[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ems_copy_t *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️⃣ *JAN HANKALI GA MASU BIBIYAR LABARIN NAN* *Labari ne da yake ɗauke da ɓangare uku, kowane ɓangare akwai muhimmiyar rawar da zai *taka. Labarin manyan taurarin cikin littafin guda uku wacce kowacce ɓangaren ta akwai tarin abubuwan da za mu yi nutso a ciki, muna da labarin ZALIKA, akwai labarin SADIYA, sannan akwai labarin JIDDA sai dai in ce ku biyo ni sannu a hakali domin jin da mai labaran nasu zai zo NGD* . Da sallama Malam Bala ya shigo gidan nasa, wanda yake sallamar kamar zai tsaga gidan, Mama Habiba da take kwalfar ruwa ta ɗago tana amsa masa a inda ya mata kallo ɗaya ya doka uban tsaki tare da ɗauke kai. Ƴan matan gidan ya shiga kwaɗawa kira ɗaya bayan ɗaya, kowacce tana ɗakin nasu da aka warr musu a gidan, jin kiran Aisha ta yatsina fuska ta ce "To fa! Watan cin ubanmu ya kama mun shiga uku yanzu Baba zai fara faɗan nashi bari mu je mu ji da mai ya zo" Malika ta taɓe baki tare da ci gaba da danna waya, haka suka fito sumi-sumi kowacce ta zo a ɗarare ta zauna a kan tabarmar gabansa ganin ya koma kan kujerar plastic ya zauna. Wani ƙullin magani ya fito daga cikin babbar rigarsa ƙullin ƙato ne ya ce "Kai ni dai na shiga uku! Allah ka bani ɗa namiji ko kangararre ne!" Mama Habiba da ta ji sautin maganrsa ya sosa ranta duk da ba yau ne ta fara jin wannan furucin nasa ba, amma dai kullum furucin yana zama tamkar sabo ne a kunnuwan ta. Gabaɗaya ƴan mata sai kowacce ta sunkuyar da kai kasancewar daga su har iyayansu suna matuƙar tsoron Baba, saboda ba ya ragawa kowa. Cikin sanyin murya Mama Habiba ta ce "Haba Malam ka daina wannan maganar wallahi babu daɗin sauraro, haba kowane jinsi ma ai kyauta ce ta ... Wata tsawa da ya doka mata ya sanya sauran maganar da ta guntso za ta amaryar masa ta haɗiye, a fusace ya ce "Habiba ina miki kashedi koyaushe a kan shiga sabgata da ƴaƴana bakya ji ko? Mai ya sa kike saka baki a abin da babu ruwanki? Ko namijin da na ce a bani ke na tambaya ki ban?" Kai ta shiga girgizawa ya ci gaba da faɗin "To ahir ɗinki, Allah na ce ya bani ɗa namiji ko kangararre ne ba ke ba, ai ko maganar ce ki bari masu haihuwa su faɗa amma ke da baki da ko ƙuda a gidan ina ruwanki" Kai ta sunkuyar idanunta suna kawo ƙwalla tana jin zafi da ɗacin gorin Malam duk da ta san Allah ne yake bada haihuwa kuma shi yake hanawa ta yi imani da hakan amma gorin mijinta yana ci mata tuwo a ƙwarya, saboda tana ganin da a ce shi ne ba ya haihuwa ko a haka za su dawwama to ba za ta taɓa masa gori ba kuma za ta rungumi ƙaddara ta zauna da shi har ƙarshen bugun numfashin ta, amma shi ban da kishiyoyi uku da ya mata har sai yana mata bita da ƙulli dulan kabarin kishiya. Mama Talatuwa da ta firo daga ɗakinta jin abin da yake faruwa duk da ba wannan ne karon farko ba, amma koyaushe idan yana yi wa Habiba cin kashin nan tana jin babu daɗi a ranta, haka ta fito tana nufar wajen da Habibar take don ta bata baki, sai dai tana dab da zuwa ta tsumayi maganar Malam yana cewa "To uwar ƴan tausayi me raunatacciyar zuciya, ke irin kishin nan ma na mata bakya yi, bakya jin daɗi mijin ki ya duzga kishiyarki, sai ki yi kamar wanda aka taɓa wata ƴar uwarki ta jini" Juyowa ta yi cikin sanyin murya ta ce "Haba Malam ai duk mace mai hankali ba za ta so ta ji daɗin don mijin ta yana tozarta kishiyarta ba, domin rayuwar duniya yau gare ka ne gobe ga waninka, kenan ni ma jifa zai iya zuwa kaina ko in ce... Hannun da ya ɗaga mata ya sa ta yi shiru ya ce "Ki ciko bokiti da ruwa ki kawo min" Da to ta amsa tana kallon Habiba da tausayawa ta nufi wajen ruwan za ta ɗakko, Mama Habiba kuwa sai ta kama hanyar ɗakin ta tana jin tamkar an ajiye mata dutsi a ƙirjinta na gorin haihuwar nan kasancewar ta mace mai son yara sai kuma ƙaddararta ta kasance ta rashin haihuwa, sannan mijin ta ba ya tausaya mata a kan rashin haihuwar sai dai ya yi ta yada mata baƙar magana tamkar ita ta hana kanta haihuwar. Mama Talatuwa bokitin ta ɗakko me cike da ruwa ta kawo gabansa ta ajiye tana kallon ƴan matan yadda kowacce fuskarta cike da damuwa. Ledar ya since ya zazzage maganin kofuna guda biyu ya sa Hafsa ta ɗakko ya gauraya ya cika kofin ya miƙawa Hafsa ya ce "Karɓi ki kafa kai ki shanye ki miƙo min, ai ni zama bai ganni ba wallahi tun da na ajiye ƴanmata kamarku a gida babu mashinshini, dole na nemi maganin farin jini ko a samu masu kwasa in kawar da ku in huta da raina, amma yara sai shagen baƙin jini, ni dai ba ni kuka biyo ba sai dai iyayenku mata tun da ni dai gashi nan sai dai na rufe ƙofa wato na auri mata huɗu, da ina da baƙin jini wa zai aureni"? Ya faɗa yana musu wani kallo ba yabo ba fallasa kowacce kai ta sunkuyar suna jin babu daɗi a ransu tun da cikin su babu wacce ta haura shekara ashin wasu ma sha takwas suke amma saboda ya ƙwallfa rai a kan su ko kaɗan ya hana kansa sukuni. Hafsa da kurɓa ɗaya ta yi wa maganin ta ji wani uban ɗaci har tsakar kanta, da hanzari ta cire kofin daga bakinta tana mayar da kallon ta kan mahaifin ta cike da tsoro, a fusace ya ce "Kin shanye kin miƙo kofin ko kuwa" Cike da tsoro ta ce "Baba wallahi maganin nan ɗaci ne da shi, na jiya ma da na sha gudawa ya sakani" Ta faɗa tana kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka. Kafin Baba ya furta wani abu Malika ta yi karaf ta ce "Wallahi Baba ko ni jiya wanda ka bamu da daddare cikina ya yi ta ciwo, kuma ma fa Baba shan magani ba bisa ƙa,ida ba yana da haɗari ga lafiyar jiki, sannan magungunan nan masu ɗaci idan ba likita ko wani masani ne ya bayar ba yawan shan masu ɗacin nan ba bisa ƙa,ida ba yana iya sakawa mutum ciwon hanta, idan akwai sinadarai masu illa lalata hanta ko ƙoda yake, duk da wasu magungunan masu inganci suna da tasiri in an yi amfani da su bisa ƙa,ida... Hannun da Baba ya ɗaga mata ne ya dakatar da ita daga ƙarasa maganar yana nuna su da yatsa ya ce "Ba ɗaci ba ko maɗaci ne kan ɗaci sai kun sha maganin farin jinin samarin nan, ina zan iya duka mata kun cika min gida, shiga goma zan yi gidan nan sai gabama ya faɗi in na ganku, kowacce ya ci a ce tana gidan mijin ta amma ƴaƴa shida duka mata kuma ɗaya na aurar haba kamar dai wanda aka mini baki, ai ina roƙon Allah ya bani ɗa namiji duk lalacewar namiji ka amfane shi, duk kangararsa wataran zai maka magani amma mace fa?" Ya faɗa yana bin su da kallo, Mama Talatu da take gefe tsaye kamar mai jiran tsammani don tana tsoron ta bar wajen ya ce ta raina shi, cikin sanyin hali da na muryarta ta ce "Haba Malam don girman Allah ka daina wannan maganar, kowane ɗa yana da ranarsa, kawai mutum ya yi addu'ar Allah bashi na gari sannan ya nema musu shiriya da kuma saka musu albarka, wani sa'in mace ma ta fi wani namijin jin ƙai da taimakon, amma kana maganar kangararran ɗa to ta ina zai tallafa maka ɗin tun da a kangare yake? Mace ma tana da tata ranar kuma wasu ma suna nan suna neman haihuwa ido rufe amma bai kamta kai da Allah ya azurtaka da su kake wannan furu... Tsaye ya miƙe a zafafe ya nuna Mama Talatu da yatsa ya ce "Keee! Kin san dai babu abin da za ki nuna mini na sanin abin da ya dace ko wanda ya kamata saboda haka kar na ƙara jin bakin ki" Yana kaiwa nan ya koma ya zauna. Kallo ɗaya ya yi wa Hafsa da ta kafa kofin sai da ta shanye tasss ta miƙa masa ya kwalfo ya ba Malika sai da ta runtse ido ta shanye ta miƙa masa kofin, kowa ya sha saura Arfat da ya miƙa mata tana yin kurɓa ɗaya amai ya yunƙuro ta da sauri ta cire kofin a bakinta tana saka hannu ya toshe bakin, jin aman yan barazanar zubowa ta ajiye kofin a wajen ta miƙe a hanzarce ta bar wajen sai da ta gama aman ta dawo Baba yana sababi ya ce "Wato ke kece shafaffiya da mai, kullum in zan bayar da magani ke ce mai yi wa mutane amai, uwarki ta ɗaure miki tsantsa a kan cewa wai tu tana goyonki kike amayar da magani ko da na asibiti ne ko ɗura miki aka yi sai ya dawo, ɗauke wannan maganin ki shanye kuma wallahi kika sake kika amayar sai na lahira ya fiki jin daɗi" Haka ta shanye maganin tana dantse bakin ta ganin bata yi aman ba. Baki ya buɗe zai yi magana amma jin kuka daga zauren ƙofar gida ya sa ya dakata, sai kuma suka fara jin wasu muryoyi ana faɗin "Ta ɓata jikin ta" Shigowar Aisha gidan tana kuka, kowa ya bi ta da kallo, Mama Talatu ce ta kalle ta da alhini ta ce "Aisha kukan me kike mai aka miki?" Aisha wacce ta ja ƙasan hijabin ta ta rufe fuskarta hannun ta riƙe da jakar buhu irin wacce ake ɗinkawa da buhu, sanye take da farar riga da wandon uniform sai farin hijbi wanda aka masa tattara da koren yadi a ƙasan ƙafar wandon ma akwai koren, bata ba Mama Talatu amsa ba, cike da tsawa Baba ya ce "Kee! Kukan uban me kike?" Da sauri ta cire hijabin fuskarta saboda ta cikin yadin hijabin nata wanda bashi da kauri kasancewar yadin ba mai tsada ba ne, ta haka ta shigo gidan sai dai bata kalli saitin inda su Baban suke ba shi ya sa bata san yana nan ba, ita kuma Mama Talatu da yake daga nan gefen da take tsaye kusa da hanyar zauren ne shi ya sa Aishar ta ganta. Mama Bilki wacce take ɗaki tana jin kaf abin da yake wakana a gidan, tun da in da sabo sun saba da wannn halayyar ta gidan duk da kasancewar kowa a gidan shi yake nemawa kansa abincin rana damkarin kumallon safe idan tuwo bai kwana ba, domin iya tuwon dare ne kawai Malam ɗin yake bayarwa a gidan shi ma wataran idan ya hana kuɗin kayan miya sai dai wacce girkin ta ne ta siya ta yi haka za a yi miyar babu maggi sai dai kowa in an zuba masa ya nemi maggi dunƙule ya barbaɗa, abincin rana kuma sai ranar da ya ga dama jifa-jifa yake bayarwa. Ba wai don bashi da halin wadata su ba, sai don sarewa irin tasa shi a tashi fatawar ƴaƴa mata kawai da ɗakin miji suka dace domin mijin ne ya dace ya ɗauki ɗawainiyar mace, shi ya sa yake ta fafutukar ya ga ya aurar da su sun bar gabansa, babu tunanin samun nagartaccen miji. Komai sai dai uwa ta ciru ta ƙullu ta nemawa ƴarta ko su ƴaƴan su nema shi abu ɗaya yake da buri kuma yake fata shi ne ya haifi ɗa namiji, a ganinsa idan namiji ne zai taya shi ɗaukan ɗawainiya amma mace yana ganin ita sai dai ya nemo ya basu ba ya tunanin haƙƙi ne Allah ya ɗora masa. Aisha cike da jin nauyin mahaifinta kuma tana jin kunya sai ta kasa faɗa masa dalilin kukan nata, ƙara zaburowa ya yi yana kumfar baki sai ga Mama Bilki ta fito daga ɗaki ta ce "Wai mene ne kike neman mayarwa da mutane gidan makoki, ke ga mai arahar hawaye?" Jin tsawar da Mama Bilki ta mata da kuma wacce Baban ya yi sai ta sunkuyar da kai hawayen yana zuba ta ce "Wai don na ɓaci shi ne ƴan ajinmu suke min dariya" Ta faɗa tana jin ɗacin abin a ranta, sai lokacin ƴanmatan kowacce ta mayar da kallonta jikin Aisha, domin sun fahimci matsalar shi kuma Baba bai ma gane inda maganar ta dosa ba hakan ya sa ya ce "Ba dole suke miki dariya ba tun da sun ga sakarya, ke da girmanki amma kuka ba ya miki wahala" Mama Talatu cike da tausayin Aishar ta ce "Haba Aisha ai da kin saka ƙunzugu a jikin ki, amma kya tafi cikin mutane a haka kuma kin san dai ƙawaye da sheƙiyanci" Wani kallo Mama Bilki ta jefawa Mama Talatu ta ce "Sai aka ce miki bata saka tsumma ba, to ta saka, zo ki wuce ki je ki gyara jikin ki" Mama Bilki ta faɗa rai a ɓace saboda gabaɗaya haushi ta ji an tsinka ƴarta, Aisha tana fara tafiya kowa ya juya ya bi bayanta fa kallo, ashe ta saka wani ɗankwalin atamfa ta ɗaura a ƙugunta hakan ya sa ba a ganin ɓacin da jikin nata ya yi. Mama Bilki cike da takaici ta ce "Ai wallahi sha'anin gidan nan sai a hankali wallahi, a ce wai sunan yara suna da uba amma kamar marayu, a ce ubansu yana da hali amma ba zai ɗauki ɗawainiyarsu ba sai dai ya ce kowacce ta ɗauki ɗawainiyar kanta, to ko namiji ne aka ce ya ɗauki ɗawainiyar kansa ai an buɗe masa hanyar yin abin da ya ga dama varw kuma ƴa mace da ake son killace ta a yi takatsantsan da rayuwar ... Kafin ta kai aya Baba ya tari nunfashin ta da faɗin "Sannu uwar kinibibi, yanzu saboda rashin godiyar Allah sai aka ce komai sai uba ya yi wa yara? Ita uwarsu mene ne amfaninta? Kun mata kun ɗauki namiji kamar bawa komai shi zai yi a gida ba za ku taimaka ba, in banda son kai yanzu audugar wata-wata ma ni zan saya musu?" Mama Talatu ta ce "Malam ai ba a ce wai lallai sai ka saya auduga ba amma akwai wasu ɗawainiyoyin da dan har ka ɗauke musu to zai zamana kuɗin da za su yi ɗawainiyar sai su sayi audugar da ƙananun abubuwan, amma a ce mace budurwa ita za ta yi wa kanta komai, hatta omon wanki da sabulu mai na shafawa ita za ta yi kai hatta ciyar da kanta ita za ta yi haba malam Allah ne fa ya ɗora maka nauyin iyalinka daga kan ƴaƴa da mata... Wata harara da yakr jifanta da ita ya sa ta yi shiru ya ce "Wato in mutu da ɗawainiya ni kullum in ƙare a tsaye? Ai shi ya sa da a ce maza na haifa da tuni ina ɗaki ina bacci da munshari su kuma suna can suna nema, in za ku kama sana,a kowa tashi ta fishshe shi. Mama Sa'ade ce ta fito daga ɗaki tana hamma ta ce "Ai lamarin gidan nan sai addu'a amma dai kam ana fama" Baba kallon ƴanmatan da suke gabansa ya yi ya ce "Kai ku tashi ku bani waje kowacce ta bar wajen nan, kuma maganin da kuka sha na farin jini duk wacce ta amayar min shi wallahi sai ranta ya ɓaci, mu ga zuwa gobe ko maganin zai yi aiki a fara min kayin neman aurenku" Ya faɗa yana miƙewa tsaye ya gyara rigarsa ya juya ya nufi hanyar ɗakinsa yana ta ƙananan maganganu da babu wanda ya ji mai yake cewa amma da alama faɗa ne yake. Mama Talatu ce ta ɗan matsa kusa da Mama Bilki ta ce "Bilki don Allah yarinyar nan ki saya mata audugar mata, wallahi babu daɗi jinin al'ada yake kunyata mace kaima babba da yaya bare kuma yaro duk sai mutum ya ji ya tozarta duk ya rasa sukuni, in har baka kintsa kanka ba sai kake ta tsarguwa ko ka ɓaci... Kafin ta ƙarasa Mama Bilki ta ɗaga mata hannu tana faɗin "Talatu bana son iyayi, idan ba za ta saka tsumma ba to ta zauna a haka, ita ba shegen girman kai ba idan aka ce ta fita waje ta soya awara ta siyar sai ta ƙi wai bata son talla, waye ubanta? Uban nata da ba ya iya ɗaukan ɗawainiyarta tun da ba za ta zage ta nema ba ai ta yi ta ganin takaici" Tana faɗar haka ta juya ta kama hanyar ɗakinta. Mama Sa'ade baki ta taɓe ta juya ta shige nata ɗakin, Mama Takatu a zuciyarta ta ce 'Wannan rayuwa ban san ina za ta je da mu ba, duk wanda ya ce ƴa mace ta ɗauki ɗawainiyar kanta ai hanyar lalacewa ya nuna mata, yanzu a ce uwa ba za ta siyawa ƴarta mace auduga ba, idan ba wata sana'a yarinya take yi ba ina za ta samu kuɗin siyan auduga duk wata? Wata ma sau biyu take yi a wata ɗaya, gaskiya akwai sake a lamarin gidan nan, a ce mutum ya ɗauki ɗawainiyar kansa Allah kyauta' Ta faɗa a zuciyarta tana nufar ɗakinta Mama Talatu tana shiga ɗakin ta sai ta samu Sadiya tana zaune ɗanta Kalifa ɗan shekara biyu yana kan cinyarta, abin mamaki kuma Sadiyar kuka take. Sai dai da alama shigowar Mamar ya yi wa Sadiyar bazata saboda saurin kawar da fuska gefe ta yi tana sharar ƙwalla da alama bata ma son Mama ta ga hawayen nata. Gaban Mama ne ya faɗi, zuciyarta ta tsinke tana fatan dai ba wata matsalar gidan auren Sadiyar ba ne ya saka take kuka, ta rasa wane irin aure ne wannan aka yi wa yarinyar nan wanda koyaushe cikin ƙunci take, da damuwa dama ta lura tun shigowarta kamar ma fuskarta a kumbure sannan kana ganinta ka ga waccr take cikin damuwa kuma babu alamar nutsuwa a tare da ita!. MAMAN AFRAH 09025576222 [10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/IQU3wL7NUTCCqrbtxkJaaz?mode=ems_wa_t *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣ *MAMA TALATU* Zuciyarta sai ta mata nauyi da ganin halin da ƴarta take ciki, a hankali ta ƙarasa shigowa falon ta zauna a ƙasa kusa da Sadiya, tana mai sauke wata nannuyar ajiyar zuciya, ranta duk babu daɗi duk da wani lokacin tana jin farinciki cewa ƴarta ita ce wacce take da aure, amma dai auren wannan wani lokacin ma da shi da babu duk uwar ubansu ɗaya, dama ta san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, mijin Sadiya dama irin mazan nan ne da basu san darajar mace ba, shi ya sa yake wulaƙantata uwa uba kuma yadda aka yi auren, daga ganin Sadiya ya ce yana so a ranar farko da ya fara zuwa ƙofar gidansu, a ranar ne mahaifinta ya ce ya turo manyansa babu wani bincike da yake dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Haka aka yi biki babu wata fahimtar juna, babu bincikar halayensa gashi nan yanzu an yi ba a yi ba rufin ƙofa da ɓarawo. Hannu Mama ta kai ta dafa kafaɗar Sadiya ta ce "Halima kukan mene ne kike yi?" Ta tambaya tana jin tsoron furucin da Sadiyar ,a ta yi a gefe ɗaya tana fatan cewa Sadiyar ta faɗa mata wani abu daban amma ba matsalar gidan auren ta ba, ita burinta bai wuce Sadiyar ta zauna a ɗakinta duk wuya duk runtsi. Hannu Sadiya ta saka ta ƙara goge hawayenta duk da hakan bai hana wasu zubowa ba, ta ja hanci tare da ru tse idanu tana cije bakinta a hankali ta buɗe baki za ta yi magana, kukan da Kalifa ya saki saboda ya tashi, shi ne ya hanata ƙarasawa. Da sauri Mama ta kai hannu ta rufe masa baki, cikin raɗa-raɗa ta ce "Kin san dai Malam bai san kin zo gidan nan ba, ina dai gani takalmanki ma sai a bayan ƙofar ɗaki na saka su, saboda yana ganin takalmi a ƙofar ɗakin zai fahimci kina nan, kuma daga ni har ke ranmu in ya yi dubu sai ya ɓaci" Da sauri Sadiya ta ɗaga kalifa zaune tana ɗan jijjiga shi ya yi shiru, yana buɗe udanun ya wartsake ya ce "Momma abinci" Shiru Sadiya ta yi tana tunanin abin da za a bashi, sai Mama ta matsa ta ɗakko wani ƙaramin filas da yake can gefe ta buɗe ta ce "Wannan kashin ɗumamen Sumayya ne na safe ta ajiye sai ta dawo daga makaranta za ta ci, bari a tsakura masa" Sadiya ta ce "Mama kin san dai yarinyar nan ba kunya gare ta ba, kina gani da muka zo ma sai da ta yaɓa min magana, ni ban san Sumy wace irin yarinya ba ce" Mama ta ce "To Halima saboda rashin kunyarta ai ba a ƙi ba yaron nan abinci ba, kuma kin san dai kuka zai yi idan Malam ya ji kukansa kuwa zai gano kuna gidan nan kuma dai kin san ƙarshen zancen, ita kuma Sumayya sai dai na ci gaba da mata addu'a kina gani dai yarinyar nan bata raga mini ko kaɗan kamar ita ce uwar ni ce ƴar ta raina ni wallahi" Cewar Mama tana ɗakko ƙaramin plate ta ɗaukawa Kalifa tuwon aka saka ruwa aka goge masa fuskar ya karɓi tuwon yana ci. Mama ta ce "Ni dai abin da zan faɗa miki Halima ki yi haƙuri da lamuran rayuwa" Mama ta faɗa don ganin ta dakatar da Sadiya daga maganar da take son furzarwa daga bakinta. Idanu Sadiya ta ɗaga tana kallon mahaifiyarta a ranta tana tunanin ita sai yaushe ne za a ɗauki lamarin gidan aurenta da muhimmanci an san tana cikin damuwa da matsaloli amma sai a hanata furta komai ake bata haƙuri, basu san irin ƙangin da take ciki ba a ƙalla ko ba za a sama mata mafita ba ai a saurari damuwarta hakan zai rage mata nauyin zuciya. Cikin sanyin murya ta ce "Mama wai mai ya sa a kullum bakya sauraren damuwata, kin san irin zaman uƙubar da nake a gidan aurena kuwa? Koyushe na zo da matsala sai dai ki dakatar da ni ki ce in cigaba da haƙuri" Mama ta ce "To Halima in ban baki haƙuri ba mai kike so na ce miki, kin san dai aurenki kamar auren zobe ne ba mutuwa zai yi ba don mutuwar aurenki daidai yake da mutuwar nawa auren, ko ma in ce daidai yake da mutuwarki, kin san dai duk cikin ƴaƴa gidan nan ke kaɗai ce mahaifinki yake alfahri da mijin da kika samu kika yi aure, ni ma ke ɗaya nake dakar ƙirji in ce kina ɗakin miji, kina dai gani har kishiyoyi haushin aurenki suke ji suna ganin nasu ƴaƴan basu samu miji ba" Sadiya ta ce "Mama wallahi wani auren da shi gwara babu, na san ba za a ce ni kaɗai ce a cikin halin da nake ciki ba dole za a samu mata da yawa da suke cikin damuwa a gidajen mazajensu amma dai wallahi da wannan auren gani nake gwara na dawwama babu... Katse ta Mama ta yi a daidai nan kalifa ya turo plate ɗin da aka tsakura masa tuwon, har ya cinye dama ba yawa ne da shi ba ya ce "Momma abinci" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke, Mama kuma gabanta ne ya faɗi, saboda ta lura so yake a ƙara masa kuma dai ta san idan aka tarki ƙara masa tuwon ba zai yi saura ba, kuma dai ta san tabbas ƙarewar tuwon nan matsala ne. Filas ɗin ta ɗaga ta juye masa sai Sadiya ta ce "Mama ya kika juye masa?" Mama ta ce "To ya zan masa Sadiya yanzu dai kin san idan ba a ƙara masa ba kuka zai yi kuma dama cikin ɗan yaye akwai cin abinci" Sadiya ta ce "Ai kuma ni Sumy nake tsoro ta zo ta yi wa mutane tijara" Mama ta ce "To mene ne baƙo a wajenmu sai ta zo ta yi abin da za ta yi" Sadiya ta ce "Mama wallahi Mama zaman gidan Nasir kamar zaman kurku yake a wajena, wulaƙancin yau daban na gobe da ban kuma iyayena kamar wanda suke sa,anninsa wallahi idan kin ga abin da yake min kare ma ba zai ci ba" Ta faɗa hawaye yana malalowa daga idanunta. Baba da ya fito daga bayi ya yi alwala, ya ɗauki babbar rigarsa ya saka ya gyara zaman kuɗaɗensa a aljihunsa, ya fito zai fita masallacin azzahar ɗin ƙarfe biyu ya ji wata yarinya tana tallar awara, kiranta ya yi ya bata ɗari biyar ta zuba masa a leda ya ƙulle ledar ya kai ɗaki ya ajiye ya kulle ɗakin ya saka mukullin a aljihu, ya fito yana gyara zaman rigarsa ya fita zuwa masallaci, a ƙofar gida suka haɗu da Sumy wacce dawowarta daga makaranta kenan, kallon ta ya yi ya ce "Sai yanzu kika dawo?" Ta ce "Sai yanzu dai aka tashemu" Ya ce "Amma mai ya sa Aisha ta riga ki dawowa bayan ku duka a S.S 3 kuke?" "Eh Baba ni ai a A nake ita kuma B na tsaya ƙarasa kwafar rubutu ne" Ya yi ɗan jim kaɗan har ya fara tafiya ya juyo ya ce "Kuma babu wani saurayi da kika haɗu da shi a hanya wanda ya ce yana sonki zai zo gidanku ya aure ki" Ɗan zumɓura baki ta yi a ɓoye sai ta ce "Ni babu wanda na gani" Ya ce "Zan dawo ai akwai maganin farin jini naki da na Aisha zan baku gwara ku yi ku tashi" Ya faɗa yana yin gaba ita kuma a ranta ta ce "Wai hanyar makaranta ma sai an tambayi mutum ya haɗunda saurayi, wai mu yi ku tashi sai ka ce wasu jiragen sama" Ta faɗa tana juyawa ta shige gidan. Ko sallama bata yi ba a tsakar gidan dama Mama Sa'ada kawai ta gani tana alwala ita ma Mama Sa'ada da ta san cewar Sumy bau ta ido ta ɗauke kanta saboda ta san yanzu sai ta mata rashin kunya yarinyar da hatta uwarta bata ƙyale ba. Labulen ɗaki ta bankaɗa ko sallama babu daga Mama har Sadiya suka ɗago suna kallon ta buɗar bakin Sumy sai cewa ta yi "Kam bala'i wane ishashshe da man ne ya ɗauka min tuwo ya ba wannan ƙwalamamman yaron?" Ta faɗa tana ƙarasowa tsakiyar ɗakin ta kama tsantsa tana musu wani kallon fitsara. Mama ta buɗe baki cikin sanyin murya ta ce "Ki yi haƙuri Sumayya ni ce na ɗauka na bashi, ke da ɗanki yunwa yake ji... Sumy ta yi saurin katse Mama da faɗin "Wallahi in na yarda shegiya nake, kuma wallahi ni kar a ƙara cewa wannan ɗana ne, a toh ɗana dai a gaba zan haifa" Mama ta ce "Allah ya baki" Sumy ta ce "Wallahi yanzu ba sai anjima ba za a biyani tuwona, tun da dai ubana ne ya nemo don ya fita kunyata ya ciyar da ni haƙƙin da Allah ya ɗora masa, shi mai ya hana shi a zauna a gidan nashi uban a bashi" Sadiya ta ce "Wallahi Sumy ki kiyayeni bana son rashin mutunci sa'arki ce ni?" Cewar Sadiya da jajayen idanunta, dama tana cikin damuwa yanzu kuma za a ƙara mata. Sumy ta ce "To ƙarya na yi ne? Na ce ƙarya na yi, ai babu wani rashin kunya in kinaso ki ja wa kanki guntun mutunci to ki zauna a ɗakin mijin naki" Tsaye Sadiya ta tashi ta ɗaga hannu za ta sharara mata mari sai Mama ta shiga tsakani ta ce "Haba Sadiya ya ina yabonki sallah za ki kasa alwala ke yanzu za ki biyewa wannan sakaran" Buɗar bakin Sumy sai ta ce "Wallahi dai Mama kike jin tsoron Allah ji daina nuba bambanci a tsanin ƴaƴa dama ai na san kin tsane ni saboda ni ban yi aure ina kawo miki abin duniya ba, kuma ki biyani kuɗin tuwona da jikanki ya cinye" Ta faɗa cike da tsiwa, ran Mama ne ya ɓace ta ce "Idan na biyewa zuciya sai na miki baki Sumayya amma ki bi duniya a sannu ni mahaifiyarki kike ɗagawa murya kina magana da ni kamar wanda kike magana da sa,arki ke kullum ba za ki gane annabi ya faku ba, kuna manta matsayin mahaifiya da ɗawainiyar da ta yi da ku?" Mama ta faɗa tana ɗaukan ɗari huɗu ta cillawa Sumy ta ce "Ga kuɗin tuwon naki nan" Babu kunya ta ɗauka ta shige bedroom don faɗan da Mama ta yi ma ko a jikinta wai an tsikari kakkausa. Komawa Mama ta yi ta zauna daɓas ranta duk yana mata ƙuna. Sadiya ta ce "Mama ki yi haƙuri da halayyar Sumy wallahi ko kaɗan bata ma ɗaukan abin da ake faɗa mata" Mama ta ce "To ya zan yi da ita Halima ai haƙuri ya zama dole in ba haka ba halayyar Sumayya sai ta saka zuciyata ta buga, dama an ce a ƙarshen duniya kuyanga za ta haifi uwar gijiyarta kuma gashi nan alamomin sun fara bayyana, tun da za ki ga ƴaƴa suna yi wa iyayensu abu kamar dai su ne iyayen" Sadiya ta ce "Allah shirye ta ta ganar da ita" Zayyanawa Mama irin abubuwan da Nasir yake mata ta yi, amma Mama ta dakatar da ita hakan ya sa Sadiya ta shiga kuka tana cewa "Mama wai mai ya sa ba za a warware min matsalolina ba, shikanan ni a haka zan ci gaba da rayuwa? ga matsalar miji ga ta dangin miji, ƙannensa sun raina ni mahaifiyarsa bata ƙaunata wallahi Mama hatta Kalifa da babu abih da ya tare musu basa son yaron nan kamar wanda agola ne sgi ba ɗan gidan ba" A daidai nan Baba da ya dawo daga masallaci zai wuce turakarsa ya fara jin tashin magana da ya ƙarasa jikin ƙofar sai ya saurara ta haka ya gane muryar Sadiya ce sai dai ba ya iya gane mai take cewa. A fusace ya bankaɗa labulen, sai kuwa ya fara tozali fa ruwan hawayen Sadiya, gabansa ya yanke ya faɗi, Mama kuwa sosai ta shiga ɗimuwa na ganinsa babu zato babu tsammani, Sadiya kuwa jikinta ne ya ɗauki karkarwa. Baba idanu ya ƙanƙance yana yatsina fuska ya shigo ɗakin ko takalman ƙafarsa bai cirw ba saboda tsabar ɓacin rai ya tsaya yana bin Sadiya da kallo tare da jefa mata wani mugun kallo a harzuƙe ya ce "Uban mai kike yi a gida Sadiya? Ko Nasirun ne ya mutu?" Ya faɗa yana jiran jin ba'asi Sadiya a zuciyarta ta ce "Ni da zai mutu ma da na huta da wannan halin da nake ciki, in banda rashin kwanciyar hankali a ce mace tana jin tamkar da mutuwa mijinta ya yi. A fili kuma ta buɗe baki cikin ladabi ta ce "A'a Baba yana nan lafiya ƙalau, dama zuwa na yi na kawo muku wuni... Saurin katse ta ya yi da faɗin "Sadiya mai ya sa kike da tada zaune tsaye ne wai? A kan mai na siyar da akuya za ta dawo taje cinye mini danga? Har ki ɗakko ƙafa ki taho ga ke ga ɗanki wuni guda cur, " Ya faɗa yana maida kallonsa kan Mama ya jefa mata tata tambayar ta hanyar faɗin " Kukan uban mai take yi?" Mama inda-inda take yi sai ya katse ta da faɗin "Ba magana nake miki ba? Ko wani sabon munafurcin ne hallaw kika saka yarinyar nan a gaba kina mata tambayar munfurci so kike ki kashe mata aurw ta dawo ta zauna a gida na samu na kawar da ita ina ƙoƙarin kawwar da sauran ƴan uwanta amma kw kina neman jiƙa mini aiki, to wallahi duk ranar da auren yarinyar nan ya mutu ki yi kuka da kanki" Ya faɗa yana nuna Mama da yatsa. Mama kai ta sunkuyar ya ƙara kallon Sadiya ya ce "Kukan mai kike?" Sadiya ta ce "Wallahi Baba ko kaɗan ba na jin daɗin gidan Nasir kawai yana ta gana mini azaba da gasa mini aya a hannu... Katse ta ya yi ta hanyar dakatar da ita. Ya buɗe baki a faɗace ya ce "Ke banda rashin hankali wane shegen ya ce miki aljanna tana samuwa da sauƙi? Ko ana nemanta ta daɗi to ki buɗe kunnuwanki ki ji Nasiru ko yankan namanki zai ke yana ci ɗanye ba zan taɓa ganin laifinsa ba saboda rage mini aiki ya yi duk wanda zai auri ƴarka ya rage maka ɗawainiya da ita, to haƙiƙa ya gama maka komai a rayuwa, ki zauna a ɗakin ki duk runtsi ƴan uwanki gasu nan barkatai ban da maganin farin jini babu abin da nake ɗirka musu ko sa samu miji ma" ,Tun da ya fara magana kanta a sunkuye kuka kawai take shi kuma Kalifa sai suɗe plate ɗin da ya cinye tuwon yake. Sai da ya numfasa ya ce "Ki tashi a kan sawunki ki koma ɗakin mijin ki" Da toh ta amsa masa tana tashi tsaye ta ɗauki Kalifa ko hannu bata wanke masa ba a haka ta saɓa shi a baya, siyam - siyam kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki ta nufi bayan ƙofa ta ɗauki takalmin dakyar ta iya furta "Na tafi Mama" Mama kuwa kai kawai ta shiga gyaɗa mata, raɓa gefen Baban ta yi ta fito duk abin nan da ake Sumy tana jin su zaune take a tsakiyar bedroom ɗin ta yi ɗai-ɗai da ƙafafu tana cin doya da ƙwai sai yankakkiyar gurasa a gefe wanda wani saurayi da ta gaɗu da shi a hanyarta ta dawowa daga makaranta, daga ya tsare ta yana tambayar sunanta da kwatancen gidansu shikenan sai ta ce ya saya mata, dama tana ta tunanin cin ɗumamen tuwon da ta ajiye. Ya siya mata ta saka a jaka bayan ta kwatanta masa gidan nasu, dama tana da abin da za ta ci amma ta kafa tijara sai da Mama ta biya ta kuɗin ɗumamen da aka ba ɗan ƴat uwarta Kalifa saboda rashin mutunci. Tana fita tsakar gidan Baba ya fara sababi yana faɗin "Saura in ga kin kwaso min ƙafafun ki a kwana kusa kin dawo min gidan nan, idan ba dubiya ko wani gagarumin dalili ba" Ya faɗa yana ɗaga murya, hakan ne ya ankarar da mutanen gidan zuwan Sadiya don lokacin da ta zo kowa yana ɗaki, amma yanzu kowa ya san ta zo. Mama Bilki da take zaune a ɗakin ta tana cin garin kwaki da suga jin furucin Baba ta sheƙe da dariya ta ce. "Wato ƴar da ake tunƙaho ta samu miji wasu basu samu ba, ita ce ake yi wa kashedin dawowa gida hummm a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta, da yake mijin ma ɗan tijara ne ba wani mai hannu da shuni ba ne da mai kuɗi ne in sau ashirin za ta zo gidan ai ba za a gaji da ita ba saboda an san nauyi za ta rage in ta zo, amma da aka san talaka ne mijin ita ma Allah baku mu samu ce ai gashi nan da tsakar rana ana korarta" Ta faɗa tana dariya Aisha da take danna waya bata ce mata komai ba. A can tsakar gidan Sadiya ta juyo ta ce "Baba don Allah ka barni in an yi la'asar rana ta yi sanyi sai in tafi, amma rana a buɗe kuma wallahi gori yake min duk ranar da na koma gida da wuri bare yau da tsakar rana" Baba ya ce "Ya miki goriba ba gori ba, ba mijinki ba ne ai in baki sani ba ki sani baki da gidan da ya fi gidan mijinki" Haka ta juya ta tsaya a zaure ta goge hawayen duk da kowa yana ganinta zai gane ta yi kuka, gashi Baba ya ƙi barin ta zauna a gidan ma bare ta yi ɗan zance nauyin zuciyarta a ragu. Baba kuwa har bayanta ta bi sai da ya zo har ƙofar gida ya tsaya ya hange ta ta kama hanyar gidanta duk da akwai tazara sosau daga gidansu zuwa gidan nata. Cikin gida ya koma ta ƙara zuwa ɗakin Mama Talatu ya ƙara kora mata kashedi sannan ya buɗe ɗakinsa, ruwa ya ɗauka tare da awararsa ya zauna ya shiga ci. A zuciyarsa yana faɗin "In banda abin Sadiya ke da Allah ya dube ki a haihuwar fari ya baki ɗa namiji yanzu wannan yaron yana tasowa ba kin huta ba, zai ke ɗaukan ɗawainiyarki, ni ba gashi nan ba sau mata rigis nake haifa" A ɓangaren Sadiya tun da ta kama hanya take ta zancen zuci, ta san yau sai dai ta tashe kunnuwanta don Nasir sai ya yayyanka mata baƙaƙen maganganu, ya faɗawa iyayenta maganar da take sosa mata rai kwata-kwata bai san darajar mutane ba. Gabaɗaya ta gaji a haka ta ƙaraso unguwar tasu, tana shawo kwanar gidan nata, sai ga Nasir a bayan mashin za su wuce ta, da alama daga gidan yake, amma kallo ɗaya ya musu ita da Kalifan ya ɗauke kai tamkar bai san su ba, kai tamkar ma babu wata alaƙa a tsakaninsu, a nata ganin ko da ita bai nuna ya santa ba, ai ya nuna ya san ɗansa tun da jininsa ne, duk da ta san ɗan nasa ma ba wani son sa yake ba. Haka ta daure ta cigaba da tafiya ga zafin rana, jikinta tana jin yadda gumi yake zuba a bayanta duk rigarta ta jiƙe. Da yake a ƙofar gidan nata akwai matakala guda biyu wanda sai ka taka sannan za ka buɗe ƙofar gidan, har sai da ta taka matakalar tana tsaye a ka ta buɗe jakarta pose wacce mukulli ne kaɗai a ciki ta zaro mukullin tana shirin saka mukulli ta buɗe jamlock ɗin amma sai ta ga wani abu a jikin ƙofar wanda ya yi matuƙar bata mamaki... MAMAN AFRAH 09025576222 [10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/IQU3wL7NUTCCqrbtxkJaaz?mode=ems_wa_t *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 3️⃣ Fitowarsa kenan daga wanka jikinsa ɗaure da towel inda kansa yake tsane ruwan da yake jikin kwantaccen gashin kansa, ƙarasowa ya yi tsakiyar ɗakin har lokacin yana goge gashin kan nasa gaban madubi ya ƙarasa ya ahiga shafawa fatarsa mayukan da suka dace da ita mayukan da suke jibge da turaruka a kan madubin tamkar an buɗe shago. Ibrahim kenan ɗa ɗaya tilo a wajen Alhaji Sule wanda yake kira da Daddy ɗa kuma a wajen Hajiya Faty wacce yake kira da Mummy. Fari ne dogo sannan ba siriri ba ne faffaɗa ne mai yalwar kwantaccen gashin kai, yana da manyan idanu wanda suka ƙawatu da zara-zaran gashin ido da gashin gira yana da ƙaramin baki pink lips, sai dai bashi da hayaniya. Ɗan gata ne na ajin ƙarshe a wajen iyayensa mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne kuma tsohon ɗan siyasa, iyayen Ibrahim suna matuƙar son sa, basa son ɓacin ransa, sai dai bashi da mata hatta budurwa ma bashi da ita, tun da ya dawo daga ƙasar america da ya kammala karatunsa yake kula da kamfanonin mahaifinsa. Burin iyayensa yanzu su ga ya yi aure domin su ga sun samu jika, kasancewar shi kaɗai Allah ya basu. Sai da ya gama shiryawa tsaf ya saka fararen wando da riga sai dai rigar tana da dogon hannu, kayan sun yi matuƙar amsar jikinsa ya ƙara komawa gaban madubi ya taje gashin ya kwantar da shi da brush kumb. Turaruka ya sake fesawa kafin ya ɗakko wayoyinsa da jakarsa da zai tafi kamfani kasancewar Daddy ya ce za su fita da wuri akwai baƙi da za su yi yau, za a tattauna a kan wasu kayan. Wayarsa ya duba sai ya ga ƙarfe tara hakan ya bashi tabbacin ya sha baccin bayan komawarsa da gari ya waye, ganin miss call ɗin Daddy a ransa ya ce "To fa! Daddy ina ga ya fita ma ya barni" Ya faɗa yana ɗakko takalminsa a wajen takalma ya saka ya shiga sakkowa daga matakalar benen, a hankali cikin hutsuwa, Ibrahim mutum ne nutsatstse kuma yana da ibada. Yana baro part ɗinsa direct part ɗin Daddy ya nufa, sai dai ya samu babu kowa sai ƙaran AC da tv a falon, fitowa ya yi ya nufi part ɗin Mummy da sallama ya tura ƙofar falon, sai dai babu kowa sai mai aiki tana goge -goge, cike da girmamawa ta shiga gaishe da shi ya amsa ko kallon inda take bai yi ba amma dai a muryarsa da ta saurara babu wulaƙanci kuma kowa ya san shi ko a bayan idanunsa suna yabonsa domin ya san daraja da muhimmancin ɗan adam. Sai da ya je tsakiyar tangamemen falon ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu ya ce "Ina Mummynah" Dakatawa ta yi da goge -goge ta ce "Yanzu ta haura sama" Iska ya hurar daga bakinsa ya ce "Ki mata magana bana son haurawa saman" A ladabce ta amsa masa tana tahowa za ta yi w Hajiya Faty magana, ganin yana danna waya ta saci kallonsa a ranta tana kissima cewa tabbas duk macen da ta samu Ibrahim a matsayin miji haƙiƙa ta dace. Kusan tare suka sakko da Hajiyar lokacin yana waya da Daddy Mummy ta ƙaraso ta zauna a kusa da shi, har ya gama wayar ya kashe yana kallonta da murmushi a saman fuskarsa ya ce "Ina kwana Mummy nah" Dariya ta yi tana masa kallo mai cike da ƙauna irin ta uwa da ɗa ta ce "Ka manta da asuba ma da kuka dawo daga masallaci ka gaishe da ni?" Ta faɗa tana dariya mai bayyana haƙora. Shi ma murmushin ya yi ya ce "To Mummy ko sau nawa ɗa ya gaishe da mahaifiyarsa ai ba wani abu ba ne" Kai ta gyaɗa masa ta ce "Mai za ka ci?" Fuska ya shagwaɓe ya ce "Ni ba na jin yunwa, tun da kuka rigani karyawa" Mummy ta ce "To Mu'azzam rigimamme, ai kai tun da sarkin bacci ne waye zai jira ka yunwa ta masa lahani, Daddyn ka ma da ya ce za ku fita gajiya ya yi da maka waya ya ce in ka tashi ka bi shi" Yana ɗan yatsina fuska ya ce "Yanzu na kira shi ya ce yana kamfanin siminti kin san baƙin nan da za a yi magana da su ba ƙaramin kaya za su saya ba" Haka suka ci gaba da tattaunawa ta zubo masa abincin ya zauna a kafet ya ci ba wani da yawa ba, dama dankali ne da wainar ƙwai sai shayi da ya sha shi ma kaɗan. Bayan ya gama ya mata sallama ta masa addu'a ya fito riƙe da jakar da wayoyinsa, ya samu an wanke gabaɗaya motocjn da suke wajen an goge sai sheƙi suke, direba da sauri ya matso ya karɓi jakar ya saka a baya yana gaishe da shi da girmamawa ya amsa, da kansa ya buɗe bayan ya shiga ya zauna direban ya rufe masa marfin ya shiga ya tada motar mai gadi ya wangale musu tangamemen get ɗin suka fita yana ɗaga musu hannu ya mayar da ƙofar ya rufe. Sun haura titi suna tafiya sai karatun qur'ani da yake tashi a ciki, wanda duk direbobin sun sani idan Ibrahim ne a mota ba a kunna masa waƙa. Sun kusa ƙarasawa kamfanin inda direban ya gangara gefen titi kasancewar ba a farko bakin titi kamfanin yake ba sai an gangara. Gangarawar da direban ya yi ya fara tafiya kaɗan akwai akwai wani wuri da ruwa ya ɗan taru da yake wajen daga gefen car wash ne da alama ruwan wajen ne ya ɗan gangaro, wasu ƴanmata guda biyu sun taho ɗaya tana ɗagawa wani napep hannu, direban cikin rashin sani tayar ta shiga cikin ruwan, sai ruwan nan ya fantsala bai yi masauki a ko ina ba sai a jikin ƴanmatan nan guda biyu, farar ita kawai ruwan ya fatsu da jikin takalmin ta ne, inda baƙar kuma gabaɗaya ruwan ya ɓata mata rigar jikin ta. Direban ne cikin nuna rashin jin daɗin abin da ya yi ya ce "Subhanallah" Ibrahim da yake danna waya ya ɗago shi sai lokacin ma ya ga abin da yake faruwa, amma sai ya rasa ma mai zai ce. A waje kuwa Aliya ce cike da masifa ta danƙaro wani ashar mai gunna ta yi tana kallon motar ranta yana matuƙar ɓaci ta ce "Wannan daga gani ƴan Allah baku mu samu ne, wato karere masu cin arziƙi don babu yadda za a yi wanda ya taka arziƙi ya san darajar wannan kyakkyawar motar ya saka ta a cikin ruwan caɓali" Ta faɗa tana kama tsantsa, yayin da direban ya yi parking a gefe yana neman izinin Ibrahim a kan zai fita ya basu haƙuri. Ibrahim ne ya ce "Sai ka kula ka ga Daddy yana kirana tun ina gida, gashi ka zi ka janyo wannan duk ta cikawa mutane kunne da hayaniya" Da to ya amsa, ita kuma Aliya kasancewar bata ganinsu da yake glass ɗin baƙi ne baka ganin wanda yake cilin motar. Jidda wacce take kallon rigar jikinta yadda ruwan nan ya ɓata, fuska ta ɓata ba tare da ta ce komai ba tana tunanin yadda za ta koma gida ba ta sauya kaya saboda duk sun jiƙe, kuma gashi makarantar fa za su je exam za su shiga. Direban yana fitowa tun kafin ya buɗe baki Aliya ta fara zaginsa tana cewa "Ai dama na san sai dai direba wanda ba a gaji arziƙi ba kuma ba a san darajar kuɗi ba, shi ya sa kake zunduma wannan kyakkyawar motar a ruwa marar kyau, da a ce ma kuɗi ne za ka biyani ladan mata min takalmin da ka yi da ba haka ba, to yanzu dai na san haƙuri ka fito ka bani kuma wallahi ina so ka sani ko za ka tafi tsirara sai ka biyani diyyar ɓata min takalmi" Ta faɗa tana ɗaga jijiyoyin wuya, shi kuma direba ya dage sai bata haƙuri yake kamar zai ari baki ya ce "Haba baiwar Allah, yanzu ki kalli ƴar uwarki ita ce aka yi wa abin da ya cancanci a bata haƙuri, kalli yadda aka ɓata mata jiki amma ke da ruwan ma kaɗan ne ya taɓa ki kike wannan abin" Jidda ganin suna hayaniya ta ce "Kai Aliya dan Allah ki yi haƙuri mana, kin zauna kina ta ɗaga jijiyoyin wuya a kan wannan abin ƙanƙ... Hannu ta ɗagawa Jidda ta ce "Dalla malama rufewa mutane baki, ana maganar waɗanda suka san ciwon kansu a kan haƙƙi ai ke bakya saka baki ba, ni idan ni ya ɓatawa kaya kamar yadda ya ɓata miki da tuni na sharara masa mari" Da sauri direban ya kai hannu ya dafe kumatunsa tamkar dai an mare shin. Jidda kuma ranta ne ta ji babu daɗi jin an ce mata bata san ciwon kanta ba, kuma dama ta san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Aliya ce ta ɗaga hannu ta miƙawa mutumin a kan ya bata kuɗi, ɗari biyun da ta rage ya fito da ita ya miƙawa Jidda, yana cewa "Baiwar Allah ki karɓa ki saya omo ki wanke kayan da na ɓara miki" Kafin ya kai kuɗin saitin Jidda Aliya ta saka hannu ta warce tana cewa "Matsiyaci wai ɗari biyu, to na karɓe dama an ce sata a gidan ɓarawo rance ce, kuma raba arne da makami ibada ne" Ta ce tana saka kuɗin a jakar hannun ta. Jidda ce ta buɗe baki ta ce "Bawan Allah da baka wahalar da kanka wajen bayar da kuɗinka ba, da ka bari za su maka amfani amma ka ɗauka ka bayar, kuma ai kowane ɗan adam ajizi ne sannan yana iya yin laifi" Kai direban ya shiga gyaɗawa jin maganar hankali da hikima duk abin da ake yi Ibrahim yana kallonsu ta glass daga cikin motar. Ya yaba da hankali da nutsuwar Jidda, sannan ya lura ta san daraja da muhimmancin ɗan adam kamar yadda shi ma ya sani. Aliya kuwa ta wuce Jidda tana aika mata harara a inda da za ta wuce ta saka hannu ta daki bayan motar, napep take tsayarwa amma bai tsaya ba hakan ya sa ta tsallaka titin ta koma ɗaya ɓangaren, a nata tunanin ta tafi ta bar Jidda don ba za ta juri har sai ta jira ta ta koma gida ta sauya kaya ba, ba ma wannan ba ita a rayuwa ta tsani take tafiya da Jidda kasancewar Jidda baƙa kuma mummuna a zahiri Jidda bata da wani kyau, baƙa ce tana da faɗin fuska sannan tana da matsakaicin tsawo, tana da manyan idanu sai daj hancinta gajere ne kuma mai faɗi. Saɓanin Aliya da take fara tas kyakkawa ajin farko, tana da tsayi sannan tana da doguwar fuska dogon hanci wanda ake yi wa laƙabi da kamar biro duk wani abu da ya danganci kyau Aliya tana da shi wannan dalilin ne ma ya sa take ganin ta ciri tutar da sai ta zaɓi miji ta darje, miji ma na nunawa sa'a mai hannu da shuni wanda take ganin ko da ɓarawo ne in dai yana da kuɗi kuma yana da kyau to fa ta ga mijin aure don shi ne zaɓi kuma burinta. Tana daga can inda ta tsallaka tana hango direban nan da yake ta faman ba Jidda haƙuri kafin ya juya zai je ya shiga mota, ita ma Jiddan tana ta ƙoƙarin tafiya Aliya a zuciyar ta ta ce 'Hmmm! Ka ji da shi cuwon ajali a ɗan yatsa, tun da dai ka gama jiƙa mutane ai sai ka san inda dare ya maka, baka san cewa wannan baƙar mummunar da ita da bola mu duk ɗaya muke ganinsu ba, ni ma nan da ka ganni ƙaddara ta haɗani tafiya da ita, saboda kan nan nawa dusa ce ko in ce fanko ne babu komai a ciki, ko bihim ban sani ba wamda zan rubuta a exam ɗin da za mu yi, shi ya sa ma nake so mu tafi tare da ita tana rubutawa ina copy, dama ita take goyani a kowacce exam' Ta faɗa tana ɗan taɓe baki, tare da duba agogon da yake hannun ta. Ibrahim kuwa da sauri ya saka hannu ya buɗe ƙofar ya fito lokacin Jidda ta fara tafiya, yana zuro ƙafafunsa farare tas da suke cikin baƙin takalmi mai yatsa, Aliya tun daga tsallaken titin da take ta hangi an buɗe bayan haɗaɗɗiyar motar wannan wacce ta gama yi wa direban motar ɗiban albarka, mamaki haɗe da al'ajabi suka haɗe suka cunkushe kwanyarta, wani irin bugawa ƙirjinta ya yi da ƙarfi lokaci guda zuciyarta ta aiko mata da wani saƙon tambaya kamar haka 'Dama akwai wani a cikin motar ba direban ba ne kaɗai, kenan mamallakin motar ne wannan ya fito?' Ta tambaya kwata-kwata ta gagara ƙifta idanunta don gani take idan ta ƙifta tamkar wanda take hangowar ɓacewa zai yi. Ibrahim kuwa lokacin da ya fito Jidda ta masa ɗan nisa, domin ta saka gabata can tana ta zabga sauri, sannan shi bai ma san sunanta ba abu ɗaya kawai ya sani shi ne saboda ita ya fito daga motar. Direban ne ya buɗe ya fito, cikin hanzari ya gewayo inda Ibrahim ɗin yake cike da girmamawa ya ce "Yallaɓai kana buƙatar wani abu ne?" Ɗan shiru ya yi kafin daga bisani ya ce "Kawai na ga baka kyautawa yarinyar can ba ne, kuma na ga ita ko uffan bata ce maka ba" Cike da alhini direban ya ce "Wallahi yallaɓai ta san darajar mutane, duk da na yi abin ne cikin rashin sani kuma dama ɗan adama ajizi ne amma sai na ji ko kaɗan ban kyauta mata ba" Iska ya huro daga bakinsa yana sanya haƙorin gaba na cilin bakinsa ya dantse leɓansa na ƙasa, idanu ya mayar hanyar da Jiddar ta yi yana iya hango gidan da ta shiga daga can gefe wasu gidaje da suke a jere, sai ya ɗan jujjuya kamar mai neman wani abu, sai kuma ya kama ƙofar zai shige motar. Aliya kuwa da take jin duk kan motsinsa tamkar da bugun zuciyarta yake, hakan ya sa ta fara tunanin ita yake nema, bata yi ƙasa a gwiwa ba ta fara ƙoƙarin tsallakowa, garin sauri har wata mota ta kusa kashe mata ƙafafu, amma hankalin ta ya yi gaba, tana fatan wannan mai kuɗin ya zamana cikar burinta da kuma mafarkinta da na mahaifiyarta, don yanzu ne take ganin za ta cika burin kyawun da Allah ya bata. Garin sauri har harɗewa take, sai gata ta ƙaraso wajen a 360, Ibrahim ya ja ƙofar yana shirin rufewa don direban tuni ya shige mazaunin direba, kawai sai ya ga mace kamar an jefo ta, tana zuwa ta kama hannun ƙofar motar ta ce "Gani" Cike da mamaki yake bin ta da kallon rashin fahimta, kunnuwansa suna dawo masa da sautin furucin da ta yi ɗazu tun daga kan ashar da kuma cin mutuncin da ta yi wa direbansa, cike da takaici ya ce "Wa yake neman ki?" Inda-inda ta fara jin tambayar da ya mata, rai ya haɗe ya ce "Dalla matsa zan rufe mota" Da baya ta ja tana jin ƙamshin turarensa na masu aji, ya kaure ko ina na mashaƙar numfashin ta, ba ma wannan ba tsananin kyau da farin da yake da shi gashi kuma a gefe ɗaya ɗan gayu ne wannan ne abin da ya damfaru a zuciyarta, tana jin inama wannan ya zama mallakin ta tabbas da ta huta, babu ita babu kukan muni ko talaucin miji, don ta raɗawa zuciyarta wannan shi ne mijon da ake kan yayi, kuma shi ne wanda za a yi ta yayi har abada!. MAMAN AFRAH 09025576222 [10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/B6ZgynXRCc3LWNggTkzg7X *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE4️⃣ IBRAHIM Yana gama rufe ƙofar ya ba direban umarnin su tafi, jan motar direban ya yi suka ƙarasa ƙofar tafkeken get ɗin kamfanin yana zuwa ya danna horn aka buɗe musu, ya cilla hancin motar cikin get ɗin. Aliya da take tsaye a wajen kamar an dasa ta, idanunta ƙurrr a kan motar da take sheƙi tana ɗaukan idon sabunta, har suka shiga bata ɗauke idanunta ba, sai da ta ga an rufo get ɗin sannan ne ta dawo hayyacin ta, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana rayawa a zuciyarta cewa tabbas idan da rai da rabo ta ci alwashin mallakar wannan kyakkyawar halittar inda kuma take ganin za ta huta domin muddin ta auri wannan ta yi ban kwana da wata kalma wai wahala ko rashin kuɗi. Idanu ta lunshe tana hango kyakkyawan farin hannunsa mai ɗaure da tsadadden agogo a idon zuciyarta, tana iya hango yadda kwantaccen gashin hannun yake a jikin hannun yanayin fatarsa kaɗai tamkar wanda ba a Nigeri'a yake rayuwa ba, bata san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata ba don har ta fara hango irin soyayya da kulawar da za ta samu idan suka mallaki juna a matsayin ma'aurata. Jidda kuwa lokacin da ta ƙarasa gida da sallama ta shiga, amma maimakon Umma ta amsa mata sai ta mata banza, sai da ta yi sau uku amma Umma ko ɗagowa bata yi ta kalle ta ba, bare ta saka ran za ta amsa mata, hakan ya sa cikin sanyin jiki ta shiga gidan tare da nufar ɗakin nasu don ta sauya kayan ta san matuƙar ta tsaya jiran sai Umma ta amsa mata sallama to har rana ta faɗa bata samu hakan ba. Gashi kuma tana son ta je kar a shiga jarabawa. Tana shiga ɗakin ta nufi wajen jakar kayanta, dakyar ta ɗakko wata doguwar rigar atamfa roba ta saka duk atamfar ta koɗe, amma a haka ta saka saboda duk kayan nata idan Abba ya ɗinka musu Umma take ƙwace nata ta bayar sai ta sayi mai araha ta bata wani lokacin ma sai ta hanata mai arahar, shi kuma Abba da yake ba a gidan yake wuni ba kullum yana kasuwa ba sanin mai yake faruwa yake yi ba. Hijabi ta ɗauka ta saka shi ma duk ya ɗan yi fari, kayan ta mayar ta rataya a saman ƙofa a cewarta idan ta dawo daga makaranta sai ta wanke tun da yau jarabawa biyu za su yi. Fitowa ta yi da jakarta a hannu, ganin Umma tana zuba ruwa a buta, ta ce "Sai mun dawo Umma" Wata uwar harara Umma ta jefa mata, da ba za ta yi magana ba ma sai dai ta ce "Ko ki dawo ko ki dawwama a can duk uwar ubansu ɗaya" Jikin Jidda sanyi ya yi hakan ya sa ta kalli Ummar kamar za ta yi kuka duk da wannan kalamai ne wanda ta saba jin su amma a koyaushe aka mata su sai ta ji su tamkar sabbi ne dal a leda aka buɗe, suna zame mata sababbi a koyaushe domin kalamai ne mararsa daɗi ƙiri-ƙiri ake nuna maka an tsane ka. Ganin yanayin da Jidda ta shiga Umma ta ce "To baƙa mai baƙar zuciya, kun ƙura min ido ni kar ki cinye ni kurwata kurrr, ni wallahi ban san dalilin da mutum zai ɗakko bare ya kawo cilin iyalinsa ba, ina dalili kawai a ɗakko mana annoba a kawo mana gida shekara da shekaru, ni yanzu ban ma san ranar da zamanki a gidan nan zai yanke ba, to wannan abu baƙiƙƙirin hanci kamar ƙofar gari abu babu fasali ta ko ina wane namijin ne ,ai kwasa? Tun da dai aure shi ne mafita ɗaya da za ki bar mana gida tun da babu dangin iya bare na Baba, babu inda za a kai ki ko ki raɓa mu ɗin dai mu ne ƙaryar taki, amma wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, dole idan kuka ƙarasa makarantar nan tun da yanzu jarabawa ta rage idan baki samu mashinshini ba ko sadaka ce ba bayar da ke ko ga ladanin masallaci ne" Umma ta faɗa tana tashi tsaye daga sunkuyon da ta yi tana zuba ruwan a buta. Jiki sanyi ƙalau Jidda ta juya tana ɗaga ƙafa kamar an mata dabaibayi a ƙafafu, fitowa ta yi daga gidan tana ɗaga ƙafa ta kamo hanya fito da wayarta keypad ta yi daga jaka ta duba ta ga lokaci ya kusa tana fatan kar a samu goslow a hanya. Hango Aliya tsaye idanu a rufe ya bata mamaki, tana ƙarasowa ta ce "Aliya lafiyarki kuwa?" Da sauri Aliya da idanunta suke rufe babu abin da take hangowa sai gasu nan sun yi aure da wannan kyakkyawan matashin tana cikin daula tana wulaƙanta ƴan aiki da kuma dangi ƴan uwa, hatta Jidda sai da ta ganta ta zo gidanta tana saka masu tsaron ƙofa su yi waje da ita wai bata santa ba. Yatsina fuska Aliya ta yj lokacin da ta buɗe idanun, a maimakon ma ta ba Jidda amsa sai ta juya ta fara tafiya, ita Jiddar sai ta take mata baya suka ƙarasa bakin titin, napep suka tsayar suka shiga. Sa'adatu Rimi suka nufa domin a can ne suke karatun N.C.E suna shekararsu ta ƙarshe saura jarabawa biyu ma su kammala karatunsu. Lokacin da suka tashi ƙarfe biyu na rana ne, lokacin rana ta take, dakyar suka samu napep ɗin, sai dai kuɗin da ya yanka musu na Jidda naira hamsin bata cika ba hakan ya sa ta nemi alfarmar ya rage mata amma ya ce ba zai rage ba saboda shi ma ba ruwa yake zubawa a napep ɗin ba mai yake zubawa, suka tsaya a kan cewa idan an kusa zuwa za ta sauka haka ta amince. A daidai wani gidan mai ya sauke Jidda saboda har rance ta ce Aliya ta bata amma ta ƙi bata kuma akwai kuɗin a wajen Aliyar. Tana ji tana gani haka ta sauka da ranar nan ga yunwa da suka kwaso. Aliya har da wani taɓe baki ta yi da sakin murmushin mugunta, dama da a tafiya ne sai ta ranta mata ko don saboda ta bata amsar exam tun da idan basu tafi tare ba sun zauna a kujera ɗaya ba sai dai ta bayar da takardar a haka ba tare da ta rubuta komai ba, kasancewar banda dusa babu komai a kan nata hasali ma bata karatun shiririta kawai take a makarantar da biyewa ƙawaye ƴan ƙarya, ita kuma Jidda karatun take yi gata da ƙoƙari kanta yana ja sosai da sosai saboda tana da mayat da hankali. Tafiya take har ta ƙaraso wajen kamfanin simintin nan nasu Ibrahim, tana tafiya sai gumi ne kwance a fuskarta kasancewar ranar da ta take, Ibrahim wanda tun zuwansu da direban ya ce direban ya tafi da motar gida, saboda da Daddy za su tafi gida, ƙarfe biyu da rabi suka tashi Daddy da Ibrahim ne a baya sai direba yana jan su, mai gadin ƙofar kamfanin ya buɗe musu get suka fito, Ibrahim wanda tun bayan zuwansa kamfanin yake ta tunanin Jidda duk da bai san sunanta ba amma tabbas ya yaba da hankali da tunaninsa yarinyar ta birge shi sosai. Suna fitowa kamar an ce ya ɗago fuskarsa sai kawai ya sauke a kan Jidda wacce take tafiya cikin natsuwa kanta a ƙasa, gabaɗaya ya mayar da kallonsa kwacakom kanta, yana ganin yadda hijabin ya mata kyau, shi dama yana son ya ga mace tana suturta jikinta, tambayar zuciyarsa ya fara yi yana cewa 'Ko ina fitsararriyar ƙawar nan tata, wacce bata san darajar ɗan adam ba, wannan ko kaɗan baku dace da zama ƙawaye ba, ana cewa sai hali ya zo ɗaya ake ƙawance amma dai ku kun sha bam-bam a halayya' Ya faɗa yana bin bayanta da kallon don lokacin ta gifta, ta kama hanyar gidan da ya ga ta shiga lokacin da ta tafi da safe, kuma yana ji a jikinsa inda ya ga ta shiga da safen nan ne gidansu, ko yanzu ya so a ce babu Daddy da sai ya tambaye ta ko da sunanta ne. Direba yana ɗan waige-waige domin zai haura hancin motar saman titi, a daidai nan Daddy ya lura da Ibrahim ya juya bayansa yana kallon waje daga cikin motar, a nutse Daddy ya ce "Mu'azzam" Amma da yake ya yi nisa bai san Daddy ya kira shi ba, duk da suna zaune a kusa da juna, sai da Daddy ya maimaita ya ce "Mu'azzam" Ya faɗa yana ɗan taɓa shi, sannan ne Ibrahim ya juyo da sauri yana ɗan murmushi ya ce "Na'am Daddy" Daddy da ɗan mamaki a fuskarsa ya mayar da hankalin wajen da Ibrahim ɗin yake kallo a ƙoƙarinsa na ganin ya hangi abin da ya ɗaukewa tilon ɗan nasa hankali. Sai dai iya ganinsa bai ga kowa ba, saboda wajen akwai mutane kowa yana dabgar gabansa sannna ita wacce Ibrahim ɗin yake kallo wato Jidda ta riga ta miƙe ta yi ɗan nisan da Daddy ba zai fahimci ita Ibrahim yake kallo ba, kuma ko da a ce ya hango ta ba lallai ya kawo cewa ita ɗan nasa yake kallo ba kasancewar ba halayyar Ibrahim ɗin ba ce kallon mata don su a halin da ake ciki ma yanzu burin su bai wuce ya fitar da mata su masa aure ba, amma ya ƙi sai ya ce wai akwai lokaci!. Daddy kallonsa ya mayar kan Ibrahim lokacin har sun haura kan titi direba ya ɗau hanya ya ce "Mu"'azzam mene ne ya ɗauke maka hankali har ya hana ka jin kirana?" Murmushi Ibrahim ɗin ya yi ya ce "Kawai dai ina kallon jama'a ne Daddy" Ya faɗa saboda ba ya son ya faɗawa Daddy cewa mace yake kallo ya san idan ya faɗa masa gaskiyar abin da yake kallon shikenan kuma yau haka za su wuni suna tsokanarsa shi da Mummy. Ɗan zantawa suka shiga yi a tsakaninsu irin na ɗa da uba. A ɓangaren Jidda kuwa lokacin da ta isa gida ta tarar Aliya da Umma suna zaune a baranda a tabarma suna hira, Aliyar tana cin abinci, babu wanda ya amsa sallamar da ta yi sai ma wani kallon tsana da ƙasƙanci da Ummar take bin ta da shi. Ɗaki ta nufa ta ajoye jakar hannun ta, ta cire hijabin ta fito ta ɗauki ruwa a buta ta shiga banɗaki, ruwa ta kama ta fito dama fashin sallah take shi ya sa bata ma yi sallah a makaranta ba. Sai da ta zo saitin su Umma ta ce "Umma ina abincina?" Kallon sheƙeƙe Umma ta mata ta ce "Wanda kika kawo na ajiye miki?" Ta faɗa tana kallon Jidda da take wasa da yatsun hannun ta. Jin bata amsa mata ba ta ce "Na ce wanda kika kawo min in dafa miki?" Kai ta girgiza, sai Ummar ta ce "Tun da kin san baki kawo ba kar ki tambayeni" Aliya jin ta ƙoshi sai ta ajiye cokalin ta ture plate ɗin gabanta ta saki wata gyatsa, haɗe da komawa ta kwata tare da ɗora kanta a kan cinyar Umma tana mai cewa "Wash Allah na ƙoshi kuma na gaji" Umma ta ce "To ba sai ki huta ba, dama an je ana taa gwagwarmayar jarabawa, Allah dai ya baki sa'a" Aliya ta ce " Amin Ummana, ai daɗin mai uwa a gaban murhu sai ya ci ya ƙoshi" Jidda jin wannan furucin ya sa ta tuna da tata mahaifiyar hakan ya sa ta ji ƙwalla ta taru a idanunta yanzu shekara goma sha ɗaya kenan da ƙada ta rufe idanunta idan ta tuna lokacin mahaifyarta tana raye duk abin da ta ci sai ta ajiye mata, ko da bata nan haka za ta ajiye mata wani lokacin ma ita ta haƙura ta ajiye mata, amma yanzu mutuwa mai rabawa ta raba su, mutuwa mai yankan ƙauna ta raba tsakani. Ɗaki ta nufa ta je ta hau kan ƙaramar katifar ta, kwantawa ta yi rubda ciki ta ɗora kanta a kan filo, idanu ta lumshe tana jin yadda yunwa takr addabar ƴaƴan hanjin ta, wanka ma take son yi amma kuma yunwa ba za ta barta ba. Idanu ta rufe wasu zafafan hawaye suna gangarowa, tana jin tamkar yau ne ta rasa mahaifanta, tana jin kewarsu a zuciya da ruhinta, abubuwan da suke faruwa bayan mutuwarsu masu ɗaure kai da kuma al'ajabi su ne suke saka take ta tunanin shin dama haka rayuwa take?. Juyi ta yi sai kuma ta ji Umma tana ƙwala mata kira, da sauri ta tashi zaune tana goge idanun ta, sai da ta tabbatar cewa babu hawayen sannan ta fito ta ce "Gani Umma" Umma ta ce "Gashi nan sai ki ɗauka, wato kin je ɗakin kin ƙule sai ya dawo ya zaci wani abun aka miki ya ishe mutane da tambaya" Ta faɗa tana turo mata plate ɗin da Aliya ta ci abinci ta rage, kaɗan aka ƙara abincin a kan sauran Aliyar, ba tare da ta ce uffan ba ta ɗauka ta juya tana dab da shiga ɗaki Aliya ta ce "Eh mana kya ɗauki ki tafi ai ko godiya babu, tun da ga baiwar ki da kika ajiye ta girka miki ta dafa ta baki" Juyowa Jiddan ta yi ta ce "Na gode Umma Allah ya saka fa alkairi" Ta faɗa jin Ummar bata amsa ba kuma dama ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne, sai ta juya ta shige ɗakin. Tas ta cinye abincin duk da bai wani ishe ta ba, amma dai ta ji yanzu ta dawo dai-dai shiru ta yi tana tunanin mai ya sa Umma ta sauya, mai ya sa a da can baya lokacin iyayenra suna raye bata nuna ta tsane ta ba sai yanzu? Mai ya sa a da take nuna mata ƙauna daga ita har Aliya amma yanzu tamkar basu taɓa son ta ba ma. Ta jima tana saƙa da warwarar kafin ta fito da kwanon lokacin ana kiran sallar la'asar banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito Umma ta kalle ta ta ce "Haka kawai kike yi wa mutane wasan ruwa da sabulu, abin da duk wankan da za ki yi ba sauyawa ,a ki yi ba kina nan a baƙar ki" Bata ce komai ba ta shige ɗakin. Bayan ta saka wani kayan ta ɗakko kayan ta da ta ɗora a kan ƙofa da safe ta haɗa da wanda ta je makaranta da shi ta wanke ta shanya. Ganin rana ta yi sanyi ta sharo ɗakin nasu duk da babu datti, tsakar gidan ta fito ta share tas ta kwashe. Kayan wanke-wanke ta haɗa ta wanke, bata gama gyaran gidan ba sai da la,asar lis. Butoci ta ciccika ta ajiye, lokacin Aliya suna ɗaki ita da ƙawarta Amatullahi. Tahowa ta yi za ta kai kwando kicin cikin rashin sani ta bige Umma da ta fito daga kicin, a ƙufule Umma ta ɗaga hannu za ta wanke fuskar Jidda da mari, a daidai nan Abba ya shigo da sallama, turus ya yi yana kallon Umma... MAMAN AFRAH 09925576222 *🩺 GHT HERBAL SOLUTIONS 🩺* *Maganin da ke dawo da lafiya, da izinin Allah!* Muna sayar da ingantattun magunguna na zamani da aka gwada kuma suka shaida aiki. *Duk wannan cutar ana warke wa sosai mutum ya dawo nml* *Ga wasu daga cikin cututtuka da muke da magani a kai:* ✅ Ulcer ✅ Hawan jini ✅ Ciwon zuciya ✅ Ciwon Suga (Diabetes) ✅ Ciwon daji ✅ Ciwon koda & hanta ✅ Zazzabi mai tsanani ✅ Ciwon gabobi & ciwon jiki ✅ Ciwon ido & kunne ✅ Asma, tarin fuka & mura ✅ HIV ✅ Matsalar rashin haihuwa ✅Gyaran data ✅Na kurajen fuska ✅Na rage kiban ✅Na Saka kiba ✅Na infection 🟢 Da sauran su... *Me ya bambanta GHT?* 🌿 Magungunan mu halal ne kuma an tsaftace su. 🔬 Sun wuce binciken lafiya da gwaji. 🌟 Suna da matukar tasiri – an samu sauki ga dama-dama. 🧕🏽 Muna kula da sirrin marasa lafiya. 🚚 Muna da isar da magani kai tsaye (Delivery available). *Kira yanzu ko shiga group ɗinmu don karin bayani da order:* 📞 [08161316781] *GHT — Magani cikin Sauki da Aminci* *“Lafiyar ku shine babban burinmu”* [10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/B6ZgynXRCc3LWNggTkzg7X *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 5️⃣ *ZALIKA* Zaune suke a ƙaton falon da ya gaji da haɗuwa, hira suke sama-sama kowanne yana danna wayarsa. Mubin ne ya jingina da jikin kujera yana ajiye wayarsa a kusa da shi ya kalli Zalika ya ce "Ina son magana da Baffa amma wallahi tsoro nake" Baki Zalika ta taɓe da kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce "Maganar mai? Kaima da ka shafawa kanka lpia da wannan tunanin ka san dai ko ma wace magana ce Baffa ba saurarenka zai yi ba gwara ma ka faɗawa Mamy, don ni yanzu na cire faɗawa Baffa abu ma saboda ba saurarena zai yi ba" Ta faɗa tana maida hankalin ta kan waya. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Ni ba wata magana nake so mu yi ba kawai dai ina so mu zauna mu tattauna, ina nufin mu yi hira irin na ɗa da uba" Ya faɗa idanunsa suna yin jawur tamkar zai yi kuka hatta a muryarsa raunin hakan ya bayyana. Zalika ta ce "Uhum in ji mai ciwon haƙori, ni wallahi har mantawa ma nake da Baffa idan magana ko damuwa ta same ni, kuma ko da na ji shauƙin son magana da shi a matsayinsa na mahaifina ina kawar da hakan domin na san abu ne mai wahala, shi ya nuna ba ya buƙata to mu ma mai zai hana mu danne zuciyarmu?" Iska Mubin ya fesar haɗe da sakin ajiyar zuciya ya ce "Ni wallahi ina kasa jurewa wani lokacin, abin yana birgeni kuma yana bani sha'awa idan na je gidan abokaina na gansu suna hira ana raha da mahaifinsu amma mu mun mallaki komai na rayuwa amma mahaifinsu bashi da lokacinmu, sannan ba wai ayyukan ne suka masa yawan da ba zai sauraremu ba, shi fa tun asali ma haka yake babu ruwansa da lamarin ƴaƴansa, sai dai Mamy ta maye mana gurbin mahaifi da mahaifiya" Mubin ya faɗa cike da damuwa. Mamy da take laɓe tana jin su duk sai jikinta ya yi sanyi, tabbas ta san kowane ɗa yana da burin mahaifinsa ya tattuna da shi ya ji damuwoyinsa, amma su basu san daɗin mahaifinsu ba gashi dai yana raye amma sun zama marayu ta ɓangarensa, ita kanta ba ya zama da ita, ƴaƴansu sai ita za ta kula da su, kama daga tarbiyarsu da zama da su ta ji abin da yake damunsu ko shawara fa sauransu. Shi abin da ya ɗauka guda ɗaya shi ne idan ya ajiye kayan abinci da kuɗi to ya gam da fannin iyali, ya ɗaura ragamar tarbiya da komai a wuyan mahaifiyarsu a cewarsa shi uba ɗaukan nauyin gidan ne kawai ya rataya a wuyansa, ita kuma uwa ita ce za ta basu tarbiya, bai san cewa tarbiya ba ta mutum ɗaya ba ce, tarbiya ta uwa da uba ce duka, ba zai yiwu a ce uwa kaɗai ta ɗauki wannan ragamar ba, don tarbiya ta kowa ce. A hankali ta fara takowa daga inda take dama a ɗan koridon bedroom ɗinta na ƙasa ta tsaya take jin hirarsu da take dakar mata zuciya. Tana tahowa tana ƙarewa falon kallo yadda aka kashe dukiya a gidan amma kuma an samu naƙasu a wajen gudanar da zaman gidan, ta rasa mijin ta wane irin mutum ne shi kaifi ɗaya da ba ya sauyawa daga kan aƙidarsa. Tana zuwa cikin falon ta buɗe baki cike da kulawa, fuskarta washe kamar gonar auduga ta yi sallama cike da kulawa da nuna soyayya da ƙauna ga yaran nata, Zalika ce ta amsa ita ma tana murmushi saɓanin Mubin da ya sadda kai bai amsa sallamar ba kuma bai kalli Mamy ba. Duk da Mamy ta ji babu daɗi a ranta na ganin yanayinsa kuma ta san damuwarsa domin ta ji abin da suke tattaunawa, ko da a ce bata ji ba to dama ta san damuwar ƴaƴan nata tun da basu da wata matsala a rayuwa sai ta mahaifinsu, matsala ce wacce tun asali aka tashi da ita kuma ta yi ƙoƙarin kawo gyara da maslaha amma abin ya ci tura!. Idanunta ne suka nemi fitar da ruwa, amma ganin Zalika ta mayar da hankalinta kwacakom kanta sai ta yi ƙoƙarin dannewa, faɗaɗa fara,arta ta yi ta ƙaraso falon ta zauna tana mai cewa "To ko dai falon iya ƴan uwa ake buƙata a ciki ni na zo na kawo kaina" Ta faɗa cike da wasa rana son kawar da damuwar da ta gani shimfiɗe a fuskar Mubin, amma har lokacin bai ɗago ba kuma bai yi magana ba. Zalika ce ta ce "Kai Mamy har ma da wani hirar ƴan uwa da za a ce uwa ba za ta zo ta ji ba, bayan ke kaɗai ce ginshinƙin mu ke kike kulamu ke kike ɗauke duk wani nauyin da zukatanmu suka yi" Ta faɗa tana kallon fuskar mahaifiyar tata. Mamy ta gane mai qannan kalaman na Zalika suke nufi amma kuma bata son ta ɗora ƴaƴanta a ragamar da za su cigaba da ganin laifin mahaifinsu duk da ta san yanzu sun yi wayo sun fahimci komai game da halayyar mahaifinsu, duk da a baya ma tun suna yara suna iya ganewa domin suna tamabayarta bare kuma yanzu da suka mallaki hankalin kansu. Cikin zolaya ta sake cewa "To ai na ga ɗan uwanki ko ɗaguwa bai yi ya kalleni ba, ba dole na ce ko zancen da ya shafi ƴan uwa kuke yi ba" Ta ce tana kallon Mubin. Mubin wanda rauninsa ne yake son bayyana kamar ba namiji ba abin da ya sa ya ƙu ɗago fuskarsa ba ya so Mamy ta ga yana cikin damuwa kuma ya san damuwarsu damuwarta ce ko kaɗan bata sukuni a duk lokacin da ɗayansu ba ya cikin walawal, sannan abu ɗaya ne ya hana shi yin magana shi ne va ya son muryarsa ta fallasa abin da yake cikin zuciyarsa. Mamy da take kallonsa cikin sanyin murya ta ce "Mubin ɗina" Zuciyarsa ce ya ji ta ƙara karaya ya fara tunanin cewa wannan kalmar tana faranta masa rai fite da tunanin mai tunani, sai dai tabbas daga ɓangare ɗaya yake jinta wato ɓangaren mahaifiyarsa, zai so a ce ya ji daga mahaifinsa ma amma ina tun da yake bai taɓa ganin wani sassauci ko kulawa da soyayya daga mahaifi ba. Idan ya ga abokansa suna yabon mahaifinsu a status ko dun ɗora hoton mahaisin suna my hero, farin cikinmu Allah ja da kwana mahaifinmu, wasu suke faɗin mahaifina abokina, wata ta ɗora bani da aboki ko abokin shawara sai mahaifina. Waɗannan kalaman suna sosa masa zuciya abu ne da bai samu ba abu ne da yake ganin mahaifinsa ya tauye musu jin daɗi da kulawa. Mamy a karo na biyu ta ce "Mubina ɗina taurarona" Bai san lokacin da ya ɗago kansa ba ya zubawa mahaifiyarsa jajayen idanunsa tamkar ranar ya fara arba da fuskarta, kallonsa suke daga ita har Zalika, idanunsa jajawur fuskarsa cike da damuwa ƙarara, a gefe ɗaya idanunsa suna kwararar da wasu hawaye. Yana ɗagowa sai ya buɗe bakinsa dakyar ya haɗa laɓɓansa ya ce "Mai ya sa sai mu? Mai ya sa daga ni sai ƙanwata ne muka rasa wannan damar Mamy? Mai ya sa mahaifinmu babu ruwansa da bamu kulawa Mamy, kullum fuskarsa a ɗaure, bama ganin dariyarsa tamkar ba a taɓa halitta tausayinmu a zuciyarsa ba" Zalika ita ma da Mubin ya sosa zuciyarta domin ita ma ƙarfin hali kawai take yi, kalamansa sun tada mata mikin da ke cikin zuciyarta a take nata idanun suka shiga tara ƙwalla, domin ta san a rayuwa babu mai gane damuwarka sai wanda yake cikin irin halin da kake ciki, ma'ana yanzu da take jin kalaman Yayanta da kuma ganin ruwan hawayensa suna kwaranya sai ta ji duk duniya babu wanda zai fahimci damuwarsa sama da ita domin ita ma tana damuwa makamanciyar tasa. Mamy kuma idanunta ta ɗauke daga kallon Mubin ba tate da ta furta ko uffan ba, ba tare da ta bashi amsa ko da ɗaya ba ce daga cikintambayoyin da ya jero mata ba, amma har ga Allah ji take tamkar ta rushe da kuka ko ta samu sauƙi da salama a zuciyarta a kan halin da take ganin ƴaƴanta a ciki, saboda ta san ita kaɗai ba za ta basu kulawar ɓangare biyu ba ko da ta yi ƙoƙarin hakan su dole zuciyarsu za take wasi-wasi a kan lamuran cikin gidan nasu wanda mahaifin nasu ne sila. Danna zuciyarta ta yi domin a matsayinta na mahaifiya a gare su babu buƙatar ta nuna rauninta a wannan waje domin damuwar za ta musu illa, hakan ya sa ta ɗago ta yi murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ta ce "Kowane ɗan adam yana da jarawarsa a rayuwa, sai dai idan ya jure watarana komai zai zama labari, komai zai zama tarihi tamkar ba a taɓa yi ba" Ta faɗa yana ruƙo hannun Mubin ta dawo da shi kusa da ita ya zamana suna zaune a tare Mamy a tsakiya su kuma kowa yana gefenta hannuwanta ta sanya ta dafo kafaɗunsu ta ce "Ku zama masu jajircewa, ku zama masu riƙe ibada tare da jajircewa a dukkan lamuran rayuwarku, kar ku bari wani abu yale rage muku jin daɗin rayuwa, duk wanda ya riƙe Allah to tabbas ba zai yi nadama ko da na sani ba" Ta faɗa tana juyawa ɓangare Zalika ta kalle ta, ta sake juyawa ɓangare Mubin ta kalle shi, su duka har lokacin da ruwan hawaye a saman fuskar kowa. Zalika ce ta ce "Mamy wallahi wani lokacin sai inmke ganin kamar ba Baffa ba ne ya haife mu, to ko yana da wata matar a wani waje da wasu ƴaƴan shi ya sa su yake musu walwala mu yake ƙume mana fuska?" Kafin Mamy ta yi magana Mubin ya yi karaf ya ce "Ko dariya ba ya yi, sai fushi da hantararmu kamar dai ba ya son mu, ai na san idan mu kaɗai ne ƴaƴan nasa to zai so shi ma yake zaunawa da mu ko ya bamu kulawa" Mamy ta ce "Sau nawa zan faɗa muku ku yi haƙuri ne wai? Na ce muku akwai lokaci yana tafe wataranan mahaifinku zai zama kamar kowane mahaifi" Zalika ta ce "Allah ya sa amma dai ina ga sai bayan mun bar wannan duniyar don Baffa ba na jin akwai ranar da zai sauya, ko ya canja ra'ayi. Mamy ce cike da harzuƙa ta ce "Wai ya kuke so in yi ne?" Mubin ya ce " Mamy mun san kin yi ƙoƙari kuma kina kan yi amma dai ni na san tarbiyya ba ta uwa kaɗai ba ce. Uba yana da rawar gani mai girma a kan iyalansa idan ya nuna ƙauna da kulawa, ya saurari yaransa, zai fi sa su girma da kwanciyar hankali da ƙima, dan aka bar uwa ita kaɗai, yara za su rasa ginshikin ɓangaren uba amma ki yi haƙuri" Mubin ya faɗa yana saka hannu ya ɗauke hannun Mamy daga kafaɗarsa ya miƙewa ba tare da ya ce uffan ba ya bar falon. *JIDDA* Gabaɗaya jikinta karkarwa ya fara ganin Umma ta ɗaga hannu za ta sharara mata mari, saboda ta san zafin hannun Umma idan har ta mare ka sai ka gwammace kiɗa da karatu. Domin tana da zafin hannu don hannun ta tamkar hannun wani namiji babu laushi ko kaɗan . Karkarwar da jikinta ya fara kwandon yana neman suɓucewa, Umma wacce sai da hannunta ya kusa isa fuskar Jidda sannan ta hangi Abba ya taho daga hanyar ƙofar gida don alamar farin yadin jikinshi ta hango, sosai faɗuwar gaba ta ziyarce ta amma saboda kissa da kisisina da iya bariki irin na Umma a take ta shiga kokawa da ƙwaƙwalwarta, don ganin ta ƙirƙiri abin da zai gusar da wannan mugun ganin da Abban ya kusa yi. Cike da tsantsar baki ta saki wata ƴar bazawarar dariya, hannun nan da ta yi niyyar marin Jidda da shi sai ta ƙarasa gefen fuskar Jiddar a hankali ta shafi kuncin Jidda ɗata hannun kuma sai ta riƙe haɓar Jiddar tana cewa "Allah ya miki albarka Jidda ya baki miji na gari inda za ki huta, ubangiji ya baki ƴaƴa masu miki ɗawainiya kamar yadda kike mini, Allah jiƙan itayenki da rahma" Wannan kalaman na Umma ne ya sa Jidda wacce ta rikice take jiran saukar zazzafan marin na Umma da sauri ta buɗe idanunta tun daga lokacin da ta ji Umma ta shafa fuskarta haɗe da haɓarta amma jin kalaman na Ummar ya ankarar da ita akwai abin da yake faruwa. Wani yawu Jidda ta haɗiye muƙut, ganin fuskarta ta tsira daga mari, Abba kuwa wanda ya yi mutuwar tsaye da ganin ɗaga hannun Umma mamaki da al'ajabi suka saukar masa ya fara tunanin mene ne halan yake shirin faruwa, sai dai lokacin guda Umma ta sauya masa akalar tunaninsa daga mummunan zaton da ya fara mata zuwa kyakkyawan zato da yake mata a kullum domin kyawawan halayenta da take nunawa a gabansa da kuma rashin nuna bambanci tsakanin Jidda yarinyar da yake riƙo da kuma ƴarta ta cikin ta wato Aliya. Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauka tare da fata ɗaga sagaggun ƙafafunsa don tun lokacin, da ya ga Umma ta ɗaga hannu ta nufi fuskar Jidda ya ji komai ya tsaya masa cak!. Baki ya buɗe cike da raha ya yi sallama, a lokacin Umma ta riƙe da gefen kaɗar Jidda, Jidda kuwa sai a lokacin ta gane dalilin da ya sa Umma ta fada aiwatar da ƙudurinta a kanta, yanzu ta fahimci ashe zuwan Abba ne ya dakar da Ummar daga marinta. Umma kuma cike da nuna bata san da zaman Mai gidan nata a inda yake ba, ta juya da sauri tana ƙara faɗaɗa fara'arta ta shiga amsa masa sallama, tare da ɗauke hannu daga saman kafaɗar Jidda da ta riƙe tana mai cewa "Maza an Jiddona a je a kai kanukan kicin" Cike da ƙarfin hali Jidda ta amsa mata da faɗin "To" Tana nufar kicin don har lokacin bata dawo daga duniyar tsoro da fargabar marin da Umma ta yi niyyar mata ba. Umma tana sakin Jiddar ta juya da fara'arta ta irin mutanen kirki masu dattako ta nufi Abba tana ta karɓi ledojin hannunsa tana faɗin "Sannu da zuwa sannu da zuwa, sannu da zuwa jan gwarzo, uba na gari ga ƴaƴansa miji na gari ga matarsa, Allah bada tsawon rai da kwana mai amfani, an dawo daga hidima da ƙoƙarin nemawa iyali abinci da za su ci, Allah yi jagora ya sauƙaƙa maka hanyar nema" Ta ringa jero addu'ar tana gaba yana biye da ita yana ta amsawa da "Amin ya rabbil alamin" Ɗakinsa ya shiga, sai da ya zauna a bakin gado ta ƙara masa sannu da zuwa sannan ta fito da ledojin ta damƙawa Jidda a kan cewa komai a ajiye shi a mazauninsa, fruit ɗin kuma ta yanka. Ruwa ta kaiwa Abba banɗakinsa na ɗaki sai da ya shiga wankan ta fito, suna haɗa ido da jidda wacce take zaune da kayan fruit a gaba tana saka su a wata roba mai ruwa tana wankewa, wata gagarumar harara ta jefawa Jidda kamar idanunta za su faɗo, da sauri Jidda ta kawar da idanunta ta maida hankali ga abin da take yi. Umma wani tsaki ta doka har guda biyu tare da juyawa ta shiga kicin ɗin kayan abincin Abba ta ɗakko ta ajiye a waje guda. Abba sai da ya yi alwala ya fito daga banɗakin jallabiya ya saka ya fesa turare ya ɗakko carbinsa ya fito, lokacin ana ta kira magriba, Jidda lokacin ta gama zubawa Abba kayan fruit ɗinsa a plate ta rufe ta ajiye a kusa da abincinsa da Umma ta ajiye, sai kuma na Ummar a wani plate ɗin sai nasu ita da Aliya a plate ɗaya, ta san wannan ƙa'ida ce in dai Abba yana nan tare suke cin abu. Umma da ta gama alwala ta buɗe baki ta ce "Jidda maza ki ajiye wannan kayan ki yi alwala ki yi salla, ƴar uwat taki ma ki musu magana su fito an kira sallah" Da to ta amsa ta shiga ɗaki za ta ɗakko abin sallah. Abba ya ce "Jidda sarkin aiki" Ya faɗa cike da kulawa yana ƴar dariya. Murmushi ta yi ta ce "Ina jin daɗin in ga ina aiki" Murmushi ya yi ya ce "To ai sai a je a gaishe da ubangiji kin dai ji abin da Ummarku ta ce" Da to ta amsa masa tana jin wani farin ciki don Abba shi kaɗai ne mai ƙaunarta tana jin daɗin yadda yake ƙaunarta. Yana fita sai ga Aliya da Amatullahi sun fito kallo ɗaya suka yi wa Jidda da take shimfiɗa tabarmi a tsakar gidan, tun da ita tana fashin sallah, waje suka fita Aliya za ta takawa Amatullahi, a ƙofar gidan suka yj sallama don ta san Abba ya dawo dama magana ce a kan saurayin da ta gani kyakkyawa tana cewa burinta ya zo gare ta ya bayyana kalmar so a gare ta ita kuwa dole ta yi watsi da Kasim saurayinta da yake mata wahala duk da bashi da wani ƙarfi sai don ƙaunar da yake mata kuma yana son ya faranta mata ganin tana son a bata. Aliya sallah ta yi haka ma Umma suka zauna, Jidda tana ɗaki gudun kar a mata wani abun. Abba sai da aka yi sallar isha'i ya shigo gidan, yana shigowa da sallama vayan an amsa ya nufi tabarmarsa ya zauna, Aliya ta masa sannu da zuwa Umma ta shiga ƙwalawa Jidda kira tana faɗin mai take a ɗakin. Jidda tana fitowa ta je ta durƙusa ta gaishe da Abba tare da masa sannu da dawowa. Ya amsa cikin fara'a yana musu addu'a Abincin da Aliya ta zubo musu a plate ɗaya suka shiga ci, Aliya tana wani jan Jidda da hirar tana ta ƴar dariya, haka ma Jiddar ta ɗan saki jiki duk da ta san kawai na ganin Abba ne. Sai da suka gama suka shiga shan fruit ɗin. Bayan kowa ya gama aka shiga hira tamkar dai babu ƴar tsama tsakanin Jidda da Umma da Aliya. Abba yana ta musu murnar kammala jarabawa da gama makarantar buɗar bakin Umma sai ta ce "An kammala karatu kam sai shafa lalle" Ta faɗa tana ƴar dariya tare da fakar idanun Abba ta yi wa Jidda wani kallo irin na za mu ga da wanda za a ɗaura miki aure. Abba gyaran murya ya yi ya ce "Tabbas dama wannan ne burina duk wacce take son ɗora karatu sai dai ta ɗora a ɗakin mijin ta" Jidda gabaɗaya ta ji hankalin ta ya tashi saboda ta san Abba bashi da burin da ya wuce ya aurar da su rana ɗaya da ita da Aliya, gashi ita ko tsayayyan saurayi bata da shi bare kuma a yi zancen aure. Aliya ma duk da haɗuwarta da Ibrahim yau hakan ya sauya mata tunani daga auren Kasim amma dai ta san ita ko da a ce mai za a yi ba za ya kasa samun miji na kerewa sa'a ba ko da a ce ana gobe ɗaurin aure ne ta tabbata ba za ta yi kwantai ba. Haka dai aka tattauna kafin daga bisani kowa ya je ya kwanta. Bayan kwana biyu. Misalin ƙarfe biyu da minti ashirin na dare ne, alarm ɗin da Jidda ta saita a wayarta ya shiga ruri, cikin bacci ta ji ƙaran da sauri ta tashi ta danne wajen sifikar wayar da ƙarfi kafin ta saka hannu da dakatar da alarm ɗin. Duk da wannan namijin ƙoƙarin da ta yi amma hakan bai hana Aliya tashi daga bacci ba cike da ɓacin rai ta buɗe idanu lokacin har Jiddar ta kunna fitilar wayarta. Zaune ta tashi tana mutsirtsika idanu, gaban Jidda ne ya faɗi amma bata ce komai ba, wata doguwar hamma Aliya ta saki ko bakin ta bata rufe ba, bata taoron shaiɗanu su shige bakin su samarwa kansu mazauni a bakinta. Cike da bala'i murya ƙasa-ƙasa gudun kar iska ta kai maganar ɗakin Abba, don ta san Abba kamar mai kunenn miciji haka yake wajen jin magana, bare shi ma da ba wani baccin dare ba yake don ta tabbatar yanzu da za a je ɗakinsa ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara a kan sallaya za a same shi ko dai yana sallah ko kuma yana karatun qur'ani. Tana mata wani kallo ta ce "Jidda wai mene ne hakan? Sau nawa zan ce miki ki dajna saka wannan ƙaran alarm ɗin yana katse mini bacci da mafarkai masu daɗi, ni wallahi ban taɓa jin wannan al'amari ba a zo gidan mutane a hana su sakat da sakewa ake damunsu da shiga haƙƙinsu" Ta faɗa cike da wulaƙanci tana wani kauda kai gefe, ruwa ne ya taru a kwarmin idanun Jidda ta tsaya tana ƙarewa ƙeyar Aloya kallo da yake ta juyar da kai gefe irin na wukaƙanci. Murya a dishashe ta shiga faɗin. "Aliya ni kike yi wa gorin gida?" Kamar an wanda Aliyar take jiran tambayar ta ce "To in fitsari banza ne kaza ma ta yi mana" Furta furucin wannan ya yi daidai da gangarowa maƙalallun hawayen da suke cikin idanun Jidda, cike da jin babu daɗi a ranta ta ce "Aliya wai kam ko kin manta Jiddanki? Ni ce fa Jidda wannan ƙawar taki tun ta yarinta, ni ce fa wacce kike so da tsananin ƙauna, ni ce wacce muke wasa bacci kawai yake rabamu, ni ce fa za mu wuni tare amma idan za mu rabu da kuka ake rabamu saboda shaƙuwa da ƙauna. Amma Aliya yanzu saboda iyayensa sun kwanta dama ƙasa ta rufe idanunsu shi ne kike min wasu abubuwa wanda ban taɓa zato da tunanina ba, shin ko kin daina so na ne? Muna rayuwa tamkar ƴan biyu babu mai shiga tsakaninmu muna son junanmu amma lamuran duk sun taɓarɓare sun jagule shin ina matsalar take?" Duk wannan jawabi da kalami da Jidda ta yi ta vayan kunnen Aliya ya wuce don ko gizau bata yi ba, bare Jidda ta saka ran cewa kalamanta za su yi tasiri a zuciyar Aliya, don ta lura Aliya ta sauya gabaɗaya, zuciyarta ma tamkar wanda ta ƙeƙashe daga tausayi da jin ƙai!. Yatsina fuska ta yi ta ce "Yankan uwa ai ya ishi ɗan tayi ishara, ke yanzu kina zaman jiran sai na furta miki kowace kalma da bakina, hankali da tunaninki basu isa su baki amssoshin tambayarki ba?" Hawayen idanunta sun fara gudu tamkar an kunna famfo, tana jin yadda ruwan hawaye yake gangatowa har ta saman hancin ta, a gefw ɗaya yana gangara har wuyanta. Cike da alhini da damuwa haɗe da sanyin murya ta ce " Au haka ne?" Aliya ta ce "Tabbas ya kamata ki fahimci RUWA CIKIN COKALI ya ishi mai hankali wanka" Tana faɗar hakan ta juya baya ta kwanta abin ta. Jikin Jidda sanyi ƙlaw ta juya za ta fita dama alwala za ta yi domin gabatar da sallar nafila, har ta je bakin ƙofar za ta fita ta tsinkayi muryar Aliya tana faɗin. "Ba za ki gane ba Jidda tabbas babu ƙarya na ƙauna ce ki kuma tamkar ƴar uwa na ɗauke ki, sai dai ba zan ɓoye miki tun daga lokacin da muke zuwa makaranta tare sai kowa yake son ki ni ko oho, idan kika yi fashin rashin zuwa makaranta ko na kwana ɗaya baki da lafiya daga malamai har ɗalibai tambayar ki suke, idan na yi fashi ko shekara zan yi babu mai nemana daga islamiya har boko. Tsananin ƙoƙarin ki da farin jini ya sa Abba ma kika ciri tuta a wajensa, tun daga wannan lokacin matsayin ki a zuciyata ya ragu sannan uwa uba da muka isa munzalin ƴanmatacin samari suka miki caaa duk da kyau da diri da nake da shi na tsarin halittar ƴa mace wacce za ta ja hankalin duk wani cikakken namiji mai lafiya a jika amma sai ya zamana kowa ke yake kallo, duk inda muka taka sai dai samari su biyo mu gida idan kuwa suka zo kowa ya aiko yaro sai dai a ce ana yi wa Jidda magana!Tun daga wannan lokacin na fara kallon kyauna a matsayin muni tun da ga shi dai ana faɗin farar mace alkyabba ta mata amma ni nawa fari da kyan ya zama tamkat shuɗaɗaɗn lokacin" Tun da ta fara magana bakin Jidda yake a buɗe ta rasa abin da za ta ce kanta gabaɗaya ya kulle tana tunanin shin dama wannn ne ummul aba,isin rabuwar kawunansu da Aliya, to ita ta ce samarin su zo nemanta ita da vata ma kula su hatta maganar malamai da ɗalibai ba ni na ce so ƙaunace ni ba ashe shi ya sa ko da muka fara karatun N.C E bata son kowa ya raɓe ni kenan hassada Aliya take min? Ta shiga jerawa kanta tambaya w zuciyarta, bata da amsar da Aliya domin tana ma tunanin lokacin sallar ta yana wucewa a banza ita kuma a rayuwa tana son ribatar lokacin ta kafin mutuwarta ta riske ta. Ko da ta fita ta yi alwala ta dawo Aliya ta juya tana bacci bata sake cewa komai ba, sallah ta yi raka ',a huɗu ta zauna ta ringa jerowa iyayen ta addu'a domin ta san tsakanin ɗa da iyayen da suka riga gidan gaskiya babu abin da suke buƙata sai addu'a. Bayan ta gama musu ta yi wa kanta da Abba, ta yi wa Umma da Aliya tare da yi wa dukkan sauran musulmi. Sai da ta yi sallar asuba ta yi karatun qur'ani sannan da gari ya yi haske ta koma ta kwanta bacci ya yi awon gaba da ita. Bayan faruwar haka da kwana biyu, Aliya ta shiga wasi-wasi a kan tunanin Ibrahim da yake yawan addabar zuciyarta, sai dai ta yi sawun zuwan kamfanin da ta ga sun je an buɗe sun shige da motarsu amma ko barin ta ta shiga mai gadin ba ya yi, sai dai ta saka a ranta idan kere yana yawo zabo yana yawo watarana za a haɗu. Ta ci gaba da riƙe Kasim ɗinta tana lallaɓawa tare da jiran gawon shanu na zuwan Ibrahim domin idan ta samu Ibrahim dole Kasim ya kama gabansa a cewar ta, shi kuma Kasim saboda ƙaunar da yake mata koyaushe sai hidima da kashe mata ɗan kuɗin da yake samu yake. Rayuwa tana ta tafiya, yau fari gobe baƙi dama haka rayuwa take a wajen kowa ta kowane ɓangare, bijirowa da fitar da abokin rayuwa da Abba ya yi wa Aliya da Jidda shi ne abin da ya saka Jidda a wani hali, domin ta san bata da kowa, ita yanzu ko wuni za ta yi tana yawo ta dawo gida babu mai tsayar da ita bare a biyo ta gida, gashi dai ta san Abba bai san cewa bata da manemi ba, tun da shi yana wuni a kasuwa sannan ya san dai da Jidda akwai manema bai san cewa yanzu kiɗa da rawa sun sauya gabaɗaya ba. Ta shiga damuwa musamman yanzu da Umma ta sako ta a gaba da rashin manemi kuma mashini tana faɗa mata cewa sai dai a bada ita sadaka tun da baƙin jinin ta ya saka bata da manemi, duk da ita Jidda ta san Allah ne yake bayarwa kuma aure lokaci ne kamar haɓo yake idan ya zo sai an yi. Gorance gorancen da Umma take mata ya sa ko zaman gidan fita yake a ranta bare yanzu da sun kammala karatu sai islamiya Jiddan take zuwa Aliya dama ta yi bankwana da zuwa islamiya saboda ta ga Abba ba zaman gida yake ba ita kuma Umma bata takura msta wai ai ta iya karatun sallah, bata san cewa uwa ita ce makarantar farko ta ɗanta ba, ilimi ya zama dole ga kowa kuma wajibi ga mace domin ita ce makarantar farko ta ƴaƴanta da ma al'umma baki ɗaya. Kamar kullum yau ma sa da ta gama aikin gidan tsaf ta yi wanka ta saka kaya tare da ɗora hijabin makarantar ta, fitowa ta yi tana riƙe da jakar islamiya, Umma da Aliya suna zaune suna tattunawa, sallama ta musu babu wanda ya kula ta, juyawa ta yi ta fita daga gidan, a zuciyarta tana tuno lokacin tata mahaifiyar tana raye yadda take ta mata addu'a da fatan alkairi idan za ta tafi makaranta amma yanzu saboda bata raye in har ba Abba ba ne to babu wani mahluƙi da yake mata addu'a ita damuwarta ma guda ɗaya ce da aba a san inda wani daga cikin danginta yake ba, tun daga kan dangin uwa kama zuwa dangin uba. Tana ta zancen zuci ta nufi makarantar ta shiga aji lokacin har an fara ɗorin karatun hadisi, kusa da aawarta Salama ta zauna ta fito da nata littafin suka ci gaba da sauraron malam. A can gida kuwa Jidda tana fita Umma ta taɓe baki ta ce "Wahalalliya ce wannan yarinyar in banda rashin aikin yi islamiya dai tun ana yara ake abu ɗaya, yanzu an zama ƴanmata har ana shirin shiga ɗakin miji amma ba za a haƙura ba" Aliya ta yi wata dariyar rainin wayo ta ce "Umma sai faɗi kike wai za a shiga ɗakin miji to in dai ba ita kaɗai za a saka a ɗakin ba waye zai kashi wanann?" Umma ta ce "Kuma fa haka ne, ai wallahi malamin nan da ya yi wa yarinyar nan maganin baƙin jini, samari suka daina wannan rawar ƙafar zuwa ƙofar gidan nan ai dole in koma in masa kyauta, yanzu shiru kike ji in ta fita ko kare ba ya biyo ta" Aliya ta ce "Wallahi kuwa Umma ai kin yi farar dabarw, da yanzu ni za ta tashi ta bari a gidan ake cewa ƴarki ta yi kwanta" Umma ta ce "Ai sai dai in bana raye, amma matuƙar ina numfashi Aliya Jidda bata isa ta tafi ɗakin miji ta barki a gida ba" Sosai suke ta hira abin su. Ibrahim tun daga ranar da ya yi tozali da Jidda bai samu sukuni ba, sosai sonta yake azalzalar zuciyarsa, kuma ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen zuwa ƙofar gidansu har sau biyu amma bai ga wulginta ba, shi kuma yana jin nauyin ya aika kiranta, kuma ma idan zai aika wa zai ce? Shi bai san sunanta ba. Daga Daddy har Mummy babu wanda ya san wainar da yake toyawa sai dai sun ɗan fara lura da yanayinsa don ya sauya, sai dai da suka tambaye shi dalili amsa ɗaya ce ita ce kawai ba ya jin daɗin jikin sa gar doctor su na gida Abba ya kira a kan ya duba lafiyarsa amma babu abij da yakr damun lafiyarsa. Kamar kullum yau ma yana zaune a tangameman falonsa da yake part ɗinsa, zaune yake a kan kujera, sai karamin tebur a gabansa, laptop ɗinsa ce da ƙaramin kofi mai ɗauke da coffee. Aiki yake a laptop ɗin amma hankalinsa yana ga tunanin Jidda, ɗan matsar da laptop ɗin gefe ya yi ya ɗauki coffee ɗin ya sha kaɗan ya mayar da kofin kan ƙaramin kofin glass ɗin ya ajiye, ganin ya rasa sukuni ya rufe laptop ɗin ya kashe fitilun duka na falon ya nufi bedroom, toilet ya shiga ya yi alwala ya fito ya hau gadonsa wanda ya sha shimfiɗar lallausan zanin gadon MAMAN AFRAH mai kyau gashi da ƙwari sannan zanin gadon mai ɗauke da bargo ne wanda aka shimfiɗa ɗin ma mai faiba a ciki ne ya yi matuƙar kyau ɗinkin. Hawa ya yi ya kwanta yana ɗakko wayarsa da take ajiye daga gefen gadon ya danna ya duba time, ajiyewa ya yi tare da yin addu,a ya shafe jikinsa tare da lumshe kyawawan idanunsa, cike da tunaninta nannauyan bacci ya ɗauke shi. Washe gari ko da ya tashi da tunanin ta ya tashi, sai ya ɗaukawa kansa alƙwarin duk inda take in har tana garin Kano sai ya nemo ta ya ba idanunsa abinci ko zai samu salama a zucuya da ruhinsa. Da yamma ya shiga ya yi wanka ya fito ya shirya cikin tsaddaden yadin kufta wanda aka yi wa adon zare na ɗinkin hannu, saƙar ɗinkin ya yj matuƙar amsar ash colour yadin. Bayan ya kamala shiryawa ya ɗakko hula mai ash mai ɗauki da ratsin fari da ɗan blue wanda bai ciza ba da aka ɗan yi wani layi-layi da shi a jikin hular, kallonsa yake a madubi yana yabawa kansa kyau ɗin da ya yi, turarukansa da suka gaji da haɗuwa ya feshe jikinsa da su a take ɗakin ya gauraye da daddaɗan sansanyan ƙamshi mai ratsa zuciya!. Mummy ya sanar cewa zai je wajen abokinsa Abeed, yana fitowa ya ɗauki wata sabuwar ash ɗin mota ya shiga sai sheƙi take sai dai glass ɗin kotar baƙi ne ba a ganin wanda yake ciki, mai gadi ya buɗe masa ƙofa yana ɗaga masa hannu da masa fatan alkairi, don da gani an ga tafiya ta musamman saboda ko direba bai bi ta kansa ba, horn kawai ya yi wa mai gadin shi ne amsar maganar da yake masa a zuciyarsa kuma yana amsa addu'ar da mai gadin ya masa. Kan titi ya nausa motar yana tafiya a hankali karatun qur'ani yana tashi a motar, tun da ya zo inda zai gangara gidan da yakr tsammanin gidan su Jiddan ne, inda ya hanga ta shiga ranar nan, gabansa yake tsanani da mummunar faɗuwa bai san dalili ba amma ya alaƙanta hakan da SO. Misalin ƙarfe biyar ya zo wajen amma kuma har biyar da rabi babu wanda ya fito ko ya shiga gidan da yake tsammanin ganin Jiddan. Dama ba a ƙofar gidan ya yi parking ba daga can gefe ne, har biyar da arba'in babu kowa sai mutane da suke ta hada -hada da kuma yara suna ficewa sai dai shi bai san ya zai yi ya ce a mata magana ba. Yana nan sai ya hangi wata budurwa ta taho rana zuwa ta nufi gidan, zuciyarsa tana raya masa ya fita ya tambaye ta amma kuma shi ko kaɗan ma yarinyar bata masa ba yanayin shigarta da ma tafiyar da take, hakan ya sa ya koma ya jingina, don hatta karatun ya kashe kawai zaman jiran tsammani yake. Bayan ta shiga gidan jim kaɗan sai gasu sun fito su biyu ransa ne ya ɓaci a lokacin da ya ga Aliya wacce suka fito da Amatullahi wacce ta shiga gidan yanzu. Ko kaɗan ba ya son ma'amalar Aliya da Jidda don a ganinsa basu dace da yin ƙawance ba ji ya yi kamar ta fito ya ce daga yau kar su ƙara zuwa gidan su Jiddan. Har suka ɓacewa ganinsa ransa a ɓace, daga can ya hango wasu ƴanɓata guda biyu sanye da dogayen hijabi, suna tahowa, idanunsa ƙurrr a kan Jidda don tun daga ganin da ya mata na farko bai taɓa manta kamaninta da kuma yanayin tafiyarta mai nutsuwa ba, ko ƙiftawa ba ya yi gani yake idan ya ƙifta zai rasa ganinta har abada. Zuciyarsa tana masa zillo so yake ya yi amfani da wannan damar ya fito daga motar ya tunkare ta ya faɗa mata sirrin zuciyarsa amma faɗuwar da gabansa yake ba ya ji ma idan ya fito bakinsa zai bashi haɗin kai na gabatar mata da kansa. Jidda wacce suke tafiya da Salama ƙawarta haka suka taho har suka zo daidai motar da Ibrahim yake ciki, dama hira suke abinsu amma maganar da suke basu gama ba kuma za su rabu domin gida Salamar ma za ta wuce. Ganin motar da take gefe a ajiye kasancewar gilashin baƙi ne basa ganin wanda yake ciki, ƙarasawa suka yi suka jingina da motar, Ibrahim da yake ciki gabaɗaya an dagula masa lissafi da farko ma da ya ga sun nufo motar ga ɗauka suna ganinsa domin ya manta cewa gilashin na waje ba ya ganin wanda yake cikin motar. Kamar ya fito ya gudu haka ya ji sai da ya ga sun tsaya a jikin motar hankalinsa ya kwanta, ya rasa dalili amma dai yana tunanin saboda bai taɓa tunkarar wata ƴa mace da sunan so ba ne. Kasancewar Jidda ba baya ta juyawa motar ba gefen kafaɗarta ne ta jingina ita kuma ƙawar ta juya baya, yanayin tsayuwar da Jidda ta yi ya ba Ibrahim damar kallonta sosai. Salama ce ta ce "Ke ma Jidda na faɗa miki ki daina damuwa kike addu'a kawai Allah zai baki mafita... 'Jidda?" Ibrahim ya furta a zuciyarsa 'Dama sunanta Jidda,.kenan Hauwa'u ce?' Ya tambayi zuciyarsa. Yana ƙara jefawa zuciyarsa tambayar 'To mai yake damunta ake bata haƙuri?' Ya jefawa kansa tambayar da bashi da mai bashi amsa. Hannu ya kai jikin gilas ɗin saitin inda take tsaye ya dafa wajen. Jidda idanunta cike da ƙwalla ta buɗe baki ta ce.... Furucin da Jiddar ta yi suka daki kunnuwan Ibrahim lokaci guda ya ga duhu ya maye hasken da yake gani, gabansa yana faɗuwa jin tashin hankalin da ya kai masa ziyara lokaci guda, da sauri ya koma ya zauna jingine da kujerar saɓanin da da ya ɗan taso yana taɓa jikin gilashin. Kansa ne ya sara da mugun ƙarfi yana jin ba zai jure wannan furucin na Jidda ba... Wayyo hannuna🥺 10 readmore😫 *Mata masu aji akwai kayayyaki na tashin kan oga fa, akwai haɗaɗɗun tsumi da daka, da matsi ba na sakawa ba matsi da za ki tasafa ki shiga hajia, akwai na gyaran breast wacce breast nata ya kwanta lifet ta zo mu saka labule idan bata son dama kunu ina da na kwaya amma ba ƙwayar bature ba ƙwaya ta gargajiya, ingantattun itace haɗaɗu masu nagarta ki min magana in kina so ga no wayata a ƙasa* MAMAN AFRAH 09025576222 ‎Shin kinason hadaddun hijabs Wanda zaki ratsa ko Ina dasu?❤️kinason sanya hijabs masu fitarda asalin kyau da kyawun fuska?😹hijab din da Ana Ganinki ansan hijab neh?🥰 Anything hijjabs ask FUA ✅ got you covered.💃…Ba hijab kadai ba muna saida: inner caps, jersey veils, chantally veils and materials gowns ,jalbab,Hijab,Umrah set,lefe package,walima anko and lots more✨Muna bada sari a aika maka koina cikin Aminchi. (location; kaduna,zaria and Gumel jigawa State,Muna delivery koina,niger,Ghana,saudia) let us be your surest hijjabs plug,we give deliver the best. [10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ems_copy_t *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 6️⃣ *SADIYA* Ranta ne ya mata ƙuna tana jin wani zafi da raɗaɗi a zuciyarta, ta fara tunanin shin mai Nasir yake nufi da ita ne? Ta yaya za a yi mace ki dawo gidanki ki haɗu da mijin ki amma ko kallo baki ishe shi ba bare ki sa ran zai miki magana ko ya yi wa ɗan da kika haifa masa. Kallon ƙaton kwaɗon da ya datse ƙofar ta yi a karo na biyu, tana jimami a zuciyarta ta ce 'Ya san ya sauyawa gidan mukulli amma bai bani ba to mene ne nufinsa? ' Ta faɗa a zuciyarta tana saka hannu ta riƙe kwaɗon tana tunanin yadda za a yi ta buɗe ta shiga gidan, tun da babu gidan wanda take shiga a umguwar bare yanzu gidan wa ma za ka je da tsakar ranar nan, to idan ka je ma ka ce mai?. Ɗan sakin kwaɗon ta yi ya bugu jikin ƙofar yana sakin wani ɗan ƙara, kanta ta jingina a jikin bangon ƙofar daga gefe tana jin ita daj bata dace sa miji ba a gefe ɗaya zuciyarta tana faɗa mata hatta mahaifin ma bata yi dace da shi ba. Ta jima a haka tana jin irin yadda gumi yake sartu a jikinta saboda zafin ranar da ake gabaɗaya ranar a buɗe take. Motsin da Kalifa ya yi ne ya dawo da ita daga duniyar saƙa da warwarar da take yi a zuciyarta. Ɗagowa ta yi tana ƙarewa layin nasu kallo babu kowa sai mutane da suke ficewa jefi-jefi idanu ta mayar hanyar da ta biyu ko za ta hango mashin ɗin da Nasir suka wuce amma ko alamarsa, ta daɗe a tsaye ko za ta ga ya dawo amma shiru tamkar maye ya ci shirwa!. Zafin rana ga goyo shi kansa Kalifa so yake ta sakko shi, ganin abin ba na ƙare ba ne, don a ƙalla ta yi kusan minti talatin a wajen a tsaye amma babu alamar Nasir zai kawo mukullin. A hankali ta sakko daga matakalar gaban gidan tana jan ƙafa ga yunwa ga baƙin ciki da takaicin ɗa namiji da yake ƙunsa mata, ga rashin adalcin da iyayenta suke mata, na rashin jin damuwarta da kuma magance mata ita. Gidan da yake kallon gidan ta, nan ta hangi inuwa da ɗan dakali a wajen, haka ta cira ƙafafu tamkar iska za ta ɗauke ta, suna zuwa inuwar ta zauna har lokacin bata sauke Kalifa daga bayanta ba. Bayan ta zauna sai ta kifa kanta a gwiwarta tana jin babu daɗi ganin duk wanda zai wuce sai ya kalle ta, har ta fara zargin ko daj sun zata mahaukaciya ce. Maganar Kalifa ta katse mata tunani jin ya ce "Mom a sakko ni" Ya faɗa cikin maganrsa ta gwaranci da bata fiye fitowa raɗau ba, hannu ta kai ta sakko shi, sai lokacin ta lura da hannunsa da ba a wanke masa ba lokacin da ya ci tuwo. Tana sakko shi ya fara ɗaga hannu yana nuna hanyar da suka baro yana faɗin ",Abba" Wani iri ta ji a zuciyarta don wannan maganar da ya yi hakan yana nuni da cewa ya ga mahaifinsa lokacin da suka wuce, baki ta buɗe cikin sanyin murya ta ce "Abbanka yana zuwa ya ke siyo maka alewa ne, kana son shan alewa?" Kai kawai ya gyara mata. Zuwa can tana zaune Kalifa a cinyarta jakarta ƙarama a gefenta a ajiye, ganin yara suna wucewa da uniform a jikinsu ta tabbatar yanzu ƙarfe uku ta yi. Wani yaro ɗan maƙotanta daga can gefe ya fito sanye da unifort riga pink me ɗigo-ɗigo yayin da wandon yake purple, tun da ya hange ta yake dariya har ya ƙaraso ya ce ",Auty Sadiya" Ya faɗa yana cike da fara'a amsa masa ta yi ya shiga gaishe ta sai kuma ya ce "Aunty ya kike zaune a waje?" Ya tambaya yana kallon ta da yake da ɗan wayonsa don zai yi shekara tara zuwa goma, rasa ma mai za ta ce masa ta yi duk ta ɗan diririce sai kuma can dabara ta faɗo mata sai ta ce "Tare da Abban Kalifa muke to mukullin ne ya faɗi shi ne ya koma ya dubo?" Ta samu kanta da sharara masa ƙarya. Dariya ya yi bai ce komai ba don shi ko kaɗan ba ya son wannan mutumin bashi da kyawun hali ya yi ta korarsu idan suka je gidansa. Wasa ya yi wa Kalifa ya fito da alewa a jakar makarantarsa ya bashi yana ɗaga masa hannu yana masa bye-bye shi ma Kalifan bye-bye ya masa. Alewar ya miƙa mata ta karɓa ta ɓare masa ya fara sha, shiru babu amo ba labarin Nasir har aka fara kiran la'asar abin ya ɗaure mata kai don ta san ko ma ina zai je ya ci a ce ya dawo tun da dai ta san ba kasuwa ya tafi ba tun da gashi nan da kasuwa zai je da wuri zai fita. Abin ya fara bata tsoro tana zaune babu sallar azahar babu ta la'asar gashi tana tsoron shiga gidajen maƙota cibi ya zama ƙari don matsawar ta shiga ya zo ya ganta tabbas akwai gagarumar matsala. Kalifa sauka ya yi daga cinyarta saboda ya gaji da zaman waje ɗaya, ya shiga kewaya wajen, yana ɗan wasa. Ta buga uban tagumi ta yi nisa cikin tunanin lamuran gidan aurenta, tana tuna irin wulaƙanci da tozarcin da Nasir yake mata, ƙaran wani birki da mai mashin ya ja shi ne ya dawo da ita hayyacinsa, a kiɗime ta tashi ta je gaban mashin ɗin da ta hangi Kalifa kwance a wajen, mai mashin ɗin wanda yake ɗauke da ƴan makarantar islamiya da ya ɗakko, kanta a take ya shiga juyawa ta yi kan Kalifan da gudu ƙirjinta yana bugu tamkar zuciyarta za ta fasa ƙirjin ta fito tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" *JIDDA* Idanunta cike da hawaye ya cigaba da magana don don duk abin da take faɗa iya gaskiyarta take faɗa komai daga ƙasan zuciyarta yake ta ci gaba da faɗin "Ni ba damuwata rashin mijin ba damuwata ɗaya yadda Umma za ta takura min idan aka yi auren Aliya ba a haɗa da nawa ba, kuma kin ga Abba ba zaman gidan yake ba, sai na gwammace kiɗa da karatu in ma bata kore ni ba, don ba gori ba har goriba sai ta min a kan rashin auren" Shiru Salama ta yi tana nazari da tunanin maganganun ƙawar tata a lokaci guda tausayin Jidda yana mamaye mata zuciya da ruhi. Ibrahim wanda ya cika da zufa tun furucin Jidda na farko wanda shi ne ya saka shi a ɗimuwa, kuma shi har ga Allah a yadda yake jin Jidda ta gama bin jijiyoyin da jinin jikinsa ba zai iya rayuwa ba sai dai ita sai dai furucin ta ya nuna masa da sauran rina a kaba, domin kuwa da wuya wai gurguwa da auren ne, shiru ya yi ƙwaƙwalwarsa tana tuno masa haɗe da dawo masa da tunanin abin da ta furta wanda shi ne ya saka shi a ɗimuwar da yake ganin dab yake da ya rasa Jidda wanda hakan kuma babban ƙalubale ne a rayuwarsa. 'Salama damuwar yawancin ƴanmtan yanzu shi ne auren namiji mai kuɗi kuma kyakyawa, yawancin kowacce burinta ne wannan, ni kuma inda muka sha bamban da saura kenan tunanina burina haɗe da ƙudurina basa kan namiji kyakkyawa kuma ba wai don hakan ya haɗa nasaba da munin da nake da shi ba, uwa uba dukiya basa gabana don ni a ra'ayina in auri talaka kuma mummuna in da zan samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta yadda kyawunsa ba zai ruɗi ruɗaɗɗun ƴanmata ba, sannan dukiyarsa ma ba za ta tsone musu idanu ba, kin ga burin Aliya ne wannan ni kuma bani da ra,ayi a kan hakan, amma zan ci gaba da addu'a Allah ya bani miji na gari daidai ni' Wannan su ne furucin da ya hargitsa tunanin Ibrahim da sauri ya saita madubin motarsa ƙan ƙarami na ciki wanda yake maƙale fuskarsa ya kalla a ciki, ganin irin kyawun da Allah ya yi masa sai da ya ƙara jin gabansa ya faɗi tamkar dai a yau ne ya taɓa ganin kyawun fuskarsa. Zuwa yanzu duk ba ya fahimtar maganganun da suke tattunawa, hankalinsa ya yi bala'in tashi yana ta tunanin ya zai yi ya mallaki Jidda, tun da gashi ba ya ma cikin mazan da take da burin aurr, na farko dai shi yana da kuɗi sannan uwa uba Allah ya hore masa kyau shi kyakkyawa ne ajin ƙarshe, zai iya tabbatarwa ya cika dukkan abin da ta lissafa zai samar mata na kwanciyar hankali a gidan aure sai dai kash! Bai sani ba ko za ta karɓe shi a matsayin kyakkyawa kuma mai kuɗi don ya tabbata shi dai sai dai a saka shi cikin masu kuɗi pan ajin farko ba ma ajin ƙarshe ba. A fili ya furta "Ya zan yi?" Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsar ta bare kuma mafita. Yana cikin wannan tunanin kamar an ce ya ɗago sai ya ga wayam babu kowa a jikin motar, dama ya ji ba ya jin maganarsu kasancewar a ruɗe yake bai yi tunanin dajna jin muryarsu da ya yi ba. Idanu ya hanga sai kuwa ya ga Jiddan za ta shige gida ta juyo tana yin bye-bye kasancewar ita yake kallo sai ya ga tamkar shi take ɗagowa hannun bai san lokacin da ya ɗaga nasa hannun ba yana mata bye-bye tamkar wani soko. Ganin ta shige gidan ya dawo hayyacinsa sai a lokacin ya yi tunanin ashe ma bata ganinsa kasancewar baƙin gilashin motar, sannan ma shi da ba saninsa ta yi ba shi kaɗai ne ya san ta ya san matsayinta a zuciyarsa. Can da ya hanga sai ya ga ashe Salama ƙawarta ta ɗagawa hannun, huci ya busar mai zafi daga bakinsa ya ɗan kwantar da kujerar tare da mayar da bayansa ya kwanta ya rufe idanunsa kawai ita yake hangowa lokacin da take yi wa ƙawarta bayani, yadda take bayani cike da damuwa shi ne abin da ya fi tsaya masa a rai. Idanun ya runtse da ƙarfi a fili ya furta "Jiddaaaa" Yana mai jan harafin ƙarshe na sunan nata, ya jima a haka har sai da aka fara kiran sallar magriba ya tashi tare da gyara kujerar ya mayar da ita daidai ya mayar da hannunsa kan mukullin motar ya kunna tare da fara ƙoƙarin janta duk da yana jin tamkar jijiyoyin jikinsa sun daina aiki, kamar dai ba zai iya jan motar ba, yana ƙoƙarin yin kwana, sai ya ga wani mai mashin da yake ɗauke da wani mutumi ya tsaya a take mutumin ya sauka yana sanya hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙawa mai mashin ɗin, yana bashi ya juya ya fara tafiya mai mashin ɗin yake miƙa masa canji amma sai ya ɗaga masa hannu alamar ya bar shi, haka ya shiga magana shi dai Ibrahim kasancewar ba a kusa yake ba bai ma san mai yake cewa ba sai dai ya san godiya yake masa. Mai mashin ya ja mashin ɗinsa ya yi gaba, a inda Ibrahim ya bi bayan Abba da kallo har ya shige cikin gidan da ya ga Jidda ta shiga. Sosai ya yaba da yanayin dattijon kuma daga gani ya san tabbas yana da dattako da tsayuwa a kan iyali. A zuciyarsa ya ce 'Wannan ne mahaifin Jidda kenan?'Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma yana ta tunanin wace ce Ummar da ya ji Jidda ta ambata tana maganar za ta mata gorin aure, in dai kuwa haka ne to tabbas ba mahaifiyar Jidda ce a gidan ba, ko dai mahaifiyarta ta mutu ko kuma bata gidan sun rabu da mahaifin ta, a take ya ji wani tausayinta haɗe da zazzafan son ta ya ƙara dirar masa, sosai yake jin son ta a jiki da ɓargonsa ya yadda yake jin tozalin da idanunsa suka yi da ita yau sai ta ƙara fasa masa wani sabon son don tamkar ta motsa masa mikin da yake cikin zuciyarsa ne. Haka ya baro unguwar ransa duk babu daɗi, gashi babu biyan buƙata sannan kuma ya yi wani mugun jin da zai hana zuciya da ruhinsa sakat. A daidai wani masallaci ya yi parking daga can gefe fitowa ya yi alwala ya yi ya bi jam'i sai da ya idar sannan ya shiga mota ya ƙarasa gida ransa duk wani iri, tabbas ya faɗa tarkon so son ma na wacce bata san yana yj ba, son da zai ringa saka shi fargaba tun da bashi da tabbacin mallakar wacce yake yi wa so ɗin. Yana shawo kwanar gidansu ya figi motar da mugun ƙarfi, don yanzu hatta motar ma haushin ta yake ji, a yau ne ya ji ya tsani kuɗi da kuma kyawun da yake da shi, yana ta tunanin cewa da shi mummuna ne kuma talaka babu abin da zai hana shi tunkarar Jidda a yau. Sai dai ta wani ɓangaren ya ji daɗin jin furucin ta ko ba komai zai yi amfani da damarsa wajen kaɓa zuciyarta sai dai ya san abin da zai yi. Horn yake da ƙarfi mai gadi da yake sallah bai zo ya buɗe ba, shi kuma bai fasa doka horn ɗin ba. Ya jima yana yi duk da ya san mai gadi ba zai ƙi buɗe ƙofa da gamgan ba, mai gadi ko da ya yi sallama daga sallah sai da ya karanta gabaɗaya azkar ɗin da ake yi bayan idar da sallah, sanna ya taso a nutse ya wangale ƙofar, ya ja baya Ibrahim ya shigo da motar da gudu yana yin wani parking a tsakiyar wajen. Fitowa ya yi daga motar mai gadi duk sai ya sha jinin jikinsa ya ɗauka ko shi ne ya ɓatawa Ibrahim ɗin rai da bai buɗe ƙofa da wuri ba, da sauri ya ƙarasa yana mai cewa. "Afwan yallaɓai ina sallah ne" Hannu kawai ya ɗagawa mai gadin ya shige cikin gidan, bai bi ta kan part ɗin Mummy ba direct part ɗinsa ya nufa yana ta sauri shi kanshi bai san dalilin saurin nashi ba. Yana shiga bai tsaya a falo ba ya shige bedroom wayoyinsa ya ɗora a kan madubi ya cire hula da rigar jikinsa ya cilla kan gado agogon hannunsa ya cire ya ajiyee yana hango shi a madubi sanye yake da farar singlet fara tass tamkar takarda sai wandon yadin da ya cire rigar, hasken fatarsa da kwantaccen gashin sa tamkar ba'indiye shi ya sa ya ji zuciyarsa ta tsinke saboda tunowa cewa masoyiyarsa bata son kyakkyawan namiji. Kan gadon ya koma yana ture hula da rigar da ya cire gefe don ba al'adarsa ce jefar da kayansa a kan gado ba shi mutumin ne mai tsafta. Amma yau yanayin da ya shiga ya sa yana abu wanda ba halayyarsa ba. Tashi ya yi ya kunna AC haɗe da ƙure mata gudu a take sanyi ya haɗe ɗakin duk a nufinsa ya samu sassaucin zafin zuciyarsa da yake azalzalarsa na rashin wacce yake so. Ya koma ya zauna wayarsa ta fara ƙara amma bai tashi daga zaunen ba, har kiran ya tsinke, wani ya shigo sai a karo na uku sannan ya tashi ya ɗakko wayar ganin suna Mummy ɓaro-ɓaro ya yi saurin ɗagawa tana tambayarsa rashin shigowarsa ɓangarenta ya sanar da ita wanka yake son yi sai lokacin ta ji ɗan dama a ranta don ta san da wuya Ibrahim ya shigo gida bai fara shiga part ɗinta ya ganta ba. Suna gama wayar kiran Abeed ya shigo ɗagawa ya yi suka yi magana ya ajiye ya koma ya kwanta reran a kan gadon idanunsa a rufe yana ta nemawa kansa mafita. Zuwa can ya tashi zaune kamar an tsikare shi da sauri ya ɗakko wayarsa, sunan direbansa ya kamo hannunsa har rawa yake don yana ganin wannn hanyar ce zai bi ya samu mallakar Jidda don zai yi duk yadda zai yi ya samu soyayyarta ya kuɓuto ta daga gorin da ya ji tana furtawa da bakinta cewa za a yi mata idan bata samu miji mai auren ta ba. Bugu ɗaya biyu direba ya ɗaya ya ce "Barka da dare yallaɓai" Ya faɗa cike da girmamawa. Amma maimakon Ibrahim ɗon ya amsa sai ya ce "Ina za a samu kayan gwanjo?" Tambayar ta zo masa a ba za ta amma sanin kyauta irin ta yallaɓai ɗin sai ya yi tunanin ko kyauta zai yi da su, duk da ya san kaya sabbi dal yake bayarwa. "Za a samu wane iri?" Ya faɗa yana jiran jin amsar sa "Daidai ni?" Maganar ta zo masa a bazata amma sai ya ce "Ana samu yallaɓai akwai wani abokina maƙocinmu ne ma yana buɗe dila ta kaya kuma masu kyau kamar sabbi... Kafin ya gama magana Ibrahim ya ce "Bana son wanda suke kamar sabbi na fi son tsoffi wanda suka ji joki idan son samu ne ma wanda suka fara gashi" Shiru direban ya yi sai kuma ya ce "To yallaɓai sai dai a karɓo ƙarshen dila irin wanda aka gama zaɓewa aka bari su ne wanda ake karyar da farashin su saboda tsufansu" Ibrahim ya ce "Yawwa su zan saka maka kuɗi a account yanzu ka je ka samo min su" Amsa masa ya yi da "To" Ƙit ya kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya. Haka direbansa ya kawo masa kayan cikin wata bakko don kuɗin da ya tura masa ko rabi ba a ɗauka ba, part ɗinsa ya kai masa ya bashi umarnin tafiya tare da crwa ya riƙe sauran kuɗin. Direban yana fita ya buɗe kayan da sauri yana fito da su, sosai sun ji jiki ba ma wannan ba warin da kayan suke irin na gwanjo su ne suka sa ya kusa yin amai, waya ya ɗaga ya kira mai wanki ya bashi kayan ya ce a wanke amma kar a goge, don a ransa ya san ba zai iya saka su babu wanki ba, don ba don Jidda ba babu mai saka shi saka gwanjo. Yana ɗaukan kayan shi kuma ya fito ya nufi part ɗin Mummy don lokacin har ya yi wanka ya saka wani kayan sun je masallacin isha'i da Daddy, a falon ya same su yana shigowa cike da kulawa suka tashi suka nufo shi, kowa ya rungumi gefen ɗaya daga jikin Ibrahim ɗin suna matuƙar son ɗan nasu. A haka suka ƙarasa saman dining ɗin in da Mummy da Daddy suka kama shi cike da kulawa suka zaunar da shi a kujera, Mummy tana dariya cike da wasa ta ce "Haba Daddyn Mu'azzam ya kake neman kayar min da ɗa bai gama zama ba fa ka janye hannunka" ,Ta faɗa tana kallon Ibrahim da yake ta murmushi kyawawan haƙoransa a waje. Daddy ma cike da wasa ya ce "Wai kina nufin kin fini son shi ne?" Mummy ta ce "Eh mana" Daddy ya ce "To bari mu ji daga bakin Ibrahim ɗin, Mu'azzam tsakanin ni da Mummynka wa ya fi son ka kuma wa ka fi so?" Ya faɗa yana daga tsaye har da kama tsantsa shi ala dole yana jiran ya ji mai za a ce kar a je ba a zaɓe shi ba. Mummy kuma ta kasa tsayar da dariyar da take marar sauti, shi kuma Ibrahim yana ta kallonsu ɗaya bayan ɗaya yana tunanin ta inda zai ɓullowa wannan diramar tasu. Mummy ta ce "Kai muke jira" Ibrahim ya ce "Duk kuna sona na sani, ni kuma na fi son... Kowa ya yi saranda yana jiran kar a zaɓi ɗan uwansa ba zaɓe shi ba, kowa ya san idan ba a zaɓe shi ba za a masa dariya. Kamar daga sama suka ji Ibrahim ya ce "Ni kuma ina ƙaunarku ku duka" Gabaɗaya sai aka kaure da dariya Mummy da Daddy suka nemi kujerarsu suka zauna, Mummy ta zubawa kowa abincin suka shiga ci cike da annashuwa. Bayan sun kammala suka koma tsakoyar falon suna tattaunawa, a nan mai aiki ta shigo ta kwashe kwanukan ta tsafta ce dining ɗin. Ibrahim ne ya musu sallama ya ce zai je ya kwanta, kasancewar dai yaƙe yake musu don kar su fahimci yana cikin damuwa, yana zuwa part ɗinsa ya shiga ya kulle, bai watsa ruwa ba kasancewar bai daɗe da yin wanka ba, jallabiyar jikinsa ya cire ya saka sleeping dress masu laushi ya kwanta tare da yin addu'a. Bayan ya shafa addu'ar ya shiga tunanin mafitar da yake a kan lamarin Jidda don a gobe ba sai jibi ba ya yi wa kansa alƙwarin sai ya je mata da kalmar so kuma son na aure!. Tunanin wani abu ne ya faɗo masa hakan ya sa ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran Abeed abokinsa bayan ya ɗauka yana ta masa surutu Ibrahim ya ce "Dalla malam ka tsaya na faɗa maka abin da ya kawo ni, ka tsaya kana ta zuba kamar lalataccen famfo" Abeed ya ce "To dama ai kamar jiran kiranka nake ka san maganata ni da kai bata ƙarewa" Banza ya masa akan abin da ya faɗa don ya san kawai surutu ne zai cika shi da shi kp ya ringa bashi labarin ball ɗin da aka ci shi kuma yanzu ba wannan ne a gabansa ba, don ba ya so ma ya faɗawa Abeed ƙudurinsa gudun ya masa dariya ko ma ya ce sai ya bishi wajen Jiddar. Cike da ƙosawa da kalaman Abeed Ibrahim ya ce "Ni tambayarka zan yi ko ka san wani mai wanda mutum zai shafa ya yi baƙi kuma ya yi muni?" Ya faɗa hankalinsa kwance don shi ya shiryawa faɗawa komai a kan Jidda. Abeed jin babu alamar wasa a furucin da abokin nasa ya yi sai ya ce "Man da za a shafa a yi baƙi da muni ko dai mai da za a shafa a yi fari da kyau?" Shi ma ya tambaya babu alamar wasa a maganarsa kamar yadda Ibrahim ɗin ya yi. Shiru Ibrahim ya yi yana ɗan nazarin kamar ba zai ce komai ba har sai da maganar Abeed ta katse masa tunani jin ya ce "Magana nake maka ka ƙyaleni?" Wani yawu ya haɗiye yana fatan dai ba cewa zai yi ba a samun man ba ya ce "A,a kamar yadda na faɗa maka mai wanda zai saka baƙi da muni, ka san dai ai ni dai in ba zabiya zan komai ba mai zan yi da fari, kyau kuma ni da indiyawa da larabawa ko za a samu bambanci bainwuce a ce ni bahaushe ba ne su kuma larabawa da indiyawa, to mai zan yi da kyau?" Abeed ya ce "Wai kana nufin kai ne kake neman wannan man da ka ambata mai za ka yi da shi?" Maimakon ya amsawa Abeed tambayarsa sai ya ce "Tambaya za ka min ko amsa min tawa tambayar za ka yi" Ya faɗa yana jin tamkar ya janyo shi daga wayar ya yi ta bugu har sai ya huce. Abeed baki ya taɓe kamar Ibrahim ɗin yana ganinsa ya ce "Kai malam ni ban san inda ake siyar da wannan man ba, to wai kai mai ya sa ma za ka shafa wannan man? Wane mai bada gurguwar shawarar ne ya baka shawarar nan, bayan kana da kyau wanda ƴanmata suke maka caaaa... Wani takaici ne ya cika Ibrahim jin abin da Abeed ya faɗa shi kuma a halinnda yake ciki yanzu gani yake ko wata mace aka alaƙanta shi da ita tamkar an ci amanar Jidda ne, wayar ya sauke daga kunne ya datse kiran haɗe da yin cilli da ita can gefe ya kwanta tare da juyawa wayar baya. Abeed kuwa dama ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, dama ya san hakan zai ta faru don ya san Ibrahim ya tsani maimaita tamabaya. Washe gari ko da ya tashi bayan ya yi shirin fita office, don yau shi kaɗai zai tafi kamfanin don Abba ya ce zai zauna ne ya yi wasu rubuce -rubuce a kan kayan da za a shigo da su daga waje na kasuwancinsa wanda duk manyan kasuwanni da shaguna yawanci wajensa suke sarar kayan. Yau ba kamfanin wajen gidan su Jidda zai je ba, ɗaya kamfanin yin shinkafa zai je, duk ransa ba daɗi don a ganinsa idan ya doshi hanyar wajen gidan su Jidda ma ai daɗi zai jia ransa. Bayan sun kammala break fast ya fito riƙe da jakar wajen aikinsa da wayoyinsa, suna tsaye da Mummy tana jero masa addu'a mai wankin da ya ba wankin gwanjo jiya ya zo yana mai cewa "Barka da safiya Hajiya" Ya gaishe da Mummy cike da girmamawa, bayan ta amsa ya juya ya ce "Barka da safiya yallaɓai" Ibrahim ya ce "Alhamdulillah, mu je in buɗe maka part ɗin nawa ka saka min kayan, ya faɗa gudun kar ya bashi mukullin idan ya tafi kafin ya dawo Mummy ta tambaye shi kayan mene ne bakko guda a cike. Bayan ya saka masa ya dawo ya mata sallama, kamar ya sani kuwa sai da ta tambaye shi kayan mene ne don Mummy tana da sanya ido a kan lamurinsa, duk da ya mallaki hankalin kansa amma tana lura da al'amuran da suka shafe sa. Sanar da ita yanyi cewa wasu kaya ne da ya saya, yana mata sallama direbansa ya buɗe masa mota bayan ya shiga ma'aikatan gidan wanda suke wajen suna ta kawo gaisuwa cike da bashi girma yana amsawa, rufe masa ƙofat aka yi direban ya shiga ya tada motar mai gadi ya buɗe suka fita ya mayar ya rufe yana musu fatan alkairi, ɗago masa hannu Ibrahim ya yi da yake yau motar da ya fita da ita mai farin glass ce ana gani. Kamar jiya ma yau ya shirya wajen ƙarfe biyar na yamma, bayan ya fito wanka bai shafa mai ko turare ba kawai wannan kayan ya ɗakko ya saka kala ɗaya riga da wando baƙaƙe, ya kalle shi a madubi, duk da tsuffin kaya ne kasancewarsu baƙaƙe sai suka ƙara haska fatarsa hakan ya sa ya ji gabansa ya faɗi don tamkar ma kyau aka ƙara masa, da sauri ya cire ya ɗauki wata jar riga wacce daga gwiwar hannun ma ta ɗan fashe, ya saka baƙin wando, duk da a cukwuikuye suke amma dai ya ga sun masa kyau. Kai ya dafe ya koma bakim gado ya zauna yana tunanin ko dai baƙin mai ko na gawayi zai samu ya dishi farin fatarsa amma sai ya yi tunanin zai koma kamar dodo kuma ba ya so ma Jiddar ta ɗauka ko mahaukaci ne ta ƙu kula shi. Wayar da ya sa direba ya siyo masa tsohuwa key pad ita ya saka sim ɗinsa guda biyu ya ajiye nasa wayoyin masu tsada a kan madubin, dakyar ya samu takalmi yana fatan kar ta gane takalmin me tsada ne, wata hular sanyi ya ɗauka duk da zafin da ake ya saka amma sai ya ga ta yi kyau, ya ajiye ya ɗauko hularsa da yake sakawa da yadi, ya ɓata karin jikin hular ya saka ya danna a kan ta rufe wannan lallausan gashin kan nasa, sannan ya fito da kunnuwan waje sai ya zama gashi nan dai kamar wani wanda ba wayayye ba amma dai in mutum yana da hankali to yana kallon fatarsa kaɗai zai gane ɗan hutu ne bai saba da wahala ba. Fitowa ya yi kasancewar Mummy yau ta fita gidana biki, bai san bikin waye ba amma ta ce masa ta tafi gidana biki, Daddy ma ya fita shi da wasu abokansa da suka zo wajensa. Part ɗinsa ya rufo ya fito ya saka mukullin a aljihu yana gama sakawa ya ga mukullin ya faɗo sai a lokacin ya lura, ashe ajjihun a yage yake, a ɗayan ya saka sai ya ga babu yaga. Tun da ya fito yake addu'ar Allah ya sa kar ya haɗu da wani daga ma'aikatan gidan, cikin ikon Allah har ya je bakin get bai haɗu da kowa ba, dama ko wajen ajiye motoci bai kalla ba kasancewar yau ba a ma managar mota. A hankali ya kama ƙaramar ƙofar ya buɗe amma sai da ƙofar ta yi ƙara ƙiiƙiii mai gadi da yake banɗakinsa ya ji ƙaran taɓa ƙofa dama yana shirin fitowa ne, hakan ya sa ya ƙara ƙaimi wajen sauri ya fito yana cewa "Waye?" Lokacin har Ibrahim ya fita ya rufo ƙofar, yana fitowa ya fara sauri don ya san dole sai mai gadi ya leƙo, kuma baya son kowa ya ganshi, mai gadi kuwa da sauri ya ajiye butar hannunsa, ɗan taku ɗaya biyu ya yi yana leƙo hanyar cikin gidan ko zai ga wanda ya shiga amma bai hango kowa ba. Da ɗan sassarfa ya nufi get ɗin ya buɗe ƙaramar ƙofa domin leƙawa ya ga ko fita aka yi tun da ba shigowa aka yi ba, Ibrahim da yake ta sauri don ganin ya bar layin nasu jin an buɗe ƙofar don ƙaran ta ziyarci kunnuwansa, da sauri ya raɓe daba jikin wata katangar wani gida yana leƙo mai gadin har ya gama kalle-kallensa ya koma ya rufo ƙofar, Ibrahim ya fito daga maɓoyarsa ya cigaba da tafiya yana fatan Allah bashi nasara a kan abin da zai je nema, yana fatan ya samu Jidda ta amince masa don ko a gobe in ta amince ya yarda a ɗaura musu aure!. Tafiyar tashi bata je ko ina ba ya ji ya gaji kasancewar bai saba da wahala ba, napep ya tare ya shiga tare da faɗa masa inda zai kai shi, sai da suka kusa zuwa inda za a gangara ya ce mai napep ya samu wuri ya sauke shi, haka ya fito tare karɓar account no mai napep ya masa transper na kuɗinsa har da ƙari, mai napep sai godiya yake kamar ya ari baki, amma zuciyarsa cike da tambayoyi da wasi-wasi don ya tabbtar wannan ba ƙaramin mutum ba ne duba da yanayin maganarsa irim ta wayayye kuma mai ilimi, sanna kana kallonsa ka ga wanda yake zaune a hutu ba a wahala ba, sai dai yanayin kayan jikinsa ya sa kana iya jiyo warin abin gwanjo daga jikinsa. Shi dai bai ƙara bi takansa ba ya fara tafiya yana ta addu'ar dacewa, dacewar kuma ba ta komai ba sai ta sa'ar ganin Jidda tare da fallasa mata asirin zuciyarsa da fatan ta amince da shi.... *Akwai abaya gwanjo masu kyau da imganci akwai dila, akwai rabin dila, akwai kwatar dila akwai sayen ɗaya* *Sannan akwai zannuwan gado, labulaye, abaya mayafai* *kayan yara takalma lesuna atamfofi shaddodi hijabai amma su sabbi ne da sauransu* *Sannan akwai magungunan mata, kama daga daka mai kyau da matsi ba wanda ake sanyawa ba wanda ake tafasawa a shiga, akwai maganin gyaran breast ga matan da nononsu ya zube ko ya yaƙune da wanda suke yi yaye da masu shirin yaye, akwai tsumi domin dawo da darajar ki wajen miji, akwai kuma sanyi wanda shi maganinsa dole ne don idan kina da sanyi ko kinnsha magani ba za ki ga kyansa ba.* *Akwai mayuka na gyaran fata, kama daga wanda zai saka fari da wanda baya saka fari wanda shi iya fata zai gyara ya saki yi glowing, akwai shower gel, da sabulai da dai sauransu* *Mai buƙata ta min magana ga no ta nan a ƙasa* MAMAN AFRAH 09025576222 [10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/C12RFYqXnWf36AhjVZWDw4?mode=ems_copy_t *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 7️⃣ *MAMY* Da kallo ta bi bayan Mubin har ya ɓacewa ganinta tana jin babu daɗi a ranta, Zalika ce ta dawo da ita daga ƙaramin tunanin da ta tafi ta hanyar faɗin "Mamy ki yi haƙuri kawai amma dai Baffa ba ya kyauta mana, tun muna yara bamu san daɗin hira ko zama inuwa ɗaya da mahaifinmu ba, gashi har mun girma abin yana mana ciwo amma hakan bata sauya zani ba" Mamy ta ɗan nisa ta ce "Zalika kin san na yi iya ƙoƙarina wajen ganar da mahaifinku kuskurensa amma ya ƙi fahimta ko ya gane bare har na saka ran cewa zai yi aiki da shawarata, kin san da yawa wasu mazan suna ganin mata basu da tunanin sannan kasancewar an ce mace tana ƙasan namiji haka ya sa wasu mazan suke ganin mace ba za ta basu shawara ba su ɗauka, bare shi da yake ganin kawai duk abin da zan faɗa ma labarin ƙanzon kurege ne don shi a tashi fatawar idan ya ba ƴaƴa abinci da biya musu dukkan buƙatunsu shikenan ya sauke haƙƙi!" Suna cikin tattaunawa suka ji mai gadi ya buɗe ƙofa, jim kaɗan sula ji shigowar mota wacce sun tabbata Baffa ne ya dawo domin lokacin dawowarsa ya yi. Zalika ce ta miƙe tsaye da sauri, Mamy ta riƙo hannunta ta ce "Ina za ki je?" Zalika ta ce "Ɗaki zan je" Mamy ta ce "Mai ya sa?" Zalika ta ce "Kin san yanzu Baffa zai shigo ni kuma ba na son yake wannan ɗaure fuskar" Jin furucin ta sai Mamy ta sakar mata hannu abin da ya ba Mamy mamaki da sassarfa Zalika ta bar falon tamkar wanda take gudun kar wani abun tsoro ya afka mata. Karaf ƙaran buɗe ƙofar falon ya ziyarci kunnuwa Mamy wacce ta yi tsuru kamar mai jiran tsammani. Kamar yadda ta tsammata ɗin hakan ce ta kasance domin yadda ya turo ƙofar kamar wani kumurcin zaki haka ya shigo ran nan nasa a ɓace kamar an faɗa masa mutuwa, ko arziƙin sallama ba a samu ya yi ba, ƙofar ya mayar ya rufe sai da ya zo tsakiyar falon ya ja ya tsaya yana ƙarewa ko ina kallo. Har lokacin Mamy bata ɗago ta kalle shi ba. Takowa ya fara yi sai dai ya zo falon sannan ya nemi waje ya zauna bayan ya ajiye ledar da ya shigo da ita, kallonta ya yi ya ce "Baki ganin mutum ya shigo kika watsa yina?" Sai da ta yi yaƙi fa zuciyarta ganin bata faɗa masa wata magana da za ta ƙona masa rai ba, a hankali ta buɗe dashashshiyar muryarta ta ce "Sannu da zuwa" Kallo ɗaya ya juya ya mata ya ga ɓacin rai kwance a saman fuskarta sannan daga hakan ma ya fahimci tana cikin damuwa don yanayinta ya sauya kuma yana iya hango sawun hawayen da ya zuba a idanunta. Sai dai kasancewarsa ba ya cikin mutanen da suka damu da damuwar iyalansu ba sai ya juya ya nufi hanyar da za ta sada shi da part ɗinsa, Mamy ɗago kai ta yj tana bin bayansa da kallo ji take kamar ta janyo shi ta buɗe kunnuwansa ta faɗa masa cewa ya gyara halayyarsa sai dai ta san wannan ba mai iyuwa ba ne. Bayan tafiyarsa da mintina kaɗan ta tashi ta goge fuskarta ta bi bayansa duk da ta san bin bayan nasa ba ƙaramin matsala ba ne amma dai tana ƙoƙarin sauke nauyin haƙƙinsa da ya rataya a wuyanta matsayinsa na miji a gare ta. Tana zuwa ta ɗan yi kamar minti uku a bakin ƙofar kafin ta tura ƙofar, taa shiga ta mayar ta rufe, Baffa da yake ɗaure da towel a ƙugunsa ya juyo ya ce "Lafiya dai?" ,Duk da ba wannan ne karo na farko ba da ya jefa mata tambayar ba amma dai ta sosa ranta. Cikin sanyin murya ta ce "Lafiya ƙalau, dama ruwan wanka zan haɗa maka" Baki sake yake kallonta kafin ya ce "Ikon Allah na zaune ya faɗi, yanzu akwai ruwa a famfo a banɗaki da komai sai an biyoni" Jin furucinsa sai ta juya cike da takaici ta fita, ledar da ya ajiye ta ɗauka ta adana kayan bata san wane irin miji ne shi ba ko ta ce bata san wace irin zuciya gare shi ba da babu ruwansa da iyalansa. Bayan an yi sallar magriba ya shigo gidan dawowarsa daga masallacin magriba kenan, sai da ya yi kamar minti uku da shigowa sai ga Mubin ma ya shigo don dama ta san ba zai bari ya bishi ba irin na ɗa da uba sai dai kowa ya yi tafiyarsa da ban. A kujera ya yada zango ya ɗauki remote ya sauya channel ya ɗan ƙara volume. Ko da Mubin ya shigo bai tsaya a falon ba, tun da ya yi wa Baffa sannu da zuwa ya amsa dakyar a ciki-ciki sai ya wuce ya tafi ɗakinsa ya kwanta yana danna waya. Zalika ma da ta idar da sallah ta zo ta ce "Baffa barka da dawowa, an dawo lafiya" Baffa ya amsa a taƙaice da "Yawwa" Sum-sum ta koma ɗakinta a kan sawunta. Mai aiki ta shigo ta jera kayan abinci a dining kamar ba gobe, Mamy ta ɗaga waya ta kira Zalika da Mubin a kan su zo a ci abincin dare duk da cewa ana cin abincin ne kamar a gidan makoki amma babu wani raha ko nuna kulawa a tsakanin iyalan, don shi wanda shi ne ginshiƙin gidan bai bada damar hakan ba. Kusan a tare suka shigo falon, lokacin Baffa yana waya da wani abokinsa duk ya cika falon da karaɗin wayar da yake bakinsa a washe kamar an biya masa kujerar makka, yana magana yana dariya har da ƙyaƙyatawa. Daga Mamy har yaran sai suka mayar da shi TV domin su sai su manta ma da ganin fuskarsa a sake sai dai idan ya bar gida ko yana waya ko a kasuwa wajen shagunansa ki ga yana ta raha da jama'a, haka ake yabonsa cewa mutum ne mai fara'a da sanin darajar mutane amma su dai iyalansa basu san wannan ba. Yana gama wayar ya haɗe rai kamar bai taɓa wani abu dariya ba, lokacin da Mubin da Zalika sun koma kan dining sun zauna. Cike da izza ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya mayar da hankalinsa kan TV ransa a haɗe kamar ba shi ne yake dariya da ƙyaƙyatawa a waya ba. Sun jima zaune kan dining ɗin amma Baffa babu alamar zai taso, Mamy ma ta je ta ja kujera ta zauna, sai kallon kallo suke a tsakaninsu. Cike da takaicinsa ta ce "Baffan yara kai muke jira fa" Ta faɗa tana kallonsa, kamar ba zai furta komai ba sai dai ya ƙara tamke fuska ya ce "Zan zo ai" Ganin haka sai Mamy ta shiga zuba musu abincin, farfesun kifi ne, wani fulas ɗin soyayyan naman kaza, ɗayan farfesun kayan ciki, abinci ma kala biyar dambun kuskus, soyayyar taliya, sinasir, funkaso, ɓarjen alkama, drinks ma iya ganinka sai wanda kake so, kallon kwanukan da Mamy ta bubbuɗe tana zuba musu abincin Mubin ya yi ya ga, ga komai amma kuma babu farinciki!. An zubawa kowa har Baffa amma har lokacin babu alamun zai taso shi ko kaɗan bai san cewa iyalinsa suna buƙatar kulawarsa fiye da kayan more rayuwa da zai wadata su da su ba. Kowa sai juya cokali yake a ciki, tausayin yaran ya sa Mamy ta ce "Baffan yara abincinka fa zai huce na zuba" Buɗar bakinsa sai ya ce "Ki ɗakko nawa abincin ki kawo min nan ba na sha'awar cin abinci a kan dining yau" Kamar wanda ya zuba mata ruwan dalma a kunne haka ta ji yayin shigar maganarsa, idanu ta runtse don bata son ganin fuskokin yaran. Mubin da Zalika kamar wanda suka haɗa baki sai kowanne ya tashi riƙe da plate ɗin abincin sa a hannu, ƙaran buɗe ƙofa shi ne ya ankarar da Mamy ta buɗe idanunsa sai kuwa ta ga wayam gabanta babu yaran sun bar wajen, mayar da idanu ta yi kan dining ɗin sai kuwa ta ga duka babu plate ɗin kowanne a cikin su. Juyowa ta yi ta mayar da kallonta kan Baffa tana so ta ga ya zai yi tun da dai ta san ya san cewa yaran sun tashi daga wajen ne saboda ba zai ci abinci da su ba. *SADIYA* Sai da ta kama Kalifa ta ɗago shi sai ta shiga duba jikinsa a matuƙar kiɗime tana son ganin inda ya ji ciwo, kamar daga sama ta ji muryar mai mashin ɗin yana faɗin "Tsorata ya yi ne da ya ji ƙaran horn, Allah ma ya kiyaye ban lura da shi ba ya taho" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har lokacin tana jin sanyin da ƙafafunta suka yi. Gefe kawai ta matsa tana jijjiga Kalifa don bata da ƙarfin halin furta masa komai, shi kuma ya ce "Allah ƙara kiyayewa ake kula da yara" Yana gaɓa faɗar hakan ya ja mashin ɗin, jakarta ta koma ta ɗakko daga inda ta ajiye don ita dama wayar tata ma ko caji babu domin bata ma riƙe caji sosai shi ya sa bata tarki kiran Nasir ba, bare ma ta san ba ɗauka zai yi ba in ta kira sai in ya ba dama. Tana nan tsaye a ƙofar gidan lokacin an fara kiran magriba wani mashin da ya karyo kwanar ta gani kamar daga sama ta hangi Nasir a bayan mashin ɗin, sai da suka zo har ƙofar gidan ya sauka daga mashin ɗin ya ba mai mashin kuɗinsa mai mashin ya ja ya bar wajen, Kalifa ne ya hau faɗin "Abba, Abba, Abba" ,Kallo ɗaya Nasir ya musu ya ɗauke kai mukulli ya fiddo daga aljihunsa ya buɗe ƙofar gidan ya shige har da ɗan turo ƙofar, wani abu ne ya tokarewa Sadiya a maƙoshi saboda abin da ya yi wa Kalifa sai ta ji duk abin da ya mata bai mata ciwo ba kamar wanda ya yi wa ɗansa , abin na matuƙar damunta ita a nata tunanin ko da a ce da Kalifa ta zo gidansa bai kamata yake yi wa yaron haka ba, bare kuma ɗansa na cikinsa. Haka ta daure ta taka matakalar ƙofar gidan ta saka hannu ta tura ƙofar ta shigo gidan ita tsabar bata da nutsuwa ma ta manta da wani abu wai sallama haka ta shigo gidan kamar wanda dama Nasir yake jira sai ji ta yi ya ce "Ke! Babu manya a gidan ko? Na ce manya sun ƙare a gidanku, idan ma akwai manyan to basu bada tarbiya ba gskiya tun da kike shiga gida babu sallama" Maganar ta mata ciwo sai abin ya zame mata zafi biyu wato ga mari ga tsinka jaka, saboda bai san darajarta ba ya barta wuni guda a titi amma ya zo yana ƙara mata wasu maganganun mararsa tushe. Daurewa kawai take amma kuka neman ƙwace mata yake, sauke Kalifa ta yi don yanzu hankalinta ya fi karkata ga yin sallolin da suke kanta hakan ya sa da ta sauke Kalifan kawai ta yi gaba don yin alwala, shi ma Kalifan kamar ya san mai yake faruwa sai ya ja ya tsaya a ƙofar falon ya raɓe yake leƙen Nasir ɗin. Inda ta cika butoci ta je ta ɗauki ɗaya ta yi addu'a ta shige banɗaki ta turo ƙofar, ta tsugunna tana kama ruwa kawai sai ji ta yi an banko ƙofar har sai da ƙofar ta gwaru da jikin bangoda sauri ta tashi tsaye don dama ta gama kama ruwan. Juyowa ta yi tana kallonsa a tsorace ganinsa a fusace tamkar wani fusataccen zaki, kafin ta furta wani abu ya ce "Wato ga ɗan iska ko saboda kin rainani ina faɗa shi ne kika yi tafiyarki kika barni in yi ta zuba ko?" ,Cikin sanyin murya da kuma ƙarfin da yunwa ta cinye mata ta ce "Ka san dai a waje muka wuni ban yi sallar azahar ba bare la'asar kuma yanzu ana kiran magrib... Tun kafin ta ƙarasa ya katse ta da faɗin "To ina ruwana da sallarki, in ban da rashin tarbiya ina magana ki tafi wannan daga gani babu tantama gida kika ɗakko halayyar rashin tarbiya, dama ai an ce tarbiya daga gida take farawa, in ba don ni ba wa zai kwasa iyayenki ma da kin ishe su da Allah annabi Babanki ya sa na aure ki, don na ɗauke masa ɗawaniniya saboda yana so ya kawar da ke, ina faɗa a ko ina ban aure ki don ki zama abokiyar rayuwata ba na san aurena da ke ƙaddara ce baƙar ƙaddara ma kuwa, a yau idan na ga dama zan yanke igiyar aurena da ke kuma in auro wacce ta fiki komai don ke baki cika mace ba!." Kallonsa take yadda yake magana cikin ɗaga murya, idanunta suka fara tara hawayen da take ta ƙoƙarin maƙale suka fara ambaliya a dakalin fuskarta, a take maganganun da ƙawarta Noor ta faɗa mata suka fara dawo mata, wanda take faɗa mata cewa take kataɓus wajen rama abin da Nasir ɗin yake yi wa iyayenta na cin mutunci tun da iyaye ai sun fi ƙarfin wasa tun da shi bashi da mutunci bai san shi ba. Jin kalamnsa kuwa ai ta tabbatar iyayen nata yake faɗawa magana, ai kuwa ta fara takowa daga cikin banɗakin sai da ta zo gab da shi ta tsaya ta ce "Nasir" Da mamaki yake kallon ta jin ta kira shi a wani gadaranci ko dai ya kira hakan da muryarta cike da fitsara. Baki ya saki yana kallon ta ta ci gaba da faɗin "Duk abin da za ka yi ka tsaya iya kaina amma iyayena ba sa,anninka ba ne da za kake faɗa musu abin da duk ya zo bakin ka ba zan ɗauki haka ba" Haɓa ya riƙw cike da mamaki ya ce "To mai za ki iya idan an sako iyayen naki ko kina da matakin ɗauka ne? Iyayen naki da basu damu da farin ciki da baƙin cikin ki ba ni fa a wajena baki da maraba da wacce aka min tallar ta ko aka bani sadaka" Ita ma a harzuƙe ta ce "Ko ma ya suke iyayena ne kuma ko ma ya suka ɗaukeni wannan tsakaninmu da su ne, ni dai gargaɗina na ƙarshe da kai kar ka sake cin mutuncin iyayena" Idanu ya ƙanƙance ya ce "Gargaɗi? Sadiya ni Nasir ne kike yi wa gargaɗi kamar wanda bakin uwa ya kamani har wata mace za take faɗa min magana" Bata bi ta kan tambayarsa ba ta ce "Ni da sakakkiya a gidan nan banbamcin mu kaɗan ne, ko kaɗan baka darajani, tsakani da Allah kana gani na amma ka tafi bayan ka san gidan a kulle na wuni a titi ni da ɗanka ko kishin iyalinka baka yi, duk namijin da ya san darajar kansa da ta iyalinsa ba zai wofintar da su su wuni a titi b... Wani gigitaccen mari ya ɗauke fuskarta da shi, da yake marin ya je mata ne a bazata sai ta ji tamkar ba da hannu aka mare ta ba, marin da Kalifa ya gani ne ya sa ya ruɗe ya fashe da wani kuka ya yi kanta ya je bayanta ya ƙanɗame ta har lokacin yana kuka, bata kula Kalifa ba duk da kukan nasa yana taɓa mata zuciya. Tana dafe da kumatun da ya mara ta kalle shi idanunta taf da hawaye ta ce "Ni ka mara Nasir?" Kamar zai kai mata wani marin ya ce "An mare ki fitsararriya ko za ki rama ne? Har ni za ki ce ban san darajar kaina ba, kuma wallahi sai na faɗawa wannan uban naki ya gargaɗe ki don zai iya zuwa ya ga gawarki matuƙar baki yi wa bakin ki linzami daga furta min kowace kalma ta zo bakinki ba" Yana gama faɗar hakan ya juya ya nufi falo, Kalifa ta ɗauka har lokacin yana kuka da alama tsorata ya yi da marin da aka mata tana ɗaukansa ya maƙalƙale wuyanta bata san lokacin da ta fashe da kuka mai sauti ba. Ta jima tana kuka mai cin rai kafin ta yi shiru ta goge hawayen, jin Kalifa ya yi shiru ya kwantar da kansa a kafaɗarta, sai ta duba sai ta ga ya yi bacci haka ta kawo shi falon ta kwantar da shi a kan kujera ta koma ta yi alwala ta zo ta kabbara sallah. Lokacin Nasir yana bedroom, sai da ta yi azzahar da la'asar tana yi tana hawaye duk sujadar da ta kai sai ta faɗawa ubangiji damuwarta a kan ya magance mata, tana shirin miƙewa ta yi mageriba sai ga Nasir daga bedroom ɗin kamar an jefo shi, gabanta ya zo ya tsaya yana riƙe da wayarsa da take ringing da alama wani yake kira don wayar a handsfree take ma. Kamar daga sama sai jin muryar Baba ta yi yana cewa " Assalamu alaikum malam Nasiru mutumin kirki" Wani murmushin gefen baki Nasir ya yi kafin ya haɗe rai kamar Baban yana ganinsa ya ce "Ni wallahi Baba ba na cikin yanayin da zan amsa sallama gabaɗaya raina a ɓace yake" Buɗar bakin Baba sai ya ce "Sadiya ce ko? Wannan yarinya mai ya sa bata jin magana wai, haka fa ta kwaso jiki wai wuni ta zo gidan nan na korata ɗakinta da tsakar rana shi ne kuma da ta dawo ta ɓata maka rai" Sosai Sadiya ta ji duk ta muzanta dole Nasir yake mata abin da ya ga dama saboda mahaifinta shi yake bashi kowace dama, shi yake zubar da kima da darajarsa, shi ya sa ba ya siya mata mutunci bata san wane irin uba ne ta samu ba. Nasir ba yabo ba fallasa ya ce "Ai Sadiya bata san darajar miji ba ko kaɗan, ban da zagi da baƙaƙen maganganu babu abin da take a gidan auren ta, yanzun nan ta gama cewa ban san darajar kaina ba da ta iyayena" Ya faɗa cike da ɓacin rai, Sadiya jin har da ƙarya ya shirga bata yi mamaki ba da ya yi haƙuri ma in dai Baba ne a kan a samu matsalar da za ta koma masa gida ba sai da ƙarya zai mata faɗa ba. Baba ya ce "Bata wayar" Wani kallo Nasir ya mata yana wani ƙanƙance ido irin na fitsararru ya miƙa mata wayar tana ƙoƙarin danna wayar Nasir ya katse ta da faɗin "Kar ki kuskura ki cire min waya a handsfree ki bari in ji, idan ma shi yake ɗaure miki tsantsa ki rainani" Yana gama faɗar haka ya koma kan kujera ya zauna tare da harɗe ƙafafu. Baba ya ce "Sadiya wallahi ki fita idona in rufe, mijin da ya rufa miki asirin kike zagi, shin wuta balbal kike son shiga Sadiya?" Kallonta ta mayar kan Nasir da ya kaɗa kai alamar ta dai ji rufa mata asiri ya yi. Kafin ta samu zarafin furta komai Baba ya ci gaba da cewa "Wallahi idan ba so kike in zo har gidan in saɓar miki ba ki masa biyayya ko wuta ya ce ki faɗa ba dole ki shiga ba Sadiya tun da mijinki ne aljannarki tana ƙasan ƙafafunsa, kin samu Allah ya tarfawa garinki nono kin yi aure amma kike tada fitina da dai ban san ki da haka ba ko ƙawaye kika samu suke hure miki kunne?" Jin Baban ya dakata ta gane kamar ya bata damar magana hakan ya sa ta ce "Baba tun da na dawo yana ganina fa ya tafi da mukullin a titi muka wuni sai yanzu ya dawo kuma bani da damar da zan nuna ban ji daɗin abin da ya yi min ba sai ya kai min hannu? Marina fa ya yi Baba yana ta faɗa wa iyayena maganganu... Cike da faɗa Baba ya katse ta ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba yana ta ɗora mata rashin gaskiya a ƙarshe ya ce idan ya ƙara jin wata magana ta ɓullo sai ya saɓar mata. Duk abin da ake Nasir yana ji, kawai murmushi yake saki jin Baba ya ce ta ba Nasir haƙuri a kan kunnensa ya ji haka ta buɗe baki ta bashi haƙurin cikin dashashshiyar muryarta, sannan Baban ya ce ta ba Nasir wayar tana jin yadda ya ringa ba Nasir haƙuri tamkar zai ari baki yana ta yi wa Nasir ɗin godiya kamar wanda ya masa kyautar kujerar makka. Juyawa kawai ta yj ta koma kan sallayar ta fara sallar magriba, tana saddaƙarwa da cewa wannan gidan auren kamar kurkuku yake a wajenta, sai dai ta san ba za ta dawwama a haka ba akwai ranar ƙin dillacin ta san ko ba jima ko ba daɗe sai Allah ya mata sakayya a kan zalincin da Nasir yake mata, ko da bayan ranta ne kuwa. Bayan ta yi har isha'i ya zo ya buɗe store ya ɗakko mata taliya rabin leda ya miƙa mata, karɓa ta yi ta nufi kicin ɗin ta shiga kunna gawayi don mahaifiyar Nasir ta yi uwa da makarɓiya ta hana ta kunna gas ɗin da Nasir ya saya tana amarya ɗan ƙarami, ta ce ita Sadiya bata dace da amfani da Gas ba saboda a gidansu da icce ake amfani. Dakyar ta samu gawayin ya kama ta ɗora tuwan zafi ta dawo falon, sai ta ji kamar ta rufe ido ta buɗe ta ganta a wata duniya daban. Tun da ya bata taliyar ya fice, ta gama dafawa ta soya manja ta zubo abincin ta ajiye ta ɗauki Kalifa ta ke ta wanke masa ido da baki tuni ya ware don dama yunwa yake ji, haka yake cin abincin kaɓr me saboda yunwa, ita kuwa kaɗan ta samu ta ci shi ma duk babu daɗi. Haka ta yi shimfiɗa ta kwantar da Kalifa ta shiga ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta saka rigar bacci marar nauyi ta yi addu'a ta kwanta har lokacin Nasir bai dawo ba, ganin an kawo nepa ta tashi ta saka cajin wayarta ta koma ta kwanta tana rungume da filo tana ta tunanin lamarin gidan aurenta, rana zafi inuwa kuma ƙuna, hawaye yana ta bin kumatun ta mafita take nema ita dai da za a ji damuwarta a magance mata da da daɗi amma babu mai saurarenka iyayenka kawai burinsu ka zauna a ɗakin miji daɗi da wuya ko da kuwa a wulaƙance ne. Tana ta wannan saƙa da warwarar bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Nasir sai wajen ƙarfe goma saura ya shigo gidan, yana can majalisa da abokai ana ta hira, yana shigowa ya rufe ƙofar gidan ya shigo gidan yana wani bada faɗi, sai kuma ya ga baiwar tashi bata ma falon tsire da coca colan da ya shigo da su ya zauna ya baje a falon ya cinye a shanye lemon ya tashi ya bar mata takarda da robar a wajen. Bayan ya gama abin da zai yi ya saka hannu a aljihu ya fito da wani ƙullin ruwan magani a farar leda ya tula ya shanye ya fito ya jefar da leda, kayansa ya cire daga shi sai singlet da ƙaramin wando ya haura kan gadon bayan ya kashe gabaɗaya fitilun. Kasancewar Kalifa a ƙasa take masa shimfiɗa a kan ƙaramar katifa da yake gidan ciki da falo ne, sai kicin da banɗaki kawai sai kuma ɗaya part ɗin inda ciki da falo sai ɗaki ɗaya wanda an fara ginin an kai linta amma ba a ƙarasa ba. Yana hawa gadon ya kwanta ya miƙa hannu ya shiga tashin Sadiya, cikin bacci ta ji yana buga mata ƙafa ta ɗago jajayen kumburarrun idanunta ta kalle shi ta cikin ɗan hasken farin wata da ya ratso ɗakin. Cike da gadara babu tausasa murya ya ce "Haƙƙina na zo karɓa" Ranta ne ya sosu wai mutumin da ya gama ci mata mutumci har marinta ya yi amma yanzu kuma ya zo da wata buƙata, a kasalance irin na wanda yake cike da bacci da gajiya ta ce "Dan Allah Abban Kalifa ka mini lamuni yau wallahi ba na jin daɗin jikina" Kamar wanda ta watsa masa wuta haka ya zaburo mata ya ce "In baki taliya ki cika ƙundunki ki shi ne tawa buƙatar ba za ki biya min ba? To in dai wancan taliyar da na ga kin ajiye mini a ƙaramin filas ce kike yi wa ki je ki ɗauka ni nama da lemo na sha, idan kin cinye sai ki zo ina jiranki da alama ƙoshi ne baki yi ba shi ya sa kike mita" Cike da ƙosawa da kalamansa ta ce "Ni ba yunwa nake ji ba kawai dai zuciyata ce babu daɗi" Zaune ya miƙe ya saka hannu ya daki kan katifar kan gadon ya ce "Ko zuciyarki da daɗi ko babu wannan ke kike sakawa kanki kuma ke kika ga za ki iya, ni dai yanzu haƙƙina dole ki bani tun da sadaki na bayar" Tun da ya yi wannan furucin bata ƙara furta komai ba ya cire kayan jikinta, babu wani ɓata lokaci ya shiga biyan buƙatarsa ya daɗe yana abu ɗaya sai da ya gaji don kansa ya ƙyaleta, ita kuma tana kwance kamar gunki don dama babu wani abu da take fuskanta a lamarin don damuwa ta gama yi wa zuciyarta katutu, shi kuma lamarin mu'amalar aure ana son gabatar da shi a lokacin da ake cikin walwala farinciki haɗe da annashuwa. *IBRAHIM* Kafin ya ƙarasa gidan su Jidda ya haɗa uban gumi sharkaf abin ka da wanda ya saba rayuwa cikin AC gida AC mota AC office ma AC. Ko da ya zo bai ƙarasa saitin gidan ba daga ɗan can gefe ya tsaya yana hangar ƙofar gidan, sai lazimi yake a zuciyarsa, yana addu'ar Allah ya sa ya dace. A can cikin gida kuwa Aliya ce take gwada wata doguwar rigar abaya maroon da takalmi haɗe da wata jaka sai murna take tana cewa "Gaskiya Kasim ya iya zaɓe" Umma ta yi karaf ta ce "Wannan ai za a je da shi, kin ga duk da ba mai arziƙi ba ne ai yana da wadatar zuciya, daga ganinsa irin mazan nan ne masu bautawa mace, kika dai yadda yake miki wahala komai ya samu ke yake yi wa" Aliya ta ce "Umma ai wanna da kike gani bawan mace ne" Umma ta ce "Ai tun da dai yana da karatun digirinsa digirgir kuma yana da ƙashin arziƙi daga gani, gashi yana sonki yana bauta miki tabbas in kika aure shi kakarmu ta yanke saƙa, wuyarta ya samu aikin gwamnati da takardun nan basa ai shi kenan kin zama babbar mace" Wani uban tsalle Aliya ta daka tana murna tana sanar da Umma Kasim ɗin ma ɗazu ya ce zai saya mata sabuwar waya. Da gayya suke ta maganganun nan da yada magana duk abin da suke Jidda tana jin su, ita damuwarta ma da jiya da daddare Abba ya tara su ya ce kowacce ta fitar da miji shi bai san cewa Jidda bata da wani tsayyaye ba, ita kuma tana jin nauyin sanar da Abban. Ta yi nisa a tunani Umma ta ƙwalla mata kira, tana fitowa ta saka ta wankin kaya, haka ta karɓa don dama yau Ummar ce ta hana ta zuwa islamiya saboda aikin gidan. Aliya ce ta gama saka kayan gabaɗaya a leda ta cewa Umma za ta je gidan su Amatullahi ta kai ta nuna mata Umma ta ce "Yawwa maza kula ki je ki nuna mata kin kece raini kuma kina da mijin da xa ki aura na nunawa sa'a" Ta faɗa tana kallon saitin Jidda da ta duƙufa wajen wankin zanin Ummar. Ko da Aliya ta ɗauki ledar ta fito ƙofar gidan, Ibrahim daga can inda ya tsaya ya hango ta, kasancewar bai shaida ta ba sai ya taho domin yana son ya tambaye ta ko Jidda tana ciki, bai gane ta ba sai da ya zo dab da ita, ita kuma Aliya a lokacin da ya ƙaraso tana ƙoƙarin kara waya a kunne don Amatullahi take kira za ta ce mata gata nan za ta nuna mata kaya. Ganinsa ya sa ta fasa kiran wayar ta kashe tana ƙare masa kallo, tabbas ko daga bacci ta tashi ba za ta kasa shaida wannan fuskar tasa ba. Fuska ta yatsina tana masa kallon ƙwaf, shi kuma gabaɗaya kansa ya kulle da ya ganta don tabbas ya shaida ta ita wacce ta ciwa direbansa mutunci ranar nan. Gabaɗaya ma sai bakinsa ya ƙi bashi haɗin kai wajen yin sallamar da ya yi niyyar mata, bare a kai ga tambayar da zai mata a kan Jiddar tana cikin gidan. Aliya kuma sai ta shiga masa wani kallon raini tana yatsina, gabaɗaya sai ya tsargu da kallon nata amma sai bai ce mata komai ba, cike da mamaki da gatsali ta ce "Oho sai yanzu na je ghana, kai duniya mutane sai a barsu, wato dai Allah ya tona maka asiri ashe dai ganin kana da kyau shi ya sa kake aron mota da kaya masu kyau kana yaudarar ƴaƴan mutane ko? Har da aron direba da yake janka a mota, wato ka zaci ba zan gane ka ba, to ta Allah ba taka ba wannan ai kai ne a wanki gara!" Ta faɗa tana wani zagaya shi, gabaɗaya sai Ibrahim ya kasa magana ita kuma ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har da faɗin ɗan talaka dama bai iya samun wuri ba wato har da cewa wa yake nemanta lokacin da ta je wajensa a motar ashe dai duk kanwar ja ce shi ma dai talaka ne bai ajiye ba bai bayar ajiya ba. Shi dai yana kallon ta tsabar mamaki ma ya rasa mai zai ce. Ganin haka sai ta ce "Shi ne ka lallaɓo koɗaɗɗun ƙafafunka da wasu tsoffin kayanka sa suka gaji da wanki, to wallahi ni na fi ƙarfinka ne, kar ma ka ɓata lokacinka wajen mini magiya ko roƙona don ina cikin mutanen da suke cewa da wuya ta kar su ai gwara daɗi ya kar su" A can cikin gida kuwa Umma ce ta ce Jidda ta ɗauki bokiti ta fita famfon waje ta ɗakko ruwa ta ƙarasa wankin, da yake ruwan ya ƙare, duk da akwai mai ruwan da yake kawo musu ruwa amma saboda ta ga Abba ba ya nan ta aike ta ɗakko ruwan, haka ta ɗauki bokitin ta fito ba don ta so ba. Aliya tana cikin masa wannan maganar har wani nuna shi da yatsa take a daidai nan ne Jidda ta fito, sai da gabansa ya buga da ya ganta sanye take da wani blue ɗin hijabi har ƙasa hijabin yana da hannu sai bokiti a hannunta fuskarta babu walwala. Tun da ta fito kallo ɗaya ta musu ta wuce da yake wajen famfon kusa da gidan da yae kusa da gidansu ne ta tara ruwan ta ciko ta ɗakko. Ta zo za ta shige gida ganin abin da Aliya take yi wa Ibrahim sai ta ce "Haba Aliya, a titi kike wannan ɗaga muryar?" Cike da ɗaga murya ta ce "An yi ɗin uwar pan shishshigi" Juyawa ta yi ta shige gidan, shi kuma kallon ta kawai yake yana son ganin gudun ruwanta, sai da ta gama masa ɗiban albarka ta ce "To a yi gaba ko a samu wata dai amma wannan Aliyar sai Kasim!." Tana faɗa ta juya ta tafi tana wani juya mazaunan da su da babu duk ɗaya. Gefe ya koma yana ƙarewa jikinsa kallo yana mamakin cewa kenan dai shi talaka a wajen wani shi ba komai ba ne, sannan wasu suna ganin duk rashin mutuncinka in har kana da kuɗi to kai mai kirki ne in kuma baka da shi da kai da babu duk ɗaya, dama ya fahimci cewa Aliyar nan ƴar son banza ce don ranar ma a idanunta ya ga son banza ƙiri ƙiri. Ko da ta je gidansu Amatullahi nan ta shiga bata labarin Ibrahim suka ringa zaginsa suna ce masa matsiyaci, Aliya ta ce "Oh har zan ce in yi saki na dafe da Kasim ɗina ashe dai ba arziƙi ba ne yake kirana tsiya ce" Amatullahi ta ce "Humm! Ba ke kike cewa wani kyakkyawa ba ne" Aliya ta ce "Ke dai bari a yau na gane cewa duk arahar kunu ta banza ce in babu gaya a ciki" Suka ci gaba da ɗaga kayan Kasim suna zuba masa albarka. Fitowar Jidda za ta ƙaro ruwa sai ta gan shi jingine da bango, amma sai ta masa kwarjini ya kasa mata magana har sai da ta ciko bokoti tana ƙoƙarin ɗakkowa ya ƙarasa wajen ya ce "Kawo in taimaka miki" Kawai da ta juyo sai ta kasa hana shi kwarjini ya mata ta ga yana da kima da kuma kamala. Ɗakko mata ruwan ya yi har ya kawo ƙofar gidan, kasancewar ya saba ruwa a banɗaki sai dai ya tara ya yi wanka tunaninsa zai ji nauyin bokiti amma da yake soyayya yake yi wa bauta sai ya ji ko alamar nauyi babu kamar dai ya ɗauki bokiti mai auduga ne. Yana zuwa ya ajiye ya ɗago yana kallon ta cike da jin daɗin abin da ya mata ta ce "Sannu da ƙoƙari na gode ƙwarai" Wani daɗi ne ya cika shi kamar ya taka rawa jin muryarta tana masa godiya da jinjina masa. Har za ta ɗauki bokitin ta juyo ta ce "Don Allah ka yi haƙuri abin da Aliya ta farfaɗa maka" Yana jinjina dattakon ta ya ce "Ni dama ...am dama ke zan ce ta yi min magana da ke shi ne ... Ya faɗa yana inda -inda Cike da mamaki ta kalle shi tsantsar mamaki yana bayyana a kan fuskarta ta ce "Ni kuma?" Ta faɗa zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, ta san dai jiya ta yi ta addu'ar ita ma Allah ya fito mata da mai son ta wanda zai aure ta ya riƙe ta da daraja idanu ta ɗan runtse ta buɗe ta ce "Lafiya dai ko?" Yana kallon yanayin ta ya ce "Na zo don in bayyana miki soyayyata wallahi ina ƙaunarki da gaskiya tun daga ranar da na fara tozali da ke" Ya faɗa zuciyarsa tana zillo kawai gani yake ba za ta amince da shi ba saboda kyaun da yake da shi tun da da kunnensa ya ji ta ce bata son mai kuɗi kyakkyawa. Jidda kuwa jikin ta ne ya fara rawa kasantuwar abin ya zo mata a bazata, kuma dai mutumin ya birge ta musamman da ta ga cin mutuncin da Aliya ta masa bai biye mata ba duk da bata san abin da ya haɗa su ba sannan da taimakon ta da ya yi ya ɗaukar mata ruwa. Rasa amsar da za ta bashi ya sa ta ce "Sai na yi tunani tukunna" Wannan furucin nata ya saka shi a wasi-wasi amma ya danne ya ce "Babu damuwa Allah sa ki yanke abin da ya fi zama alkairi " Yanayin yadda ya yi maganar ya sa ta ji wani iri kamar dai bata kyauta masa ba kamar dai bai ji daɗin furucin ba. Bata ce masa komai ba ta sunkuya ta ɗauki bokiti har ta fara tafiya ya ce "Jidda" Har tsakiyar kanta ta ji kiran sai ta ji tamkar shi kaɗai ne ya iya kiran sunanta daidai, sai dai bata san dalilin hakan ba, juyawa ta yi bayan ta ajiye bokitin ta ce "Na'am" Ta faɗa idanunsu suna sarƙewa da juna da sauri ta yi saurin kawar da nata, kasancewar sai ta ji kallon da idanunsa suka jefe ta da shi ya sha bamban da kallon kowane mutum. Iska ya ɗan hurar daga bakinsa ya ce "Ki daure ki bani phone no ki" Kamar ba za ta ce komai ba har ya cire rai za ta bashi sai ya ji ta fara karanto masa, nan ya shiga rubutawa a ƙaramar wayar da ya taho da ita. Tana gama faɗa masa va tare da ta jira cewarsa ba ta juya ta ɗauki ruwan ta shige gidan. Tsabar murna bai san ya isa bakin titi ba don ko wahalar tafiyar ba ya ji, wani irin farinciki da yanayi marar misaltuwa da yake ziyartarsa, haka ya yi kwanan farinciki amma dai ya kasa kiran wayarta don sai ya rasa mai zai ce idan ya kira. Bayan kwana biyu, har lokacin bai koma gidansu ba kuma bai kira ta ba, sai dai yana ta dakon soyayyarta. A ɓangaren Jidda tun daga wannan ranar ta ji ta damu da Ibrahim sai dai rashin kiranta a waya sai ta ji duk babu daɗi, tun tana jiran kiransa har ta cire rai, da ko baƙuwar no ta gani sai ta yi tunanin shi ne har dai ta cire rai daga kiran nasa. Sai da aka yi sati sannan watarana da yammaci yana zaune a ƙasan wata bishiya a wata unguwa yammaci ne mai cike da ni'ima sassanyar iska tana kaɗawa, yana zaune saman motarsa ya kamo sunan ya shiga kiranta, Jidda tana hura wutar da take tuwon dare ta fara jiyo ƙaran wayarta, amma bata je ta ɗakko wayar daga ɗaki ba. Har kiran ya tsinke bata je ba, Ibrahim kuma sai ya fara wata zufa hankalinsa ya tashi ya fara tunanin ko dai ta yanke shawara marar kyau a kansa, kuma da ya yi tunanin ai bata san numbersa ba sai ya ji hankalinsa ya ɗan kwanata a ƙara gwada kiran. Tunanin ta ma ko Salama ce ita ce idan ta fara kira bata san ta daina ba, hakan ya sa ta iza wutar ta nufi ɗakin, tana ɗaukan wayar ta ga baƙuwar no dama gidan babu kowa sai ita kaɗai duk sun fita gidan biki. Bata san mai ya sa ba amma sai da gabanta ya faɗi tana dannawa ta ƙara wayar a kunne. Sassanyar muryarsa mai amo mai daɗi da ita ya fara mata sallama, idanu ta lumshe kaɗan ta buɗe su bata san dalili ba amma sai ta ji ta yi farin ciki da kiran, bata san ko don ta daɗe tana jiran ya kira ta ba ko kuwa mene ne oho. Amsa sallamar ta yi sai ya ce "Sunana Ibrahim ni ne kika ba numberki ranar da kika ɗauki ruwa" Wani murmushi ya kuɓuce mata marar sauti a zuciyarta tana raya da a ce ya san cewa bata da wani saurayi da bai wahalar da kansa wajen tuna mata ranar da suka haɗu ba. Cike da murnar da bata bari ta bayyana ta a fili ba ta ce "Na gane ka" Ya ce "Ya batun tunanin kin yanke hukuncin" Ta ce "Hukuncin me?" Ya ce "Hukuncin na cancanta ki kula ni ko ban kai ki kula ni ba" Maganarsa ta bata dariya hakan ya sa ta dara har yana iya jiyo sautin dariyar ta cikin wayar. Jingina ta yi da bango ta don dama a tsaye take ta ce "Ban amince ba" Gabansa ne ya buga da ƙarfi a take ya ji gabaɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi, ɗan walwalar da ya tsinci kanaa sanadin magana da ita duk sun gaushe. Bata tantance ba ta ji saurin maganarsa cikin tashin hankali yana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Bata san dalili ba sai ta ji zuciyarta babu daɗi ta ji duk ta damu da yanayin sa ya shiga bata san lokacin da ta ce "Da wasa fa nake maka na amince" Daga ita har shi dariya ce ta ƙwace musu. Sun daɗe suna hira kamar sun saba daga bisani ta ce masa aiki take saboda ta ga abin nasa ba na ƙare ba ne, wayar ta ajiye ta fita ta ƙarasa tuƙa tuwon, sai bayan ta kallama aikin ta yi wanka ta zo ta ɗauki wayar ta yi saving no da IB tana ta maimaita hirarsu a zuciyarta. Washe gari tun da asubar fari Aliya ta ishe ta da cewa saura sati guda a kawo mata kayan saka rana, amma Jidda ta yi kamar vata ji ba daga ƙarshe ta ce Allah sanya alkairi amma sai Aliya ta ce baƙin ciki take. Ita kuwa ko da Abba ya sake tambayarta sai ta ce za ta turo wanda zai gaishe shi ya ce za a aiko suna shiri ne daga haka Abban bai sake tambayarta ba. Bini-bini waya da Ibrahim da Jidda har dai ta kai ta kawo yana zuwa hirar tsakanin magriba da isha, a hakan Aliya ta sha yanka masa magana wai laila ta ƙiya an koma caca. Ranar da ya zo ma kayan gwanjon ya sako abinsa, bayan Jidda ta koma gida Aliya take cewa wai wannan mai zuwa wajen nata matsiyaci ne. *BAYAN SATI GUDA* Ana ƙoƙarin kawo kayan saka ranar Aliya sai gobe, sai Ibrahim ya sanar da Jidda cewa zai aiko in ta amince duk da basu daɗe da haɗuwa ba, ita kuma ta yarda da shi ta yaba da halayyarsa don haka ta amince cewa ya aika a samu Abban nasu, lokacin da ya sanar da su Mummy cewa ya samu wacce yake so sun yi matuƙar mamaki sun yi murna ƙwarai . Daga haka ne ma ya samu damar saka kayan gwanjonnsa babu ɓoye-ɓoye ya ce saboda yana son ya auri mai sonsa da gaskiya ne ba wai don dukiya ba, basu san cewa yana amfani da kayan va ne saboda ita wacce yake so ɗin kuɗin basa gabanta. Ya fahimci Jidda tana son ss duk sa ya san nasa son ya linka nata. Bai san dalilin da ya kore mata ƙuduri da burin auren kyakkyawa ba. Tun da yake zuwa ko biyar bai taɓa bata ba, ko da Ibrahim ya sanar da ita za a je gaisuwar iyaye ta faɗawa Umma a kan ta sanar da Abba saboda tana jin kunya Umma ta ce "Shi ma dai wannan zai kwasawa kansa jangwam, ko don talaka ne ai dama talaka ya saba da wahala" Jidda bata ji daɗin maganar ba amma babu yadda za ta yi. MAMAN AFRAH 09025576222 [10/18, 9:27 AM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/C12RFYqXnWf36AhjVZWDw4?mode=ems_copy_t *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 8️⃣ *SADIYA* Tana yin sallar asuba ta fita ta hura gawayi ya kama ta ɗora ruwan zafi, tuwon masara ta tuƙa wanda Nasir ya bata garin ta yi miya ta gama ta ɗora ruwan ɗumi ta dawo ta fara gyaran falon, lokacin ƙarfe bakwai da arba'in. Bayan ta kammala lokacin Nasir ya taso ya shiga wanka ya shiga bedroom ɗin zai shirya lokacin tana gyaran gado yana kawo kai ya ce "Sadiya warin mene ne a ɗakin nan? Yanzu da girmanki kike sakarwa mutane tusa a ɗaki gabaɗaya ɗaki ya ɗumi da wari?" Ya faɗa yana saka hannu ya toshe hanci yana mata wani kallo. Ɗagowa ta yi daga sunkuyen da ta yi tana totsa zanin gadon sai lokacin ita ma ta ji ɗakin ya haɗe da wari cike da ladabi ta ce "Haba Abban Kalifa tun da nake a gidan nan ka taɓa jin warin tusata?" Bata bashi damar magana ba ta ɗora da faɗin "Wannan ba halayyata ba ce gaskiya sai dai ko Kalifa ne ya yi" Bai amsa mata ba ya ɗauki kayansa a drower ya ɗauki man shafawa ya fita falo a daidai nan Kalifa da ya yi juyi ya tashi zaune sai ta ji warin ya tsananta hakan ya sa ta fara tunanin ko kashi ya yi, net ɗin ta cire tana dubawa kuwa sai ta ga kashi ya yi gabaɗaya kashin har ya ɓata shimfiɗar, Kalifa ya ce "Momma ruwa" Ta ce "To Kalifa kalli kashin da ka yi duk ka mata shimfiɗa wannan kashin haƙorin naka da yake baka wahala ne ya dawo maka" Ta faɗa tana ɗago shi ta fito da shi, suna zuwa falo tana dab da fita a zuciye Nasir ya ce "Sadiya mene ne wanann wai? Mai ya sa kike son shiga rayuwata kike hanani sukuni, kin cika ɗaki da wari na fito falo sannan kin kawo min wari falo" Ranta ne ya sosu da furucin sa tana riƙe da yaron ta ce "Shin ni na yi kashin?" Tambayar da ta masa sai ya ga ta raina masa hankali hakan ya sa ya ƙara ƙufula, ganin bai ce komai ba sai ta juya ta saka silifas ɗinta ta kai Kalifan waje ta tsayar da shi, dawowa ta yi ta kwashe shimfiɗar ganin kashin bai taɓa katifar ba sai ta fito da kayan waje, wankewa Kalifan ta yi ta juye ruwan zafin da ta ɗora ta masa wanka tas. Kayan ta wanke ta shanya kafin ta ɗakko Kalifan suka dawo ɗaki turaren tsinke ta kunna duk da zuwa lokacin ma warin ya fita dama saboda kashin haƙori yana da wari ne, kaya ta sakawa Kalifan sai kuwa ya fito falon wajen uban yana ƴar dariyarsu ta yara ya je gaban Nasir da yake danna waya ya ce "Abba" Nasir bai amsa ba fitowar Sadiya sai ta ga Kalifan yana tsaye a gaban Nasir ɗin ne ya ɗora hannunsa a kan gwiwar Nasir ɗin. Kalifa ya sake cewa "Abba" Maimakon ya amsa sai ya ɗago daga dannar wayar da yake ya ce "Sadiya ni kika cewa wai ke kika yi kashin?" Sadiya da take tsaye ta zauna a kujera ta ce "Wannan maganar da ta wuce mene ne na dawo da ita?" Nasir ya ce "Ban da shashanci da rashin sanin ciwon kai a ce yaro yake kashi a kwance wannan ai sangarta ce, ke ce baki koya masa ba amma sauran mata da suke da tarbiya ai suna koyawa ƴaƴansu abubuwa" Baki sake take kallonsa kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta ce "Yanzu yaro ɗan shekara biyu ne za a ce wai ba a koya masa tarbiyar kashi a kwance ba, shin kana ganin yana kashi a kwance idan ba na jinya ba, wanna fa kashin haƙori ne, kuma ko da a ce akwai famfas a jikinsa kashin zai iya fitowa saboda wani lokacin ko famfas ba ya riƙe shi, wai don Allah Nasir mai na maka a rayuwa? Mai ya sa koyaushe cikin neman laifukana kake don ka hukuntani, komai na yi ban iya ba, mai ya sa ban taɓa birgeka a rayuwa ba duk abin da zan yi kuwa... Wani dogon tsaki da ya ja ne ya sa ta maƙale sauran kalamanta, ga haushin bai yi wa Kalifa magana ba sai ta ce "Kalifa zo nan" Juyowa Kalifan ya yi ya kalle ta amma bai je ba ya sake buga gwiwar uban ya ce "Abba" Ajiye wayar Nasir ya yi ya kama hannun Kalifan duka biyu ya ce "Na'am Kalifa" Wani irin washe baki Kalifan ya yi da alama ya ji daɗin hakan. Sadiya kuwa sai ta ji sanyi a ranta ganin walwala a fuskar yaron ta. Nasir ya ce "Kalifa kai da jiya ka tafi ka barni, ka tafi gidan kakanka wuni kuma ya koro ku" Ya faɗa yana dariya, sosai Kalifan yake dariya da alama ya ɗauka wata kalma mau daɗi ce abinka da yaro, Sadiya kuma sai yanzu ta gane cewa ya yi haka ne don ya baƙanta mata zuciya, kuma cin fuska ne yake mata kai ta sunkuyar sai Nasir ɗin ya ce "Maza je a zuba maka tuwo" Yana ta dariya ya juya zuwa wajen Sadiya, ɗago kai ta yi ta kalli Nasir ya sakar mata wani murmushin gefen baki tare da ɗaukan wayarsa ya cigaba da dannawa, ta rasa mai ya sa Nasir in dai zai ga walwala a fuskarta sai ya san yadda ya yi ya daƙusar da ita, ya fi so ko yaushe ta kasance cikin ƙunci. Fita ta yi ta zubo musu tuwo ta ajiyewa Nasir, shi ma Kalifan ta ajiye masa har zai zauna ta ce "Baka cewa Abbanka ina kwana ba" Da sauri ya masa yana washe baki ya ce "Abba nawana(Ina kwana)" Amsa masa ya yi ya koma ya fara cin tuwon bayan ta sa ya yi bismilla da bata fita a bakin ba.Bayan ya gama ci ta wanke masa hannu suna shirin juyowa zuwa ɗaki sai kawai ta ji ƙaran kashi sai ganinsa ta yi kamar ruwa yana biyowa ta ƙasan wandon sai Kalifa ya ce "Momma foo" Haka ta cire masa ta wanke masa ta ɗora shi, wandon ta wanke ta wanke masa ta ɗauke foo ɗin tana taɓa jikinsa ta ji zafi sosai zazzaɓi ya rufe shi, haka ta ɗakko shi ta dawo da shi ta saka masa wandon ta kwantar da shi. Nasir da ya gama zai fita kasuwa ta kalle shi ta ce "Ina son zan kai Kalifa asibi... Tun bata ƙarasa ba ya ce "Sadiya baki san wahalar da maza suke sha ba a wajen neman kuɗi ko? Wato daga yaro ya yi kashi sai ki ce wai za ki kai shi asibiti to ni bani da kuɗi idan kuma har kinnga sai kun kai shi ga hanya nan ba zan hana ki ba, amma naira biyar tawa ba za ta yi kuka ba" Kamar za ta yi kuka ta ce "Wallahi yanzu ma jikinsa zafi kuma kashin fa ya sake yi kar ya ci ƙarfinsa don All... Bata ƙarasa ba ta ji ƙaran aman Kalifan dama haka yake jinyar haƙori kashi da amai ga zazzaɓi kansa zafi. Bedroom ɗin ta nufa, tana zuwa duk ya kelaya amai haka ta ɗane kayan shimfiɗar ta goge masa bakin gabaɗaya har jikinsa ya yi sanyi alamar abin ya fara ci ƙarfinsa. Tana fitowa falon ta ga Nasir ya kara waya a kunne, Nasir kuwa mahaifiyarsa yake kira. A can gidan su Nasir mahaifiyarsa ce Hajiya Mariya wacce suke kira da Hajiya suna zaune ita da yaranta ƙannen Nasir ɗin guda biyu Husna da Hibba karyawa suke dankalin turawa ne da wainar ƙwai sai shayi mai kauri da kuma farfesun kifi suna ci suna hira wayar Hajiya ta yi ƙara ɗagawa ta yi ta ce "Hello Nasir" Nasir ya ce "Hajiya ina kwana" Amsa masa ta yi tana faɗin ga abincinsa ya amsa mata da gashi nan zuwa sai ya ce "Kalifa ne yake kashin haƙori da amai da zazzaɓi shi ne Sadiya ta ce za ta kai shi asibiti" A harzuƙe Hajiya ta fara faɗa tana cewa "Wai Nasir sau nawa zan faɗa maka cewa wasu matan munfukai ne, suna faɗar jinyar ƴaƴansu ne kawai don su tatsi kuɗin miji, wato ta ɗauka kai sokon namiji ne to ahir ɗinta wallahi wani kashin haƙori ne za a kaiwa likita to likita ya bashi mai, sau nawa zan faɗa maka laulayin haƙori ba ya jin magani, shi ne za a wahalar da kai a yaudare ka ai wallahi ɗana ya fi ƙarfin mace ta ci kuɗinsa rabu da ita naira ɗari ta isa ta biya buƙata zan bada maganin a kai mata" Sosai ya ji wani daɗi a ransa yana son yadda mahaifiyarsa take taya shi tattalin kuɗinsa, ya gama wayar lokacin ta dawo falon ya kalle ta a wani wulaƙance ya ce "Hajiya ta ce za ta bada maganin a kawo" Sai da ta kai zuciyarta nesa sannan ta ce "To" Store ya je ya ɗakko shinkafa da wake daidai wanda yake bayarwa a dafa ya kawo ya bata ya juya ko sallama bai mata ba ya fice ya banko ƙofar gidan. Shiru ta yi tana ta tunanin rayuwarta a ce kai baka da wata kima ko daraja a wajen miji bare ƴan uwansa ɗanka bashi da wata daraja yanzu a ce ɗansa bashi da lafiya amma ya hana a kai shi asibiti sai mahaifiyarsa ce za ta ce masa za ta bada maganin, kwanciya ta yi a kusa da Kalifa tana ta tunani. Zuwa can ta tashi ta fita ta fara wankin banɗaki tana cikin yi ta fara jin ƙaran wayarta, kafin ta zo har kiran ya katse wani ya shigo, tana ta tunanin ko lafiya sai ta ga sunan Babanta gabanta ne ya faɗi ta fara tunanin Allah sa alkairi ne. Jiki sanyi ƙalau ta ɗaga wayar ta gaishe shi ya amsa tana jin muryarsa raɗau babu alamun damuwa hakan ne ya bata tabbacin babu wata damuwa ko matsala. Baba Ya ce "Sadiya kiranki na yi in ce ki tayani godiya wajen mijinki kai Allah sakawa Nasir da alheri" Shiru Sadiya ta yi sai dai bata bayyanawa Baba mamakinta ba ta ce "Godiyar mai Baba?" Baba ya ce "Ka ji yaron arziƙi ashe ma bai faɗa miki ba, shi ya sa fa ake so in mutum zai yi alheri ya yi tsakani da Allah ba sai wani ya sani ba, shi ya sa aka ce hannun hagu kar ya san na dama ya miƙa" Sadiya ta ce "Haka ne Baba" Baba ya ce "Wallahi Sadiya wayata na ji tana ta ƙara ina dubawa na ga mijinki ne bawan Allahn nan na gaishe shi" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tsayawa Sadiya jin Baba ya ce wai shi ya gaishe shi ba ma Nasir ɗin ne ya gaishe da Baban ba. Baba ya ci gaba da faɗin "Kawai bayan ya amsa gaisuwata sai ya ce Baba ka tuwo akawun lamba, bai jira na ƙara magana ba ya yanke kiran, ni kuwa ban yi bori da sanyin jiki ba na kwashe lambobin akawun ɗina na tura masa, ina turawa na kira shi ban san lokacin da na ce ranka ya daɗe na tura ba" A take hawaye suka fara sartu a fuskarta wai Baban ne ya cewa sirikinsa ransa ya daɗe saboda kawai ya ji maganar kuɗi wannan wace irin zubar da kima ce. Baba ya ce "Da to ya amsa min ya kashe ana jimawa sai ka dubu ɗai-ɗari dubu na dukan dubu har dubu goma ya ce in ɗauki dubu biyar in ba tsohuwarki dubu biyar, na rinƙa masa godiya, yanzu dai na bata dubu uku ni na ɗauki bakwai shi ne na kira ki kema ki tayani gode masa, yaron arziƙi ai ke da shi sai mutuwa ce za ta raba" Sadiya a zuciyarta ta ce ',In sha Allah ba zan mutu a gidan Nasir ba ina saka ran wataran zan fita daga wanna rayuwar marar ƴanci rayuwa marar galihu, rayuwa marar daraja' A fili kuma ta ce "Amma na ji daɗi Allah saka masa da alkairi kuma in ya dawo zan yi ta gode masa tare da yaba masa" Haka Baba ya mata sallama cike da jin daɗi. Tana ajiye wayar za ta juya wani kiran ya shigo, ta ɗauka Baban ne amma tana dubawa sai ta ga Mama ɗauka ta yi bayan sun gaisa ta ɗauka Mamar za ta tambaye ta yaya aka ƙare jiya da ta dawo ko dai wani abu makamancin haka, ko ma dai ta tambaye ta damuwarta kamar yadda ta je mata da ƙorafin jiya ko ba komai sai ta lallashe ta ta tausasa mata yadda za ta rage mata raɗaɗi a matsayinta na uwa amma sai ta shiga faɗa mata alkairin da Nasir ɗin ya musu tana ta msta godiya da musu fatan haɗin kawunansu, haka dai Sadiyar take bata amsa cikin ƙarfin hali daga ƙarshe suka yi sallama. Tana kashe wayar ta koma ta zauna daɓas tana tunanin kenan dai Nasir ya ƙara ƙirƙirar wata hanyar toshe duk wata ɓaraka, ita tana gidan yana musguna mata ko kuɗin kai ɗanta asibiti bai bata ba gashi a can kuma yana bajinta wato zai wanke laifinsa ko da ta je musu da magana ba za suke amincewa ba, tun da suna masa kallon mutumin kirki wannan alama ce ta sun zaɓi farincikin ɗan wani a kan farin cikin nasu ƴar!. *JIDDA* Ranar da aka kawo kayan saka ranar Aliya da yamma, guɗa ƙawayen Umma suka cika gida da shi Umma tamkar za ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, saboda ganin kowacce a wajen ana kawo mata kayan saka rana sallayoyi dabino, kuɗi, wasu ma kuɗin ake kai musu amma sai gashi Aliya har da ƙaramar akwati wannan dalilin ya sa maƙota suke ta zuzuta abin har kan Mama da Aliya ya fashe. Da dare bayan an watse Aliya sai gwada takalman take tana wani bada faɗi a tsakar gida lokacin Abba baya nan yana waje tare da baƙi sai murna Aliya take tana cewa "Umma na wuce raini a unguwa, na kere sa'a wallahi Kasim yana matuƙar sona, ya kankaro min mutunci a wajen ƙawaye irin wannan takalma kala goma atamfofi kala biyu da turaruka ina ga in aka ga lefe ai ina jin ƴan baƙin ciki sai sun zauce" Ta faɗa tana ɗaga murya. Umma ta ce "Aliya kin yi sa'ar miji, mijin nunawa sa'a mijin bugar ƙirji ki nuna a ko jna saboda duk namijin da aka ce miki zai iya bugun ƙirji ya faranta miki to tabbas yana da kyakkyawan buri idan ya samu maƙudan kuɗi ina ga sai kyautar miliyoyi" Suka kwashe da dariya duk abin da suke Jidda tana ji don ita tun da aka kawo kayan da aka buɗe a gaban mutane ta gani bata sake gani ba, don ko bayan mutane sun watse da ta je ta fara ɗaga takalman Umma ta ce "Jidda kar ki ƙara ɗaga kayan nan, wato kina ɗagawa zuciyarki tana ƙuna ko? Abu ne da ba za ki taɓa samu ba, wataƙila ma mijin naki ya ƙoƙarta ko dubu talatin ne kuɗin lefen da na saka ranar har ma sadaki tabbas aurenki bashi da maraba da sadaka Jidda" Lokacin d Umma ta mata wannan furucin ta ji ciwo amma kuma tuno yadda take jin Ibrahim a ranta da zuciyarta sai take gani ko babu ko kwabo za ta aure shi ta zauna da shi tsakani da Allah, kuma za ta masa matuƙar biyayya har ƙarshen numfashinta!. A fili kuma sai ta tashi siyam-siyam ta nufi ɗaki tana jin babu daɗi a lan abin da Ummar ta mata ko don ba ita ta haife ta ba, amma ita Jidda a zuciyarta daɗi da farinciki take na kayan da aka kawowa Aliya kuma bata jin ƙyashi ko baƙinciki kuma bata wani tunani a kan cewa tana jin tana son wani abu makamancin abin da aka kawowa Aliyar bare ma ita kamar yadda Ummar ta faɗa ta san ma hakan ne tun da a yadda take kallon Ibrahim bata taɓa zaton zai ce da aure yake son ta ba, tunaninta bai shirya auren ba duk da baka san tanadin mutum ba amma ita bata da buri a haka take son kayanta. Abba yana wajen yake ganin matan jefi-jefi suna zuwa suna gani tare da yin Allah sanya alkairi. Abba bayan baƙin sun tafi ya jima zaune yana ta jimami da mamaki sai dai ya san ba a mamaki da jimami da lamarin ubangiji hakan ya sa ya rasa ma wa zai tunkara da wannan magana, jin wai ashe ɗan gidan Alhaji Sule ne ya zai auri Jidda, mutumin da babu inda za a ambaci sunansa a kasa gane shi babban mutum mai dukiya da ya yi shura, lallai Allah, Allah ne yana yin yadda ya so a lokacin da ya so, yana ba wanda ya so sanda ya so Wayo ko dabara ba ya ba mutum abu Allah kaɗai yake bayarwa, Allah shi yake bayarwa a gode masa ya ƙara!. Abba ya nisa tare da sakin wata ajiyar zuciya yana duba naira miliyan uku a gabansa wanda 500k guda shida kowanne nannaɗe da kyaure, yana tunano yadda suka gabatar masa da kansu a matsayin baƙinsa da suka yi waya cewa za su zo bayan sallar isha'i bai taɓa saka ran zai gansu ba shi ya sa da ya ga zuƙeƙiyar mota ma bai kawo cewa baƙin nasa ba ne. Yadda suka karrama shi duk da yana da labarin Alhaji Sule bashi da wulaƙanta ɗan adam ya san mutuncin mutane amma sai ya ga abin ya fi yadda ake faɗa, tabbas zai yi alfahri a ko ina da mijin da Jidda za ta aura saboda ko da ya zo ya gaishe shi haƙiƙa ya yaba da hankali da tunaninsa, kuma a yadda ya ganshi bai taɓa tunanin masu hannu da shuni ne har haka ba, amma ya zo gidan talakawa neman aure haƙiƙa duk wanda ya auri Jidda ya dace da mace kamila kuma ta gari, duk da ba shi ya haifi Jidda ba amma yana alfahri da ita, kuma ya yi wa su Alhajin bayanin wace ce Jidda kuma sun ji sun gani. Kuɗin ya fara tattarawa yana tunanin yadda zai yi da wannan kuɗin, tun da shi kaɗai ya karɓi baƙin nasa, duk da naira miliyan goma suka bayar a matsayin kuɗin gaisuwar uwa da uba da kuma kuɗin kuɗin saka rana gabaɗaya suka kawo amma ya ce shi ba zai karɓi miliyan goma ba ya yi yawa dakyar ma ya ɗauki miliyan uku. A fili ya furta "Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka bani iko zan sauke nauyin marainiyar nan, zan damƙa ta a hannu na gari Allah ka taya mijinta riƙo ka bashi ikon kulawa da ita!" Gabaɗaya ya kwashe kuɗin ya saka a babbar riga bayan ya ware dubu goma ba don komai ya yi hakan ba sai don kar ya saka Umma ko Aliya jin wani abu marar daɗi a ransu saboda shi kansa bai zaci haka ba kuma ya ga suna farinciki da abin da Kasim ya mata, kar su fara raina abin da ya yi. Gidan ya shigo ya same su suna zazzaune, suna cin abinci ɗaki ya shiga ya ɓoye gabaɗaya kuɗin yana sakawa a ransa cewa bayan bikin zai samu kadara ya sayawa Jidda da kuɗin wannan don bai yarda ya ba kowa kuɗinta ba. Bayan ya fito ya zauna ana hira yana cin abinci sai da ya kammala ya yi gyaran murya ya ce "Ummar yara" Umma ana washe baki aka ce "Na'am" Ya ɗan nisa kaɗan tare da zaro dubu goman aljihunsa ya ajiye ya ce "Ga kuɗin gaisuwa da saka ranar ƴarki Jidda!." Gaban Jidda ne ya bada wani rasss a inda Umma da sauri kafin ta furta komai ta miƙa hannu ta ɗauki kuɗin a fili ta fara irgawa tana cewa "Dubu ɗaya, dubu biyu, dubu uku, dubu huɗu, dubu, biyar" Da ta zo kan dubu biyar sai da ta ɗago kai ta kalli Jidda wacce kanta yake sunkuye saboda kunya ita kuma Aliya bakinta washe tana kallon hannun Umma saboda tana ganin kuɗin hannun Ummar da take irgawa ya kusa ƙarewa. Umma ta ci gaba da irgawa tana murmusawa cike da ƙeta a ranta ganin dai kuɗin bashi da maraba da sadaka, da ta zo dubun ƙarshe sai da ta ƙara sautin ta ta ce "Dubu goma cass" Ta faɗa tana kallon Abba da yake murmushi kafin ya furta wani abu Jidda ta tashi da sauri saboda kunya ta nufi ɗaki. Umma a zuciyarta ta ce 'Shegiya aniyarki ta biki wato ba za ki iya kukan baƙin ciki a gaban mutane ba sai kin shige ɗaki taɓɗi lallai iska tana yawo da mai kayan kara in banda matsiyaci kika kwaso har yaushe zai kawo dubu goma' Maganar da Abba ya mata ne ya dawo da ita daga maganar zucin da take ya ce "Kin gama irgawa" Tana dariya mai sauti ta ce "Wallahi na gani abin arziƙi yarinya ta yi goshi" Aliya ta ce "Umma dubu goman ne goshi" Ta faɗa tana ƴar dariyar yadda Jidda za ta ji, Abba ya ce "Ke ba na son shashanci tashi ki tafi ki ba mutane waje" Da sauri ta tashi ta shige ɗaki tana shiga ta rungume Jidda ta ce "Amarya ta ango ya kawo mata dubu goma" Jidda duk sai ta ji kamar ta nutse ita kuma Aliya murna take ganin ta fi Jidda komai dama ta san babu yadda za a yi ita kyakkyawa mummuna ta fi ta komai na aure!. Tun da aka saka rana wata guda sai soyayya da shaƙuwa suka ƙara tsananta a tsakanin masoyan biyu wato Jidda da Ibrahim, kowa ƙoƙarinsa ya ba ɗan uwansa kulawa tamkar ƴan biyu haka suke rayuwarsu kamar dai ƴan uwa ba wai wanda soyayya ce ta haɗa ba!. Abba ya yi ƙoƙari ya saya musu kayan ɗaki iri ɗaya daidai ƙarfinsa, a inda ya saya kayan kicin ma komai babu bambanci. Sai dai Umma tana ta sayan kayan kicin tana turawa ƙasan gado don bata yarda a ce da Jidda marainiya da kuma Aliya mai uwa a raye an musu komai da komai iri ɗaya ba. Jidda sosai suke murna ita da ƙawarta Salama Jidda za ta yi aure!. Mummy yau saura kwana biyu su dira a Nigeri'a za su dawo daga Dubai inda suka tafi sayyayar kayan lefe. Yau saura kwana biyu a kawo lefe don ranar ta kama gabaɗaya tare za a kawo domin Abba ya sanar da kowanne ɓangare na maza cewa rana ɗaya za a kawo. Aliya da Amatallahi suna ta rawar kai sanadin wasu hotuna da Kasim ya turawa Aliya na wasu lesuna ya ce kaɗan daga cikib kayan da aka saka a lefe ne sauran sai an kawo ta kashe ƙwarƙwatar idanunta. Wannan dalilin ya sanya Amatullahi da Aliya cewa ranar kawo kayan lefen a ɗakin Umma za su ɓuya babu inda za su tafi domin a kawo a kan idanunsu saboda Aliya ta sanar da Kasim cewa a samo motar da za ta kawo masu kawo kaya, hakan ya sa ya ce ai dole ma ya samo motoci, kanta ya fashe suna ta yadawa Jidda magana wacce ita bata wani damu da abubuwan da suke faɗa ba. Har yau bata san waye Ibrahim ba shi kuma yana jin daɗin mu'amala da ita a hakan rayuwar duniya bata dame ta ba kuma har yau ko ɗankwali bai bata kyauta ba bare naira biyar sai dai yana mata wani tanadi na musamman a cikin gidanta wanda farinciki ne da kwanciyar hankali in sha Allah. Yau ya kama alhamis ranar da za a kawo lefen Jidda tun da rana ta shirya ta cewa Umma ta tafi gidan su Salama, suna can suna ta murna da kuma sakawa a ransu cewa duk abin da aka kawo za su karɓa su yi farinciki!. A zaure Abba da ɗan uwansa da kuma amininsa da maƙota guda biyu. Umma ita da ƙawarta sun kasa zaune sun kasa tsaye suna ta tunanin yadda za a kawo kayan nan sun da Umma tana ganin kayan saka rana ma an yi musu bajinta bare kuma lefe mai kankat. Kuɗi ma sai da aka ɗora dubu ashirin. A can gidan Daddy zuƙa zuƙan motoci kuma galla galla sabbi dal, sai sheƙi suke na sabunta da kuma gani ka san sun ci kuɗi. Guda uku aka ware inda ma'aikatan gidan suke fito da wasu kyawawan kwatuna suna lodawa a motocin sai da suka gama saka wa tas, maza biyar ne wanda za su tafi kai kayan inda kowacce mota da direba. Wata baƙar mota sabuwa wacce ita ma gabaɗaya kujerunta ledojin sabunta ne za an buɗe get motocin za su fita Daddy ya zaro mukullin daga aljihu ya miƙawa wani direban da yake a tsaye karɓa ya yi ya shiga motar suka jera suna tafiya a laye sabuwar baƙar motar ce a tsakiya suna fita aka rufe get ɗin suka lula a saman titin da tamkar domin su aka yi shi, suka tasamma gidan su Jidda. Ibrahim da yake kallonsu ta saman windown a bene ganin fitarsu ya ɗaga hanni yana godewa Allah tare da fatan Jidda ta ci gaba da amincewa da shi don ya san yau kayan lefensa za su tabbatar mata da waye shi, tun da ta faɗa masa an kawo dubu goma kuma bai ga alamar rainuwa a tare da ita ba, tabbas ya san Jidda tana masa wani ɓoyayyan so duk da tana bayyanawa amma ya san baki ba zai iya furta yawan son da take masa ba. Duk da ya san wanda take masa ba zai kai wanda yake mata ba. A can gidan su Kasim, Kasim ne tsaye a ɗakinsa ya rasa yadda zai yi saboda ya faɗawa mahaifinsa cewa ga abokansa nan za su zo su kai su a motoci shi ne yake ta masa faɗa yana mene ne wani abin motoci kar wani mai motar da ya zo masa ƙofar gida, a ƙafafunsu za su je suna tafiya suna hira, haka yana ji yana gani Baban nasa ya kirawo wani mai ruwa ya ce ya zo da zai yi hayar baro, haka ya ɗakko baron aka ɗora akwatuna biyu sai ƙaramin kit guda ɗaya suka nufi gidan su Aliya. Mai baron yana gaba maza guda uku suna binsa a baya shi kuma Baban Kasim ɗin ya koma cikin gidan. MAMAN AFRAH 09025576222 https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ems_copy_t *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 9️⃣ *SADIYA* Ta daɗe tana nazarin rayuwa kafin daga bisani ta tashi ta haɗa kayan wanke-wanke ta wanke. Kalifa da ya ƙi kwanciya saboda zafin jikinsa ta ɗauke shi ta goya shi zuwa can ta ji yana mimmiƙewa alamar tana son sauka ga wani ƙananan kuka da yake tana sakko shi ta ga har ya fara kashin kamar ta yi kuka haka ta je ta gyara shi ta dawo dasho ta kwantar ganin ya kwanta ta je ta yi wanka ta fito ta shirya. Sai neman magani take amma babu na zazzaɓi babu na gudawa gashi bata da kuɗin da za ta saya masa maganin hakan ya sa take ta takaicin rashin sana'a domin sana'a makami ce kuma jigo a rayuwa in har kana yi ko yaya za ka fi ƙarfin abubuwa. Nasir tun da ya fito ya turawa Baba wannan kuɗin bayan sun yi waya, gidan Hajiya ya nufa ana sauke shi a mashin ya shiga da sallama. Bayan ya zauna ya gaishe da Hajiya Husna da Hibba suka gaishe da shi, ya amsa suna ta raha abinsu. Hajiya ta kalle shi yana cin abincin ta ce "Gaskiya wannan matar taka an yi makirar mata wallahi, ita kullum bata da aikin sai son ta ɓanɓari kuɗi a jikin ka, ai wallahi an kusa dai yin ta ta ƙare daga ka auri Meenal ka huta yarinya mai hankali da sanin ya kamata kuma ka ga ita ko nawa ka kashe mata baka yi asara ba amma wannan ita ƴar gidan faƙirai ba wani saba kama kuɗi ta yi ba sai shegen munafurci" Ta faɗa tana yatsina fuska. Karaf Husna ta ce "Hajiya ai daga matar nan ta Yaya sai baya wallahi sumi-sumi kamar munafuka ko kaɗan bata da hali" Hibba ta ce "Ai gwara ya auri Meenal ƴar ƙwalisa ta zo gidansa ya huta ita ma ta huta" Hajiya ta ce "Wallahi kuwa abinsu tuwona maina" Sai da ya kurɓi shayinsa ya ce "Ai ni in ban da ƙaddara babu abin da zai saka na auri Sadiya, kuma yanzu ma tun da har ubanta ya nuna zaman auren yake so ta yi to za ta rayu a wahala kuwa" Hajiya ta ce "Ai karka saurara mata, dama mashinshi ne ta rasa ya yaɓa maka da yake kai ne mai tsautsayin" Suna ta faɗin maganganu a kan Sadiyar har ya gama cin abincin yana faɗar ya yi daɗi sosai, Hajiya tana faɗin ai shi ya sa ta ce ake yin abincin da shi yake ci yana murmurewa tun da bakinsa ya saba da cin mai daɗi da mai maiƙo saɓanin Sadiya da dama ta saba da cin tuwo, dubu ashirin ya fiddo ya ba Hajiya dubu goma su kuma kowa dubu biyar sai wata tsohuwar ɗari biyi da Hajiyar ta ce ya bada za a siyowa Kalifan magani, daga haka ya musu sallama ya ce ya tafi kasuwa. Almajiri aka ba ya je maƙota ya siyo maganin rana da maganin kashi na gargajiya Hajiya ta ce su je su kai mata ta haɗa musu da fanadol ta ce su kai a jiƙa a ɗura masa maganin zazzaɓin, bayan ta san maganin yara ya kamata a bashi ba na manya ba. Basu tashi tafiya ba sai da suka gama ɓata lokaci, lokacin da suka zo ƙofar gidan da ƙafa Husna ta tura ƙofar gidan har sai da ƙofar ta bugu da jikin bango da ƙarfi wanda hakan ya falkar da Kalifa daga baccin da yake a tsorace yana kuka, ko ba a faɗa ba ta san mai mata wannan ɗabi'ar don haka kawai sai ta shiga jiran zuwan su don ta san ƙannen mijinta ne. Hibba ta ce "Gafaranmu dai" Ta faɗa a gadarance, amsa musu ta yi domin ta san rainin hankali ne maimakon su yo sallama shi ne suka yi hakan, tana kallonsu ta window tana jijjiga Kalifa suna ƙarewa gidan kallo labule suka bankaɗo suka shigo ɗakih suna wani yatsina suka zauna. Babu wacce ta yi magana cikinsu Sadiya ta ce "Su Husna ne yau a gidan namu" Hibba ta ce "Gidanku ai yana can gidanku sai ko ki ce yau mu ne a gidan yayanmu, kuma zuwa gidan nan ai ya zama farillah saboda gidan ɗan uwanmu ne sannan kuma ki sa a ranki nan ba da jimawa ba za ku zama ku biyu don yayanmu dole a gallo sabuwar amarya irin matan da ake yayi wayyayu" Ta ji ciwon maganar amma sai ta basar ta ce "Gidansa ne kam, to Allah ya kawo ta" Daga haka babu wacce ta tambaye ta ya maia jiki Husna ta dangwarar mata da maganin a tsakar ɗakin ta ce "Saƙo daga Hajiya ta ce gashi nan in dai magani ne da na kashin da na rana har da na zazzaɓi ki jiƙa amma batun wai kike cewa Yaya za a kai shi asibiti bai taso ba" Ɗago idanu ta yi ta kalle su kowacce ta tamke fuska a gadarance amma Sadiya bata ce komai ba sai Husna ta ce "Wato a faɗa miki saƙon uwar tamu amma ki wofintar saboda ba saƙon taki uwar ba ne" Sadiya ta ce "Karki zageni Husna, kuma ai na ji saƙon ta ko kin ga na yi musu" Basu bata amsa ba suka ce uhm a tare suna masu tashi suka fita, tana ji suka fice daga gidan babu wacce ta yi ƙoƙari rufe mata ƙofar gidan!. Ledar ta ɗauka ta duba abubuwan da suke ciki tana jin babu daɗi a zuciyarta tabbas duk macen da bata yi dacen miji ba kuma vata dace da uwar miji ba, sannan dangin miji basa ƙaunarta lallai ba za take jin daɗin zaman gidan aurenta ba. Nasir soyayya suke shi da Meenal kamar su haɗiye juna, sai dai yanayin yadda take zuwar masa da buƙatar kuɗi abin yana damunsa sai dai da ya faɗawa Hajiya sai ta ce wuyarta a yi auren za ta daina wataƙila da yarinta duk da yarinyar tana da tunani da hangen nesa in ji Hajiya. Yau ya kama talata inda Hajiya ta sanar da ƙawarta mahaifiyar Meenal za ta kai musu ziyara. Da yammacin ne Meemal da mahaifiyarta suna zaune a falo suna hirar bikin da ake son saka rana Meenal ta ce "Ni wallahi Momi ba don dai saboda ke ba da babu yadda zan yi in aure wannan Nasir ɗin" Ta faɗa tana jan dogon tsaki, baki Momi ta taɓe ta ce "To ya za a yi tun da ya nuna yana son ki kuma mahaifiyarsa ma ta nuna tana ƙaunar wannan haɗin, ai sai a yi tuwona maina" Ta faɗa tana wata ƴar bazawarar dariya. Ƙwafa Meenal ta yi ta ce "Hummm!. Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ni wallahi ba zan ɗauki raini da cin kashin da suke yi wa wannan Sadiyar ba, tsaf za mu raba raini don wallahi ko ita Hajiyar ba saurara mata zan yi ba bare wannan riƙaƙun ƴanmatan ƙannen nasa duk sai na gasa musu ƙasa a hannu, shi kuma Nasir hummm sai ya zama mijin ta ce" Momi ta dara har da ƴar shewa ta ce "To Meenal idan baki yi wannan abubuwan da kika zayyano ba kenan ma baki cika ƴar halak ba, ai ba baiwa na kai musu ba ki ƙwatawa kanki ƴanci a gidan miji karki yarda da rainin kowane shege" A daidai nan kiran wayar Nasir ya shigo a inda hakan ya yi daidai da tsayawar napep ɗin da ya ɗakko Hajiya a ƙofar gidan su Meenal ɗin. Da sallama ta shigo gidan Momi ta amsa tana mata maraba tare da cewa ta shiga, ita kuma Meenal da sauri ta tashi ta shige bedroom tana kashe murya suka fara magana da Nasiri. Nasir ya ce "My love na matsu mu yi aure ko ma zama tsintsiya maɗauri ɗaya, ke ce taurauwa a gidana ke za kike murza kambunki wancan ta cikin gidan ma karki ba kanki wahala wajen sakata a layin kishiyarki don daga kin zo gidan komai ya dawo hannunki" Ya faɗa yana jin tamkar ya janyo ranar auren nasu da ba a saka ba duk da ana dab da sakawa. Wannan dariyar tata mai ƙaramib sauti wacce take nuni da tana jin kunya ita ta sakar masa tare da cewa "Ni ka sa ina rufe fuska kunya nake ji Allah" Wani daɗi ne ya lulluɓe shi ya ji tamkar ya yi ihun daɗi don yana mugun son mace mai kunya duk da ya san Sadiya tana da kunya da kawaici amma dai shi yanzu hankalinsa yana kan Meenal ɗinsa wacce yake ji ɗaya tamkar goma, wacce kuma yake riritawa kamar ƙwai. Hira suka ci gaba da yi tana ta nuna masa tana jin nauyinsa a inda shi kuma yake ji babu ya shi don yadda Meenal take bashi girma sai yake jin ladabin Sadiya kamar dai ma ba wata biyayya ce take masa ba, sun jima suna hirar daga bisani suka yi sallama ya kashe wayar yana sauke nannuyar ajiyar zuciya a inda a wani ɓangaren na zuciyarsa yana jin daɗi yau har sun yi waya sun gama bata buƙaci wani kuɗi daga gare shi ba, saboda ya lura ita bata san yawan tambayar abu kima yake zubarwa da mace!.Don roƙo yana taka muhimmiyar rawa wajen daƙile mutucin wanda yake roƙon, shi ya sa ma wani ya tambayi manzo S.A.W shin mai zai yi Allah ya so shi sannan mai zai yi mutane ma su so shi. Manzon Allah S.A.W ya cewa mutumin ka guji duniya Allah zai so ka, sannan ka guji abin hannun mutane mutane ma za su so ka, kenan duk wanda kake son abin hannunsa yau da gobe kimarka raguwa take a wajensa. Suna yin sallama ta saki wani gajeran ɓoyayyan tsaki ta ture wayar gefe tare da kwantawa male-male a kan gadon a fili ta ce "Wahalalle kawai, mutum kai baka son ka ɓamɓaru wato ka ji yau ban roƙi kuɗinka ba shi ne gudun kar na roƙa har wani saurin yi min sallama kake, ai zan shigo cikin gidan" Ta faɗa tana janyo wayat ta shiga wtsapp take ta chart ɗinta. A falo cike da fara'a Momi ta tarɓi Hajiya a inda suka gaisa daga nan hirarsu ta ƙawaye ta ɓarke e tsakaninsu, Hajiyar tana faɗin cewa ƴan uwan mahaifin Nasir za su ji dangin mahaifin Meenal su kai kuɗin gaisuwa, saboda daga Baban Nasir har na Meenal basa raye. Suna ta tattaunawa zuwa can sai gashi Meenal ta fito falo tana taku cike da nutsuwa, gaban kujerar da Hajiya take zaune ta je ta tsugunna tana mai sunkuyar da kai ƙasa ta ce "Hajiya ina wuni" ,Hajiya cike da farinciki ta ɗora hannu a kan Meenal tana amsa gaisuwar tare da yaba hankalin Meenal ɗin, tana ganin idan suka samu Meenal a family nasu sun warke. Cike da ladabi ta tashi ta fita, Hajiya ta kalli Momi tana murmushi ta ce "Ƙawata wallahi kin iya haihuwa sannan kin iya tarbiya, haka kawai ya je ya kwaso masa jangwam ai wallahi Nasir da Meenal ya fara aura babu dalilin da zai sa ya auri wata Sadiya kuma wallahi yanzu ma ruwanta ne bai ƙare ba daga zama ya ƙare dole ta fita ta bata waje saboda gidan Nasir na Meenal ne ita kaɗai" Dariya Momi ta yi ta ce "Ai ƴarki ce komai kika yi daidai ne!." Dariya suke suna ci gaba da tattaunawa, a inda Meenal ta dawo ɗauke da ruwa da lemo a faranta sai kofi ta zo ta durƙusa cike da ladabi da zubawa Hajiya ruwan ta tashi ta bar wajen Hajiya tana ta yabawa Meenal ɗin bata san cewa lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi ba. Ta jima a gidan sai la'asar liss sannan ta musu sallama ta fito za ta tafi lokacin Meenal tana ta aikin munfurci ita kuma Hajiya tana yaba mata a nata ganin taimakawa Momi take. Bayan tafiyarta suka zauna suna ta tsara yadda abubuwan za su kasance idan Meenal ta shiga cikin gidan. Hajiya tana fita daga nan gidan da ta tari napep sai gidan Sadiya, Sadiya tana tuƙa tuwo lokacin Kalifa yana wasa saboda ya ɗan ji ƙwarin jikinsa ta jiyo Hajiya tana kwaɗa sallama, amsawa ta yi tana mai tasowa daga bayan ta rufe tukunyar dama ta gama tuƙa tuwon. Tun da ta shigo take yi wa gidan wani kallo na rainin wayo tana wani tattaɓe baki Kalifa kuwa kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai shi kuwa da yake ba wani shaƙuwa ya yi da ita ba wasan sa yake ko wajenta bai nufa ba. Sadiya cike da ladabi ta ce ",Sannu da zuwa Hajiya" Bata amsa ba ta ce "Ke dai Sadiya ki ji tsoron haɗuwarki da Allah"Sadiya tana kallonta tana jiran ƙarin bayani don ita bata ga abin da ta yi da za a mata wannan furucin ba a nata ganin ita ce ya dace da ta jefe su da wannan kalmar. Hajiya bata jira cewar Sadiya ba ta ɗora da faɗin "In banda shegen son kuɗi kike ɗorawa yaro jinya ga yaro nan yana wasa amma har kina ikirarin kai shi asibiti wannan da maraya ne Nasir ba na raye kika aure shi da ya taɓa ya ji gabaɗaya sai kin talautashi a shegen kawo buƙatun naki!" Sadiya kai ta sunkuyar ƙasa ta rasa ma abin da za ta ce mata amma duk da haka sai ta yi ƙarfin cewa "Wallahi bashi da lafiya ai shi Abban nasa ya... Hannun da Hajiya ta ɗaga mata ne ya saka ta haɗiye sauran maganar da ta guntso a bakinta. Hajiyar ta ce "Ai komai ya kusa zuwa ƙarshe zai auro mace mai ladabi da tsoron Allah, mai tattala masa dukiya wacce ta san darajar dangin miji wacce za ta ɗaukeni tamkar ni ce silar zuwanta duniya" Idanu Sadiya ta ɗaga ta kalleta ta haɗiye ɓacin ran da ya ziyarci zuciyarta, don ta ji ba daɗi da ta lissafa abubuwan kenan duk waɗannan abubuwan ita bata da shi, ta ce "Hajiya ki shiga ɗaki mana baki zauna ba kina tsaye" Baki ta taɓe ta ce "Ai tuni aka bani wurin zama a inda aka san darajata, aka bani ruwa ana girmamani ai in sha Allah shekara ba za ta rufa ba sai Meenal ta tare a gidan Nasir!" Tana faɗar hakan bata jira komai ba ta juya ta fice daga gidan ta bar Sadiya tsaye tana maimaita sunan Meenal a zuciyarta ita dai Meenal ɗaya ta sani ƴar gidan ƙawar Hajiyar don ta taɓa zuwa gidan ma ita da su Husna lokacin tana amarya suka zo. Juyawa ta yi ta nufi wajen tukunyar tuwonta, a ranta tana mamakin mutum nawa take aure, Nasir ya ci zarafinta ƴan uwansa ga kuma mahaifiyarsa su basu ma san auren ya fice mata a rai ba don bata da yadda za ta yi ne. *GIDAN BABA* Wajen ƙarfe goma na safe Baba ya fito daga ɗaki yana gyara zaman babbar rigarsa ya janyo ƙofar ɗakinsa ya rufe ya kalli Mama Habiba da take wanki ya washe baki ya ce "To mu fa Allah ya yi aure da marar kwabo za mu tafi na san yau dai ɗari biyar ɗina da nake sayan awarar rana ta huta" Ɗagowa ta yi daga wankin da take tana masa kallon rashin fahimta ta ce "Yau ɗumaman tuwon safen ne ya ƙosarka sosai da gar ba za ka buƙaci abincin rana ba?" Wata dariya ya yi irin ta ba za ki gane ba ne ya ce "Ana ga yaƙi ke kina ga ƙura!. To Baban abokin abokina ne ya rasu kuma gidansu masu mugun kuɗi ne wato uban ya bar tarin dukiya kin san kuwa wajen zaman makokin za a ci jar miya, ni ban ma taɓa ganin wanda Baban nasa ya mutun ba kawai dai labari abokina ya bani cewa jiya sun yi ciye-viye da suka je gaisuwa shi ne na masa Allah annabi ya rakani in yi gaisuwa, kin ga gwara mu tafi tun da wuri da zafi -zafi ake bugun ƙarfe sannan da sanyin safiya ake kama fara" Duk abin da yake faɗa matan gidan da suke cikin ɗaki kowa yana jinsa kasancewar shi ba ya magana a hankali, fitowar Sumy daga ɗaki ne ya dakatar da Mama Habiba daga maganar da take son yi ta ce "Baba don Allah ka bani kuɗi zan saya maganin guduwa kwana na yi ina yi" Kamar wanda ta watsa masa wuta a take ya fitittike yake masifa annurin fuskarsa ya dishe ya ce "Ah uban gudawa kike ba gudawa ba Sumayya, ku babu dama ku ga mutum sai ku ringa jero masa buƙatunku, shin ina uwarki ma take ko ni kaɗai na haife ki? Wallahi shi ya sa kullum nake fatan Allah ya bani ɗa namiji ko kangararre ne duk tsiya ya taimaka mini amma a ce ƴaƴa mata kitika-kitika sun cika mini gida har baba gane su tsakaninsu da iyayensu mata to duk sun girma sun yi kwantai kowa sai dai ya kawo maka buƙatu ba zai taimaka maka ba... Mama Habiba ta ce "Haba dan Allah, yanzu ina amfanin wannan maganganun da kake" Baki sake yake kallon Mama Habiba kafin ya juyo bayansa cike da gatse ya ce "To uwata Habiba ai sai ki min hukuncin duka" Ɗan baya ta ja tana faɗin "Ni ban ce zan dake ka ba amma dai wasu maganganun basu da amfanin faɗa ƴaƴa mata ai rahma ne" Wata harara ya jefa mata ita kuma ta ɗauki ƙaramar jakarta da take ajiye a gefe ta buɗe ta ɗakko naira ɗari ta ba Sumy ta ce ta je ta saya maganin. Juyawa Sumy ta yi tana wani taɓe baki a ɓoye tana aikawa Baba harar ƙasan ido ta koma ɗakin. Malika ce ta fito daga ɗaki sanyi cikin doguwar rigar dakakken leshi mai tsada sai ƙaramin mayafi da ƴar jaka ta yi kyau abinta ganin Baba sai da gabanta ya faɗi don ita da ta jiyo muryarsa lokacin tana shiryawa tunaninta fita ma ya yi dab gidan. Gabanta yana faɗuwa amma sai ta ji ya ce "Ke ina za ki je haka?" Ya faɗa yana kallon shigar jikinta duk da ya san mahaifiyarta bata da kuɗin da za ta saya mata kayan sannan iya ma yarinyar haka amma ba zai tuhume su inda suke samun komai ba shi dai ɗawainiyarsu ce ba zai ɗauka ba in ya suke samu ma wannan ba damuwarsa ba ce Cike da ɗan jin kunya ta ce "Wani Alhaji ne yake jirana a waje" Wani irin washe baki ya yi ya ce "Allah sa ya miki maganar aure" Ɗan shiru ta yi sai kuma ta ce "Eh ya ce aure lokaci ne amma dai da shirin aure ya zo" Baba ya ce "Haka nake so, akwai kati a wayarki? Ina so na yi waya bani da kati" Kai ta gyaɗa masa tana mai cire pswrd ɗin cikin hanzari ta yi saurin fita daga wtsapp ɗin don ta ga tana ma cikin acc ɗin Alhajin inda suka gama hirar banza da ture-turen hotunan banza, tana fitowa ta bashi wayar ya karɓa ya fito da tasho wayar ya kwafi lambobi ya danna kira ya kara a kunne, abokinsa ya kira yana faɗa masa ya shirya shi kuma ya faɗa masa inda za su haɗu su wuce gidan makokin. Wayar ya kashe zai miƙa mata sai ya ga hoton kan wayar hoton ta ne da wani mutumi Babban mutum suna cikin mota a zaune ta ɗora kanta a gefen kafaɗarsa suna dariya, jim kaɗan ya yi yana kallon hoton ita kuma gabanta yana dukan uku-uku sai dai kuma sai ya ga hakan ba komai ba ne tun da ba wani abu ya gani ba sannan ya tuna ta ce zai aure ta don yana tunanin shi ne Alhajin da ta ce yana jiranta a waje. Yana bata wayar ta juya ta fita, Mama Habiba tana jifansa da kallon Allah wadaran naka ya lalace, a ce wai kai baka sayawa yaro sutura ba baka saya masa waya ba amma kana ganinsa da abubuwan da sun fi ƙarfin ya mallake su ba za ka tsawatar ba ko ka tuhume shi a kan abun. Yana baza babbar riga ya juya yana nufar hanyar ƙofar gidan ba tare da ya yi wa sauran matan sallama ba ya ce "To mu sai Allah ya dawo da mu" Mama Habiba ta ce "Allah tsare" Ko amsawa bai yi ba ya nufi ƙofar yana sauri so yake ya cimma Alhajin da Malika ta ce yana jiranta a waje ya je ya masa maganar aurr cewa ya fito za a yi aure. Malika ko da ta fita ta samu Alhajin yana jiranta a mota tana wani yauƙi da rawar kai gaɗe da girgiza jiki domin yanzu ta gane hakan ne yake ɗauke hankalin maza ƴan iska har su kai ga bata kuɗi ta magance matsalarta, Alhajin kuwa wanda ya haife ta ya washe baki haɗe da miƙo hannu ya buɗe mata ƙofa ta shiga yana mata kallon ƙwaf tana magana tana iyayi ya ce "Sai ina?" Kallonsa ta yi cike da masa wani kallo ta ce "Sai inda muka saba zuwa" Haɓa ya sosa yana sakin shu'umin murmushi domin ya gane Hotel za su je, yana ƴar dariya ya ce "Baki da dama Baby Malika" Suna cikin haka ta hango Baba ya taho yana ɗaga babbar riga da sauri ta ce su bar wajen, haka Alhajin ya ja motar Baba sai ƙurar ya tarar a ransa yana faɗin ' Za ka dawo ka same ni wataƙila ya je siya mata cakuleti ne, dole ka fito a yi aure kuwa ka ɗauki ɗawainiyarta' Ya faɗa yana kama hanya domun ya je wajen abokinsa su tafi. Alhaji tun da ya ja motar suka tafi suna hirarsu, Malika tana jin yanzu ta samu sabuwar rayuwa ta huta da zama da yunwa ko kuma ɗauka ɗawainiyar kanta na abubuwan buƙata na rayuwa, tun da yanzu za ta bada mutuncinta a bata kuɗi a kuma mata duk abin da take so, shi kuma Alhajin yana ganin ya samu yarinya ɗanya sharaf tabbas a nasa tunanin ya tsinci damu a kala sai dai yana tuya yana mantawa da albasa wato akwai ranar ƙun dillanci domin duk abin da mutum ya yi wa ƴar wani shi ma sai an yi wa nasa ƴaƴan, shi yana ganin ya killace nasa ƴaƴa ya zo yana lalata da ƴaƴan wasu duk da su ma wanda ake lalatar da su da laifinsu don su suka siyar da mutuncinsu suka zubar da kima da darajarsu na ƴaƴa mata, domin ai sai bango ya tsage ƙadangare yake samun waje shiga!. Baba tun da suka je gidan makokin basu samu ganin abokin abokin nasa ba, kaaancewar yana cikin gidan wajen wasu baƙi da suka zo haka suka samu waje a rumfa suka zauna suna ta hira ana zuwa ana gaisuwa. Har wajen sha biyu sannan suka samu suka ga abokin inda ya nuna jin daɗinsa da karamcin Baba na zuwa yi masa ta'aziyya duk da basu da wata alaƙa, bai san cewa cin banza ne ya kawo Baban ba wai gaisuwar Allah da annabi ba. Har aka kira sallar azahar ba a kawo abinci ba, Baba sai doguwar hamma yake, idanun nan sun kaɗa sun yi jawur don hatta tuwon safe kaɗan ya ce yana tunanin abubuwan daɗin da abokin nasa ya faɗa cewa tun da ya je wajen gaisuwar ake sauke kayan motsa baki. Amma dai shi ban da ruwan roba da ya ga ana ta wadaƙa da shi a wajen bai ga komai ba, tun zuwansu daga an ɗan jima sai a fito da ruwan roba masu sanyi ana rabawa, mai raba ruwan ko da ya zo zuwan farko ya ba su Baba haka Baba ya karɓa ajiye a tunaninsa idan an fara kawo kayan daɗin zai sha ruwan idan ya ci tun fa lokacin babu komai a cikinsa ba ya jin ruwan ma zai samu wuri. Sawu na biyu ma wani ya ƙara miƙo musu Baba ya karɓa ya ajiye suka zama biyu a gabansa, yana jiran tsammani, a rabo na uku mai rabawar ba miƙawa yake ba ajiyewa mutane yake a gaba ai kuwa ya zo ya ajiyewa abokin Baba yana shirin ajiyewa Baba ai kuwa Baba ya yi farat ɗaya ya ce "Haba bawan Allah, ruwan nan kun kawo, kun sake kawowa tsakani da Allah dai ko shanaye ne mu ruwan da aka raba ya isa a ce ya kashe mana ƙishirwa, tun da muka zauna a wajen nan muke karɓar gaisuwa ana Allah jiƙansa muna cewa amin amma ku babu aikin da kuke sai ku shiga cikin gida ku jido ruwa kuna ba mutane, bakwa duba yadda idanun jama'a ya yi zuru-zuru haba ku tsagaita da bada ruwan nan tun da shi kaɗai za ku raba, in ba haka ba ni dai kar ka ƙara tunkaroni da ruwa na gabana ma ya isheni" Tun da Baba ya fara magana abokinsa Malam Lurwanu yake danne dariyarsa gudun kar ya saki dariya a wajen makokin a ce bai damu da mutuwar ba, duk da dai wajen dama gefe ne suke zaune kuma ana ɗan hayaniya ba a lura da abin da yake faruwa ba. Mai raba ruwa cike da mamaki yake kallon Baba, hakan ya sa ya ɗauki ruwansa ya bar wajen, Baba wanda ya kauda kai gefe yana muzurai, babu abin da yake tunowa sai abubuwan da abokinsa ya bashi labari da kuma abin da ya faɗawa Mama Habiba amma gashi dai wankin hula yana son kai shi dare. Ko da aka tashi yin sallar azahar abokinsa yana masa dariyar ƙeta a ɓoye, aka idar da sallar da yake ba masallaci aka je ba a nan wajen aka yi jam'i shi kuma abokin da aka yi wa mutuwar suna can suna ta karɓar gaisuwar jama'a. Ko da aka idar da sallah Baba yake yi wa abokin masifa wai sai sun tafi gida a nan ya ce masa su dakata wataƙila ko an yi jinkirin kawo abincin ne, ana jimawa aka fara kawo abinci da nama kala -kala Baba ya zage ganin banza ta faɗi ya ci abinci musamman naman da ya ci ya yi yawa, lemuka ma sai da ya saka biyar a aljihu fanta, cola, mirinda nutrimilk lacasera. Duk a aljihun babbar riga ya zunduma su daga an miƙo masa lemo sai ya karɓe bakin nan washa-washa da sai wangale shi yake. Sai da ala'sar sakaliya suka yi wa wa wanda suka je dominsa sallama, abokin Baba sai jin Baba ya yi da za su masa sallama yana faɗin "To Allah jiƙansa, Allah sa kwanciya hutu ce sai goben idan Allah ya kaimu da abin aro za mu dawo" Amsa masa aka yi ana musu godiya. Lokacin da Baba ya dawo gida ya nufi ɗakinsa ya ajiye lemukan nan, sai dai ciwon ciki yake damunsa tun a hanya ya fi zaton ko naman da ya ci da yawa ne ya saka masa ciki. Wani murɗawa da cikinsa ya yi sai banɗaki yana can ya fito ya sake komawa zuwansa uku Sumy da take ɗakin Mama ta ji yana zabga mata kira yana faɗin ",Sumayya kawo min maganin gudawar nan da kika siya da safe" *JIDDA* Suna can ita da Salama suna ta hira abinsu, Kasim kuwa tun da ya faɗawa Ummarsa cewa ga yadda Babansa ya ce haka ta bashi baki a kan cewa ya yi haƙuri ya bar maganar don ya san cewa Babansa kaifi ɗaya ne ba zai lamunci wani abu ba bayan wanda ya yanke hukunci a kansa, sannan zai ga kamar ƙarya ce idan aka ce sai an kai a mota. So yake ya sanar da Aliya halin da ake ciki amma kuma yana tsoron abin da zai biyu baya, saboda ya san sai ranta ya ɓaci amma duk da haka ya san ai umarnin mahaifinsa gaba yake da nata, hakan ya sa ya koma ɗaki ya kwanta yana ɗan jin fargaba yana fatan kamar yadda ta yi farincikin kayan saka rana wannan ma ya faranta mata rai fiye da wancan lokacin!. Aliya dai ta gaji da zumuɗi ta ɗaga waya ta kira Kasim, Kasim ganin kiranta sai da gabansa ya faɗi da ƙarfi har kiran ya tsinke bai samu zarafin ɗagawa ba, kiran ya shigo a karo na biyu har ya tsinke bai ɗaga ba, sai faman kallon sunan ta da yake a saman wayar. A karo na uku ya yi ta maza ya ɗaga yana ɗagawa ya tsinci muryarta cikin farin ciki tana faɗin "Hello" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, sai lokacin ya ji hankalinsa ya kwanta wannan alama ce ta nasara wato ranta bai ɓaci ba sanadin kai kaya a baro bayan ya mata alƙwarin kai kaya a mota kamar yadda ta buƙata, kuma da alama kayan ma sun birgeta hakan ya sa cike da ƙarfin gwiwa ya ce "Barka da wannan lokaci amarya kuma sarauniyar zuciyata" A can ɓangaren Aliya ta murmusa lokacin da suke wayar suna saman wani katakonda suka taka ita da Amatallahi a ɗakin Umma suna window suna jiran ganin masu kaya don su ganewa idanunsu. Cike da farinciki ta ce "Na'am sarakin zuciyata" Ji ya yi kamar ya taka rawa don murna. Suna magana Amatulllahi tana musu tsiya wai basa kunyarta a daidai nan ayarin masu kawo kayan Kasim suka yi wa gidan su Aliya tsinke!. A kan idon Aliya mai tura baro mai ɗauke da akwari biyu da ƙaramin kit ya taho inda mutanen suna biye da shi, wani ihu Aliya ta saki wanda ya ɗauki hankalin Amatullahi ta juya ɓangaren da ta ga Aliyar ta kalla a take ta yi arba da abin da Aliya ta gani, Kasim kuwa ihun da Aliya ta yi sai da ya cika masa kunne ya fara tunanin mene ne wannan wanda ya saka ta farinciki lokaci guda kafin ya gama wannan tunanin muryar Aliya ta dawo da shi daga tunanin ta hanyar faɗin "Kayan Jidda a baro aka kawo akwati biyu da kit" Take faɗa tana tuntsurewa da dariya, mamaki al'ajabi da kuma tsoro suka ɗarsarwa Kasim a zuciya mamaki na farko shi ne shin dama abu iri ɗaya suka ti shi da mijin Jidda da yake ganinsa bashi da wani hali sannan kuma shi ma a baro ya aika lefen ko kuwa? Tsoron da ya ziyarce shi kuma yana tunanin shin kenan ita Aliya bata ga nata lefen ba dama, kafin ya samu wannan amsar tambayar da yake yi wa kansa sai ya ji Aliya ta ce "Kasim ina zuwa za mu yi magana an jima akwai gwarama" Kafin ya bata amsa ƙit ya ji ta kashe wayar.Zaman dirshan ya yi a saman katifarsa yana jin wani faɗuwar gaba yana fatan dai kar idan ta ga nata kayan ta ce ta fasa aurensa, tun da dai ya ga gashi nan tana yi wa Jidda dariyar an kawo mata kaya a baro. A ƙofa mai baron ya tsayar da baron inda su kuma masu kawo kayan su Abba suke musu marhabin, a daidai lokacin wannan da Amatullahi da Aliya suka diro daga saman bencin da suka taka suka fito tsakar gida a sukwane suna haɗa baki wajen faɗi "Umma wallahi kayan Jidda a baro aka kawo, kuma akwati biyu da kit" Daga Umma har ƙawayenta guda biyu wata guɗa suka saki a tare sai bayan sun yi suka tuntsure da dariya har da tafawa, kafi suka yi ayari suka shige ɗakin tare da su Aliya, domin su ƙyaƙyata dariya son ransu gudun kar su Abba suke jiyo tsegumin da za su yi. Suna ta dariyar ƙeta inda Umma ta ce wallahi sai ta ga ƙwal uwar daka don sai ta ga baron ma, haka aka riƙe mata ta ɗane katakon har ɗaya ƙawarta tana faɗin da kin yi haƙuri har gida za a shigo da su. Tana hawa ta yi ido huɗu da baro lokacin mai baron yana sakko da akwatunan, dariya har da hawaye garin dariya kaɗan ta faɗo daga saman bencin haka ta diro har tana cewa su Aliya suke sassauta murya kar Abbansu ya san suna gidan tun da kamar rashin kunya ne a kawo maka kaya kana gida. Su Umma a ɗakin suka bar su Aliya suka fito waje suka zauna suna ƙusƙus ransu fari ƙal suna fatan ba abin arziƙi ba ne a akwati biyun don a ganinsu lefen ma kamar na bazawara. Su Umma suna fita su Aliya suka koma saman bencin suka kasa suka tsare a windwon kamar a mafarki kyawawan motocin suka yi wa layin tsincke kowacce tana fitar da ƙyalli na sabunta, a jere suke iya ganinka dole su birgeka daga Amatullahi har Aliya mutuwar tsaye suka yi baki sake domin motocin su tafi da su, sai dai abin da ya sa suka shiga ruɗu shi ne motocin basu tsaya a ko ina ba sai a ƙofar gidan su Aliya, kallon kallo aka shiga yi tsakanin Aliya da ƙawarta, bakin Aliya kamar ƙofar gari ya ƙi rufuwa sam saboda mamaki tana tunani a ranta cewa dama Kasim har yana da abokan da suke da motoci na alfarma haka, amma bata taɓa ganin sun zo da su wajenta ba ko dai abokan nasa ne suka masa hanya ya samo wannan motocin irin wanda take mafarkin samu, ko da sau ɗaya ne tak ta shiga ciki ta yawata, amma kash! Bata da wannan damar, basu tsinke da lamarin ba sai da suka fara ganin mutanen ciki suna fitowa suka ga gabaɗaya babu kalar talauci a cikinsu sai kuma direbobin da suka fito suna buɗe ƙofofin motocin inda guda ɗaya direba ya saka hannu ya fito da wata ɗirkekiyar akwati wacce kai kana gani ka san an kashe maƙudan kuɗi wajen sayan akwatin kaɗai, jikin Aliya karkarwa ya fara saboda farinciki jin ta take tana yawo a cikin gajimare. Yadda ake ta fito da akwatin nan kala-kala ne ya sa ta tabbatar cewa ba iya goshi ta yi ba har da ƙeya!. Da sauri ta diro daga saman bencin ta tsaya a tsakar ɗakin hannunta yana karkarwa ta dokawa Kasim waya, Kasim wansa yake kwance lifet a katifa yana jiran kiran ko ta kwana daga Aliya jin ƙaran wayarsa gabansa ya ninku da faɗuwa amma haka ya daure ganin sunanta ya ɗauki wayar ya danna ya kara a kunne kamar daga sama ya ji muryarta rana faɗin "Na gode Kasim, na gode!. Na gode, wallahi na matuƙae gode ina sonka Kasim zan rayu da kai har ƙarshen rayuwata!" Bata jira ya ce komai ba ta kashe wayar don bata cikin nutsuwar da za ta tsaya ta ji mai zai ce. Lokacin da take wayar nan Amatullahi ta diro daga saman bencin ta yi tsakar gida tana faɗin "Umma wallahi a motoci haɗaɗɗu aka kawo kayan Aliya, kuma akwatunan ni kaina ban iya irga yawansu ba, kamar ma va set ɗaya ba kuma ba biyu ba ni ban ma san nawa ba ne kuma ma su tsada!" Wata wawiyar guɗa Umma ta saki sai da ta yi uku a jere ƙawayenta suna taya ta, inda Aliya da Amatallahi suka haɗu da su Umma aka rungume juna!. Bayan an gama murna su Aliya suka koma ɗaki. Jim kaɗan wasu samari guda biyu suka shigo ɗaya yana riƙe da akwati ɗaya, ɗayan kuma akwati da kit ɗin nan su ne kayan da aka kawo a baro. Bakin Umma a washe ta nuna musu kan ƙaramar tabarma da take shimfiɗe a gefe ta ce su ajiye, suna ajiyewa har rige-rigen tsegumin mene ne a ciki suke. Suna fita aka fara shigo da akwatuna masu kyau wannan karon samarin guda huɗu ne suke shigowa da akwatunan, Umma garin saurin ɗakko manyan tabarmi har zaninta neman faɗuwa yakr duk sun ruɗe don Aliya da take windown da yake tsakar gidan suna leƙowa daga falon Umma har ta fara tunanin ko dai dama Kasim mai kuɗi ne ya rufe ta amma daga ganin kayan abin ya fi gaban wasa an kashe naira. Dozin biyu haka aka jere a gefe Aliya ko zama ta kasa yi da mazaunanta hango irin iyayin da za ta ɗiga take a wajen ƙawayenta. Wayar Jidda ta kira da Jiida ta ɗauka ta ce "Jidda an kawo akwatunan ki guda biyu da ƙaramin kit" Buɗar bakin Jidda sai ta ce "Ubangiji ya sa albarka a auren" Wani uban tsaki Aliya ta ja kafin ta kashe wayar tana kiran Jidda da ƴar wahala!. Atamafa kala takwas leshi kala biyar shadda uku material uku, takalmi da jaka kala biyu sai takalmi marar jaka kala biyar mayafai buyar hijabi huɗu, sai sauran tarkacen kayan shafawa da sarƙoƙi ƙaramar kit kuwa qur'ani ne da sallaya. Su ne kayan da suke cikin akwatunan biyu kayan bacci ma huɗu ne da kuma under wears. Akwatunan kuwa na leshi da ban akwatin atamfofi da ban kaya ne iya ganinka kamar hauka, hatta sarƙar gwal ma kala uku ce a ciki tun su Umma suna ganin kayan da marmari har suka gaji da ɗagawa kawai faɗi suke shikenan Aliya da Umma sunw arke. Aliya kamar wanda taɓi ya same ta gami take za a taɓa ta a ce ta tashi daga nannauyan baccin da take, a nata ganin kawai mafarki ne take yi. Baba kuwa daga zauren gaba suka yi saboda bayan masu kawo kayannsun tafi sai mata suka fara tururuwar zuwa daga maƙota, Umma ta maƙale gwal a cinyarta sai dai a gani a bata don mutane da suka cika gidan wasu ko akwatunan nan masu biyu da kit wato na Aliya wanda suke a mazaunin na Jidda babu wanda yakr ɗagawa kowa kayan akwatunan nan yake gani wanda suka san iyayen Kasim suna mamakin inda Kasim ya tara wannan dukiyar da ya yi wanna kayan kamar an buɗe shago!. Ibrahim ya kasa tsaye ya kasa zaune jira yake ya ji ta bakin Jidda kar ta janye ƙudurin aurensa idan ta san waye shi, hakan ya sa bini-bini sai ya buga mata waya amma sai ya ji bata ce masa komai ba, sai dai ta ce masa har yanzu tana gidan su Salama. Sai da aka yi isha'i Abba ya shigo gidan, lokacin Aliya har ta gaji da gwada tsadaddun abayoyin Jidda na lefe wanda take tunanin nata ne, takalmi da jaka ma har rasa wanne za ta gwada ta yi ga sarƙoƙi fassion abin kawai ba a magana komai ya yi. Jin motsin zuwan Abba hakan ya sa ta gudu ɗaki don dama Amatallahi tuni ta tafi gida tana faɗin sai ta dawo ganin kaya na biyu don ta fi so sai ta zo ta musu ɗai-ɗai za ta gani. Lokacin da Baba ya zo gabaɗaya an ajiye akwatunan a waje ɗaya sai sheƙi suke, ga guda biyu da kit su ma a gefe don ba a ma haɗa su waje guda ba. Bayan ya zauna ya ci abinci Umma tana ta masa surutu kamar za ta ari baki, sai faman faɗin Aliya ta sha kaya take ta yi sai kuma ta ce Jidda ma ba laifi tana yin hakan ne don kar Abba ya ce ta nuna bambanci tsakaninsu. Tana ta faɗa masa abubuwan da suke ciki a daidai nan ne Jidda da Salama suka yi sallama suka shigo bayan an amsa. Abba suka gaisa da shi sai suka shige ɗaki, yau ko fuska Aliya bata tanke musu ba sai ma labarin uban kayan da aka zuba mata a lefe take basu akwatuna 24 Jidda sosai ta ji farincikin jin Aliya ta samu kaya masu yawa, suna cikin haka Umma ta dage ta ƙwalawa Salama kira Salamar da Umma ta tsani ma ta ga ta zo gidan amma yau saboda tana so ta mata kaju kuma ta tura mata haushi. Amsawa Salamar ta yi ta fito ta zo cike da ladabi ta ce "Umma gani" Umma ta ce "Cewa na yi to kya shiga ɗaki ai sai ki zo ki ga kayan ƙawar taki da na ƴar uwarta idan kina ɗagawa ma har Abban naku ya gani shi ma yanzu ya shigo" Abba ya murmusa yana jin daɗin yadda Ummar bata nuna bambanci ba ya ga tana farinciki da abubuwan da kowa ya samu ashe dai ta yarda kowa rabonsa yakw samu, tunaninsa ko za ta ji ƙyashi ashe ma gurguwar fahimta ya mata da ya ƙi bayyana kuɗin da aka kawo. Salama ta durƙusa a gaban akwatunan da Ibrahim ya yi Umma ta yi karaf ta ce "Ke kuwa ai da kin fara da na ƙawar taki" Ta faɗa tana nunawa Salama akwatunan nan guda biyu wanda Kasim ya kawo har da cewa "Ku ne iyayen zuwa islamiya gashi nan har qur'ani da sallaya ya saka a kit ɗin maimakon sarƙoƙi da ake sakawa" Cike da Mamaki Abba yake kallon akwatunan da Umma ta nuna sai lokacin ya tuna ashe fa bai cewa samarin nan su ce ga na Aliya ga na Jidda ba. Zaune ya tashi daga ringishen da yake ya yi gyaran murya ya ce "Wancan akwatunan mai guda biyu su ne lefen Aliya fa" Aliya da take ɗaki a tsaye tana danna waya suna chart da Kasim bata san lokacin da ta saki wayarta ba, Jidda kuma jin furucin Abba gabanta ya buga da mugun ƙarfi tana tunanin to ta yaya hakan zai kasance bayan ta san Ibrahim talaka ne, sannan abin mamakin dai guda ɗaya maganar daga bakin Abba ta fito bare ta ce akwai gyara a ciki. Umma wacce ta saki baki tana kallon Abba ta ce "A'a fa Abban yara, wannan akwati guda biyu da kit su ne na Jidda waɗan nan guda 24 su ne na Aliya" Abba ya murmusa ya ce "Tsakanin ni da ke waye ya fara karɓar kayan?" ,Hankalin ta ne ya fara tashi ta ce "Kai kuwa mene ne na wasa?" Hannu ya sa a aljihu ya ciro wani mukulli ya ajiye a gabansa ya ce "Magabatan Kasim su suka fara zuwa da wancan akwatunan biyi da kit a baro, wannan akwatunan 24 su ne magabatan Ibrahim suka kawo a mota, dama miliyan goma suka kawo kuɗin gaisuwa da saka rana ni ne na ƙi karɓa dakyar na karɓi miliyan uku, to yau kuma kin ga lefen da suka kawo wannan mukullin motar ta ne haɗe suke a lefen motar ita ce a waje tana nan!" Jidda ƙarfen windown ta dafe idanunta suka fara hawaye a inda Aliya ta yanke jiki ta faɗi ji kake yaraf, Umma tsaye ta tashi a kiɗime tana zare idanu... MAMAN AFRAH 09025576222 [10/20, 3:08 AM] Maman boy: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E3Pn5QPLfOVGFdNgMR6ltU?mode=wwc *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 🔟 *JIDDA* Cikin sauri ta saki ƙarfen windown da ta riƙe ta yi kan Aliya da gudu tana kiran sunanta, Umma wacce ta tashi tsaye a kiɗimen jin lefen Jidda da miliyoyin da ta ji ya lissafa amma sai ta wayence tana sakin murmushin yaƙe, sai kuma ta yi ɗaki da sauri tana tambayar abin da ya faru duk da ta san musabbabin abun domin zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi ma'ana ta san cewa furucin Abba ne ya saka Aliya faɗuwa. Salama ma wacce take son fahimtar inda abin ya dosa musamman ma da yake ta san abubuwan da suke faruwa a cikin gidan ita ma bin bayan Umma ta yi, a kusan tare suka ƙarasa da Abba da ya biyo bayanta yana tambaya. Jidda ce cikin kuka ta ce "Ni ban san mene ne ba na ga ta saki wayarta da take dannawa, kuma sai ta yanke jiki ta faɗi" Abba ya ce "Subhanallahi dama bata da lafiya ne?" Jidda ta ce "Lafiya take Abba" Abun ya ɗaure masa kai, Umma kuma kuka ta fashe da shi tana mai ɗaga Aliyar, wanda kukan ya zame mata biyu ga na canjin lefwn bazatan da ya ziyarce ta ga kuma faɗuwar Aliya tana fatan dai abin ya tsaya iya faɗuwa kar wani ciwon ya samu Aliya, ta san a yadda zuciyar Aliya take da riƙe abu da kuma ƙyashin Jidda ta samu wani abu ta san da wuya idan wannan abin bai mata mummunar illah ba. Jidda bil haƙƙi kuka take saboda ganin ƴar uwarta kuma ƙawarta a cikin wani hali domin ko numfashi bata yi ta sandare kamar wata gawa. Gabaɗaya Jidda ta ma manta da cewa an faɗi abin da ya gigita mata tunani na kaya da kuɗin da aka ce Ibrahim ya kawo mata, yanzu damuwar Aliya ce a zuciyarta tana son Aliya da soyayyar Aliya ta tashi sai dai daga baya da Aliyar ta sauya mata shi ne babu yadda za ta yi yanzu ma ji take tamkar ta cire duk wata damuwar Aliyar ta mayar kanta. Abba ganin Umma tana kuka wiwi ya ce "Haba Ummar yara yanzu mene ne abin kukan" Tana riƙe da kan Aliya a cinyarta ta ce "Bata numfashi fa, ya hankalina ba zai tashi ba, ƴar ɗaya tallin tal kamar rai" Ta faɗa tana rushewa da wani kukan. Salama kuwa sai taɓe baki take don ta san zuciyar Umma da ta Aliya ko kaɗan bata da kyau. Abba ganin sun rikita gidan da koke -koke sai yanzu ma tunanin yayfa mata ruwa ya zo masa, da sauri ya ce "Salama maza ɗakki ruwa a kofi" Juyawa ta yi bayan ta amsa da to ta ɗakko ruwan da sauri ta kawo, Abba yana karɓa ya fara yayyafa mata amma Umma cikin kuka cewa take "Ni dai a samo abin hawa mu tafi asibiti" Kafin ya samu zarafin bata amsar sai Aliya ta sauke wata zuciya inda Umma ta shiga rarraba ido tana kiran sunanta amma idanun Aliya a rufe, Jidda ma sunanta take kira inda Umma ta faki idanun Abba ta aikawa Jidda wata muguwae harara don ta san ita ce ummul aba,isin faruwar komai ji take kamar ta samu filo ta dannawa Jidda har sai ta daina numfashi!. Abba ganin tanyi ajiyar zuciya kuma tana motsi ya ce "Alhamdulillahi ta farfaɗo, ni ban san mene ne ya sanya ta yanke jiki ba" Ya faɗa yana riƙe da kofin Salama a zuciyarta ta ce 'Mene ne kuwa zai sa ta yanke jiki in ba baƙinciki kyashi da kuma hassada ba' A fili kuma ta ce "Wataƙila ko dama bata da lafiya ne" Jidda kuwa har lokacin kallon Aliya take da tausayawa, Aliya wacce idanunta yake a rufe ta fara magana don har lokacin bata ma san insa take ba ta ce "Wallahi akwatunan masu ashirin da huɗu haɗe da mota su ne lefena" Baki Abba ya buɗe da mamaki inda Salama a zuciyarta ta ce "Humm! Ai dama zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, sai dai ki yi gawa kuwa wallahi don akwati biyu da kit ne naki sai dai in baron da aka kawo kayan za a koma a karɓo ta zama motarki, am a mota ai sai Jidda' Umma kuma gudun kar Abba ya fara zarginsu sai ta yi saurin kai hannu tana rufewa Aliya baki tana cewa ."Yi shiru Aliya, na san bakya cikin hayyacinki dama an ce idan mutum ya mutu yana tashi ne a ƙiyama da abin da ya mutu yana aikatawa, to ina ga suma ma idan mutum ya yi to yana farfaɗowa ne da ambaton abin da ya suma ana ambato wato lokacin da ta suma ana maganar akwatuna ne shi ya sa ta farfaɗo da maganar akwatin. Abba sai ya ji ya gamsu da maganar da Umma ta yi tana share hawaye, dama shi bai zargi komai ba tun da iya sanin sa bai san da wata maƙarƙashiya a ƙasa ba. Umma kamo hannayen ta ta yi tana kiran sunanta idanu ta buɗe warai tana kallon kowa, a take ta fara zubar da ruwan hawaye daga idanunta wanda ba hawayen komai ba ne sai hassada da baƙin cikin abin da aka yi wa Jidda, a take ta ji ta tsani Kasim domin ya yi mata abin da ya tozarta ta ya zubar mata da kima, bayan tana ganin mutanen unguwa da ƴan uwa duk sun gama ganin kyawawan akwatuna da manyan lesuna a matsayin kayanta yanzu kuma a ce akwati biyu da kit mai sallaya shi ne nata kayan da gabaɗaya idan za a haɗa ba za su kai yawan kayan da suke cikin akwati ɗaya na kayan Jidda ba!. Muryar Abba ce ta katse ta da ya ce "Sannu Aliya mene ne yale damunki?" Aliya cike da kukan baƙinciki wanda take rerashi a zuci wanda ya fi na fili ciwo ta ce "Abba ni ma ban sani ba, kawai dai na ji cikina ya murɗa mini sai kuma ban ƙara sanin inda nake ba, amma yanzu ba na jin komai" Abba ya ce "Ah Alhamdulillahi to, bari na shiga na watsa ruwa" Ya faɗa yana juyawa ya fice. Yana fita Salama ta ce "Sannu Aliya Allah baki lafiya" Banza Aliya ta mata don yanzu a halin da ake ciki duk wani abu da ya shafi Jidda ta tsane shi tsana ta har abada kuwa!. Jidda tana share hawaye ta ce "Sannu Aliya" Tamkar ta watsa mata ruwan dalma haka ta ji a kunnuwanta, bata taɓa jin tsanar Jidda da ƙyashin alkairin da ya same ta ba sai yau, wani baƙi ta ga ta ƙara yi gashi kanta ya kulle tana son yin nazarin cewa kenan dai Ibrahim ɗin nan matsayinsa na farko wanda ta fara ganinsa a matakin a ranar farkon da suka haɗu shi ne dai matsayinsa, kenan basaja da ɓadda kama ya yi ko mai yanzu take jin da na sanin wulaƙanta shi a ranar da ya zo unguwarsu ta watsa masa ƙasa a ido, da yanzu ita ce da duka waɗannan abubuwan da Jidda ta mallaka tana jin dama bata riƙe wulaƙanta mutane a matsayin wata turba ba, kenan dai wasu mutanen suna cikin rigar tsiya ne yayin da kuma su masu arziƙi ne, a zuciya ta furta 'Na tsane ki Jidda kin hau matsayin da nake so na taka!" A fili kuma sai ta mayar da idanunta ta rufe saboda ganin Jidda baƙanta mata rai yake ƙara yi. Salama kuwa juyawa ta yi ta koma kan tabarmar tsakar gida. Umma tana hararar Jidda kamar idanunta za su faɗo ta ce "Baƙar munafuka, wato mu za ku haɗu ku rufa ke da wannan soloɓiyon, ashe dai shi kura ne lulluɓe da fatar akuya, har mu za ku yi wa bazata ni za ki kunyatw a idon duniya Jidda? Ni za ki sincewa zani a kasuwa, in rufa miki asiri in riƙe ki tun kina ƙanƙanuwarki amma yau za ki kunyata ni a idanun jama'a kenan yanzu dole in ke cewa akwatuna ashirin da huɗu naki ne?" Gabaɗaya idanun Jidda ya cike da hawaye da sauri ta sunkuyar da kanta don bata son irin kallon ƙiyayyar da Umma take jifanta da shi. Bata samu bakin magana ba ita yanzu tunanin da take ma ta matsu ta yi waya da Ibrahim ta ji ya aka yi aka haihu a rageya. Kiran da Salama ta ƙwala mata shi ya sa ta tashi ta fita daga ɗakin, da take jin ta tamkar a kan ƙaya. Fitowar Abba daga ɗakinsa bayan ya yi saka jallabiya shi ya dakatar da Umma da Aliya da suke kukan takaici marar sauti, ta hanyar kiran da ya ƙwalawa Umma. Sumi-sumi Umma ta fito daga ɗakin tana ta fatan Allah ya taimake ta kar kuka ya ƙwace mata ta fi so ta ci gaba da yaudarae Abba yadda ba zai taɓa gane ko ya fahimci mugun hali da mugun nufin da take da shi a kan Jidda ba. Tana zuwa ta zauna a kan tabarmar kamar wata zautacciya sai baki take washewa don kar a gano jirginta, Jidda da Salama da suke tsaye daga can gefe suna magana Abba ya ce "Salama zo ki buɗe min kayan na gani mana" Da to ta amsa ta taho tana raya yadda za ta turawa Umma haushi, Jidda kuma ɗaki ta nufa tana shiga Aliya ta ja wani uban tsakin da ya sa Jiddar kallonta babu shiri, dama ta san a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Aliya wacce ganin screen ɗin wayarta ya yi raga-raga sanadin faɗuwar da ya yi ranta ya ɓaci tana tunanin wannan matsiyacin da ya kawo akwati biyu ina ma zai iya sauya mata sabuwar waya, duk da shi ya kawo mata wannan ɗin. Jidda kuma sai ta koma gefen katifarta ta zauna tana ɗaukan keypad ɗinta ta fara latsawa ganin miss call ɗin Ibrahim babu adadai ta ji duk ranta ya ɓaci domin ita yanzu tuhumarsa ma take a zuciyarta shin waye shi, kenan ba shi ne asalin Ibrahim ɗinta ba ne da take so da ƙauna mene ne manufarsa na ɓoye kansa mai ya sa bai bayyana mata waye shi ba tun asalin shin anya yana da gaskiya ma. Aliya harara take ta aikwa Jidda da take danna waya, tana tunanin da a ce bata wulaƙanta Ibrahim ba da yanzu ita ce a wannan yanayin. Amma yanzu ta yi wa arziƙi dundu da gwiwar hannu ma ba wai da hannun ba. A tsakar gida kuwa Salama sai ɗaga lesuna take suna ta walwalin tsada Umma ji take tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu zai fi mata sauƙi a kan cewa lefen Jidda ne take gani wanda babu haɗinsa da na tilon ƴarta Aliya. Cike da ƙarfin hali ta ce "Kai ga wani leshi mai shefen kyau ai kayan nan babu na banza" Abba yana dariya ya ce "Wallahi sun yi kaya kam shi ma mijin Aliya ai ya yi ƙoƙari a iya ƙarfinsa" A zuciyar Umma ta ce 'Indai akwati biyu da kit ne ƙoƙari Allah tsine ƙoƙari' A fili kuma sai ta ce "Ai sun yi ƙoƙari matuƙa Allah sa abokan arziƙi ne" Abba da Salama suka amsa da amin duk da Salama ta san addu'ar Umma iya fatar baki ne, haka Salama ta yi ta ɗaga kayan har suka ƙare kaf babu wanda bata ɗaga ba, kafin ta janye su gefe ta janyo akwatunan Aliya ta buɗe tana ɗagawa Umma ji take tamkar ta ce ta daina ɗagawa saboda haushin da take ji na Jidda kuwa ji take da za ta samu dama da ta babbaka musu ashana sun ƙone ƙurmus har akwatunan. Musamman a na Aliya da aka zo wajen kit ɗin nan aka fito da qur,ani da sallaya ta ji haushin Kasim kamar mai. Umma gani take Salama da gayya take wani jujjuya atamfofin da basu da maraba da ƙanana. Bayan sun gama ta yi musu sallama ta ce za ta tafi haja suka fita da Jidda za ta taka mata zuwa waje. Suna fita Salama ta sassauta murya ta yi ƴar guɗa yadda iya ita da Jidda ne za su ji ta ce "Kai Allah abin godiya Allah ka ci gaba da ɗaukaka ƙawata aminiyata, yanzu dai na san jikin ta ƙaura ya yi la,asar tun yanzu an fara gane shayi ruwa ne, domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa!". Ta faɗa tana wani rawar kai Jidda wacce gabaɗaya damuwar da take ciki ta bayyana kanta ta dubi Salama cikin sanyjn murya ta ce "Na lura ke farinciki kike, baki hango damuwar da zan shiga ba Salama, ni ba ma wannan ba Ibrahim ina ya samu kuɗi da ya yi wannan sayayyar sannan har ma da na kayan saka ranar da Abba bai bayyana ba?" Ta faɗa tana jingina da bangon gidan nasu da suke tsaye a kusa da shi tare da harɗe gabaɗaya hannayenta a ƙirji. Salama ta kalleta ta ce "Tabbas ina yi masa kyakkyawan zato, na san ba sata ya yi ba kuma tabbas yana da tasa hujjar da ya yi hakan kuma dole ki karɓe shi da hannu biyu, sannan kuma ni murna yanzu na fara don da akwai ruwa a kusa da sai na zuba a ƙasa zan sha Jidda, duk iya ƙoƙarin mutanen nan na son ganinki a tsakiyar rana sai gashi Allah ya kai ki inuwa, a i uwar ma ya lulluɓe ki da bargon rahma" Shiru Jidda ta yi tana tuno irin kallon tsanar da Umma take jifanta da shi hatta yanayin kallon Aliya ya tsaye mata a rai, ita basu san ba bata da burin auren kyakkyawan miji bare kuma kuɗi wannan ba ya daga cikin burikanta, Ibrahim ma saboda karamcinsa ya sanya ta amince da shi bayan kasancewarsa kyakkyawa. A kasalance ta ce "Salama zan dakatar da Ibrahim domin na fasa aurensa!" Kallon mamaki Salama ta jefa mata, Jidda ta ɗauke idanunta daga kallon Salama tana kallon gefe guda tana tuno irin ƙaunar da take yi wa Ibrahim amma kuma ya zama dole ta haƙura da shi hakan ya sa ta ce "Baki hangi abin da nake hanga ba Salama, baki san su waye Umma ba duk abin da nake baki labari kaɗan za ki fahimta da abubuwan da idanuna suke gani, zan jure rasa shi a rayuwata a kan na rayu a kan wani giɓi na tsantsar ƙiyayyar waɗanda su ne kaɗai nake kallo a matsayin dangi kuma ƴan uwa!" Idanun Salama suka tara ruwa ta ciro hannayen Jidda daga ƙirjin Jiddar ta haɗe hannayensu a waje guda duk da akwai wayar Jidda a hannun nata suna kallon juna Salama ta ce "Jidda!!!" Amsawa Jiddar ta yi tana kallon Salama kamar yadsa take kallonta ita ma Salama ta ce "Ina so ki sani abin da Allah ya rubuta ya daɗe da rubutawa, sannan Ibrahim bashi da mugun nufi a kanki don haka kar ki zarge shi ina so ki bashi dama, ya furta miki dalilansa a kan abin da ya yi, na sani ni shaida ce kina son sa kuma ban taɓa ganin kin so wani ɗa namini ba sama da Ibrahim idan kika ce za ki fasa aurensa tabbas zai cutu kuma ke ma za ki cutar da taki zuciyar. Abu na gaba ko ki aure mai kuɗi ko ki auri wanda ya fi mijin da Aliya za ta aura to fa ki sani ba za ta sauya zani ba, babu wani abu da zai sauya a lamarinsu ita kyakkyawar manufa saga zuciya take, duk abin da aka ce miki zuciyar mutum bata da kyau to har abada ba za a iya masa ba, ko da duniya za ka mallaka masa ke ko da za ka ciro zuciyarka ka damƙa masa a hannunsa" Sai da ta numfasa ta ɗora da faɗin "Idan zuciya ta gyara to dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta ɓaci dukkan jiki ya ɓaci, su Umma ci gabanki ne basa so don haka shi kuma ubangijin da ya fi kowa sonki yana son ki huta shi ya sa ya baki mijin da za ki aura nagartacce kuma kamili don haka kawai ki fawwalawa ubangiji lamuranki, ki dage da addu,a kamar yadda na sanki tabbas babu wani abu da zaj yi tasiri sai dai alkairi" Tana zuwa nan a maganarta ta damƙe hannun Jiddar da ƙarfi, su duka idanunsu sun cika da hawaye. Bayanin da Salama ta mata ya sa ta ɗan ji wani ƙwarin gwiwa, shi ya sa take alfahri da ita kasancewarta ƙawar arziƙi a gare ta, duk ƙawar da za ta baka shawarar mai kyau ita ce ƙawa ta har abada, don haka yanzu ta ji tana da ɗamarar jin ta bakin Ibrahim in har bata samu akasin wani abu ba to za ta duba lamarin aurensa kuma ta shirya fuskantar duk wani ƙalubale da za ta tsinci kanta a sanadinsa, aon ta san muddin ta aure shi to bayan dara akwai wata caca!. Sun daɗe suna magana Salama tana kwantar mata da hankali, kafin daga bisani suka yi sallama Salama ta kama hanya. Jidda kuea ganin Salama ta tafi sai ta ɗan tsaya tana nazarin maganganun tana kuma son kamo bakin zaren, kamar daga sama ta ga wata mota ta shigo layinsu a 360 yanayin yadda aka shigo da motar tuƙin ya yi kama da na ganganci ko dai babu lafiya. Ta gabanta motar da ta zo a guje ta sassauta gudun tana zuwa da ta gifta ta kaɗan sai ta tsaya, Jidda gabaɗaya ta tsorata ma ta fara tunanin ko dai mamallakin motar yana shaye-shaye kar ya je ya fito ya cutar da ita hakan ya sa ta fara ƙoƙarin shiga gida. Ibrahim wanda ya hango Jidda tana shirin shiga gidan ya fito daga motar a sukwane, Jidda tana shirin shiga gidan sai ta ji muryarsa mai sanyi yana kiranta, gabanta ne ya harba da ƙarfi ta juyo cikin sauri da jajayen idanunta tana son ganin gaskiyar abin da kunnuwanta suka jiye mata, tana juyowa ta yi arba da shi gabaɗaya bashi da nutsuwa ta ga ko marfin motar bai rufe ba, daga gefen inda motar lefenta take ajiye, yana zuwa gabanta sai kawai ta ga ya zube a kan gwiwoyinsa, hawayen da ta gani kwance a saman fuskarsa sannan hannuwansa biyu a haɗe alamar roƙo, ba ya ma kunyar mutanen da suke wucewa jefi-jefi su ganshi durƙushe a gaban mace. Wani iri ta ji zuciyarta, gabaɗaya sai ta ji hankalinta ya tashi kafin ta samu damar furta wasu kalmomi ya buɗe baki cikin dashshshiyar muryarsa ya ce "Jidda, don Allah da manzonsa karki gujeni Jidda, ke kaɗai ce farincikin ruhina wallahi ina ƙaunarki fisabililillahi, ki sani ban yi komai ba sai don gudun ki suɓuce mini" Tun da ya fara maganar tamkar an ƙara gudun hawayensa kuka yake haiƙan abin da ya ƙara saka jikinta ya yi sanyi. Jin bata ce komai ba ya ɗora da faɗin "Tun ranar da na fara ganinki kyakkyawar alaƙar ki da direbana da ya watsa miki ruwa shi ne abin da ya kwaɗaitar da zuciyata ta wuni da ke a ranar, tun daga wannan lokaci ta hanani sukuni Jidda koyaushe ki take ambato!. Na bibiyeki ban samu ganinki ba har dai Allah ya sa a watarana na ganki ke da ƙawarki Salama a inda kuka tsaya kuna tattaunawa a jikin motar da nake ciki, a cikin kalamanki Jidda na samu abin da kike so da wanda bakya so wato kyakkyawan namiji kuma mai kuɗin, wannan furucin ya sa na fara sauya taku ba don na yaudareki ba don yaudara bata cikin tsarina, sai dai kyaun da nake da shi bai ɓuya ba kuma sai Allah ya sa baki gujeni ba, Jidda ki min hukuncin komai amma karki rabo da ni, rabuwarki da ni zai jefani cikin damuwa kuma kin san da hakan, don Allah ba don no ba ki tausayawa wanda ya ƙaunace ki domin Allah" Kallonsa kawai take yadda yake rarraba hannuwa yana roƙonta gashi kalamansa masu kashe jiki domin kalamai ne da wanda ake yi wa su zuciyarsa za ta raunatu!. Jin bata ce komai ba ya ce "Idan har za ki yarda ki rayu da ni na yarda zan rabu da duk wani abu da na mallaka wani yake alaƙa da dukiya, in har hakan zai saka ki farinciki Jidda!." Yanayin yadda yake mata magiya sai ta ji duk tausayinsa ya kamata, a kanta ita Jidda har zai iya sadaukar da komai nasa lallai ƙaunar da yake mata ba ƙarama ba ce. Zuciyarta ce ta mata jagora wajen tsugunnawa a gabansa sai dai ita bata saka gwiyoyinta a ƙasa ba. Tamkar an masa albishir da kujerar makka haka ya ji tun da ganinta tsugunne ya tunatar da shi cewa ba za ta rabu da shi ba amma ganin da yana ta kiranta a waya bata ɗauka ba sai zuciyarsa take ta masa zulumin cewa za ta rabu da shi. Idanunsa jajaye ya kafe ta da su yana duba nata idanun inda ya ga alamun ta sha kuka duk da ya san kukan ba ya rasa nasaba da gano waye shi amma sai ya ji tausayinta ya kama shi shi ji yake da yana da iko Jidda ba za ta taɓa shiga ƙunci ba a rayuwa ya gwammace duk wata damuwarta ya haɗa da tasa damuwar ya saka a zuciyarsa ita ta rayu cikin salama. Cikin sanyin murya ta ce "Na gamsu da jawabinka kuma ko a mafarki ban taɓa tunanin za ka taɓa cutar da ni ba, ina so ka sani ni Jidda ina sonka, kuma zan rayu da kai daɗi ko wuya ina tare da kai, sai dai inaso na ci gaba da kasancewa cikin addu'o,inka kamar yadda kake min a kullum!" Tana gama faɗar hakan bata jira cewarsa ba ta miƙe tsaye kafin ta dawo daga mamakin da ta shayar da shi wuff ya ga ta shige cikin gida. Tamkar an saka masa daskararriyar ƙanƙara a saitin zuciyarsa haka ya ji, wani sanyi ya baibaye ta haɗe da wani farinciki marar misali a take ya tafi ƙasa ya kai goshinsa ya yi sujada yana miƙa godiyarsa ga mahaliccin da bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, don ya san shi ne ya bashi komai kuma shi yake masa komai. Yana ɗagowa daga sujadar ya tashi ransa fari ƙal ya koma ya shiga mota ya tada ya bar unguwar cikin tuƙi na hankali ba kamar yadda ya zo a kiɗime ba. Ko da ta shiga gida Abba har ya shige ɗaki sallamar da ta yi ma Umma bata amsa ba sannan akwatunan babu ko ɗaya a tsakar gidan da alama suna ɗakin Abba. Aliya tun bayan fitar Jidda wayarta ta shiga neman ɗauki wanda ba kowa ba ne sai Kasim wanda ta wa laƙabi da sabon suna wato faƙiri ɗan anace. Ya daɗe yana kiranta kafin ta ɗauka a kufule ta farfaɗa masa maganganu mararsa daɗi wanda suka sosa masa zuciya a ƙarshe ta ce ya aiko a kwashe wannan akwatunan bata so kuma kar ya ƙara tunkarar ƙofar gidansu. Hankalinsa ya tashi amma ya san ɓacin rai ne yana fatan zuciyarta ta sasauto. Haka suka kwana suƙuƙu, don Jidda ta lura Aliya bata runtsa ba a ranar sai tunane tunane sai dai bacci ɓarawo, don ko da ta tashi sallar dare ma Aliya idonta biyu ko alamar bacci amma kuma ba za ta yi nafila na yi addu'a ba tana dai kwance kamar an soya idanunta amma zuciyarta tsanar Jidda ce fal kuma ta ci alwashin warware duk wani abu wanda zai kawo mata damuwa a zamantakewarta wanda Jidda za ta samu ita bata samu ba, don ta ci alwashin ko mene ne Jidda ta mallaka a rayuwa sai ta dawo da shi gareta ko mene kuwa ta ƙudurta hakan a rai da zuciyarta. Yadda Umma ta ga rana haka ta ga dare bata runtsa ba, zuciyarta kamar ta buga. Washe gari da wuri Abba ya tafi kasuwa, don haka Umma da Aliya suna ɗakin Aliya suna ta shirya yadda abubuwa za au kasance ba tare sa sun kunyata ba. Aliya ta ce "Umma tun jiya da wani zazzaɓi ya rufe ni har yanzu bai sauka ba, ni fa akwatunan nan na gama yin status ɗinsu haka ma ƙawayena hatta grp ɗinmu na makaranta da muke ciki da wanda muka yi karatu na tura musu hoton da kuma hoton akwati biyu da kit ina cewa na Jidda ne yanzu kuma ido ya juye da mujiya?" Umma ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya tana tuno yadda ta yi ta alfahri a idanun mutanen unguwa jiya da kuma ƴan uwa a kan lefen yanzu ya zan ce da mutane wallahi dariya za a yi mana" Aliya ta ce "Ni tunanina ma gidan da za a kai Jidda da kuma inda za a kaini ai juma,ar da za ta yi kyau saga laraba ake ganeta wallahi Kasim ya cuceni!" Umma ta yi shiru tana nazari ta ce.. "Na samo mafita, tun da Abbanku ne kaɗai ya san maganar akwatunan ba naki ba ne, shi kuma ba mazaunin gidan ba ne, ita kuma Jidda ko a gabanta aka ce naki ne ba za ta ce komai ba, kawai yanzu a barshi a mazaunin duk wanda ya zo ganin kaya akwati ashirin da huɗu da mota naki ne, akwati biyu da kit na Jidda" Wani daɗi ya ziyarci Aliya jin an rufe mata wani asirin, sai kuma ta ce "Umma idan kuma aka kaimu gidajenmu fa ai ƙawaye da mutane ba mahaukata ba ne da za su yarda cewa wanda ya yi akwatuna da mota zai kai ni gidan matsiyatan da Kasim zai kaini" Umma ta ce "Dole zan zage dantse a komai Aliya, ba zai iyu ƴar karo ta fi ƴar gida, wato mummuna ta fi kyakkyawa samun gidan hutu da arziƙi" MAMAN AFRAH 09025576222 [10/22, 4:33 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DNhoKsIb9qP8PlVQdpQ4BW?mode=ems_copy_c *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️⃣1️⃣ *ZALIKA* Rayuwar gidansu ta ci gaba da kasancewa a ƙunci sanadin takurewar da mahaifinsu yake musu, rashin walwala da kuma damuwa da al'amuransu sakin fuska ko yin hira da su matsayinsa na mahaifinsu. Gashi hatta mahaifiyarsu ba a bakin komai take a wajensa ba hasali ma tana jin tsoronsa ne. Ya zame musu tamkar kumurcin zaki a cikin gida, kowa tsoronsa yake duk abin da suke idan ya shigo gidan kowa taitayinsa yake shiga. Duk yadda take ta ƙoƙarin fahimtar da shi a kullum ba ya fahimta yana mata ganin tamkar bata san ma abin da take yi ba ne, shi dai ɗabi'a da al'adarsa ce babu ruwansa da ƴaƴansa suke ciki babu fahimta ko ja a jiki ko kima jin ƙai a tsakaninsa da iyalinsa, abu ɗaya ya sani kuma yake la'akari da shi, shi ne tarbiya ta uwa ce, uwa ita aka sani da tarbiyantar da yara amma uba shi kawai buƙatun yaran su ne abin da zai yi sauran kuma ita ta ji da sauran lamuransu. A kwana a tashi rayuwa tana tafiya al'amura suna sauyawa abubuwa suna taɓarɓarewa. Tun da suka shiga makarantar gaba da secondry ta fara ganin sauye-sauye amma ba na komai ba sai na sun daina faɗar damuwarsu game da mahaifinsu wato sun daina mata ƙorafi a kan ƙin basu lokacinsa sai dai ta fara nazari da tunani sai dai bata samu komai a kan lamarin ba. Ta fara ayyana ko dai sabo da lamarin mahaifin nasu, tana tunanin ko abin ya zame musu jiki ne ta yadda suka daina damuwa ko kuma yaya ne ita dai bata sani ba, don haka ko da ta zaunar da su a kan ta ji daga bakinsu sai kowanne ya nuna mata babu komai, duk da bata gamsu da hakan ba. Abun da ya sake ɓullowa dangane da yaran nata shi ne, yanzu ba sa dawowa gida da wuri duk da ba tare suke ba amma kowa dai yanayin zamansa a gida ya sauya, idan ta yi wa kowane daga cikinsu magana sai ya kare kansa da cewa yana school ko dai ya ƙirƙiri wani abu da ba zai gamsar da ita ba, ta yi faɗan ta yi nasihar amma bata sauya zani ba. Abin ya fara ci mata tuwo a ƙwarya ya fara tsamarin da take son tuntuɓar mahaifinsu a kan abin da ya shafi ƴaƴan amma tana tsoron mai zai biyo baya, tsawon wata biyu tana fama da hakan shi kuma ba mai zaman gidan ba ne idan ma ya dawo gidan ko bai gansu ba babu abin da ya shafe shi ba zia tambaya ba ma. Yau ta kama talata, a yau ne kuma ta yi ƙarfin halin yanke hukuncin tunkararsa ko da zai bata wata mafita tun da tunaninta ba zai zama ɗaya da nashi ba, duk da ta wannan ɓangaren yana so ya bata shugabancin!. Tun da ta fito falon yana zaune yana karatun jarida, da ta yi sallama ma bai ɗago ya kalleta ba ya dai amsa amma a ciki-ciki. Daga gefensa ta zauna ta juya ta kafe shi da ido sai ta ga babu annuri ko walwala a fuskarsa. Idanu ta mayar kan dining da ƴar aiki take ta aikin jera abincin yanzu lokaci na tsakanin magriba da isha'i amma daga Zalika har Mubin babu wanda ya dawo kuma yau shi ne karo na farko da suka kai ya haka basu dawo gidan ba, shi ya sa ta rasa sukuni da natsuwar zuciya ta zo domin tattaunawa da mai gidan nata, duk da ta san da wuya ya bata haɗin kai. Idanu ta ɗauke daga kan dining ɗin ta mayar kansa tana mai sauke ajiyar zuciya, kamar mai tsoron furta kalmomin bakinta ta yi ta maza dai ta ce "Barka da hutawa" Bai amsa ba kuma bai daina abin da yake ba. Ita dai burinta su samu mafita a kan canjin da rayuwar ƴaƴansu ta yi, ko da a ce bai yi komai ba shi a matsayinsa na namiji idan ya tsawatar wataƙila su daina. Duk da banza ya yi da ita kuma ta ji haushi duk da ba wannan ne karo na farko ba, amma ta danne ta ce "Ya gajiyar kasuwa?" A taƙaice ya ce "Lafiya" Ta ɗan nisa ta ce "Wallahi dama ina tafe da magana ne mai muhimmanci, a kan maganar yaran nan wallahi al'amarinsu ya fara bani tsoro ta yaya za a ce... Wata tsawa da ya daka sai da ta tsorata!. Ya yi wurgi da jaridar hannunsa yana mai ɗaga mata hannu ya ce "Ya ishe ki haka, ta yaya duk inda kika ga na samu nutsuwa sai kin rusa shi? Na tafi kasuwa nema na dawo amma ba za a barni na huta ba sai a zo a sakani a gaba da matsalolin gida, mai kuka nema kuka rasa a gidan nan, komai akwai babu ta inda na tauyeku Allah ya min arziƙi na rufin asiri kuma ina muku komai, amma saboda son zuciya a ce hatta matsalolin ƴaƴa ma tare za mu raba? Ke ba za ki ji da tarbiyarsu ba?" Tun da ya fara maganar zuciyarta take ƙuna. Kafin ta ce wani abu ya cigaba da kora mata warning yana cewa "Kamar yadda na faɗa miki a baya, duk wata matsala da za ya kunno kai ke za ki magance ta, tarbiya ta mace ce shi uba abinci da sauran ɗawainiya yake yi don haka idan har kika ci gaba da damuna da lamuran gidan nan walllahi wallahi wallahi kin ji na yi rantsuwa kuma ba zan yi kaffara ba to igiyar aurenki tana rawa" Idanunta sun kawo ƙwallah amma ta rasa ma mai za ta furta masa ya gane cewa ba ƙaramar matsala ba ce yake mayar da ita ƙarama. Yana gama faɗar hakan ya tashi a fusace ya nufi dining da ido ta bi bayansa da kallo, yana zuwa ya yi saving kansa ya ci ya tashi, ya fita masallacin isha'i don har lokacin yaran babu wanda ya dawo. Lokacin da aka fito daga masallaci ya dawo gidan, yana zuwa ya zauna a falon ita kuwa har lokacin tana wajen a zaune kamar an dasa ta dama tana hutun sallah amma kuma abinci ma bata da nutsuwar cinsa, hankalinta yana wajen inda yaranta suke musamman Zalika wacce ta kasance mace!. Yana zama ya fito da waya yana ta magana tana raha, tsaye ta miƙe tana son barin falon sai kawai aka buɗe ƙofa aka shigo, ganin Zalika riƙe da jaka da sauri ta nufe ta tana kiran sunanta, amma sai ta ga Zalikar hankalinta kwance ta amsa da faɗin "Na'am Mamy" Hankali tashe Mamyn ta ce "Daga ina kike Zalika, mai ya zaunar da ke a makaranta har zuwa wannan lokacin?" Ta jero mata tambayar zuciyarta cike da fargabar amsar da Zalika za ta bata tana riƙe da kafaɗar Zalikar. Duk wannan abin da ake Baffa ko kallo basu ishe sa ba wayarsa yake hankali kwance. Zalika ta ce "Haba Mamy ki kwantar da hankalin ki mana" Hannun Zalikar ta kamo suka ƙaraso tsakiyar falon, Zalika ko a ranta bata ji fargabar tambayar da Baffa zai mata ba saboda ta san ma ba zai taɓa tambayarta daga ina take ba. Lokacin da suka ƙaraso ya gama wayar ta ɗan rusuna ta gaishe sa, ba tare da ya kalle ta ba ya amsa mata, tashi ta yi ta nufi ɓangarenta Mamy ta take mata baya, Mamy da fara tafiyarta ta ji maganar Baffa ya ce "Kike dai kulawa da nauyin da yake kanki don ni tuni na sauke nawa nauyin" Yana kai wa na ya yi shiru ita kuma bata amsa masa ba kuma bata juyo ba ta ci gaba da tafiya don dama ta san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi wato yana nufi ta kula da tarbiyarsu shi ya sauke nauyin abin da yake kansa na ɗawainiya. Zalika tana zuwa ɗakinta ta jefar da jakar a kan gado ta zauna kenan sai ga Mamy kamar an jefo ta ta shigo ta zauna a bakin gadon kusa da Zalika tana kallonta ta ce "Wai daga ina kike?" Zalika ta ce "Daga makaranta mana" Mamy ta ce "Makaranta?" ya war haka mai kike a makaranta?", Hannu ta miƙa ta ɗakko jakarta wani littafi ta nunawa Mamy mai ɗauke da rubutu wanda a ƙalla ta yi sati ma da yin rubutun ta nuna mata ta ce "Wannan rubutun na zauna yi, ina hostel wajen su Islam ina kwafar rubutun da na ce ta ara min littafin in taho da shi gida sai ta ce karatu za ta yi cikin dare wannan ne dalilin da ya sa na kai yanzu" Ƙuri Mamy ta mata da idanu kawai dai a ranta tana jin maganar bata gansu ba amma yadda Zalikar ta yi magana babu alamun ƙarya sai ta ji hankalinta ya kwanta. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Amma mai ya sa wayarki a kashe" Zalika ta ce "Ai kuwa wayata a kunne sai dai matsalar netwrk" Mamy ta ɗaga wayarta ta kira Zalika sai ga waya tana ringing, bayan kuma duk tsawon lokacin tana kiran wayar amma a kashe, haka ta amince da maganar Zalika sai kuma hankalinta ya koma kan Mubin tana tunanin rashin nasa dawowar. Shi ma wayarsa a kashe amma Zalika tana ta cewa da daina damuwa ai shi yanzu ba yaro ba ne, ita kuma tana zulumi da tunanin shi yaro ai ba a gama tarbiyarsa, sannan sai ka kwashe shekaru kana ba ƴaƴanka tarbiya amma sai a samu rana ɗaya wasu su warware maka tsohuwar saƙar da ka yi ta shekara da shekaru. Baffa yana gama uzurinsa ya koma ɓangarensa hankali kwance ya kwanta, bai ƙara bi ta kan cewa Mubin ya dawo ko kuma bai dawo ba, Mamy kuma tana ɗakinta ta kasa sukuni, duk hankalinta a tashe, wajen sha ɗaya da rabi ta ji mai gadi ya buɗe get da sauri ta tashi ta leƙa window sai kuwa ta ga hancin motar Mubin ya shigo harabar gidan, hango motar Zalika a ajiye a rufe ya sa ta gane Zalika yau ba da mota ta fita ba. Har sai da ya fito daga motar ya rufe, ya nufo ƙofar da za ta sada shi cikin gidan, cikin sauri ta fito daga ɗakinta ta nufo falon domin jin abin da Mubin zai ce mata wato daga ina yake da wannan tsohon daren. *SADIYA* Rayuwa ta ci gaba da gudana yau fari gobe baƙi, har ila yau bata sauya zani daga wajen Nasir haka ma ɓangaren mahaifiyarsa da ƙannensa, sun mayar da ita wata banza kowa yana kwaso sharar da ya ga dama ya watsa mata, a ganin Sadiya ba kowa ba ne ya jaza mata wannan sai iyayenta wanda su suka ja mata raini da wulaƙanci a wajen miji!. Koyaushe tana zulumin kai musu damuwarta domin babu wanda zai magance mata matsalarta, watarana ma idan Nasir ya kuntuka mata wani abun, haka za ta zauna kwana da kwanaki tana ƙunsar takaici sai dai idan ta shirya da nufin ta je gida don a sama mata mafita, tana zuwa gidan dai ta tarar da gidan a kacame Baba yana ya masifa ya hana kowa sakat yana yi wa sauran ƙannen nata tijara a kan rashin mijin da basu samu ba, wannan dalilin yake saka ta danne tata damuwar ta koma gidanta. Ka zalika ita ma mahaifiyarta da ita take ganin mace ce kuma bahaushe yana faɗin ciwo ƴa mace na ƴa mace ne, sai dai idan ma ta yi ƙoƙarin sanar da ita sai ta dakatar da ita ta hanyar bata haƙuri ba tare da ta bari ta ji matsala da damuwar ba. Sannan ita tana ma jin tsoron a tunkari Nasir da wata magana domin ba ya ganin kan kowa da gashi, ta san ma muddin aka masa magana tamkar an zubawa wuta fetur ne a maimakon a samu sauƙin lamarin sai abin ya ƙara hauhawa. Yau ya kama asabar wanda ya yi daidai da kwana uku tana fama da zazzaɓi mai zafi, sannan ko naira biyar bata da ita shi kuma ya ƙi siya mata magani bare a yi maganar zuwa asibiti, sai dai ta ji su Baba suna batun ta basu kuɗin bayan ita ko naira biyar ba ya bata. Gashi ita har gajiya take da faɗawa ƙawarta Noor buƙatunta abin da kunya kullum ka ce a baka. Kwance take ta kasa tashi tun da ta yi sallar asuba shi ma a zaune ta yi, zafin zazzaɓin da ya dira mata har cikin ta rasa ya za ta yi, Kalifa yana kwance a gefe yana bacci. Nasir ne ya fito daga bedroom ɗin kasancewar a falo suke, cikij shirinsa na fita sai buɗaɗa ƙamshi yake yana mata wani kallon rashin mutunci ya ce "Ni wallahi Sadiya ban san irinki ba a ce mutum bashi da aiki sai jinya, mace kullum tana bin katifa tana kwanciya haba" Idanunta da suke mata wani raɗaɗi tsabar zafin zazzaɓin ta ɗaga ta kalle shi ta ce "To ya bawa zai yi da abin da ubangiji ya jarafce shi da shi" Wani kallon ƙasan ido ya mata ya ce "Ke dai ce mai yawan jinya ai abin a jikin ki yake, yanzu dai yau kwana biyu kenan ina fita ina sayen abincin titi" Muryarta wacce bata fita sosai ta ce "Amma Abban Kalifa ka san dai duk runtsi ina yin girki tun da ka ga haka abin ne ya ci tura!. " Wani tsaki ya yi ya ce "Ragwanta dai" Yana faɗar hakan ya kaɗa kansa zai fita yana gyara zaman hularsa, yunƙurawa ta yi ta tashi zaune dakyar yana dab da fita daga ɗakin ta ce "Dan girman Allah ka siya min magani, wallahi ina jin jiki" Kamar ba zai juyo ba sai ya juyo ya ce "Aikin kenan ke kullum kamar asibiti baki da aiki sai ta,ammali da magani kamar wata ƴar shaye-shaye" Ta ji haushin maganar amma sai ta danne tana rayawa a ranta wataran sai labari, waya ya ɗaga yana magana ya saka takalminsa ya fita. Yana fita ya hangi wani al,amajiri a ƙofar wani gida yana bara kiransa ya yi da ya zo ya ce "Gani" Nasir ya ce "Kai ɗan malam ka san majamfari" Shiru yaron ya yi yana tunani sai Nasir ya ce "Wani ganye da ake dafawa sai a saka zani a rufa da zafib ruwan ganyen" Da sauri yaron ya ce "Na sanshi, mu ma malaminmu yana sawa mu cirowa matansa idan za a dafawa yaransa in suna zazzaɓi, ai har kwaɗonsa ana yi a ci in ana zazzaɓi" Nasir ya ce "Dakyau" Waje ya nema ya zauna ya ce yaron ya ajiye kwanonsa ya je ya ciro masa, da yake daga can gaba da su akwai wani gida bayan gidan kuma akwai gona amma sai an yi tafiya amma ba wani sosai ba kasancewar a kusan ƙarshen gari suke. Zuwa can sai ga yaro ya taho hannunsa cike da ganyen nan ya ciro su, yana kawowa Nasir ya karɓa ya bashi naira hamsin almajirin yana ta murna ya karɓa ya tafi. Yana kwasowa ya shigo gidan, Sadiya da ta ɗauka tafiya ta yi ta ji ya turo ƙofa sai gashi ya shigo ko sallama babu, labulen ya ɗaga ya ce "Sai ki fito ki dafa ki rufa da zani ki ɗauki ganyen ki yi kwaɗo ki ci" Baki sake take kallonsa yadda aka libgo ganyen kamar za ta yi kuka ta ce "Mene ne wannan Abban Kalifa" Kallon kin raina min hankali ya mata ya ce "Kar ki mayar da ni ɗan iska mana majanfarin ne za ki ce baki sani ba?" Cikin sanyin murya ta ce "Na sani" Ya ce " To tun da ke baki da aiki sai jinya gashi nan naira hamsin ɗina ta biya min buƙata, idan kin ji kin ware sai ki ɗora abinci" Yana gama faɗa ya ajiye mata a ƙofar ɗaki ya juya sai ƙaran rufowar ƙofar gidan ta ji, tagumi ta buga tana tunanin ita dai ta san ana tafasawa a rufa da zani zafin ya bugi mutum amma bata taɓa jin ana ci ba. Haka ta lallaɓa ta dafa ta rufa, cikin ikon Allah sai zazzaɓin ya sauka, sai rashin ƙarfin jiki, haka ta gyara gidan ta wanki Kalifa ita ma ta yj wankan ta ɗora girki. Da yamma sai ga Noor ta zo duba ta, suna hira sai ga Mama ita ma ta zo, bayan tafiyar Noor Mama ta yi ta yabawa Nasir a kan hidimar da yake yi da su, ita dai sai dai ta ce "Allah ya biya shi" Da dare tana zaune tana cin tuwon da ta dafa ba don tana jin daɗin bakinta ba sai don kar ta zauna da yunwa, Kalifa ya yi bacci da wuri tun ana magriba. Nasir da ya zo kamar abin arziƙi ya zauna ya gama ƙare mata kallo ya ce "Sadiya ina da magana da ke" Dakatawa ta yi da cin tuwon tana kallonsa ta ce "Ina ji" Ya ce "Sadiya ya kamata ki kama sana'a zamanki haka ba zai iyu ba, a ce ke komai sai dai a ɗauki ɗawainiyarki ke babu abin da za ki taimakawa mutum da shi" Tana masa kallon rashin fahimta ta ce. "To taimakon kuma na mene ne, sannan ai sana,a sai ana da jari... Tun kafin ta kai ƙarshen maganar ya katse ta da faɗin "Ba dole ba ko an faɗa miki mace bata taimakawa a cikin gidan, zamanki haka ba zai iyu ba sana,a ita ce mutuncinki dole ki kama sana,a domin ɗaukan ɗawainiyar kanki ni ma har kya taimaka min da buƙatub cikin gidan, a wannn zamanin macen da bata sana,a bata da daraja in ma baki sani ba ki sani, mace idan tana kama kuɗi ta fi daraja a idanun miji in mace bata da sana,a namiji gabansa har faɗuwa yake idan ya ga ta buɗe baki sai ya yi zaton buƙata za ta tambaya" Idanu ta ɗago tana binsa da kallon mamaki ta fara fahimtar nan gaba ɗawainiyar kanta ma ita za take ɗauka tun da gashi tun ba a je ko ina ba har ya fara gajiyawa da wasu abubuwan duk da dama wani haƙƙin yana tauyewa ne. Tana kallonsa ta ce "Amma ni da ba zaman kaina nake yi ba zaman aure nake sai in ke ɗaukar ɗawainiyar kaina" Sheƙeƙe ya kalleta ya ce "To Sadiya kar ki nemi sana'a ki zauna a haka" Yana gama faɗar hakan ya tashi ya nufi ɗaki da kallo ta bi bayanshi har ya ƙulewa ganinta, wani uban tagumi ta doka tana tunanin mafita, ita dama tana son sana'a sai dai rashin jari, ba ma wannan ba ita tun da ta yi auren nan tsawon shekara uku bata da wata nutsuwa sai dai damuwa. Ko da ta shiga ta kwanta haka ya zo mata da buƙatarsa, babu yadda ta iya ta sauke nauyin haƙƙin duk da bata da wani ƙwarin jikinta sai dai tana tsoron kwanciya da nauyinsa sannan tana fargabar mala'iku su kwana suna tsine mata idan ta bijirewa umarninsa. Washe gari da safe ta gama ɗumama tuwon ta zuba ta kawo masa har ta zubawa Kalifa ma, tana zaune ta yi shiru tunani ya yi awon gaba da ita ƙamshin miyar ne ya daki hancinta tana shaƙa kawai sai ta ji zuciyarta ta tashi, wani amai ta ji yana yunƙuro mata amma saboda ƙarfin hali take ƙoƙarin mayar da shi sai dai hautsinawar da cikinta ya yi shi ya sa babu shiri ta yi waje a gudu-gudu domin jin aman bashi da niyyar dakatawa.Tun da ta je bakin makwaranya take sheƙa amai kamar za ta amayar da ƴaƴan hanjinta, Kalifa ne jin ƙaran ƙololon aman tashi ya fito ya zo ya tsaya yana kallonta, har ta gama ta gyara wajen bayan ta wanke baki da fuskarta, duk sai ta ji jikinta ya mata nauyi hannun Kalifa ta kamo yana cewa "Momma amai" Amsa ta bashi kawai, suna shigowa falon ta ga Nasir ya dakata da cin abincin da yake tana shigowa ya zuba mata idanu tamkar yau ya fara ganinta, ba ma wannan ba yadda yake mata wani irin kallon tuhuma shi ne abin da ya ɗaga mata hankali duk ta ji ta tsargu, duk da bata gama gane inda kallon nasa ya dosa ba. Saurin kawar da kanta ta yi ta nufi inda ta tashi ta zauna, tana cewa Kalifa ya zauna ya ci gaba da cin tuwon. Kamar daga sama ta ji Nasir ya ce "Kin san dai ba na son amai, a kan mai ina cin abinci za ki wani ƙwaƙulo amai kawai ki sa duk abincin ya fita daga raina, ai sai ki zo ki ɗauke tun da burinki ya cika na daina ci sai ki ajiye kw kya ci anjima" Danne abin da ta ji ya yunƙuro mata na takaici ta yi, ta tashi ta ɗauke ta fita ta kai kicin ta dawo, tana shigowa ya ci gaba da mata kallon ƙwaƙwaf sai da ya bari ta zauna ta ji ya jefo mata wata tambaya da ta saka ta tafi wata duniyar tunanin da bata yi shi ba, ya ce "Wai aman mene ne kike yi Sadiya, kar dai ki ci min ciki ne da ke?" Wannan tambayar da ya mata ta sanya ta luluƙa duniyar tunani da zargin kanta, na farko tabbas wannan watan bata yi al'ada ba (priod) Sannan ta lura ma sai take ta jin kasala sannan kuma daga ta ci abu ma sai ta ji babu maganar da ya yi ce ta katse mata tunani ya ce "Magana nake miki Sadiya" A tsorace ta ce "Ni bani da wani ciki" Wani kallon ƙurilla ya mata ya ce "Ai dama kar ma ki fara don ni ba na son haihuwa a kai a kai, yaro shekara biyu a masa wani ƙani, ai haihuwa ma kamar mage bashi da wani alfanu shi ya sa ake son tsarin iyali" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, har ya tashi ya haɗa kan wayoyinsa ya ajiye ya je ya sake wanke bakinsa saboda tuwon da ya ci ya ɗauki abubuwansa ya juya zai fita ta ce "Baka bada abinci ba" Ya juyo cike da gajiyawa ya ce "Abinci, abinci, abinci" Sai da ya maimaita sau uku sannan ya yi wani tsaki, store ya je ya buɗe ya ɗakko taliya guda ɗaya ya rufe ya fito ya ce "Gashi nan kuma wallahi kar ki juye duka, idan kika zuba rabi sai ki ɗan ƙara ki ajiye idan na dawo zan mayar store" Cikin sanyin murya ta ce "Ka bada kuɗin cefane babu kayan miya sannan mai ma saura kaɗan, sai in ba almajiri ya siyo" Cike da tijara ya ce "Wallahi naira biyar ba zan bayar ba wannan idan kina jero buƙatu ai sai ki talauta ni, wallahi shi ya sa nake so in yi aure ko na samu sassauci na san amaryar da zan auro za take tarairayar aljihuna tana buɗe bakin jakarta don ta tallafa mini" Yana kai wa nan ya saka takalmansa ya fice. Bayan ta gama gyaran gidan ta yi wa Kalifa wanka ita ma ta yi, wanke wanke ta yi da wankin banɗaki ta gyara kicin tas. Ganin Kalifa ya yi bacci ta haɗa kayan wanki ta je ta wanke, duk abubuwan nan da take gabanta yana faɗuwa domin tana ta juya maganar Nasir a ranta a kan maganar ciki, ita kanta bata son ta samu ciki yanzu ba ma yanzu ba ita idan son samu ne Kalifa ya zama shi kaɗai ne wanda zai zama rabo tsakaninta da Nasir domin ta san gidan nan ba gidan dauwamarta ba ne, babu ma alamar zaman zai ɗore duk da ta san mutuwar aurenta tamkar rasa wani sashe na zaman lafiyarta ne a gidan mahaifinta amma dai tana zaman jiran tsammanin ta inda mafita za ta zo mata watarana!. Tuno da tsinken pt na awon ciki wanda lokacin da take shayar da Kalifa Nasir ya zargi ciki ne da ita ya ringa mata rashin mutunci da hana rayuwarta sakat, shi ne da ya ga babu haza ya siyo pt ɗin ya ce ta gwada, tana dubawa babu ciki shi ne ya ringa jero hamdala kamar dai wani abu ne daban, sai ka ce ba shi ne mamallakin cikin ba, kamar dai ba shi ne yake lallaɓowa ya karɓi haƙƙinsa ba. Kasancewar lokacin guda huɗu ne sai ta ajiye ukun yanzu ta ɗakko guda ɗaya domin ta gwada, sai ta ajiye masa idan ya zo ya ga layi ɗaya ne babu ciki sai ya sakar mata mara ta yi fitsari. Tana ɗakkowa ta je ta samu wani ɗan murfi ta shiga bayi ta yi fitsarin ta fito gabanta sai faɗuwa yake tana fargabar sakamakon. Ko da ta zo ta ɓare pt ɗin ta tsoma a fitsarin ta ciro yayin da fitsarin yake tafiya a cikin pt ɗin domin fitar sakamako tare da matsananciyar faɗuwar gabanta yake tafiya. Lokacin da ya gama tafiya idanunta ra runtse da ƙarfi tana ta karanto addu'a a a zuciyarta a kan Allah ya sa ba ciki ne da ita ba, in ban da ma irin rayuwar da ta samu kanta a ciki a ce wai kana fargabar ganin kana ɗauke da ciki sai ka ce wani cikin shege!. Hannunta karkarwa yake, kai gaba ɗaya ma sai jikin nata yake karkarwa shahada ta yi ta buɗe idanunta warai sai a kan sakamakon layi biyu ne a jiki raɗo-raɗo ƙafafunta da ta ji suna barazanar jumurin ɗaukar gangar jikinta da sauri ta zube ƙasa tana zaunawa zaman dirshan a fili tana furta "Innalillahi wa inna ilahi raji'un" *JIDDA* Kunnuwanta ta sakawa auduga daga maganganun da su Umma suke yadawa a cikin gidan, duk wanda ya shigo gidan ganin kaya tana jin yadda Umma take nuna musu akwatuna 24 a matsayin lefen Aliya ta faɗa musu har da mota duk da motar Abba ya ɗauke ta ya kai gidan abokinsa aka ajiye ta, sannan sai ta nuna akwati biyu da kit a matsayin lefen Jidda mutane su yi ta faɗin Aliya ta yi goshi don wasu ma ganin kayan ya sa sun ɗauka wani hamshaƙin mai kuɗi ne Aliyar ta aura. Umma duk ta kasa sukuni sun hana ransu sakat da ƙyashi da hassada ji take tamkar ta sauyawa Aliya da mijin Jidda a nata ganin ai Jidda ba za ta auri wanda ya fi mijin ƴarta Aliya ba. Hassada suke nunawa a fili amma ita Jidda ko a jikinta, sai dai kuma da ya rage saura sati guda biki sai Umma da Aliya suka keɓe a lokacin da Jidda bata nan tana gidan su Salama sun tafi rabon cingam da kati, duk da har gidansu Ibrahim Salama ta rakata da Mummy ta ce sai ta je ta gaishe ta, sun ga tarɓa ta mutuncin kuwa a nan Jidda ta fahimci ta samu surukar arzii, sannan ta ƙara fahimtar ba ƙaramar ƙauna take yi mata ba, hakan ya sa ta ƙara jin hankalinta da kwanta da auren Ibrahim ko ba komai idan uwar miji tana sonka za ka samu salama a gidan mijinka. Umma ce ta kalli Aliya da ta zuba uban tagumi, duk ta bi ta rame ta yi duhu ta ce "Aliya na faɗa miki ki dajna saka damuwa a ranki, kar ki je ki samu wani ciwon kin san dai dama an ce hassada mugun ciwo ce bare kuma ta haɗu da damuwa a zuciya abin sai ya miki illa don abin sai ya yi yawa wai shege da hauka" Aliya ta buɗe bakinta da kuka yake son ƙwace mata ita damuwarta idan ta tuno kayan akwatin Jidda sai ta ji duniyar ta mata zafi, gani take gabaɗaya kayan da ita suka dace ba da Jidda ba saboda ita ce kyakkyawa kuma ita ce ma dai ta dace da auren miji kamar Ibrahim ba Jidda ba. Tana jan hanci ta ce "Wai Umma ya kike so in yi ne? Ina zan saka raina yanzu gwala gwalan da aka sakawa Jidda a lefe ni fa idan aka cire zoben ciki gabaɗaya sai ya saya kayan lefena har da canji, ga wasu miliyan uku a ajiye, sannan da kunnena na ji Salama tana cewa wai miliyan biyu ya bada kuɗin ƴanmatanci amma saboda Jidda matsiyaciya ce dakyar ta karɓi dubo ɗari biyu shi ma sai da Salama ta saka baki, yanzu da ni ce ba shikenan na samu wajen baje hajar karɓar kuɗaɗe ba, kina dai gani dakyar Kasim ya bani dubu hamsin shi ma yana min ƙorafin babu a rayuwa na tsani a furta min kalmar babu yanzu dubu hamsin mai za ta mana" Umma ta sauke ajiyar zuciya tana jin babu daɗi ta ce "Ai ni yanzu ban san ba ya za a yi ma, wallahi na rasa mafita ko kaɗan gashi su Jidda ita da ƙawayenta Ibrahim ya biya musu kuɗin gyaran jiki ya kwaso kayan da za ta raba ya kawo mata suna nan jibge a ɗaki kamar babu gobe" Aliya kawai sai ta rushe da kuka ta ce "Har kuɗin ƙunshi ya biya fa, jiya da dare ma kuɗin da ya bata ta miƙo min dubu ɗari wai ko za mu ƙara ni kuwa na jefa mata kayanta kar ma ta yi tunanin kuɗinta wata tsiya ne a wajena" Umma tana zaro idanu ta ce "Dan ubanku kika bata kuɗin? Wane shegen ya ce miki ana mayar da hannun kyauta baya, ai kai faƙiri baka biyewa mai arziƙi bayan kin san kina da buƙatar kuɗin" Aliya ta ce "Umma akwai damuwa fa a ce wai ni ce Jidda za ta taimakawa, ki ga wata shegiyar haɗaɗɗiyar mota wallahi da ni motar nan ta dace Umma" Ta faɗa tana kukan takaici. Umma tana jin tamkar ta dishashe auren ma, amma abun da Allah ya nufa ya daɗe da yi, hakan ya sa ta ce "Yanzu tun da dai Abbanku ya ce walima za a yi kin ga kayan can da Ibrahim ɗin ya kawo mata ya isa ku rarrabawa ƙawayenku to ya za ki yi tun da Allah ya ƙadarta miki talaka za ki aura, ai kawai mu bada kai bori ya hau" Cikin rashin fahimta ta ce "Umma ban gane ba" Umma ta ce "Aliya dole mu sauya taku, dole mu ɗauki haƙuri da jumurin halin da muka tsinci kanmu, ina nufin yanzu dole mu fito mu nunawa Jidda soyayyar ƙarya, mu danne duk wani ɓacin rai da za mu ji a tattare da ita, mu jata a jiki ta haka ne za mu samu shiga jikinta ta saki jiki da mu ko bayan an yi auren in ya so sai mu yi amfani da damarmakinmu wajen cika duk wani buri da muke da shi nan gaba!" Shiru Aliya ta yi tana nazarin maganar Umma duk da tana jin hakan da wuya ta iya amma kuma in har hakan ne dole ko da dariyar yaƙe ta yaƙi Jidda ta ga ko za ta yi nasara a kanta! Tsaye Aliya ta tashi ta rungume Umma ta ce "Umma ta kin fi ta kowa, Umma mikiya mai hangen nesa, tabbas ta haka ne za mu samu abin da muke so, don na ci alwashin sai na mallaki Ibrahim ko ta halin ƙaƙa, sai na zamewa Jidda ƙadangaren bakin tulu" Ta faɗa tana sakin Umma ta shiga juyi a tsakiyar ɗakin ta ce "Umma kalli diri da kyauna ban dace da Kasim ba da Ibrahim na dace, ban dace da rayuwar talauci ba da gidan arziƙi na dace" Umma ta ce "Ai ki saka a ranki ƙwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wahala ba, ke ko zaman kishi ne gwara ki yi da Jidda" Aliya ta ce "Wallahi kuwa tun da ba uwarmu ɗaya ba uban ma kowa da nashi, bare a ce auren miji ɗaya ya haramta a garemu!". Haka suka ringa tsara yadda abubuwa za su kasance wajen yaƙi da zukatansu ganin basu nuna ƙiyayya a fili ba. Da daddare Ibrahim ya zo wajen Jidda bayan ta fita sun gaisa suna ɗan tattaunawa tana zaune kan wani dakali da yake daga can ƙofar gidan shi kuma yana tsaye ta jingina da jikin motarsa, hira suke cikin natsuwa da kwanciyar hankali, tsaftatacciyar hira ba irin hirar da wasu ƴanmata da samarin zamani suke yi ba wacce hira ce da ta saɓawa addini da kuma al'ada, wanda yawanci wasu samari da ƴanmatan sun ɗauki hakan a matsayin wayewa, bayan ba wayewa ba ce jahilci ne da rashin tsoron Allah da kuma tuna makoma. Hira da taɓa jikin juna, ko hirar marar kyaun sauraro, gabaɗaya ya saɓa addini sannan daga ke har shi ba za ku yi daraja a idanun junanku ba sannan ko da Allah ya yi kun yi aure za kuke zama da zargi!. Cikin hirar tasu ne Ibrahim ya ce "Jiddanah!" Murmushi ta yi ta ɗago tana kallonsa ta ce "Na'am" Ya ce "Ina so na miki wata tambaya amma ina jin nauyi" Ta ɗan yi shiru tana jin babu daɗi a ranta don ta yi tunanin ko magana zai mata a kan lamarin Aliya sai da ta ɗan ɗaure fuska don ita bata son wai don za ta auri namiji ko kuma bayan ta aure shi, ta tsaya yake sanin sirrin gidansu ko kuma yake faɗawa wasu daga danginta magana ba za ta lamunci hakan ba, ko yaya naka-nake ne sannan duk daren daɗewa ana iya sauya miji amma ɗan uwa ba a sauya shi, don haka duk yadda nake yake to naka ne idan ka ba namijin ƙofar ya san sirrin gidanku to tabbas wataran gori ko wulaƙanci zai iya biyo baya idan ma hakan bai samu ba babu wani alfanu ga mace take kwashe sirrin gidansu tana faɗawa miji. Ta ɗan sauke ajiyar zuciya ta ce "Ka faɗa in har da sarari zan faɗa maka" Ya hurar da iska daga bakinsa ya ce "Kawai idan ba damuwa ne ina son sanin tarihinki ma'ana ina son sanin asalin labarinki na san mahaifanki sun rasu amma bayan haka ban san komai ba, kuma ba don wai wani abu ba kawai dai ina son sani" Sai da ta kalle shi sannan ta mayar da idanunta tana kallon ƙasa ta ce "Sunana Hauwa ana kirana da Jidda, mahaifina ɗan asalin ƙasar Niger ne a wani gari da ake kira Doso, mahaifina saboda halin babu da kuma wasu matsalolin wanda yarinta bata bari na san su ba kasancewar lokacin shekarata goma. Wannan dalilan ne suka saka ya baro ƙasarshi ya dawo Nigeri'a , lokacin da ya zo ya dira a garin Kano bai san kowa ba cikin ikon Allah suka haɗu da Abba ya taimaka masa, ka ga wancan gidan shi ne gidan da muka zauna da mahaifana a ciki muka rayu" Ta faɗa tana nuba masa wani gida da yake kallon gidan Abba, wanda gidan yanzu a rufe ma yake babu kowa a ciki, waiwayawa ya yi ya kalli gidan kafin ya juyo yana kallonta ganin idanunta sun cika da ruwa, bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ɗora da faɗin "A kwana a tashi abota mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu don Allah har kasuwa tare suke zuwa da mahaifina Malam Abdullahi, koyaushe mahaifina yana faɗawa mahaifiyata girma da darajar Abba a wajensa a ganinsa ba kowane mutum nr zai nuna karamci kamar yadda Abba ya nuna masa ba, abotarsu ta saka ƙawance mai ƙarfi ahiga tsakanina da Aliya, koyaushe muna tare muna son junansu sanann mahaifanmu mata ma basa nuna mana bambanci gidanmu tamkar gidansu Aliya haka nima. sai dai ita Umma bata ƙawance da mahaifiyata sai dai in an haɗu a gaisa ko wani dalili mai ƙarfi" Ta faɗi hakan tana jan hanci da alama dai akwai wani abu da take kusa zuwa wajen faɗa yadda ya ji muryarta tana rawa, ko kuma labarin da take bashi ne yake taɓa mata zuciya. Ta ci gaba da faɗin "A watarana wacce ba zan taɓa mantawa da ita ba, ita ce ranar babu makaranta domin ranar asabar ce, muna zaune muna ta hira da mahaifiyata na ce mata wajen Aliya zan tafi haka na fito zan tafi muka haɗu da mahaifina a ƙofar gida zai shigo, nan na masa sannu da dawowa ina faɗa masa wajen Aliya zan je yana faɗin ai dama ya san zancen gizo bai wuce na ƙoƙi, a nan har yake nuna min ledar hannunsa yana cewa maƙocinsa ne na gaba da mu kaɗan ya bashi ɗanyen rogo da yake ya noma kasancewar ina son rogo na hau murna ina cewa zan dawo in ci idan an gama dafawa, wannan ita ce baƙar rana, wannan ita ce rana mafi muni kuma mafi tarihi a cikin rayuwata" Ta faɗa tana kuka tare da share hawayenta shi ma Ibrahim hawaye yake yana bata haƙuri sai da ta ɗan numfasa kafin ta ce "Ashe wannan rogon shi ne ajalin iyayena, ni kuma kwanana ne a gaba shi ya sa ban ci ba, bayan mahaifiyata ta wanke ta dafa ta zuba min nawa ni da Aliya ta ajiye mana suka ci nasu daga cin wannan rogo sai ciwon ciki babu wanda ya san ciwon cikin har ya yi ajalinsu gabaɗayansu sai da muka je ni da Aliya mu ci rogo a nan na yi tozali da gawar mahaifana kwance kowa da dafara a bakinsa" Kukan da take yi ne ya hana ta ci gaba, sai da ta tsagaita ta ce "Ashe dai wannan rogon taki ne aka zuba mai ƙarfi a gonar wanda gubar da jikin takin da yake jikin rogon bai fita ba shi ne ya yi ajalinsu duk da cewa an dafa shi amma dai takin bai bar jiki ba" Daga shi har ita kuka suke ta ci gaba da faɗin Tun daga wannan rana na yi bankwana da iyayena, sannan Abba ya je har Doso amma neman duniyar nan ba a samu wanda ya san mahaifana ko wani wanda yake da alaƙa da su, riƙona ya koma hannun Abba har kawo yanzu" Ta faɗa tana share hawaye, ko a fuska bata faɗa masa irin ƙalubalen da ta shiga bayan mutuwar iyayen ba da irin canjin da ta samu daga Umma da Aliya ba wanda shi ne har yau bata sauya zani ba, a ganin Umma babu yadda za a yi Abba yake riƙe da ƴar da bai san wani dangi nata ba, sai kuma ƙoƙari da farin jininta wanda shi ne ummul aba,isin faruwar komai. Ya daɗe yana jimanta abin sai ya ji wani mugun tausayinta ya shige shi, tabbas tsautsayi ba ya wuce ranarsa sannan rashin sani ya fi dare duhu da sun san rogon zai yi ajalinsu da basu ci ba, amma dama rai ba bakin komai yake ba. Haƙuri ya ringa bata har dai ta huce da za ta shiga gida ya ɗakko waya iphone 16 ya bata a kwalinta, dakyar ta karɓa sai da ya ɓata ransa, don dama kayan fitar biki da ya ɗinka mata cewa ta yi kar ya kawo saboda ita ko kaɗan bata son ran Aliya ya sosu. Da sallama ta shiga gidan, Umma ta amsa tana washe baki, suna zaune da Abba suna magana ita kuma Aliya tana ɗaki ko da ta shigo a kan tabarmar ta durƙusa ta miƙawa Umma kwalin wayar tana mata bayanin wanda ya bata, Umma sosai ta nuna murna tana nunawa Abba ya karɓa ya saka albarka, Umma ta miƙo mata ta karɓa ta nufi ɗaki, abin mamaki tana shiga Aliya ta ce "Ƙawata ƴar uwata" Lafazin ya zo mata a bazata har ta kasa riƙe farincikinta ta ajiye kwalin wayar a kan katifa ta je ta rungume Aliya tana faɗin "Aliyata ta dawo gareni haƙiƙa na yi farin ciki" Ta faɗa har lokacin tana rungume da Aliya, tabbas tana son Aliya, Aliya kuwa ji take tamkar ta shaƙe Jidda amma haka ta daure ta danne zuciyarta ta nuna mata farincikin ta. Bayan sun saki juna ta ɗakko wayar cike da murna ta nuna mata wani abu ya caki zuciyar Aliya wai Jidda ce za ta riƙe Iphone bayan ita tana fama da waya mai screen a ragargaje, haka ta danne zuciyarta ta nuna mata farincikin ƙarya, don yanzu dai ta ga Jidda ta kere ta a komai. An shiga hidimae biki a inda Umam ta ɗauko duka kayan kicin ɗin da ta saya domin Aliya ta raba a biyu ta ce kowa ya ɗauki ɗaya a fili tana nufin saboda soyayya amma a baɗini ta bayar ne don su ƙara saka yarda a zuciyar Jidda, ita kuma Jidda sai take ji tamkar bata yi rashin mahaifiyata ba irin yadda Umma take nuna mata soyayya da kukawa. Ana saura kwana huɗu biki aka je aka yi jere mutane anguwa da kuma ƴan uwa, gidan Aliya suka fara zuwa ciki da falo da banɗaki sai ɗaki ɗaya da kuma kicin shi ma ba mallakin Nasir ba ne mahaifinsa ne ya bashi a kan cewar kafin ya mallaki nasa. Ranar da ya kasance saura kwana uku aka je aka yi wa Jidda sam barka jama,a suna ta yabon gida da kuma yadda kaya ya amshi gida faɗa ma ɓata baki ne. Amare sun sha gyara don sai Aliya da ƙawayenta suka bi ayarin gyaran jikin su Jidda komai dai a na Jidda aka musu suka fito gwanin sha,awa an sha lalle ja da baƙi. Umma aka samo mata number maman afrah marubuciya a jikin littfinta ta ruɓaɓɓiyar igiya, jin ana ta yabon kayan matan maman afrar mai suna DARAJAR MATA haka ta saya musu tsumin ƙorama, maganin sanyi mai suna a fatattaki sanyi kasancewar duk wani maganin mata ba ya aiki in dai akwai sanyi a jikin mace. Daka mai suna sirrin ma,aurata wanda yake saukar da ni,ima ga mace sai ɓulɓul na gyaran breast sosai maman afrah ta musu haɗi na kece raini wanda zai kankaro musu mutunci wajen mazajensu Umma ta yi hakan ne don Jidda ta yarda ɗaya suke da Aliya. Mai buƙatar maganin sanyi ko magungunan mata ya yi wa maman afrah magana a 09925576222 Duk haɗe haɗen da aka musu amma Aliya don ta fi Jidda sai da ta samo wami group na wata mai siyar da supplement mai suna mom farhan ta saya wani haɗi na combo wanda ta ga an rubuta a jikin set ɗin kamar haka Hajia indai mgnr emergency ne toh wanan shine kankat Indai matsalar ki rashin niima da matsi ne toh ki siya wnn combo din zaki gode min, ina masu cewa sun sha magani har sun gaji basu taba sanin ya dadin se yake ba toh dan ALLAH ki gwada wannan combo din, ai Aliya tana ganin haka ta kwafi no admin ɗin kamar haka 0814 153 5308 ta mata magana ta turawa mom farhan hoton combo ɗin ta faɗa mata kuɗin ta tura mata aika aika mata ta ɓoye don ma kar Jidda ta gani. An yi biki an sha kyau amma Aliya saboda baƙin hali duk wanda suka zo ƴan makarantar su sai ta faɗa musu cewa ai Jidda riƙw ta ake yi a gidansu ita ba uwarsu ɗaya ba ba ubansu ɗaya ba, amma a bayan idanun Jiddar take faɗa. A masallacin unguwar aka yi walima ranar yini da yamma inda aka cika aka ɗakko malama juwairiyya ta yi wa,azi a kan biyayyar gidan aure, sai magriba aka tashi, duk da Aliya ta so Abba ya bari an yi bidi,a a bikin amma ina, don kafin ma a tafi walimar an sha hotunan amare da angwaye da kuma abokai da ƙawaye. Aliya tana ganin ta fi Jidda yin kyau amma dai kowa da irin nasa kyan. Amare sun shirya tsaf sai ƙamshi suke, sun shirya cikin fararen laffaya mai goldin ɗin flowers sun yi kyau har sun gaji, Abba ya musu nasiha a kan biyayya da kauda kai a kan komai mutum ya ji kamar bai ji ba ya gani kamar bai gani ba. Umma sai hawaye take sharewa na rabuwa da yaran a fili amma a baɗini kukan rabuwa da Aliya take yi, sanna kuma tana kukan takaicin Jidda za ta tafi gidan jin daɗi da hutu. Kasim ya kawo mutoci guda huɗu a inda motocin ɗaukan Jidda sun fi ashirin motoci ne na alfarma, sannan Abba ya ce a tare za a tafi idan aka kai ɗaya sai a wuce a kai ɗaya. Jama,a sun shiga motoci inda mota ɗaya aka saka amare a ciki sai iyaye guda biyu don amaren ne a tsakiya, Jidda tana kukan rabuwa da gidan a gefe ɗaya tana kukan tunano iyayenta musamman da ta kalli gidan da suka rayu da mahaifanta amma kuma yanzu gashi za ta tafi ɗakin miji ba tare da suna duniyar ba rayuwa kenan. Motoci sun miƙa a kan titi suna tafiya a laye inda amare suke ta kuka abinsu. Gidan Jidda aka nufa inda yake unguwar GRA a ƙofar wani tanfatsetsan gida motocin suka fara tsayawa horn ɗin da aka saki a kusan tare-tare shi ne ya ankarar da Aliya da take zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka wanda ya zama kuka biyu na rabuwa da Umma da na baƙincikin Jidda. Matan cikin motar ƴar uwar Umma da Abba ne suka haɗa baki wajen faɗin "Kai jama'a wannan gida tamfatsi, tamkar ba a nigeri,a ba wannan ai shi ne aljannar duniya!". Aliya wacce maganar ta su ta saka ta faɗuwar gaba mai ƙarfi bata san lokacin da ta ɗago da kanta ba, don wannan furucin ya tabbatar mata gidan Jidda aka fara zuwa, domin ta san da gidanta ne ba za a faɗi haka ba, ɗago kan da za ta yi ya yi daidai da wangale get da mai gadin ya yi, motocin suka fara shigewa ciki a jere, a inda Aliya da ta ɗago ta sauke a kan wani haɗaɗɗan gida na masu aji kuma masu hannu da shuni, wanda ko ita bata taɓa tunin za ta shiga ba bare wata Jidda baƙa mummmuna!. Ganin gidan ya sa hankalinta ya tashi irin tsaruwarsa da yadda wasu kyawawa fitilu suka masa ƙawanya, tana ganin hakan ta cikin laffyar da ta lulluɓa ita kanta bata san lokacin da ta cire lulluɓin ba, babu zato da tsammani ƴan cikin motar suka ji ta ce "Wayyo Allah na shiga uku!!!". MAMAN AFRAH 09025576222 https://chat.whatsapp.com/DNhoKsIb9qP8PlVQdpQ4BW?mode=ems_copy_c *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️2️⃣ *SADIYA* Tun da ta zauna take ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un, tashin hankalinta ruɓanya yake idan tana tuna cewa Nasir ba ya son haihuwa kuma ko ɗazu yana nannagon ta , sannan tun yanzu tana ita kaɗai da ɗa guda ɗaya yana nuna gajiyawa da ɗaukan ɗawainiyarta bare kuma aka ce ta sake haihuwa, mutumin da yake batun ta kama sana,a don take tallafawa a cikin gidan bayan kuma ko ciyarwa ƙauro yake sai abin sa ya ga dama zai bayar. Hannu ta ɗaga idanunta yana zubar da hawaye ta ce "Ya Allah kai kake bayarwa, kuma kai ne kake hanawa, wasu bayinka suna neman haihuwa baka basu ba, ina godiya da ka bani kuma ka ƙara min, ya Allah bam gajiya da kyauta da ƙarin da ka min ba,ya rabbi ka sassauto da zuciyar Naasir kar ya wulaƙantani a kan cikin nan" Tana gama faɗar hakan ta koma ta jingina da jikin kujera tana ta saƙa da warwara kan cewar ta sanar da shi ko kuma ta ƙyale shi, idan ra sanar da shi ba tira za ta yi daga matsalarsa ba sannan idan ta ƙyale ɗin ma akwai ranar ƙin dillanci tun da shi ciki ɗan duba ne duk daren daɗewa, zai bayyana kansa!. Bayan kwana biyu bata faɗa masa ba, tana nan tana ta nuƙu-nuƙun sanar da shi tana tsoron abin da zai biyo baya, saboda haka ko yana gidan idan ta ji amai yana yunƙuro mata sai ta yi ta dannewa tana addu'ar Allah rufa mata asiri kar ya gane, saboda idan ya sani a ɗaya za a yi biyu ko dai ya sake ta ko kuma ya ringa ƙuntata mata a cikin gidan. Bayan sati guda da sanin tana ɗauke da ciki har lokacin Nasir bai san wainar da take toyawa ba, ita kaɗai ta san tana da ciki sai kuma ƙawarta, amma duk wani laulayi da take fama da shi dannewa take duk ta yi baƙi ta rame. A wata ranar alhamis ne bayan ya fita dama yau bata ga ya yi shirin fita kasuwa ba, zuwa can sai ta ji daga windown ta da yake ta waje ana cewa daga nan za a ajiye bulo, da siminti ta yi mamakin masu ajiyewar don bata ji muryar Nasir ba hakan ya bata tabbacin ko dai wasu ne suka kawo ajiya. Bayan kamar awa guda ta ji ƙaran babbar mota, motar bata tsaya a ko ina ba sai ta ji ƙaran tsayawarta a ƙofar gidan, motar yashi ce don haka tana ji aka juye yashin motar ta tafi. Muryoyin mutane ta ji sai kuma ta ji muryar Nasir yana cewa su kwaɓa yashin da siminti sai kuma ta ji an turo ƙofa wasu matasa suka yi sallama sai ta ji Nasir tana cewa su shigo da shi, tana ɗaga labule ta ga bulo ne suke ta shigowa da shi, hakan ya bata tabbacin ginin ɗaya part ɗin ne za a tada da alama auren nasa ne ya kusa. Bai sanar da ita cewa za a yi aiki ba, don haka sai take saka hijabi idan za ta fito tsakar gidan, haka ma,aikata suka fara aikin ƙarasa ginin nan tuƙuru ita dai babu wanda ya ce mata ita ma kuma bata ce ba. Cikin sati ɗaya aka gama komai na ɓangaren, an saka ƙofofi an yi fenty hatta wuta an ja ɓangaren, da yake har da ɗakin Nasir ɗin mai bayi a ciki, ɗayan kuma ciki da falo ne da banɗaki a ciki. Ita dai bata ce komai ba tana ganin ikon Allah. Ranar wata juma'a da safe tana zaune haka kawai ta ji tana jin amai ta yi iya ƙoƙarinta na ta dakatar amma abin ya ci tura, haka ya sa ta fita da sauri ta shiga sheƙa aman, kamar an jefo Naair sai ganinsa ta yi ko riga babu ya zo ya tsaya yana wani zazzare idanu ko aman bai tsaya mata ba ya buɗe baki cikin hargowa ya ce "Wai aman mene ne kike yi bayan lafiyar ki ƙalau?" Tambayar ta kiɗima ta haɗe da ruɗa mata ciki don ta ji tsoro sosai don da alama ko ya fahimci wani abu dangane da ita. Sai da aman ya tsagaita mata ta wanke bakinta da fuskarta a famfon wajen duk ta galabaita a daidai lokacin ne ya sake jefo mata wata tambayar tamkar zai hau ta da duka. "Sadiya na ce aman uban mene ne kike yi?" Idanu ta ɗaga tana kallonsa ƙirjinta yana dokawa da ƙarfi, ta san dai ko da a ce cikin ne ai ya san ba a waje ta samo ba, tun da sh ne maijinta kuma shi ne mai yawan buƙata kullum abu ɗaya, sannan ai ita ba za ta hana ubangiji ikonsa ba. Bakinta ne ya yi nauyi tana tunanin ta ina za ta fara, kafin ta samu ƙarfin gwiwar amsa masa, don a ganinta baƙin alƙalami ya bushe, kawai ya kamata ta sanar da shi in ma yankata zai yi to gwara ta faɗa ta fita daga zulumin da take kwana take tashi da shi tamkar wacce ta yi cikin shege!. A hargitse ya ce "Idan baki faɗa min ba wallahi na lahira sai ya fiki jin daɗi in har ya yi aiki mai kyau!" Cike da karkarwar baki ta ce "Lafiyata ƙala...Tun kafin ta ƙarasa faɗa ya katse mata hanzari da faɗin "Yanzu ba lafiyarki nake tambaya ba aman mene ne?" Kamar zuciyarta za ta fasa ƙirjinta ta fito haka ta ji ganin yadda yake zare ido, a take ta fara tunanin cewa dama haka wasu matan suke fuskanta idan mazajensu basa son haihuwa? Kuma ya kasance macen ta samu ciki haka suke shiga fargaba da tashin hankali?. Maganarsa ta katse mata tunanin inda ya ce "Wai ba magana nake miki ba Sadiya? Wato kin mayar da ni kare in yi ta haushi?" Cikin inda -inda ta ce "Ci...ci...ciki ne da..." Wata wawiyar tsawa da ya doka ita ce silar tashin Kalifa da ya koma baccin safe sai kukansa ta ji, Nasir ya ce "Wato kin samu ciki shi ne kike ƙunbiya-ƙunbiya baki faɗa mini ba, wato ga Nasir ɗangote ko Nasir A A Rano shi ya sa za a ke mini haihuwa a kai-akai tun da ni me dukiya ne ko? Ɗan rufin asirin da Allah ya mini kike so sai kin kwantar da ni Sadiya ki tara min ƴaƴa tsufa ya hau ni, a zamana bani da kataɓus sai ƴaƴa to wallahi baki isa ba!" Ya faɗa yana nunata da yatsa, fitowar Kalifa ya sa ya kalli Kalifan yana sakin wani wawan tsaki, shi kuma Kalifan da sauri ya kauce daga hanyar da Nasir ɗin yake tsaye ya yi wajen Sadiya yana ɗan kuka tare da murza idanu. Fuuuu ya juya tamkar zai tashi sama, ɗaki ya shiga jim kaɗan sai gashi da rigar a hannu haɗe da singlet, a ƙofar ɗakin ya saka singlet ɗin ya ɗora rigar hannunsa riƙe da waya ko maɓallin rigar bai ɓalla ba hatta takalminsa tana gani a baibai ya saka, ƙofa ya nufa sai jin rufowar ƙofar gidan ta yi gararaf!. Kalifa ta kama ta tsayar a gefe ta wanke wajena ta ɗakko shi suka nufo ɗakin, tana zuwa ta zauna a kan kujerar Kalifa yana kan cinyarta, bata ankara ba sai ta ji hannun Kalifa a kan fuskarta yana share mata hawaye, kallonsa ta yi tare da rungume shi, tana jin son ɗan nata har ciki ranta, tana rayawa a ranta ta san komai daren daɗewa za ta fita daga cikin wannan uƙubar, sannan tabbas ta san Nasir ranar nadama tana zuwa zai gane shayi ruwa ne, amma dai a juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe, don rayuwa tana cike da darasi ne sai dai mutum bai ga damar ɗauka ba, amma a kowane sakan a kowace awa akwai abubuwan da mutum zai koya kuma ya gane sai dai ruwansa ne ya yi aiki da shi ko kuma ya watsar amma dai shi ubangiji mai yin hisabi ne a kan komai!. Wajen ƙarfe goma ta ji an turo ƙofa, sallamar Hajiya ce ta fara tashi a cikin gidan, cike da ladabi Sadiya ta amsa, sai dai fitowarta daga ɗakin domin yi wa Hajiya iso lokacin Kalifa yana biye da ita dama wanka ta masa tana shafa masa mai. Gabaɗaya fuskar Hajiya a haɗe take tamkar an faɗa mata mutuwa ko wani mugun abu, amma sai Sadiya ta daure ta ce "Sannu da zuwa Hajiya bismillah ki shigo" Wani kallo ta jefi Sadiyar da shi ta ce "Ba abin da ya kawoni ba kenan, ko an ce miki zama na zo idan zaman nake son yi in zauna a gidana a ɗakina mana, kin san dai ai kujeruna sun fi naki komai sau miliyan" Sadiya ta ji babu daɗi a ranta amma sai ta danne ta yi murmushin yaƙe wanda iyakarsa leɓe ta ce "Haka ne sun fi nawa " Wani kallon ke kika sani Hajiya ta mata ta ce "Nasir ya je mini da wata maganar banza wai ciki ne da ke" Abin ya yi wa Sadiya ciwo wato cikin sunna ne ma maganar banza hakan ya sa ta ce ."Eh gaskiya ne" Hajiya ta ɗan yi mamakin amsar da Sadiya ta bata duba da Sadiyar bata fiya kausasa harshen ba amma amsar tata sai ta ji tamkar dai a fitsarance ta yi amma sai ta ce "To abin da nake so da ke shi ne, mun yanke shawara da Nasir da ƴan uwansa cewa wannan ciki zubar da shi za a yi" Da sauri Sadiya ta ɗago kai tana kallon Hajiya cike da mamakin kalamanta. *BABA* Duk kiran da yake yi wa Sumy tana jinsa amma ta ƙi amsawa hakan ya sa ya fara rafkawa Mama Talatuwa kira, Mama jin kiran ta tunkari ɗakinsa tana zuwa ta ganshi a ƙasa a kwance yana sharɓa uban gumi ta ce "Subhanallahi Malam lafiya" Baba da ya buɗe baki zai bata amsa jin gudawar ta taho sai ya ji tamkar idan ya buɗe baki kashin zubowa zai yi bai yi wata-wata ba ya sake komawa banɗaki, sai gashi yana tafiya yana ɗan sunkuyawa yana dafa bango yana faɗin "Wayyo Allah, gaskiya gudawa bata da daɗi ko in ce bata da imani, kalli yadda ta ƙarar min da ƙarfi lokaci guda, ɗan katan daɗi da na ci duk ta saka na kai masai(Toilet ) Haba ai sai na gwammace daman awara na ci don ji ba don idan ban yi gudawar nan ba a wando za ta zubo da ba zan yarda in yi kashin abinci ƴan gayun nan da na ci ba" Tana ta kallonsa har ta samu ya zauna tana son amayar da magana amma tana tsoron masfifarsa sai da ya zauna da sauri ya zame ya kwanta yana cew "Ni wallahi ina ga mazaunan nan nawa ba za su zaunu ba ma, kai jama,a lokaci guda mutum lokaci guda ba mutum ba" Mama Talatuwa ta ce "Dama haka cuta take yanzu mutum yanzu gawa... Kafin ta ƙarasa ya ce "A bakin ki Talatuwa kuma sai kin rigani mutuwa, ni nan tsawon rai zan yi sai na haifi na miji ko kangararre ne ya taimaka min na san daɗin haihuwa sannan zan mutu" Cike da mamakin maganarsa ta ce "Allah ya huci zuciyarka dama ni ban maka fatan mutuwa ba, ai cuta ba mutuwa ba ce" Shiru ya yi don jin cikinsa yana kartawa ya ce "Ki nemo Sumayya ta kawo min maganin gudawar da Habiba ta bata ta saya da safe" Da to ta amsa ta tashi ta fito, ɗaki ta nufa ta samu Sumy ta ce "Sumayya Babanku ya ce ki kai masa maganin gudawa" Shiru ta yi sai kuma ta tashi ta fita, tana zuwa ɗakinsa ya fara masifa "Ke saboda ke shegiyar yarinya ce ina wannan halin amma ba za ki kawo min maganin ba?" Tana danne ƴar dariyarta ganin Baban ya yi zuru-zuru don ta tuna matsayinsa na mahaifinta bai nuna tausayawa ba gareta ya bata kuɗin maganin ba sai yanzu kuma zai ce ta bashi hakan ya sa ta ce "Baba dama fa guda huɗu ne ni kuma duka na shanye" Cike da masifa ya ce "Si kike dai in fitar da kuɗi ko in banda ma almubazzaranci a ce magani biyu ma bai isa ki shanyw ba sai kin sha huɗu" Bata yi magana ba ya ce "Ai kuwa da in banda hamsin ko ɗari a siyo min maganin gwara na zauna gudawar da kanta in ta gaji da fitowa ta tsaya min" Haka Baba ya yi ta gudawa har dare amma bai sha magani ba, sai da ya ga yana dab da rasa ransa sannan ya bada naira hamsin aka siyo masa ya sha. Washe gari ma haka gudawar ta dawo don haka ya galabaita ma, sai masifa yake yana cewa ƴaƴansa basu da amfani da a ce maza ne da yanzu sun kai shi asibiti Arfat ce ta lallaɓa lokacin baccin wahala ya ɗauke shi ta je ta auno shinkafa kwano biyu ta ɗora ta dafa ta lallaɓa aljihun rigarsa ta ɗauki dubu biyar ta yi miya har da naɓa don dama mahaifiyarta ce da girki. Aka dafa shinkafar nan har dare kowa yake wadaƙa da ita ya ci ya ƙoshi don dama cikin wacce ya noma ce da ya jibge sai kayan abinci sun yi tsada zai fito da ita ya sayar, shi ma da ya tashi haka Mama Bilki ta kai masa shinkafa da miya da nama ya karɓe ya ci yana ta saka albarkar cewa ashe tana son sa tun da har bakin girkinta tana sayen abinci ta dafa kowa ya ci lallai yana alfahri da ita. Ko kaɗan bai san cewa abincinsa ba ne kuma a aljihunsa aka samu kuma a aljihunsa kuɗin cefanan ma ya fita, yana da halin da zai wadata iyalansa amma ya gwammace ya musu ƙwauro ya ce kowacce ta je ta nema ba ya musu kallon su mata ne kuma ba ya tsoron hakan ya zama hanyar lalacewarsu. *JIDDA* Daga ita har sauran wanda suke kusa da su na motar kallon Aliya suke, hatta direban motar sai da ya taka wani uban birkin da sai da wanda yake bayansa ya kusa buga masa tasa motar, Allah ya rufa asiri ma lokacin ba wani gudu ake yi ba tun da suna ƙoƙarin kutsa kai cikin gidan Jiddan ne. Kowa ya hau tambayar ko lafiya, shi dai direban ƙarasawa ya yi ciki ya yi parkin don duk girman gidan sai da gabaɗaya motocin suka shiga ciki. Ƴar uwar Ummar ce ta ce "Lafiyarki Aliya mai yake damunki" Aliya da shigowarsu cikin get ɗin gidan ya sa ta sake susucewa hankalinta ya ɗuguzuma da tashi, ganin gidan da ƙwayaye tarrr ya haske ko ina kamar rana ga motoci ne tamkar wajen aiyar da su suna gefe a lulluɓe, hakan ya sa ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu. Ita ma ƴar uwar Abban ta ce "Ko dai jifa aka yi wa yarinyar nan ne a kan aure in ba haka ba yanzu nan take lafiya ƙalau amma kuma a ce ta gigice haka?" Ƴar uwar Umma wacce ranta gabaɗaya ya ɓaci na ganin gidan Jiddan ta ce "Allah ne ya san karatun kurma" Jidda kuma duk ranta ya sosu ta ce "Aliya mene ne ?" Aliya ji ta yi da Jidda ta yi magana tamkar ta ɗauki wuƙa ta daɓawa Jiddar ai dai dole idan Jiddar ta mutu Ibrahim ya aure ta, ta zauna a wannan gidan mai kyau wanda a ganinta kowacce mace za ta yi buri da mafarkin samu!. Direban ma gabaɗaya ya maido hankalinsa kansu shi da abokinsa na gafensa, Aliya kuma da sauri ta danne abin da take ji ta tattaro nutsuwar ta ta buɗi baki tana mai miƙa hannu wajen ƙafarta ta ce "Wani abu ne na ji ya cije ni a ƙafa ta" Ƙofofin motar aka buɗe suka suka fito sauran jama'a kuwa da basu san mai yake faruwa ba duk sun fito daga motocinsu suna shige ciki suna son ba idanunsu abinci domin su kashe ƙwarƙwatar idanunsu, haske-haske aka shiga yi ƙasan kujerun amma ba a ga komai ba, har ma ana tunanin ko kunama ce amma ta ce ba kunama ba ce. Ƴar uwar Umma ce ta kama lafayar ta rufa mata tare da riƙe hannunta, a inda ƴar uwar Abba ta kama Jidda wacce duk ta shiga damuwa da yanayin da ta ga Aliya. Ƙofar sa za ta sada su da ainihin cikin gidan suka nufa mata sai sakin guɗa ake yi, amma Aliya suna dab da shigewa ƙofar ta ja ta tsaya ta ce "Aunty ni ba zan shiga ba" Ƴar uwar Umma ta ce "Me ya sa mu shiga mana ki raka ƴar uwarki kin san dai ba zama za a yi ba yanzu za a fito a tafi raka ki naki ɗakin, kuma kin san dai Abbanku yance hatta ƙawaye kar a bar kowa a gidan amarya su zauna wani siyan baki gabaɗaya za a tafi a bar amarya" Aliya wacce take jin idan ta shiga ciki ta ga ɗakunan tamkar za ta haɗu da taɓin hankali hakan ya sa ta ƙara togewa duk wanda ya zo sai ya raɓe su ya wuce. Ƴar uwar Umma ta rasa ya za ta mata gashi dai ita bata shiga ba, suna nan sai ga wasu daga cikin matan sun fara fitowa suna shiga mota hakan ya sa Auntyn ta kama Aliya ta mayar da ita motar duk da motar ma tana ɗaya daga cikin motocin da suka zo ɗaukan Jidda daga ɓangaren Ibrahim. A can ciki kuwa tun da aka shiga da Jidda bata bari addu'a ta kufce mata ba, don sai da ta yi lokacin fitowa daga gida, da za su shiga gidan nata ma ta yi a zuciyarta duk da lokacin ne Aliya ta tada musu hankali. Har aka zaunar da ita a bakin gado tana ta maimaita addu'o,in neman tsari inda mutane suke ta mata sam barka da addu'ar zaman lafiya, wasu kuma ƴan baƙin ciki suna taɓe baki musamman Amatullahi ƙawar Aliya wacce take jin haushin ni'imar da Jiddar ta samu, wasu kuma suna mata fatan alkairi, wasu suna jin dama su ne suka samu wannan daukar da wannan kyakkyawan mijin, don kana shigowa babban falon da tangamemen hoton Ibrahim za ka ci karo yana wannan kyakkyawan murmushin nasa mai tafiya da zukatan ƴan mata da yawa!. Jidda tana bakin gadon a zaune tana lulluɓe kanta a sunkuye sai wasa take da yatsunta da suka sha kyakkyawan ƙunshin baƙi da ja duk da kasancewarta baƙa amma lallan ya haska hannun tamkar ka gudu da hannun. Sai dai idanunta yana ta hawaye rana ta tuna mahaifanta sannan zuciyarta a cunkushe da damuwar da ta lura ƴar uwarta Aliya. Salama ce ta je ta dafa ta ta ce "To amarya za mu tafi sai mun sake dawowa, a toh wallahi ba don Abba ya hana a zauna ba da sai na jira zuwan abokan ango!" Ta faɗa tana dariyar wasa Jidda ta buɗe dashashshiyar muryarta ta ce "To yanzu ma sai ki zauna" Murya Salama ta rage tana magana ƙasa-ƙasa ta ce "Ko na zauna na miki zaman ɗaki?" Daga cikin lafayan take kallon ta Jidda da take kallonta don ta san zolayarta ne take yi. Jin Jiddar bata ce komai ba sai ta ɗora da faɗin "Taɓ ba zan zauna ba wannan angon naki ya yi ƙuli-ƙulin kubra da ni don daga gani ya shiryawa wannan ranar a toh za a kashe arna" Wata ƙawarsu da ta zo kusa da su ta ce "Ai yau angon nan va arna kawai zai kashe ba musulmin ba ba zai barsu ba" Suka fashe da dariyar zolaya ita da Salama duk Jidda tana jinsu. Jin ana ta horn suka fara mata sallama suna fitowa. Ƴar uwar Abba ko da ta fito ganin Aunty da Aliya a tsaye a gefe da Amatullahi ta ce "Haba Aliya ai dai kin raka ƴar uwarki ɗaki kun yi sallama amma ji zo har cikin gidan baki shiga ɗakin ba wannan ai sai wani ya ɗauka wani abu ne, kin san dai mutane ba a iya musu" Jin hakan sai Aliya ta yi tunanin kar Jidda ta yi tunanin wani abu da ban hakan ya sa ta ce za ta shiga don yanzu ba ta son wani abu da zai nuna rashin ƙaunar Jidda a tattarw da ita, duk da ta ciki na ciki, ta fi so suke basaja kamar yadda suka shirya hakan da Umma. Ƴar uwar Abban ce ma ta kama hannunta suka nufi ciki, Aliya daga cikin laffayar ta kafe hoton Ibrahim da yake kafe a falon a take ta ji wani abu ya tsarga mata, tana tunanin da a ce ita ce yau a wannan gidan da kuma wannan mijin lallai da ƙawaye da dangi sai sun raina kansu amma dai gashi Allah ya san halin jaki da bai bashi ƙaho ba!. Dakyar take taka ƙafafunta daurewa kawai take, a haka suka wuce ɗakin da Jidda take wanda a ƙasa yake ba a sama ba, wani sanyi da ni,imtaccen ƙamshin turarukan wuta wanda aka siya a wajen Zainab Muhammad tahir wacce take da zafafan turarukan wuta ƴan sudan kowa ya san yadda turarukan wutan sudan suke da ƙamshi nata sun sha bamban domin turarukan wutan suna kama ɗaki ƙamshin su mai daɗi da sanyaya rai 0814 209 8878 ta number wannan suka mata magana suka mallaki nasu ga duk mai buƙata zai mata magana tana siyar da ɗaya tana bada sari a farashin sauƙi siyan na gari mayar da kuɗi gida!. Yanayin yadda kayan ɗakin suka karɓi ɗakin tamkar dama don su aka ƙera ɗakin tangameman wadataccen ɗaki, Allah ne kawai ya sa Aliya bata yanke jiki ta faɗi ba, ko da suka shiga ɗakin cikin ƙarfin hali ta furta "Jidda!" Jidda ta ɗago kai tana kallon Aliya ta amsa kawai sai Aliya ta je gaban gadon ta rungume Jidda tana sakin kuka, a zahiri kukan rabuwa ne amma a baɗini kukan baƙin ciki ne. Jidda ma ta fashe da kukan sai da suka yi mai isar su ƴar uwar Abban tana basu haƙuri kafin Aliya ta ce "Jidda ƴar uwata ƙawata da bani da tamkar ki, mun zauna shekara da shekaru amma yau aure zai raba tsakaninmu sai dai zumunci amma babu kwanan gida ɗaya a ɗaki ɗaya, ina roƙon ki yafe min iya zamanmu sannan ina miki fatab alkairi" Jidda jin kalaman bogin da Aliya ta yi sai zuciyarta ta yi rauni hakan ya sa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tana cewa ta yafe mata ita ma ta yafe mata, haka aka fita da Aliya rai cike damƙuna da hassada!. Sun saka ta a mota tana ta kuka wanda kukan ya zame mata biyu, hassada babban ciwo da kuma kukan zuwa gidanta da take ganin bashi da maraba da kurkuku a wajenta ita yanzu sam Kasim ba ya birgeta. Jidda lokacin da ta ji rufowar get sai gabaɗaya ta fashe da kuka har da sheshsheka. Bayan kamar minti hamsin ta ji horn da kuma ƙaran buɗe get, shigowar motoci ta ji amma dai ba za ta bambance biyu ne ko uku ba, jim kaɗan ta fara jin ƙaran rufe ƙofofin alamun fitowar wanda suke cikin motar. Hayaniya ta fara jiyowa a falon inda take jiyo muryar Ibrahim yana faɗin "Daga na kirawo ta kun gaisa za ku fita ku tafi gwauraye su je ɗakin gauranci masu aure su tafi wajen matansu" Ya faɗa cike da zolaya. Tana jin yadda falon ya kaure da maganganinsu amma bata iya gane mai suke cewa sai dai ta san tsiya ce suke masa don ta ji sai dariya suke yi. Shigowarsa ɗakin ya sanya gabanta faɗuwa, sai ta ji duk wani nauyinsa take ji tamkar dai ba wannan Ibrahim ɗin nata da suke kasancewa kullum a waya suna magana ba ko idan sun haɗu kamar ba za su rabu ba. Duk wata kunya ta rufe ta sai take jin dama su Salama basu tafi ba duk da ta san umarnin Abba ne hakan, amma a ganinta da suna nan za ta ji sauƙin kunyar da ta mata ƙawanya a zuciya duk da ta san dai ko suna nan dole za su tafi ba za su kwana a gidan ba. Abin mamaki lallai sai lokacin ta tabbatar maza basu da kunya ita tana jin nauyinsa da kunyarsa da ya shigo ɗakin amma shi kuma yana kusanto kansa gareta, domin bai yi wa kansa masauki a ko ina ba sai a kan gadon inda take zaune ya zauna dab da ita kafaɗarsa tana gugar tata kafaɗar, wani ƙamshin turarensa wanda take jin na yau ya sha bamban da na kowacce rana ko don kasancewar yau ranar ta musamman ce a tarihin rayuwarsu Allah masani. Yana zama sai ta ji tamkar ta nutse jin jikinsa yana gugar nata, abu ne sabo tsakaninsu da bai taɓa faruwa ba ko ta ce abu ne sabo wanda a iya rayuwarta bata taɓa kasancewa da wani ɗa namiji da kusanci kamar hakan ba, sai ta ji duk jikinta ya fara wata irin tsuma. Tana cikin wannan tunanin sai kawai ta ji ya ɗora hannunsa a kan hannuwanta da take wasa da su, wani irin yammm ta ji tamkar an haɗa shokin bata san lokacin da ta yi saurin janye hannun ba, sai dai saurin ƙara riƙo hannun nata wannan karon hannu biyu ya saka ya riƙe nata, cikin wata murya mai sanyi da daɗin amon a kunnen mai sauraro kuma ga ma,abota soyayya ya ce "Habibty an zo lafiya?" Bakinta bai bata haɗin kai ba wajen bashi amsa sai ta ji ya sake ɗorawa da faɗin "Ina fatan kin zo da shirin tarɓar mai gidan naki domin kuwa zai zame miki raƙumi da akala, sannan zai zama tamkar ƙaramin yaro a wajenki karki manta sarauniya kike a fadata, amma ni zan zama tamkar bawa a fadar sarki a gare ki wallahi ina sonki Jidda ba zan iya daina sonki ba har ƙarshen numfashina!" Kalmomin nan da ya ambata sun sanya kunnuwana yin dummm har lokacin ban ce komai ba sai ya saki hannun ya ɗage laffayar da ta masa shamaki da ganin fuskata, yana buɗewa ya yi saurin saka hannu yana share lemar hawayen da suke kwance a fuskata sannan ya ce "Karki ƙara zubar mini da hawayenki, hawayenki suna da matuƙar muhimmanci Jidda kin zo inda ba za ki sake zubar da su ba sai dai kukan daɗi amma ba na baƙin ciki ba, aure ana yinsa ne don faranta ran juna ni kuma zan zamo mai faranta miki, zan zama daban a cikin maza je, don sai na saka kin zama da ban a cikin mataye" Mainakon in daina kukan kamar yadda ya ambata sai wasu sabbin hawayen suka zubo don in har abin da yake faɗa haka ne haƙiƙa na yi dace da miji na gari kuma mijin ƙwarai. Ban yi zato ko ankara ba sai na ji ya rungumeni wani irin fargaba na ji kasancewar karo na farko a rayuwata da faruwar hakan, ɗiff na yi ina jin yadda ƙirjina yake dakan lugude, shi kuma Ibrahim bai ma san mai take yi ba abu ɗaya ya sani hakan ya haifar masa da wata irin nutsuwa mai wuyar misaltawa. Kiran da Abeed ya shiga masa shi ya ankarar da shi, da sauri ya sake ni yana faɗin "Taso mu je kar wannan ya fasa min dodon kunne" Yana faɗar hakan ya miƙe tsaye, tare da kama hannuna na miƙe ya saka hannu ya lulluɓe min fuskar kamar yadda ya same ta a lalluɓe yana faɗin "Kar a gane min fuskar amaryata, ni dama in ban da sun kafa min tsiya da babu wanda zai rako ni" Ni dai ban ce komai ba kawai dai na ji hannunsa cikin nawa ya kama, babu yadda na iya haka na biyo shi muka fito kunya duk kamar na nutse. Tun da muka zo falon suka mana caaa wai mun Ibrahim ya ƙule da amarya a ɗaki ya manta da su, shi dai cewa yake "Ko ma mai na yi ai ba haramun ba ne" Suna ta wasa da dariya, ya zaunar da ni tare da zama a kusa da ni, nan aka shiga yin addu'o i da kuma mana ƴan nasihohi daga ƙarshe suka mana fatan alkairi suka mana sallama suna cewa ya zo ya raka su yana faɗin ai ko nan da ƙofa ba zai fita ba, haka suka tafi suna mana tsiya, ina jin lokacin da suka fice mai gadi ya rufo get ɗin. Suna fita ya buɗe min fuskar ya kama ni, wani ɗaki muka shiga kusa da ɗakin da aka kaini, komai na ɗakin sabo dal amma ba kayan ɗakin da Abba ya saya min ba ne na ɗakin da aka kaini nan ne kayan da Abba ya saya mana, haka ma kujerun falon, banɗaki muka shiga tare bayan mun saka takalman da suke ƙofar bayan sabbin silifas ne yellow da kuma ja. Ni dai na tokare a bakin ƙofa na sunkuyar da kai ganin haka ya shiga yin uzurinsa ni dai ina jin ƙaran ruwa amma ban san ruwa yake kamawa ba ko kuwa alwala, jim kaɗan ya ce "Wuce ki yi alwala ko kuma ni in zo in miki... Tun kafin ya ƙarasa na rama gefensa na wuce kasancewar banɗakin ma yana da girma tamkar ba banɗaki ba. Shi kuma dariya na ga ya min sai ya ɗaga hannu ya fatsa min guntun ruwan hannun nasa a fuska, har hakan ya sa na murmusa, juyawa ya yi ya fita yana dariya ni kuma na yi tsarki tare da yin alwala na fito, a ɗakin na ga ya shimfiɗa sallaya gida biyu, ɗaya tashi a gaba tawa a baya haka ya yi kabbara muka gabatar da nafila raka'a biyu bayan mun salance ya ɗaga hannu ya yi addu'a muka shafa. Bayan ya juyo ya dafa kaina ya yi addu'a sannan ya tashi ya fita jim kaɗan ya dawo ɗauke da leda babba sai kuma plates. Bayan ya ajiye ya fita sai gashi ya dawo da lemuka da madara masu sanyi ya jera ya koma ya ɗakko kofuna na glass duk tana kallonsa sannan ya dawo ya zuba komai sai ya ce "Ki sa hannu mu ci" Ta ce "Na ƙoshi" Hannu ya kai ta lakato hancinta ya cr "Yau akwai ɗura kenan" Idanu ta ɗaga tana kalle shi tare da sauke idanun a kan gasashshsiyar kazar da take ta turiri kai ta shiga girgizawa kafin ta samu furta wani abu sai gani ta yi ya yago naman kazar tsoka ya nufi bakinta tare da faɗin "Jiddanah yi bismillah" ,Yadda ya yi furucin kawai ya isa ya nuna maka tabbas yana cikin mazan da zai ba mace kyakkyawar kulawa da nuna soyayya a zaman aure!. *ALIYA* Tun da suka fito daga gidan Jidda ranta yake suya ji take dama a ce mafarki ne take ba wai zahiri ba. Motoci suna ta wulwula gudu saman titi tana zancen zuci cewa yanzu duk rabi da kwatan motocin na domin ɗaukan Jidda suka zo ita kawai albarkaci take ci. Sun yi tafiyar mai nisa kafin suka kusa wata unguwa da hasken fitilun motocin ne kawai suka haske unguwar, motar gaba wacce ita ce abokin Kasim yake ciki su ne jagora zuwa gidan amarya Aliya, Aliya sai saukar guɗar mata take ji kamar za su cire hanci ita kuma tana jin guɗar har tsakiyar kanta. Wani gida madaidaici wanda yake ɗan sheƙin fenti don yanzu tana satar kallon windown don ta ga gidan da za a kaita hasken fitilun ne suka nuna mata sabon fentin da aka yi wa gidan, don motocin da suke gaba sun fara tsayawa a saitin gidan, idanu ta runtse da ƙarfi tana jin tsanar Kasim a ranta, ganin gidan Jidda duk yawan motocin sai da suka samu matsugunni a cikin gidan amma sai gashi ita babu get ɗin da ko mota ɗaya za ta samu mafaka, hasali ma ƙaramar ƙofa ce a gidan, ba ma wannan ne abin mamaki ba yadda bata hango hasken ƙwan fitila a gidan ba sai ta fara zancen zuci tana faɗin 'Kar dai Kasim don baƙin talauci inji ma bai saya ba, saboda babu nepa a ce gidan amarya, amaryar ma kamar ni amma babu haske?' Ta faɗa a zuciyarta tana saka haƙorin sama na bakinta ta dantse leɓenta na ƙasa bata ankara ba ta ji Aunty ƴar uwar Umma tana faɗin "Fito da Bismillah Aliya, kin zo gidanki, ki shiga da addu'a Allah sa gidan zamanki ne Allah sa abokin rayuwa ne sai mutuwa ce za ta raba" A fili Aliya ta sako ƙafarta ta fito a zuciyarta kuma ta ce 'Ba amin ba' Ƴar uwar Abba ita ce ta amsa da amin, mata kuwa sai guɗa suke rafkawa an samu abin da ake so, mata kenan akwai son shagalin biki su dai su je biki (Lol) An fara cusuwa zauren gidan inda ake ta faɗin "A jira wasu su gama shiga mana, ai zauren ne ƙarami" Aliya da ake riƙe da ita kamar ta kurma inu haka take ji, sun shigowa gidan hakan ua yi daidai da jan ƙaramin inji da aka yi wato aka tada, amma wajen ja uku injin bai tashi ba, a ja na huɗun ne sai ga haske tarrr ya haske gidan, mata aka fara faɗin "Haba haske ai rahma ne" Wata mata da Aliya bata gane wace ce ba sai ji Aliya ta yi ta ce "Gidan Jidda kuwa haske tarr har muka tafi bamu san ma ta inda hasken yake zuwa ba babu ƙara injin" Wata ta kusa da ita ta ce "To ko sola ce" Sai matar ta ce "Abinki da babban gida wataƙila wajen injin ma da aka tanafa na musamman ne yadda ba zai damu masu gidan ba" Aliya kamar ta zazzage su haka ta ji. Falon aka shiga da amarya, hakan ya yi daidai da mutuwar injin sai fitulun waya aka kunna wata mata tana faɗin "Gyara fa ake yi shi ya sa" Ɗakin aka wuce da amarya tana ganin ɗakin na Jidda ya yj biyar ɗin nata, Jidda ta samu komai idan ta ce komai tana nufin komai ciki kuwa har da kyakkyawan miji. Har aka watse in ji bai tashi ba tana jin ƙaran ƙwale-ƙwalen ƙarafe a tsakar gidan da tashin maganar mutanen guda biyu, da alama ma in jin ba sabo ba ne ko kuma dai matsala ya bayar. Tana jin motocin suka tashi suka tafi, tana zaune dilim a duhu sai hasken fashashshen screen ɗin wayarta. Lulluɓin ta fisge tana ƙarewa ɗakin kallo ɗakin ya yi kyau babu laifi har jeren da aka yi amma saboda hassada da hangen na sama da ita gabaɗaya baƙin gidan da ɗakin take gani Sai da aka yi wajen minti talatin kafin suka samu injin ya tashi, sallamar Kasim da wasu da bata san su waye ba ta ɗauki dai muryar abokinsa Salis, tana ji masu gyaran injin suka tafi su kuma suka shigo falon suka zazzauna, suna ta yi masa tsiya ango na amarya tana jin suna faɗin "Wai ina amaryar ne?" Kasim ya ce "To ku haka za ku ga amarya ba a muku iso ba, ai sai na nema muku izini sannan zan kawo maka ita" Gabaɗaya suka hau masa tsiya shi dai ya nufi ɗakin domin kawo amarya. Maimakon ya ganta a lulluɓe sai ya ga fuskarta warai babu lulluɓi abin ya ɗaure masa kai ma tamkarnwata zararriya haka ya ganta, mamakinsa ya danne ya ƙarasa yana sakin yaƙe duk da gabansa yana faɗuwa don ya san ko kaɗan Aliya bata ɗokin aurensa tun daga ranar da ya kai lefe a baro. Zaunawa zai yj sai ya ji a faɗace ta ce "Karka zauna a kusa da ni don ban gayyatoka ba" Fasa zaman ya yi ya shiga mata nuni da hannu yana mata alama cewa da mutane a falo a gefe ɗaya yana mata alama da cewa ta yi ƙasa da muryarta. Cikin hargagi ta ce "Ina ruwana da mutane, ko akwai wanda na kaiwa katin gayyata, da suka kwaso koɗaɗɗun ƙafafu suka zo, to yadda suka zo haka za su ɗauki ƙafa su koma inda suka fito" Kalamanta sun kusa saka ya zauce saboda ɗimuwa, ya san dai duk abokansa sun ji abin da ta ce, bai taɓa zato ko tsammanin hakan ba, wannan ranar babbar rana ce a gare shi mai ɗimbin tarihi amma yanayin Aliya ya nuna so take ta rusa komai, so take ta tada fitina, so take ta shayar da shi ruwan guba mai ɗaci ba ruwan zuma ba, a ce a ranar farkonta a gidansa tana magana kamar za ta kai masa duka anya zaman zai iyu?. Kafin ya gama shan ruwan mamakin da Aliya ta shayar da shi, ji yake kamar ya nutse don kunya shi bai ma san ta ina zai fita falo kuma da wane ido zai kalli abokan nasa ba don ya san sun ji komai, kawai sai ya ga ta miƙe tsaye ta shiga warware laffayar jikinta, ya zamana daga ita sai leshin jikinta, wanda ya matuƙar amsar kyakkyawar fatar jikinta baƙin lalle da ja da ya ƙara haska kyakkyawar fatarta, ji yake yana son kaɗaicewa da ita a wannan daren mai ɗimbin tarihi amma hakan zai iyu?. Na ce muku hakan zai iyu😃😃😃 ku bani amsa wato cmmnt ma sai kun bushi iska kuke yi a toh nima ai kuna gani a ƙwaryar shanku sai na bushi iska nake typin😒😕 labarin nan yana da tsayi akwai darasi akwai cakwakiya, abubuwa masu kamar almara za ku ji yadda.... Ba zan dai faɗa ba kawai ku biyoni mu cigaba da tafiya ko ni ina jin labarin a cikin raina. MAMAN AFRAH 09025576222 https://chat.whatsapp.com/I3Lo5jRFh1CDcU1leu8VXW *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️⃣3️⃣ *SADIYA* Maganar Hajiya ta saka Sadiyar shiga ruɗani sannan abu ne wanda bata taɓa zaton cewa ko a mafarki Hajiyar za ta ambata ba, domin cikin ai ba na shege ba ne da za a yi maganar zubar da shi. Maganar da Hajiya ta ƙara yi ne ya dawo da ita hayyacinta jin Hajiyar tana faɗin "Don haka ki ɗakko mayafi ki zo mu tafi a cire cikin, saboda gidan nan ba matattarar yara va ce ta yaya za a ce daga yin yaye har kin sake ɗurar wani cikin " Cike da jin nauyi da kuma jin kunya Sadiya ta ce "Hajiya ni ma Allah ne ya ƙaddara ya bani wallahi ba da sani na ba ne... Hajiya tana ɗaga mata hannu a harzuƙe ta ce "Sadiya an ce miki jahila ce ni ban san Allah yake bayarwa ba?" Kai Sadiya ta shiga girgizawa alamar a'a, Hajiya bata jira cewar Sadiya ba ta ɗora cike da ɓacin rai take faɗin "Ke duk ƴan dabarun nan na mata bakya yi, shin mai ya sa vaki saka tsinke a hannu ba ko kuma kin je an saka miki na bakin mahaifa, ko ki sha magani abubuwan tsarin iyali gasu nan barkatai amma kika yi hirim da ke kika sake ɗaukar ciki, saboda baƙin hali da mugun kishi saboda za a yi amarya ku mata dama damuwarku gado shi ya sa baku da aiki sai gasa a haihuwa so kike kafin ta zo kin tara bataliyar ƴaƴa yadda ba za ta taddo ki ba, to albishirinki ba wani dogon lokaci za a ɗauka ba da har kike tunanin tara ƴaƴa a kwana kusa Nasir zai angwance" Idanu Sadiya ta ɗaga ta kalli Hajiya sai kuma ta sunkuyar da kai. Hajiya ta ƙara kallon Sadiyar kallo irin na ƙasƙanci don ita duk ladabi da biyayyar Sadiya da kuma haƙuri ba wani birgeta yake yi ba ta ce "Ina so ki sani ciki dole a zubar da shi idan kuma har ƙin ƙi to shawara ta ragewa mai shiga rijiya, ko ya faɗa ko kuma ya sauya shawara, zaɓi biyu ne ko dai ki yarda a zubar ko kuma ki zauna ki raini cikin amma ki sani ɗawainiya ce kika ƙarawa kanki, don Nasir bashi da ƙarfin riƙe mata biyu da yara biyu a yanzu ga kuma hada-hadar shirye-shiryen aurensa shin da wanne zai ji? Wallahi wasu matan baku da lissafi" Sadiya a fili ta ce "Ki yi haƙuri Hajiya amma ba zan iya kisan kai ba" A zuciyarta kuma ta ce 'Duk irin rufin asirin da yake da shi ai a samun Nasir ko ƴaƴa goma ne ba zai gagara ya riƙe ba amma saboda son zuciya da sarewa sannan kuma bai yi dacen mahaifiya ba shi ne kuke raina ni'imar da Allah ya bashi' Hajiya ta sake cewa "Dama na zo in kai ki a zubar ne amma tun da kin ce kin ji kin gani to ga wajen nan" Tana faɗar hakan ta juya ta fice, zuwa jimawa can sai ga Nasir kamar an jefo shi mamaki ma take dama bai tafi wajen kasuwancin ba, ko arziƙin sallama basu samu ba haka ya shigo kamar wanda ya zo filin yaƙi, yana shigowa ya ce "Sadiya wato kin rainani kin raina mahaifiyata, Hajiya ta zo har gidan nan amma ki ambula mata ƙasa a ido ke ga ishashshiya da mai ko? To ki sani tun da kika ƙi zubar cikin nan ni ba zan dawwama da wahala ba kullum kuna jinya ke da yara ga shirin auren nan" Ya faɗa yana tada jijiyoyin wuya. Sadiya a zuciyarta ta ce 'Wai namiji da Allah ya ɗora masa gabaɗaya ɗawainiyanda kulawa da iyalansa amma shi ne yake gajiyawa, bayan babu wani abu da Allah ya ɗorawa mace ta sayawa kanta ko ta sayawa ƴaƴa sai dai don kyauatatawa gabaɗaya ɗawainiya kan namiji take kama daga ciyarwa shayarwa tufatarwa lafiya da sauran abubuwan da baki ba zai iya furtawa ba' Ganin ban ce komai ba ya ce "Aure dai babu fashi idan ma kin yi haka ne don in ji tsoron ɗaukar ɗawainiya in janye batun aurena, ko kina so ko bakya so sai wata ta shigo gidan nan, don mi ban gina gidana don mace ɗaya ta zauna ba, ni mijin mace huɗu ne!". Cikin halin nuna tashin damuwa da kalamansa ta ce "Allah nuna mana, ya sanya alkairi!." Wannan maganr da ta yi ta ƙara fusata shi, ya so a ce ta ji haushi ya ƙuntata mata amma sai ya ga bata damu ba, a zuciyarta ta ce 'Mace tana kishi ne a inda aka san darajarta, zuciya tana damuwa da wanda ya damu da ita ne wannan shi ne cancanta mafi daraja amma mijin da bai ɗaukeka a bakin komai ba mijin da yake wulaƙanta ka kishin mai za ka yi a kansa?' Kamar zai kai mata duka ya ce "Idan ma ba har zuciyarki kika faɗa ba can ta matse miki" Yana faɗar hakan fuuuu ya fice daga gidan, Sadiya tana mamakin mahaifiyar Nasir da bata kawo zaman lafiya a cikin gidansa ita da ƴaƴanta kullum ƙoƙarinsu su famfa shi, su rura wutar gutsiri tsoma a gidan bata tunanin su Husna ma mata ne kuma dole watarana gidan miji za a kai su, basa ma tsoron a musu abin da suke yi wa wani tun da duk abin da mutum ya yi shi ake yi masa. Tun daga wannan rana sai al'amura suka ƙara taɓarɓarewa a cikin gidan, idan Nasir ya bada ɗanyen abincin da ba zai isa su ci ba sannan sai ya hana kuɗin cefane, gashi babu abin da take siyarwa bare ta samu abin da za ta yi amfani da shi, ta yi masa magiya har ta gaji amma ko a kwalar rigarsa, sannan wani abin ɓacin ran ta fahimci yanzu abincin gidan ma sai ya ga dama yake ci, sai dai ita da Kalifa su ci wataran ma sai dai ta saka musu ɗan gishiri su ci ko babu mai don yanzu abin na Nasir ya ta,azzara ko maggi ya daina siya bare mai komai yanzu ya janye jikinsa daga siya, ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta. Duk da kasancewarta mace mai sirri da ƙin bankaɗa damuwarta amma haka take faɗawa ƙawarta Noor wasu abubuwan tun da ita Mama ko ta kira ta a waya za ta zayyana mata damuwarta sai ta dakatar da ita idan ma ta fara faɗa sai ta ƙaryata tun da har yau Nasir yana hidima da su in aka shafi kwanaki yana basu kuɗi wannan dalilin ya sa suke ganin ma kawai shaci faɗi ne don dai ta ɓata masa suna. Tun da a ganinsu idan har gida bai ƙoshi ba ai ba a ba wa na waje ba da a ce a gidansa bai wadata su ba ai ba zai ke ba sirikansa ba, basu san duk wannan yana cikin shika-shikan rashin mutuncin Nasir ɗin ba. Noor ita take kwantar mata da hankali sannan ita take bata ɗan wani kuɗin ta saya wani abu da bta da shi, duk da bata fitowa ta faɗi komai da komai sai dai bahaushe ma yana cewa labarin zuciya a tambayi fuska. Akwai lokuta da dama da wani yake cikin damuwa ko cikin halin son a taimaka masa saboda wata matsala amma kuma bakinsa yana da nauyi wajen sanarwa da wasu damuwar tasa, sai dai ba kowane lokaci ne sai mutum ya faɗi ainihin a taimaka masa ba, ko kuma sai ya bayyana buƙatarsa, wani a ɗan fashi baƙin da zia faɗa ko bai warware komai ba hakan ya isa a gane a taimaka masa inda hali ba sai ya yi roƙo ba wani yana jin nauyin ya roƙa, wannan halayyar ce take faruwa tsakanin Noor da Sadiya. A wannan halin ne har ta kwashe wata biyu, sai dai daga ɓangaren Nasir bata sauya zani ba don har lokacin yana nan a kan bakansa na ƙin wadata su, sai kuma ƙuntata mata da ya ci gaba da yi don a zuciyarsa burinsa damuwa ta mata katutun da zai yi sanadin zubewar cikin don shi yanzu buri da fatansa da duk wani tunaninsa yana kan amaryarsa Meenal. A wata ranar talata da safe ta tambaye shi zuwa gidan kakarta mahaifiyar Babanta, hakan ya amince cike da zumuɗi don shi ya fi so ma take yawo amma kullum tana gida bata yawan fita, sannan ya san gidansu ba wani iya riƙe ta za su yi ba shi ya sa ko ta je da wuni uban yake koro ta, wannan ya sa yake cin karensa babu babbaka kuma yake gara Sadiyar don ya san zaman gidansa ya zame mata dole sannan kuma farilla ne tusa a cikin bacci. Ta shirya tsaf ta shirya Kalifa ta rufe gidan duk da akwai tazara amma haka suka yi tafiyar ƙasa don bata da kuɗin napep. Da farinciki Kaka ta tate su tana ta yi wa Kalifa wasa, zama suka yi ta ɗakko fura wacce ta ji nono ishashshe ta dama musu suka sha, sannan Kalifa ya ci gaba da wasan sa. Zuwa can Kaka ta ce "Halima" Sadiya ta amsa Kaka ta ce "Kowa ya ganki ya san kina cikin damuwa dubi yadda duk kika lalace kin yi baƙi kin rame duk kin fita hayyacin ki" Sadiya ta ce. "Kaka ina cikin damuwa tabbas, kuma mafita ce ma bani da ita, kin san dai yadda aka yi auren nan to yanzu Abban Kalifa yana takura min ne kamar ma ya gaji da auren shi kuma Baba ko gidan na je babu wanda yake sauraron damuwar da nake ciki daga shi har Mama, da a ce suna jin damuwata kuma su ja masa kunne da abubuwan za su yi sauƙi, amma sun nuna masa bani da daraja, wataran ma Baban haka zai ce in koma ko da kuwa sun san zaluntata ake yi" Kaka ta ce "Sadiya tabbas Bala ba shi da hali kina gani dai ban isa in shata masa layi a kan komai ba, ni sai in manta ma ban ganshi da idanun nan nawa ba, idan ma ya zo a tsaitsaye zai gaisheni ya kama gabansa" Ta faɗa cike da takaici bata san mai ya sa wasu ƴaƴan ko kaɗan basu san darajar iyayensu ba. Sadiya ta ce "Yanzu babu ruwansa da damuwarmu so yake ma in ke ɗaukan ɗawainiyar kaina tamkar wacce take zaman kanta ko kuma zaman zawarci, wallahi kwanaki har gorin sana'a ya min ni kuma bani da jari sannan shi ba tallafa min ba zai yi" Kaka ta nisa ta ce "Dama idan mace tana gidan aure kuma take son yin sana'a ai mijinta ne zai tallafa mata ya bata jari sannan ya bata ƙwarin gwiwa amma in baka da shi ina ake so ka je ka samo? Ko sata ake son ka yi, wasu mazan basa yi wa kansu adalci suna da halin da za su wadata iyalansu da abu amma sai su hana su sannna su fita waje suna yin bajinta da birge wasu mutanen, in ba bajinta ba ke bai baki ba ya je yana ba iyayenki" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke mai nauyi kafin ta ce "Ai lamarin Nasir sai dai addu'a amma ya fiya son kansa da yawa duk da yana samun gudummuwar mahaifiyarsa" Kaka ta ce "Kowa ya yi na gari kansa Halima, sannan komai zai wuce ya zama kamar ba a yi ba, idan har yana sane yake yi Allah zai ƙwatar miki haƙƙin ki watarana zai gane kurensa sakayya tana nan tun da Allah ba ya yafe laifin wani a kan wani" Sadiya ta ce "Haka ne" Kaka ta ce "Wancan ƙatuwar akuyar tawa zan siyar dama jiya maƙocina ya saya ragon nan da na turki, to zan siyar da ita sai a cika, akwai Fauziya wancan amaryar da gidanta yake kallon gidan nan, na ji tana cigiyar wanda zai saya firjinta da yake ƙarami ne ita kuma tana siyar da pure water da kemon mango, da zuɓo sana'ar ta karɓe ta shi ne take so ta siyar ta sayi babbar freezer, sai in fansa miki nata firjin in auna miki zoɓo in bak ɗan kuɗin da za ki riƙe na siyan pure water ki je ki fara sana'ar kayan sanyin idan Allah ya saka miki albarka sai kin samu warakar wasu matsalolinki" Da sauri Sadiya ta matsa kusa da Kaka ta rungume ta idanunta har da ƙwallar farinciki cike take da murna jin Kakarta ta sama mata mafita abin da mahaifiyarta da ta san ciwonta ta kasa yi mata lallai yau tana cike da murna. Kaka tana ta dariya tare da faɗin kar ta karyata, Kalifa ma ganin abin da yake faruwa ya taho ya zo ya tsaya yana kallonsu yana dariya duk da bai san musabbabin farincikin ba. Ta yi ta godiya ta kuma yi wa Kaka addu'a daga ƙarshe Kaka ta ce mata za ta kira ta a waya idan ana kammala cinikin sai a ba mai baro ya kai mata. Sai da ta yi magriba ta baro gidan Kaka zuciyarta washe. Ko da suka dawo gidan ƙofar babu mukulli da alama mai gidan yana ciki, da sallama ta shigo ya amsa ciki ciki ta masa barka da gida, zaune yake yana cin doya da ƙwai da kuma naman balangu sai lemonsa fanta a gefe doyar ya ɗaukamda naman yanka biyu ya miƙawa Kalifa amma abin mamaki sai Kalifan bai karɓa ba, shi kansa Nasir ya yi mamaki sai ya ɗauki kofi ya tsiyaya lemon ya bashi sai ya karɓa ya sha ya miƙa masa kofin. Tana shirin shiga ɗaki ta ji ya ce "Yau har aka kai dare lallai ko don gidan Kaka ne shi dama Baba ai ba ya ma bari a zauna a gidansa" Bata ce masa komai ba don ta san magana ya yaɓa mata, haka ta shige bedroom ɗin. Da dare bayan ta kwanta, bacci ya kasa ɗaukarta, saboda farincikij da take ciki, ko da ya hayo gadon sai bai mata magana ba ya shiga latsa waya, yau a falo ta yi wa Kalifa shimfiɗa don ra ga ya fara wayo kar wani lokacin ya je ya falka suna wani abin wannan dama lallata tarbiya ne wato kwanciya da yara masu wayo ɗaki ɗaya. Sai da ya gama danne -dannensa ya ajiye wayar ya juyo yana fuskantar ta dama bai kai ga kashe fitilar ɗakin ba ya ce "Sadiya an Baba" Furucinsa kaɗai ya tabbatar mata da cewa lokacin amfaninta ya yi wato lokacin da zai nemi biyan buƙatarsa, tun da a wannan lokacin ne take iya ganin farin haƙorinsa ko mata magana babu hantara. "Uhmm" Ta ce ba tare da ta kalli shi ba. Ya ce "Haƙƙina nake so yau kwana nake so in yi ina aiki" Cike da tsoro ta yi saurin kallonsa ya ɗage gira ɗaya ya ce "Yes" ,Ta marairaice fuska ta ce "Ka ga dai ƙaramin ciki ne da ni amma ya za a yi ka kwana kana abu ɗaya?" ,Ya ce ",Oh wato ke har wani lissafi kike da ban, to ni wannan cikin ma na manta da shi kuma ba na saka shi cikin lissafi" Maganar ta mata ciwo amma ta ƙyale shi, tare da bashi haƙƙinsa sai danya gaji don kansa ya barta, bayan komai ya lafa ta yi wanka ta zo yana zaune yana goge ruwan kansa ta ce "Ina so za mu yi magana" A taƙaice ya ce "Ina jinki" Ya faɗa yana ɗaure fuska dama ta san ƙarshen maganar tun da da ta gama masa amfani. Cike da fargabar amsar sa ta ce "Kaka za ta siya min frige in fara sana'ar siyar da ruwa da zoɓo ina ga har ƙanƙarar yara zan ke siyarwa... Tun bata ƙare maganar ba yake aika mata mugun kallo wani tsoronsa ne ya ɗarsu a ranta don ita bata buƙatar ko kaɗan ya ci mata zarafi baƙaƙen maganganunsa rai suke ɓata mata sai dai ta san akwai lokacin da Allah zai ganar da shi shayi ruwa ne!. Cike da gadara ya hau faɗin "Wato saboda tona min asiri roƙo kika je kika yi don ki zubar mini da mutunci ko Sadiya, to da na ce ki yi sana'a ai ba sanar kayan ruwa za ki yi ba don babu wani ƙato da zii shigo min gida sayen wani abu" Yadda yake rada jijiyoyin wuya kamar dai ba shi ne ya gama samun buƙatarsa yanzu daga gareta ba. Kamar za ta yi kuka ganin tana farincikin samun mafita amma yana neman daƙilewa saboda cuta, tana sassaita kalamanta ta ce "Don Allah karka hanani sana,ar nan kuma ai kakata ce ba wai na tona maka asiri ba ne, ta ce za ta siya min ne ganin Baba bai siya min ba sannan na maka alƙawarin babu wani namiji da zai shigo gidan nan sayen abu" Tun da ta faɗa masa take ta karanto sunayen Allah a zuciyarta a kan Allah ya ɗora ta a kansa, maimakon ya ce wani abu sai ya ce sai ya yi shawara, haka ya kwanta ita ma ta kwanta ranta duk babu daɗi tana taraddadin ko zai amince?. Da safe yana zaune Kalifa ya je wajen ƴar yawo zai taɓa wayar jiki, ai da ya masa wata tsawa take yaron ya kiɗime ya yi wajenta da gudu yana ƙanƙame ta tare da sakin kuka, wani abu ta ji ya soke ta a zuciyarta, ganin Nasir bai san jan yaro a jiki ba bai san nunawa yaro soyayya ko kulawa ba kawai dai ya haifi yaron ne amma babu wani jin ƙai irin na mahaifa a tattare da shi. Bayan ya fita wajen Hajiya ya je bayan ya karya da break fast mai rai da lafiya, su Sadiya kuwa waina ce ya siya musu ta ɗari uku ba don ta ishe su ba kasancewar gidan kakar da ta je bata yi tuwo ba shi ma sai da ya gama mita sannan ya sayi wainar. Hajiya ya korawa bayani jin haka kuwa ta yi uwa da makarɓiya cewa ai dole ma ya bar Sadiya ta yi sana'ar ba don wai tana son ƙwatawa Sadiya ƴanci ko haƙƙi ba sai don ta nuna masa alfanun hakan zai ke ƙaruwa ne tana bauta masa a gidan, sai lokacin ya ji sanyi a ransa da ya ji shi ma zai ƙaru da sana'ar don shi ya sha'afa da cewa ya ce mata ma ta kama sana,a kawai dai da ya ji cewa har frige xa a saya mata bayan ya ɗauka sana,ar ƙarama za ta yi yadda daga ya sakar mata da abubuwan gidan jarin zai karye katsak saboda mugunta. Ta ji daɗi da ya amince ta yi ta masa godiya kamar ta ari baki, shi kuma a ransa yana gani kansa ya yi wa gata. Bayan kwana uku da yamma sai ga mai baro da Kaka, mai baron ne ya fara kawo frige ɗin da ledar pure water goma sai kuma Kaka ta zo a napep frige ɗin yana da tsayi amma ba sosai ba yana da murfi biyi sama da kuma ƙasa sannan dama da yake na amarya ne bai ji jiki ba zoɓo kwano uku da su kayan haɗa zoɓo har da kayan ƙamshi, sai kayan haɗin mangon da leda da kuma jarkokin lemo wanda za take zubawa a ciki su ma cikin buhu. Har da kukanta tana ta yi wa Kaka godiya, haka Kakar ta musu sallama ta tafi. Sadiya ta wanke frige ɗin tas ta goge ta ta jona dama akwai nepa ta jera pure watern a ciki, ta rasa inda za ta saka ranta don daɗi. Wani almajiri da ya yi bara ya faɗa mata makarantarsu bata da nisa da gidanta, shi ta aika maƙota ta ce ya faɗa musu abubuwan da za take siyarwa, sannan ta ce masa zai ke zuwa yana mata talla ya amince cike da murna, don dama idan suka yi karatun safe sai a tashe su ƙarfe tara, kowa sai ya tafi bara sai kuma karatun yamma da na dare, sai yance zai ke mata tallar daga ƙarfe tara zuwa ko ƙarfe uku ne, ta ji daɗi haƙiƙa Allah ya karɓi addu'arta don yaron yana da hankali. Ko da ta faɗawa Mama da Baba a waya fatan alkairi suka yi Baba har da cewa "Sadiya to ita amfanin sana'a dama don kake yin alkairi a ciki, don haka idan ana samun kar ake mantawa da iyeye don su saka albarka" Jin haka ta gane mai yake nufi sai ta ce masa "In sha Allahu Baba" Nasir ko da ya dawo ya ga sha tara ta arziƙin da Kaka ta kawo a ji daɗi, don haka jarkokin da ta wanke da soso da klin ta zuba zoɓonta mai daɗi ya ji kayan haɗi, sannan ta haɗa mango ɗin ma da kayan haɗin mango ta saka kala, sosai ya yi tamkar kana sha lemon mango ta kamfani har ya fi na wani kamfanin ma daɗi!. Bayan kwana biyu sana'a ta kankama, ƙanƙarar yara haka yara suke zirya daga unguwa da kuma islamiya idan an fito musu tara, ga almajirin bashi da wasa daga ya fita da kayan kamar wanda yake rabawa kyauta, don duk wanda ya sha sai ya yaba da daɗinsa. Kafin meye wannan sana'a ta fara ƙarfi mazan unguwa sai su ba yara su siyo musu babu mai zuwar masa gida, sai ya zamana yanzu Sadiya kawai ta mayar da hankalinta kan sana'ar ta kuma duk abin da take so haka take fitarwa ta yi abinta sana'a mai daɗi ko wulaƙancin da Nasir yake mata yanzu ya ɗan rage saboda dama wani don za ta ce masa ya mata wani abin ne. Sai dai wuyarta ya shigo kawai frige yake buɗewa ya ɗauka ya sha, daga an jima ya ƙara ita kuwa ko a ka bata kawo shi, tun da ta san duk abin da zai yi sai ta fita, don kayan sana'ar ruwa suna da riba sosai. Bayan sati guda tana zaune bayan ta gama ɗura zoɓo da yamma, da yake yau ya ƙare tas har ana nema, yanzu pure water ne a ciki da zoɓon da ta saka yanzu, da sallama Nasir ya shigo bakinsa yana washewa, abin da ya bata mamaki har da ɗauka Kalifa shi kuma yaron ya ƙi sakewa da shi kasancewar ba sabawa ya yi da hakan ba. Mukulli ya ɗaga a hannunsa yana karkaɗa mata bayan ta masa sannu da zuwa duk da ta ga yau ya dawo da wuri sai dai tana mamakin fara,arsa. Cike da alamun tambaya a fuskarta ta ce "Mukullin mene ne?" Ya ce "Sabuwar amarya na yi wato mota" Ya faɗa yana washe baki, sosai ta ji daɗin maganarsa, ba wai don ya ce ya yi mota ba, a,a sai don fara,ar da yake ko yaya ɓacin rai ko nuna isa da gadara basu da wani alfanu ga namiji yake yi wa iyalinsa. Sosai ta nuna farincikin ta, dama ta san yadda kasuwa take gara masa ai yana samu sosai kawai dai don abin a zuciya yake wato mammaƙon nasa a zuciyarsa yake. Hijabi ta saka suka fito ƙofar gidan motar tana sheƙin sabunta dark blue ya juyo ya ga yadda take ta fara'ar sai maganarsa ta katse mata hanzarin fara,arta ya ce "Na sayi motar nan ne saboda Meenal, Meenal ta faɗa min tana son duk inda za ta je in kaita a mota, sannan bata son ƙawayenta su rainata su ce mijinta bashi da mota!" *BABA* Gabaɗaya ya mayar da hankalinsa ga son banza, don yanzu kowa ya gane yana jin daɗin a masa abinci mai daɗi, don haka yanzu da daddare idan yana bacci cikin dare za a lallaɓa wata daga cikin ƴaƴan ko matan za ta sace mukullinsa, a je a auni shinkafa a store a mayar a rufe, don da abin nasu ma ya yi tsamari sai a auni kwano uku biyu a dafa a gidan kwano ɗaya sai a siyar a yi cefane da nama ko kifi a yi girki lafiyayye kowa ta ci Baba a yi masa zubi ya ci yana santi da saka albarka, har yau bai san cewa tanadin da ya yi domin ya siyar ba ne ake kwasa ana ci tare da shi. Yanzu ma bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin malamai da masu siyar da maganin gargajiya yana siyan maganin farin jini domin ya samu ya aurar da ƴaƴan nasa, malamai kuma yana sakawa su yi roƙon Allah, amma shiru kake ji malam ya ci shirwa da alama dai addu'ar ta samu jinkiri ne, babban abin da ya ƙara tada masa hankali ma yanzu Sumy da Aisha da suka kammala karatun su na secondry yanzu kam waɗanda yake son ya aurar sun yi yawa. Shi ya sa ba ya ma son Sadiya ta kawo ƙorafi a ganinsa tun da dai ita Allah ya sa ta samu miji to duk wani ƙalubale ta haƙura ta rungumi ƙaddara!. *MUBIN* Da sanɗa ya shigo babban falon yana waige-waige sai dai ganin dalon wayam kamar yadda ya yi tsammani hakan ne ya sa ya ji ɗan daɗi a ransa, domin a ganinsa lokaci ne da kowa ya yi bacci idan ya shige ɗakinsa to zai zamana ko ma mene ne zuwa safiya Mamy ta huce daga fushin don ya san sai dai Mamy don Baffa ko a kwalar rigarsa. Takalmansa a hannu ya yi saɗaf-saɗaf kamar daga sama ya ga hasken fitila ya manaye falon, abin ya masa bazata hakan ya sa ya ji gabansa ya buga da ƙarfi, sai jin muryar Mamy ya yi kamar yadda ya tsammata ta ce "Mubin daga ina kake?" Shiru bai bata amsa ba ta sake cewa "Mubin irin tarbiyar da na baka kenan? Wannan ne sakayyar da za ka mini, maimakon ka zama ɗa nagari mai biyayya da bin umarnin iyaye, yi na yi bari na bari amma shi ne duk fadutukar da nake yi kake son watsa min ƙasa a ido" Ta faɗa lokacin zuciyarta ta fara karaya saboda tausayin kanta a nata ganin ba uwa ce kaɗai za ta kula da tarbiyae ƴaƴa ba haɗaka ya kamata iyaye mata da mazan su yi tarbiyar ƴaƴan amma shi ya bar mata komai ta yaya hakan zai yiwu gashi yaran suna neman kangare mata. Mubin cikin inda-inda ya fara maganar da rashin gaskiya ya hana shi furta abin da yake gaskiya ne dama hausawa sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. *JIDDA* Gabaɗaya Ibrahim ya rikita mata lissafi ya sa duk tana jin wata muguwar kunyarsa, ya sa tana jin ashe ita ma tana da wani matsayi don yadda yake yi mata jin ta take tamkar wata sarauniya. Ta tafi gajeran zancen zucin nan na wucin gadi kawai sai ta ji yatsansa a saman leɓɓanta, abin da ya dawo da ita hayyacinta kenan, tana dubawa sai ta ga tsokace ya gutsuro yake ƙoƙarin bata a baki. Cikin wata murya mai kwantar da zuciya ya ce "Idan baka ci naman nan ba kuka zan miki Jiddanah" Yanayin yadda ya fara bata ga alamar wasa a tattare da shi ba hakan ya sa ta danne guntun kunyar ta buɗe masa bakin ya saka, yana sakawa ta saka hannunta na dama ta rufe bakin da tafin hannunta saboda duk kunyarsa take ji kasancewar rashin sabo. Idanunsa ta ji yana yawo a jikinta alama ce ta ya tsare ta da kyawawan idanunsa hakan ya sa ta kasa ɗagowa ta kalle shi shi kuma ji yake tamkar ya mayar da fuskarta cikin idanunsa ya zamana ita zai ke kallo a koyaushe. Muryarsa tana sarƙewa saboda yanayin da ya tsinci kansa na kasancewa da ita a waje guda kuma matsayin mamallakiyarsa hakan ya sa ya ce "Idan naman ya miki taurin da ba za ki iya taunawa ba, wallahi zan tauna miki shi Jiddanah, ji nake kamar don ni aka halicce ki wallahi ina jin kamar idan ban kyautata miki ko na faranta miki ba kamar dai na ci amanar ƙaunar da zuciyata take miki" Wani ruwa ne ya taru a ƙwayar idanunta, a zuciyarta tana godiya ga Allah da ya bata mijin marainiya, ita kuma ta yi alƙawarin ba za ta kasance daga cikin mata azzalumai ba wanda idan sun samu namiji yana ƙaunarsu suke cutar da shi ko su mayar da shi bawa, wata ma malamai take bi don ta samu yadda take so amma daga ta ga duniya a tafin hannunta sai ta fara gara mijin kamar ƙwallon ƙafa, bata san cewa duk abin da aka nema ta ɓarauniyar hanya ma'ana duk abin da aka yi ba ta hanyar Allah ba to ba zai taɓa dawwama ba!. A kunya ce ta ce "Zan iya taunawa, kaima ka ci" Jin furucin ta sai ya ji ya ƙara samun nutsuwa haka ya ringa ɗauka yana ci yana bata, don ya san a kunyar Jidda yau dai ba za ta iya bashi abu a baki ba sai ko nan gaba idan ta kwana biyu ta saki jiki da shi. Sun ci amma ba wani mai yawa ba, sai kuma ya tsiyaya musu lemon amma shi madara ya zuba, bakinta ya nufa da kofin amma sai ya ga ta miƙo masa hannun nan nata mai tafiya da hankalinsa wanda yake ɗauke da kyakkyawan jan ƙunshi da baƙi. Miƙa mata ya yi ta ɗan sha ta ajiye, shi kuma madarar ya shanye duka, ko da ya zuba mata sai ta girgiza kai. Tana nan zaune ya kwashe duka kayan, sai ganinsa ta yi ya dawo, yana tsaye a kanta ita dai bata ɗago ba, kamar a mafarki kawai sai ta ji ya sure ta, ɗaukan jarirai ya mata, wata irin kunya da bata taɓa samub kanta a ciki ba ce ta ziyarce ta, hannunta biyu ta sanya ta rufe idanunta, bata ankara ba ta fara jin alamun sama suje haurawa, sai da ya gama hawa ta ji wani irin ƙamshi yana tashi na turarukan wuta, ƙaran ƙofar da ta tura da ƙafarsa hakan ta sa ta gane sun zo wani ɗakin ne daban, a wani lallausan gado ya mata masauki wanda ta ji tamkar dama katifar bata da tauri kawai wani irin laushi ne da ita tamkar auduga. Yana ajiye ta ya juya ta ji fitarsa, hakan ya sa ta janye tafukan hannayenta don yin tsegumin ɗakin da take ciki, ai kuwa ta ga aljannar duniya, tana cikin kallon ɗakin da yadda aka ƙawata shi hatta bedsheet ɗin ya sha lailaya a gadon. Ƙaran hayowarsa benen ya ankarar da ita ya dawk da sauri ta yi rubda ciki tana ambaton Allah, a zuciyarta don ta san dai an ce daren farko shi ne daren amarci kuma ango ba wai zai ɗaga ƙafa ba ne, bare wannan mijin nata yadda yake rawar ƙafa a kanta da yadda yake sonta tabbas zai famshe soyayyarsa. Da sallama ya shigo amma bakinta ya mata nauyi bata amsa masa ba tana jin lokacin da ta mayar da ƙofar ya rufe tamkar da bugun zuciyarta ya rufe ƙofar, dilim ta ga ya kashe wutar ɗakin sai ta gefen gado wacce hasken nata yake blue wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke a ranta tana raya Aliya da Kasim suna can su ma suna soyewa. Sai dab da asuba komai ya daidaita, wata irin kulawa da soyayya yake nuna mata, ita kuma tana narkewa kamar wata ƙaramar yarinya, shi kuma yana jin tamkar babu mata sun ƙare a duniya idan ya tuna yadda ya samu Jidda tabbas wannan rana ce mai matuƙar tarihi a rayuwarsa. Shi ya taimaka mata ta tsarkake kanta bayan ta gasa jikinta sai sannu yake jera mata ita kuma tana raki. Sai da suka yi sallar asuba sannan ya sauya zanin gadon suka koma suka kwanta sanye da wasu kyawawan kayan bacci masu taushi da ya fito da su daga drower wanda iri ɗaya ne kawai bambancin nata na mata ne nashi na maza. Wajen ƙarfe tara suna cikin ramuwar baccin da basu runtsa daren jiya ba wayarsa ta shiga neman ɗauki har ta katse babu wanda ya san mai ake yi, Mummy da take faman kiransa tana tsaye ga direban da za ta aika gidansa yana tsaye riƙe da kwandon da ta sa aka shirya musu lafiyayan abinci, don ta ce sai an kwana biyu za a kai ƴan aikin girki yanzu dai masu shara da goge -goge ne za suke zuwa suna gyara mata gidan, don bata so a je a dame su a hana su sakewa da juna, tun da shi ma Ibrahim ya ɗauki hutu a wajen aiki. Ƙara kiransa ta yi cikin bacci ya ji ƙaran wayarsa a hankali ya buɗe jajayen idanunsa da suka masa nauyi ya miƙa hannu kan bed side drower ya ɗakko wayar tana saurin dannawa gudun kar ya tashi Jidda. Ganin Mummy ya ɗaga yana kai kunnensa ta ce "Mu'azzam a kan mai za ka bar mini yarinya da yunwa tun yaushe nake kiranka baka ɗauka ba, kar fa ka bar yarinyar nan ta shiga kicin" Bai san lokacin da murmushin gefen baki ya suɓuce masa ba idanu ya mayar kan Jidda wacce take bacci cikin kwanciyar hankali hular kanta ta zame yana iya ganin gashin kanta ya ce "Mummy masu ƴa, to ita ƴar taki ma bacci nake bata tashi ba" Mummy ta ce "Ga direba nan zai kawo abinci" Ya ce "To Mummy ina kwana, ina Daddy" Mummy ta ce "Sai yanzu ne za ka gaishe ni? Daddynka gashi can yana karyawa bai fita da wuri ba yau" Ibrahim ya ce "To ai na ga ta ƴarki kike bakya ma ta ni" *ALIYA* Ganin ya zuba mata mayun idanunsa yana kallon ta sai ta ga ma tamkar baƙaƙen maganganun da ta faɗa masa sun zame masa busar sarewa, saboda ya shagala da kallon kyawun halittar ta, kyawun da take taƙamar tana da shi, ji take tamkar ta tauna ganyen maina( Dalbejiya) A bakinta saboda wani ɗaci da bakinta yake yi mata, kallo ɗaya ta yi wa Kasim ta ga bai cancanci ma ya zama mijinta ba, Ibrahim jawai take gani a ƙwayar idanunta kuma shi take da buri da kuma muradin samu, Kasim babu da wanda ya dace sai Jidda ita baƙa kuma mummuna marar gata wato wacce bata da galihu wato marainiya. Wata tsawa da ta daka masa tamkar uwarsa ita ce ta dawo da shi daga zalamamman kallon da yake jifanta da shi. Har sai da ya runtse idanunsa sannan ya buɗe saboda yadda ta masa, tamkar wanda bakin uwa ya kama shi. Murya ya sassauta don shi ko mai za ta masa ba ya son ta hana shi kanta a wannan ranar, ya ƙwallafa rai a cin amarci amma tana neman kawo masa cikas. Yana ɗan haɗa hannaye biyu waje guda ya ce "Aliya ki sassauta muryarki ko kuma ki dakata daga wannan lafuzan mararsa daɗin sauraro, ki bari in abokaina suka tafi ko me za ki min na amince ki mini" Ya faɗa yana magana kamar raɗa, wani haushi take ji in tana tozali da fuskarsa ji take tamkar ta wanke masa fuskar da gigitaccen mari ko ya dawo hayyacinsa ya gane Aliya ba tsararsa ba ce. Wani wawan tsaki da ta doka shi ne ya sa ya gane haƙarsa bata cim ma ruwa ba domin ya gane ihu ya yi a bayan hari da alama maganar da ya mata ta bi ta kunnen hagu ta fita ta kunnen dama. Ya jima yana roƙon ta fito don saboda abokansa amma ta ba bango ajiyarsa, ganin wankin hula yana son kai shi dare ya fito jiki sanyi ƙalau yana tafiya kamar an yi wa ƙafarsa dabaibayi. Yana fitowa ya gansu a tsaye su duka da alama ma suna shirin tafiya ne, ji ya yi tamkar ya nutse saboda kunya, akwai damuwa a ce a ranar da amaryarka ta tare amma tana maka wannan cin fuskar a kan kunnen abokan ka. Yaƙi ya yi da zuciyarsa da bakinsa ya saki wani murmushin yaƙe wanda iyakacinsa fatar baki, gabaɗaya sai ya lura babu annauri a fuskar kowa yana fitowa falon ya ruɗe da faɗin "Kasim za mu wuce Allah sanya alkairi ya bada zaman lafiya da haƙuri da juna" Wannan furucin nasu ya tabbatar masa da cewa ai tun yau ya fara karyawa da haƙurin. Amsawa ya shiga yi yana ji kamar ya nutse haka suka fara fitowa yana biye da su a baya, har waje ya rako su. Suka masa sallama suna watsewa Salis ne kaɗai ya tsaya ya kalle shi cike da damuwa ya ce "Kasim wannan wace irin baƙar rana ce a ce a ranar farkon aurenka da matarka da kuka yi auren soyayya amma ta watsa maka ƙasa a ido, ko ma mene ne ai duk gaggawar asara ta jirayi samu ko wato duk son ta buɗaɗa maka ƙasa a ido ta jira mu tafi" Iska ya hurar daga bakinsa ya ce "Ni kaina ban gane kan gadon wannan lamarin ba har tsoron komawa nake cikin gidan, don da alamu babu sassauci a lamarin Aliya kamar wacce ta sha ƙwaya" Salis ya ce "Babu wata ƙwaya tsabar rashin mutunci ne" Sun jima suna jimantawa kafin Salis ya fito da wata ƙwayar magani ya ba Kasim tare da masa raɗa a kunne, daga bisani suka yi sallama, shigowa ya yi ya rufe ƙofar gidan ya tarar falon sai ledar kazar amarcin da abokansa suka yi haɗin gwiwar siya masa, da lemukan a ajiye. Ko ta kansu bai bi ba ya nufi bedroom, samunta ya yi ta yi kaca-kaca da akwatin ta guda ɗaya ɗaya daga akwatunan da ya mata na lefe tana zuzzubar da kayan ganin kayan bacci a jikinta riga da wando hakan ya gane cewa kayan ta ɗauka a ciki, tattarewa ya yi ta rufe akwatin. Zaune take a bakin gado duk abin duniya ya ishe ta kawai falon Jidda ne yake mata gizo da kuma farfarjiyar gidan wacce ta fara tozali da ita ganinta take tamkar yanzu ne take ganin ta. Muryarsa ce ta katse mata tunani ya ce "Aliya amaryata" Watanuwar harara ta galla masa kamar idanunta za su faɗo, falon ya fito ya ɗauki lemon tana fakar hanyar ɗakin ya buɗe five alive ya jefa maganin da Salis ya bashi a ciki ya mayar ya rufe. Duka ya ɗauka ya shiga ɗakin ya ajiye a gaban gadon ya koma falon bayan ya ce mata shi zai kwanta a falon tun da bata buƙatar ya zo inda take banza ta masa son ko magana ya yi haushi yake bata. A doguwar kujera ya kwanta yana jin duniyar ta masa zafi. Aliya kusan awa biyu ta ɗauka a zaune, cikinta da yake mata ƙugi ta ɗauki lemon da aka saka magani ta buɗe ta kafa kai ta sha ta ajiye ko rufewa bata yi ba, jim kaɗan ta fara hamma bata san ta kwanta a gadon ba bacci ya yi awon gaba da ita da mafarkin gidan Jidda, tana ta gani a mafarki gata nan a gidan Jiddansuna rayuwa da Ibrahim matsayin mijinta. Zuwa can Kasim da ya yi tsai yana jin babu motsin Aliya a ɗakin, lallaɓawa ya yi ai kuwa ya ga ta yi bacci, hakan ya sa ya ci karensa babu babbaka a nan ya ɓingire bacci da mafarkin Aliya da take kusa da shi yau dai burinsa ya cika. Aliya wacce maganin baccin ya saki, ta riga shi tashi a bacci don lokacin har gari ya fara haske, tana tashi ta ga abin da ya faru wanda ya ɗaga mata hankali sai dai a ƙwaƙwalwarta tana iya tuno kamar a cikin baccin ta ga ta bashi haɗin kai, kamar kuma ba a bacci ba ne kamar dai a zahiri ne kallo ta shiga ƙarewa Kasim da yake shararar bacci ko kayan jikinsa bai mayar ba. Hannu ta kai ta rufe bakinta gudun kar ihun da take ƙoƙarin wwace mata ya fita, a kiɗime ta sauka daga kan gadon tsabar ruɗani bata san ma ina take jefa ƙafafunta ba, ko kaya babu a jikinta haka ta ɗakko wayarta da ta gani a kan madubi da hanzari ta fito daga falon tsakar gida ta nufo tana fitowa ta yi tozali da injin da bashi da maraba da tsoho wani haushi ya turnuƙe ta duk da halin da take ciki ya doke wannan. Kicin ta nufa ta kamo sunan Umma, Umma da take kan sallaya Abba bai dawo daga masallaci ba, tun da ta idar da sallah take zaune a kan sallayar ta doka uban tagumi tana tunanin Aliya da gidan da ta tafi zaman aure babu abin da ya fi ƙona mata rai da akance gidan Jidda haske ral amma gidan Aliya ana shiga da amarya inji yana mutuwa dakyar aka samu ya tashi sai da masu gyara suka masa ribdugu. Tunani da damuwarta ɗaya Jidda tana can ta kwana a gida mai kyau Aliya kuma a gidan ya ku bayi. Tana cikin wannan tunanin ta ji ƙaran wayarta gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta nufi wayar don tana tsoron ko sanarwae mutuwa za a faɗa mata, sai dai ganin sunan Aliya ya sa ta danna Ok da sauri tana karawa a kunn Aliya ta fashe da kuka ta ce "Umma kin san wa na aura?" Gaban Umma ya bada dididdimdimmm a tsorace ta ce "Aliya ba Kasim kika aura ba" Aliya ta ce "Umma ki bar maganar wai Kasim na aura eh shi na aura amma Umma akwai ɓoyayyan al'amari wallahi mai firgitarwa Innalillahi wa inna ilaihi Umma ... Na aura!". Umma da take tsaye sai gata gata ta yi zaman ƴan bori idanunta tamkar za su faɗo numfashinta yana barazanar guduwa ya barta... *KU JE KU DISKANTA SHIN WACE CE A CIKIN KU ZA TA BANI AMSAR WA ALIYA TA AURA? NA BAKU GARI😃* *AMMA* *KO NI NA TSORATA SA ABIN DA TA FAƊA LALLAI KASIM YA SHAMMACE MU, SAI DAI AMSAR TANA NEXT PAGE IN MUNA RAYE* Shin wai bakwa neman maganin mata mai inganci don ku birge mazajenku? Ku kankarowa kanku mutunci da magungunan sa nake siyarwa akwai maganin sanyi akwai atamfofi lesuna zanin gado takalma kayan yara akwai plazzo set na yara da manya kai komai ma akwai mai so ya min magana don mallakar nasa har kayan kicin duk akwai a farashi me sauƙi MAMAN AFRAH 09025576222 https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=ems_copy_t *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️⃣4️⃣ *SADIYA* Duk da kasancewar ta mai haƙuri da kawar da kai, komai ya farutana yin kamar bata gani ba idan kuma ta ji tana yin kamar bata ji ba, sai dai wannan furucin nasa ya taɓa mata zuciya. Ta yaya za a yi ya faɗa mata cewa saboda Meenal ya saya mota ita da bata zama matarsa ba duk da za ta zama, wato su iyalinsa basu kai matsayin da za a sayi mota saboda su ba, har ya duba ƙwayar idanunta yana faɗar saboda Meenal ya sayi mota don kar ƙawayenta su ce bashi da mota. Danne abin da ya ɗarsu a zuciyarta ta yi tare da ƙoƙarin ƙirƙirar wani murmushi don a a rayuwa ba komai ba ne sai mutum ya magantu a kansa, ba komai ne sai ka yi magana ba, ba a kowane abu ake ƙorafi ba!. Tana murmusawa ta ce "Amma fa ka yi namijin ƙoƙari!.Gaskiya gwara da ka siya ko don ka fitar da ita kunyar ƙawaye"Ji ya yi kansa ya masa wani girma yana riƙe da Kalifan ya washe baki ya ce "Ai kam kin san an ce amarya sai da lallashi" Tana dariya ta ce "Gaskiya kam amarya ai hukuma ce sai da lallashi" Yana kallonta don ya ji daɗin furucin ta ya ce "Uwar gida fa?" Wani murmushin ta sake yi ta ce "Uwar gida sai haƙuri" Ya ɗan yi jim sai ya ce "Kenan ita uwar gida sai haƙuri mai ya sa kika ce haka?" Ta ce "Kawai dai na ga dacewar hakan" Iska ya ɗan hurar ya ce "Kuma maganarki haka take" Sadiya ta ce "Dama mana" Kalifa ya miƙa mata ya juya ya ce mata yana zuwa ya rufo ƙofar, cikin gidan ta dawo tana jin lokacin da ya tada motar ya yi gaba, don dama ya iya mota, Kalifa ta ajiye ta ɗauki abin wasa ta bashi, ta cigaba da uzurinta don ita yanzu sana'ar nan ta fiye mata komai don ta lura ita ce gatan ta kuma rufin asirinta. Kwanci tashi asarar mai rai yanzu cikin jikinta yana da wata bakwai, ya fito sosai, sana'a kuwa yanzu ta kafu, duk unguwa an san ta wasu ma daga wani wurin suna zuwa siya, don yanzu har da nono take ɗaurawa mai kyau sannan ribar da take ɓoyewa ta haɗa ta siyar da frige ɗin ta cika ta saya freezer amma ba sabuwa ba sai dai babu abin da ya same ta. Da yake Allah ya saka mata albarka sosai ta bunƙasa, yanzu duk ƴan ƙananun kayan jarirai tana saya wanda za a iya sakawa maza da mata, duk da tana zuwa awo amma ita take yi wa kanta komai kama daga kuɗin napep zuwa asibiti da kuma abubuwan da za ta buƙata har magunguna, tun da idan ma ta faɗa masa cewa za ta je asibiti iyakarta ya ce "Sai ta dawo" Har ta saba da wannan furucin ita yanzu tun da dai tana sana,ar nan kuma tana rufa mata asiri bata damuwa ma da watsi da kuma wofantar da haƙƙoƙinta da yake yi. Yanzu ta fara siyar da farin man Ok da kuma manja, curry da sauran kayan miya na amfanin gida, yanzu gidan koyaushe baka rasa wanda zai zo siyan abu. Hatta kayan gwanjo siya take nata da na Kalifa sai ta saya kamar sabbi ta wanke ta goge suke saka abin su don haka dogayen riguna da wando da riga da kuma riga da skirt duk ta saya tana kwalliyarta a cikin gidan ta fito abinta tsaf idan ma tana marmarin abu sai ta siya ta dafa kayanta shi ma Nasir ɗin ya ci, hakan ya sa yake ba su Hajiya labarin ai kuwa Hajiyar take ce masa dama ai ta faɗa masa idan ma tana sana'ar duk a hidimar gida kuɗin zai ke ƙarewa, basu san sana'a sirri ba ce, tana yin alherinta a ciki. Yau ta kama juma'a bayan ta gama ayyukanta, lokacin Kalifa ya yi bacci, tana so ma ta tashe shi saboda yamma ta yi amma kuma gudun rigima sai ta ce idan ta yu wanka ta shirya sai ta tashe shi. Bayan ta yi wanka ta shafa fowder ta lips stick, riga da wando na plazzo ta saka da hularsu kalar dark blue kayan sun karɓe ta ta shafa turare sai ƙamshi take buɗaɗawa. Cikn ta da ya fito ya yi ɗas a cikin rigar, ta je kusa da Kalifa za ta tashe shi don lokacin miyar dare ce kawai take dahuwa a kan gawayin ta gama tuwo. Sallamar wata yarinya ce ta dakatar da ita, inda ta ce ta bata farin mai kwalba guda da kuma curry ɗaurin ɗari biyu guda biyar sai zoɓo na ɗari uku, kasancewar dama man ɗaurawa take ta ajiye kowane awo ta bata duka ta bata canjin, ta karɓa ta juya ta fita ita kuma ta je za ta ajiye kuɗih kawai sai ta ji ƙaran tsayuwar mota a ƙofar gidan, ƙaran rufe ƙofofin motar ta ji sai kuma ta ji an turo ƙofar gidan, muryar Nasir ta fara jiyowa yana ɓaɓɓaka dariya, sai ta ji yana shigowa sai kuma take jiyo takun takalmi ƙwas-ƙwas wanda hakan yake nuni da ƙaran takalman mace ne, sai kuma zuciyarta ta bata tare da su Husna yake ƙannensa, har ta fara fargabar zuwansu saboda rashin arziƙinsu kar su mata halin nasu na rashin mutunci tun da su ba sa tunanin makomar nasu auren idan sun yi tun da su ma mata ne watarana gidan miji za su je!. Wasu muryoyi ta ji sun sallama a gadarance, muryar ɗaya ta so ta san mai ita sai dai bata gama tantancewa ba, sai kawai ta jiyo muryar Nasir yana faɗin "Haba ku da gidanku, sai wani rafka sallama kuke yi kamar baƙi" Wata murya ta jiyo ta ce "Gaskiya dai ai gidanta ne kuma gidan yayanta abu ne ya haɗe mata biyu" Duk wannan maganar da suke kafin su shigo tsakar gidan ne wato daga zauren gidan, kafin ta gama dawowa daga shan ruwan mamakin maganganunsu ta yi saurin amsa sallamar tana fitowa daga falon nata. Hakan ya yi daidai da shigowarsu tsakar gidan suka yi ido huɗu da Sadiya wacce shigar da ta yi ta ɗauki hankalinsu ganinta tsaf tamkar ita ce amaryar ta yi ƙiba abinta kamar bata da wata damuwa, don dama ita damuwa sai idan mutum ya buɗe cikinsa ake sanin yana da ita duk da a lokuta da dama tana iya bayyana kanta a gangar jikin mutum. Ba ma wannan ne ya ɗan taɓa musu zuciya ba, yadda cikin jikinta ya mata cif-cif shi ne abin da ya ɓatawa Meenal rai, a take ta ji wani kishi ya baibaye mata zuciya tana jin tamkar ta maƙure Sadiyar ita bata ma san tana son Nasir haka ba sai da ta ji kishin Sadiya ya tokare mata maƙoshi ya ƙi gaba kuma ya ƙi baya!. Basu kaɗai lamarin Sadiya ya tafi da su ba hatta Nasir ta shammace shi, saboda kayan jikinta bai taɓa ganinta dansu ba sabbi ne, da ta saya wajen maman afrah don tana siyar da set ɗin plazzo na yara da manya sannan tana siyar da iya wandon plazzo ɗin. Ba wai don bata yin kwalliya ba sai dai don ɗinkin ya fita ne yadda wandon ya baje sosai ya ƙara mata kyau rigar kuma cif kamar don ita kaɗai aka ƙirƙire ta. Sadiya ganin su Meenal ya taɓa mata zuciya a nata ganin ba ƙaramin cin fuska ba ne namiji ya shigowa da mace matarsa da zai aura, kuma bai sanar da ita ba sai dai kawai ta gansu sun shigo, duk da cewar Babarsa da Babar Meenal ƙawaye ne amma ai ya kamata a ce an sanar da ita, kai ita gaba ɗaya ma bata ga alfanun hkan ba domin mai suke ci na baka na zuba ai in dai gida ne kamar yau ne za ta shigo shi, tun da yanzu biki bai fi sati uku ba kuma an kammala mata komai na ɓangarenta. Sadiya bata so su ga lagwanta daga su har Nasir ɗin don haka sai ta ƙirƙiri bariki kamar yadda su ma suka mata bariki cikin wani salon murya ta ce "Oyoyo baby sannunka da zuwa, kenan dama ba sai an yi sallar magribar za ku zo ba, ka ce mini sai an yi sallar magriba za ka kawo su?" Ta faɗa tana wani rausaya kai gefe tare da yin fari da ido, mamaki al'ajabi ne ya kama kowane ɗayansu, musamman Nasir da hakan ya fi kasancewa baƙon abu a wajensa hakan ya sa ya saki baki galala yana bin ta da kallo. Meenal kuwa wani takaici ne ya turnuƙe ta tana jin tamkar ta kurma ihu tana ganin Sadiya bata isa ba bare ta kai har Nasir ya yi wata magana da ita musamman yadda ƙannensa suke sanar mata ita ba komai ba ce a cikin gidan, amma yanzu gashi ta ga akain haka, don bata taɓa tunanin Nasir zai sanar da Sadiyar zuwanta ba, ta so a ce Sadiyar bata san da zuwanta ba domin ta ƙona mata rai sai gashi sun samu saɓanin abin da suke zato, wato ma yadda ta so ta ɓatawa Sadiya rai na zuwanta gidan sai gashi ta ga ko a jikin Sadiyar wai an tsikari kakkausa. Maganar Sadiya ce ta katse su da faɗin "Sannunku da zuwa amarya bakya laifi" Wani irin haɗe rai Meenal ta yi ita kuma ƙawarta ta ɗauke kai tamkar ta ga kashi tun da sun gama shiryo yadda za su ƙular da Sadiya ta yadda abin zai tsaye mata a rai har ya hanata sukuni. Shi kuma Nasir sai ya tsinci kansa da faɗin "Eh dama yanzu ne za su zo" Shi kansa vai san dalilinsa na faɗin hakan ba tun da ya san basu yi maganar da Sadiyar ba. Murmushi Sadiya ta yi ta ce "To ai ita da gidanta ma za ta iya zuwa koyaushe duk da dai ba a kawo ta ba" Kallon kallo aka shiga tsakanin Meenal da ƙawarta Meenal a zuciyarta tana rayawa a ranta cewa dole idan ta shigo gidan nan Sadiya ta faɗawa aya zaƙinta. A hankali ta fara wani taku tana jijjiga jiki yadda za ta ɗauki hankalin Naair ɗin ta yadda zai shagala da kallonta har Sadiya abin ya bata haushi sai dai aka samu akasi shi kawai sai ya ji kamar wanda aka jarabce shi da kallon Sadiya kawai ji ya yi tamkar an sanya maganaɗisu a tsakaninsu wani abu yake ji yana fusgashi dangane da ita. Ƙawar Meenal ta ja wani gajeran tsaki ta kama hanyar ɓangaren Meenal ɗin kamar yadda ta ga Meenal ta yi sallamar wani yaro ya katsewa kowa hanzari inda ya ce a bashi farin mai na dubu biyu da ɗari biyu, kasancewar a ƙulle suke a wajen sannan kuma gashi kuɗin nasa ba canji banne dubu biyun ce da ɗari biyun sai Sadiya ta ce "Ɗan yi haƙuri ka ji ka zo a daidai lokacin da zan nunawa ƙanwata ɗakinta, bari in zo in baka" Shi kuma Ibrahim jin wannan furucin sai ya ce "Bari in bashi" Ya faɗa yana nufar wajen zai ɗakko masa man, shi ya yi hakan nr don ya birge su Meenal su ga kamar dai ba ya wulaƙanta matarsa saboda ya san an ce wasu matan sun tsani namiji mai wulakanta matarsa ya gida, saboda suna ganin su ma wataran idan sun shigo gidan zai musu hakan. Da to ta amsa masa ta fara bin bayansu don lokacin Meenal har ta murɗa ƙofar za ta buɗe, zuwan Sadiya ya sa ta dakata da abin da take a ƙufule ta ce "Ba ma buƙatar taimakon ki" Sadiya sai ta saki murmushi ta ce "Ayya!. Dama don an ce baƙon ka annabinka amma tun da haka ne babu damuwa s fito lafiya" Nuna rashin damuwa a kan lamarin abin da ta faɗawa Sadiya ya sa ta ƙara jin zafi a ranta, ita kuma Sadiya ta juya ta koma lokacin har Nasir ya ɗakko man yana nuna mata cewa wannan ne? Su dama tsabar ma ransu da ya ɓaci suna shiga suka fito na farko dai yanayin yadda suka samu akasin yadda suka yi zato daga matar gidan da kuma yanayin ginin da aka yi sai ta ji bai wani kwanta mata ba tun da lamarinta akwai ƙarya a ciki, haka ya sa suka fito buguzum-buguzum Sadiya kuma da ta bashi amsa da shi ne man sai ta je za ta karɓa ta tsaya dab da shi wani ƙamshin turarenta ya buge shi, bai san lokacin da ya yi murmushi ba ita kanta Sadiyar abin ya bata mamaki sai dai sakin murmushin da ya yi a kan idanun Meenal wacce ta ƙara cin karo da haɗuwar hannayen Sadiya da Nasir a daidai lokacin da zai bata man, ko kallo basu ishi su Meenal ba sannan ta yi da na sanin zuwanta gidan, don tana ganin cin fuska Nasir ya mata da gangan. Hanyar waje suka nufa, Nasir ya shiga kiransu amma ko waiwaye babu wacce ta yi a cikinsu. Bao bi ta kan Sadiya ba wacce ta karɓi man ta ba yaron a take ya takewa su Meenal baya yana faman rafka musu kira, yaron ma fita ya yi Sadiya a fili ta ce "Ku kuka sani ku ƙare ƙalaw" Ta faɗa tana mai shigewa ɗaki hannunta riƙe da kuɗi. Su Meenal ko kallon inda motar Nasi take basu yi ba, haka suka fara tafiya kamar za su tashi sama, Meenal ta ce "Wai ni Nasir zai yi wa barikanci,saboda na ce zan je in ga ɗakina saboda tsare -tsaren kayan da za a saka a ciki shi ne har zai ke kula matarsa da ya san yana son ta uban wa ya ce ya ce zai aure ni?" Ta faɗa tana yin ƙwafa tare da raya cewa zai san ya yi da ƴar halak. Ƙawarta Huzaifa ta ce "Wai baki ga har wani yauƙi take ba, yanzu wannan matar ce za a ce tana fuskantar wulaƙancin ɗa namiji anya ba rufarki aka yi ba?" Ran Meenal ne ya ƙara ɓaci tana cin wani alwashi a kan komai kamar ta yi kuka ta ce "Abin ya zo da rainin wayo, wai ni ba ma wannan ba sana'a take yi fa da alama kina gani ana sayen mai, ni da babu uwar da nake siyarwa kuma wallahi ba zan siyar ba amma zan ɗauki mataki bari na shiga gidan, ai duk wanda ya iya allonsa wankewa yake yi" Huzaifa ta shiga zuga ta tana ta jin kanta dole ta yi wani abu duba da yadda shi ma Nasir ta ga yana yi wa Sadiya wani kallo tamkar bai san da su ba a wajen. Nasir tun da ya fito ya hangi sun kama hanya sun tafi, daga haka ya gane akwai gagarumar matsala, hakan ya sa ya fara sauri ya take musu baya, yana tunanin abin da ya musu don shi kansa ya sha'afa da yadda ya mu'amalanci Sadiya a gabansu. Yana binsu yana magaiyar su tsaya amma basu saurare shi ba suka ba banza ajiyarsa. Yana dab da ƙarasowa da yake sauri suke kamar su tashi sama, kawai sai gani ya yi sun tsare mai napep, sun shiga da ɗan gudunsa ya taho sai dai kafin ya zo mai napep ɗin ya tada sun tafi, ya san kuwa hakan ba ya rasa nasa ba cewa umarni su Meenal ɗin suka baiwa mai napep ɗin. Tsaye ya yi a wajen yana riƙe da ƙugu ya rasa mai yake masa daɗi, ya jima a tsaye yana ta tunani don gano laifin da ya yi, sai daj a rai da rubinsa yana tunani da fatan Allah ya sa kar Meenal ɗin ta ce ta fasa aurensa. Da na sani ne ya lulluɓe shi da ya tuno ko dai don saboda abin da ya yi wa Sadiya ne Meenal ta ji haushi, a take ya ji wani haushin Sadiyar yana ta sakin tsaki a kai-a kai shi bai ma san dalilin da ya saka ya sakarwa Sadiyar fuska a gabansu ba sannan kuma ai ya rasa yaushe na Sadiya ta san cewa wai Meenal za ta zo tun da shi dai a iya saninsa bai faɗa mata ba. Ya fara tunanin ko dai wani makirci ne Sadiyar ta yi a ƙufule ya juya ya dawo, a wajen motarsa ya tsaya ya ɗakko wayarsa a aljihu ya shiga kiran Meenal har ta katse bata ɗauka ba hakan ya sa ya ƙara hawa tamfa, sake kiranta ya yi ta ɗaga yana jin yadda ta hayayyaƙo masa har sai da gabansa ya faɗi, a ransa yana raya anya wannan za a yi abin arziƙi da ita daman yana ganinta shiru -shiru ashe dai a she dai sai kuma wani sashe na zuciyarsa ya ce wataƙila ɓacin rai ne kawai ba wai halinta ba ne. Haƙuri ya shiga bata sai dai da alama ta yi nisan da jin kira zai mata wuya, sai faɗin ya disga ta a gaban Sadiya take, har tana cewa dama ya kawo ta ne ya nuna mata iyakarta don ta ga Sadiyar ma har wani harararta take tana mata gwalo a fakaice bai gani ba. Haƙuri ya shiga bata yana faɗin zai ɗauki mataki kafin ya ƙarasa ta kashe wayar. Mota ya shiga ya bi bayansu zuwa gidansu, ko da ya je dakyar suka saurare shi ita da ƙawarta sai dai a ƙarshe ta nuna ita ba za ta zauna da kishiya ba sai dai ya zaɓa ko ita ko Sadiya!. Nan ya shiga faɗa mata shi da a ce don ta shi ne da tuni ya daɗe da tsinke igiyar aurensa da Sadiya, don dai ita ce da ƙwawa sannan da a ce tana da zuciya da tuni abubuwan da yake mata ma ta nemi sakin auren ko da kuwa a kotu ne!. Ita dai ta nuna babu ruwanta yanzu zaɓi ya rage gare shi, tana gama faɗar hakan sula shige gidannsula barshi ita da Huzaifa. Ko da ya jima yana tunanin mafita a ƙarshe ya juya ya shiga mota ko gidan Hajiya bai je ba bare ya shawarce ta don ya san ƙarshen aleewa ƙasa ne, kuma dai ko ya shawarce ta ko dai ya ranke hukunci da kansa to tabbas ba wani abu za ta ce ba tun da ya san ita ma dai daga ita har ƴan uwansa ba ƙaunar Sadiya suke ba. Sadiya tana haɗawa Kalifa kunu wanda ta dama masa take zuba madara don yanzu madara ma ƴar aune take siya kwata sai take musu amfani da ita, don sana'ar ta ta rufa mata asiri sosai, ana cikin hakan ta ji tsayuwar motarsa da yake ɗazu bai rufe ƙofar gidan ba shi ma yaron da ya fita bai rufe ba, don haka shigowarsa ta ji kamar an jefo shi. Sai da ya shigo ya tuna dole ya yi takatsan tsan don kar ta gane manufarsa. Fuskarsa ya gyara tare da saita yayinsa yana ƙirƙirar murmushin yaƙeyana shigowa ya zauna ya ce "Sadiya manyan ƙasa ni kam ya aka yi kika san Meenal za ta zo ko in ce yaushe na faɗa miki da dare za su zo?" Ya faɗa a zahiri bai nuna komai ba amma a baɗini kamar ya wanke ta da mari don ta rusa masa komai, bata san cewa zaman alaƙaƙai yake da ita ba. Ɗan murmusawa ta yi sai kuma cike da kissa irin ta mata ta ce "Ayya Abban Kalifa dama na yj hakan ne don kar su ɗauka baka sanar da zuwansu ba, na yi haka ne don in wanke ka" Jim ya ɗan yi sai kuma ya ce "Amma kin yi dogon tunani gaskiya irinku basu da yawa a cikin mata" Tana ba Kalifa kunun ta yi dariya ba tare da ta ce komai ba amma da a farko ta ji faɗuwar gaba gudun kar dai laifi ne hakan. Ya jima bai ce komai ba sai ƴar magana da yake kiran Kalifa da ita sai kuma ya ce "Abin nan da kika yi kin birgeni shi ya sa na ce ki tashi mu je gidan Baba mu gaishe da su" Da sauri ta ɗago fuskarta tana bayyana tsantsar mamaki, don abu ne da bai taɓa faruwa ba wai a ce ya je gaishe da iyayenta daɗin daɗawar ma har da ita. Cike da zumuɗi bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba tana cewa Kalifa sai mun dawo ka sha kunun. Shi kuwa Nasir yana mata kallon baki da hankal. Hijabi ta saka dogo har ƙasa ta ɗauki Kalifa tana cewa gidan Baba za su je, saboda kissa har da buɗe mata mota, a take ta fara jin lallai addua,arta ta fara karɓuwa ta samun ƴanci a gidan miji!. A ƙofar gidan su ya yi parking tana ta washe baki ya ce "Ki min sallama da Baban idan yana nan sai na gaishe da su" Ranta fari ƙal tana jin kanta ita ma kamar kowace mace, yau dai ta zo gidansu cikin kwanciyar hankali ba za a kore ta ba ko a kyare ta cewar ta koma tun da yau mai kankat aka yi wato har da mijin. Da sallama ya shiga gidan, kowa yana hada-hadarsa Baba yana zaune a kan dutsi yana alwalar magriba don wasu masallatan sun fara kira. Yana ganinta ya dangwarar da butar ya ce "Sadiya wace jarabar ce ta kawo ki gida da gabannin magribar wannan? " Ya faɗa don tunaninsa laifi ta yi suka yi faɗa ko kuma ƙara ta kawo da sauri ta ce "Baba tare da Abban Kalifan muke shi ya kawo mu a mota yana waje ya ce ka je ku gaisa" Wani irin washe baki Baba ya yi tuni ya tashi yana saɓa babbar rigarsa tare da gyara zaman hularsa matan gida da aka fara ƙusƙus jin abin da Sadiyar ta faɗa, Baba a zaure har tuntuɓe ya yi da wani dutse yana jin kansa wai yau shi ne sirikinsa ya zo har ƙofar gidansa gaishe da shi kuma a motar da akam ce sabuwa ce ma, ya san yau kam Nasir zai masa sha tara ta arziƙi, sai dai kash!. Yana fitowa bai ga komai ba sai sawun motar Nasir don tuni ya cikawa rigarsa iska!. ALIYA Ranta yana ƙuna ta ji Umma ta ce "Tsakaninki da Allah Aliya ko dai don kin daina ra,ayinsa kika faɗi haka Aliya ban da sharri" Umma ta faɗa tana yin ƙasa da murya don tuni idanunta sun raina fata sun yi jawur kamar ta sha ƙwayar da ta fi ƙarfin kanta. Aliya tana kuka ƙasa-ƙasa ta ce "Umma wallahi ganin idona Kasim ba asalin namiji ba ne" Umma cike da ruɗu ta ce "Ya aka yi kika gane Aliya kar fa ki yi abu da ka" Aliya tana jin tamkar dai ta shiga kwakwalwar Umma ta cusa mata abinnda take so ta fahimta. Ta ce "Umma idan baki yarda ba in koma ɗakin in ɗakko miki hotonsa ki ga zahir... Tun bata ƙarasa ba Umma ta ce "Kina da hankali Aliya ina ni ina ganin gaban siriki tsakani da Allah wannan ai mugun ji ne, to ke in ban da ma tonon silili Aliya amarya tana langwaɓewa namiji ya mata bauta a daren farko amma ke kin... Aliya ta katse Umma da faɗin "Umma ana ga yaƙi kina ga ƙura Umma ba zan taɓa zama da mata maza a matsayin miji ba" Umma tana ƙara da murya ta ce "Aliya kar fa kisa in ke ɗaga murya kin san dai akwai sauran ƴan biki da basu tafi ba suna ɗakinku ku, dama jiyaa ana ta batun kyawun gidan Jidda ke babu ma wanda yake batun ki in dai aka sako maganar gidanki sai dai in zancen mutuwar inji za a yi haka jiya na sha ƙunsar takaici, dakyae bacci ɓarawo ya sureni wallahi cikin baccina na yi mafarki ke kin koma gidan Jidda matsayin matar Ibrahim ita kuma ta koma gidan Kasim matsayin matarsa " Aliya ta ce "Ai haka ne ma Umma wannan ba gidan zamana ba ne babu wani kyau da armashi ga miji yana ɗauke da baƙar ƙaddara, ni dai Umma ki faɗawa Abba ana jimawa daga gari ya waye zan taho gi.. Umma ta katse mata hanzari da faɗin "Aliya ki rufa min asiri wallahi kinnsan dai halin Abbanku, sannan tonuwar asiri ne a ce kin fito a ranar da kika yi kwana ɗaya da tarewa a gidan miji, ƙaramar bazawara kike son zama?" Aliya ta rushe da kuka ta ce "Ni dai ba zan zauna in haifi mata maza ba" Umma ta ce "Aliya wa ya faɗa miki ana gadon haihuwar mata maza? Ai baba gadon haihuwar kawai dai halitta ce amma ba a gado" Umma ta faɗa cike da son ganin ra lallaɓa ta duk da ta san tabbas gaskiya ta faɗa ba a gadon haihuwar amma dai ita yanzu duk ta rasa nutsuwa in ta tuno Jidda tana can maƙure da nata mijin a gidan daula cikin kwanciyar hankali sai ta yi ta tsine mata a zuciyarta. Sun jima suna waya Aliya tana kuka Umma tana lallashin ta duk da ita ma kaɗan ya rage ta rushe da kukan, amma ta bari sai bayan sun gama wayar ta keɓe ta sharɓi kukanta son ranta, suna cikin wayar Abba ya shigo da sallama da sauri Umma ta danne makunnar wayar har sai da wayar ta mutu, tana kirkirar murmushi tare da ɗauke kai kar ya ga fuskarta. Aliya kuwa ko da ta ji wayar ta ɗauke ta sauke ta daga kunnenta ta duba aai ta ga kiran ne ya katse, ƙara kiran Umma ta yi amma sai ta ji wayar a kashe, hakan ya sa ta fito daga kicin ɗin har wani duhu take gani tsabar ɓacin rai ta nufi ɗakin tana tuna irin uƙubar da za ta shayar da Kasim a zaman ta d shi a gidan, tun da har shi ya ga ya ji ya gani. Tana shiga ɗakin ta ɗauki riga ta saka har lokacin yana bacci sai jan munshari yake, wani haushinsa ya turnuƙe Aliya ta tsaya tana ƙare masa kallo, Kasim bawan Allah kamar ya san mai take ya ɗan yi juyi kaɗan, sai kuwa ya ɗan yamutsa fuska kafin ya buɗe idanunsa tarrr a kan Aliya wacce take tsaye riƙe da ƙugu tana jifansa da mugun kallo hawaye yana zuba kamar an buɗe famfo. Sai lokacin ma ya gama wartsakewa da sauri ya lura da babu kaya jikinsa faɗuwar gabansa ya tsananta tunowa da ya yi cewa akwai ɓoyayyan al,amarin da yake tare da shi wanda Aliya bata sani ba. A kiɗime ya tashi zaune tare da rarumo gefen zanin gadon ya rufa a gabansa... MAMAN AFRAH 09015576222 https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=wwt *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️⃣5️⃣ SADIYA Tun da Baba ya fita ta fara zuwa tana gaishe da matan gidan cike da girmamawa, duk cikin ƴaƴan gidan babu mai haƙuri da ladabi da biyayyar Sadiya tamkar dai ba a gidan take ba, don Sadiya daban ce a cikin ƴaƴan gidan ta kowane fanni. Lokacin sa ta je ta gaishe da Mama Habiba har za ta tafi Mama wacce ta ɗauki Kalifa ta ɗora cinya tana cewa "Tun da dai baka son in ɗauke ka to zan maka saki uku"Ta faɗa tana dariya shi ma dariyar yake duk da bai san manufar maganar tata ba amma dai ya gane wasa take masa. Mama Habiba ta kalli Sadiya da take zaune kusa da ita ta ce "Sadiya ki ci gaba da haƙuri a gidan aurenki, ki sani aljanna kike nema duk wani abu da namiji zai ƙunsa miki na baƙin ciki da ɓacin rai to ki sani wannan ɗacin da za ki ji a zuciyarki idan kika danne Allah zai baki ladan haƙuri sannan shi aure dama ɗan haƙuri ne, ita aljanna ba a samunta ta sauƙi, kuma duk ko da a ce mutum ya tauye maka haƙƙi ko yana maka abubuwa da gangan idan ka yi haƙuri wataran za ka ci riba. Na sanki da haƙuri to ki ci gaba wataran in har muna raye za ki ce na faɗa miki domin sai kin ga sakamakon haƙuri da juriyar da kika yi" Sadiya ta ɗago kai ta kalli Mama Habiba idanun Sadiya suka cika da ƙwalla tana jin Mama Habiba tamkar dai mahaifiyarta Mama Habiba tana mata abin da Mamarta bata mata, tana nusar da ita abubuwa masu yawa. Cike da rawar murya ta ce "In sha Allahu Mama, na gode sosai ina alfahri da ke" Hannu Mama ta kai ta dafa kafaɗar Sadiya ra ce "Babu komai Sadiya haƙuri ba ya taɓa yin tawa ko kuma a ce ya ƙare ita dama rayuwar cike take da ƙalubale, kowa da jarawabarsa haka kowa da ƙaddararsa wata ƙaddararta rashin samun mijin auren, wata kuma ta samu amma kuma babu kwanciyar hankali, wata kuma kishiya ce matsalarta ta hana ta sakat ta hana ta zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta kange komai ta hana ƴaƴanta su wayata" Sadiya kai kawai take gyaɗawa kamar ƙadangaruwa don ta san duk abin da Mama take faɗa haka yake!. Suna cikin hakan ta ce ta je ta yi alwala, alwalar ta yi ta dawo ɗakin ita ma Mama ta yi suka tada sallah shi kuma Kalifa yana zaune yana cin biskit ɗin da Mama Habiba ta ɗakko ta ɓarw ta bashi. Bayan sun idar Mamar ta ci gaba da mata nasiha a kan kishiyar da za a mata tana ta nuna mata yadda za ta yi ta zauna lafiya duk da ta san Sadiya bata da hayaniya kuma tana da kawar da kai amma dai dole ta ƙara koyawa kanta juriya kasancewar yanzu abubuwa za au sauya idan da mijinta ne matsalarta yanzu kuma wata za ta shigo gidan kuma ba a san da mai za ta shigo ba, galibi ko yawanci mata ba wai suna tsoron kishiya ba ne sai dai suna tsorob da mai za ta shigo? Shin zaman lafiya ne zai kawo ta ko kuma kawai zuwa za ta yi ta hargitsa gidan, wata sai ta fitar da matar gidan kuma ta zo ta bar gidan, shi ya sa kishiya kala-kala ce wata ta zaman lafiya wata akasin haka. Sadiya ji take tamkar a cikin ƙwaƙwalwarta Mama take kissima maganganun, don sosai suke shigarta, duk da kasancewarta wacce ta taso a gidan kishiyoyi har huɗu amma dai shi zaman aure makaranta ce mai zaman kanta da babu wacce za ta fane sai wacce ta yi auren, kazalika kishiya ma abu ce mai zaman kanta da babu wacce za ta fahimci zama da ita sai wacce aka yi wa duk da ba a taru zan zama ɗaya ba, tun da ita Sadiyar shaida ce tun da gashi yanzu kishiyar mahaifiyartw ce take nusantar da ita. Ba wai don tata mahaifiyar bata gidan ba, tun da da ta gaishe da Mamar ta je wajen Mama Habibar. A ɓangaren Baba tun da ya yi turus ganin babu motar Nasir sai abubuwa da dama suka shiga masa gizo a ƙwaƙwalwa ya shiga saƙa da warwara sai dai idan zuciyarsa ta kissima masa abu marar kyau dangane da kawo Sadiya gida da Nasir ya yi sai ya yi saurin kawar da hakan, yana ƙara faɗawa kansa cewa ba da wata manufa Nasir ɗin ya kawo ta ba, tun da idan ya tuna fuskar Sadiya ai ya ga babu wata damuwa ko alamar ɓacin rai sannan ya ga Sadiyar ta murmure ta yi kyau abin ta babu wata rama ko yanayin da ya saba ganinta a can baya, ya ƙara haɗa hakan da cewa Nasir ne yake vata kulawa bai san cewa ita ce ta samarwa kanta mafita ba da taimakon Kaka, duk da ya san da maganar amma dai bai san sana,a ce mafarin komai ba, sana,a ce ta kaita ga wannan ɓigirin na walwala da mirmurewa don ta wuce jira a bata da kanta take yi wa kanta abubuwa babu ruwanta da jiran a bata bare a wulaƙantata, tun da wasu mazan masu son abin hannunsu wanda basa ɓanɓaruwa basa son sauke nauyin iyali wansa ya rataya a wuyansu suna yin hakan ne don sun gaji da bani- bami na mace koyaushe a ce ana buƙatar wani abu daga gare su amma in kina sana,a za ki ga sauyi domin ke kanki sai kin san akwai bambanci da ka ɗauki abinka da kuma bambanci da a baka. Ba a taru an zama ɗaya ba amma dai Allah shi kaɗai ne ba ya gajiya da a roƙe shi. Baba ya jima yana ɗan kaiwa da komowa gani yake kamar sai Nasir ɗin wani waje ya je ya dawo, har sai da ya kama hanya zai koma cikin gidan sai dai jin liman ya yi kabbarar harama sai ya nufi masallacin yana bazama riga kamar zai tashi sama, botocin da ya gani da ruwa ya ɗauki ɗaya ya yi alwala da sauri, saboda dama bai ƙarasa alwalar da yake yi a gidan ba, da ya ji Nasir ya zo ya fita. cikin masallacin ya shiga sa,arsa ɗaya liman ya ja doguwar sura shi ya sa ba a wuce shi ba. Tun da ya yi kabbarar shi dai gashi nan ne yana sallah amma dai sheɗan ya yi wa tunaninsa linzami don kawai bai ankara ba sai ya ji ya tafi tunani, kuma tunanin ba a kan komai ba sai a kan kawo Sadiya gida da Nasir ya yi. Tun da aka kai sujadar ƙarshen Baba ya daddage yana addu,a yana cewa "Allah ka sa Nasir ba da wata manufa ya kawo yarinyar nan gida ba, Allah ka taimake ni kar ya ƙara min wahala a kan wacce nake sha ta riƙon ƴaƴan nan Allah ka dube ni ka bani ɗa namiji wanda zai tallafa mini ya ɗauki ɗawainiyata" Har aka kusa yin sallama bai ɗago ba sai can ya ɗago ya fara tahiya. Ko da aka idar babu wani azkar da ya yi shi ne na farkon tashi tsaye a masallacin, tamkar dama jira yake a idar shi ya fara fitowa daga masallacin idanunsa a ƙofar gidansa amma babu alamar motar Nasir don a tunaninsa ko zai dawo. Tsabar ya saka abin a ransa takalmin ma a juye ya saka yana jin wani maƙocinsa yana masa magana wanda ya fito daga masallacin amma bai waiwaya ba bare ya amsa don shi gani yake yana cikin gagarumin tashin hankali na rashin sanin matsaya kuma takamaiman maganar zuwan Sadiya. Yana shiga gidan ya fara ƙwalawa Sadiya kira tamkar zai fasa gidan, bai ma damu da sauran wasu ƴan matan da basa gidan ba, don shi dama tarbuyar ba damunsa ta yi ba shi dai damuwarsa ya aurar da su ya huta kuma bai damu da nagartar miji ba sannan ko da mai zuwa wajen ƴaƴan ne bai damu ya ga wani nutsatstse ko wanda ya san mai yake ba babu ruwansa da nakasun mutum. Sadiya wacce Mama Habiba ta kawowa tuwon ta da aka kasa aka bata ta tsoma hannunta kenan ta ɗauki loma za ta kai baki Baba ya ƙwala mata kiran da ya sa ta ji wata irin faɗuwar gaba, da sauri ta mayar da tuwon hannun nata ta miƙe tsaye tana amsawa amma bai daina kiran ba ita gabaɗaya ma ya tada mata hankali ba ita kaɗai ba hatta Mama Habiba tsaye ta miƙe tana zulumin anya lafiya? Mama Talatuwa ma mahaifiyar Sadiya gabanta ne ya faɗi dama tana ta tunanin inda Sumy ta tafi har yanzu babu ko da ƙurarta kuma yanzu bayan Sadiya ta sanar da ita da Nasir suka zo amma ta san kowa ya ji yanayin kiran da Baba yake mata to ba na lafiya ba ne, don duk wanda ya san Baba to ya san wannan muryar tasa ta ɓacin rai ce. Mama Talatu a zuciyarta ta ce 'Ko dai wani laifin Sadiya ta yi Nasir ɗin ya kawo ƙarar ts, Allah sa dai ba a kan maganar aurensa ta yi wani abun ba, haka kawai muna zaman zaman mu za ta tada mana zaune tsaye' Ma ta faɗa tana kasa kunne don jin mai zai biyo baya domin ta san a wannan hargagin da Baba yake to tabbas maganrsa sai kowa ya ji don bai iya faɗa a hankali ba. Sadiya da ta fito jiki sanyi ƙalau tana tafiya kamar ƙwai ya fashe mata a ciki, abubuwa da dama suna mata kai kawo na saƙa da warwara amma ta rasa makamar da za ta kama na dalilin wannan kiran da Baba yake mata. Cike da masifa ya ce "Sadiya mai kika yi wa Nasir?" Tambayar ta saka zuciyarta tsinkeww ƴaƴan hanjinta suka hargitse tana zare ido cike da tsoro ta ce "Baba wani abun Nasir ya ce na masa?" ,Ta tambaya kamar zuciyarta za ta fasa ƙirjinta ta fito. Baba takalminsa ya ciro daga ƙafa wanda na hagun ne amma a ƙafar dama tun da garin sauri ya sako a baibai da takalmin ya shiga nunata sai kuma ya ɗaga takalmin ya yi kanta zai kai mata duka da sauri ta tashi ta yi baya don dama da ta zo tsugunnawa ta yi a gabansa, Mama Habiba da sauri ta ƙaraso ta shiga tsakani gabaɗaya kowa ya fito ya yi carko-carko don yanayin yadda Baba yake hargagi babu abin da zai sa mutum ya kasa yunanin sakin Sadiyar aka yi kuma wani babban laifi ta aikata. Kalifa ma fitowa ya yi hannunsa duk miyar da yake cin tuwo ɗaya hannun kuma riƙe da ƙaramar wata roba da Mama ta zuba masa tuwon don dama a nata ta ɗauka masa ta ba Sadiya sauran. Baba ya ce "Ina tambayarki kina tambayata", Tana girgiza kai ta ɓuya a bayan Mama Habiba ganin kamar zai duke ta da takalmjn sai kumfar baki yake. Mama Habiba tana bashi baki cike da jin haushin ta ya saka hannu ya matsar da ita gefe guda yana nuna ta da takalmin hannunsa ya ce "Na sha faɗa miki ki fita sabgata da ta ƴaƴana amma rawar kai ya hana ki" Bai jira cewarta ba ya matsa kusa da Sadiya ya ce "Uban mai kika masa ya kwaso ki ya dawo da ke gida?" Cike da rawar baki da na jiki ta ce "Wallahi Baba iya sanina ban masa komai ba, ina zaune ina ba Kalifa kunu ya shigo muna hira da shi har yana dariya ya ce in zo mu zo mu gaishe da ku" Shiru ya yi yana nazari don wani ɓangare na zuciyarsa ya fara raya masa cewa ko dai da gaske babu abin da ta masa ko dai ya je wani waje ne ya dawo amma kuma hankalinsa ya ƙi kwanciya da hakan. Cike da tuhuma ya ce "Kuma kin tabbata babu wani tsohon laifi da kika masa? Ai sau da dama ana yi wa mutum laifi sai yake tarawa rana ɗaya ta yi hukunci" Kia kawai take girgizawa domin yanzu Baba ya ƙure duk wani ƙwarin gwiwarta musamman da yance ko tsohon laifi ne aka tara, tun ba a je ko ina ba sai ta ji gabaɗaya gidan ya gundure ta, kai a rayuwa a ce gidan mahaifinka baka da kataɓus ko ikon zuwa ka ji daɗi sai dai koyaushe ana tsoron mutuwar aurenka kamar a kanka aka fara aure, bayan aure babu inda aka haramta mutuwarsa sai dai kawai sakin halattacen abu ne da ubangaiji ba ya son sa saboda a duk lokacin da aka yi sakin aure sai al,aeshin ubangiji ya girgiza. Jifa ya yi da takalamin gannunsa sai lokacin ma ya gane ashe ba daidai ya saka takalmin ba, yana jan wani uban tsaki ya gyara saka takalmin, gabaɗaya bashi da wata nutsuwa, waya ya ɗakko a aljihunsa ya shiga dokawa Nasir kira sai dai ba a cewa a kashe amma dai wayar bata shiga da alama dai Nasir ɗin ya saka lambar Baba a wani waje da baban ba zai same shi ba ko dai black list ma ya daka shi oho. Ya kira ya yi sau goma amma waya bata shiga ba, ƴan gida sai ƙusƙus ake, Mama Talatu tana daga bakin ƙofar ɗaki ko yawu ta kasa haɗiya tana fargabar ko dai Nasir ya saki Sadiya idan kuwa haka ne tabbas nata auren ma yana cikin jalala kamar yadda Baba ya sha jadda da mata a baya cewa matuwƙar dai ta zuga Sadiya ta kashe aurenta to tata igiyar auren ma tana cikin wani hali. A zafafe ya ce "Kira min shi in ji dalilin kawo ki gidan nan da duhun magriba ya tafi babu wani ƙwaƙƙwaran bayani" Duk ta rikice da masifar Baban hakan ya sa ta ma manta da batub wata waya. Sai da ta tuna sannan ta ce "Am na...na... bar wayar a gida" Baba da ƙarfi ya ce "Allahumma ajirni fi musiba" Kai Sadiya ta sunkuyar tana jin zafin furucinsa, sai kuma cike da gargaɗi ya ce "Bari in jira a yi ishsha,i idan har bai dawo ba ki jira nawa hukuncin" Na'am ta yi da maganarsa bai yi wa kowa magana ba ya juya fuuu ya yi ɗakinsa. Juyawa ta yi za ta koma ɗakin Mama Habiba ganin Mama Sa'ade tana mata wata dariyar ƙeta, sai kuma ta ji Mama Talatu ta kira ta hakan ya sa ta jiya alkalar tafiyar tata zuwa ɗakin Mama Talatun. Tana zuwa ƙofar ɗakin Mamar ta juya ta shige ɗakin Sadiya ta mara mata baya, Kalifa kuma Mama Habiba ta tafi ɗakinta da shi, tana shiga Mamar bata wani damu da halin da take ciki ba ta ce "Sadiya mai kika yi wa Nasir ya dawo da ke gida?" Sadiya ta amsa tambayar sa har ta gaji da amsawa kamar yadda ta ba Baba amsar cewa babu abin da ta masa haka ma ta ba Mama amsa. Amma Mama ta ringa bala'i tana faɗin akwai dai wata a ƙasa domin ai ruwa ba ya tsamu banza, sai dai duk rantse -rantsen da ta yi Mamar bata yard ba. Zuwa can aka kira sallar ishsha,i ta fito ta wanke hannu ta sake wata alwalar, tana jin da za ta gifta ta gaban Mama Bilki tana mata habaici, wai sun zama ɗaya da sauran yaran gidan da ake yi wa gorin rashin samun miji Allah ya ƙara tun da yanzu ita ma ta dawo zaman zawarci. Bata ce komai ba illa iyaka ta wuce ta shige ɗakin Mama tun da dai yanzu abin ya haɗe mata biyu wato rana zafi inuwa kuma ƙuna. A tsanake ta yi sallar ta ta ringa kai kukan ta wajen ubangiji a cikin sujadarta don ta san shi kaɗai ne zai yi mata mafita ta alkairi kuma shi yake tafiyar da dukkan lamuranta. Baba tsabar damuwa da ɗorawa kai babu abin da ya ci don har da man shanu da ya siyo wanda ya ce zai ci tuwo amma tsabar rashin nutsuwa ko kallon kwanukan tuwon da aka ajiye masa bai yi ba. Ana yin sallar ya shigo gidan, don tunaninsa ma da ya fito daga masallacin zai ga motar Nasir amma shiru maƙatau babu shi babu alamarsa. Kiran Sadiya shi ne sallamarsa, lokacin Sumy da sauran wanda basa nan duk sun dawo, kowa kunne ya kasa don ya ji mai Baban zai ce, Sadiya wacce ta amsa ta taso jiki yana rawa Sumy dama tun da ta shigo take faman yada maganar ganin Sadiya da dare don ta san dai ruwa ba ya tsami banza. Tana fitowa Baba ya ce "Wuce mu tafi in mayar da ke ɗakin ki" Cike da marairaicewa ta ce "Baba ina jin fa zai dawo" Ta faɗa don ganin Baban bai mayar da ita domin a ganinta matsawar dai ya mayar da ita ba ƙaramin raini zai ƙara janyowa mata a wajen Nasir ba ta fi so ya dawo da kansa tun da a iya saninta bata masa komai ba, amma dai ya kamata da a saurara a ji ta bakinsa amma kamar zubar da kima ne namiji ya maido mace gida da kansa kuma a mayar da itw, sai dai shi Baban babu mai faɗa masa ya ji. Cike da hargowa ya ce "Wane shegen ne ya ce miki zai dawo, da a ce zai dawo ai da tuni ya dawo amma har an yi ishsha babu shi babu labarinsa, dole ki koma ɗakinki shi ne mutuncina da kwanciyar hankalinki " Da to ta amsa masa ba don ranta ya so ba sai dai don babu yadda za ta yi, takalmi ta saka ita tsabar ɓacin rai ma ta manta da Kalifa da yake ɗakin Mama Habiba. Maganar Baba ta katse mata hanzari da ya ce "Ina Kalifan yake?" Fitowar Mama Habiba riƙe da Kalifan ne ya dakatar da Sadiya daga bashi amsa, shi ya karɓi Kalifan ya yi gaba Sadiyar tana biye da shi Mama Habiba tana bin ta da kallo cike da tausayawa. Suna fitowa ya tare wani mai napep tsayawa ya yi wani matashin saurayi ne wanda kansa yake rawa ya ƙure kiɗa sai rausaya kai yake haka suka shiga Baba ya faɗa masa inda zai kai su suka tasamma gidan Nasir. ALIYA Sai da ya yi da gaske wajen yaƙi da zuciyarsa ganin tsananin razanar da ya yj bata bayyana ba duk da ita Aliya ta fahimci ya tsorata, tana tunanin to da shi mene ne nufinsa da har zai yi tunanin ba za ta ga abin da yake ɗauke da shi ba, tun da dai aure ai zama ne na dindindin ba ya buƙatar ɓoye-ɓoye don duk abin da aka ɓoye watarana sai ya bayyana. Wani yawu ya haɗiye muƙut yana ɗan wayincewa ya ce "Yau ban yi sallar asuba ba har gari ya yi haske" Ya faɗa har lokacin ba ya cikin nutsuwarsa wani kallon tsantsar tsana Aliya take binsa da shi ganin haka ya fara jan mazaunai har ya zo bakin gadon, yana zuwa ya sako ƙafafunsa ƙasa har lokacin sai jan zanin gadon yake yana rufe jikinsa tamkar dai wanda ba ya ƙaunar a ga ko da cinyarsa ne bare kuma wancan babban wuri da ya san ya adana sirrinsa a wajen wanda babu wamda ya san da hakan sai mutane ƙalilan. Tsaye ta tashi a kan ƙafafunsa da suke barazanar gaza ɗaukar gangar jikinsa sabosa ji yake kamar ba zai iya taka su a kan ƙasa ba bare har su kai shi zuwa wani waje. Gabaɗaya ya naɗo zanin gadon ya cire shi daga kan gadon, ya shiga ɗaura zani tamkar wata mace sai da ya ɗaura ya ji wani ɗan kwanciyar hankali ya saukar masa tamkar dai yana rayawa a ransa cewa Aliya bata ga komai ba tunanin hakan ne kaɗai yake ganin zai saukar masa da nutsuwar da har zai iya fuskantar ta. Ya ɗan sassauta murya ya ce "Ki yi haƙuri Aliya na far miki ba tare da amincewarki ba wallahi kin san ba zan iya haƙuri ba, bare har na jure a daren farkon ki a gidana matsayinki na mallakina wani abu bai shiga tsakaninmu ba pls ina roƙon ki mini wannan afuwar!". Ya faɗa yana haɗa hannunsa wajen roƙon ta. Ji take tamkar ta samu mashi ko tsinin wuƙa ta raba ransa da gamgar jikinsa, tsantsar tsanarsa ta ninku a zuciyarta, ninkuwar da bata jin akwai ranar da farashin ta zai yi ƙasa. Bai jira cewarta ba don ya ga ta zaɓi masa kallon tuhuma da tsana a kan ta furta masa kalamin da yake son ya ji ta faɗa ko ya san inda ya dosa. Ya ƙara kalallame murya ya ce "Mu je ki gasa jikin ki kin ji Aliyata, mu yi wankan tsarki mu yi sallah lokaci yana ƙurewa" Kamae wanda za ta fasa ɗakin saboda ƙaraji haka ya ji tashin sautin maganarta tana faɗin "Kasim ya isheka, ka riƙe wannan daɗin bakin da kake yi kai kanka ka san ni Aliya babu wani daɗin bakinka da zai yi tasiri ba, abu na farko da zan faɗa maka shi ne na tsane ka ba na ƙaunarka ka yaudare ne zan ma iya cewa ka damfare ni" Gabansa ne ya shiga dokawa da ƙarfi ya fara tunanin wace irin baƙar rana ce, shi dai ya san bacci take lokacin da ya gabatar da sunna bare ya ce ko abin da ya yi ne bai gamshe ta ba wato bata samu abij da take buƙata daga gareshi ba kasancewarsa na namiji ba. Cike da fargaba ya ce "Haba Aliya kar ki manta soyayya ce ta gina alaƙa ta da ke fa... Hannu ta ɗaga masa ta hanyar dakatar da shi ta ce "Ya isa! Na ce ya isa haka, ni ba wasan kwaikwayo nake yi ba idan wasan kwaikwayo kake so za ka iya kunna su Adam zango da Ali Nuhu idan a ɓangaren mata ne kana iya kallon Momi Gombe, ni Aliya a gaskiya nake faɗa maka magana babu wasa a ciki na tsane ka ka yaudare ne Kasim ashe kai mata-maza ne???" Da sauri ya kalle ta har zanin gadon da ya nannaɗa a jikinsa yana neman suɓucewa da sauri ya riƙe ya ce "Aliya ban ɓoye miki hakan ba sai don na ga ba wani nakasu ba ne hakan, tabbas an haife ni da baiwar mata -maza amma kuma an yi maganin wannan larurar tun ba yanzu ba wannan wajen ma da kika gani wajen ɓangaren matantakar ne da likitoci suka yi min aiki har suka ɗinke wajen, sannan wajen ai ya zama ma bashi da wani tasiri tun da ni namiji ne can ma na fi ƙarfi ta ɓangaren maza, za ki ga ma ko breast ɗina sak na maza ne bai fito irin na mace ba, kin san shi mata -maza ana samunsu da breast su girma sak na mace sannan al'aurarsu ma waje biyu ne ɓangaren mazantaka da kuma ɓangaren matantaka sai dai kowa da ɓangaren da ya fi ƙarfi" Ganin ta zuba masa ido tana sauraron abin da yake cewa sai hakan ya bashi tabbacin tamkar dai abubuwan da yake faɗa suna shigarta hakan ya da ya ɗora da faɗin. "Idan har aka yi wa mata -maza aiki su ma za su rayu kamar kowane mutum wanda ba mata-maza ba, sannan suna haihuwa kamar kowa daɗin daɗawa ba a gadon haihuwar mata maza, wato a ce mata maza ya haifi wanda yake mata maza" Idanu ta runtse don idan tana jin kalmar mata -maza ji takr kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, gashi ya karɓe ɗan budurcin da take alkintawa tana jin yadda ƙasanta yake mata zafi da raɗaɗi amma sanin jinsin Kasim ya daƙushe kowane ciwo da take ji, tabbas don ya shammace ta amma da bai isa ya karɓi budurcin nan ba Lokacin da ta runtse idanunta babu abin da take hangowa sai Jidda kwance a lallausan gado, mai kyakkyawar shimfiɗa da zanin gado mai laushi, tana kwance a lallausar fatar Ibrahim. Hakan ya sa da ta buɗe idanun sai ta ga Kasim ya zama wani baƙiƙƙirin. Idanu ta ɗaga sai ta ga ashe ma wandonsa ya shimfiɗa a kan gadon ya gabatar da sunnar a ka don tana iya hangar abubuwa masu wuyar faɗuwa a jikin wandon. Juyawa kawai ta yi ta fita wanka ta yi amma na farin ruwa wato wanlan janaba, tana gamawa ta ɗauro alwala ta fito, a bakin ƙofa suka ci karo da Kasim ya matsa mata ta wuce, sallah kawai ta yi ta sake sauya wata rigar ta koma falo ta zauna ta harɗe ƙafa, har ya gama abin da zai yi ya zo ya yo sallar ya koma ya zauna a kan sallayar ya jingina da bango. Wajen ƙarfe tara ya fito ya zo ya ce "Aliya mai za ki ci" Ko kallo bai iishe ta ba, ya ɗauki filas ɗin ruwan zafi a kicin ya jona ruwa a kyatil ya kunna ƙaramin gas ɗin ya ɗauki ƙwai guda uku ya fasa ya saka maggi da albasa ya shiga soyawa don shi ba ya jin ma zai iya cin wani abu. A lokacin da yake kicin lokacin ne kiran Umma ya shigo wayar Aliya Umma da ta ƙule a ɗaki saboda kar baƙin da suke tsakar gidan su ji wayar da za ta yi don Abba ya fita, bayan Aliya ta ɗauka Umma ta ce "Aliya ya fita Kasim ɗin?" Aliya ta ce "Umma babu inda zai je yana nan fa" Umma ta ce bari na kira ki an jima" Tana faɗar hakan ta kashe wayar. Shayi ya haɗa mata ya ajiye a gabanta da wainar da ya yi amma ta saka ƙafa ta ture kofin shayin ya zube ta saka ƙafa ta taka wainar, wannan abin da ta yi ba ƙaramin ƙonawa Kasim rai ya yi ba har ta ga gabaɗaya fuskarsa ta sauya, amma sai bai ce mata uffan ba ya ɗauke ya zo ya gyara wajen, ɗaki ya koma ya kwaso kayan shimfiɗar ya wanke ya shimfiɗa wani zanin. Ganin goma ta yi ya saka takalminsa ya fita daga gidan ko magana bai mata ba. Don yanzu zuciyarsa ta fara masa wasi-wasi a kan Aliya ya ga abin nata ba na ƙare ba ne, ya san a iya saninsa Aliya ita ta amince da aurensa ba ya manta ranar da aka kai mata kayan saka rana yadda ta yi ta gode masa kamar ta goya shi amma yanzu komai ya sauya tun daga ranar da aka kai kayan lefe kenan dama abin hannunsa take so ba shi b? Ko da ya fita wuri ya samu ya zauna a waje ya kira Salis yana faɗa masa cewa Aliya ta ga halittarsa tana masa tijara sannan ya faɗa masa abin da ta masa da ya mata girki. Salis cike da ɓacin rai ya kawo wani zagi mai maiƙo ya danƙara ya ce "Wai wannan yarinyar mai take nufi da kai, ya za ka je kana neman zama matar kana neman bata matsayin naka da Allah ya baka na namiji, ai mace ita ce a ƙasan namiji amma kana neman mayar da kanka wani nusari, a wannan zamanin har ta samu namijin da zah shiga kicin ya sama mata abinci amma take neman ta yi wasa da damarta na lura Aliya ba albarkar zaman aure take nema ba, wallahi jiya sai da na zo na kwanta abin da ta maka a kunnen abokanmu ya ɓata min rai" Kasim kamar zai yi kuka ya ce "Wallahi na ga abin nata ba na ƙare ba ne abin ma kamar dai ci gaba yake" Suka ci gaba da tattaunawa. Aliya kuwa yana fita ta ɗaga wayarta mai fashashshen screen ta shiga kiran wayar Amatullahi, bayan ta ɗauka ta ce "Ƙawata amarya wato an kwana ana kwasar amarci shi ne yanzu da aka wartsake aka kirani" Ta faɗa cike da zolaya Aliya ta ce "Dalla can malama rufewa mutane baki ana ga yaƙi kina ga ƙura, mutumin da ya min fyaɗe" Amatullahi ta fashe da dariya ta ce "Batun nawa dai ya zo wato an ci amarcin dai ai ni dama na san duk wayon amarya dole sai an sha manta" Wani tsaki Aliya ta doka ta ce "Idan kika ƙara ambaton amarcin nan sai mun ɓata, na kira ki ne in faɗa miki wani sabon tashin hankali da na tsinci kaina a ciki" Cike da ɓacin rai ta ce "Subhanallahi Allah rabamu da tashin hankali ni fa dama jiya ganin kina kumbure-kumbure shi ya sa ban tsaya yi miki sallama ba, saboda na ga sai ki mini rashin m... Aliyanta katse ta da faɗin "Amatullahi Kasim mata maza ne" Amatullahi zaune ta tashi daga kan doguwar kujerar da take kwance a falon gidansu tana mai saka hannu ta toshe bakinta ta ce "Mata maza fa? Ke yanzu Aliya duk bita da ƙullin da kike yi wa mutumin nan sai kin bishi da sharri?" Aliya cike da haushi ta ce "Wai sharrin mai kike nufi? Ina miki maganar tsakani da Allah mata maza ne Kasim amma kina wani batu" Amatullahi ta ce "Innalillahi mun shiga uku, kuma kika zauna a gidan Aliya?" Aliya ta ce "To ya zan yi?" Amatullahi ta ce "To ke ba shikann ba kin samu maƙalar rabuwa da shi sai ki ce ya yaudare ki bai sanar da ke ba in ya so kin ga kin samu hanuar yakice shege daga rayuwarki dole ya sake ki tun da babu wacce za ta zauna da mata maza, kin ga burinki yana dab da cika na auren mijin Jidda tun da ba uwa kuka haɗa da ita ba, sannan ba uba kuka haɗa ba bare a ce ya hakan ya haramta" Dididim gaban Aliya ya buga a take ƙwaƙwalwarta ta fara mata safa da marwa lokaci guda wani abu ya ɗarsu a zuciyarta, sai dai furucin Amatallahi ya katse matq hanzari in da ta ce "Ina fatan dai babu abin da ya shiga tsakaninku, don mar a je yin abu sau ɗaya ya ɓata miki abubuwa dubu!" Aliya cikin rashin fahimta ta ce ban gane ba?" Amatallahi ta c "To idan yi ɗaya an samu ƙaruwa fa kin ga ko sakin ki ya yi ya barki da jelar goyon ciki da reno" MAMAN FRAH 09025576222 [11/7, 9:00 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/GTq4oSxwxZfLKU7Amx5My1?mode=wwt *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) *NA* *MAMAN AFRAH* BOOK 1️⃣ PAGE 1️⃣6️⃣ Wannan grp ni MAMAN AFRAH na buɗe shi ne domin masu soh saya kayan sallah su yi adashe, za ka zaɓi abin da kake so ka zuba kuɗinka ya danganta da yadda kake so. Duk abin da ka zuba a rubuce yake daga ka gama za a baka kaya. 1-Leshi 4-abaya 2-Atamfa. 5-kayan yara 3-shadda 6-Mayafai 7-Takalmi da jaka 8- Takalman yara Da sauransu idan har kin san ba yi za ki yi ba karki shiga min grp don cire ki zan yi, ba wasa ya taramu a ciki ba. Maman afrah 09025576222 *SADIYA* Tun da suka ɗauki hanyar gidan gabanta yake faɗuwa, tunaninta ɗaya kar Nasir ya yi wa Baba tijara a gabanta domin ba za ta ji daɗin hakan ba, duk da shi Baban yana ganin yana musu ruwan kuɗi amma da alama har yau bai san waye Nasir ko kuma dai ya sani takewa yake yi. A ɓangare ɗaya na zuciyarta yana cike da fargabar ko dai Nasir ya sawwaƙe mata ne babu laifin fari bare na baƙi duk da cewa ita ba tsoron sakin take yi ba kawai tana shayin halin Baba ne yadda yake da son aurar da ƴaƴa tamkar rai da mutuwa. Duk da yanzu ta samu sassauci na zaman gashin ƙumar da Nasir yake mata a cikin gidansa kuɓa ba komai ba ne ya kawo mata wannan sauƙin sai sana'ar da take yi don ta lura da cewa idan har kana da sana,a to baka ma jin zugin ɓacin rai idan an maka saboda wani sa,in rashin zaman lafiyar da yake wanzuwa tsakanin wasu ma,auratan har da ganin matayensu basu da sana,a bare aikin yi, suna ganin duk wata ɗawainiyar mace su za ta ɗorawa amma ba duka aka taru aka zama ɗaya ba wani namijin ko kina sana,a ko aiki babu ruwansa da harkar kuɗinki kuma zai yi abin da ya dace da ɗaukan gabaɗaya ɗawainiyarki da sauke haƙƙinki da ya rataya a wuyansa. Wani namijin kuma shi yana jin daɗi ya ga matarsa tana da abin yi wato ta tsaya da ƙafafunta har ma da kansa zai ke ƙara mata ƙarfin gwiwa, wani kuma sai dai ma ya san duk yadda zai yi domin ganin ya murƙushe komai don kar ki ci gaba saboda yana baƙjn ciki wani kuma yana tsoron ki samu wani ci gaba ko ɗaukaka ki fi ƙarfinsa kowa dai da yadda ya ɗauki rayuwa kuma da yadda yake kallon ta. Sadiya bata san sun shigo layin gidan nata ba domin ta yi nisa a duniyar tunanin da ta lula maganar Baba ce ta katse mata tunanin har hakan yansa mai napep ɗin jan wani uban birki don ya tsorata da furucin Baba ya ɗauka ma wani gagarumin abu ne ya faru, jin Baba ya ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Wannan furucin da ya yi da ƙarfi tamkar wanda ya hango wani gagarumin haɗari ya tunkaro su,shi ne ya sanya Sadiya dawowa hayyacinta a kiɗime tana ciccira ido domin ganin abin da yake faruwa, shi kuma mai napep har da sauri kashe kiɗan da ya ƙure ya tsayar da napep ɗin tare da juyowa ya ga abin da ya faru. Baba kuwa kuwa babu ruwansa da kiɗimar da ya saka su bai yi bori da sanyin jiki ba ya ce "Wai don Allah mai ya sa Nasiru yake son tona mini asiri ne? Ya zai mayar mini da ƴa gida kuma ya garƙamawa gidan mukulli gidan uban wa ya tafi to?" Ya faɗa ya ɗorawa Sadiya Kalifa a cinya, ita Sadiya sai lokacin ta lura da gidan a kulle kuma ta gane duk wannan ɗaga jijiyar wuyan da Baba yake saboda gidan a rufe ne da yake ma basu gama ƙarasowa gaban gidan ba, dogon wuya Baban ya yi ya hango. Baba kuwa fita ya yi daga cikin napep ɗin duk ya gama tada hankalinsa sai baza uwar babbar riga yake tana neman taɗe shi, Sadiya ta ma rasa bakin magana ikon Allah kawai take kallo, shi kuma mai napep da ya gane mai Baban yake yi wa baloƙoƙon sai ya ja wani ƙaramin tsaki ba tare da kowa ya ji ba. Baba kuwa ƙarasawa bakin ƙofar ya yi ya taka matakalar ƙofar gidan ya taɓa kwaɗon (Padlock)Ɗin da aka rufe gidan cike fa faɗa ya ce "Sadiya wai ni kika rako ko kuwa ke na rako da kika zaune a adaidaita sahun? " Cikin sanyin jiki Sadiya ta fito tana cewa "Baba gani na yi gidan a rufe" Yana harararta ya ce "Kuma don gidan a rufe sai ki zauna a ciki kamar wanda dai so kike ki koma gidana" Bata tanka masa ba ya tsaya tare da kama ƙugu yana hangen ta inda Nasir zai fito. Mai napep kuwa ya wani sako ƙafa waje ya ɗauki mataji(Kumb)Ya ɗan taja gashin kansa cike da tantiranci ya ce "Yallaɓai karka manta dai duk tsayuwar da nake yi a wajen nan a kuɗi take don haka yawan jiran da zan yi yawan hauhawar farashin kuɗina" A zuciye Baba ya ce "Abin da ya fi hauhawar farashin kuɗinka, sai ka ce sata kana tsaye ba tafiya kake yi ba bare ka ce mai kake ƙonawa amma kake batun kuɗi yo ba zan biya ba, bayan ma zuwan nawa babu biyan buƙata" Wani irin durowa ya yi daga napep ɗin ya tsaya Baba yana jifansa da wani kallo, mai napep ya waiwaya ya ga layin ba kowa yana ɗaga rigarsa sai ya zaro wata zarɓeɓiyar wuƙa soke a jikin wandonsa, da sauri Baba ya matsa a kiɗime har yana zamewa ya surmiyo daga saman dakalin ƙofar gidan, mai napep ya ce "Bani haƙƙina, in ba haka ba in farɗe maka ciki daga kai har ƴaƴan naka" Da sauri Sadiya ta ƙanƙame Kalifa cike da tsoro dama ita sai ta ga ma tamkar wani ɗan shaye-shaye ne Baba hannunsa yana rawa ya saka a aljihub babbar rigarsa sai ga kuɗi ya fito da su ƴan dubu-dubu kusan dubu ɗari biyu bakinsa yana rawa yake faɗin "Nawa ne kuɗin naka har na jiran da ka yi" Mai napep ya ce "Dubu da ɗari biyar" Baba hannu yana rawa ya ce "Ga dubu biyu ka riƙe canjin" Karɓa mai napep ɗin ya yi ya mayar da wuƙar ya koma cikin napep ya ɗakko ɗari biyar ya jefawa Baba ya ce "Ni da kake ganina haƙƙina nake nema, babu ruwana da sai na karɓi haƙƙin wani shi ya sa ba na sata, na gwammace duk runtsi na nemi na kaina na kaucewa wulaƙanci, kuma ni da kake gani ko akuya ban taɓa kashewa ba ita ce dai dabba bare kuma mutum kawai barazana ce saboda masu ci da haƙƙin wani" Yana gama faɗar hakan ya shiga napep ɗinsa ya tada ya kunna waƙa ya yi kwana ya bar wajen a guje. Baba ɗari biyar ɗin ya ɗauka ya zauna a kan dakalin yana faɗin "Wasu yaran zamanin fitsararru ne, ashe ma duk bige ne ba iya caka wuƙar zai yi ba, ai wallahi da na san haka ne da dubu ɗaya zan bashi" Ya faɗa yana haɗa kan kuɗin ya mayar aljihu, Sadiya kawai kallonsa take da mamakin kalamansa duk da babu wani abu sabo a lamarin Baba. Ranta ƙuna yake bai dace a ce ya yi mata abin da ya mata ba, ta yaya za a yi a ce mijinta ya kaita gidan ya tafi ahi kuma ya dawo da ita. Waje ta samu ta zauna take ganin ikon Allah sun kwashe ya fi minti arba,in amma babu alamar Nasir sai mutane da suke wucewa, Baba sai hamma yake a jere can da ya gaji ya ce "Tashi mu je gidan mahaifiyarsa ki zauna w can ki jira shi, ai in ya dawo ya je can ya ɗakko ki" Wasu hawaye ne masu zafi suka kwaranyo mata, jin wai gidan sirikarsa zai kaita, sirikar da ita ce silar duk wasu abubuwan da suke faruwa, sannan ta yi imani da Allah sai sun yi wa Baban wankin babban bargo sannan kuma ya bar mata abin gori na cewar ubanta ne ya dawo da ita. Kamar daga sama ƙwaƙwalwarta ta kai mata wasu tunani a take ta zaɓi ta yi wa Baban ƙarya don tsira da daraja da mutuncin ta, duk da ƙarya ba ɗabi'arta ba ce kuma ba halayyar ta ba ce. Cike da danne abin da ya ɗarsu a zuciyarta ta ce "Baba ai Hajiyar bata gari ta yi tafiya" Kamar wanda ta faɗa masa saƙon mutuwa ya ce "Subhanallahi bata gari kuma? Amma ai ba za a rasa sauran ƴaƴan nata a gidan ba" Da sauri ta ce "Tare suka tafi" Ya numfasa ya ce "Kai ni dai na ga ta kaina wallahi yaron nan yana son tada mini hawan ruwa, to ke dama baki ɗauki mukulli ba" Sadiya ta ce "Shi ya datse gidan da kansa" Baba ya ce "Dama ya shirya shuka tsiyar nan amma dai mu je gidan, kuma wallahi sai dai mu tafi a ƙafa ba zan biya kuɗin adaidaita ba" Yana faɗa ya fara tafiya, haka Sadiya ta bi bayansa tana ɗauke da Kalifa a kafaɗarta, ranta har ya mata daɗi ganin Baban bai zubar mata da mutunci a wajen Nasir da mahaifiyarsa ba, duk da ta san da wuya ne idan bai faɗa masa cewa ya rakata gidan a rufe ba. Suna tafiya yana masifa wayar Nasir kuwa ya kira ya fi a ƙirga amma bata shiga, ko da suka koma gidan ɗakinsa ya shiga ita kuma ta je ɗakin Mama Talatu. Mama ta ce "Sadiya yankuka dawo har gabana ya faɗi ko dai dama yaji kika yi shi ne kika yi ƙaryar tare kuk?" Kai kawai ta girgiza. Sai a ɗakin Mama Habiba suka kwana saboda Sumy ta kafa rashin mutuncin Kalifa ba zai kwamta a katifa ya musu fitsari ba, shi kuma ɗakin ƴanmatan dama bata ma tarki zuwa ba saboda ta san rashin kunya za su mata. Baba washe gari bai je kasuwa ba, ya kasa fita saboda gani yake tamkar igiyar Sadiya ce za ta tsinke idan ya bar gidan, wato kamar in baya nan Nasir zai dawo ya kawo takardar saki, amma idan yana nan ko da ya zo da niyyar sakin zai roƙe shi ya fasa sakin. Har wajen goma wayar bata shiga, wayar Arfat Baba ya karɓa ya saka lambar Nasir ya hau doka masa kira sai kuwa ya ɗauka da ta kusa katsewa. Nasir ya ce "Hello" Baba ya ce "Buɗe muryarka da kyau Babanka ne mahaifin Sadiya" Da sauri Nasir ya cire wayar daga kunnensa ya duba ya dai tabbatar da numbar Baba ba ce dona ya san ya saka duka lambobin Baba a black list. Jin haka sai Nasir ya ce "Hello ba na ji" Ya faɗa yana ciro wayar daga kunne ya shiga hura iskar bakinsa da ƙarfe, yadda Baban zai ji, Baba jin haka ya buɗe baki yana faɗi "Baka ji na Nasir" Nasir da sauri ya katse kiran, yana shirin saka lambar a black list sai kiran ya sake shigowa haka ya ɗauka Baba ya ce "Nasir mai ya sa ka kawo Sadiya gida" Nasir yana taɓe baki ya ce "Laifi ta yi" Baba ya ce "Amma wannan an yj shegiyar yarinya amma ta ce babu abin da ta yi ka kawota" Nasir ya ce "Ruwa ai ba ya tsami banza" Nan Baba ya shiga bashi haƙuri duk da bai ji laifin da ta yi ba yana cewa zai saɓar mata Naair ya ce "Baba kawai a kan maganar matar da zan aura za ka ja mata kunne, ta ce bata son raini in ya so yanzu zan kira wacce zan aura ɗin sai na faɗa mata ka bani haƙuri in ta haƙura to" Baba tsabar son zuciya bai ma ji zafin maganar Nasir ba ya ce "Amma Sadiya an yi sakarai kishiya ai abokiyar zama ce, kuma ita a gidan ubanta ba mata huɗu ta tashj ta gani ba, ka bata haƙuri za a ja mata kunne" ,Nasir ya amsa yana kashe wayar, don dama jiya daga gidan Baba gidan Hajiya ya je ya faɗa musu komai sai dai su Husna suka ce kar a sake ta saboda gwara ta zauna ta ƙunshi baƙin ciki. Haka Nasir ya kira Meenal ya bata haƙuri yana faɗa mata wai Baban Sadiya yana bashi haƙuri don kamar ma a muryarsa kuka ya ji yana yi, saboda tsabar ƙarya irin ta Nasi, iya kuma Meenal kanta ya mata girma jin ana bata haƙuri kuma yanayin yadda aka ce Baban Sadiyar ya bata haɗuri hakan na nufin Sadiyar bata da wani galihu a wajen ubanta, domin haka ya sa ta ƙara ɗaura ɗamarar yin duk yadda ta so idan ta shiga gidan, don mayar da Sadiya gida da ya yi ba ƙaramin matsayi ta gane tana da shi a wajen Nasir ba don har Hibba ta kira ta tana faɗa mata yadda aka mayar da Sadiyar gida, sosai abin ya faranta mata, sai dai abin da bata sani ba shi lamarin duniya yau naka ne gobe na ɗan uwanka, in dai namiji yana wulaƙanta matarsa to indai ita wacce bata shigo gidan ba tana da hankali to ba murna ya kamata ta yi ba illa jajantawa kanta, tun da duk abin da aka yi wa ta cikin gidan ke ma wataran zai iya miki. Mama Habiba wacce ta shigo ɗakin Baba ta same shi yana waya ta ce "Wallahi abin da kake baka kyautawa, kai ba za ka ƙwatawa ƴarka ƴanci ba sai dai ka zubar mata da kima a gidan aure, baka san wannan zubar mata da daraja zai yi a wajen miji da kishiya kai har ma da dangin mijin ba, ai kamata ya yi ka nuna musu ita ma ƴa ce ka nuna ƴarka ta fi ƙarfin wulaƙanci, ka nuna masa tana da gata tana da galihu sannan kuma ko yau ya sakar maka ita za ka iya riƙe ƴarka, amma ya kawo ta gida ya tafi ka kasa samunsa a waya ka ɗauke ta ka matar da ita yanzu ka ari waya ka kira shi yana maka maganar banza. Ai ita mace tana da kima da daraja, kuma kamata ya yi a kowane lokaci a sauarari kukanta a ji matsalolinta da take ciki na gidan aure, a maganace mata matsalarta a ƙalla wannan shi ne gatan da za ta samu, kuma mijin ma ya gane ba shi kaɗai ne gatanta ba anuna masa ta fi ƙarfin wulaƙanci, amma kai da ya maka laifi ya dawo maka da ƴa babu wani dalili me ƙarfi ka zo kana bashi haƙuri shin wannan kaɗai ba zai saka gobe ma ya ƙara ba?K... Miƙewar Baba tsaye a zafafe ya hana ta ƙarasa maganaryana kumfar baki ya ce "To uwata Habiba faɗa mini yadda zan yi tun da ke ce mijin ni ne matar" Mama Habiba ta ce "Ni dai ban ce ba amma ita gaskiya dama ɗaci ne da ita" Baba ya ce "Kin zo kina ta tada jijiyoyin wuya, shin ke kin san ciwon ɗa ma? Ke da baki taɓa sanin zafin ɗaukan ciki da naƙuda ba baki san ya son ɗa yake a zucuyar iyaye ba har kika zo kina wata maganar banza" Jin furucinsa ta tashi tsaye ba tare da ta ce komai ba ta juya ta fice a ɗakin ra saka takalmin ta ta tafi. Baba kuwa Nasir ya ƙara kira sai Nasir ɗin ya ce babu komai, don dama ita ma Meenal an gama zugata a kan cewa kar ta yarda a saki Sadiyar ta bari su zo su jera don Sadiyar ta fahimci ruwa ba sa,an kwando ba ne. Hakan ya sa Baba ya ji daɗi a ransa a ƙalla dai daga ƙarshe Sadiya za ta koma ɗakinta tun da ba sakinta aka yi ba, Arfat ya ba wayarta ya je ya samu Sadiyar ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, yana ta batun kar ya sake jin an kawo ƙaranta a kan ta yi wa matar da Nasir zai aura wani laifi don haka ta saka a ranta ba da ita kaɗai zai rayu ba sannan ko bayan an yi auren idan ma cewa Nasir ɗin ya yi take gaishe da matar tasa to take yi ai durƙusawa wada ba gajiyawa ba ne kuma zama lafiya ya fi zama ɗan saki. Ƙirjinta tamkar an saka dutsi haka take jin zafin maganganun Baba amma ta danne ta amsa masa, saboda yin biyayya ya zama dole tun da bai saɓawa addini ba. A take ya saka ta shirya ya ce ta kama hanya ta tafi har da bata kuɗin napep ɗari biyar. Tana fita ya tafi kasuwa, ita kuwa dama gidan maƙota ta shiga ta saka yara suna duba mata ana cewa ya tafi ta dawo gidan, sai da la'asar sannan ta tafi saboda Mama Habiba ce ta ce ta yi haka kar ya ga ta koma da safen wani rainin ya biyo baya duk da dai babu rainin da Baba bai ja mata ba. Babu wanda ma ya kawo ta a ka bare har a faɗa masa cewa bata tafin ba. JIDDA Har ya gama waya da Mummy amma Jidda ko motsi bata yi ba bare ya sa ran za ta tashi, ƙara gyara filonsa ya yi ta hanyar daidaita kansa bisa filon, hannunsa ya rungume a ƙirjinsa idanunsa ƙirrr a kan kyakkyawar fuskarta da yake jin babu wata mace da ta kai masa Jiddansa kyau, sosai yake jin sonta da sabuwar ƙaunar ta da ta ƙara dasawa a zucuyarsa a daren jiya yana ƙara huda masa zuciya, lallai ya yarda babu abin da ya fi ga ɗiya mace sama da ta kai mutuncin ta gidan aurenta, saboda hakan ba ƙaramin daraja yake ƙara mata ba wacce ba za ta yanke ba har abada a wajen mijin nata, domin yau sai ya ji kima da darajar Jidda ya wuce na koyaushe a zuciyarsa sannan alƙwari ne ya ɗaukawa kansa cewa zai kula da ita sannan ya mutunta ta don ta sadaukar da komai saboda shi, idan ya ce komai ciki har da aurensa. Idanunsa suna a kan fuskarta bacci ya ƙara wartarsa, bayan wani lokaci kaɗan Jidda ta ɗan yi motsi sai kuma ta runtse idanunta da ƙarfi kafin ta ɗan buɗe su, ata musu masauki a ko ina ba sai a kan Ibrahim da yake bacci, ita kanta ta ba kanta dariya domin kuwa sai da ta ji gabanta ya ɗan bada rass sakamakon ganinsu a gado ɗaya sai sannan ne ta tuna ashe fa sun yi aure!. Murmusawa ta yi a lokaci guda tana tuno da ƴar uwarta Aliya tana rayawa a ranta cewa Aliya ma ta kwana cikin wannan shauƙin mai wuyar fassaruwa. Zaune ta tashi tana son ta sauka ƙasa don zuwa ta samar da abin da za a yi break fast da shi, tana zura ƙafafunta ƙasa Ibrahim da tun tashin ta zaune motsin ta ya katse masa baccin. Tana dab da sauka sai ta ji an riƙo mata hannu wata kunya ce ta turnuƙe ta tana ta tunanin da wane ido za ta kalle shi, sai ta ji ya ce "Haka ake tashi daga kan gadon miji babu sanarwa? Ko dai sai na koya miki yadda ake kula da miji?" Ya faɗa yana kama ɗaya hannun nata ya juyo da ita suke fuskantar juna amma yana daga kwance, ita kuma duk kunya ta lulluɓe ta sai kawai ta sunkuyar da kai tana kallon ƙasa sai dai yanayin fuskarta yana nuni da mrmushin da take da alama maganar da ya yi ce ta bata dariya. Bai jira mai za ta ce ba ya ce "Ai ni in baki iya kula da ni ba sai na koya muki yadda za ki kula da ni, amma sai kina buyana albashi duk wata" Bata san lokacin da dariya mai sauti ta suɓuce mata ba, bata san mai ya sa su maza basa jin kunya ba. Tana cikin wannan dariya ta ji ya ce "Wato dariya na baki ko? To tayani in tashi zaune, kin san yana daga cikin ba mijin kulawa matarsa ta kama hannunsa ta tashe shi zaune" Idanu ta runtse ta ma rasa ya za ta yi ko dai ta furta masa da bakinta cewa kunyarsa ta mata shamaki da furta komai sai dai laɓɓanta sun ƙi bata haɗin kai. Yana riƙe da hannuwan nata ya tashi zaune sai dai bai sakar mata da ƙarfinsa ba, sai da ya zaune gwiwarsa tana jingine da jikinta ya ce "Kar ma ki ce ke kika ɗagani domin ni na tashi kaina, ai ni yanzu na gane bani da gata ita ma Mummy ɗazu da ta kira ni sai faɗa take kar na bar mata ƴa da yunwa, Allah sarki ni babu mai kulani sai dai ko Daddyna" Idanunta a ƙasa ta ce "Shi ɗin ma Daddyna ne" Bakinta ya ƙurawa ido yadda ta yi maganar tamkar ba daga bakinta maganar ta fito ba, sakin ɗaya hannun nata ya yi ya saka hannunsa ɗaya ya ɗago haɓarta idanunsu suka sarƙe da na juna duk wanda zai ga yadda kallon yake wakana haƙiƙa zai gane soyayya ce mai cike da ƙaunar juna, kulawa sadaukarwa haɗe da tsantsar yarda da juna ce a tattare da masoyan, sun daɗe a haka kowane ɗaya daga cikinsu ba ya son ya ƙifta musayar kallo ne na soyayya yake afkuwa, kowa ya tsinci kansa a yanayin ne ba tare da shiryawa hakan ba. Ɗaya hannun ya kai ya riƙe gefen fuskarta ya ce "Jidda ina ƙaunarki da dukkan zuciya da ruhi, hatta gaɓoɓin jikina kowace gaɓa ta san da zaman soyayyarki Jidda" Murmushi ta yi ta ce "Ni ma ina ƙaunarka" Bata ankara ba ta ji ya saki riƙon fuskarta da ya yi da kuma tallafo haɓarta sai gani ta yi ya ɗaga hannu sama yana godewa Allah, ita ma sai ta tsinci kanta da ɗaga nata hannun tana maimaita duk wata godiya da kirari da ta ji yana yi wa ubangijin talikai. Wanka suka ƙara yi da ruwa mai ɗumi bayan sun fito yana shiryawa sai suka ji horn hakan ya sa ya gane saƙon Mummy ya iso, yana jin lokacin da me gadin ya buɗe ƙofa. A saman ta baro shi yana shiryawa ta sakko ƙasa bayan ta saka kayan da ta cire, Ɗakin da aka kaita ta shiga, ita sai yanzu ne ma take ƙarewa falon kallo tamkar a wata ƙasa take da ban. Bayan ya gama shiryawa cikin farar shadda gezna sai sheƙi take tana ƙamshi ga turaruka masu aji da ya feshe jikinsa da su. Nocking ya ji a bakin ƙofar ya sakko cikin nutsuwa yana ɗaura agogo a hannunsa, yana buɗewa mai gadi ya gaishe da shi cikin girmamawa, amsawa ya yi ya karɓa kwandon da ya kawo yana sanar da shi direba ne ya kawo daga gidan Mummy. Faɗwa mai gadin ya yi cewa ya san da zuwan nasa shi kuma ya juya Ibrahim ya rufo ƙofar ya dawo ya nufi kan dining ya ajiye kwandon amma a ƙasa a gaban dining ɗin. Ɗakin ta ya nufa lokacin tana gaban drower ɗinta bayan ta bar gaban madubi inda ta tsaya shafa kwalakca da humra da sauran body spray da shuwa masu bala,in ƙamshi don kan madubin ya sha jere tamkar an je shago, drower da ta buɗe yadda kaya suke a jere sai da ta ji wani iri yau ita Jidda ce wacce Umma take ƙwace mata duk wasu kaya masu kyau da nagarta idan Abba ya ɗinka musu amma gashi komai ya zama tarihi tun da gashi yanzu kaya masu tsadar da bata tama tunanin ko a mafarki za ya saka irinsu ba. Tabbas komai na rayuwa idan ka yi haƙuri zai zama tarihi watarana!. Yanzu gashi komai ya wuce, yana sako kanshi ɗakin tsabar ƙamshin turarukan da suka bugi hancinsa hatta sallama suɓuce masa ta yi, kasancewar tamkar wanda aka yi ɓarin turare a ɗakin abin birgewar ma ba za ka taɓa gane wane irin ƙamshin turare ba ne. Jin alamun mutum ya sa ta waiwayo kasancewar tana ɗaure da towel da yake da ta shigo kayan ta cire ta ɗauki wani towel sabo ta ɗaura, ganin ya tsaya a rungume hannunsa yana mata wani kallo bata san lokacin da ta ce "Sannu da zuwa" Maganr tata ta bashi dariya sai ya ce "Kin manta kin gaisheni ɗazu yanzu kuma sannu da zuwan ta mene ne?" Bata amsa ba din ita kanta ta ba kanta dariya. Bata ankara ba sai ta ganshi ya zo dab da ita ya kama dantsen hannunta duka biyu sai gani ta yi ya janyo ta ya zaunar da ita a bakin gado, wucewa gaban drower ya yi ya tsaya yana ta ƙarewa kayan ciki kallo amma sai ta ga ya rufe, wata ya buɗe sai kawai ta ga ya ɗakko wata riga daga gani ba za ta wuce gwiwa ba sannan sai aka mata ƙaramin hannu, daga gaban rigar akanyi hoton heart babba daga ƙara aka rubuta GIRL da manyan baƙi. Miƙo mata kawai ya yi ya ce "Ita nake so ki saka" Karɓa ta yi a ranta tana cewa "Ka ji kaɗan ka ji da yawa, ni Jidda dama a gidan auren miji ne yake zaɓa maka kayan da za ka saka?" Ta tambayi kanta sai ta ji yana cewa "Ba zan ɓoye miki ba Jidda tun da na shigo ɗakin nan na tsinci kaina a wani yanayi mai wuyar fassara, sai dai ina tausaya miki kasancewar daren ki na farko ne kuma na yi dogon zango amma ba don haka ba, da sai kin mayae da ni ruwa" Kallon rashin fahimta ta masa ya ɗora da faɗin "Ina shigowa da na shaƙi ƙamshin turaren nan sai ya sakani a wani yanayi, tabbas turare yana taka muhimmiyar rawa wajen haifar da yanayi a tsakanin mace da namiji, shi ya sa aka haramtawa mace ta saka turare ta fita waje maza suna jin ƙamshin, dalilinnda ya sa ake rubuta mata alhakin zina saboda ƙamshi yana tada sha'awa ne duk wani namiji idan ya ji ƙamshin turaren zai ji sha,awarta" Kai kawai take kaɗawa bayaninsa yana shigarta duk da mafi yawan mata sun yi watsi da wannan maganar suna cin karensu babu babbaka, musamman da ya kasance yanzu har kabbasamata suke yi a kayansu, su gama turara kaya su saka su fita sun manta da haramcin hakan. Yana faɗa mata ya buɗe ɓangaren bra da panties ya ɗakko mata fararen set ya bata, bra ɗin pant ɗin, ganin tana wani juyawa kamar kunya take ji sai ya fita yana dariya, ta saka tare da ɗora rigar da ya zaɓo mata, jin yana kiranta ta fito tana amsawa wani mugun kyau ya ga rigar ta mata hakan ya sa ya ga tamkar dama don ita aka yi rigar tabbas aure rahma ne, Allah azurta kowa da mace da kuma miji na gari. ALIYA Wani irin bugawa da ƙarfi zuciyarta ta yi har numfashin ta yana barazanar mata wahalar shaƙa, jin furucin Amataullahi, a take bakinta ya bushe babu ko ɗigon lemar da za ta sanya laɓɓanta da suka yi gaggawar bushewa su jiƙu. Bata san tana da zafin nama ba sai da ta ganta tsaye ƙiƙam a kan ƙafafunta da zuwa lokacin sun fara karkarwar gaza ɗaukar gangar jikinta ba komai ne abin da ya razana ta haka ba illa furucin Amatullahin da ta ce tarayyarta da Kasim sau ɗaya zai ruguza mata abubuwa dubu, sannan in har a tarayyar da aka yi an samu ƙaruwa hakan yana nufin zai barta da jelar ciki da reno ma'ana shikenan ya yi sanadin rugujewar burikanta ciki kuwa har da mallakar Ibrahim matsayin miji da kuma zama kishiyar Jidda don ta mata gashin ƙuma!. "Hannunta yana dafe da ƙirjinta ɗayan kuma tana riƙe da wayar da take kunnenrta ta ce "Na shiga uku Amatullahi, wallahi ya yi tarayya da ni" Amatullahi ta ce "Wato ya kalamance ki da kalamansu na maza ko har kika yarda ya karɓe budurcin, kenan daman jiya duk burin kunyar ƙarya ne kike yi?" Cike da takaici Aliya ta hau labarta mata cewar ita fa ba wai da saninta ba, gabaɗaya ma vata cikin hayyacinta abubuwan suka faru. Nana Amatullahi ta ce "To kuwa ba a bori da sanyin jiki, za ki iya ƙwatarwa kanki haƙƙi, tun da wannan ai an yi zamba cikin aminci, an sakanyaudara a lamarin tun da an rufe ku, ta yaya za ki auri mata-maza Aliya, duk kyau da ajinki amma ki ƙare a mai mafitsara biyu, Allah dai ya sa ma dai bashi da breast a ƙirji a toh don idan mun zo gidan kar muke kasa bambance tsakanin aya da tsakuwa, ma'ana muke kasa gane ki da kuma shi tun da baku da bambanci a halitta" Kuka Aliya ta fashe da shi ranta yana ƙuna tana jin tsanar Kasim ta ce "A yau ba sai gobe ba Kasim zai sakeni!. Ba zan zauna da shi ba, wannan ai yaudara ce tsantsa, ko kotu na kai shi ya cancanci kowane hukunci" Tana maganar tana kuka, ita kuma dama tana jin haushin Aliya ta yi aure ta barta hakan ya sa ta ringa zuga Aliya don ta kashe auren su zama ɗaya. Sai da ta gama ɗora Aliya a tamfa sannan ta kashe wayar Aliya ko kiran Umma bata tsaya yi ba, ɗaki ta nufa a sukwane ta saka kaya kala biyu a kit ɗinta ta ɗauki hijabi ta saka, hannu ta miƙa za ta ɗauki wayarta da ta ajiye wani takaici ya sake cikata ganin screen ɗin kwatsa-kwatsa tana tuna cewa wai yanzu ita Aliya ce da wannan ƙazamar wayar Jidda kuma da bata isa komai ba mummuna ita ce mai iphone, sannan ita tana wannan ƙazamin gidan Jidda tana katafaren gida, daɗin abin haushin shi ne Jidda lafiyayyan namiji take aure ita kuma mata-maza tabbas wannan yana nuni da cewa ba ƙaramar tazarw ba ce a tsakaninsu. A zuciye ta ɗauki wayar kamar ta buga ta a bango sai dai ta lallashi zuciyarta don ta san yanzu dai bata da wata wayar sai wannan, fitowa ta yi lokacin tana tsakar gidan ta ga kiran Umma yana shigowa hakan ya sa ta kashe wayar ma baki ɗaya, don ta ƙudurta a ranta sai dai Umma ta ganta a gida, duk da cewa wata zuciyar tana bata shawarar kar ta je gidan saboda kar ta fusata Abba ya ɓata mata rai, amma kuma in ta tuna cewa lamarin mata-maza saj ta ga ba magana ce da za a yi sanya ba, watsar da shawarar zuciyarta tata ta yi kan maganar zuwa gidansu Kasim don ta fi so ta je gidansu in ya so idan Abba ya zo ya ji abin da yake tafe da ita sai ya yi magana da mahaifin Kasim a kawo mata takarda, don ta yi imani da Allah babu wani wanda zai do ƴarsa ta zauna da mata maza ga shi uwa uba ma ƙin sanar da ita da aka yi kafin auren. Kasim da suka gama waya da Salis sai ya shiga wani shago da yake gefe yana son sayan alewa ya yi sadaka, domin wannan lamarin na Aliya sai da sadaka, shigewarsa shagon ya yi daidai da fitowarta don haka ko ƙofar gidan bata karo ba ta bar masa ita a buɗe wayam. Ɗaya ɓangaren ta yi ba inda shagon da Kasim ya shiga ba, don haka bai ganta ba, tana riƙe da kit ɗin tana tafiya kamar za ta ci da ka ta matsu ta ganta a gida ko ta amayar da abin da yake bakinta don bata gane cewa a babbar matsala take ba sai da ta yi magana da Amatullahi hmmm wai ita Aliya da ta gama shirya rayuwar gidan aurenta ta jin daɗi da holewa ita ce ta ƙare da auren mata maza har ana cewa wai ba za a bambance su idan yana da breast a ƙirji!. Napep ta samu ta tsare suka kama hanyar gidan. A can gidan kuwa Umma lokacin da ta ƙule a ɗaki tana dokawa Aliya kira tana so ta bata baki, bayan Abba ya fita amma kuma sai ta ji an katse wayar a ƙarshe ma ta ji wayar a kashe. Fitowa tsakar gidan ta yi duk baƙi an karya wato an ci abinci, wasu suna hira wasu kuma suna wankan yaransu don suna cewa tafiya za su yi yau. Wata daga ciki ta c "Lubabatu an aurar da ƴaƴa yau an yi bacci fa munshari kowace ta shiga ɗakinta lafiya" Umma ta ce "Wallahi kuwa, ai mun yi waya ma da su ɗazu, ai kam duk wanda ya kai ƴa mace ɗakin miji kam dole ya yi bacci da munshari, saboda fargabar tarbiyar ƴa mace duk da cewa duk tarbiya ɗaya daga ta yarinya mace har ta yaro namij" Nan aka shiga yin hira ana ta yaba gidan Jidda wanda hakan yake haifarwa da Umma wani ɓacin rai kamar ana soka mata ƙahon ƙarfe a zuciya. Tsayuwar napep a ƙofar gidan sai kuma shigowar wani yaro ƙarami yana cewa wai a ba mai adaidaita kuɗi, kafin su samu damar bashi amsar wanda ya aiko shi, kukan Aliya da ya fara ratsa kunnuwansu tamkar an yi mutuwar da ba a ɗauke gawa ba ya saka gabaɗaya idanun kowa ya koma can... MAMAN AFRAH *Ina manyan matan? Na buɗe muku adashe mai so ga link nan ya shiga grp, ko a min magana pc idan kin san ba yi za ki yi ba bana son harkar ɓata lokaci.* *ABUBUWAN DA ZA A YI ADASHEN SU NE* *Leshi, atamfa jaka, takami kayan yara, takalman, yara, abaya, mayafai na shago, mayafai beadwrk, adire, kamfala, shadda, shaddales sai kuma kayan kicin da zanin gado ga mai buƙata* . *Amfanin yin adashen domin samun sauƙin siyan abu idan kana zuba kuɗin da kaɗan zai baka damar samun abin da kake so saɓanin za ka ga wahalar siye a dunƙule, Allah sa mu fara a sa,a mu gama cikin nasara.* [11/13, 12:45 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/GTq4oSxwxZfLKU7Amx5My1?mode=wwt *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️⃣7️⃣ *ALIYA* Gabaɗaya kowa baki sake hankali tashe yake binta da kallo, kowa da abih da ya fara rayawa a zuciyarsa, wasu suna raya cewa ko mijin ne ya mutu, wasu suna tunanin ko dai bata kai masa mutuncinta ba ne shi ya sa ya mata shegen duka a koro ta, saɓanin Umma da tuni ta harbo jirgin abin da ya maido da Aliyar gida. Umma a take ta ji wani abu yana juyata tabbas ta san yau Aliya ta gama kunce mata zani a kasuwa ta tona mata asiri ita da take son komai ya zama na sirri amma ta kwaso ƙafa ta taho gida tana ɓare baki kamar dai an sanar da ita mutuwar wani shaƙiƙi nata. Umma tamkar ta saka kuka haka ta ji don ta fara tunanin yadda za ta ɓoye matsalar nan amma da alama matsalar ba za ta ɓoyu ba, tun da dai gashi nan ta yi wa kanta fallasa auren bashi. Salatin da matan suka kwasa shi ya dakatar da Umma daga saƙa da warwarar jin ana ta jerawa Aliya tambayar lafiya? Sai dai kukan Aliyar ya hana ta bada amsa hakan ya da zargin da yake ran kowanne ya ninku fiye da farko, maganar yaron nan ta sake katse musu zulumi da ya ce "Wai mai adaidaita sahu ya cw a bashi kuɗin" Umma da wasu kuɗi suke gefenta ta ɗauki ɗari biyar ta cillawa yaron ya ɗauka ya fita da gudu, Aliya ƙarasawa kan baranda ta yi ta zauna zaman dirshan cike da kuka ta ce "Wallahi Umma ba zan zauna da shi ba" Kowa sai ya matso don jin ba,asin maganar don furucin ta ya nuna ba ita ce da laifi ba kamar yadda zuciyoyinsu suka saƙa musu a farko, kowa sai ya buɗe kunne don jin dalilin. Umma ji ta yi kamar ta dannewa Aliya baki don kar ta faɗa domin ta san muddin ta yi maganar to kuwa shuka za ta yi a idon makwarwa don kowa sai ya ji labarin matsalar gidan aurenta, sani ne Aliya bata yi ba yanzu zancen duniya iya faɗawa baba ne, wuyar ta ka yi furuci sai ya bazu wani ma sai ya gama ƙara gishiri da maggi a maganar don ta yi armashi idan zai bada labari. Umma ta rasa ma mai za ta ce duk da tana ta ƙoƙari wajen ganin ta dakatar da Aliyar daga abin sa take son faɗa, amma Aliya duk yadda Umma ta kai ga mata magana da ido amma ko idanun Ummar ma bata kalla ba,ɗaya daga cikin matan ta ce "Aliya dama auren ƙiyayya ne aka miki? Kafin ta bata amsa wata daga cikinsu rai a ɓace ta ce "Ko auren ƙiyayya ne a kan mai za akai ta gidan miji ta taho gida? Ko ma mene ne ba sai ta zauna a magance matsalar ba, amma ta kamo hanya ta dawo gida wannan ai tonon asiri ne kuma dole idanun mutane ya dawo kanta, tun da yanzu kiwon mutum ake yi ba dabba ba" Aliya cike da muryar kuka ta ce "Ba dole in taho gida ba, mutuminnda yake ɗauke da mugun abu" Salati akam kwasa Umma kuwa kai ta ɗauke gefe tana jin kamar ta tsinewa Aliya don takaici gashi bata son ta dakatar da ita su ce bata ɗauke su a matsayi iyayen Aliyar ba tun da daga dangin Abba sai kuma nata ƴan uwan. Wata ƴar uwar Abba da ta zo daga ƙauye tana dafe ƙirji ta ce "Wayyo Allah, mun shiga uku Allah sa bai kwanta da ke ba Aliya" Matar ita tunaninta mugun abun da Aliya ta ce tana nufin cutar HIV ita kuma Aliya sai ta ji zuciyarta ta ƙara karaya sannan ta ji daɗina ranta a ƙalla ta san dai wannan babban batu da za a raba auren tun da ta ga ana batun bai yi tarayya da ita ba, tana murje idanu ta ce "Wallahi ganin idanuna na ga wajen facin da aka masa, ba don na gani ba da ba zan taɓa yarda ba" Umma a ƙufule ta ce "Facin ubanki Aliya, shegiya sai ka ce wata tayar mota za ki ce faci wallahi ki kiyayeni" Ta faɗa tana tashi tsaye tana gyara ɗaurin zanin ta da yake barazanar barin jikinta, tana jin kunya kamar ta nutse don kunyatawa dai yau Aliya ta kunayata ta a bainar jama,a. Baki aka hau ba Umma ana faɗin ta mata a hankali ai babbar magana ce ta sanyata baro gidanta, Aliya buɗar bakinta sai ta c "Kuma wallahi da na san mata-maza ne ba zan aure shi ba, wajen ɗinkin tabon nan ba zai taɓa ɓacewa ba har ya mutu, da shi zai koma kabarinsa, ni ba zan ma je in ke haihuwar mata maza ba" Wasu sun ɗauki abin da girma don suna tunanin a mata maza Kasim ɗin ya fi ƙarfi ne ta ɓangaren mace basu san ma namiji ba ne kawai tsanarsa ce ta ƙoƙon ran Aliya har take ganin za ta rabu da shi. Umma ɗaki ta shige jin kamar za ta nutse don kunya, tsayuwar nape a ƙofar gidan da kuma sallamar Abba da ya yi kana ganinsa ka ga wanda hankalinsa yake a tashe shi ya dakatar da ɗaya daga cikin matan da take ba Aliya baki. Abba wanda maƙocinsa ya kira shi a waya yana tambayarsa lafiya ya ga Aliya an sauke ta a a daidaita sahu tana kuka ta shiga gida. Nan Abban ya nuna masa bai san ma da dawowar tata gidan ba, tsabar ruɗewa ma kasa kiran Umma ya yi a waya shi ya sa ya kamo hanya ya dawo. Ransa a matuƙar ɓace ya kalle ta ya ce "Aliya mai ya dawo da ke gida" Gabaɗaya sai ta ji shakkar Abban ta kamata sannan sai ta tsinci kanta da kasa faɗa masa asalin abin da ya dawo da ita gidan, kallon mutanen wajen ta yi ko wata za ta ari bakin ta ta ci mata albasa amma sai ta ga kowa ya yi shiru hakan yana nuni da ana son waƙa a baki mai ita domin ta fi daɗin ji. Wani irin tsoron Abba ne ya lulluɓe ta tsoron da bata yi tunaninsa ba lokacin da za ta taho don yanayin yadda ta ga fuskar Abba ya nuna mata bai ji daɗin abin da ta yi ba sai dai ya za ta yi a nata ganin bata da wani zaɓi da wuce hakan, wata tsawa da Abba ya duka mata wacce sai da fitsari kaɗan ya ƙwace mata jin ya ce "Ba magana nake miki mai ya rabo ki da ɗakin mijinki a kwana ɗaya tak da kika yi a gidansa" Ba Aliya ba hatta Umma da take ɗaki maganar yadda ya yi ta cikin ƙaraji ya hargitsa ƴaƴan hanjinta. Aliya cike da fargaba bakinta yana rawa ta ce "Abba, ma...ta...ma...za... ne Ka...sim...ɗin" Ta faɗa a tsorace tana danne kuka mai ƙarfin da yake son ƙwace mata, tana fatan ta samu goyan bayan Abba a kan maganar nan. Abba wanda ko kaɗan bai fuskanci abin da ta faɗa ba kasancewar a rarrabe ta yi maganar, juyawa bayansa ya yi ya ga wani bokiti wanda aka yi wanki aka ajiye ya ɗakko zai kwaɗa mata, aka shiga bashi baki yana tada jijiyoyin wuya cike da ɓacin rai ya ce "Za ki faɗa min sakarcin da ya sa kika baro gidanki ko sai na sauya miki kamanni?" Aliya bata san lokacin da ta ce "Abba Kasim ɗin ba namiji ba ne sak!." Sai da ta yi furucin sannan ta ji wata kunya ta lulluɓe ta, maganar ta ɗaurewa Abba kai ya fara tunanin to ita Aliya a ina ta san namiji da har za ta ti ikirarin shi Kasim ba namiji ba ne, bayan jiyan ne ranar farko da ta kaɗaice da na miji ba ma wannan ne abin mamakin ba yadda har ta baro gidan miji a kan wannan ƙaramar matsalar don iya hasashen sa dai kamar tana nufin bashi da wani kataɓus a wajen aiwatar da sunna ma'ana yanayin jikinsa ba zai gamshe ta ba. Ba kallon ita ba hatta Abba sai da ya ji kunya amma dai ɓacin ran da yake ciki ya danne kunyar Aliyar ya ƙara buɗe baki yana ƙwalawa Umma kira, sai ga Umma a sukwane zaninta riƙe a hannu don yau an damalmala mata lissafi damuwa da takaicinta in ta tuna mummuna Jidda tanaa can hankalinta kwance ita kuma da kyakkyawar ɗiyar ta suna nan hankali tashe, ƴar tata ta since musu zani a kasuwa. Umma tana fitowa ya hau ta da faɗa duk da haƙuri da kawar da kai na Abba amma yau kam ta gane shayi ruwa ne don a yanayin yadda yake faɗa tamkar babu abin da zai hana shi kai hannu ya ce "Saboda ban isa ba yarinyar ta baro ɗakinta a kasa samun wanda zai kira ni a waya ya faɗa mini, sai dai daga waje a sanar da ni, yanzu wannan abin kunyar ina za a kai shi a ce wai saboda wani dalili marar tushe saboda Aliya ta raina mutane ta kamo hanya ta dawo gid" Umma da sauri baki yana rawa ta ce "Baka fuskanci abin da take hufi ba Kasim ɗin ne yake da halittar mata maza" Ɗan shiru Abban ya yi yana tunanjn ya aka yi daga ɓangaren Kasim ba a sanar da su da wannan babbar larurar ba, amma dai babu yadda za a yi a ce ta baro ɗakinta ba tare da ta sanar ba wannan shi ne abin da ya ƙona masa rai. Abba ya ce Mai ya sa baki yi waya kin faɗa ba za ki kamo hanya ki taho bakya bari a je can a sulhunta" Aliya ta ce "Abba ni ba sai an sulhunta ba na haƙura da shi kawai" Abba hannu ya ɗaga ya wanke fuskar Aliya da mari ba tare da ya ce komai ba ya juya a ƙufule ya fita waje, Umma duk kunya da takaicin mutanen wajen ya kama ta amma dai gwara a warwate matsalar ita bata ma ƙaunar Aliya ta dawo gida da zama a nata ganin da Jidda ce za ta yi kwantan rashin miji sai gashi yanzu tata tilon ƙar tana neman yin kwantai don a ganinra kwana ɗaya a ɗakin miji ma ai zai karya lagon ƴanmatancin Aliyar don ta san ma ai tuni ta zama bazawara idan ya sake ta sannan bata da tabbacin ba a samu rabo jiyan ba tun da dai ta san tun da har Aliyar ta ga halittar da yake ɗauke da ita to tabbas an aiwatar da sanna. Abba yana fita ya ɗaga waya ya kira Baban Kasim yake labarta masa abin da yake faruwa, nan da nan ya sanar da Abban cewa gashi nan zuwa gidan Abban. Baban Kasim yana kashe waya sai ya shiga kiran Kasim don jin ba a sin yadda aka yi ya bar matarsa sabuwar amaryar kwana ɗaya tak ta tafi gida, tun da wannan abu ko shi ne aka yi wa ƴarsa hakan ba zai ji daɗi ba don wannan abin kunya ne abin takaici ka kai ƴa ɗakin miji ta dawo gida. Kasim da yake shirin fitowa daga shagon nan kiran Babansa ya katse masa hanzari yana ɗagawa Babansa ya ce "Kasim mene ne dalilin da ya sa ka bar matarka ta taho gida? Kai baka mata bayanin cewa tun kana ƙarami aka maka tiyata cewa kai ba mata maza ba ne kuma mata maza suna iya rayuwa kamar kowa su haihu kamar kowa, sannan suna da dama kamar kowa ba?" Baban Kasim da ya katse gaisuwar da Kasim yake kawo masa ya faɗa cike fa hargagi har Babar Kasim da take kicin ta jiyo abin da yake faɗa, hakan ya sa gabanta yankewa fa faɗi a nata ganin ta aurar da ɗan nata amma kuma wata wutar tashin hankali yana tunkaro su. Kasim a take ya ji bakinsa ya bushe wani tashin hankali ya saukar masa maimakon ya ba Babansa amsar tambayar da ya masa sai ya ce "Gani nan zuwa Baba" Baban nasa kuwa ya yanke kiran, shi kuma Kasim ya yi hakan ne son kawo ƙarshen maganar saboda yana mamaki da tantamar anya Aliya ta tafi gida kuwa? Tun da ya san a gidan ya barta. A rikice ya yi cikin gidan yana ƙwala mata kira, amma shiru ko ƙutarta bai gani ba banɗaki ya nufa amma bai ganta ba, kicin ma haka duk da ba ya saka ran ganin ta a kicin ɗin saboda ya san babu abin da za ta je yi, yana komawa ɗaki da ya je bedroom a nan ya tabbatar da maganar Babansa don ya ga alamar hargitsa kaya da Aliya ta yi. Bai yi wata-wata ba ya fito daga gidan sai da ya zo ƙofar gida ya tuna bai ɗakko mukulli ba ya koma ya ɗakko ya fito yana cikin datsewa ya ji wani yana cewa "Ango ka sha ƙamshi" Yana juyawa ya ga wani abokinsa ne, hannu kawai ya iya ɗaga masa ya tsare mashin ya hau don ya lura idan ya tsaya zai iya gane ba ya cikin hayyacinsa. Suna cikin tafiya kiran Babansa ya shigo yana ɗagawa Baban nasa ya ce "Kasim ka zo gidan Abba muna can" Gabansa ne ya hau dakan lugude yana fatan kar wannan zaman da za a yi a saka ya warware igiyar aurensa da Aliya. SADIYA Da kamar ta nufi gidan Kaka amma sai ta daure ta ƙarasa gidan, tana zuwa sai ta ga babu mukulli a ƙofar gidan mamaki ya kama ta kenan mai yake a gidan bai fita ba ko dai ya dawo daga kasuwar ne ko kuma mene ne dalili da wannan saƙe-saƙe ta shiga gidan tana jin babu daɗi a ranta na wunin ranar yau bata sayar da kayan sana'ar ta ba bayan ta saba kama kuɗaɗenta. Tana shigowa ta fara sallama amma shiru ba a amsa ba sai dai ta ga takalminsa a ƙofar ɗakin sai da ta yi sau uku amma babu alamar zai amsa haka ta shigo ta ɗaga labaulen falon ta shigo dama Kalifa bacci yake a bayanta a ranta tana raya ko ina motar tasa kuma tub da baya ganta a ƙofar gida ba. Ko da ta shiga ɗakin yana gaban madubi yana idaidaita hula a kansa amma ko kallo bata isheksa ba, kamar dai ba a yi ruwanta a wajen ba. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi wanda take fatan hakan ya narkar da takaicin da yake danƙare a ƙirjinta. Ta ɗan daure ta ce "Barka da yamma" Bai amsa ba illa ya saki hular tasa ya riƙe ta da hannu ɗaya saɓanin lokacin da ta shigo hannuwansa biyu suka riƙe suke da hular, ɗaya hannun marar hular ya yi amfani da shi wajen ɗaga mata hannu alamar ta dakata hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru tana kallon ikon Allah duk da bata san dalilin dakatar da ita ɗin ba. Ya kusa minti huɗu yana daidaita hular har sai da ya ga ta masa yadda yake so ita kuma tana jira ta ji abin da zai ce. Da ya gama gyara hulae bai juyo ba yana kallon madubi sai da suka hala ido ta cikin madubin ta ji ya ce "Ki daina kalle mata kwalliyar" Cike da mamakin furucinta da kuma rashin sanin inda maganar ta dosa sai kuma ya ce "Na ji kina mini barka da yamma ke ai ya kamata a yi wa barka ko?" Da nuna alamar tambaya a fuskaryta ta ce "Ban gane ba barkar mai?" Ya ce "Barkar dawowa ɗakin ki mana, ai nan Baba ya kirani a waya yana ta bani haƙuri, na ce bari na tambayi Meenal ɗin in ta haƙura sai ki dawo" Har sai da idanunta suka ciko da ƙwallah tsabar ɗacin da maganar ta mata wato dai Baba ya zubar mata da mutunci da kima a ce ya kaita gida amma saboda ta zauna a gidan aure yake bada haƙuri gashi yanzu ya ja mata raini har ana mata barka da dawowa ɗakinta, wato ta ga samu da ta rashi ɗan kawar da kai gefe ta yi tana danne abin da ta ji ta ce "Allah sarki Baba yana son ƴaƴansa su yi zaman aure ne ai sannan mutum ne mai son zaman lafiya ba ya son tashin hankali shi ya sa ya zaɓi ya bada haƙuri a kan ciccira magana" Ta ce tana jin kamar mai. Wata ƴar dariya ya yi wacce ta yi kama sa ta yi kama da ta raninin hankali ya ce "Allah ko?" Bata tanka masa ba ta zaɓi ta bar ɗakin don ta ga abin cin fuska ne. Tana dab da fita daga ɗakin ya ce "Da farko na dakatar da ke ne da kika min mafana saboda ina saka hula bana so ta karkarce kin san idan za a yi wa amarya kwalliya abin a tsara ne don a birge ta" Murmushi ta yi ta ce "Wannan gaskiya ne" Bai jira ta ce wani abu ba ya ce "Na ce kina kalle mata kwalliyae ne saboda ta ce mini kar in bar ƴan mata su kalle mata ni" Maganar ta ɓata mata rai amma sai ta zaɓi mayar da martani cikin ruwan sanyi ta ce "To ai ƴanmata ta ce ka ga bata ce har matarka ba kenan matarka ta fi damar ta kalle ka don halaliyarka ce" Tana faɗa ta juya ta fita. Shi kuma ya murmusa don yana ganin Baba ya ƙara bashi damar wulaƙanta ta tun da yana nuna dole sai ta zauna a gidan, tun da yana faɗa masa sauran ƙannenanta suna nan babu mashinshi ni. Tana zuwa falon ta sauke Kalifa ta ɗora a kan kujera ta fara shirin gyara gidan, sallamar wata yarinya da ta zo siyan manja ya sa ta fito daga ɗakin ta je ta bata ta dawo, tsintsiya ta ɗakko bayan ta kunna gawayi don yin tuwon dare. Fitowarsa daga ɗaki yana buɗaɗa ƙamshi ita shaddar ma kanta aabuwa ce dal yau ya fara sakawa hatta hula da agogon duk sabbi ne yadda kayan ya masa kyau tamkar ranar ɗaurin aure kamar abin arziƙi ya ce "Sadiya baki tambaye ni ina mota ta ba" Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce "Na ga bata waje to tunanina ko ka ba wani ne ɗani" Ta faɗa cikin zolaya. Washe baki ya yi ya ce "Kamar kin sani kuwa ai Meenal ce suka karɓa aro ita da ƙawarta za a koyawa Meenal ɗin mota" Ɗan jim ta yi tana tunanin ba ya ma gudun matsala sai ta ce "Ma sha Allah, Allah ya tsare ya sa a koya a sa'a" Da amib ya amsa yana saka takalmi ya fita a daidai lokacin kuma suka ji ƙaran tsayuwar motar ya waiwayo yana cewa "Kin ji ƴan halak suna dawo" Ita dai bata amsa masa ba ganin ya zama wani sauna a kan mace duk don ya ga bata nuna damuwa a kan lamuransa shi ya sa har yake faɗa mata komai ya zo bakinsa yana ganin ba za ta ji ciwo ba. Yana fita ya rufo ƙofar Sadiya ta cire takalmi ta yi saɗaf-saɗaf ta je zauren ta shiga leƙawa daga wata ƙaranar tulla da take jikin ƙofar, tana ganin lokacin da suka fito daga motar wata farar budurwa wacce fuskarta har wani jaja take saboda bikicin ita ce ta fito daga mazaunin direba ita kuma Meenal ɗin daga mazaunan mai zamana banza. Suna ta dariya shi kuma ya harɗe hannu a ƙirji yana ta kallonsu, Meenal ta zunɓura baki tana magana cikin ɓaci ta ce "Ka ga ko, ta kusa jefa maka ni a kwata" Ƙawar tana dariya ta ce "Ka ji ni da mata za ta min sharri wai ni ce ma zan jefa ta a kwata to ita ce ta kusa jefa mu a wata ƙatuwar kwata, ɗazu ma kaɗan ta kaɗe wani tsoho" Gabaɗaya aka yi dariya, kafin ita ƙawar ta shiga baya ita kuma Meenal ta shiga gaba shi kuma ya shiga ya tada motar da yake a jiki ta bar mukullin, haka suka bar layin duk abin da suke a kan idanun Sadiya sai da suka tafi ta juyo ta dawo cikin gidan ta fara aikin gabanta. Yau saura sati ɗaya biki Nasir duk ya mayar da hankaki kwacakwam kan lamarin bikinsa sai hidima yake daga shi har su Hajiya da ƙannensa tamkar dai wannan ne karon farko da zai taɓa aure. Duk da Hajiyar ta faɗawa Sadiya cewa su a wurinsu wannan ne auren fari da Nasir ɗin zai yi, kuma wannan ne auren da suke gani za su yi biki na kece raini, maganganu maarar sa kai da ƙafa dai Sadiya ta ji su sai dai tana toshe kunnuwanta ta yi kamar ba ta ji ba, saboda Hajiya ita tana ikirarin biki biyu za ta yi wato ɓangaren amarya da na ango abin ta tuwona maina. Tun da aka zo aka yi jere ake ta kulle ƙofofin ɓangaren amarya, sannan duk wanda zai shigo gidan cikin nuna halin ko in kuka yake ga Sadiya hatta gogan yanzu ta rasa kansa da ƙafarsa babu wani abu da yake shiga tsakaninsu ba ya cin abincin gidan kwata-kwata sannan idan ya fita ma wani lokacin sai dare. Ita yanzu ko ya zo ma baya yake juya mata a kan gadon, domin ta lura gabaɗaya zumuɗin son kasancewa da sabuwar amarya yake ɗibansa, komai ya mayar da shi ga amarya, ana saura kwana biyu ɗaurin aure ya haɗa kayayyakinsa ya kwashe rabi da kwata ya kai ɗakin amarya, duk wasu abubuwa na amfaninsa to ya mayar ɗakin amarya, tamkar dai cewa aka yi ita Sadiyar ba matarsa ba ce duk da ayyukansa ya nuna cewa da alamar hakan amma dai ita ta bashi lokaci. Ko naira biyar bai bata ba a matsayinta na uwar gida bare ta saka ran wani kayan da ake yi wa uwar gidan duk da malamai suna ganin hakan ba wajabci ba ne sai dai sun faɗa hakan kyautatawa ce sannan kowace rai tana son a kyautata mata amma Sadiya bata samu hakan ba. Ita ma ganin da kuɗinta hakan bai wani dame ta ba, tun gabatowar bikin a littafin maman afrah ruɓaɓɓiyar igiya ta ɗauki lambarta ta kira ta ta faɗa mata tana son atamfofi lokacin ana saura kwana biyar biki ne. Nana maman afrah ta ce ta mata magana ta whatsapp ta tura mata atamfa da les da takalmi da jaka, sai kayan Kalifa kala biyu ta bata acc no ta saka kuɗi sai ga mai napep ya kira ta a waya ya ta faɗa masa unguwar ya kawo mata, sun yi kyau sosai kamar yadda ta gansu a hoto haka suke shi ne ta bayar aka mata ɗinki. Sai aka mata buɗaɗɗe kasancewar tsufan da cikinta ya yi. Ko bayan ya kwashe kayansa daga ɗakin tana gyara masa drowersa ta ga ya ajiye wasu magunguna na maza hakan ya sa ta gane tanadin amarya ne murmushi ta yi abinta tana musu fatan wanyewa lafiya. A ɓangaren amarya Meenal kuwa ta saya magungunan mata ciki kuwa har da wani na matsi mai suna gamgam wanda take fatan ma dawo mata da budurcinta ba tare da angon nata ya farga cewar ta yi fatali da mutuncin da ake fata da burin kowace mace ta kai gidan miji. Yau za a kawo amarya bayan an yi gagarumin bikin kece raini kamar yadda Hajiya ta buƙata, Sadiya ma ta yi ɗan taro na maƙota da ƙwayenta, ta saka atamfarta poplin da ta ɗinka da yake ɗinkin doguwar riga ne sai ya mata cif abinta. Dirin tsayuwar motoci a ƙofar gidan ya ankarar da kowa ƙarasowar amarya, kasancewar akwai nepa, ife-ifen yara da guɗar manya ita ce ta karaɗe unguwar, sai yi suke suna maimaitawa Sadiya da ta fara jin faɗuwar gaba ta shiga ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagisu aslihli sha,ani kullahu wala takilni ila nafsi ɗarfata ain. Haka suka shigo kamar da gayya suna ƙara guɗa, su kuma maƙoa suka shiga musu sannu da zuwa amma sai suke yi wa Sadiya da mutanenta kallon ƙasƙanci. Babu wansa ya ƙara tanka musu, suka nufi sashen amarya. Bayan kowa ya watse an yi wa Sadiya sallama tare da bata haƙuri hatta wasu saga cikin ƙannenta ma sun zo. Zaune take a falo da kankana a gabanta wacce ta ɗakko daga frige lokacin Kalifa ya yi bacci, tana cikin sha ta ji tsayuwar mota jim kaɗan ta ji shigowar Nasir da abokansa suna sallama, ita ce ta amsa kasancewar part ɗinta ya fi kusa da ƙofae gidan. Sai dai da suka shigo babu wanda ya nufi inda take suka yi ɓangaren amarya. Zuwa can ta ji fitowarsu tana jin tashin muryoyin ƴanmata hakan ya bata tabbacin ƙawayen amarya ne. Bayan sun fita sai kuma ta ji dawowar Nasir shi kaɗai don ta ji lokacin da ya garƙama sakata a gidan, sannan kuma da safe da ta je gyara masa drower ta ga duk ya kwashe magungunnsa, hakan ya bata tabbacin za a kwashi amarci a daren yau!. Shiru-shiru ko zai shigo ya mata sallama, ko kuma ya kawo mata ɗan abin taɓawa da wasu mazan suke siyowa har uwar gida, duk da bata saka rai ba amma bai kai mata komai ba, sannan bai kawo amarya ya haɗa su ba, wannan ya ƙara tabbatar mata za a yi wani zama a cikin gidan. Babu zato da tsammani sai jin ƙaran rufo ƙofar falon amarya ta yi. *Ga link nan wansa yakemson shiga adashen kayan sallah ya shiga zubi duk sati 3k idan ka gama zubi sai ka karɓi kayan da ka zaɓa, in kin san ba yi za ki yi ba karki shiga min grp* Ko a shiga grp ko min magana ta wtsapp MAMAN AFRAH 09025576222 [11/15, 12:55 PM] 😍: *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️⃣8️⃣ AMARYA MEENAL Tun da aka watse gabanta yake ta faman dukan tara -tara domin abin ya ma zarce dukan uku-uku tunaninta guda ɗaya shi ne, kar a je Nasir ya fahimci sirrin da take ganin ta haƙa rami ta binne wato ya gane ɗanyen aiki da ta yi wa tinƙahon kowacce mace wanda ake fata da burin ta kai ga mijinta na sunna amma ita tuni ta ɓarar da wannan damar a titi. Sannan fargabar ma bata wuce cewa shi Nasir yana mata kallon mutuniyar kirki sannan mahaifiyarsa tana mata kallin mai ladabi da biyayyar da har suke ganin ta zarta uwar gidansa Sadiya bayan duk abin da suke zato ba haka ba ne. Yanzu ta fi mayar da hankali ga cewar an ƙare lafiya ita da Nasir a daren faekon nan ba tare da ya fahimci cewa an masa riga malam masallaci a abin da yake ɗoki da zumuɗin samun a daren farko a wajen amaryarsa. Duk da ta san da wuya gyara ya yi kamar sabo amma dai an bata tabbacin abubuwan da ta yi amfani da su Nasir ba zai taɓa gane ita ba cikakkiyar budurwa ba ce, sannan uwa uba wani magani da za ta yi amfanu da shi wajwn daƙile masa wannan tunanin duk ƙwawa da ƙwaƙwarsa bai isa ya yi wannan tunanin ba, dole ko ya yi yunƙurin hakan abin ba zai yi ba. Tana zaune bakin gado abin duniya goma da ashirin ya kwaɓe mata sai saƙa da warwara take, jin lokacin da ya turo ƙofar falon tare da mayarwa ya rufe, tabbas gabanta ya bada sautin rasss ta yadda daƙyar ta iya saita kanta yadda ba zai fahimci yadda jikinta take karkarwa ba,duk da an ce marar gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake amma dai za ta yi ƙoƙarin wajen daƙile wannan karin maganr na bahaushe ba tare da hakan ya faru ba don ba za ta taɓa barin Nasir ya gane ba. Yanayin sallamarsa da ya yi zuwa bedroom ɗin ya sa ta fahimci tana cikin farinciki sannan a muryarsa ta gane yana cike da ɗoki, dunƙulallan maganin hannunta wanda shi ne zai gusar da tunaninsa wajen gane an ci da rabinsa tun a waje, shi ta yi dabarar sokewa a ƙugugunta kasancewar laffaya ta ɗaura a saman kayan jikinta. Tana zaunen tana ɗan qasa da yatsunta ya ƙaraso gaban gadon yan daɗin "Amarya kin sha ƙamshi" Kamar yadda bata amsa sallamar tasa ba haka nan bata amsa kirarin amaren da ya mata ba tana son ƙara tabbatar masa da cewa ita mace ce mai kunya, wannan abin da ta yi na sunkuyar da kai ba tare da ta furta komai ba shi ya farantawa Nasir yana ji a ransa burinsa ya cika ya auri wacce yake so mace mai kunya da ladabi haɗe da biyayya ba irin Sadiya ba da yake ganin bata masa biyayya, sannan yana murnar zai ɓarje amarci sa sabuwar amarya tun da a nasa tunanin Sadiya ta zama tsohon yayi yanzu domin yana ganin ma ai an daɗe da cin moriyar ganga dole a yada korenta. Babbar rigarsa ya cire ya samu wuri ya ajiye, ya ƙaraso gaban gadon ya tsaya a gabanta hannu biyu ya saka ya ɗaga mayafin laffayar da take kanta, ya kai hannu ya ɗago haɓarta sai ya ga ta rufe idanunta wani irin daɗi da farin ciki yake ji a ransa tabbas ka auri wanda t kake fata da buri shi kaɗai ma abin alfahri ne. Saɓanin a zuciyar Meenal ba haka ba ne illa fargaba sai yanzu take tunanin dama haka ƴanmtan da suka watsar da mutuncinsu a waje suke tsintar kansu a fargaba da tashin hankali idan an kai su gidan miji. Bata ankara ba ta ji hannunsa cikin nata, ya kama ta ya tada ita tsaye tana wani kauda kai ita ala dole kunya cike da wata murya da bata san ma yana magana da irinta ba, duk da ta san yau amarya take kuma a ranar farko don haka yana iya mata magana da kowane lafazai mai daɗi ji ta yi ya.ce "Duk kunyar nan yau zan cire miki ita" Ƙara sadda kai ta yi a haka ya kamata ya kai ta ƙofar banɗakin bedroom ɗin, ya tsaya ya ce "Za ki iya yin alwala mu gabatar da sallah ko ni zan miki da kaina" Kafaɗa ta ɗaga masa alamar a,a wato bata son fa mata alwala, hakan ya sa ya ɗan yi murmushi don ya gane kunya take ji. Nan ta bar shi tsaye ta shige banɗakin ta rufe ƙofar ya saki wani murmushi don shi ma ya mata uzurin ba zii bita ba don ya san dama yau dole a rina wai an saci zanen mahaukaciya wato dole kunya ta lulluɓe ta. Meenal tana shiga banɗakin ta ɗakko wannn dunƙulallan abun ta tura a matancin ta, ta ɗan ji sawaba a zuciyarta jin da za ta saka abin ya shiga dakyar alama ce ta matain ya yi sai dai tana ta wasi-wasin anya hakan ya yi kuwa. Ruwa ta kama ta ɗaura alwala ta gyara laffayar ta, ta buɗe ƙofa ta fito sai da ya kama hannunta ya kaita har falo ya zaunar a akan kujera kafin ya koma yana cewa ta bashi mintina kaɗan yanzu zai ɗauro tashi alwalar, jim kaɗan sai gashi ya dawo ko sallaya basu shimfiɗa ba suka yi sallar kasancewar komai sabo ne wato wajen yana da tsafta tun da kafet ne. Bayan sun idar suka ɗan taɓa kayan maƙulashen su duka babu wanda ya ci abin kirki shi yana zumunɗin amarci ita kuma tana fargabar ya ji ba daidai ba, don ta san muddin ya gane akwai matsala saboda komai ya kwance mata duk wani ƙuduri da za ta aiwatar a gidan ba za ta samu dama ba komai zai ɓalɓalce wanda bata fatan hakan. Suna gamawa bai bari ta taka da ƙarfarta ba ya sungume ta gabanta yana dak-dak-dak bayan sun yi shirin kwanciya ya kashe wutar ɗakin, daga nan kuma abubuwan da suke da wuyar durtawa a baki suka fara faruwa, shi dai Nasir a hankalce tun da ya kai ziyarara wannan waje ya so dai ya fahimci wani abu sai dai ya kasa gane mene ne sai ya ji kamar ya manta mai yake so ya gane wanda kamar dai akwai matsala amma ba zai ce ga matsalar ba. Ko da komai ya lafa Meenal ta ga bai nuna komai ba hakan ya sa ta gane maganin da ta karɓa wajen malamin nan ya yi aiki duk da ta san ya ce mata abun zai iya warwarewa amma dai ta san in aka wuce wannan ranar to ita bata da wata damuwa. Ko da safe haka ta narke ta ƙi fita ko falo wai ita ala dole ƙafafunta basa haɗuwa, ko banɗaki za ta shiga kamar ƴar shayi haka take tafiya tana son nuna masa cewar shi ne dai farkon wanda ya fara saninta a mace. Abu kaɗan za ta hau raki shi dai duk ya kasa ganewa. A ɓangaren Sadiya tun da ta sha kankanar nan duk da bata wani sha da yawa ba, sai ta mayar frige ta je ta yi shirin kwanciya, bayan ta kwanta sai ta ji zuciyarta ta mata ƙunci, tana ta mata saƙe-saƙe cewa yau ce ranar farko da za ta kwana ita kaɗai a ɗakin sannan ita kaɗai a gadon ba tare da Naair ba. Zuciyarta tana azalzalarta a kan cewa yanzu yana can tare da wata matar da ita ba, yanzu haka suna kaza da kaza sun yi kaza jin dai shaiɗan yana neman haddasa mata baƙinciki haɗe da rashin bacci sai ta shiga karanto addu'o,in a take ta ji duk wani ƙunci da baƙinciki ya yaye tamkar bata da wata damuwa. Bata ma san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ita ba. Bata tashi ba sai da asuba, dakyar ta sakko daga gadon saboda jikinta ya mata nauyi cikinta yana ƙara girma sosai. Bayan ta idar da nafila raka,atainil fajr ta yi sallar asubar sannan ta zauna ta yi ta addu,oi haɗe da karatun qur'ani. Bayan ta gama ta ɗan jingina da jikin gado bayan ta miƙe ƙafafunta da ta ga yau sun kumbura bacci ɓarawo ya sace ta. Ko da ta tashi daga baccin wanka kawai ta shiga ta saka wata doguwar riga marar nauyi, Kalifa har lokacin bacci yake, madara da ta bayar aka auno mata kwata da milo sacet guda ta haɗa shayi mai kauri ta sha domin har lokacin akwai nepa hakan ya sa ta jona ruwan, jin yunwa abin cikinta sai motsi yake. Ɗakinra ta gyara tass ta kunna turaren wuta ɗan tsinke, lokacin Kalifa ya tashi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta haɗa masa shayi ta bashi da biredi ya cinya ƙoshi tun da jiya ana taro bata yi tuwo ba. Har ƙarfe goma babu alamar amarya da ango, wajen goma da kwata Sadiya tana wanke-wanken ƴan kwanuka da suka rage babu wanki don jiya sai da aka wanke duk kwanukan da aka ɓata. Nocking ɗin gidan aka shiga yi, ta tashi tana ɗan jin yadda bayanta yake riƙe mata, Kalifa kuwa yana ta wasan sa, tana zuwa zauren ta ce "A nan ne? Waye?" Ta tsinkayi muryar Husna cike da gadara ta ce "To sarkin ƴan ƙarfin hali ɓarawonda sallama, ki buɗe mana gidan tun da yanzu dai ya zama mallakin ku, ku biyu" ,Bata ce komai ba ta buɗe, ko tsayawa bata yi ba ta juya su kuma Husna da Hibba suka shigo sai da suka zo ƙofar ɗakinta sannan suka yi sallama a daƙile amsa musu ta yi ba tare da ta ƙara bi ta kansu ba ta wuce wajen da take wanke-wanke Hibba ta kalli Kalifa don ganin ta ƙular da Sadiya ta ce "Yaro ɗan sabuwar amarya yau babanka ya kwana yana shan amarci ko?" Shi kuma kawai kallonsu yake don ba wani sabawa da su ya yi ba. Sadiya ko kallo basu ishe ta ba ta cigaba da ɗaukan kaya tana shiga da su kicin ta baiwa banza ajiyarsu, ta fito ta sunkuya dakyar tana wanke wajen sai Husna ta yi karaf ta ce "Sadiya ba sai kin mana banza a gidan ɗan uwanmu ba, mu ai mun isa mu saka ƙafarmu a ko ina a gidan nan ba tare da shamaki ma ko kin manta shi ne ya sha nono ya bar mana?" Hibba ta karɓi maganar ta ce "Ke kika kula ta ma, bata san zamanta a gidan nan ɗorin ɗosano ba ne" Husna ta ce "Wallahi kuwa ai kawai saboda Kalifan nan ne amma ai da wannan cikin ma saj dai a haife a gidan tsohon... Kafin ta ƙarasa faɗa Sadiya ta miƙe tsaye a zuciye ta saka hannu ta finciko mayafin Husna rai a ɓace ta ce "Husna duk abin da za ki yi ya tsaya iya kaina amma karki kuskura rawar kanki ya kai ga mahaifina wallahi za ki yi nadamar hakan" Husna duk da ta tsorata da yanayin da ta ga Sadiyar amma sai ta yi ƙarfin halin cewa "Dalla malama saka min mayafina" Gamgam Sadiya ta riƙe bata saki ba sai da Husnar ta fisge sannan Sadiyar ta sakar mata Hibba kuwa bata furta koɓai ba ta yi ɗiff sai da suka yi hanyar ɓangaren Meenal Hibba ta ce "Kyaji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, wato wutar kishi tana nuƙurƙusar zuciyarki shi ne za ki sauke a kanmu" Ko kallonsu bata yi ba suka nufi ƙofar ɗakin Meenal dama ɗauke suke da kwando mai food flask masu kyau da alama abinci suka kawo. Ƙwanƙwasawa suka yi amma shiru waya Husna ta duba lokacin goma har da rabi hakan ya sa suka kalli juna suna danne dariyarsu. A can cikin ɗaki Meenal da ta narke tana zuba shagwaɓa ce jin ana bugawa sai Naair ya ce zai je ya buɗe buɗar bakinta sai ta ce "Ka rabu da ita Sadiya cw kishi yake cinta take son rabamu fa" Murmushin yaƙe ya yi shi dai ya san yau ranar farin ciki ce amma kuma ya kasa gane ta ina walwalarsa ta samu naƙasu, kawai dai ya rasa ma mene ne yake damunsa. Kamar raƙumi da akala haka ya tsinci kansa da bin umarninta, ya koma ya hau gadon tare da kwantawa ita kuma ta mayar da kanta ta ɗora a cinyarsa yake shafa gashin kanta. Sun jima suna bugawa amma babu alamar za a buɗe Hibba ta buɗe baki ta ce "Yaya!" Jin muryar Hibba sai ya yi karaf ya ce "Kin ji ashe ma Hibba ce ba Sadiya ba" Ya faɗa yana washe baki, tamkar ya sanar da ita mutuwa haka ya haɗe rai ta ce "To mene ne idan su ne, shin basu san yau ranar mu ba ce ba ma buƙatar hayaniya?" Wani abu mai kama da mamaki ya ɗarsu a zuciyarsa duk yadda ya ga tana haba-haba da su amma kuma yau sai ta canja fuska sai dai ya yi tunanin ko dai don tana cikin raɗaɗin amarcin ne bata ware ba. Idan Hibba ta ƙwala masa kira sai Husna ma ta kira shi amma Meenal ko amsawa ta hana shi ya yi. Sadiya tana jin su tana danne dariyarta, har suka gaji da tsayuwa suka zauna a ƙofar ɗakin suna zaman jiran tsammani saboda zuciyarsu ta faɗa musu cewa ko suna cikin halin da ba za a iya ganinsu ba. Tana ganin yanayinsa ya canja ta san kuwa saboda ta hana shi zuwa wajen ƙannensa ne saboda ta san son su yake kamar mai amma dai ta yi alƙawarin takawa wannan alaƙar tasu birki. Wayarsa ce ta shiga ruri bata masa magana ba ya ɗ kko a kan bedside drower yana ganin sunan Hibba da sauri ya ɗauka cike da shagwaɓa ta ce "Yaya mun jima a ƙofar ɗakin amarya muna jiranka, Hajiya ce da kanta ta tashi tun asuba ta muku girki, abin da ya sa ma bamu ƙaraso da wuri ba saboda cewa ta yi mu bari rana ta ɗan yi kar mu yi sakko baku tashi ba" Ba tare da ya kashe yana cewa Meenal "Bari na karɓo abinci ne suka kawo in ji Hajiya" Baki ta taɓe ta juya ta kwanta tana rayawa a ranta cewa kwa ji da shi ciwon ajali a yatsa. Yana fita ya karɓo, su kuma sai suka yi ƙoƙarin bin bayansa wai za su gaisa da Meenal tun da a tunaninsu babu wani abu domin ya fito sannan tun da gidan ba su kaɗai ba ne a ganinsu ai ba sa zauna suna ta yin abu ɗaya ba. Samun kansa ya yi da kasa dakatar da su, suka shigo falon suka zauna suna ganin falon sai wani daɗi suke ji Meenal matar yayansu.. A falo ya ajiye kwandon suna ta hayaniya ya shiga ɗakin gar lokacin tana kwance ta juya baya yana ɗan washe baki ya ce "Abinci ya hallara ranjki ya daɗe sannan kin yi baƙi" Juyowa ta yi ta ɗan yatsiina fuska ta ce "Baƙi kuma? Daga ina aka samu baƙi da sassafe" Ya ji abin da ya ɗaure masa kai ɗan ƙara washe bakin ya ya yi ya ce "Ƙannenki ne fa, kuma yanzu maganar ƙarfe sha ɗaya ake kin ga kuwa ai ya fi sassafe" Bata bashi amsa ba yake tsaye kamar wani itace duk abin da ake a kan kunnen su Husna sai dai basa gane mai ake cewa amma tabbas suna jin alamun magana. Sai da ya sake maimaita mata ta ɗan yatsina fuska haɗe da karyar da kai yadda ba zai fahimci da gangan za ta yi abin da take shirin faɗa ba ta ce "Ka ce musu su dawo an jima" Sheƙeƙe yake kallonta saj ta yi abin tausayi na kissa ta ce "Ƙafafuna ne suke cewa kuma fa ka san duk kaine ka yi wannn aika-aikar ina fita za su fahimci wani abu" Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauke don furucin nan nata na ƙarshe ya kauda duk wani zargi da ya ɗarsu a zuciyarsa da farko ya ɗauka dai zaɓen tumun dare ya yi ma,ana bata ƙaunar ma ƴan uwansa tun da abu ne sabo da bai saba da shi ba daga wajen Sadiya wato wofintar masa d ƴan uwa ya san Sadiya ba kallon ƴan uwansa ba duk wanda zai sako ƙafarsa gidan ba zai yi kuka da ita ba. Yana nuna tausayawa don shi ma ya san tana tafiya kamar ta sabbin ƴan shayi sai ya karɓi uzurinta. Fitowa ya yi ya same suka zuba masa na mujiya don tunaninsu a yadda suka saba da ita za ta fito daga ta ji shigowarsu amma sain gashi da har da aike ta gagata fitowa kamar wata sarauniya. Shi sai da ya zo falon ma ya tuna bai tanadi abin faɗa musu ba sosa ƙeya ya yi ya ce "Bacci take" Junansu suka kalla da mamaki din sun san sun ji muryarta sai kumamsuka kalle shi, sai lokacin ma ya gane ɓaran ɓaramar da ya yi don ga san za su iya jin dirin muryoyinsu Hibba ce ta ce "Baccj kuma yaya? Ko dai ba za ta samu ganinmu ba?" Saurin ɗaure fuska ya yi ya ce "Ƙarya zan muku kenan?"Kai suka shiga kaɗawa kamar ƙadangaru sai ya ce "Ku tashi ku wuce gida an jima kwa dawo" Sum-sum suka tashi kowacce tana gungune sula fita, bayansu ya bi ya rufe ƙofar, lokacin Sadiya tana tsaye jikin windon falonta daga wajen tana gogewa, kallo ɗaya ta musu ta gane a jone suke wato ransu a ɓace ko kallo bata ishe su ba, suka fita fuuuu. Tun da suka fita a hanya suke ta mita suna mamakin faruwar hakan, ko da suka je gida suka faɗawa Hajiya sai ta musa tana faɗin ai ƴarta Meenal ba za ta yi haka ba wataƙila ma tana cikin yanayin farkon amarci abinka da sabuwar rayuwar da ba a saba ba. Haka dai suka haƙura amma ba don sun yarda ba suna da mamaki kawai!. Sai sha biyu ta sako ƙafafunta daga kan gadon lokacin har an maimaita abin da aka gabayar jiya na amarci, abin da ya ɗaurewa Nasir kashi ne kamar wanda ya kai zicyara ƙofar gari haka ya ji hanyar zurum babu wani birki, don lamarin ya fi ƙarfin na darw har gwara da dare da sauƙi. Sai dai abin mamakin daga ya gama aikata sunnar sai dai abin ya tsaye masa a rai ga abu na damuwa amma ya kasa tuna mene ne. Sannan yadda take raki bashi da banbanci da farin shiga bai sai duk ana yin hakan don a kawar masa da zargi duk da ta san maganin da ta yi amfani da shi jiya da dare sai ya fi aikinngusar masa da mummunan zato fiye da kissa da kisisinar da take yi . Shi ya jona tuwan kamar dai wanda ya jona musu na farko ya kai ya haɗa ta shiga tana mita irin ta sabbin amare abun da bai sani ba har wankin ciki an taɓa yi mata wanda suka santa ba mutum ɗaya ba ba biyu ba ta daɗe tana gararamba da mutanen banza kuma har yanzu suna da contact na juna ba wai an rabu ba ne ana tare!. Sai da suka fito falon ya buɗe kwanukan tana zaune tana wani yaɓe baki, plate ya fito ya ɗakko da kofuna, lokacin Sadiya tana ɗaki kallon ɗakinnta ya yi yana tuna irin romon amarcin da ya sha kwasa tana farkon zuwa sannan da ya kasance mace ce mai kula da kanta har yau ba za ka ji wani sauyi mai yawa daga gare ta ba duk da ta haihu, shiru ya yi yana son ya tuna mene ne bambanci tsakanin Meenal da Sadiyar mene ne aibun da ya bambanta su sai ya ji kansa ya sara, haka ya wuce da plate da kofunan ya koma part ɗin amarya. Ko da ya zuba musu komai ya haɗa shayi kofi biyu da madarar da Hajiya ta ƙullo da milo a leda bata ce masa komai ba sai da ya gama ya ce "Sakko mu karya" Da yake a kan kujera yake a zaune kallon sheƙeƙe ta masa don dama babu labarin da bata sani a kan lamarin gidansa da uwaraa take tafiyarwa ba ita kuma ko a mafarki ba za ta ɗauki wani renin wayo ba dole akwai sake!. Ɗan haɗe fuska ta yi ta ce "Ni fa wannan abinci ba ci zan yi ba, to da yanzu abincin ne sai an kawo mana daga gidanku kamar wasu almajirai" Ƙaran wayarsa ne ya katse masa martanin da zai mayar ganin sunan Hajiya ya ɗaga yana gaishe ta daga ɗaya ɓangaren ta ce "Nasir Allah sa dai wannan matar taka bata ga dankali da ƙwan wannan ba ka santa da zalama kar ma ta saka tai don na ƴata Meenal ne, kuma ka ga tun da kai a nan kake karyawa tun da yanzu ka yi amarya wacce ta saba da cin cima mai kyau sai ake ɗauka muku kashinku amma iya abincin safe shi ya sa ma na tsakura muku kayan shayin wannan na san zai muku kwana uku don ƴata na san akwai tattali" ,Tun da ta fara magana yake kallon farantin da ya juye dankali da wainar sannan yana kallon ledojin kayan shayin da ya zazzage su duka, tun da dai ya san a gidan Hajiya mai kauri take haɗa musu. Yana ƙirƙirar dariya ya ce "Eh, mana" Hajiya ta ce "Ban gane eh mana ba?" Ya sake cewa hakan ya yi. Meenal ya ji ta taso ta ɗora hannu a kan wayar ta karɓa amma bata gaishe da Hajiyar ba ta ce ",Hajiya" Jin muryar Meenal ta ce "Na,am ƴata ya kuka tashi ya kwanan baƙunci, ai ke ki sha kuruminki babu ke babi cin tuwon safe dama hausawa sun ce mai uwa a wurin murhu ba ya cin abinci gaya" Ta faɗa tana ƴar dariya Meenal ta ce "Hajiya ni dai ba zan lamunci a ce kullum sai ana ɗakko wani kwando da kwanuka ana biyo layi a kawo min ba kowa yana ganin ana bani abinci kamar mai neman sadaka, dankali da doyar da kuma ƙwan da komai za a kwaso a maido gidan nan, su Hibba suke zuwa da safe suna soyawa idan ana gama na tsakura muku naku na ɗauki nawa da na Nasir, shi ma kayan shayin sai nake ƙulla muku a leda suna ɗauka suna tafiya!" Ba Hajiya ba hatta Nasir maganar ta bashi mamaki ganin tana zaro magana mai kama da rashin kunya ko taunawa babu tana faɗawa mahaifiyarsa, wanda abu ne da bai taɓa ganin makamancinsa daga wajen Sadiya ba ko da kuwa an ɓatawa Sadiya rai. Hajiya kuma kasaƙe ta yi tana bin su Husna da suke gefenta da kallo su ɗin ma ita suke kallo bakinta ma ya ƙi rufuwa tsabar mamaki, tana tunanin wuta a maƙera amma tana shirin ganinta a masaƙa lokaci guda ta fara tunanin mai hakan yake nufi ko dai a mafarki take dokar da ta shimfiɗa amma yarinyar da take wa kallon babu mai hankali da ladabi da biyayya irinta amma tana faɗa mata magana gatsal har ita za ta ce ƴaƴanta suke zuwa suna yin abinci a gidanta wai ita za take ɗauka mata tana tsakura mata kayan shayi bayan ita ta tsugunna ta haifi Nasir abin mamakin ma a kwana ɗaya tak!. GIDAN BABA Rayuwa ta kacame a gidan Baba yanzu duk abu ya ƙi da daɗi don yanzu sai samo maganin farin jinin yake yana basu suna sha amma har yanzu babu ci gaba babu wanda ya fito ya ce zai aure su. Sai dai kowacce yanzu sai sha,anin gabanta take tana samun kuɗin biyan buƙatunta da ɗauke ɗawainiyarta da mahaifin nasu ya kasa ɗauka sai dai yanzu Arfat ta samu wani mukulli da yake iya buɗe store ɗin Baba da zarar idanunsa ya kauda za a kwaso shinkafa a dafa a wadace duk wacce take da girki ita za a ba mukullin ta ɗauko idan aka samu zaƙaƙura hatta da daddare sai a ci tuwon shinkafa. Idan ya bada hatsin tuwon sai a aunarwa maƙota a yi cefanen miya har da nama. Baba ya samu ya ci har da saka albarka don yanzu ya fara ganin amfanin nasu tun da suna ciyar masa da gida sai dai babu tuhumar inda suke samun kuɗin suke siyan shinkafar. Da yake a store ɗin inda ya ajiye shinkafar da ban inda hatsin ma yake daban ita shinkafa a lulluɓe take ya ɗora wasu manyan duwatsu sannan tun da mukulli a wajensa yake ya san babu mai shiga hakan ya sa ba ya ma wani dubawa. A haka sai da aka cinye buhu biyu aka fasa na uku shi ma ya yi rabi. Ranar da ya ji labari a kasuwa kayan abinci sunnyi tashin gauron zabi kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha don murna yana ta lissafin yadda zai samu kuɗin don a yadda yake ma tunanin yana son ya yi sabon aure don yana saka ran ko matar za ta haifa masa jari wato namiji. Yana ta jiran wacce ruwan shanta zai ƙare a gidan ya sake ta. Bayan ya dawo ya buɗe store yana murmushi ya shiga sauke duwatsun yana yaye buhun ya yi mugun gani da sauri ya ja baya gabansa yana faɗuwa ya shiga ƙirga buhun nan ya gane babu guda biyu sannan ga ɗayan ma saura rabi, wani ihu ya yi sannn ya ji jiri ya kwashe shi bai sake sanin inda yake ba. Lokacin da matan gidan suka ji haka aka zo ana shiga da ƴaƴan aka ganshi yashe ba ya lumfashi, kowa ya fahimci dalilin suman baba haka aka kinkime shi aka kai shi ɗakinsa, sai da aka ta sheƙa masa ruwa kafin ya fardaɗo yana faɗi "Wayyo shinkafa ta" Ganjn bai gama wattsakewaba aka shiga bashi baki sai da warware ya tara mutanen gidan duka, yana gargaɗin wanda yake shiga masa store amma kowa ya ce ba shi ba ne. Jin hakan sai a sallami kowa amma dai kowa gabansa yana faɗuwa ana tunanin hukuncin da zai yanke. Aisha ce ta yi laɓe yana waya da abokinsa ta ji yana faɗin yana zargjn ko dai shinkafarsa ce ake ci a gidan idan har ya yi bincike ya gane hakan tabbas rai zai yi mummunan ɓaci, sannan zai fasa fita kasuwa na kwana uku don ganin wanda yakr masa aika-aika idan matarsa ce daga ranar zai yanke igiyar aurenta, idan a ƴaƴa ne zai tsinewa ko wace ce kuma ya kore ta daga gidansa. Kowa ya tsorata da lamarin basu san abin zai yi tsamari ba hakan ya saka duk mai girki sai ta san yadda za ta yi ta bayar a auno shinkafa ta dafa da miyar dik ta yi cefane. Baba ya auna sauran shinkafar da ta rage a buhu ya san yawanta amma kuma gashi ana dafa abincin a gidan sai dai ahinkafar buhun idan ya sake aunawa sai ya ga tana nan yadsa take, hakan ya sa abin ya ɗaure masa kai ya kasa gane inda matsalar take, a wani ɓangaren na zuciyarsa ya fara tunanin ko dai aljannunne suka masa satar. Kwana uku yana gadin store amma babu wanda ya gani ya shiga sannan abin da ake ci a gidan ba a a daina ba, hakan ya sa ya gane matsalar ba daga iyalansa ba ne!. Lokacin da ya tafi masallaci sai Hafsat ta ce yau za ta tashi da dare domin ta kawar wa da Baba zargi ko ya haƙura ya fara zuwa kasuwa sannan ya daina zargin kowa za ta zo a matsayin ɓarawon shinkafa da dare sai dai tana fatan Allah ya sanya saɓanin tsakaninsu kar ya karya mata ƙafa kasancewar da wani ƙaton icce yake kwana!. Dare ya tsala kowa yana ɗaki ya yi bakam amma ba barci ake yi ba, don kowa yana fargabar zuwan Hafsat a matsayin ɓarawo sai dai ana tsoron ya za ta kasance don kowa yana tsoron hukuncin da za a yanke musaman da abin ya shafi kowa. Riga da wando ta ɗauka a ɗakin Baba wanda ya ware zai bayar wasu tsoffin kayansa ne da suka ga jiya da yau har ma da shekaran jiya domin sun tsufa har sun gaji. Misalin ƙarfe biyu ne na dare ta tashi ta saka kayan bayan ta karɓi mukullin store ɗin da suke amfani da shi a wajen Arfat. Lallaɓawa ta yi ta buɗe store ɗin a hankali ta tura ƙofar a hankali hakan ya yi daidai da falkawar Baba da bacci ɓarawo ya sure shi, zaune ya tashi a ransa yana raya rana dubu ta ɓarawo ɗaya tak ta mai kaya. Ƙoton icce da yake rinjayarsa ya ɗauka yana ayyana cewa yau sai dai uwar ɓarawon nan ta haifi wani amma idonsa -idonsa sai ya rotsa masa iccen a kansa. ALIYA Tun da Baba ya kira ta zaure inda suke zaune da sirikinta gabanta yake faɗuwa a ranta tana fatan Allah sa zaman nan da za a yi ya yi silar warwarwwar aurenta tun da dai har suka rufe ta aka aura mata mata maza a matsayin miji. Tun da ta zo ta gaishe da sirikin nata ya amsa sai kuma suka shiga tattuna maganar sai dai tana jin yadda mahaifin Naair yake ta ƙoƙarin kare ɗansa ranta sai ya fara ƙuna jin nata mahaifin yana gamsuwa da bayanin Abba ya ce "Kenan dama an daɗe da magance matsalar?" Baban Kasim ya ce "Ai tun da aka haife shi a haka muka garzaya asibiti nan likitoci suka yi bincike suka gano cewa ya fi ƙarfi a ɓangaren namiji hakan ya sa da na ji kuɗin aikin a lokacin bani da kuɗin da za a masa aiki, har ya fara tasowa zuwa shekara bakwai a lokacin ne abokansa yara uke tsokanarsa kullum ya fita waje sai ya dawo da kuka suna tsokanarsa da mata maza har a makaranta ma wannan dalilin ya sa muka ƙauro muka dawo gidan da muke a yanzu to a nan babu wanda ya san larurar da yake ɗauke da ita har Allah ya hore mini na samu aka masa aikin gabaɗaya ma wajen matantakar sai tabon aikin da aka yi a wajen, ni kuma abin da ya sa ban faɗa ba tunanina ya faɗa mata shi Kasim ɗin kuma dai da na ga yanzu a ɓangare ɗaya yake sannan likitoci sun faɗa mana idan aka yi wa mata maza aiki yana rayuwa kamar kowa sannan ba a gadon haihuwar mata maza kuma su ma za su haihu kamar kowa" Abba ya ce "Allahu akbar!. Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai halitta yadda ya so, ka yi haƙuri wallahi ni ban san ma haka abun yake ba ka san yaran zamani duk tunanina har yanzu akwai larurar da na san haka ne ai babu dalilin da zai sa na kira ka a waya" Aliya wacce kanta yake sunkuye bata san lokacin da ta ji wasu zafafan hawayen baƙinciki suna kwaranya mata ba saboda ta ɗauka Abba zai fitittike ya ce sai an sakar masa ƴa amma sai take jin saɓanin hakan. Wannan barazana ne ga cikar burinta na auren Ibrahim kuma dai hakan ba zai sare mata gwiwa ba ko ta halin ƙaƙa sai ta aure shi sai ta tarwatsa zaman Jidda a cilkin gidansa ta maye masa gurbinta!. Ana cikin wannan tattaunawar da ake ne Kasim wanda gabansa yake zuwa da dawowanya ƙaraso gabaɗaya a firgice yake dakyar ma yake ganin gabansa lokacin da ya shiga zaure da sallama bayan an ce ya shiga, saura kaɗan ya faɗa kan Aliya da take gefe saboda kiɗima da faɗuwar gaba, haka ya daure ya zauna tare da gaishe da su Abban. Jin Abba ya amsa masa fuska sake ya fara tunnain wataƙila Abban ya fahimci shi kuma ya masa adalci!. Abba ya buɗe baki ya ce "Aliya yanzu dama maijinki ba ya ɗauke da larurar an magance amma kika ɗakko ƙafa kika taho gida?" Gabanta ne ya faɗi don tabbas tana taoron Abba amma dai a yau saboda cikar buri da son zuciyarta ya zama dole ta wanke idanunta ta ƙwatarwa kanta ƴanci tun da dai ai ta san ba a sauyawa tuwo suna, ma'ana tun da har aka kira Kasim da mata maza to wannan suna ne da zai zama linzami har mutuwarsa don haka ba za ta so a ci gaban da ambaton ta a matsayin matar mata maza ba!. Baki ta buɗe ta ce "Abba ni abi ban sani ba kawai na ɗauka akwai larurar har yanzu" Kasim jin ta yi magana cikin lafazi mai taushi sai da ya sauke ajiyar zuciyar da har sai da gabaɗaya mutanen zauren suka ji. Abba ya ce "To na miki uzuri don haka yanzu tun da kin ji bayanin da aka yi ki tashi ki bi mijinki tun kafin idanun mutanen unguwa ya kai ga abin da yake faruwa" Tuno da maganar Amatallahi ƙawarta ya sa ta ce "Abba ni na haƙura da zama da shi" Ta faɗa ko gizau bata yi ba don ta gwammace ran Abban ya ɓaci a kan ta haƙura. Abba tsabar mamakin furucinta bakinsa ya ƙi rufuwa ba furucin ne kaɗai abin mamakin ba wato na komawa gidan illa yadda ta iya furta maganar a gabansa da gaban sirikinta a gefe ɗaya bga mijinta shi dai ya san ƴaƴansa ya basu tarbiya da sanin girman na gaba sannan uwa uba kunya sai dai furucin Aliya yasa ya fara tunanin lallai ta yi watsi da tarbuyar gidansa!. Cike da mamaki ya kalleta ya ce "Aliya ɗago fuskarki" Dakyar ta ɗago a nan ya ga abin mamaki fuska shaɓe shaɓe da hawaye, ya kalli idanunta ya ce "Ni kike faɗawa wannan maganar?"Da sauri ta kawar da idonta daga kallonsa. Kasim kuwa furucinta kaɗan ya rage ya rafka ihu hatta mahaifinsa maganar ta girgiza shi yana ganin ya aurawa ɗansa ƴa ƴar gidan mutunci amma kuma abu yana neman kwaɓewa. Kai ta girgiza ya ce "Baki ji bayanin da aka miki ba kenan yanzu idan ƙaddara ta faɗawa abokin zamanki ba za ki rungumi ƙaddara ki zauna da shi ba? Shin baki san aure sadaukarwa da juna ba ne, kuma shi ɗan adam ba a gama masa galitta har sai ya bar duniya mutane nawa ne suke da idanunsu amma yau an wayi gari idanun sun salwanta ta silar afkuwar wata ƙaddara? Mutane nawa sike da ƙafafu amma sanadin wata ƙaddara an yanke musu wano ƙafa ɗaya wani kuma duka biyu. Mutane nawa suke da hannu amma yanzu wani babu hannun wani haƙuransa ya rasa sanadin haɗari ko wata ƙaddarar, wani asalinsa yana da kuɗi ƙaddarar karayar arziƙi ta faɗa masa, wani kuma shanyewar ɓarin jiki wani kuwa nan da nan ba zai iya takawa ba sai an tashe shi zaune sai an kwantar duk wannan ba ƙadsara ba ce? Kuma sai ƙaddarar da halitta ce aka haife shi da ita sannan an magance amma ke za ki ce wai kin fasa zama da shi wannan adalci ne kuwa, shin ina soyayya da ƙauna ina sadaukarwa irin sadaukarwar da take ahiga tsakanin ma,aurata ko masoya irin wacce ake kira da duk wuya duk runtsi ana tare?" Sosai ta saddar da kanta amma a zuciyarta babu alamar rusuna ko da na sani bare sauya ra,ayi a nata ganin duk matar ko mijin da ya ɗauki ƙaddarar da ta afkawa abokin zamansa shi ya ga zai iya amma ita kam sam babu wannan sadaukarwar. Hatta mahaifin Kasim kai yake jijjigawa irinn yabawa da bayanin Abba. Kasim kuwa ji yake ai babu ma yadda za a yi ta ji wannan bayanin ta kasa cire ƙudurinta shi gani yake ma har wancan haushin nasa da take ji kafin ta ga yanayin halittarsa duk za ta zubar da makaman yaƙi, domin wannan bayanin na Abba ya haɗo komai idan ya ce komai yana nufin komai. Amma buɗar bakinta sao ta ce "Abba ni kawai na haƙura da zama da sh... Tun kan ta kai aya Abba ya wanke fuskarta hagu da dama mahaifin Kasim yana hana shi amma ran Abba ya ɓaci dama mai haƙuri bai iya fushi ba sannan Abba tsayayyan mutum ne a kan iyalansa. Rai ɓace yake nuna ta da yatsa tana riƙe da kumatun ta shi kuma Kasim tamkar shi aka mara haka ya ji Abba ya ce "Na fi ƙarfin ɗiyar da na haifa ta watsa min ƙasa a ido, ba a yi ki ba Aliya wallahi idan shawara aka baki ma ko son zuciya ki sani na fi ƙarfin ƴata ta juya ni, bani da buri ko ƙudurin yi wa ƴaƴana auren dole hakan ya sa na baku dama kuka fitar da zaɓinku don haka wallahi kin yi ƙarya!." Ya faɗa lokacin da ya tashi tsaye yana ta kumfar baki hatta ƴan cikin gida suna iya jiyowa Umma kuwa tana zaune ta rafka tagumi hannu bibiyu, a ranta tana raya ta so a ce Aliya ce a gidan miji hankali kwance Jidda ce ta dawo gida ake wannan ɗauki ba daɗin sai dai abin ba haka ba ne. Mahaifin Kasim yana ta bashi baki haka Abban ya nuna masa ya haƙura sai dai Kasim yana tsaye ya rasa abin yi don bai ga Aliya ta ji wannan maganar da aka mata ba, haka ya sa Abba cike da ƙaraji ya ce. "Yanzu ba sai an jima ba ki tashi ki bi mijinki idan ba haka ba ki fitar mini a gida, sannan ki sauya wani uban na yafe ki a matsayin ƴata!" Gudun kukanta ne ya ƙaru Abba ya ba mahaifin Kasim hannu suka yj masabiha ya tare mashin ya hau ya tafi, shi ma Abba mashin ya hau don komawa kasuwa. Kasim napep ya samo ya fi minti ashirin yana jiranta tana cikin gidan zuwa can sai gata wata mata ta rako ta, tana riƙe da hannun Aliyar da take rafkar kuka tana ta bata baki haka ta shiga shi ma ya shiga mai napep ya ja domin sadar da su ga gidan nasu. Ji take kamar ta shiga bugun Kasim har sai ya daina numfashi, ranta ƙuna yake musamman da ta gansu a napep ita da shi don hassadar tata ce ta motsa a kan Jidda tana rayawa a ranta da a ce Jidda ce da Ibrahim mota sai wacce suka zaɓa za su hau amma ita gashi a napep za su tafi gidan da babu get ko keke babu bare a yi maganar mota a zuciyarta ta ce 'Allah tsinewa tsiya da kuma matsiyaci,!". Tun da ta koma gidan sai ta ji ta ƙara tsanarsa sannan tun daga wannan ranar bata ƙara yarda wani abu ya shiga tsakaninsu ba, ita Amatullahi bata taɓa bata shawarar kirki kullum cikin zugata tana nuna mata ita ce ta dace da zama matar Ibrahim ba Jidda ba. Bayan sati guda ta yi dogon tunani da nazari don cim ma burinta sai dai wani hanzari ba gudu ba ta gane cewar wannan ƙudurin ba zai cika ba har sai ta shirya tsakaninta da Kasim, wannan ne zai bata damar ta shirya da Abba sannan kuma hakan zai kaita ga cim ma nasara a kan burikan ta Ta sauya takunta don yanzu ta sakko tana nunawa Kasim kulawa sannan bata nuna masa komai hakan ya sa ransa ya yi fari ba tare da ya zargi komai ba ya danganta hakan da addu,ar da yake yi ce ta karɓu. Bata hana shi kanta sannan komai yake so tana masa bayan kwana biyu sai ta bijiro masa da buƙatar kuɗi dubu goma amma sai ya ce bashi da shi, hakan ya sa ta nema a wajen Jidda sannan bata nuna masa ta damu da bai bata kuɗin ba. Jidda ta tura mata kuɗi naira dubu hamsin tun da ita yanzu bata da matsalarsu haka kawai ma idan ta yi kwalliya ta birge Ibrahim sai dai ta ji ya ce ta kawo acc no. Amatullahi ta turawa kuɗin ta siyo mata waya ta dubu talatin da sim sabo ta kawo mata a ɓoye ta samu waje ta ɓoye don sim ɗin mai register ne. Sai da Kasim ya fita ta saka sim a waya bayan ta mata caji ta tura whatsapp ta buɗe da sabuwar lambar, sai kuma ta saka no Ibrahim wacce ta sata a wayar Jidda tun suna gida no da ta yi haddar karatun fatiha don ko daga bacci aka tashe ta za ta iya faɗar lambar wayar Ibrahim. Da yamma tana kwance a falonta wayar sabuwar riƙe a hannunta ga kuma lambar Ibrahim da take son kira bayan ta yi ta sauya muryar da za take masa magana da ita yadda ba zai taɓa fahimtar cewa ita ba ce so take ta yi amfani da damarmaki ta fara gina kanta a zuciyarsa yau da gobe kafin ta masa dirar mikiyar da duk runtsi duk wuya sai ya aure ta. Tafiya yake a mota ya kusa ƙarasawa gida, ya ɗan fita ne shi ne ya dawo, yana tafiya yana tuno masoyiyarsa da yadda ta sauya gabaɗaya rayuwarsa idan ya tuna Jidda babu abin da yake sai saka mata albarka da fatan gamawa da duniya lafiya. Wayarsa ce ta shiga ruri, tunaninsa ma ita ce sai dai ɗago wayar ya sauya masa akalar tunaninsa domin kuwa wata baƙuwar lamba ce a rubuce a saman screen ɗin raɗo-raɗo. MAMAN AFRAH 0902557622 [11/18, 12:08 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=wwt *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 1️⃣9️⃣ *BABA* Cikin sauri yana ɗauke da iccen ya nufi store ɗin Hafsat da take tsaye laɓe daga bakin ƙofa ta ciki, riƙe take da kwano wanda ta ciko da shinkafar, Baba babu tunanin komai ya nufi ɗakin tana jin yana dab da shigowa ta saki kwanon shinkfar ya faɗi, a bakin ƙofar suka ci karo amma sai Hafsat ta shammace shi ta fita ba tare da ya kwala mata iccen ba, da gudu ta nufi wajen katangar gidan Baba ya rufa mata baya iccen yana rinjayarsa tana zuwa ta ɗare katangar dakyar kasancewar ba wani tsawo ne da ita ba Baba kuwa ganin za ta tsare kuma ba zai iya ɗagawa ta yadda zai rafka mata ba, don yau iya ganinsa sai ya rotsa kan ɓarawon shinkafarsa tun da dai har Allah ya nuna masa shi muraran. Ganin ba zai iya ɗaga iccen ba sai ya yi wurgi da shi saboda ƙarfin hali ya kama katangar shi ma ya ɗare don ya yi alƙawarin ko a shi ko a ɓarawon shinkafa. Hafsat ganin Baba ya hayo saman katangar sai gabanta ya shiga faɗuwa saboda kar ya je ya gane ta, duk da ta saka hular sanyi a kanta ba zai ga gashinta da zai nuna mace ba ce kuma ba lallai yadda yake a rikice ya yi la,akari da duk wani abu na jikinta da zai alamta masa ba namiji ba ne. Baba kuwa ganin ɓarawon zai dira sai ya miƙa hannu ya kama rigar Hafsat a zuciyarta ta ce "Shikenan na shiga uku yau in asirina ya tonu daidai yake da barina gidan nan ko makamancin haka, amma ba zan yarda ba duk sai na tona asirin kowa matuƙar nawa asirin ya tonu" Bismillah ta yi a zuciyarta ta saita ƙasa ta dira inda Baba ya riƙe a jikin rigarta kasancewar rigar yadin ya gama cin duniyarsa bashi da wani ƙarfi saboda tsufa kawai sai ta yage ya zamana gutsuren yana hannun Baba ita kuma ta dira waje. Baba ya kalli gutsuren rigar ɓarawon a hannunsa takaici y ishe sa har zai dira sai ya hango ɓarawon ya zura da gudu, sannan ya hanga ya tabbatar tsakar dare ne ba ya hango kowa sai haushin karnuka, tunnainsa ɗaya kar ya bi bayan ɓarawon ya je ya shaƙe shi a banza a wofi wannan tsoron da ya ɗarsar masa a zuciya yana tunanin kar ma dai ko akwai wuƙa a aljihun ɓarawon kamar yadda mai napep ɗin da ya kai shi gidan Sadiya da zai mayar da ita ranar da Nasir ya dawo da ita ya shammace shi ya fito da wuƙa, bai yi wata-wata ba cikin sauri ya duro daga saman katangar ko ta kan iccen bai bi ba ya nufi ɗakinsa ko ɗakin shinkafar bai koma ba, yana shiga ɗakin duk sai wani tsoron ya ɗarsu a ransa yana tunanin da mai ya kai shi zai je ya bi bayan ɓarawo ya kashe shi ya kashe banza. Bai runtsa ba har asuba yana ta tunanin ɓarawon nan ashe dai zuwa yake yana ɗauka har yake zargin iyalansa ashe dai su hidima suke masa da kuɗinsu. Sai da aka shiga masallaci sannan ya fito ya yi alwalar ya buɗe ƙofar gidan ya fita, ita kuwa Hafsat tun lokacin da ya koma ɗaki da aka jima ta lallaɓo ta hayo katangar ta dawo gidan. Yana dawowa daga masallaci ya kewaya bayan gidan nasa yana duba sawun ɓarawo sai dai tun da daga gefen gidan ne kaɗai ƙasa da yake kuda da kwalta ne babu inda sawun ya je, haka ya haƙura ya dawo gidan. Yana zuwa ya shiga store ɗin ya ga yadda aka zubar da shinkafar nan ransa ya ɓaci a nasa ganin wannan ɓarawon ya ga makwancinsa. Haka ya sha masifa a gidan babu wanda ya kula shi a ƙarshe ya je ya siyo ƙaton kwaɗo ya datse ɗakin tun da ya ga ashe taƙadarin ɓarawon har mukullin gare shi tun da gashi yana buɗewa. BAFFA Rayuwa ta ci gaba da kaaancewa a gidansa har yanzu babu abin da ya dame shi da matsalar iyalinsa, Mamy kuma koyaushe cikin zulumi take dangane da yaran nata kowane yanzu abubuwan da yake ɓullowa da shi da ban, daga ta toshe waccan ɓarakar sai su fito da wata sabuwa. A ɓangaren Zalika yanzu kanta ya fashe domin kuwa na zaɓawa kanta rayuwa marar kyau da take ganin ita ce mafita a wajenta, rayuwar da wasu daga cikin ƴanmatan zamanjn nan suka zaɓawa kansu wanda ta biyewa shawarar ƙawarta Islam wacce tuni ta yi nisan da vata jin kira rayuwar siyar da mutunci wanda suke ganin holewa ne, bata yi la,akari da yadda mahaifiyarsu take ƙoƙarin inganta tarbiyarsu ba tun da mahaifinsu bai damu da tarbiyarsu ba ya sakarwa mahaifiyarsu ragamar komai. Zaune suke a wani wajen shaƙatawa su biyu sai wani baƙin Alhaji da mai ƙaton ciki ya gyara zama yana mai saka hannu a aljihu ya ciro waya yana cewa "Gaskiya islam baki da dama yanzu kuɗin shan ice cream ɗin ne har 500k" Ya faɗa yana ɗan dariya irin tasu ta manyan riƙaƙƙun ƴan duniya a ƙalla ya haife su amma ba ya tunanin abin da yake musu za a iya yi wa nasa ƴaƴan kawai duniyar ce a gabansa. Islam ta yi wani farrr da idanu ta ce "To kai Alaji 500k nawa take a wajenmu ai dama sai dai shan ice cream ɗin ka san dai mu manyan yara ne" Dariya ya yi ya kalli Zalika da take ɗan danna waya ya ce ",Wai haka ne?" ,Ya tambaya yana ɗaga gira ɗaya wani murmushi ta yi ta ce "Kai za ka ba kanka wannan amsar" A maimakon ya saka musu 500k sai ya tura musu 1m Islam tana ganin alert sai kawai ta karkaɗa kai tare da cewa "Yesss Alaji shi ya sa kake birgeni ka iya kyauta babu beb ɗin da za ta maka rowar komai tun da kana buɗe bakin aljihu" a faɗa tana mayar da kallonta kan Zalika da take darawa. Ji ya yi kansa ya fashe saboda haka sai kawai ya ce "Zalika mu mayar da Islam makaranta sai mu je hotel mu ɗan huta ko" Tana murmusawa ta tashi tsaye Islam ɗin ma ta miƙe tana musu tsiya cewa wato ƴar wariya ce. Sun kaita har cikin makarantar kafin ya karya kan motar suka wuce hotel Islam ta nufi cikin makarantar tana jin daɗin haɗuwa da Zalika kasancewar ita Islam ƴar talakawa ce kuma tana da son ƙarya da son abin duniya, inda ita kuma Zalika ba son abin duniya ne a gabanta ba kawai ta zaɓi wannan rayuwar ne da aka nuna mata ita ce mafita tun da tana ganin mahaifinta bai damu da su ba, sannan dama waje nan ne inda kowane uba zai sakawa ɗansu ido saɓanin ita uwa da take gida sai abin da ya zo kunenta na labari, don uban shi ne jagaban gida duk da uwa ma tana nuna tata bajintar domin dole a jinjinawa uwa ma wajen bada tarbiya. Sai dab da magriba ya ajiye ta a inda suka yj za su haɗu da Islam, kuɗin suka raba inda ta tari napep ta koma gidansu. Yanzu kam tana jin tashen balaga, don Mamy ta lura da sauyin Zalika kan dana shayinta ko jin tsoronta yanzu ko faɗa take mata ma sai ta ga dama za ta tanka bare har ta bata haƙuri. Kawai kamar rai bata ma son a mata faɗan don haka Mamy har ta yi faɗan ta gaji!. Da daddare misalin ƙarfe uku na dare Mamy ta tashi ta nufi ɗakin Zalika, a hankali ta tura ƙofar ɗakin ta mayar ta rufe, tana ta bacci hankali kwance, don ta ga shi ma Mubin sai wajen tara ya dawo dik abubuwa sun haɗe mata goma da ashirin. A hankali ta lallaɓa ta ɗauki jakar da Zalika ta fita da ita yau ta fito daga ɗakin ta rufe mata nata ɗakin ta nufa tana son a matsayinta na uwa ta fara binciken sirri ba tare da sanin Zalikar ba, tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar ta nufi bakin gado ta zauna gabanta sai faɗuwa yake, don dama ta duba wayarta jiya sai ta ga ta saka pswrd, tana son ta san abin da take aikatawa don tana jin zargi a ranta. Hannunta yana karkarwa ta buɗe jakar ta ciro komai na ciki ta birkice sai dai bata ga wani abu da ya danganci rashin gaskiya ba haka ta haƙura tana ɗn jin sanyi da sawaba a zuciyarta, tana dab da mayar da kayan saj ta ga ƙaramun zip daga ciki har za ta rufe jakar sai kawai wata zuciyar ta bata shawarar dubawa ko za ta samu wani abu da zai tabbatar mata wani abun. Tana zige zip ɗin abin da ta gani a ciki ya yi masifar faɗar mata da gaba, a take hankalinta ya tashi don bata san ma ta miƙe tsaye da abin a hannunta ba sai da ta ganta riƙe da abun tana tsaye a kan ƙafafunta cankarkar, jiri ya fara ɗaukanta.... MEENAL Ko a jikinta yayin da take furucin Hajiya kuma cike da mamaki ta ce "Meenal ko dai makuwa kika yi?" Meenal ta ce "Ban gane ba Hajiya rass nake a cikin hanklina nake magana, yanzu ke idan su Husna ne suka yi aure a gidan mijinsu za ki so uwar miji ta takura musu? Ni ma nan gidan nawa mijin ne kuma wallahi abin da na ga dama zan yi babu mai taka min bare ya zubar" Tana kaiwa nan ta sauke wayar daga kunenta ta yanke kira ta koma kan kujera ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Nasir kallonta kawai yake jin ya rasa bakin magana ma Hajiya kuma sai ta saki baki tana bin su Husna da kallo wanda su ma ita suke kallo suna jiran ƙarin bayani duk da yanayinta ya so basu wata amsa amma basu fuskanta ba. Hibba ta ce "Mene ne wai Hajiya?" Hajiya ta danne leɓe da haƙuri ta ce "Ikon Allah wai ni ko dai aljannu sun hau kan wannan yarinyar ne a daren jiya? Gaskiya ba ƙalau take ba ina jin sai an nema mata magani wallahi ba Meenal ba ce" Su ma kalkonta suke nan ta shiga furta musu abin da ya wakana sai Husna ta ce "Gaskiya abin fa da mamaki ai ko Sadiya da ba ma goyon bayanta bata yi wanna abin da Hajiya akwai dai abin da yake faruwa" Ajiyar zuciya ta sauke don sai yanzu ta ji daɗi da ta yi wannan tunanin amma in a ce gaske ne abin da yake faruwa to tabbas babu maraba akwai gagarumar matsala don ba za ta lamunta ba. Kiran wayar Nasir ta shiga yi amma ba a ɗauka ba har ta katse, Meenal cike da yatsina fuska ta ce "Ko ka karɓi wayar ka ɗauki kiran ko ka kashe don i wallahi ba na son ƙara takura min yake" Kamar wani soko haka ya ga ya koma ya karɓi wayar kafin ya amsa kiran ta katse sai ta sake kira yana kara wayar a kunne ta cr "Nasir lafiya dai ko, mene ne yake shirin faruwa" Kallon Meenal ya yi sai kuma ya ce "Babu komai Hajiya" Hajiya ta ce "Ban gane babu komai ba ko dai akwai matsala ka matsa daga kusa da ƴar tawa zan yi magana da kai" Da to ya amsa ya tashi ya nufi hanyar bedroom muryar Meenal ta katse shi da faɗin "Wallahi duk wata ƙulla ƙulla da aka yi ba zan ɗauka ba don ni ba bauta na zo ba, in ban da ma ana son yin wata ƙullalleniya ya za a yi ina matarka sai ka matsa za a yi magana da kai" Bai tanka mata ba ya koma ɗaki Hajiya ta rage murya ta ce "Nasiru wai daga jiya zuwa yau baka fahimci akwai sauyi a tare da yarinyar nan ba?" Nasir ya ce "Eh na gani Hajiya wani abu ne" Hajiya ta ce "Allah sarki Meenala ni wallahi na san ba ita ba ce yarinyar kirki me biyayya Allah sa ba jifanta aka yi ba wallahi ka san gidan kishiya" Nasir ya ce "Jifa kuma Hajiya daga zuwa sai a jefe ta, kum... Bai ƙarasa ba ta balbale shi da faɗa tana cewa ya je ya bata kulawa ya mata abin da take so ko ta takale shi da faɗa kar ya kulata don ba a hayyacinta take ba, ba don ya yarda ba ya amince kuma sai ya ji suna saka masa tsoronta a aransa. Yana zuwa falo ya ce "Yanzu mai za ki ci" Ta wani rausaya idanu ta ce "So nake ka je ka ce Sadiya ta soya min doya da dankali ta dafa min shayin goruba" Kallonta ya yi ya ce "A gidan nan babu dankali ko ƙwaya ɗaya, bare doya Sadiya ai tuwo take yi dama kayan dankalin a gidan Hajiya suke shi ne nake ci a can kuma yanzu tun da ke ƴarta cw shi ne ta aiko har da ke amma Sadiya ko a cokali bata taɓa aiko mata dankali ba" Kamar daga sama sai ji ya yi ta ja tsaki da sauri ya ɗago ya kalle ta ya ce "Wa kike wa tsaki" Banza ta masa ya buɗe ƙofar ya fita ba tare da ya ci abincin ba. Yana fitowa ya fice daga gidan dama ya ɗauka mukullin motarsa a falon yana zuwa ya tada mota, ita kuma ta koma ɗaki ta ɗauki waya ta kira ƙawarta ta ce "Ƙawata" Daga ɗaya ɓangaren ƙawarta ta amsa da faɗi "Inyee amarya ki ce ta waru, wato dai an dace an tsallake rijiya da baya, tun da na ji muryarki na gane ba matsala amma da ina nan cike da fargaba" Dariya ta fashe da ita ta ce "Ai na faɗa miki komai ya yi daidai wallahi da bakinsa bai furta ba kuma bai nuna wata alama ba ke gabaɗaya babi wannan maganar fa" Ta faɗa suna ta darawa abin su Safiyya ta ce "Shikenan ƙawata sai ki sha sha,aninki gida naki" Meenal ta c "Ai ki ƙaddarw ni kaɗai ce a gidan nan bani da kishiya kuma sai na koyawa kowa hankali" ,Safiyya ta ce "Girmanki ne ai yanzu zan haɗo kan ƙawayenmu yuya guda mu zo" Nan ta bata labarin yadda suka ƙare da Hajiya tana kashewa ta kira Momi mahaifiyarta bayan sun gaisa Momi ta ce "To ya kika ga yanayin zaman karki kuskura a rainaki matsawar dangin miji suka rainaki kowa kanki zai zuba shara da bola gwara a raba rani kowa ya ɗauka ko ita Hajoyar karki raga mata domin kowa kansa yake so ita ma duk yadda muke da ita ɗanta za ta fara so" Nan Momi take ɗora ta har tana faɗawa Meenal cewa za ta je wajen malamin ta ya dasa soyayyarta a zuciyar Nasir da kuma ƙin son rabuwa da ita duk runtsi!. Nasir yana fita ya nufi gidan Hajiya, ya samu Hajiya zaune suna ta magana da ƙannaensa Hajiya ta dube shi ta ce "Wai Nasir ya na ganka duk a firgice kamar ba mai sabon aure ba" Nasir ya busar da iskar da ya cika bakinsa da ita ya ce "Hajiya wasu halayya ne nake gani daba wajen Meenal duk abin ya ɗaure mini kai ... Tun kan ya kai aya ta tari numfashinsa da faɗin "An faɗa maka ba cikin hayyainta take ba amma ni na san ƴata ba irin ƴnmatan zamani ba ce" Ya yi ɗan shiru ya ce "Gabaɗaya ta sauya kamar ma ba sabuwar amarya ba" Nan Hajiya ta fara faɗin sai ta je ta samo mata magani wataƙila jifanta aka yi ko dai an yi mata wani abu da ya saiya mata tunani. Ko faɗawa ƙawarta mahaifiyar Meenal bata yi ba ta kama hanyar gidan malami ta ce ya bata karya tambaya bayan ta gama rattabo masa bayanin abin da yake faruwa ya bata tabbacin idan aka yi amfani da maganin komai zai warware. Lokacin da ta baro gidan malamin bata zame ko ina ba a napep sai gidan Nasir lokacin Nasir ya koma gidan ganin taron ƙawayenta sun cika falon wasu ma yana iya jiyo hayaniyarsu a bedroom, hakan ya sa ya faɗa mata zai ɗan fita bayan ya ɗakkowa Sadiya tsakuran abin da za ta dafa wanda ba zai isa ba ya bata. Shi a tunaninsa ƙawayen kawai ratsowa ne suka yi sai kawai Meenal ta ja shi gefe ta ce masa "Nasir ina mukullin store" Da mamaki yake kallonta sai dai kuma ya danne mamakin ya ce "Mukulli kuma?" Ta ce "Tambaya kake ko neman sani?" Lafazin da ta yi ya so bashi mamaki don shi abubuwa ne sabbi a wajensa Sadiya bata taɓa masa tambaya ko bashi amsar rainin hankali komai cikinn girmamawa da mutuntawa matsayinsa na mijinta. Cike da mamakin dai ya ce "Mai za ki yi da mukullin store?" Ta ce "Wai ban gane ba shi mukullin store ɗin har wani abu ne da za ake tuhumar mutum don ya ce a bashi?" Hannu ya saka a lajihu ya fito da mukullin daga ciki da yake mukullayen suna da yawa a haɗe sai ya nuna mata wanda shi ne na store ɗin, tunaninsa ko zuwa za ta yi ta ga yanayin store ɗin sai kuma ya ga ta saka hannu ta cire mukullin daga jiki ta miƙa masa sauran, tsabagen mamaki ma ya kasa magana ko ƙara bi ta kansa bata yo ba ta yi gaba, duk abin da suke Sadiya tana kallonsu kasancewar labule windonta a ɗan ɗage yake sannan kuma tana iya hangon su. Wani murmushi ta yi a zuciyarta ta ce "Mafari kenan" Kicin ta wuce tana ƙarewa kicin ɗin kallo ta ga kayanta a gefe kayan Sadiya ma haka a wulaƙance take kallon kicin ɗin duk da a share yake tas a goge sai gawayi da yake gefe da Sadiya ta ɗora ruwan abinci a ƙaramar tukunya ita saboda ana zaluntar ta ma ko kuɗin mahaɗin ba a bata ba bare kuma a bata don mugunta saboda ya ga tana sana,ar mai, amma duk da haka bata ma tanka masa. Meenal ganan cooker gas ɗinta ta ƙarasa ta ga silindar gas ɗin babu komai ai kuwa da sauri ta fito tana ƙwala masa kira don har ya juya ya je zaure ya juyo ya dawo shi ya rasa ma mai ya sa ba ya mata tsawa ko kuma rainin hankalin da yake yi wa Sadiya wacce duk wani cin kashi yake saukewa a kanta. Yana zuwa yake binta da kallon rashin fahimtar kiran da ta masa, yana ayyanawa a ransa wannan wace irin amarya ce da bata kara ko kunya a kwana ɗaya tak ta saki jikinta tana sha,anainta tamkar dai dama ta daɗe a gidan, ba ma wannan ba sai ya ga yanzu ta daina wannan tafiyar da take tana tale ƙafa. Wani farr ta yi da idanu ta ce "Ka tafi da wannn silindar a sako gas" Ɗan dimm ya yi abu ne da bai saba ba shi har ya manta ma da ya sayi wani gas tun lokacin da Hajiya ta dakatar da ake sakawa Sadiya ta ce ta koma amfani da gawayi ai kuɗin ya yi wani amfanin da shi sai gashi kuma yanzu za a ɓallo masa ruwa, tunanin da yake kenan ita Meenal ɗin ba za ta yi amfani da gawayin ba ko yaya? Tunaninsa ya katse ne daga inda ta ce "Amma fa karka sako mana have a ciko shi sosai" Da alamun tambaya a fuskarsa don ya kasa jurewa ya ce "Dama ba a gidansu amarya ake ciko silinda ba?" Wani yatsin fuska ta yi ta ce "Haba Alhaji Nasiru uwata ce za ta cika maka gas ɗin ma sai ka ce ita za a dafawa abincin" Bai tanka mata ba ya wuce ya ɗauki silindar ransa duk babu daɗi, yana kusa da ƙofar zaure ta ce "Nasir ka siyowa ƙawayena snacks da drinks masu sanyi saboda yanzu rana ta yi idan suka ci sai su yj girki sun ce min basu karya ba, kuma iya sauran abin da muka ci da dare suka ci" Tsabar mamaki ma sai ya ji kamar ya wanka mata mari yana ta tunanin to ita bata da aiki sai kawo buƙata daga tarewarta jiya bayan sun kwaso yuya guda babu izininsa sun cika masa gidan sannan banda abincin da za su girka ake batun ya siyo wani bayan shi abincin ma bai samu natsuwar ci ba sai ma yake ga kamar bata damu da shi ba. Ƙarfin hali ya yi ya ce "Haba Meenal yanzu ƙawayen nan naki kusan rai goma duk ni zan siyo musu abu?" Tana masa kallon ko dai ka kasa ta ce "Nasir su goma sha biyar ne fa, wasu ma don basu zo ba yadda nake da farin jinin ƙawaye ai baka ga komai ba wasu ma a gaba za suke kawo mini yini ka ga kuwa ai dole a tarɓe su don ni ba zan yi abin kunyar da ƙawayr za su yi gaba suna gulmata ba" Ta faɗa ba tare da ta jira cewarsa ba ta juya ta shige falo sai shewarsu ya jiyo. Kai ya kaɗa ya fita ya buɗe but zai saka silindar tsayuwar napep ɗin Hajiya ya dakatar da shi, fitowa ta yi tana ba mai napep kuɗinsa. Bakin Hajiya kamar ƙofar gari haka yake a buɗe don tana miƙawa mai napep kuɗi ne amma idanuta suna a kan silindar gas. Da sauri ta juyo tana rufe bakin jakar hannunta ta ce "Nasir mene ne wannan ? Ina za ka je da shi" Cikin sanyin murya ya ce "Gas zan sako" Hajiya da mamaki ta ce "Gas kuma Nasir na ɗauka ma siyar da silindae za a yi" Nasir ya ce "Meenal ta ce in ciko musu da gas" Hajiya ta c "Ka ciko musu kuma, yaushe yarinyar nan zuciyarta ta zama kare ya ɗauke yanzu har ta ɗauki kishiya wata tsiya da za ta ce a ciko musu gas, ni yanzu dama an saya mata kuka gas ne Meenal ɗin to mai ya hana a ciko mata da gas ɗin daga gida wannan ai ɗora nauyi ne ko zazzaɓin haɗa lefe bai bar aljihunka ba hallaw za a ɗora maka wahala" Ta faɗa tana kumfar baki Nasir ya ce "Hajiya ba fa ita da Sadiya ba ƙawayenta ne fa a gidan suka zo za su yi girki" Har da dafe ƙirji ta ce "Girki kuma? Ni ina tunanin abincin da na aiko da safe ya isa ku ci har rana kai da ita dai don cikinku kaɗai, shi ne yanzu za ta tsiro da girki bata san ni duk abin da zai hargitsa lissafin aljihunka ba so nake ba, su ƙawayen biyu ne ko uku, wannan ai tada mai gida tsaye ne ba don ba a hayyacinta take ba wallahi ba za a yi wannan rashin hankalin ba" Ta faɗa tana kumfar baki. Nasir ya ce "Su goma sha biyar ne ƙawayen kuma ta ce in taho musu da snacks da drinks kafin a ɗora abinci" Haɓa ta riƙe tana nuna da sake amma babu mai nakasta mata aljihun ɗa fon haka sai ta ce ya je ya tafi za ta yi wa tufkar hanci don sai dai idan ya kawo snacks da drink ɗin kowacce shegiya ta ɗauka ta nufi gidan ubanta amma ba za a zauna a dafa musu abinci ba su masa ƙasa da tattalin abincinsa. Yana jan motar ita kuma tana shigewa gidan duk ranta a ɓace da a ce ba Meenal ba ce ta yi wannan ɗanyen aiki da sai ta saɓar mata, da sallama ta shigo Sadiya da za ta je ta duba tukunyarta ita ta amsa mata da fara,arta cike da girmamawa wani irin taɓe baki Hajiya ta yi a zuciyarta tana faɗin 'Gulmammiya uwar ƴan kissa" Ta juya ta kalli Kalifa ta masa magana tana mai ɗaga masa hannu ta ce "Biyoni ɗakin ƴar gwal sabuwar uwarka ka ga ɗaki kamar a turai yarinya ta sha jere iya ganin mutum, duk hassadarsa sai ya yaba ko da a zuciyarsa ne ba a fili ba" Ta faɗi hakan ne dama don ta faɗawa Sadiya magana Sadiua kuwa bata ce komai ba sai ma ta ce "A fito lafiya" Shi dai Kalifa bai bita ba, tun kafin ta shige ɗakin take jin hayaniya da shewa irin na ƴan mata. Da sallama ta shuga amma tsabar surutun da suke basu amsa ba kuma ba wai don basu ji ba suna ji kawai ba za su iya katse hirar da suke ba. Har ta ƙarasa tsakiyar falon wasu a ƙasa a zaune wasu duk sun baje a kan kujerar wasu suna danna waya, sai wata da taee riƙe da plate tana cin dankalin daga cikin wanda suka ci na wajen Hajiya da ta aiko. Ran Hajiya ne ya ɓaci ita da take son a cancana abinci amma dai waɗannan sun zo za su yi almubazzaranci. Ganin babu wanda ya bata waje ta zauna irin cikin girmammawa a matsawa babba waje ya zauna ko a tashi a bashi wajen, sannan ta lura babu Meenal a falon hakan ya sa cike da nuna gadarar ta ita a dole uwar miji wato mamallakin gidan ta ce "Wai ku babu manya a gidajenku, ya kuna ganina babu wacce ta mayar da ni mutum kowacce tana sabgar gabanta?" Tamkar tana magana da bango aikuwa ta harzuƙa cike da masifa take faɗin "Yanzu za ku haɗa ya naku ya naku ku san na yi" Ta faɗa tana dosar bedroom ɗin da take jin wasu suna hanyaniya a inda take jin har da muryar Meenal ƴarta. Daga mai taɓe baki sai masu mata shewa. Tana shiga ta ga su huɗu ne kowacce ta waigo tana kallonta biyu a bakin gado a zaune kasancewar an sauya bedsheet ɗin sai dai babu wanda ya share don a cewar Meenal ma ɗakin bai ci a shere shi ba bashi da wani datti. Ɗaya tana tsaey gaban madubi tana shafa powder sai Meenal da take tsaye gaban gadon ta dafa kafaɗar ɗaya daga cikinsu suna magana, baki sake suke kallon Hajiya da Meenal ta ƙanƙance idanu saboda tsabar mamakin ganin uwar miji a ɗakinta ba ma falo ba, abun ya mata ciwo amma sai ta danne ta tsaya jin dalili don ta saka a ranta matuƙar tijara Hajiya za ta mata a kan maganar dankali da doya da ƙwai da kayan shayi sai ta yi wa Hajiya tass sai dai koma mai za a yi a yi don babu wani mahluƙi da zai taka mata birki dangane da cin kayan kowane abinci sai ta zaɓa ta darje. Hajiya ta kalle su a gadarance ta ce "Ku bamu wuri za mu tattauna da ɗiyata" Da kallo kawai suka bita sai Meenal cike da tsaurin ido na ƴanmatan zamani ta ce "Hajiya ni da su duk ɗaya ne ai za ki iya faɗar komai a gabansu waɗanann shaƙiƙan aminai na ne ko baki faɗa a gabansu ba sai na faɗa musu gwara ma ki rage min aiki kin ga in suka ji a kan kunnensu ba sai na maimaita ba" Hajiya kaɗan jakar hannunta ta suɓuce tsabagen mamakin kalaman Meenal amma kuma tuno da cewa ba hayyacinta take ba sai ta ce "Haba ke kuwa wanna ai sirri ne tsakaninmu" Kafin Meenal ta ce wani abu ƙawarta Safiyya ta ce "Ƙawata bari mu je waje bani mukullun store ɗin" Meenal ce ta miƙa mata mukullin ta ce "Yawwa ku auno kayan abincin yadda zai isa, kun ga an jima wasu za su zo sannan da yamma ma ba za a rasa masu zuwa ba bana so abinci ya yanke in kuma za ku shiga kicin sau biyu to" Ta faɗa tana ƴar dariyar tsokanarsu don ta san ba za su yarda su shiga kicin sau biyu ba sai Safiyya ta ce "Kema kin san ba za mu shiga kicin sau biyu ba sai dai mijin naki angonki ya siyowa sauran baƙin da za su zo abinci, amma dai yanzu za mu lodo isasshe wanda kowa zai isa sai a juye sauran a kuloli" Meenal ta ce "Kuma za a kai gidanmu kun san akwai baƙin da basu tafi ba kuma ba na son Momi ta yi wahalar bada abinci tun da ina gidan miji kin ga ta huta" Juyawa suka yi suna mata na,am da maganrta Hajiya kuwa tun da suka fara tattunawa ta zama mutuntume, tamkar gunki haka ta koma, ta rasa ma abin faɗa tsabar mamaki wato mukullin store ne a hannun Meenal har take da damar ba ƙawaye su lodo ɗanyen abinci su dafa duk yawan ƙawayen nan a ce wai akwai wasu da za su zo, sannan ma wai har gidan mahaifiyarta za a kai don kar ta sha wahala wato ita nata ɗan ya wahala ya nemo tabbas da sake ko kima da badaƙala don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, dole ta magance matsalar nan ta hanyar maganin dawo da Meenala hayyacinta ta san abin da take ta dawo mai ladabi da sanin ya kamata kamar yadda ta aurawa ɗanta ita a farko!. Muryar Meenal ce ta katse ta da ta c "Hajiya ina jinki" Ta faɗa wani gatsal babu sakayawa irin na girmamawar da ta saba tana mata, tana maida kallonta kan Meenal sai ta ga tana riƙe da ƙugu. Hajiya ta sassauta murya ta ce "Ƴata Meenal" Sai Meenal ta ce "Ashe dai arziƙi ne ya kawo ki ba tsiya ba ni wallahi na ɗauka maganar dankali ce ta kawo ki har na fara tanadar kalaman da zan mayar da martani, ah to in ce Hajiya an faɗi babu nauyi yanzu a ce a kan dankali ki taso tun daga gida" Ta faɗa tana ƴar dariya kamar a wasa. Abin ya baƙantawa Hajiya rai duk da tana tunanin ba cikin hayyacinta take ba. Danne zuciya ta yi ta ce "Ba wannan ya kawo ni ba Meenala" Ta faɗa tana buɗe jakarta ta ɗakko wani ƙullin magani a leda fara da baƙa. Ta ce "Wannan na farar ledar ki jiƙa a ruwa ki yi wanka, shi kuma na baƙar ledar sai ki sha a shayi" Ta faɗa tana bata amma bata karɓa ba ta jefe mata tamabayr "Maganin mene ne?" Hajiya sai da ta ɗan waiwaiya gudun kar wata ta taho daga cikin ƙawayen ta ji ta juya tana fuskantar Meenal tana sassauta murya gudun ma kar Sadiya ta musu laɓe ta waje ta ce "Maganin karayar asiri ne, da alama jifanji aka yi Meenal tun da safe bakya cikin hayyacinki" Wata bazawarar dariya Meenal ta yi ta ce "A hayyacin wa nake to? Mai ma na yi?" Hajiya ta ce "Meenal maganganu karazube kike yi babu taunawa bayan ba haka kike ba duk kin sauya ko ni kina min magana kamar sa,arki, haka su Hibba da suka zo da safe ma kika ƙi ganinsu ina jin ma baki san sun zo ba saboda bakya cikin hayyacinki, dama zama da kishiya sai da takatsantsan babu abin da ba za ta yi ba din ganin ta dusashe haskenki a idanun mutane da na dangin miji, jin an ce kina da ladabi da biyayya da girmama na gaba da ke ta shiga ta fita za ta ɓata miki asali" Meenal ta ɗan lunshe idanu ta buɗe ta ce "Bari ki ji in faɗa miki rasss nake, ke baki san a zamanin da ake ba ne yanzu? Ya za a yi kyakkyawa da ni yarinya ɗanya sharaf ƴar zamani in zauna miji ko uwar miji suna juyani kamar wata waina? Idan ma za ki ɗauke idanunki daga sabgar gidan ɗanki to ki kauda idanunki ki bar mu mu shaƙata mu more amma in kika ce za kike shiga sabgar da ba ruwanki ki yi uwa da makarɓiya wallahi hawan jini fa ciwon zuciya zai kashe ki" Meenal ta faɗa cikin halin ko in kula tana cikin faɗa wayarta ta yi ƙara ta duba ta ga Nasir ne sai da ta shawaɓe fuska alamar shagwaɓa ta kara wayar a kunne tana wani buga ƙafa kaɗan a ƙasa ta ce "Baby ka je ka zauna ka barni da kewa" Hajiya neman mai Jijjigata take yi don ta tashi daga mafarkin da take don abin ya shallake tunaninta an barta riƙe da ledojin maganin da sai da ta zare naira na gugan naira har naira dubu goma aka bata, duk don a dakatar da rawar kan Meenal a dawo da ita hayyacinta take mata biyayya ya zamana ita take jan ragamar gidan ɗanta amma sai gashi Meenal tana tababtar mata cikin hayyacinta take da alama ma inda kunya take Meenal ko ta wajen bata bi ba. Daga ɗaya ɓangaren Nasir ya ji wani daɗi da ta masa magana shi dama ba ya son wannan gadarar da take masa hakan ya sa ya washe baki daidai nan Meenal ta danna handsfree Hajiya ta jiyo muryarsa yana faɗin "An ciko gas ɗin taɓ kuwa amma ya ci kuɗi ko dama tsada yake ko don na daɗe ban saya ba na saba siyan buhun gawayi kuma Sadiya da adani sai ki ga ya daɗe tana amfani da shi" Hajiya jin an ce gas ya ci kuɗi ranta ya ɓaci ta fara tunanin yawan kuɗin kamar a aljihunta aka fitar tana tunanin yanzu idan hsr haka gidan Nasir zai ci gaba da kasancewa a hannun ƴan sari to ya za a yi da auren Hibba da Husna bayan shi ne komai nasu. Meenal bata amsa masa maganar wancan ba ta ce "Sweet heart lemukan nan fa ba kala ɗaya za ka siyo ba ka haɗo kaloli, sannan ka ƙaro da mararsa sanyi kamar katan biyar sai a saka a frige saboda baƙi" Da to ya amsa mata sai da ta saci kallon Hajiya da take cike kamar za ta yi bindiga ta sassauta murya ta ce "Ka taho min da fanadol jikina duk ya ɗau zafi saboda aikin da ka kwana kana yi Shi kuma ya ce Ai kam jiya na... Kafin Hajiya ta gama jin mai zai ce ta juya har tana haɗawa da gudu ta yi hanyar falo.... MAMAN AFRAH 09025576222 [11/19, 6:12 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣0️⃣ *HAJIYA* Har tana tuntuɓe a ɗan tudun ƙofar da ya raba falo da bedroom sai da ta zo falon ta ja birki kamar wacce aka biyo da gudu ko kuma wacce aka saka tsere. Mutanen falon da kallo suka bita suna tunanin dalilin gudn nata don duk a firgice take, sai da ta ga sun zuba mata ido ta gane ashe dai a guje ta fito. Wani takaici da haushin Meenal ne ya turnuƙe mata zuciya tana ganin ta yaya ma za a yi a ce tana surukarta take maganar kwana da miji, ba ma wannan ma ko da an ɗauke matsayinta na suruka ai tana matsayin uwa a wajenta tun da ƙawar uwarta ce. Meenal kuma tana ganin abin da ya faru sai ta fara danne dariyarta marar sauti don abin ya bata dariya ta tabbatar duk tijarar hajia matsayinta na uwar miji ba za ta so jin yadda daren farkon ɗanta ya kasance ba kuma ma a kan kunnen nata ɗanta ne zai ja ragamar bayanin. Ɗan wayincewa ta yi tana faɗa masa ya taho da panadol ɗin kafin ta yanke kira a fili tana furta "Wallahi in dai ni ce mu zuba ni da ku ɗan halak ka fasa don wallahi ba zan ɗauki rajnin hankali ba sai dai mu yi ta bugawa ni da ku muna fafatawa domin idanuna a buɗe suke rasss." Hajiya ɗan wayuncewa ta yi ta nemi waje daga can ƙaramar kujera ta zauna tana jiran Meenal ɗin ta gama wayar don ta fara tunanin ba hayyacinta take ba har yanzu domin da a hayyacinta take yarinya me kunyar kamar Meenal ba za ta yi magana da mijinta irin wannan a gabanta ba, shi ya sa har yanzu take ƙarfafa cewa bata san ina kanta yake ba. Abu na gaba tana tsoron ta fita tsakar gidan ta ci karo da abin da aka ɗakko a store ɗin ɗanta gani take zuciyarta bindiga za ta yi, in akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce a ce wani abu da zai taɓa lafiyar kuɗin Nasir ba shi kaɗai ta haifa namiji kuma shi ne nauyin dukkan ɗawainiyarsu idan har ya haɗu da kangararriyar mata ta san shikenan sun shiga uku a yadda ta fara ganin take-taken Meenal in har a zahiri ne daidai take gani ba wai jifanta aka yi ba wato ba asiri ba ne gaskiya babu tantama sun faɗa hannun ƴan sari!. Meenal tana gama wayar ta zauna ta ɗora waya da dadironta suna ta shan soyayyarsu don tana ƙara tabbatar masa babu rabuwa tsakaninta da duk wani abokin holewarta don ta yi wani aure, babu abin da za a fasa. Zaman da ta yi ta san duk ƙwawar hajia dole ta gaji ta haƙura domin ta san za take ta tunanin bata gama wayar ba. Hajiya kuma sai jera hamma take don da yanzu a gida ne da ta fara haramar cin abincin rana amma yanzu babu hali bata ma cikin nutsuwa da kwanciyar hankali an barta tana ta tangaririya a titi tun da sanyin safiya tana zuwa wajen malami tare da kashe naira dubu gomar magani bayan gashi shi kansa maganin ba a karɓa ba bare ta saka ran Meenal ɗin za ta yi amfani da shi. Suna gama wayar sai kiran Mominta ya shigo hakan ya sa ta ɗauka cike da farinciki suke waya Momi ta ce "Ta gaban goshi fatan dai babu matsala" Meenal ta ce "Momi ki bar batun matsala ko a mafarki ai tun da dai ni ce ƴarki to kin yi bakwana da matsalar damuwar ƴa mace a gidan aurenta don kin san babu wanda zan yarda ya yi awon gaba da ƴancina a gidan miji" Momi ta jinjinawa ƴarta tana ƙara bata ƙarfin gwiwa da jaddada mata kar ta kuskura ta bada fuskar da za a rainata a gidan aure!. Meenal ta ce "Momi ni dai zan yi iya iyawata don ganin ba a tozarta ni ba duk da na san wani lokacin duk ƙoƙarin mutum na gujewa natsala sai ta afka masa sannan matsaloln gidan aure ba kidahumanci ne yake kawo su ba ko rashin wayo, sai dai ya danganta da wanda ka dace da shi a matsayin abokin rayuwa ko kuma suruka da dangin miji, duk da akwai matan da suke bayar da kansu suka sakin jiki a musu kowane cin kashi duk da cewa mace ƴar biyayya ce amma ba ce ta bada fuskar da za ta zama baiwa ko kuma abar wulaƙantawa ba" Tun da ya fara bayani Momi take jinjina mata daga na ta hau faɗin "Kar ki kuskura ki ragawa Hajiya na faɗa miki daga ita har ɗanta ki koya musu karatun ta nutsu don na ga da sauransu a karatub duniya sun ɗauka don kina ƴata za su ci kashi a kanki ko su juye kowace bola a kanki to ba haka take ba" Meenal ta hau ba mahaifiyarta labarin yadda abubuwa suka wakana tsakaninta da Hajiya da Nasir har ma da zuwan Hajiyar gidan ta kawo mata magani wai bata cikin hayyacinta sai dai bata faɗawa Momi wayar da ta yi a gaban Hajiyar ba. "Magani Meenal hauka ake za ki karɓi magani a wajen wani barw ki yi amfani da shi, karki manta ni da Hajiya tif da taya muke hakan ba zai hana ta tarwatsa ko farraƙa tsakaninki da ɗanta ba don son zuciya irin nata kin sani bata ƙaunar a ɗanɗani arziƙin ɗanta ta fi son koyaushe daga ita sai ƴaƴanta don haka tana iya karɓo maganin da za ta rage miki matsayi a wajensa don kar yake kyautata miki, ko kuma ta yi maganin da za ki koma kina mata biyayya kamar vaiwa ta taka ki yadda ta so kamar yadda suka mayar da wannan uwar gidan marar ƴanci da galihu a wannan gidan" Meenal ta ce "Momi dama ina sane ba zan yarda ma na yi amfani da shi ba, sai faman faɗi take wai bana hayyacina ta fi so in ci gaba da ƴasƙantar da kai irin yadda nake nuna mata kafin ya aureni bata san kawai shigo shigo ba zurfi ba ne" Momi ta ce "Ai na san kin haifu a cikina gwara ki nuna mata shayi ruwa ne, sannan ki nuna mata tsakanin zuma da maɗaci akwai bambanci, kuma dole ne ki bambanta mata tsakanin aya da tsakuwa banda zubar da girma mai za ta je yi gidan yara a ranar farko ga ƙawayenki nan bata tunanin za a rainata duk son abin ɗanta ya rufe mata idanu"" Meenal ta ce "Ai da ni take zancen sai na gasa mata aya a hannu in shayar da su ruwan mamaki in bata kauda idonta ba sai na bayar da darasi a kanta yadda uwayen miji za suke barin matan ƴaƴansu su sake da mijinsu, ni ba zan lamunci cin mutunci ba ni babu wanda zan ragawa ko ita matar tasa sai ta san da zamana" Suna cikin haka Meenal daga wutsiyar ido ta hango Hajiya ta leƙo kanta cikin ɗakin, da sauri ta yi sallama ta kashe wayar ta nufi wajen tana faɗin "Hajiya dama baki tafi ba?" Wata ajiye zuciya da har sai da Meenal ta ji ita Hajiya ta yi a fili kafin ta ƙaraso tana faɗin "Ƴata Meenal baki karɓi magani ba ina na samu damar tafiya, kuma bakya tunanin ƙawayen can naki su yi aika-aika a store da kika basu mukullin?" Hajiya ya faɗa don jikinta sai yake bata kamar za su yi sata a store ɗin ko su yi almubazzaranci don ta ga ita Meenal ɗin bata ma damu ba da mukullin da ta basu. Ɗan yatsina fuska ta yj ta ce "Hajiya bari na miki gwari gwari yadda za ji fahimta, wallahi summa tallahi rass nake babu wani fitar hayyaci idan kuma akwai wani abu da kike so in tabbatar miki ki yarda za ki iya faɗar abin da kike so na faɗa miki, sannan kuma mukullin store ɗin ne sai an bi mutum don an bashi aika-aika a kan abinci sai kamce wasu ɓarayi to ni ko ɓarawo in ya saci abinci gani nake ba sata ba ce tun da idan ya ci ma maganin yunwa ya yi kuma za ka samu ladan sannan ai abinci kashinsa za a yi ba kadara ba ne da za ake alkintawa" Tsabar mamaki Hajiya kallon Meenal kawai take dakyar ta yi yaƙi da bakinta ya iya furta "Abincin ne ba kadara ba Meenal baki san mace ana so ta zama mai adana dukiya da komai na miji ba yanzu idan abincin ya salwanta a taron nan na amarcinki sai fa Nasir ya sake fafutukar kawo wani ai a tausayawa miji, sannan da kike batun ɗaukan abinci ba sata bane ai duk abin da mutum zai ɗauka in har ba nashi bane kuma ba a bashi ba sunansa sata k... Meenal hannu ta ɗagawa Hajiya wanda ya sa ta dakata da maganar cike da mamakin hannun da ta ɗaga mata tamkar wata sa,arta sai kawai ta ji ta ce "Hajiya ya kamata kisan inda dare ya miji karki manta nan gidan mijina ne ina da damar yin komai, sannan ba huruminki bane da zaki baro naki gidan sabodan zubar da girma ki zo kina bin diddigin abin da yake faruwa a gidan ɗanki sannan shi Nasir ɗin ai tun da kika ga ya yi aure ya shirya tarɓar kowace buƙata dole ta nemo idan babu kuma wallahi summa tallahi babu mai mini shamaki da abinci ko wani abu a gidan mijina, yadda kike taƙama ɗanki ne haka nake taƙamar mijina ne na ma fiki iko da shi yanzu" Furucin Meenal na yanzu ya sa Hajiya ta yi tsai tana lura da yanayin maganar ta a nan ta fahimci cewa tabbas a hayyacinta take babuwwasu alamu na fitar hayyaci a tare da ita kawai tsabar rashin kunya ne da fitsara hakan ya nuna ba ma sai ta ɓata loakci wajen cewa Meenal ta yi wani abu da zai nuna tana hayyacin ta hakan ya sa a zafafe Hajiya ta ce 'Wallahi ƙarya kike Meenal! Babu wanda zai yi iko da Nasir sama da ni" Meenal ta kalle ta ido cikin ido ta ce "Kina musu da hakan?" Bata jira amsar Hajiya ba ta ce "Idan kin musa ki zo ɗakin nan da daddare akwai wata shegiyar rigar bacci da nake da ita da kuma shu,umar humra mai tada kan maza zan saka rigar in shafa humrar zan faɗa wa Nasir ya zauna a wuri ke kuma ki ce ya tashi in zai bi umarninki mu gani!." Wani salati da Hajiya ta kwasa sai da ya so ba Meenal dariya son ta lura Hajiya ta shaƙi takaici kuma abin ya ɗaure mata kai Meenal ta murmusa ta ce "Ki saka takalmanki ki koma gidanki sannan ki ɗauke idanu a kan lamuran gidan nan idan kina son kanki da girma da arziƙi in ba haka ba wallahi takaici sai ya kusa kasheki" Tana gama faɗar hakan ta fito falo ta bar Hajiya tsaye kamar ta saki ihu tana fitowa falon ƙawayenta suka hau mata kirarin amarya har da masu mata waƙar amarya da Ali Jita ya yi wa amarya. Suna ta abin su Hajiya tana bedroom tsaye da jaka maƙale a hamata ƙullin magani guda biyu a hannu, waiwayawa ta yi ta kalli ɗakin ta ƙare masa kallo sai ta hangi gajeran wandon Nasir da rataye saman ƙofar banɗakin juyowa ta yi ta fito falon ko kallon tarkacen ƙawayen Meenal na falon bata yi ba ta yi waje don zuwa lokacin ma Meenal ɗin ta yi tsakar gidan. Sadiya tana alwalar azahar a famfo Meenal tana tsaye wajen ƙawayenta da suka ɗakko kayan abincin a store suna nuna mata, suna cewa abincin da yawa tana faɗa musu dama fa ba wai za a kai gidansu ba ne yau kawai ta faɗa ne don ta cusawa Hajiyar haushi. Fitowar Hajiya daga falon Meenal za ta saka takalmi ya yi daidai da shigowar Nasir da ya kinkimo silindar gas yana tafiya a ɗan duƙushe alamar mutum ya ɗaga abu mai nauyi bayansa wasu matasa ne guda uku suna ɗauke da katan ɗin lemo coca cola biyu mirinda ɗaya sai fanta biyu. Hajiya tsabar yadda ta ruɗe da ganin lemukan da ya siyo ga gas tana tunanin kenan dai maganar Meenal ta zama zanen dutse sai da ya aikata, a ƙwaƙalwarta tana ƙiyasin kimanin nawa aka kashe a hakan ta saka takalminta ɗaya nata ɗaya kuma na wata daga cikin ƙawayen amarya sannan kowanne ba ƙafarsa ba ce. Kiran sunan Nasir take Sadiya da ta gama alwala dariya tana neman ƙwace mata da ta ga ƙafar Hajiya ta yi saka takalmi kamar ƙafar ƙananan yara sannan takalman daban-daban ne uwa uba yadda ta tikce tana kiran Nasir. Nasir faɗi yake "Ina zuwa Hajiya" Ya yi hanyar kicin ya daidaita musu silindar a jikin gas ɗin, tsakar gidan kuma samarin nan suna tambayar inda za su ajiye lemukan Meenal ta yi karaf ta ce "Ku kai ƙofar wancan ɗakin" Ta faɗa tana musu nuni da ɓangarenta sannan ta hau ƙwalawa wasu daga cikin ƙawayenta ta ce su karɓa su saka a frige har tana musu tsiya wai sun zauna a ɗaki ba za su fito su yi aikin abincin ba. Suna faɗin sai sun ci wani abu hakan ne ya ankarar da saƙon su da Nasir ya bari a mota. Yana zuwa gaban Hajiya ya sassauta murya ya ce "Hajiya kin ga ƙafarki kuwa?" Hajiya wacce duk takaici ya ishe ta ta san Nasir da izza da nuna isa a kan Sadiya amma yau ta ga ya zama kamar wani sauna sai abin da aka ce masa. Sadiyar da ko kuɗin magani ba a bata idan bata da lafiya haka ma idan Kalifan bashi da lafiya suna idon a bata kuɗi duk ƙanƙantarsa sai gashi wata ta zo rana tsaka za ta kawo wargi a lamarin aljihun Nasir ɗin duba da yadda ya siyo komai da aka faɗa babu musu. Tana ganin yadda ta yi masanyan yakalmi kuma ba ƙafafun bane sai ta juya da sauri don kar a lura bata san Sadiya ta gani ba hatta Meenal ma ta gani kawai dai ta ce a zuciyarta 'Kaɗan kika gani wallahi mu zuba mu gani' Nasir kuma kafin Hajiya ta ɗakko takalmin ya juya ya fita matasan yaran nan suna biye da shi da suka fita ya basu ɗari biyu su raba, bayan motar ya buɗe ya ɗakko manyan ledojin da aka yi take away na snacks da drinks masu sanyi haka ya shigo gidan da ledojin riƙi-,riƙi. Meenal ganin Sadiya ta baro wajen famfo sai ta aikawa Sadiya harara kuma Sadiyar ta gani amma ta yi kamar bata gani ba Meenal kuma a zuciyarta ta ce 'Ina nan zuwa kanki kema' Hajiya kuma tana sako takalmi ta ga babu Nasir kafin ta gama tambayar kanta ina yake sai gashi ya shigo da ledojin wannan Meenal ta nufi inda yake ta tare shi tana aika masa sannu, haɗe da miƙa hannu ta maƙalo bayansa suke tafiya inda shi kuma yake ta kaucewa alamar kunyar Hajiya amma Meenal ta ƙi sakin sa har da saka ɗaya hannunta ta sumbaci hannun nata ta kai masa saman nasa bakin. Hajiya kallo ɗaya ta musu ranta ya ɓaci ga ƴanmatan nan su Safiyya a kicin sai ƙaran kwanuka take ji alamar hada-hadar girki waau suna yayyakan kabeji so take ta ce masa ya yi taka-tsan tsan da mukullinsa sannan ya matse hannu da aljihu amma kuma ta kasa tsayawa saboda yadda Meenal ta ƙaƙabe masa. Hanyar waje ta yi tana faɗin "Nasir ka zo waje ina son ganinka" Sadiya da tun da ta koma ɗaki ta laɓe a labule tana kallon dirama, komawa kan kujera ta yi ta kwanta tana ta dariya Kalifa yana taya ta duk da bai san dariyar mene ne take yi ba. Meenal tana ganin Hajiya ta fita ra sake shi, ta karɓi kayan sai kuma ya juya ya fita don amsa kiran Hajiya, ko da ya zo ƙofar gidan ya same ta tsaye tana riƙe da ƙugu ga kuma jaka a rataye sai kai komo take bata ma san ya zo wajen ba sai da ya kira sunanta da sauri ta waigo tana faɗin "Nasir mu shiga cikin mota maganar nan ba ƙarama ba ce akwai gagarumar matsala don da alama abubuwa sabbi za su kunno cikin rayuwarmu da muke lallaɓawa" Ta faɗa bata jira cewarsa ba ta buɗe gaban motar ta shige cike da rashin fahimta ya shiga mazaunin direba tun bai gama zama ba ta shiga faɗin ya rufe ƙofa rufewa ya yi sai kuma ta ce "Nasir akwai matsala wallahi" Cike da faɗuwar gaba ya ce "Allah ka mana maganin matsala, Hajiya matsalar mene ne?" Idanunta da suka kaɗa suka yi jawur saboda ɓacin ran abubuwan bazatan da ta ƙunsa daga Meenal ta ce "Nasir Meenal ce matsala" Cike da rashin fahimta ya ce "Meenal kuma?" Hajiya a faɗa ce ta ce "Meenal mana bari na faɗa maka abin da baka sani ba tana cikin hayyacinta babu wani jifanta da aka yi ta tabbatar min da hakan da bakinta da alama yarinyar nan zaɓen tumun dare muka yi Nasir wallahi bata da ƙudurin sa ya wuce ta rusa mu ta faraƙa mana dangi, ka ga kai kaɗai ne gatanmu ni da marayun Allahn nan su Husna yanzu wannan yadda daga juya zuwa yau take saka ka ɓarin kuɗi kuma Nasir ko musu baka yi duk abin da ta lissafa sai ka siyo sannan uwa uba ka ɗauki mukullin store ka bata" Ɗan dimmm ya yi sai kuma kafin ya ce wani abu ta ce "Wallahi so take ta mallake ka ka fi ƙarfina ta mamaye gidan nan don haka dole ka tashi tsaye ka zama namiji ka matse bakin aljihu ka ƙwace mukullin store karka sake bata ita ma kake tsakura mata abincin kamar yadda kake tsakurawa Sadiya wallahi da ni take zancen dankalin ma an fasa aiko mata can za kake zuwa kana ci kamar yadda ake yi wa Sadiya kuma a gobe ba sai jibi ba Meenal za ta fara ɗora tukunyar tuwo, kuma gawayi za take hurawa wannan gas ɗin dole a kai min gidana ko ka je ka aiyar da shi amma ba a gidan ɗana ba" Tun da ta fara maganar yake kallonta ya mayar da hankali kanta yana sauraro da nazarin ta inda zai fara wannan gagarumin faɗan da take son kwasowa don ya lura Meenal ba kanwar lasa bace kuma ba za ta lamunci wannan abubuwan da aka zana ba kenan da sauran rina a kaba. Baki ya buɗe zai yi magana sai dai ƙaran ƙwanƙwasa ƙofa da aka yi shi ya dakatar da shi daga furta komai, daga shi har Hajiya suka juyo don ganin mai bugawa sai dai wanda suka gani tsaye ya basu mamaki ba kowa ba ne illa Meenal da take tsaye riƙe da tsantsa hannunta ɗaya riƙe da wani ƙaton kwando, ganin sun maido da kallonsu kanta ta saka hannu ta buɗe ɓangaren da Hajiya take haɗe rai ta yi ta ce "Na gama jin duk abin da kuka ce dama tun da na ga kin ce ku je wajw kuma na san halinki shi ya sa ban yi ƙasa a gwiwa ba na biyo bayanku na laɓe a zaure ina kallonku ta jikin tular ƙofa, kuna shigewa na zo jikin ƙofar na tsaya amma kasancewar hankalinku ba ya wajena babu wanda ya ganni har na koma na ɗakko kwando na dawo, don haka abin da nake so da ke Hajiya ki dakata da wannan faɗan don wallahi ba za ki iya ba, kuma ba za ki ci gabala ba kawai ki sakar mini" Hajiya baki sake take kallon Nasir ganin bai yi kataɓus ba wajen tsawatarwa Meenal a zafafe ta ce "Nasir ya ka tsaya kamar sauna kana jin abin da ta ce?" Kafin Nasir ya ce wani abu Meenal ta ce "Ina shawartarki Hajiya da ki cire ido da hannunki a gidan ɗanki shi ne kima da mutuncinki don wallahi ko ana mutuwa ana falkowa ba zan taɓa ɗora girki a gawayi ba, sannan mukullin store daga yau ya bar hannun Nasir in kin ga ya taɓa mukullin store to tabbas kayan abinci ya siyo za a saka a ciki, abu na gaba ba uwar miji yanzu babu ruwanki da aljihun ɗanki a kan lamarin gidansa tun da matar mutum ita take ɗauke ɗawainiyarsa ta cikin dare don haka ta cancanci a mata komai shin in ba matarsa ba waye zai ɗauke masa wannan ɗawainiyar? Don haka ni nake kwana da miji kuma ni zan yi iko da abina ba wai a mini iko da shi ba ikonki ya tsaya iya ke da shi... Hajiya ta hankaɗa ƙofar ta sako ƙafa waje tana nuna Meenal da yatsa ta ce "Wallahi ƙaryar rashin kunya kike da a ce na san haka kike da Nasir bai aure ki ba" Meenal ta ce "Daga baya kenan wai an yi sadaka da karuwa, to ai duk ɗaya an ce da karuwa hayo gado yanzu ma lokaci bai ƙurw miki ba za ki iya saka ya warware igiyar" Nasir da ya buɗe baki zai yi magana sai ya ji kansa ya sara hakan ta sa ya zuba musu na mujiya, domin cikin maganin da ta saka da dare har da mallaka ciki. Hajiya ta ce "Daga na gidan uwarki zan je, in mata bayanin yadda kika sauya halinki a kwana ɗaya, ai ni ƙawar uwarki ce ko wannan kaɗai kya duba" Meenak ta ce "Ai in dai tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ke baki duba dangantakar ba kike mini taka haye?" Tsaki kawai Hajiya ta yi don ta hango yadda za ta magance wannan matsalar Meenal kuma ta rausayar da kai tare da zumɓura baki tana wani shagwaɓe fuska cikin muryar ɓaci ta ce "Zumana wannan kwandon gidan Hajiya za ka kaini zan kwaso dankali, su Safiyya suna son sakawa a miya ƙwan ma za su yi amfani da shi, ka ga sai a kwaso kayan duka in ya so gobe in za a yi break fast ɗin sai su Husna su zo su yi in ɗauka musu na Hajiya ka ga ni ba zan iya aiki ba jikina ciwo yake" Ta faɗa tana yin farrr da idanu, Hajiya tsabar mamaki na ganin Meenal ko kunyarta bata ji ya sa ta kasa magana, da sauri ta juya don ta ga abin da Nasir ya yi kawai sai ta ga ya saki baki yana murmusawa. Kafin ta ce wani abu Meenal ta ce "Hajiya ɗan koma baya ni sai na shiga gaban, kin san masoya sabbin ma,aurata, ko kuma ya tare miki napep" Kakaraf Hajiya ta ƙarasa hankaɗa ƙofar har ra buga jikin kwandon hannun Meenal don ta ga kamar kare ya ɗauke zuciyar Nasir hakan na tavbatar mata da cewa za su shiga tsaka mai wuya dole ta magance matsalar nan da kanta don ita bata taɓa jin amarya a ranar farko tana fita daga gidan miji ba. Tana fitowa daga motar ta ce "Allah tsine soyayya, ni za ki gwadawa bariki, tattabaru kuke ƙarewa aure" Ta faɗa tana ɗaga hannu za ta zabgawa Meenal mari. ALIYA Aliya gabanta yana faɗuwa a lokacin da kiran yake shiga tana fatan ya ɗauka kar ya kawo mata matsala domin zuciyarta ta kwaɗaitu da son jin muryarsa, ta yi kewar ganinsa bata san ma haka take ƙaunarsa ba sai yanzu da suka yi nesa da juna, tun da ta san tun da ya fara zuwa wajen Jidda in har ya zo tana ganinsa amma yanzu tun da ya ɗauke Jidda ai kuma babu inda za take ganinsa abin haushin ma ko hotonsa bata da shi, rabon da ta sanya shi a ido tun ranar da suka kai Jidda gidanta da ta yi ido huɗu da hotonsa a falo. Sai dai har kiran ya tsinke bai ɗauka ba dama shi ba ma,abocin ɗaukan kiran baƙuwar lamba ba ne. Tun da kiran ya katse ta zurawa wayar idanu tana ta kallin numbersa tamkar dai tana ƙidaya yawan lambobin ne duk da ta san lambobin Nigeri,a basa wuce guda goma sha ɗaya, amma sai ta ji tana tantamar ko dai ba daidai ta kwafi lambar ba, sai dai kuma tun da tana shiga daidai ce wataƙila bai ga damar ɗauka ba ne. Kiran ta sake yi a karo na biyu, ɗan tsaki ya yi kiran yana shirin tsinkewa ya ɗauka tare da kara wayar a kaunnensa, tana tuƙi a hankali da hannu ɗayan. Sallama ya yi da kyakkyawar muryarsa mai sanyi da ratsa dodon kunnen mai sauraro musamman Aliya da take jin ta yi kewarsa tamkar wanda ta shekara bata ji muryarsa ba, domin ta saba ko da wucewa za ta yi ta ji muryarsa yana magana da Jidda, ita bata ma ƙara sanin zuciyarta ta damu da Ibrahim ba sai da ta yi nesa da shi, tabbas tana son abu guda biyu daga gare shi wanda au ne suka kai zuxiyarta ga wannan ɓigiren. Abu na farko dai dukiyarsa ita ce a farko sannan kuma sai son sa da take yi tana jin ko za a raba ta da numfashinta sai ta auri Ibrahim sai dai Jidda ta yi gawa!. Jin muryarsa ya sa ta lumshe idanu tana jin muryar har ƙoƙon ranta, ji take dama ya yi ta magana tana sauraronsa. Shi kuma jin ba a amsa sallamar ba sai ransa ya ɓaci ya tsani a kira shi a waya kuma a yi shiru. Ita kuma ta sha,afa ma da cewar ita za ta amsa sallamar da ya yi. Ɗan gyaran murya ta yi ta amsa da wata murya da babu wanda zai gane muryarta ce. Tana tunanin abin faɗi ta ji ya ce "Wa ke magana?" Sai lokacin ta fara tunanin faɗin "Sunana Surayya dama na samu numberka ne a wayar yayana ina so za muke gaisawa" Da mamaki ya ce "What?" Wani yawu ta haɗiye jin ya yi magana cikin hargagi. Cike da sassauta murya yadda zai ji tausayinta ta ce "Idan hakan laifi ne Allah ya baka haƙuri na yi kuskure" Ta faɗa tana jiran jin ko zai sassauto, shi kuma ba tare sa ya san wane abokin nasa ba kawai sai ta jo ya yanke kiran. Lokacin ta ƙaraso saitin gidansa ya shiga yin horn mai gadi ya buɗe masa. Hancin motar ya danna a cikin get ɗin kafin ya ƙarasa parking space ya ajiye motar ya fito yana riƙe da ledar da ya siyo mata ice cream da wayoyinsa ya nufi ciki. Ko da ya shigo falon bata nan sai karatun qur,ani da yake tashi a wayarta sai kuma ƙamshin turare, duk ɗakunan ya duba bai ganta ba, sai kuma ya haura sama yana zuwa ya tura ƙofar ɗakinsa a can ya same ta bayan ya shiga da sallama ta amsa masa cike da fara,a tana takowa gabansa bayan ta ajiye filon hannunta da take sauya masa riga dama bedsheet ta zo canjawa a gadon. Kallonta yake yana murmushi wanda ita ma murmushin take, hannunsa ya saƙalo a ƙugunta bayan ta karɓi ledar hannunsa, bakinn gadon suka ƙarasa ya zauna tare da ajiye wayoyinsa sannan ya zaunar da ita a kan ƙafafunsa yana lakato hancinta ya ce "Sarkin aiki wato kece agogo sarkin aiki ko Jiddana" Ya faɗa yana haɗa hannayenta waje guda. Tana ƴar dariya ta ce "Ni babu wani aiki fa" Ya ce "Wannan mene ne kike yi?" Ta kalli gadon da ya nuna mata tana ganin yadda ta ɗame gadon tamkar wanda ko an zauna shimfiɗar ba za ta ɓaci ba, a taƙaice ba za ma ka ce hannu ne ya yi shimfiɗar ba. Ɗan murmushi ta yi ta ce "Ni fa ba na jin daɗi in zauna ba na yinw wani abu, sai ma in ke jin duk jikina babu daɗi na saba in yi aiki" Hannunsa ya kai ya haɗa leɓɓan nata waje guda ya riƙe don kar ya bata damar magana ya ce "Nan gidan hutunki ne Jidda ba a so ki wahala ba a so ki yi komai, ni zama a cikin gidana ma da aurena da kika yi Jidda wallahi sai in ke ganin kamar alfarma kika min, kin min komai a rayuwa Jidda da kika auren wani lokacin sai innke rasa da mai zan saka miki?" Duk da bakin nata da ya rufe hakan bai hana aka ji sautin dariyar da take yi ba. Bai sakar mata bakin ba ya ce "Kin gama min komai a rayuwa, ni kuma zan yi iya yi na don na faranta miki da kuma yaƙi da duk wanda zai baƙanta miki.. Ƙaran wayarsa ne ya katse musu magana, bai kalli wayar ba har kiran ya katse hankalinsa yana kan Jidda. Sai da wani kiran ya shigo yana waiwayawa ya ga Mummy bakin Jiddan ya saki ya ɗakko wayar ya kara a kunne tun kafin ya yi magana Mummy ta ce "Ina ƴata?" Dariya ya fashe da ita sosai ya ce "Wai Mummy ni ɗin yayeni kika yi, wai kawai yanzu in kika kira waya sai ki ce ina ƴarki gaskiya ina kishi" Ya faɗa lokacin da ya saka handsfree Jidda da take musu dariya ta cigaba da sauraron abin da Mummy take cewa "Ni ai yanzu babu ruwana da kai na yi ƴa ka san idan aka yi sabon sarki mai za a yi da murabus" Baki ya zumɓura jin rana batun ya ba Jidda wayar. Miƙa mata ya yi bayan ya sakar mata hannu, tana kara wayar ta shiga gaishe da Mummy cike da girmamawa tana ɗan rusuna kai, Mummy ta amsa tana tambayarta ina wayarta sau biyu ta kira ba a ɗauka ba nan ta sanar mata ta bsr wayar a falon ƙasa. Mummy ta shiga faɗa mata ta kira ta ne don ta ji lafiyarta, inda har lokacin bakin Ibrahim a zumɓure kamar bakin jaɓa shi a dole fushi ya yi an daina sonsa sai Jidda kaɗai. Da gayya ya saka hannu ya yi wa Jidda cakulkuli a cikinta inda dariya ta so ƙwace mata ita kuma take yaƙi da dariyar don kar ta yi Mummy ta ji. Suna yin sallama Mummy ta kashe tana batun gobe masu aiki za su zo. Tana kashe wayar ta shiga asa kalamai tana lallaɓa shi da yaƙi lallashin ta shiga masa gwalo tana tsokanarsa suka shiga kewaya ɗakin yana binta zai kamo ta, wai sai ya ga mai ƙwatarta a daren yau. Sun daɗe suna wasan cike da soyayya kafin ta ɗakko ledar ice cream ɗin ta sakko ƙasa za ta saka a frige ɗin ƙasa. Tana tsaye gaban frige ya sakko hannunsa da wayoyi ya ce "Sai ki bar waya take ta yi, bayan ke bakya falon bare a ce sauraron karatub kike" Sai da ta kashe karatun bayan ta rufe frige ɗin, gudun kar suke magana karatun yana yi sannan ta ce "Ai karatu ba sai mutum yana waje ba, a haka ma zai ke kore shaiɗanu" Yana shirin bata amsa wayarsa ɗaya ta shiga ruri yana dubawa ya ga wannan number ta ɗazu wani tsaki ya doka ba tare da ya ɗauki wayar ba har kiran ya katse, ita kuma Jidda ko a jikinta don ita a tsarinta babu ruwanta da uzurin miji ko saka masa ido a lamuransa. Aliya kuma tun lokacin da ya kashe sai da ta ji kamar ta yi kuka, a ranta tana raya cewa wataƙila yana tare da wannan baƙar mummunar matar tasa wacce take saka rai nan gaba kaɗan za ta maida rayuwarta a gidan ta zama tarihi ita kuma ta zama mamallakiyar gidan da mai gidan, idan ma bata jera da ita zaman kishin ba don ta gasa mata aya a hannu sannan ta mata gashin ƙuma wanda da ƙafafunta za ta bar gidan, fatan ta dai kar rabo ya shiga tsakanin Jidda da Ibrahim din ta fi so ita kaɗai ce za ta haifa masa ƴaƴa yadda za su ci gadon dukiya a daidai!. Ko da ta ɗauki lokaci ma jira take a jima ne ta ƙara kiransa sai dai kuma rashin sa'ar da ta yi ya sa ranta ya ɓaci na ƙin ɗaga kiran da ya yi, sai dai ta yi alƙawarin da sannu zai dawo tafin hannunta ta yadda wurin zama ma sai an nuna masa zai zauna. Washe gari ta sake gwada sa,arta amma sai bai ɗauka ba, hakan ya sa ta yanke hukuncin buɗe whatsapp ɗin da ta buɗe da sabuwar lambar ta rattaba masa sallama, da kuma gaisuwa tana masa fatan alkairi cikin kalamai na jan hankali, sai dai wuni guda curr bai mata replay ba ita kuma daga an ɗauki ƴan mintina sai ta tura mata hoton emoji na yatsa manuniya alamar tana masa nuni da saƙon da ta tura masa, ta tura masa yatsa ya fi sau goma amma Ibrahim bai mata replay ba kuma tana ganinsa online don saƙon ma ya yi tik biyu alamar an isar masa buɗewa ne kawai bai yi ba. Ganin haka sai ta yi wa Jidda magana da sabuwar lambar ta whatsapp ta farfaɗa mata maganganu baƙaƙe. Bayan wata guda ta rasa mafita hakan ya sa suka yi shawara da ita da Amatullahi, ai kuwa Amatullahi ta ce "Rabu da ɗan iska in laila ta ƙiya sai a koma caca, mu zai yi wa tashin balagar tsintsaye wallahi ya yi kaɗan sai kina mallake shi ƙawata" Amatullahi ta faɗa tana nuna mata daga sun samu kan Naair sai ta kashe aurenta, ita kuma Aliya daɗin shawarar ta ji bata san cewa Amatullahi tana baƙin cikin Aliya ta yi aure ta barta tana gararamba a layi ba, so take ta kashe auren ta zama bazawara su dawo suke yawo a layin tare domin a hankalce ta san Ibrahim ba zai aure ta ba. Sun shirya ƙarya ita da Amatullahi don haka ta sanar da Kasim cewa za su je duba babar ƙawarsu, shi kuma da yake dama yanzu lallaɓata yake sai hakanya masa daɗi ganin an tambaye shi neman izini. Wajen sha ɗaya na safe suka tafi a napep suka tafi suka je tasha suka hau mota a bakin titi ta ajiye su suka ƙarasa shiga surƙuƙin dajin a ƙafa. Ko da suka ƙarasa wani ɗakin kara ne a dokar dajin a gindin wata bishiya hakan ya sa suka nufi wajen don Amatullahi ta ce ƙawarta ce ta rako wajen aiki take kamar yankan wuƙa don bokanya ce ba boka ba ne ma. Tun kan su ƙarasa ciki ɗakin bukkar da yake kewaye da kara sai jikin Aliya ya fara karkarwa amma Amatullahi ta harare ta tana nuna mata cewa ranar biyan buƙata rai ba a bakin koma yake ba. An sanar da su su cire takalmi sannan da baya -baya za su shiga sainda suka shiga saura kaɗan Aliya ta taka faifan gaban bokanya mai ɗauke da ƙasa a ka tsawar da aka mata ta matsa gaba da sauri sai da ta musu umarnin juyowa sannan suka juya suka zauna. Kafin su fara bayani ta sanar da su ta san da abin da suke tafe, Aliya sai kallon baƙar matar take wacce babu alamun ɗigon imani a wajenta nan ta ce "Zan yi miki aiki kuma za a samu biyan buƙata idan har buƙata bata biya ba to ba daga garemu ba ne kin saɓa lamba ne, amma matuƙar kika yi yadda na ce to an wuce wajen" Kai Aliya take kaɗawa kamar ƙadangaruwa sannan sai bokanya ta ce "Za ki kawo mini cokalin da yake cin abinci da shi a jikin cokalin zan yi aikin, sai kuma ki mayar da cokali a tabbatar ya ci abinci da shi idan haka ta faru to ƙurunƙussss!. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Amatullahi da Aliya jin wata gadar zare da aka musu, ita Aliya tunanin da ta farw ta yaya za ta gane cokalin da yakencin abinci sannan har ta mayar ta tabbatar ya ci abinci wannan ai abu ne mai wahala tana cikin wannan maganar muryar bokanya ta katse ta da faɗin "Ba ma magana a musa mana, komai muka faɗa sai an aikata in ba haka ba akwai yiwuwar ciwon hauka ga mutumin da ya zo neman taimako wajenmu kuma bai yi abin da aka ce ba" Didididiiimmmm gaban Aliya ya buga da ƙarfi idanunta suka ciko da ƙwalla. MAMAN AFRAH 0902557622ALIYA Aliya gabanta yana faɗuwa a lokacin da kiran yake shiga tana fatan ya ɗauka kar ya kawo mata matsala domin zuciyarta ta kwaɗaitu da son jin muryarsa, ta yi kewar ganinsa bata san ma haka take ƙaunarsa ba sai yanzu da suka yi nesa da juna, tun da ta san tun da ya fara zuwa wajen Jidda in har ya zo tana ganinsa amma yanzu tun da ya ɗauke Jidda ai kuma babu inda za take ganinsa abin haushin ma ko hotonsa bata da shi, rabon da ta sanya shi a ido tun ranar da suka kai Jidda gidanta da ta yi ido huɗu da hotonsa a falo. Sai dai har kiran ya tsinke bai ɗauka ba dama shi ba ma,abocin ɗaukan kiran baƙuwar lamba ba ne. Tun da kiran ya katse ta zurawa wayar idanu tana ta kallin numbersa tamkar dai tana ƙidaya yawan lambobin ne duk da ta san lambobin Nigeri,a basa wuce guda goma sha ɗaya, amma sai ta ji tana tantamar ko dai ba daidai ta kwafi lambar ba, sai dai kuma tun da tana shiga daidai ce wataƙila bai ga damar ɗauka ba ne. Kiran ta sake yi a karo na biyu, ɗan tsaki ya yi kiran yana shirin tsinkewa ya ɗauka tare da kara wayar a kaunnensa, tana tuƙi a hankali da hannu ɗayan. Sallama ya yi da kyakkyawar muryarsa mai sanyi da ratsa dodon kunnen mai sauraro musamman Aliya da take jin ta yi kewarsa tamkar wanda ta shekara bata ji muryarsa ba, domin ta saba ko da wucewa za ta yi ta ji muryarsa yana magana da Jidda, ita bata ma ƙara sanin zuciyarta ta damu da Ibrahim ba sai da ta yi nesa da shi, tabbas tana son abu guda biyu daga gare shi wanda au ne suka kai zuxiyarta ga wannan ɓigiren. Abu na farko dai dukiyarsa ita ce a farko sannan kuma sai son sa da take yi tana jin ko za a raba ta da numfashinta sai ta auri Ibrahim sai dai Jidda ta yi gawa!. Jin muryarsa ya sa ta lumshe idanu tana jin muryar har ƙoƙon ranta, ji take dama ya yi ta magana tana sauraronsa. Shi kuma jin ba a amsa sallamar ba sai ransa ya ɓaci ya tsani a kira shi a waya kuma a yi shiru. Ita kuma ta sha,afa ma da cewar ita za ta amsa sallamar da ya yi. Ɗan gyaran murya ta yi ta amsa da wata murya da babu wanda zai gane muryarta ce. Tana tunanin abin faɗi ta ji ya ce "Wa ke magana?" Sai lokacin ta fara tunanin faɗin "Sunana Surayya dama na samu numberka ne a wayar yayana ina so za muke gaisawa" Da mamaki ya ce "What?" Wani yawu ta haɗiye jin ya yi magana cikin hargagi. Cike da sassauta murya yadda zai ji tausayinta ta ce "Idan hakan laifi ne Allah ya baka haƙuri na yi kuskure" Ta faɗa tana jiran jin ko zai sassauto, shi kuma ba tare sa ya san wane abokin nasa ba kawai sai ta jo ya yanke kiran. Lokacin ta ƙaraso saitin gidansa ya shiga yin horn mai gadi ya buɗe masa. Hancin motar ya danna a cikin get ɗin kafin ya ƙarasa parking space ya ajiye motar ya fito yana riƙe da ledar da ya siyo mata ice cream da wayoyinsa ya nufi ciki. Ko da ya shigo falon bata nan sai karatun qur,ani da yake tashi a wayarta sai kuma ƙamshin turare, duk ɗakunan ya duba bai ganta ba, sai kuma ya haura sama yana zuwa ya tura ƙofar ɗakinsa a can ya same ta bayan ya shiga da sallama ta amsa masa cike da fara,a tana takowa gabansa bayan ta ajiye filon hannunta da take sauya masa riga dama bedsheet ta zo canjawa a gadon. Kallonta yake yana murmushi wanda ita ma murmushin take, hannunsa ya saƙalo a ƙugunta bayan ta karɓi ledar hannunsa, bakinn gadon suka ƙarasa ya zauna tare da ajiye wayoyinsa sannan ya zaunar da ita a kan ƙafafunsa yana lakato hancinta ya ce "Sarkin aiki wato kece agogo sarkin aiki ko Jiddana" Ya faɗa yana haɗa hannayenta waje guda. Tana ƴar dariya ta ce "Ni babu wani aiki fa" Ya ce "Wannan mene ne kike yi?" Ta kalli gadon da ya nuna mata tana ganin yadda ta ɗame gadon tamkar wanda ko an zauna shimfiɗar ba za ta ɓaci ba, a taƙaice ba za ma ka ce hannu ne ya yi shimfiɗar ba. Ɗan murmushi ta yi ta ce "Ni fa ba na jin daɗi in zauna ba na yinw wani abu, sai ma in ke jin duk jikina babu daɗi na saba in yi aiki" Hannunsa ya kai ya haɗa leɓɓan nata waje guda ya riƙe don kar ya bata damar magana ya ce "Nan gidan hutunki ne Jidda ba a so ki wahala ba a so ki yi komai, ni zama a cikin gidana ma da aurena da kika yi Jidda wallahi sai in ke ganin kamar alfarma kika min, kin min komai a rayuwa Jidda da kika auren wani lokacin sai innke rasa da mai zan saka miki?" Duk da bakin nata da ya rufe hakan bai hana aka ji sautin dariyar da take yi ba. Bai sakar mata bakin ba ya ce "Kin gama min komai a rayuwa, ni kuma zan yi iya yi na don na faranta miki da kuma yaƙi da duk wanda zai baƙanta miki.. Ƙaran wayarsa ne ya katse musu magana, bai kalli wayar ba har kiran ya katse hankalinsa yana kan Jidda. Sai da wani kiran ya shigo yana waiwayawa ya ga Mummy bakin Jiddan ya saki ya ɗakko wayar ya kara a kunne tun kafin ya yi magana Mummy ta ce "Ina ƴata?" Dariya ya fashe da ita sosai ya ce "Wai Mummy ni ɗin yayeni kika yi, wai kawai yanzu in kika kira waya sai ki ce ina ƴarki gaskiya ina kishi" Ya faɗa lokacin da ya saka handsfree Jidda da take musu dariya ta cigaba da sauraron abin da Mummy take cewa "Ni ai yanzu babu ruwana da kai na yi ƴa ka san idan aka yi sabon sarki mai za a yi da murabus" Baki ya zumɓura jin rana batun ya ba Jidda wayar. Miƙa mata ya yi bayan ya sakar mata hannu, tana kara wayar ta shiga gaishe da Mummy cike da girmamawa tana ɗan rusuna kai, Mummy ta amsa tana tambayarta ina wayarta sau biyu ta kira ba a ɗauka ba nan ta sanar mata ta bsr wayar a falon ƙasa. Mummy ta shiga faɗa mata ta kira ta ne don ta ji lafiyarta, inda har lokacin bakin Ibrahim a zumɓure kamar bakin jaɓa shi a dole fushi ya yi an daina sonsa sai Jidda kaɗai. Da gayya ya saka hannu ya yi wa Jidda cakulkuli a cikinta inda dariya ta so ƙwace mata ita kuma take yaƙi da dariyar don kar ta yi Mummy ta ji. Suna yin sallama Mummy ta kashe tana batun gobe masu aiki za su zo. Tana kashe wayar ta shiga asa kalamai tana lallaɓa shi da yaƙi lallashin ta shiga masa gwalo tana tsokanarsa suka shiga kewaya ɗakin yana binta zai kamo ta, wai sai ya ga mai ƙwatarta a daren yau. Sun daɗe suna wasan cike da soyayya kafin ta ɗakko ledar ice cream ɗin ta sakko ƙasa za ta saka a frige ɗin ƙasa. Tana tsaye gaban frige ya sakko hannunsa da wayoyi ya ce "Sai ki bar waya take ta yi, bayan ke bakya falon bare a ce sauraron karatub kike" Sai da ta kashe karatun bayan ta rufe frige ɗin, gudun kar suke magana karatun yana yi sannan ta ce "Ai karatu ba sai mutum yana waje ba, a haka ma zai ke kore shaiɗanu" Yana shirin bata amsa wayarsa ɗaya ta shiga ruri yana dubawa ya ga wannan number ta ɗazu wani tsaki ya doka ba tare da ya ɗauki wayar ba har kiran ya katse, ita kuma Jidda ko a jikinta don ita a tsarinta babu ruwanta da uzurin miji ko saka masa ido a lamuransa. Aliya kuma tun lokacin da ya kashe sai da ta ji kamar ta yi kuka, a ranta tana raya cewa wataƙila yana tare da wannan baƙar mummunar matar tasa wacce take saka rai nan gaba kaɗan za ta maida rayuwarta a gidan ta zama tarihi ita kuma ta zama mamallakiyar gidan da mai gidan, idan ma bata jera da ita zaman kishin ba don ta gasa mata aya a hannu sannan ta mata gashin ƙuma wanda da ƙafafunta za ta bar gidan, fatan ta dai kar rabo ya shiga tsakanin Jidda da Ibrahim din ta fi so ita kaɗai ce za ta haifa masa ƴaƴa yadda za su ci gadon dukiya a daidai!. Ko da ta ɗauki lokaci ma jira take a jima ne ta ƙara kiransa sai dai kuma rashin sa'ar da ta yi ya sa ranta ya ɓaci na ƙin ɗaga kiran da ya yi, sai dai ta yi alƙawarin da sannu zai dawo tafin hannunta ta yadda wurin zama ma sai an nuna masa zai zauna. Washe gari ta sake gwada sa,arta amma sai bai ɗauka ba, hakan ya sa ta yanke hukuncin buɗe whatsapp ɗin da ta buɗe da sabuwar lambar ta rattaba masa sallama, da kuma gaisuwa tana masa fatan alkairi cikin kalamai na jan hankali, sai dai wuni guda curr bai mata replay ba ita kuma daga an ɗauki ƴan mintina sai ta tura mata hoton emoji na yatsa manuniya alamar tana masa nuni da saƙon da ta tura masa, ta tura masa yatsa ya fi sau goma amma Ibrahim bai mata replay ba kuma tana ganinsa online don saƙon ma ya yi tik biyu alamar an isar masa buɗewa ne kawai bai yi ba. Ganin haka sai ta yi wa Jidda magana da sabuwar lambar ta whatsapp ta farfaɗa mata maganganu baƙaƙe. Bayan wata guda ta rasa mafita hakan ya sa suka yi shawara da ita da Amatullahi, ai kuwa Amatullahi ta ce "Rabu da ɗan iska in laila ta ƙiya sai a koma caca, mu zai yi wa tashin balagar tsintsaye wallahi ya yi kaɗan sai kina mallake shi ƙawata" Amatullahi ta faɗa tana nuna mata daga sun samu kan Naair sai ta kashe aurenta, ita kuma Aliya daɗin shawarar ta ji bata san cewa Amatullahi tana baƙin cikin Aliya ta yi aure ta barta tana gararamba a layi ba, so take ta kashe auren ta zama bazawara su dawo suke yawo a layin tare domin a hankalce ta san Ibrahim ba zai aure ta ba. Sun shirya ƙarya ita da Amatullahi don haka ta sanar da Kasim cewa za su je duba babar ƙawarsu, shi kuma da yake dama yanzu lallaɓata yake sai hakanya masa daɗi ganin an tambaye shi neman izini. Wajen sha ɗaya na safe suka tafi a napep suka tafi suka je tasha suka hau mota a bakin titi ta ajiye su suka ƙarasa shiga surƙuƙin dajin a ƙafa. Ko da suka ƙarasa wani ɗakin kara ne a dokar dajin a gindin wata bishiya hakan ya sa suka nufi wajen don Amatullahi ta ce ƙawarta ce ta rako wajen aiki take kamar yankan wuƙa don bokanya ce ba boka ba ne ma. Tun kan su ƙarasa ciki ɗakin bukkar da yake kewaye da kara sai jikin Aliya ya fara karkarwa amma Amatullahi ta harare ta tana nuna mata cewa ranar biyan buƙata rai ba a bakin koma yake ba. An sanar da su su cire takalmi sannan da baya -baya za su shiga sainda suka shiga saura kaɗan Aliya ta taka faifan gaban bokanya mai ɗauke da ƙasa a ka tsawar da aka mata ta matsa gaba da sauri sai da ta musu umarnin juyowa sannan suka juya suka zauna. Kafin su fara bayani ta sanar da su ta san da abin da suke tafe, Aliya sai kallon baƙar matar take wacce babu alamun ɗigon imani a wajenta nan ta ce "Zan yi miki aiki kuma za a samu biyan buƙata idan har buƙata bata biya ba to ba daga garemu ba ne kin saɓa lamba ne, amma matuƙar kika yi yadda na ce to an wuce wajen" Kai Aliya take kaɗawa kamar ƙadangaruwa sannan sai bokanya ta ce "Za ki kawo mini cokalin da yake cin abinci da shi a jikin cokalin zan yi aikin, sai kuma ki mayar da cokali a tabbatar ya ci abinci da shi idan haka ta faru to ƙurunƙussss!. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Amatullahi da Aliya jin wata gadar zare da aka musu, ita Aliya tunanin da ta farw ta yaya za ta gane cokalin da yakencin abinci sannan har ta mayar ta tabbatar ya ci abinci wannan ai abu ne mai wahala tana cikin wannan maganar muryar bokanya ta katse ta da faɗin "Ba ma magana a musa mana, komai muka faɗa sai an aikata in ba haka ba akwai yiwuwar ciwon hauka ga mutumin da ya zo neman taimako wajenmu kuma bai yi abin da aka ce ba" Didididiiimmmm gaban Aliya ya buga da ƙarfi idanunta suka ciko da ƙwalla. MAMAN AFRAH 0902557622 https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE2️⃣1️⃣ MEENAL Rai a ɓace ta saka hannunta ta riƙe hannun Hajiya wanda takaici ya sa Hajiya ta fashe da kukan takaici bata taɓa zaton akwai irin wannan tanar da har matar ɗanta za ta riƙe mata hannu ba. Nasir da sauri ya fito daga motar ya nufi su yana faɗin "Meenal ki saka mata hannu" Haka Meenal maimakon ta saki hannun sai ta warɓar da hannun, ita kuma Hajiya sai ta fara tunanin tun da har Meenal ta iya riƙe mata hannu ta warɓar da alama ko marin nata ta yi ba za ta ajiye hannunta ba za ta rama. Faɗa Hajiya take yi kamar za ta ari baki sai Meenal ta kalle ta ta ce "Hajiya da kin adana kalamanki wataƙila nan gaba za su miki amfani, don yanzu aka fara wasan, sannan ki mayar da wuƙar ni ba zuwa gidan ki zan yi ɗaukan dankali ba, amma ki sani ɗan naki dai da bakya so a ɓanɓare shi, shi zai ƙara cire wasu kuɗin ya siyo kuma muddin kuna so ku ci dankali sai dai ƴaƴanki su zo su soya a tsakura muku don ni ba baiwa kuka ajiye ba" Tana faɗar haka ta juya ta shige gidan. Bak sake Hajiya ta bi bayan Meenal da kakko yadda ta tafi tana karkaɗa mazaunai irin na yaran da suka riƙa a rashin ta ido. Nasir ne cikin sanyin murya ya ce "Ki yi haƙuri Hajia... Kafin ya gama faɗa ta katse shi da faɗin "Haƙurin da ta mutu sadakar nawa ka bani? Kana raye za a yi min cin kashi Nasir har ni matarka za ta ce wai za ake tsakurawa abinci kamar wata almajira" Shi dai baki yake bata amma ta yi banza da shi hatta motar tasa ta ƙi shiga. Napep ta tare ta nufi gida ta je tana ta kumfar baki su Husna suna taya ta, sai da yamma ya shirya ta nufi gidan ƙawarta mahaifiyar Meenal ko da ta je baƙi basu gama watsewa ba wasu kuma suna ya shigowa yin Allah sanya alheri. Tana shigowa Momi ta hau mata lale marhabin tana faɗin "Ka ga manyan mata maganin ƙanana ƙanana, ka ga ƙirjin biki uwar amarya uwar ango"Dariyar yaƙe kawai Hajiya ta yi ta nemi wuri ta zauna sai da aka kira magriba ƙafa ta fara ɗaukewa sannan Hajiya suka keɓe da Momi Hajiya ta ce "Ƙawata akwai matsala wallahi" Cike da nuna damuwa Momi ta ce "Subhanallahi Allah rabamu da matsala mai ya faru?" Hajiya ta ce "Wallahi yarinyar nan Meenal ina ga an samu wasu ƙawaye mararsa imani da tarbiya sun bata sabon darasi da shawarwari a kan zaman gidan miji da kuma uwar miji ganaɗaya ta sauya halayya" Momi ta hau faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raji,un wane ƙawaye ne wannan waye ya miki wannan bayanin" Hajiya ta ce "Ni da idona na gani" Ta faɗa tana kwashe komai ta faɗawa Momo, Momi ta ringa tafa hannuwa tana salallami tana faɗin amma dai bata ɗauki shawarar ƙwarai ba. Hajiya sai ta ga ma yadda take zaton Momin za ta ɗauki maganar sai ta ga bai kai hakan ba, sai ta fara tunanin ko dai son kai ne. Hajiya ta ce "Yanzu mene ne mafita?" Momi ta ce "To wace itin mafita kuma ai tun da har ƙawaye suka ɗorata a kan wata turba wacce ba tarbiyar gidansu ba sai dai a hankali a fahimtar da ita kin san yaran yanzu, dama fa kana tarbiya sai kana haɗawa da addua amma ƙawaye da abokai su ne matakin farko na warware saƙar da ka ɗauki lokaci kana yi shi ya sa ake so iyaye sukr saka idanu a kan ƴaƴa su ga waye abokinsu kuma su waye ƙawayensu" Baki ta saki tana kallonta ai a ganinta wannan son kai ne ta ɗauka Momin za ta kira Meenal ko a waya ne ta kutuntuma mata ashar ta ƙara fahimtar da ita matsayin Hajiya amma sai ta ga abin ya sha bamban. Haka ta baro gidan ranta babu daɗi tana tunanin mafita don ba za ta ƙyale wannan abinnya tafi a haka ba amma za ta ɗauki mataki kawai bata so ne zumuncin su ya yi rauni amma duk da hakansai dai zumuncin ya gurɓace. Ko da Hajiya ta tafi Momi ta kira Meenal ta faɗe mata biri har wutsiya nan ta ƙara zugata da jaddada mata kar ta sake ta saki jiki a rainata, kar ma ta yarda a ga makwancinta ta ƙwaci ƴancin ta duk wanda ya ce kule ta ce casss!. A haka rayuwar gidan Nasir ta ci gaba da kasancewa sai abin da Meenal ta ce ake zartarwa don sun gama barbaɗawa Nasir magani a abinci ya cinye yanzu sai abin da ta zartar ake yi. Sadiya bata ma su take ba ta saka sana,arta a gaba duk yadda Meenal ta so takalar ta da faɗa bata kula ta sai ta yi kamar bata ji ba gorin duniyar nan babu wanda bata mata ba na cewa ai babu abin da bata sani va game da halin gidansu kawai bata biya ta su yi faɗa nr don tana tsoron komawa gida mahaifinta ba zai bari ba. Hatta abinci ita take aunaw Sadiya tamkat ba ita ce uwar gida ba, sannan a ba Meenal kulin cefane ita a hanata, duk wani abu na bambanci ko rashin adalci shi ake yi a gidan, ita ta yi girki da gawayi ita ta ɗora a gas sannan ita Meenal tana da mai wanke wanke almajiri ita kuma Sadiya da kanta take yi. Hajiya sai da ta ga dankali da kayan shayi ya ƙare kaf sannan ta ce Nasir ya siyo wani buɗar bakinsa ya ce "Hajiya yanzu idan akamce zannke siyan ƙwai doya dankali da kayan shayi ruɓi biyu gaskiya za a samu matsala ga mota ta yanzu tana yawan bani matsala sai kuɗin gyara take ci sannan yanzu Meenal bata taɓa yin girki babu nama" Hajiya ta ce "To mai kake nufi yanzu?" Nasir ya ce "Sai dai idan har kuna sona dankalin su Husna suke zuwa suna aikatawa sai Meenal take ɗauka musu suna kawo muku kamar yadda Meenal ta tsara, amma na san ita Meenal ba za ta yarda ta girka muku ba" Da bala,i Hajiya ta ce "Bata isa ba dole ta girka don na fahimce ka na rashin siya a can gidan da kuma nan ni ma bana so ka wahalta aljihunka saboda auren ƙanannka amma dai tun da ita uwar muyane ba za bari a dafa a nan a bata ba dole ta dafa" Nasir jikinsa ya yi sanyi hakan ya sa ya ce ",Ba komai kawai zan saya muku " Yana barin gidan ta kira Meenal tana ɗagawa ta ce ",Hajiya ya ne? Ƙalau dai ake kirana" ,Ran Hajiya ya sosu da ta ji wannan batu amma sai ta ce "Fitsararriya mai ido a tsakar ka, ina so in ƙara tabbatar miki da cewa ɗana ni na haife shi dole ya mini abin da nake so gashi can zai sayo mana kayan kari in kin isa mu zuba ni da ke!" Tana faɗar hakan ta kashe wayar ta bar Meenal da waya a kunne. A ƙufule Meenal ta kira Nasir ta ce "Yanzu kai baka isa da ƙannenka ba saboda na ce suke zuwa suna mana girkin safen kawai shi ne za ka je ka siyo wasu kayan saboda ka nunawa ƙanennka ban isa da mijina ba su rainani na gode" Tana kai wa nan ta fashe da kukan kissa ta kashe.. Nasir ya kira ta yana ta aikin lallashi ya ce ya fasa siyowa zai tilasta su Husna zuwa. Kawai Hajiya sai kiran Nasir ta gani tana ɗagawa ta ce "Yawwa ka kira a kan gaɓa dama yanzu nake son kiranka in ce mun fi son dankalin mai manya manya douar kuma sabuwa muke so ta fi daɗi" Nasir ya ce "Hajiya ya za a yi a ce ni ban isa da su Husna ba bayan an ce babban wa uba, kawai suke zuwa gidana suna girkawa" Salati ta hau yi ta kashe suka hau jajantawa ita da su Husna Hibba sai ɗurawa Meenal ashar take yi suna cewa ta mallake musu ɗan uwa Hajiya kuwa har da kukan takaici wai an fi ta iko da ɗa. Washe gari suka ƙi zuwa sai Hajiya ta yi musu tuwon shinkafa suka ci kaɗan sun saba da kayan dankli da kwai da shayi mai kauri yau kuma sai bunu suka sha wato lipton. Haka suka yi ta mita wata washe garin saj suka kwashi ƙafa suka tafi gidan sun daɗe zaune a ƙofar ɗakin Meenal suna jiranta kafin ta fito a shelaƙe ta basu kayan da za su yi aikin kuma din takaici ta ce kar su taɓa mata cooker gas ta ce su yi da gawayi haka suka yi wahala suka gama ta zo ta ɗauro musu kayan shayin kamar wani ƙullin roƙo kuma a waje ɗaya ta haɗa madara da milon. Basu gama sanin bata da mutunci ba sai da ta ce sai da su koma su kawo kwanon sa za a zuba ko ta zuba a leda haka suka tafi suna ta tsene mata har da uwar ta sai da suka tsinewa haka ma Hajiya ta ringa zaginta da ta ga kayan shayin ta ɗakko wani ramgameman fulas ta basu, suna kaiwa Meenal ta tsakura musu wani a ƙasan kwano ko Hajiyar ba zai isa ba bare su. Haka suka tafi ransu duk a ɓace sai da suka je sai suka fara zancen da a ce Sadiya ce ta samu wannan damar da ba za ta musu haka ba. Kullum haka suke zuwa su girka ta basu su tafi dama yanzu da kwano suke tafiya Sadiya kuwa babu ruwanta da sabgarsu ko Nasir rabon da ya taka ƙafarsa a tsakiyar falonta ma tun kafin Meenal ta tare bare a yi zancen biyan haƙƙi. Ga cikinta ya tsufa tana dab da haihuwa. Wata ranar laraba sai kawai Meenal ta ce Nasir ya sa maau aiki su buga kicin na langa langa Sadiya ta kwashe mata kaya daga kicin haka kuwa aka yi, Sadiya ta kwashe komai nata, don ita yanzu in banda gayan kayan abinci babu abin da ake bata a gidan shi ma ba ishashshe ba. Yanzu da ta lura Kalifa yana ganin dankali da ƙwan da ake soyawa sai ta saya kokai ta ajiye su ma take soya musu tun da Allah ya rufa mata asirin da sana,ar da take yi wanda wannan abu shi ne ya tsayewa Meenal a rai don ko buga gidan aka yi za a saya abu ta ringa masifa tana cewa ana katse mata bacci. Yau lemon mango tun safe ake saya haka ya sa gabaɗaya ma kayan sanyin suka ƙare da yake tana da ƙanƙara kuma akwai nepa sai ta zauna ta haɗa wani tana zubawa a robobi. Gidan da aka buga ya sa ta yi magana aka ce ƴan nepa ne bill ne muka kawo, ta je ta karɓo yana nannaga mata idan ba a biya yau ba gobe za su dawo su yanke. Za ta zuna sai Meenal ta fito a gadarance sanye take da baƙin wando da ya kamata tree quarter da farar riga kai babu ɗan kwali sai wani kaɗa jiki take tana fitowa ta ce "Kawo wannan bill ɗin tun da ba ɗakin ki zai shiga ba tun da ma ke ai baki da bakin kwana a gidan nan" Sadiya bata ce komai ba ta ba Kalifa ta ce ya kai mata, haka ta karɓa ta shige ɗaki. Ko da ya dawo gidan suna zaune da daddare ta yi filo da cinyarsa sai ta ce "Ga bill can ƴan nepa sun kawo, sun ci gobe za su yanke in baka biya ba" Ya yi shiru ya ce "Ni yau kasuwar nan bata yi kyau ba" Wani daɗi ta ji don an zo wajen da take fatan a zo Sassauta murya ta yi cike da kissa ta ce "Honey ni kana bani mamaki ya za a yi a ce wai kullum kai kake biyan nepa" Da mamaki ya ce "Wa zai biya min" Ta ce "Sai kuke raba daidai da Sadiya ai ta fi kowa morar nepa a gidan nan, amma yanzu idan ka tunkare ta da maganar ba lallai ta bada kuɗi ba kawai idan ƴan nepa sun zo sai su tanke mata ɓangarenta in ya zo nan gaba idan aka ce ta bayar ba za ta yi musu ba" Shiru ya yi sai kuma ya miƙa mata hannu suka tafa yana jin lallai shawarar ta yi daidai da ma,ana sai ya ce "Wallahi ƙwaƙwalwarki tana aiki ban taɓa wannan tunanjn ba" Murmushin cin nasara ta yi. Da safe kafin ya fita ya bata kuɗin nepa ya ce idan sun dawo ta basu, amma sai ya yanke wani kaso daga kuɗin ya ce ta ce su yanke ɓangaren Sadiya. Sadiya yau tun da almajirinta ya ɗauki kayan yake dawowa yana ƙarawa gashi daga unguwa ma sai zuwa ake nan da nan ya ƙare tas. Ta zauna ta sake wani ta jera a frige. Ta gama zubawa kenan sai ta ji ana bugawa da aka yi magana aka ce ƴan nepa ne a kawo kuɗin wuta, Meenal ta ɗauki kuɗin ta je da takardar ta basu, ta musu bayani babu musu suka yanke ɓangaren Sadiya, Sadiya tana tsakar gidan tana jin ƙaran tvn Meenal kasancewar ta ƙure ƙara, amma tana shiga falonta sai ta ga ƙwayayen basu kawo ba ta duba ko ina ta ga babu nepa ta ƙara fitoea ta ci gaba da jin ƙaran tv a ɗakin Meenal a nan take ta fara tambayar kanta "Ya haka?" ALIYA Amatullahi ce take mata alama da ido alamar ta amince a take ta shiga kaɗawa bakanya kai, sai kuma suka tambaye ta kuɗin aikin ta ce sai sun kawo cokalin an yi aikin tukunna. A tsorace suka baro wajen suna tafiya har suka fito daga surƙuƙin dajin suka zo bakin titi sun daɗe suna tsaye suna tattaunawa Amatullahi tana faɗawa Aliyar kawai daga nan ta wuce gidan Jidda ta san duk yadda za ta yi ta ɗakko cokalin tun da gobe dole su dawo su kawowa bokanyar cokalin. Bayan sun sauka a motar suka shiga napep kowa daban ta shiga tun da Amatullah gidansu za ta tafi ita kuma gidan Jidda. A ƙofar gidan Jidda napep ya sauketa ta fito ta bashi kuɗin tana lissafin sauran kuɗin nata ya kusa ƙarewa gashi bata san ma da mai za ta biya bokanya kuɗin aikin ba, duk da bata san nawa ne kuɗin ba sai dai ta san za ta yi ƙaryar da za ta yi ta ɓanɓari kuɗin aikin a jikin Jidda tun da ita ita ce mai kuɗi ita kuma Allah ya tauye mata nata samun sannan shi ma mijin fuƙara,u ne. Tana tsaye gaban tangamemen get ɗin tana ƙarewa gidan kallo ranta tana ƙuna tana ƙiyasto ranar da za ta tare a cikin gidan. Ƙaran sohuwar wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin ganin sunan Kasim ta doka wani uban tsaki, a zuciyarta tana faɗin 'Ɗan anace uban shegen naci ko mai zai bani zai kafa mini kira' Ta faɗa sai dai kiran yana dab da tsinkewa ta ɗaga tana karawa a kunnenta ta ji hucin iskar sa ya busa yana faɗin "Aliyata sarauniyata" Wani ɗaci ta ji a zuciyarta tana galla masa harara tamkar yana ganinta, sai kuma kamar an mata dole ta ce "Uhmmm" Ya ce "Fatan kina cikin ƙoshin lafiya, baki koma gidan ba?" Ya tambaya yana sararon amsar ta. Ɗan jim ta yi sai kuma ta ce "Eh dama ai ban jima da fita ba kuma Amatullahi ce ta ɓata mana lokaci yanzu ma ko asibitin bamu ƙarasa ba" Fatan alkairi ya mata yana faɗa mata yadda ya yi kewarta baki ta taɓe a zuciyarta tana raya shi aka bari da yawo da zance don ita yanzu tana nan tana yaƙin yadda za ta samarwa kanta kyakkyawar rayuwa. Ƙaramar ƙofar get ɗin ta tura amma sai ta ji a rufe gam hakan ya sa ta yi nocking. Mai gadi da yake zaune kan benci yana ɗann gyangyaɗi ya taso ya buɗe mata tun da lokacin ƙarfe ɗaya saura. Yana ganinta amma bai bata hanya ba sai ya tare ta da tambayar "Baiwar Allah wa kike nema?" Maimakon Aloya ta bashi amsa sa ta shiga ƙarewa kanta kallo tana duba ko akwai wani waje da ya gani wanda ta yi kama da mai neman taimako da har zai jefe ta da wannn tambayar cike da gadara ta ce "Matsa min in wuce ko ka ɗauka irin mutanen da suke neman taimako ne ai ban maka kama da mai allazi ahidin ba " Ta faɗa tana neman bangaje shi ya ƙara tare ƙofar yana cewa shi a kan aikinsa yake, nan ta shiga ɗaga murya tana faɗin gidan ƴar uwarta ne, shi dai bai kulata ba ya fito da waya a aljihunsa ya kira Jidda yana faɗin ,"Hajiya akwai wata baƙuwa a waje tana cewa sai ta shigo kina da baƙuwa ne Ta ce ƴar uwarki ce?" Jidda da take kicin ta ɗan yi jim sai ta ce "A,a amma ka barta ta shigo" Cike da girmamawa ya amsa. Matsa mata ya yi ta wuce tana faman faɗin da bai matsa ta shiga ba da sai ya rasa aikinsa. Nocking ƙofar ta yi jim kaɗan Saude mai tayata aiki ta zo ta buɗe dama tare suke da Jidda a kicin tana taya ta aiki. Buɗe mata ƙofar ta yi tana mata sannu da zuwa Aliya ko amsawa bata yi ba ta ce ta wuce cikin babban falon inda tana shiga wani ƙamshi mai daɗin gaske ya baibaye mata hanci, fitowar JIdda ta hango Aliya a tsakiyar dalon da sauri ta ƙaraso fuska cike da fara,a bakinta ya ƙi rufuwa. Aliya kuma ganin Jidda ta yi ƴar ƙiba ta murmure ga wani kyau da fatar ta ta yi tamkat wacce take rayuwa a ƙasar waje wani tuƙuƙin baƙin ciki ya cika mata ciki tana tunanin da yanzu ita ce a wannan daular ita ce ta yi kumari ta warware. Danne abin da ya ɗarsar mata a zuciya ta yi domin ta san wannan damar tana dab da zuwa gare ta ta kusa ta shuga tsakanin ma,auratan biyu wato ta zo ta kafa tata fadar a birnin zuciyar Ibrahim ba tare da wani ta kawo mata cikas ba. 'Oyoyo Aliya shi ne ma ko sanarwa " Ta faɗa tana ƙarasowa suka zauna a kujera a tare Aliya sai yaƙe take, don ita zuciyarta cike take da yadda za ta ɗauki cokali. Tana ƴar dariya ta ce "Yanzu don zan zo ganin ƴar uwata jinina sai na sanar da ita? Ai dama na ce bari na zo tun da ke har yanzu kin gagara zuwa na ce wataƙila ku masu kuɗi bakwa ziyartar gidan talakawa" Jidda tana mata ƴar hararar wasa ta ce "Haba dai wannan wace irin magana ce dama ranar juma,ar nan nake cewa zan je gida in gaishe su sai na ratsa gidanki, daga nan sai na je gidansu Ibrahim na gaishe da ita" Ta faɗa tana kallonta. Nan suka shiga ƴar hira Jidda tana jin kamar ta goya ta saboda daɗin sa ta ji. Saude ce ta zo da sallama tana ɗauke da plate wanda yake ɗauki da lemon roba guda biyu da ruwan roba guda ɗaya masu sanyi, sai kofi ta zo ta durƙusa ta ajiye a gabanta tana ƙara gaishe ta amsawa ta yi hankalinta a kan Jidda tana ta ƙare mata kallo kamar dai ba wannan Jiddar wulaƙantacciya ba a wajensu amma yanzu gashi ta samu ƴanci, ƴancin ma mai lasisi. Lemon ta tsiyaya mata ta miƙa mata da hannu biyu kafin ta tashi ta bar wajen, Jidda ta ce "Saude ki goge kan cooker gas ɗin idan wajen ya huce sannan ki kwaso kwanukan ki jera a kan dining" ,Cike da ladabi ta amsa ran Aliya yana ƙuna wai yau Jidda ce da mai aiki bayan a gida ita ce baiwar gidansu lallai wannan bahaushe yake kira rana ɗaya Allah kan yi bature. Suna hira inda Jidda take tambayar Kasim wani ɓacin rai ne ya zicyarci zuciyarta ita ba don larura ba ta tsani a kira sunan Kasim ma. Ita ma ta daure ta tambaye ta Ibrahim kafin ra bata amsa wayar Jiddar da take kan ɗaya daga cikin kujerun ta shiga ringing, tashi ta yi ta tafi za ta ɗauko gabaɗaya idanun Aliya a kanta tana ganin yadda doguwar rigar rantsatstsan leshin ta kamata daga baya tamkar dama a jikinta aka yi ɗinkin tana murmushi ta amsa wayar, Aliya tana jin yanayin yadda suke wayar cike da kulawa ta gane da Ibrahim take magana. Sai bayan sun kammala wayar ta ce "Kin ganshi ma ɗan halak shi ne ya kira ai yana office" Ɗan runtse idanu Aliya ta yi ta buɗe tana tunanin yanzu shi yana can a office cikin AC ita kuma nata mijin yana can cikin rana a kasuwa yana fafutuka. Sun jima suna ɗan taɓa hira ita dai Saude ta koma ɓangaren su na ƴan aiki inda suke tare da wata dattijuwa kakarta mai suna Baba kuluwa. Kiran sallah ya sa Jidda ta ce su je su yi sallah, bedroom ɗin da aka ajiye ta ranar da aka kawo ta suka shiga Aliya ta shiga banɗaki ita kuma ta fito ta hau sama jim kaɗan ta dawo ta tarae tana sallah ita ma alwalar ta yi ta zo ya kabbara tata sallar. Bayan ta idar suka fito falo ta kawo musu abinci suna cikin ci Ibrahim da ya taho daga office yau da wuri kasancewar kansa yana ciwo bai faɗa mata ba sai ya taho don baya so ta tada hankalinta. Da sallama ya shigo gaban Aliya y buga da ƙarfi Jidda kuma ganinsa yanzu ya sa ta gane akwai damuwa musamman da ta kalli yanayinsa, cokalin hannunta ta ajiye ta miƙe tsam Aliya kuma ta gaishe da shi fuska babu walwala ya amsa kawai sai take ganin kamar dai ya gane ita ce take kiransa ko kuma ya san ƙudurinta, da sanyin jiki Jidda ta nufe shi yana kallon yadda yanayinta ya sauya da idanunta ta shiga isar da saƙon tambayar dawowarsa a wannan lokacin amma maimakon ya furta mata komai sai kawai ya langaɓar da kai gefe yana lumshe kyawawan idanunsa da suka ɗan kaɗa suka ja tana ƙarasowa sai ta karɓa jakarsa ta office ɗin amma shi ba wannn tallafin ya fi buƙata ba ya fi son jin fatar jikinta a jikinsa ko ya ji sassauci don ya yi ammana Jidda wani tsagi ce na jikinsa yana ji a jikinsa tabbas idan babu Jidda ba zai rayuwa ba ko da ya rayun zai yi rayuwa ne irin ta akwai ruhi amma gangar jiki kamar gawa!. Hannunsa ya kai ya rungumota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya, hannunta ta saƙala a bayansa suka shiga takawa a hankali don ita tuni har yanayinta ya sauya ta fara jinta tamkar marar lafiya, ita da take ji ana cewa idan ɗa bashi da lafiya mahaifiyarsa tana jin jikinta tamkar marar lafiyar wani lokacin ma tare ake yin jinyar da uwa da ɗan ashe dai gaske ne tun da gashi ita ma da yae mijinta har ta ji nata jikin ya amsa. Aliya kuma sai suka zame mata TV don sai ta zama tamkar mutuntumi a wajen tamkar dai ma basu san da ita a wajen ba, suna riƙe da juna suka fara haurawa sama, Aliya ta kafe su da idanu, har suka ɓacewa ganinta, wani haushi ya cika mata zuciya tana tunanin da yanzu ita ce wannan kyakkyawan yake gwadawa wannan soyayyar wannan a gaban mutane ma yana yi wa matarsa haka ina ga in suka keɓe a ɗaki ɗaya ta san ai sai dai a kira matarsa ƴar gata, don a haka ta fahimci tsantsar kulawa ce da soyayya. Da nannuyar ajiyer zuciyar da ta sauke ta dawo hayyyacinta tana sakin wami tsaki a fili, duk da daɗin abincin da take ci a take ta ji ya zame mata maɗaci a fili ta furta "Zan farraƙaku nan ba da daɗewa ba dole za ku rabu, ni kuma in gina fada ta" Ta faɗa a fili tana tunanin tashi ta yi abin sa ya kawo ta gidan amma kuma tana tunanin ya za a yi ta gane cokalin. Ƙaran wayarta ne ya katse mata tunanin da take tana dubawa ta ga Umma ɗagawa ta yi tana ɗan waiwayawa ta ga tabbas babu kowa dama wannan ƴar aikin take ji tana karawa a kunne ta ce "Hlo Umma" Umma ta ce "Aliya ke kaɗai ce?" Aliya ta ce "Eh Umma amma ban koma gida ba" Umma ta ce "Ayyo dama ina son jin kanun labarai ne to na tambaya cewa ke kaɗai ce don kar in je ko wannan mata mazan yana kusa" Wani takaici ne ya turnuƙe ta da aka ambaci sunan mijinta tana sassauta murya ta ce ",Umma ina gidan Jidda zan kira ki" Umma da mamki ya gama ɗarsarwa a zuciya na tambayar kanta mai ya kaita gidan Jiddar sai dai tun da ta ce tana can babu damar tambaya sai ta fara ƴar dariyar yaƙe wacce ta soyayar ƙarya ce ta ce "Kuma yanzu Aliya kina gidan ƴar tawa shi ne kike sanya baki haɗamu a waya ba maza bani ita" Aliya ta ce "Hmmm! Umma bata kusa fa sun hayr sama ita da mijin" Umma ta ce "Aikin banza da wofi idan tusa tana hura wuta ai za mu gani" Tana faɗar hakan ta kashe wayar tana tunanin dole a samo maƙarƙashiyar da za a yankewa Jidda jin daɗin da take ciki domin ita Umma saboda hassada mugun ciwo ko gidan Jidda bata taɓa taka ƙafarta ba tana ta faɗar wai ɓanya basu fiya zuwa gidan yara ba sai da dalili. Tana ajiye wayar ta tashi tsaye gabanta yana faɗuwa za ta tafi neman cokali hanyar kicin ɗin ta kama har ta tafi ta dawo jin ƙaran wayarta ta ɗauka ma Umma ce sai ta ga sunan Amatullahi ta ɗaga Amatullahi ta ce "ƙawata ya ake ciki ne Allah sa dai aikin gama ya gama?" Aliya ta ce "Ina nan yanzu na samu dama zan je in duba" To mai kike jira ko sai kin rasa damar da kika samu" Aliya ta ce "Ni wallahi tunanina ma wanne ne cokali" Amatullahi ta ce ",Dalla malama ki yi aiki da hankali da tunaninki " Tana faɗar hakan ta kashe wayar ita kuma ta ajiye ta nufi kicin ɗin da sauri,sai kuma ta dakata ta yi wajen dinning ɗin sai kuwa ta ga gabaɗaya kayan abincin ne ba a ajiye plate da cokula ba tsaki ta yi ta je ta tura kicin ɗin wani ƙamshin girki da bai gama barin kicin ɗin ba ne ya ziyarci hancin ta, amma ba wannan ne a gabanta ba sai ta shiga wurwurga idanu manyan kwanduna ne gasu nan da dankali da doya kainiya ganinta komai gashi na a wadace ban da ma ita ai babu wani abunda zai bata mamaki domin gidan dukiya ta zo mai za ta gani ƙwai ma kamar abin banza gashi nan kiret kiret ita kuwa tun da ta ragargaje na amarcin yanzu sai dai ranar da ya ga yana da kuɗi ya siyo guda biyu wasu manyan robobin spices da curry masu ɗauke da sunan MAMANA AFRAH SPICES ta gane jere da nauikan abubuwa da ta tabbatar duk kayan girki ne, tsaki ta yi ta je inda ta ga cokulan ta fara tunanin wanne za ta ɗauka kar ta je ta ɗauki wanda ba nasa ba a samu matsala babu zato da tsammani ta ji an turo ƙofar wanda hakan ya sa ta tsorata sosai hantar cikinta ta kaɗa sai ta ga wannan ƴar aikin ce da ta ji an kira da Saude. Cike da girmamawa ta ce "Ayya ban san kina ciki ba shi ya sa ban nema izini ba" Kallon ƙasƙanci Aliya ta jefe ta da shi ita Saude tana mamakin matar tun da ta san Jidda bata wulaƙanta su tamkar ma ba ƴan aiki ba amma ita wannan sai hararrata take frige ɗin kicin ɗin ta buɗe ta ɗakko ruwan roba guda biyu ta rufe har ra je bakin ƙofa sai Aliya ta ce "Ina za ki kai ruwan wato kin ga bata nan za ki yi sata" Saude ta ce "Sha za mu yi fa" Aliya ta ce "Lallai samun wuri har ruwan roba kuke sha?" Saude ta ce "Aunty Jidda ta ce bata mana shamaki da duk wani abu ba" Tana faɗar hakan ta juya ta bar kicin ɗin. Jidda ko da suka shiga ɗakin ta ajiye jakar a kan ƙaramar lokar gefen gadon bayan ta taimaka masa ya zauna, yana dafe kai duk sai tausayinsa ya kamata. Cike da kulawa ta ce "Kanka ne yake ciwo?" Kai ya gyaɗa mata, taimaka masa ta yi ta kwanta bayan ta ja masa filon ya kwanta sai ta shiga masa addu'a bayan ta masa cikin sanyin murya mai cike da nuna kulawa da kuma damuwa da wanda ake yi wa magana da muryar ta ce "Mu tafi a kai ka asibiti ina direban ne" Dakyar ya mata magana ta hanyar faɗin "Ba sai na je asibiti ba, direbana na aike shi a bakinnget ma na ce a ajiyeni" Ta ce "To ba ga direbobi a gidan ba" Ya ce Ki bar batun asibitin nan" Ta rausayar da kai kamar za ta yi kuka ta ce "To a kira likita ko in kira Mummy sai ta faɗawa Daddy?" Maimakon ya bata amsa sai ya saka hannunsa ya riƙe dantsen hannunta kawai ya mayar da idanunsa ya rufe yana faɗin "Ki bani magani bana son kowa ya sani idan na sha magani na samu bacci zai daina" Shiru ta yi tana bhn kyakkyawar fuskarsa da kallo yadda zara zaran gashin idanun da suka ƙawata idanun suka ƙara masa kyau sai kuma yadda fuskar ta yi fayau da ita. Tana cikin kallon ta ji cike ta kulawa ya ce "Kar ki saka damuwa a ranki kin ji Jiddana" Idanun ta lumshe ta buɗe ta ce "Ita damuwar da kanta ta san na cancanci na saka ta a raina domin da kanta ta ziyarce ni tun a kallon farko da idanuna suka maka, a inda ƙwaƙwalwa ta harba saƙon kana cikin damuwa tun a lokacin gaɓɓaina suka yi sanyi yanayin jikina ya sauya" Furucin da ta yi ya tabbatar da sun zama hanta da jini shi da ita, don shi ma haka ne yake faruwa da shi idan ya ganta a damuwa!. A hankali ta zame riƙon da ya mata fitowa ta yi domin ta samo masa abinci kaɗan ya ci ya sha maganin, sai da ta sakko ƙasa da ta ga kwanukan abincin da suke ci da Aliya sannan ta tuna cewa Aliya tana gidan don gaba ɗaya ta manta damuwar Ibrahim ɗinta ya dishashe tunanin komai. Tunaninta ko ta shiga bedroom ne za ta shiga bayi, dining ta nufa tana zuwa sai ta ga ashe bata ajiye masa plate da cokula ba hakan ya sa ta nufi kicin ganinsa a ɗan buɗe ta tura sai kawai ta ga Aliya tana tsaye, Aliya kuma sai da ta ji gabanta ya faɗi domin bata tsammaci zuwan Aliya a yanzu ba don ita zuciyarta ma tana faɗa mata cewa suna can suna soyayya saboda bata san cewa bashi da lafiya ba. Cike da wayuncewa ta ce "Kawai kicin ɗin nake ƙarewa kallo kin san ina son ganin jeran kicin, nawa ma sai na yi ta kallonsa duk da bai haɗu kamar wannan ba" Jidda bata san lokacin da ta yi dariya ba ta ce "Kina da abin daariya yanzu saboda kallon kicin ɗin ne kika bar cin abinci?" Aliya ta ce "Haba Jidda ya za a yi in iya ci bayan tare muke ci kika haura sama" Jidda ta ce "Ai da kin ci ni yanzu abinci zan kai masa kaɗan ya samu ya ci ya sha magani ba ya ɗan jin daɗi ne" Aliya ta ce ",Wayyo Allah sawaqe" Jidda ta amsa da amin Kicin wear ta nufa ta ɗauki plate guda biyu, sai kuma ta je wajen na cokula ta ɗauki cokali a inda gabaɗaya cokulan iri ɗaya ne a wajen sai kuma ƙasan wasu ne amma masu mariƙa ja ne wanda ta ɗauka kuma coffee ne jikin inda ake riƙewar. Ta haɗa da saving spoon suka fito tare tana tsokanar Aliya wai har ta gama kallon kicin ɗin ita kuma sai take ta murna a ranta ta gane cokalin da yake amfani da shi. Ita ta tsaya a dining tana zuba masa abincin ita kuma ta ƙarasa ta ci gaba da cin abincin amma naman kazar take ci don ta yi amanna ba za ta rage naman ba saboda ta san idan ta koma nata gidan miya ce zallah ko naman miya babu sai ranar da ya ga da sarari ta siyo naman miyar ko kifi a saka, in kuma kasuwa ta yi kyau sai ya siyo naman a dafa ita a da ne ta matsu ya samu aiki amma yanzu da samun aikinsa da rashinsa duk ɗaya tun da dama tana so ne tun da ta ga yanzu shi yaron kasuwa ne ba wai hamshaƙin ɗan kasuwa ba kenan duk abin da yake nemowa buga-buga ne. Jidda tana gama zubawa ta rufe da ɗaya plate ɗin ta haura sama Aliya tana raka bayanta da harara kamar idanunta za su faɗo. Tana gama daina hangota da sauri ta tashi ta nufi kicin ɗin ta ɗauki cokalin ta tsaya tana kallon cokalin tana dariyar cin nasara kasancewar bata rufe ƙofar ba Saude da ta dawo ta ga abin da take lokacin da ta kawo kai kicjn ɗin, mamaki ne ya kama Saude dalilin murna da kuma dariyar a kan ganin cokali Aliya kuma da ta ga mutum sai kawai gabanta ya faɗi don bata ma gama tantancewa cewa Saude ba ce duk tunaninta Jidda ce ta dawo bata san lokacin da ta ɓoye cokalin a baynta ba wanna ya sanya wani abu ya ɗarsu a zuciyar Saudr tun da ba yarinya ba ce budurwa cenza ta yi shekara sha buyar zuwa sha shida. Aliya kuma da ta dawo hayyacjnta daga duniyar tsoron ta ga Saude ce ta doke tsaki ta ce "Wai uban mene ne kike diddiftu a kicin ɗin nan?" Saude ta ce Dama Baba Kuluwa ce ta ce mura take ba za ta iya shan ruwa mai sanyi ba na canjo mata" Aliya ta ce "Aikin banza da wofi duk samun wuri kuka yi wallahi da wasu ƴan aiki ne za a ba ruwan roba in ban da asarar abu bakwa shan ruwan famfo, ai duk laifin Jidda ne ni akwai wani ɗan aiki da zai saki jiki in na dawo gidan nan" Sai da ta yi furucin ta gane wautar da ta yi don dama tana nufin idan ta dawo gidan da aure wato bayan ta auri Ibrahim, ita kum Saude sai ta fara tunanin in ta dawo gidan yaushe? Maganar da Aliya ta yi ta cire mata shakkun tunani ta hanyar faɗin ,"Idan na dawo gidan nan watarana in Jidda ta haihu na zo zaman wanka" Tana faɗar hakan Saude ta mayar da ruwan ta ɗauki marar sanyi ta yi tafiyar ta ita kuma Aliya ta fito da sauri ta dawo falon ta bule jakarta ta saka cokalin. Ranta fari ƙal har ta fara hango ta a wannan haɗaɗɗan gidan tana baza capacity tana zuba tashin mutunci don daga dangi har sangin dangiro sai sun san bata da mutunci musamman mutane makwaɗaita za su ɗanɗana kuɗarsu. Jiida kuwa dakyar ta samu ya yi cokali biyu ta bashi maganin da ya sha sai bacci ya ɗauke shi plates ɗin abincin ta ɗakko ta fito ta rufe masa ƙofa ta sauko ƙasa. Nan suka zauna suna hira sai Aliya take cewa Umma ta kira a waya ta ce a bata lokacin tana sama, kiran Ummar Jidda ta yi Umma cike da fara,a amma ta ciki na ciki ya hau magana da Jidda cike da nuna soyayya ta ƙarya. Bayan sun gama ta ce ta gaishe da Abba suka yj samma Umma tana jin kamar ta shaƙo Jiddar daba cikin wayar. Wajen ƙarfe biyu da wani abu Aliya ta ce tafiya za ta yi Jidda ta ce ta bari a yi la,asar amma ta ce tana so ta je ta yi girki saboda Kasim ya kira ta ya ce da wuri zai zo nan Jidda ta ma rasa mai za ta bata don daɗi haka ta je ta samu lece da atamfa ta zuba mata a leda Aliya sai godiya take haka ta rako ta bakin ƙofa sai Aliya ta ce "Kai jama,a talaka ya shiga uku wallahi aka bar mutum da kuɗin adaidaita sahu kaɗai ma sai ya kashewa mutum gwiwar zumunci" Jidda cike da tausayawa ta ce "Ayya karki karaya ai shi zumunci hanya ce ra shiga aljanna sannan duk wanda ya yanke shi Allah zai yanke shi daga rahmarsa, bari na saka direba ya kaiki gidan... Tun kafin ta kai ƙarshen zancen Aliya ta ce "Lah ki bari kawai na biya adaidaitan" Ta faɗa tana juyawa za ta tafi sai Jidda ta ce "Bari na saka miki a acc sai ki biya shi" Ta faɗa tana komawa ta ɗakko wayar sai ta tura mata dubu ashirin ta ce ta yi wani abu da canjin tun da ko jiya Mummy dubu ɗari biyu ta turo mata. Godiya Aliya ta yi suka yi sallama ta zo ta wuce mai gadi yana mata a sauka lafiya ko kallonsa bata yi ba ta buɗe ƙofa ta fice a zuciyarta ta ce 'Duk ranar da na auri Ibrahim ka tabbata ruwan shanka ya ƙare!' Ta faɗa tana duba alert ɗin da Jidda ta mata na dubu ashirin tana cewa a fili "Matsiyaciya kin biya kuɗin aikin da za a yi a fatattka tsakaninki da mijin naki a sama mini gurbin zama" Ko da ta dawo gida ta shiga kiran Amatullahi tana bata labari sai dai Amatullahi ta ce gobe su je su kai cokalin amma kuma ba a gobe za a kai cokalin gidan Jiddar ba saboda kar ta zargin wani abu na zuwa gidan a jere a kwana kusa. Bayan sun gama ta kira Umma tana zayyana mata ƙusurinsu na fitar da Jidda daga gidan da kuma samawa Aliya gurbin zama Ibrahim ya auri ta. Buɗar bakin Umma ta ce "Kun yi min daidai ƴan albarka ubangiji ya muku albarka ke da Amatullahi ƙawar arziƙi, ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha dole a fitar da Jidda daga gidan wannan idan ma har hakan ba zai iyu ba sai dai ke ki shiga a rufewa kowa baki hatta uban naku sai an rufe masa baki ruff in ya so sai ta rayu cikin uƙuba a gidan ta zama da ita da babu duk ɗaya da samuwarta da rashinta duk ɗaya!" Umma ta faɗa tana tunano irin yadda za ta baza capacity idan ta zama sirikar Ibrahim babu abin da take so irin ta ga Aliya a gidan nan da ake ta bada labari. Bata ƙara bi ta kan Ibrahim ba sai ta tattara shi ta ajiye bata sake kiransa a waya ko masa saƙon whatsapp ba, tun da dai tana ganin aski ya zo gaban goshi, saura ƙiris ta koma gidansa sannan a matsayin matarsa. Washe gari bata tambayi Kasim fita ba sai kawai ta bari da ya fita Amatullahi ta kira a waya ta faɗa mata su haɗu a marabar bamin titin suna haɗuwa suka tafi, ko da suka kai wa bokanya cokalin ta shafa wani magani ta ringa wani siddabaro tana ambaton sunan Ibrahim. Da ta gama ta ɗakko wani jan ƙyalle da baƙi ta ajiye a gefe ta shafa wani magani da mai sai kuma ta saka baƙin ƙyallan ta goge cokalin sannan ta saka jan ta ƙara gogewa sai da ya dawo tass sannan ta miƙawa Aliya ta ce "Karɓi da ƙafarki ta hagu" Haka Aliya gabanta yana faɗuwa ta miƙa ƙafar hagu bokanya ta saƙala mata cokali ta ce "Sai kuma ki ɗauke shi daga ƙafar taki da hannun dama" Haka Aliya ta aikata sai bokanya ta ce "Kamar yadda ƙafar hagu take a gefe hannun dama a gefe basu haɗa hanya ba to idan Ibrahim ya ci abinci da cokalin nan haka zai yi gabas Jidda ta yi yamma, ba zai sake kallonta da idon soyayya ko idon rahma ba babu wacce zai so sai ke kaɗai!". Bakin Aliya kamar ƙofar gari wani daɗi da sanyi ya ziyarce ta har ta fara hango yadda za ta yi idan ta shiga gidan naira saboda da butulci ma ko da ta sauke idanunta a kan Amatullahi a zuciyarta ta ce 'Sai dai ki yi haƙuri Amatullahi idan na shiga daula zan sallame ki da kuɗi masu kauri sai dai dole na sauyaki a matsayin ƙawa don babu ni babu ƙawa da talaka ko hanya ba za mu haɗa ba, sai dai na samu matan masu kuɗi kuma mata masu aji, sannan ma ke barazana ce ga shiga ta gidan Ibrahim kar watarana faɗa ya haɗomu ki tona mini asiri!' Aliya ta ce "Bokanya kuma batun toshiyar baki fa mahaifina ba zai taɓa bari na auri mijin Jidda ba, sannan mutanen gari za su zargi wani abu uwa uba mijin Kasim ban san ya zai sake ni ba!" Da wata dariya bokanya ta bushe mai ban haushi ta jima tana dariyar kafin daga bisani ta haɗe rai tamkar bata taɓa yin dariya ba ta ce "Wannan aikin da aka miki na cokali ya haɗa komai da kowa, babu wanda zai buɗi baki ya ce din me, babu wanda zai yi musu kuma Kasim a take kina ambata takardar saki zai baki shi ma mahaifinki ba zai tambayi dalilin wani auren ba ko dalilin mutuwar auren naki, sannan ruwanki ne ki bari ki yi idda kuma ruwanki ne ki yarda a ɗaura auren a ranar da aikin ya afku, sannan Jidda in kin ce ya sake ta ba zai yi musu ba kuma in kin ga dama zaki iya barinta a gidan kike gana mata uƙuba!" Sosai ta ji daɗi sai murmushi suke dokawa ita da Amatullahi don sun dara jin ƙamshian nasara. Sun sanar da ita saboda taka tsantsan za su bari sai bayan kwana biyu Aliyar ta je gidan Jidda saboda kar su zargi wani abu, bokanya ta ce ko shekara ɗari za su yi babu matsala kawai dai a tabbatar Ibrahim ya yi amfani da cokalin. Dubu sha biyar ta karɓa kuɗin aiki Aliya tana jaddada mata sai sun dawo kawo mata gagarumar kyauta idan aiki ya ci!. Daga nan basu zame ko ina ba sai ƙyamis ta saya ƙwayar hana haihuwa pills don ta ce kar tsautsayi ya sa cikin Kasim ya shiga gwara ta fara planning don haihuwa sai a gidan Ibrahim. Ko da ta dawo gida Kasim bai dawo ba don haka ta samu waje ta ɓoye cokalin da take jin tamkar da bugun numfashinta yake rayuwa!. Bayan kwana biyu ta kira Jidda ta ce gata nan za ta kawo mata ziyara wai Kasim ne ya yi tafiya zai raka abokinsa wani gari ɗaurin auren yayan abokin kuma yance kwana zai yi don garin da nisa hakan ya sa ta ji kaɗaici ya ishe ta za ta je ta wuni, Jidda ta ji daɗi kuma bata kawo komai a ranta ba. Bayan ta je gidan Jidda wajen sha biyu na rana, suna ta hidimar girki tare Aliya tana maƙale da jakarta mai ɗauki da cokalin siddabaru. Har aka gama abinci bata ga Jidda ta zuba na Kasim ba kawai su Saude ta kwasawa a ƙaton fulas, ta ɗauka musu ita da Aliya. Suna cin abinci ta ce "Ni ina mai gidan kuwa" Ta tambaya gudun kar ta ce ina abincin sa din marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, nan Jidda ta sanar da ita yana office yance yana da aiki da yawa ba zai dawo ba sai ƙarfe biyar. Bayan sun yi sallar la,asar Jidda ta zauna ta yi azkar ɗin maraice kamar yadda take yj kullum safe da yamma domin kariya daga dukkan sharri. Bayan ta idar ta shiga kicin ta fara ɗora tukunyar tuwon shinkafa da mai gidan ya ce ta masa da miyar agushi Aliya tana falo a kwance tana ta charting ita kuma Jidda suna kicin ita da Saude sai Baba Kulu da ta zo ta yi goge -goge ta fita. Sai da ta kammala komai Saude tana taimaka mata da miƙa mata abin da ta buƙata na amfani. Bayan sun gama ta ɗora masa a kan dinning ta ɗakko plate da cokali ta ajiye da saving spoon ta bar Saude tana gyara kicin ɗin tare da wanke abubuwan da suka ɓata. Aliya ta ce a ƙoshr take ba za ta ci tuwon ba tun da basu daɗe da cin abincin ba, ranta dai fari ƙal tana murna don ta je ɗakko ruwa a frige ta hangi cokalin da aka ajiye masa sak wanda aka mata magani a jiki kenan ko ta sauya ba za a gane ba. Hatta Jidda sai da ta fahimci Aliya tana cikin farinciki. Lokacin da ya dawo Aliya ta gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska har yana tambayar Aliya mai gidan nata, ba komai ya sa ta saki fuska ba sai Jidda da ta masa magana ranar nan ta ce bata ji daɗin yadda ya amsawa ƴarnuwarta gaisuwa a daƙile ba, hakan ya sa ya karɓi kuskurensa shi kuma kawai ra,ayin Aliya ne ba ya yi. Sai da ya yi wanka ya shirya da kayan da ta fitar masa sannan ya ce ta zo ta ɗakko masa abincin a sama zai ci, a daidai lokacin Aliya kuma ta fito da cokalin tana shirin zuwa ta sauya sai kawai ta ga Jidda kamar an jefo ta hakan ya sa ta wayince bata sanin bata taki sa,a ba sai da ta ga Jidda ta ɗauki kwanon miya da plate mai ɗauke da cokolan ta haura sama da su. Har sai da ta yi ƙwallah don takaici, jim kaɗai sai ga Jidda ta sakko tana cewa bari ta watsa ruwa tana sanar da ita yanzu za ta fito sai ta fito ma za ta zubawa Ibrahim abinci hakan yana nuni da ba za ta daɗe a banɗakin ba. A can sama kuma bayan ta kai masa abincin sai ta samu ya buɗe system yana ɗan wani abu hakan ya sa ya ce kar ta zuba abincin bari ya ɗan kammala sai ta ce za ta sauka ta watsa ruwa sannan ya gama sai ta zo ta zuba masa. Aliya tana zaune jugum abin duniya ya haɗe mata goma da ashirin sai kawai ta hangi Ibrahim ya sakko da waya a kare a kunnensa yana cewa "Wallahi na manta shi gani yanzu zan duba amma dai kamar na taho da shi daga office, yana buɗe ƙofa ya fita Aliya ta tsam ta tashi tsaye gabanta yana tsananta faɗuwa da sauri ta yi hanyar bedroom ɗin da Jidda ta shiga ta je ta kara kunne a jikin ƙkfar ɗakin tana iya jiyo ƙaran ruwan da take wankan, da sassafa ta fara haura saman tana haɗa matakala biyu, don ta saka a ranta sai ta sauya cokalin nan a yau! Idan kuna comment tabbas za a ke posting a kan lokaci amma ku ci gaba da karantawa wasu suna yi wasu suna yin ɗifffff ni ma sai in ke ɗiɗifffff😃 MAMAN AFRAH . 09025576222 https://chat.whatsapp.com/DsxFGh957C5EvfrSjJDdgO?mode=wwt *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣2️⃣ ALIYA Da tsananin faɗuwar gaba ta ƙarasa hawa saman benen ko fargabar ɗaya daga cikinsu bata yi ya zo ya ganta. Sai da ta gama hawa ta je ta rasa ma wace ƙofa ce za ta buɗe inda za ta ga inda aka ajiye abincin ta canja cokalin tana rarraba ido duk ta rikice burinta kawai ta aikata abin da fa kawo ta sai dai bata san ya za ya yi abin ya tabbata ba tare da wata matsala ta biyo bayan hakan ba. A hanzarce ta yi hanyar ƙofar ɗaya ta tura ta shige saboda ƙarfin hali har da karo ƙofar sai dai kash sai bayan ta shiga ta gane ba ɗakin da take nema ba ne don babu alamar wani abinci a ɗakin.Da sauri ta fito tana ta tunanin rashin nuysuwar da take da shi wanda ya sa bata gane inda za ta shiga ba sai dai ta san dama ba za ta samu nutsuwa ba saboda kawai tunaninta ya ta,allaƙa ne ga samun cikar burinta wato canja cokalin ne kawai a gabanta wanda take tunanin daga shi burinta na duniya ya cika. Ɗaya ƙofar ta tura a nan ne wani farinciki ya baibaye zuciyarte, domin tana buɗewa ta yi arba da system da kayan abincin da Jidda ta kai sannan uwa uba cokalin da yake kan plate ɗin tabbas shi ne dai wanda bokanyan ta yi aiki a kansa, wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Aliya maimakon ma ta yi abin da ya kaita sai ta tsaya ta ƙarea ɗakin kallo tana ƙiyasta nan da wasu kwanaki da basu taka kara sun karya ba ɗakin zai zama ya dawo ƙarƙashinta wato ita take iko da shi. Ƙarasawa ta yi ta tsugunna a gaban plate ɗin ta saka hannu ta ɗauke cokalin kan plate ɗin ta ɗora na hannunta wanda ta zo da shi, sannan sai ta ɗaga bra ɗinta ta saka wanda ta ɗauke wancan ɗin. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta samun nasara. Baki ta taɓe tana tashi tsaye har hango ta take yi tana zuba ƙasaita sai motar da ta ga dama kuma ta yi ra,ayi za a ta shiga hatta dangi da ƴan uwan Ibrahim ɗin ma kansa sai sun dawo ƙarƙashinta. Dama Abba ne matsalarta to gashi an ce aikin da aka yi mai gabaɗaya ne wato kowa da kowa. A zuciyarta ta ce "Uhmm Aliya rufawa kanki asiri ki koma ƙasa ki zauna ki naɗe ƙafa kamar baki motsa daga wajen ba, tun da dai Allah ya ida nufi kin canja cokalin' Ta faɗa tana zuwa ta miƙa hannu za ta buɗe ƙofar, kamar abin almara kawai sai ta fara jiyo ƙaran takun takalmi alamar ana hayowa saman, idanu ta zaro ƙirjinta yana fatfat waiga bayanta ta yi tana jin faɗuwar gabanta yana tsananta a take ta shiga tunanin waye a cikinsu yake ƙoƙarin hayowa saman shin Jidda ce ko kuma shi mai gabaɗayan ne wato Ibrahim. A fili kuma a hankali ta furta "Na shiga uku asirina yana dab da tonuwa" Ta faɗa tana haɗiye wani yawu muƙut. Tunani ta fara shin idan Ibrahim ne ya same ta a ɗakin nan wane zargi zai yi mata da wane idon ma za ta kalle shi ko da a ce a saman ya same ta ba ma a ɗakin ba mai ya kaita ɗakinsa a lokacin da shi da Jidda basa wajen. A gefe ɗaya tana tunanin idan Jiddar ce kuma fa? Wace amsa za ta bata shin mai Jidda za ta ɗauka dangane da sauya akalar tsanarta zuwa tsantsar ƙaunar ƙarya da suka yi don kawai ta auri mai dukiya, tabbas ta san duk wanda ya yi ido huɗu da ita yanzu to haƙiƙa sai ya mata kallon tuhuma domin gabaɗaya alamomin rashin gaskiya sun bayyana ƙiri-ƙiri a tare da ita. Jin takun yana matsowa dab alama ce ta mai hayowar ya kusa ƙare tako matakalar da sauri ta koma ta shiga waige waige tana son gano inda za ta ɓuya ta gwammace ta kwana a ɓoye idan har hakan zai yiwu a kan a ganta zargi marar adadi ya hau kanta!. Abin da yake kai kawo aranta shi ne idan kuma Jidda ce dole ai za ta ga bata falon sannan komanta tana falon ita cw bata nan mai za ta ce mata kai abin ya haɗe mata goma da ashirin. Amma hakan ba zai sanya ta karaya ba don cikar burinra da na Ummarta ya fi komai a halin yanzu. Kaf ɗakin bata ga wajen da za ta ɓoye ba tare da an ganta ba hakan ya sa ta yi wajen drower za ta shiga tsakanin drower da bango ta takure ko Allah zai tseratar da ita kar a ganta, sai daj tana zuwa ta ga wajen ya yi mata kaɗan ta shige domin dole za a hango ta a kiɗime ta fito ganin babu mafaka sannan sirinta yana dab da tonuwa sai kawai ta buɗe ƙofar banɗaki ta shige tana shiga ta mayar da ƙofar ta rufe. Jikinta har karkarwa yake da ta ji an turo ƙofar ɗaki ta shiga fargabar sa sai take jin tamkar ko numfashi ta yi sai an ji. A ɗarare ta samu wata tula a jikin ƙofar ta leƙa taakar ɗakin gabanta ya bada sautin dimmmm ganin Ibrahim ne ya shiga a nan ta tabbatar kashin ta ya bushe domin ta san tun da ya dawo ɗakin dole Jidda ma ta yi wa ɗakin kutse. Yana shigowa ya ajiye wayoyinsa a kan gadon ya hau cire rigar jikinsa a take Aliya ta yi wa idanunta masauki a kan kyakkyawar lallausar fatarsa kasancwar ya bata baya nw yana juyowa sai da ta kusa zaucewa ganin kyakkyawan gargasa shimfiɗe a faffaɗan ƙirjinsa ya kwanta lifet kallon tsari na kyawun halittar da Allah ya masa kawai take a take ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin lallai Jidda ta more da samun kyakkyawa kuma nagartaccen miji kowacce mace ta samu miji irin wannan tana ganin a duniya an sallame ta ta wannn ɓangaren. Gaban ta ne ya buga da ƙarfi da ta yi wani tunani cewa ko dai wanka zai yi a take ta ji shagalar da ta yi da kallon nasa tana yaba kyawunsa ta ji ya ɓace mata yawun bakinta ya ƙafa ta ji bakin ya bushe. Jikinta ne shiga karkarwa tana hangowa cewa idan ya buɗe banɗakin ya same ta ya za ta yi tana cikin wannan tunanin sai ta ga ya juya ya nufi wajen drower ya buɗe ya ɗakko wasu kayan ƙanana ya saka coffe ɗin wando da wata farar riga mai hoton damisa coffe a jiki a hanzarce ya ɗauki wayoyinsa tana jin yana waya ya buɗe ƙofar ya fita. Bayanta ta juya ta jingina a jikin ƙofar bayan ta rufe idanunta tana sauke ajiyar zuciyar tsalllake rijiya da baya, yanzu abin da ya rage sai ta bari idan ya ɗan jima da fita sai ta fito ta lallaɓa ta koma falon ƙasa. A haka ta lallaɓo ta fito tana sauri sai da ta leƙa daga jikin ƙofar ta ga tana hango step ɗin na benen alamar Ibrahim ya fita sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta fito kamar wanda aka jefo Jidda haka Aliya ta hango ta gashi ta riga ta fito daga ɗakin har ta rufe ƙofae babu damar ta koma hakan zai sa Jiddar ta ji ƙaran ƙofa da hanzari Aliya ta ji gefen jikin bangon da yake gefe ta laɓe, haka Jidda ta hayo tana sanye da wata doguwar riga mai tattara a hannun wacce gabaɗaya rigar kamar an halitta ta a jikinta yadda ta kama jikinta dole kowane namiji mai lafiya ya kalleta ba zai iya ɗauke idanunsa ba sannan dole sai wani abu ya ɗarsar masa a zuciya, tana riƙe da fulas ɗin tuwon don dama na miyar ne ta kai da plate da cokulan. Addu,a take a zuciyarta kada Allah ya sa Jiddar ta waiwayo bayanta don tana juyowa za ta ganta sai dai Jidda da hankalinta yake a gaba bata waiwayo ba ta wuce tana takunta ta nutsuwa wanda gabaɗaya rigar da ta kamata duk takun da za ta yi sassan jikinta suna rausayawa. Tana tura ƙofar ta rufe ta nufi inda ya cire kayansa ya ajiye ta shiga linkewa za ta saka a kayan wanki don ita al,adarta ce kaya ko na wanki ne saj ta linkeshi. Aliya tana shirin kama gabanta ta sauka ƙasa sai kawai ta ji ƙaran takalmi ana hayowa sama, idanu ta zaro da sauri ta lallaɓa ta tura ƙofar ɗaya ɗakin a hankali ba tare da ƙofar ta yi ƙara ba ta shige ta rufo gabaɗaya ta haɗa gumi tana leƙowa ta hango Ibrahim yana hayowa, duk ta haɗe gumi na tsurewar da ta yi,. ta ji lokacin da ya tura ƙofar ɗakin Jim kaɗan ta ji an sake buɗewa sai ta fara jin maganarsa yana cewa "Ba jimawa zan yi ba ina ɗakko saƙon zan dawo na yi tunanin ma a mota na bar shi amma da na duba ban gani ba na san yana office" Sai ta ji Jidda cikin wata sassanyar murya mai tafiyar da nutsuwar miji tana cewa "Yanzu wannan tuwon da ka sa na maka haka zai yi ta jiranka" Ta faɗa ta karashe tana wani yin kamar ƙaramar yarinya ta ji lokacin da ya ce "Kin san dai wannan tuwo dole ne ma in ce ai har ɗumame zaki min da safe ko Jiddana?" Ya faɗa cikin sigar wasa da lallashi. Wani daɗi a cika ran Aliya jin yana batun cin tuwon sai kuma ta ji Jidda ta ce "To ni dai karka daɗe ka ji" Ya kalle ta yana dariya ya ce "Idan na daɗe tsallan kwaɗo za ki saka ni" Tana kumbura baki ta ce "Kuka zan yi" Hannunsa ya saka a bakinsa yana ɗorawa a kan laɓɓansa guda biyu ya ce "Karki yi min kuka da wannan idanun naki in ba haka ba zan rama da tsakiyar dare" Da hannu biyu ta rufe fuskarta tana jin yadda koyaushe son Ibrahim yake ƙaruwa a zuxiyarta saboda ya iya tafikar da mace ya san kalamai da ayyukan da zai yi mace ta so shi tabbas Ibrahim ya iya koyawa mace yadda za ta so shi. Aliya duk da bata ganinsu amma tana jin yadda tattaunawar tasu take gudana haka nan kuma ranta yana ƙuna da abin da suke faɗa, sai dai ta sa duk ihu ne bayan hari, sannan saura ƙiris tarayya da alaƙarsu ta zama tarihi babu abin da ya fi faranta mata irin da ta ji ya ce sai ya ci tuwon nan har da ɗumame da safe ai kuwa ta san shikenan burinta ya cika!. Tana jin yana mata sallama har yana cewa da dare za su je su gaishe da Mummy duk don ya farwntawa Jiddan tun da ya san tana ƙaunar Mummy ita ma Mummy tana ƙaunarta. Tana jin ƙaran saukarsa daga benen sannan ta ji lokacin da Jidda ta koma ɗakin ta rufo. Aliya tana maƙale a ɗakin a jikin ƙofa kamar wata ƙadangaruwa, sai da aka ɗan jima ta tabbatar yanzu Ibrahim ya bar falon ƙasa wato ya fita kafin ma ta gama wani tunani ta jiyo ƙaran buɗe get ɗin gidan haka ya bata tabbacin ya fita ma. Yanzu ne take so ta shammaci Jidda ta fito ta yi saurin sauka ƙasa tun da ta tabbatar yanzu Jidda ta san bata falon thn da ta fito ta ga bata ganta ba, saboda haka dole ta tanadi hujjar da za ta kare kanta da ita duk da wannan ba matsalarta ba ce a halin yanzu matsalarta ta fi karkata ga sauka daga saman wannan kafin asirinta ya tonu. Juyawa ta yi tana kallon ɗakin da take ciki tana ƙiyastawa a ranta yanzu haka Jidda gyaran ɗaki take ta san kuwa abu ne mawuyaci ta kasa shigowa ɗakin da Aliyar take ta gyara. A zuciyarta ta ce "Uwar shegiyar tsaftar jaraba, dama wannan bata dace da ƴan aiki ba ni ce na fi dacewa a kawowa ƴan aiki wannan kalar ma,aikata ce ba kalar hutu ba ma,aikatan ma ƴan wanke-wanke' Ta faɗa tana jan ƙaramin tsaki. Cikin sanɗa ta buɗe ƙofar a hankali ta mayar ta rufe ta fara lallaɓawa tana takawa a hankali sai da ta je tsakiyar benen kawai ta ji ta yi wa ƙafarta masauki a cikin lema, kafin ta tantance sai ji ta yi suuuuuu ta yi wata uwar sufer da ta ganta zaune jaɓar tana gangarawa bata yi masauki ba sai a step na ƙarashe jin ƙaran buɗe ƙofa a sama ya sa ko hutawa bata yi daga gangarowar ba ta tashi da sassarfa ta tashi jin ƙugunta ya riƙe ta miƙa hannu ta riƙe tsantsa tana takawa dakyar da sauro ta yi tsakiyar falon Saude da take haɗa kayan wanke wanke a kicin tana ganin abin da yake faruwa a idonta ta shiga dariya marar sauti har da riƙe ciki. Aliya kuma sai ta shiga sauri-sauri gudu-gudu ta yi hanyar ɗakin da yake kusa da wanda Jidda ta shiga yin wanka, tana wani cangala ƙafa kamar kwaɗo, don tafiyar kamar tsalle haka take tana shigewa ɗakin ta rufo. Saude kuwa har lokacin tana ta dariya duk da bata san dalilin da ya kai Aliya saman ba amma kuma dai ta san ba wani abin kirki ba ne tun da babu yadda za a yi take sauri tana son guduwa alamun bata so a ganta duk da faɗuwar da ta hanga ta yi daga saman benen amma ko fatsarwa bata yi da jin ciwon ta tashi tana tafiya kamar wata sabuwar yar shayi tana tale ƙafa tana riƙe ƙugu ga wani ɗan tsalle da take tana cangala ƙafa. Akiya tana shiga ɗaki kawai sai ta kwanta a ƙasa sa,arta ɗaya ma kafet ɗin ɗaki da yake da laushi sosai, birgima take tana ambaton wayyo a hankali ji take kamar ta yi ihu amma babu hali don gwiwar hannunta ma da ta bugu ciwo take mata. Haka ta daure ta shiga banɗaki ta wanke ƙafa sai fuskarta ta fito sai da ta ɗan ji jikin nata ya ɗan koma daidai ta buɗe ƙofar ta fito tana ƙoƙarin gyara ɗankwalin kanta. Jidda kuma tana ɗakin bayan ta ɗan ƙara ɗame gadon duk da shimfiɗar bata waji ɓaci ba. Dama cikin zannuwan gadon da Mummy ta aiko mata ranar nan ne wanda ta ce a wajen MAMAN AFRAH marubuciya ta saya domin babu abin da bata sayarwa, guda huɗu ta bata zanjuwan gadon da mai haɗe da labulaye da mai bargo sai mai filo huɗu dukka na ɗinkawa ne sai kuma wani lumtsumeme shi kuma na kamfani ne. Sun yi kyau sosai don da ta kira Mummy tana mata godiya sai ta ce za ta bata lambar MAMAN AFRAR ko za ta saya wani abu saboda kayanta suna da inganci tana siyar da labulaye zannuwan gado, takalman yara da manya, kayannyara ɗinkakku da na kamfani mayafai atamfofi lace abaya hijabai tutaren wuta, magungunan mata maganin sanyi, kayan sanyi, kayan kicin da sauransu. Tana cikin gyarawar ne ta ji rigif alamar faɗuwar wani abu dalilin da ya sa ta fito kenan sai dai abin mamakin tun daga can saman take waige -waige har ta zo ƙasa bata ga alamar komai ba, sai dai ta ji ta taka lema da bata san ya aka yi hakan ta faru ba. Tana zuwa tsakiyar falon hakan ya yi daidai da zuwan Aliya ma sai kawai Jidda ta kalle ta ta ce "Wai ina kika shige ne ni wallahi na ɗauka ma fita wajen kika yi ko saƙo aka kawo miki" Tambayar nan ta sake saka Saude a shakku don yanzu ta ƙara tabbayarwa Jidda bata san da zuwan Aliya sama ba, hakan ya sa ta fara hasashen dama ko sho dalilin da ya saka ta taho a gaggauce har tana faɗowa daga matakalar, don dama ita ta taho daga ƙofar da take sada ta da falon Jidda idan aka taho daga ɓangaren su na ƴan aiki lokacin sa ta yi wa falon tsinke ta hangi wulgin Aliya ta yi sama to duk tunaninta Jidda ma tana saman, sai bayan tana kicin kuma ta ga fitowar Jidda daga ɗaki ita ma ta zo ta nufi saman, don ta ji lokacin da Jidda take cewa Aliya ina ta yi kuma. Dama ita Saude tana zargin Aliya da wani abu na rashin gaskiya don yanayin da ta ganta ranar nan a kicin ma rashin gaskiya ne ɓaro ɓaro iya nazari da tunaninnta tana ganin tsantsar tsana da kuma ƙyashi a idanun Aliya da take yi wa Jidda. Da gangan ta ɗauki ruwa ta je ta zuba a matakalar don ta san tun da har Jidda bata san ta hau saman ba bayan a can turakar mai gidan take to ta san tabbas akwai wata maƙarƙashiya. Shi ya sa ta zuba tuwan domin ta san tun da Jidda ta hau samn to Aliya za ta yi ƙoƙarib kuɓuta, bayan ta zuba ne kuma ta ga Ibrahim ya dawo ga hau saman tana ta addu,ar Allah ya sa kar ya ga ruwan ko kuma ya taka, duk da ma akwai takalmi a ƙafarsa ba lallai santsin ya kwashe shi ba, bayan ya fito ne kuma sai ta ga ma yanayin yadda Aliya ta taho kaɗai ya isa ta gangaro idan ta samu kufcewar take matakala sai kuma Allah ya sa ta taka ruwan ta faɗo. Ta so a ce Jidda ta ganta sai dai kash an samu akasin lissafi. Amsar da Aliya ta ba Jidda ya ƙara saka Saude a tarkon mamaki domin cewa ta yi "Dama na san idan baki ganni ba sai kin tambaye ni cikina ne ya hautsina min, ganin kina banɗakin wancan ɗakin shi ne na je na shiga na wancan ɗakin" Ta faɗa tana ƴar dariya Jidda ma dariyar ta yi ta matsa kusa da Aliyar ta ce "Ki ce rage ciki kika tafi, Allah sarki har na tuna rayuwarmu ta yarinta idan na je gidan Umma daga na ce ina jin kashi sai ke ma ki ce kina ji, in riga ki shigewa banɗaki kike ta cewa in yi sauri karki yi a wando" ,Ta faɗa tana dariya sosai, Aliya ma daeiyar take duk da hannun Jidda da ya taɓa kafaɗarta ji take tamkar an ɗora mata garwashi saboda tsantsar tsanar Jiddar da take ji amma babu halin nunawa. Aliya ta ce "Umma sai ta ce ku dama kamar ƴan biyu ɗaya ba zai yi abu ba sai ɗayan ma ya ce zai yi Allah na tuba kashi dai ba a matse shi ba sai a ce ana ji idan ɗaya ya ce zai yi wa ya sani ma ko da kanku kuke ƙwaƙulowa" Aliya ta maimaita maganar cikin kwaikwayar muryar Umma suke dariya. Kan kujera suka ƙarasa har lokacin hannun Jidda rataye a wuyan Aliya kamar yadda suke dafa kuna lokacin da suke yaran, Jidda tana jin wani daɗi da farincikin ganin sauyawar rayuwarta a ƙanƙanin lokacj, wato a da ta rasa duk kulawa da soyayyar ƴan uwantaka da ta ƙawance tsakaninta da Aliyarta uwa uba tsantsar tsana daga Umma amma yanzu gashi komai ya shiga littafin tarihi. Suna zama Jidda ta ɗauke hannunta tana cewa "Ni wai har alwala kika yi ne " Ta faɗa ta sigar wasa dariya Aliya ta yi don dama da gayya ta wanke ƙafa da fuska don ta cirewa Jidda shakku a kan cewa daga banɗaki take sai da ta gyara ɗaurin ɗankwalinta ta ce "Kawai dai fuska tw ce na wanke" Saude an barta da tsantsar mamaki tana tunanin makirce da ƙarya irin na Aliya hakan yansa ta ɗarsa zargin akwai wani abu da ya kai Aliya saman wanda kuma bata jin alkaiti ne don ta san dai ai Aliya bata ce zuwa ta yi kawai don ta ga saman ba idan har ganin saman take son yi ai ba sai a ɓoye ba sai dai za ta yi amfani da hankali da basira don ta gane inda Akiya ta dosa sannan ta yi alƙawarin duk wani abu da Aliya za ta yi ga uwar ɗakinta Jidda to ba za ta bari ba matuƙar tana numfashi sai dai abu wanda yake dama Allah ya rubuta a littafin Jidda wanda yake ƙaddara ne ita kuma ƙaddara duk runtsi babi mai guje mata. Ƙaran wayar Aliya ne ya katse tana ɗago wayar ta ga sunan Kasim dimm ta ji faɗuwar gaba don bata san dalilin kiran ba, sai kuma ta maje don kar Jidda ta fahimci wani abu tun da dai ta faɗa mata baya gari duk da shi bata faɗa masa za ta fitan ba sai kuma wani tunani ya faɗo mata tana jin Allah ya sa tana ɗaga wayar ta ji muryar wani daban wato a ce mata mai wayar sun yi haɗari ya mutu, shikenan ta jefar da kwallon mangwaro ta huta da ƙuda. Tana ɗagawa ta kara a kunne tare da yin shiru tana jiran jin labarin mutuwar Kasim Sai ta ji muryar wani yana cewa "Ai abin babu kyan gani gabaɗaya babu wanda ya tsira a motar duk sun mutu" Aliya bata san lokacin da ta ce "Alhamdulillahi ba" Don tsabar son ta ji sanarwar mutuwar Kasim bata gane cewa wani ne a gefe yake maganar ba, ba wai a wayar da aka kira ta ake maganar ba, Jidda kuma idanu ta zuba mata jin ta jero hamdala. amma sai ta ji muryarsa rangaɗaɗau yana faɗin "Hlo Aliya tawa mai aka samu ne na alkairi ake hamdala haka" ,Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare ta har sai da Jidda ta ga ɓacin rai ya bayyana a fuskarta sai kuma ta ƙirƙiri murmushi ta ce "Kawai dai jin muryarka kana lafiya shi ya sa na yi hamdala, tun ɗazu nake son kiranka in ji ya hanya sai nake sha,afa" Kasim ya ce "Hanya Alhamdulillahi ai gamu nan mun kusa zuwa ma ashe ma garin ba wani nisa ne da shi sosai ba kuma mun samu lafiyayar mota don ana ɗaurawa ma muka juyo ki dafa min jallof na taliya mai ruwa ruwa" Aliya ta amsa da to ba don ranta ya so ba kuma gashi a kan kunnen Jidda ya ce ta masa girki, gashi tana son cikar burinta wato ganin Ibrahim ya ci abinci da cokalin da bokanya ta gama asircewa. Tana sauke wayar ta ce "Kin ji wai ya taho ma yana faɗin in masa girki gashi la,asar lis ma ta yi" Jidda ta ce "Ya fasa kwanan kenan" Aliya ta ce "Eh ya fasa kawai ina hira da ƴar uwata zai katse min " Ta faɗa cikin kissa Jidda tw ce. "Ai ni ma zan kawo miki wuni" Aliya a fili ta ce "Amma ranar da na ji daɗi" Ji A zuciyarta ta ce 'Yarinya daga yau za ki yi bankwana da kwanciyar hankali da nutsuwar da har za ki yi tunanin kai wa wani ziyara" Jidda ta ce "In sha Allah" Ɗan ƙaran ƙofar kicin ne da Saude ta buɗe ta fito don dama a karawa ta yi take tsegumin da take yi shi ya ankarar da su da akwai mutum Jidda ta juya ta ce "Saude dama kina kicin?" Saude ta.ce "Eh ina ciki ina ware kayan saman kanta da suka yi ƙura ina gogewa ina jera su" Gaban Aliya ne ya faɗi ta fara tunanin shin tun yaushe Sauden take kicin? Ba dai tana kicin ta faɗo daga saman bene be? Ko dai lokacin da ta shige ɗaki ta shiga bamɗaki tana wanke fuska ta zo ta shiga, gaban Aliya ne ya faɗi don ta ji yanayin yadda aka buɗe ƙofar kicin ɗin bai yi kama da cewa ƙofar a rufe take ba ya fi alama da dama ƙofar ba a rufe take duka ba. Kallon tuhuma ta fara jifan Saude da shi bayan ta fakaici idanun Jidda, ita dama ta tsani Sauden nan don ta lura ruwan munafukai ne da it, ita kuma Saude sai ta ɗauke idanunta ta fara takawa za ta bar falon don ko alama bata ma nuna ta san Aliya tana aika mata saƙon harara ba. Ta kama hanyar fita sai ta ji Jidda ta ce "Saude zo ki bamu kunun gyaɗa" Da to ta amsa ta juya ta shiga kicin ɗin, ita kuma Jidda sai ta ce tana zuwa ta tashi ta shiga ɗaki jin wayarta tana ƙara, tana shiga ta ga Salama ce suka ɓige da hira. A falo Aliya ta tashi sai ta sunkuya za ta ɗauki jakarta, a daidai nan Saude da take ɗauke da kofuna biyu da cokali a cikin kowanne ta zo za ta ajiye kawai sai idanunta ya sauke a ƙirjin Aliya nan ta hangi cokali kane-kane a cikin bireziyar Aliya, idanu ta zaro gabanta yana faɗuwa da sauri ta kawar da idanunta ta ajiye kufunan ta juya za ta bar wajen daidai nan Aliya da ta ɗauki jakar tata ta ɗago cikin kaushin murya ta ce "Keee!" Amma Saude ko gizau bata yi ba bare ta juyo ma ko nunawa bata yi akwai wata halitta a wajenta ba ta yi tafiyar ta tana dab da shiga kicin Aliya ta sake cewa "Ke Saude aba da ke nake magana ba" Juyowa ta yi cike da nuna rainin hankali ta ce "Au wai dama da ni kike? Ai na ji kin ce kee ni kuma da aka yanka rago Saude aka raɗa mini" Ran Aliya ne ya ɓaci hakan yansa ta yi jifa da jakar a kan kujera ta nufi Saude a fusace tana zuwa ta damƙi rigar Saude daga kafaɗa ta ce "Ke ni kike faɗawa hakan?" Saude ta yi shiru batance komai ba don dama fitsararriya ce ta ajin ƙrshe don ta ga aiki take shi ya sa bata zaƙewa. Aliya ta kalle ta cike da tuhuma ta ce "Tun yaushe kike cikin kicin" A fili ta ce "Lokacin da Aunty Jidda ta dafa kafaɗarki kuna tsaye a can lokacin ne na zo na shiga" Ta faɗa tana nunawa Aliya inda suka tsaya ɗazu sai Aliya ta ji daɗi don hakan ya nuna bata ganta ba a zuciyarta ta ce 'Tun lokacin da kika haye sama' A daidai nan Jidda ta fito daga ɗaki sai Aliya ta ƙirƙiri dariya tare da sakin riƙon da ta yi wa Saude ta ɗan buga kafaɗar Sauden da wasa tana cewa "Kina birgeni Saude" Saude ganin barikin da Aliya ta yi sai ita ma ta yj dariya tana cewa "Na kuwa gode Aunty Aliya bari na kawo muku sugar" Juyowa ta yi ta dawo falon Jidsa tana riƙe da wayarta tana dariya don ita sai ta ga sun birgeta tana ta mamakin sakkowar Aliya yanzu ta zama mai sauƙin kai sai take ganin hakan ne ya dace domin dama duniyar kanta nawa take da mutum zai ke ɗagawa da girman kai. Ko da ta kawo musu sugar suka sha kunun Aliya ta ce tafiya za ta yi Jidda ta saka direba ya kaita gidan, tun da ta san Jidda ta ji Kasim ya kira ya kusa dawowa sannan kuma tun da bata faɗawa Kasim ta fita ba duk da ta san idan ma ya san ta fita ɗin ba wani abu zai mata ba amma kuma dai tun da lallaɓawa take ta samu cikar burinta za ta daure ta kuma cije!. Ta haɗa mata sha tara ta arziƙi tana cewa sai ta kawo mata nata wunin, ko da ta rako ta bakin motar bayan ta saka dogon hijabia sai Aliya ta ƙame a gefe ta ce direba ya fito daga mazaunin direna ya buɗe mata haka ya fito ya buɗe ta shiga ya rufe wani daɗi take ji lalai mulkar wani akwai daɗi dole ta baza iko iya iko idan ta karɓi ragamar gidan Ibrahim. Da suka zo wucea mai gadi ya buɗe musu get sai da ta buɗe glass ta wurga masa uwar harara. Ana kiran magriba direba ya kaita ƙofar gidanta ya buɗe mata ta fito tana wani shan ƙamshi tana riƙe da ledar da Jidda ta bata wanda bata ma san mene ne a ciki ba sai kuma jakarta, tana jin ranta fari ƙal don ta yi aikin da ya kaita gidan. Tana shiga suka ringa waya da Amatullahi suna ta murna Amatullahi har da guɗa Aliya za ta zama matar manya, sai dai kuma sai ta ji tana baƙincikin cewa Aliya ta yi aure ta barta a gida sannan yanzu za ta ƙara yin wani auren ta shiga gidan arziƙi ita tana nan samarin kullum ta ce su fito sai su fita da gudu. A gidan Ibrahim yana shigowa gidan shi ma ana kiran magriba alwala ya yi ya wuce masalaci, lokacin da ya dawo suka haura sama ya ce Jidda ta zuba masa abincin haja ta zuba masa yana cewa "Idan na cinye sai kin ƙara mini domin kin san ina son tuwo" Dariya ta yi ta ce "Ai idan ka cinye na fulas ɗin ma sai a ƙaro maka a kicin" Dariya ya yi ya ce "Mai kika sanya mini idan na cinye?" Tana kallonsa ido cikin ido ta ce "Mai kake so in sanya maka kuɗi ko mota?" Ɗan ɓata rai ya yi ya ce "Kuɗi abin so ne, saboda da su ne ake abubuwa na rayuwar yau da kullum, mota kuma wani abu ne na ƙawa a duniya sai dai ba dole sai da ita ake rayuwa ba, kamata ya yi ki saka mini abu mai muhimmancin da ya fi wannan" Da alamar mamaki take kallonsa ta ce "Kamar me?" Kafe ta ya yi da idanunsa wanda take jin suna yawo a duka jikinta tamkar yadda jinin jikinta yake zagayawa a cikin jijiyoyinta ya ce "Jiddarh,?" Ta ce "Na'am" Ya ce "Kamata ya yi ki bani kyautar kanki ina nufin ki saka mini kanki a cin abincin nan sai na fi ci da yawan da zan baki mamaki" Wani murmushi ne ya ƙwace mata wanda bata yi zato ko tsammani ba ta ce ",Banda abinka ni dama ai taka ce" Hanunsa biyu ya miƙa ya tallafo gefen fuskarta ya ce "Na sani Jidda dama ke tawa ce amma ki ce za ki rayuwa da ni za ki kasance da ni rayuwa ta har abada, za ki zauna da ni a runtsi da duk wuya, duk halin da na tsinci kaina ba za ki taɓa guje min ba Jidda, da ke nake rayuwa kr ce sanyin idaniyata na faɗawa Mummy ke ar aljanna ce Jidda na faɗa mata in har miji ne yake ɗaga ƙafa matarsa ta shiga aljanna Jidda ki saka kanki cikin sahun matan aljanna, aljannar ma firdausi" Ƙwalla ce ta taru a idanunta kafin ta cika idanun sai kawainta gangaro saman kumatunta da sauri ya saka manyan yatsunsa ya goge hawayen don ba ya son ganin kukan Jidda. Muryarsa ce t bayyana cikin rauni ya ce "Mai ya sa kike kuka Jidda? Wallahi ba na son zubar hawayenki" ,Ƙasa ta yi da idanunta don ta ga damuwa ƙarara a fuskarsa sannan idanunsa sun yi ja, tana ta tunanjn duk da ana cewa a farkon aure ana bada kulawa da nuna damuwa sai tafiya ta yi tafiya zama ya yi zama sannan zaman ya koma zaman haƙuri amma gaskiya a yadda Ibrahim yake nuna mata soyayya da kulawa bata jin har iya numfashin sa zai canja mata. Muryarta tana rawa ta ce "Na ji kana min kalamai ne wanda suke nuna kamar kana mini ban kwana ne tamkar dai kalamai ne masu alamta kana mini sallama sai dai ban san wace irin sallama ba ce" Murmushi ya yi don kauda damuwar fuskarta wacce har ta sa ta zubar masa da hawayenta ya ce "Kawai dai ina nuna miki girma da muhimmancin Jidda a rayuwar Ibrahim ne" Ɗagowa ta yi ta kalle shi ya gyaɗa mata kai alamar gaskata maganar. Idanunta ta juya ta ce "Muhimmancinka a zuciyar Jidda tamkar alaƙar gangar jiki da numfashi ne, idan aka cire rai a jikin gangar jiki to gangar jiki ta zama gawa ba za ta amfanu ba sai cikin ƙasa wato kabari haka kake da girma a zuciyar Jidda" Yana kallonta shi ma ya ce "Allah ya dawwamar da soyayya da ƙaunar junana har abada ina fatan na riga ki barin wannan duniyar domin idan kika fara tafiya Allah ya sani ni dai rayuwata za ta tagayyara ne" Jidda ta ce "Ni ma hakan take" Hannuwansa ya ɗauke daga fuskarta ya mayar wuyanta tare da kai fuskarsa ya ɗora goshinsa a kan tana goshin hancinsa yana kan nata hancin ya ce "Tare za mu rayu kuma tare za mu mutu, don sanarwar mutuwar ɗayanmu shi zai sa zuciyar ɗayar ta buga shi ma a take ya bi ɗan uwansa sai a sakamu a kabari ɗaya" Su duka suka ƙyalƙyale da dariya don wannan ne buri da fatansu kar ɗaya ya mutu ya bar ɗaya baka jin komai a ɗakin sai sautin dariyar su sannan ya koma ya zauna. Plate ɗin ta tura masa gabansa ya ɗauki cokalin yana gyara zamansa, gutsiro tuwon ya yi a cokalin ya ya saka miya tare d ambaton "Bismillah" Nufar bakinsa ya yi da tuwon sai dai ƙaran wayarsa ya katse masa Jidda da wayar take kusa da ita ta furta "Mummy ce take kira" Ta faɗa tana ɗakko wayar ta miƙa masa. Da hannun hagu ya karɓi wayar hannunsa na dama yana riƙe da tuwon a cokalin, ya danna ok tarw da kai wayar kunnensa. Kukan Mummy ne ya saka ya saki cokalin hannunsa tare da tashi tsaye yana faɗin "Mummy lafiya?" Jidda ma tsaye ta tashi gabanta yana faɗuwa ganin hankalinsa ya tashi... *Na muku promo na kayan maganin mata a zo a mini ciniki* 💃💃💃💃💃 *🎉 PROMO NA ƘARSHEN SHEKARA GA MATA! 🎉* *Ki bar tsohon shekara da matsala, ki shiga sabuwa da gyara!* Mun yi sabbin kaya don nuna soyayya da kulawa ga wanda suke son mallakar ɗaya daga cikin waɗannn abubuwan ko kuma duka. *Ga kayanmu masu inganci da kike bukata:* 1️⃣ *Maganin Matsi Gam-Gam* Don matsi 1500 maimakon 2500 2️⃣ *Maganin Sanyi* Yana kawar da dukkan nau’in infection da wari, ƙaiƙayi, ƙuraje rikicewar al,ada 2500 maimakon 4k. 3️⃣ *Sabaya 3 in 1* Gyara breast, hips sannan tana gyara jiki 5k maimakon 7k. 4️⃣ *Maganin Gyaran Breast* Yana ciko da breast, ga masu shirin yin yaye da kuma wanda breast nasu yake buƙatar gyara 3k maimakon 4500. 5️⃣ *Daka* Tushen ni’ima 1500 maimakon 2500. 🎁 PROMO NA MUSAMMA Ranar ƙarshe 31 ga Disamba, 2025 Ki gyara jikinki, ki faranta ran mijinki, ki shiga sabuwar shekara da armashi. 09025576222 https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣3️⃣ SADIYA Ta jima abin yana bata mamaki sai dai bata san wa za ta faɗawa ba ma tun da abu ne da vai taɓa faruwa da ita ba. Ta so ta tambayi Meenal mai ya sa ita akwai nepa a ɓangarenta ita kuma babu sai dai gudun abin da zai je ya zo ko kuma a bata amsar da za ta mata ciwo sai ta ja bakinta ta tsuke. Meenal kuma dama ta yi hakan ne don ta turawa Sadiya haushi amma abin mamakin sai ya ga bata ga ko alamar damuwa a fuskar Sadiyar ba bare ta kai ga furtawa hakan ya sa ranta ma ya ɓaci ta taso a fusace lokacin Sadiya ta fito ta ɗaurawa wata maƙocoyarsu curry da ta saya curryn nan mai kyau da kala ga ƙamshi wanda ta auna wajen maman afrah, hakan ya sa Meenal faɗin "Sadiya wai ni ke wace irin ishashshiya da mai ce? Wato saboda girman kai da nuna ɗagawa ke ba jinin sarauta ba amma shi ne koke zaune ɓangarenki babu wuta ko ki tambaya tun da ni ai gashi nan kina jin ƙaran TV a ɓangarena" Ta faɗa tana jifan cikin jikin Sadiya da wani mugun kallo. Matar ta lura da kallon tsanar da Meenal take jifan Sadiya da shi hakan ya sa ta jinjina al,amarin amma sai ta g Sadiya ta yi murmushi irin murmushin nan da ake kira da sa kishiya haushi, ta ce "To ai na ga ba zaman kaina nake yi ba zaman aure nake, sannan ke ɗinma zaman auren kike ni da ke babu wanda yake zaune a ƙarƙashin wani, don haka nake jiran shi wanda shi ne ginshinƙin gidan sai in ji ta bakinsa" Kallon ashe ke ma dai kin yj baki Mrenal ta mata kafin ta taɓe baki ta ce "To shiknan zan nuna miki ni nake iko da mijin da kike taƙamar kina zamansa kuma zan nuna miki ni ƴar halak ce matsawar kina son ci gaba da neman taro da sisi da firjinki dole ki biyo ta hannuna ko ki dawwama babu nepa a ɓangarenki" Tana faɗar hakan ta juya fuuuu rai a ɓace, sai matar nan ta ce "Sadiya ki yi haƙuri don Allah karki tanka mata, ki bari har Nasir ɗin ga dawo" ,Tana faɗar hakan ta ɗan dafa kafaɗar Sasiya sai kuma ta juya za ta tafj muryar Meenal ta katse ta da faɗin "To almunafunfun, dama ku ne baƙaƙen munafukan unguwa masu haɗa kishiyoyi faɗa saboda gulma da tsugudidi" ,Kallo ɗaya matar ta yi wa Meenal ta ce "Ke idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri don wallahi ni jna danne banza in lakaɗa miki na jaki in yi gaba" Bata jira cewarta ba ta kaɗa kai ta tafi don ta san ta turawa Meenal ɗin haushi. Matar tana fita Sadiya ta shige ɗakin ba tare da ta kula maganganun da take ta yadawa a tsakar gidan ba, duk da abin ya mata ciwo a ce tana uwar gida amma amarya tana neman yin iko da ita, amma dai mai haƙuri yana dafa ditse watarana har ya sha romonsa. Tun da ta shiga ɗaki take waya da chartong da samarinta har la,asar jefi ,-jefi tana yin baƙi su gaisa a tsaitsaye su tafi. Yanzh ta fara tunanin yadda za ta fara fita ci gaba da barikinta tun da dai yanzu zaman ya fara kankama ita kuma ta saba da bin maza tana ganin Nasir shi kaɗai ba zai wadace ta ba.. Sai dai gida ne ba ita kaɗai ba bata san ya za ta yi da Sadiya ba duk da ta san ba lalai ta kai ƙaranta wajen miji ba sai daj ido mudu ne. Lokacin da Meenal ta ji ƙaran motar Nasir da sauri ta ƙirƙiri kukan ƙarya har ya shiga ɗakinta ya ganta zaune a bakin gado ta takarkare tana ta sharɓar kuka hankalinsa ya tashi ya ma rasa ya zai yj sanann lallashin duniyar nan da kumambada baki ya yi amma ko gizau bata yi ba bare ya saka ran za ta amsa masa. Sai da ya sha fama kafin ta ce ",Tun da ƴan nepa suka zo na basu kuɗin nan suka yanke ɓanbaren Sadiya shi ne fa matar nan ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, baƙaƙen maganganu sai da na yi da na sanin zuwana cikin gidan nan har da wata maya da ta zo siyayya wurinta suka haɗu sika ci mini mutunci, wai baƙincikin san,a nake mata saboda ni ba na siyar da caass bare asss" ,Cike da mamaki Nasir ya ce "Ita Sadiyar ce da ɗanyen aikin wannan ita bata san albarcinki take ci a gidan nan ba ba don ke ba da tuni ta cikawa rigarta iska fa," Wani daɗi ne ya cika zuciyarta tana rayawa a ranta indai tuggu ne da kutungwila ai sai ta gane shayi ruwa ne. Meenal ta ce "Ina fa ta sani wai har da ce mini zaune gari banza ce ni wai ina zaman kashe wando bana sana,ar komai, wai Nasir ɗin ma ba ya jin maganata wai ban isa in saka kaki mayar mata da nepa ba" ,Nasir jin tana magana cikin muryar kukan da ta yi wa muryarta ado da shi ya sa ya miƙe zumɓur yana faɗin "Zo mu je ni ba na son munafurci" Tun daga ƙofar ɗakin Meenal yake kwaɗa mata wani mahaukacin kira, amma bata amsa ba tana jinsa dama riga take sakawa kasancewar jo ta yi rigar jikinta ta ɗame ta duk bata jin daɗin yadda ta kamata shi ya sa ta gwammace ta cire ta duka. Tana jin baloƙoƙon da yake amma bata tanka masa ba ko kiran bata amsa ba so take ya shigo ɓangarenta. Sai da ya kira sau uku a na huɗu ta amsan tana fitowa daga ɗaki ta samu kujera ta zauna a falon tana cewa "Shigo mana Baban Kalifa" Ransa ne ya ɓaci jin wai shi take kira ma wato ita ba za ta je ta zama ɓarjajjiya da mai. Fuuuu ya taho Meenal ta take masa baya domin so takr ta ga ƙwaƙwaf sannan tana so ta nunawa Meenal ita ce da gida ba Nasir ba. Yana shiga falon a faɗace ya ce ,"Yanzu kenan sai na zo ke ba za ki iya zuwa ba" Sadiya ganin Meenal a bayansa ta shigo mata ɗaki sa ta sauya akalar murya da ta fuskarta ta ce "Ayya sorry Baban Kalifana na taho zan zo sai kawai ƙafata ta riƙe shi ya sa na dakata" Ta faɗa tana kallallame murya don ta luta in bata zama ƴar bariki ba kishiya za take kissar haɗa ta da miji wannan yana daidai da kashe mata aure yanayin yadda ta yi magana sai ya ji zuciyarsa ta ɗan sauka, ba kamar lokacin da ya taho a fusace ba. Meenal ganin bai yi magana ba sai abin ya bata mamaki Sadiya ta yi saurin faɗin ",Sannu da zuwa ya kasuwa" Kawai sai Meenal ki ta yi ya ce. "Kasuwa sai godiyar Allah" ,Ya faɗa yana ɗan sassauta muryarsa Meenal jin zuciyarsa ta sauka ba kamar da ba sai ta karkata murya cikin ɗan jan hanci ta ce "Ni ma Allah zai bani abin yi Sadiya, kowa rabonsa yake samu kuma sana,a ma lokaci ne yadda Allah ya baki jari nima zai bani watarana!". Tana faɗar haka ta juya za ta tafi Nasir ya riƙo rigarta ya ce "Haba Mrenal ai zan yi mata magana" Sadiya kuwa tana tunanin maganar mai sai kuwa ya tsuke fuska ko kula Kalifa da yake faman kiransa bai yi ba ya ce "Sadiya a kan mai za kike mata gorin sana,a har kike cewa wai ita ce mai zaman banza" Kallon ni kika yi wa haka Sadiya ta yi wa Meenal sai dai kuma sanin tuggun mace ya sa ta ce "Ka yi haƙuri ni ban yi da wata manufa ba" Nasir ya haɗe girar sama da ƙasa ya ce "Ai in har dai nepa ce to ba za a mayar yanzu ba sai na nuna miki Meenal ma ta isa a gidan na kamar yadda kike matata haka take ita ma don haka ki kiyaye a kan Meenal komai yana iya faruwa" Ganin ya juya zai tafi Sadiya ta ce "Ina son magana da kai " Ya juya ya kalli Meenal da ta kashe masa ido ɗaya ya ce ",Ki faɗa a nan kawai don ko a bayan idanunta kuka faɗa tamkar a kan idonta ne don da ni da ota mun zama tif da taya" Meenal fakar idon Nasir ta yi ta aikawa Sadiya gwalo Sadiya kuma sai ta yi kamar bata gani ba don bata yarda ta nunawa Meenal cewa hakan ya mata ciwo ba. Danna ɗacin da ya ziyarce ta ta yi ta ce "Dama ina son zuwa gidan Noor ne gobe" Cike da mamaki ya ce "Kuma shi ne za ki faɗa min tun yanzu tun da dai ai na san ba yau za ki je ba... Meenal ta yi karaf ta ce "Ka san da yake yanzu bata da ranar girki shi ya sa da ta ganka yanzu ta faɗa maka don karka suɓuce mata ka san fa ko wayarta in kana ɗakina ba ɗagawa kake yj ba" ,Abin ya yi wa Sadiya ciwo duk da ta san ko ma mene ne ba laifin kowa ba ne illa na Nasir shi ya sa Meenal take ɗaukanta ba a bakin komai ba duk da ta san shi ɗin ma ba komai ba ce a wajensa. Ɗan murmushi ya yi ya ce "Kuma haka ne fa, gaskiya amarya da zafinki kika shigo fa" Meenal ta ce "Ai ƴan magana sun ce da zafi-zafi ake dukan ƙarfe ko ka ga laifina" Ya amsa mata da a,a suka ƙyalƙyale da dariya, wato sun mayr da Sadiya kamar wata mahaukaciya, hakan ya sa ta miƙe tsaye ta kalli Meenal tana nuna ta da yatsa cikin ɗaure fuska ta ce "Ki fitar min a ɗaki!" Meenal da mamaki take kallon yadda Sadiya ta haɗe rai hakan ya sa ta taɓe baki ta juya ta fita, tana fita Nasir ya juya zai bi bayanta Sadiya taku ɗaya biyu ta yi ta sha gabansa ya tsaya da mamaki yana kallonta tana hucin ɓacin raj ta ce "Duk abin da kuke mini a gidan bai isheku ba har sai kun biyoni har ɗakina khna ci mini fuska?" Ta faɗa tana kafe shi da idanunta. Ganinnya sha jinin jikinsa ya kasa furta komai ta ci gaba da faɗin "Yaushe rabonka da ka shigo ɗakin nan matsayina na matarka? Ni da ɗanka mun zama saniyar ware? Ka na ba amaryarka cimar da take son ci mu kuwa ko oho, hatta abincin da za a tsakura mana wanda va zai isa ba ake bamu babu mahaɗi sai dai no in nema, shin wnanan shi ne adalci? Allah cewa ya yi ku aura mata biyu biyu, uku uku ko huɗu huɗu in ba za ku yi adalci ba ku aura ɗaya, amma ka san ba za ka kwatanta adalci ba ka aura biyu ka zo kana tauye haƙƙin ɗaya? A zafafe ya ce "Ya isheki Sadiya wai yaushe har kika ga makwancina da kike daɗa mimi maganar da ta zo bakinki? Haƙƙin me na tauye miki? Idan har haƙƙin kwanciyar aure kike magana ke ba taimakonki na yi ba a wannan jikin naki kina fama da tsohon ciki za ki iya ɗaukan ɗawainiyar miji? Mai za ki iya taɓukawa daga wannan haƙƙin sai wanne aka tauye? Ita baka ganin sabuwar amarya ce komai za ta ɗauke ke kuwa ki ji da fama da kanki mana" Tsabar mamaki ma ta rasa mai za ta ce sai binsa da ido take ganin haka ya ce "Idan baki da abin faɗi zan tafi" Ganin ya juya tana shirin tafiya ta ce "Ita kuma nepar da aka ware ɓangarena aka yanke fa ko ita ma duk tana cikin tsohon cikin da nake ɗauke da shi?"Ta faɗa tana kafe shi da ido. Rasa mai zaj ce ya ce "Kuɗin wuta ne bakya biya ya kamata tun da kina samun kuɗi kike biyan wani kaso daga kuɗin nepa" Kallonsa take rana son tantance abin da yake faɗa cike da mamaki ta ce.. "In ke biyan kuɗin wuta saboda ina sana,ar firjin, shin nauyina ne na biya kuɗin nepa, duk abubuwan sa nake ɗaukan ɗawainiyar su wanda Allah bai wajabta mini ba har da witar nepa kuma? Shin baka san ko da a ce mace za ta tara kuɗin duniya misali a ce tana da miliyan ɗari mijinta yana da dubu ɗari shi ne zai ɗauki ɗawainiyar ta Allah bai wajabta mata ɗaukan ɗawainiyar kanta ba ko da ta fi mijin kuɗi sai dai idan ita ta ga dama bisa kyautatawa... Katse mata hanzari ya yi da faɗin "Dalla dakata malama wa,azi za ki mini? Wa ya ce ana buƙatar kuɗinki, ko an ce miki an lura ma da wannan taro sisin da kike samuto ke kika ɗauki wannan kuɗi ki riƙe babu mai neman komai a wajenki, sanann tun da baki da abin faɗa ni zan tafi" Ya faɗa yana juyawa ya fice daga ɗakin, Sadiya sai ta jiyo muryar Meenal tana faɗin "Baka dai amince a mayar mata da wutar ba?" Sadiya da sauri ta fito tsakar gidan ta gansu tana zuwa ta ce "Bai yarda ba ya ce sai ina biyan kuɗin nepa hankalinki ya kwanta?" Kawai sai ta ƙyalƙyale da dariya har da tafa hannu ta ce "Wannan ai tsakaninku ne kun fi kusa baki da haƙori ke ai uwar gida saraitat mata ce" Ta faɗa da gatse Sadiya ta kalle ta ta ce "Sau da dama ko in ce a koyaushe ana maimaita karin maganar CIWON ƳA MACE NA ƳA MACE NE, sai dai duk wannan furucin a baki ne kawai domin kiwa a zahiri CIWON ƳA MACE BA NA ƳA MACE BA NE saboda mata mu ne matsalar kanmu da kanmu, da a ce kowacce mace za ta yi tunani da dogon nazari a rayuwa da bata zama sanadin zubar hawayen ƴar uwarta mace ba, idan miji ne mace ƴar uwarki ce za ta yi sanadin samar da rashin zaman lafiya a tsakaninku, ko da kuwa ke baki tare mata komai ba, idan ƴaƴa ne duk da su babi ruwansu a kishin da take amma sai wata ta gurmata musu rayuwa ta kore ki daga gidan bayan ta yi silar fitarki sannan ba za ta riƙe miki ƴaƴan ba. Idan saurayi ne yake son ya auri wata macen da yake so uwarsa ce za ta yi uwa da makarɓiya ta hana wannan auren ba don koɓai ba sai don ita take iko da shi ko da ta bari an yj sai ta dawo ta sakawa matar ɗan nata ido mai ya mata mai yake mata. Idan namijin ne ƴar uqarsa ko mahaifiyarsa tana gani yana wulaakanta matarsa maimakon a bashi shawara ya daina a nuna masa muhimmancin iyali a,a sai dai a aara rura wutar kawai saboda ƴar wani ce ta kowane fanni mata mu ne matsalar kanmu da kanmu. Idan saurayi da vudurwa ne suke soyayya ata ce za ta yi ƙoƙarin janye hankalinsa ya koma gareta ya zaman ta yaudari waccan ta shiga halin ƙunci ko da kuwa ita wacce ta yi wwacen saurayin ba aurensa za ta yi ba... Meenal ce ta yi sanadin dakatar da Sadiya daga maganar ta hanyar ɗaga mata hannu Sadiya ta yi shiru duk da tana faɗar maganar ne daga ƙasan zuciyarta, domin kuwa ta san tabbas kaso tamanjn cikin ɗari ƴa mace ita take silar assasuwar faruwar qasu abubuwa domin ita shaida ce gashi nan tana ganin yadda mahaifiyar Nasir ta tsane ta sanann suke take zuga ɗan nata duk da sun san yana tauye ta amma ba za ta tsawatar ba sai dai ma ta ƙara nuna masa hanyar sa zai musguna mata, haka zalika su Husna su ma mata ne kuma suna mantawa watarana su ma za su je gidan auren basa tunanin a musu abin da suke yi mata domin faɗar ma,aiki S.A.W ma ne kama tudinu tudan duk abin sa ka yi sai an maka, haka zalika gashi nan abin sa Meenal ta mata duk da bata taka ta zubar mata ba amma ta zo tana zuga mijin a kan ya tauye mata haƙƙin ta. Meenal tana kallonta ta ce "Wannan damuwarki ne ke ya shafa ni bai shafe nj ba, ni idan zuciyata ta yi fess bani da damuwa a wajen miji zuciyar uban kowa ta yi baƙiƙƙirin" Tana faɗar hakan ta buga cinya ta juya ta nufi ɓangarenta Nasir ta take mata baya ko waiwayen Sadiyar bai yi ba, tana juyowa ta ga Kalifa a tsaye a bayanra ta ƙirƙiri murmushin yaƙe ta kama hannunsa suka koma ɗaki tana tunanin wannan abubuwan da ake mata ba komai ba ne domin ta san watarana sai labari sannan wani lokacin sai take ji a jikinta kamar idan da sauran numfashin ta za ta yi farinciki watarana!. Washe gari ko da ta tashi wayarta ma babu caji don yanzu ta saya wata wayar ba waccan wacce take amfani da ita ba ce, ko da safe da ta tashi suka yi kiciɓis da Nasir a tsakat gidan zai je kicin ɗaukan abu, bayan su Husna sun zo sun yi break fast Meenal ta tsakura musu kamar kullum sun tafi, ta bi bayansa ta tsaya a ƙofar kicin ɗin ganin bai fito ba sai ta shiga ta ce "Ina kwana" Ya amsa da lafiya" A taƙaice Ta ce "Dama ina so in tambaye ka nawa ne kuɗin nepar da za a mayar mini ka san ina siyar da abu ba na son kasuwar ta tsaya" Kamar ba zai furta komai ba ya juyo ya ce "To sai mai idan kasuwar ta tsaya? Ba taƙamarki kina samun kuɗi ba ke ma har kin yi bakin da kike kallon tsabar idanuna kina faɗa mini son ranki, to ki sani mayar da nepa ba yanzu ba ko da kuɗin naki sai kin gane muhimmancin wutar sannan da kike batun kasuwa shin kayan sanyin da kike siyarwa su kaɗai ne sana,arki? Ita kuma Meenal da bata siyar da komai fa? " Yana zuwa nan ya raɓa ta gefenta zai wuce sai ta tare hanyar a daidai nan Meenal da ta ji shiru bai dawo ba daga ɗaukan kofi da ƙaramar wuƙar cokali ta biyo shi, tana kwala masa kira kamar wani ɗanta, yana daga kicin ɗin ya amsa yana faɗin "Gani nan fa" Ita kuma dama tun da ta fito ta ji dirin maganar Sadiyar a kicin shi ne dalilin da ya sa ta ƙarasa domin ta yi alƙarin ta ringa yi wa Sadiya kissa da kisisina har sai ta fitar da ita daga gidan don tana so take watayawa a gidan samarinta na banza suke zuwa suna ɗaukanta sannan ma idan ya tafi kasuwa Nasir tana kawo su gidan suna holewa abinsu. Kicin ɗin ta ƙarasa Sadiya ta juyo ta kalle ta sanye take da wasu kayan bacci masu net riga ce mai siririn hannu kuma ko ciniyarta bata rufe ba, sai ƙaramin wandon rigar wanda kaɗan ya fi panta kanta babu ɗankunne kallo ɗaya Sadiya ta mata ta ɗauke kai saboda bai ma dace Meenal ta fito a haka ba idan shi mijinta ne ita duk da tana mace bai dace ta ganta a wannan shigar ba, uwa uba wannan idan gidan yarana ne zai ɓata tarbuyar yara domin ta ga sau tari sai namiji ya ƙara aure idan amaryar ta je gidan ta tarar da yara amma hakan ba ya hana ta saka kaya masu fitar da tsiraici a ganinta maijinta take yi wa kwalliya bayan kuma yaran suna ankare da komai, wasu ma hatta wata runguma da sumbata sai su yi wa mijin a gaban yaran wannan ba daidai ba ne yana ɓata tarbiya, su kuma mazan suna ganin ana yi ne don a faranta musu sai ya zamana basa ma iya yin kataɓus wajen hanawa ko dai don jin daɗinsu ko kuma don tsoron zuciyar amaren. Tana zuwa ta kama tsantsa ta ce "Wato ma cin amanata ake a kicinta" Cike da diriricewa Nasir ya ce "Amana kuma Meenal wace irjn cin amana" Tana ƙirƙiro ƙwallar kissa tare da yin muryar kuka ta ce "Daga ɗakko kofi da wuƙa za a yanka biredi shikenan ka ƙi dawowa ashe dai kuna kicin kuna cin amanata bayan ka san girkina ne" Sadiya kawai baki ta dantse da haƙori ita da ba a ma shiga ɗakinta mai ta ce sai ita ce har take da bakin magana bakin maganar ma sharri ne. Baki ya buɗe zai yi magana ta tari numfashinsa tw ce "Tun da na taho daga windown kicin na hangoku rungume da juna" Da sauri ya juya ya kalli Sadiya nufinsa Sadiya ta furta wani abu ma,ana ta musanta zargin da Meenal ɗin take yi sai ka ce ita ba matarsa ba ce. Ganin Sadiya ta kauda kai gefe bata ce komai ba sai ta shiga rantse rantse yana cewa ko yatsan Sadiya bai taɓa ba. Meenal ta ce "Wallahi ba zan yarda ba tun da dai haka ne sai dai ka kira a mata kicin ɗin langa-langa ni ta kwashe kayanta ta bar mini wannan kicin ɗin tun da dai idan ka shiga kicin bin bayanka take kuna cin haƙƙina" Ta faɗa tana sanya hannu ta rufe fuska tare da rushewa da wani kuka kamar an faɗa mata mutuwa. Cike da son ganin ya lallashe ta da gudun ɓacin ranta ya ce "Shikenan an gama yau za a buga mata kicin ɗin langa -langan sai ta bar miki wannan ɗin hakan ya miki" Kai ta gyaɗa tana share hawayen da ta kirkira. Sadiya da sauri ta kalle shi jin furucinsa tana kanne ido tsabar mamaki kafin ta furta wani abu ta ji Meenal ta ce "Ka ga daman kicin ɗin langa-langa ya fi dacewa da ita tun da a gawayi take girki ni kuma da nake amfani da cooker gas wannnn ne ya fi dacewa da ni"Ta faɗa tana fakar idonsa ta yi wa Sadiya gwalo tare da mata wani kallo mai alamta mu zuba mu gani. Kallon Sadiya ya yi ya ce "Bani hanya in wuce, sannan ki fito da duka abin da kika san mallakin ki ne daga kicin ɗin ki ajiye a gefe guda, daga an gama haɗa miki naki kicin ɗin sai ki mayar can" ,Yana kaiwa nan ya raɓa gefenta ya wuce, ita kuma Meenal ta saƙala hannunta a kafaɗarsa shi kuma ya saƙalo hannunsa wanda babu kofin ya riƙe ƙugunta suka tafi ɓangaren Meenal ɗin. GIDAN SU ZALIKA Gabaɗaya Mamy ta gigice hankalinta ya tashi ji take tamkar zai gushe mata domin abu ne da take gani tamkar ba a zahiri ba addu,a take a zuciyarta Allah ya sa mafarki take, domin sai hakan ya fi mata sauƙin rayuwa a ce wannan abin a zahiri ne. Juya kwallin take a hannunta tabbas pills ne, wato maganin hana ɗaukan ciki. Hannunta yana karkarwa ta buɗe kwalin ta ga duk an ɓalli maganin alamar an sha kenan wato an yi amfani da shi. A fili ta furta "Allazina iza asabathum musibatun ƙalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un"A take ta ji wasu hawaye masu zafi suna zubowa daga kwarmin idanunta zuwa dakalin fuskarta, kuka take sosai marar sauti ko ta ji sauƙin abin da take ji a ranta, yau ita ce da matsalolin gidan miji sannan mijinta ya yi watsi da ƴaƴansa tamkar ba ya raye, ya bar mata ragamar komai kuma duk da tana iya bakin ƙoƙarinta amma sai da aka fara samun tangarɗa a lamarin tarbiyar a fili ta furta "Ina godiya a gareka ya ubangiji da wannan jarabawar, ya Allah ka bani ƙarfi da ikon rungumar duk wata jarabawa da za ka jarabceni da ita, na san ka na ji kuma kana gani ya rabby ka kawowa baiwarka mai rauni ɗauki bani da tsumi bani da dabara" Ta faɗa tana rushewa da wani sabon kukan, ta jima tana kuka har sai da ta ji zuciyarta ta ɗan saki, duk da ta san abu ne mawuyaci wannan mummunan dafin ya fita daga zuciyarta amma dai tana fatan Allah ya yaye mata domin shi babu abin da ya gagare shi. Maganin ta je ta sanya a drower ɗinta, ta dawo ta ɗauki jakar ta mayarwa Zalika ɗakinta wace har lokacin tana ta shan bacci abinta. Da safe ta je ɗakin Zalika ta same ta ta fito wanka kana zaune gaban madubi tana shafa mai sannan ga kayan da ta fitar za ta saka a kan gado a ajiye. Ta rufe ƙofar ta je ta samu waje ta zauna bayan ta yi sallama Zalikar ta amsa tana cigaba da abin da take. Mamy ta ce "Zalika wajenki na zo ina son magana da ke" Zalika tana shafa powder ta ce "Ok Mamy" Sai da ta kammala ta zo ta saka kayantw sannan ta zauna a kusa da Mamy tana danna waya. Mamy ta ce "Bani jakar can taki zan yi wani abu" Gaban Zalika ya buga kasancewar ta san akwai maganinta a ciki kuma ba za ta so Mamyn ta gani ba. Tana ɗan nuna alamar tambaya ta ce "Mamy jakata kuma mai za ki yi da ite?" A nan ne Mamy ta ji wani abu kamar kibiya ya caki zucuyarta, domin kuwa hakan yana nuni da cewar maganin ne Zalika bata so ta gani, hakan yana nuni da cewar Zalika tana neman maza, duk da Mamy ta san a jakartw ta gani amma zuciya irin ta uwa gani take ba maganin hana ɗaukan cikin ba ne duk da ta san haka ne amma so takr ta buɗe idonta ta ga mafarki ne hakan zai zama mafi sauƙi ga ruhinta. Mamy tana danne abinda take ji ta ce "Mene ne a jakar da na ga kin razana? Ba handout ne da biro da wasu abubuwan amfani na makaranta ba, mene ne baƙo a ciki, ko kin manta tun kina nursary ne nake haɗa miki school bag ɗinki idan kin dawo ma ni nake adana miki ita yaushe abubuwan suka sauya kuma" Zalika tana ɗan diriricewa ta ce "No babu komai Mamy kawai dai ina sauri ne na je na yi break fast sannan ina da lacture ne ba na son na makara" Idanun Mamy suka cika da ƙwalla tana kallonta ta fito da kwalin hannunta da ta ɓoye ta buɗe tafin hannunta gaban Zalika ne ya buga da ƙarfi tana kallon kwalin hannun Mamy inda jikinta ya ɗauki karkarwa tana ƙoƙarin baɗa laɓɓanta don ganin ta ce wani abu sai dai gabaɗaya alamomin rashin gaskiya sun bayyana a gare ta a inda Mamy ta gama fahimtar cewa tabbas ba mafarki take ba Zalika dai ƴarta tallin tal guda ɗaya ƴa mace wacce daga ita bata da wata ƴa macen sai Mubin ita ce ta san namiji, namijin ma ba mijin aurenta ba namijin titi shin zarginta gaskiya ne ? Idan ba gaskiya ba ne da mai zalika za ta kare kanta? A take zuciyar Mamy ta shiga raya mata 'Lallai akwai aiki ja a gaban iyaye mata wajen sanya idanu a rayuwar ƴaƴansu yanzu a ce har yarinya tana iskanci a waje amma uwarta bata ankara ba, shin ina fitar budurci da ake gane cra wannan ne karo na farko da yarinya ta fara sanin ɗa namiji? Amma a ce uwa bata lura ba duk da kasancewata uwa mai sanya idanu a rayuwar ƴaƴana amma har abu ya yi nisa ban sani ba, kenan wayon ƴaƴan yanzu har ya kai su ɓoye abin da babba zai kasa ganewa! Mad about you Delina de merly My way intense Gucci guilty men Vanilla 28 kayali Khamrah I want choo Creed aventus Amber oud Sugar baby Club de nuit Olympea Stronger with you Reef 33 Dior sauvage 212 VIP man Blue de channel Pink shiffon Jadore Bombshell Pure seduction Versace bright crystal La vie est belle Versace Eros man *🎉 PROMO NA ƘARSHEN SHEKARA GA MATA! 🎉* *Ki bar tsohon shekara da matsala, ki shiga sabuwa da gyara!* Mun yi sabbin kaya don nuna soyayya da kulawa ga wanda suke son mallakar ɗaya daga cikin waɗannn abubuwan ko kuma duka. *Ga kayanmu masu inganci da kike bukata:* 1️⃣ *Maganin Matsi Gam-Gam* Don matsi 1500 maimakon 2500 2️⃣ *Maganin Sanyi* Yana kawar da dukkan nau’in infection da wari, ƙaiƙayi, ƙuraje rikicewar al,ada 2500 maimakon 4k. 3️⃣ *Sabaya 3 in 1* Gyara breast, hips sannan tana gyara jiki 5k maimakon 7k. 4️⃣ *Maganin Gyaran Breast* Yana ciko da breast, ga masu shirin yin yaye da kuma wanda breast nasu yake buƙatar gyara 3k maimakon 4500. 5️⃣ *Daka* Tushen ni’ima 1500 maimakon 2500. 🎁 PROMO NA MUSAMMA Ranar ƙarshe 31 ga Disamba, 2025 Ki gyara jikinki, ki faranta ran mijinki, ki shiga sabuwar shekara da armashi. MAMAN AFRAH 09025576222 https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣4️⃣ JIDDA Da matuƙar tashin hankali a tattare da ita take faɗin "Lafiya mai ya faru?" Ta faɗa duk ta diririce saboda yadda ta ga mijin nata hankalinsa a tashe. Bai bata amsa ba don hankalinsa yana ga wayar da yake amsawa sai ta ji yana faɗin "Gani nan Mummy" Yana gama wayar ya yu hanyar fita daga ɗakin cikin sauri lura da ta yi kamar hankalinsa ya bar jikinsa ta yi saurin riƙo rigarsa ta baya, tare da yin sauri ta sha gabansa suna fuskantar juna tamkar za ta saki kuka ta ce "Ina tambayarka ko lafiya amma shi ne baka faɗa min ba" Kallonta ya yi sai kuma ya ga ta bashi tausayi hannunsa ya kai ya shago gefen fuskarta ya ce "Ki yi haƙuri hankalina ne ya tashi, Mummy ce ta ce Daddy ya yanke jiki ya faɗi " Cike da tashin hankali ta ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ƙofar ya buɗe suka fito dagaɗaya ta ga ya fice a hayyacinsa, suna sakkowa ƙasa ya nufi hanyar fita Jidda ta ce "Ka jirani in ɗakko hijabina" Bata jira cewarsa ba ta yi hanyar ɗakinta sai gata ta ɗakko hijabi a hannu a falon ta shiga sakawa tana gama sakawa sai ta ga Baba Kuluwa riƙe da plates za ta shiga kicin ta buɗe baki ta ce "Baba zan fita za mu je gidan Mummy" Baba Kuluwa ta ce "Lafiy Hauwa'u" Jidda ta ce "Daddy ne ba ya jin daɗi" Fatan samun lafiya ta masa Jidda tana juyawa sai ta ga Ibrahim ɗin ba ya nan da sauri ta fita ganin ya bar ƙofar ma a buɗe. Ko da ta fita ta same shi har ya shiga mota, tana zuwa ta ce "Ka ba direba ya kaimu na ga kamar ba za ka iya tuƙin ba" Cikin sanyin murya ya ce "Zan iya" Bata sake magana ba ta buɗe ta shiga mai gadi da suke zaune suna hira da sauran ma'aikatan gidan ya tashi buɗe musu get kowa yana ɗaga musu hannu cike da girmamawa suka fita, gidan Mummyn suka kama hanya ko magana Ibrahim ba ya yi kasancewar jin muryar mahaifiyarsa da ya yi tana kuka a waya ƙaran wayarsa da take ajiye a gefe ne ya sanya Jidda ɗaukan wayar ta miƙa masa ganin sunan Mummy da sauri ya danna ya kara a kunnensa, ji ya yi Mummy tana faɗa masa sun tafi asibiti adirshin asibitin ta faɗa masa don haka ya juya kan motar suka kama hanya. Ko da suka zo asibitin sun je ɗakin da aka kwantar da Daddy yana kwance lifet kamar gawa sai likita da yake sanya masa ruwa a hannu Mummy tana zaune a gaban gadon ta kifa uban tagumi idanunta jajawur. Haka su ma suka tsaya suna ganin ikon Allah. Bayan likitan ya gama abin da zai yi sai ya ce da Ibrahim su je office suka fita aka bar ɗakin daga Mummy sai Jidda da take ta faman ba Mummy baki. Mummy ta ce "Jidda lafiyarsa ƙalau fa, babu abin da yake damunsa, muna hira kawai miƙewar da zai yi ya yanke jiki ya faɗi sumamme" ,Jidda ta ce "Subhanallah ki yj haƙuri Mummy in sha Allahu zai samu lafiya" ,Mummy tana share hawayen da ya gangaro mata ta ce "Allah ya sa amma na tsorata da lamarin nan, gaskiya rayuwa abin tsoro ce " A haka Ibrahim ya shigo direban gidan Mummy yana biye da shi riƙe da ledar magunguna sai kuma katan ɗin ruwan roba. Har lokacin Daddyn bai farka ba don dai yanzu numfashin sa ya dawo kawai dai bacci yake, Ibrahim ya ce zai je masallaci ya yi sallah direban ma dama yana ajiye ledojin ya fita Jidda ma sallar ta yi ita dama Mummy tana hutun sallah ne Wajen ƙarfe tara da rabi Mummy ta ce au tafi gida saboda Jidda sai Ibrahim ya ce zai kaita gidan ya dawo ita ma Jidda ta ce a asibitin za ta kwana amma Mummy ta ce a kaita gida.. Suna tafiya tana ta kwantar masa da hankali ga tausayinsa ya kamata, ko abinci bai ci ba ga rashin lafiyar Daddy mai gadi yana buɗe musu get ya shiga da motar mai gadi yana rufe get inda mai ba flowers ruwa ya taho da sauri ya zo yana ƙoƙarin buɗe masa motar cikin girmamawa amma sai ya dakatar da shi yana faɗin ba fitowa zai yi ba. Jidda ce ta juya ta kamo hannunsa ta sanya cikin nata ta matsa yatsunsa tare sa rausayar da kai ta ce "Annurin zuciyata idan fuskarka ta zama babu walwala sai na ji komai ya sare mini, sannan sai na ga gabaɗaya duniyar ta mini ƙunci tare da yi mini wani irin duhu" Iska ya fesar daga bakinsa ya riƙe sitiyarin motar da hannu ɗaya duk da ba tuƙi yake ba, ya saka ɗaya hannun da take murzawa ya riƙe nata gamgam ya ce "Ki bari har na dawo daidai Jidda yanzu damuwar Mummy da halin da Daddy yake ciki ya rufe komai amma ki sani zuciyata a buɗe take tana sane da ke sannan da ke take rayuwa" Kallonsa take yadda fuskarsa ta yi fayau ta ce ",Plss mu shiga ciki na haɗa maka shayi mai ɗan kauri ka sha" Kai ya shiga kaɗawa alamar ba zai sha ba, amma ganin ta shagwaɓe fuska sai ya ji yana so ya faranta mata hakan ya sa ya yi na,am sai suka fito a tare tana riƙe da hannunsa suka shige cikinm gidan, a falon ƙasa ta masa masauki a kujera ta nufi kicin ko hijabin bata cire ba, shayi ta haɗo masa ta ɗoro a ƙaramin kofin tamgaran da ɗan ƙaramin plate ɗin kofin ta zo tana juyawa da tea spoon. Ko miƙa masa bata yi ba ta shiga bashi a baki har sai da ta ga ya shanye tasss sannan ta ajiye a ƙasan kafet tsaye ya miƙe yana mata sallama ya juya zai fita yana dab da fita daga ƙofar falon ya juyo sai kuwa ta ƙarasa da sauri ya buɗe mata hannunsa ta shige ya rungumeta sannan ya yi kissing goshinta ya ce "Ni zan tafi sai Allah ya kaimu gobe" Amsa masa ta yi ya ɗaga mata hannu alamar bye-bye ita ma ta ɗaga masa ya fita. Tsakiyar falon ta koma ta aunkuya za ta ɗauke kofin shayin sai ga Saude ta zo ta karɓa ta je kicin ta wanke ta ajiye, ta fito sai ta ga Jidda zaune hakan ya sa ta mata ya mai jiki bayan ta faɗa mata da sauƙi sannan ta masa fatan samun sauƙi. Sama ta haura jim kaɗan ta fito da kayan tuwon nan bayan ta ɗauke cokali da tuwon da Ibrahim ya gutsiro zai ci lokacin da Mummy ta kirashi wanda kiran ya yi sanadiyyar rasa nutsuwar zuciyarsa sanadin rashin lafiyar mahaifinsa. Tana sakkowa ta yi kiciɓis da Saude hakan ya sa ta ba Saude kayan tuwon ta ce ta kai kicin, karɓa Saude ta yi Jidda tana komawa sama Saude ta shiga kicin har da rufe ƙofa ta tsaya ta ƙarewa tuwon kallo tana ganin gurbin da akamcire a jikin tuwon wanda da alama cokali ɗaya ne kuma ga gutsuren lomar nan a gefen plate ɗin, wata ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala don ta san akwai abin da Aliya ta yi a saman, wanda tana zaton hakan zai kasance wani abu ne ta barbaɗa a miyar tuwon sannan zarginta da take ta rayawa a ranta cewar cokali duk da ba za ta iya hasashen ainihin abin da ya yj silar ganin cokali a bra ɗin Aliya ba amma kawai ta gwammace ta salwanatar da cokalin haka ta juye tuwon duka da miyar a baƙar leda ta wanke kwanukan ta gyara kicin ɗin. Ta fita da wata doguwar wuƙa a hannunta da kuma ledar da ta sauye tuwo da miyar sai wannan cokalin. Sai da ta je garden ɗin gidan can tsakanin wata bishiya ta haƙa babban rami ta jefa ledar da cokalin ta yi addu,a ta mayar da ƙasar ta rufe wajen sai da ya yi kamar ba a taɓa tona wajen ba, sannan ta bar wajen tana jin wani shauƙi. Ko da ta yi shirin kwanciya ta saka kayan bacci pink colour masu laushi sosai ta shafa turare, ta hau gadon ta kwanta sai ta ji gabaɗaya ɗakin da gadon sun yi mata girma kasancewar babu tauraron zucuyarta Ibrahim. Filonsa da yake kwanciya ta janyo kusa da ita tana shaƙar ƙamshin turarensa tana jin tamkar tana kusa da ita tun da basu taɓa nesa da juna ba tun da suka yi aure. Daga ƙarshe ta ɗakko ƙafafunta ta sakko ƙasa ɗakinta ta nufa ta je ta kwanta a ganinta za ta samu sauƙi salama da sasaauci na tunanin Ibrahim da take ji tamkar shekara suka yi ba sa tare da shi. Aliya tun da ta gama waya da Amatullahi sai ta kira Umma tana sanar da ita cewa aiki ya kammala, Umma ta ringa rawa da juyi a ɗakinta tana jin daɗin yau sun hau turbar zama masu arziƙi. Ko da Kasim ya dawo shi kansa ya yi mamakin ganin yadda fuskarta take a washe bata sai wani nan nan take da shi, bai san cewa tana yin hakan ne don ta hango tsantsar wata dama da za ta samu a rayuwa. Indomie ta dafa masa yau don badangarci da hannunta take bashi a baki ba ma da fork ba. Gabaɗaya daɗi ya cika Kasim ya kalle ta yana murmushi ya ce "Haƙiƙa ni a cikin maza ɗan gata ne a wajen matata, matata tana sona!" Ya faɗa yana buɗe baki ta bashi indomie ɗin. A fili ta ce , "Idan miji bai zama ɗan gata a wajen matarsa ba a ina zai zama" Ta faɗa tana kallonsa. A zuciyarta kuma ta ce 'Wanda dai nake so da muradi yana can sai dai very soon zai dawo gare ni tabbas zan murza kan naira har sai ta tabbatar ta zo hannun da za a bata wahala" Suna ta hira har suka kammala don ita ko a bakinta ta ce a ƙoshe take wani irin farinciki take ji irin farincikin nan mai hana ka cin komai duk da dama bata tare da yunwa. Ko da suka zo kwanciya ma bayan ta sha maganinta a ɓoye na hana ɗaukan ciki tana rayawa a ranta cewa ta kusa daina shan magani da zarar ta auri Ibrahim za ta yi ban kwana da shan magani domin ta je inda za ta saki jiki ta haihu ta zubar da ƴaƴa yadda za su ci gado son ransu, tamkar dai sun ƙauro duniya. Ranar Kasim ya san ya yi aure domin kuwa zagewa ta yi ta nuna masa kulawa ta musamman a wajen mu,amala, sai ta sa yake jinsa na miji sak babu sirki kamar yadda ake kiransa mata maza. Duk bai san tsabar farincikin da take ciki ba ne. Washe gari da safe har ta matau ya fita ya bar mata gidan saboda tana son dara shirin barin gidan saboda ta san abubuwan da bokanya ta faɗa mata na cewa Kasim zai sake ta sannan za a rufe bakin Abba da duk wani ɗan tsurku da zai kawo tsaiko a lamarin. Yau Kasim shiga ya yi ta musamman son yau jinsa yake tamkar aabon angon da aka ɗaurawa aure a ranar, ko da ya zo mata sallama ma ya daɗe tana ta furzo mata kalaman soyayya tana amsa masa a fili amma a zucuyarta wani haushi ma yake bata. Yana fita ta doka wani uban tsaki ta koma ɗaki ta zauna tana duba waya don ganin lokaci so take ta kira ta tabbatar amma kuma ganin ƙarfe goma sai ta ba zuciyarta haƙuri a ɗan jima domin kar a zargi wani abu. Ahawara ta yanke ta kira Amatullahi ta ce "Ƙawata ya ne?" Amatullahi ta faɗa tana jiran kanun labarai duk da zuciyarta tana cike da zulumiin jin labarin tana jin babu daɗi don ta ita ma ta matsu ta samu miji ta yi aure ƴan unguwa sun ishe ta da tambayar aure da kuma masu faɗa mata magana a fakaice wato gorin aure tamkar dai a kansu take ko kuma su suke ciyar da ita da ɗaukan sauran ɗawainiyarta, mutane basa tunanin cewa shi aure lokaci ne idan har mutum bai yj aure to lokaci ne bai yi shi ma ba a son ransa ba, don wasu ƴanmatan ana sakawa suke jjn tamkar su kai kansu ɗakin miji saboda yadda ake nuna musu habaici da gorin auren, bayan auren nan ba farilla ba ne sunna ne kawai me ƙarfi. Wasu kuma in suka samu miji sai ɗagawa da girman kai su dole matan aure suke nunawa wanda basu yi auren ba tamkar su suka hana kansu auren. Aliya ta ce "Wallahi ni kaɗai na san irin farincikin da na kwana da shi, ai hatta Kasim ya dangwali albarkacin farinciki da nake ciki" Amatullahi ta ce "Shegiyar uwa sai bukka wato dai shi ala dole ya ɗauka faranta masa aka yi bai san abin ne hawan hawa ba,, to yanzu mene ne kanun labarai?" Ta tambaya cike da fargabar jin amasar tambayarta Aliya sai da ta yi wata dariya mai haɗe da shewa ta ce "Babu tantama kuma babu wani tunani tabbas na san aiki ya kammala saura abu ya dara aiki don a yadda na fahimta mutumin mayen tuwo ne kin ga kuwa ai tuni ya antaya tuwon nan cikinsa sauran kuma ya fara fuskantar mulkin mallaka daga gareni ke hatta Jidda wallahi sai ta gane ni asalin maƙiyarta ce don sai ta gwammace kiɗa da karatu domin matsawar na samu wata dama a kan Jidda wallahi sai na gasa mata aya a hanhu sai na sa ta wulaƙanta!" Ta ƙarashe maganar tana haɗe rai tamkar dariya bata taɓa kai ziyara fuakarta ba. Amatullahi ta ce "Kin min daidai ai wallahi kowa ya samu dama kar ya yi wasa da damarsa" Aliya ta ce "Ke dai bari ai abin yana min cuwo a ce Jidda ta mallaki abubuwan rayuwa ban mallaka ba wai har ni ce zan koma tamkar ƴar maula a wajenta wato tana ɗakko kuɗi ta bani wai ni Aliya kyakkyawa me aji da jiji da kai ni ce Jidda ta bani kuɗi wai da kuɗin Jidda na saya waya taɓɗi!". Sun jima suna tattaunawa suka yi sallama ta ce duk yadda ake ciki za ta sanar da ita. Tana kashe kiran sai kiran Umma da shigo ta ɗaga Umma jin muryar Aliya fess cikin shauƙi tun bata gama jin kanun labaran ba ta carara guɗa, ita ma Aliyar guɗar ta ɗauka kafin daga bisani suka ɗauki shewa kamar wasu sa,annin juna ba uwa da ƴa ba. Umma tana gyara ɗaurin ɗankwali ta maido da shi gaban goshi ta ce "Wallahi ba ke kaɗai ba Aliya hatta ni zan tsula tsiyata musamman idan aka rufe baki da ƙwaƙwalwar wanann uban naki, dama shi yake taka min birki yana hana ruwa gudu" Aliya ta ce "Bari dai Umma sirikar Ibrahim ai an buga an barki sai kin zama zakaran gwajin dafi a cikin sirikan masu kuɗi" Suna ta tattunawa suka yi sallama Aliyar tana faɗin bari ta kira Jiddar ta ji za ta zo ta kira Umma ta faɗa mata yadda ake ciki. Sunan Jidda ta kamo ta shiga kiranta, lokacin Jidda tana tsakiyar falon ƙasa tana sanya hijabin ta za ta tafi asibiti don har ta faɗawa direba kuma ta ji ya fito da motar jiran fitowarta yake, duk da sun yi waya da Ibrahim ya ce Daddy ya farfaɗo sai dai rashin ƙarfin jiki da kuma gefen bakinsa ma da ya ɗan karkace don yana da hawan jini. Sai ta ce za ta taho asibitin ya mata na,am don yana ta so ma ya koma gidan ya yi wanka amma ya kasa tafiya duk da damuwar Mummyn ma ta ragu. Saude ce sunkuye a gabanta tana jera kwanukan a cikin kwandon da za a tafi da abincin asibitin, Saude tana ɗauke da kwandon tana biye da ita sai ga Baba Kulu ta fito tana cewa ta yi wa mai jikin sannu amsawa ta yi cikin girmamawa domin tana ganin Baba Kulu tamkar uwa a gare ta saboda Jidda ta san muhimmacin furfura. Baba kulu ta juya ta koma tana ci gaba da abin da take yayin da wayar Jidda ta shiga ruri tana dubawa ta ga sunan Aliya ɗagawa ta yi tana faɗin "Barka da safiya ƴar uwa rabin jiki fatan kin je gida lafiya" Aliya da ta koma ta kwanta a doguwar kujera haɗe da ɗaga ƙafafu sama ta ɗora daga can saman kujerar, hannunta ɗaya yana tallafe da wuyanta tana yatsina fuska ta ce "Lafiya" Ta faɗa a takaice don har ta fara wulaƙancin da za ta gara Jidda tun daga yanzu, don duk tunanin magani ya ci Bayan sun gaisa Jidda take faɗa mata Baban Ibrahim ne ba lafiya a asibiti ma ya kwana yanzu ma can za ta tafi, Aliya ta ce "Amma jiya baki faɗa min ba" Jidda ta ce "Ai rashin lafiyar jiya da dare ne" Aliya ta yi shiru tana son jin kanun labarin yadda aka ci abinci da cokali sai dai ta rasa ta ina za ta fara zuwa can wani tunani ya faɗo mata hakan ya sa ta ce "Allah bashi lafiya, ki masa sannu sannan ki wa Ibrahim ɗin ya mai jiki" Jidda ta ce "Zai ji in sha Allah ai a can asibitin ma ya kwana" Aliya ta ce "Ayya bawan Allah sarkin son tuwo" Ta faɗa haɗe da sakin kunnuwa don jin abin da Jiddar za ta ce, ƙirjin Aliya yana sama yana ƙasa duk da ta san ba za ta ji wani labari makamacin wanda take tunani ba, amma dai sai ta ji tan fargabar jin amsar, domin ta san tabbas ta yi furucin da za ta samu amsar tambayarta. Jidda ta ce "Wallahi kuwa ke dai bari ai duk ƙaunarsa da tuwon nan jiya sai da ya gutsura zai kai bakinsa aka sanar da shi rashin lafiyar Daddyn wallahi tsabar ruɗu bai san ya saki cokali mai ɗauke da tuwon ba, tuwon da ko a bakinsa bai ɗanɗana ba jiyan" Dummm dududummmmm gaban Aliya ya buga da ƙarfi a take ta ji numfashinta yana neman barin gangar jikinta, bata san ya aka yi furucin ya fito ba ta dai ji bakinta ya furta "Bai ci tuwon ba? Ko a bakinsa bai ci ba kika ce Jidda?" Ta taɓbaya a ruɗe tana tashi zaune cike da firgici, Saude kasancewar wayar ana iya jiyo maganar kuma tana tsaye ne daga gefen Jidda tana riƙe da kwandon a kan kunnenta ta ji maganar Aliya da take yi a gigice cikin diriricewa fakar idanun Jidda ta yi ta kauda kai gefe tana sakin dariyar gefen baki tana danne dariya mai ƙarfi da take son ƙwace mata, domin ta gama harbo jirgij Akiya ai dama ta san Aliya ba za a yi abin kirki da ita ba ta gama fahimtar cin duduniyar Jidda take. Jidda kuwa duk da ta ji yanayin da Aliya ta mata tambayar sai bata kawo komai ba, tunanin ta ko yadda ta ji an ce yana son tuwon kuma bai ci ba shi ne take jimantawa, amma ai a ganin Jidda lafiyar mahaifi ta fi komai. Baki ta buɗe ta ce "Wllahi ko ɗanɗanawa bai yi ba ai tuwon ma ya lalace an zubar an wanke kwanon" Aliya bata ce komai ba illa sakin wayar da ta yi ba tare da ta sani ba, taimakon ta da Allah ya yi a kan kujera ta faɗi tsaye Aliya ta miƙe cike da tashin hankali tana tunanin abin da Jidda ta faɗa mata. Jidda kuwa da ta gaji da faɗin hello hello sai kawai ta datse kiran ta shiga mota Saude ta ba direban kwandon ya saka a a motar aka wangale musu get suka fita daga gidan. Tsaye Aliya ta tashi hannu biyu a kanta, hatta ɗankwalin kanta tuje shi ta yi tamkar mahaukaciya sabon kamu haka ta koma, tana tuna irin tarar aradu da ka da ta yi wajen isar da cikalin wannan sannan yanzu ita idan har an kwatsa cokalin a cikin ƴan uwansa cokula ba za ta taɓa sheda shi ba wataƙila ma asirin jikin ya karye, tunanin ta ɗaya idan ta je ta sanar da bokanya abun da ya faru kar ta ɗakko mata jan aikin da ba za ta iya ba, tun da a ranta tana raya babu gudu babu ja da baya! BABA Ya yi baƙincikn rasa gutsuren tsumman rigar da ya gutsure a jikinnrigar ɓarawo da a tunaninsa da ita zai riƙe matsayin sheda ko wataran za a ga wanda ya saka yagaggen kayan sai ya gane amma dai ya sanya a ransa idan kere yana yawo zabo yana yawo watarana za a haɗu. Bai san cewa ƴaƴansa ne suka ɗauke yadin ba sannan aka haɗa aka ƙone da wanda ya gutsure ɗin da kuma gutsuren saboda tsaro ba don tsoro ba. Zaune yake da kwanon tuwonsa a gabansa yau a tsakar gidan yake a zaune tun da ya kai lomar tuwon farko ko taunewa bai yi ba bare a samu damar haɗiyewa da sauri ya dawo da ita yana tofara kamar wanda ya ci kashi. Hannunsa ya tsame ya shiga ƙwalawa Mama Bilki da ta yi zaman dirshan a tsakiyar ɗakinta tana cin tuwonta bayan ta barbaɗa masa maggi dunƙule jin kiran ya ƙi ƙarewa ta fito tana suɗe hannu ta ce "Haba Malam kira sai ka ce makaho ai ya kamata kake numfasawa" Baba ya ce "Abin da ya fi numfasawa zan yi, ke yanzu wannan ba abin kunya ba ne ki ɗauki wannan tuwon naki ci karka mutu ki kaiwa miji, ban da rashin tunani kina zaune gidan kishiyoyi uku ke ta huɗu amma baki iya tattalin miji ba? Bari ki ji mata wanda suka gama karantar hakayyar maza a kwanon mazan suke samun gurbi a zuciyar miji" Kallon sheƙe ta masa ta ce "Wane gurbi kuma Malam ai gurbi ina ga an riga an cike in dai a zuciyarka ne" Sanin halinta ya sa ya ce "In ji wane shegen?" Ta ce "Ah to ka tuntuɓa dai amma na san babu gurbin zama a zuciyarka" Tunaninsa ko ta fara sakkowa ne da vayanin nasa dama tunaninsa bai wuce ta ringa masa lafiyayyan abinci ba hakan ya sa ya ce ",Wallhi tsaf mace za ta saye zucuyata in dai ta harkar abinci ne, ai ki dafa shimkafa miya ta ji nama wallahi kin kasa kin sayar a zuciyata" Da dariya ta bushe ta ce "To ni yanzu an ce maka neman wajen zama nake, to ai ko ni kake kawo mini abincin da naman gurbin zama zan baka w tawa zuciyar" Jin furucinta ya gane nasa furucin bai samu shiga ba hakan ya sa ya saka ƙafa ya haure kwanon miyar ta tu tsure a wajen ya shiga ƙwalawa Hafsa kira ta fito ya ce "Ki duba idan akwai mai da yaji ki mini kwaɗo da tuwon nan in samu in kashe yunwar cikina wanna uwar taki bata neman albarkar gidan aure, a ce maggi mace ba za ta saya ta saka a miya ba" Har ta juya za ta tafi ta juyo ta ce "Kai daniya hatsi ko masara kake badawa wataran ma ka ce hatsi ya di tsada ka auna ka kai kasuwa ka siyar ka ɗauke canjin saman ka saka a aljihunka sai ka auno masarar ka kawo, mace za ta bada kuɗin surfe ta biya na niƙa sannan ta saya kayan miya ta maka miyar haba ai wannan macen ko banki ce ita ka gama daƙushe ta" Jin haka ya miƙe yake masifa yana faɗin ya rasa lokacin da suka fara daina tsoronsa har kowa yana da bakin mayar masa da martani!. Bayan kwana biyu sai ya tsiro da wani abu wani daga yau ya daina basu hatsi ko masarar tuwon ma don ya ga neman ake a kassara shi tun da har yanzu ƴaƴan babu wata wacce ta fito da miji hakan ya sa ya ce iyayansu mata ne suka ɗaure musu tsantsa, don haka sai dai su suke ciyar da su amma shi dai kam ya daina bada ko ƙwayar hatsi. Tun daga ranar ya ƙara haɓaka kayan store ɗinsa daga ya ji wani ya matsu zai sayar da hatsi haka zai je ya saye ya zo ta libga a store iyalinsa ko oho, watarana ya je yana ciniki da wani maƙocinsa daga yamma sai mutumin yake cewa ai buhun hatsi da zai sayar iyalansa zai aunawa masara sun ce sun gaji da cin tuwon hatsi, shi ya sa ya ɗakko buhu ɗaya daga ciki zai musu canji tun da shinkafa iya ta rana ce kaɗai ake yi. Buɗar bakin Baba ya ce taɓ amma kai wahalalle ne ai ni nan na gama gane idan ka biyewa iyali sai sun ga ka yi gawa don komaj naka sai ya ƙare saboda kullum sai an ce ka kawo abinci. Shi kuma yake faɗa masa cewa ai wannan nauyi ne da Allah ya ɗorawa mutum ko bai sauke ba sai Allah ya tambaye shi, amma Baba bai ji ba haka ya saya ya je a jibge shi kuma mutumin ya siyowa iyalansa buhun masarar don ya faranta musu. A washe garin ranar da ya sayar sai Allah ya buɗa masa ta hanyar da bai zata ba. Store ɗin Baba ya cika da shinkafa da hatsi dawa da masara, ko masakar tsinke babu, amma nauyin iyali an ƙi a sauke, kullum haka za suke zaune cikin yunwa ƴaƴan sai dai kowa ya je ya yi buga buga masu roƙon samari su roƙa, masu bada mutuncin su a basu kuɗi su bayar wanda kuma za su ɗauka ma ba a basu ba a wani waje sai su ɗauka don duk su saukewa kansu nauyin haƙƙin da ba nasu ba, haka matan ma wata sai ta kwanta da yunwa idan bata da kuɗi yanzu dai kowa shi yake ciyar da kansa. Kullum da asuba sai ya je ya buɗe store ɗin kafi ya tafi masallaci, ya ga komai lafiya domin yanzu kwaɗon da yake datsewa ba ya buɗuwa da kowane mukulli sannan idan ya dawo daga masallaci ma a store ɗin zai yada zango yana kallonsu yana murmushin jin daɗi yana ganin arziƙi gashin hanci ne, sai dai ya manta da karin maganar bar ganin ka tara ka kiyayi mai nema. Yau ya kama litinin yana zaune da azzahar yana ganin waccen ta jiƙa garin kwaki, wancan ta shigo da awara kowa da abin da yake, shi kuma yana zaune da a ce wani zai miƙo masa da karma zai yi. Mama Habiba ce ta zo ta ce "Mallam don Allah ka bamu hatsi a yi tuwon nan, wallahi jiya ma da yunwa na kwanta kasancewar bani da kuɗi da safe ma ban karya ba ga rana ta yi yanzu, wallahi... Kafin ta kai aya ya katse ta yana masifa yana faɗin ko ƙwayar hatsi ba zai bayar ba, tashi ta yi jikinta babu ƙwari ta kama hanyar ɗakinta, kamar daga sama kamar almara sai Baba ya fara hango hayaƙi yana fitowa daga jikin ƙofar store ɗinsa kafin ƙiftawar ido gabaɗaya store ɗin ya kama da wuta sosai gobara ta kama.. SADIYA Har suka shige tana tsaye bakinta a sake, tana jin ana cewa maza suna juyawa uwayen gidansu baya idan suka samu wasu matan ma,ana idan suka ƙara aure duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, amma daj kam abin na Nasir ya fara wuce gona da iri, domin ta lura shi babu ruwansa ma da wani adalci in ba rashin adalci ba da rashin sanin muhimmancin matarsa uwar gidansa ta yaya za a yi a ce wai ita ce za ta ɗauke kayanta a mata kicin na langa langa saboda ita bata da ƴanci sannan bata da wani galihu a cikin gidan. Duk da ta san idan ɓera da sata to daddawa ma da warinta, ma,ana idan har da laifin Nasir wajen mayar da ita ba komai ba a cikin gidansa to da laifin iyayanta musamman mahaifinta, da shi babu ruwansa da ƴanci ko kwanciyar hankalin ƴarsa a gidan aure shi kawai burinsa a riƙe masa ƴarsa a ɗauki ɗawainiyarta, kowane namiji kuwa ya ga babu wanda ya damu da kai hasalima iyayan so suke a ɗauke musu nauyinka dole sai yadda ka gani don wulaƙanci an saya maka shi kwando -kwando. Abin takaicin ma shi ne mahaifiyarta duk da ta san mahaifiyarta bata isa da Baba ba amma dai ya dace a ce ita a matsayjnta na mace tana tausaya mata da sauraron halin da take ciki, ba wai ta yi watsi da damuwarta ba in ta zo za ta faɗa ta ƙi saurarenta, kuma rashin amayar da damuwar ne yake ƙara daskarar mata da damuwa a zuxuyarta, gashi saboda cikin da take ɗauke da shi ba ta son take saka damuwa a ranta sai dai shi faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi. Kicin ɗin ta shiga Kalifa yana buye da ita ta shiga kicin ɗin, jin ƙafarta ta ƙara riƙe mata sai ta samu waje ta zauna a kan kujerar katako irin ta mata ta tsakar gida, tana zama kawai da takaici ya cika mata zuciya bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba,bata ankara ba sai ta ji hannun Kalifa a kumatunta tana share mata ya ce "Momma ki daina kuka" Ya faɗa cikin muryarsa ta yara sai lokacin ta ankara da abin da take da sauri ta saka hannu ta ƙarasa goge hawayen, domin ko kaɗan bata son Kalifa yake ganin zubar hawayensa idan ya tashi da haka lokaxin da ya yi wayo zai iya fahomtar abin da ya saka ta zubar hawaye a baya. Abu na gaba idan har yaro yana ganin hawayen mahaifiyarsa koyaushe yau da gobe zai sa ya ɗauka su hawayen ba wani damuwa ba ne idan ana zubar da su, hakan zai zamana ya saba gani nan gaba ko da a ce ya girma idan zai ga hawayen mahaifiyarsa hakan ba zai zama damuwa a garesa ba wanda zai sa ya ji wani iri domin ya saba gani, idan har yara suna ganin hawayen zai zamana basa ɗaukan kukan uwa da muhimmanci, basa ɗaukan zubar hawayen mahaifiyrsu a bakin komai. Murmushi ta yi tw ce "Ba kuka ba ne yaji ne ya shiga idanuna" Ta faɗa tana kama hannuwansa biyu ta riƙe tana dariya, shi ma dariyar ya yi ya ce "Yaji ne Momma?" Ta ce "Eh" Daga haka ta yunƙura ta tashi tsaye don sai da ta dafa ƙasa ma ta tashi. Kayanta na kicin ɗin ta shiga haɗawa domin hanyar lafiya a bi ta da shekara domin idan da ita kaɗai ce matar Nasir yanzu sun zama su biyu in har ta yi wani abu da zai yi sanadin Nasir ta kaita gida, to ta san Baba haƙuri wataƙila har sai ya durƙusa wannan kuma abin kunya ne a gareta kishiya ta san waye mahaifinta mene ne matsayinta a gidansu duk da ta san waccen kaita gidan da ya yi har sai da Nasir ɗin ya ba Meenal haƙuri. Haka ta ringa fito da kayan Kalifa ma yana ɗakko ƙananan abubuwa har suka kwashe tass. A waje guda suka tattara lokacin Nasir ya fito daga ɗaki Meenal tana biye da shi, haka Meenal ta wuce ta gabanshi ta nufi kicin ta riƙe da plate mai ɗauke da kofuna kicin ɗin ta je ta ajiye tare da rufo kicin ɗin ta juya ta kalli Sadiya ta ce "Ko ke fa" Tana faɗar hakan ta zo ta tsaya gabansa tana masa magana cikin kwarkwasa amma Sadiya sai ta ba bango ajiyarsu kamar ma bata san da zaman su a wajen ba. Bayan ya fita Meenal ta kalle ta ta ce "Ya kamata ki fara shirin haƙura da wasu abubuwa da dama daga cikin gidan nan domin ni da ke za mu yi wani zama da ba lallai ki jure ba, amma zai fi kyau ki haɗa kayanki ki nufi gida don sai hakan ya fi zamar miki kwanciyar hankali, amma a shawarce idan kuma kin ga za ki jure to ga fili ga mai doki... *Idan Allah ya sa muna raye a page 30 za mu gama Book 1 sai mu tafi book 2 wanda shi ne za mu yi har ƙarshemkn labari, sai dai tafiyar tamu tana da nisa, domin labarin yana da ɗan tsayi sannan akwai sarƙaƙiya da abubuwan mamaki al,jabi tausayi dasussa, sai wanda ya bibiyi labarin ne zai gane abin da nake nufi.* MAMAN AFRAH *09025576222* https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣5️⃣ ALIYA Zaman dirshan ta yi a tsakiyar dalon tana kuka haiƙan, gabaɗaya duniyar ta mata matsi da ƙunci ji take tamkar ta kashe kanta ta huta wannan wace irin ƙaddara ce a cw Ibrahim wai ko ɗanɗanar tuwon bai yi ba don baƙinciki da takaici ma a ce wai wurgi ya yi da cokali me ɗauke da asirin a jiki kawai saboda an faɗa masa rashin lafiyar ubansa zai shikenan zai jiƙa mata aiki. Bayan ta sha wuya da kuma kasada wajen zuwa ta sauya cokalin da kuka mai ƙarfi ta rushe tana faɗin "Na shiga uku na lalace Allah ya isa tsakanina da uwar Ibrahim da ta kira shi ta faɗa masa rashin lafiyar ubansa har ya yi sanadin fasa cin tuwon da ya yi, daman ma uban nasa mutuwa ya yi mu ga tsiya" ,Ta faɗa tana haura ƙafafu duk ta cakuɗa gashin kanta, ɗifff ta yi kamar ruwa ya ci tw, tana saƙa da warwara ranta in ya yi dubu a ɓace yake gabaɗaya sai tsanar mijinta Kasim mata maza ya turnuƙe mata zuciya tana tuno irin yadda ta bashi haɗin kai a gadon su na sunna a daren jiya duk don tana cike da ɗoki da farincikin cikar burinta na auren Ibrahim ashe dai bata san tufkar da ta yi an warware mata ita gabaɗaya ba!. Sai da ta sha kukan takaicin ta tsagaita sannan ta janyo wayarta ta kamo sunan Umma ta doka mata kira Umma tana ganin kiran ta ɗauka cike da murmushi ta ce "Tilon ƴata ki ce aiki ya kammala yanzu za mu fara baza capacity, wallahi naira sai ta ci ubanta a wajenmu, motoci da gidaje masu kyau sai sun san mun yo kuɗi mun kerewa wulaƙanci!" Ta faɗa tana jiran Aliya ta fara kora mata bayani Maimakon ta ji muryar Aliya cikin farincki tana mata bayani sai ta ji Aliya ta fashe da kuka Umma hankali tashe ta ce "Kukan me kike Aliya? Buɗe bakin ki ki faɗa min wallahi gabana faɗuwa yake kar dai ki faɗaa min mummunan labari mai ya faru?" Aliya cike muryar kuka ta ce "Umma bai ci tuwon ba" Umma tana zare ido tamkar kwarton da aka kama ta ce "Bai ci tuwon ba to uban mai ya ci ko dai Jidda ce ta yi wani mugun tuggun da ya sa bai ci ba, ko dai ta harbo jirginki Aliya ke kike haukarki?" Ta tambaya cike da zaƙuwar son jin dalilin. Aliya ta ce "Wannan tsohuwar tasa ce ta masa waya wai ubansa bashi da lafiya ya yanke jiki ya faɗi shi ne ya jefar da cokalin tsabar ruɗewa a sibiti ma ya kwana tuwon ya lalace an zubar" Ta faɗa tana kwashe komai ta faɗawa Umma da take jin ɓacin rai tamkar ta yi ƙaramar hauka, sosai ranta ya ɓaci ta ce "Ki daina kuka Aliya in har ina numfashi a doron ƙasa saj kin cika burinki, ko ma in ce burinmu sannan a shirye nake na yi fatali tate da tarwatsa aniyar duk wani wanda zai kawo tsaiko a lamarin nan" Aliya sai ta ji ta ɗan samu ƙwarin gwiwa hakan ya sa ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya nan Umma ta yi ta bata baki a kan cewa ta kwantar da hankalinta in dai gidan Ibrahim ne ta gama shiga ta gama. Sun yi sallama bayan sun jajantawa juna Aliya saboda takaici ko da Jidda ta ƙarasa asibitin ta kira ta don ta ce ɗazu suna magana basu gama ba ta daina jin ta amma sai Aliya ta ƙi ɗaukan kiran don yanzu kawai haushin Jidda take ji. Washe gari Umma ta kira Aliyar tana faɗa mata tare za su je ajen bokanyar don ta faɗa musu abin da ya dace a yi domin ita yanzu ta gwammace ko salwantar da rayuwar Jidda ne a yi in har za a samu biyan buƙata duk da tana son a bar Jidda a rayw domin su ƙunsa mata baƙinciki irin baƙincikin da za ta gwammace gwara mutuwarta amma in hakan zai zama matsala gwara ta bar duniyar ma su su ci tasu duniyar da tsinken tsire mai tsini. Daga Abba har Kasim babu wanda aka faɗawa fitar hanya suka sata suka tafi yana kowane ya fita kasuwa. Ko da Amatullahi ma ta tambayi Aliya sai ta faɗa mata da Umma za su je wannan karon. Suna isa bokanya ta musu izini suka shiga. Bayan Aliya ta gabayar da Umma a matsayin mahaifiyarta sai kuma ta shiga rattabo mata bayanin yadda al,amura suka kasance wato yadda ba a dace da cin abinci da cokalin da aka yi asirin nan ba. Ta yi mamaki kuma ta jimanta abin domin tana tabbatar musu cewa da a ce ya ci abinci da cokalin nan da matsalar su ta kau har abada!. Sai dai matsalar idan aka yi aiki ba a maimaitawa sai dai a yi wani sabo. Nan Umma tw ce kawai a yi wani aikin. Bokanya ta yi jim ta ce "Aikin da za a yi yana da hatsari kuma yana da ci, domin idan aka yi har sai ya fi na cokali zafi sai dai shi wannan aikin ana faɗar ladan da za a biya na aiki a nan take ta sanar da su za a biya kuɗin aiki dubu ɗari biyu. Daga Umma har Aliya kallon kallo ake domin kaf cikinsu babu mai dubu goma ma ta kansa a halin da ake ciki dai yanzu babu kuɗi sannan kuma suna buƙatar a yi aikin da gaggawa. Bokanya ta basu kwana biyu a kan cewar idan an kawo kuɗi za a yi aiki. Tun da suka taho suka shiga zulumi da tunanin yadda dubu ɗari biyu za ta fito, idan suka yi hasashen kuɗin da yawa sai kuma su tuna tasirin da aikin zai yi, tun da idan Ibrahim ya shiga hannunsu sai sun fanshe abubuwa da yawa. Sun rabu a kan cewa za su yi waya bayan sun tsara cewa Umma ce za ta kai wa Jidda kukan buƙatar kuɗin tun da suna ganin tana gidan daula ba za ta rasa kuɗi ba. Washe gari aka sallamo Daddy daga asibiti ya ware tass sai dai ɗan abin da ba a rasa ba. Jidda tana zaune a bakin gado Ibrahim ya zo ya zauna ya ce "Habibty rufe idanunki" Wani kallon ƙasan ido ta masa sai kuma ta murmusa haɗe da runtse idanun, ya ce ta buɗe hannunta haka ta buɗe hannun sai da ya ajiye mata mukullin a kan hannun sannan ya ce "Buɗe idanun" Tana buɗewa ta ga mukulli a hannunta mukullin mota, nan ta shiga tambayarsa ya sanar da ita cewa Abba ya siyawa mota, don dama yana da niyya. Wata iriyar runguma ta masa tana ta murna tare da jero masa wasu addu,o,i masu daɗi hakan ya sa ya ji matsayinta ya ƙara ƙaruwa a zuciyarsa. A ranar ne ta shirya domin zuwa ta isar da saƙonsa zuwa ga Abba bayan magriba tare suka je a motar direbansa yana biye da su don haka yana ajiye ta ya bata mukullin ya shiga motar da dirwban ya zo da ita ya ce an jima zai dawo ya ɗauke ta. Da sallama ta shiga gidan lokacin Abba bai dawo daga masallacin ishsha,i ba. Umma da take zaune a tsakar gida a kan tabarma ta buga uban tagumi ko da ta ji sallamar ma sama sama ta ji sai da ta ɗago ta amsa duk a diririce musamman da ta ga Jidda cikin shuga ta alfarma cikin shigar manyan hajiyoyi wani dakkaken leshi wanda ya amsa sunansa leshi da ƙaton mayafinta da ya rufe mata dukkan ilahirin jikinta, sai takalmi da jaka masu aji sarƙoƙin gwal ɗin da ta saka suna walwali su ne suka saka Umma jin zuciyarta har wani ɗaci-ɗaci take, ita kuma Jidda ba ita ce ta ɗakko kayan ba gabaɗaya Ibrahim ne ya ɗakko mata a cewarsa gwara ta je gida a ganta a ce ya iya kiwo sannan ya riƙe amana haka ya faɗa mata cikin wasa lokacin da ya ɗakko mata kayan. Umma dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta ta ce "Jidda sannu da zuwa farae amarya" Ta faɗa tana washe haƙora tare da nuna tsantsar murnar ganinta amma a zuciyarta baƙinciki ne fal domin jin wata tsanarta take ji, Jidda kuwa sai ta ji wani daɗi take ganin tamkar mahaifiyarta ce a gidan, sosai take jin Umma har ranta. Umma sai nan nan take yi da ita amma shigarta ta tsaye mata a rai kuma ta tsone mata ido!. Sun gaisa ta ɗakko mata ruwa, tana jin a ranta tamkar ta zuba maganin mutuwa Jidda ta sha ta mutu kowa ya huta a kan yadda take ganin ya sha gabansu, take ganin tana zaune cikin haɗaɗɗe kuma tsararren gida amma tata ƴar tana can gidan mata maza, mata mazan ma Allah baku mu samu. Ruwan ta sha tana ta yi wa Umma godiya don har mamaki take idan ta ga Umma tana nuna mata so da kulawa tamkar ba waccan Ummar da ta bata wahala ba, tamkar ba Ummar da ta ɗora mata karan tsana ba. Umma cike da wasa a zahiri ta ce "Ai na ɗauka ma ko bakya iya shan ruwan gidan namu ba" Ta faɗa a zuciyarta kuma tana cewa 'Kin kusa zama tarihi a wajen Ibrahim ɗin da kike taƙama da shi' Jidda tana ƴar dariya ta ce "Haba Umma ta yaya haka zai faru ni da gidanmu ni da na taso na girma ina shan ruwan" Umma ta.ce "Ai da na ga yanzu kin saba da ruwan faro wato ruwan roba" Sosai Jidda take dariya Umma kuma a fili fuskarta ɗauke da murmushi amma a zuciyarta tana fatan Allah ya kawo ranar da wannan murmushi da farincikin zai bar kan fuskar Jidda ta dawwama cikin ƙunci. Suna ta taɓa hira tana cewa ta zuba mata tuwo ta ce a ƙoshe take, a nan har tana bata labarin yadda take jin daɗi idan Aliya ta kai mata ziyara a fili Umma ta ce "Ke da ƴar uwarki haba Jidda in Aliya bata je wajenki ba waye zai je" A zuciyarta kuma ta ce "Ita ma tata ce take kaita, za ki gane baki da wayo ne lokaci yana zuwa sannan za ki yi hankali ki gane ba kowa ake ba yarda ba a rayuwa, domin kamar yadda bahaushe ya ce 'Makashinka yana tare da kai!' Sunanta taɓa hira har Abba ya dawo, ya yi farincikin ganin Jidda musamman da ya ganta cikin farinciki da kwanciyar hankali, tabbas yana son Jidda yana jinta a zuciyarsa tamkar ƴar da ya haifa wani lokacin har tana jin son Jidda yana barazana ga son da yake wa Aliya wato son Jidda yana neman linka shi. Ta gaishe da Abba cike da girmamwa tana jin ya maye mata gurbin mahaifinta har abada, bata da wani uban da ya wuce shi tana bashi matsayi irin matsayin da baki ba zai iya fasaltawa ba. Umma tana jin haushin yadda yake nunawa Jidda kulawa amma haka ta danne. Tana tsokanarsu wai ƴa da uba an daɗe ba a haɗu ba. Bayan an ɗan jima ta buɗe jakarta ta ɗakki mukullin motar ta miƙa masa tana faɗa masa Ibrahim ne ya saya masa mota buɗar bakin Abba ya ce "Mota kuma Jidda?" Umma ranta a matuƙar ɓace amma haka ta daure ta nuna murna. Jidda tana dariya ta ce "Mota Abba ita ce dai za ka ganta a waje sabuwa dadal" Ta faɗa tana dariya. Idanun Abba suka kawo ruwa yana jin cewa shi ya sa aka ce ba a yi wa ɗa da dukiya mugunta domin baka san mai amfanarka ba. Ya yi farinciki har ya rasa da wane baki zai ambata murnarsa sai albarka yake sakawa Jidda da Ibrahim yana ta musu fatan alkairi a rayuwar aurensu, tare da nemar musu tsari daga dukkanin sharri. Jidda sai amin take cewa inda Umma duk ta ji kamar ta fasa ihu saboda takaici da baƙinciki musamman yadda yake ta zabgo addu,ar nema musu tsari da kuma ta dawwamar da farinciki sai take ganin kamar addu,ar da yake yana adawa ne da cikar nasu burin. Farincikinsa ya kasa ɓoyuwa har sai da Ibrahim yan dawo ɗaukan Jidda ya kira ta a waya inda ta sanar da su zai shigo haka ya shigo Abba ya yi ta masa godiya da kuma addu,a Umma ma haka ta daure tana masa godiyar amma ko da wasa bata yi addu,a ba. Sun musu sallama inda suka tafi. Washe gari da yamma Jidda ta fito wanka tana zaune gana mudubi tana shiryawa shi kuma dama ta bar shi a sama yana ƙarasa wani aiki, ƙaran wayarta ne ya dakatar da ita daga shafa powder da take ta ajiye sosan shafa powder ta ɗakko wayarta ganin sunan Umma ta ɗauki wayar da murmushi bayan sun gaisa Umma ta shiga tambayar lafiyarta da ta mai gidan har tana faɗa mata da safe sun je gidan su Ibrahim ɗin ita da Abba sun duba Daddyn nashi. Bayan Jidda ta musu godiya sai kuma Umma ta yi shiru har sai da Jiddan take tambayat shirun da ta yi, Umma ta ce "Wallahi dama wata damuwa ce nake da ita Jidda ina fata za ki share mini hawaye" Jidda ta ce "Subhanallahi damuwa kuma Umma?" Umma jin duk Jidda ta rikice tana nuna damuwa sai Umma ta cr "Wallhi kuwa wani ɗan uwana ne a ƙauye jeji suka shige shi ƙafa tana nan suntum sai wari take to an kai shi wajen me magani sai aka yanka kuɗaɗe masu yawa, har dubu ɗari biyu da hamsin to yanxu sun haɗa dubu hamsin dubu ɗari biyu suke nema na ce bari na gwada sa,a ta a wajen ɗiyata mai tausayi ko za a dace!" Ta faɗa tana aikawa Jidda harara ta cikin wayar. Ajiyar zuciya Jidda ta sauke ta shiga faɗa mata cewa bata da kuɗi don jiya ta yi sayayyar wasu kaya a online za kawo mata sai dai za a iya samun dubu saba,in. Umma ta ringa faɗa tana cewa "Yanzu Jidda har sai an koya miki dabarar zaman aure a gidan mijin, tun da har kika samu kika auri mai aljihu da maiƙo ai kamata ya yi kike farauto mana karki yarda ki zauna kanki da murfi don yanzu kowa ya waye" Jidda cike da rashin fahimta ta ce "Wallahi Umma ba na iya tambayar Ibrahim kuɗi ina nufin ba na iya roƙonsa, sai dai a ɗan jinkirta idan har da kansa ya bani kuɗi sai na cika miki" Umma ta hau faɗin "Kidahuma kike so ki zama?" Wannan ya yi daidai da zuwan Ibrahim bakin ƙofar ɗakin Jidda jin tana cewa "Umma in saci kuɗin Ibrahim kuma? Gaskiya ni ba zan iya yin sata ba ko kuɗin waye in dai ba nawa ba ne bare na Ibrahim" A daidai nan ya tura ƙofar gabaɗaya ta rikice ta saki wayar ma daga hannunta ta faɗi ƙasa sa,ar ta ɗaya wayar bata yi komai ba. Sai ya nuna mata bai ji abin da take faɗa ba, dama kuma ya san ba za a taɓa haɗa baki da Jidda a cuce shi ba ya yarda da ita 100% Wayar ta ɗauka ta kashe da sauri jin yana cewa har yanzu bata gama shiryawa ba, duk ta rikice yanayin da ya ga ta nuna har ya so bashi dariya amma ya danne. Umma wani ƙuduri ta ƙudurta a ranta cewa za ta yi maganin Jidda don sai ta mata abin da wani maƙiyinta ma idan ya ganta sai ya tausaya mata. Wani filinta ta je ta ɗaga ta sayar Abba ma bai sani ba suka haɗa kuɗin suka nufi wajen bokanya. Bayan sun damƙa mata kuɗin ta tashi tsaye tana riƙe da wani ƙaramin kasko take kewaya ɗaki a take hayaƙi ya fara fitoa daga kpwace sukurwa ta ɗakin. Lokaci gida hayaƙi ya baibaye ɗakin su duka a tsorace suke sai da ta gama ta koma mazauninta ta zauna ta dube su ta ce "Yanzu mai kuke so a yi" Umma ta yi karaf ta ce "So muke a saka masa son Aliya yadda ba zai taɓa rabuwa da ita ba yadda zai tsani duk wanda ya kushe ta ko ya nuna sai ya rabu da ita, sannan a saka soyayyarta a zuciyar surukan nata wato iyayan Ibrahim ɗin, shi kuma mahaifinta wato mijina a saka masa son auren nata kuma kar ya taɓa tambayar dalili ita kuma Jidda a sanya ta zama akwai ya babu kakar wajen uba" Aliya ta ce "Kawai gwara ya danƙara mata saki lokaci guda idan dai ya yanke igiyar auren dolenta ta tafi ai" Bokanya ta gyaɗa kai tana wani haɗe halen magani sai kuma ta shiga kiran sunayen wasu aljannu kafin ta buɗe hannu su Umma sai ganin wani magani suka yi kulle a farar leda an ɗorowa Bokanyar a tsakiyar hannun. Nan ta miƙawa Umma magnin ta ce "Wannan garin maganin za a saka shi a hancin sabuwar gawa ta namiji, bayan an masa wanka an saka likkafani kafin a rufe kan za a cire audugar hancin sai a zuba maganin a duka ƙofofin hancin sai kuma a mayar da audugar a rufe, yadda gawar nan bata da wani sauran amfani haka Jidda ba za ta sake amfani a wajen mijinta ba kuma a take zai sake ta, sanann son Aliya zai shiga zuciyarda daram, sai kuma mahaifinta da ko ma waye ba za su taɓa kawo tsaiko a kan auren ba, babu ma mai tambayar don mai aka yi " Umma tana dafe da ƙirji da hannu biyu sai karkarwa take jin furucin bokanya, tana tuna naira dubu ɗari biyu da suka bayar yanzu kuma ga wani ɗanyen aikin da take ji har gwara na cokalin da Aliya ta yi. Aliya tana zare ido ta ce "Bokanya ko za ki sauya aiki?" Umma ta shiga gyaɗa kai alamar gamsuwa da maganr Aliya ita kuma Bokanya ta ce "Ai in mun faɗa sai an yi kuma ba za a canja ba, mene ne abin wahala a wannan aikin ku da kuke neman biyan buƙuta ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, da kuka ci sa,a ma ban ce ku yi ridda ba" Suna haɗa ido suka juya suna kallonta suka haɗa baki wajen faɗin "Ridda?" Bokanya ta ce "Ridda mana mutane nawa ne suka yi ridda saboda su samu biyan buƙata, mutane nawa za su zo mu basu hutun yin sallah na kwana arba,in ko satittika ko watanni kuma su yi" Umma ce cikin sanyin murya ta ce "To ai bokanya ta yaya za a yi mutum ya iya zuwa wajen gawa har ya yi abin da kika faɗa ba tare da tonuwar asirinsa ba?" Da wata mahaukaciyar dariya ta bushe ta jima tana yi sannan ta haɗiye dariyar ta hanyar haɗe rai sai kuma ta ce "Komai a tsare yake, don haka akwai maganin da zan bayar da kowa sai ya suma a take a wajen " Umma suna gyaɗa kai ita da Aliya kamar ƙadangaru Bokanya ta miƙa "Wnanan maganin ne na sakawa a hanci, wannan kuma daga kin shiga gidan makokin sai ki ambaci sunan mamacin tare da fakar idanun mutane ki juye garin maganin a hannunki sai ki hura da baki ta yadda maganin zai bi iska kuma ko wani ya gani ba zai tambaya ba, kina yin haka kowa zai faɗi sumamme har ki je ki gama abin da za ki yi idan kin gama sai ki ƙara ambaton sunan mamacin kowa zai tashi kuma kowa ba zai taɓa sanin ya suma ba" Sun karɓo sun taho Umma tana ta adana maganin, don Bokanya ta ce a tsakanin su kowa zai iya yin aikin tun da an yi maganin da sunan waɗanda ake so aikin ya ci, don haka sai Umma ta ce za ta yi ita kuma Aliya dama ta ce tsoro take ji. Aliya gida ta wuce, Umma ma ta wuce gidan don Abba bai dawo daga kasuwa ba. Umma ta je ta ɓoye maganin a wata sabuwar samirar ta, tana zaune da magriba bayan ta idar da sallah, tana jingine da bango Abba yana masallaci lokacin sai kawai daga masallaci ta ji ana sanarwa ana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji,un Allah ya yi wa malam kalla rasuwa, za a yi sutura da ƙarfe bakwai na safe, Allah jiƙansa ya gafarta masa" Zuruf Umma ta miƙe tsaye gabanta yana faɗuwa, don ta san lokacin aiwatar da aikinta ya yi duk da tana da mugun tsoron gawa, amma haka za ta durfafi wannn al,amari saboda malam kalla maƙocinsu ne daga can gefe!. SADIYA Da tsananin mamaki ta ɗago tana kallon Meenal wacce take tsaye hankali kwance take zaro baƙar magana, ta rasa mai ta tsare mata a gidan bayan ita ta zo ta samu a gidan amma tana son fitar da ita daga gidan mijinta ta ƙarfi da yaji!. Meenal ta ƙara haɗe rai haɗe da yatsina fuska ta ce "Ina fatan kin fahimta, ko kina kokwanto a kan hakan ne in nuna miki zahiran" Ta faɗa tana kama ƙugu da hannu ɗaya, Sadiya danne takaicin da yake ranta ta yi ta ce "A kan mai zan yi mamaki ai shi mutum ba a gane shi a fuska sai dai ɗan adam bai isa ya zartar da abu a kan mutum ba sai abin da Allah ya rubuta a kansa, idan har ruwana ya ƙare a gidan nan dole zan bar gidan idan ruwan shana bai ƙare ba kuwa babu wanda ya isa ya dakatar da hakan" Ido ɗaya ta kanne tana bin Sadiya da kallo kawai sai ta juya tare da yin ƙwafa ta shige ɗaki. Zuwa jimawa aka fara sallama, bayan an amsa masa ya sanar da cewa mai yin kicin ne da mai gidan ya kira, Sadiya dai ta masa iso ta ja ɗanta suka shige ɗaki. Nasir kuma yana fita da ya je ya gidan Hajiya ya same tw zaune ta duka uban tagumi duk ta yu baƙi ya rasa ma mene ne ummul aba,isin hakan ya zauna bayan ya gaishe ta ta amsa tana sakin doguwar hamma ta ce "Nasir yanzu sai da na maka waya shi ne za ka zo? Yanzu sai ka kwana ka tashi baka ma zo inda muke ba Nasir?" Ɗan sosa ƙeya ya yi ya ce "Wllahi Hajiya abubuwan ne suka sha kaina amma baki da lafiya ko" Ta ɗan kai hannu ta taɓa wuyanta da ya yi ƙashi ta ce "Amma da duk abubuwan da suka maka yawa duk safiyar Allah sai ka zo gidan nan, kuma da kake maganar ko ina lafiya ai yunwa ita ce babbar rashin lafiya" ,Da mamaki ya ce "Rashin lafiya kuma? Yunwar ce rashin lafiyar hajiya bakwa cin abinci ne" ,Ya faɗa lokacin da ya ga Hibba da Husna ma sun fito sun zaune su ɗin ma duk sun yi rama. Hajiya ta ce "Yanzu Nasir har sai wani ya faɗa maka ba ma girki ai ba girki ne ba ma yi ba ƙoshi ne kawai ba ma yi, yanzu a ce yaran nan su je su yi bautar girkwa yarinyar nan Meenal abincin kari amma take tsakura mana wani ɗan mitsitsi kamar wanda muka roƙa yanzu saboda isa ma wai hatta madara da milon ta daina tsakura mana sai dai mu sha lipton kawai kp yau da suka kawo sai haƙura na yi na sha koko haba a kan mai yarinya ƙarama z ta zama ita take juya ragamar gidanka Naasir" Iska ya hurar yana kallon yadda su Hibba suke zumɓura baki ya ce "Haba Hajiya ita fa Meenal gidanta ne su kuma yaran nan su ma idan suka je gidajensu sai su dafa abin da suke so, sannan maganar madara cewa ta yi ta kusa ƙarewa a bari ita take sha idan tana tskurawa ba zai isa ba to kin ga ba sai an saka mata rani ba, sannan maganar rashin zuwana Hajiya da fa abincin safe nake zuwa ci yanzu kuwa kin ga acan gidan ake dafawa... Tun kafin ya kai ƙarsheb maganar Hajiya ta fashe da wani kuka mai kamar jiniyar motar ƴan sanda, ta ce ",Yanzu Nasir ni kake faɗawa wannan maganar? Wato har gorin aure kake wa ƴan uwan naka saboda wanncan matar mai ƙira kamar ta barewa, to ahir ɗinka idan ma ƙarfinka aka fi zan yi maganin abin" ,Tsaye ya miƙe cikin halin ko in kula ya ce "Ni zan wuce, dama zuwa zan yi in kira me aikin kafinta zai je can gidan ya yi aa Sadiya kicin ɗin langa langa saboda Meenal ta ce bata son wannan haɗen kicin ɗin" ,Ya faɗa yana tashi tare da gyara zaman hularsa da yake ji kamar bata zauna ba. Da kallo sula bi shi su duka, don yanzu babu wanna soyaya da kulawar da yake basu kawai tamkar ma hankalinsa ba a kansu yake ba, sannan ita Hajiyar ko ta tsawatar a kan rashin adalcin da ta ji za a yi wa Sadiya na yi mata kicin ɗin langa-langa duk da dama abu ne da suka saba na tashin yi mata a adalci da alama Allah en ya fara kawo wacce za ta mata maganinsu. Yana fita sai da suka ji tashin motarsa sannan Hibba ta ce "Hajiya Yaya Nasir da tamkar ba ya cikin hayyacinsa wallahi ina jin an fi ƙarfinsa ne wato an masa asiri" Husna ta karɓe maganar da faɗin "Ai dama daga ganin abin ma a hankalce an sana cewa Yaya ba zai aikata haka ba" Hajiya ta goge wani hawaye mai zafi ta ce "Ni wallahi abin nan neman fin ƙarfiba yake domin na kasa gane kai da ƙafar abin nn na yi da na sanin auren nan da ya ƙara sannan ina zargin Meenal da mahaifiyarta a kan komai duk da mahaifiyar tata tana nuna min bata ma san abin da Meenal take yi ba sai ta ce wai ita ba za ta tsawatar mata ba ai ni da ita babu bambamci zan iya tsawatar mata bayan yanzu yarinyar nan ji take kanta ɗaya da ni ta ɗauke ni tamkar sa,arta, wai har ni Hajiya Mariya ce sirija take juyawa sannan har ta bada umarni muka bi ni da ƴaƴana wai ƴaƴana ne suke zuwa suna mata girki kullum da safe sannan ta tsakura mana abincin son ranta, wallahi ko a mafarki ban taɓa tunani ba" Hibba ta ce "Hajiya ai wallahi yadda kika san wani tsoronta aka saka mana a rai" Haka suka ci gaba da jajantawa suna tunanin yadda za su samo mafita a shawarar da suka yanke dai zuwa wajen malami ne sai dai babu kuɗinnzuwan don yanzu kuɗin da Nasir yake basu duk ya ɗaure bakin aljihunsa sai na annabawa. Naair yana fita ya bugawa me aikin waya ya sanar da shi su haɗu a gidan nasa, sai ya riga Nasir ɗin zuwa yana dawowa gidan ya nuna masa inda za a yi kicin ɗin haka suka tafi suka siyo komai na aikin mai baro ya kawo langa langa da katakon aka shiga aiki tuƙuru!. An gama kicin tass mai aikin ya tafi don sai da ya sallame shi ya tafi kasuwa. Bayan ya tafi Meenal ta fito daga ɗakinta Sadiya tana jin lokacin da ta je take cewa "Kai amma kicin ɗin ya yi kyau ji langa langan gar sheƙi yake, amma shi ma me aikin nan da ɗaurin tsantsa yake wato gar wani wajen ɗora kwanuka ya mata to Allah kyauta, din dai dama da irin wannan kicin ɗin ta dace" Sadiya bata ce komai ba ta yi kamar ma bata san mai take cewa ba don ta san tana faɗa ne don ta ji. Ko da aka kawo nepa haka ta ƙure kiɗa a gidan don ta turaw Sadiya haushi kan rashin nepar ita kuma sai ta tishe kunnuwanta kamar ma bata san tana yi ba, domin ko da almajirinta ya zo ɗaukan talla ta ce masa firjin ya samu matsala don haka ta kwashe gabaɗaya kayan cikin ta bashi ta ce ya je ya sadakar kar su lalace!. Meenal duk wannan abin sa ta yi wa Sadiya bata haƙura ba tun da burinta ta baƙanta mata rai ita kuma Sadiya tun da ta lura Meenal tana cikin mata masu kishin kissa da kisisina sai ta tattara kamarinta ta ajiye a gefe kuma ta saka a ranta duk runtsi za ta saka haƙuri da juriya ta san da cewa watarana sai labari kuma duk abin da ka yi haƙuri to watarana Allah zai maka sakkaya a kansa, domin wanda aka zalunta babu shamakin addu,arsa uabnagiji zai karɓe ta ko da bai yi adsu,a ba za a masa sakkaya wannan kaɗai take sakawa a ranta ta ji salama. Meenal ganin Sadiya ta danganta da maganar yanke wuta don da kuɗinta ma Naair ya ƙi ya saka a amayar mata jawai donnya nuna bata da kima da muhimmanci, sannan bata da wani galihu a wajensa, bai san darajarta ba, ganin ta mayar da hankali a kan sauran kasuwancinta na cikin gidan tana damƙar cikinikinta, kuma sai ta ga kullum tamkar ƙara buɗe mata hanyoyin samu ake don jama,a haka suke turruruwa wajen saye mata jayan tamkar kyauta take rabawa, don sai ma ta fara zargin ko dai wajen malamai ta je ta nemi kasuwa wato ko da maganin kasuwa take amfani shi ya sa take samun ciniki.. Abin da bata sani va shi ne Sadiya babu abin da ta riƙe sai addu,a idan ta yi sallah tana ɗaga hannu ta faɗawa ubangiji damuwarta sannan ta roƙe shi ya kawo mata kasuwa me albarka ya ƙara kawo mata masu sayen kayanta ta ko ina, hatta bashi da sauran masu kasuwanci suke kuka da shi idan an karɓi kayansu bashi ba a biyansu ko a basu rabi a hana rabi wata ma ta cinye kenan, to Sadiya babu mai riƙe mata kuɗi kuma addu,a ce makamin saboda tana faɗawa ubangiji ya raba ta da ƴan bashi duk wani wanda zai cinye mata kuɗinta Allah ya nesanta ta da shi. Yau ya kama Laraba Sadiya ta tambayi Naair zuwa gidan Kaka dubiya saboda Kaka tana zazzaɓi danyake jiya ta faɗa masa da ta ganshi a tsakar gida kuma ya amince, don har yau Nasir bai shiga ɗakinta da sunan tana da baki ko matsayinta na matarsa ba ita bata ma taɓa jin ƙarin aure irin wannan ba a duk da tana ji a labari ana cewa wata idan aka mata kishiya mijin yana neman ta bashi kwananta ya ƙarawa amarya wani ya siya wani kuma ya ƙwata ta ƙarfi, kwanaki ta ji labarin matar da ta ce tun da mijinta ya yi aure shekara uku bai kusance ta ba, kai ɗakinta ma sai ya ga dama zai shiga kuma ba ya yin sama da minti goma zai fita, ashe dai ita ma al,amarin yana zuwa kanta rayuwa kenan. Yana tafiya kasuwa ta shirya ta shirya Kalifa ta tattara kayan sana,arta ta saka a kicin ta janyo kicin ɗin ta kulle haka ma falonta. Meenal da bata san Sadiya ta tambayi Nasir fita ba sai ganinsu ta yi da shirin fita Sasiyar tana sanye da atamda glitter da ta saya a wajen maman afrah an mata ɗinkin ya yi kyau sai hinabi mai ƙasan net wanda yake pink ya yi daidai da wata ƙananun fulawowi pink da suke jikin atamfar sai takalmin ta marar tudu. Ta yi kyau sosai ga Kalifan ma sanye da riga da wando ƴan kanti sun yi kyau da ɗan takalminsa sosai suka fito abinsu sai kawai ta ji ƙyashi cewa wannan fa da kuɗin sana,a Sadiyar ta saya tun da ta san cewa Nasir ba zai saya musu ba. A zuciyarta ta ce 'Wannan matar matuƙar tana sana,a za ta fara haɗa kafaɗa da ni tabbas amma zan yi maganin abin' Ko kallo bata ishi Sadiya ba ta kama hannun Kalifa suka fice daga gidan sai ƙaran rufowar ƙofar gidan ta ji. Ranta yana ta ƙuna ta koma ɗakinta. Can zuwan an jima ta ji ana ta buga gidan ta taso rai a ɓace ta zo ta ce "Wai waye? Bashi ko tara za a damu mutane da buga ƙofa?" Muryar wani namiji ta ji yana tambayar mai gidan yana nan ta ce masa ba ya nan ta juya tana jan wani tsaki ta dawo gidan kamar an ce ta duba ƙasa a gabanta sai kawai ta ga mukullai, kallon mukullin take sosai tana son sanin mukullin mene ne don ta san ba na Nasir ba ne. A zuciyarta ta ce "Sadiya" Kai ta shiga gyaɗawa alamar tabbayarwa ta tsugunna ta ɗauka tana duba mukullan a take wani tunani ya faɗo mata, da sauri ta koma ta sakawa ƙofar gidan sakata ta dawo da sauri mukulli ɗaya ta saka anjikin ƙofar ɗakin Sadiya sai ya shiga sai dai bai buɗe ba sai da ta sake gwada wani ya buɗe ƙofar wani tsalle ta yo da ihu a fili ta furta "Tsuntsu daga sama gasasshe" Falon ta shigo wani ƙamashin freshner mai sanyin ƙamshi ya dakar mata hanci ko ina tsaf a gyare wajen freezer ta nufa ta buɗe tana taɓe baki sai ta ga babu komai a ciki an ma goge ta tass. Wani tsaki ta ja a fili ta ce ",Ba ke ce a gabana ba, bakya cikin target ɗina, tun da ke na gama da nake ɓangaren tun da an cire wutar nepar baki da sauran wani amfani sai zama a wajen" Ta faɗa tana jan murfin ta rufe freezer ta nufi cikin bedroom. Yadda gadon yake a ɗame shi ne abin ya bata mamaki sannan zanen gadon fari ne tass mai manyan flowers blue baki ta taɓe tana kallon kayan kan madubin. A fili ta ce "Yanzu zan yi abin da ya kawoni" Ta faɗa tana ajiye mukullin hannunta da yake da ta buɗe ƙofar da shi ta shiga, tana ajiyewa a zuciyarta ta ce 'Da zafi-zadi ake dukan ƙarfe, kuma da sanyin safiya ake kama fara, ba zan tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mini ƙafa ba, in dai zaman kishi ne ni babu macen da za ta iya gagarawa da ni domin sai na mata kishi da kissa ƴar ƙasa yadda sai ta ji tsanar gidan mijin da kanta don sai na takurawa kishiya" Ta faɗa tare da buɗe drower Sadiya ta shiga bincike kayan kawai take watsowa ƙasa amma bata ga abin da take nema ba. Haka ta gama bincikenta ta mayar da su yadda suke tamksr bata taɓa su ba domin ta iya takunta. Haka ta gama dubawa amma bata ga abin da take nema ba, ranta sai wuya yake saboda ta san tabbas yau wata dama ce da ta samu wacce ba lallai ta same ta ba. Ƙarƙashin gado ta shiga dubawa amma bata gani ba, tsaye ta tashi ta tsaya rana riƙe da tsantsa ta damƙe fatar bakinta da haƙorinta na sama. Duk cikin wani abu da take gani za a ɓiye abin da take nema ta duba amma bata gani ba, gadon ta taka ta duba saman drower nan ma babu sai da ta sakko ta lura da ƙaramar lokkar jikin bed side drower da sauri ta jufi can ta buɗe sama da ƙasa amma babu. Kasancewar biyu ne sai ta koma ɗaya gefen ta buɗe ta saman sai ta ga panties ɗin Kakifa ne a ciki wanda suke a laye, tsaki ta yi ta tuƙunɗuna su ta tura ta rufe lokar, tana janyo ta saman sai ta ga wata ƙaramar jaka pose taɓa jakar ta yi ai kuwa ta ji ɗan tudu da sauri ta fito da jakar tana fatan a dace tana buɗewa kuwa ta ga abin da take nema wani murmushi mai bayyana haƙora ta yi ganin kuɗaɗen a ciki a laye suke kasancewar pose ɗin tana da ɗan girma, ƴan dubu dubu ne a laye sai ƴan ɗari biyar biyar sai ɗari bibiyu da ƴan ɗari ɗari. Ganin kuɗin cunkus sai abun ya bata mamaki a ƙiyasce tana tunanin kuɗin nan zai iya kusan kaiwa dubu ɗari. Fito dansu ta yi duka ta zige zip ɗin ta buɗe ɗaya gefen sai ta ga ƴan hamsin hamsin ne da sauran canjuna a ciki su kuma dai ba su fi dubu biyar ba fito dansu ta yi duka a fili ta furta "Wai dama sana,ar cikin gida tana kawo kuɗi har haka? Lallai wannan ake cewa bar ganin ka tara ka kiyayi mai nema ashe har tana samun rufin asiri a sana,arta haka lallai na yi sake!" Ƙaran bugun ƙofar gida ne ya ankarar da ita vata san lokacin da ta tashi tsaye daga zaunen da take ba, ga kuɗin duk ta baza haka ta shiga haɗa su tana karkarwar jiki don ta san asirin ta zai iya tonuwa tunanin ta ma Sadiya ce ta dawo duba mukullin da ta jefar. Lokar ta mayar ta rufe ta naɗo ƙasan rigarta da ta zuba duka kuɗin sai da ta zo faon a guje sannan ta tuna da mukullin da suri ta juya ta ɗakko har lokacin tana ji an bugawa fitowa ta yi amma bata rufa ɗakin ba ta ce "A nan ne? Waye?" Ta faɗa tana jiran jin muryar Sadiya kawai sai ta ji muryar wata yarinya ta ce " Mango da zoɓo za a bani" Wani uban tsaki ta ja ta ce "A kan wani mango za ki zo ki damu jama,a to an dajna siyar da mango da zoɓo a nan" Yarinyar ta ce "To akwai pure water?" Meenal ta ce "Babu pure water sai ubanki" ,Ta faɗa a zuciye yarinyar ta ce "Na gane ki ba anty Sadiya ba ce kishiyarta ce ƴar baƙin ciki wataƙila antyn bata nan" Tana faɗar hakan ta ɗauki dutsi ta buga a ƙofar da ƙarfi ta zuga da gudu, Meenal tana so ta zo ta buɗe ƙofar ta kikkifawa yarinyar mari amma kuma abin da take yi ya fi wancan. Ɗakin ta koma ta ɗakko jakar ta rufe lokar ta tsaya ta tabbatar da komai yana yadda yake ta fito ta zo ta kulle ɗakin. Ɗakinta ta nufa da sauri ta je ta juye kuɗin a jakarta ta fito da pose ɗin a hannunta kicin ta je ta ɗakko ashana ta xo ta kyarta ta sakana jikin pose ɗin ganin jakar ta kama ta sheƙe da dariyar mugunta, sai da ta ƙone ƙurmus ta tattara ta kwshe ta je ta yi fuloshin ɗinsa a toilet. Mukullan ta ɗakko ta zo wajen zaure ta jefar da su a ƙasa ta koma ta kwanta a bedroom ɗinta tana lissafa kuɗaɗen da ba da guminta ba ta samu tana jin daɗinsu. A fili ta ce "Sadiya mu zuba ni da ke yanzu dai baki da tsumi baki da dabara idan musgunawa ta ta ishe ki ke da kanki za ki san na yi" Tana cikin wannan maganar sai sheɗan ya ƙara kissima mata wani mugun abun da sauri ta tattara kuɗin ta mayar tana mayar da jakar drower ɗinta ta fito daga ɗakin, mukullan ta sake ɗauka sai kawai ta nufi kici ɗin Sadiya ta buɗe ta dawo ta buɗe ƙofa ta aiki wani yaro ya siyo mata kananzir ta rufe ƙofar ta je ta yi abin da za ta yi ta mayar ta rufe ta ta kai ƙaramar jarkar lemon coca cola da aka sayo a ciki ta ba wani almajiri shara ya zubar mata dama jarkar tana ciki. Sadiya sai bayan magriba ta dawo bata ma san ta jefar da mukullin ba sai da ta dawo ta buɗe aljihun jakarta ta ga ba ya nan ɗan ja baya ta yi tana haska fitilar wayarta kawai sai ta ga Kalifa ya miƙo mata mukullan ta tambaye shi sai ya nuna mata ƙasa kusa da inda take tsaye hakan ya sa ta gane a gabanta ya ɗakko sai ta yi tunanin yanzu da ta buɗe jakar ya faɗo bata sani ba. Hankali kwance ta buɗe musu ƙofar suka shiga don zuciyarta wasai take ji babu damuwa domin Kaka ta mata nasiha da kuma ƙara bata haƙuri a kan lamarin zaman auren ta tana nuna mata komai ya yi farko yana da ƙarshe don kowace gona tana da kunyar ƙarshe ta faɗa mata idan dai mace ta haɗu da fitinanniyar kishiya ko fitinanniyar uwar miji ko dangin miji sai ta yi haƙuri duk mai haƙuri watarana zai dafa dutse har ya sha romonsa. Ta ƙara koya mata dabaru da kissa da za take nunawa kishiyar duk abin da take mata ba ya damun ta. Sai batun ƙauracewa ɗakinta da Nasir yake da ma ƙaurace mata baki ɗaya shi ma ta ce ta yi haƙuri lokaci ne, sannan shi lokaci alƙali ne watarana da kansa zai neme ta don Kaka ta faɗa mata cewa namiji tamkar sauyin abinci haka ya ɗauki mace ta bata misali da cewa shin za ta juri cin abinci ɗaya kullum? Wato koyaushe a ce ta ci shinkafa da miya sai Sadiyar ta nuna za ta so sauyi watarana mana yau ta ci shinkafa gobe taliya jallof jibi wake da shinkafa ta haka Kaka ta nuna mata cewa to akwai ranar da Meenal za ta gunduri Nasir ɗin ya ji yana son kasancewa da Sadiya don kowacce mace halitta da baiwar ta da ban wata ta fi wata kawai dai idan kana da kyau sai ka ƙara da wanka!. Sai da ta buɗe drower za ta ɗakko rigar bacci bayan ta yi wanka sai kawai ta ga kamar dai kayan ba haka suke ba, saboda Sadiya tana da lura da al,amura kawai sai ta fara zargin kayanta ba haka ta bar su ba duk kuwa da Meenal sai da ta gyara komai, a ƙarshe Sadiyar ta saka a ranta cewa ita da ta kulle ƙofar ɗakinta kuma ma ai babu yadda za a yi a shigo mata ɗaki me ma za a yi a ɗakinta. Bayan sun kwanta Kalifa ya yi bacci, don tana jin lokacin da Nasir ya dawo amma ko ɗakinsu bai zo ba dama kuma ta san da hakan. Kuɗin da maƙociyar Kaka ta bata na kayan kori da spices da ta ce a turawa maman afrah za a kawo musu curry kwano ɗaya spices na shayi rabin kwank sai spices na girki kwano ɗaya, jan yaji rabi yajin daddawa kwano ɗaya, sai kuma kuka da kuɓewa da niƙƙaƙƴiyar daddawa. Don ita ma natan babu, kuɗin ta ɗakko ta lissafa tana tunanin da safe za ta yi wa maman afrah magana ta tura kuɗin sai a sako musu a mota. Lokar da take ajiye kuɗaɗenta ta buɗe za ta saka kuɗin a ciki domin tana da kuɗi a monie point sai ta yi wa maman afrar transper, tana buɗewa ta ga wayam babu jakar gabanta ya buga da mugun ƙarfi, ta sake dubawa amma babu jaka babu alamar ta, lokar ta ciro daga ciki dukanta ta shiga leƙwa amma jakar ta ce ɗaukeni inda kika ajiye!. MAMAN AFRAH 09025576222 https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣6️⃣ SADIYA "Innalillahi wa inna ilaihi raji,un" Sadiya ta furta a fili tana miƙewa tsaye ta shiga dudduba wajen tamkar dai jakar za ta gani gabanta yana faɗuwa ta shiga dubawa amma bata gani ba duk hanklinta ya tashi saboda kuɗinta ne da take son fita kunya idan ta haihu duk wani tanadinta yana cikin kuɗin amma ta rasa yadda aka yi ta rasa jakar, tun da ta tabbatar a lokar ta saka tun da kafin ta fita ma ta saka kuɗi a ciki. Da sauri ta janye ƙaramar bedside ɗin daga wajen ta duba bayan bed side drower ko ɓera ne ya ja don ra fara tunanin ko lokar a fashe take daga baya amma sai ta ga babu wani waje da yake da alamar fashewa a jiki. Lokar saman ta janyo tana birkicewa wai ko dai a ciki ta saka duk da Sadiya bata da mantuwa komai nata a nutse take, ma,ana ta san a lokar da ta saka kawai dai tana dubawa ne amma wayam babu ko alamar jaka bare a je batun kuɗi.Birkice ta shiga yi a ɗakin amma babu jaka babu alamarta haka ta fito falo kamar zautacciya domin ita ta san irin wahalar da ta sha a kuɗin tun da halaliyarta ce duk wani mai neman halal kuwa ya san neman halak da wuya!. Duk hankalinta ya tashi sai da ya dawo ta ga kuɗin da ta karɓo na curry da sauransu sai ta yi tunanin wancan kuɗin ne da take nema amma sai da ta zo ta tuna haka ta dawo ta zauna tana ta ambaton Allah a zuciyarta har dai ta samu nutsuwa a zuciyarta. Tana iya jiyo ƙaran TV daga ɓangaren Meenal kuma ta san shi ma mai gidan ya dawo amma ko leƙo ta bai yj ba domin ta ji zuwansa. Ita dai ta san ɗakinta a kulle kuma ko ma ba a kulle ba abu sabo abu ne da ba a taɓa.yimata ba wato sata, saboda ta san in har ba ita ta yi niyyar yin alheri ta ba mutum kuɗinta ba babu mai ci sai dai ko Nasir idan son kuɗinsa ya tashi ya ce ta bashi don kawai taƙamar tana matarsa bayan kuma shi ba bata yake ba. Haka ta jure ta haƙura ta kwanta tun da babu wanda za ta tunkara da maganar, haka ta yi addu,a ta kwanta tana ta tunani da ciwon rai ya ishe ta kawai sai hawaye ne suke zuba, ta jima tana hawayen nan har da sheshsheka kafin daga bisani bacci ya yi awon gaba da ita bata falka ba sia wajen ƙarfi biyu da kwata haka ta tashi ta yi alwala ta yi nafila bayan ta idar ta zauna ta yi karatun qur,ani sannan ta karanta sunanyen Allah tare da salatin annabi S.A.W ta ɗaga hannu ta ce "Ya Allah kai kake ƙaddara komai a lokacin da ka so, ya Allah na san kai kake bayarwa kuma kai kake hanawa Allah ka san damuwata a kan jakata da na rasa ya Allah idan rabona ce ka bayyana min ita idan kuma babu rabona ka sauya min da abin da ya fi alkairi, na yarda da duk wani abu da za ka ƙaddara min" Haka ta gama faɗawa ubangiji tana hawaye tare da jero wasu buƙatub nata sannan ta ƙara yin salatin annabi S.A.W ta shafa addu,ar Ta koma takwanta sai ta ji zuciyarta ta yi wani irin sanyi duk damuwa da nauyin da zuciyar ta yi babu shi!. Da asuba ta yunƙura dakyar ta yi sallah ta sake karatun qur,ni da yin addu,o,in ta. Da safe da ta fito sai take jin duk babu daɗi yadda babu nepa a ɓangarenta ita bata san ma wanda za ta faɗawa ba, ɓangarenta basa son ta kai ƙaransa shi kuma nata ɓangaren basu damu da ita ba basu san muhimancjn ta ba, sai dai kawai ta san akwai sakayya. Tsakar gidan ta nufa, da yake wajen ƙarfe bakwai ne ruwan zafi za ta ɗora saboda yunwa take ji kasancewar mace mai ciki akwai jin yunwa, ga shi kuma ita bata da nepa bare ta jona a nepa. Tana zuwa ta buɗe kicin ɗin sai lokacin ma ta tuna gawayin nata ya kusa ƙarewa, a haka ta ɗauke na ƙasan buhun duk da ya zama ƙareci duk ƙanana ne, ta samu ta hura da ya kama ta ɗora ruwan. Waje ta samu ta zauna a kicin ɗin tana jiran ruwan ya tafasa tana zaunen tana kallon kayan sana,ar da suke gefe a cikin kicin ɗin aajiye manja farin mai da sauransu tana tuna yadda jakar kuɗinta ta ɓace jiya, tunaninta ɗaya yanzu idan suka ƙare yadda za ta haɗa kuɗin ta saro wasu domin ba lallai ta haɗa kuɗin ba kasancewar asarar da ta same ta duk da ta san Allah ne ya ƙaddara mata. Da ta dama kokon, sai ta ɗauki sauran fulawar da ta rage mata wacce ita ta saya ta kwaɓa ta musu waina ta saka a fulas ta gaa sai ta ɗora ruwan zafin wanka wanda ta san ma ba lallai gawayin ya isa dafawa ba. Kicin ɗin ta janyo bayan ta ɗakko jug ɗin kokon da kuma kwanon wainar. A falo ta ajiye sai ta koma ta ɗakko plate da kofi da cokali ta dawo ta zuba wainar da kokon da ta saka sugar ta zauna tana ci bata ma ra,ayjn ci da ya ji sai da ta ji ta ƙoshi ta rufewa Kalifa sauran. Tana jin lokacin da su Husna suka buga gidan aka buɗe musu wajen ƙarfe takwas kuma Meenal ce ta buɗe tana jin yadda take musu masifa wai sun ɓata lokaci ba su zo da wuri ba, haka ta ji suna bata haƙuri kamar wata uwarsu. Har suka gama suka tafi bata fito ba Kalifa kuma har lokacin bacci yake kasancewar jiyan ya yi ta gijifgijiftu a gidan kaka, saboda gajiya shi ya sa bai tashi da wuri ba. Bayan tafiyarsu sai ta gyara ɗaki ta share tas ta yi goge goge sai ta kunna turaren tsinke, tsakar gidan ta shiga sharewa, sai ta ta je tana tattarawa sai kawai ta ga wani abu da ya bata mamaki, da sauri ta kai hannu ta ɗakko tana juya shi a hannunta gabanta ya buga da ƙarfi domin tabbas ko tantama babu zip ɗin jakarta ne, abin da ya sa ta game shi zip ɗin jakarta daga aarshensa a ɗan lanƙwashe yake ba komai ya lanƙwasa shi sai wani lokaci ya cije ya ƙi ziguwa shi ne ta maƙala shi jikin ƙofa ta cisga da ƙarfi shi ne ya lanƙwashe daga wajen kamawar, abin da ya bambanta wannn da nata shi ne wannn baƙiƙƙitin da shi kamar wanda aka ƙona shi. Tsaye ta miƙe tana aara ƙare masa kallo fitowar Nasir da Meenal daga ɗaki ya sa ta yi saurin juyowa, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai kamar ya ga kashi sai dainita ba wannn bane a gabanta saboda yanzu abinnda yake gabanta na mamaki da al,ajabi ya danne komai. Ba ta san lokacin da ta ce "Wallahi wannna ƙarfen zip ɗin jakata ne" Dududdummm gaban Meenal ya harba da ƙarfi amma saboda ƴar bariki ce sai ta basar tana mayar da kallonta kan Nasir tana wani kashe murya shi kuma yana biye mata bai ma damu da maganar da Sadiyar ta yi ba sai da Sadiya ta ankara da abin da ta ce sannan cike da sanyin murya ta ce "Ina kwana Abban Kalifa, an tashi lafiya" Ta faɗa a tare don gabaɗaya ta shiga ruɗu da tunanin yadda aka haihu a ragaya. Amsawa ya yi kamar an masa dole ganin haka sannan kuma ta ga alamar Meenal ba za ta bari su yi maganar ba sai ta ce "Wallahi jakata da nake ajiye kuɗin cinikina ne ta ɓata rasa ta na yi kuma abin mamaki yanzu da nake shaarar nan sai na ga ƙarfen zip ɗin a can" Ta faɗa tana nuni da inda ta ga zip ɗin. Meenal kai ta kawar gefe domin kar a hango jirginta shi kuma tamkar ta faɗa masa saƙon mutuwa ya gaɗe girar sama da ƙasa ya ce "To ko ni ne na ɗauka?" Ya tambaya cike da gatse. Kai ta girgiza alamar a,a ganin yana neman ɗora mata jakar tsaba kaji su bi ta sai ta ce "Kawai dai ina mamaki ne wallahi abin kamar almara"Hankalinsa ya mayar kan Meenal da take magana cikin muryar ɓaci duk ta wani shagwaɓe fuska. Meenal tana ta mamakin yadda aka yi da ta ƙone jakar bata ɗauke da ƙarfen zip ɗin ba. Ya fara tafiya Sadiya ta ce ",Ina da magana " Ya ce "Za ki iya faɗa tun da babu bare a nan" Kallon fuskar Meenal ta yi wacce ta murmusa fuskarta ta nuna alamar murmushin ƙeta wato da alama ta zama ƙarfen ƙafa komai ma a gabanta za a faɗa. Daurewa ta yi tana danne takaicin da suke ƙunsa mata wanda watarana sai zuciya ta zuga ta a kan ta rama sai kuma wata zuciyar ta ce ta ƙyale watarana saj labari!. Tana kallon yanayin fuskarsa ta ce "Gawayina ne ya ƙare ɗazu ma dakyar ya isa na yi amfanj da safe... Numfashin ta ya tara da faɗin "Sadiya ni ba na son almubazzaranci ta yaya za a yi gawayjn a ce har ya ƙare to ni ba ni da kuɗj yanzu sai dai ko in bada itace a kawo miki" Ƙwalla ta taru a idanunta bayan da gawayi take amfanj Meenal tana amfani da gas sannan kuma tana cancantawa amma kuma yanzu a mata maganar ita ce jin hakan Meenal ta ce ",Gas ɗina ni ma fa ina ga ya kusa ƙarewa" !Wani irin washe baki ya yi ya ce "Tohm zan saka miki idan na dawo" ,Tana masa bye bye ya fita ya tafj Sadiya kuma ta kasa motsawa ma daga wajen, wannan abubuwa ne masu tarin yawa da suke nuni da cewa Nasir ya gaji da ita, sai dai tana jiran ranar da Allah zai kawo mata mafita a lamuran nan. Tana jin yadda Meenal take dariya har da ƙyaƙyatawa da ta ga ta nufi ɗaki, ko da ta shigo ɗakin zaman dirshan a falon tana tunanin ƙarfen zip ɗin da ta tsinta ta rasa ta yaya haka ya faru ta rasa kalar tunanjn da za ta yi, iya hasashe da tunanin ta bata samu amsar ba da a ce a buɗe ɗakinta yake za ta zargi komai ma sai dai a rufe yake sannn da mukulli ta fita idan ba aljannu ba waye zai ɗauka?. Kukan da Kalifa ya saki ne ya dawo da ita daga tunanin da take. Zuwa can aka zo sayen manja ganin babu ƙullal ne a leda saj ta buɗe jarkar ta tsiyaya a za ta ƙulla saj ta ji warin kananzir cike da faɗuwar gaba ta kai hancinta jikin ƙofar amma sai ta ji warin tamkar ta shinshina jarkar kananzir, da sauri ta saki murfin jarkar ta nufi ɗayan ta farin mai gabanta yana faɗuwa ta buɗe amma cikin ikon Allah sai ta ji babu warin hamdala ta yi a ranta tana ta kissima abubuwa a ranta duk da an ce zato zunubi amma kam tana ta zargi a zuciyarta. Ko da ya tafi ko ƙeyarsa babu bare a samu wanda zai kawo mata itacen da ya ce, da rana dai gari da madara da sugar ta haɗa musu suka sha, tana tausayin Nasir ranar da haƙƙi zai tambaye shi musamman haƙƙin ɗansa Kalifa domin shi yaron ko kaɗan bai san daɗin uba ko kulawarsa ba ga shi koyaushe daɗa wayo yake, ita damuwarta ma yadda yaron idan ya ga ana mata abu yake nuna rashin jin daɗi ta hanyar kukansa ko kuma yake goge mata hawaye yana ambaton Momma Abba ne? Duk da tana iya yinta don ganin bata kuka a gabansa. Tana tsakar gida lokacin almajirin Meenal yana mata sharar baranda, ita kuma ta kinkimo jarkar man mai warin kananzir sai kawai suka yi ido huɗu da Meenal ta mata dariya, hakan ya sa a ƙufule Sadiya ta ce "Wai mai kika mayar da ni ne Meenal sai kike kallona kina min dariya kamar wata mahaukaciya kika gani?" Dariyar ta ƙara yi a karo na biyu sai Sadiya ta ce "Ko mai mutum ya yi ya je shi da Allah domin yana can a madakata yana jiransa duk daren daɗewa akwai mutuwa sannan akwai hisabi shi dai ubangiji ba ya yafe haƙƙin wani a kan wani" Ɗan dum Meenal ta yi sai ta ji ta kasa cewa komai domin zuciyarta ta fara raya mata ko dai Sadiya ta gane ita ta mata sata kuma ita ta zuba mata kananzir a cikin jarkar manja, domin yanayin furucinta ya bayyana kamar dai akwai wani abu. Ɗakinta kawai ta wuce ba tare da ta ce komai ba. Da yamma Sadiya ta masa waya tw ce za ta je gidan Hajiya bai musa ba don ya san wani neman wajen ne za ta je tun da Hajiya dai ba ra,ayinta take yi ba, sannan kuma ya san tana zuwa za ta dawo a kan sawunta tun da ba ma lallai a ƙara mata magana daga gaisuwa ba. Ko da ta je gidan Hajiya ta samu Hajiya zaune a gindin murhu tana tuƙa tuwo, sai goge ido take saboda hayaƙi, ta amsa mata babu yabo babu fallasa don su Hibba ma ba sa gidan sai ita kaɗai. Tabarmar da aka shimfiɗa a wajen ta zauna, ko Kalifa Hajiya bata wa magana ba. Sai da ta rufe tukunyar bayan ta gama tuƙawa ta taso ta shiga ɗaki ta jima sannan a shelaƙe ta fito ta zo ta zauna daga can bakin barandar Sadiya ta ce "Dama wata magana na zo da ita... Hajiya ta tari numfashin ta da faɗin "Sadiya ni ba na sin kinibibi da gutsiri tsoma, wace irin magana ana zaune ƙalau dama duk mace ai sai ta yi haƙuri a gidan miji sannan dama idan kika san ma ba ke kaɗai ba ce sai dai ki kauda kai saboda wani namijin idan ba ya ra,ayin ɗaya ya fi ra,ayin ɗaya a cikin matansa sai dai wacce ba ya ra,ayi ta ɗauki dangana, idan ma ta ce sai ta ga yadda take so tabbas iska tana yawo da mai kayan kara ne!" Ɗago kai Sadiya ta yi suka yi ido huɗu Hajiyar ta kauda kai gefe, sai Sadiya ta ce "Ba a kan wani abu ba ne dama, kin san ina sana,ar kayan sanyi to shi ne ƴan nepa suka cire wutar ɓangarena shi kuma ya ce sai ina biyan kuɗin wuta ... Hajiya ta tare mata numfashi da faɗin "Ai ya yi daidai! Kina neman kuɗi kuma a ce sai ya biya kuɗin wuta? Ko shi kike ba kuɗin cinikin yake sakawa a aljihunsa" Girgiza kai Sadiya ta yi daman ta san ba za a mata adalci ba hakan ya sa ta ce "Yanzu ai na ce zan ke biya amma kuma bai san an mayar mini ba, ana zuwa neman kayan sanyin ina cewa babu kada kasuwar ta mutu shi ya sa dama na ce bari na zo na faɗa miki ko za ki masa magana" Hajiya ta ce "Sai ki ɗauki na annabawa ki jira lokacin da idan ya gama busar iska zai sa a gyara miki, abin da sana,ar da kike ta fi goma ko kin ɗauka ba sani ba ne, tun da laila ta ƙiya sai a koma caca, ai a yadda kike caskar kuɗina wannan gidan da ke matan da suke son miji ne da ko aikin hajji ne ma kin biyawa Nasir tun da ta dalilin zaman gidansa da albarkarsa kike samun kuɗi" Shiru Sadiya ta yi ta ma rasa mai za ta ce sai kuma ta daure ta ce "Yanzu gawayina ya ƙare kuma na faɗa masa ya ce ba shi da kuɗi ita kuma ta ce babu gas ya ce zai saya mata.. Hajiya ta katse mata hanzarin wajen faɗin "Ya isa Sadiya na gaji da jin ƙorafinki ai dama tun da na ga kin ɗakko ƙafafu da ciki tirtsi tirtsi ke ga kaza sarkin haihuwa san sai dai ƙorafe ƙorafen ne zai kawo ki Allah na tuba gawayin me duk neman kuɗin da kike ma ai ke ya dace kike ciyar da kanki, kuma da kike maganar gas ni baki ga da abin da nake amfani ba tun da gas ɗin ya ƙare sai kawai mai baro na gani da itace Nasir ya aiko, tun da ya haɗu da mace mai jan akala da ragamar rayuwarsa sai dai mu zuba ido" Sadiya ta ce "Amma ni ma ai haƙƙina ne ya saya mini, kuma duk arziƙin da mace take da shi Allah bai ɗora mata ɗawainiya da kanta ba, ko da ta fi mijin nata kuɗi haƙƙinta na komai yana wuyansa sai dai idan ita ce ta ga dama bisa kyautatawa!" Hajiya ta ce "Yi min wa,azi Sadiya kin san ai ni kidahuma ce babu abin da na sani" Sadiya ta ce "Ba haka ba ne Hajiya, wallahi jiya da na fita gidan Kaka na dawo na rasa jakata da nake saka kuɗaɗe a ciki, sannan jarkar manja na tarar da kananzir a ciki... Tun bata kai aya ba Hajiya ta ce "Bakya fitar da zakka ne, ai dama wanda ba sa fitarwa da dukiya zakka su asara take faɗawa" Kallon Hajiya kawai take sai kuma ta ce "Ai sana,ar tawa bata kai munzalin da zan fitar mata da zakka ba, ina sadaka dai" Hajiya ta ce "Ke kika sani da yake matsaloli ne suka baibaye ki shi ne kika zo kina zana mini kamar mai biya mini karatun hadda, to sai ki ɗauki ƙafarki ki koma inda kika fito, ko a tunaninki zan zaɓe ki ne in ajiye ƴata Meenal a kan maganar siyan gawayi da gas ai wata kusar ta fi wata kinnga tafiyata" Hajiya tana kaiwa nan ta tashi ta shiga kicin ta ɗakko robar da za ta kwashe tuwo ta yi ajen murhu, Kalifa sai kallonta yake abin takaicin ko uffan bata ce masa ba wai yana jikanta ɗaya tal duk duniya. Haka ta baro gidan ranta yana ƙuna, tana tafiya tana ta addu,a da karanta sunayen Allah a kan ya kawo mata mafita, ƙaran wayarta ne ya katse mata tunani ta ɗaga ganin sunan ƙawarta Noor tana ɗagawa ta ce "Albishirin ki" Sadiya ta ce "Goro fari ƙal" Noor ta ce "Sunanmu ya fito a wannan tallafin da muka cike an ce gobe za a je a karɓi 75k " Sadiya kawai sai ta ce "Alhamdulillah, Alhamdulillah" Sai da ta faɗa sau uku Noor ta ce "Wannan hamdalar fa?" Ta faɗa tana dariyar tsokana Sadiya ta ce "Wallahi kawai wata hikima ce ta ubangiji Allah maji roƙo ne, duk wanda ya dogara da shi zai kawo masa mafita, na san wannan sakamakon addu,a ta ne da na yi da yaƙi ni" Noor duk da bata san komai ba sai ta ƙara mata ƙarfin gwiwan na ta ce idan sun haɗu goben za su yi maganar. Ko da Nasir ya dawo ta faɗa masa cewa ya saka a mayar mata da nepa za ta biya kuɗin sai ya nuna mata ba yanzu ba, ai kuwa ta ƙyale shi. Washe gari suka je suka karɓo kuɗin duk da sun samu layi, dama NIN no da BVN ne ake buƙata da aka cike aka muau hoto sai aka basu ATM mai ɗauke da kuɗin suka cire suka taho gida Sadiya ranta fari ƙal. Lokacin da ta dawo sai ta ga ƴan nepa su biyu a ƙofar gidan wani maƙocinsu daga can gaba suna mayar masa da wutar da suka yanke, ai kuwa ta musu magana ta biya suka mayar mata da tata wutar ɓangaren nata. Meenal ta fito daga ɗakinta sai kawai ta ga hasken ƙwan ƙofar ɗakin Sadiya ya kawo hakan ya tabbatar mata da cewa an mayarwa da Sadiya nepa ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, ta ƙufula tana jiran ya dawo don a tunaninta shi ya sa aka mayer da wutar. Lokacin da ya dawo Sadiya ta fara jiyo hayaniya sosai ana ta tafka faɗa, sai dai bata san abn da suke faɗa ba, tana zaune tana cin farar da ta siyo sai gashi kamar an jefo shi yana shigowa ya ce ,"Wane shegen ne ya mayar miki da nepa?" ,Ya tambaya ransa a matuƙar ɓace kamar zai hau ta da duka. Ko gizau bata yi ba ta dake ta ce "Ni ce nan na saka aka mayar mini, saboda na ga baka da niyyar sakawa a maida, ni kuma ina da buƙatar ta, tun da dai ba ni da galihu a matsayjna na matarka da zan aamu wutar nepa a ɓangarena duk da na ce zan biya shi ya sa da na gansu a unguwar suna mayarwa da wasu na ce su zo su mayar mini na biya su kuɗinsu" Kallonta kawai yake yana kissima yaushe Sadiya ta zama haka har take mayar masa martani ko ɗarɗar babu. Meenal da take laɓe a ƙofar ɗakin Sadiya don son jin ƙwaƙwaf domun ita bata yarda da maganarsa ba da ya ce ba shi ya sa aka mayar ba sa ga shi kunnuwanta sun jiye mata. Da yatsa ya nuna ta ya ce "Har ni zan saka doka a gidan ke ki ƙetara?" Tsaye ta miƙe ta ce "Ka sa an yanke min wuta na ce a mayar ka wofantar da maganar bayan ka san sana,a nake, na faɗa maka na rasa jakar kuɗina amma ko a jikinka, bayan fitarka daga gidan na samu jarkar manja na ɗauke da kananzir saboda na san ma ba ɗaukan maganar za kamyi da muhimmanci ba ko faɗa maka ban yi ba, na ce maka gawayi ya ƙare ka ce baka da kuɗi, na je na faɗawa mahaifiyarka amma bata goyi bayana ba, ka ga kenan ni idan na biye maka zan dawwama ne babu ƴanci shi ya sa na saka aka mayar mini saboda wannan sana,ar da ita nake tallafawa kaina" ,Tana kaiwa nan ta ɗauki ledar farar ta ta ci gaba da ci. Rasa ma abin da zai ce ya yi sai kawai ya juya fuuu ya fita, Meenal da take laɓe bata zaci fitowarsa a lokacin ba, sai kawai ta gan shi, rai a ɓace ta sha gabansa cike da ƙaraji ta ce "Tun wuri ka saka ƴan nepa su zo su yanke wutar nan tun da babu yawunka wajen mayarwa, kana mai gida mace ta yi abu babu izininka kenan ka zama mijin ta ce, nan gaba duk hukuncin da ka zartar ba za ta bi ba" Shiru ya yi yana nazarin maganarta, ya juya kenan zai koma yan saukewa Sadiya ya nuna mata bata isa ba sannan ya saka a yanke mata wutar sai kawai ya ga Sadiya ta fito kamar an jefo ta rai ta haɗe ta kalle su ta ce "Idan bai zama mijin ta ce ba ai ya zama mai ɗaukan zugar mace!. Wato dama ke kika saka shi aka yanke mini wutar ɓangarena, to wallahi wallahi wallahi ki fita idona na rufe don shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne, kuma wutar nan yadda aka mayat da ita ta maidu in dai kuɗin wuta ne zan ke biyan kayana, amma furucinki ya nuna ba wai a kan kuɗin wutar ba ne baƙincikin sana,ar ne kike... Hannu Meenal ta ɗaga mata tana faɗin "Ahir ɗinki Sadiya!. Na fi ƙarfin na miki baƙnciki a kan wannan sana,ar da bata taka kara ta karya ba" Sadiya tana riƙe ƙugu ta ce "Guntun gatarinka ya fi sari ka bani," Sai kuwa Meenal ta fara masifa tana cewa ta msta gorin sana,a shi kuma yana tsaye ya kasa crwa komauɓi don Sadiya ta goge masa hadda bai zaci za ta rikice har ta ƙwatawa kanta ƴanci ba. Faɗa ne ya kacame a tsakanin su amma Meenal ce take ta kumfar baki a dole sai an cirewa Sadiya nepa ita kuma Sadiya ta ce wallahi babu wanda ya isa ya cire mata nepa. Haka ta koma ɗaki tana faɗin "Wallahi idan aka cire mini nepa sai na kirawo ƴan nepa sun cire wutar gidan gabaɗaya sai dai kowa ya zauna babu nepa, in kuwa har wani ɓangare na gidan nan zai zauna da nepa to dole ya kasance nawa ɓangaren ma akwai wuta, domin ni ma mutum ce kuma ni ma matar gida ce kamar yadda kike matar gida" Tana jin su suna ta bala,i ita dai gabanta ma faɗuwa yake lokacin da take yin faɗan, amma ta daure ne saboda ta lura matsawar bata ƙwatawa kanta ƴanci to tabbas shan ruwa a gidan ma sai ya gagare ta, ga shi yanzu za ta yi haihuwa ta biyu kenan ita da ƴaƴanta za su rayu babu ƴanci a cikin gidan. Nasir ya sha masifa a wajen Meenal don tana faɗin ya zaɓi da Sadiya a kanta. Ranar a kan gado ya kwana shi kaɗai ita kuma a ƙasa don kawai ta nuna masa tana fushi, ta ɗauka zai saka a cire nepar washe gari sai ta ga ɗiff bai yi maganar ba ma hakan ya sa ta saka a ranta dole ta je gida domin ta kaiwa Momi kuɗi a je a yi aiki a kansa wato ya dawo sai abin da ta ce masa. Sadiya kuwa a daren ta haɗa mango juice da zoɓo ta saka a frezer ɗinta. Tana ta addu,ar Allah ya ɗota ta a kansu, tun da ta ga dole sai tana kataɓus wajen ƴancinta tun da babu mai bin bayanta ya ƙwatar mata haƙƙinta daga gidansu har gjdansu Nasir ɗin. Tuni kasuwar kayan sanyi ta dawo, bayan kwana biyu aka sake kafe sunayen ƴan tallafi Allah da ikonsa sunan Sadiya ya sake fitowa amma wannan karon ban da Noor dama an ce wasu hsr sau uku ma sunan su yana fitowa haka ta je ta karɓo kuɗin nan, tana ta al,ajabi duk da ba a mamaki da lamarin ubangiji ga shi dai ta yi asara amma da yake Allah maji roƙo ne ya mayar mata a lokaci ƙanƙani, sai ta sauya wajen ajiya kawai ya zamana ƙananan kuɗi take ajiyewa a gida, su manyan kuɗin kawai sai ta ba almajirinta ya je pos ta rubuta masa acc no ta a je a tura mata, ya zamana ba ta ma ajiye cash ɗin bare a ɗauke. Meenal kuwa wuni ta tambaya zuwa gidansu, ta haɗa kan kuɗin wajen Sadiya wanda ta sata, da na wajen Nasir da take masa sata yadda ba zai gane ba, ko ya ce zai sauke ta a gida sai ta ce masa ya je za ta hau napep. Waya suka yi da wani Alhajinta cikin wanda suke holewarsu kafin ta yi aure sannan suna shirmensu a waya ma, haka suka haɗu a hotel ya kama musu ɗaki suka sheƙe ayarsu, ya mata alƙawarin za ta ji alert mai nauyi domin a lokacin wai bankinsa ya samu matsala kuma ba shi da cash. A ƙofar gidansu ya sauke ta, dama ta yi wa Momi waya haka suka fito Momi ta tare musu wani mai napep, su biyu ne a ciki mai napep da kuma wani a gefensa a zaune, Momi ta kwatanta musu inda za su kaisu, don sosai sai an fita ma daga gari wani ɗan ɗauye ne haka suka yi ciniki, sai suka yanka musu kuɗi da yawa Mominta dage tana neman ragi buɗar bakin Meenal tana dariya ta ce "Momi akwai kuɗi fa, kuɗi ba matsala ba ne kawai mu je ai biyan buƙata kawai ake so, ai tun da Nasir har ya fifita wanann ƙazamar matar tasa marar aji sai ya gwamamce kiɗa da karatu" Momi ta ce ",Yaushe ta zama ƙazama bayan na ji ana cewa tsaftar masifa gare ta" Meenal ta ce ",A,a kawai na faɗa ne" Haka suka ci gaba da tafiya suna tafiya su Meenal da Hajiya suna ta tattauna zancen kuɗin da yake a jakar. Momi ta ce ,"Wallahi gwara da kika raba shegiya da kuɗin ai da sannu zaman gidan zai gagare ta," Meenal ta ce "Ai bokan nan ko nawa ya buƙata zan basho, dama akwai ma wani alƙawarin kuɗi da aka mini" Sun saki baki suna ta zuba, basa lura da cewa basu san su waye masu napep ɗin ba, kawai mutane in suka shuga napep ko motar haya sai su saki baki suna ta zance, wani ma sirrinsa zai ke faɗa abubuwa dai barkatai ba a takatsantsan. Duk abin da suke masu napep ɗin suna jin su, sannan suna ta yi wa juna magana da ido don sun gama shirya komai ba tare da su Meenal sun sani ba. Sai da suka yi nisa a tsakiyar daji gaba babu kowa haka ma baya sai kawai mai napep ta taka birki ya tsaya Momi ta ce "Ya dai?" Sai ya ce "Mai ne ya ƙare shi ne zan zuba wani" Meenal ta ce "Don ma kana da akwai da yanzu a nan ina za a samu wani mai" Mai napep ta ɓangaren Momi ɗayan da ya fito ta ɓangare Meenal dama majiya ƙarfi ne, hasali ma ba masu napep ba ne arowa suka yi a wajen abokinsu don su yi damfara sai kuma tsautsayi ya faɗa a kan su Momin. Duka suka yi wa su Momin suka ƙwace jakar Meenal da wayoyin su, sai da suka musu lilis sannan suka shiga napep ɗin suka kwasa a guje, suka bar su yashe a nan tsakiyar hanyar tsakar daji, kowacce tana murƙususu don hatta bakinsu da hanci ya sha naushi, basu ma da ƙwarin gwiwar hadda ce lambar jikin napep ɗin! Yau Sadiya kawai muka taɓo ina da uzuri ne. MAMAN AFRAH 09025576222 https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣7️⃣ UMMA Da tsananin faɗuwar gaba take kallon ƙullin maganin guda biyu da bokanya ta bata, tana jin tsoron tunkarar sabuwar gawar tare da taraddadin kar ta je asirinta ya tonu domin tana ganin ta yaya za a ce daga ka fesar da magani ya bi iska kowa zai suma? Wannan lamari ne mai girma sai dai tun da ta yarda da aikin sihirin bokanya sai ta cire kokwanto a ciki tana rayawa a ranta wannan lokacin sai an samu nasara fiye da lokacin da aka faɗi babu nasara wanda Aliya ta yi aikin cokali, sannan wannan lokacin ba za ta yarda ta yi asarar kuɗin da aka biya na maganin ba. Sai da ta sakko daga barandar ƙofar ɗakinta ta shiga tunanin ya za ta yi da Abba? Tun da dai ta san yana masallacin sai dai tuna sai an yi sallar isha yake dawowa hakan ya sa ta ji dama dama wai kibiya a ido. Fitowarta daga gida kenan ta tsaya tana kalle-kalle tun da dai ta san ita inda za ta je aiwatar da aikin nata aiki ne mai haɗari, sai dai dole ta yi takatsan tsan waje tafiya gidan Malam Kalla saboda yanzu dai ai maganin bai fara aiki ba tun da sai ta je ta fwsa maganin ne kowa zai suma sannan bakin kowa ya mutu komda wani ya gani bau mai tambya kamar yadda bokanya ta faɗa. Ko da ta tafi tana jin tsoron yana ƙara mamaye ranta, sai dai mugun nufinta a kan Jidda na sai ta dawo ƙarƙashinsu sun ƙasƙantar sa ita, Ibrahim ɗin da ya zama gatanta sun maido da shi soyayyar Aliya ce take mulki a cikin zuciyarsa, hakan ya sa ta ji wani irin ƙarfin gwiwa a zuciyarrta ta ce 'Jidda dole ne ki ƙarƙanta! Dole ki zama abin tausayi kuma abin kwatance amma ba kwatance mai kyau ba sai dai kwatance na tausayawa, ko maƙiyinki sai ya tausaya muki Jidda, domin yanzu ƙiyayyar da nake miki ta linku ba zai taɓa iyuwa ba ke kina rayuwa a cikin daula ke da baki da wani gata ko galihu, baki da wani kyakkyawan asali ke asali mai munin ba babu shi, har ki fi ƴata samun gata da kulawa kina rayuwa a haɗaɗɗan gida mai cike da ƴan aiki ana miki hidima ana girmamaki, kina juya kan naira ta yadda kika so, kina ado da zinare hmmm wai ke ce har mijinki yake yi wa uban da ba shi ne silar dirowarki duniya ba kyautar mota, ni tawa ƴar tana can mijinta yana yawo ranar duniya tana ƙarewa a kansa a kasuwa, tabbas da sake!' Ta faɗa tana ƙara sauri don ganin ta aiwatar da abin da ta yi niyya domin maganar zucin da ta yi ya ƙara ingizata a kan aiwatarwar. Tun da ta fito take cin karo da mutanr jifa jifa ana tafiya gidan, da alama jajanta mutuwar ne ko dai mutanen suna da alaƙa da mamacin wato ƴan uwa na kusa tun da dai an ce sutura sai gobe. Ta kusa ƙarasawa gidan ta hangi su Abba su uku shi da ladan ɗin masallacin nasu da kuma liman sun nufi gidan rasuwar, da sauri ta faɗa gidan ta tsaya daga bayan ƙofar gidan a cikin zauren ta laɓe a jikin ƙofar tun da ta san maganin bai fara aiki ba Abba yana ganinta zai tambaye ta ba,asi duk da mutuwa ce a maƙota yana da kyau a yi haƙƙin maƙota don jajantawa amma sai ya san ai duk gaggawar asara ta jirayi samu, ma,ana duk saurin zuwan da take ta jira ya dawo daga masallacin ta tambaye shi. Tana ganinsu suka shige, baki ta taɓe zuciyarta tana ingizata. Ƙullin maganin ta buɗe hannunta saboda ɗan duhun da ya fara ratsa duniya na magriba sai ra kasa tantance wanne ne na fesawa a cikin gidan wanne ne na sakawa a hancin gawar!. Gudun kar ta yi ɓaran ɓarama ta fesa na hancin gawa su ƙi suma mutanen gidan sai ta yi saɗaf saɗaf ta fita dagan zauren, tana fita ta ga wata yarinya tana tafiya tana ƴar waƙa da fitila a hannunta, kiranta ta yi ta ce ta ara mara fitilar ta karma ta haska maganin ta bambance sai ta ba yarinyar fitilar ta juya cikin gidan. Tana iya jiyu yadda ake ta koke-koke a cikin gidan, amma son zuciya ya hana ta yi tunanin cewa, idan gawarta ce ko ta wani nata za a yi wa hakan ba za ta ji daɗi ba, shaiɗan ya hana ta fahimci aairi babu kyau saɓon Allah ne, ta kasa fahimtar haɗarin da yake tattare da neman biyan buƙata ta haramtacciyar hanya, wato aiki da maganar boka da kuma amfani da gawar da a yanzu babu abin da take buƙata sai addu,a da neman gafara sannan kowa yana iya zama gawa a kowane lokaci, da ciwo ko babu, babu jinkiri ga wanda lokacinsa ya yi sannan babu gaggautawa ga wanda lokacinsa bai ƙarasa ba!. Zuwa wurin boka haramun, aiki da maganarsa ya saɓa da addini, sannan ba ta ma tunanin shi aure lokaci ne bare ma ƴarta tana da auren sun raina samun mijin ne da kuma matsayinsa, kuma hakan yana nuni da yin aure ta tilas domin shi wanda za a yi aikin a kansa tilasta masa za a yi, kuma akwai haɗari ga aiki da bokanci ko yin sihiri. Da sauri ta zazzage maganin a tafin hannunta tana fatan Allah sa dai babu ita a suman da aka ambata mutanen za su yi tun da idan aka suma har ita yaya kenan. Babu ɓata lokaci ta zage murya ta ce "Malam Kalla" Tana faɗa ta shige tsakar gidan ta hura maganin gabaɗaya ya bi iska. Kamar almara take ganin kowa ya zube a inda yake ya sume, tamkar gawarwaki haka ta ga mutanen babu wani mai motsi. Daga can gefen wata tabarma ta hangi Abba da su Liman suna yashe tamkar gawar su ɗin ma. Ba ta hira komai ba ta nufi ɗakin Malam Kalla, malam kalla malami ne mahaddacin qur,ani sannna mai ruƙo da addini. Ɗakin a cike yake da mutane matansa ne sai manyan ƴaƴansa amma kowanne babu bambanci da gawar domun duk sun sume. Yana kwance a miƙe zumbet an lulluɓe shi da zanen gado, yanayin yadda suke ya nuna ba a daɗe da yin rasuwar ba ma wataƙila ma yana rasuwa akan sanar a masallacin. Ta na nufarsa gabanta yana tsananta faɗuwa sai dai ba za ta yi wasa da wannan damar da ta samu ba din ta san tana gama yin aikin komai zai daidaita su fara cin duniyarsu da tsinkena tsire. Ba ta tunanin su ko za su tsallake wannan rana ba su mutu ba tub da ajalin ba sallama yake yi ba, kowa mutuwar tana zuwar masa ne bagatatan. Tana taugunne a gabansa ƙafafunta na karkarwa amma haka ta saka hannu ta buɗe gawar ta ganshi idanunsa a rufe ruf kamar mai bacci. Maganin ta buɗe daga leda ta saka yatsu biyu ta tsakuro, ta nufi hancin gawar za ta zuba sai dai me sai ta ga gawar kamar ta ɗan motsa, gabanta ya bada rass amma sai ta saka a ranta cewa tsabar ruɗanin da take ciki ne domin gawa ai ba ta motsi duk wanda ya mutu ya mutu. Ƙara nufar hancin nasa ta yi ta ƙara ganin gawar ta ɗan motsa hannun gawar ne yake ɗan motsi amma kaɗan sai ka lura za ka gani, ɗan jim ta yi amma sai kawai ta ƙara nufar hancin gawar za ta zuba maganin sai kuwa ta ga kan gawar ya ɗan motsa Umma ta tsaya cak! Ta juya ta dubi ƙofar shigowar amma babu kowa kuma gidan shiru sannan har lokacin babu wanda ya ƙara shigowa gidan. Kallon mutanen ɗakin ta yi don ta tabbatar da cewa ita kaɗai take ganin gawar tana motsi ko akwai wanda yake tayata gani amma ta ga babu kowa sai ita kaɗai. Kawai sai zuciyarta ta raya mata cewar gizo ne idanunta suke mata domin su hana ta aiwatar da ainihin abin da ta zo yi wanda ta samu wata dama, tana tono kuɗin da ta bayar na aikin sai kawai ta ajiye ledar a gefe ta saka hannun ɗaya ra riƙe hancin gawar ta nufi hancin da ɗaya hannun mai maganin.Kamar daga sama kuma kamar almara Umma ta ga hannun gawar nan mai motsi ya ɗago kafin ta gama tantancewa hannun gawa ya damƙe hannunta! Tashin farko ta ji kufcewar fitsarin da ba ta shirya masa ba, a yadda take a tsugunne ta ji zaninta jagaf, ga tsananin tsoro da tashin hankali da kuma da na sanin yin wannan aikin tun da dai ta san gawa ba ta motsi amma ita bayan motsin da gawar ta yi ga shi har hannun ta ta riƙe. Jan hannunta take amma sai ta ji tamkar an saka mayen ƙarfe domin gawar ta riƙe hannun gamgam kamar tare da hannun aka halicce ta. Umma abin ya fara wuce gona da iri domin abin ya fara wuce hankali da tunaninta, ita da ta zo don aiwatar da aiki a cikin ƴan mintuna amma ga shi wankin hula yana so ya kai ta dare. Ganin abin ba na ƙare ba ne ta shiga ture gawar amma gawar tana ƙame kawai dai ta riƙe hannun Ummar ne. Umma ta fara tunanin kar fa asirinta ya tonu tun da dai sai ta ambaci sunan mamaci sannan kowa zai dawo daga suman da ya yi ga shi kuma yanzu gawar ta ƙi sakin ta kenan hakan yana nuni da tonuwar asirin ta ko yaya?. Abu dai ya faskara!. Don yanzu Umma kokarin kwatar kanta kawai take ta ma saddaƙar cewa yiwuwar aikin da ta zo yi sai sa,a. Tana kiciniyar kwakwace kanta ta zubar da maganin hannun nata wanda za ta zuba a hancin gawar, amma ba ta shi take ba wannan lamari ya girmi tunanin ta. Jan hannun ta yi da ƙarfi aikuwa sai ta ji gawar ta saka ɗaya hannun ta damƙi ƙafarta guda ɗaya shikenan sai Umma ta sare cewa asirinta rana dab da tonuwa, don ta san ida har wani ya shigo gidan wanda shi ba ta yi aikin watsa magani da shi ba to ta fara zargin zai ganta wannan yana nufin Abba zai san abin da ta zo yi kuma sakamaon ta ta sani ba sai an faɗa mata ba kuma kowa zai san mai ta zo aikatawa tun da gawar ba ta wani nata ba cw sannan mai ya kaita wajen gawa da har ta riƙe mata ƙafa da hannu!?. Wajen kiciniyar ƙwaƙwace kanta ɗan sauran maganin da ya rage a ledar wanda take ganin shi ne ya rage mata tun da na hannun ya zube, tana rayawa a ranta idan ta samu kwace hannunta sai ra tura maganin a hancinngawar amma a kokarin ganin ta tsira ta ture ledar gabaɗaua ya zube dama ba wani yawa ne da shi ba don ta ga ledar ma iska ta matsar da ita daga kusa da ita ta yi can gefe guda. Kukan takaici ne na zuci wannn da ya fi na fili ciwo ya kufce mata, don tabbatar an kuma mace ta haifi mace wato asara dai ta wannan aikin ma an yi ta kamar yadda aka yi asarar aikin cokali, yanzu abu ɗaya ya rage mata yadda gawar za ta sake ta. Addu,a ta fara son karantowa don ta ga yanzu ita kaɗaice ta rage mata amma addu,ar ta kasa ambatawa ko da a zuciya ne domin dama ba ta da ƙarfin gwiwar furtawa a fili. BABA Hankali tashe yake kallon yadda hayaƙi yake biyowa daga cikin store ɗin nasa wanda ya tabbatar da cewa karkaf kayan amfanjnsa ne a cikin ɗakin wannan abin daidai yake da karayar arziƙinsa a cewarsa kenan hakan ya sa ya takarkare ya zandama ihun da kowa na gidan sai da ya fito a sukwane domin yanayin yadda ya yi ihun tamkar wanda aka daɓawa wuƙa a ƙirji. Ganin abin da yake faruwa sai kowa ya yi turus suna ganin wuta tana ci tamkar wanda aka kunna ta, Baba kuma sai miƙa hannu yake kamar mai neman sadaka duk ya gigice dama ga shi mai sarewa a kan abu barw kuma wannan yana gani ƙiri-ƙiri wuta tana cin store ɗin nashi da yake ji da shi wanda hatta iyalansa yana musu ƙauro. Zaman dirshan ya yi yana kuka wiwi tamkar an ce masa Kaka ce mahaifiyarsa ta mutu. Hafsat ce ta yi waje tana cewa. "Gobara jama,a a kawo ɗauki" Lokacin har Mama Habiba da Mamar Sadiya sun fara ɗakko ruwa suna watsawa don yanzu hatta ƙofar ɗakin ta cinye. Samari ne suka shigo gidan wanda suke zaune a ƙofar gidan aka shigo ana ta zubawa wutar ruwa dakyar aka samu ta mutu, sai dai gabaɗaya ta ƙone komai na ɗakin ƙurmus. Samarin nan suna ta jajantawa Baba gobarar amma sai faɗi yake "Ku kawo ɗauki jama,a na taiyace na talauce wayyo ni" Ganin kamar ba a hayyacjnsa ba y a yake suka jajantawa matan gidan suka tafi sama gabaɗaya cikin ƴaƴan babu wacce ta taimaka wajen kashe wutae kafin samarin su zo su ma matan daga Mama Habiba saj Mamar Sadiya ne kawai suka kaiwa wutar ɗauki. Mamar Sadiya da Mama Habiba ya ce "Habiba ke da Talatuwa ku zo ku kamani ku kaini ɗaki, na ga ku ne kuka fi tausayina ku ne kaɗai kuka kaiwa wutar nan ɗauki, sauran kamar ma farinciki suke da faruwar hakan" Haka suka zo suna masa kama-kama duk ya saki jiki sai sharɓar kuka yake, sai da suna dab da shiga ɗakinsa kawai sai ya zauna kamar wanda aka turo ya kifa uban tagumi yana cewa "Wayyo hatsina wayyo shinkafata da na san wannan ƙaddarar za fa faɗa musu da na daɗe da kaiku kasuwa na karɓi kuɗina" ,Ya faɗa yana face hanci. Mama Habiba ta ce "Haba Malam ina kake so ka kai imaninka ne ai baka da tsumi ko dabara a kan hakan, tun da Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru haka za ka rungumi ƙaddara... Ko ƙarasawa bata yi ba ya hayayyaƙo ta da masifa yana faɗin "Saboda ba kayanki ba ne ko, shi ya sa ma kuke nuna bai dame ku ba, na lura kamar ma ni kaɗai abin ya dama ban da lalacewar zamani a ce mace kadarar mijinki ta ƙone amma babu wacce cikin ku ta matse hawaye ko da ba na gaskiya ba ne, a ƙalla a kowacce ko da kukan kissa ne ta yi na ƙarya ai na ɗan ji daɗi amma kowacce fuskarta washe kamar gonar auduga ni kaɗai nake shan kuka da takaicina" Kallon kallo aka shiga tsakanin Mama Talatuwa da Mama Habiba ganin shi tsaninsa da Allah yana so su taya shi kuka a kan kayan abincin da sai ranar da ya ga dama yake ciyar da su, Mama Sa,ade da Mama Bilki kuwa dama tuni suka ba banza ajiyarsa kowacce tana ɗakinta haka ma ƴaƴan. Mama Talatuwa ta ce "Malam ko mu yi kuka ko kar mu yi wannan ƙaddarar ba mu isa mu kankar ta ba, kai da Allah ya tseratar da kai da iyalanka babu wanda wutar ta ƙone ai an ci ta varka, baka ga ko gidan jaje aka je ba idan iya dukiya ko amfani wuta ta ci ba har barka ake yi wa mutum saboda ba ƙaramar ni,ima ba ce saboda ubangiji yana iya yin komai amma ya tsayar iya haka wato ya taƙaita" Yana kallon ta da jajayen idanunsa ya ce "Barka fa? Kika ce a yi barka to duk wanda ya tako gidan nan ya yi mini barka sai ya cire masa ƙafa" Mama Habiba ta ce " Kenan baka godewa Allah da wannan abin da ya maka ba, da ka gode masa sai ya dawo maka da abin da ka rasa ta inda baka yi zato b... Kafin ta ƙarasa ya ce ",Rufe mini baki Habiba ai ina ga ma ke ce kika mini baki, da kika zo riƙona in bada abinci a dafa baki da kuɗin da za ki sayi abin da za ki ce wataƙila ma sanadinki ne gobaear ta kama, ni ban san ma wace jarabar ce ta sa nae zaune da ke ba har yau Habiba, to mace ke dai ba haihuwa kike ba sannan kawai dai ni ne nake ciyar da ke don haka kawai ina ga zan hukunta ki... Mama Talatuwa ta katse shi da sauri da faɗin "Haba Malam kaima ka san wannan dai son zuciya ne kawai ka yarda da ƙaddara saj ka samu sauƙi a zuciyarka, amma wannan zargi ne kake hakan kuma zai saka maka kokwanto a zuciyarka baka yarda da ƙaddarar da Allah ya aiko... Ƙasa ya dafa ya miƙe tsaye duk da ƙafafunsa karkarwa suke saboda gabaɗaya abin da ya faru ya ruɗa shi. Da yatsa ya nuna Mama Talatuwa ya ce "Idan akwai shegen da zai faɗa min yadda zan yi a rayuwata sai in gani, don haka ni nake da damar yin abin da na so a lokacib da na so" Mama Habiba tun maganar da ya faɗa ta gorin da ya mata hawaye ya daɗe da wanke mata fuska a zuciyarta tana addu,ar Allah ya bata haihuwa watarana, Baba ya kalle ta ya ce "Habiba ki je na yanke igiya ɗaya daga cikin igiyoyin da suke tsakanina da ke" Mama Habiba ta ɗago fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Tohm Malam ina roƙon Allah ya sa haka ya zama mafi alkairi a garemu" ,Bai tanka mata ba sai Mama Talatuwa da tar rafka salati, ita kuma Mama Bilki da take jiyo abin da suke daga ɗakinta ta leƙo ta tsaya a ƙofar ɗakinta ta kama tsantsa ta ce ",Allah ya yanke miki wahala Habiba, yo ai ke gaba ta kaiki gobarar titi, zaman gidan nan ai jarabawa ne, duk lokacin da Allah ya yanke maka sai ka gode wataƙila gaba ta fi ba ya yawa!" , Baba ya ce ",To mai bakin reza, wato ke ishashshiya da mai to ai hausawa sun ce riƙon mahaukaci sai sarki, kuma wallahi kika cika baki kafin ta isa gidansu ke ma kin kama hanyar naku gidan" Baki sake take kallonsa. Mama Habiba ba ta tanka musu ba ya wuce ɗakinta jiki sanyi ƙalau ranta duk bau daɗi tana tunanin ashe dama shi ya sa ubangiji ba ya son saki duk da abu ne halactacce, saboda gabaɗaya ta ji wani ɗaci a ranta lallai ta tabbata saki ba shi da daɗi. Kayanta ta haɗo a jaka ta fito ta zo ta yi wa matan da yaran gidan da suka fito sallama ta kama hanya ta fita. Tana fita Baba ya ce "Yawwa yanzu kuma na ragewa kaina wahala amma dai ba zan gushe ba ina son ɗa namiji ko kan gararre ne sai ranar da na haifi ɗa namiji dole ne ma yanzu in samu budurwa ko sakin wawa in auro" ,Yana faɗar hakan ya ja ƙafafunsa yana yin ɗan kukan takaicin ƙonewar kayan abincin sa. A tsakar gidan kuwa Mama Talatuwa ce kaɗai take cike da jimamin barin gidan da Mama Habiba ta yi sai dai tana fatan ta samu sauyi mafi alkairi tun da ta lura rashin haihuwar ne kaɗai yake saka Baba yake mata yadda ya so. Washe gati da maƙota suka riƙa shigowa gidan suna jajantawa Baba. Duk magidancin da ya shigo sai Baba ya ce ",Kun ga dai yadda Allah ya jarafceni da ƙonewar kayan abincin, wannan lamari ne da yake buƙatar taimako da tallafin jama,a sannan kamata ya yi mutanen unguwa su yi gangami a yi meeting a sanar a masallaci ake haɗa kuɗin tainakon da za a bani wataƙila kuɗin su zama silar warakata dagaa baƙin talaucin nan" ,Duk wanda Baba ya faɗawa haka sai ya nuna ya yi na,am kuma hakan abu ne mai kyau sai dai babu wanda ya zauna ya ce a yi shawarar haɗa masa kuɗin domin Baba bai san cewa kaf unguwa babu wanda bai san halin da gidansa yake ciki ba, ya manta cewa yanzu kiwo na mutum ake yi ba dabba ba. Ko da Mama Talatuwa ta kira Sadiya a waya ta sanar da ita abin da yake faruwa ta yi jimami sosai kafin daga bisani ta fawwalawa Allah komai dama ai ta san halin mahaifinsu na rashin wadata iyali wanda bai san hakan cewa ba iyalinsa kaɗai yake tauyewa ba hsr da kansa yake tauyewa domin sai ya sauke nauyin haƙƙinsu ne Allah zai ƙara buɗa masa, sai dai shi ya kasa fahimtar hakan gani yake rashin wadatarwar shi ne zai haɓaka arziƙinsa. Ko da ta je gidan ta jajanta masa sai da ya ce "Sadiya kin faɗawa Nasir ɗin na samu gobara komai na kayana abincina ya ƙone? Na kira wayarsa sau biyu bai ɗaga ba kuma bai biyo kiran ba, ai kin ga a matsayinsa na surukina ɗaya ƙwallin ƙwal ya kamata ya kawo ɗan wani abu mana, don na ga jama,ar unguwar nan babu niyya ango ya kwana da wando, tun jiya an gagara kawo ko ƙwayar gero bare a saka ran kawo shinkafa, ni wallahi na ɗauka zuwa yanzu an tara buhun shinkafa ƴar gwammani buhu bakwai a lalace na hatsi biyar dawa huɗu amma har yanzu shiru maƙatau, ko dah taimakon ƴan siyasa zan nema ne?" Sadiya ta danne takaicin da ta ji ta ce "Baba wataƙila ko yana kasuwa lokacin da ka kira shi, amma dai maganar kawo tallafi dama ba lallai ba ne tun da yanzu rayuwar ce sai a hankali kowa ta kansa yake... Hannu ya ɗaga mata ya ce "Ke dalla rufewa mutane baki, ba ta kai ba idan ma ta ƙafa ake ai ba za su rasa amfanin abinci a gidansu ba a lalace ko kwano biyar biyar ce mutum in zai zo jaje sai ya taho da shi, amma don asara sai su taho babu komai kowa haka zai shigo hannu yana dukan cinya su zo su ishi mutane da cewa, ka yi haƙuri malam Bala haka Allah ya ƙaddara Allah mayar da alheri" ,Ya faɗa yana kwaikwayon yadda mutanen suke faɗa in sun zo masa jajan tare da jan wani dogon tsaki yana muzurai. Haƙuri ta shiga bashi ta ɗakko dubu goma ta ba shi, ya karɓa ko godiya bai mata ba bare ya saka albarka, saboda shi yanzu wasu kuɗaɗe masu kauri yake so su faɗo masa. Kamar zai yi kuka ya ce "Wllahi shi ma limamin nan na masallacin nan ba shi da tausayi ina ga ma in daina sallah a masallacjn nan in koma wani, mutumin nan yana kallo tun kan ladan ya kira assalatu na fita na je masallacin nan na ringa sallar nafila ina ɗaga hannuwa sama idan na idar ina ta addu,a amma na ɗauka da aka idar da sallar asubar zai yi sanarwa a lasifika cewa a taimaka mini amma shiru maye ya ci shirwa, haka da aka idar da sallar azzahar na kifa kaina da gwiwoyin ƙafata wai duk don a fahimci ina cikin damuwa da halin ƙaƙanika yi amma babu wanda ya bi ta kaina" Haƙuri dai Sadiya take ta ba shi, bayan ta jo sallamar mutane a zaure ta amsa suka shigo don Baba yana jin sallamar ma ya ƙi amsawa ya rage murya ya ce "Sadiya da kin ƙyale su, don ba wata tsiyar suka kawo ba in banda zance" Ita dai ba ta amsa ba haka suka shigo Baba kuwa ya haɗe fuska yana muzurai don dakyar yake amsa jajan da ake masa. Sadiya sai da suka keɓe da Mama Talatuwa take faɗa mata sakin da Baba ya yi wa Mama Habiba, salati ta yi hankali tashe tana jimanta abin, don ita da ta shigo ta ga ɗakin Mmar a rufe ta ɗauka ko unguwa ta tafi cike da damuwa a fuskarta ta ce "Mama wai su maza haka suke ne?" Mama ta ce ",Kamar yaya?" Sadiya ta ce "A yadda na fahimta yawancinsu ba su da uzuri, sannan duk daren daɗewa suna manta halacci, kuma su babu ruwansu da daɗewar da mace ta yi tare da su da sadaukarwa da taimakonsu da ta yi a rayuwa, haka kawai wani namijin sai ki ga an ce sun kwashe shekaru da matarsa tun ba shi da komai tun suna gidan haya, wani ma ko aikin yi ba shi da shi, sai ya fita ya nemo za a samu a ci watarana ma a haƙura idan bai samo ba, wani kuma matar ce za ta ciru ta ƙullu ta ciyar da gidan wata rana, wata ma bashi za ta ci, wata kuma ta haka jarinta da take juyawa zai salwanta a wajen taimaka masa, amma daga ya samu dama sai ya manta da duk abubuwan da suka faru a baya, sai ki ga bai mata halacci ba, sai ki ga tukucin da zai mata shi ne rabuwa da ita sai ya sake ta, ya auri wata ya ci gaba da rayuwa da waccan ɗin wacce ta zo ta samr shi cikin arziƙinsa wacce ba ta san wahalarsa ba amma ita za ta ji daɗin ita wacce ta sha wahalar sai ki ba ba ta da darajar da za ta zauna a gidan nasa ma mai ɗan mutunci shi ne wanda zai zauna da matar bai sake ta ba, amma dai wata duj da tana gidan sai ki ga wulaƙanci yana biyowa baya" Cewar Sadiya tana hawaye. Mama ta ce "Eh maganrki tana kan hanya Sadiya duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba" Sadiya tw ce "Ni ma ai wasu na ce Mama, dimin wasu sun san halacci wani ba ya taɓa mantawa da halaccin, wani yana darajawa da mutunta matar ko da a ce ya auri wata matar to fa ya san darajar waccan da suka sha wahalar tare" Mama ta ce "Ai wasu mazan sai addu,a domin wani namijin a ya riƙe alƙawari amma mafi yawanci ƴa mace ta fi yin halaccia a kan ɗa namiji, mace ta fi riƙe alƙawari duk da su ma mazan akwai masu tsananin riƙe alƙawari" Sadiya ta ce "Mai ya sa?" Mama ta ce "Saboda za ki ga ƴa mace ko mijinta ne ba shi da lafiya wato duk tsananin jinya za ta zauna ta kula da shi, sannn ko da nakasa ya samu sai ki ga ta ƙarar da ƙuruciyarta wajen kula da shi, babu ruwanta da sai ta je ta auti wani ta ci gaba da rayuwa da wanin, amma ita kuma macen idan bata da lafiya ko zazzaɓi ne ya yi tsananin sai dai a kaita gidansu iyayenta su yi jinya, idan ta warke sai ta dawo gidan mijin" Sadiya ta ce "Kenan lafiyarta ce a bar amfana?" Mama ta ce "A,a ina faɗa miki yawancin abin da yake faruwa amma akwai wasu mazan da suke kula da matansu fiye da tunaninki" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke amma dai ta ji ɗacin sakin da Baba ya yi wa Mama Habiba. Ko kiran magriba ba a yi ba ya ringa ƙwala mata kira yana faɗin ta ɗakko Kalifa su zo su tafi gida. ZALIKA Tana karkarea take kallon kwalin duk ta diririce tunanin ta ya tsaya cak sai faman haɗo tunanin take amma hakan ya gagara, ta ma rasa abin da za ta shirya don ta kare kanta don ta ji ƙwaƙwalwar ta da kuma yanayin da jikinta ya nuna suna neman ƙin bata haɗin kan da zai taimake ta, domin ganin ta kawar da zarginta a kan wannan mummunar ranar da za ta fallasa asirin da take ɓoyewa, duk da ta san saɓon ubangiji ne sanna duk lokacin da za ta aiwatar da saɓon ta manta cewa shi wanda ya haramta hakan hakan yana ganinta, kuma duk abin da ka ɓoyewa wani mutum ba za ka ɓoyewa Allah ba, haka kuma duk wani abu da kake ɓoyewa don kar mutane su sani akwai ranar da ubangiji zai tona maka asiri duk daren daɗewa kuwa sai an sani!. Maganar da Mumy ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta kai ziyara na ɗan daƙiƙu, da kuma zillon da zuciyarta take yi ta ji Mamy ta ce "Zalika ki amsa min da bakin ki cewa mene ne wannan? " Mamy da gabaɗaya hawaye take kwaranyowa daga idanunta ta faɗa cike da tsananin damuwa Allah ne kaɗai ya san damuwa da firgicin da yake cikin ranta, sai take jin anya duk iya uƙubar da take ciki dangane da zaman aurenta ta taɓa jin raɗaɗin baƙinciki irin wannan ba, sai yau take jin makamancin raɗaɗin da uwa take ji dangane da abin da ya samu budurcin ƴarta, ta sha ji a rediyo ta sha ji a social media ana labarin an yi fyaɗe ga wasu ƴaƴan wasu ma ba ƴanmata ba ne wasu yara ne ƙanana masu ƙarancin shekaru amma ake samunwwasu mararsa imanin suna raba su da mutuncinsu, ashe haka kowace uwa take jin wannan raɗaɗin? Ta san da ciwo amma bata zaci ciwon har ya kai haka ba, ciwo ne mai tafe da rashin nutsuqar zuciya, duk da nata ciwon ya sha bamban da sauran ciqukan da sauran iyayen mata suke ji domin su sauran fyaɗe ne wato abu ne da ya faru da su ba da amincewar su ba, amma nata fa? Nata abu ne ba tsautsayi ba hasali ma alamomi da dama sun tabbatar mata da cewa tata ƴar da amincewarta tun da ga shi har tana yawo da maganin tsarin iyali wanda bai dace a ganshi a wajen macen da bata da aure ba sai dai mace mai aure!. Zalika tana jin tashin hankali ta yi ƙoƙarin dannewa tare da saita kanta don hakan ya bata damar linke mahaifiyarta ma,ana domin ta faɗa mata abubuwan da zai sa ta yarda da ita abin da ake kira wasa da hankali da tunani Cikin sanyin murya ta ce "Mamy mene ne ya sa za ki zubar da hawayenki a kan abin da ba gaskiya ba? Mai ya sa za ki shiga tashin hankali a kan abin da zargi ne? Wannan abubuwan fa gbaɗay zargi ne sannan yanayin yadda kika tunkareni da maganar ya sa na shiga cikin ruɗu" Mamy wani sashe na zuciyarta yana mata albishir da cewa duk abin da ta sanya a zuciyarta ba haka ba ne shaiɗan ne yake mata linzami, shi kuma wani sashen yana faɗa mata cewa Zalika rainin hankali take mata sannan ta yi hakan ne don ta yi wasa da hankalin ta. Durƙusawa Zalika ta yi ta saka hannuwanta biyu ta dafe gwiwar Mamy ta yi raurau da idanunta ta ce "Mamy ni ce fa Zalikar ki da kika yarda da ni, ni ce fa wacce kika bani tarbiya kika kula da motsina da dukkan komai na, a kan mai zan ci amanar wannan abubuwan da kika min a rayuwa? " Ta faɗa tana runtse idanunta hawaye suka zubo wani yana bin wani. Mamy kawai kallon fuskarta take ta rasa ma matakin da za ta saka wannan al,marin, amma dai ta dakatar da zucuyarta zuwa lokacin da za ta ji abin da za ta faɗa mata duk da zuciyarta tana gargaɗinta a kan kar ta yarda, don yanzu Zalika ta goge mata hadda ta sanya tana jin tsoronta. Ta ci gaba da faɗjn "Mamy akwai wata abokiyar karatuna matar aure ce sunanta Fatima Abdulƙadir to ita ce ta saka maganin nan a jakata ta manta da shi, ni kuma abin da ya sa na tsorata da kika nuna min saboda na san zai yi wuya ki fahjmce ni, amma dai ina kyakkyawan zato a kanki mahaifiyata na san ko da duniya za ta zargeni a kan aikata wani abu marar kyau, ke kaɗai ce za ki shaide ni yanzu Mamy idan baki bani shaida mai kyau ba waye zai miki shaidar Zalikar ki?" Ta faɗa tana ɗago kai ta saka idanunta da suke zubar hawaye ta saka a cikin na Mamy da take yi wa Zalika kallon da take son gane iya gaskiyarta. Jin Mamy ba ta ce komai ba sai Zalika ta fahimci kalamanra suna tasiri a wajen Mamy duk da ba ta gama gansuwa cewa Mamyn za ta yarda da abin da take faɗa ɗin. Ta ci gaba da faɗin "Tana tafiya da maganin ne school saboda time ɗin shan maganin nata lokacin muna makaranta ne, ba ta so lokacin ya wuce ya zamana sai ta dawo daga makaranta za ta sha, shi ya sa take zuwa da shi tana ɓalla tana sha, yau da ta ɓalla shi ne ta saka a jakata lokacin muna sauri za mu shiga lacture ni kuma da muka fito sai na manta ita ɗin ma ina ga mantawar ta yi" MAMAN AFRAH 09025576222 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣8️⃣ MEENAL Ihu take da iya ƙarfin ta tana ɗaga hannu kamar makauniya neman ɗauki take don a ƙwace kuɗin nan duk da ba halaliyarta na ne wato ba da guminta ta tara ba. Momi kuwa sai juyi take a tsakiyar hanyar gabaɗaya jikinta ya yi busu-busu da ƙasa ita ihun ma ba ta iyayi sosai saboda nauyin da bakinta ya mata. Su duka kuka suke jina-jina domin sun doku sosai sai dai son zuciya bai bari kowacce daga cikinsu ta fahimci cewa alhakin wacce aka sacewa kuɗin ba ne da ta tara da gumin ta. Meenal tana yin wani juyi ta ce "Momi sun gudu da kuɗin wayyo na shiga ukuna" Momi maimakon ta furta wata kalma kawai sai ta ɗaga hannuwa biyu tana kaɗawa tana yi wa Meenal zancen bebaye, wani takaici ne ya ƙara rufe Meenal ɗin ta ce "Haba Momi yanzu duk wannan halin da muke ciki amma sai kike mini zancen kurame?" Momi tana ɗan ƙoƙartawa wajen ganin ta tashi zaune saboda yadda jikinta yale tsananin ciwo tsabar dukan da ta ci, ganin tashin ba zai iyu ba ta buɗe bakinta da ya kumbura suntum saboda naushin da ya sha kamar ana saka ƙaton ƙuli-ƙuli daga cikin kumatun ta ce "Haba Meenal baki ga yadda na daku ba kamar sakawara a turmi, wannan yara mararsa imani a ce ko tausayin shekaruna ba su ji ba suka nakaɗa mini na jaki... Shiru ta yi sai da ta ɗan huta saboda yadda take jin ciwo in tana mganar tamkar an saka gishiri a ciwo ta ce "Ai tsakanina da su Allah ya isa!" Meenal ta ce "Haba Momi yanzu ta dukan da kika sha ma ke kike yi, bakya ta maƙudan kuɗin da suka ƙwace wanda ko bokan ba a kaiwa ba ya yi maganin, kuma sia magana kike kamar kin cika baki da abinci" Tsaki Momi ta ja dakyar ta ce "Wane shege ne ya ce miki ban damu da kuɗin ba amma ai lafiya ta fi komai, kuma da kike maganar na saka abinci a baki ba gwara in saka abinci sai dubu a bakin ba da wannan masifaffan dukan da na sha, baki ya kumbura suntum ai wannan sai na nemi mansileta" Ta faɗa tana ƙara bajewa a tsakiyar hanyar domin tana jin idan ba kama-kama aka mata ba to ita dai ba za ta iya tashi ba. Meenal ta ce "To da ba ke kaɗai suka duka ba, kalli hancina ji nake kamar jini ne yake zuba duk sun dauje mini, ga fuskata ma sai raɗaɗi take" Momi ta ɗan ɗago kai ta kalli fuskar Meenal wata dariya ta so wwace mata amma bata son ta yi saboda yadda bakinta yake zugi. Ganin Meenal ta yi kamar an yi murjin taliyar hausa a fuskar tata, ga wata ƙasa da ta yi buɗuɗu kamar wanda ta ziyarci yaƙin badar. Sun jima a kwance a tsakiyar hanyar amma banu wani mahluƙi da ya biyo hanyar ma bare ya taimaka musu, haka suka ba kansu shawarar tashi su lallaɓa. Momi ɗankwalinta sa yake can gefe ta ɗaukko ta ɗora a kanta ya kalli gabas maso kudu, amma bata damu ba burinta su samu su bar tsakiyar jejin. Haka ta ɗauki mayafinta ta yaɓa a kafaɗa tana riƙe da zaninta da ta tattare tamkar za ta yi tseran gudu. Meenal ma ta lallaɓa ta miƙe tana jin ƙugunta kamar ba a jikinta yake ba,ga shi duk haushi ya cika ta a haka ta ɗauki jakar da banu ko sisi a ciki takaicin ma da har da wayoyinsu aka ƙwace. Haka suka tashi suna tafiya kamat masu tatata, Momi a gaba zanin nan a tattare a hannunta Meenal tana biye da ita, Meenal ta ce "Wallahj Momi ina ga mutanen nan ƴan iska ne, ni fa ɗayan nan sai da ya jimƙe hannunsa ya dage ƙarfinsa ya kirɓa mini naushi a mazaunai" Wani gajeran tsaki Momi ta yi ta ce "Kukan daɗu kike Meenal wallahi allon kafaɗar nan tawa kamar an buga mini filankin katako, wai hannu ne ya yi wannan aiki, ba gwara ma mazaunai wajen tsoka ba ne ni fa wajen ƙashi ne kin ga ai ni na ji abin da na ji, daga rakiya haka kawai an illa ta ni gani nan duk na fita hayyacina" Banza Meenal ta mata don ta ga kamar ma bata damu da abin da ta faɗa ba, haka suke ta tafiya amma sun kasa ganin ko mashin ne. Suna cikin tafiya sai suka wani ƙaton mutum a amalanken shanu haka suka tare shi dama daga wata hanya ya ɓullo, suna ɗaga masa hannu da maaa magiya sannan ya tsaya, ganinsu a firgice sai ya ƙara ɓata rai, nan Momi ta dage tana sheƙa masa ƙarya cewa zumunci za su je waji kauye m nisa ziyara shi ne suka haɗu da haɗarin ƴan fashi suka musu duka duka musu ƙwace, shi dai bai ce komai ba sai cewa da ya yi su shiga tun da sun nema ya rage musu hanya. Dakyar yake tafiya su dai suna baya sun zazzaunai suna tafiyar dakyar ƙiƙar ƙiƙar. Suna cikin tafiya tsabar wahala Momi tana jingina bayanta sai kawai gyangyaɗi ya kwashe ta, a cikin bacci ta yi mafarkin sun cim ma mummunar manufarsu, Meenal ta mallaki manyan gidaje da motoci suna mulkar Ibrahim yadda suka so. Meenal da ta kalli Momi tana gyangyaɗi har neman tuntsurawa take sai abin ya ɓata mata rai a nata ganin su da suke cikin wannan yanayin ina suka ga damar wani bacci in banda dai shi bacci ba ka sanin lokacin zuwansa. Wasu ƴan mata ne suka ɓullo su biyu daga wata siririyar hanya, ya kasance suna gaban su Momi kamar an ce yanmatan su ɗago suka hangi amalanken shanun nan suna ganin mau tuƙawar sai suka kwasa a guje suka koma hanyar da suka fito suna faɗin "Audu kwarto, Audu kwarto" Momi wannan ihun ne ya falkat da ita daga ɗan guntun gyangyaɗin ita kuma Meenal sai ta fara tunanin inda kwarton yake, kamar daba sama suka ji muryar mai amlanken ya ce "Ƙarya suke mini" Momi a zuciyarta ta ce 'In ba rami mai ya kawo rami?" ,Wato da shi suka tun da kaf dajin babu wani sai shi, kallon kallo aka shiga tsakanin Momi da Meenal don mutumin wani jibgege ne dukwanda ya sake ya damƙe shi to bai isa ya ƙwace ba. Shi kuma ya ji haushin bayyanar ƴanmatan don ya san da gaske suke tin da shi ne yake lalata ƴaƴan mutane. Momi da ido ta yi wa Meenal signa duk da Meenal ta saba da banbaɗar da mutuncin ta ga maza sai ta ji wannan tana shayinsa shi kuma dama a nasa ƙudurin sai ya ƙarasa fa su gidansa da yake wata hanya zai tilasta musu shiga gidan don zai sanar da su zai ɗauki wani saƙo sai su wuce amma ba saƙo zai ɗauka ba, dama zai sheƙe ayarsa ne a tattare da uwa da ƴar gabaɗaya wato Momi da Meenal. Momi ba ta yi wata-wata ba ta yi tsalle ta dira ita ma Meenal ta mara mata baya, Audu kwarto sai jin dirarsu ya yi da yake shi ya mayar da hankali gabansa, ai kuwa ya ji haushi domin ya gama sakawa a ransa cewa ya samu mata har biyu kasancewarsa hariji. Momi suna dira suka yanke wata hanya a guje ko waiwaiye ba sa yi don ita Meenal hatta jakarta ta barta a cikin amalanken shanun, Momi da take ɗingishi lokacin tahowarsa amma yanzu ta ware ƙafa sai zabga gudu take, tsayar da shanun ya yi ya diro duk da girman jikinsa ba ya jin nauyinsa lokacin gudu a kan cikar burinsa don haka ya gwammace ya bi bayansu in ya so idan yana da rabo ko ɗaya ce a cikinsu ya kama a dokar dajin ya biya buƙatarsa. Meenal ce a baya Momi har ta fi ta ware ƙafa su duka ko ciwon jikin da suka ce suna ji na dukan da ɓarayin kuɗi da wayar nan suka musu ba sa ji, ta ware murya ta ce "Momi ga shi nan ya biyo mu" Momi da sauri ta waiwayo sai ta ga ya dage tana sheƙa gudu, su duka ƙafa mai na ci ban baki ba, suka ƙara zage dantse wajen zabgar gudun famfalaƙi. gudu suke babu mai ko takalmi domin sun watsar da su. Ganin yana neman cim musu ya saka Momi ta sha wata kwatar cikin ciyayi ta durƙusa Meenal ma ta mara mata baya, suna durƙushe a wajen suna hakin gudun da suka yi, sai ga Audun ya zo sai dai ya ga hanya ta rabu biyu sannan ya rasa ina suka bi ya duba sawun su ya ga babu hakan ya sa ya ɗan tsaya yana dube dube. Yana tsaye a dab da su sai dai ya basu baya ne, jikinsa yana bashi suna wajen domin bai ga samun su na wucewa ba. Momi bakinta har kumfa yake wajen karanto ƙulaƙuzai wa to falaƙi da nasi, sai dai a hankli take yi ba a fili ba gudun tonuwar asirinsu. Ita Meenal sai zare ido take tana kallon girmansa hatta mazaunansa kaɗai girmansu sai ya tsorata mutum. Momi ba ta dakata da adsu,a ba don ba ta san iya mugun nufinsa a kansu ba. Ɗan ja da baya ya yi sai kuwa ya yi wa ƙatuwar ƙafarsa masauki a kan hannun Meenal, wani raɗaɗi ta ji don haka ta shiga zare ido tana ƙoƙarin rafka ihu sai dai Momi tana ta mata nuni da hannu a kan ta rufa musu asiri kar ta yi ihun. haka ta daure tana rausaya kai tamkar mai magogon naƙudar haihuwa. Idanun ya kaɗa ya yi ja sai dai a zuciyarta tana jin kamar ta hankaɗa shi ɗan gyara tsayuwa ya yi hakan ya sa Meenal jin tamkar wanda ya murtsuka ƙafar tasa wato tsananin azaba ya ƙara ratsa ta Momi kuma sai jan addu,a take duk wacce ta zo bakinta daga inda take iya hango gaban rigarsa ya ɗaga sosai daga saitin mararsa hakan ya sa ta yi mugun gani duk da cewa daga gafe ne take hange. Ajiyar da take mararsa tana ta harbin iska da alama a buƙace yake hakan ya tabbatarwa da Momi duk macen da ya damƙa sai ta gwammace kiɗa da karatu. Meenal tana ta hawaye cikin ikon Allah kamar wanda aka ce ya tafi sai suka ji ya ce "Ina jin gaba suka yi sai suka samu mafaka shi ya sa ban gan su ba, bari na bi bayansu wataƙika sun sauka daga tsakiyar hanya ne suna bin gefe inda da ciyayi shi ya sa na daina ganin sawunsu" Yana gama faɗar hakan sai ya zabga da gudu ya ci gaba da tafiya. Meenal ta ce "Momi wayyo hannuna kalli yadda ya kumbura" Momi ta ce "Meenal wa yake ta kumbuarar hannu, ki tashi mu kama hanya kar ya dawo ya iske mu a wajen nan, don wallahi wannan ya samu mace sai ya kumbura mata matantaka in ma bai ɓarɓarka ta ba" Babu yadda suka iya haka suka tashi cikin lallaɓawa suka kama hanyar da suka baro tun da ba zai yiwu su ci gaba da tafiya ba, gudun kar su yi arangama da shi!. Gudu suka babu ƙaƙƙautawa har sai da suka ga sun zo bakin hanya" Sai haki suke suna da na sanin hawa amalanken Audu kwarto. Motoci suna wulgawa sai dai duk wacce suka tsayar sai su ƙo tsayawa don ana musu kallon kamar basu da cikakken hankali duba da kowacce babu takalmi sannan kuma kowacce ba ta da nutsuwa. Dakyar suka samu wani mai mota ya ɗauke su da suka faɗa masa ziyara suka je ƙauyen ƴan uwansu a hanya ɓarayi suka tare su suka musu ƙwace tare da musu dukan tsiya, ya taimaka musu donnhat ƙofar gidan Momi ya kawo su, saboda ba motar haya ba c kuma shi kaɗai ne a motar. Godiya kamar za su ari baki. Sai da suka dawo gidan ƙofar gidan ma sai ɓalle ta aka yi don mukullin ma ba a san inda ya faɗi ba. Bayan sun shiga gidan suka zauna suna mayar da yadda aka yi, a nan Momi tana nunawa Meenal kuskurenta na yin maganar kuɗi a gaban wasu tun da ta lura maganar kuɗin ce ta ankarar da su akwai kuɗin a atare da su, shi ya sa ake so mutum ya kama bakinsa idan ya je wajen da bai san mutane ba, tun da ba a goshin mutum za a rubuta waye shi ba, idan mugu ne ko akasin hakan. Ruwan zafi Momi ta dafa suka yi wanka sannan suka ci abinci suna maganar za su koma wajen bokan don cim ma manufarsu domin ba su daddara da abin da ya faru ba, hakan ya san Meenal ta ce akwai wasu kuɗaɗe da za su shigo mata da zarat sun shigo za su koma, Momi ma da yakr zuciyar a bushe take ta goya mata baya. Sai da Nasir ya dawo daga kasuwa ta biya suka ya ɗakko ta. Tana shigowa gidan ganin Sadiya tana shanya kafa ta aika mata saƙon mugun kallo, abin mamaki sai Sadiya ta ji Nasir ya yi sallama, amsawa ta yi ta juyo tana masa sannunda zuwa ya amsa da fuska a sake, yana tambayar ta Kalifa ta ce yana ɗaki yana wasa, maimakon ya shige ɗakin Meenal sai Meenal ta ga ya juya da ledojin hannunsa ya nufi ɗakin Sadiyar. Gaban Meenal ne ya faɗi a take ta shigar zargin ko dai da saka hannun Sadiya a rugujwar shirin da suka yi yau, wani ɓangarr na zuciyarta yana zargin ko dai Sadiya ta je tanyi wani abu ne da har Nasir ya kula ta yau. Abin da Meenal ba ta sani ba shi ne wani maƙocin Nasir ne a kasuwa suke tattaunawa a kan yana gobe zai kai matansa kasuwa za su yi sayayya kowacce ta zaɓi abin da ranta yake so, a nan maƙocin yake cewa "Ina tsoron shanyewar rabin jikina a ranar ƙiyama shi ya sa ba na nuna bambanci a cikin matana, ko da a ce ba zan iya daidaita matsayi da soyayarsu a zuciyata ba tun da dama Allah ba ya amfani da fifikon soyayyar a zuciya kawai adalci ne na zahiri shi ya sa nake ƙoƙarin kiyayewa" Wannan furucin ne ya sa Nasir ya tuna rashin adalcin da yake yi wa Sadiya hakan ya sa ya ɗan sakko domin ya mata adalcin ko da kaɗan ne ba da yawa ba, sai dai ita Sadiya ganin abin da Nasir ya yi bai ba ta mamaki ba domin ta san tana kai kukan ta wajen ubangiji don haka ta san addu,ar ta ce ta fara karɓuwa. Tana gama shanyar ta nufi ɗakinta. Meenal tun da ta ga ya kama hanyar ɗakin Sadiya sai ranta ya hau suya, dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta ta shiga ɗakinta, shi ma don kar Sadiya ta gane ainihin ta razana da alamarin duk da an ce labarin zuciya a tamabayi fuska!. Tana shiga ɗakin ta yi jifa da mayafin Momi wanda ta sako don hatta kayan jikinta na Momin ne har takalmi. Da sauri ta shiga leƙo tsakar gidan don ganin abin da yake wakana, ganin Sadiya ta nufi ɗakinta da turtsetsen cikin ta sai ta ji zuciyarta tana zafi. Safa da marwa ta fara a tsakar ɗakin tana son kiransa a waya ta tamabaye shi wannan sabon salon fa, sai dai tunowa da crwa ɓarayi sun yi sama da faɗi da wayar sai ta rungumi na annabawa. Ta kasa zaune da tsaye gabaɗaya ba ta da nutsuwa tana ganin wannan raini ne yake ao ya ja mata. A ɓangaren Sadiya ko da ta shiga ɗakin ɗauke da sallamaa bakinta, tana shiga ta ganshi zaune a kusa da Kalifa ya buɗe masa biskit ɗin da ya fito da shi daga leda wanda dama shi ya siyowa, yaron sai murna yake yana ta taɓa jikin Nasir ɗin ganin yau bai kyamace shi ba, kuma bai dakatar da shi ba daga taɓa shi sannan bai haɗe masa fuska ba, uwa uba har da biskit ya siyo masa, sannan yana ta biya shi suna magana duk da gwarancin maganar ta shi ba komai ne ake fahimta ba. Ranta ta ji ya yi wani sanyi, tana kallon Kalifa da tausaywa shi ma ga shi yau ya samu ƴanci irin na sauran yara da suke samu a wajen mahaifinsu, shi ma yau yana ta dariya da farinciki sai ta ji gabaɗaya laifukan Nasir sun wanke daga idanunta duk da dama ba ta sakawa a zuciyarta amma dai ta san yana mata laifi. A rayuwa tana so a ce ko da ita ba ta samu komai ana kulawa ba to tana son ƴaƴanta su samu hakan zai rage raɗaɗi. Kalifa ya kalle ta ya ce "Momma kalli Abba ya siyo mini biskit" Ya faɗa yana ɗago mata biskit ɗin fuskarsa a washe, har ƙwalla idanunta suka tara ganinncewa yaro ma ya san kyautatawa bare kuma babba. Murmushi ta yi masa, sai ya taho yana ɗakko guda ɗaya ya nufi bakinta hakan ya sa ta buɗe bakin ta gutsuwa, shi kuma Nasir sai yake kallonsu yana murmushi. Allah kaɗai ya san yadda Sadiya take ji a ranta abu ne da suka rasa a iya zamansu a gidan amma yau rana ɗaya ga shi sun samu wannan yake nuni da cewa mahaƙurci mawadaci!. Sannu da zuwa ta ƙara masa ya amsa yana murmushi, leda ɗaya ya ɗakko ya miƙa mata ta karma da hannu biyu. Kallonsa ta yi ta ce "Za ka yi wanka?" Ya ce "Akwai ruwa mai ɗumi?" ,Ta ce "Eh akwai" Ta faɗa masa don ta cika filas ɗin shayin, ruwan wanka ta je ta haɗa masa ya tashi ya je ya yi wanka ya yi alwala ya fito. Bayan ya shafa mai dama kayan jikinsa ya mayar kasancewar babu kayansa a ɗakin duk suna ɗakin Meenal shi turakar tasa ma dama ba zama yake a ciki ba kawai ɗakin Meenal ne yake zuwa. Bai ce mata komai ba sai ta ga ya fito falon ya ɗauki ɗaya ledar da ya ajiye a gefe ya juya zai fita sai Kalifa ya bi bayansa abin mamaki sai ta ga ya kama hannun Kalifan sun fita. Gabaɗaya ta yi ɗiff tana ta mamakin abun kamar a mafarki. Ɗakin Meenal ya nufa yana shiga lokacin tana banɗaki, ledar ya ajiye a kan madubi, ya buɗe drower kayansa ya ɗakko kayansa lodi guda ya fito Kalifan yana biye da shi, kayansa gogaggu wajen kala goma ya shigo ɗakin da su, yana shigowa ta tashi ta karɓa, ta nufi bedroom don saka masa a drower. Yana bata ya ƙara komawa hannunsa riƙe da na Kalifa jallabiyarsa ya ɗakko guda uku, har lokacin Meenal ba ta fito ba, ita kuma ta ji shigowarsa domin ta ji motsi sai dai ta san shi ne ya shigo tana son sai ta gama abin da take ta fito ta zo ta sauke masa ruwan masifa. Ba ta zaci kaya yake ɗauka ba, lokacin da yake shirin fita daga ɗakin yana riƙe da kayan da hannu ɗaya ɗaya hannun ya riƙe Kalifa sai kawai ta buɗe banɗakin ta fito, tana fitowa ta yi mugun gani da sauri har tana neman faɗuwa ta nufo shi ta ce "Nasir mene ne nake gani haka?" Ta faɗa ranta a ɓace. Yana ɗan murmushi ya ce "A ina fa?" A gadarance ta ce "Oh ni kake tambaya? Baka ga ko da muka shigo gidan nan ban sake saka ka a idanuna ba, sai yanzu ka shigo kuma yanzun ma kana shirin fita,wannan kayan fa ko na bayarwa ne" Ɗan jim ya yi sai ya ce "Yau a ɗakin Sadiya na sauka" Duk da ta san hakan amma yadda ya furta sai abin ya mata ciwo, hakan ya sa ta ce "Mai kake nufi? Ba dai rabon kwana za ka fara mana ni da ita ba?" Ya ce "A,a kawai dai ita ma zan kwana a ɗakinnta ne... Ta katse masa hanzari da faɗin "Kar ma ka fara wallahi" Bai jira cewar ta ba ya juya ya bar ra a tsaye kamar ta rafka ihu tsabar takaici haka ta ji, wani tsaki ta duka tana juyawa ta yi ido huɗu da ledar kan mudubin ba ta yi wata-wata ba ta ɗauka ta yi wurgi da ita kayan ciki suka tarwatse. Ko da ya koma ɗakin bedroom ya shiganya sauya kayan jikinsa ya fito da jallabiya a jikinsa ya ce mata zai je masallaci ta ce masa sai ya dawo, yana fita Meenal ta jiyo rufowar ƙofar gida hakan ya ba ta tabbacin ya fita da sauri ta fito har tana tuntuɓe a barandar ƙofar ɗakinta, ta ji yadda yatsanta na ƙafa ya bugu amma ba ta damu da zugin da yake mata ba, burinta ta shiga ɗakin Sadiya. Sadiya tana bedroom tana linke kayan da ya cire a lokacin Meenal ta faɗo falon ko sallama babu ta, Kalifa yana ganin shigowarta ya tashi yana riƙe da alrwar tsinkensa ya kama hanyar bedroom a kiɗime don shi tsoronta yake. Sadiya tana ganinsa ta hau faɗin mene ne hankali tashe don ta yi zaton Nasir ɗin ne ya dawo ya zare masa ido tun da Nasir ɗin ma da ba ya sakar masa fuska tsoronsa yake. Kafin ya bata amsa ya riƙe ta sai ta jiyo muryar Meenal tana faɗin "Kai ina uwar taka take?" Sadiya ta gane da ita take kuma ta fahimci ita Kalifa ya gani ya gudo amma sai ta ba falon ajiyarta, hakan yansa abin ya ƙonawa Meenal rai ganin ta ƙi fitowa. Murya ta ɗage ta ce "To baƙar munafuka idan ma wani ƙulle-ƙule kika yj kika shiga tsakanina da shi ki sani na fi ƙarfin zama bora a gidan miji" Jin haka sai Sadiya ta fito tsabar ma ta ƙonawa Meenal rai sai ta fito hannunta riƙe da gajeran wandon Nasir da take linkewa wanda ya cire ta ce "Shiga tsakani kuma? Kin taɓa gani an shiga tsakanin mace da miji? Kenan ni da ba ya zuwa ɗakina shiga tsakanina kika yi da shi?" Tambayar rainin wayon nan ta ƙara hasala Meenal har ta fara tunanin yaushe Sadiya ta yi baki? Ganin gajeran wandonsa a hannunta ya yi wa Meenal zafi a zuciya, tana ganjn kenan har Sadiya ta fara samun ƴancin taɓa gajeran wandon Nasir bayan tin daga lokacin da ta zo gidan hatta suturarsa ta bar ɗakin nata. Cike da kashedi ta ce "Ki sani wannan abin da kika yi tamkar shuka ne a idon makwarwa, kuma ina sanar da ke ni da Nasir nan gani nan bari farar tumfafiya, da sannu zai dawo gareni yadda zai zamana sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya tada kai ua yi kallo" Baki Sadiya ta taɓe ta ce "Kanki ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya" Tana faɗar hakan ta juya ta shige ɗaki, dana a can ta bar Kalifa don bai biyo ta ba, Meenal ganin Sadiya ta barta a faɗo wato ta mayat da ita kamar mahaukaciya, hakan ya sa ta ji takaici wata zuciyar tana raya mata cewa kamar ita wannan marar galihun za ta faɗawa magana ta tafi ta barta a tsaye a wajen. Jiki babu ƙwari ta juya fuuuu ta fita suka ci karo da Nasir da shigowarsa gidan kenan ya mata kallon mamakin ganin ta daga ɗakin Sadiya ya ce "Lafiya dai kika fito daga ɗakinta a fusace ni fa ba na son gutsiri tsoma ki kama kankj" Da yatsa ta nuna kanta tana faɗin "Ni kake faɗawa hakan Nasir tabbas na yarda ba a hayyacinka kake ba an fi ƙarfika" ,Bai ce mata uffan ba ya raɓa ta ya shige ɗakin ya barta shanye a wajen, baki ta dantse da haƙori idanunta suna cikowa da ruwan takaici, tana kissima sai ta turbuɗe tauraron Sadiya da ya farw haske a zuciyar Nasir sai ta san yadda ta yi ta ƙwace komai ya dawo hannun ta fiye da baya. Ko da ta koma ɗakinta dakyar da iya yin sallah tana ta tunanin Alhajin da ya mata alƙawarin kuɗi idan ya tura mata ma ta ina za ta gani ita ba da waya gare ta ba, duk sai ta ji ta raina kanta yau ɗaya rana da Nasir zai kwana ba a ɗakinta ba tana ganin hakan kaɓar gazawarta ne a ce mijinta ya koma hannun matar da take ganin ba ta da aji fa kimar da za ta yi gogayya da ita wajen haɗa miji, duk kuwa da cewar ita Sadiyar ita ce ta fara auren Nasir ɗin. Sadiya wainar fulawa ya ce mata yana son ya ci haka ta masa ta kawo masa ya ci ya sha shayi mai kauri wanda Sadiyar ta haɗa masa da kayan shayinta da take saya. Ganin yau a ɗakinta yake kuma bata shirya hakan ba duk da ita dama ba ta tsark da ruwan sanyi tun da ta san tsarki da ruwan zafi yana haɗe mace sannan yana hana ciwon sanyi infection samun wurin zama a wajen macen da take amfani da ruwan zafin wajen tsarki. Hakan yana sa mace ta kasance koyaushe a haɗe, saɓanin ruwan sanyj da yake buɗa mace sanann sanyi ya samu wajen zama inda shi kansa sanyi yakan saka mace ta zama a buɗe sannan ko da ta yi amfani da maganin mata ba ta ganin alfanu saboda cutar sanyin. Yana nan zaune a falon yana danna waya Kalifa yana zaune a wajensa, ta ɗauki pure water ta shiga ɗakin da kofi da cokali ta tsakure dakan ni,ima na maman afrah ta zuba ta haɗa da madara ta ɗaga kofin ta shanye, wata ƴar roba ta ɗauka ta buɗe ta fito da ƙwallon dabino ta ɗauki guda huɗu ta rufe robar ta mayar ta fito daga ɗakin tana riƙe da kofin, kaskon turaren wuta ta ɗauka ta ɗakko gwarwashi ta haɗa kanamfari da ƙwallon dabinon ta je banɗaki ta zuba su a garwashin ta tsugunna. Sosai ta ji ya mayar da ita kamar sabuwar budurwa duk da dama Sadiya mace ce wacce tamkar ba ta haihu ba. Bayan ya dawo daga masallacin isha,i lokacin Kalifa ya yi bacci, ya tarar ta masa shimfiɗa a falo ta ɗaura masa net, ita kuma tana sanye da wata figigiyar rigar bacci da bai taɓa ganinta da ita ba gabaɗaya rigar ta bi ilahirin jikinta ta manne kallo ɗaya ya mata ya luka duniyar ƙaunar kasancewa da ita. Sun ƙule a ɗakin yana mata hira ƙasa ƙasa duk sai ta ji abun banbarakwai wai namiji da suna Hajara. A wannan lokacin ne Meenal ta zo ƙofar ɗakin da suka ryfe take bugawa tamkar za ta ɓalla, haka ya taso ya fito sanye da gajeran wando ko singlet babu ransa a matuƙar ɓace domin da kawo masa tsaiko a lamarinsa da Sadiya da yake jin tamkar yau ne ranar farko da zai kasance tare da ita ko don an daɗe ba a haɗu ba. Ta windown ya tambaye ta ba,asin zuwanta da kiransa, ta ce magana take so ta yi da shi, shi kuma ya ce ba zai samu dama ba sai gobe, haka ta koma ranta yana ƙuna, tana kissma mummunan ƙuduri a zuciyarta. Sosai ya ji sauyi game da Sadiya don shi kansa ya sani Sadiya ta da ban ce a cikin mata ta fita da ban ko da kuwa mata dubu ya tara!. Washe gari ko da su Hibba suka zo girkin safe, ranar sun gama tsara yadda za a ke yi su da Hajiya cewa yanzu su daina bari sai abin da Meenal ta ɗauka musu suna zuwa suna zama da yunwa kawai suke ɗaukan dankalin a ɓoye, soai suka ji daɗin shawarar nan tun da suna ganin ai ɗan uwansu ne yake siya ba ita ba, kuma har mahaifiyarsa za a ci. Lokacin da suka zo sun yi mamakin ganin yayan nasu ya fito daga ɓangaren Sadiya, sannan sai suka ga Meenal tana cika tana batsewa, ko da ta ɗauka musu ɗanyen dankalin ɗaki ta koma hakan ya sa suka samu damar ƙara ɗanyen dankalin a ɓoye suka ƙara fiƙewa suka yayyanka suka shiga kicin. Soyawa suka yi tare da soya wainar ƙwan. Ledar da Hajiya ta bayar Hibba ta fito da ita daga aljihun rigarta suka kwashi dankalin da wainar mai yawa sai ƴar dariya suke a ɓoye suna jin daɗin yau za su ci dankali ya ishe su. Bayan sun gama Husna ta je ƙofar falon Meenal ta ce sun gama ta daɗe kafin ta fito a shelaƙe tana wani taɓe baki tana shan ƙamshi. Kicin ɗin ta je ta ɗauka musu dankalin ko waina ba ta saka musu ba haka kuma ta ƙi tsakura musu kayan shayin. Fulas ɗin ta kinkima don yau ita kaɗai za ta ci ba ta niyyar ba Nasir tun da ya kwana a ɗakin Sadiya. Sun fito za su tafi lokacin tana dab da hawa barandar ɗakin ta, kamar wanda aka ce ta juya haka ta juya sai kuwa idanunta suka sauka a kan aljihun doguwar rigar Hibba da ya yi tudu, hakan ya sa ta kafa ayar tambaya don ta san ita dai lokacin da suka zo ba ta ga wata alama ba a jikin ta. Sai dai ba ta taɓa kawowa cewa dankali ba ne ita ta fara tunanin ko a kayan kicin ɗin ta ne suka ɗauki wani abun za su fara mata zari ɗai-ɗai. Murya ta buɗe ta ce "Ke Hibba ku dakata!". Cak!. Suka tsaya suna jiran tsamani domin ita Hibba har ta fara ƴar karkarwa don dama ƴan magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Fulas ɗin hannunta ta ajiye ta tunkaro su, tana zuwa ta ce "Mai kika ɗauka min a kicin?" Husna ce ta yi ƙarfin halin yin magana domin ta ga Hibba tana neman bayyana lamarin ta yanayinta. Husna ta ce "Ɗaukan abu a kicin kuma sai ka ce wasu ɓarayi" Meenal ta ce "Ke Husna dakata!. Kar ki ƙara faɗa min magana garangatsai kamar wata sa,arki ni ba da ke zan yi ba, domin ni ba tsararki ba ce" Ta faɗa ta miƙa hannu za ta taɓo aljihun Hibba ta matsa gefe tana zare ido. Ƙiiii Meenal ta janyo rigar Hibba tana saka hannu ta ƙarfi suna kokawa ta taɓo dankali yadda ta ji shi da zafi tana leƙawa ta fito da shi ta buɗe leda sai ga dankali ba kaɗan ba da waina. Idanu ta zaro cike da mamaki ta buɗe murya ta ce "Ihu ɓarayi, ihu ɓarayi jama,a a zo ga ɓarayi" Nasir da yake wanka ya yi saurin ɗauro towel jikinsa duk kumfa domin ya ji wannan baƙon al,marin alama ce ta babu lafiya, Meenal ganin Hibba tana ƙoƙarin rufa tabarmar kunya da hauka ne Meenal ta ɗaga hannu ta kifa mata mari, da sauri ta dafe kunci cike da mamakin sa ya sa bakinta ya ƙi rufuwa, hatta Husna ta tsorata da matakin da Meenal ɗin ta ɗauka, a daidai lokacin ne Kusan tare Nasir suka zo da Sadiya don jin ba,asin abin da yake faruwa.... MAMAN AFRAH 09025576222 https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 2️⃣9️⃣ UMMA Addu,a take amma kukan da take na hawaye, kuka ne marar sauti wanda ambaliyar ruwan hawayenta ne kaɗai suke nuni da cewar kuka take sai bakin ne kaɗai yake kai komo, kai komo na addu,a da kuma kai komo na kukan da na sanin abin da ta aikata tun da dai ga shi ba a kai ga samun biyan buƙata ba matsaloli maau tarin yawa sun baibaye ta matsala ta farko riƙe ta da gawar ta yi matsala ta biyu gabaɗaya maganin ma ya zuba kuma ba a yi aikin da ya dace a yi da shi ba, wato aiki dai bai kammalu ba. Jin ta kakare a wajen karatun da take sai ra ji ta ƙi gana ta ƙi ba ya sai wani abu da take ambato wanda ita kanta ta kasa bambance cewa karatu ne ko kuwa waƙa. Jin ta take kamar ba a duniya ba idanu ta rufe gam tana tunanin mafita, ji ta yi an ƙarawa hannu da ƙafarta kaimi wajen riƙo, hakan ya sa ji duniyar ta mata zafi tana jin ina ma tana da damar da za ta tashi jama,ar gidan wataƙila su su kawo mata ɗauki amma yanzu lamarin sai saɓ barka. Kafin ƙiftawar ido sai ganin Malam Kalla ta yi a hankali yana tashi zaune har ya kai ya zauna dangargar. Salatin da ta warto a bakinta wanda ba ta sanya da aka yi ba har ya fito fili ya karaɗe ɗakin tamkar landan ya taƙarƙare yana kiran sallah. tun daga salatin nan bakin Umma bai samu damar warto wani furuci ba ko da kuwa waƙa ce ba karatu ko addu,a ba. Sai kuka da take yi kamar an buɗe famfo zuwa yanzu taimako take nema ba ta ankara ba sai kawai ta ga Malam Kalla ya ɗauke hannun sa daga riƙon da ya mata na ƙafa da hannu ya ya ɗauke ta ya ɗora a cinyarsa duk da ƙoƙatin fisge kanta da take yi daga gare shi, tashin hankali wanda ba a saka masa rana jinta zaune a cinyar gawa har gawa tana miƙa baki saitin kunnenta tana mata raɗa da ƙarfi ƙirjinta ya buga wata irin karkarwa da jikinta ya ɗauka ita ta saka ta buɗe idanunta sai lokacin ta gane ba gaske ba ne a idanun zuciyarta ne da sauri ta mayar da kallonta kan gawar ta ganta tana a yadda take hannun gawa riƙe a ƙafa da hannunta wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke a fili. Sai lokacin ta fahimci cewa tsabar halin firgici da ruɗanin da take ciki ne ya sa ta kissima wannn abun na ganin gawar ta ɗora ta a cinya, wannan ya ƙara ruɓanya halin tsoron da take ciki hakan ya sa ta saka a ranta duk runtsi sai ta kuɓuta, jan ƙafarta ta fara tana daga tsugunnen amma sai ta ji gawar kamar ta fisge ta, hakan ya sa ta yi zaman ƴan bori a cikin ruwan fitsarin da ta yi ɗazu. bata damu da hakan ba ta shiga jan jikinta don ta gwammace ko da rarrafe ne ta bar gidan. Gani ta yi yadda take jan jiki za ta gudu tare suke da gawar domin motsi kaɗan sai ta ga gawar ta biyo ta ma,ana daga Umma ta ja sai ta ga haɗe take ja da gawa, amma bata damu da hakan ba ta bari idan suka je bakin ƙofar gida ta san yadda za ta yi ta tsere in ya so ko da a ce a wajen ne ta bar gawar a ɗauke gawar daga baya a kan ta zauna cikin wannan balai,. In ban da ma son zuciya irin nata kuma saboda neman biyan buƙata a yadda take da masifar tsoron gawa ba ta taɓa.zaton har za ta zo wajen gawa ba. Dakyar take jan jikinta saboda nauyin gawar Malam Kalla da take ja, a haka ta daure har ta fito tsakar gida inda su Abba duk suke yashe kamar matattu. Har lokacin gawar a ƙame take, sai dai kash! Umma tana shirin kama hanyar ƙofar gida sai ta ji gawar ta fara rimjayarta Umma a zuciyarta ta ce ko ana ha maza ha mata sai ta ƙwaci kanta. A haka tana ja har wajen ƙofar fita sai dai tana shirin yadda za ta yi ta ɓanɓare gawar sai kawai ta ji kamar wanda aka ɗaga su sama daga ida har gawar ta gansu suna tafiya luuuu ba au yi masauki ba sai a tsakiyar ɗakin inda suke a ɗazu wato gawa ta koma gurbinta inda aka ajiye ta gaka ma Umma ta koma mazauninta inda take a gaba gawa. Umma ganin hakan ya sa ta rushe da kuka mai sauti a fili tana faɗin "Wayyo na ga ta kaina, Aliya kin haɗani da jaraba ke kina can ɗakin mijinki, ni yau bami da tabbas ma zan kwana a ɗakina, sannan igiyar aurena ma tana wala,ali" Ta faɗa jikinta duk yana karkarwa Allah ne kaɗai ya san halin tsoron da take. Kuka take wiwi tana rayawa a ranta shiknn asirinta ya gama tonuwa tun da gawa ba za ta ɓanɓaru daga jikimta ba, sannan wani babban tashin hankalin ma da ta tuna cewa matsawar gawar nan ba ta sake ta ba idan gari ya waye za a iya samun wasu jama,ar su zo sannan ya zama wajibi kowa ya ganta kenan asirinta ya tonu. Kamar ƙiftawar idanu sai ta ji an saki hannunta an kamo wuyan hijabinra da farko ma ta tsorata fiye da kima domin a tunaninta maƙogwaro za a shaƙe mata a kashe ta ita kuma ganin gawa muraran tana rike da ita ya ƙara saka mata tsoron mutuwa, nan suka shiga kiciniya iya da gawa har hijabin ya yage!. Kamar daga sama ta ji wata murya ta ce "Lubabatu!" Gaban Umma ya buga da ƙarfi har ba ta san lokacin da wata tusa mai balain ƙara ta kuɓuce mata ba sai ƙara ta ji bobott tana fitar da iskar. Jikinta kamar mazati haka yake rawa bata taɓa jin tsoro irin na yau ba gabaɗaya wani gumi ya wanke ta kamar an sheƙa mata ruwa, faɗuwar gabanta ta tsananta yanzu kam ta tabbatar sai yadda hali ya yi shiga motar mai taɓi, don ta ga gawa ba ta da niyyar sakinta wato babu niyya ango ya kwana da wando!. Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, jin sunanta da aka kira kuma ba ta ga kowa ba sannan gawar dai ba ita ce take magana ba hakan ya sa Umma ta fara tunanin ko dai taɓin hankali ne ya samu ƙwaƙwalwar ta da za ta ji an kira sunanta. Sunanta da aka kira a karo na biyu ta shiga amsawa a tsorace sai ta ji an ce "A gobe da safe za a rufe ku a kabari tare da Malam Kalla, don haka kina da damar ƙarasa aikinki na zuba maganin, don wannan hannun ba zai taɓa.sakin jikinki ba sai dai a binne ku a tare" Idanu Umma ta hau wurwurgawa jin wannan batun sai da hakan uanyi sanadiyyat ƙwacewar wata ƙaramar gudawa, ta sassauura murya a ranta tana faɗin to ko dai mala,ikan mutuwa ne ya zo mata a ɗakin Malam Kalla. "Cikin faɗuwar gaba ta hau faɗin "Yanzu zan tafi gida, dama don bai saka min ƙafa ba ne, wallahi tallahi ina da rai ban mutu ba shi ne ya mutu!" Wata irin dariya aka sheƙe da ita Umma sai kallon kowa na ɗakin take amma ta ga ba su ba ne. Ta ji ana magana da murya kamar gargaɗi aka ce "Ɗayan biyu ko dai a binneku tare ko dai a datse mki ƙafa da wuya sannan ne za ki kuɓuta" Umma tana hawaye ta kalli ƙafarta da take manne da gawa ta fara kwatanto yadda ba za ta yi kyan gani ba idan babu hannu da ƙafa, wato babu hannu ɗaya babu ƙafa ɗaya. Kamar al,mara sai ta ga idon Malam Kalla guda ɗaya ya buɗe da sauri ra rufe nata idon tana son tuno wata addu,a da ta iya domin komai ya kwance mata, cikin ikon Allaj ta samu ta kamo sunan Allah Al,maliku ta shiga maimaitawa sai hawaye da suke zuba kamar an buɗe famfo. Tana cikin hakan kamar a mafarki sai kawai ta ji hannun gawa ya fara sakin wuyan hijabin da aka shake da alamar an fara sassauta riƙon, kaimi ta ƙara wajen ambaton sunan Allahn amma ko idanun ba ta buɗe ba, a haka sai da ta ji ƙafa da wuyan sun saki, sannan cikin faɗuwar gaba ta yi saurin jan mayafin ta rufe gawar, ba ta jira komai ba ta fara rarrafe saboda ta san a halin da take ciki yanzu ba za ta iya tashi tsaye ba haka ta rarrafo ta fito cike da tsoro da fargaba, tana fatan Allah sa haka ne bakin wahalarta, wato kar sai ta zo fita daga gidan a ƙara mayar da ita ɗakin. Tana haki ta warci takalmanta a hannu ba don ma kar a ga baƙon takalmi ba, da babu abin da zai saka ta ɗaukan wani takalmi tashin hankalin da take ciki ma ya ishe ta. Haka ta taho gwiwarta tana zafi saboda yadda take cin karo da dutsi da kuma ƙananan itace suna cake mata gwiwoyin. Sai da ta fita daga gidan ta sako bakinta a zauren gidan ta dage ƙarfinta ta ce " Malam Kalla!."Ta na faɗa ta juya da rarrafe hannunta da takalmanta ta ci gaba da rarrafawa tana fatan Allah sa dai muyane gidan sun falka daga suman dolen da ta saka su wanda ga shi ita kanta ba ta samu biyan buƙata ba. Sai da ta ɗan yi tafiya sannan ta je kusa da wani bangon jikin wani gida ta dafa ta miƙe tsaye har lokacin gabanta yana dukan lugude tsabar faɗuwar da yake. Haka ta samu ta lallaɓa gida tana jin jikinta kamar an cire mata ƙarfi kwata -kwata, dakyar ta shiga ta yi wanka shi ma ruwa kawai ta kwara babu nutsuwar yi da sabulu kasancewar tana tsoron Abba ya dawo ya ganta da kaya a jiƙe ga shi har da ƴat guntuwar gudawarta da ta saki a cikin kayan. Alwala ta yi ta koma ta zauna hat lokacin gananta yana faɗuwa. Tana jin yadda wayarta take ta ruri amma ta kwanta lifet a kan tabarta tana jin yadda har lokacin ƙirjinta yake fat-fat. Ta san kuma ba kowa ne mai wannan kiran ba sai Aliya za ta dame ta ita kuma yanzu ita kanta ba ta da nutsuwar yawan surutu, don gabaɗaya a firgice take fatan ta Allah sa ta iya yaƙi da zuciyarta kar Abba ya gano a halin da take cjki. Ta jima a kwance tana ta jan lahaula wala quwwata illah billahi aliyal azim. Don daga ta rufe idanunta sai ta ga Malam Kalla ta rasa yadda za a yi ta daina jin bugun zuciyarta yana tsananta tana tsoron kar wani ciwon ya kama ta sanadin yawan firgicin nan.. A can gidan Malam Kalla kuwa Umma tana ambaton sunansa sai kowa ya tashi daga gajeran suman da ya yi, haka aka ci gaba da koke-koke tamkar babu wanda ya suma to kowa ma ya manta abin da ya faru, su Abba ma haka suka jajanta wa iyalan nasa tare da masa addu,a suka fito suka nufi masallacin don yin sallar isha,i. Umma tana nan yashe a kan tabarma, jin wayarta ba za ta bari ta huta ba ta tashi tsaye za ta ɗakko wayar ta amsa, wani bugar jikin ƙofar gidan da aka yi hankali tashe Umma ta yi cikin ɗakin zaninta da ya suɓuce ya faɗo ko ta kansa ba ta bi ba haka ta yi cikin ɗaki daga ita sai ƙaramin siket da ake sakawa a ciki. Ko da ta shige ɗakin a guje ta banko ta saka sakata ta jimgina bayanta da jikin ƙofar tana numfarfashi. Tunanin ta ko Malam Kallan ne ya sake biyo ra har gida idan haka ne har ta fara tunanin yau sai dai bango ya tsage ta shige!. Barar da almajirin ya fara rafkawa a tsakar gidan, shi ya ankarar da Umma almajiri ne ya bugi ƙofar. Wani wawan tsaki Umma ta ja tana mai tashi tsaye ta buɗe ƙofar ta fito tsakar gidan tana luƙawa almajirin zagi wai duk ya kasa bara a bakin ƙofa sai ya zo yana bugar ƙoga kamar za a yi yaƙi. Susum almajirin ya fice daga gidan, ita kuma ta hau masifa tare da sunkuyawa ta ɗauki zaninta a fili tana cewa "Wannan ai shashanci ne ka zo ka ruɗawa mutane ciki, dama ni da nake a ruɗe ka zo ka ƙara ruɗani nake tsere ni kaɗai a tsakar gida, har ina yada zani wallahi ka ɗauki alhakina" Ta faɗa tana ɗaukan zanin ta ɗaura, daidai na kiran ya sake shigowa a fusace ta ɗauki wayar don haushin Aliya take ji ba ta san irin rijiyar da ta tsallake ba, rijiya mai gaba miilyan ma ba gaba dubu ba. Ɗagawa ta yi sai kuwa ta ji Aliya tana faɗin "Umma aka ce Malam Kalla na unguwar nan ya rasu, ina ta kiran ki in ce ki shirya rangaɗaɗau ki je ki ɗura masa aganin nan a hanci ko kakarmu ta yanke saƙ... Ba ta ƙarasa ba Umma ta ce "Aliya na je gidan Malam kalla" Aliya ba ta gama.jin ba,asi ba ta carara uwar guɗa don tunaninta aiki ya kammala. Umma kuma tsabar takaici sai ta kasa magana sai da ta gama guɗa da ife-ife ta ce "Allah ne kaɗai ya aan karatun kurma Umma, a yau ba sai gobe ba zan nemi takardar saki a wajen Kasim, ni ba don mutane ƴan sanya ido ba da wallahi babu wata idda da zan zauna yi kawai sai in auri Ibrahim ɗin, don na ƙosa fara gasawa Jidda baƙar aya mai tsakuwa a tafin hannunta yanzu ne za mu nuna mata dama mu asalin maƙiyanta ne ƴar daular da ta afka ciki ce ta aanya mu ka sassauta tuƙin gangancin ƙiyayyar da muke yi wa rayuwarta... Umma jin batutuwan da Aliya take ba su da alamar ƙarewa ita kuma ta san ba a zo wajen wannan maganar ba domin an samu saɓanin abin da ita Aliyar take zato, cike da muryar mai ɗankaren sanyi ta ce "Aliya aiki fa bai kammalu ba, don na je har ɗakin gawar Malam Kalla amma wallahi magani dai bai samu shiga hancinsa ba... Tun Aliya ba ta gama jin komai ba hawaye suka yi wa fuskarta tsinke ba komai ne ma ya ɓata mata rai ba sai yadda Umma ta samu damar da ta yi wasa da damarta don ta ce har ɗakin gawar ta je kuma dai ta san bokanya ta bata maganin da za ta barbaɗawa mutanen gidan su sume kenan idan har kowa ya suma sannan ta shiga ɗaki mai ta tsaya yi ba ta aiwatar da aikin ba?. Cike da muryar kuka mai nuna tsantsar takaici da baƙinciki ta ce "Haba Umma da kin san ba za ki iya ba wallahi da ni na yi, ni fa ɗazu Amatullahi ta kirani take ce min Malam Kalla ya mutu tsabar farincikin an samu sabuwar gawa ta namiji kuma a unguwar sai da na nuna jin daɗina da har Amatullahin ta kusa harbo jirgina domin ban faɗa mata aikin da za ki yi a kan gawa ba kin san ba komai ne kake kwashewa ka faɗawa mutum ba duk da ta san komai" Umma maganganun Aliya sun sosa ƙoƙon ranta haka ta fara magana cike da masifa ta ce "Aliya ni za ki cewa ba zan iya ba, ai da kin zo ke kin je kin zuba, da kin san irin rijiya da bayan da na tsallake wallahi da baki yi wannan furucin ba, ni da gawa ta riƙe min hannu da ƙafa muka ringa rigima da gawa" Ƙirjin Aliya ta dafe da hannu ɗaya tana zare ido a take ta ji tsoro ya baibaye ta ta ce "Umma dama bai mutu ba ne? Mun shiga uku Umma kar dai asirinki ya tonu?" Umma ta ce "Ai shi ya sa ake aso mutum ya fara jin ba,asi kafin ya yanke hukunci, to da asirina ya tonu ai da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, wallahi ban san mai ya sa wannan gawar ta mini haka fa ke ƙarshe da na matsa sai na gudu haka na janyo gawar nan ƙiiii wallahi har bakin ƙofar gidan Aliya, amma yadda kika san ana saka mini maganaɗisu ko kuma a saman iska haka aka ɗagamu daga ni har gawar aka mayar da mu" Umma ta faɗa tana kwashe komai ta faɗa mata. Tsoro duk ya mamaye Aliya ga shi Kasim bai dawo daga masallaci da ta fita ba sai ta ji gidan gabaɗaya ya mata girma, amma saboda zuciya marar kyau da kuma mugun ƙuduri wannan abin da Umma ta faɗa bai zame musu aya ba sai ta ce "Amma ai da sauran maganin ko Umma?" , Umma ta ja tsaki ta ce "Sai ki yi kuma Aliya, an ce miki muna ta fafatawa da gawa guntun na ledar ya kife iska ta ɗaga ledar ma ni ba zan ce ga inda ledar take ba to ana ta kai wa yake ta kaya? Wallahi da a ce ke ce kika ganki riƙe a hannun gawa kuma gida babu kowa ta riƙe ki gamgam har da su shaƙe wuyan hijabi da tuni kin suma" Aliya ta yi shiru tana jin ɓacin rai tare da tunanin shin mai ya sa ba ta da sa,a a rayuwa mai ta sa duk aikin da aka bada a yi a kan abubuwan da za su saisaita rayuwar ta sai an samu akasin lissafi sai komai ya rushe, kenan ita haka za ta dawwama a talauci Jidda a daula, Umma ba ta ankara ba ta ji Aliya da ƙarfi ta ce "Ba zai yiwu ba, ba zai taɓa yiwuwa ba, akwai wanda yake saka mana hannu a aikin nan ina zargin Jidda ce in ba ita ba ya za a yi a ce duk abin da za a shirya a kanta ko kan mijinta abu ba ya yiwuwa in har ba saka hannunta ba ya za a yi a ce gawa ta yi motsi har ana kokawa wananna abin da sake kuma wallahi duk ranar da nufina ya cika sai ta wulaƙanta iya wulaƙanta a wajena" Ta faɗa tana rushewa da kukan baƙinciki. Suna cikin wayar Abba da ya dawo saga masallaci ya yi sallama, da sauri ta ce "To madalla Aliya ka gaishe da Kasim ɗin, to zai ji Abban naki ai ga shi nan ma ya shigo" Ta faɗa don ta ankarar da Aliya Abba ya dawo haka ta datse kiran tana ɗan wayincewa ta tattaro nutsuwarta amma gabanta yana faɗuwa game da Abba tana jiran ta ji kanun labarai shin Abban ya gano ta je gidan mutuwar ko kuwa kowa ma ya sani tun da ba ta san yadda aka ƙarƙe ba. Ganin jikinsa sanyi ƙalau tun kafin ya ƙarasa zama ta ce "Kai Allah sarki Malam Kalla lokaci ya yi!" Ta faɗa cike da jimantawa, ya gama zama ya ce "Wallahi ke dai bari Lubabatu na ji mutuwar bawan Allahn nan, duniya ba matabbata ba, watarana mu ma haka tamu mutuwar za ta risƙemu" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke jin babu wani batu bayan na mutuwa hakan ya sa ta zage suka ci gaba da jajantawa. Ko da dare ya yi ta zo kwanciya sai tsoro ya mamaye mata zuciya daga ta rufe ido sai take ganin kamar gawar za ta zo mata haka ta kwana idanu a buɗe don ba ta so ta rufe idanun sai take hangar gawar kamar ta zo gidan, haka ta kwana a firgice. Da safe sa ciwon cikin ƙarya ta tashi amma tana ta nuna za ta tafi sutura Abba ya ce tun da ba ta da lafiya ta zauna, daɗi ya cika ranta don ita ba ta so ma ta je suturar gawar da ba ta da tabbacin ta mutu. Ko da Abba ya tafi suturar ya dawo haka ta ce "Oh duniya ba tabbas har an binne shi ko, rayuwa kenan, yanzu mutum an jima gawa rayuwa kenan, duniya kenan yau kana tafiya a saman ƙasa watarana kuma kana ƙarƙashin ƙasa" Abba ya ce "Bari ke dai ai muna rayuwa ba mu san rana da lokacin mutuwarmu ba bare yanzu da ake yawan mutuwar nan ta bagatatan mutuwar fuju,a yanzu za ka rabu da mutum an jima ka ji an ce babu shi" Umma dai ba ta ji amsar tambayarta ba hakan ya sa ta ce "Wallahi kuwa Allah sarki marigayi Malam Kalla su tasu ta ƙare saura tamu tun da sun shiga kabari" Abba ya ce "Kai ina tsoron mutuwa ranar da zan ganni ga ni ga mala,ika, ranar da za a saka ni a kabari ranar da zan ganni a cikin kabari, ya Allah ka rabamu da duhu da azabar kabari da nauyin ƙasa" Umma ta takarkare ta ce "Amin" Amma duk ranta ya ɓaci ita so take ya ce an binne shi don tana tsoron ya faɗi abin da ya faru tun da tana ganin bai mutu ba. Har ta yi shiru sai ta ce "Ko ba a yi suturar ba ne" Abba ya ce "Haba ke kuwa sutura ta nawa kuma tuni ma da an dawo mai zai dawo da ni gida in ba a kai shi makwancinsa ba, dama dawowa na yi idan na karya sai na koma idan na ɗan jima wajen karɓar makokin sai na dawo na shirya na tafi kasuwa" Umma ta ce "Haka ne" Ta faɗa tana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Aliya kuwa tun da ta ji bayanin da Umma ta mata ta gane cewa Abba ne ya dawo, Umma tana datse kiran wayar ta ajiye kawai take kuka wiwi don rashin cikar burinta kuma tana tunanin yadda za a samu wani kuɗin aikin. Ko da Kasim ya dawo sai da ya fahimci ta sauya amma sai ta nuna masa kanta ne yake ciwo shi kansa haushinsa take ji ta gaji da sakar masa fuskar da take ta gaji da nuna masa tana zaune da shi ne da zuciya ɗaya, bai san cewa da wata manufa take zaune ba burinta yana cika zaman gidansa ya ƙara don ta fi ƙardin zaman aure da talaka, talakan ma mata -maza. Ko wayar ta da ya gani sabuwar ta nuna masa Jidda ce ta saya mata duk da ta fahimci bai ji daɗi ba amma haka ta make abinta tun da ta san shi dai koyaushe cikin fafutukar na abin da za a rufawa kai asiri yake ita ba ta taɓa hango masa zai taka matakin masu arziƙi ba duk da an ce arziƙi kashi ne amma ita ba ta hango arziƙi a tare da wannan mata mazan ba gani take a haka zai ƙare ita kuma ta fi ƙarfin zama da shi yadda take kyakkawa ajin farko da gidan daula ta dace, gidan daular ma ba kowane iri ba. Bayan nan suka ringa waya da Umma saboda tana tsoron ta je gidan su haɗu da Abba saboda ba ua son yawan zuwa gida babu dalili, shi yawo ba ya yi wa mace kyau a wajensa a ce yau tana can gobe tana can ko da budurwa ce kuwa bare matar aure, ya tsani fita babu dalili. Haka dai suka shirya suka je wajen bokanya don sanar da ita abin da ya faru. Ko da suka je bokanya ta ɗauka za su faɗi kyakkyawan labari amma sai ta ji saɓanin haka, mamaki ya kamata hakan ya sa ta yi wani surkulle ta ɗakko wani ganye tana karkaɗawa tana ambaton wani suna, zuwa can sai suka ji magana ta karaɗe ɗakin ana cewa "Ya ke bokanya mai kike buƙata a aiwatar miki?" Bokanya ta ce "Ina so sanin dalilin da ya sa gawar da za a sakawa maganin da na bayar ta motsa har ta riƙe wacce za ta yi aikin" Mai maganar bisa muryar tsoro ya sheƙe da wata dariyar da har sai da su Umma suka razana sai da dariyar ta lafa ya ce "Akwai wani abokin aikin ki boka Naladidi wanda sa,insa ta shiga tsakaninku a watan da ya wuce har ya ci alwashin sai ya ɓata miji duk wani aiki to shi ne yake kan bakansa, shi ne ya yi komai" Cike da rashin fahimta ta ce "Mai ya yi" Muryar ta ci gaba da cewa "Ya aika aljani ɗan ƙundalo ya je ya ture Daddyn Ibrahim ɗin da kika yi wa asiri a cokali, shi ne aka kira Ibrahim ɗin aka sanar da shi a lokacin da zai ci abinci wannan dalilin ya sa bai ci abincin da cokalin ba bare har aikin ya ci, sannan shi ya aika aljani gidan gawar Malam Kalla, aljanin ya ɗauke gawar mamacin ya kwanta a wajen da aka ajiye mamacin bayan ya sauya kamanni irin na mamacin ai ba gawar ba ce aka yi ƙoƙarin sakawa maganin ba aljanin ne, da shi suka yi kokawar har sai da ya ga komai bai yi ba a aikin sannan ya koma ya sanar da bokan cewa ya cika aiki hakan ya sa ya ƙara cin alwashin duk aikin da za ki yi sai ya san yadda ya yi ya ɓata aikin bai yiwu ba" Tun da ya fara bayani jikin Umma yake karkarwa musamman idan ta tuna cewa wai da aljani ta yi fafutuka jiya ashe aljani ne ta ja hat zaure duk sai ta ji tsoro ya baibaye ta a ganinta har gwara gawa mutum ce a kan aljani. A neman duniya za ta je ta yi abin da aljannun ma za su ɗauke ta a banza. Daga haka bokanya ta sallami aljanin da ya mata bayani don har wasu ayyukan da ta yi wa mitane aka samu akasi sai da ya faɗa mata dalili duk aikin bokan Naladidi ne. Tsaye ra miƙe rai a ɓace tana surutai da cin alwashi a kan bokan, nan ta ce idan su Umma sun samo kuɗi su dawo za ta musu maganin da ba a isa a saka hannu ba, don ta ce gabaɗaya wwaɗancan maganin da ta musu duk da an nuna matsalar rashin dacewar aikin daga gare ta ne amma ba za ta musu wani maganin ba sai sun sake biya shi ne Umma ta faɗa mata babu kuɗi sai ta ce su je in sun samo kuɗaɗe masu nauyi su dawo haka suka taho jiki babu ƙwari a hanya Umma ta ce "Oh ni Lubabatu yanzu ashe da aljani na fafata, ashe ɗauke gawar aka yi kenan da na tafi sai aljanin ya dawo da gawar kai jama,a lallai sai a bar aikin aljannu, ai ni dai na daddara da aikin matar nan" Aliya ta ce ",Kenan Umma sai dai na haƙura sa cikar burin nawa?" Umma tw ce "Sai dai idan an samu kuɗin mu tuntuɓi wani wajen don wallahi ba zan ke zuwa muna danbarwa da aljannu ba wataran ma su ji haushi su ɗauke i su kaini matattararsu, tun da ni da naci in ce sai na yi aikin ko na gawar ma ba nacewa na yi ba kin ga da akwai tsautsyi sai aljanin ya ɗaukeni, amma ni dai tun da bokanya tana da abokin adawa suna faɗa mu cire kanmu daga zuwa wajenta" MEENAL Kafin ta sauke hannunta Husna ta ɗaga nata hannun ta kifa mata marin duk da abin ya zo mata a bazata amma sai ta dake ta dafe kunci da hannu tana rushewa da kuka, zuwan Nasir sai ya kasa fahimtar mene ne tun da ya ga an yi kuma Meenal ya ga an mara sai dai marin da Husna ta yi wa Meenal a kan idanunsa da na Sadiya, sai dai ita Sadiya kasancewar a gaba take ta ga marin da Meenal ɗin ta zabgawa Hibba. Meenal kunci ta dafe da hannu ɗaya ɗayan tana riƙe da ledar dankalin amma kuma yana dafe a cikinta.Tana rayawa a ranta cewa Husna ta taɓo gidan rina din sai ta mata sharrin da ba za ta fitar da kanta ba tun da har ta iya saka hannu ta mare ta, Nasir kuma yana mamakin faruwar abin don ya san dai ya ji an ambaci ɓarayi kuma ya fito ya ga saɓanin abin da kunnuwansa suka ji. Don haka bai tambayai ba a si ba sai ya ce "Husna mene ne hakan? Matata kike mari a cikin gidana?" Husna da Hibba sun buɗe baki za su yi magana sai Meenal ta ce "Darling wai fa kawai don na ce ihu ɓarayi shi ne ta naushe ni a ciki kuma ta mareni, dama tun ranar nan suke cewa ban isa in haihu a gidan nan ba tun da dai har na saka kake sakawa suna zuwa suna mini aiki" Baki suka saki jin wata kissar da ta musu sannan a yanayin yadda suka ga ya nuna a fuskarsa kamar dai ya yarda da maganganunta, sai dai kafin ya yi magana sai Sadiya ta ce "Ya kamata ka fara tambayar abin da ya faru kafin ka ɗorawa ɓangare ɗaya laifi ka fara yin bincike domun tabbatar da abin da idanunka ba su gani ba karka yanke hukunci da abin da idanunka suka gani... Tun kafin ta kai aya Meenal ta ce "Malama tun da ba da ke ake ba ki yi shiru mana kuma ai zuwa da kai ya fi saƙo sannan gani ya kori ji shi da idanunsa suka ga abin da ya faru tamabayar mai zai yi" Nasir shu takaicinsa ɗaya ma da suka saka ya fito da kuma a jikinsa ko wanka bai gama ba, shi ua rasa wannan wace irin rayuwa cw kuma wace irin cakwakiya ce a ce kullum sai sun zo nan za su dafa abin da za su ci hakan ya sa ya ce "Meenal mai ya sa kika musu ihun ɓarayi?" Meenal duk da ta ji haushin tambayar ganjn kamar ma ita yake son ɗorawa laifi sai ta ɗago masa ledar ta ce "Dankali Hibba ta sata suka saka aljihu shi ne Allah ya toni asiri su na gani" Hibba sai ta ji duk kunya ta kamata shi kuma sai ya ma rasa abin cewa sai Husna ta ce "Yaya dankalin ne fa takr bamu kaɗan ba ya isarmu kullum sai dai mu yi kashi kamat wasu mararsa galihu, shi ne muka ƙara yawan dankalin da muka soya muka kwasa yadda zai ishemu" Ya ɗanyi shiru ya ce "Kuma sai ku ɗauka bakwa cewa ta ƙara muju wanda take baku ba ya isa" Hibba ta ce "Ka ga fa ɗan wanda take bayarwa bai fi cikin mutum ɗaya ba" Ganin dankali ransa ya ɓaci kamar wanda aka roƙa ganin yana neman yarda da maganrsu Mrenal ta ce "Ƙarya suke munafukai ne wallahi a kicin suke tsayawa su cin iya cinsu sai su kai ɗan kaɗan gida, amma ya za a yi na zuba musu wannan" ,Gabaɗaya ma sai ya rasa maganst wa zai ɗauka su kuma su Hibba suna mamakin sharrin da take ƙullawa da kuma tsabar iya kissa. Ɗan jim kawai ya yi ya ce "Bani dankalin na ledar" Miƙa masa Meenal ta yi sai ya miƙawa Husna ya ce "Gashi nan ku juye a cikin wannan ɗin ku je ku tafi gida" Meenal ta doka uban tsallw tana masifa da kumfar bakin ya goyi bayan ƴan uwansa ta kama ledar hannun Husna ta riƙe ta ce babu wanda ya isa ya fita da dankalin daga gidan tun sa ita ba ta basu ba. Nasir ya ce "Wato ni da nake da ikon a kan abincin ban isa na gindaya magana ba sai kin yi jayayya ko?" Ta yi raurau da ido na kissa ta ce "Shikenan ni bani da kima da daraja a idanunka ka saka ƙannenka za au rainani, Husna ta ɗaga hannu ta mareni amma babu wani mataki da ka ɗauka sannan har naushina ta yi fa, ai da ƴar gwal aka taɓa Sadiya da tuni kana tada jijiyoin wuya, kuma wallahi bashi suka ci indai ni ce wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha mu zuba ni da su ɗan halak ka fasa!." Nasir ya ce "Mari ne kin yi an rama, to ya kuke so in yi da raina, kuma wallahi idan kika sake wani abu ya biyo baya ni da ke ne sannan ki saka mata ledar wannan su tafi" Jin haka sai ta ƙara harzuƙa ta saki ledar tare da ɗaga hannu za ta wankawa Husna mari Husna ta yi saurin durƙushewa Meenal ta mari iska, shi kuma hakan ya yi daidia da hannunsa da ya miƙa ya cafe hannun Meenal. Baki sake take kallonsa tana tunanin wanna wace irin baƙar rana ce, lallai zama bai ganta ba dole ta tashi ta ƙwatarwa kanta ƴanci don ba za ta yarda ta zauna ba a haka a ce ana mulkarta ba wannan rayuwar ta tsarawa kanta ba. Yana riƙe da hannunta yake faɗin "Idan kika sake kika mare ta wallahi daga yau na soke zuwansu miki girkin safe, yaran suna yi kansu da ƙafarsu amma kina raina musu" Jin ya faɗi haka ta gane zai aikata tun da ta ga take*tkensa ita kuma ta fi so a ce yanzu aka fara wasa wato idan har suka daina zuwa aiki komai zai canja domin za su tashi daga mulkarsu da takr sannan ba za ta ci gaba da samun damarmakin da yake fatan samu ba wanda za ta ambula musu ƙasa a ido su d uwarsu. Baki ta dantse da haƙori ta ce. "Ai abin bai kai haka ba, sannan karka manta ba fa ni kaɗai suke yi wa bautar ba har da kai sannan har da kansu da kuma mahaifiyarsu, kuma ai a ganina harshe da haƙori ma ana saɓawa a ci gaba da zama" Bai tanka mata ba don ya matsu ya je ya ƙarawa wankansa Sadiya kuwa dama tuni ya kama gabanta, kallon su Hibba ya yi ya ce su yi tafiyarsu, sai dai Meenal ta ci alwashin rama abin da aka mata. Ko da suka tafi a hanya suna ta maganar abin da ya faru, suna zuwa gida suka rattabawa Hajiya abin da ya faru tsabar haushi da takaici ta yi ta tsinewa Meenal har da uwarta ma. Sai dai da ta ji cewa Husna ta wanka wa Meenal mari sai ta ji da dama dama wai kibiya a ido amma dai tabbas ta lura yarinya ƙarama tana juya su, sannan ko da su Hbbar suka ba ta labarin cewa Nasir ya shiga ɗakin Sadiya har ma yana mata faran faran sai ta nuna jin haushi har da cewa a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta!. Meenal sai da ƙawarta ta zo gidanta washe gari sanann ta ari wayarta ta saka ta kira alajin ta da ya mata alƙwarin kuɗi don haka sai ta masa ƙorafin abin da ɓarayi suka yi na ƙwace kuɗi da kuma wayarsu. Ko da ya ji hakan sai ya ce idan zai yiwu ta zo su haɗu yau a hotel ta karɓi sabuwar waya dadal a kwali. Don haka tare suka fita da ƙawarta Safiyya ganin Nasir ba ya nan ya tafi kasuwa, sai da ta gama sheƙe ayarta ta dawo gidan amma kafin ma lokacin dawowarsa ya yi ta dawo, tana dawowa ta saka sabuwar wayarta a caji da sim ɗinta wani da take da shi a ajiye kafin ta yi welcome back na wancan. Rashin ishashan kuɗi ya hana ta zuwa su koma wajen boka, ita da Momi sai dai hatta wayar ta faɗawa Nasir Momi ce ta siya mata don ba ta bari ya san ma an mata satar waya ba. Ganin yanzu adalci yana neman wanzuwa a gidan hakan ya sa ta ci alwashin tarwatsa duk wani abu da yake alaƙa da farincikin Sadiya a cikin gidan, don yanzu babu laifi suna samun kulawa ita da Kalifa saɓanin baya da ake nuna musu watiyar launin fata. Ƙaryar da Meenal ta tsiro shi ne ta ringa zazzaɓin ƙarya ta amai, ko da ya ce ta je asibiti ta ce ba ta son zuwa Safiyya ta kawo mata tsinkena gwajin ciki da ake yi da fitsari wato PT wanda wata ƙawarsu ta auna tana da ciki domin kuwa ya nuna layi biyu ɓaro -ɓato. Shi ta yaudari Nasir da shi ta faɗa masa tana da ciki, abin mamaki sai ya ɗora rai a kan cikin yake ba ta kulawa tun da yanzu yana ƙoƙarin daidaita adalci. Meenal ta ci alwashin sai ta nunawa Sadiya ita ba kowa ba ce a wajen Nasir kamar yadda take a baya. Babban abin da Meenal da Safiyya suka shirya shi ne daƙile duk wata soyayya da kulawa da Sadiyar take samu ba ta kowacce hanya ba sai ta hanya guda ɗaya wacce suke ganin idan har abin da suka shirya ya tafi daidai to tabbas Sadiya za ta tsinci talatar ta a laraba!. Yau ya kama asabar a yau ne suka gama shirin aiwatar da komai hakan ya sa Meenal sanya idanu a dukkan motsin Sadiya domin kawo ƙarshen zamanta a gidan, sannan yau ya kasance ranar girkin Sadiyar. Yau ko da ya fita da wuri ya dawo saboda sun shirya za su je duba baban wani abokinsu hakan ya sa ya yi wa Sadiya sallama ya tafi. Sadiya tana zaune a ɗakinta sai ta tashi ta shiga banɗaki ta bar Kalifa a ɗakin yana bacci. A lokacin ne kuma Nasir ya kira Meenal yana tambayerta ya jiki sannan ta faɗa masa tana son ya taho mata da jan apple. Sadiya tana fitowa daga banɗaki ta shige ɗaki ita kuma Safiyya ƙawar Meenal tana can ƙofar gidan Sadiyar ta maƙale a jikin wata katanga, sai kuma Nasir wanda yake dab da ƙarasowa gidan. Sadiya a bakin gado ta zauna, zamanta ke da wuya kenan tana ɗan hakin tafiyar da ta yi sai kawai ta ji Meenal ta ƙwala wani gigitaccen ƙara, Sadiya gabanta ne ya yanke ya faɗi domin abin da ya fara zuwa zuciyarta shi ne ko dai mciji ne ya sari Meenal ɗin ko dai wani abu mai kama da haka domin ƙara ya yi kama da na mai neman ɗauki da gaggawa. Gabanta ne ya faɗi ta taso tana ɗan tura cikinta, sai kuwa ta ji ta sake ƙaran a karo na biyu, sai kuma kiran sunan Sadiyar ya biyo bayan ƙaran da ta saki, Sadiya a kiɗime ta fito daga ɗakinta da zuciyarta ɗaya domin zuwa ta taimaka mata tun da dai ta san tun da her Meenal ta kira sunanta to tabbas tana neman taimako. Kiran sunan Sadiya take hakan ya sa Sadiyar nufar ɗakinta a kiɗime. A ƙofar gida Safiyya da take laɓe ta hango motar Nasir ta shawo kwana da sauri ta fito daga maɓoyarta ta fara tafiya tamkar yanzu ta zo layjn take tafiya, yana ƙarasowa tana ɗaga ƙafarta za ta shiga gidansa ya fito suna gaisawa a daidai nan ne suka ji wani irin ƙara da Meenal ta saki, har rige rige suke wajen shiga gidan don ganin abin da yake faruwa. A can cikin gidan kuwa bayan Sadiya ta nufi ɗakin Meenal tana zuwa sai ta ga Meenal kwance a kan kujera saman fuskarta ɗauke da filo sai jujjuya kai take tana ihu, da sauri Sadiyar ta ƙarasa wajen ta miƙa hannu za ta ɗauke filon kenan sai Meenal ta sake sakin wani ƙaran wanda ya yi daidai da shigowar Nasir da Safiyya wanda shi Nasir ko takalmi bai cire ba tsabar kiɗima da ruɗewa. Shigowarsu ya yi daidai da faɗin da Meenal take cewa "Don Allah karki kasheni Sadiya wallahi indai Nasir ne zan bar miki shi, a yau zan bar gidan nan" Wannan furucin ne ya sanya Sadiya da ta miƙa hannu biyu kan filon da yake saman fuskar Meenal za ta ɗauke mata ta dakata gananta yana faɗuwa jin furucin ta, jikin Sadiya ne ya ɗauki karkarwa ganin Nasir da Safiya suna zarw ido suna faɗin "Innalillahi wa inna ilahi raji,un" Da sauri Nasir ya ɗauke filon saman fuskar Meenal wacce ta haɗa uban gumi, har ture Sadiya ya yi lokacin da zai wuce sai a sannan Sadiya ta fahimci ta faɗa tarkon kishiya ba ta gama gane tuggu ba ne aka haɗa mata sai da Nasir ya ɗago filon ta ga ashe filon ra ne wanda yake kan gadonta nan da nan ƙwaƙwalwarta ta shiga tunanin ta yaya filonta ya zo ɗakin? Tana cikin wanann halin ta ji muryar Nasir yana faɗin "Kisan kai Sadiya?" Meenal da Safiyya juna suka rumgume suna fashewa da kukan kissa. Sadiya kai ta hau girgizawa ta rasa ma abin da za ta faɗa... *Saura page 1 mu gama Book 1 dama na faɗa muku a page ,30 za mu gama book 1 sai kuma mu shiga book 2 wanda shi ne zai kaimu har ƙarshen labarin. Ga wanda yake da buƙatar book 2 naira ,500 zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222. Sai dai akwai turka turka akwai cakwakiya, faɗi tashi sadaukarwa haɗe da ƙalubale da kuma sakamako a book 2 sai dai wanda ya karanta har ƙarshe zai gane hakan kun san dai alƙalamin maman afrah ba ya rubuta shirme. Daga ɗari biyar babu ragi domin 700 ne sai na rage muku don a samu sauƙi idan na kammala book 2 800 ne* https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1 *RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka) NA MAMAN AFRAH . *Daga marubuciyar* *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* *09025576222* BOOK 1 PAGE 3️⃣0️⃣ *End of book 1* SADIYA Gabɗaya ta ma rasa wane tunanj za ta yi kanta ya kulle sannan mamaki haɗe da al,ajabi suka mata dirar mikiya lokaci guda, idanunta taf da hawaye take kallon yadda Meenal da Safiyya suke kuka wiwi bayan kuma ta san sharri ne aka ƙulla mata, tabbas ta yarda da kishiya mai makirce sai ta ɗaura maka sharrin da za ta sa ka yi gidan kaso!. Furucin da Nasir ya yi ne ya ƙara hauhawar farashin tashin hankalin ta da ya ce "Sadiya yanzu rashin imani har ya kai ki dannawa abokiyar zamanki filo za ki kashe ta? Ki tako tun daga ɗakinki ki biyo ta har ɗakin ta ribar mai za ki samu idan kin ida nufinki a kanta? Shin ke duniyar kika ƙauro?" Bakinta ne ya shiga karkarwa ita a rayuwa ko kaza ba ta jin za ta iya kashewa bare kuma ɗan adam ta yaya Nasir zai yi wannan furuci kenan shi har ya yarda, ɗagowa ta yi ta kalle shi yana riƙe da filon ta ga yafda fuskarsa ta sauya ya haɗe rai ɓacin rai tsantsa ya bayyana a tate da shi cikin sanyin murya ta ce "Wallahi Abban Kalifa ban yi yinƙurin kisan kai ba ka yarda da ni" Ta faɗa cike da ɗari-ɗarin da ya sa ya ƙara zarginsa a kanta. Cike da ɗaga murya yakr magana tamkat zai kai mata bugu ya ce "Tun wuri Sadiya karki yi zaton zan yarda da wannan marairaicewar taki, wannan magana ba fa ƙarama ba ce babba ce magana ake ta kisan kai kuma ba faɗa mini aka yi ba da idona na ganki shin kuma wace magana za ki yi wane furuci za ki yi da zai sanya har na ƙaryata abin da idanuna suka gaskata?!. Safiyya cikin muryar kukan kissa ganin Nasir ya hau keken ɓeran da suka ɗora shi ta ce "Ni dama waya ta min ta ce min ba ta jin daɗi ashe dai rabon idanuna su yi mugun gani ne, Allah ya sa ma ka zo gidan wataƙila da babu namiji a kusa ta haɗa ni da Meenal ɗin mu baƙunci lahira" Kallon ki ji tsoron Allah Sadiya ta yi wa Safiyya kafin muryar Meenal ta karaɗe falon da faɗin "Ni dama bacci ne ya ɗauke ni sai kiran Nasir ya tashe ni bayan mun gama wayar sai na ji idanuna suna rufewa alamar baccin ne bai isheni ba kawai sai na ji kamar daga sama an rufa min wani abu a fuska ina ta ƙoƙarin janyewa abu ya gagara numfashina ma babu wajen shaƙa don an fi danna abin a saitin hancina, Allah ya kawo ku kuka ceceni ni ban taɓa zaton ma mace ce ba wallahi na ɗauka namiji ne ashe dai mace ce macen ma Sadiya, shi ya sa bahaushe ya ce makashinki yana tare da kai" Ta faɗa hawaye suna tseren fitowa daga idanunta Safiyya ma tana taya ta. Nasir kansa ne ya kulle ya fara jin wata tsanar Sadiya yana ganin zama da wanda zai iya kisan kai ba shi da wani amfani shi dama tun ba yau ba yake son yakice ta daga rayuwarsa kawai dai wannan uban nata ne yake maƙala masa ita sannan dai ya san kawai lokaci ne bai ƙare ba na zamansu tun da duk son ka da rabuwa da mutum in har zaman bai ƙare ba babu yadda za ka yi sannan idan har kana son zaman da mutum in zaman ya ƙare dole sai rabuwa ta gifta. Sadiya ta ce "Allah shi ne shaida kuma zai bayyana gaskiya" Gabaɗaya sai su Safiyya suka kalle ta tun da dai sun san babu wani da zai bada shaida a gidan tun da daga ita sai ita. Ta ci gaba da cewa "Ni ba zan iya kashe mutum ba kuma na san duk wani abu da mutum ya yi a ɓoye zai bayyana watarana, don Allah ba ya barin zalunci, sannan ni dai na san fitowa ta daga banɗaki kenan na koma ɗaki na ji Meenal tana ƙara tare da kiran sunana , hankali tashe na taho don in taimaka mata, don ni duk tsakanina da mutum in har yana neman taimako zan taimaka masa duk da ba wata jituwa ce tsakanina da ita ba. Ina zuwa na same ta kwance da filo rufe a fuskarta tana jujjuya kai, da hanzari na nufe ta zan cire mata a lokacin ne ku kuma kuka zo, wallahi ni ban lura filona ba ne ma sai da kuka shigo" ,Ta faɗa tana share hawaye, Nasir ɗiff ya yi domin ƙwaƙwalwarsa ta karɓi caji ya rasa wane tunani zai yi duk da Sadiya tana maganar ne a rikice alamar har lokacin a tsorace take amma hakan bai hana shi gano ƙamshin gaskiya ba sai dai ya san an ce mata suna da tuggu da kuma kissa wannan ya sa ya kasa gane a ciki waye mai gaskiya Meenal ko Sadiya?. Zama Meenal ta yi ta ce "Lallai ɗan adam wato yanzu ni kike son ɗorawa laifi?" Ita ma da Nasir ya tsura mata ido sai ya ga babu shakka ko alamun rashin gaskiya hakan ya sa ya gane aikin sai mai shi wato shari,a sai sai al,ƙali. Wuri ya samu ya zauna tare da dafe kansa ya rasa ta ina zai fara baka jin komai a falon sai sautin kukan Meenal da Safiyya. Sadiya ce ta ɗaga hannu sama ta ce "Ya Allah kai ne mafi ji da gani, kai ne sarkin sarakuna, iko da mulki naka ne, Allah kai kaɗai ka san mai gaskiya ya rabbi ka bayyna gaskiya ka wanke ni daga zargin da ake mini" Gaban Meenal ne ya buga da ƙarfi jin wannan addu,ar da Sadiya ta yi sai kuma ta raya a ranta cewa kawai dai Sadiyar tana faɗa ne amma dai ba ta da shaida. Muryar Nasir ce ta katse da faɗin "Wannan maganar ba ƙaramar magana ba ce tana buƙatar a saka manya a ciki" Jin wannan furucin nasa ya sa Meenal ta ji wani takaici ita ta so ya saki Sadiya a lokacin in ya so koma mai zai biyo baya ihu ne bayan hari, din haka sai ta yi tunanin wata dabarar ko hakan zai sa Sadiya ta amsa laifin hakan ya sa ta ce "Ai dama babu wanda zai yi laifi ya ce shi ne ya yi, kuma wannan magana ba zan yarda ba sai na yi ƙara, domin yunƙurin kisa ba ƙaramin abu ba ne" Ta faɗi hakan ne ko Sadiya za ta saduda ta karɓi laifin dimin idan ta amsa laifin ta san Nasir zai fusata ya saki Sadiyar in ya so sai ta ce ta fasa ƙaran. Amma sai ta ga Sadiya dai tana kan bakanta. Safiyya ta ce "Wannan laifin dama ai sai an dangana shi ga hukuma don a yi hukunci saboda ƴan baya ma su hankalta" Waya Meenal ta ɗauka ta kira Momi tana labarta mata tana kuka duk da dama ta sanar da Momin abin da za ta aikata. Ba a ɗauki lokaci ba sai ga Momi a firgice ta shigo gidan saboda ta nuna ta firgita ta lamarin takalmi ma da ta zo zauren gidan tsayawa ta yi ta cire ta saka shi hagu a dama dama a hagu tana zuwa ta rungume Meenal tana hawayen kissa ta kalli Sadiya kallo na ƙasƙanci ta cr "Ƴar tawa guda ɗaya to in har suniya kika so ta bari ba sai kin biyo ta haka ba, da kin faɗa ma cewa kina neman raba ta da ranta da tuni ta bar miki gidan, ba dai a kan namiji ne za ki yi kisan kai ba, ku mata sai shishshigi komai ku aikata a kan maza wasu mazan ma ba su damu da ku ba, to ni ina ƙaunarta iya kaɗai gareni sannan sai kin fuskanci hukunci domin ba za mu bar wannan maganar ba" Nasir sai haƙuri yake ba ta amma ko gaisuwarsa ba ta amsa ba tana ta masifa wai za a kashe mata ƴa bai ɗauki hukunci ba. Sadiya tana ta rantse rantse amma kuma sai harara take samu da tukuicin masifar Momi. An fito tsakar gidan Momi tana riƙe da hannun Meenal saboda ta ce ma ba ra jin ƙarfin jikin ta Momi ta ce "Wannn cikin da kika samu ne ake miki hassada ba a so ki haihu a gidan wato sai ita ce za take haihuwa shi ya sa ta yi tunanin raba ki da duniya" Nasir dai ɗakin Sadiya ya nufa domin ya tabbatar da cewa filon natan ne suna tsaye a tsakar gidan sai Momi ta ce gabaɗaya za a shiga ɗakin Sadiya haka suka shiga yana gaba suna biye da shi sai dai da aka zo bedroom ɗin za a duba filon a tabbatar sai ga hula a tsakar ɗakin da sauri Nasir da ya ga hular ya ce "Meenal wannan ba hular ki ba ce?" Ya tambaya domin ya gane hular tata ta net ce kuma da zai fita lokacin tana kwance hular tana kan ɗayar kujerar falon a ajiye ta ce ya miƙo mata ya karɓa ta saka a kanta wannan dalilin ya sa ya gane hular. Idanun kowa na ɗakin suka sauka a kan hular inda Meenal gabaɗaya ta rikice har ta kasa haɗa haruffan da za ta bashi amsa, amma saboda ƙarfin hali sai ta ce "Lah hula ta ce" Ta faɗa da mamakin ganin hular tana mai miƙa hannu ta taɓo kanta, tana sake cewa "Ikon Allah mai kuma ya kawo hulata ɗakin nan hular da tana kaina na yi bacci ɗazu" Momi ta yi karaf ta ce sato ta aka yi za a shirya miki wata maƙarƙashiya, wataƙila malami ne ya ce a kawo hular da take kanki zai yi wani aiki," Wani daɗi ne ya cika Meenal jin mahaifiyarta ta kawo mata haske, duk da gabanta ya faɗi da ganin hular kuma ta tsorata da lamarin, saboda ko kaɗan ba ta san hular ta faɗi daga kanta ba lokacjn da ta zo ɗaukan filon. Safiyya ta ce "Lallai maso abinka ya fika dibara, ban da ƙarfin hali ɓarawo da sallama hula a kankam a je a ɗauke kai zaman kishi sai ka shirya zama da kishiya gaskiya ba wasa ba ne" Sadiya gabanta ne ya sake faɗuwa jin za a ƙulla mata wani sharri wato ana ƙoƙarin watsa mata tsaba kaji su bita. Cike da tausasa murya ta ce "Wallahi ban san da zaman hular nan a nan ba na rantse da Allahn da ya halicceni ba ni na ɗakko ta ba" Nasir da ya gaji da abubuwan nan ga shi ya ga sirikar tasa ma kamar ƙoƙarin ƙara kunna wutar bala,in take sai ya ji duk ransa ya ɓaci hakan ya sa ya ji haushin Sadiya domin dai hakan yana tabbatar masa da cewa abubuwan da ake zargi a kanta haka suke tun da ga shi an ga hular Meenal a ɗakinta kuma tana rainawa mutane hankali a fusace ya ce "Hular ce ta zo da ƙafarta" Kallonsa ta yi idanunta taf da hawaye ta ce "Wallahi Abban Kalifa ba ji ba ce" Momi ta ce "Sadiya ya kamata ki daina yi wa mutane wasa da hankali kawai ki fito fili ki faɗi gaskiya dama an san gaskiya ciwo ne da ita, don haka kawai ki faɗa kanki tsaye ni kuma na miki alƙawarjn za a rufa miki asiri matuƙar kika amsa laifinki" Sadiya kallonta ta mayar kan Momi ta ce "Wallahi duka abubuwan da ake zargina ban aikata ba hasali ma na je ɗakin Meenal don na taimaka mata amma shi ne take mini bita da ƙulli dukan kabarin kishiya" Meenal ta ce "Allah sarki ni, wato Sadiya saboda kin ga mu biyu ne a gidan nan babu na uku wanda zai yi shaida shi ne kike faɗar son ranki" Sadiya ta ce "Ni Allah ne shaidata kuma tun da nake ban taɓa zuwa wajen boka ko malam ba, bare na faɗa masa buƙatata ni Allah na dogara, kuma shi ne shaidata cewa ban ɗauko hulamdon na yi magani ba kuma ban ɗauki filo na je don na rabata da numfashinta ba" Momi ganin ramin da ta yi wa zSadiya don ta rufta ba ta rufta ba sai ranta ya yi mugun ɓaci ta ce "Mu da wa muka ce miki muka dogara? Mu ma Allahn dai ne abin dogaranmu" Meenal ta durƙusa za ta ɗauki hularta sai Nasir ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ya ce "Meenal karki kuskura ki taɓa hular nan" Sadiya ta kalli yadda fuskarsa ta sauya lokaci guda ɓacin rai ya baibaye fuskarsa. Meenal ɗagowa ta yi da mamaki tana kallonsa kowa ma shi yake kallo hatta Momi sai da ta ji shayin yanayinsa ta ce "Kai Nasir lafiya kuwa, ya haka yarinya da hularta kuma ka hana ta ɗauka?" ,Sadiya kuwa har fuslarta ta jiƙe da hawaye ta san shikenan hukuncin kanta zai sauke tabbas ita dai tana ganin jalala a gidan aurenta sai dai ta san duk wanda ya jura wahala ko ƙalubale a rayuwa to tabbas watarana nasara za ta zo, watarana zai taka tudun tsira, saboda hausawa ma suna cewa mai haƙuri yakan dafa dutse, duk wanda ya yi haƙuri zai samu sakamako duk daren daɗewa. Nasir ya fara magama cike da ƙaraji tamkar ba da Momi yake magana ba ya ce "Momi ana batun kisan kai ne fa wannan abubuwan da muke yi gabaɗayanmu ba aikinmu ba ne" Momi a tsorace da lamarin ta c "To aikin su waye" Ya ce "Aikin hukuma ne mana, hukuma ce ya kamata ta yi bincike don tabbatar da gaskiya, wannan lamarin dole sai hukuma ta shiga" Ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya fito da waya, Momi dakyar ta haɗiye tsoron da ta dirar mata ta ce "Kai haba dai Nasir wace hukuma ana zaune lafiya, ai abu ne na gida, da Sadiya da Meenal ai duk ƴan uwana ne ba kishiyoyi ba ai an zama ɗaya, in zama ya haɗa da aure da haihuwa ai sai an ruguma haƙuri da dangana" Meenal ta karɓe da faɗin "Ai dama abin bai kai nan ba" Suka faɗa kowa yana tsoron furucin da Nasir ɗin zai yi game da maganar da suka yi, domin sun san muddin ya sako hukuma su ne a ciki, domin daga an cika bincike su za su kwana a ciki shi ya sa suke ƙoƙarin naɗe tabarɓar kunya da hauka. Sadiiya ta ce "Ni wallahi na amince a kira hukumar saboda in har za a yi bincike za a gani gaskiya" Safiyya ta ce "Ke Sadiya ya ana so a kashe wuta kina rurata, shi fa bincike ba shi da wata rana ko da a addini" Sadiya ta ce "Addini ma ba irin wannan binciken ya hana ba, amma ni dai in har za a cire zargin da ake min to na yarda a saka hukuma" Nasir ya ce "In dai hukuma ce an saka ta ma an gama don ni ba zan iya wannan abin ba, ina zamana lafiya a zo ake jaza mini gwara... Momi ta ce "Nasir ni ai tamkar mahaifiyarka nake, kuma Sadiya ai yarinya ce magana ta ya dace ka bi kawai a kashe maganar a gida ba sai an fitar ba wani ma ya ji, kawai Sadiya ta karɓi kuskurenta" Sadiya ta ce "Wallahi ni dai ba zan taɓa karɓar aikin da ba ni na aikata ba, kawai a saka hukumar don ba na so a zo a ɓata mini suna ana cewa na yi yumƙurin kashe kishiyata saboda kishi ko kuma na ɗauki hularta zan mata asiri in raba ta da miji amma in hukuma ce in har jna da gaskiya za ta wanke ni" Momi a zuciyarta ta c "Wannan ƴa ƴar bala,i ce, neman since mini zani a kasuwa take dole na samu mafita tyn kafin ranar jin kunya ta bayyana' A fili ta ce "Lallai Sadiya dama haka kike da kafiya da taurin kai? To mu ba damu ba ni ba tsohuwar banza ba ce ba zan je ina yawon bin hukuma ba duk su ƙwace mini kuɗi a karshe babu biyan buƙata" Sadiya ta ce "Ai ba kowace hukuma ba ce take karɓar kuɗi akwai wanda gaskiya kawai za su fitar" Meenal ganin Nasir yana bin Momi da kallon kamar bai yarda da ita ba da take maganar rashin kai wajen hukuma da sauri Meenal ɗin ta ce "Wai mene ne ake ta jayayya to a je wajen hukumar ma wane shegen yake tsoron ra mutu bare ta yi rai," Ta faɗa tana kallon Momi da ta mata alama da ido a kan ta ɗauke hularta ta ƙara sunkuyawa Nasir ya hana ta ɗauka a karo na biyu sai Momi ta sunkuya da kanta za ta ɗauka da sauri Nasir ya hana ta ɗauka yana faɗin "Ai babu wanda zai taɓa hular nan sai hukuma sun zo" Momi da sauri ta ce "To uban mai zai haɗa hukuma da hula?" "Nasir ya ce na gaji da wannan jayayyar da ake yi gwara a je wajen hukuma kawai ta nan ne za a tabbatar da gaskiya, kuma wannan hular babu mai taɓawa, hukuma ne kaɗai za su yi aikin su, za su tabbatar da mai laifi za a su gane idan har Sadiya ce ta kawo hular za su gane idan kuma Meenal ɗin ce ta shigo ɗakin da kanta ta jefar da hular shi ma za su gano" Gaban Meenal ne ya bada saurin rasss aka fara kallon kallo a tsakaninsu Nasir ya ci gaba da magana babu alaɓun wasa ko sasaauci ya ce "Za a ita ganowa ta hanyar fingerprint (Yatsun hannu) Idan Meenal ce ta taɓa hular za a gano idan kuma hannun Sadiya ne a jiki shi ma duk za a gano, kenan ta hanyar gano hannun jikin hular ne za a bambance tun da yanzu filon da aka yi amfani duk yataunmu suna jiki" Momi ta ce "Ikon Allah" Ya ci gaba da faɗin " Za a iya gano cewa Meenal ce ta ajiye hular a ɗakin Sadiya ta hanyoyi biyu da suka shafi DNA da binciken yatsun hannu (fingerprint) Fingerprint Analysi idan Meenal ta taɓahular da hannunta kai tsaye, za a iya samu yatsun hannunta a jikin hular masu bincike za su ɗauki hular, su fitar da fingerprints da ke jiki, su kwatanta da na Meenal. idan yatsunta sun bayyana, to shikenan hujja ce kai tsaye cewa ta taɓa ko ta bar hular a can. DNA Analysis idan akwai gashin kanta a cikin hular (ko 'yan ƙwayoyin fata), za a iya fitar da DNA Sannan a gwada da nata idan ya dace, to lallai ita ce ta bar hular wannan hanya ce mafi ƙarfi wajen tabbatar da asalin mai abu musamman idan babu fingerprints., Idan kuɓa Sadiya ce ta taɓa ma duk za a gano" Su duka sun tsorata da furucinsa sai dai Momi da ta san duniya ta lalace ana iya siyan komai da kuɗi wato tana iya sayen gaskiya da kuɗi ma amma kuma furucin da ya yi yanzu ya tarwatsa ƴaƴan hanjin su dukansu. Yana tabbatarwa da faɗin "Ba zan ba kaina wahala a kan wannan ba sai da sharaɗi wallahi wallahi kowacece aka gano ita ce da laifi sai na yanke duka igiyoyon aurena a kanta, ina nufin idan har aka yi bincike duk wacce ita ce da laifin sai na sawwaqe mata aurena, zan raba alaƙar aurena da ita saki ɗai-ɗai ha uku!" Gaban Sadiya ya fi na kowa bugawa duk ta san tana da gaskiya, amma yanzu gaskiya ta yi ƙaranci a duniyar nan ,don tana tunanin idan har aka tauye mata haƙƙi tabbas ita ce za ta samu takardar sakin ina za ta je da wannan tsohon cikin bare ta san halin Baba. BABA Tun yana jiran taimakon mutanen unguwa har ya cire rai kasancewar babu wamda ya ɗakko ko naira biyar bare a ɗakko ko da ƙwayar hatsi ko shinkafa a bashi haka ya sha baƙaƙen maganganun a kan cewa duniya ta lalace yanzu mutane ba sa taimakawa, bai san cewa kowa ya san abubuwan da yake yi wa iyalinsa ba na tauyewa domin yanzu an daina kiwon dabba an koma kiwon mutum. Haka ya ci gaba da fafutukarsa ta zuwa kasuwa dama kuma yana da kuɗi kawai dai rashin wadatar zuci ne sai dai kuma tun da wannn gobara ta faru sai lamuram gidan suka sake caɓewa ba ya bada ko kwabo iyakarsa idan an tambaye shi abinci sai ya cw shi da tsautsayin gobara ya faɗawa ina ya ganshi, sai dai su bari har wata damuna ta zo idan ya yi shuka ya samu sannan zai ci gaba da basu abinci ko da kuwa iya na dare ne. Yanzu kowa ya zage dantse yana nema da masu sana,a da kuma masu bada kansu a basu kuɗi shi dai burinsa ya aurar da su ya huta, duk da yanzu ya mayar da hankali ne ga nasa sabin auren da yake son ya yi, don ya ɗora rai a kan sai ya auri namiji. Babu wanda ya san Baba yana neman aure wata yarinya ce ya samu budurwa mai rawar kai kuma idanunta a buɗe suke tas. Tun da ya ƙyalla idanu ya ga yarinyar ya ɗora rai a kanta ba komai ya fi tafiya da shi ba irin farar fatarta da ta sha mayukan bilicin sannan uwa uba kaf gidansu maza ne ita kaɗai ce mace, wannan ya sa yake ganin zai samu irin haihiwa tun da an ce ana gadon haihuwa, sannan ko mahaifiyar yarinyar ma su biyu ne mata a gidansu ƴan uwan mahaifiyar tata maza har goma, sannan ita ƴar uwar mahaifiyar tata ma kaf ƴaƴanta maza ne ba ta taɓa haihuwar mace ba wannan ya sa Baba ganin kakarsa ta yanke saƙa. Duk wani burin Baba yana kan Badariyya wacce ta gama gano lagon Baba na son haihuwar namiji sannan ta gane tsantsar jahilcinsa da rashin godiyar Allah na ƴaƴa matan da ya bashi. Gabaɗaya sai take masa wayo da kuma kawo masa buƙatu shikenan duk da son kuɗin Baba amma haka yake kashe mata kuɗi musamman da yake ganin samari suna zuwa wajenta don ya ɗauke mata hankali daga kansu. Bai san cewa su samarin nata ƴan rage dare ba ne babu wani na aure sai an ce su fito sai a neme su a rasa yanzu shi kaɗai ne wanda take jalabtawa don shi ne na auren. Hatta wayar hannunta Baba ne ya saya shi ya gwammace ko nawa ne ya kashe tun da dai zai samu cikar burinsa na haihuwar ɗa namiji tun da yana ganin zai auri tsatson haihuwar maza. Jarabawarsa a kan Badariyya shi ne soyayya gabaɗya sai ya ji yana ƙaunarta kamar ma a kanta ne ya ƙara tabbatar da mene ne so duk da kasancearta yarinya. Sai ya zamana tana juya shi kamar waina a tanda saboda soyayyar da yake mata hidima tamkar dai ba Malam Bala mai mammaƙo da son abin duniya ba. Babi wanda ya san wainar da Baba yake toyawa sai da ya zamana biki saura sati biyu sannan ya tara matan nasa ya sanar da su babu wacce ta yi wani baƙinciki kowa ta ce masa Allah kawo amarya lafiya, domin dama tun da suka ga ana gini sun san a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Ƴaƴan gidan kuwa ya tara su yana gindaya musu sharuɗɗa kasancewar Badariyya ta gama faɗa masa abubuwan da take so da wanda ba ta so, haka yake ta kumfar baki ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ranar ɗaurin aure ya sha farar shaddarsa sai sheƙi take tana baza ƙamshin turarensa, Allah ne kaɗai ya san iya farincikin da yake ciki domin yana ganin kukansa ya ƙare nan da watanni tara cif yana da ɗa namiji mallakinsa. Sadiya ko da ta ji labarin auren Baban haushi da takaici ya baibaye ra son ta san saboda haihuwar namiji ya yi auren,, ita dai da farko ma ta ji haushin sakon Mama Habiba da ya yi amma yanzu daɗi take ji don ta san Mama Habiba albarkacin haƙurin da ta yi a gidansu to tabbas Allah zai musanya mata da mafi alkairi tun da ba wani wuce aure da haihuwa ta yi ba. Ɗakin amarya ya sha jere da dare aka kawo amarya, ko da ƴan kawo amarya suka watse Baba ya je ya bankawa gidan sakata, ya shiga ɗakin amarya ya banke ƙofa ya shiga bedroom yana washe haƙora, amarya tana ɗan jin kunya haka ya ce su yi alwala su yi sallah, bayan sun yi sallar nafila Baba ya hau cire Babbar riga ya rataye, ya kalli amarya ya ce "To amarya Bismillah" Ta masa kallon sheƙeƙe har sai da ya sha ruwan jikinsa ta ce "Ban gane Bismillah ba, banga kayan maƙulashe ba" Ya ɗan yi jim yana kallonta ya ce "Wane kaya kenan?" Ta ce "Ina kazar amarci sa sauran kayan sanyi?" Ya dafe kai ya ce "Kash!. Ai kwata kwata na sha,afa wallahi garin saurin in zo wajenki na manta ana kawowa amarya wani kayan maƙulashe kuma laifin su malam Lurwanu ne da ba su tuna min ba" Tsaye ta miƙe tana cewa "Ni Badariyya aka manta kazar amarcina sai ka ce wata amaryar kyankyaso" Baba ya ce "Haba an Badry nah ai kaji a gidan nan sai kin ture, ki yi haƙuri mantuwa ce kuma kowa ma yana yin mantuwa yanzu dai ki mini afuwa zuwa safiya sai in rama miki" Wani kallo ta masa ta ce "Bari ka ji Bala" Da sauri ya kalle ta ganin yau babu ɗan sunan soyayyar ma ta faɗi sunansa gatse-gatse cike sa rashin ta ido yarinyar da ya haife ta ta ci gaba da faɗin "Ni Badariyya ƴar Mama ban san babu ba koɓai da nake so ake min ko ka manta ƙanwar maza ce ni, kowa ji yake da ni saboda ni kaɗai cw macw in za ka buɗe bakin aljihu ka buɗe" Wani yawu ya haɗiye yana fatan dai kar wannan yarinya da niyyar talauta shi ta zo ga shi kuma sonta yana ɗawainiya da shi. Haka ya lallaɓa ta ya saka babbar rigar ya fita ya buɗe gidan ya fice duk mutanen gidan suna jin fitarsa. Haka ya je wajwn mai kaji aka faɗa masa kuɗaɗensu, kamar ya yi kuka haka ya duba wata ta dubu biyar kamar tattabara saboda ƴar ƙarama ce, haka aka sako masa a leda ya ratsa ta siyo mata lemon roba guda ɗaya ya tafi. Sai da suka zauna tana ƴar dariya ganin an kawo mata kaza ƙawayenta in sun zo gobe ai babu raini ana fito da kaza sai ta ga lemo ɗaya tana mamaki ta ce "Babban yaro ya na ga haka kuma lemo ɗaya kamar ka roƙo ko dai alakoro aka saka maka?" Ya kalle ta yana washe baki don Allah kaɗai ya san daɗin da yake ji in ta ce masa Babban yaron nan sai ya ji ya koma yaro ɗanye sharaf yake jin kansa ɗaya da samari. Yana kallon ta ya ce "Ai da yake ni ba sha zan yi ba cikin ki dai ke kaɗai ya ishe ki" Ta ce "A,a wannan ai sai a ce mini marowaciya baka san ƙawaye suna zuwa su ga ƙwaƙwaf washe garin kawo amarya ba, so kake ake cewa da saurayi na aura da sai na ture lemuka kuɓa bayan na san an ce ku manyan kun fi ba macw kulawa da nuna soyayya da bautata mata" Murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce "In dai lemo ne da safe zan siyo miki kafin su zo" Amincewa ta yi sai da ya buɗe ledar kaza ta ga ƙaramar kaza wani salati da ta kwasa sai da ya ji tamkar mutuwa aka sanar mata, yana kallonta ya ce "Lafiya?" Ta ce "Wannan ƴar tsakuwar kazar fa? Haba Babban yaro kamar wanda dai baka sona ka da za ka samo ƙosasshiya" Ta karɓa tana murɗe cinyar kazar duka biyu ta cire su tana ɗagawa tana nuna masa, ta ce wallaho sai ya canjo kazar in ba haka ba ita a gado za ta kwana shi a ta saka masa katifa a ƙasa tun da bai kawo kazar amarci ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga lallaɓa ta don ba zai yarsa ranar yau ta wuce bai yi sunna ba saboda yau ma tana cikin lissafinsa don ya fara sakawa a ransa ma a yau za a aamu ƙaruwa. Haka ya buɗe ƙofa ya fito da ledar kazar yana jin takaici ya rasa ma mai ya sa ita ko ɗan kawaicin nan ma na amare ba ta da shi, haka ya fito yana jin haushi, lokacin Mama Bilki ta fito daga banɗaki riƙe da buta ta ce "Malam, Malam, Malam" Sainda ta kira shi sau uku sannan ya juyo, yana amsawa kamar an masa dole ta ce "Lafiya kake ta zaryar fita daga gida ko siyan bakin ne bai kammalu ba" Ya kalle ta yana jin kamar ya wanka mata mari ya huce takaicin amaryar a kanta ya ce "A,a siyan ƙafa ne bai ƙare ba, ba na baki ba, na ce siyan kai da ƙafa ake" Ta yanayin furucinsa ta gane a ƙufule yake ta ce "Ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Wani tsaki ya ja yana juyawa ta sake cewa ."Ango ka taho min da maganin gudawa ka ganni tun daɗewa nake zarya banɗaki kamar angon da amarya take aike" Banza ya mata ya juya ya tafi tana jin lokacin da ya banko ƙofar gidan ta sheƙe da dariya a zuciyarta tana faɗin 'Kaɗan ma ka gani" Don ta fahimci akwai wani abun da yake faruwa duk da ba ta san mene ne ba, amma in tusa tana hura wuta za a gani. Haka ya sake daɓawa a ƙafa domin dama a ƙafa ya je ɗazu saboda mammaƙon kuɗinsa ba zai hau mashin ba, ga shi kuma da ɗan tazara, ko da ya je mai kaza ya ce wallahi ba zai karɓi kazar da aka jawalwala ba tun da ya ga gabaɗaya ma cinyoyinta da ban suke ba sa jikinta. Kamar zai yi kuka haka ya cire naira dubu sha ɗaya ya siya kazar aka haɗa masa da waccan ya kamo hanya har ƙwallar takaici ya share. Haka amarya ta zage ta ci kaza don ƙaramar nan sai da ta cinye tas, iyaka ta ciro ƴar ƙaramar tsoka ta saka masa a baki ya lamushe saboda ta hana shi ya saka hannunsa wai ba girmansa ba ne tana waje yake ciyar da kansa. Ita kuma sai ta yago ƙatuwar tsoka ta cika bakinta ta kalle shi ta ce "An ce amarya in ba ta ci kaza ba ma dole a sha manta" Bai tanka mata ba illa dariyar yaƙe da yake. Haka ta ɗaure sairan wai ta ƙwayaenta ce idan sun zo gobe sai su haɗa da lemukan da zai kawo. Haka Baba ya sha amarcinsa, yana fatan an samu ƙaruwa a ranar. Tun daga ranar yake lallaɓa amarya. Hankalinsa kwacakwam ya koma kan amarya dama shi bai damu da zuwa wajen mahaifiyarsa ba sai ya daɗe bai je ya ganta ba bai san cewa gabaɗaya albarkar rayuwarsa tana dangane da farincikin da ya saka mahaifiyarsa ba Ranar da amarya ta cika kwana goma sha biyar a ranar ne bayan ta gama cin abinci ta fito tsakar gidan tana kelaya amai, lokacjn Baba shigowarsa kenam ya hange ta, da gudu ya yi wajenta yana zuwa ya faɗi ƙasa daga can gefenta ya yi sujada yana yi wa Allah godiya.Sai da ta gama ya bata ruwa ta wanke baki ya ce "Sannu uwar maza, Allah raba lafiya kin gama min komai da za ki haifa min namiji" Langwaɓewa ta yi sai shi ya kama ta yana jera mata sannu. Washe gari da zai dawo daga kasuwa sai ga shi ya siyo rigunan jarirai maza guda biyar wai taro za a fara. Amarya sai tsiyarta take tsulawa a gidan don dama tun da ta zo ba ta yi girki ba sai dai ta zaɓi abin da take so ya siyo mata. Ranar da ta cika kwana uku da yin aman tana kwance a saman doguwar kujera tana danna waya ya shigo ya ce "Badary nah, tashi mu je za ki rakani" Haka ta yafo mayafi suka fito tare ya kulle ƙofar ɗakin nata yana faɗin da a ce yana da iko da ya hana ta ko da tafiya ce ahi zai ke yi mata tafiyar. Napep ɗin da ya kira suka tarar yana jiransu suka shiga baya ya ja suka fara tafiya kanta ta kwantar a kafaɗarsa ta ce "Wajen shaƙatawa za ka kaini Babban yaro?" Mai napep da sauri ya juyo jin furucinta ya kallesu shi ya ɗauka ƴarsa ce sai ya ji banbarakwai wai namiji da suna hajara ana kiransa da babban yaro. Baba ya kalli mai adaidaita sahu ya ce "Sanan,a ka fito ko kallon matan mutane?" Bai tankawa Baban ba ya ƙyale sai Baban ya ce "Haba Badary nah ina na samu sukunin zuwa wajen shaƙadawa ni fa hankalina yana kan ki nan da abin da za ki haifa ai daga yanzu har zuwa lokacin haihiwarki ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo" A ƙofar wajen scanning aka ajiye su, Baban ya ce "Mu shiga" Ta kalle shi za ta yi magana ya ja hannunta suka shiga sai da layi ya zo kansu Baban ya ce scanning za a mata a gano masa mai za ta haifa, ko da aka tambaya cikin watansa nawa sai Baba ya ce ai ba a yi sati uku ma da auren ba. Nana aka sanar da shi ba yanzu za a gane cewa ga abin da yake cikin ba saboda abin da yake cikin bai gama zama halitta ba har yanzu yana gidan jini. Ko da aka faɗi haka Baba ya ce su tafi suna hanya yana ta mita yana faɗin ai dama ya san mai za a haifa namiji sai dai yana son a gani biyu ne ko ɗaya ne. Amarya ta tsiro da rashin mutuncin cewa sai Baba ya aurar da duka ƴaƴansa tun da dai duka mata ne wai kakarta ta taɓa cewa idan mace mai ciki tana kallon abu to abun yana washe ta, wato tun da su mata ne za su washe ta ta haifi ƴa mace. Tun da Baba ya ji wannan batu hankalinsa ya tashi saboda shi kansa ya san ana cewa mace mai ciki ana wasar ta, amma dai bai san cewa gaske ba me ko kuma camfi ne, don haka maganin kar a yi kar a fara. Haka ya tara gabaɗaya ƴaƴan masa ya ce su fito da miji ya basu sati guda. Kowacce jikinta ya yi sanyi dimin sun san ba su da wani tsayayye babu wani wanda za ka fitar ya aure ka tun da dama ba don aure suke son su ba kawai ana sheƙe aya ne. Ko da sati ya cika babu wacce ta fito da miji kowacce sai ta ce saurayin bai shirya ba ita kuma amarya abu ya ci tura don har ƙin fitowa tsakar gidan take, kuma ba komai ya sa ta musu haka ba sai Arfat da ta ga tana mata wani kallon raini gabaɗaya ma ƴanmatan gidan suna mata gani-gani. Shi ya sa take so ta nuna musu ta isa da ubansu. Yau ta kama alhamis Baba ya shigo da dare ya tattara su cike da masifa ya ce "Na gaji da zamanku a gidan nan na ce ku fitar da miji kun ƙi kun zauna za ku washi Badary ta haifi mace, kun fi so na ƙare a wahale babu mai taimaka mini amma in ta haifa mini namiji ai shikenan na huta, tun ina siyan maganin farin jinin har na gaji saboda kamar ma baƙin jini nake ƙara muku, ku ba muni ba amma a ce gabaɗayanku babi wacce take da mijin aure yau na yanke hukunci kowacce ni zan zaɓa mata miji ba za ku rufa sati a gidan nan ba sai dai a gidan mazajenku" Yana gama faɗar hakan fuuu ya yi hanyar waje. Washe gari da asuba aka ji sanarwa a masallaci cewa Malam Bala ya ce tun daga kan liman har ladan da sauran dattijan unguwa mai son ƴaƴansa da aure zai aura masa!. Matan gidan sun yi takaicin wannan hukunci da Baba ya yanke sai ka ce mai neman kai da ƴaƴan. Babu wanda ya tanka masa don sun san babu wanda zai zo ya ce zai aure su. Amarya sai dariyar ƙeta take tana yada magana a tsakar gida wai gwara dai kowacce ta san na yi kar a saka ta haifi mace. Da yamma sai ga shi ya zo ya tara su ya ce "Kowacce ta samu wanda zai aure ta wallahi har raina ya yi fari sai na ji gabaɗaya zuciyata kamar an sauke mini dutse zan aurar da ku in huta da wahala" Ya faɗa tare da fara lissafo sunayen mutanen da suka sani a unguwar wanda manya ne ciki kuwa har d liman ko da ya zo kan Arfat ya ce "Arfat ke Ayodele nw ya ce zai aure ki" Cike da mamaki kowa na gidan ya fito wanda suke ɗaki su kuma ƴanmatan sai suka fara kallon kallo, amarya kuma tana ƙofar ɗakinta ta kama tsantsa tana sakin murmushin ƙeta. Arfat idanunta taf da hawaye ta ce "Baba Ayodele fa ka ce wane Ayodelen?" Cike sa masifa ya ce "Ayodele nawa kika sani a unguwar nan? To Ayodele shugaban coci" Mama Sa,ade ta ce "Wallahi babu wanda ya isa ya aurawa ƴata arne" Baba cike da nuna isa ya ce "Duk duniya babu wanda ya isa ya hanani aura masa tun da ƴata ce tun da ai ba a ce in ta aure shi ta koma kafirci ba kuma shi ma ya ce babu ruwansa da addininta kowa ya yi addininsa kin ga kuwa babu gudu babu ja da baya, tun da kaf unguwar nan babu wanda ya zaɓe ta sai shi kuma ba zan aurar da sauran ƴan uwanta ba ita ta zauna mini a gida domin haka babu gudu babu ja da baya!" MAMY Rai a matuƙar ɓace ta ce "Dakata Zalika!. Kar ki raina min hankali mana, kenhar kin isa ki yinwasa da hankalina Zalika? Ita ƙawar taki ta rasa inda za ta yi ajiya sai a jakar ki, ta rasa mai za ta ajiye a jakar ki sai ƙwayoyin hana ɗaukan ciki?" Zalika ganin Mamy ta rikice mata tana son janyo mata ruwa sai ta marairaice ta ce "Wallahi Mamy ki yarda da ni ba ƙarya na miki ba, ko kaɗan ba da wata manufa ta ajiye ba, yanzu Mamy ni kika zargi da shan wannan maganin ko kuwa?" Mamy a harzuƙe ta ce "Dole ne na zarge ki Zakika saboda kin yi abin da za a zarge kin, shin idan babu rami mai ya kawo rami? Tun yaushe kika sauya Zalika mai zai sa na ƙi zarginki ai wannan ba ma zargi ba ne na tabbatar" Kuka Zalika ta fashe da shi ta ce "Mamy ko da wani zai zargeni na ɗauka ke ce za ki shaideni, kuma wannan abu ne da baki da tabbaci a kansa, kuma ko a musulunce zargin zina fa lamari ne baba kuma mai girma da yake buƙatar tabbatarwa, saboda ita zina ko za a zargi mutum sai an tabbatar sai an ga mutum turmi da taɓarya sannan sai an tara shaidu mutum ɗaya ba ya wadatar da ganin mazinaci... Hannu Mamy ta ɗaga mata alamar dakatarwa, domin a furucin Zalika duk inda ta ambaci kalmar zina ran Mamy zafi yake sannan sai gabanta ya faɗi, ita a rayuwa babu kalmar da take jin nauyin furtawa a harshenta sama da kalmar zina, ta tsani kunnuwanta su saurari kalmar saboda nauyinta da kuma ƙazantarta don zina abun ƙyama ce, mai yinta abun ƙyama ne kuma abin a nisanci mu,amala da shi ne saboda zina Allah cewa ya yi ko kusantarta kar a yi bare a aikata ta. Mamy ta ce. "Zalika ni na haifeki ina so ki sani duk wani lafazi naki a tafin hannuna yake, na fi ƙarfin ki rufe ni da murfin ƙarya da yaudara, ina so ki faɗa mini tsawin wane lokaci kika ɗauka kina wannan mummunar ɗabi,ar?" Zalika ta ɗaga idanu ta kalli Mamy ido cikin ido ta ce "Mamy ki yarda da ni ban taɓa aikatawa ba idan kuma har kina kokwanton maganar ni zan kira wacce ta saka maganin ta zo har gida ta miki bayani" Ta faɗa tana kuka wiwi Nannauyar ajiyar zuciya Mamy ta sauke tana jin wani zafi a zuciyarta ta ce "Ba na buƙatarta duk bakinku ɗaya, kafin ta zo kun gama tsara yadda za ku faɗa mini ƙaryar da kuka shirya, za ki faɗa mini gaskiyar yaushe ne kika kai matsayin da har kika fara amdaninda ƙwayar hana ɗaukan ciki, ɗabi,ar da take lalata tarbiya ɗabi,ar da take lalata suna kina mace amma za ki lalata rayuwarki ki cuci kanki ki cucemu sannan ki bar wa ƴaƴanki baƙin fentin da har jikokinki sai abin ya shafa" Baki Zalika ta buɗe za ta ci gaba da faɗin maganar da take alamta musu da zargin Mamy hakan ya sa zuciya ta ɗauki Mamy ta wanke fuskarta da ƙwararan maruka har biyu. Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Mamy da Zalika, Mamy tana hakin baƙinciki kamar wacce ta yi tseren gudu yayin da Zalika take dafe da kumatun ta. Mamy ta ci gaba da faɗin "Abin da kika yi irin na iyaye masu sakaci da tarbiyar ƴaƴansu ne duk da a lokuta da dama idan ƙaddara ta zo gifta maka babu yadda ka iya wajen kauce mata, amma na yi iya ƙoƙarina don baki tarbiya sannan ina komai naki kafin komai ya sauya" Zalika ta ci gaba da kuka wiwi tana son yin wasa da hankalin Mamy, kallon ta Mamy ta yi tana rayawa a ranta cewa sai ta nunawa Zalika akwai bambanci tsakanin tunanin yaro da na babba. Taku ɗaya biyu Mamy ta yi hannuqanra biyu suna goye a bayanta ta tsaya tarw da ɗaga kanta sama tana kallon silin hawaye suka wanke fuskarta masu matuƙar zafi, a hankali ta sauke kanta daga kallon saman silin ɗin ta juyo tana kallon Zalika da ita ma tuni nata idanun sun rine da saboda kukan da take yi don wasa da hankalin Mamy. Ƙure ta da ido Mamy ta yi kamar mai tuna wani abu sai kuma ta fara magana cike da kaushin murya ta ce "Zalika tun da har kin ƙi faɗa mini gaskiya kina wasa da hankalina zan yi abin da zai cire zargi da kokwanto a tsakanina da ke game da wannan maganar " Zalika ta ci gaba da yi wa Mamy kallon tsoro don ba ta san abin da za ta faɗa ba. Mamy ta ce "Zan duba ki Zalika, idan har kin taɓa sanin ɗa namiji ma daga na duba zan gane domin akwai bambanci da tazara mai tarin yawa tsakanin macen da ta taɓa sanin namiji da kuma wacce budurwa ce dal a led" Zalika ta yi matuƙar razana da kalaman Mamy domin ta san an zo wajen da wayo da dabarar ta ba za su yi amfanin komai ba, matuƙar Mamy ta duba matantakar ta za ta san ta mu,amalanci namiji sai dai ta fara tunanin wace hanya za ta bi domin kaucewa wannan ƙudurin na Mamy shin Mamyn za ta yarda da wani wasa da hankalin kuwa anya?. JIDDA Zaman lafiya mai wanzar da nutsuwa suke yi tsakaninsu kasancewar ba ta mugun nufi ga kowa a rayuwa ahi ya sa ba ta taɓa kawowa cewa wani ɗan adam zai nufi rayuwarta da sharri, ɗan adam ɗinma wanda suka kasance na kisa da zuciyarta wato Aliya da kuma wacce take ganin ita ce ta maye mata gurbin uwa wanda ta rasa!. Sai dai kash rashin sani ya fi dare dunu domin zaton da take ba haka ba ne, saboda ta bar kashi ranar kwasa!. Tun ran gini rana zane duk abin da bawa ya ƙaddara masa to sai ya faru da shi daɗi ko akasin haka, kyakkawa ko mummuna, wannan kaɗai ta saka a ranta take rayuwa hankali kwance ba tare da ta yi tunanin ta bar wani giɓi ba wanda ya kamata ta cike shi. Soyayya da ƙauna haɗe da kukawa da ba su da iyaka ko kuma hanyar misaltawa su ne abubuwan da ta yi amanna tana samun su daga Ibrahim sai dai ita ma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba tana ba shi kulawa daidai gwargwado domin matsayjnta na matarsa iya ma abubuwa da dama da ya shafe sa aun rataya a wiyanta. Daga Umma har Aliya babu wansa ya saduda ko kuma yin da na sani ko kuma zuciyarsu ta rusuna game da mugun ƙudurinsu a kan Jidda wacce ba ta taka ko ta zubar musu ba. Suna nan suna ta shiri a kan yadda za su samu kuɗin da za su tafi ga mataki na gaba domin sun ci alwashin sai sun cika mugun burinsu banu gudu babu ja da baya. Sun yi ta buga buga inda za su samu kuɗi abin ya fassakara hakan ya sa suka yi dogon nazarin ganin inda ya dace au sosa, saboda Umma ta ce kar su tamabayi Jidda ba lallai ne ta basu kuɗi ba yun da ita tana ganin ba za ta iya ɗakko musu daloli a kuɗin mijin nata ba. Umma ce zaune tare da Aliya su biyu a gidan sun haɗa kai suna shirya yadda za su samu kuɗi Umma ta ce "Aliya sai kin yj taka tsantsan wajen yin abin da ya dace, kin dii ga yatinyar nan mai mugun hali matsawar za mu jira sai mun samu daga wajenta to tabbas za mu ci gaba da dawwama a talauci tun da ita sahegen sanabe ya sa ta je tana riƙon amana ni ban ga amfanin ta ba" Aliya cike da sheƙiyanci ta ce "To Umma ko a danganta ta da barzahu?" Ta faɗa.cike da ingilanci Umma tana zare ido ta aika mata saƙon harara ta ce "Baki da hankali Aloya, ai maƙiyi ka bar shi yake ganin ci gabanka, sai baƙinciki ya so halaka shi, bare mu ai tuggunmu na gaba a kan Jidda shi ne wulaƙanci daman ɗan hakin da ka raina.. " Alia ta ce "Watarana shi zai tsokane maka idanu" Jinjina mata Umma ta yi suka ci gaba da tsara komai Aliya ta ce "Umma ko dai set guda za a sato?" Umma ta yi saurin dafe ƙirji tana dogon wiya alamar babu wanda yake jinsu ta sassauta murya ta ce "Haba Aliya ke baki iya sirri ba yanzu idan akwai wani a laɓe ai shikenan ya gama jinmu, sai asirinmu ya tonu, sannan kuma idan kika je kika kwaso set ai ganewa za a yi kawai dai ki samu ko ɗan zobe ne ki ɗakko na san za mu samu biyan buƙata a iya zoben ma" Murmushi Alia ta yi ta ce "Shi ya sa nake son ki Umma ke mikiya ce mai hangen nesa" Sun gama tsara komai bayan kwana biyun Aliya tana zaune a falonta tana kallon daɗin kowa an yanka ta tashi sai kiran Jidda ya shigo amma har ya katse ba ta ɗauka ba sai saƙon harara da ta kake aikawa lamba da sunan Jidda da ya fito a jiki tamkat dai Jiddar ce sai da kiran ya ɗauke sannan ta saki wani gajeran tsaki. Sai da Jidda ta yi sau uku na ukun yana dab da yankewa sannan ta ɗauka cike da fara,a ta amsawa Jidda nan Aliya ta ce mata tana kicin tana aiki yanzu ta shigi falon ta tarar da wayar tana yi. Sun ɗan gaisa sai Jidda take faɗa mata gobe za ta zo gurinta ta wuni gaban Aliya ne ya buga ta fara tunanin ko dai Jidda ta gano gaskiya cewa gobe za ta je gidan ta zuwa na baza ta don aiwatar da aiki amma yanzu tana shirin fitowa. Har sai da Jidda ta ƙara magana a kan ta yu shiru Aliya ta marairaice murya ta ce "Allah sarki ƴar uwata rabin jiki wato na yarda da aka ce jinin ƴan uwa a haɗe yake tun da ga shi nima una shirin zuwa gobe domin har na tambayi mai gidan ya ce ya barni" Shiru Jidda ta yi ta ce "To sai kin zo ƴar uwa ni dama cewa na yi bari na sanar dake amma tun da har kina da shirin zuwa to na yi maraba da hakan" Sun jima suna magana kafin daga bisami suka yi sallama kowa ya kama sha,anin gabansa. Washe gari Aliya ta wanki ƙafa da yamma ne ma sai gidan Jidda ko da ta zo ta shiga gidan sai ta tarar babu Jidda a dalon ƙasan sai take tambaya nan Saude ta ce.mata ai tana wajen wasan motsa jiki, Saude ta saka ta nuna mata hanyar da za ta bi don ta sada ta da wajen saboda tana kiran wayar Jidda ba a ɗauka kuɓa ta ganta a kan kujara. Tana tahowa tun daba ɗan nesa ta fara hangen ya filin wasan da yake a zagaye, sanye suke da kayan ƴan ball riga mai dogon hannu wandon ma dogo kanta da hula saɓanin shi da ba shi da hula yellow ne kayan sai ratsin fari a jiki kala iri ɗaya Jidda ce da Ibrahim yana riƙe da ball ɗin ya ɗaga ta sama ita kuma tana ta ƙoƙarin sai ta karɓa idan ya riƙe a hannun dama tana zuwa wajen hannun dama sai ya ga ta raja,a da hannun damar ta kusa kamowa sai ya yi saurin mayarwa hannu dama suna ta yin abin cikin nishaɗi. Sosai ran Aliya ya hau ɓaci domin da ta ga inda ake soyayya ruwa ruwa mai cike da tsantsar kulawa, amma ita ta kasa nutsuwa ma bare ta zauna a nata gidan kullum cikinnya za ta rusa rayuwar wasu ta gina tata. Ta jima tana kallonsu ganin Ibrahim ya ɗago zai kalli inda take da sauri ta laɓe ta ci gaba da leƙo su. Sai da aka jima sai ga su sun taho hannunsu cikin na juna, sai dai wannan lokacin Jidda ta ɗorw hijabi a kan kayan. Kasancewar ba ta son fitar da jiki kuma gidan yana da ma,aikata maza duk da inda suke idan har suna can babu ma mai yin hanyar wajen sannan ta inda suke bi ma ta can cikin gidan ne. Ta gaban Aliya da take laɓe a korido suka wuce wani irin ni,imtaccen ƙamshi ya bugi hancin ta, suna wucewa ta doka uban tsaki dama su ba su ma lira da ita ba. Jim kaɗan ta biyo bayansu lokacin da ta zo falon sun haye sama Jiddar ta haɗa masa ruwan wanka sai ta sakko za ta je ɗakinta a nan ne ta samu Aliya. Da sauri ta rungume Aliya tana mata oyoyi iya ma Aliyar tana mayar mata da mrtanin dariyat da iyakarsa fatar baki. Bayan sun gaisa ta ce za ta je ta watsa ruwa kasancewar wasan motsa jikin fa suka yi, nan take taɓbayar Aliyar ma ya aka yi ba ta mata waya ba da ta zo sai ta ce ai ta kora wayar ba a ɗauka ba sai dai ba ta faɗa mata cewa ta je ta gansu suna cikin wasa suna nishaɗi ba. Ɗakin da ta shiga yin wankan ba a can ne Aliya za ta yi nata aikin ba, don haka jim kaɗan ta tashi ta ajiye jakarta tana fatan wanna Sauden mai shegen rawar kai kar ta dawo ɓangaren har ta gama abin da za ta yi. Ko da ta je ta buɗe ƙofar ɗakin cikin sanɗa ta tabbatar Jiddar tana wankan domin ta ji ƙaran ruwa da sauri ta rufo mata ƙofar ta fito tana waige-waige irin na marar gaskiya. Ta buɗe ɗakin ɗaya ta shige ta rufo ganamta yana faɗuwa tana fatan dacewa da abin da ta je nema. Aliya zuciyarta ba ta huta ba tana ta kai kawo wajen buga mata gabanta yana faɗuwa, zuciyarta cike da ƙiyayya da hassadata buɗe drower ta shiga dubawa amma ba ta gani ba. A zuciyarta ta ce 'Wannan karon Jidda har dukiyarki sai ƙiyayyata ta taɓa ta wato ke mai son rai ba za ki iya ba mahaifiyata kuɗi ba saboda ba uwar da ta haifeki ba ce, to ai in laila ta ƙiya sai a koma caca' Ɗayar drower ta buɗe nan ma babu sai da ta buɗe ƙaramar lokar ƙasan drower ta can ƙasa sannan ta ga abin da take neman domin Jidda ranar nan suna hira a kan tanadi Aliya tana cewa ita ba ta da tanadi Jiddar ta fi ta, sai Jiddar take cewa ni kam ina da tanadi yanzu duk abu mai muhimmanci wajen da nake ajiyarsa da ban, komai wajensa nake ware masa ke hatta ɗankunnenayena ma,ajinsu daban. Wannan ya sa Aliya yjn dogon nazari tana buɗe lokar sai ga wani ƙaramin akwati mai kyau yana sheƙi da sauri ta buɗe sai ga sarƙoƙin Jidda. Shagala ta yi da kallonsu tana tunanin ba don Umma ta ce kar a ɗauki set ba da babu abin da zai sanya ta ɗauki zobe kaɗai. Sai da ta duba wani mai ɗan girma yana ɗauki da harafin J a jiki wayo farkon sunan Jidda ta ɗauka da sauti ta mayar da ɗan kir ɗin ta rufe lokar ta ɓoye zoben, da sauri ta shiga banɗaki ta ɗan taɓa tuwa alamar ta shiga banɗaki, sannan ta daidaita nutsuwarta ta fito, a daidai nan Ibrahim yana sakkowa daga saman sanye da ƙananan kaya. Haɗe rai ya yi ota kuma ta sha jinin jikinta har tana rayawa a ranta ko ya gane ta yi wani abi a ɗakin Jiffar na rashin gaskiya, haka dai ta dauri tana ɗan ƙirƙirar murmushi ta gaishe shi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa yana mai buɗe ƙofa ya fita. Bayansa ta bi da kallo tana sauke ajiyar zuciya a fili tabbas ba ƙarya Ibrahim ga haɗu a duk lokacin da za ta yi tozali da shi sai ta ji wani itin sonsa da ƙaunarsa. Yana fita kamar haɗin baki Jidda tana fitowa sanye da wata abaya mai kyau. Lemo da kofi ta ɗakkowa Aliya wacce ba ta da nutsuwar shan wani lemo ma kawai so take ta tafi sai dai ba zai yiwu ba tun da dai yanzu tana fita sai an ɗarsa zargi a kanta duk da ta san Jidda ba za ta zarge ta ba amma dai maganin kar a yi kar a fara. Tana shan lemo suna gaisawa lokacib ne Saude da Jidda ta kira a waya ta zo ɗaiki da tire da aka jera kwanuka a ka ta ajiye tare da gaishe da Aliyar a raine sai dai Jidda ba ta lura ba tun da tana latsa waya lokacin ita kuma da ido ta mata kallon rainin tana taɓe baki, sosai abin ya yi wa Aliya ciwo sai dai ta zargi ko dai Sauden ta san abin da take aikatawa ne sai kuma ta kawar da zargin. Tana rayawa a ranta akwai ranar ramuwar gayya wacce ta fi ta gayya zafi. Ta ɗaga kofin lemon za ta kurɓa lokacin ne Jidda ta ce ",Ƴar uwa albishirinki" Aliya ta ce "Goro" A takaice, Jidda cike da fara,a ta ce "Allah ya yi zan taka ƙasa mai tsarki" Ƙwaruwa Aliya ta yi saboda baƙinciki domin maganar ta zo mata a bazata, sai da Jidda take buga mata bayanta tana kera mata sannu sannn ta samu tarin ya lafa zuciyarta ta cika da baƙincikin da har ta kasa yin furucin komai, tana jin wani tuƙuƙin baƙincikin wai Jidda ce za ta shiga jirgi ta bar ƙasa ta je makka. Dakyar ta taushi zuciyarta ta nuna mata farincikin da iyakarsa fatar baki, amma zuciyartw baƙiƙƙirin. Nan Jiddar take faɗa mata har sun jr an yi mata passport amma umra ce za su je ita da mahaifan Ibrahim dama Daddy ne da Mummy za su je, sai Mummy ta ce sai an tafi da ita domin shi Ibrahim yana da aiki a office ban da shi za a je shi sai hajji za su je tare da Jiddar. Shi sai ba ya ma son tafiyar nan don sai ya ji ko kaɗan ba ya son Jidda ta yi nesa da shi, ga shi da yawan buƙata iya kuma ba ta gajiyawa da biya masa buƙatarsa. Sosai Aliyar ta nuna rashin jin daɗin rashin faɗa musu da Jidda ba ta yi ba sai lokacin take faɗa mata dama yau zuwan da za ta yi gidanta don ta faɗa mata ne ba ta zo ta faɗa mata a waya, nan take cewa sai da dare ma za ta je gidan Ibrahjm zai kaita ta faɗawa su Abba. Sai dab da magriba ta tafi shi ma dakyar ta daure saboda ba ta son ta tafi da wuri kawai sai take ganin kamar dai za a gane akwai wani abun kuma kawai zarguwa ne, dama bahaushe ya ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Jidda shiryawa ta yi da suka yi sallar magriba suka tafi ya kaita gida don faɗawa su Abba domin saura kwana huɗu su tafi. Umma ta yi baƙinciki sai dai haka ta daure tana ta sakin dariyar yaƙe Abba kuwa sai godiya yake jerawa Ibrahim ɗin don ya ji matuƙar farinciki. Umma dama da Aliya ta kira ta ta faɗa mata don ba ta bi ta gida ba da ta dawo daga gidan Jiddar saboda magriba ta gabatota san dole za su haɗu da Abba. Washe gari da Umma da Aliya suka tafi kasuwa bayan Abba ya tafi kasuwa hala shi ma Kasim. Ko da suka kai zoben ba a saya ba duk inda suka je sai a ce sai sun kawo risit ɗin. Sun taka waje kusan bakwai amma duk inda suka je amsar ɗaya ce don kpwa sai ya ce ba zai saya ba in babu shaida domin kar su saya abin sata, duk da rantse rantse da su Umma suka sha yi a wurare da dama kan cewar gobara suka yj da daɗewa ya ƙone risit ɗin, amma sai a ce musu ai da sun koma wajen wanda suka saya sun masa bayani ya rubuta musu wani. Haka suka gaji da yawo suka koma gida rai babu daɗi .Washe gari ma haka, sai da suka gaji da yawo a kasuwa har wajen ƙarfe ɗaya sannan suka haɗu da wata mata ta ce ita ta san inda za ta raka su a saya don shi mutum hatta kayan sata saya yake kua har yau dubunsa ba ta cika an kama shi ba, tashin farko da suka ji kuɗin sun tsorata domin cewa ya yi miliyan biyu da dubu ɗari da naira dubu uku. Haka ya karɓa ya transper suka tafi suna murna da sharaɗin ko da wani abu ya ka je ya zo karki su kuskura su ambaci sunansa don ya gane alamomin rashin gaskiya a tare da su daga ganin yadda suka razana da kuɗin zoben ya fahimci ba mallakinsu ba ne. Kuma shi ma a hakan ma ya musu zururun dubu ɗari biyar. Cike da farinciki suka koma Umma ta wuce gida ita ma Aliya ta wuce nata gidan, suka ce sa ƙarasa maganar a waya don dama a akawun ɗin Aliya aka tura kuɗin. A ranar da su Jidda suka tashi a ranat nr su Umma suka samu labarin wani hamshaƙin boka da ƙawar Umma ta musu jagora. Sun sha baƙar wahala wajen zuwa kasancewar a cikin surƙuƙin daji yake sannan gidansa a kan wani dutse.Bayan an basu izini sun shiga nan ya kwashe abin da yake tafe da su ya faɗa musu ya ce domin an sanar da shi zuwansu da kuma abin da yake tafe da su. Ya ce zai yi aikin amma da sharaɗin Aliya za ta bashi kanta, sun razana da lamarin buƙatar bokan, sai ƙawar Ummar take mata alama ta amince domin hakan zai sa burinsu ya cika. Sai Umma ta ce sai dai ita ta bashi kanta amma boka ya ce ai sharaɗin a kan Aliya yake don ita ce wacce za a yi wa aikin idan kuma ba za su amince ba su ɗauki takalmansa su bar masa gida. Aliya jin an cr aikinsa kamar yankan wuƙa yake hakan ya sa ta ce kawai ta amince don a neman duniyar da take zuciyarta ta ƙeƙashe ji take komai ma za ta iya sannan tana ganin cewa ba kanta farau ba kuma ba za a ƙare a kanta ba, ta sha jin ana cewa mata da dama sai sun bada jikinsu a wajen boka wa,iyazubillah. Ita kanta zina ba a ɗauke ta a bakin komai ba yanzu a wannan zamanin ba ga ƴanmata ba, ba ga matan auren ba ba ga mazan auren ba sai wanda Allah ya tsallakar amma akwai wanda ko yatsunsu ba sa bari wanda ba muharraminsu ba ya taɓa kuma duk lalaewat zamani ba za su saɓaw Allah ba. Umma da ƙawarta waje suka fita Aliya suka shiga can cikin ɗakin da bokan yana faɗin aikin da za a yi yana daga cikin wannan sharaɗin in har ta yarda a lokacin da yake tarayya da ita ne zai fara aikinsa. Haka suka yarda da ƙaryarsa ba su san cewa babu wano aiki da zai yi da wannan tarayyar ba kawai ƙishirwarsa yake kashewa da mata mararsa kamun kai masu neman duniyar wanda suka manta cewa komai suka samu a duniyar za su bar shi, hatta ɗankunne ko zobe ba za su shiga kabari da shi ba daga su sai likkafani sannan duk abin da suka saɓawa Allah sai an azabtar da su, da yawa ana mantawa da makoma ne. Sai da ya gama watsewarsa da Aliya wacce ta manta matsayinta na matar aure, sannan ita kanta zina ko baka da aure haramun ce kusantar ta ma Allah cewa ya yi kar a yi. Sun dawo yana ta washe bakin garaɓasar da ya samu. Ya ce sai bayan kwana bakwai za su dawo. Sai da aka yi kwana bakwai sannan suka kwaso ƙafa suka zo, sai dai ranar su biyu suma zo babi waccrn ƙawar ta Umma da ta rako su, dama ƙawarta ce da suka zauna unguwa ɗaya malotan gidan su Umma ce. A ranar da suka dawo ranar ne ta cika kwana biyar da mutuwa kuma lafiya ƙalau kawai ƙarar kwana ta yanke jiki ya faɗi sai gawarta. Wannan kaɗai bai fahimtar da su cewa duniyar ba za a tabbata a cikinta ba. A waje ya ce Umma ta dakata zai yi wa Aliyar bayani nan Umma ta fita ta zauna saga gefen dandazon mstan da suke zaune dodo guda suna jiran zuwan layinsu, don su kaiwa boka buƙatarsu zuciyoyinsu sun karkata ga kaiwa wanin Allah buƙatarsu da faɗa masa damuwarsu sun manta Allah kaɗai yake maganin matsala da damuwa wajensa kaɗai ake samun biyan buƙata. Yana fita boka ya ɗakko wata ƴar kwalba ya ce "Wannan kwalbar maganin ciki za ki samu abinci ko na sha ki zuba masa a ciki" Idanu Aliya ta zaro jin wani baban lamati don ba ta manta tababar da ta sha wajen sauya cokali ba, amma sai ta amsa da cewa to. Ya ci gaba da faɗin "Wannan maganin idan kin tabbatar ya cj abin da kika saka maganin ko ya sha sai ki saka a ƙasanki sannan ki shafa wannan turaren " Ya faɗa yana miƙa mata. Karɓa ta yi tana jiran ƙarin bayani ya ce "Idan ya sha abin shan duk inda mace take burinsa ya yi tarayya da ita kinnga ke kuma kina nan to za ki yi duk yadda za ki yi tun da kin ce matarsa ba ta ƙasar ma" Aliya cike da ɗoki ta ce "Malam ka tabbata zai mu,amalanceni"?" Ya kalle ta ya ce "Ba saka kokwato a aikinmu" Ta ce "Ai na sani kawai dai mutumin yana da taurin rai ne, sannan ya tsane ni ko ganina ya yi sai fuskarsa ta sauya, kuma ko magana ba ta haɗamu hasalima iya gaisuwa ne yake haɗamu" Boka ya ce "Ba kallon ke mace ba kuma mutum to ko da a ce dabba ya gani wato ki ƙaddara bayan ya sha maganin ya ga akuya to saa ya haike mata kawai zai ji yana son kaɗaicewa da duk wata halitta indai mace ce" Murmushjn nasara ta yi tana faɗin "Na gode sosai boka Allah ya... Hannu ya ɗaga mata ya ce "Sai kuɗin aiki dubu ɗari biyar ne" Transper ta masa sannan yana nannaga mata sai nan da kwana bakwai ko takwas za ta aiwatar da aikin. Tun da suka taho Umma takr mata nannago a kan ta san idan za ta ajiye maganin don ita Umma ta tsani ma a ce wai magani ba za a aiwatar da aikinsa ba sai an ƙayyade masa kwanaki saboda ta fi son sha yanzu magani yanzu. A yadda Jidda ta faɗa musu cewa sati uku za su yi sai dai daga baya ya zamana sati biyu ne kuma sai ta sha,afa ba ta faɗa musu ba. Duk da sau biyu suna waya da Abba amma tun da ta ta fi ba su yi waya da Aliya ba sai Umma ce da suka gaisa a wayar Abba lokacin da ta kira shi, domin sau biyu tana kiran wayar Umma ba ta samun ta. Sun yi ibada sosai Jidda ta mayar da hankali wajen yin addu,a da neman tsari sannan uwa uba ta sha yi wa iyayenta addu,a da nema musu gafara da rahmar ubangiji aljanna kuwa ta roƙa musu mafi girma da ɗaukaka haka kanta da kuma ginshiƙinta mijinta abin alfahrinta Ibrahim. Ta tsawaitawa Abba addu,a bisa jajircewarsa na kasancewa tsani kuma matakala da ya maye mata gurbin mahaifi. Su Umma ma ba a barsu a baya ba domin tana jinsu a tsakiyar zuciyarta a ƙarshe ta sha saka jama,ar musulmi a addu,ar neman shiriya da samun zaman lafiya mai ɗorewa. Yau ya kama talata a yau ne suka kammala komai yau ne jirginsu zai tashi zuwa Nigeri,a ƙarfe sha biyu na rana jirginsu ya taso daga jidda awa shida ya kawo su Nigeri,a jirginsu ya sauka ƙarfe shida na yamma. A ɓangaren Aliya yau ya cika kwana takwas daidai da dawowarsu daga wajen boka kuma yau ne ya dace ta aiwatar da aikin da zai zama cikar burin nasu. A nata hasashen kuma iya saninsu saura sati guda Jidda ta dawo wanda sun yi imanin idan ta sauka a Nigeri,a lokacin ta zama tarihi a zuciya da rayuwar Ibrahim. Ko da ta ga dab da magriba ta tabbatar lokacjn yana gida domin wani matashin saurayi ɗan zauna gari banza da ta saka shi zama a unguwar yake kular mata da motsi shige da ficen Ibrahim a ranar. Bayan ya sanar mata ya ga shigarsa gidan, don haka lokacin da ta zo sai da ta leƙa wata tula ta tabbatar da mai gadi ba ya harabar wajen, ta yi saɗaf saɗaf ta turo ƙofar domin ta tabbatar yana banɗakin. Har ta shiga falon da yake ƙasa ba ta samu kowa ba a falon shiru don ta ji Jidda ta ce su Saude za su koma ƙauyensu har sai ta dawo. Bayan kujera ta samu ta haura wanda yake da ɗan faɗi inda yake daga wajen kwana ta bango aka saka kujerar kasancewar kujerun irin wanda ba a saka su har bango ne. Ƙaran tahowarsa ne ya sa ta shige wajen gabanta yana faɗuwa, tana ganinsa ya wuce daga tsakanin kujera da take hangensa, frige ya buɗe ya ɗakko maltina ya nufi saman dama tun da Jidda ta tafi sai dau ya sha drinks da snacks. A daidai nan ta lallaɓa ta haye saman saboda kasada idanunta ya rufe a kan cikar burinta.. Sai da ta hau saman ta fara dawurwurin inda za ta ɓuya domin ta kasa gane a wane ɗaki yake. Ɗan ƙaran faɗuwar abu ta ji a ɗaya ɗakin ta haka ta tabbatar yana ɗakin. Daga jikin mariƙin ƙofa ta leƙa ta hangeshi zaune a bakin gado da ƙaramin tebur a gabansa sai maltinar a ka gabansa kuma kofin glass ne wanda ya suɓuce daga hannunsa ya faɗi ya fashe. Ganin ya miƙe tsaye ta matsa daga ƙofar gabanta yana harbawa ko da ta samu mafaka sai ta ganshi ya zo ya sauka ƙasa domin shi ransa fari ƙal yau Jiddansa za ta dawo gare shi, sai dai yana ta kiran wayarsu ba ta shiga ya san wataƙila suna hanya ne yana jiran su sanat masa sun dira ya je ya ɗakko su. Yana sauka ta fito daga maɓoyarta ta shiga ɗakin a sukwane dama ta buɗe maganun tana shiga ta ɗaya murfin maltinar kasancewar ya buɗe kwalbar bai kai ga zubawa ba kofin ya fashe. Duka ta juye ta mayar da murfin ta yi saurin fitowa daga ɗakin, ɗaya ɗakin ta shige tana fargaba da addu,ar Allah ya sa kar ya buɗe ɗakin da take ciki. Tana shiga ɗakin ta ɗakko abin sakawa a ƙasan ta saka, don ta tababtar aiki yana dab da kammaluwa matsawar ya yi tarayya da ita to ba zai sake marmarin wata ƴa mace na har abada!. Sannan daga ranar ta zama sarauniyar zuciyarsa zai aure ta ya zauna da ita kuma babu mai tambayar wani ba,asi sannan Jiddar za ta fuskanci ƙasƙanci. Kayanta ta cire gaba ɗaya saboda toshewar basira ba ta ma bari ya je ya sha maganin ba dimin ta sa a ranta shan magani ai kamar an yi an gama, sai da ta shafe turaren nan kaf a jikinta ta ɗauki ɗankwalinta ta ɗaura a jikinta, a daidai lokacin ne ta fara jiyo takunsa zuwa saman murna fal cikinta sai dai gabanta ya harba da ƙarfi a lokacin da ta ɗan leƙo da tillar makamar ƙofar ta hange shi ya doso ɗakin da take, idanu ta zaro tana tunanjn shikenan dubunta ta cika tana hango taɓarɓarewar al,amura matuƙar ya buɗe ɗakin ga kayanta nan a tsakar ɗakin da bata ma ɗauke ba kuma matuƙar ta ce za ta tsaya ɗauka sannan ta nemi maɓoya akwai matsala don sai ya shigo ba ta samu mafita ba saboda ita kanta a rikice take. Tunanin tsakaninsu da Jidda ta yi komai zai rushe shikann Jidda za ta zama ta san cewa su ba masu ƙaunarta ba ne tun da har ga shi za ta zo har cikin gidanta a lokacin da ba ta nan don kawai ta cim ma manufarta, ta san shikann kuma Jidda ba za ta sake yarda da su ba, ƴar soyayyar ƙaryar da suke nuna mata za ta daina yarda da ita ba ma lallai ta sake sakin jiki da su ba bare har su zo inda take su cika ƙidirinsu da mafufarsu a kanta!. Ibrahim handle ɗjn ƙofar ya kama ya buɗe ƙofar Aliya da take bayan ƙofar gabanta yana dukan lugude ta yi tsuru tsuru. Shi kuma ko ɗakin ma bai kalla ba ya dai buɗe ɗakin ne hankalinsa ma ba a wajen yake ba don ya waiwaya bayansa ne, ko mai ya tuna sai ya ja ƙofar ya rufe a juya tare da buɗe ɗaya ɗakin ya shiga. Aliya komawa ta yi ta jingina da bango tana sauke ajiyar zuciya a fili har lokacin ƙirjinta yana tsananta bugu kamar zuciyarta za ta fito. Yana shiga ɗakin ya kwashe kofin da ya fashe ya zuba a kwandon sharar da yake cikin ɗakin daga can gefe wanda babu komai a ciki sai tissue. Saurin saka kayansa ya yi yana son tafiya airport ɗakko su Jidda. Yana ɗaura agogonsa ya tsiyaya maltinar a kofin da ya sake ɗakkowa da ya sauka ƙasa. Kai ya kafa ya sha ya ajiye tare da miƙa hannu zai ɗakko wayarsa da ta ɗauki ruri yana dubawa ya ga Mummy ce hakan yana bashi tabbacin sun dira. Sai dai kafin ya ɗauka mararsa ta murɗa masa da wani irin ƙarfi, fuska ya yatsina yana kai hannunsa ya dafe mararsa a take ya ji komai ya sauya wata irin buƙata ce da bai taɓa ji ba ta mamaye ilahirjn jikinsa ji yake idan ya ƙara wasu mintuna bai samu biyan buƙatarsa ba tamkar numfashin sa zai bar jikinsa gabaɗaya idanunsa sun rufe mafita yake nema ta ko ina. Aliya da ta gama kallon abin da yake faruwa ta ƙaramar tular jikin ƙofar hannu ta saka domin buɗe ƙofar ɗakin da yake ciki, ɗankwalin da yake jikinta ko mazaunai bai rufe mata ba. Tana shiga dama ya ba ta baya sakin ɗankwalin jikinta ta yi ya faɗi ƙasa kafin ta fara taku ta nufe shi tana wani malmalƙwashewa kamar macijiya!. A can ƙofar gida su Jidda ne da Mummy, jidda da Mummy a baya sai Daddy wanda yake gaba direba yana tuƙawa. Sun yi ta kiran wayar Ibrahim bai ɗauka ba kuma shiru bai zo ba, hakan ya sa Daddy ya kira direba ya je ya ɗakko su. Mai gadi ya wangale musu get suka shigo Jidda ta fito daga motar Mummy tana cewa ta gaishe shi wataƙila bacci ya yi. Ga magriba ta gabato. Mai gadi yana ta mata sannu ta amsa lokacin su Mummy motar su ta har ba zuwa titi. Riƙe da akwatin ta ta tura ƙofar ta shiga tare da mayarwa ta rufe tana tunanin abin da ya hana Ibrahim zuwa ɗakko su bayan ta san ya san lokacin da jirginsu zai sauka. *Ni ma dai maman afrah a nan na dasa aya, don gabaɗaya turka-turkar ɓangarorin nan uku ta sha min kai, domin samun cigaban labarin bar ƙarshe 500 ne shiga group za a biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay, sai a tura min shaidar biya ta lambata 09025576222 idan na kammala littafin complete docment 800*