KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari Mansur Usman Sufi Website:- www.arewanovels.com.ng 08137237071 Babi na biyar A da can baya kimanin shekaru dubu ɗaya da ɗoriya da suka gabata, lokacin da Ƙarfin sihiri da na jarumataka suka zamto jari hujja, zalunci gami da yaudara suka yi katutu a zukatan bil'adama, kowanne sarki burin shi ya kai farmaki zuwa ɗan uwanshi ya mamaye ƙasar shi ta dawo izuwa ƙarƙashin masarautarshi. A wannan lokaci akwai manyan biranen duniya da suka shura, waɗanda gaba ɗaya sune ke tafiyar da mulkin duniya baki ɗaya. Biranen sun haɗar da birnin Sin, Rum, Misra da birnin Hindu. Birnin Sin na ƙarƙashin mulkin sarki Abul-uyum. Abul-uyum ya kasance gwarzon mayaƙi mai dakawa maza gumba a hannu, an ce saboda Jarumtakarshi yana iya shafe tsawon kwana uku yana yaƙi ba tare ya ci ko ya sha ba ballantana gajiya, batun ƙarfin sihiri, dukiya da rundunar mayaƙa kuwa ya yiwa gaba ɗaya sarakunan yammacin duniya zarra. Bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamto gagarabadau kuma ƙadangaren bakin tulu ga sarakunan nahiyar. Birnin Rum yana bisa jagorancin sarki Fitinatul-muluk ibnu Larab, Fitinatul-muluk ya kasance hatsabibin matsafi, gwarzon jarumi ma'abocin tarin dukiya dangin lu'ulu'u da dabbobin ni'ima, masu hasashe da bincike sun tabbatar da cewa a iya fadar shi akwai dakarun aljanu da na bil'adama guda miliyan ɗaya, bayan waɗanda aka tanade su domin kai farmaki izuwa birane da ƙasashe domin FATAUCIN BAYI, kusan komai dake fadar shi an samar da shi ne da ƙarfin sihirin tsafi. Bisa wannan dalili ya sanya sarakunan ke yi mashi laƙabi ya da ANNOBAR SARAKAI. Sarki Hubaizu ibnu Shardas kuwa shine ke riƙe da Kambun birnin Hindu. Hubaizu mutum ma'abocin sadaukantaka ta gaban kwatance, sanin alƙalumman sihiri, gami da tarin dukiya. A jerin sarakunan da aka yi a birnin Hindu shine sarki na saba'in, ya hau karagar mulki tun yana matashi ɗan shekara sha biyar, kuma a halin yanzu yana da shekaru saba'in cif a duniya, bisa binciken bokaye da masu hasashe sun gano cewa a kowacce rana sarki Hubaizu yana samun sabbin sirrikan tsafi guda miliyan ɗaya, yana samun sirrikan ne a duk sa'adda da sadu da wata kuyangarshi. Bokayen sun gano cewa duk sa'adda da hakan ta faru ƙarfin damtsenshi yana ƙaruwa sau hamsin cin ɗari. Bisa wannan dalili ya sanya ya zamto wa sarakunan nahiyar ANNOBA ƊARI. Birnin Misra na bisa jagorancin wani gwarzon mayaƙi ne da ake yiwa laƙabi da Ayumul-barƙas ibnu Zairul. Sarki Ayumul-barƙas mutum mai tattare da abubuwan al'ajabi ba ya tsafi kuma sihiri ba ya tasiri akan shi, komai yawan sirrikan tsafinka idan kayi arba da shi take za su daina amfani. Gaba ɗaya sarakunan biranen huɗu, Abul-uyum, Hubaizu, Fitinatul-muluk da sarki Ayumul-barƙas sun kasance basa ga muciji da juna, burin kowannen su shine ya kawar da abokan gabar shi domin ya zamto sarkin SARAKAI na duniya. Bisa binciken da sarakunan suka gudanar shine ɗyan su ba zau iya cimma wannan buri na shi ba face ya mallaki wani kundi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN AL'AJABI dake ajiye a kogon GARUL-SHAMMAR. shi dai KUNDIN AL'AJABI na ɗauke da sirrikan tsafi guda miliyan dubu hamsin, babu wani mahaluki a doron ƙasa walau mutum ko aljan da zai mallaki kundin face ya zamtowa duniya gagarabadau kuma ANNOBA ƊARI. Koda mutum ya mallaki KUNDIN AL'AJABI ba zai iya sarrafa shi ba face ya mallaki wata kuba da ake yiwa laƙabi da Miftahul-sihir, a halin yanzu kubar Miftahul-sihir ta rabu kaso huɗu, kowanne sarki daga cikin sarakunan huɗu yana ɗauke da ɓari guda, dukkaninsu sun mallaki ɓarin kubar a hannun mahaifan su. Sa'adda sarakunan huɗu suka ga wannan al'amari a cikin halarar tsafin su sai hankulansu suka dugunzuma ainun, abu na farko da ya dugunzuma hankulan su shine. Ta ya ya ɗayan su zai yaƙi sauran abokan gabar shi har ya raba su da sassan kubar guda uku, bayan cewa fiye da shekaru goma suna kwabza yaƙi tsakanin su amma babu nasara, sai dai a samu asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa. Abu na biyu da yafi tayar masu da hankali shine a cikin su babu wanda yake da ikon shiga kogon GARUL-SHAMMAR har ya ɗauko KUNDIN AL'AJABI face wani barde da ake yiwa laƙabi da Yasiran jin Taufid. Yasiran ya kasance mafarauci, fiye da rabin rayuwarshi ya yi ta je a daji tare da iyalan shi. Abun tambaya anan shine ta ya ya ɗayan su zai mallaki mafarauci Yasiran? Bisa dogon nazari da sarakunan suka yi sai suka samu mafita tsakanin su. Mafitar kuwa ita ce kowannen su zai bayar da ɓarin kubarshi a haɗe waje guda, sannan a nemi taimakon mafarauci Yasiran, idan ya so bayan ya samu nasarar ɗauko KUNDIN AL'AJABI sai a kwabza yaƙi tsakanin su, duk wanda ya yi nasara sai ya mallaki kundi da kuba. Kamar yadda sarakunan suka tsara haka al'amarin ya kasance, wata rana da la'asar sakaliya mafarauci Yasiran da matarshi Zarilat sai ni 'yarsu Sulaiza muna zaune a cikin bukka muna fira cikin nishaɗi sai kawai muka jiyo ƙarar takun sawaye haɗe da haniniyar dawakai sun cika dajin baki ɗaya. Cikin matuƙar kaɗuwa abbana na miƙe tsaye zumbur yana mai ɗaukar KWARI DA BAKAN shi ya yunƙura ya durfafi ƙofar fita, har na yunƙura zan bi shi a baya sai ya dakatar da ni ta hanyar dafa kafaɗuna ya dube mu ni da mahaifiyata ya ce "ya farin cikin rayuwata bana so wani abu ya ɗaga maku hankali kawai ku zauna naje na duba domin naga mene ne ke faruwa". Koda jin wannan batu daga bakin abbana, sai idanun mahaifiyata suka ciko da ƙwalla kuma ta janyo ni ta rungume ni a ƙirjinta, sannan ta dube shi muryar ta cike damuwa ta ce " ya muradin zuciyata kayi sani cewa yau tsawon shekaru ashirin muna zaune a wannan daji ba a taɓa samun wata muguwar dabba, ko dakarun sumame sun kawo mana farmaki ba sai a yau, jikina ya bani cewa babu alheri a tare wannan fita taka". Koda jin wannan batu daga bakin mahaifiyata sai ya dube mu cikin alamun matuƙar tausayi ya ce "ya abar kaunata ki kwantar da hankalinki da yardar abun bauta zan dawo gare ku cikin ƙoshin lafiya". Koda gama faɗin hakan sai mahaifina ya juya ya fice daga turakar yana mai kunna kai izuwa ɓangaren da yake jin takun sawayen, yana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai mahaifina ya yi arba da waɗansu zaratan mayaƙa su huɗu zaune a bisa ingarmun dawakai, dukkanin su suna shirye cikin gagarumar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro sun rufe fusakunsu idanunsu kaɗai ake gani. Kafin abbana ya yi wani yunƙuri sun yi mashi ƙawanya suna masu kewaye shi, cikin dakewar zuciya mahaifina ya dubi mayaƙan cikin matuƙar fushi ya ce "ya ku waɗannan mayaƙa shin mene ne nufin ku a gare ni? Koda jin wannan tambaya sai kowannen su ya ɗora hannunshi a kanshi ya cire hular ƙarfenshi take fusakunsu suka bayyana a fili ƙarara. Sa'adda mafarauci Yasiran ya yi arba da fusakun na su sai hankulanshi ya dugunzuma ainun tsoro ya kama shi, Domin a iya tsawon rayuwarshi bai taɓa gani ko jin labarin sadaukai masu matuƙar kwarjini da ban tsoro tamkar mayaƙan ba. Daga can sai wani daga cikin mayaƙan mai ƙirar samudawan farko fuskarshi a murtuke take babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ya ce "ya kai Yasiran ibnu Taufid ka yi sani cewa bamu zo gare ka domin cutar da kai ba sai domin mu taimaki juna tsakaninmu, don haka sai ka tsaya ka saurari bayanin da zan yi maka da idanun basira. Ya kai Yasiran kayi sani cewa bakomai ne ke tafe damu izuwa gare ka ba, face muna so ka tafi izuwa tekun Bahar-rum ka shiga kogon GARUL-SHAMMAR domin ka ɗauko mana wani littafi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN AL'AJABI, domin mu tseratar da al'ummar ƙasashenmu daga annobar fari da junya dake addabar su, ka yi sani cewa matsawar ka cika mana wannan buri namu, ni Ayumul-barƙas da sauran 'yan uwana Fitinatul-muluk, Hubaizu, da sarki Abul-uyum zamu baka ladan dukiya mai tarin yawa wacce kai da zuri'arka ba su taɓa cinye ta har tattaɓa kunnen ka, sannan kai da kan ka zaka zaɓi inda kake don ka zauna tare da iyalan ka a ɗaya daga cikin biranen mu huɗu". Lokacin da sarki Ayumul-barƙas na birnin Hindu ya zo dai-dai nan a zancen shi sai sauran sarakunan suka gyaɗa kai dake nuni da tabbatar da maganar da ɗan uwansu ya faɗa, suna masu cewa a ransu haƙiƙa sarki Ayumul-barƙas ba ƙaramar hikima ya yi ba da ya ɓoyewa Yasiran gaskiyar batun KUDNIN AL'AJABI ba, amma a ɓangare guda zukatansu cike suke da mugun tanadi. Tsawon daƙiƙa hamsin mafarauci Yasiran yana nazarin maganar da sarki Ayumul-barƙas ya yi mashi. Abu na farko da ya faɗo mashi a rai shine, mene ne ya sanya waɗannan sarakuna suka zaɓe shi a matsayin wanda zai ɗauko masu KUNDIN AL'AJABI bayan cewa dukkanin su manyan jarumai ne da za su iya aiwatar da hakan? Sannan ma shin wane tabbaci kake da shi cewa zaka dawo ka tarar da iyalanka cikin ƙoshin lafiya, wani ɓangaren a zuciyarshi kuma na cewa da shi ka tuna asarar miliyoyin rayukan jama'ar da zaka ceto idan ka ɗauko KUNDIN AL'AJABI. Sa'adda mahaifina yazo nan a tunanin shi, sai kawai ya cire kai ya dubi sarki Ayumul-barƙas, sannan ya yi gyaran murya ya ce "na amince zan biya maku wannan muhimmiyar buƙata amma ina buƙatar ku bani lokaci na yi nazari". Koda jin wannan batu daga bakin abbana sai sarakunan suka sake duban juna gami da yiwa juna murmushi mai tattare da tsantsar mugun tanadi. A can dajin Harbul-zawat kuwa ina zaune tare da mahaifiyata cikin tashin hankali, sai mu kaji abbana ya yi gyaran murya ya tura ƙofar hujjar, koda muka yi arba da shi sai muka riga izuwa inda yake suka faɗa kan ƙirjinshi ya rungume mu, muna masu fashewa da kuka. Sai daga bisani ne ya janye jikinshi daga namu ya dube mu fuskarshi cike da annuri, nan take ya zayyane mana abin da ya wakana tsakanin shi da sarakunan tun daga farko har ƙarshe. Koda jin wannan jawabi sai mahaifiyata ta cika da matuƙar farin ciki, amma kuma sai hankalinta ya dugunzuma ainun, abin da ya dugunzuma hankalin nata shine shin akwai tabbacin cewa abbana ba zai rasa rayuwarshi wajen shiga tekun Bahar-rum ba? Sannan wata shaida gare shi dake tabbatar da cewa sarakunan ba su ci amanar shi ba? Cikin alamun matuƙar damuwa mahaifiyata ta dubi abbana ta ce "haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki bisa jin wannan gagarumin aikin ceton al'umma da zaka yi, sai dai ina matuƙar tsoron ka rasa rayuwarka a wannan hali, sannan kar mutanen da ka aminta da su suci amanarka". Koda jin wannan batu daga bakin ummina sai mahaifina ya yi murmushi a gare ta ya ce "ki kwantar da hankalinki babu wani sharri da zai same ni, kar ki manta cewa NASARA DA ƊAUKAKA na tare da ma'abocin gaskiya da riƙon amana, kuma ciki da gaskiya wuƙa bata huda shi. ke dai ki kasancewa mai yi mani fatan alheri a kodayaushe. Koda jin wannan batu sai muka sake rungume shi cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Babi na shida A ranar da tafiya kogon GARUL-SHAMMAR ta zo mun sha kukan baƙin cikin rabuwa da mahaifina, tamkar ba za mu ƙyale shi ya tafi ba. Tun daga wannan rana ummina ce ke ɗawainiya da rayuwata, kullum cikin kewar abbanmu nake, wasa-wasa sai gashi ya shafe tsawon mako uku ba tare da mun ji ɗuriyar shi ba, al'amarin da ya sanya mahaifiyata ta fara tsammanin ko ya rasa rayuwarshi ne. Al'amarin abbana kuwa tun sa'adda mu kayi bankwana muna masu zubar da hawayen rabuwa da juna, sai kawai ya kunna kai izuwa cikin daji yana tafiya cikin hanzari, tafiyar daƙiƙa hamsin kacal ya yi ya iske su sarki Fitinatul-muluk zaune a bisa kan wani narkeken aljani mai matuƙar kwarjini muni da ban tsoro shi kaɗai suke jira, ba tare da wani ɓata lokaci mahaifina ya haye bisa kan aljanin ya zauna kamar yadda sarakunan suka yi. Cikin kuzari aljanin ya buɗe manyan fuka-fukanshi ya luluƙa izuwa sararin samaniya yana mai keta gajimare cikin matuƙar sauri tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya. Tafiyar sa'a uku kacal aka yi aka iso tekun Bahar-rum, cikin hanzari aljanin ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luhh! Ya sauka a dai-dai ƙofar shiga kogon, cikin hanzari sarki Ayumul-barƙas ya fara sakkowa sai Fitinatul-muluk, Hubaizu, Abul-uyum mafarauci Yasiran ne a ƙarshe. Ba tare da wani jinkiri ba sarakunan suka zira hannayensu a aljihun rigar su sai ga shi kowannen su ya fito da ɓarin kubarshi, fuskokinsu cike da murmushin mugunta suka haɗa su a waje guda, faruwar hakan ke da wuya sai aka kwantsama wata tsawa da walƙiya a sararin samaniya, kubar ta kammala jikinta baki ɗaya. Fuska a murtuke babu annuri sarki Fitinatul-muluk ya miƙawa abbana kubar ya sa hannu ya ƙarba, sannan ya dube shi fuskarshi babu yabo babu fallasa ya ce "ya kai Yasiran kayi sani cewa wannan kuba ta Miftahul-sihir da muka baka da ita ne zaka buɗe kofar wannan kogon dutse har ka samu nasara ɗauko KUNDIN AL'AJABI daga cikin shi". Koda jin wannan daga bakin Fitinatul-muluk sai mahaifina ya yi jim! Tamkar mai tunanin wani abu, koda ganin halin da mahaifina ya shiga sai sarakunan suka bayyanar da murmushi akan fuskokinsu, da ganin hakan sai abbana ya ji ya samu nutsuwa kawai sai ya juya ya durfafi ƙofar kogon GARUL-SHAMMAR yana isa ya sanya kubar a cikin wani kwaroron rami da ke jikin makekiyar ƙofar kogon da aka yi ta da zallar mulmulallan baƙin ƙarfe, ya murɗa kubar sau huɗu da dukkan ƙarfin shi, take sakatun suka shiga ƙara, zuwa can sai ƙofar ta yi wani ƙara da ya cika dajin baki ɗaya, sannan ta buɗe kanta, wani irin tururin hayaƙi ya surnano daga ciki, ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, mahaifina ya kunna kai izuwa cikin kogon tare da sanya kubar Miftahul-sihir a cikin aljihunshi, lokacin da ya kammala shiga sai ƙofar ta mayar da kanta ta rufe ruf!. Daga ciki kogon GARUL-SHAMMAR ya kasance makeke mai matuƙar tsawo da faɗi, yana ɗauke da saƙarƙaƙiya da lunguna, gaba ɗaya gine ginen dake ciki an yi su ne da waɗansu manyan duwatsun wuta masu ƙwarin gaske, gaba ɗaya kogon dutsen a haskake ta yadda koda allura ce ta faɗi a ƙasa da ya duba zai gani, kuma a ƙasa a zube akwai kwarangwal ɗin bil'adama da wasu halittu gasu nan birjik. Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, inda a ce abbana ya san abin da zai faru da bai ya gangancin kutsawa kai cikin kogon ba, domin abin da bai sani ba shine, waɗannan kwarangwal ɗin sun kasance tarin miyagun aljanu. Lokacin da ya zamana ya iso tsakiyar kwarangwal ɗin, nan take ruhikansu suka fara dawo jikkunansu kuma surar tana haɗuwa, kafin cikar daƙiƙa hamsin baki ɗaya halittun sun miƙe tsaye. Aljanun sun kasance gabza-gabza masu ƙirar samudawan farko, jikkunansu irin na bil'adama ne amma kawunansu irin na tsuntsun batoyi ne, idanuwansu jajur suke tamkar garwashin wuta, a ƙugunsu suna maƙale da wata murtukekiyar jela irin ta kada, sannan dukkanin suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini muni daban tsoro, a hannayensu suna ɗauke da waɗansu irin makaman yaƙi masu kama da zarto. Haƙiƙa Waɗannan aljanu sun kasance ababan tsoro da razani ga duk wata halitta mai numfashi. Lokacin da mahaifina ya yi arba da halittun sai jikinshi ya kama tsuma yana kyarma saboda matuƙar tsoro, amma sai ya yi wuf! Ya zare takobinshi aka fara kallon-kallo tsakani, tsawon daƙiƙa arba'in ɗayan su bai yunƙurin afkawa abokin gwamin shi ba. A lokaci guda tamkar haɗin baki dakarun suka ɗaga makamansu suka yi ɗauki kan Yasiran suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, tare da kai mashi miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Take mahaifina ya tare su aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, a lokacin da dakarun suka yanyame shi tamkar yadda dandazon ƙudaje ke yanyame ƙwallon mangwaro. Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa, kuma KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka saba gwagwarmaya a filin fama, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihu da hargowar dakarun aljanun ta cika kogon baki ɗaya, kuma kogon ya ɗauki zafi ainun, tamkar zai yi bindiga ya tarwatse, sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari uku ana wannan ɗauki ba daɗi. Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa aljanun kai kenan kuma ya ba su mamaki, domin fiye da shekaru dubu biyu suna gadin wannan kogon na GARUL-SHAMMAR ba su taɓa ganin halitta mai matuƙar zafin nama da ƙwarewar yaƙi tamkar na mahaifina ba. Al'amarin mahaifina kuwa lokacin da ya fahimci cewa babu alamun nasara, kuma koda alamun gajiya babu a tare da dakarun sai hankalinshi ya dugunzuma ainun ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita, koda samun mafitar sai kawai ya mayar ta takobinshi izuwa cikin kube, ya yi wuf ya zaro kubar Miftahul-sihir ya shiga dukan dakarun da ita da dukkan ƙarfin shi. Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, idan kiɗa ya canja dole ne rawa ma ta canja, nan fa abbana ya gano lagon tsuntsayen ya zamana cewa duk wanda ya daka da kubar sai kaga ya kurma wawan ihu ya tarwatse, nan fa ihu da kururuwar shaiɗanu ta ƙara cika kogon, kafin shuɗewar rabin sa'a, nan fa dakarun suka ɗimauce suka kama guye-guje da ifice-ifice, wasu suka shiga ƙoƙarin ƙwace kubar Miftahul-sihir daga hannun abbana, wasu na kai mashi sara da suka cikin matuƙar zafin nama, domin ganin sun kai shi ƙas. Ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin aljanun ya shammaci mahaifina ya kafta mashi sara a cinya, take inda ya yanke shin ya dare jini ya yi tsartuwa, abbana ya kurma ihu sakamakon zafi da raɗaɗin da ya ji amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN DUNIYA sai ya ci gaba da yaƙin a haka ba tare tsaida zubar jinin ba, haka ya ci gaba da yaƙin jiri na ɗibar shi a wasu lokutan har yanke jiki yake ya faɗi ƙasa amma sai ya miƙe tsaye zumbur ya ci gaba da yaƙin a haka. Kaico! Haƙiƙa jarumtaka baiwa ce daga Ubangiji, dukiya, mulki basu bayar da ita face baiwa daga Allah, komai hassadar mutum idan ya ga yadda mahaifina ke ragargazar dakarun cikin baƙin zafin nama da kafin tsiya, dole ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa ya cika gwarzon mayaƙi mai ƙarfi na Allah ya isa. Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA YAFI SARKIN ƘARFI qna cikin wannan artabu ne mayaƙan suka samu nasarar kai abbana ƙasa suna niyyar hallaka shi, koda ya ga irin mawuyacin halin da yake ciki da yake tsakanin RAYUWA DA MUTUWA, bai san sa'adda ya buga kubar Miftahul-sihir a ƙasa ba, faruwar hakan keda wuya nan take wani farin haske ya yi fitar burgu daga kubar, ya shiga sassan jikkunan sauran aljanun, nan take suka kama ci da wuta suna ihu da kururuwa neman taimako, kafin wani lokaci mai tsawo baki ɗayan su sun sheƙa barzahu. Cikin matuƙar farin ciki abbana ya miƙe tsaye da ƙyar ya sake kunna kai izuwa cikin kogon, Tsawon daƙiƙa ɗari huɗu yana tafiya sannu-sannu, lokacin da rabin sa'a ta shuɗe a dai-dai lokacinne ya iso wani waje mai matuƙar sanyi, hatta durakun dake wajen na dusar ƙanƙara ne, babu wani waje da mutum zai ajiye ƙafarshi face dusar ƙanƙara ce. Sa'adda mahaifina ya tsinci kanshi a cikin wannan hali sai hankalinshi ya dugunzuma ainun, domin baya sanye ɗauke da rigar kariya daga sanyin. Cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya kama mahaifina jikinshi ya kama ƙyarma, tun yana iya takawa da ƙafafuwanshi har ya zamana ya zube a ƙasa magashiyan nunfashin shi na fita daƙyar. Yana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai kawai wani irin ƙatuwar halitta tayo fitar burgu daga dusar ƙanƙarar ta fito waje, Ita dai halittar takasance wata shirgegiyar macijiya mai kauri tamkar bishiyar kuka, jelar murtukekiya ce, bayan ƙaton kanta tana ɗauke da ƙarin wasu guda biyu, na farko yakasance na zaki, ɗayan kuma na raƙumin dawa. Kaico! Wannan halitta ta kasance mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, babu wani jarumi da zai yi arba da ita face ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa. Babi na bakwai A can bakin ƙofar shiga kogon GARUL-SHAMMAR sarakunan duniya huɗu suna tsaitsaye suna jiran fitowar mahaifina fuskokinsu a murtuke babu annuri cike da matuƙar kiyayyar juna. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai suka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! Tamkar DARE UKU ne ya haɗu waje guda mutum koda tafin hannunshi baya iya gani. Sannu a hankali duhun dake sararin samaniya ya fara raguwa, sai ga waɗansu halittu masu tarin yawa suna ketowa daga cikin gajimare suna sauka a kan tekun Bahar-rum. Koda ganin hakan sai sarki Fitinatul-muluk da sarki Hubaizu suka yi wuf suka fito da maduban tsafin su suka shiga gudanar da bincike, koda kammala binciken sai suka taƙarƙare suka bushe da dariyar mugunta, ba komai suka gani ba face halittun da suka bayyana sun kasance rundunar sarakunan duniya biyu, sarkin aljanu baƙaƙen fata da farare. Sun turo tawagar ne domin su ƙwaci KUNDIN AL'AJABI da kubar Miftahul-sihir da zarar mahaifina ya samu nasarar ɗaukowa. Sarki Hubaizu na birnin Hindu ya katse shirun da ya wanzu a q hanyar duban sauran 'yan uwanshi fuskarshi a murtuke babu annuri ya ce "yaku manyan abokan gaba a gare ni ku yi sani cewa waɗancan dakarun aljanu da suka bayyana ba su ba ne face Tawagar sarakunan aljanu da suka zo domin ɗaukar kubar Miftahul-sihir haɗe da KUNDIN AL'AJABI, saboda haka yanzu dole mu haɗa kai mu kawar da waɗannan sabbin abokan gaba, idan ya so daga baya kuma sai a raba rai tsakanin mu ga wanda zai zamo zakara a, da zai zamo mamallakin KUNDIN AL'AJABI". Koda jin wannan batu daga bakin sarki Hubaizu na birnin Hindu sai sauran sarakunan uku suka zare makaman yaƙin su suka yi ɗauki kan dakarun aljanun, koda ganin hakan sai aljanun suka tare su suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. *** A cikin kogon GARUL-SHAMMAR kuwa kafin mahaifina ya yi wani yunƙuri wannan macijiya ta kafta masa sara a hannayenshi da ƙafafuwanshi, nan take nunfashin shi ya fara sarƙewa kuma ya faɗi ƙasa magashiyan". Lokacin da kyakkyawar baƙuwar jaruma ta zo dai-dai nan a labarin da take bamu sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta. Al'amarin da ya sanya jikinmu ya yi sanyi ni da Raudat har ƙwalla ta zubo mana. Cikin alamun matuƙar tausayi na dubi jarumar na ce "haƙiƙa labarin mahaifinki cike yake da abun tausayi darasi da abubuwan al'ajabi. Kuma ya cancanta ki ɗauki ko wane mataki domin daukarwa mahaifinki fansa, duk da cewar ba mu ji ƙarshen abin da ya faru tsakanin abban ki da manyan sarakunan duniya huɗu ba, duk da cewar da farko mun nufi mu yaƙe ki, amma a halin na ji a raina ni da abokiyar tafiyata za mu taimaka miki ki cimma wannan buri na ki. Amma bisa sharaɗin cewa ba za ki cutar da wani mahaluki ba idan har kin samu nasarar mallakar makaman yaƙin sarkin bokayen duniya". Sa'adda na zo nan azance na sai fuskar baƙuwar jarumar ta faɗaɗa da murmushi mai taushi, ta dube mu sannan ta yi gyaran murya ta ce "ya ku waɗannan jarumai haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki da wannan taimako da za ku ba ni, kuma ina mai tabbatar maku da cewa ba za ku same ni da wani abu na cin amana ko yaudara ba. Kuma a halin yanzu ba zan iya ci gaba da ba ku labarin mahaifina ba sai dai anan gaba, sai dai ban sanar da ku suna na, mahaifna na kira da suna Sulairat bintu Yasiran". Sa'adda Sulairat yar mafarauci Yasiran ta zo dai-dai nan azancen ta sai na yafito aljani Jauharul-layal dake tsaye a gefe guda da hannu da ya iso inda muke, taku ɗaya kacal ya yi ya iso gare mu ba tare da wani jinkiri ba Raudat, Sulairat suka haye gadon bayan shi, take na yi koyi da su ina mai zama da daf da inda suke yazamana tazarar dake tsakaninmu bata huce kamu ɗaya ba, A halin yanzu tafiya ta sauya salo daga mutum biyu izuwa uku, wato ni Raudatul-abyad sai jaruma Sulairat. Sai da muka shafe tsawon sa'a huɗu muna keta gajimare cikin matsanan gudu na keta sa'a, ɗa ya daga cikin mu bai ce uffan ba, a wannan lokaci ne Raudatul-abyad ta lura da cewa Sulairat na satar kallo na lokaci zuwa lokaci, koda ganin hakan sai ta daka mata wata harara dake nuna tsantsar kishi da soyayya. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai mu ka ga aljani Jauharul-layal ya tsaya cak! A sararin samaniya, cikin fushi Raudatul-abyad ta dube shi tana mai daka mashi tsawa ta ce "ya kai Jauharul-layal shin ina dalilin wannan tsayuwa ta ka bayan ka san cewa muna so mu isa fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar cikin sauri ? Koda jin wannan tambaya sai Jauharul-layal ya risina cikin ladabi ya ce "ki gafarce ni ya shugabata bakomai ne ya sanya na dakatar da tafiya ba face bisa jiyo ƙanshin 'yan uwana aljanu a daf da mu, hakan ya tabbatar min da cewa akwai waɗanda ke biye da mu…" Karfin jauharu ya gama rufe bakinshi kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka ga tawagar waɗansu zaratan aljanu kimanin dubu hamsin, sun bayyana a suna masu yi mana ƙawanya, su dai aljanun sun kasance bakaƙe wuluk, masu girma, kwarjini da munin gaske, fuka-fukansu irin na mikiya ne, a gadon bayansu suna ɗauke da wani ƙusumbi da ya tamkar duwatsu aka saka masu, duk sa'adda da suka buɗe bakunan sai wani ruwa mai yauƙi mai warin gaske ya zubo. Baki ɗayan su suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, kuma girman kowannen su ya ninka na aljani Jauharul-layal sau goma. Wohoho! Haƙiƙa waɗannan tawagar ifritai ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, nan fa muka zo tamkar an ajiye kyanwa a gaban garken raƙuma. BABI NA TAKWS Lokacin da boka Matawus yazo dai-dai nan a hikayar da yake bawa sarki Sabrul-marhut sai ya ja dogon goron numfashi sannan ya ɗora da cewa. Lokacin da aka fara kallon-kallo tsakanin mu na tsawon daƙiƙa arba'in sai daga bisani ne shugaban tawagar ifritan aljanun ya ratso ta tsakiyar ya matso daf da mu ya dube mu da turɓunanniyar fuskarshi da ninka ta sauran muni, cikin wata irin kakkausar murya mai kama da saukar aradu ya ce "ya ke Raudatul-abyad tare da tawagarki kiyi sani cewa yau tsawon shekaru dubu da ɗoriya ina jiran zuwan wannan rana da zan karɓi taswirar fadar sarkin bokaye daga hannunki, tsawon shekaru ina bibiyar mahaifinki domin ya mallaki taswirar amma saboda sirrin dake tare shi ban samu wannan dama ba sai a yanzu". Koda jin wannan batu daga bakin shugaban tawagar sai Raudat ta tari numfashinshi tana mai daka masa tsawa ta ce "ya kai wannan rafkananne kuma tsohon AZZALUMI ka yi sani ce wa, ire-iren ka ba za su taɓa cimma buƙatar su domin mallakar wannan taswira ba, domin shimfiɗa BAƘIN ZALUNCI, shawara ɗaya zan baka ita ce ka janye waɗannan 'yan tsakin mayaƙan na ka, idan kuwa ba haka ba zaka yabawa aya zaƙinta…". Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-abyad sai shugaban tawagar ya fusata ainun jikinshi ya kama tsuma ya ƙyarma tamkar mazari, idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur, ya buɗi baki a karo na biyu cikin matuƙar fushi har wani irin tururin baƙin hayaƙi na fita daga ƙofofin hancinshi, baki da kunnuwa ya ce " kaicon ki yake wannan ƙaramar ƙwaruwa haƙiƙa kin tafka babban kuskure, wanda ba zan iya yafe miki ba face na shayar dake gidauniyar azabata da dukkanin abokan tafiyar ki, sai dai kafin hakan akwai buƙatar na sanar dake wane ne ni, da farko dai suna na ifritu Sulsainil-auman ibn Turbus, shugaban ifritan aljanun duniya baƙaƙen fata. Da wannan nake yi miki bankwana ga maza nan bisa kan ki". Koda shugaban ifritai Sulsaini ya zo nan a zancen shi sai ya yi ihu da kururuwa mai firgita GWARAZAN JIYA a FAGEN FAMA ya afka Raudatul-abyad, take sauran yaran shi suka afka mana ni da Sulairat da Jauharul-layal. A can ƙololuwar sararin samaniya inda Allah (SWT) ya yiwa dukkan halittu iyaka kuwa, anan ne uwar mayu Ummul-sharri ta kafa fadarta domin gudanar da ƙasaitaccen mulkinta, A wannan lokaci Ummul-sharri tana zaune a bisa karagar mulki a cikin gawurtacciyar fadarta, Ita dai fadar ta ƙasaitacciya tamkar gari guda, gaba ɗaya ginin fadar an yi shi ne da zallar waɗansu irin duwatsu masu ƙwari gaske suna sheƙi da ƙyalli tamkar gilashi, duk inda mutum zai ajiye ƙafarshi wani irin koren gilashi ne mai kama da darduma, idan mutum ya kalla yana iya ganin surarshi, gefe guda kuwa 'yan majalisa na jinsin mutum da aljan na zaune bisa ƙayatattun kujeru na alfarma, a kowa ce kusurwa a fadar dakarun tsaro ne na jinsin mutum da aljan ɗauke da miyagun makamai suna kai komo domin tabbatar da cikakken tsaro, a bisa wata matattakala mai hawa goma anan aka ajiye karagar mulki da aka yi ta da sallar jauhari, kai tsayawa masalta tsaruwa da ƙawatuwar fadar ya huce hankali, kai wani abun ma ko jin sunan shi bai taɓa yi ba, kana gani ka san aiki ne na sihiri. Shiru ne ya mamaye wajen tamkar mutuwa ta kawo ziyara, uwar mayu Ummul-sharri ce ta katse shirun da ya wanzu ta hanyar sanya hannunta a aljihun rigarta ta ɗauko madubin tsafinta da girmanshi bai zarce faɗin tafin hannuna ba, ta shafe da hannunta na hagu gami da runtse idanuwanta ta karanta waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama furtawa sai ga taswirar gumurzun dake wanzu tsakanin tawagar ifritu Sulsainil-auman da su jarumai Raudatul-abyad ya bayyana a kan madubin. Koda ganin hakan sai uwar mayu ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, mai kama da haniniyar dawakai, sautin ta ya mamaye fadar baki ɗaya, al'amarin da ya firgita wasu daga cikin jama'ar fadar kenan cikinsu ya ɗuru ruwa, domin sun san cewa duk sa'adda uwar mayu tayi wannan dariya to za ta zartar da wani baƙin zalunci, tsawon daƙiƙa arba'in tana cikin wannan hali sai daga bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko mata da WASIƘAR AJALI, kawai sai ya mayar da madubin izuwa ma'ajiyar shi, kana ta dawo da dubanta zuwa ga wani mummunan aljani daga cikin 'yan majalisarta, tamkar ya san abin da take nufi kawai sai ya miƙe tsaye ya matsa daf da karagar mulki ya zube ƙasa ya yi sujjada a gare ta, sannan daga bisani ya ɗago kanshi a ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce "gani gare ki ya SARAUNIYA MAI DUNIYA, gajimare kike mai shayar da duniya mugunyar annoba. Guguwar musiba mai share TAWAGAR ZARATA. ina gagararre ko hatsabibi ya zo ga GAWURTACCIYA uwar matsafan dunya" Kin ci dubu sai ceto kin yi KARO DA DUBU kalacen safe, ina mazan suke ne ga sa gudu maganin ƙi gudu" ANNOBA ƊARI kike duk wanda ya ja dake zai baƙunci barzahu". Lokacin da ɗan majalisar ya zo nan a kirarin na shi sai uwar mayu ta yi murmushi mai kama da yaƙe da ya ƙara tona asirin munin fuskarta, bisa jin daɗin kirarin da yake yi mata. Sannan ta buɗe tafkeken bakinta mai ɗauke da waɗansu wargatsattsun haƙora baƙaƙe babu kyawun gani ta ce "an gaishe ka ya kai Darmanu maganin ƙananan ƙwari abin da nake so a gare ka shine ka tafi cikin hanzari izuwa gaɓar dajin Zarutul-shammar domin ka ƙwato min taswirar fadar sarkin bokaye a hannun jaruma Raudatul-abyad, ina mai farin cikin sanar da kai cewa burina ya kusa cika na shiga fadar sarkin bokaye domin na gaje komai nashi, sirrikan tsafi da kayan yaƙinshi, dole ne duniya ta zamto a tafin hannuna, na juya ta tamkar yadda ake sarrafa waina a tanda, Wannan ita ce dama ta ƙarshe a gare mu domin shiga fadar sarkin bokaye don haka ina mai gargaɗarka ka kula sosai kar a samu kuskure a cikin wannan aiki”. Sa’adda Uwar mayu Ummul-Sharri ta zo nan a jawabinta sai aljani Darmanu ya risina ya ce “an gama ya shugabata wannan aiki abu ne mai sauƙi a gare ni tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai”. Ummul-Sharri ta ce “tsafi ya baka kariya ka dawo cikin aminci ya kai Darmanu”. Koda gama faɗin hakan sai Darmanu ya risina ga uwar mayu sannan ya rikiɗa izuwa wani baƙin haske ya ɓace ɓat daga fadar tamkar bai taɓa wanzuwa ba. Wannan shi ne abin da ya wakana a fadar uwar mayu ta duniya matsafiya Ummul-Sharri. Lokacin da muka kacame da azababban yaƙi tsakaninmu da shugaban ifritai Sulsaini da yaranshi sai muka wanzu muka kaiwa juna hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, ana fara wannan artabu ne dukkaninmu suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin matuƙar zafin nama gami da ƙarfin damtsen ifritan ya ninka namu sau biyar, babban abin da ya dugunzuma hankalinmu shine yadda duk sa'adda makaman yaƙinmu suka sari jikkunan ifritan sai mu ji tamkar dutse muka sara, ko gezau ba sa yi sai dai tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara ƙal! Ƙal!. A duk sa’adda makaman yaƙinmu suka haɗu da juna sai ka ji an kwantsama wata tsawa gami da walƙiya, nan fa sararin samaniyar ya cika da ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu gami da hargowar MAZAJEN DUNIYA. Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu da goma ana wannan ɗauki ba daɗi babu sassauci. A cikin wannan artabu ne na fahimci Sulairat tafi mu ƙarfin damtse da salon dabarun yaƙi, domin a hankali yanzu tana iya samun nasarar yankan jikkunan ifritan, koda suka fahimci irin ɓarnar da Sulairat ke yi masu sai suka yanyame ta suna kai mata sara da suka gami da yakushi da faratansu. A ɓangaren aljani Jauharul-layal kuwa ya wanzu yana kai FARMAKI da fuka-fukanshi, bakinshi gami da faratan hannunshi, cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Lokacin da shugaban ifritai Sulsaini ya ga cewa sa'a ɗaya ta shuɗe ana wannan baƙin artabu sai ya fusata ainun zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone, ya fahimci cewa wankin wula zai kai su dare, wani abu da ya fusata shi shine tun da yake yin GABA DA GABA da jarumai bai taɓa haɗuwa da bil’adama masu matuƙar zafin nama da ƙarfin damtse tamkar mu ba. Lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi, sai ƙarfin damtsenmu ya fara raguwa yaran ifritu Sulsaini suka fara galabaitar da mu, faruwar hakan ke da wuya sai Aljani Sulsaini ya yi ƙara luhhh! Domin ya zillewa ifritan, amma sai hakan ya faskara domin kadoni ya kai ga hakan wani daga cikin ifritan me nacin tsiya ya kafta masa sara a kafaɗarshi, saboda matuƙar ƙarfin sara sai da Jauharul-layal ya kurma wawan ihu, saboda raɗaɗi da zugin da ya ji. Sa’adda jaruma Sulairat taga halin da muke ciki, kuma ta fahimci cewa a koda yaushe ɗayanmu na iya raya rayuwar shi, sai kawai ta shiga amfani da ƙarfin shirin tsafi amma ya zamo a banza, domin da idan ta yi TSATSUBA ta turawa ifritan Kibbau na huta da zarar sun doshi inda suke sai suka zama farin haske su ɓace ɓat! Ana cikin wannan wannan fafatawa ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin samaniya tayi duhu dunɗum! Tamkar DARE BIYU ne ya haɗu waje guda, kuma aka dinga kwantsama tsawa da walƙiya kai ka ce za’a kece da ruwan sama tamkar da bakin ƙwarya. Daga can sai aka ga wata shirgegiyar halitta ta bayyana a sararin samaniya, halittar tana da matuƙar girma fiye da aljani Jauharul-layal, tana ɗauke da fuka-fukai goma a tsakiyar kanta tana ɗauke da wani zabgegen ƙaho mai kama da na rago, batun munin fuskarta kuwa sai abin da idanu suka gani kawai, a gadon bayanta tana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi. Kaico! Haƙiƙa wannan halitta ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, ba wata ba ce wannan halitta ba face aljani Darmanu manzon uwar mayu Ummul-Sharri, wanda ta tura domin ya ɗauko mata taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar. Sa’adda kowa ya yi arba da aljani Darmanu sai aka tsayar da yaƙi kallo ya koma kanshi. Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo sai daga bisani aljani Darmanu ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da saukar aradu wacce ta ɗimauta duk wata halitta dake wajen hatta ifritu Sulsaini da yaranshi, a lokaci guda ya tsuke bakinshi ya fara magana cikin wata irin kakkausar murya mai kama haniniyar doki yana mai cewa “Ya ku waɗannan ƙananan halittu ma’abota ƘARAR KWANA ku yi sani cewa ban zo nan domin kallon fafatawar da kuke yi ba, face sai domin ya karɓi taswirar fadar sarkin bokaye domin na kaiwa uwar matsafan duniya Ummul-Sharri, kira na a gare ku shine ku gaggauta miƙo min taswirar cikin ruwan sanyi domin na yi maku kisa mafi sauƙi ba tare da kun sha wahala ba, ta hanyar da daddatsa sassan jikkunanku. Kafin Darmanu ya gama rufe bakinshi ifritu Sulsaini ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana mai daka masa tsawa ya ce “ ya kai wannan maƙetaci kuma wanda rarraunar zuciyarshi ke yaudarar sa ka ji sani cewa ka tafka babban kuskure, da kake tunanin za ka ƙwaci taswira daga hannun Jaruma Raudatul-abyad, bayan muna gab da mallakarta, wato kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi”. Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Sulsaini sai aljani Darmanu ya fusata ainun, idanunshi suka kaɗa suka yi jajur, gashin jikinshi ya mimmiƙe, kawai sai ya miƙa hannunshi izuwa sama sai ga wata zabgegiyar takobi ta bayyana ta haske, take ya yi ɗauki izuwa kan Sulsaini da tawagarshi, ana haɗuwa aka yi KARON BATTA, nan fa aka garƙame da sabon gumurzu mai matuƙar muni ban tsoro gami da tashin hankali, a wannan karon sai artabun ya canja salo, domin a wannan karon duk inda aljani Darmanu ya sanya a gaba sai dai kaga yaran ifritu Sulsaini na sheƙawa barzahu, takobinshi na raba sassan jikkunansu. Nan fa muka shiga raba idanu domin ba su san wane ɓangare zamu shigarwa yaƙin ba, tun da dukkanin su abokan gabarmu ne. Muna cikin wannan hali ne wata dabara ta faɗo min, koda samun mafitar sai kawai na yiwa aljani Jauharul-layal inkiya ta wutsiyaar idanu, koda ya fahimci abin da nake nufi sai ya faki idanun TAWAGAR ABOKAN GABA ya kaɗa fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! ya keta cikin gajimare ya fara tsala azababban gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya muka ɓace ɓat! Har muka daina hango so. Lokacin da muka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu suna gudun tsira da rayuka, sai ƙarfin gudun Jauharul-layal ya fara raguwa ainun saboda gumurzun da aka sha, domin hakan sai aka yanke shawarar mu yada zango domin mu huce gajiyar dake tattare da mu, cikin hanzari Jauharu ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! Ya sauka a turba, inda muka saukar ya kasance daji mai tattare da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, duwatsu, ƙoramu gami da sarƙaƙiya, muna sauka ne dukkaninmu kowa ya sha jinin jikinshi, domin da ganin dajin ba a rasa miyagun halittu masu cutarwa ba. Da yake akwai inuwar bishiyu sai ya zamana cewa bamu kafa tanti ba, aka fito da abin kalaci kowa ya shiga kimtsa cikinshi. A wannan lokaci ne jaruma Sulairat ta duba mu tayi gyaran murya sannan ta ce “tun da a halin yanzu dukkaninmun mun samu natsuwa zan cigaba da baku labarin abin da ya wakana da abbana tare da manyan sarakunan duniya uku, inda ta ɗora da hikayar kamar haka:- Mu haɗu a littafi na 3 domin jin cigaban wannan kayataccen littafi Mansur Usman Sufi 08137237071