[13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎 👑 By Ashanty love. (M Afnan) ASHANTY©AREWABOOKS.COM ✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯ Gargaɗi Ban yarda a juyar min da littafi ta ko wace siga ba ba tare da iznina ba. ✍️𝑩𝒊𝒔𝒎𝒊𝒍𝒍𝒂𝒉𝒊 𝒓𝒂𝒉𝒎𝒂𝒏𝒖𝒏 𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎. P 1/2 Sauri nake kaman zan fadi saboda gudun dukan malam Halliru. Sam bashi da mutunci idan a kan duka ne. Ko ubanki ne ya mutum idan baki kawo masa uzuri kwakkwara ba ki yi fashin makaranta zagewa yake ya zane mutum bare kuma ka makara ko na minti daya ne. Tun daga nase na hango dalibai yan makara durƙushe gaban sa da sharɓeɓiyar duruna sai haƙuri suke bashi wasu har sun fara sharar hawaye tun ma bai taɓa su ba. Matsanan cin faɗuwa gabana ya ke na tsani abunda zai tabamin lafiyar jiki duk da kuwa idan duka ne ya zamemin sabu ,idan shi bai dake ni ba to Baba Lantana za ta yi har ya zama duk irin dukan da za'a min bana kuka,wannan rashin kukan da nake ko reacting nasan ba karamin ciwo yake masa ba ni kuma naki bashi satisfaction d'in da yake nema. Duk irin uzurin da zan kawo masa bazai hana ya fasa duka na ba na lura har so yake yaga na makara dan kawai ya dake ni. Duk ranan kuwa dana zo da wuri toh ya dinga sunturi cikin ajin namu ko zaiyi kuskuran kamamu munyi wani abu da zaisa ya dake mu. Mugun murmushi ya yi hango ni da ya yi nabi sawun ƴan makara. Inda nake durƙushe ya tako "Yau kuma wane uzuri gare ki?" Duk da nasan cewa ba yarda zai yi da abunda zance ba ban fasa ɗago kai na kalle shi ba ,abunda ban iya ba shi ne karya duk ɗacin abu sai na faɗe shi. "Baba lantana ce ta aike ni na kai mata niƙa kuma da naje sai na tarar da layi" "Baba Lantana kaza,Baba Lantata kaza. Ita bata sanin lokacin aike sai lokacin makaranta?" Baki na zumɓura"toh nikam ban sani ba sai dai ko zaka tambaye ta" "Rashin kunya za kimin?" Ban bashi amsa ba na ɗauke kai na gefe . Dan tsabar mugunta da yazo kaina sai da ya yi min bulala goma a maimakon biyar da yake yi. Yana gamawa na kaɗe hannuna na shige aji. Ƙarfe biyar dai-dai muka tashi ban jira Sahiba ba dan yau ina da suyar awara. Shi kaɗai ne abunda nake samun y'anci idan nayi ciniki mai maiko to ranan zanci na koshi har sai na ture. Saboda haka nake ta zuba uban sauri dan naci burin awarar nan da muka kwana biyu ba muyi ba tun safe ban saka wani abuncin kirki a ciki na ba. A kofar gida na hango Baffa na zaune kan tabarma da ya saba zama a koda yaushe. Baffa na (Ridwan Mus'ab) dattijon mutum ne da a ƙalla ya doshi shekaru 57. Bashi da wata cikakkiyar lafiya saboda halin girma. Yana yawan fama da ciwon kafa shi yasa sau tari da sanda yake takawa. Baba Lantana abokiyar zaman Mama nace. Niɗin marainiyace dan uwata ta rasu tun bayan haihuwa ta. A yanda Kaka ke gayamin mu biyu kawai ta haifa akwai yayata da shekara biyu kawai ta yi a duniya Allah ya karb'i a bunsa. Har sun fidda rai samun wata haihuwar dan cikin farko ma saida ta shekara biyu kafin ta same shi, sai kuma Allah ya basu cikina. Tana haihuwa ta ance ko ganina bata yiba Allah ya yi mata rasuwa. Da Mama na da Baffa na duk yan Abzunawa ne (NIGER). Baffa ya fito ahli mai girma suna da yawa shi ne na uku a gurin ne Kaka. Sai ya kasance suna da ɗan hali in mutum ya ɗan tasa sai a nema masa aiki Nigeria, kaman zaman Gadi, Derebanci da sauransu. Toh shi Baffa na sai aka samo masa Gadi anan jahar Gombe da a yanzu muke zaune cikin ta. Bayan samun da ya yi anan ɗin da karɓar da yake ganin Gomben ta masa ya dawo nan da zama. Wani hutu da ya koma gida Niger ne ya ga Mamana(Fateema Harun) dake da shekarun kuruciya a lokacin. Shekara biyu da Auren su ya dawo ya ƙara dawowa neman wani aikin ya ƙara samun gadi a nan ne ya haɗu da Baba Lantana suka yi aure. Yar maƙocin wani mai gadi ne da suke maƙota dashi. Shida iyalen sa suke zaune a gidan da yake gadi. Ganin farko tace duniya babu wanda take so sai shi. Mutuncin da dattakon Baban ta yasa ya amince mata bai tashi dawowa ba sai da auren Baba Lantana a kanshi. A lokacin Mamana nada tsohon ciki. Daga zuwan Baba Lantana ta amshe gidan dan ta girmewa Mamana. A yanzu haka yaran Baba Lantana Biyara akwai Hadiza Rabi Ibrahim ,Baba lantana ta b'ata masa suna da Iro, kowa haka yake kiran sa Iro. Rakiya Sai autar su Bilkisu. Duk sunyi aure banda Iro da Bilkisu da muke sa'a ɗaya da ita . Yaran Hadiza uku, Rabi biyu, anma na biyun ya koma. sai Iro da Baffan mu ya tura shi karatu chan zaria . sherakun mu ɗaya da Bilkisu wata biyu kawai ta bani amma nike yin komai a gidan tana kwance ko cokali bata ɗauka sai dai a kawo mata. Wani irin shagwaɓa ta Baba Lantana ta yi saboda Bilkisu duk tafi sauran yaran ta kyau ita kaɗai ce tayo hasken Baffan mu da kuma gashin sa. Har wani kirari za kaji tana mata wato Bilkisu mai gadon zinare Mijinki sai sarki ko attajiri. A hanzarce na ƙarasa gaban sa na durƙusa ina yi masa sannu da gida. Murmushi ya yi min cike da so "Kin taso Uwata?. (Sunan Kaka naci wato SAHLA) , sannun ki da dawowa, maza kije gida ki huta kici abinci Allah ya yi miki Albarka " Cikin jindaɗi na amsa da "Amin" na shige gida. Bai taɓa sanin irin halin muguntar da Baba Lantana takemin ba nunawa take a kan idansa tamkar ita ta haifeni ,dani da ƴaƴanta duk ɗaya muke a gurin ta. Wannan salon kissar tata yasa ta ƙara samun matsayi mai girma a gunsa saboda sanda yaga tana nuna min. Yasan ina yin awara shima da maganganu da daraba ta shawo kansa ya barni dan sam baya son suyan awarar nan da nake a ƙofar gida ,ta fake da ace Bilkisu na da cikakkiyar lafiya babu abinda zata sa tace na mata suyar awara bare ya nuna mata cewar ba ita ta haifeni ba . Toh sai Allah yasa titi ya biyo ta layin namu baka rabon layin namu da samari a koda yaushe. Kaka babu irin faɗan da bata yi ba a kan hakan har cewa ta yi idan shi bazai iya tsayawa a kaina ya jajir ce ba toh ita zata ɗauke ni na koma gurin ta can Niger da zama.tun wani hutu ne da tazo nan Gombe taga ina yin awara ta tada billi sai ta tafi dani. Nima naso binta ko na huta da jarabar Baba Lantana amma da yake akwai ta da iya kissa sai ta zauna tana kuka wai Kaka ta nuna mata matsayin ta ashe dama bata ɗauke ta a matsayin Uwata ba , yanda ta ɗauke ni tamkar ƴar data haifa bata taɓa banbance ni tsakanina da yaran ta. Iri-ire wannan kalamai ne ya sakarwa da Kaka gwiwa ta fasa tafiya dani da sharaɗin ba kullum zan dinga yi ba. A sati sau uku kawai nake yi. Laraba,Alhamis da kuma juma'a kafin ta tafi sai da ta tambayi dalilin da yasa Ita Bilkisu bata suyan awarar sai dai kullum tana kwance kaman kasa. Buɗar bakin Baba Lantana itama tace mata wai bata ishashiyar lafiya ne. Har yau kuma taki faɗan taƙamaiman wane irin ciwo ke damunta. Maganan dai ɗaya ce a koda yaushe bata da ishashiyar lafiya. Tsakir gidan na tadda su. Bilkisu kwance kan tabarma tana danna waya kirar tencnor ƙarama da Baba lantana ta dage sai yayyen ta sun siya mata ita yar gatan su. dole a bata waya. da Baffa ya yi magana sai tace ai Bilkisu ta girme ni in an bata ba laifi bane tunda takai munzalin riƙewa,kuma ai ƴan uwan tane suka siya mata,dole ya haƙura ya ƙyale ta. Can gafe Baba Lantanan ce ke kwashe awara data sauke a kan wuta. Sannu nayi mata nayi saurin shigewa d'akin mu na ajiye jakata na cire uniform na chanza zuwa riga da sket na atamfa da hijabi. Kai tsaye na d'auki kayan yaji na fara dakawa na fito waje na sami yaro ya fara fitomin da kayan suya ta. "Gashi nan awarar dubu biyu da dari uku ce, ko guda d'aya ta bata sai kinci ubanki a gidan nan " Ban amsa ba na kwashi kayan nayi waje . Wannan babatun nata baya hanani cin awara yanda naga dama idan na dawo ta jibgeni amma gobe bazai hana na k'ara ciba. Tun tana dukan tana zagin har ta daina sai ta daina bani abinci. Duk ranan da hakan ta faru ta babu ni a kwanan abincin dare, dama ba ci nake na koshi ba gani da shegen cin tsiya amma ba auki. Kaman ka bushe ni na fad'i. Shi yasa nake san yin awarar ko babu komai zanci na koshi bazan kwana da yunwa ba. Ina fitowa kuwa maza suka yi caa a gurin kowa da kuɗin sa a hannu. Daga mai ta hamsin,d'ari,biyu da sauran. Babu fashi duk kaskon dana sauke sai na ci d'aya ko biyu. Har Baffa dake can zaune kofar gida na zubawa a d'an plate na kai masa. Toh a gidan ba bashi ake ba sai tace wai bayanan aka fita da ita kuma kayan sana'a indai kullum za'a dinga d'ebar masa zai karya mata kasuwa,ita daga ita sai y'ar ta. Shi yasa idan na fito sai na tabbatar da na soya masa yanda zaici ya koshi. Gabansa na ajiye ya kalle ni da murmushi kan fuskarsa kana kallon ta kasan bada san ransa nake wannan Awarar ba fin karfin sa aka yi. Baya son yana ganin yanda samari ke layi a kaina. "Allah ya yi miki Albarka Uwata" Na amsa da "Amin" na koma gaban awara ta ina cigaba da sallaman mutane. Can gefe na naji hirar wasu samari dake kan layi. Hankali na baya kansu amma kalman Dan sarki Saif da naji na fita cikin hirar tasu yasa na kasa kunne ina saurara. "Wai kaji labarin wannan hatsabin yaron sarki ya shigo garin kuwa?" "Wai kana nufin KING AJ?" "Shi fa, tantirin yazo Nigeria, jiya aka ce gaba d'aya masarauta basu yi barci ba suna gudun tashin hankali sa. Ni na rasa wane irin dan iskan mutum ne shi dan baza'a kirashi da yaro ba. A kalla fa ance zai doshi 30 amma kaga yaki yin hankali lamuran sa sai kara tabarbarewa suke. Kasan wancan zuwan da ya yi cewa aka yi wata Baiwa ta bige shi cikin rashin sani walh in kaga irin jini da majinan da aka ce ya had'a mata sai ka tausaya mata. Har kwanciya ta yi gadon asibiti bai barta ba saida ya yi sanadin barinsu garin Gombe gaba d'aya da dangin ta. Bashi da imani ko kaɗan wlh" Mugun tsaki dayan yaja ya wani karkace kai gefe irin na gogaggun yan iska yana cewa"ina zaiyi imani ka manta waye shi ne?. AJ ne fa. Kasurgumin Dan iska bayahuden banza. Kaga kuwa zuciyar kafirai gareshi tunda har yanzu babu tabbas ya karb'i musulunci. Ga dai Baban sa Dattijon mutum mai tsanani tsoron Allah malinta ya gaje ta gaba da baya amma Allah ya had'ashi da yara fitinannu musamman ma AJ, ko da yake ai ance uwarsu ce Baturiya ta kuma ki yarda su karb'i musulunci duk irin sanda Maimartaba yake na ganin yaransa sun karb'i Addinin gaskiya. duk cikinsu AJ ne kawai yake zuwa gurin Uban nasu kuma shine karami cikin su shi kuma Maimartaba yake burin ganin ya gajeshi tunda shi kaɗai ne namiji cikin ya'yansa, shi yasa yake ke ta k'ok'arin wajen ganin yaron ya shiryu har aure naji an shirya yi masa da wata yar cousin din Maimartaba, amma zuwan sa ance bai bar kasar ba sai da ya tabbatar ya lalatawa yarinyar rayuwa ta hanyar yi mata ciki. Allah ya taimaka ance cikin ya zube zance aure kuma ya rushe." Na ukun cikin su da tunda suka fara maganan bai tofa ba sai yanzu yace "Ni kuwa kunga yana masifar burgeni. Mulki ya gajeshi ta uwa ta uba. Gaba da baya kenan tantiranci ai sai inda maina ya tsaya .wlh idan nike da gatan da Aj yake dashi sai nayi abunda yafi wanda yake. MULKI duniya ne wlh ka taka wanda ka ke so ,kayi abunda ranka keso babu uban da ya isa ya tsawatar ma musamman ma MULKI irin na AJ. Uba sarki Uwa sarauniya. Sarauniyar ma ta kasar waje ai sai dai kawai Allah ya yafe mana. Ni wai naji ana cewa ma kaman AJ d'in inkiya ne ake masa. Ainihin sunan ALEXANDER ALEX sunan da uwarsa ta rada masa kenan, J d'in kuma sunan sane na yanka da Maimartaba ya saka masa JABEER. Kaga sunan ya tashi AJ. Can abokan sa na waje ance suna kiran sa KING " Oh gulma irin ta mutanen mu.ka take naka laifin ka hango na wani. Kalle su dai duk cikinsu babu mai shigar arziƙi amma na wani suke hange Allah ya kyauta yanzu mene abun burgewa kan wannan kedarin da suke fad'a?asthagfurulla, har yanzu babu wanda yake da tabbas ya karb'i musulunci ko A'a amma yana yawan zuwa Nigeria ganin ubansa duk cikin su,su uku shi kaɗai ke san Ubansu sauran sunki zuwa suna gudun zuwa dan basu san su rabi bak'ar fata sun kuma k'i jinjin talaka. Sai gashi sun fito daga tsatson bakin mutum wata kila da suna da hali sai sun chanza uba. K'aramin tsaki naja ina k'are musu kallo ta kasan ido. Kana ganin su kaga tantiran yan iska sunci wasu shegon kananan kaya ga wando anyi masa Assdown underwear duk a waje. Babu abunda yafi bani takaici irin gashin kansu. An tara uban gashi ya cukurkude babu kyan gani. An aske ta gefe da gefe an masa wani nannad'a cibiri-cibiri ya zubo gaban goshi. Harda mai kitso ma cikin su. Yoo ai dole ya burge su domin dai kallo d'aya zaka musu kaga tantiran yan iska kaman yanda suke kiran wani. Nima da shegen gulma da sa ido. "Ya dai Sahla Baby har yanzu layin baizo kanmu bane. " "Ta nawa za'a sa muku?" "Ta dari shida mana Sahla Baby, har kin manta ne?" Ban basu amsa ba na zuba musu ina k'ok'arin kulla musu yaji yaro da bai wuce shekara goma ba ya k'araso gurin. "Aunty Sahla wai inji Baffan ki Awarar bata k'are bane?" Juyawa nayi inda Baffan ke zaune gaba d'aya hankalinsa da nutsuwar sa yana kaina. Murmushi nayi nasan saboda wannan yan duniyan ya turo yaro. Kwanun awarar na kalla da bata wuce ta hamsin ba wani ya yi wuff ya mik'o kuɗi . "Gashi ki bani ta ragowar data rage" Karban kuɗin nayi na miƙawa samarin tasu a gurun suka hauci da yake akwai benci. Yaron na kalla da ke tsaye . "Fara kwashe min kayan nan Imrana ka miƙa min su gida." Saida muka gama kwashe kayan tas muka shige gida. Kaman ni take jira ina shiga hannu kawai ta miƙo na bata kuɗi. Dubu biyu na lale cis na bata. Bayan ta gama kirga kuɗin ta d'ago rai a bace tana kallo na. " me ya samu chanjin d'ari ukun dake kai?" Shiru nayi ban bata amsa ba. Ta taso a fusace ta zubamin rankwashi mai shegan zafi ta kama kunne na. Bilkisu dake kwance sai dariya take. "Nace uban me ya samu chanjin d'ari ukun dake kai?,wato kin zama mai taurin kai ko?,duk dukan da zanyi da zagin da zanyi bazaki fasa sacemin awara ba, dan wannan sata ce tunda ba baki nayi ba. Za kici ubanki cinikin da ki ke yasa nake kyale ki amma zanyi maganin ki . Zan cire wannan shegon idan naki da suke kaman na mujiya tashi ki bani guri" Tashi nayi na zumbura baki ina sosai kai dan rankwashin ya shige ni. Kaman yanda nayi zaton kuwa ba'a bani abinci ba nima kuma bansa rai ba dan naci na koshi a waje.Kayan jikina na cire na d'ora hijabi kan daurin kirjina na fito dan watsa ruwa. Duk da cewar dare ya yi amma garin dal yake da hasken farin wata da kuma fitolu da alhaji Maishinkafi yasa aka dasa layi-layi. Da yake lokacin zafi ne. Ruwan babu sanyi na watsa a gurguje na fito nayi sallan magriba. Ina kan dadduma ina tilawa a kayi kiran isha. Dan haka ina yin ishan na miƙe na kwanta kan katifarmu dake d'akin sai barci. [13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎 👑 By Ashanty love. (M Afnan) Marubuciyar NOOR SILAH KAIDIN MACE & NOW MULKI ASHANTY©AREWABOOKS.COM ✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯ P 3/4. Baffan mu mutum ne da bai damu da ilimin boko ba sai na islama. Shi yasa kaf cikin mu babu wanda yake da ilimin boko amma akwai na addini. Sauka ta biyu duk da karancin shekarun da nake dasu ina shirin yin ta uku. Bilkisu ce har yanzu bata sauke ba amma babu wanda bai sauke ba cikin mu. Idan Baffa ya yi magana Baba Lantana tace yana takura mata. Kowa da irin tashi kwakwalwar itama za ta yi. Toh ta ina? makarantar ma da sai taga dama take zuwa. Ba abun mamaki bane idan aka ce har yanzu bata iya had'a baki ba. Sai dai kullum tana kwance ,da daddare sai ta raba dare tana hira da samari. Har mamaki take bani. Duka-duka nida ita shekara 17 muke ,amma yau ka ganta da wancan saurayin gobe ka ganta da wani. Kodan ta fini girman jiki ne shi yasa ake yi mata kallan mai shekaru tana da k'iba tayo Baba Lantana. Ni kuwa tsigarallahu sai tsayi babu laifi. baza'a kirani gajera ba ina da tsayi na daidai misali. Wani lokacin har mamakin cikar Kirjin Bilkisu nake. kirjinta a cike yake fam kaman wadda keda shekaru masu yawa. Ni kuwa nono na mitsi-mitsi ne kaman kwallon mangoro. Sai dai ina da hips kuguna a baje yake amma cikina a mugun shafe yake kaman bana cin abinci. Ina da dogon gashi mai santsin gaske da ko ribbon baya kamawa sai da dabara. Bani da haske. Bakuma zaka kirani bak'a ba bak'ina irin bakin nan ne mai shek'i.(brown skin) .ina da manyan ido da koda yaushe sai an tanka su ga kwayar idon tawa bak'a waluk da ita. Shi ne abu na farko da ake fara hangowa a tare dani. Ni mutum ce da ke masifar san hijabi. Gashi dai ba wani jikin kirkine dani ba amma in bansa hijabi ba sai naji kaman ina yawo tsirara. Ko barci bana iyawa saida hijab. Haka yake jawomin bakar magana gurin su Baba Lantana da Bilkisu. "Abu kaman itace ko me take boyewa ohoo.? Ki bari masu abun boyewar su boye mana. Kina fama da wani kirji kaman kwallon mangoro" Bana tankawa ,zaginsu kuma bai hanani sa hijab ba. Gadai Baffa na mutum da baisan karatun Boko amma nikam Allah ya jarrabeni dasan karatun Nasara. Ina so nayi ilimi mai zurfi na zama wata a duniyar. Kaji ana professar Sahla, ko Dr Sahla, ko lawyer Sahla,ko ..ko. ina da buri da yawa da basu da adadi,Shi yasa indai muka had'u da Sahiba sai nasa ta koya min kad'an daga cikin karatun Nasara. A yanzu nasan kalmomi kaman Yes. Eh Welcome. Barka da zuwa. Hello. Sallama Name. Suna Goodbye. Sai anjima Kaf ranakun nasansu da turanci. Wato Monday,Tuesday,Wednesday,Thursday, Friday, Saturday, Sunday. Inka cire wannan babu abunda na sani game da harshen Nasara. Har sha'awa nake idan naga yara da uniform na makarantar boko. Ina da burin ganin nayi wannan ilimin ban kuma cire rai ba babu Abunda yafi karfin Ubangiji. Idan banyi ba toh dama baya cikin kaddarata ne. Yau tunda na tashi ban zauna ba. Daga tace yi kaza sai tace yi kaza. Har Allah-Allah nake ayi sallan Azhar na tafi makaranta ko na huta . Anayin azahar kuwa nayi shirin makaranta na fito a sukwanne zan fice Allah ya taimake ni Baba Lantana ta shige banɗaki. Nayi wuf zan fice Bilkisu dake zaune tana fama da waya ta kwale baki "Ina zakije bayan naji Baba na cewa zata aike ki gurin Hamisu ki karbo min d'inki na" Mugun kallo na zuba mata mai dauke da harara. "Kije da kan ki bazanje ba d'in." Baki ta hangame "ni ke kewa rashin kunya?" Ina k'ok'arin mayar mata da martani naji muryar Baba Lantana dake k'ok'arin fitowa daga bayi. Tsabar masifa da jaraba tana bayin ma bata hak'ura da bala'i ba. "Ki bari nazo nan na same ki Bilkisun ce take magana ki ke mayar mata?". Harara na k'ara zuba mata nayi wuff na fice da gudu dan banga wanda ya isa hanani zuwa makaranta ba sai ikon Allah. Yau tunda naje makarantar na lura da cece kucen da ake sam na kasa fahimtar abunda ya jawo wannan surutu duk inda ka wuce za kaga an had'a karamin grp ana kuskus ko me ke faruwa a makarantar oho. Wajen la'asar ne bayan mun fito Sallah muka had'u da Sahiba. Muna Alwala ne nace "wai menene yake faruwa ne naga har Malamai ba'a barsu a baya wajen hada grp da alama kuma magana ce suke mai zafi" Y'ar dariya ta yi "wai baki san me ya faru ba?,ko da yake taya zaki sani keda ba waya ce dake ba bare ki hau social Media" "Sooyal me?" "Social media" "Sooyal medea" Dariya Sahiba tayi "social media ake cewa mana Sahla kar ki bani kunya duk san koyan turancin naki kuma kin kasa fad'an wannan kalma da ba wani wuya ne da ita ba" baki na turo cikin jin haushi nace "Ki gayamin ni abunda ya faru kawai" "Kinji labarin ance Yarima yazo gida ganin Maimartaba ko?" Kai na d'aga mata ina sauraran ta, ta cigaba da cewa " toh in gaya miki wai yau ya fito shawagi gari cikin k'aramar mota shi kaɗai babu masu tsaro. yana tafiya kan titi wani ya yi irin overtaking d'innan nasa saboda yanda yake tafiya shi bai tafi ba bai kuma bari wasu sun wuce ba. Shi wai dan mai wani zai shiga gabansa yana tuki. Ina gaya miki tsakiyar titin ya faka mota ya fito ya tare titin. Gaba da baya ya hana kowa wucewa ya had'a uban go slow kan titi. Kuma ya haukan motar ya zauna yana shan taba kaman ba hakkin mutane ya shiga ba. Kinsan babu wanda ya tab'a ganinsa a waje mutane suka yi caa a kanshi zasu rufeshi da duka sai ga masu tsaron lafiyar sa. Anan ne cikin kowa ya d'uri ruwa duk wanda yake kan titin nan dana mota,mashing, kafa, keke sai daya yaci ubansa ya hana kowa wucewa masu sauri zuwa gurin aiki, majinyata da sauran mutane. Saida aka yi awa hud'u tsaye kowa yana tsoron gudun dan ance wasu shegon sojojine jajayen fata da shegun bindigo suka tsare titi kar mutum ya motsa su harbi shi. Labari yaje kunnen Maimartaba saida ya tako da kansa yazo ya lallabashi sannan yabar mutane suka shaki iska suka fara wucewa. Ya sha zagi kuwa da tsininuwa yau d'innan. Cikin k'ank'anin lokaci labari ya baza social media. Amma abinda yafi d'aukan hankalin yan media shi ne matsanancin kyau da aka ce yana dashi. Duk matan da ki ka ga suna hiran nan zancen kyansa kawai suke mata sun mutu a kansa" Dogon numfashi ta sauke har ta bani dariya. Kai amma dai mutane sai a barsu. Yanzu su basu ga abunda ya yi ba sai kyansa kawai. Nina rasa gane mene ma abun burgewa game dashi . Ba ance ba musulmi bane?ai kome kyansa tunda baida hasken musulunci banga abun burgewa ba?. Kai Allah ya kyauta gaba d'aya sun k'ara samin tsanarsa duk da ban taɓa ganinsa ba sai labarinsa da nake ji. Kaf labaran nasa kuma babu wanda ya taɓa fad'an abun arziƙi a kansa sai sharri. Toh wai dama haka Mulkin yake ne?. Indai kuwa haka yake Allah wadai da irin wannan Mulki. Allah kuma ya tsaremu da rab'ar masu irin wannan Mulki. Sai bayan mun tashi ne nafara fargabar komawa gida bansan abunda zan tarar ba. Jerewa mu kayi da Sahiba da wasu yan ajinmu. Ana tafe ana maida zance Ai KING AJ ya had'u su basu tab'a ganin Namiji mai kyan sa ba. Wace tsiya wace arziƙi. Harda masu cewa in dai zai so su koda bai musulunta ba da gudu zasu amince su sun tsallake sai dai na k'asa yasha kallo. Bansan sanda naja mugun tsaki ba saboda takaici su ko kishin k'asarsu da Addinin su basa yi. "Sahla Ridwan " Da sauri na juya inda naji sunan. Malam Halliru ne tsaye jikin gate na makaranta kaman mai jiran abu. Yau kuma me nayi da ya tare gate yana jirana. Da wuri dai nazo balle yace nayi makarar da na saba. Fuska babu walwala na k'arasa gabansa na durkusa ina gaishe shi. Ido kawai ya zubamin na wasu yan sakanni baice komai ba har na fara jin haushi. Ya titseni gaba yana kallo dan tsabar wulaƙancin. Da yasan ba wani abu zaice babya kirani. A dan fusace na d'ago zanyi magana sai idanmu suka had'u. Kasa furta masa maganan nayi dan wani irin kwarjini naji ya yi min yau. Da murya mai sanyi yace "Baffan ki yana nan anjima bayan sallan magriba?" Nayi saurin ce masa "A'a baya nan yaje duba Kaka" Haka kawai zaije gurin Baffa. Yace masa me? karo na farko kenan da yasani karya. Ido ya zubamin kaman bai yarda da abunda nace ba. "Shikenan tashi kije" Da sauri na tashi nayi wajen su Sahiba dake jirana ana ta gulma. Ina k'arasawa kuwa Barira ta yi suarin cewa "Anya kuwa Sahla Malam Halliru ba sanki yake ba? Kinga kallan da yake miki kuwa?ko ba haka ku ka gani ba?" Ta juya tana kallan su Sahiba. Gaba d'aya suka had'a baki "Walh muma dai haka muke tunani" "Allah ya sauwake nayi Soyayya dashi. Kunsan wanda kuke magana a kai kuwa?,malam Halliru fa,mutumin dake buri yaga ya tab'a min lafiyar jiki sannan kuce wai yana sona?,wlh ko maza sun kare a duniya babu abunda zanyi da mugu Azzulumin mutum" Fuu na wuce su dan sun masifar bani haushi. In banda ma rainin hankali malam Hallirun za suce yana sona?. Toh har muka k'arasa gida muna cece-kuce dasu. Su fad'a na fad'a kafin muyi sallama kowa ya kama gabansa. Kaman koda yaushe Baffa na zaune riƙe da charbi da littafin Addini baje a gabansa gefensa Musaddiq ne mak'otan mu. Saurayi ne da a kalla ya yi sha tara. Yana san karatu sosai duk lokacin da Baffa ya fito indai yana nan shima zaka ganshi kusa dashi yana karatu. Sai da na gaishe su sannan na shige gida cike da tarar radin abunda zan tarar d'azu nayi laifi nasan kuma Baba Lantana baza ta hak'ura ba. A soro na labe ina leke d'an sakar gidan namu dake fes yasha suminti sai shek'i yake. Babu kowa sai tukunyar awara dake yashe a k'asa an kwashe ta cikin buhu. Takarmina na cire da sand'a na shige kaman barauniya. Ina zuwa kofar d'akin mu nayi wuff na fad'a ciki ina sauke ajiyar zuciya Bilkisu dake kwance kan gado rik'e da waya ta kalleni taja mugun tsaki. Aikin kenan dai. "Da kin bar wahalar da kan ki babu abinda zai hana Baba hukun taki cikin gidan nan. Yanzun ma ta fita ne wajen Sahura ta siyo kayan miya" Haba shi yasa ko karfe nawa zan kai ina guje-guje nasan sai ta jirani. Ban kulata ba na ajiye jakata na cire uniform dina na ninke su na zuba cikin yar drawer mu dake d'akin. Ina k'ok'arin fitowa dan fara shirin fita da kaya waje sai ga sallamar ta. Da sauri na koma na labe a bayan kofa. Da masifar ta ta shigo. " su mutane in basuyi san zuciya ba basu jindaɗi. Yanzu ina kayan d'ari biyar a nan. Komai sai an cuce ka kayi magana kuma a nuna anfika baki" Haka dai kullum. Ni na rasa da Baba Lantana da Sahura wa yafi wani masifa cikin su. Gashi dai kullum suka had'u basu rabuwa lafiya amma a haka kawaye ne na kut da kut. Dama ance ai ba'a kawance sai hali yazo d'aya. Ajiyar zuciya na sauke da alama ta manta dani koma mene ya faru tsakanin su ya mantar da ita nawa Laifin dan haka da sauri na fito na fara kwashe kayan ina yin waje dasu ko kallo na bata yiba tana ta mita. Saida na gama fita da komai na dawo d'aukan awarar data gama yankawa harzuwa lokacin bata daina mita ba. Bilkisu ta fito a guje "Baba kinga, kinga hoton Yarima. Wayyo Allah na ina san shi wlh Baba" Nima da shigiyar gulma nayi kansu da sauri ina leka wayar. Ina so naga wanene wannan Yariman da duk inda ka wuce sai kaji anyi maganan sa. Tsabar yanda nake miƙe wuya kaman zai tsinke. Da sauri na matsa ina sosai kai dan wani rankwashi ta zubamin masu zafi a kai. "Dan ubanki zaki wuce min daga nan ko kuwa. Ina sane dake ban manta ba. Awarar yau ta dubu uku da d'ari biyar ce. Bazan ce kar ki fasa ci ba kici kinji Allah ya baki sa'a " Baki na zumbura na kwashi bokitin nayi waje dashi ina kunkuni. Da kallo Baffa ya bini. "Zonan Uwata" Gabansa na durkusa "akwai abunda yake damun ki ne ?,Lantana ta yi miki wani abu ne ban sani ba?" Kai na girgiza masa ina murmushi "babu komai Baffa. Nida Bilkisu ne" Dan jim ya yi "ni nasan akwai abubuwa da yawa da ki ke b'oyemin Uwata. Amma tunda kince babu komai tashi kije Allah ya yi miki Albarka ". ♥︎♥︎♥︎ Toh ina ajiye kayan kuwa maza sukayi caa a gurin kaman jira suke na fito. Babu bata lokaci na fara suya da sallaman mutane yau Imrana na taimaka min. Gab da magriba awarar tawa batafi ta d'ari biyu ba ta kare a lokacin Sai wata irin kururuwa da hayaniyar mutane ta fara doso layin namu. Zo kaga gudu ana yin inda hayaniyar ke fitowa kai mutane da gulma nima dake zaune sai d'aga wuya nake dan san ganin abunda ke faruwa. Wani irin mashin ne katon gaske baki wuluk dashi mai masifar kyau Ya shigo layin namu da wani irin gudu kaman iska. Shi kanshi wanda ke kan mashin d'in bakaken kaya ne a jikinsa har hular kwanon dake kansa. Abu d'aya ne ba baki ba kyallin sarka dake wuyansa da ya fito da ita waje. Mashin d'in ga shegen kara kaman zai fasa kunne. Tuni maza suka rud'e kaman had'in baki suka d'auka AJ, AJ, AJ, Ai tuni na manta da suyar awarata na tashi a guje na k'ara matsawa dan ganin wannan AJ. fuu ya wuce kaman guguwa wasu shegon motoci suka rufa masa baya. Duk wani dake kan titin saida ya sauke gefe ya bashi hanya. Zo kaga mata,yara da manya yanda ake tururuwan fitowa daga gida. Har Bilkisu sai gata a guje Tsulun kaman an wulluta. Yatsa na cize dan banga fuskar tasaba saboda hulan kwanan dake kansa mai Glass. Amma daga ganin yanayin suffarsa a mashin d'in kaga basamude mutum. NAMIJIN ZAKI. [13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎 👑 By Ashanty Love. (M Afnan) ASHANTY©AREWABOOKS.COM ✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯ BABY AK TAWA WANNAN PAGE NAKI NE KAMAN YANDA NAYI ALKAWARI. KAR KI BAWA KOWA😂 P 5/6. Sai da k'ura ta lafa ne bayan wucewar sa na tuna da awara ta da na bari da sauri na juya ina Addu'a Allah yasa ba'a samu wani d'an iskan ya kwashe ba. Addu'a ta kuwa bata karb'u ba dan an kwashe ragowar nan tas ko marmashi babu. Hannu na dora aka ina salallami. Ni bama abunda Baba Lantana za tamin bane ya dameni dama ragowar na ajiye zan soya mana nida Baffa sai gashi an samu wani matsiyacin yamin bakin ciki. Kai amma walh ko waye wannan wuta balbal ban yafe ba. Inda Baffa ke zaune na kalla har yanzu dai yana nan zaune kuma da alama ya ga duk wanda ya kwashe ragowar awarar nan amma bai hana ba. Amma anyi d'an akuya koma waye ya kwashe min awara. Yasan Baffa na kallan sa amma ya murje ido ya kwashe saboda baisan wani abu wai shi kunya ba. Ko da yake laifin AJ ne, shi dai duk inda yabi babu Alkhairi. Yanzu ta sanadiyar sa gashi na rasa abincin dare. Niba awarar ba kuma abincin ba. Allah ya isa wlh ko uban me ma ya biyo dashi ta layin mu oho. Hayaniya dai bata k'are ba dan kaman an had'a dandazo ne na guggun mutane ana ta yi. Can na hango Bilkisu da k'awayen ta suna ta ihu kaman sunga Annabi. Tsaki naja marasa aikin yi kawai. Kayan na kwashe ina ta mita ni kaɗai. Zan shiga gida Baffa ya kirani na zauna kan tabarma ina zumbura baki. "Me ya faru ki ke bata rai" "Amma Baffa kana kallon wanda ya kwashe awarar da zan soya mana ka yi shiru baka hana ba" "Shi ne abunda ya bata miki rai?" Kai na d'aga ina ji kaman na fashe da kuka. "Ta nawa ce ta rage?"nayi wuff nace "saura ta d'ari biyu Baffa " Murmushi ya yi yana lalube cikin aljihun wandon sa ya fito da chanji d'ari biyar. Mik'o min ya yi "Gashi ki cire kuɗin awarar sai ki riƙe chanjin ki siyi abunda ranki ke so" . dad'i ya kamani yaushe rabo da na riƙe kuɗi nawa na kaina. Duk da cewa Baffa yana k'ok'arin wajen ganin ya biya mana bukatunmu na gida dana waje ban cika tambayar sa abu ba saboda halin rayuwa. Idan kaga na tambayi abu toh ta kama dole ne babu yanda zanyi. Sautari yana kirana ya tambaye ni ko akwai abunda nake so nace A'a sai bukatun makaranta kawai nake gaya masa. Shi yasa indai yana da d'an kuɗi zai bani y'ar dari biyar na cire d'ari biyu na ajiye sauran cikin banki. Cas na lale kuɗin Baba Lantana na damka mata a hannu ita kanta tayi mamaki ai kuwa naga fara'a sosai kan fuskarta da kanta take min tayin abinci. "Maza kije ga abinci can kici ki huta " Ohh wato kuɗi shegen abu ne. Duk irin laifin da mutum zai maka idan da kuɗi mantawa ake Allah ya kyauta. Kwanon na jawo tuwon shinkafa ne miyar d'anyan kub'ewa. Duk da cewa babu komai a ciki amma biyar tayi dad'i sosai. Ka dai bar Baba Lantana da masifar ta da bala'in ta amma ta iya sarrafa abinci kaji kaman ka had'a da Kwanun ka cinye. Sai da naci nayi nak na shige d'aki na cire nayi banɗaki dan watsa ruwa. Bayan nayi salla nayi karatu nabi lafiyar gado na kwanta raina fari tass sai a lokacin Bilkisu ta shigo gidan ko daga ina take oho?. Ina jin fad'an Baffa da ya biyo bayan ta bayan ta shigo Baba Lantana na kare ta barci mai nauyi ya d'auke ni banji yarda suka yi ba. ♥︎♥︎♥︎ Yau tsawon sati d'aya kenan da zuwan AJ layin mu. Har yau da nake gayama maku maganan zuwansa bai mutu ba duk inda kaga group na samari to ana maida zancen kayan jikinsa, ko mashin d'in da yazo dashi na k'asar waje wai bekk(BIKE) ko kaji ana zancen motocin da suke binsa ance duk matakan tsaron sa ne kuma duk turawa ne. Ance..ance.. kai har na gaji dajin zancen wannan AJ wlh. Shinkafa nake gyarawa da yake yau asabar ne da wuri naje kasuwa na dawo zan dora abinci da wuri saboda yau karfe d'aya zan shiga Islamiya. A koda yaushe dai gimbiyar tana zaune gefe tana fama da waya. Baffa tun safe ya fita wasu daurin aure da ake yi a unguwar su ne kuma wakilai. "Yauwa Sahla maza ki gama na aike ki gurin zubairu ki karb'o min mankuli zuryan, sai ki biya gurin Hamisu ki karbo wa Bilkisu d'inkin ta" Kaman nace ita Bilkisun fa nadai fasa na amsa mata da toh. Takarmi na kawai masa na fito . Kasuwan na fara zuwa na siyo mai har zan karya hanya na biyo ta lungu nace kai bari kawai nabi titin abuna yafi sauri. Ina gabda k'ara sawa shagon Hamisu telar wani irin mahaukacin horn ya rudani na kwasa a guje na koma gefe duk da a gefen nake tafiya ashe nayi kusa da kwata sai jina nayi chab'al cikin ta. Wata irin motace mai shegen girma kaman jirgi bak'a wuluk da ita ta wuce a guje babu alamun duk wanda ke tukata zai tsaya ya bani haƙurin ya tsorata ni na fad'a kwata. A fusace na miƙe na rarimi dutse dake kusa dani katan gaske na saita motar da iya karfi na na jefa. Ina jin yanda gurin ya dauka da "ke, ke kul" ai ina tuni aikin gama ya gama cikin ikon Allah kuwa na samu glass d'in motar ta baya. Ji kake tasss Wani irin mugun birki motar taci ta tsaya chak bata motsa ba kan titi. Wani dake gefe ne ya ce "Innalilllahi kinsan abunda ki ka yi kuwa kinsan waye cikin motar nan?" A fusace nace "koma uban waye, bashi da hankali zai dinga yiwa mutane irin wannan horn yana tsorata su?,yanzu dubi yanda yasa na fad'a cikin kwata da kuma asara da nayi" Har yanzu motar na tsaye tsakiyar titi. Ita bata tafi ba,ita bata dawo ba. A fusace nayi motar ina masifa mutane na hanani. "Kowane d'an iska ne ya fito. Saboda kuna cikin mota mai tsada ne ku ka fi karfi ku bada hakuri?. Kuɗin banza da wofi. In Allah ya yarda kafin kaje gida sai tayar motar ta lalace bama tayar kad'ai ba harda motar ita kanta sai inga ta isa da tunkaho". Gaban motar na tsaya ina bugata da iya karfina da naga dai ba fitowa mai motar zaiyi ba na dawo bangaren direba na hau dukan glass d'inta da karfi kaman zan fasa motar dan raina ba k'aramin baci ya yi ba. Jikina gaba d'aya tun daga kuguna zuwa kafata kwata ce har diga nake. Duk wannan bai dameni ba akan man Baba Lantana da ya ke laye cikin kwatar. Babu irin kashedin da bata yimin ba akan kuɗin mannan dubu hud'u da dari bakwai cif ta bani na kwalba biyu. K'ok'arin bode motar da naga ana yi naja baya kad'an ina jijjiga jikina. Da wani irin slow kofar ta buɗe sai kafa ta biyo baya sanye cikin wani farin cambas mai kyan gaske. Kafar kawai ya fito da ita ya ajiye waje wajen minti biyu kafin ya janyo jiki ya fito. Wani irin ingarman namiji ne ya fito ya tsaya gabana sanye cikin wasu kananan kaya rigar kaman ta sanyi mai hulan mai mad'auri ruwan toka sai wando na jeans light blue mai haske. Duk yanda naci burin d'ud'd'ura masa zagi sai na tsinci kaina da rawar jiki wani irin mugun tsoran sa ya shige ni amma na boye hakan a fuskata. Jingina ya yi da motar ya zubamin wasu tsumanmun idansa masu girman gaske da suke gasu nan su ba fari ba baki ba(grey eye's). Ikon Allah shi kuma har kala yake sawa a ido?. Ko da yake alamu sun nuna kaman bature ne. A zafafe nace "kai wane irin mutum ne zaka tsorata mutane haka. A gefen titi nake tafiya ka yiwa mutane wani shegen horn ka tsorata su. Duk kan titin bai isheka tafiya ba sai ka had'a da gefen titi? Wlh sai ka biyani asarar da kasa nayi bazan hak'ura ba" Maimakon ya bani haƙurin sai ya ciro wata irin taba daga aljihun wandon sa ya dora ta gefen bakin sa ya fito da wata lighter ya kyesta. Dago kai ya yi yana wani iran zukar ta na fara tari dan dad'in ta sam babu dad'i. Hannu nasa na toshe hanci ina karkade hayakin dake yowa inda nake. "Malam ka biyani dubu hud'u da dari biyar d'ita dan walh baza kasaci bulus ba" Motar ce ta bud'e wajen mai zaman banza wani hadedden saurayi ya fito sanye cikin manya kayan. Doguwar riga ta shadda fara da wando ta. Yana fitowa ya fad'a kalman data hausana min ciki "AJ, what did she wants?" Au Allah. Toh badai uwata ba walh. Nace a zuciyata. AJ. Ido na zare bayan sunan ya kara dawowa kunyar kai na nayi saurin maida hankali kan sa. Take na fara zikiri cikin zuciyata Wainnahu min suleimanu wainnahu bismillah rahmanun rahim, kalu Innalilllahi,hasbunnallahu wa ni'imal wakil.A tsorace na ja baya ganin shi gab dani . Kai wannan mutum badai tsayi ba. Kawai sai ji nayi ya fesamin tabarnan a fuska ta. Tari ya mugun sarke ni tuni tsoron nasa ya bace na hau masifa "Allah ya isa wlh bazan yafe ba. Mugu Azzulumi " "Ke baki da hankali kinsan dawa ki ke magana kuwa?" "Koma waye shi ai ba Allah bane. D'an Adam duk inda yake dajara ce dashi shi kuma bai isa ya wulaƙantani ba na kyale" Baki d'an uwan nasa ya hangame yana kallo na cikin matsanancin mamaki da Alama yaune rana ta farko da aka yi musu haka. Sai kuma ya kwashe dariya na kara tunzura zan kwaba masa bakar magana kawai naji hannunsa kan fuskata ya cafki lebena da iya karfinsa. Ji nayi kaman na saki fitsari saboda azaba dagewa nayi na gartsa masa mugun cizo da har saida na huda hannun nasa. Da sauri kuwa ya sakarmin baki yana yarfe hannu da wata irin kaukausar murya tamkar a shake (deep voice) ya yi magana. "Fuck" Tsabar bakin ciki hawaye suka biyo kuncina amma bakina bai mutu ba. "Allah ya isa daka tab'a ni dan iska kawai ,kedarin banza,kedarin wofi. Ka d'auka kowama irin kane dan iska da zaka dinga tab'a mutane. Allah sai ya sakamin wlh " yawu na tofa masa na juya fuu ina sharar hawayen bakin ciki. Har waye shi dazai tab'a ni cikin mutane salon yaja ace nima y'ar iskace irin sa. Duk inda na wuce sai an tambayeni me ya faru bani da bakin magana sai kuka har naje gida. Da ace Sahla zata juya taga irin kallon da ya bita dashi to dah tabbas sai taji kaman ta ruga a guje tana fitsari. Kallo d'aya ya yiwa gungun jama'ar dake gurin suka fara tseren gudu tamkar wanda suka yi gamo. Zuka d'aya yawa tabar ya shanye ta ya jefar a k'asa ya take ta yana kallon bayanta tana tafiya kaman zata kifa tsabar sauri duk inda tayi ruwan kwata na binta kaman zuba mata ake. Harshen sa ya taune cikin bakin sa idansa ya yi wani irin ja ya kalli hannunsa dake digar jini. "I will destroy you" Ya juya a zuciye ya shige mota. D'an uwan nasa da suke tare ya yi saurin shiga motar shima dan yanda yake a fusacen nan tsaf zai iya tafiya ya barsa a gurin. Gaskiya yaga k'ok'arin yarinyar da alama bata tab'a jin labarin AJ ba tunda har tayi jarumtar cizon sa bata tsaya a nan ba harda tofa masa yawu? Gaskiya yaga k'ok'arin ta. Gashi ta janyowa kanta masifar da babu ranan karewar ta. ♥︎♥︎♥︎ "Uwata, subhanallahi me ya same ki haka?" Ai ina jin muryar Baffa na k'ara rushewa da kuka nayi inda yake tsaye da wani. Saboda yanda bana cikin nutsuwa ta ban kula da Malam Halliru bane. Cikin damuwa ya k'ara jefamin wata tambayar. "Me ya faru jikin ki duk kwata haka? " Ina kuka na kwashe duk abunda ya faru na gaya masa amma ban fad'a masa ko waye ba dan nasan fad'a zansha idan yaji wancan tantirin yaron ne. Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi. "Shiga gida ki gyara jikin ki, zan shigo na samu Lantana " Shigewa nayi ina sharar hawaye. Ai tana ganin shigowa ta ta rafka salati tana tafa hannu. "Ni dama nasan sai anyi haka. Wlh wannan yarinyar da mugun hali ki ke. yanzu dan tsabar bakin ciki saida kika salwantar min da kuɗi. To ahir d'inki sai kin biyani wlh " Ban kula taba tana ta banbami kaman zata dokeni nasan muryar Baffa da taji a kofar gida ya hanata. "Da Allah ki matsa a kan mu mana haba, kinzo kin tsaya mana a ka da warin kwata wa ya sani ma ko kina sane kika jefa kan ki tunda ba kece da asara ba. Ai wlh Baba karki raga mata sai ta fito miki da kuɗin ki" Ji nayi kaman na rufe su da duka gaba d'ayan su. Tana kwance kan cinyar ta tana yi mata susar kai. Wuce su nayi na shige banɗaki na barsu tana ta masifa. Har na fito bata daina banbami ba na shige d'aki. Ina sallah naji Baffa ya shigo yana mata bayanin abunda ya faru yasan halin Lantana da rashin hak'uri sai daya lale kuɗin nan ciff ya biya ta dan kafewa ta yi kuɗin sana'a ne kuma gaba d'aya dan jarin ta tattare ta bani na suyo mai dashi. Makarantar da banje ba kenan ranan na kwanta ko tsakar gidan ban fito ba sai da aka yi sallan la'asar na fito nayi alwala na d'auki abinci na dake cikin kwano na shige d'aki. Haka na wuni sungun -sungun da fargabar abunda zaije ya dawo. [13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎 👑 By Ashanty Love. (M Afnan) ASHANTY©AREWABOOKS.COM ✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯ P 9/10. Yau tsawon kwana biyu kenan da zuwan Halliru da sakon soyayyar daya kawo. Malam Hallirun ma na daina cewa sai Halliru dan yasan bazai samu damar da yake buri ba. Harta islamiya a kwana biyun nan Kin zuwa na yi da niya nake janyo wani aike da lokacin makarantar ya yi saboda kawai kar naje. Ita kanta Baba mamaki take yanda nake rawar jiki idan ta aike ni. Baffa kuwa bai tab'a tambaya ba dan yasan bana fashin makaranta dole sai da kwakkwaran dalili, shi yasa yanzun ma ya sawa ransa haka ne. Yau da kaina nakai markad'en awara can bayan layin mu sabida almajirin da yake kaiwa ya tafi garin su noma dan muna cikin lokacin rani ne. Bansan me yasa ba amma tunda na fito sai nake ji kaman ana kallo na. Na juya gabas,kudu,arewa amma banga alamun hakan ba kowa sabgar gabansa yake. Yo ma ina abun kallan ni dai nasan ba wani kyau ne da ni ba sannan abun da ke jan hankalin mazan ma suke kallan matan ni bani dashi. Har naje nakai markad'en na dawo jikina bai daina bani haka haba. Gabda zan shiga gida naji sallamar Halliru kusa dani. Chak na tsaya ina kallan sa gefe na sanye cikin shadda fara yau babu hula a kansa gashin kan nasa yana ta zuba shek'i yasha gyara. Babu laifi ya yi kyau kam dan baza ka kirashi da mummunan ba yana da kyau daidai misali. Baki ne shi dan na fishi haske ga wani gemu daya tara yasha gyara. Sannan bashi da tsayi sosai kusan zan iya cewa da kad'an ya fini. "Sahla, slma nayi sallama baki amsa ba" Sanin darajar sallama yasa na amsa masa a cunkushe na cigaba da tafiya yana bina. "Markad'e ki kai ne?,kawo na riƙe miƙi mana" "A'a ka barshi na gode" "Sahla, don Allah kar mu tsaya muna ja-inja a kan titi ki kawo na riƙe, ai ni nace ki kawo" Badan naso ba na miƙa masa dan nima bana san maganan tayi tsayi tsakanin mu. Har muka k'arasa kofar gida magana yake cikin Jan hankalin da nutsuwa duk da ba bashi amsa nake ba sai naji yau haushin nasa da bnke ji ya ragu. A kofar gida naja tunga na miƙa hannu zan karb'i markad'en ya riƙe. "Baki bani Amsa taba Sahla, kin amince min na fito? " Rasa abunda zance masa nayi kawai na d'aga masa kai dan na kagu ya bani kayan na shige gida. Dan in muka cigaba da tsayuwa anan tsaf zan kwarfe shi wlh. Wani irin murmushi ya sakarmin ya miƙo min bokitin na karb'a na shige gida da sauri. "Ke da waye nake jin maganan ku a kofar gida" "Malam Halliru ne" "Waye kuma wani malam Halliru? Halliru ne ko jafaru? Wato kin fara jaye-jayen maza ko?,bari ma..." Bilkisu ta yi saurin katse ta "Baba shi ne fa Malamin nasu da naji Baffa yana miki magana ranan " "La'ilaha illallahu Muhammadu rasulullahi (S.A.W), wato labe ki ke mana kenan idan muna magana ko?" "Nifa Baba ba labe nayi ba kin manta a tsakar gida ya yi maganan ranan " Tayi maganan tana kunkuni alamun taji haushin kalman da Baban ta furta. "Au toh yi hak'uri y'ar lele na manta ne ai shi yasa daina fushi " Kai kawai na girgiza na shige d'aki na barsu nan tana ta faman lallashi. Tun ranan da Baffa ya yi magana kan saurayin Bilkisun ya fito wata sabuwar tarairaya ta tashi. Wani irin kulawa Baban ke bawa Bilkisu saboda burin ta ya cika Bilkisun ta ta samo attajirin mai kuɗi dake yi musu b'arin dukiya ba kad'an ba. Kullum da irin abunda Bilkisun ke shigowa dasu. Da Baffa ya gani ranshi ya masifar b'aci ya dinga fad'a ta inda ya shiga bata nan yake fita ba. Sai ya zama yanzu duk abunda ya bata sai a shigo dashi a boye ba'a barin Baffa ya gani a yanzu haka ma ya chanza mata Babbar waya babu abinda bata yi cikin ta. Ni dama basa bi ta kaina tunda sunsan ba fad'a zanyi ba. ♥︎♥︎♥︎ K'aramar motace kirar BMW fake chan gefen titi bak'a mai bak'in titi. Amin dake zaune mazaunin direba ya juya yana kallan AJ dake kwance bayar motar ya zuba mata ido yana zukar had'addiyar walking stick dake hannunsa gold colour (taba). "What are we doing here ne AJ?, Akwai wanda za ka gani ne? Almost 1hr kenan munanan baka cemin komai ba" "I need to know" Shi ne kawai kalma da ya furta masa. Kan Amin ya k'ara d'aurewa da wannan maganan tashi. Juyawa ya yi shima inda yaga ya maida hankali. Ido ya d'an zare yana kallan yarinyar nan data musu rashin kunya kwana ki. Tabbas ita ce. Tafiya take amma sai waige-waige take kafin ta shige wani lungu riƙe da katon bokiti. K'are mata kallo ya yi bata da wani abu da zata ja hankalin AJ kanta ya .yaga irin y'an matan da suke bibiyar AJ kaf dinsu mata ne da suka amsa sunan Mace. Mata ne da suke so Booby da Assy amma ita wannan gatanan baiga alamun tana dasu ba duk da cewa ta zurma wani uban hijabi ne dake Jan k'asa. Yes a fuska kam tabarakalla dan tana da kyau zaice yasha ganin mata kyawawa na bibiyar AJ da har kyan nasu da ya yi yawa yasa duk kyan ki yake ganin ki saffa-saffa. Abun tambayar anan shi ne me yasa AJ yau da kansa ya d'auko sa suka zo nan ba tare da matakan tsaron sa ba?. Sunzo kuma sun b'uge da kallon wata yarinya? . Shi yasan tun ranan data yiwa AJ wannan rashin kunyar bai d'auki mata ki a kanta ba akwai lauje cikin nad'i ,tabbas kuma zai gano koma mene. Sunanan zaune sai gata ta dawo still dai riƙe da bokitin kafin ta kauracewa idan su kuma wani ya tare ta suka jera suka tafi tare. Wani irin mugun smirk AJ ya yi yana zuk'ar tabar sa idanshi a kanta har ta shige gida. "Let's go" Amin bai musa ba ya tada motar suka bar gurin ba tare da yace komai ba. ♥︎♥︎♥︎ Ni kaina ina mamakin yanda duk na zubar da maka maina a kan Halliru. Yanda naci burin wulaƙan tashi sai abun ya juye yanzu ina matuƙar ganin girmsa da jin kunyar sa. Bazan iya cewa ga takamaiman abunda nake ji akan sa ba amma nasan kasancewa ta dashi yana sani farin ciki. Ya iya kalamai ne ga kulawa bansan ta yarda zan kwatanta ba. Ana cewa malamai basu soyayya, ni kuma sai nake ganin sunfi samarin ma iya zuba kalamai na love dan gashi cikin dan k'ank'anin lokaci ya chanza min tunani. A yanzu maganan mu tayi nisa dan har iyaye sun shiga ciki sati mai zuwa nake tunanin za'a kawo kayan sa rana da lefe. Bilkisu ita saurayin nata wai ya fita amruka sai ya dawo Baffa yaso a had'a amma daya ga sunfi so s𝐮yi nata bidirin daban sai ya kyale su kawai. Hira muke nida Sahiba bayan mun taso daga makaranta. Babu irin tsokanan da basuyi min ba bayan sunji labarin soyayya ta da malam Halliru gashi abu ya yi nisa. Tun ina fushi muna fad'a har na hak'ura. Daidai layin su muka yi sallama ta wuce gida nima sai na karya hanya nabi ta lungu ina ganin zanfi sauri ina kuma da suyar awara. Dankareriyar motace bak'a wuluk tasha gabana kaman zata bugeni. Da sauri na matsa gefe na d'ura uban ashar.kam bala'i ai kuwa da an tab'a ni da yau anga bala'i wlh. Bud'e motar a kayi gabana ya yanke ya fad'i. Wannan face d'in da har sallan dare nake Allah karya k'ara had'a ni da ita yau gashi a gabana sanye cikin kananan kaya gajeren wando da riga mai yankakken hannu. Wani salo har ta gashin kansa a tufke yake a tsakiyar kansa dama maza na tufke gashi ne?. Zikiri na fara ina kallansa tsoron sa fal cikin zuciyata amma fuska ta tamke. Ya kara wani irin girma kaman wani bijimi .rigar ita kanta duk da ba mai kamawa bace amma ta kamashi dam kaman kirjinsa zai yaga ta. Da wata irin tafiyar izza ya tako gabana sai dana d'aga kai na kall𝐞 sa. Kai MashaAllah ubangiji ya yi haliitta a nan. 🙆‍♀️ANYA KUWA AJ?ME KAKE SHIRYAWA NE? [13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎 👑 By Ashanty Love. (M Afnan) ASHANTY©AREWABOOKS.COM ✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯ P 7/8. Sati d'aya kenan da haɗuwa ta da AJ. Tun ina fargaba da tunani har na sake na cigaba da sabgogi na. Labari dai ya bazu cikin unguwa tun ana fad'an sa daidai ya zama an k'ara masa sukari da wasulalluka. Harda masu cewa ai bashi da karfi dana riƙe wuyan rigars na dinga ta mule dashi ina zuba masa mari sai da ya bani haƙuri, wasu suce A'a ai shine ya dinga zabga min mari na tawo hanya ina kuka. Kuji min mutane da neman min masifa da bala'i?toh Ta Allah ba tasu ba hakan bazai faru ba. A rana idan ban maida zancen nan sau biyu ko uku ba to zanyi sau hud'u. Sosai nayi suna fa duk wanda ya sanni da wanda bai sanni ba yazo wai na gaya masa ya akayi me ya faru ne?. Naga AJ ido da ido?. Ya kamanni sa suke?da gaske yanda ake fad'a yafi haka a fili?. Bilkisu da ba shiri muke da ita ba sai naga mun kulla zumuncin karfi da yaji. D'an abu kad'an za kaji ta jehoni a ciki. ikon Allah. Yanda labarin ya bazu unguwa ya kai har kunnan Baffa ranan nasha fad'a ba kad'an ba rabon da Baffa ya yi min fad'a irin wannan na manta. Baffa shi laifi na ya gani wai da ban kula shi ba na kyale shi inzo shi in gaya masa zaisan yanda zaiyi da Baba Lantana. Yau tun safe Baba Lantana ta fice ita da Bilkisu wai suna biki can dangin Baban ta. Kananin ta ke Aurar da yarinyar sa. Dana gama abunda na ke miƙewa nayi na kwanta sai barci. Sai wajen la'asar na tashi. Bayan nayi salla na fito ina k'ara kimtsa gidan ina wanke- wanke Baffa ya shigo. "Uwata ajiye aikin nan ki wanke hannu kije maza kinyi bako a waje" Da matsanancin mamaki nake kallan Baffa Bako kuma? Toh ni yaushe ma nayi saurayin da har zaizo gida zance? "Tashi mana kina zaune" Jiki a sanyaye na wanke hannu hijabi kawai na chanza na fito ina dube -dube. Saboda ya juyamin baya yasa ban gane shi ba na tsaya a bayan nasa ina k'are masa kallo. Shadda ce a jikinsa Ash data sha guga ya karya hula a kai. Gyaran murya nayi tare da yar sallama kad'an. Da sauri ya juyo kuwa na mugun haɗe fuska. Idan ba ido bane kemin gizo to tabbas malam Halliru ne sai wani murmushi yake. "Kinyi mamakin ganina ko?" Ido kawai na zuba masa ban bashi amsa ba. Ji nayi kaman na rufe shi da duka me yake nufi ne wai? Allah yasa ba maganan su Barira ce take shirin zama gaskiya ba?in kuwa haka ne toh wlh bai isa ba. Sai ya katse min tunani da cewa "Nasan za kiyi mamaki da ganina a nan. Sahla ni ba yaro bane bazan tsaya ina b'oye- b'oye ba, tabbas abunda ki ke tunani haka ne. Ina sanki Sahla kuma ba wasa nazo yiba nazo ne da maganan aure dalilin da yasa na fara neman izni gurin Baffan ki. Amincewar ki kawai nake nema ki bani dama na nuna miki soyayya ta inshaAllahu sai kinfi kowa farin ciki zan kasance mai faran ta miki. Zan baki lokaci kiyi tunani amma ina rokon ki don Allah kar kice A'a " Kutmelesi da alama dai yaci kai ne walh. In banda rainin hankali ya gama cin zalina yanzu ya kewayo wai sona yake?. "Ki zauna kiyi tunani mai kyau don Allah. Zan dawo gobe danjin amsar ki na barki lafiya" Da ido na bishi kaman na bishi na kwarfe da wani d'an gololon wando wai shi uztaz. Tsaki naja mai karfi na shige gida ina zagin sa cikin raina babu damar yin hakan a fili dan Baffa yana nan. Maza wlh Sam basu da kunya. Wane baisan irin karan tsanan daya d'oramin ba a makaranta. Bani da ikon yin wani d'an kuskure zai jibgeni kaman ya samu jaka shi ne yanzu dan rashin kunya zaice yana so na yazo da wata y'ar k'aramar murya yana roko? Kwafa nayi na cigaba da wanke- wanke Baffa na bina da kallo. Ina gamawa na d'ora mana wake da shinkafa. Zama nayi kan tabarmar da Baffa ke zaune na fara daka mana yaji. "Uwata" "Na'am Baffa" "Na yaba da hankalin yaron nan. Dama duk wani d'a na kwarai kafin ya fara tare yarinya a waje sai ya fara neman izni gurin iyaye. Saboda haka na amince masa nace duk lokacin da kuka gama daidaita kanku ya turo iyayen sa kawai basai an tsaya ana Jan wani lokaci ba sai a had'a keda y'ar uwarki don itama Lantana ta dad'e da kawomin wani wai yana sonta kuma da gaske auran ta zaiyi" Wani irin dum naji a kirjina. Abunda bazai tab'a yiwowa ba kenan babu zanchen dai-daita kai. Kai na sunkuyar bance komai ba shima Baffa bai k'aramin maganan ba muka hau zanchen Kaka muna dariya a haka su Baba Lantana suka riske mu. ♥︎♥︎♥︎ PG/18+ THE PALACE. Katon d'aki ne da idan ka k'are masa kallo ya yi girman wani k'aramin gida guda. Wata irin chandler ce a saman falon da ta kusa cinye rabin silin saboda girma da tsayi. Chan gefe wata katuwar TV ce kaman glass bango gudu sai k'asan d'akin glass ne da wani irin blue ruwa ansa wasu irin kifaye masu masifar kyau suna yawo cikinsa kaman AQUARIUM. Hasken ruwan yasa gaba d'aya d'akin ya bada wani irin blue dim light mai masifar kyan gaske idan ka shiga kaman kar ka fita. (ALJANNAR duniya kenan) Ga wasu irin kujera kaman koshin farare da swing chair a chan gefe. Babu wani tarkace a falon hakan ya kara kawata shi sosai. Slow music ke tashi cikin d'akin dum-dum kaman d'akin zai ruguje. Chan kan wata kujera da tafi ko wacce girma kaman gado tana swinging a hankali yake kwance daga shi sai gajeren wando dake so tight a jikin sa. Wasu y'an mata ne guda biyu turawa d'aya kan cinyarsa d'aya gefen sa. Wani irin lap dance suke bashi suna striping kayan jikin su . Yanda d'ayar ke zaune kan kugun sa tana juya mazaunai kan mini d'in sa wadda ke gefen sa tana shafa kirjinsa da packs dinshi cikin wani irin salo yaci ace imma release ne ya yi sau uku ko biyu. Awa biyu kenan tun d'azu suna abu d'aya amma nothing babu wani reaction yana nan kwance kaman lawashi. Su kansu sun gaji basu isa kuma su furta hakan ba. Tabar dake bakinsa ya zuka ya buɗe manyan grey eye's dinshi dake rufe. kallan yarinyar dake kan cinyarsa ya yi da wata irin deep voice yace "Leave " Tun bai k'arasa furta leave din ba suka miƙe a guje suna tsince kayan su dake yashe a k'asa. Wasu rafars na dollars ya d'iba guda biyu ya watsa musu a guje suka kwashe sukayi waje basu da matsalar komawa gida. Private jet ya tura tun daga can London aka d'auko so, za kuma a mayar dasu. Ya jima a kwance bayan tafiyar su kaman wanda aka tsikara ya wani tashi a fusace ya yi tankamemin toilet nashi dake k'asa. Had'addiyar shower d'inshi ya shige da aka kewaye da glass. Komai na toilet din gold colour ne( waya sani ma ko gold dinne ba kala bace.haha). Ruwan sanyi ya sakarwa kanshi hannushi dafe jikin bango ruwa nabin kansa da bayan sa. Idansa dake rufe ya buɗe saboda jijiyarsa da yaji ta wani harba kaman wutan nefa. Dif ta kawo ta d'auke. Ba komai ya jawo hakan ba sai flash na wannan bak'ar yarinya data yi masa gizo lokacin da hannunsa ya tab'a ta. A 31 life nashi wannan shi ne karo na farko da ya samu wani reaction game da mace koma macen ma bak'ar fata da yake ganin su kazamai munana shi yasa takanas ya yi hayan turwa tun daga waje, kalar sa.ko matan da suke bibiyar sa babu bak'ar fata sai in bakin naki ya kasance mai haske kaman na yan Morocco ko Ethiopians or Black Americans, but wannan bak'a ce. She is black. Shi kanshi ya yi mamakin kansa da a wancan ranan bai chanza mata kamanni ba wannan feeling shi ya yi holding dinsa back. Ya tsani mace ko wace iri ce ta rab'e shi amma yau gashi da kanshi bayan wasu shekaru da suka shud'e ya hayo strippers tun daga London dan ya tabbatar da abunda yaji ranan. Yana so ya tabbatar wa kansa ba ita ce ta janyo masa wannan reaction ba ,baya yafiya he will soon destroy her. Wani irin harbawa ta k'ara yi ya yi wuf ya damke ta cikin hannunsa ya matse ta da karfi. Sai kuma diff ta k'ara d'auke wa kaman an kashe wutan nefa ta koma kaman lagwani. Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi ya kaiwa bango naushi. "What the f*ck just happened? " Ya yi tambayar da babu mai bashi amsa . All this facade da yake sawa na Bad boy characters yasan cewa deep down his not A REAL MAN. Ya yi hiding the Real AJ a wannan fuskar. ♥︎♥︎♥︎ Cikin matsanancin damuwa ya juya ya koma inda ya fito sakamakon karo da yaci da y'an matan da suka fito daga bangaren AJ. A Koda yaushe addu'ar sa guda d'aya ce duk sanda ya kai goshin sa k'asa. Allah ya shirya masa yaran sa su dawo kan hanya mai kyau. Hajiya Kilishi dake kishingid'e cikin kayatatcen falon ta bayi na kanta wasu na mata tausa da firfita wasu na bata labari dan nishaɗi. Yana shigowa duk suka miƙe cikin girmamawa suka fice daga d'akin. Guri ya samu ya zauna kusa da ita cike da damuwa. A duk masarautar nan ita kaɗai ce macen da yake samun nutsuwar zuciya a tare da ita saboda macece dake da nasibi da kuma hangen nesa. Tasowa ta yi har inda yake zaune ta durkusa gaban sa tana murmushi mai k'ayatar wa. "Wanene ya tab'a min Baban JABEER , mijina abin sona abin alfahari na. Bacin ranka babban tashin hankali ne a gari ni farin cikin ka tamkar ammin albishir ne da Aljanna. Gayamin waya tab'a min kai ka ke fushi yanzu nan na d'auki mataki a kansa" Duk irin damuwar daya shigo da ita saida ya saki murmushi. A duk lokacin da yake cikin damuwa irin wannan tasan hikiman da zatayi ta mantar dashi damuwar da yake ciki shi yasa yake alfhari da ita. Tafi mishi sauran matan shi da babu abunda suka sa gaba sau kishi. "Kinsan maganan gizo bata wuce ta koki. Nida wancan yaron naki ne. Na rasa yanda zanyi da JABEER ya nutsu ya daina duk abinda yake. Lamarin sa kullum sai k'ara tabarbarewa yake. Yanzu na fito daga sashen sa naci karo da mata suna fitowa babu ko suturar arziki a jikinsu. Yanzu me ki ke tunani zai faru idan aka ji wannan babu cikin masarauta? Kullum da abinda za'ace Jabeer ya yi. Ni na gaji ina ganin zance masa ya moma gurin uwarsa kawai dama ai ita take d'aure musu gindi har suka zama abinda suka zama, da tabani su tun-tuni dana ce ta bani da duk hakan bata kasance ba" Cikin matsananciyar damuwa ya k'ara maganan kaman zaiyi kuka. Kuss dashi ta zauna duk cewa girma ya kama su bai hana ta mayar dashi yaro karami ma a duk lokacin da suke tare. Janyosa tayi ta kwantar kan cinyar ta tana shafa masa kai a hankali kaman maiyi masa tausa. "Addu'a zamu dage mu cigaba dayi masa inshaAllahu Jabeer na kan gab'ar shiriya.kar kace haka. Ita jarabawar Ubangiji tana kan kowa ne. Sai kaga suna hannun naka amma idan Allah ya yi da wannan hali shima bazasu fasa yinsa ba. Bana so kana ganin Laifin MaMa QUEEN akan haka. Tana K'ok'arin itama a kansu .Kasa a ranka kaman ya shiryu ne da yardar Allah zaka zama mai alfahari da haihuwar sa bama kai kad'ai ba harmu kanmu ,Ba'a yanke kauna da rahamar Ubangiji. Shi mai harama ne a koda yaushe. Mu dage dayawan Addu'a da kuma sadaka ka kuma kasance mai adalci ga al'ummanka ,ka kasance mai tausayi da duba na k'asa dakai. ALLAH bai baka mulkin nan ba dan kafi wani ne. A'a shima mulkin yana d'aya daga cikin kaddarar ka ne. Mu dage dakai masa kukan mu Allah zai amsa mana da yardar sa" Bata yarda yabar sashen taba saida ta tabbatar damuwar daya shigo da ita ta ragu. A lokacin da yake bangaren nata kuwa tuni labari ya cika masarauta Yarima ya d'ebo karuwai daga kasar waje sarki da kanshi ya gansu amma ya kasa taɓuka komai a kai. Magana taita yad'uwa ana ta cece-kuce. Mak'iya suka samu abun fad'i wajen ganin sun kawo karshen Mulkin sarki Saif da D'ansa Yarima AJ ko nace King AJ. [13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎 👑 By Ashanty Love. (M Afnan) ASHANTY©AREWABOOKS.COM ✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯ MMN MEENAL WANNAN PAGE NAKI NE,KIYI DUK YANDA ZA KIYI DASHI😎 P 11/12. Last free pages. Cikin dakiya nace "Lafiya dai malam?" Sai da ya d'auki wajen minti biyu kafin ya fara magana da d'ai-d'ai. Har na kosa ina shirin juyawa a fusace na bar gurin. "Did- you- think -you- will -get away -with -what you have done?" La'ilaha illallahu Muhammadu rasulullahi (S.A.W). Shi kenan yau ya zage ni har tattaba kunne. Uwarki,ubanki,kakar ki? Har Baba Lantana bai kyale ba saida ya sata Babar ki Lantana?. Eh toh banji haushin zagin ta da ya yi ba ita .Aikuwa na d'ora hannu aka ina ihu "ya zagarmin iyayi har tattab'a kunne, toh wlh badai uwata ba ta mutu sai dai ko in taka" Wani irin kallo ya min ya k'ara matsowa gab dani sosai nayi saurin ja baya sai ji nayi na jingina da bango ginin wani kango d'aya sha gabana. Gaba d'aya ya saka hannu ya dafe saman kai na ya sani tsakiyar sa . Wani irn bugawa kirjina ya yi na fara wurga ido ko zan hango gilmawan wani shegen layi shima kaman anyi ruwa an d'auke babu kowa . "Kaga ni ba yar iska bace ka matsamin na wuce" Kaman ba bada mutum nake magana ba dan hankalinsa gaba d'aya ya kar kata kan wani abu daban. Da sauri nima na kai kallo na inda ya maida hankali. Gaba d'aya hankalin sa da nutsuwar sa na kan kirjina ne babu wani alamun damuwa ko shakku a tare da shi. Wani irin ihu na saki da kururuwa bansan sanda nakai masa mari ba na fashe da kuka. Da azama na durkusa na fita ta karkashin sa. "Allah ya isa, dan iska arnan banza da wofi." Fuu na wuce ina kuka harda d'an gudu na da share majina. Eh lallai na yarda shi din hatsabin dan iska ne. Yanzu duba yanda ya tsaya yana karewa kirjina kallo ba tare da wata damuwa tattare dashi ba abin haushi a titin Allah?. Allah ma ya taimake ni babu kowa yanzu idan an ganmu a haka me za'a ce? . Gabda zan shiga Layin mu na tsaya na saita fuskata kaman babu abunda ke damuna. ♥︎♥︎♥︎ Matsanancin mamaki yasa shi daskarewa a tsaye ya kasa motsi har ta b'acewa ganin sa . What the f*ck? Yau shi AJ wata k'aramar banzar yarinya ta mara? Shi AJ da a kewa inkiya da King? . Shine fa ko sunan sa aka ji yara da manya suke firgita .shi ne fa, shi ne fa..wai what the f*ck is happening ne da yake kasa reacting a kanta kaman wadda take saka abu ta d'aure .what kind of magic take amfani dashi a kansa da wani irin zuciya ya fisgi murfin motar zai bud'e tsabar yanda yasa kwanji gaba d'aya murfin ya baro daga jikin motar kai kace irin abu ne mai sauki da ana tab'a shi zai b'alle. Wurgi ya yi da murfin motar ya fad'a ciki haka a zuciye ya tada motar da wani bala'in gudu ya harba ta kan titi. Ta baya ya shige inda yake ajiye motacin sa da sunfi gudu ashirin latest duka-na dukan wannan. Duk da cewa a sirrance ya shigo amma labari tuni ya baza masaurata yarima ya dawo rai bace ga motar da yafita da ita babu murfi. Tuni aka fara shiga taitayi da gujewa haɗuwa dashi. Maimartaba yana fada da wasu manya baki da suka zo daga zaria. Magana suke akan sarkin zazzau ya turo su dan k'ara karfin zumuncin dake tsakanin su ta hanyar had'a yaran nasu aure. Har suka gama jawabi sarki Saif bai iya cewa komai ba sai murmushi da ake cewa yafi kuka ciwo. Harga Allah zaifi kowa san wannan had'in amma bazai so ya zama mai san kansa ba. Kwata-kwata gimbiyar Juwairiya bata dace da wannan tak'a d'irin d'an nashi ba. Yana mamaki yanda yaran sarakai da suke mutunci suke nacewa JABEER dinsa duk da sunsan halin sa da kuma tarbiyar da yake da ita shi yasa idan sunzo yake fad'a musu gaskiya amma sai yasha mamaki da amsar da suke bashi sunsan halinsa sunsan wane shi a hakan kuma suke so a had'a. Bazai manta had'in da ya yi ba da yarinyar sarkin Abuja. Sai da ran kowa ya baci amma duk da haka basu saduda ba har yanzu suna bibiyar yaron nasa. Kasa cewa komai sarki ya yi har suka gama jawabi. Waziri dake zaune ya karbe zancen "In banda abun Gimbiya Juwairiya me za tayi da d'an iskan yaron da kowa yasan halinsa na bin mata da shaye-shaye. Ga yara nan masu hankali da nutsuwa ga Amin d'an gurina abunda ya yi Yarima ai shi ya yi amma tarbiyar ba d'aya bace tunda shi yana da hankali sai tafi kowa farin cikin samun sa a matsayin miji". Wani irin abu ne mai daci ya daki kirjin Maimartaba. Bashi da wani abu dazai furta ko kare d'an nasa dan gaskiya ya fad'a. Duk da haka Murmushi ya yi mai ciwo yana kallan mijin yayar tashi dake kuma wazirin sa. Kaf fad'in masarautar nan su uku kawai Allah ya bawa margayin Sarki Baban su daya rasu shekaru da d'an dama. Khalisa ita ce babba sai shi Saifullahi sai kuma autar su Zeenat da suke kira Gimbiya. Ita tana can US da mijinta da yaran ta dan taki zaman nan. Tun kuruciya shida Khalisa sun taso ne masu banbancin ra'ayi. Tana da san mulki da nuna isa da iko. Da ace ita da take babba Allah ya yi ta namiji toh da tabbas ita zata maye gurbin mahaifin su. Toh sai Allah yasa tazo a mace ya kasance shi ya gaji babansu. Wannan dalili yasa basu jituwa da ita sosai dan har yau bata fidda ran cewa d'an ta Amin zai gaji mulki ba tunda shi ya yi mulki toh itama dole ne wani nata ya yi mulki dalilin da yasa tasan duk yanda za tayi aka dora mijin ta (Shazali) a matsayin Waziri dan tace ba'a isa shi kaɗai ya yi mulki ba da nashi iyalan itama dole tana da hakki a kai. "Allah yaja da ranka wannan sako ne daga sarkin zazzau, kafin muzo ma saida ya kara jadda cewar yasan halin sa yasan kuma halin ubansa. Saboda halin sa baza a kii had'a zuri'a ba mai inganci. InshaAllahu zai shiryu shi d'a ai nakowa ne babu wanda Allah baya jarabawa da irin su .Baban sa mutumin arziƙi laifin d'an sa bazai shafe saba tunda kowa yasan irin k'ok'arin da yake a kansa. Kasan ance aure ma yana gyara mutum inshaAllahu Juwairiya zata bada nata gudun mawar wajen jawo hankalinsa ya zama nutsutstsen yaro bacin haka ma ita da kanta tace taji ta gani tana san sa a haka. Mudai fatan mu ku bamu amincewar ku" Kululun bakin cikine ya tsayawa Waziri ya kasa maida martani dan sun d'aure shi. K'aramin tsaki yaja da Maimartaba kad'ai dake zaune kusa dashi yaji ya saki murmushi yana mai jindaɗin wannan kalma da suka furta. Kama wanda aka jeho ya shigo fadar rai b'ace .tafiyar sa kad'ai ya isar musu da shigowar sa tun kafin ya bullo idon su. Tsakiyar fadar ya tsaya yana zuba uban huci ko kaɗan bai damu da mutanen dake cikin fadar ba bare su samu arziƙin sallama bare gaisuwa. "Kunga abinda nake fad'a muku, baya ganin kowa da daraja. Yanzu fisabillahi me za'ayi da wannan a matsayin miji da baya ganin girma da darajar iyayen sa bare na gaba dashi." Wani irin mugun kallo AJ ya wurga masa ya yi saurin d'auke kai koda wasa baya iya furta magana irin haka a gabansa sai dai bayan idansa ko gaban Sarki tunda yasan yanda Sarkin keda sanyi duk irin zagin da cin mutuncin da zaiyi bazai d'aga kai ya kalle sa ba. Wani lokacin shi ke k'ara hura wuta wajen ganin ya b'ata AJ cikin masarauta. Wato daga shi har Khalisa komai nasu iri d'aya ne shi yasa suke zaune har yanzu ba tare da anji kansu ba. Suyi ta had'a tuggu da munafurci. Runtse ido Maimartaba ya yi zaciyarsa kaman zata buga ya buɗe su ya yi d'an murmushi na yake ya miƙe yana bawa bak'in hak'uri da inshaAllahu zasuji daga garesa nan bada jimawa ba. Wuce AJ ya yi dake tsaye har zuwa lokacin yana huci cikin kowa ya d'uri ruwa babu wani wanda ya k'ara motsi tunda ya shigo fadar. Kaf dinsu ya bisu da shegen kallo kafi ya juya a zafafe ya bi bayan Maimartaba. A katon falon shi ya riske sa tsaye ya zubawa k'ofar da zai shigo ido yana ganin sa kuwa ya saki ajiyar zuciya ta taho gabansa ya kama hannunsa zuwa tsakiyar falon. Ido ya zubawa d'an nasa yana nazarin sa. Hakika Allah ya yi wa yaron nasa baiwa da ba kowa keda ita ba. Idan ka kuruwa idan nasan ido sai kaga kwayar har wani kyallin take kaman zaiba. Numfashi yaja mai karfi "Jabeer, kana so ne zuciyata ta buga sabodan bak'in cikin ka ne, me yasa a koda yaushe kake son gani na cikin bacin rai?,kafi burin ka ganni ne a kwance na kwanta ciwo?" Kai ya sunkuyar jikinsa ya yi sanyi amma fuskar nan tana nan cunkushe. "Sorry Dad" Dago fuskar tasa ya yi suna kallon juna. "Mene ya samu fuskar ka naga alamun hannu" Ai kuwa ya k'ara tunzura ya fara muzurai ³ "She slap me" "Ita wa?" Cikin matsanancin mamaki Maimartaba ya kara jefa masa tambayar. Leb'ensa na k'asa ya cije kaman zai fasa leb'en. Da sauri ya kai hannu kan fuskar tasa yana girgiza masa kai. "Wacece ta mare ka Jabeer?,what did you do" Haushi ya kamashi wato ma bai damu da marin da wata banza tayi masa ba sai abunda shi ya yi mata? "Me kayi mata Jabeer?, Allah yasa baka cutar da y'ar mutane ba" A harzuƙe yace " I did nothing, ...I did nothing " fuu ya wuce shi yana zuba uban huci. "Am going back to mom right this moment" . Bam ya bugo k'ofar. Ya jima a tsaye yana k'ara maimaita kalman a zuciyar sa. Murmushi ne ya kubce masa a karo na farko a rayuwar Jabeer wani ya masa abu bai d'auki mataki ba? Wanin ma mace?. Wacece wannan YARINYAR?. dole ma a nemo masa yarinyar duk inda take. ♥︎♥︎♥︎ ANONYMOUS PERSON Boyayyen Mutum. D'aki ne k'aramin mai masifar duhu tamkar a karkashin k'asa. Sosai d'akin ya yi kama da perfect hiding spot da in ba wanda yasan dashi ba babu ta yanda za'ayi a sani. Dim light ne a d'akin red mara haske dan dole in kashiga sai ka kunna torch saboda rashin hasken fitilar. Y'ar igiya ce mai tsayi a d'aure lungu da sak'o da wasu hotona birjik a jikin ta kaman shanya. Can gefe yake tsaye jikin wani tebir kato yana duba wasu hotuna dake kai . Kofar aka buɗe a ka shigo bai juya ba tunda yasan mai shigowa. Daga shi sai wanda ya shigo suka san da wannan d'akin. "Ya ya ake ciki ne?, ka samu wani news ne?" "Kaman dai koda yaushe babu cigaba dan gane da wannan harkar sai yau nema muka samu wannan duk da nasan ba wani abu ne mai muhimmanci ba" Wani hoto ya d'auko daga cikin ruwan wanki yana nuna masa. Murmushi ya yi mai k'ayatarwa. "Wacece wannan d'in yake tare da ita haka a kan titi?ina so a binciko min ita ko wace kayi editing hoton nan sosai ta yarda babu yanda za'a gane ba gaskiya bane hoton. " "Amma ita yarinyar fa?kana ganin baza'a a sata cikin matsala ba, alamu sun nuna batayi kama da irin karuwan da yake hurda dasu ba?" "I dont care. Tunda har ta rab'i AJ tasan rayuwar data jefa kanta. So edit this pictures ka bani mu jira perfect opportunity da zamu sake so" K'arasa maganan ya yi da wani mugun smirk ya juya ya fice a d'akin. ♥︎♥︎♥︎ Tun ranan da wannan abu ya faru tsakanina da AJ nake Allah ya isa da Allah wadai da masu hali irin nasa. Ko kaɗan ban bari damuwar da nake ciki an fuskanta ba a gida ina iya k'ok'arina wajen b'oye wa. Gobe ne nake tunanin zuwan y'an uwan Malam Halliru kaman yanda muka lissafa. Da wuri yau Baffa ya dawo da kayan cefane. Gaba d'aya yau wunin ranan aiki mukayi ta yi har Bilkisu sarkin san jiki ta dan tab'a wani abu babu laifi. Ana yin sallan isha kuwa na watsa ruwan zafi na kwanta sai barci. Washegari da safe da wuri na tashi nayi duk abunda zanyi karfe takwas na fice daga gidan zuwa gidan su Sahiba duk da nasan cewa ba lallai ne zasu zo da wuri ba amma gwanda nabar gidan da wuri. Dariya Sahiba ta kwashe dashi tana kallo na. Tun zuwana take yimin wannan dariyar kaman mahaukaciya har ta bani haushi tun ina masifa na daina kula ta. "Yanzu wai da gaske kin kusa zama ta Malam Halliru?, oh ni Sahiba inga idon wadda take cewa Allah ya kiyaye tayi soyayya da Malam Halliru ko maza sun k'are. Har na hango y'ay'anku wa yaga Sahla a gidan Halliru " Sai ta kara kwashewa da wata dariya na kuwa cika nayi fam kaman zan fashe. Da nasan iskancin da zata sani gaba tanamin kenan da banzo ba nayi zamana a gida. Karar wayarta ne ya katse ta ta daina dariyar ta d'auki wayar tana dubawa. Sai naga ta miƙe zaune daga kwancen da take da sauri ido waje tana kallan fuskar wayar. Matsowa nima nayi dan naga abunda take kallo har ya raza nata haka. Mugun sarawa kaina ya yi take naji wata hajijiya ta kamani duk da a zaune nake saida na zube k'asa warwas. Innalilllahi wa Innailaihi raji'un. Wayyo ni Sahla meke shirin faruwa dani ne?? 🙆‍♀️🙎‍♀️! Me kuke tunanin ya faru ne?? Sarki zai sa a nemo masa SAHLAN KUWA?. Idan ya nemota mu kuke tunanin zai faru? Shin AJ Zai kyale Sahla bayan duk irin wannan rashin mutunci da tayi masa? Mene AJ YAKE BOYEWA NE da babu wanda ya sani sai shi sai Allah daya haliccesa?. Su waye waɗannan mutena da suke had'a wannan tuggu ta karkashin k'asa?. Auren Sahla da Malam Halliru mai yiwuwa ne ko A'a? Karku bari a barku a baya ku biyoni dan muyi tafiyar daku. KAMAN YANDA NACE A K'ARSHEN LAST FREE PAGE ZAN K'ARA SAKA WANI NOTE. GASHI 👇 NAN MUKA KAWO KARSHEN FREE PAGES NA LITTAFIN 'MULKI'. DUK MAI BUKATAR CIGABA ZAI BIYA NAIRA 400 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER D'IN. 👇 3078293374 AISH SANI DANJUMA FIRSTBANK A TURO SHEDAR BIYA TA WANNAN NUMBER. 👇 08140754777