace ta farko da kika fahimci ina boye miki wani abu." "Gimbiya ma ta sani." Na faɗa ina kallon shi, sai ya kalle ni cikin mamaki. A hankali na warware mishi yadda muka yi da ita. Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Allah Sarki ƴan mata na. Ina son ku wallahi." Ai ni ko jin sa ban yi ina cam na tafi duniyar tunani. Aure. Aure fa Yallaɓai ya ce zai ƙara, in a da ina raba shi da kwana biyu ne yanzu fa sai dai kwana huɗu. Kai innalillahi. Haka nake faɗa a ƙasan zuciyata. Gabaɗaya jikina ya yi sanyi kamar an yi mini duka. "Da man lokaci na ke jira na same ki mu yi maganar nan. Wallahi tallahi ban da ke ko Nene da yan uwana ba su san da labarin Rabi'atu ba." "Nima ai ban sani ba, ba ka faɗa mini ba sai da na gani da kaina." Na faɗa kamar zan yi kuka sai ya rumgumo kafaɗata yana faɗin" Allah shi ne shaida na. Niyyata cikin satin nan na ke da niyyar faɗa miki, kin san ba ni da wata abokiyar shawara sama dake. Ni da ke mun kai wani matakin da ba zan iya ɓoye miki komai ba, da man na ce sai na yi magana da ke sannan zan je na yi magana da Nene." "Uhm" Kawai na faɗa domin na kasa magana ko na ce  ba ni da ta cewa ne kwata kwata kamar an shafe manganganun dake cikin ƙwaƙwalwata. "Da gaske na ke yi Sadiya ta " Ya faɗa yana wasa da yatsun hannuna guda ɗaya da ya kama ya riƙe. "Ko da gaske ne ni na isa na hana ka ƙara aure ne? Ai kamar yadda ka yi na farko ban iya hanawa ba wannan ma sai dai na sake yin maka fatan alheri." "Na san baki isa ki hana ba. Amma ai kin isa na yi shawara da ke ko? "Sabo da mene? Na faɗa ina kallon shi. "Saboda ke kin zama TURKEN GIDA na. Ban isa na zartar da wani hukunci ba tare da na nemi shawaran ki ba. Duk da ba ki isa ki hana ba amma kin isa ki nuna mini abin da nake ƙoƙarin yi in mai kyau ne ko akasa sa,  Sadiya kina da wata daraja mai girma a zuciyata da na ke girmama manganganunki. Na ke kuma kambama tunanin ki a kaina. Na tabbata ke mai adalci ce mai kau da kai mai haƙuri da hangen nesa. Kamar yadda kika saba ba ni shawara da zuciya ɗaya yau ma ina da yaƙinin da zuciya daya zaki ba ni dukkan shawarwarin da na ke son samu daga gare ki" Koda a ce daɗin baki ne na Maza to ni dai wallahi ya yi tasiri a kaina, har ban san ina ta mirmishi ba kaina ya yi girman da na ji ashe nima na isa a wajem mijina ban sani ba. "Da gaske Yallaɓai na? Na faɗa ina yi masa mirmishi duk da a ƙasan zuciyata nauyi na ke ji, amma bai hana daga can sama wata tsoka ta jin daɗi ta motsa mini ba. "Haba. Kike tantama? Ke ce fa mafarin Yusuf, ke ce da shi a shekaranjiya da jiya har da yau. Bayan iyayena ke ce macen ta farko da zan nuna da ta yi ma rayuwata hidima. Ki sani ke ɗin ta musamman man ce a wajena. Anan ƙarƙashin nan na ke jin tarin hidimarki a gare ni " Ya faɗa yana taɓa wajen zuciyarsa da hannuuwana da ya riƙe, sai gani kamar shashasha ina ta dariya da mirmishi. "Na gode da Martabawa Yallaɓai." "Nima da na gode da hidimantawa My Sady" A tare muka kalli juna sannan muka yi mirmishi sai na faɗa jikinashi ya rumgumeni cikin rumfar hannayensa masu zame mini garkuwa a koda yaushe. "Wata shawara kake buƙata daga gare ni? Na faɗa ina kwance a saman ƙirjinsa. Sai ya dago ni muna kallon juna kafin ya riƙe dukka hannayena guda biyu ya fara faɗin. "Rabi'atu yar maiduguri ce amma zama ya kawo ta nan Kano. Akwai Baffanta a nan garin ƙanin mahaifinta kenan bayan rasuwar mahaifinta shi ya karbeta ta dawo hannun shi tun tana JSS3. Ga shi yanzu har tana karatu anan BUK ajin ta ɗaya." "Ina jin ka." Na faɗa ina kallon Yallaɓai domin ganin yadda ya natsu kamar Nene ce a gaban shi ba ni ba. "Mun fi wattani biyu da haɗuwa. Kuma ni dai yanzu ina matakin na gabatar da kaina a wajen Baban nata ne." "A ina kuka haɗu? Na samu kaina da yi masa wannan tambayar Saboda ni dai a sanina ba ruwan Yallaɓai da yan mata amma sai ga shi ya zaunar da ni yana ba ni labarin budurwa. "A bakin BUK new site. Na je yi ma wani abokin karatun mu murna ya samu koyarwa a wajen shi ne bayan na fito na haɗu da ita tare da ƙawayenta su biyu." "Sai ka rage musu hanya ko? Na faɗa ina kallon shi sai ya fara dariya kafin ya ce" E. Ranar alhamis ne, daga cikin makaranta za su je gida Weekend. Sai na rage musu hanya na kai ƙawayenta gida itama na kai ta daga baya." Sai na samu kaina da yin mirmishi kawai. "Kuma suka yadda suka shiga motarka ba su san ka ba? "Ni na yi ta bin su ina yi musu magiya." Ya faɗa mini gaskiya da na ji da man ban tambaya ba. Da man bayan ni akwai wata macen da Yallaɓai zai iya yi ma magiya! Kin manta da Gimbiya? Wata zuciyar ta tunasar da ni. "To kin ji yadda muka haɗu da Rabi'atu" Sai na kalle shi, na ɗauka bayan ni Yallaɓai ba zai ji daɗin faɗin sunan wata mace ba, sai ga shi a gabana yana kiran sunan wata macen cikin shauƙi da muradi. "A hostel take zaune kenan? "E. Can take zaune sai bayan sati uku take zuwa gida Wekeend" "Can kake zuwa taɗi kenan? "E to wani lokacin. Amma har gidansu ina zuwa." "Can Maidugurui? Sai ya zaro mini ido kafin ta ya ce" Gidan Babanta dake Kano dai, Maiduguri wataƙila sai mun je ɗaurin aure." Sai na jinjina kai na ma kasa mgana. Yallaɓai ya riga ya gama tsara komai shi da yarinyar. "Kana son ta ne haka sosai? Sai ya fara sosa gira. Sai kawai na yi mirmishi kafin na ce" Ko ba ka faɗa ba labarin zuciyarka fuskarka ta bayyana mimi. To ita nata sonka kamar yadda kake son ta? "Ofcourse. " Sai muka kalli juna sai ya rage zumudin ya dan saussauta murya kafin ya ce" Na ce mata bana som auram ya wuce wata uku ta ce ta amince." To da mam za ta ki ne, me Yallabai ya rasa?  In ba ya faɗa ba ba mai ganin sa ya ce ya kai shekaru arba'in da tara, yana nan a matashin sa, kamar ɗan shekara talatin da ɗoriya. Balle ga ƙudi ga rufin asiri ga iya gayu ga kalamai ta same shi me za ta tsaya jira ban da ta amince? "Me kika ce? "Me zan ce? Na faɗa ina kallon shi. "Kice koma me za ki ce" "Ba abin da zence sai fatan alheri. Allah ya tabbatar Allah ya haɗe kawunan mu ya kauda da fitina." "Amin Amin My Sady. Amma wattanin ukun ba matsala? "Babu tun da ka shirya." "Gida ne, kuma in ba su ƙarisa ba zan ce a gyara mata shashe ɗaya ta fara tarewa. In ya so bayan bikin in an gama gyara na ku ke da Daughter sai ku tare a lokaci ɗaya." Sai na kalle shi kafin na ce" Kana ganin Matarka za ta amince? "Me ya sa ba za ta amince ba? Ai ba cewa na yi ba za ku tare gabaɗaya ba. Kuma tun da kika amince itama za ta amince in sha Allahu." Sai na samu kaina da cewa Allah ya sa. Ban ce ina son ganin hoton ta ba amma sai da ya nuna mini a cikin wayarsa.. Ba Yallaɓai da yake matsayin namiji ba har ni mace kyan yarinyar ya dake ni. Tabbas yar maiduguri ce fara ce tas ga gashi har gadon baya ga diri. Masha Allah hancin nan har baka, ga ta doguwa sai dai yarinya ce wannan ko za ta girmi Jidda da ƙadan ne. "Ta yi kyau. Allah ya sanya alheri." "Amin Amin. Itama na nuna mata hoton ki." Ban yi magana ba sai dai ina ta kallon shi. "Ta ce ganin ki ya fi jin ki." Ya faɗa yana dariyan nishaɗi. "A ina take jin labarina? "A bakina mana. Ai ba za mu hadu mu rabu ba ta ji sunan Sadiyata a bakina ba." Na yi zuru ina kallon Yallaɓai yana labarin budurwansa cikin nishaɗi. "Ta ce duk yadda aka yi ina ji dake. Na ce sosai ma ko ita na faɗa mata in har tana so ta kama babbar fada to ta kama kafa dake domin har ni juyanj kike yi " Ni kaina sai da na yi dariya kafin na ce" Kar ka jawo mini ta shigo da shirinta sabo da ni." "Haba. Ai Rabi'atu ba ruwanta." "Uhm" Na faɗa a ƙasan makoshi to wai ba ruwanta Yallaɓai da neman suna. "Tana ce mini Yallaɓai na ce ta bari kada ki ji ta. Ko a ma'aikatana ba mai kirana da Yallaɓai sai dai Oga ko Injiniya saboda ba na jin daɗin sunan a bakin kowa sai a bakin ki." "Ai sai na bar mata sunan. Ita ce amarya mu ai mun tsufa." Na faɗa ina kallon shi hAr na fara tausayin Gimbiya. Domin rawan ƙafan da Yallaɓai zai yi a kan yarinyaa nan, sai ya ce bai yi komai a lokacin auran ta ba. "Ta ce tana som sunan sai dai ku riƙa kirana ke da ita." "A'a ni fa na bar mata sunan. Ai na ɗana ina laifi mun sha miya ita kuma yanzu take." Yana wata dariya nishaɗi kafin ya ce" To ni kuma sai na koma wani suna a wajen ka? "Ah sunan ka mana." "Yusuf gatsal? Ya faɗa yana waro mini ido sai na gyaɗa masa kai ina yar dariya. "Tab. Ban yadda ba, sannan ban amince da wannan maganar ba. Sai ita ta sauya amma ni ba zan sauka daga kam mikamina ba " Ni dai sai bin Yallaɓai nake yi da kallo ina jin abin a zuciyata. Yallaɓai na zaunar da ni yana ba ni labarin wata macen cikin jin daɗi da annushuwa. Da bakin shi yake faɗa mini yau na sun fita ne, ya je makaranta ya ɗauke ta sun je shooping daga nan suka biya restaurant suka ci abinci anan ne ya ci wani ferfesun kifi ya lalatamai ciki kwana ya yi yana gudawa. Sai da asuba na bashi sauran flajin ɗin da nake da shi ya samu ya sha guduwan ya tsaya amma har da ciwon ciki shi ya sa da safen bayan ya yi wanka ya fita ya ce zai fara tsaya ta asibiti a ba shi magani. Sannan ya biya makaranta su Baby kafin ya wuce office tun da ya ce mata zai shigo makarantan na su yau. Har ya fita ya bar ni, ina cikin mamakin manganganunsa jiya, shi kenan kuma tun da ya faɗa mini sai ya samu kofa in dai yana gidana sai ya kawo sanadin da zai yi labarin Rabi'atu. Aikin sa kenan tana gaishe ni na ce ina amsawa, ban san yadda suka kare da ƴan uwan shi ba amma ni dai kawai ya ce mini ya yi magana da Nene, na san da man ba za ta hana shi ba shi ya sa ban matsa sai na ji amsarta ba. Ni dai ban yi taɗin da kowa ba ko su Munnira saboda na kasa iya sarrafa harshe wajen ba da labarin wai Yallaɓai zai ƙara auro zai auro yar yarinya ɗanya shakaf, mu kuma da man tafiya ta tafi jiya ba yau ba. Ko naƙi ko na so ba zan koma kamar Sadiya a jiya ba. Sai dai na koma Sadiya a yau har shekara arba'in da wani abu a duniya. Duk gyare-gyare na ban isa na koma kamar budurwa ko yarinya ba. Dole dai wajen ya saki tun da jiya ba yau ba ne. Itama Gimbiyar ni da ita duk samkal ne,  tun da tsere yan mu a shekaru ba nisa sosai itama ai ta kama gidan arba'in. Tun da yana da kuɗi zai buƙaci canji yanayi. Duk ƙoƙarina na kar ƙarim auran Yallaɓai ya dame ni na kasa. Abin ya tsaya mini a zuciya amma ina ƙoƙarin yakicewa saboda na zauna lafiya. Yallaɓai da bakinsa ya faɗa mini Kawu zai zo za su je su gabatar da kansu wajen baban Rabi'atu. Kuma ya zo sun je ɗin ya dawo yana faɗa mini ya yi musu karamcin amma ya ce su je zai neme su da kan shi. Yallaɓai rawan ƙafa kawai yake yi bai ƙi a ce gobe ma an ɗaura auran nan ba gyaran gida kam tuni ya tsaya bangaren da Rabi'atu za ta fara tarewa ma'aikata suka raja'a duk da namun ma fenti ne ya rage sai tayels da za a sanya amma ita bangarenta har tayels ɗin an saka kaɗan yarage a ƙarisa. Da bakinsa yake sanar da ni in ma an gama da wuri ba zai bari a saka lokacin bikin ya kai wattani uku ba.   Duk wannan bidirin da yake yi ban sam bai sanar da Gimbiya maganar da wuri ba. Na ɗauka yadda ya faɗa mini itama ya same ta sun yi magana ashe bai sanar da ita da wuri ba, ni kuma gani na yi ba hurumina ba ne shi ya sa ban yi azaɓarɓaɓin bakin kiranta in faɗa mata tun da ba ni ba ce mijinta. Kawai sai wayarta na samu kwana biyu tsakani da zuwan su Yallaɓai gaban Baban Rabi'atu. "Maman Jidda kin manafunce ni." Haka ta fara ce mini da na ɗauki wayarta da sallama. "Ikon Allah. Munafuncin mene kuma? Wataƙila kuka take yi domin tana ta jan hanci. "Ba ki faɗa mini Daddy aure zai ƙara ba. Sai da kowa ya gama jin magana sannan ya faɗa mini." "Ai ba hurumina ba ne na sanar da ke. Shi ya sa ma kika ji ban yi miki maganar ba." Na amsa mata, gaskiya na faɗa mata ba bangarena ba ne. "Amma ai mun yi magana da ke na ce ki bincika a bangarenki nima haka. Abin da muka sani mu faɗa ma juna me ya sa kika boye mini? Ahalin da bakin shi ya faɗa mini ke ya fara yi ma maganar kafin ma ya sanar da Nene? Sai na saki baki kawai kamar tana ganina saboda na ga kamar tana neman ta ɗora mini jakar tsaba ne. "Nima bai sanar da ni ba sai da na ga kiranta sannan na tambaye shi wace ce ya faɗa mini. Ki yi haƙuri in rashin faɗa mikin da ban yi ba ya yi miki ciwo. Na ga ba hurumina ba ne sanar dake shi ya sa" "Wallahi Daddy bai isa ya auro wannan yarinyar ba.  Anty Bahijja ta faɗa mini yarinya ce ƙarama kamar sa'ar Jidda shi ko kunya bai ji ba? Da me muka rage shi? "Ta ɗan girme ma Jidda gaskiya." Cikin mamaki a muryanta ta ce" Kin santa ne? "A'a ya dai nuna mini hoton ta na ganta. Kuma ya faɗa mini shekarunta." Sai kawri Gimbiya ta yi wani jan numfashi kafin ta ce" Da man yana ta cika baki da cewa Ko a lokacin aurena ba ki bashi matsala ba wannan ma yana fsɗi da fahari ba za ki bashi matsala ba. " "To matsalan me? Ai ko na yi kishi da hauka ba shi zai saka ya fasa ba. Sai ma ni na zubar da ƙimata. Kema ina mai baki shawara ki yi haƙuri duk da akwai zafi amma in ka daure sai komai ya zo ya wuce." "Tab. Wallahi ni ba zan yi munafunci saboda namiji ya so ni ba. Matsala kuma a wajena yanzu ya fara gani." Kafim na na yi magana ta katse kiranta sai na bi wayar da kallo kafin na furta" Ikon Allah! In na fahinceta ni ce mai yin munafuncin saboda Yallaɓai ya so ni, sai da na yi mirmishi Gimbiya kenan, ni fa ba zan yi tashin hankali da faɗa saboda Yallaɓai zai ƙara aure ba, yadda ban yi a baya ba yanzu ma ba mai sskani na saka kaina a cikin damuwa. Na san ba zai fasa ba kuma a yadda Yallaɓai ke ji da yarinyar nan wallahi Gimbiya ta ce za ta bashi matsala to shi zai iya nesa da ita saboda ya samu masalahan na shi muradin. Tana tunanin ina yin haka ne saboda ya yabe ni, ba ta sanni ba ne ni fa ban yarda na zubarma da kaina ƙima saboda namiji ba, a je dai a dawo suna ne zai yi tambari na bar ma kaina da ƴaƴana abin kunya daga ƙarshe ya yi auran shi to wa gari ya waya? Shi ya sa na koma ga Allah ina faɗa masa damuwa da fatan ya cire mini damuwa da tunanin ƙarim auren da Yallaɓai zai yi. Kuma Alhamdulillah na fara ganin canji. Yadda ko ƴan uwana ban yi zencen da kowa ba. Haka ƴaƴana kamar yadda ya sanar da su na auran Gimbiya wannan ma ya sanar da su da bakin shi. Jidda jarabawa ma suke yi jibi za su gama za ta dawo gida Baby kuma sun fara Jsce ta gama ajin ukun ƙaramar sakandiri. Duk ta buɗe tantanin budurci ya bayyanar mata. Wancan watan ta fara jinin al'ada gashi ta fi Jidda manyan gabbaina tun ba ta yi wani shekaru nanna sun cika mata ƙirji. Hankalina na mai da kan kula da tarbiyan yayana. Yallaɓai yanzu ba ma gaban shi hankalin shi da duka tunanin shi na kan yadda zai mallaki Rabi'atu ne shi ya sa nake yi masa uzuri. Ni ko da muka yi magana da Gimbiya ban yi ma ko Yallaɓai zencen ba, nima bai nuna mini a yanayin da suke ciki ba. Shi ya sa nima ban tusa kaina a cikin abin da ba ruwana. Jidda ta gama jarabawa ta dawo gida sai gidan ya yi daɗi na rage kaɗaici, har Yumna yanzu ta fi karsasshin wasa da dawowar Jidda har uban gayyar ma ya yi murna da dawowarta yana faɗa mata gidan ba daɗi da ba ta nan. Ban san me ya faru ba kawai na ga Yallaɓai ya kwaso mini su Khalipa da Anwar, na tamnaye shi lafiya? Ya ce ba komai. Ina maman su? Ya ce mini ta je Rano ta dawo. Ni kuma har ga Allah ban kawo ma kaina tunanin matssla suka samu da zuciya ɗaya na karɓi yaram gidan sai ya zama active saboda ɗan hayaniyarsu  in sun tafi makaranta Jidda da Baby suna gida, in sun dawo gidan ya sake rikicewa da wasannin su tun ballanta Yunma da Yallaɓai ya gama ɓata ta da mugun wasa. Kwana uku tsakani ranar wata laraba Munnira ta kira ni a waya tace ko ina gida na ce mata ina gida. Sai ta ce mini gata nan zuwa, da maganar mu ba a daɗe ba sai ga ta tun da na ganta na san da magana. Na kuma san bai wuce labarin auran Yallaɓai da suka samu labari. A daran jiya yake faɗa mini Baban Rabi'a ya neme sa yau zai je su sake ganawa. Ina kuma da tabbacin ya gama binciken shi ne zai ce ya turo magabantan sa. Tun da Yallaɓai ba shi da abin ƙin daga asalin shi har rayuwarsa duk da ɗan adam tara yake bai gama cika goma ba. "Kwana biyu ke da Hauwa kun ɓoye? Na faɗa lokacin da na shigo falon, da man ina cikin bedroom ɗinna Jidda ta sanar da ni zuwanta. "Wallahi ya gida? Ta faɗa tana ɗaukan ruwan da Jidda ta kawo mata na gora ta zuba a kofi ta fara sha sai ni kuma na zauna gefenta ina faɗin" Ya yara? Kwana biyu ba mu haɗu ba." Sai da ta gama shan ruwa ta dire kofin a saman centetr table ɗin dake falon sannan ta ce" Uhm ke ce ai kin ɓuya. Yanzu ma dalili ne ya sa na neme ki." "Wai auran Yallaɓai? Na faɗa ina dariya. "Au ashe ma kin san abin da ya kawo ni." Ina mata murmishi na ce" Na san dai yanzu shi ke trending." "Uhm wai ashe Yallaɓai aure zai ƙara ba ki sanar da mu ba Sadiya? "Wallahi na kasa iya faɗa ma kowa. Amma na bari in an saka ranar sai na kira ku mu yi maganar." "Da gasken gasken dai auren zai ƙara? Ta faɗa cikin tantama. "Ya wuce wai fa. Yau ma yace mini zai sake komawa Baban Rabi'atun ya sake neman shi." Na faɗa ina kallonta. "Sunanta kenan? Rabi'atu? "E. Yar maiduguri ce amma an riƙeta anan Kano. Yarinya ce ƙarama ajinta ɗaya ma jami'a." "Duk a ina kika san wannan labarin? "A ina kuwa? A bakin uban gayyae mana." Na faɗa ina dariya sai Munnira ta gyara zama tana faɗin" Ba Shakka." Sai kuma ta yi shuru. "Ke a ina kika ji? Na tabbata dai maganar ba ta fita ba sosai." "A bakin Jamila na fara ji, sannan jiya da daddare labari ya kawo labari Nasir ke faɗa mini. Ashe wai har sun samu matsala da mutuniyarki? "Wac ce? "Gumbiya mana." Sai na ware ido kafin na ce" Subhanallah da shi Yallaɓan? Munnira ta yi dariyan mugunta kafin ta ce" Wai ita ana dole ba zai yi mata kishiya ba. Ta manta ke ma da ita aka yi miki kishiyar? Wanzami ba ya son jarfa" "Me ya faru ne! Ni wallahi ban sani ba. Na ga dai ya kwaso mini yara ya kawo mini da na yi magama sai ya ce bata nan ta je Rano." "Af yaji ta yi " "Yaji? Na faɗa ina zaro ido. "Wallahi faɗa suka yi a yadda Nasir ya ce shi Ya Tafidan ya faɗa massa. Tun da ya faɗa mata zai ƙara aure ba su samu fahintar juna da zaman lafiya ba ranar kawai ta saci wayarsa ta dauki lambar yarinyar ta kirata ta yi mata zagin kare dangi. Ashe yarinya yar gari ce ta yi recording yana zuwa ta kunna masa shi kuma da ya dawo sai ya hau ta faɗa shi ne ta miƙe yana faɗa tana faɗa daga ƙarshe zai bar mata ɗakin ya ce ta ja masa riga har tana yaga masa, ta kuma ci kwalan shi ta ce in dai ya rantse sai ya yi auren nan da wannan yarinya ita kuma sai ya sake ta. A cewar sa ya yi ta ƙi sakin shi sai ya fizge kan shi ya ture ta gefe ta faɗi shine ta hau kuka wai ya daketa akan wata banza gari na wayewa ta tafi Rano har yau ba ta dawo ba shi kuma ya ce ba zai je ya yi bikonta ba tun da abin da ta yi rashin tunani ne." Tagumi kawai na yi na ma kasa magana. Sai da na ce mata ta bi a hankali. Amma sai take ganin kamar ni ina goyon bayan Yallaɓai ne. "Na je Gwammaja jiya har Nene ba ta saka baki a maganar ba ta ce Gimbiyar ce ba ta kyauta ba.. aure ya ce zai ƙara ba wani zunibi ba" "Ina su Anty Bahijja? "Ohom musu. A bakin Suwaiba na ke jin Mimiaco ce kawai da Nene ke bayan Tafida. Anty Maimuma da Anty Bahijja duk yan bayan Gimbiya ne kar a yi mata kishiya." Ban san ina dariya ba sai da na ga ina ƙyaƙyatawa. "Wato kar a yi mata kishiya tuj da ta su ce? Ni da bare ce ai suna gaba gaba wajen ba shi goyon bayan ni ya yi mini ko? "To da man. Ai ni farinciki na yi da zencen ƙarin auren na. Lokaci ya yi da Gimbiya za ta ɗanɗana abin da kika ɗanɗana ta ji in da daɗi." "Wallahi. Welcome to the Game." Na faɗa ina dariya har muna tafaww. Ba wai ina murna ba ne amma dai na ji daɗi a kallah dai za su san cewa yau gare ka ne gobe ga wanin ka jibi ma a kanka ne zai faru. Muna tare da Munnira har bayan la'asar sanman ta tafi, Yallaɓai da wuri ya dawo ya yi wanka aka saka manya kaya ana ƙamshi ya tafi. Tun kafin ya dawo ya kirani a waya da albishir ɗin Baban Rabi'atu ya ba shi da man ya tura magabantan shi. Murna kamar Yallaɓai zai yi hauka da ya dawo haka ya rumgumeni cak kuma ya ɗagani yana juyi da ni a tsakiyar falo gaban yara. Ni dai na daki kafadan shi ina faɗin ya sauke ni. Ai na ga abin mamaki haka ya bi su Jidda ɗaya bayan ɗaya yana rumgumansu cikin farinciki. "Abba me ya faru ne? Ko ka samu wasu kudaɗe ne? Jidda ta faɗa tana dariya. "Abin da na samu ya fi kuɗi daraja My Jidda. Ƙaramar Anty zan sake kawo muku." Daga ita har Baby shuru suka yi kamar ba su gane ba. "Jidda Baby, aure zan ƙara. Baban Antynku ne ya ce na turo da magabatana." "Allah ya sanya alheri Abba" Jidda ta faɗa cikin natsuwa its ko mara kai Baby sai ta fara tsalle tana faɗin" Abba yaushe bikin? "Ba zai ɗau lokaci ba? Ya faɗa yana shafa kanta falona ya kaure da ihun su har da su Khalipa da ba su san me ake ciki ba. Yumna ya ɗaga sama yana mata wasa kafin ya kalleni yana faɗin" Rabi'atu ta ce ita fa Yumna za ki ba ta." "Ba dai uwata ba kam! Na faɗa da iya gaskiyata sai ya fara dariya. "Jidda zaki ba ta ko Baby? "Jidda ai ɗiyar Gimbiya ne. sai dai ko Baby ko Khalipa." "Ta fi son mace ta ce mini. Kin san tana ganin hotin su a wayata. Ita dai Yumna take so." Ni tsabar mf zumuɗin Yallabai ya sa ban samu amsa masa ba. Abinci ma bai ci ya ce ya ci a can wai an kawo Baba ya ce sai ya ci shi kuma ya kasa yi masa gardama su Baba manya. Ina so na yi maganar Gimbiya ina jin tsoro kar ya ce na yi shisshigi, ganin yana cikin farinciki yasa na yi kumdunbala na yi masa maganar amma sai ya shashantar da maganar da cewa na ƙyaleta za ta dawo. "To ko za ka je ka dawo da ita ne? Ka yi mata uzuri kishiya fa zaka yi mata? Kawai ya taso mini kamar ni cw na yi masa laifin "Ke ba kishiyan na yi miki da ita ba, kin tada mini hankali? Ke da sai bayan an ɗaura ma kika sani kin sama mini zaman lafiya sai ita da na faɗa mata cikin lalama amma ba yadda ba. Kin ji irin zagin da ta yi ma Rabi'atu ba domin ta yi hankali ba ta biye mata ba daya kike tunanin lamarin zai tsaya? Kuma na so ina nuna mata kuskurenta amma daga ƙarshe ni ta yi attaking ina matsayin mijinta. Ban ce ta tafi ba amma tun da tafi wallahi kafata ba zai taka zuwa Rabo saboda ita ba kar Allah ya sa ta dawo ta gani in za a fasa komai ne saboda tafiyarta." Ni dai haƙuri kawai na ke bashi domin na ga ya ɗau zafi da yawa. "Wallahi ko Nene na faɗa mata ta cire bakinta ba in da zan je kuma haka nan ta ƙyaleni . Kema abin sda zan ce miki kenan ki zura ido kawai ba ruwan ki a wannan maganar." Tun da na ji har Nene ma an bata haƙuri ni a suwa sai na kama kaina.. Yadda ma yake ta shirin turawan nan tuni ya shafe babin Gimbiya. Aure fa ya tabbata da gaske Ya Usman daga porthercout ya zo Kano saboda maganar. Shi da Tafidan Rano Baffan Gimbiya da Kawu Sa'adu da Kawu Abba da Tariq suka je neman ma Yallaɓai auran Rabi'atum Sun je da kudin gaisuwar iyaye dubu ɗari huɗu, ga kayan saka rana mota guda. An yanke musu sadaki dubu ɗari biyar, sanaan an yi maganar tana karatu zai barta ta cigaba. An saka rana wata ɗaya cikin na biyu. Ƙarshen January, shi Yallaɓai ma ya so ƙarshen watan Desember ne amma iyayenta suka ce aa a ba su lokaci suma ai suna da na su shirin sannan a garin maiduguri a gidan mahaifinta za a ɗaura auren . Duk da suka dawo a can gidan Nene suka yada zango. Ni kuma a bakin uban gayyar na ji labarin yadda ta kaya da ya dawo da daddare. "Ma sha Allah. Lamari ya yi daɗi Allah ya sanya alheri ya nuna mana lokacin da rai da lafiya." "Amin Amin Abar ƙaunata." Har yana sumbatar leɓena cikin farinciki, ranar a gaba ma Yallaɓai ya yi waya da Rabi'atun har ya na ba ni ita muka gaisa. Tana wani maƙale murya da na ce Allah ya sanya alheri ya nuna mana lokacin da rai da lafiya. "Amin Anty na gode." Ta faɗa cikin sanyin murya. Ta tambayi su Jidda na ce suna nan gida an yi hutu. "Ina ta yi ma Yallaɓei magiyan ya kawo mini su ya ce sai ya tambaye ki " Ina kallon shi na ce" Ba ruwana ai shine shugaba abin da ya ce shi za a yi. Yadda ya dama haka muke sha." Tana ta dariya ni kuma na yi mata alƙwarin in su Khalipa sun yi hutu zAi kawo mata su gabaɗaya sai da na ba shi wayar ya kashe bayan ya ce mata zai kira daga baya yake faɗa mini karshrn watan nan itama za ta je maiduguri. Sai dai ya kai su wani sati ta gan su. "Tana son yara na. Ko da yaushe sai ta yi mini ƙorafin na kai mata su. Jidda ma zan ba ta lambar wayarta itama zan ba ta nata su riƙa gaisawa." "Hakan ya yi " Domin ni yanzu yar bi ce, in dsi akan auren nan na Yallaɓai nr, ga Gimbiya tana can har an saka rana shaida ba abin da za a fasa. Anty Zabba ta kirani a waya tana ta dariyan mugunta ta ce ai da Ya Usman ya faɗa mata ta buga guɗa. Itama har ta ji labarin Gimbiya ta yi yaji. "Sakara kawai. Wa ya faɗa mata ana cin riban namiji in har ya tashi ƙara aure? Ai da ta kwantar da hankalinta da ta ci riba." Ni dai ban furta ba, domin har a cikin zuciyata ban ji daɗin tafiyarta ba ba ni da yadda zan yi ne. Maganar auren Yallaɓai ta fasu a gari tun da duk an sanar a groups ɗin su na gida,nima sai na faɗa ana gidanmu. Ya Aina ta ce af ita ai ta san za a rina Ma'u ta yi ta masifa wai Yallaɓai ya cika haɗa ma har Ya Auwal ya fito ya ce ba ma son gaskiya. Shima yana da niyyar sai ya yi huɗu in sha Allahu muna ta dariya. Hauwa da Munnira sun yi ta ƙorafin me ya sa na amince amarya ta fara tarewa a sabon gida? "To miye a ciki? Mijin ma gabaɗaya za ta mu raba shi tare miye abin damuwa a gida. Ta tare can ya gama mararinta daga baya mu sai mu koma." Daga haka na kashe bakin su, Gimbiya sama da sati biyu sannan ta dawo, shi kuma da kan shi ya faɗa mini har yana faharin shi bai je ba, su Anty Bahijja ne suke je suka dawo da ita Bayan Tafidan Rano ya yi mata faɗa sosai. Har kuma ta dawo su Khalipa na gida ba su koma ba, shi bai ma yar da su ba nima ban ce su koma ba na bar su ko itama za ta samu kwanciyar hankali. In da ta ji shawarata wallahi da duk haka bai faru da ita ba. Kwana ɗaya tsakanin faɗa mini da ya yi ta dawo. Ranar ma a gidan ta ya kwana da safe da ya ke ranar laraba ne su Khalipa na makaranta suna Jarabawa ne ina cikin bedroon su Jidda ke da gidan yanzu tun da suna nan daga ita har Baby ba na yin aikin komai sai dai na kwanta na tashi na ci kawai. Haihuwa mai rana Ina cikin ɗakin Baby ta zo ta ce mini ga Gwaggo Bahijja da Anty Gimbiya nan sun zo, na yi ta mamakin zuwan su. Ban ɓata lokaci ba na saka ɗankwali na fita falon Yallaɓai in da suke zaune Wallahi na tsausayama Gimbiya duk ta faɗa ta yi zuru zuru ba gayu yau. Na yi mamakin da muka gaisa da Anty Bahijja faram faram kamar ba mu taɓa samun matsala ba ashe alfarma aka zo ci dole a yi mimi haba haba. Wai Anty Bahijja ke faɗa mini mu haɗa kai da Gimbiya domin mu rusa wannan auren tun da Yallaɓai na jin maganata. "In ma auren ba zai fasu ba. To ku tabbata bayan an yi aurwn yarinyar nan ba ta ji daɗin zama da shi ba. Ku haɗe kan ku ke da ita domin ku tsira tare." In ji Anty Bahijja. "Kuma ma har da maganar gida. Ke sai ki amince yarinyae can ta fara tarewa? Wallahi ba zan yarda da." In ji Gimbiya. "Yauwa har maganan gidan ku haɗe kai ku ce ba ku yarda ba. Ko ya gyara ku fara tarewa kafin auren ko itama ya nena mata wajen zama ta jira ku tare gabaɗaya ko ba gaskiys ba." Anty Bahijja ta faɗa tana kallona. "Gaskiya ne." Na faɗa ina ƴar dariya ina mai kallon su a ɗage ɗaya bayan ɗaya.. Sai yanzu ne suka san ina da amfani? Wato na haɗa kai da Gimbiya saboda su mafitarsu suke nema. Ni kuma wallahi ba wacce ta isa ta saka ni na zubar da girmana. Yallaɓai ya nuna ma yarinyar nan ina da daraja a rayuwarsa shima ya nuna ma duniya ina da ƙima a wajen sa saboda kishiyar da ba ta ɗauke ni a bakin komai ba ba zan yi wasa da mutumcima ba. "Ku yi hakuri zencen gaskiya ki cire ni a wannan lissafin ba zan iya aikata ko ɗaya a ciki ba ' Na faɗa ina kallon su, suma ni suke kallo cikin mamaki. "Aurn da zai yi umarnin Allah ne. Maganar gida kuma gidan shi, don ya ce ga yadda za a yi ni ban isa na ce ba haka ba. Allah na tuba mijin ma aka yi sharing ɗin sa da ita sai gida ne zama abin damuwa ? Ni a ganina wannan ba hanyar ɓulllewa ba ce, hakuri shi ne kawai. Amma ba abin da za a fasa." "Da man na faɗa miki ba za ta yadda ba. Ita fa jin dadi take yi Saboda ni za a yi mawa ba ita ba tana bashi goyon baya." Gimbiya ta faɗa ma Anty Bahijja. "Naga alama." Sai kawai na miƙe ina faɗin" Duk yadda kuka ɗauka dai dai ne. Ni dai Allah na gani ba zan yi hauka saboda Yallabai zai ƙara aure ba, in ke za ki yi haushi to ki yi shi kaɗai amma ba tare da ni ba. Sannan sai yau da zai ƙara aure na ke da amfani a wajen ku? Ai ba ki taba kawo ta ko ce mu haɗa kai ba sai yau. Saboda amfanin ku ne, to ba zan yi ba kowa tashi ta fishshe shi." Ina gama faɗin haka na bar musu falon na san sun yi suman zaune da mamakina. *Janafty**TKGB3018* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gkzmhd0zmnFChYrdONLFYp Bedroom ɗina na koma na yi zama na ban san lokacin da suka tafi ba, har ga Allah ba ina murna da ƙarin auren Yallaɓai ba ne saboda kishiya ai sunan ta kishiya nima a zaman matar mijina take. Na so Gimbiya ta ji maganata ta kwantar da hankalinta saboda ta tsira da sauran mutumcinta amma taƙi jin maganata tana biye ma su Anty Bahijja. Wanda na tabbata in aka juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe, dole akwai bangaren da za ta nuna mata Yallaɓai ne jininta na kusa ba ita ba. Abin da nake yi ita a ganinta ina bin bayan auran Yallaɓai ne saboda ita, abin da ba ta sani ba da na bi baya da ban bi baya ba ban ga dalilin da zai saka Yallaɓai ya fasa wannan auran ba, yau ko Nene ce ta hana shi na tabbata zai yini yana yi mata karatun da za ta gane har ta amince domin bai ɗauko maganar auran nan don ya fasa ba. Shi ya sa gwara ta kwantar da hankalinta domin ba abin da za a fasa. Rasa wanda zan kira na tseguminta masa zuwan Gimbiya da Anty Bahijja sai Munnira ina faɗa mata ta yi dariya da shewa kafin ta ce. "Sai yanzu suka san ana haɗa kai? Wato sai yanzu da suke neman mafitar su." "Wallahi, ni kaina zuwan su ya ba ni mamaki. Har Anty Bahijja na faɗin wai mu haɗa kai ko ba mu rusa auran ba mu hana su zaman lafiya har sai ya gaji ya sake ta" Na faɗa, ina riƙe baki domin sai a lokacin na ke jin ma ƙarin mamakin zuwan su da magangansu. "Lalle. Ni ban yi mamaki da man na san za a zo wajen. To ke me kika faɗa musu? "Na ce ni ba zan haɗa kai domin a yi tashin hankali da ni ba itama ina na faɗa mata gaskiyan ta bar ma komai ta kwantar da hankalinta. Amma ba ta ji ba ita a ganinta ina goyon bayan Yallaɓai saboda ita ne, ni kuma wallahi ba haka ba ne Munnira. Kin sanni ba ni da wanman muguntar, ina tausaya mata ne domin a irin rawan kafan da Yallaɓai ya ke yi a kan auran nan ni ko ita wallahi ba mu da darajan da za mu iya dakatar da shi, shi ya sa na koma gefe na zama yar kallo na shafa ma kaina lafiya." "Haba na sani wallahi. Kin huta da man a irin wannan lokacin in baku sauke a kai ba sai a samu matsala. Kuma su Anty Bahijja ne za su ɗora ta akan keken ɓera su kaita su baro ta." Na amsa da wallahi, domin in ta kwaɓe su kan su ba za su iya ba. Wai maimakon su ce ta yi haƙuri ta ma yar da lamarin ta ga Allah, amma suna zugata ta yi tashin hankali da miji. Har muka gama waya da Munnira ita kanta ta ce da Gimbiya ta kwantar da hankalinta da zai fi mata alherin akan wannan haukan kishin da ta ke yi, nima abin da na hango mata kenan. Bayan Munnira ban faɗa ma kowa zuwan su Gimbiya ko Hauwa ba mu yi taɗin da ita ba, a satin na je Ɗorayi gai da su Alhajinmu ina faɗa masa ƙarin auran Yallaɓai, sai ga magana tiryan tiryan a bakin Alhaji. "Har nan falona in da kike zaune nan megidanki ya zauna ya sanar da ni zai ƙara aure, ya kuma dawo ya roƙeni na shirya aje nema masa aure da ni sai kuma aka yi rashin sa'a ranar zan je Yashe shi ya sa ban samu zuwa ba amma na yi masa alƙawarin zuwa masa ɗaurin aure." "Maidugurin Alhajinmu.? Na faɗa ina zare ido saboda mamaki. Sai kawai Alhajinmu ya yi dariyar su na manya kafin ya ce" In sha Allahu in dai muna raye zan je. Ai ya girmama ni matuƙa nima zan ma yar masa da girmamawan sa." Uhm kawai na ce na ma kasa magana saboda mamakin Alhajinmu wai zai je har Maiduguri ɗaurin auran Yallaɓai, ni bai ma taɓa nuna mini ya zo ba ashe ya zagayo sai da na koma gida da Yallaɓai ya zo yi mana sallama a daran nake masa mganar aahe ya wanke kafafunsa ya je ya faɗa ma Alhajinmu maganar aurensa. "Ya ba zan faɗa masa ba! Me kike nufi? Alhaji ai uba ne dole na je na same shi na faɗa masa komai dangane da aurena. Bai ma samu zuwa maganar auren ba amma ya yi mini alƙawarin zuwa ɗaurin aure har can maiduguri " Kallon Yallaɓai kawai na ke yi, a fatar baki na ce Allah ya kaimu da rai da lafiya. Tun da Alhaji ya yi niyya wa ya isa ya hana shi, ni ma kafin na fito sai da ya sake yi mini nasiha sosai akan haƙuri na zauna kuma da kowa tsakani ga Allah, ina jin daɗin manganganun Alhajinmu shi dai har na zama mai ɗaga ma mijina hankali. Na zama mace mai samar masa da zaman lafiya a cikin gidan shi, haƙurin da na yi a farko yanzu na ninka shi, nan gaba kaɗan zan ga riban haƙurina ko ya ce zan ƙara gani domin ribar haƙuri na gan shi tun da har gobe  mijina ya yaba mini da hallaya masu kyau. Tun da aka sanya lokaci Yallaɓai bai zauna ba shiri kawai yake yi kamar zai yi auran farko. Ko da yake budurwa zai ɗauka dole ya yi rawan jiki, ranar sati na zuwa Yallaɓai ya ce na shirya yara za su je su gaida Gimbiya. Shi ya sa ya ƙi ma yar da su Khalipa gida, ni na ma manta da zencen amma shi yana sane bai manta ba faɗa mini yake yi ai ta riga ta gama shirin tarɓansu tun da ya faɗa mata za su zo, Jidda na saka ta shirya yaran suma na ce su shirya sun ci gayun su ni dai ba ni da komai Hijabi da mayafi na ba ma Jidda na ce ta kai ma Antyn na su. Yallaɓai kamar bakin shi zai yage saboda farinciki shima ya ci gayu yana rawan jiki har sai da na yi masa magana. "Yallaɓai wai ba can za ka bar yaran ka wuce office ba? "E ina tunanin haka akwai baƙin da zan gani." Sai na yi shuru domin na ga yana rawan kafa ne har ya wuce misali, har yana yi mini godiyan saƙon da na ba da akaikace na ce bakomai yiwa kai ne. Shi ya ɗauke su a motar shi, tun wajem sha ɗaya na safe, ina jira na ga Yallaɓai ya dawo mini da yara amma shru har la'asar shi kuma na kira wayarsa bai ɗauka ba sai na kira Jidda ina mata faɗan zaman me suke yi ne har yanzu ba su dawo ba. "Umma Abba ya ce mu jira shi zai dawo ya ɗauke mu." "Kenan shi kuke jira? Na faɗa ina mai kama baki, kafin ta yi magana sai na ji an yi mini sallama cikin sanyin murya ina jin murya na gane na Rabi'atu ne Gaishe ni ta yi na amsa nima cikin sakewa kafin na ce" Yau an kawo miki gidan gabaɗaya hayaniya ya dame ki ko? Tana mirmishi ta ce" A'a ni da man su kwana Anty" Sai nima na yi dariya kafin na ce"Haba dai. Ba yanzu ba ki jira saura ƙiris wata rana ma sai kin kore su saboda gajiya." "Ni ba zan kore su ba. " Ta faɗa tana yar dariya, godiya ta yi mini na saƙo na ce mata haba yi wa kai ne. Na ce su kira Yallaɓai in ba zai samu komawa ya ɗauke su ba Jidda ta  yi jagoranci su samu a daidaita su dawo gida yamma ta yi. "Ya ce zai dawo ya ɗauke su. Na san yana hanya." Ai ni sai na kasa magana tun da ga abin da ya ce. Ni dai ban ga yara ba sai bayan sallar isha'i, Yallaɓai bai isa can ba sai bayan mangariba can suka ci abinci sannan ya tarkato yara suka taho. Baby ke faɗa mini a mota suka jima Abban su na cikin falo da Antyn na su. Ni fa tsoron rawan jikin Yallaɓai na ke yi a kan yarinyar nan har ta haukata shi, sun dawo da kayan zaki kaya guda kamar za a buɗe shago su bickit ne da su katan ɗin boo na yara. Yallaɓai yana faɗa mini ya ce ta bar shi amma ta fara fushin yana nuna mata su Jidda ba ya'yanta ba ne, ni dai ban yi magana ba saboda ba ni da ta cewa Godiya ma shi ya yi mini na ci sai na kirata na yi mata godiya kamar wani laifi ne in ban yi mata ba haka nan na ce Jidda ta kira ta a wayarta tun da sun karɓi lambar wayar juna. Shi ne na samu na yi mata godiya tana ta jin kunya da man iyayin Yallaɓai ne amma ni na san har tsaraban ma duk shi ya siya ba wai ita ba, in ita ta siya ma da kuɗin shi ne. Washegari Lahadi Gimbiya ta aiko aka tafi da su Khalipa. Da man ko ba ta aiko ba ina shirin na roƙi Yallaɓai ya ma yar da su to sai ga shi bayan fitan shi, ta aiko Salisu ya zo ya tafi da su. Da ya  dawo a daran da man yana gida ne, ya ga bai gan su ba ya tambaya na ce sun koma gida. Sai ya fara faɗan wai ba na jin maganarsa me ya sa zan ma yar da su ba tare da izinin shi ba. "Ah ni fa ba ni na ma yar da su ba kana fita mamansu ta aiko Salisu ya tafi da su." Sai ya yi shuru bai yi magana ba amma ya yi ƙyafci alamun ran shi ya ɓaci ni ko a raina na ce can ku ƙarata ba ruwana. Sai da muka zauna ne Baby ke ba ni labarin da suka je gidan su Antyn ta su haka ake ta zuwa ganin su, a raina na ce dole a zo a gan ku Jidda ba ta magana ita da man Baby ce da man yar surutu amma faɗa mini take yi Antynsu na da kirki gidan ta za ta koma na ce Allah ya ba da sa'a. Jidda ce mini kawai ta yi She is young Umma, ko ba ta faɗa ba na san ƙaramar yarinya ce Yallaɓai zai aura. Kuma yadda yake rawan kafa wannan in aka yi auran sai Allah kawai kar Yallaɓai ya lalace a gindin yarinya ƙarama. Ni ban san a in da Gimbiya ta ji labarin su Khalipa sun je wajen Antyn ta su ba amma na fi tunanin a bakin Khalipa ta ji tun da yana da magana shima. Kawai bugo mini waya ta yi da man tun zuwan su gidana na ce ba na tare da su ba mu ƙara magana ba. Ni wai Gimbiya ta buga ma warning akan me ya sa zan yanke hukunci kan ya'yanta? Me ya sa na tura su gidan wata banza ba tare da sanin ta ba. Ni ko cikin mamaki na ce' Umarnin megidan ne amma ba ni na tura su ba " Sai ta fara masifa tana faɗar manganganu wai da sanina aka yi komai da ban ba da goyon baya da ba a tura mata yara gaida wata banza ba tare da sanin ta ba. "To ki yi haƙuri." Haka kawai na ce mata ganin kamar ni ce take jin haushi yanzu ba mijinta da zai ƙara aure ba. "Ahto ni dai a kiyayeni. Ya'yan dai nawa ne ba wani ya haifa mini ba, in kina son neman sunan ki aika na ki ƴa'ƴan amma ban da nawa." "To in sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba' Kawai sai ta yi mini tsaki mai girma har ina jin sa a cikin kunnuwana sannan ta kashe wayarta ta bar ni sake da baki. Ni zan fita? Ina ruwana a wannan maganar da abun zai dawo kaina? Raina ya ɓaci amma sai na danne zuciyata na ɗau girma na yi haƙuri shi ya sa ko zencen ban yi ma Yallaɓai ba. Nima bai  yi mini ba. Mun shiga tsakiyar watan December, Yallaɓai na ta shirin shi na gida ina ga ma an gama gyara bangaren da Rabi'ar za ta zauna sai maganar lefe ya fara yi mini. Da cewa ya yi magana da Mimisco ta ba shi shawaran kawai ya ba ma ita Rabi'an kuɗi ta siya komai da kanta. Nima da ya faɗa mini na ce hakan ya yi, tun da Mimisco ita ce kaɗai ke supporting ɗin sa sai su Suwaiba amma su Anty Bahijja sun ja tunga shi ko ya ce uwarsa ba ta hana shi ba ba wacce ta isa ba. A bakin Suwaiba na ke jin wasu mangaganun, sun ce ni ce ke zuga shi saboda na ga ba ni za a yi ma kishiya ba ni in suna faɗar haka har mamakinsu nake yi mijina ne fa zai ƙara aure? Ni ba mace ba ce ba zan yi kishi ba? Ba dangin Yallaɓai kaɗai na ke shan zagi ba hadda na su Giimbiya a can Rano. Sameena ta kira ni a waya tana faɗa mini mganganun da ta ji a kaina marasa daɗi. Wai na ki yadda mu haɗa kai da Gimbiya na koma gefe ina munafutarta wai tun kafin Amaryan ta shigo na ke ta tusa kaina a wajen yar cikina. Mangaganu dai marasa daɗi, ni ko na yi mata rantsuwan duk abin da ta ji ƙarya ne na yi mata cikaken bayanin abin da ya faru  da wanda ke faruwa. "Sameena na isa na hana Yallaɓai aure? Ni ban isa ba shi ya sa na koma gefe na zama yar kalllo. Itama shawaran da na bata kenan ba ta ɗauka ba, ta biye ma su Anty Bahijja suna faɗa mata cewa ni ina jin daɗin auren da Yallaɓai zai yi sabo da ita. Sun manta nima ɗin mijina ne kuma mace ce ni, ina da kishi sai da na saka haƙuri kuma na roƙi Allah ya cire mini zafin kishi. Kuma ya cire mini shi ya sa na ke zaume lafiya su kuma shi ne ba su so, sun so ne yadda take hauka nima na biye mata duk mu zama mahaukata." Sameena ta ce "wannan gaskiya ne. To kuma ba a kishiya ke kika bari aka auro ta,? Duk ta manta baya? Wallahi tana ta rigima domin jiya ma mun yi waya da Hajiyar mu take faɗa mini case ɗin gida ma ake yi " "Gida? Na furta cikin mamaki domin ni ban ma san da maganar ba Sai da ta yi mini bayani ashe Gimbiya ta yi tsalle ta ce Amarya ba ta isa ta fara tarewa a gidan ba kafin ita ba. "Ikon Allah." Na faɗa ina jinjina kaina. "Wallahi an ce magana har Baba Tafida ya shiga ciki. " "To ya ake ciki yanzu? "Ban sani ba. Amma dai an ce Ya Tafida ya ce in har ta ga ta tarewa a gidan nan to kema kin tare ne amma tun da ta saka tsiya sai ya gani ɗin." Ni ma kasa magana har muka yi sallama da Sameena. Kenan da gaske Gimbiya take yi? Illau ko kwana biyu da maganar mu da Sameena Yallaɓai ya shigo mini gida da rana kamar kabubuwa ranar a gidan Gimbiya ya kwana ban san kuma me ya faru ba kawai ya ce nima na shirya za mu tare a sabon gida a ƙarshen wata bai ma ba ni damar magana ba ya fita ya shiga mota ya ta fi. Hankalina ya tashi saboda ban shirya komai ba ina ni ina tariya ni da Yallaɓai ya yi ma manyan falo uku da bedroom huɗu na su Gimbiya ne falo Biyu bedroom biyu. Ina na ga kayan da zan yi wannan tariya ai ba tariyan sauri ba ne sai na natsa. Na rasa yadda zan yi, a yadda Yallaɓai ya zuciya ban isa na kawo wata magana ba. Domin a daran ma da ya dawo ina fara magana ya dakatar da ni. "In dai maganar tariyan gida ne bana son jin komai. Ki shirya ki tare a ƙarshen wata nan." Tun da na ji haka na san akwai matsala na rasa wa zan tun kara, na yi niyyar na yi sabbin labulaya. Da Zannuwan gado da ɗan abin da baa rasa ba sauran abubuwan daga baya in Allah ya hore mini sai na yi. Ni kwata kwata ban shirya ba, har ya faɗa ma yara suna ta Murna su Jidda har sun fara parking ɗin kayan su har Yumna tsalle take yi za su koma sabon gida. Ganin ya ƙi saurarena ya sa na kira Mimisco na sauke murya ina faɗa mata uzirina. "Ke ma kin yi magana Sadiya. Amma kin sani ki yi shuru kar ki yi masa mgana a yanzu yana cikin tsini ne, ki bari nan da sati ɗaya in ya huce sai na yi masa mgana." Sai na ce mata to, ban tambayeta ba da kanta ta fara faɗa mini matsalan da aka samu. Gimbiya ta matsa sai ta fara tarewa magana har magabanta ta sun shiga. Hajiyar Tafida ta goyo bayan yarta har tana cewa Tafida bai yi adalci ba ta ya ya wata can za ta fara tarewa ba mu ba, in ni ba zan tare ba amma ya zama dole ita Gimbiya ta fara tarewa. Shi kuma ya ce ba za ta taren ba, ya ɗauka ta gama fahimtarsa ashe ba haka ba ya cije ya yi taurin kai sai da magana ta kai wajen Nene ita ta tursaashi ya amince amma da sharaɗin sai dai mu tare ni da Gimbiya amma ba ita kaɗai ba. Ni dai Gimbiya ce ta kusa ja mini bala'i ina zaman zamana amma tun da Mimiaco ta ce za ta saka baki na san za ta yi mini iya ƙoƙarinta illai kuma ta yi domin sai ga Yallaɓai da kan shi ya zo mini da maganar. "Me kika ce ma Mimisco? Sai na gyara zama ina faɗin" Na fada mata ta roƙar mini kai. Ka yi mini alfarman tariyana sai bayan bikin ka sai na tare a tsanake." Kallona ya yi amma bai yi magana ba ganin haka yasa na gyara zama ina sake faɗa masa hujojina, bai wai ya gamsu ba ne kawai dai ya dakatar dani da cewa" Shike nan tun da kowa abin da ya ga dama ya ke yi. Ni dai Allah na gani ina iya bakin ƙoƙarin sauke nayin da ke kaina. Wacce acikin ku take ganin ina cutar da ita Allah ai yana sama yana kallo." Sai na ji wani iri a cikin zuciayata da maganaganunsa. "Ka yi haƙuri. Bari kawai sai na tare tun da haka kafi so." "Kar ki damu, ki yi na ki tsarin itama can ta tare a lokacin da ta so ba shike nan ba." Sai na kasa magana saboda a daƙune ya yi maganar kuma tun daga lokacin bai sake ɗaga maganar ba sai na fahimci Gimbiyar ta gama ɓata ma Yallaɓai rai kan mganar gidan nan ba ma ya son maganar kwata-kwata amma ni tun da na samu ya amince shike nan na kama kaina ban shiga abin da ba ruwana ba. Ya faɗa mini ya fara ba ma Rabi'a wasu kuɗi na lefe tun da farkon wata mai kama za ta koma can maiduguri sai an ɗaura aure kamar wasa na ce ya ba ni kwangilan hijabai da iners na Amarya ban ɗauka zai amince mun yi maganar yau washegari ya zo mini da maganar na yi list ɗin komai amma mu yi magana da Rabi'atun na ji size ɗin ta. Jin zan samu nawa a sama ya sa da gudu na amince, na neme ta a wayar Jidda muka yi magana ta tura mini size ɗin bra ɗin ta pant, sai na hijabi adadim yadin da take sawa duk ta tura mini da kalolin da take so.   Nan take na tura bangaren Hijabai, inears ɗin kuma na shirya da kaina Jidda ta rakani muka shiga kasuwa a rana ɗaya muka siyo komai. Na ci riba domin Yallaɓai bai yi mini ƙauron kuɗi ba isassu ya ba ni. Kuma da ya dawo ya ga kayan shi kan shi ya yaba. Sai da aka kawo hijaban sannan ya kwasa ya kai mata ta haɗa da sauran kayan, abin da aka yi daga ni sai Yallaɓai sai Rabi'atu sai ga magana na yawo a dangin Yallaɓai wai saboda neman gindin zama ni ce na haɗa ma Amarya lefe. Hauwa ta kyanƙyaa mini maganar ta ce a bakin Halima ta ji, sai ga shi na je barka gidan Jamila da ta haihu muka haɗu  da Anty Bahijja ta shaguɓa mini magana da cewa na dai na murna na sani duk abin ka yi shi za a yi maka. Ni ko na amsa da cewa haƙƙun kuma in ka shuka alheri ka ga alheri in sharri ne ma shi za ka gani. Na kuma ƙara mata da cewa a wannan zamanin ma abin ba ka yi ba shi ake yi maka ballanta ka yi. Abin da ke ba ni mamaki a ina maganar ta fita? Sannan ma ba za a faɗi gaskiya ba sai an ƙara da sharri. Ni su Hauwa kawai na faɗa ma gaskiyan magana sauran ban damu ba su cigaba da yaɗa duk abin da suka ga dama. Sai da na yi ma Yallaɓai magana na ce ko shi ya yi maganar da wani a can Gwammaja? Sai ya ce ya faɗa ma Nene ina jin haka na ce wata ƙila ita ce ta yi zencen da ya'yanta su kuma da man suna adawa suka ƙara ma labarin gishiri da maggi tun da ba sa son zaman lafiya. Tuni na fita batun su na kama harkan gabana fafutaka na samu yan kudaɗen da zan rage siyayyan tariyan sabon gida. Na samu na labule sauran cafet da zannuwan gado cikin riban siyayyan Amarya Yallaɓai sauran kuɗin da ke hannuna duka zan haɗe su waje ɗaya mu ga abin da Allah zai yi. Shi ya sa duk na faɗa ma su Ya Hamza za mu tare a sabon gida kuma akwai falo ɗaya da bedroom biyu ban san me zan saka ba. Ya Auwal ya ce na saka karikitai mana, ina laifi Ya Hamza kuma ya ce ni na ma samu duniya tun da har falo  huɗu Yallaɓai ya yi mini. To ya cika ladan shi ya yi kayan ɗakin mana ni dai na yi dariya ban yi magana ba. Na san ba domin hidiman auren da ya ɗauko ba Yallabai zai iya yi mini abin da ma ya fi haka in dai bai fi ƙarfin shi ba. Amma dai yanzu kan bam ma saka rai ba shi ya sa nake ta fafutakana na samu na rufa ma kaina asiri.  Har a raina ban saka rai da samun wasu kuɗi daga Yallaɓai ba, sai ga shi ya ba ni 200k ya ce ba yawa yara kuma 100k  na yi musu siyayyan kayan fitar biki na yi ta godiya domin ban yi tsammani ba. Atamfa kawai na siya mana sai leshi sauran kuɗin na adana, da gayya da Munnira ta yi mini maganar Anko na ce a fitar mana da shi, nan take ta fitar mana da kamfala mai ja da ruwan madara mai kyau, kuma ni na tura ta a group ɗin gidan su Yallaɓai na ce ankon bikin Yallaɓai, kalilan ne suka fito suka yi magana amma su Anty Bahijja gum, na san kuma na sha zagi da man kuma ina kan sha ne. Ai wannan ankon da na fidda kamar za su saka ni a cikin wuta. Yallaɓai ko da ya ji labari daɗi ya ji nan take ya sake tura mini 50k namu ni da yara har da Gimbiya da aka kawo na aiki Jidda ta kai mata sai ta dawo mini da shi da cewa Allah ya kyauta ita ba ta so, da ya dawo na faɗa masa tsaki kawai ya yi kawai ya ce na yi kyauta da shi. Ho ho ina shan zagi, Mimisco ta ce abin da na yi ya yi dai dai, hankalinta ya ɗauke ba ta yi tunanin haka ba, ba takura wanda ya ga dama ya yi wanda ba zai yi ba, ba takura. Su a cewarsu miye na fidda anko? Ai sai a jira a fidda a bikin Adnan na ce kowa da ranar auran shi saboda haka mu dai mun fidda wanda ya ga dama ya yi, wanda bai ga dama ba ya bar shi. Su Suwaiba ce kawai suka siya sai su Jawahir, Halima kuma Jamila ta kirani a waya tana faɗa mini irin zagin da ta zo gidanta tana yi mini wai ba na kishi ina ta murna har ina fidda anko. Kamar zan kirata na ja mata kunne sai na fasa na ce bari na jira bikin na ga ni in ta isa ta hana abin da Allah ya tsara. Ni dai da tawagata muna gefe muna shirin mu Ankon Gimbiya kuma Rahila na ba ma ta ɗinka har Amina ta siya za ta zo mini biki. Gimbiya ba ta gayyace ni tariya ba, ban kuma san za ta tare ba sai a bakin Hauwa na ke ji ta tare a sabon gida a ranar 31 ga watan December, na ce Allah ya sa rai ya mora, ba ta gaya mini ba ban kuma je ba shima uban gayyar bai sanar da ni ba. Hauwa dai ta je amma Munnira ba ta je ba, ita ta zo mini da labarin ina shan zagi wajen su Anty Bahijja na ce sai su yi ta yi, ni kam ba sa gabana. Sun ce wai tarewaar ma saboda ina da mugun nufi na ce sai daga baya to tun da na nuna haka shike nan sai mu zuba su gani. Na rasa me na tare musu suka ɗora mini karan tsana, ga Ɗan uwan su da zai yi aure ba su yi masa haka ba sai ni? Miye nawa saboda nima ban yi haukar da Gimbiya ke yi ba? To in dai haka ne sai dai su yi ta tsana ta amma ni ba zan yi wannan haukar ba a baya ma ban yi ba, ballatana yanzu da girma ya kamani ba ruwana. Su je su yi faɗa da Yallaɓai shi da ya ɗauko auren ni dai ba ruwana shirin auren sa baya gabana, a gefe ɗaya ina ta shirin tariyata da zan yi bayan auren Yallaɓai amma na ce sai ya gama cin amarcinsa sannan zan koma, ba zan iya juran ganin shi yana rawan ƙafa kan wata mace ce. Ita Gimbiya da ba ta gane ba ta kai kanta. Hausawa suka ce ai ƙazantar da baka gani ba sunanta tsabta amma ita kazantar ta je gani Allah kuma ya ba ta sa'a ina nan ina zaman zamana na san za ta yi nadaman abin da ta yi. ***** Biki ya ƙarato tun da mun shiga sabuwar shekaran 2023. Jidda na shirin komawa makaranta amma za ta je ta biya kuɗin makaranta da na hostel,  sai ta dawo tun da karatu bai kamkama ba sai bayan bikin babanta za ta koma, amma ko a yanzu ba zaman banza take yi ba kullum cikin cin kayan fulawa muke yi a gidan nan Cake kam har kyauta nake yi da shi. Donut kuma sai ya yi sati tun da shi ba ya lalacewa da wuri. Jidda ta gayyato kawarta Ummu Salma Hamza. Baby ce uwar gayya har da yan haddar su, su ba ruwansu murna kawai suke yi, a na saura sati biyu da wani abu biki Yallaɓai ya ce Rabi'atu a ranar ta koma Maiduguri na ce lalle za ta sha tafiya. Sai ya ke ce mini ai jirgi ta bi amma daga nan gida sati na sama za su tafi da  sauran kayan a mota. Ban ma tambaye shi ba shi da kan shi yake faɗa mini suma a jirgi za su je ɗaurin aure. A raina na ce ai kana da shi ko birnin sin ne za ka biya domin ku je, yana yi mini list ɗin da waɗanda za a je ɗaurin aure Alhajinmu na sahun gaba shi da Tafidan Rano. Sai shi da aminan shi, sai Ya Usman da a can za su haɗu sai Musbahu. "Kuma duk kai za ka biya kuɗin jirgin? Yana dariya ya ce" Kawun ki  ya ce zai ɗau nauyi" Na jinjina kai zai iya tun da shima ya ta da kai. Har anko ya siya ma Marwa kuma da kan shi ya zo ya karɓan mata da ya shigo garin. Tariq ne da man bai kamo su ba amma shima yana da rufin asirin shi. Yallaɓai bai faɗa mini ya yi kashe kashe kuɗi ba amma ni na san ya yi auran yar maiduguri ba wasa ba, ya faɗa mini an yi masa maganar kuɗin gyaran jiki na ce ai su can kamar al'ada ne. Amma shi fa bai damu ba murna kawai yake yi ba ya damuwa da kashe kuɗin. Ni ce ma na gaji na tambaye shi gidan da Gimbiya ta tashi ya zai yi da shi? Ya ce mini bai yi tunani ba yanzu an rufe shi in ya yi shawara zuwa gaba zai san yadda zai yi da shi. Wallahi har raina nake son gidana ba na son tashi, amma tunda cigaba ne ya samu ba ni da mafita amma ina son gidan nan kuma ina da tarihi mai ɗimbin yawa a cikin shi. Yallaɓai ya tsara tun da ban riga na tare ba a gidana za a yi taron biki ba Gwamnaja ko sabon gida ba. Ni da man ban ce kowa ya zo ba iya ni da yan uwana da wanda ya ga zai zo. Gimbiya da man ta ce ita ba biki za ta yi ba gidan matar de za ta zo, saboda haka mukkarabanta can za su sameta a sabon gida. Ni kuma ina gidana da jama'ata. Tun satin biki Yallaɓai ya fara ƙyallin amarci ni kuma sunan shi ya tashi daga Yallaɓai ya koma Ango da ko na ce Ango zai washe baki yana jin daɗi..komai na buƙata ba abin da Yallaɓai bai kawo ba. Ya ba ni kudin kunshi da gyaran kai ni da yara kuma mun yi, mai kunshi ta zo har gida ta yi mana na yi gayya domin kaf yan gidanmu ban ce na ɗauke ma kowa daga su har yaran su. Ana jibi biki Amina ta diro daga Kaduna. Faridan Tariq tazo aamma ita sai ana gobe biki. A kuma ranar su Yallaɓai suka daga maiduguri tun da in an ɗaura aure kuma za su juyo da amarya amma akwai sauran kayan da wasu za a kawo su ta mota. Jere kuma a ranar jumma'an da man daga nan Kano dangin su suka zo suka yi, ni ce na yi musu abincin tarba domin Gimbiya ta ce ba za ta yi ba Yallaɓai ya kirani ya ce na dafa na aika akai musu. To ba ma ni na dafa ba su Mubeena ne su kuma suka kai musu abincin can gidan shinkafa da miya da pepe chicken, sai kunin aya da zoɓo. Suka dawo suna faɗa mana irin dukiyar da aka sanya ma Amarya a shashenta da tsaruwan sabon gida. Da man Mubeena da Marwa ne suka je kai musu. Suka ce Gimbiya na bangarenta ana ta shewa ta shirya rashin mutumci na ce ya ƙare mata can ni ba ruwana da ita. Wannan abin da na yi haka Yallaɓai ya kirani yana ta yi mini godiya sai da na ji wani abu ya motsa a cikin tsokar ƙirjina. Me na yi masa? Komai shi ya kawo kawai nawa na ba da umarni an dafa kuma na aika da shi. Washegari 30 Jan ranar asabar ƙarfe sha daya na safe aka ɗaura auran Yallabai da Rabi'atu kuma sha sha ɗaya da mintina ni ya fara kira ya sanar mawa. "Alhamdulillah. Ma sha Allah Allah ya ba mu zaman lafiya ya kaɗe dukkan fitina." "Amin na gode Sadiyata. Na gode ƙwarai da girmamawan ki." Ya faɗa cikin farinciki ina jin ta hayaniya ta wayar sai ya kashe. Sai da na ji tahowar ƙwalla amma sai na yi saurin yar da ita. Na yi kwalliya tun da har mai kwalliya na kira na gayyaci su Maijidda da samira duk sun taho mini biki. Waina aka yi da shinkafa sai alele sai zoɓo ga ruwan gora da lemuka sai wanda ka zaɓa. Na diba abincin tun da aka gama na aika da shi Gwammaja. Su Suwaiba ne suka zo mini bioi sai su Jawahir, sai su Hauwa da yan gidanmu duk wanda bai zo ba yana gidan Gimbiya. Na ce duk abin ta dai ga shi ba a fasa ba. Sai ga Ummu Salma da mahaifiyarta sun zo mana biki kuma wallahi na ji daɗi har da su turarenka wuta ta kawo mini da mayukan gyaran jiki ba su kwana ba, bayam la'asar suka juya ta ce sai za mu koma sabon gida za su dawo in sha Allahu. Haka na yi taron biki lafiya aka gama lafiya mun shan ankuna mun sha hotuna kuma duk na tura ma Yallaɓai shima ya turo mini na su da su Kawu sai na shi shi da Amary ta sha lafaya yar maiduguri sak ba ta yi makeup ba fuskarta sak ta bayyana. Mimisco ta watsa hotunan a can group ɗin su na gida Musbahu ma dake can ya riƙa turowa ma su jin haushi suna gefe suna ji ba su da yadda za su yi. Tun kafin su Yallabai su ta so ya kirani ya faɗa mini, ya ce akwai ma wasu y'an uwa Rabi'atu da tun jiya suka taho. A yi abimci na tarban Amarya na ce ma to. Su Munnira na bar ma aikin,shinkafa suka dafa priderice, sai ferfesun nama da pepe chickenn da kuɗin hannuna na yi amfani ya ce in ya dawo zai ma yar mini. Ba a samu kunin aya ba amma an yi zoɓo sannan ga lemuka da ruwa Da aikawa na so na yi amma Yallaɓai ya kirani da kan shi ya ce na je gidan na tarban masa Amarya. "Sai na je? Ba ga Gimbiya da su Anty Bahijja? "Na san da su na ce ke. In kuma ba za ka yi mini ba ne sai na ji." Ina jin haka na ce masa ya yi haƙuri zan je, ina ma gidan Mimisco ta biyo ɗaukata ita ta yi tsire ne mai yawa na tarban Amarya nima da su Hauwa da Munnira da Farida muka fara yin gaba sauran kuma na ce su hawo adaidaita. Motata kuma Amina ta tuƙo yan gidanmu zuwa cam. Mun iske bangaren Gimbiya cike da su Halima itama bangaren Amaryam akwai yan uwata a ciki masu jiran tarban ta. Saboda dai a zauna lafiya sai Mimisco ta ce mu fara sauka a bangaren Gimbiya amma na san ita kanta ta yi nadama. Wulakanci suka yi mana, kamar ba su taɓa sanin mu ba, Naja ba ta gaisheni ba amma ta gaishe da uwarta Anty Bahijja ba ta gidan sai Anty Maimuna kamar ta kashe nu in tana da iko. Sai Gimbiyar da ƙawayenta sai yanuwanta daga can Rano. Haka suka yi mana kallon banza wai ni Halima ke yi ma habaicin a yi dai mu gani in tusa za ta hura wuta. Da Mimisco ta ce in Amarya ta zo a fita gabaɗaya a yi tarba shuru suka yi wallahi da ta iso ƙin fotiwa suka yi, Adnan ne ya ɗauko ta da ita da ƙawarta da kanwar mamanta daga filin jirgi, dagqani sai tawagata sai Mimisco muka yi tarban amarya. Mimisco ta yi tarba da Turaman zannuwa uku da 50k. Nima na yi da 20k da cimgam da su minti kuma wallahi sun ji daɗi, Rabi'atun tana cikin lafaya fara ne a rufe amma tana ganina sai da ta gane ni ta riƙe mini hannu. ."Barka da zuwa Amarya." Bi sa al'ada bangaren Gimbiya muka fara yi musu jagora. Kanwar mamanta ta tambaya an ce tana da abokan zama guda biyu. Mimisco ta nuna ni ta ce ni ce uwargida ban riga na tare ba ne amma na taho tarban Amarya sai Gimbiya. Wacce ba ta ma fito falon ba duk da ko Mimisco da kanta ta kirata amma wallahi ta kunya ta mu a gaban mutane abin gudun ban takaici.  Kanwar maman Rabi,a ta ɗan fahimci wani abu sai ta yi ta cewa a yi haƙuri da juna a zauna lafiya. Rabi'a ƙanwa ce a gare mu mu tsawarta mata in ta yi ba dai dai ba, haka nan muka kwashi sanyin jikin mu muka raka su bangaren Amarya. Ni na ɗauka a gidan Nene za tafara sauka Mimisco ta ce sai gobe za a kaita. Itama ranta ya ɓaci na ga ta kira Naja da Maimuna tana yi musu faɗa ni dai ba mu zauna ba, muna danƙama dangin Amarya abinci muka yi ta kan mu bayan na sanar da ita in tana bukatar wani abu ko ta kirani ko ta kira Yallaɓai za a kawo mata ta ce to. A daran ma Yallaɓai ba a gida ya kwana shi da su Kawu a hotel suka kwana sai washegari da safe na gan shi da suka shigo gidan. Yallaɓai ana ta baza baban riga yana washe baki da an kira shi Ango ya yi dariya har tana fidda sauti. *Janafty* /*TKGB3019* *EID MUBARAK FANMILY. ALLAH YA MAIMAITA MANA. SON SO. Da ma Amina ce da Faridan Tariq sai Marwa suka kwana a gidan. Yallaɓai yana ganin Amina ya washe baki yana ce mata ashe ta zo? Ita ko saboda ta kunna shi sai ta ce ai zuwa bikin nan ya zame mata dole. Ba kunya ya ce ya ji daɗin zuwanta. Megidanta ya tambaya da yara tace suna nan lafiya. Faridan Tariq kuma tsiya ta fara yi masa wai ya yi biyu ba zai haƙura ba sai ya haura uku. Yallaɓai na dariyan nishaɗi ya ce" Ta in da za ki gane ni gwarzo ne ba. Ba matsaroci irin mijin ki ba." Ya faɗa yana nuna Tariq wanda ke gefe yana magana a waya ne tun shigowarsu gidan Kawu Abba kuma muna gaisawa da shi ne. Shewa Farida ta yi kafin ta ce" In dai tsoro ne to Allah kar ya cire masa wannan tsoron har abada." "Muguwa kike Farida? In ji Yallaɓai yana dariya. "Sadiya kina jin kawarki ko! Ya faɗa yana kallona ina dariya na ce" Bar ta sai dai in bai gano wata yar faka faka kamar yadda ka gano ba." "Wallahi da man na ga a can yana bin yan mata gidan su Rabi'atu da kallo ko ya ga ni yana so ne? Ya faɗa yana dafa kafaɗan Tariq daidai lokacin da ya gama wayar. "Nima na lura da munafukin yana ta kallon wata yar fara nan ƙasa ƙasa." Kawu ya faɗa yana shafa sajen sa, Farida ta ce ba su gani da kyau ba tana kare ma mijinta. "To ke ina ruwan ki? Ba shi da bakin mgana ne? Yallaɓai ya faɗa yana dariya. Kawu ya ce ina zai yi magana ya san gaskiya. "Ko dai kai ne ka ƙyallo wata kana son ka yi mini kage Kawu? Tariq ya faɗa yana kallon Kawu shi kuma sai ya buɗe baki amma ya kasa mgana ni da Farida muka fashe da dariya. "Ina matarsa? Ina marwatun? To ta shirya wata ƙila za mu koma Maiduguri karshen shekara." "Tariq haka ka zama? Kawu ya faɗa yana rike baki. "Ƙarya na yi? Kai Tafida ba ka gan shi a ranar ɗaurin aure da muka je gaisuwan surukai yana tambayan sunan wata budurwa ba? "Kamar fa na gan shi." Yallaɓai ya faɗa yana danne dariya. Kawu ya jinjina kai kafin ya ce" Yaran nan abin tsoro ne. Mu ɗan bangaji juna ne lokacin da za mu shiga za ta fita ita kuma, sai ta ba ni haƙuri na ce ba komai amma saboda ku magulmata ne har kun hango wai ina tambayan sunan ta ba? "Ashe dai ka yi magana da ita." "Na yi sai ka hana ni Ubana." Kawu ya faɗa sannan ya kalleni yana faɗin" Surukata ni fa ban ga matata ba ban ga yayana ba." Ina dariya na ce suna ciki bari na yi mata mgana. Sai ya koma ya zauna saman kujeran falon yana faɗin" Yauwa Uwargida ran gida. Ke ce ke da gidan gabaɗaya. A ɓata miki rai mu yi tawaye wallahi " Ya faɗa yana hararan Yallaɓai kamar ya san da shi ake yi ya ɗaga sannu alaman sarander kafin ya ce" Ba ma mai ɓata mata. Ni kaina in na ɓata mata abin a yi mini hukunci ne " Kawai ba zato zan wuce na ji Yallaɓai ya rumgumeni ta baya ina ƙoƙarin ƙwace kaina ya sumbace ni a gefen fuska yana faɗin. "Na gode Abar ƙaunata. Ubangiji ya ruɓanya miki a ranar lahira." Farida da su Tariq suka amsa da Amin har da Kawu. "Gaskiya Sadiya tana da kawaici. Wallahi ni ba zan iya abin da ta yi ba har ga Allah. Tun auran Gimbiya na san ita jaruma ce to ga wannam ma. Gaskiya na jinjina mata." "Gaskiya abin a jinjina mata ne." In ji Tariq. "Shi ya sa nake ƙara jadaddaa ma Tafida cewa ya riƙe ta da kyau. Domin kaf cikin matansa ba mata kamar Sadiya. Domin a wannan zamanin ka samu macen da ka yi mata abubuwa da dama ta kauda kai, ta yi maka kara ta mutumta rigarka a idanuwan danginka da danginta ba abar tozartawa ba ce." "Gaskiya ne." Tariq ya sake faɗa, ni kunya ma suka kamani na ƙwace kaina ina faɗin" Ka bari mana Yallaɓai. "Wai ina miki godiya? Ya faɗa yana kallona da ka gan shi za ka san yana cikin farinciki. "Ni me na yi? Ai umarnin Allah ne ban isa na ja da hakan ba." "Duk da haka Na gode miki." Ya faɗa yana mai kallona tare da yi mini mirmishi. "Muna godiya Madam" Tariq ya faɗa sai na amsa shi da cewa" Kai dai kana tsoro ko? Ko ƙawata ta bake ko'ina ne? Na faɗa ina dariya, ita kuma Faridan tana cewa ita ba ruwanta ya yo mana ai ba kanta za ta zauna ba. "Ba wani cika baki. Ba ke kika hana shi ya ƙara ba." In ji Yallabai. "Kuma wallahi tsoron ta yake ji." In ji Kawu nan suka haɗe mata kai suna ta caccankanta da cewa kamar fitilar besfa Tariq dai ya ƙi kara aure sai ita kaɗai haba ai gwara dai ya ƙara ko ɗaya ne. Shi dai Tariq na gefe yana dariya. "To ku ba shi matar ya ƙara mana? Wallahi ko a jikina tun da ba kaina za ta zauna ba amma gaskiyan mgana ba zan iya abin da Sadiya ta yi ba wallahi." "Ka ji ba " Kawu ya faɗa yana dariya kafin ya cigaba da faɗin" Za ko mu ba shi mata mu ga karyan cika baki. Kai ka zo Rano na duba maka cikin dangi." "An gama Kawun mu." Tariq ya faɗa yana dariya. "Amma tare da shi za ku ƙara ko? Yallabai ya tare shi. "Me? "Auran mana." "Ah ni kam ai na tsufa, na fara furfurta matata Marwatu ta ishe ni." "Kai ma tsoron matar taka kake yi kenan? Farida ta faɗa, sai ya sosa keya kafin ya ce" Ki fahimta mana " Tariq ya shuri kafar Kawu yana faɗin"Ka iya addabata da maganar aure kai ma fa? Me ya hana ka ƙarawan? Ga tafida har ya yi ta uku? "Na ce muku matata ta isheni kar ku tsananta bincike" "Sai mun tsananta." In Tariq. "Ko ba ka da lafiya ne? Yallaɓai ya kwaɓo magana ni da Farida muka tafa muna sunne kai. "Ba shi da lafiya ya haifi su Abdallah munafuki lafiyan sa ƙalau" Tariq ya faɗa yana dariya da Kawu ya ga sun dame shi kawai sai ya kalle su kafin ya ce" Ba ni da karfin mazukutan da zan tara mata shike nan kuke son ji? Sai suka yi shuru suna kallon shi, ni da Farida saboda kunya sai muka kama hanyar barin falon saboda kunya. "Matata ma haƙuri take yi da ni. Ta ina zan jajiɓo wata? Kawu ya faɗa a maganarsa ba alamun wasa. "Wallahi ƙarya kake yi munafuki." Tariq da Yallabai suka haɗa baki wajen faɗa ni da Farida muka bar falon muna dariya in dai su ne in suka fara to sai kowa ya yi shuru ya bar su. Marwa na ce ma ta je mijinta na kira ta ce to da man ta tsaya yi ma su Abdallah wanka ne. Jidda na tura da kayan kari falon iyayenta sai ma ta dawo da shi ta ce sun ce a sun yi beakfast daga hotel ɗin da suka kwana, sun jima a gidan sama da awa sannan suka fita. Tariq da Kawu duk a ranar za su koma. Sun ce ma matan su su shirya kafin su dawo. Marwa ke son zuwa gida sai na ce ta yi sauri ta je ta dawo kafin su dawo. Amma ba ta tafi ba sai da suka ta ya ni muka gyara gidan sannan muka yi abincin rana Allah ya sa ba mu dafa da yawa ba tun da sai da na kira Yallaɓai a waya na yi masa maganar bangaren Amarya da danginta ya ce kar na damu Mimisco ta kira shi ta ce za ta yi direba zai kai sai na ce shike nan ta hutattashe ni. Farida na ta mamaki wai kuma sai na dafa na kai! Na ce me ye a ciki? Ita kam ta ce ba za ta iya ba. "Ba zan ta yar da hankalina balle na zama abin tattaunawa a dangi ba amma wallahi ba zan yi ba." Ina ta dariya ita ko tana shan wallahi. Shi ne har muka gangaro maganar Gimbiya ina ba ta labarin duk abubuwan da suka faru kafin auran nan. "Ba irin shawaran da ban ba ma Gimbiya ba ta ƙi jin maganata. Ni yanzu haka makiyayarta ce. Su Anty Bahijja ne masoyanta su ta rike suna zugata tana yi ma mijinta rashin kunya. Jiya fa a gaban dangin Rabi'a ta kunyata ni da Mimisco abin ba daɗi wallahi." "Ai ga shi nan ta bar ma kanta abun faɗa. Sai yi da ita ake da cewa mijinta zai ƙara aure tana ta hauka. Gaskiya abin da ta yi ba aji ba ne, ni kaina ba ta wani yi da ni tun ma kafin auranta da Tafida. Bayan auran su kuma ganin muna tare ba ta shigo ni ba." Ina dariya na ce" Ko yau kika je Allah ya sa ma ta kalle ki. Za ta ce kina murna tun da kika zo biki kika kwana a gidana." Farida ta ce to sai dai ta ce amma ita ina ruwanta? Tun kafin auran ta da Tafida ya ke aminin mijinta kuma ko shi yayan nata ai ya je ɗaurin auran "Allah na tuba su maza ina ruwan su? "Ai shi kan shi ya yi ta faɗa da ya ji labari kin san Tafidan bai sanar da shi ba sai Hajiya ce ta kira shi tana faɗa mai akan na gida ne ma. Kai tsaye ya kira shi ya ce in ta sake yi masa gaddama ya kora ta gida." Na riƙe baki ina faɗin" Lamarin har ya kai haka? To Allah ya kyauta." "Ni in na je zan yi mata faɗa ruwanta ne ta ji ko kar ta ji ta gyara " Ni dai da man ba komawa zan yi ba, zuwa la'asar suka barni ni kaɗai a gida har su Jidda sun tafi Gwammaja. Farida tun wajen biyun na rana ta wuce Gwammaja daga can za ta ƙarisa sabon gida. Amina da Marwa tare suka fita zuwa Ɗorayi, har Yumna da ita Baby suka tafi suka bar ni kaɗai. Zuwa can Yallaɓai ya kira ni ya ce yan uwan Rabi'a za su kawo ta nan gidana na ce sai sun zo. Na tashi na ɗan ƙara gyara gidan na saka turaren ƙamshi Ganin ba kowa a gidan har zan kira Munnira na ce ba za su dawo ba ne! Sai ga su ita da Hauwa sun shigo, na ce wayar dake hannuna su nake shirin kira na ce za a kawo mini amarya babu yan tawagata suna ta dariya. Sai gabda mangariba suka zo. Musbahu ne ya kawo su a motar Yallaɓai, daga Gwamnaja suke an kai ta wajen Nene da su Maman Farko. A can kuma sun fara kai ta shashen Gimbiya. Hauwa ke faɗa mana Mimisco ce ta yi mata fata fata shine da aka kai mata Amaryan ta fito ta karɓa. Ni ma sun kawo min ita suka kuma damƙata amana a hannuna a matsayina na babba na kuma riƙe hannunta na ce na karɓa Allah ya zaunar damu lafiya. Matar Baffan Rabi'atun na Kano da take zaune a gidan su ce ta kalle ni tana mai faɗin"Rabi'atu ƙarama ce a cikin ku don Allah a kula da ita. In ta kauce a karkato da ita, duk da ba kwa gida ɗaya tun da ke ce babba ki taya mu riƙe wannan Amanar don Allah" "In sha Allahu. Da yake ba daɗewa nima zan koma can ba matsala Allah ya ba mu zaman lafiya." Aka amsa da Amin gabaɗaya sannan aka yi addu'o'i sun kawo mini kayan su fulawa har da su dakuwa da nakiya sai tarurukan kamshi na ɗaki da na kaya sai atamfa da kololi sai filantai da kofuna har da kayan kwalliya kaya fa himiɗi ni na ce ma su rage kayan sun yi yawa suka ce ina tuwon girma a miyan shi nama. Sun kai ma surukanta da ɗayar abokiyar zaman nata. Muka karɓa su Munnira suka taya ni godiya nan na tsayar da su suka yi salla sannan suka tafi bayan sun sake yi mini sallama tun da sun ce suna ma yar da ita gida suma za su wuce. Baƙin Maiduguri kuma asuban cin gobe za su ɗau hanya A bakin Musbahu nake jin suma su Nene haka aka kai musu himilin kayan arziƙin nan ita da su Maman Farko, har da na yayyen miji. Ina ta mamaki daga baya kuma sai na cire shakku suna da al'adu sannan daga gani suna da hali da rufin asiri. Sannan kamar yadda suka ce ne Tuwon girma miyan shi nama shima Yallaɓai ya yi harkan girma in sun yi masa kara babu laifi a ciki. Ban bari su Muniira sun tafi ba na ce su tsaya mu raba kayan nan suka ce bai kamata ba na bari in Yallaɓai ya zo ya gani sannan sai da suka faɗa na yi wannan tunanin. Dare ya yi sosai shi ya sa ban kai su gida ba tun da Yallaɓai ya hana ni tukin dare tun da na faɗa rami wata rana na dawo daga ɗorayi ni da Baby da Yumna mota ta maƙale na kira Yallaɓai a waya. Ƙarshen ta dai nan motar ta kwana sai washegari aka ciro ta daga ramin. Mun yi waya da Marwa sun wuce. Farida ce ta ce mini tana Gwammaja can za ta kwana sai a safe za su ɗau hanya. Ni da kaina na faɗa mata kayan da dangin Rabi'atu suka kawo mini sai itama take ce mini. "Haka suka kai ma Gimbiya. Sannan nan ma bayan na su Nene har da na yayyen miji, har maza suna da kula. Waliyi kuma Baba Tafida na da shadda." Na riƙe baki ina faɗin" Haka Musbahu ya ce. Ma sha Allah. Allah ya saka da alheri ya ba mu zaman lafiya." Ta amsa da Amin ta cigaba da faɗin" Ai Gimbiyar da kyar ta fito fuskar nan ta kumbura saboda kuka na ce sakarya zauna ki kashe kanki saboda namiji. Shi kin ga bai fasa ba, ba kuma zai fasa ba ko da mutuwa za ki yi" "Wallahi.." Na faɗa ina jinjina kaina. "Da zai fasa tun boren da ta yi a farko da ya fasa ɗin." "Ai ba zai fasa ba wallahi. Ko don ya ga karshenta ma sai ya ce sai ya yi. Ai an ce da safe Mimisco ta je ta yi mata faɗa akan abin da ta yi jiya. Nene ma an ce ta kira ta a waya shi ne har yau ta ɗan saki jiki kaɗan." "Allah ya kyauta " Na faɗa ta amsa da Amin sannan muka katse wayar. Su Jidda sai wajejen goman dare Adanan ya dawo da su ina ta ma kiran wayarta ba ta ɗauka ba suna shigowa na fara masifa sun barni ni kaɗai a gida ta je sun yi zaman su. "Ki yi hakuri Umma. Ba mu samu me dawo da mu ba ne. Uncle Musbabu ne kuma Anty Mubeena ba lafiya ya tafi gida. Sai Uncle Adnan ne shima bai daɗe da dawowa ba." "Ba sai ki fito ki jagoranci ƙannen ki ku samu adaidaitasahu ku dawo gida ba? Sannan ina kika saka wayarki ina ta kira ba ki ɗauka ba? "Ban ji kiran ba Umma tana jaka " Hararanta na yi ta wuce tana dariya. Adnan da man bai shigo ba yana ajiye su ya juya. Baby ce ta fara mini surutu wai Amaryan Abba an kawo ta Gwammaja, kaf labarin abin da ya faru sai da ta ba ni Yumna saboda Gajiya a can ta fara barci ko da suka shigo tana saɓe a kafaɗan Jidda. Sai na ce ta shigar mini da ita ciki. Sai da duk ta gama surutunta sannan ta ce mini wai yunwa take ji. "To ni ce zan ta shi na dafa miki abin da za ki ci kenan uwata Maimuna? Na faɗa ina hararanta sai ta miƙe tana dariya ta wuce na rakata da tsaki. Kayan da man su Munnira suka kama mini na kai shi ɗayan bedroom ɗin da niyyar sai Yallabai ya gani sannan zan yi kasafin shi. Na ɗauka zai shigo yi mini sallama ne amma tun da na ga sha ɗaya ta yi na cire rai. Ni kaɗai a falo su Jidda sun gama duduman su sun shige ciki. Nima dole na tashi na kashe komai na shiga ciki. Tiolet na shiga na kama ruwa ina fitowa na ga wayata na haske kafin na ƙarisa wayar ta katse. Yallabai ne, ina shirin bin bayan kiran shi sai ga saƙon shi ya shigo. "Ku kwanta sai da Safe Sadiya ta. Tariq ya rako ni yanzu haka ma muna ƙofar gidan." Sai na ji jim ina sake bin saƙon sa da kallo, to mi ye na sai ya wani faɗa mini za a raka shi ɗakin Amarya. Duk da na so kar na ji zuciyata ta motsa sai da kishi ya taso mini. Shi ya hana ni mayar masa da amsa, ganin kamar zuciyata ta ɓaçi sai na juya na koma tiolet na ɗauro alwala na zo na yi shafa'i da wuturi na yi addu''o'ina da Allah ya cire mini damuwa a wannan daran ya sanyaya mini zuciya. Na yi ta maimaita LA'ILAHAILLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN. Sau arba'in har sai da na ji zuciyata ta yi sanyi. Ina idarwa na yi shirin barci Yumna da man tuni ta kai england. Gefenta na kwanta bayan na yi mana addu'an barci na shafe mu gabaɗaya wutar ɗakin na rage sannan na kunna suratul Maryam a wayana na ɗan rage ƙara na saka shi gefena na rumgume y'ata muka shige bargo. Da farko sheɗan ya fara hasko mini abubuwan da ba su kamata ba na yi ta ta'awizi a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai barci ya fara fizgata ban daɗe ba barci ya sace ni, ba ni na farka ba sai asuba na kuma ta shi wasai kamar ba ni ba. Na ɗauka zan ga Yallaɓai a ranar shima haka aka yi har dare ba shi ba wayarsa da Amina ta zo yi mini sallama ma nuna mata kayan sannan na diɓa mata kayan fulawan da kayan kwalliya na ce ta kai ma su Afra sai filet da kula guda ɗaya. Tun da gogan yana can yana cin amarci bai samu fitowa ba, aka sake kwana ba Yallaɓai ba wayarsa ni kuma ban neme sa ba na riƙe mutumcina amma in na ce zuciyata ba ta motsa ba wallahi na yi ƙarya daurewa kawai na ke yi. Amma ni kaina na san Yallaɓai ya samu chajiin Lambu ba zai yi wasa da ban ruwa ba.   Da na ga ba shi da niyyar zuwa ranar laraba da yamma Rahila da Ma'u da ke da tsohon ciki suka sake leƙoni da man ina da niyar kiran Hauwa ko Munnira ne su taya ni na raba kayan sai ga su Rahila. Su suka taya ni muka zauna na kasa shi, har Gwaggo sai da na dibar ma turaren wuta da kayan fulawa haka su Ya Aina. Hauwa da Munnira ma daidai da nawa na ɗibar mana saboda a sha'anina ko ya'nuwana albarka yadda suke tsaya mini. Kayan kwalliyan kuma suka ce na bar ma yara tunda ƴaran mata gare ni, Alhajinmu ma zaɓa masa yar kula mai kyau na ce zan kai masa Atamfar kuma suka ce na ɗinka tunda ni suka ba mawa. Su suka tafi da y'an gidanmu har na Gwaggo da Alhajinmu tun da Dorayi suka ce za su fara sauka kafin su wuce gidajen su, jin haka yasa na diɓi kayan fulawan da turare na ce Ma'u ta kai ma Baaba, duk da ta daɗe a can Yashe sai a satin nan ta dawo Kano. Sun fita ba daɗewa aka kira mangariba ina cikin yin salla na ji ana ta kiran wayata sai da na idar na duba na ga Yallaɓai ne sai bayan kwana biyu ya tuna damu. Jidda ma sai jiran shi take yi tana so ta komawa makaranta ranar lahadi. Ta ce mini ta kira shi bai ɗauka ba, na ce kar ta sake kiran shi ai ya san da komawar na ta. Sau biyu yana kirana ina salla sai da na idar ya sake kira wayar na hannuna na ƙi ɗauka haka kurum na ji ina jin haushin shi. Har kwana biyu muna gari ɗaya amma Yallaɓai bai neme ni ba! Gwara Gimbiya suna gida ɗaya na tabbata ba zai kwana su tashi ba ta gan shi ba. Sai da ya kara kira na huɗu sannan na ɗaga tana ma gabda katsewa. "Umma Sadiya." Ya faɗa yana ɗariya. Sai na ji zuciyata ta ƙuntata, wai Umma Sadiya sai yau na ji kamar da gayya ya faɗi sunan e mana na zama Umma shi ko yanzu ai sabuwa gare shi. "Uhm Ango." Na faɗa ina ƙoƙarin daidaita yanayina. "Uwargidata." Yallaɓai ya iya bariki da ban sani ba sai da ya auri Gimbiya na san ko lauya ya karanta sai haka in dai wajem lauya zence ne. "Ina yini? Ya amarci? Na faɗa ina ƙoƙarin sakin fuska kamar yana gabana. "Lafiya lau. Ya yarana  ya gidan? Sai kuma kika manta da ni Abar ƙaunata? Kamar na yi masa ashar sai kuma na fasa. Cije baki na yi kafin na ce" Ah na bar ka ne ka ci amarcinka. Ina Amarya? "Ga ta nan tana jin ki." Ya faɗa yana yar dariya. "Ayya ka gaisheta. Ina fatan ba ta yi baƙunta ba? "Ta yi fa, ta na ma kan yi, ga ta nan ma kwance sai rakin tsiya." Kasa magana na yi saboda na ma rasa me zan ce. Hakan bai sa Yallabai ya yi shuru ba ina jin sa yana dariya yana mata magana a ƙasa ƙasa wai ga ni ina son magana da ita ni yaushe muka yi haka da shi? Ina hamgame da baki ban rufe ba na ji muryanta tana yi mini Sallama. "Umma ina yini" Shike nan daga Anty na koma Umma, Yallaɓai ya gama da ni. Sai na danne na saki fuska kamar tana ganina na amsa mata gaisuwar ina tambayanta baƙunta ta yi mirmishi. "Ki saki jikin ki kin ji ko? Ai gidan ki ne" "Yaushe su Jidda za su zo mini? Ina riƙe baki na ce" Ba yanzu ba. Sau nan gaba Jidda ma ranar lahadi za ta koma makaranta in sha Allahu." Sai ta ce Allah ya nuna mana, sai ya karɓi wayar yana ce mini gwara dai na yi mata faɗa taki sakin jiki. "Ka yi haƙuri za ta saki na ɗan lokaci ne. Kuma ka san haka ke faruwa da kowacce amarya." "Wallahi na tuna kema haka kika yi ta mini. Da na matso kusa dake ki fara mini kuka kina faɗin don Allah kar ka taɓa ni ba na so." Ya ƙarishe faɗa yana kwaikwayin muryata wai, baƙinciki da takaici suka yi mini rufdugu kamar Yallaɓai ya ruɗe, ni na ma kasa mgana ina shirin ma na kashe wayata ne na ji yana faɗin" To itama haka take yi mini, in na kalleta ke kawai na ke tunawa a wancan zamanin Sadiya ta." "Uhm" To me zan ce? Ko na ce wani abu ba zai gane ba giyar amarci ne ke ɗiban sa. "Maganar komawar Jidda makaranta ranar lahadi ne." Na faɗa da ƙoƙarin na kaudar da maganarsa. "E wallahi na sha'afa sai da na ga kiranta jiya. Zan tura mata kudi ta yi siyayya kafin na shigo gidan.' Wato ba ma yanzu ba? Duniya sabuwa a wajen Yallaɓai. Ban ce masa yaushe zai zo ba? Na ce Allah ya kaimu. Yumna ya tambaya na ce masa tana falo na ɗauka ya kirani ne mu gaisa amma sai na ji yana faɗa mini kwana daya daga gidan Mimisco aka kawo musu abinci jiya ko da yau ma duk takeway ya yi musu. "Gaskiya. Ga Gimbiya a kusa ai ita ya kamata ta baku abinci har sai Rabi'atu ta yi bakwai." Sai ya yi shuru maimakon ya amsa maganata sai kawai ya ce" Ina neman alfarman daga gobe ki dan riƙa dafawa damu, sabon direba zai riƙa zuwa yana ɗauka." Na buɗe baki kamar yana ganina kafin na ce" Har sai an zo nan? Miye amfanin matarka dake gidan? "Ai na san da ita na kira ki Sadiya." "To me ya sa sai ni? Kana da tabbacin zan amsa alfarman taka ne? Sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Nima ban san me ya sa a komai nawa in ya taso ke nake son kira ba. In wata bujata ce wajen ki nake son fara zuwa. Ina da yaƙinin ko ba ki yi mini abin da na ke so ba in na faɗa miki kina bani mafita." Kalamansa suka kashe mini jiki da na kasa mgana. "Ita ta ce ba za ta yi ba Sadiya ba zan kuma taɓa matsa mata ba. Ke ce na ke da yaƙinin kina yi ma zaman auren mu kara na kuma san wannan karan ma ba za ki ƙi yi mini karan da kika saba ba." "Uhm" Na faɗa a ƙasan makoshi. "Ba zan takura ba, in kina ganin ba zai yuyu ba sai mu bar shi na cigaba da oder. Amma kamar bai kyautu ina da matan aure har biyu na riƙa siyan abinci a waje ba, sannan ita kanta ya za ta fassara lamarin? Sai na ga kuma gaskiya ya faɗa duk da wata zuciyar na ce mini na ce ya cigaba da siya amma na kasa. Sai da na tuna da kalaman Alhajinmu da ya ce  na yi ma abokan zamama alheri da ƙarfina da jikina da aljihuna. Ruwan su ne su ma yar da alheri da alheri ko su ma yar da alheri da sharri. Ni dai in dai na yi don Allah ladana na wajem Ubangiji kuma ya gani na sauke haƙƙi da nauyin zaman tare. Sai kawai na ce masa to shike nan da yaushe da yaushe za a riƙa zuwa karɓan abincin? Cikin murna ya ce" Ko sai ɗaya a rana is ok." "Shike nan Allah ya ba ni iko." "Na gode Abar ƙaunata. Allah ya kare mini ke." Na amsa da Amin a ƙasan maƙoshi, ban wani ja mgana ba muka yi sallama bayan ya ce mini za a kawo cefane a raina na ce tunda hidimar amarya ya tashi ba. A washegari aka kawo cefane har da su Nama da kaji, Sadi ne ya kawo sabon Direba Salisu Yallaɓai ya ɗauke shi ya koma direban kamfani. Sai Salisun ya kawo Sadin a matsayin madadin shi anan gida tun kafin ma bikin ga shi shima har an saba ya fara zama ɗan gida ya kai yara makaranta ya dawo da su sannan ya yi aike aike da kawo cefane. Ban faɗa ma kowa ba, ni na ke yi abincin Sadi na kai ma Yallaɓai da Amarya. Kuma a satin na je gidajen su Hauwa na kai musu sakon su amma ban amince na yi musu ma zencen ba, dalilina shi ne ba komai ne na aure ya ke buƙatar fallasa ba na bar ma cikina. Kuɗi Yallaɓai ya tura ma Jidda ita da direba suka tafi kasuwa ta yi siyayya. Kayan abinci da man daga gida take ɗiba kayan kwalama ne su bickit sai mayuka da su pad da kayan tea ta je ta siyo. Anan gida ta yi miyanta ta yi cincin  da Donut za ta tafi da shi, tun ina sa ran zuwan Yallaɓai har na cire ma raina, ganin ma daga wajen Amarya sai ya fara dawowa wajena kafin ya koma wajen Gimbiya shi ya saa na kira Surayya Dee ta aiko mini da haɗin kazar sababi na uwargida. +234 803 277 3332 Sai kuma a gida ina ta cin ganye da kayan marmari, ba domin wai na gyara ma Yallaɓai ba aa sai domin nima macece ina bukatar na gyara kaina. Ko da na ba ma arba'in baya ban tsufa ba akwai  ruwa a jikina har yanzu kuma ko gobe ai ruwa na mganin dauɗa nima asabuwar Yallabai ya aure ni muka gurji juna har ta kawo mu ga yau, saboda haka in ma ya manta mafari zai dawo mafarin na shi dolen shi dai. Ba Yallaɓai ya zo gidana ba sai ranar lahadi da safe ranar da ya cika sati ɗaya a ɗakin Amarya. Kun gan shi da wata bakar jallabiya ya yi kiɓa ya yi haske ga tumbi ya ƙara tasawa. Shima dalilin zuwan saboda tafiyar Jidda ne. Adnan ne zai ma yar da ita. Ita ta kira shi ta ce za ta tafi ba su yi sallama sai ga shi da jallabiya iriin ma fitowar na dole ne. Baby da Jidda suna ta murna ganinsa suka dafe shi suna ihun ga Abba ni ko kallon su ban yi ba. Yallaɓai ya ba ni mamaki muna gari ɗaya? A wayar ma sai ya ga dama yake kira ko kuma in ta shi buƙatar ya taso shi zai kira yana rage murya yana daidaiciyar mgana. Jidda na tafiya kunya ce ta hana shi shima ya wuce sai ya ɗan shigo ciki. Ni ko abun kari ban yi masa ta yi ba sai ya ce wai na ware shi kamar ba ɗan gida ba. "Na ɗauka ka ci kai da Amarya." "Ba mu tashi ba wayar Jidda ce ta tashe ni, na baro ta can tana barci.' Ko kunya Yallaɓai ke faɗa mini haka na tusa buredi a bakina na yi masa wani kallon renin wayau bai ma gani ba yana can yana mgana da Baby, Yumna kuma ta ishe mu da kiran sunan shi Abba sai ya amsa sai ta yi shuru sai kuma ta sake kiran shi. Tare da mu ya zauna ya karya yana hira da ya'yan shi, ni ina gamawa na shig ciki sai da zai wuce ya biyo ni yana yi mini sallama nan ne na ke nuna masa sauran kayan da dangin Rabi'atu suka kawo mini sannan na faɗa masa na yi kyauta da wasu. "Kar ki damu kayan ki ne fa. Ke suka kawo mawa kina da damar yin abin da kika ga dama da shi, yau ko da ma nawa ne tuni na yarje miki ki aiwatar da gabaci in dai ba na nan." Ban bari daɗin bakin shi ya yi tasiri a kaina ba na yi masa sallama. Har yana cewa ko rakiya babu? Na shige tiolet ina faɗin fitsari ya matse ni ya fita yana dariya shi kam shi ya san na zille ne kawai sai da na ji tashin motarsa sannan na fito ina ƙunƙuni ni kaɗai. A ranar na kira Alhajinmu na gaishe shi shi ne yake faɗa mini jiya Yallabai ya kawo masa Amarya ta gaishe shi Amarya ta kawo masa kyautar turare. Sai na saki baki ina jin Alhajinmu kawai ina mamakin Yallaɓai bayan daɗin baki yanzu har makirci duk ya iya. Kafin mu yi sallama Alhajinmu Jadadda mini yake yi na zauna lafiya da abokan zamana don Allah , na ce to ni kam ai ban isa na ƙara komawa gida na ce Yallaɓai ya yi mini wani abu ba sai Alhajinmu ya ce sharri na yi masa. Can da yamma sai ga kiran Yallaɓai da cewa anjuma zai kawo su Gimbiya gidana zai yi zama da mu. "Har sai ka tarkato su gidana ? Ka yi musu duk maganar da za ka yi acan ni in ka zo sai ka faɗa mini ba ni da matsala." Na faɗa masa haka har a cikin zuciyata Kawai sai ya fara mini faɗa wai ni zan faɗa masa ga yadda zai yi? "A'a yi hakuri daga shawara." "Riƙe shawaranki sai na ce ina ɓukata. Malama za mu zo anjuma nan sai ki hana ɗin." Daga haka ya katse wayarsa sai na bi wayar da kallo ina riƙe da baki da man tun lokacin da ya kira wayar na ji muryansa a sama ina kyautata zaton shi da Gimbiyarsa ne aka tafka wata tsyar shi ne zai sauka akaina ƙaramin tsaki na ja ina tura baki kamar yana ganina Ni da Baby mu ka share gida muka goge. Tare kuma muka yi girki cous-cous da kayan lambu mai hanta sai na yi mana kunin Aya da zoɓo muna gamawa na bar mata gyaran kitchen na ce kuma ta jera komaI a saman dining ni kuma na shiga wanka. Gayuna na ci da man ni duk wanda ya sanni ya sani da ban yarda da zama haka ban gyara kaina da jikina ba. Wata doguwar rigar amfata na saka sabuwa ban ma taɓa sata ba, ɗinkin A shafe ne ta yi min ɗas a jiki na kashe ɗaurina na maryam babangida. Da man na yi kitso Maman Nana ranar asabar ta zo ta yi mana ni da yara har da Jidda tun da ana gobe za ta koma ne. Na idar da sallar isha'i Saude ta kirani a waya na tsaya muna gaisawa. Har suka iso ma ban sani ba sai da Yallaɓai ya shigo ciki da kansa. Ji kawai na yi an ruƙumƙumeni ta baya tunda na ji  kansa a saman wuyana na san shi ne in Yumna ce kafafuwana take rumguma Sama sama na yi sallama da Saude ina ture Yallaɓai. "Ke ba ki iya zuwa tarban miji ba ko? Hararan shi na yi kafin na ce" Mijin wa? "Mijin Sadiya mana." Ina dariya na ce" Ai ni na bar ma su  Rabi'atu kai." "Wallahi ba ki isa ba" Ya faɗa kai tsaye har yana wani shan mur sai ya ba ni dariya. "Ahto ban yarda ban kuma lumta ba. In ke za ki iya haƙuri da ni, ni ba zan iya haƙuri da ke ba My Sady" Ya faɗa yana ƙara rumgumomi wannan karan ban kwabe niyarsa ba nima sai na rumgumeshi ƙamƙameni ya yi yana shinshinan ƙamshina. "I miss you" "Na yi kewar dumin jikin ki.' Ya sake faɗa yana shafa bayana zuwa ƙuguna. "Na yi kewar ban ruwa a nan." Hannun shi na ture ina faɗin" Wani kewa? Kai da ka samu sabon lambu ba irin nawa tsohon da ya ji tsatsa ba." Kallona ya yi cikin ido kafin ya ce" Haka nan na ke son shi, ai tun yana sabon shi ni na riƙa gurzan shi har ya yi tsatsan kin ga ko dole na so shi a haka" Na buɗe baki zan yi magana ya matse ni ya haɗe bakin mu sai da ya tsotse jan bakina tas sannan ya sake ni ni da shi gabaɗayanmu muna sauke numfashi. "I miss everthing about you Sadiya ta. Har da wannan jan bakin." Ya faɗa yana shafa bakin sa, baki na tura masa ina ƙunkƙuni "In kika sake tura mini baki wallahi zan turmushe ki sai na yi ɓarnan ruwa." Ai ina jin haka da gudu na fice ina jin sa yana ƙayƙyatan dariya. Sai da na daidaita kaina har ɗaurina ya kwance sai da na sake yin wani sannan na fita can falo, na iske Rabi'atu da su Baby, ta saka dogon hijabin ta har kasa sannan ba ta yi kwalliya ba amma da ka ganta fuskar nan ta yi fresh alamun dai ana shan amarci. Gimbiya ko na gefe ta kame a kan kujera mai zaman mutum ɗaya an ci gayu da mayafi a saman kafaɗa, Ammar na hannunta Amwar na gefenta Khalipa ne kawai tare da su Baby. Rabi'atu na ganina ta fara gaisheni cikin girmamawa na amsa ina tambayanta baƙunta ta sunkunyar da kai. Gimbiya ko ni da gidana ni ce na fara gaisheta ta amsa kamar ba ta so. Ban damu ba Yallaɓai na fitowa na ce na haɗa mana dinner mu fara da cin abinci. A gaban su ya ɗan rumgumo gefen kafaɗata ya sumbaceni kafin ya ce" Allah ya yi ma matata Sadiya albarlka" Na amsa da Amin Rabi'atu ta yi gaba ita da su Yumna Gimbiya ce a wajen amma ba ta amsa ba ina ganin ma tana hararan mu ko shi ne ya ja mini ban sani ba. Dukkanmu har da yaran muka zauma a dining muka ci abincin. Gimbiya kunin aya kawai ta sha ta tashi ta koma saman kujeran falon ta ce ita dai ta ƙoshi. Ni da Yallaɓai ne a wajen ke ta hira sai ni in na sako Rabi'a ciki ta ɗan yi mirmishi kuma ta ci abincin sosai ta sha kunin aya. Da ma ina cewa ta ci mana ta daina baƙunta nan ma ai gida ne. "Za ta ci fa, a can gida in kika aiko mana da abinci ta riƙa santin  cewa gaskiya Umma ta iya girki " Ya faɗa yana kwaikwayonta ni da shi muna ta dariya ita ko ta sunne kai, ina son ta tana da kunya sosai. Anan ne na ke masa taɗin ashe ya kai ta wajen Alhaji. "To ni da babana kuma? Ko sai na tambayi izini." Ina dariya na ce ba ruwana, mun tattauna mganar makaranta ya ce ai itama Rabi'atu cikin satin za ta shiga cikin makaranra ta yi risgtration suma sun koma sai ina zolayansa na ce shi zai kai ta? "A'a sati ɗaya ban je aiki ba gobe zan koma office. Amma ina tunanin na haɗa ta da Musbabu ko Adnan" Ni ko na ce sai dai Adnan din Musbahu ma ayyuka sun yi masa yawa ita ko tana gefe ta ce ai za ta iya fa ita kaɗai, sai ya ce bari dai ya gani in ba buJata sai ya haɗata da direba. Baby ta yi zencen nata makarantan ya ce gobe zai shiga makaranta ta zama cikin shiri za ta fara SS1. Ni ko na ce ga Yumna a saka mini ita a Ajin yara. "Mugunta ko? Wannan jarriyar ne zan kai makaranta to ni ba da ni za a yi haka ba " Ina dariya wai Yumna ce jaririya ina roƙon Yallabai ya kai ta bakinta ya buɗe da karatu ya ce sai  ta kai shekara huɗu zai saka ta a makaranta wai Baby ta riƙa koya mata a gida tun da na ga ya dage na yi shuru na san ba zai amince ba. Muna gama cin abincin na saka Baby ta gyara wajen sannan Yallaɓai ya ce duty ɗin ta ta tattara yara su koma can falon su a zauna lafiya ban da hayaniya har Ammar sai ta karɓe shi hannun Gimbiya ta tafi da shi can falon su, saboda ya ce kar a yi hayaniya shi ya sa suka yi shuru kamar ba su a gidan. Farko Yallaɓai ya buɗe taro da addu'a sannan ya yi nasihohin shi, da tunasarwan cewa dukkanmu ya aure mu ne domin yana son mu ne, Gimbiya da  ya aurota ni ban gaza ba haka itama Rabi'atun ya faɗa mata Gimbiya ba ta gaza ba. Duka matsayin mu ɗaya mu yi haƙuri mu zauna lafiya mu rike juna da Amana. Ya ce ni ce Babba ya san ina ƙokari to don Allah na ƙara Rabi'atu ƙarama ce a cikin mu, mu zauna da ita bisa gaskiya da Amana. Ya ba mu damar magana ni dai na ce in sha Allahu ba matsala daga bangarena Gimbiyar ma ta ce haka itama Rabi'antun ta ce haka sannan ya yi mata gargaɗin ko ba aure ba a shekaru mun girme mata ta yi mana biyayya in ya ji saɓanin haka zai saɓa mata ta ce hakan ba zai faru ba. "To na ji daɗin  haka. Maganar rabon kwana mu bar shi 2dys ɗin ne ko ya ya?   Sai na ce a bar shi a haka ɗin ai ya yi. Amma sai Gimbiya ta ce ba ta yarda ba sai dai a ma yar da shi kwana ɗaya. "Miye wani kwana ɗaya,? Da ba biyun kuke yi ke da Sadiya ba? "Da ka ce yanzu ko mun ƙaru gwara ɗayan saboda kar a cuci kowa." Gimbiya ta faɗa cikin gatsali, zai fara faɗa na dakatar da shi da cewa" Ba komai a yi kwana ɗayan ai duk ɗaya ne." Bai haƙura ba yana so ya dai yi magana na ce"Ka yi haƙuri a bar shi a haka don Allah" Jin haka yasa sai ya yi shuru. Zaman dai haka ya shi ba wani kwarjini, shi da ya kawo su  shi ya ɗauke su ya ma yar da su yafi awa da tafiya sannan ya dawo ni kuma ban tuhume shi a in da ya tsaya ba da kan shi yake faɗa mini Rabi'atu ke kuka wai tsoro ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, shine ya tsaya yana lallashinta da nuna mata ga Gimbiya a gidan kar ta ji tsoro. "Allah sarki. E kafin ta saba ko a gida ta ɗauko yarinyar da za ta ɗan rika taya ta kwana in baka gidan." "E mun yi wannan mganar to can gidan baffan nata ba yara fa, ni da man Baby na ce ta riƙa zuwa tana taya ta kwana kafin ta saba." Na ma kasa mgana ni shike nan ya'yana Yallaɓai yana raba su tsakanin matansa ba tare da izinina ba kala ban ce masa ba. Mu ka yi shirin kwanciya amma bai bar mu mun kwanta ba sai da ya yi ɓarnan ruwa har yana yi mini sambatun ya yi kewar gidan ruwan shi a raina na ce ka ji da shi dai da asuba ma ya koma ruwa. Da safe kuma tun safe ya yi shiri ya tafi office da yamma da ya dawo ya biyo ta nan gidan ya ɗauki wasu kaya sannan ya wuce can gidan yana ƙara jadadda mini na fara shirin tariya, a nan ne ma ya ke faɗa mini gidan da Gimbiya ta tashi Kawu ya bashi shawaran ya saka yan haya, ni dai na ce kar ya saka yan haya a gidana don Allah. "To a bar miki za ki rika zuwa partime kenan? Na ce masa e, saboda ina son gidan ya fita yana dariya wai duk abuna sai na tashi na koma sabon gida na samu cigaba ni ina noƙewa bai san yadda na ke son gidan nan ba ne ne har raina ni kaɗai ce fa anan can ko da gayyar kishiyoyi. Ganin ya matsa ya sa dole na fara shiri Baby dai ta koma makaranta an zama manya yanzu, ni dai labulayan na samu na siya sai cafet na falo biyu sauran kuma na tattara aka kai wanki na ce na yi amfani da su. Yallaɓai na yi ma maganar falo guda ɗaya ba kujeru ban saka rai ba ya ce na yi magana nawa za a yi saffa saffa gado da kujeru da gudu na je na tambayo, can ɗan kusa da gidanmu na Dorayi ne kafinta  ya ce 800k na zo na faɗa masa ya ce a yi mini ganin na samu sauƙi na ce a yi mini ƙaramin gado da wardrope na ɗayan bedroom ɗin sauran kuma kaya na kuma da su zan koma, na so tariyan ya zama bayan biki ko da wata ɗaya ne amma bai samu ba sai da ya kai wajen bayan biki da wajen wata biyu sannan saboda an ƙarisa aiki a shashena. Allah ya taimake ni bangarena na haɗe da bangaeen Yallabai ne. Na Rabi'atu ne da Gimbiya suke a haɗe. Ranar wata asabar ce na tare a sabon gida. Da man tun satin mota ta zo ta kwashe kayana zuwa can gidan y'an uwana suka taya ni muka gyara komai. Ban yi gayya ba daga ni sai su Munnira sai y'an gidanmu sai Marwa da ta zo, sai dangin Yallaɓai, mun dai yi girki saboda ma su zuwa. Bangarena babban bangarene kamar gidana sai dai nan na samu ƙaruwan falo da ɗakuna amma duk samfur ɗaya ne. Dining na so na yi sabo rashin kuɗi ya sa na dawo da tsoho. Amma zencen gaskiya gidan ya yi kyau Yallaɓai ya kashe kuɗi sosai masha Allah. Gimbiya tun da ta leko sau ɗaya ban ƙara ganin ta ba Rabi'atu kuma tana zuwa makaranta amma in dai ta dawo ta nan tare da mu da ita duk muka gyara ɗakuna na. Gaskiyan magana ba ruwanta ba ta da hayaniya ga kunya. Hatta su Munnira sai da suka yabe ta ga girmama na gaba da ita. Su Suwaiba da su Jamila duk sun zo mini amma ban ga su Anty Bahijja ba Mimisco ta zo ta ga waje ta saka albarka. Maƙotana na can anguwan da na shiga na yi musu sallama suma sun zo mini ganin gida sun saka albarka. Ga wargajejen fili, ga motata, ga na Gimbiya ga na Yallaɓai amma ko rabi ba a cika ba sannan ga maigadi, na yi hoton shashena na tura group ɗin gidanmu su Ya Hamza suka ga gaggani, suka saka albarka Amina na ta santi ta ce wallahi shashema duk ya fi kyau haka su Munnira suka ce, har fentina ya fi kyau sannan Yallaɓai ya siya mana manyan palasma guda biyu ni ɗaya Gimbiya ɗaya. Sai na yi amfani da na tsohon na falona a falon yara na tsohon  faalon Yallaɓai kuma na saka shi a falona na yanzun sabon kuma na saka shi a sabon falon Yallaɓai. Sai na raba abun falon farko na Yallaɓai ne na biyu kuma nawa na ukun na yara. Bedroon na farko na nawa ni da Yallaɓai na biyu kuma na yara sauran kuma sai na bar shi a na baki. Sannan kitchen ɗina na nan wargajaje har fridge dina da frizer anan na saka su disspanser ne kawai na saka a falon Yallaɓai. A satin kaf ban samu fita ba ana ta leƙo mini Allah ya sanya alheri, Baby da Yumna kamar an saka su a aljannah. Sun haɗe gida ɗaya da su Khalipa in sun dawo makaranta haka za su yi ta wasa a haraba. Rabi'atu kuma in dai tana gidan ba ta je makaranta ba tana tare da yaran Ni da ita zaman mu lafiya. Amma Gimbiya ta ware kanta gefe, ni da man ba ta yi da ni ballatana Rabi'atu yar baya baya. Ban san tsakanin ta da Yallaɓai ba tun da ba faɗa mini abin da ke faruwa a tsakaninsa yake yi ba. Ba ni na fara fita ba sai da aka shiga satin bikin Datti sannan muka fara zaryan zuwa Ɗorayi. *Janafty**TKGB3020* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732 Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰 Bikin Datti ya taho gadan-gadan mu mun ɗauka ma za a ɗaga bikin ne ganin ba a yi shirye-shiryen komai ba amma su Ya Hamza suka ce ba za a ɗaga ba tun da Datti ya kusa gama haɗa lefensa ta hannun Anty Laila a can  Abuja. Gidan da za su zauna kuma haya ya kama anan garin Kaduna kusa da ma'aikatansu. Ya Hamza ya turo da kuɗi Ya Abubakar da Ya Muntari sun yi ja gaba an yi fentin gidanmu ciki da bai. Sannan an gyara ɗakin Mama an yi waje da wasu kariki tai an rufe shi saboda nan Amarya za ta sauka sai sun yi sati sannan za su wuce Kaduna ita da angonta. Duk da can za a yi mata jere amma Kano za a fara kawo ta in ji Datti. Kuma y'an uwansa suka yi naam da haka mu da man namu kawai to ne da bi, saboda ƙurewar lokaci shi ya sa ba mu tara kuɗi masu yawa ba amma kowa ya yi abin da zai iya dai'dai ƙarfin sa mun damƙa ma Datti, amma ni da Amina mun ƙara masa da leshi guda biyu da atamfa aka ƙara cikin lefen shi. Gida da man su Ya Hamza sun ɗauke komai hatta da abincin da za a ci har a gama biki, balle kuma Alhajinmu na da hatsi a store sai abubuwa suka taho mana da sauƙi. Ana saura kwana huɗu aka kai lefe. Daga Abuja Laila suka kawo shi Zaria bayan duk mun gama ganiwashegari ni da Ya Murja da Ya Aina  da Inna Mariya muka tafi da su Kaduna muka haɗu da Amina a gidanta sannan direban mijinta ya tuƙamu zuwa gidan su Amaryan mai suna Badariya. Mun samu kyakyawan tarba sai godiya akwati bakwai muka kai kuma mun yi daidai abin da ya kamata wanda ba za a raina ba. Kuma ba su raina ba ɗin mun ci mun sha har da guzuri sannan sun bamu tuƙwaici muka ce ma ba za mu karɓa ba suka matsa mana. A gidan Amina muka kwana sai washegari har da ita da yara muka tattaro Kano gabaɗaya. Muna zuwa muka iske mutanen Zaria sun iso da mutanen Yashe gida ya fara ɗaukan harama. Dangin Mama na gandun albasa da man ni ce na sanar da su bikin suna ta faɗa domin ba a faɗa musu da wuri ba amma duk da haka sun haɗa kudaɗe sun aiko mana da shi, har gobe ba su yada wannan zumuncin ba. Jidda ta kira ni a waya har tana mini shagwaɓa wai na bar ta tazo bikin Uncle Datti na ce mata ni ba ruwana ta kira babanta, ita kanta ta san ɓata ma kanta lokaci ne ba zai bar ta ba, nan da nan ya ce ta zauna makaranta ta yi karatunta ga bikin Adnan nan in ya ga cancantar ta taho zai tura aje a ɗaukota. Ta kirani kamar ta yi kuka tana faɗa mini ina yi mata dariya. Sai a lokacin ma take faɗa mini har Rabi'atu ta saka ta yi ma baban na su magiya amma bai amince ba ni ta so na saka baki ni kuma na ce ba ruwana ta zauna ta yi karatunta kamar yadda ya ce ba a gama ba, ga bikin Adnan nan tsakaninsu sati uku ne su har sun fidda anko ma, mu dai na Datti ba mu fitar ba lokaci ya kure kowa na shi zai saka. Ban raba cinghan ɗin gayyata ba amma na sanar da baki. Kaf dangin Yallaɓai suna da labarin ƙanina zai yi aure. Balle ma na san Yallaɓai zai sanar a group ɗin su na gida nima kuma Munnira ta sanar a wanda muke ciki ta ce muna gayyatar kowa da kowa. Rabi'atu da Gimbiya ko kowacce har shashenta na kai mata kati na sanar da ita. Rabi'atu ce ke murna ita da Baby amma Gimbiya ce mini ta yi itama ranar tana da biki a Rano can ma za ta kwana. Ni kuma sai na ce in ta yi ma addu'a ya wadatar. Yallaɓai kuma ya ce mini zai je ɗaurin aure sannan Datti ya kirani ya ce na taya shi godiya 100k Yallaɓai ya tura mai da na yi masa godiya sai ya shafa kumatuna yana faɗin" Nima ai Datti ƙanina ne." Sai na jinjina masa kai amma duk da hakan dai na yi masa godiya. Ana gobe biki acan na kwana ni da Yumna kaya ma Baby ce da safe suka taho mini da shi ita da Rabi'atu. Na ga kara sosai su Munnira tun safe suka zo mini biki su Suwaiba duk sun leƙe min har Mimisco ta zo, ta ba ma Gwaggo 10k. Gimbiya dai da safe ta leƙo ko minti talatin ba ta yi ba ta ce mini za ta wuce Rano na yi mata godiya na rakata har waje. Da yake ɗaurin auren na safe ne zuwa la'asar tuni har yan ɗaurin aure tun kamo hanya da Amarya. Yallabai da Kawu sun je ɗaurin aure Tariq da dake can ya samu zuwa, mu kuma muna gida muna shirin tarban su, sun iso wajen biyar na yamma kai tsaye gida suka taho da ita muka tarbeta a ɗakin Mama aka sauke su ita da y'an uwanta da ƙawayenta abinci da komai ba su da matsala duk mun tanada. Marwa tun jiya itama ta na nan, Mubeena ce kawai ba ta zo mini biki ba tana gidansu ba ta da lafiya laulayi. Ta samu ciki sau biyu yana zubewa sai yanzu ta sake samu. Ma'u ma sai fama da tsohon ciki, riki riki ita abokan zamanta sun zo mata biki, ni kam da man Rabi'atu tana gidan nan tun safe sai dare sannan Yallaɓai ya zo ya ɗauketa suka koma gida. Ni da yara duk nan gida muka sake kwana. Dangi an haɗu gabaɗaya kamar kar a rabu yan gandun albasa ma sai ranar lahadi suka koma, mu kam sai litini sai da aka ci aka suɗe a ranar duk su Ya Hamza suka koma da matan su, a bikin ne muka ji an saka ranar auren Anti ɗiyar Ya Murja, Ya Balki ma ta ce mai son Firdausi an turo, ina tunanin bikin nan zai yi mana rudgudu, yanzu dai sai dai in Ma'u ta haihu za mu sake haɗuwa. Muka baro gida da Amarya sai Gwaggo da Baaba amma dangin ta sun kawo kayan fulawa da kololi, da sauran kayan al'ada kuma duk an rarraba mana har dangin Mama suma an ɗibar musu na su kason Ranar litini gidan ya watse. Ni kaina sai dare na koma gida ni da yara. Sadi ne ya je da mota ya ɗauko mu Rabi'atu har ranar lahadi ta dawo sai mangariba ta tafi, litini kuma da man tana da makaranta ko a hakan ma na gode. A bikin ma su Suwaiba na ji suna taɗin  su Anty Bahijja sun ce wai na haɗa kai da ƙaramar yarinya saboda na ƙuntata ma Gimbiya maganganu dai gasu nan ni ban biye musu ba, saboda in da sabo na saba da ire-iren mganganun su a kaina. Ni ban haɗa kai da Rabi'atu ba amma dai na san daga ita har Rabi'atu ina da zaune da su tsakani ga Allah, ita ce kawai yarinyar take darajani ta kuma ɗauke ni da ƙima fiye da yadda ita Gimbiyar ta ɗauke ni,sai a ga laifina don ina kula mai kulawa da ni? In fa tana gida a shashena take rabin yini na in ba ni ce na ce ta koma bangarenta ba, barin ma in Yallaɓai na ɗakinta sai na ce su je Baby ta ta ya ta ayyuka shine fa za ta tafi, amma in dai yana bangarena ne, ko bangaren Gimbiya sai dare sannan zai rakata ta koma shashenta ita da Baby dake tayata kwana nan take cin abincin ta yi koman ta ta zauna da yara su yi ta hira, barin ma Yumna da har ta saba da ita, da ta ganta za ta dafe mata. Sannan ko y'anuwanta wallahi suna darajani in dai suka zo gidan nan sai ta fara kawo su bangarena mun gaisa sannan su ke wucewa shashenta. Kuma in za su tafi za su yi mini sallama Gimbiya ko sai mu kwana uku ba mu ga juna ba muna gida cikin gida ɗaya kofar bangarenta ma yana rufe ne, ba ta neme ni ba ni ko ai ba zan lalace a kanta ba. Ni dai ba na gaba da ita in muka haɗu ko ba ta gaisheni ba zan gaisheta. Yallaɓai ba ya yini yake yi a gida ba ni kuma ba ni da halin ƙorafi balle na sanar da shi wasu abubuwan. Shi dai tun da bai taɓa jin an samu wata matsala bq sai hankalin shi ya kwanta. Ba ruwana da sanin tsakanin matan shi kamar yadda nima ba sab tsakanin mu ba. Na kama kaina gefe sai kuma na samu zaman lafiya. Kafin tafiyar su Datti Kaduna ya kawo mini Amarya har gida ta gaishe ni, ba ni ba kaf ɗin mu haka bi da ita gida gida ta gaishemu. Ranar sati na zagayowa suka wuce Kaduna. Ni kuma anan Gwammaja muka shiga hidimar bikin Adnan, abin da ya sa na shiga sha'anin Adnan nawa ne kamar Musbahu ne, mun yi anko gabaɗayanmu Yallaɓai ya siya mana har da su Jidda da ya amince za a ɗaukota ta yi biki ta koma. Adnan anan Kano zai ɗauko matarsa a can tarauni, shima ya haɗa lefensa na gani na faɗa da taimakon yanuwan shi, sai da bikin ya matso na ji labarin Adnan a gidan da Gimbiya ta tashi zai zauna Yallaɓai bai faɗa mini ba amma sai na yi masa uzuri ayyuka sun yi masa yawa wataƙila ya manta ne. Gida an ce an yi mass fenti tas ya dawo kamar sabo a bakin ni Hauwa na fara ji tace itama Mutaƙƙa ya faɗa mata sai da na koma gida a daran Yallaɓai na shashena na tambaye shi sai ya ce mini haka ne. Ganin ba shi da gida zai kama haya shi kuma tun da yana da gidajen sai kawai ya ce bari ya bashi guda ɗaya ya zauna. Na ce tabbas ya yi tunani Allah ya bar zumunci. A satin bikin aka kai lefe ni kaɗai na je Gimbiya ba ta je ba Rabi'atu tana makaranta su Anty Bahijja ne yan gaba gaba da yayarsa Ummu salma da su Nasara. Mu dai muna gefe ba mu yi baya ba kuma ba mu tusa kan mu ba.   Sai da muka haɗu a sha'anin bikin Adnan ne sannan Anty Maimuna ke yi mini Allah ya sanya alherin auran Datti na amsa amma sai da na yi musu tsiya da gayya  kuma Anty Bahijja na wajen na yi musu jirwaye mai kamar wanka na ce na tare kowa ya zo ya ga waje ya saka albarka ita da Anty Bahijja ban gan su ba. "Sai mun sake komawa? Ai ina ce in mutun ya yi zuwa ɗaya shike nan." In ji Anty Maimuna. "Shi na gani. Duk  ba gida ɗaya ba ne. Mun je lokacin tariyan Gimbiya kuma da auren Tafida da yarinyar nan" Haka Anty Bahijja ta faɗa Allah ya sa Rabi'atun ba ta nan da ta ji wani iri kamar ba ta san sunanta ba. "Bisa adalci kun je ma Gimbiya. Kun je domin Rabi'atu ni kuma sai ku kasa zuwa saboda ni? An ya kun yi adalci kuwa? Sai suka kasa mgana ganin na daure su da mgana. Anty Maimuna tace shike nan bayan bikin za su zo in sha Allah. Nene na wajen ta ce ba su kyauta ba ya kamata su je su saka albarka. Anty Bahijja ta yi muƙus ba ta yi magana ba ni ko na gama faɗin abin da ke raina na kama harkan gabana. Har su Anty Zabba sun taho sha'anin bikin Adnan, ranar jumma'a Sadi ya je ya ɗauko Jidda sai murna take yi a bikin nan na sha surutu kau da kai kawai na yi, ganin har da Dangin Rabi'atu da suka zo ni suka fara nema na kuma yi musu jagora falon Nene na sanar da ita iyayen Rabi'atu ne sannan ganin ta tana tare da su Jidda, in wani abu take ɓukata za ta zo ta ce mini Umma kaza shike nan aka saka mini ido a gidan bikin nan da nan su Anty Bahijja suka fara yawo da ni da cewa na haɗa kai da yar cikina saboda neman suna. Gimbiya kam tana gefe da man ko a sha'ani ba ma zama bangare ɗaya amma na san ba haka ta so ba, ta so ne wata ƙila itama Rabi'ar ta fi ma rashin ganin darajata hauahi take ji ta bakin Munnira ganin yarinyar ta ɗauke ni da daraja. Anty Zabba ta ce mun ba ta sha'awa na riƙe Rabi'atu ta gam bisa Amana hausawa sun ce kai ma ka gaida mai gaishe ka. Nan Gwammaja aka fara kawo Amarya bayan isha'i. Muka tarbeta gabaɗaya bayan an shisshiga da ita ko'ina. Dangin mahaifiyar Adnan ma suna gefe sai dai in an kira su amma dai an sauke ta a farko a shashen mahaifiyar Adnan ɗin ne. Misalin wajen tara na dare za su koma da ita sai aka ce mu yi mata rakiya gabaɗayanmu za mu je c a motocin gida tun da ga abokan Adnan nan duk da motocin su, har mun shiga mota sai na ga ban ga Rabi'atu ba, ban ga Jidda ba sai Baby ta ce mini ta bi motar Uncle Musbahu. Rabi'atun ne tana shashen Hajiya Iya tana salla in ji Jawaheer. Ni kuma jin haka sai na ce don Allah a ɗan jira ta. Kawai sai Anty Bahijja ta fara faɗa wai ba ta son sanabe in ta idar da salla ga motoci nan su kawo ta mana. Da man Mimisco ce ta ce a tafi gabaɗaya kar ace za a raba tafiyar. "Baƙuwa ce fa bai kamata mu tafi mu barta ba." Na faɗa har a cikin zuciyata." "Gaskiya ne kuma" In ji Anty Zabba. Gimbiya na cikin mota ita da Naja da Halima sai ga sun fito suna tambayan ba a si. "Uwar iya ce ta ce ba za a tafi ba sai an jira Amaryan ku." In ji Anty Maimuna. Kawai sai Gimbiya ta yamutsa fuska kafin ta ce" To sabon salo tusa a lasifika." "Ni fa ban ce ku tsaya jiran mu ba ku yi gaba za mu taho daga baya." Na faɗa ganin suna neman su taso mini har su Hauwa na ce su yi gaba cikin gida na koma sai ma muka haɗu da su a tsakar gida ita da Nafisan Kabir sun ɗauko kololin abinci Mimisco na bin bayan su. Sai take ce mini an manta ba a tafin musy da abinci ba, sai na ce Rabi'atu ta kawo kulan amma taƙi ba ni. Ko da muka fito sun tafi sai da muka jira Musbahu ya dawo ya ɗauke mu zuwa can gidan mun iske gida cike da dangin amarya da mu kanmu da man ashe akwai wasu masu ganin gidan Amarya da ba su zo nan Gwammaja ba.   Har ga Allah ban san abin da aka dafa ma yan kawo Amarya ba ni dai na ga Mimisco ta saka su Naja sun yi abinci ashe shinkafa ce jalop da kaza sai alele sai pepe chicken, amma ita Rabi'atu ta gani muna zaune a falo tare da su Hauwa ta zo gefena ta yi mini raɗa wai za ta ci alale amma tana jin kunyar tambaya sai na miƙe ina fadin bari na je na samo mata. Anty Zabba na gefe tace mene da ba za a faɗa a fili kowa ya ji ba. "Sirri ne" Na faɗa ina dariya ita kuma sai ta sunkuyar da kanta akwai kunya ita, Munnira na yi mata tsiyan ko Yallabai ne ya yi kira sai ta saka kanta cikin mayafi tana dariya. Nan da nan suka bushe mata da dariya. "Amaryan Tafidanmu akwai kunya." In ji Jamila kuma ba ganin ido ba tana da kunya, ba ta iya haɗa ido da wanda ya girmeta. Duk sai hankula ya dawo kan mu, Rabi'atu kanta na ƙasa sai mirmishi amma ba ta mgana. Hauwa na ce ma ga amana nan bar mata zan je na dawo sai ta ce ta karɓa ta dawo kusa da Rabi'atu tana faɗin" ƙyalesu  ƙanwarmu." Munnira ta daddage ta saki guɗa tana dariya, ni ma dariyan na ke yi, Gimbiya na gefe ita da Halima kamar su mutu saboda baƙin ciki. Amma ba halin mgana. Ciki na shiga in da dangin Amarya suke na ga suna ma zuba abincin wata cikin su na yi ma mgana ina son alele, sai ta ce mini haba bakomai ta samu filet ta saka mini guda huɗu sai da na ce ta rage za ta sanya mini nama na ce wallahi ta bar shi, wannan ɗin ma sha'awa ce wata ƙanwata ke so. "Allah sarki hala kwaɗayin ƙaramin ciki ne? Sai na yi dariya kafin na ce" Muna dai saka ran haka" Sai itama ta rakani da dariya sai da ta faɗa sai na yi jim a zuciyata ina tunanin ko dai an samu rabon ne? Amma kuma ban ga alamun ciki a wajen Rabi'atu ba da man na san ta akwai son alale ko ni in na yi har ajiyewa take yi. Itama tana yawan yin shi sai na cire tunanin haka a raina. Na fito falon dai dai ana cewa mu ta shi  mu tafi, tun da mun rako amarya gida fa kamar ba shi da yake sun yi jeren su da wuri Gimbiya kafa ɗaya kan ɗaya kamar falonta ta manta ya tashi daga falonta yanzu ya koma na wata. Kowa ya ganni da alele bai yi nagana ba sai Anty Maimuna tana tambaya ta ni kuma kai tsaye na ce" Rabi'atu ke so shi ya sa na samo mata.". Matar nan ba sai ta fara faɗa ba. "Miye haka? Ta son tana so tun a can ba ta yi magana ba sai da muka zo nan? "Renin wayau ne " In ji Halima. Anty Bahijja na can gefe tana waya tana gamawa itana ta zo aka faɗa mata ba ta bi ba a si bq sai ta ara ta yafa wai wulaƙanci mu zo da abinci daga gida amma mu koma muna roƙo saboda zubar da kai. Sai Rabi'atu ta ba ni tausayi sun ta so mata, cikin rawan murya ta ce" Ban san an yi alelen ba ne sai yanzu na gani raina ya biya. Ku yi haƙuri " Ta faɗa kamar ta fashe da kuka har ta ma fara hawaye. Sai Anty Maimuna ta fara faɗin"To daga mgana sai kuka? Ta faɗa cikin mele baki ni kasa ma mgana na yi, na ba ta alalan baiwar Allah ta ce na ma yar ba za ta ci ba. "Karɓi abin ki  me zai hana ki ci? Sai ta yi shuru. Suwaiba ta ce na samu leda na saka mata in mun je gida ta ci amma yadda aka taso mata yanzu za ta ji ya fita ranta ne. Sai na yi haka na koma na tambayo leda a ciki aka bani mai girma na juye mata alalan ina fitowa da karfi Anty Bahijja ta kira sunana gaban mutane har da waɗanda ba ahalin mu ba. Na amsa mata duk da na san kiran ba na arziƙi ba ne. "Ke wai ba za ki kama girman ki ba ne, ji yadda kike rawan jiki a ƙan ƙaramar yarinya? Sai na buɗe baki amma na ma kasa mgana. "Ai ba da ita ya kamata ki haɗa kai ba. Gimbiya ce dai da ke sai ita data ke ƙarama ta bi bayan ku amma abin da takaici ji yadda kika ma y'ar da kan ki baya a kan yar cikin ki, domin ko za ta girme ma Jidda da kaɗan ne." Na ji na muzanta amma ban bari ta fahimta ba sai na yi mirnishi kafin na ce" Ai kema kin ce sa'ar y'ata ce. Shi ya sa sai nake yi mata kallon ƙanwa. Kuma maganar na ma yar da kaina baya ba haka ba ne, ni ina daraja wanda ya san ina da daraja, da Rabi'atu da Gimbiya duk ɗaya suke a wajena. Tun da matan Yallaɓai ne, abin da za ki fahimta wanda ba ya yi da kai ba za ka takura shi sai ya yi da kai dole ba. Wanda kuma yake yi da kai kar ka kwabe masa ƙokarinsa ka ta ya sa nuna girman karramawan da ya yi maka." Sai na dakata ina kallon Anty Bahijja kafin na sake yin mirmishi na ce" In dai wannan shi ne kike kira na zubar da kaina na yarda ki yi ta ɗauka a hakan." Jamila ta kada baki ta ce" Ni ban ga abin ceceku ce a kan wannan maganar ba wallahi ina laifin yarinyar nan? Duk in da Sadiya ta yi tana biye da ita sai kawai ta wulakanta ta! Haba Anty Bahijja kuma ai ba komai za ku rika mgana ba " Jin kowa ya taso yana mgana yasa sai ta yi shuru. Baiwar Allah har sun saka ta kuka. Yumna ce ta je wajen ta hau jikinta ta ɗauketa shi ne ma ta daina sharan ƙwalla duk sai na ji ban ji daɗi ba. Gimbiya sai taɓe taben baki da fuska take yi amma ba ta yi magana ba, daga nan Gwamaja muka koma, Sadi na kira ya zo ya kai mu gida Yallaɓai na can tare da su Kawu, Gimbiya sai daga baya ta dawo kamar Direban Naja ne ya mai do ta. Na yi ta ba ma Rabi'atu haƙuri da ta ce ba za ta ci alalen ba. "Karɓi abin ki ki ci, haka suke kin san kowani dangi suna da na su matsalan. Sai kin kauda kai akan maganganun Anty Bahijja ko Anty Maimuna. Gimbiya kuma tana gaba dake so karki ɗauka da wani abu. A hankali za ki saba." Sannan ne ta karɓa, kuma na ga hankalinta tun da har kwana biyu da faruwan abun ban ji Yallaɓai ya yi magana sai na tabbatar ba ta faɗa masa ba. Jidda ranar laraba ta koma makaranta laraban ma da ta kai ni ce na saka baki da litini tun safe Yallaɓai ya ce ta koma na ce ya barta ta ɗan yi wanki da sauran shiri, sannan ya amince. Tun bayan bikin Adnan kuma sai na natsa a gida ba in da nake zuwa. Gimbiya tana fita shago ko wajen aiki Rabi'atu kuma makaranta ita da yara ni kaɗai ce ake bari ina gadin wannan wargajejen gidan. Su Inna Mariya da iyalan Gandun albasa sun zo mini ganin gida gabaɗayansu sun saka albarka kuma wallahi na ji daɗi. Suma dai nasihan su na yi haƙuri na zauna lafiya da abokan zamana domin samar ma da mijin mu kwanciyar hankali na ce In sha Allahu. Gimbiya ce ta fito da tsarin kwana ɗaya amma daga baya sai ta ce wai ba ta ganewa mu ma yar da shi kwana bibbiyu. Har falona ta zo ta sameni wata ranar asabar da safe. Baby da su Khalipa sun tafi Tahfez Yumna ce kawai ita kuma tana shashen Rabi'atu wajen Yallaɓai da safe da ya shigo mu gaisa ta dafe shi. Kallonta na yi cikin mamaki ni da man na san tun da na gan ta a falona na san banza ba ta kai zomo kasuwa. "Kwana ɗaya nan gaskiya bana gane mishi. Mu koma biyun kawai Maman Jidda." Ta sake faɗa sai na yi dariya kafin na ce" Ba matsala da man ni biyun na ce ke ce a baya kika ce mu ma yar da shi ɗaya." "Gaskiya mu dawo biyu nan ɗayan nan bana gane mishi." Sai da na sake murmusawa sannan na ce mata shike nan. "Za ki faɗa ma Baban su Khalipa ne? Yau ba Daddy su Yallaɓai an koma Baban su Khalipa na fahimci tunda ya yi auren nan ta daina kiran shi da Daddy sai da Baban su Khalipa." "Ina ruwan shi? In dai duka mun amince shi ba shi da matsala kin sani " Sai ta gyaɗa kafin ta miƙe tana faɗin" To sai ki faɗa ma ita Rabin" Sai na amsa mata da cewa zan faɗa mata har ta bar falona ina mamakinta. Ranar Yallaɓai sai Yamma ya fita, Rabi'atun da ta shigo na faɗa mata mun sauya tsari ta ce to, Yallaɓai kuma na manta ban faɗa masa da ya bar ɗakin Rabi'atu ɗaki na ya dawo ya yi kwana ɗaya ya koma ɗakin Gimbiya ya yi kwana ɗaya, ashe ita a tunanin na sanar da shi ni kuma na sha'afa saboda a ranar da yake wajena aka yi ma Ma'u C.S An ciro mata jariri ba rai ta zubar da jini sosai hankulan mu duk sun tashi mun ɗauka ma ba za ta yi rai ba. Ba gidan nake yini shi ya sa ban ma yar da kaina na sanar da shi ba. Ina gidan Ma'u tun da an dawo da ita gida. Baaba ke kwana da ita can muka kai dare tare da su Ya Aina Yallaɓai ya kira wayata ni na ɗauka zai yi mini faɗan na kai dare alhalin ya hana ni yin dare in dai na fita da mota. Sai na ji muryansa a kausashe sannan ina jin tashin mgana amma ban san ko ta wace ce ba. "Kin taho ne? Lokacin takwas ne da wani abu na dare kenan yau ya dawo gidan da wuri. "A"a zan dai ta so. Ban san ma lokaci ya tafi ba ka yi haƙuri " "Ki taho yanzu ina jiran ki" "Me ya faru? "In kin zo za ki ji " Ya faɗa sannan ya kwashe wayar ina jin haka na san ba lafiya, ina jin haka ban tsaya ba na yi musu sallama tare muka fita da su Ya Aina na ajiye su a juction na wuto gida. Abin da ya ba ni mamaki Yallaɓai na haraba yana jirana shi da Gimbiya kamar yaƙi. Ina gama parking ɗin motana  na fito Gimbiya ta taroni da cewa" Maman Jidda baki faɗa ma Baban su Khalipa mun sauya tsarin kwanaki kwana ba ne? "Ban faɗa masa ba me ya faru? Na faɗa ina kallonta saboda mamakin abin da ke faruwa. Yallabai na kalla kawai sai na ga ya juya zai shiga shashen Rabiatu Gimbiya ta bishi tana faɗin"Ai ka ji sai ka dawo bangarena sai gobe ne za ka koma mata." "Ba zan koma ba. Wannan tsarin ku ne ba nawa ba, nawa wanda na sani jiya na shiga ɗakin ki, yau da daddare na fita zan kwana a bangaren Rabi'atu." "Wallahi ba ka isa ba" Gimbiya ta faɗa cikin ɗaga murya ta juya zai shiga ta sha gaban shi har tana riƙe masa riga. Ni dai sai na yi tsaye kawai ina ganin ikon Allah. "Ba ni hanya in wuce." "Ba fa za ka koma shashenta ba sai gobe wallahi " "To ni kuma yau a nan zan kwana in kin isa ki hana ni " "Ni kuma wallahi in har ka kwana a ɗakin yarinyar nan Da haƙƙin kwana na Allah ya isa ban yafe ba" Gimbiya ta faɗa har tana shan wallahi. Shi kuma Yallaɓai ya fizge rigar shi ya tureta gefe ya shiga yana faɗin" Da sauki tun da ba tsine mini za ki yi ba " Ta kwashi kururuwa za ta bi shi ciki, shi ko yana shiga ya rufo ƙofar ta ciki sai ta fara bugu tana kiran sunan shi. "Yusuf ni za ka wulaƙanta? Wallahi in har dai ka kwana a ɗakin nan ban yafe maka ba tun da dai haƙkina ne yau " Kawai sai ta fashe da kuka ni wallabi ban saba ganin haka ba yasa sai jikina ya yi sanyin da na kasa motsi. Ganin maigadi na gefe yana kallon komai ita kuma tana ta kuka tana buga ƙofa tana Allah ya isa ba ta yafe ba. Yau ba Baban Khalipa Yusuf ne kai tsaye. Ƙarisawa na yi ina mai saɓe da yumna da ta fara barci a mota na ƙarisa wajen Gimbiya ina kiran sunanta amma ba ta ji na. "Haba don Allah wannan ba girman ki ba ne. Ki zo mu tafi bangaren ki." Amna bata saurareni ba, ganin kamar ba ta cikin hayyacinta yasa na saka hannu ɗaya na rike ta ina fadin" Megadi na ji fa kar ki jawo mana mutane don Allah." "Gwara ya ji. kowa ya ji cewa ba ya adalci. Maman Jidda yau fa yana dawowa shashen yarinyar nan ya tare na shiga na yi masa mgana a bangarena yake ya fara masifa shi bai san da haka ba. Ita kanta ta ce masa kin faɗa mata amma bai yarda ba ya kira ɗin ma ya tabbatar daga bakin ki amma ki duba fa a gabanki ya shige ciki saboda zalunci har yana rufe mini ƙofa saboda tozarci? Ta faɗa tana kuka, abin da Yallaɓai ya yi bai kyauta ba amma ita ta ja ma kanta, da ƙyar na lallasheta na ja ta bangarenta. In da Allah ya taimaka yara suna bangarena tare da Baby. Haka na zauna ina ba ma Gimbiya haƙuri amma tana ta kara shan wallahi in dai ya kwana a bangaren Rabi'atu ba ta yafe masa ba "Ki yi hakuri mana. Ki yi masa uziri tun da bai sani ba." "Da bai sani ba amma ai yanzu ya sani." Ta faɗa tana jan majina. "Ki yi haƙuri zuwa da safe sai mu yi magana gabaɗaya " "In yana so na saurare shi to ya fiti daga ɗakin yarinyar nan in kuma ya kwana wallahi ba zan saurari kowa ba " Jin haka yasa na ɗaga waya na kira Yallaɓai sai da ta katse na sake kira ya ɗaga ko mgana bai yi ba daga gani ranshi na ɓace ne. "Yallaɓai don Allah ka fito mu yi magana." "Ba zan fito ba. Ke ma ina mai ba ki shawara karki dame ni in ba haka ranki ya ɓaci." Ya faɗa a fusace. "Ka yi haƙuri ka fito don Allah." "Ta ce Allah ya isa to zan kwana Allah ya bi mata haƙƙin ta kamar yadda ta ce." "Ba za a yi haka ba. Ka dai yi haƙuri " Da ƙyar na samu ya anince zai fito mu yi magana da ya fiton ma cewa ya yi ba zai shiga bangaren Gimbiya ba jan shi na yi zuwa bangarena mu ka yi magana, ina ba ma Yallaɓai haƙuri yana yi mini tsawa. "Ina ruwan ki? Ki ƙyaleni kar ki dane ni " "Kar ka yi haka. Ka je ka kwana ba gobe ba ne shike nan! "Ba zan kwana ba " Ya katse ni, sannan ya cigaba da faɗin" Kina faɗa mini wai ta fada za a dawo kwana biyu ni kun faɗa mini ne? Kuma ma haka za ta zo tana mgana da ni gaban Rabi'atu tana yi mini rashin kunya? "Ka yi haƙuri ai ta fada mini laifina ne da ban faɗa maka ba" "To kema ki fita idanuwana. Ke ce ke aurana da za ki riƙa yanke hukunci a gidana ba tare da sanina ba? Ai ina jin haka sai na yi shuru, ya riƙa masifa har da rantsuwan  zai gyara bangaren shi da yanzu sai dai bishi can in ya ga dama ya kori kowa ya kwanta shi kaɗai. "Ka yi haƙuri ' Nawa kenan ban haƙuri, dakyar na samu ya amince zai kwana a ɗakin Gimbiya. "Ka yafe mata Allah ya isa da ta yi sheɗan ne " "Ke ina ruwanki da abin da zan yi mata? Sadiya kina mini abin ba na so wai nan gidan gidan ki ne ko gidana? Ina dariya na ce"Gidanmu dai Ranka ya daɗe " Sai da na saka shi dariya. Na samu dai ya shige ban san yadda suka ƙare ba, yara ma a bangarena suka kwana da safiyar Allah Gimbiya ta bugo mini waya tana sharban majina wai da na sani na ƙyale Yallaɓai ya yi kwanciyarsa a in da yake so. "Tun da ya shigo ya ke faɗa sai abin da ya manta bai faɗa mini ba. A falo ya kwana a kan kujera da asuba da na gaishe shi wai in na ma sake gaishe shi zai yi mini Allah ya isa." Ni gabaɗaya ma sun sakani a tsakiya. Yallabai tun bakwai na safe ya fita na kira shi a waya Yace kar na dame shi kamar ya san maganar Gimbiya ne ya taka mini burki. "Sadiya in dai ba ke kika auro mini Saudatu ba to ki fita a mganata da ita. Tsakanimmu ne ba ruwanki." "To ta zo tana mini ƙorafin kai ma kace in ta sake gaisheka Allah ya isa." Kawai sai ya yi tsaki kafin ya ce" in ta sake zuwa ki kore ta. Ki faɗa mata ni na ce ba ruwanki" Zan yi magana ya tare ni da cewa"Wallahi kema zan yi miki Allah ya isa in baki ƙyaleni ba haba." Ai ina jin haka na kama kaina daga ƙarshe ya ce in na sake yi masa magana wallahi zai yi mana yaji kuma in ya tafi ba zai dawo ba sai ya ga dama." "Abin har ya kai haka? To Allah ya huci zuciyarka " Ya ce Amin a fusace ya kashe wayarsa tun da na ji haka na cire kaina a ciki. Da Gimbiya ta dawo tana faɗa mini wai ita Baban su Khalifa zai wulakanta saboda wata zaunar da ita na yi na faɗa mata gaskiya da cewa ta yi haƙuri ta kauda kanta a kan Yallabai da Rabi'atu in ba haka ba wata rana komai zai iya faruwa. Ta koma gefe ta zama yar kallo amma ba ta ji ba. A cikin kwanakin ma sun sake wata rigima wai in ya shiga ɗakin Rabi'atu da daddaee zai yi mata sallama yana ɓata lokaci, rigima suka yi sosai Gimbiya ta sake masa Allah ya isa a kan haƙkinta shi kuma ya ce ya gaji ya ɗaga waya ya kira Nene ya faɗa mata. Sai da Nenen ta zo gidan sulhu ne na ji labari gabaɗaya ta taramu ta yi mana faɗa shi dai ta jadadda masa ya yi adalci ne. "Nene ina iya bakin ƙoƙarina. Saudatu ta cika ƙorafi sannan ba ta da hakuri tun da na yi auren nan ba ta bar mu mun zauna lafiya bq" Ita kuma tace me ya sa yake mata rashin adalci in yana da gaskiya ai ba za ta riƙa mgana ba. Rabi'atu dai shuru bata mgana, Yallaɓai ya rantse ya ƙara rantsewa  in  Gimbiya ta sake masa Allah ya isa zai dauƙi mummunan mataki a kanta Nene ta yi mata faɗa ta kuma sakata ta bashi haƙuri nima ta yi mini faɗa da nariƙa nuna ma Gimbiya wani kuskureta in ta yi wani abun "Ko ta nuna mata wannan zata ji ta ne? Wallahi Nene Sadiya ba ta taba ɗaga mini hankali da zan auero Saudatu  ba a wannan auren ma bata ɗaga mini ba. Amma kin ga wannan y'ar taki? Haƙuri na ne ya ƙare amma ta yi mini diɓar albarka ba adadi ina shanyewa." Nene dai ba ta bar gidan ba sai da ta yi musu sulhu. Kwana biyu kamar an samu canji. Rabi'atun ma na nuna mata ta riƙa bin Gimbiyae har ɗaki tana gaisheta. To na ga tana shiga, amma fa kishi Gimbiya take yi da ita kamar hauka kishin da take yi da ni ne ya koma kan Rabi'atu tun da ta ga Yallabai a gaban mu ma yana nuna mata rawan jiki. Rigima ta lafa sama da wata ɗaya kawai a wani dare muna kwance da Yallaɓai yake faɗa mini ya siya ma Rabi'atu mota saboda zirga-zirgan makaranta cikin satin nan za a kawo motar. Kamar zan yi masa mgana na ce ya manta da Gimbiya! Domin ko kwanaki ta yi masa mganar ya sauya mata mota ko ciko ne ya yi mata ta saida tata ta siya wata ya ce sai zuwa gaba. Kar yace ina baƙin ciki ya sa ban ce komai ba. Mun yi maagana da kwana biyu mota ta iso, Musbahu ya tuƙo ta ya kawo ta gidan Corolla ce Gimbiya ta ɗauka motarta ce har ta fara murna sai gogan ya ce na Rabi'atu ne. Gimbiya ta cika ta yi fam Rabi'atu ta yi ta santin mota tana murna nima dai na fito na gani na taya murna lafiya lau muka kwanta da mota amma ko da garin Allah ya waye gabaɗaya an yi ma gilashen motar nan rugu rugu. *TKGB3020A* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732 Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰 Ni dai har ga Allah bayan fitan Yallaɓai masallaci na ji kamar ƙaran fashewar abu amma sai ban mayar da kai ba tunani kunnuwa ba su jiyo mini sautin daidai ba. Ashe ko acikin gidan ne tun da Yallaɓai ya ce har ya fita sallar asuba motar na nan lafiya ba abin da ya same ta. Kenan bayan fitan shi ne koma me ya faru ya faru ɗin. "Innalillahi ko jifa aka yi ne daga waje Yallabai? Na faɗa ina riƙe baki saboda duk mun fito haraba har da su Baby gabaɗaya ana ta jimami amma Gimbiya ba ta ko buɗe ƙofar shashenta ba. "Wani jifa? Wannan aikin da gangan ne, da kuma niyya aka yi shi an fasa gilashin gaba an fasa gilashin window just imaging fa Sadiya" Ya faɗa yana zagaye motar yana dubawa, Rabi'atu ta yi tsaye da hijabi ta kasa magana wannan shi ne ta ga samu ta kuma ga rashi. "To waye ya yi wannan aikin? "Ko waye ma za mu sani yanzu." . Yallaɓai ya nufi wajen Megadi Yumna ce ke zillo daga hannuna ya ce kar na sauke ta saboda gilasan da ke watse a wajen. Mu dai muna tsaye da ni da Rabi'atu da Baby ina riƙe da Yumna muna jajantawa Baby faɗi take yi" Za a iya gyara motar Anty Rabi'atu kar ki damu." Nima ganin ta damu ina ta ce mata kar ta damu za a ce a saka wasu gilasan ba damuwa ba ce ni fa har tunani na yi ko tsawa ce sai na tuba ba damuna muke ba, amma ban taba kawo ma kaina Gimbiya ce ta aikata wannan ɗanyen hukuncin ba. Muna nan tsaye sai gani kawai muka yi Yallaɓai ya dawo daga wajen megadi a fusace kamar zaki ya zo ya wuce mu ina ts kiran shi amma bai saurareni ba. Kofar shashen Gimbiya ya fara bugawa kamar mahaukaci yana kiran sunanta da tsawa abin da ban taɓa ji ba, ina jin ko ita Rabi'atu ba ta taɓa jin muryan sa cikin fushi haka ba. "Saudatu!. Saudatu! Saudatu!" Haka yake kiranta lokaci ɗaya yana buga ƙofa kamar zai balla na ruɗe na biyo shi ina faɗin" Subhanallah lafiya Yallaɓai? Ko kallo na bai yi ba sai ma ya matsa baya kaɗan ya fara tokarin ƙofar da ƙafarsa. "Haba Yallaɓai wai miye haka ne? Na faɗa ina ƙoƙarin rike shi ya fizge jikinshi yana ce mini na matsa baya. "Ɓalla ƙofar kuma za ka yi? "E ina ruwan ki? In ma na ɓalla ma ba gidana ba ne? Hake ya ce mini a tsawa ce sai na yi shuru kawai na kasa mgana ina kallon shi. "Ki koma baya in ba za ki yi zama yar kallo ki koma bangaren ki " Na sake yunƙurin mgana ya kira sunana a tsawace kafin ya ce" Kar ki sake yi mini mgana." Tsawa ya yi mini sai da na yi baya Yunma ta tsorata ta fashe da kuka ai sai na yi gefe ina maimaita innalilllahi a ƙasan raina ina tunanin meke faruwa ne?  Ganin ni kaina an yi mini tsawa ya sa Rabi'atu ma ba ta matso kusa ba, balle Baby da ta maƙale a bayanta jikinta na rawa. Duk wannan bugun da hayaniyar Gimbiya na ji ba ta buɗe ba, har ta window ya je yana kiran sunanta sai da ta ga dama sannan ta buɗe bayan har handle ɗin kofar sai da Yallaɓai ya kar ya shi wajen jan shi, ta fito daga ita sai rigar barci doguwa a cikinta da hula mai raga raga ta fa gan mu duk tsaye ga uban gayya na huci kamar zaki amma duk ba ta sha jinin jikinta ba. "Topha!  Lafiya na ga an taru a ƙofar bangarena? Ta fada tana mai kallon mu ɗaya bayan ɗaya. Mamaki ya hana ni magana shi kuma Yallaɓai ban san dalilin ba ina tunanin shima dai mamakin ne sai cije baki yake yi alamun yana ƙoƙarin sarrafa ɓacin ran shi ganin haka yasa na yi saurin tare ta da cewa. "Ke yanzu duk ba ki ji abin da ke faruwa ba? "Ban ji ba me ya faru? Ta faɗa cikin halin ko in kula. Motar na nuna mata ina faɗin" Motar Rabi'atu ne muka wayi gari an yi mata haka' Sai ta wani kama baki kamar na mamaki da firgici kafin ta ce" Subhanallah garin ya ya haka ya faru? "Shi ne ake son sani yanzu" Na bata amsa sai na ga ta wata dariya ta ce" Ikon Allah! To ko aljanu ne suka yi haka? "Aljanu ko ke da kanki? Yallabai ya katse mata mgana a fusace, sai na kalle shi jin abin da yace ita ko sai ta ware ido kafin ta ce" Ni kuma? "E ke" Ya faɗa yana takawa kusa da ita ƙokarin kare rabin jikinta take yi da ƙofar ya saka ƙafa ya tokari ƙofar ta buɗe sai ta yi baya da sauri tana faɗin" Ban gane ba daga ganin abu sai kawai ka ce ni ce na yi? Ina ruwana? Ta faɗa cikin rashin kunyar da ta saba da shi a kwana biyun nan. "Saboda ke ɗin ce mai muguwar zuciya a gidan na." Ya faɗa yana mai kallonta kamar ya jawota ya fara dukanta a yanayin shi. "Oho dai kai ne mai mugun zuciya wallahi. Ban da rashin adalci tun yaushe na ke bin ka da ka saiya mini mota amma kaƙi shi ne ko kunya za ka siyo ma matarka mota ni ba ka siya mini ba! Hakan da ka yi adalci ne? Wallahi kai ne ba ka da zuciya mai kyau kuma duk cutata da ka yi saboda wannan yarinya Allah na sama." "Bum!!" Ya saka hannu ya buge mata baki kafin ta karisa magana sai da na ji tsoro ganin abin da ban taɓa gani ba. Yallaɓai na kai hannun shi jikin mace. "Tun kafin Megadi ya tabbatar mini da ke ce da man naa ji a zuciya ke ce kika yi haka? Ni za ki yi ma asara saboda shegen kishin ki na banza da wofi? "Wallshi da man na ce sai dai kowa ya rasa" Ta sake faɗa har tana rantsuwa sai a lokacin na gama fahimtar komai wato dai Gimbiya ce ta yi wannan ta'asan. "Ba ka yi adalci ba sai ka siyo biyu in kana so a zauna lafiya ko ka fara siya mini bayan an kwana biyu sai ka siya mata amma ko kunya ba ka ji ba ka je ita ka siya mata ni kuma ko oho? Wallahi ba ka isa ba in dai ina gani ba wanda ya isa ya yi mini rashin adalci ban yi magana ba." "An yi miki rashin adalci ki yi duk abin da za ki yi" Ya faɗa a fusace kafin ya ce" Kuma wallshi ki sani ba ni kika yi ma asara ma kanki kika yi mawa. Sai kin biya duk abin da kika bannatar kin ji ma na rantse." "Wallahi ba zan biya ba. Rashin adalcin ka ya jawo maka asara " . Ta faɗa har tana rikr kugu ina so na shiga na yi magana amma ina tsoron kar ya haɗa da ni amma hayaniyarsu ta fara yawa ga su Khalipa har sun fito suna tsaye sannan ita bakin ta yaƙi yin shuru shima haka tana fada yana faɗa. Ganin haka yasa na ce ma Baby ta tattara yaran su koma shashena. Rabiatu ma da na duk ta tsorata na ce su shige ciki sai da na samu sun shige ciki sannan na koma wajen su Gimbiya abin har ta kai ga tana kiran shi Azzalumi kuma sai Allah ya kama shi. "Alhamdulillah na ji ni azzalumi kuma kin ga ba za ki cigaba da zama da mai zalunci ba. Zo ki fice mini daga gidana Saudatu wallahi nima na gaji da zama dake." Jin haka yasa na yi zaraf na shige tsakaninsu ina faɗin" Haba Yallaɓai." "Ta zo ta fice mini dags gida na ce ko! Ya sake maimaitawa, ita kuma jin haka sai jikinta ya yi sanyi ta fashe da kuka. "Ni yau kake kora a gidan ka Yusuf? "Na kore ki gidan ki ne ko gidana? Wallahi na gaji dake da halin ki, da man tun tuni ya da ce na kore ki, kin fara yi mini asaran dukiya wata rana rai za ki kai ma hari." "Duk abin da ya faru kai ne sila. Domin da ka yi adalci da haka ba ta faru ba maimakon ka yi nadama amma sai ka kore ni? Ni za ka tozarta a kan wancan yarinyar? "Ba sunanta yarinya ba. Sunan ta Rabi'atu ce matatace kamar yadda kike matata. " Gimbiya ta sake sakin kuka kafin ta ce" Saboda ita yau kake kora ta? "E saboda ita ne domin ita ba mahaukaciya ba ce kamar ke" Sai Gimbiya ta fara kururuwa har tana zama a kasa hannu a saman kai tana faɗin Yallabai ya zageta ya ce mata mahaukaciya. "E na faɗa in ba mahaukaciya ba wacece za ta yi abin da kike yi? Ita yarinyar da kike kishi a kanta wallahi na tabbata ba za ta yi haukan da kike yi ba. To tun da ni ba ki bani farimciki nima kuma ima zaluntarki gwara ki zo ki tafi garin ku na gaji" A fusace ta mike tana faɗin" Nima wallahi na gaji " "Ni na fara gajiya" Yallabai ya faɗa har yana sakin tsaki, ina so na yi magana sun hanani da wannan ya dire wannan zai ɗauka. "Sai ka sake ni domin na je ma da iyayema da shaida." Gimbiya ta faɗa tana tsiyayan hawaye duk sai jikina ya yi sanyi. "Sakin kike bukata? Yallaɓai ya faɗa idanuwansa sun yi jajir. "E ina buƙatar shaida." "Fine. Zan ba ki shaida." Ya faɗa yana mai juyawa da gudu na fito na sha gaban shi ina kiran sunan shi amma ya raɓa ni ta gefe ya wuce na riƙe bayan rigan shi ina faɗin. "Don Girman Allah Yallaɓai kar ka yanke hukumci cikin fushi." Fizge rigan shi ya yi kawai ya shige bangaren Rabi'atu na taho ya banko mini kofa a fuskata sai na yi sororo, ba. Buga masa ganin mun riga mun bar ma Megadi abin faɗa duk da bai fito ba amma yana cikin ɗakin sa yana jiyo duk hayaniyar dake faruwa. Shashen Gimbiya na koma tana cikin bedroom ɗin ta, tana haɗa kaya a cikin babban akwatinta tana kuka. Duk ta zubo su daga cikin wardrope ɗin ta. Hankalina ya tashi na fara tare ta ina hanata saka kayan a cikin akwatin da ta ɗauko sai na karɓe ina faɗin" Haba don Allah miye haka kile yi? "Ba ji ji me ya ce ba ne? Ya ce na zo na bar masa gida tun da ba na bashi farimciki." . Ta faɗatana mai ƙara fashewa da kuka. Duk taƙamar cikin mintina har ta fita kamaninta sai na dafa kafaɗanta ina lallashinta. "Ki yi hakuri kema bacin rai ne shima haka in zuciya ta yi sanyi za a daidai ta." "A'a Maman Jidda ki bari kawai na tafi. Sakina fa yaje ya rubuto ya kawo mini zaman me zan yi? "Ba zai sake ki ba. Ba aure ki don ya sake ki ban" Na faɗa ina mai kara dafata, cikin kuka ta ce" Ya ce fa da kanshi ya gaji Maman Jidda. Ni wai yau Yusuf ke yi ma wulaƙanci saboda wata ƙaramar yarinya? "Laifin ki ne me ya sa kika fasa motar nan? Duk da shima bai kyauta ba amma da kin yi shuru kin jira ki ga iya gudub ruwan shi. Sannan ai shi mijin ku ne shugaban ki, bai kamata yana faɗa kina faɗa ba. Duka ranku ya baci shi ya sa kuka yayyaba ma juna mganganu." Cikin hawaye ta kalleni kafin ta ce" Na kasa haƙuri a nan wajen na ke jin ƙuna in na ga Yallaɓai na fifita wannan yarinyar a kaina? Na kasa hakuri ne" Ta faɗa tana mai nuna mini saitin zuciyarta sai kuma kawai ta yi zaman dirsham a ƙasa tana cigaba da gurzan kuka. Sai na bi ta nima na zauna a gefenta ina ɗan bubbuga kafaɗanta alamun lallashi. "Shi ya sa na sha ce miki Gimbiya ki yi haƙuri domin duk abin da haƙuri zai ba ka rashin sa ba zai ba ka ba. Da kin yi hakuri don Allah duk wannan abin da ya faru zai zo ya faru? Sai ta yi shuru ta kasa mgana sai kuka ni kuma sai na cigaba da faɗin" Kana gani za a cuceka ayi maka abu na rashin adalci amma sai ka yi shuru ka yi haƙuri ba wai don an fi karfin ka ba sai domin hakurin shi ya fi alheri. Tashin hankali ba shi da daɗi da a ce kin same shi ta lalaba kin tambaye shi Baban Jidda ni fa tawa motar sai yau she za ta zo? Duk amsar da zai wuce kema na ki na hanya ba ai yana da ilimi ya kuma san abin da yake yi. Ba ina kare masa ba ne amma ina so na faɗa miki gaskiya. Yallaɓai na kamanta adalci, nu ya faɗa mini zai siya ma Rabi'atu mota saboda makarantar ta, duk da bai yi mini bayani ba na san ya fara siya mata ne saboda ita ke ɓukata yanzu. Ke kuwa kina da shi canji kike so nima haka shi ya sa ya fara siya mata kafin ke daga baya." Sai na ɗan dakata ina kallonta ganin ta natsu tana saurarena amma ba ta shassheƙan kuka ba. "Da kin yi abin cikin lalaba da duk wannan abubuwan ba su faru ba. Ga shi yanzu zuciya ta ɗebe ki kin aikata abu. Ran ki ya ɓaci shima na shi ya ɓaci fisalillahi ina daɗin shi.? Cikin jan majina ta ce" na kasa hakurin ne. Wallahi na kasa." Ta fada hawaye suna mata ambaliya sannan ta sake kecewa da kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Duk surutun da na gama yi a banza domin Gimbiya ta miƙe ta cigaba da haɗa kayanta ta kuma ce sai ta bar masa gidansa tun da ya ce ba ta bashi farinciki. Ganin ta ƙi saurarana ya sa na fita zuwa shashena na iske su Baby sun yi jugum har da ita kanta Rabi'atu ni saboda tsshin hankali na manta da yau suna da makaranta sai da Baby ta yi mgana. "Kun makara ki shiga kitchen ki sama muku abin da za ku ci. Rabi'atu yau ba ki da shiga makaranta ne? A sanyaye ta ce suna da lecture, sai na ce ta koma bangarenta ta shirya mana. Ta amsa mini ni dai na shige ƙurya na dauki wayata na danna ma Nene karon farko domin mi ban taɓa kiran ta da sunan wata matsala ba sai dai gaisuwa. Bayan ta ɗauka mun gaisa ba ɓata lokaci na zayyana mata duk halin da ke faruwa ta ja salati ta dire kafin ta ce" Ya sake ta ne? "Ban sani ba amma dai ya shiga ɗaki ya rufe kansa." "Innalillahi Saudatu ba ta jin mgana. Sadiya don Allah ki hana ta tafiya bari na kira Zuwaira." Sai na amsa mata da to, muna gama wayar na fito sai na ga ba Rabi'atu Baby kuma tana kirchen yaran kuma sun saki suna ta wasan su sai na fita, haraba na ci karo da Rabi'atu tana buga ƙofar shashenta. "Yana ciki ki yi magana in ya ji muryan ki zai bude." Ban tsaya ba na shige bangaren Gimbiya na same ta har ta gama haɗa kayanta ta zurma hijabi, na janye akwatin na ce ba ta za ta tafi ba. "Maman Jidda ki bar ni na tafi, ya ce sakina zai yi" "Shi bai ce ba ya dai ce ki bar masa gida amma bai ce zai sake ki ba ke ce kika furta haka" Cikin kuka tace" To ai manufarsa kenan. Miye ma'anar miji ya kore ka daga gidan shi? An ya an taɓa yi ma wata mace tozarci kamar yadda yau Yusuf ya yi mini? Ina mata mirmishi na ce" Nima mun taɓa faɗa da Yallaɓai na ce zan bar masa gidan sa ya ce na tafi bs zai hana ni ba' Sai ta kalleni baki buɗe tana mai mamaki. "Wallahi kuma a kan ki ne. Ban taɓa faɗa ma kowa ba ranar a gidanmu na kwana." Sai na ga ta koma ta zauna gefen gadonta amma na kasa mgana, ni ma sai na zo na zauna a gefemta amma ina riƙe da akwatinta a hannuna. "Shi ya sa na faɗa miki haƙuri ake yi ba kyau yanke hukunci cikin fushi." "Ya ce ki bar masa gida? Ke ma ɗin! Sai na gyaɗa mata kai ina dariya kafin na ce"Yes na kuma yi tafiyata saboda lokacin raina ya ɓaci komai ma zai iya faruwa." "Wa ya dawo da ke? "Alhajinmu ya yi mini faɗa ya nuna mini kuskurena. Sannan shi kuma ya zo ya tafi da ni washegari da Safe." "Da man kuma samun sabani a kaina? Na ɗauka ke ba ki da kishi Maman Jidda? Ta faɗa tana kallo na kuma da gaske take yi abin da ke ranta ne ta faɗa. Ban san na kyalƙyalce da dariya ba sai da na ga ina yi. "Da gaske ina ta so na tambayeki tuntuni. Miye sirrin ki da ke ba ki damu da mu ba? Lokacin komai matsala za mu samu ni ce zan zama sila ba ke ba. Kuma sai na ga kamar ba ki da kishi a kaina, ga ma Rabi'atu yadda kike mu'amalamta kamar ba kishiyarki ba, da gaskr nake yi na sha tunanin ko dai ba ki da zuciya ne? Ba kya jin irin zafin da muke ji in mun gan shi da ke? Kai na girgiza ina faɗin" Me ya sa ba zan ji kishi ba ai nima mace ce Gimbiya ina da zuciya a kirjina.' "Amma me ya sa ba ki nunawa? "Nunawan ba shi da amfani in har ka bari wasu daga waje suma fahimta. Amma ina nunawa a yanayin da Allah ya hallice ni, mun sha yin faɗa ba adadi ni da Yallaɓai. Amma sirrina shi ne haƙuri gaskiya na saka haƙuri a kan komai ko na ji wani abu ya motsa mini sai na kira sunan Allah na danni zuciyata na yi haƙuri. In abu ya dsme ni Ubangijina na ke zama ina faɗa mawa ina, shi na kuma roƙa ya cire mini mugun kishi a zuciya na ce ya saka mini salama domin na samun zaman lafiya." Gimbiya ta buɗe baki ta rufe kafin ta ce" Ikon Allah. Ni fa sai nake ganin duk wanda ya ce na yi haƙuri kamar ba ya sona ne." Ta faɗa har tana yin tagumi. "Haka za ki ji da farko. Amma in kika yi haƙurin wata rana ke ce da riba. Sai dai riban  ya kan ɗau lokaci kafin a cinmma riban amma watan wata rana mai hakuri dai shine ke da riba." "Haka ne." Gimbiya ta faɗa cikin sanyin jiki, ni kuma ina ta mata dariya ta ce wai ko ba ni da zuciya ne bana kishin su. "Kawai na saka ma raina ba don ni kaɗai Ubangiji ya hallici Yallaɓai ba. Kuma ni ban isa na hana shi abin da Allah ya ce ya yi ba. Sannan ina yi ma zamantakewar mu kara saboda nima ya yi mini kara, ya yi mini hallaci kamar yadda na yi masa shi ya sa nake tausan zuciyata ina karɓan duk wani abu da ya fito daga bangaren shi da zuciya ɗaya. " Kai ta girgiza alamun gamsuwa kafin ta ce" Ga shi kuma kina ta ganin riban haka. Ki yi haƙuri a da ina yi miki kallon kin gama da Daddy domin yadda yake darajs ko sunan ki aka kira abin mamaki ne. Ya taɓa faɗa mini bayan Nene ke ce macen ta farko da yake jin kunyar ki roƙi sa abu ya kasa yi miki. Ya taba ce mini ke ce ragamar gidan shi, wakilyarshi da ba shi da haufi a kan karan da kike yi masa. Ke ya taɓa faɗa mini cewa ke ɗin ta musammance a rayuwar shi da har gobe ba ki samu madadiya ba." Sai na kalleta ita kuma ta cigaba da faɗin" Ni ban gane ba na yi ta fada da shi a kan ki. Karshe dai ni ce ba na cin riba. Sannan su Anty Bahijja su yi ta nuna mini yana jin tsoron ki. Halima ma har ce mini ta yi in ban dage ba saboda ke Daddy zai iya rabuwa da ni." Bsn wani ji mamaki ba da man na san ai ba sa sona. Saboda haka ba za su faɗi alheri a kaina ba. Kamar an matsi bakin ta nan ta shiga faɗa mini mganganun da suke fada a kaina ba daɗin ji, da bakin ta da ke cewa duk in da Halima ta zauna sai ta zage ni, ta ce mini Naja ce ma kr kwaɓanta wani lokacin amma su Anty Bahijja sai dai su yu ta zugi in abu ya kwaɓe su koma gefe. Ko a nan hatsaniyar auren Rabi'atu duk suka kai ta suka baro miji duk ya gaji da ita. "Kin gani ko? Kuma da abubuwan da kika yi ta yi ne yake tarawa shi ya sa ya ce ya gaji. Na sha faɗa miki ki yi hakuri domin hakiri shine mafitan ki, wata rana akwai wani abun da zai faru da za su nuna miki sun fiki kusa da shi akan ki." "Gaskiya ne" "To gwara ki gyara tun kafin lokaci ya ƙure miki " Sai ta yi shuru amma ta daima kuka sai jan majina. muna zaume muka ji ƙaran buɗe get sai na miƙe lna leƙe ts window ina faɗin" Ga ta man ina jin ta iso" "Wa kika kira? "Nene" Na bata amsa sai ta ware ido  ina dariya na ce" Ba ita ba ce ta zo Mimisco ta kira." "Na shiga uku Kin san faɗan Momi kuwa? Gimbiya ta fada tana ɗora hannu a kanta. "Ai gwara ta yi miki faɗa" Kafin ta samu zarafin magana muka ji ana taɓa kofa ni na fara fita falo sai muka haɗe da Mimisco sama sams muka gaisa na yi mata jagora zuwa ciki yadda ta ga an yi baza baza da kaya ba sai ma ta tambaya ba. "Me ke faruwa ne Nene ta kirani cikin damuwa da cewa na zo na gani  Sadiya ta kira ta ce kun sami saɓani da Tafida har yana mganar saki? Ta faɗa tana kallon Gimbiya ko zama ba ta yi ba. Sai Gimbiya ta kasa mgana ta fara matsan ƙwalla. "Ba kuka na ce ki yi mini ba malama" Bakinta na rawa ta fara faɗa mata tana zuwa wajen fashe gilasan mota Mimisco ta ce" Amma dai ba ki da hsnkali ko Saudatu? Sai ta fashe da kuka tana faɗin"Momi.." Hannu ta ɗaga mata kafin ta ce" in kina hauka ne Tafida ya fi ki hauka. Saboda kishi ki jawo masa asara? Ina ruwanta ita ta siya motar! Ba kuɗin mijin ki ba ne? Ke da Allah ya rufa ma asiri amma kina ma yar da kan ki baya? Kin taɓa jin an ce ga Sadiya can da Tafida suna rigima sabo da ku! Ko ita ba mace ba ce? Ta ƙarishe faɗa cikin faɗa har tana yi mata tsawa. "A yi hakuri Mimisco." "Sadiya Saudatu ba ta jin mgana gwara Tafidan ya sake ta ko za ta yi hankali." "Ba za a yi haka ba in sha Allahu.' Sai a lokacin ta zauna a gefen gado tana faɗin'" Ina shi Tafidan? Na ce mata yana bangaren Rabi'atu. "Tun bai iya fada ba kin ko ya ma Tafida iya tsiya kala kala. Ina daɗin shi don Allah? Ita dai Gimbiya tana ta kuka wayarta ta ɗauko jaka ta kira shi, har sau biyu bai ɗaga ba. "Nima ya ƙi daga kirana." "Ki je ki same shi ne." "Mu je to ki rakani.".. Ta mike tana faɗin haka. "Ke kuma ki gyara ɗakin nan ki ma yar da wannan akwatin ƙaryan na ki." Ta ce ma Gimbiya da ke kuka "Kukan me kike yi! Ai ba ki yi kuka in dai kr ba za ki ji magana ba! Me ye ban faɗa miki ba? Na ce ki yi haƙuri ki kauda kai, ki yi ko yi da Sadiya amma ba ki ji ba? Wallahi in yaƙi saurarena ba zsn matsa masa sai ki tattara ki tafi can Rano wajen Hajiya burin ki ya cika kina ta kawo mana matsaloli a dangi." "A yi hakuri Mimisco " Na faɗa sai ta yi gaba tana faɗin" Sadiya lamarin Saudatu kamar ka yi ta dukan ta ne " Muna tafe tana ta faɗa ni kuma ina bata haƙuri muna kofar shashen Rabi'atu take kara tambayata abin da ya faru na warware mata komai. "Kin ki ko? Ina tarbiya mijin na faɗa kana faɗa? Ai bai burgeni ba da dukan tsiya ya yi mata ba kumbura baki ba." Sai da na yi dariya sai a lokacin na tuna ashe bakin Gimbiya da ya ta sa Yallabai ne ya make mata baki a ɗazu da suna mgana. kiran shi ta sake yi aka samu sa a ya ɗaga sai ta ce ga ta nan a ƙofar shashen Rabi'atu tana jiran shi, ganin ta samu ya ɗauka sai na ce mata zan je na duba yara. "Je ki Sadiya. Ni ba ri na yazo na ga ko zai saurare ni." "ZAi saurareki In sha Allahi." Na faɗa ina dariya. "To tunda ke ma yau aka ƙi sauraran ki nima da sauƙi." Ni dai ina ta dariya na shige bangarena na iske Baby ta gama soya dankali da kwai suna karyawa ita da su Khalipa nima sai na bi bayan su bayan mun gama na ce Baby ta je ta yi musu wanka ni zan gyara wajen,. Sama da awa biyu ina bangarena ba wanda ya kirani har Baby ta yi ma su Khalipa wanda da yake akwai kayansu a bangarena ba su da matsala suna can falon su, suna ta wasannin su Ni ko sai dai waya a hannua Jidda ta kirani muka gaisa ta ce tana ta kira Abban na su ba ya ɗauka na ce wata ƙila yana da bsƙi ne na yi mata ƙarya. Ta ba ni har Ummu Salma mun gaisa sannan muka yi sallama sai can Mimisco ta kirani ta ce na fito za ta fito. Na fito na gan ta tare da gogan yana ts wani cin mgani ko mgana bai yi mini ba a gabana ya sake rantsewa sai Gimbiya ta biya asaran da ta yi masa ita kuma ta ce ba damuwa za ta saka a zo a ɗau motar a kai wajen gyara. "Shike nan? Ta faɗa tana kallon shi,  kamar ba ya son mgana ya ce" Shike nan amma dom ke ce. Da na sha alwashin sai ta bar ta je Rano ta yi wata tukunna za ta dawo." Mimisco ta yi dariya kafin ta ce" Na gode daka ji mganata. Ka yi hakuri ai ta baka hakuri kuma na ce ta sake baka." "Ya rage nata." Ya faɗa yana zakuɗa kafaɗa hannayen shi cikin aljihun wandon dake jikinsa. Ni Mimisco ta kalleni tana faɗi " Sadiya ki sake ba ma wannan rigimammen mijin naki haƙuri. Na samu ya hakura na hada su na yi ma Saudati faɗa ta kuma ji ta ce ta yi nadama na sakata ta duka ta bashi haƙuri ya ce ya wuce. Don Allah ki sake kwaɓar ta kin ji ko? "In sha Allahu ' Na amsa mata ina mirmishi ganin Yallaɓai na ta hararata sai ka ce ni ce na yi masa laifi. Direba ne ya kawo ta tace na gai da yara tana sauri ne yau baban su Naja zai bar kasar yana gida yans jiranta. Ta shiga mota direba ys ja suka fice daga gidan Yallaɓai ya juya zai wuce bai yi mini mgans ba. "Yallaɓai." "Ba ruwanki da ni to." Ya faɗa yana haɗe rai sai na yi mirmishi kafin na ce"Allah ya baka haƙuri." "Ni da gidana duk hukuncin da zan yamke sai kin ce ba haka ba? Ki fita daga idona Sadiya Tam" "In na fita idon wa zan shiga Yallaɓain? Na faɗa ina masa wani kallo. "Uhm za ki yi bayani ne." "Sorry Oga." Na faɗa ina dariya ganin yana mirmishi sai da ns saka shi ko dariya ƙarshenta ma bangarena muka koma tare ya je wajem yara ya daɗe a tare da su sannan ya zo ya na challagin ɗina wai me ya sa yaran shi ba su je makaranta ba? Ina hararan shi na ce" Tun asuna ka fara mana yaƙi a gida ne za ka zo kana tuhumata." Sai ya fara dariya wanka  ya yi bangarena ya shirya. Ya ce zai sauke Rabi'atu a makaramta zai wuce office tun ɗazu Musbsbu ke kiran shi akwai waɗanda ke jiran shi na yi masa fatan dawowa lafiya. Bayan fitan su na rana na leƙa Gimbiya ta sha dai kuka amma dai an warware kaya. Ni dai na sake jadadda mata ta yi haƙuri  in tana so ta zauna lafiya. Ranar girki ma duk Baby ta yi mana itama nan shashena ta ci abinci muna tare da ita har dare sannan ta kwashi yaran ta suka koma bangarenta. A ranar Yallaɓai ys ƙarishe kwanan shi a ɗakin Rabi'atu washegari ya dawo ɗakina ya yi kwana biyu sannan ya koma na Gimbiya. Ni ban san halin da suke ciki ba na ɗauka komai ya daidaita ashe ba haka ba ne, Yallaɓai dai na kwana a bangaren Gimbiya in ranar girkinta ya zagayo shima a falo kuma baya jin abincinta baya mgana da ita daga gaisuwa sai gaisuwa. Ni ban sani ba sai da ta zo tana kuka tana faɗa mini na ce ta sake bashi haƙuri amma duk da haka bayan kwana biyu ta dawo ta ce mini ba abin da ya sauya. Jin haka da zuciya daya na ce zan yi masa mgana amma in ɗauko magamar yadda ya fara yi mini ihu a saman kaina ne na san cewa Gimbiya ta gama ɓata ma Yallaɓai rai ya gama jin haushinta shi ya sa kallonta kawai yake yi. "To tun da ta baka hakuri ka haƙura mana? Shi kenan ita ba za ta yi kuskure ka ba ta da mar gyarawa ba? Kawai sai Yallaɓai ya ce tun da ni ce Nene na yi masa faɗa saboda na ce abin da yake yi bai kyauta ba Allah zai kama shi. "Ki bari Ubangijin nawa ya kamani amma ba ke ba." Zan sake magana ya ɗaga mini hannu. "In kika sake tare ni da mganar da ta shafi Gimbiya wallahi zan kai ƙaran ki wajen Allah. Haba kin dame ni? Kin fi sanin abin da ya kamata ne? Ko sai na ce Allah ya isa ne sannan za ki ƙyaleni da wannan mganar ne? "Allah ya ba ka haƙuri. In sha Allahu ba zan ƙara mgana bam" "Better for you." Tun da ya yi mini haka na koma gefe itama Gimbiyar na faɗa mata tun da ta bashi hakuri ya ƙi haƙura ta fita batun shi in ya gaji zai seuko da kansa na faɗa mata nima irin tijaran da ya yi mini daga faɗan gaskiya. Gaskiya ne yanzu Yallaɓai ya zama masifaffe abu kaɗan sai ya fara faɗa yana yi ma mutane ihu. Maganar gaskiya Gimbiya ta ba ni tausayi duk ta rame ta saka ma kanta damuwa kuma Mimisco washegarin ranar da ta zo ta saka aka zo aka tafi da mota aka aka gyaro ta dawo kamar sabuwa. Kamar ma wani abu bai same ta ba Yallaɓai da kan shi yake sake koya ma Rabi'atu mota duk da iya amma hannunta bai faɗa ba, sannan abin da na ɗan fahimta Rabi'atu ta fara raina Gimbiya ba ta jin kunyar kallonta cikin ido kuma ba ta jin kunyarta kamar farko domin akwai rana tana shashena Gimbiyar ta shigo wallahi ba ta gaisheta ba sai da na yi mata mgana. Da man abin da na kr gudu kenan yarinyar nan ta zo ta fara raina ta, ba ta da yadda ta iya. Ban san ta in da mganar abin da ya faru ya zaga dangin su Yallaɓai ba. Amma na fi tunanin Gimbiyar ce ba ta dandara ba ta fidda mganar. Sai ga Munnira ta kirani tana ba ni labarin jiya ta je Gwamnaja Anty Bahijja tana ta masifan wai Gimbiya mahaukaciya ce za ta jama Tafida asara ita sun lura kishinta na hauka ne da man shima ina ta jiye ma Gimbiya kar ta kai wannan lokacin sai ga shi da kanta ta zo har falona tana kuka tana faɗa mini Anty Bahijja ta je ta same ta a shago sai abin ta manta ba ta faɗa mata. Wai har tana cewa in haukan ta ya tashi ya tsaya a kanta kar ta sake gigin taɓa kayan Tafida tun da ita ba ta da hankali. "Allah ya kyauta amma ni na san irin wannan ranar za ta zo" Haƙuri na yi ta bata tun da ni kam ba ni da yadda zan yi da su Anty Bahijja nima ai haƙuri na ke yi da su. Na ji daɗi dai Gimbiya ta fahimci duk da tana na su akwai wani wajen da za su iya nuna mata Tafida ne ya fi kusa da su kuma tun ba a je ko'ina ba ta fara ganin haka har kuma lokacin Yallaɓai bai sauko ba ni na ba ta shawara ta kira Baba Tafida ta faɗa masa komai shi ya tako har gidanmu ya hada su ya yi musu sulhi mu ma ya tara mu ya yi mana faɗa. Dalilin zuwam Baba Tafida ys sa Yallaɓai ya sauko ya dawo yana sauraran Gimbiya amma ta ɓarar da alfarmanta mai yawa a wajen Yallaɓai motar da ta gama faɗa a kanta tana ji tana gani Rabi'atu ke hawa motarta tana zuwa makaranta, tana kuma shiga gari da abin ta amma ita miji ke jin haushi har Rabi'atu tana ɗaukan Gimbiya a mai yi mata hassada tun da na san za ta faɗa ma dangin ta kuma kowa da maganar da zai kawo mata Balle na ga tana da ƙawaye suna biyo ta gidan ni dai ba ruwana nawa ido ne tun da mijinta bai hanata tarkacen ƙawaye ni a wa? Iyaka dai in sun zo za ta kawo su har bangarena su gaisheni abinci ma ni nake ba su wani lokacin tun da in dai tana makaranta ni ke dafa abinci da ita ba kuma wanda ya sakani ni na saka kaina ganin wata rana sai yamma take dawowa ta gaji ba za iya wani girki ba shi ys sa nake yi dafa abincin da ita. Mota kuma Yallaɓai ya ce bai siya ba in Gimbiya ta isa faɗan ya sa ya siya. Na ce ta yi shuru ta ƙyale shi, sai yanzu ne Gimbiya ke son dawowa jikina ta makara amma duk da haks ban gwasale ta ba. Ina ba ta shawara kamar yadda zan ba ma kaina kums ni daga ita har Rabi'atu daya na ɗauke su. ***** Mun yi azumin watan Ramadana mun yi salla. Jidda ta dawo gida salla amma ana fice sallata koma saboda za su fara jarabawa. A bayan salla muka muka yi auran Anti yar wajen Ya Murja Kaduna muka kai ta muna gama nata muka faɗa ma Firdausin Ya Balki. Ita kuma Funtua muka kaita auran gida babanta ya yi mata. Duk fa mun zama iyaye girms ya kams mu tun da mun aurar mun kai ga jikoki ma. An saka ma zainab ƙanwar Ma'u rana itama dangin  mahaifinta a can kura ne za su aurar da ita ga ɗan katsina. Lokacin da muka yi sha'anin Rabi'atu ba ta nan ta tafi Maiduguri ganin gida, Gimbiya ce kawai ta zo mini biki da ƙannenta har da Maryama da muka taba samun matsala. Yanzu sai gaisuwar mutumci ina anfanin to rigima? Har su Munnira duk na ce su saki tun da itama ta saki a cewar Munnira wai da ta ga uwar bari ba, domin abin mamako har su Anty Bahijja yanzu Rabi'atu na zuwa gidajensu lafiya lau kamar ba su ne masu taya Gimbiya a dawa ba. Da ta dawo daga maiduguri tazo da tsaraba ba wamda ba ta ba shi ba, ni kaina turaren wuta har ina kyautar shi.Yarinyar an yi mata huɗuban kyauta yadda za ta siye kowa to haka take yi ko Gwammaja za mu je ba za ta zuwa hannu rabbana sai ta riƙe ma su Nene wani abun. Cikin lokaci kaɗan Rabi'atu ta yi farimjini a dangin Yallaɓai wai har Anty Bahijja wata rana a ɗakin Nene mun je gaisheta ni da Gimbiya da yara ta zauna tana yabon Rabi'atu tana faɗin yarinyar akwai hankali sai daga baya ta yi ma Tafida uziri shi ya ga abin da ya gani. Har Nene yabon ta take yi in ta zo gida nan ta yi wannan ta yi wannan har kunshin su na yan maiduguri take zuwa na musamman ta ƙun sa ma Nene a kafa da hannuwana duk wani abinci da ta san Nene na so in za mu je za ts yi ta je mata da shi, wani abun ma ni ke faɗa mata. Mimisco da man ba ruwanta ko ita tafaɗa ta ce Yarinyar nan tana da wayau ta san dubarun zaman duniya. Kuma ita ba ta ware kowa ba, kowa na ta ne, har su Suwaiba haka take girmama su shi ys sa cikin lokaci kalilan kowa ya san Rabi'atu har mazan fa in suka zo gidan haka za ta yi ta musu rawan jiki. Yallaɓai ko sai jin daɗi yake yi yana fahari Gimbiya ko sai kuka da nadama ba ta da yadda za ta yi ƙaramar yarinya ta zo ta sha gabanta. Muna gidan Halima za ta zo ba ta shiga shashen Gimbiya ba ta yini a bangaren Rabi'atu ba abin da ba ta bata in dai ta gani ta ce tana so za ta ce ta ɗauka. Ni dai ta so ta sake shigowa jikina na ce nahi. Ai kin ci taliyar ƙarshe amma dai muna gaisawa sannan in ta zo gidan tana shigowa mu gaisa ni ce ba na sakar mata. Da baffan Rabi'atu ya je makka shi da Antyn ta, Har Nene da su Maman farko sun samu tsaraba Yallaɓai Jallabiya da Darduma da casbaha da dabino da ruwan zam+zam. Ni kaina an siyo mini abaya yara ma kowa da na shi har Jidda dake makaranta Gimbiya ma ta samu abaya. Ni kaina wayon yarinya na ba ni mamaki sumu sumu da ita ashe ta san abin da take yi. Su Anty Bahijja ko duk an bi su da dabino da ruwan zam-zam suna ta taɗin suna jin daɗi. Ni dai ban damu ba da duk abin da take yi ba lokacin ta ne ta yi wata rana ba za ta yi ba mu kan mu ai duk mun yi wannan bin a farko muka gaji muka haƙura Gimbiya ce ke damuna kuma na faɗa mata ta yi haƙuri amma fa ba ta da yadda ta iya da Rabi'atu. Wacce ko zazzaɓi Nene ta yi kaf yan gidan su sun zo duba ta. Na cen maiduguri su kira waya me ya sa Yallaɓai ba zo so ta ba? Nan da ya samu hatsari Allah dai ya tsare buguwa ya yi a hannu sai gocewa a ƙafa haka suke tururuwan zuwa duba shi danginta na nan Kano na can ko suna ta kiran waya. Kamar ta goya Yallaɓai haka take ki da shi, biyayya take yi masa ko abi za ta ba shi sai ta rusuna ni fa ina gefe ne amma ni kaina na san yarinyar nan bariki kawai take gwada mana. Ni kaina zuciyata na motsawa ballanta Gimbiya? Ga shi kaumar yaran mu take yi kamar ita ta haife su an ce mai ɗa wawa. Har ta su Khalipa yanzu in dai tana gida suna bangarenta ita kenan ba su abubuwa suna ciye-ciye an ce mai ɗa wawa Yallabai gani ya ke yi a kan Rabi'atu xai iya faɗa da kowa. In Jidda za ta koma makaranta ba ta zaune ba ta tsaye sai ta ga ta koma ita ce kawo mata wancan ta ya ta wancan kuma duk ya gani kuma wallahi hakan yana tasiri. Baby ko daman ta zam yar ɗakin ta ko gidansu muka je wani abu ya faru ita da danginta kamar si goya mu. Itama in ta shiga damu dangin haka za ta daraja su. Maganar gaskiya sai dai ƙin gaskiya amma Rabi'atu tana da hallaya mai kyau. Ta bakin Gimbiya ta kan ce an yi ma Yallaɓai surkullrn yan maiduguri ya ruɗe kan yarinya na kan yi dariya na ce ba surkulle sannu ciwon kai ne kawai. Mun yi babbar salla Rabi'atu ba lafiya ashe ciki ne. Yallaɓai kamar bai taɓa haihuwa ba Gimbiya baƙuwa a harkan mu ai mun zama yan gari. Haka yake kiran waya yana faɗa ma mutane Rabi'atu na da ciki. Tarewa gabada ya yi a bamgarenta yana kula da ita tun da laulayi take yi mai zafi, Ni ko duk abin da yake so a yi masa ni zai kira itama in tana son wani Umma kaza Umma kaza,  na roƙi Allah ya cire mini kishin nan na hauka shi ya sa da ni ake renon cikin Gimbiya ko sai dai kuka a ɓoye in ta yi magana cibi ya zama ƙari lokacin da ya tare a bangaren ta yi magana da cewa ai muna gida ɗaya ba sai ya tare a wajemta ne zai kula da ita ba buɗe bakin Yallaɓai sei cewa ya yi ya tare ɗin sai ta hana shi ganin ya harzuƙa ya sa na shiga tsakani na lallaɓa shi ita kuma Gimbiya na ce mata ta yi bamza da shi duk abin shi dai ba zai dauwama a wajen ta ba. Gimbiya  faɗa mini take yi ba za ta iya jarumta na ba. Ba za ta iya juran ganin Yallaɓai na rawan jiki akan wata na da ciki ba. Na ce gwara ma ta saba domin yanzu aka fara. Wataƙila bayan Rabi'atu ma ya ƙaro wata itama ta zo tana gasar haihuwar to ya za ka yi in ba ka yi haƙuri ba? *Janafty* *TKG320B* *Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.* Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732 Rawan jiki da ɓare-ɓare kam Yallaɓai na yin shi a kan cikin Rabi'atu ga shi cikin na ta ya zo da laulayi ga shi ba ta son cin abinci in ku ka ga yadda Yallaɓai ke lalacewa a gaban yarinyar sai kun yi mamaki. Ni kuma duk abin da ta ce tana so haka zai marairace yana roƙo na domin na samar mata, ni kuma tausayi take ba ni ko bakomai nima uwa ce, wani lokacin kuma Baby yake sawa dafe-dafe nan Gimbiya dai ya san ko giwan wake ya sha ba zai tunkareta ba domin ba ma yi za ta yi ba iyakarta da Rabi'atu sannu Allah ya ƙara lafiya. Kwanciyarta asibiti biyu sannan ta ɗan samu kanta sai da ta koma gida ta yi satuttuka. Antynta ta ɗauke ta ganin wahalan da take sha, Yallaɓai ya so ya hana na dakatar da shi da cewa ya barta a gidansu a kula da ita. Ya bari ɗin amma fa can yake tarewa in ya dawo daga aiki sannan ya dawo gida ya zaunar da ni yana bani labarin in na ga Rabi'atu sai na yi mata kuka ta rame kaza kaza, ni har gajiya na ke yi kamar a kanta aka fara samun ciki su 'ƴaƴan gidan ba a gaban sa aka samu cikinsu ba daga sama ya gan su, duk dauriyata sai da ya riƙa motsa mini zuciya. Tana gidansu sau biyu yana sakani muna zuwa duba ta ni da yara Gimbiya dai an tashi zuwa sai ta ce ba ta da lafiya duk da ya san ƙaryanta ne ba ya matsa mata sai ni. Ni dai na yi sakacin da gabaɗaya Yallaɓai ya gama raina ni in dai akan lamarin matansa ne ko abu ne ba zai tunkari Gimbiya ba sai ni. Saboda ina yi masa kara shi kuma hakan sai ya bashi damar ya rika cin ko wata kasuwa a saman kaina , yanzu kuma lokaci ya kure mini na yi sakacin da ba zan gyara komai ba tun farko da ban bashi fuska zan iya ɗauka ba da wataƙila nima zai shakkar tunkarata da sha'anin matarsa kamar yadda ya ke jin shakkar tunkaran Gimbiya. Ba ni kaɗai ba dangin shi ma sun ta sintirin zuwa duba ta zuwan mu na ƙarshe can na ga Halima ta yi baje-baje kamar a falon Nene ban yi mamaki tun fa yanzu ai Rabi'atu uwar ɗakin ta ce. Gimbiya ta ɗauka bayan ita ba wata macen da Yallaɓai da dangin sa za su yi ma rawan jiki saboda samun ciki sai ta ga ma suna abin da ya fi wanda suka yi mata a baya. Sai ta sha mamaki domin tun cikin na ƙaramin sa Yallaɓai ya gama tsara in mace ne ga sunan da zai saka Aisha in namiji ne kuma Alhajinmu zai yi ma takwara zai yi zai yi kaza har na haddace su a kaina. Gimbiya ta yi ta ƙunci in an yi wani abu da ya bata haushi ta same ni da mganar na gani ko? Na ce na gani mana amma ban nuna na ji ko na gani ba itama in ta yi haka sai ta zauna lafiya. Amma ba ta ji shawarata ba kafin Rabi'atu ta dawo gida sai da suka yi tsiya akan ranar girkinta yana kai wa dare a can. Ta ga fa nima har ranar da yake ɗakina abin da yake yi kenan amma ta na gani ban ma na nuna na gane abin da yake yi ba, amma ita da shegen kishi ta yi masa mgana har tana saka ni a ciki wai na faɗa masa gaskiya ba ya adalci tunda yana jin mgana ta. "Tana gidan nan ma rashin adalci yake yi mana Maman Jidda. Ba ta gidan ma ba zai daina ba." Ina zaman zamana a bangarena ta kira ni a waya sha ɗaya saura na dare. Na ji dawowarsa ba daɗewa ni na ma ɗauka wani abu ne ya same shi amma sai na iske shi zaune fuskar nan kamar hadari ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a saman kujera yana karkaɗawa alamun yau fa akwai masifa in Gimbiya ta cigaba da zungurin sa. Kallonta na yi, Baiwar Allah ta yi masa kwalliya da fa zafi ka zauna jiran miji har sai ka siƙe sannan zai dawo. Amma yanzu in na ce bai kyauta ba daga ni har ita zai iya cewa mu bar masa a gidansa a yadda dai yake zaman taƙama nan yana kaɗa kafa ji yake yi yana daidai da koma wacece. "Fisabillahi yana kyautawa? Sai ya je ya shantake? Tun ƙarfe nawa na gama shirina ina jiran shi? Ni ban hana shi zuwa ba amma sai ya yi abin na shi da tunani a ciki.' "Ok wato kina so ki ce ba ni da tunani ko Saudatu? Ya faɗa yana daga zaune, a ɗan kuma fusace domin ni fa na daɗe ban ji yana kiran ta da Daughter da ya saba ba itama tuni Daddy ya kama kan shi Babansu Jidda ne ko Abban Khalipa. "Ni ban ce ba amma dai na ce ba ka yin tunani in za ka yi wani abu." Kawai sai ya yi wani mirmishi na san in ya tashi magana ba zai faɗi mai daɗi ba ita kuma ta harzuƙa za a iya yin abu mara kyau. "To ke kiyi haƙuri don Allah. Zuwa gobe in hankula sun kwanta cikin tsanaki sai ki nuna masa in da bai yi daidai ba sai ya gyara." "Ba zan gyara ba." Ya katseni a fusace na yi jage ina kallon shi sai kawai ya miƙe kamar zaki ya fara nuna Gimbiya da yatsa kafin ya ce" Ke wai me ya sa kin raina ni ne! Komai abin kishi ne a wajen ki? Rabi'atu ba ta da lafiya na je gidansu na dubata na shigo kin yi tunanin ki ce mini ya mai jiki.? Matata ce fa ke kuma y'ar uwan ki ce fa? "Aa ni wallahi ba yar uwata ba ce. Ta tsaya iya dai matsayin matarka dai." Ta faɗa har tana ɗaga masa hannu sai ya yi wani slow kafin ya cigaba da faɗin"Ok yanzu na ma gano ki. Duk wannan ihun da kike yi cikin ne baki so ta samu ba ko? Ta buɗe baki za ta yi mgana ya hanata ya ɗaga mata hannu yana cigaba da faɗin" Ba sai kin yi magana ba na gano ki baƙinciki ne da hassada dankare a zuciyarki. To bari ki ji na faɗa miki haihuwa yanzu Rabi'atu ta fara sai dai ki mutu wallahi" "Haba Yallaɓai." Na faɗa saboda na ga kalaman na shi sun yi tsauri amma sai ya juyo ya balla mini harara kafin ya ce" Ki yi mini shuru kema ai zan iso kan ki." "Topha" Na faɗa a zuciyata me kuma na yi? Gimbiya ta ba ni tausayi ta jawo ma kanta cin mutumci Yallaɓai haka yake ta jifanta da manganganu wai ita kaɗai ce matarsa! Ni me ya sa ban taɓa masa ƙorafi ba sai ita daga dawowarsa ta san abubuwan da suka faru da shi yau? Ta san wani hali ya yini a ciki ba tarba ba kalamai ma su daɗi kawai ta zaunar da shi tana challanging ɗin sa a kan mganar banza! To wallahi in ya ga dama sai ya kwana a duk in da ya ga dama kuma ba wacce ta isa ta hana shi. "Allah ya ba ka sa'a ka koma gidan su Rabi'atu a ba ku ɗaki sai ka riƙa kwana " Gimbiya ta faɗa tana tsane hawayen baƙin ciki. Ba ita ba ni kaina wallahi na ji zafin mganganunsa haba wai kamar Yallaɓai ya fara haukacewa. Ni ina ta tsoro ma kar su Khalipa su ta so. "Ina ruwan ki? In ma a hotel zan ɗauke ta mu je mu kwana wannan duk ba damuwarki ba ce. Matata ce." Da na so ba zan ƙara mgana ba amma ganin lamarin ya fara lalacewa shi ya sa na sake mgana. "Don Allah Yallaɓai ka yi haƙiru ke ma Gimbiya ki yi hakuri ku bar mganar nan. Dare ne kar ku ta shi su Khalipa." Ita dai Gimbiyar ta yi shuru tana ta jan majinar kuka shi ko uban gayyar komawa ya yi ya zauna yana huci shi kaɗai da man ina tsaye ne ban zauna ba sai na ce" Sai da safe" "Dawo nan kema" Ya kira ni a ɗan zafafe, ni fa ban san me na yi masa ba amma na fahimci ba mganar Gimbiya ba da man yau a fusace ya shigo ita kuma kishi ya rufe mata ido ba ta gane ba ta je ta taɓo shi. "Na'am kana kirana ne? Wajen zama ya nuna mini a kujeran da ke gefen shi ta zaman mutum ɗaya sai na zauna ina jiran na ji ni kuma me za a sauke mini? Gimbiya ya kallah kafin ya ce" Da kika kira Sadiya ita ɗin uwa ce ita! ? Daga ni har Gimbiya sai da muka kalli juna sannan muka dawo muna kallon shi saboda mamaki. "Zugwai-zigwai kin ɗaga waya kin kirata na ce ita din Nene ce? Dukkan mu mun kasa mgana daga ni har ita saboda ba mu da abin cewa. "Sadiya ke aurena ko ni nake auran ta? Ni ne shugaba a gidan nan a cikin ku ba wacce ta isa na faɗa muku." "Ikon Allah" Na iya faɗa a saman leɓena kamar an turo fa Yallaɓai. "Kar ki ƙara mini wannan sakarci muna mgana ki je ki kira mini wata wallahi in kika ƙara ranki sai ya ɓaci na ma faɗa miki." Ya faɗa yana nuna Gimbiya da yatsa, ni ta kalla sai na gyaɗa mata kai alamun ta ba shi haƙuri. "Ka yi haƙuri." Ko sauraranta bai yi ba ya juyo kaina ai ni na yi suman zaune tun da yau Yallaɓai ya ke kirana da wata ai na san kuma sai abin da ya manta. "Ke kuma ki daina ganin ina jin mganarki ki ɗauka ko wani abu na rayuwata sai kin shiga. Ba ruwan ki da tsakani da kowacce a cikin matana. Ki tsaya in da na saka ki, ni ne mijinki ba ke ce mijina da za a ce komai ya faru ki tasani kina yi mini faɗa kamar wani ɗan ki ba. Ba na so na faɗa miki bana so" "Ka yi haƙuri " Na faɗa cikin sanyin murya. "Ban yi ba." Shima ya ma yar mini a fusace. "Allah ya huci zuciyarka." "Amin." Ya faɗa a ƙufule kafin ya tashi ya shige bedroom har yana bango mana ƙofa. Gimbiya ta kalleni kafin ta riƙe baki tana faɗin" Kin gani ko Maman Jidda? Wallahi ba ƙalau yake ba" Miƙewa na yi tsaye kafin na ce" Lafiyar sa ƙalau. Da a ce kin ji shawara da duk ba ki jawo ma kan ki tozarci ba, nima da ba ki jawo mini wannan jan kunnen da ya yi mini ba. Don Allah Gimbiya ki daina sakani cikin rigimarki. Ba zan iya da Yallaɓai ba nima kina dai ji ya ce ni ba Nene ba ce ina yi masa shisshigi, in dai kin san ba za ki dinga haƙuri da wasu abubuwan ba nima to ki yi ma Allah ki daina saka ni a ciki." "Ki yi hakuri." . Ta faɗa a sanyaye to itama ai ta gani yadda ya zauna yana ta yaɓa mana mganganu. "Na ce miki ki riƙa kauda kan ki. Ba fa komai ne sai ka yi mgana ba. Ki bar shi ya yi ta kai wa daran mana in kin ga za ki iya jiran shi ki jira shi in ba za ki iya ba ki yi kwanciyarki. Ke in ya ga dama duk ranar girkinta ya je can ya kwana me ye na ki? Gidan shi abin da ya dama shi za mu sha, kuma Allah ai yana sama yana kallon shi cikin mu duk wacce ya danne ma haƙƙi sai Allah ya tambaye shi. Duk tsiyar shi ba zai kwana can ba zai dawo kuma yau da gobe ba ta bar komai ba in kika yi haƙuri itama ai wata rana za ta zama ɗaya da mu. Ai mace ce haihuwa za ta fara. Kamar yadda ya ganta ya auro wata rana haka zai ga wata ya auro itama a fara gwagwarmaya da ita ba, ai Namiji ne shi a rayuwar namiji mai ya yi ne da kuma ɗauka da ajiyewa ke dai ki zura ido kawai ki daina ma tanka shi, ki nuna ma kamar ba ki san abin da yake yi ba shi da kan shi zai shiga taitayinsa." "In sha Allahu ba zan ƙara mgana ba." Ta faɗa tana miƙewa itama. "Ya dai kamata gaskiya." Ba mu ji ko ƙaran buɗe kofa ba sai ganin shi muka yi kawai a kan mu a falon, ban san ko ya ji manganganun mu ba ko kallon mu bai yi ba ashe ya manta wayarsa a saman kujeran da ya tashi ita ya ɗauka a fusace ya koma ciki ina ganin haka na kama hanyar fita ina yi ma Gimbiya sai da safe, mganganun sa ba su wani dame ni ba Gimbiya ce washegari ta ce ba ta iya barci ba a raina na ce ba za ki yi ba kam nima haka na kwana kuka a ranar da Yallaɓai ya ce ina baƙin ciki da su Khalipa. A cikin zuciyata na ce Gimbiya Welcome to the Game. Wannan tsiyar da Gimbiya ta jawo ta aka yi ita ta ja mana Yallaɓai sati ya yi daga ni har ita yana yi mana cin mgani ko abincin mu ba ya ci da gani har ita, sai ma bangaren shi da ya turo ma'aikata suka fara ida sa gyarawa ko gaya mana bai yi ba, ni in ranar kwana na ba yan gaisawa ba ma mgana sai dai ya yi ta aikinsa a kan system ko kuma ya yi wasannin shi da ƴa'ƴan shi, nima ko ganin haka na kama kaina ban ga abin da na yi masa na bashi haƙuri tun a falon Gimbiya ban san kuma me ya ke so ba ko so ya ke yi na kwanta masa saboda yana fushi da ni, ni ko na ce a cigaba da tafiya gabar nan ce ya san ni na fi shi kwarewa. Da na fahimci ba ya cin abincina sai na daina ma yi masa ta yi, Gimbiya ta ce itama haka ba ya mata mgana in ta yi masa mgana da kyar yake amsawa. Ita duk ta damu kamta ni fa na faɗa mata an riga an zo matakin da ɗan zaki ya riga ya girma ni Yallaɓai ai ya daina hana ni sukuni da takaicinsa tuni na ke tattara shi na watsar na kama sabgogin gabana. Balle da na dawo da sana'ar hijabai na gadan-gadan ina na gama ta lokacin shi, da man hatsiyar tariyar da bukukuwa ne suka saka na yi sanyi ganin ina so ma na taba jarin kuma ga mutane na so shi ya sa kawai na saka aka ɗinko mini da yawa aka aiko mini da shi. Gimbiya ko ga shagonta ga aiki amma duk da haka ta zauna Yallaɓai na neman kasheta da haushi. Wai tana faɗin ya fara gyaran bangaren shi bai sanar damu ba na ce ina ruwan ki? Shi da gidan shi da kudin shi? Ni ko a gefen gyalena to da Rabi'atu za ta dawo bai sanar da mu ba ranar ni ba na nan na je gidan Ma'u na duba ta tun da ta haihu ɗin ba ta ƙara lafiya ba lafai lafai ce, Gimbiya kuma tana shago yara suna makaranta danginta suka zo suka yi mata gyaran bangarenta sannan da daddare suka dawo da ita. Ni ina muka sani ba sai dai muka gan su ba kawai ni dai na shiga bangaren Rabi'atun na yi musu sannu da zuwa itama na yi mata sannu duk ta yi wani fari ta rame. "Ai mun zo ɗazu gyaran bangaren Rabia megadi ya ce duk ba ku gidan" Kai tsaye na ce ni na je dubiya ne Gimbiya kuma daga wajen aiki ta wuce shago. Kuma ba mu san yau za su dawo da ita ba. "Ai ko dai tun jiya ma Megidan ya so ta dawo Allah bai yi ba sai yau." Wato kenan yana sane mu ne dai bai ga damar sanar damu ba ya yi ma kansa ruwa na kawo musu ba su ma  sha ba. "To ga Rabi'atu nan mun san ana ƙoƙari kula da ita Allah ya ba da lada." Na amsa da Amin Gimbiya sai da suka fito haraba ta leƙo suka gaisa direban da ya kawo su ya kwashe su ya ma yar. Na koma na sake duba Rabi'atun muna ɗan yi hira kaɗan ta ji sauki sai dai ta rame. Ni dai na ga abin mamaki yarinyar nan tana jin diran shigowar mota ni ko ina zaune na ce ina jin Yallaɓai ne ai sai da na yi suman zaune saboda barikin da na gani ganin idanuwa. Yarinyar nan tana zaune amma sai ga ta kwance ta narke kamar ruwa, yana shigowa da man bangarenta ya nufo, yadda ya ganta kwance tana wani lumshe ido ko lura da ni bai yi ba ya nufeta duk ya  rufe ya tarairayota jikinsa yana tattaɓa goshin ta. "Baby me ya faru jikin ne? Kan ki ke ciwo? Ko zazzaɓin ne? Ya ke faɗa yana taɓa kanta da cikinta ita ko ta narke masa tana shagwaɓa kamar wata jaririya. "Abba uhm" Ta ke faɗa har da gutun hawaye, shi kuma gabaɗaya ya ruɗe. "Me Abba ya yi? Uhm faɗa mini." "Ba kai ne ba' Kawai sai ta fashe masa da kuka cikin rawan jiki ya ƙamƙameta yana faɗin"Abba ne ko? To Abba ba zai ƙara ba kin ji ko? Ɗankari! Haka na faɗa a zuciyata. Gimbiya ta daɗe tana ce mini yarinyar nan muguwar yar bariki ne ban sani ba, sai yau da ta nuna mini Umma na ke ita kuma Rabi'atu ina zaune tana abin da ta ga dama in shi bai ganni ba ita ai ta san da ni. Zuciyata ta motsa amma ban bari na zubar dakaina a gaban su ba sai na miƙe ina mirmishin ƙarfin hali. "Mu kwana lafiya Rabi'atu." Sai a lokacin shi ya farga da ni, ya ɗan yi shock tun da har ya ɗan sake ta, ta bar cinyarsa ta zauna da ɗuwawunta a saman kujera. "Umma to sai da safe." Ta faɗa cikin sanyin murya ji na yi kamar ma juya na kamata na yi bugu. Ban taɓa jin kishinta da haushinta irin na yau ba. "Sadiya da man kina nan zaune? "Sannu da dawowa." Na faɗa ban jira amsar shi na bar musu falon, duhu duhu hazo hazo na ke gani kafin na kai bangarena. Na yi shuru zaune ina tunani,ko ma me ya faru yarinyar nan da gangan ta yi, tun da ai ni da ita ne zaune muna hira, raina ya ɓaci kenan ta shirya mini wulakanci ne? Daga abin arziƙi duk abin da ta ga ina yi mata darajan Yallaɓai ne da sauke haƙƙoƙin zaman tare amna ni ai ba ta isa na koma bayan ta ba. Amma tun da ta ce haka mu zuba mu gani, ni ko zan nuna mata na riga ta zuwa duniya ita yarinya ce har yanzu. Ranar raina a bace na kwana ko Jidda ta kira ni a waya ban wani saurareta ba na ce ina jin barci washegari da safe sai ga Yallaɓai ya shigo yana yi mini kame kame ya ɗauka zan nuna masa wani abu ne ya ga bayan gaisuwa kallon musulumci ni ban yi masa ba ma shima ai munafukin ne. Ko kunya bai ji ba yana faɗa mini Rabi'atu na son tuwo, na ɗauka zai ce ne ni na yi mata wallahi da in na fara faɗa masa mgana sai abin da na manta sai ya taimaaki kan shi ya kira Baby ya saka ta. Asabar ne ba makaranta Tahfiz kuma suna ajin bita ne yau ba ta je ba. Tun da y'arsa ya saka ban yi magana ba na yi shuru kamar zan ce ta je can bangaren nata ta yi mata sai na fasa ganin gogan yana can ya tare. Ranar ko fita bai yi ba har su Adnan gida suka zo suka same shi Gimbiya ko tun safe ta wuce Rano an yi musu rasuwa sai gobe za ta dawo shima Yallaɓai in dacewa zai yi ai ya dace ya je tun da yaron ƙanin Hajiya ce ya rasu saurayi ne ma Gimbiyar take faɗa mini to yarinya ƙarama ta saka shi a gaba har lahadi bai fita ba Baby ya samu tana yi mata wahala ranar ma da na ce ta wuce ta je Tahfiz hanawa ya yi wai ta bari wani sati kawai. Ban yi magana ba saboda na shirya mafita na. Ranar litini da safe ya fita ya ce mini za su je Rano gaisuwa. Na ce Allah ya tsare ni da man mun tsara da ni da su Munnira Gimbiya gobe za ta dawo ranar bakwai za mu koma tare da ita amma na kira ta a waaya ta haɗa ni da Hajiya na yi mata gaisuwa. Tun ranar nan da na kama shi yana wannan ɓare ɓare jikin ya daina sha mini ƙamshi, ni ko na yi kamar ban ma gane shi ba tare suka fita da Rabi'atun ya sauke ta a makaranta ai ko ta gane ba ta da wayau sai yamma ta dawo gida ban yi kuma abinci da ita ba. Sai ga ta shigo shashena ta zauna ta ɗauka irin baya ne in ce ta shiga kitchen ga abincin ta ga na yi mata kiri ƙiri. "Umma ba ki yi sauran abinci ba? Kai tsaye na ce mata yau ban yi girki ba indomie ce Baby ta dafa da suka dawo makaranta. Ba su nan kuma sun tafi islamiya na samu an saka su wata islamiya anan anguwar da muka dawo ba nisa. Su Khalipa da man wajena Gimbiya ta bar su da za ta fi. "Ki je ko yar indomoe ki sulala ki ci.' Ta ce mini to, ta tashi ta wuce na rakata da harara ba wai haushin abin da ta yi mini ba ne a'a haushin yadda ba ta raga mini ko don karan da na ke yi mata ba. Na yi kyafci na ce za ki gane ba ki da wayau yarinya. Tun daga ranar na daina ije mata abinci sau biyu tana zuwa tambaya na ce yara sun cinye daga nan ta fahimci dai ba zan ba ta ba ta kama kanta. Sai Yallaɓai ya ce ba ta da lafiya ba ita iya komai amma ranar girkinta su kule ba ka jin motsin su to da man ni ce na ɗaukar ma kaina kuma na yaye Gimbiya da man yar gaskiya ce ba za ta yi ba shi ya sa bai taɓa saka ta ba. Da Gimbiya ta dawo kamar zan faɗa mata sai na fasa kawai na share saboda kowa ya ji sai ya yi mini Allah ya ƙara. Munnira ta zo ranar jumma'a mganar tafiyar mu Gobe muka shiga wajen Rabi'atu ta duba ta. Da ya ke muna ta knoking shuru ni kuma na ɗauka ko tana salla me tun da bayan mangariba ne sai muka tura kofar tun da a buɗe yake muka shiga abin mamaki ta gyara ɗakin nan tas  yana tashin ƙamshi sai na tuna ashe yau gogan yana ɗakin ta ne, sai muka zauna saman kujera muna jiran ta ba ta ji shigowarmu ba sai ga ta fito da wata shigewar riga marabanta da tsirara kaɗan ne. Ko ta yi tunanin shi ne ya dawo ko da man dai haka take yawon ta a ɗakin ta ban mu sani ba da ta gan mu ta ji kunya da gudu ta koma ɗaki ta ɗauko hijabi ta saka ta fito muka gaisa tana rufe fuska muna fita haraba Munnira ta kalleni kafin ta ce. "Ke na taɓo ki da mgana. Wai yarinyar nan ne ta kile haka? Ina dariya na ce" Ras. Ai Namiji ya kilar da ita." Munnira ta riƙe baki kafin ta ce" Wallahi in ka ganta kamar ka saka mata yatsa a baki ba za ta iya cizawa ba.' Uhm kawai na ce saboda Rabi'atu ta sauya idanuwanta sun buɗe ko na ce yanzu ta san daɗin namiji shi ya sa. "Kin ga idanuwanta ƙif ƙif na marasa kunya yanzu." Mirmishi kawai na yi ban yi mgana ba. "Ba shakka Tafida ya ba ta zuma ta ɗanɗana. Sadiya sai ku shirya za ta haɗa kafaɗa da ku yanzu." "Me ya rage? Ai tama fara haɗawa." Na fada ina danne abin da ke ta so mini, yarinyar da Yallaɓai ya ce kwana take yi da zazzaɓi ne haka shi ya sa da man ya ce ita ba za ta je Rano ba ni da man na yi masa mgana ne kar daga baya ya ce an ware ta tun da yanzu ba ya so wani abu ya same ta. Washegari su kaɗai muka bar ma gida da yara kaf muka tafi ya ba mu mota Sadi ya kwashe mu, su kuma su Hauwa suna motar gidan Mimisco har da su Anty Bahijja aka yi tafiyar da Mubeenan Musbahu da tsohon ciki har ina ta faɗa na ce kamar dole ta zauna a gida mana tun da cikin ta ya tsufa. Can muka yini sai dare, Amma mun je gidan Marwa an haɗu ana ta hiran duniya mun haɗu da Sameena ta ce mini gobe ma za ta koma tana dariya ta ce ya ta gan mu da mutuniyar nima ina dariya na ce ta ji wuya ne ta dawo muka haɗa kai don Allah, Sameena na ta dariya ina ta ya ta. Sai bayan isha'i muka koma gida muna mota Jidda ta kirani tana faɗa mini wai Abban su ya kirata ya ce in sun samu break ta zo gida ta duba Anty Rabi:atu ba ta da lafiya sosai. Kamar Jidda ce Yallabai na rufe ta da faɗa ta in da na ke shiga ba ta nan na ke fita ba. "Ko hutu kuka samu ki tafi gidan Ya Hamza ma ji kin kamo hanya kin dawo sai na ci uban ki Jidda. Saboda kawai duba Rabi'atu sai ya ce ki bar karatun ki  taho! Gaskiya Yallabai ya fara samun matsala." Ita dai da ba ta san mafari ba hakuri ta ba ni ta ce wai ta faɗa masa suna ma test ne, bayan mun gama wayar na kalli Gimbiya ina faɗin" Kin ji mijin ki ko Gimbiya? Ta yi uhm kafin ta ce" Wallahi ni dai ina tunanin ba haka nan ta bar sa. Ba ki ganin yadda ya ke fita hayyaci a kanta ne? Wai Jidda ta zo dawo makaranta kawai saboda ta duba yar gold? Da wani abun ne ya taso tsaye zai yi ya ce ba za ta zo ba amma da ya ke yar gold ce ya ce a zo a duba ta mana." Ni takaici ma ya hana ni mgana, ko da muka isa gidan yana bangarenta shi dai ya zo ya yi mana bangajiya ban da ita ni Gimbiya ta ma ce mini ko gaisuwa ba ta yi mata ba da a ce da ne zan yi mata mgana yanzu ko kiɗa ya sauya shi ya sa rawa ma ya sauya. Shi kuma gogan bai nuna mata abin da ya kamata ba. Yadda bai nuna mini ya kira Jidda ba nima ban nuna masa na ji aikin da ya yi ba. Sai da kan shi ya zo yana ce mini Jidda ta so ta zo gida amma tace suna test a raina na ce ta so ko ka so,  ya na neman ya riƙa kashe ma Baby karatu saboda matarsa kawai sai ya ce ta zauna ta yi ma Rabi'a girki ne ga an yi sau ɗaya sau biyu ana uku na ce ba zai yuyu ba. "Ba zai yuyu ba kika ce Sadiya? Ya faɗa da safiyar lahadi sun shirya Sadi na jiran su zai kai su Tahfiz wai Baby ta zauna ta je bangaren Rabi'atu ta yi mata shara sannan ta tambayeta abin da take so ta dafa mata yarinya ta ce hadda za ta je tana bita yau amma ya ce ta haƙura ai jiya ta je. "E gaskiya ba ta yuyuwa ka kashe ma yarinya karatu kawai saboda bukatar matarka. Yallabai ta ɗauko wata daga can garin su ko ka samo mata wacce za ta kula da ita fakat kenan." Sai ya kasa mgana ni ko na yi masa mai gabaɗaya sai na ce" Kuma ni ban ga aikin da zai gagareta ba ai ba ta ciwo tun da ta iya ji da hidimarka to za ta iya ji da hidimar kanta da gidan ta ma" Tun da ya ji na faɗi haka ya kiyayi tsayar mini da karatun yarinya ban san ko maganar da na yi masa ba ne, ko da man sun tsara hakan sai ga wata yarinya an kawo kamar za ta ɗan girmi Baby ƙanwar Antyn ce ta yi candy aka kawo ta taimaka ma Rabi'atun ta bakin Gimbiya ta ce da man akwai wacce za ta taimaka man aka bar shi yana ta faman wahala. Tun da ga lokacin kowa ya samu lafiya ta warke tun da yanzu laulayin ya bi jiki amma tun da makira ce a ko da yaushe nuna masa take yi tana cikin ciwo saboda ya lalace a kanta. Mubeena ta haihu amma aiki aka yi mata da nagudan ya taso mata ni Musbahu ya kira uku na dare na ce ya zo gida ya ɗaukeni tun da ba zan iya driving ba. Yallaɓai na ɗakin Gimbiya a waya na kira shi sai ga shi ya fito, da man ina haraba ina jiran Musbahu yana zuwa bayan sun gaisa kawai ya ɗauke ni muka tafi, muna asibitin har safe ba ta haihu ba kan yaro ya jirkice suka ce aiki za a yi mata Musbahu ya saka hannu. Bawan Allah duk ya ruɗe sai da Adnan ya zo yana bashi baki. Da safen Yallaɓai ya zo shi ya biya ma kudin aikin da aka yi mata an samu nasaran fito mata da yaron ta namiji ƙato mai kama da uban shi.  Ba ni na koma gida ba sai da na ga ta farfaɗo y'anuwanta sun zo suna ta mini godiya domin ni ce na tsaya a tare da ita har ta samu kanta na ce ba komai Musbahu da Mubeena sun ɗaukeni da daraja shi ya sa nima nake daraja duk abin da ya shafe su. tun da kuma aka yi haihuwar bana zaune kullum sai na je asibitin kwanan ta huɗu suka koma gida to can ma gidan haka nake sintiri , suna an ɗaga sai sati biyu kan lokacin maijego ta ji sauki. Y'anuwanta sun ce za su dauketa bayan suna da Musbabu ya nemi shawara ta na ce ya barta ta je gidan kamar gobe ne. An yi suna yarinya ta ci sunan Hajiya iya Hafsat. Musbahu ya yi ƙoƙari ya yi abin da kowani uba zai yi raguna biyu aka yanka mata Ya Usman ya siya ragunan sunan. Mun sha suna har Nafisan katsina ta zo da Safiiya ni da man mune yan gaba gaba Gimbiya da wuri ta zo har yara da suka dawo makaranta na saka Sadi ya kawo su, Amaryan Yallaɓai sai yamma ta zo daga makaranta saboda kuma tuƙo kanta ta yi ba ta yi dare ba da dokar megidan ban da tukin dare. Wannan kan gaskiya ne daga ni har Gimbiya in muka fita da mota muka kai dare ba mu dawo ba haka zai yi ta kira yana mana faɗa. An yi suna lafiya an watse bayan suna da kwana huɗu yanuwanta suka ɗauketa zuwa gida sai dai ya riƙa zuwa yana ganin ta. Ni dai na yi mata atamfa da kayan Baby iya karfina. Sai da ta gama wanka za ta dawo ne Musbahu ya zo da kanshi ya ke faɗa mini abin arzikin da Yallaɓai ya yi masa ni ban ma sani ba cewa ya yi ya tashi daga gidan shi ya yi ƙarami ya bashi gidan da na taso ya zauna a ciki ya bar masa na wajen na shi sai ya saka haya a ciki. Kai na yi masa murna kuma na san Yallaɓai ya yi haka saboda ni, domin ko kwanaki da ya ce zai saka haya magiya na fara yi masa ina son gidan nan bana so na ga an bama wani can bare gwara na gida. Da na yi ma Yallaɓai  godiya hararata ya yi kafin ya ce" To ya zan yi? Gidan nan ji kike yi da shi kamar me. In na ce zan siyar ki ji haushina in na ce haya ma kice aa. Shi ya sa sai na yi tunanin gwara na ba ma Musbahu shi sai ya bar mini na shi, tun da na ga in shi ne zaki ji daɗi yaron ɗakin ki ne" Ina ta dariya ban yi magana ba wai zan ji daɗi yaron ɗaki na ne kuma na ji daɗi sosai. An je an yi ma gidan fenti da gyare-gyare Mubeena ta dawo, ta kuma zo har gida ta yi mini yini ita da Anna(Hafsat) daga baya nima na je gidan na da wuri sai na ke ganin kamar zan waiwaiya na gan ni ina shiga ina fita a gidan wasu shuɗaɗdun al'amura ba za su taɓa shuɗewa ba, saboda a gidan nan abubuwa da dama sun faru sai dai godiya tun da yanzu mun samu cigaba ne. Kowa ya ji labari sai ya yi ma Musbahu murna tun da ya samu cigaba gidan shi kuma Yallaɓai ya saka yan haya. An gama gyara shashen Yallabai falo ɗaya ne da bedroom uku. Ni har mamaki yawan bedroom ɗin na yi da na tambaye shi cewa ya yi ba ruwana na jira mana na gani. Sai na kama bakina. Ya yi shirin shi har kayan funitures ya siya ya gyara bangaren shi tas kuma kowani ɗaki ya saka gado, wato dai wulaƙanci Yallaɓai ya ƙaro ashe wai kowacce ranar girkinta da ɗakinta in kin fita ki rufe ranar da kike da miji ki zo ki gyara ku kwana da miji in kin fita kina da key dinki ki rufe. Ranar da ya ta ramu yana faɗa mana na kasa haƙuri sai da na yi dariya. "Na zama abin dariya ne? Ya tambaya a daƙune ganin ya ji haushi ya sa na ce" Ni tsarin ne ya ba ni dariya wai ranar girkin ki da key ɗin turaka ki je ki gyara in kin fita ki rufe" Shima sai da ya yi dariya  kafin ya ce" Maganin ƙorafi na yi. Kowa da turakanta magana ta ƙare." To ni dai ko rawan jiki ban yi ba tun asali na tsani turakan miji wallahi, Shi ke nan Yallaɓai ya fara buɗa jiki in kina da girki sai dai ki bi shi har dining ya saka a bangaren na shi duniya sabuwa. Ni fa ranar girkina mantawa na yi na yi barci a bangarena da safe na tuna tsarin har abinci a can za ki haɗa masa ke fa can za ko tare sai kin fita girki ni ko na ce ba zan iya ba ya'yana fa. Yallaɓai ya ce to na yi ta kwana a bangarem nawa shi dai ya gama bin kowacce daƙinta tana yi masa yanga. Ina gani Rabi'atu da Gimbiya ana gogawa. In suna da turaka aka kasa zaune aka tsaye. Rabi'atu in ranar ta ce ƙamshi turare har haraba. Ita da Salima kanwar Antyn tasu su zage a yi ta girke-girke. A sauya zanin gado a yi wannan a yi wannan haka itama Gimbiya sai suka koma suna gasa shi ko Yallaɓai na jin daɗi sun zaɓi dakunan su ni na karshe suka bar mini, na san dai in dai ranar girkina ne da safe zan je na gyara ko na saka Baby  ta gyara na kuma shiga ɗakin na gyara na wanke tiolet a bangarena na ke yi abinci na kwasa na je na jera masa bana yin wannan rawan jikin na su to Allah na tuba wani kuma dare ne jemage  bai gani ba  ai sai daran mutuwarsa? In muka kwana da asuba nake gudawa bangarena sai dai in zai fita ya biyo ni ranar har ce mini ya yi in bana son  kwanan nan ne na faɗa masa. "Aa kawai dai ban saba ba ne wallahi ina jin wani iri." Wani kallo ya yi mini kafin ya ce" Gwara ma ki saba malama turaka yanzu kika fara zuwa." Shuru kawai na yi, ni bai san ban wani damu ba ta kaina na ke yi, duk da wannan rabawan da ya yi bai hana an samu matsala ba Gimbiya ta ce Rabi'atu tana ɓata kitchen da falo ba ta gyarawa haka take fita tun da can take girki, saboda da daga Rabi'atu sai ni ne daga baya abin ya birkice ni na dawo farko, sai Rabi'atu sai Gimbiya, rigima sosai sai da ya tsawarta musu da cewa zai kori kowa a turakan na shi sannan aka zauna lafiya bayan an yace kowcce ta zo ta ɓata waje ta gyara kafin ta fita ni ina gefe ban shiga ba ina ruwana na yi magana ya ce ina yi masa shissshigi. Na koma gefe na zama yar kallo tsakanin Rabi'atu da Gimbiya ne suke ƙwama film acikin gidan nan wani abun ma kamar ka yi ta dariya wani abun kuma hauahi ka ji kamar ka yi ta dukan su. Cikin Rabi'atu har ya fito wata biyar amma ya yi girma sosai. Har ni kaina ina mamaki, sai da ta yi scan Yallabai ya zo bakin shi kamar  zai kai kunne yana faɗa mini an ce yan biyu ne a cikin Rabi'atu mace da namiji. Sai a lokacin ya ke faɗa mini wai maman Rabi'atu yan biyu ne namijinta ya rasu ne. Labarin yan biyu Rabi'atu za ta haifa kusfa kusfa Yallaɓai ya kai labarin nan da man fa yana da shegen surutu da faɗi ba a tambayeka ba. Gimbiya ko ta ce ya dai bar murna domin likita ba Allah ba ne, shi ko ina ruwan shi yana ta shirin haihuwa kamar an ce gobe ne ballanta yanzu da kuɗi suke huda shi ai komai ma zai yi. Haka nan muke zaune muna gungura rayuwar mu, ba a sati Gimbiya da Rabi'atu ba su yi tsiya ba, kuma duk fa kan turaka da miji, ni wallahi har na gaji da baa su haƙuri na saka musu ido, kuma in dai aka yi sai Gimbiya ta zama mara gaskiya saboda ta cika ƙorafi da mgana ita kuma Rabi'atu wayau da bariki da haka take cutar da ita ba ta sani. Ni dai ba mai yi da ni Yallaɓan ma kan shi isata yake yi na tattara shi na bar musu ranar har mgana ya kwaɓa mini wai ya fahimci na koma gefe yanzu na yaye shi kamar ba mijina ba, ba na damuwa da al'amuran shi. "Ba haka ba ne. Gani na yi bayan ni kana da biyu irina masu kula da kai." Hararata ya yi kafin ya ce" Wato ina da biyu! Ai ko goma ne ina nan a matsayin mijin ki kuma dole a ce ma mijin iya Baba." "Dole ne wannan" Na faɗa ina masa dariya ganin ya shaƙa sai kawai ya jinjina kai yana faɗin"Na gano ki wato kin gama cin moriyar gangan za ki yada ƙwaron ta ko? Dariya har ina faɗowa daga kan kujera. "To wallahi ba ki isa ba." Yallaɓai da karfi hali shi wai a dole ban shiga ana kishin sa da ni ba a raina na ce ba kuma zan tusa kaina ba, ai ni tun da na yi karatun namiji na daina ta yar da hankalina a kan shi. Ya gaji da mitan shi ya haƙura domin ni kam ta kaina na ke yi, haƙkin shi dai ina ba shi ina iya bakin kokarina amma ba na rawan jiki da na ƙafa a kan shi. Na gama yin wannan tun a baya yanzu duk abin ma ya fita kaina. To jiya ai ba yau ba. Siyayyya kayan haihuwa komai biyu aka siya dangin Yallaɓai kowa uwar biyu yake kiran Rabi'atu  da shi har Nene fa in ta kira waya sai ta ce ina uwar biyu? Na ce lalle duniya juyi juyi yanzu uwar biyu ce a layi ba mai farar haihuwa ba. Cikin Rabi'atu na wata bakwai ya yi ƙasa ga shi ya girma yana rinjayan ta, ba ta aiki komai da man daga kwanciya sai in za ta shiga makaranta ya ma hana ta driving shi ya ke kaita ko Sadi, Salima na nan tare da ita tana kula da ita amma da wannan ƙaton ciki ba ta fasa zuwa turaka ba tana ganin ƙya shin ta haƙura har sai ta haihuwa na ce yar wahala kawai in dai namiji ne ke ce a baya ba shi ba.  Danginta sun yi maganar a al'adansu gida za ta koma ta haihu megidan ya ce bai amince ba da kan shi ya zo yana faɗa mini na ce Allah ya kyauta ban san yadda suka ƙare ba daga baya ya ce mini in ta haihu an yi suna za ta je can Maiduguri ta yi wanka tun da sun matsa a raina na ce to ni ina ruwana? In na yi magana ya ce ina yi masa shisshigi ni dai iyakata Allah ya kyauta da Allah ya raba lafiya. Ciki na kai wata tara ta daina fita ko'ina saboda ta yi nauyi ba sai an faɗa maka ba kana ganinta sai ka ce amma dai yan biyu ne acikin nan ko? Saboda girman shi ya yi yawa gaskiya Rabi'atu ta zama ɓukekiya ciki ya ma yar da ita babban mace. Edd ɗinta bai gama cika da kwana goma ba aka yi mata aiki ta haihu a wani daran jumma'a.  Da ya kama 13 Nov. 2023. Ni Yallaɓai ya taso ina barci lokacin da ta fara naguda da man cikinta na shiga wata tana ya tara mu ni da Gimbiya ya ce zai riƙa kwana a bangaeen Rabi'atu saboda cikinta ya shiga watan haihuwan shi, ni dai ko a jikina na ce Allah ya ba da sa'a. Gimbiya ce ta ɗan nuna ba ta yadda ba ya shi ba yardanta yake bukata ba shi ya sa ba ma amfanin mganar tun da abin da ya  yi niyya ba zai fasa ba. Ta kasa haihuwa da kanta sai da aka yi mata C.S an fito da jarirai biyu mace da namiji. Kwana muka yi zaume a asibitin nan ni da Yallabai da Salima sai da safe aka fito da ita sannan ya kikkira jama'a ya sanar da su. Da safen na koma gida ni na ke ma faɗa ma Gimbiya da yara Rabi'atu ta sauka an samu yan biyu. Su Baby suna ta murna, Sai da huta can da yamma na koma asibitin Gimbiya ta ce mini sai gobe za ta je shago za ta leka. Ko da na je asibiti ta cika makil da dangin Rabi'atu da na Yallaɓai su Anty Bahijja  ana bakin gadon mejogo ana ta yi ma jarirai hotuna. Faɗi take yi an yi haihuwan da ba a taba yi a gidan Tafida ba haka ta yi posting ma a status. Shi kan shi angon ƙarnin ya kasa sukuni ina jin all contact ya yi wajen tura sakon an yi masa haihuwa saboda yadda yake yini amsa wayoyin yan barka. Washegari tare muka koma da Gimbiya da yamma da yara ai ko ta sha mamakin ganin su Anty Maimuna ana ta rawan ƙafa a gabanta ma sun sake faɗa an yi ma Tafida haihuwan da ba a taɓa yi masa ba ta cika ta yi fam har tana ba su amsa da cewa sai dai a kira su da ƙannen su Khalipa Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya ba aure gare ta ba ta san ita kanwarta ce dukan tsiya za ta yi mata suka bar Gimbiya da tura baki tana ƙwalla ni dai ban tofa ba amma da man na san wata rana itama za ta ji irin abin da na ke ji a can baya. Kwanan Rabi'atu shidda a asibiti aka sallamota suka dawo gida. Yayenta biyu sun taho daga Maiduguri da kanwar babansu Yakumbo ita za ta zauna da ita har bayan suna. Gida fa sai kamshin masu jego, an shirya suna gagarumi tun da haihuwa ce da ba a taɓa yi ba. Kuma mun ga haka mukan mu kowaccen mu 100k Yallaɓai ya ba mu ni da Gimbiya na fitar kayan suna. Jidda ma ta zo gida lokacin ai dole ta zo Yallaɓai fa haka ya dinga kiranta wai ta zo gida ta ga k'annenta yan biyu. Kuma yara sun ci sunan Sulaiman da Aisha. Ya cika alƙawari ya yi ma Alhajinmu takwara. Alhajinmu ko har gida ya taho barka ya kuma turo Gwaggo. Tun da an yi ma ubana takwara ai dole na ware kudi na yi hidima cikin kuɗin da ya ba ni ne na siya ma yaran riga da pampers uwar kuma atamfa na yi mata. Gimbiya dai kayan jarirai kawai ta yi ni kuma ba ni da da man zillewa Yallabai ya gama yaɗa ma Duniya Alhajinmu ya yi ma takwara shi ma can Alhajimmu ya gama yaɗawa shi ya sa kaf yan  gidanmu sai da suka zo barka na nesa su Amina suka kira waya.   Sa guda Yallaɓai ya gada da raguna biyu, shagalin suna abinci ma daga reataurant aka dafo shi. An yi kayan rabo su robobi jaka memo da hotunan yara, Jidda dai ta yi kayan fulawa su cake da donut uban kuma ya ba da kuɗi ta yi har da cake, Rabi'atu kuma ta shiga ta fita da kayan alfarma. Ni dai kala biyu na saka da man ina da su Gimbiya ko da man tana da sutura ina tunanin ba ta yi ma sabon ɗinki ba. Yan uwansu na Maiduguri ba su zo da yawa ba gaskiya saboda nisa sai dai dangin Yallaɓai ne suka cika gidan har da mai kiɗan kwarya su Halima suka kira suka cashe, wata zabiya cikin masu kiɗan ƙwarya tana waƙe mai jego. "Ina mai jegon ta ke ne? Rabi'atul badawiyya farar mace alkyabban mata. Farar mace fitilar gida. Amaryan Yusuf mai yan dubu dubu kin iya haihuwa da kika tashi biyu kika haifa ki shigo fili ki taka domin yau ranar ki ce" Anty Maimuna ta fito da maijego  suna ta mata barin kuɗi sai ga Yallaɓai ya zo gidan zabiya na ganin shi hau yi masa kirari. "Ga ni ga Alhajin Naira. Alhaji yusuf angon Rabi'atu mijin fara baban farare. Mijin mai kyau daga Maiguduri, uban biyu kake dole dai a ce da mijin iya Baba." Nan fa Alhajin naira ya zaro bandir ɗin yan dubu dubu yana ta ɓari waje ya ruɗe da murna da ihu. An yi hotuna mai hoto kam ya haska ya fi kala ɗari, mu dai muna gefe muna mirmishi in ka yi baya ace kana bakinciki Gimbiya tana bangarenta ma ba ta fito ba. Su Anty Bahijja sun kuma haɗa ma Rabi'an kayan suna ya kai atamfa goma ga kayan jarirai ga kuɗi, Mimisco kanta da ba ta kasar suna spain ita da megidanta super ta aiko Naja da shi da less mai tsada. Ana ta ɗagawa ana yabawa,  Baban biyu ma ai ya yi wasa da naira yana da shi yanzu komai ma zai yi ba ya ƙya shi. An yi suna lafiya an gama an yo soye soye kuma duk sun ba mu domin lokacin ma da suka gama sai da suka kirani na ce su dibar ma mejego da mijinta sai na bangaren su da namu bangarem mu dai yan gida gabaɗaya suka dibar mana da yara na dangin Yallaɓai Gwammaja akai tare da yaji mai yawa da turaruka. Na Yallaɓai kam har naman sai da ya kai ma Alhajinmu da kan shi na sunan takwaran shi kuma Alhaji shima za a riƙa ce masa. Alhajinmu haka ya zaunar da ni da na je yana yi mini faɗan na zauna lafiya kar ya ji kar ya gani na zama silar tashin hankalin mijina ai ba ni da ta cewa. Yallaɓai ya gama kama Alhajinmu a hannu da makircin su na maza Macen kuma Ayush za a riƙa kiranta. Tariq ya zo ya ga jarirai ya yi barka haka ma Kawu. Abokan aikin Yallabai duk sun zo barka shi ya sa sai bayan suna da wajen kwana goma Rabi'atu da y'anuwanta biyu da Yakumbo suka bi jirgi zuwa Maiduguri sauran kuma suka bi motar haya da kaya. Sun yi mana sallama da za su tafi muka rabu da faɗin Allah ya sa mu gana. Tun da Rabi'atu ta tafi sai da ta yi wata biyu a gida  sannan Yallabai ya je ya kwana biyu suka dawo tare. Su Alhaji sun yi kiɓa ɓulɓul kamar Yumna tana ƙarama sai dai su farare ne irin su uwar su, bayan ta dawo kuma ta fara ɗan zaga gidajen dangin miji ga shi kuma da man karatunta ma ya tsaya na ji Yallaɓai na faɗin diparing za ta yi. Rabi'atu ta dawo da sarkan ƙafa na kwalliyar mata da hudun hanci Yallaɓai kuma ya ce ya yi mata kyau ta yi kiba ta ƙara yin kyau sannan ta dawo s da wata yarinya Zafira ɗiyar yayarta ce wata kila a wajenta za ta zauna megidan dai bai ce mana komai ba. Satin da ta karɓi girki Yallaɓai kamar zai yi hauka saboda rawan ƙafa, har zuwa ya yi ya same ni wai tun da ta daɗe ba ta nan mai zai hana mu bata sati ɗaya na ce ni na bata sati biyu ma sai dai Gimbiya. Itama ban san Aljanun sukunin da suka shiga kanta ba ta ce su yi ma wata ba ta damu ba ina ga itama ta fara dawowa daga rakiyan Yallaɓan ne shi ya sa aiko ya ji daɗi suka yivta gwangwazan amarci, daɗin da ya ji ne a watan ya sauya ma Gimbiya sabuwar mota balle ma mun shiga sabuwar shekaran 2024 harkoki suna ta budewa. Yallaɓai yanzu sai godiya ya samu kwangila ginin wani kamfani a zaria zai je ya yi kwana biyu ba kwana kwana ya ce Rabi'atu ta raka shi muka ce Allah ya tsare baban biyu da uwar biyu sun fi kwana huɗu sannan suka dawo Jidda ta ce sun kawo mata ziyara ita yanzu ajin ta uku a Jami'a Baby ce ke SS3 Yumna da Ammar tuni an saka su a makaranta. Watan su Ayush shidda Gimbiya ta fara laulayi da azumin watan ramadana ashe ciki ne. Bawan Allah ya yi ta murna domin Yallaɓai na son yara a rayuwan shi. Nima yana ta mini dan biki wai ban gama sai na ƙara ko ɗaya ne, ba ni da sanin gaibu amma sai na ke jin kamar na gama haihuwa tun daga kan Yumna. Itama Gimbiya cikin na ba ta wahala kuma tabbas itama ya kula da ita amma fa uwar biyu da biyunta dabam suke, su ke shan sharafinsu na ɗauka son da yake yi ma su Khalipa na daban ne sai da biyu suka zo na gane su Khalipa ba su ga komai ba in dai gata ne. *Janafty**Ƙarshe* Yau ta kama asabar ɗin karshen mako ne tun bayan da na idar da sallar asuba na koma barci kamar ƴar maye, sakamakon a gajiye na ke, wancan satin muka yi bikin yar gidan Ya Aina ƙanwar Marwa ta biyu, tun da satin bikin ya kama ba mu huta ba muna ta zirga zirga da shirye-shirye, sannan Amarya Katsina muka kaita ni da Ma'u da Rahila muka je, bayan mun dawo kuma aka yi mana rasuwa a Yashe ƙanin Muntarin Rahila ne ya rasu magidanci kwanan mu uku acan sai jiya da daddare muka dawo, na kuma dawo gidan na iske Yallaɓai baya nan yana Abuja kan wani project da man mun yi mgana a waya ya ce mini sai yau asabar yake saka ran dawowa. Barcin gajiya na ke so na yi shi ya sa ma da safe da Baby ta ce za su je Gwammaja su yini na ce ta tattara yaran su tafi gabadaya. Yan biyu kaɗai aka bari wajen uwarsu, Gimbiya kuma ba ta fita kwana biyu megidan ke faɗa mini ta yi ta fama da zazzaɓi sannan itama da ta kira ni ta ƙara yi mini gaisuwa na ji muryanta shake nan take ce mini ba ta da lafiya mura da zazzabi. Jiyan dai da na dawo sun shigo ita da Rabi'atun sun yi mini barka da dawowa. Su Baby na tafiya na rufe kaina a ɗakin barcina na kuma kashe wayata na kwanta ina ta barci ban san meke faruwa ba sai da na ji ana ta buga mini ƙofar bedroom lokaci ɗaya ana kiran sunana. "Umma" Can a cikin barci na ji buga ƙofar bayan na ɗan motsa sai kuma na ji kiran sunan nawa, da hanzari na miƙe zaune ina mutsike idanuwana. "Maman Jidda" Na ji an sake kira sai na diro daga saman gado ina laluban hular da zan rufe gashin kaina, ina kuma tunanin waye? Kamar ban ɗau muryan ba. "Waye? Na faɗa ina isa kusa da kofar, hannuna guda ɗaya ina ƙara tusa gashin kaina da ya hargitse cikin hulan da na sanya yanzu yanzu. "Ni ce" "Salima? Sai da ta ce ita ce na ganeta. Na buɗe kofar lokaci ɗaya ina kiran sunanta. Salima ce ƙanwar Rabiatu. "Lafiya kuwa Salima? Na fada cikin mamakin ganin ta har ƙofar ɗakin barcina abin da ba ta taba yi ba iyakarta falo ko ɗakin Baby. "Anty Rabi'atu ne da Maman Khalifa suke faɗa." Ta faɗa tana haƙi, ai sai na yi sansarai domin kamar an mantar da ni ma ko su waye sai daga baya na fahimci mganarta. "Faɗa? Innalillahi a ina? Na faɗa ina yin gaba sai da ta biyo bayana lokaci ɗaya tana faɗin" A can bangaren Maman Khalifa." Ban tsaya ko saka takalmi ba, daga ni sai rigar barci Allah ya taimaka ma doguwa ce, kuma tana da kauri haka na fito haraba na kwashi gudu zuwa bangaren Gimbiya Salima na bin bayana hankalina a tashe. Ban ɗauka lamarin ya lalace haka ba ni da ta ce suna faɗa na ɗauka cacan bakin da suka saba ne, ashe ashe abin ya yi muni ko da na shiga bangaren Gimbiya a tsakiyar falon ta na iske Gimbiya kan ruwan cikin Rabi'atu tana kilarta, Rabi'atu na kuka tana neman ɗauki Gimbiya ko maruka take kai mata lokaci ɗaya tana faɗin. "Don ubanki na yi miki kama da sa'arki ce? Ni za ki ja da kokuwa? Yau sai na nuna miki bambamcin aya da tsakuwa." Da gudu na yi kan Gimbiya ina salati ina ƙokarin ɗagata amma tana fizgewa. "Subhanallah. Gimbiya me ye haka? Don Allah ɗagata haba mana." Amma ba ta jini ba kai mata duka kawai take yi itama bakin Rabi'atu bai mutu ba. "Allah ya isa muguwa, an ja ki da faɗan ke din banza." Sai da na ce Salima ta matso tare da ita muka samu muka ɗaga Gimbiya daga kan Rabi'atu. "Haba Gimbiya me ya kai ki yin dambe da Rabi'atu?  Ba girman ki ba ne wallahi sannan kar ki manta ba ke kaɗai ba ce fa." Na faɗa ina rike ta, tana haki ta fizge hannunta tana gyara wuyan riganta. "Bar ni Maman Jidda, yadda yarinyar nan ta raina ni gwara da nuna mata ƙyaleta na ke yi amma ba ta fi ƙarfina ba." Lokaci ɗaya tana hararan Rabi da Salima ta taimaka mata ta ɗagata. "Me ya faru ne? Ke Rabi'atu me ya sa wai ba ki jin mgana ne? Kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin" Ai ita ce ba ta da gaskiya daga na zo ina mata mgana shi ne ta shiga zagina." Gimbiya ta tare ta da faɗin" Maƙaryaciya. Yarinyar nan yar bariki ne," "Wai me ya haɗa ku ne? Na fada ina katse su saboda na gaji da hayaniyarsu. "Kan turaka dai Maman Jidda, shekaranjiya da zan karbi girki haka na iske shashen kaca kaca ta fita ba ta gyara ba, ban yi mgana ba na gyara nima ko yau de zan fita na ce ba zan gyara ba na bar mata shi ne da ta je shashen ta gan shi haka ita ishasshiya ta zo har shashena tana faɗa mini mganar banza. Na je na gyara yau Mijinta zai dawo ban isa na kwana da miji ta yi mini bauta ba, ni kuma sai na ce ai bauta ta gama tun da sai da na jagwalgwala na ba ta take suɗewa daga faɗin haka sai yarinyar nan ta ce wai in ban tashi na je na gyara ba zan ga abin da zai faru ni kuma na ce in ta fasa, saboda tsabar ta raina ni kawai ta jawo ni ina kan kujeran nan sai da na faɗo ƙasa ni ko da raina ya ɓaci ina miƙewa na kifa mata mari shi ne ita ishasshiya ta jani da dambe shi ne na nuna mata ba ta isa ba." Gimbiya ta gama bani labari tana faman haƙi Kallonsu kawai na ke yi ina mamaki har yauahe ne za su daina fada kan wancan turakan da Yallaɓai ya samar da ita a cikin gidan nan ne? Shi kamar ma jin daɗi yake yi suna ta kara kaina akansa. Kai na girgiza kafin na ce" Haba don Allah wai mene ne da Turakan nan? Ko da yaushe a kanta ne kuke faɗa? Na faɗa ina kallon su gabaɗaya "Ita ta ja, da ta san ba ta gaskiya me ya sa ba ta tashi ta je ta gyara ba? Kuma ai Abba ya ce duk wacce za ta fita ta gyara abin da ta ɓata." "Ba zan gyara ba, ke da kika fita a gyaren kika bar mini? Sai ke ce mai bakin mgana? To na ƙi na gyara ki ɗau matakin da za ki ɗauka." Gimbiya ta faɗa har tana sake rike kugu, ga cikinta har ya fito amma ba ta ko jin nauyin jikinta. "Za ko ki gani wallahi." Rabi'atu ta faɗa tana cije baki, har ya tasa ga jini a lebenta ta daku, ganin ga Salima a wajen yasa na kalleta ina faɗin" Salima koma bangaren Rabi'atu ki zauna da su Ayush." Sai ta amsani da to ta sake ta Rabi'atu sai ta ce tare za su tafi ni kuma na ce ta tsaya ina da mgana da su ita da Gimbiya sai da Salima ta fice sannan na kalleta ina faɗin" "A wannan rigimar gaskiya ke ce ba ki da gaskiya Rabi'a." "Ni kuma"? Ta fada tana wani tura baki, na ko haɗe rai ina faɗin." ƙwarai  ke fa, ai ke ce ƙarama, yau ko da Gimbiya ce mara gaskiya ya dace ki biyo ta bangarenta kina yi mata rashin kunya? Ban da Yallaɓai da auro ki ya goga kafaɗarki da ta mu ke kin isa ma ki haɗu damu a hanya ki yi mana mgana ballanta har sa'in sa ya haɗa mu? Na fahimci kwana biyu nan kina ji da rashin kunya to ki kama kanki ko ba aure Gimbiya ba sa'ar yin ki ba ce ballatana tana gaba da ke a gidan nan, abin da kika yi ba dai dai ba ne, tun da kin yi itama ta rama ba shike nan ba? Amma saboda fitina sai ki biyo mata har bangarenta ki ja ta da Dambe? Ai gashi nan kin sha wuya gaba ma sai ki ƙara." Kawai sai yarinyar nan ta saka kuka tana faɗin" sai ki yi son kai ki goyi bayan ta ? Sai kawai  ki yi ta mini faɗa akan gaskiyata ai Abba ne ya ce kowa ya ɓata ya gyara." "E an yi miki faɗan, kin yi ba dai dai ba ba za a gaya miki ba? Abba ya ce wacce ta gyara ta bata kema kin ɓata ta gyara itama ta ɓata ba sai ki gyara ba? Da gaske ne ba ki da kunya ki kuma daina wannan halin ba zai ɓulle da ke ba, ni dai gaskiya na faɗa miki." Kawai sai ta juya har tana yi mini tsaki. "Mtswww. Bari Abba ya dawo wallahi sai na faɗa masa." "To in kin fasa faɗa masa kin raina kan ki. Shashaaha kawai." Raina ya baci daga faɗan gaskiya bayan fitan kan ta Gimbiya na koma ina ta mata fadan me ya kai ta dambe da wannan yarinya a ga shi nan ta raina ta nan gaba ko a ina ne ba za ta ji shakkar jan ki da faɗa ba "Da ko da ta daku wallahi kambu" Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" Ba ki kyauta ba me ye sa  kika biye mata ba." "Har fa ɗakina ta biyo ni? Sai na raga mata? Ni haushi ma ya hana ni mgana na bar mata bangarenta na koma nawa, ina barcina sun hanani sukuni, dole na yi wanka na  iske Baby ta soya doya da ƙwai sai na hada tea na ci da shi, ina yi ina tsaki saboda takaici da man kwana biyun can rashin kunya na fahimci Rabi'atu na fama da shi, ba kuma kowa ya ja ba sai Yallaɓai shi ya ja mana wannan wulaƙancin, ya sa ƙaramar yarinya tana ganin ɗaya take damu, ni wallahi daga Yallaban har matan na shi da gidan sun fita daga raina, ina can cikin yan uwana na ma manta da wannan hatsaniyar. Yini na yi a bangarena ban fita ba, har yamma daga Gimbiyar har Rabi'atun ban san isalinsu ba, su Baby sun dawo ba daɗewa sai ga Yallaɓai ni da na ga ma Yamma ta yi ban ɗauka a ranar zai dawo ba sai ga shi, kuma a turakarsa ya sauka, ni kuma ban yi rawan jiki zuwa na gaishe shi ba, ina idar da sallar mangariba na zauna ina duba wayata, Baby da sauran yaran suna shashen Gimbiya. Kawai sai ga kiran Yallaɓai ban kawo ma kaina har Rabi'atu ta kai mganar nan ba sai da na ɗaga kiran na ji shi a fusace har yana yi mini ihu a waya. "Ki zo bangarena yanzu Sadiya." Kuma yana gama faɗin haka ya katse wayar, wayar na koma ina bi da kallo cikin mamaki kafin na furta a fili" Ikon Allah!. Na yi niyyar zuwa a lokacin amma ina miƙewa sai cikina ya karta, shi ya sa na tsaya sai da na shiga tiolet na rage ciki ina fitowa da man na yo alwala jin ana kiran sallar isha'i na tsaya na yi sallata ina yi ko sai kiran wayata ake yi tun kafin na sallame na san shi ne, ban ɗauka ba saboda na san ihu zai yi mini shi ya sa da hijabin jikina na fita zuwa bangaren Yallaɓai. Ina shiga na gan su tsaye a falo cirko-cirko shi da matansa, Gimbiya na tsaye kiƙam rike da kugu shima haka hannayensa a bayan shi yana ta kai gauro da mari a falon Rabi'atu kuma na zaune tana sunne kai, falon na sake bi da kallo kaca kaca, alamun dai Rabi'atu ba ta gyara ba kamar yadda ta rantse. Tun kafin na kariso ciki Yallabai ya tare ni da hargagin shi da ya koya yanzu. "Sadiya ni za ki wulakanta? Ni za ki yi ma wulaƙanci? "Me na yi kuma? Na faɗa cikin mamaki, domin ganin su Gimbiya kawai na tabbatar mini da Rabi'atu ta kai masa labarin abin da ya faru ɗazu. Ni ko ina ruwana da zai sako ni a ciki don Allah? "Ban sani ba. Na ce ban sani ba kar ki raina mini wayau kin ji ko? Kallon shi na yi ganin shi a fusace kamar yana jirana ina kokarin danne abin da ke taso mini na ce" Gani ina fatan lafiya? "Ko lafiya lau ya dace na kira ki sama da minti talatin ki shanya? Kin kyauta kenan? Ina yamutsa fuska na ce" Ka kirani ina shirin zuwa cikina ya motsa na shiga makewayi, bayan na fito na ji ana kiran salla shi ne na tsaya na yi salla, ban ɗauka ai kana jirana ba ne" Na faɗa ina mai zaman kan kujera mai zaman mutum ɗaya domin na gaji da tsayuwa. Kasa mgana ya yi yana kallona ni ko na haɗe rai domin na yi alƙawarin yau ba zan yarda na ɗaukin renin wayau Yallaɓai da matan shi ba wallahi, gwara na tsage musu gaskiya in ba haka ba zai san ina yi mishi kawaici da kara ba ne. Ya gama cika yana batsewa sannan ya kalleni kafin ya ce" Me ke faruwa ne a cikin gidana wanda ban sani ba? Na yi kamar ban ji ba, saboda sai na ga tambayar ba ta shafe ni ba, tun da ya ce gidan shi a matsayin shi na megida ya saka ido mana ni ina ruwana. "Da ke fa na ke mgana Sadiya kin yi mini banza" "Ni? Na faɗa ina nuna kaina. "Aa ni " Ya faɗa a fusace, ban bari ya sake ɗauko wata mgana ba na tare shi. "To ai na ga tambayar kamar ba tawa ba ce shi ya sa na yi shuru. Gidan nan fa naka ne in ma wani abu na faruwa kai ne shugaba kai ya kamata ka fara sani ba ni ba" Wani kallo ya yi mini kafin ya ce" To na ji ni ina yini a gidan ne? Ke ce walikiyata duk abin da ya faru ki tsaya ki wakilceni in na dawo kuma ki zo ki sanar da ni." "Ko? Na faɗa ina kallon shi, sai ya kasa mgana su kuma sun yi shuru suna jin mu. "E shi ya sa yau kika ɓata mini rai, ya za a yi har a yi dambe a gidana ba ki kira ni kin faɗa mini ba? Sannan kuma kika yi hukunci har kina zagin Rabi'atu kina cewa ita ce ba ta da kunya? Ita Gimbiyar kin binciketa kin san abin da ta yi mata har ta kai su ga Dambe? Ya faɗa yana kallona ni baki na saki ina kallon shi, na jinjina kai na juya ina kallon Gimbiya itama sai ta kalleni baki a buɗe. "Koma me ta yi mata ya dace ta yi dambe da ita! Sa'arta ne? Ban da siyar ma da kai mutumci, ji yadda ta kumbura ma matata baki? Koma me ya faru ba za a iya jirana na dawo ba ne? Ya faɗa yana tsare ni da ido, mamakin shi na ke yadda idanuwanshi suka rufe akan Rabi'a.. "To ni yanzu me ye nawa a cikin wannan mganar? Na tambaye shi ganin kamar ni ya fi jin haushi. "Naki shi ne ba ki yi hukuncin kan gaskiya ba, kin goyi bayan Gimbiya tun da kuna tare, sannan ni ba ki kirani kin gaya mini ba? Kin kyauta kenan? Girman kenan? Na buɗe baki haa ina kallon Yallaɓai Gimbiya ta saki sheewa ta tafa hannu ni ko na ma kasa mgana tsabar mamaki. "Ni fa Abba abu ɗaya ya yi mini zafi, wai Maman Jidda ta ce ina yi musu rashin kunya! Kuma ni wallahi ba wacce cikinsu na ke yi ma rashin kunya Maman Khalifa ce yau daga zuwa na yi mata mgana ta fara zagina" Ta karishe faɗa har tana shessheƙan kuka, kawai sai Yallaɓai ya juya wajenta yana faɗin" Ki yi shurun ki ai na san halin kowa a cikin ku, tun tuni ba ki yi rashin kunya ba ne sai yanzu? Da man ita Saudatu fitinnaniya ce, na san za ta aikata ita kuma Sadiya ban san ta da bangarenci ba sai yau, amma duk zan yi mganin abin yanzu nan." Ya faɗa yana nuna mu da yatsa, a kausashe, Gimbiya ta sake sakin shewa kafin ta ce" Za ka sake mu ne? Shi ne karshen mganin mu da ka ce za ka yi ko? Ta faɗa tana tsare shi da ido, shi kuma sai ya taso mata tana faɗa yana faɗa, har yana ce mata hakuri kawai yake yi da ita darajan iyayansu. na gaji da hayaniyar sai na saka baki. "Don Allah ku yi hakuri wannan fa ba girman ku ba ne." Daga ba da hakuri kawai nima Yallaɓai ya dawo kaina yana yi mini masifa. "Ai duk laifinki ne, haɗa kai kuka yi za ki kashe mini mata ko? Don kun gan ta yarinya ko? Ban san na mike ba sai da na ganni tsaye kan kafafuwana. "Dakata."! Na faɗa da karfi ina ɗaga ma Yallabai hannu idanuwana har rufewa suke yi saboda bacin rai da bakin ciki wallahi tun da bai san ina yi masa kara ba yau sai na yi ma yallaɓai wankin babban bargo. "Ka dakata Yusuf.." Na sake faɗi cikin ɗaga murya, saboda raina ya baci zuciyata ma tafasa take yi a lokacin. Ba shi ba, har matan na shi tsayawa suka yi suna kallona saboda mamakin tsawar da na daka masa. "Ni kike yi ma ihu Sadiya?? "An yi maka Ihu, an yi maka ihun Yusuf ka yi abin da za ka yi don Allah Haba." Na faɗa ina yarfa hannu, bayan na nuna shi da hannu, sai na ga kawai ya tsaya yana kallona cikin mamaki. "Maman Jidda yau ba Yallaɓan? Gimbiya ta faɗa cikin mamaki. "Na bi yallabai da gudu, haba ka isheni a cikin gidan nan da fitinarka, na yi maka shuru na yi maka shuru amma na fahimci ba ka san kara ba, kuma ba ka san ina yi maka kawaici ba, to wallahi na gaji, na gaji da jidalinka da na matanka na gaji Yusuf" Na ƙarishe faɗa ina ƙara daga murya saboda a lokacin ji na yi zuciyata ta yi duhu ko gani ma bana yi saboda bacin rai. Sai falon ya yi shuru ganin na harzuƙa. "To yi hakuri zauna mu yi mgana." Yallaɓai ya faɗa cikin sigan lallashi ganin yadda na taso masa ya san halina in na fusata ba ni da kyau. "Ba zan zauna ba, lokacin da na ke zaune ba ka so a yi mganar cikin laluma ba, yanzu sai dai kai ka koma ka zauna ka saurareni domin ni ce zan yi mgana." Ban jira cewarsa ba na cigaba da faɗin" Yusuf auren soyayya ne a tsakanina da kai, a shekarun mu har zuwa matakin yau ba ka taɓa fahimtar cewa ina yi maka kara ba ne? Ba ka taɓa jin cewa a ranka kana yi mini wasu abubuwan da suka yi kama da cin fuska ina kyaleka ba! Mene ne ba ka yi mini ba, mene ne ba ka faɗa mini akan auran ka da Gimbiya ba? Wani baƙincikin matanka ne ban ƙunsa ba? Wani takaicin yan'uwanka ne ban ƙunsa a cikin zuciyata ba? Mun yi aure tun ba ka da komai muka yi gwagwamaryan arziki tare, daga baya da me ka saka mini? Ka yi mini gorin haihuwa na yi haƙuri, ka yi mini na gida na yi hakuri, ka yi ta mini alƙawaruka amma ba ka cika ba, na yi maka mgana? Ka nuna mini bambamci a kan matanka na taɓa yi maka mgana? Ka goyi bayan yan uwanka a kaina na yi maka mgana? Gimbiya ta yi mini abubuwa ta ci kasuwa a kaina kala kala amma duk ban ɗaga kaina ba, saboda kai Yusuf. Saboda karan da na ke yi maka, shi ya sa duk kake yi mini wasu abubuwa ba na ɗaga kaina, ba wai don bana jin zafi ba ne, sai domin ina kauda kai saboda kai, saboda ina daraja zaman mu da kai, ina daraja auran mu da soyayyarmu, ina kambama tarbiyan da iyayena suka ba ni, sabo da ina girmama bautar ubangijina, ka danne mini haƙƙi, ka yi mini wulaƙanci akan matanka, ka tozartani a kan su na taɓa yi maka mgana? Ka taɓa zama ka yi tunanin abubuwan da kake yi mini rashin kyautawa ka ware rana ɗaya ka ba ni haƙuri? Don ina matarka uwargidanka sai na zama bolarka, don ina haƙuri da kai sai na zama mazubin sharan da kai da matan kuke zuba duk dattin ku a kaina? Ɗauka ka ke yi alfarma ce ka ke yi mini da na ke zaune da kai? Wallahi tallahi na rantse da wanda raina ke hannun shi Darajan aure ne, bautar ubangiji ne ya sa na ke raga maka, amma ba domin haka ba wallahi tallahi ba ka isa na zauna kana cin kasuwa a kaina ba. Ba ka isa ba Yusuf ba ka isa ba wallahi, daga kai har waɗanan matan da ka ajiye a cikin gidan ba ku isa ba." Na karishe fada ina nuna shi da yatsa manuniya, bayan shi suma na nuna su ɗaya bayan ɗaya cikin baƙin ciki, domin gabaɗaya na rasa control a kan ɓacin raina ji na ke yi auran na Yusuf kwata kwata ya fita kaina da gidan shi da matan na shi duk na yi nisa da su ko zan samu salama da kwanciyar hankali. Na sake buɗe baki in yi mgana na kasa Kuka ne ya taso mini da ya sa na kasa ƙarisawa, su ko gabaɗaya sun yi shuru sun kasa mgana dukkansu sun nemi waje sun zauna saboda mamakin maganganuna. Ina da tabbacin ko shi da muka kwashi shekaru tare, bai taɓa ganina na yi masa hauka ba, sai yau balle su da suke baƙin ganin ɓacin raina. Ina kuka na cigaba da faɗin. " Sha'anin matanka da komai na su ka sanyani shiga ciki, na shiga saboda ina yi maka kara, lokacin da za ka auro Rabi'atu ka yi abubuwa ba domin na kauda kai ba da ba za mu kawo yanzu ba, ka aurota ka ce na ja ta a jikina na bi umarninka, in ba domin kai ba ita ta isa ne? Ba ta isa ba amma saboda ina yi maka kara bana daga kai akan komai da kake yi mini a cikin gidan nan, ita kanta ta sani bana kishi da ita kamar Jidda na ke kallonta amma ita ka tambayeta ni kamar uwar jidda take kallona?? Ka bata dama tana cin kasuwa a kaina, duk bai isheka ba sai kaima ka zo ka ci kasuwar ka a saman kaina? Komai ya taso na matanka sai ka danganta shi da ni? Ina ruwana a ciki? Na san an yi? Ba sai da suka yi faɗansu sannan salima ta zo ta faɗa mini ba? Ka ce na yi son kai na shigar ma Gimbiya saboda muna tare, ka ce mun taru za mu kashe maka mata, Yusuf kai kake faɗin haka? Da bakin ka? Yau ko ba auran ka a kan Gimbiya ya dace Rabi'atu ta yi faɗa da ita? Sa'arta ce? Balle tana gaba da ita a shekaru, tana gaba da ita a wajenka da gidan nan, in har ina da mutumci da daraja a wajenka ya dace a gaban matanka ka kirani kana yi mini ihun cewa ban yi adalci a kan matanka ba? Ya dace? Me kake nuna musu? Ban da daraja kuma cewar da kake yi ni ce wakiliyarka duk karya ce tun da kalamanka na yanzu sun bayyana yadda ka ɗaukeni." Na dakata ina sauke numfashi, saboda ina mgana ne zuciyata na zafi saboda bacin rai murya ta har ta dishe saboda kuka. "Sadiya ki bar mganar nan ki yi hakuri kin ji ko? Yallaɓai ya faɗa cikin lallashi har yana tasowa zai rikeni na matsa baya ina mai ɗaga masa hannu lokaci ɗaya ina faɗin. " Ba mganar hakuri ba ne, hakuri ai na yi shi da ban yi ba, da ba ka ganni zaune a gidanka ba. Da a ce ina riƙe da irin cin kashin da kake yi mini na rantse da Ubangijina da tuni wata rana ka wayi gari ka ga bana cikin gidan ka. Kawai ina so ka san cewa kawaici na ke yi maka, kuma shi ne kuskure na, yau da ban nuna maka zan ɗauka ba, da duk wannan cin mutumcin bai biyo baya ba." "Don Allah ki yi haƙuri." Ya faɗa cikin lallashi kamar zai yi kuka, ashe karyan iskanci ne abin na shi. "Ki yi hakuri Maman Jidda." Gimbiya ta faɗa jiki a sanyayye. "Ki yi hakuri." In ji Rabi'atu ita kanta jikinta ya yi sanyi. "Ba komai ni ce  na yi sakacin da komai ma ya faru. Ni na sabama Yallabai da hakan shi ya sa ba ya jin shakkar yi mini ihu akan matan shi, amma ina so ku sani daga yau sai yau, ba ruwana da abin da ya shafe ku, kai ma kar ka kara sakani cikin sha'anin matanka, mganar ni ce wakilayarka ba ta, gida na ka ne dukkanmu muna karkashinka ne, kar ka sake kirana akan su ko ka ce za ka yi mini ihu ko ka faɗa mini mgana nima ba zan sake shiga hurumin su ba, duk kawaicin da na ke yi maka na daina domin na fahimci baka daraja haka." Ina gama faɗin  haka na juya da gudu na bar falon ina jin sa ya biyo ni yana kiran sunana ban jiyo ba sai da na fita haraba na saita kaina har na kai bangarena duhu duhu na ke gani saboda bakinciki, ina shiga na kulle kaina a bedroom ina ta kuka, ya zo ya yi bugu yana yi mini magiyan na buɗe ban buɗe ba, har Gimbiya ta so itama da magiyan na yi hakuri na buɗe itama na yi mata banza Baby ta zo tana kirana da Umma ki yi hakuri ki bude itama na yi mata banza, har Jidda dake makaranta ina jin Ubanta ne ya kirata ta yi ta kirana a waya ban ɗauka ba, kukana na sha, har na koshi sannan na lallashi kaina da alƙawarin  Yallaɓai ya gama cin kasuwa kaina in dai akan matan shi ne. Sai da safe na buɗe kofa na fito fuska a kumbure, Yumna da Baby suna rige rigen gaisheni fuska ba yabo ba fallasa na amsa, ba su zauna ba suka shirya direba ya kwashe su zuwa Tahfez tun da jiya ba su samu zuwa ba. Tea kawai na sha, na koma falo na kwanta, da na kuma san Yallabai zai shigo mini da ɗaki zan koma amma sai ya ritsani, Yallaɓai duƙa mini yayi har ƙasa akan gwiyoyinsa yana bani hakuri faɗi yake yi "Ki yi hakuri Sadiyata. Wallahi na san ina yi miki wasu abubuwan na kure hakurin ki amma baki taɓa mgana ba. Na sani kina yi miki kara da kawaici ban kyauta ba don girman Allah ki yafe mini." "Ai da ba yafiya Yusuf da ban sake kallonka ba,  da ban sake ba ka wata dama ba kawai ka kiyaye kar ka ƙure ni na yi abin da ban saba ba." "Ba zan kure ki ba in sha Allahu. Ki yafe mini Sadiyata" Duk yadda ya so bai ga dariyata ba, da gaske na ke yi na daina yi masa alfarma kuma ya san haka shi ya sa ya ruɗe, bayan fitan shi sai ga Gimbiya itama hakurin ta yi ta bani. "Ba komai fa, abin da ya wuce, wani abun ai da ba a hakuri da ba a kawo wannan matakin ba maman khalipa" Itama Rabi'atu ta zo tana bani hakuri itama na ce mata ni ba komai, domin in da ban yi hakuri ba da ba ta zo ta iske ni ba, tun daga ranar na tsame kaina daga sha'anin Yallaɓai da matan shi, kuma daga lokacin na samu sauki daga shi har matan na shi suka fara shakkata domin gabaɗaya na dauke musu wuta, ashe da gangan ne Yallabai ke yi mini wulakanci sai da na buɗe bakina na yi mgana na fahimci yana sane da abin da yake yi, tun daga ranar na shata masa layi sai na zauna lafiya ya kiyayeni suma suka kiyayeni, kuma abu in dai ya shafeni yana rawan jiki, suma haka matan na shi, saboda yadda na fidda kaina daga duk abin da ya shafe su na gyara kuskuren da na yi sakaci tun farko. Aka ce mai hali ba ya fasa halin shi, ya riga ya saba da kwaso mini ko wata mgana amma yanzu da ya zo ya fara, kallo kawai in na yi masa zai shiga taitayinsa, in ma ban kalleshi ba, banza na ke yi da shi har ya gama ɓaɓatun shi kanzil bana cewa, in ya gaji sai ya ce Sadiya ta ba ki ce komai ba! In ma na ɗago na yi masa wani sakaran shi da kan shi ya ke kama kanshi ya tashi yana kame kame,  wallahi aure bauta ne ba domin bautar ubangiji ba da Yusuf bai isheni kallo ba wallahi. Shima ganin yanzu ya fita zuciyata shi ya sa duk wani abu na kyautatawa ba wanda ba ya yi mini. Ni ce wai Yallaɓai ke yi ma tsaraba in ya fita bini bini Sadiya ta ko kina son wani abu? Kafin na yi mgana ya yi mini alheri jikinsa na rawa da zuciyarsa a kaina ni ko bai san na riga na gama sanin shi ba ba kuma wani yaudaran da zai zo da shi ya sake ruɗata. Ni dai tun da sun kiyayeni daga shi har matan shi shike nan na samu salama da zaman lafiya. ***** *BAYAN SHEKARA ƊAYA DA RABI.* NOVEMBER. 2025. Alhamdulillah Rayuwa ta miƙa Ubangiji ya ara mana dama. Ya ba mu rai da lafiya sannan ya azurtamu. Ba abin da za mu ce sai godiya ga Ubangijin mu. Yau da jiya da gobe ba su bar komai ba tun muna kirga kwanaki mun koma na wattani ga shi muna kirga shekaru ashirin da huɗu cikin na biyar da auren na da Yallaɓai. Rayuwa ta zama sai godiya kawai mun faro gwagwamarya kuma ba za ta kare ba har mu koma ga Allah amma dai muna fatan ko da yaushe mu yi kokuwa da matsalar mu mu ga bayan ta ba wai ace ita ce za ta ga bayan mu ba. A halin yanzu shekaruna na haihuwa arba'in da biyar Yallabai kuma girma ya zo an gangangara gidan hamsin da biyu har da ɗoriya. Rayuwa ba za ta koma jiya ba sai ta yi ta gaba kana karuwa a fuskantar yarintarta ka. shekarun mu sun mika amma kuma mun samu wadatar rayuwa sai godiya. A shekara ɗaya da rabin da suka gabata abubuwa na alheri da aka sin sa duk sun faru amma na alherin da farincikin sun fi yawa. Gimbiya ta haihu ta samu yarta mace ta ji sunan Hajiyar Tafida. Ahalin yanzu ma Rabi'atu ta na da ciki kimannin wattani biyar. Tuni har ta yaye yan biyu tun da suna cikin shekaru na biyu ne. A gidan Yallabai tsakanin Gimbiya da Rabi'atu ne ake gasan haihuwa da kishi ni kam na koma gefe na zama Umma, sai dai na ba da shawara ko na raba in na ga abin da bai kamata ba. Na yarda na amince ina da wani hali da ba zan iya barin shi ba, duk yadda na kai ga kauda kaina ga sha'anin Yallaɓai da matan shi in na ga abin da bai kamata ba, ba na iya shuru sai na tanka, na ɗauki hakan a matsayin hallita ce ta Ubangiji, ba ni da riƙo sannan kyakyawan zuciyata ba ta barina na daɗe ina jin haushi wani a cikin zuciyata. Yallaɓai har gobe bai dai na faɗin bai cire rai ba bai kuma haƙura ba yana fatan bayan Yumna na sake haihuwa ni kuma na kan ce masa na gama. Ga su Gimbiya nan dai su yi ta cika mana gida da yara Alhmdulillah.  A tsawon zamana da Yallaɓai ya yi mini tarin alhern da suka goge sharrinsa a wajena amma babban abin da ya yi mini da ya ƙara samun daraja a cikin zuciyata shine ya biya mini kujeran makka a wannan shekaran na je na sauke farali sannan ina dawowa na yi cukun_cukun buɗe shagon Saloon ɗin da na ke buri, domin na fahimci Yallaɓai ba zai iya cika mini alƙawari ba, Musbahu na saka a jagoranci sai dai Yallaɓai ya ji labarin an kama shago a wajen ƙaninsa domin ni ban faɗa masa ba, sai ga shi ya zo yana borin kunya shi da man yana da niyyar da na dawowa daga Saudiya ya buɗe mini shago shi ne target ɗin shi, har yana faɗan me ya sa na yi masa haka? Ni ko na ce kar ya damu ba komai ai na san abubuwa ne suka yi masa yawa, ba na ce ban gode masa ba ne na gode tun da ya yi sanadin da na je ɗakin Allah, amma mganar buɗe shago bana son tunawa saboda tsabar renin wayau da renin hankali Yallaɓai ya yi mini shi, tun yaushe? Mgana ce tun auran mu, yana da shi ba wai ba shi da shi ba ne, kawai bai yi ra'ayin cika alƙawari ba ne shi ya sa na kuɗiri niyyar sai dai ya ga ana yi, da jarin hijabaina da kudaɗen hannuna na haɗa na kama shago na yi siyayyan wasu kayan shi kuma Gogan sai ya ji kunya ya dunkule 800k ya bani da na ce ma ba zan karɓa ba wajen Alhajinmu ya kai ni kara shi ya tursasani na karɓa sannan a ɓoye ya saka aka yo mini oder ɗin kujeru da sauran kayan injinan shagon sai dai na ga an kawo sannan ya shiga ya fita sai da aka gyara shagon nan ya ga komai ya kamallah, har yana yi mini mganar ko zai kama mini wani babba ne! Ya ga kamar wannan ya yi ƙarami na ce na gode ƙaramin ma ya ishe ni. Gabaɗaya dai kunya ta hana shi suƙuni ni kuma ko a fuska ban nuna masa ba, shi ne dai ya san bai kyauta ba yana ta kame kame na yi banza da shi. To ni Yallaɓai ai ya daina damuna, na tattarashi da sha'aninsa na watsar tun a baya. Da shago na ya kamallah mai suna S.S YASHE BEAUTY SALOON. Na yi Farinciki da ban san iyaka ba da man ina cikin farimcikin ne na je na ga ɗakin Allah A shekaran tare muka je da Alhajinmu Hajji da Ya Hamza da Ya Auwal suka haɗa kudi suka kai shi sai Ya Usman da Anty Zabba Allah ya taimaka a masauƙi ɗaya muka sauka. Yallabai ya girmama ni tun da ya ce ni ce uwargidan shi ni zan fara zuwa amma daga baya ɗaya bayan ɗaya zai kai su Gimbiya. Suma ɗin ba su nuna damuwar su ba sun yi fatan Allah ya sa suna da rabon zuwa ita Gimbiya ma ta taɓa zuwa Umra tsohon mijinta ya taɓa kai ta, Yallaɓai ma a shekarslan da ya biya mini ya je Umra ya dawo. Kamfanin Yallaɓai ya shahara fiye da tunanin mai tunani yanzu haka yana ma shirye-shiryen buɗe reshe ne a jihar Kaduna. Yanzu in dai kamfani ne na gine-gine da zane-zane in sunan kamfanin Yallabai bai shiga gaba to zai jera a na biyu. Dukiya kam ya nema da aiki tuƙuri kuma ya sa mu, yanzu haka dukkan mu ya siya mana sabbin motoci, ni da Gimbiya da Rabi'atu ni tawa Ta kamfanin toyota ne, tawa kuma ta fi tasu tsada ni fara ya siya mini. Na su kuma na kamfanin camry ne, duka kalan ruwan toka. Sannan can Gwammaja an sake gyara gidan an ƙawata shi ya siya ma Nene mota har da direban da zai riƙa zirga-zirga da su ya ɗaukan musu. Ba abin da suka nema suka rasa sai godiya. Munnira Nasir ya samu aiki a Taraba ya koma can daga baya ya zo ya ɗauke mana Munnira suka koma can sai dai mu yi magana ta waya. Daga ni sai Hauwa da itama Alhamdulillah Mutaƙƙa ya samu buɗi da rufin asiri. Duk sun sake haihuwa har Marwa yanzu yayanta uku ta zama uwar mata. Datti ma matarsa ta haihu gidan mu na ɗorayi shashen farko su Ya Hamza sun rushe shi sun gina shashe mai kyau in da suke sauka da iyalansu in sun zo. Cikin gida ma komai ya sauya Gwaggo ta na nan kwance ta samu ciwon ɓarayin jiki Baaba ce ke kula da ita amma Alhajinmu har gobe yana nan da ƙarfinsa. Ma'u ta sake haihuwa amma ta samu matsala har sai da aka cire mata mahaifa ta fi wata a asibiti tana jinya daga baya ta ji sauƙi ta koma gida. A yashe mun yi rashi shima Baba Aminu mun rasa shi mahaifin Ya Muntari rayuwa sai godiya. Bayan rasuwar Baba Aminu ko wata shidda ba a yi ba mahaifiyarsa ta saka shi ya auro ɗiyar kanwarsa tana nan gida ɗaya da Rahila. Auran da ya sha mganganu ita kanta Rahilan har cewa ta yi sai Muntari ya zaɓa ko ita ko amaryan da zai aura. Da nasihan Alhajinmu da shawarwarin irin mu Rahila ta haƙura domin na sha faɗa mata ta yi haƙuri wata rana za ta ci riba.  Su Ya Aina kowa sai hamdala rayuwa ta yi kyau ana lallaɓawa. Amina ma ta sake haihuwa ƴaƴanta biyar kenan tana zaune cikin farinciki da mijinta. Ya Abubakar ma ya ƙara aure tun da shima ya kama babban aiki yanzu ba gida ɗaya suke da Amaryan ba tuni Zaituna ta shiga taitayinta ta gyara bayan lokaci ya kure mata. A yanzu haka Jidda na Aji huɗu ne za ta je biyar a jami'a. Kuma tana da shekaru ashirin da huɗu ne, an sanya mata ranar aure shekara mai zuwa ita da Uncle ɗin kawarta Ummu Salma auta ne a ɗakin mamanta. Sun yi bikin yayar Ummu salman Jidda ta je musu biki anan ya ganta. Abdullahi pilot ne matukin jirgin sama ne. Kuma ba jira ya nemi soyayyar Jidda ta amince ganin duk abin na gida ne an zama ɗaya tun da har bikin na je  ni da Baby sai ya gabatar da kansa a wajen Yallaɓai. Sai ga shi Yallaɓai na zuwa da wata magana wai ba yanzu zai aurar da y'arsa ba sai ta gama makaranta. Ƙiri-ƙiri fa yana abu kamar wani ɗan fari ni ko ganin zai yi mana salalan tsiya ga Jidda na son abin ta na kai shi ƙara wajen Ya Usman kai tsaye ya ce na ba ma yaron lambarsa ya neme sa. Ai sai dai Yallabai ya ji labari daga baya Uban Jidda Alhaji Usman ya ba ma Abdullahi dama ya cigaba da neman Jidda. Ba shi da bakin mgana balle da Tariq da Kawu suka ji labari kamar su tsire shi, suka ce ya yi musu katsalanda ina ruwan shi ai sune ma su ba da auran yar su. Hakan ne ya sa ya koma gefe ko maganar auren da saka ranar Ya Usman ne da su Kawu anan Kano ya zo aka karɓi maganar a Gwamnaja aka saka rana wattani goma ma su zuwa. Baby da ta ke aji ɗaya a BABA AHMAD UNIVERSITY KANO tana da manemin ta. Shi kuma yaron ƙanwar mijin Mimisco ne likita ne an asibitin Aminu Kano. Shima Yallaɓai ya fara faɗa wai Babyn nawa ta ke? Ba ta isa fara samari ba shima sai da na yi masa ido da ido sannan ya bari Hafiz na zuwa duk Weekend suna ganawa da Baby tun da na gida ne amma fa ya sha sharuɗɗa kamar zai auri wata gold Yallaɓai fa ya ƙaro wulakanci wai shi nan haushi ya ke ji duk za a tattare mai ya'ya lokaci ɗaya. Ina dariya na ce wanzami ba ya son jarfa shi amma ya tattare ya'yan mutane a gidan shi? Sai an yi mgana ya ce ƴaƴan shi ba su isa aure ba sai sun gama karatu. Su Musbahu suna nan an zama magidanta Mubeena ya'yanta biyu. Ga Adnan ma yan baya baya matarsa ta haihu shima. Rayuwar gidan Yallaɓai sai abin da ya yi gaba. Domin Rabi'atu mace ce mai tsananin kishi har ta ce ma Gimbiya ba ta iya kishin ba, ga ta da wayau da iya bariki, duk yadda Yallaɓai ya kai ga bacin rai a kanta ta san lagon sa. Ita kuma Gimbiya abin da ke cutar ta har yau rashin haƙurin ta ne da shegen saka baki a komai na yi na yi na raba ta da wannan halin na kasa sai na koma na zura mata ido. Ba sa sati ba su yi cacan baki ba lokacin ma ina Saudiya har Dambe suka yi Yallaɓai bai faɗa mini ba amma ita Gimbiyar da kanta ta faɗa mini. Kuma wai a kan yara ne ita Rabi'tu mace ce mai ƙulafucin ƴa'ƴa ba mai taɓa mata su a gidan nan ya zauna lafiya. Kuma suna ƙananu dole kan manya su taɓa su, masu taɓa su Yunma ce da Ammar iyayen mugunta ni wallahi ko suna yi ba na bi ta kansu ina bangarena Gimbiya ce take fitowa suna tanka tanka. Ga y'an biyun nan da tsiwa da tsokana su kuma su Yumna ba ɗaukan reni sai dai ka ji sun make su. In Rabi'atu na makaranta suna gida ƙanwarta Salima na wajenta tana makaranta tare da su Khalipa in tana gidan itama kamar yayarta ba ta bari a taba su in kuma yayar ta dawo ta faɗa mata ita kuma saboda rashin tunanin sai ta zo ta ce za ta rama musu. An ce hakan ce ya janyo faɗan Rabi'atu ta biyo Ammar har ɗaki wai za ta rama ma Ayush ya daketa. Gimbiya ta ce ba ta isa ba ta kai hannu za ta dake shi Gimbiya ta tare dukan ya sameta daga nan ta ce ita za ta daka ta saka hannu ta mareta sai Dambe. Yallaɓai na zuwa ya ce kowaccen su ta je gida shi gidan shi ba gidan Dambe ba ne shine suka je Gwammaja acan Nene ta kashe faɗan. Kowa ya san Rabi'atu ce ba ta da gaskiya amma su Anty Bahijja ita suka goya ma baya saboda ta kama su a hannu ta riƙe gam! Kamar ta yi musu sujuda shi ya sa in suka zo gidan nan wani abu ya faru shashenta suke shiga Gimbiya ce ke bin su can ta gaishe su ni dai ko sun ƙi ko sun so na zama turken gida  a gidan Yallaɓai ba su da yadda za su yi da ni. Sun buga da ni sun gaji sun bar ni, na san ba zan taba fari a idanuwansu ba, nima ban matsa ma kaina sai sun so ni ba, da man ba kowa ba ne zai so ka, wani har gaban abada ba ya sonka, sai dai in ya gaji ya hakura da adawa da kai in ya ga kafi karfin shi. In sun zo gidan  Har shashena za su leko sannan mu gaisa tun ballatana da suka fahimci ni yanzu ba na ta kansu sabgogina sun sha gabana. Rabi'atu Da Gimbiya sune faɗa kan turaka ƙananun mganganu dai ba sa ƙarewa. Ni kenan kullun ban hakuri ko faɗan aka yi in Yallabai ya dawo ko da Rabi'atu ce ba ta gaskiya ta iya lauya in ana ma yar da mgana sai dai ta zauna kanta a ƙasa tana kuka ita ko Gimbiya harshe a sama shi ake  cutan ta Yallaɓai kuma ya tsani yana mgama tana mgana yanzu zai harzuƙa kuma da man kuranta ta yi kuka a wajen shi ya riga ya making ɗin ta a matsayin mace mai fitina, in kuma ranar da ya ke jin tsiya ne sai ya ce har da laifina wai yanzu ba ni da amfani a gidan  ni ko ta kan shi ba na bi, to lokaci da na ke gidan kenan da na fara fita shago nima ba na gidan ban san sun yi ba, Kuma sun fi yi da daddare tun da Gimbiya ma na zuwa shagon ta itama Rabi'atun makaranta ba yini muke a gidan ba sai dare ya yi in sun haɗu a yi ta hararan juna. Ni wallahi dariya ma suke ba ni, Gimbiya ce duk ta bi ta raina kanta shi ya sa Rabi'ar ta raina ta Yallabai da man tuni ya dawo rakiyarta tuni aka daina kiran Daughter Saudatu ne itama Baban Khalipa ko Baban su Jidda. Ita kam Rabi'atu Abba ne ko Yallaɓan mu ni kuma da man yara da su kan su Umma ne har Gimbiya yanzu Umma ta ke kirana har Yallaɓan ma in yana jin nishaɗi Umma Sadiya ya ke kirana in kuma zai kirani har yau har gobe Sadiya ta ne ko abar ƙaunata nima ko shekara ɗari ya yi a duniya ba zan iya daina kiran shi da sunan Yallaɓai na ba, domin na riga na saba. Matsalan da ke faruwa yanzu shi ne ita Rabi'atu tana ware ya'yanta tana nuna kamar dabam suke, shi kuma Yallaɓai ba zai aminta da haka ba ya yi mata faɗa ta ƙi dainawa ya faɗa mata ya'yan shi duk ɗaya ne kar ta zo ta nuna bambamci ta raba masa kan yara amma ba ta jin mgana. Ko a cikin satin nan sai da Baffanta ya zo kwana biyu ta hana yara fitowa a bangarenta take kulle su suna son fitowa su yi wasa da y'an uwan su ta ki barin su. Tun ballanta sun saba da wassanin su a haraba har raga na ƙwallo Yallaɓai ya saka aka saka musu a haraba in yana gida Weekend zai ta wasa da su shi ne su yi ƙwallo wasan gudu, chinese wasan ɓuya to yaran sun saba da wassani ko baya gida za su fita haraba su yi ta yi. Yunma ma da ke mace  in ta ware kafa ta kai duka kamar wata namiji Yallaɓai duk ya gama koya ma yara wasan banza ko a jikin shi, mu kan mu in za mu fito zai so haka tuni ya ce mu riƙa fitowa muna rage kitse na ce ni kam ya ƙyaleni da kitsena. Ni ban ma kai su Gimbiya kiba ba su ne sun zama wasu Hajiyoyi da su ni dai na san na yi kiba amma ba ta yi mini muni ba, ko don bana haihuwa ne su kuma suna haihuwa da wannan ta sauke wannan ta ɗauka sun ma yar da abin na su gasa. ***** *RUFEWA.* Lahadi 20 DECEMBER 2025. A sati sau biyar na ke zuwa shago ina da mai ɗan taimaka mini Nana ce ɗiyar mai yi mini kitso Maman Nana ta gama sakandiri ba ta shiga makaranta ba. Yanzu haka muna stimin, saloon, wash and set, kitso gyara kafa na ke so mu fara tun da ina shiga clases ɗin online ina ƙarin sanin wasu abubuwa. Ba na zuwa asabar sai dai Nanan kaɗai ke zuwa duk na koya mata ba abin da ba ta iya ba. Sai Baby ta kan leka itama ranar asabar ko in ba ta shiga makaranta ba tun da itama ta yi sauka an yi musu walima a Tahfiz. Jidda ma in ta dawo hutu tana zuwa, ita yanzu ta yi ƙarfi wajen yin snaks, in dai ta dawo hutu tana yin na biki da na birthday. Ranar lahadi kuma muna gida ba ma buɗe shago. Haka itama Gimbiya dukkan mu muna gida muna kula da mijin mu da yaran mu. Yallaɓai ma ba ya fita ranar ta iyalai ce. Ranar duk muna gida gabaɗaya har Jidda na gida ta zo hutun karshen shekara. Da ni da su da yara tare da Gimbiya mun je min duba Hajiya Iya da hawan jini ya kwantar da ita mun ɗan jima a Gwammaja sai gabda mangariba muka dawo gidan Rabi'atu ba ta je ba, tana fushi da mu gabaɗaya daga mijinta ya yi mata faɗan in ba ta daina rufe su Ayush a ɗaki ba za su samu matsala ta bar su su fito su yi wasa da yan uwan su in ba haka ba ranta zai ɓaci shi ne ta yi ta kuka tana kumburi tun da ya yi mata faɗa a gaban mu shike nan ta daina ma fitowa shi kan shi mijin ƙamshi ake shakar masa sai dai ya bita cikin ɗakinta mu dai ba ma bin ta yara dai ta ji faɗa ta barsu yau ɗin ma tare muke je Gwammajan da su bayan mun dawo ma a shashena muka ya da zango. Yallaɓai dai ya ce yana ganin har da cikin da ke jikinta ke saka ta fushi, ga kishi ko mgana ce yanzu in ta ji mganar kishiya za ta sauya fuska ta fara kumbura. Ita a dole ba ta son wata ta shigo. Kuma duk abin ta in Allah ya so Yallaɓai zai cike ƙofa. Can kwanaki ma har ma'aikatan shi ta riƙa zuwa lokacin da ya dauƙi wata sakatariya, tun da yanzu kamfanin ya na ɗaukan ma'aikata mata, ba ta yi sukuni ba sai da ya maye gurbinta da namiji sannan hankalin Rabi'atu ya kwanta. Ko Gimbiya yanzu ta shafa ma kanta lafiya ba ta wani rawan ƙafa a kan Yallaɓai. Gabaɗaya ita ma ta tattara shi ta bar ma Rabi'atun. Mun dawo mun iske Yallaɓai ba ya nan ya fita, ni ce ma na kira shi a waya sai ya ce mini ya ɗan fita ne zai dawo ba daɗewa ba. Da ya ke ni ke da shi a turaka shi ya sa muna dawowa na zage na shiga na share falon na gyara bedroom na wanke tiolet, na ɗauko sabon zanin gado na shimfiɗa wani ja mai love a saudiya na siye shi, sannan na koma bangarena na shiga kitchen na ɗora  ruwan zafi a tukunya. Yau amarci na ke so mu tuna, rabon da mu hada shimfiɗa da Yallaɓai sama da wata uku, kwanakin baya in ranar girkina ne ban ma cika bin shi turakan ba in ya yi magana na ce barci ya dauke ni na manta, in kuma na je babu abin da na ke yi sai barci ko ma ya neme ni sai na kawo masa ƙorafin na gaji, tun da ya fahimci haka sai shima ya ba ni lokaci amma ya shafa faɗa mini Sadiyata kin sauya, amma don Allah ina roƙon ki, kar ki sauya ni, har duniya ta tashi kar ki manta ruwa na mganin daula, shi ya sa yau na ce zan faranta mishi. saƙo na tura masa. "Yallaɓai na yau me kake son Sadiyarka ta da fa maka? Na ma ɗauka bai ga saƙon ba har tsawon mintina sha biyar sannan ya dawo mini da amsa. "Kin tuna tuwon shinkafar da kika taɓa yi mini kina Amarya? Har na yi ta gudawa? In kin tuna to ki yi mini irin shi Sadiya ta." Da na ga saƙon shi sai da na yi dariya ina tuna lokacin. Na tuna kwana Yallaɓai ya yi yana zagayawa tiolet na zambaɗa ma miyar yaji. Rayuwa kenan. Tuni na mike na shiga kitchen Jidda ta shigo ta ce za ta taya ni na ce ta fita ta ba ni waje, yau girkina mijina zai ci. "Kai Umma" "E yau dai a fita a ba ni waje ni da kaina zan yi ma mijina girki" Jidda ta kwashe da dariya har tana kiran Baby tana faɗa mata abin da na ce suka zo suna yi mini shaƙiyan ci. "Umma kawo mu taya ki" "Bana son rashin kunya. Tun kafin ku zo duniya na ke dafa ma mijina abinci." "Yau Yallaɓai sharr da shi" In ji Baby tana dariya na yi kamar zan kai mata duka suka fice suna yi mana dariya. Na duƙufa ina ta faman aikina ina da naman rago ga man shanu, sai da na tuƙa tuwo na je na yi salla isha'i, Yumna ta biyo ni tana kukan yunwa ta ke ji na saka Baby ta dafa mata indomie, Ammar ma yana gani ya ce zai ci su Khalipa ma suka ce yunwa suke ji, na ce su Jidda su ji da su ni dai ina ta mijina ne. "Umma ma su miji." Ta faɗa tana dariya. "E ɗin na ji " Na faɗa ina murguɗa mata baki suka kwashe da dariya har suna tafawa da Baby. "Mara sa kunyan yara." Gimbiya ta shigo da man ta kan shigo a yi hira ta iske ni ina ta aiki tana tambaya Baby ta ce" Yallaɓai ake yi ma girki." Gimbiya ta zauna gefen su Baby ɗauke da Afiya tana faɗin" Lalle yau za mu sha gara." "Yallaɓai kika ji an ce ba ku ba" Na faɗa ina haɗe rai Gimbiya da ya'yanta suka kwashe da dariya. "To Yallaɓai zai sha gara " "Yauwa gwara da kika gyara." Faɗi take yi ta zo ta ya ni na ce ta yi zamanta wannan ba huruminta ba ne ina Kicthen ina kai da kawo sun haɗa kai suna gulmana. "Ku yi ku gama" Na faɗa ina kyfaci sai suka kwashe mini da dariya. Na yi banza da su na cigaba da aikina tas na lailaya tuwo a leda miya kuma ta ji nama da manshanu ga ganyen ogun da ya ke mun shukata muna da shi a gida na saka Baby ta ɗebo mini na yanka na wanke na yi amfani da shi. Zuwa takwas da rabi na gama tun da ba da yawa na yi ba bai kai ko leda goma ba ma tuwon Wanka na yi na shirya cikin wando plazo bakin wando da jan riga mai ratsin baƙi. Na gyara gashina da ya ke ban yi kitso ba na saka bakin dankwali na yi ɗauri da shi na feshe jikina da turare na fito falo ina tashin ƙamshi. Ihu suka saka mini yaran nan kamar wasu sa'ar su Gimbiya na ta ya su. "Su Umma manya." In ji Jidda. "Umma an sha kyau.". In ji Gimbiya na yi mirmishi na yi fari na ɗau wayata ina faɗin" Bari na kira Yallabai na ji ko yana ina ne? Baki suka sake suna kallona ina kiran shi ya daga. "Uwargida ta." "Yallaɓai na " Na kashe murya kawai sai suka saka mini ihu sai na yi ɗaki da gudu ina dariya. "Su waye ke ihu? "Su Jidda ne da Gimbiya suna ta mini tsiyan wai yau na ce za mu tuna da zan yi maka girki mu sha soyayya " Yana dariya ya ce" Share su. Kazan amarci zan siyo mu ci mu sha mu kwana ɓarnan ruwa." "Allah ya ja zamanin ka Yallaɓai na." "Sai na iso.' Muka yi sallama cikin shauƙi Yallaɓai a muryan ma za ka gane yana cikin farinciki Ɗaure fuska na yi na fito suna kallona suna kunshe dariya. Jidda Abdullahi ya kira ta ta bar falon Baby ce suke hira da Gimbiya akan tana son ta yi ma Yallaɓai mgana za ta fara koyon mota. "Na ji yana mganar kuwa. Ki tuna masa." "To Anty in sha Allahu." Kusa da Baby na zauna muka saka ta a tsakiya muna ta hira. Gimbiya ta ce Rabi'atu fushin ne har da mu? " Mijin ki ya jawo mana." Mijin ki dai." Gimbiya ta mayar mini da amsa dukkan mu muna dariya. Kamar wasa sai ga Rabi'atun ta shigo ita da Salima ina jin gajiya ta yi da zaman shuru yaran duk suna nan shi ya sa ta fito. "Umma barka da dare. Sannu Anty Gimbiya." Ta faɗa tana zama a kan kujeran da ke fuskantan mu Muka amsa mata cikin sakewa, ni dai ce na kara da cewa ta gama fushin ne? Sai ta rufe fuska tana dariya. "To mu da ba laifi ba an share mu." Na faɗa ina dariya. "Ni fa ba na fushi." "To mene na ɗauke mana? Kwana biyu kenan ko hira ba kya fitowa.' Sai ta ce ba ta jin daɗi ne muka yi mata fatan sannu hancinta ta bude kafin ta ce Umma na ji kamshi me kika dafa mana ne? Kafin in yi magana Baby ta ce tuwo ne mai daɗi amma na Yallaɓai ne" Rabi'atu ta ce" Umma wallahi ina son ci ki taimaka." Ba ni da yadda zan yi na ce ita za ta ci Gimbiya ta ce itama sai ta ci na sawo musu ya'yansu suka ta so suma sai sun ci. "Ah ku na yi ma girki kawai." Na faɗa ina tura baki. "Na mijina ne fa." Na  sake faɗa ina riƙe haba. "Umma ki ba mu kawai mu cinye Abba ya sha tea ya kwanta." Jidda ta fada bayan ta dawo falon. "Ba ku isa ba" Muka ji muryan Yallaɓai daga sama ba ma wanda ya ji shigowarsa yaran na ganin shi suka ruga suna oyoyo Abba. "Jidda haka za mu yi da ke? Ya faɗa yana karisowa falon Baby ta tarbi ledan hannun shi guda ɗaya ya sakar mata ɗayan kuma ya ce" Wannan na ku ne ku da iyayen ku. Wannan kuma na My Sady ne." Sai Jidda da Baby suka saka dariya. Gimbiya ta ce" Son kai dai kake nuna mana kamar yadda itama ta nuna mana yau." "E ɗin an nuna muku son kai ɗin." Ya faɗa yana zama a gefen Rabi'atu da take zaune a ƙasa tana cin tuwo Afiya na miƙa hannu sai ya ce A kawo masa ita Yumna ta mike ta ɗaukota. "Yauwa my super women ɗina." Haka yake kiran Yumma a cewarsa tana da karfi. Sannu da zuwa muka yi masa gabaɗaya ya amsa yana kallon mu ɗaya bayan ɗaya har yaran yadda suka ba je a falo suna cin tuwo. "waye ya yo gayyar a cinye mini abinci." Ina dariya na ce masa Rabi'atu na bashi labarin kwaɗayi ya sa ta jiyo kamshi ta bar fushin ta shigo. "Ai da man cikin nan nata akwai son daɗi" "Abba wallahi tuwon ya yi daɗi ka ce Umma ta karo mana " In ji Rabi'atu "Ni kuma sai ma ci me? "Ka sha tea mana." "Hararanta  ya yi kafin ya ce" Ke ki sha tea ɗin mana. Na ki wayau wanda kuka ci sabil ne" Na ce ƙwarai, dole suka haƙura aka ba je kajin da tsiren da Yallaɓai ya siyo suna ci suna hira, Yallaɓai ya miƙa ma Gimbiya ɗiyar ta ya miƙe yana faɗin. " Sadiya ta mu je kin ji." Ya fada har yana miƙo mini hannu na kama yaran nan suka saka mana ihu. "Kuna fita za mu cinye tuwon nan" In ji Gimbiya Yallaɓai na jin haka ya ce" To koma ki haɗo komai ki same ni a can" Ya wuce ya fita bayan ya ba ni ledan hannun shi. Na koma kitchen na hada ƙomai a saman ƙaton faranti na saka lulluɓi na fito ina faɗin" Jama'a mu kwana lafiya." "Mu kwana lafiya Uwargidan Yallaɓai." In ji Gimbiya Rabi'atu dai ba ta yi mgana ba ita har gobe ba ta iya boye motsuwar kishinta. "Umma sai da safe" In ji Jidda na amsa ina faɗin su rufe kofa in za su kwanta. Yumna ta biyo ni tana faɗin" Umma nima za ni wajen Abba" Yarinyar nan shegen wayau ne da ita haka nan na rasa yadda zan yi da ita da na ce Jidda ta kamata ma kuka ta saka haka nan na ta sa ta gaba muka tafi. Ko da na je har Yallaɓai ya shiga wanka sai na kunna mata cartoon ni kuma na shirya mana dining sai da na kira wayar Jidda na ce su kawo min kunin aya da na haɗa yana nan a fridge da Baby ta kawo ne na samu na yi ma Yunma wayau na ce ta ma yar mini da mayafina ganina nan zuwa. Sai da na gama shirya komai a falo sannan na shiga ciki na samu Yallaɓai ya fito wanka yana ɗaure da babban towel a ƙugunsa. "Sadiya ta." "Yallabai na." Muka kalli juna muna mirmishi. Ni na taya shi ya shafa mai ya saka jallabiya baka muka fita falo, a kasan cafet ya ce mu zauna nan muka ba je muna cin tuwo muna tuna rayuwar amarcin mu muna dariya. Ya shayar da ni kunun aya nima na shayar da shi. Ya zaunar da ni a kan cinyarsa ya ba ni kaza a baki nima na ba shi, bayan mun gama na kwashe komai na kai kitchen na gyara falon muka je tiolet muka wanke baki. Na cire dankwali na bar masa gashin tunda yana so shima daga shi sai gajeren wando ya cire jallabiyan muka kashe hasken falon sai na tibi muka makale juna muna kallo muna kuma sumbatar juna. "Sadiya ta." "Uhm" Na amsa ina kwance a kirjinsa. "Na gode' "Na gode." "Godiyar ta mene ne? "Da kika zama ni na zama ke. Da kika yi ta hakuri da duk wani gwagwamaya har tarihin mu ya kawo yau. Na gode da zamowarki TUKEN GIDANA. na tabbata ban yi turken banza ba. Kin kasance mai karfon da duk matar da na auro a kan togacin ki za ta kafa na ta igiyan. Na gode a jiya da shekaranjiya na gode a yau na kuma gode miki a gobe." "Kai ne turkena Yallaɓai na." Na amsa masa ina mirmishi sai ya ɗago ni ya fara sumbatata nima sai na tallabe shi. Na tsawon mintina muka saki juna muna ma yar da numfashi. "Sadiya ta " "Uhm" "Har yanzu dai ruwa na mganin dauda." Ina mirmishi na ce" Yana yi sosai ma." Na faɗa ina shafa kirjinsa zuwa kasan maran shi hannuna ya riƙe jikinsa na rawa. "Sadiya. Ta" Uhm"    "Yau zan shanye ki ne fa." "Nima zan shanye ka." Na faɗa cikin wani yanayi, a wannan daran a saman wannan kujeran Yallaɓai ya biga half time ɗin shi sannan muka ranka ya ciki ya buga roud ɗin shi da kyau. Ba mu muka yi barci ba sai biyun dare da asuba bayan ya dawo sai da ya ƙara saka muka yi facal-facal da ruwa.  Ya kwanta barcin safe na fita na je na duba yara da kwana sai na tsaya na yi masa abin karyawa na yi wanka har Sadi direba ya tafi da yara makaranta Yallaɓai saboda gajiya bai fito ba. Na koma shashen shi domin na tashe shi ina shiga bedroom na ga baya nan na ɗauka ma yana tiolet ne ina jiyowa na gan shi a bayan ƙofa sai ya fara takowa gabana yana yi mini mirmishi. "Yallaɓai ka sake biya mini Umra ne? Na faɗa ina mirmishi har hakorin makkan da na sanya yana bayyana. "Assalamu alaikun farincikina! gani na zo gun mai haskaka raina !" Na kwashe da dariya ganin Yallaɓai ya dage yana yi mini waƙa. "Yallaɓai yau ka zama romie ne? '"kar ki manta ke ce kaɗai abin faharina." Ya faɗa yana mai ɗaga hannuna yana juyi da ni ina ta dariya dariyan farinciki da muradi mai girma. "SADIYA KAR KI SAKE DA NI KO WATA RANA,...!" Ya faɗa yana mai sumbatar goshina. Shigewa jikinsa na yi ina mai ƙamƙame shi. "Ba zan bar ka ba ko wata rana Yallaɓai ko mutuwa ce ta bari sai mun tsufa sai ta ɗauke mu a tare." "in sha Allahu." "Ina son ki Halimatuna." "Ina son ka Yusuf ɗina." Sai na dago kaina na ɗage kafafuwana na tallaɓo kan shi na fara sumbatar shi, shi kuma sai ya riƙe keyata ya juyar da ni ya haɗa ni da jikin ƙofa ya fara mayar mini da martanin gayyatata da zafi zafi. "ALHAMDULILLAH* _ALHAMDULILLAH KARSHEN LABARIN TURKEN GIDA, ABIN DA NA RUBUTA NA DAIDAI ALLAH YA BA NI LADAN TARE DA KU GABAƊAYA. KUSKUREN CIKI ALLAH YA YAFE MINI, KU YI HAƘURI WATAƘILA, NA KARKACE TA WANI BANGAREN. KUN SAN ƊAN ADAM AJIZI NE, TARA NA KE BAN CIKA GOMA BA, NA GODE BISA JIMARIN BIBIYATA, NA GODE BI SA MARTABAWANKU, NA GODE BISA GIRMAMAWANKU, NA GODE BISA YARDA DA AMINCEWARKU GA RUBUTUNA, NA GODE UBANGIJI YA YI MA RAYUWARKU ALBARKA ALLAH YA BIYA KU, YA KUMA HAƊA MU A ALJANNA. NA GODE SOSAI._ *SAI MUN SAKE HAƊUWA A WANI SABON LABARIN IN RAN MU YA KAI. NA GODE* *Janafty* 20 March 2025. SUN/09/2025.