🕊️🕊️ *Hammad zairah*🕊️🕊️ *Boss lady* 🦅Mikiya writer's asso..... 🔞Ki watsar da na banza ki dau na kirki. Please idan zuciyar ki ba mai ƙarfi bace kada ki fara sister *Labari ne mai bangare uku* *Meeyrah* *Hammad* *Jannat* *Littafi dai Free ne*😜 *Dedicated to nimcylove* 1️⃣✅3️⃣ Katsina 2pm 18 nov 2024 Yanayin garin ya yi dai dai da irin lokacin nan na sanyi saboda yadda yanayin garin ya yi hazo hazon na sanyi kowa ka gani lokacin da rigar sanyi jikin shi wasu ma harda first mas sun rufe fuska saboda yanayin garin' wanda a wannan lokacin kuma duƙe ta tana aikin da ta saba Kuka take mai cin rai sosai kamar zata shiɗe ta kalli ƙannen nata a karo na ba adadi ta furta innalilahi wa'innailahir raji'un Allah kai mana ɗauki ƴar ƙaramar yarinyar ta matso kusa da ita ta ce "Anty Mereeh please am sorry in sha Allah komi zai zo mana da sauƙi mu rinƙa addu'a Allah zai kawo mana ɗauki kada ki damu da abin da baba sabo yai mana in sha Allah asiri zai tonu mu bar ma Allah kawai" Aliyu kanin Mereeh ya miƙe ya ce "Aunty bari na tafi zuwa anjima zan dawo ki kula da su yai gaba abin shi" Mereeh ta tashi wani ɗanɗumamen tuwo ne kulli uku, ta sa ɗan gawayin ta ɗumama su'ta malla ma kowa nashi ta samu wata tsohuwar kula ta sama kanin nata a kula ta maida ta aje gefe, wajen karfe uku na rana sai gashi da farin ciki a fuskar shi kamar wanda aka biya ma maka ta fito tare da mai sannu da zuwa ya miƙa mata wata leda ta amsa tare da faɗin mai muka samu friend ba dai ka gajiya da hidima da auntyn ka ko?? Murmushi ya yi tare da sosa ƙeya yace"Aunty uhmm dako nayi a can tasha shine sai na siyo mana kofin shinkafa sai ɗan barkonon da na siyo a dafa maci mai da yaji wallahi bana san muna zama da yunwa ba ma Kamar taslim ita da take ƙarama" murmushin dake ƙara ma fuskarta ƙyau tai mashi tare da faɗin Allah ya dafa mana, ta aje mai towon da ta aje mai tunda rana duk da haka sai da ya tasa su ita da taslim suka ƙara ci. Innalillahi Allah mun tuba ka yafe muna ya Allah' ta kuma jawo taslim jikinta Wadda take kwance shame_shame kamar gawa ta ce "Aliyu Please ka bari idan naje gidan baba sabo ɗin abinda muka samu sai a kaita asibitin" "Kinsan dai baba Sabo bai da mutum ci ko kaɗan am nasan ko da munje neman taimako nasan ba bamu zai ba, amma tunda kin dage sai ki tafi ya rungumo taslim ɗin ita kuma ta ɗauki hijabin ta baƙi wanda cikin hijabin nata shine mai ɗan dama tana fita ta samu napep ta hau bai sauke ta ko ina ba sai ƙofar gidan baba sabo, daidai lokacin kuma ya fito sai mita yake an bata mashi rai" ......... "Don Allah sameer kada ka aikata min haka kai kasan kaine aure na na biyu idan kai mun haka ka cuce ni ka cuci rayuwata am idan wani abu na maka don Allah ka yafe mun in sha Allah ba zan kuma ba ka taimaka min!" Ƙafarshi da ta riƙe ya fisge ya falla mata mari ya ce" idan hauka kike to ki dawo haiyacin ki banza mara hankali kuma ki tafi gidan ku nasa ke ki saki ɗaya" wani irin takaici ne ya kamata ta Marasa mai zata ce mashi yanzu illa bin shi da ido dake, wayar shi ya ɗauka tare da kiran beb din shi daman ita tace ala dole sai ya saki matar shi ko zata aure shi kuma ya cika mata aikin da tace tana so cikin farin ciki da murna yake sheda mata ya ai watar da abin da take so, sulalewa tai ƙasa tama rasa mai zata yi zaune suke ƙalau amma yau rana ɗaya ita ce sameer zai ma haka ta ma rasa wane irin tunani zata ai watar kanta ya ƙara ɗaukar zafi kwanciya tai bakin gado Cikin zuciyarta ta na faɗa mata kada ta tafi ta tsaya ƙila ya maida ita ɗakin ta, wanka ta tashi tai tare da ɗaura indomi domin ta sama ma cikin ta abincin don yunwa take ji ba kaɗan ba" ........sameer ban ɗauka cewa da gaske zaka iya rabuwa da matar ka ba yanzu! ƙara damke hannun ta ya yi cikin nashi ya mata murmushin gefen baki tare da faɗin uhmm ke kinsan ina san ki har cikin jinin jikina ina jin san ki, so ba abinda zaki ce na maki na kasa i love You so much nimrah. Wani daɗi ne ya ƙara kama mata zuciyarta Saboda abinda ya faɗi mata ko ba gaske bane tabbas taji daɗin abin da ya faɗa' suka cigaba da firar masoya abin su bai koma gida sai after 10pm dai-dai lokacin kuma jannat tana zaune kan darling table tana jirar dawowar sa ƙarar buɗe get ne yasa ta mike da sauri ta fito don tarar shi ita ta ma manta da abin da ya faru ɗazu! ________________________ Baffa ina ƙwana? Cewar matashiyar yarinyar da ke duƙe gaban ɗan madaidaicin mutum. Dafa kanta ya yi ya ce" alhamdulilahi fatsuma idan Allah ya kaimu anjima ina san na tafi jeji ɗebo magungunan in sha Allah" Baffa ina so na bika nima. a'a fatsume kada kice haka kinga Yanzu ma kina da aikin ki da zaki ki hakuri idan na ɗebo dai kin daka min su. Wacece fatsume Malam habu bafulatanin asali ne fari ne dogo yana da hanci yana da mata maryam mace kamula mai san jama'a suna da yarinya ɗaya fatsume suna nuna mata so da kauna' fatsume tana da shekaru goma sha uku Allah ya ɗauki ran maryam sun sha kuka ita da baban ta har kuma yau bai ƙara aure ba Saboda yana gudun Kada ya auri matar da zata cuci mai ƴar marainiyar ƴar sa, yana kiwon shanu kaji awaki kuma yana bada magani..... fatsume tana da tarbiyya sosai ga San mutane kamar uwar ta, tana da ɗan ilimin zamani na mahammadiya ma akwai dai-dai misali. Wannan shine takaitaccen tarihin fatsuma..... baffa ya ɗauki ƴar jakar shi da yake zuwa jeji ɗibar magani ya tafi ita kuma ta fara aikin gida!! .....Lafiya na ganki anan??cewar baba sabo. Durkushewa tai ƙasa tana kuka tare da faɗin don girman Allah baba sabo ka taimaka mana ba don mu ba "taslim ce ciwon ta ya tashi gashi bamu da kuɗin zuwa asibiti" A tsawace baba sabo ya ce" ikon Allah wai don Allah mai kuke san maidani ne haba nace ki fidda miji ki aure amma kin ki saboda kina samun abinda kike so shi ne dalilin da kika ki aure" A'a baba wallahi ba haka bane mudai yanzu muna neman taimakon kuɗin da zamu kai ta asibiti don Allah a taimaka mana da ko nawa ne.. Wani irin mungun tsaki yaja tare da miƙa mata dubu biyu' tai mai godiya tare da mikewa ta nufi titi don tarar abin hawa.. Buge ta ya yi da hannun shi na hagu tai sauri ta duƙa tana mai dafe bakin ta da hanci jini tagani a hannun ta da sauri ta shiga ɗakin ta bayi ta faɗa tana mai kuka tana wanke bakin nata.... Ammi ammi ammi tana ɗan jijjigata tana ƙwalla ta ce ammi komi ya yi farko zai yi karshe ina ji a jikina ɗan uwana na raye bai mutu ba! Ƙwallar ta ta share karo na uku kenan da take share shi ta riƙe hannun ƴar ta ta, jidda nikai na ina jin haka amma kuma bazan tabbatar da hakan ba har sai nagan shi a gabana. Mai martaba ne ya shiga cikin ɗakin nata jidda ta gaida shi tare da barin wajen don su gana da ita ya ce" Allah subhanahu wata'ala ya halicce mu ne ba don komi ba sai don mu bauta ta masa Akwai ƙaddara mai ƙyau da akasin haka idan muka karba hannu biyu sai Allah ya dube mu da idon rahama kullum ina ƙara faɗa maki halima kidaina wannan kukan ki ta addu'a har Allah ya bayyana na mana shi.... ta ƙwanta kan kafaɗar shi ta ce wallahi ko naji a Cikin rai na na dangana sai kuma naji zuciya ta tai rauni narasa mai ke damuna. Baki ya ƙara bata tare da ƙwantar mata da hankali.. ........Ta mutu ta mutu aunty mereeh tun da kika tafi ba daɗe wa ba Allah ya mata rasuwa haka yake sheda mata yana kuka! Duƙawa tai ta rufe mata ido tana mai mata addu'a Allah ya jikanta' shikenen yanzu su biyu suka rage daga ita sai kanin ta Aliyu baba da mama sun yi hatsari a motar kuma ba abinda aka fitar komi ya kone a motar yanzu kuma gashi taslim ta rasu ta barsu, kuɗin da baba sabo ya bata akai mata hidima dashi don kaita gidan gaskiya sun sami makota suka taya su zaman makoki, baba sabo yazo masu ta'aziya ranar da akai addu'ar uku yazo masu da rabin tiyar dawa wai suyi towon dawa, zai tafi ne Aliyu ya bi bayan sa don su yi magana!! Tom lafiya kuma "Ali ka biyo ni nan?" Uhmm daman baba ina san kuɗin gadon mu a ɗan bamu wani abu cikin gadon mu idan ba damuwa. Kai dalla can banza kuɗin gadon ku daman kuna dashi ne? Bana san sha shan ci. Ɗaga murya Aliyu ya yi ya ce" haba baba sabo kuɗin mu hakkin mu ai suna gunka mun nema ka bamu hakkin mu amma kana Magana maganar banza idan ka cinye ne ai sai ka faɗa musan mai muke ciki........ mutanen da ke gun ne suka taso suna ma Aliyu magana kan ya yi hakuri amma ina zuciya tazo wuya ya ce wannan macuci ne ya hana mu hakkin mu yana ganin muna wahalar rayuwa amma ko in kula damu ya ki bamu hakkin mu.. Limamin Masallacin ne wanda dashi ake zaman ya ce" baba sabo tabbas cin dukiyar maraya ma bai da amfani idan har da gaske yaron nan yake ka taimaka ka basu hakin su tun kafin Allah ya tambaye ka, nan dai ya fara mai wa'azi, amma ina wanda ya yi nisa bai jin kira" Gado na ce na cinye daidai lokacin kuma wani daga cikin abokan Aliyu ya ce ya faɗa mata tafito ta ce" haba Aliyu ba nace kada ka kara mai wannan Maganar ba idan har kana jin magana ta don Allah ka kyale zancen nan bana so' shi da yaji yaje can zamu haɗe Inda bashi taja hannun Aliyu suka shiga cikin gidan" Tafe yake a hankali yana dibar maganin shi sannu a hankali duk ya dibi ganyen da yake so, wani mutum ya gani kamar mai lafiya amma irin kayan da ya gani jikin yasa ya tabbatar mai da ba Lafiya ba ya isa gare shi ya ce bawan Allah, amma ina shi dai sai bin shi da ido yake.... Littafin nan free page ne idan naga ruwan comments zan cigaba daga inda aka tsaya Boos lady taku ce Mai san magana dani sai ya min magana a 08160647868 🕊️ *hanmad zairah* 🕊️ *Boss lady* Dedicated to nimcyluv 🦅mikiya writer's asso.... 4️⃣🔸5️⃣ A ƙwana atashi ba wuya a gun Allah yau har taslim tai ƙwana bakwai da rasuwa jin gidan suke ba daɗi daman wani lokacin ita ce mai sasu dole sai sunyi magana yanzu ko bata, Aliyu ya miƙe tare da faɗin Aunty na bari na ɗan fita... Kai ta gyaɗa mai shi kuma ya fita wajen ƙarfe 12 na rana wata ƙawarta tai mata sallama da murna a fuskar ta ta tare ta suka gaisa tai mata gaisuwa lokacin da akai rasuwar basu nan sun fita ita da su mummyn ta hutu, saboda ita ta cigaba da school mereeh ce dai ba halin ci-gaba ruwa ta ɗebo ma a kofi cikin tausan ta ta furta ƙawata kuma wai kawun naku bai baku rabon na ku ba?? Murmushi tai mata saboda ita har mantawa take ma da wani baba sabo, uhmm hanan wannan kuma ai sai dai kawai mu bar shi da Allah saboda ko lokacin nan sai da muka mashi magana ya ce ya cinye mun bar ma Allah!! Oh my god hanan ta furta tare da faɗin am sorry mereeh komi zai dawo dai-dai. kuka tasa ta ce" ina maganar dai-dai hanan mun rasa mama mun rasa ba ga taslim ita ma ta tafi ta barmu, wannan duniyar bana jin daɗin ta ji nake kamar na kashe kaina na huta😭😭" Dafa mata kai tai tare da bata hakuri sai da ta tabbatar da ta hakura sannan ta ce bani account ɗin ki ko ba yawa nasa maki. Saboda buƙatar kuɗin yasa ta bata nan take ta tura mata dubu ɗari biyar ta ce ba yawa tai mata sallama ta tafi gida. Ko da Aliyu ya dawo gida ya tadda abin farin cikin nan yaji daɗi sosai nan ta ce ya koma makaranta saboda sun yi jarabawar shiga aji na na huɗu a sakandire ya ji daɗin haka kuwa, kasuwa ta tafi wata tsohuwar firiza ta siya don ta riƙa sai da ruwa sobo da kunun aya suga ko za'a dace...... Wajen ƙarfe 8pm suka ji Kwankwasor ƙofar gidan nasu Aliyu ya fita don ganin su waye, mota ce cike take da kayan abinci wanda ya buga ya ce "sako ne daga hanan ta ce akawo nan gidan!" Da sauri Aliyu ya basu hanya suka dinga shiga da abincin cikin gidan alhamdulilahi kawai mereeh take maimaitawa buhun shinkafa uku' wake buhu ɗaya taliya katan biyar sai jarkar mai da manja ya miƙa mata wani leda ta amsa tare da mai godiya suka tura gidan hamdala kawai suke ita ɗan uwan nata suna shiga cikin ɗakin ta buɗe kuɗi ne naira dubu 50 ta wata ƙaramar takarda an rubuta.. "Ƙawata kiyi hakuri da wannan su mummy ne suka baki saboda na faɗa mata halin da kuke ciki ga kuɗi nan sai ku cefane" Ƙwallar farin ciki ce ta mamaye ta ta furta"Aliyu kagani ko Allah mai rahama mai jin ƙaine Allah mun gode maka" Rungume Aunty mereeh ɗin ya yi suka sa kukan farin ciki.. Jalingo ƙauyen malam idi _______ Yaro baka magana ne? Shi dai sai bin shi yake da ido don bai san mai zace ba, ya kama hannun shi suka fito cikin jeji gida suka nufa inda ya iske fatsume har ta gama masu komi na aikin gida sallama ya yi. Da sauri ta fito don tarar baffan nata sai kuma tai turus ganin shi da kaɗo suna tare ta ce" baffa sannu da zuwa" Murmushi ya mata ganin irin kallon da take bin kaɗo dashi ya ce" fatsuma shimfiɗa mana tabarma" shimfiɗa wa tai tare da basu ruwa a kwanon sulba ta ɗauko fura ta aje nan ma ta koma gefen su ta zauna".. Jannat kiran ƙawarta tai tare da laburta mata abinda ya faru tsakanin ta da sameer salatı tai ta nuna mata ırin damuwar da ta shiga ciki da suka gama wayar ne ta taɓe baki ta ce Allah ya kara sauran saki ma da idasa mata ta tashi ta shirya don taje gidan jannat din... Sameer ne ya fito ya zo inda take ya ce wai baki da gidan uba ne da ba zaki tafi ba ne komi?? Don Allah ka.. Mai dani ɗaki na ba don ni ba ka taimaka min. Wani banzan kallo ya watsa mata ya ƙyalƙyale da dariya ya ce saboda gidan tsoho babu dadi kike tsoran tafiya kumi? Na naki daga nan zuwa jibi ki bar min gida duk wani abu naki ki tattara ki bar min gida ya fita cikin gidan rai ba ce.. Cikin ƙankanin lokaci ta Isa gidan jannat yadda ta sameta Abin ya mata, tai taba baki kan ta hai hakuri komi zai dawo dai-dai amma cikin ƙasan zuciyarta ba haka ba da ta duƙa a kan cinyar ta tana kuka ita kuma dariya take mata harda gwalo suna cikin wannan yanayi ne sameer ya dawo gidan gaisawa sukai da ƙawarta ta kamar ba abin da ya faru tsabar munafunci irin na maza harda matsawa kusa da jannat tare da faɗin beb baki mana abinci bane?? Da kallon mamaki ta bishi don ya daure mata kai abin' cikin zuciyar ta kuwa tunani take kila ya maida ita ne har wani tsallen daɗi take ji ta furta mai yanzu nake san wai na ɗaura mana kaina ke ciwo!! Ai tunda ga ƙawarki sai ta girka mana kin huta. Ƙawarta sai ta shiga ruɗu to ko daman karya jannat keyi mata saboda Yadda taga abin ya koma mata wasan kwaikwayo.. Mai martaba ne zaune kusa da matan nashi sun sashi tsakiya ya ce" fulani a ƙalla yau wajen kwanan wata da bacewar yaron nan amma banji kin furta min komi ba". Wacce aka kira da Fulani kanta a ƙasa ta ce Allah ya gafarce ka ranka ya dade ai min hakuri wallahi abubuwan ne sai a hankali duk lokacin da nazo maka zancen sai na ƙasa Saboda ina jin san yaron nan tamkar nice na haifeshi har cikin ran mai martaba yaji dadin abinda tace don fulani karshe ce wajen iya tsara zance.. Hakuri taba abokiyar zaman nata ita ma bata nuna mata komi ba, daga nan ya basu hakurin rashin samun shi da har yanzu ba'ai ba amma har yau ana cigaba da neman shi. ........ alhamdulilahi yanzu buɗi ke ta zuwa masu ta inda basu tsammani ba, ta koma sana'a tana sai da sobo kunun aya tana shinkafa da wake saboda kusa dasu an buɗe wata makaranta Aliyu kuma ya koma makaranta, tana zaune baba sabo ya shigo cikin gidan kai tsaye ko sallama ita gaban ta ma faduwa ya yi saboda ganin mutum ba tai tunani ba. Ya ce" naji wani labari wai kina sai da abin ci mereeh ba dai zaki fidda miji ba dai ko?" A'a baba sabo ina wuni ya su gwaggo? Ehh muna sai da abincin ne domin rufa ma juna asiri.. Ko haka zaki ce ance min har masu motoci suna tsayawa don ki basu Kunun aya' ban yarda da cewa shi kaɗai suke karba ba harda wani abun dai to ki shirya na maki miji akwai wani malam Musa abokina nane sosai yana da mata uku yara kuma guda 47 ne nan da sati biyu nake san ai bikin sai ki sai abinda ya kamata! Ƙwalla ce ta zubo mata ta furta billahillazi bazan aure shi ba, ai yanzu ba'a auren dole tabbas Dole baba sabo kabar wannan zancen tana cikin wannan magana sai ga Aliyu daga makaranta ganin shi ya sa ya haɗe fuska kamar bai taba dariya ya ce mai ya kawo ka gidan mu malam? Ohh yara dai rashin kunya kuka koya dai cewar baba sabo to nazo ne batun auren yayar ka da na mata miji nan da sati biyu masu zuwa.. Kutt mar duma du kenan' duk duniyar nan Uban waya isa ya mata auren dole ai sai mahaifanta kuma basu raye' don haka ka daina wannan batu kada ma rai ya ɓaci mai kasani game da ita cin ta shan ta suturar ta sai kawai muga mutum daga sama ya zo da zancen banza, bari kaji sabo sai batun ya ba shi mamaki. Yau ba baban mun fidda kai a matsayin ɗan uwan uba kowa ya yi hidimar shi... " Duk zancen da yake mereeh kuka ta ke sai yanzu ne tasa baki da taji furucin Aliyu wai sun fidda shi ta ce don Allah Aliyu kai shiru haka" Dalla can Aunty mereeh idan ke baki da baki ne zaki tsaya a cuta Maki nine Yanzu zan rinƙa tare maki duk wani shege zan iya dashi ko waye wallahi ya fizgi hannun ta ya tura daki ya yawo ƙofar ya rufe, ya juyo gun baba sabo tare da nuna mai kofar fita ya buga mai woning kada su ƙara ganin kafar shi gidan! ....baffa ya mai wanka ya canza mai kaya shi dai bin su yake da ido ko magana sukai mai sai dai ido baffa dai yana ta mai magani kuma suna ganin sauki sai dai Maganar ce da har yanzu ya koma kamar karamin yaro, kamar kullum yau ma sun gana shan fura baffa ya tafi daji ita kuma ta kaɗa shanu suka tafi kiwo sun je inda shanu zasu sha ruwa sai taji Muryar ƙaramin yaro ya ce canu lale yana tsalle!! Da sauri ta juyo don ganin waye wannan kaɗo ta gani ba ta tabbatar ba sai da taji ya kuma canu lale sannan da murna tace su koma gida sun isa gida ba da jimawa ba baffa ya dawo ta laburta mai komi ya ji daɗin haka ya fara magana... Taliya baffa ya fita garin yayi cefa ne ya dawo domin ta dafa masu "habu dake zaune ya amsa ya ce cannu da cuwa baffa" da yake sunan da suke kiran shine habu, murmushi baffa ya yi ya ce kai ma ƴar kanwarka ta dafa mana"! Da gudu ya shiga cikin gidan mutum har mutum amma ba hankali ya ce" baffa ya ce na kawo maki yana waje" Amsa tai ta daura masu.... minti 30 ta gama komi ko wajen cin abinci mai sai da habu ya bata kayan shi Please contuie Ku riƙa share fisabidillahi redear saboda suma wasu su gani Masu comments ina godiya Phone number 08160647868 Boos lady taku ce 6️⃣🔸🔟 Alhamdulilahi suna ganin alamun sauki sosai sai dai ya koma yaro abin da suka ci karo dashi bai masu daɗi ba saboda mai gari ya ce" kaɗo ba zai zauna mai gari ba tabbas sai dai ya bar garin ko su tafi tare ba, duk garin babu mai magani gargajiya irin baffa amma akai mai wannan wulakancin Saboda kaɗo ya samu masu gina yar bukka aka gina mashi mai daki biyu shi da kaɗo ita kuma fatsume ita kaɗai, mai gari bai tunanin zai yarda ya bar garin ba gashi ko ya yi nisa da garin sosai don sai kayi ƴar tafiya sosai zaka iske gidan baffa" sun tare Lafiya lau baffa kuma ya cigaba da bada maganin shi sai dai a same shi can ƴan kuɗin da yake tarawa na magani ya siyo ma habu kaya kala biyar na gwanjo ita ma fatsume ya sai mata kala biyar shi ko bawan Allah kala biyu ne nashi haka suka cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa kamar kullum yau ma habu ne zai tafi kiwo saboda yanzu ya iya yana zuwa shi kaɗai ya dawo lafiya".. "Cikin dake jikinta nake so malam a zubar min saboda iddar ta takare a zaman gidan da take don ya mai da ita" Cikin ta zai fita amma kinsan ai sakamakon abin ko? Ɗan zare ido tai saboda tasan mai yake nufi ta ce" idan wannan ne ban da damuwa malam idan har ya fita ni kuma zani baka shi". Wani magani ya bata ya ce ta tabbatar ko da a cikin lemo ne tasha shi tabbas idan har tasha komi zai waka yadda take so.. Murna ce fall ranta saboda ta samu abin da take so idan "jannat ta har ta bar gidan ko da asiri ne sai ta auri sameer kuwa, ta mike tare da mai godiya tana wani ban ƙare kirji shi kuma yana taɓa su kamar wani tsohon maye" ________________ Mereeh tashin hankali tana cikin shi duk tasa ma kanta damuwa da abin da baba sabo ya mata gashi cikin lokacin da ya ɗiba mata har anci kwana takwas ranar na tara ne "malam Musa yazo mata zance babban mutum ne mai kimanin shekaru 67 bakin shi duk ya ci goro haƙora sunyi ja kamar barkono, suka gaisa ta ce baba kunun aya ɗin za a kawo" Malam Musa ko duk ya ruɗe da yaji muryar mereeh ya ce" baba kuma mu da muke shirin zama ma'aurata zaki kira da baba ƴar nan mijinki ne ni da sabo ya maki" kallon mamaki take mashi lalle mutumin nan bai da ma kunya ko kaɗan a ƙalla zaiyi jika tanawa da ita amma wai ita ce zai yi mata da ita cirr yana cin jalala kuwa!! "Kikai shiru baby na" Da sauri ta ɗago don kallon bakin da ya kirata da baby ta ce" Malam wai ko kunya babu wai baby Allah ya kyauta gaba" Sameer kwance kan gadon jannat shi da budurwar shi suna watsewar su hankali kwance ita kuma ya mata duka wai ta ɗaura masu girki tun kafin ya ƙara mata wani haka ta tafi kitchen ɗin don ta mai abinda ya sata.. ....... tunda nasa akai mai kurciya yanzu ni ai ban da damuwa wallahi' Fulani take faɗi hankali ƙwance ko fargaban wani yaji ma bata yi duk maganganun da take hanan ƙanwar hammad najinta amma matar nan bata tsoron Allah ko kaɗan tana ganin yadda ake ta fama da mummy bata lafiya amma ko ajikin ta lalle gidan sarauta ana abu mara hankali sai da taji wani zancen kofin hannun ta ya faɗi ƙasa ji kake tassss ya fashe lokacin Fulani ta juyo don ganin waye a gun hanan ta gani ta ruga da gudu tana kuka innalillahi wallahi sai nayi maganin ki banza zan mai dake kurma yadda ko maganar ba bazaki ba wallahi mara hankali.. Ko da hanan ta koma part ɗin su kuka take Kamar mai "mummy sai ta bata hakuri tare da bata umarnin ta tashi tunda suna da class yau ta tafi makaranta, haka ta shirya jiki ba ƙwari ta tafi driver bai nan ita zata tuka kanta ta shiga ciki tun da ta hau titi ta lura akwai masu Binta a wata baƙar mota ba ta tabbatar da hakan ba har sai da ta ƙara gudu ta ga suma sun yi kanta canza titi tai ta hau na zoo road suka bita sai da sukai nisa motar ta ta fara jaking salati tasa ta tsaya zata buɗe ta gudu sai ganin mutane tai zagaye da motar sun rufe ta wani tsumma suka sa mata a hanci wanda daga nan bata kuma sanin inda kanta yake ba" Dare ya tsala sosai irin ƙarfe 2 na dare mutane ne kan katan gan gidan "Malam Musa suka dura basu zame ko ina ba sai ɗakin shi mari suka falla mai ihun ya yi suka nuna shi da wuka ya masu shiru ya ce don Allah mai na maku da zaku zomin banda kudi ni talaka mai ci da ƙyar" Wata irin dariya ɗayan su ya yi yace kana ci da ƙyar amma kake shirin ƙara aure Musa? Aure kuma ni bazan yi Aure ba matana mun isheni ga yara ga jika, ina zan saka matar... Oho kai da kake neman ɗiyar sabo fa da ina zaka saka ta?? Nafasa wallahi kunji na rantse na fasa indai don ita ce kuka min haka, da safe in sha kallahu zan faɗi mai na janye.. Wani yace in sha Allah ake cewa ba in sha kallahu ba... Please ku hakuri da wannan banda caji 🕊️ HAMMAD ZARAH 🕊️ BY boos lady Phone number 08160647868 Bismillahir rahamanir rahim Mikiya writer's asso..... Dedicated to fan's of convention room hammad zairah masu comments only 🥰🙏godiya Mai tarin yawa love You so much. "Wani bakin ɗaki aka saka hanan wanda ko hannun ka baka Isa kagani ba balle kaga na kusa dakai, kan wata katifa mai laushi suka ajeta tare da rufe ɗakin suka fito cirko cirko suke saboda kadafa asirin su ya tonu wannan aikin shine na farko da suka fara gashi sun fara da mai hatsari sace ɗiyar sarki lalle sun taro match idan asiri ya tuni, babban su ya ce dalla ku kwantar da hankalinku ai samu akai ba wai haka nan bane don ra'ayin kan mu" Bangaren jannat kuwa tasamu da ƙyar"sameer ya maida ita sai dai sharaɗin da ya mata na yadaina bata abinci ta nema da kanta kawai dai sunan tana aure amma duk wani abu da miji zai ma mata bazai mata ba, kuma a haka taji ta amince rana ta farko da mai da ita duk wani Kayan abinci ya kwashe Allah ya taimaka mata tana ɗinki to sai ta zuba asusu wasu kuɗin dashi ta ɗauka ta siyo kullum ɗari gyaɗa ta 50 suga 50 ta samu ta haɗa a nepa ta jona ta sha, da rana ko garin kwaki tasha da kuli haka ta cigaba da rayuwa ga ciki tana Tare Da shi iya wahala tana shan ta gashi Wajen hakkin shi sai ya amsa ko bata so!! Kamar kullum yau ma tana zaune ya shigo cikin gidan ko sallama babu Amma haka nan ta mai sannu da zuwa, ko kallo bata ishe shi balle ya amsa mata ya wuce ciki tasan lokacin dawowar shi ruwan wankan shi na a haɗe ya shiga ya yi yana cikin ɗaki ne ya ji sallamar auntyn jannat gaban shi ne ya tsinke ya faɗi ta gaida ita amma ko ta amsa ta furta jannat lafiya kika kode kikai baƙi kamar ba jannat ƴar gayu ba Lafiya kuwa?? Kan jannat ta bada amsa ya yi wuff ya fito ya mata sannu da zuwa ya ce" Aunty nikaina abin na ban mamaki wallahi bata da lafiya munje asibiti an bata magani amma bata sha bata san cin abinci ko kaɗan yanzu ma fama nake da ita ta tashi ta shirya mutafi asibiti amma ina ko kallo na ta ki balle nasan zata".. salati Aunty tasa ganin irin abin da ƙanwar ta take ma mijinta tace anya jannat kina san rahamar Allah? Mijin naki kike na musu lalle tabbas kin canza Daga Yadda kike yaushe kika fara mai wannan iskancin zaki tashi ko sai na buge ki a nan!! Kuka ne ya ci ƙarfin" jannat ganin sharrin da sameer ke san mata lalle ya iya makirci tayi wanka doguwar riga tasa mara nauyi ta sa hijabin ta suka fito don tafiya asibitin" Baffa don Allah kabar ni naje kallon shadi Yau kaga na dade banje ba ina so yau cewar fatsume! Shaɗi kuma fatsume? Bana san fitar yamma kinsani amma ke da wa zaki? Dama dama haka ta dinga faɗa Saboda ba gaskiya.. Tafi maganar ki kai tsaye mana fatsume haba.. baffa nida yayana zani mu kalla mudawo! Shi ya ce yana san zuwa ne to a dawo Lafiya ya faɗa tare da cigaba da kulla maganin shi......ta fito tare da cewa yaya ya ce mu tafi. Aliyu Yanzu kaga saukar ku nazuwa alhamdulilahi gashi ka kammala school mun samu cigaba da karatun ka kyauta tunda gwamnatin mu ta ɗau nauyi yanzu sai mu fara shirin zuwa University ko ta faɗa tana dariya.. Cush "Aunty mereeh nidai sai second term sannan zan yi rijistar ma Allah karatu da wahala sosai fa". Ware hannu tai irin na mai mamakin nan ta ce a'a ai so kake kaji no wahala komi? Tab kasan haka nasha fama gashi an gama ba aiki sai addu'a amma in sha Allah Aliyu gadanga zai sami aiki da zai kula da yayar shi".. uhmm ai yanzu aiki sai wanda Allah ya cida kalli dai ƙawarki don baban ta kusa ne a gwamnati shine tasamu da yanzu kema tare kuke amma Allah ya ban kuɗi na gina maki asibiti ta kanki. Ameen ta faɗa dai-dai lokacin kuma an kira sallar mangariba ya tashi don tafiya masallaci. ...... innalillahi ta furta ganin ko hannun ta bata gani ta kurma ihun azo a taimaka mata wannan shi ake kira da ihun ka banza' saboda gun ba kowa suna kan su sun fita suje su dawo tashi tai tana lalube ko zata samu hanya amma ina ta duƙe tana kuka kamar ranta zai fita ba wanda take tausai Kamar mummy tana can hankalin ta a tashe yanzu.. tashi tai tare da laluba bangon ɗakin amma babu alamun da fitila haka ta koma ta kwanta tare da kiran sunan Allah. Hajiya gaskiya wannan aiki da kika samu mai wahala ne babba! Fulani dake gefen su ta ce Please bana san kuna cewa haka ina so ne nan da sati sannan ku saketa amma kada ku mata komi, kada naji wani zance daban.. OK ma! Babban cikin su ya amsa kudi ne masu uban yawa ta ce wannan ku fara rikewa kafin ku gama aikin ku na sallame ku, kuma abinci mai dadi nake so a rinka bata. Suna gama magana ku san minti 30 ta wuce gida rai fes... .____________asibiti ciwo ne har ya ci karfin ta ga ciki na barazanar barewa ga yunwa ta kama mata hanji sosai, kwantar da ita sukai sai ta samu sauki sosai ko zasu sallame ruwa suka sa mata tare da mata allurar bacci ta samu relief, aunty ta koma gida don ta sanar ma su umma tana tafiya sameer ya fita shima gida ya koma ya kira kawar jannat suka sheke ayar su a dakin ta na sunna bai koma asibiti ba har sai wajen karfe 5 na yamma ya shiga kamar wani munafuki, ga gaida umma da wasu yan uwan nata suka tashi don su zanta da matar shi suna fita ko ya matso kusa da gadon ta ya ce munafuka saboda karya an hada baki da likita dan kawai a ci mun kudi to zan nemi sallama mu tafi gida ba!! "Allah ya sani Meer ina ƙaunar ka saboda san ka cikin jinin jikina yake Allah ne ya daura min tawa kaddarar a haka, gashi ka canza min kamar ba auren soyayya mu kai ba tabbas zuciyata tana fada min an canza min kai ne". Wata dariyar mara kunya ya mata ya ce nine dai sameer ba wani canza ni akai ba harda wani munafunci wai Meer nace bana san wannan sunan! Ƙwallar da take shirin zubo mata ta goge saboda bata san tai kuka, idan tai tasan sameer ya samu nasara tace "abba ya aiko mun da dubu hamsin nasha lemo kafin ya zo" Tsaki ya buga mata mtsssss wai Lemo kawai dai ki ban su na sai mana kayan abinci malama ya fada da wani jan idon shi shi ga oga.. Kallon mamaki ta bishi da shi tace"sameer ka manta rabon da kaban abinci yau wata nawa?? Da kanka ka furta min kai yanzu ba zaka rinka ban abinci ba na nema yanzu kudin mai kuma kake so na baka haba don Allah a sa tunani ciki mana Meer, tana gama magana ta juya mai baya" Shake mata wuya ya yi yana don uban ki sai kin bada su wallahi ko na illa taki, daidai nan aunty ta turo kofa sai ya wa yin ce yana sannu beb bari naje ko nama ne a restaurant sai a sai maki.... Banaso ta ce. Aunty tace har yanzu dai kina mai rashin kunyar nan ashe kina kwance gadon asibitin ma zaki ci ubanki.. Dadi yaji da bata ga shake ta da ya yi ba har take shigar mai... ____________ Lalle yau sai anyi ruwa da kankara cewar "Mariam kawar Meerah" Murmushi tai har dumpling ɗin ya losa tace saboda lokacin hadari ne ai dole ayi mana, zama tai kusa da ita tare da fadin mummy fa? Tom sarkin mummy tafi ta taje kasuwa ta dawo kinsan mummy da al'adun ƙauye wai wani yaro ne nan aka yaye shi ne driver bai nan balle ya siyo mata kayan ni kuma wai kar na mata shirme ta tafi da kanta.. 😅 Dole ai zaki dariya saboda kinsan kina shirmen dakin ta suka koma ana ta shan firar yaushe gamo, ta fito ta diba mata abinci da lemo ta kai mata tana ci suna fira abin gwanin burgewa, sai ga mummy an dawo da kaya masu uban yawa ko madara ta sai ma yaron gwangwani uku suka dawo falo ana fira sai ga "abban mubeen ya biyo don su gaisa da mummy shi dan Wan baban Mariam ne, tunda ya daura idon shi kanta yaji ya kamu da san ta ko mummy taga haka tai shiru shi da yazo da niyar minti 30 sai gashi ya kwashe fin a waya yana taya su Mariam fira ana labarin shan wuyar school" Ya ce"tom ke kenan yanzu baki samu aiki ba? " Sai ta dan sosa keya tare da fadin ehh muna dai nema har yanzu..... OK Allah ya taimaka, daga nan ya masu sallama ya tafi gida..... Can gida ko yarda ya tafi ya bar komi haka yadawo ya same shi ba gyara ko kayan mubeen tun na safe har yanzu da yamma tai sune jikin shi, wani takaici ne ya kama shi ya rasa ma mai zai ce ko da ya shiga cikin dakin zaune take kan gado tana aiki da lapton.... Ya watsa mata wani banzan kallo wanda da taga haka tasan zuciyar yan maza ta ɓaci ta furta "My hero well come wallahi Nadawo gida ga aiki na banga ma na taho gida amma please yanzu just 30 mints zan gyara komi".. Bai iya furta komi ila to ya nufi dakin shi. Meerah sai dare ta fito har sai da Aliyu ya fara kiranta sannan ta tashi tai mata sallama lokacin kuma driver yadawo aka sa ya kai ta gida!!! Suna isa ya bata 5k ta amsa tare da godiya mai yawa..... Tana shiga ya rufe ta da fada haba don Allah ai wannan aikin rashin hankali ne ace kin fita saboda kuna fira ba zaki duba time ba idan zaki daina ki daina ko wallahi aunty Meerah sai kin zo fita na hana ki.. Yanzu Aliyu ya zame mata ma jin gina shine bangon ta Please ku hakuri da wannan no caji muna fama da rashin nepa😭😭 Masu comments ina godiya Masu Shere na gaida ku Masu like a dage Littafin hammad zairah free ne 🕊️ HAMMAD ZAIRAH🕊️ BY boos lady 1️⃣ 1️⃣↪️1️⃣5️⃣ _Alhamdulilahi mun dawo business kunji shiru ne Saboda bana post asabar da Lahadi, juma'a kuma saboda banda lafiya shine dalilin da banba amma na samu sauki alhamdulilahi_ "Bangaren abban mubeen kuwa da sauƙi za'a ce saboda ko a office bai da tunanin da ya wuce na mereeh, duk ya rasa ta ina zai ɓullo ma lamarin ɗaukar wayar shi ya yi tare da kiran Maryam kira ya yi sau biyu bata kusa sai da ta dawo ta mai plashing sannan ya kira ya ce hello ƙanwata" "Hey abban mubeen" A karo na biyu ya ce" ba dogon zance ba ina ne gidan su ƙawarki dana ganta ranan da nazo?" Ohh wai "mereeh muna ɗan nisa ai daman tunda naga kana mata wani kallo nasan da magana a bakin ka" Murmushi ya yi mai sauti wanda ya ƙara ma fuskar shi ƙyau ya furta' kema kinsan idan ƙare na shinshina takalmi so yake ya ɗauka ɗan bani ɗan tarihin ta? Ok nan ta kwashe komi ta faɗa mashi. Yasha mamaki na kanin uban nan nasu tare da allah wadai dashi. ........ malam ai duk abinda kace na aikata wallahi yau ma banyi sallar asuba ɗin ba! To to hajiya yau kam aikin ki zai cika tabbas amma sai kin kawo abin nan da nace maki... Dole ne sai dashi?mai zai hana to nalam nace ko asa aljani ya nemo ne tunda kagana fito yau ba da sanin mai martaba ba?? Wani kallo ya mata irin anzo wajen ya furta idan ko haka ne "aljani lurudu shine zai amfani dake shi kenan aiki ya gama" ........................ Jannat kuka take mai cin rai gashi ciwo ya ishe ta ta rasa ina zata sa kanta, ta furta a karo na biyu don Allah meer ka bari idan na samu sauki sai na dawo gida please. Matse mata hannu ya yi da ƙarfi tare da faɗin '' noo jannat yau sai kin koma gida don haka ki fada ma gidan ku yau gida zaki". Meer na yarda yau zan tafi amma ka bari mana doctor yazo sai mu tafi.. Haka yai ta jiran doctor su zo su sallamesu, amma har wajen karfe 3pm na rana basu zo ba saboda yajin aiki da suka tafi, sai karfe hudu na yamma yan gidan su jannat suka zo ta ce" Aunty don kice a sallame mu mana? '' Kina da hankali''kuwa jannat saboda kin fara gane kanki shine zaki matsa a sallame ku komi haba, bana san irin wannan abu kina dai jin abin da doctor yace kan lafiyar ki"...... Kuka tasa mai cin rai saboda tasan idan har basu sallamesu ba tabbas zata sha hukunci gun sameer amma ya zata iya, doctor ne mai duba jannat yazo ya duba bata sosai ya mata tambayoyi ta bashi amsa allura ce ya rubuta ya ba aunty ta siyo'tana fita jannat tace don Allah doctor ka sallame mu mana haka mu tafi gida bana san zaman asibitin nan wallahi.. Ohh madam sameer kin kosa dai ki tafi gida shima ɗazu sameer yazo ɗazo don na baki sallama'kun dai gaji da zaman hospital ko saboda baku samun damar ganawa kun takura?? So sai gobe zan baki sallama ya idasa maganar yana murmushi. _______________Please help me now cewar hanan! Suna jinta tana magana amma suka share ta, da karfi tace idan wani abu kuke so mana ku fada zan baku? Idan kuna san kudi ko nawa ne zan baku, kuka take tana rokan Allah da ya bata mafita....... Wani cikin su ne ya shigo da wuka a hannun shi ya ce idan baki mana shiru ba wallahi zaki tabbatar da kin zo hannun kiddanaping, shasha mara hankali don Allah ya taimake ki bamu maki komi ba Allahu ya so ki wallahi Fulani tace kada mu maki komi amma da min kwashi romo!! Ta ce"fulani kuma wace fulanin kuke magana innalilahi hasbunallahu yanzu abinda ta ma yaya bai mata har sai ta dawo kaina innalilahi Allah ka duba lamuran mu take fada'. Da sauri dayan ya shigo tare da buge mai baki ya ce uban wa yace ka fada mata wanda ya samu? '' ............ Am sorry bayin Allah na roke ku da kumin uzuri da kumin hak'uri don Allah ku sallameni, kunga dai "mummy na tana can hankali tashe bata da cikakken lafiya".... Ke ya falla mata mari tare da mata kargagadi da tai masu shiru!! "hamma habu hamma habu take ta fada cikin yaran su na Fulani, da sauri ya taho ya ce miye ne adda shima dai duk da yaran nasu na Fulani'' Wani ƙaton maciji ne ta nuna mai.. Shi ko cikin himma da ƙware ya yi nasararkama wannan macijin ya kashe shi' kullum haka suke cikin walwala da jin dadi baffa bai nan saboda ya tafi gidan yan uwan dangin maman fatsume don ya sanar masu da cewa zai aura mata ƙadon da yake ma magani nan da sati biyu, wasu sun amince wasu kuma sukar abin suke don gani suke kamar sai da ita zai yi.. Daga can bangaren bukkar baffa akai masu bukka mai kyau da kwalliya'sai bayi guda biyu na wanka da ba haya baffa ya kashe masu kudi sosai saboda har sola aka sa masu don ganin haske..... Boka ya saka Fulani a daki ya yi ku san 24hours yana abu daya tasha azaba kuwa ya bata wani magani na ruwa da an bata tasha shi kenan, ta amsa tafi to sai inda aka aje hanan taje ta bada maganin aka bata sannan aka fito mata da ita suka tafi gida hankalin Fulani kwance ta shiga gida da murna ta kiran mummy mummy mummy fito ki gane ma idon ki.. Ba'a abun da '' hanan keyi sai kuka saboda taga yadda matar uban su ke wahalar dasu, mummy ta fito ta rungume yar tata tana tattaba jikin ta tana mai yasa meta waye ya dauke ta ne? '' Zatai magana amma ina taji baki ya din ke ta kasa aiko sai sabon kuka ''mummy ta ce innalilahi hanan baki iys magana lafiyar ki lau kuwa?''. Nan ma dai kukan ne kawai take kamar ranta zai fita cikin zuciyar ta kuma tana mai ja ma Fulani Allah ya isa!! Fulani ta ce"a'a hanan ki fada mana komi man kin tsaya kuka? Iskanci ne ai kin aje mutena amma kina mana kuka ohh saboda yawon iskancin kika tafi shine zaki kasa fada Allah ya kyauta gaba ta fada tare da shiga cikin part din ta"...... Mummy bata ji dadin abin da ta fada ba amma ya Zatai haka taja hanan ta hada mata ruwan wanka ta bata abinci hanan nasan yin nagana amma abu ya kasa... :::::::::::::::::::::Aliyu bana san rashin kunya fa don Allah basu mana wannan su ai ƙannen kane'don baba sabo ya mana abu bashi ke nuni da cewa zamu raba da iyalin shi ba tunda dai ƙannen mune!! Wai aunty meerah wace kalar zuciya ce dake, da baki jin takaici abinda suke mana!! Please am sorry naji update shiru wallahi rasuwa akai mana shine dalilin Masu san magana dani 08160647868 Nagode sosai fans HAMMAD ZAIRAH 🕊️ BY BOOS LADY 🦅Mikiya writer's association 1️⃣ 6️⃣➡️2️⃣0️⃣ "Mummy ta rasa inda zata saka kanta yau kwana uku da dawowar ta gida amma har yanzu shiru ba magana ba labarin magana, innalilahi mai martaba ya yi shige da fice don nema ma yar shi magani amma ina ba'a dace ba kullum hanan kuka take sosai saboda halin da suke ciki gashi ko rubuta abinda take san fada ta kasa ga abin a zuciyar ta amma ta kasa fada mai martaba ne ya ce zai fidda ita waje don a gane matsalar a can"... Kamar kullum yau ma tana zaune mummy ta miƙa mata abinci amma ta girgiza kai alamun bazata ci ba! Haba hanan idan baki ciki ba so kike ciwo ya kama ki komi? Gwanda aji da abu daya don Allah ki amsa kici bana san gardama irin taki hanan cewar mummy. .... Jin mummy ta hada ta da Allah ta amsa ta tsakura kadan taci. Bayan wata biyar Gidan nasu cike yake da makota da ƴan uwan su na garin funtua anzo taya Aliyu murnar sauka da hadda ya kuma samu sukolashif daga nan sai kasar waje don yin karatun Dr alhamdulillah kawai zasu ce, shiri sukai mai kyau meerah ta sa wani farin lees shima aliyu wani shadda ce blue da hula baki haka takalmi saboda shine sukai anko yan islamiyyar karfe goma na safe zasu fara walimar, tara kowa ya shirya maryam ta dauki mereeh a motar ta shi kuma daman aliyu yayi gaba sauran yan uwa kuma aka samu mota suka tafi.... An fara cikin farin ciki wani abba nasir shine yazo na daya' Aliyu kuma shine yazo na biyu a hadda kuma shine first wow sun samu kyauttuka daga manya sosai inda wani gwammana yaji dadin karatun alkur'ani mai girma ya karanta nisa'i tare da fassara ta ya bashi kyautar mukullin mota takai ta miliyon uku haka ya bashi ita saboda yaji dadin karatun nashi sai wajen karfe 3pm aka tashi... !!!!!!!!!!!!!! Ohh Allah anya to kaɗon nan bai masu asiri ba da har suka yarda '' fatsume zata aure shi'' wata dake gefen ta tace ina fa wai fa saboda idan sukai auren zai samu sauki shine fa zai sadaukar mashi da ita.. İnnalilahi kenan kyauta zai bada ita lalle amma an cuci fatsume kila don dai ganin uwar ta bata raye ko? Haka dai suke ta wannan surutu mara amfani suna yi suna cin shinkafa da wake... Yau ya kama juma'a kuma yaune daurin auren fatsume da habu' an sakko masallaci ne aka daura kan sadaki naira dubu goma murna sosai baffa ya yi!!. ... 😭 Dukan ta yake ta ko ina ta rasa ta ina zata tare saboda ko ta ina kai mata dukan yake' tashi tai da sauri. Da gudu ta nufi kitchen ta dauki wuka tace wallahi sameer idan har ka kuma duka na sai na illa ta ka haba wai ance so hauka ne komi don nace ina sanka bashi ne zai nuna maka ka rinka min wulakanci ba malam nagaji ta burkice mai kamar mai aljanu tsoro duk ya kama sameer saboda yasan dai jannat ko rashin kunya bata mai amma yau gashi ita ce wai da wuka zata kashe shi, ya yi baya ya fita ya ƙwafa daga bakin kofa yace ki dafa min abinci kuma... Duƙawa tai ta cigaba da kuka ita tarasa wane irin aure ne wannan bata san ta koma gida bata san yadda mahaifinta zai karɓe taba, tashi tai tare da gyaran gidan ta ɗaura ruwan wanka ta gasa jikinta wata taliya ce guda ɗaya ta dafa mai da yaji ta ci tata ta zuba mai tashi a kula ta samu gu ta zauna tare da tunanin Rayuwar ta ta baya.. Wacece jannat Ƴace ga Alhaji Mamman matar shi ɗaya da yara uku mata biyu namiji ɗaya yana can ƙasar waje da matar shi da yaran su ɗaya sai babban yayar su dake aure nan kusa da gida, jannat ita ce karama ta taso cikin gata da kulawa inda ya haɗu da sameer suka kulla soyayya mai zafi mahaifin jannat ya gane ba mutumin kirki bane duk da yaga ya mata amma ta nuna sai shi ɗin wai ai zai gyara halin in sha Allah haka sukai auren abban ta yace ba yaji ba kawo kara balle ya sake ta tayo nan gidan kuma tace ta amince da hakan duk zuwan da su Aunty suke bada sanin shi ba saboda ya hana su, ko kuɗin da suke tura mata ya hana ƴar gayu jannat mai sa kanshi ko ina amma yanzu babu wannan gayu ta lalace sosai wannan shine Tarihin jannat.. Back to story .....an kai amarya ɗakin ta wow dakin na bukka ne amma ciki babba ne akwai karamin gado ɗaya da babba sai sif da kayan jere ga kujera ɗaya dakin ya haɗu iya haɗuwa karfe 7 na dare duk a watse baffa ya fita yar tasha ya siyo masu indomi da kaza ɗaya ya ba habu wajen ƙarfe 9 ya mashi sallama ya tafi gun amaryar shi..... zuciyar baffa ko tausan yaran ne ya kama shi ga na habu da ake fatan ya samu Lafiya ga na fatsume da take ƙarama yau zata girma! Kafin aure.. Fatsume ba wai zan aura maki shine don na cuce kiba a'a ki hakuri haka ƙaddarar ki tazo in sha Allah wannan shine makarin ciwon shi na farko maganar shi zata koma daidai sai matsalar ƙwaƙwalwar nan har sai ranar da yaga dangin shi zai koma daidai da izinin Allah kiyi hakuri ki ma mijinki biyayya kada ya kawo mun ƙarar ki kinji yar albarka!! murmushi tai tare da cewa Amin baffa.. Ango da sallama ya shiga cikin dakin shi ganin ta ya yi kwance har ta fara barci ya tashe ta sukai Sallah tare da cin abincin wani lemo ne baffa ya bashi yasha kafin yazo yasa mai magani ciki don.... fatsume ta tashi ta cire kayan nata tare da sa jani da yar ƙaramar riga ta koma babban gado shi kuma ya kwanta ƙaramin gado barcinta ta cigaba da yi yayin da shi kuma Malam habu inniniya ta ishe shi🫢 ...... mereeh don Allah ki magana mana bana san wannan shirun cewar abban mubeen! Ajiyar zuciya ta sauke tare da furta uhmm ni wallahi ba auren mai mata ba a ki zaman lafiya shine nake tsoro. Dariya yayi mai sauti wanda har sai da tsigar jikin mereeh ta tashi ya ce" ke matsoraciya ce kenan Allah ki shirya don maman mubeen tana da kishi sosai, yau nake so naje gun baba sabo don jin ya zata kaya" Ohh Allah abban mubeen kenan komi da gaggawa haka? Nidai yanzu zan fita aiki kar na makara!! Hmmm a dawo lafiya meeran. ta ce"bangane ba mai hakan ke nufi'' Kinga sunan ki meerah' mijin ki imran idan aka hada karshen sunana da farkon naki shine zai bada meeran! Dariya tai sosai, sannan tai mashi sallama....... Abban mubeen ya saman mata aiki a asibitin da yake aiki fannin mata shi kuma yana fannin masu c,s ne!! ...... Kai yaro yanzu ita '' meerah ɗin ce ta turo min kai saboda bata da kunya? To ai ni na fita daga matsayin uban ta ta nemi wani uban" İmran ya aje mashi kuɗi masu yawa sannan yace mai zan tafi ni yanzu! Har ya tashi ya kusa kofar fita ganin wannan kudi yasa baba sabo cewa yaro dawo mana! Zama ya yi '' baba sabo ya furta a hankali kamar wanda ke jin tsoron wani yaji ya ce yaushe kake san ai auren? Ni ko gobe kace ma alhamdulillah sai a daura''........ A'a baba sabo daman nazo magana ne ina son na turo iyaye na don jin magana. To shi kenan ai sai sun zo haka ya mai sallama ya fito ya kunna mota tare da kiran meeran bugu uku ta dauka tare da yin sallama! Jin sallamar ya yi har cikin ran shi ya ce'' zuciya ta nazo baba sabo bai kalleni ba dole kinga zamu tafi funtua kun dangin mama''..... Uhmm in dai shine zai maka fiye da haka ma, amma kai ta addu'a funtua kuma gaskiya.... Sai kuma tai shiru kamar tana jin tsoro. Ya ce'' fadi mainene bazaki bane? '' Noooooo ta fada a hankali.... Sai da ya gama jan aji sannan ya fada mata gaskiya har cikin zuciyar ta taji dadin abin da ya faru!! ...... Tashi ya yi da sauri ya rungume ta ta baya yana mai wani irin numfashi tai saurin farkawa tare da ture shi tace a'a yaya habu lafiya? Bai bari ta idasa ba ya hada bakin su waje daya yana shafa wani sassan jikinta..... Kwalla ce take ta zuba mata tana so ta kwace amma ta kasa rigar jikinta ya yaga tare da kwantar da ita kan gadon..... Tofa fans ku biyo ni don jin cigaba 08160647868 🕊️HAMMAD ZAIRAH🕊️ BY boos lady Mikiya writer's asso... Alhamdulilahi wannan shafin naku ne masoya na a duk inda kuke sanku na cikin raina💘🔓 Bismillahir rahamanir rahim 2️⃣1️⃣▶️2️⃣5️⃣ "Bangaren abban mubeen kuwa baida aiki da ya wuce tunanin mereeh kullum haka yake, ya tashi aiki ya nufi gidan hajiya domin su gaisa da ita daga can ya wuto da mubeen yana shiga cikin gidan da sallama a bakin shi mubeen ya taso da gudu yana ga abba ga abba hajiya dake gefen shi ta ce dawo daga nin mutum sai kace kasan shi" murmushi ya mata tare da gaida ita ya ce akwai abinci kuwa? Akwai mana mai zai hana ni ɗaura tukunya nida ba ma'aikaciyaba imrana ai wannan aikin sai ma'aikata.. tunda yaji wannan maganar sai ya yi shiru ita kuma ta shiga ta zubo mai jolop ɗin taliya taji kifi sosai ya gyara zama tare da ci yana ci yana santi ya ce" hajiya kinsanme mainene na samu mata mai hankali da nutsuwa fa ina san ƙara aure'' Ta washe baki Allah abban mubeen?? Ina ka same tane? Yar gidan waye? Allah ya sa dai mai mutumci ce ba irin hamdiya ba? Yace noo "mereeh ai mace ce wadda tasan mai take wallahi ga ladabi Hajiya yarinyar ta haɗu sosai sai dai ai min fatan nasara' nan ya kwashi labarin mereeh ya faɗa mata duka aiko taji tausan ta tare da karfafa mai gwiwa sannan ya fito gidan Cikin farin ciki ya nufi gida, ko da ya isa sai da ya gyara gidan sannan ya zauna tare da kiran gimbiya mereeh don jin ya take" .................... Mai mata hidima ce ta shigo tare da faɗin ranki ya daɗe' ga wata mai magani nan tazo don gwada sa'ar ta! Ta girgiza kai tare da cewa kice mata ta shigo...tunda mai martaba ya sanar cewa duk wani mai magani da ya ma yar shi magani tadawo daidai suna da kyauta mai tsoka masu magunguna suke zarya idan sunyi basu iyawa shikenen' shiga tai cikin ɗakin tace a samo mata rushi ta fara hayaki nan ɗaki ya ɗauki kauri su ka fara tari haka tai ta yan dabaru amma babu Sa'a Sannan ta tafi.. Hanan tai mata nuni da hannu wai kada a ƙara bari wani mai magani yazo bata so karya ce suke yi ba magani ba! Murmushi mummy tai tare da faɗin a'a ai sai kiga an dace... .......kai nake jira fa "Aliyu ka tashi kai wanka muci abincin nan Please ina san fita ne yau aiki na na rana ne fa" Ohh wai yau ma danadawo Aunty mereeh sai kinje aiki? Ki hakura yau dai kawai tunda gobe asabar a haɗe a monday! Tai sakato tana kallon shi saboda ita sai taga don mai bazata ba haba, da ƙyar ta lallaba shi ya yi wanka ya fito zaman cin abincin shima nan sai da ya ɗauki lokacin mai tsawo ya fita.....ganin mutum tai ya dafe kai tare da faɗin wash Aunty kaina ya faɗa kan kujerar dake kusa dashi da sauri tayi kan shi ta na duba shi shiru, ta nufi daki dan ɗauko akwatin taimaka mai' yana ganin haka ya buɗe ido tare da dariya yace ai yau no aiki zo kisamun ruwa ko naji karfin jiki na ma ai nasha tafiya! ........ Fatsume tunda ta sume bata farka ba sai sanyin asuba da ya tashe ta' da ƙyar ta buɗe idon ta da ya mata nauyi ta ja jikinta ta ɗauko robar da baffa ya bata ta watsa mai ruwan idan haka ta faru shikenen' ta na zuba mai sau ɗaya amma ba motsi sai da ta zuba sau uku sannan ya tashi ita kuma ta jawo zanin gadon tare da rufe jikin ta' da sauri yayi kanta tare da rungume ta saboda ya tuna mai ya aikata mata yana mata sannu ɗaukar ta zaiyi tasa ƙara tare da faɗin was Allah hamma habu zafi nake ji... Haka dai ya lallaba ta ya ɗaura gado tare da rufe mata jiki' ɗan gas ɗin da baffa ya siya masu ne ya ɗaura ruwan wanka roban su yaje ya fara tare da zuba wasu ya dinga saka ta a robar tana kukan zafi a haka ya gyara ta ta kwanta gado, ya gyara karamin gadon tare da zuwa ya kwanta bayan ta, zuwa safe jiki ya gashe da zazzabi (Ga yan comments room sun zuba ido ganin ƙwaf) ________________________ "Fulani sai jin daɗi take maganin na aiki gashi yanzu tai wanda za'a a kori mummy gidan ma ga baki ɗaya tabbas malamin nan nata da tai sabo yana aiki yadda ya kamata, tana zaune ya ce kije kice subarmiin gida kafin nan da dare" ta zaro ido ta ce ranka ya daɗe' ai wannan aikin kane saboda sai a ga kamar nice nasa hakan ta faru!! Ya wani shafin gefen fuskar ta ya furta duk wani da yace kece ki kawo shi fada yaga aiki na!! Haka mai martaba ya fita tare da masu korar wulankaci, mummy tasa mai mata aiki nemo mota suka kwashe kayan tsaf suka fito tana wayeyen gidan tana ƙwalla ..... .......an sai da kujerun "jannat masu rai da lafiya amma ba wani tsada gashi an kori sameer Saboda rashin gaskiya da ya yi masu na cin kundin ma'aikata shi ne dalilin tunda yaga ta saida suka dawo zama Lafiya kamar bashi ne mai mata duka ba, ita kuma ta ɗauka ya gyara halin shine yanzu ya daina kawo yan mata gidan sai dai su haɗe can waje kamar kullum yau ma tunda ta tashi ta gyara gidan yayi kyau ta ɗaura masu abincin safe zuwa 7 daidai ta gama komi ta tashe shi ya yi wanka suka karya ta ce ina san zuwa gidan Aunty na" Jannat ba wai bana san kina zuwa gidan bane a'a sai taga kamar ina Cutar ki... No my "meer bazata ce haka ba kasan dai Aunty ma nasanka Please kai hakuri bazan daɗe' ba" meer kuwa Cikin zuciyar shi daɗi yake ji Saboda yau yasha sha'anin shi yadda yake so yace to kikai dare sai nazo mu taho tare! Rungume shi tai tare da mai kiss ta tashi tasa hijabi da jaka ta fito tare da mai sallama daman tasan dai ita ce zata ma kanta kuɗin mota.. ......ruwa tasa mai aiko barci ya ɗauke shi tana Cikin cin abinci ne kiran abban mubeen ya shigo suka gaisa yaji Muryar ba dai-dai ba yace Lafiya sarauniya?? kukan dake boyewa ne ya fito ta faɗa mai Aliyu ne bai da lafiya yanzu ma ruwa take samai' sannu ya mai tare da faɗin anjima zai zo ya kashe wayar! Hamdiya da tadawo aiki Yanzu kuma taji wayar da yake ta shigo a fusace tare da faɗin uban wacece gimbiya ɓacin gani?? Murmushi ya yi tare da riko mata hannu yana zauna mana "maman mubeen haba ya da zagi haka Please, ƙanwar kice ai da zan kawo don kula da gidan kinga ke aiki kike". Ta mike da sauri tace lalle Imran sai yanzu ne tabbatar da kai ma yaudari ne na gaske.... A'a hamdiya kina Min girki gyaran gidan nan ɗaki na kula da mubeen kina yi ko?? Ta share ƙwalla tare da faɗin ai nace a nemi mai aiki kace kai baka so to kaga ko sai dai ka kawo ta matsayin yar aiki ba da aure ba!! No no no yadda kike aure ita ma haka zatai sai dai ita ce mai kula da miji da yaro yai gaba abin shi tare da sa ma kofa mukulli.. Da safe sai ga "baffa da koko da kosai ya kawo masu ƙofar bukar su ya kira fatsume sai habu ya taso yace barci take yana ganin habu yasan komi ya wakana ya bashi kokon tare da gaisawa shi kuma ya koma ciki inda ya tada ita ya bata tasha da ƙyar, robar maganin su na gargajiya ya nemi magani ya bata ta koma ta kwanta gashi shi kuma magani bai sake shi ba..... (ya haɗa da Yan comments room) Mai aikin ta ce" mummy ina zai kaimu?" Ta share ƙwalla tare da faɗin muje gidana dake tudun Wada Wanda ba kowa ɗin nan, can suka nufa mai kofa ne haka matasan layin suka tunda shiga da kayan cikin gidan ta biya mai mota suka shiga daki uku ne sai kitchen bayi ɗaya amma akwai bayi a ɗaki suka cigaba da gyara zuwa mangariba sun kammala komi mummy ta bada kudi a siyo taliya su dafa!! Wow ganin Yadda ya fito yadi ne pink yai kyau ya fito don tafiya "hamdiya tace ina ya ture ta gefe ya fito mota ya tada mai gadi ya buɗe mai gida ya fita, sai da ya sai kayan dubiya sannan ya shiga cikin layin nasu, ya kira ta gashi nan zai shigo ta sa hijabinta sai gashi ko da sallama a bakin shi ya shiga inda ta amsa tare da shigar dashi cikin ɗakin don duba Aliyu sai taga ya wartsake suna ta fira da shi anan ne yake faɗa daman yayi haka ne don kar taje aiki" Aiko abban mubeen ya mun tsine mai kunne tare da faɗin sannu idan ka kuma ma sarauniya ta haka zan rama mata! Ya tashi ya shiga cikin dakin inda ya barsu anan suna fira.. ....... hamma habu dai sai laluben fatsume yake tana ture mai hannu saboda jiya tasha wahala yanzu ma mai yake nufi? Murya na rawa tace don Allah kayi hakuri idan laifi na maka ka daina hukuntani ta haka na rokeka. Jin Muryar ta yake kamar tana kara zuga shi ya danne ta tare da magana a hankali ki hakuri fatsuma na sau daya zanyi!! tace........... Please contuie 08160647868 HAMMAD ZAIRAH🕊️ BY boos lady Mikiya writer's asso.... 2️⃣6️⃣⏹️3️⃣0️⃣ Mummy komi ya sauya mata inda Allah ya taimaka mata tana da gidan da take bada su haya Sannan akwai wasu kuɗi a account ɗin ta nan ne ta samu sauƙi ta maida mai aikin ta kamar yarta komi tare suke' hanan ta daina damuwa yanzu ta bar ma Allah komi amma har yanzu tana tuna Fulani gashi ba bakin faɗa baiwar Allah, suna zaune mummy ta kalli mai masu hidima tace Binta ko dai shago zamu buɗe a kofar gidan nan kinga kafin aje kasuwa sai a rinƙa yi nan?? Kuma haka ne "mummy Allah ya taimaka mana a samu dacewa cewar Binta, haka sukai ta shawara dai har suka saida magana ɗaya harda na aune ma zasu rinƙa yi" ......... Aunty Wallahi ban cuta mai hasali ma zaune muke Lafiya nida shi. Jannat bance kina cuta mai ba' amma don Allah duk wani hakki nashi kada ki rinƙa danne mashi kinji yar ƙanwata ta faɗa tare da da fata!! Murmushi tai tare da faɗin tom aunty, suka cigaba da firar zumunta sai ƙarfe 8pm Sannan sameer yazo don su tafi ko da zata tafi Aunty wajen dubu hamsin ta bata sukai mata sallama tare da fitowa.. "Mereeh na Please kidaina mun hukunci da irin wannan abu don Allah ko so kike na haukace akanki". Ita abun ma kunya ya bata ta furta noo hibban am sorry amma sai gobe zan shigo aiki wallahi yau ƙanwar mama tazo ta funtua kaga ba halin zuwa" ......lah kinga asirin ki ya tuno da bazaki faɗa ba nazo na gaida ita ba ko? Idan na taso aiki zanzo! Uhmm... Uhmmm hibban rigima daman zam faɗa maka' to shikenen gata ku gaisa kafin kazo!! Bata wayar tai suka gaisa tai masu fatan alheri sukai sallama... ________ Kullum fatsume tana Cikin zulmi saboda abin ya zama kamar wani mara kai' a ƙalla sai yayi awa wajen ɗaya ko biyu gashi kullum ba daga kafa tunda akai auren nan basu haɗu da baffa ba yau kwana biyar da bikin gashi sai anyi goma kafin ya dawo normal ta bushe ta rame, sai ta ƙara ƙyau da tai ramai hancin ya fito kamar biro tana zaune taga alamun dai so yake ya yi tace hamma bayi zani.... Ɗaukar ta yayi cak ya kaita bayin ya taho ɗaki idan ta gama buƙatar ta sai ta kira shi, tana gama fitsarin ta fito a hankali take tafiya har ta wuce shashin nasu ta tafi can inda rafi yake ta zauna tana cilla dutse Cikin ruwa!! Bangaren hamma habu kuwa yana ɗaki injiniya ta damaisa' ya fito domin yaga ta gama ya yi magana shiru sai ya leka mai zai gani babu ita ya tafi wajen baffa don yaga ko can ta tafi yana zuwa suka gaisa ya tambaye shi fatsume ya sosa kai tare da faɗin tana Lafiya ya gama zaman shi bata ba labarin ta yayo daki don ganin ko ta dawo... Fulani Yanzu abu yaci gaba saboda har mata yan lasbian gare ta, yanzu ma bikinta ake ita da wata ita ce ango....mai martaba bai gari sai ita kaɗai da hadimai ko cikin hadiman ma wasu nata ne sun fi samun albashi mai tsoka sama da Wanda basu bata kansu basu da albashi mai tsoka wasu ma ta ko resu daga aikin!! Fatsuma tana jin tafiyar hamma habu ta lallaba ta fito bayan gari ta nufa inda rafi yake' ta zauna tana mai jefa dutse Cikin ruwa tana yar wakar ta carman dudu carman duduwa haka take tana ta nishadi sosai kuwa, murmushi tai da ta tuna ta guduma hamma ne kusan awa uku tana gun wajen la'asar sai ga hamma wajen don ya duba ko tana gun tun daga nesa ya gane ita ce murmushi ya yi ya isa tare da rufe mata ido ta baya jin hannun shine yasa taji sanyi har taji tsoro fa tace nagane hamma ne... "Uhmm shine kika gudu ko?" A'a ba gudu nayi ba kawai dai nazo rafi ne! yasha fuskar ta tare da faɗin abun ba gaiya na raka ki? Ko da yake nasan mai kike ma gudu yarinya. Dariya tai tare da rufe fuska taji kunya ta ce" hamma kaine ba daga kafa kullum abu ɗaya, ni kuma zafi nake ji fa sosai" Ohh Allah sarki "fatsume na duk lokacin da zan ganki wata zumar kaunar ki ce kesa har naji ina ƙwadayin na kasance dake a zumfiɗa ɗaya ba wani abu ba amma ki hakuri, kinga ko anan ma kiban kaɗan" Ware ido tai kamar zatai kuka ta ce" bakin rafi fa muke ko ka manta ne?" Idanun shi suka Kada tare da yin ja kamar barkono ya furta a hankali cikin sigar lallashi yace'' sanyin ido na ki tashi mu tafi gida na gaji da zama nan wallahi"...... Ba dan taso ba haka tashi suka tafi abin da bata so ɗin dai sai da ya faru! .................... Ƙarfe tara na dare yazo suka tafi gida sai da suka gama watsewar su can sannan ya taho suka tafi, abin gwanin tausaya ma jannat harda Aunty ta bata dubu hamsin suna kan mota ta bashi kuɗin aiko ya biya ya sai masu kaza ɗaya da yogout suka wuce gida....idan yau taji daɗi gobe akasin shi haka take rayuwa a gidan ta.. Kiran ta yayi tare da faɗa mata gashi a ƙofar gidan su! Ta kalli mama A'isha tace bari naje na shigo dashi ya iso.. tana isa taga mubeen a hannun shi ta isa da murmushi a fuskar ta dimple ɗin ta ya losa ta gaida shi tare da miƙa ma mubeen hannu ya makale kafada.... Mubeen mami ce jeka kaji.. Yaron ya yi dariya tare da faɗin "dady mamina ce ita ma wannan ko zata rinka sai mun alewa da madara irin na hajiya?" Kafin ya bashi amsa har mereeh tace ehhh "mubeen zan sai maka harda yogout" ai da sauri yaro ya miƙa hannu ya tafi gunta suka shiga ciki sun gaisa da mama A'isha sosai taji daɗin haɗin nan inda ya faɗa mata ai gidan da zai saka ta daban da na dayar sun sha fira mereeh dai ta tashi ta shiga kitchen ta haɗa mai abinci ta kawo inda mama A'isha ta koma ciki ta barsu, mubeen na kan cinyar ta tana bashi a baki shima yana ta mata surutu sosai ya ce'' ita mummy tana dafa mana nama harda da dady muke ci tana bamu a baki ko dady" Murmushi tai tace" idan ana cin abinci ba'a surutu kaji mubeen?" Ya ce tom mami zaki gidan mu ko ki rinƙa min wanka da kwalliya sai mutafi gidan hajiya ko? Ta bamu madara! Haka dai yaro yai ta surutu sosai har suka kammala ta gyara mai jikin shi, sukai mata sallama suka tafi tazo kwashe kayan da abban mubeen yaci taga kuɗi 20k ta kira shi tare da faɗin ka manta kuɗin ka!! Noo na baki ne saboda karramani da kika yi thanks so much My baby mereeh' mubeen sai kuka yake nan zai kwana wai... Ohh Allah sarki baby mubeen wata rana zai kwana' yanzu ai sai yasa mamanshi ta daure ni...dariya ma Maganar ta bashi sosai sukai sallama! ... .. . wallahi Hajiya da gaske yake aure zai yi ni kuma har ga Allah bazan iya aje aiki na ba don Allah ki faɗa min ya zanyi da raina Hajiya ta faɗa cikin kuka!! hamdiya tunda "abban mubeen ya furta maki auren nan tabbas sai yayi shi, tun farko kece baki bashi kulawar da ta kamata nafada maki akwai ranar da zaki zo kina da nasani kan aikin ki amma kika nuna ke a'a ba wannan maganar yau ga ranar tazo" hajiya wallahi ina san mijina kuma ina san aiki na, yanzu dai ba abinda zaki mun wanda zai fasa ko ki mai magana ya janye?? Innalillahi "Hajiya ta faɗa tare da faɗin don uban ki hamdiya so kike ki turani bin malamai? Idan wani ya baki shawarar haka wallahi maza ki tuba karda naji kin je gun wani don hana auren nan idan ko kika je zaki ga matsala" tana jin Hajiya tai wannan maganar ta kashe wayar ta' tare da kwantawa kan kujerar tana rusar kuka a haka ya dawo ya sameta tana kuka da sauri ya isa gare ta tare da faɗin "Lafiya mummyn mubeen?" ta rungume shi ta ce'' abban mubeen don Allah kada ka kara auren Please zan samo mai aiki da gaske nake maka" What kina da hankali kuwa? Mai aiki ita ce girki na? Gyara min ɗaki? Wanke min kaya? Ohh my god mai kike nufi hamdiya dani so kike ki ɗauke ki sakarai komi? Please foget da wannan maganar bana san ta!! Mubeen da murnar shi ya ce" mummy munje gidan su mami har ta ban abinci a baki shima dady a filat ta zuba mai munci abinci mai daɗi mummy harda sobo ko dady" sai hankalin ta ya koma kan mubeen tace wacece mami kuma? Mummy sabuwar mami dady yace zai min ta rinƙa min wanka harda abincin mai daɗi mu rinƙa zuwa gun wasa da ita, ya ida maganar tare da tsalle.... Fatsume zaune take kan abin sallah yau dai satin su biyu da aure alhamdulilahi tagama shan wahalar Yanzu sai dai kuma jikin hamma habu ya dau zafi ana ta magani... Please contuie Ana ta shirye shiryen biki ta kowane ɓangare suna ta murna "maryam tadawo daga kasar waje daman taje karo karatu ne, yanzu saboda bikin tadawo gida don ayi biki sai takoma" Yau dai walima' ƙawayen ta na makaranta da asibiti sunzo taya ta murna ana cikin yine sai ga hamdiya tazo da zugar ta aka fara fada dole aka shige cikin palo, maryam ta daga waya ta kira abban mubeen ta fada mai abin da ke faruwa ko minti 30 ba'ai ba sai gashi yazo ya kora su ita kuma bai ce komi wani kallo ya watsa mata ya yi gaba, duk abinda ake suna kallo ta windom sai da suka fita sannan sukai addua aka bar walimar haka.... .........aunty ita ce ke kula da "jannat alhamdulilahi tana samun sauki sosai kwananta uku kila yau a sallame su"........ Aunty kila yau dai a sallame mu ko?? Ehh jannat tunda an samu sauki... Wajen ƙarfe 8:30 dr yazo ya rubuta mata magunguna da sallama aunty taje ta siyo maganin sannan tahada masu kayan suka tafi gida, har yanzu alhaji bai barta tazo ganin taba amma kullum dai suna waya sosai taji jikin da sauki, motar aunty suka hau suka tafi gida kai tsaye... Ko da suka isa wanka jannat tai tare da shan tea mai zafi ta kwanta sai barcin gajiya, ita kuma tacigaba da aikin gida! ............. Sameer tunda ya saki "jannat yake holewar shi wannan daban ta anjima daban kuɗin shi dake account dasu yake ta facaka, yana kashe ma ƴan mata kudi sosai kullum a haka yake abinci sai dai ya siya yanzu harka ta ɓudi har maza yana amfani da alhazawa kamar me".....kamar kullum yau ma yana zaune ƴan mata sun kai biyar kowacce kuma tana shafa jikin shi kamar me shi kuma yana kwance yana jin su.. Da yamma ya sallamai su duka' wacce take uwar daka bata fito ba ya shiga cikin dakin suka daura,. Cikin dare ko gobara ta kama gidan har dakin da suke da ƙyar aka fidda sameer jikin shi duk yaci wuta ita kan ba ma a gane fuskar ta.. Yau ya kama asabar an ɗaura auren mereeh da Imran kan sadaki dubu ɗari uku' sai murna kowa ake inda aka kai amarya gidan ta bai haɗa su da matar shi ba kowa nashi daban-daban ne saboda bai san tashin hankali... Ƙarfe 8pm ya shiga cikin gidan hamdiya tare da mata sallama zai tafi tace ita bata san wannan ba sai dai su tafi tare ya ce ina, haka dai ya tafi ba dan ranta taso ba ya tafi gidan amarya mereeh can ya iske sauran kawayan ta suka mai sallama daman shi suke jira su tafi kar su barta ita kaɗai, ya masu sallama mai tsoka inda suka yi alwala tare da Sallah ya mata tambayar addini kuma ta bashi amsa kaza ce suka fara ci ita dai duk a tsorace take suka gama ta wanke baki suka haye gado daga nan ne zance ya sauya tana kuka tana rokon shi da ya kyale ta amma ina yaki haka sai da ya yi abin da ya keso sannan.. .... Fulani komi ya watse mata wulakanci sosai ya ke mata mai martaba dan sauƙin ta ɗaya har yanzu hankalin shi bai dawo sosai ba, bai tambayi su hanan ba gashi yanzu duburar ta bata riƙe bayan gida idan taji shi to tai sauri ta tafi in ba haka ba anan zai zubo, tana san zuwa asibiti tana soron a kira mata wani ciwon hatta gaban ta ya koma wani iri ba ƙyan gani... Fulani wai Lafiya kike ne cewar mai martaba? A'a mai kagani kuma? Lafiya ta lau sai dai idan idanun ka ne. Oh shikenen sai naga kamar kin rame da yawa shine dalilin tambaya. ................... Alhamdulilahi jannat Alhaji ya yafe mata yanzu haka tana gaban mummy tana kula da ita sosai tadawo jannat ɗin ta sosai ta ƙara ƙyau kamar ba ita ba Samari ko da masu mata sai kunno kai take harda wanda yake zuwa siyan wainar fulawa gidan ta harda shi, ita ta ma rasa wane zata zaba cikin su, wanda ya fi kwanta mata dai Umar mai siyan wainar fulawa! ......hanan an samu tunda har ana ɗan iya buɗe baki tai magana amma ba wanda zai ji Sakamakon da bata iya ko buɗe bakin, sati ukun da ya basu ya cika kuma yau ne suke so su tafi ko sati ne su samu a can.... ........wayyo Allah hamma bayana don Allah ka min addu'a mutuwa zanyi a taimaka min wayyo Allah na zan mutu ni fatsume! Duk ya bi ya ruɗe ya kira baffa yana gani ya ce" wannan asibitin birni zamu tafi gaskiya tunda cikin bakwai ne kila bakwaini zata haifa" Allah sarki kamar ya kurma ihu haka yake ji mota suka samo suka tafi ya kira Yan uwan innar fatsume aka tafi tare sun isa kenan na kuda ta kara kamata gadan gadan ba'ayi minti 30 ba ta sulbulo ƴar ta mace mai kyau mai kama da hamma tunda lafiyar ta lau aka sallame su tare da faɗa masu ƙaidojin kula da yarinyar banda jagula, suka isa gida aka ɗaura ruwan wanka inda aka sa ma jariri yar lalle duka jikinta na Hausa sai da yayi minti 10 aka wanke tare da mata wanka aka sa mata kayan sanyin ta ita ma mai jego aka mata wanka an sha dai kuka wai ruwan zafi da ƙyar aka mata shi ko....... A'a sannu malam naga ai ana cikin hidima tunda muka iso! Murmushi ya mata tare da faɗin kuyi hakuri wallahi wai yar waje na ce ta haihu Yau shi ne fa, amma suna cikin koshin lafiya. Masha Allah cewar mummy tai mai Barka nan ya fara masu maganin sai ihu hanan take tana kuka sosai, mummy kuma fita tai don har ga Allah bata iya ganin yadda hanan ke wahala, haka dai akai ta mata magani tana kuka mummy taje ma fatsume Barka da daddare lokacin angon jego bai dawo ba..... Sai ƙarfe 8:30 ya dawo gida ta bashi labarin yan birni sun zo mata barka ya ce angode! Cikin dare ikon Allah bakin hanan ya fara magana ta ce'' mummy tashi yau Allah ya yanke min wahala" Kamar a mafarki mummy taji Maganar hanan da sauri ta tashi don ganin gaske ne ko a'a aiko suka kama murna har da kuka fita sukai sukayi alwala tare da yi ma Allah godiya, da safe sun karya hanan tace zata je tai mata barka ita ma... Amarya dai ana shan kula gun mijinta kullum da safe yana zuwa don ganin hamdiya haka da daddare ya mata sallama ya dawo gida, yau ma ya shiga ya iske ta kwance wai bata lafiya ya mata tambayar duniyar nan mai take ji taki faɗa haka ya fita shi da mubeen ya dawo gida, mereeh taji daɗin ganin yaron da ya kawo mata shima sai murna yake yaga mami ta dauke shi zai mai dashi yaro yace a'a fa sai kuka haka aka barshi ya kwana gidan amarya.. Sameer kafa ta lalace gashi ba kuɗin aiki sai dai suka tattara suka dawo gida sai tsutsa ƙafa ke yi, ya ce inna don Allah kuce jannat ta yafe min don Allah nan ya basu labarin irin cutar da ya mata sun tausaya mata sosai, suka ce ma alhakin ta ne ya kama shi... .....an sa ranar bikin jannat da Umar duka wata ɗaya saurayi ne soyayya take sami da bata sami ba ada yanzu ko har ta manta da wata damuwa.. ...... hamma yana zaune bakin gado ita kuma fatsume tana zaune daga can sai mai ma jariri yar wanka tana mata, hanan tai sallama ta shiga suka gaisa tai mata Barka bata lura da mutum ba sai ji tai ance Yanzu mai zaki ci bana san ki zauna da yunwa gashi kina jego.... Ji tai kamar Muryar....ta daga kai don gane ma idon ta waye aiko ta tashi da sauri tare da faɗin innalillahi wallahi wannan ɗan uwa na ne ta fita da gudu sai wajen mummy! Shi ko kallon ta ya yi yace ko bata da hankali ne oho... Mummy ita tsoro ma abin ya bata ta riƙe ta tare da faɗin hanan lafiya kike wannan gudun kuwa? Mummy hammad ɗin ki nagani Wallahi shine hanmad shine Allah kuwa ki tashi muje ki gani..... tunda hanan ta fara magana gaban mummy ke fadi tace muje to.. Daidai lokacin ya fito sukai ido biyu da mummy ya daga hannu zai yi magana ya faɗi ƙasa sumamme... Da sauri mummy ta tafi gun shi tare da rungume shi tana kuka, sai ga baffa jin kukan su su fatsume sun tsaya kallon ikon Allah... Ke Fulani idan har baki nemomin matata ba da yara na sai na maki hukunci mai zafi. Ita kanta Fulani a zaba take sha ba kaɗan ba saboda gaban ta har tsutsa yake fitar wa, masu mata iskancin ma sun gudu ganin Yadda ta koma kuka take mai cin rai gashi ta koma gun boka ya rasu ga wannan abu da mai martaba ya bullo dashi yanzu ina zata sa kanta.. Bayan wata uku Mereeh anyi kyau yanzu tana da ciki wata biyu inda rainon mubeen ya dawo hannun ta kula take samu sosai har ta bangaren Hajiya bata da Malama.. Jannat anyi bikin su na cikin rufin asiri gidan ta mai kyau gashi ya sama mata aiki... ....... Ɗaukar shi baffa ya yi ya fara mai magani kwanan shi uku ya dawo haiyacin shi, ya na tashi ya fara da salati tare da kiran don Allah kada ku kashe ni mummy hanan mai martaba Please help me.... Baffa sai mai addu'a yake nan dai baffa ya basu labarin Yadda ya samai tare da aura mai yar shi don ya warke..... mummy taji daɗin taimakon da ya masu sosai ga hanan ta warke ga danta ga jikar ta. Fatsume ce ta shigo Tare Da faɗin baffa hamma habu ya dawo tunanin shi ko alhamdulilahi. Mummy tace zo nan ƴata ta isa gare ta tana sunne kai ita kunya shi ko hamma kallon soyayya mai zafi yake ma fatsume.. Sai a sannan ne wasu abubuwan suke dawo mashi ta bashi tausai yarinya ta ci sunan Marigayi ya Maryam ana kiran da ilham ranar suna suka tarkata harda baffan aka tafi burni can, ba da jimawa ba wai ana sallama da mummy a waje. Fita tai don ganin waye mai idon ta zasu gani inba mai martaba ba rufe ido tai ta buɗe ko gizo yake mata nan ya duka yana bata hakuri sosai kuwa tace ta yafe mai ya shiga cikin gidan ya gamsu zaune shi ma aka bashi Labarin abin da ya faru... Gida a zoo road ya ba hammad shi da matar shi...yar tsohuwa makociyar su mummy aka ɗaura aure da baffa mai martaba ya canza masu gida sosai ya yi ƙyau inda Binta ta samu miji tai aure ita.. Bayan wasu shekaru Sakkowa yake daga kan bene ta biyo shi a baya tana ohh Allah wai yanzu hibban haka zamu yi da kai wallahi naso zuwa amma kaki yarda ko? Rungume ta ya yi tare da faɗin zairah na kalli cikin ki so kike ki wahalar mun da baby ne? Ki hakuri mutafi da ilham... Yar ƙwalla ta share ba dan yaso ba haka suka tafi tare bazaka taba cewa fatsume ce ta koma haka ba. Fulani kuma an haukace tuburan.. Mereeh an haifi yan biyu' an sa sunan baba da mama.. Sameer kuma an yake ƙafa Bara yake fita yanzu Jannat an samu ciki sai shan lallaba take Matar hammad an kara haihuwa Yan uku ɗaya namiji sauran mata yasa sunan mai martaba macen Fatima sunan matar shi sai humaira Tammat bihamdulilahi Alhamdulilahi anan nakawo karshen littafin HAMMAD ZAIRAH Taku har kullum BOOS LEDY WRITER Sai mun hadu ana gaba