*K'ADDARAR SO* (Destiny Of Love) *©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi SHINFID'A *Shin, wace k'addara ce za ta sa 'yar uwa ya tsani 'yar uwarta ta jini?.* *Shin, yaya za ka yi a lokacin da kika tsinci kanki a tarkon son wanda 'yar uwarki take so.* *Shin, me ya kamata ka yi a lokacin da wanda kake so yake gudunka?* *Shin, wace k'addara ce za ta raba kan 'yan uwa?.* *Shin, K'ADDARAR SO za ta iya sawa d'an adam ya aikata komai?.* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* Chapter 1 *SURURE, LAGOS NIGERIA* Shekara ta 1995 "Mimi nahhh?" Cewar wata matashiyar budurwa dake sakkowa daga kan matakalar bene. Da gudu ta k'ara su inda Mimi take zaune, kiran da take kwala mata ne yasa, Mimi tashi tsaye. Kallonta Mimi tayi ta ce "nikam Lalaah miye hakan?, kike ta kwala min kira fisbilillahi, baga ni ba ina zani" Turo baki Lalaah tayi tana bubbuga k'afarta a shagwab'e, harda lauye kai ta ce "Mimi wani labari fa zan baki, zuwa na shopping na had'u da wan..... K'asa k'arasa maganar tayi ganin kallon da Mimi ke jefa mata. Can kuma Mimi tayi wani murmushinsu na manya, da sauri taja wo Lalaah a kusa da ita, ta zaunar da ita ta kalleta a tsanake. Tukun ta ce "Lalaah ta, bani labari, hala an samomin siriki ne ba?". Kallon Mahaifiyarta Lalaah tayi, cike da d'unbin k'aunarta, domin Mimi irin iyayen nan ne, masu mugun sauk'i kai ga yaransu, idan tana tare da yaran nata kamar wasu jikokinkita haka suke tafiyar da rayuwarsu cike da farin ciki da kwanciyar hankali. Sai dai kashhh wannan magana da Lalaah zata furta ma, Mimi ita, ita ce zata Yi sanadiyar da zata tarwatsa komai, da tasan da abunda zai biyo baya ko shopping d'in ma bazata je ba, bare har suyi tozali dashi, kware shi su duka shine mafarin K'ADDARAR SU, ARMAN HARUN, sai dai kashh sanin gaibo sai Allah. Kuma duk dabarar ka sai ka iske K'ADDARAR KA, a duk inda take. Katse mata tunani Mimi tayi ta sake cewa."i hear you Lalaah told me" Turo baki Lalaah tayi ta sake shagwab'e fuskar nan tata mai d'auke da wani sahihin kyau, kai tsaye idan ka kalleta baza tab'a cewa nan take kyakkywa ba ce, sai kayi mata kallon tsane ke da kyanciyar hankali, tukun zaka fahimci kyan nata bana tashin hankali bane. "Mimi, who do I see in my shopping today?" "Well, I know, you told me, you are sad" "Sorry Mimi nahh, Mimi ai kinsan Doctor Arman Harun Maleek?" "Ni ko nasan Doctor Arman Harun. koba shahararran likitan nan ba, wadda duk duniya tasan da zamansa, waye bazai sansa ba, tunda ko ina ansha fira dashi a gida jan yad'a labarai na k'asar nan dama k'etare. But you are talking about him, you have never seen him before, eyes and eyes since he is not living in the country" Tab'e baki Lalaah tayi ta ce "No, Mimi, did he come to the country, did you not see it in the news?, And shopping d'in dana je ne, muka had'u dashi har mukai magana, zaki yi mamakin shine ya kawo ni har k'ofar gida. with those who fear him, people are so surprised that he stays with me, because the women's movement does not bother him, he even stops to talk to them. kin san Mimi hatta jami'an tsaron sun sha bala'in mamakin hakan da Ogansu harya tsaya ya kula ni ma" ""You're pausing that I don't understand, shi Arman Harun d'in ne, ya sauk'e ki k'ofar gidan nan. I don't want to lie Lalaah" Tab'e baki tayi kamar zata fashe da kuka, ta ce "haba Mimi kin san bana miki k'arya Allah kuwa da gaske" "Na shige su ke miya had'aki dashi harya miki magana, karfa kija azo ace za'a sace mu, yo ganinki da irin wa'innan masu arzik'in ai sai a d'iga ayar tabbaya akanmu, duk arzik'in Ubanku da kuke gani, ko kama k'afarsa baiyi ba, a hakan da ake ganinmu masu arzik'i, kinga Lalaah ki rufa mana asiri". Mimi ta idasa maganar tana waro ido waje, na tsananin mamakin Lalaah, yo taya ma za'ai ace taga wani Arman Harun wadda duk duniya ko ina ansan da zamansa, mutane attajirai kullum na turorowar zuwa ganinsa da sun zuwa asibitin da yake. but they don't get to see him. That's why they hear about him so much, when Lilaah, Lalaah's sister, was working in the hospital at *ARMAN HARUN'S HOSPITAL FAMILY'S*, she was always in the middle of the day, she knew that she would also come back with his story. "to ke Lalaah miye na farin cikin hakan, dan kawaii ya d'akko ki" "Hmm Mimi ni dai kawai na tsinci kaina da farin cikin hakan, ba wata magana mukai dashi ba, hasali ba ko sunana bai tabbaya ba. we didn't say anything to him, in fact, my name is not certain, the stranger knows that he just went to follow him, and I couldn't do it to him, when he saw me looking for a vehicle, kin san ban fita da mota ta ba yau, tana wajan Lilaah" "Who's still Lilaah riding a car for you?. wato ita taga tata, ta fara tsufa ta fara lalacewa, taki kuma sabowa baki je kika lalatata ba wajan iyayi irin nata, wato ita bari ta lalata takin yanzu, ke kuma da yake komai ta nuna tana so ko kina sonsa sai ki d'auka ki bar mata ko?" Mimi ta fad'a rai a b'ace. D'an rausayar da kai Lalaah tayi, cikin kwantar da kai dan kar aga laifin y'ar uwartata ta ce "a'a Mimi wallahi ba ita ta tabbaya ba, ni ce na ga motar tata sai a hankali shine fa na bata tawa. you know Mimi or leave her, I can do it, since you think I'm not going to work, she's going to work". "Ke ni rufe min baki, kowa ai da tasa baiwar, ke ba zane-zanen gini kike ba, wani lokacin ai ana d'aukar ki aikin kwangila wani kanfanin domin kije ki zana masu irin ginin da suke so, sai kuma ki ce baki zuwa aiki, kawai son kan Lilaah yayi yawa wallahi, ai duk Abbien ku ne shike d'aure mata gindi idan tayi wani abun". "And what did I do?" Cewar Lilaah, dake shigowa parlon, sanye take da doguwar abar y'ar Dubai dake jikinta sai kuma farar rigar doctor's dake saman rigar, rik'e take da jaka dake cike da takardu na aiki, sai d'ayan hannunta dake rik'e da key na mota. Can kuma saita d'an ya mutse baki, tana binsu da kallo. D'an dakatawa tayi jin muryar, Mimi dake kiranta a zafafe. Domin tunda tayi magana ta farko na cewa, miye tayi, kawai tana idasa k'arasowa ta fara hayewa sama, inda d'akinsu yake, domin a gajiye take lik'is, ga b'acin rai na Doctor Arman data kwaso, a yau d'in. Tayi dana sanin zuwa gidansu Doctor Arman, duk Bilkees ce tasa ta zuwa, wai taje domin ta gaisar da Mahaifiyarsa. Kware Mahaifiyarsa wacce suka ji ake kira da, My love a gidan, sun samu tarba ta mutumci, Bilkees y'ar uwarsa ce wacce suke Uba d'aya da Arman ita doctor ce, jinisu ya had'u da doctor Lilaah domin zan iya cewa, halayya yazo d'aya. They all love the life of lies and lies and show that they are others, they want a false life, and then God gives them the wealth to show in luck. Zuwan da sukai, sunyi tozali da Ya Arman wadda zasu fito shi kuma zai shiga gidan, Bilkees ta fito domin raka Lilaah wajan motar ta sukai kicib'os. Ta gaida sa sarai yaji, amma yayi k'unnan uwar shegu da ita. Dai-dai gwargwado ta shak'a, yarfin da yayi mata, domin ita macece marar son raini, amma tasan ita ta Siyama kanta rainin tunda ta nuna tana mahaukacin sonsa, kuma ya sani. Shine yake wulakantata. Sai Bilkees ce keta bata baki, kan cewa, ta kwantar da hankalinta insha Allahu Ya Arman ita ce zai aura. Wannan abunne kwai da Bilkees ta ce mata ya sanyaya mata zuciya. But her soul is missing until she returns to the house now, she finds Mimi saying that she loves herself completely. Katse mata tunani Mimi ta sake yi k'aro na biyu, tana kallonta cike da takaici ta ce "wai ke Lilaah yaushe zaki canza wannan halin naki, na rashin sallama, idan zaki shigoma mutane gida?, kuma kin shigo kin iske mutane bak'o gaisuwa, haka na koyar dake?" K'aro na barka tai taja d'an k'aramin tsaki yadda Mimi bazata ji ba, domin ko banza suna tsoron Mimi duk da wasan da take yi dasu hakan baisa taja sun raina ta ba. kai hatta Abbie suna shakkarsa sai dai kuma banda Lilaah, domin shike nuna yafi ji da Lilaah komi take so kota tabbaya kai tsaye yake bata, abunda Lalaah bata yi kenan, yawan tabbayarsa abu, domin ita tana samun kud'i sosai wadda harya d'ara albashin Lilaah, komai dasu take yi, hatta motar ta da Lilaah ke hawa yanzu ita ce ta sake ma kanta, mai tsadar gaske, wadda ba k'aramin tashin hankali ake ba a gidan, a ranar da Lalaah ta sayi motar, sai da Mimi ta nuna b'acin ranta tukun, da Abbie so yayi ya amsheta su duka su zauna babu, sai da Mimi ta nuna sam bata lamunce ba, ta kuma tuna mai da cewa, "ka manta Abbie Lilaah mota nawa ka sake mata ba tare da ka saima Lalaah, tun wacce ka sai masu tare, baka sake sai mata wata motar ba, bayanta ka sake ma Lilaah mota ta kai uku, amma Lalaah bata tab'a d'aga kai ta ce danmi ba, sai yanzu ta samu na kanta ta saya kuma za'a ce baza tai anfani da ita ba, ina ganin hakan ba adalci bane, gaskiya abar mata motarta ta hau". Bai sake maganar motar ba, amma Lilaah ta matsa mai kan cewa, itama fa sai ya sake sai mata mota, wacce tafi ta Lalaah kyau da tsada, dole ya rarrasheta, aka sake mata sabuwar mota wacce tafi ta Lalar, sai dai ba'a je ko ina ba, ta lalata motar. Ta Lalaah kuma tana nan, ganin hakan yasa ta aje tatan take arar ta Lalaah domin fita kunya, dan ita ta tsani, seeing her seen is not enough, ko bata kai ba, tafi son taga tafi kowa haka take so, ita haka take ganin shine dai-dai. Jin muryar tayi tsakiyar kanta, wata iska taji ta gifta mata, kamar tafin hannun mutum ta gani, sai kuma taga han rik'e hannun, da hanzari ta d'ago tana duban Mimi, data d'aga hannu zata sharara mata mari, da sauri kuma Lalaah ta k'araso wajan, ta rik'e hannun Mimi, tana zare ido. "Please Mimi, I'm sorry, I think she didn't hear what you were saying, and kinga yana yin data shigo kamar bata cikin hankalinta fa". Lalaah ta idasa maganar tana sakin hannun Mimi da ranta yake a b'ace Wani kallon tsananin takaici Mimi ke aikama Lilaah ta ce "wato kin maida ni y'ar iska, tun d'azo nake b'ab'aton zance amma kinyi shuru kin kyale ni, yau ga y'ar iska na magana, kuma sa'arki ba?" Bata ce komai ba, sai Mimince ta sake cewa "ai kina jina, mi yasa kika d'au motar Lalaah kika fita da ita, shekaran jiya ba munyi dake zaki ba, Yayanku Aliyu idan ya dawo daga Abuja ba, aje ya tabbayi Abbie ya basa kud'in gyaran motarki a gyara kici gaba da hawan motarki, ki kyale mata tata ba. Didn't we do that?" Lilaah da wani bak'in ciki da hassadar y'ar uwarta ya kamata, wato zama tayi tana zuga Mimi, domin idan ta dawo gida ta k'ara tsanarta akan wacce take yi. "Tabbayarki nake kin tsare ni da ido" K'asa tayi da kanta, jin wani abu wai shi kunya an dizgata danmi za'a mata fad'a gaban K'anwarta, akan wata aba mota, kai ita ce ma ta zubar da darajarta. Why did she borrow it?. "Mimi, you know that Abbie is not in the country, he should not be there and he is called to say something to him, that's why I didn't call Ya Aliyu" Lilaah ta idasa maganar tana duban Mimi "Eh ba shakka, yau kika san da hakan, da da kike kiran nasa yana can fa idan kina son abu, ki dame sa da kira da naci harsai ya baki koya turo miki, sai yanzu da ba kiyi niya ba iyee?" Wani abu ne ya tsaya mata a wuya, har bata san sadda ta ce "ni dai Mimi indai mota ce ga abarta can bazan sake hawa ba, shikenan?" "Da dai yafi miki, dama zakiyi zuciyar hakan" Cewar Mimi tana komawa ta zauna akan kujerun parlon. Wani kallo Lilaah ta watsama Lalaah, ta juya ta haye sama. Da sauri Lalaah tabi bayan y'ar uwar tata, domin Allah ya sani bata son b'acin ran y'ar uwar tata........ *K'ADDARAR SO* ( Destiny Of Love) *©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* Chapter 2 *FUNTUWA, LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA* "wato kin mai da ni y'ar iska, nasa ki aiki, inje gidan da nake aiki na dawo, shine baki yi ba ko?, ko arzik'in tashi ma baki yi ba saboda kin raina ni, makira algunguma", ta idasa maganar tana k'ara shaud'ama wata matashiyar budurwa bulalar dake rik'e a hannunta, data ke jibgar yarinyar, dake k'asa sai uban kuka take tana shure-shure, yarinyar bazata wuce shekara goma sha biyar ba zuwa bakwai. "Wai baki jin mi nake fad'a ba, shegiya y'ar iska tanbad'd'a mai kunan k'ashi?" Yarinyar da har yanzu kuka take, harda majina shab'e-shab'e akan fuskar tata, ta kalli uwar ruk'on ta, wacce tunda iyayenta suka rasu, k'anin babanta ya d'auki ruk'onta, ya kawota wajan matarsa Inna Saude. Gasu a gidan haya, kusan d'aki biyar ne zuwa bakwai a gidan. Tunda tazo gidan take fuskartar tsangwama da kyara wajan Inna Saude. Ta tsane ta, yaranta kawai ta sani su uku, Nanah sai Mafida, sai kuma k'aramar su Hauwa. Yaran basu da kunya ko misik'ala zarratin, gashi basu da kintsi, kamar yadda ubansu yake. Kawun nata shima, (Mahaifinsu Hauwan), shima ba wani kintsatstse bane, domin gari-gari suke bi, suna kid'an Duma, na kwarya da kanguna, gida jan gala, da gidan karuwai, da gidan biki, shine sana'arsa. Baya ba Inna Saude duka wasu hak'k'inta, kullum cikin barinta yake da yinwa, ita ce buga can buga nan, domin dai ta ciyar da y'ay'anta. Sai dai Y'ay'an sun mugun raina ta, ita kuma bata da aiki sai d'ura masu ashar na kwashe albarka, da zagi na fitar hankali, shi yasa ga yaran nan, kullum ba kintsi sai k'ara tab'arb'arewa suke a kullum, Mafida kuwa tafi kuwa rashin kunya da iya tantiranci, dan ita, saita kwana biyu bama ta kwana a gidan ba, kuma ba d'an albarkar da zai ce danmi, garama Nanah duk dai itama sai hankalin, amma Mafida ta ce ban waje, domin duk iskancin da iyayenta suke ji, to ta dame su ta shanye, dama can wajan bariki iyayen nasu suka had'u da juna, shi yasa kullum cikin fad'a suke, kamar kaji. To tunda ya kawo, ma Inna Saude d'iyar K'aninsa Maryam, ta bigi k'irji ta ce bata lamunce ba, shi kuma ya ce sai dai tabar masa gida. Wata shewa ta saki tana cewa "ahayee nanaye, ai nida kai Jafaru, sai dai mutuwa, kuma bari kaji, koda ka sake ni, kasan mazan rasa mazan aure ba, ka kalle ni da kyau Jafaru. Kuma yarinya tunda ka ce dole saita zauna tare damu, shikenan kai ka siya mata kwandon wulakanci da wahala, kai ko kunya ma baka ji, d'aki d'aya kwallin kwal muda yara, komi zamuyi sai mun bari yara sunyi bacci tukun, yaran zamanin da sun san komai, kuma kaje ka sake k'aro mana wani nauyin, kai da bama iya ciyar damu kake ba". Kallonta kawai Jafaru yayi yana yin kwafa ya fice daga d'akin. To tun lokacin Maryam take ganin izaya kala-kala a gidan, ita ce wankau ita ce girki ita share gidan hayar gaba d'aya, ita ce wankin band'aki, kuma duk Inna Saude ce ta yanka mata wannan uban aiki, wankau d'in ma da take yi Inna Sauden ce ke amsowa gidan da take aikatau, idan ta amso saita tulama Maryam su, ta wanke tas kuma bata bata ko asi. To yanzu ma ta bar mata wanki ne, tazo ta tarar da ita, bata yi ba, shine take mata wannan uban dukan na fitar shari'a. Wani kalar mari Inna Saude ta kaima Maryam, ba shiri ta zabura ta mik'e, jikinta na b'ari ta ce "wallahi Inna Saude, Umma ce ta sani gyara mata wake da zatai k'osan yamma, dashi kuma na gaya mata kin sani aiki amma ta ce ita ba babu ruwanta dole ni ce zanyi mata". Maryam ta idasa maganar kanta a k'asa. Kama k'ugu Inna Saude tayi tana jijjiga, tana cewa a zuciyarta "lallai ma Ummar nan, wai ko dan taga gidanta suke zaune ne?, take masu mulkin mallaka haka, kuma ba damar ayi magana ta ce zata kori mutum, da ta san yadda zatai wallahi da sai sun tashi daga gidan hayar nan, domin duk mai kama haya a gidan Umma, idan ka d'ora tukunya to da kasonta a ciki, dole a d'ibar mata, kuma duk dokar data sa dole ne aike binta, saboda wani lokacin basa biyan kud'in hayar kyale su kawai take, suna cin arzik'i, shi yasa ba ubanda ya isa ya tanka mata duk uwar watsin da zatai". Can saita dawo da dubunta wajan Maryam dake rakub'e. Ta ce "to munafuka, ai sai ki tashi kiyi wankin yanzu, tunda kin gama ma y'ar mulkin gidan nan aiki, kuma wallahi na baki nan da awa uku ki tabbatar kin gama wankin nan, domin nayi al'k'awari ina dawowa za'a aika masu da kayan wankinsu". Shuru Maryam tayi, tana jawo kayan wankin ta fara cikin sauri, tana yi tana share hawaye, ga bayanta dake mata wani shegen rad'ad'i. *SURURE LAGOS NIGERIA* Da sauri Lilaah take sakkowa daga sama, tana kallon Mimi dake zaune akan darning table, suna cin abincin safe, ko kallon inda Lalaah take bata yi ba. Ta kalli Mimi ta ce "please Mimi key d'in mota zaki ban, ta hawa gaba d'aya gidan nan, driver sai kaini asibiti.and Mimi, I hope we have food to go with?" Mimi kallon tsaf tayi mata, tana aje k'ofin data kurb'i ruwa a hannunta tukun ta ce "kayan abincin suna a mota ai. I know who you are eating for two days, sometimes it is brought back without eating, Lilaah, I don't like the shashincin, you know" Fatar gushin Lilaah ce ta d'an tattare ta d'an tab'e baki, ta ce "No Mimi ai kin san waye nake mawa night.I just want to pass now and come back" Tana gama fad'a ta wuce da sauri dan bata ma k'aunar Mimin ta sake tsayar da ita, da wani zancan kuma. Da kallon takaici Mimi ta bita itama, sai kuma ta dawo da kallonta wajan Lalaah ta ce "now you are going to go to the company?". "Yeah Mimi yanzu zan wuce, suna so ne idan naje kawai nan take na zana masu irin saffarin ginin da suke so.I will be back for a long time, Mimi, pray for us" Lalaah ta k'arasa maganar tana tashi ta d'au jakarta, sanye take da abaya y'ar Dubai itama, ruwan k'asa tayi mata mahaukacin kyau, sosai ta haskata sosai, sai key d'in mota dake rik'e a d'ayan hannun nata, sai kuma wasu tagardu dake rik'e a d'ayan inda ta rik'e jakar, kayan sun d'an mata yawa, amma haka ta rik'e su sosai, tana niyar barin darning d'in. Taji muryar Mimi tana koro mata addu'a, amsawa take cikin jin dad'i, harta dawo tana mata kiss a goshi, sai kuma ta fice da sauri domin ta makara sosai *K'ADDARAR SO* (Destiny Of Love) *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* Share Fisbilillahi *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* Chapter 3 Ficewa tayi, tana zuwa motarta ta shiga tayi mata key, ta bar unguwar. Wani kata faran company tayi faking d'in motar, a wajan aje motoci. Kota ina motoci ne cike da wajan, mutane nata hadada, d'aga kanta tayi tana karantar sunan Company d'in, gabanta ne ya d'an fad'i, ganin harda sunan Haruns Family a ciki, kardai shima wannan companyn sa ne?, to amma sukam haka suke da d'unbin dukiya?, company nin su nawa ta sani a cikin Lagos, koda yake ko nawa aka ce mata zasu iya mallaka, ba wadda bai san HARUNS FAMILY ba. Girgiza kai tayi gabanta na fad'uwa sosai, har sai da ta dafe k'irjinta, addu'a ta somayi, a sadda ta kutsa kanta ainahin cikin company d'in, sai da jami'an tsaron wajan suka dubata da jakarta, tukun aka bata waje ta wuce, shima sai da ta nuna masu shaidar wace ita. Wani gilashi ne a k'ofar wadda sai ta shiga ciki ta dai-daita kanta na'orurar dake wajan ta tantance ta bata da abun cutarwa, tukun ta bada alama, ta wace. Sauk'e lumfashi tayi dai-dai k'ofar ta bud'e kawaii ta ganta a cikin company d'in, mutane ne da yawa ma'aikata sai hada-hadarsu suke, da yawa ma turawa ne, wani iri taji, ga wani sahihin k'amshi dake fita tare da sanyin AC dake busuwa kota ina, bata san sadda ta lumfashe idonta ba. Kalle-kalle ta fara yi tama rasa ina zata nufa. Daga bayanta taji wata magana ana cewa "are you saying that the person who was invited will do the construction design for Oga?" Ma'aikaciyar ta fad'a dake sanye da kayan aiki, sai Lalaah taga tana mata kallon kamar mamaki kamar irin baza ta iya ba. Tsuke bakinta ta d'an yi ta ce "Yeah I say" "Okay Follow me" Shine abunda kawaii ta ce. Bin bayanta Lalaah tayi, tana kallon irin tsaruwar company nan, hak'ik'anin gaskiya company nin yayi wani mahaukacin kyau na fitar hankali, har idan kana ciki baza ka tab'a gane cewa wai akwai rana a waje ba, bare kayi tunanin a Nigeria kake ma. Tunaninta ne ya k'ara kwancewa ganin sun shigo wani Office mai kama da aljannar duniya, kware haka zata kira sa, saboda had'uwar Office d'in bata san sadda ta had'e wani miyau daya tsaya mata a mak'oshi ba. Kallon Office d'in take cike da d'unbin mamakin had'uwarsa, baza ka tab'a cewa mutum ne ya tsarashi ba, ga girma ga fad'i gashi an zuba kayan more rayuwa a ciki. Wani k'aton table ne mai d'auke da gilas a jikinsa, mai fad'in gaske sai d'aukar kyalli yake, sai kuma wata kujera dake a gabansa dake jujjuyawa, ba kowa samanta da alama nanne shugaban Office d'in yake zama. Sai kuma wasu kujerun guda biyu kamin ka k'arasa da jikin table d'in sai wani d'an k'aramin table dake a tsakiyar su, alama na tarbar bak'i ne idan sunzo, daga can b'angaran dama kuwa, da hagu ko ina AC ce ke busuwa tare da wani mugun k'amshi mai kwantar da hankalin mai shak'arsa. Hannunka na dama kuwa idan ka shigo Office d'in an aje kayan zane, dama ansan da zuwan mai zanen babu abunda ba'a aje ba, ga wani tantausan kafet da aka malala a wajan, daga gefen wajan kuma ga wata firiza nan, sai kujera mai d'an tsawo da aka aje wajan allon zanen. Tunanin Lalaah ne ya katse da barin kallon Office d'in da take yi da kallo na k'urulla, jin matar data kawota take cewa "it's a lot of your artwork and everything, it's Oga's office here. He didn't reach the end, he stopped at his hospital and reduced his work a little, he would like you to finish the drawing, I will pass". Cewar ma'aikaciyar tana dubana, gyad'a mata kai kawai Lalaah tayi. Tana juya kenan tana gaf ficewa daga Office d'in, ita kuma Lalaah ta k'arasa inda zatai aikin daya kawota, taji matar ta sake juyowa ta ce "if you need someone, here's the phone, call me and I'll come" "Okay" kawai Lalaah ta amsa mata dashi, ita kuma ta k'ara juyawa ta fice. Tana fita Lalaah ta sauk'e ajiyar zuciya, ta fara zanenta a tsanake cikin kwanciyar hankali. Ta d'au awa uku tana abu d'aya kamin ta kammala zanan gaba d'aya, ita kanta data gama zanen gaba d'aya, sai da ta kalla ta sake kallo, wayarta ta zaro tana d'aukar zanen, domin yayi mata kyau sosai, ta baje basira a zanen. Dai-dai ta gama d'aukar zanan hoto, taji an turo k'ofar Office d'in, har gabanta ya d'an fad'i, sai kuma taga ma'aikaciyar nan ce ta farko wacce tayi mata jagora zuwa office d'in, d'auke take da wani faranti mai shegen kyau wadda yake shak'e da abinci lafiyayye. Tana k'arasowa wajan ta aje kan table dake wajan, ta matsa jikin firiza ta d'akko lemo ta aje, tana cewa "hello, Oga is about to arrive, am... Maganarta ce ta mak'ale ganin zanen da Lalaah tayi idonta yayi mata tozali dashi. Waro ido waje tayi cike da tsananin mamaki al'ajabi, ta rik'e baki tana cewa "Omo, You are now saying that you have done this design so well?" D'aga kanta kawaii Lalaah tayi tana murmushi, domin ta saba jin haka wajan mutane mabanbanta, idan tayi zane, wasu ma k'aryatata suke har sai tayi a gabansu sun sheda. Matar sosai ta rud'e itama ta d'akko waya tana d'aukar zanan hoto, Ta dad'e tana santin zanan, har tana cewa"lallai Oga zai yaba sosai da wannan zane gaskiya na jinjina miki" D'an kallonta Lalaah tayi jin yanzu tayi mata Hausa, domin tunda suke magana ta d'auka bama tajin hausar ai, ashe tana ji girgiza kai kawai tayi tana murmushi, ta d'an zauna. Ita kuma ta fice ta zan can zanen da Lalaah tayi. Ta kusa rufe awa d'aya a wajan, da gamawa tana zaune kawai ita bata ci abincin da aka aje mata domin ba jin kuma zata iya cin wani abinci a waje ba gida ba, domin bata saba hakan ba. Zamanne ya fara gundurarta, har ta d'an fara sakin tsaki a ranta, a ranta take mitar sofa masu kud'in nan dama haka suke, su wani ajiye ka kana faman jiransu, sai ka ce maula ta zo, ta sake sakin tsaki a fili yanzu. Tana cikin wannan tunani taji an turo k'ofa, a d'an gajiye ta mik'e bata kalli wadda ya shigo ba bare ta shaida waye domin ta juya baya ne, tana cewa "Ohhh, my sister, I'm tired, I think I'm going to go, when your Ogan comes back and asks for my address... Ta fad'a dai-dai tana juyowa had'e da d'an turo k'ara min bakinta, fuskarta ta nuna alamar shagwab'a. ARMAN HARUN, daya shagala da kallonta tun maganar farko data yi, yake dubanta, kallon sani yake mata yana mamakin ina ya tab'a ganinta, sai da ta juyo gaba d'aya ya shaida ashe fa a shopping suka tab'a had'uwa harya rage mata hanya. Sai da PA d'insa yayi gyaran murya tukun, Arman ya lura da irin kallon da yake binta dashi. Sai a lokacin itama taji wani azababben k'amshi ya k'ara bud'e Office d'in, yasa gabanta yayi wata irin bugawa, har k'irjinta na d'agawa. Tama kasa koda motsa d'an yatsanta ne. Har sai da suka iso wajan, Arman kai tsaye inda take tsaye ya nufa, yana takunsa na k'asaita da birgewa, PA d'insa kuwa kai tsaye inda zanan yake ya nufa, yana waro ido tare da zuba santin zanen sosai. Duk abunda PA yake fad'a basa jinsa, domin kuwa wani arnan kallo Arman yake bin Lalaah dashi, har sai da jikinta ya fara d'an rawa, had'e da k'ara turo baki, ciki-ciki ta ce "nifa na tsani kallo" "And I'm the one I'm opinionated about" Taji saukar muryarsa akanta D'agowar da zatai a mamakince domin bata tab'a tunanin yana ma kusa da ita har haka ba, bare yaji miye take cewa, tayi maganar ne iya mak'oshinta, sai dai d'agowar data yi ta gansa gaf da ita, har sai da ta d'an matsa baya kad'an, tana d'an kallonsa ta k'asan ido. Kwarjininsa duk ya cika wajan, sai taji duk tayi muguwar takura, duk da PA d'insa dake wajan, bata so yake ba yana can yana ta zan can zane. Binsa take da kallo, harga Allah Arman, kyakykyawa ne, ba irin shima kallo d'aya zaka kirasa da mai kyau ba, ba fari bane kuma ba bak'i bane, gashi nan dai tsaka tsakiya yake, amma fa dogo ne tubarkallah, dan daya tsaya gabanta saita hango kanta a k'arama. Jikinsa da dantsan hannunsa a murd'e suke, alamar yana kula da jikin nasa, k'irar k'arfi garesa had'e data sadaukai, girarsa had'e take da y'ar uwarta, wadda gashin idonsa zara-zara kamar macen da aka k'arama gashin ido irin na idon mace, sai dai shi nashi ne na asali, bakinsa dake d'auke da jan leb'e, bakin nasa madai daici ne, sai idonsa masu girma amma kai tsaye idan kamai kallon tsaf baza tab'a wace idonsa masu girma bane, domin kullum a shanye suke kamar mai jin bacci, sai idan yana cikin b'acin rai ko wani abu, ya ware su zaka san idonsa masu girma ne da haske kamar farin wata, ciki kamar an zuba masu madara. Muryarsa taji kamar ana busa mata iska mai dad'i ko na ce sarewa, saboda taushinta da kaurinta, yana cewa "look, don't eat me" Wata muguwar kunya ce taji ta kamata, ashe haka ta jima tana kallonsa, dan har ya kai kujerar table d'in ya zauna, ita tana a tsaye harya gifta ta ya wuce bata ankara ba, sai da taji saukar muryarsa. PA d'insa ya d'akko zanen yana nunama Ogan nasa. Shi kansa daya yayi tozali da zanen sai da d'ago da sauri yana binta da kallon mamaki, jinjina kansa yayi yana nazarinta, lallai nan gaba ba k'ana nan kud'i wannan yarinyar zata samu ba kuwa. Tattare kayanta ta fara yi tana idasawa, ya dubeta a tsana ke, ya lura ko abincin da aka kawo mata bata tab'a ba, sai yaji ta k'ara birgesa, alama bata cin abinci a ko ina, haka kawai ta sake shiga ransa. Amma idan ya kalleta tana mai kama da ciwon kansa wato Lilaah kenan, amma shi sai ya d'auka ko kawai shike ganin kamar, kodan kullum tana damunsa da soyayyar shirmanta a kullum, wadda ta gama felank'enta baya ko kulata ko yanzu da ciwon kanta data sashi ya baro hospital d'in. Katse tunanin Lilaah yayi, yana kallon Lalaah alama yayi PA d'insa, PA na ganin haka yasan miye. PA ya juyo inda Lalaah take ya ce "Oga ya ce zaki iya bada katin ki da account number zaki ga sak'o" "Okay" kawai ta ce tana sa hannunta a jakarta ta d'akko wani firin kati mai d'auke da komai da suke buk'ata, ta mik'a ma PA d'in, tana mik'a masa tayi godiya ta fice, PA d'inma na gode mata. Ogan naku kuwa wasu ayyukan ya kama, amma hankalinsa rabi na gareta, harta fice, a sadda ta idasa ficewa ya samu kansa da sauk'e wata irin ajiyar zuciya, daya rasa ta miye... *FUNTUWA, LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA* K'as k'as k'as, sautin taunar chingum d'in da Mafida ke tauna a bakinta, ya karad'e tsakar gidan, harta idasa shigowa tsakar gidan, d'auke take da tallar mangwaro da Kawu Jafaru ya k'irk'ira samata, kuma ya d'aure mata gindi na zuwa tallar kwaro-kwaro gari-gari. Wadda har Inna Saude tana ganin ana ciniki tasa hannun jarinta. Sai dai kuma duk sadda kud'inta suka b'ace ko y'ar biyar ce ranar Mafida mugun duka take ci, ko kuma suyi bigi in bugu ita da uwar. Yauma tana shigowa, ta aje kayan tallar, tana yamitse biki, Maryam dake zaune tana tsintar waken Umma, daya zame mata dole a yanzu, a kullum kuma, duk da Inna Saude bata so kullum cikin yada ma Umma magana take, amma fa sai idan bata a cikin gidan. Da sauri Inna Saude ta yaye labulan d'akinta tana fituwa gaba d'aya, tana bin Mafida da wani kallo, sai can ta ce "to yar iska daga ina?, yau kwananki biyu baki gida gidan ubanwa kika je shegiya, kuma ina kud'in mangwaro na bani bani maza tunkan na sab'a miki kamanni wallahi" Sautin k'as ne ya k'ara fitowa daga bakin Mafida tana duban uwar tata a wulakanci ta ce "ke ni Inna Saude ba sai ki bari na d'an huta ba tukun ko miye sai ayi". Haka suke kiran uwar dashi babu ruwansu yadda kowa yake kiranta dashi haka soma. Wani kallon baki isa ba wallahi Inna Saude ta bita dashi. Matsowa Inna Saude tayi, tana sa hannunta ta warce wata y'ar jaka dake k'ugun Mafida. Sauke numfashi tayi ta koma gefe ta k'irga kud'in dake ciki yafi a k'irga ganin basu kai ko kwatar kud'inta ba, yasa ta warga ma Mafida wani kallon zaki ci uban ki yau kuwa. Mafida ko a jikinta ta ce "Inna Saude ki daina min haka, dakin bari a tsanake na baki kasonki tunda kinga bake kad'ai keda shi ba". Ta idasa maganar cike da rashin kunya tsantsarta. Wani kukan kura Inna Saude tayi ta jawo Mafida ta tuma da k'asa ta taushe ruwan cikinta ta fara kai nata naushi kamar ta samu abokin danbe, Mafidar itama batai wasa ba wajan kai mata cizo da yakushi, amma ko a jikin Inna Saude, dama ga Inna Saude jikinta a murd'e yake, saboda aikin wahalar da take yi ita ce buga can buga nan, ga k'arfi kamar na doki, kwata-kwata suffar Inna Saude kamar bata mata ba, kamar wani basamudan k'ato. Yanzun kar kaso jin k'arar naushin da take kaima Mafida, sai ihu take, Inna Saude na kwashe mata albarka tana cewa "ai wallahi gara na jifgi kud'i na, gobe ma ki sake kashe min kud'i, kina can d'akin k'ato kin kwana kin kashe mai kud'i mai makon ke ki samu kud'in amma da yake ke y'ar iska ce wacce ubanta ya gama lalatawa ya d'oraki kan hanyar da bazata b'ille ba gara...... Maganar Inna Saude ce ta mak'ale jin an rik'e mata hannu, juyowa tayi tana duban, D'an Lami, D'an daudu ne daya lak'aba ma kansa dole Lami sunansa, shima haya yake a cikin gidan. Fisge hannunta Inna Saude tayi, tana bin D'an Lami da kallo, da yake tab'a hannu yana y'arfar dashi, yana lauye hannu tare da rik'e k'ugu yana cewa "Ohhh ni Lami miye zan gani haka?, haba Inna Saude ya zaki turmushi K'awata haka, kina jifga kamar kina dukan k'ato, kin san fa mu mata ba'a mana irin wannan dukan...... Katse sa tayi a zafafe tana cewa "kai dalla rufe min baki, d'an daudu kawai dake, kana garjejen k'ato dake kike kiran kanka da mace, Allah wadaranka wallahi" "A'a Saude bari kiji na gaya miki ni Lami ba'a min haka yawwa, yada magana zaki rink'a maida ni namiji k'ato fisbilillahi, ya Hakan" D'an Lami ya idasa maganar yana tab'a hannu tare da yin fari da ido. Wani takaici ne ya kama Inna Saude wani dogon tsaki taja tana sake cewa "kaga d'an Lami.... "Ahh ahh dakata Saude ya haka wai, kike kira na da D'an Lami, Lamin ce baza ki iya cewa ba ko mi?, ya kike maida ni namiji ne wai" D'an Lami ya katseta yana daka tsalle kamar wata mace. Maryam dake gefe tana jin abunda ke faruwa, wani ya sata murmushi wani takaici. Tana tunanin lallai Nanah tayi sa'a da aka d'auketa aikatau a can Abuja, gidan da Inna Saude ke masu aikin abinci nan ne d'iyar gidan tayi aure a Abuja, ta haihu, shine suka nemi mai tayata aiki mai mata rauno, Inna Saude bata b'ata lokaci ba, wajan bada Nanah, yanzu kusan shekara d'aya Nanah bata gidan, Maryam tana tunani lallai dama ita ce tabar gidan, da ace Nanar na nan, da itama yanzu tabi layin Mafida wajan yawon banza da rashin kan gado......... *K'ADDARAR SO* (Destiny Of Love) *©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* Chapter 4 *SUKUNTUNI, K'ARAMAR HUKUMAR KANKIA KATSINA STATES* Da gudu ta shigo y'ar k'aramar bukar su, zan birki tayi jin yadda Inna Wuro ke kuka kamar ranta zai fita. Zubewa tayi k'asa tana zare ido k'irjinta na bugawa kamar zai rab'e gida biyu. Idonta har yanzu Baffanta yake gani kwance cikin jini a tsakar d'akin da alama kukan da Inna Wuro ke yi kamar na mutuwa ne, wata wawar faduwar gaba ce ta rinki Fulani dake zare ido har yanzu tama k'asa magana. Inna Wuro tayi saurin juyowa jin motsi a bayanta, kuka ta sake saki tana cewa "Fulani sun kashe mana Baffanki, ki duba tunda abun nan ya faru suka sassare shi bai k'ara lafiya ba, mi yasa baza su gane mu ba y'an ta'adda bane?, muma kanku masu satar mutanan idan suka samu sace mu suke, mutum nawa aka d'auka a rugar nan, amma mutane sunk'i su barmu mu huta, ki duba fa Baffa bai san hawa ba bai san sauka ba, kawai cikin dare suka shigo suka kamasa da duka, wai ai shine ya sace masu D'an uwa, wayyo Allah ya suke su muyi da rayuwarmu ne?" A yadda Inna Wuro ke rusa kuka tana dawo da abunda ya wuce na baya zaka san cewa ta fara fita daga yaccinta ne, domin sai surutu take zubawa hawaye na mata kwaranya a idonta. Rushewa da kuka Fulani tayi iya k'arfin kamar ranta zai fita, jikinta har wani jijjiga yake. Tsoro ne ya kama Inna Wuro ganin yadda Fulani ke yi, kamin tayi wani yunk'uri Fulani ta zube a sume. Wata gigitacciyar k'ara had'e da salati Inna Wuro ta ramka, wadda ya zawo hankalin mutane wajansu. Fitowa Inna Wuro tayi rik'e da Fulani tana kwalama sauran yaranta kira ba k'ak'k'autawa, da gudu samari guda biyu suka shigo cikin gidan. Sai yanzu ne na k'are ma gidan kallo, ashe ginin k'asa ne, sai ka shigo daga cikin gidan zaka iske buka guda biyu, sai d'akuna biyu sai inda suke sanwa dake gefe. Usman ne yayi saurin amsar Fulani gabansa na fad'uwa yana cewa "Inna, ba munce karki bari Fulani taga gawar Baffa ba?, mi yasa kika bari ta gani". Ya idasa maganar cike da ciwon abunda akaima Mahaifinsu. "Usmanu, ya za'ai bazata sani ba wadda ko gawar ba'a shirya ba ta shigo da gudu, dama daji taje wai samo masa maganin ciwon k'afarsa da aka bugeta sosai ita duk d'aukarta zata iya samo masa gani, bata san ashe Baffa tafiya zaiyi ya barmu ba". Inna Wuro ta k'are maganar kuka na sark'eta. Audu dake gefe bai tanka ba, daka kallesa zaka san a zuciye yake, idonsa yayi jawur ba alamar hawaye sai bala'in dake cikinsu na d'aukar fansa tsantsarta. Juyawa yayi kawai zai fuce waje, Inna Wuro tayi azamar tsayar dashi ta ce "ko kusa ko alama ban lamunce maka d'aukar wani mataki ba, indai akan abunda ya samu Baffanku ne, ku barsu suda Allah, ko suwa ye sukayi hakan" "Amma Inna, saboda mi?, da kin kyale ni munje nida abokai na mun tada fitina a cikin garin nan, dole a fiddo mana wadda suke wannan aikin" "Kaima baka ji mi kake cewa bane Audu?, babu dad'in ji, wai fitina miye affanin tada ita to, tunda bamu san su waye sukai mai hakan ba, sanin kanka ne ka sani cikin talatainin dare suka shigo gidan nan, sukai mai wannan ta'asar ku kyale komai ya wuce. Yanzu abunda nake so duka kai Usman shiga da Fulani cikin bukka, kar a watsa mata ruwa har sai ankai Baffah Mlm makwancinsa na gaskiya, idan yaso sai a watsa mata ruwa ta farka, domin suma tayi, bana so ta sake tashi taga gawarsa wani abun ya sake samunta itama" Inna Wuro ta k'are maganar, har yanzu hawaye ke zuba a idonta, dauriya ce kawai take, domin ji take kamar zata had'iye zuciya ta mutu itama. Ba yadda Audu yayi iya, haka aka kira mutane aka sallaci Baffa aka mik'asa makwancinsa na gaskiya, sai lokacin Audu ya shige d'aki yana durzar kuka kamar ba gobe. Shi ko Usman sai da Fulani ta farka, tana kuka mai ban tausayi ne ya rungumeta shima ya fashe da kuka. Inna Wuro dake dubansu ta ce "ya kamata ku daina kukan nan haka nan, addu'a kawaii yake buk'ata" Fulani ta d'an janye daga jikin Usman ta ce "shikenan yanzu Baffa na, ya tafi bazan sake ganinsa ba kenan?". Wasu hawaye hawaye Usman ya sake share mata ya ce "ki daina kuka haka nan kinji, baga muba tare da ke kuma zamu ci gaba da kasancewa a tare da ke". Wata irin fad'uwar gaba ce haka nan Fulani taji ta sameta lokacin da Usman ke yin maganar, wani irin kallo take binsa dashi, har sai da ya hura mata iska yana mata murmushin yak'e yana sake cewa "ya da wannan kallo haka kamar na baza ki sake gani na bane, muna tare fa". Da sauri ta lumfashe idonunta gabanta na tsananta fad'uwa, kyakykyawar fuskarta duk tayi ja saboda da kukan data sha, har yanzu wasu hawaye ke sake wanke mata fuska, domin harga Allah fad'uwar gaban da take ji tayi yawa, ga girarta da hagu da take ji tana mata motsi sosai, ga wani irin k'uncin zuciya dake taso mata, duk maganar mutane da su Inna Wuro ke mata na ta kwantar da hankalinta haka nan, amma ina tayi nisan kiwo, ita kad'ai tasan miye take ji a cikin jikinta. *HARUN'S FAMILY HAUSE, LOGAS NIGERIA* "Ai Binta nake gaya miki shegen yaron nan ya dawo, ya kama aikinsa kamar yadda ya saba, inaga fa asirin nan da boka ya bamu bai kamasa ba kwata-kwata nake gaya miki, abun ya fara bani tsoro, yaro sai ka ce aljani komai akai mai baya kamasa dandanan, koya kaman bai wuce na y'an kwanaki abun ya b'aci". Haj Shuwa ta fad'a ranta a b'ace, rik'e take da waya a manne a kunnanta. Daga cikin wayar Aminiyarta ta ce "ai ko dole a sake sabon shiri, domin a tarwatsa rayuwarsa, shi d'in mi Aunty Shuwa har da zaki tsaya kina b'ata ranki a banza, kika ma b'atar da wasu kuma suka b'ace duniya bata sake jin d'uriyarsu bare Arman shi a wa, dole ya fad'a tarkonmu karki wani damu idan yasan wata ai bai san wata ba". Wata shewa suka saki, sai kuma Haj Shuwa ta sake cewa "amma fa ina ganin kamar y'ar iskar abokiyar zaman can tawa itama fa tana shirin wani abo, domin duk ina ganin take-takenta so take Bilkees ta auri Arman, ita kuma Bilkees bata sonsa, bai cikin wadda take so, so take tayima wata k'awarta kamunsa wai wata mai suna Lilaah, duk ina sane da duk abunda suke k'ullawa". "Lallai Bilkees bata da wayo, mutum kamar Arman ka ce wai baka sonsa. Amma Aunty, kina ganin baza mu sake shiri ba, nasa Salma ta dawo gidanku da zama, ko Allah zai sa muma mu had'ata da Arman aure, muci dukiyar, idan yaso daga baya musa ta kashesa, amma ya kike gani" Wani shuru ya d'an gifta sai can Haj Shuwa ta ce "tabbas kin kawo shawara mai kyau y'ar uwa, ai da duk ni ban kawo hakan ba, kinga ni dama kinga Bobo baida wani aiki saici gashi nan yayi wata shegiyar k'iba, ina so ya zama wani abu amma ya za'ai ya zama yana a haka?" "Karki damu Aunty, Bobo shine zai gaji dukiyar Alhaji" "Nasan da wannan amma, ni dukiyar Alhaji Harun nake so, bawai dukiyar Mijina ba, domin Alhaji baida dukiyar Alhaji Harun ko kama k'afarsa baiyi ba, wajan dukiya, kina fa gani duk arzik'insa muke shida yaronsa tilo Arman, da uwarsa Haj Badiyya, ko kishiya fa bata da ita, daga ita sai yaranta su biyu, Arman da Sa'adha. Sai mune y'an cin arzik'i nida kishiyata, wacce aka laluk'a min ita, shi Alhaji Harun baiyi auran ba sai K'aninsa da aka zugasa yayi, shida maida wani abun duniya, ai wallahi duk wadda ya zuga Alhaji ya auro wancan guzumar ban yafe masa ba". Haj Shuwa ta k'are maganar idonta jawur. Binta dake cikin wayar ta ce "ya kamata duk ki manta da wannan abun wadda ya wuce, ki tuna fa, kinyiwa k'awar Haj Badiyya kurciya tabar gidan nan da cikin, mijinki, wadda shekara kusan goma sha takwas kenan babu amo babu labarinta, sai bayan b'acewarta ne aka sa ya auro Haj Zulaihat, harta zo ta haifi Bilkees, itama Haj Zulaihat d'in dakin bada dama da tuni an kawar miki da ita" "Na tuna da wannan, ni nama shafe babinta ai tuni, ta mutu ita da cikin insha Allahu, sana kuma Haj Zulaihat ita ina da wani babban shiri kuma k'udurin da nake son cikawa da ita. Ita na barta ne a bisa dalili nawa, zaki jisa nan gaba kad'an" Motsin bud'e k'ofa, Haj Shuwa taji, hakan yasa sukai sallama da Binta, suka tsayar da maganar Salma zata dawo gidan. Inna Kande ce mai aiki ta turo k'ofar d'akin. A wulakanci Haj Shuwa kuma a tsawace ta ce "Kee kee ya haka, zaki rink'a shigo min d'aki bako sanarwa, bana hanaki shigo min d'aki haka kawai bane?" Ta k'are maganar a tsawa ce "Haj kiyi hakuri dama Haj Babba ce ta ce na kira ki abinci za'a fara ci ya kammala a darning table" Wani dogon tsaki taja, tana cewa "naji gani nan fitowa" Da sauri Inna Kande ta juya tana rufo k'ofar a hankali kamar wacce ke jin tsoro karda k'ofar ta b'alle. Sai da ta sha iska, da mula dan kanta tukun ta fito, a yanzu asha wani wanka na fitar hankali ansha ado sai walwali take. Domin Haj Shuwa irin matan nanne wadda kota ina basu so suga an wuce su kota ina, sunfi son suga sune gaba, game da komai. Kwasss kwasss kwasss. Takun tafiyar Haj Shuwa dake sakkowa daga matakalar bene dake shashinta, ta nufo parlo. K'atoton parlo ne, wadda tsayawa ma fasalta maku shi b'ata baki ne. Gaba d'aya ginin gidan irin na K'asar India ne, irin na masu kud'in cikin K'asar, wadda girmansa da fad'insa, sai wani d'an k'aramin K'auye su zauna a cikinsa, har yayi masu yawa. Kai hatta darning table d'in girmansa ya isa, kalar ruwan zinari ne, gaba d'aya parlon hatta kujeru kuwa, su kansu kujerun sun k'eru iya k'eruwa, kamar na gidan sarauta, haka kalar su take, da tsarinsu, ga wasu mahaukatan labulaye iya ganinka, kai tunda nake ban tab'a ganin irin saffarinsu ba, iya kyale-kyale an zubasa a wanga parlo ga wasu mahaukatan Ac ta k'asa data sama, da suke bada wani mugun k'amshi ko ta ina busowa suke, komai yaji sai wadda ya gani, kai ko fadar shugaban k'asa iya abunda za'a iya zubawa kenan. Ba wadda bai d'ago ba ya kyalleta sai mutum biyu, My love, da Arman dake zaune a kujera dake kallon juna. Tana kallonsu, sai zuba mata tab'ara yake, amma ba wadda yake fuskantar hakan, sai su biyu ne kad'ai. Ita kuwa Haj Shuwa tunda ta sakko idonta na akansu, wani kalar bak'in ciki ne da hassada ya turnuk'eta. Idonta ne ya kai kan Haj Zulaihat data ciki ta batse, saura kad'an tayi bindiga, Saboda yadda taga Alhaji na bin Haj Shuwa da kallo. Itama tabbas tayi gayun iya gayu, amma sai take ganin na Haj Shuwa yafi nata nesa ba kusa ba, hatta kayan kai da ka kallesu zaka shaida tsadar kayan ba d'aya ba ce da nata, shaid'an ne ya fara zugata, a zuci take cawa "wato Alhaji dama kud'i yake ba Haj Shuwa ita da y'ay'anta, ita kuma yake ware ta da nata Y'ay'an, idan ba shi ba waye zai bata kud'i harta sayi irin wannan kaya haka, gwala-gwale. Wani farin ciki ne kuma ya kama Haj Shuwa ganin kishiyar tata ta shak'a iya shak'a kuwa, dama haka take so tark'onta ya kama. Gaba d'aya ahalin gidan suna zaune ne akan darning table d'in, sai wasu y'an tsiraru ne da babu, wadda Y'ay'an y'an uwa ne. Arman ne farkon tashi yana ma Mahaifiyarsa kiss gushi, yayi mata sallama tare da iyayensa Maza, yayi Maza ya fice domin ya makara yau wajan aiki. Yana tashi Haj Zulaihat ta zunguri Bilkees dake kusa da ita, murya k'asa-k'asa ta ce "shashasha, ki tashi ki bisa ku tafi tare mana. Duk ba waje d'aya kuke aiki ba, na ce ki rink'a d'an shige mai yasan da soyayyarki amma kullum ina tufka kina warware wa ko?" "Haba Momy, kullum fa saina mai-maita miki cewa Bestie na Lilaah ke son Arman, ni kuma zan iya sadaukar mata da komai kin sani" "Bestien ta ce bura ubata, kinji?. Kiji min shashashar yarinya, wacce bata san inda ke mata ciwo ba, ai da alama Lilar ta fiki hankali, wacce mace ce zata bari irinsu Arman su sub'oce masu. To bari kiji tun wuri ma gara ki fito ki fad'a mata kece keda Arman, ba ita ba, domin ina doran duniya dai ba wacce zan bari ta auri Arman bake ba, dan sai inda k'arfi ne ya k'are" "Haba Momy kiyi magana a hankali mana sosai, nidai gaskiya bazan iya iyama Lilaah haka ba, dan baki san yadda take sonsa bane in.... Buge mata baki tayi, ba wadda ya lura da su. Sai dai Haj Shuwa tana ankare da duk abunda suke, saboda fad'in darning table d'in kuma nesa suke da kowa, shi yasa ba wadda yake lura da rad'ar da suke yi. Haj Zulaihat ta sake cewa "zaki tashi ki bisa ko kuwa, sai ranki yayi mummunan b'aci?" Turo baki Bilkees tayi tana tashi a hankali yadda ba wadda zaiji sai Momyn tata, ta ce "nifa Momy bazan tab'a iya abunda kike fad'a ba, kuma indai Arman ne kin san zuwa yanzu ya tafi, tunda kinfi kowa sanin halinsa, ba jirana zaiyi ba, kuma koda na ce ya tsaya mu tafi tare ba yi zaiyi ba, kin san yadda ya tsani mace wacce take zubar da darajarta ta mace kuwa a wajansa?, to ko Lilaah kullum cikin damuwa take da fama dashi, har yanzu ba wani kulata yake yi ba, nikam bazan iya wannan abun..... Maganar Bilkees ce ta mak'ale ganin wani kallo na takaici da Haj Zulaihat ke binta dashi, ba shiri ta rataya jakarta da d'aukar farar rigarta ta doctor's ta sagalata a hannunta, tana ciro key d'in motarta ta k'ara gaba. Tana mitar mutum da motarsa amma ace yaje yana k'aramar murya. Ta idasa fad'ar hakan a ranta, dai-dai ta k'araso inda ake ajiye motoci, ta shiga tata, tayi mata key, aka bud'e mata kafcecan k'aton get d'in, wadda masu tsoron wajan zasu kai su biyar, baccin masu tsoron gidan dake shawagi a harabar gidan, kota ina. Harta fice suna d'aga mata hannu masu aiki a harabar gidan, masu ba fulawowi ruwa, tare da masu wankin motocin gidan........... *K'ADDARAR SO* (Destiny Of Love) *©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* Chapter 5 *FUNTUWA, LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA* Tunkwal tunkwal tunkwal. Sautin dakan da D'an Lami keyi a tsakar gidan, yake bada wannan sautin. Dakan yake abunsa, yana yi yana chab'e tab'aryar, yana wak'ar umar m sharif, yana tab'awa had'e da rik'e k'ugu. Yanzu ma d'an dakatawa yayi da dakan gana duban Maryam dake wanki a duk'e a k'asa, fari yayi da ido, yana cewa "ke y'ar uwa ke kuma a haka zaki k'are da zaman gida, da bautawa wasu, ya kamata dai ki san abunyi kinji k'awalli?" Dubanta ya sake yi jin babu abunda ta ce, kai bama ta d'ago ba bare har yasa ran zata tanka masa. Tsaki yaja yana cewa "miskila kawai" yana murgud'a baki. "Ahayee nanaye". Ya saki wata shewa ganin Mafida an fito za'a tafi yawon data saba. Matsawa yayi suka tab'a da Mafida, suna sakin shewa kamar wasu abokai. "Kai kin ganki kuwa ta waje na, kyau iya kyau, dan uban namiji dole ya sara miki, dole k'anwar nak'i kici kud'in k'ato, ahh ahhh haaayeee", ya idasa maganar tare da sakin wata shewar Fari tayi da ido, tana cewa"kai Lami shi yasa fa, duk gidan nan, nafi shiri dake, ke d'in k'awar arzik'i ce. Ni ko ya maganar mu ta zuwa wajan Malamin nan, ka amso mana ganin nan, kasan wannan harkar dole ake had'awa da Malaman tsubbu" Wata shegiyar dariya ya saki yana tab'a hannu, ya ce "ai kin san Lami bata wasa da Malaman tsubbu kwaro-kwaro lingu-lingu, ba inda bata san inda Malamai suke ba, ai ko nan da birnin sin ne, indai nasan Malamin tsubbu yake to sai na je can, domin duniyar nan ba'a zama haka" Dariya suka sake saki had'e da shewa. Maryam dake jin mi suke cewa, yasa ta saki ajiyar zuciya, tana binsu da kallon takaici, bare ma Mafidar wai y'ar uwarta ce haka, ita kam baccin ance dangin Mahaifiyarta ba'a san inda suke ba, kawai dama K'anin Kawu Jafaru ya had'u da ita, ya taimaka mata ya aureta, amma harta koma ga Allah basu san danginta ba. Wasu hawaye ne taji suna shirin zuraro mata, ba shiri ta kai hannu ta share su, tana addu'ar duk inda dangin Mamarta suke, watan wata rana, Allah ya sadata dasu. *SUKUNTUNI K'ARAMAR HUKUMAR KANKIA KATSINA STATES NIGERIA* "Zauna Fulani ina so na sanar dake wata magana wacce ya kamata ace kin sani a yanzu, domin ina ji a jikina kamar lokacin sanar dake ne yayi" Da mugun sauri Fulani ke duban Inna Wuro dake maganar, ganin ta d'akko wani k'unshin zani had'e da wata sark'a. Usman ne ya jawota a jikinsa ya zaunar da ita. Audu kuwa bai so Inna ta sanar da Fulani abunda ya dad'e da shud'ewa ba. Inna ta ci gaba da cewa "hak'ik'anin gaskiya, Fulani, nida Baffa Mlm ba mune muka haife ki ba..... Wata irin hajijiya Fulani, ta fara gani, duk da a zaune take, amma gani take kamar juyata ake, maganar ce ta dake ta tunda take a duniya bata tab'a jin magana makamanciyar wannan ba. "Inna, amma dai wasa kike min ba?" "Fulani mun tab'a wasa irin wannan dake ne?, ki natsu kiji abunda nake son sanar dake" Kwata-kwata Fulani ji take kamar ba'a duniya take ba, wasu zazzafan hawaye taji suna zub'o mata, kai ina hakan bazai yuwu ba, tunda taso ita su Baffa ne ta sani a iyayenta, koda wasa basu tab'a nuna mata wata alama da zata fahimci cewa ita ba y'arsu bace, amma rana d'aya azo ace mata wai ba sune iyayenta ba, ina hankalinta bazai tab'a d'auka ba. Tashi tayi a zabure tana girgiza kai, tana cewa "wallahi Inna bana son sanin gaskiyar, ni dai ki barni a hakan, dan Allah Inna ki ce min wasa kike" Wata tsawa Audu ya daka ma Fulani, wacce tasa ta koma ta zauna ba shiri, jikinta ya kama kyarma hawaye na zuba kamar an bud'e fanfo. Inna Wuro ta kalli Audu tana watsa masa harara, k'asa yayi da kansa yana batsarwa. "Fulani ba wasa nake yi ba, tabbas ba mune muka haife ki ba, ki bani aron hankalinki kiji ya aikai kika kasance tare damu" *Shekarun baya da suka wuce* Tsaye Baffa Mlm yake, ya gama yo itacensa yana niyar d'auka domin ya nufi gida, Usman dake can yana k'ora masu shanaye da basu wace guda goma ba. Kamar ance Baffa ya juya ya hangi, wata mata yashe a k'asa duk taji ma kanta ciwo kamar bacci take kamar a sume take, ga k'aton ciki da take d'auke dashi. Da zafin nama, Baffa Mlm ya kwad'a ma Usman kira, ba shiri Usman ya zo da saurinsa harda had'awa da gudu, ya iso wajan. Ganin abunda Baffa ya gani ne yasa ma Usman d'an tsorata, d'an ja baya yana cewa "Baffa, ko dai aljana ce karka tab'a ta Baffa" "Haba Usmanu, ya zaka ce karna tab'a ta, kama min ita muje gida da ita domin mu bata taimako, baka ganin tana bukatar hakan, kuma ba aljana ba ce mutum ce, kuma koda aljanar ce ai mu da niyar taimako muka zo". Ba yadda Usman ya iya haka ya taimaka Baffa wajan kama matar, domin yasan Baffah bazai fasa taimaka mata ba, shi haka yake da tsananin tausayi da kuma taimakon jama'a. Shigowarsu cikin gidan, Inna Wuro dake madafa tana d'umamen tuwo, taji Baffa na kwala mata kira. Da sauri ta fito daga madafar, abunda ta tarar ne yasa itama waro ido waje, gabanta na fad'uwa ta ce "Baffa ina kuka samo wannan kuma?". "Yanzu dai kije ki samo min ruwan zafi, zan had'a mata magani, sana ki taimaka mata kiyi mata wanka, ki gyara mata jikinta, kayan dake jikinta ki tabbatar kin adana su saboda da nan gaba" Da to kawai Inna Wuro ta amsa, tana tashi domin cika umarnin mijin nata. Duk abunda ya kamata sai da Inna Wuro tayi, kayan kuma ta idana su, hatta wata sark'a dake wuyan matar Inna Wuro ta b'oye su kamar yadda Mlm ya buk'ata. Kwana biyu matar nan bata farka ba, anata mata maganin hausa, da yake Baffa Mlm yana bada taimakon magani matane da yawa a garin shi ke basu magani. Yau kusan sati kenan matar nan dai bata farka ba. Zaune suke a tsakar gida, Inna Wuro ta kalli Baffa ta ce "ni ko Mlm, anya matar nan zata farka kuwa, abu shuru kamar wacce ke baccin mutuwa?" "Zata farka insha Allah, ai inda zaki lura, tana lumfashi a yadda take, motsawa ne kawai bata yi, bugun zuciyata na tafiya ina ganin kamar dogowar suma tayi, kuma kamar akwai sihiri tare da ita" "Haka Mlm nima na lura da hakan" Suna cikin tattaunawa akan zancan ta suka ji ihu daga cikin bukar da matar take kwance. Ai ko da gudu suka nufi bukar, Mlm na cewa Alhmdllhi. Koda suka shiga, a zaune suka iske ta, sai bin d'akin take da kallo, babu um babu umm umm tana ganinsu ta sake tsorata, da kyar da kyar suka samu ta d'an saki jiki dasu, a tak'ace dai sai dai suyi mata magana ta d'aga masu kai, amma baki babu shi. A haka ta shafe wata d'aya a tare da su, harta yi sabo da su, a hankali a hankali kuma bakin nata shima ya bud'e sosai sukai sabo da Inna Wuro. Watan haihuwarta yana kamawa, da Baffa da Inna kai harma da su Usman ko ta ina ganin gata take, inda ko sunanta ta manta shi, sai inna dake kiranta da Fulani kawai. Wata rana ta tashi da nak'uda sosai hankalin Inna ya tashi dan har Baffa yaso a kaita asibiti, amma ganin haihuwar ta taho gadan-gadan, data zo kuma saita tsaya hak'ik'a tasha wahala sosai, kamin Allah ya sauk'eta lafiya, ta haifo y'an biyu duka mata. Karku so ganin irin farin cikin dasu Baffa suka tsinci kansu a ciki, Baffa kuwa kamar shine akai ma haihuwar. Kulawa iya kulawa, Inna Wuro nayi ma Fulani sosai suke bata duk wata kulawa data dace. Ranar suna aka sama yara sunansu na asali wato Hassana da Husaina, Baffa ne ya yanka masu rago har biyu da shano. Wata rana da su Baffa baza tab'a mantawa da ita ba, ranar da suka tashi da safiya babu Fulani babu labarinta sama da k'asa suka nemeta suka rasa, ita da babynta guda d'aya, sai dai ta tafi ta bar mana ke Fulani. Wadda ni ce nasa miki sunan Fulani na maida miki yadda muke kiran Mahaifiyarki dashi, domin Allah yayi muku kyau kamar Fulanin asali, hakan yasa nake kiranki da hakan keda ita. Wadda Baffa yayi kukan rashinta , ke hatta muma da kyar gidan nan ya dawo yadda yake, domin kamar kurciya akayi mata ne, take yawo gari-gari, kuma tana tashi tayi gaba da y'ar uwarki, amma tabar miki kayan jikinta data zo dasu, da sark'ar dake a wuyanta ranar da su Baffa suka kawo ta gidan nan". Inna ta idasa maganar hawaye sun wanke mata fuska, kuka kawai Fulani keyi, ta rungume kayan Mahaifiyarta, tare da kallon sark'ar, gaba d'aya kayan ta had'a ta rungume tana rusar kuka. Usman dake kusa da ita ya rungumeta yana d'an bubbuga bayanta alamar lallashi, idonsa shima yayi jawur tuno da Mahaifiyar Fulanin mace mai kirki da sanin ya kamata. Da kyar suka lallashi Fulani da daina kuka, amma duk ta zama suku-suku ko magana yanzu wahalar yi mata take, sai dai tabi mutum da ido, gashi wannan fad'uwar gaban har yanzu sake jinta take, sosai. DARE 11:00Am na dare Garin sukuntuni ya d'auki shuru, kowa yana makwancinsa yasa hak'ik'arinsa domin ya huta. A dai-dai wannan lokacin kuma Fulani ta tashi domin shan ruwa, wata irin k'ishir ruwa ce ta tayar da ita. A sanan kuma mafarin K'ADDARAR ta zai soma, domin yanzu bata ga komai ba, harta kai ga matakin nasara a rayuwarta. Haska fila tayi, tana kallon Inna dake bacci, fita tayi gabanta na tsananta fad'uwa, bakin randar ta tsaya. Ta kai hannunta domin d'ibar ruwan kenan, taji wata irin k'arar Bindiga, had'e da kururuwar mutane, kamin kota ina k'arar Bindigogi su k'arad'e gaba d'aya ilahirin garin nasu, ihun mutane had'e da kururuwa, tashin k'arar Bindigogi kawai kunnuwanta ke jiyo mata. Sakin k'ofin Fulani tayi ruwan da bata Sha ba kenan, jikinta ya kama kyarma kamar wacce aka jonama wutar neper. Da gudu su Inna Wuro suka fito daga d'aki, tsayawa sukai tsakar gidan hankali a mugun tashe. Inna ta ce "mun shiga uku, Audu ba dai y'an Bindiga bane yau a garin nan, Innallihi wa'inna alaihir raju'on" Da sauri taje ta kama Fulani tana cewa "wayyo Allah Usman ku ceci y'ar uwarku kurku bari a kasheta bata sadu da y'an uwanta ba" Inna na idasa maganar suka ji an banko k'ofar gidan, an shigo, wata wawar bugar zuciya ce ta riskesu su duka. Zubewa su kai gaba d'ayansu a k'asa, gani y'an Bindigar sun shigo gidan, sun zagaye su, ga Bindigogi nan rik'e a hannunsu masu hatsarin gaske. "Dan darajar Allah kuyi hakuri karku yi mana komai in..... Wata uwar tsawa wani daga cikin y'an Ta'addar ya bugama Inna dake maganar, ya ce "kai jirin miye kuke dasu, ku kashe kowa amma banda wannan y'ar shilar, da ita zamu tafi sana ku koro shanayensu gaba d'aya" Kamin ya rufe baki ma, wani ya sakarma Usman harsashi a tsakiyar kansa, nan take ya zube babu rai a tare dashi. "wayyo Allah na shiga uku na lalace sun kashe mana Y Usman wayyo Allah Inna kin gani" Cewar Fulani da gaba d'aya ta fice daga yaccinta. Wata gigitacciyar tsawa suka bugama Fulani wacce tasa tayi suman wucin gadi ba shiri ta had'e maganar dake bakinta. Kamin ta dawo duniyar mutane taji k'arar sukar harsashi guda biyu. Wata irin k'ara ta fasa, ganin Inna Wuro ce da Audu aka harba gashu nan yashe a k'asa babu lumfashi. A lokacin itama da za'a d'au rayuwarta itama da zata so haka. Tashi kawai tayi tana matsawa kan gawar Inna Wuro, sai da ta tab'a fuskarta ta k'ara tab'awa, ganin fa babu rai a tare da ita, yasa kawaii Fulani fad'awa kanta ta fashe da wani irin kuka, mai matuk'ar ban tausayi. Kuka take tana surutai wadda basu da kan gado. Tashi ta sake yi ta matsa kan gawar Usman shima, maganar take tunawa inda yake cewa "ki daina kuka haka nan kinji, baga mu ba tare da ke, kuma zamu ci gaba da kasancewa a tare da ke" "Wayyo Allah na Y Usman ina al'k'awarin da kayi min na kasancewarku tare dani har abada, ya zakuyi min haka?, ya zaku tafi ku barni cikin wannan duniyar mai d'auke da azzalumai, dan Allah nima ku kashe ni". Ta Idasa maganar tana duban wani daga cikin y'an Ta'addar dake tsare da ita sauran sunje koro shanayensu. Wani abu Fulani ta tuna da sauri tayi cikin d'aki, d'an Ta'addar harya saita bakin Bindigarsa zai sakar mata ita, kawai yaji wani ya ce "kyale ta dole dai sai ta bimu tunda Oga ya ce banda y'an mata irinta, su a taho dasu kawaii yake so". Fulani kayan Mahaifiyarta ta d'akko ta k'udundune su a mararta sark'ar kuwa, a cikin gashin kanta ta sata ta d'aureta, sosai yadda ba wadda zai ganta, kuma bazata tab'a fad'u ba. Wani ne yaje har d'akin ya janyota ya tasa keyarta a gaba yana dungurinta da bindiga yana zaginta, suka fito waje, a yanzu kam Fulani zuciyarta ta bushe sai kallon gidan take had'e da kallon gawar su Inna, a cikin zuciyarta wani irin rad'ad'i mai azabar zafi take ji, a yanzu kam sai had'iyer zuciya take, idonta sunyi jawur......... *K'ADDARAR SO* (Destiny Of Love) *©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* Chapter 6 *ARMAN HARUN'S HOSPITAL LOGAS NIGERIA* Turo k'ofar Office d'in, tayi cike da yanga da takunta mai jan hankali. Sai dai d'an k'aramin tsaki taja, ganin wadda take danshi ko arzik'in ya d'ago ya kalleta ma baiyi ba. "My Arman" "Uhum" Shine kawai abunda ya amsa mata "Haba Arman ya kamata ace zuwa yanzu kasan irin d'unbin k'aunarka da nake you should give me a chance, I don't want to love you for myself, you should stop like that to me. Bubi fa yanzu ko kallo ban isheka ba, wallahi kaine kad'ai kake iya min wannan dizgin". Ta idasa maganar cike da takaicin kanta Cike da izzarsa ya d'ago dararan idonsa yana cire d'an gilashin dake manne a idonsa yana d'an dubanta kad'an. And ko kad'an Lilaah bata birgesa, duk da yasan ba k'aramin so take mai ba. But shi baya sonta ko kad'an. But the one he loves is different, and he knows that there is definitely a dust every day that he says to the one he loves. Katse mai tunani tayi da cewa "My Arman, please give me a chance and you will be happy with me" Murmushin gefen baki Arman yayi wadda yasa ma Lilaah fad'uwar gaba, saboda wani bala'in kyau data ga ya k'ara mata, ga wani sonsa dake fisgarta. Kai wallahi idan bata samu Arman ba akwai matsala, tana jin babu abunda bazata iyayi ba akansa. Ta shagala da kallonsa, har bata san ya tashi daga inda yake ba, sai da taji saukar muryarsa, yasa tad'an saki ajiyar zuciya. ""Lilaah, you should be patient now. Nasha gaya miki ni bana son mace wacce zata iya furta tana son namiji. If you were yourself, you would have kept your love for me in your heart and maybe you would have valued yourself. And ni yanzu naga wacce nake so Nan........ ""What are you saying Doctor Arman" ta fad'a a zabure D'an taku ya d'anyi ya matso gabanta ido cikin ido ba shakka fuskarsa babu wasa ya ce "what you heard me say is, I won't reveal who I want soon" ""It will never be possible, surely whoever I can kill by God against you, I am jealous of you. Arman ina bazai tab'a yuwu ba wallahi" "You are saying that it will never be possible, and knowing yourself must be possible, where life and life are my choice" Maganganun da yake gaya mata, daya san yadda take jin saukar su a cikin ranta da gangar jikinta da ko kad'an bazai d'akko maganar wata yana danganta kansa da shi ba. She felt a kind of heartache, including a very jealous feeling, lokaci d'aya taji ta tsani wacce yake ikirarin zai aura, lokaci d'aya taji duk duniya ba wacce ta tsada sai wannan halittar da zatai mata shamaki da samun cikar burinta. Dole ne cikin biyu ayi d'aya, kodai Arman ya aureta a zauna lafiya, ko kuma yaje yayi aure ta hanasa zaman lafiya, daga shi har wacce ya zab'a ma kansa. *ARMAN HARUN'S FAMILY HAUSE LOGAS NIGERIA* K'as k'as k'as sautin taunar chingum ke tashi a tsakiyar parlon. Humaira dake sakkowa daga kan bene tana nufar kitchen, ta d'an tsaya tana duban, Salma dake tsaye da akwati, sanye take da wasu y'an iskan k'ananan k'aya, ance matsu ga wani kafcecan gilas data manna a idonta, tana bin parlon da kallo. Ganin Humaira yasa ta k'ara wani kame kanta yatsine baki tayi, bata da niyar tanka mata, tana niyar barin wajan, ta nufi hanyar da zata sada ta da part d'in Haj Shuwa, taji Humaira na cewa "Ohh su Salma ne a gidan namu" D'an juyawa tayi, a hankali tasa hannunta kamar bata so ta cire gilas d'in dake manne a idonta, tayi mata wani kallo kamin ta ce "hmm kware mune a gidan naku, kuma da alama munzo kenan" "Allah sarki, ai kin san mu dama masu taimakon mutane ne, kowa yazo zai iya zama gidanmu domin yaci arzik'i yabar arzik'i inda yake" Da sauri ta dube Humaira data yi maganar kamar wacce ba ita ce tayi ta ba, maganar ta shigeta kamin ta ce "uhum koda yake mufa munfi k'arfin muzo muci arzik'i domin muma ansan ba matsiyata bane, da abun duniyarmu a hannunmu, kuma da alama mun kusa zama masu gidan gaba d'aya, sai dai azo aci namu arzik'in" Humaira zata sake magana kenan, Momma ta fito tana duban Salma, duk taji mi suke cewa, d'an murmushi tayi irin na manya, duk abunda matan gidan suke akan d'an nata tana sane, kuma duk wani takunsu nason had'a y'ay'ansu da yaronta d'aya tilo tamkar da dubu ta sani. "Humaira abunda yasa kika sakko kenan?, son magana, bana hane ki da sa baki a maganar da bata shafe ki bane?" K'asa tayi da kanta ta ce "sorry My love" tana Idasa fad'ar haka ta Idasa shigewa k'aton kitchen d'in nasu. Salma kuwa, ko kallon inda Momma take bata yi ba tayi shigewarta part d'in Haj Shuwa. Girgiza kai kawaii Momma tayi, tana tunanin a haka zata amince d'anta ya auri wannan yarinyar marar tarbiyya, ina ai bazai tab'a yuwu ba kam. Da gudu taje ta rungume Haj Shuwa dake tsaye tana waya. "Ahh ahh, harkin iso, mutanan Abuja da alama jirgin safe kika biyo yanzu muke waya da Mamarki Binta ai take sanar dani ai kin taho" "Uhum, Umma ai dama kin san nafi son tahowar safe" "Hakane y'ar albarka fatan kin iso lafiya?" "K'alau Umma na iso" "To madallah, ai kin san abunda muke ciki ba sai na sake miki baya ni ba. Karki sakan kance ki fad'a sonsa da gaske domin kuwa nan gaba kad'an zamu aika sa inda ba'a dawowa" Wata dariya Salma ta saki tana duban Umma ta ce "ai Umma a shirye nake kawai umarninku nake jira" "Tabbas dama nasan zaki iya, to amma fa akwai y'ar matsala guda d'aya" "Wacce irin matsala kuma Umma?" "Hmm Arman Malamina ya gaya min cewa akwai wacce ya fad'a tarkon k'aunarta, kuma da alama akwai wani rabo mai zafi a tare da ita, Mlm ya ce dole mu bari ya aureta shine kawai zamu bari burinmu ya cika yadda muke so, dole saita shigo gidan nan tukun, zamu iya cin galaba akansa harma ita, a lokacin zamu sa masa tsananin k'aunarki zamu sa Mlm yasa masa kasalar Ibada ta yadda zamu ci galaba akansa da wuri, ke kuma zamu sa ki rink'a shige masa ta yadda zaki rink'a had'a husuma tsakaninsa da matarsa, komai a shirye muke, ita kad'ai muke jiran zuwanta cikin gidan nan" Tashi tsaye Salma tayi sab'anin da, da take zaune kusa da Haj Shuwa Ta ce "tabbas kuwa kun iya dabara, ni kuma sauran aikin ku barsa a hannu na Umma". *SURURE, LOGAS NIGERIA* "Wai mi kake cewa ne, Aliyu, na kasa fahimtarka Husainar ce aka nema ta aka rasa" Mimi ta k'are maganar had'e da tashi tsaye manne da waya a kunnanta daga cikin wayar Aliyu muryarsa hankali a tashe ya ce "wallahi Mimi sai da na ce mata tahau jirgi idan zata tafi katsina tayi min gaddama. Mimi is privileged and pregnant, my mind is awake" "Wai abunda ban gane ba, kai kana ina harka bari hakan ta faru, kasanfa katsina hanyar bata cika kyau ba, the kidnappers have attacked the town a lot" "Mimi knows that, he talked to her since I told her to go and see home, ni kuma nabar mata komai na baro Abuja ina kwatano ni yanzu haka, munzo wani taro ne ashe ita kuma tasa direban gida ya kaita.I took my plane, she got on "Insha Allah zata dawo lafiya, ka nemi wayarta ne?" "Mimi tun d'azo nake neman layinta baya shiga. And they didn't get enough from morning to night, Mimi hankali ya kasa kwanciya kamar matata na cikin matsala hankali a mugun tashe yake wallahi" Sauk'e lumfashi Mimi tayi tana k'ara kwantar mai da hankali, daga k'arshe ta ce "ina so karka sanar da danginta tukun muga mi Allah zaiyi, karmu tada masu hankali kasan Mahaifiyarta bata cika lafiya ba" "Insha Allah Mimi, amma idan lokacin sanar dasu yayi dole su sani" "Na sani Aliyu amma kabi komai a hankali tunda bamu tabbatar an sace tan ba, ni nafi ba ko dai motarce ta lalace masu kan hanya" "Hakane Mimi" Sallama suke Mimi ta dawo dubanta wajan Lalaah dake tsaye a kusa da ita, tana ta dumunta da cewa mi yake faruwa hankali a tashe itama. Fitowarta kenan, da murnarta na ta fad'ama Mimin Doctor Arman ya turo mata kud'in zanenta kusan Million goma, ita da bata d'auka yawan kud'in zai kai haka ba, ta d'auka bai wuce a bata dubu d'ari ba. Sosai ta rud'e har sai da Arman d'in da kansa ya kirata, tayi mamakin kiran sa. Inda take ce mai kud'in sunyi yawa, ina zata kai su?, sai dai yayi mata murmushi ya ce ta bada sadaka idan ba abunda zatai dasu, daga nan yayita janta da fira, har lokaci yaja. Tayi mamakinsa matuk'a yadda lokaci guda ya sake da ita, har ya tsaya yana zuba mata surutu haka, wadda ji take kwata-kwata kamar ba doctor Arman data sani take jin labarinsa ba, take gani a gidajan Tv da redio, wai shine a cikin waya yake mata sauk'in kai haka, ta kasa gaskata abun. Ta sakko ne da murna domin ta sanarma Mimi ta iske wannan tashin hankali da Mimi take ciki, na Y'ay'ansu Aliyu da matarsa, wadda auransu bai wuce shekara biyu da yinsa ba, matar y'ar asalin garin Katsina ce, acan suka gamu wajan wani taron kasuwancin Abbie d'aya wakilta zuwa suka had'u da Husaina. "Bari Lalaah muna cikin tashin hankali, why da Husaina baza ta hau jirgi ba?, tasan hatsarin hanyar dake garin su" "Dan Allah Mimi ku kwantar da hankalin ku insha Allah Aunty Husaina tana nan cikin k'oshin lafiya, kawai isane basu yi da wuri ba" Lilaah ce ta shigo parlon itama duk hankalinta ba'a kwance yake ba. Amma ita damuwarta daban take da taso, domin ita dama kullum damuwarta bai wuce ta Arman ba. Ganin su haka yasa ta d'an tsaya kamar abun arzik'i ta ce "Mimi mi yake faruwa ne haka, na ganku haka" "Hmm Aunty Husaina ce ta d'auki hanyar katsina daga Abuja gidanta, shine har yanzu bata isa ba, kuma wayarta ita da drivern bata shiga har yanzu kuma tun safe suka d'auki hanya, amma Kinga yanzu har tara na dare shuru basu isa ba. Can gidan nasu ma hankalinsu ya fara tashi soma, danma Y Aliyu na b'oye masu wani abun" D'an jim Lilaah tayi kamar wacce zata ce abun arzik'i sai kuma ta ce "ai kaji matsalar d'an k'auye wallahi, ai shine yaji ya gani, Allah ya bayyana ta" Ta na idasa fad'ar haka tayi sama abunta. Mimi cike da takaici zata mata magana Lalaah ta girgiza mata kai, alamar tayi hakuri. Lilaah kuwa gani take ai ita wannan ba damuwarta bane. Shi Aliyun shita shafa, gashi dama haushinsa take ji yaje ya auro masu y'ar k'auye taso ya auri Bilkees k'awarta......... *K'ADDARAR SO* (Destiny Of Love) *©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* Chapter 7 *FUNTUWA LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA* Tsaye take tana dakan surfen wake. Da gudu Inna Saude ta fito daga d'aki, d'an dakatawa tayi tana duban Maryam dake surfe. "Kan uban nan kayyasa, ke ina kud'i na dana aje a cikin d'aki jiya?, na duba ban gansu ba, kuma ke ce kad'ai kika ga inda na aje su, na rantse da sarkin da ke butsan lumfashi idan baki fiddo min da kud'i na ba, sai nayi miki bugun mutuwa wallahi, inga ubanda zai zo ya kwace ki" Jikin Maryam ne ya kama rawa, had'e da tashin hankali, wani irin bak'in ciki ne ya cika mata zuciya, wani abu mai d'aci taji ya tokare mata mak'oshinta. Sharrin sata, abunda bata tab'a yi ba, ka aje abunka ta d'auka, koda kwana dubu zaiyi zaka zo ka same shi inda ka gansa, bata tab'a shi ba, bare har ta canza mai waje, ita kanta Inna Sauden ta sani, yau dai rashin mutumcin nata akanta zai k'are kenan?. Kamin ta dawo cikin tunani taji an tsinka mata mari, fauuuuu. Da mugun sauri ta dafe kuncinta wasu zazzafan hawaye suka b'alle mata. "Ke kin mai da ni y'ar iska ina magana kinyi banza dani, wato ga banza na magana nayi na gama kin d'auka kenan ba?, nayi abunda zanyi" "A'a a'a Umma na rantse ban d'aukar miki abu ba, kin sani ban tab'a miki sata ba" "Dalla rufe min baki munafuka, na sani ko kin canza hali ne, d'an Adam da ba wuyar canza hali yake ba. Wallahi sai kin fiddo min da kud'i na, ko kuma nayi miki dukan da zaki kasa tashi" Izuwa yanzu kam, Maryam kukan nata har shashshaka take, duk'ewa tayi k'asa tana sake cewa "na rantse ban d'aukar miki kud'i ba, ki sake dubawa dai" Wani hanb'ari ta kai mata, da k'afa Maryam ta tafi ta bige goshinta. Goshin nata bai sauka ako ina ba sai akan wani dutsen da ake had'a murho, buguwar data yi yasa goshin fitar da jini dandanan ya kunbura. Wani ihu marar sauti Maryam ta fasa, wata irin azaba ce taji ta shigeta. "Ahh ahh mi zan gani ni Lami?, ke Saude kiji tsoron Allah wallahi, yadda kike azabtar da wagga baiwar Allah" Juyowa Inna Saude tayi a zafafe tana nuna d'an Lami da shigowarsa gidan kenan ya tarar da abunda Inna Sauden kema Maryam shikam bai iya gani ya kyale Ta ce "Lami kake ko d'an Lami?, koma dai minene ka fita a harka ta, ka daina shigar min hanci d'an Lamiiiii" Taja sunan da k'arfi tana nunasa da d'an yatsa. Wata shawa D'an Lami ya saki yana tab'a hannu had'e da rik'e k'ugu ya ce "ai idan baki daina yima Maryam mugunta ba a cikin gidan nan to wallahi ni kuma bazan daina tanka miki ba a'ato eheee kiji da kyau" "Maryam d'in K'anwar uwarka ce kota ubanka?, D'an Lami zan karta ma rashin M wallahi" Zai sake magana sai ga Mafida ta shigo d'auke take da kaya a saman kanta, a roba ce k'atuwa kayan mata ne shak'e da rabor data koma saidawa kwanan nan, gida gida take bi gari-gari take talla gidanjan aure na mata. Sauke kayan tayi tana duban Inna Saude ta ce "ke Inna kin cika fitana mike faruwa ne?" "Ubanki ne ke faruwa shegiya y'ar iska, miye ruwanki a ciki?" "Kinga Inna Saude ki ban amsa, k'ila ma ina da sa hannu a ciki kawai ki gaya min minene" D'an Lami zaiyi magana, karaf Inna Saude ta dube sa da sauri ta ce "to d'an san a sani, fad'i ba'a tabbaye ka ba, kaga d'an Lami ka daina min haka zan fyato ka kana shigar min hanci fa" D'an Lami zaiyi magana Mafida ta kyafta mai ido. Shuru yayi domin ya d'au haske. "Kinga kud'i ne na aje masu yawa, kud'in aikina da aka biya ni na wata, na nema na rasa kuma y'ar iskar yarinyar nan kin ganta ita kad'ai taga inda nake sak'a kud'i na" "Hmm Inna Saude kenan, ai kin san dai Maryam ba abunda zatai da kud'i ko?, ni ce to na d'auke su na k'ara jari na kayan matan da nake saidawa in..... Kamin ta Idasa maganar ma, kawai sai dai taga Inna Saude a gabanta taci kwalar rigarta ta shak'e mata wuya. Zare ido Inna Saude tayi tana cewa "ai ko uban kuturo yayi kad'an bare na makaho, yau duk gidan ubanda zaki samo kud'i na sai kin bani, idan ba haka ba uhmm wallahi Mafida sai na barki kwance" D'an fincike cikinta Mafida tayi daga na uwar, kamin ta ce "a'a dakata Inna Saude ai dad'in uban na zuba jari kuma na maida kud'i na, dan haka kinga kud'inki" Zaro y'ar jakarta Mafida tayi tana k'irga kud'i, ta k'irgo dubu goma ta dank'ama Inna Saude. Zaro ido Inna Saude tayi tana washe baki ganin iyayen kud'in da Mafidar ke k'irgawa. Ta ce "kai y'ar albarka ki ce sana'ar da kika fara akwai riba haka sosai, ai ko nima zan zuba jari a ciki. Yanzu dai a bani riba ta tunda da kud'i na akayi sana'ar kuma an samu" Wani duba Mafida tabi uwar dashi. Sai kuma ta kalli d'an Lami dake kallon Inna Saude cike da mamaki suka had'a baki wajan cewa "to yau Inna Saude mune y'an albarkar, wai yau za'ayi ruwa harda k'ank'ara kuwa" Sai kuma taga sun had'a hannu sun tab'a a tare, suna sake sakin wata shewar. Rik'e baki kawai Inna Saude tayi, lallai duk yadda take d'aukar Mafidar tata, ta wuce Nan...... *SUKUNTUNI, K'ARAMAR HUKUMAR KANKIA KATSINA STATES NIGERIA* Fulani ba k'aramin tashin hankali tayi ba, ganin yadda garin nasu ya koma. Kota ina kururuwar mutane kake ji, ga k'arar Bindigogi dake tashi a gidajan mutane, kallon ko ina take ganin yadda y'an Bindigar suka zagaye duka ilahirin garin. Y'an Bindigar tare suke da motoci manya-manya, had'e da Mashina sunfi guda d'ari. Gaba d'aya dukiyoyin mutane sun kwashe sun tasa wasu gaba cikin dokar daji sunyi gaba dasu. Y'an matan da suka kwasa kuwa zasu kai su goma irin su Fulani. A k'asa aka tasa k'eyar su Fulani suna tafiya cikin dokar daji ga dare ya tsala. Wasu na kuka da kururuwar rasa iyayensu da sukai. Ita ko Fulani kukan ma izuwa yanzu hawayen sun k'afe babu sai zuciyarta dake mata zugi da rad'ad'i. Abu biyu ne ke mata kai kawo a zuciyarta had'e da tsainin damuwa, na rasa su Inna Wuro data yi, ji take inama da ita suka had'a suka halbe, da itama ta huta da wannan duniyar mai cike da d'unbin abun tsoro da azzalumai da suka zagaye duniyar. Sai kuma na cewa wai su Innar ba sune suka haifeta ba, kai wannan abu na mata ciwo sosai har yanzu ta kasa gasgata abunda ke faruwa da ita. Halbin bindiga taji, ba shiri sauran y'an matan suka fasa ihu, ganin yadda aka halbe wata, data d'auke wai ita bazata iya tafiya ba ta gaji, ganin zata b'ata masu lokaci suka halbe ta nan take. Take zuciyar Fulani ta kama wani zullo yanzu mutanan nan kwata-kwata su kashe rai ba'a bakin komai suka d'auke shi ba, Innallihi wa'inna alaihir raju'on, wani sabon tashin hankali ne taji ya rufe ta. Tafiya yankin azaba, domin kuwa tafiya suke wacce babu tsayawa ko a hutawa, idan ka ce zaka tsaya kuwa, zaka yi a bakin ranka ne. Ga dare gashi Fulani ko arzik'in takalmi bata saba, kai ba ita kad'ai ba bata jin ma gaba d'ayansu sun sa wani takalmi, ai sai da kwanciyar hankali ake iya tuna komai. Wata irin k'arar azaba Fulani ta saki, jin wani irin rad'ad'in azaba data ji shi daga k'asan k'afarta, har izuwa kwanyarta, Tabbas tasan k'aya ce ta taka, amma tasan ko k'aran hauka ya cijeta bazata tsaya ba. Wata mai suna Fyushind'o dake kusa da ita, ta zaro ido, fuskarta shab'e-shab'e da hawaye ta ce "Fulani ba dai k'aya kika taka ba?, wallahi karki tsaya kashe ki zasuyi kinga kusan mutum biyu suka kashe saboda irin tsayawar nan" Wani kalar miyau Fulani had'e mai d'aci, ta ci gaba da d'angyashe k'afar tata, bata ce komai ba. Suna tafiya tana runtse idonta saboda ita kad'ai tasan yadda take jin rad'ad'i da k'afar tata ke mata. Sun shafe daren gaba d'aya suna tafiya, masu raunin cikinsu tuni suke zubewa a kasa, su ko y'an Bindigar basu tsayawa wani b'ata lokaci suke halbe mutum, izuwa yanzu sun kashe mutum ya kai biyar. Har sanyin Asuba ya fara kunnu kai, babu alamar zasu tsaya. Fulani kuwa izuwa yanzu ta galabaita ainun ga tafiya da d'angyashi ga k'ayar dake har yanzu a jikin k'afarta, tana kallon yadda k'afar ke zubar da jini harta d'an yi fushi ta kunbura. Safiya ce tayi masu, amma ga mamakin Fulani bafa wata alamar zasu tsaya wa'innan mutane, wani kalar dokar daji su Fulani suka tsinci kansu a ciki wadda basu tab'a ganin irinsa ba, ga duhu gashi ko tarin mutum baga ji, babu gida baya babu gida gaba, tsabar dokar dajin ce kawai. Fulani tasan sunyi tafiya mai tsayin gaske wacce ma bazata iya cewa ga adadi nisanta ba, tana da tabbacin sun baro nahiyarsu gaba d'aya sun shigo wata nahiyar kuma, baza suce dai ga inda suke ba, domin ko ina daji ne wadda baza'a iya kiran sa da gari ba. Wata irin rana mai zafin gaske ake kwanyarawa, ga azabar yunwa data fara nuk'urk'usar wasu daga cikin su, dauriya kawaii suke ga bala'in tsoron su tsaya suyi k'orafi a kashesu, tafiyar kawai suke mai cike da tsananin azaba. Wani irin sansani, su Fulani suka ga sun iso, mai d'auke da y'an Ta'adda, zagaye da wajan, an kafa wata runfa guda uku, gashi nan harda murhu a wajan, kota ina sune zagaye da wajan wasu a tsaye rik'e da bindigogi, wasu a zaune suna zuk'ar sugari wasu kuma shayi suke sha irin na buzaye, kai da ka kalli idanuwansu zaka shaida lallai babu imani a tare da su. *SURURE LAGOS NIGERIA* "Wallahi Mimi sune suka d'auke ta" Cewar Aliyu da isowarsa kenan, a garin Logas. Cike da tsananin tashin hankali ta ce "ka daina fad'ar haka in.... "Mimi ya za'ai bazan fad'i sace ta akai ba?, Mimi kina gani fa Abbie yasa an baza jami'an tsaro a can hanyar katsinar kawai abun tashin hankalinma an tsinci motar da suka tafi da ita tare da gawar drivern, Mimi wallahi sune, Mimi kuma sunk'i koda kiran waya ne su fad'i ko nawa suke so a basu, wallahi Mimi ko dukiyata zata k'are zan basu su sakar min mata". Ya idasa maganar tare da fashewa da kuka, kamar mace. Mimi zuwa yanzu ma kukan take itama, dole tasa kawai ta tashi ta haye sama tana hawaye, domin idan ta ce zata cigaba da zama inda Aliyu yake itama kukan zasu had'u suyita yi. Lalaah dake rik'e da Aliyu itama ta d'an kwanta akan k'irjinsa tana sakin wani sassanyan kuka itama. Sai can ta tashi ta ce "Y Aliyu ba kuka ya kamata mu zauna muna yi mata ba, kamata yayi mu tashi muje muyi alwalla muyi sallah, Allah kar ya basu ikon cutar da ita, musa a sauke al'qur'ani mai girma Allah ya bayyana ta" Share hawayen yayi wasu kuma na sake zubowa, cikin muryar kuka ya ce "Lalaah akan Husaina ni mai rauni ne wallahi, ina matuk'ar tausaya mata ita da abunda ke cikinta, kina gani fa d'auke take da ciki a jikinta, wa'innan mutanan basu da imani fa ko kad'an ina gudun kar suyi mata wani abu, ita da abunda take d'auke dashi". Wasu hawaye Lalaah ta sake share mai duk da itama hawayen ne ke zuba a cikin idon nata. Da kyar ta lallab'a shi yayo alwalla, sai da taje tayi sallar tata harta dawo ta iske shi bai ma sallame ba, yana sallar yana kuka, yana kai kukansa wajan Ubangijin sammai da k'assai. A wajan Mimi ma tana shiga d'akinta, dama bata rabo da alwalla, ita kullum zaka same ta da alwalarta. Kawai ta kabbara salla itama tana hawaye. Bayan ta gama taji wayarta na tsuwwa. Da sauri ta duba sai taga ashe Abbie ne, da azama ta d'auka kamin ma ta ce wani abu ya ce "na kusa dawowa dole na aje komai na dawo k'asar domin aji da wannan abun, dole a baza jami'an tsaro kota ina dake cikin garin katsinar da wajenta" "Amma Abbie baka ganin kar ayi hakan, saboda kasan su y'an Ta'addar nan, basa su ana sa masu jami'an tsaro a cikin abun su, ya kamata dai mu bari muga ko zasu kira waya" "Hmm Mimi kenan tunaninku kenan na Mata amma dole asa Jami'an tsaro a ciki, ai an riga dama ansa sun, domin sune suka binciko inda motar da suka fita take, tare da gawar driver, kinga kuwa duk motsinmu zasu sani, kuma yanzu haka suna kan bincike ne ma" Girgiza kanta kawaii Mimi tayi, har yanzu Abbie bai san suwaye y'an Bindiga ba, su da suke kamar aljanu idan aka ce yanzu haka sun san da Jami'an tsaron da akasa cikin lamarin ba'a gaddama, yanzu haka sun d'an dakata ne suga iya gudun ruwansu. Sallama sukai kawaii inda take shaida mai ya tsaya ya idasa abubuwan dake gabansa, zata sa a ci gaba da addu'oi had'e da sauk'e al'qur'ani mai girma, su had'u kuma suyita mata addu'ar Allah ya k'are ta daga duk wani sharrinsu. Bai wani yadda ba, shi dai yasan dole ne cikin satin ya duro Nigeria......... *K'ADDARAR SO* (Destiny Of Love) *©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* Chapter 8 *ARMAN HARUN'S FAMILY HAUSE LOGAS NIGERIA* Yau ta kama weekend ne, kowa yana gida. Safiya ce mai cike da nishad'i domin garin hadari ne ya had'u sosai ya saki wata irin ni'ima, garin yayi luf-luf dashi gwanin ban sha'awa. Babban parlon gidan ko ta ina ma'aikata ne ke aikinsu, masu shirya darning table nayi, sunfi ba darning table d'in mahimmanci wajan jera abincin safen da masu gidan ke gaf sakkowa domin su ci. Kamin a shafe y'an mintoci, sun shirya kan darning table d'in, had'e da gyara parlon ya d'au wani k'amshi na daban. A hankali a hankali mutanan nan gidan suka rink'a sakkowa suna zama kan darning table d'in. Ga wata ma'aikaciya tsaye kana zama ita ce mai tabbayar ka miye kake son ci, zata zubama abunda kake ra'ayi da son ci, wannan shine aikinta kawai. Kowa ya sakkowa harda su Daddy amma banda Arman a wajan. Salma ce ta d'an duk'a dai-dai inda Haj Shuwa ke zaune suna kusa da juna ta ce "Umma ya banga Arman d'in ya fito ba, kowa kuma yana ya hallara?" "Hmm rabu da miskilin banza, yanzu haka yana can ya tsaya yangarsa, shifa ba wani abinci yake ci sosai ba, bari kiga koda ya zo ba wani zama yake ya dad'e a cikinmu ba" Tab'e baki Salma tayi tana d'aga k'afad'arta irin ko a jikinta d'in nan. Haj Zulaihat ce nufo darning table d'in, itama fitowarta kenan Bilkees dake danna waya ko kallon su Salma batai ba, bare ta san miye suke ciki. Humaira ce ma dai da Sa'adha dake kusa da juna, suke duban Salma yadda ta wani hakimce kamar wata sarauniyar gidan, Sa'adha bata dad'e da dawowa gidan ba, tana k'asar India tana karatu tazo hutu ne, Humaira kuwa d'iyar k'anwar Momma ce, dama ita gidan take zaune tun asali tare suke da Sa'adha, Humaira tafi son karatun k'asarta ta haihuwa, ita ko Sa'adha tana da ra'ayin fita. Hakan yasa iyayen Humaira dake zaune k'asar India suka bata goyan baya, take zaune a gidansu ita kuma d'iyarsu Humaira dama can ba zama k'asar take ba, tunda wayonta ta baro India ta komo gidan Momma, baka tab'a gane cewa ba Momma ce ta haife ta ba, haka itama Sa'adha idan tana can India baka tab'a cewa ba Iyayen Humaira ne suka haife ta ba, haka suke rayuwarsu cike da tsananin son juna. Salma kuwa da biyu tayi dama, duk tana sane dasu. Tana cikin tunani Arman k'amshinsa kawai ya fara masu maraba da cewa gashi nan isowa. Su Sa'adha murmushi suka saki a tare, suna waigawa, suna duban Yayan nasu. Kai ita kanta Salma sai da ta had'e abincin dake bakinta ba shiri. Wani mayen kallo take binsa dashi, yaushe rabon data sashi a idonta, gani tayi yayi mata wani mahaukacin kyau, ita kanta bata san sadda ta saki wani murmushin munafurci ba, a zuciyarta take cewa. Tabbas Arman ka cika Zakin Maza dole y'an mata zasu rink'a harinka kota ina, na samu na shiga gidanka dai, amma ni nayi daban da y'an matan dake hauka kanka, ni dukiyar taka muke da buk'ata, ko kwanciya kayi dani wannan ma kad'ai ya wadatar dani. Ta k'are maganar tana k'ara fad'ad'a murmushinta. Kowa ya gaisar dashi, amsawa yayi a takaice, shi kuwa kai tsaye sai da ya fara zuwa kusa da Daddy da Abba, ya kwashi gaisuwa suna ta samai albarka. Kamin yaje kusa da Momma ya rungumeta yana mik'a gaisuwarsa, cike da k'auna take samai albarka. Wajan zamansa ya zauna, da kanta Momma ta tashi ta zuba mai abunda tasan yana yana so. Haj Zulaihat ta zunguri Bilkees tana d'agowa ta banka mata harara, k'asa-k'asa ta ce "wato ke dai baza ki daina halinki ba ko?, wato ke ta danna waya ma kike, bana ce idan ya fito ki rink'a zuwa kina amsar Momma ki rink'a zuba mai abincin da kanki ba?, da haka zai saba dake har ki d'an samu matsagunni a zuciyarsa sakarai dake komai sai ance kiyi" Turo baki Bilkees tayi bata ce komai, itafa gaskiya abunda Momy ke son ta had'a tasan ba mai yiwuwa bane. Haj Shuwa k'asa k'asa itama yadda Haj Zulaihat zata jita ta ce "hmmm ayi dai mu gani idan tusa na hura wuta" Wani kallo mai cike da takaici Haj Zulaihat ke aikama Haj Shuwa tana kama leb'enta na k'asa ta d'an ciza, kwafa tayi tana kallon Salma, wato kenan Haj Shuwa ta canza shawara itama, so take wannan d'iyar y'ar uwar tata itama ta samu shiga wajan Arman kenan?, kan uban nan kayyasa ai ko da sake wallahi, ita Haj Shuwa zatai ma haka?, dan taga tana so itama tata yarinyar ta samu shiga. Wani dogon tsaki Haj Zulaihat ta saki, wadda yaja hankalin gaba d'aya mutanan wajan, kallo ne ya dawo kanta, basarwa tayi tana tashi gaba d'aya daga kan darning table d'in, tana ma Bilkees inkiya da ido akan ta biyo ta d'aki yanzun nan. Domin idonta ne yayi mata tozali da yadda Salma ke bin Arman da mayen kallo, kuma tuni ta harbo jirginsu ita da Haj Shuwa. Bilkees na shigowa part d'in nasu, Haj Zulaihat ta kalleta ta ce "wai ke sai yaushe zaki gane abunda nake hango miki dangane da auran Arman ne?, har yanzu baki da wayo wallahi Bilkisu" "Momy please wallahi kwata-kwata bana son kina min maganar had'a ni aure da Arman, na k'ara gaya miki cewa K'awata ke sonshi kamar ranta, bana jin idan Lilaah ta rasa Arman zata iya rayuwa" "Ke dalla rufe min baki, kona d'ora miki ashar yanzu nan, harni zaki tsaya kina cewa wai k'awar ki idan bata sameshi ba akwai matsala, to tama mutu mana, ina ruwana. Nidai na k'ara gaya miki ki maida hankalin ki wajan jawo hankalinsa gare ki, idan ba haka ba kuma, wallahi Bilkisu ranki zaiyi mummunan b'aci ne" Shuru Bilkees tayi, wani haushin Momy na kamata, kallonta kawaii take, yadda take ta sako mata maganar Arman, komai Arman kowa Arman, ita fa bata ga abunda suka hango har suka rud'e sai shi ba. Harta gama b'ab'atunta Bilkees bata ce komai ba, tana gamawa Bilkees ta juya ta fice daga d'akin. Tana fita Haj Zulaihat ta jawo wayarta, ta dannama wata K'awarta kira, bugu d'aya kuwa aka d'auka. Kamin ta cikin wayar ta ce komai Haj Zulaihat ta ce "Luba akwai matsala fa" "Wacce irin matsala kuma Haj Zulaihat?" "Akan abunda tun yarinyar nan na k'arama nake so na had'a domin cikar burina, amma yarinyar nan tana son b'allo min ruwa fa" "Ai kece tuni Haj Zulaihat na ce miki ki fara aiki da Malaman tsubbu da bokaye, kiga aiki kamar yankan wuk'a, kika wani tsaya ai kissa da dabara zata sa ta fahimce ki, yo hatta mijin naku, keda wannan mai kama da ifiritan farko Haj Shuwa da tuni kin gama da ita wallahi, da yanzu sai dai watanta ba dai ita ba, bata isa ta d'aga miki koda d'an yatsa bane" "Kinga Luba, nifa gaskiya zan k'ara gaya miki ban yarda da Malaman tsubbu nan ba, abu d'aya na sani nayi yak'i da kaina na samu abu yafi, kuma ko yanzu Mijina yana sona na sani, kowa da matsayinsa" "To kin san da haka mi kika bugo nayi miki?, Fisbilillahi nifa kin sani da Malaman tsubbu nan na dogara, su suke min aiki har nake janyo y'an samari na tatse su kud'i yadda nake so, tunda na kaso aure na nake cin kare na babu babbaka" "Hmm Luba kenan yanzu ba shawarar da zaki bani, ko na d'au haske" "Haj Zulaihat kenan, nifa bari na k'ara gaya miki ga abunda zakiyi kiga buk'ata yanzu yanzun nan, ba b'ata wani lokaci, idan kuwa na ce ga abunda zakiyi to nayi k'arya ni ban san wannan y'an dabarun ba da kissar nan, a'a ni Malamai kawai na sani. Idan kin shirya binsu to ina sauraran kiran ki". Tana fad'ar haka ta tsinke kiran. Wani tsaki Haj Zulaihat taja tana magana ita d'aya "Shi yasa fa ban son kiran Luba, komai ita sai kabi wasu bokaye abunda aikinsu na d'an kwanaki ne, nida nake so nayi abun ya zama sai dai mutuwa zata raba". Momma kuwa, duk tana ganin abunda ke wakana a tsakanin Matan K'anin mijinta, har tsakin da Haj Zulaihat ta saki tasan can tsakaninsu ne ita da Haj Shuwa. Wani murmushi ta saki tana k'ara sama d'an nata albarka. Haj Shuwa ce itama tsaye tana waya da Binta. Salma ce ta shigo hakan yasa Haj Shuwa tsinke kiran. "Umma wai baki ganin yadda waccan matar Haj Zulaihat ke miki tsaki ne?, mi yasa baki ci ubanta bane?, nifa wallahi Umma bana d'aukar raini, shi yasa zuwa na gidan nan, muka had'u da waccar Humairar ta nemi tayi min iskanci na ce ubanta gaban Momma wallahi" "Kin yi min dai-dai ai, shegiya sai ka ce ita ba cin arzik'in take yi ba" "Hmm kema kin fad'a Umma, ai ko taji magana wallahi" "Ni yanzu waccar Haj Zulaihat d'in ke son bamu matsala, amma abu d'aya zai tsaida mu shigowar yarinyar da Boka ya ce ne, amma data gane shayi ruwa ne, data gane cewa ba'a buga wasa da Haj Shuwa bata cinye wasan ba, amma nan gaba kad'an zata ga sakamakon wasan". Dariya suka saki a tare harda su tab'a hannu kamar wasu sa'annin juna. *SURURE LAGOS NIGERIA* Wayar dake manne a kunnansa ce ke shirin fad'uwa, tsabar yadda jikinsa ke kyarma. Ba shiri Mimi dake kusa dashi hankali a tashe ta tarbe wayar tana sata a amsa kuwwa yadda kowa zai ji. Miye ya tada hankalin Aliyu?. Sai tabbayarsa suke tun d'azo da ya amsa kiran, ya koma tashi a zabure amma yak'i basu amsa, gashi ya tsaya kamar wadda gangar jikinsa ta daina aiki. Abunda suka ji ne suma ya kusa tarwatsa kwanyarsu da tunaninsu. Domin daka ji yadda ake magana da wata basamudiyar murya, irinta gaggan y'an Ta'adda zaka sheda wadda suka sace Husaina ne suka kira. Suna cewa "da alama baka so matarka ta dawo da ranta, mundun kuka sake sa Jami'an tsaro a lamarin, to matarka zata iya mutuwa ako wane lokaci, a sadda kuka shirya ta dawo gare ku zamu neme ku, amma yanzu baka shirya ta dawo gare ka da wuri ba. Suna fad'in haka suka datse kiran. Wata irin hargowa Aliyu keyi yana amshe wayar daga hannun Mimi yana cewa "hello hello dan girman ku tsaya, wallahi na shirya amsar matata, ko nawa kuke so ku fad'a zan baku, kuma Jami'an tsaro za'a cire su daga zancan, baza mu sake sanar dasu abunda ake ciki ba, hello hello hello". Maganar yake cike da fitar hayyaci. Mimi da ke hawaye ta ce "haba Aliyu sunfa katse kiran" Wata irin zabura yayi sai gashi ya zube a k'asa a sume. Wata irin kururuwa Lilaah ta saki had'e da salati........ *Ina so na sanar daku cewa Free pages zai tsaya daga na 10 ne game bukatar TAFIYA dashi na wanga book d'in zai biya D'ARI BIYAR NE KACAL, ba sai na tsaya yin wani dogon jawabi ba, kun dai san wanga book akwai k'ura a cikin akwai matsaloli masu tarin yawa, akwai sirrikan dake binne wadda duk za'a warwaresu nan gaba* Zaka iya turo kud'inka ta wannan account d'in 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank Sai ka turo shedar biya ta wannan number d'in 👉 08130479973 Zaka iya turo kati MTN D'ari biyar ne kacal *K'ADDARAR SO* *©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi *END OF FREE PAGES* Chapter 9-10 *SANSANIN Y'AN TA'ADDA* Kwance Fulani take a k'asa cikin ciyayi, sai juyi take k'afarta na mata wani irin rad'ad'i mai shiga kwanya, duk da ta zare k'ayar data shige mata k'afa amma k'afar har yanzu zugi take mata. Murk'ususun wata mata taji kusa da ita tana shashshakar kuka, ba shiri ta tashi a zabure tana duban matar dake d'an nesa da ita. Kallon ko ina tayi gasu nan an zube su a cikin rana ba abinci ba ruwa, rabonta data ce tasha wani abu tun kamin Inna Wuro ta bata labarin basu ne suka haifeta ba. Yanzun ma yunwa tayi mata mummunan kamu da kyar take had'e miyau, ga k'irjinta data ke ji yana mata zafi, kamar mai shirin kamuwa da cutar kwalsa. Gabanta ne ya fad'i ganin yadda matar ke kallonta ko kyafta ido babu, kallon matar take itama, ganinta d'auke da k'aton ciki, haihuwa yau ko gobe. Gani tayi suna mugun kama, amma kamar bamai fisgar mutum bace kace nan take ai kamar ta b'ace ko kuma ace ai su iri d'aya ne, a'a kama ce wacce da an gani za'a ce ta jini d'aya ce amma game hankali da tunani. Fulani bata san sadda ta rarrafo ta nufi matar dake rik'e da cikinta tana zubar da hawaye ba. Wani d'an Ta'adda ne ya kwasama Fulani tsawa da cewa "ke y'ar gidan matsiyata, koma ki zauna inda kika taso, kona fasa kanki da bindiga yanzu" Ko kallonsa batai ba, domin ita yanzu mutuwar kawai take so, tazo ta d'auke ta ko kuma su su kasheta da kansu, ta gaji, ta gaji da wannan duniyar gaba d'aya. Rai a b'ace d'an bindigar zai nufi inda Fulani take, da wannan matar, Ogansu ya dakatar dashi ya ce "rabo da ita, da alama yarinyar zatai taurin kai" Shuru yayi sai can ya ce "yo Oga ba sai yanzu ka bani Okay na fasa kanta da bindigar nan ba, yanzun nan lahira tayi bak'o" "Batta dai ba yanzu ba tukunna" Fulani duk tana jin miye suke cewa, wasu hawaye ne keta zuba a idonta, ita wallahi da sun kasheta a yanzun da sun kyauta mata ma. Tana isa ga matar ta tallafo kanta suna kallon juna, lokaci d'aya suka ji gabansu ya fad'i. Sharewa Fulani tayi cike da tausayi ta ce "baiwar Allah kema sato ki suka yi ko?, ga ciki koma nak'uda kike yi naga kin rik'e cikin?" ."a'a y'ar uwa ba nak'uda bace, da sauran lokaci, amma ko yanzu zan iya haihuwa saboda tashin hankalin da nake ciki. Ni ba har gida suka je suka sace ni ba, akan hanyata ta zuwa garinmu Katsina, suka tare motar da nake ciki, suka kashe driver na suka taho dani" "Innallihi wa'inna alaihir raju'on wai su wa'innan mutanan basu da imani ne ko kad'an kashe rai kai jama'a" Fulani ta fad'a hawaye na mata zuba har yanzu. Matar ta sake damk'e hannun Fulani tana jin k'aunar yarinyar har cikin ranta duk da zasu zo sa'anni da juna, har shekaru sai dai ita zaka iya cewa nan take ta girmeta saboda auran data yi kuma ga ciki sai ya k'ara bud'ata ta koma kamar wata babbar mace. Ta ce "ya sunanki?" "Ni sunana Fulani" "Fulani" ta mai-maita sunan, sai can ta sake cewa "ni kuma Husaina" Fulani haka kawai data ji sunan ta sake jin wata fad'uwar gaba, had'e da k'ara jin matar a jikinta "Amma mi yasa kike kuka tunda aka kawo ki jiya, kuma kina rik'e da cikinki?" Murmushin daya fi kuka ciwo Husaina ta saki tana duban Fulani wacce kamar akwai sauran yarinyata har yanzu dabe sake ta ba, ta ce "hmm Fulani kenan, ya za'ai bazan kuka ba?, ina tuna halin da mijina zai shiga ne da sauran dangina shi yasa kika ga ina kukan nan. Rik'e ciki kuma ina tausayin abunda zan haifa ne a wajan nan, fatana ace sun sake ni kafin na haihu, to amma banga alamun hakan a tare su ba, kamar so suke suga baya na ne, bamu san mi muka tare ma mutanan nan ba, ji nake a jikina kamar bazan sake sa Mijina a idanuwana ba sabo...... Toshe mata baki Fulani tayi tana girgiza mata kai ta ce "ki daina fad'ar haka, ai gara ma ke ni kin ganni nan sai da suka kashe min kowa nawa, shi yasa banga anfanin su sake ni da raina ba ma, su kashe ni kawai na so ace tun can cikin y'an uwana nima sun had'a dani sun kashe, ban san miye hikimar tahowa dani da sukai ba" Tashi Husaina tayi a zabure tana duban Fulani ta ce "wai kina nufin garinku suka je suka kashe maku kowa, hasbinallahu wa'imar wakil" Cewar Husaina, bata san sadda ta rungume Fulani suka fashe da kuka a tare ba, kamar wasu wadda suka dad'e da sanin juna. Wata tsawa aka daka masu wacce tasa ba shiri suka zabura, suna kallon d'an bindigar dake tsaye da bindiga a wajansu. Yana cewa "munafukan banza, idan muka sake ganinku kuna wa'innan maganganun wallahi sai mun kashe ku gaba d'ayanku" Shuru su Fulani sukai suna k'ank'ame jikinsu waje d'aya. Wani garin kwaki aka jefo masu cikin wani kwano, ba magi ba gishiri an dai jik'asa sai uban yaji da aka dank'ara mai, sai ruwa guda d'aya da aka jefo masu, su biyu kowa kwano mutum biyu, ga garin bai wuce kayi loma uku dashi ba. Kamin ka ce mi wasu sun lashe nasu, suna tand'e hannu. Duk rashin dad'insa su kam ba wani ji sukai ba, ruwan ma haka suka d'an kurb'a badan an k'oshi ba. Fulani ta kalli Husaina ta ce "y'ar uwa ki d'auka kici kawaii kinga ke kina da ciki, bai kamata ki zauna da yinwa ba" "To ke kuma fa?" "Ke dai kawai kici ni yanzu bazan iya cin komai ba, garama na bari yunwar ta kashe ni da wa'innan kafuran Allah Ta'ala su kashe ni" "A'a Fulani ki iya bakinki ki daina cewa haka please, karma suji ki kizo muce tare kawai idan ba haka ba nima ba ci zanyi ba" Da sauri ta waiga inda Husaina take girgiza kai tayi ta matso tana cewa "shikenan mu ci tare" Da kanta Fulanin tayi ta ba Husaina abincin a baki, wadda bata lura ba ita Husainar duk rabi ita ta ci sa, loma d'aya kawai Fulani tayi tabar mata sauran tana bata a baki, ko ruwan ma Fulani ba wani sha tayi ba. Washe gari ma basu samu abinci ba, kusan kwanan su had'u yau kenan a wajan, a yanzu sun gane idan aka basu abinci yau to gobe fa babu maganar cin wani abincin. Ko a ranar bazai wani wadace ka ba, abinci kamar wadda za'a ba kyanwa shi. Wata irin kururuwa had'e ihu, su Fulani suka ji. Kai ba shiri suka zabura suna kallon inda ihun ke fitowa. Zare ido Fulani tayi gabanta na wata irin mummunar bugawa. "Wayyo Allah na shiga uku ku taimaka min zai lalata min rayuwa, wayyo Allah ba wadda zai taimaka min ne?" Fulani bata san sadda ta ce "Fyushind'o, Innallihi wa'inna alaihir raju'on, su kuma wa'innan harda fyad'e suke ma yara mun shiga uku, nan gaba muma zai iya zuwa kanmu" Kwata-kwata duk mutanan dake wajan hankalin su yayi mummunan tashi ganin cewa su harda lalata yaran mutane suke, shi yasa kenan suka jido y'an mata, wadda suka kashe masu iyaye ba wadda zai kawo kud'in fassarsu, anfani zasuyi rink'a yi da su kenan?. Wani kalar kuka Fulani ta saki tana shigewa jikin Husaina sosai kamar wacce zata koma ciki, Husainar ma hawaye take wadda tsabar tashin hankali da firgice har saida taji d'an cikinta ya mata wata irin juyawa, wadda har saida ta d'an saki y'ar k'ara. Ba shiri Fulani ta saketa tana dubanta hankali a tashe tana tab'a cikin tana cewa "Y'ar uwa ko haihuwa ce zakiyi muna cikin wannan tashin hankali?". Girgiza mata kai kawai Husaina tayi, amma ita kad'ai tasan azabar da take ji a yanzu. Ga Fyeshind'o dake kururuwar ihu, ba wadda yayi gangancin nufar inda aka aje Fyeshind'o y'an Ta'addar sun zagaye wajan da Bindigogi ga Ogan nasu wani rusheshe dasu yana niyar kwab'e wando, kai tsabar rashin kunya da rashin imani ma a gaban jama'a a bainar nasi yake shirin keta ma y'ar yarinya haddi. Fulani ta kasa kallon inda abun ke faruwa, kuka take kawai jikinta na d'aukar wata irin kyarma, daga ita har Husainar hankalinsu a mugun tashe yake, da za'a auna su a wannan lokacin to za'a iya cewa jininsu yayi mugun hau sosai. Wani tsoho ne wadda shi an dad'e da kawo shi wajan ya tashi yana isa inda Ogan ke shirin keta haddin baiwar Allah, ya d'uke k'asa yana rok'ar suyiwa Allah karsu lalata wannan y'ar k'aramar yarinya. Wata hanb'ara da sukaima wannan tsoho ya tafi ya bugu da k'asa hancinsa ya fashe, kamin ma ya dawo hayyacinsa kawai suka ji saukar harsashi had'e da k'arar Bindiga. A saitin kansa suka halbesa ko shurawa baiyi ba. Bakin Fulani bud'e yake kowa dake wajan yayi shuru kamar anyi ruwa an d'auke masu taya Fyeshind'o kuka, suma kukan ya yatsa cak yadda wajan ya d'auki shuru kai ka ce babu halittar dake rayuwa a wajan. Husaina kuwa d'an cikinta ne ya sake motsawa, had'e da naushinta, runtse idonta tayi da mugun sauri tana dafe mararta jikinta ya fara d'aukar kyarma, zufa ta fara keto mata. Ita kam yanzu tasan haihuwa ce tazo mata ba shiri tashin hankali yasa haihuwa zuwa a sadda lokacinta baiyi ba. Wani d'an Ta'adda ne ya juyo inda suke cike da muryarsa marar dad'in ji ya ce "duk d'an iskan daya k'ara zuwa wajan nan da sunan ya rok'e mu idan muna aiwatar da abu, to zai tafi inda muka aika wannan tsohon". Tsoro ne ya k'ara rufe su. Wadda suke kukan ma dole tasa suka toshe bakunansu, hawaye ne kawai kake iya gani na zuba a fuskokinsu. Fulani hankalinta ya rabo kashi biyu, danta lura wallahi fa Husaina haihuwa ce tazo mata a wannan hali. Kamin su gama dawowa hankalinsu suka ji Fyeshind'o ta kwallara wata gigitacciyar k'ara had'e da cewa ta shiga uku ya kashe ta. A sadda ya keta mata mutumcinta da rashin tausayi da rashin imani kuma, saboda da mugunta da k'arfi ya shigeta. A dai-dai lokacin kuma Husaina ta saki wata irin gigitacciyar k'ara had'e da salati a bakinta. Ba shiri wani daga cikin y'an Ta'addar ya ce "kai kardai waccar matar haihuwa zata mana a wajan nan?, Ai ko kuje ku tsaya inda take tana haihuwa ku amshe abunda ta haifa ku kashe shi, domin baza mu zauna da jariri yana damun mu da kuka ba" Husaina da Fulani na jin wannan abu hankalisu ya k'ara tashi ainun, Husaina ta damk'e hannun Fulani tana girgiza kai cikin azabar ciwo ta ce "Fulani kiyi min al'k'awarin cewa duk wuya karki bari azzaluman can su kashe abunda na haifa, nabar miki komiye na haifa halak malak Fulani ni nasan mutuwa zanyi, Fulani ki ceci kanki da abunda na haifa dan Allah" "Innallihi wa'inna alaihir raju'on" kawai Fulani ke iya cewa tana rik'e da hannun Husaina ta tare ko ina, ga y'an Ta'addar da suka zagaye su. *FUNTUWA LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA* "Ke Nana zaki fad'a mana, gidan ubanwa kika samo wannan kud'in, ko sai na mak'ure kin mutu kowa ma huta?, Ashe dama acan Abujar haka kike yi gidan mutane yawon bazan, da tsayawa da samarin banza?, Suke baki wa'innan kud'in ko kuwa?" Cewar Inna Saude dake zaune a Babban parlon, gidan da take aiki. Da aka aika kiranta yau tazo an dawo mata da d'iyarta Nanah a bisa da bata jin magana ko kad'an, a can Abujar. Shi yasa tajawo Jafaru suka taho tare suna matsifa yarinya zata ja masu salalan tsiya, so take d'an arzik'in da suke ci a yanke masu cinsa. Kawu Jafaru ne yayi kukan kura ya zafga mata marin daya sa ta wuntsila ta fad'i tana sakin kuka. Ya ce "kin ga y'ar banzar yarinya ana miki magana kina banza da mutane kaga y'ar iskar yarinya, y'ar bak'in ciki, so kike kiyi mana bak'in ciki kenan?" "Ya isa haka Jafaru" Cewar Mai gidan, "Wallahi ranka ya dad'e daka barni na barta kwance dole ta sanar damu gidan ubanwa ta samo kud'in nan" Kamin ma Jafaru ya rufe baki Inna Saude ta tashi haye ruwan cikin Nanah sai duka take kamar ta samu k'ato. "Subhanallahi ke Saude miye hakan?" Cewar Alhaji yana ma Inna Saude tsawa. Dakatawa tayi da dukan nata tana cewa "Alhaji daka rabu dani in kasheta kawai wallahi. Kuma zaki fad'a min gidan uwar da kike samu kud'in nan, ko ki bari idan muka koma gida, insa wuk'a in kashe ki kowa ya huta, ni daga baya an d'aure ni" Kuka Nanah keyi harda majina tana cewa "wallahi Inna kud'in makaranta ne fa da suke bani nake tarawa suka zama haka" "Rufe min baki munafuka, kud'in makarantar ne zasu zama haka, algunguma sababbin kud'in bugun Abujar da nake gani yanzu sune kud'in makarantar" Jannat da ita ce akaba Nanah take zaune wajanta ta ce "ni dai Daddy daka bari munbar ta wajan iyayenta, domin kaga yanzu ma k'arya take gaya ma iyayen nata, mu da ba bata wasu kud'i muke ba, komai muna dashi a gida, idan zata tafi babu abunda bata dafawa domin tafiya dashi har biskit da alawa ina ajewa a gidana domin dai ita da Hana idan zasu school na basu. Na maida ita kamar fa ba y'ar aiki ba kamar y'ar uwata haka na d'auke ta" Kamin ma Alhaji ya ya ce wani abu karaf Inna Saude ta amshe da cewa "kiyi ma Manzon Allah kuyi hakuri, kun san ka haife d'an yau ne kawai amma baka haifi halinsa ba" Alhaji ya nisa ya ce "na sani Jannat zaku koma da ita, idan ta sake ni na ce ku dawo masu da d'iyarsu. Abunda yasa na ce haka shine, ba yadda za'ai ku dawo da ita a yanzu tunda kun rik'e ta tun tana y'ar yarinyarta yanzu kuma ta zama budurwa, kune keda alhakin yi mata kayan d'aki, kinga yanzu ba yadda za'ai ku dawo da ita salin alin haka nan kawai, hakan ba adalci bane" "Daddy shi ai ya ce a gaya masu idan ta tashi auran a gaya masa zaiyi kayan d'akin da komai ba dole sai tana wajanmu zamuyi mata kayan d'aki ba" "Nasan da hakan, nasan Sageer dama bazai k'i mata komai ba, amma ni na ari bakinsu na ci masu albasa, a bata dama ta biyu idan ta sake ku dawo da ita, ba maganar bada hakuri kuma" "Ai insha Allahu Alhaji bazata sake ba, shegiyar yarinya kawai" Cewar Inna Saude dake kallon Nanah tana banka mata harara Alhaji ya ce "kuyi mata addu'ar shiriya shine kawai ba ku rink'a zaginta haka ba, saboda shi bakin iyaye dandanan yake kama yaro ku kiyaye ma yaranku baki" "To to to Alhaji insha Allahu" Cewar Jafaru yana zare ido yana kyaf-kyafta su. Bayan an sallame su suka taho akan hanya ma sai zagin Nanah suke suna kwashe mata albarka. A k'ofar gida, Jafaru ya iske Barau Mai Caca. Da zai juyo ya gudu ai ko Barau yayi kukan kura ya cafke sa. Yana zare mai ido ya ce "ka san Allah Jafaru na fika d'anyan kai, ko ka biya ni kud'in sadakin dana biyu, na al'k'awarin da kayi min zaka bani auran d'aya daga cikin y'ay'anka mata, ko nayi ma dukan da zaka kasa tashi. Kaje ka cinye su, ko kuma wallahi na kira maka y'an Sanda su zo su tafi da kai, kuma kasan wallahi har gidan yari sai kayi" "Dan girman Allah ba sai ta kaimu da haka da kai ba, ai nayi ma al'k'awari zan baka Mafida in..... Wata irin ashar Inna Saude ta lailayo ta dank'ara tana cewa "kutumar Uba, ai wallahi baka isa ba, uban kuturo yayi kad'an bare na makaho, ai na rantse da sarkin da ke busan lumfashi, sai dai idan bana raye, zaka d'au y'ata kaba wannan tanbad'd'an mutunan, ai wallahi sai dai ka d'au d'iyar d'an uwanka Maryam ka basa, amma ba dai cikin Yara na ba wallahi" A dai-dai lokacin da Maryam ke kawo kai zata fito daga cikin gidan, taji abunda Inna Saude ke fad'i. Gabanta yayi wata irin bugawa, har saida ta dafe k'irjinta tana kallon mutunan da ake son k'ak'uba mata shi yanzu. Miya kai Kawu Jafaru amsar kud'in sadaki a wajan Caca na Y'ay'ansa?, wannan wacce irin rayuwa ce suke haka?. Maryam ke fad'a a zuciyarta wasu hawaye taji suna zub'o mata a kumatu. Tabbas ko zata mutu wallahi bazata auri wannan mutunan ba. Tunaninta ne ya tsinke jin a abunda Kawu Jafaru ya ce. Wadda yasa ma jinta da ganinta d'aukewa na wucin gadi tsabar tashin hankali da firgice... *ARMAN HARUN'S HOSPITAL LOGAS NIGERIA* Tsaye take tana share hawaye, tunda aka kwantar da Y Aliyu hawayenta suka k'asa tsayawa, gaba d'aya ahalinsu a tashe yake tashin hankalin da suke ciki yasa gaba d'aya komai nasu ya tsaya cakkk. Mimi kuwa canta baro ta d'akin da aka kwantar da Y Aliyun tana sallah tana rok'ar ma d'an nata samun lafiya da addu'ar kare sirikar tata a duk inda take. K'amshin turaransa yayi mata sallama tun kamin ya iso wajan da take, ta waiga tana masa wani irin kallo mai wuyar fassarawa shima hakane, kallonta yake duk yadda lokaci d'aya ta rame ta fice daga yaccinta. Tunda suka zo asibiti shine ya amshi Y Aliyu. A sadda Lalaah ke mai jawabin abunda ya faru tana kuka, bai san sadda ya rungumeta yana lallashinta ba, a sannan ne kuma ya sanar da ita sirrin dake cikin zuciyarsa, da ya dad'e yana dako a kanta. Ta k'asa gasgata abunda take ji yana fitowa daga bakinsa, ga wata irin fargaba data tuna cewa fa shine Yayarta Lilaah take so kamar ranta. Kawai ta fito daga Office d'in tana rusar kuka kamar wacce akai ma mutuwa. Har yanzu hawayen sunk'i tsaya mata, koda yazo saitin inda take ya mik'a mata wani kyalle mai taushi da k'amshi ta share hawayen dake zuba mata. Amsa tayi kawaii can taji muryarsa yana cewa "please muje Office ki zauna ki samu natsuwa" Bin bayansa kawai tayi kamar wata sakarai. A dai-dai lokacin kuma Lilaah ta shawo kwana zata nufi Office d'in Arman d'in. Tana gaf bud'e Office d'in taji Bilkees na kwala mata kira. D'an dakatawa tayi da bud'e Office d'in. A cikin Office d'in kuwa, Arman na k'ara jaddama Lalaah shifa auranta yake sonyi, kuma duk duniya ita ce kad'ai ta tab'a tasiri a zuciyarsa, ita ce kad'ai yake jin wani abu dangane da ita. Ita kuwa kallonsa kawai take hawaye na mata zuba. Tama rasa miye ya kamata ta ce "wai yau ita ce Arman Harun Maleek ke fad'a yana sonta haka?, so bana wasa ba, a yadda take ganin tsantsar sonta a cikin idonsa, anya ba mafarki take ba kuwa?, Arman dai wadda ta sani shahararran likitan nan mai ji da kyau da kud'i da iko kota ina, wai yau shine zaune a gabanta yana mata magiyar ta soshi, ita kam mi zata ce ma Ubangiji. Sai dai abu d'aya ke mugun bata tsoro da damunta, Lilaah fa? miya sa abun zaizo masu a haka?" abunda take cewa kenan a zuciyarta "Ina ta kiranki tun d'azo wayarki bata shiga lafiya dai?, Kuma naga an kwantar da Y Aliyun ku a nan hospital d'in mi yake faruwa ne Lilaah?" "Wallahi wai sumewa yayi saboda y'an Ta'addar da suka kira shi suna shaida masa idan aka sake sa Jami'an tsaro a ciki zasu kasheta ne" "Subhanallahi ah ahh dole Y Aliyu ya suma, masu garkuwa da mutanan nan fa ba imani ne dasu ba" "Hmm hakane kam" Cewar Lilaah ko a jikinta, da kaga yarda take bata amsa zaka san ita abun bai wani dameta ba. A tare suka nufi Office d'in domin shiga sun tura k'ofar kenan suka ji saukar muryar Arman yana cewa.......... *To laifin dad'i aka ce k'arewa a nan na kawo k'arshen Free pages. Game bukatar tafiyar nan dashi k'ofa a bud'e take* Ina so na sanar daku cewa Free pages zai tsaya daga na 10 ne game bukatar TAFIYA dashi na wanga book d'in zai biya D'ARI BIYAR NE KACAL, ba sai na tsaya yin wani dogon jawabi ba, kun dai san wanga book akwai k'ura a cikin akwai matsaloli masu tarin yawa, akwai sirrikan dake binne wadda duk za'a warwaresu nan gaba* Zaka iya turo kud'inka ta wannan account d'in 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank Sai ka turo shedar biya ta wannan number d'in 👉 08130479973 Zaka iya turo kati MTN D'ari biyar ne kacal