♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa) *Heart you so much* *************************⬇********************** ************* Top Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.thn.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > tophausanovels@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Top Hausa Novels Twitter: Top Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels Telegram Group: https://t.me/tophausa Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Top Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *labari ne ƙirƙirarre,banyi dan cin zarafin wani ko wata ba,idan yayi dai-dai da rayuwar ki to an samu daidaito ne amma ba wai niyar tozarci ko wani abin ba*. *Masoyana wa'inda na sani da wa'inda ban sani ba ina miƙo godiya ta a gare ku,sannan ina fatan zaku bani haɗin kai a wannan kamar yadda kuka bani a ƙareenateey,sai dai ina me baku haƙuri domin kuwa wannan zai fi ƙareenateey tsayi sosai duk da wancan ɗin ma yankewa nayi amma wannan babu wannan maganar dan haka ina fatan zaku bani haɗin kai sannan kuma zakuyi jimirin bibiyar shi har izuwa ƙarshe nagode sosai*. Bismillahir-rahmanir-rahim. 📖📖01-02📖📖 Jejin dake hanyar Abuja idan ka baro kaduna,tafiyar mita ashirin daga ƙauyen banguwa,wani madaidaicin gida wanda yake kusan ginin ba'a ƙarasa shi ba. Manya-manyan Bishiyoyi sune suka yiwa gidan ƙawanya inda baka hangen komai daya shafi gidan,ƙaton get ne irin na da wanda keda nauyi da kuma daɗewa. Daga cikin gidan kuwa,wata irin farfajiya ce me girman gaske wanda ciyayi da kuma rairayi suka rufe wajen ba zaka iya gane yanayin ƙasar wajen ba. Ƙofar da zata sadaka da ciki kuwa ƙofa ce ta ƙarfe me matuƙar nauyi,daka shiga wani falo ne ƙarami me duhun gaske wanda idan baka yi da gaske ba zaka iya bugewa,babu wani tarkace a falon banda kujeru da kuma tum-tum wanda suke ajiye a ƙasan carpet ɗin ɗakin. Ta ƙaramin corridor kuwa doguwar hanyace wacce ke ɗauke da ƙofofin ɗakuna jere masu yawan gaske,daga ƙarshen corridor ɗin kuwa wani falon ne wanda yake babu kyan gani,saboda komai na ciki kalar ja ne,sannan ga wani irin tururin hayaƙi da yake fita me matuƙar ban tsoro da tashin hankali. A ƙalla mutanen dake jere tsaye sanye da zani babba kalar ja jikin su babu riga,fuskar kowanne na nuna damuwa da ɓacin rai,sama dasu ishirin,kowanne kanshi babu koda ɗigon gashi. Wani mutum duka suke kallo wanda yake zaune saman wata ƙatuwar kujera wacce gefen ta kuwa gunkin zakuna ne hannun dama dana hagu,gaban shi kuma ƙwarya ce babba wacce ke saman wuta tana ci sosai da sosai. Tsayin minti biyar babu wanda yayi magana kafin can wani dake gefe yace cikin fusata da damuwa. "haba Tuge wai wayo kake son ka gwada mana ko kuwa ɗan naka so yake yafi ƙarfin ka,yau shekara ashirin da biyar kenan da yiwa *oregbu* alƙawarin bashi jinin matar ka da ɗanka amma babu ɗaya daya samu". Wannan dake zaune saman kujerar ya ɗago idanun shi da suka kaɗa suka yi ja ya zubawa wani mutumi wanda yake durƙushe gaban wannan ƙwaryar,cikin fusata yace; "bakaji tambayar da akeyi maka bane ko kuwa baka da amsar da zaka bayar ne?". Cikin matsananciyar damuwa yace; "nayi iya yina *Appu* amma abu ya gagara matar nan ko gidan ta bata bari na kusanta kuma kun san hakan sannan dai-dai da rana ɗaya bata taɓa barin jikin su babu kariya ba shi kan shi yaron nawa ba sani na yayi ba,kuma fa kun riga da kun san hakan kuma tunda na yiwa Oregbu alƙwarin jinin sa aikuwa babu makawa jinin nashi ne". Wannan daya kira da Appu ne ya miƙe tsaye sannan ya ɗauko wata sanda doguwa daga saman ta kuma tsini gare shi kamar kibiya ya ɗaga ta sama sannan yace; "har yanzu Tuge da sauranka,baka cika aƙawarin daka ɗauka ba dan haka sandar zama magaji tana nan a ajiye sai lokacin daka cika sannan Oregbu ya fara gajiya idan har baka kawo jinin ɗaya daga cikin su ba nan da lokaci kaɗan ba zaka fuskanci fushin shi". Tuge ya buɗe baki zai yi magana Appu cikin tsananin tsawa yace; "maganar Oregbu itace magana baya buƙatar martani ko kuwa gardama,a fara gabatar da wankan tsari",dole yaja bakin shi yayi shiru. Wani me ƙaton ciki ya taho cikin sauri ya ciri wannan ƙatuwar ƙwaryar dake saman wuta ya ɗaga ya miƙawa Appu shi ya fara sha sannan ya kwarara jinin a jikin shi wanda bana da tabbacin jinin na meye sannan aka miƙawa Tuge shima yayi yadda Appu yayi sannan sauran mutanen dake wajen. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 *HAYIN RIGASA,KADUNA*. ƴan mata guda biyu ne suka sauka daga Keke Napep a bakin titi,dukan su suna sanye da pink din hijab wanda ya saukar musu dan har ya wuce gwiwa,ɗayar fuskar ta tasha make-up ɗaya kuwa babu wani kwaliyya a fuskar ta sai dai duk da haka kyawun ta ya bayyana,dukkan su kama ɗaya gare su wanda hakan ya tabbatar mini da cewa ƴan biyu ne kenan. Wacce tayi make-up ɗin ta ya mutsa fuska tace; "Ramluv,wallahi na gaji sosai",wacce aka kira da Ramluv ɗin tayi murmushi kawai tana buɗe purse ɗin dake hannun ta,ta ciro ɗari biyu ta miƙawa me Keken tace; "malam bamu canjin mu". Me Keke Napep ɗin ya leƙo da kan shi yace; "haba Hajiyoyi ai bakuda canji,tun daga Tudun nufawa sannan ku nemi canji haba mana". Wacce tayi make-up ɗin da yawa ta kalle shi ta wurga mishi harara tace"wallahi baka isaba sai ka bamu canjin mu ai dama ɗari da hamsin muka yi da kai sannan koda ka kawo mu baka shigar damu cikin unguwa ba mun kuma ƙyale ka shine zaka ce ba zaka bamu canji ba wallahi sai ka bayar". Shima ɗan Keke Napep ɗin ya fito ya tsaya cikin faɗa da fitsarar ƴan zamani yace; "idan kuma na hana me zaki yi mini?",ta kalle shi taja tsaki tace; "au tambaya kake ma to wallahi zaka sha mamaki kaɗan daga aiki na wallahi na saka ayi maka dukan tsiya ƙaryar rashin mutunci kake". Ɗayar ta kalli wajen sannan ta kalle su yadda kowanne keji da ɗanyan kai ga kuma waje ya fara cika cikin murya me rauni tace; "Rimluv dan Allah kiyi haƙuri kizo mu tafi",ta juyo ta balla mata harara sannan ta cigaba da masifar ta. Yadda suke kamar zasu yi dabbe ga jama'a a wajen,gashi taƙi ta dena ya saka ƴar uwar ta fara hawaye wanda ita bama ta lura da ita ba,ita kuwa daman ƙoƙarin ta taja ƴar uwar tata su bar wajen. "banza ɗan iska mara mutunci",Rimluv ɗin ta faɗa cikin fusata,hannu ya ɗaga domin sauke mata mari ya sauke akan ƴar uwar ta wacce ke ƙoƙarin raba su,Rimluv ta kalli ƴar uwar tata tace; "ka mare ta wallahi ba zaka ci bulus ba",itama ta ɗaga hannu ta kwashe shi da mari,wanda hakan yayi dai-dai da zuwan wani dattijo. Cikin sauri yace; Nusreen kece da dambe da maza a titi harda mare-mare?",ganin wanda yayi maganar yasa ta saukar da kanta ƙasa tana cuno baki. Cikin daka tsawa yace; "kin wuce gida ko sai na ɗauke ki da mari shegiya me baƙin hali",ta ɗago da zummar yin magana ƴar uwar tata tayi saurin matse hannun ta,shiru tayi tana ƙwafa sannan ta kalli me Keke Napep ɗin ta harare shi,hamsin ɗin da yake miƙo mata ta fuzge sannan ta juya tayi gaba tana faɗin"matsiyaci kawai". Kowa a wajen da abinda yake faɗa,ita kuwa gaba tayi tana tafe tana masifa,dattijon nan yace; "ki rufe mini baki ko kuma nayi miki duka a wajen nan me mugun hali irin na uwar ta",shiru tayi tana jin wani tuƙuƙi a cikin ranta wanda hakan ba ƙaramin takurata yayi ba na rashin bata damar maida mishi da martani da ta hanata yi. Can ƙarshen layin wani gida na rufin asiri za'a ce dan kana gani ka san talakawa ne,duk da dai ya sha sumunti sannan da ƙofa irin ta zamani a jiki,gaban gidan kuwa siminti ne a shinfiɗe wanda ya ƙara fito da gidan. Tana shiga ta banko ƙofar wanda saura kaɗan wannan Dattijon ya buge,aikuwa ya fara ɗebe mata albarka yana banbamin faɗa,ita dai hannun ƴar uwar ta taja suka shige ciki. Tsakar gidan kuwa yana nan yadda suka zata,duk tarkace alamun tun safe ba'a yi shara ba kenan,gefen famfo wata matace ƙatuwa tana zaune tana faman tace ƙullun wara wanda hakan ke nuni da kayan sana'ar tane. Nusreen taja tsaki bayan sunyi sallama bata amsa ba,tace; "mutum dai wuta zai shiga idan yayi wasa domin kuwa rayuwar yanzu bata da tabbas kayi aiki nagari ma yaka cika balle kowa ya san da cewa Sallah da salati bata dami mutum ba ai ba abin mamaki bane idan mutum yaƙi amsa sallama". Wannan matar ta taso cikin masifa tace; "ke mara kunya fitsararriya wallahi idan baki dena shiga harkata ba a gidan zan jibge ki naga wanda ya tsaya miki". Nusreen ta wulla mata harara tace; "gwara ni Allah ne ya tsaya mini ba boka ba",wannan maganar caraf a kunnen Dattijon nan wanda ya shigo yana nashi masifar. Kanta yayi da gudu,ita kuma ta zuba da gudu tayi wani ɗaki wanda yake daga can lungu tana faɗawa ɗakin ta rufo ƙofar. Cikin haki yace; "wallahi zaki zo ki same ni ne shegiya me zubin mayu,matar tawa kike faɗawa haka shegiya da haihuwar ki gwara ɓarin ki,zan kuma zo kan uwar taki ne wacce ke ƙara zuga ki",yana faɗin haka ya juya. Dai-dai ƴar uwar tata ya tsaya wacce ke faman zare idanu domin tasan akan ta abin zai ƙare aikuwa kamar yadda ta zata yana zuwa ya zuba mata rankwashi sannan ya kama kunnen ta ya murɗa yace; "ƴar iska munafika kina zare idanu kamar ƙwan nufawa",ta girgiza kai hawayen azaba yana zubowa daga idanun ta. Sai da ya gaji dan kan shi sannan ya saki kunnen,ya fice yana bambami,wannan matar me ƙiba ta kalle ta cikin huci,da sauri ta nufi ɗakin da ƴar uwar ta ta shige amma kan ta kai taji saukar kwano a kanta wanda yasa ta ƙwalla ƙara saboda azabar zafi. Nusreen na daga ɗaki tana jin ihun ƴar uwar ta ta yunƙura zata tashi mahaifiyar su dake zaune ta wurga mata harara,bata son ɓacin ran mahaifiyar tasu hakan yasa ta koma ta zauna tana wuci. Ita kuwa Nusram ganin babu sarki sai Allah yasa ta miƙe ta ƙaraso bakin ƙofar ta ƙwanƙwasa,Nusreen tayi sauri taje ta buɗe mata sannan ta riƙo ta suka shigo tare cikin ɗakin. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 *UNGUWAR SARKI,KADUNA*. wani katafaren gida wanda kana ganin shi ka san ƴan gidan sunci kuma sun tada kai,wanda zaka iya cewa basu ma san talauci ba,ko'ina ka duba a bakin gida securities ne ke kaikawo domin tsare lafiyar ahalin gidan. Daga cikin gidan kuwa a ƙaton falon wanda yaji kayan more rayuwa,samari guda biyu na hango zaune saman kujera,sai mace ɗaya dake zaune a ƙasa rungume da filo tana danna waya,daga gefe kuma wata yar budurwar ce gefen ta yaro wanda ba zai wuce shekara goma sha biyu ba hannun shi riƙe da littafi da alamu karatu take koya mishi. Jin taku da kuma wani fitinannen ƙamshi yasa dukan su ɗaga kai suka kalli Upstairs ɗin suna jiran ɓullowar me wannan ƙamshin,wata matashiyar macece wacce a ƙalla zata kai shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar,fara me ɗan ƙiba,tana da tsayi wanda shiya ƙara ɓoye ƙibar tata,jikin ta sanye da wani danƙareren lace wanda a ƙalla zai kai dubu tamanin zuwa tamanin da biyar,ɗinkin borno wanda yake plain zani ne da kuma rigar iya gwiwa wacce taji aikin wuta,kafaɗar ta kuwa ta yafa wani gyale milk shima me tsadan gaske ƙafar ta sanye da takalmi high hill hannun ta na hagu saɓe da riga baƙa irin ta lawyers,wanda take sanye da wani siririn agogon azurfa wuyan ta sanye da siririyar sarƙar zinare,hannun ta na dama riƙe da jakar ta ƴar ƙarama kalar ruwan madara da kuma key tana kuma rike da wayar ta wacce kuma kunnen ta ke sanye da eye piece da alamu ma ya nuna waya take amsawa,sai dai yadda take murmushi zai tabbatar maka da cewa wanda take wayar dashi mutum ne me matuƙar mahimmaci a rayuwar ta. "Baby,maganar ƙarshe da zanyi shine dole ka dawo gida a cikin satin nan idan ba haka ba zaka sha mamaki na",ta ɗan yi shiru alamun na can ɓangaren magana yake yi. Cikin damuwa tace; "Baby ba zan canza magana na fara gajiya da halin ka,kodan kaga na damu da kai zan kira Daddyn ku Allah na faɗa mishi wannan halin naka,and maganar ƙarshe shine ka biyo jirgi gobe ka dawo gida ko kuma ka ganni a England ɗin na dai faɗa maka",bata jira cewar shi ba ta kashe wayar sannan ta kalli yaran nata da suka zubo mata idanu tace; "zan tafi wajen aiki fatan baku da wata matsala",ɗaya daga cikin wa'innan samarin yace; "Mum,maganar canza mini motar fa,kinga......". "Tameer,ya isa haka! Ina mun gama wannan maganar ka jira Daddyn ku nan da sati biyu",ta faɗa,cikin sauri ya buɗe baki zai yi magana tace; ya isa haka! Sai na dawo",daga haka ta fice. Wanda ta kira da Tameer yayi ƙwafa yace; "wallahi na gaji da halin Mummy me yasa bata damu da halin da muke ciki ba amma ta damu da wancan wawan?". Ɗayan saurayin wanda suke kama sosai daka gansu ka san ƴan biyu ne yace; "Tameer ka dinga ƙoƙarin ɓoye fushin ka mana,Abdul fa ɗan uwan mu ne". Cikin fushi Tameer yace; "Abdul! Na tsani wannan yaron kamar yadda na tsani mutuwa ta",wannan budurwar dake zaune tana danna waya tayi tsaki tace; "nifa Yaya Tameer wallahi ina bayan ka kuma ko ni na tsane shi dan dai bani da yadda zan yi dashi ne". Ɗayar dake koyawa yaron nan karatu tace; "Kai Aunty Surayya ki dena faɗin haka Yaya Abdul fa ɗan uwan ku ne ya kama ta ku dinga sassauta tsanar da kuka yi mishi",cikin fushi Surayya tace"dallah rufe mana baki,keda Yaya Sameer ai naga bakwa kishin kanku kuma wallahi ko ku canza ko kuma kuna gani zaku mutu babu yadda zaku yi mu dai zamu san yadda zamu yi". Sameer yayi murmushi yace; "Surayya Sumayya fa ta fiki gaskiya,koma meye dai ɗan uwan mu ne",Tameer ya juyo yace; "eh ɗan uwan mu ne amma kuma Mummy bata ɗaukar hakan kana gani abinda ya faru da ace Abdul ne ya nemi ta canza mishi mota data canza amma da yake ni ne sai dai na jira Daddy". Sumayya tayi murmushi tace; "Yaya Tameer kaifa kana da kuɗin da zaka canza motar ka me zai sa ka jira Mummy?",suka yi shiru duka,ita kuma ta kalli yaron tace; "Fahad tashi muje kayi wanka",tana faɗin haka ta ja hannun shi suka shige ɗaki ta bar su nan tsaye. Surayya na ganin haka tayi ƙwafa ta wuce itama ta barsu,Tameer shima yayi tsaki yace; "Sameer duk kuɗi na ya kama ta ace tunda na tambaya Mummy ta siya mini,kada ka ɗauka iya kaina hakan zai tsaya wata rana zai tsallako kanka",daga haka shima ya wuce ya bar Sameer a tsaye. Sameer yayi ƙwafa yace; "mahaukata waye yace musu ana fito da ƙiyayya oho! Abdul ka ƙwace mana komai taya kuwa zan so ka???". #LIKE #SHARE #COMMENT * Babyn Abdul,Maman Meenal,Elham da kuma Farouk* *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖3-4📖📖 Nusram ke zaune bakin famfo tana wanke-wanke, tana ta sauri domin tayi ta gama gudun kada tayi lattin zuwa makaranta, Mama Jummai ta fito da tarkacen kayan kwanukan ta ta zube gaban Nusram tace, "gashi nan tunda ba za'a fito da miji ayi aure ba sai a zauna ayi mana bauta", Nusram ta saukar da kanta ƙasa kawai tana me jin zafin magan-ganun na Mama Jummai. Nan ta zube su ta juya tana mita; "to dama meye amfanin ku a gidan yara tun nonowa suna kirji har sun faɗi amma kun ƙi ku fitar da mazaje,ai wallahi dani daku ne a gidan ga uwar can tsohuwar munafika kullum tana ɗaki a kile kamar kayan wanki Musa a baki Fir'auna a zuci", Nusram ta ƙara kallon hanyar bayin inda ta tabbatar da cewa Nusreen na jiyowa fatan ta dai ace bata jiyo duka ba,sai dai ta makaro domin kuwa duka magan-ganun Mama Jumman a kunnen ta suke kuma Allah-Allah take ta gama ta fito domin bata amsa. Tana fitowa Nusram tayi sauri ta miƙe, idanun ta cike da hawaye tace; "Pls Rim kada kice mata komai dan Allah", Nusreen ta galla ma ƙofar ɗakin Mama Jumman harara sannan tayi ƙwafa ta wuce, Nusram kuwa ganin hakan yasa tayi ajiyar zuciya sannan ta cigaba da wanke-wanken ta, Kan wani lokaci ta gama sannan ta kwashe nasu ta kai ɗaki ta ɗauki na Mama Jumman ta kai mata itama ƙofar ɗaki sannan ta juye nata ruwan ta shiga wanka. Bata jima ba ta fito inda ta shiga ɗaki ta tarar da Ummi na zaune tanawa Kubra tsifa yayin da Nusreen ke faman sheƙa kwalliyya, Nusram ta kalle ta tayi murmushi kawai sannan itama ta hau shiryawa. Atamfa ta saka me kalar pink da ash sai ratsin fari da baƙi kalar ta jikin Nusreen ɗin sai dai banbancin shine ɗinkin domin kuwa Nusreen tata fitted gown ne ita kuma Nusram tata me buɗewa ce daga ƙasa, bata tsaya kwalliyya ba kamar ƴar uwar ta mai da hoda kawai ta shafa sai kwalli data zizara ta ɗauki hijab ta saka kalar ash wanda ya kasance kalar uniform ɗin makarantar kenan ta tada sallah, haka itama Nusreen ɗin sai da ta gama tata ƙyale-ƙyalen sannan tayi sallah suka fice cikin sauri suna yiwa Ummi sallama akan sun tafi islamiyyar. Ummi tayi musu addu'a da fatan nasara sannan ta ɗaga Kubra domin ta gama yi mata tsifar saura wanke kan. Suna fitowa suka iske yaran Mama Jumman Atika da Ameera sun dawo daga tallan shinkafa da waken data ɗora musu, Nusreen ta kalle su tayi tsaki tace; "mutum bashi da aiki sai yawon tallace-tallace wata rana garin jarabar son kuɗi a kwasowa mutum abinda zai jefa shi a masifa", Mama Jumman ta fara balbalin masifa ita dai Nusram taja hannun ta kawai suka fice. Kan hanya ma sai faman masifa take ita dai Nusram bata kula ta ba har suka iso bakin makarantar, ana ta taron latti amma da yake Nusreen ɗin akwai rigima haka ta wuce cike da taƙama tana taku ɗai-ɗai. Nusram kuwa da sauran ɗaliban suka tsaya suna kallon ta, Malam Abbas shima ya bita da idanu da sauran malaman dake bakin wajen, ganin da gaske take yasa shi daka mata tsawa yace; "Nusreen Abdullahi Dabai ki dawo nan", ta juyo cike da ƙasaita tace; "sunan haka yake malamin addini babu kuskure", duka wa'inda ke wajen sai da suka kwashe da dariya wanda hakan ya kuma tunzura Malam Abbas ɗin yayo kanta da bulala. Tsayawa tayi ƙyam tana kallon shi harya kawo kusa da ita kafin yaja dan kan shi ya tsaya, tana ganin ya tsaya ta saki murmushin ƙasaita tace; "ya ka fasa ai da ka zuba mini a jiki kawai", ta ƙarasa tana mishi wani kallo. Duk abinda yake faruwa akan idanun shi kuma yana kallon meke faruwa ganin idan beje ba za'a yi abinda be kamata ba yasa ya taho wajen da sauri. "meke faruwa ne?", ya tambaya, Malam Abbas yace; "latti tayi amma tazo ta wuce kamar zata shiga ɗakin su", Malam Saleem yayi murmushi sannan yace; "Malam Abbas ai kun riga da kun san halin wannan domin samun maslaha ka ƙyaleta kawai ta wuce", haka dole yasa Malam Abbas ya barta ta wuce ya koma kan sauran yana jibgar su, koda yazo kan Nusram sai da ya sauke haushin Nusreen akan ta tsaf sannan ya ƙyaleta gaba ɗaya ya farfasa mata hannu, haka ta tafi aji tana kuka. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 Ta ɗagawa ƴar matashiyar data kawo mata Coffee ɗin hannu tana me cigaba da amsa wayar ta hankali kwance. "Baby ban san wannan ƙorafe-ƙorafe,dole fa ka dawo gida gobe na ƙara jadadda maka, shiru tayi alamun magana yake har zuwa lokaci me tsayi kafin tayi murmushi tace; "yauwa ko kaifa", ra ƙara sakin murmushi tana fadin; "Mummy loves you more, bye", daga haka ta ƙatse wayar. Cikin isa da ƙasaita ta hau kiran; "Aziza! Aziza!!", kan tayi kira na uku ta iso gare ta, cikin isa da bada umarni tace; "kije ki faɗawa sauran ma'aikatan gidan kan cewa Baby yana kan hanya gobe sannan ki tura Salma ta buɗe ɓangaren shi gani nan zuwa na gyara mishi", jiki yana rawa Aziza ta amsa da"to", haka ta tafi cikin murna da farin ciki domin kuwa sun san cewa hanyar ƙofar samun su ta kusa dan akwaishi da kyauta sannan ko ita kanta uwargidan tasu bataso yin abu ba indai kayi kamun ƙafa dashi tofa aikin ya gama cika,koda ta sanar da ma'aikatan gidan nan suka hau murna suna sam barka da dawowar tashi. Babu jimawa ta miƙe ƙafafunta sanye da slippers ta fice daga ɗakin nata zuwa part ɗin shi, a falon ƙasa ta tarar dasu kamar koda yaushe, Surayya ta danna waya, Sumayya kuma littafi ke hannun ta da alamu karatu take, Sameer kuma yana operating system ne yayin da Tameer ke kwance idanun shi a lumshe kamar me barci, duka suka yi mata sannu da fitowa ta ɗaga musu hannu sannan ta kalli Surayya tace; "kije kan drower a ɗaki na zaki ga box saƙon sarƙar ki ne da kika ce". Cikin farinciki ta hau godiya, kallonta ta mayar kan Tameer kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta kalli Sumayya tace; "ina Auta na?", tayi murmushi tace; "Mummy Auta yayi barci", ta nufi hanyar fita kan tace; "kije ki tashe shi yamma tayi", ta amsa da to sannan tace; "Mummy ina zaki je?", sai da ta juyo ta kalle ta sannan tace; "Baby zai dawo gobe zanje na gyara mishi part ɗin shi ne". Sumayya tayi tsallen murna sannan tace; "Mummy nazo na raka ki", tayi gaba tana faɗin; "ki fara tashin Fahad daga barci tukunna", Sumayya cikin murna tayi hanyar ɗaki domin tashin Fahad ɗin. Tameer ya buɗe idanu sannan yaja tsaki yana faɗin; "aikin banza kawai", Sameer ya kalle shi ya girgiza kai kan ya cigaba da abinda yake yi. Babu jimawa Sumayya ta tashi Fahad, sai da tasa Salma tayi mishi wanka sannan ta fito cikin gaggawa, tana zuwa falon Tameer yace; "banza mara tausayin kanta", ko kallon shi bata yi ba ta wuce. A buɗe ta tarar da part ɗin da kuma alamu Mummy ta riga da ta fara aikin ta, aikuwa kamar yadda ta zata tana shiga ta tarar falon ƙyal-ƙyal ko'ina tsaf-tsaf, tayi hanyar bedroom ɗin, Mummy na tsaye tana gyara kan madubi ta ɗago ta kalle ta, Sumayya tayi murmushi tace; "Mummy na gama", ta ɗaga mata kai tana me cigaba da abinda take yi. Sumayya na tsaye tana kallo har ta gama gyaran bedroom ɗin ta canza bedsheet saman gadon sannan ta shiga bathroom ta wanke tass, Sumayya tayi murmushi tana me jinjina soyayyar dake tsakanin ɗa da uwar, ta san cewa idan zata kwana tana tambayar ta akan ta bari ta taya ta ba zata bari ba shiyasa taja baki tayi gum. Tana gama wankewa ta ɗauko turare ta zuba a burner ta kunna sannan ta hau fesa Room freshner sai da ta tabbatar da ko'ina ya ɗauki ƙamshi sannan ta fito daga bedroom ɗin Sumayya tana bin bayan ta. Ɗakin dake kallon wannan ta shiga, shima bedroom ne sai dai a maimakon gado sai aka saka ƙatuwar katifa babu wasu tarkace a nan, wardrobe ne sai dressing mirror shikenan, sai dai jikin bangon dake ɗauke da manya-manyan hotunan ƴan ƙwallo. Shima ta gyara shi tsaf ta saka mishi turare ta wanke bayin sannan ta rufo ɗakin ta fito Sumayya ma na bayan ta, haka ta rufe part ɗin ta fice. Suna isowa parking space ta ɗaga kai ta kalli motocin dake wajen, "Bala! Bala!!", cikin sauri ya ƙaraso, ta dube shi tace; "banga ka gyara motocin da za'a ɗauko Baby bane". Ya shafa kanshi yace; "Hajiya walllahi Tameer ne yace na wanke tashi na bar wa'inn..", kan ya ƙarasa ta dakatar dashi ta hanyar cewa; "dakata mini, Bala ban san cewa Tameer ka fara yiwa aiki ba sai yau", jiki na rawa ya fara bata haƙuri, bata kalle shi ba tace; "kasan bana iya haƙuri da abinda ya shafi Baby a gidan nan amma kake neman ka maidani abokiyar wasan ka". "Hajiya dan Allah kiyi haƙuri", ta girgiza kai tace; "magana ta ƙare kaje wajen Aziza ta baka dubu hamsin ka kama gaban ka bana buƙatar ƙara ganin ka", jiki na rawa ya tsuguna yana bata haƙuri haka tayi wucewar ta. Nan sauran ƴan aikin suka fara bashi haƙuri shi kuma yana kuka, yaje ya tattara kayan shi sannan yaje wajen Aziza ya amshi kuɗin. Aziza tace; "ka bari gobe idan ƙaramin oga ya dawo sai ka dawo ka roƙe shi", ya yarda da shawarar ta sannan yayi godiya ya tafi. "waye nake magana yake canza mini ita a gidan nan", ta tambaya bayan ta shigo ta sami Tameer da Surayya a zaune, ganin yadda fuskar ta ke ɗaure yasa duka suka sauke kan su ƙasa. "ina tambayar ku, wane ishashshe ne wannan?", ta faɗa cikin daka tsawa, a sanyaye duka suka hau bata haƙuri, ta ɗaga hannu ta nuna su tace; "har yanzu dai nice Brr Farida suna na be canza ba, kuma nima ban canza ba", tana faɗin haka ta kalli Tameer tace; "kaje ka cewa Ali ya mayi aikin Bala a fito da motocin da za'a je ɗauko Baby a wanke su", tana faɗin haka ta wuce sama ta barsu cike da baƙin ciki. Tameer na ganin ta wuce ya buga tsaki cikin ƙuluwa yace; "wallahi idan na cigaba da zama a gidan nan wata rana mutuwa zan yi", Surayya tace; "to Yaya ka fito da mata mana kayi aure", yace; "ai dole ma idan ba haka ba baƙin ciki sai ya kashe ni", haka dole ya tafi inda ta aike shi cike da jin haushin wannan so da Mummy ke yiwa ƙanin shi. Haka ya basu umarni daga nan ya wuce part ɗin su dan haushin halin Mummy yake ji, gashi basu da yadda zata yi, ita komai Baby. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 Koda aka taso su daga makarantar a hanya Nusram keta bata baki akan abinda take yi, "haba Rim kinga fa rashin jin magana da kuma yiwa babba rashin kunya baya haifar da komai face ci baya, dan Allah ki dena". Nusreen tace; "Allah ko! Yau kuma wa'azi kika koma, to bari kiji ni ba zan iya rayuwa kalar taki ba ina kallo ana cuta ta nayi shiru ko kuma na koma ina kuka wannan ba zai taɓa yiwuwa ba". Nusram tace; "ai na sani amma dan Allah ki rage tsiwar nan ko zamu sami wanda zai kalle mu, muma mu wuce gori", Nusreen ta kwashe da dariya tace; "kice ga inda maganar ki ta dosa ta ki sani wannan kuma daga Allah ne ba daga ni bane kuma ki faɗa mini shekarar mu nawa ne just 24yrs da ƙuruciyar mu fa". Nusram tace; "Nusreen ki duba fa kiga ƙannen mu nawa aka yiwa aure, uku fa sannan ki duba ƴaƴan Auntyn Tudu, itama ta aurar da yara biyu Safeena da Halima kuma duka mun girme su, dan Allah ki maida hankali". Nusreen ta kalli ƴar uwar ta na wani lokaci sannan tace; "Ram ba zan taɓa yin aure na barki ba kema kin sani kuma alƙwari ne na ɗauka kan cewa sai kin sami naki mijin sannan nima zan tsayar beside ma duk wa'inda ke zuwa waje na babu wanda yayi mini". "Rim ki manta da ni kiyi auren ki wataƙila tawa ƙaddarar kenan, bazan taɓa samin miji ba ke kuwa fa ko jiya fa wani yazo kan yana son ki kika ƙi fita". Nusreen ta taɓe baki tace; "ai sai kiyi tayi wallahi ba zan yi aure na barki a wajen wannan matar mara tausayi ba ta dinga muzguna miki a hakan ma wai duk da tana tsoro na ya aka cika ina ga na tafi na barki, kuma maganar wai ke taki ƙaddarar kenan ashe kema zaki iya yanke ƙauna daga rahamar Ubangiji?, to bari kiji Allah yana sane dake kuma na san addu'ar da mahaifiyar mu take mana ba zata taɓa faɗuwa ƙasa banz.....", bata ƙarasa ba saboda ruwa da wata mota ta shiga ya fallatso mata duk ya ɓata mata jiki. Nusram na ganin yadda ta haɗe rai yasa tayi saurin riƙo ta tace; "dan Allah Rim mu tafi kada kice komai", Nusreen ta ɓalla mata harara tana kallon motar da ta rage gudu a hankali kuma motar ta fara dawowa baya. Nusreen na ganin motar tayi parking ta fincike hannun ta daga na ƴar uwar ta tayi kan motar cikin sauri kuma ɗauke da fushi. Tana zuwa yana fitowa ta galla mishi harara kafin tace; "kai ɗin waye da har zaka zubawa mutum ruwa kuma ka cigaba da tafiya, kodan kana taƙama da cewa mahaifin ka nada kuɗi shikenan dama haka halin ku yake kallon talaka kuke a banza a wofi to wallahi ni ba irin sauran bace banda haƙuri mutum nayi mini zan yi mishi, mutum ya hayo titi kamar na ubanshi to kaji ka sani ba ɗauka zanyi", ya tsaya yana kallon ta cike da mamaki. Ta ɗaga hannu ta nuna kanta tace; "kalle ni da kyau na wuce raini kuma idan taƙamar ka kuɗi ni kuma ina da Allah domin shiya tsaya mini......", kafin ta ƙarasa abinda zata faɗa aka buɗe ɗayar ƙofar aka fito. Wata dattijuwar mata ce fara sosai, tana ɗingisa ƙafa ta ƙaraso gaban ta, tayi murmushi sannan tace; "Ƴan mata kiyi haƙuri bada sani bane, sauri yake ya kaini airport domin zan tafi syria inda za'a mini aikin ƙafa da take damuna". Nusreen ta kalle shi, shima dai itan yake kallo yana murmushi ta galla mishi harara tace; "Allah ya taimake ka da wallahi saina ɗauke ka da mari", tana gama faɗin haka ta juya ta bar wajen. Nusram ta saukar da kai ƙasa tace; "dan Allah kuyi haƙuri kuna sauri mun tsayar daku", ta maida kallon ta kan shi wanda shima ita yake kallo cike da mamakin kamar ta da waccen har muryar su sai dai ita wannan muryar ta sanyi-sanyi take; "kayi haƙuri ba haka take ba ranta ne ya ɓaci, Mama Allah ya baki lafiya yasa ayi aikin a sa'a", tana gama faɗin haka ta juya tabi bayan ƴar uwar ta. Duka suka bita da kallo wanda kowa da irin nashi ma'anar, shi yana mata kallon girmamawa yayin da mahaifiyar shi ke mata kallon sha'awa da birgewa tana fatan inama ƴar ta ce. Ta maida kallon ta kan ɗan nata sannan tace; "Shureim muje ko", yayi ajiyar zuciya sannan ya shiga motar ya jata suka tafi. Nusram duk iya saurin data yi bata tarar da ƴar uwar tata ba har ta isa gida, tun kan ta shiga gidan ta jiyo muryar ta tana faɗin; "wallahi mutum yayi mini na mishi dukan mutuwa". Tana ƙarasa shiga, Mama Jummai na fitowa tana faɗin; "to shegiya fitsararriya sai kizo ki dake tan a gaba na, anƙi aure anzo an ishi ƴaƴan masu gida", Nusreen tace; "to mu ai sai a sheganta mu, yadda yake gidan uban su haka yake gidan uban mu, maganar aure kuma naga wata ma tsabar daɗewa sai da ta shekara talatin da biyar sannan tayi auren fari, aka kuma tafi da me daka gidan mijin gwara mu ma muna da kyan jiki, mtsew abu kamar guzuma", saukar mari taji wanda ya hanata ƙarasawa ta juyo ta kalli Ummi, Ummi kuwa cikin ɓacin rai tace; "wuce ɗaki", babu musu ta wuce tana faɗin; "wallahi sai na dake ta sai dai ta dena fita". Mama jummai kuwa sanin da ita Nusreen take yasa tana huci tana faɗin; "bari uban naki ya dawo sai na tambaye shi idan shi ya zauna ya kitsa miki, shegiyar ƴar tasha". Nusram ta fara zubar da hawaye tana me baƙin ciki da halin da gidan nasu yake, Allah yayi ta da rauni shiyasa hayaniya koya take bata iya jure ta. Ummi ta kallo ta cikin tausayawa kasancewar ta mahaifiya gare su ta san halin su ya bambamta duk da kamar da suke, tace; "Nusram jeki cire hijab ɗin mana kizo ki share gidan", ta amsa da to sannan ta wuce. Tana shiga ɗakin ta tarar da Nusreen har ta fara gyara ɗakin, ta wuce ta ta ajiye hijab ɗin sannan ta fito ta ɗauki tsintsiya ta share gidan tas. Ummi kuwa kan lokacin ta gama girki dan haka ta tattara kayan da Ummin tayi amfani dashi ta wanke sannan ta wuce tayi alwala ta shiga ɗakin nasu domin yin sallah. Koda suka idar nan suka zauna kowa yana nashi karatun har aka yi kiran isha'i sannan suka tashi suka yi sallar. Sun fara cin abinci kenan suka jiyo Mama Jummai na kasawa yaranta tallan kunun aya da kuma ƙwai, Nusram cike da baƙin cikin halin Mama Jumman ta kauda kai kawai. Nusreen kuwa bata ce komai ba banda zama data gyarawa Kubra suna cigaba da cin abincin su, babu jimawa Baban nasu yayi sallama ya shiga, gaban Nusram ya yanke ya faɗi. Suna gama cin abincin Nusreen ta kwashe kwanukan ta gyara wajen sannan ta koma kusa da ƴar uwar ta suka yi zaman fira. Babu zato babu tsammani ya banko ɗakin ya shigo, yana hango su yayi kan su ya hau dukan su, yana faɗin; "marasa mutunci kawai". Nusreen ta miƙe domin guduwa yasa ƙafa ya taɗiyo ta ta faɗi a wajen yayi kanta yana duka, daman ita yake so ya daka rashin gane wacece a ciki yasa ya haɗa su duka amma da ƙoƙarin gudun da tayi ya gano itace wacce yake nema dan haka ya rabu da Nusram yayi kanta. Nusram kuwa tana kuka tana bashi haƙuri amma yaƙi haƙura, Ummi kuwa tunda ta saukar da kanta ƙasa bata kuma ɗagowa ta kalle shi ba, ganin hakan yasa Nusram faɗawa jikin ƴar uwar tata tana tare mata dukan. Haka ya haɗa yayi musu duka sannan ya ƙyale su ya fice, ganin fitar shi yasa Nusram janye jikin ta cikin wahala domin ita fatar ta bata jure duka ko yaya yake, ita koda wanki ne ya cika yawa sai ya fasa mata hannu balle duka gashi kuma dama ɗazu tasha na Malam Abbas yanzu kuma tasha na Yayan su Isa. Da ƙyar itama Nusreen ɗin ta miƙe ta zauna tana dafe da gefen cikin ta inda tasha ƙasa ɗazu, sai dai abin baƙin ciki kan su gama jimamin wannan duka suka jiyo hargagin mahaifin nasu ya nufo ɗakin nasu. Nusreen haka taja jiki ta gudu ɗaki yayin da baƙin ciki ya hana Nusram tashi daga wajen, yana shigowa ya fara zuba mata wayar wutan dake hannun shi, tun tana zaune har sai da ta kwanta a wajen haka ya bita ya cigaba da duka sai da ya tabbatar da ko yatsa ba zata iya ɗagawa sannan ya ƙyale ta. "kuma wallahi ko ku fito da mijin aure ko nayi ta azabtar daku a cikin gidan nan shegu masu baƙin jini irin na mahaifiyar su", ya cillar da ragowar wayar yayi waje yana bambami. Sai da suka dena jiyo hargagin shi sannan Nusreen ta fito da sauri tazo ta kama ƴar uwar ta, Ummi kuwa tsabar ɓacin rai numfashin ta har sarkewa yake yi. Duk yaji mata ciwo a fuska da jikin ta, Nusreen tace; "Ram ki dinga guduwar wa dukan Baba dana Yaya Isa", yadda tayi da fuska ya tabbatarwa da Nusreen cewa ranta ya ɓace. Ummi ta miƙe ta juye mata ruwan data ɗora saman murhu bayan ta sauke abinci, kaɗan ta sirka mata sannan tace; "Nusreen kai mata bayi, ke kuma ki tashi ki cire kayan kije ki gaggasa jikin ki", babu musu duka suka miƙe suka hau aikata abinda Ummi ta umarce su. Mama Jummai tayi shewa tace; "ai dama ni na wuce tunanin mutum gobe ma ki kuma turo su suyi mini rashin kunya ni kuma na kuma sa su gashi ahayye sai ni Jummala ƴa ga Habu sarkin wanzamai", babu wanda ya kula ta har tayi ta gama. Nusram kuwa taji daɗin jikin ta data gasa tana fitowa Nusreen ta shiga tayi nata wankan. Koda Nusram ta shigo ɗaki Ummi ta miƙo mata mansileta tace; "amshi wannan ki shafa", ta amsa ta shafa inda hannun ta ba zai kai ba Ummi ta taya ta ta shafa sannan ta miƙo mata wata doguwar riga mara nauyi hannun vest gare ta tace ta saka ta ansa ta saka sannan ta kwanta. Nusreen ma koda tayi wanka kayan barci kawai ta saka riga da wando,rigar iya gwiwa sai wando dogo tana gama shiryawa ta haye bayan ƴar uwar ta ta kwanta. Ummi ta kalle su cike da tausayawa tana me tausayin su, gasu duka mata Allah ya basu sai dai Allah ya bata ɗaya wacce ita ke ɗan ƙwato musu ƴancin, ta share hawayen ta tace; "Allah kana kallon wannan zalunci". *WACECE NUSRAM DA NUSREEN*. #LIKE #SHARE #COMMENT *babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖5-6📖📖 Malam Abdullahi haifaffen ƙauyen dabai ne, mahaifin shi tun yana ƙarami Allah yayi mishi rasuwa sai mahaifiyar shi ta auri me garin Dabai. Me garin Dabai kamar yadda yake tura ƴaƴan shi suyi karatu haka ya tura Abdullahi shima Zaria domin yin karatun, da yake me ƙwazo ne ya samu ya gama secondry yana dawowa me gari ya haɗa shi aure da Maimuna ƴar wazirin shi. Sun zauna a garin dabai tsayin shekara ɗaya cikin so da kulawa daga nan sai ya sami aikin messenger na wani company a kaduna hakan shine silar dawowar su Kaduna, Tudun Nufawa Anan Allah ya azurta su da yara guda biyu duka mata, shine aka saka musu Nusram da Nusreen, Malam Abdullahi ƴaƴa maza yaso amma Allah be bashi ba haka dole ya haƙura ya barwa Allah. Anan inda suke suka haɗu da Hajiya Kaltume wacce ke zaune tare da mijin ta itama sai dai su suna da rufin asiri babu laifi. Kamar ƴan uwan juna haka suke ita da Maimuna, ita ta raini Nusram kasancewar tafi Nusreen haƙuri tun suna ƙanana, babu ƙyashi ba komai duk abinda ta samu zata basu. Har su Nusram suka kai shekaru bakwai amma Maimuna bata kuma samin ciki ba wannan fa ya soma kawo matsala a tsakanin zaman Abdullahi da kuma Maimuna. Ita dai sai dai idan abin ya ishe ta tayi kukan ta godewa Allah, haka suke zaune cikin rufin asiri. Nusram yarinya ce data biyo halin mahaifiyar ta na haƙuri da rashin son tashin hankali, yayin da Nusreen ta kasance me tsiwa da faɗa ga saurin fushi, sha yanzu magana yanzu. Haka rayuwar su take gangarawa har lokacin da Abdullahi ya samu aikin zama a plaza wanda shine silar tashin su suka koma Hayin Rigasa domin can zai fi mishi sauƙi. Maimuna da Kaltume sun ji zafin rabuwa da juna sai dai basu da yadda zasu yi, ita Kaltumen a lokacin tana da yara guda shida, Sulaiman shine babba sai Halima,mai bi mata Safeena sai Sadiya, Musa sai ƙaramin su Adam. Shi kanshi Sulaiman ɗin shekara ɗaya kacal ya bawa su Nusram yayin da sauran ƙannen nashi duka su Nusram sun girme su da shekara biyu saboda shekara uku ke tsakanin ƴaƴan Kaltumen. Anan wajen aiki anan Abdullahi ya haɗu da Jamila wacce ake kira da Jummai, ta kan kawo abinci ɗan gaban wajen kaɗan inda su kuma ƙananan ma'aikata su kan fita su siya. Nan soyayya ta ƙullu a tsakanin su, har ta kaisu ga yin aure, Jummai macece da take ganin ta kai ta isa wacce taƙi aure da wuri tana ganin ai yawancin masu jinkirin nan sun fi samun mazaje masu kuɗi, sai da ta shekara ashirin da takwas sannan ta fara neman ya zata yi ta auru, nan fa mazaje suka ce basu san wannan ba. Ana haka wani yaro wanda ba zai wuce shekara ashirin da biyar ba ya fito a kan yana son ta, nan fa ta hau tsalle tana murna ita da mahaifiyar ta Iya Nafi, ganin su zaman alkhairi ne. Yayan ta Adamu ya kira ta yayi mata faɗa ya kuma yiwa yaron tatas domin ya san yaron zai yi wuya ya aure ta, aikuwa ta miƙe ta ci mishi mutunci ita da mahaifiyar ta ganin haka sai kowa ya saka musu idanu. Aikuwa ta kira yaro suka cigaba da soyewa kan ta ankara ya ɗirka mata ciki ya gudu, koda suka farga sun ji takaici da haushi yayin da sauran ƴan uba suka shiga farin ciki da murna. Babu abinda ba'a ɗurawa cikin ba amma da yake Allah ya raya kayan shi babu abinda ya sami cikin wannan ya ƙara ɗaga hankalin su, suna ji suna gani ta haifi yaron nata aka saka mishi suna Isa. Daga nan mahaifiyar ta ta cigaba da rainon yaron inda ita kuma ta cigaba da ɗaukar tallar duk da ranta baya so tana ganin ta wuce talla haka mahaifiyarta ta lallaɓa ta domin kuwa idan tayi a gida babu me zuwa ya siya sai dai a barta dashi. Lokacin da Abdullahi ya nuna yana son ta, sunyi matuƙar farin ciki da hakan, jin tsoron kada ya fasa idan yaji tana ɗa a waje yasa suka je aka rufe bakin shi ruf. Lokacin da labarin auren yaje kunnen Maimuna bata wani tada hankalin ta ba domin kuwa babu rashin ci ko rashin sha, ƴaƴan ta suna zuwa makaranta dan suna primary five islamiyya ma sukan je kuma yana biya dai-dai gwargwado. Ana auro Jummai komai ya fara taɓarɓarewa, amma duk da haka Maimuna ta cigaba da zaman haƙuri da Abdullahi. Haka ta ɗauko ɗan shegen ta tazo dashi kuma Mal Abdullahi ya nuna yafi son shi sama da ƴaƴan daya haifa, tun yana ƙarami dan ya girmi su Nusram da shekara huɗu suka taso da ƙiyayyar juna, haka Jummai zata saka yayi musu dukan tsiya amma duk da hakan sai Nusreen ta san yadda tayi itama ta rama. Sai da Jummai ta shekara guda sannan ta sami ciki, murna wajen Mal Abdullahi ba'a magana inda yake ganin zai sami ɗa namiji ta ɓangaren ta wannan ya bata lasisin shuka rashin mutuncin ta yadda take so. Bayan wata tara sai gashi ta santalo ƴar ta mace aka saka mata Habiba, wannan shine abinda yaso ya kawo matsala tsakanin su sai dai da yake da asiri hakan be wani tasiri ba. Kafin Habiba ta cika shekara ɗaya Jummai ta sake samun wani cikin nan fa sabuwar murna ta tashi, a lokacin kuma Nusram suka gama primary suka shiga aji ɗaya a secondry yayin da Isa ke aji uku a secondry. Nan ma ta sake haifo mace inda murnar Malam Abdullahi ta koma ciki, ranar suna aka saka mata suna Sahura, sai da Sahura ta shekara Uku sannan ta sami wani cikin ta haifi mace aka saka mata Sakeena, to daga nan fa sai haihuwar ta ɗan tsaya mata. Bata kuma samun ciki ba sai da su Nusram suka shiga aji huɗu a secondry shi kuma Isa yana aji shida a secondry sannan ta kuma samun ciki ta haifi ƴar ta mace aka saka mata suna Atika bata kuma cika shekara ba ta sami wata ƴar inda taci sunan mahaifiyar shi Kareema ake ce mata Ameera daga nan bata kuma samin wani cikin ba. Nusram kuwa suna aji na shida a Secondry sannan maman su ta sami ciki, babu kunya ba tsoron Allah Malam Abdullahi ya fara murna akan zai sami ɗa namiji, nan kuma bakin Jummai ya mutu. Su dai suka zubawa ikon Allah idanu, babu inda Jummai bata je ba don asiri amma kuma ciki yaƙi zubewa hakan ne ya ƙara tada hankalin ta. Ciki na shiga watan haihuwa ta haifi ƴar ta mace, ranar Jummai har party sai da ta haɗa a gidan, su Habiba suna gama jss 3 ta cire su daga makaranta ta fara ɗora musu talla. Haka Malam Abdullahi na kallo amma bashi da yadda zai yi da ita dole ya ƙyale ta, Kubra nada shekara ɗaya aka fara gane cewa aljanu sun taɓa ta wannan dalilin yasa Malam Abdullahi ya dena kwana a ɗakin Maimunar wai tsoron ta yake ji. Ummi kuwa magani ta shiga nemawa ƴar ta, ta manta dashi, Nusreen kuwa ta buga tsalle tace Mama Jummai ce tayi mata asiri, sai da Ummi ta tsawatar mata sannan ta bari. Tun daga lokacin da faɗa ya taɓa haɗa su da Nusreen ta kama ta zata dake ta Nusram taji haushi ta shiga. Dama ance faɗan me haƙuri be iya ba, haka ta jibgi Mama Jummai da itace a kai dalilin kuwa Habiba ta fara tsayawa da saurayi sai takewa Nusreen ɗin habaici shine ita kuma ta gaza haƙuri har ta tsinkawa Habibar mari a lokacin Mama Jumman bata ce komai ba. Sai da ta bari Nusreen ta saka guga a rijiya taje ta rufe ta da duka, Ummi tana zaune tana kallo bata ce komai ba, Nusram kuma na riƙe da Kubra tana shafa mata maganin da Auntyn Tudu (Hajiya Kaltume) ta amso ta kawo mata. Wani haushi da zuciya ya taso mata, dama Maman ta ɗora abincin siyarwa tana dafawa ta saki ta tafi duka, wajen murhun ta nufa tana zuwa ta ɗauki itace ɗaya tayi kan Maman. Tasa hannu ta janyo ta ta haɗa da bango, ta sa itacen ta dinga rafka mata a kai tun tana faɗin ta sake ta har ta gaji ta fara ihu, da kan ta Nusram ɗin ta sake ta Ummi bata ce komai ba. Tunda ta sake ta, Maman tayi ɗaki bata fito ba a ranar girkin ma Habiba da Sahura suka ƙarasa suma a tsorace suke da Nusram ɗin domin sun san ba halin ta bane. Baban na dawo ta faɗa mishi aikuwa har ɗaki ya bisu yayi musu shegen duka, wanda har ya jiwa Nusram ɗin ciwo a goshi wannan tabon shike bambace Nusram ɗin da Nusreen ɗin dan be ɓace ba sai dai ya disashe yadda sai ka ƙura idanu zaka ganshi. Haka da Isa ya dawo ta sake faɗa mishi, shima ya kuma yi musu duka amma tun daga wannan lokacin ta tsorata bata kuma kai hannu ta daki Nusreen ɗin ba duk iya abinda zata yi mata in dai ta san Nusram ɗin tana nan sai dai suyi ta fatar baki, sai dai cewa da tayi tunda haka ne su da aure sai dai suga anayi. Wannan be dame su ba domin sun san ta Allah ba tata ba, sun gama karatun su na secondry amma babu wanda ya taɓa zuwa sallama dasu. Nan fa Baban ya kuma takura su da masifa ga Maman tana nata habaicin, Ana haka Habiba da Atika suka sami nasu tsayayyun nan fa gori da masifa ya sake tashi. Babu me tanka musu sai Nusreen, haka abu yayi ta tafiya har aka zo aka yi biki ƴan dabai sun zo nan suka dinga shan surutu dan ma Nusreen ɗin tana mai da musu. Bayan biki ne Auntyn Tudu ta bawa Ummi shawara maimakon zaman da zasu yi haka me zai hana su cigaba da karatu wannan dalilin yasa suka fara fafutukar shiga jami'a. Lokacin da labari ya isa kunnen Baba cewa yayi ba saka hannun shi haka Ummin kan yi wankau da sana'ar ƙulle-ƙulle domin samun na rufin asiri. Daga haka ma wata rana yace; "shifa ya gaji da ciyar da ƙatti dan haka zai dena bata kuɗin cefane", bata ce komai ba haka taje Dabai tasa aka siyar da shanun da take kiwo guda biyu. Wanda wannan ne ya saka ta sami kuɗin dasu Nusram suka yi registration sauran kuma ta siyo shinkafa da taliya,macaronic,siga,gishiri,magi wake da sauransu ta fara siyarwa a gida. Ita kuma dama Nusram ta iya kitso da lalle dashi suke samun rufin asiri, da taimakon Abba( mijin Kaltume) suka sami addmission a nan KASU inda Nusram ke karantar Business administration Nusreen kuma ke karantar Mass com. Isa kuwa dama diploma yayi akan inter sci ya sami koyarwa a wata makaranta dake kusa dasu nan yake gangara rayuwar shi. Duk da makaranta hakan besa su Nusram ɗin zama haka ba sukan je wajen Auntyn Tudu su amshi kayan ƙamshi, wato turaren tsinke dana wuta,humra,kwalakca, detol da air freshner su shiga dashi makaranta su siyar. Abban ya buɗewa Sulaiman plaza inda yake siyar da takalma kayan sawa da sauran su wannan yasa har Takalma da sarƙoƙi sukan amsa su shiga dashi makaranta su siyar. Suna aji ɗaya a jami'a Sakeena ta sami miji itama aka yi mata aure, wannan karon har duka sai da Baban yayi musu dan haushi. Rufin asiri dai-dai gwargwado suna samu, Nusram kuwa idan ta sami lokaci har amarya ta kan shirya kwaliyya da komai-komai tana yi sai dai ita ɗin ba ma'abociyar yin kwalliyar bace a fuska sai dai takan yiwa wasu. Nusreen dai ita tafi son karatun sama da sana'ar hannu wannan dalilin yasa bata cika maida hankali akan komai ba sai dai ta kan taya Nusram ɗin wajen kwalliya. Wannan shine taƙaitaccen labarin su inda yanzu suke da shekara Ashirin da huɗu a duniya kuma har lokacin basu da tsayayyen saurayi gwara ma Nusreen ta kan samu sai dai tace bata so sai lokacin da ƴar uwar ta ta samu nata mijin. *CIGABAN LABARI*. Sai da Nusram tayi jinya na kwana uku sannan ta warke inda Allah ya taimake ta ƙarshen mako ne babu makaranta, Nusreen kuwa haushi ta dinga ji kamar me gashi Ummi ta hanata magana washe gari. Yau litinin zasu shiga makaranta da wuri hakan yasa suka tashi suka fara aikace-aikace, sai da suka yi wanka suka shirya Nusram tayi wanke-wanke ta share gidan tsaf, Nusreen kuwa ta ɗora musu abin kari, kunu da dankali soyayye. Nusreen ta fara shiga tayi wanka sannan itama Nusram ta shiga, kamar kullum sai da Nusreen ta fante fuskar ta ita kuwa Nusram bata wani tsananta ba, wani material ligaht blue da ɗigon fari da pink a jiki suka saka, hijab kalar light blue suka saka haka takalmin su. Shaf-shaf suka karya sannan suka kwashi littattafan su domin tafiya makaranta, Ummi ta miƙo musu ɗari biyar tace; "gashi Allah ya kiyaye hanya", suka amsa da ameen sannan suka fito. Mama Jummai na gaban murhu tana kwashe koko cikin ƙatuwar roba gefen ta Atika ce ke ɗauraye robobin zuba kokon, Ameera kuma na ƙoƙarin fifita wutar da samanta aka ɗora kaskon suya da mai a ciki wanda hakan ke nuni da cewa na suya ne. Nusreen ta taɓe baki sannan tace; "ayi dai mu gani aikin banza", Nusram ta balla mata harara sannan tace; "ina kwana Mama?", haɗiye amsar da tayi niyar bawa Nusreen tayi sannan ta amsa gaisuwar Nusram ɗin shima a ɗan ɗage. Nusram taja hannun Nusreen ɗin suka fice yayin da Mama take cewa; "an tafi yawon ta zubar ɗin ne", suna daf da shiga zauren gidan Nusreen ta juyo tace; "gwara mu fita muke muna yi wasu kuwa har zauren gidan uban su ake biyo su ana dannewa", basu jira me zata bada amsa ba domin kuwa Nusram jan hannun ta tayi suka fice kawai. A ƙofar gida kan dakali suka sami Baba zaune gefen shi Isa ne, da alamu lissafi suke yi domin ga kuɗi ne ajiye a saman dakalin, Baba na ganin su ya haɗe rai, Nusram tace; "Baba ina kwana?", sai da ya ɗan ja tsaki sannan ya amsa da lafiya, ta juya wajen Isa tace; "ina kwana Yaya isa?", shi kuwa juyar da kai kawai yayi yana wullawa Nusreen harara. Nusreen ta taɓe baki sannan tace; "Allah ya ƙara wai ke uwar biyayya ni Uwar mutum ma bata ishe ni kallo ba balle shi", daga Baba har Isan suka miƙe suka yo kanta, cikin sauri tayi gaba abinta. Cikin tsananin jin haushin abinda ta faɗa Isah ya juyo ya kife Nusram da mari, Nusram ta saukar da kai ƙasa sannan tace; "kayi haƙuri Yaya Isa", tana faɗin haka ta juya tabi bayan ƴar uwar ta. Har ta kusa bakin titi sannan ta tarar da ita, Nusram tayi yaƙe tace; "kai Rim gaki da tsokana ga tsoro, da haka kawai ne da sai na ta haɗaki da Allah akan ki ɗago ƙafa amma da yake kin san kinyi tsokana ai gashi har kin kusa titi", Nusreen tayi dariya tana faɗin; "ai wallahi ba zan tsaya aci zalina ba", haka suka ƙarasa bakin titi suka tari mota suka wuce makaranta. Koda suka sauka kowa faculty ɗin shi ya nufa, sai wajen ɗaya sannan Nusram ta gama nata don haka tana fitowa ta fara bin wa'inda ta san ta basu kaya suka haɗa mata kuɗaɗen ta sannan ta nufi faculty ɗin su Nusreen. Taje ta same su suna daf da shiga wata lecture ɗin hakan yasa ta sami garden gefen masallaci ta zauna ta ɗauki litattafan ta tana karantawa. Basu suka gama ba sai uku, tunda suka fito take jiyo hayaniyar ta, cike da mamakin halin ƴar uwar tata, ta ɗago tana kallon saman steps ɗin da suke tunda hall ɗin a sama yake. Bata bar surutun ba har suka sauko ƙasa, ita da wata budurwa ne suka bi bayan wata mata wacce daga gani ita sukewa hayaniyar, Nusram ta tashi ta ƙarasa kusa dasu sannan ta kalli ɗayar tace; "wallahi kema Yasmeen kina bani mamaki in banda haka meye na biyewa wannan". Wacce ta kira da Yasmeen ɗin ta juya idanu tace; "kai Ram ashe haka zaki ce kin san me tayi ne takalmi da sarƙa ta amsa amma har yau bata biya ba kuma sati biyu kenan". Nusreen ta wullawa matar harara, Nusram ta juya ta kalli matar tace; "kiyi haƙuri Maman Waleed wa'innan sai shiriyar Ubangiji kawai, kada ki damu duk lokacin da kika samu sai ki bada", Nusreen tace; "Ram kin san......", cikin sauri Nusram ta tari numfashin ta tace; "dakata ya isa haka ki dinga yiwa mutane uzuri mana haba". Maman waleed ɗin ta kalle su ta watsar tace; "ai wallahi kun bani mamaki ashe ƙoƙarin tona mini asiri kuke yi to Allah ya fiku, kuma idan banda ƴar uwar ki wallahi da na bar ɗaukan kayan ki har abada, banza mara mutunci". Nusreen abin nema ya samu dan haka tace; "tab ashe yau zan naɗawa mata duka nice mara mutuncin", Nusram ta kai mata duka tace; "wai ke me yasa kina girma ne kina hauka matar auren zaki daka??", Yasmeen tace; "koma wacece", Nusram tace; "Dalla ku rufe mana baki ku wuce muje", sai da Nusreen ta doka mata harara sannan ta bi bayan ƴar uwar ta yayin da Yasmeen itama ta bita. Har suka fita bakin titi Nusram bata kula su ba, haka suka sami mota suka shiga, a Anguwar Mu'azu suka sauke Yasmeen sannan suka wuce. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 Surayya ta fito cikin shiri, jikin ta sanye da doguwar riga ƴar kanti wacce taji stones ƙanana masu kyau, rigar kalar light blue, ta ɗauki kwalliya sosai sannan duka komai to match ta saka. Cikin sauri ta sauko ƙasa, Mommy ta kalle ta sannan ta wulla mata harara tace; "kin raina ni ko? tun ɗazu muke zaman jiran ki". Surayya ta sunkuyar da kai ƙasa tace; "Mum kiyi haƙuri", Brr Farida ta ɗaga mata hannu tace; "ya isa haka, ku wuce muje". Sai da ta juya ta fara tafiya sannan na lura da kayan dake jikin ta, wata ƴar ubansun shadda ce me tsadar gaske, kalar blue dark, kanta kuwa head ne wanda aka mata ɗaurin steps gashi ya buɗe sosai wuyan ta kuwa murjani ta saka me tsada sosai, ƙaramin space ne sanye a fuskar ɗan ƙarami, jikin shaddar kuwa aikin hannu ne wanda ya fita sosai, mayafi ta yafa a kafaɗa kalar ruwan madara me haske haka takalmin dake ƙafar ta, agogon azurfa ne ke sanye a hannun ta fuskar ta kuwa tasha kwalliya ga wani annuri dake fita duk da irin girma da mulkin ta hakan be hana bayyanar farin cikin ta ba, wayar dake hannun ta take cillawa a hankali kuma kaɗan-kaɗan, cike take da nishaɗi da farin ciki. Gefen ta kuwa, Fahad ne dake sanye da riga ja da wando blue jeans sai takalmi cover shoe baƙi me kyau, fuskar shi sanye da ƙaton glass. Daga gefen daman ta kuwa Tameer ne shima sanye yake da ƙananan kaya irin na jikin Fahad ɗin wanda hakan ke nuna kenan anko suka yi, daga shi har Surayya fuskar nan tasu babu wani fara'a. Tafiya suka yi me tsayi kan su ƙaraso harabar gidan inda take cike da securities maza da mata kowannen su sanye da suit, suna zuwa aka buɗe musu manya-manyan motocin dake jere suka shiga kafin sauran securities ɗin suka shiga sauran motocin, a haka motocin suka fara ficewa daga gidan. *CANCANGI AIRLINE, KADUNA*, inda suka nufa kenan, koda suka isa wajen basu wani sha wuya ba domin kuwa ana ganin su ake kauche musu daga hanya dan kowa ya san familyn *NAGIMI* cikin Kaduna da kewaye balle kuma wannan da sun san ko wacece wato *Brr Farida Mus'ab Alƙali* ɗaya daga cikin member na *ALƘALI'S FAMILY*. Ƙasa-ƙasa Tameer yaja tsaki yana me kallon agogon dake ɗaure a hannun shi, kusan da ragowar minti goma sha biyar kafin jirgin nasu yayi landing, cike da jin haushi ya ɗago ya ƙara kallon wajen, kusan kowa idan yazo sai ya kalle su kasancewar burin jama'a kenan ganin wannan ishashshen familyn domin kuwa family ne guda biyu masu ji da kuɗi da izza da taƙama da mulki kowanne ba baya ba wajen iya mulki da kuma ƙasaita sai ya kasance sunyi autayya sun haihu aikuwa abin kallo naga wannan wa'inda jini biyu ya gauraye a jikin su. Ƙara jan tsaki yayi sannan ya kuma kallon jama'ar dake wajen wanda suka zubo musu idanu, maida kallon shi yayi kan Mummy wacce ke faman murna da farin ciki, cike da jin haushi yace; "ji yadda take murna sai kace Dad ne zai dawo", Surayya ta ɗago ta kalle shi fuska a ɗaure sannan ta nuna mishi hannun ta alamun lokaci. Ya ɗan tura kan shi inda Mum ɗin take yana mata nuni da tayi mata magana, zaro idanu tayi sannan ta girgiza kai, Mum ta juyo ta kalle ta hakan yasa dole suka ɗan yi yaƙe gudun kada ta zargi komai. Fuskar tace ta cika da farin ciki jin an fara sanarwa da isowar jirgin, ji take kamar ta ruga da gudu taje ta taro shi, Surayya da Tameer kuwa banda taɓe baki babu abinda suke yi. Haka mutanen suka fara fitowa ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, yayinda Brr Farida ta ƙara zuba idanu tana jiran ganin ta ina ɗan lelen nata zai ɓullo. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *ban san wane irin haƙuri zan baku ba, Kuyi haƙuri insha Allahu zamu shiga cikin novel ɗin sosai domin ina fatan komai ya dai-daita zaku dinga ganin shi kullum insha Allahu atleast sau huɗu a sati ko biyar, nagode* 📖📖7-8📖📖 Saukar mari kake ji tasss, kasancewar inda suke kamar hall haka wajen yake, inda aka ƙawata shi da jan labulaye, gashi kuma dare yayi sosai hakan yasa marin ya amsa a ko'ina. Cikin tsananin fushi da ɓacin rai yake kallon shi, shi kuwa ya saukar da kanshi ƙasa, Appu ya nuna shi cikin karaɗi da gargaɗi yace; "ka kiyayi fushin Oregbu idan ka bari ya fusata zai tsine maka ya kuma cire duk wata alfarma da yayi maka". kanshi a ƙasa yace; "ina neman afuwar Oregbu sannan kuma fatan hucewar zuciyar ka data Oregbu, nayi iya ƙoƙari na akan ganin na kawo shi nan amma wannan shegiyar matar ta hana gaba ɗaya taƙi bamu dama, amma yanzu tunda zai dawo ina ganin wannan wata damace a gare mu". Cikin tsananin fushi Appu yace; "baka iya yi mishi komai ba yana can shine zaka wani ce ya kusa dawowa idan ma ya dawo ba zaka iya ba", Tuge ya buɗe baki zai yi magana Appu ya dakatar dashi sannan yace; "a fara gabatar da kwankwale". Dole Tuge ya dakatar da maganar da yake so yayi ya koma baya, nan suka fara ɗaga hannaye suna wasu irin magan-ganu marasa kan gado, can wani jibgege ya shigo hakan yasa duka suka saukar da kan su ƙasa. Nan ya fara zuba sassan jikin mutane cikin madaidaicin plate ɗin yana miƙa musu, haka suka hau ci gwanin ban ƙyama da tashin zuciya, su kuwa babu ruwan su daka gani sun riga da sun saba. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 Cikin ƙasaita yake takowa, saurayi ɗan shekara ashirin da biyar kenan me jini a jika wanda yake da kyau da kwarjini ga kuma cikar zati da haiba. Dogo ne yana da haske dai-dai gwargwado yana da zubin ƙarfafa, jikin shi sanye da riga kalar Ash da wando jeans blue-black ƙafar shi yana sanye da takalmi cover shoe me ruwan ash, fuskar shi me ɗan faɗi wacce take cike da haiba da kwarjini, me ɗauke da ɗan mitsitsin bakin shi wanda ƙananan haƙoran sa farare tas ke ciki, ɗan sajen shi irin na samarin yanzu wanda yasha gyara shiya ƙara ƙawata fuskar shi, Hannun shi na dama ya ɗago wanda yake da hsske saman fatar cike da gargasa baƙa wacce ta kwanta sai agogon Rolex dake maƙale a hannun ya shafa sumar kanshi wacce take kwance luf baƙa wuluk daga gani tana samun kula ta musamman ya shaƙi iska yana lumshe idanun shi wa'inda suke dama can kamar a rufen domin dogayen lashes da Allah yayi mishi, murmushi ya saki wanda har sai da gefen kumatunshi dama da hagu suka lotsa, haka ƙananan haƙoran shi farare suka bayyana. Idanun shi ya buɗe a hankali sannan ya fara bin mutanen wajen da kallo a ƙoƙarin shi na gano ina abar ƙaunar shi take, wani ƙayataccen murmushin ya kuma saki sannan ya nufi inda take cikin sauri. Brr Farida kuwa daman kamar ta kwasa da gudu ta tari ɗan lelen nata haka take ji, cikin tsananin kewa da ƙaunar juna suka rungume juna suna masu tsananin murna. Tameer da Surayya suka taɓe baki suna juyar da kai cike da baƙin ciki, wanda su kuwa basu san ma suna yi ba. Brr Farida ta ɗago ta shafa fuskar shi tace; "Welcome back, son", murmushi ya saki sannan yayi peck ɗin ta a goshi. Hannun su sarƙe da juna suka juyo kowa ya kalle su sai sun birge shi ganin yadda kowanne ke ji da ƙasaita, Brr Farida ta kalli Tameer tace; "ka saka securities su ɗauko kayan", daga haka ta juya suka tafi. Tameer kuwa kamar ya ɗora hannu a kai ya ƙwala ihu haka yake ji, wannan wane irin masifa ce, idan banda yana shakkar mahaifiyar tashi da ba zai taɓa aikata abinda aka saka shi ba, cike da jin haushi ya fizgi akwatin da kuma ɗaya jakar kamar su suka bashi haushi. Kan ya ƙaraso har sun shiga mota hakan yasa ya ajiyewa securities kayan sannan ya buɗe motar ya shiga, su kan su securities ɗin sun fahimci akwai abinda yake damun shi dan haka suka kauce suka bashi hanya. Cikin sauri suka saka kayan duka sannan suka buɗe motocin su suka shiga don zuwa gida, a cikin motar da aka ɗauko shi kuwa, kan shi na saman kafaɗar mahaifiyar tashi, yayin da ita kuma take ta sakin murmushi cike da farin ciki. Surayya ta kalle su ta taɓe baki sannan tace; "barka da dawowa", kamar ba zai amsa ba tsayin daƙiƙa takwas sannan ya ɗaga mata kai ya maida idanun shi ya lumshe. Surayya kuwa wani baƙin ciki yazo mata wuya ya tokare idan da ace babu Mommy a wajen babu abinda zai saka ta kalle shi balle har magana ta haɗa su. Tsaki taja ƙasa-ƙasa gudun kada mahaifiyar tata taji tace; "mutum ba ɗan sarki ba ba kowa ba amma sai iya mulki da wulaƙanci", Tameer dake zaune kusa da ita yayi ƙwafa. Brr Farida ta maida kallon nata kan Tameer tace; "kai baka ga ɗan uwan naka bane?", shafa kai yayi yace; "Mum tsakanin nida shi waye gab......", cikin daka tsawa tace; "shut up my friend, ina tambayar ka kana tambaya ta", ya saukar da kai ƙasa sannan yace; "kiyi haƙuri", ya ɗan kalli Abdul ɗin da idanun shi ke rufe yace; "Barka da dawowa". Be buɗe idanu ba balle ya saka ran zai samu amsa sai dai ɗaga mishi hannu kawai yayi, Surayya duk da ɓacin ran da take ciki sai da abin yaso bata dariya, aikuwa ta hau tarin ƙarya dan ta san yadda Tameer ya kai matuƙa wajen ɓacin rai tana yin dariyar zai sauke akan ta. Tameer kuwa ya maida kallon shi kan Brr Farida yace; "Mum ki ganni yadda yayi mini fa? Amma baki ce komai ba", Brr Farida dake danna waya ta ɗago tace; "ya gaji ne ka bari idan ya huta zai maka magana ne ai", daga haka motar tayi shiru kuma aka cigaba da tafiya. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 *HAYIN RIGASA, KADUNA* Koda suka isa gida Nusram ƙin kula Nusreen tayi, har zuwa lokacin da suka shirya domin tafiya makarantar islamiyya. Ummi ma dai bata bi ta kan su ba, Nusram data fito daga wanka ta kalli Kubra tace; "Autar mu kina hutawar ki Ummi na ji dake", yarinyar ta ɓangale baki tana dariya. A ɗan fizge ta kalli Nusreen wacce keta faman kwalliya, jikin ta sanye da shadda kalar orange doguwar riga, Nusram ta taɓe baki sannan ta hau nata shirin. Kusan a tare suka gama sai dai kallon farko da Nusreen ta yiwa Nusram jikin ta yayi sanyi ganin ita sanye take da Atamfa me ruwan toka da ɗigon baƙi wanda ba haka sabon su yake ba, kasancewar Nusreen ɗin ke fara wanka dan tana daɗewa a shiri sannan duk kayan data saka yana nufin shi Nusram zata saka kenan, duk ranar data canza to tana fushi da ita kenan. Nusram nada haƙuri sosai da kau da kai sai dai akwai kafiya sannan idan tayi fushi tana jimawa bata sauka ba, yayinda Nusreen take sha yanzu magani yanzu amma fa da angama ya wuce kenan. Haka suka fito domin tafiya, Nusram ta buɗe jaka ta ɗauko sweet guda biyu ta miƙawa Kubra a hannu tana faɗin; "Ummi sai mun dawo", ta amsa tana bin yaran nata da kallo domin daga ganin banbancin kaya a jikin su ta san sun yi faɗa kenan. Suna fita tsakar gida Ameera tana wanke-wanken kayan da suka siyar na rana, Mama Jummai kuma na kusa da ɗakin ta a zaune da ɗaurin ƙirji tana faman lissafa kuɗi. Tana ganin sun fito tayi shewa tace; "kaga irin haihuwar da ake so ba irin wacce za'a dinga yawo kwararo-kwararo ba da sunan karatu dan an rasa mashinshini", yau dai tayi sa'a domin kuwa Nusreen ko kallon ta bata yi ba. Kamar kurame haka suka tafi har izuwa makarantar, basu yi latti ba hakan yasa kawai suka shiga aji, har aka tashi babu wanda yayi wa juna magana. Haka har suka iso gida, a ƙofar gida suka tarar da Baba a zaune a dakali yana jin labarai, suka mishi sannu da hutawa amma ko kallo basu ishe shi ba. Suna shiga suka tarar da Mama Jummai gaban murhu tana ta faman iza huta, gefen ta kuma Ameera ce take shirya jarkunan kunun aya dana zoɓo. "ba dole mutum kullum yayi ta baƙi ba, koda yaushe yana gaban murhu", faɗan Nusreen kenan, Mama Jummai ta wullo mata harara tace; "tunda jikin na Uban ki ne ba sai ki hana ni zama gaban murhun ba". "ai dama nashin ne sanin dai ne da ba'a yi saboda ba'aje makaranta bane an san haƙƙin miji", ta bata amsa ba tare da shakka ba. Mama Jummai ta ɗaga hannu ta nuna Ummi dake ƙofar ɗaki tana wanke shinkafa tace; "kin ga wacce bata yi makaranta ba kuma bata san haƙƙin miji ba", ta buɗe baki zata bata amsa Isa yayi sallama ya shigo. Ta kalle shi ta kauda kai sannan tace; "ai naga saboda tsabar sanin haƙƙin mijin ne yasa aka taho da ɗan gaban fatiha", tana ƙarasa ta zuba da gudu tayi ɗaki. Nusram data ɗauko tsintsiya domin share gidan ta girgiza kai kawai cike da takaici ta tsugunna ta cigaba da sharar ta, Isa kuwa cikin tsananin takaici yace; "shegiya ƴar isa ai da kin tsaya da yau sai na ɓalla ki a gida nan", cikin salon mugun ta ya sakarwa Nusram dundu a gadon baya wanda ta jishi har saman kanta. Ƴar ƙaramar ƙara ta saki sannan ta durƙushe a wajen, yaja tsaki ya fice ya bar maman shi tana zuba masifar ta a tsakar gida. Ummi bata ko ɗago kai ta kalle su ba, Nusram kuwa sai da tafi minti biyar sannan ta iya miƙewa ta cigaba da sharar ta tana yi tana share hawaye. Koda ta gama sharar sannan ta ɗaura alwala tana kallon Nusreen tana leƙowa domin tabbatar da fitar Isa, sallah ta tayar ta ƙyale ta. Bayan sun idar da sallah nan suka zauna har kiran isha sannan suka yi sallar, suna idarwa suka dawo falo suka zauna domin cin abinci. Kasancewar garin da zafi yasa Nusram ɗaukar tabarma ta shinfiɗa musu ƙofar ɗaki sannan suka fita duka. Suna cikin cin abinci Nusreen ta maida kallon ta zuwa ga Nusram tace; "wai Ram meye nayi miki ne da tun ɗazu kike share ni". Jin hakan yasa Nusram tsame hannun ta daga abincin tace; "Rim magana kike fa akan dukan matar aure, wallahi Rim bana son wannan halayyar taki, kiga fa yadda kika dinga ɗaga murya kina faman faɗa akan abinda be taka kara ba balle ya karya haba Nusreen kina girma kina cin ƙasa, ki sani ba ko da yaushe ba ake faɗan abinda kaga dama ba, kwata-kwata Nusreen baki da haƙuri gaba ɗaya kin lalata rayuwar ki da tsiwa". Nusreen tayi shiru tana sauraren ƴar uwar ta kamar da gaske, kafin tace; "tunda bakya so insha Allahu zan dena", Nusram ta saki murmushi tace; "yauwa ko kefa", haka suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa, Ummi kuwa murmushi kawai take yi domin taji abinda ƴar tata ta faɗawa ƴar uwar ta kuma hakan ya birge ta. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 *UNGUWAR RIMI, KADUNA*. Shureim ne kwance saman sofa wacce take ɗakin shi, idanun shi a lumshe babu abinda yake dawo mishi banda magan-ganun yarinyar yadda take juya idanu da yadda take tsiwar tata. Ya saki murmushi a karo na babu adadi, ya ƙara gyara kwanciyar shi cike yake da muradin ƙara ganin ta, sai dai yana shakkar yadda zata tarbe shi dan da gani yarinyar babu raini a tattare da ita. Abokin shi Naufal ya ƙaraso ya zauna kusa dashi sannan ya bubbugi gefen sofa ɗin, cikin sauri Shureim ya buɗe idanun shi sannan ya kalli abokin shi yace; "ya akayi ne kake tashin mutane suna barci?". Naufal yayi murmushi yace; "ka dena magana irin haka mana, bafa barci kake ba idanun ka biyu don yadda kake murmushi wallahi yadda ka san sabon bazawari", tare suka hau dariya. Sai da suka tsagaita sannan Shureim yace; "tsiwa ta", Naufal yayi tagumi yace; "yau kuma me tsiwar taka tayi?, kun kuma haɗuwa ne?", Shureim ya girgiza kai yace; "ina fa sai dai yau ina so ka shirya muje binciken gidan su na gaji wallahi". Naufal ya ɗan haɗe fuska yace; "gaskiya ka bari ba yau ba dan nima ina da wajen zuwa", Shureim ya miƙe zaune yace; "lallai Naufal ni kake faɗawa haka ko saboda na gama yi maka amfani amma kada ka manta lokacin da kake neman auren Futuha na tsaya maka sosai". Naufal ya girgiza kai yace; "gaskiya ka san Futuha tana da kishi sosai wallahi taji zan raka ka taɗi to abin ba zai ƙare mini da kyau ba". Shureim yace; "banza matsoraci dan Allah wallahi ba zan bari mu daɗe ba", Naufal ya saukar da numfashi yace; "shikenan angon tsiwa", suka sake yin dariya. Shureim yace; "yadda Mamie ta ƙosa nayi aure ne shiyasa bana so ta dawo ta samu magana ba tayi nisa a tsakanin mu ba, na kuma san zata ji daɗi". Naufal yace; "ni ba wannan ba kada fa taje tayi ta mana tsiwa ne", Shureim yayi murmushi yace; "ai wallahi abinda nafi so tayi kenan", haka firar tasu ta cigaba cike da annashuwa. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 *UNGUWAR SARKI, KADUNA*. motar na yin parking Sumayya ta kwaso da gudu, shima cikin farin ciki ya buɗe mata hannu ta faɗa jikin shi tana faɗin; "Oyoyo Yaya na". Ya riƙo hannun ta sannan yace; "fatan na same ku lafiya", cikin fara'a tace; "lafiya lau sai dai kewar ka da muka yi kawai". Haka ya riƙe hannun ta suka shige cikin gidan, Fahad na zaune yana kallon cartoon ganin shigowar su yasa ya miƙe ya nufi inda suke. Abdul ya tsugunna dai-dai tsayin shi yace; "little angel ya school", Fahad yace; "lafiya lau Yaya", Abdul yayi murmushi fahad ya ɗora hannun shi dai dai dimple ɗin shi yace; "Yaya na daina ganin wannan". Ɗauke shi yayi cak ya ɗaga sama yace; "to ai yanzu na dawo zaka cigaba da gani", Brr Farida tace; "yanzu kaje ka huta anjima sai kazo kaci abinci". Cikin shagwaɓa yace; "gaskiya ba zan iya haƙuri da cin abincin ki ba First love har sai anjima", Sumayya tace; "Yaya kamar ka san yayi daɗi kuwa". Ya kama hannun Sumayya suka nufi dinning tana zuba mishi surutu shi kuma yana murmushi bayan shi kuma Brr Farida ce ita da Adnan. Sai lokacin na juya na kalli falon babu kowa alamu ya nuna Surayya da Tameer sun bar falon kenan🤔. Brr Farida da kanta tayi serving ɗin shi, haka ya dinga ci yana santi su kuma suna dariya, sai da ya gama sannan Brr Farida ta bari su Sumayya suka ci. Shi dai yana gamawa ya miƙe ya nufi part ɗin shi domin hutawa, a hanya suka haɗu da Surayya, ta kalle shi ya kalle ta, cike da takaici ta nufi part ɗin su Sameer. Ya taɓe baki yana me shigewa nashi part ɗin, lumshe idanu yayi jin irin ƙamshin dake tashi a ɗakin ya san aikin mahaifiyar shi ne shi yasa yake matuƙar ƙaunar ta. Sai da yayi wanka sannan ya saka singlet da three quater ya kwanta, be wani jima ba barci ya ɗauke shi. #LIKE #SHARE #COMMENT *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖9-10📖📖 Surayya cikin kuka ta shiga falon, Sameer dake kwance saman kujera ya tashi da sauri, wajen shi ta nufa tana zuwa ta faɗa jikin shi tana sakin kuka. "wai meya faru ne?", ya tambaya, cikin sheshsheƙar kuka tace; "Yaya wallahi na kusa haɗiyar zuciya na mutu saboda baƙin cikin Yah Abdul da Mummy". Cikin sauri Sameer ya miƙe yace; "wai me yasa kuke haka ne komai Abdul! Abdul!! Haba ya kamata ace kun canza wata maganar ok mutuwa zaki yi to kuwa sai ki shirya mutuwar domin kuwa Mummy ba zata taɓa dena son Abdul ba dan wannan kam daga Allah ne", yana gama faɗin haka ya kwashi wayoyin shi yayi waje. Part ɗin Brr Farida ya nufa yana tafe yana tunani; "tabbas abinda ƴan uwan shi suke complain shima yana damun shi sai dai kuma shi ba zai yi wauta irin tasu ba". Yana daf da shiga itama tana fitowa, jikin ta sanye da doguwar riga baƙa ƙirar Saudia, tayi rolling da gyale kalar peach, hannun ta riƙe da wani ƙaton littafi kamar diary. Da sauri ya ƙarasa wajen ta yace; "sorry Mummy banzo yiwa ɗan lelen ki sannu da zuwa ba barci ne ya kwashe ni". Ba tare da komai ba tace; "kada ka damu amma gaskiya banji daɗi ba", ya kwantar da kanshi saman kafaɗar ta yace; "sorry Mum", ta shafa kanshi tana faɗin; "ya wuce ai bari nayi sauri na tafi zan kaiwa Brr Isma'il wannan documents ɗin ne yanzu", ya kamo hannun ta yace; "muje na raka ki bakin get", babu musu yaja hannun ta suka tafi. Suna tafe suna fira har suka iso bakin get ɗin, Securities cikin sauri suka buɗe mata ƙofa domin ta shiga, Brr Farida kuwa lokacin da ta saka ƙafa domin shiga cikin motar gaban ta ya yanke ya faɗi, cikin sauri ta juya ta kalli hanyar part ɗin shi. Sameer yace; "Mummy lafiya kuwa?", da sauri tace; "Sameer Abdul", cike da takaici amma ya danne yace; "Mummy me zai same shi kuwa? Kawai ki tafi kada ki ɓata lokacin ki". Ta kalle shi sannan ta girgiza kai tace; "bari dai naje na dubo shi na dawo", da sauri Sameer ya riƙo hannun ta yace; "kije Mum zan je na binciko shi I promise you", bata saurare shi ba ta nufi hanyar part ɗin nashi. Shi kuwa da yake barci wanda yake cike da mafarkai marasa daɗin gani, wai gashi a ƙulle jikin wata ƙatuwar tukunya ƙasa kuma wuta ke ci ga wasu mutane dake sanye da jajayen kaya babu abinda suke kira sai *Murad*. So suke su riƙe shi amma wutar taƙi ta basu dama, a duk lokacin da suka kawo hannu domin riƙe shi sai wutar tayo sama kaman zata taɓa su, wanda shi kuma yo saman da wutar take ba ƙaramin ƙona shi take ba. A dai-dai wannan lokacin kuwa Appu ne gaban ƙatuwar ƙwaryar tsafin su, wacce take cike da jini da kuma wasu irin ganyayyaki kalar ja da shuɗi. Sunan *Murad* yake ƙwala kira cikin ƙaraji da kuwwa, tar fuskar Abdul ta fito cikin wannan ƙwaryar yana kwance yana barci. Wata mahaukaciyar dariya yayi sannan ya kira Tuge akan yazo ya gani, cikin sauri ya matso gaban katuwar ƙwaryar, tabbas shine wanda suke nema ruwa a jallo amma ƙaƙababbiyar matar nan ta hana taƙi basu dama su nufe shi da sharri. Wani magani Appu ya ɗauko me kalar baƙi ya fara wasu surutai yana watsawa cikin ruwan, ya jima yana watsawa sannan ya cigaba da ƙwala mishi kira, a cikin ruwan ya buɗe idanu sannan ya fara yunƙurin tasowa zuwa gare su. Sosai duka wajen suke murna ganin aikin su na tsayin shekaru ashirin da biyar zai cika, ta ruwan Appu yake ƙoƙarin janyo shi. Sai dai shigowar Brr Farida yasa wajen ya dauki wata irin ƙara Ƙwaryar kuma ta kama da wuta wanda yayi sanadiyar matsawar su baya cike da tashin hankali gudun kada fuskokin su su ƙone. Brr Farida kuwa ganin yadda Abdul ke haɗa zufa ga wata irin jijjiga da yake yi yasa tayi saurin jijjiga shi tana kiran sunan shi cike da tashin hankali. A matuƙar razane ya buɗe idanun shi wa'inda tsabar masifa da tashin hankali suka canza kala da grey colour suka koma ja da yellow-yellow a haɗe, cikin matukar tsoro da tashin hankali ya faɗa jikin ta ya rungume yana sakin ajiyar zuciya. Ta fara shafa bayan shi tana karanto addu'o'i tana tofa mishi, tun jikin shi na rawa har ya dena a hankali kuma ya numfashin shi ya fara dai-dai ta. Sai da nutsuwar shi ya dawo sannan ya zame daga jikin ta ya kwanta saman gadon, Brr Farida kuwa ganin hakan yasa tace; "ai dama na faɗa maka indai ba zaka dena kwanciya barci baka yi addu'a ba hakan ba zai dena faruwa da kai ba, yanzu da ban shigo ba fa? Abdul ka dinga addu'a amma abu ya gagara". Ya juyo ya riƙe hannun ta sannan yace; "First love kiyi haƙuri barcin ne yazo mini ban shirya ba, amma ba zan kuma ba", tayi peck ɗin shi a goshi tace; "yauwa Baby na, kada ka kuma kaji". Ya ɗaga kai kawai, sai da ta kuma yi mishi addu'ar tsari da kariya sannan tace; "ka cigaba da barcin ka yanzu zanje na kaiwa Brr Isma'il wannan takardun na dawo". Cikin sauri ya miƙe yace; "First love bari na shirya mu tafi tare", yana gama faɗin haka ya shige bayi domin wanka, be jima sosai ba ya fito inda ya samu har Brr Farida ta fito mishi da kayan da zai saka. Haka ya shirya cikin riga peach da kuma baƙin wando, takalmi ya zura ya fito yana ƙoƙarin ɗaura agogon hannun shi. Brr Farida dake tsaye tana kallon shi, gaban ta sai da ya faɗi ganin irin kyawun da yayi gashi yana tsananin kama da mahaifin shi. Ya hura mata iska a ido, ta lumshe idanun sannan tace; "kayi kyau ɗana", ya riƙo hannun ta yace; "duk kyau na ai ban kai ki ba", haka suka jera gwanin ban sha'awa har waje. Sai da ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan ya zagaya securities suka buɗe mishi shima ya shiga ya zauna, cikin natsuwa driver ɗin yaja motar sauran motocin suka rufa musu baya. *FEDERAL HIGH COURT, KADUNA* bakin wajen Brr Farida suka yi parking, ta kalli Abdul da idanun shi ke ƙasa tace; "Baby ka jira ni bari na shiga na fito yanzu", kamar wani ƙaramin yaro haka ya maƙe kafaɗa, Brr Farida ta saki murmushi sannan suka fito duka, hannun su sarƙe dana juna suka nufi ciki. A wani office suka sami Brr Isma'il ɗin yana zaune yana rubuce-rubuce, ta miƙa mishi documents ɗin sannan suka fito. Sun ɗauki hanyar komawa gida Abdul ya kalli mahaifiyar shi yace; "First love in tambaye ki, wai waye *Murad*?". Cak ta dakatar da tapping ɗin laptop ɗin da take yi tana zuba mishi idanu na tsayin minti biyu, har gaban shi ya fara faɗuwa, "a ina kaji wannan sunan?". Abdul ya sunkuyar da kai yace; "mafarkin da nayi ne ɗaz....", tayi saurin dakatar dashi tace; "ya isa haka Abdul mafarki ne kawai kuma mafarki shirme ne". Daga haka ta ɗauki waya tana dialing number ɗin mijin ta wato *DR ABUBAKAR YUNUSA NAGIMI*, tace; "Daddyn ku yace baka kira shi kace ka sauka lafiya ba". Ya shafa kai yana faɗin; "ganin ki ya mantar dani shi", ta saki murmushi sannan ta kara wayar a kunnen ta, tana faɗin; "Assalamu alaykum hasken ruhina farin cikin Farida angon brr", a tare suka yi dariya yayin da Abdul ya kauda kan shi yana sakin murmushi, soyayyar mahaifiyar shi da mahaifin shi tana matuƙar birge shi sosai sam basa gajiya da juna sannan babu ruwan su da yaran su kullum cikin bege da ƙaunar juna suke. Miƙo mishi wayar da tayi shiya katse tunanin da ya tafi, sai da yayi ɗan jim sannan ya amsa, cikin ladabi ya gaishe dashi, shi kuma ya amsa cike da so da kulawa. "na san Mummyn ka tana ƙoƙari da kai sosai, babu wata matsala ko?", kamar yana gaban shi sai da ya ɗaga kai sannan yace; "eh babu", Dr yace; "to masha Allahu na yi muku order ɗin motocin ku kai da ƴan uwan ku nan da next week zasu iso". "Daddy yaushe zaka dawo?", tambayar daya jefa mishi kenan, sai da yayi shiru sannan yace; "nan da lokaci kaɗan Insha Allah, kaje Hayin Rigasa?", shima ya jefa mishi tambayar. " a'a, amma insha Allah zan je zuwa gobe", ya bashi amsa,Dr yayi murmushi yace; "to Allah ya kaimu, ka ƙara kulawa kaji", yace; "to", haka suka yi sallama sannan ya miƙawa Mummyn shi wayar wacce ta zuba mishi idanu. Kauda kai yayi yana sakin murmushi, can ya kuma ɗagowa idanun nata yana kanshi, ya kwaɓe fuska yace; "First love, me kuma nayi?". "ina zakaje kake faɗawa Daddyn ku nan da gobe?", ta tambaye shi, ya riƙo hannun ta sannan yace; "Mum muna magana ne akan zuwa na Hayin Rigasa", kauda kai tayi kamar bata ji me yake cewa ba shima kuma yayi murmushi ya kwantar da kanshi saman kujera. Be san meke tsakanin Mummyn shi da dangin mahaifin nashi ba sai dai ya lura basa wata mu'amala sosai, shine ma me ƙoƙarin zuwa amma sauran basa zuwa sosai kuma itama bata tilasta musu suje kuma shima Daddy haka be wani damu da suje ba sai dai abinda ke bashi mamaki yadda Daddyn ke tilasta mishi shi yaje duk da Mummy bata so, to shi kanshi yaje sai ran shi ya ɓace wani lokacin sai dai duk da haka yana ƙaunar gidan. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 *HAYIN RIGASA, KADUNA.* Shureim ya kalli Naufal yace; "yauwa kaga wa'incan masu hijab ɗin ruwan toka to ɗaya daga cikin su ce, sannan suna wucewa zamu bisu a baya", Naufal dake ƙunshe dariya ya ɗaga kai duk da suna daga nesa ba zai gane yanayin su ba. Idanu ya zuba musu har suka matso, duka kyawawa ne, masu haske sannan marasa ƙiba sosai, suna da idanu manya wa'inda suke farare hanci su dogo ne sai bakin su daya kasance ɗan madai-daici duka suna sanye da hijab me ruwan toka wanda ya ƙara fito da ainihin kyawun su, sannan kuma daga gani shine Uniform ɗin islamiyar tasu. Ɗayar ya kalla, yadda take buɗe ƙananan haƙoran ta farare tas take faman zuba magana yayin da ɗayar ke sakin murmushi inda gefen kumatun ta ke lotsawa duka biyu tana kuma lumshe idanu da har yadda zarazaran gashin idanun ta ke rufe idanun ruf. Iya kallo na ƙurilla yayi musu amma ya kasa gane makusar su sannan kuma ya kasa banbance su, duka kamar su ɗaya baya jin ko mahaifiyar su zata iya banbance su, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya maida kallon shi kan abokin nashi wanda shima su ya zubawa idanu yana kallo. " to anan waccece tsiwar taka?", ya jefa mishi tambaya, Shureim yayi murmushi yace; "kaima daga gani ai ya kama ta ka bambamce mana, kalle su da kyau ka gani ƙwaƙwalwar ka ta hasaso maka", ya ƙarasa yana kai duba gare su tare da sakin murmushi kamar wani ɗan can haka 🙄. Naufal ya ƙara kallon su, izuwa yanzu kuwa sun matso sosai kusa dashi kuma yana iya ganin su tarr da suna daf da gifta su, shi dai har yanzu ba zai banbance su ba domin kuwa ko agogon dake maƙale a hannun su me ruwan toka kala ɗaya ne haka zobe dake yatsun su na hannun hagu, sannan atamfar da suka saka me Blue da light yellow duka kala ɗaya ne haka flat ɗin takalmin dake ƙafar su shima kala ɗaya ne wanda ya kasance blue. Shi dai bashi da wani abu da zai bambamce su, ya maida kallon shi kan abokin nashi daya zuba musu idanu kamar zai cinye abin ban dariyar shine yana ganin sun yi murmushi shima zai, Naufal ya kalle shi ya kuma kalle su ya kwashe da dariya yana faɗin; "Allah Shureim kana daf da ka zare", Shureim ya kwaɗa mishi harara yace; "so kenan ake faɗa maka malam". Naufal ya kuma juyawa ya kalle su dan har sun gifta su yace; "nifa bana jin ko mahaifiyar su zata banbance su", Shureim dake tada motar yace; "me zai hana ta bambamce su tunda ita tayi naƙudar su ko kai kayi mata?", ya girgiza kai yana taɓe baki. Bin su suka yi a baya har zuwa lungun da gidan nasu yake,daga bakin lungun suka yi parking sannan suka fito suna kallon gidan da suka shiga, gida na uku a cikin jerin gidajen dake lungun. Nusreen da Nusram kuwa suna shiga gida suka tarar da Sahura da uban jibgin kaya a gaba sai kuka take sha, Mama Jummai kuma na gefe tana kallon ta. Nusram tace; "sannun ku da gida Mama", Mama Jummai tace; "yauwa sannu", sosai hakan ya basu mamaki saboda zagi ne ke biyo baya amma yau ta amsa jiki a sanyaye. Nusram ta kai dubanta ga ƴar uwar ta tace; "lafiya kuwa ke kuma?", Mama Jumman ta taɓe baki tace; "ina fa lafiya Nusram Nura ne ya sake ta saki ɗaya mahaifiyar shi tace idan be sake ta Allah ya isa shine ya sako ta". Sosai Nusram ta tsorata, ta tsugunna kusa da Sahurar tana bata haƙuri, Sahura dake zubar da hawaye ta galla mata harara tana jan tsaki. Nusreen haushi ya cika ta itama kuwa ta ja tsaki tace; "ai ga shi nan garin neman gindin zama kin jawa kanki raini a wajen ƙanwar ƙanwar ki, dama ai duk abinda mutum ya shuka shi zai girba kuma taya zaka kasance mowa a gidan mijin ka ƴaƴan ka ma kace dole sai sun zama wannan ƙaryane yadda kake gasa ƴaƴan wasu haka za'a gasa naka". Mama Jummai ta miƙe tana wuci tace; "wallahi ki fita hanya ta Shegiyar ƴar Allah bani", Nusreen tayi shewa tace; "ga ƴaƴan Allah bani nan ana korowa gidan Mama, ai duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba nashi ko ɗumi ba zata yi ba". Mama jummai cikin hayagaga tace; "ai gwara su an shaida dan har aure sun yi kufa babu wacce keda mashinshini,ai ko yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli yaci riba", ta ƙarasa tana cewa. "ai da aure irin na ƴaƴan ki wallahi gwara na zauna har abada babu aure, auren jeka nayi ka ita kanta wannan ɗin da take kamar muciya saki biyu ke akanta, waccan kamar turmin( Sakeena🤣) saki ɗaya ƴar baƙa ma(😂 Habiba) itama saki ɗaya gaskiya ki canza boka wannan inaji batirin shi yayi sanyi😮. Ba Mama jummai ba har Ummi dake ƙofar ɗaki tana girki sai da ta ɗago ta kalli yarinyar tata balle Nusram da har kusa faɗuwa sai da tayi, duka kallon Nusreen ɗin suke yi ita kuma ta maze kamar babu abinda tayi. Sahura ta taso cikin rashin kunya tace; "malama ya ishe ki haka, ai naga aiki da bokan ba ita kaɗai ta fara ba wata ma abinda take yi kenan, banza wacce taƙi auruwa". Mari ta kai mata da sauri Nusram ta tare tace; "kada ki fara ai ke kika janyo ma kanki", Nusreen ta gallawa Nusram harara tace; "ai wallahi sai na mare ta, sai na nuna mata niba sa'ar yin ta bace sa'ar yin uwar ta ce". Sahurar itama cikin haki da masifa tace; "kamar yadda nake ba sa'ar yin ki ba sa'ar yin taki Uwar ce ba", ai kuwa tana rufe baki Nusreen na sauke mata tafi a fuska. Jijjiga ta tayi ta wullar ƙasa ta hau kai ta fara duka, Nusram kuwa ta tsaya tana kallon ikon Allah, Mama Jummai ta ɗauki roba ta fara ƙwalawa Nusreen ɗin tana faɗin; "au baƙin ciki yasa zaki kashe mini ƴa ne?",. Ummi ta kalli Nusram tace; "zo ki wuce ciki", babu musu ta ƙyale su ta wuce ta ɗauki buta domin yin sallar magrib, Nusreen kuwa sai da ta gama kirɓar Sahurar sannan ta ɗaga ta dan kanta tayi ɗaki. Mama Jumman ta dinga jero mata zagi, yayin da Sahura ke zabga ihu domin ta daku sosai, haka taja jikin ta tayi ɗaki domin dai ta jibgu sosai da sosai. Nusreen na idar da sallah ta kalli ƴar uwar ta, Nusram taja tsaki tana miƙewa ta bar wajen, Nusreen tayi murmushi tana shafa fuska ta san cewa sai da ta ƙara yin ladabi kafin su shirya da ƴar uwar tata. Ta kalli Ummi, Ummi kuwa ta zuba mata harara hakan yasa ta saukar da kai tace; "Ummi kiyi haƙuri", shiru ne ya biyo baya domin sallamar wani yaro. Mama Jummai dake waje ita ta amsa tana faɗin ya akayi me zaka siya?", yace; "yan biyu aka ce na kira", Mama Jummai taja tsaki cike da takaici da kuma mamaki wanda ya bayyana ƙarara a kan fuskar ta. Nusram dake yanka latas ta ɗago ta saci kallon ƴar uwar tata, ita kuwa Nusreen dama neman hanyar yiwa ƴar uwar tata magana take dan haka tace; "Ram baki ji ba ana kiran ki". Nusram ta juyar da kai tace; "kada Allah yasa ki tashi kije ki zauna neman magana har Baba ya dawo kinga koda ace kuturu ne ya nemi ɗaura muku aure", ai kan ta ƙarasa ta miƙe ɗauki hijab ɗin ta. Koda ta fita Mama Jummai ce kawai a waje hakan yasa tayi waje kawai, Mama Jumman tace; "Allah yasa gurgu ne", Nusreen ta saki dariya tana ƙarasa ficewa. Suna tsaye suna kallon ƙofar gidan, kallon su take ƙasa zuwa sama, ita dai ba zata tuna kosu waye ba domin bata san su ba, amma kuma daga ganin su kaga wa'inda hutu ya samu waje ya zauna a jikin su. Suna sanye da shadda bugaggiya kalar ruwan madara wacce tasha aikin wuta sosai a jiki, ɗayan kan shi da hula ɗayan kuma babu hula, duka har agogon su kala ɗaya ne haka takalmin su. Ɗaya baƙi ne ɗayan kuma yana da haske kuma yana da ƴar ƙiba kaɗan yayin da ɗayan yake dogo, dogon baƙin wanda ya zuba mata idanu itama haka ta zuba mishi idanu. A hankali ta fara takowa zuwa wajen su, Shureim kuwa ji yake kamar ya ɗauke ta su gudu tsabar son da yake mata, Nusreen kuwa sai da ta matso kusa dasu sannan ta gane shi. Wani irin ɗaure fuska tayi tana mishi kallon uku saura kwata, tana sakin musu harara ganin yadda ya raina mata wayo wato har ma ƙofar gidan su yazo kenan?, da alamu sai ta nuna mishi ita ba sa'ar shi bace. " marin kazo nayi maka ko kuwa waccan wankin dana yi maka yayi kaɗan ne? Ko dai kazo ƙara zuba mini datti ne? Ko ƴan sanda ka kwaso mini? Ko kazo ganin ni ƴar wacece?", duka ta jero mishi tambayar idanun ta na kanshi. Shureim da Naufal suka kalli juna cike da mamaki, Naufal kam da ƙyar ya iya riƙe dariyar dake cin shi ganin yadda abokin nashi ke zare idanu, gashi ita kuma ta ɗaure fuska yadda kasan uwa ta titsiye ɗan ta yayi mata laifi, shi kuma sai zare idanu yake kamar yayi wa sarki ƙarya. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖11-12📖📖 Tsit wajen yayi Shureim dai kallon ta kawai yake yi cike da birgewa yayin da gaban shi ke dukan uku, Nusreen ta kuma balla mishi harara tace; "baka da baki ne?". Cikin sauri Shureim ya girgiza kai yace; "abinda ya kawo ni daban". "me kenan? Ko kana bina bashi ne?", ta ƙara jefo mishi tambaya, wacce tasa Naufal ya kasa riƙe dariyar shi. Ta juya ta kalle shi ta taɓe baki tace; "kai kuma ka sami taɓin hankali ne, ko kuwa sabon wulaƙanci ne da kuka samo ku ƴaƴan masu kuɗi", Naufal ya kauda kai yana mamakin ƙarfin halin yarinyar da kwata-kwata ta hana su maganar. "ya wani je ya kwaso ka, kai kuma ka wani biyo shi dunƙul-dunƙul, to ko zaka tare mishi, wai yanzu zamani yazo da rashin mutunci ma har ƙofar gidan ku ake zuwa ayi maka, to wallahi ku tattara komatsen ku kubar nan kafin nasa ayi muku rashin mutunci na ƙarshe wanda ko hanyar nan ba zaku kuma kallo ba", tana gama faɗar haka ta shige gida ta bar su a tsaye. Shureim ya dafe kai da sauri, shi kuwa Naufal banda dariya babu abinda yake yi, lallai wannan yarinyar ta wuce yadda yake tunani, cikin masifa Shureim ya kalle shi yace; "nifa ba na kira ka nan bane ka ƙara mini matsala, matsala ta nazo ka warware mini amma ji yadda kazo ka lalata komai", Naufal ya kuma tuntsirewa da dariya. Shureim kamar zai yi kuka yace; "na gode da irin sakamakon da kayi mini", nan ya shige motar ya barshi, shima Naufal ɗin haka ya gaji ya shigo sannan yaja suka bar unguwar. Nusreen na shiga gida ta nemi waje kusa da Nusram ta zauna, Nusram dake cin abinci ta kalle ta, ta kauda kai. Nusreen ta janye abincin dake gaban Nusram din ta hau ci, Nusram kuwa bata ce mata komai ba sai tashi da tayi ta wanko hannun ta. Ummi ta dube ta tace; "wai waye yazo ne?", Nusreen ta taɓe baki tace; "nima ban san shi ba wai ashe kwatancen da akayi mishi ne ba dai-dai ba", Ummi ta bita da kallon tuhuma, ita kuma ta fuske tana me cigaba da cin abincin ta. Tana gama cin abincin Baban su yayi sallama ya shigo, duka suka amsa mishi, ɗakin Mama Jummai ya nufa suma kuma basu wani damu ba. Ita kuwa sai dai tayi wata ƴar shewa sannan ta bishi ɗakin nata, Nusreen ta taɓe baki tana jan tsaki. Ummi ta dube su tace; "tashi ku shiga daga ciki aje a kwanta", babu wanda ya musa haka suka tashi suka shige cikin ɗakin. Sun kwanta babu jimawa Baban yayi kiran Nusreen, ta amsa tana ƙunƙunai, "shi baban nan ya iya kiran mutane idan tashi ce ta haɗo ku amma hakan nan ba zai tsaya yaji matsalar ku ba", haka ta fice tana mita, ita kuwa Nusram tana jin ta murmushi tayi tana me yiwa ƴar uwar tata fatan shiriya. Baban ya kalle ta yace; "ance wani yazo wajen ki", ta ɗago ta kalli Baban sannan ta juya ta kalli wacce ke bayan shi Mama Jummai, ta ɗan ja tsaki ƙasa-ƙasa tace; "nifa wallahi gulma ce bana so". Baba yace; "me kika ce?", ta girgiza kai tana faɗin; "babu komai, ni babu wanda yazo waje na". Mama Jummai ta sako baki tace; "waye zai miki ƙarya, ina zaune aka aiko kiran naki zaki ce babu wanda yazo ko dadiron naki ne, yara basu son aure sun fi so su zauna suyi ta iskancin su a gidan uban su". Baba ya ɗaga mata hannu sannan yace; "ya isa haka! Kince babu wanda yazo ko?", Nusreen ta ɗaga kai, yace; "tashi kije zan saka a bincika mini idan na samu akasin abinda kika faɗa sai na ɓata ranki kuma, tashi ki bani waje". Babu musu ta miƙe kamar mutuniyar arziƙi tayi ɗakin su, Mama Jummai baƙin ciki ya ishe ta hakan yasa ta tashi fuu tayi nata ɗakin. Baban ya kalli Sahura yace; "ke kuma sai ki faɗa mini lafiya kika dawo gida", cikin sauri tace; "Baba Nura ya sake ni", sai da Baba ya zage Nuran tas sannan yace ta tashi taje zai nemi nuran. Nusreen na shiga ɗaki ta tuntsire da dariya, jin hakan yasa hankalin Nusram ɗin kwantawa don tayi tunanin ko wani abu ne ya faru. Nusreen ta zauna gefen katifar su tace; "Ram kinji Mama Jummai da gulma wai har ta kaiwa Baba gulmar wani yazo nema na?", Nusram ta juya kwanciyar ta tana ƙara runtse idanu. Nusreen taja tsaki tace; "dama na san ba zaki kula ni ba tunda yanzu kin dena ƴar uwar dani", har lokacin Nusram bata motsa ba hakan yasa Nusreen ɗin taɓa ta tace; "Ram ki tashi kiji me nake cewa mana". Ta turo baki tace; "ai dai nace kiyi haƙuri ba zan kuma ba", saura kadan Nusram da Ummi su kwashe da dariya amma suka dake, Nusram ta tashi ta zauna sannan tace; "Nusreen kin cika ladabin ƴan Jos 🙄 ne, yanzu zaki tuba anjima ki sake komawa ki aikata kalar wannan aikin, wannan ba hali bane me kyau". Nusreen tace; "kiyi haƙuri na dena", Nusram ta girgiza kai tace; "ai wannan abin da kike shine ladabin ƴan Jos ɗin, ba dai kince kin dena ba to gobe ma kuma yi zaki yi nafa san halin ki". Nusreen ta riƙo hannun ƴar uwar ta tace; "Nusram tunda nace na dena na dena ne ba zan kuma ba ki yarda dani", Nusram tace; "shikenan zamu gani idan da gaske ne, ni nafi so ki fahimci wani abu Mama mahaifiya take a wajen mu dan tana auren mahaifin mu atleast u deserves our respect, amma ke bakya ganewa yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba sannan ki sani babu alkhairi a barin wa ƴaƴan ka tarihi ko tabon rashin kunya, ki fahimta wasu abubuwan kauda kai ake yi kada ki manta daba dan haƙurin manzon mu ba da yanzu addinin musulunci be kawo mana ba amma da yayi haƙuri fa ba gashi yayi nasara ba, wallahi haƙuri akwai nasara da dacewa a cikin shi ba komai ake maka kace sai ka rama ba ki dinga sanyawa zuciyar ki haƙuri da salama mana ko zaki dace wajen koyo da ma'aiki". Kamar da gaske Nusreen tayi shiru tana saurara d most funny part ɗin ma yadda ta maida fuskar ta kai kace da gaske maganar na shigar ta, cikin sanyin murya tace; "nayi nadama sosai ƴar uwata kuma insha Allahu zan yi koyi da Annabin mu(SAW), nasan kina ƙauna ta shi yasa kike faɗa mini gaskiya na gode sosai". Nusram tace; "yauwa ƴar ƙanwa ta yanzu mu kwanta ko sai da safe", babu musu Nusreen ta zame ta kwanta, Ummi ta girgiza kai tana me yin murmushi. Sau nawa ana yin irin hakan amma babu abinda ya canza yanzun ma bata jin zata canza zani. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 *UNGUWAR SARKI, KADUNA*. Brr Farida dake zaune ta zuba tagumi tana kallon gefen ɗaya wanda alamu ya nuna cikin damuwa take, gefen ta Surayya ce ke danna waya sai Adnan dake game a tab dake hannun shi. Wani irin ƙamshi ne ya ziyarci falon kafin ya sako kai ciki bakin shi ɗauke da sallama, cikin sauri Brr Farida ta ɗago tana kallon shi. Riga ce a jikin shi kalar Blue sai wando fari, sosai kayan suka yi mishi kyau, dan duk kayan da zai saka to suna amsar shi sosai, Surayya kallo ɗaya tayi mishi ta kauda kai, Adnan kuwa wajen shi ya nufa da gudu. Abdul ya riƙo hannun shi yace: "yauwa boy", Adnan yayi dariya sannan yace; "Ya Abdul zaka je dani wajen Farha?", Abdul yayi murmushi har kumatun shi ya lotsa sannan yace; "me zai hana kuwa?", Brr Farida ta ɗaure fuska tana me kallon gefe. Kusa da ita yazo ya tsaya, ta juyo ta kalle shi yana rataye da ƙamar jaka wacce ya zuba kayan amfanin shi a ciki, fuskar ta ɗauke da damuwa tace; "fatan ba zaka jima ba a can ko?". Riƙo hannun ta yayi yace; "eh bana jin zan wuce sati ɗaya", wani kallo ta wurga mishi sannan tace; "sati ɗaya shine baka jima ba?, ko dai kafi son zaman can ne?", ya girgiza kai yace; "haba first love taya zan so zaman wajen da babu ke". "to kayi kwana biyu kawai ka dawo", ta faɗa tana kallon shi, yayi murmushi yace; "shikenan First love to amma bakya ganin Daddy zai ce ban cika umarnin daya bani ba munyi dashi one week fa?". "kaga Allah ya kiyaye hanya", tana gama faɗin haka tana fara ƙoƙarin barin wajen, cikin sauri ya sha gaban ta fuska ɗauke da damuwa yace; "bana so muyi irin wannan rabuwar Mum, dan Allah kada kiyi fushi dani, idan hakan ya ɓata ranki, to kiyi haƙuri", ya ƙarasa muryar shi na rawa. Ita kanta bata san wane kalar so take wa ɗan nata ba, tana ji dashi sosai kuma bata son ganin shi a damuwa, amma kuma zuwan shi Hayin Rigasa ta san ba wani kula zai samu a can ba. "shikenan zan haƙura amma da sharaɗi", cikin sauri ya tambaya; "meye sharaɗin?", ta riƙo hannun shi sannan tace; "zaka yarda securities su raka ka har can. Yayi ajiyar zuciya dama ya san sharaɗin ba zai wuce wannan ba to shi kuma ba wani birge shi hakan yake yi ba balle hakan ya ɗaɗa shi da ƙasa sannan kuma shi baya son hayaniya amma ya zai yi tunda shiri yake nema. Yace; "shikenan, na yarda", tayi murmushi tana me amsar jakar hannun shi tace; "muje na raka ka", haka suka jera har zuwa inda motocin suke sannan suka shiga a ka jasu, yayin da baya da gaba take cike da motocin securities. Duk inda suka gifta kallon su ake wanda hakan shine abinda Abdul ɗin baya so amma babu yadda ya iya. Cikin mintina kaɗan suka iso Unguwar, haka suka fara shiga cikin ta, shi dai ba zai ce ga yanayin da yake ciki ba amma ya san cewa gaban shi yana faɗuwa. Ya kwantar da kan shi saman kafaɗar Brr Farida yana me lumshe idanu, bakin shi ɗauke da addu'a. A bakin ƙaton estate ɗin suka dakata, sai da securities ɗin suka duba su sannan suka bar su domin su shiga. Gida ne me apartment daban-daban gasu nan jere sama da ashirin da biyar kowanne kalar shi ɗaya da ɗan uwan shi, gefe da gefen titin da aka shinfiɗa kuwa flowers ne aka jera wanda suka ƙara ƙawata wajen. Daga saman get na biyu naga an rubuta *NAGIMI'S ESTATE*, nan ma sai dai aka duba aka ga ko su waye sannan aka basu hanyar wucewa. Nan fa suka fara wuce gidaje dake jere wa'inda duka kalar su ɗaya, kuma kowanne da get ɗin shi, babu kowa a waje sai masu aiki suma jefi-jefi sun yi tafiya me tsayi kafin su iso ƙarshen wannan titin inda wani get ɗin ke kallon su. Sai da suka yi horn sannan aka buɗe musu get ɗin suka shiga, gida ne madai-daici me cike da ƙawa da kayan alatu kai daga gani ka san me gidan yana da dukiya sosai. Haka suka jera parking a harabar wajen, Abdul ya kalli Brr Farida yayi murmushi sannan yace; "First Love muje ko?", wani shegen kallo ta wurga mishi sannan taja tsaki tana kauda kai. Ɗan langwaɓar da kai yayi sannan yace; "Mum pls ki shiga ki gaida Malama dan na san tana nan ga kuma Hajja itama", cikin haɗe rai tace; "amma ai bance maka ina da buƙatar gaishe dasu ba ko sannan suma basu gaya maka cewa suna buƙatar tawa gaisuwar ba ko?". "Mum sufa ɗin Ƴan uwan Daddy ne sannan surukai suke a wajen ki dan Allah ki shigo", ba dan ranta yaso ba tace; "sauka muje". Cikin jin daɗi ya sauko suka fito tare, haka suka jera har cikin gidan, koda suka shiga falon farko babu kowa a ciki dole haka suka shiga falo na biyu wanda wata yar ƙaramar varender ce ta raba tsakani. Ƙarami ne wannan falon don kujeru set biyu ne kawai a ciki sai wajen dinning a gefe sai ƙofofi guda biyu nan ma babu kowa sai dai hayaniyar su da ake jiyowa daga ciki. Ya janyo hannun ta yana faɗin; "Mummy mu shiga daka ciki ina jin suna falon ciki", babu musu suka ƙara kutsa kai ƙofar dake ɓangaren daman su. Shima falon babu tarkace sosai a ciki dan shi be kai falon tsakiya girma ba, suka yi sallama matar dake zaune saman kujera gaban ta ƙaramin table ne tana rubutu a sama ta ɗago tana kallon su. Da mamaki take bin su da kallo tana me ƙara duba zuwa gare su, wacce ke zaune saman dinning ce ta amsa sallamar tasu tana me cigaba da cin abincin ta. Sun tsaya sama da minti biyar kafin Brr Farida ta haɗe fuska ta ƙarasa cikin falon ta sami kujera ta zauna, ganin hakan yasa Abdul wucewa ya shiga ƙofar dake can corridor. Da sallama ya shiga ɗakin, Ƴar tsohuwar dake zaune saman dardumar da alqur'ani gaban ta, ta ɗago tana me kallon shi. Kusa da ita yaje ya zauna ya ɗora kan shi saman ƙafar ta, ta saki murmushi tana me shafa kanshi, ya lumshe idanu yana ajiyar zuciya. A hankali yace; "First love na falo tana jiran ki", ya ɗago yana kallon ta, fuskar ta babu yabo babu fallasa don haka ba zai tantance yanayin da take ciki ba. Sai da tayi jimm sannan tace; "tashi muje", babu musu ya miƙe haka itama ta miƙe, sai lokacin naga irin tsahon da matar take dashi gata fara sosai. Cikin taƙama da ƙasaita take takun nata, na dafe baki ina faɗin; "Lallai Abdul baka yardar a ƙasa ba ashe abin naku gado ne?". Yadda ya shiga ya barsu haka ya dawo ya ssme su, baya jin magana ta haɗasu a tsakani, shi kam wannan abu yana bashi mamaki. Har sai da suka zauna sannan Brr Farida ta ɗago daga danna wayar da take yi ta kuma sauke ƙafar ta ƙasa tace; "Ina wuni?", sai da tsohuwar tayi daƙiƙu kafin ta amsa da ; "fatan kuna lafiya". Brr Farida tace; "lafiya lau", daga haka babu wanda ya kuma magana a tsakanin su, fin minti biyar sannan aka buɗe ƙofar falon aka shigo da sallama. Taɓ 🤔! Kallo ya koma sama shaho ya ɗauko giwa 😂😂. Wata ƴar ƙwalisar tsohuwa ce baƙa ta shigo falon tana taku ɗai-ɗai, ko kayan jikin ta ka kalla kasan cewa ba ƙamar mace bace dan ita mayafi ta yafo saman atamfar da ta saka Holland, ɗinkin doguwar riga wanda ya zauna a jikin ta sosai babu abinda take sai tashin ƙamshi me shegen daɗi. Kallo ɗaya ta yiwa Brr Farida ta ɗauke kanta, itama kuma Brr Farida bata kalle ta ba, sama da minti biyar shiru sannan Brr Farida tace; "ina wuni". Taja tsayin lokaci me nisa kafin ta iya cewa; "lafiya lau, ƴar mulki", Brr Farida ta saki wani murmushi na ƙasaita. Wacce ke saman dinning ɗin ta gama cin abincin ta sannan ta sauko itama kujerar tazo ta zauna ta ɗauki remote ta kunna plasma ɗin dake maƙale a jikin bango. Ɗan juyowa tayi ba tare da ta kalli ɓangaren Brr Farida ba tace; "ina wuni Brr?", Brr farida ta amsa da ; "lafiya lau Fatima". Babu wanda ya kuma magana hakan ya bawa Abdul damar gaishe da kakanin nashi guda biyu duka sun amsa babu yabo ba fallasa sai dai wannan ƙasaitar tana nan. ; "Ina wuni Aunty?", Fatimar ta kalle shi tace; "lafiya lau, fatan ka dawo lafiya", ya amsa da lafiya, wacce dai ke rubutu ce har yau bata ɗago ba balle ma naga ya fuskar ta take. Abdul yace; "Ina wuni Brr", cak ta tsaya da zana biron da take saman takardar sai da taja lokaci kaɗan sannan ta ɗago. Kyakkyawa ce ajin farko dan sai nace ta kusa kamo Brr Farida a kyau, fara ce sosai wanda farin ta har ɗaukar idanu yake yi kana ganin ta ka san ƴar hutu ce gaba da baya. Cikin hausa irin ta ƴan boko da kuma zamanin yanzu wacce take cike da ƙaƙale tace; "brr!? Ashe haka kake kiran uwar ka kenan?". Brr Farida ta saki wata irin dariya me cike da nishaɗi da annashuwa kafin ta janyo ɗaurin ɗankwalin ta ya dawo gaba tace; "wallahi idan kina ƙoƙarin haɗa kanki dani Brr Hauwa dariya kike bani sosai, kema fa cewa ki kayi Uwar shi ai kin san tsakanin mu da bambamci". Brr Hauwa cikin fushi tace; "ai a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe ne Brr Farida", aikuwa babu sanya tace; "nifa na riga da na zama ƙadangaren bakin tulu zama dani ya zama dole". Brr Hauwa tace; "kada ki manta kayan aro har abada na aro ne, kuma wata rana gaskiya zata yi halin ta". "ko a yanzu kasuwa ta faɗi ɗan koli yaci riba sannan ki sani ni ɗin ruwan jakara ce idan baki sha ni a kauye ba zaki sha ni a birni". Cikin sauri kafin Brr Hauwa tayi magana Fatima ta dakatar dasu ta hanyar cewa; "wai meye hakane kuke abu kamar yara ƙanana ku baku haɗuwa waje ɗaya ne sai kun nuna halin ku". Brr Hauwa tace; "wane kalar hali ai wallahi ko yanzu na san sama tayiwa yaro nisa sai dai ya ɗaga kai ya kalla, domin kuwa idan na raina kasuwa ko sautu bana bayarwa". Brr Farida ta miƙe tsaye ta taka har gaban Brr Hauwa tace; "nafi ƙarfin ki kira ni da ƙarama domin kuwa ke kanki kin sani hangen dala ba shiga birni bane kuma ba girigirin ba tayi mai, irin ku masu cika baki suna bani mamaki sosai ki sani ni ɗin ce Brr Farida Alƙali har yanzu sunan a haka yake be canza ke in banda ruwa ya daki babban zakara da idan aka ce ki kalle ni ki faɗa mini wata maganar da ba zaki yi ba wallahi koda kuwa kuɗi aka baki kada ki manta nifa itace kabari ce na danne uban kowa dakalin majina a hauni a zame na hau mutum na zauna dai-dai, murucin kan dutse ban fito ba sai da na shirya, kainuwa dashen Allah ba dashe na mutum ba. "da bamu san asalin ungulu ba sai muce daga misra take, dama dangin ku ai dangin taƙama ne da taka haye", amsar brr Hauwa kenan wacce ke tsaye gaban Brr Farida. "kada ki manta tunkan a haifi uwar me sabulu balbela take da hasken ta kuma dama ɗawisu ai kowa da zanen ta ya ganta, ke ƙaramar yarinya ce Hauwa ki bini a sannu idan ba haka ba zan koyar dake darasin da ba'a taɓa yi miki ba", daga haka Brr Farida ta ɗauki jakar ta sannan ta juya wajen tsofaffin biyu dake kallon su tace; "zan tafi Malama, Hajja sai anjiman ku", tana gama faɗin hakan ko Abdul ɗin bata yi zaman jira ba tayi waje kawai. *tofa abu ya fara fin ƙarfin jin Deeje ƴar gidan Ahmadu jikan inusa, ni kaina a dunƙule suka bani shiyasa nima na baku a haka amma zan ajiye biro na haka har sai naje na tambayo fassarar wa'innan maganganun dan kada inje ko bindige ni suke nufi ayi*. *kuyi haƙuri da abinda kuke samu daga gare ni kunji na san ina yin delay ɗin posting ɗin amma ku ƙara haƙuri saboda ina da uzururruka a gaba na sosai*. #LIKE #SHARE #COMMENT #VOTE *Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *godiya gare ku*. *Aishatu Babayo*. *Salamatu( kaka ta)*. *Hafsat A garkuwa* *Aunty Ummee* *Kamal no love* *Rukayyat Imam (Mama na)* *Ibanatu* Na gode sosai da sosai ku ɗin aminan ƙwarai ne kuma mutanen kirki ina ji daku sosai da sosai. *ina cigayar Khairat aminullah, da Hajjaju dan Allah wanda ya gane mini su ya taimaka yace One Love na neman su*. 📖📖13-14📖📖 Hajja tace; "lallai wuyan ki ya isa yanka Farida har gida kizo ki zage mu tas", ita dai Brr Farida bata san suna yi ba dan tayi nisa da tafiya. Brr Hauwa tace; "yaushe dama take da wata tarbiya irin tarbiyar gidan su kenan, kuma irin ta take bawa yaran dakta tunda shi yaji ya gani". Fatima tace; "dan Allah ya isa haka, ku bar naganar mana", Hajja tace; "ba zamu bari ba Uwar mu sai munji duka". Abdul kuwa a hankali ya sulale ya bar musu ɗakin domin ya san idan sun gama kan shi zasu dawo nan aka barsu da cece kuce ɗin su wanda baya ƙarewa. Ɗakin ya tura ya shiga a hankali yana nan yadda yake, komai a tsaftace, ya saki murmushi sannan yace: "Fadil kenan akwai tsafta", gefe ya ajiye jakar shi sannan ya faɗa saman gadon. Ya jima yana tunani wanda shi kanshi be san na meye ba, sannan ya miƙe ya nufi bayi yayi wanka, cikin riga shirt mara nauyi fara da kuma wando jeans fari ya shirya. Koda ya fito falon dai ya nufo babu kowa a ciki sai yara guda biyu da suke wasa, suna ganin shi suka nufo shi, ɗai-ɗai ya dinga ɗaga su sama yana ajiyewa. Namijin yace; "Uncle A baka zo da Adnan ba?", ya ɗaga mishi kai yace; "ai yana gida saboda makaranta", Yaron yace; "da kazo dashi da ba sai mu dinga tafiya daga nan ba". "au hakane kuma fa! To yanzu dai kayi haƙuri sai idan na sake dawowa", yaron yayi murmushi, maccen kuwa ita daga gani bakin ta ma be buɗe ba dan haka ya riƙo hannun su zuwa falon ya zaunar dasu. Ɗakin dai wannan tsohuwar ya nufa, tana zaune tana linke kaya, tunda ya shigo take kallon shi tana murmushi har yaja ya zauna kusa da ita. Shi dai be san me yasa yake son matar ba kuma yake ganin tsananin ƙaunar shi daga idanun ta a iya sanin shi kishiyar mahaifiyar baban shi ce. Wayar shi ya zaro ya nemo number ɗin Mum ɗin shi, sai da tayi ringing sosai sannan ta ɗaga. "Baby sai yanzu ka tuna dani kenan?", ta faɗa tana dariya wacce dariyar tana zuwar mishi har cikin kunnen shi. Ya shafa sumar kanshi kamar yana gaban ta yace; "First Love barci ne ya kwashe ni", sai da tayi jim sannan tace; "fatan dai kayi addu'a", ya ɗaga kai yace; "eh sosai ma". Haka suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa, har take fada mishi ashe Daddyn su yayi musu oder na motoci?" yace; "eh amma ni nafi so ya dawo ne". Ta ɗan yi dariya sannan tace; "ai zai dawo ne yace ƙarshen watan nan in Allah ya yarda yana hanya, yauwa na san mota ɗaya tayi maka kaɗan shi yasa nake jin zan ƙara maka koda biyu ne su zama uku kenan". Yayi shiru na wani lokaci kafin yace; "Mum ki bar ɗayar kawai ta ishe ni rayuwa", tace; "ba zai yiwu ba dole ka ƙara tunda kaga baka da wata motar a yanzu, gobe idan kazo office ɗina za'a turo mini da hotuna sai ka zaɓa kawai, maganar fara aikin ka fa?". Ya shafa gefen fuskar shi yace; "Mum ni ina so na fara idan Daddy ya dawo saboda komai yana buƙatar tsari sannan kinga ban san ina su Yaya Tameer suka tsaya ba". "hakane shikenan mu bari idan ya dawo ɗin, I love you", yace; "love you too", sannan ya katse wayar. Malama taja dogon ajiyar zuciya tana ɗauke idanun ta daka barin kallon shi domin kuwa duk tsayin wayar da suka yi tana kallon shi ne har ya gama, haka kuma wani abu yana taso mata daga ƙasan zuciyar ta. Abdul yace; "Malama wai ina Fadila ne da Fadil?", tace; Fadil na wajen aiki Fadeela ma haka", shiru ya biyo baya kafin kuma ya dube ta yace; "nifa yunwa nake ji". Bata kalle shi ba tace; "kaje wajen Hajja mana nasan ba zaka rasa abinda zaka ci ba ko kuma ka tafi part ɗin Abban ku". Girgiza kai yayi yace; "bari dai naje Part ɗin Abban amma wajen Hajja ɗin nan da sauƙi dan na san su Husna basa nan suna makaranta ba lallai a samu abinci ba", daga haka ya fice. Shiru ƴar tsohuwar tayi tana me bin inda ya fice da kallo, sosai ta kasa daurewa ta saki kuka me cin rai wanda ni dai ban san dalilin kukan nata ba. Tunda ya fita yake haɗuwa da matasa da ƴan matan gidan wa'inda wasu sun dawo aiki wasu kuma sun dawo makaranta, haka suke gaisawa cikin mutunci duk da dai halin nan nasu na shariya da taƙama da wasu suka ɗebo. Shifa tsarin gidan su yana bashi mamaki, sai mace ta kai shekara ashirin da biyar bata yi aure ba wata talatin duk wai da sunan boko don dole ne sai kin gama university kuma sai kin fara aiki shi yasa dan kuɗi fa akwai su haka ilimi. Wani gidan dake ɓangaren daman shi jeri na huɗu gida na biyu nan ya ƙwanƙwasa me gadi ya buɗe mishi suka gaisa cike da girmama juna sannan ya shiga ciki. A garden ya jiyo hayaniyar su wanda hakan ya nuna mishi suna can kenan, a can kuwa ya tarar dasu. Ƴan mata guda uku da samari guda huɗu sai mahaifiyar su dake zaune a gefe da laptop a gaban ta alamu ya nuna aiki ma take yi. "Lallai muna da manyan baƙi ga baƙon India a gidan mu", ɗaya daga samarin ya faɗa, Abdul ya harare shi yace; "bana son yawan surutu fa Kabeer har ka dawo kenan?". Ya miƙa mishi hannu suka gaisa sannan yace; "ban daɗe da dawowa ba dan ma na biya na ɗauko Aunty Khaleesat ne a office daba dan haka ba da tun Uku zan dawo". Sauran ya miƙawa hannu suka gaisa duk suna tsokanar shi, shi dai kawai murmushi yake yi, ɗaya daga cikin matan data kafe shi da idanuwa. Ya kalle ta ya zaro idanun nashi yace; "ya akayi ne Saleema", Murmushi tayi tana kauda kai, biyun suka kalli juna suka kwashe da dariya. "Wallahi Abdul ina ji gaba ma cewa zaka yi ka girmi har su Abba jifa wai Salima babu ko ɗan Sister ma a jiki". "to ai ba wai ta girme ni bane da yawa", Maman nasu ta riƙe haɓa tace; "kai Abdul lallai na shaida son girman ka to ba Saleema ba ko Hafeeza ta girme ka, kaifa sa'an su Fadil ne da Fadeela kaga kuwa tsirar ka da Muhibba wata biyu ne Muhibba kuma su Fadeel wata ɗaya suka bata, ai daga Kabeer sai Kamal sune ƙannan ka amma duka sauran sun girme ka". Ya juyar da kai yana murmushi, Hafeeza tayi dariya sannan tace; "Mummy ta tona maka asiri dai", ya ɗan juyo ya harare ta kaɗan sannan yace; "nifa yunwa nake ji". Cikin sauri Saleema ta miƙe tana faɗin bari nayi maka setting ɗin table sai kazo kaci", babu wanda yayi magana sai fira da suka cigaba a tsakanin su. Gidan Ambassador Ibraheem Yunusa Nagimi kenan, Jakadan Nigeria a ƙasar Italy, shi mahaifin Abdus-samad yake bi, yana can ƙasar Italy ɗin sai dai lokaci zuwa lokaci yake kawo ziyara ƙasar ta nigeria. Yana da mata guda biyu amaryar ita ke can inda sukan yi wata shida-shida ne sai ɗaya ta canji ɗaya, doka ce ta familyn basa fita waje suyi gida hakan yasa dole ya ajiye yaran nashi a nan. Ƴaƴan shi takwas biyu ne kacal suka yi aure yanzu haka shida suna nan basu yi aure ba, cikin wa'inda suka yi auren akwai Muhsina da Maryam, Muhsina ita ke aiki a bank Maryam kuma lecture ce a nan KASU dake kaduna. Sai Adam wanda yake aiki da companyn NNPC yana da shekara talatin har da biyu sai Saleema dake cikakkiyar likita me shekaru talatin, sai Hafeeza me ashirin da takwas ita kuma tana aiki a ɗaya daga company na gidan ne sai Muhibba me shekaru ashirin da shida sai Kabeer me ashirin da biyar sai Kamal me ashirin da uku daga kan Muhibba zuwa ƙasa su karatu suke yi. Saleema ta ƙaraso inda yake tace; "na gama zaka iya tasowa", babu musu ya miƙe ita kuma ta biyo bayan shi. Ta wata ƙofa ƙarama suka biyo sai gasu a ƙaton falon gidan, inda yake cike da kayan mire rayuwa dinning area suka nufa wanda nan ɗin ma wani sabon kallo ne a wajen. Da kanta tayi serving ɗin shi sannan ta koma gefe ta zauna tana kallon yadda yake cin abincin, cikin natsuwa sosai babu wata hayaniya ko tashin hankali. Sai da ya gama sannan ya juyo ya kalle ta yace; wannan kallon fa ya kusa yayi yawa", tayi murmushi tana kauda kai gefe shima murmushin yayi yana miƙewa tsaye. Da sauri ta miƙe tsaye ta matso kusa dashi cikin sauri ta riƙo hannun shi tace; "Abdul kayi kyau", ya sakar mata murmushi yace; "na gode sosai", daga haka ya zame hannun nashi ya fice. Tana tsaye tana kallon shi har ya fice daga falon, ajiyar numfashi tayi tana me dafe kumatun nata da hannuwa biyu. Ita tun ba yanzu ba Allah ya jarabce ta da tsananin son ƙanin nata wanda ta kan rasa ina zata saka kanta. Shi kuwa Abdul yana fita suka haɗu da Muhibba tayi ihu tana yo kanshi, cikin sauri ya kauce ya balla mata harara yace; kefa matsala ta dake rashin hankali". "au dan ma na nuna farin ciki da ganin ka", Kabeer dake kwasar dariya yace; "Allah na rasa ina ƙasaitar ta take tafiya idan ta ganka", Muhibba ta cilla mishi harara. Juyowa tayi tana kallon Abdul ɗin wanda shi kuma yake ƙoƙarin ficewa daga gidan, "ina zaka je ne?". Be juyo ba ya bata amsa da zan tafi part ɗin su Hajja ne", da sauri ta biyo shi tana faɗin; "muje na raka ka", ya dafe kai shi dan dai yana jin yunwa ne yazo gidan nan amma hayaniyar su ta dame shi sosai. Suna tafe tana mishi surutu shi dai kawai kallon ta yake yi sai murmushi lokaci zuwa lokaci, haka har part ɗin Hajja. Suna shiga Fadila dake zaune a saman kujera ta tashi da sauri tana ihun murna, ya girgiza kai yana me yin murmushi ƙarfin hali. Kujera ya samu ya zauna yana faɗin; "bismillah", Muhibba ta zauna a gefe Fadila a ɗayan gefen, haka suka saka shi a tsakiya kafin su hau fira. Firar da suke ma ba wata me hayaniya bace sai dariyar su kaɗa-kaɗan da zaka dinga ji lokaci zuwa lokaci. A haka har Fadil ya fito, ɗan saurayi dashi wanda suke kusan sa'anni da Abdul ɗin, sai dai abinda zai baka mamaki yadda duk Abdul ɗin ya ɗarasu kyau kasancewar yanayin shi daban. Fadil yace; "kaga Sarki ka taso mu wuce ka rabu da wa'innan", babu musu ya miƙe, yayin da Muhibba ta turo baki tana faɗin; "kai Yaya Fadil sai kazo ka wani janye shi, kai baka zauna anyi firar zumunci da kai ba shima sai ka wani hana ayi dashi". Kafin ya basu amsa Abdul ɗin ya fito sanye da kayan ƙwallo kalar na jikin Fadil ɗin, yana zuwa suka fice. Bayan sun fita Abdul yace; "nifa bana son na wannan Estate ɗin mu ɗan je na gamji mana", Fadil yace; "to shikenan ai Abban Nihal baya nan zamu iya tafiya", haka suka fice daga cikin gidan. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 *HAYIN RIGASA, KADUNA*. Nusram ta harari Nusreen tace; "wallahi kiyi sauri mu tafi dan na gaji gashi kuma ina buƙatar hutawa", Nusreen ta yamutsa fuska tace; "to a haƙura da zuwa Tudun Nufawan mana". "sai kunje shi na san duk kece kike so ki janyo salalan tsiya to wallahi baki isa ba kin san gobe akwai bikin Wasila ƴar gidan Malam Hassan kuma ta riga tazo ta tambaya akan Nusram take so tayi mata kitso da kwalliya ko amma shine kike so ki janyo abinda zai hana ku zuwa gobe bata da lokaci idan kuma kika sake kuka fasa zuwa yau to gobe zaki je ke kaɗai kenan?". Nusram ta girgiza kai tana faɗin; "Ummi zamu tafi yanzu Rim dan Allah kiyi ki ƙarasa", Ummi tace; "ku dai kuka sani", ta cigaba da ƙulla sigar ta. Nusreen ta miƙe tsaye, tana sanye da atamfa kalar blue da ratsin ja da kuma ruwan toka sosai atamfar ta haska kalar fatar ta, fuskar nan ta ɗauki kwalliya sosai. Hijab ta ɗauko kalar ash ta saka takalmi da jaka ƴar ƙarama swagger kalar ja ta saka sosai tayi kyau wanda itama Nusram ɗin shigar da tayi kenan sai dai ita fuskar ta babu wata kwalliya sosai. Ummi ta irgo kuɗi ta miƙa musu tace; "gashi nan ku kai mata kuce zamu yi waya anjima, sannan ta ƙaro muku Curry da thyme harda citta duka domin ta waje na ta ƙare saura ku daɗe". "insha Allah da wuri zamu dawo", faɗar Nusram kenan tana ƙoƙarin saka kuɗin cikin jakar ta. Kamar koda yaushe Mama Jummai ta tsakar gida tana faman ɗora manyan tukwane domin girkin siyarwa, Ameera da Sahura suna taya ta. Haka suka fice ba tare da sunyi mata magana ba wanda ina ganin dalilin Nusreen da bata so su kuma ɓatawa da ƴar uwar tane. Koda suka isa bakin titi basu jima ba suka sami abin hawa inda suka hau zuwa Tudun Nufawa. Har ƙofar gidan me Keke Napep ɗin ya kaisu, Nusram ta ciro kuɗin shi ta miƙa mishi, gidan babu laifi ya haɗu domin kuwa harda get a jiki. A hankali suka tura suna masu jero sallama, daga can cikin gidan aka amsa sannan suka shiga, ɗakin dake gefen hannun hagu suka ga takalma wanda ya nuna musu Auntyn tasu tana cikin ɗakin. Ɗaki ne wanda take sana'ar ta a ciki komai na kayan ta to a ciki yake haka ma idan masu siye sun zo nan take kaisu. Suna shiga suka tarar da Ƴan mata uku da kuma wata ƴar matashiyar mace wacce ba za'a kira ta da tsohuwa ba, Matar tana ganin su ta sakin murmushi tace; "yauwa Allah ya kawo mini ku, kamar kun san aiki yayi mini yawa". Nusreen ta yamutsa fuska tana cuno baki, Nusram kuwa zama tayi sannan tace; "meya faru Aunty?", Wacce ta kira da Auntyn tace; "dama wa'innan da kike gani muke gyara dasu yau kwanan mu goma sha takwas kenan, to yau kinga aiki yayi mini yawa ga kaya zan je amsowa domin ɗazu an aka kira ni akan kaya sun iso ina so naje na zaɓo kada a riga ni ga kuma jakunkuna da zan haɗa guda hamsin da biyar wa'inda ƙanwata Kaltume zata wuce dasu Borno to aikin duk ya caɓe mini tunda kunzo sai ku taya ni". Nusram tace; "babu komai Aunty, ga wannan ma inji Ummi tace a kawo miki wai zaku yi waya ga kuma wannan kuɗin kayan mu ne dubu talatin da biyar ga na Yaya Sulaiman shima dubu arba'in sai ki ajiye mishi, naso muje can ɗin da kanmu amma tunda kina da aiki zamu hakura kawai sai ki ce mishi ya sake haɗo mana wasu kayan zuwa gobe na rigunan kuma da turarruruka idan kin dawo sai ki bamu ko?". Auntyn tace; "yauwa ƴa ta yanzu wanne zaki yi", Nusram tace; "bari na fara yiwa amaren dilka idan yaso Rim kuma sai ki bata sample ɗin jakar sai ta fara yi miki kafin na gama". Auntyn ta gallawa Nusreen harara sannan tace; "ai banga alamar zata yi mini ba ganin yadda take yatsina fuska", Nusreen tayi dariya tana fadin; "haba dai Aunty zan yi miki mana sai dai kin cika saka aiki ne idan mutum yazo". Aunty ta riƙe baki tana faɗin; "Nusreen ni ɗin lallai wuyan ki ya isa yanka", Nusreen ɗin tace; "wasa nake miki ina Adam fa?". "yana gidan Halima sai gobe zai dawo", Nusram tace; "Aunty kije ki manta da wannan kawai", aikuwa", Auntyn ta faɗa kawai tana miƙewa domin zuwa ta shirya. Ita kuma Nusram ɗin ta cire hijab sannan ta kwaso kayan da zata fara nata aikin, nan ta shiga haɗawa, su kuwa amaren babu abinda suke sai mamakin yadda wannan matashiyar zata musu gyara. Haka dai suka fara gyaran inda nan suka cika da mamaki ganin yadda take gyara su cike da bai, Nusreen kuma tana gefe tana haɗa jakun-kuna dama su kan taya ta hakan yasa suka iya domin duk wanda zai zauna da ita tofa ba zai yi zaman banza ba. Kan wani lokaci ta gama gyaran sannan ta koma kusa da Nusreen ɗin tana taya ta haɗa jakun kunan, suna fira tsakanin su sama sama. Yayin da suma amaren suke nasu firar lokaci zuwa lokaci, haka har magriba ta kusanto, tashi Nusram tayi ta sirka musu ruwan da zasu yi wanka wanda ruwan ma da wasu itatuwa da sinadarai masu ƙamshi. Sai da suka fito sannan ta ɗauko wani ƙaramin roba me cike da wani mai me shegen ƙamshi ta basu suka bi jikin su suka shafa. Ɗayar ta kalli Nusram tace; "gaskiya kin huta da kika koyi sana'a ba ruwanki da zama haka bayan kin yi aure", Nusram tayi murmushi kawai, haka suka yi sallama cike da birgewa da mutuntawa. Nusreen ta ajiye ta hannun ta tace; "gashi Aunty har yanzu shiru ko lafiya?", kan suce wani abu tayi sallama ta shigo. "kuyi haƙuri na jima sosai ban dawo ba", ta faɗa tana ajiye uban kayan dake hannun ta, Nusram tace; "babu komai, na manta ince miki Ummi tace ki bata wasu cittan da curry da thyme na hannun ta sun ƙare". Auntyn tace; "bari na haɗo muku", ta faɗa tana ƙarasa miƙewa domin haɗo musu yayinda su kuma suka hau zaɓar kayan domin tafiya da nasu. Sai da suka haɗa komai sannan suka yi mata sallama, ta ciro ɗari biyar da ta basu haka suka yi mata godiya suka fice daga gidan cikin sauri akan zuwa jibi zasu dawo domin amsar ragowar kayan. Haka suka fice daga gidan da kaya niƙi-niƙi Allah yasa babu nisa ma zuwa bakin titi,sun ɗan jima kafin su samu abin hawa kasancewar magriba ta gabato. Ana kaisu suka sauka, haka Nusreen ta bashi kuɗin shi sannan ta ɗauki nata kayan itama Nusram haka, da ƙyar suke tafiya da kayan dan suna da yawa sosai. Nusreen wacce ke gaba da kaya a hannun ta, su biyu suka taho a jere Fadil na riƙe da kwallo yayin da Abdul ke gefen shi a iya saurin su shine kada magriba ta iske su akan hanya. Ɗan bangajar hannun Nusreen yayi wanda yasa kayan dake hannun ta faɗuwa, ita kanta sai da ta kusa faduwa saboda gajiyar da tayi sosai Allah ya taimake ta Nusram ta riƙo ta da sauri. Abdul kuwa cikin sauri ya tsuguna ya ɗago jakar dake cike da kayan, Nusreen kuwa wani irin haushi yazo mata wuya. Da sauri ta tsuguna ta fizge jakar tana faɗin; "Malam dallah bani jaka ta mutum yana tafiya kamar wani makaho ai ba kowa kafi sauri ba kuma yadda kake da uzuri haka kowa ma yake da uzuri na rasa me yasa irin ku basu san darajar mata b..........". Kasa ƙarasa tayi saboda ɗagowar da yayi domin ganin wacece wannan, ita kuwa Nusreen maganar taji ta tsaya mata a maƙogoro saboda wani kwarjini da yayi mata ga idanun shi masu kama dana mage daya kafe ta dasu wanda ya haddasa mata daburcewa. Ba ita ba ita kanta Nusram babu abinda ƙirjin ta yake sai dukan uku-uku, tunda take bata taɓa haɗuwa da mutumin daya firgitata kalar wannan ba a zahirin gaskiya ba uta yake kallo ba amma ji take kamar a gaban kotu take, jikin ta har rawa yake yi tsabar ruɗewa. Ya miƙe tsaye sosai sannan ya matso kusa da Nusreen yace; "ina gain tunda har na baki haƙuri ai ya kama ta ki haƙura ko, *MENE NE RIBA TA??* (littafin zaratan marubutan Golden pen, wanda mutum biyar ke aikin rubuta shi domin kawowa masoyan su) dan naci zarafin mace wacce bata da ƙarfi kuma take da rauni, ya kamata ace kin kula da martabar ki da darajarki ki dena ɗaga murya a titi duk kuwa da irin abinda aka yi miki", daga haka ya juya ya tafi Fadil yabi bayan shi. A tare suka sauke ajiyar zuciya kafin Nusreen taja tsaki jiki a sanyaye ta ɗauki kayan nata suka wuce gida. Koda suka isa gidan sun tarar da mutanen gidan na cikin ɗaki domin yin sallah hakan yasa kayan kawai suka ajiye suma suka fara ƙoƙarin yin sallah. Har lokacin jikin Nusram a sanyaye yake domin har zuwa yanzu sautin muryar shi be bar kunnuwan ta ba, haka tayi sallah sannan suka zauna lissafi. Sai da suka fitar da komai sannan wani yaro ya shigo yana faɗin ana sallama da ƴan biyu, Nusram tace; "Rim tashi kije kina jin abinda yaron nan ya faɗa". Dole tasa Nusreen wacce har yanzu bakin ta ya gagara buɗewa kamar da ta miƙe tana jan tsaki ta ɗauki hijab tayi waje. Kamar yadda ta zata kuwa sune dai a tsaye cike da jin haushi ta ƙarasa wajen su, Shureim kuwa babu abinda yake yi banda kallon ta yana jin wani farin ciki a cikin zuciyar shi. Naufal kuwa dama drama ɗin su yasa ya biyo abokin nashi dan haka tun fitowar ta ya fara kunshe dariya dan yadda ta fito kawai zai tabbatar maka da babu wasa. Ɓangaren Abdul kuwa yarinyar ta bashi mamaki sosai ga wanu haushin ta da yake ji a rayuwar shi ya tsani mace me tsiwa da hayaniya ko rawar kai, dalilin da yasa kenan yaji abin ya ɓata mishi rai sosai. Fadil yace; "kai amma gaskiya sun haɗu wallahi daga gani ƴan biyu ne", Abdul yace; "suwa kenan?. Fadil cikin mamaki yace; "kai wai baka lura dasu biyu bane?", Abdul cikin jin haushi dan yanzu ya fahimci dawa yake ko ince wacce yake nufi dan haka yaja bakin shi yayi shiru. Haka Fadil ya cigaba da wani zuzuta kyawun su yayin da Abdul yake ji kamar ya kwashe shi da mari. "wai kai me yasa kake mini hakane yarinyar da babu abinda ta iya sai tsiwa shine zaka wani dame mu da maganar ta idan son ta kake ai sai kaje ka aure ta, mtseww yarinyar ƙarama sai rainin wayo". Fadil yace; "ai kai kayi mata laifi ya kamata ace ka ɗauki duk wani abu da yazo daga gare ta wai kai baka lura da tsananin kyawun da take dashi ba, ai wallahi da ace zan sami kalar ta na auro ta a nan familyn to da sai na ɗinga ɗaga kai domin kuwa na san na sami mace me kyau". Abdul yaja wani tsakin sannan yace; da alamu ka samu taɓin hankali, ai wannan ba wata me kyau bace abu mummuna da ita ka wani dage sai koɗata kake yi ai wallahi ka cuci familyn mu daka haɗa su da ita". Fadil yace; "ai kuwa kaf familyn mu babu me nuna mata kyau bayan kai dan dai baka tsaya ka kalle ta da kyau bane". Cikin sauri Abdul yace: "dan Allah na gaji da jin wa'innan shirmen kazo muje muyi alwala mu wuce muyi sallah", haka dole Fadil yaja bakin shi ya tsuke. Nusreen kuwa sai da ta bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya tana yatsina fuska, dama ga haushin waccen daya gama raina mata wayo ya kuma hana ta fitar da abinda ke ranta ga kuma wannan ɗan anacen da yake neman takurawa rayuwar ta. #LIKE #SHARE #COMMENT #VOTE @ wattpad_ 13 deeja. *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖15-16📖📖 shureim yace; "barka da wannan lokacin gimbiyar mata", Nusreen tayi mishi wani kallo sannan tace; "wai kai meye matsalar ka ne dani?". Yayi murmushi sannan yace; "ni kuwa nake da matsala dake, tun daga lokacin da muka yi wannan haɗuwar har yanzu ban kuma samin kwanciyar hankali ba kullum da tunanin ki nake kwana nake tashi ki taimaki bawan Allah ki amshe shi hannu biyu dan Allah". Mamaki ya hana Nusreen magana, lallai ma wannan ya raina ta cab, cikin masifa tace; "au sakar maka fuskar da nake yi har yasa ka fara tunanin tara ta da wannan maganar lallai ma dole na ɗauki mataki akan ka". Shureim ya kalli Naufal dake faman ƙunshe dariya yace; "Naufal ka dena irin haka ma ya ana maganar rayuwa ta kai kuma kana faman dariya". Naufal yace; "yi haƙuri, amm ƴan mata ki daure ki bashi dama akan laifin da yayi miki ya samu damar gyarawa, dan Allah ki amsa mishi kada hakan ya zama matsala a rayuwar shi". Nusreen tace; "ai rayuwar shi ba'a hannu na take ba dan da a hannu na take da sai na bashi idan yaso ya dauwama a duniyar". Naufal yace; "yanzu dai ba wannan maganar ba yayi miki laifi kiyi haƙuri kinji, ki amshi ƙoƙon barar shi ko ya samu sauƙi na abinda yake damun shi". Nusreen ta yamutsa fuska tace; "sai nayi tunani akai", sosai Shureim yaji daɗin hakan. "to yanzu ya sunan ƙanwar tawa?", Naufal ya tambaya, sai da Nusreen ta harare shi ta ƙasan ido sannan tace; "Nusreen". Cike da shauƙi Shureim ya sake maimaita sunan; "Nusreen! Nice name", Nusreen tace; "bari na tafi kawai gida kada Baba na yazo ya same ni a nan". Tana faɗin haka tayi shigewar ta gida, Shureim kuwa kamar ya ɗaga Naufal sama haka ya dinga ji. Naufal yace; "ka bari mana har sai ta amsa", Shureim yace; "wallahi naji daɗi sosai", haka suka tafi cike da farin ciki. Tana shiga ta tarar da Nusram na harhaɗa kayan da suka amso daga Tudun Nufawar, Nusram tace; "har kin dawo kenan?". Nusreen ta bata amsa tana me zama gefen katifar su tace; "eh har na dawo ban daɗe ba ko". Bata bata amsa ba sai da mai da komai inda yake sannan tazo ta zauna kusa da ita tace; "Rim faɗa mini gaskiya waye yazo". Nusreen tace; "ina wannan wanda ya taɓa watsa mini ruwa har yace maman shi zai kai Airport", Nusram ta ɗaga kai alamar ta gane. Nusreen ta cigaba da cewa; "to shine yazo wai yana so na", Nusram farin ciki ya lulluɓe ta tace; "Alhamdulillahi ashe dai kema kina da rabon yin aure, Rim dan Allah kada ki dakatar da wannan domin kuwa tun lokacin da muka haɗu na lura yana da tarbiya sosai". Nusreen tayi murmushi sannan tace; "amma kin san duk son da nakewa ɗa namiji ba zan taɓa aminta dashi ba har sai kema kin samu naki ko?". Jikin Nusram a sanyaye tace; "Rim kada muyi haka dake idan kuma Alƙah ya ƙaddara ba zan taɓa yin aure ba fa?". Nusreen tace; "nima shikenan ba zan yi ba", Nusram ta riƙo hannun ta cikin alamar lallashi tace; "dan Allah ki daure ki janye wannan maganar taki domin kuwa zaki ɗaura mini laifin da bazan iya kare kaina ba a wajen Allah, kiyi haƙuri ki tsaida miji kiyi aure". Nusreen ta taɓe baki tana me miƙewa tace; "ba zan taɓa canzawa ba Ram, kuma ina nan akan baka ta har sai ranar da kika sami miji sannan nima zan tsaida mijin aure na", tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin. Nusram ta buga uban tagumi tana me tunanin halin ta da halin da ta tsinci kanta, Ummi dake tsaye saman kanta, ta dafa ta tace; "Nusram ki dena damuwa kowa da kika gani da tashi ƙaddarar". Nusram cikin jimami tace; "Ummi da ace ina da wanda ya taɓa cewa yana sona yau dana fito dashi a matsayin miji ko dan Nusreen, Ummi ko Nusreen bata faɗa mink ba na san cewa ba zata taɓa canzawa ba akan abinda ta faɗa, sannan bana so tayi asarar wannan mutumin domin kuwa daga ganin shi yana da nagarta kuma zai iya jurewa halin ta, sai dai kash babu wanda ya taɓa furta kalmar so a gare ni". Ummi cikin tausayin ƴar tata tace; "kada ki damu ki miƙawa Allah lamuran ki shine kawai wanda zai iya share miki hawayen ki". Ranar haka Nusram ta kwana cike da zullumi da tunanin mafita, yayin da Ummi ta kwana tausayin ƴar tata ganin halin da take ciki. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 Yana zaune ya tasa laptop a gaba sai faman shagwaɓa yake zubawa da alamu dai waya yake yi shida Brr Farida domin yadda yake yi kaɗai zai nunar maka da hakan, Fadil kuwa in banda dariya babu abinda yake yi. Abdul ya ɗago ya dalla mishi harara sannan ya cigaba da amsa wayar shi, "First Love ki bari dan Allah su fara zaɓa idan yaso wacce suka bar mini ina son ta a haka". Brr Farida tace; "shikenan tunda haka kace amma ka sani ko bata yi maka ba tunda kai kaso haka zaka amsa". Ya ɗaga kai alamar ya yarda, Brr Farida tace; "nayi kewar ka sosai yaushe zaka dawo ne?", ya shafa sumar kan shi yana murmushi yace; "nan da kwana uku". Sosai Brr Farida ta ɓata rai sannan tace; "wai kai me kake samu daga wannan gidan ne da ka nace shi kake son zaman cikin shi duk irin yadda ƴan gidan suke nuna maka ƙiyayya". "yaushe Daddy zai dawo ne, yace mini gobe amma kuma banga alamun hakan ba", ya faɗa cikin son kaudar da waccen maganar. Sanin halin ɗan nata yasa tace; "eh yace sai nan da sati me zuwa idan Alƙah ya kaimu, nima ina so naje Dubai saboda kayan hannu na ya ƙare". "kai First Love yanzu sai kiyi tafiya ki barni gaskiya zan biki", ya faɗa cikin shagwaɓe fuska, tayi murmushi tace; "idan ka dawo daga nan ɗin ba idan kuma baka dawo ba yaro sai dai kaji na wuce". Ya noƙe kafaɗa yace; "idan kika tafi ni kuma sai inyi zama na a nan gidan in ƙi dawowa", Brr Farida tayi dariya tace; "in dai Rigasa ne ai gaka ga ta nan da ƙafar ka zaka gudu domin yanzun ma dan Abban Husna baya ƙasar ne". Shiru yayi shi yana mamakin yadda Maman shi ke sanin wasu abubuwan da yake faruwa a gidan koda ace bata nan, ya ɗan dafe kan shi yace; "bye Mum zan kwanta". Tace; "ok shikenan sai da safe kada ka manta kayi addu'a kaji I love you", ya bata amsa da "love you too", ya katse kiran. Ta baya ya faɗa saman gadon kanshi na kallon sama, tunanin rayuwar su yake yi yana kuma mamakin wasu abubuwan gashi idan zai kwana yana tambayar Maman shi ba zata bashi amsar da yake so ba kuma shi ya san tabbas akwai wani abin. "Kana tunani akanta kamar yadda nake yi?", muryar Fadil kenan yayinda ya katse mishi tunanin shi. Abdul yace; "waye kenan?", Fadil yace; "wacce muka haɗu ɗazu mana, gaskiya yarinyar ta haɗu wallahi". "just shut up", ya faɗa cikin fushi, ina cikin farin ciki zaka lalata mini da wani zancen banza". Fadil yayi murmushi yace; "Allah ka sake tunani, wallahi yarinyar zaku dace sosai barin ma ɗayar dan naga ita tana da hankali sosai kuma itama wannan ɗin banga wani aibunta ba", jin shiru ya tabbatar masa da idan zai kwana yana magana ba zai amsa mishi ba hakan yasa yaja bakin shi yayi shiru. Abdul kuwa sai da ya tabbatar da yayi addu'a sosai sannan ya gyara kwanciyar shi domin yin barci wanda kuwa be jima ba barcin ya ɗauke shi. Washe gari da wuri suka tashi domin zuwa ƙwallo ta ƙaddara, sai dai sauƙin ta a cikin estate ɗin suka buga. Suna ƙoƙarin shiga Brr Hauwa na ƙoƙarin fitowa, dan haka cikin sauri ya kauce ya bata hanya, ta mishi wani kallo sannan taja tsaki ta wuce. Hakan be wani dame shi ba domin ya riga ya saba da halin na ƙanwar mahaifin nashi, wacce yake mamakin abinda yasa bata ƙaunar shi. A kan dinning suka tarar da sauran, dan haka suma zama kawai suka yi, Husna ta jefa mishi wani kallo sannan tace; "Ina kwana". Ko kallon inda take beyi ba hakan ba ƙaramin bata haushi yayi ba amma haka ta daure ta miƙe a ƙoƙarin ta na haɗa mishi abin kari. "am ok", abinda ya faɗa kenan yana ƙoƙarin miƙewa, Hajja tace; "kai bana son iskanci koma ka zauna kaci abinci". "Hajja nifa ba yanzu zanyi break fast ba", ya bata amsa, cikin ƙasaita ta kuma cewa; "ba wannan na tambaye ka ba, umarni na baka". "haba Hajja tunda yace ba zai ci ba ki ƙyaƙe shi man........", cikin ƙaraji Hajja tace; "ke kuma waye ya saka bakin ki a ciki ƙaramar alhaki, ki sani idan ina sha'anin ƴaƴa na bana buƙatar bare ya saka mini baki". Fadila ta kalli Malama wacce fuskar ta ke ɗauke da damuwa tace; "kiyi haƙuri bada wata manufa na faɗa ba", tana gama faɗin haka ta miƙe ta bar wajen. Abdul kuwa dan dole ya koma ya zauna, sai da ya harari Husna sannan yace; "serve me", jikin ta har rawa yake wajen zuba mishi. Sai da Hajja taga ya fara cin abincin sannan ta bar wajen, yana ganin ta shige ɓangaren ta yaja tsaki yana kauda abincin. Husna tace; "Yaya ai baka ci komai ba", ya balla mata harara sannan yace; "duk ranar da kika kuma gigin shiga rayuwa ta sai na kusan sumar dake banza mara hankali". Husna ta cuno baki, Saleema tayi sallama ta shigo, jikin ta sanye da riga da wando pakistan sai hannun dake riƙe da rigar lapcoat ɗayar kuma tana riƙe da kula. Tayi kyau sosai ga kuma murmushin daya kuma ƙawata fuskar tata, tunda ta shigo idanun ta ke kanshi tana me ƙara washe baki. Yayi mata kyau sosai dan yana sanye da wando fari ne da riga blue kanshi kuwa yayi combing ɗin shi hakan yasa gashin ya kwanta sosai. Shima kuwa da murmushin ya bita, har kusa dashi ta ƙaraso, Fadil da Fadila suka gaishe da ita, ita kuma ta gaishe da Malama. Malama ta amsa tana me tashi ta bar musu wajen, Sayyada ma ta gaishe da ita ita kuwa Husna gefe ta kalla tana me sakin tsaki ƙasa-ƙasa. Murmushi suka kuma sakarwa juna sannan tace; "ina kwana", ya ɗan sosa kai yace; "lafiya lau, har kin shirya". Sai da ta juya idanu sannan tace; "eh har na fito na jira kazo breakfast baka zo ba shine na biyo ka dashi". "am ok na riga naci abinci anan", sai da murmushin dake fuskar ta ya ɗauke cikin damuwa tace; "nifa da kaina na shiga kitchen na haɗa maka amma babu komai nasan maybe dan baka san zan maka bane". Wani irin murmushi yayi wanda ya tafiyar da imanin su gaba ɗaya, shi kanshi yana jinjinawa haƙurin Auntyn tashi wannan kuma ke janyowa take matuƙar birge shi yana son mace me sanyin hali. Saleema da take ji kamar ana ƙarawa zuciyar ta wutar son shi ta juya tace; "bari na wuce wajen aiki", tana faɗin haka ta fara tafiya. Cikin sauri ya miƙe ya biyo bayan ta yana faɗin; "bari na raka ki", ya ƙarasa yana amsar jakar hannun ta. Sosai Saleema taji daɗin hakan kuma ta san cewa yayi ne dan ya sanyaya mata rai na rashin cin abincin ta da beyi ba. Husna kuwa kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu haka take ji yayin dasu Fadil suka kasa riƙe dariyar su sai da suka dara sosai. Husna kuwa abin ya ƙara baƙanta ranta dan haka ta nufi ɗakin Hajja tana kuka, su kuwa suka cigaba da dariyar su. Suna fita harabar gidan motar Abban su Fadil na shigowa, da sauri Saleema ta buɗe motar ta shiga yayin da shi kuma Abdul ɗin ya mika maya jakar tata. Abba daya fito daga cikin tashi motar yabi motar ta da kallo yana girgiza kai, Abdul ya shafa kai sannan ya gaishe da Abban. Cikin fara'a Abban ya amsa, hakan ba karamin daɗi Abdul ɗin yaji ba ganin yadda ɗan uwan mahaifin nashi ya sakar mishi fuska. Haka ya riƙo hannun Abdul ɗin har cikin gidan, da gudu Fadil da Fadila suka yi wajen mahaifin su nan suka gaishe dashi ya amsa yana tambayar su ina wajen aikin ba, nan suka bashi amsa da yanzu zasu tafi. "to ayi sauri a tafi bana son wasa da aiki", dole suka ƙarasa shiryawa da wuri suka fice, hannun shi cikin na Abdul suka shiga ɗakin Hajja. Hajja tace" na rasa me dangin Malama suka baka da kake naniƙe muku kabi duk ka wani manne dasu, to ka sani su ɗin rabin ƴan uwan mahaifin ka ne". Abdul ya saukar da kai ƙasa cike da kunya ga Abban su Fadil amma bata ji kunyar faɗin haka ba. Abban Fadil kuwa yayi murmushi kawai idan da sabo yaci su saba da halin Hajjar; "ina kwana Hajja". "mun tashi lafiya?", amsar data bashi kenan, beyi fushi ba yace; "lafiya lau", daga haka bata kuma cewa komai ba. "bari na ƙarasa na gaishe da Malama, ga wannan a sa mana albarka", ya ciro ƴan dubu-duɓu ɗauri biyu ya ajiye a gaban ta. Da ƙyar ta iya cewa; "an gode Allah yayi albarka", Abban Fadil ya amsa da Ameen yana me jinjina mulki irin na Hajja. Yana miƙewa Abdul shima ya miƙe, Hajja tace; "to ɗan annace ina kuma zaka je?", kamar ba zai amsa ba sai kuma yace; "gidan Abba". "wane Abban?", ta ƙara jefa mishi tambaya shifa ya fara gajiya dan haka a ɗan ƙarage yace; "Abban Kabeer", wani ɗan murmushi tayi sannan tace; "a dawo lafiya". Har ya juya sai kuma ta kira shi, ba dan yaso ba ya juyo ya dawo, " yauwa ɗazu meya haɗa ka da ƴar uwar ka Husna". Sai da yayi jim sannan yace; "meta ce miki?", Hajja cikin hasala tace; "ina tambayar ka kana tambaya ta?". Yayi shiru be tanka ba, sanin cewa ba zai faɗa mata bane yasa itama bata kuma magana ba haka suka zauna tsayin minti goma sha biyar kowa yana ji da nashi miskilancin, dan kanshi ya miƙe ya fice, ita ma kuma bata ko kalli inda yake ba. Yana fita ma ya fasa zuwa can ɗin dan haka ya nufi ɗakin Malama, har Abban Fadil ɗin ya fita. Da kyar ya iya yin sallama ya shiga, ganin hakan itama Malamar tunda ta amsa mishi bata kuma cewa komai ba sai ma sallah data tayar. Kan gadon ta kawai ya faɗa wanda yake tsaf-tsaf ya san aikin Fadila ne domin tare suke kwana da Malamar yana kwanciya babu jimawa barci yayi awon gaba dashi. Malama tana idar da Sallah ta juyo tana kallon shi, cikin idanun ta babu abinda kake gani sai Ƙauna, tausayi da kuma bege, a hankali ta ƙarasa gaban shi tana kallon shi. Hannu ta kai wanda har rawa yake yi ta shafa fuskar shi hawayen da ban san kona meye ba ya zubo daga idanun ta. Baki take motsawa alamar addu'a take yi, sai da ta gama sannan ta shafa mishi tana cigaba da zubar da hawayen ta, tana gamawa ta tashi ta koma kan sallayar ta tana me ɗaga hannu sama tana addu'o'i hawaye na kuma zubowa wanda hakan zai nunar maka da tana cikin baƙin ciki. Sai bayan azahar sannan ya farka, babu kowa a ɗakin hakan ya nuna mishi kenan Malama ta fita. Ya sauko daga saman gadon ya shiga bayin ta yayi Alwala sannan ya fito, yana fitowa daga ɗakin Hajja na fitowa daga nata ɗakin. Ta kalle shi cikin masifa tace; "ina raba ka da Malama da abinda ta haifa kana ƙara maƙale mata ko?, kana sane da cewa ba ita ta haifi Uban ka ba amma kabi duk ka shige mata, so kake yadda ta cinye ƴar ta kaima ta cinye ka?". Ya juya cike da jin kunya domin kuwa Malama dake tsaye a wajen ya kuma san taji abinda Hajjar ta faɗa. Malama cikin rawar murya tace; "Hajja me yasa kike faɗin haka ne taya uwa zata lashe kuruwar ƴar ta?, meyasa kike so ki raba ƴan uwan taka ne ki sani da Fiddausi da Baban Abdul Uban su ɗaya fa". Hajja tace; "ai Uba kika ce ba Uwa da Uba ba sannan Baban Abdul ɗana ne Fiddausi kuwa ƴar ki ce wacce tsabar maita kike lashe kuwar ta dan haka ki tattara ki ƙyale mun jika dan yafi karfin ki". Malama kasa cewa komai tayi dan haka ta shige ɗakin ta yayinda Abdul ya juya ya bar wajen da sauri. *Fiddausi* shi kuwa ya jima yana jin wannan sunan, domin kuwa sunan Muhibba kenan, sannan Nihal ma sunan ta kenan sunan wata ne suka ci?. Shi tunda yake be taɓa jin wannan sunan a wajen Mummyn shi ba, amma ya kan ɗan ji shi cikin Estate idan ya shigo wanda alama ya nuna ƴace ga Malama kuma ta rasu ne shekaru masu yawa. Sai yamma sannan su Fadil suka dawo nan ya manta duk sauran damuwar shi ya dawo dai-dai. Suna fitowa sanye da riga baƙa yayin da Abdul yasa wando fari, shi kuma Fadil ya saka baƙi sunyi kyau sosai idan ka gansu. Sai dai duk da haka Abdul ya ɗara Fadil ɗin kyau, Saleema tayi sallama ta shigo jikin ta sanye da abaya baƙa tayi rolling da farin gyale. Murmushi ɗauke a fuskar ta, Fadila da Husna da suka fito, suka kalli juna Fadila ta kwashe da dariya yayin da Husna ta ja tsaki. "Yaya Abdul dan Allah mu tafi kawai", faɗar husna kenan cike da kishin ƴar uwar tata kuma yayar ta. Saleema ta dubi Abdul tace; "fita zaku yi ne?", gira kawai ya ɗaga mata tayi murmushi tace; "da naga babu abinda zan yi ne shine nace bari nazo muyi fira amma tunda fita zaku yi shikenan bazan dakatar daku ba Allah ya kikaye hanya". Abdul ya ɗan yi jim sannan yace; "ko dai zakije ne kinga sai muyi having fun tare?", Saleema ta ɗan yi dariya tace; "anya kuwa naga tafiyar ta yara ce amma tunda anyi mini tayi bana ƙi ba", da fadil da fadila suka kwashe da dariya saleemar na taya su. Abdul kuwa kallon shi ya kai kan Husna yana sakin wani murmushi na rainin wayo, Husna kamar tayi kuka ta juya. Fadil yace; "ya haka Husna kizo muje mana", cike da jin haushi tace; "ba zani ba na fasa", kan su ce wani abu ta shiga ɗakin Hajja. Basu ƙara bi ta kanta ba suka yi waje, Abdul ke tuƙi a motar Saleemar yayin da Saleema ke gefen shi sai Fadil da Fadila a baya. Ba wani fira suke ba dan Abdul ya maida hankalin shi kan tuƙi ne, ita kuma Saleema kacokan ta maida hankalin ta kan kallon shi, tana jin wani irin wuta ta ƙaunar shi kuma tane me fatan zamowa mata agare shi duk da tarin kunya da matsalar data hangowa a game da hakan. Sun ɗan taɓa tafiya sannan ya juyo ya kalle ta yace; "Gamji get ko Peach palace?, wani irin abu taji daga kanta har zuwa ƙafafunta wanda yasa ta koma ta jingina da kujerar tana me lumshe idanu. Tsinkayar muryar Fadila suka yi tana faɗin; "Abdul B mall Pls", ya juyo ya kalle ta sannan yace; "shikenan muje can ɗin kawai". Yana tada motar ita kuma tana tsallako titin zata shiga unguwar su hakan yasa ya ɗan bangaje ta, da yake bangazar mota ne da mutum dan haka sai da ta faɗi kayan hannun ta suka zube. Cikin sauri ya fito yana jan Innalillahi, suma su Fadil duk suka fito, kusa da ita ya ƙarasa yana taimaka mata wajen miƙewa. Sai da ta miƙe tsaye sannan ya tsuguna yana tattaro mata kayan da suka zube sai dai abin ban haushi duk wasu sun fashe don taje kasuwa ne ta siyo, Flask, glass cup dinner set sai kuma plates na roba wanda Ummi ta bata kuɗi akan ta siyo mata. Anyi sa'a dai dinner set ɗin da kayan robobin basu fashe ba amma flask da glass cup duk sun fashe. Ya ɗauko dinner set ɗin da robobin ya zuba mata a ledar, ta ɗan ƙuje saman goshin ta sai kuma gwiwar hannun ta. Sai da ya fara miƙa mata kayan sannan ya ga fuskar ta, gaban shi ya faɗi ganin yarinyar rannan wacce ya buge har ta nemi ta zage shi. Itama Nusram gaban ta sai da ya faɗi sannan jikin ta ya ɗau rawa, ita kuwa bata son idanun wannan mutumin a kanta, ta kauda kai. Abdul ya taɓe baki sannan yace; "kiyi haƙuri kuskure ne, ga wa'innan sauran kuma sun fashe". "babu komai ai tsautsayi ne, na gode", ta faɗa in cool voice tana amsar kayan, mutanen dake wajen dai cece kuce suke yi. Ya juya wajen Fadil yace; "akwai kuɗi a hannun ka?",Fadil ya girgiza kai yace; "babu wallahi Atm ne kawai". Saleema da tausayin yarinyar ya kamata tayi saurin zaro kuɗi cikin jakarta dubu goma sha biyar ta miƙa ma Abdul akan ya bata. Yayi murmushi yace; "thanks", sannan ya amsa ya miƙawa Nusram. Nusram ta girgiza kai tace; "ba sai kun biyani ba tunda Allah yayi saiya fashe koba ta sanadiyar ku ba zai fashe ɗin". Abdul ya damƙo hannun ta, wani yar suka ji gaba ɗaya hakan yasa ya kuma riƙe hannun, ita kuma da sauri ta ɗago ta kalle shi, kuɗin ya saka mata a tafin hannu sannan yace; "ba wai biyanki muka yi ba kya rage asara kiyi hakuri", daga haka ya saki hannun ta ya juya ya bar wajen. Har suka tada motar suka tafi tana tsaye a wajen kamar statue sai da taga ɓacewar su sannan taja numfashi ta damƙe kuɗin ta juya ta fara tafiya itama jiki a sanyaye, mutanen wajen suna ta faɗin Allah ya kyauta amma ko samun damar amsa musu bata yi ba. #LIKE #SHARE #COMMENT #FOLLOW @ WATTPAD 13DEEJA #VOTE *ga tambaya yau dai ku amsa mini naga masu bibiyar buk ɗin nan*. -waye yafi birge ki a cikin su kuma ki kawo dalilin da yasa yafi birge ki?. -wacece a cikin ukun nan kike tunanin itace jarumar littafin *Saleema,Nusreen ko Nusram* sannan ki kawo dalilin ki?. -shin ko zaki iya cankar meke saka Malama kuka? Kuma menene dalilin da yasa Brr Farida tafi son Abdul kan sauran yaranta?. -wai meke tsakanin Brr Farida da Brr Hauwa da yasa basa zama waje ɗaya, kuma meke tsakanin Brr Farida da surukanta wanda yasa bata son yayan ta suje gidan musamman ma Abdul?. -Wai waye a tunanin ki su Tuge suke son kaiwa gaban matsafin su domin su bada jinin shi?. -zuwa yanzu wane darasi kika koya daga wannan littafin? Idan babu ko ɗaya shin kina ganin a nan gaba zaki dauki wani darasi a ciki?. -ya kika ɗauki littafin a ranki? *bari muga wa'inda ke bibiyar littafin, idan kun amsa mini a dadinku ya kai na cigaba da idan baku bani amsa ba na dakata da littafin* *Babyn Abdul, Maman Elham, Farouk da Meenal*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *Zulaihat isma'il kamar yadda na alƙawaranta ga page ɗin ki ke ɗaya na gode sosai* *Aunty oum deedat ina godiya sosai keda Aunty Ummee*. *My Aunty Fatima mazadu barka da dawowa Allah ya kawo twins next time ya kuma raya mana baby*. *ibnatu Baballe kinfi kowa son littafin nan kema na gode da kulawa* 📖📖17-18📖📖 Abin ya haɗe mata biyu ga yanayin da take ciki ga kuma dama sanyin da take dashi dan haka sai taga kamar an ƙarawa gidan nasu tsawo. Tana shan kwanar lungun gidan su ta haɗu da Isa zai fito hannun shi riƙe da jaka, yana ganin ta ya washe baki, ita kuwa ta saukar da kanta ƙasa tana ƙoƙarin wucewa. Ganin bata tanka ba ya gane Nusram ce dan haka ya ƙara washe baki sosai yana faɗin; "ƴar ƙanwa ta har an dawo", sosai mamaki ya kashe Nusram ganin ba haka suka saba ba a duk lokacin da suka haɗu hantara ce da tsana ke biyo baya. "dama ina so muyi magana dake anjima fatan zaki tsaya ki saurare ni", ya katse mata tunani. Kai kawai ta ɗaga mishi domin har yanzu tana jin hannun wannan mutumin a jikin ta ga yanayin daya saukar mata a jiki. "yauwa ki same ni anjima bayan isha'i anan waje", nan ma dai ɗaga kai kawai tayi, daga haka ya wuce itama kuwa ta wuce. Tana shiga ta tarar da Aziza da Ameera suna wanke-wanken kwanukan da suka yi talla yau gefe kuma sahura keta rizgar kuka. Nusram ta matsa kusa da ita tace; "Sahura lafiya kuwa?", Sahura cikin zubar da hawaye tace; "Nusram har yanzu Idris be zo ba biko ni kuma na gaji da zaman gidan nan wallahi ina so na koma ɗaki na". Sai da Nusram ta waiga taga babu kowa sannan taja Sahurar suka yi wajen famfo, ƙasa-ƙasa gudun kada a jiyo su tace; "Sahura ki faɗa mini ainihin abinda ya haɗaki da mijin ki". Sahura ta ɗanyi shiru sannan tace; "Wallahi Nusram komai yana kawo mini ya ajiye to wani lokacin bana da kuɗin adashi shine sai na ɗauka na siyar ko kuma idan ina so na canza wani abin kamar shinkafa ko taliya tofa shine mamar shi ta faɗa mishi wai satar abinci nake mishi shine ya mini faɗa ni kuma naja tsaki shine ya tsinka mini mari ya koro ni gida". Nusram ta ɗan yi jim sannan tace; "kinga Sahura ki yiwa kanki karatun ta natsu ki tsaya ki gyara gidan auren ki, ki san yadda rayuwar gidan nan take idan kuma ba tallan kike so ki sake komawa cikin shi ba to shikenan, kina ganin yadda har yanzu muke fama da rayuwa gashi nan Allah be kawo mana masoya ba da wuri dan haka ki tsaya ki yiwa mijin ki biyayya, ki bani number ɗin Idris ɗin zan neme shi gobe duk yadda muka yi zaki ji". Sahura ta washe baki tana faɗin; "wallahi kinfi Nusreen hankali ke har Baba kinfi shi hankali, gashi nan ina so na koma ina tsoron na tunkare shi". Nusram tayi murmushi har dimple ɗinta ya lotsa tace; "kai Sahura kece ai tun farko baki fada mishi gaskiya ba, ki bani zuwa gobe sai na neme shi kawai". Sahura tace; "yanzu kuwa ƴar uwa Allah ya baki miji wanda yafi ɗan gote kuɗi muzo mu kwashi arziƙi", Nusram ta kwashe da dariya tace; "kada kiyi mini wannan fatan ai kuma sai abin ya shafe ku, kuna son gani na abu ya gagara ke dai bani kawai kada wani yazo ya gan mu tare, idan zakiyi mini addu'a kice ne Allah ya bani nagari". Sahura ta janyo wayar ta Techno T345 ta nemo number ɗin shi da ƙyar sannan ta bata, ita kuma Nusram ta kwafe Number ɗin. Tana miƙawa Sahura wayar ta Mama Jummai na fitowa daga ɗaki, ta kama baki tace; "au yanzu kuma abinda aka koma kenan? Kai ni Jummala ina ganin abu a gidan nan, ke kuma uwar me kike tare da wannan uwar matan?". Sahura ta zumɓuro baki tace; "kai Mama wannan ai tsakanin mu ne ba sai kinji ba", Mama Jummai tace; "ni kike faɗawa haka wallahi idan baki baro wajen nan ba sai na kusa karya ki". Ta ƙara zumɓurar baki tace; "ai shiyasa nake so na koma gidan miji na kona huta da matsalar ki, kinji Nusram sai gobe kawai duk yadda kuka yi ki neme ni". Mama Jummai ta buga salati tana tafa hannu; "Sahura ba dai mijin ki kika bawa wannan ba? Sahura yaushe zakiyi hankali ki fahimci me sanki ne da wanda basu son ki, shikenan ta fitar mini da ƴa ita kuma tana so ta shiga gidan wallahi bari uban ku ya dawo sai na faɗa mishi". Nusreen dake tsaye a ƙofar ɗaki dan hayaniyar Mama ta fito da ita taja tsaki tana faɗin; "me za'a yi da wannan me zubin ƴan daudun". Nan Mama Jummai tayi kanta dama kamar jira take yi, ita dai Nusram ɗaki kawai ta shige domin bata da lokacin tsayawa shirmen su dsn yanzu abin ya dena bata tsoro ya koma bata dariya suyi ta abu kamar ƙananan yara. Ummi dake tsaye bakin ƙofa Nusram tace; "Ummi dan Allah kizo ki zauna ki ƙyale wa'innan da suka koma kamar Annabi da kafiri". Ummi ta shigo ɗakin ta tsaya kusa da ita tace; "Nusram faɗa mini gaskiya meya haɗa ki da Sahura kuma meta baki a wayar ta". Nan Nusram ta kwashe komai ta faɗa mata, Ummi ta ɗan yi jim sannan tace; "eh to hakan ma abu ne me kyau amma baki tunanin wata matsalar ta biyo baya?". "insha Allahu babu abinda zai biyo baya sai alkhairi", abinda Nusram ta faɗa kenan tana maida kallon ta kan Nusreen ɗin data shigo tana faman haki. Ummi tace; "ke wai yaushe zakiyi hankali ne, wannan fa matsayin mu ɗaya da ita a wajen ku amma ke kullum baki da abokiyar faɗa sai ita". Waje ta nema ta zauna tana faɗin; "zan dena ne Ummi, Ramluv muga kayan?", Nusram ɗin tayi banza da ita. Nusreen ta taɓe baki, "nifa na shiga uku na manta nayi alƙawarin denawa yanzu sai na sake ladabi kenan", ta faɗa cikin ranta. "wallahi Ramluv na manta da munyi alƙawarin na dena kuma ai kinga itace ta fara nema na da faɗa, kiyi haƙuri ba zan sake ba na miki alƙawari". Nusram ta mata wani kallo sannan tace; "alƙawarin ki na banza Nusreen anjima nan karya shi zaki yi dan haka ki hutar da bakin ki kawai bana buƙata", daga hakan ta juya ta maida kallon ta kan Ummi sannan ta fara bata labarin abinda ya faru amma ce mata tayi kawai tazo tsallaka titi suka bugeta ta kuma ɗauko kuɗin ta nuna ma Ummin. Ummi tace; "Allah sarki an gode sosai amma kuɗin yafi na kayan da kin sani ma baki amsa ba". Nusram tace; "wallahi Ummi naso naƙi amsa amma yadda suka bani tasa dole na amsa", Ummi tayi ajiyar zuciya tace; "shikenan ai". Nusreen tace; "yauwa Rimluv sai mu siyo cooler kawai dashi", Nusram tayi kamar bata ji ta ba, Ummi tace; "eh hakan yayi idan yaso gaba sai ku siyo flask ɗin". Nusram tace; "shikenan Ummi yadda kika ce haka za'a yi", Ummi tace; "yauwa Allah yayi muku albarka amma cooler ɗin ki siyo ku biyu". Nusram tayi murmushi tace; "Ummi cooler ta nawa-nawa kenan ki bari dai gaba idan na sami kuɗi na sayi tawa". Haka Nusram ta ƙara yinin ta tana me share Nusreen ɗin, ita kuma Nusreen ɗin abin duk ya dame ta hakan yasa ta dinga aunawa Mama Jummai harara a ganin ta itace silar ɓatawar ta da ƴar uwar ta. Da daddare suna zaune suna cin abinci, Baban nasu ya shigo kamar ko wane lokaci be amsa sannu da zuwan da Ummi da Nusram suke mishi ba. Suna jiyo lokacin da Mama ke faɗa mishi ƙarya da gaskiya akan wai Nusram tana so ta ƙwacewa Sahurar miji. Nan ya fara bambami tun daga ƙofar ɗakin nasu, yana faɗin; "ba'a nan gidan ba kina babbar banza har yanzu kin kasa fitar da miji yanzu kuma muguntar da zaku koma kenan?". Nusreen ta cuno baki, yana ƙarasowa kusa dasu ya rarumi itace yayi kansu, Nusreen dai Allah ya taimake ta tayi ɗaki da gudu dan haka dukan akan Nusram aka sauke shi. Babu wanda yace yayi haƙuri sai Sahura dake ƙoƙarin fahimtar da Baban ba haka bane, amma ina bema bi ta kanta ba, Isa ne daya shigo yayi kan Baban ya samu ya ƙwace itacen yana bashi haƙuri. Tunda yaga Baban na duka ita kuma bata motsa ba ya tabbatar mishi da Nusreen ce, dan haka yaje ƙwatar ta. Allah yasa beji mata ciwo ba sai dai duk jikin ta ya tashi, kuma ko ɗigon hawaye domin kuwa idan da sabo yanzu ta saba da dukan baban nasu. Isa yace; "Baba kayi.mata haƙuri ba zata kuma ba, ke Nusram ki sako hijabi ki same ni a waje", bata amsa ba domin baƙin cikin dake cikin ranta. Yana fita itama ta miƙe ta shige ɗaki domin zuwa lokacin Nusreen ɗin ta buɗe ƙofar tabbatar da cewa Baban ya fita zuwa lokacin. Nusreen na ganin Nusram tace; "Ramluv ki dena tsayawa Baba na dukan ki", wata irin tsawa ta daka mata sosai Nusreen ta tsorata dan haka ta ja baya. "idan ma ya kashe ni ina ruwan ki, ko kina da asara ne?", Nusreen kam ta kasa magana sai dai binta da idanu dan ta san tana misbehave zata iya jibguwa a hannun ta dan idan tayi zuciya babu kyau. Nusram taja tsaki sannan ta ɗauki hijab ta fice, Mama Jummai na zaune tana guɗa tana kuma sakin habaici. Nusram ta matsa kusa da Ummi tace; "Ummi zan je kiran Isa ba zan daɗe ba zan dawo", Ummi ta ɗaga mata kai kawai, ita kuma ta juya ta fice. A saman dakali ta same shi zaune, jiki na rawa ya miƙe yana bata wuri ta zauna, Nusram dai abin har mamaki yake bata. Sun ɗan jima a haka yana kame-kame kafin yace; "abinda yasa na kira ki shine, kinga wannan dukan da Baba yake miki bana jin daɗin shi kwata-kwata shi yasa na yanke wani hukunci akan mu ni da ke, kinga dama banyi aure ba kema kuma kina zaune bakiyi aure ba shine nace me zai hana mu auri juna kawai". Wani irin bugawa zuciyar ta tayi bata taɓa kawo haka ba idan tayi la'akari da yadda yake ɗaya daga cikin maƙiyan su na cikin gidan, cikin kiɗima da tashin hankali tace; "me kace Isa ban fahimta ba?". Yace; "ina nufin mu dai-dai ta kanmu kawai ki amince mini naje da maganar gaban Baba akan cewa mun dai-daita juna a ɗaura mana aure hankali kwance na san Baba ma zai yi farin ciki sosai domin hakan kamar taimakon juna ne". Wani irin gumi ne ya karyo mata tasa hannu ta share, miyan da zata haɗiya ma.ya gagare ta, gaba ɗaya ƙwaƙwalwar ta bata aiki hakan yasa kawai ta lumshe idanu tana me karanto duk addu'ar da tazo ranta. Can wata dabara ta faɗo mata rai dan haka ta kalle shi tace; "Isa ka bari naje nayi tunani a kai", ya jinjina kai yace; "shikenan na baki wannan damar amma ki sani idan har kika sake kika ƙi amince mini wallahi sai na faɗawa Baba cewa mun amince da juna sannan kuma in aure ki in gallazawa rayuwar ki sai kin gwammaci zaman ki a nan gidan dan haka kada ki sake ki ƙauracewa magana ta". Nusram ta girgiza kai hawaye ya zubo mata tace; "dan Allah Isa ka bari na san abinda zan yi akai", Isa ya ɗaga kafaɗa yace; wannan kuma ruwan ki ne?", yana gama faɗin hakan ya wuce ya barta a wajen. Ta saka hannu ta share hawayen daya zubo mata sannan ta juya domin shiga gida. Cikin sauri Naufal yace; "Nusreen", jin sunan yasa taja tsaya, juyowa tayi tana kallon su, mutane biyu ne a tsaye kasancewar da hasken farin wata kuma suna cikin hasken yasa ta hango su sai dai basa kusa hakan yasa bata gane ko wasu waye ba. Jiki a sanyaye ta ƙarasa kusa dasu, ta bisu da kallo Nuafal yace; "sannun ki ko?", ta kalle shi sannan ta kalli wanda ke gefen shi gani take kamar ta taɓa ganin fuskar amma ta manta waye. "yauwa sannu", Naufal ya kuma cewa; "dama muna neman wanda zai kira ki ne ashe kece ma a nan waje". Cikin tsananin kisha Shureim yace; "fisabilillahi haka muka yi dake? ni ina can na kasa samun sukuni saboda zullumin amsar da zaki bani amma ke kina nan kina rayuwar ki tare da wani na wai ya kike so nayi ne?". Naufal ya galla mishi harara domin tunda suka fahimci itace Shureim ɗin yaso yaje ya yiwa saurayin nata rashin mutunci ya hanashi kuma ko yanzu sai da yace; "idan tazo kada yayi mata maganar". Nusram tayi murmushi domin sai yanzu ta fahimci waye domin kuwa Nusreen ta faɗa mata yadda suka yi, tace; "ya jikin Mama fatan anyi aikin cikin nasara?". Shureim yace; "kinga ni ba wannan na tambaye ki ba waye wancan daya tafi yanzu?", Nusram ta koma yin dariya sannan tace; "baka gane ni ba ko? To ni ba Nusreen bace ƴar uwar Nusreen ɗin ce dai Nusram". Wayyo! Ji yayi kamar ƙasa ta tsage ya shige, shifa tsabar kishi ya manta cewa su ƴan biyu ne, ya shafa kai yace; "ayya! Wallahi na ɗauka itace, aikin kam anyi shi sai dai mu jira sakamako kawai". Tace; "to Allah yasa muji alkhairi bari na kira maka Nusreen ɗin", tana faɗin haka ta juya ta tafi. Naufal ya kalli Shureim yace; "wallahi yau Allah ya taimake ka amma daba haka ba yau da babu me kwatar ka sai Allah kai da ba'a gama amicewa da kai ba amma har ka sami bakin tuhuma Allah ya soka". Shureim yayi murmushi yace; "Allah sarki baiwar Allah, me kyawun hali ga hankali", cikin tsokana Naufal yace; "to kodai ita zaka komawa ne?", Shureim ya harare shi. Nusram kuwa ganin saurayin ƴar uwar nata ya ɗan rage mata damuwa kaɗan don haka da ƴar ƙarfin gwiwar ta ta shiga gidan. Nusreen na zaune Kubra na saman ƙafar ta yayin da take shafa mata magani Ummi kuma na gefe suna fira. Da sallama ta shiga kafin ta zauna kusa da ƴar uwar tata cikin farin ciki ta kalle ta tace; "yauwa Rim kawo Kubrar na ƙarasa shafa mata maganin kije waje kina da baƙo". Nusreen ta washe baki domin kuwa ta san Alƙah ne ya taimake ta har Nusram ɗin ta sauko ta san zuwan mutum ɗaya ne zai dawo da walwalar ƴar uwar tata amma duk da haka cikin salon tsokana tace; "waye kuma?". Nusram tace; "waye kuwa banda Shureim yana nan a waje dan Allah tashi kije kada ya gaji da jira", Nusreen ta taɓe baki ita ta rasa me yasa ƴar uwar tata ke sonta da Shureim ɗin. Nusram ta miƙo mata hijab wanda yake a linke tace; "amsa ki saka tashi maza kije", to ya zata yi da naciyar Nusram ɗin gashi tunda ta lura Nusram ɗin na son ta dashi take ganin zata iya amsa mishi. Amsa tayi ta saka sannan ta yiwa Ummi sallama ta fita, Nusram tace; "yauwa Rim a dawo lafiya", Nusreen ta girgiza kai tana dariya kawai. Tana fita ta hango su yanzu sun dawo inda su Nusram suka zauna ɗazu domin nan babu hasken wata sai dai ta san su biyu ne kamar koda yaushe dan haka ta hade fuska domin janyowa kanta girma ta fara takawa zuwa inda suke. Tunda ta fito Shureim ya zuba mata idanu kamar ya maida ta ciki haka yake ji, da sallama ta ƙaraso suka amsa mata sai da suka gaisa sannan Naufal yace; "munzo jin amsar mu ne me aka yanke?". Nusreen ta dan yi jim sannan tace; "akwai alƙawari da na yiwa ƴar uwata zan jira ta har zuwa ta sami mijin aure dan haka idan kaima zaka iya haƙura zuwa lokacin shikenan". Naufal yayi murmushi yace; "kafin ayi maganar aure ai za'a yi ta soyayya ko yanzu ita ta kawo mu", Nusreen tace; "tunda ƴar uwata tana sona dashi nima na amince ko dan farin cikin ta". Naufal yace; "ah lallai mun gode sosai sai ki miƙa mana gaisuwa gare ta, lallai na jinjina mata kuma tayi mana ƙokari", Shureim yayi ajiyar zuciya yace; "Alhamdulillahi na gode sosai". Naufal yace; "yanzu shikenan zamu sami Baba mu nemi izinin shi dan ya san da zaman mu", Nusreen tace; "shikenan", nan dai suka ɗan taɓa fira. Suna daf da yin sallama Baban ya iso, da torch light ya haska su, ganin Nusreen yasa yace; "to ƴar banza yau kuma iskancin har ƙofar gida na?", Nusreen ta zumɓuro baki cike da jin haushi. Su Shureim suka gaishe da Baban ya amsa sannan ya maida kallon shi kan Nusreen yace; "kin wuce kin bani waje ko kuwa?", ba dan ranta yaso ba tayi cikin gida. Baba ya kalli Shureim yace; "ku kuke lalata mini yara ko?", Shureim ya girgiza kai yace; "a'a Baba", Naufal ya ɗora da cewa; "dama munzo neman amincewar tane kafin muzo neman izini wajen ka". Baba yace; "su har wani neman izinin ta kuke yi?, waye yake sonta a cikin ku?", Naufal ya nuna Shureim. Baba ya kalli shureim yace; "yaro ya sunan ka? Kuma wacce kake so a cikin su?", Shureim ya shafa kai yace; "Nusreen nake so kuma sunana Shureim". Baba yayi murmushi yace; "Shureim in dai Nusreen ce na baka ita kaje ka turo magabanta ka kawai a tsaida rana bana so ta kai wata me zuwa a gida na". Shureim da Naufal suka kalli juna, su dai tunda suke basu taɓa jin anyi aure haka ba, Naufal yace; "to shikenan Baba mun gode sai dai wani hanzari ba gudu ba, Mahaifin shi ya rasu sai Mahaifiyar shi, Mahaifiyar shi kuma bata ƙasar tana can ƙasar Syria za'a mata aikin ƙafa to muna neman alfarma a bamu dama har zuwa lokacin da zata dawo". Baba yayi jim sannan yace; "shikenan Allah ya kaimu, kai fa idan har kana so zan iya baka ƴar uwar ta", Naufal ya girgiza kai yana faɗin; "a'a Baba ina da mata". Baba yace; "to shikenan amma ƙofa a buɗe take idan har da wanda kake ganin zai iya auren ta to kawai ka turo mini shi koda babu akwati sadaki kawai ya isa kaima kuma kada ka takurawa kanka", Shureim ya amsa da to. Naufal ne ya matsa kusa da motar shi ya ɗauko rafas ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ya haɗo da ƴar takarda, biron dake jikin aljihun rigar Shureim ya zara sannan yayi rubutu ya haɗa ya miƙawa Baba yace; "Baba ga wannan a saka mana albarka wannan kuma Number ɗin abokina ne dan Allah a bawa Nusreen ɗin ace ta kira shi dan Allah". Baba ya washe baki yana faɗin; "ah lallai za'a je daku na gode sosai Allah yayi albarka insha Allahu ina shiga zan bata", ya amshe yana saka musu albarka, nan suka yi sallama ya shige gida su kuma suka tafi. Ɓangaren Nusram kuwa tana gama shafawa Kubra magani ta ɗauketa ta kaita kan shinfiɗar ta, sannan itama taje tayo alwala tazo ta kwanta. Abubuwan da suka faru yau su suka dawo mata cikin kai, haka harta gangaro kan zuwan ta kasuwa da bigeta da wannan bawan Allah yayi, dawowar ta gida zuwa ga matsalar Sahura, dukan da Baba yayi mata da magan-ganun da suka yi da Isa. Tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata, yanzu ina zata saka kanta?, gaskiya ko aure zata yi ba zata auri Isa ba sanin cewa ba wai zai iya riƙeta bane. Ta miƙe ta zauna taja ajiyar zuciya tana ganin kawai gobe zata kai tallan kanta ne masallaci wanda ta yiwa sai yazo ya rufa mata asiri, to kina da tabbacin shi yana da hali me kyau?, abinda zuciyarta ta faɗa nata kenan. Sai dai duk halin da take ciki bata so Nusreen ta rasa wannan saurayin domin tana ji a jikinta zai zamewa ƴar uwarta alkhairi. Faɗuwar ƴar uwarta jikin ta ya katse mata tunani, Nusreen ta rungume ta tana dariya, Nusram ma cikin dabara ta goge hawayen fuskar ta. Ta ɗago Nusreen tace; "Rimluv ban labari na sha meya faru", Nusreen tayi dariya tace; "Ram na amince da Shureim domin shima ya amince da sharadi na". Nusram tace; "bangane ba? Wane sharaɗi?", Nusreen tayi fari tace; "sharaɗina mana na ba zai nemi aure na ba sai kin sami naki mijin". Shiru Nusram tayi na ɗan lokaci kafin tace; " haba Rimluv wannan wane irin sharaɗi ne?, gaskiya ki janye", Nusreen ta miƙe tana taɓe baki tace; "babu abinda zan canza". Har suka kwanta kowa da tunanin da yake yi, ita Nusram tunanin ta shine yadda zata nemo mafita akan abu biyu na farko shine matsalar ta da Isa na biyu kuma matsalar ta da Nusreen. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 Haka suka isa Mall ɗin cike da nishaɗi domin kuwa Abdul tunda suka rabu be kuma tuna abin ba, hakan yasa ya washe suka cigaba da farin cikin su. Sai da suka yi siyayya sosai duk inda suka gifta kallon su ake cike da sha'awa, Saleema kuwa yau ji take komai ya warware mata kamar damuwarta ta ƙare gata ga abinda zuciyar ta ke muradi. Shi yaja mata weelbasket ɗin ita kuma tana zaɓar abinda take so a haka har suka gama siyayyar sannan suka wuce park. Ƙayataccen waje suka samu suka zauna inda masoya kan zauna domin fira da kuma jin daɗin soyayyar tasu. Saleema tace; "Abdul ban san dalili ba amma yau naji kamar nafi kowa sa'a", yayi murmushi yana kashe ido ɗaya yace; "da gaske ko?". Ta ɗaga kai tana ƙara jin son shi har cikin ranta, wayar shi ya zaro sannan ya danna kiran mahaifiyar tashi. "Baby sai yau ka tuna dani ko?", ta faɗa tana dariya, Abdul ya shafa kai yace; "First love da safe ma munyi waya fa". "baka san yadda nake ji bane da ko awa ɗaya ba zaka yi ba sai munyi waya, ina kewar ka sosai", ta ƙarasa da alamar damuwa. Abdul yace; "nima nayi kewar ki Mom jibi zan dawo", Brr Farida tace; "taɓ ai kuwa gobe zan wuce Dubai", ya ƙwalalo idanu yace; "da gaske to gaskiya sai kin dawo zan dawo nima". Brr Farida ta kalli Sumayya dake gefen ta tace; "to ai ga ƙanwar ka nan duk ta damu ka dawo", cikin sauri Sumayya ta amshi wayar daga hannun mahaifiyar ta. "Yaya Abdul dan Allah ka dawo", ta faɗa cike da shagwaɓa, Abdul yayi murmushi yace; "sai idan Mum ta dawo kinji zan dawo kada ki damu nima nayi kewar ku sosai". Sumayya ta noƙe kafaɗa tace; "ni dai ka yiwa Mummy magana gobe ta barni nazo wajen ka". "shikenan zanyi mata magana nasan zata barki", Sumayya tayi ihun murna tace; "that's my lovely bro, bari na bata", ta faɗa tana miƙawa Brr Farida wacce ke faman hararar ta tunda taji ta ambaci zuwa wajen shi ta haɗe rai. Tana amsa tace; "kada ma ka fara dan ba zan bari ba", Abdul ya shafa kai yana murmushi wanda Saleema ke ƙara ɗimaucewa duk da waya yake yi yayinda ita kuma ta zuba mishi idanu. "Kai First love please ki barta dan Allah wallahi zan kula da ita", Brr Farida tace; "kaima ka san son da nake maka ba zaka taɓa neman abu na hanaka ba". Yayi murmushi yace; "nagode my Mum", Brr Farida tace; "babu komai gobe driver zai kawota and please ka kula da ita soaai dan bana so wani abu ya sameta dan zaman ta kusa da Brr Hauwa barazana ne gare ni". Abdul yace; "insha Allahu babu abinda zai same ta", nan suka yi sallama cike da ƙaunar juna. Ya kalli Saleema yace; "Aunty muje gida ko?", tayi murmushi tace; "yadda kace Abdul", yace; "to taso muje", babu musu ta tashi suka tafi. Abdul ya dubi Fadil da Fadila yace; "to ku kuma idan kun gama sai kuzo mu wuce", Fadil yayi dariya sannan suka miƙe. Haka suka dawo gida cike farin ciki, sai da suka ajiye Saleema a gidan su sannan suka wuce. Duka ɗakin Malama suka nufa, tana zaune saman sallaya dattijuwar akwai ibada koda yaushe cikin bautawa ubangiji take. Fadila taje ta kwanta a jikin ta, Abdul ya kalle ta ya taɓe baki yace; "katuwar banza kawai", Fadil yayi dariya. Abdul ya shiga bayi yayi Alwala sai da ya fito sannan Fadil shima ya shiga yayo tashi alwalar sannan suka tafi masallaci. Basu shigo gida ba sai bayan isha'i dan haka direct dinning area suka nufa inda dama duk mutanen ɓangaren na zaune a wajen. Suna zama Husna ta miƙe ta fara serving ɗinsu bece mata komai sai dai harara daya dalla mata. Ita kuwa batama san yana yi ba, dan haka abincin kawai ta zuba ta turo mishi gaban shi yaja ya fara ci. Koda ya gama tashi kawai yayi ya shige ɗakin Malama, Hajja tace; "wallahi ka fito daga ɗakin nan domin ba ita ta haifa mini Abubakar ba" kota kanta bebi ba. Kan gadon Malama ya faɗa kawai ya gaji sosai hutawa yake buƙata, ya gyara kwanciyar shi yana me jan tsaki, gaskiya idan Daddy ya dawo aiki zai fara ya gaji". Ya lumshe idanu fuskarta ta dawo mishi da sauri ya buɗe idanu, me kenan? Yarinyar da kwanaki ya ganta harta nemi tayi mishi tsiwa amma yau kuma ta canza hali koda yake dama mata ai canzawa suke kamar hawainiya". Ƙara gyara kwanciya yayi kawai yana kawar da tunanin ta, a haka barci ya kwashe shi me cike da abubuwan mamaki. #LIKE #SHARE ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖19-20📖📖 *MURAD* shine sunan dake mishi yawo a ƙwaƙwalwa, cikin tsakiyar daji yake masu dogayen bishiyoyo, babu abinda ke tashi a wajen sai wasu irin muryoyi cikin ɓacin rai da hargitsi suke ƙwala wannan kiran. Yasa hannu biyu ya toshe kunnuwan sa yana me tsugunawa a wajen, jikin shi sharkaf da zufa cikin ƙanƙanin lokaci numfashin shi ya fara sama-sama wanda a dai-dai wannan lokacin Malama ta ɗago shi a tsorace tana kiran sunan shi. Kamar wanda aka jefa rami ko rijiya me zurfi haka numfashin shi ya dawo, cikin tashin hankali da kiɗima ya buɗe idanun shi, Malama ke zaune tana tofa mishi addu'o'i gefen ta kuwa Fadila ce da Fadil duka idanun su na kanshi. A hankali numfashin shi ya dai-daita sannan idanun shi suka buɗe gaba ɗaya, kamar wanda aka watsawa ruwa haka jikin shi ya jiƙe sharkaf da zufa. Ganin ya dawo hayyacin shi yasa Malama cewa; "ka dena wasa da addu'a, ya zaka zo ka kwanta barci ba tare da kayi addu'a ba idan wani abu ya same ka fa ina kake so na saka rayuwa ta". Duka suka bita da idanu suna mamakin furucin ta, ganin kallon da suke mata ne ya tunatar da ita meta faɗa dan haka cikin sauri ta riƙo hannun Abdul tace; "bana da abinda zan faɗawa Kakarka da mahaifiyar ka don haka ka kiyaye", jinjina kai kawai yayi sannan ya fara ƙoƙarin miƙewa. Fadil yazo ya taimaka mishi har ya dai-daita a tsaye sannan suka yi musu sai da safe suka fice. Koda suka koma nasu ɗakin sai da yayi alwala sannan ya kwanta, yana kwanciya wayar shi nayin ƙara. Ganin wake kiran shi kuma baya son ɗaga mata hankali dan ya san har yanzu ba wai ya gama dawowa dai-dai bane dan haka ya maida wayar silent kawai ya koma barcin shi. Washe gari, da safe sai da suka shirya tukunna suka fito zuwa falo, akan dinning kamar kowanne lokaci suka same su, sanin halin Hajja yasa bema nufi kan dinning ɗin ba. Daga saman kujera ya gaishe dasu ɗaya bayan ɗaya suka amsa mishi, Husna da tunda ya fito take kallon shi don yayi mata kyau sosai. Jikin shi ƙananan kaya ne as usual, wando fari da riga blue gashin kanshi yasha gyara sosai, ƙafar shi sanye da slipper irin na maza shima kalar blue, babu abinda yake tashi a jikin shi banda ƙamshi. "Ina kwana Yah Abdul", be ɗago ya kalle ta ba yace; "lafiya", sosai amsa gaisuwar ya ƙular da ita amma sai ta share kawai. Sayyada kam babu ruwan ta hakan yasa gaisuwa sosai ke shiga tsakanin su har ya kan tsokane ta ma. Bayan sun gama karin nasu kowa ya kama gaban shi, Fadil da Fadila suka wuce wajen aiki, Husna da Sayyada suka wuce makaranta, Hajja da Malama kuma falo suka dawo suka zauna saman kujeru. Hajja ta saka glass ta ɗauki jarida ta fara karantawa yayinda malama kuma ke riƙe da husnul muslim tana karanta addu'o'i. Abdul kuwa yana kwance ne idanun shi a lumshe, a haka zaka zata barci yake yi amma kuma idanun shi biyu. Fuskar yarinyar jiya kawai yake gani, koda yayi ƙoƙarin kauda fuskar sai ya kasa hakan yasa ya ƙara gyara kwanciya kawai. Babu jimawa sosai Brr Hauwa ta fito cikin riga ja iya gwiwa da wando baƙi jeans, kanta kuwa tayi rolling da ɓaƙin gyale yayinda ta sako ƙaton shade. Dan kyau tana dashi kuma jikin ta baya nuna tsufanta domin macece me kwalliya, kan kujera ta ajiye jakar sannan ta zauna itama tana gaishe da Iyayen nata. Wayar Abdul tayi ƙara hakan yasa ya buɗe idanun shi sannan ya buɗe idanu, a hankali ya zaro wayar ganin me kiran ya sashi sakin murmushi kafin ya ɗaga. "Morning mom", daga can ɓangaren tace; "morning Baby ya ka tashi?", ya ɗan shafa kanshi sannan yace; "yadda kika tashi haka na tashi mama na". Tayi murmushi tace; "jiya na kira ka but u didn't pick d call hope kana lafiya dai ko?", lafiya ta lau kawai at dat time nayi barci ne kuma ban duba call logs ɗina ba yau da safe sorry". "Never mind, yanzu zan wuce airport ga Sumayya nan yanzu driver zai kawo ta ita da Adnan sannan idan na fita zan maka transfer na kuɗi domin bana so kan na dawo kuɗin hannun ka su ƙare kazo kana complain". "ba zan yi complain ba Mom kawai ki bari akwai enough kuɗi a waje na", cikin basarwa tace; "mun canza shawara inaji idan na gama abinda nake yi zan wuce England wajen Daddyn ku kawai sai mu taho tare dashi on monday". Abdul yace; "hakan ma yayi, zamu baro rigasa ranar lahadi kenan?", Brr Farida tace; "duk yadda kuka yi ma ya rage naku", yayi dariya kawai. Itama dariyar tayi kafin tace; "bari na wuce sai ka sauka idan na saka sim zan nema ka bye bye I love you". 'Love you too, take care", ta amsa da insha Allah", daga haka suka katse wayar, yana me jin daɗi. Brr Hauwa taja tsaki, Hajja da Malama dai babu abinda suka ce, Abdul yace; "Ina kwana?", kamar ba zata amsa ba sai kuma tace; "lafiya lau", daga haka ta miƙe ta fice. Shima Abdul ya taɓe baki kafin ya miƙe ya fice, Gidan su Saleema ya nufa, kamar yadda ya zata duk sun fice daga gidan sai Muhibba itama tana shirin fita. "ina zaki je?", tace; "zanje gidan su Nihal ne dan kaga nan babu kowa", ya ɗan shafa kanshi sannan yace; "fara taimaka mini da abinci tukunna", babu musu ta ajiye gyalen hannun ta tayi hanyar kitchen shi kuma ya zauna saman Sofa wacce take falon. Babu jimawa ta fito hannun ta ɗauke da tray, yam balls da kunun gyada sai Fried egg da tea da kuma bread. Sai da yayi bismillah sannan ya fara ci yayinda ita kuma Muhibba ta zauna tana zuba mishi idanu domin yanayin cin abinci ma abin kallo ne cike da natsuwa. Sai da ya gama ta maida kayan sannan ta fito, yana gaba tana bin shi a baya ganin ya nufi hanyar fita daga Estate ɗin yasa tayi saurin tsayar dashi. "Ya Abdul ina zaka ne?", sai da ya ɗan ja tsaki sai kuma yace; "akwai inda nake son zuwa ne", ta langaɓar da kai tace; "ko nazo na rakaka ne?". "jeki inda zaki je kawai", yana faɗin haka ya cigaba da tafiyar shi, ganin hakan yasa Muhibba biyo shi da gudu, koda ta ƙarasa inda yake be kalle ta ba kawai ya cigaba da tafiya a haka har suka fice daga gidan. 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 Nusram ta gama shirin ta hankali kwance, ganin tana da sauran lokaci dan yau sai bayan an sakko sallar juma'a zasu shiga makaranta. Ta kalli Nusreen wacce ke kwance tana malelekuwa saman katifa kunnenta kare da waya tana amsawa cike da farin ciki. Nusram ta taɓe baki tace; "kinibabbiya ana so ana kaiwa kasuwa", Nusreen tayi dariya tana juya idanu. Nusram ta ɗora da cewa; "zan je in dawo yanzu ba zama zanyi ba munyi waya da Idris yace mu haɗu a Juny Caft, ko zaki je ne", Nusreen ta girgiza kai kawai. Nusram ta juya ta fice tana faɗawa Ummi sai ta dawo, Ummi ta bita da adawo lafiya, kamar yadda suka shirya da Sahura akan zata fara yin gaba haka kuwa akayi. A can saman layin nasu ta iske ta, Sahura ta bita da kallo itace ƙanwar su a ƙalla shekara biyar zuwa huɗu tsakanin su amma ba zata nunawa Nusram ɗin ƙuruciya ba. Doguwar riga ta saka ta yadin rariya wacce aka yiwa ɗinkin gown ta buɗe sosai fari ne yadin da ɗige-ɗigen ruwan goro,hijab ɗin data saka kalar goro ne hakan ya ƙara haskaka kalar fatar ta. Fuskar ta babu kwalliya sosai dan haka a washe take, sai lips ɗin ta data sakawa man baki kalar orange me ɗan turuwa sosai tayi kyau. "muje mana idan kuma kallo na zaki tsaya yi to bismillah", Sahura tayi dariya kawai, me Keke Napep suka tare inda ya ɗauke su har can Sardauna crescent. Sanda suka shiga caft ɗin yana zaune yana jiran su, koda ya gansu cikin farin ciki ya miƙe tsaye. Baƙi ne amma kuma babu laifi yana da kyau, idan ka ganshi yaro ne ba wani babba ba, ga tsafta komai tsaf-tsaf hakan yasa Nusreen ke cewa ɗan daudu domin kuwa komai nashi a tsaftace yake harma yaso yafi wata macen ƙyale-ƙyale. A mutunce suka gaisa, sannan Nusram tace; "Idris kayi haƙuri naji duk abinda ya faru daga bakin ta kuma nayi mata faɗa dan haka insha Allahu ba zata sake ba, kaga zaman a gida bashi da wani amfani ka daure ka maida matarka kawai". Idris cikin girmamawa yace; "shikenan babu komai Aunty amma idan wani abu ya taso daga baya to gaskiya zan haƙura kawai". Nusram tace; "insha Allahu babu abinda zai faru, zata kiyaye na gode sosai dan Allah anjima kazo sai ka ɗauke ta". Idris yace; "shikenan ta shirya ɗin idan na dawo daga kasuwa saina biyo mu tafi amma ta sani wallahi mahaifiyar ta, idan ta faɗa mini mara daɗi tafiya ta zan yi". Sahura tace; "ai bama sai ka shigo ba kana zuwa ka kira waya ta kawai zan fito", Idris ya gamsu da hakan dan ya san wacece Mama Jummai. "to yanzu me za'a kawo muku?", Nusram ta girgiza kai tace; "Alhamdulillahi a ƙoshe nake sai dai ko matar taka". Sahura ta riƙe haɓa tace; "ni ba zan iya cin wani abu a nan ba kawai dai na gode", duka sai da suka yiwa maganar ta dariya, Nusram kam murmushi ɗauke a fuskar ta, koda ta ɗago caraf idanun ta a cikin nashi. Gabanta ne ya faɗi cikin sauri ta kauda kanta ƙirjinta na cigaba da dukan uku-uku, ta kalli Sahura da suke faman fira tace; "to ni dai zan wuce idan kun gama ki wuce gida kawai". Sahura tace; "ina zaki je?", Nusram da duk ta gama tsorata da yanayin kallon da yake mata tace; "zanje shagon Yaya Sulaiman ne ba zan jima ba zan dawo,sai anjiman ku", tana faɗin haka ta bar wajen cikin sauri. Abdul na ganin ta fita ya kalli Muhibba yace; "ina zuwa?", da sauri ta miƙe tana faɗin; "ina kuma zaka je wanda muke jiran fa br ƙaraso ba", be kalle ta ba sai ma key ɗin dake ajiye saman table ɗin ya ɗauka cikin sauri ya fice. Koda ya fito nan ya fara dube-duben inda zai hango ta, can ya hange ta harta tare abin hawa, dan haka cikin sauri ya nufi tashi motar. Ganin hakan yasa Nusram ɗin tace da Me Keke Napep ɗin su tafi kawai ko gama dai-daitawa basu yi ba. "shi kuma wannan me tayi mishi da zai dami rayuwar ta haka?, oh na shiga uku ni Nusram ko dai Aljani ne?", ita kaɗai take maganar ta. Leƙowa tayi aikuwa ita yake bi domin motar shi na bayan tasu, kaɗan ya rage bata yi suman zaune ba "idan kuma ɗan garkuwa da mutane ne fa?, to me nake dashi da har zan damu kaina", haka dai take da wasi-wasi a ranta har suka ƙaraso inda zata sauka. Ji take kamar kada ta sauka, "Hajiya.mun ƙaraso fa", me Keken ya sake maimaitawa, bata da yadda zata yi haka tayi shahada ta sauko daga ciki. Ta miƙa mishi ɗari biyar ta ƙara gaba cikin sauri kamar wacce ake hankaɗawa, Me keken na ta tsaya ta amshi canji amma ita bata wannan take ba. Abdul dake hangen duk abinda yake faruwa dan haka ya fito ya jingina da jikin motar yana kallon ƙofar shagon data shiga. Me keke kuwa ganin bata kulashi ba yasa yaja keken shi yayi gaba abin shi. Tana shiga tayi ajiyar zuciya tana me neman waje ta zauna tana maida numfashi, kamar wacce tayi gudun fanfalaƙi haka take jin ta. Sulaiman dake cikin ɗan ɗakin dake shagon yana hango ta dan haka yayi murmushi a ranshi yana faɗin; "Nusram kenan sarkin tsoro", ganin ba zata ƙaraso bane yasa ya miƙe ya nufo inda take. "kamo ta nan", abinda ya faɗa kenan wanda yasa Nusram ɗin zabura tana neman ficewa, Sulaiman ya kasa riƙe dariyar shi aikuwa ya dara. Nusram ta sauke ajiyar zuciya ganin wanda ya tsorata ta sannan tace; "Kai Ya Sulaiman dan Allah", shima cikin kwaikwaiyar yadda tayi yace; "Kai Nusram dan Allah". Ta shagwaɓe fuska kamar me shirin yin kuka, ya kauda kai yana dafe baki yace; "Lalala babu ruwa na", yadda yayi ba ƙaramin dariya ya bata ba, tana dariya tana tafiya zuwa inda table ɗin shi yake. Har ta wani manta da ɗan garkuwar ta, wanda ya kusa sace ta🤣, Ya Sulaiman kuwa cikin shagon ya shiga ya fara haɗo mata kayan da zata tafi dashi. Sai da ya haɗa tas sannan yazo inda take, cike da wasa da dariya suka gaisa yana yi yana tsokanar ta, wani tayi dariya wani kuma ta ƙyale shi. "wai ina waccen me tsiwar ne?", ta san wacce yake nufi dan haka tace; "me tsiwa yanzu tsuntsun so ke shawagi da ita a sama", ya ɗaga gira ɗaya ta jinjina mishi kai. Nan take bashi labarin yadda akayi da abinda Baba ya faɗa na ya bashi ita, Sulaiman ya zaro idanu yace; "Babu bincike?". Nusram cikin jimami tace; "kaima kamar ka manta halin Baba kenan?", Sulaiman yayi ajiyar zuciya sannan yace; "zan so haɗuwa dashi kuwa inajin gobe na shigo layin naku idan yaso duk abinda muka yi zan je na sami Abba shi zai san abin yi akai amma ya za'a yi a ɗauki ƴa kamar wata kaza a bashi haka kawai to ko kaza ce ai a bincika a gani ba ɓarawo bane", Nan dai yayi ta faɗan shi ita dai Nusram bata ce komai ba. "To ke kuma fa?, har yanzu?", Nusram cikin jimami ta bashi labarin abinda Isa ya faɗa, a zuciye ya miƙe tsaye sannan yace; wallahi yayi ƙarya a ɗauki ƴa me asali a bawa shege". Nusram dama ta san hali, cikin zuciyar ta tace; "aifa abin nema ya samu", cikin lallashi ta miƙe tace; "Ya Sulaiman nifa abinda nake so shine mu rabu lafiya ka san yadda Baba ke son shi yana faɗa mishi Baba yarda zai yi". Sulaiman yayi huci yace; "naga uban daya isa ya aura miki wannan ɗan iskan me kama da mata-maza", Nusram kamar tayi dariya amma tana tsoro yanzu abin ya ƙare akanta dan haka taja bakin ta tayi gum. "to yanzu dai mu ajiye maganar Isa a gefe, ayi ta Shureim tunda zaka shigo gobe zan faɗawa Nusreen ɗin sai tace yazo goben sai ku haɗu, yanzu bani kayan na wuce". Ya galla mata harara, Nusram tayi murmushi tace; "haba Angon Aisha", shi kanshi sai da ya murmusa sannan ya miƙe ya biyo ta. Yana gaba riƙe da kayan tana bayan shi haka har suka fito waje, tana ɗaga idanu ta sauke a kanshi aikuwa saura kaɗan ta faɗi saboda tsorata. Wannan wane irin mutum ne ace duk wannan daɗewar yana tsaye yana jiranta, shi kuwa Sulaiman bema lura dashi ba dan haka nesa dashi kaɗan suka tsaya. Abin hawa ya fara wuya idan akayi la'akari da lokacin Sallah daya matso, sun jima a tsaye kafin Sulaiman yace; "to kodai zaki koma shago ne ki zauna idan yaso in mun sauko daga masallacin sai na kaiki ko kuma lokacin zaki sami abin hawa?". Ta girgiza kai tana fadin; "a'a Yah Sulaiman kawai kaje masallacin ni zan tsaya Allaha zai kawo kaga ana saukowa zamu wuce makaranta kuma bana so waccen tayi ta jira na ka santa da ƙorafi". Ya ajiye kayan sannan ya ciro dubu ɗaya ya miƙo mata yace; "shikenan sai anjima idan kuma har an sauko kina nan to", ta amsa tayi godiya yayin da shikuma ya koma shagon domin shiryawa. Abdul da duk yana tsaye yana jin me suke cewa domin tazarar dake tsakanin su bata yi nisa sosai ba sannan kuma hankalin shi gaba ɗaya yana kansu. Nusram kuwa tsaye take amma kaɗan-kaɗan takan ɗago ta kalle shi, sai dai a yadda yake zaka ɗauka wayar dake hannun shi yafi bawa mahimmanci. Tayi ajiyar zuciya ganin ko kallon ta beyi ba sai dai ta makaro domin kuwa yana kallon yadda duk ta wani tsargi kanta kamar mara gaskiya, minti biyar suna tsaye a haka kafin ya ɗago sosai ya kalle ta shi take kallo amma ganin yana ɗago yasa tayi saurin kauda kanta. Kamar ta koma haka take ji, tana kallon shi ta gefen ido harya maida wayar shi cikin aljihu sannan ya fara takowa zuwa inda take. Ta kalle shi ganin ya nufo ta gadan-gadan yasa tayi saurin juyawa amma sai dai kan tayi wani taku ya ƙaraso inda take. Kayan hannun ta ya riƙo ganin taƙi saki yasa ya kalle ta, cikin sauri kuwa ta saki, yayi murmushi sannan ya fara takawa zuwa wajen motar tashi. Sai da ya kai kayan ya buɗe booth ya saka sannan ya juyo ya dawo, hannun ta riƙo ta cije ganin hakan yasa ya fizge ta da ƙarfi, ko tayi ihu bashi da amfani domin kuwa babu mutane sosai kasancewar duk sun tafi masallaci. Shagon Sulaiman ɗin ma ya rufe domin kuwa ta ƙofar baya suke bi su tafi masallacin tana ji tana gani ya buɗe motar ya saka ta sannan ya maida ya rufe ya zagaya ya shiga. Ita dai sai idanu babu baki ga kuma kirjinta dake dukan tara-tara,😂, haka har ya tada motar bata iya ce mishi komai ba. Ganin da gaske tafiyar zai yi cikin rawar murya tace; "dan Allah kayi haƙuri mu bamu da wasu kuɗin da zamu baka Baba na talaka ne Mama na itama talaka ce dan Allah ka kayi haƙuri ka sauke ni na tafi gida Mama na hankalin ta zai tashi haka ma ƴar uwa ta, wallahi bamu da wani kuɗi rufin asiri kawai muke dashi". Magan-ganun ta yake juyawa cikin ranshi, wato ita kallon me garkuwa da mutane take mishi kenan?, be san lokacin da murmushi ya ƙwace mishi ba. Ita kuwa ganin yayi murmushi yasa idanun ta kawo hawaye cikin sheshsheƙar kuka tace; "idan kuma masu yin fyaɗe ne kayi haƙuri ka maida ni gida Baba na zai iya kashe ni idan hakan ta faru Mama na kuma zata shiga damuwa sannan maganar idan ta fita za'a iya fasa auren ƴar uwata dan Allah kada ka lalata mini rayuwa ka bata sunan gidan mu kasa Mama ta sami abin yiwa Ummi gori",. Ga abin dariya amma babu halin yi hakan yasa kawai ya maida hankalin shi kan titi, ganin hakan yasa Nusram ta fara addu'a domin ta san yau tata ta ƙare cikin uku za'a yi ɗaya ko dai yayi mata fyaɗe ko kuma ɗan garkuwa da mutane ne ko ɗan yankan kai. Ta ciro wayar ta a hankali ta kalla, Number din Nusreen ta nemo ta tsurawa number ɗin idanu haka kawai taji wani kukan yazo mata shikenan ita kuma tata ta ƙare. Nima kaina nace; "Allah sarki Nusram RIP 😭. #LIKE #SHARE #COMMENT #VOTE #FOLLOW @13deeja *Babyn Abdul,Maman meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖21-22📖📖 Wayar dake gefen shi tayi ƙara ganin Muhibba ce me kiran wannan yasa ya dannan amsawa, "Haba Abdul kana ina ne?", abinda ta faɗa kenan?. "Abdul!", Nusram ta sake maimaita sunan a cikin ranta, inbox ta shiga ta rubuta summary ɗin abinda ya faru harda sunan data ki wata ta kira shi. Wayar na hannun ta tana juyawa tana me fatan koda ace ya kashe ta ne to wani ya tsinta domin kuwa bata ga alamun wasa ba a fuskar shi. "Nifa gani a hanyar gida kawai ki nemi abin hawa ki wuto gida", amsar daya bawa Muhibba kenan. Cikin jin haushi Muhibba tace; "haba Abdul amma dai ai hakan ba adalci ban.......", kafin ta ƙarasa ya katse wayar. Nusram data zuba mishi idanu, ta kauda kanta ganin sun ɗau titin da zai kai su Hayin Rigasa yasa ta saki ajiyar zuciya har sai da ya juya ya kalle ta. Dai-dai kwanar hanyar gidan nasu yaja ya tsaya wato inda ya bige ta, bece mata komai ba itama ganin hakan yasa tayi shiru tana saƙe-saƙe a ranta. Cikin ɗan ƙarfin hali ta kai hannu ta fara ƙoƙarin buɗe motar sai dai abin ban haushi taƙi buɗewa hakan yasa kawai ta koma yadda take ta zauna. Ta kalle shi, ba ita yake kallo ba kuma yaƙi ce mata komai, hakan yasa ta fara murza zoben hannun ta. Abdul dake kallon ta amma idan baka sani ba sai kace idanun nashi a lumshe suke saboda yadda yayi, shi jira yake ta nuna mishi hanyar da zasu bi ita kuma ta kasa fahimta. Nusram ganin zaman yayi yawa yasa ta kada baki tace; "dan Allah ka buɗe mini na fita", jin yayi shiru yasa ta sake kallon fuskar shi. "so cute", abinda ta faɗa kenan ganin idanun shi a rufe, sai kuma tace; "very arrogant", be san lokacin da murmushi ya suɓuce mishi ba wanda hakan ba ƙaramin kyau yayi mishi ba. Nusram kuwa idanu ta zaro tana me dafe ƙirji, ya buɗe idanun shi gaba ɗaya a kanta, sosai ta daburce har jikin ta ya fara rawa. "wai baki gaji da gani na bane da kika barni a nan?", abinda ya faɗa kenan, yadda yayi maganar idan ba kana kusa ba, ba lallai kaji ba. Nusram cikin in-ina tace; "to ai......to ai......to....ai kaine baka buɗe mini ba", shima cikin kwaikwayar ta yace; "to ai......to ai.....to....ai kece baki faɗa mini hanyar da zan bi ba". Hannu ta ɗaga sannan ta nuna mishi hanyar shi kuma ya tada motar ya shiga, haka tayi ta nuna mishi hanya har zuwa ƙofar gidan nasu wato lungu daga shi kana hango gidan su. Sai da ta fita sannan shima ya buɗe motar ya fito, boot ya buɗe ya ɗauko mata jakar kayan sannan ya ƙaraso inda take tsaye. Ita kuwa kallon shi kawai take yi tana yaba kyawun da Allah yayi mishi, mutum kamar balarabe, yaran dake wasa a wajen su kansu duk shi suke kallo don ganin balarabe a layin su. Ya miƙo mata jakar kafin yace; "nifa bana son yawan kallo", cikin sauri ta amsa sannan ta juya ta fara tafiya, Abdul kuwa yabi bayan ta da kallo, har tayi nisa sannan ta tsaya. Ta juyo ta kalle shi sannan tace; "na gode", ya jinjina kai kawai ita kuma ta juya sai dai idanun ta yayi mata mugun gani domin kuwa Isa ne a tsaye a gaban ta. Cikin masifa yace; "uban waye wancan daya ajiye ki", Nusram ta kauda kai gefe, cikin takaici yace; "wallahi baki isaba domin baki da mijin da ya wuce ni", ya nuna ta yace; "wato dan iskanci har yanzu baki bar bin maza ba kenan, kuma wai abin ban haushi balarabe kika komawa to wallahi tun kan ki bar mana abin faɗa yau zanje na sami Baba na faɗa mishi meke tsakanin mu". Nusram cikin sauri tace; "amma Isa ai ban riga na amince ba ko", shima cikin sauri yace; "wannan kuwa ke ta shafa", ya wuce ya barta a tsaye. Ta juya a hankali ta kalli inda yake tsaye sai dai babu shi, wato ya tafi tun ɗazu kenan?, taja ajiyar zuciya sannan ta shige gida. Abdul kuwa yana ganin suna magana da wani mutumi yaja motar shi ya tafi, yana tafe yana mamakin yadda har ya taimaki wannan yarinyar. Koda ya isa gida har an sauko masallaci hakan yasa kawai ya wuce ɗakin Malama, bayin ta ya shiga yayi alwala. Yana fitowa ta kalle shi tace; "lafiya baka sami sallah ba?", ya ɗan sosa kai sannan yace; "wallahi wani abu ne ya ɗauke mini hankali, kuma kan na iso an sauko". Cikin haɗa rai tace; "ka maida hankali akan addinin ka, ka dena wasa dashi", yace; "to Malama". Da kanta ta shinfiɗa mishi abin sallah ya hau ya fara, Malama ta kalle shi tayi murmushi. Bayan ya idar da sallar ya juyo ya kalli Malamar yace; "Sumayya tazo ko?", tace; "eh kana fita ɗazu ɓaka jima ba ta iso ina jin tana ɗakin Hajja ko kuma tana gidan Mukhtar(Abban Nihal). Ya jinjina kai kawai ba tare da yace komai ba ya haye saman gadon ta ya kwanta, baya son zuwa gidan Abban Nihal Allah ya sani har cikin ranshi, a haka har barci yayi awon gaba dashi. Malama ta matsa kusa dashi tayi mishi addu'a, tana kallon shi cike da tsananin ƙauna. Har su Fadil suka dawo tana zaune kusa dashi ta kasa tashi ta barshi, Fadil da Fadila suka kalli juna suna mamakin abinda Malama take yi akan Abdul kwata-kwata bata son abinda zai taɓa shi tun suna ƙanana haka rayuwar take. Fadil yayi gyaran murya da sauri Malama ta tashi daga kusa da Abdul, Fadila ta nemi waje ta zauna saman center carpet din dake shinfiɗe tana faɗin; "wash wallahi na gaji". Fadil ya harare ta sannan yace; "kamar wani aiki tayi a office ɗin ina kallo fa Hafeez ne yayi aikin kina gefe", tayi murmushi tana kauda kai gefe. Sumayya ta shigo da sallama sannan ta ruga da gudu tana ihu, Fadil ya buɗe hannu ta faɗa jikin shi. Firgigit Abdul ya farka, cikin sauri ya dafe kai sannan ya kalle su yadda suke ihu yaja tsaki. Su kam bama su san yana yi ba, Fadil kuwa ya koma kamar wani yaro sai biye mata yake yi, Abdul cikin jin haushin tashin shi da suka yi ya ɗauki filo ya cilla musu. Sumayya ta kalle shi ta shagwaɓe fuska, ya cilla mata harara kan yaja tsaki ya miƙe, Fadil kuwa dariya kawai yake yi dan ya san sun gama bawa Abdul haushi dan ya tsani yana barci a tashe shi. Bayin Malama ya shige, su kuwa bama ta shi suke ba dan haka suka cigaba da hayaniya a ɗakin, inda Sumayya ke basu labari su kuma suna dariya. Fadila tace; "ai ni kam naso zuwan Surayya ko dan na kwashi dariya", Sumayya tace; "taɓ kema kin san Aunty Surayya ba zata zo ba sai dai Daddy idan ya dawo". Fadila tace; "ai da yake Family meeting ya kusa zuwa nan da two months fa", Sumayya tayi ihu tana faɗin; "yes gaskiya naji daɗi". Abdul daya fito daga bayi yana nemi waje ya zauna ya dafe kanshi, Malama ta dafa shi tana tambayar lafiya. Yayi murmushi yace; "kawai hayaniyar wa'innan ne take damuna", Malama ta miƙe tana murmushi kawai. Sai da suka gama shirmen su sannan suka fice waje, Fadila ta kalli Abdul tace; "wallahi har ɗakin yayi shiru", bece mata komai ba sai wata harara daya jefa mata. Ya jima a zaune kafin ya miƙe ya fice, ɗakin su yaje yayi wanka sannan ya fito falo inda su Sumayya suke a zaune. ****** ******* ****** Ɓangaren Nusram kuwa tana shiga gida kamar yadda tayi zato, Nusreen keta surfawa Mama Jummai rashin kunya yayin da Mama Jumman take surfa mata zagi. Nusram tayi ajiyar zuciya kan tayi sallama ta shiga gidan, Nusreen na ganin Nusram tayi shiru sannan ta shige ɗaki. Mama Jummai kuwa cikin hargagi tace; "shegiya mara kunya ai da kin fito kin cigaba daga inda kika tsaya kuma ni nan na faɗa kuda aure wallahi sai dai kuga ana yi", Nusram dake daf da shiga ɗaki ta juyo ta kalli Maman kan ta juya ta shige ɗakin. "kya juyo ki kalle ni mana shegu masu yawon ta zubar", Maman Jummai kenan wacce ke sake cigaba da bambami. Nusram na shiga ɗakin ta sami Ummi na zaune tana ƙulla man ja da man gyaɗa yayin da Kubra ke gefen ta, tana wasa domin kuwa yanzu ta kan zauna har ma ta dinga wasa da abinda aka bata. Sannu ta yiwa Ummi sannan ta shige uwar ɗaki anan ta tarar da Nusreen tana ƙara gyara fuskar ta, domin su tafi makaranta. Jakar hannun ta ta ajiye sannan ta juya ta fice, alwala ta ɗoro tazo ta data sallah sai da ta idar sannan ta kwashi litattafan ta sannan suka tafi. Bata faɗawa Nusreen abinda ya faru tsakanin ta da Isa ba domin sanin hali yafi sanin kama, hakan yasa taja bakin ta tayi shiru. Basu baro makaranta ba sai yamma, Nusreen na rataye da jaka inda Nusram ke rungume da littattafai haka suka jero. Suna karyo kwanar lungun su suka hango Mahaifin nasu tare da wani mutumi wanda yake tsaye jikin motar shi. Nusreen da Nusram haka suka gaishe da baƙon baban nasu, hakan Baban nasu yayi ta washe baki shi kuwa baƙon bin su yayi da idanu kamar wani maye har lashe baki yake yi. Suna shigewa gidan ya haɗiye yawu sannan ya kalli Baban su Nusreen ɗin, Baban yace; "kayi haƙuri Alhaji Baballe insha Allahu nan da ƙarshen wata zan haɗo maka kuɗin ka". Alhaji Baballe ya girgiza kai yace; "a'a Malam Abdullahi dan dai dubu ɗari ai ba zai gagara na bar maka ba dan haka ni yanzu wata magana nake so muyi da kai". Malam Abdullahi yace; "ina jin ka Alhaji", Alhajin yace; "wa'innan ƴan shilan ƴaƴan waye ne?", Baba yace; "wai Nusreen da Nusram ƴaƴa na ne ka gansu nan sai dai garari a gari babu wanda yazo domin auren su na rasa yadda zanyi dasu". Alhaji Baballe ya washe baki yace; "to ai ni dai in dai ba'a musu miji ba sai ka aura mini ɗaya daga cikin su kawai", Baba ya washe baki yace; "aikuwa na gode da wannan alfarmar da zaka yi mini, sai dai Nusram da ita Nusreen wani yazo kwanaki duk da akwai yarjajeniya a tsakanin mu". Alhaji Baballe yace; "koma wacece ni dai a cikin su ina son ɗaya", Baba yace; "in dai Nusram ce na baka sai dai mu jira lokaci kawai". Alhajin yace; "ka tambayi yarinyar kada yazo bata amince ba dan itama tana da haƙƙi a kai", Baba ya ja tsaki yace; "ba dai kana son ta ba ai magana ta ƙare". Alhaji Baballe yace; "a'a fa kada a takura mata dan ka san yaran yanzu ka dai tambaye ta idan ta amince sai ka sanar mini ina jira". Baba ba dan son ranshi ba yace; "shikenan zan tuntuɓe ta ɗin", haka suka yi sallama da Alhajin sannan Baban ya wuce masallaci jin an fara kiraye-kirayen sallah. Cikin gidan kuwa suna shiga Nusreen ta ja tsaki tace; "banza maye kawai", Nusram dai bata ce mata komai ba. A bakin ƙofa suka sami Ummi tana kwashe abincin data gama nan suka yi mata sannu da zuwa. Ummi cikin farin ciki tace; "yauwa sannun ku ƴan mata na, yau da alamu anyi ciniki kenan naga babu ko ɗaya da kuka dawo dashi". Nusreen ta miƙawa Ummi kuɗin tana faɗin; "gashi ki ajiye wallahi kaya yau sunyi kasuwa gaskiya yau Yaya Sulaiman ya bamu kaya designer". Nusram kuwa tsintsiya ta ɗauka ta hau shara, sai da ta gama sannan ta ɗauki buta domin yin alwala. A bakin famfo ta sami Sahura, Nusram tace; "ke ina Idris ɗin?", Sahura tayi dariya tace; "yana nan mana amma mun canza shawara sai gobe zai zo domin yace yana so na ɗan gyara kafin na koma". Nusram tayi dariya tace; "ah lallai kace sababbin ango da amarya kuke kenan?", duka suka kuma yin dariya. Sahura tace; "dan Allah gobe idan baki da ayyuka masu yawa sai ki yi mini ƙunshi da kitson ko?", Nusram tace; "shikenan Allah ya kaimu amma kuɗin dubu biyar", Sahura ta riƙe haɓa tace; "ai wannan tsakanin ke da ƙanin ki", Nusram ta harare ta tace; "kinji wani daɗin baki". Nusram ta kuma cewa; "amma ya kamata a yau ki faɗawa Baba da Mama kada su ga kawai kin bi mijin ki gobe", Sahura tace; "shikenan sai yadda kika ce haka za'a yi", daga haka Sahurar ta bar wajen. Nusram tana idar da sallah kiran mahaifin nasu ya iso kunnen su, Nusreen ta taɓe baki tana faɗin; "wallahi matsalar gidan nan yawa yake dashi". Duka suka miƙe suka fice, ɗakin Mama Jummai zasu je kuma harda Ummi, tun daga ƙofar ɗaki suke jiyo bambamin Maman. Haka suka yi sallama suka shiga, Mama tace; "yauwa ku shigo ina kinibabbiyar take har ta san ta sasanta tsakanin miji da mata". Gaban Nusram ya yanke ya faɗi, ko daga ji ta san da ita take, suna zama Baba yace; "Ina Nusram?", Nusram tace; "gani Baba". Baban yace; me yasa kika haɗu da Idris har kike neman juyar mishi da tunani?", Sahura ta yi tsagal tace; "Baba wallahi ba haka aka yi ba nina same ta nace ina son na koma gidan miji na shine taje ta bashi haƙuri ni kuma tayi mini faɗa". Baba yace; "oh har kin kai girman da zaki sasanta aure kenan?", Nusram ta girgiza kai tana faɗin; "kayi haƙuri Baba ita ta same ni da maganar". Baba yace; "shikenan kin hutar dani ne kuma dama zaman nata ya ishe ni, magana ta gaba da nake so muyi shine akan ku", ya faɗa yana nuna Nusram da Nusreen. "ɗazu kun wuce ni da Alhaji Baballe, kun dai san shine manager a inda nake aiki to ya nuna yana son na bashi ɗaya daga cikin ku, na dai faɗa mishi Nusreen akwai wanda na bawa ita to ke Nusram tunda baki da kowa ke na bashi dan haka sai ki shirya ina ganin gobe ko jibi zai zo sai ku ƙara fahimtar juna, kuma na faɗa musu duka su biyun bana so bikin naku ya wuce wata ɗaya to amma dalilin shi Shureim wato manemin Nusreen ya bada uzurin mahaifiyar shi da bata ƙasar to hakan yasa na ɗaga ƙafa amma duk da haka bana so ya ɗara wata biyu nan gaba". Mama Jummai tace; taɓɗijam yanzu Abdullahi auren su Nusreen ɗin za'a yi lallai da sake", Baba yace; "me za'a sake ɗin, ai.magana ta ƙare nine mahaifin su kuma na tsayar musu da miji dan haka nan da ɗan lokaci kaɗan wallahi zasu bar gaba na haba na gaji kullum ni kenan ana zagi na babu dama na saka sabon kaya sai kaji ana cewa dama na bar yara a gaba na sunki aure ai dole na dinga shiga ina fita to wallahi ya isa haka dan haka aurar dasu babu fashi kai koda da almajirai ne sai na aurar dasu". #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 🎶🎶🎶 *Idanu na tsimin su ganka, Abdul kana ina*🎶🎶🎶 🎶🎶🎶 *Baki ya yawaita ambatan ka, hannu ya jinjina*🎶🎶🎶 🎶🎶🎶 *sanya mini shinfiɗa ta fuska, bango na jingina*🎶🎶🎶 🎶🎶🎶 *Abdul in zaka zo ka wulga, nima ba zan ƙi waiwaye ba*🎶🎶🎶 📖📖23-24📖📖 Nusreen ta zunɓuro baki sannan tace; "haba Baba muna ƴaƴan ka amma ka gaji damu, ai wannan babu adalci a ciki, gaskiya ni wallahi ba zan yarda ba aure kamar wasu kaji......", Baba ya kai mata duka cikin sauri ta kauche. Yace; "wallahi Nusreen tsakanin ni da ke zanga wanda ya isa da wani", bayan Ummi ta shige tana ƙunƙunai. Mama Jummai ta taɓe baki tana faɗin; "zan san abin yi don ba zai yiwu ba", babu wanda yabi ta kanta, Baba ya miƙe yana faɗin; "na riga da na gama magana". Ummi ta miƙe haka Nusreen, Nusram kuwa ta daɗe zaune ko kanta bata ɗago ba tana tunano halin da zata shiga, cikin dabara ta goge hawayen idanun ta domin bata so Aziza da Ameera su gani. A bakin ƙofa taci karo da Mama Jummai ta kalle ta tace; "ai wallahi da sake, zaman gida be ƙare muku ba tukunna dai", Nusram cikin jin haushi tace; "ai bake bace Allah" faɗar haka ta wuce ta bar Mama Jummai a tsaye. Mama Jummai kuwa bata kuma cewa komai ba domin Allah ya sani tana tsoron Nusram idan har tayi zuciya dan bata da sauƙi. Tana shiga ɗaki ta tarar da kowa na harkar shi dan haka itama zama kawai tayi, Nusreen ta dawo kusa da ita tace; "Ramluv ki kwantar da hankalin ki babu wanda zaki aura sai wanda kike so kinji". Nusram ta kalleta tace; "to yanzu waye yace miki bana son shi?", wani kallo Nusreen ɗin ta yiwa Nusram sannan tace; "Ramluv kada ki cuci kanki, na san cew......" da sauri Nusram ta ɗagawa Nusreen hannu sannan tace; "Rim dan Allah ki rabu dani barci nake ji haka", sanin halin Nusram ɗin yasa Nusreen miƙewa ta koma kusa da Ummi ta zauna. Nusram kuwa ganin haka yasa ta miƙe ta shige uwar ɗaka, kan katifar su ta faɗa sannan ta saki ajiyar zuciya, ita bata taɓa ganin rashin adalci irin wannan ba taya za'ace anyi aure kalar wannan?, hawaye suka gangaro daga idanun ta. Tana ji lokacin da Nusreen ɗin ke waya da Shureim baya ta shigo ɗakin ta kwanta, har suka gama Nusram bata bar zubar da hawaye ba domin kuwa abin yayi mata yawa, ji take kamar ta gudu ta bar gidan. Nusreen tana gama wayar ta juyo tana me haska bayan Nusram ɗin sannan a hankali tace; "Ram!", haka ta kuma kiran sunan amma shiru Nusram bata amsa ba, ganin haka yasa ta ja bakin ta tayi shiru domin ta sani yanzu tana misbehave sai ta daku a hannun ƴar uwar tata. Nusram kuwa tana jin Nusreen ɗin amma tayi banza da ita domin bata so Nusreen ɗin.ta gane halin da take ciki wannan zata barwa cikin ta ne don wata dama ce da Allah ya bata domin ƙubucewa daga hannun Isa sannan kuma domin bawa Nusreen ɗin damar yin aure. Duk yadda barci ya iya sata a daren nan sai da ya bar Nusram ta kuma sha kuka har ta ƙoshi sannan ta kaiwa ubangiji kukan ta domin shi kaɗai zai iya share mata hawaye. Ummi kuwa duk abinda Nusram keyi tana sane dashi, wannan yasa ta ƙudurce a ranta idan har Nusram ɗin bata son wannnan Alhajin to dole ne tayi fito na fito da Baban nasu akan wannan hukuncin domin ba zata so ƴaƴan ta su fuskanci irin abinda take fuskanta ba a gidan auren ta barin ma Nusram wacce take da zurfin ciki da kuma haƙuri. Nusram koda tayi sallar asuba komawa tayi ta kwanta domin kuwa barcin dama ba'a cin bashin shi a zauna lafiya. Nusreen shigowar ta uku kenan domin ta tashi Nusram ɗin ta karya amma abu ya gagara, zama tayi gefen katifar tasu sannan tace; "Ram dan Alƙah ki tashi", kamar ma bada ita take ba. Nusreen ta bubbuga filon da Nusreen ɗin ta ɗora kanta a kai, a matuƙar kasala Nusram ɗin ta buɗe idanu sannan tace; "Pls ki ƙyale ni haka ma Nusreen", Nusreen ta cuno baki tace; "Ummi tace ki tashi fa, ga abin karin ki har yayi sanyi". Nusram ta kuma maida idanun ta ta rufe kawai ta cigaba da kwasar barcin ta, ganin hakan yasa Nusreen miƙewa. Nusreen ɗin na cikin shiryawa Sahura tayi sallama ta shigo, Nusreen ta amsa tana me cigaba da abinda take yi, Sahura tace; "Nusreen ko Nusram", Nusreen taja tsaki hakan ya alamtawa Sahurar ko wacece. "Ina Nusram take?", cikin masifa Nusreen tace; "kin bani ajiyar tane?", Sahura ta ja tsaki ta juya wajen Ummi tace; "Ummi Nusram fa?", Ummi tace; "tana ciki tana barci ko tashi bata yi ba har yanzu". Sahura tayi hanyar uwar ɗakin, tana shiga ta fara tashin Nusram ɗin, haka dole tasa ta miƙe sannan ta kalli Sahura tace; "me kuma ya faru", Sahura ta washe baki tace; "lallai da kitso mana". Nusram ta dafe kai tace; "wallahi na manta gashi barci nake ji sosai", Sahura tace; "dan Allah kizo kiyi mini", Nusram tace; "to bari na karya", haka Sahura ta miƙe ta baro ɗakin. Babu jimawa itama Nusram ɗin ta fito tana zabga hamma, nan ta gaishe da Ummin sannan ta fita tayo brush ta dawo, Nusreen tace; "to ni dai na tafi". Nusram dake ƙoƙarin kai kunun bakin ta tace; "ina zaki je?", Nusreen tace; "zanje Tudun Nufawa Yaya Sulaiman yana nema na", Nusram ta sauke kofin daga bakin ta tace; "a dawo lafiya", Nusreen ɗin ta amsa da ameen tana me ficewa daga ɗakin. Sai da Nusram ta gama karyawa sannan ta miƙe ta cewa Ummi; "bari naje na siyo Lallen da zan yiwa Sahura", Ummi tace; "a dawo lafiya", doguwar riga ce a jikin ta kalar ruwan ƙasa ta ɗora hijab ruwan madara a sama ta fice. ******** ********* Kamar yadda suka saba a saman dinning suka tarar da ƴan gidan, haka suka bi su ɗai-ɗai suka gaishe dasu, kowa ya amsa musu amma banda Brr Hauwa. "lallai Farida ta samu sake idan banda haka mu data guje mu meye na turo mana yaran ta suzo su zauna damu?". Fatima tace; "wai meye haka ne Brr abinda kuke yi sam be dace ba", da sauri Hajja ta katse ta sannan tace; "faɗa mini abinda be dace ɗin ba?", Fatima ta juyar da kai sannan tace; "ni na tafi", Hajja taja dogon tsaki. Babu wanda ya kuma magana tsakanin su banda cin abinci da suke yi, Abdul kuwa wayar shi ce a hannun shi yake dannawa. Hajja ta kalle shi tace; "kai kuma ba zaka ci abincin bane", ya miƙe cikin sauri domin abinda Brr Hauwa ta faɗa ya bashi haushi yace; "Idan zan ci zanje gidan Abban Fadil naci". Ai kamar ya ƙara zuga ta ne nan ta hau sababi, "tunda shi Jabeer ɗin uban ka ne ai dole kaje gidan shi", Abdul kam hannun Sumayya ya riƙe ya fincike ta dole ta tashi ko gama cin abincin bata yi ba. "to sake ta ta dawo taci abinci", abinda Brr Hauwa ta faɗa kenan, kamar be ji ta ba haka ya cigaba da tafiya, taɓ ai ji tayi ya gama raina mata hankali tana magana yayi banza da ita a gaban yara ƙanana kan ta buɗe baki ta kuma magana ya fice hakan yasa itama ta miƙe cikin fushi ta kwashi kayan ta. Suna tafe yana tunanin halin gidan su ya rasa meke tsanin su da Mom ne haka da yayi zafi har haka?. Koda suka shiga gidan kusan kamar ko wane lokaci babu kowa ya zaunar da Sumayya saman kujera sannan ya nufi sama. Yana ƙoƙarin shiga tana ƙoƙarin fita, da sauri suka ja suka tsaya, a tare suka saki murmushi me ƙayatarwa, Abdul ya bita da kallo tun daga sama har ƙasa. Tana sanye da doguwar riga, Dubai abaya kalar ruwan kasa me haske, kanta kuwa blue ɗin mayafi ne wanda tayi rolling dashi, ƙaramin gilashi ne maƙale a idanun ta wanda yawancin likitoci suke sakawa. Hannun daman ta saƙale da riga ta aikin su, sai kuma hagun ta inda take riƙe da ƙaramar jakar ta da kuma wayar ta babu abinda ke tashi a jikin ta banda ƙamshi. Ya langaɓar da kai, Saleema ta zuba mishi idanu fuskar ta cike da annuri na ganin ƙanin nata kuma masoyin ta abin ƙaunar ta. "yau kam zan iya cewa nafi kowa sa'a", ta faɗa cikin sanyin murya wanda kusan halin ta kenan, ya saki ƙayataccen murmushi kan yace; "ni kuma gashi yunwa nake ji balle ma na tantace na tashi a sa'a ko akasin hakan". Ta ɗan zaro idanun ta sannan tace; "me yasa baka kira ni ba da yanzu na haɗa maka ai", ya kauda kai sannan yace; "gashi kuma naga kin gama shiri da alama direct sai wajen aiki, bari kawai insa Hanne ko Muhibba su dafa mini", ya ƙarasa yana ƙoƙarin juyawa. Cikin sauri ta riƙo hannun shi tana faɗin; "ayya ba za'a yi haka ba gaskiya bari na shiga kitchen ɗin na sama maka abinda zaka ci", tana gama faɗar haka ta nufi downstairs da sauri, Abdul yabi bayan ta yana me jinjina irin soyayyar da take yi mishi. Saleema ta ƙara washe baki ganin Sumayya a zaune, Sumayyar ma cikin farin ciki ta gaishe da yayar tata, nan Saleemar ta barsu ta wuce kitchen domin sama musu abinci. Sumayya ta matso kusa da ɗan uwan nata sannan ta miƙa mishi wayar tana faɗin; "Ya Abdul kalli motar da Daddy ya siya muku". Amsa yayi yana kallo, motoci ne guda uku masu kyau sosai, ɗaya baƙa ɗaya ruwan ƙasa ɗaya ja, ya miƙa mata yana faɗin; "na san dai baƙar suka bar mini ko?". Sumayya cikin alhini tace; "babu yadda Mummy bata ba akan Ya Tameer ya bar maka wannan amma ƙememe yaƙi bar maka wai ita yake amma naji Mummy tace zata maka order ɗin wasu guda biyu", ya jinjina mata kai kawai ba tare da yace komai ba. Wato ya san da biyu Ya Tameer ya zaɓi baƙar ya bar mishi ja domin ya san yadda ya tsani mota ja, haka kuma kowa a gidan ya san Tameer ɗin ke son mota ja har ma su kan tsokane shi da kalar mata ce, amma shine ya zaɓi baƙa kawai dan ganin ya ɓata mishi rai. "Ya amma gobe ba da wuri zamu tafi ba ko?", Sumayya ta katse mishi tunanin da ya tafi, ya ɗaga kai kawai, sun cigaba da fira inda yawanci kawai ɗaga mata kai Abdul ɗin yake yi domin tunanin shi baya kanta yana kan wannan yarinyar ta jiya. Saleema ta fito hannun ta ɗauke da tray, da sauri Sumayya ta tashi ta amso ta, Sumayya tace; "sannu Aunty Saleema da aiki ai da kin saka Hanne". Saleema tace; "kada ki damu ƴar ƙanwata kun wuce kuci abincin Hanne a waje na bayan ina gidan", ta ƙarasa tana kallon Abdul ɗin wanda shima idanun shi yana kanta domin ya san akan shi take maganar ba wai dan Sumayya ba. Yayi murmushi sannan yace; "aikuwa mun gode da wannan karramawar, kuma munji daɗi sosai, abinda zamu ce kuma shine adawo lafiya", ta saki murmushi tana ɗaga musu hannu ta fice. Tare suka ci abincin kamar suna gida suna yi suna fira wacce bata da hayaniya sosai, a haka Mummyn ta fito ta tarar dasu nan suka gaishe ta, da yake itama da shirin office ta fito hakan yasa ta wuce su kawai. Ya miƙe tsaye itama Sumayya haka ya kalle ta yace; "ni zan fita kije wajen Nihal na san tana nan", daga haka ya juya ya fice. Motar Fadil yaje ya ɗauka sannan ya fice daga Estate ɗin gaba ɗaya, wajen Akram yake so yaje wanda zasu haɗu a jiya amma saboda Nusram basu samu damar haɗuwa ba. Har ya gifta ya hango kamar ita a tsaye a bakin titi, sai fama duba waya take wanda alamu ya nuna sauri take kuma bata samu mota ba, a hankali ya fara dawowa da baya da baya har yazo kusa da inda take. Yana sauke glass ɗin suka haɗa idanu, Nusreen ta ja ƙaramin tsaki tana me kauda kai, Abdul kuwa abin ya bashi mamaki, a jiya tsoron shi yake gani a idanun ta amma a yau kuma yaga masifa da tsiwa kawai ke cin ta. Ya jima a haka ita bata waigo ba shi kuma be wuce ba, Abdul ya kuma juyawa ya kalle ta, Atamfa ta saka me ruwan ganye da ratsin ja da fari haka Hijab ɗin jikin ta fari ne, tayi kyau sosai domin kuwa fuskar nan ta ɗauki kwalliya. Abdul ya taɓe baki domin ganin shi jiya tafi kyau don jiya babu kwalliya a fuskar ta, ya duba agogon hannun shi sannan ya buɗe motar ya fito. Gaban ta ya je ya tsaya, Nusreen kuwa kamar bata san dashi a wajen ba duk da yadda gaban ta ke faɗuwa dan yana yi mata kwarjini sosai. Abdul kuwa cikin bada umarni yace; "shiga muje", wani shegen kallo Nusreen ta wulla mishi kan tace; "sannu Malam Abdullahi🙊". Abdul ya kafe ta da ido yayin da Nusreen ɗin taƙi yarda su haɗa idanu, hannu ya kai zai riƙo nata da sauri taja baya sannan tace; "wallahi ka sake ka ɗora hannun ka saman jiki na sai nayi maka ihun kwarto", sosai hakan ya bashi mamaki kan yace wani abu motar Shureim ta tsaya kusa dasu. Shureim ya fito cikin sauri yace; "afuwan Sarauniyar mata wallahi na ɗan tsaya amsar saƙo ne", Nusreen ta cilla mishi harara sannan tace; "ka kyauta daka shanye ni a nan har wasu marasa ilimi da hankali suke tunanin ko ni ɗin ina da araha har haka", ta ƙarasa tana kallon inda Abdul ke tsaye wanda tun lokacin da Shureim ya ambaci Sarautar mata yaji wani abu ya daki zuciyar shi. Shureim ya kai kallon shi inda Abdul yake, cikin sauri ya ƙarasa yana miƙa mishi hannu; "barka da hutawa yallaɓai", Abdul yayi murmushi yace; "Shureim dama kana nan shine ko ziyara babu". Shureim ya shafa kai yace; "kayi haƙuri yallaɓai wallahi abubuwa ne sun yi yawa sannan ban jima da dawowa najeriyar ba don ina Egypt karatu". "ina Ammie? Fatan tana lafiya", Abdul ɗin ya tambaya, Shureim yace; "Ammie tana Syria wallahi ciwon ƙafa ne ya matsa mata". "ayya amma ya ƙafar yanzu", Abdul ɗin ya tambaya, Shureim yace; "eh to wai likitan da ake saka ran zaiyi mata aiki ne sai nan da kwana uku zai dawo Dr John Burlin". "John Burlin ai na san shi ka bari zan kira shi sai a san yadda za'a yi aikin", nan fa Shureim ya fara godiya. Nusreen ta baje hanci da baki tana kallon su bata yi tunanin sun san juna ba, ganin abin bana ƙare bane yasa tace; "wai Habibi a waje zaka barni ne ko kuwa zaka wuce muje?", da sauri Shureim yace; "Afuwan Sahiba shiga muje", ya faɗa yana me buɗe mata ƙofa sai da ta harari Abdul ta ƙasan ido sannan ta shige. Shureim ya kalli Abdul yace; "yallaɓai mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi", babu abinda Abdul ya iya samun dama banda ɗaga mishi kai da yayi, yana kallo Shureim yaja motar ya tafi. Abdul ya buɗe motar shi ya shiga sannan ya kifa kanshi saman sitiyarin motar, babu abinda ke mishi yawo a idanu banda meye haɗin Shureim da wannan yarinyar?. "ai amsar a fili take saurayinta ne", zuciyar shi ta bashi amsa, da sauri ya furta; "Impossible!", sai kuma wata zuciyar tace; ina ruwan ka ne?", ya ɗaga kafaɗa alamun babu haka yaja motar shi ya bar wajen. Nusreen bayan sunyi nisa ta kalli Shureim tace; "meye haɗin ka da wancan?", Shureim yace; "lokacin da mahaifina yake da rai a ƙarƙashin mahaifin shi yake aiki, ke kuma meye haɗin ki dashi", ya dawo mata da tambaya. Nusreen ta taɓe fuska tace; "babu komai ni ban ma taɓa ganin shi ba sai yau", Shureim yayi murmushi kawai domin sanin halin Nusreen ɗin. Abdul kuwa koda ya ƙarasa wajen abokin shi Akram ɗin kasa zama yayi dan haka ya miƙe yana faɗin; "ina ji gida zan koma kawai". Akram ɗin ya miƙe yana faɗin; "haba Abdul yaushe kazo da har zaka koma?, gashi ko maganar da zamu yi ma bamu gama ba", Abdul ya ɗan ja tsaki sannan yace; "kada ka damu idan na dawo next time zamu yi maganar". Dole haka Akram din ya rako shi har wajen masana'antar, tuƙi kawai yake yi amma hankalin shi naga Shureim da kuma wannan yarinyar ya rasa me yasa abin ya tsaya mishi a rai. Yana zuwa dai dai layin kamar ance ya kalli hanyar ya hango ta sanye da doguwar riga me ruwan ƙasa da kuma hijab kalar ruwan madara. Cike da mamaki yake binta da kallo to ko dai aljana ce amma abin da mamaki a yadda yaga tafiyar su ya tabbatar inda zasu je ma da wuya idan sun kai balle har su dawo. A hankali ya fara bin bayan ta har zuwa ƙofar gidan nasu wato lungun da zaka iya hango gidan su, Nusram da bata san ana bin ta ba ta shige gidan hannun ta riƙe da ledar data siyo kayan lalle wanda ta san zata buƙata wajen yiwa Sahura. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖25-26📖📖 Abdul na ganin ta shige gida ya juya da kan motar shi ya fita a layin, lallai akwai wani abu a tattare da yarinyar amma ko meye zai yi ƙoƙari ya gano shi. Nusram kuwa tana shiga gidan ta tarar Sahurar na jiran ta, dan haka ruwan dake saman murhun su ta juyo, yayin da Nusram ta shiga ɗaki ta ɗauko haɗin man da take wanke kai. Sai da ta fara shafa mata haɗin Kanumfari da Kaltufah, ta saka leda ta rufe sannan ta ɗauko abin lallen ta fara kwaɓawa, sai da kan yayi tsayin minti goma sha biyar sannan ta buɗe kan, ta ƙara tajewa kafin suka je bakin famfo ta wanke mata. Kan yayi kyau sosai dan babu laifi Sahurar ta ɗan kwaso dangin mahaifin nasu, Ameera ta Kalli Aziza ganin yadda kan yayi kyau yake kuma sheƙi. Sai da ta tsane kan gaba ɗaya sannan ta ɗauko haɗin mayukan musulunci, Man zaitun, man hulba, man habbatus-saudaa, man maciji da kuma ɗigon man ayu, ta ware mata kan tana shafawa tana tajewa haka tayi har kan ya saki sannan ta naɗe mata gashin inda take so ko'ina man ya shiga, idan kaga gashin Sahura a lokacin zaka ɗauka taje wajen masu wanke kai ne. Ita kanta sai da ta kasa yin shiru tace; "Nusram Allah kuwa da zaki buɗe wajen gyaran kai da jiki ko ba ƙaramin ciniki zaki yi ba", Nusram tayi murmushi kawai ba tare da tace komai ba. Jan lalle ta fara tsantsara mata, sannan ta ɗora mata baƙi a sama, kan wani lokaci ta gama zana mata lallen, sannan ta ɗauko kibiya ta hau yi mata kitson. Mama Jummai dai sunyi sa'a dan ko kallon inda suke bata yi ba, aikin gaban ta take yi wato ƙoƙarin ɗora abincin siyarwar ta kenan take yi domin rana ta fara yi. Ƙananan kitso Nusram ɗin ta yarfawa Sahurar wanda yayi kyau sosai, kan wani lokaci sun gama domin kuwa Nusram ɗin tana da sauri akan ayyukan nata. Tashi tayi taje tayi Alwala sannan ta shige ɗaki inda ta bar Sahura a zaune domin barin ƙunshin nata ya ƙara ja, koda Nusram ta idar da sallah sannan ta ɗebi abinci. Tana ci tana yiwa Kubra wasa wacce itama kwanon abincin ke gaban ta, duk ta watsa shinkafar a ƙasa. Ummi ta kalli Nusram sannan tace; "ina so ki faɗa mini gaskiya Nusram shin kina son wannan auren da mahaifinku zai muku?". Nusram tayi murmushi tace; "Ummi me kika gani?, nifa wannan be dame ni ba kuma ina farin ciki ko babu komai zan bar gidan nan sannan ƴar uwa ta ma Allah ya cika mata burin ta wato zamu yi aure lokaci ɗaya". Ummi ta kuma cewa; "amma ai ya kamata ki tabbatar da cewa kina son shi kafin auren bana so kiyi abinda zaki yi nadama sannan bana so ki fuskanci matsala a gidan auren ki". "Insha Allah Ummi ba zan fuskanci wannan matsalar ba, zan yi farin ciki kamar yadda kike mini burin yi", abinda Nusram ɗin ta bawa Ummi amsa kenan. Ummi tace; "shikenan tunda haka kika ce Allah ya baku zaman lafiya, amma ki sani shi aure ba abin wasa bane idan har kun haɗu kinji bakya son shi to ki sanar dani ni kuma zan yi iya ƙoƙari na wajen ganin ba'a ɗaura wannan auren ba". Nusram ta riƙo hannun Ummi tace; "kada ki damu kanki Ummi, Insha Allahu zan so shi kamar yadda kowacce mata ke son mijin ta", ba don Ummi ta yarda da abinda Nusram ta faɗa ba ta ƙyale ta. Sai wajen biyu sannan Nusram ɗin taja ruwa a rijiya inda ita kuma Sahura ta miƙe taje wajen ta, Nusram da kanta ta wankewa Sahurar lallen sannan ta shafa mata muhallabiyya aikuwa yayi kyau sai shinning yake yi. Sahura sai washe baki take yi ganin yadda tayi kyau sosai ga wani ƙamshi da tafin hannun nata yake yi, domin dai kowa ya san ƙamshin muhallabiyya akwai daɗi sosai. Koda ta shiga ɗakin su da murnar ta ta nunawa Mama Jummai, Mama Jummai tace; "na fani yayi kyau sai dai ki cirewa ranki komawa gidan Idris". Sahura ta turo baki gaba kafin tace; "amma ai Baba ya yarda ko?", Mama Jummai taja tsaki tace; "ai ya yarda ne saboda kada ya dinga cefane dake, yau Alhajin da zai auri Nusram zai zo don haka ina so ki san yadda zaki yi ki ɗauke hankalin shi daga kanta". Sahura ta kalli Mama Jumman sheƙeƙe sannan tace; "Mama ke kina ganin muna da kyawun da zan iya karawa da Nusram ɗin?, to wallahi bana dashi sannan kuma ba zan taɓa aikata mata haka ba kuma ni Mama miji na ya maida ni dan haka ba zan yi aure kan aure ba, gidan miji na zan koma yau ko ki so ko kada kiso". Mama Jummai cikin hargagi tace; "Sahura ni kike faɗawa haka, to wallahi kinyi kaɗan kuma baki isaba zanga ta yadda zaki fita kibi mijin naki", ba tare da damuwa ba Sahurar tace; "za kuwa ki gani". Mama Jummai cikin ranta tace; "ina dole na sake dabara idan ba haka ba wanki hula zai kaini dare", tana gama faɗar haka ta ɗauki hijab ta fice. Nusram tana ƙoƙarin ɗora girki Nusreen tayi sallama ta shigo hannun ta ɗauke da kaya, Nusram ɗin da kanta ta miƙe ta taro ƴar uwar tata. Ɗaki suka shiga dashi, Nusram cikin farin ciki tace; "wa'innan fa daga ina?", Nusreen tace; "wallahi Auntyn Tudu tace na taho dashi zata zo sati me zuwa kin san bikin Ya Sulaiman wai sati uku suka saka". Nusram ta ƙara washe baki tana faɗin; "ah lallai kace Yaya Sulaiman ɗin ango yake, ya akayi to?", Nusreen ta tabe baki sannan tace; "ashe ma wai ya san Shureim ɗin baki ga yadda suka dinga fira ba, amma duk da haka yace zai ƙara bincike akan shi, wai daman Maman Shureim ɗin a wajen Ya Sulaiman ɗin ma take siyayya". Nusram tace; "shikenan ma ashe abin yazo da sauƙi", Nusreen ta cire hijab ɗin jikin ta sannan tace; "na bashi labarin naki angon baki ga yadda ya dinga faɗa ba, yace ma zai zo koda zuwa sati me zuwa ne ko kuma gobe". Nusram ta harari Nusreen ɗin tace; "to waye yace ki ɗin ki faɗa mishi?", Nusreen tayi dariya sannan ta juya wajen Ummi tace; "gashi nan inji Aunty tace zuwa gobe ko kuma sati me zuwa zata zo wai sai kuyi magana". Ummi tace; "Allah ya kaimu", suka amsa da ameen, Nusreen ta kwanta yayin da Nusram ta koma wajen girkin ta don so take taci ƙarfin girkin kafin lokacin da zasu tafi makarantar. Ƙarfe huɗu sun idar da sallah inda suka saka atamfa duka a jikin su riga da zani sannan suka ɗora hijab wanda ya kasance na makaranta sannan suka yiwa Ummi sallama suka tafi. Nusreen ta kalli ƴar uwar tata sannan tace; "Ramluv kin san me?, yanzu tunani na shine anya kuwa Baba zai yi mana kayan ɗaki masu kyau?". Nusram tace; "ke kuma abinda ya dame ki kenan kai Rim Allah ya shirye ki, abinda nake so ki gane shine duk abinda Allah ya hore mishi wannan zai yi mana dan haka kada ki damu ga kuma kuɗin da muka tara a wajen Auntyn Tudu na san sati me zuwa zata zo dasu a shiga kasuwa sai a siyo koda kayan kitchen ne tunda a ƙalla zai kai dubu ɗari da saba'in sannan akwai wa'inda muke tarawa a gida kinga duk Allah zai rufa asiri dai, ni dai burina yanzu shine na bar gidan kawai". Nusreen tace; "hakane kuma, kai amma sana'a tana da rufin asiri yanzu fa kinga da bamu yi da shikenan", Nusram ta harare ta tace; "kamar wata gwanar sana'ar ai zan bawa Shureim shawara kawai ya buɗe miki boutique ne kada ya tsaya ɓata kuɗin shi". Nusreen tace; "nifa gidan radio zan yi aiki na", Nusram tace; "da auren naki ko?", eh mana me za'a fasa", Nusram tace; "Allah ya baki sa'a to", ta amsa da ameen, haka suka cigaba da firar tasu har suka isa makarantar. Koda suka taso, sauri kawai suke tayi domin su ƙaraso gida dan basa so ayi kiran sallar Magrib suna kan hanya. A.ƙofar gida suka tarar da Idris, cikin girmamawa ya gaishe dasu, suma suka amsa sannan suka shiga ciki. "ni Sahura ban isa na faɗa miki magana kiji ba kenan?, Sahura dani kike ja ko, ki koma babu inda zaki je", maganar Mama Jummai kenan wacce ta iso kunnen su. Su ka kai duba, zuwa inda take ta kama Sahurar ta cukuikuye ita kuma Sahurar tana ƙoƙarin fizgewa, idan kaga yadda suke sai abin ya baka dariya. Nusreen data kasa riƙe dariyar ta nan ta hau yin ta babu ƙauƙƙautawa, Mama Jummai ta jefo musu harara tace; "shegu mayu, wallahi Allah ya isa tsakani na daku". Nusreen ta ƙara kwashewa da dariya harda shewa, wanda hakan ba ƙaramumin ƙular da Mama Jummai ɗin yayi ba, itacen dake cikin wuta ta ɗauko ta nufo Nusreen ɗin gadan-gadan sai dai ganin yadda Nusram ta haɗe rai take kuma kallon ta yasa ta kasa ƙarasawa kusa da Nusreen ɗin, tana haki ta nuna Nusreen ɗin tace; "zamu haɗu ne shegu sunƙi aure". Baba yayi sallama ya shigo, inda ya samu Mama Jumman ta sake cukuikuye Sahurar tana ƙoƙarin tura ta ɗaki, Baba yace; "yanzu dan Allah meye haka?". Mama Jummai tace; "yauwa gwara daka zo, nice nan nace babu inda zata je, wai amma yarinyar nan sai ƙoƙarin ja dani take yi a gidan nan tana tona mini asiri, kuma wa'incan ƴaƴan mayun sune suke ƙara zugata". Baba yace; "to ke meye na hana ta tafiya ki barta taje mana, bafa na son rigima", cikin hayagaga tace; "au haka ma zaka ce Abdullahi?, to wallahi ba zai saɓu ba". Baba yasa hannu ya rabata da Sahurar sannan yace; "ke wuce kibi mijin ki", Sahurar kuwa ta nufi hanyar fita tana murna inda take ɗagawa Nusram hannu, Nusram ta mayar mata sannan ta wuce nasu ɗakin. Suna idar da sallah Ummi tace; "Nusreen ke ba zaki dena ɗauko mini magana ba a gidan nan ko?", Nusreen ta cuno baki tace; "yanzu me nayi ko dariya ma ta zama rigima a gidan nan kenan bamu da ƴancin muyi dariya kenan?", Ummi ta kai mata duka Nusreen ta fice da gudu. Nusram kuwa tabarma ta shinfiɗa musu a ƙofar ɗaki sannan ta zubo musu abinci, Nusreen ta ɗauko Kubra ta fito da ita, Nusram kuma ta ɗauko babbar roba sannan ta saka hijab tace; "bari naje na siyo mana ƙanƙara", daga haka ta fice. Kasancewar gidan babu nisa da nasu yasa bata wani jima ba ta siyo sannan ta nufo hanyar gida, a ɗan lungun kusa da gidan su ta hangi mota, bata kawo komai ba ta shiga lungun. Ganin shi sai da gaban ta ya faɗi, Babban mutum ne sanye da fararen kaya, hannun shi riƙe da waya yana dannawa, hasken wayar shiya haska mata fuskar shi ina da a take a lokacin ta gane ko waye. Tana daf da shiga gida ya ɗago sannan yace: "amm ji mana", cak Nusram ta tsaya gabanta na faɗuwa, "idan kin shiga kice ana sallama da Nusram dan Allah", ji tayi kamar ta dawo ta kwaɗa mishi mari amma haka ta daure ta shige gidan kawai. Koda ta shiga bata kuma bi ta kanshi ba, wajen randar su ta nufa ta ciko jug da ruwa ta buɗe tiyara ta zazzage a ciki ta juya sannan ta sassaka ƙanƙarar ta kawo ta ajiye musu. Kusa da Nusreen ta je ta zauna amma ta kasa cin abincin har sai da Nusreen tace: "Ramluv, kin ƙi cin abincin?", da sauri ta jefa hannun ta sai dai tana kai lomar bakin ta yaro yana rangaɗa sallama. Mama jummai dake nata ƙofar ɗakin ta amsa mishi domin yawanci su kan shigo domin yaranta ko kuma siyayya, yaro yace; "wai ana sallama da Nusram", Mama Jummai taja tsaki. Nusram kuwa abincin da bata kai ga haɗiyewa ba shine ya dawo ya shaƙe ta inda gaba ɗaya ya haddasa mata tari me ƙarfi, Nusreen ta miƙo mata ruwa ta sha. Yaron ya kuma maimaitawa, Mama Jummai cikin fushi tace; "dallah fita ka bawa mutane waje ai mun ji ko?", Nusreen tace; "kaje kace tana zuwa". Tana zaune tana ƙoƙarin dai-daita nutsuwar ta taji sallamar Baba inda ya hau surfa mata faɗa akan ta bar mutum a tsaye, dole hakan tasa ta miƙe tayi cikin ɗaki. "au ɗaki kika shige ba zaki fito ba sai na biyo ki ciki?", Ummi tace; "amma ai ka bari ta shirya ko?", rufe mini baki ɓammbaƙar munafika duk waye ya ɓata yaran idan bake ba", hakan yasa Ummi taja baki tayi shiru. Nusram dake ɗaki ta fashe da matsanancin kuka, ita tunda take bata taɓa ganin uban da yake yiwa ƴaƴan shi abinda Baban nasu yake yi musu ba, haka bata taɓa ganin mijin da yake yiwa matar shi abinda Baban nasu yake yiwa maman nasu ba. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *Note:-* masu cewa basu gane rayuwar waye ake so a nuna ba an ce rayuwar Abdus-samad amma kuma ana kawo rayuwar Nusram, kada ku dama idan har kuka ƙara haƙuri zaku fahimci ina littafin ya dosa amma be kamata tun a yanzu ku yanke hukunci ba ya kamata ku haƙura har zuwa lokacin da littafin yayi zurfi sosai kada ku manta fa ko pages talatin ba'a yi ba kuma tun farko na faɗa muku littafin nada tsayi why d eager??. Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai ga masu complain suna duba whattpad amma basa gani kuyi haƙuri wallahi ko ƙareenateey na kasa ƙarasa balle na fara saka wannan amma zan dage kan azumi na saka su duka acan ɗin tnxs for ur love😘. 📖📖27-28📖📖 Jiyo muryar Baba yana ƙara wage baki yana ƙwala mata kira yasa Nusram saurin goge hawayen fuskar ta, sai da ta ɗan gyara fuskar dan bata so kowa ya gane halin da take ciki. Tana fitowa Baba ya kai mata ranƙwashi tsakiyar kai yace; "shegiya me baƙin hali irin na uwar ta, ko kare be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yana son ki ba shine kinyi sa'a yanzu Alhaji Baballe zai rufa mana asiri ya rufa miki kema shine kika tsaya nurƙufanci ko?", Nusram bata iya cewa komai ba ta gifta mahaifin nata cikin baƙin ciki da damuwa. A inda ta bar shi a nan ta dawo ta same shi, yana hango ta ya hau washe baki, Nusram kuwa cikin mutunci ta gaishe dashi. Ya amsa yana ƙara washe bakin shi, "kinga dai yadda Allah yake ikon shi ko, wato dalilin da yasa kenan ko Sauro be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yazo wajen ki ba ashe ke ɗin rabona ce". Nusram ta haɗiye wani abu me ɗaci daya tsaya mata a maƙogoro, wato har labari ma Baba ya bashi kenan, bata iya cewa komai ba banda "Um ko u'um", yayin da shi kuma ya dinga yi mata surutu. "abu na gaba da ya kamata ki sanu shine mata na guda biyu, yarana Ashirin da ɗaya cif, amarya nada goma uwargida nada sha ɗaya, kinga ke idan kika zo sai kiyo dozin". Nusram ta kalle shi ta kauda kai, wai dozin lallai ma, suna nan tsaye Isa ya dawo, fuska a murtuke ya kalli Alhajin sannan ya shige gida. Nusram ta ajiye ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, shi kuwa Alhajin da yake be san me take ciki ba be wani damu ba, sai ƙarfe tara da rabi da ƴan mintuna sannan yayi mata sallama ya tafi. Nusram kuwa har wata iska me daɗi taji tana kaɗata domin dai Allah ya gani ji take da atakure take, tana shiga zaure ta tarar da Isa a tsaye yana jiran shigowar ta. Yana ganin ta ya nufo ta sannan ya ɗaga hannu hannu ya sharara mata mari, cikin masifa yace; "ni ina can na shanya baki ina jiran ki ashe ke kina nan kina taɗi da wani ƙato ko, to wallahi ko kina sona ko bakya so na baki da miji sai ni", yana ajiye aya Nusram ta raɓa ta wuce. Ya fizgo ta ya haɗa da jikin bango sannan yace; "wallahi kina wasa dani da yawa ko, matuƙar naga zaki kuɓuce mini sai na raba ki da budurcin naki naga uban me mijin naki zai samu". Gaban Nusram ya yanke ya faɗi, cikin sanyi tace; "Dan Allah ka sake ni na tafi mana", ya ture ta har sai da ta kusa faɗuwa sannan ya fice ya barta. Nusram ta tsuguna a wajen ta saka kanta tsakanin ƙafafun ta sannan ta fashe da kuka, ita kaɗai ta san ya take ji a cikin zuciyar ta. Ta daɗe a wajen dan sai da taji alamun Baba zai shigo sannan ta miƙe cikin sauri ta shige gida, a bakin ƙofa ta tsaya ta gyara kwalliyar ta sannan ta shiga. Nusreen dake tsaye da hijab a hannu da Ummi dake kan abin sallah suka bita da kallo, Nusram tace; "ke kuma lafiya na ganki tsaye da hijab?", Nusreen tace; "Allah dama naga kin daɗe ne shine wai zan biki naga ina kika tsaya ne ko lafiya", Nusram tayi murmushi sannan ta juya tace da Ummi; "har ya tafi bari naje na kwanta, Rim muje ciki na san dai Shureim ba zai zo ba tunda tara ta wuce", Nusreen kam kai kawai ta ɗaga. Sai da suka gama shirin barcin su sannan Ummi ta shigo, ta kalli Nusram tace; "Nusram ki faɗa mini tsakanin ki da Allah kina son wannan alhajin?", Nusram babu ko ɗar ta ɗagawa Ummi kai, Ummi tayi ajiyar zuciya sannan tace; "shikenan tunda haka kika ce, ku kwanta kawai amma ki sani matuƙar bakya son shi to ki sanar dani domin rayuwar aure ba ɗaya take data gida ba", tana faɗin haka ta fice. Nusram ta saki ajiyar zuciya sannan ta kwanta, Nusreen ma haka sai data jima sannan ta sami damar cewa; "wai Ramlove da gaske ne kina son Alhaji Baballe?". Nusram tace; "sosai ma kuwa, mutumin nan babu ruwan shi gashi da sauƙin hali ga barkwanci baki ga yadda ya dinga saka ni ina dariya ba, ni dai gaskiya yana birge ni sannan ina jin daɗin mu'amalata tare dashi", Nusreen tace; "amma fa kin sani Nusram Alhaji Baballe tsoho ne sannan baya da mutunci akan kuɗi a gaban ki fa Baba yake zagin shi akan baya da mutunci yanzun ma idan kika bibiya kuɗi ne ya haɗa su ake so a saka ki a tsakiya". Nusram tace; "bana jin abinda Baba yake faɗa akan shi gaskiya ne kin dai san halin baba, sannan maganar kuɗi kuma zato kike yi dan haka kada ki tada hankalin ki akan hakan", Nusreen tace; "amma dai ni ƴar uwar ki ce ko, dan haka ba zan taɓa so wani abu ya cutar dake ba kamar yarda kike ƙoƙari wajen ganin kin bani farin ciki kin kuma kare ni daga duk wani abun cutarwa Nusram kece fa kawai wacce nake da ita, ƴar uwa ta rabin jiki". Nusram ta balla mata hararar wasa sannan tace; "ina kika bar Kubra, Sahura dasu Ameera kiji mini yarinya". Nusreen tayi dariya tace; "Allah da gaske basu kai mini ke ba, Nusram tare fa muka kwanta a cikin mahaifiyar mu tsayin wata tara abincin da zamu ci yana haɗe dana juna, muka fito tsayin shekara biyu mahaifiyar mu na ciyar damu da abinci kala ɗaya wanda har kika sha ki saki na kama kema kuma na kan sha na saki ki kama tun lokacin da muka fara wayo har tana Pant kala ɗaya muke sakawa kuma bamu taɓa raba wajen kwana ba, taya zan haɗaki da wasu, ke ɗin *Bloody*😭 na ce". Ummi ta katse zancen ta hanyar cewa; "tabbas abinda Nusreen ta faɗa gaskiya ne, kunfi kusanci da juna sama da duk sauran ƴan uwanku Kamar yadda bakya son wani abu ya same ta haka itama bata so wani abu ya same ki, dukkanku kuna son junan ku sai dai ba zai taɓa kaiwa koda rabin son da nake yi muku ba, nice mahaifiyar ku na ɗauki wahalar ku tun daga lokacin da kuke ciki na, a cikin abincin da naci a ciki kuke samu kuma kuci, lokacin da cikin ku ya kai wata takwas bana iya barci kwata kwata sai da rana da ranan ma a zaune, nazo naƙudar ku haka nasha wahala kamar zan mutu, bayan na haifo ku nayi tunanin wahala ta ƙare ashe yanzu wata sabuwa zan ɗora domin kuwa da ɗaya ta fara kuka ɗayar zata ɗauka, haka zan ta rarrashin ku, kuyi barci da rana ni kuma da daddare ku hana ni yin barcin amma duk da haka banji a raina cewa wai bana son ku ba, naci fitsarin ku naci kashin ku, naci tunɓuɗin ku amma duk da haka ban gaza, daga baya nauyin kula daku ya dawo kaina haka kuma nake ta haƙuri, ki sani Nusram shekarun dana ɗauka ina wahala dake ba zai saka nace na gaji dake idan ma kina tunanin dan ki kauce mini da wahalar da nake ba to ki sani koda zaki ƙara shekara ashirin ko sama da haka matuƙar ina da rai ba zan taɓa gajiya dake ba", Nusram cikin kuka ta haɗa su duka ta rungume. "tawa ƙaddarar kenan ba zan taɓa samun farin ciki ba a rayuwa ta, kuma tabbas aure ya zamar mini dole ko dan gudun samun matsala da kuma ɗaukewar farin ciki a rayuwar ku", abinda take faɗa kenan a cikin ranta. Sun ɗan taɓa fira a tsakanin su kafin su kwanta barci, sai lokacin Nusram ta ɗan sami sauƙin abinda yake ranta don ko babu komai firar da suka ɗan yi ta rage mata damuwa ba kaɗan ba. ******** ********** Jikin shi sanye da Wando jeans fari da kuma rigar polo t shirt kalar blue da ratsin fari, ƴar ƙaramar jakar shi ce riƙe a hannun shi, Fadil kuma yana bayan shi haka suka shigo da sallama. Kamar koda yaushe suna saman dinning table inda zasu yi breakfast, Sumayya dake cin abinci ta gaishe dashi, ya amsa fuska a sake sannan ya gaishe dasu, kowa ya amsa kamar kowanne lokaci amma banda Brr Hauwa. "idan kin gama tashi mu tafi", Sumayya tace; "to Yaya", sannan ta miƙe, cikin rawar jiki Husna tace; "Ya Abdul kai ba zaka ci abincin bane?", be kalle ta ba balle ta saka ran samun amsa daga gare shi. Hajja tace; "baka ji ana yi maka magana bane?, ni ina mamakin halin ka domin iya sani na uban ka ba halin shi ba kenan, anya kuwa kai ɗan shi ne?". Wata irin ɗagowa Abdul yayi sannan ya kalli Hajja, itama Malama kamar zata zubar da hawaye take bin Hajjan da kallo. Ganin yadda ranshi ya ɓace yasa Hauwa cewa; "waye ya sani ko a yawon neman shaidu aka samo shi aka zo aka ƙaƙabawa ɗan uwa na, ni dama na jima ina tunanin haka dan ko kama baya yi da ƴaƴan Doctor". Hajja ta girgiza kai tace; "tabbas hakan zata iya kasancewa bari Abubakar ɗin ya dawo dole azo ayi bincike kada a lalata mana zuria da bara gurbi". Wannan karan kam da Sumayya da Malama kasa daurewa suka yi dan haka Sumayya ta saki kuka, Malama kuwa hawaye ta hau sharewa, Fadil kan shi na ƙasa sai dai yadda ya tsuke baki zai tabbatar maka da cewa yaji haushin abin. Fadila kuwa kasa bari tayi dan haka ta miƙe tace; "yo Hajja dan Abdul yayi nurƙufanci ai ba abin mamaki bane idan aka yi duba da halin Brr Hauwa shima haka yake kinga kenan ita ya ɗauko, taƙama da ƙasaita kuwa kowa ya san halin ki ne ko ince a jinin ki yake, dan wani dalili naku kuke son haramta ɗan sunnah anya abinda kuke yi kuwa dai-dai ne, in dai a neman yawon shari'ah ake samo ɗa ai ya kamata kema Brr a bincike ki gudun ɓata zuria nan gaba", sanin halin Brr Hauwa yasa tana gama faɗar haka taja ƙafar ta, ta bar wajen ɗakin Malama ta shige ta dannan key. Brr Hauwa kuwa kan ta gama haɗa magan-ganun Fadila, Fadila ta ɓace a wajen, Fadil kuwa jin ɓaranɓaramar da Fadila tayi yasa ya kama hannun Sumayya suka fice daga gidan. Hajja cikin masifa tace; "ai wallahi zaki zo ki same ni yaushe yaran gidan nan suka ɓace har haka, bari Abban Nihal ya dawo ni Fadila take zagi kuma Malama kina kallon ta?". Malama har lokacin hawaye take zubar wa, Hajja ta fashe da kukan munafirci tana faɗin; "Brr kaini wajen Ahmad", jin hakan yasa Brr Hauwa miƙewa ta ja hannun Hajja domin tafiya. Malama na ganin sun fita ta miƙe da sauri taje ƙofar ɗakin ta, sai da ta ƙwanƙwasa tana ƙwalawa Fadila kira sannan ta buɗe, cikin sauri Malama ta janyo hannun ta sannan tace; "zo ki bi su Abdul Hajja ta yafi wajen Ahmad kuma kin san sauran idan har labarin yaje kunnen shi, babu inda kike da mafaka sai wajen Farida dan haka fito maza". Ita kanta Farida jin sunan wanda aka ambata yasa jikin ta ya hau rawa, Ahmad shine babban ɗan Hajja tsohon sojane, yana ji da Hajja kuma duk abinda ta faɗa dai-dai ne yana taka duk wanda ya taka ta. Malama ta kamo hannun ta sannan ta haɗa dana Abdul tace; "maza ku tafi tare idan lokaci yayi da zata dawo zan kira ka sai ta dawo kaji", Abdul da har lokacin damuwar fuskar shi bata kauce ba ya ɗaga kai kawai yana me jan hannun Fadilar. A waje suka sami Fadil da kuma Sumayya, inda kana gani ka san haƙuri yake bata Abdul yayi murmushi yace; "kuzo mu tafi ko?", ba tare da sun ce komai ba suka bishi a baya. Fadil ke tuƙa su yayin da Sumayya ke gefe, baya kuma Abdul ne da Fadila, babu wanda yayi magana tsayin lokaci kafin Fadil yace; "Sumayya kuyi haƙuri kun riga da kun san halin Hajja tun ba yanzu ba be kamata hakan ya dame ku ba". Sumayya ta share hawayen ta tace; "Yaya Fadil da na san abinda zan zo naji kenan a bakin Aunty Hauwa da Hajja da ban matsa sai nazo ba". Fadila ta saka hannu ta dafa Sumayya tace; "kada ki damu kanki Sumayya baku kaɗai take wa haka ba har mu duk tabi ta dame mu". Fadil yace; "hali ne kowa da kalar nashi gashi ban san me yasa duk tabi ta tsani Abdus-samad ba, kamar ba jinin ta ba". Sumayya tace; "amma abinda take yi be dace ba kuma ni ba zan kuma zuwa gidan nan ba", Fadila tace; "aikuwa dole kizo domin kuwa nan shine asalin ki". Sumayya ta taɓe baki tace; "asali na kuma? Bayan basa kauna ta", Fadil yace; "amma ai muna sanki mu ko?". Abdul kuwa yana jin su amma be ce komai ba domin kuwa kwata kwata baya son hayaniyar ta dinga damun shi sanin cewa sai dai yayi ta jin ƙunar abin kuma haka shine su Hajjan suke so. Ya fahimci abu ɗaya shine Brr Hauwa shine tafi tsana yayinda Hajja kuma jinin First love ne bata so. Yana buɗe idanu yabi kwanar hanyar da kallo, ba zai ce ga abinda yake tunani akan yarinyar ba amma tabbas ya san akwai wani al'amari a rayuwar ta, ya sauke ajiyar zuciya yana me maida kanshi ya kwantar saman kujera. Sun jima suna tafiya kafin suka iso unguwar tasu, wato *Unguwar Sarki* unguwar da kowa ke rayuwar shi ba ruwan wani da wani, wannan yana ɗaya daga cikin abinda yasa yake son unguwar tasu. A bakin get aka tsayar dasu, ganin sun tsaya yasa Abdul ɗago kai yana kallon wanda ya tsayar dasu ɗin, mutumin kuwa sai faman washe baki yake yi. Sumayya ta juyo tace; "Yaya kai fa Bala yake yiwa magana", Abdul ya sauke glass ɗin ɓangaren shi sannan suka gaisa. Bala cikin durƙusar da kai yace; "dama ƙaramin oga wallahi tun wancan satin nake zuwa neman ka amma aka ce mini kana Rigasa". Abdul yace; "ya akayi ne Bala?", Bala ya shafa kai sannan yace; "alfarma nake nema a wajen ka da kayi haƙuri na dawo bakin aiki na, Hajiya ta sallame ni akan kuskuren dana aikata kuma gashi yanzu gari babu aiki na nema wani ban samu ba, ga yarinyata da aka kwantar a asibiti shine da naji cewa ka dawo nace bari nazo to.kuma sai na taki rashin sa'a bakanan shine da nazo jiya ake ce mini yau zaka dawo to Allah da ikon shi tun safe nake zaman jiran ka". Abdul ya dafe kai, wannan wane kalar dogon bayani ne haka, ya ilahi! Sai kuma ya ɗago yace; "ka shiga ciki bari mu shigo mu ma", da sauri Bala ya shige har yana ɗan haɗawa da gudu. Fadil ya kwashe da dariya domin ya san dogon bayanin Bala ya ɓatawa Abdul ran shi, Abdus-samad kuwa kauda kai gefe yayi. Ko kan su ƙarasa parking space ɗin har Balan yaje can yana jira, Abdus-samad yace da Sumayya; "menene aikin shi", Sumayya ta bashi amsa da; "wankin motoci yake yi". Suna gama parking ɗin da kanshi yazo ya buɗewa Abdus-samad ɗin ƙofa, Abdul kuwa ya haɗe rai yaƙi fitowa, Fadil da ya san hali ya dubi Bala yace; "ka maida ƙofar ka rufe baya so ana buɗe mishi", cikin sauri Bala ya maida ƙofar ya rufe. Abdul yayi murmushi sannan ya buɗe ya fito, masu aikin ya kira sannan yace; "waye ke aikin Bala a gidan nan", Idris yace; "nine nan". "a da meye aikin ka?", Abdul ya kuma jefa mishi tambaya, Idris yace; "gyaran fulawa", Abdul ya kalli Bala yace; "ka koma bakin aikin ka kawai", yana faɗar haka yayi hanyar part ɗin shi. Su Fadil kuwa mamaki ne ya cika su, na ganin direct ya bada umarni, Sumayya kuwa murmushi tayi kawai sannan tace: "kuzo muje, idan har kuna gidan nan sai kun dena mamakin ikon da Ya Abdul yake dashi". Haka suka bi bayan Sumayya, duk ƴan gidan suna falo dan haka Adnan ya nufo su da gudu yana murna, Fadil ne ya ɗaga shi sama yana faɗin; "Oyoyo autan gidan". Fadil ya ƙarasa kusa da Sameer da Tameer ya basu hannu suka gaisa, Fadila kuma ta gaishe dasu daga inda take. Surayya tace; "yau kunzo mana gidan kenan? Ko kuwa dai kuma ɗan lelen kuka rako?", Fadil yace; "bangane ɗan lele ba?", ta miƙe tsaye tana me kwashe littattafan ta sannan ta juyo tace; "waye ɗan lele banda Ya Abdul", tana faɗar hakan ta nufi hanyar ɗakin ta. Fadil da Fadila suka kalli juna cike da mamaki, sun san akwai ƙiyayya tsakanin ƴan gidan da Abdus-samad amma basu ɗauka tayi zafi haka ba. Sumayya ta fara ƙwalawa Aziza kira, jima kaɗan ta ƙaraso Sumayya tace; "ki kawo wa baƙi ruwa mana", Aziza ta amsa da to sannan ta miƙe ta tafi. Sameer yace; "ina Abdul ɗin yake?", Sumayya tace; "yana part ɗin shi", Sameer yace; "be san cewa munyi kewar shi bane shine zai wani tafi nashi wajen", ya ƙarasa yana miƙewa domin tafiya, Tameer yaja tsaki yana gyara kwanciyar shi. "ya Allah! Wannan wane kalar gida ne babu daɗi", abinda Fadil ya faɗa kenan a ranshi, Sumayya ta.miƙe sannan tace; "Aunty Fadila zo muje ɗaki na", Fadila ta miƙe tabi bayan Sumayyar. Fadil shima ganin yadda gidan yake yasa ya miƙe ya fice kawai, Part ɗin Abdul ɗin ya nufa, ƙofar a buɗe take dan haka ya shiga kawai. Baya bedroom ɗin amma yana jiyo ƙarar ruwa hakan ya tabbatar mishi da wanka yake yi kenan?, Fadil ya zauna saman bed ɗin yana me bin ɗakin da kallo, kai kace ɗakin wani hamshaƙin me kuɗi ne komai kuma yana inda ya dace. Abdul ɗin ya fito ɗaure da towel sai ƙarami kuma da yake goge kanshi dashi, ba tare da ya cewa Fadil ɗin komai ba, Fadil kuwa ya bishi da idanu. Gaban dressing mirror yaje ya tsaya yana shafa mai, har ya gama yayi combing kanshi Fadil kallon shi yake yi, Wardrobe ya bude ya ɗauko kayan da zai saka. Riga ƙarama baƙa da wando fari jeans three quarter ya saka sannan ya fito daga wajen canza kayan, tuararruka ya hau fesawa nan fa ɗakin ya buɗe da ƙamshi, ya ɗauki zoben shi ya maida yatsan shi yana cikin ɗaura agogo ya ɗago ya kalli Fadil ɗin ta madubi, ganin yadda yake binshi da kallo yasa ya ɗaga mishi gira ɗaya alamar lafiya. Fadil ya girgiza kai yana murmushi, shima Abdus-samad ɗin murmushi kawai yayi yana me juya kanshi zuwa gefe. Wayoyin shi ya kwasa sannan yace da Fadil ɗin; "muje ko?", tare suka fito daga bangaren, a harabar gidan suka tarar da sauran duk sun fito. Kusa da Tameer da Sameer yaje sannan yace; "barkan ku da hutawa", Sameer yayi murmushi yace; "barka da fitowa ɗan lelen Mommy ai na shiga amma kana bayi lokacin". Ba tare da Abdul ɗin yace komai ba ya lumshe idanun shi, Tameer yaja tsaki yana kauda kanshi gefe, hannun Abdus-samad Sameer yaja ya kai shi har gaban motar tashi sannan yace; "ga gift ɗin Daddy daya turo.mana da ita", murmushi kawai yayi kafin yace; "thanks" yana faɗar hakan ya juya ya koma inda yake ya zauna. Shi kanshi Sameer yaji haushin abinda Abdul ɗin yayi.mishi haka ma su Fadil ɗin, Tameer kuwa murmushi yayi yana yin ƙwafa. Sumayya ta zauna kusa da Abdus-samad ɗin ta riƙo hannun shi, ta buɗe baki zata yi magana ya buɗe idanun shi gaba ɗaya a kanta. Wani irin abu taji wanda gaba ɗaya kamar ya janye duka miyau na bakin ta, maida bakin tayi ta rufe, a hankali yace; "pls kaina ciwo yake yi i need some space". Tashi tayi ta bar wajen dan ta san tunda ya faɗi hakan to hakan yake nufi wato baya son damuwa. Fadil da Fadila kuwa kallon su kawai suke yi, Surayya waya ce a hannun ta take latsawa Tameer ma haka, Sameer kuwa yana zaune ne yana kallon wani wajen. Fadila cikin raɗa tace; "anya kuwa zan.iya zaman gidan nan?", Fadil yace; "zaki iya mana, meya faru?", tace; "kalli kaga fa basa fira tsakanin su ni da har ina cewa na baro kurkuku na dawo waje me ƴanci ashe gwara can da nan?". Fadil ya girgiza kai yace; "taɓ gaskiya na tausaya miki to ko zamu tafi tare ne?", Fadila ta ƙwalalo idanu tana faɗin; "Abba Major fa?". Fadil ya ɗaga kafaɗa, Fadila ta girgiza kai tana faɗin ka barni kawai a nan", Fadil yace; "to shikenan". Ɓangaren Abdul kuwa wannan mafarkin daya saba shi yayi, sai dai wannan karon fuska ce wacce babu nama ko ɗaya a jiki take tsaye a gaban shi, iya fuskar kawai sannan tana ƙwala wannan kiran na *MURAD* a gigice ya farka duk ya haɗa zufa, duka suka bishi da kallo. Ya sauke ƙafafun shi daga saman kujerar yana me dafe kanshi, Fadil ya ƙarasa inda yake ya dafa shi, Abdul ya ɗago ya kalle shi. "lafiya kake kuwa?", abinda Fadil ɗin ya tambaya kenan, Abdul yayi murmushin dole yace; "lafiya ta lau", Fadil yace; "shikenan to bari nazo na tafi gida", Abdus-samad ya miƙe domin rakashi. Sai da Fadil ɗin yayi musu sallama sannan suka ƙarasa kusa da motar shi, Abdul ya buɗe mishi ya shiga inda shi kuma Abdul ɗin ya juyo ya dawo ciki. Fadila kam zaman gidan duk babu daɗi take ji amma bata da yadda zata yi dole hakan nan ta zauna a gidan dan shine rufin asirin ta kawai. Wajen Sumayya ta koma inda nan suka fara fira domin ita kanta ta lura kamar zamar gidan ya ishe Fadilar hakan yasa tayi ƙoƙarin ɗauke mata hankali. Abdul kuwa yana zaune a wajen ne amma kuma sanyi-sanyi yake ji hakan yasa dole ya miƙe ya koma part ɗin shi ya kwanta sai dai yana kwanciya zazzaɓi ya rufe shi. Sai wajen Magrib sannan zazzaɓin ya sake shi, bayi ya shiga yayi wanka tare da ɗoro alwala yazo ya tada kabbarar sallar la'asar yana idarwa ya janyo waya domin kiran Fadil yaji ya yaje gida. Ganin missed calls na Mommyn shi yasa yayi murmushi, tun safe daya kira ta akan zasu taho be sake kiran ta ba, number ɗin Fadil ya kira inda nan ya mishi ya yaje gida. Fadil yace; "lafiya ƙau, ya jikin?", Abdul ya ɗan basar sannan yace; "na sami sauƙi, ni kuwa in tambaye ka mana?", Fadil yace; "ina ji". Shiru yayi na ɗan lokaci kafin yace; "barshi ma kawai, sai anjima ka gaishe da Malama", Fadil yayi dariya yace; "shikenan ni.kuma ka gaida mini ƴan biyu ta", daga haka suka rabu. Number ɗin Mummyn shi ya kira nan ya dasa mata shagwaɓa ita kuma tana ta yi mishi dariya, "Allah Mummy gidan babu daɗi da bakya nan har zazzaɓi sai da nayi baki ga yadda na rame ba". Brr Farida tayi dariya tana faɗin; "asha yaron nawa rago ne ban sani ba, to idan na mutu fa", ya ƙara turo baki gaba kaman tana kallon shi yace; "nima mutuwa zan yi balle ma sai na riga ki mutuwa", cikin sauri Brr Farida tace; "ya isa haka, ina ƴan uwan ka?". "nifa ina ɗaki na tun kan la'asar", Brr Farida tace; "kada kace mini a ɗaki kayi sallah", yace; "barci ne fa ya kwashe ni kuma da gaske nayi zazzaɓi yanzu ne na sami sauƙi". Brr Farida tayi ɗan jimm sannan tace; "shikenan, Allah ya sauƙe, tahowar wuri zamu yi gashi ma ina ta haɗa kayan mu ka san mu yanzu dare yayi sosai". Ya ɗan shafa kai yace; "hakane fa, bari naje nayi sallah bye", tace; "bye take care", yace; "sure love you", sannan ya katse wayar ya miƙe ya fice domin amsa kiran ubangiji. Sai bayan isha'i sannan ya shigo gidan, a saman dinning ya tarar dasu, shima nan ya zauna suka ci abincin tare. Firar dai sama-sama ce dan ji da kansu ba bari yake suyi wata fira ba, sai bayan sun gama ne ma ya ɗan taya su Fadila firar kafin ya nufi part ɗin shi domin kwanciya. Laptop ɗin shi ya janyo inda ya kira Mummyn shi, bata yi barci ba dan haka kuwa suka shiga fira, duk da su can daren yayi nisa sosai, sun jima suna fira har barci ya ɗauke shi. Brr Farida tabi ɗan nata da idanu tana murmushi, soyayyar shi daban take a zuciyar ta wacce ta san Allah ne ya saka mata shi, ko yaya zai ji a ranar da duk ya san gaskiyar rayuwar shi. "kada ki damu zai ɗauki haƙuri", Daddy ya faɗa, ta juyo ta kalli mijin ta cikin karaya tace; "ina tausayawa halin da zai shiga Abban Adnan". Dr Abubakar ya rungumo matar tashi yace; "kada ki damu komai zai zo da sauƙi, sannan ma bana jin zai san gaskiyar al'amari tunda kin riƙe amana sannan ba duka mutane bane suka san ainihin waye shi ba". "amma kuma Malama ta sani, sannan shi kanshi ya fara mini tambayoyi akan waye Murad ga Alhaji Mustapha dake raye kuma na san har yanzu yana bibiyar rayuwar Abdus-samad ɗin". Dr Abubakar yace; "kada ki damu hakan ba zai zama wata barazana ba domin kuwa Allah zai mana tsari dashi", haka ya dinga lallashin ta har ya samu hankalin ta ya kwanta. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai* 📖📖29-30📖📖 Fadila tana gyara ɗaurin ɗan kwalin ta Abdul ya turo ƙofar ya shigo, koda ta kalle shi sai da numfashin ta ya kusa ɗaukewa ganin irin kyawun da yayi. Sumayya dake ƙoƙarin ɗaure gashin ta, ta juyo tace; "wow Ya Abdul ka haɗu kamar yau ne ɗaurin auren ka", ya gyara links ɗin shi sannan yace; "ku fito fa, dan bana so First love tayi zaman jiran mu". Fadila ta ɗaga kai alamun to, tana ƙara kallon ɗan uwan nata, cikin shigar manyan kaya wato shadda kalar sararin samaniya wacce taji aikin hannu. Kanshi babu hula sai dai kwantacciyar sumar shi wacce ke ƙara mishi kyau, ya juya cikin ƙasaita ya fice daga ɗakin. Fadila ta saki wata irin ajiyar zuciya har sai da Sumayya ta kalle ta, cikin sauri Fadilar ta basar tana me zama gefen gadon Sumayya. Yana tsaye ya juya baya yana amsa waya suka fito dukan su, ganin waya yake yi yasa duka suka tsaya Surayya ita ma ta fito sanye da riga da skirt na atamfa. Abdul tace; " ka bari later kawai yanzu zamu je ɗauko Mummy ne a airport", yana faɗar haka ya katse wayar. Ya juyo ya kalle su, Surayya ita kanta sai da taga kyawun Yayan nata don haka cikin sauri ta kauda kai, ita fa abinda ke hanata tafiya tare dashi kenan sai tayi wanka na ƙasaita yana yin nashi sai ya shafe nata. Suna gaba yana baya haka suka fito harabar gidan, anan suka tarar da Tameer da Sameer, kowannen su cikin shirin ɗauko iyayen nasu. Abdul yayi murmushi yace; "to muje", yana ƙoƙarin buɗe mota, Tameer yace; "amma dai ya kamata ace mun hau motar da Daddy ya siya mana ko?". Sai da Abdul yayi ɗan jimm sannan yace; "to shikenan", Tameer yace; "idan ma baka son jar ne, ga makullin tawa", Abdul ya kalli yayan nashi da mamaki sai kuma ya kauda kai cikin sauri yace; "nop bari naje a tawa kawai". Tameer ɗin ya taɓe baki yana me nufar tashi motar, shima Abdul ya nufi tashi, Abdul da Sumayya sai Adnan a baya, sai Sameer da Fadila dan tace ba zata shiga jar mota ba kamar ta ƴan shan jini, Surayya kuwa ta Tameer ta shiga domin tafiyar su zata fi dai-dai. Haka suka fice daga gidan cikin farin ciki domin zuwa ɗauko iyayen nasu babu ma kamar Abdus-samad wanda yake jin kamar ya shekara ne bega mahaifiyar tashi ba. ********* ********** Nusreen ta kalli Nusram wacce ta zuba ubam tagumi, itama cikin damuwa ta ajiye zanin gadon dake hannun ta, ta zubawa ƴar uwar tata idanu. Ummi da Auntyn Tudu suka shigo tare wanda hakan shiya dawo da Nusram daga duniyar tunanin data tafi, cikin sauri ita da Nusreen suka amshi kayan dake hannun su. Sai da suka zauna Aunty tace; "Wash wallahi na gaji, Allah yasa ma wancan yaron ya amso ragowar", Ummi tace; "tunda har kin faɗa mishi zai amso ne kada ki damu". Kaya ne na kitchen sai kuma sauran kayan da zasu yi amfani dashi na bikin, nan aka baje ana gani, ita dai Nusram nata idanu ne babu abinda take tunani sai auren da zata yi. Nusreen ta juyo ta kalli ƴar uwar tata sannan tace; "Ram koba haka ba?", Nusram ba tare da ta san me Nusreen ɗin ke magana akai ba ta ɗaga mata kai kawai tana miƙewa ta bar wajen. Duka suka bita da kallo, Aunty tace; "Allah sarki ni dama na san Nusram ba zata taɓa farin ciki da wannan auren ba kawai dai zata yi shi ne". Ummi tace; "nima na lura da bata wani farin ciki da bikin amma ko meye addu'a zamu taya ta dashi sai dai har yanzu ina kan baka ta matuƙar tace bata son shi to kuwa sai dai a fasa auren". Nusram kuwa kan katifar su ta faɗa hawaye na zubo mata, ita ta san ba zata ce ga wani zaɓi da take dashi na wanda zata aura ba amma tabbas bata son auren me yara irin wa'innan yaƴa ashirin da ɗaya!". Haka ta dinga zubar da hawaye cikin baƙin ciki da zafin abinda ke faruwa a kanta, cikin ƙarfin hali ta miƙe a zuciyar ta tana maimaita addu'ar da mutum keyi idan musiba ta same shi tana kuma me neman zaɓin Allah. Haka ranar Auntyn wuni tayi a gidan suna ta shirye-shirye domin kuwa gobe ake saka ran dawowar mahaifiyar Shureim ɗin. Kuma tabbas Baba ba zai ɗaga auren ba dan yace tana dawowa da sati biyu ko sati uku, Shureim kam dole ya amsa a hakan har yaje ya sanar da dangin mahaifin shi. Su kansu sai da suka ce; "wannan wane kalar aure ne kamar an gaji dasu ai a bari mu muyi bincike idan su ba zasu yi ba ko", shi dai Shureim beda abin cewa nan suka gama maganganun su kafin wan baban nashi ya saka ƴaƴan shi guda biyu akan su zo suyi bincike. Alhamdulillahi koda suka zo suka yi bincike basu sami wata tangarɗa ba domin kuwa an basu amsoshi me kyau sosai, dan an sheda musu ma ko ƙawa basu da ita mahaifiyar su ma basu taɓa ganin tana yawon gidan maƙwabta ba. Sun komawa da mahaifin su da sakamako me kyau inda ya kira Shureim ya sheda mishi, aikuwa Shureim yayi murna sosai da sosai wannan shine abinda ya kira Abdus-samad ɗin yana faɗa mishi. Sai dare sannan Yaya Sulaiman yazo ɗaukar Aunty, duka suka fito domin rakata Auntyn tace; yanzu sai ku fara zuwa gyaran jiki ko?", Nusreen ta amsa da to shikenan. Yaya Sulaiman yace; "ke kuma meye ya ramar dake haka?, ko duk fargabar auren ne?", Nusram tayi yaƙe kawai. Auntyn tace; "to ni dai kunji abinda na faɗa muku dan haka zanyi zaman jiran ku idan har kun dawo daga makaranta sai ku dinga wucewa can. Yaya Sulaiman ya kalli Nusram bayan sun matsa gefe yace; "ƴar ƙanwata faɗa mini matsalarki mana", Nusram ta sauke ajiyar zuciya sannan tace; "babu komai, yauwa kayi bincike akan Shureim ɗin". Yayi murmushi yace; "bashi da wata matsala, hakama mahaifiyar shi da mahaifin shi kan ya rasu, gidan su gidan mutunci ne, yanzu abinda ya rage shine wannan alhajin naki Baballe". Nusram tayi saurin girgiza kai tace; "a'a kada kayi Yaya domin koda kayi ko baka yi aurena dashi babu fashi", Yaya Sulaiman cikin tsokana yace; "duk soyayyar ce haka?", Nusram ta saukar da kai ƙasa. Haka suka yi sallama cike da ƙaunar juna kamar ƴan uwa na jini sosai, suna ƙoƙarin shiga Isa ya ƙaraso, Nusram taja hannun Nusreen dan su shige ya tare hanyar. Ta gefe ta koma nan ma ya sake tarewa, ita dai Nusreen kallon ikon Allah take yi, Nusram ganin hakan yasa tace; "Rim shiga ciki gani nan zuwa", Nusreen ta taɓe baki sannan ta wuce. Isa ya matso kusa da Nusram ɗin ta ja baya, ya kuma matsawa ta kuma jan baya, har sai da ta kai jikin bango, hannu ya kai kan saman fuskar ta, Nusram ta runtse idanu tana faɗin; wai Isa meye haka ne an faɗa maka ni ƴar iskace ko me?". Yace; "ok nine ɗan iskan kenan? To ki ajiye a cikin ranki kema sai na maida ke ƴar iskar, sannan ki sani wallahi matuƙar baki janye auren da kike so kiyi ba nima ba zan janye ba nayi miki alƙawarin sai kinzo kina roƙo na akan na aure ki", yana gama faɗar haka ya fice ya barta a wajen. Nusram taja dogon numfashi sannan ta shige cikin gida, Mama Jummai ta kalle ta tayi tsaki tace; "ayi dai mu gani". Ita dai Nusram bata wani kula ta ba, koda ta shiga ɗaki ta samu an kawar da kayan nasu hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba domin bata ƙaunar ganin kayan daya danganci bikin kwata-kwata. Da yamma zasu tafi makaranta Nusreen tace; "baki faɗa mini meye tsakanin ki da Isa ba", Nusram ta kwashe komai ta faɗawa Nusreen ɗin nan fa Nusreen ta hau masifa. Ita dai Nusram ɗin sai toshe kunne tayi dan yanzu hayaniya damunta yake yi, haka har suka isa makarantar Nusreen bata bar mita ba. Ƙarshe dai Nusram ɗin ta bar mata bencin, koda aka tashi haka ta dasa daga inda ta tsaya faɗi take; "wallahi ke kika bashi dama idan banda haka taya zai iya buɗe baki ya faɗa miki cewa wai yana son ki ko an gaya mishi bamu san asalin shi bane?, yaushe zai haɗa ɗan sunnah da ɗan zina". Nusram cikin takaici tace; "wai ke Nusreen kin manta a kan titi muke ne", Nusreen ta dalla mata harara tace; "ina ruwa na ko filin arfa muke", jin hakan yasa Nusram ɗin ƙyale ta. ********** ************* Cikin farin ciki take saukowa daga matattakalar jirgin babu abinda idanun ta ke son gani kamar ɗan nata. Dr Abubakar ya riƙo hannun ta ganin tana ƙoƙarin barin shi, cikin kunnen ta yace; "haba mana rabin raina ya zaki tafi ki barni", Brr Farida ta saki murmushi. Abdul dake tsaye a can wajen da ake jiran ƴan tafiyar ya saki murmushi ganin yadda iyayen nashi suka yi, sai da ya ɗauke su hoto. Dole Brr Farida ta jira mijin nata suka jero tare, Abdul ya saki hannun Adnan ɗin ya nufi wajen Mummyn tashi, ta buɗe hannayen ta ya shige ciki suka rungume juna cike da ƙauna da so. Daddy kuwa wajen ƴaƴan nashi ya ƙarasa inda ya bisu ɗai-ɗai yana rungume su, suma cikin farin ciki suke. Brr Farida ta shafa kan Abdus-samad tace;"nayi kewar ka sosai", shima cikin shagwaɓa yace; "nima ai kika tafi ki barni", taja kumatun shi tana faɗin; "kai ai ka fara tafiya ka barni", suka yi dariya duka. Hannun su sarke dana juna suka ƙaraso inda sauran suke, Abdus-samad ya saki hannun Brr Faridar ya ƙarasa wajen mahaifin nashi suka rungume juna. Dr Abubakar ya shafa kan Abdul ɗin yace; "Allah yayi maka albarka", Abdus-samad ya amsa da ameen, itama Brr Farida haka tabi yaran nata duka ta rungume su har da Fadila har tana tsokanar ta, Fadila kam murmushi kawai tayi. Abdus-samad ya haɗa rai ganin sun nufi motar Tameer, Brr Farida tayi dariya tace; "sarkin kishi to muje na shiga taka", Dr Abubakar ya riƙo hannun ta yace; "gaskiya ban yarda ba, nifa kin ga kishi nake yi dashi", duka akayi dariya. Abdus-samad ya shafa sumar kanshi yace; "shikenan kuje a tashi kawai", Brr Farida tace; "Surayya kije motar Abdus-samad ɗin". Surayya ta zunɓuro baki tace; "ni wallahi ba zan shiga jar mota ba kamar wata ƴar shan jini", Brr Farida zata kuma magana Fadila tace; "Mummy ki ƙyale ta zo ki shiga ta Yaya Sameer ni bari naje ta Abdul ɗin". Surayya ta shiga ta Sameer ɗin, Adnan kuwa yana wajen Mummyn shi, dan haka Sumayya da Fadila sune suka shiga motar Abdul ɗin. Motar Sameer ɗin ke gaba sai motar Tameer sai ta Abdul, suna cikin tafiya Fadila ta kalli Abdul ɗin tace; "gaskiya yau kun birge ni". Ya saki murmushi yace; "meya birge ki", ta ɗan kaɗa idanu tace; "yadda kuke son junan ku mana", Sumayya dake baya tace; "ai dama muna son iyayen mu sosai", Fadila ta jinjina kai tana faɗin; "na tabbatar da hakan". Sumayya ta buɗe baki zata yi magana Babbar mota ta nufo inda suke, kan Abdul yayi wani yunƙurin kaucewa motar ta buge su. Dr Abubakar ya kalli matar tashi, hannun ta ya riƙe yace; "na lura gangar jikin ki ke nan amma zuciyar ki na wajen Abdul". Brr Farida ta ƙara kai kallon ta jikin madubin a karo na babu adadi tayi murmushi tace; "ka dena haɗa kanka da ɗana fa", kan ta rufe baki ta hangi abinda ya faru, cikin sauri tace; "innalillahi wa'inna ilaihir-rajiiuun. Cikin sauri suka tsayar da motocin nasu, sai ga Brr Farida na gudu zuwa wajen motar tasu yau babu ƙasaita ba mulki ba gayu. Duka su Daddy suma suka nufi wajen, can gefen titi motar ta faɗa kusa da wata bishiya, gashi wajen babu mutane kasancewar bayan gari ne basu riga sun shiga cikin gari ba suna kallo me motar ya gudu. Da ƙyar aka iya zaro Fadila da Sumayya daga ciki, Abdus-samad kuwa sai da aka juya motar duk ta komatse, haka aka zaro shi kamar gawa. Brr Farida ta faɗi a wajen sumammiya, Tameer ya kira abokin shi wanda ya kasance likita ne aka turo musu da ambulance, Sumayya kuwa dama ɗan kujewa tayi, Fadila kuwa hankalin ta na nan amma kuma gefen fuskar ta da hannun ta na dama duka jini ne, Abdul ne ko numfashi babu tare dashi. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai* 📖📖29-30📖📖 Babu wanda hankalin shi ke jikin shi, koda suka isa asibitin cikin sauri aka wuce dasu *A&E* aka fara basu taimakon gaggawa. Daddy kuwa duk da kasancewar shi likita ya kasa taimakawa da komai. Sumayya da Fadila aka yiwa dressing ɗin inda suka ji ciwo, har ita Fadilan aka ce ta ɗan kwanta domin ta huta. Likitan ya fito yana cire handgloves ɗin hannun shi, da sauri suka bishi suna tambayar lafiya??. Likitan yace; "Dr ka biyo ni Office", haka Daddy ya bishi, sauran kuwa ji suke kamar suyi tsuntsuwa su ji abinda ke faruwa. Tameer ya zauna yana dafe kanshi, Sameer ya dafa shi yace; "ka dena damuwa Allah zai basu lafiya", Tameer yayi ajiyar zuciya yace; "yanzu wani sai yayi tunanin nina turo a kashe shi alhalin ba ni bane", Sameer ya girgiza mishi kai yace; "ka dena faɗin haka". Cikin tashin hankali Tameer yace; "Sameer ko ma meye Abdul ɗan uwana ne kuma ba zan iya cutar dashi ba", ganin yadda hankalin Tameer ɗin ya tashi Sameer ɗin ya fara kwantar mishi da hankali. "haba Tameer ai kowa ya san ba zaka taɓa iya aikata hakan a gare shi ba, domin kuwa ɗan uwa ya wuce wasa", Tameer dai babu abinda yake fata da buri banda Allah ya basu lafiya musamman ma Abdul ɗin wanda yake gani kamar shike da alhakin ciwon nashi. Likitan yayi gyaran murya yace; "Dr ku kwantar da hankalin ku be wani ji mugun rauni ba, ya tafi doguwar suma ne saboda tsoratar da yayi, mun duba babu internal injuries a jikin shi, sai matar ka ita kam munyi mata allura domin ta samu ta huta kuma shima ɗin muna saka ran nan bada jimawa zai farka, Allah ya kiyaye gaba", Daddy ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha yace; "ameen yana me fita daga ɗakin". Koda ya shiga ɗakin, suna kwance zaka iya tunanin barci ma suke, sai dai shi Abdus-samad ɗin hannun shi ɗaure da drip. Sameer da Adnan suna jikin gadon mahaifiyar su, Tameer kuwa yana can zaune a gefe ne jikin window ɗin ɗakin tana kallon waje yanzu ya gama waya da Surayya yana faɗa mata abinda ya faru. Daddy ya koma jikin gadon Abdus-samad ɗin ya tsaya, yana me tausayawa yaron wannan wane irin abu ne rayuwar yaron tana cike da hatsarrurruka gashi be san komai daga rayuwar shi balle ya dinga ƙoƙarin kare kanshi daga hatsarin. Surayya ta buɗe ƙofa ta shigo hankalin ta a tashe, ta faɗa jikin mahaifiyarta tana sakin kuka sosai. Tameer da Sameer suke rarrshin ta dan Adnan ganin Auntyn shi tana kuka shima kukan ya fara Daddy kuwa ya kasa ce musu komai. Ta goge hawayenta tana mata addu'ar samun sauƙi, can ta ɗago kanta; "ina Sumayya?", kanta rufe baki Fadila ta bude ƙofa ta shigo bayan ta kuma Sumayya ce. Itama Sumayyar wajen ƴar uwarta ta nufa suka rungume juna suna kuka, Surayya ta sake ta sannan ta janyo Fadila itama ta rungume". Daddy kam ikon Allah yake kallo, babu wanda ya kalli gadon da ɗan nashi yake kwance lallai ya tabbatar da cewa har yanzu Brr Farida bata shirya kan yaran nata ba. Daddyn Fadila yayi sallama ya shigo tare da mahaifiyar su, cikin sauri Fadilar tayi wajen iyayen nata ana jajantawa juna, Fadil da Salima sune suka shigo daga ƙarshe. Wajen gadon Abdus-samad ɗin suka nufa su direct, cikin damuwa Fadil yace; "Daddy har yanzu be farka bane?", Daddy ya dafa kanshi yace; "zai farka insha Allahu nan bada jimawa ba kuyi haƙuri tukunna. Nan suka koma suka zauna jugum domin kuwa daga Brr Faridar har Abdul ɗin babu wanda ya farka har zuwa lokacin kowa kuma a ciki fatan shi shine su tashi lafiya lau. Salima na riƙe da hannun shi tana zubar da hawaye domin kuwa hankalin ta ya kasa kwanciya, bata so ta rasa abinda take so. Fadila ta kalle ta sannan ta taɓe baki, ita fa ba wannan bane ya dameta, kuma ta san suna son abinda ba zasu taɓa samu bane daga Husnar har Salimar. Fadila ta dubi Fadil tace; "ina su Hajja banga sun zo ba?", Fadil ya taɓe baki yace; "kema kin san halin ƙasaitar matar nan waye zai iya zaman jiran ta, Malama tana so ta biyo mu amma matar nan ta hana wai sai dai ta jira ta su taho tare, baki ga yadda hankalin Malama ya tashi ba ina jin har kuka sai da tayi amma wai Hajja taƙi bari a taho da ita......". Daddyn shi ya kai mishi duka a ƙeya yace; "Fadil baka da hankali ko uwar tamu kake faɗawa haka muna wajen", be kuma cewa komai ba sai shafa wajen da yayi yana turo baki. *********** ************ *UNGUWAR RIMI, KADUNA* Shureim ya zauna kusa da mahaifiyar shi wacce ke zaune cikin kayayyaki, tunda taji labarin bikin nan hankalin ta ya koma kai. Tace; "ya akayi fatan an gama komai, ka san bana so azo a sami matsala ga Sharifa har yanzu bata iso ba", Shureim yace; "me kuma Aunty Sharifar zata yi?", Mama tayi mishi daƙuwa tace; "zaku je a ƙaro abubuwan da babu ne, Usman ma munyi waya akan sarƙoƙi da zai ƙaro ya dai ce yana tunanin a satin nan kayan zasu iso". Shureim ya kwantar da kanshi jikin mahaifiyar tashi yace; "Mama lallai kina ji dani", ta shafa kanshi tace; "wa nake dashi banda kai, Shureim kai nake gani na tuna da mahaifinka, dole na fito na nuna bajinta akan aurenka, ɗana guda ɗaya tilo. Sharifa tayi dariya tana karasa shigowa gidan tace; "Aunty kenan, kullum firar ku kenan". Mama tace; "to idan bashi ba ɗin da waye zanyi", Sharifa ta zauna kusa ɗa ƴar uwar tata sannan ta tura mata ledar gaban ta tace; "gashi mun riga da mun siyo da naga mun biyo ta wajen Mall ɗin tare da Baban Naufal shine nace mu ƙarasa kawai mu siyo". Mama ta fara ɓuɗewa tana faɗin; "yauwa gaskiya na gode sun kuma yi kyau sosai", ta ƙarasa tana ɗaga ɗogunayen rigunan". Aunty Sharifa tace; "nima sun birge ni shi yasa na ɗauko su", Shureim ya miƙe yana faɗin; "bari na tafi wajen aiki". Mama tace; "yanzu ƴar tawa sai bayan biki zan ganta kenan?", Shureim yace; "Mama kinfa santa ina wacce ranar da zan kai ki Airport.....". Kafin ya ƙarasa ta miƙe tana washe baki tace; "madallah kamar ka san yarinyar tana cikin raina, saboda hankalin ta nayi maka sha'awar ta gaskiya naji daɗi na san zan ji daɗin zama da ita ba kamar ƴar uwar ta ba, yarinya sai tsiwa". Gaban Shureim ya faɗi kada dai Mama tace bata son Nusreen. Aunty Sharifa tace; "wai wacece kuke magana akai", nan Mama ta shiga bata labarin ƴan biyun da suka haɗu a hanya da yadda ɗaya tayi musu rashin kunya ɗayar kuma ta basu haƙuri. Sharifa ta washe baki tana faɗin; "lallai kam tana da hankali sosai kuma ta cancanci ta shigo cikin wannan familyn". Shi dai Shureim a jiki a sanyaye ya bar falon domin kuwa abun yana so ya caɓe masa dole ya san yadda zai yi, ya kira Naufal a waya nan ya shiga faɗa mishi abinda ke faruwa. Naufal yace; "yanzu meye abin yi tunda dai biki ya matso ni ina ganin kawai ka faɗa mata gaskiya, dan koda baka faɗa mata ba wata rana zata gane idan kayi la'akari da yadda Nusreen take da tsiwa ba iya ɓoyewa zata yi ba". Shureim yace; "nima abinda nake tsoro kenan kada fa garin son zuciyana na nemo abinda zai zo ya ɓatawa Mama ya kuma janyo matsala tsakani na da ita, banda kowa a yanzu sai ita". Naufal yace; "hakane amma duk da haka baka sani ba ko meye dalilin da abubuwan suke faruwa a haka ba ta yiwu alkhairi ne auren ku". Shureim yace; "hakane", Naufal yace; "ni ina ganin ka faɗa mata kawai", Shureim yace; "shikenan zan gwada ɗin", daga nan kuma Naufal ya koma tsokanar Shureim ɗin har sai da Naufal ɗin yaga Shureim ya saki jikin shi sannan suka rabu a wayar. ******** *********** *HAYIN RIGASA, KADUNA* Ummi ta zauna kusa da Nusram wacce ta zuba uban tagumi kamar anyi mata mutuwa, ta dafa ta tace; "Nusram na faɗa miki tƴmun farko idan har bakya son wannan auren to ki faɗa mini ni kuma zan saka a hana". Nusram ta ɗago idanun ta wanda yake cike da hawaye tace; "Ummi kada ki damu da wannan insha Allahu zan yiwa Baba biyayya koda kuwa me zai faru". Ummi tace; "ban tambaye ki biyayya ga mahaifinki ba ko akasin hakan, tambayar da nayi miki shine kina son shi ko bakya son shi?". Nusram tayi murmushi me ciwo tana saukar da kai ƙasa, sanin cewa ba zata yi magana ba yasa Ummi miƙewa tana faɗin; "ke kika sani tunda ba zaki iya buɗe baki kiyi magana ba". Nusreen dake ƙoƙarin shigowa hannun ta riƙe da babbar leda don ta dawo ne daga Tudun Nufawa tace; "Ummi meya faru". Ummi tace; "meye kuwa be faru ba ni da ƴar uwar ki ne gata can taƙi ta faɗi abinda ke ranta game da auren nan". "ni wallahi abin na damuna Ummi, Nusram duk tabi ta lalace ta ƙare, gashi wajen gyaran jikin ma ta dena zuwa kana yi mata magana sai kuka Ummi ina tsoron kada damuwar da take ciki ya kaita ga halaka", Nusreen ta ƙarasa cikin damuwa. Ummi taja tsaki tace; "to ba ita taso ba, Nusreen ta fito ta cewa Baban ku bata son auren ta kasa sai dai ta zauna a cutar da ita". Nusreen tace; "bari naje wajen ta naji meke faruwa", tana faɗin hakan ta wuce Ummi zuwa cikin ɗakin. A zaune kamar yadda Ummi ta barta haka ta zo ta same ta, Nusreen tace; "Nusram ki yiwa Allah ki faɗa mana menene damuwar ki". "auren ne Nusreen bana so, kuma ba zan iya faɗawa Baba ba", wannan shine abinda zuciyar ta ta faɗa amma sai tace; "Nusreen ki taya ni da Addua kawai". Koda Nusreen ta takura mata kuka ta sakar mata kawai, cike da tausayi Nusreen ɗin ta biye mata suka dinga rera kukan tare sai da Ummi ta shigo tayi musu tatas sannan suka yi shiru. ********* ********** *UNGUWAR SARKI, KADUNA*. Tameer ya kalli agogo sannan ya kalli Daddy yace; "Daddy har yanzu shiru basu farka ba kome ke faruwa kuwa". Daddy shima cikin damuwa yace; "ku cigaba da addu'a zasu farka ne", haka suka yarda da shawarar mahaifin nasu. tana tsugunne tana kuka cikin tashin hankali, taji an dafa kafaɗarta, cikin sauri ta waigo fuskar da ba zata taɓa mantawa bace take kallon ta. Itama ta tsaya tana kallon ta, waccen matar tace; "Bestyy kin yi sanyi dole ki ƙara gudun tafiyar ki idan ba haka ba Mustafa yana daf da cin miki". Cikin yanayi na rashin madogara da kuma karyewar zuciya Brr Farida tace; " taya zan aikata hakan bayan ban san inda Abdul yake ba, ji nake kamar ya tafi ya bar ni, Abdus-samad shine ƙarfi na yanzu kuma babu shi". Matar tayi murmushi tace; "kada ki damu ɗanki na nan be tafi ba, zo muje ki ganshi", ta kama hannun Brr Farida zuwa wani kyakykyawa Lambu ta ɗaga hannu ta nuna mata inda Abdus-samad yake zaune fuskar shi ɗauke da murmushi yana kallon ta. Cikin jin daɗi ta nufi inda yake sai dai kafin ta kai wani irin jibgegen Shaho da jajayen kaya yazo ya sungume Abdul ɗin yayi sama dashi, nan fa Brr Farida ta fara Kuka tana ƙwalawa Abdul ɗin kira. Daddy ya riƙo ta yana tofa mata addu'a, ita kuwa da bata san yanayi ba kukan ta kawai take sha tana kiran sunan Abdul ɗin. A hankali kuma idanun ta ya fara buɗewa har ta buɗe shi tas, shiru tayi tana kallon su ɗai-ɗai sai taji ranta yayi sanyi sanin cewa mafarki take yi. Tayi murmushi tace: "kaga ashe mafarki ma nake yi, ja ɗauka gaske ne ina Abdul ɗin?", Dr Abubakar yace; "calm down My Brr ɗanki yana lafiya", jin hakan ya tuno mata da mafarkin ta. Sai tayi murmushi tace; "ina yake My Dr ina son ganin shi, na san duk inda nake zai kasance a wajen?", Sumayya ta ƙaraso kusa da ita tace; "Mummy Abdul barci yake yi yanzu ko kina so a tashe shi ne?". Ta girgiza kai da sauri tana lumshe idanu sai dai cikin sauri ta buɗe su sannan ta sauke kan Fadila wacce kanta ke manne da plaster, a hankali kuma komai ya fara dawo mata cikin kai. Cikin sauri Brr Farida ta fara yunƙurin miƙewa amma Dr Abubakar ya hanata, gaba ɗaya ta ruɗe tana faɗin; "shikenan sun kashe mishi shi". "yanzu meya faru dashi ya mutu ko?, na dena ganin shi?", magan-ganu dai kala-kala, ganin bata hayyacin ta yasa Dr Abubakar riƙo ta jikin shi ya rungume ta saki kuka me ƙarfi. Kowa yana tausaya mata, Abban Fadil sai da jikin shi yayi sanyi sanin irin ƙaunar da take yiwa ɗan nata, ya kalli gadon da Abdul ɗin ke kwance kamar gawa. Malama da Saleema kuwa duk idanu ya kumbura tsabar kuka, Hajja ce ma dai ta dai yi hawayen amma ba kamar su ba dan itama yadda tazo ta same su abin ya bata mamaki. #LIKE #SHARE #COMMENT *babyn abdul maman meenal elham da farouk* *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *Ga masu cewa ina jan littafin ne dan na samu kuɗi, Wallahi ba haka bane domin kuwa da ina son siyar da littafi da tuni nayi sai dai ina so ku sani kuɗin ku bashi ne a gaba na, duk wanda ya ɗauki wani abu ya bani ya bani dan raɗin kanshi ne ba wai dan na tambaye shi ba, hasalima kyautatawa ce tsakani na dasu, rubutun novel buri na ne dan haka bana fatan ko gaba nayi novel ɗin siyarwa, na gode sosai to ai hikenan😉*. *Godiya ta musamman ga Zuciya ta, da kuma Matar so ina miki son so sannan ina jin daɗin sharhin ki sosai Shabihaty fans club kuna ƙarƙashin zuciyar One Love* *Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai* 📖📖31-32📖📖 *UNGUWAR SARKI,KADUNA* Cikin sauri ya buɗe idanun shi yana faɗin; "innalillahi wa'inna ilaihir-raji'uun", ƙoƙarin miƙewa yake yi Brr Farida ta riƙo shi cikin sauri. ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya, Brr Farida kuwa harda ƙara ƙaƙumeshi hawaye yana saukowa daga idanun ta. Tameer ya shigo tare da likitan da yaje kira, sai a lokacin suka saki juna allurar barci ya kuma yi mishi babu ɓata lokaci barcin ya kuma kwashe shi. Hajja tace; "tunda yayi barci bari muzo mu tafi Allah ya ƙara sauƙi, Mus'ab(Abban Fadil) ka tashi muje ka sauke mu a gida". Haka ba dan sun so ba suka miƙe dukkan su, bayan sun tafi Brr Farida ta kalli Surayya tace; "kuma ku wuce gida, na san zuwa anjima zasu sallame mu", haka suma suka tafi cikin jimami Sameer ya tafi kai su. Ya rage saura Tameer da Brr Farida da Dr Abubakar, hakan yasa wajen yayi shiru, ita dai Brr Farida tana riƙe da hannun Abdul ƙam-ƙam kamar za'a ƙwace mata shi. Lokaci zuwa lokaci take sauke ajiyar zuciya, kallon shi take cikin tausayawa tabbas da saka hannun wani a wannan lamarin to waye kenan?. Amsar da ta kasa samu kenan, bata da tabbacin wanda take zargi domin kuwa bata da wata hujja. Kamar ance ta ɗaga ido ta kalli saitin window idanun ta ya hasko mata dattijon dake tsaye jikin window. Ƙara zaro idanu tayi gabanta yana dukan uku-uku, shima kuwa ganin ta hango shi yasa yayi saurin barin wajen. Brr Farida ta miƙe a kiɗime, Dr Abubakar da be san meke faruwa ba yace; "My Brr ina zuwa kuma?", ta bashi amsa yayin da take ficewa daga ɗakin; "ina zuwa". Sauri take yi kamar ƙafarta zata tsinke ta fice ta zagaya bayan window ɗin, sai dai kash baya wajen nan ta hau jefa idanu tana neman ina zata ganshi. Har bakin get taje neman shi sai dai Allah be bata sa'ar ganin wanda taje nema ba haka ta gama zagayen asibitin ta dawo. Tana daf da shiga ɗakin idanun ta ya sauka a kanshi, da sauri ta ƙarasa kusa dashi, shima kuma ita yake kallo fuska gwanin tausayi. *MUSTAPHA ABUBAKAR TUGE* sunan data ambata kenan a bayan ta iso kusa dashi, ya kalli mutanen wajen sannan ya maida idanun shi kanta itama ta kalle shi ta ɗaga gira ɗaya. "ko nace Mustapha Sulaiman harɗo, wanne yafi dai-dai? Yadda kake da fuska biyu hakama sunan ka yake". Alhaji Mustapha ya kalli kanshi ya ƙara kallon jama'ar wajen yana da tabbacin dan basu gane ko waye shi bane da yanzu sun cika wajen dan kowa ya san shi a faɗin garin kaduna kai kaf Nigeria yana ɗaya daga cikin masu kuɗi na farko-farko, gashi kuma da taimakon jama'a sosai wannan ya ƙara mishi farin jini. Cikin kwantar da murya yace; "Brr dan Allah kizo muje garden ina so muyi magana dake". Brr Farida tace; "babu magana tsakani na da kai domin babu abinda ya haɗa ni da kai", ta ƙarasa cikin ɓacin rai. Ya sauke ajiyar zuciya sannan yace; "naji ance Murad yayi hatsari ne shine nazo duba shi, naga jikin nashi ma da sauƙi hankali na ya tashi sosai ina ƙasar Mali labarin yazo mini", ya ƙarasa fuskar shi ɗauke da damuwa. Brr Farida ta taɓe baki sannan tace; "kamar da gaske yadda ka maida fuskarka sai kace na Allah, to bari kaji kana ɗaya daga cikin prime suspect ɗina kuma zan yi bincike matuƙar da saka hannun ka akan abinda ya sami Abdul bar ganin kana da kuɗi zan tarwatsa farin cikin ka ne". "haba Farida ya kike magana haka, kada ki manta nine mahaifin Murad ba zan taɓa iya cutar dashi ba, waccen ma baki fahimta bane kuma Fiddausi ma..........". "dakata ya ishe ni haka! Ka tabbatar ka bar wajen nan domin dai ka sani koda wasa ba zan taɓa bari kaje kusa da ɗana ba ko?, Sannan nayi maka gargaɗi ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba akan ka fita harkata nida ɗana kaƙi ji ko? To wallahi zan ɗauki babban mataki akan ka", tana gama faɗar haka ta shige ta barshi a tsaye. Alhaji Mustapha ya tsaya cike da takaici gashi yana so ya ga lafiyar ɗan shi amma babu dama, ya kalli kayan dake jikin shi riga daban wando daban sai hula irin taɓani kaji hadisin nan, wannan duk yayi ne dan yazo yaga lafiyar yaron nashi amma abu be yiwu ba haka ya tafi. Brr Farida kuwa tana shiga ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dai-daita natsuwar ta kafin ta ƙarasa inda yake. Abdul daya farka yana tambayar ina Mummyn shi ganin ta yasa ya danyi murmushi amma be samu martani ba zama kawai tayi gefen gadon. Ya ɗora kanshi saman kafaɗar ta, ita kuma ta lumshe idanu har yanzu ƙirjin ta be bar bugawa ba, Dr Abubakar ya zuba mata idanu kawai ganin yadda fuskar ta tayi ya san akwai abinda yake damun ta. Sun jima a haka sannan likitan ya shigo, yayi murmushi yace; "da alamu dai wannan jinyar ta ƙare ganin yadda majinyacin ya zama ɗan lele", duka suka yi murmushi banda Brr Farida. Nan ya bashi magunguna sannan ya fice, da ƙyar aka samu ya sha maganin sai shagwaɓe fuska yake yiwa Mummyn nashi ganin yadda fuskar Brr Faridan yake yasa ya koma serious. Sai da ta gama bashi sannan yace; "First love lafiya? Meke damun ki?", ta riƙo hannun shi sannan tayi yaƙe tace; "kada ka damu babu komai me zai dame ni bayan ɗana ya buɗe idanun shi bayan doguwar sumar da yayi". Yinin ranar haka Brr Farida tayi shi sukuku domin kuwa motsi kaɗan sai taga kamar Alhaji Mustaphan zai dawo inda suke yazo ya cutar mata da ɗa. ******** *********** *HAYIN RIGASA, KADUNA* Kwanci tashi babu wuya gashi Allah ya nuna mana lokaci domin kuwa yau saura sati ɗaya bikin su Nusreen, duk ɓangaren uku shirye-shirye suke babu kama hannun yaro. Nusreen a lokacin idan ka ganta kamar ka sace ta ka gudu tsabar kyawun da tayi saboda ta tsaya sosai Aunty ta gyara ta kuma yadda ya kamata jikin ta har wani sulbi yake yi ga wani yelo-yelo da tayi tsabar haske da dilka data sha. Saɓanin Nusram da tayi baƙi ta rame sai idanu zuru-zuru, irin farin cikin nan da amarya take yi kam to banda Nusram domin kuwa tunda satin bikin ya kama ta tabbatar da cewa auren za'a yi mata da Alhaji Baballe ta kwanta zazzaɓi ya rufe ta. Yanzun ma tana kwance jikin ta yayi zafi rau, sai rawar sanyi take yi Nusreen ta shigo ita da Yasmin ƙawarta, sun dawo daga rabon kati duk wani wanda ya kamata su kaiwa to suna ta ƙoƙarin kai mishi. Gaba ɗaya hidimar daya kamata ayi ta da Nusram sai Yasmin ce ta wakilce ta, Halima ma tazo duk da ba sa'ar su bace amma takan taimaka musu wajen yin hidimar bikin. "wallahi na gaji sosai gashi gobe ma sai mun sake fita", Nusreen ta faɗa tana ƙoƙarin zama gefen katifar da Nusram ke kwance. Yasmin tace; "ai gobe kinga Hayin banki zamu shiga sai kuma Shaheeda da take Unguwar Sarki shikenan sai mu dawo". Nusreen ta yamutsa fuska tana faɗin; "nifa dan dai kin matsa ne amma da bazan wani kaiwa Shaheeda ba", Yasmin tace; "aikuwa ya kamata, dan Shaheeda tana da ƙoƙari kuma ta gayyace ki bikin yayan ta, dan dai kin ƙi zuwa ne". Nusreen bata ce komai ba sai hannu data kai kan jikin Nusram; "kai Ram jikin ki zafi fa baki da lafiya ne?". Nusram ta ɗaga kai kawai hawaye na zubo mata, Nusreen tace; "to kin sha magani", nan ma Nusram ta ɗaga mata kai kawai, "Allah ya baki lafiya to", Yasmin tace; "ameen dai". Nusreen ta miƙe taje ta zubo musu abinci ta kawo nan suka fara ci, ita dai Nusram zazzaɓin banda ƙara rufe ta da yayi ga wahala, shaƙar ƙamshin abincin da taji amai ya taso mata. Tayi ƙoƙarin miƙewa ta fice daga ɗakin tana ƙarasawa bakin famfo ta fara sheƙa amai me wahala domin kuwa babu komai a cikin ta wanda zata fitar dan rabon data kai abinci bakin ta tun jiya da rana shima sai da Nusreen tayi kuka a gabanta sannan ta yarda ta ci da dare kuwa tun kan Nusreen ɗin ta fara kuka ita ta fara domin bata son cin komai dan ɗaci yake yi mata sosai. Aunty dake tsaye a ƙofar ɗaki suna lissafin kuɗi da alama matar da zata yi musu dubulan da cin-cin ne tayi saurin ƙarasowa kusa da Nusram ɗin tana yi mata sannu. Ita ta taimaka mata har ta gyara jikin ta sannan ta wanke wajen tas, ta ƙwalawa Nusreen kira babu ɓata lokaci ta fito. "kamata kuje ɗaki", Nusreen tace; "to Aunty aman tayi ne?", Aunty tace; "eh wallahi ai inajin Yayan ku yana zuwa zasu tafi asibiti tare". Mama Jummai dake kusa da murhu kamar koda yaushe tayi shewa tace; "ai amai yanzu ta fara shi kuma muddin ina raye bata ba aure", babu wanda yabi ta kanta. Da yamma Yaya Sulaiman ya tasa Nusram a gaba suka je wani ƙaramin asibiti nan aka dubata aka bata magun-guna suka dawo gida. ********* *********** *MAƘARFI ROAD, KADUNA*. ya zauna yana me ajiyar zuciya, meke faruwa ne, shi kanshi baya da tabbas ɗin abinda yake faruwa yanxu". Ɗayan mutumin dake zaune kusa dashi yace; "ka kira ni tun ɗazu amma baka ce mini komai ba, meke damun ka ne Tuge?". Alhaji Mustapha ya sauke tagumin da yayi sannan yace; "Brr Jibril ina cikin tashin hankali, ɗana baya da lafiya yana asibiti". Saura kaɗan tray ɗin da matar ta shigo dashi a hannu ya faɗi, yar kyakkyawa da ita baƙa mara tsayi, kana ganin ta zaka tabbatar da cewa itace matar gidan. Sai da ta dai-dai ta natsuwar ta sannan tayi sallama ta shiga, kusa da Brr Jibril taje ta ajiye tray ɗin sannan ta matsa kusa da mijin nata tana miƙa mishi hannu, yayi kissing hannun. "Abban Khausar zan koma wajen aiki domin yanzu muka yi waya da Md yace nazo da sauri", matar ta faɗa. Alhaji Mustapha yace; "a dawo lafiya", daga haka ta fice cikin sauri. Brr Jibril yace; "ya jikin nashi fatan da sauƙi dai ko?", Alhaji Mustapha ya ɗaga kai yace; "da sauki sosai sai dai Brr Farida bata barni na ganshi sosai ba". Brr Jibril yace; "kada ka damu Alhaji wata rana komai zai zamo me sauƙi insha Allahu ka dage da addu'a kawai". "Brr Jibril tana zargina da yunƙurin kashe ɗan dana haifa", Alhaji Mustafa ya faɗa cike da damuwa, Brr Jibril yace; "kada ka damu just pray", yayi mishi sallama sannan ya fice. Cikin tashin hankali take tuƙi, bata ma jira masu tsaron lafiyar nata ba, sai da ta gangara can wajen Kaduna by pass sannan ta gangara zuwa wani gidan gona. Tayi horn me gadi yazo ya buɗe mata sannan ta shiga, tana yin parking sannan ta fito daga motar kamar zata tashi sama tana shiga ciki ta sami kujera irin ta shaƙatawa ta zauna. Mutumin dake cikin ruwan tare da wata mace suka fito a tare, duka kallon ta suke yi cikin alamun tambaya. "Abdus-samad be mutu ba", ta faɗa cikin takaici, ɗayar tayi murmushi tace; "na san da hakan ai tun jiya dan har su Malama da Hajja sun je dubo shi". Mutumin yayi dariyar mugunta sannan yace; "aikin Razor beyi ba, dan haka na tura Scorpion da saƙo zuwa gare shi". Dukkan su sun san saƙon kona meye dan haka suka yi murmushi, Mutumin yaja kujera kusa da Matar ya zauna sannan ya riƙo hannun ta yace; "Salma kada wannan abin ya ɗaga miki hankali, Abdus-samad zai mutu dole ne wannan koya so ko be so ba domin babu wanda ya isa ya hanani kauda shi daga bayan ƙasa". A'a bawan Allah akwai Allah fa, kuma dama idan kwanan mutum ya ƙare ai dole ya mutu😏. Hajiya Salma ta saki ajiyar zuciya sannan tace; "tabbas hakane amma Alhaji Sa'eed ina tsoron abinda zai biyo baya, bana so mustafa ya mutu ace bani zan gaji dukiyar shi ba ni da yarana kawai nake so su gaji ɗumbin dukiyar shi". Alhaji Sa'eed yayi murmushi yace; "kada ki damu ke da ƴaƴan ki kawai zasu gaji dukiyar Tuge sai dai zaki san mana nida Baby na", ya ƙarasa yana kanne ido ɗaya. Salma ta kalli Brr Hauwa suka yi murmushi tare, Alhaji Mustafa yace; "yanzu zan sami biyan buƙata ko?". Salma tace; "me zai hana sai dai kayi da sauri dan bana so Alhaji ya fahimci daɗewar da nayi gashi ban fito da Securities ba". "ba matsala just one hour ma yayi", ya faɗa yana riƙo ta daga nan suka shige ciki inda suka bar Brr Hauwa zaune a wajen tana shan iska. Alhaji Mustafa kuwa ya jima kafin ya tashi ya fito, a falo ya sami yaran nashi guda biyu da Khausar babbar kenan wacce a satin nan ta dawo daga ƙasar Singapore inda take karatun likitan mata, sai mai bi mata Khaleesat wacce take NIGERIAN TURKISH INT ABUJA, tana secondry. "Yauwa Daddy dama maganar shopping ɗin da muka yi", Khaleesat ta faɗa cikin shagwaɓar yaran masu kuɗi. "yanzu duk kuɗin dake account ɗin ki Khaleesat sai kin tambaye ni?, kije wajen Habu ya kaiki zan miki tranfer yanzu". "yauwa amm.......", yayi saurin dakatar da Khausar dake ƙoƙarin yin magana yace; "ina buƙatar hutu", daga haka ya wuce kawai. Khausar ta taɓe baki, Khaleesat kuwa murna sosai tayi sannan ta haye sama inda ta hau shiryawa domin tafiya siyayya ɗin. Sai bayan magrib sannan Hajiya Salma ta dawo, sai da ta shiga nata ɗakin tayi wanka ta sake shiryawa cikin riga da skirt ɗin material me kyau da tsada sannan ta fito. Kitchen ta shiga ta haɗa Coffee sannan ta nufi sama inda ɗakin me gidan nata yake. Ta shiga da sallama, yana yin waya ne dan haka koda ta ajiye sai ta nemi waje ta zauna, Alhaji Mustafa ya kalle ta sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin, Hajiya Salma ta taɓe baki. "Alhaji Mustafa ka bani mamaki yanzu har kaine zaka iya zuwa dubo ɗan ka ba tare da sani na ba". Alhaji Mustafa yayi jim sannan yace; "amma dai Alhaji Sa'eed ka san da cewa yaron nan shi kaɗai ne ɗana namiji ko, sannan kuma dole sai na shiga jikin su sosai kafin na iya aiwatar da umarni Oregbu a kanshi". Alhaji Sa'eed yayi murmushi sannan yace; "hakane kuma tabbas, yanzu ya jikin nashi", Alhaji mustafa ya sauke ajiyar zuciya yace; "Brr Farida bata barni na shiga ba". "toh! amma dai ina so na ƙara tuna maka da cewa saɓawa umarnin Oregbu dai-dai yake da ɗaukewar numfashin ka dan haka kada son ɗanka ya saka ka saɓa mishi". Alhaji Mustafa kamar zai zubar da hawaye yace; "na sani kuma zan aikata hakan insha Allah", daga haka ya katse wayar. Ya jingina da jikin steps ɗin yana sauke ajiyar zuciya, ya zai yi ne?, ɗan shi ƙwara ɗaya tal wanda yake tsananin ƙauna shi zai bawa Dodo ya sha jinin shi, meya saka tun farko ma.yayi wannan alƙawarin". Oho maka dai kai ka sani😏 Me kan gwanda. Aishatu Babayo ta ranƙwashe ni tace; "idan kika kushe shi ai kamar kin kushe Abdul ne baki ganin kamar su ɗaya". Na taɓe baki ina me ƙare mishi kallo, tabbas abinda Zuciya ta(Aishatu Babayo) ta faɗa gaskiya ne kamar su ɗaya da Abdul bambamcin su kawai girman jiki dan Alhaji Mustafa ya ɗan manyan ta. *Na san wasu zasu ce yau kuma ina One love ta tafi, naji sabbabin suna to ai dama sabbabin suna ba xasu ƙare a buk ɗin nan ba har sai mun kai tsakiya ko ince kusa da ƙarshe sannan ba lallai ku fahimci littafin ba sai munje ƙarshe shima ko.ince tsakiya, fatana dai kuyi haƙuri ku cigaba da bina duk da dai na san ina muku ƴar zilliya amma kamawa tayi ina kuma ƙara baku haƙuri domin kuwa na san cewa kuna haƙuri sosai*. #LIKE #SHARE #COMMENTS *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖33-34📖📖 *UNGUWAR SARKI, KADUNA*. Sai da Abdul ya ƙara kwana biyar a asibiti sannan aka sallame shi, kuma Alhamdulillahi jikin shi yayi sauƙi sosai da sosai. Sameer ya kaisu har gida inda ya tarar da su Suraiya suna mishi barka da dawowa, yaji daɗi sosai hakama Brr Farida ita da Dr Abubakar duka sun ji daɗi. Ɗakin shi ya wuce yayi wanka sannan ya kwanta domin ya huta, sai dai kanshi da yaji yana sara mishi wanda hakan yasa barcin yaƙi zuwa. Ya jima a kwance kafin wayar shi ta hau ƙara, ya ɗauko ya kara a kunne, "yallaɓai y gida ya aiki?", dama cewa nayi bari na tuna maka ɗaurin aure na 28th Feb 2020, nan da jibi kenan". *************************⬇********************** ************* Top Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.thn.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > tophausanovels@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Top Hausa Novels Twitter: Top Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels Telegram Group: https://t.me/tophausa Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Top Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Abdus-samad yace; "insha Allahu ba zan manta ba zan zo kuma", Shureim yace; "yauwa nagode sosai na bawa Fahad IV zai baka". Yace; "shikenan, sai anjima", daga haka suka yi sallama, be jima ba barci ya kwashe shi. Sai wajen la'asar ya farka, yayi alwala ya rama sallar dake kanshi sannan yayi wanka ya fito, a falo ya sami Fadila da Surayya suna fira. Duka suka yi mishi sannu da jiki ya amsa shima, waje ya fita kawai inda ya tarar da Sumayya da Tameer a zaune. "barka da fitowa Yah Abdul ɗazu ai naje wajen ka amma kana barci sai na ƙyale ka", cewar Sumayya, Abdus-samad yayi murmushi yace; "hakane, Yaya Tameer barka da hutawa". "barka ya jikin", ya tambaya, sai da ya shafa gashin kanshi sannan yace; "da sauki", daga haka babu wanda ya kuma magana a tsakanin su. Abdul yana zuba musu idanu da alama fira suke yi akan wani abu me mahimmanci, "Yaya ni ina ganin kawai ka sami Daddy da maganar". "kin san halin Mummy shiyasa nake so ki fara sanarwa da Daddy ke da kanki idan yaso sai ni nayi mata magana daga baya", Sumayya tayi dariya tace; "to Yaya na". "tunda kina son a fita dake anjima ba", ta kuma yin dariya tace; "Yaya ai kaima buƙatar kanka ta tashi", yace; "to ya isa haka". Motoci suka fara shigowa gidan dan haka duka suka maida hankalin su kan motocin, sai da suka gyara parking sannan Brr Farida ta fito ita da mijin ta. Abdus-samad ya miƙe da farin ciki ya tare ta, ta mishi peck a goshi sannan tace; "ka gama barcin kenan?, na shiga wajen ka ai Daddyn ku na raka wajen wani tsohon abokin shi wanda ya kusa aure". Duka suka yi dariya, Brr Farida ta harare su duk suka yi shiru banda Abdus-samad, tace; "kai kuma ba zaka dena ba kenan?". Ya ɗora yatsun shi biyu saman leɓen shi, Tameer yace; "saboda Allah me sa'an Daddy zai yi da mata?", Brr Farida tace; "sai kaje ka tambaye shi". Abdus-samad ya kauda kai gefe yace; "ni tsorona ma ace tare da Daddy zasu angwance, dan maza ba abin yarda bane". Brr Farida ta kalli Dr Abubakar da sauri, cikin sauri ya girgiza mata kai yana faɗin; "me zan yi da wata amarya a yanzu ai ke kin ishe ni". Brr Farida tace; "kai dai ka sani wallahi ka sake ka ƙara aure kai da matar sai na maka ku kotu", suka kwashe da dariya, cikin jin haushi ta shige cikin gidan ta barsu. Dr Abubakar ya gallawa Abdus-samad harara yace; "kana neman janyo mini tashin hankali ko", ya saukar da kanshi ƙasa yace; "yi haƙuri Daddy", ya rasa me yasa duk soyayyar da mahaifin nashi yake nuna mishi baya iya sakewa dashi kamar yadda yake sakewa da Mahaifiyar shi, sai ya dinga jin nauyin shi sosai. Nan ya zame yayi part ɗin shi ya barsu suna cigaba da yiwa Daddy dariya dan haƙiƙanin gaskiya ya kasa shiga gidan. ******** ************* Baba ya gyaɗa kai bayan ya gama sauraren bayanan Ummi sannan yace; "Maman Kubra wa'innan yaran ƴaƴa na ne dan haka ki fita daga cikin wannan maganar". Ummi tace; "ni dama ba wani abu nace ba gani nayi ita waccen ba lafiya ta cika ba.......", be bari ta ƙarasa ba ya katseta. Cikin tsawa yace; "sai akayi me kuma? Nawa ake kaisu gidan miji basu da lafiya?", Ummi ta girgiza kai sannan tace; "maganar gaskiya fa ba son auren nan take yi ba kawai ina gani a fasa shi, don gaskiya bana so tayi irin wannan auren". Baba ya ɗauke ta da mari hagu da dama, hakan ya janyo hankalin dangin ta da dangin shi wanda suka zo daga Dabai, sun ɗauka shawara suke yi a tsakaninsu amma zuwa yanzu sun fahimci cewa faɗa ne suke yi. Inna Gaje( Ƴa ga me gari wacce take kamar ƙanwa a wajen Abdullahi), ta ƙaraso da sauri tana faɗin; "ashsha meya kawo faɗa kuma yanzu". Baba ya nuna Ummi yace; "wallahi kar ki ɓata mini rai idan ba haka ba zaki sha mamaki na, kuma ki sani aure babu fashi matuƙar baki goyi bayan shi ba to zaki bar garin nan ki koma Dabai kuma ba'a matsayin matata ba a matsayin bazawara dan wallahi duk wanda ke adawa da wannan auren zan iya rabuwa dashi ko waye, kuma itama munafikar ki fada mata matuƙar ba zata mini biyayya ba to ta tattara kayanta ta bar mini gida kuma ta nemi wani uban dan babu ni babu ita". Nusram ta fashe da kuka bayan sauraren bayanin Baban, Ummi ta share hawayenta tace; "kiyi haƙuri kinji", Nusram ta ɗaga mata kai kawai domin bata da bakin magana a lokacin. Nusreen kuwa jikin ta yayi sanyi sosai ganin yadda mahaifiyar tasu take zubar da hawaye, wannan wane kalar cin mutunci ne ace a bainar jama'a sai Mahaifin nasu ya nuna basu da galihu. Aunty ke aikin rarrashin Ummin, tana kuma ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Ba jimawa wayar Nusram ta ɗauki ƙara ganin Yaya Sulaiman yasa ta ɗauka. "fito waje ina jiran ki", abinda ya faɗa kenan ya kashe wayar, Nusram ta miƙe duk da jikin ta babu ƙwari, Nusreen ta miƙe da sauri tana so ta taimaka mata amma Nusram ta dakatar da ita. "kada ki damu Ya Sulaiman ke nema na a waje", abinda ta bata amsa dashi kenan sannan ta saka hijab ta fita. A tsakar gida ta sami Mama Jummai da Babbar ƴar ta Habiba sai ƙaramar wacce bata yi aure ba Atika a tsaye suna magana amma suna ganin ta suka dena. Nusram ta kauda kai domin ita Habiba dai ƙanwar tace amma bata wani birge ta dan yarinyar akwai shige-shigen boka, kwanaki ma garin hakan ne wani ɗan damfara ya damfare ta dubu ɗari uku. Idan kaje ɗakin ta babu komai ko leda babu amma kuma ta san inda take fito da kuɗin zuwa wajen boka, shi yasa sam basa shiri da Nusram kwata-kwata. Atika kuwa ta cika girman kai da gani-gani hakan yasa Nusram ko kulata bata yi dama dai waccen ƴar neman rigimar ce amma ita kam ko kallon inda take bata yi. Dama cikin su masu sauƙin biyu ne Sahura da Ameera sune kuma wa'inda Nusram ke kula su. Su kuwa duka biyun shakkar Nusram ɗin suke yi hakan yasa basa shiga sha'anin ta, ko kwanaki sai da Nusram ɗin ta kama Atikar ita da wani ɗan iskan yaro suna taɓe-taɓen su, hakan ya tsorata Atikar amma taga koda ta dawo gida Nusram ɗin ko kallon ta bata yi ba haka duk ƴan gidan babu wanda yayi mata magana hakan yasa take ƙara shakkar ta( rashin kula ɗan iska da mara kunya ya kan ƙara maka kwarjini). Habiba tabi bayan ta da harara tana me jan tsaki, Mama Jummai tace; "barta duk ta gama iyayin ai na yau ne". Habiba tayi dariya tace; "ina fa wani iyayi mutum ya kuma kamar tsinke", Atika tace; "ina jin iskancin da take yi ne acan ta samu HIV", suka kwashe da dariya. Habiba ta ciro ƙullin magani guda ɗaya da turare da kuma laya guda ɗai-ɗai, ta ɗaga maganin tace; "wannan yace duk yadda za'ayi a tabbatar Baba yaci a cikin abinci yau da daddare". Ta miƙawa Atika turaren tace; "wannan kuma ke ce zaki shafa shi yanzu idan Alhaji Baballe yazo kije ki gifta ta gaban shi abinda ake buƙata kawai yaji ƙamshin, sai wannan layar ita kuma ki sami kusa da rijiya anjima bayan kowa yayi barci ki haƙa ki saka ta a wajen shikenan aikin". "yace da zarar Baba yaci abincin nan to zai ƙara tsanar ta ne sannan duk abinda kika ce zai aikata, shi kuma Alhaji Baballe da zarar yaji ƙamshin wannan turaren to duk abinda Baba yace mishi zai aikata, yadda layar nan take a binne haka bakin shegiyar zai ɗaure ba zata iya ƙaryata komai ba haka kota ga Bangis ba zata mishi ihu ba", suna gama jin bayanan Habibar suka shewa. "wato na lura Habiba kin fini tsanar wa'innan yaran, shi yasa kika fi waccen soloɓiyon". "ai dole nayi kishi dasu kinga akwatin ɗazu da ina ganin saura kaɗan jini na ya hau, barin ma na Nusram goma sha biyu fa kai dole ma su koma na Atika". Mama Jummai ta kuma washe baki tana faɗin; "yauwa ƴar albarka haka nake son ji daga bakin ki", Atika kuwa sai faman murna take yi jin duk wa'innan uba uban kayan zasu koma nata. A saman sabuwar motar shi ta same shi, shima dai Yaya Sulaiman ɗin saura kwana ashirin da biyar nashi bikin shi, tayi sallama ya amsa mata yana binta da kallon tausayawa. "Nusram wai me yasa ba zaki rungumi ƙaddarar ki ba kiyi haƙuri ko Allah zai baki lada, haba Nusram kamar ba musulma ba". Hawaye ya zubo mata, cikin sheshsheƙar kuka tace; "Ya Sulaman nifa na haƙura kuma na yarda da duk abinda ya same ni daga ubangiji ne sannan ina neman lada a wajen shi, sai dai wasu abubuwan ne dole naji takaicin faruwar su". Yace; "ya isa haka, be kamata ace har yanzu kina zubar da hawayen ki ba, ki zama jaruma mana", ta jinjina kai tana goge hawayen fuskarta. Yace; "yauwa ko kefa, yanzu amshi wannan ɗinkin ku ne wanda zaku saka gobe akwai shadda a ciki kalar brown ita zaku sa da rana anko ne gaba ɗayan mu", ta amsa da to tana mishi godiya. Ya ɗan ja ta da fira har ta sake tana maida mishi da fara'ar ta, kan wani lokaci ma har ta soma kwasar dariya, tabbas Sulaiman ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar ta Nusram. Koda su Shureim suka zo Nusreen ta fito wajen su, tayi mamakin hangen ƴar uwar tata tana fira da dariya, tunawa da cewa a gidan su Sulaiman ɗin ta taso kuma tare suka taso yasa ta taɓe baki ta wuce. Nusram kuwa da yake ƙofar gidan da jama'a hakan yasa bata ma lura dasu Shureim ɗin ba, sun jima suna tsaye sannan motar Alhaji Baballe ta karyo kwanar layin. Duk ƴan wajen sai da suka bi motar da kallo don ta haɗu sosai daka gani ka san mamallakin ta ya ci ya sha ya tada kai. Shi kuwa Alhaji Baballe hasko Nusram da yayi tana kwasar dariya ba ƙaramin ɓata mishi rai hakan yayi ba, wato dalilin da ya saka tace mishi ta yafe zuwan da zai dinga yi wajen ta kenan. Cikin jin haushi ya fito daga motar, Nusram ta kalli Ya Sulaiman tace; "bari naje wajen Alhaji na dawo", yana tsokanar ta tana dariya haka ta bar wajen. "waye wancan ɗin", ya tambaya cikin fushi da kuma yatsinar fuska, Nusram ta kuma kai kallon ta kan Ya Sulaiman daya ke danna wayar ta da alama wani abu yake kallo ganin yadda ya ɓata fuska kuma ya natsu. Ta juyo ta kalli Alhaji Baballe rai ɓace bata taɓa jin haushin titsiya ba sai yau bata sani ba dan ko babu ɗigon son Alhajin a ranta bane oho, tace; "Yaya na ne". Alhaji Baballe yace; "shine kuma sai ku fito titi kuna fira kamar wasu saurayi da budurwa", tsabar haushi da takaici Nusram kasa cewa komai tayi. Sallamar Atika yasa ta ɗago tana kallon ta, taci kwalliya cikin atamfa doguwar riga da wani siririn mayafi saman kafaɗar ta, fuskar ta kuwa taci kwalliya sosai ga wani uban turare da ta saka wanda saura kaɗan kan Nusram ya juya. Cikin kissa ta tsugunna tace; "ina wuni Alhaji", ya amsa yana kallon fuskar ta, ta saki murmushi ta maida kallon ta zuwa Nusram tace; "Aunty Nusram waccen ne ya aiko ni". Nusram tabi inda Atikar ta nuna da kallo wani gajere ta hango sai dai bata gane ko waye ba kasancewar wajen babu haske dan haka bata ganin fuskar shi. Atikar tayi murmushin mugun ta tace; "gashi yace in baki", ta ƙarasa tana miƙo takardar hannun ta wacce take linke. Nusram ta saka hannu ta amsa ta dube ta tace; "Atika waye wancan ɗin", cikin salon munfinci tace; "Aunty wannan saurayin naki ne fa wanda kuke yawan fita tare dashi wanda kwanaki Baba ya mishi gargadi akan ya dena zuwa ƙofar gidan nan saboda ya kamaku tare a zaure kuna aikata abinda be kamata ba, bayan anyi haka kika gudu wajen shi har kika kwana biyu har Baba yasa aka je aka kama shi da ƴan sanda to ya ce mini ɗazu aka sako shi shine ya sami labarin za'ayi auren ki, shine yazo". Kan Nusram ta gama fahimtar me Atika take nufi Atikar tayi gaba da sauri, Alhaji Baballe kuwa jin abinda Atika ta faɗa yasa yayi saurin fizge takardar daga hannun Nusram ɗin. Cikin fushi ya ɗago bayan ya karanta wasiƙar yace; "lallai kin cika ƴar iska amma duk da haka bari kiji abinda zan faɗa miki auren ki dai ba zan fasa ba kuma ki kuka da kanki idan kika shigo hannu na, kada ma kiyi ƙoƙarin cewa kin fasa domin kuwa kuɗin da mahaifin ki ya ci mini ba zai taɓa iya biya ba har ƙashen rayuwar shi dan haka auren mu babu fashi". Yana faɗar haka ya ciro bandir ɗin ɗari biyar-biyar guda uku ya cilla mata yace; "gashi nan kuɗin da zaki yi amfani dashi ne gobe tunda kince bakya buƙatar komai na biki", yana gama faɗar haka ya wuce ya barta. Har ya shiga motar shi ya rufe ƙofa sai kuma ya buɗe ya cillo mata takardar sannan ya maida ƙofar ya rufe ya figi motar tashi ya bar wajen. Nusram ta saki kuka tana tsugunnawa a wajen, ga mutane duk a wajen har sun fara cece kuce, Ya Sulaiman yazo ya ɗagota sannan ya tsugunna ya kwaso mata kuɗin da takardar. "Nusram kiyi haƙuri, kada wa'innan abubuwan dake faruwa su dame ki, ki sani bayan wuya sai daɗi kuma a dukkan tsanani akwai sauƙi na faɗa miki wata rana sai komai ya wuce kamar ba'a yi ba", Nusram ta gyaɗa kai kawai. Kuɗin ya zuba a aljihu sannan yace; "zan je na ajiye wa'innan kuɗin ba zaki taɓa ko biyar ba, duk abinda kike buƙata kiyi mini magana zan kawo miki amma bana so kiyi amfani da komai na Alhaji Baballe". Takardar ya linke bayan ya gama karantawa sannan yace; "zan ajiye takardar itama kada kuma ki faɗawa su Ummi wannan abin kinji", ta ɗaga kai. Hannu ta kai tace; "dan Allah ka bani na karanta", ya miƙa mata takardar:- *Assalamu Alaykum, zuwa ga masoyiyata Nusram, ki sani na fito ɗazu daga cell kuma naji yadda tsohon ki yake son rabani dake, dan haka na yanke shawarar gobe zan zo mu gudu da daddare dan haka ki shirya komai naki zan zo sai mu gudu kawai.* *daga Bangis(ur love)* Nusram ta miƙawa Yaya Sulaiman takardar kawai domin kuwa ta san ba zata fahimci komai a ciki ba dan bata san inda maganar ta dosa ba. Shureim kuwa ganin abinda ya faru yasa suka sallami Nusreen da sauri ganin yadda hankalin ta ya koma kan ƴar uwarta. "Ram meya faru ne tsakanin ki da wancan ƙaton?", Nusreen ta tambaya bayan ta ƙaraso kusa dasu. Yaya Sulaiman ya galla mata harara sannan yace; "wuce ki bar nan wajen", ta wuce tana ƙunƙunai har ta shige gida. Yaya Sulaiman ganin ta tafi ya ƙara jawa Nusram kunne akan kada ta sake ta faɗaws ƴan gidan abinda ya faru sannan yace taje ta kwanta domin dare ya fara ja. Tana shiga zaure taji an fincikota, kanta ya bugu da jikin bango ta saki ihun wahala, sai dai be fita ba domin an toshe mata baki. Ɗakin Isa dake zaure nan aka hankaɗa ta, ta faɗi ƙasa cikin kiɗima ta juyo tana bin inuwar mutumin da kallo, ɗakin babu haske sosai dan haka bata ganin ko fuskar waye. Cike da tsoro tace; "waye dan Allah", ba'ayi magana ba sai dai janta da aka yi zuwa ciki kan katifar ɗakin aka cillata sannan mutumin yayo kanta yanzu kam ta gane meke shirin faruwa da ita dan haka suka shiga dambe. Sun jima a haka yana ƙoƙarin kaita ƙasa amma abu ya faskara, shi kanshi Isan yayi mamakin ƙarfin ta be taɓa tunanin haka take da ƙarfi ba, ƙara ƙaimi yayi inda Allah ya bashi sa'ar cire hijab ɗin dake jikin ta, ya kuma yaga rigar jikin ta. Ya ɗaga ta ya buga a katifar sannan ya saka ƙafa ya danne ta, haiƙam yake son rabata da kayan jikin ta, Nusram kuwa zuwa yanzu ƙarfin ta yayi ƙasa gashi dama ba wata lafiya ta cika ba wanda dole ta saduda. Shi kuwa ganin ya sami dama a kanta yasa ya saki jiki sosai yana ƙoƙarin aikata mata abinda zuciyar shi ke raya mishi. Hannu Nusram ta miƙa Allah ya taimake ta taji ta riƙo wani abu wanda ba zata bambamce kwalbace, ƙarfe ne ko kuma roba bace duk da haka tana fatan ya kasance abinda zai taimake ta ne. Ragowar ƙarfinta ta tattaro ta hankaɗe shi, ganin hakan ga ƙoshi ga kwanan yunwa ya ƙara harzuƙa Isa dan haka ya ɗauke ta da mari wanda sai da ta kifa, wannan abin ta ɗaga ta kwaɗa mishi a kai iya ƙarfin ta. Ya saki wata irin ƙara me ƙarfi wacce ta ratsa duka gidan, Nusram kuwa jin hakan yasa tayi saurin dirowa tayi hanyar waje. Sai dai kanta kai ga fita yasa ƙafa ya taɗiyo ta, ta faɗi a wajen hakan kuma yayi dai-dai da ƙarasowar mutane. Ɗaki ya gauraye da haske, nan fa Mama Jummai ta saki ihu tayi kan Isa tana riƙo shi tana tambayar shi abinda ya faru. Babu abinda yake faɗi sai " Nusram zata kashe ni", jin abinda ya faɗa yasa Mama Jummai saka salati. Tayi kukan kura ta faɗa kan Nusram wacce ke kwance tana sake ƙudundune jikin ta da hijab ɗin ta wanda ta ɗauka bata kai ga sakawa ba. Aunty taje ta bangaje Mama Jummai sannan ta ɗago Nusram tace; "haba Jummai a sai ki tsaya kiji meya faru". "wane kalar meya faru? Kina ganin Kaltume zata kashe mini ɗa", Aunty ta taɓe baki tace; "to sai ki bibiyi meya faru tukunna", Mama Jummai zata kuma magana Baba yace; "duka a tafi ɗakin Jummai domin ayi maganar". "dakata Jummai ba ita bace babba dan haka ɗakin Maimuna za'a je", cewar Baba Sailuba yar Malam Abdullahi. Haka aka ɗunguma zuwa ɗakin Ummi, aikuwa ɗaki ya cika maƙil dan harda ƴan Dabai wa'inda suka zo biki. "meya haɗa ka da ƴar uwar ka?", Baba ya tambaya, Baba Sailuba tayi saurin cewa; "a ina ta zama ƴar uwar tashi? Ban sani ba Abdullahi ko kai kayi mata cikin shi a waje?". Cikin sauri Baba yace; "a'a Yaya wallahi da ɗanta na ganta", Baba Sailuba tace; "yauwa yanzu naji batu ka tambaye shi meye haɗin shi da ƴar sunnah bayan shi shege ne bashi da uba", Mama Jummai ta wulla mata harara. Isa ya saukar da kai yace; "dama ina kwance ne kawai sai na ga mutum a tsaye a kaina kan nayi wani motsi ta faɗo jiki na tana faɗin wai sai na biya mata buƙata". Nusram ta girgiza kai hawaye yana zubo mata jin irin sharrin da Isa yake mata, Baba yace; "ni kam na shiga uku yanzu iskancin naki gida ya dawo kenan?, wallahi idan kika cigaba da ɗauko mini magana zan tsine miki kibi duniya". Nusram hankali tashe ta rarrafo zuwa gaban Mahaifin nata cikin kuka tace; "dan Allah Baba kayi haƙuri wallahi ba haka bane nazo shigowa gida ne shine ya jani ɗakin shi don yayi mini fyaɗe har ya yaga mini riga amma wallahi bani naje ɗakin ba". Mama Jummai tayi salati tana tafa hannu tace; "yanzu Nusram waye zai miki ƙarya Isa ko waye", Baba yace; "bar shegiya me baƙin hali". Baba Sailuba tace; "shegantata zaka yi Abdullahi yanzu ɗan shege yafi ɗan sunna a wajenka, lallai ba banza aka barka ba". Baba yace; "Yaya ki duba wannan lamarin fa", ta ɗaga mishi hannu tace; "ya isa haka Abdullahi maganar yarinyar nan abin dubawa ne be kamata ka goyi bayan ɗaya daga cikin su ba zaka yi dana sani fa". Nan dai Baba ya tafi yana bambamin shi, Baba Sailuba ta ɗago Nusram tace; "kinji kiyi ta addu'a Allah yana sane da ke", Nusreen ta amshi Nusram ɗin suka shige ɗaki suna kuka. Ummi kuwa banda hawaye babu abinda takw gogewa Aunty na ƙara kwantar mata da hankali, to dai magana ta shiga unguwa domin kuwa jama'a duka sun ji, wasu sun yarda da abinda Nusram ta faɗa wasu kuma sun ƙarya ta jin abinda ya faru tsakanin ta da Alhaji Baballe ɗazu. Ranar dai kam gidan ba kowa yayi barci ba wasu hidimar biki wasu kuma ɓacin rai ya hanasu barci ciki kuwa harda Nusram wacce tasha kuka ta godewa Allah. Washe gari da safe kuwa da ƙyar take buɗe idanun ta saboda kumbura da yayi, Nusreen ma dai idanun ta yayi ja sosai dan itama kwana tayi tana kuka don taya ƴar uwar ta jimami. Koda Aunty tazo ta same su a kwance nan ta rufe su da faɗa, haka dole Nusreen ta tashi tayi wanka ta shirya don an kusa ɗaurin aure. Nusram kuwa magani tasha sannan ta koma ta kwanta, ta ɗaga hannu ta kalli lallen dake zane a hannun ta wanda da ƙyar ta bari akayi mata shi sai da Ummi tayi mata kuka sannan ta bari aka yi shi. A yanzu kam babu abinda ta tsana kalar auren nan nata, ta ɗaga kai ta kalli yadda jama'a ke hada-hada. Nusreen ake sheƙawa kwalliya me kyau da kuma ɗaukar hankali, Aunty ta shigo ganin Nusram ɗin a kwance yasa tace; "au yanzu baki tashi ba kenan? haba Nusram tashi dan Allah mana", ta ƙarasa tana kamo Nusram ɗin don ta miƙe. A haka jikin ta babu wani ƙarfi ta miƙe ta ɗauke sosa da sabulu tayi bayi, ta tarar Aunty ta haɗa mata ruwa me kyau da ƙamshi nan tayi wankan sannan ta fito. A wajen famfo suka haɗu da Atika wani lace ne me tsada ta saka a jikin ta, sosai taci kwalliya zaka iya tunanin ma itace amaryar. Nusram ta kauda kai gefe batare da tace mata komai ba, Atika kuwa ta saki murmushi na izgilanci tana sakin shewa. Tana shiga Aunty ta jata zuwa uwar ɗaka nan suka tarar da Safeena tana zaman jiran su dan haka tana shigowa ta fara aikin ta wato kwalliya. Sadiya ta buɗe ledar kayan da Yaya Sulaiman ɗin ya bata jiya ta ɗauko mata shaddar, doguwar riga ce wacce taji stone work har zuwa ƙasa tayi kyau sosai. Babu yadda Safeena bata yi da ita akan ta tsaya ta ɗaura mata ɗan kwalin ba amma taƙi, dan haka gyale fari ta yane kanta dashi zuwa kafaɗar ta kawai. Tana zaune tana kallon Nusreen yadda take ta sakin murmushi cikin farin ciki da annashuwa. Nusram ta miƙe tsaye sannan ta ɗauki ɗan ƙaramin memo wanda ke ajiye saman cabinet ɗin su, ta zame ta fice. Jan gyalen tayi ta rufe rabin fuskar ta hakan yasa har ta gifta Ummi da Aunty wainda ke tsaye suma sanye da shaddar duka kala ɗaya da tasu basu lura da ita ba. Koda ta fito ƙofar gida babu kowa domin kuwa duk suna masallacin dake gaban gidan kaɗan inda anan ne za'a ɗaura auren. Haka kawai zuciyar ta ke zafi dan haka ta yanke shawarar fitowa ta dan miƙe ƙafa domin ta ɗan sha iska. A hankali take tafiya hawaye na zubowa daga idanun ta, yanzu shikenan ta san cewa ba zata taɓa farin ciki a rayuwar ta ba kamar mahaifiyar ta ƙila gwara Ummi ma domin ƙila tana amarya ta ɗan ji daɗi. Abdus-samad dake sanye da shadda kalar ruwan toka yayi kyau sosai duk da be cika wannan shigar ba, tare suka zo da Fadil domin halartar ɗaurin auren saboda Shureim. Jin hayaniya tayi yawa yasa ya fito daga masallacin domin ya sha iska, yana tsaye yana danna waya ta bullo hanyar. Jin ƙamshi me daɗi da sanyi yasa Abdus-samad ɗagowa ya kalle ta, ganin wannan yarinyar ce yasa gaban shi faduwa, ya tsura mata idanu. Tayi baƙi ta rame yabi ta da kallo tun daga sama har ƙasa tayi kyau sosai sai dai kuka take kuma hankalin ta baya kan inda take tafiya. Ba lallai ka lura da kukan da take yi ba idan ba ka lura sosai ba, tana zuwa daf dashi ta ɗan bigi hannun shi wayar ta faɗi. Sai lokacin hankalin ta ya dawo jikin ta, cikin sauri ta tsugunna domin ɗauƙo wayar, a tare suka miƙa hannu domin ɗauƙo wayar. Da sauri ya janye hannun shi ta ɗauka, tana ƙoƙarin miƙewa gyalen kanta ya zame gashin ta ya bayyana wanda yake dogo ga baƙi ga santsi wanda kuma ya sha gyara da mayuka me kyau da ƙamshi. Saura kaɗan Abdus-samad ya suma a wajen domin Allah yayi shi da son mace me gashi, baya manta lokacin yana yaro haka zai zaunar da First Love ɗin shi ya saka mata rigima akan zai mata tsifa yayi ta wasa da gashin. Kan ya ankara har Nusram ta miƙe tana ƙoƙarin gyara gashin nata, Abdus-samad ya kai hannu ya ɗauko ribbom ɗin ta ya miƙe domin miƙa mata wanda itama Nusram din sai lokacin ta lura da ko waye. Zaro idanu tayi jikin ta ya ɗauki rawa, da sauri ta fara ja da baya kafin ta juya da sauri, Abdus-samad yayi saurin binta domin amsar wayar shi ya kuma bata ribbom ɗin ta amma ina ko ƙeyar ta be gani ba. Cikin sauri yake bin lungunan domin neman ta sai can ƙarshen lungun ya hango ta, tana tafe tana waige-waige kan ya ƙaraso ta fice daga lungun. Tana isowa ƙofar gida ta samu jama'a cike alamu dai an gama daurin aure, Sahura ta tare ta tace; " Yaya Nusram ina kika shiga", da sauri Nusram ta juya ganin Abdus-samad ya kusa ƙarasowa inda take yasa taja hannun Sahurar suka shige cikin gidan. Abdus-samad ganin ta shige gidan yasa yayi murmushi yana faɗin; "Nusram! Nice name". Fadil ya ƙaraso wajen shi da sauri Abdus-samad ya saka ribbom ɗin cikin aljihun shi gudun kada Fadil ya gani. "ina ka shiga ne ga Shureim.can da abokanan shi suna neman ka", Fadil ya faɗa, Abdul yace; "muje wajen nasu yanzu me zasu yi?". "zasu shiga a gaisa da ƴan uwan amarya ne", Abdul yace; "ok to.muje wajen nasu", haka suka ɗunguma zuwa cikin gidan su Nusram ɗin. Sun gaisa da jama'a an kuma ɗauki hotuna inda suka yi al'adar kaduna wato kiɗan ƙwarya nan abokanan ango suka cashe da kakanin amarya akayi wasa da dariya kafin suka bawa kakar su Nusreen ɗin kuɗin cin goro sannan suka fito ana ta sam barka. Abdus-samad dai duk yadda ya baza idanu Allah be bashi sa'ar hango Nusram ɗin ba haka ya haƙura suka tafi. Nusram kuwa suna shiga gidan ta saki hannun Sahurar sannan tayi nasu ɗakin, anan ta tarar dasu Ummi ana ta guɗa ana faɗin; "an ɗaura". Zuciyar Nusram kamar ta faɗo ƙasa tsabar takaici, tana shiga wata cikin abokan wasan su tazo ta turare ta hau fesa mata, Nusram ɗin ta saki kuka sannan tayi cikin ɗaki. Tana shiga taji ana sanar da shigowar su Shureim ɗin dan haka ta koma gefen katifa ta zauna tana me sauke ajiyar zuciya tana kallon su Nusreen suna leƙe ta window amma ta ita ta kasa leƙawa har suka fita. Babu jimawa aka sanar da shigowar Alhaji Baballen tare da nashi tawagar, nan suma aka yi wasa da dariya inda ya bawa kakannin Nusram ɗin maƙudan kuɗi na cin goro nan fa waje ya ɗauki shewa da guɗa. Anan wasu suka ƙara jinjina kuɗin na Alhaji Baballe inda Baba keta washe baki shi a dole ga sirikin me kuɗi. Abdul dake ƙoƙarin shiga mota yaji an riƙo mishi hannu, da sauri ya kalli wanda ya riƙo shin. Cikin tsananin mamaki yake kallon shi ya kalli inda Fadil yake yaga hankalin shi yana kan abokan ango. Cikin mamaki ya nuna shi, da sauri yaja hannun shi ya bar wajen dashi, sai da suka isa inda babu mutane sannan ya sake shi, Abdus-samad yace; "waye kai". Alhaji Mustapha yayi murmushi yace; "Ka tambayi Brr Farida kace waye Mustapha Tuge a wajen ka?, ka sani koda baka tare dani ni ina tare da kai idan kaje ka tambaye ta", daga haka ya bar wajen. Abdus-samad ya daɗe be motsa daga wajen ba, ya ja ajiyar zuciya sannan ya koma inda motar shi take har lokacin Fadil yana tare da Angon dan haka ya danna mishi horn cikin sauri ya taho dan ya san kaɗan ga aikin shi ya tafi ya barshi. Koda yazo sai da yaja tsaki sannan yaja motar suka tafi. Bayan sallar isha'i aka fara cewa amare su fito nan fa idanun amaren ya fara raina fata, Nusram da Nusreen suka rungume juna suna kuka me tsanani. Sai da suka saka mutane da yawa a wajen kuka, kafin a samu a raba su, an kaisu wajen Ummi inda suka yi musu nasiha sosai da sosai suna zubar da hawaye suka rabu Ummi tana saka musu albarka da yi musu addu'ar tafiya a sa'a. An kaisu wajen Mama Jummai wanda babu abinda ta dinga faɗa banda habaici, Baba ma dai cewa yayi idan sun zauna kansu idan basu zauna ba to sai dai su nemi wani uban ba dai shi ba. Nan aka saka kowacce a mota domin tafiya dasu zuwa gidajen su, nan fa mutane suka rabu gida biyu wasu suka tafi raka Nusreen wasu kuma Nusram. Aunty tace; "Nusram ki shiga da ƙafar dama", haka ta shiga da kafar dama tana me addu'a, duk da gabanta dake faɗuwa. Gida fa ya haɗu sosai da sosai dan faɗan kyawun shi ɓata lokaci ne, kowa sai yaba kyawun gidan yake yi. Amma Nusram ita kyawun gida bashi ya dame ta ba, sai ma zazzaɓi daya rufe ta, babu jimawa ƴan kawo amarya suka gama abinda zasu yi sannan suka tafi, suka bar amarya daga ita sai halin ta. #LIKE #SHARE #COMMENTS *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *yau kam kamar na zubar da hawaye saboda comments ɗin ku naji daɗi sosai Allah ya bar ƙauna. *godiya gare ku ABDUS-SAMAD FANS CLUB, naji dadin comments ɗin ku, ku sani ina son ku sosai akan san ku zan iya shanye maltina gwangwani biyu😁*. *Innalillahi wa'inna ilaihirraji'uun, haƙiƙa wannan jarabta ce da Allah ya saukar miki Zulaihat Ubangiji Allah yasa ayi aikin cikin nasara ya bata lafiya yasa ya zama kaffara, ya kuma ƙara muku juriya ya bata lada domin lallai cuta bata da daɗi*. *ƴan uwa muna barar addu'ar ku za'a yiwa yarinyar ƴar uwarku a musulunci Zulaihat Isma'il aiki yanzu haka suna Asibiti a India dan tana fama da heart attack, dan haka muke roƙon ku taya mu da addu'a Allah yasa ayi a sa'a ameen*. 📖📖35-36📖📖 *HAYIN RIGASA, KADUNA*. Abdul ya shiga get ɗin Estate ɗin sannan ya sami waje yayi parking motar, cikin sauri Fadil ya kalle shi yace; "me hakan ke nufi?" bece komai ba sai ma kifa kanshi da yayi akan steering motar. Sanin cewa ba zai tanka mishi bane yasa Fadil buɗe motar ya fice, be jima sosai da fita ba Saleema ta ƙaraso wajen motar ta buɗe ta shiga. A hankali ta dafa shi sannan tace; "kayi haƙuri, komai yayi zafi maganin shi Allah ka kaiwa Allah kukan ka shi zai share maka hawaye". Ya ɗago yana kallon ta, tayi murmushi sannan tace; "damuwa da tashin hankali bata yiwa wannan kyakkyawar fuskar kyau, a koda yaushe murmushi da dariya sune suke ƙara ƙawata wannan fuskar me girma da kwarjini, shin ko kasan murmushin ka yana sanyaya zuciya nawa ne a gidan nan?, suna da yawa ciki kuwa harda tawa fatan za'a duba tamu zuciyar a dena shiga damuwa". Wani sanyi yaji yana ratsa zuciyar tashi, haƙiƙa iya magana ma wani abu ne lallai kam a cikin mata Saleema ta ciri tuta. Ya saki murmushi sannan yace; "kai Aunty na ke ɗin ta dabance", itama tayi murmushi kan ta riƙo hannun shi tace; "kai ɗin wani ɓangare ne na rayuwata na sani cewa zuciya ta tana girmama abinda duk ya shafe ka". Kan wani lokaci me tsayi sai ga Abdus-samad harda dariya, sai da Saleema ta tabbatar da bata bar Abdul cikin damuwa ko kaɗan ba sannan ta buɗe motar ta fice. A hankali ya ja motar ya fice daga gidan, Husna taja tsaki tace; "katuwar banza ta ɓige a wajen ɗan cikin ta", sannan ta juya cikin gida cike da kishi. Dr Saleema kuwa da batama san Husna nayi ba ganin ya bar gidan yasa ta koma cikin gidan su tana me jin daɗin yadda ta sami nasarar kawar wa da masoyin nata damuwar da yake ciki. Koda ya isa gida duka ƴan uwan nashi suna falo, Fadila da Sumayya suka hau rige-rigen yi mishi sannu da zuwa, ya amsa musu duka yana ɗaga Adnan sama yana cillashi yayin da shi kuma Adnan ɗin ke yin dariya. Dr Abubakar da Brr Farida da suke saukowa daga sama suna fira da dariya, Dr Abubakar yace; "kai lallai ma maza sauke mini autana kada ka faɗar dashi". Brr Farida tayi dariya tace; "aikuwa dai Baby ba zai taɓa faɗar da Autan ka ba, sai dai ya ƙara kula dashi", Abdul yayi dariya har gefen kumatun shi ya lotsa yace; "dat's mah first love". Dr Abubakar yace; "lallai ma wato shigar mishi kika yi kenan?", tace; "a'a fa ni ban shigar mishi ba", nan suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa. A hankali Abdul ya zame ya shige nashi ɗakin, wayar Sumayya ya kira akan yana neman ta, babu jimawa ta ƙaraso hannun ta ɗauke da ƙaramin bowl me ɗauke da Fruit salad. "Ya Abdus-samad gani", ta faɗa tana gyara tsayuwar ta dan ta fara gajiya, ya ƙara gyara ƙafar shi dake saman ƙaramin table din dake tsakiyar ɗakin. Yana cigaba da danna laptop ɗin dake saman cinyar shi yana yi yana cin fruit salad ɗin, kamar ba zai amsa ba dan har ta cire rai da amsawar tashi sai kuma taji yace; "ranar nan firar me kuke yi ke da Yaya Tameer?". Sumayya ta zaro idanu tace; "wallahi Yaya yace.....yac......yace kada na faɗ........kada na faɗ", kallon da yayi mata yasa tayi saurin haɗiye wani yawu. "ki bani amsata kawai", ya faɗa yana cigaba da abinda yake yi, tace; "dama cewa yayi na shawo kan Mummy akan......akan.....aka......akan yarinyar da yake so ya au.....aura", ta ƙarasa tana jan numfashi. Abdus-samad ya ɗago ya mata wani kallo sannan yace; "ke zaki mata maganar aure ko wato kin girma ko? Kema auren kike so kenan?", da sauri ta girgiza kai, cikin daka tsawa yace; "fita ki bani waje shashasha", har tana harɗewa wajen fita. Sai da ta ganta a waje sannan tayi ajiyar zuciya kafin ta bawa bujen ta iska, Fadila dake kallo a falo ganin yadda Sumayyar ta shigo yasa itama ta ruɗe. Nan ta hau tambayar ta abinda ya faru ba tare da ta bata amsa ba ta wuce ɗakin su, Surayya tayi murmushi tana girgiza kai. "kada ki damu da wannan mashirmanciyar wata ƙila laifi ta yiwa Ya Abdul shi yasa ya tsoratata haka", Fadila banda ɗaga kai babu abinda take yi. Koda aka yi kiran sallar la'asar ta ƙofar baya ya fice inda yaje yayi sallar shi sannan ya shigo ta ƙofar gaba. Tun daga nesa ya hango su a tsaye da alama akwai abinda suke tattaunawa, ya ƙaraso wajen su da sallama, ya miƙawa Sameer hannu suka yi musabaha sannan ya kalli Fadila yace; "kinyi sallah ne?". Ta girgiza kai da sauri, ya mata wani kallo babu shiri har tana harɗewa wajen barin wajen, Sameer na ƙwala mata kira amma ko juyowa bata yi ba, dan bata manta yadda Sumayya ta shigo ba ɗazu. Sameer ya ɓalla mishi harara yace; "ka kore ta ko?", Abdul ya shafa gashin kanshi kan ya kalli Sameer ya taɓe fuska yace; "dan Allah yanzu me kuma nace ni", Sameer yayi dariya yana dukan kafaɗar Abdul ɗin. Tameer daya shigo ya kalle su yace; "me kuke yi kuma anan?", Abdul yace; "firar auren ka muke yi Yaya", Tameer ya harare shi yace; "ina wasa da kai kenan?", Abdul ya shagwaɓe fuska. Tameer yace; "maganar gaskiya na kasa tarar Mumny da maganar, wallahi", Abdul yace; "shikenan sai ka zauna a matsayin gauron ka", Tameer ya riƙo shi yace; "dan Allah mana, ka faɗa mata", yace; "me zance". Tameer ya sosa kai yace; "ka gane yarinyar da nake so ne na tabbatar Mummy ba zata amince ba, ƴar wani ma'aikaci ne a company ɗin mu, kuma kasan halin Mummy tafi son ƴar me kuɗi". Abdul ya ɗaga kafaɗa yace; "taɓ ai ra'ayi ne me sunan shi da sunan ta?", Tameer ya kuma washe baki yace; "Sunan ta Bilkisu ƴar Malam Sunusi Ladan", Abdul yace; "shikenan zan gwada sa'a ta". Tameer yace; "nama san zata amince dan inda kaine magana ta ƙare", Abdul yace; "to idan ta amince meye tukuici na?", Tameer yace; "baƙar motar ka", Abdul ya shafa kai yana murmushi. Sameer kuwa dariya yayi ganin yadda ɗan uwan nashi ya sallama haka da wuri, Abdul na barin wajen Sameer ya janyo Tameer yace; "anya kuwa soyayyar da kake nunawa Abdus-samad yanzu ta gaske ce?". Tameer yace; "har cikin raina da gaske nake a da ɗin ma ina tunanin shine matsalar rayuwata ne sai da naga na kusa rasa shi sannan na tabbatar da ina son shi sai dai maganar gaskiya har yanzu ina kishin shi", Sameer yayi murmushi. "bari naje nayi sallah", daga nan Sameer ɗin ya fice shi kuma Tameer ɗin ya shige cikin gida domin kuwa shi yayi sallar shi dama. Fadila tana zuwa ta tarar da Sumayya ta idar da sallah, cikin sauri ta shige bayi ta hau alwala, Sumayya ta kwashe da dariya domin ta san kome ya faru. Ta san cewa Abdus-samad babu abinda ya tsana irin mutum me wasa da Sallah duk shirin da kuke yi idan har kana wasa da Sallah to lallai zai ci ƙaniyar ka ne. Fadila ta fito daga bayi, ganin Sumayya na dariya yasa ta kwaɗa mata harara sannan ta tada kabbarar sallah sai da ta idar sannan ta bata labarin abinda ya faru. Nan itama Sumayya ta bata nata labarin, lokacin Surayya ta shigo haka suka haɗu suka dinga yiwa juna dariya. Surayya tace; "haba Aunty Fadila ina shekarun ku kusan ɗaya me yasa kike tsoron shi", Fadila ta galla mata harara sannan tace; "ke baki san wannan bane wani lokacin fuskar yara gare shi wani lokacin kuma babu wasa wallahi ban san lokacin dana bar wajen ba", suka kuma kwashewa da dariya. A falo ya same su zaune Bayan Sallar isha'i, ya kalle su yace; "kun yi sallah ko?", duka suka amsa da eh, yace; "First love fa?", Surayya tace; "tana sama", be kuma magana ba ya nufi saman. Da sallama ya shiga ɗakin, Dr Abubakar na zaune saman carpet inda Brr Farida ke gefen shi tana mishi fira, Abdus-samad yayi murmushi soyayyar dake tsakanin iyayen shi abin yana bashi mamaki kuma yana birge shi. Brr Farida ta tashi ta riƙo hannun shi har suka zo suka zauna, Dr Abubakar cikin zolaya yace; "gaskiya na kusa fara kishi da kai, waye ma ya kawo ka a wannan lokacin da nake buƙatar kulawar mata ta". Abdus-samad yasa hannu biyu ya rufe fuskar shi, a dole nan yaji kunya, Brr Farida ta kwantar da Abdus-samad saman ƙafar ta sannan ta harari Dr Abubakar ɗin cikin wasa tace; "ai shi koda yaushe nake kulawa dashi kaine ma kake da ƙaiyadajjen lokaci". Dr Abubakar ya ciza yatsa yace; "wayyo Allah na zasu haɗe mini kai", su kam banda dariya babu abinda suke yi. Abdus-samad ya gyara zaman shi sannan yace; "Daddy dama magana nazo muyi", Dr Abubakar yace; "akan me fa?". "dama magana ce akan Yaya Sameer da Yaya Tameer sune suka samu wa'inda zasu aura shine suka ce a sanar maka". Ya ɗan saci kallon Brr Farida idanu kawai ta zuba mishi ya kauda kai ya maida kan Dr Abubakar sannan yace; "To shine nace bari a sanar da kai", Dr Abubakar yayi murmushi sannan yace; "ka kira mini su yanzu", Abdus-samad ya ɗauki wayar shi ya kira su duka wanda babu ɓata lokaci suka zo. Dr Abubakar ya kalle su yace; "naji saƙon ku a wajen Abdus-samad kuma insha Allahu zan bibiya na kuma yi bincike akan gidajen nasu yanzu sai ku mini bayanin su waye?". Sameer ya shafa kai sannan yace; "ni dai yarinyar da nake so ita ce Fadila", Dr Abubakar yace; "wace Fadilar?", Sameer yace; "Fadilar nan gidan". Brr Farida ta zaro idanu cikin sauri tace; "ba zai taɓa yiwuwa ba da raina ba zaka janyo mini abin ɓacin rai ba wallahi tun wuri ka canza ba zan taɓa amincewa ba". "me yasa kike hakane Farida?", da sauri Brr Farida ta miƙe tace; "dangin ka Dr dangin ka fa ba zai taɓa yiwuwa ba kaima ka sani ba zan taɓa amimcewa ba". Dr Abubakar yace; "Farida ki tsaya ki duba wannan lamarin mana", ba dan ranta yaso ba ta koma ta zauna ta wurgawa Sameer harara. Dr Abubakar yace; "naji naka saura kai kuma", Tameer yace; "Bilkisu ce ƴar gidan Sunusi Ladan". Brr Farida ta miƙe cikin sauri tace; "wane Sunusin ba dai wannan talakan ba?", Tameer ya ɗaga kai cike da tsoron kada taƙi amincewa. Ta girgiza kai sannan tace; "ni Farida Alƙali zaka ɗaukowa ƴar talaka wanda beda cin yau balle na gobe, ni talaka wallahi ba zai yiwu ba". Duka suka bita da kallo cike da mamakin abinda take faɗa, duk tabi ta birkice lokaci kaɗan. Dr Abubakar yace; "ku tashi ku tafi Allah yayi muku albarka", suka amsa da ameen jikin su duk a sanyaye. Dr Abubakar ya kalli Abdus-samad yace; "kaima jeka mana", Abdus-samad cike da damuwa ya fice daga ɗakin. Bayan fitar shi sannan Dr Abubakar ya miƙe ya riƙo hannun ta, kusa dashi ya zaunar da ita sannan ya cika kofi da ruwa ya miƙo mata, ta amsa ta shaye tass. Ya matse hannun ta sannan yace; " haba My Brr ki dena irin wannan shifa komai a rayuwa yana zuwa ne dai-dai yadda ka ɗauka, ki daure ki rage ƙiyayyar da kike yiwa ƴan uwa na da kuma talaka". Brr Farida ta zame hannun ta sannan tace; "Dr har kana tunanin zan manta ƙiyayyar da ƴan uwan ka suka nuna mini?, ko kuwa na manta abinda talaka yayi mini ya rabani da abar ƙauna ta ƙawata aminiya ta wacce nake matuƙar ƙaunar ta". Dr Abubakar yace; "Assha! Be kamata ace kin riƙe abinda ya faru a baya ba a cikin ranki, ki sani su ɗin yan uwa na ne kuma ba zan taɓa canza su ba shin ke ba zaki ɗauke su a matsayin ƴan uwa ba, haba Farida ki dinga haƙuri mana babu fa abinda yake tabbata a rayuwa komai da kika gani wucewa yake yi kada ki riƙe abinda ya faru cikin ranki, sannan maganar talaka ina so ki fahimci wani abu a ciki talaka akwai mutumin kirki akwai wanda yake akasin haka, haka acikin masu kuɗi akwai mutumin kirki akwai akasin haka, sannan baki san me Allah ya shirya musu ba a rayuwa, ki saka musu Albarka a matsayin ki na mahaifiyar su sai suga haske a rayuwar auren nasu amma fushin da zaki yi dasu shine zai bawa maƙiyin su da kuma wanda yake ƙoƙaerin cutar dasu dama wajen aiwatar da nufin su". Lallai magan-ganun na Dr Abubakar ya shige ta, cikin sanyin jiki tace; "shikenan Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi", Dr Abubakar yayi murmushi yace" yauwa ko ke fa". Zata yi magana ya dakatar da ita yayinda yace; "tashi muje muci abinci", Brr Farida ta miƙe haka suka jero cikin farin ciki. Akan dinning suka same su, duka uku babu wanda ya iya cin abinci, fatan Sameer da Tameer shine Mummyn tasu ta amince da zaɓin nasu yayin da Abdus-samad kuma tunanin halin da ya baro Mahaifiyar tashi shine yasa. Yana ganin su yayi saurin miƙewa ya ƙara inda take ya rungume ta, Brr Farida tayi dariya tace; "My Baby kenan?", shi ya ja mata kujera ta zauna. Ganin yadda yaran nata suke cikin damuwa yasa ta fara jan su da fira har suka sake da ita, nan suka ci abincin su cikin annashuwa. Bayan sun gama suka koma saman kujeru suka zauna, Abdul ya ɗora kanshi saman ƙafar ta yace; "First love na tambaye ki?". Tace; "eh Baby na", ya yi murmushi sannan yace; "Waye Mustapha Abubakar Tuge", Brr Farida taji saukar sunan kamar saukar aradu. Cikin sauri ta ture kan nashi daga jikin ta sannan tace; "a ina kaji wannan sunan kuma waye yace ka tambaye ni?". "shi da kanshi ne ya faɗa mini, kuma muna kama sosai dashi, kin san na sanshi tun a london domin kuwa yana yawan zuwa ɗaya daga cikin attajiran dake Africa". Brr Farida tace; "to wannan shine amsar tambayar ka, shi ɗin me kuɗi ne wanda ake ji dashi a Africa, sai kuma me kake son sani?". Abdus-samad ya girgiza kai domin yadda Brr Faridar tayi magana ya nuna a hasale take. "yauwa First love ya kira ni da Murad", ya faɗa yana me kallon mahaifiyar tashi, Brr Farida ta miƙe tsaye cikin hasala tace; "na faɗa maka Murad baya nufin komai a wajen ka, kada kuma ka sake tara ta da wannan maganar idan ba haka ba ranka zai ɓace", tana gama faɗar haka ta bar falon. Abdus-samad ya kalli Dr Abubakar, cikin sauri kafin Abdus-samad ɗin yace wani abu, ya kalli Sameer yace; "ka shirya gobe zamu je Hayin rigasa daga nan zamu wuce Abuja", yana gama faɗar haka ya wuce ya bar falon. Abdus-samad ya kalli Sameer, Sameer ya ɗaga mishi kafaɗa alamun i don't care, shima Abdul ɗin ya taɓe baki kafin ya miƙe ya fice. Kida ya shiga part ɗin shi bayi kawai ya wuce yayi wanka, a gaban mirror ya tsaya yana ƙara kallon kanshi, so yake ya gano meye suke da bambamci da wannan mutumin na ɗazu wato Alhaji Mustapha. Komai nasu kala ɗaya ne gaba ɗaya kamar tasu har ta ɓace, bambamcin su kaɗan ne wato bakin shi ƙarami ne ba kamar na wancan ba, banda wannan kuwa babu abinda suke da bambamci da juna sai tsufa kawai. Ya lumshe idanu, ganin fuskar ta yasa yayi saurin buɗe idanu, babu abinda yake tunawa sai lokacin da gashin ta ya bayyana. Cikin sauri ya ɗauko kayan daya cire ɗazu ya hau binciken ribbom ɗin nata, babu jimawa ya ganshi a aljihun shi, ya riƙe a hannun shi yana kallo. Tuno yadda fuskar ta ke nuna tsantsar tsoro a duk lokacin da suka haɗu yasa yayi murmushi a hankali ya furta; "Nusraaaaaam!". Yasin yana Abdul yana ruwa 🙄🙄🙄. ******** *********** *MAƘARFI ROAD, KADUNA (GIDAN AMARYA)*. Nusram ta miƙe cikin yanayi na rashin lafiya ta nufi bakin ƙofa ta fice daga ɗakin, bata taɓa tunanin Alhajin zai kai zuwa yanzu be shigo ba. Ta tsaya tana kallon falon nata, bata san lokacin data ja tsaki ba inama ace wannan kuɗin da maman nata da Auntyn ta suka kashe gidan wanda take so ne. Kanta da yake sara mata ta dafe sannan ta nufi wata ƙofa data gani, ganin ta a inda take zato wato Kitchen yasa taji daɗi sosai. Buɗe-buɗe ta fara tana neman abinda zata ci, babu komai wanda zata iya ci dan haka dole ta fito, hango fridge yasa ta nufi can. Allah ya bata sa'a domin ta sami ruwa pure water a ciki me sanyi dan haka ta ɗauko ɗaya daga ciki ta wuce ɗakin nata. Bincike ta fara yi har Allah yasa taga kayan dubulan ɗin ta nan kuwa ta ɗiba ta hau ci hannu baka hannu ƙwarya, sai da ta ƙoshi sannan ta kora da ruwa. Ta kai kallon ta kan agogon ɗakin ƙarfe sha biyu da rabi duk inda ango yake ya kamata ace zuwa yanzu yana cikin gidan shi. Mema zai saka ta damu bayan ba wani son shi take yi ba, ita kanta tayi mamakin rashin tsoron data nuna, Allah sarki Nusreen ko yaya take yanzu oho, ko ta dena kuka zuwa yanzu bata sani ba. Nan taji hawaye yana zubo mata, Allah yasa ma Shureim yana tare da ita ta san cewa yanzu zai rarrashe ta, ita fa bata da kowa, ta share hawayen daya zubo mata sannan ta nufi bayi. Alwala ta ɗoro domin tazo tayi nafila, ta ɗauki hijab ta saka, Sallama taji a falo kafin tayi wani yunƙuri taji an nufo ɗakin ta wanda yayi dai-dai da fitowar mutum daga cikin wardrobe ɗin ta. Kallon shi take bakin ta ɗauke da addu'a don a tunanin ta Aljani ne, ya matso kusa da ita yace; "yauwa masoyiyata kiyi sauri mu tafi kafin wancan ƙaton ragon ya shigo". Alhaji Baballe da yayi niyar shigowa jin abinda ke gudana a cikin ɗakin yasa ya turo ƙofar cikin fushi, ya bisu da kallo yadda fuskar Nusram ya nuna tsoro da kuma hijab ɗin dake sanye a jikin ta ya gasgata abinda yaji. Ya nuna ta da hannu "wato sai da kike nuna ban isa ba haka Uban daya haife ki ma be isa ba wallahi, dan haka sai na sauya miki kamanni ta yadda gobe wani namiji ba zai ga wannan kyawun naki ba har ya janyo hankalin shi gare ki", yana gama faɗar haka ya kulle ƙofar inda ya tafi neman abin duka. Ganin haka yasa Bangis ɗaga window ya dira yayinda ya bar Nusram kamar statue, bata dawo hayyacin ta ba sai da taji ana buɗe ƙofar. Alhaji Baballe ta gani hannun shi riƙe da zabgegiyar bulala irin ta wayar wuta, nan jikin Nusram ya fara rawa; "ka dakata kaji wallahi ba abinda kake tunani ban.......", bata samu damar ƙarasawa ba sabida saukar bulalar da taji. Sosai ta daku a hannun Alhaji Baballe wanda dama kamar ƴa take a wajen shi, dan dai kawai aure ya ratsa tsakanin su ne, dama fatar Nusram fashewa take idan taji duka dan haka dan danan ya fasa mata jiki. Tana bashi haƙuri tana zagaye ɗakin haka yake binta yana duka, har ta faɗi a ƙasa amma haka yasa ƙafa ya dinga takata yana huci. Sai da ya gaji dan kanshi ya ƙyale ta, a lokacin gaba ɗaya kukan ma ya dena fita sai dai hawaye kawai da take yi na tsabar azabar da ta sha. Ta dafe cikin ta wanda ke mata wani irin tsananin ciwo, tana ji tana kallo ya kira police akan suzo gidan shi, amma bata da damar yin magana. Ya tashi ya shiga bayi ya taro ruwa ya fita be jima ba ya dawo hannun shi riƙe da bokitin ya nufi inda take ya shara mata ruwan. Nusram ta runtse idanu tana jujjuya kai cikin wahala da tsananin raɗaɗin da take ji a inda ya zuba mata ruwan. Ya kamo wuyan ta ya shaƙe yana faɗin; "ina ɗan iskan saurayin naki yake?", Nusram babu baki wuya kam ta sha ta, idanun ta yayi ja babu abinda take jira banda mutuwa tazo ta tafi da ita. Ƙarar isowar motar ƴan sandan ya ƙwace ta daga hannun Alhaji Baballe, hijab ɗin ta ya kama ya jata har zuwa waje inda ƴan sandan suke tsaye sannan ya cilla musu ita yace; "ku tafi da ita ku rufe mini ƴar iska kada ku sake ku bada belin ɗinta". Ya juya cikin gida yana huci, Nusram ta daɗe kwance a wajen kafin ta iya miƙewa tsaye jiri na iyabar ta, ta kalli ƴan sandan dake tsaye a wajen su kansu sun tausaya mata duk da basu san laifin da tayi mishi ba. Ɗaya daga ciki ya ɗago ankwa din hannun shi, Nusram cikin baƙin ciki ta miƙa hannun ta kamar wata ɓarauniya ko wacce tayi wani babban laifi. Haka suka tasa ƙeyar ta cikin motar, Nusram ta ɗaga hannu ta kalli ankwar hannunta ta fashe da kuka tana me tausayin rayuwar ta. Ta saka hannu ta janyo hijab ɗin ya rufe gefen fuskar ta a haka har suka isa ofishin ƴan sandan, haka suka shiga ciki, sai sa suka tambayi sunan ta ta faɗa musu suka ɗan yi rubuce-rubuce sannan suka ce ta cire ƴan kunnayen ta da zobunan ta haka ta cire duka dama babu komai a hannun ta dan haka suka iza ƙeyar ta zuwa cikin cell bayan sun saka ta cire hijab ɗin ta. Koda suka maida suka rufe a wajen Nusram ta durkushe tana kuka me cin rai, wai yau itace a rufe a cell abinda bata taɓa tunani ba kenan, Aunty tace wata rana zata yi farik ciki ko sai yaushe wannan ranar zata zo??. #LIKE #SHARE #COMMENT *babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖37-38📖📖 Ranar duk iya satar barci sai da ya ƙyale Nusram, ga sauro ya sanyi ga raɗaɗin ciwon ta ga kuma zazzaɓin dake jikin ta ga damuwa da fargaba. Kuka kam ta sha shi har ta bawa uku lada, tana yi tana istighfari; "Astaghfullah Allah idan laifi nayi maka kake jarabtata da wannan masifun domin na tuba ya Ubangiji ina me ƙanƙan da kai zuwa gare ka Allah ka amshi tuba na", abinda ta kwana ambata kenan. Koda safiya tayi haka ta tasa fararau-fararau ɗin koko da ƙosai ƙwara uku a gaba tana kallo tana hawaye, duk yadda suke a gidan su basu taɓa irin wannan karin ba abinda ke ƙara bata mamaki shine yadda yau aka kawo ta Cell gashi ma har ta kwana. Da safen ragowar wa'inda suka kwana a gidan biki ƴan Dabai ne kawai dan jiya tunda aka kai amare kowa ya wuce gidan shi. Su ke ƙoƙarin haɗa abin kari babu wanda ya kula Mama Jummai wacce ke faman shewa da murna to babu wanda ya san ma me take yiwa murnar. Tun da asuba Bangis ya kira Habiba ya shaida mata aiki yayi kyau, wannan shine silar murnar tata sai dai ba'a sami dama kan gidan Nusreen ba saboda lokaci ya ƙure. Mama Jummai tace; "babu komai ai tunda ka ƙwato mana me maiƙon waccen zan ji da ita daga baya kada hakan ya ɗaga maka hankali". To wannan shine ya saka su a cikin murna kuma suna jiran sakamako me kyau. Wajen goma suna zaune sai ga Baba ya fita da sauri, Mama Jummai ta kuma aashe baki tana murna tana fatan ace aikin su ne yaci. Baba kuwa ganin Alhaji Baballe harda ɗan duƙawa wajen gaishe dashi, Alhaji Baballe ya amsa a fuzge sannan ya miƙowa Baba takarda yace; "ka takardar matsiyacoyar ƴar ka nan na sake ta saki uku, sannan na baka nan da kwana uku ka dawo mini da duk wani kuɗi daka san na baka shi". Baba ya ƙwalalo idanu waje, cikin rawar murya yace; "haba Alhaji me yayi zafi haka, meta aikata maka wanda ta cancanci wannan sakamakon?". Alhaji Baballe yace; "oho sai kaje ka tambaye ta ni dai na gama magana ka dawo mini da kuɗi na kawai", Baba yace; "dan Allah Alhaji kayi haƙuri, kada muyi haka da kai na san cewa Nusram yarinya ce me biyayya ga haƙuri kuma". Alhaji Baballe yace; "ne haƙuri fa kace, yarinyar dana kama da saurayin ta zasu gudu ranar da aka kawo ta gida na, har cikin gida na ƙato ya shigo zai tafi da ita". Baba ya hau salati yana tafa hannu, cikin jimami yace; "Alhaji ka dai sake bincikawa amma ba halin ta bane, na san Nusram ciki da bai". "oho wannan kuma kai ta shafa bani ba kaji na faɗa maka ka dawo mini da kuɗaɗe na kawai ni ba zan iya zama da ƴar iska ba". Baba yace; "bafa za'a yi haka ba akwai ƙanwarta idan kana so yanzu ma sai a ɗaura muku aure", Alhaji Baballe ya girgiza kai. Baba ya hau roƙon shi da Allah dan ya amince, sun jima a haka sannan Alhaji Baballe yace; "na yarda shikenan zanje na dawo zuwa ɗaya sai a ɗaura, kaima ka shiga ka faɗawa naka ƴan uwan", Baba yayi ajiyar zuciya ganin Alhaji Baballe ya amince yace; "insha Allahu yadda kake so haka za'a yi, yanzu ina ita Nusram ɗin take?". Ba tare da damuwa ba yace; "tana ofishin ƴan sanda", yana faɗar haka ya shige motar shi ya tafi, Baba kuma ya shiga gida. Ɗakin Mama Jummai ya shiga ya zuba tagumi, cikin Kissa tazo tace; "meya faru ne Baban Atika". Ya ɗago ya kalle ta sannan ya bata labarin komai da yadda suka yi da Alhaji, cikin damuwa yace; "ni yanzu ban san ko zasu amince ba gashi nayi mishi alƙawarin wata". Mama Jummai cikin ranta kamar tayi me dan murna amma a fili sai tace; "Ashsha gaskiya Nusram bata kyauta ba sai dai dama shekaranjiya Atika tace mini wani ɗan iska ya aike ta wajen Nusram ɗin amma na kwaɓe ta dan kasan surutun yara". Baba yace; "kira mini Atikar", Mama Jummai kuwa rai fes ta ƙwalawa Atika kiea, dama tana laɓe tana ji dan haka babu ɓata lokaci ta amsa tana shigowa ciki. "Atika ki taimaka ki rufawa Mahaifinki asiri ki yarda ki auri Alhaji Baballe dan Allah ki mini wannan alfarmar". Atika ta ɗago tace; "Baba magana kake fa akan mijin ƴar uwata Nusram ai hakan ba zai yiwu ba na aureshi bayan yana matsayin mijiɓ ƴar uwata kuma suna tare". Baba ya ƙara saukar da kai ƙasa yace; "Atika ki tsaya ki saurare ni, yanzu haka takardar Nusram tana hannu na ya sake ta saki uku, kuma yace sai na dawo masa da kuɗin shi, Atika kema kin san hakan bame yiwuwa bane dan ko gidan nan na ɗaga na siyar ba zai kai kuɗin daya bani ba Dan Allah ki rufa mini asiri kinji". Atika ta ɗan yi shiru sannan tace; "shikenan Baba insha Allahu zan share maka hawayenka, zan kuma yi maka biyayya Allah yasa hakan shiya fi". Baba har ƴar ƙwalla sai da yayi jin abinda ƴar tashi ta faɗa, faɗi yake; "Atika Allah yayi miki albarka", sannan ya miƙe ya fice. Yana fita Atika tayi tsalle ta faɗa kan mahaifiyar ta, suka hau murna suna jin daɗi, Sahura ma na zuwa suka bata labarin abinda ya faru nan itama ta hau taya su murna sannan fa suka fara shirye-shiryen yadda bikin zai kasance. Baba dake tsaye ƙofar ɗakin Ummi yace; "Maimuna! Maimuna!! Fito yau da ƴa ɗaya na haifa da sai dai na haɗiyi zuciya na mutu to Allah yasa ina da wata". Ummi ta ɗan yi jimm sannan tace; "Baban Nusreen meya faru ne?", cikin ɗaga murya yace; "meye ma be faru ba Maimuna", ya zaro takardar ya miƙa mata. Ummi ta juya takardar sannan tace; "ai baka ce komai ba ka san ba iya karantawa zan yi ba". Mama Jummai dake bakin ƙofa ta tuntsire da dariya tace; "matsalar ka kasance jahili kenan", babu wanda yace mata komai. "ƴar ki na Police Station mijin ta ya kamata *A DAREN FARKO* zata bi saurayi su gudu shine ya kai ta caji ofis yanzu haka acan ta kwana, wannan kuma takardar sakinta ne ya sake ta saki uku, na nemi alfarmar ɗaura mishi aure da ƴar uwar ta kuma ya amince dan haka yau ƙarfe ɗaya za'a ɗaura auren, yanzu zan je kasuwa na ƙara siyo abubuwan da babu sai a cigaba da biki kawai kayan ɗaki da komai da komai kuma za'a barwa ƴar uwar ta ne". Yana gama faɗin haka ya juya yana faɗin; "bari Hansai( ƴar uwar shi daga Dabai) tazo muke kasuwa tare sai ta taho da abubuwan da babu", Ummi kuwa tana tsaye ne kawai ta rasa meke mata daɗi. Baba Sailuba ta fashe da kuka aka shiga bata haƙuri tace; "ku dena bani haƙuri yau naga meke faruwa gidan Abdullahi, lallai ba hakanan ba Maimuna ki tattara kayanki kawai mu tafi gida, dan ni yanzu zan bar garin nan". Ummi ta girgiza kai sannan tace; " Baba meye amfanin tafiyata a yanzu bayan nasan cewa babu me amso mini ƴata wajen hukuma idan har na tafi to haƙuri na na shekaru ashirin da ɗoriya ya tashi a banza kenan dan haka Baaba kiyi haƙuri zan zauna kawai a nan". Baaba Sailuba tace; "shikenan na fahimci wane irin zama ake a gidan Abdullahi, dan haka ku haɗo kayanmu, mu tafi gida kawai", ta ƙarasa tana goge hawayen daya zubo mata. Haka yawancin ƴan Dabai suka tafi sai ɗai-ɗai ku wa'inda ke goyon bayan Abdullahin, Ummi kam banda zubar da hawaye babu abinda take yi. tun daga waje suka fara jiyo faɗan Aunty, tana shigowa taja wata doguwar ajiyar zuciya sannan ta kalli Ummi ta balla mata harara tace; "Wallahi idan kika zauna sai baƙin cikin ɗa namiji ya kashe ki", muryarta na rawa tace; "yau wai Nusram ce tayi kwanan Cell!?", ta fashe da kuka. Ummi ta taso zata riƙe ta, Aunty ta dakatar da ita ta ɗora da faɗin; "kada ki taɓa ni Maimuna, haƙurin ki a da ke yake cutarwa amma yanzu ya fara taɓa ƴaƴan ki, abin ban haushi kamar mara gata mace da kwanan Cell, dan yana da kuɗi shikenan sai kuma ya dinga taka duk wanda yaso haka ake rayuwa wannan ba adalci bane, wallahi ko ki tashi ki ƙwatarwa kanki da ƴaƴan ki ƴanci ko kuma daga yau kada ki kuma nema na". Ummi ta koma baya ta zauna sannan tace; "shikenan Kaltume kije kawai inaji gawata kuke so a ɗauka a gidan nan, na ɗauka ke kin fahimce ni ashe ba haka bane, Kaltume banda yanda zanyi". Aunty tace; "ke kuwa kike da yadda zaki yi amma idan har kika zauna kika zuba idanu to wallahi zaki kamu da ciwon zuciya kuma ba matsalar su bane". Tana gama faɗar haka tayi waje a zuciye, sauran ƴan ɗakin suka riƙo ta, ta kalli ɗaya daga ciki tace; "sakeni Hadiza dole ne mu kwaso kayan mu domin kuwa babu ƙwandalar ubanta a ciki". Ummi tayi saurin miƙewa tace; "kiyi haƙuri Kaltume ki bar wannan maganar", ta juyo cikin fushi tace; "ba zan bari ba", ganin abin kamar zai zama faɗa yasa Hadiza da Karima suka riƙe Aunty suka yi waje da ita, tana kuka Ummi na kuka haka suka rabu kowa rai babu daɗi. Ummi ta share hawayen fuskarta tace; "Allah kana ji kuma kana gani idan har dan inyi biyyaya ga umarnin daka bayar na cewa mata ta yiwa miji biyyaya, Allah ka duba halin da nake ciki ka ceto mini yarinyata sannan ka shirya wa'inda suka mata wannan sharrin Allah ka bani ikon ganin ƙarshen su", Hadiza dake tsaye tace; "ameen dai". Aunty kuwa sai da ta tsaya a zaure ta goge hawayenta sannan ta ɗauko waya ta kira Sulaiman ta faɗa mishi halin da ake ciki. Cikin tashin hankali yace; "yanzu Mama zan je duk wani police station na nan kusa domin sanin wanne aka kaita", Aunty tace; "yauwa maza kaje dan Allah yanzu zan kira Baban ku shima domin ganin ta yadda zai taimaka mana". Yaya Sulaiman na ajiye wayar yayi saurin fita daga shagon cikin sauri, mota ya shiga hankali tashe yana kuma mamakin irin wannan abu dake faruwa ga wannan baiwar Allah". Babu inda be zaga ba amma abin haushi duk inda yaje cewa ake yi ba'a kawota nan ba abinda be sani ba shine Alhaji Baballe ya bada umarni akan kada su sake su nuna an kawo ta nan. Har zuwa yamma Yaya Sulaiman be sami inda aka kai Nusram ba, duk wani Police Station da ya sani na kusa dana nesa yaje amma be samu ba, har ya fara fita yankin nasu wato Kaduna North, har zuwa dare babu labari. Aunty kuwa sai yamma ta koma gidan, hankalin ta ba wani a kwance yake ba, koda ta isa magana ta yiwa su Hansai akan su fito a tafi buɗar kai amma abin mamaki suna fitowa Baba ya maida su. "waye zai kai Atika ɗakin mijin ta idan har kuka kwashi jiki kuka tafi kuma", Hadiza tace; "Haba Yaya amma a al'ada yau ake buɗar kai", Baba ya karkata kai yace; "to ni nace a fasa ba shikenan ba, Atika ta fito ku wuce kawai". Aunty cikin zafin zuciya ganin duk sun tsaya tayi hanyar waje, wayar Halima ta kira da ta Safeena sai Sa'adatu da bata yi aure ba, babu jimawa suka iso nan tace; "su shiga gidan su kwaso mata kaya zasu wuce buɗar kai". Sun so tambayar ta abinda ya faru amma ganin yadda take ranta a ɓace yasa suka ja bakin su, suka yi shiru koda suka fito da kayan nan suka haɗu da maƙwabta guda biyu da kuma Hadiza wacce ta kasance ƙanwar Ummi da kuma Karima suka wuce buɗar kan Nusreen. Sun shiga mota sannan Sulaiman ya kira Aunty, "Mama babu inda banje ba amma wallahi ban sami inda suka kaita ba", Aunty ta ɗanyi jim sannan tace; "na kira baban ku yace zai kira dpon yankin amma shiru har yanzu ka kira shi kaji ya suka yi", Sulaiman yace; "to". Koda suka isa Unguwar Rimi gidan Amarya Nusreen, dole Aunty ta saki fuskarta gudun zargi, sun tarar da gidan akwai sauran baƙi, nan suka yi duk abinda ya kamata. Sun zo tafiya Nusreen ta riƙo Aunty hakan yasa su Halima suka fice, Aunty ta dubi Nusreen tace; "ya akayi ne Amarya", Nusreen ta saukae da kai ƙasa tana wasa da yatsunta. Aunty tace; "akwai abinda kike buƙata ne", Nusreen tace; "dama ɗazu ne naje gaishe da Mamanshi, shine wasu a wajen suke ta mini habaici naga ba zan jure ba na rama shine fa Maman shi ta kira shi ta dinga mishi faɗa wai ita bani take so ba Nusram take so", ta ƙarasa kamar zata zubar da hawaye. Aunty taja hannun Nusreen suka zauna bakin gado sannan tace; "Nusreen haƙuri akeyi a komai yanzu sannan kada ki sake ki kuma faɗawa kowa abinda ke tsakanin ki da dangin mijinki, domin idan kika faɗa mana zamu riƙe su a ranmu ki koyi riƙe sirrinki sannan ki sani nan da gidanku da bamabanci dole ki koyi haƙuri kinji", Nusreen ta ɗaga kai, Aunty tace; "yauwa Allah ya miki albarka", Nusreen tace; "ameen, kunje gidan Nusram ne Aunty". "eh ya akayi?, daga can muke muka yo nan", Nusreen ta kuma cewa; "na kira wayar ta ba'a ɗaga ba", Aunty ta miƙe sannan tace; "idan kika cigaba da gwadawa zata shiga ne, sai anjima", ta fice kafin Nusreen ta kuma cewa komai. Ba tare da Aunty ta koma gidan ba, haka suma yaranta kowa gidanshi ya wuce, Yaya Sulaiman ya dawo wajen goma amma babu sa'a domin dai kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba. Nusram na can a kulle a cell banda kuka babu abinda take yi, ga tunanin halin da ƴan uwan ta suke ciki. Amarya kuwa bayan tafiyar su Aunty Baba yasa su Hansai suka ɗauke ta sai gidan Alhaji Baballe, buri ya cika domin dai babu abinda aka taɓa na Nusram sai washe baki take yi don ta san ta mori gida sama dana duk ƴan uwanta. ********* *********** *UNGUWAR SARKI, KADUNA*. Koda ya shigo gidan washe gari a falo ya sami Sumayya da Fadila suna fira, ganin shi yasa suka yi shiru, yace; "ina First Love?". Sumayya tace; "tana sama bata sauko ba", ba tare da ya kuma cewa komai ba ya nufi saman, Fadila ta bishi da kallo. Shigar ƙananan kaya ce kamar koda yaushe a jikin shi, blue ɗin riga anyi rubutu da farin kala a gaba sai wando jeans fari hasken fatar shi ya fito sosai. Da sallama ya shiga ɗakin, Brr Farida dake duba takardu wanda alamu ke nuna na aikinta ne, ta ɗago ta kalle shi sau ɗaya ta komar da kanta ta cigaba da aikin da take yi. Ya ƙaraso kusa da ita, kan carpet ɗin yaja filo ya kwanta a gabanta, bata ce komai ba har lokacin, hannu yasa ya ɗauki takarda guda ɗaya amma be gane komai a ciki ba. Ya taɓe baki sannan ya ajiye, yana kallonta tana aikinta shi kuma ya maida kai kawai ya lumshe idanu. Har lokaci me tsayi sannan ta gama ta hau tattara takardun nata, ya buɗe idanu yana kallon ta, cikin sauri ya riƙo hannun ta sannan yace; "am sorry", ta balla mishi harara. Ya cuno baki cikin shagwaɓa yace; "ai na baki haƙuri", Brr Farida tace; "kai baka ji ko? Waye yace kaje kayi magana akan wannan matsalar? Ni bance kada suyi aure ba amma su nemo ƴar babban gida". "inda First love kike da naƙasu kenan", ya faɗa a cikin zuciyar shi, amma a fili yace; "nima First love ai na kusa auren nan na huta", Brr Farida tayi mishi wani kallo ba tace komai ba ta miƙe. " matar ka Baby har yanzu ma ba'a ƙerata ba tukunna, ni zan nemo maka matar da zaka aura ƴar babban gida me asali da ji da kuɗi ba wai ƴar talaka ba matsiyaci", jan bakin shi yayi shiru dan ya san idan maganar ta cigaba da tsayi to abin ba zai yi kyau ba. Be san dalilin da ya saka Mahaifiyar tashi ke tsananta ƙiyayya ga talaka ba, ita dai me kuɗi in dai aka zo batun aure amma kuma sauran mu'amala zata yi da talaka. wai matar shi ko ƙerata ba'a yi ba?, me hakan ke nufi zai sami jinkiri kenan kamar sauran ƴan gidan kenan?, ya saki murmushi yana shafa sumar kanshi. Tsakanin kwana biyu da maganarsu Tameer Dr Abubakar ya gama komai daya dace sai dai kuma matsalar shine ta ɓangaren Sameer dake son Fadila. Dr Abubakar yace a bari sai sun je Family meeting wanda zasu yi ƙarshen wata me zuwa sai a daddale duk da yana cike da tsoron mahaifiyar tashi wato Hajja be san yadda zata dauki maganar ba. Brr Farida kuwa bata cewa komai game da auren nasu da anyi magana sai dai tace Allah ya kaimu kawai kowa ya fahimci bikin be wani ɗaɗata da ƙasa ba. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖39-40📖📖 "ina ganin Mijin Nusreen zai iya taimakawa tunda Mahaifin shi kan ya rasu babban mutum ne shima ta yiwu ya san wasu manya", cewar Aunty. Yaya Sulaiman ya ɗan yi shiru kafin yace; "shikenan zan mishi magana sai muji yadda za'a yi", yana faɗan haka ya fice daga gidan. Aunty da Ummi suka bishi da kallo kawai, a ƙa'ida bayan bikin su Nusram da sati biyu za'a yi nashi amma har yanzu basu sami kwanciyar hankali ba, Aunty ma tana maganar a ɗaga ne amma Ummi tace a'a. Malam Isma'il Mahaifin Sulaiman shima dai duk iya ƙoƙarin shi a yanzu shine Nusram ɗin ta baro hannun Police. Da ƙyar ya samu yaga Dpo sai da ya bayar da cin hanci ma tukunna sannan ya sami ganin shi, Nan ya bashi bayanin abinda ya kawo shi. Sosai ran Dpo ya ɓaci, yayi faɗa sosai taya za'a bar mace a cell tsayin wannan lokacin?, nan ya kira wani Sergent akan ya binciko mishi inda aka kai Nusram ɗin. Ya amsa da to ya fita, Dpo yace; "kuyi haƙuri manyan ƙasan nan ke amfani da wawayen cikin mu ana ɓatawa Police suna, yanzu zanje a fitar da ita insha Allah, kuma duk lokacin da abu makamancin haka ya faru ga number na ka kira ni kawai". Abba ya amsa yayi godiya sosai, babu jimawa ɗan sandan ya dawo nan ya shaida mishi tana headquarter dake Barnawa. Dpo ya kalli Abba yace; "tashi muje Alhaji da kaina ma zani domin a fitar da ita", Alhaji Isma'il yace; "to". Motar Abban suka shiga, nan Abba ya fara neman wayar Sulaiman ɗin domin ya faɗa mishi yadda akayi. Sulaiman kuwa sai da ya kira wayar Shureim yaji cewa yana gida sannan ya ƙarasa, a harabar gidan ya tsaya nan Shureim ɗin yazo ya same shi, bayan sun gaisa yace; "ba zaka shiga ba, na faɗawa ƙanwar ka cewa kana hanya". Sulaiman yayi murmushi yace; "sai dai nace ka gaishe ta amma ni ba zan shiga ba don akwai abinda ya kawo ni", Shureim yace; "meya faru?", Yaya Sulaiman ya bashi labarin komai. Hankalin Shureim ya tashi sosai, ya fara salati yana jimamin abinda ya faru, yace; "bari na shirya sai muje gidan Kwamishinan ƴan sandan kawai". Yaya Sulaiman yace to, Shureim ɗin ya tafi kenan wayar Sulaiman tayi ƙara, ganin kiran mahaifinshi yasa ya ɗaga da sauri nan ya faɗa mishi yadda suka yi da Dpo ya kuma ce mishi ya biyo su Barnawa, Sulaiman cikin farin ciki yace; "to Abba gani nan". Nusreen dake zaune tana jiran shigowar tasu jin an buɗe ƙofa yasa ta miƙe da sauri sai dai ganin mijin nata shi kaɗai yasa tace; "ina Yaya Sulaiman ɗin fa". Ya dafe goshi yace; "Sorry Nurulƙalbiy, ashe bashi bane ya iso wani abokina ne Yaya Sulaiman ɗin ya kirani akan wai ba zai samu zuwa ba", ya ƙarasa yana wucewa bedroom. Babu jimawa ya fito da shirin fita, cikin sauri tace; "Hayateey ina kuma zaka je, kayi mini alƙawarin yau babu inda zaka je fa". Ya riƙo hannunta cikin sigar lallashi yace; "Nurulƙalbeey kiyi haƙuri ki bari na fita wani abokina ne Custom suka riƙe mishi kaya shine yazo akan yana so na raka shi kinji ba daɗewa zan yi ba", tace; "shikenan amma idan ka dawo zaka kaini gidan Ramluv ko?", ya ɗan yi jimm sannan yace; "to shikenan sai na dawo ko", ta ɗaga kai, har bakin ƙofa ta rako shi sannan ya tafi. Ita kuma ta juya ta koma wajen Mama kawai ta wuce don bata son zama ita kaɗai, da sallama ta shiga Mama dake yanke farce ta amsa sallamar da murmushi a fuskarta, tun tana adawa da auren har ta haƙura yanzu. Nusreen ta ƙarasa ta amshi Nail Cutter ɗin tana cigaba da yanke mata, suna fira jefi-jefi har ta gama. Yaya Sulaiman yace; "munyi waya da Abba yanzu yace mu wuce Badarawa", Shureim yace; "to muje can ɗin", suka shiga motar Yaya Sulaiman ɗin suka tafi. Suna zuwa ana fito da Nusram, Yaya Sulaiman sai da hawaye ya zubo mishi ganin yadda ta koma, fuskarta tayi baƙi sosai kamar almajirar data shekara bata ga ruwa ba, tana tafiya tana ɗingishi ga rama da tayi sai idanu Zuru-Zuru kamar ba Nusram ɗin daya sani ba tsayin lokaci, ya tabbatar da ace a hanya suka haɗu tabbas ba zai ganeta ba. Shureim da Abba suma duka jikin su yayi sanyi sosai, Dpo kuwa ranshi ya ɓace sosai ya rufe su da faɗa suna ta bashi haƙuri sai da yayi warning ɗin su sosai sannan aka cike takardu na beli kan a basu Nusram ɗin. Nusram da duk jikinta take ji kamar an ɗaure shi tamau ga wani irin ciwon kai dake damunta, ƙafar ta kuwa tsabar zama waje ɗaya ne gashi dandamaryar siminti take wuni ta kwana har kwana uku wannan shine dalilin riƙewar ƙafar. Sulaiman ya buɗe mata ƙofa ta shiga da ƙyar sannan shida Shureim suka shiga gaba, Nusram ta jingina kanta da kujera tana cigaba da share hawayen fuskarta. Ita yanzu rayuwar gaba ɗaya ta sire mata, ji take dama ta mutu ta huta kawai, wannan wane irin tozarci ne. Tana jin lokacin da Yaya Sulaiman ya kira Aunty yake faɗa nata gasu nan sun taho amma sun bar Abba a can. Suna isa gida Nusram ta yunƙura ta fito, bata tsaya ba dan bata so mutane su ganta sai dai ina ta makaro domin kuwa mutane sun riga sun san meya faru dan haka wa'inda ke waje nan suka tsaya kallon ta. Tana ɗingisa ƙafa ta shiga gidan, Shureim ya kira likitan su akan yazo ya duba ta koda wata matsala, babu jimawa ya iso. Nusram kuwa tana shiga gidan Mama Jummai ta rangaɗa guɗa, Amira kuwa ta hau dariya, Aunty ta fito da sauri ta taho wajen ta suka rungume juna suna kuka. Ummi tace; "ai da sai ku ƙaraso ba wai ku tsaya a nan ba", Aunty ta taimakawa Nusram ɗin ta ƙarasa ɗaki. Ummi da kanta ta juyewa Nusram ruwa me zafi ta kai mata bayi, Aunty ta taimakawa Nusram ɗin ta shiga wanka tayi saɓi sama da sau biyar sannan taji iska me daɗi ta shigar ta wannan ya tabbatar mata da ta fita kenan. Ta ɗan ji ƙarfi a jikin ta domin kuwa da kanta ta fito har zuwa ɗaki, cikin kayan ta wanda Ummi bata riga ta kyautar ba Aunty ta ɗauko mata doguwar riga Buba ta saka. Tana zama likitan da Yaya Sulaiman da kuma Shureim suka shigo, bayan sun jajanta abinda ya faru sannan likitan ya shiga aikin shi. Ya duba ta sosai sannan yace; "akwai allura yanzu zanyi mata guda biyu sai kuma magunguna wanda zan rubuta muku suma guda biyu sai a siyo ta shanye insha Allahu zata sami sauƙi stress ne kawai sai rashin barci da kuma sanyi daya shige ta. Aunty tace; "to Allah ya kyauta gaba", duka suka amsa da ameen, Shureim da Yaya Sulaiman suka fice daga ɗakin sannan likitan yayi mata allura daga nan ya fice shima. Ummi ta miƙowa Nusram ɗin liptin me zafi wanda aka sawa citta da kanunfari tace; "ki shanye yanzu", ta amsa ta shanye tas. Aunty ta ciko cokali da man tafarnuwa ta miƙo mata tace; "ki dinga sha kullum cokali ɗaya da safe ɗaya da yamma", Nusram ta ɗaga kai kawai. Ruwan zafi da ƙyalle me kyau Ummi ta miƙowa Aunty inda ita kuma ta amsa, ƙafafun Nusram ɗin ta saka a ciki ɗaya bayan ɗaya tana gasawa har zuwa cinya. Har lokacin Nusram ɗin bata ce komai ba, sai dai kallon su kawai da take yi, tun tana ɗan janye ƙafar har ruwan ya fara yi mata daɗi hakan yasa ta lumshe idanu kawai. Aunty bayan ta gama ta kuma shafe mata ƙafafun da man tafarnuwar sannan tace; "to kwanta", Nusram ta kwanta yayin da Aunty ta ɗauki ruwan ta fita dashi. Aunty na bakin famfo wata mata ta shigo ɗaya daga cikin maƙwabta, suka gaisa da Aunty sannan ta wuce, da sallama ta shigo, Nusram na jinta amma ta ƙara lumshe idanu. "oh ashe haka kuma abu ya faru Allah ya kyauta gaba", sai da Ummi tayi jimm sannan tace; "ameen", hakan be ishe ta ba sai da ta kuma cewa; "ina zaune sai ga Hassan da gudu yana faɗin Mama fito kiga Nusram ko Nusreen ɗin gidan Jummai me abinci an dawo da ita, yana faɗin hakan nace Nusram ce domin kuwa itace take folistashon saboda mijinta ya kamata da ƙato cikin daren da aka kai.........". Bata ƙarasa ba Aunty dake tsaye a bakin ƙofa ta shigo tana huci a katse ta; "ya isa haka munafikai masu zuwa lahira da ƙoƙon masaki, masu barci da ido ɗaya, wato abinda kuke so kenan kuji inda wani abun ashsha ya faru ku yaɗa to ki sani wannan ƙaddarace ta hau kanta kuma bata wuce kan kowa ba". Matar ta riƙe haɓa tace; "ke baiwar Allah kada ki ɗorawa ƙaddara yaran da suke sakaka babu mafaɗi waye be san yadda motoci ke ɗaukar su yana ajiyewa ba, ai itama waccen aiki ne yaci mijin wannan kam daga gani ya riƙe Allah da ƙarfi ne", Aunty ta ɗaga hannu domin kwashe ta da mari Ummi tayi saurin riƙewa tace; "a'a Maman Adam kada ki aikata wannan kuskuren", Aunty ta fuzge hannun ta. Matar taja tsaki ta miƙe tana faɗin; "dama ai tabarmar kunya da bori ake naɗeta yara sun zama annoba a gari mu dai idan abin ya fara ƙarfi zamu kai ƙara ne kawai wajen me unguwa", tana faɗin hakan ta fice. Aunty tace cikin ɗaga murya; "ki tafi Zaria ne wajen Sarki, kada ki tsaya wajen me Anguwa, banzaye shashashu", Mama Jummai dake zaune a waje tana ji ta tuntsire da dariya tayi shewa tace; "sai ni Jummai ƴa ga Habu da Lantana ai duk wanda yaja dani sai ya faɗi". Aunty ta balla mata harara kanta ja tsaki, Mama Jummai tayi shewa tace; "wai ɗan karo ma ya samu sake", cikin jin haushi Aunty tace; "ɗan karo ya wuce agola ya kaiwa ƴar masu gida hari", Mama Jummai bata kuma jan maganar ba sai tayi gum. Har yamma Nusram na kwance bata tashi ba, Sai wajen biyar sannan ta tashi ta rama sallolin da ake bin ta, zuwa lokacin ta ɗan sami sauƙi. Yaya Sulaiman da yazo ɗaukar Aunty ya ƙara mata sannu da jiki, murya a dashe tace; "na gode sosai da ɗawainiya", ya ɗan ranƙwashe ta na wasa yace; "ina wasa dake ne". Su Ummi suka yi dariya, sunyi sallama inda Ummi ke ƙara godiya a gare su, Aunty tace; "kada ki damu ai ɗa na kowa ne kuma Nusram idan kin tuna dama tawa ce". Haka suka tafi suka bar su, abin mamaki har dare ƴan shigowa ganin ƙwaƙwaf basu dena shigowa ba, Mama Jummai kuwa tafiyar Aunty sai ta bude shafin habaici, babu wanda yace ci kanki. Koda Isa ya dawo Nusram na jin lokacin da take faɗa mishi, yayi shiru kafin yace; "Allah ya kyauta gaba", Mama Jummai ta balla mishi harara. Bayan sallar isha'i Nusram na zaune saman abin sallah tana lazimi, Isa yayi sallama ya shigo, a sanyaye ta amsa. Kusa da ita ya tsuguna sannan yace; " ya jikin?, ta amsa da; "lafiya lau", Allah ya kyauta gaba", tace; "ameen", ya jima tsugunne a wajen Nusram tayi banza dashi. Da kanshi kuma ya miƙe ya fice daga ɗakin, Nusram ta sauke ajiyar zuciya hawayen baƙin ciki yana zubo mata. Ta koma ta kwanta tana jiyo muryar mahaifin nata a tsakar gida amma ko leƙowa beyi ba, hasalima sai lissafe-lissafe suke yi shida Mama Jummai da alamu dai bashinta yaci. Cikin dare Ummi taji saukar numfashi da kuma kakari, da sauri ta miƙe ta ƙarasa wajen Nusram ɗin, tana kwance tana murƙususu gefen ta kuwa Kubra ce ke barcinta. Ta juyo da ita hankali tashe tace; "Nusram meke damun ki", Nusram ta nuna cikin ta hawaye na zubo mata. Ummi ta buga uban tagumi, yanzu me take dashi wanda zata nemawa yarinyar ta magani duk wani kuɗi da tayi tanajin sa ta kashe shi wajen bikin nan, ta sauke ajiyar zuciya tace; "Allah ka dube ni". Hijab ta ɗauko ta saka sannan tazo ta kama Nusram ɗin ta miƙe, sai da ta taimaka mata wajen saka hijab ɗin sannan ta riƙe mata hannu a ɗurkushe Nusram take tafiya har suka fito daga ɗakin. Ummi ta duba agogon wayar ta Sha biyu harda rabi, ta kalli Nusram tace; "Nusram bari na faɗawa Baban ku, ko zai taimaka mana", Nusram ta ɗaga kai tana durƙusawa a wajen dan wani irin murɗawa da cikin yayi. Ummi kuwa ƙofar ɗakin Mama Jummai taje tana bubbugawa, sun jima sosai kafin azo a buɗe, Mama Jummai ke baya sai Baba a gaba. "meye kuma yanzu kika zo zaki dame ni?", Ummi ta haɗiye wani abu me ɗaci tace; "Nusram ce bata da lafiya shine nace ko zaka taimaka a kaita asibiti", Baba yaja tsaki zai koma ciki Ummi tayi saurin ɗurkusawa tace; "dan Allah Baban Nusreen ka duba girman Allah ka zo mu kai yarinyar nan asibiti kada ta mutu". Cikin fushi Baba yace; "ta mutu mana waye ya damu yarinya taje ta gama iskancin ta, ta nuna mini ban isa ba ta kwaso abin kunyar ta shine zaki zo ki tasa ni a gaba wai sai na kaita asibiti, to wallahi babu inda zanje, ai inda Allah ya taimake ni ba ita kaɗai na haifa ba da sai dai a ɗauki gawata a gidan baƙin cikin ta ya kashe ni". Ummi cikin kuka tace; "dan Allah ka taimaka kazo a kaita asibiti duk wannan idan ta sami lafiya ayi maganar", Baba yace; "wallahi Maimuna babu inda zanje ina saurayin da yayi cikin yazo ya kaita mana", be bari ta kuma cewa komai ba ya maida ƙofar ya rufe. Nusram zuwa yanzu jikin ta har rawa yake yi, ga zafin ciwo ga kuma baƙin ciki na magan-ganun da Mahaifinta yake faɗa akanta. Ummi ta jima a tsaye a wajen tana share hawaye kafin ta koma wajen Nusram ɗin ta taimaka ta ɗago ta suka fara tafiya a hankali har suka fice daga gidan. Garin yayi tsit ga duhu, haka dai suke tafiya a hankali idan cikin ya murɗa sai dai ta tsugunna a wajen idan yayi sauƙi sai su cigaba da tafiya. A haka har suka ƙaraso bakin titi, babu mutane sosai sai jefi-jefi kuma yawanci sai dai su kallesu kawai su wuce wasu ma basa ko kallon inda suke. Duk motar da Ummi tayi ƙoƙarin tarewa bata tsayawa, ita dai Nusram na tsugunne tana riƙe da cikinta duk addu'ar da tazo bakin ta ita take yi. Zasu kusa rabin awa a wajen sannan wata mota da har ta wuce ta kuma dawo da baya ta tsaya, mutumin ya leƙo da fuskar shi yace; "ina zuwa Hajiya da daddare haka". Ummi tace; "kaga yarinya tace bata da lafiya shine nace ko zaka taimaka mana ka kaimu asibiti, wand ake kusa duk idan dare yayi rufewa suke yi". Ba tare da ɓata lokaci ba ya buɗe musu ƙofa suka shiga, sannan yaja suka tafi, sun yi tafiya me ɗan nisa sannan suka iso asibitin. Sai da ya taimaka ma Ummi suka shiga har cikin asibitin, aka bata gado har aka shiga duba ta domin babban mutum ne, ya duba agogon hannun shi ya kalli Ummi kafin ya ciro kuɗi a aljihun shi ya miƙo mata yace; "gashi ko zaku buƙaci wani abin, yanzu idan zan fita zan muku clearing bill ɗin ku", Ummi tsabar murna kamar ta tsuguna a ƙasa ta mishi godiya. Yace; "kada ki damu ɗa na kowa ne Allah ya bata lafiya", Ummi ta amsa da ameen, haka ta bishi da kallo har ya fice daga asibitin, ga dai shi babban mutum amma kuma yana da sauƙin kai sosai. Ta jima zaune a wajen kafin likitan ya fito sannan Nurses suka fito janye da gadon da Nusram ɗin ke kai a kwance, likitan yace; "ki bisu zasu kaita ɗakin da zata huta Alhaji Mustapha ya riga ya biya duk wani kuɗi da za'a yi muku aiki a nan, dan haka zuwa safe zaki je Pharmacy ki amso mata magun-gunan ta, inda ta buge ne ko kuma takata akayi dai ban sani ba to wajen ne ke mata zafi yaso ma ya taɓa mahaifarta amma Allah ya kiyaye be taɓa ba ɗin yanzu munyi mata allura insha Allahu nan da safiya zata sami sauƙi", Ummi tace; "to an gode sosai", tabi Nurses ɗin don kai Nusram ɗin ɗakin hutu. Ɗaki na musamman aka kai su, su kaɗai ne a ciki ga couch nan sai gado har da tv wato plasma ga sanyi babu wani hayaniya, sai da suka jona mata drip sannan suka fice daga ɗakin. Ummi ta shiga bayi ta ɗauro alwala sannan tazo ta shinfiɗa ɗan kwalin ta, dan bata ɗauko komai ba ta hau kai ta tada sallah. Ta jima tana sallah kafin barci kuma ya kwashe ta wanda bata farka ba sai asuba, tana idar da sallah Nusram itama ta farka, zuwa lokacin ruwan ya kusa ƙarewa Ummi ta ɗauko mata roba me faɗi ta taimaka mata tayi alwala sannan tayi sallar a saman gadon. ***********⬇️⬇️⬇️****** *MAƘARFI ROAD, KADUNA*. Hajiya Salma ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da kofi, ya juyo ya kalle ta, da sauri ta ja ɗan ƙaramin table ta ajiye a kai sannan ta nufi inda yake. Ta taimaka mishi ya ƙarasa shirin shi, sannan ta riƙo hannun shi ta zaunar dashi, ta ɗauki cup ɗin data ajiye ta fara bashi a baki da kanta. Tana gama bashi ya miƙe ta bishi da kallo yace; "meya faru ne Hajiyata?", tayi fari da idanu sannan tace; "account ɗina yayi low", yace; "zan miki transfer yanzu, baki da matsala sai ta kuɗi", ta ɗaga kai tana murmushi. Ya matso kusa da ita yace; "har ni ba zaki yi kewa ba?", ta riƙo hannun shi cikin kissa tace; "shine ma kan gaba da zanyi, muje na raka ka, kada kayi missing flight", yana gaba tana bayan shi hannun ta riƙe da jakar shi don tafiya. Suna saukowa akan steps yace; "ki kula da Khausar kin san yanayin rawar kanta and dan Allah ga amanar gidana nan da kuma yarana da dukiya dake kanki na damƙata a hannun ki, ki kula kinji". Tace; "kada ka damu yadda ka tafi ka barmu haka zaka dawo ka same mu, zan kula da duk wata amana taka har kaje ka dawo". Har bakin mota ta raka shi, masu tsaron lafiya suka buɗe mishi mota ya shiga, tana ɗaga mishi hannu har ya fice. Taja tsaki tace; "taya zan so ɗanka bayan ni baka son nawa ƴaƴan", ta juya cikin sauri ta nufi cikin gida. Tana shiga falon ta tarar da Khausar ta fito sanye da wando ɗan ƙarami zuwa cinya sai kuwa riga iya cibiya. "kin tashi Baby?", Hajiya Salma ta faɗa, Khausar ta ɗaga kai sannan ta nufi dinning table domin karyawa yayin da Hajiya Salma kuma ta nufi ɗakin ta. babu Jimawa Hajiya Salmar ta fito jikin ta sanye da Riga pink da ratsin fari sai wando pink, ta ɗora after dress a sama pink me shara-shara, sai ƙaramar jaka data rataya itama pink sai kuma makulli, ta yiwa Khausar peck a kumatu tana faɗin; "Baby na tafi sai na dawo", Khausar tace; "to Mummy". Tana fita masu tsaron lafiya suka taho tayi saurin ɗaga musu hannu hakan yasa suka koma, motarta ta shiga ta tayar ta fice daga gidan cikin sauri. Khausar na ganin fitar Mahaifiyar tata, ta ɗauki waya ta fara kira, bayan an ɗaga tace; "Baby dan Allah kiyi sauri ina jiran ki". Ba'a ɗau lokaci ba sai ga ƙwanƙwasa ƙofa, cikin sauri Khausar ta buɗe mata ƙofa, suka kalli juna fuska ɗauke da murmushi kafin Khausar ta rungumo yarinyar suka yi cikin falon. Hajiya Salma tana fita bata zarce ko'ina ba sai guest house ɗin Alhaji Sa'eed, kamar koda yaushe a can ta same shi sai dai wannan karon shi kaɗai ta samu babu Brr Hauwa. "Kamar yadda muka tsara Alhaji Mustafa ya bar ƙasar nan", cewar Hajiya Salma kenan lokacin da take ƙoƙarin cire After Dress ɗin dake jikin ta. Alhaji Sa'eed yayi murmushin mugun ta daga kwancen da yake yace; "kamar yadda muka tsara komai yana tafiya dai-dai, saƙon mutuwar ɗan shi zata riske shi a can", Hajiya Salma tayi murmushi tana kwanciya a jikin Alhaji Sa'eed. ******* *********** *HAYIN RIGASA, KADUNA*. sai da gari yayi haske sannan Ummi ta miƙe tace da Nusram; "bari na fita na ɗan zagaya na san ba za'a rasa abin siyarwa nan kusa ba da zaki karya dashi", Nusram tace; "to", dan har lokacin bata gama dawowa dai-dai ba. Ummi kuwa ficewa tayi daga asibitin domin neman abinda zasu karya ɗin hannun ta riƙe da wasu daga cikin kuɗin da bawan Allan da taji an kira da Alhaji Mustafa. Bata daɗe da fita ba Nusram taji anyi sallama an turo ƙofar, ta ɗago tana me amsa sallamar, tsayawa tayi tana kallon mutumin, tabbas fuskar shi ce, wannan dai wanda takewa laƙabi da ɗan yankan kai sai dai wannan ya ɗan manyanta. Duk ta ruɗe jikinta har rawa yake yi mata, tunanin ta shine kada dai canza kama yayi yazo domin cin galaba akanta wato ya tafi da ita. Alhaji Mustafa ya zauna saman kujerar yana satar kallon yarinyar, a ranshi yana mamakin meye dalilin birkicewar ta lokaci ɗaya. Sun jima a haka ɗakin shiru babu wanda yayi magana a tsakanin su, Ummi ta shigo da sallama hannun ta ɗauke da baƙar leda me ɗan girma. Tana ganin Alhaji Mustafan ta washe baki tana faɗin; "sannu da zuwa Alhaji", ya shafa kanshi tare da yin murmushi har kumatun shi ya lotsa yace; "sannu da ƙoƙari ya me jikin". Kaɗan ya rage Nusram ta suma, lallai ma wannan wato canza kama yayi dan yazo ya yaudare su kenan?, "tabbas shine wannan", Kallon da suke mata yasa ta gane a fili tayi maganar. Ummi tace; "waye kenan?", Nusram kuwa duk yadda gabanta ke faɗuwa be hana tace; "wato kazo ka yaudare mu ne ko?, shine har da yin shigar dattijai to Allah ya tona maka asiri", bin ta kawai suke da idanu. Ganin hakan yasa ta cigaba da cewa; "to ai na gane ka, dan fuskarka bata canza ba sannan ɗabi'ar ka ma haka", Ummi tazo kusa da ita ta riƙe ta. "Nusram ki dawo hayyacin ki, wannan fa shine mutumin daya taimake mu jiya ya kawo mu nan asibitin", Nusram ta kalli Ummi tace; "na sani mana Ummi ai ba yau ya saba ɗauko ni ba kwanaki ma haka ya kawo ni.har ƙofar gida sai dai ba mutumin arziƙi bane kamar yadda kike faɗa, wannan da kike gani mugu ne ɗan yankan kai ne". Tofa! Nan zufa ta fara karyowa Alhaji Mustafa, cikin inda-inda yace; "karya take yi ni ban taɓa ganin ta ba sai jiya daga taimako", Ummi tace; "ina jin dai bata hayyacin ta ne bari na kira likita", ta ƙarasa tana ficewa da sauri. Alhaji Mustafa ya kuma kallon yarinyar, Nusram ta balla mishi harara tace; "wallahi idan ma wayar ka kake so ka amsa ba zan taɓa baka ba har sai ka bani ribbom ɗina, me fuska biyu kawai, a wajen bikin da akayi kwana huɗu daya wuce kayi shigar yarinta amma anan kayi shigar tsofaffi". Kafin Alhaji Mustafa yace wani abu likita da Ummi sun shigo dan haka yaja bakin shi yayi shiru, banda zare idanu babu abinda yake yi, likita ya dubata babu abinda yake damunta amma gudun kada Alhaji Mustafa yace be san aikin shi ba gashi ya san cewa babban mutum ne yasa yayi mata allurar barci. "kada ki damu stress ne yayi mata yawa insha Allahu zata dawo dai-dai zuwa anjima", Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace; "to likita angode sosai". Bayan fitar likitan Alhaji Mustafa yace; "ni zan wuce dama na biyo na duba yadda jikinta yake ne, ga wasu kuɗin ko zaku nemi wani abin, yanzu zan bar ƙasar ne gabaki ɗaya Allah ya ƙara mata lafiya", Ummi ta amsa da "ameen", tana kuma me amsar kuɗin da ya miƙo mata. "Alhaji a ƙara haƙuri dai, shirme ne irin na mara lafiya", Alhaji Mustafa yace; "babu komai Allah ya bata lafiya", daga haka ya fice daga ɗakin. bayan fitar Alhaji Mustafan Ummi ta kira Aunty a waya ta faɗa mata cewa suna asibiti, Aunty tayi salati tana me faɗin gata nan zuwa yanzu Sulaiman zai kawo ta. Ummi ta zubawa Nusram idanu lallai Allah kaɗai ya san wahalar da yarinyar nan tasha, abu kuma harda taɓin ƙwaƙwalwa. Koda Aunty tazo kamar ta zubar da hawaye dan tausayi bayan Ummi ta gama bata labarin abinda ya faru, shi kanshi Sulaiman ɗin ya kai matuƙa wajen ɓacin rai. "ki zauna dai Maman Nusreen wata rana sai kin kashe kanki da kuma yaranki, kada ki miƙe ki ƙwaci ƴancin ki", faɗar Aunty kenan. Ummi ta miƙe tace; "ba haka ba Maman Adam haƙuri shine kan gaba kuma shine gimshiƙin zaman aure, bari naje gida na bar Kubra ita kaɗai babu kowa na san ba wanda zai kula da ita a gidan", Sulaiman ya miƙe yace; "muje tare Mama sai na rage miki hanya", tare suka fice yayinda suka bar Aunty a wajen Nusram ɗin. Alhaji Mustafa kuwa koda ya dangana da motar shi, babu abinda yake sai sauke ajiyar zuciya, kada dai ace yarinyar nan ta san ainihin abinda yake aikatawa. Magan-ganun ta babu abinda ya tsinta a ciki sai shirme wai ribbom da waya? Yaushe kuma akayi hakan?, ya kasa fahimtar inda ta dosa. Can naga ya saki murmushi har kumatun shi ya lotsa, ya lumshe idanu yana ƙarara gasgata abinda zuciyar shi ke raya mishi🙄. Ya girgiza kai yana me yin dariya, a fili yace; "lallai ta haɗu da Murad ne wajen ɗaurin auren su Alhaji Baballe". Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace; " *ABDUS-SAMAD ƊANA GUDA ƊAYA TILO, YAUSHE ZAKA DAWO GARE NI NE?*. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk* *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖41-42📖📖 Kwanan Nusram biyu a asibiti sannan aka sallameta, zuwa lokacin kuwa ta sami sauƙi sosai sai dai har lokacin gefen cikin ya kan mata ciwo lokaci zuwa lokaci, likitan kuwa yace kada ta damu zai dena a hankali. Babu wanda yazo daga gida dan ya dubata, dama kuma bata saka rai ba, Aunty ce dama ita kullum sai tazo. Babu yadda Ummi bata yi ba akan Nusram din ta bari Yaya Sulaiman yazo sai ya kaisu gida taƙi yarda, domin ita asibitin ya ishe ta dole hakan nan Ummi ta tattara musu kayan su, suka taho. Me Keke Napep suka ɗauka shata har ƙofar gida, abin ban haushi suna dawowa maƙwabta suka fara leƙe, ita dama Nusram Kubra ta ɗauka suka shige gida. Tana jiyo yadda mutane ke ƙananan magan-ganu suna dariya, wasu harda yiwa Ummi ya mai jiki, ta ɗauka da zuciya ɗaya ne ko kuwa ta sani ita dai Nusram taji ta amsa daga nan kuma ta shige bata ƙara jiyo su ba. Ameera na zaune tayi sallama amma ko ɗago kai bata yi ta kalle ta ba, Mama Jummai dake bayi tayi wuf ta fito, ta kalli Nusram ta riƙe haɓa tace; "eh lallai Abdullahi yayi gaskiya ciki ne fa aka zubar gashi nan tayi haske kamar me jego". Nusram ta bita da kallo kawai, Ummi na zuwa ta ja hannunta, ta kaita ƙofar ɗaki sannan ta buɗe mata ƙofar tace; "shiga ciki", Nusram tabi umarnin Mahaifiyar ta. Kubra ta ajiye saman kujera sannan ta fara kakkabe ɗakin kafin ta ɗauko tsintsiya ta hau shara, Ummi kuwa ruwa ta ɗora saman murhu don suyi wanka. Yana yi zafi Nusram ta juye ta fara yi ta sawa Ummi wani, ta fito daga wankan kenan Isa ya shigo, bata ko kalli inda yake ba. Ya matso kusa da ita yace; "ya jiki?", ba tare da ta kalle shi ba tace; "da sauƙi", yace; "Allah ya ƙara lafiya ya kawo me amfani", bata amsa ba sai dai cigaba da tayi da abinda take yi wato shanya Soson wankanta a sama. Ya kuma cewa; "Nusram ni duk abinda kika yi a hakan ina sonki, kada ki damu tunda dai an zubar da cikin kawai ki amince muyi auren mu", ta ɗan juyo ta kalle shi kan ta juya tayi tafiyar ta. Isa cikin takaici ya bita da kallo, wato abinda ya faru da ita har shine take da damar jan aji ko?, ya yi murmushi mugunta yace; "zan riƙe ki ne a hannu na", shima ya juya ya fice. A hankali komai ke tafiya haka ranaku ke kwaranyewa kamar ƙiftawar idanu, yau dai bikin Nusreen keda wata ɗaya yayin da bikin Atika yake da wata ɗaya babu kwana ɗaya. Idan kaga Nusram a lokacin ta dawo yadda take babu wani abu dake damun ta, bata dai fita ko'ina saboda Baba ya hanata kai koda ace ma be hanata ba zata iya fita ba saboda tsegumin ƴan unguwa. Bayan sunci abincin dare Nusram ta shafe Kubra da ruwan Addu'a sannan ta kwantar da ita, daga waje ta fara jiyo muryar Baba yana faman ƙwala mata kira. Cikin hanzari ta ɗauki hijab ta saka sannan ta fito, yana tsaye a ƙofar ɗakin shi ya kalle ta sannan yace; "kira mini uwarki", sai da ta ɗan yi jim tukunna ta juya zuwa ɗakin nasu. A zaune ta tarar da Ummi da alamu taji abinda Baba ya faɗa dan tana zuwa ta miƙe tace; "muje", Nusram ta juya kawai suka kuma ficewa. Da sallama suka shiga ɗakin, Baba na zaune gefen shi kuma Isa ne sai Mama Jummai itama tana zaune a wajen. Baba yace; "kin dai san kowa ya san meke faruwa a rayuwar ku ko, kuma tarbiya daidai gwargwado na baku amma da yake ance duk wanda ya hau motar kwaɗayi zai sauka a tashar wulaƙanci, gashi dai abinda kika gani ko ince kike kan gani". "babu irin abinda bana yi muku a gidan nan babu rashin ci🙄 Babu rashin sha, amma kuka zama karuwan cikin gida kuma a gida na wannan ya ɗauka wannan ya ajiye na yanke shawara ta ƙarshe shine aurar daku, Alhaji Baballe yazo da Allah na haɗa shi ya amince zai aure ki ya rufa mana asiri, kowa ya sani babban mutum ne a Nigeria gabaki ɗaya, amma kika ɗebi ƙasa kika watsa mini a idanu abin ban haushi a daren da aka kaiki gidan mijin ki Nusram kwarto aka kamaki dashi, ya ɗirka miki ciki kuka je zubarwa yazo da matsala shine kuka kwana biyu a asibiti, ina faɗa miki wa'innan magan-ganun ne dan ki san cewa na san duk abinda kike aikatawa, Nusram Allah yayi miki baƙin jini ko kare be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yana son ki ba, ga Ameera nan ƙanwarki ce amma ta fiki yawan samari, na kuma ƙoƙarta domin sauke nauyin da Allah ya ɗora mini naku amma kika aikata yadda kike so saboda ban isaba, Nusram ba zan yi miki baki ba amma kije yadda kika baƙanta mini kema zaki gani". Izuwa yanzu kukan Nusram ya fara tsananta, jin abinda Mahaifin nata yace yasa ta ɗagowa tana girgiza kai, cikin kuka tace; "Baba kayi haƙuri kada kayi mini baki wallahi bana da masaniya akan duk abinda kake magana akai". Baba yace; "ayya Nusram rayuwace fa gaki ga tanan, ni dai Allah ya gani nayi iya ƙoƙarina a kanki na ganin na sauke haƙƙin dake kanku, sannan magana ta biyu shine ɗazu ɗan uwanki Isa yazo mini da wani batu, yace shi ya yadda a duk yadda kike zai aure ki dan haka na saka ranar bikin ku nan da wata biyu". Ummi ta miƙe tace; "a matsayina na Mahaifiyar Nusram ban amince ba, maganar da kake yi duka naji kuma bazan amince ba, kana magana akan haƙƙin yara daka sauke kai bakaji kunyar kanka ba, wanne haƙƙi nasu ka sauke ci ko shayarwa ko kuwa tufatarwa? Wallahi matuƙar ina numfashi ba zan taɓa bari ƴata ta auri wanda beda asali ba". Duka ɗakin tsit yayi, abin mamaki yau Ummi da kanta take maida martani akan abinda ake mata a gidan, Mama Jummai ta kalli Baba ganin ba zai yi magana ba yasa tace; "au Abdullahi kana ji dan za'a rufawa ƴarta asiri shine take cewa bata amince ba wai har karuwa tana da damar da zata zaɓi miji". Ummi ta kalli Mama Jummai tace; "me zai hana kuwa tunda har ɗan shege ma ya sami damar zaɓar mata ai ina ganin ba laifi bane dan karuwa ta zaɓi nata, da kike wannan maganar naga ke har sheda kike dashi gashi nan a gabanki, kuma kike tare mishi faɗa to wallahi babu wanda ya isa ya kuma takani ko ƴata a gidan nan". Mama Jummai tace; "haka kika ce? To shima ya fasa auren nata", Ummi tace; "wannan kuma matsalarku ce", ta kama hannun Nusram zasu fice Baba ya dakatar dasu. "dawo ki zauna kun gama naku nima yanzu zanyi nawa", Ummi ta dawo kamar yadda ya umarta ta xauna. "na riga na gama magana aure tsakanin Isa da Nusram babu fashi, tunda ita bata da wanda zai aure ta", Nusram ta girgiza kai tace; "Baba kayi haƙuri ni bana son Isa dan Allah ka nemo wani amma ba Isa ba". Baba yace; "to shikenan tunda baki son Isa sai ki kawo wanda kike so na baki nan da sati biyu idan baki kawo wanda kike so ba zan aura miki Isa nan da sati uku". Ummi tace; "ko bata kawo wanda take so ba, ba zan bari ta auri Isa ba", Baba yace; "to idan kuwa har sati biyu ya cika bata kawo wanda take so ki tattara kayanki ki tafi Dabai". Cikin dakewa Ummi tace; "na yarda zan tafi amma ka sani ko bayan bana nan ka aurar da Nusram wa Isa ba zan yafe ba", Baba ya juya ya kalli Nusram yace; "to auren Mahaifiyar ki a hannun ki yake idan kin so kada ki kawo wanda kike so", ya miƙe ya fice. Isa cikin takaici ya miƙe yace; "ni na tabbata baki da wanda kike so, nine kika tsana kuma ki sani aure na dake babu fashi, ƙarin gargaɗi shine matuƙar kika shigo hannu na to wallahi sai na illata ki, ki sani sai ka fanshe duk wani wulaƙancin da kika yi mini". Ummi ta riƙo hannun Nusram tace; "ta Allah ba taka ba", daga haka taja hannun Nusram suka fice. Mama Jummai tana huci tace; "wallahi sai na wulaƙanta Maimuna da zuri'ar ta, gobe dole mu koma wajen Malam", Isa ya ciza yatsa sannan ya fice. Baba ya tsaya a waje yana mamakin yau yadda Maimuna ta iya maida mishi da martani kuma a yadda ya sani tsaf zata iya rabuwa dashi, gashi suɓutar baki yasa shi yin katoɓara. Shi kuwa ya zaiyi da rayuwar shi🙆 Allah yasa dai Nusram ta sami miji kan lokacin, idan ba haka ba to be san ya zai yi ba dan be shirya rabuwa da matar shi wacce itace rufin asirin shi ba. Ummi kuwa koda suka koma ɗaki bata nuna wata damuwa ba, sai ma sakayau da take jin ranta da zuciyar ta tayi ashe haka mutum yake ji idan har ya maida martani na wani abu da ake mishi lallai ƴanci yana da daɗi. Ta kalli Nusram wacce ta zuba mata idanu cike da fargaba, tayi mata murmushi tace; "ki kwanta mana kada wani abu ya dame ki", Nusram jiki har rawa yake yi wajen cika umarnin Mahaifiyar ta. Ummi ma sallah tayi sannan ta kwanta, babu ko ɗar a cikin zuciyar ta, tabbatar ko yanzu ta koma Dabai bata da wata matsala domin kuwa tana da gatanta. Nusram tayi shiru dama gashi dare ya tsala sosai, tunani ta faɗa na neman mafitar abinda ya tinkaro ta, yanzu ita a ina zata sami mijin aure🙆. Ba zata taɓa yadda ta zama sanadin rabuwar iyayen ta ba, kai bama ita ba ta san Nusreen da Kubra ba zasu yafe mata ba idan ta zama silar gutsirewar auren nasu musamman Kubra wacce take halin buƙatar iyayen nata, gata dai a kwance shekara shida tana kwance babu ƙafa sai dai zama. Ta tashi ta zauna tare da zuba uban tagumi yanzu ina zata saka ranta?, bata da mataimaki sai Allah kullum da abinda ke tinkarota. "ina da ɓuƙatar ganin Nusreen dole, muyi magana da ita", to wacce waya kike dashi? Wayar ta tun ranar da aka kaita gidan Alhaji Baballe bata kuma sanin inda take ba. Zumbur naga ta miƙe, wata jaka dake rataye ta fara zazzagewa cikin sa'a kuwa ta gano wayar data ajiye tun ranar bikin nasu. Kamar wacce ke tsoron taɓawa ta ɗauko, addu'arta ɗaya Allah yasa babu password, tana dannawa hoton shi ya bayyana. Kyakkyawan saurayi, me zubin fulani, jersey a jikin shi blue da ratsin fari, gashin kanshi a kwance ya jingina da kujerar da yake zaune idanun shi ya ɗan ƙara ware su da alama wani abu ya gani ko kuma style ne na ɗaukar hoto bata sani ba, murmushi ke kwance saman fuskar shi har sai da ƙananan haƙoranshi farare tas suka bayyan. Ta kai hannu daidai kumatunshi daya lotsa ta shafa, bata san ta shagala da kallon shi ba, itama dai murmushin take yi kawai, tama manta da wata matsala dake gaban ta. *********⬇️⬇️⬇️******** *UNGUWAR SARKI, KADUNA*. Ya ƙara kallon agogon dake hannun shi sannan yayi tsaki, suna tsaye suna magana, ya kalli Sumayya sannan yace; "ba zaki wuce ki shiga ba", Sumayya ta zunɓuri baki kafin ta buɗe motar ta shiga. Ya ƙara kai kallon shi gare su sannan ya taɓe fuska kamar yana gaban first love ɗin shi, ya shiga motar sannan ya danna musu horn. Brr Farida ta kalli Fadila tayi murmushi tace; "kije idan ba haka ba wancan ɗan ujilar zai.iya tafiya ya barki, ku tabbatar kun zaɓo kayan daya dace ki kuma saki jiki ki zaɓi abinda kike so kinji, dalilin na san zaki fi sakewa yasa nace kuje tare da Baby dan na san sai kunfi jin daɗin siyayyar jeki ƴata Allah yayi muku albarka". Fadila ta juya cike da kunya, Brr Farida ta bita da kallo tana murmushi a baya bata wani son auren amma yadda yarinyar ta natsu yasa taji auren ya kwanta mata a rai. Koda ta shiga motar sai da Abdus-samad ya harare ta sannan yaja motar suka fice yayin da masu tsaron lafiya suka biyo bayan su. Suna tafiya kowa ya natsu babu wanda yayi magana, Fadila tace; "wai yaushe zaka je wajen Malama ne?", yace; "kina son komawa gidane", ta ɗaga kai. Suka kalli juna shida Sumayya sannan suka yi murmushi, yace; "yarinya ai kinzo kenan", Fadila ta ɓata fuska, su kuwa suka sami damar tsokanarta har suka ƙarasa Mall ɗin. Yana gaba suna binshi a baya har ciki, kowacce taja kwando yace; "Sumayya an sami abinda ake so ko?", tace; "Yaya Abdul ai dai ba'a kuɗin ka bane". "duk Daddy ne ya ja mini da ya barni na fara aiki na ai da babu yarinyar da zata raina ni", suka tafi suna mishi dariya. Kiran wayar shi yasa ya ɗan matsa baya domin amsa kiran, "Aunty na barka da warhaka", ta ɗan ja numfashi kan tace; "idan kace mini Aunty sai naji wani iri". Yayi murmushi yace; "dole na baki girmanki Saleema", ta ɗanyi jim kan tace; "kai baka iya kiran mutum ba sai dai a kira ka ko?", ya ɗan shafa gashin kanshi yace; "afuwan zan dage na koya yanzu lafiya kuwa". "ina zaune naji ba zan iya haƙuri ba sai na kira ka, zuciya ta ke bani kamar wani abu ya same ka shine na kira naji ko lafiya?", Abdul yabi inda yake da kallo yace; "lafiya ta lau yanzu ma ina Kareem Shopping Mall na kawo Sumayya da Fadila siyayya". Tayi murmushi tace; "hmm da ace ban gaji ba da nazo sai na taya ka fira, sannan ka faɗa musu kada su sake su wahalar mini da kai, ka kula da kanka". "an gama ranki shi daɗe, na kuma gode da kulawar ki, kema ki kula", daga haka ya kashe wayar. Idanun shi ya sauka a kan ribbom ɗin da suke jere a saman canter, yabi su ɗaya bayan ɗaya da kallo har yazo kan wani ya tsayar da idanun shi a kai, ya jima yana kallon shi sak kalar na Nusram wanda ya amsa a wajen ta kalar golden. Hairat ta kalli Khausar tace; "kinga me na gani kuwa?", Khausar tace; "na gani mana", Hairat ta runtse idanu tace; "damn Sexy, gaskiya gayen ya haɗu dole na shawo kanshi" ta faɗa tana ƙoƙarin zuwa gare shi. Khausar tayi saurin janyo ta baya tace; "wannan ai yafi ƙarfin ki Baby sai dai ni, amma abinda yake bani mamaki yana kama da Daddy na", Hiarat ta ƙaro zaro idanu tace; "tabbas hakane". Khausar taja hannun Hairat tace; "zo muje dole na shawo kan wannan gayen", suna isa kusa dashi Khausar ta kai hannu ta kwaso Ribboms guda biyu ta ƙaraso gaban shi hannunta janye dana Hairat. "amm pls dan Allah duba mana wanne kala yafi kyau", ya juyo ya kalle su, nan fa ƙafar Khausar ta fara rawa ji tayi kamar shi kaɗai ne a cikin Mall ɗin gaba ɗaya ya cika wajen. Abdul ya kalle su sama da ƙasa, Khausar riga da wando ne a jikin ta daga ƙugunta belt ta saka ta ɗaure shi, sai Hairat data saka pencil skirt baki da kuma riga fara, babu ko mayafi a jikin su. "kina da magana ne?", ya faɗa yana ƙara buɗe idanun shi a kansu, Khausar tace; "am dama......dama........dam......dama.......nac......nace......ko zaka duba.........ko zaka duba mana wanne yafi kyau". Ya ɗan taɓe baki sannan yace; "banda sani akan kayan mata", da sauri Khausar taja hannun Hairat tace; "shikenan muje na gode", sai lokacin Hairat ta sami damar haɗiye miyau ɗin dake bakin ta. Har suna harɗewa wajen fita, basu ɗauki komai ba dan haka basu tsaya wajen cashier ba. Abdul ya bisu da harara, kamar ance ya kalli ƙasa yaga ƴar ƙaramar purse ɗin Khausar a ƙasa wato tsabar ruɗewa harta yarda abinda ke hannun ta. Yana tsugunawa ya ɗauka Fadila da Sumayya suka ƙaraso, dan haka hanyar waje kawai ya nufa, babu bata lokaci aka lissafa kayan ya miƙa Atm ɗin shi aka cira sannan suka fice inda kuma za'a saka a kai musu kayan su mota. Koda suka fito ya bi wajen da kallo, can ya hango su, da alamu jakar suke nema dan buɗe motar su, ya kalli Sumayya yace; "amshi makullin nan, ki buɗe ku shiga ku zauna ina zuwa" ya ƙarasa yana juyawa ya tafi. Hajiya Salma ta kalli Alhaji Sa'eed suka yi murmushi, wato tun zuwan Abdul suke wajen kuma duk suna kallon shigar shi da fitosar shi. "yanzu ne lokacin daya kamata mu aiwatar da nufin mu", faɗar Alhaji Sa'eed kenan yayin da yake danna wayar shi, motar yaran shi dake gaba. Yana ɗagawa yace; "Scorpion ka aikashi lahira kawai", Scorpion yace; "an gama ranka shi daɗe yanzu lahira zata yi baƙo", ya ajiye wayar sannan ya zaro pistol daka aljihun motar shi ya saita ƙirjin Abdul wande ke nufar motar su Khausar ɗin dan bata jakar ta, kasancewar motar su Khausar ɗin tana gaban ta scorpion ɗin, babu ɓata lokaci ya harbi Abdus-samad ɗin. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *brr zahra Allah ya ji kanshi yasa Aljanna ce makoma ubangiji ya yafe mishi kurakuren shi*. Godiya ga ƙungiya ta guda ɗaya tamkar da dubu ko ince miliyan, *GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION*, musamman jajurtattun cikin ta *UMAR ƊALHAT da kuma *SHAMSIYYA IBRAHEEM ƊAN MUSA*. *JINJINA GARE KU* *Auntyna Amina Alhassan (Oum deedat)* *Auntyna Ummee Yusuf(oum yusuf)* *Sumayya Abdullahi Babayo(Sumiee B)*. *Faridaty(Ƙafar yawo)* *Harira Aliyu(ƴar fillo)* *Ummeeteey Yusuf* *Fatima Batula(Bloody)* *Maryam Shahada* *Maryam ankudi* *Shatu* Da duk sauran da ban ambata ba, Allah ya ƙara haɗa kanmu ya tsare mu daga sharrin mahassada. 📖📖43-44📖📖 Cikin tashin hankali da kiɗima Sumayya da Fadila suka yi ƙasa da kai jin karar harbi, Abdul kuwa hannu yasa ya taro Khausar dake ƙoƙarin zubewa bayan ta ƙwala wani irin ihu na azaba da raɗaɗi. Hajiya Salma ta zaro idanu ganin wacce aka samu, cikin sauri ta buɗe motar ta fito ta nufi inda suke, kan wani lokaci wajen ya hargitse, ganin hakan yasa su Scorpion jan motar su suka gudu. Da taimakon Securities na wajen aka saka Khausar cikin mota, sannan suka rankaya asibiti, wayar Saleema ya kira yana tambayar ta tana asibiti. "meya faru ne? Wani abu ne ya same ku?, bana asibitin amma bari na taho yanzu", ta faɗa duk ta gama rikicewa, Abdul kuwa ajiye wayar yayi ya dafe kanshi. Suna isa asibitin aka amshe ta, sai da suka yi rubuce-rubuce kafin aka fara dubata, ta zubar da jini da yawa dan ma bullet ɗin a kafaɗa ya same ta. Hajiya Salma zuwa lokacin hawaye kawai take yi tana ihu ganin zata rasa ƴar ta, Alhaji Sa'eed ke lallashin ta, Sumayya da Fadila ma kuka suke yi dan basu taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba. Kasancewar da sanayya sai a lokacin Police suka iso, Abdul ko magana ya kasa yi ranshi a ɓace yake ya rasa menene dalilin da yasa ake kai ƙoƙarin kashe shi. Sun ɗauki report sannan suka ce zasu dawo zuwa lokacin da Khausar ɗin ta farka, Dr Saleema ta fito daga ɗakin ta dube su tace; "ta rasa jini da yawa dan haka dole sai an ƙara mata leda biyu". Hajiya Salma ta ɗora hannu akai tace; "na shiga uku ƴata zata mutu ta barni garin son zuciy.....", Alhaji Sa'eed be bari ta ƙarasa ba yayi saurin cewa; "haba Hajiya Salma kada kije kiyi saɓo mana". Abdul dai kallon su kawai yake yi amma a yadda alama ta nuna wannan ce mahaifiyar yarinyar, yace; "kiyi haƙuri insha Allahu komai zai koma dai-dai, yanzu zan je sai a ɗebi nawa a sa mata", Dr Saleema tace; "Abdul........". Ya riƙe hannun ta yace; " muje kawai Aunty", bata da yadda zata yi dole suka tafi Lab ɗin tare, ita dai Salma ba'a son ranta ya bada jinin shi ba. "yanzu Abdul sai ka bawa stranger jinin ka wacce ma baka santa ba?", Abdul yayi murmushi yace; "kada ki ce mini imanin ki ya gaza a nan mana, haba ina kallon ki a matsayin me tausayi, muje a saka mata", Saleema tayi ajiyar zuciya tace; "ka koma ka kwanta bari naje a saka mata". tana fita ya lumshe idanu yana tunani, su waye wai ke son ganin bayan shi ne?, ya san Mahaifiyar shi ta san wani abu daya danganci hakan amma kuma ba zata faɗa mishi ba. Dr Saleema tana zuwa ta same su a tsaye harda Brr Hauwa, Brr Hauwa kuwa ganin ta sai da ta ɗan tsorata ita kuwa Dr Saleema duk da yadda zuciyar ta ke mata kokwanto amma sai ta kauda kai kawai ta shige. Shi kanshi Abdul lokacin da ya fito sai da abin ya bashi mamaki, amma bece mata komai ba, ita kuwa Brr Hauwa nunawa take ai Alhaji Sa'eed ɗin ita ce lauyar shi. Sai da komai ya dai-daita sannan Abdul yace da Fadila da Sumayya su tashi su tafi, har wajen Hajiya Salma yaje yace; "kiyi haƙuri insha Allahu zata sami sauƙi". Cikin ƙufula tace; "wallahi idan yarinya ta, ta mutu sai nayi shari'a da kai, an kawo maka hari amma yanzu ƴata ce a cikin wahala", har ya fara tafiya yaja ya tsaya ya juyo yana kallonta. Alhaji Sa'eed da Brr Hauwa kuwa fuskar su ƙarara ta nuna rashin gaskiya, bece komai ba ya juya ya tafi, ita kanta Dr Saleema tayi mamaki sosai, cikin sauri ta biyo bayan su. "dama kai aka kawowa harin?", yaji saukar tambayar, ya juyo yace; "eh amma ai babu komai ya riga da ya wuce", dr Saleema tace; "Allah ya kyauta gaba", suka amsa da Ameen. Ko a mota yana jin Fadila tana tambayar Sumayya wai dama shi aka kawowa hari, itama Sumayyar tace; "wallahi ban sani ba banda yanzu da tayi maganar". shi dai bece komai ba har suka isa gida, Brr Farida dake zaman jiran su ta taso da sauri, "har kun dawo?". "eh", abinda ya faɗa kenan ya wuce part ɗin shi, Brr Farida ta bishi da kallo kafin ta juyo ta kalli Sumayya tace; "meya faru", Sumayya ta bata labarin duk abinda ya faru. Hankalin Brr Farida ya tashi sosai, " ku shiga ciki ina zuwa", nan suka wuce suka shiga falo ita kuma tayi hanyar part ɗin Abdul. Ya shiga bayi wanka ta fito dan haka ta samu waje ta zauna tana jiran fitowar shi, koda ya fito da sauri ta miƙe taje wajen shi ta riƙo hannun shi tace; "Baby meya faru a wajen siyayyar". Yace; "babu komai", ya fara goge sumar kanshi, Brr Farida ta kuma cewa; "amma Sumayya tace an kai maka attack", be juyo ba ya cigaba da abinda yake yi. "Abdul magana nake maka fa", ya juyo hannun shi riƙe da Comb yace; "First Love me kike so kuma nace miki, sun baki labarin abinda ya faru ai". Brr Farida tace; "shikenan, Allah ya kiyaye gaba", ta fice daga ɗakin, da kallo Abdul ɗin ya bita tana fita yayi wurgi da comb ɗin hannun shi. Kanshi ya dafe da hannu ɗaya yace; "tabbas akwai abinda kike ɓoye mini, menene wannan?". Be fita ba har akayi kiran sallar la'asar sannan ne ya yi Alwala ya wuce masallaci, be dawo gidan ba sai dare. Ganin dare yayi kawai sai ya wuce part ɗin shi, Brr Farida tana hango shigowar shi tayi ajiyar zuciya sannan ta juya ta wuce ɗakin mijin ta. "yanzu hankalin ki ya kwanta ko, tunda ya dawo", ya faɗa, tayi murmushi tana ɗaga kai, "sai dai ya fara zargi na a al'amuran shi", Dr Abubakar ya riƙo hannun ta yace; "ki kwantar da hankalin ki, na san Abdul ba zai taɓa ganin laifin ki ba koda ace ya san tarihin shi gaba ɗaya dan haka ki kwanta kiyi barci, gobe zan fara shirye-shirye dan ina so ya fara aiki a watan nan", Brr Farida cikin tsoro tace; "kada kayi haka dan Allah ka bari ba yanzu ba". "dole ne Abdus-samad ya fara aiki, kin san dai ba zai zauna a haka ba ko, Tameer da Sameer duka aiki suke yi, ga Surayya itama sannan rashin fara aikin shi hakan zai janyo cece kuce a cikin family", Brr Farida ta kau da kai kawai. Bata kuma cewa komai ba ta kwanta, haka shima Dr Abubakar ɗin kowa da abinda yake tunani. ******** ******** "yanzu irin abinda kika fuskanta kenan, Ram amma shine babu wanda ya faɗa mini", Nusreen ta faɗa cikin kuka bayan Nusram ta gama bata labarin abinda ya faru. Nusram ta dafata tace; "ya isa haka, ki share hawayen ki, dani da Atika duka ɗaya ne, ni yanzu abinda yafi damu na shine yadda zan sami miji cikin sati biyu, Rimluv bana so ta dalilina auren shekara talatin ya warware", Nusram ta ƙarasa cikin damuwa. Nusreen kuwa cikin fushi tace; "ya lalace mana, me auren ya tsinana mana, ko kuma ita Ummin me Baban yake tsinana mata, nifa dama can na gaji". "amma ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, mu kuwa auren yayi mana wani abu domin ya bamu sunan uba, martaba da daraja wacce sai wanda aka haifa ta hanyar aure yake da ita, idan banda abin ki ko Isa ma ai sheda ne a wajen ki, sannan Ummi da kike maganar ita ai ko babu komai tana da daraja da matsayi wacce budurwa ko bazawara bata da shi dan haka ki dawo cikin hayyacin ki bana so na kuma jin kinyi wannan maganar". Nusreen ta zumɓuro baki tace; "ai ke dama ba'a yi miki abin arziƙi, daga magana sai kiyo kan mutum da wa'azi", Nusram ta ɗauki jakar ta tace; "kinga tafiya ta tunda ba zaki tsaya ki saurare ni ba". Da sauri Nusreen ta janyo ta tace; "haba rabin jikina, dawo ki zauna wannan shine zuwan ki na farko gidan nan yaushe zaki zo kuma kice zaki tafi haka". babu yadda ta iya haka ta zauna, sun yi fira sosai duk da rabin firar dai ta ƴan gidan su ce daga nan kuma suka yi kitchen inda suka dora abinci. "bari dai naga meye a jakar nan da kike ta yawo dashi", Nusreen ta kai hannu ta ɗauke jakar Nusram tana dariya. Nusram tace; "ban son bincike dan Allah ki bani kayata", tana buɗewa ta zaro wayar cikin mamaki take bin Nusram ɗin da kallo. Nusram ta kauda kai, ita har ta manta da wayar ma a ciki, "wannan fa daga ina?", Nusreen ta jefo mata tambayar. Nusram ta taɓe baki tace; "ina tahowa ne wani a bayan me mashin ta faɗo daga jikin shi, nayi mishi magana amma be ji ba shine na ajiye da fatan anjima ya kira". Nusreen ta girgiza kai tace; "me wannan wayar ya wuce me hawa mashin, ki faɗa mini gaskiya", Nusram tace; "ƙaryata ni zaki yi kenan?". tayi dariya tace; "ba haka bane, Allah yasa ya kira da wuri", Nusram ta amsa da Ameen, nan suka wuni tare har gaishe da Hajiya tare suka je, nan Nusram taga tsantsar ƙauna. Data tashi tafiya haka Hajiya ta haɗo mata kayan kwalliya da kuma atamfa Nusram tayi godiya, Haijya cike da sha'awarta tace; "kada ki damu ƴata, ki ɗauke ni kamar mahaifiyar ki", Nusram tayi murmushi tace; "to Hajiya". Har bakin get Nusreen ta raka Nusram ɗin, "to.ki gaida Ummi da Kubra, wallahi sai nake ji kamar na bi ki mu tafi", Nusram ta dalla mata harara. "ina ji nan da one week zanje gidan Yaya Sulaiman shima naga wace wainar yake toyawa", Nusreen ta kwashe da dariya. Haka suka rabu cike da farin ciki, ta jima a bakin titi tana jiran abin hawa sai dai yanayin unguwar da kuma yadda yamma ta fara yi yasa gaba ɗaya hanyar take shiru. Nusram ta danna wayar dake ƙanƙame a hannun ta, ƙarfe shida da minti ashirin, nan da lokaci kaɗan za'a fara kiraye-kirayen sallar magrib, a hankali ta fara takawa hannun ta riƙe da kayan da Hajiya ta bata ɗayan kuma riƙe da wayar sai ƙara ƙanƙamewa take yi. Abin haushi har aka kira sallah Nusram bata sami abin hawa ba, gashi gari ya fara duhu nan fa ta ƙara sauri dan bata so wani abu ya same ta kan hanyar. Ɗaya ya kalli sauran biyun dake zaune yace; "gafa wata kaya nan tana tahowa", ɗayan ya bita da kallo, ya lashe baki yace; "gaskiya Baaba yarinyar ta gama haɗuwa", ɗayan yace; "ai ni nama kasa cewa komai kace yau akwai sharholiya", suka fashe da dariya. Nusram da taji ƙarshen maganar tasu ta ƙara ƙanƙame kayan hannun ta, tana me ƙara yin sauri, a baya suka biyo ta suna faɗin; "ƴan mata sai ina?", bata kula su ta ƙara sauri. Ganin sun kusa cin mata yasa ta fara gudu, suma kuwa suka rufa mata baya, gudun su da nata ba ɗaya bane dan haka suka cimmata. "dan Allah ku ƙyaleni na tafi", suka sheƙe da dariya, daya yace; "bari na tambaye ki, kina jin tsananin yunwa da ƙishirwa sai kawai kiga abinci lafiyayye da ruwa me sanyi zaki ci ko zaki bar shi?", ta girgiza kai hawaye na zubo mata tace; "dan Allah kada ku cutar dani". Ɗaya ya saka hannu ya finciko ta, ta faɗi ƙasa, Nusram ta saki ihu suka kwashe da dariya, kayan ɗaya ya kalla ya tsuguna ya ɗauka yace; "kai Baaba harda abin arziƙi take tafe dashi, amsa mun sami na zuwa canje wajen sholay gobe ya bamu kaya", ɗayan kuwa ya ɗauki ledar kayan. Nusram ta miƙe tsaye tace; "dan Allah ku barni na tafi to", Babu fa inda zaki je sai mun kwashi namu rabon malama", ya ƙarasa ya yaga hijab ɗin dake jikinta. Tasa hannu ta kare ƙirjinta, tana fashewa da kuka, ɗayan ya kalle ta yayi dariya yace; "lallai nifa na lura Abba yawanci masu saka wannan abin sunfi kaya wai ya hakane, kenan rowa kuke yi mana ko", ta girgiza kai. Wanda aka kira da Abban ya kalli wayar dake hannun ta yace; "kai yasin babbar karuwace kalli wayar dake hannun ta", jin hakan yasa ta ƙara ƙanƙame wayar. "ke bamu wayar nan", Nusram ta matsa baya tana girgiza kai tace; "dan Allah ku ƙyale ni haka na tafi ba tawa bace", ganin zata ɓata musu lokaci yasa ɗayan yayi kanta dan ƙwatar wayar ita kuma ta hana, yana ƙoƙarin karɓa tana karewa ya saka hannu ya murɗeta. Be kai ga amsar wayar ba, mota taja ta tsaya, duka suka bi motar da kallo, na ciki be fito ba haka be tafi ba, ganin sun shagala da kallon motar yasa ta hankaɗe wanda ya riƙe ta, ta koma kusa da motar ta tsaya. Fin minti biyar Abdus-samad ya bin su da kallo, yana kuma kallon yadda suke ƙoƙarin wulaƙanta mace duk da be san wacece ba, ganin yadda yake ƙoƙarin riƙe yarinyar ne yasa ya ƙaraso gaban su. Sai dai zuwan shi ya fahimci wacece hakan ya kuma fusata shi, a hankali ya ɓalle murfin ƙofar ya fito, kallon kallo suka yi da juna, cikin mamaki da firgici suka juya a guje suka bar wajen. Ganin hakan yasa ya juyo ba tare da ya bisu ba ya kalle ta, tana tsugune a wajen tana kuka, ya ɗan ja tsaki cike da jin haushi kan yace; "dallah Malama tashi ki shiga mota". Ta ɗago fuskarta a firgice sai dai ganin ko waye ya ƙara firgitata, jikin ta ya hau rawa, hakan da tayi ya tuna mishi da tsoron shi take ji fa dan haka ya jingina da motar yana kallonta. Bata bar kukan ba kuma bata tashin ba, "zan fa tafi na barki kuma idan na barki a wajen nan ba mutum uku ba har mutum shida zasu iya kawo miki hari", jin hakan yasa ta miƙe da sauri tana waige-waige. Ya buɗe gaban motar, ta tsaya tana tunanin ta shiga ko karta shiga, shi dai kallon ta kawai yake yi yana murmushi dan yanzu abin nata nishaɗin yake saka shi. Ita kuwa tsakani da Allah take tsoron shi, dan bata mishi kallon mutumin arziƙi sai canza kama yake yi mata, bata kai ga ƙarasa tunanin ta ba taga ya nufo inda take, cikin sauri ta juya zata gudu, taku ɗaya ya ƙara ya cafko ta. Janta yayi, faɗi take; "dan Allah ka ƙyale ni na tafi wallahi ina da ƙanwa da mama, kada ka cutar dani nima ba'a son raina ranar nan na faɗa maka magan-ganun nan ba", be saurare ta ba sai da ya tura ta cikin motar sannan ya maida ƙofar ya rufe kafin ya zagaya ya shiga ya tada motar suka fara tafiya. Nusram gabanta banda faɗuwa babu abinda yake yi, gani take kawai ɗaukar fansa yake so yayi akanta na rashin kunyar da tayi mishi washe garin ranar da ya kaita asibiti. Shi kuwa Abdul a hankali yake tafiya, lokaci zuwa lokaci ya kan juyo ya kalle ta, babu wanda yayi magana a tsakanin su, ita dai tana ƙanƙame da wayar shi har suka ƙaraso wani botique. Ya fito ba tare da yace mata komai ba, Nusram dai tana zaune tana zare idanu, ɓangaren ta yazo ya bude sannan ya saka hannu yaa janyo ta, hannun ta ya riƙe gam sannan ya fara tafiya, zuwa lokacin Nusram ta fara cire rai da ƙara numfashi dan kawai ta kawo cewa gidan yankan kai ne ganin irin yadda wajen ya ƙayatu. Yana shiga ƴan wajen suka fara gaishe dashi, Nusram na rungume da wayar shi a ƙirjinta, idanun ta ya kawo ƙwalla, wato ma shine babba a wajen kenan, wayyo! Ummi🙆. Wani mutumi ɗan saurayi ya ƙaraso inda yake bayan sun gaisa sannan ya shiga gaba suna binshi a baya har zuwa wata ƙofa, ya buɗe musu suka shiga. Wani ɗan ƙaramin falo ne me cike da kayan alatu, ga sanyin ac, be zauna ba ya kalli ɗan saurayin yace; "Nura hijab zaka ɗauko mata". Wanda aka kira da Nuran yace; "yallaɓai wane kala?", Abdus-samad ya kalli Nusram, doguwar riga ce a jikin ta, ta yadin saytin kalar blue da pink, ba tare da ɓata lokaci ba yace; "kawo blue", Nusram ita dai banda zare idanu babu abinda take yi. Babu jimawa yaron ya dawo hannun shi ɗauke da leda, ya miƙowa Abdus-samad ɗin, shi kuma ya nuna mishi Nusram dake tsaye. Da murmushi a fuskar shi yace; "Madam ga hijab ɗin ko?", kamar wacce zata zuba da gudu tace; "ni?", yace; "eh mana", ta kai hannu a tsorace sai kuma ta janye. Tana tsoron kada ta taɓa taji ance masu shan jini idan suka baka abu ka taɓa shikenan sai ka zama doya ko wani abin ko kuma ka ɓace gaba ɗaya. Nura ya kuma cewa; "haba Madam ki amsa mana dan Allah", Nusram ta share hawayen daya zubo mata tace; "Allah ba zan amsa ba kar naje na ɓace, su kuke ku shanye jini na", Nura dabe fahimci me take magana akai ba ya maida kallon shi kan Abdus-samad ɗin yace; "yallaɓai........". Abdul dake danna waya amma jin abinda ta faɗa yasa ya tsaya, wato har yanzu bata dena mishi kallon mugu ba kenan? Lallai zai koya mata hankali, ya miƙe ya matso kusa da Nuran yace; "bani hijab ɗin jeka kawai". Nura ya miƙa mishi sannan ya juya ya fice, inda take tsaye ya nufo, da sauri ta fara ja da baya, ganin ta kai bango yasa ta fara faɗin; "dan Allah ka tsaya, nifa ba ƴar iska bace". Ya saka hannu ya dafa bangon yace; "to waye ɗan iskan kenan" ta runtse idanu tace; "dan Allah kayi haƙuri ka barni na tafi", hannun shi ya kai saman kanta sai kuma ya fasa, ya ɗan matsa baya sannan ya miƙo mata hijab ɗin yace; "saka mu tafi", taƙi amsar hijab ɗin kuma taƙi kallon shi. Cikin jin haushi ya finciko ta, ta dawo gaban shi sannan ya warware hijab ɗin ya saka mata kafin ya kama hannun ta yaja suka fice. Har sun kusa ƙofar fita sai kuma yaja ya tsaya, janta ya kuma yi suka koma ciki, basket yaja ya fara ɗebar kaya, kayan make up na mata turarruka da kuma atamfofi da lace. Be jima ya kuma janta aka zuba musu kayan a leda sannan suka fice daga wajen, sai da ya buɗe mota ya saka ta sannan ya koma ya buɗe baya aka zuba kayan, ya shiga mota yaja suka tafi. Babu wanda yayi magana har suka isa Hayin Rigasa, har ƙofar gida ya kaita, tana ƙoƙarin buɗe ƙofa yace; "heys!, duk ranar da kika kuma gani na kika tsorata to tabbas daga ranar sai na kai jinin ki wajen gunkin mu", yana faɗar haka ya buɗe mata ƙofar. Nusram jin abinda ya faɗa yasa ta fara yarfe hannu tana bashi haƙuri, ta miƙo mishi wayar tace; "dan Allah in dai dan wannan ne kake bibiyar rayuwa ta kayi haƙuri ga wayar ka". Ya jingina da kujrerar da yake kai, ya saka hannu ya janyo ledar ɗazu ya miƙa mata yace; "gashi kayan da wa'incan suka amsar miki, yanzu fita ki bar mini mota". Ta share hawaye tace; "ka amshi wayar ka, kayan kuma bana so na gode ni dai dan Allah kayi haƙuri", ya ɗaure fuska yace; "zaki amsa ki fice ko sai na canza ra'ayi yanzu na wuce dake wajen gunkin mu", kan ya rufe baki ya wafce ledar baki na rawa tace; "Allah ya baka haƙuri, na gode", ta fice daga motar. Abdus-samad ya bi ta da kallo har ta shige gida, yayi murmushi wato dai duk girman mace da wayonta a tafin hannun ɗa namiji take kenan?. Cike da nishaɗi yaja motar shi ya tafi, babu abinda yake yi sai murmushi dama asibiti zai je sai ya fara biyawa wajen Ƙawar Brr Farida ya kai mata saƙo, shine fa suka haɗu dan haka kai tsaye ya wuce asibitin. *********⬇️⬇️********** Hajiya Salma ta kalli ƴar ta cikin ɓacin rai amma da yake Alhaji Mustafa yana wajen sai ta daure tayi murmushi tace; "haba Khausar tunda yace zai dawo ai zai dawo ne, ki daure kici abinci nan kinji". Alhaji Mustafa da be daɗe da shigowa ƙasar ba ya sami wannan mummunan labarin ko gida be jeba daga Airport ya wuto asibitin hankalin shi a tashe. Kusa da ita yazo ya zauna sannan ya riƙo hannun ta yace; "ki daure kici abincin kin ji zai zo yanzu", Khausar ta maƙe kafaɗa alamun bata yarda ba. Hajiya salma ta buɗe baki zata yi magana ya turo ƙofar tare da yin sallama, Alhaji Mustapha jikin shi har rawa yake yi ganin wanda ya shigo. Abdus-samad shima dai da kallo ya bishi, cikin ranshi yana mamakin dama wannan ƴar Mustapha Abubakar Tuge ce?. Hajiya Salma kuwa kamar ta ɗora hannu akai tayi ihu haka take ji, ya gaishe dasu sannan ya ƙarasa inda take. Khausar ta saki murmushi tace; "ina ka tsaya tun ɗazu nake zaman jiran ka?", ya ɗauki plate ɗin abincin ya ɗebo ya nufi bakin ta dashi. Ta buɗe baki ta amsa, yayi murmushi har kumatunshi ya lotsa yace; "dama yunwa kike ji kenan?", ta kai hannun kan kumatun shi tana murmushi, haka ya bata abincin har ta cinye. Da kanshi ya taimaka mata ya gyara mata kwanciya, ta riƙe hannun shi gam, be hanata ba sai ma fira da suke yi sama-sama. "ban sani ba ko jinin da ka bayar ne yasa nake gani kamar mun jima da sanin juna", ya ɓata rai yace; "waye ya faɗa miki". "baka san ina da ƙawa a nan asibitin ba?", ya ɗaga mata gira ɗaya tayi dariya tace; "ai nima likita ce amma ɓangaren mata", ya ɗaga mata yatsu alamun jinjina👍. Haka suka cigaba da fira tsayin lokaci sannan yace; "to yanzu ki kwanta sai da safe ko?", tace; "to amma gobe zaka zo da safe?", ya girgiza mata kai "sai lokacin dana sami dama, bye", daga haka ya fice. Alhaji Mustapha ya miƙe da sauri ya bishi, har ya kusa parking lot, "Abdus-samad", ya kira shi, ya ja ya tsaya. "mun gode sosai da kulawar daka nuna mata", abinda Alhaji Mustapha ya faɗa, Abdus-samad ya ɗan yi murmushi yace; "babu komai, Allah ya bata lafiya dai kawai". Ya shiga motar shi yaja ya bar Alhaji Mustafa a tsaye cike da mamaki farin ciki da kuma damuwa. Gashi ga ɗan shi amma bashi da damar zuwa kusa dashi, hasalima ƙara matsar ɗan nashi da zai yi hakan barazana ce ga rayuwar yaron dan a haka ma koda yaushe cikin barazana yake da takurawa akan yadda zai kawo ɗan nashi wajen Appu domin sadaukar da jinin shi ga oregbu. Haka ya juya ya koma cikin asibitin cike da damuwa, Hajiya Salma dake laɓe tayi ajiyar zuciya kafin itama tayi saurin barin wajen tana godiya ga Allah da asirin su be tono ba. Washe gari da safe Abdus-samad be samu damar zuwa asibitin ba, domin Brr Farida da ta tsare shi suka tafi court tare. Hajiya Salma ta kalli jug ɗin dake cike da haɗaɗɗen juice taja tsaki, ta maida kallon ta kan Khausar wacce ke kwasar barci hankali kwance ta gama zaman jiran shi be zo ba. Ta zaro wayar ta ta kira Alhaji Sa'eed, "yau fa bezo ba gashi tun ɗazu na haɗa mishi nake zaman jiran shi", Alhaji Sa'eed yayi dariya yace; "kada ki damu ina ji a jikina mun kusa yin nasara". Brr Hauwa ta amshi wayar tace; "kada ki damu zai zo ne abinda ya kamata ki maida hankali akai shine ki tabbatar ya sha kafin ya bar asibitin. Tace; "tabbas kuwa zai sha kafin ya bar asibitin nan, ku dai ku jira kirana kawai dole wannan shegen yaron ya mutu". Alhaji Sa'eed yace; "da kyau, haka nake son ji, muna zaman jiran ki", ta amsa da to sannan ta kashe wayar. Babu jimawa Abdul yayi sallama ya shigo, Hajiya Salma ta washe baki bayan sun gaisa tace; "ai ta gama rigimar baka zo ba tayi barci", ya matsa kusa da Khausar ɗin yace; "to bari na tafi kawai na dawo da yamma". Da sauri Hajiya Salma tace; "a'a ka zauna mana ko wani abu ne ka sha tukunna sai ka tafi ya juya yace; "kada ki damu Hajiya nagode", tace; "aikuwa ba zai yiwu ka tafi yanzu ba", dole tasa ya koma ya zauna ta miƙo mishi. Kiran wayar shi ya hana ya kai kofin bakin shi, sun ɗan jima suna magana kafin ya katse wayar ya duba Hajiya Salma yace; "idan ta farka kice mata nazo na tafi amma wata kila anjima na dawo", kamar zata yi kuka tace; "shikenan amma da ka sha koda kaɗan ne", yayi murmushi yace; "am ok, thanks" daga haka ya fice. Hajiya Salma kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu, cikin jin haushi ta kira Alhaji Sa'eed ta bashi labarin abinda ya faru. Shima dai ranshi ya ɓace amma yace kada ta damu komai nada lokaci idan ya tsallake yau wata rana zai faɗa ne. Sai da suka ƙara kwana biyu sannan aka sallame ta, zuwa lokacin ta sami sauƙi sosai, Alhaji Mustapha kuwa kullum sai ya zo asibitin ko dan haduwa da ɗan nashi suna haɗuwa amma ba yadda ko wanne uba Ke so ba. zuwa lokacin kuma saura kwana sha biyu Family meeting ɗin su Abdul ɗin, dan shi tunda aka sallami Khausar daga asibiti be kuma zuwa ba hasalima be je gidan su ba ko sau ɗaya. cikin kwanakin da Baba ya ɗibarwa Nusram har anci kwana bakwai, zuwa yanzu kam hankalin Nusram ya fara tashi sosai domin kuwa bata da hanyar da zata sami mijin da yake shirye ya aure ta cikin sati ɗaya. Tunda kwanakin nan suka matso kullum sai Nusram tayi tsayuwar dare tana addu'ar Allah ya fitar da ita daga wannan halin da take ƙoƙarin faɗawa. Ummi kuwa a haka zaka ganta cikin jarumta amma da zarar ta keɓe babu abinda take sai kaiwa ubangijinta kukan ta, Aunty ma duka abin ya dame ta sai dai bata da yadda zata yi. Yau ta kira Nusram ta waya tace tazo tana nemanta, duk da yamma ta fara yi haka Nusram ta shirya, niƙaɓ ta ɗaura a fuskar ta domin kuwa sa idon na ƴan layin su ya fara yin yawa. Koda ta isa gidan ta sami ƴan gyaran jiki da kuma masu siyayya, Nusram ta taya ta wajen gyaran amaren da kuma tattara kayan. Bayan sun gama ta kalli Aunty tace; "Aunty bari na shiga wajen Aisha yanzu zan dawo", Aunty tace; "to kada ki daɗe kinji", ta amsa da to. Gidan dake jikin gidan Auntyn nan ne inda Yaya Sulaiman yake da amaryar shi, lokacin bikin Nusram bata sami damar zuwa ba saboda Baba da ya hanata fita ko'ina. Ta sami Amarya Aisha sun jima suna fira domin tana da kirki sosai, sai da ta tsare ta har taci abinci sannan ta ƙyale ta taho. A zaune ta sami Aunty kusa da Abba gefen shi kuma Yaya Sulaiman ne, ta yi mishi murmushi sannan ta maida kallon ta kan Abba ta gaishe dashi cikin mutunci ya amsa da sakin fuska har yana tsokanarta. Sai da ya ɗan yi shiru sannan ya kira sunan Nusram, ta amsa tana me ƙara yin ƙasa da kanta. "kin san dai tun kina ƙarama kike gidan nan ko?, anan kika tashi har kika girma, mun san halin ki mun san abinda zaki iya aikatawa da wanda ba zaki iya aikatawa ba, Nusram ni da Auntyn ki kallon ƴa muke yi miki, haka Sulaiman da ƙannen shi kallon ƴar uwa suke yi miki, abinda ya shafe ki ya shafe mu haka abinda ya shafe mu na san ya shafe ki, in da yau zaki ganmu cikin matsala na tabbatar da cewa zaki yi duk yadda zaki yi kiga mun fita daga wannan matsalar to dan haka dole ne muma idan muka ganki a cikin matsala muyi ƙoƙarin fitar dake daga cikin ta, jiya Auntyn ki ta same ni na faɗa mini halin da kike ciki keda mahaifiyar ki, na san da cewa ba zaki taɓa so ace ta dalilin ki auren iyayen ku ya rabu ba, a gaskiya da ace tun farko mun san da cewa hakan zai faru to tabbas da Sulaiman ba zai auri kowa ba sai ke amma da yake Allah shine masanin komai, abin be faru ba sai bayan auren, kin san dai da cewa samin miji a zamanin nan wuya yake yi, wanda kuka shekara kuna soyayya ma sai yaci amanarki balle wanda kake nema cikin abinda yake ƙasa da sati ɗaya to kallon wannan yasa muka yanke shawara shine Sulaiman dai ɗan uwan ki ke dan haka mun bashi izini zai aure ki nan da sati ɗayan in Allah ya yarda, naso ma tun jiya naje gidan ku na sami mahaifin naki amma Sulaiman ɗin ya roƙeni akan mu bari mu ji ta bakin ki tukunna wannan shine dalilin da yasa muka ce to kizo, kin amince da zaɓin da muka yi miki?". Nusram kuwa tun lokacin da suka haɗa ta da Yaya Sulaiman numfashin ta ya fara sama, hannu ta saka ta dafe ƙirjinta tana addu'o'i har ta samu numfashinta ya ɗan dai-daita. Ta kalli Aunty haƙiƙa su ɗin masoyanta ne wa'inda ba zata taɓa mantawa dasu ba, ba zata iya kallon Aunty tace; "bata son ɗan da ya fito daga cikin ta ba, idan tayi la'akari da yadda ta ɗauke ta kamar ƴar data haifa, tun tana ƙarama take ɗawainiya da ita". Abba mutumin da yake nuna mata kulawa wacce ta rasa daga mahaifin daya haife ta, shiya tsaya mata a lokacin da take buƙatar taimako, lallai ba zata taɓa kallon shi tace bata son abinda ya fito daga jikin shi ba. Yaya Sulaiman wanda ya zame mata yaya guda ɗaya tamkar da dubu, taya zata kalle shi tace ma bata son shi, wanda yayi hidima da ita tun tana ƙarama, har ta girma ko ranar bikin su duk kayan data saka ko kuɗin da tayi amfani dashi shine ya basu ba zai taɓa yiwuwa taƙi shi ba. Taja ajiyar zuciya goshin ta sharkaf da zufa ta buɗe bakin ta wanda yayi nauyi tace....................". *ZUCIYATA WHERE ARE YOU, gafa Nusram ɗin ki cikin tasku, kizo ki taimako ta, godiya gaba ɗaya kacokam ga *RAYUWAR ABDUS-SAMAD FANS CLUB* da kuma *ZAMA NA AMANA 2* musamman ma *ZAKARIYYA KHADIJA, AISHATU BABAYO(ZUCIYA TA), ABDUL ƘIRU, IBNATU, MAMAN ABDUL* banda bakin yi muku godiya. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk* *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖45-46📖📖 Tace; "nagode Aunty, kin nuna mini ƙauna wacce koda ace ke kika haife ni iya wacce zaki bani kenan, Abba ka kula dani kulawar da ko Mahaifina be bani ita ba ban ɗauka a komai ba face kai ɗin matsayin Uba, me zan iya ce muku da kuka bani Yaya wanda yake kula dani a matsayin ƙanwar shi, abinda yasa kullum hankalina ke kwanciya saboda Allah ya bani madadin duk wani abu dana rasa, da farko ya bani Uwa biyu yazo ya bani Uba kamar ka Abba sannan ya haɗa mini da Yaya idan ban godewa Ubangiji ba ai nayi mishi butulci". "wallahi umarnin ku ni mai yin biyayyace, sai dai kuma kada mu duba kanmu a kowanne lokaci mu dinga duba wasu ma wa'inda zamu iya cutar dasu suma, Aisha amarya ce da yin auren su befi sati biyu ba nan kuma da sati ɗaya sai ayi mata kishiya anya kuwa an mata adalci?". "Aunty ki ɗora wannan abin a kanmu idan da ace Safeena za'a yiwa haka ko Halima fa? Na san ba zaki taɓa jin daɗi ba, to a bar magana tasu ma idan kuma ni aka yiwa fa?, ko Nusreen data ɗebi kwanaki a gidan ta ba zamu ji daɗi ba ace anyi mata wannan, to yadda ba zamu ji daɗi iɗan anyiwa namu ba to muma kada mu yiwa wani, na gode ƙwarai da wannan shawara sai dai nima ku duba nawa magan-ganun dan Allah". ɗakin yayi shiru, kowa yana tunani daban dana ɗan uwan shi, Nusram ta kuma cewa; "dan Allah kada mu aikata aikin da za muyi dana sani amma idan har kuna ganin abinda kuka yanke shine dai-dai to ni meyi muku biyayya ce". Abba yace; "tabbas abinda kika faɗa Nusram gaskiya ne, mutane zasu zage mu sannan bamu san wane irin kallon dangin ta za suyi mana ba, dan haka zamu cigaba da taya ki da addu'a kawai". Nusram tayi ƙasa da kai tace; "na gode Abba, Allah ya ƙara girma", Yace; "Ameen, Allah yayi muku albarka, Sulaiman tashi ka maida ita gida". Ya amsa da to sannan ya miƙe daga gaban iyayen shi, itama ta miƙe tana yiwa Aunty Sallama, Aunty tace; "Allah ya tashe mu lafiya Nusram Allah kuma ya dube ki, ki gaishe da Maman ki", tace; "to. Har suka isa ƙofar gidan su Nusram babu wanda yayi magana, kowa kuma abinda yake tunani daban. Nusram harta yunƙura zata buɗe ƙofa ta koma ta zauna, tace; "Yaya kayi haƙuri da abinda ya faru ba wai ba zan iya auren ka bane a'a zan so ace kaima ka fahimce ni kamar yadda suma suka fahimce ni". Yaya Sulaiman ya numfasa yace; "kada kice komai, waye zai fahimce ki sama dani, mun rayu tun muna yara tare kallon abu kika yi na san me kike nufi balle har ta kai ga kin furta, kije gida kawai sai da safe nima zan taya ki da addu'a". Tayi murmushi tace; "na gode sosai sai sa safe", yace; "Allah ya tashe mu lafiya", tana fita ta haɗa ido da Baba wanda ke tsaye yana jiran fitowar Isa da alamu lissafi zasu yi ko wani abin. Yaya Sulaiman ya danna mata horn ta juya ta ɗaga mishi hannu, ya ɗago mata hannu sannan yayi reverse ya bar wajen. Cikin natsuwa ta fara tafiya, "barka da dare", abinda ta faɗa kenan lokacin da tazo gifta Mahaifin nata, Baba yace; "waye ya ajiye ki a mota yanzu?". "Yaya Sulaiman ne", cikin daka tsawa yace; "rufe mini baki gantalalliya ni zaki rainawa wayo, wato Sulaiman ne ya kawo ki ko, kai ni kam banyi sa'ar haihuwa ba, to bari kiji wallahi daga kwanakin dana ɗibar miki babu ƙari, nan da sati ɗaya idan baki fito da miji ba ni da ke ne", Nusram tace; "to Baba", ta wuce gida. Tana shiga zaure Isa na fitowa daga ɗakin shi, ya kalle ta ya kwashe da dariya yace; "baki da miji da ya wuce ni ɗin nan". Bata kalle shi ba ta shige cikin gida, Mama Jummai dake gaban murhu tace; "an gama yawon ta zubar ɗin kenan?", itama dai Nusram bata kulata ba. Ɗaki kawai ta shiga, ta yiwa Ummi sannu da gida, Ummi tace; "ya kika baro su", tace; "suna lafiya sun ce ma a gaishe dake", Ummi tace; "masha Allah". Har zuwa lokacin da suka kwanta Ummi bata tambaye ta ya suka yi da Aunty ba itama kuma bata faɗa mata ba. Ta zurfafa kanta cikin tunani ganin cewa gobe fa saura kwana shida kenan, dole tayi wani abu a kai idan ba haka ba tana ji tana kallo matsalolin gidan su zasu fi ƙarfin ta. Shawarar da taji ta kwanta mata a rai ita ta fara ƙoƙarin bi, dan haka cike da ƙwarin gwiwa tayi barcin ta. Washe gari da safe duk wasu ayyukan da ta san zata yi duka tayi sannan tayi wanka taci abinci. Kayan siyarwa da Ummi take siyarwa ta tayata suka ƙulla na ƙullawa sannan ta tashi ta wanko hannun ta. Tana tsaye a tsakar gida, Atika tayi sallama ta shigo, Nusram ta kalle ta, itama ɗin ita ta kalla fuska ɗauke da murmushin mugunta. Wani rantsattsen lace ne a jikin, kalar ash da orange, yayi kyau sosai, ita kanta Atikar tayi ƙiba tayi freah, Nusran ta kauda kai daga kallon ta. Atika tayi shewa tayi juyi sannan ta nufi hanyar ɗakin mahaifiyar ta, bata jima da shiga ba aka fara shigo da buhunan abinci. Shinkafa buhu biyu, taliya kwali uku, buhun semonvita guda ɗaya, ƙaramin buhun gishiri, sai sugar itama ƙaramin buhu, man ja da man gyaɗa duka galan ɗaya, sai tarkacen maggi. Nusram kuwa ɗaki ta shige dan wannan dama basu bane a gabanta, ko Ummi bata bawa labari ba, tana daga cikin ɗaki ta jiyo sallamar Habiba, nan suka hau murna suna shewa a tsakar gida. Ummi ta kalli Nusram, Nusram kuwa hankalin ta naga wayar Abdus-samad tana dubawa kamar wacce ta san kanta, Ummi tace; "bafa kiyi mini bayani akan wayar hannun ki ba". Nusram tace; "Hajiyar Shureim fa ta bani haɗe da kayan nan", Ummi tace; "aikuwa an gode sosai, amma da kin sani baki amso duka ba, kayan sun yi yawa". "nima sai da nace mata ba zan amsa ba ta tilasta, shiyasa na amsa ɗin dan kada nayi jayayya da ita", Ummi bata kuma cewa komai ba. Suna jiyo lokacin da suke ta hidimar su akan kayan da Atikar ta kawo, babu wanda yace wani abu, Nusram ma cikin ɗaki kawai ta shige. Tun ranar data dawo da kayan ta ajiye a kullum tana son ɗauka amma hakan ya gagara saboda gani take idan ta ɗauka ɓacewa zata yi. 🤣🤣🤣🤣🤣 Nusram baki ɓace ba da kika dauki wayar shi sai kayan daya siya miki a boutique?. Kwanciya tayi, tana tunanin rayuwar ta har barci ya ɗauke ta, sai lokacin da zata ɗora girkin rana sannan ta farka. Ta fito ta haɗa wuta inda ta ɗora abinci, Sahura ta fito da sauri, Nusram ta kalle ta tayi murmushi, suka gaisa cikin mutunci. "ina mijin naki?", tace; "yana gida yace a gaida ke", Nusram tayi ajiyar zuciya tace; "ina amsawa", sun ɗan taɓa fira kaɗan kafin Sahurar ta tafi. Nusram na gama abinda zata yi ta shige ɗaki, tare da Ummi suka ci abincin, daga nan suna juyo abubuwan dake waka na a tsakar gidan. Nusram ta taɓe baki kawai tana cigaba da abinda yake gabanta, Ummi ma bata ce komai ba. "ayyiririririiiiiiiii, gaka inda aka iya haihuwa, ni Jummai waya ganni a saudia", faɗar Mama Jummai kenan kafin kuma suka hau tiƙar rawa ita da Ameera da Habiba, Atika na musu kiɗa. Sai da suka gama cashewar su sannan Mama Jummai ta kuma cewa; "kai haihuwa me daɗi, ai dama haihuwa suna ta tara mu dai tamu kam sam barka". Duk da Nusram da Ummi suna jiyo su amma babu wanda ya tanka musu, haka suka gama shewar su da habaice-habaucen su. Koda yamma da Baba ya dawo, ana nuna mishi kayan da wai Alhajin ya bada a kawo ya hau murna. "Maimuna ina kike?", ya hau ƙwalawa Ummi kira, ta fito Nusram ma ta biyo bayanta. "ki kalli inda ake abin arziƙi, kin gani ko wannan shine haihuwar da ake so ba kalar taki ba ƴaƴa sun zama kamar masu farar ƙafa babu ɗaya ƙwakkwara na kamawa". Ummi tace; "an gode Allah ya saka da alkhairi", Baba da Mama Jummai suka ce Ameen, inda da gaske kike", Ummi tayi murmushi kawai kafin ta juya. "haba me ake da yaran da basu san su kyautatawa iyayen su ba, ita waccen shegiyar har yanzu ko gidan bata leƙo ba", tsaf Ummi ta san da Nusreen yake amma bata tanka mishi ba. Sai bayan sun shiga ɗaki sannan ta sami damar share hawayen daya zubo mata, Nusram ita kanta jikinta yayi sanyi, ta miƙe ta shiga ɗaki hijab kawai ta ɗauko kafin tazo ta fice. Ba tare da sanin inda ta nufa ba, wani lungu tabi sannan ta tsaya tana maida numfashi, lallai ya kamata tayi wani abin kodan ragewa Ummi damuwar da take ciki, to amma yanzu me zata yi?. Tana nan tana saƙe-saƙe aka fara kiraye-kirayen sallah, ta miƙe sannan ta fara takawa cikin natsuwa. Masallacin da ta san mahaifinta baya zuwa haka ma Isa nan taje ta laɓe, tana kallon yadda mutane ke hada-hadar su na ƙoƙarin yin alwala. Wanda ta hango a can gefe idan zata iya canka zai kasance shine liman, tana kallo yana alwala sai da ta tabbatar mutane sun yi alwala sun shige masallaci sannan ta sami damar ƙarasa gaban shi. Tayi mishi sallama ya amsa, yana cigaba da alwalar shi ta tsaya har sai da ya ƙarasa sannan ta gaishe dashi, ya amsa yana bin ta da kallo. Tace; "dama.......dama mijin.........dama mijin aure ......nake nema shine ........shine nace bari ......nazo nan masallacin idan dame buƙatar ƙara mata sai yaje ya sami......sami mahaifina", ta ƙarasa muryarta na rawa tana wasa da yatsun hannunta. Limamin yayi ɗan jimm kan yace; "to shikenan ki jira mu nan waje, amma kamar ƴar gidan Malam Abdullahi", cikin ladabi tace; "eh nice", ya jinjina kai sannan yace; "ki jira bari na shiga muyi sallah tukunna Allah yasa a dace. Wani gida dake kusa da masallacin nan ta shiga ta rakuɓe, addu'ar da take yi Allah yasa a dace ta sami mijin aure ko ta bar gidan nasu mahahifiyar ta, ta sami kwanciyar hankali. Tana jiyo lokacin da suka idar da Sallah, liman ɗin yayi sanarwa, bata da tabbacin me suke bada amsa, amma liman ɗin ya sanar musu sannan ya faɗa musu ƴar gidan ko waye yace; "idan dame buƙata sai ya nemi mahaifin nata", daga haka yayi addu'a aka watse. Daga inda Nusram take tana jiyo wasu samari suna faɗin; "kai haba dai waye zai kai kanshi wajen yarinyar da a ranar da aka kaita gidan miji aka kamata da kwarto". Ɗayan yace; "kai da ka gane kenan Auwalu, kwananta goma sha biyu fa a gidan kaso", Auwalu yace; "kai Idi a dai wajen ƴan sanda ba gidan kaso ba, shima kuma kwana takwas ne ba goma sha biyu ba". Ɗayan yace; "ni naji ance ma wai da saurayin suka haɗa baki, suka gudu sai da ya ɗirka mata ciki sannan ya dawo da ita, Mahaifiyar ta itace take goyan bayan duk abinda take aikatawa, sunje zubar da cikin aka sami matsala sai aka kwantar dasu a asibitin kwanan su shida sannan aka sallamo su". Idi yace; "ai zasu aikata wallahi, kana ganin mahaifiyar nan tasu a haka sumimi kasai, kamar wata mumina da gaske, ta ganku tana wani sunkuyar da kai kamar sabuwar tunkiya, amma ita take tura yaranta karuwanci". Auwalu yace; "kai raba kanka da irin wa'innan matan yasin, bar ganin ta a haka da zumbulelen hijab waye ya san ita me take aikatawa, shi kanshi mijin nata ai asiri tayi mishi to ance fa ya sake ta amma taƙi barin gidan yanzu haka ma kuɗin da suka yi karuwanci dashi suke ciyar da kansu". Nusram ta tsugunna a wajen ta fashe da kuka, wato kallon da ake yi musu kenan, lallai rayuwa kenan, sai da gari yayi duhu sosai sannan ta sami damar barin wajen. Har lokacin kuma basu bar firar su ba, taja hijab ɗin ta rufe rabin fuskar ta sannan ta tafi. Koda ta isa gida Ummi bata ce mata ina taje ba haka itama bata cewa Ummi ga inda taje ba, Koda tazo kwanciya sai da tasha kukanta ma'ishi kafin barci ya ɗauke ta ************* ************* Khausar dake kwance saman couch ɗin ɗakin ta wanda yaji kayan more rayuwa. tana sanye da riga doguwa iya gwiwa, kwananta biyu kenan babu inda taje, Mahaifiyar ta harta gaji da buga mata ƙofa akan ta buɗe amma taƙi. Yanzun ma Hajiya Salma dake tsaye bakin ƙofar ta kuma bubbugawa tace; "wai Khausar ba zaki buɗe ƙofar nan ba", shiru babu amsa. Khausar kuwa dake ciki tayi juyi tana jan tsaki, wai me yasa ƴan gidan nan basa ganewa ne itafa Abdus-samad kawai zasu nemo mata shine samun kwanciyar hankalin ta. Alhaji Mustapha dake zaune saman dinning ya buga uban tagumi, lokaci zuwa lokaci ya kan share zufar da take tsattsafo mishi. Brr Jabeer yayi sallama ya shigo, cikin sauri Alhaji Mustafa ya miƙe ya isa wajen shi, saman kujera duka suka zauna. Alhaji Mustapha yayi ƙasa da murya yace; "Brr ina cikin tashin hankali, ƴata Khausar tace babu wanda take so sai ɗan uwan ta Abdus-samad". Brr Jabeer ya zaro idanu waje yace; "taya suka haɗu a ina kuma ta san shi, shin ko dai ta san sirrin da kake ɓoyewa ne", Alhaji Mustapha yace; "ko Mahaifiyar ta bata sani ba balle ita". "tun da suka haɗu a wajen siyayya shikenan ta maƙale, yau kwanan ta biyu kenan ta rufe kanta a ɗaki babu ci babu sha wai shi take son gani". Brr Jabeer yayi shiru tsayin wani lokaci kafin yace; "ni ina ganin kawai abinda za'a yi shine ka nemo shi, kga daga nan zaka sami hanyar da zaka ja sha jikin ka". Alhaji Mustapha yace; "hakane kuma, amma kai kanka Brr kasan wacece Brr Farida ba sai na faɗa maka komai ba, idan har na sake nayi wani motsi a kai to zata kaini kotu kuma ka san cewa kaini kotu dai-dai yake da tonon asiri na". Brr Jabeer yace; "kuma hakane tabbas, to amma yin shirun kana ganin shi yafi", Alhaji Mustapha ya jinjina kai yace; "tabbas kuwa shi yafi, idan ta gaji da kanta zata buɗe ƙofar", Brr Jabeer yace; "shikenan". Tare suka miƙe da Alhaji Mustaphan, inda Hajiya Salma ke tsaye tana fama da Khausar akan ta buɗe ƙofa suka je. Brr Jabeer yace; "Khausar ki buɗe ƙofar nan ni kuma nayi miki alƙawarin baki number ɗin shi", Khausar jin hakan yasa ta diro daga saman couch ɗin tazo ta buɗe. Hajiya Salma da Alhaji Mustapha kuwa gaban su ya faɗi, Hajiya Salma abinda take gudu shine alaƙa ta shiga tsakanin su bata fatan abinda zai kawo Abdus-samad ɗin cikin rayuwar su wancan ma tsautsayi ne. Alhaji Mustapha kuwa tsoron shi shine be san ta yadda zai kare kanshi ba idan har asirin shi ya tonu. Khausar ta kalli brr, shi kuma yayi mata murmushi sannan yace; "idan kika kashe kanki a ɗaki Khausar taya zaki iya zuwa wajen Abdus-samad ɗin ko kin haƙura dashi ne?", ta girgiza kai. Ya riƙo hannun ta yace; "idan mutum yana son abu ba wai shiga ɗaki yake yi ya rufe kanshi ba a'a zai iya iyakar yin shi nr ganin wannan abin yazo gare shi, wannan shine abinda ya dace kiyi, kinji ƴar Baba". Khausar tayi murmushi tana sauke kanta ƙasa, Brr Jabeer kuwa murmushi yayi kafin yayi musu sallama ya fice daga gidan. Alhaji Mustafa ya kalli ƴar tashi yace da ita; "haba Khausar yanzu kina ganin abinda kika yi kinyi dai-dai kenan". "kayi haƙuri Daddy ba zan kuma ba", ta faɗa cikin sanyin murya, zai kuma magana Hajiya Salma ta dakatar dashi tace; "Khausar wuce kije kici abinci". Sai da ta bar wajen sannan Alhaji Mustafa yace; "wai me yasa bakya son na yiwa yaran nan faɗa ne?". "to Alhaji wane irin faɗa kuma bayan ta riga ta fito daga ɗakin ai shikenan dai ko, ni zan wuce wajen aiki", ta ƙarasa tana tafiya. Alhaji Mustapha ya bita da kallo har ta fice sannan yayi ajiyar zuciya kafin ya ciro waya ya hau kiran Alhaji Sa'eed. "Alhaji ina cikin tashin hankali", abinda Alhaji Mustapha ya faɗa kenan bayan Alhaji Sa'eed ya ɗaga wayar. Alhaji Sa'eed yace; "innalillahi, ka bari anjima mu haɗu a guest house ɗin ka dake by pass", Alhaji Mustapha yayi ajiyar zuciya yace; "to", daga haka suka katse wayar. Ya nemi waje ya zauna ya dafe kanshi, idan har yayi wasa tofa wanki hula zai kaishi dare, dole ya san abinda ya kamata yayi, be shirya zuwa gidan yari yanzu ba. ******** *********** Abdus-samad ke gaba yayin da Fadila da Brr Farida suke bayan shi, yana sanye da ƙananan kaya, jar riga da kuma baƙin wando as usual shigar ƙananan kaya. Brr Farida tace; "yauwa kije insha Allahu nan da sati ɗaya zamu zo kuma za'a yi maganar auren ku, kinji ko". Fadila ta sunne kai tana murmushi, Brr Farida itama tayi murmushi sannan ta kalli Abdul tace; "Baby ka tafi da ita a hankali banda gudu ka san amarya tsautsayi gare ta". Sameer da Tameer dake tsaye a wajen parking lot ɗin suka kalli juna suka kwashe da dariya. Abdus-samad ya shagwaɓe fuska yace; "kai First Love ni na lura yanzu ma ba wani sona kike yi ba ta wannan me kan gwandar kike". Brr Farida ta riƙo hannun shi tace; "idan banda abinka, ai kai ne na gaban goshi, ita kuma a ƙeya take", wannan yasa suka kuma dariya. Sameer yace; "mu dai ka wuce ka kaita zamu jira ka a office idan kayi latti kuma zaka amsa query", Abdus-samad ya murguɗa mishi baki. Sameer zai kuma magana Brr Farida ta dakatar dashi tace; "dan Allah ka bari su tafi kawai". Dr Abubakar da ya fito cikin shirin tafiya wajen aiki yace; "au har yanzu baku tafi ba kun tsaya wasa ko". Brr Farida ta ƙarasa wajen mijinta tace; "nima abinda nake faɗa musu kenan, su tafi kawai Baby kuje Allah ya kiyaye hanya idan Ka kaita ka wuce company zaka sami Daddyn ku yana zaman jiran ka", Abdus-samad ya amsa da to. Suna tsaye suna ɗaga musu hannu har suka fice daga gidan, kafin kowa kuma ya shiga tashi motar ya bar gidan, domin tafiya wajen aiki. Kamar yadda Mahaifiyar tashi ta umarce shi a hankali yake tuƙin, Fadila ta kalle shi tayi murmushi. Shima murmushin yayi sannan yace; "kin san umarnin uwa dole na cika shi", Fadila tace; "ni ina tsoro sai nake gani kamar Hajja ba zata amince da wannan auren ba". Abdul cikin halin ko in kula yace; "to kada ta amince mana, ai ba ita keda iko da ke ba", Fadila kai tsaye tace; "amma ai tana da iko da iyayen mu ko". Bece komai ba banda hankalin shi daya mayar kan tuƙin shi, dai-dai kwanar layin nasu yabi da kallo, tuno yadda suka yi kwanaki yasa yayi murmushi kawai. Har ƙofar appartment ɗin su Hajjan ya kaita, Fadila ta buɗe ƙofa sannan ta waigo tace; "na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ga wannan dan Allah kada ka manta ka taho mini dashi". Ya amshi ƴar paper ɗin, rubutu ne wanda shi ba zai tantance meye a jiki ba, ya kalle ta yace; "meye wannan", ta ɗan kauda kai tace; "abin amfani ne kai dai kawai ka siyo mini", ya balla mata harara yace; "wato har kin fara aike na kenan". Tayi dariya tana ficewa daga cikin motar, shi kuma ya girgiza kai kan ya ja motar ya tafi, ya san ko yace zai shiga su gaisa ran shi ne kawai zai ɓace, gashi zuwa yanzu ya san Fadil baya gida yana wajen aiki. Hanyar Companyn kawai ya ɗauke, gudu yake shararawa sosai domin kuwa ya san yayi latti gashi zuwa yanzu ya san Mahaifin nashi yana can yana zaman jiran shi. *FARIDA AND SONS NIG LMTD*, sunan companyn nasu kenan, wanda kusan yayyin shi ke jan ragamar companyn, yana parking ma'aikatan suka fara gaishe dashi, ya tsaya suka gaisa cikin mutunci da girmama juna. Kai tsaye ya wuce office ɗin CEO ɗin, inda a can ya sami Dr Abubakar na zaman jiran shi, koda ya shiga basu wani jima ba. Dr Abubakar ya kalli Sameer wanda ya kasance shine CEO a wajen yace; "ga ɗan uwan ka nan zamu je yanzu mu dawo sai ka nuna mishi nashi office ɗin". Sameer yace; "to", daga haka ya juya ya fice Abdus-samad ɗin na bin shi a baya, motar Dr Abubakar ɗin suka shiga dukan su. Suna tafiya ya juyo ya kalli Abdus-samad yace; "abinda yasa zaka yi aiki a wancan companyn shine dan ka matsa kana so ka fara aiki amma yanzu zamu je inda nake company ɗin yake ana ta aikin shine amma insha Allahu nan bada jimawa ba za'a gama sai ka koma can", Abdul ya amsa da to. Da ɗan tazara tsakanin wancan Companyn da wanda suka.je yanzu, a girma da faɗi wanda suka baro yafi wannan sai dai yadda tsarin wannan yake ya bambamta da wancan. Dr Abubakar yace; "wannan shine Compnyn ka shiga kaga yadda tsarin shi yake ni zan wuce wajen aiki ne, idan naje zan saka driver ya kawo maka mota sai ka koma wajen naka aikin", Abdus-samad yace; "to". Dr Abubakar ya tafi yayin da Abdus-samad ahi kuma ya shiga ciki domin ganin yadda tsarin companyn yake da duk yadda masu ginin ke aikin nasu. ********* ************ Nusram ke tsaye bakin titin da zai sadaka da Unguwar tasu, fuskarta tayi ja tsabar kukan da taci, yau shine cikar kwanakin da aka ɗibar mata gashi har zuwa lokacin bata sami wani wanda ya amsa zai aure ta ba. akai-akai takan saka hannu ta share hawayen da yake zubo mata, kasancewar hanyace babba wacce mutane kan gifta suna hada-hadar su kowa yazo wucewa sai ya bita da kallo. Ita kuwa duk ta ruɗe duk yadda ta dauki abin ya wuce haka, ta kalli samarin dake tahowa, baya ta koma kaɗan ta jingina da ginin dake kusa da ita. Koda suka ƙaraso gare ta, tayi musu sallama, duk suka kalle ta, cikin rawar murya tace; "dan Allah mijin aure nake nema", wannan maganar ta basu dariya suka kuwa dara. Nusram ta share hawayen daya zubo mata tace; "auren mahaifiyata Babana ya ɗora akan nawa yace idan ban fito da miji nayi aure ba a bakin auren ta, dan Allah ku taimake ni". Suka yi shiru suna kallon ta, dan kyau akwai kyau, hijab pink ta saka dogo har ƙasa hakan ya hana ni ganin wane kalar kaya ne a jikin ta, ta janyo hijab ɗin ya rufe rabin fuskar ta wanda sai ka natsu sosai zaka iya fahimtar wacece. Ɗaya ya kalli ɗaya yace; "Bello ko zaka shiga daga ciki ne, ni dai ka san yanzu ba zai yiwu na ɗaɗɗako aure ba ko?". Wanda aka kira da Bello yace; "kai Aminu rabani da kyawawan matan nan, nifa gwara na nemi dai-dai ni na aure, kaga kalar wa'innan kayi shiru kawai, waye ya san me take aikatawa da mahaifin nata ya koro ta, ni dai kam ba zan iya ba kai dai idan zaka aure ta to bismillah sai muje a toshe ƙofar naka ɗakin a maida shi ta cikin gida". Aminu yace; "bakada hankali ne yanzu ina naga kuɗin aure, sadaki akwati, waye yace maka mace kamar wannan zata iya zama a irin gidan mu, ɗaki ciki ɗaya". Jikin Nusram har rawa yake yi wajen durƙusawa ƙasa tace; "wallahi zan zauna, ni dai dan Allah ku taimaka mini", suka kalli juna kafin Bellon yace; "kai anya kuwa wannan mutum ce Aminu yau munyi gamo", da sauri suka fara tafiya. Nusram ta bisu kamar sabuwar mahaukaciya tana kuka tana roƙon su, ganin hakan yasa suka zuba a guje kowa na ƙoƙarin ceton ranshi. Nusram kuwa ganin sun gudu yasa ta tsaya tana share hawayen da ya zubo mata, bata taɓa ɗauka matsalarta zata girma ta kai hakan ba. Duk masallatai da kuma ƴan layin su kowa gudun ta yake yi, yanzu gashi tazo inda ba'a santa ba nan ma kallon aljana suke mata. Tun safe take garari a hanya tana neman me auren ta amma ta rasa kowa ya kalleta sai yace tafi ƙarfin shi, ko kuma be san me take aikatawa wasu ma kallon zararriya suke yi mata. Jin an fara kiran sallar Magrib yasa ta matsa can jikin wani masallaci ta zauna dole ta sake tunani, ta jima zaune tana kuka tare da tunanin halin da zata shiga ta kuma jefa auren mahaifiyar ta a ciki, kafin ta miƙe ta fara tafiya cikin galabaita. Har ta ƙaraso gida babu wanda ya yarda da buƙatar ta, tana shigowa zaure Isa na fitowa ganin yadda tayi.wujiga-wujiga yasa ya kwashe da dariya yace; "lallai na ciri tuta ai dama na faɗa miki baki da miji sai ni", bata kula shi ba shi kuma be fasa faɗan abinda ya ke son faɗa ba. "ki shiga ciki Baba na zaman jiran ki ai", jin hakan yasa gaban Nusram faɗuwa, cikin sanɗa ta leƙa tsakar gidan, Baba ne kuwa zaune saman tabarma yana faman masifa. Ta jima tsaye tana tararrabin ta shiga ko kada ta shiga, a ƙarshe dai haka ta yanke shawarar shiga cikin gidan. "eh da yake ni an raina ni.wato ke kaɗai zaki je Saudiar to naga wanda zai barki kije ɗin" maganar da Baban keyi kenan wacce ta daki kunnuwan Nusram ɗin. Nusram tayi sallama ta shiga, Baba yace; "yauwa an dawo daga yawon barikin, zo nan", jikin Nusram ya kama rawa. Ta tsuguna tace; "Baba gani", Baba yace; "ke wato dai sai kin kashe ni sannan hankalin ki zai kwanto ko", Nusram ta girgiza kai. "to wallahi baƙin cikinki ba zai kashe ni ba, kinfi ƙarfin kowa yanzu sai dai mu zuba miki idanu ko?, ina ita me ɗaure miki gindin?". Ummi dake zaune ƙofar ɗakin ta tace; "ina jinka ai faɗi abinda kake so ka faɗa", Baba yayi ƙwafa yace; "yauwa ai ina so kiji da kunnen ki ne". Ya kalli.Isa da Mama Jummai yace; "kuma ina so kuji abinda zan faɗa domin ina so ku zama sheda". Ya dawo da kallon shi kan Nusram sannan yace; "kin sami mijin auren", Nusram ta girgiza kai tace; "dan Allah Baba kayi haƙuri". Baba ya ɗaga mata hannu yace; "sati me zuwa ɗaurin auren ki da Isa", Ummi tace; "wannan ne ba zai taɓa yiwuwa ba wallahi matuƙar ina da rai". Baba ya miƙe yace; "shikenan sai ki fara shirya kayan ki na tafiya Dabai", babu tsoro ko shakka Ummi tace; "to shikenan". Nusram ta fashe da kuka ta riƙo ƙafar mahaifin nata tana faɗin; "dan Allah Baba kayi haƙuri", ya zare ƙafar shi yace; "wallahi matuƙar wanda zaki aura be zo gobe ba to sai Uwar ki ta bar gidan nan sannan kuma auren ki da Isa babu fashi", be jira me zata ce ba yayi ficewar shi. Nusram ta cigaba da kukanta cikin baƙin ciki, yanzu shikenan tayi sanadiyar rabuwar iyayen nata kenan, Ummi tazo ta miƙar da ita tsaye tace; "kada ki damu muje ɗaki". Mama Jummai tayi shewa tace; "ahayye! Zamu gani dai idan tusa zata hura wuta ai duk wanda yaja dani sai naga bayan shi". Ummi ta juyo tace; "ta Allah ba taki ba, duk sharrinki akan ki zai ƙare", daga haka taja Nusram suka shige ɗaki. Mama Jummai tace; "ni yanzu ba zan ce miki komai ba amma ki sani ƴar ki zata shigo hannun mu ne nan da lokaci kaɗan zaki gane ruwa shayi ne". Nusram ta zuba tagumi tana kallon Ummi na haɗa musu kaya, Nusram tace; "Ummi dan Allah kiyi hakuri ki bari na auri Isan kawai, in dai hakan zai saka ku cigaba da zaman aure da Baba". Ummi tace; "ki bar wannan maganar Nusram, ki haɗa naki kayan domin kuwa tare zamu tafi dan wallahi ba zan taɓa bari ki auri Isa ba". Nusram ta saka kuka tace; "ni kuma Ummi ba zan iya bari auren ku ya rabu ta dalilina ba, Ummi me zan ce da Nusreen da kuma Kubra", Ummi tace; "ba wannan na tambaye ki ba, ki tashi ki.haɗa kayan ki kawai". Dole.haka Nusram ta fara haɗa kayan ta, tana yi tana kuka, Ummi kuwa ta miƙe ta fice don ɗauro alwala tazo ta tada sallah. Ganin.fitar Ummi yasa Nusram miƙewa, jakar ta ƙarama ta ɗauko, kuɗin da Aunty ta bata ranar da taje gidan ta ɗauko ragowar ta saka a ciki ta ɗauki wayar wannan da bata san ko waye ba ta saka a ciki sannan ta saka hijab ta fice. Akan ta dai ake faɗa ko to gwara ta bar gidan, dan ita ganin ta hakan shine maslaha kawai ba zata iya zama taga wannan ranar ba wacce zata kasance itace ta zama silar rabuwar iyayen nata. Sai yanzu take data sani ta amsa auren Yaya Sulaiman ɗin wata ƙila ta sami mafita akan wannan bala'in da yake tinkaro ta, ta juya ta kalli gidan Allah sarki! Ummi ko yaya zata ji idan ta gane cewa guduwa Nusram ɗin tayi?. Wane hali Ƴar uwar haihuwar nata zata ji a yayin da labari ya iske mata akan abinda Nusram ɗin tayi, yanzu ƴan layi dasu Mama Jummai zasu sami damar gorantawa Ummin, anya kuwa abinda kike so ki aikata Nusram ba kuskure bane?"abinda zuciyar ta ke faɗa mata kenan. Ta girgiza kai tace; "wannan itace kawai mafita akan abinda ke damuna, dama ace Ummi zata yarda ne na auri Isan da rabuwar auren su ai gwara auren Isan", ta ƙara sauri a ƙoƙarin ta na ganin ta bar inda aka santa. Haka ta iso bakin titi, lokacin ma yawanci mutane sun shiga sallar Isha'i, ta ƙara damƙe jakar dake hannun ta, kuɗin ciki tana tabbacin zai ishe ta ta sauka wani garin idan yaso sai ta siyar da wayar nan ta sami wajen zama da kuma jarin da zata riƙe kanta. #LIKE #SHARE #COMMENTS *babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ 📖📖47-48📖📖 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Addu'a A Kan Abokan Gaba اَللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ اْلأَحْزَابَ، اَللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَزَلْزِلَهُمْ. Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar'a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa alzihlum. Ya Allah! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan gaba. Ya Allah! Ka karya su, ka girgiza su. *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖47-48📖📖 Abdus-samad yayi miƙa tare da yin hamma, agogon hannun shi ya duba ƙarfe shida harda rabi, gaskiya ya gaji daga fara aikin shi yau. Cikin sauri ya fara tattara kayan shi domin tafiya, Tameer ya turo ƙofar ya shigo, ganin yadda yake haɗa kaya yasa yayi dariya yace; " duk ɗokin aikin kuma har ka gaji". "amma dai ka san lokacin tashi ya wuce ko, a ƙa'ida 4 ya kamata ace na bar nan", Tameer ya buɗe baki cikeda mamaki yace; "a matsayinka na Co-ordinator". Ya.lumshe ido yace; "as normal staff bari ka gani na gudu wajen First Love", be jira me zai kuma cewa ba ya fice. A harabar Companyn ya haɗu da Surayya, "yauwa wuce mini da wannan gida, ki cewa First Love zan je Rigasa", ta amsa da to. Ya shiga motar shi ya tafi, a hanya a ka fara kiraye-kirayen sallah wannan dalilin yasa ya sami masallaci yayi parking sai da ya idar da sallah sannan ya tafi. Wani ƙaramin Mall yayi parking, ya ɗauko takardar ya juya ta a hannun shi, shi dai gaskiya babu abinda ya fahimta game da takardar. Ya duba cikin Mall ɗin mutane ɗai-ɗaiku ne a ciki, wata matashiyar budurwa ya hango da sauri ya nufi inda take. "amm dan Allah taimaka mini da wannan takardar", Yarinyar ta juyo, a tare suka zaro idanu. Cikin mamaki Khausar tace; "Abdus-samad", yayi murmushi yace; "dama kecce", ta jinjina kai tana dariya. "me kazo yi, mu ga takardar", ta faɗa tana miƙo hannu, ya saka mata takardar, ta ɗan jima tana dubawa sannan ta ɗago tace; "na san dai ba ƙanwarka ta aiko ka ba haka ba Mama bace, faɗa mini gaskiya budurwar ka ce ko?". Ya shafa sumar kanshi yace; "in faɗa miki gaskiya, ƙanwata ce ta aiko ni", a tare suka yi dariya. Ta janyo kwando ta miƙo mishi tace; "to sai ka riƙe muje ko?", be musa ba, tana gaba yana bayan ta haka suka dinga zagaya wajen sai da ta tabbatar da ta ɗauki duk abinda ke list ɗin sannan suka wuce wajen biyan kuɗi. Atm ya miƙa musu suka zare kuɗin su duka, sannan suka zuba musu a leda, duka ya ɗauka suka fice. Khausar ta tsaya jikin motar ta tace; "to daga barin asibiti kuma shikenan sai naji shiru". "wallahi abin ne ya kwanta mini sosai, amma kiyi haƙuri na miki alƙwari zan zo insha Allahu", Khausar taja ajiyar zuciya kafin ta saka hannu cikin purse ɗin ta sannan ta zaro wayarta ta miƙa mishi tace; "idan na baka number na gaba cewa zaka yi ka manta amma yanzu ka saka mini taka sai ni na nemeka dan ni ba zan manta ba". Abdus-samad yayi murmushi kafin ya amshi wayar ya rubuta mata sannan ya miƙa mata tare da ledar siyayyar ta, yace; "na gode sosai, bye", ta ɗaga mishi hannu. Wajen motar shi ya nufa, ya buɗe ya shiga sannan ya tada ya tafi, Khausar tayi dariya cikin farin ciki tace; "mafarkina zai zama gaskiya🙄, cikeda murna ta shiga motarta ta bar harabar wajen. Koda ya isa Hayin rigasa, cikin Estate ɗin a cike yake da mutane, sai da ya tsaya suka gaggaisa da mutane ya san dama hakan zata kasance idan yayi la'akari da yadda family meeting ɗin su ya matso duk wani na nesa cikin wannan satin suke saka rai da zuwan shi. Da sallama ya shiga falon, yaron dake wasa ya nufo inda yake, Abdus-samad ya ɗaga shi sama ya cilla sannan yace; "my Boy yaushe kuka dawo", yaron yace; "jiya muka zo tare da Daddyna". Ya ajiye shi ƙasa sannan ya riƙe hannun shi, Brr Hauwa ke zaune saman sofa gabanta Laptop ne tana dannawa sai Fatima ita kuma takardu take haɗawa. Abdus-samad ya gaishe dasu, babu laifi duka sun amsa musamman ma Fatima dan ita basu da wata matsala a tsakanin su. Hanyar ɗakin Malama yayi, Fatima tayi saurin kiran shi, ya juyo zuwa gare ta, "Hajja na ciki ka shiga ka gaishe da ita tukunna", abinda ta faɗa kenan. Ya san me take nufi don haka babu wata gardama ya nufi nata ɗakin, a kashingiɗe take da jarida a hannun ta. Yayi murmushi, "wato yau bokon ta tashi kenan da daddare", ya faɗa cikin ranshi ta ɗago tana amsa mishi sallamar da yayi. A ƙasa kusa da ƙafarta ya zauna, ta dube shi ta ɗauke kai, "barka da dare Hajja, ina wuni", ta ɗebi sakwanni kafin ta amsa da "lafiya", daga haka be kuma cewa komai ba itama bata kuma cewa komai ba. Tsayin lokaci babu wanda yayi magana, ya miƙe yace; "Hajja sai da safe", har ya fita be ji amsar abinda ta faɗa ba, ta bi bayan shi da sannan tace; "Allah ya tashe mu lafiya". Tun kafin ya shiga ɗakin yake jiyo muryar su wanda hakan yake tabbatar mishi da cewa fira suke kenan. Da sallama ya shiga ɗakin, ya zauna saman kujera yana dafe kanshi, Fadila ta ƙaraso inda yake ta janye hannun nashi tace; "duk gajuyar ce". Ya balla mata harara sannan ya miƙe, kusa da Malama ya koma, "ina wuni?", sai da ta shafa fuskar shi sannan ta amsa da "lafiya lau, ina Maman ka?", yayi murmushi yace; "tana lafiya". Ledar daya ajiye Fadila ta ɗauka tana murmushi tace; "ah lallai matar ka ta huta", bece mata komai ba sai ma miƙewa da yayi. Fadil yace; "ba dai har zaka tafi ba", ya lumshe idanu yace; "Fadil na gaji da yawa, dole ce ma ta biyo dani nan ɗin amma da gida zan wuce wallahi", Fadil ya miƙe domin raka shi nan ya yiwa Malama sallama sannan ya fice. Yadda ya bar su haka ya dawo ya same su, sai dai wannan karon Brr Hauwa, waya take amsawa, sai da safe yayi musu sannan ya fice. "to bari na bar ka a nan sai da safe", faɗar Fadil kenan bayan sun ƙaraso inda ya ajiye motar shi, ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha sannan ya buɗe ya shiga. Ya kunna motar kenan, Saleema ta ƙaraso da murmushi a fuskarta ta ƙwanƙwasa glass ɗin, sai da yayi jim sannan ya zuge glass ɗin. "wannan wane kalar zagaye ne, ya zaka shigo ka tafi dan danan?", ya lumshe idanu yace; "Aunty Saleema na gaji ne sosai". Ta langwaɓar da kai tace; "amma ai ka ƙaraso ko ganin ka nayi kafin ka wuce ko?", ya shafa gashin kanshi yace; "wallahi sauri nake yi". "dan Allah mu ƙarasa mana, jin zuwan ka har na shiga kitchen na dafa maka abinci yanzu kuma kace sauri kake yi", ya ɗaga kafaɗa sannan ya buɗe mata ƙofa. Tayi murmushi sannan tace; "yauwa ko kaifa", ta shiga sannan ya tada motar suka ɗauki hanyar Part ɗin su. Tare suka jera har cikin gidan, duka suna zaune a falo, yana shiga suka yo kanshi, ya dafe goshi wannan dalilin yasa baya son zuwa gidan gabaki ɗaya. Saleema ta jera mishi abincin a gaban shi, Haɗaɗɗen spouch chicken da kuma milk shake, be wani ci da yawa ba domin gajiyar dake tattare dashi a yanzu kawai kwanciya yake buƙata. Sallama yayi musu sannan ya fito inda Saleema ta biyo shi don ta rakashi, "yausha Abba zai dawo", ta ɗan yi jimm sannan tace; "ba zai wuce sati me zuwa ba Abban Nihal kuwa yana hanya", ya ɗan ja numfashi sannan yace; "Allah ya kawo su lafiya", ta amsa da ameen, da haka suka yi sallama inda ya shiga motar shi itama kuma ta juya cikin gida. Shi ya san ba lallai a ƙare lafiya ba, a duk shekara babu ranar da yake tsoron zuwan ta irin wannan ranar ba ta yin meeting ɗin su, ya shafa kan shi yana faɗin; "ya Allah!". Kamar ance ya kalli gefe ya hangota tsaye a bakin titi, kallon ta yayi sosai ya lura kamar bata cikin hayyacin ta, har ya gifta sai kuma ya dawo a hankali ya yi parking. Glass ɗin ya sauke sannan ya leƙo da kanshi, Nusram dake zare idanu, tana ƙare damƙe jakar dake hannun ta, ganin wanda ya leƙo yasa ta ɗan ja baya kaɗan. Yayi murmushi yace; "ina zaki je?", Nusram ta haɗiye wani mugun yawu sannan ta fara tafiya cikin sauri, ai gwara ta koma gida ko kuma ta hau titin mota ta bige ta da wannan mugun mutumin. Abdus-samad kuwa ganin hakan yasa yayi saurin buɗe motar ya fito, ganin tana ƙoƙarin kwasawa da gudu yasa ya cafkota. Ta wage baki zata yi ihu yayi saurin saka hannu ya toshe bakin, "kin manta abinda na faɗa miki kenan ko?", da sauri ta girgiza kai. Kasancewar kowa hada-hadar shi yake yi ya saka babu wanda ya lura da halin da suke ciki, hannun ta ya riƙe ya jata har zuwa mota ya buɗe ya saka ta sannan shima ya shiga ya ja suka bar wajen. Nusram babu abinda take yi banda zare idanu, tunanin ta ɗaya shine ta gama rayuwa ita kam tata ta ƙare. "ina zaki je?", kamar daga sama taji tambayar, bakin ta na rawa tace; "ina so na bar garin nan ne", ya ɗan juyo ya kalle ta kana ya sami waje ya tsaya. Sosai yanzu yake kallon ta yayin da ita kuma take faman wasa da yatsun hannun ta, sai da ya nazarce ta sosai kana yace; "kada dai kice mini gida kika bari". Ta ɗaga kai tana cigaba da abinda take yi, ya girgiza kai yace; "kada ki sake ki fara wannan kuskuren, kin san me zaki tarar a inda zaki je ko kuwa kina tunanin matsalar da kike ciki wacce zaki tarar ba zata kaita ba, kina da tabbacin wani abu ba zai same ki ba, kina da iyaye wane hali zasu kasance? Kina da ƴan uwa bakya tunanin su, kin san kalar rayuwar da zaki shiga, kin san meye matsayin mace me zaman kanta?". Ta girgiza kai, ya ɗan ja numfashi yace; " *KARUWA*!, kin shirya amsa wannan sunan", Nusram idanun ta ya kawo ƙwalla. Hannu ya saka ya zaro tissue ya miƙa mata, ta amsa ta goge hawayen dake fuskarta tace; "to ai na rasa wanda zai aure ni ne", ya ɗan yi jim sannan yace; "kamar ya kenan?". "Baba ne yace na fito da mijin aure kafin sati biyu, gashi sati biyun ya cika ni kuma bana da tsayayyen saurayi wanda zai aure ni". Ya jima sosai kafin yace; "yanzu bari na maida ke gida gobe zan zo na sami mahaifin naki", ta ɗago da sauri ta kalle shi tace; "zaka aure ni ne?". Shiru yayi be tanka ba, Nusram ta kuma cewa; "idan har ka san ba aure na zaka yi ba kawai ka barni na tafi", kamar an fizgo maganar yace; "naji na amince zan aure ki". Daga haka babu wanda ya kuma magana, ya tada motar ya juya zuwa maida ita gida har suka isa ƙofar gidan babu wanda ya kuma magana. Bayan yayi parking be ce komai ba, ganin hakan yasa Nusram buɗe ƙofar, har ta saka ƙafarta waje sai kuma ta dawo. "ka tabbata zaka zo goben", babu wani dogon tunani ya ɗaga mata kai, tayi murmushi tace; "ni ban damu da sai munyi zaman aure ba, koda dai sati ɗaya ne, sai ka ƙyale ni na tafi", ya gyaɗa kai, tayi murmushi ta juya ta fice. Abdus-samad ya bi bayanta da kallo yana tunani haka gaban shi yana faɗuwa, "wane matsala kake ƙoƙarin jefa kanka a ciki ne?", ya faɗa yana dafe saitin zuciyar shi dake bugawa da ƙarfi. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖49-50📖📖 cikin natsuwa yaja motar shi ya bar ƙofar gidan, duk yadda yaso yayi tunani abin yaci tura dole ya watsar da komai ya maida hankalin shi kan tuƙin da yake yi. Ƙarar shigowar saƙo wayar shi yasa ya kalli wayar, be duba ba dan be kawo wani me mahimmanci bane. Ta ƙofar baya ya shiga gidan nasu domin baya so ya haɗu da kowa babu abinda yafi buƙata a lokacin irin ya kwanta ya huta. Yana shiga ɗakin shi bayi kawai ya wuce kanshi ya sakarwa shaya, ruwan na sauka a jikin shi ya lumshe idanu, gaba ɗaya abubuwan daya faru ya fara dawo mishi. Cikin sauri ya buɗe idanun shi yana dafe kanshi yace; "me ka janyowa kanka Abdus-samad?", tambayar da babu amsa kenan. "koda yake ai idan ka yiwa mahaifinta bayani zai fahimce ka domin kuwa babu wanda zai so ƴar shi ta faɗa wannan halim", abinda zuciyar shi ta faɗa mishi kenan. Koda ya fito ya tsane jikinshi sannan ya ciro kayan barci ya saka, jikinshi ya feshe da turare kana ya janyo wayar shi. *love is hard and will always be, but remember somebody loves u and that one is me* Abdus-samad ya taɓe baki, number ne babu suna dan haka be damu da sanin waye ba domin kuwa irin wa'innan saƙonnin har gajiya yake da buɗe su. Be jima sosai ba barci ya kwashe shi, Brr Farida kuwa jin shirun yayi yawa yasa ta nufo part ɗin shi, kamar yadda ta zata ya dawo ɗin, zuwan ta na uku kenan sannan ta tarar dashi. Ɗakin da duhu sai dai ƴar fitilar gefen gado dake kunne, tayi murmushi sannan ta taka zuwa kusa da gadon. Ta jima tana yin addu'a kafin ta tofa a hannun ta kana ta shafa mishi a jiki, yayi juyi cike da gajiya, Brr Farida tayi murmushi kawai. Ta san dama hakan zai faru shiyasa koda ya dage akan zai fara aiki ta hana, ranar farko kenan duk yabi ya gaji. Cikin natsuwa ta fara mishi tausa, aikuwa malam Inusa🤣 harda ajiyar zuciya, ta jima sosai kafin taja mishi blanket ɗin, peck tayi mishi a goshi kafin ta fice daga ɗakin. Nusram kuwa koda ta shiga gida bata sami kowa a tsakar gidan ba, cikin sauri ta tura ƙofar ɗakin nasu wanda tana da tabbacin Ummi ta turo ƙofar ta shige. Ummi dake saman abin sallah ta juyo tana kallon Nusram ɗin, Nusram ta saukar da kai ƙasa tana wasa da hannun ta. Ummi tace; "daga ina?", Nusram tace; "Ummi dan Allah kiyi haƙuri", Ummi ta girgizai kai kawai, cikin sauri Nusram ta shige cikin ɗaki. hijab ɗin jikin ta, ta cire sannan ta faɗa saman katifar su, lallai rayuwa kenan, wayar dake cikin jakar ta ciro kamar koda yaushe hoton shi dai shine take kallo. "ashe dai a cikin masu shan jini akwai nagari? To kodai kema siyar dake zai yi ko kuma ya bawa gunki jinin ki?", abinda zuciyar ta take raya mata kenan. Zumbur ta miƙe zaune, "koda yake ma ai gwara ya bawa aljanin jini na ko na huta da wannan rayuwar", wata zuciyar ta sake faɗa mata haka. Addu'a tayi kafin ta kwanta, bata jima ba barci ya kwashe ta, tana me fatan gobe ta sami mafita. Washe gari da safe bayan sun idar da sallar asuba, Baba yazo ƙofar ɗakin nasu ya ƙwalawa Ummi kira. "Maimuna fito", Ummi ta miƙe ta fice, ya kalle ta ya kauda kai yace; "fatan dai kin haɗa kayan ki na tafiya ko?", Ummi cikin dakiya tace; "eh ko korata kake ne na tafi yanzu", ya ɗaga kafaɗa yace; "kusan hakan ai". Ummi ta girgiza kai sannan ta juya zuwa ɗaki, Nusram dake tsaye tana jiran Ummin domin taji duk abinda ya gudana, Ummi ta kalle ta tace; "ɗauko jakunkunan mu tafi". Nusram hawaye ya kawo mata, ta girgiza kai, da sauri Ummi ta girgiza mata kai tace; "kada ki soma Nusram ya kamata ace zuwa yanzu kin sami.ƙarfin zuciya, ɗauko kinji", Ummi ta ƙarasa tana ɗaukar Kubra kasancewar bata tafiya har lokacin. Ummi na gaba Nusram tana bayan ta suka fito, zuwa wannan lokacin Mama Jummai da Amira harda Isa duk suna tsaye a waje. Baba yace; "wai keda waye zaki tafi?", Ummi tace; "bangane ba, nida yarana mana", duka wajen suka kwashe da dariya, banda Nusram dake sharar hawaye. Baba ya harare ta yace; "to ai dana auro ki ba tare dasu aka kawo ki ba", Ummi ta haɗe rai tace; "kamar yadda banzo na tarar dasu a nan gidan ba", daga haka ta nufo hanyar fita. Baba ya saka hannu ya finciko Nusram yace; "wannan dai me kama da aljanun zaki iya tafiya da ita amma wannan kam babu inda zata je, ba zata gama ɓata yaran birni ba ta koma ƙauye ta ɓata na can, idan naje ana mini kallo arziƙi ta zubar mini da mutuncina ba". Dan haushi Ummi bata ko juyo ba, jakar dake hannun Nusram ta fincike ta fice kawai, Nusram ta fashe da kuka tana kiran Ummin, amma bata juyo ba. Baba ya rufe Nusram ɗin da duka yana faɗin; "shegiya ƴar iska, yanzu ke har kina da bakin ihu, ne baƙin jini kawai, ko karya takan sami karen da zai bita amma banda ke". Nusram kuwa banda sunan Ummi babu abinda take ambata, babu wanda ya bawa Baba haƙuri har sai da ya gaji dan kanshi ya ƙyale ta. bayan tafiyar shi Mama Jummai ta kwashe da dariya tace; "ai duk wanda yaja dani dole ya yi nadama, wato tunanin ki zaki je Dabai ki huta ko, to babu inda zaki je kina nan tare dani, aure kuma sai dai kiga anayi". Isa ya ɓata rai yace; "kin manta Jummai nine fa zan aure ta", Mama Jummai tace; "ai auren ku da rashin shi duk ɗaya ne domin na rantse ba zata taɓa jin daɗin auren ta ba". Suka kuma fashewa da dariya, Nusram kuwa hawaye kawai take yi har lokacin, ga ƙafarta dake zafi. har wajen sha biyu tana tsugune a wajen, babu wanda ya tanka mata, sallamar Nusreen itace ta dawo da ita hayyacin ta. Cikin sauri ta miƙe, Nusreen kuwa ganin halin da ƴar uwarta take yasa ta taho da sauri, Nusram ta ƙarasa kusa da ita suka rungume juna. "Rim Ummi ta tafi ta barmu", jikin Nusreen a sanyaye ta janye Nusram ɗin daga jikinta tace; "me kike cewa ne?". Nusram taja hannun Nusreen ɗin suka nufi ɗakin nasu, kan kujera ta zaunar da ita sannan ta bata labarin abinda ya faru. Nusreen ta fashe da kuka, Nusram ma tana sharar hawaye tana rarrashin ƴar uwar tata. "Ram haƙiƙa kina ganin rayuwa, kowa yana da tashi ƙaddarar ke kuma taki kenan, Nusram waye zai tunanin mahaifin daya haife mu shike bin mu da mugun baki", ta ƙarasa tana kuma fashewa da kuka. Nusram tace; "kiyi haƙuri Rim kowa da yadda rayuwa take zuwar mishi, Nusreen Ummi bata a cikin gidan nan ya zanyi da rayuwa ta". Nusreen ta share hawayen fuskarta kafin tace; "zan yiwa Hubby magana sai mu tafi tare dake idan yaso sai ki zauna a wajen Hajiya, kin san dama tana sonki sosai". Nusram ta girgiza kai tace; "ba za'ayi haka ba, nifa jiya na sami wanda zai aure ni", cikin sauri Nusreen tace; "waye kenan?". Nusram ta janyo wayar dake jakar ta sannan ta miƙawa Nusreen tace; "kalli kiga hoton shi", Nusreen ta zuba mishi idanu kafin tayi murmushi tace; "wannan ai Abdus-samad Abubakar Nagimi, ɗan attajirin me kuɗi ne ina kuka haɗu dashi". nan Nusram ta kwashe duka labarin komai ta bawa Nusreen ɗin, Nusreen baɓu abinda take banda murmushi. "baban shi shine ogan Hubby kafin ya rasu, mutumin kirki ne Nusram ba wai ɗan yankan kai bane, har bikin mu yazo fa", ta ƙarasa tana kwashewa da dariya tunawa da tayi da yadda Nusram ɗin ta dinga shirme, Nusram tayi murmushi kawai. Sai lokacin ta lura da yadda Nusreen ɗin tayi ƴar ƙiba ga haske data ƙara, Nusram ta girgiza kai tace; "kinga yadda kika koma kuwa?", Nusreen tayi dariya. Suna zaune wayar Nusreen ɗin tayi ƙara, ganin Aunty ke kira yasa ta ɗaga, nan ta bata labarin abinda ya faru. "kada ki damu Maman ku ta kira ni ta faɗa mini komai gobe zan zo na tafi da Nusram ɗin", Abinda Aunty ta faɗa kenan. Nusreen tace; "Allah ya kaimu shikenan Aunty sai anjima", daga haka suka katse wayar, nan ta bawa Nusram labarin abinda Aunty ta faɗa. Nusram kuwa tagumi kawai tayi, tunani kala-kala shine cikin ranta, shin zai zo, ko kuwa zata cigaba da zama da Mama Jummai ne ko kuwa Aunty zata sami nasarar rabata da gidan?, wa'innan sune abinda ke kai kawo cikin ranta. Abdus-samad dake zaune cikin office ɗin shi, ya dafe kai, ba zai ce ga dalilin daya saka lokaci zuwa lokaci abin yake faɗo mishi a rai ba. Iska ya furzar daga bakin shi, be san yadda abubuwa zasu tafiyar mishi ba, amma dai tabbas yana ji a jikin shi wani abu zai faru dashi jin yadda gaban shi ke faɗuwa akai-akai. Biyar ya bar company ɗin ya ɗauki hanyar hayin rigasa, be shiga cikin gidan ba, ɗakin Fadil kawai ya wuce. Wanka yayi ya canza kaya kafin ya shiga ciki, babu kowa a falo hakan yasa ya wuce ɗakin Malama kawai. Tana zaune da alƙur'ani a gabanta, ya saki murmushi matar tana birge shi saboda yawan bautar da take dashi. Malama ta miƙo mishi hannu alamun ya taho, Abdul kuwa kamar dama abinda yake jira kenan dan haka cikin sauri ya nufi inda take. Kan ƙafar ta ta kwantar da kanshi sannan ta saka hannu tana shafa gashin kanshi, dama ga damuwa tayi mishi yawa ga gajiya kuma dan haka babu jimawa barci ya ɗauke shi. Malama ta tsurawa fuskar shi idanu, hawaye ya taru a idanun ta, ta fara karanto addu'a tana tofa mishi. Cikin barci yaji ana jijjiga shi, ya buɗe idanu ganin Fadil yasa yaja tsaki, Fadil yayi dariya yace; "ka tashi malam shida tayi fa", jin abinda Fadil ya faɗa yasa yayi saurin miƙewa zaune. "please taso muje ka rakani", abinda Abdus-samad ɗin ya faɗa kenan yana miƙewa, Fadil yace; "ina zaka je?", Abdul yace; "kai dai muje kawai". A motar Fadil ɗin suka fice, suna tafe duk yadda Fadil ke tambayar shi inda zasu je be bashi amsa ba har suka ƙaraso ƙofar gidan. Fadil ya kalli ƙofar gidan sannan ya juyo ya kalle shi yace; "har yanzu baka bani amsata ba", Abdul ya buɗe motar kawai ya fito. Baba da Isa dake zaune saman dakalin ƙofar gidan suka bi su da idanu, Abdus-samad suka yi musu sallama suka amsa. "amm dan Allah me gidan nan nake nema", Baba yace; "gani nan yaro ya akayi", Abdus-samad yace; "dama nazo ne muyi magana dan Allah idan babu damuwa". Baba ya tashi ya bi shi suka dan matsa gaba, Baba ya kalle shi yace; "kai nake sauraro", Abdus-samad yace; "dama nazo akan maganar ƴar ka Nusram ne abinda ya far.......". Yayi saurin dakatar dashi yace; "ba dai akan maganar Nusram kazo ba?", Abdus-samad ya jinjina kai, Baba ya kamo hannun shi yace; "muje". Abdus-samad cike da mamaki yake bin shi, Baba ya kalli Isa yace; "tashi mu ƙarasa masallaci", Isa ya miƙe, haka Fadil ma ya biyo bayan su. Masallacin dake kusa dasu suka ƙarasa, kasancewar lokacin sallah ya matso hakan yasa mutane keta alwala, dan haka Baba ma ya ɗauki buta. Ya kalli Abdus-samad da Fadil dake tsaye yace; "bismillah mana kuyi alwala", cikin sauri duka suka ɗauki buta domin alwala, shi dai Abdul gaba ɗaya jikin shi a sanyaye yake. Be gama girgiza ba sai da aka idar da sallah yaji Baba yana sanar da akwai ɗaurin aure dan Allah, ya matsa kusa da Liman suka ɗan tattauna sannan ya kalli Abdus-samad yace; "matso mana ɗan nan". Abdul ya matso kusa da Baban, Liman yace; "menene sunan ka?", Abdul yace; "Abdus-samad Abubakar", gana nan yaga Baba ya ciro kuɗi daga aljihun shi ga miƙawa liman yace; "sadakin ma ni na biya dan Allah ɗaura kawai". Kafin Abdul yayi dogon tunani yaji kawai Liman yana sanar da ɗaurin aure, ya kalli Baba ya kalli Liman ɗin da kuma maƙwabcin Baban wanda shine yake wakili ga ango, shi dai su suke kiɗan su suke rawar su. *AN ƊAURA AUREN ABDUS-SAMAD ABUBAKAR TARE DA NUSRAM ABDULLAHI DABAI, AKAN SADAKI NERA DUBU GOMA SHA BIYAR LAKADAN BA AJALAN BA!!!* dogon bayanin dake yawo cikin ƙwaƙwalwar Abdus-samad kenan. Cikin firgici da kuma razana ya ɗago yana kallon Baban yana girgiza kai, maida kallon shi yayi kan Fadil ɗin wanda yake zaune kamar gunki dan idan banda numfashi dake sauka babu yadda zaka fahimci akwai rai a jikin shi. *To masu karatu, zan dakata anan saboda isowar Azumi idan Allah ya kaimu gobe da rai da lafiya dan haka ina taya kanmu murnar zuwan wannan wata me albarka Allah ya magance mana wannan babbar annoba da take damun mu wato Covid19, Allah yasa muga ƙarshen watan lafiya, idan Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya zamu ɗora daga inda muka tsaya*. *godiya ta musamman gare ku, mabiya wannan littafin, irin su, Abdul Ƙiru, Ibnatu Baballe Barau, Maman Abdul, Aishatu Babayo, Faɗimatu, Khadija Zakariyya da duk sauran wa'inda ban.amabata ba na gode sosai Allah ya haɗa mu da rai da lafiya*. *HAPPY RAMADAN IN ADVANCE* #LIKE #SHARE #COMMENTS *babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖51-52📖📖 Abdus-samad be dena zare idanu ba har aka watse daga masallacin, Liman ya ɗan taɓo shi sannan yayi firgigit ya miƙe tsaye. "ku taimake ni kada ku ɗaura auren nan nifa ba soyayya muke da ita ba", abinda yake faɗa kenan. Baba cikin fusata yace; "bangane abinda kake nufi ba ina dama kai kace maganar ta kazo mini, ni kuwa na san idan banda maganar auren ta babu abinda zai kawo saurayi waje na, ko kana cikin kwartayen ta ne?", Abdus-samad ya girgiza. "amma baka fahimce ni ba, nifa maganar da nazo muyi daban taya zaku ɗaura mana aure babu sanin iyaye na?", Abdus-samad ya faɗa cikin damuwa. Abba ya ɗaga kafaɗa yace; "wannan kuma matsalar kuce ni dai yanzu zata bar gidana idan yaso tunda baka sonta kaje ka kashe ta", wani abu Abdus-samad ya haɗiye jin abinda Mahaifin nata ya faɗa. Liman yace; "ya isa haka, ku zauna ayi maganar data dace", duka suka sami waje suka zauna kamar yadda yace. "kai menene ainihin abinda ya kawo ka wajen Malam Abdullahi?k, tambayar da liman ya jefowa Abdus-samad ɗin kenan. Labarin komai ya kwashe ya faɗa mishi na yadda ya ganta zata gudu da yadda yayi mata magana akan gobe zai zo ya ɗora da cewa; "gani na mahaifin ta ne shi ba zai so ƴar shi ta bar gidan shi ba dole zai janye maganar aurar da ita kota yaya ne". Liman ya jinjina kai yace; "tabbas yaro kana da gaskiya, Malam Abdullahi wato duk wani abu dake faruwa akan yaranka babu wanda bamu sani ba, shiru kawai muke yi saboda gudun katsalandan domin kuwa iyayen yanzu basu so ana musu irin wannan shisshigin Malam Abdullahi matsi da takura akan yaran yanzu daman irin abinda yake haifarwa kenan, yanzu baka gudun ace lokacin data tafi taje ta faɗawa abinda be kamata, gaskiya wannan abin sam be dace ba ka gyara ƴaƴa amanace Allah ya bamu kuma idan bamu riƙe su da kyau ba zamu fuskanci fushin shi dan haka ya kamata mu gyara tarbiyar yaran mu". Sannan kai, ya faɗa yana juyowa ya kalli Abdus-samad; "sai dai kayi haƙuri aure dai ya riga da ya ɗauru amma tunda iyayen ka na nan zamu je sai ayi musu bayani". Cikin sauri Abdus-samad yace; "a'a nima zan iya yi musu bayani da kaina, amma dan Allah ku raba auren nan". Baba yace; "aifa sai dai duk abinda zai faru ya faru amma wallahi yau ta bar gidan nan, bari ma ku gani", ya miƙe tsaye sannan ya fice daga masallacin. Duka suka bi shi da idanu kafin Liman ɗin ya kalli Abdus-samad yace; "haƙuri ya kamata kayi Abdus-samad kaga yarinyar nan tana ganin rayuwa a cikin gidan mahaifin ta, dan a dalilin rashin auren nata yau sai da mahaifiyar ta, ta bar gidan......" nan Liman ya bashi kaɗan daga cikin abinda ya sani wanda yarinyar take fuskanta. Ya nuna kanshi yace; "ni nan da kaina ta kawo mini cigiyar miji kwana uku da suka wuce tana kuka tana roƙona to abinda yasa ma dan bana da ɗa namiji ne kuma matana huɗu amma da na tsame ta daga damuwar da take ciki, sai dai hakan be samu ba domin kuwa babu wanda ya amince saboda waccen abinda ya faru ranar auren ta, kayi haƙuri ka amshi auren nan domin kuwa wataƙila kai ne Allah ya turo domin ka taimake ta ka fitar da ita daga cikin ƙangin da take ciki shekara da shekaru, yarinya ce me haƙuri da sanyi zaka ji dadin zama da ita, dan Allah kada ka juya mata baya, laifi dai mun riga da munyi domin ya kamata ace mun tambaye ka kafin mu ɗaura auren sai dai ance kaddara ta riga fata, dan haka kayi haƙuri ka amshi auren nan hannu bibbiyu ina fata da kuma buri akan ba zaka yi dana sani ba. Shi kanshi Abdus-samad zuwa yanzu jikin shi yayi sanyi a hankali ya kai kallon shi kan Fadil, Fadil ya jinjina mishi kai, Abdus-samad ya maida kallon shi kan Liman yace; "shikenan Baba Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, zan yiwa iyaye na magana na san zasu fahimta". Liman ya washe baki yace; "yauwa ɗana idan suka ƙi yarda ma kazo ka ɗauke ni ka kaini ni nan da kaina zan musu bayanin komai", Abdus-samad yace; "insha Allahu". "Allah yayi muku albarka dai yanzu tashi muje ya fito muku da matar taka sai ku tafi ko?", duka suka miƙe suka bishi. Yana gaba suna baya har ƙofar gidan Malam Abdullahi, Abdus-samad dai gaban shi banda faɗuwa babu abinda yake yi, sai saƙe-saƙe yake yi. Cikin gidan kuwa Nusram da Nusreen ke fira duk da ba wata me yawa bace yawanci labarin abinda ya shafi rayuwar su suke yi, sai kuma jimamin abinda ya faru. Ganin duhu ya fara yi yasa Nusram ta kalli Nusreen tace; "wai ba zaki tafi gida bane?", Nusreen tayi murmushi tace; "ai jira nake Hubby yazo sai mu tafi". Nusram ta buɗe baki zata yi magana taji sallamar Baba, jin yana ƙwala mata kira yasa gabanta faɗuwa. Ta kalli Nusreen tace; "Allah yasa lafiya", kafin Nusreen tace wani abu ya ɗago labulen ɗakin ya shigo". "kaga mini ƴar banza ashe kinajina kika yi shiru, to maza tashi ki shirya mijin ki na waje yana jiran ki". Mama Jummai dake bayan shi jin abinda ya faɗa yasa tayi shewa tare da yin guɗa, "Lallai ma, amma dai Abdullahi wasa kake yi ko?". "wasa! An taɓa wasa da aure ne?, kinga kada ki ɓatawa mutane rai ki shirya maza ki fito", daga haka ya juya ya fita. Mama Jummai ta ja tsaki tace; "wallahi da sake matuƙar angon be gamshe ni ba dole a canza wannan abin", ta fice fuuuu. Su dai cikin.su babu wanda yayi magana, Nusram ta fashe da kuka, Nusreen tayi saurin riƙota tace; "dan Allah kiyi haƙuri ki dena zubar da hawayen ki haka, ina ji a jikina wannan auren naki alkhairi ne". Nusram ta girgiza kai hawaye yana zubo mata tace; "Nusreen komai na rayuwata ya canza, babu farinciki babu karatun da nake matuƙar ƙauna babu mahaifiya wacce take kula dani". Nusreen ta dafata tace; "ki kwantar da hankalin ki ƴar uwata, kowa da yadda rayuwa take zuwar mishi, sannan idan kuma yayi haƙuri sai ki gani wata rana kamar ba'a yi ba". Nusram dai tayi shiru kawai, Nusreen ta riƙo hannun ta tace; "tashi ki shirya, ki dinga addu'a Allah yasa ƙarshen wahalar ki kenan", ba dan taso ba ta miƙe. Ruwan da Nusram ɗin ta ɗora bayan ta gama yi musu abinci shi ta juyewa mata, sannan ta koma ta faɗa mata. Babu yadda ta iya haka ta nufi hanyar bayi, ita kuma Nusreen ta fara shirya mata kayanta, ita harga Allah tana jin matsalar ƴar uwarta yazo ƙarshe kenan insha Allahu. Tana gamawa Shureim ya kirata a waya kan gashinan zuwa ɗaukar ta, ta amsa da to, koda Nusram ta fito a wajen ta sami Mama Jummai da Isa harda Ameera duk sunyi cirko-cirko. "ni wallahi Jummai banso wannan auren ba, hakan nan sai naga samu naga rashi", faɗar Isa kenan. Mama Jummai tace; "kada ka damu nan babu jimawa zaka ƙara gani ta dawo gidan nan wannan karan bama ita kaɗai ba har waccen da take firirita kamar kazar mayu". Ameera taja tsaki tace; "ni duk haushi ya ishe ni wallahi, amma komai zai zo ƙarshe ne", Mama Jummai tace; "insha Allahu". Ba tare da Nusram ta kula su ba ta ajiye bokitin ta shige ɗaki inda ta tarar da Nusreen na zaman jiranta. Doguwar riga ta shadda ta saka kalar ruwan bula me haske, sai farin hijab, duk yadda Nusreen tayi da ita akan ta tsaya tayi kwalliya ƙi tayi dan haka dole ta ƙyale ta, hoda da man baki kawai ta goga kaɗan. Ƴan kunne da sarƙa ta maƙala kafin ta juyo ta kalli Nusreen tace; "Rim gabana sai faɗuwa yake yi", Nusreen ta riƙo hannunta tace; "ni kuwa zan so ace kin daure kodan maƙiya da suke so suga ya zaki yi". Ta miƙa mata ƴar ƙaramar jaka kalar kayan jikinta, ta ɗauko turare ta feshe ta dashi sannan tayi murmushi tace; "muje Amarya", kamar me tsoron tafiyar haka ta fara takawa. Sai da suka fito falo kafin Nusreen ta ajiye mata takalmi me tudu ta saka, Nusreen ta ɗaukar mata duk wani abu da ta san zata buƙata ta saka cikin ƙatuwar Trolley bag ta ɗauka. Suna fitowa tsakar gida Nusreen ta rangaɗa buɗa, Mama Jummai taja dogon tsaki, Nusreen kuwa ƙara sakin wata buɗar tayi ta ciri turare tana kuma fesa mata. Har zasu fice Baba yace; "to sarakan zumuɗi an kwana biyu ba'a sami namijin da za'a ɓata ba shine yanzu har sauri kuke yi ko to ai sai ki dawo". Nusreen ta juya tana zumɓurar baki, Nusram kuwa wajen Baban ta nufa, yace; "wajen Mamanki zaki je gata can a tsaye". Nusreen data kusa ficewa daga gidan ta juyo tace; "a'a Baba ba sai taje wajen ta ba, ai na riga nayi mata faɗan da Uwa ke yiwa ƴarta". Baɓa ya ɗauki takalmin dake kusa dashi ya jefa mata, da sauri tayi waje tana janye da jakar Nusram ɗin. Koda ta fita sai da gaban Abdus-samad ya faɗi, Shureim yayi saurin taro ta ya amshi jakar. ta juyo sannan tace; "ina angon yazo ya buɗe mana booth", Fadil dake tsaye yayi saurin zuwa ya buɗe mata Booth ɗin ta saka. "yanzu ina zaki je?", Shureim ya faɗa ganin zata koma gida, ta kalle shi tace; "Hubby zan shiga ne ciki zan fito babu jimawa", daga haka ta shige. "to kina dai gani da ƙyar kika samu wanda ya aure ki, shima ana bashi yana ƙin amsa da ƙyar aka shawo kanshi dan haka kada naji kada na gani, idan kika sake kika kashe wannan auren sai dai ki nemi wani uban ba dai ni ba", abinda Baba ya faɗa kenan kafin ya miƙe. Nusram kuwa hawaye kawai take yi, wai shima ana bashi yana ƙin amsa, ita kuma haka take da baƙin jini🙆. "tashi mana muje suna jiran ki", jin hakan yasa ta miƙe, suna zuwa zasu fita Nusreen na shigowa, ta riƙo hannun ƴar uwar tata kafin suka fice, Mama Jummai da Ameera da Isa suna bin su a baya. Fadil na cikin mota a zaune, Shureim kuma yana jingine da motar yayinda nesa kaɗan Abdus-samad ke tsaye tare da Liman suna magana. Suna fitowa waje, Nusreen ta rangaɗa buɗa Mama Jummai ta wulla mata harara, ta turo baki tace; "tunda ke ba zaki yi mana kara ba ai sai.muyi da kanmu", ta sake rangaɗa wata guɗar, hakan shine ya janyo hankalin Maƙwabtan nasu. Fadil kam ji yake kamar wasa wai Abdul da mata, gashi har yanzu basu samu damar yin magana ba balle yaji taya akayi hakan ta kasance. shi ya buɗe motar Nusreen ta riƙe hannun ƴar uwarta, sai lokacin Nusram ta samu hawaye suka zubo mata, rungume ƴar uwarta tayi suka fashe da kuka. Baba dake tsaye bayan su ya ja tsaki yace; "wannan kuma wane sabon iskanci ne, dallah saketa su tafi kuna ta faman ɓata musu lokaci". Nusreen ta saki Nusram tayi murmushi tace; "kada ki damu ƴar uwata ina ji a jikina ƙarshen wahalarki kenan?", Nusram ta jinjina kai. Abdus-samad ya dafe kai, wannan wane irin ƙaddara ce, ya kuma kallon su ya ɗan taɓe baki sai faman ƙanƙame juna suke yi. Baba yazo ya fincike hannun Nusram sannan ya sakata a mota, Nusreen ta zumɓuro baki, Baba ya harare ta yace; "kema wuce ki tafi gidan mijin ki". Daga haka Baba ya kaɗa kai yayi gida, Liman ne ma ya ɗan ƙara yiwa Abdus-samad ɗin nasiha kafin su tafi. Nan suka yi sallama da Shureim inda shima ya ɗauki matar shi suka wuce gida, sun fara tafiya Fadil yace; "Abdul me kenan?". Bece komai ba, shima ganin hakan yasa yaja bakin shi yayi shiru, har suka shiga Estate ɗin babu wanda yace komai. "dakata anan", cikin sauri Fadil ɗin yayi parking, Abdus-samad yayi ajiyar zuciya yace; "fito sai muyi magana", Fadil ya amsa da to yana fita. Kan wasu kujeru suka ƙarasa suka zauna, wajen dama daga gani irin na hutawa ne, Abdus-samad ya dafe da kanshi. Fadil yace; "ka kira ni kuma ba kace komai ba", Abdus samad yaja ajiyar zuciya sannan yace; "Fadil banda abinda zance maka ne yanzu, shawarar ka nake nema kaina gaba ɗaya ya kulle, kaga tun ɗazu First Love ke kirana amma na kasa ɗagawa saboda tension ɗin dana shiga", ya ƙarasa yana ɗago mishi wayar shi. Fadil ya tsaya yana kallon shi, Abdus-samad ya cigaba da cewa; "ka dai ga duk abinda ya faru yanzu wace shawara zaka bani?". Fadil yace; "to ni dai ban san me zance maka ba a halin yanzu, dan na san ko giyar wake ka sha ba zaka doshi su Abba kace wai an ɗaura maka aure ba, haka ma Mahaifiyar ka, wannan kam ba me yiwuwa bane idan kayi la'akari da tsarin gidan nan". Abdus-samad yayi shiru yana nazari tabbas abinda ɗan uwan shi ya faɗa gaskiya ne, yanzu me zai yi kenan, ya dafe kanshi. Shi ji yake ina ma ace Baba wuƙa ya samu ya caka mishi ko kuma marin shi ya dinga yi, wannan wane irin abu ne?🙄. Haka dama ake auren ko kuwa nashi ne yazo a haka, yanzu waye zai tunkara da wannan auren?, Abban Nihal ko Abban Fadil?, taɓ babu ko ɗaya, First Love ya san abinda ba zai yiwu ba kenan, me zai ce mata yaja bawa Uba haƙauri akan kada ya aurar da ƴar shi, shi kuma ya aura mishi ko me?". Fadil yace; "ina jin ina da shawara", da sauri Abdus-samad ya buɗe idanu, Fadil yace; "me zai hana ka faɗawa Malama, idan yaso sai ta riƙe yarinyar a matsayin ƴar aiki?". Ya jima yana kallon Fadil ɗin kafin ya girgiza kai, "wannan ba zai yiwu ba, taya kake ganin Malama zata iya ɓoye baban al'amari kamar wannan?". Fadil yace; "hakane kuma gaskiya, sannan Hajja zata iya matsawa abin da bincike, to ka kai ta wani gidan mana sai ka ɓoye ta". "wannan ma bana ji hakan me yiwuwa ne, ka duba ka ga yanayin yarinyar tana buƙatar me ɗebe mata kewa wanda zasu ɗan dinga fira, idan na kaita gida na ajiye ita kaɗai ban yi mata adalci ba". Fadil yace; "kai sai ka dinga zuwa", wani kallo Abdus-samad yayi mishi kafin ya ɗauke kai, "kaima ka san Firzt Love ba zata yarda da fita ta any how ba, dole ta dinga bincikar ina naje, ina jin tsoron ranar da zata gane cewa mace na ajiye a gida nake kula da ita, ka nemo wata shawarar". Fadil ya miƙe yace; "to ni gaskiya banda wata shawarar, ko kuma zaka kaita wajen Fadila ne sai ta kasance a matsayin ƙawarta?". Abdul yayi jim kafin yace; "Fadila da zata yi aure babu jimawa, dole idan tayi aure na samu wajen ajiye ta", Fadil yace; "hakane kuma ka san bikin Familyn nan ba wani jan shi suke yi ba". Shiru ya biyo bayan haka, kowa tunanin da yake yi daban, sun jima a haka kafin Fadil yace; "to ka kaita wajen Aunty Saleema mana". Sai da ya tsaya yayi nazari kafin yace; "kana ganin hakan zai yiwu kuwa", Fadil cikin ƙwarin gwiwa yace; "tabbas kuwa zai yiwu, Aunty Saleema nada sauƙin kai kaga kenan zaka sami sauƙin kula da ita, na san soyayyar da take yi maka zai sa ta kula da ita sosai kuma kaga bata da wata damuwa sosai", Abdul ya jinjina kai. Wayar shi ya zaro ya kira Saleemar akan ta same shi Garden yana jiran ta, cikin ɗoki da murna ta amsa da gata nan zuwa, shi kanshi sai da yayi murmushi saboda yadda ta nuna murnarta a fili. Anya ba kasada zai yi ba, idan kuma kishi yasa ta ƙi amsarta fa ko kuma ta tona mishi asiri fa?, wannan kam anya ba ganganci bane zai aikata🙄. #LIKE #SHARE #COMMENTS. *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖53-54📖📖 Tunda ya hangota gaban shi ya yanke ya faɗi, kada fa garin neman mafita ya jefa kanshi a matsala idan kuma bata amince bafa ta faɗawa Abban ta. Ƙarasowar ta shine abinda ya katse mishi tunani, cikin natsuwa tayi sallama suka amsa mata, da murmushi taja kujera ta zauna sannan ta kalle shi tace; "lafiya kuwa?". Abdus-samad ya juya ya kalli Fadil wanda dama shi yake kallo, Fadil yayi saurin girgiza mishi kai, Abdus-samad ya maida kanshi ya lumshe idanu. Shiru ya biyo baya, ganin ba zasu yi magana bane yasa Saleema riƙo hannun shi tace; "Abdus-samad ka faɗa mini meke faruwa mana, damuwarka ai tamu ce, kada ka manta bakada wanda zai yaye maka damuwarka bayan Ubangijin daya halicceka sama da mu, idan har akwai shi to bayan mu yake kada kaji komai ka faɗa mini abinda ke faruwa nayi maka alkwari zan taimakeka kuma zan rufa maka asiri". Ya buɗe idanu ya kalleta, gaban shi babu abinda yake yi banda dukan uku-uku ga wasi-wasin ya faɗa mata ko kada ya faɗa mata, can ya girgiza kai baya jin wannan mafitar zata ɓulle mishi. Fadil yayi gyaran murya, ta juya ɓangaren shi nan ya bata labarin iya abinda ya sani akan yadda aka ɗaura auren ɗan uwan nashi da yarinyar da haƙuri yaje bawa Babanta. Saleema tayi murmushi bayan ta gama jin abinda ya faru ta maida kallonta kan Abdul wanda ita ya zubawa idanu yana so yaga yanayin yadda fuskarta zata yi. "taɓ, yanzu me kuke so ayi?", ta tambaya, Fadil ya sosa kai yace; "dama wai cewa muka yi ko zaki kaita appartment ɗinku, sai kice ƙawarki ce kafin komai ya dai-daita". Saleema taja ajiyar zuciya tace; "Abban Nihal ya dawo jiya, Abban mu kuma nan da kwana biyar zai dawo amma zan yi ƙoƙari naga ba'a sami matsala ba, yanzu tana ina?". "tana mota", amsar da Fadil ya bata kenan, bata kuma cewa komai ba sai wajen motar data nufa ta ɗan ƙwanƙwasa, Nusram da har lokaci banda kuka babu abinda take yi ta saka hannu ta buɗe ƙofar. Saleema ta sakar mata murmushi sannan tace; "fito ko?", babu musu ta fito a ranta tace; "gidan yankan kai harda mace?", bata samu amsar tambayar ta ba, Saleema ta riƙo hannun ta suka nufi inda su Abdul ke zaune. Tunda suka taho Abdus-samad ya zuba mata idanu, gaban shi sai faɗuwa yake yi, suna zama Nusram ta ɗago ta kalle shi yayi saurin kauda kai yana zaro wayar dake aljihun shi wacce keta faman tsuwwa tun ɗazu, kamar yadda ya zata Brr Farida ke kiran shi. "Hello First Love", bata amsa ba sai cewa da tayi; "haba Baby ina ka shiga ne?, me kake aikatawa haka ka san dai ban fiye son yawo ba jiya ma Surayya tace mini da wuri ka bar Company amma baka taho gida ba yauma haka". Abdul yaja numfashi yace; "First Love bafa wani waje naje ba, ina........", tayi saurin dakatar dashi; "kaga niba wannan ba duk inda kake ka tabbatar ka iso gida nan da minti talatin", tana faɗin haka ta katse wayar, ya bi wayar da kallo yana sakin ajiyar zuciya. Saleema tace; "abinda za'ayi shine ka tafi gida kawai insha Allahu babu me sani har zuwa lokacin da zaka faɗa musu, zan yi iya ƙoƙari na mu bar wajen nan kada wani yazo ya gan mu", duka suka miƙe itama hannun Nusram ta kama suka miƙe tare. Ta ɗan saki hannun ta sannan ta juya ta sauka, Fadil ma fita yayi daga rumfar, ya kalle ta ya kauda kai me kenan? Wai su nan sun bar su suyi sallama, yayi wani miskilin murmushi. Nusram kuwa gabanta ke faɗuwa kawai, Abdus-samad yace; "kinga zaki zauna da wannan da tazo na san zata yi miki bayanin komai ki kwantar da hankalin ki insha Allahu komai zai dai-daita, yanzu ba zan iya fitowa nace an ɗaura mini aure dake ba duk abinda kike buƙata ki mata magana", be jira me zata ce ba ya fara tafiya. Nusram ta saka hannu ta share hawayen dake zubo mata daga idanu kafin ta fito itama daga wajen, a bakin mota ta same su, Fadil na fito mata da kayanta. Saleema tace; "ya sunanta ne?", Abdus-samad ya ɗan kalle ta ya basar, maida hankalin shi yayi kan Fadil yace; "zan tafi sai da safe", Fadil yace; "baka ji abinda Aunty Saleema tace bane?". Ya ɗan lumshe idanu shifa wannan auren har ya fara zama takura a gare shi,cike da ƙagara yace; "Nusram", yana faɗin haka ya buɗe mota ya shiga. Saleema na riƙe da hannun Nusram tana murmushi har suka dena hango shi, Saleema tayi murmushi kafin ta kalli Fadil tace; "shigar mana da kayan", suna gaba yana bin su a baya. Da sallama suka shiga Mommy dake karatun jarida ta ɗago ta kalle su, Dr Saleema taja Nusram suka zauna a kujera. "wannan fa daga ina?" ta jefo mata tambaya, Dr Saleema tace; "ƙawata ce dake karatu a KASU bata sami Hostel ba shine ta roƙe ni akan tana so ta zauna anan na ɗan wani lokaci", Mommy ta jinjina kai tana ƙara bin Nusram da kallo. Nusram sai sake saukar da kai ƙasa take yi, cikin dashashshiyar muryar ta gaishe da Mommyn, ta amsa babu yabo ba fallasa. Dr Saleema tace; "muje ciki ki ɗan huta tukunna", daga haka ta miƙe itama Nusram ta bita a baya, kayan da Fadil ya shigar mata dashi Dr Saleema ta gyara musu wajen zama sannan ta kalli Nusram tace; "ga bayi nan ki shiga kiyi wanka sai kizo muyi magana", ta amsa da to. Hijab ta cire, Dr Saleema gabanta ya faɗi ganin irin yadda Nusram take da kyau na halitta, lallai kwanan nan Abdus-samad zai fara sonta, towel ta miƙa mata cike da kunya Nusram ta cire kayan ta ta saka towel ɗin, ita dai Dr Saleema babu abinda take sai binta da idanu, "fatabarakallahu Ahsanal khaliƙeen", abinda Dr Saleema ke maimaitawa cikin ranta kenan. Nusram ta jima a bayin tana kuka ganin yadda rayuwa take wulagegeduwa da ita, daga nan sai nan, sai da Dr Saleema taji shirun yayi yawa sannan ta ƙwanƙwasa bayin, cikin sauri Nusram ta fara wankan. Koda ta fito wajen madubi ta nufa, mayuka da turarruka da kayan kwalliya duka ta gansu masu tsada da kyau duk da kasancewar ta me yin kwalliya kuma tana yawan binciken kayan kwalliya ta network amma sai da taga abinda bata sani ba. Mai ta shafa da powder sai ɗan man baki, ko kwalli bata saka ba, wajen jakarta ta nufa ta zage ta ciro riga half gown da wando blue and pink ta saka, ba tare da ta ɗaura ɗankwalin ba ta ɗora shi saman kai kawai. Kusa da Dr Saleema tazo ta zauna kafin tace; "na gama Aunty", Dr Saleema tayi murmushi tace; "kinga nan shine gidan mu ni da Babana da Mama na da kishiyar ta da kuma ƴan uwana, gidan da kike ciki gida ne me mutane da yawa saboda haka sai kinyi taka tsantsan, kasancewar kinga mun kusa Family meeting duk wani wanda yake da jinin gidan nan zai halarta dan haka ki ƙara kulawa, kamar yadda nace ke ƙawata ce to zaki zauna a matsayin ƙawata, kullum idan zan tafi wajen aiki zan tafi da ke idan na dawo ma zamu dawo tare kin fahimta". Nusram ta ɗaga kai, Dr Saleema tayi murmushi tace; " na san zaki ce me yasa Abdus-samad be kaiki gidan su ba ya kawo ki nan, dalili kuwa shine kinga gidan nan gidane na ƴan boko duk wanda kika gani a ciki mace da namiji ko ɗalibi ko ma'aikaci, sannan namiji aƙalla yakan kai shekara talatin kafin a bar shi yayi aure mace kuma ashirin da bakwai zuwa da takwas har ma sama da haka dan haka wannan shine dalili, ina so ki ɗauke ni ƴar uwar ki duk wani abu da kike buƙata kizo ki tambaye ni insha Allahu zan yi ƙoƙari ganin baki zauna cikin damuwa ba, Abdus-samad nada mahimmaci a rayuwata saboda haka duk wani abu daya dangance shi ina mahimmanta shi kin fahimta". Nusram ta kuma ɗaga kai, Dr Saleema ta ɗan kishingiɗa jikin couch tace; "yanzu ki bani labarin rayuwar ki", Nusram tayi murmushi me ciwo kafin ta fara bata labari. Dr Saleema har da hawaye sai da ta yi, cikin shesheƙar kuka tace; "lallai duk wanda kuka haɗu dashi akwai dalilin haɗuwar ku, kuma ko a jima ko a daɗe zaka ga akwai wani abu wanda kuke kamanceceniya dashi, kin ganni Nusram shekaruna talatin da huɗu na kusa shiga talatin da biyar amma babu aure". Nusram tace; "babu wanda ya taɓa cewa yana son ki ne kamar ni", Dr Saleema ta girgiza kai tace; " na samu samari lokacin da nake tashen ƴan matanci amma sanin halin gidan mu yasa dole na ɗauke kaina, a cikin su akwai wanda ya nace sosai har gidan nan sai da ya turo amma iyayena suka ci mishi mutunci dalilin haka mahaifan sa suka yi fushi suka ce ko a hanya ya kuma kulani basu yafe ba, na damu sosai amma haka na haƙura yanzu gashi da zama na likita shekara takwas kenan, Nusram kuɗi iya kuɗi ina dashi babu abinda nake nema, duk wani abu da kika sani ina da kuɗin siyan shi sai dai aure kawai". Nusram ta kuma cewa; "toke yanzu baki da wanda kike so ne", Dr Saleema ta share hawaye tace; "ina dashi mana sai dai na sani cewa ba zai taɓa maido mini da soyayya ba, ni kaɗai kawai nake son shi, a da dai ina saka ran koda da idanun rahama zai kalle ni amma zuwa yau na tabbatar da yayi mini nisa Nusram ba zan taɓa samun shi ba". Kafin Nusram tace wani abu Dr Saleema ta ƙwalawa Sakina ne aikin su kira, ta shigo cikin sauri. "ki kawo mini abinci", abinda ta faɗa kena, Sakina ta amsa da to sannan ta fita, Dr Saleema ta miƙe ta fara cire kaya, ita dai Nusram tana ta binta da kallo har ta shige bayi. Nusram tayi shiru tana mamakin rayuwar wannan baiwar Allah, ta sake ɗaga kai ta kalli ɗakin nata komai yaji dangane da alatu na rayuwar duniya, ta shafa gadon da take zaune a kai shi kanshi royal bed ne me tsada, ƙaton wardrobe wacce ta cike bango ɗaya, change room da kuma dressing mirror, wasu irin manya-manyan glass masu shape ɗin duniya sai me heart a tsakiya, cikin su wasu irin ruwa ne me ƙalƙali, ƙasa kuwa italian carpet ne me taushi da kyau, sai flower vase dake kusa da window guda biyu manya-manya, duka kuma ash and milk ne, Tana nan zaune Sakina ta shigo da ƙaton tray a hannun ta, ƙaramin teburin dake jingine ta janyo ta ɗora tray ɗin sannan ta juya ta fice bayan ta yiwa Nusram sannu. Dr Saleema ta fito ta kalli Nusram tace; "ya baki ci abincin ba", Nusram tayi murmushi tace; "jira nake ki fito sai muci tare", bata kuma cewa komai ba sai ma nufar madubi da tayi. Nan fa ta hau ƙalƙale jiki, itama ba wata kwalliya tayi sosai ba, powder ne sai jan baki light pink da kwalli shikenan. Ta buɗe wardrobe ta ciro rigar bacci me shegen kyau pink colour ta saka, nan ta hau feshe jiki da turare, kan kace me ɗakin ya hau ƙamshi. Sai da ta dawo ta zauna sannan tace; "komai ma zai zo da sauƙi tunda dama kina karatun ki kinga da an koma makaranta sati biyu masu zuwa sai ki cigaba da karatun ki kawai, zuwa ƙarshen satin nan zamu je muyi registration", Nusram cikin farin ciki ta amsa da to, abinda ta cire rai akai. Lafiyayyen tuwun shinkafa ne da biyar taushe, ba me yawa ba ta zuba musu suka hau ci, babu sabo a tsakanin su hakan ya haifar da yin shiru, suna gamawa suka wanke hannu. Dr Saleema ta janyo laptop ta fara dannawa ganin hakan yasa Nusram zama ta zuba mata idanu. Sun jima a haka kafin Dr Saleema tace; "kiyi shirin barci mana", cikin sauri Nusram ta miƙe, kayan barci ta ciro cikin jakar ta sannan ta hau sakawa. Dr Saleema tayi mata kallo ɗaya ta kauda kai, wani abu ta danna sai ga plasma yana fitowa, Nusram ta ƙwalalo idanu, Dr Saleema ta miƙa mata remote ɗin tace; "gashi idan zaki rage dare", Nusram ta saka hannu ta amsa sannan ta koma ta zauna. Tana zaune tana kallon kamar dole don ita ba wai ya dame ta bane, haka har barci ya ɗauke ta wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba. Dr Saleema ta kalleta tayi murmushi, ta ajiye Laptop ɗin ta matso gare ta, kallonta tayi sosai tana jinjina kyawunta waye za'a bawa mace kamar wannan yaƙi amsa tabbas Abdus-samad ta tabbatar yanzu yafi ƙarfinta, ta share hawayen da ya zubo mata kafin itama ta fara canza kaya zuwa na barci. Kan couch ta kwanta har lokacin ranta a cunkushe yake, a yanzu kam tana jin cewa wata kila harta koma ga ubangijinta bata da rabon yin aure. ******** ************ koda ya bar gidan babu abinda yake yi banda tunani, Allah ne ya taimake shi har ya kai gida lafiya, yana yin parking suka haɗu da Sameer. "kai kam zaka tashi office da wuri amma duk zamu riga ka isowa gida", cewar Sameer ɗin kenan, Abdus-samad yayi murmushi kawai. Part ɗin shi ya fara wucewa, sai da ya shiga bayi yayi wanka kafin ya fito ya hau shiryawa, gaban madubi yaja ya tsaya hannun shi riƙe da comb, wai yau shine da mata!?, shi Abdus-samad Abubakar Nagimi?, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Turo ƙofar da akayi itace tasa ya kalli wajen, duk da sanin wacece ta shigo, kamar yadda ta zuba mishi idanu haka shima ya zuba mata idanu, tsoron shi ɗaya kada ace ta gane cewa an ɗaura mishi aure. Dr Farida ta kauda kai tace; "idan ka gama shiryawa kazo kaci abinci", be amsa ba itama kuma bata tsaya jiran amsar tashi ba. Tana daf da fita sai kuma ta juyo tace; "wai baka kuma magana akan yarinyar da aka harba ba a shopping mall?". Ya ajiye comb ɗin hannun shi ya ɗauki kwalbar turare ya hau fesawa, har ta cire rai da zai yi magana sai kuma taji yace; "First Love komai yana faruwa saboda ɓoye mini abubuwa da yawa da kuke yi". Cikin sauri ta kalle shi ya kauda kai yama cigaba da abinda yake yi, ta jima tsaye ko zai kuma cewa wani abu amma be kuma magana ba hakan yasa ta ɗaga ƙafa ta fara tafiya, wannan murɗaɗɗen hali irin na uban shi ne", abinda ke ranta kenan ita kanta duk da take lauya wani lokacin idan yayi magana a murɗe ta kan jima bata fahimta ba. "ita ɗin ƴa ce ga Alhaji Mustapha Tuge", abinda ya faɗa kenan tana dafa da fita, Brr Farida gabanta ya yanke ya faɗi, cikin sauri ta juyo ta sake kallon shi kamar ma bashi yayi maganar ba. Taja ajiyar numfashi tace; "Baby ita ɗin ta faɗa maka haka?, taya akayi ka sani ko ka sake binta asibitin ne?, kun haɗu dashi Alhaji Mustaphan?", duka ta jero mishi tambayar babu amsa ɗaya da ya bata hakan yasa ta fice kawai. Abdus-samad ya bi bayanta da kallo tana ficewa ya saki ajiyar zuciya, ƙarar wayar shi itace ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa. Number ce babu suna hakan yasa be ɗaga ba, tana yankewa wata ta shigo itama tana yankewa wani kiran ya sake shigowa, ya saka hannu ya ɗauka ya kai kunne. "Hi!", shine abinda ta faɗa, a gajarce shima yace; "barka", ta ɗan yi gyaran murya sannan tace; "ka gane me maganar". Cikin ƙagara yace; "a'a wacece?", jin abinda ya faɗa yasa jikin ta yin sanyi, "Khausar ce", ta faɗa cikin sauri. "oh ya gida?, fatan komai lafiya", ya tambaye ta, murmushi tayi kana tace; "lafiya lau, dama cewa nayi bari na kira mu gaisa", ya ɗan shafa gefen fuskar shi yace; "na gode" kan ta kuma magana ya yanke kiran. Sororo ta tsaya hannun ta riƙe da wayar, Hajiya Salma data ji duk abinda ya fara ta taɓe baki tace; "wai ke qace irin wahalalliya ce?, bafa shi kaɗai bane namiji". Khausar ta saki murmushi tace; "ni fa Mommy ina son shi kodan kama da yake yi da Daddy", ta ƙarasa tana me juyawa ta kalli Mahaifin nata. Alhaji Mustapha kuwa banda zufa da take karyo mishi babu abinda yake yi. be iya cewa komai ba. "Daddy ai ka ganshi kwanaki ko?, kana nan yazo gaishe dani a asibiti, wallahi da badan na san cewa nida Khalee kawai Mummy ta haifa ba da sai nace ɗan kane". "Umm", shine abinda Alhaji Mustafan ya faɗa, Hajiya Salma ta ƙunshe dariya, Khausar zata kuma magana Hajiya Salma ta dakatar da ita. "wai ke baki ga Mahaifin naki baya son surutu bane, gobe ƴar uwar ki zata dawo dan haka kije ki kwanta kin san dai isowar wuri zata yi", Khausar ta miƙe tana zumɓurar baki tayi ɗaki. Hajiya Salma ta miƙe itama ta shige nata ɗakin, Alhaji Mustafa ya dafa kanshi da hannu biyu yana sauke ajiyar zuciya. "wannan wane irin masifa ce take tunkaro shi, ƴar shi ta cikin shi ke son ɗan shi na cikin shi?, taya zai fito ya shaidawa duniya cewa Abdus-samad ɗin ɗan shi ne na cikin shi?, akwai babban al'amarin da ko tunawa baya son yi". Wayar shi ya zaro ya fara kiran Alhaji Sa'eed, sai dai kash ana amfani da layin, miƙewa yayi cikin sauri kana ya fara zagaye ɗakin. Daidai lokacin kuwa Hajiya Salma ce da Alhaji Sa'eed suke waya, "Alhaji wallahi ban san yadda zan yi da yarinyar nan ta fahimci halin da ake ciki ba, bana ƙaunar ganin yaron nan a raye gashi na rasa yaya zan yi". Alhaji Sa'eed yace; "kada ki damu Hajiya Salma, zamu iya amfani da ita wajen tunowar asirin mijin ki, na san cewa idan har abinda yake ɓoyewa ya fito fili to tabbas yaran nashi zasu tsane shi tsana me tsanani, sannan shi kan shi Abdus-samad ɗin zai tsane shi tsana mafi muni sannan kinsan Nagimi's Family dole zasu ɗauki mataki, zasu maka shi kotu kuma kin san hukuncin da za'a yanke mishi ɗaurin rai da rai ne". Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya tace; "Alhaji Sa'eed har yanzu baka san waye abokin ka ba, ko tafiyar nan da yayi hannun jari yaje ya zuba a wani company dake Hong Kong ƙimanin dala billion sha biyar, sannan yana ɗaukar kaso mafi tsoka a babban companyn dake ƙera gwalagwalai a Dubai, dan haka bana jin kuɗin Familyn nan zai iya da nashi, ba zasu taɓa iyawa ba ka chanza shawara". Jim yayi yana tunani, yayin da Hajiya Salma take tunanin mafita yake nemo musu, shi kuma a nashi ɓangaren kuɗaɗen ne suka fara girgiza shi, lallai wato Alhaji Mustaphan ashe yana ɓoye mishi wasu abubuwan, shi dai kawai ya san cewa yana da Companyn ƙera motoci a Dubai da kuma lagos, sai Company biyu da yake da hannun jari a India da kuma Bangkok ashe likafa ta cigaba kuɗin nashi ya fara wuce tunanin shi kenan?. "Me zai hana kawai idan Khausar ta gayyace shi gidan nan mu saka mishi guba a abinci sai ya mutu, idan yaso Baban shima daga baya sai muji dashi?". Abinda ta faɗa ya katsewa Alhaji Sa'eed duniyar tunanin daya fara kenan, ya girgiza kai kamar tana gaban shi yace; "hakan bame yiwuwa bane Brr Farida a sanin da nayi mata ba zata taɓa ƙyale abin a haka ba, bana so muyi abinda zamu shiga ciki". Hajiya Salma taja tsaki tace; "yanzu meye abin yi?", Alhaji Sa'eed yace; "watan gobe Brr Farida zata tafi Korea yin wani case ina ganin zamu yi amfani da wannan damar ne kawai". Hajiya Salma tayi murmushi tace; "shikenan Allah ya kaimu da rai da lafiya, amma wallahi na ƙosa komai ya dawo hannu na, nima na zama ɗaya daga cikin matan da ake lissafawa masu kuɗi a duniya". Alhaji Sa'eed yayi wani munafikin murmushi sannan yace; "nima na ƙosa wannan lokacin yazo ke dai kome ke akwai ki dinga sanar dani", ta amsa da to. A haka suka rabu, Alhaji Sa'eed na katse wayar ya miƙe tsaye cikin sauri, Brr Hauwa dake kwance jikin shi tayi saurin miƙewa tana tambayar shi lafiya. "babu komai, dan Allah ina buƙatar yin tunani yanzu bana son damuwa ko zaki tafi ne?", Brr Hauwa ta ɗaga gira ɗaya tace; "kuɗin da Hajiya Salma ta faɗa maka Alhaji Mustafa na dashi shine ya tsorata ka ko me". Jin abinda ta faɗa yasa ya ɗan saki rai yace; "ba haka bane, mafita nake nema dole Abdus-samad da Alhaji Mustapha su mutu, kuɗi Hauwa dole ya dawo gare mu, ni dake". Brr Hauwa tayi murmushi tace; "ka kwantar da hankalin ka, har yanzu fa Brr Farida bata faɗawa Abdus-samad komai ba, suna ganin sannan sirrine tsakanin ta da Alhaji Mustafa banda su biyu babu wanda ya sani". Alhaji Sa'eed yace; "amma shi Alhaji Mustaphan ai ya san na sani ko", ta shafa fuskar shi tace; "amma kuma ai ya yarda da kai sosai ko". Ya koma ya zauna kana ya girgiza kai yace; "bana tunanin hakan Brr a da Alhaji Mustapha baya yin komai sai da sani na amma a yanzu ya canza sosai", miƙewa yayi ya ɗauki wayar shi kana yace; "bari naje wajen Oregbu zamu haɗu gobe kawai dan yau till down zamu yi". Brr Hauwa ta figi jakar ta sannan tace; "muje ka ajiye ni a gida ko?", daga haka suka fice daga gidan. #LIKE #COMMENT #SHARE *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖55-56📖📖 Alhaji Mustafa ke tsugunne jikin shi sanye da jan ƙyalle iya gwiwa, tsaye a saman shi Appu ne shima sanye da jan ƙyalle a kwankwason shi sai dai shi ya yafa wani saman kafaɗar shi. Wani abu dogo ne riƙe a hannun shi, wani ƙaton mutum me ƙaton tumbi ke gefe tsaye da ƙwarya ƙatuwa a hannun shi, Appu ke saka wannan abin cikin ƙwaryar yana yayyafawa Alhaji Mustapha yana zagaye shi yana wasu irin surutai. Sauran kuwa kansu na ƙasa duka a tsaye suke sanye da jan kaya riga da wando, wajen yayi tsit sai tashin muryar Appu dake wannan surutan. Sun jima a haka kafin wani hayaƙi ya fara cika wajen, basu motsa ba kai daga gani kasan sun saba da yanayin, sai dai wasu ƙalilan da suke zubar da hawaye kasancewar hayaƙin akwai zafi sosai amma babu halin rufe idanu. Sun jima a haka wajen awa ɗaya kafin komai na wajen ya ɗauki rawa, wutar dake kunne koda yaushe wacce take saman wata ƴar ƙaramar ƙwarya ta ɗauke, nana fa ko'ina a wajen ya ɗauki duhu. Minti talatin da faruwar hakan sannan hasken ya dawo, Alhaji Mustafa ya kalli inda yake tsugunne jini ne a gaban shi malala wanda har ya gangaro ya tarar dashi, sai yara guda biyu da suke kwance a wajen cikin su a fafe wanda yake nuna alamun tana nan ne aka sha jinin nasu. Appu ya fashe da dariya kafin ya matsa, wajen wata giggimemiyar kujera yaja ya tsaya sannan ya nuno Alhaji Mustapha yace; "haƙurin Oregbu ya kusa ƙarewa Tuge, dole ka kawo jinin ɗanka na cikin ka idan ba haka ba fushin sa zai sauka a kanka, shekara talatin kenan da yi mishi alƙawari amma har yau ka gaza cikawa, tun ana rarrashin shi yana amsar jinin wasu wata rana fa ba zai aminta ba", ya juya ga sauran mutanen ya nuna mutum biyu a cikin su yace; "Oregbu yace a gaya muku ya ji daɗin sadaukarwa da kuka yi mishi, dan haka yayi matuƙar murna shi kuma zai canza muku da abinda kuke so". Ya nuna wani dogo fari a cikin su yace; "yadda ka bashi ɗan ka yace a gaya maka kaine zaka dinga juya shugaban ƙasa wanda za'a rantsar hasalima ma ƴan majalisu kai zaka yi list ɗin su ka bayar mulkin nijeriya naka ne". Cikin murna yayi sujjada yana godiya, ya nuna ɗayan da hannun shi yace; "kai kuma ka bashi jini me daɗi sosai na ƴar ɗan uwanka dan haka sai ka zama babu babban ɗan kasuwa a ƙasar Ghana wanda yake sama da kai", shima cikin murna ya durƙusa ya hau murna. Appu ya ɗaga mishi hannu kana ya ɗora da cewa; "abu guda zaku yi tare abu guda kuma kowa da nashi wanda zaku yi tare shine ku baiwa almajirai guda uku sadakar dubu goma amma jefa musu zaku yi". Ya nuna na farkon yace; "ka samu yaro wanda bai gaza shekara goma sha takwas ba kada ya wuce haka kayi luwaɗi dashi a masallacin ƙofar gidan ka sha biyu na daren gobe". Ya nuna ɗayan yace; "ka sami jariri sabuwar haihuwa ɗa namiji ka ɗauke shi ƙarfe ukun dare kayi jefa dashi a tsakar gidan ka bayan kayi zindir idan be mutu ba ka sake yi mishi haka har sai ya mutu, buƙatar ku ta gama biya", jinjina kai suka yi sannan suka matsa baya. "Alhaji Sa'eed Yahya Tsillo, da kai da Alhaji Mustafa Abubakar Tuge, Oregbu yace a faɗa muku yana son jini daga gare ku ƙafin nan da sha bakwai ga watan gobe". Alhaji Sa'eed yace; "ayi mini afuwa ƴaƴa biyu suka rage mini yanzu", cikin daka tsawa Appu yace; "ka kawo ko ka haukace", Alhaji Sa'eed yace; "zan bayar". "zaka iya bayar da na ƴar ƙanwarka Azeema domin Oregbu yace jinin ta akwai wuyar samu", cikin murna Alhaji Sa'eed yace; "zan kuwa kawo ta". Appu ya juya ga Alhaji Mustafa yace; "ko dai ka kawo jinin Abdus-samad ko kuma ka kawo jarirai guda goma", Alhaji Mustafa yace; "tunda jinin Abdus-samad yaƙi samuwa kona bayar dana Khaleesat ko Khausar mana". Appu yayi ihu yayi kirari kafin ya girgiza kai yace; "wa'innan ba jinin ka bane, jinin ka na asali yake so, kada ka kuma kawo zancen su", cikin sauri ya amsa da to. Nan suka cigaba da kafurcin su da tsibbace tsibbacen su, har zuwa gabatowar asuba kafin suka watse. Alhaji Mustafa da Alhaji Sa'eed tare suka taho, sun shigo garin Kaduna ana kiraye kirayen sallar asuba dan haka suka sami masallaci suka yi sallah. Bayan an idar Alhaji Mustafa ya dubi masallacin babu kowa domin kowa ya kama gaban shi ya kai kallon shi ga abokin shi yace; "Alhaji Sa'eed ka taimaka mini mana, ban san ya zanyi ba". Cikin ɗaure fuska Alhaji Sa'eed yace; "meka maidani Mustapha, nifa lura jinin Murad ɗin ne baka son bayarwa". Ya girgiza kai yace; "ba haka bane ka duba da kyau ka gani matsaloli sun fara yawa tun da suka haɗu da Khausar ta liƙe shi take so, Brr Farida taƙi ko kusa ta faɗa mishi cewa nine mahaifin shi balle na samu damar raɓar shi, sannan yaron be cika shige-shige ba balantana na sami wata dama akan shi, ga Salma yadda take sona take kula dani ta yarda dani ba zan iya kallon idanun ta ince mata wai ina da wani ɗa ba". Alhaji Sa'eed yayi murmushi yace; "hakane kuma gaskiya, to amma yanzu abinda za'a yi shine ya kamata ace muna kula da takun Brr Farida domin na san shirun ta ba wai yana nufin shiru ɗin bane dan haka me zai hana mu tura wata matar ta sami aiki a gidan ta idan yaso sai ta dinga kawo mana rahoton abinda yake faruwa". Alhaji Mustafa yace; "Alhaji Sa'eed duk abinda ya kamata kayi ni dai kayi amma ka tabbatar da cewa asirina dana rufe shekara Ashirin da bakwai be tonu ba". Alhaji Sa'eed yace; "kada ka damu kai dai ka bar mini komai a hannu na baka faɗa mini meya kaika Dubai ba?". Alhaji Mustafa yace; "hannun jari na zuba a wani company, so nake gaba kaɗan na siye companyn gaba ɗaya haka ma Brr Jabeer ya bani shawara". "to amma ya maganar takardun gidan gonarka dake By Pass?", Alhaji Mustafa ya ɗan yi jim kafin yace; "suna nan, akwai matsala ne?", Alhaji Sa'eed ya girgiza kai. Sai da gari yayi haske sannan suka fito daga masallacin kowa ya shiga motar shi ya nufi hanyar gidan shi. ********* ************** *HAYIN RIGASA, KADUNA*. Da asuba suka tashi tare kamar haɗin baki, Dr Saleema ta fara alwala kafin Nusram itama ta miƙe ta shiga bayin domin alwala. Koda Nusram da Dr Saleema suka idar da sallah babu wanda ya tashi daga inda yake, hakan ya tabbatar da cewa dukkan su, suna da kamanceceniya ta wajen halayyar su. Sai bakwai kafin Dr Saleema ta miƙe ta shiga bayi, wanka tayi bayan ta fito ta dubi Nusram tace; "ki shiga kema kiyi wankan zamu wuce asibiti", Nusram ta jinjina kai sannan ta miƙe ta shige. Nusram na fitowa ta sami Dr Saleema tana shiryawa itama ta hau nata shirin kafin wani lokaci duka sun gama shiryawa. A jere suka fito, Muhibba da Kamal ke saman dinning, yayin da Kabeer da Hafeeza ke zaune a saman kujera suna haɗa taƙardu. Duka idanu suka zubo musu wanda hakan yasa Nusram jin ta fara takura, bayan Dr Saleema ta shige. Koda suka ƙaraso saman kujera Dr Saleema taja hannun Nusram ta zaunar da ita sannan itama ta zauna. Kamal da Kabeer suka sauke ajiyar zuciya a tare, shiru ya ɗan biyo baya kafin suka fara gaishe da yayar tasu. Ta amsa cikin sakin fuska, tana miƙewa Mummy na shigowa, "ina kwana Mummy?", ta amsa da lafiya lau, Nusram itama ta gaishe da ita kafin duka suka nufi dinning. Muhibba tayi serving ɗin su, ita dai Nusram gabanta banda faɗuwa babu abinda yake yi ga wani irin kallo da mazan ke binta dashi. Ta kasa cin komai banda juya cokalin da take yi, Kabeer ya kalli ƴar uwar tashi sannan ya kuma kallon Nusram wacce kanta ke sauke a ƙasa. Tayi kyau sosai sanye take da atamfa me ruwan goro da ɗige-ɗigen kore, hijab ɗin dake jinkin ta shima kore ne wanda ya ƙara haskaka fatar ta. Hannun ta riƙe gam da wannan wayar dai ta Abdul domin kuwa barci ne kawai ke rabata da wayar amma kusan koda yaushe tana hannun ta. "Wai Yaya Saleema ina kika samo wannan kyakkyawar ne?", Dr Saleema ta ɗan kalle shi kafin tace; "Ƙawata ce ta fara karatu anan Kaduna shine tazo zama anan". "oho! Na gane sannu baƙuwa", Kabeer ɗin ya faɗa, Nusram ta ɗanyi murmushi wanda yasa dukan su sakin baki tace; "yauwa sannun". Zai kuma magana Mummy ta dakatar dashi don haka dole yaja bakin shi ya tsuke, suna gamawa Dr Saleema ta miƙe inda itama Nusram ɗin ta miƙe. "Yaya Saleema kika ce makaranta take yi da ai sai ki bari mu tafi tare da ita ko?", cewar Muhibba wacce ta miƙe ta roƙo hannun Nusram ɗin. Hafeeza ma ta miƙe ta kalli Kamal tace; "kai tashi mu tafi, kada mu makara", har ya miƙe Mummy tace; "amma da dai da Kabeer kuka tafi shine fa zai je ɗauko Daddynku a Airport". Hafeeza ta duba agogon hannun ta kana tace; "ya dai kaini idan yaso ya dawo daga nan ma sai yayi signing kawai", Mummy tace; "shikenan", daga haka suka juya suka fice. Ɓangaren su Dr Saleema kuwa ta kalli Muhibba tace; "wannan amanace a waje na ki bari idan kuka ɗan saba sai ku cigaba da tafiya tare kinji". Muhibba ta zumɓuro baki gaba tace; "ni wallahi Yaya Saleema ina sonta da ƙawa", Dr Saleema tayi murmushi kana tace; "kada ki damu, Nusram muje ko". Da Muhibba da Kabeer suka maimaita sunan cikin birgewa; "Nusram!!", Kabeer yayi murmushi yace; "nice name", Muhibba ta kwashe da dariya. Ita dai Dr Saleema ganin abin nasu bana ƙare bane yasa taja hannun Nusram ɗin suka fice daga gidan. Koda suka shiga mota babu wanda yayi magana, gaba ɗaya Dr Saleema ta maida hankalin ta kan tuƙi yayin da Nusram kuma ta kunna wayar tana kallon hoton da ya zamar mata jiki wajen kallon shi domin har yanzu bata san password ɗin wayar ba hakan yasa sai dai ta kalli hoton idan ta gaji da kallo ta kashe ta ajiye. A ɗan kaikaice Dr Saleema ta kalle ta, ta ɗan yi murmushi ganin hankalin ta ya tafi gaba ɗaya kan wayar, bata ce da ita komai ba har suka iso babban asibitin garin Kaduna inda Saleemar ke aiki. Suna tafe suna gaisawa da jama'a har zuwa office ɗin Dr Saleemar, ga dai shi asibitin gwamnati ne amma office ɗin babba ne hakan ke nunarwa da Dr Saleemar babbace a asibitin. Kan kushin ta nunawa Nusram ita kuma ta hau kujerar aiki inda ta fara ganin marasa lafiya, ita dai Nusram na zaune tana kallon su haka har barci ya kwashe ta. Bata farka ba sai daf da azahar, Dr Saleema data gama ganin marasa lafiya tana shan coffee ta kalle ta tace; "lallai sannu da barci", Nusram ba tare da tace komai ba ta miƙe ta zauna. Babu jimawa wata Nurse ta shigo kiran Dr Saleemar, dan haka cikin sauri ta miƙe, ta kalli Nusram tace; "Nusram zan shiga Theatre yanzu ga remote nan kiyi kallo idan anyi kiran sallah ga bayi nan sai kiyi alwala kiyi sallah, idan kuma kina jin yunwa ga wannan ki danna za'a zo sai ki faɗi abinda kike son ci, wata ƙila na jima sosai, wata mata ce take naƙuda to kuma abin yazo da gardama bari naje kinji", Nusram tayi mata fatan nasara kafin ta fice tana murmushi cike da yaba hankalin Nusram ɗin. Ta jima zaune kafin akayi kiran sallah, bayin ta shiga tayo alwala sannan tazo tayi sallarta, koda ta idar a wajen ta zauna tana tunani. Rayuwa kenan! Ko yaya ƴar uwarta take oho?, wane hali Ummi take shima bata sani ba, ƙaddara duk ta raba su kowa ya kama nashi wajen. Gashi bata da Number ɗin Nusreen balle ta kirata sai dai tana da number ɗin Ummi da ta Auntyn Tudu dan haka zata roƙi Dr Saleema ta ara mata waya sai ta kira su ko zata sami sauƙi. To yanzu ma ina mijin da aka ɗaura mata aure dashi, waye ya san inda yake ma?, tun jiya ko wane hali ta kwanta be dame shi ba. Wata zuciyar ta ce mata; "ke Nusram shiga hankalin ki, kin manta cewa Baba ya ɗauke ki kamar wata sanda ya bashi babu bincike ba komai, waye ya sani ma ko sadaka ya bashi?, bata san lokacin da hawaye suka fara kwaranya a idanun ta ba. Tun daga farkon tashinta ta fara tunani har kawo i yanzu, Baba be taɓa nuna musu ƙauna ba ita da ƴar uwarta, ka ɗauki mutum sukutum da guda ka bawa wanda baka sani ba. Shin wai haka duk iyaye maza suke, basu da tausayi, imani da kuma ƙaunar akan yaran su kodai sune basu yi dacen Uba ba?. Ta girgiza kai, ba haka bane ai tana zuwa gidan su Auntyn Tudu tana ganin yadda Abba ke haba haba da yaran shi har fira suke zama suyi dashi. Kwatanta halayyar mahaifinta tayi data Abban, kwata-kwata basu da kamanceceniya, tunda ta taso zata iya irga Albarkar da Baba ya taɓa saka musu, haka tunda take dashi be taɓa zama sunyi fira dashi ba kuma be taɓa tambayar me suke so ba ko meye damuwar su ba, shi dai kawai tunda ya haife su gani yake ya gama komai. hannu taji saman fuskarta wanda hakan shine ya dawo da ita duniyar tunanin data faɗa, ta ɗago idanun ta jajur ta zuba mishi su. Shima ɗin ita yake kallo, tun jiya daya koma gida ko barci be yi ba saboda tunanin halin da yake ciki. Ya kasa yanke shawara guda ɗaya shin ya faɗawa Brr Farida ne ko kuwa yaja bakin shi yayi shiru?, ƙarshe dai dole yaja matsaya akan kada ya faɗa mata. Yarinyar tana bashi tausayi idan yayi duba da irin yadda aka barota daga gida aka ɗauke ta aka damƙawa mutumin da ko sanin shi ba'a yi ba, dan ya tabbatar yanzu da zai koma wajen mahaifinta ba gane shi zai yi ba. Aiki ya taso dan shi a ƙa'ida huɗu yake tashi ko biyar, kamar ya wuce gida amma sai yaga rashin dacewar hakan, dan haka ya yanke shawarar zuwa ya duba halin data kwana. sanin cewa Saleema na asibiti yasa ya taho kuma yana da tabbacin Dr Saleema ba zata taɓa barin ta a gida ba. Ya daɗe tsaye kanta amma bata sani ba saboda dogon tunanin data tafi, ya kauda hannun shi daga fuskarta yace; "meke damun ki?". Kanta kawai ta saukar ƙasa, ganin bata bashi amsa ba yasa ya taɓe baki sannan ya miƙe ya koma saman kujera ya zauna. Nusram kuwa a yanzu shi kanshi haushin shi take ji domin kuwa shima yana tuna mata rayuwar ta da kuma zamowar shi silar barowar ta gida, duk da dai ta san cewa taimakon ta yayi. Jin an zare wayar hannun ta yasa ta kalle shi, wayar ya juya kafin ya kunna, hoton shi ya bayyana yayi murmushi sannan ya maida wayar ya ajiye. "da alamu dai ita kaɗai ta rage miki kadara ko?", ya faɗa, Nusram kuwa ko arziƙin kallo be samu daga gare ta ba, ya ɗan jingina da kujera yana kallon fuskar ta sosai. Bata ɗago ta kalle shi ba har yanzu kuma bata ce dashi uffan ba, ya kuma taɓe baki sannan ya kira Brr Farida. Tana jin shi har ya gama wayar shi, sannan ya kuma maida kallon shi kanta yace; "wai ke kurma ce kome?", nan ma bata yi magana ba. Ya sunkuyo dai-dai fuskarta a ɗan hasale yace; "haka daman aka koyar dake zaman auren?", har lokacin dai bata ce komai ba. Zuwa yanzu fa ya fara hasala ya riƙo fuskarta yace; "ni nake miki magana kina banza dani, baki san koni waye ba ko?". Nusram kuwa ganin ya takura mata ga halin da take ciki na damuwa yasa ta fincike fuskar ta, ta miƙe cikin sauri ƙafin taja tsaki ta juya domin tafiya. Ko taku biyu bata yi ba ya damƙota, hannunta ya murɗe ta baya ya jingina jikin ta da nashi. "ni kike yiwa tsaki?", ya faɗa a fusace, Nusram hawayen azaba ya zubo mata, ta runtse idanu tana me sakin kuka wanda hakan yayi dai-dai da shigowar Dr Saleema. Sai da gabanta ya faɗi wani abu ya taso ya tokare mata maƙogoro, ta juya tana ƙoƙarin ɗaukar laptop ɗin ta kana tace; "in tafi in barku ne ko kuwa zata zo mu wuce?". Babu wanda yayi magana a cikin su, sai lokacin taji shesheƙar kukan Nusram ɗin, da sauri ta juyo ta kalle su. Abdul kuwa kamar ma ba wani abun yake mata ba, ta kalli Dr Saleemar cikin tsananin azaba tace; "Aunty Saleema hannu na". Jin hakan yasa da sauri Dr Saleemar ta nufo inda suke, ganin yadda ya murɗe mata hannu yasa tayi saurin ƙarasawa inda suke. Hannun shi ta riƙo tace; "Abdul meye haka, dan Allah ka sake ta", kamar ba zai sake ta ba can kuma ya hankaɗe ta kana ya juya ya fice. Nusram ta faɗa saman carpet ɗin wajen kanta ya bugi kujera, taja numfashi sannan ta saki kuka. #LIKE #SHARE #COMMENTS *Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖57-58📖📖 Cikin sauri Dr Saleema ta ƙarasa kusa da ita, ta janyo zuwa jikin ta sannan ta saka hannu tana jijjiga ta alamar rarrashi. Sun jima a haka kafin Nusram ta tsagaita da kukan nata sannan Dr Saleema ta taimaka mata ta miƙe, da kanta ta kwaso mata jakarta da kuma wayar ta sannan suka fice daga office ɗin hannun su sarƙe dana juna. Ko da suka fara tafiya babu wanda yayi magana a tsakanin su har suka isa gida, suna yin parking motar Fadil ma na shigowa. Dr Saleema ta kalle shi tayi murmushi, shima da murmushi a fuskar shi ya gaishe ta, ta amsa cikin mutunci. Ya maida kallon shi kan Nusram, Nusram kuwa kanta na ƙasa tana shafa hannunta wanda yasha murɗa. "ina wuni?", ya faɗa, ba tare da ta ɗago ba tace; "lafiya lau", Fadila kam data kasa haƙuri ganin ƴar kyakkyawar baƙuwa a Estate ɗin su yasa tace; "Aunty Saleema ina kika samo wannan kyakkyawar". Dr Saleema tayi murmushi tace; "ƙawata ce dake karatu a nan KASU", Fadila ta matso kusa da Nusram ta riƙo hannun ta. "zaki zama ƙawata?", tambayar da Fadila tayi kenan, Nusram ta ɗago idanun ta kana ta zuba shi akan Fadila lumshe idanun tayi sannan tayi murmushi tana jinjina kai. Cikin jin daɗi Fadila tayi dariya tace; "Allah na gode maka na samu ƙawa kyakkyawa, ni sunana Fadila, mu ƴan biyu ne kinga ɗayan nan", ta faɗa tana nunan Fadil wanda ke tsaye yana kallon su. Shi sai yanzu yake ƙare mata kallo, lallai kyakkyawace yarinyar kuma ɗan uwan nashi ya sami mata me kyau, sai dai yadda auren nasu yazo ne abin babu daɗi. "yauwa kefa ya sunan ki?", Fadila ta kuma tambayar Nusram, Nusram tace; "sunana Nusram", cikin matuƙar murna Fadila ta maimaita sunan. "Wow! Nice name", zata kuma magana Dr Saleema taja hannun Nusram kana tace; "Fadila bari mu shiga ciki kinga yanzu muka dawo kuma duk mun gaji kuma kuje ku huta muma zamu huta anjima sai ku haɗu ko gobe". Daga haka suka yi sallama sannan suka tafi, Fadila dai sai santin kyawun sabuwar ƙawar da tayi take. Suna shiga suka sami Muhibba zaune da ita da Kamal, cikin sauri suka miƙe dukan su, Muhibba ta ƙaraso wajen Nusram da sauri. Ta riƙo hannun ta kana tace; "Nusram ɗita kun dawo, tun ɗazu nake zaman jiran ki", Nusram tayi murmushi, abin mamaki Kamal shima daya zuba mata idanu murmushin yayi. "Muhibba pls bakiga duk ta gaji bane ki bari ta huta mana", faɗar Dr Saleema kenan, Muhibba ta cuno baki tace; "Aunty to ki bari muje da ita nawa ɗakin sai ta huta ko?". Dr Saleema ta galla mata harara sannan taja hannun Nusram ɗin suka shige ciki, bayan sun zauna ta dube ta tace; "ki shiga kiyi wanka", bata musa ba ta miƙe ta fara kwaɓe kayan jikin ta. Dr Saleema ta miƙe ta fice wayarta a hannun ta, tana ƙoƙarin kiran Abdus-samad ɗin, be ɗaga ba har ta gama ringing ɗinta, dole ta haƙura. Nusram kuwa tuna irin yadda gidan suke sonta sai taji farin ciki, kowa ƙoƙarin janta yake yi, "Allah sarki Nusreen kin faɗi gaskiya, ina jin matsalolina sun ƙare kenan, da alamu lokacin farin ciki na nima yazo". Nace; "anya kuwa Nusram abinda kike tunani hakane?". Tana fitowa ta hau shiryawa, jar doguwar riga ƴar kanti ta saka mara nauyi, ba tare da ta ɗaura ɗankwalin ba ta yafa shi saman gashin kanta. Dr Saleema tayi sallama ta shigo itama jikin ta sanye da riga doguwa zubin buba amma ita dark blue, da alama wanka tayi ta shirya a wani ɗakin. "yauwa yanzu ki fito muje mu ɗan tattaka ko?", Nusram tace; "to Aunty", sannan ta biyo ta, haka suka jera har waje. Wannan karon babu kowa a falon sai Mummy, suka yi mata sannu da gida ta amsa kana suka fice, a ƙafa suke tafiya. Tafiya sosai suka yi, sun wuce gidaje, Nusram sai kalle-kalle take yi, akwai jama'a sosai a Estate ɗin kuma wasu idan sun zo wucewa sukan gaishe su ko kuma su su gaishe dasu. Abinda ta fahimta shine akwai girmama juna a tsakanin su, sannan kasancewar su ƴan boko yasa suke yin komai a waye babu gidadanci. Sun je wajaje da dama kamar filin ƙwallo, Cinema, Clinic, Hall etc, sosai Nusram ta yaba da tsarin Estate ɗin. Ana kiran sallar magrib suna shigowa gidan, sun samu falon babu kowa hakan ke nuni da sun tafi sallah kenan, don haka suma suka wuce suka yi alwala suka yi sallah. Basu tashi a wajen ba har sai da aka kira isha suka yi kana suka miƙe suka fito, duk suna kan dinning dan haka suma suka yi joining nasu domin cin abinci. Kamar dda safe Kamal da Kabeer idanun su na kan Nusram yayin da ita kuma duk ta jita a takure domin irin kallon da suke binta dashi. Haka dai har suka gama sannan suka koma saman kujeru suka zauna, Dr Saleema tace; "wai ina daddyn ne?". hafeeza tace; "wai ashe a Abuja ya sauka sai zuwa gobe zai sake biyo flight ya zo Kaduna", Dr Saleema ta jinjina kai alamar gamsuwa. Ɓangaren Nusram kuwa Muhibba ta maƙale mata sai surutu take yi mata yayin da Kamal da Kabeer suka maida ita abin kallo. Wani ta bata amsa wani kuma tayi murmushi kawai, Dr Saleema ta miƙe kana tace; "Nusram tashi muje ko?". Muhibba tace; "haba Aunty dan Allah yanzu ba zaki bari muyi fira ba, idan ma kunje ɗakin fa aiki zaki yi yayin da ita kuma sai dai ta zauna tayi shiru ko kuma tayi barci dan Allah ki barmu muyi fira ko Nusram ɗita?". Nusram ta ɗaga kai alamar eh, Dr Saleema zata kuma magana Mummy ta dakatar da ita; "ya isa haka ki tafi ki bar su mana", ba dan taso ba ta tafi ta barsu a falon. Har ƙarfe sha ɗaya da rabi suna tare suna fira kuma alhamdulillahi firar tasu ta ɗauke mata damuwar da take ciki, a yadda ta lura Muhibban babu ruwan ta akwai fira sannan idan ta kalle ta ta kan tuna mata da tata ƴar uwar wato Nusreen. Su Kabeer ma jefi jefi suka saka musu baki a firar tasu kan wani lokaci sai ga Nusram na kwasar dariya sosai. Mummy ta kalle su tace; "firar ta isa haka, Muhibba raka Nusram taje ta kwanta, kuma duk ku tashi haka sai da safe kuma". Muhibba ta riƙo hannun Nusram ɗin suka miƙe suka tafi, koda suka shiga sun samu Dr Saleema har tayi barci dan haka Muhibba tace; "kinga tayi barci kizo muje ki kwana a nawa ɗakin". Nusram tayi saurin girgiza kai tace; "a'a ki bari mu haɗu gobe", Muhibba taja numfashi tace; "shikenan, amma kinyi alƙawari gobe zaki zauna tare dani?". Nusram ta girgiza kai tace; "sai dai idan mun dawo tare da Aunty tukunnan", Muhibba tace; "shikenan Allah ya kaimu, gobe zaki shiga makaranta ne?", Nusram ta girgiza kai tace; "sai sati me zuwa asibiti dai zamu je tare da Aunty". "shikenan, amma sati me zuwan ki tabbatar kin neme ni kinji", Nusram tayi murmushi tace; "to shikenan", maimakon su rabu sai da suka ƙara ɓata awa ɗaya kana suka yi sallama da juna Muhibban ta tafi. Ranar Nusram da farin ciki ta kwana, tuni ta manta da abinda Abdus-samad yayi mata, lallai mutane rahama ne. ********* *********** *UNGUWAR SARKI, KAƊUNA* Abdus-samad na barin asibitin kai tsaye gida ya wuce, be samu Brr Farida a gida ba, dama kuma yayi tunanin hakan domin kuwa suma sun fara shirye-shiryen tafiya meeting. Sumayya ta taso da gudu ta tarbo shi, "Yaya sannu da dawowa", ya kama kumatun ta yaja yace; "yauwa ƴar ƙanwata". "Mummy ta tafi Court tace daga can zata wuce gidan Alƙali (Family House ɗin su)", jin abinda ta faɗa yasa yayi ajiyar zuciya sannan yace; "shikenan Allah ya dawo da ita lafiya, bari naje na huta", Sumayya ta amsa da to. Yana shiga bedroom ɗin shi wayar shi nayin ƙara, Khausar ce dan haka ya ɗan yi jim kafin ya ɗaga. "Hi, barka da yamma", abinda ta faɗa kenan bayan ya ɗaga, kamar wanda aka tilastawa yace; "ya kike?". "Lafiya lau nake, sai dai har yanzu da ka ƙi yarda mu kuma haɗuwa shine abinda ke damuna". Beyi magana ba saima kwaɓe kaya da ya fara yi, jin yayi shiru yasa ta kuma cewa; "dan Allah ka bani address ɗin ka idan yaso ni sai nazo". "zan shiga wanka, na gode da gaisuwa ko?", ya kaudar da waccen maganar, ta ɗan yi jim alamun ba haka taso ba cikin sanyin murya tace; "shikenan sai anjima", be bata amsa ba ya katse wayar. Yana ajiyewa kiran Dr Saleema ya shigo, kamar tana gaban shi ya haɗe rai, tunowa da abinda yarinyar tayi mishi a rayuwar shi ya tsani mace me tsiwa. Da ganin tana da rauni yasa yake tausayin ta amma abinda tayi mishi yau sai ya saka yaji ya tsane ta sosai, wayar ya ajiye kana ya shige bayi. koda ya fito shiryawa yayi kawai cikin kaya marasa nauyi sannan ya fice daga ɗakin, babban falo ya nufa inda ya sami Brr Farida zaune ga kaya a gabanta. Ya ƙarasa inda take ya kwanta saman ƙafar ta, Brr Farida da suke lissafi da Tameer da Sameer ta ɗago ta kalle shi, murmushi tayi kafin suka cigaba da abinda suke yi. Yana kwance yana jin su har suka gama sai da aka fara kiran sallah sannan ya miƙe, itama Brr Faridar ta miƙe hannun su sarƙe dana juna suka nufi sama. A bayin ta yayi alwala sannan ya fice masallaci, inda ita kuma tayi tata alwalar ta kabbarta sallah. Be dawo ba sai da akayi isha'i, yana shigowa Daddyn su shima ya shigo dan haka tare suka jero. Suna yin sallama, Adnan ya taso da gudu yana; "Oyoyo Daddy", Dr Abubakar ya ɗaga ɗan nashi sama yana cillawa yana dariya. Brr Farida ta ƙaraso inda suke, ɗan rungume juna suka yi kana tace; "barka da dawowa Likitana". "sannu da ƙoƙari Lauyata", suka saki dariya a tare, Abdus-samad ya kauda kai yana murmushi, hannun shi Brr Farida ta riƙe. Ya ɗago ya kalleta yana ƙwaɓe fuska, kafin yace wani abu taja hannun shi sun shige ciki, kan dinning duk suka ƙarasa. "ku bamu minti goma sha biyar muna zuwa", ta faɗa sannan taja hannun Dr Abubakar suka hau sama. Sun jima kan su sauko, a maimaikon coat dake jikin Dr Abubakar ɗin yanzu jallabiya ce dark blue alamu na nuna wanka yayi kenan. Sun ci abinci sannan suka koma saman kujeru inda suka dasa fira, shi dai Abdus-samad da idanu kawai yake bin su. Yana da tarin tambayoyi wanda ya san Brr Farida ba zata amsa mishi su ba, tabbas yana ji a jikin shi a rayuwar shi akwai wani al'amari me girma. To menene wannan? Amsar da baya da ita kenan, kuma wacce keda ita ba zata taɓa yarda ta faɗa mishi ba, to akan wane dalili kenan?. har suka tashi daga firar ya saƙa wancan ya warware wancan haka ya tafi ɓangaren shi cike da tarin tambayoyi a ranshi wanda be samu amsar su ba ko kaɗan. Koda ya kwanta barci bezo mishi ba dan haka duniyar tunani ya faɗa wanda ba zai amfane shi da komai ba. Brr Farida dake tsaye saman kanshi taja numfashi, tun ɗazu ta shigo amma be sani ba kuma idanun shi biyu. "anya kuwa nayiwa yaron nan adalci kuwa?, to me zan fada mishi? Taɓa shin da tayi shine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa, "First Love har kin shigo?". Ta riƙe hannun shi tace; "Baby bana so kana damun kanka, ka kwantar da hankalin ka ka dena tunanin akwai abinda nake ɓoye maka, abinda nake son ka dashi shine ka cigaba da addu'a kawai". Abdus-samad ya ɗaga kai, ta shafa fuskar shi tace; "yauwa My Boy", addu'a tayi mishi sosai kafin ta fice daga ɗakin. Abdus-samad yabi bayan ta da kallo yana mamakin yadda take nuna mishi babu komai bayan alamu sun nuna akwai abinda take ɓoye mishin. Haka ya cigaba da tunani har barci ya kwashe shi be sani ba. yau saura kwana biyu su tafi Rigasa meeting, duk wani abu da suka san zasu samar dashi ta ɓangaren su to sunyi kamar kayan da zasu saka, abinda za'a tafi dashi da sauran su. Brr Farida da kanta ta shiga gyara yaran nata, sai da ta tabbatar da komai ya tafi dai-dai sannan hankalin ta ya kwanta, washe gari kawai hanya zasu ɗauka domin ana gobe kowa ke zuwa kuma ba'a dawowa sai washe gari kwana biyu kenan da ɗan gari da wanda ba ɗan gari ba duk sai sun hallara. Taro ne wanda yake da girma sosai sau ɗaya suke yi a shekara dan haka kowa yakan bar duk abinda yake yi domin ya halarta. Yau dai Abdus-samad yake ƙoƙarin amsa gayyatar Khausar a karo na farko, dan haka koda ya taso wajen aiki part ɗin shi ya wuce wanka yayi kafin ya shirya domin tafiya. Farin yadi ya saka me shara-shara wanda babu hayaniya tare dashi domin kuwa aikin da akayi mishi kaɗan ne, kanshi sanye da hula zanna bukar sai maiƙo take yi. Ya feshe jikin shi da turare sannan ya kwashi wayar shi da makulli ya fice. Tunda ya doso falon ƙamshi ke tashi, duka suka bishi da kallo, Sumayya tace; "wow! Yaya ka ganka kuwa gaskiya kayi kyau". Tameer yace; "wannan wanka haka sai ina?", Sameer yace; "kai daga ganin wannan wankan ai sai wajen ƙanwar mu ko?", shi dai be ce komai ba sai murmushi da yake yi. Jin abinda Sameer yace yasa ya kalli Brr Farida, itama shi take kallo tana so ta gano gaskiyar abinda Sameer yace hakanne, hasaso me take ƙoƙarin yi yasa shi saurin kauda nashi idon kafin yace; "First Love bari naje wajen wani abokina na dawo". Kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa, cikin sanyin murya tace; "a dawo lafiya", ya amsa da ameen sannan ya juya ya fice. Brr Farida ta bishi da kallo kana tayi ajiyar zuciya, idan kuma abinda Sameer ya faɗa gaskiya ne fa?, tuna hakan yasa gaban ta faɗuwa. Zata yarda da komai amma ba zata lamunci wai Babyn ta yaje taɗi wajen wata ba, ita da kanta zata nemo mishi mata me kyau da asali da dukiya ba wai ƴar matsiyata ba. Cikin sauri ta janyo wayar ta, wata number ta nemo wacce aka yi saving da Jameel, wajen message ta shiga. *Ga Abdus-samad nan zai fito yanzu ku tabbatar kun bishi kunga inda yaje, ku kira ni ku faɗa mini*. Wannan shine abinda saƙon nata ya ƙunsa, tana turawa ta ajiye wayar cikin damuwa, yaran ta kuwa sanin inda damuwar ta take yasa suka tashi suka bata waje. Duk suna mamakin yadda ƙarara bata so a jinginawa Abdus-samad ɗin budurwa, ko meye dalilin ta oho!. Abdus-samad kuwa kai tsaye ya yiwa Unguwar su Khausar kutse, ya sami securities a tsaye a bakin wajen, be wani sha wahala ba domin kuwa Khausar ɗin ta sanar dasu zuwan nashi. Ɗaya daga cikin masu tsaron gidan shine yayi mishi jagora har cikin falon baƙin, Abdus-samad yabi falon da kallo sosai tsarin falon ya birge shi. Gida ne wanda ya amsa sunan shi ya ƙayatu sannan kana gani ka san cewa mamallakin gidan me kuɗin gaske ne bana wasa ba. Wata ƴar matashiyar budurwa ta tura ƙofar ta shiga, tana zaune saman kujerar kwalliya tana fuskantar madubi, budurwar ta ɗan taɓe baki. Tun da aka gama kwalliyar take zaman kallon kwalliyar wacce aka kashe maƙudan kuɗi domin yin ta, gaba ɗaya jiya zuwa yau ta hanasu sukuni da zuwan baƙon nata. "Aunty baƙon ki ya iso yana falon ƙasa Hassan yace a sanar dake", jin abinda aka faɗa yasa tayi wuf ta miƙe, turare ta ɗauka ta kuma fesawa a jikin ta a karo na babu adadi ta kuma kai kallon ta jikin madubin. Ta kalli matashiyar nan tace; "dan Allah nayi kyau kuwa Siddiƙa kina ganin zan iya birge shi". Siddiƙa tace; "wallahi kin yi kyau sosai kuma koshi dutse ne sai yaji kin birge shi", jin abinda Siddiƙar ta faɗa yasa tayi ihu ta runguma Siddiƙar. Sai kuma ta sake ta kafin ta ƙara gyara kanta sannan ta fice, cikin yauƙi da yanga ta nufi falon baƙin. Hajiya Salma dake hangota ta taɓe baki tana jan dogon tsaki, yaushe zata yarda shirin ta ya ruguje, tuno abinda suka shirya yasa ta saki dariya. Cikin sauri ta nufi kitchen ɗin kulolin dake saman cabinet ɗin ta buɗe lafiyayyen girki ne wanda Khausar ɗin ta saka akayi domin tarba Abdus-samad. Sai da ta leƙa ta tabbatar babu wanda ya taho sannan ta ciro wani ƙullin magani ta buɗe ta zuba a ciki, cikin sauri ta rufe ta fice daga kitchen ɗin. Khausar ta shiga da sallama a bakin ta, Abdus-samad ya amsa mata, ta ƙaraso da sauri kamar zata shige jikin shi. ya ɗan janye daga jikin ta, "finally yau gashi kazo gidan mu", yayi murmushi kawai. Jameel ya kira Brr Fairda ya faɗa mata cewa Abdus-samad gidan Alhaji Mustapha Tuge ya shiga, sosai hankalin ta ya tashi jin abinda aka faɗa. Meye alaƙar shi da Alhaji Mustapha ne da har yaje gidan, lallai dole ta ɗauki mataki idan ba haka ba asirinta yana daf da tonowa. "oh! mustapha na tsane ka a rayuwata", abinda ta faɗa kenan. Khausar ta ƙwalawa Siddiƙa kira, cikin sauri tazo, "muje mu kawowa baƙona abin motsa baki", hakan ta faɗa sannan suka fice daga ɗakin. Babu jimawa suka dawo ɗauke da wa'innan kololin, Hajiya Salma dake laɓe ta saki murmushi a ranta tace; "taka ta ƙare Abdus-samad". ta kalle shi tana me tura mishi plate ɗin tace; "dan Allah kaci mana, tun safe nake wahala akan wannan girkin dan Allah kaci". Abdus-samad yayi murmushi sannan yaja plate ɗin gaban shi, cokali ya saka ya ɗebo haɗaɗɗiyar fried rice ya kai bakin shi...... *ban san haka littafin nan haka yake da masoya ba sai jiya, gaskiya naji daɗi sosai Allah ya saka da alkhairi nagode sosai*. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouƙ*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* *Fatima Janyau (Teeymer) Shadown mu, keda Fatima Umar Modibbo (Bloody na), ku sani nima ina sonku sosai kamar yadda kuke sona* 📖📖59-60📖📖 Ƙarar wayar shi shine yayi sanadiyar da ya fasa kai abincin bakin shi, ya zaro wayar daga aljihun shi ganin Brr Farida yasa gaban shi faɗuwa. Miƙewa yayi cikin sauri sannan ya ɗaga, Brr Farida najin an ɗaga cikin tashin hankali tace; "Abdus-samad meye ya kaika gidan Alhaji Mustapha?? Me kake nema wanda banyi maka shi ba?? Me yasa baka gudun ɓacin rai na duk irin son da na nuna maka shine kake ƙoƙarin juya mini bay............", bata sami damar ƙarasawa ba saboda kukan daya kufce mata, cikin sauri ta katse kiran. Idan hankalin Abdus-samad ya kai dubu to sai da ya tashi, sakato ya tsaya riƙe da waya a hannun shi, what! A dalilin shi First Love ke zubar da hawaye🙄 Lallai ya aikata laifi mafi girma a rayuwar shi. Khausar dake tsaye bayan shi tayi saurin ƙarasowa kusa dashi, hannu ta kai ta riƙo nashi tace; "Abdul meya faru?". "Dan Allah ki ƙyale ni", abinda ya sami damar faɗa kenan yana kuma ƙoƙarin zare hannun shi dake cikin nata. Khausar ta kuma riƙe hannun gam tace; "Abdul dan Allah kada ka rabu dani, ka tsaya dan Allah.....", wata tsawa ya daka mata wacce ta saka da sauri ta janye daga inda yake. Ya jefe ta da wani kallo kafin ya juya ya fice daga falon, dai-dai zai shiga motar shi Alhaji Mustapha ya shigo, kallo ɗaya Abdus-samad yayi mishi ya ɗauke kai. A halin yanzu duk sai yaji ya tsani Alhaji Mustaphan da duk wani abu daya shafe shi, ba zai iya jure ganin abinda zai zama sanadiyar zubar hawayen Mahaifiyar shi ba. Cikin sauri ya buɗe motar shi ya shige kana ya fice daga gidan cikin matuƙar tashin hankali. Alhaji Mustapha ya bishi da kallo hankali tashe, meya same shi?, ko dai wani abu ne ya faru dashi?", menene silar shi zuwa gidan?". Cikin sauri ya nufi hanyar da zata sada shi da cikin gidan shi amma hakan ya gagara, dan haka ya juyo ɗaya daga cikin securities ɗin shi ya kira. "Muhsin ka tabbatar da cewa yaron da ya fita ya isa inda yake son zuwa cikin ƙoshin lafiya", abinda ya faɗa kenan kana ya juya ya shige gida. Ɓangaren Khausar kuwa tana ganin fitar Abdul ɗin ta saki wani irin kuka me ban tausayi, ita kuwa ya zata yi da rayuwar ta kenan?", kamar wacce aka tsikara ta miƙe da gudu ta bar ɗakin. Hajiya Salma dake zaune tana huci, duk abinda ya faru akan idanun ta ya faru, kwata-kwata sun kasa ida nufin su kan wannan yaron gaba ɗaya so yake ya zamar musu *RAINA KAMA*. Duk wani buri nasu da suke dashi ba zai taɓa cika ba matuƙar wannan yaron yana raye a duniya lallai dole su san yadda zasu yi ya bar duniya. Faɗowar Khausar jikin ta shine ya dawo da ita daga kogin tunanin da ta faɗa, Khausar cikin kuka tace; "Mummy soyayyar Abdul zata kashe ni". Wannan maganar karaf a kunnen Alhaji Mustapha, saukar ta kuma dai-dai da saukar aradu ya jita, cikin sanyin jiki ya ƙaraso falon inda Hajiya Salma ke aikawa da Khausar ɗin harara. "yauwa Alhaji gwara daka dawo, yarinyar nan kan wannan yaron so take ta kashe kanta", abinda Hajiya Salma ta faɗa kenan cikin jin haushi. Alhaji Mustapha dake zare idanu kamar wanda yayiwa Sarki ƙarya cikin inda-inda yace; "ki barni da ita Hajiya sai na ɗauki mataki akan ta tukunna zata ƙyale yaron nan, Khausar wannan yaron ba sa'an auren ki bane, ki manta dashi da wata banzar soyayyar da kike yi mishi kinji". Khausar ta cuno baki kana ta miƙe ta bar wajen, ita bata san me yasa iyayen nata suke ƙinta da Abdul ba, ita kuma tayi alƙawari akan soyayyar Abdus-samad babu gudu babu ja da baya. Hajiya Salma ta miƙe ta bar falon cikin sauri, ita wallahi da be ci ba ji take kamar ta ɗora hannu a kai ta saki ihu ko zata sami sauƙin abinda taƙe ji a ranta. Ta zaro wayar ta sannan ta kira Alhaji Sa'eed, yana ɗagawa tace; "Alhaji kaga wacan ɗan iskan yaron beci wannan abincin ba?". Alhaji Sa'eed yayi wani ihu kana ya zunduma ashar yace; "Salma wasa kike yi mini ko?, kin san kuɗin dana kashe wajen samo wannan maganin ko kin san irin wahalar dana sha kan na samo wannan maganin?". Jin shiru ya kuma hasala shi, cikin ɗaga murya yace; "sai da naje har ƙasar India, a Kashmir na sami bokan daya bani wannan maganin, da ƙafa na hau saman dutse me ƙanƙara, ya bani tabbacin mutuwar Abdus-samad wanda ba zata bar alamar komai ba, zai yi hauka kafin nan ya mutu mutuwar wulaƙanci, na yarda dake na ɗauki maganin na baki ga dama ta samu amma kika bari har ya tafi be ci wannan maganin ba?". Salma tayi huci tace; "wallahi komai ya tafi dai-dai bansan ɗan iskan yaron nan meya tuna ba wanda ya hana shi kai abincin nan bakin shi". Alhaji Sa'eed yace; "duk yadda za'a yi ki tabbatar da cewa yaci wannan abincin idan ba haka sharrin da zai biyo baya ban san nima wane kala ba ne", daga haka ya katse wayar. Hajiya Salma ta zuba uban tagumi yanzu ita yaya zata yi ta janyo Abdus-samad ɗin har yaci wannan abincin?, tunawa da bata kwashe abincin ba a wajen yasa ta miƙe zumbur. Ɓangaren Alhaji Mustapha kuwa jiki a sanyaye ya wuce nashi ɗakin, zarya ya fara yi tsakanin falo zuwa bedroom ɗin shi, lallai dole ya ɗauki mataki idan ba haka ba kwaɓar shi zata yi ruwa. Hannu ya ɗaga sama yace; "ya Allah duk da na san cewa ni me laifi ne amma ina roƙon ka daka kawo mini mafita da gaggawa". Wayar shi ya ciro ya fara kiran Brr Jabeer, bata jima tana ringing ba Brr Jabeer ya ɗaga. "Alhaji dama ina so mu haɗu domin magana akan takardun wannan companyn naka na garin jos". Alhaji Mustapha ya tare shi; "dakata Brr ba wannan yasa na kira ba, Brr asirina yana daf da tonowa, Khausar da gaske son Abdus-samad take yi, na rasa ina zan saka kaina". Brr Jabeer ya ɗan yi jim kana yace; "Alhaji Mustapha lokaci yayi daya kamata ka fito ka shaidawa duniya cewa Abdus-samad ɗan ka ne koda Brr Farida taso ko bata so ba". Alhaji Mustapha yace; "wannan ba zai taɓa yiwuwa ba, Brr nafi so wannan maganar ta cigaba da kasancewa sirri sama da bayyanar ta domin idan ta bayyana tofa tawa ta ƙare". Brr Jabeer yace; "Alhaji Babu fa abinda yake kasancewa sirri har abada dole watan wata rana Abdus-samad ya san gaskiyar abinda ya faru". "bayan mutuwa ta ko?, da wane idanu kake so na kalli yaron nan idan gaskiyar lamari ya fito wallahi bana da wannan ƙarfin halin, dan haka ka canza shawara kawai". "to shikenan Alhaji duk yadda kayi ma ai dai dai ne domin kuwa banda shawarar data wuce wacce na baka, sai anjima zan shigo insha Allahu". Daga haka ya katse wayar, Alhaji Mustapha dai shiru yayi yana nazari kan wannan lamarin dake neman dagula mishi lissafi. ******* ******** *HAYIN RIGASA, KADUNA* Yau saura kwana biyu a gudanar da meeting ɗin iyalin na wannan gidan wanda yayi dai-dai da kwanan Nusram takwas a gidan. Zuwa wannan lokacin Nusram ta saba da ƴan gidan sosai musamman ma Dr Saleema wacce bata barin ta cikin kaɗaici sannan ga Muhibba da kuma Fadila wa'inda suka bi suka liƙe mata. Duk yadda Nusram taso kaucewa Kabeer da Kamal abin ya faskara domin da zarar sun zauna ita da Muhibba a falo tofa suma zasu zo su zauna ga kallo da suke binta dashi. Ɓangaren Nusram hankalinta ya kwanta sosai da sosai, sai dai har lokacin tunanin ta da zuciyar ta yana kan ƴan uwanta da mahaifiyar ta, sauƙin ta ma da yake yau suka je suka yi registration, wannan abu shine ya ƙara sauƙaƙa mata abinda yake damun ta domin ta san cewa idan har ta shiga makaranta zata samu damar ganin ƴar uwarta. Abdus-samad kuwa rabon data ganshi tun ranar da yazo ya murɗe mata hannu, bata damu da rashin ganin shi ba domin Dr Saleema ta tsaya mata akan komai. Gidan sosai ya kacame domin duk wani na nesa ya iso, na kusa kuma washe gari ake saka ran na kusa su iso suma, wannan dalilin yasa Nusram ja baya don tunda suka dawo daga asibiti bata leƙo falo ba domin komai taga na ƴan boko ne. Dole Muhibba da Fadila suka biyo ta har ɗaki suna tambayar ta lafiya nan dai ta sanar dasu ita lafiyar ta lau, ita kuwa Dr Saleema bata ce mata komai ba dan itama ba hayaniyar ta cika so ba. Ɓangaren Abdus-samad kuwa a gigice ya isa gida, ko gyara parking beyi ba ya afka cikin gidan. A falo ya sami Brr Farida ƴaƴan ta kuma duka sun zagaye ta fuskar su ɗauke da damuwa. Cikin sauri ya nufo inda take amma tsawar data daka mishi shine silar da ta saka ya dakata. Ta ɗago fuskarta tayi ja alamun tasha kuka ta ƙoshi da hannu take nuna mishi hanyar waje. Wannan karon kam har su Sameer sun tsorata da yanayin mahaifiyar tasu, "ba magana nake maka ba ka fita nace!!!!", ta sake faɗa da ƙarfi Abdus-samad gaba ɗaya ruɗewa yayi ya rasa ina zai saka kanshi, shin fitar zai yi ko kuwa tsayawa zai yi. Brr Farida ta miƙe a fusace tace; "tunda kai ba zaka fita ba ni bari na fita", jin hakan yasa da sauri Abdus-samad ya juya ya fice daga gidan. Kan sitiyarin motar shi ya ɗora kanshi yana sakin ajiyar zuciya, idanun shi jajir saboda tashin hankali, be taɓa zaton ƙiyayyar da Mahaifiyar shi take yiwa Alhaji Mustapha ta kai haka ba. Yanzu ina zai saka ranshi kenan?", wata zuciyar tace; "ka wuce Hayin Rigasa kawai", ya girgiza kai a fili yace; "babu inda zan je". Shigowar motar Dr Abubakar itace ta saka shi sauke ajiyar zuciiya, cikin sauri ya fito, Dr Abubakar ɗin yayi saurin taro shi zuwa jikin shi ganin halin da yake ciki. "Meya same ka?, baka da lafiya ne?", tambayar da Mahaifin nashi ya cillo mishi kenan. Abdus-samad ya girgiza kai, cikin dasashshiyar murya yace; "Daddy First Love ce". jin sunan da ya ambata ya saka hankalin Dr Abubakar tashi sosai a gigice yace; "meya same ta ne?". Abdus-samad ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar dashi, sai lokacin hankalin Dr Abubakar ya ɗan kwanta. Ya riƙo hannun Abdus-samad yace; "Abdul Mahaifiyar ku tana ƙoƙari wajen inganta rayuwar ku ya kamata ace duk abinda ta nuna bata so to ku guje shi", ya ɗan yi mishi nasiha sannan yace su shiga ciki. Babu kowa a falon don haka sama suka wuce ɗakin ta, Brr Farida dake jikin window tana kallon komai ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna saman gadon ta. Ita da kanta tace ya bar gidan amma kuma zuciyar ta taƙi bata haɗin kai, ta gode Allah da mijin nata ya dawo dashi, bata so ta nunawa maƙiyanta ta gaza. Sallamar da suka yi itace ta dawo da ota daga tunanin da take yi, kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kai. Ta miƙe zata bar ɗakin Dr Abuɓakar yayi saurin riƙota, "Haba Brr kada ki kwashe ladan aikin da kika yi tsayin shekaru ashirin da bakwai mana". "dan Allah First Love kiyi haƙuri, banyi tunani zuwana gidan Alhaji Mustapha zai ɓata miki rai har haka ba" , Brr Farida tayi shiru kamar bata ji shi ba. Kusa da ita ya matsa ya ɗora kanshi saman kafar ta, bata kalle shi ba balle ya saka ran zata saurare shi, zuwa yanzu ya fara gazawa. Cikin murya me rauni yace; "na san nayi laifi dan Allah ki yafe mini, idan baki yafe mini ba ban san inda zan saka raina ba", zata ture shi Dr Abubakar ya girgiza mata kai. Cikin dauriya tace; "naji zan yafe maka amma da sharaɗin ba zaka kuma aikata wannan kuskuren ba, matuƙar ka kuma gigin zuwa inda Alhaji Mustapha yake to sai dai ka nemi wata uwar bani ba". Ya ɗan yi jim yana kallon ta, a matuƙar tsorace yace; "First Love naji na amince amma dan Allah kada kiyi mini baki", ta ɗan yi murmushi tace; "ba zan yi maka baki ba Abdul ko dan soyayyar da nake yi maka, amma matuƙar ka cigaba da bibiyar Alhaji Mustapha tofa zamu raba hanya dan mutum ne dana tsane shi na tsani wanda ke son shi". "to ki faɗa mini abinda ya shiga tsakanin ku har kike mishi wannan ƙiyayyar", kamar ya watsa mata wuta haka ta miƙe, idanun ta ya kaɗa yayi jajir, da hannu ta nuna shi tace; "ba sai kaji ba, na sha gargaɗin ka da cewa ka fita tsakani na da Alhaji Mustapha ba abinda ya shafe ka bane amma kana neman ka zama mara jin magana ko". Ganin abin zai yi tsayi ne yasa Dr Abubakar jan hannun Abdul zuwa waje, "Abdul ka rufawa kanka asiri ka dena tambayar mahaifiyar ku menene tsakanin ta da Alhaji Mustapha idan ba haka ba zaka nemowa kanka bacin rai ne kawai". Kan shi a ƙasa yace; "in Allah ya yarda Daddy ba zan kuma ba dan na lura abinda ke tsakanin su be shafe ni ba", Dr Abubakar ya jinjina mishi kai. Abdus-samad cikin sanyin jiki ya juya ya bar wajen, Dr Abubakar ya bishi da kallo cikin tausayawa, rayuwar yaron tana cikin hatsari me girma gashi shi kanshi yaron be san menene takamaimai ainihin abinda ya janyo hakan ba, tun ba yanzu ba yake fama da matar tashi akan ta fito ta faɗawa yaron gaskiya amma hakan ya gagara. kuka ya same ta tana ta faman yi, Dr Abubakar ya zauna kusa da ita ya riƙo hannun ta kana yace; "Brr Farida ya kamata ace zuwa yanzu kin zama jarumar da zaki dena zubar da hawayen ki akan Alhaji Mustapha, ki dinga daurewa idan ba haka ba zaki saka shakku a zuciyar yaran ki musamman Abdus-samad". Brr Farida ta girgiza kai cikin kuka tace; "Alhaji Mustapha ya cuce ni, cutar da bazan taɓa yafe mishk ba, kuka kuma dole ne inyi ko dan rage raɗaɗin da zuciyata take yi mini". Cikin tausayawa ya janyota zuwa jikin shi, yace; "Brr Farida ki zama jaruma sannan ki daure ki bari a sanar da Abdus-samad abinda ya shafi rayuwar shi idan ba haka ba zai cigaba da zama da maƙiyan shi kana kuma yana musu kallon masoyan shi". Cikin kuka tace; "tsoro nake ji dakta, kada Abdul ya guje ni, kada hakan yayi sanadiyar rushewar farin cikin shi, kada na shiga jerin wa'inda zai dinga zargi, ba zan iya ba, a kullum idan naga farin ciki da ƙaunata a idanun shi ina jin farin ciki sosai bana so wa'innan abin so kuma ƙiyayya da kuma damuwa ba zan so abinda zai nisanta ni da ɗana ba". #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖61-62📖📖 tunda ya bar ɗakin, part ɗinshi ya wuce kai tsaye, saman gadon shi ya faɗa, ya saki ajiyar zuciya me ƙarfi, be san meyasa ba sai yake jin kamar akwai wani abu da Mahaifiyar tashi bata so ya sani. "zan barta har zuwa lokacin data faɗa mini da kanta", wannan shine abinda zuciyar shi take faɗa mishi. Runtse idanu yayi ga gaban shi dake faɗuwa, gobe ne zasu tafi Hayin Rigasa be san me zai faru ba wajen taron. Tashi yayi ya faɗa bayi, yayi wanka sannan yazo ya kwanta, ya san cewa rayuwar shi yanzu ta fara zama abin tausayi. Brr Farida ta turo ƙofar a hankali ta shigo, ja tayi ta tsaya tana kallon shi, ɗakin babu haske sosai sai dai dim light daya kunna wacce ke gefen gado, da wannan ta sami damar ganin fuskar tashi. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kana ta matsa kusa dashi, tun daga saman kanshi ta shafa har zuwa fuskar shi, hawayen dake kwance gefen idanun ta suka zubo. Ta haɗiye wani abu me ɗaci a maƙogoronta, bata so ta bata da kanta, bata so ace Alhaji Mustapha yaci nasara akanta, amma babu yadda zata yi tausayin abar ƙaunar nata ya hana ta nuna jarumta. A nutse ta fara jero addu'o'i haka hawayen dake fuskarta be dena zuba ba, ta shafe mishi jiki dashi. Hannun shi ta riƙe gam tana sakin kuka me ban tausayi, "ya zanyi Abdus-samad, tausayi da ƙaunar da nake yi maka tana neman ta zamar dani raguwa", hannun ta sumbata kana ta miƙe ta fice daga ɗakin tana sharar hawaye. Washe gari da safe kowa ya kama shiri domin tafiya Hayin Rigasa, shi dai Abdus-samad ba wani daɗin tafiyar yake ji ba, dan gaba ɗaya gaban shi faɗuwa yake yi. Brr Farida dake shirya abubuwan da zasu buƙata ta kalle shi sannan tace; "meya faru ne?", ya shagwaɓe fuska yace; "First Love bana son wannan tafiyar". Brr Farida tayi mishi hararar wasa tace; "so kake yi kenan ka ɗauko mini magana, daman nice kullum me laifi". Sameer yaja tsaki yace; "nifa wallahi wannan gidan ba ɗaɗa ni da ƙasa yayi ba, haka kawai duk sun bi sun ishi mutane, dan dai baka da yadda zaka yi ne". "to idan baka je ba waye kake gani zai yi maganar auren ku, ni dan Allah tashi ka bani waje", abinda Brr Farida ta faɗa kenan. Sameer ya tashi yana ƙunƙunai ya fice, duk wannan abin dake faruwa idanun Abdul a lumshe suke, har wannan lokacin baya jin tafiyar a cikin ran shi. ******* ********* Fadila ta tuntsire da dariya, Muhibba ta harare ta kana tace; "ai wallahi gadkiya na faɗa, kuma zaki gani gobe ko kwalliyar da zan yi sai tafi ta kowa kyau". Fadila ta kuma dariya kana tace; "hakane sarauniyar gidan mu, amma dai kin san a kwalliya akwai Nihal ko sannan akwai kuma akwai Abdus-samad, dan haka kema kin san ba zasu bari ki kada su gobe ba amma Allah ya kaimu goben ban san wane tanadi kika yi ba". Muhibba taja tsaki tace; "sai anyi magana ki wani kawo maganar waccen banzar nifa bata dame ni ba, kowa ma ai ɗan gatan iyayen shi ne". Nusram dai kawai da idanu take bin su, ita kanta zuwa yanzu ta fara shan jinin jikin ta domin baƙin da suke zuwa da kuma yadda estate ɗin ke cika. Dr Saleema ta shigo ɗakin hannun ta riƙe da foil paper, "ku baku san kuyi shiru bane duk kun damu mutane da hayaniya", duka suka ja bakin su suka yi gum. Hannun Nusram ta riƙo tace; "taso muje ki rakani wani waje", Nusram ta miƙe yayinda Fadila da Muhibba suka turo baki gaba. "dan Allah ke Aunty Saleemar nan sai muna cikin farin ciki zaki zo ki wani ɗauke ta", faɗar Fadila kenan. Dr Saleema tace; "ni dan Allah ku ƙyale ni, Saloon zamu tafi tare da ita", da sauri duka suka miƙe suna faɗin muma zamu je. Dr Saleema tayi murmushi tana faɗin; "ai sai kuyi sauri ku shirya, bari naje na kaiwa Abba wannan saƙon", ta ƙarasa tana jan hannun Nusram ɗin. Wata ƙofa taga ta buɗe sai wani siririn corridor da suka bi, sun ɗan yi tafi me tsayi kafin suka iso matattakala, nan suka hau suna buɗe ƙofa wani haɗaɗɗen falo suka shigo. Nusram ta saki baki tana kallo, koda wasa ba zaka ce gidan ya kai girman haka ba, shiru falon sai tibin dake magana. Wani mutumi suka samu zaune wanda Nusram ke kyautata zaton shine mahaifin nasu dan ita basu taɓa haɗuwa ba tunda yazo. Ya ajiye jaridar dake hannun shi yana kallon su, Dr Saleema ta ƙaraso da sauri kusa dashi, ɗan sunkuyawa tayi ta sumbaci goshin shi sannan tace; "barka da hutawa ga sandwitch ɗin", ta ƙarasa tana ajiyae foil paper ɗin hannun ta. Bece komai ba sai ɗaga kai da yayi, ta juya kenan aka buɗe wata ƙofa aka shigo, wata mata ce me kauri gajeruwa sai dai tana haske sosai koda ba'a faɗawa Nusram ba ta san cewa wannan itace kishiyar maman su Dr Saleemar. "barka da hutawa Aunty", bata ma kalle ta ba ballantana ta amsa mata, Dr Saleema ta juya ta kama hannun Nusram. "wacece wannan?", tambayar da Mahaifin nasu yayi mata kenan wanda yasa suka tsaya, ba tare da shakka ko fargaba ba tace; "ƙawata ce". Bece komai ba sai dai kallo daya bi Nusram ɗin dashi, har taji kamar ta harɗe ta faɗi, suna fita tayi ajiyar zuciya. Dr Saleema ta kalle ta tace; "ya dai?", Nusram tayi murmushi tace; "babu komai", babu wanda ya kuma cewa komai har suka ƙarasa harabar gidan. A wajen suka sami Fadila da Muhibba da kuma Fadil, mukullin ta miƙawa Fadil ya amsa. Duka suka buɗe suka shiga, Nusram, Muhibba da Fadila suna baya, yayin da Dr Saleema ke gefen Fadil ɗin a gaba. Nusram taba hanyar da kallo, sai hada-hadar shigowa ake yi ga manya manyan motoci da suke shigowa cikin Estate ɗin wannan yake tabbatar mata da gaskiyar yanayin gidan wato gidane na ƴan boko. suna daf da shiga motar su ta sako kai,, Fadil yayi murmushi yace; "gafa manya nan sun iso, Familyn Alƙali", ya ƙarasa yana dariya. Fadila tace; "da gaske?", ya nuna mata motar yace; "gasu nan kina gani", tayi ihu tana faɗin; "ashe yau akwai show kenan?". Ita dai Nusram bata fahimci me suke magana akai ba dan haka ta ja bakin ta tayi shiru, haka har suka isa wajen saloon ɗin. Ko kallon wajen kayi ka san cewa waje ne na manya, abin mamakin suna zuwa aka tare su cikin sakin fuska hakan ya tabbatarwa Nusram da cewa an san Dr Saleema sosai. Duka suka zauna, Dr Saleema aka fara yiwa kana Muhibba da Fadila, Nusram itace a ƙarshe. Kasancewar duk ta fisu gashi yasa nata yafi kyau, Dr Saleema ta kalleta ta gefen ido tayi ajiyar zuciya, babu abinda zata ce ta ɗari Nusram ɗin dashi. Muhibba da Fadila kuwa sai santi suke ita kuwa Nusram ɗin banda murmushi babu abinda take yi, gyaran fuska ƙafa da hannu akayi musu. Kowacce a cikin su masha Allah domin dama ance idan kana da kyau ka ƙara da wanka, lalle aka fara yarfa musu me kyau. Ɓangaren su Abdul kuwa, koda suka iso can wajen su Hajja suka sauka, ko'ina a cike yake dan haka babu tsayawa ɓata lokaci wajen ƙananan magan-ganu kowa gaisawa ake yi dashi cikin sakin fuska. Ɗakin Malama Abdus-samad ya wuce, sai dai babu wasu mutane a ciki, banda Ummin su Fadil da kuma ƴaƴan ta, cikin girmamawa ya gaishe ta, ta amsa itama cikin sakin fuska. Ita dai yaron yana birge ta sosai, Malama dake saman kujera hannun ta riƙe da littafin hisnul muslim ya sauke littafin. Abdus-samad ya matsa kusa da ita ya gaishe ta, tayi murmushi ta amsa har tana ɗan tsokanar shi. Wayar shi ya ciro kafin yace; "ina Fadil ne?", Malama tace; "ina jin ya tafi kai su Fadila gyaran kai", Abdus-samad ya taɓe baki. Shifa baya jin zau iya wannan aikin, wai su mata basa gajiya da wannan ƙyale-ƙyalen kenan?. Tashi yayi ya fito daga ɗakin, karo suka kusa yi da Surayya, ta turo baki tace; "kai Yaya Abdul, daga zuwa kuma sai ka gudu, Fadila na ciki ne?", bece mata komai ba ya raɓa ta gefen ta ya wuce. Har ya fito Husna ta biyo shi da gudu tana ƙwala mishi kira, Abdus-samad ya ɗan ja tsaki shifa wannan takurar ce baya so. "haba Yaya na sai kuma ka zo amma ko nema na baka yi ba", ya kalle ta sama zuwa ƙasa, riga da wando ne a jikin ta pakistan, tasha gyaran jiki ga wata ƙumba da aka saka mata zaƙo-zaƙo, haka an mata ƙarin gashin gira sai ƙifta ido take kamar ƴar baby. Tayi fari da idanu tace; "Yaya na nayi kyau ko?", ya ɗan yi murmushi yana kauda kai gefe, shi dariya ta bashi ma, tafiya ya fara yi yayin da ta biyo shi a baya. Shifa ta kasa fahimtar wani abu ne wannan shirmen da haukar basa wani birge shi yafi son natural beuty, Husna ganin hanyar da suka ɗauka yasa ta haɗe rai. Ko kallon ta Abdus-samad beyi ba, ta ɗan ja tsaki ƙasa ƙasa, bata da yadda zata yi haka dole suka shiga appartment ɗin tare. Da Kabeer da Hafeeza ke zaune saman kujerun dake balcony sai Aunty Maryam dake tsaye tana waya. Sai da ya jira ta kammala ya gaishe ta sannan ya shiga ciki, Kamal da Aunty Muhsina ke zaune suma suna fira. Ya gaishe da Muhsina ɗin ya kalli Kamal yace; "ina Saleema?", Kamal yace; "gaskiya ban sani ba sai dai ɗazu naga sun fita tare da Fadil amma ban san inda suka je ba". Be kuma cewa komai ba sai kwanciya da yayi saman kujerar, har wajen ƙarfe shidan yamma basu dawo ba, kasa haƙuri yayi ya fara kiran Dr Saleemar. "Hello Abdul, ya akayi?", abinda ta faɗa kenan bayan ta ɗaga, ya ɗan yi jim kafin yace; "kuna ina ne?". Ta kalli gefen ta, "muna wajen gyaran gashi ne dake Sardauna crescent,an ma kusa gama mana ba jimawa zamu yi ba", bece komai ba ya kashe wayar. Kiran sallar magrib aka fara wadda shine silar da ya saka ya tashi, Husna ta kuma miƙewa ta bishi suka fice, ganin yayi hanyar waje yasa tace; "Yaya na ina kuma zaka je". "masallaci", abinda ya faɗa kenan a taƙaice, Husna taja ta tsaya tana kallon shi har ya ɓace daga ganin ta, tayi ajiyar zuciya kafin ta juya domin komawa appartment ɗin su. Koda aka idar da sallah kiran Dr Saleema ya kuma yi amma ta sanar dashi basu taho ba tukunna. Tana ajiye wayar ta maida kallon ta kan Nusram wacce gaba ɗaya hankalin ta ma baya kansu, take taji wani irin kishin ta, domin ita a ganin ta Abdus-samad ya damu su dawo ne saboda ita. Koda ya isa gidan har sun fara shirye-shiryen cin abinci, dan haka shima saman dinning ɗin ya hau domin cin abinci. Gaba ɗaya suka ci abinci cikin ƙaunar juna, kuma abin birgewar shine rashin samun matsala tsakanin Hajja da Brr Farida dan Brr Hauwa ma bata gidan kwata-kwata. Shi dak Abdul kallon su kawai yake yi, suna gamawa ya riƙo hannun Brr Farida suka koma falo, kanshi ya kwantar saman ƙafar ta. Ta saka hannu a saman kanshi tana shafawa, "baka ci komai ba fa?", ta faɗa fuskar ta ɗauke da damuwa, ya ɗan yi jim sannan yace; "bana jin yunwa ne". Ta ɓalla mishi harara tace; "idan kana wani abin sai kace ƙaramin yaro amma kasan dai rabon ka da abinci tun a gida ko?", ya riƙo hannun ta yayi murmushi. "First Love zan ci ne zuwa anjima kada ki damu", bata kuma cewa komai ba, kallon agogo yayi har takwas tayi. Number ɗin Dr Saleema ya kuma kira, "wai har yanzu ba'a gama muku bane?", ya faɗa bayan ta ɗaga. "eh idan an gama ai zamu taho ko, saura kaɗan a ƙarasa", ta faɗa a ɗan hasale domin ita a tunanin ta ya damu ne saboda matar shi. Ya katse kiran kafin ya miƙe, Brr Farida tace; "ina zaka je ne?", be kalle ta ba yace; "zan je wajen Dr Saleema ne tun ɗazu ace wai ba'a gama ba, ko meye amfanin gyaran jikin ma oho". Ita dai Brr Farida bata kuma cewa komai ba, juyawa yayi ya fice, a harabar gidan suka haɗu da Sumayya tace; "yaya wai ina Yaya Fadil ya shiga ne tun ɗazu nake neman shi?". "nima ban ganshi ba", ya faɗa yana yin gaba, da sauri ta kuma biyo shi tace; "ina zaka je", be mata magana ba sai mota daya buɗe ya shiga, babu shiri Sumayya ta buɗe ɗayan gefen ta shiga, shi kuma yaja motar suka fice daga Estate ɗin. Sai da suka yi nisa kafin ya kira Fadil, yana ɗagawa yace; "ka bani address ɗin inda kuke gani nan zuwa", Fadil yayi wani murmushi kafin yace; "ka gaza haƙuri ne mu dawo, kada ka damu yanzu zamu taho fa an kusa gama musu me kake ci na baka na zuba ai yanzu zata zo ka ganta". Abdus-samad ya ja tsaki yace; "nifa ba wannan na tambaye ka ba, ka bani kawai idan zaka bani". "kusa da Bio......graphics sabon Mall ɗin nan da aka buɗe to opposite ɗin shi", yana gama faɗar hakan Abdus-samad ya katse wayar. Babu jimawa suka iso wajen, Fadil ya taso da sauri ganin ɗan uwan nashi, side hug suka yi da juna, Sumayya kuma ta gaishe dashi, Ya amsa yana tsokanar ta ita kuma tana dariya. Ana haka suka buɗe ƙofar wajen suka fito, Muhibba da Fadila suna gaba sai Saleema da Nusram a baya, su Muhibba na ganin shi suka saki ihu sannan suka nufo wajen shi cike da murna. Ya cire yatsun shi biyu daya saka ya danne kunnen shi yana hararar su, "kuna girma kuna cin ƙasa", Fadila ta kwashe da dariya tace; "aifa gyambo sarkin ƴan son girma ya zo". Muhibba ta ɗago hannun ta tana nuna mishi lalle baƙi dake zane a hannun nata, "ga gayun da muka tsaya yi", ya kalla kana ya taɓe baki yace; "dama hutar da kanku kuka yi dan beyi kyau ba", Fadil ya kwashe da dariya yayin da Muhibba ta ɗaure fuska. ya kai kallon shi wajen Dr Saleema wacce ta haɗe rai, gaban shi ya faɗi dan sam yama manta da ita, ita kanta Nusram din sai yanzu data ganshi ta tuna dashi kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannun ta. muryar Fadil ta dawo dasu daga yanayin da suka shiga, "ni dai dan Allah kuzo mu tafi". Duka suka nufi motar Fadil ɗin, dan dai ita Dr Saleema haushin shi take ji ganin kallon da yake bin Nusram dashi, ita kuma Nusram bin Dr Saleema kawai take yi. Suna daf da shiga suka tsinkayi muryar shi yana faɗin; "Dr Saleema zo ku shiga nan", ita ba ƙaramar yarinya bace ta fahimci me yake nufi dan haka ta janyo hannun Nusram suka koma tashi motar. Sumayya na gaba su kuma suna baya, Sumayya tace; "Aunty Saleema ina kika samo wannan kyakkyawar?". Dr Saleema tayi yaƙe tace; "ƙawata ce karatu take a nan kaduna", Sumayya ta dinga santin Nusram. Ita dai Nusram kanta yana ƙasa don duk ta takura kasancewar duk ɗagowar da zata yi zasu haɗa idanu ta madubi wanda yake saitin ta. Haka har suka ƙarasa gida bata ce ko um ba, duka suka fito suka rankaya zuwa gidan, Abdus-samad ya saka hannu ya janyo Nusram ɗin ta dawo baya. Hannun daya riƙe yake kallo, be taɓa ganin lallen daya birge shi kalar wannan ba, ja ne babu ɗigon baƙi ko kaɗan sai dai ya kama hannun nata sosai. Dr Saleema dake baya ganin babu Nusram yasa ta juya, yayin da sai da tayi dana sanin juyar tata domin ganin abinda ke faruwa. Cikin matuƙar damuwa ta sake juyar da kanta tana cigaba da tafiyar ta, wato Nusram ɗin ta san Abdul ya fi son lalle ja shiyasa taƙi yarda ayi mata baƙi don su dukkan su baƙi aka yi musu. Hannun yake shafawa cike da birgewa, ya ɗago ya kalle ta kafin yace; "yayi kyau sosai", bata ce komai ba sai ƙoƙarin ƙwatar hannun ta da take yi. Bata yi aune ba taga ya janyo ta jikin shi, hannu ya saka ya zame mayafin dake saman kanta, ya kuma zame ribbom ɗin dake kanta gashin ta ya sauka har gadon baya. Cike da jin haushi Nusram ta fara ƙoƙarin ƙwacewa, doghnut ɗin da akayi shi da ƙyar saboda santsin gashin ta da kuma yawa shine ya kama ya wani kwance mata. Bata dawo daga takaicin da take ciki ba taga ya buɗe motar shi ya shiga kana ya saka hannu ya janyo ta, kan jikin shi ta faɗa. Hawayen takaici ya zubo mata, ita fa yanzu bata so ana takura mata, kanta ya ɗora saman ƙirjin shi ya saka hannun shi tsakiyar gashin ta yana shafawa a hankali. #LIKE #SHARE #COMMENT *Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *RAYUWAR ABDUS-SAMAD* ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ *✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊 w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶, s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶. α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶. *_daga alƙalamin ✍_* *ƴar mutan zazzau* *(one love)* *sadaukarwa gare ku* *Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)* *Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)* *Heart you so much* 📖📖63-64📖📖 Shiru Nusram tayi domin yadda yake yi mata kamar tafiyar tsutsa, sai dai takaicin ta da kuma baƙin cikin ta yadda yake lalata mata adon da aka yiwa kan. Abdus-samad kuwa wata irin natsuwa ke saukar mishi a duniya yana ƙaunar mace me gashi, ko dan wannan yake ji a ranshi zai iya zama da yarinyar. Sun kai minti ashirin a haka, jin saukar numfashi a ƙirjin shi hakan ya tabbatar mishi da barci take yi, sannu a hankali ya ɗago da fuskar ta, fuskar ya zubawa idanu ba zai ce ga abinda yake ji akanta ba. Idanun shi ya kai saman leɓen ta, barci take amma ta cuno shi gaba, "akwai tsiwa wannan", abinda ya faɗa kenan. Abdul idan da kuma Nusreen ce fa🙄. Bakin shi ya kai kan nata ya sumbata, yana ɗagowa suka haɗa idanu, saurin haɗe fuska yayi ya kauda kai, itama Nusram ɗin ta fara ƙoƙarin ƙwacewa. Be sake ta sannan bece mata komai ba, sai ma kara ƙwaƙume ta da yayi, ganin ta kasa ƙwatar kanta yasa ta kalle shi tace; "dan Allah ka sake ni, Aunty Saleema na can na jira na". Be sake ta ba kuma bece komai ba, shiru wajen yayi na ƴan daƙiƙu kana yace; "dama ashe kina magana kenan amma shine kika ganni a matsayi na na mijin ki ko gaisuwa ko?". Nusram ta kauda kai tana taɓe baki, wai miji!? Shi har wani kiran kanshi miji yake yi, hannu ya saka saman fuskar ta shine abinda ya dawo da ita daga tunanin data faɗa. "me kike tunani haka?", tace; "babu komai", hannun ta ya ɗago ya kuma kallon kunshin dake kwance saman fatar tata, "waye yayi miki wannan?". "nima ban san sunan wajen ba, amma inda muka je da Aunty Saleema, beyi kyau ba ko", ita kanta bata san ƙarashen maganar ta fito ba. Ya kalli ƙwayar idanun ta wacce ta kafe shi dashi tana jira taji me zai ce, ya ɗan kauda kai yayi murmushi yace; "idan nace beyi kyau ba me zaki ji", bata ce komai ba sai cuno baki da tayi gaba. Ƙarar wayar shi ya katse shirun da suka yi, ganin First Love a jiki ya sa shi ɗagawa, ajiyeta yayi saman pocket ɗin motar ya maida ta handsfree. "Baby kana ina ne?", tun daga jin sunan Nusram ta miƙe zumbur, cikin ranta ta maimaita "baby, lallai ma wato budurwar shi ce kenan?", kallon shi tayi shima ita yake kallo suna haɗa idanu ta wurga mishi wata harara kafin ta fara ƙoƙarin fita daga motar. Lumshe idanu yayi sannan ya saka hannu ya maida ta jikin shi ya ƙara matsewa yadda tayi ba ƙaramin birge shi abin yayi ba ga wata dariya da tazo mishi, wai ita kishi take ko me?. Nace; "oho muku munasirai😏😏 Kuna so kuna kaiwa kasuwa". "hello Baby kana jina kuwa?", Brr Farida ta ƙara maimaitawa, cikin kasala yace; "First Love ina jin ki". "kana ina?", tambayar data jefo mishi kenan, kai tsaye yace; "naje taɗi ne", cikin tsananin mamaki da tashin hankali tace; "tadi kuma?", bece komai ba. Ta kuma cewa; "kaga minti biyar na baka ina buƙatar ganin ka, bana ciki da shirmen ka, kana jina minti biyar idan ka wuce ranka sai ya ɓace kana jina", bata jira me zai ce ba ta katse wayar. Kallon shi ya maida kan Nusram data runtse idanu babu abinda take ji banda wani haushin shi wato sai ya nuna mata bata da amfani kenan. Gefen fuskarta ya shafa, sannu a hankali ta buɗe idanun, kallo ɗaya tayi mishi ta kauda kai sakin ta yayi suka fito daga motar, kafin yace wani abu harta nufi ciki da sauri. Cikin sauri ya biyo ta, hannu ya saka ya riƙota ya dawo da ita baya, wani kallo ya aika mata kana yace; "baki da hankali ne a haka zaki shiga gidan?". Wannan yayi dai-dai da fitowar Dr Saleema wacce ta kasa haƙurin jure barin nasu tare, tunda ta shiga hankalin ta ke kansu idan tayi kamar ta kauda kai sai ta kasa. Ƙarshe ma dai ɗaki ta shige tana zubar da hawaye, sosai hakan ke taɓa ranta ta rasa ina zata saka kanta a wannan lokacin ji take da ace tana da yadda zata yi ta cire soyayyar Abdus-samad ɗin a ranta da tayi kodan ta huta da wannan takaicin da tashin hankalin. Fitowa tayi ta nufi waje domin dai haƙurin ta gaza yin shi, sai kuma tayi rashin sa'a da mugun gani domin wannan maganar tashi a kunnen ta ta sauka ga kuma yadda taga Nusram ɗin, mayafi da ribbom a hannu ga gashi a warwatse. Runtse idanu tayi zuciyar ta na bugawa da sauri, shikenan aikin gama ya gama, ko ba'a faɗa mata ba yanayin yadda ta gansu kawai zuciyar ta bata me afkuwa ta afku. kasancewar Nusram ta juya baya yasa bata ga Dr Saleemar ba, shi kuma Abdus-samad ɗin hankalin shi na kan Nusram ɗin bema lura da bayan ta ba. Cikin kishin da bata san tana dashi ba tace; "a'a ba First Love ba saura Last Love", ta ƙarasa tana ajiyar zuciya. Hannu ya saka a ƙugunta ya janyo ta jikin shi, fuskar su ya haɗe kafin yace; "ai zan samu Last Love ɗin kwanan nan", kan tace komai ya sumbaci goshinta da saman hancin ta. Yana ƙoƙarin kaiwa bakin ta Dr Saleema da ta kasa haƙuri ta kira sunan ta, "Nusram!". Da sauri suka waiwayo, Dr Saleema ta ɗan ja numfashi kafin tace; "dare nayi bana so Abba yazo ya same ki a nan ki shiga matsala nima ki jefa ni ya kamata ki dinga kiyayewa". Hannun ta tazo ta kama, Abdul yayi saurin sakin ta, daga Dr Saleemar har Nusram ɗin babu wanda ya kalle shi suka wuce. Ya bisu da kallo yana murmushi, a hankali ya shafa gashin kanshi yace; "na shiga uku na ni Abdus-samad", kowacce kishi take yi, ita Nusram tana kishi da First Love😁, ita kuma Dr Saleema da Nusram dan yadda fuskar ta tayi ya tabbatar mishi da ranta a ɓace yake. Juyawa yayi ya shiga motar shi ya bar gidan, koda ya ƙarasa Appartment ɗin su Hajja da sauri ya shiga ciki. Kafin ya ƙarasa falo ya sami Husna a tsaye kallon shi tayi idanun ta jajir alamar kuka tasha. Cikin ɓacin rai tace; "Yaya na me nayi maka da baka so na?, me waccen yarinyar ta fini dashi, ka san irin son da nake yi maka amma baka taɓa kallo na a matsayin masoyiyar ka ba, sai dai kullum nayi ta wahala da son ka a cikin raina, ba zan hanaka zuwa taɗi ba amma zan ji zafi duk lokacin daka tafi, sai dai duk da haka ina roko da fatan Allah yasa nima wata rana ka soni kamar yadda kake son waccen", tana gama faɗar haka ta shige ciki tana cigaba da kukan ta. ya sa hannu ya dafe kanshi, shi kam yau yaga ta kanshi kowacce tana fushi dashi da kuma nuna kishin ta ƙarara abin dariyar kuma kowacce akan abu mabambamta, ita kuma wannan me ta jiyo ne?. Lokacin da yake faɗawa Brr Farida yana wajen budurwar shi ne ai tana wajen a lokacin, wannan shine abinda ya 9 hankalin ta. Ya saki wani murmushi, shi abin nasu dariya ma yake bashi, lallai me mata uku yana ƙoƙari to ina shi ina wannan aikin ai ko biyu da wuya ya iya haɗawa kodan gudun irin wannan. Da sallama ya shiga, mutane da yawa ke zaune a falon amma babu Brr Farida, gaishe dasu yayi wasu daga cikin su har suna jan shi da wasa shi dai sai dai kawai yayi murmushi. Ɗakin Hajja ya nufa a tunanin shi Brr Farida na can, bata ciki don haka ya fito ya nufi ɗakin Malama anan kuwa ya same ta, zaune tare da Ummin Fadila suna fira. Su kaɗai ne a ɗakin dan haka ya shiga da sallama suka amsa mishi, Brr Farida ta bishi da kallo har ya ƙaraso kusa da ita. Ganin kallon yaƙi ƙarewa ya saka shi taɓe fuska yace; "First Love wannan kallon fa?", hannu ta saka ta kama kunnen shi tace; "wannan kunnen baya jin magana ko?", ya ɗan saki ƙara yana turo baki. Malama ta shigo da sallama itama, ganin shi yasa tace; "ashe har ɗan naki ya shigo kenan?", Brr Farida ta saki kunnen shi ta maida kallon ta kan Malama tace; "eh gashi nan ya shigo yanzu". Gefe ya koma ya zauna yana turo baki gaba, Brr Farida kuwa ta juya suka cigaba da firar su da Ummin Fadila, ganin tayi banza dashi yasa ya matso kusa da ita. Bata juyo inda yake ba, gaban ta ya dawo ya zauna harda tankwashe ƙafa, Brr Farida ta balla mishi harara tace; "matsa ka bani waje", ya shafa gashin kanshi yace; "First Love yunwa fa nake ji". "ai na ɗauka ka ƙoshi da soyayya ne, ita budurwar taka bata baka abinci ba?", tuno mishi da hakan yasa ya saki murmushi yana lumshe idanu. Brr Farida ta saka hannu ta mintsini kumatun shi har sai da yayi ƙara, cikin sauri ya tashi daga kusa da ita ya koma kusa da Ummin Fadila wacce ke dariya, suna birge ta sosai yadda suke ƙaunar junan su. "dawo nan" ta faɗa tana ƙunshe dariya, ya noƙe kafaɗa yace; "Allah yau First Love mugunta kike jin yi mini da alamu yau kin dena sona", yadda yayi maganar ya saka su dariya. Malama ce ta dawo hannun ta ɗauke da plate dan tunda taji yace yunwa yake ji ta fita, a gaban shi ta ajiye kafin ta juya ta kuma fita. Ya buɗe plate ɗin, fried rice taji kayan lambu gefe kuma rabin kaza ce soyayya 😋, ya ɗago ya kalli Brr Farida kafin ya cuno baki. "meya faru kuma?", bece komai ba sai abincin daya ɗauko ya matso kusa da ita ta gane me yake nufi dan haka ta amshi cokalin ta fara bashi a baki. Ummin Fadila tayi dariya tace; "har kuma an gama faɗan kenan?", Brr Farida tace; "to dama waye ke shiga tsakanin faɗa na da Baby, aikuwa dai daya sha kunya ko?", ya ɗaga mata kai. Malama data shigo hannun ta ɗauke da gorar ruwa da kuma exotic ta kalle su ta kauda kai tana sakin murmushi wanda ni dai bangane inda ya dosa ba. Sai da yaci ya ƙoshi kafin ya janye kanshi ya koma gefen ta, kanshi ya ɗora saman kafaɗar ta ya lumshe idanu. Yana jin su suka cigaba da firar su har zuwa wani lokaci kafin barci ya fara kwasar shi, Brr Farida ta ɗan taɓa shi ya buɗe idanu wanda suka yi ja. "au barci ma kake yi kenan?, to ka tashi kaje ka kwanta mana", sumba ya kai mata a goshi kafin ya miƙe yana faɗin; "sai da safe", ya fice. Ɗakin su Fadil ya wuce dama nan ne inda yake sauka, yana shiga ya same shi tare da ƴan mata gidan, bece musu komai ba ya wuce, kan gado ya faɗa sai barci. wajen sha ɗaya sannan Fadil ya samu suka rabu dashi, ya kalli Abdul dake sharar barcin shi yayi murmushi kawai, domin kusa abinda ya faru ɗazu duk akan idanun shi ne. Yana kallon lokacin daya janyo Nusram ɗin jikin shi ya kwance ribbom ɗin, hakan yasa ya bar wajen yana mamakin halin ɗan uwan nashi kuma a ganin shi zuwa yanzu ɗan uwan nashi ya fara jin wani abu a kanta. Bayi ya wuce, yana shiga Brr Farida ta shigo ɗakin, wajen Abdul ta ƙarasa ganin yadda yake barcin ta tabbatar beyi addu'a ba. Tana cikin yin addu'ar Fadil ya fito, kallon su yayi kafin ya kauda kai yana murmushi, shi kuwa yana mamaki shekara da shekaru a haka ya san su wai basa gajiya da ƙaunar juna ne?. Tana gamawa ta shafa mishi a jiki kana ta juya domin tafiya, Fadil yace; "sai da safe Mummy", ta amsa sannan ta fice. ******** ******** Da sallama suka shiga gidan kowa da abinda ke ranshi, Kabeer ya taso da sauri yana faɗin; "yauwa kunga na duk wanda zai fi kyau dan na san nata ne me kyau", ya ƙarasa yana ƙoƙarin riƙo hannun Nusram ɗin. "Wow!, dama na faɗa kamar a india", ya faɗa yana shafa inda zanen lallen ya bi, cikin sauri Nusram ta ƙwace hannun ta a ɗan hasale tace; "meye haka Kabeer bana so", ta ƙarasa fuskar ta a ɗaure. Dr Saleema taja tsaki ƙasa-ƙasa kafin ta wuce ɗakin ta, Fadila cikin jin haushi tace; "ai wallahi nima nawa yayi kyau kuma ko ka yaba ko kada ka yaba ni na san dai yayi kyau". Muhibba tace; "ai kuwa dai wallahi itama wannan ɗin na san me kake yiwa ai", ta ƙarasa tana murguɗa baki gefe, Mummy dai bata ce komai ba. Nusram ta ƙaraso kusa da Muhibban ta zauna har lokacin ranta a dagule yake, Muhibba ta kalli ribom ɗin hannun ta tace; "lalala garin yaya kika kwance doghnut ɗin kanki, ina ma kika tsaya ne?", itafa wa'innan tambayoyin sun fara isar ta. Kafin tace wani abu Muhibban ta saka hannu ta cire gyalen dake saman kanta, gashin ta ya bayyana, ba iya Kabeer da Kamal ba har Aunty Maryam da Aunty Muhsina sai da suka sauke numfashi. Aunty Muhsina tace; "kamar a india, gaskiya yayi kyau", Nusram kuwa ta maida kallon ta kan Ƙabeer da Kamal wa'inda suka kafe ta da idanu kamar su haɗiye. Ta kalli Muhibba dake ƙoƙarin maida mata da ribbom ɗin kanta amma ta kasa tace; "dan Allah Muhibba ki ƙyale ni haka, in sha Allahu zan maida da kaina", ta ƙarasa kamar zata yi kuka. Muhibba zata yi magana Abban su dake zaune da jarida a hannu yace; "Hibba bata ribbom ɗinta". Nusram kuwa gabanta ya faɗi saboda jin muryar Abban nasu, bata taɓa tunanin shima yana falon ba, ta ɗago ta saci kallon shi, shima dai idanun shi yana kan ta, da sauri ta miƙe tsaye. Ta karɓi ribbom ɗin a hannun Muhibba tayi hanyar ɗakin Dr Saleema da sauri, ko ba'a faɗa mata ba tana ji a jikin ta idanu sunyi yawa a kanta. Da sallama ta tura ƙofar ta shiga, Dr Saleema ta ɗago ta amsa tana me cigaba da ɗauko kayan da zata saka daga cikin wardrobe. Bata kuma kulata ba, itama sai kawai ta fara cire kayan ta, towel ta ɗauka ta ɗaura sannan ta nufi bayi, Dr Saleema ta bita da kallo har ta shige kafin taja tsaki, zuciyar ta kawai ke bata wankan tsarki zata yi😂😂. Nusram kuwa koda ta shiga bayin wanka kawai take yi amma tana mamakin meya canza yanayin Auntyn nata da wuri haka?. Tana fitowa ta sami Dr Saleemar saman bed ɗinta hannun ta riƙe da waya tana dannawa, wajen dressing mirror ta wuce inda ta fara shiryawa. Sai da ta gama duk abinda zata yi kana ta wuce wajen kayanta ta ɗauko rigar barci maroon colour me tsantsi ta saka, gashin kanta da taji ya dame ta dalilin da ya saka ta fara ƙoƙarin ɗaure shi kenan amma ta kasa. Kusa da Dr Saleema ta matso tace; "Aunty dan Allah ɗaure mini gashi na", Dr Saleema ta watsa mata wani kallo sannan tace; "da ni nake ɗaure miki gashin ko kuwa shi wanda ya kwance meyasa baki ce ya ɗaure miki ba". Shiru Nusram tayi gaban ta yana faɗuwa, Dr Saleema taja tsaki tace; "aikin banza ni bana son iyayi, sai da kuka gama soyayyar ku yanzu zaki zo ki wani isheni, tashi ni ki bani waje". Cikin sanyin jiki Nusram ɗin ta miƙe, har ta fara tafiya ta dawo ta tsaya gaban Dr Saleemar tace; "Aunty dan Alƙah kiyu haƙuri", ta ƙarasa muryar ta na rawa. Cikin sauri ta juya tayi hanyar fita tana share hawaye, ita kuma meye laifin ta a nan, ɗakin Muhibba ta buɗe ta shiga, da Fadila da Muhibban suka bita da kallo, bata ce musu komai ba ta faɗa saman gadon tana fashewa da kuka. Ɓangaren Saleema kuwa jikin ta ne yayi sanyi, amana fa aka bata amma ji yadda ta yiwa yarinyar, gashi yanayin sanyin yarinyar na birge ta, ta sani itama kanta yadda tayi mata bata kyauta ba. Wayar dake hannun ta, ta ajiye kafin ta miƙe tabi bayanta, ta shiga ta samu su Fadila sun tasa ta a gaba suna tambayar ta lafiya kuwa ita kuma babu abinda take faɗi sai "kiyi haƙuri", Dr Saleema jikin ta ya kuma yin sanyi. A hankali ta taka har gaban ta, Nusram idanun ta a runtse yake dan haka bata ji zuwan ta ba har sai da ta kira sunan ta, da sauri ta buɗe idanun ta kana tashi ta zauna. Ɓare baki tayi zata yi kuka, Dr Saleema ta dakatar da ita, "ya isa haka tashi muje", babu musu ta miƙe tabi bayan ta. Fadila da Muhibba suka kalli juna suka taɓe baki alamar su suka sani, cigaba suka yi da firar su dan sun san wata ƙila wani abu ne ya faru tsakanin su. Suna shiga ɗaki Dr Saleema taja hannun ta har saman kujera ta zaunar da ita, sai da ta runtse idanu kana ta kama gashin nata. Abinda ya bata mamaki yadda taji shi a bushe, duk a tunanin ta zata jishi a jiƙe, nan da nan taji wata irin kunya ta kamata, ta ɗan saci kallon Nusram wacce ke faman sauke ajiyar zuciya. Taci wuya sosai kafin ta iya ɗaure gashin, ta saki ajiyar zuciya sannan tace; "muje mu kwanta ko?", ta kama hannun Nusram ɗin suka ƙarasa saman bed ɗin suka kwanta. Kallon juna suke yi har na tsayin lokaci kafin Nusram tace; "dan Allah Aunty kiyi haƙuri wallahi babu abinda ya faru tsakani na dash..........". Da sauri Dr Saleema ta dakatar da ita tace; "ya wuce raina ne a ɓace, amma ai ba laifi kika yi ba tunda dai mijin ki ne kuma ko gaba ya buƙaci wani abu a wajen ki to lallai ki bashi dan sai ya ɗaga kafar shi zaki shiga aljanna kinji", ta ɗaga kai. "yauwa to yanzu ayi barci ko, sai da safe kuma", tana faɗin haka ta juya baya, duk da barcin take ƙoƙarin tilasta kanta tayi amma abin ya gagara, data rufe idanu sai taga lokacin da Abdus-samad ɗin ke ƙoƙarin kissing Nusram ɗin a gabanta. #LIKE #SHARE #COMMENTS. *Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*. *ƳAR MUTAN ZAZZAU*. *************************⬇********************** ************* Top Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.thn.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > tophausanovels@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Top Hausa Novels Twitter: Top Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels Telegram Group: https://t.me/tophausa Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Top Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************