✨✨✨✨ *WATA KISSAR* ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' ______Bismillahir rahmanirrahim Ban rubuta wannan littafi dancin zarafin wani ko wata ba, nayi shine dan ɗebewa masoya na kewa sakamakon hutun da zan tafi da se Allah ya kaimu September zan cigaba da kawo muku littafin AƘIDA TA, Se dai kash farincikin ku shine nawa, zan baku wannan gajeren labari dan ɗebe muku kewa, ina fatan mu amfana da darusan dake ciki Amma zamu tafi in random direction ne, babu specific lokacin posting, zan Bismillahir rahmanirrahim Ban rubuta wannan littafi dancin zarafin wani ko wata ba, nayi shine dan ɗebewa masoya na kewa sakamakon hutun da zan tafi da se Allah ya kaimu September zan cigaba da kawo muku littafin AƘIDA TA, Se dai kash farincikin ku shine nawa, zan baku wannan gajeren labari dan ɗebe muku kewa, ina fatan mu amfana da darusan dake ciki Amma zamu tafi in random direction ne, babu specific lokacin posting, zan iyayi a kowane lokaci, bazan samu kawo posting akai akai ba saboda uzurrurikan da suka shamin kai, dan Allah include me in your prayers. * a kowane lokaci, bazan samu kawo posting akai akai ba saboda uzurrurikan da suka shamin kai, dan Allah include me in your prayers. Page 1 Tuƙin Babur ɗin a daidaita sahun sa yake cikin nutsuwa da ƙwarewa, yana yi yana duba agogon hannun sa, ga dukkan alamu yana hanzari ne yaje wani guri, kiraye kirayen sallar la'asar da'ake ne yasa shi yin parking ɗin baburin nasa domin bin jam'in salla. Koda'aka idar da salla, komawa yayi cikin baburin sa ya cigaba da tuƙi. Wata ƙaramar Unguwa ya nufa, me ɗauke da gidajen talakawa, wani matsakaicin gida ya nufa yaje yayi parking ɗin baburin sa. Da Sallama ya shiga gidan, amma yanayin sallamar tasa kaman anyi masa dole ya furta. Wata babbar mace ce da wasu mata guda biyu kewaye da ita suna hira, da gani kasan 'ya' yan tane, saboda kamar da take da su. Amsa masa Sallamar suka yi gaba ɗaya, tare da yi masa Sannu da zuwa. Ba wadda ya kula a cikin su ya shiga ɗakin sa, ya ɗau kusan mintuna Ashirin sannan ya fito ya nufi matsakaicin kitchen ɗin dake tsakar gidan. Yana shiga ya fara buɗe tukwane, wani uban tsaki yayi ya fito tsakar gida ya kalli inda Mahaifiyarsa da yayyen sa suke yace "Umma wai ba wani abu se tuwon nan, dan Allah ki dafa min wani abun, ni bana son tuwon nan" Kallon sa ɗaya daga cikin matan tayi tace "iyeee wai har yanzu Ammar baka dena wannan taɓarar ba? Ayi Abinci amma kai se wanda kake so?" Haɗe rai yayi yace "ina ruwan ki? Gidan ki ne?" Ɗayar tace "Taɓɗijan nikam Zanga abunda za'a dinga girkawa a gidan ka, ka fiye ƙaƙale Ammar" Tsaki yayi yace "Umma dan Allah akwai wani Abincin ne?" Umma tace "Dan Allah kar kuyi min faɗa, ba yadda zaku haɗu se kunyi rigima, nasan dama ba cin tuwon zakayi ba, duba na dafa maka shinkafa da miya yana ɗakina" Bece komai ba ya nufi ɗakin mahaifiyarsu domin ya ɗakko Abinci. "Hmm gaskiya Umma kina sangarta Ammar, Abinci se wanda yaga dama? Har yanzu be dena wannan iyayin ba? Wallahi matar Ammar ta shiga uku, ga masifa da zafin rai, ga jin kai da isa" "Taɓ lallai Yaya Maryam akace miki zeyi wa matarsa ne? Taɓɗijan ai irin sa in suka shiga hannun mata se yadda akai da shi, baze mata wannan muzuran ba, musamman ya haɗu da yaran zamanin nan masu wankaken ido" Ammar yana jinsu ya fito ya kalle su yace "har yanzu ba'a haifi yarinyar da zata juyani ba, ƙare wa ni bazan auri yarinya ba, sena samu wadda aƙa llata kai shekara talatin, dan bazan ɗauki hauka da rawar kai daga kowace yarinya ba, Munafukai kunzo se zigamin uwa kuke, baku da aiki se zarya a gida, wallahi nine mijin ku baku isa ba, bazan yadda da wannan gantalin naku ba" Yaya Maryam tace "'yar shekara talatin fa sa' arka kenan? Kana shekara talatin da biyar ka auri 'yar talatin da biyar?" "eh' yar shekara talatin ɗin, wadda tasan meye zaman Aure, ba wannan banzayen yaran masu rawar kai da fitsara ba" Amina tace "mhmm wai Mune munafukan, Allah ya bamu rai da lafiya, zamu ga matar Ammar, zamu ga irin zaman da za'ayi, 'yar shekara talatin din tayi maganin ka yarinya ba tayi ba" "Ba' a haife ta ba, macen da zata juya Ammar babu ita" Yaya Maryam tace "to ina batun Amirar gidan Baffa salmanu, ai kaga ita da girman ta dan zata kai shekara ashirin da biyar, da ko ita seka aura" "Nine zan auri wannan yarinyar? Banda hauka da yarin ta babu komai akan ta, ko ciwon kanta bata gama sani ba" "shekara Ashirin da biyar ɗin ce bata san ciwon kanta ba? Umma tace "dan Allah ya isa haka, ku idan kun haɗu baku da aiki se faɗa, jeka kaci Abincin ka, ni ɗazu gidan Malam Lawan sunzo, sunce dan Allah ranar Lahadi zaka kai musu 'yan ɗaukar Amarya, ka faɗi nawa zasu baka" Yamutsa fuska yayi "ɗaukar Amarya kuma?" Umma tace "Eh mana, ko ba kaji me nace ba?" "Bazani ba" ya bata Amsa "me yasa?" "Ni bazan ɗauki wannan mahaukatan yaran ba, in tafi titi suna hauka da ihu a cikin babur ɗina ba, dan sam hankali be ishi matan unguwar nan ba, daga su har iyayen su, basu da kintsi, duk gayyar ballagazai, bana san shirme ko nawa zasu bani ba zani ba" Maryam tace "hada mu kenan? Tunda muma 'yan unguwar ne" Wani mugun kallo yayi mata yai gaba abun sa ba tare da ya bata amsa ba ********** Tafiya take a sannu uniform ɗin ta na makaranta sun ɗau guga, dukda lokaci ya ƙure kusan tara da rabi na safe, ta makara sosai amma tafiyar ta take cikin nutsuwa. Tana isa makaranta ta shiga kanta tsaye ba tare da fargabar komai ba ta nufi hanyar Ajin su. Ji tayi an ƙwala mata kira daga bakin staff room "Mufeeda" tsayawa tayi ta dai daita nutsuwar ta sannan ta juyo ta nufi inda ake kiran ta, yanayin tafiyar ta zaka kalla kasan bata da lafiya. Discipline Master ne tsaye shida megadi tana zuwa ta zube har ƙasa ta gaishe shi, ya amsa ransa a haɗe ya kalle ta "ke se yanzu ake zuwa makaranta?" Cikin sanyin murya tace "Sir am sick that's why I come late" Ta faɗa tana ɗan yamutsa fuska tareda ƙwalla a idon ta alamar tana jin jiki. "Meyasa kika zo bayan kin san baki da lafiya"? "Naji na ɗan samu sauƙi ne shiyasa" "Shikenan jeki Allah ya sawwake" "Ameen thank you sir" Ta miƙe tana juya masa Baya ta kama dariya tareda gwali ta tafi Aji. Bayan an fita break an dawo, class ya kaure da surutu da hayaniya, prefect ne suka zo sukayi magana a class ɗin akan principal yace ayi shiru yana da baƙi, sannan a rubuta masa noise makers duk wanda sunan sa ya fito a 'yan surutu akwai horo me tsanani . Hakan yasa ajin yin tsit, dan ko kwakwaran motsi kika fiye yi se a rubuta sunan ki, saboda punishment ɗin principal ba sauƙi. Mufeeda ta kalli ƙawar ta Fati tace "Kin san meyasa na makara yau?" Fati ta girgiza kai, Mufeeda tace "Anguwar su Anty murja na biya, naje na samu Yaya Usman me mana ɗinki nan ƙanin mijin ta na sauke masa kwandon bala'i, na gaya masa an jima da yamma zan koma ya bani dinki na kona masa rashin mutunci, dan wulaƙanci biki saura sati ɗaya amma be gama min ɗinki na ba, Anty murja ta hanani kuɗin mota wai tunda nayi wa ƙanin mijinta rashin mutunci ba zata bani kuɗin mota ba, ni ko nai amfani da kuɗin makaranta na, nai taho wata" "Mufeeda wallahi zan rubuta sunan ki, tun ɗazu kike surutu fa" cewar class captain ɗin su Cikin tsiwa mufeeda tace "eh da yake nika ɗai kika raina ba, karki fasa saka sunan nawa" Aikuwa aka rubuta sunan Mufeeda cikin masu surutu. "Fati dan Allah bayan la'asar zanzo gidan ku ki raka ni, idan be gama ba koda me yake yawo seya bani kayana" Seda Mufeeda tayi surutun ta me isar ta sannan ta fara tunanin me zata yi wanda zesa ta ɓata sunayen 'yan surutu da' aka rubuta. Miƙewa tayi ta tafi gurin zaman class captain ɗin su, tana zuwa ta fizge takardar sunayen, "Kai lallai wannan sunayen hada san kai a ciki, ku saurara kuji sunayen wanda aka tsana, aka rubuta sunan su" Nan Mufeeda ta shiga karanto sunayen wanda babu su a cikin takardar, nan da nan aka ɗau hayaniya, wanda suka san ba su yi surutu ba suna son jin ba'asin dalilin rubuta sunayen su. Nan da nan Class ya kaure da hayaniya, class rep na ƙoƙarin kare kanta akan bata rubuta sunan wasu ba, yayin da Mufeeda ta hana ta magana, aka yaga takaddar sunaye, se zage zage da hayaniya sosai. Ana cikin hayaniyar ne head girl ta leƙo ajin tace "SS2 on your knees under the sun inji PC" Nan suka fara salallami, wanda basu jiba basu gani ba suna Allah ya isa. Dama sun saba shan punishment, saboda tsabar rashin jin 'yan ajin. Sunyi tsit a rana suna kneel down, ga ranar ta ɗau zafi sosai, kasa jurewa Mufeeda tayi dan haka ta miƙe ta ƙwalla ihu, ba shiri ba tare da sauran ɗaliban sun san me yasa ta ihun ba suma suka miƙe suka sa gudu suna ihu, hakan ya bata damar ɗaukar jakar ta ta nufi gate ɗin fita. Tana zuwa ta daidaita nutsuwar ta, ta kalallame me gadi akan cewar bata da lafiya ne zata gida ta sha magani, da yake ɗazu a gaban sa ta gayawa discipline master bata da lafiya. Ya barta ta tsere abun ta. Aikuwa da principal yazo, babu wani gamshashashen bayani da yasa suke ihu, haka yasa aka zane su aka basu noma, yayin da wadda tai laifin tuni ta tsere. ************* Ƙarfe huɗu Mufeeda ta shirya zata fita, duk yadda tayi maman ta ta bata kuɗin mota hana ta tayi, tace "na gaji da kisan kuɗin da kike sani babu dalili, ni auren 'ya ne a gabana tafi ki bani guri" haka ta haƙura ta fita, naira ɗari biyu ce kawai da ita. Ta tafi gidan su Fati domin ta raka ta unguwar da zasu karɓo ɗinki, suna tafe Fati na bawa Mufeeda labarin irin Azabar da suka sha a makaranta yau, sakamakon abunda tayi, Mufeeda kam se dariyar mugun ta take. Suka hau napep, tafiyar naira ɗari biyu a ɗari aka kaisu, suna zuwa telan ya kalleta ya ɗakko wata leda ya miƙo mata yace "gashi nan jarababbiya na gama" "Ai wallahi da baka gama ba sena kwaso maka 'yan sanda, kabani kayana kuma kabani kuɗi na" Telan yace "daga yau bazan ƙara karɓar kayan ki ba mara kunya" "haba kai ka isa haushi ka bani shiyasa na maka hakan ai" Ya kalli abokan aikin sa yace "baku ga tijarar da tayi min ba ɗazu akan dinkin ta da sassafe tazo seka ce zata ritsa ɓarawo" Ɗaya ya kalle ta yace "Muffy dama haka kike?" "Wallahi ba haka nake ba, rashin cika Alƙawarin sane ya sani haka" "Naji jeki karki ƙara kawo min kayan ki" "wallahi sena kawo, sedai in zaka dena ɗinki gaba ɗaya" Haka suka bar shagon ɗinkin nan suka fito titi domin samun babur su tafi gida, Mufeeda ta tsaya ta saimusu guava ta canjin naira ɗarin nan. Fati tace "Mufeeda da kika kashe kuɗin a me zamu koma gida?" Mufeeda tace "Ai na Allah basa ƙare wa, bari kiga semun zaɓi Napep me kyau, me kiɗa da tsafta me ƙamshin turare, semu hau muce ya kaimu gida sabil". Wani me Napep ne yayi parking a gefen su, ya sauke wasu 'yan mata su uku, me Napep ɗin tsaf da shi ba kace shike tuƙin babur ba, seka zata zaka ganshi da haɗaɗɗiyar mota, yayi shiga ta kamala gashi kyakywa a nutse yake, Napep ɗin nasa ma fes da shi. Ɗaya daga' yan matan tace "dan Allah ko zaka bamu lambar ka, in zamu wani gurin semu kira ka" Fuskar nan tasa babu alamar wasa yace "malama kubani haƙƙina in tafi, ba raba lamba ne ya fito dani ba". Dariya Mufeeda ta dinga yi ganin abunda yake faruwa, se yarfa 'yan matan nan yake, da alama ko magana ma baya son yi. Mufeeda tace "bari a gama waccan rigimar, wannan Napep ɗin zamu hau wallahi" Ɗan zare ido fati tayi "kina ganin yana yiwa wannan haɗaɗɗun ' yan matan muzurai, muka raina masa hankali ai zane mu zeyi" "Dalla matsoraciya zuba ido kiga" Jan babur ɗinsa yayi ze wuce, Mufeeda tai sauri ta ɗaga masa hannu ya tsaya, fati ta gaya masa inda ze kaisu, har zasu hau mufeeda tace "Zahradeen" Waigowa yayi ya kalle ta yace bashi bane. Mufeeda tace kai "wallahi kaine Zahradeen ne mana" Tsaki yayi yace "in ba hawa zakuyi ba zan tafi" "Yi hakuri zamu hau" suka hau Napep sun fara tafiya Mufeeda tace "Gaskiya nayi mamaki daka ce ba kaine Zahradeen ba, anya ba wasa kake min da hankali ba?" Fati tace "dan Allah ki ƙyale shi yace bashi bane ba, waima waye Zahradeen ɗin ne?" Mufeeda tace "Saurayi na ne, Amma yanzu ya maze wai bashi ne Zahradeen ba" Waigowa yayi ya kalleta, ya kalli yarinyar da ba tafi shekaru sha shida ba amma tana kiran saurayi girgiza kai yayi ya ci gaba da tuƙin sa. Mufeeda tace "dan Allah Zahradeen ka dena min wasa da hankali" A fusace yace "ke niba Sunana Zahradeen ba, Sunana Ammar" Ɗan lumshe ido tayi dama abunda take sonji kenan "Wow sunan ka me daɗi Yaya Ammar, Amma kayi kama da Zahradeen ɗin da ya yaudareni" Ita kam Fati abun mamaki ya bata wai Yaya Ammar daga haɗuwa da mutum harta liƙa masa Yaya, gaskiya halin Mufeeda se ita Shiru yayi bece komai ba, bata damu ba tace "Kasan wani Abu Yaya? Ka birgeni gaba ɗayan ka a nutse kake ba kaman wasu daga cikin masu Napep ba, ga shigar ka ta kamala, ga komai naka a nutse da gani baka da hayaniya irin na sauran 'yan uwanka masu babur" Ɗan girgiza kai yayi, sam ko gajiya ba tayi da surutu, gata wata ƙwaila da ita amma se zuba uban iyayi take yi tana surutu. Sam shirun da yayi mata be bata haushi ba. "Yaya Ammar kalli wancan me Babur ɗin ta nuna wani me napepe " kalli Askin kansa da shigar jikin sa, ina me hankali ze shiga babur ɗin sa? Da irin su ake haɗa kai a cuci fasinja, ko a haɗa maza da mata a Napep ɗaya, Amma kai tunda ka ɗauke mu baka ɗauki namiji ba" Ammar yace "Idan na ɗauki Namiji ya zakiyi?" Ɗan murmushi tayi dan ba tayi zaton ze magana ba "Ai nasan ba zaka ɗauka ba ma Yayana, Samun nutsatsen me Babur irin ka ai se an tona, gentle da kai sam ba kayi kama da tuƙin Napep ba ma" Ammar yace "Meyasa banyi kama da me Napep ba?" "Taɓɗijan yadda maza ke mugun raina sana'a ne namiji kaman kai ze tuƙa Napep, aini ba ƙaramin burgeni kai ba Yayana, wani kaman kai ɗin nan ga kyau ga nutsuwa baze tuƙa Napep ba, cewa zeyi se aikin office or something like that" Ɗan girgiza kai yayi yace "Hmm" Duk rashin son maganar Ammar haka Mufeeda ta dinga jansa da surutu, jefi jefi yana mayar mata, gaba ɗaya mamaki ya cika Fati, yadda suka ganshi ɗazu yana wa wasu 'yan mata muzurai, Amma se jansa da hira Mufeeda take yi. A titi suka yi ze sauke su, Amma seda Mufeeda ta jashi ya kaisu har ƙofar gida fati ta sauka a bakin layin su, ya ƙarasa da Mufeeda. Se a lokacin ta tuna ashe sun kashe kuɗin motar tasu. "Yaya Ammar dan Allah kayi haƙuri ban gaya maka tun kafin mu hau ba, kuɗin motar mu muka zubar garin ɗakko kuɗin mota muka zubar da kuɗin bamu sani ba, Amma kaga gidan mu nan bari in shiga in karɓo maka. Shiru yayi yana kallon ta, ƙasa tayi da murya tace "please Yayana am sorry, nasan bamu kyauta ba, a lokacin nan daka ɗau zafi dana gaya maka ba lallai ka ɗakko mu ba, kayi haƙuri dan Allah ba haka halinmu yake ba, bari in shiga in karɓo maka, ka yi haƙuri kaji Yaya Ammar" ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya. Shi gaba ɗaya yadda yarinya ƙarama ke wannan iyayin da kwarkwasa shike bashi mamaki. Kunna baburin sa yayi ze tafi, Mufeeda tace "Haba Yaya Ammar Allah yasa ba fushi kayi ba? Ka tsaya in shiga in karɓo maka dan Allah" "Ku bashshi kawai" ya ja babur ɗin sa yai gaba. Yana tafiya Mufeeda tai tsalle, "wo ni Autar Baba na, Allah ya bani Yaya a titi" Tai shigewarta gida tana dariya Maman ta ta kalleta "ke ina kayan ɗinkin? Kika shigo kina dariya" Zumɓura baki tayi "ba hanani kuɗin mota kika yi ba, na je na karɓo me Napep ɗin ya ajiyeni a titi nikuma na manta da kayan a Napep" Buɗe baki Maman tayi "Kayan kala biyar kika barmin a a daidaita sahu dan uban ki, kuma ko a jikin ki kike dariya? Kinyiwa kanki ranar bikin se dai ki bar gidan nan, inda na gode Allah bani na sai miki ba uban kine ya siya, shashasha mara hankali" Indai faɗan Mama ne Mufeeda ta saba shansa, dan haka ko a jikin ta, ta shige ɗakin su, wani irin farinciki ke ratsa zuciyar ta wanda bata san dalilin hakan ba, tasan dole Ammar ya dawo saboda kayan da ta bari da gangan a Napep ɗin sa. Kwana Mufeeda tayi mafarkin Ammar, da tuno shi se ta saki murmushi. Yayar ta ta kalleta "professor Autar Baba wai farincikin me kike haka? Mama se faɗa take kin bar kayan ki a ɗan sahu, amma baki damu ba? Yanzu me zaki saka ranar bikin?" "haba Yaya ke an isa ayi bikin ki bani da kayan sawa ne? Ko naki sena saka, ina Addu'a insha Allah nasan me Napep ɗin ze kawomin abuna" "ya akayi kika san hakan?" "jikina ne ya bani". Inma be kawomin ba baba ze saimin wasu. ************ Wasa2 kwana biyu Ammar be dawo ba, yauma tana makaranta sam bata walwala, Fati tace "Muffy wai yana ganki haka?" "ke barni har yanzu Yaya Ammar fa be zoba" "to mezezo yai miki?" "wallahi fati so nake kawai in kuma ganin sa ya haɗu, a Napep din fa nabar ɗinkuna na, Amma har yanzu be dawo ba" "kayan naki kika bari a Napep, gaskiya baki da kai, yanzu idan be kawo miki ba fa?" Mufeeda ta taɓe baki "ke nifa bata kayan nan nake ba, Baba baze bari ayi biki bani da sabon kaya ba, ni kawai shi nake so in kuma gani" Tsaki fati tayi tai bar gurin dan ba ƙaramin ƙular da ita Mufeeda tayi ba. ************ Bayan magariba Mufeeda na kwance tayi shiru tana ta tunanin Ammar, ji tayi ta gaji da kwanciyar, ta miƙe ta fito tsakar gida, Maman su haushin ta take ji, sam bata shiga sabgar ta saboda batar da kayan da tayi, shirye shiryen biki kawai sukeyi. Yaro ne yayi sallama yace "wai ana sallama a waje, inji wani" Mufeeda bata tsaya jiran meza'ace ba, ta zari hijjabi tai waje, kaman yadda ta zata Ammar ne a tsaye a gefen Napep ɗin sa. Da sauri ta ƙarasa inda yake "Yaya Ammar kaine? Ina wuni?" "Lafiya ƙalau, dama nazo in tambaye ki ne, ko kune kuka manta kaya a Napep ɗina, tun shekaranjiya nake yawo da su" Ajiyar zuciya tayi "Kayan ɗinki nane Yaya, na shiga damuwa sosai, zuciya ta ta bani zaka kawomin dama, dan na yarda kai me amana ne" "Seki kiyaye gaba, idan kin shiga abun hawa ki dena surutu, in ba haka ba wataran dake za'a tafi" Ya Ɗakko kayan ya miƙo mata Bata karɓa ba ta tsaya tana kuma ƙare masa kallo, murmushi ta sakar masa tace "bana surutu a abun hawa ai, ranar ma dan kai ne, nagode sosai Yayana, Allah ya ƙara Arziki, ya kiyaye ka daga sharrin maƙiya, Allah ya azurta ka da halal ya nesan taka da haram, Allah ya sakawa iyayen ka da Alkhairi Addu'ar su da tarbiyar suce ta sa ka zama mutumin kirki " Ammar yana mamakin yadda yarinyar ke sarrafa harshen ta. Ba ta karɓi kayan ba tace " Dan Allah ina zuwa" Ta koma cikin gida, ba tafi mintuna biyar ba ta fito hannun ta ɗauke da leda, ta miƙawa Ammar. Ya kalleta yace "menene wannan?" "Yaya Ammar yaba kyauta tukuici, bani da abunda zan biya ka, kawai dai na baka ne" Girgiza kai yayi "bazan karɓa ba, ungo kayan ki, ina sauri zani wani guri ne" Kallon sa tayi "zaka zance ne? Idan baka karɓa ba zan barka da kayan sedai ka koma da su ko ka barsu anan dan wallahi bazan karɓa ba" Tai maganar tana kallon cikin idon sa, dagaske take abunda take faɗa. Hannu yasa ya karɓa, sannan ta karɓi kayan ta, cikin iyayi tace "yauwa ko kaifa Yayan Mufeeda" A ransa ya maimaita "Mufeeda" Tace "ungo wannan invitation ne, bikin yaya ta za'ayi a wannan satin dan Allah kazo kaji Yaya na" "ban miki Alƙawari ba gaskiya, Amma Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya" Wani irin kallo take masa wanda ya kasa gane kallon menene haka? "Idan ba kazo ba bazanji daɗi ba, kuma zanga kaman kamin wulaƙanci ne, ko kuma maybe... Shikenan dai nagode ka gaida Mama, Allah ya kaika gida lafiya, ya tsareka daga sharrin maƙiya" Ta juya ta nufi gate ɗin gidan su, yai shiru na ɗan lokaci ya shige baburin sa ya tafi. Ɗakin Baban su ta nufa, tana zuwa ta tarar da yayyen ta na gidan Aure sun cika falon baban su da mahaifiyarsu suna ta hira ana shirye2. Tana zuwa taje gaban Maman ta ta ajiye mata kayan ɗinkin tace "Mama ga kayan nan, me Adaidaita sahu ya kawo min, seki dena haɗemin rai" Wani daga cikin yayyen ta ya kalle ta "Ahh kaga professor, kuma Autar Baba da Maman ta" Mufeeda Ta ɗan tura baki "Autar Baban dai, Mama tafi son Yaya akaina, kuma na fasa zama professor ana aurar da Yaya nima Aure zanyi" Dariya suka dinga mata, Babbar yayar su tace "kiji min yarinya da rashin kunya, kin fasa zama professor kafin kiyi auren?" "Na fasa dan Yaya na barin gidan nan Mama zata kasheni da sa aiki, dama kaman bata sona nima Aure zanyi" Mama tai murmushi tace "naji bana sonki ɗin, nafi son Amina ke kam baki da nutsuwa ga wauta, tunda babanki yana sonki ai shikenan, waye ma ze aure ki a haka, baki iya komai ba, se son jiki da rashin kunya, ko Saurayi baki da shi" "Wallahi na samo Saurayi, me Adaidaita sahun da yakawo min kayana nake so" Yanayin yadda tayi maganar ne kanta tsaye da confidence ɗin ta yasa ta bawa kowa dariya, suka ɗau maganar tata shirme. Domin gyara, sharhi, ko shawara 07063065680 Kuma yaseen ba comments se Allah ya kaimu September zan cigaba da typing. ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) Page 2 *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com "ke bama son shirme, ubanwa ze miki wani aure, tafi kije kici Abincin dare ki kwanta" cewar Yayan Mufeeda Baba yace "kaga Abubakar ku ƙyalemin professor auta, yadda take so haka za'ayi, tunda gidan su ne, ku yanzu duk ba 'yan gidan nan bane ba' yan karo ne" Mufeeda tace "Yawwa Baba gaya musu, dan Mama tafi sonsu, yanzu idan muka ga dama duk korarsu zamuyi kowa ya tafi gidan sa" "sosai makuwa Auta na" Haka Baban mufeeda ya ci gaba da zigata tana ta zuba taɓarar ta. ************* Mufeeda se rawar kai take tana iyayi, anata shirye shiryen biki, sati guda ta dauka ta dena zuwa makaranta se yawon rabon Katin gayya ta, komai da ita ake yi, yayin da gefe guda kullum cikin tunani take yi, zuciyar ta na son sake saka Ammar a idon ta. Mufeeda duk kayan gyaran fatar da Amarya take yi itama se tayi, tare suka je ƙunshi da gyaran kai, komai angone ya biyawa Mufeeda yadda ya ya biyawa Amarya, gidan su mufeeda su takwas ne, huɗu maza huɗu mata, daga Yaya Amina se Mufeeda, shekaru biyar ne tsakanin Amina da Mufeeda. Angon Yayar Mufeeda yasan Mufeeda sosai, saboda ba ƙaramar gudunmuwa ta bashi ba lokacin da yake neman Auren yayarta, ita ta taya shi campaign gurin Yayar ta, duk saurayin da Amina za tayi indai beyi wa Mufeeda ba in ta dinga kushe shi se Amina taji bata son mutumin nan sun rabu. daga tace wancan be iya sa hula ba yana da ƙaton kai, ko kunnuwan sa sun fiye tsayi, se tace wancan ƙatuwar ƙafa ce da shi idan ta aure shi zata haifi ɗan se an je kamfani za'a masa takalmi, se tace wancan kwaɗayayye ne kullum yazo aka bashi abu se ya karɓa, harta kai ta kawo idan Amina tayi Saurayi se tace "Mufeeda zo kiga wannan saurayin yayi kuwa?" Mama taita faɗa tana "Amina baki da wayo, kina zaune ƙanwar bayan ki, shekara kusan biyar kika bata, Amma ita ke zaɓa miki Saurayi ki biye mata haka zakiyi ta zama a gida ba aure" Mufeeda bata da jiki sosai, tana da hasken fata, ba doguwa ce can ba, Amma tana da kyau dai dai gwargwado, kana ganin ta kaga yarinya, Amma akwai baki, ga iyayi da rawar kai, dan kusan duk tafi yayyen ta baki, yayyen ta ba ruwan su da hayaniya a nutse suke, basu da yawan magana, Amma mufeeda ta fita zakka, ita akwai baki da neman rigima ga rashin haƙuri, shiyasa sam basa shiri da maman ta. **************** Ammar yana zaune a tsakar gida dashi da 'yar Yayar sa Halima, Halima itace Babbar jikar gidan su Ammar, daga Yaye Umman sa ta riƙe ta. Halima ta gyarawa Ammar ɗakin sa ta fito da invitation a hannun ta tace "Uncle Ammar, waye ya gayyace ka biki ne?" Seda yaga katin ya tuna, ya ɗanyi tsaki yace "wallahi wata fitinanniyar yarinya ce ta bani wai bikin yayarta, yadda shi kawai" "haba Uncle baza ka bikin ba? Ba kyau fa a gayyace ka walima kaƙi zuwa, Amma gayamin ko Anty na ce?" Haɗe rai Ammar yayi yace "ke bana son shashanci, yarinya ce fa ƙarama kin girme ta" "Amma ya akayi harta baka invitation? Wallahi uncle seka ga 'yan yaran fa munfi iya soyayya" "kunfi iya hauka dai, koke baki isa Aure ba, ina zanje ina kula' yar da da aure nayi da yanzu na haife ta" Dariya Halima tayi "Allah ya ja da ran uncle ɗina, to ai da haka da haka" Haɗe rai Ammar yayi kaman bashi ke hira ba yanzu "Ke rufemin baki, yaushe na fara wasa dake?" "Allah ya baka haƙuri" Gyaran murya suka ji a soro, alamar za'a shigo, mahaifin Ammar ne ya shigo ya kalli Ammar yace "kai dai kam kaji kunya wallahi, Allah Ammar da kai mace ne masallaci zanje in samu duk wanda yayi min in Aura masa kai sadaka, ace mutum ba zuciya duk sa'aninka da ƙannen bayan ka sunyi Aure amma kai kana zaune, se anyi magana ka kama wani kai se 'yar shekara talatin kai bazaka auri yarinya ba, dama wace yarin ya ce zata aureka, duk ka tsofe a titi ka zama tuzuru, tun wuri kayiwa kanka faɗa kafin ayi da kai kai kake yi da kanka, in ba sokake daga ga shiga guri mutane su fara kaffa kaffa da yaran su mata ba, saboda ka tsofe ka zama tuzuru ba Aure, wanda da kayi Aure tuntuni da yanzu kaima nan da 'yan shekaru zaka aurar da' ya" Ture Abincin da yake ci yayi, dan ji yayi yana tsaye masa a wuya Ire2 wannan faɗan na mahaifinsa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba, ba dama ya shiga cikin gida ya zauna mahaifinsa ya dinga masa mita kenan akan maganar Aure. Mahaifiyar Ammar ta fito daga ɗaki tana faɗin "dan Allah malam ka dinga haƙuri, Shifa Auren nan lokaci ne, kuma Alhamdilillah tunda rashin auren besa yana ɗakko maka magana a waje ba, ba ruwan sa da 'yar kowa, kuma yin Aure ai se mutum nada ƙwaƙwƙwarar sana' a ko?" Mahaifin Ammar yace "ai dama ke kike goya masa baya yake ƙara sangarcewa, kalli kowa gidan nan yau faten wake ya sha amma shi kinyi masa girkin sa daban, shi bazeci faten wake ba, yace se ya gama karatu degree biyu yayi, yace seya samu sana'a wannan babur ɗin da yake ja be isheshi ba indai ba ƙarya ya ɗorawa ransa ba, ni anya ma ba Aljana ce ta aure shi ba?" Ammar kam ya kai ƙarshe a ƙuluwa da irin wannan faɗan na baban sa, dan haka ya miƙe ya bar Abincin, Mama tace "Ammar Abincin fa?" na ƙoshi ya faɗa a taƙaice yai waje Mahaifin sa yace "Eh haka dai, daga nan kuma ze wuce gurin bautar yahudu, gurin ƙwallon ƙafa aikin sa kenan, shi wace mace ce ma zata iya jure wannan baƙar zuciyar tasa, komai abun fushi ne a gurin sa" Haka mahaifin Ammar ya ci gaba da faɗan sa har ya gaji yai shiru. Ammar be koma gida ba se gurin ƙarfe tara na dare, ya zauna suna hira da mahaifiyar sa, tana ta ƙara yi masa Nasiha kan ya dinga haƙuri da halin mahaifinsa Ammar yace "Umma wallahi na rasa me yasa Abba kaman baya son ganina? Sa ya ganni seya fara faɗa" "Ammar ba sonka ne ba yayi ba, gaskiya yake gaya maka, a duniyar nan kafin ayi da kai kake yi da kanka, kai namiji ne kuma dukkan lafiyayyen namiji a shekarun ka ya kama ta ace ya ajiye iyali" "Umma baƙin Aure nake ba, yanzu fa zamanin mu da naku ba ɗaya bane ba, da yawa 'yan matan yanzu me kuɗi suke so, ni kuma bani da su, ga kwalin karatu amma babu ƙwaƙwƙwarar sana' a, haƙurin da kuke dashi ku iyayen mu, matan yanzu ba haka bane a gurin su, ba kowace yarinya ce tasan menene zaman aure ba, zama ne na haƙuri wadda zata fuskanci yau in akwai gobe babu, wace yarinyar zata yadda ta aureni ina tuƙa babur ɗin sahu?" "Ammar duk lalacewar zamani akwai na Allah Ammar akwai matan ƙwarai" "Hakane amma duk da haka nafi son in samu macen da ta gama hankali ko bazawara ce, danni bazan auri yarinya ƙarama da bata gama hankali inzo ina fama da shashanci ba" Girgiza kai Maman Ammar tayi tace "yaro dai yaro ne" **************** Gidan su Mufeeda ya fara ɗaukar harami, baƙi daga sassa daban daban sun hallara ana ta shirin fara Shagalin biki, duk inda Amarya da ƙawayen ta suka saka ƙafa nan Mufeeda take maida tata, ko aike Mufeeda ƙin zuwa take balle asa ran zata taya aiki. Aka fara Shagalin biki, kowane ranar event Mufeeda ta sha kwalliya kaman itace amarya, taji a ranta inama ace Yaya Ammar zega kwalliyar nan tata data ji daɗi, nan ta fara tunanin yadda zata samu lambar sa tare da addu'ar Allah yasa kafin agama bikin nan ko taro ɗaya ya zo mata. Ranar ɗarin Aure aka ɗaurawa Yayar Mufeeda Aure, gida ya cika da jama'a anata shiga ana fita. Maman mufeeda ta bata kaji da snacks akan faranti tace maza taje ta bawa wasu 'yan uwan baban su yanzu zasu juya su tafi. Mufeeda ta fito da tray a hannun ta, anata tsokanar ta, suna ce mata professor Mufeeda sarkin rigima, da yake ƙofar gate ɗinsu an buɗe ta gaba ɗaya, hakan yasa kana hango masu wucewa, gidan su Mufeeda yana da kyau, ba babba ne can ba amma yana da tsari, yanayin Abincin da'ake shiga ana fita da shi ze nuna Akwai rufin Asiri a gidan. Idon ta ta sauke akan Ammar, ya saka yadi Ash da baƙar hula, yana ƙoƙarin kunna babur ɗinsa. "Kenan yazo amma be nemeni ba?" Ai dire tray ɗin tayi bata san ma wa ta bawa ba, ta fyalla da gudu tai waje tana faɗin "Yaya Ammar ɗina" Juyowa yayi yana kallon inda take tahowa, purple ɗin shadda ta saka, ta sha surfani tun daga sama har ƙasa, hannun ta ya sha lalle, ga zobuna da abun hannu, tayi ɗaurin ture kaga tsiya, tayi parking ɗin gashin ta da keta sheƙi, tayi kyau matuƙa kaman itace Amarya. Ta ƙaraso inda yake se nishi take, ya kalleta yace "ke bakya jin kunya kike gudu a gaban mutane?" Ajiyar zuciya tayi tace "haba Yaya Ammar yanzu da tuni ka tafi bamu haɗu ba, harna fidda ran zakazo" tai maganar a ɗan shagwaɓe "hmm to ai gashi nazo, ya taro?" "Alhamdilillah" "Allah ya basu zaman lafiya" "Ameen Yaya Ammar, Amma ba har tafiya zakayi ba, kaci Abinci kuwa? " No bashi nazo ci ba, nazo an ɗaura aure nayi Addu'a" yai maganar tare da shiga babur ɗin sa ze kunna, hannu ta sa ta riƙe makullin tana kallon sa. Haɗe rai yayi yace "Ya haka? Cika min ina sauri ne" Dukda wani uban kwarjini da yayi mata musamman daya haɗe rai, bata nuna masa ta tsorata ba ta dake tace "kai kullum cikin sauri kake ne? Ni gaskiya idan baka shigo ba bazanji daɗi ba, ya za'ayi in gayyace ka kuma ka tafi baka ci komai ba?" Ammar yace "ke wai haka kike? Cikamin key ɗina zan tafi" Ƙwalla ya gani a idon ta, tana zumɓura baki, tana karya wuya kaman za tayi kuka, ta ƙara riƙe key ɗin gam, ji yayi kaman ya balbaleta da masifa amma yaga ta wani nutsu ta koma kalan tausayi. Ɗan gajeren tsaki yayi yace "muje" Murmushi tayi tareda cewa "ko kaifa" Amma still ta cire mukullin ta riƙe a hannun ta dan karma yace ze tafi. Cikin gida ta shiga dashi har falon baban ta, yana zaune yana gaisawa da baƙin sa tace "Babana ga Yaya Ammar wanda ya kawo min kaya na dana bari a mota na kawo maka shi ku gaisa" Ammar ya durƙusa suka gaisa da mahaifin Mufeeda, yai masa Allah ya Sanya Alkhairi. Baba yace "Masha Allah, Yaya Ammar mungode fa, dan saura ƙiris Auta ta sha duka a hannun Mama, Allah ya saka da alkhairi, mungode sosai" Ammar yace "bakomai" Ya miƙe suka fito yace "ke bani key ɗina zan tafi" Ta marairaice tace "dan Allah kayi haƙuri saura Mama ku gaisa ba dan hali na ba dan Allah" Haka ta kuma Jan Ammar inda mahaifiyarta take, ya gaishe ta ya musu Allah ya Sanya Alkhairi, Nan ma Mama tayi masa godiya. Mama tace "Mufeeda kawo masa kayan ɗaurin Auren shima" Ammar yace "A'a a barshi yana sauri ne" Mama tace "Ai ba'ayi haka ba, kazo mana taro kace ba zaka karɓi komai ba" Mufeeda Ta shiga ta haɗo masa kayan ɗaurin Aure fal viva, kaji da lemuka, kayan snacks, Alewa da goro seda ta cika viva da shi, da ta fito da ledar Seda Mama ta bita da kallo ganin haukan da Mufeeda tayi, ba damar tayi magana tunda a cikin taro ne. Yana tafe tana biye da shi har bakin Napep ɗin sa, yace "bani key ɗina kuma bazan ƙara zuwa gidan ku ba" "Saboda me?" "Saboda kin fiye rawar kai, ni kuma bana son rawar kai" "to yi haƙuri na dena" Wani kallo yai mata sannan yace "bani mukulli na in tafi" Miƙa masa key ɗin sa tayi, Amma ta tsaya a jikin Napep ɗin ta zubawa Ammar ilahirin idanuwan ta tana ƙare masa kallo. A ran ta tace "Masha Allah gaskiya Ammar yana da kyau" Ammar ya fara fusata da lamarin Mufeeda, dan dana sanin zuwa gurin ɗaurin auren ma yake, a zuciye yace "ke Matsa zan tafi, kin sani a gaba kina ta ƙare min kallo" Memakon taji haushin tsawar da yayi mata, sajen sa ne ya ƙara birgeta, ga ƙamshin turaren sa duk ya gauraye gurin a hankali cikin wani salo me cike da jan hankali ta furta "Yaya Ammar" Wani Yarrr yaji a jikin sa, tsigar jikin sa ta tashi sakamakon yadda ta furta sunan nasa, ɗagowa yayi yana kallon ta "Yaya Ammar se yaushe?" Kallon ta yayi galala "kamar ya se yaushe? Me zanzo inyi miki? Kin bar kayan ki na kawo miki, kin gayyace ni biki nazo miki, me kuma ya rage?" "Alfarma ɗaya nake so kamin Yaya na" "Ina jinki" Seda ta ƙara kwantar da murya cikin shagwaba tace "Zaka min kuwa?" Gaba ɗaya yadda ƙwailar yarinyar ke magana na nema ya jefa shi cikin wani yanayi dabe zata ba. A ƙagauce yace "ina jinki" Miƙa masa wayar ta tayi ta ƙara ƙasa da muryar ta tace "dan Allah ka samun lambar ka Yaya na" Hararar ta yayi yace "ke bana son damu bana son shirme matsa ki ban guri, ko in bige ki da babur ɗin nan" Noƙe kafaɗa tayi "Allah bazan tafi ba se dai muyi ta tsayuwa, ko ka bigeni da babur ɗin, kuma fa ba damun ka zanyi ba, gaisawa kawai zamu dinga yi fa" Dafe kai Ammar yayi, wasa2 sun kai mintuna Ashirin a tsaye a gurin nan. "ke wai bakya ganewa ne ko ba kya ji? Ki matsa nace!" Seda hantar cikin ta ta kaɗa, Amma memakon yaga tsoro ko karaya a fuskar ta, ɗan rintse ido kawai tayi alamar bata son shouting, ta buɗe idon ta ta kalleshi, ta langaɓar da kai tace "please Yayana nifa ƙanwarka ce why are you shouting at me? Allah bazan takura maka ba" Ta miƙo masa tanfatsetsiyar wayar ta, ganin Mufeeda na neman ɓata masa lokaci, kuma ci gaba da tsayuwar su haka zata jefa shi yanayin da ze sha wuya, ya karɓi wayar a gaggauce yasa mata lambar sa ya miƙa mata wayar ta. Karɓar wayar tayi tare da yin murmushi tace "Nagode Yaya na, Allah ya baka ladan zumunci ka gaida su Mama" Ta matsa daga jikin Napep ɗin ya kunna yayi gaba yana mamakin hali irin na Mufeeda. Ta juya zata shiga gida, ɗan Autan su Umman ta ya kira ta, ƙarasawa inda yake tayi, ya kalleta yace "Mufeeda waye wancan?" "Yaya nane" "kamar ya Yayan ki?" ɗan tura baki tayi tace "dan Allah Uncle karka tsanan ta bincike mene ne?" Girgiza kai yayi yace "tun ɗazu Yaya ke nemanki, tace ta baki Abinci ki kaiwa ƙannen baban ku, Amma babu ke babu saƙon" Se yanzu ta tuna dire tray ɗin tayi ta tafi gurin Ammar, taɓdijan ashe zata kaɗe a gurin Mama "Uncle zomu koma gefe tambayar ka zanyi" Ba musu ya bita suka samu guri suka zauna tace "uncle dan Allah me yake sa kaji kana tunanin mutum? Ko ka dinga son ganin sa ko yawan mafarkin sa" Murmushi yayi yace "Autar Baba kenan, Soyayya ke kawo haka" Murmushi tayi ta miƙe tace "nagode uncle" tayi gaba abun ta. Mama a ƙule take da Mufeeda, Amma saboda taro bata bi ta kan ta ba ta ƙyaleta se an gama biki. Aka gama biki dare yayi za'a kai yayar Mufeeda ɗakin ta, aka kaita gurin Baban su yai mata nasiha sosai, se kuka take kowa ya shigo se yayi wa Amina nasiha akan Aure wannan nayi wancan nayi. Amina ta rungume Mufeeda tana kukan zata rabu da 'yar uwata dan sun shaƙu sosai. Mufeeda idon ta ƙyar babu alamar hawaye tace "haba Yaya dan Allah kidena kukan nan, haba se kanki yayi ciwo? Ai ni yakamata inyi kuka bake ba, dan kina tafiya zan shiga uku da aiki a gidan nan, dan Mama ba zata bari in huta ba, dan ta tsani taga ina hutawa, wallahi ina candy zanyi Aure in bar mata gidan " Wasu nawa Mufeeda dariya wasu na mamakin fitsarar ta. Wata ƙanwar kakar su ce na ƙauye suka shigo da 'yan uwan su, suka fara yiwa Amina Nasiha akan aure, buɗar bakin mufeeda se cewa tayi "Dan girman Allah ku kyale ta haka Inna haba tunda kuka zo ake abu ɗaya kuke maimaitawa ai ta haddace, abu ɗaya kuke nana tawa yi nayi bari na bari, wannan ai tun zamanin ku aka dena wannan yi nayi bari na barin," "Ubanki Mufeeda kinji ko?" ta jiyo muryar Mama, sam bata san Mama ta shigo ɗakin ba. Jan bakin ta tayi tai shiru, Mama tace "inna Ladidi ga motocin can sunzo, kuje a raka ta, Amina na Allah ya bada sa'a" Ƙara fashewa da kuka Amina tayi, Mufeeda tace "Mama dan Allah su Inna Ladidi su hau wata motar, ya za'ayi a haɗa ta da tsofaffi su ƙara samin ita kuka, mota ɗaya zamu hau nida ita in rakata" Mafici Mama ta ɗauka ta jefi Mufeeda amma ta kauce Mama tace "Babu gidan uban da zaki, kina nan dama a ƙule nake dake, zaki gamu dani ne, fitsararriya" Seda Mufeeda taga da gaske Amina tafiya za tayi sannan tasa kuka, ita kanta Mama dakewa kawai take yi, Mufeeda kam kuka sosai seda aka kaita gurin Baba shi ya dinga aikin rarrashi, dan in aka ƙyaleta Mama seta zane mata jikin ta. Kowa ya watse ana ta aikin gyara kayan da'aka ɓata na biki, Amma Mufeeda ta maƙale a gurin Baban ta. Mufeeda ta shiga ɗakin Mama dan ta canza kaya, Yayyen ta wasu basu tafi ba, se Washegari in an gama gyara gida za su tafi, Mama ta kalli Mufeeda tace "zan gauraya dake Mufeeda, saboda wulaƙanci na aike ki da kaya ki kaiwa su faruku aka neme ki aka rasa bake babu kayan, kinzo da baƙo daga cewa ki bashi kayan biki kika ciko uwar viva kika bashi se kace ke kika saimin, har aka yi taron nan aka gama magana kike sani, zaki shigo hannu na zakiyi bayani uwar wauta " Mufeeda ta tura baki tace "Haba Mama, Amma lokacin su Anty Murja in suka zo da saurayin su ai ba haka kike musu ba, ke kike cika musu ledoji fa, Amma ni dama bakya sona shiyasa zaki ce na miki wauta" Anty Murja ce tace "Wait ƙanwa ta, ki kace me a daidaita sahu ne saurayin ki, wanda kika shigo da shi ɗazu fa? Shi kuma waye?" Murmushi Mufeeda tayi cikin shagwaba tace "To ai shi ne fa, Shine sirikin Maman, Amma take min mita dan na bashi abu, ranar fa da ta hanani kuɗin mota kyauta ya kawoni gida, na manta kayana ya kawomin, na gayyace shi biki yazo, ai yana da kirki ko Yaya fadila" Wata irin dariya da shewa Yaya Murja da kuma Fadila suka yi, ita kam Mama baki ta saki tana kallon wauta. Fadila tace "kan bala'i indai wanda kuka shigo ɗazu ne me ash ɗin yadi, wallahi mufeeda yarinta da ƙuruciya ke ɗawainiya da kanki, kai! kofa ƙirjinsa baki kai ba, inaga da kaɗan kika wuce cikin sa a tsaye, kina ganin namiji a murɗe gashi ko fara'a bayayi" Cikin tsiwa tace "Wallahi Ammar yafi mijin ki kyau, kuma ina ruwana da girman sa aiba goya shi zan dinga yi ba" Yaya murja tace "Mufeeda in ma Auren ne ki samo dai dai ke kinji professior Auta, waima ba cewa kikayi se kinyi degree ba, zakiyi Aure?" "ba wani professor Aure zanyi, kuma Yaya Ammar nake so" Tofa More Comments More Typing Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) Page 3 *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Ammar ne yayi sallama ya shiga gida ɗauke da leda a hannun sa ya tarar da halima na tsakar gida tana wa Umman sa kitso, mahaifinsa kuma na gefe akan dadduma yana sauraren radio. Amsa masa Sallamar suka yi gaba ɗaya, ya samu guri ya zauna a gefen tabarmar da Umman sa ke zaune yace "Abba sannu da gida" "Yawwa Ammar ya aikin?" Ammar yace "Alhamdilillah" sannan ya miƙawa maman sa ledar vivan da ya shigo da ita. Baban Ammar yace "Ammar ka rage wannan ɗawainiyar da kake mana a cikin gidan nan mungode, ni abunda nafi damuwa da shi ka adana ƙudinka ka tara ƙuɗin aure" Dafe kai Ammar yayi yace "Abba ba wani abune na siyo ba kayan ɗaurin aure ne da naje aka bani" "haka dai se aukin yawon zuwa auren wasu amma kai sai jin kan da fushi" Ammar yayi shiru bece komai ba. Halima ta ɗakko faranti aka juye kayan akai, Umma ta jinjina kai tace "kai kam Ammar ɗaurin auren waye haka aka baka wannan kayan kaman kaine angon?" Halima tai farat tace "Wallahi umma wata ce ta gayyace shi, da na zata baze je ba amma..... Uwar harar da Ammar yai mata ne ya tilasta ta yin shiru. Abba yace "me tayi maka kake mata wannan mugun kallon? Ke Halima gayamin ina jinki" Cikin kame2 Halima tace "Amm.. Dama.. Dama katin ɗaurin Auren na gani a ɗakin sa yace min wata ce ta bashi na bikin yayarta ne" Abba ya kalli Ammar yace "A ina take kuma 'yar waye? Meye haɗin ka da ita har da zata baka wannan kayan haka?" "Abba wallahi bakomai a tsakanin mu, kawai na ɗauke ta ne ta bar kayan ta a Napep ɗina, shine na kaima ta, ta bani katin ɗaurin aure, yau da naje shine ta bani wannan kayan" ya ƙarasa maganar yana ɗan ɓata rai. Abba yace "Ammar ka gayamin gaskiya, ba ina maka haka ne dan in ɓata maka rai ba ina gaya maka gaskiya ne, idan kuna son juna ne in shige gaba in tambayar maka, Ammar ya kamata ka ajiye iyali, ba seka tsofe a titi ba" Da sauri Ammar ya kalli Abban sa yace "Abba yarinya ce fa ƙarama, Halima ta girmeta sosai, da shekaru na in auri 'yar mitsitsiyar yarinya ko fa secondary bata gama ba zaman Aure zanyi ko kuma raino?" "Rufemin baki, meye a ciki zaman aure ba' a shekaru bane, kaiwa kanka faɗa dai wallahi" Se yanzu maman Ammar tace "Malam dan Allah kayi haƙuri, shi Aure lokaci ne" "kullum haka kike cewa shiyasa yake ƙin auren yake ƙara sangarcewa" ******************** Sosai Mufeeda take kewar yayarta Amina, gefe guda ga son Ammar dake ƙara mamaye zuciyar ta ba tare da sanin ta ba, da farko dai niyyar rainawa Ammar hankali tayi amma tunda ta tambayi uncle ɗin ta ya tabattar mata da alamomin da take ji game da Ammar alamomi ne na soyayya, duk wanda yace yana son Mufeeda daga lokacin zata dena ganin mutuncin sa ta tsane shi, Amma yanzu soyayya ta mata mugun kamu. Dukda tana da lambar wayarsa amma tana fargabar kiran sa, dan da alama baya son raini, ɗan haɗuwar da suka yi bata taɓa ganin dariyar sa ba, tana tsoron karta kira ya yarfata, wanda babban abunda ta tsana a rayuwar ta be wuce a dizgata ba. Tunani duk yabi ya addabe ta, ta ɗanfi jin daɗi idan taje makaranta amma da zarar ta dawo duk se walwalarta ta ɗauke, da Mamanta ta zata kewar Yayarta ne yake damun ta kafin daga bisani taga damuwar tata kaman ƙara yawa take. **************** Kamar kullum Mufeeda taje makaranta amma abun mamaki yau babu sunan ta a 'yan surutu, babu' yan makara tsit kaman bata ajin, kusan kowa yasan ta a makarantar nan mussman saboda laƙanin ta na professor, ga rashin ji duk wani laifi da ita a ciki, wani lokacin ko laifi akayi aka rasa su waye se asaka sunan ta, wasu malaman kance professor marasa jin magana. Aka tashi daga makaranta zasu tafi gida ita da fati da yake hanyar su ɗaya, Fati tace "Mufeeda wai me yake damun ki ne? Ko baki da lafiya ne?" Girgiza kai Mufeeda tayi tare da ajiyar zuciya tace "Fati ni abunda ke damuna ba zaki iya maganta min ba" "to gayamin inji meke damun naki?" Taja Fati suka tsaya jikin wata bishiya sannan ta kalle ta "Fatee ina missing ɗin Yaya Ammar sosai, tun ranar da yazo ɗaurin Auren Yaya ban kuma saka shi a idona ba, wallahi duk inda na zauna tunanin sa nake" Wani dogon tsaki Fati ta ja tace "ke kam anyi wahalalliya, daga haɗuwa da mutum a titi shikenan se kuma ki dinga tunanin sa, to me kike nufi da hakan?" Mufeeda tai murmushi tace "tabbas son Yaya Ammar nake kaman yanda alamomi suka nuna" "Taɓɗijan amma kinci kai wallahi, tashi mu tafi ni rana ta nayi" "Fati idan har baza ki tsaya ni neman mafita ba karki ƙara tambaya ta meke damuna, kuma ki yi tafiyar ki dan sena gama tunani zan tafi" Tausayin Mufeeda ne ya kamata dan iya sanin ta da ita idan mutum yace yana son ta shikenan ta samu abokin gaba, Amma yau da kanta take furta ta faɗa soyayya in dai hakane to tabbas dagaske take. Cikin kulawa fati tace "Mufeeda bazan iya barinki cikin damuwa ba, Amma ta yaya zaki cigaba da son mutumin da kuka haɗu a titi, ke kike sonshi ba shi ke sonki ba" "waya gaya miki baya sona? Ke nifa harna faɗa a gidan mu shi nake so" Ɗan zaro ido fati tayi tace "to shi yace yana sonki ne?" "oho masa inma baya sona ni dai ina sonshi, tashi mu tafi gida kar Mama taimin faɗan nata akan na daɗe" Suka tafi ba tare da Mufeeda fa kuma cewa komai ba. Yanzu ma a kwance Mufeeda take tana jujjuya wayar ta, tana kallon Lambar Ammar da ta rubuta Yaya Ammar ɗina, ta rasa ta inda zata fara, ita dai bata taɓa soyayya ba, bata san ya take ba amma tana ganin wasu sunayi a lissafin ta yau sati uku rabon ta da Ammar, Amma kullum ta rufe ido shi take gani. Zuciyar ta ta dinga bata shawarar ta kira lambarsa taji ko yana lafiya? Danna lambar tasa tayi taita ringing be ɗauka ba, ta sake gwada kiran wannan karon ya ɗaga cikin muryar sa me kama da ta me Izza yace "Asslam Alaikum, a kira anjima zanyi salla ne" Lumshe ido tayi jin muryar sa tasa ta sakin murmushi, ba tare da tace komai ba ya yanke wayar. Miƙewa itama tayi ta gabatar da sallar isha'i ta nemi Abincin dare taci seda ta gama abunda take ta hau kan gadon ta ta kuma kiran Ammar, seda ta kusa yanke wa sannan ya ɗauka tare da yin sallama. Se Ajiyar Zuciya take amma ta kasa cewa komai "ina ji wake magana" "Yaya Ammar nice" tana magana gaban sa ya faɗi, yaji ƙirjinsa na bugawa da ƙarfi, shi yama manta da yarinyar nan amma ya ƙara tsuke fuska yace "Ke wa?" "Ƙanwar ka ce Mufeeda" "Ya a kayi?" "Na kira in gaishe ka ne, ka manta dani" "to Nagode ki gaida mutan gidan" ya katse kiran, Zuciya ce ta ɗibi Mufeeda saura ƙiris ta yi jifa da wayar ta amma ta fasa, ta ji haushin abunda Ammar yayi mata sosai tunanin mene mafita ta shiga yi ta nawa kanta tambayar "dama haka soyayyar take? Wahala da ɓacin rai, ji yadda raina ya ɓaci a banza, da ina zamana lafiya nikaɗai Amma tunda na haɗu da kai na rasa nutsuwa ta, kai kuma kana can kana hutawar ka, kalli yadda ya amsa min waya, na kira shi dan inji sassauci amma ya watsan ƙasa a ido, aikam baka isa ba dani kake zancen bazan sha wannan wahalar nika ɗai baZan nuna maka WATA KISSAR... (SAI MATA) " haka ta ci gaba da surutu kamar taɓaɓɓiya har Mama ta shigo ɗakin tace "ke Mufeeda surutun uban me kike ne haka?" "bakomai Mama" Ƙarasowa Mama tayi gefen gadon Mufeeda ta zauna tace "Mufeeda ki gayamin meke damunki ne? Tun bayan bikin Amina na lura kin zama wata iri, gayamin mene ne?" Ai kaman Mama ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi ba fargaba kanta tsaye tace "Mama Yaya Ammar ne" "Waye kuma hakan?" Mama ta tambaya "Mama me A daidaita sahun da ya kawomin kaya na" Ɗan ƙara nutsuwa Mama tayi tace "Me yayi miki?" "Mama tun ran bikin Yaya ban kuma ganin sa ba fa" A fusace Mama ta kalleta tace "idan kika bari na tashi sena samo Madoki nazo na casaki a gurin nan, jimin Shashar yarinya, yarinya ƙarama dake kike wani zancen kina son wani ƙwaya nawa kike? Ki maida hankali akan karatun ki ki bar zancen wannan yaron in ba haka ba ni da kene" Cikin shagwaɓa tace "Mhmm Wallahi Mama ina son Yaya Ammar ɗina ni ba wani karatu da zan iya idan wata ta rigani Auren sa fa? dan Allah Mama ina candy ni Aure zanyi na ci gaba idan nayi Auren" Riƙe haɓa Mama tayi tace "Mufeeda rashin kunyar taki har ya kai ki kalli tsabar idona kice min ke ba zakiyi karatu ba Aure zaki yi, to yanzu in gaya miki mace mai Ilimi tafi daraja a gidan Aure" "Haba Mama kefa kika ce bamu da sama dake duk abunda ke damunmu mu gayamiki ko mu tattauna a tsakanin mu, baki yadda wani yaji sirrin mu ba, ke kikace babu kunya tsakanin mu dake, Amma na gaya miki abunda nake so se hantara ta kike yi, kuma da su Yaya ne ba haka zakiyi musu ba" Mama tace "Hakane Amma, ke kin san meye Aure kuwa? Mufeeda har yanzu ba ki gama hankali ba, kinyi ƙanƙanta da Aure, tsaya ma idan an miki Auren me zaki je kiyi? Me yasa kike son yin Auren?" Seda Mufeeda ta kusa ƙyalƙyalewa da dariya, a ranta tace "Mama me kika ɗaukeni ne" Amma ta maze tace "to Mama Auren wani abune me wahala, ba Kawai in dinga dafa masa abinci bane, yi nayi bari na bari da akai ta gayawa Yaya Amina, nifa wallahi kawai son Ammar nake, kar wata ta rigani auren sa" Miƙewa Mama tayi tace "baki da hankali, shi kansa Auren baki san menene ba, babu uban da ze miki Aure yanzu, tun wuri ki ɗakko litattafan ki ki ci gaba da karatu keda Aure se naga hankali ya gama ratsaki, a yadda kike ɗin nan baza ki iya kula da miji ba" Bayan Mama tabi da kallo harta fice daga ɗakin, murmushi Mufeeda tayi tace "Mama kenan aikuwa zan baki mamaki, idan baki yadda ba zanje in yiwa Baba bayani nasan shi ze fahimce ni" Wayar ta ta ɗauka ta shiga lambar Ammar ta tura masa saƙo "Wulaƙanci be kamaci mutum me karamci da Amana kaman ka ba Yaya na, ka kula da wanda ya damu da kai, Allah yasa in ganka ko a cikin mafarki ne zanji daɗi Sosai. Allah ya tashemu lafiya ya tsare ka daga dukkanin sharrin abun ƙi, a gaida Mamana. Your sister Mufeeda" Ammar na ɗakin Abokin sa Jabir da Aminu suna hira, shi Aminu yana da Aure shikuma Jabir ya kusa su Ammar kuwa ba labari, ƙararrawar saƙo ta buga alamar Saƙo ya shigo wayar Ammar, gaba ɗaya suka bishi da ido, wayar na gefen Aminu ya kalli screen ɗin wayar yace "Ammar an turo maka saƙo kuma lamba ce" Ammar ya karɓi wayar ya buɗe saƙon, juya saƙon ya dinga yi badan tasa sunan ta a ƙarshen saƙon ba cewa zeyi ƙaryane ba ita ta rubuta ba, wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ce ta zauna ta rubuta wannan saƙon? shiru ya ɗanyi yana nazari kafin daga bisani ya aje wayar tare da jan gajeren tsaki. Jabir yace "ya dai naji kana tsaki meye ya faru?" Wani tsakin ya kuma yi sannan yace "wani shirme aka turomin" "shirme kamar yaya? Waye ya turo maka?" "Hmm wata fitinanniyar yarinya Allah ya haɗa ni da ita daga na ɗauke ta a babur ɗina duk ta addabeni" Dariya Aminu yayi yace "Malam kaimana bayani kai tsaye, Ashe kawai mu fara tara kuɗin goro" "Aminu meye haka? Yarinya ce fa ƙarama, kuma kasani bani da ra'ayin Auren ƙaramar yarinya" Jabir yace "kaifa abun haushin ka yafiye yawa, ƙaramar yarinyar wataran ba ita zata zama babbar ba?" Aminu yace "ganemin hanya dai" "Bazaku gane ba, bafa tafi shekaru goma sha biyar ba, in tayi wuta shekara sha shida, uwar me zanyi da Jaririya dan wannan bata isa zaman Aure ba se dai ayi rainon ta" Wata irin dariyar ƙeta su Aminu suka yi Jabir yace "Wallahi Ammar kai ba ƙaramin ɗan rainin hankali bane, to meye a ciki ka raine ta harta zama yadda kake so se kuyi zaman Auren" "Allah ya kiyaye, wannan yarinyar me shegiyar tsiwa, tana magana kaman wata tsuntsuwa ga iyayi" Aminu yace "Ahhh kaman tsuntsuwa yabonta fa kayi gaskiya ɗankwali ya ja hula" Banza Ammar yayi masa ya haɗe rai a ransa yake tambayar kansa "dagaske yabonta nayi kenan?" Jabir yace "Abun mamakin ma Aminu shine ya akayi ta samu lambar sa?" Aminu yace "ƙwarai kuwa, gayamana ta yaya tsuntsuwa ta samu lambar maza gumbar dutse" Tsaki Ammar yayi ya miƙe ya ɗau wayar sa dan sun fara bashi haushi, dama gashi ba wuya yayi fushi. Aminu yace "Ammar ina Zainab ne?" banza yai masa ya fice ya bar musu ɗakin. **************** Mufeeda tayi sallama ɗakin baban ta yai mata izini ta shiga, ta shiga ta tarar da shi yana 'yan rubuce2, "me girma professor barka da zuwa Auta na, ya akayi ne zoki zauna" Ƙarasawa tayi kusa da Baban ta ta zauna, ta kalli Mahaifinta tace "Baba na sirri nazo muyi da kai nasan zaka fahimce ni, ita Mama komai nayi laifine a gurin ta" Murmushi yayi yace "Ai ta nayi ne saboda son da take miki" "A'a ai kai baka yimin yadda take min, a hankali kake gyara min laifina banda Mama ta fiye faɗa, dama tunda bikin yaya Amina take jin haushi na, na gaya mata abunda ke damuna amma taƙi saurara ta" Dattijon ya gyara zaman sa yace "Ina jinki Autana" "Baba nifa na fasa zama wannan professor ɗin a yanzu" "Meyasa?" "Baba" sekuma tayi shiru Baba yace "karki damu Baba ne fa, me zaki ɓoye masa, mun saba yin sirri mu tattauna karki ji komai gayamin" "Yawwa baba na, dama.. Amm dama.. Gaskiya Baba ni idan nayi Candy.. Yaya Ammar nake so" Shiru yayi yana nazarin ta sannan yai murmushi yace "Wannan me Napep ɗin?" Da sauri tace "Yawwa shi Baba" "Me yasa kike son shi, kuma kika zaɓi ki aure shi?" "Baba yana da kirki ne sosai, kuma ni ban san yadda akayi na fara sonshi ba, kawai kullum in ta tunanin sa na tambayi uncle yace min wai sonshi nake" Baba yakuma murmushi irin na manya sannan yace "Autar Baba daɗi na dake faɗar gaskiya komai ɗacin ta, gayamin me yayi miki, ko me yake gaya miki haka daya sa kike sonshi haka, har kika janye ƙudurinki na zama professor?" Nan ta kuma zayyane masa yadda ya kawota gida da zuwa bikin Amina da yayi. "niba abunda yamin ko ya gayamin, yana da kirki ne, kuma ɗan gayu ne, ai ka ganshi ranar ko?" Baba ya jinjina kai yace "hakane ɗaan gayu ne kam, yanzu idan kinyi candy aure zakiyi?" "Baba zanyi candy kafin in cika shekaru goma sha bakwai ne, sefa na jira na shekara sha takwas zan shiga University, kuma gashi wasu suyita zagin matan da suke zuwa jami'a, ko kuma su dinga musu kallon marasa tarbiyya, Amma idan nai Aure sannan nayi karatun ai se anfi ganina da mutunci, kuma fa badan Ammar ina sonshi ba bazan ce zanyi Aure yanzu ba, kullum se naita tunanin sa nafi son in dinga ganin sa kullum" Jinjina kai Baba ya dingayi sannan yace " 'yar ƙarama me tunanin manya, maganar ki gaskiya ne Auta na, indai ze barki kiyi karatun ai babu damuwa, dama ita soyayya ai gamon jini ce, wani halinsa ne kawai zesa kaji kana sonsa, in dai yayi miki kuma nai bincike akan halayen sa na yadda da halayen sa babu damuwa kije ki gaya masa ina son ganin sa" "to Baba nagode da fahimta ta da kayi sannan... " Shigowar Mama ce tasa ta yin shiru, Mama ta Harare ta. Mufeeda tace "Baba zan dawo mu ƙarasa zancen mu" "to shikenan Auta na" Ta miƙe ta fice. Ta koma ɗakin ta tana ta farinciki, se kuma ta shiga zullumin me zata cewa Ammar wanda ze kai ga yazo yaga mahaifin ta har ya yadda da maganar auren su?. "Taɓɗijan ga ƙoshi ga kwanan yunwa" (Duk abun nan fa Oga Ammar bece yana son ta ba 🙄🙄🙄) More Comments More typing. In ba comment zan aje littafin gaba ɗaya Domin sharhi, gyara ko kuma shawara A tuntube ni akan wannan lambar What's App Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Page 4 Juyi kawai Mufeeda take akan gado tana tunanin mafita, Amma ta kasa samawa kanta mafita, ji tayi kanta ya fara sarawa dan haka tai Adduoin ta na bacci ta rufe ido. Maman Mufeeda ta kalli mahaifin Mufeeda tace "Wai yanzu dagaske yarinyar nan zuwa tayi ta same ka akan maganar nan? Ban san lokacin da Mufeeda za tayi hankali ba, waya gaya mata zaman Aure aikin rago ne, guda nawa Mufeeda take da har zata tun kare ka da batun ita Aure take so" Mahaifin Mufeeda yace "Kwantar da hankalin ki maman yara, Abun ai duk bana zafi bane, ki sani tarbiyar da kika yiwa su Murja a zamanin su idan har kika ce irin ta zakiyi wa Mufeeda a wannan zamanin da muke ciki zata iya bijirewa" "Hakane dan taurin kanta yayi yawa, halinta ya fita daban dana 'yan uwan ta kaman bani na haife ta ba, ace yarinya ba kunya sam" Yai murmushi yace "Karki manta a tarbiyar da muka yi wa yaran mu babu kunya tsakanin mu dasu, mun ɗora su akan kome ke damunsu game da rayuwar su mu zamana mune mutane na farko da zamu fara sani, karki manta kowace yarinya kafin in Aurar da ita babu wadda ban san date ɗin da take Al'ada ba, ni nake siya na basu abunda za suyi amfani da shi lokacin Al'ada, hatta ƙanan kaya inner wears ɗin su in sun lalace kai tsaye suke tunkura ta su gayamin haƙƙi nane inyi musu, kuma babu inda Addini yace hakan haramci ne, idan haka ne wace kunya kike tunani tsakanina da su? kin fi kowa sanin ban yadda da kunya tsakani na da 'ya' ya naba, basu da sama damu jansu a jiki da muka yi ne ya sa suke iya bayyana mana matsalolin su, me kike tunani idan har da kika gwale Mufeeda nima Gwale ta nayi? Tana kan ƙanan shekarun ta na Adolescent period komai ze iya faruwa musamman idan tana ta'ammali da gurɓatattun ƙawaye, inda na godewa Allah Mufeeda rawar kan ne kawai da surutu amma tana kula da kanta" Ɗan lumshe ido Mama tayi tace "Hakane Amma menene mafita? Tayi ƙanƙanta da Aure" "Ke kike ganin tayi ƙanƙanta, a hirar da mukayi da ita na fuskanci cewar Ita ba wai Auren ya dame ta ba, tana ƙaunar yaron ne sosai, na bugi cikin ta inji ko wani ke zigata ko wani abun yaron yake mata take sonshi, kin santa bata rufemin komai, yadda na fuskanta Soyayya ce kawai, tana sonshi sosai kuma mafita ɗaya ce shine zan cewa yaron ya fito " Da sauri Mama ta kalleshi tace " haba shekarun ta nawa da za'a aurar da ita? Dr. kana kallon yadda nake fama da ita a cikin gidan nan ta yaya zata iya riƙe miji? Kuma karatun ta fa?" "Sarat shekarunki goma sha huɗu nikuma ashirin da biyu muka yi aure, muna tare ki kayi karatun sakandire har zuwa diploma, ko kin manta? yadda kika iya riƙeni itama zata iya" "Dr. Yanzu fa ka gama faɗin zamanin mu na da, da yanzu ba ɗaya ba, mazan yanzu ga rashin tabbas da rashin haƙuri ta yaya mufeeda na zata iya zama da miji yarinya ce ƙarama fa" "Calm down my wife, muyi mata Addu'a, Soyayya ba ruwan ta da shekaru kin san a baya, ko zancen Aure bata so dan baya gabanta, da kanta tace tunda ni ban kai ga zama professor ba ita zata zama, tana son karatu matuƙa, Amma tunda tace yanzu ta fasa. kuma ta bani gamsassun hujjojin ta na son yin aure kafin karatu. Kuma da yaro ƙaramine tace tana so nasan wannan shashanci ne, Amma naga yaron kaman yana da shekaru ba yaro ne ƙarami ba, muyi mata Addu Allah ya sanya musu Alkhairi " Haka Baba ya ci gaba da rarrashin ta, yana kuma nuna mata illar rashin amincewa da bukatar 'yar autar tasu. ***************** Ammar ya sai Sabuwar waya, ya maida simcard ɗin sa kai, yayi setting WhatsApp ɗin sa da sauran Abubuwansa sannan ya ajiye wayar ya kwanta. Cikin Bacci Mufeeda ta farka da zazzafan zazzaɓi da ciwon kai, yamutsa fuska tayi ta juya da nufin ta ci gaba da bacci amma abu ya gagara, ta ture abun rufarta ta tafi banɗaki tayi wanka ta dawo ta kuma kwanciya tana tunanin zazzaɓin ze sauka. Sosai zazzaɓin ke kuma hawan ta se rawar sanyi take yi, bata son taje ta ɗagawa iyayen ta hankali a daren nan. "ko wayar Baba zan kirane?" ta faɗa a fili taita tunani ta rasa menene mafita. Kasa komawa bacci tayi ta ɗakko wayarta ta ga ƙarfe sha biyu saura na dare. Ta rasa lambar wa zata kira, data ɗin ta ta buɗe saƙonni suka dinga shigowa, ta shiga what's App ɗin ta tana duba contact, ba zato ba tsammani taga lambar Yaya Ammar ɗina tayi appearing a contact ɗin ta. Da sauri ta miƙe zaune dukda zafin da jikin ta ya ɗauka, ta shiga kan hoton dp ɗinsa, tabbas shine hoton sa ne a tsaye a gaban Napep ɗinsa hannun sa ɗauke da makulli da handkerchief kalar kayan jikin sa, ya ɗanyi murmushi ba ƙaramin kyau yayi wa mufeeda ba, zooming ɗin hoton tayi tana ajiyar zuciya "You are handsome my man" ta furta a fili tana kuma ƙare masa kallo, message ta tura masa "Asslam Alaikum warahmatullah, Yaya Ammar dama kana what's App amma baka kulani ba?" Ta ci gaba da kallon hoton sa, sannan tayi murmushi ta ajiye wayar ta kwanta, Amma bacci yaƙi zuwa tamkar jira zazzaɓin yake ta kwanta, kanta ya dinga sarawa ga cikin ta ya ƙulle yana ciwo, Nan ta dinga shrara kuka ita kaɗai a ɗaki, se juyi take ga Amai yana taso mata. Wayar ta ta kuma ɗakkowa da nufin ta kira Mama a waya, amma tana cire key ɗin kan wayar ta hoton Dp ɗin Ammar ne bata fita ba. Wani saƙon ta tura masa, Tana gama tura saƙon ta saki wayar ta faɗo ƙasa daga kan gadon daga nan bata ƙara sanin inda kanta yake ba. ***************** Alarm ɗin Ammar ya buga ƙarfe uku na dare, ya miƙe ya shiga banɗaki yayi alwala ya zo ya tada salla, yai nafilolin sa ya ɗakko wayar sa ze karatun Al'qur'ani amma yaga data ɗin sa a buɗe messages suna ta shigowa. Rufe data yayi ba tareda ya duba saƙonnin ba yai karatun sa be koma bacci se Da yayi sallar Asuba. ************* Mufeeda kam se farkawa tayi ta ganta a gadon Asibiti an ɗaura mata ruwa, tana ganin haka ta fashe da kuka, Baba ya ƙaraso da sauri bakin gadon ta yana faɗin "Sannu Auta na yi shiru kin gammu a kusa da ke, sannu ya jikin naki?" Jinjina wa Baba kai tayi ba tare da tace komai ba, ta cigaba da kukan ta. Mama tace "Ke meye kuma na kukan kiyi mana shiru, idan mutum bashi da lafiya addu'a yake ba kuka ba, meye Amfanin kukan?" Cikin kuka Mufeeda tace "Na dauka na mutu ne fa" Dariya Baba yayi yace "A'a baki mutu ba, meyasa baki da lafiya baki gayawa kowa ba? seda Asuba Mamanki taje tashin ki ta ganki a ƙasa a sume a cikin amai, me yasa baki faɗa ba?" Maimakon ta amsawa Baba tambayar sa sema fashewa da ta kuma yi da kuka tace "Baba ciki na da kaina ciwo suke min" "Ya isa haka yi shiru, yanzu likita zezo ya duba ki" Ammar ya bayan sallar asuba ya ɗan koma bacci. Ƙarfe takwas na safe ya farka daga bacci ya ɗakko wayar sa yana duba saƙonni. Message ɗin Mufeeda yaci karo da shi a what's App ɗin sa kafin ya buɗe message din ya buɗe hoton kan dp ɗin ta, itace akan dp ɗin da kayan dinner ɗin yayar ta, tana sanye material maroon, tayi kyau matuƙa. Ɗan taɓe baki yayi ya buɗe voice message ɗin "Yaya Ammar ɗina bani da lafiya, kaman zan mutu nake ji, narasa me ke mun daɗi kamin Addu'a dan Allah" Shiru yayi yana kuma kunna message ɗin yana ƙoƙarin gane da gaske take yi ko kuwa dai wani abun take shiryawa, tsaki yayi ya ajiye wayarsa ya fita yai brush ya yi breakfast ya ɗau babur ɗin sa ya fice. Seda Mufeeda ta kwana huɗu a Asibiti, likita ya tabbatar musu typhoid da malaria ke damun ta, da yake Asibitin kuɗi ne, kusan duk seda likitoci da Nurses ɗin Asibitin suka santa, kullum cikin kuka take, ko ya taji ciwo se kuka, idan Mama ta takura ta taci Abinci se ta hau kuka, idan akazo Allura kuwa ba ƙaramin dambe ake sha da ita ba, ga rashin son magani taɓara daban2 kafin a sallame su, Baba ne ke lallaɓa abarsa Mama kam kusan dukan ta take yi. Aka sallame su da sauran magungunan su suka tafi gida, Alluran da akai mata suna da ƙarfi saboda ta sha wahala, dan haka tun kan suje gida take cewa bacci take ji, suna zuwa gida ɗakin ta fes mama ta gyara. Bata fara neman komai ba se wayar ta, ta kunna tana sa ran ganin saƙon Ammar kona ya jiki ne amma bata ga komai ba. Haushi ne ya kamata kaman ta sa kuka, ji tayi kan ta kaman ze cigaba da ciwo ba shiri ta ajiye wayar ta kwanta domin ta samu bacci. Hausawa suka ce sabo turken wawa. A kwana huɗun nan Ammar ya fara tunanin anya yarinyar nan ba dagaske take bata da lafiya ba? Last seen ɗin ta tun lokacin da ta tura masa message ɗin nan, Zuciyar sa na ta gaya masa abubuwa daban2. Yaya Fadila tazo gida domin sake duba Mufeeda, taje ta tarar tana bacci amma duk ta rame sosai, Fadeela tace "lallai Autar Baba an sha jiki, duk ta rame" Mama tace "Aikam ta sha jiki, kuma ta ƙarawa kanta wahala dan bata shan magani, ai zaman jinyar nan tata ba ƙaramin ɓata min rai yayi ba, ta fiye rakin tsiya kaman ba mace ba shiyasa bana so tayi rashin lafiya" Suna cikin hirar wayar Mufeeda ta fara ringing a gefen pillow ɗin Mufeeda, A hankali Fadeela tasa hannu ta ɗakko wayar. My Yaya Ammar shine akan screen ɗin, dariya Fadeela tayi tace "Mama sirikinki ne fa ya kira" Tsaki Mama tayi tace "sirikin Dr. Dai" Fadeela tai murmushi ta ɗaga wayar tayi sallama Ammar ya amsa ba tare da wata doguwar magana ba yace "Ina me wayar?" ba ƙaramin mamaki Fadeela tayi ba saboda abune mawuyaci ka banbance muryoyin su in ba ka zauna da dukan su ba, Amma sallama kawai tayi yasan ba Mufeeda bace, gashi cikin gadar yake magana, Fadeela tace "bata da lafiya bacci take" be kuma cewa komai ba ya kashe wayar sa. Fadeela tace "Ikon Allah yau ni naga isa da izza, kinji yadda yake magana kuwa Mama?" Mama tai tsaki tace "Ai se taje taita yi yaron da ko damuwa beyi da ita ba tun ranar ɗaurin Auren Amina wata na biyu kenan ban ganshi a gidan nan ba, ko dubiya bezo ba ni na kasa gane kan wannan shirirtar, ga baban ku ya goya mata baya yace zece ya fito, ko lokacin da yazo gidan nan ko ɗan murmushi babu a fuskar sa da ganin sa zeyi masifa " Fadeela tace "Mama yadda auta take da rawar kai da shagwaba ta auri gayen nan zata sha wahala, a muryar sa zaki gane yana da izza da isa, kuma Mama ya mata girma kalle shi fa ki kalli ƙirar jikin sa, ita kuma kalli ɗan nata jikin wallahi mama kiyi wani abu akan lamarin nan, kar ku biye wa haukan ta" Cikin damuwa Mama tace "Fadeela ya zanyi nayi2 babanku ya gane amma yaƙi, ya goyi bayan ta yace yadda take sonsa ɗin nan idan bamu goya mata baya ba zata iya shiga wani halin, nayi rarrashin nayi nasihar amma ina kin santa da kafiya musamman idan baban ku ya goyi bayan ta akan abu" Haka suka ci gaba da tattaunawa akan lamarin. Se kusan la'asar Mufeeda ta tashi daga baccin, tayi wanka ta ɗanci Abinci shima seda suka haura da Mama. Fadeela tace "professor Auta wannan gardin ya kira ki fa" A ya tsine Mufeeda ta kalli Fadeela "Waye kuma gardi?" "Wannan Saurayin naki me fuskar shanu, wanda yazo bikin Amina" Da farko Mufeeda bata yadda ba, ta harari Fadeela tace "Mama ki gayawa Yaya Fadeela babu ruwan ta dani karta ƙara cewa Ammar ɗina gardi, sedai mijinki ne gardi" Fadeela tace "Ashe har da zuwa ki ga yawa Baba ke Aure kike so ko? Hmm yarinya ba dai Aure ba? ba zaki gane ba yanzu" Share fadila tayi ta koma ɗakin ta, ta ɗakko wayar ta, da mamakin ta tana duba call log sega kiran Ammar, tsalle Mufeeda ta dinga yi a ɗaki tana murna. Ta nemi guri ta zauna tana tunanin ko ta kira shi? Se kuma ta fasa tace se dare tasan maybe yanzu yana aiki. Se bayan sallar isha'i kusan tara da rabi na dare sannan ta ɗakko wayar ta ta kira Ammar, Amma abun haushi be ɗaga ba, missed call biyu tayi masa amma ne ɗaga ba. Haushi ne ya kamata ta ajiye wayar a gefen ta ta kwanta tana zumɓura baki kaman tana gaban sa. Bacci ne ya fara ɗaukar ta, cikin baccin ta ji wayar ta na vibrating, Ammar ne seda ta saki murmushi sannan ta ɗaga wayar tasa a kunnenta sallama yayi mata Seda ta ƙara ƙasa da muryar ta sosai kaman tana jin jiki sannan ta amsa masa Sallamar (tafa warke har faɗa suka kusa yi da Yaya Fadeela ɗazu saboda an ce masa gardi amma ya kira ta noƙe murya kaman yanzu take jin rashin lafiyar 🙄🙄🙄) "Na kira ɗazu kina bacci ya jiki?" Seda ta ƙara ƙasa da murya cikin shagwaba da wata irin sassanyar murya tace "Ni banji sauƙi ba bani da lafiya har yanzu, banji sauƙi ba ji nake kaman zan mutu, Yaya Ammar ba zaka zo ka duba ni ba?" Kaman an masa dole yace "meya same ki?" "komai ma ya dameni zazzabi nake sosai, kwana na huɗu a Asibiti, dan Allah Yaya Ammar kazo in ganka kar in mutu bamu haɗu ba please" Ji yayi gaba ɗaya wata kasala ta saukar masa yanayin yadda auta ke magana, seda ya numfasa sannan yace "zuwana baze hana rashin lafiyar ki ba, sedai zan miki Addu'a Allah ya baki lafiya" Kawai ta saka kuka babban abunda Ammar ya tsana a rayuwar sa kenan kuka "nidai dan Allah kazo, idan na ganka zanji sauƙi, in kazo dubani zaka samu ladan gaida mara lafiya, kai na fara gayawa bani da lafiya amma bazaka zo ka dubani ba ko? Shikenan nagode dama ni na damu da kai in na mutu Baba ne kawai ze kewa ta" Ta ajiye wayar ta ci gaba da kukan ta, da yake bata katse kiran ba Ammar yana jin sheshsheƙar kukan ta. Katse kiran yayi tare da dafe kai yace "Ohh My God" Mufeeda kam ta sha kuka, da surutai "nikam wace irin ƙaddara ce na kama son wanda be damu da niba, Ni dama haka son yake? Wayyo Allah na" Ji tai kanta ya fara nauyi dan haka ta lumshe idon ta tana jiran bacci ya ɗauke ta. Ammar ya rasa yadda zeyi, haka nan idan ya tuna kukan da Mufeeda take a waya se yaji idan be je ya duba ta ba kaman be kyauta ba, Amma a matsayin wa zeje dubiyar? Baya son tambayar su Jabir shawara yanzu zasu raina masa hankali, dan haka kawai ya share. Mama ta lura kaman jikin mufeeda ya dawo, dan wuni tayi a kwance ko Abinci ta kasa ci se complaint take da kanta. Da ƙyar ta samu tayi sallar magariba shima a zaune tayi saboda ciwon kan da take ji sosai. Yaro ne ya shigo yai Sallama ya tarar da Mama a tsakar gida ya gaishe ta da yake ɗan maƙotan su ne, yaron yace "Wai Mufeeda taje inji Ammar" Mama ta taɓe baki kaman tace baza ta zo ba, Amma ta fasa tace "kace tana zuwa" Mufeeda kuwa dukda tana fama da kanta tana jin jiri amma haka ta miƙe ta ɗauki ɗankwalin Abayar ta ta yafa ta fito waje Mama ta kalleta tace "yau naga tsiya kekina fama da kanki amma shine har kin fito, kai Allah yayi miki magani" Mufeeda ba tace komai ba ta shiga ɗakin Mama ta ɗakko Babbar Dadduma tai waje abun ta, zuciyar ta cike da farinciki da ɗokin ganin Ammar. A jikin gate ɗin su ta tsaya ta na kallo shi daga inda yake tsaye opposite ɗin gate ɗin yana danna wayarsa, ita dai a duk lokacin da ta ganshi ƙara yi mata kyau yake da kwarjini. Ta tura masa message "Ka shigo gareji, Yanzu Baba ze dawo, ya ganni a waje ze min faɗa" Ɗaga kansa yayi ya hango ta, ya taka a hankali ya shiga gate ɗin gidan su, har ta shimfiɗa daddumar ta zauna, da yake da wuta ko ina da haske. kana kallon ta zaka gane bata da lafiya, dan ta rame sosai ta ƙara haske. Ƙamshin turaren sa ya kashe mata jiki tare da ƙara masa kwarjini a idon ta gaba ɗaya ta kasa ɗaga kai ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa. Sema da ya zauna akan daddumar ya zama na yana daf da ita, suna jin Ƙamshin turaren juna, taji gaba ɗaya kamar yau ta fara ganin sa. kaman kullum yauma fuskar sa babu wata fara'a A hankali tace "ina wuni?" Ya kalle ta yace "lafiya Ashe ma kin warke?" Ai kaman ya taɓa mata inda yake mata ƙaiƙayi ta tura baki kawai ta fara share hawaye. Ya tsuke fuska yace "Meye kuma abun kukan? Kince inzo in duba ki nazo kuma seki dinga min kuka? Wannan se ace wani abun nayi miki ai" yai maganar in very serious tone Maimakon ta shiga taitayin ta sema wasu hawayen dake kuma bin fuskarta wannan karon hadda sauti, cikin shagwaba ta fara magana "Ni wallahi ban warke ba, ko sauƙi banji ba, yau ma a kwance na wuni, Yanzu Yaya Ammar ba dan na roƙe ka ba ba zaka zo ka duba ni ba ko? Cikin dare rashin lafiya ta kamani ba wanda ya sani kai na fara gayawa a sume aka kaini Asibiti, Amma kaƙi zuwa duba ni, ni ka tsane ni kuma ban san me nayi maka ba" Ta ci gaba da kukan ta cike da shagwaɓa kaman wata 'yar yarinya ƙarama hawaye wani na bin wani. Ammar yai ƙarfin halin cewa "look ko ki dena wannan kukan, ko kuma in tashi in tafi" "to zan dena" "ba cewa zakiyi zaki dena ba, kidena kawai, goge wannan hawayen" Ta ɗan lumshe ido sannan tace "Niba handkerchief a gurina sedai ka bani naka in goge" Kallon ta yayi galala ya haɗe rai yace "goge da mayafin ki" Noƙe kafaɗa tayi "A'a ni da handkerchief ɗin ka nake so zan goge, nasan yana Ƙamshin turaren ka" "naga Alamar kin warke, Allah ya ƙara afuwa" yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa Ta kwantar da kai tare da kwantar da murya tace "dan Allah da manzon sa karka tafi yanzu" "Ni wannan abubuwan da kike ne bana so, shi yasa bana son zuwa inda kike, ina sauri ne ana jira na ai nazo na duba ki" "Yanzu tafiya za ka yi?" Shiru yayi mata ya durƙusa ya ɗau mukullin babur ɗin sa da wayar sa, ya tsaya yana gyara links ɗin hannun rigar sa itama ta miƙe tsaye, Amma abunka da mara lafiya jiki ba ƙwari tana tashi taga duhu a idon ta duniyar tana juya mata, dafe kanta tayi data ji ya sara mata. Yuuuuu ta tafi zata faɗi, Cikin zafin nama Ammar ya riƙo ta. Da ƙarfi zuciyar Ammar ta buga, gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, be taɓa riƙe macen da ba maharramarsa ba yana sane se yanzu, jikin ta rau yake da Zazzabi me zafin gaske. "Wash Allah kaina ze fashe" Tsoro da fargaba ne suka kama Ammar, kar wani yazo ya ganta a jikin sa, ga kuma jikin ta zafin daya ɗauka. Jingina ta yayi a jikin bango yace "zaki iya tafiya ko inyi magana cikin gida a zo a shiga dake?" Girgiza masa kai tayi tace "na rage jin jirin zan iya shiga gida da kaina" "Sannu ɗan ƙara hutawa seki shiga" Ta jinjina masa kai Baba ne ya dawo ya tarar da Ammar yana shirin tafiya, mufeeda kuma zata koma cikin gida, Ammar ya tsaya ya gaida Baba, yai masa ya me jiki. Baba ya amsa masa cikin mutunci ya kalli Mufeeda yace "Auta na ya jikin naki" "Da sauƙi Baba" "Masha Allah" Baba ya dawo da kallon sa kan Ammar yace "Ammar ko?" Ammar ya jinjina kai yace "Eh hakane" Baba yace "Yawwa dama ina son ganin ka, biyo ni" Galala Ammar yayi yana fatan "Allah yasa ba riƙe Mufeeda da yayi ya gani ba yai zafon wani abun" Murmushi Mufeeda tayi tare da yin gaba abunta ba tare da ta kuma waiwayo ba More Comments More typing Domin sharhi, gyara ko shawara Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com *ELEGANT ONLINE WTITERS* Page 5 Cikin gida mufeeda ta koma tana me farinciki tare da roƙon Allah yasa Ammar ya amince. Har falon Baba Ammar ya shiga suka ƙara gaisawa da baba, Baba ya dube shi yace "Ammar a wace unguwa kake sannan menene sana'ar ka?" Ammar yaji gaban sa ya fadi tare da mamakin wannan tambayar amma ya dake ya bawa Baba amsar tambayar sa, Baba ya cigaba da yi masa tambayoyi game da shi yana bashi amsa. Baba ya nisa yaxe "to dama abunda yasa na kira ka kuna nayi maka wanna tambayoyi ba komai bane face auta tazo ta sameni da maganar ka, kuma yanayi ya nunamin kanada hankali da nutsuwa, to nidai gaskiya mutum me son abunda yaran sa suke so matuƙar be saɓawa shari'a ba, da farko Auta karatu take sonyi amma katsam ta sauya tunani, kuma bana tauye abunda yarona yake so ince lallai se yabi nawa abunda nake so, tunda harta furta ta zabi Aure akan karatu nace bari inyi maka magana idan ka shirya ka turo magabatanka, ina so abun ya zamana anyi shi anan kusa, sedai ina son bayan auren ka barta ta ci gaba da karatun ta" Ras! Ras!! Ras!!! Gaban Ammar ya faɗi, ya ɗago ya kalli mahaifin Mufeeda da nufin ya sanar da shi shi babu wata alaƙa ta soyayya a tsakanin sa da Mufeeda, Amma ya ga dattijon ya masa matuƙar kwarjinin da baze iya kallon sa ya gaya masa hakan ba, nan da nan gumi ya dinga tsatstsafo masa ta ko ina. "baka ce komai ba" "To Baba nagode insha Allah zanyi magana da magabata na" Baba yace "yayi kyau, Allah ya Sanya Alkhairi a tsakanin ku" Da ƙyar Ammar ya baro gidan nan zuciyar sa na bugun uku uku, shi dai gaskiyar magana Mufeeda tayi masa ƙanƙanta a aure, ta ina zeyi zaman Aure da wannan jaririyar yarinyar? Shi sam babu wani abu makamancin son ta da yake ji a ransa, shi be taɓa jin yana son wata ba balle yace ga yadda akeji, ita kanta budurwar sa zainab bawai dan yana jin yana sonta yake niyyar auren ta ba, se dan tana da irin shekarun da yake son mace ta kai kafin ya aure ta, gashi tsoron sa da take ji da kwarjinin sa baya bata damar nuna masa soyayya, dan sam Ammar kallon shiririta yake wa wannan abubuwan na soyayya. Allah ne ya kai Ammar gida lafiya, ba dan yasan a yadda yake tuƙin ba. Yana zuwa gida ba wanda ya kula ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofa ya samu guri ya zauna yayi shiru "Waima yaushe nace wa yarinyar nan ina sonta da har za tayi min haka?" Wayarsa ya lalubo a fusace ya nemo lambar ta ya danna kira. Tana daga kwance ta janyo wayar tasa a kunnen ta, ai tana ɗagawa Ammar ya fara masifa "ubanwa yace miki ina sonki? Me yasa zaki je ki gayawa mahaifinki ni kike so? Ni sa'anki ne ko sa'an Auren ki ne ni? Kina jarirya da ke har kin san wani menene aure wata ƙwaila da ke, ni bani da ra'ayin auren ƙwailar mace mara aji kamar ki dan haka tun wuri ki koma ki gayawa mahaifinki kin fasa" Sosai Mufeeda taji zafin maganganun Da Ammar ya gaya mata, jaririya! Ƙwaila! Mara aji! Dakewa tayi ta kwantar da murya tace "Wash Allah kaina, har yanzu fa ban warke ba yaya Ammar a kwance nake, ka bari idan na warke seka gayamin abunda kake son gayamin, idan kuma na mutu shikenan ka huta" Jikin sa ne kuma yayi sanyi, dan ya manta ɗazu a yanayin da ya barta, tsaki yayi ya katse kiran ta ajiye wayar tace "hmm Ammar kenan wannan izzar da ta kemin ɗawainiya da kai sena sauke maka ita, nice Jaririya kuma ƙwaila sena nuna maka WATA KISSAR.. Se Mata, zaka ga ƙwaila ganin idon ka" Ta gyara kwanciyar ta, ta kwanta ta ja bargo ta rufe jikin ta. ****************** Kusan kwana uku Ammar ya kasa gayawa kowa abunda ke faruwa duk a takure yake ya rasa meke masa daɗi Yau Da safe Ammar ya tashi sam babu walwala ya shiga ya gaida Umman sa fuskar sa a haɗe alamar bayan rashin fara'a akwai damuwa a tare da shi. Halima ta kawo masa kayan karin kumallo ya zauna ya ɗan cakali kaɗan ya miƙe ze fita, umman sa tace "Ammar zauna za muyi magana" ba musu ya nemi guri ya zauna "Ammar me yake damunka ne? Kwana biyu naga sam baka walwala, ko Abincin kirki baka ci, gayamin meke faruwa ne?" Kaman ya ƙi gaya mata, amma yaga idan yai shiru be gayawa mahaifiyar sa ba waze gayawa? Dan haka ya zauna ya warware mata komai tunda ga hɗuwar sa da Mufeeda zuwa yau, murmushi tayi tace "Masha Allah a ina ne gidan su yarinyar? " Ammar yace "Umma ba fa sonta nake ba, yarinya ce me ƙarancin shekaru da rawar kai, tayi min yarinta da yawa ni bazan iya auren ta ba" Umma tace "kaga dakata, ai Addini be hana aure tsakanin ku ba, kuma ƙarancin shekaru ba'a nan zaman aure yake ba, dan haka zamu ci gaba da Addu'a, dan dama na gaji da yawan saɓani da kake samu da mahaifin ka akan rashin auren nan" Ammar yace "haba Umma kinfi kowa sanin bana son in auri yarinya tazo ta dingamin hauka, ta rainani yarinyar nan da kaɗan tafi yayayyiya fa, nifa bana son auren yarinya ƙarama tazo ta dingamin shirme" Kallon sa Umma tayi tare da yin murmushi tace "yaro man kaza, kana raina ta kana ce mata jaririya se kaga jaririyar ta baka mamaki, ai duk mace mace ce komai ƙanƙantarta, da kasan baka sonta ai tun a lokacin seka gayawa mahaifin ta, ko kuwa se yanzu daka Gaya masa unguwar da kake da gidan ku sannan zaka ce baka son ta in kayi haka baka kyauta ba" "Umma ni dai dan Allah ki sama mun mafita amma gaskiya bana son ta" Umma tace "karka kuma cewa baka son ta, ko da wasa karka kuskura ka kalli idon mutumin da yace yana sonka ka gaya masa baka sonsa, ba'a haka kaima Allah ze iya jarabtar ka wataran, tashi kaje seka dawo ma cigaba da maganar" Umma ta sallami Ammar ya tashi ya tafi yana ƙara zullumi da tunanin wannan lamari a ransa. Da magariba Ammar ya dawo gida dan yana jin yunwa, bayan yaci Abincin dare, yai sallar isha'i a gida, dan ya rasa jam'i, kuma yana son ya ɗan zaga ya ɗau fasinjan dare, ya gama abunda zeyi ze fita Baban sa ya shigo ya tsaya ya gaida Abban sa, ya kalle shi yace "fita zaka kuma yine Ammar?" "Eh Abba zani na ɗan zaga in samu fasinjan dare" Abba yace "ɗan tsaya kafin ka fita ɗakko min tabarma a ɗaki" Ammar yaje ya ɗakko tabarma ya shimfiɗa wa Abban sa ya zauna. Abba yace "kaima zauna" Ammar ya cire takalmansa ya samu guri ya zauna Abba ya kalle shi yace "Ammar mahaifiyarka tayi min bayanin abunda yake faruwa, ance ka fito, nayi farinciki da jin hakan ƙwarai, yanzu abunda nake so da kai zuwa rana ita yau kaje banki ka ɗakko abunda ya samu da kake tarawa zanyi wa kawunka magana, Insha Allah zamuje akai maka kuɗin Aure" Ƙuuuuuu cikin Ammar ya bada wata irin ƙara ya kalli mahaifin sa yace "Abba wallahi ba sonta nake ba" Abba yace "mu muna son ta, aini duk wanda yake ƙaunar ku Ammar nima ina ƙaunar sa" "Abba wallahi yarinya ce sosai, bata fi ayi rainon ta ba" "Ammar duk yarinyar data nuna tana sonka a yadda kake ɗin nan, ga fushi da saurin zuciya ga jinkai, kai ba kuɗi ba kai ba mulki ba amma tace tana sonka, harta ga yawa mahaifin ta a irin yadda da yawan 'yan matan zamanin nan masu son abun duniya tace taji ta gani tana sonka, wallahi Ammar ka bari yarinyar nan ta suɓuce maka zakayi babbar asara, ina me tabbatar maka zata iya zama da kai a halin akwai ko babu" "Abba ya za' ayi in zauna da macen da bana so, kuma fa akwai wadda nake zuwa gurin ta fa" "Ammar ni tunda muke baka taɓa cemin kana da wadda kake zuwa gurin ta ba, dan haka kayi haƙuri Allah yasa haka shine mafi alkhairi" Gaba ɗaya Ammar be taɓa tunanin abubuwa zasu hargitse masa haka ba, wannan wace irin jaraba ce, daga haɗuwa da yarinya ta zame masa gum (glue inji bebi 😂) shi sam beta ɓa kawo batun aure a nan kusa ba mussman auren ƙaramar yarinya amma lokaci ɗaya al'amura na ƙoƙarin sauya masa. ******************* Kwana biyu Mufeeda ta warware harta koma makaranta, Baba be gayawa Mufeeda yadda suka yi da Ammar ba, Sannan ya yanke shawarar a aji biyar na sikandire Mufeeda zata zana jarrabawar kammala sikandire ya aurar da ita. Ammar be kuma bi takan ya jikin Mufeeda ba, itakam mufeeda addu'a take idan Auren Amma ze zame mata alkhairi Allah ya tabattar idan kuna babu alkhairi Allah ya zaɓa mata mafi Alkhairi amma tabbas zuciyar ta na matukar son Ammar. Sati ya zagayo cif Ammar be kuma yiwa mahaifin sa batun maganar kai kuɗi ba, ranar kwana na goma da maganar, Ammar yana kwance yana bacci da safe Abba yazo yana buga masa ƙofa, da sauri Ammar ya tashi yazo ya buɗe ƙofar. Abba yace "Ammar idan kai baka gudun magana toni baza ka maidani ƙaramin mutum ba, ka amsawa mutane zaka tura magabatanka yau kwana goma dayi maka maganar ka kawo abunda yake hannun ka amma kayi biris dani, ban isa in gaya maka magana kaji ba ko Ammar?" "Abba bahaka bane, nifa kuɗin da nake da su basu fi dubu talatin ba, kuma ni... Abba ya katse shi ta hanyar cewa "Sa kayanka kaje ka ciro su ni akwai dubu ashirin a gurina, gobe insha Allah zamuje mu kai" "Amma Abba kaga" "nagama magana Ammar, in na isa da kai kayi abunda nace in ban isa ba kuma shikenan" Abba ya juya ya fice, Ammar ya zauna akan katifarsa ya dafe kai. Ya fara tunanin Anya aka kai dubu hamsin baza su raina ba? Mahaifin Mufeeda yana da rufin Asiri kuma yayyen ta suna auran masu kuɗi anya baza'a wulaƙanta shiba, dan shi babban abunda ya tsana kenan a rayuwar sa wulaƙanci, waima yanzu ba abun kunya bane ace kaman shi da shekarunsa ya gama cika baki amma ya auri Mufeeda, yasan Idan ya auri Mufeeda dashi da wanda bashi da aure duk ɗaya dan wannan yarinyar bata isa komai a gurin sa ba. A fili yace "Allah yasa su raina kuɗin suce baza su karɓa ba" Hakanan jiki babu ƙwari ya miƙe ya tafi banki ya ciro kuɗi. *************** Mufeeda ta dawo daga makarantar boko a matuƙar gajiye, data dawo tayi mamakin ganin Mahaifinta a gida a wannan lokacin, taci Abinci tai shirin ta tsaf ta tafi Islamiyya. Bayan ta dawo da daddare Baban ta yasa akai kiran ta, taje ta sameshi shida Maman ta a zaune. "Gani Baba" Baba yace "Mufeeda yau gidan su Ammar suka kawo kuɗin auren ki, sun kawo kuɗin su har naira dubu hamsin, ɗazu da safe kina makaranta kuma nayi dukkanin binkicen da ya kamata inyi akan sa an tabbatar min da cewar mutumin kirki ne ɗan gidan masu mutunci dan haka na tsaida ranar Auren ku nan da watanni shida" Da sauri ta kalli Baban nata tace "to ai lokacin ban gama makaranta ba" Baba yace "Eh wannan shekarar zakiyi Waec i know you can do it, zan sama miki gurin extra lesson, kuna kammala jarrabawa mu sha biki" Se a lokacin wata kunya ta saukar mata, ta ɗanyi murmushi ta tashi ta fita ta bar ɗakin Mama kam gaba ɗaya ranta a ɓace yake, gani take ta ko ina an cutar mata da yarinya, ga ƙarancin shekaru da Mufeeda ke da su, ga yarinyar ta babu laifi tana da kyau, sannan izifi talatin ne na Al'qur'ani akan ta amma ace dubu hamsin za'a bata kuɗin aure kamar wata bazawara. Tunda aka kawo kuɗin Mama take mita, Amma ɓangaren Baba yaji daɗin ganin 'yan uwan Ammar, mutane ne masu karamci da yakana, mahaifin Ammar da kanshi ya sanar da Mahaifin Mufeeda cewar "Ammar yayi karatun sa na zamani, Amma rashin aikin yi ya sashi fara sana'ar babur ɗin a daidaita sahu, ya tabbatarwa mahaifin Mufeeda cewar Ammar baya raina sana'a komai ƙanƙartar ta idan ya samu zeyi yasan Insha Allah ze iya riƙe Mufeeda. Da Baba ya gaya musu ya saka watanni shida lokacin biki ƙanin mahaifin Ammar yace "yallaɓai wata shida ai bamu gama shiri ba abunka da masu ƙaramin ƙarfi" Baba yace "karku damu, duk abunda ya sawwaƙa kuka kawo zamu karɓa karku takura kanku, aini duk wanda yake son ɗana ya gama min komai, Ammar ɗana ne komai ya kawo Allah ya amfana zan bashi Auta" Baban Mufeeda yaji daɗin wannan bayanin dan yana son mutane masu gaskiya. Ganin da Baba yayi Mitar Mama taƙi ƙarewa ya sashi fara yi mata nasiha "Sarah wani lokacin bakinmu da kuma ayyukan mu suke lalata auren yaranmu, aure beje ko'ina ba aita samun fitintunu, yanzu wannan kushewar da kike wa auren nan ze iya jefa rayuwar Auren ta cikin hatsari, kina maganar duk yaranki babu wadda ta auri talaka kaman Mufeeda, seki ga kaf yaran babu wanda ya samu kwanciyar hankali a gidan aure kamar ta, Sarah Auren me zuciya yafi auren me dukiya, dan Allah kidena kushe auren nan kisa musu albarka kawai " Ita dai Mama jinsa kawai take amma sam bata ƙaunar auren nan. Mufeeda kam murna ta dinga yi, tana faɗin " Yaya Ammar har yana da ƙarfin daze iya bada dubu hamsin kuɗin aure na? Alhamdilillah amma me yasa be gayamin za'a kawo kuɗin ba? " Har ta ɗauki waya zata kira shi, ta tuna wulaƙancin da yayi mata yace "mata jaririya kuma ƙwaila" fasa kiran sa tayi ta tura masa saƙo "Yaya Ammar Jaririyar ka tayi mamakin kuɗin da'aka kawo mata, dama darajar ta ta kai haka a gurinka? Jaririya na godiya, Allah yasaka maka da alheri, Allah ya ƙara Arziki da rufin asiri, nagode sosai Yaya Ammar ɗina" Tana gama tura masa saƙon ta kira Yaya Amina a waya dan sunfi shiri da ita. *************** Tunda Baba suka tafi kai kuɗin nan Ammar ya rasa meke masa daɗi daya tuna se yaji wata damuwa ta mamaye zuciyar sa, tunda ya fita da safe be kuma komawa gidan ba se dare. Yana zuwa kuwa ya tarar da Abba a tsakar gida yana jiran sa. Ba walwala haka ya shiga gidan, Abba yace "Yawwa dama kai nake jira, naga yau tunda ka fita sam baka dawo gidan ba, balle kaji yadda muka yi da gidan su matar ka" Ammar a ransa yace "Ji Abba da ɗigimi wai Matata" Ammar yace "to gani na dawo" Abba cikin fara'ar sa yace "gaskiya Ammar iyayen yarinyar nan suna da dattako, dana ga gidan su na zata mahaifinta ze raina abunda muka kai, Amma yaita murna yana sa Albarka, dukda banga yarinyar ba naji har raina ina ƙaunar ta, Allah ya sanya muku Alkhairi, Baban ta yace ya saka watanni shida insha Allah za'ai bikin " "wata shida Baba me nake da shi daza'a saka biki nan da wata shida?" "Yana hannun Allah Ammar, munyi wa mahaifinta magana akan hakan yace duk abunda kake da shi ka bayar Allah ya amfana, kuma muma ba samaka ido za muyi ba zamu tallafa maka da abunda ya samu, fatanmu dai ka riƙe yarinyar nan Amana" Shiru Ammar yayi bece komai ba, wannan wane irin lamarine yazo masa a gaggauce haka, ba shiri ba komai abubuwa se faruwa suke. Umman Ammar ta fito daga ɗaki tana faɗin "Ai Baban Ammar a jikina ina jin Allah ya karɓi addu'armu Ammar ya dace da matar ƙwarai samun irin su ita kanta yarinyar da iyaye masu dattaku wahala yake a yanzu, nidai har raina nake son batun Auren nan Allah ya nuna mana lokacin" Ammar bin mahaifiyarsa yai da kallo a ransa ya maimaita "wai matar ƙwarai dan basu ga yarinyar ba befi a saka zani a goye ta ba" Shidai Ammar be kuma cewa komai ba ya miƙe ya fice ya bar gidan. Kai tsaye ɗakin Jabir ya wuce, yana zuwa ya tarar Aminu ma yana can, yana zuwa be kula su ba ya samu guri ya zauna. Gaba ɗaya suka bishi da kallo Aminu yace "Mutumin ya akayi ne? Ya muka ganka a haka?" Shiru ya musu yana jan ƙaramin tsaki, se wani huci yake bayan 'yan mintuna ya kuma jan tsaki sannan yace "Kuɗin Aure Abba ya kaimin" Jabir yace "what are you serious Man? Kai wallahi dani mace ne se nayi guɗa, Alhamdilillah" Aminu yace "to kuma menene abun ɓata ran abun farinciki ya same ka sannan kazo kana cunkushe mana fuska" Jabir yace "wait wai meyasa baka gaya mana za'a kai kuɗin aurenka ba? Wace me rabon ce ta rabauta da samun a very hardworking man as you?" Seda Ammar ya kuma tsaki yai musu bayanin komai sannan ya ɗora da cewa "ni faruwar abun har tsoro yake bani ji yadda komai ke faruwa cikin gaggawa" Aminu yace "Ammar da yawa suna neman damar daka samu basu samu ba, a wannan marrar ka bawa yarinya budurwa dubu hamsin kuɗin aure iyayen ta su karɓa da murna har suce komai Allah ya hore ma ka kawo zasu baka gaskiya kayi dace" Ammar yace "wacece budurwar? Ana gaya muku ƙwaila ce kuna wani surutu" Jabir yace "kai Ammar kai duk wannan ne ya dame ka? Ba'a nan take ba ɗan nuna mana hoton ta mu gani mana muga wai me yasa ka damu da cewar ƙwaila ce" "Ni bani da hotonta sedai akan dp ɗin ta" ya faɗa yana cunkusa fuska Yana ɗakko wayar sa yaga message ɗin ta tana godiyar ya kai kuɗin auren ta dubu hamsin. Shiru yayi yana wani tunani, buɗe what's App ɗinsa yayi ya nuna musu hoton ta na kan DP ɗin ta, ta canza hoto, iya fuskarta ne kawai akai tayi murmushi. Aminu yace "wow Masha Allah, wallahi Ammar karkayiwa kanka sagededuwa, see fine Baby" Jabir yace "dan Allah in baka so, ni zan ƙara dubu hamsin abani" Harar Jabir yayi yasa hannu ya fizge wayar sa sega kira ya shigo, Ammar ya ɗaga kiran kafin yayi magana ta fara "Yaya Ammar ɗina, bani da lafiya Amma baka kuma cemin ya jiki ba, na turo maka message bakayi responding ba, Anyway nagode sosai ban zaci zaka bada wannan kuɗin a matsayin kuɗin aure na ba, Nagode sosai Baby na" "What!! Baby kuma?" Ai take su Jabir suka ƙyalƙyale da dariya dan Ammar ya tsani yaga ana wannan abubuwan. Mufeeda tace "ba cemin kai ni jariri ya ce ba, gara in maida kai Jariri kaman ni se komai ya tafi daidai, Yaya Ammar dan Allah kazo in ganka please" "Ke ki rabu dani ki dena wannan rawar kan, Auren nan ba yuwuwa zeyi ba, ni bazan auri ƙaramar yarinyar mara Aji ba kamar ki ba bana son shirirta" Mufeeda ta kwantar da muryarta cikin kissa da murya me ɗaukar hankali tace " Ammar ɗina ni kaɗai, kuma Angon ƙwaila to be insha Allah, you know what? Am very lucky daga haɗuwar mu zuwa yanzu komai yana tafiya dai dai, Amma Idan har dan nace ina sonka shine bani da Aji me zakace game da Auran Sayyada khadija da manzon Allah salallahu alaihi wassalam? Idan har kace na maka ƙanƙanta da aure me zaka ce game da Auren Sayyada Aisha da manzon Allah salallahu alaihi wassalam? Haba Yaya Ammar ɗina babu rashin aji a abunda nayi fa" Shiru Ammar yayi, yayin da Aminu yai ƙasa da murya yace Jabir "Wallahi yarinyar nan ta fi Ammar iya siyasa, kan uba a yanayin hotonta yarinya ƙarama amma tana tsara zance" "Baby na zan kwanta bacci ka gaidamin dasu Mama, Sannan ka cewa Abokan ka kowa ya tafi gidan su abarmin kai ka huta dan Allah" Domin gyara sharhi ko ƙorafi Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 6 Shewa su Jabir sukayi, Jabir yace "karki ji komai matar mu zamu tafi yanzu mu barshi ya huta" Tana jin hayaniyar su ta kashe wayar ta tana murna, gaba ɗaya Ammar ransa ƙara ɓaci yayi yace "Jabir meye haka wai kuke yi, sekunsa ta fara rainani meye hakan kukayi?" Aminu yace "kai Ammar saurara tun wuri kasan abunda yake maka ciwo, wannan yarinyar kana ganin ta a haka nan gaba in bakayi wasa ba seta dinga juya ka, dan ta fika baki kai fushin kawai ka iya da zare ido" "Allah ya kiyaye wannan abar ta juyani" Jabir yace "ƙyale shi Aminu ze ga wannan abar ganin idon sa, abun da zamuyi yanzu shi ne, ka bamu sunan ta zamu je ayi muku sticker da keyholder za'a haɗa da chewngum wanda zata rabawa ƙawayen ta" "Amma bada kuɗi na za'ayi wannan shirmen ba ko?" Aminu yace "kwantar da hankalin ka da kuɗin mu zamu yi ba, da namu zamu yi dan haka akeyi, Amma lokacin da zakayi na kuɗin naka muna gefe" Jabir yace "Ammar dan Allah kayiwa yarinyar nan hallaci, karka watsa mata ƙasa a ido ji musamman ta kira take maka godiya akan kuɗin nan dan Allah kadena wannan fushin kaman wanda za'ayiwa auren dole" Ammar yace "to meye wannan in ba auren dolen ba?" Aminu yace "ka gama muzuran ka a yanzu in ka shiga hannun ƙwaila se yadda tayi da kai" Ɗaukar wayar sa Ammar yayi ya fice ya bar ɗakin ************ Haka nan badan mama taso ba ta fara shirye2 da siyayyar kayan auren Mufeeda aka sanar da 'yan uwa da abokan arziƙi an saka ranar auren Autar baba, wasu na san barka wasu na ya akayi ita za' a mata aure yanzu bayan 'yan uwan ta seda suka fara karatu (mutane kenan komai se sunyi magana) Ɓangaren Ammar ma shiri suka fara yi sosai,' yan uwa da abokan sa na ta taya shi ƙoƙarin haɗa kayan aure, dukda baya son auren saboda Yadda iyayen sa suka ɗaukaki auren nan ya sashi dole shima yake nasa ƙoƙarin. Yau yayyen mufeeda duk sunzo gida da yake sukanyi haka lokaci lokaci mussman lokacin farinciki, sukai ta caccakar Mufeeda akan tana murna Ammar ya bada dubu ɗari kuɗin auren ta ita dai tai musu banza taƙi kula su. Yaya Fadeela tace "yarinya man kaza ba dai aure ba? Namiji ko gaki gashi nan, yau shiyace yana son ka yaka ƙarke balle kuma kafi damuwa dashi, inaji Mama tana mitar zuwan sa gidan nan befi uku ba amma kin manne masa ko damuwa beyi dake ba, kuɗin aure ya rasa nawa ze kawo se dubu hamsin" Anty Murja tace "ni ba wannan bama da ganin wannan koba a faɗa ba yafi ƙarfinki yayi miki girma maimakon ki samo dai dai ke, kin ɗakko wannan murɗaɗen kaman ɗan dambe" Sarai Mufeeda ta gane inda zancen su ya dosa amma ta basar ta zumɓura baki tace "ni wallahi bemin girma ba ai ba a bayana zan dinga goya shi ba, ina ruwana da girman sa" Fadeela tace "Ji shashasha bama tasan me'ake nufi ba se ƙoƙarin rashin kunya, zaki cu uban ki kije ki aure shi, zakiyi bayani yadda ya kamata ba dai aure ba? Idan baki goya shi a bayanki ba zaki gane in kin shiga" Haka suka dinga tsorata ta, Yaya Amina tace "haba Anty Murja dan Allah, wallahi abunda kuke be dace ba ya zaku dinga razana ta, so kuke tace ta fasa? Dan Allah ku dena" Mufeeda tace "ƙyale su Yaya Amina bazan fasa ba suyi tayi nidai ina son Yaya Ammar sosai" Ita Amina Tausayin Mufeeda takeji sosai, rayuwar da suka yi tare su Fadeela ba suyi ta tareda Mufeeda ba. Mama ta shigo ta same su, suka dinga caccake mufeeda wai tayi rashin kunya ga rashin aji yadda take rawar kai akan Ammar, gashi shiba Wani shahararren mutum ba amma se girman kai da isa a cikin sa. Ƙarshe mufeeda se bar musu ɗakin tayi, dan taji dana sanin zuwan yayyen ta gidan nan. Yaya Amina ta fita tsakar gida zata je kitchen ta zubo Abinci, ta jiyo sheshsheƙar Mufeeda a ɗaki. fasa zuwa zuba Abincin tayi ta shiga ɗakin ta samu Mufeeda ta haɗa kai da gwiwa tana kuka cikin tausaya wa Amina tace "Mufeeda meyasa kike kuka?" "Yaya Amina daga ke se Baba ne kawai kuke goyon bayana, Wallahi yaya Amina dana san dagaske Mama zata ƙi Ammar dana haƙura, wallahi ban san yadda akayi nake sonshi haka ba, baki ji yadda nake ji a zuciya ta ba ko sunan sa aka ambata, Amma Mama da su Anty Murja se hantara ta suke yi, idan har Mama bata son auren nan nasan idan nayi bazan zauna lafiya ba" Mufeeda ta riƙo hannun yayarta tace "kin san wani abu Yaya Amina" Amina ta girgiza kai cike da Tausayin Mufeeda "Yaya Amine karki gayawa kowa, nasani Nina ke son Ammar bashi yake sona ba, Amma kullum idan na roƙi Allah abunda yafi Alkhairi se inji ina ƙara ƙaunar sa, idan na roƙi Allah ya zaɓa min abunda yake alkhairi ba son zuciya ta ba se inga al'amura na gudana yadda yakamata, ban taɓa tunanin Ammar ze amince ya kawomin kuɗin auren sa ba a haɗuwa uku rak da muka yi ba, ina da damuwowi da yakamata in tattauna da Mama ko Anty Murja amma sunfi karkata ga kushe abunda da nake so, yaya Fadeela harda wai zan auri matsiyaci ɗan napep, naso in mayar mata amma kinga ta girmeni sosai kuma Mama zata min faɗa, Amma ita soyayyar gaskiya ai ba ruwan ta da wannan, dukda Aurena da Ammar be saɓawa addini ba, Yaya Amina dan Allah ki sani a cikin Addu'arki" Rungume Mufeeda Amina tayi tace "Autar Baba insha Allah zan ta yaki da addua, Sannan ni har ga Allah ina sonki da Ammar dan ni banga aibunshi ba, musamman yana da nutsuwa ba irin mashiritan matasan nan bane, me ake da namiji mara aji, Ai Ammar ɗin ki yana da class ne shiyasa yawan dariya ai bashi da amfani, karki damu da ana cewa baya fara'a yana da izza wallahi indai zaki masa biyayya kiyi Amfani da wata kissar kin gama da shi, ki dena kuka kinji" Murmushi Mufeeda tayi tace "shiyasa nake ƙaunar ki Yaya Amina" Bayan tafiyar su Yaya Fadeela Yaya Amina bata tafi ba saboda mijin ta bezo ɗaukar ta ba, Mufeeda kuma ta tafi Islamiyya. Amina tace "Mama be kamata ki dinga biye su Yaya murja ba akan auren Mufeeda, Mama wasu suna nan saboda se sunyi boko sun bawa shekara talatin baya babu aure, Kuma abunda auta tayi na faɗar aure take so ba tayi laifi ba, da kuma zuwa tayi ta ɗakko muku magana fa? Mama dukkanin mu 'ya' yankine da aurar da Mufeeda cutar da itane Baba baze yadda ba, ɗazu fa kuka ta tafi ɗaki tana yi, bata jin daɗin yadda kuke kushe Ammar dan Allah mama kidena biye wa su Fadeela " Ajiyar zuciya Mama tayi tace "ba ƙin abun nake ba Amina Ni gani nake kaman yaron nan zata sha wuyar zama dashi ya mata girma nesa ba kusa ba, zuwan sa fa uku kacal gidan nan sam bata gaban sa ko waya banga suna yi ba" "Mama kina tunanin akwai hijabi tsakanin mu da addu'ar kine? Tun muna yara kike mana addu'ar miji nagari, ki sawa ranki wannan shi ne mafi alkhairi a gurin auta, Mama ba kuyi tarbiyar mu akan kwaɗayi ba da son abun duniya, kuma a haka muka tashi, shiyasa kika ga Auta ma abun duniya be dame ta ba, duk abunda ta ɗaga tace tana so, to tana son sa dagaske, dan Allah mama kija Auta a jiki tun yanzu itama ki fara nuna mata zamantakewa kaman yadda muma kikayi mana, in ba haka ba ta fara iƙrarin zata fasa tunda bakya so, kuma idan ta fasa mekike tunanin za tayi gaba? " Ajiyar zuciya Mama tayi dan jikin ta yayi sanyi tace " hakane Amina, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Amma ni auta da wanne ma zan fara mata ne? Ni ƙanƙantar ta nake gani, ta ina zan fara nuna mata dabarun zaman auren?" Dariya Amina tayi tace " ta inda kika fara mana" ************** Abokan Ammar suka tambayeshi cikakken sunan Mufeeda saboda sticker daza'ayi musu amma yace be sani ba Aminu ya sha mamakin abunda Ammar ya faɗa, Jabir yace "Ammar wannan abubuwan fa da kake yawa ne, haba dan Allah ya za'ayi ace baka san cikakken sunan ta ba?" Ammar yace "to nasani ne? Nafa gaya muku da haɗuwar mu a titi da saka auren nan haɗuwa uku ce zuwa huɗu rak ta yaya zan san sunan ta, nidai naji ana ce mata kome? Muneefa ko Mufeeda i thinks Mufeeda ne" Aminu ya riƙe haɓa yace "tirƙashi yau nake ganin ikon Allah, Sunan nata ma baka sani ba, Allah kaɗai yasan dalilin daya haɗaku, Allah yasa itace maganin wannan haɗe ran naka" Jabir yace "Ammar ka kira ta ka tambaye ta dan Allah" Ammar ya kallesu "Allah ya kiyaye" "to bamu mu semu kira ta" Ammar ya miƙa musu wayar sa, Jabir ya ɗakko wayar sa ze ɗau lambar Mufeeda, Ammar yace "ka kira ta a waya ta" Haɗa ido Jabir suka yi da Aminu suka ƙyalƙyale da dariya Ammar ya ƙara haɗe rai dan baya son raini. Mufeeda kam tana kitchen tana wa Mama girkin dare wayarta ta fara ringing, tana ganin lambar Ammar jikin ta na rawa ta ɗaga wayar "Hello Yaya Ammar ɗina" Jabir yace "Ahh yi haƙuri Amaryar mu bashi bane, fatan kina lafiya?" Yamutsa fuska Mufeeda tayi, tace "ina Yaya Ammar ɗin?" "yi haƙuri shi yace a kiraki, cikakken sunan ki yace ki gaya mana akwai abunda za'ayi da shi" Tura baki tayi cikin shagwaba tace "shi meyasa baze tambayeni da kansa ba? Dan Allah yana ina?" Jabir yace "taɓ lallai abun naku nayi ne, kai ungo wayar ka" Ammar ya haɗe rai yace "idan bazata faɗa ba shikenan ba zan karɓa ba, bana son shashanci da yarinta" Mufeeda na iya jiyo abunda Ammar yace, ji tayi hawaye na ƙoƙarin zubo mata jiki a sanyaye tace "Shikenan nagode sosai, jin muryarsa da nayi ya tabattar min yana lafiya nagode Allah, my regards to him" ta kashe wayar ta. Tausayin ta ya kama su, Aminu yace "A gaskiya Ammar ka canza salon ka, masoyi ko mahaukaci ne be cancanci wulaƙanci ba, ji yadda yarinyar nan ke murna tana ɗoki a baka waya, Amma kalli abunda kayi mata haba Ammar" Jabir yace "Ammar irinka idan Soyayya ta tashi kama ka ko, se mutum ya tausaya muku, irin wannan halin 'yan matan mu na Hausawa suke tsoro shiyasa basa iya nuna soyayyar su ga maza, Ammar so baya duba girma da shekaru, da yana dubawa da yayi wa Mufeeda Adalci daba ta faɗa soyayya da mutum irin ka ba" Sosai suka dinga caccakewa Ammar shi kuwa yayi shiru ya ƙyalesu ko uffan be ce musu ba. ************* Daƙyar Mufeeda ta ƙarasa girkin nan ji take kaman an ɗora mata dutse a kirjin ta, bata taɓa zaton zata so wani ɗa namiji ya dinga yi mata wulaƙanci haka ba, yayin da wani sashi na zuciyar ta ke ƙara azalzalarta da ƙaunar Ammar. Mama ce ta kira Mufeeda ɗakin ta suka zauna, Mama tace "Mufeeda ya Saurayin naki?" Murmushi tayi ta sunkuyar da kai, Mama tace "yaushe kuma kika fara jin kunya ta, ɗago kanki magana za muyi, naga tunda aka kawo kuɗin nan bezo ba meyasa? Anya kuwa yana sonki"? Da sauri Mufeeda ta ɗago tace "yana sona mana" "to Amma ai ya kamata ai ya dinga zuwa tunda aure zakuyi, da haka zaku fuskanci juna tunda zama zakuje kuyi na dindindin" "Mama kin san yanayin sana'ar sa baya samun zama" Mama tace "dukda haka idan har kana son abu yana da kyau ka dinga zaga shi kana ganin sa, yana da kyau ya dinga zuwa yana ganin ki" Nan Mama ta dinga yiwa mufeeda nasiha game da rayuwar aure da kuma mahimmancin haƙuri, mufeeda a ranta tace "Mama na kenan duk wannan abubuwan na sansu tun abaya da kike gayawa su Yaya Fadeela na haddace su, amma ta yaya zan gaya miki halin da nake ciki nasan tabbas idan na gaya miki abunda ke faruwa zaki iya soke maganar auren nan ni kuma ina ƙaunar Ammar" A zahiri kuwa shiru tayi tana sauraron Mama, seda ta gama sannan ta sallami Mufeeda. Ammar daya koma gida yana ta tunanin maganganun su Jabir, idan ya tuna yadda tayi magana a sanyaye daga ƙarshe se yaji babu daɗi Tausayin ta ya kama shi, gefe kuma zuciyar sa tace "ai ba kai kace kana son ta ba, koma menene ita taga zata iya" Ya zauna yana hira da Umman sa a tsakar gida, Umman sa bata da zance se tsare2 da shirin yadda bikin tilon ɗanta namiji ze kasance. Umma tace "Ammar yaushe zaka gurin sirikata ne? Ɗazu naje kasuwa naga wata sarƙa me kyau na siyo da sauran kaya a saka mata a lefe" Ɗan taɓe baki yayi yace "kaman kin san tana yawan cewa a gaishe ki" "Allah sarki yarinyar kirki, Amma baka taɓa gayamin ba, nikam Ammar ka nunamin hoton ta mana" Be ce komai ba ya nunawa Umma hoton mufeeda akan dp ɗin ta, Umma ta karɓa tai shiru tana kallon ta a ranta tace "tabbas yarinya ce ƙarama, Amma ina fatan ta zama mace tagari sannan sanyin idaniya ga ɗana" A fili tace "tubarkallah Ammar sirikata ba dai kyau ba masha Allah, Ammar dan Allah ka riƙe yarinyar nan da Amana, jikina yana bani ita alkhairi ce a tare da kai, banda hantara da tsangwama dan Allah Ammar na san halin ka" Halima ce ta fito daga ɗaki tana faɗin "Umma in ganta" Ammar ya karɓe wayar sa ya shige ɗaki ba tare da Halima ta ganta ba. Koda Mufeeda ta koma ɗakin ta, kuka ta zauna tana yi, tana goge hawaye gaba ɗaya ranta babu daɗi, wayar ta ta janyo zata kira Yaya Ameena taga miss Calls ɗin Ammar, take wani farinciki ya mamaye ta amma se wata zuciyar tace mata "ƙila ma abokan sane suke kira bashi ba" tayi tsaki zata ajiye wayar saƙon Ammar ya shigo wayar ta "Meyasa bakya ɗaga waya?" Kallon message ɗin take yi ya kuma kiran ta, ɗagawa tayi tasa a kunnen ta tayi shiru, ya saba idan ya kirata da karsashin ta take ɗaga wayar sa, hakan yasa shi yin Sallama dan tabattar da ko ta ɗaga, a hankali ta amsa sallamar tasa "har yanzu baki da lafiyar ne?" "lafiya ta ƙalau" Ammar yace "Meyasa na kira baki ɗaga ba" Kawai ta fashe da kuka, tsaki Ammar yayi yace "meya haka? Meye na kuka kuma? Kinsan abunda ba naso kenan" "Yaya Ammar ji nake kaman inje in cewa Baba na fasa Auren nan" Maimakon yayi farinciki da abunda tace se yaji ƙirjinsa yayi mummunar bugawa da ƙarfin gaske Cikin kuka ta cigaba da magana "Yaya Ammar meyasa kake wahal dani haka? Yaya Ammar ba laifi na bane da nace ina sonka, Ana ta tambaya ta me muke shiryawa game da shirin biki bani da amsa ko ganin ka kaƙi kazo inyi" ta kasa ƙarasa maganar se fashewa da ta sake yi da kuka, shiru Ammar yayi yace "Zaki gayamin sunan ne ko zaki cigaba da kukan?" Cikin fushi tace "bazan faɗa ba ɗin kuka zan cigaba, kuma Insha Allah sena dena sonka tunda baka da tausayi" ta kashe wayar ta. Sam irin wannan matsalolin Ammar yake gudu shiyasa sam baya soyayya yake mata kallon shirita, musamman Soyayya da ƙanƙanuwar yarinya, banda wannan dalilin akwai abunda zesa yarinya ƙarama kamar Mufeeda tayi masa tsawa haka? Ƙwafa yayi ya ajiye wayar tare da jan ƙaramin tsaki Daga baya mufeeda taga rashin kyautawar abunda tayi ta zauna ta tsarawa Ammar message ɗin ban haƙuri ta tura masa. Yayi mamakin abunda tayi beyi zaton zata bashi haƙuri ba, maimakon yayi responding seya shareta daga nan bata ƙara neman sa ba shima kuma be ƙara neman ta ba. Baba ya biyawa Mufeeda kuɗin WAEC da NECO tana ta zuwa extra lesson, duk yadda suke da Fatee da irin surutun Mufeeda bata gaya mata Ammar ya kawo kuɗin Aure ba. Mazewa kawai take yi, bata jin daɗin yadda bata samun damar jin muryar Ammar, sam baya nuna damuwar sa game da ita, amma ta dake ta watsar da shi ta ci gaba da Addu'a, dukda ba ƙaramin azabtar da zuciyar ta take ba, Amma hakan baya hana ta ta tura masa saƙonin barka da safiya, barka da juma'a ko kuma saƙonin kwanciya bacci tare da yi masa addu'oin tsari. Ammar yana gani amma baya tankawa, amma duk lokacin da ya ga saƙonin yana jin daɗi, duk lokacin daya ga tayi jinkirin turo masa saƙo ya dinga duba wayar sa kenan, Amma fa baze iya ce mata ya gode ba, ko kuma yaji daɗin ganin saƙon ba. Mama tayi mitar tayi tambayar harta gaji akan dalilin da yasa Ammar baya zuwa, ta zuba mata ido tana taya 'yar tata da addua, dan sam ta kasa gane inda wannan al' amri ya dosa ga tana yin magana mahaifin Mufeeda zece tana sukar lamarin auren ne. Sam walwalar Mufeeda tayi baya, duk ta rame. Yauma tana kwance akan gadonta ta zubawa fankar dake saman ɗakin ta Ido Mama ta shigo ɗakin ta kalleta tace "to seki tashi yau yaga damar zuwa, yace ai masa sallama dake" Mufeeda najin haka ta miƙe zaune da sauri, Mama ta kalle ta ta girgiza kai, Mufeeda bata taɓa tunanin Ammar zezo ba, ba tayi zatonsa a wannan lokacin ba. Mufeeda ta shiga ta wanke fuskarta, ta zira doguwar rigar material baƙi da ja tayi rolling da mayafi baƙi ta fesa turare ta fita. Yau shida wani ta ganshi sunzo wanda bata san wanene ba, suna ƙofar gida a tsaye, a hankali ta ƙarasa inda suke ta kalli abokin nasa tace "ina wuni?" Jabir ya kalleta yace "lafiya ƙalau Amaryar mu, ya haƙuri da abokin mu?" Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba. Ammar ya lura tayi rama kome ke damunta oho? So yake su haɗa ido amma taƙi dan ƙwalla ce a idon ta, a hankali tace "mu shiga ciki" Jabir yace "ina nan a sha soyayya lafiya" Hararar Jabir Ammar yayi sannan yabi bayan Mufeeda cikin takunsa na ƙasaita. Cikin sitting room dake harabar gidan ta shiga yana biye da ita. Gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren sa, Guri Ammar ya samu ya zauna, Mufeeda ta samu guri itama ta zauna. Ba tare da ta kalle shi ba tace "ina wuni?" "lafiya, ya Mutan gidan?" Goge hawayen ta tayi tace "suna lafiya" Ɗan ƙura mata ido yayi sannan yace "ke wai ke kuka baya baki wahala ne? Me kuma nayi miki yanzu?" Tura baki tayi tace "ni meye ma ba kayi min ba, Yaya Ammar yaushe rabon da in ganka? In tura maka saƙo babu reply, baka kira na a waya, ji nake kaman in haƙura kowa cemin yake baka sona" Ƙura mata ido yayi yadda take magana tana tura baki, tana shagwaɓe fuska tana wani lanƙwasa wuya kaman karta dena. Ammar ya kalleta yace "Aini dama ban iya soyayya ba, ban san yadda ake yi ba, ke kikace kina sona, ni dama irin wannan shirmen ƙuruciyar ne bana so shiyasa nake son in auri babbar mace wadda ta gama hankali" Murmushi tayi dukda fuskarta da guntun hawaye tace "Hmmm ni bani da hankali kenan?" "ina me hankali ze zauna yaita kuka kaman ƙaramin yaro koda yake ai yarinyar ce, dan baki fi a sa zani goya ki ba" A ranta tace aikuwa zaka ga yarinta yadda ya kamata, Sosai tayi dariya tace "daza'a goya ni da naji daɗima, dana dena kukan" Ɗan murmushi yayi abunda bata taɓa gani yayi kenan ba, dama idan yayi murmushi yana matuƙar yin kyau haka? Leda ya miƙa mata bata karɓa ba tace "menene wannan?" "karɓi ki gani mana" Hannu tasa ta karɓa, shi kuma ya miƙe ze tafi ita ma ta miƙe da sauri "Haba Yaya Ammar mintunanka nawa zaka tafi? Ni dan Allah karka tafi yanzu" Ɗan tsuke fuska yayi yace "Zaki fara ko?" "Yaya Ammar yaushe zaka dawo?" "Se wani lokacin" "idan ka tafi seka daɗe baka zoba fa" "Me zanzo inyi miki? Kallon wannan shiriritar taki da yarintar ta kokuwa?" "Nice nake shiritar ko? Shikenan ka gaida Mama, Nagode sosai Allah ya ƙara Arziki" Be amsa ba ya juya ze fice tace "Yaya Ammar" Ya waigo, ta tako gaban sa, ta ɗan ɗauke idon ta daga kallon cikin idon sa tace "I Love you so much My Ammar" ji yayi zuciyar sa ta shiga bugawa da sauri da sauri. Ta raɓa ta gefen sa ta wuce Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 7 Gida Mufeeda ta shige dauke da ledar da Ammar ya bata ta nufi ɗakin Mama ta ajiye mata ledar Mama tace "wannan fa?" "shine ya bani" Mama tasa hannu ta buɗe ledar, keyholder ne da sticker na engagement se kuma cingam da tarkacen chocolates, Mufeeda ba ƙaramin jin daɗi kyautukan nan tayi ba, ta koma ɗakin ta ta dinga murna. Ammar kam Jabir ya sashi a gaba da tsokana "gaskiya Ammar yarinyar nan tana da kyau tubarkallah kayi dacen mata, fatana Allah yasa ka riƙe ta amana" Ammar yace "wannan ce matar? Anyi dacen haɗani da raino dai dan banda yarinta da shiririta babu abunda ta iya" "kai kake ganin haka, Amma ni banga ƙanƙantar nan ba da kake ta faɗa sedai tana da ƙarancin shekaru kam" "Hmm bazaka gane ba, ni nasan halin ta, amma ina wannan 'yar yarinyar ta isa aure, yarinya ƙarama da ita sedai ayi rainon ta" Jabir yayi dariya yace "idan aka gama rainon nata sekuma me?" "Sekuma ƙaniyar ka" Ammar ya bashi amsa, sosai Jabir yake dariya yana son ganin yadda wannan dramar zata kaya Mufeeda ta rubutawa Ammar saƙo "Babyn baby naga saƙonka nagode sosai Allah ya ƙara buɗi kaman kasan ina son chocolates sosai nagode agaida Mama" Washegari Mufeeda taje makaranta, ajinsu yayi tsit babu malami a ajin, ana rubuta sunan masu surutu kowa yaja bakin sa ya tsuke, banda Mufeeda da bakin ta yaƙi rufuwa saboda farincikin da take ciki, ta ɗakko leda ta ajiyewa Ƙawarta fatee akan cinyar ta. Fatee ta buɗe leda taga sticker da key holder da yawa a ciki, ta ɗakko keyholder ta karanta ganin sunan Ammar da Mufeeda a jiki yasa ta sakin wani ihu, gaba ɗaya attention ɗin 'yan aji ya dawo kansu, fatee tayi saurin toshe bakin ta, ta kalli Mufeeda cikin mamaki tace "Mufeeda ni har kin fara bani tsoro, dan Allah dagaske wannan me napep ɗin ne ya kawo miki kuɗin aure? Ke kuwa me kika yi masa haka, ya amince dake?" Mufeeda tace "Allah ne ya haɗa ba wayona ko dabara ta ba" Fatee tace "shekaru nawa aka sa?" Mufeeda ta Harare ta tace "six months yanzu saura wata huɗu da rabi ma" "Amma Mufeeda lokacin ai ko ss3 bamu shiga ba, kuma karatun naki fa? Wallahi kinyi ƙarama da Aure" "ke kika ga nayi ƙarama, karatu kuma na cigaba a gidan Yaya Ammar, wannan ki rabawa 'yan aji" Haka kuwa aka yi Fatee ta bi mutane ta raba musu, nan da nan aji ya ɗau sowa, da hayaniya Mufeeda zata yi aure, kowa da abunda yake faɗa ita kuwa ta maze ta haɗe fuska. *************** Gidan su Ammar suna ta shir sosai, dukda Ammar ba farinciki yake da auren ba amma yana ta ƙoƙari akan abunda ze haɗa na kayan lefe, dan baya son an kai kuɗin aure kaɗan kuma ace kayan lefe ma na kirki ya kasa samuwa, akwai wani gidan mahaifiyarsa na gado tace yaje ya gyara can ya zauna ko ya siyar a sai wani a wajen gari, haka kuwa aka yi aka saida gidan kuma yayi daraja sosai ya sai wani a wajen gari ɗan matsakaici me kyau, sauran kuɗin ya ci gaba da shirye2. Kasancewar Unguwar su Mufeeda ma cike take da masu ƙaramin ƙarfi nan da nan unguwar ta ɗauka akaita surutai wai wannan 'yar yarinyar mara kunya za' ayiwa Aure, kuma abun kunya duk bokon baban su ace ɗan a daidaita sahu zata aura, hada wanda suka tari mahaifinta wai mezesa ya aurar da ƙanƙanuwar yarinya kaman Mufeeda, shi kuma ya kan basu amsa da "wannan abune da ya shafi iyalina, kuma nan duniya duk wanda ze ƙauna cesu a bayana yake, dan haka banga laifin hakan ba" Hatta malaman su Mufeeda sunyi mamakin jin aurar da Mufeeda za'ayi kasancewar mahaifinta ɗan boko wanda yasan mahimmancin Ilimi, shima seda suka gayyace shi makarantar amma ya ƙara tabbatar musu da baze canza ra'ayin sa ba, ba wanda ya gayawa Mufeeda da kanta ta nuna aure take so. Haka mufeeda ta cigaba da fama da Ammar, mutum ne da baya son raini shi gani yake idan har ya sakewa Mufeeda raini ne ze shiga tsakanin su dan sam ba sa'ar auren sa bace, kaman yadda ya barwa zuciyar sa wannan ba aure zeyi ba kawai dai an hada shi da aiki ne. Ita kuma Mufeeda ta sawa ranta cewar idan harta shiga gidan Ammar zata tabbatar masa da wata kissar se mata, seta sauke masa wannan zafin kan nasa, zata nuna masa itafa mace mace ce, komai ƙanƙantar ta kuwa. Idan ta kwana biyu bata ji muryar sa ba, duk seta damu seta kira shi kota tura masa saƙo, dan harta gaji da magiyar yazo inda take, shima ɓangaren sa idan aka kwana biyu beji ɗuriyar ta ba se yaji babu daɗi amma baze iya kiran ta ba gani yake idan yayi hakan tamkar ya faɗo ne. Mufeeda ta fara zana jarrabawar ta ta WAEC, ta dawo gida ta gaji ta tarar da 'yan uwan baban su na ƙauye sunzo. Mahaifin Mufeeda ɗan garin garko ne dake jihar kano, yayi karatun sa na boko dana arabiya, Matar sa cousin sister ɗinsa ce duk' yan uwane bayan ya kammala degree ɗin sa na farko ya samu aiki ya dawo cikin gari zama, yana da yara bakwai huɗu mata uku maza Mufeeda itace ƙarama. Mufeeda na zuwa ta tarar dasu, suka dinga mata guɗa suna ga amaryar su. Mufeeda ta shiga suka gaisa ta wuce ɗakin ta tai wanka ta zubo Abinci Mama tace "ya jarrabawar?" "Alhamdilillah Mama Jarrabawa tazo da sauƙi na amsa mafi yawa daga tambayoyin" "Allah ya bada sa'a" "Ameen Mama" Mama ta fita 'yan uwan Baba suna ta tsokanar Mufeeda, wata ƙanwar baban ta tace "ya kamata kizo in fara koya miki yadda rayuwar aure take tunda ke an saka naki auren a ƙurarren lokaci, kuma ke kaman har yanzu baki gama wayo ba balle kisan dabarun zama da miji" Mufeeda ta ɗago ta kalleta tace "ki koyamin mene gwaggo? Taɓɗijan ai na haddace irin wannan faɗan naku da akaita nanatawa Yaya Amina yi nayi bari na bari, wannan karatun naku na mutan da ai munce wannan ƙarnin" "Au haka ma zakice?" "Eh mana ko akwai wani bayan wannan?" Gwaggo safiya tace "hmm ai wannan yarinyar in baki rage wannan kaifin bakin naki ba da tsiwa wahala zaki sha a gidan aure lokacin mu, ai ƙasa ƙasa akewa miji magana, har tsuma kake karka yi wani kuskure daze ɓata masa rai" Mufeeda ta ƙyalƙyale da dariya tace "Hajiya gwaggo ashe kuma kun iya iyayi, aini gani nake zamanin ku tsoron mazanku kuke ji, ni mijina baze zama abun tsoro a gurina ba, zan masa biyayya amma ba dai inji tsoron sa ba, saboda shine Abokin wasa na, Abokin shawara ta kuma Abokin kuka na" Gwaggo sahura tace "ai kinji irin ta shiyasa auren yanzu baya zuwa ko ina" Mufeeda tace "haba gwaggo sahura akan me zan auri miji bazan dinga wasa da shi ba se dai in dinga jin tsoron sa? Ba dani ba" Gwaggo safiya tace "ba cewa akai kiji tsoron sa ba, ki girmama shi, zamanin mu kinga kwanon abincin miji kawai da butar sa girmama su muke bama son wani abu ma ya taɓa su balle mijin" Gwaggo sahura tace "ai Safiya mu miji na bisa mu muna ƙasa a zaune, idan magana yake duk nutsuwar mu muke tattarawa muna sauraren sa, miji na kujera mu muna ƙasa a zaune" Mufeeda ta kwashe da dariya tace "Wallahi baze zauna akan kujera in zauna a ƙasa ba se kace zaman fada, ai yana kan kujera ni kuma ina kan cinyarsa" tai maganar tana watsa shinkafar ta a baki, ai gaba ɗaya suka ɗau salati, ta ɗago tana kallon su tace "wai Salatin me kuke haka?" Gwaggo safiya tace "A'a bakomai ke wannan sha'anin naki babba ne" Mufeeda tai murmushi a ranta tace "ai maganin ku zan dinga yi ba zaku takuramin da wannan faɗan ba, ni se an koyamin wani zama da miji na haddace wanda aka koyawa su Yaya, yaushe zakumin huɗubar mutan da, shikenan bazan yi walwala da miji ba" **************** Mufeeda tana ta Jarrabawa, Ammar har yayi ɗan wuya dan shirin aure ba na rago bane, dukda 'yan uwa da abokan arziki na tallafa masa amma shirin aure a gurin me ƙaramin ƙarfi abun akwai tausayi. Ɓangaren su Mufeeda suna ta shiri suma, Yayyen ta har sun gaji da tsangwamar ta akan batun aure duk shawarar da zata yi akan shirin bikin ta da Baba take yi ko Yaya Amina. Mama kam ta kasa sakin jiki tayi wa Mufeeda bayani sosai akan Aure da ƙalubalen dake cikin sa, kaman yadda take wa 'yan uwan ta a baya tana ganin ƙanƙantar Mufeeda sosai sedai lokaci2 tana gaya mata abunda ba'a rasa ba. Se Mufeeda tayi sa' ar gaske ta haɗa da mita sannan Ammar zezo, idan yazo baya fin mintuna biyar ze tafi. Babban abunda yake bashi mamaki yake kuma burge Ammar da Mufeeda bata taɓa ce masa ya sai mata abun naira biyar ba, ba ruwan ta da wannan bata roƙar sa komai, yana jin yadda Jabir ke complain akan yawan roƙon sa da wadda ze aura take yi amma sam Mufeeda bata wannan, yakanga Haliman gidan su da abubuwa tace saurayine ya bata amma shi ba wani abu da yake bawa Mufeeda amma sam bata taɓa masa magana akan hakan ba, sannan ko gurin ta yaje ta dinga murna kenan tana godiya, sannan wataran da yaje haka za ta haɗoshi da kayan ciye2. Mufeeda Ta kammala Waec tana jiran lokacin fara Neco ta tura masa saƙon ta kammala jarrabawar Waec, yaga saƙon amma bece mata komai ba dan haka ta kira shi a waya "Yaya Ammar shine nace maka na gama Jarrabawa ko kayi min Addu'a ko?" "Na miki addu'a ai ɗazu da nayi salla" "dagaske nagode sosai, ya kake yasu Mama?" "lafiya ƙalau, zan ci gaba da tuƙi yanzu se anjima" ya kashe wayar sa, ɗan ƙaramin tsaki tayi ta ajiye wayar. Daddare ta kasa bacci ta ɗau wayar ta seta ga Ammar ya turo mata da katin naira dubu biyu seda ta zare ido, har zata tura masa message ɗin godiya amma ta basar dole ta nunawa Ammar itama mace ce me cikakken aji. ta buɗe data hira take da ƙawayen ta suna ta tsara yadda bikin Mufeeda ze kasance hirar tayi mata daɗi Sosai dan haka har bayan sha ɗaya tana chatting. Ammar yayi mamakin ganin ta online kuma bata tura masa saƙo ba, dan haka ya tura mata "what are you doing online by this time?" "chatting nake" ta bashi amsa "keda wa?" "Me sona wanda ya damu dani yake bani kulawa" Dummm zuciyar Ammar tayi be ƙara tura mata komai ba, ya kashe wayar gaba ɗaya, Abun mamaki bacci ya gagari Ammar yaji zuciyar sa tayi masa babu daɗi sam beji daɗin baccin yau ba. Washegari da ya fita ma daya tuna abunda Mufeeda tace masa se yaji ransa ya ɓaci "da kuɗin auren nawa akan ta take gayamin haka?" Ammar ya yanke shawarar zeje gidan su yau. Mufeeda bata san da zuwan Ammar ba da yamma ta shirya taje ta kai ɗinkita gurin ƙanin mijin yayar ta Naziru da yake a anguwar su Yaya murja gidan nasa yake Naziru yace "Mufeeda se naji wai aure zaki yi wallahi ba amana, duk yadda na dinga nuna ina riƙo ina jira ki kammala secondary in bayyana manufa ta amma kawai inji wannan mummunan labarin" Mufeeda tace "a gurin ka yake mummunan labari amma a gurina me daɗi ne, kuma ranar da nazo na karɓi ɗinkina da bikin yaya Amina a ɗan gaban shagon ka muka haɗu da shi" Naziru yace "wallahi Mufeeda banji daɗi ba, nima ina so fa" Mufeeda tace "sekuma kayi kana son nawa ne idan aka kawo ɗinkin gidan mu ka ɗinka na kowa kaƙi ɗinkamin nawa" Kwastomomin dake shagon da abokan aikin sa suka saka dariya sun san dayake sun san Mufeeda sosai Naziru yace "Ai duk cikin son naki ne, ina son inga kina wannan tsiwar ne shiyasa se in ajiye ɗinkin naki in ƙiyi miki" "wallahi zaka sa in raina ka, ka kiyayeni" "Raini na nawa kuma? Ai kin daɗe da rainani, tijarar da kikayi min da bikin Amina ma ai ta isa in san kin rainani, amma ai inada kyau ko? Har Anty Murja fa na gayawa ina kamu" "Kai Naziru dan na dena ce maka Yayan, wallahi mijina yafi ka komai kyakkyawan gaske ne in gaya maka, kuma ka nemi wata ko ka jira idan na haihu in baka 'yata" Dariya Naziru ya dinga yi "lallai kin gama raina ni Autar amma nikam ba gudu ba ja da baya" Ganin abun Naziru bane ƙarewa bane ya sata fice tayi tafiyar ta, gidan yaya murja ta tsaya seda aka yi sallar magariba Mijin Yayar ta ya dawo shima tsokanar ta yake "Allah sarki autar mu ta kusa zama amarya, amma mijinki zeyi fama da wannan bakin naki" Anty murja tace "Kuma wallahi idan ka ganshi ko fara'ar kirki ba yayi, yazo ɗaurin auren Amina dan dai ba lallai ka gane shi bane, Amma wannan banga alamar yana son hayaniya ba, naga yadda za'ayi wannan zaman, gashi da wani jin kai" "Ni ban san me Ammar ɗina ya tsare miki ba wallahi duk kinsa mana ido, haka nake son abuna" Mijin Anty murja yace "ƙyale Antyn nan taki ki cigaba da son abunki, Allah ya baku zaman lafiya, aishi namiji indai yana son mace duk wata izza baze mata ba" Haka ya ci gaba da zigata, se wajen sallar isha'i sannan Mijin Anty Murja ya maida Mufeeda gida a motar sa da rakiyar ɗansa. Ammar tun sallar magariba yake unguwar su Mufeeda akace bata nan taje gidan Yayar ta, daya ke ba da napep ɗinsa yazo ba ya samu guri yana jiran ta, amma ga mamakin sa ya hango Mufeeda ta fito daga motar wani, seda ta ɗan tsaya suka yi sallama da me motar ta ɗaga masa hannu sannan ta shige gida. Ammar ji yayi duniyar tayi masa zafi yaji zuciyar sa tamkar ta fasa ƙirjin sa wani abu ya tokare masa rai. Har ya yanke shwarar yayi tafiyar sa amma ya fasa ya kira ta a waya, seda yayi mata missed calls uku wayar tana cikin jakar ta a ɗakin ta bata sani ba, kaman wadda aka mintsila ta ɗakko jakar ta taga wayar ta na ringing ta ɗaga da sauri tace "Am Sorry My Ammar wayar tana cikin jakata ne" "Ina kofar gidan ku" shine abunda ya furta da ƙyar. Da murna ta ajiye wayar ta kalli kanta a mudubi, tsaf da ita kwalliyar fuskarta tana nan, janbaki ta ƙara ta sake gyara ɗaurin kanta ta fesa turare ta leƙa ɗakin Mama tace "Mama Yaya Ammar ne yazo bari inje" Mama tace "au be tafi ba dama, tun magariba yazo ai na ɗauka ya tafi" Mufeeda tace "Allah sarki Yaya Ammar ɗina, Allah yasa saurk be cije shi ba" Ƙwas ƙwas da takalmin ta me tsini tai waje da sauri. Tana zuwa ta leƙa bata ganshi ba, ta kira shi a waya, se gashi ya ɓullo ta lungun dake kallon gidan su Mufeeda ta juya ta koma sitting room inda idan yazo take saukar sa. Yana shigowa ta fara magana cikin shagwaɓa Yaya Ammar ashe tun ɗazu kazo baka kirani a waya ba, yau Allah yayi zan ganka ba tare da nayi magiya ba, kallon sa tayi taga fuskarsa a ɗaure babu annuri hakan yasa tasha jinin jikin ta. Ammar yayi niyyar ya nuna mata ainihin waye Ammar amma maimakon haka seya kasa yi mata faɗa yadda ya ƙudurta a ransa, gani yayi ma yau tayi wani irin kyau sosai ko dan yau ba kukan take ba, amma daya tuna a motar wani yaga an sauke ta se ya ɗaure fuska sosai cikin kakkausar murya yace "Daga ina kike?" "ɗinki na kai" ta bashi amsa cike da fargaba "ɗinkin ne se yanzu zaki dawo? Daga motar wa kika fito?" Ya faɗa yana ɗan ɗaga murya, gaba ɗaya mamaki ya lulluɓe Mufeeda tace "Wace motar kuma?" "Tambaya ta ma kike yi? Waye ya sauke ki a mota? Sannan ina kika je? Bari kiji in gaya miki bazan ɗauki rainin hankali ba, tun wuri idan kin san abun da zaki dinga yi kenan ki koma ki janye batun auren mu, bana son rawar kai, saboda kin rainamin hankali jiya har sha biyun dare kina chatting na tambaye ki kince wai dame sonki kike chatting, yau kuma dan ki tabbatar min shine aka sauke ki a mota ko? Tun farko inkin san me motar kike so meye na cewa kina sona har in kawo kuɗin aure, me yasa baki tsaya a me motar ba kika ce kina son talaka kamata, idan har kinsan kina da hange karki soma yadda da aure na" ya tako har gaban ta ya kusa haɗe ta da bango yace ki gayamin waye ya sauke ki a mota" Gaba ɗaya jikin ta ya mutu, wani irin ƙamshin turare yake me daɗin gaske, yayin da shima dakewa yayi dan ƙasan zuciyar sa na yaba kyawun da tayi. Idonsa ta tsaya tana kallo taji zafin maganganun sa, amma tana iya ganin tsagwaron kishin ta a cikin idon sa, a ranta tace Ammar kenan a fili kuwa tuni hawaye ya wanke mata fuska. "ina tambayarki kina min kuka, kin san abunda bana so kenan, ki gayamin abunda na tambaye ki" "tabbas da ina da hange kuma so zemin adalci dabe yi gigin kaini ga afkawa son wanda bana gaban sa ba, idan har ina hangen me kuɗi ne to bazan kalle ka ba, amma zuciya ta ta makance kai kaɗai nake gani, ni kaina ina ganin kaman na fiye zaƙewa, jiya da nake chatting daka tsaya munyi waya zanji daɗi a raina ɓacin ran abunda kamin da tunanin wane irin mutum Allah ya haɗa ni dashi zamuyi zaman aure ya hanani bacci na ɓige da chatting muna shirye2 biki da ƙawaye na, yanzu kuma ɗinki na kai unguwar su Anty murja ina tsoron hanya shiyasa mijin ta ya dawo dani gida, mahaifina mutum ne me matuƙar tsauri akan tarbiyya baze taɓa bari na inje unguwa inyi dare a kawoni a mota ba, kuma mijin yaya Aminar ma akwai ɗanta da yayi mana rakiya, Amma Allah ya baka haƙuri Allah ya huci zuciyar ka insha Allah zan kiyaye faruwar hakan a gaba" Ta juya zata tafi ya kira sunan ta "Mufeeda" banza tayi masa ta ƙara sauri hawaye na bin idon ta tana jinsa taƙi ko waiwayowa tayi gaba abunta. Gaba ɗaya se jikin Ammar yayi sanyi tare da tunanin meyasa yayi mata faɗa haka gashi ya sata kuka (🙄🙄🙄) Kuma inba comment zan ajiye typing ɗin littafin nan Domin sharhi, gyara ko shawara Ayshercool 07063065680 [23/06, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 8 Ammar bashi da zaɓin daya wuce ya tafi, a zuciyar sa yana jin kaman be kyauta ba abunda yayiwa Mufeeda. Ita kam data koma gida seda ta sha kuka tayi ya ishe ta sannan ta hau Addu'a "ya Allah kai ka jarabceni da son wannan bawan naka Allah ka kawomin mafita" Seda ta idar da addu'ar ta ɗakko wayar ta, ta buɗe hoton Ammar ta ƙura masa ido sannan tace "Yaya Ammar kenan faɗan kawai ka iya amma sam bazaka yi wahalar sarrafawa ba, kace baka iya soyayya ba amma ina ganin kishina ƙarara a idonka, ba a kishi idan babu soyayya, se ƙwaila ta baka mamaki" Ammar yaji ya fara damuwa da abunda ya aikata tsaki yayi yace "toni ina ruwana ma meye zan damu kaina akan wannan ƙaramar yarinyar" Shirye2 se nisa suke lokaci na ƙaratowa, ba tare da Ammar da Mufeeda sun samu wata kyakywar fahimtar juna ba. Mufeeda ta shareshi ta dena kulashi, tana kallon sa online amma ba zata kula shi ba saƙonnin ma ta dena tura masa. Dukda can ƙasar zuciyar sa seya dinga jin zafin shareshin nan da tayi amma shima ya ƙyaleta. Mufeeda ta maida hankali akan Neco exams ɗin ta, duk ta ƙara ramewa ga pressure ɗin exams ga na shirye2 biki dukda tana ta shan gyara ta ƙara kyau hakan be hana ramar da tayi fitowa ba. Tana kwance tana chatting tana kallon Ammar online taƙi kulashi ya turo mata saƙo "ki gayawa su Baba ranar Asabar insha Allah za'a kawo kayan lefe" Zumbur ta miƙe zaune tana ƙara juya saƙon, maimakon taje ta gayawa Mama seda ta kira Yaya Amina ta fara gaya mata suka yi ta murna tare sannan taje ta sanar da Mama, Mama tace "to Allah ya kaimu" Sam bata nuna ma taga saƙon ba balle tayi wa Ammar replying. Mama tayi shirye2 tarbar masu kawo lefen aka yi sa'a mazane suka kawo, Akwatuna uku da kida ƙaramin buhun shinkafa da bagcco na takalma, aka basu tukuici suka ce ba zasu karɓa ba. Mama tayi mamakin kayan da'aka zubowa Auta, dukda ko kaɗan basu kama ƙafar wanda aka kawowa 'yan uwan ta ba, amma ba laifi yayi ƙoƙari a matsayin sa name ƙaramin ƙarfi yayi ƙoƙari dan kayan ta ba masu arha bane. Ammar shikaɗaine namiji gidan su, yayyen sa uku mata se biyu ƙannensa, suna ta tsokanar sa "Bana Allah yayi, Allah ze yaye masa gwauran taka, Allah yayi an samu wadda tayi nasarar shiga ran 'yan mazan umma" jinsu kawi yake yi, dan shi be ɗau wannan auren nasa wanu auren kirki ba kawai dai sunan zeyi aure ne. Labari ya ishe budurwar sa a da wato zainab wai Ammar zeyi Aure, ta shiga tashin hankali da damuwa dan ba ƙaramin so take masa ba dukda tana masifar tsoron sa saboda zafin kansa da izzarsa, amma tana matuƙar son Ammar, kasa jurewa tayi ta ɗau waya ta kira shi. Akayi sa'a yana gida dan ya gama cin Abincin rana kenan ta kira shi bayan sun gama gaisawa tace "Ammar dagaske aure zakayi?" Ammar sam be san wani abu rarrashin mace ba se kace ba cikin mata ya taso ba dan haka yace mata "Eh aure zanyi, nima auren ne yazomin ba shiri Allah ya kawo auren" "Amma Ammar duk son da nake maka, na sakankance sekamin haka" "ke nima fa auren nan ba wai da son raina zanyi shi ba, kawai dai Allah ya nufi zanyi ne, ba yadda zanyi" "Ammar bakamin adalci ba, ina nan na sakankance kawai se inji labarin zakayi aure, kuma ma wai ƙara mar yarinya, bayan ka gama cemin kai ba zaka auri yadinya ƙarama ba ashe dama duk yaudara ta kake yi?" Ajiye wayar Ammar yayi dan bashi da lokacin cigaba da sauraren ta tana ɓata masa rai, ya gaya mata gaskiya amma tana ƙoƙarin kaishi bango. Zainab ta taɓa aure shekarar ta biyu suka rabu da mijin, maƙwabciyar yayarsa ce Jidda, acan suka fara haɗuwa ta nuna tana sonsa, Jidda ta ƙara haɗasu ta ƙarfafa abun, shi dai Ammar kawai yayi niyyar auren Zainab ne saboda tana da shekaru a ganin sa itace tasan meye zaman aure, yanzu ma da aka kai kayan lefen nan Yayar sa Jidda se kushe abun take yi saboda yaƙi auren Zainab, dan ita zainab take so ya aura, koda taga kayan da Ammar ya haɗa ma se kushewa take tana "akace ƙwaila ce kuma a haɗa duk wannan kayan akai mata, naji cewa kayi kai ba son ta kake ba" Ammar kam da baya son raini ya haɗe rai yace "dan bana sonta bazan wulaƙanta musu yarinya ba, 'yar manyan mutane ce meye riba ta idan ankai musu kaya a tsiyace mutunci na ne ze zube, ba ruwanki da abunda zan kai" Ummansa ce tai tayiwa Jidda faɗa akan sam abunda tayi be dace ba a matsayin ta na babba. Mufeeda tayi murna mara misaltuwa ganin duk kayan nan nata ne, sam ba tayi tunanin wai yayyen ta an kawo musu da yawa ba, ita nan duniya gani take tamkar Ammar yafi kowane namiji bajinta. Yayin da unguwar su ta ƙara ɗaukar gulma wai dan tsiya akwati uku aka kawo mata, dama ya za'ayi zaton wani kayan arziki a gurin ɗan keke Napep. Mufeeda tuni ta manta da batun suyi faɗa da Ammar ta kira shi a waya, yana gaban umman sa a zaune da yaya Jidda da sauran 'yan uwa, yana ɗagawa ko gaishe shi ba tayi ba cikin murna ta fara magana "Yaya Ammar ɗina naga kayan da aka kawomin nagode Sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah ya ƙara maka buɗi ni ban san ma wane irin godiya zan yi maka ba nagode sosai" Kana jin muryarta kasan yarinya ce sosai, Ammar yace "Ameen ki gaida mutan gidan" ya katse kiran, umma tace "Haba Ammar be kamata kayi haka ba, kayan da aka kai ba wani na kirki bane amma se murna take tana godiya gaskiya yarinyar nan tana da hankali" Halima tace "nikam Yaya Ammar ta burgeni wallahi se murna take yi" Jidda kam taɓe baki tayi tace "wai Umma me kike so yace mata ma, dole tayi murna tunda ba sonta ake ba ta cusa kai" Sam Ammar baya son irin wannan shirmen na mata dan haka ya tashi ya fice. Mufeeda ta kammala jarrabawar ta lokacin saura sati uku biki, shirye2 sunyi nisa sosai kai ya fara ɗaukar caji, ƙannen Mama ne suka je suka gano gidan domin su san yanayin kayan da za a sai mata, gida ne ƙarami amma harda gate da matsakaicin tsakar gida, akwai wadataccen falo da ɗakuna guda biyu a ciki kowanne da banɗaki, se kitchen a falo, da ɗaki ɗaya a tsakar gida da toilet, ta gefe jikin bango kuma an shuka flowers, daidai gwargwado gidan yayi kyau ana ta jinjinawa ƙoƙarin Ammar. Baba ya saiwa Mufeeda duk abunda ya kamata, yana matukar jin damuwar aurar da ita daze yi da ƙarancin shekaru amma yana mata addu'a Allah yasa haka shine mafi alkhairi. Mufeeda kam se shan gyara take tayi fes da ita kaman ba ita ba, tana zaune a gida tana cikin ɗakin ta tana chatting ta jiyo ana gayawa Mama tsegumin ana tayi dasu a anguwa, ana kushe mijin Mufeeda ana zata auri talaka kuma har wadda take surutun abun a unguwa aka gayawa Mama, kuma abun takaicin makwabciyar su ce take yaya ta abun tana kushewa bayan ita 'yan mata huɗu ne a gaban ta babu wadda ta aurar. Mama taji haushin abunda aka gaya mata ana faɗa akan auren autar tata, ai kafin mama tayi magana tuni mufeeda ta fito daga ɗaki fuskarta murtuk cikin ɓacin rai tace "ita wadda take kushe min miji' ya'ya nawa ne a gaban ta? Nayi imani da Allah da yaran ta suka sami wanda be kai nawa ba so zata yi, yara daga me bleaching seme soya awara saboda rashin miji, kuma wallahi se naje har gidan ta na mata rashin mutunci tun...... "Ke rufemin baki" mama ta daka mata tsawa "ki ƙyalesu suyita surutun mana ze fito a jikin kine? Kowa yayi nagari kansa meye na tada jiniyoyin wuya? Ke ko gajiya ba kyayi da faɗa" "Amma Mama ina ruwan ta dani? Ni zan auri me a daidaita sahu nata mijin fa faskare yake yi da 'yan kame2, ni wallahi idan banje na zazzage mata ba zuciya ta ba zata yi sanyi ba" Mama tace "to sekin dawo ina magana ki nayi, matar data haifeki ki ƙyalesu suyi tayi karki ɓata farincikin da kike ciki mana, wuce ki koma ɗaki" Mufeeda ji tayi kaman zuciyar ta ta fashe, taso mama ta ƙyaleta taje taiwa matar nan rashin mutunci daga ita har 'ya' yan ta, dukda rashin kunyar mufeeda akan sa'anin ta ya ƙare amma yau kam taso mama ta ƙyaleta tayi wa matar nan saukale. Ta koma ɗaki tana ta ɓacin rai, tana ƙoƙarin gano meye aibun sana'ar Ammar da ake kushe mata shi, kuma ai ba dole ne dan yayyen ta na auren masu kuɗi ace itama seta auri me kuɗi ba. Tana ta wannan tunanin Kiran Ammar ya shigo wayar ta, ɗaga wayar tayi tareda yin shiru, Ammar yace "ina waje" da yake indai yazo haka yake ce mata Dukda ranta a ɓace yake taji daɗin zuwan nasa dan akwai abubuwan da take so su tattauna. Ɗakin mama taje ta sanar mata zata fita Ammar yazo sannan ta wuce, tai masa iso ya shigo inda suka saba zama, duk lokacin daya zo fuskarta ɗauke da fara'a da shauƙin ganin sa yake ganin ta amma yau sam fuskarta a haɗe, tunanin sa ko tun akan saɓanin da suka samu ne ranar daya ganta a mota, da yake tun lokacin be ƙara zuwa ba se yau. A hankali cikin turo baki ta furta "ina wuni" Seda ya ɗan tsura mata ido a ransa yace "ikon Allah a da ko a mafarki akace zan auri 'yar mitsitsiyar yarinya kaman wannan cewa zanyi ƙaryane, amma abun mamaki waini ammar ni zan auri wannan' yar ficikar" yai ajiyar zuciya sannan yace "baki da lafiya ne?" Girgiza masa kai tayi alamar A'a, "to me akayi miki?" Kaman ya taɓo abunda yake damunta tace "ɓatamin rai akayi, 'yan unguwar nan ne suke cewa wai zan auri me a daidaita sahu, na cewa mama ta bari inje in rama ta hanani" ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata. Tabbas akwai ƙuruciya a cikin maganar ta, haka nan seyaji ta bashi tausayi yace "kinga matsalar ki ko? Daga tambaya se kuka meye hakane? Kinga da tun farko baki ce ni zaki aura ba babu memiki gorin zaki auri me a daidaita sahu, amma gayamin me yasa kike sona?" Ɗan ɗagowa tayi ta kalle shi tace "nima ban sani ba" "Akwai dalili ki gayamin" "nifa ban sani ba" "shikenan tunda haka kika ce, kin fi son a cigaba da yi miki gori kin auri talaka, kalli gidanku fa kalli motar Baba kalli suturar da kike sakawa, amma kince ke se talaka kaman Ammar kike so dole aita ɓata miki rai, baki dace da Auren talaka kaman Ammar ba, karatu ne ya dace dake idan kin gama ki samu wani haɗaɗɗen mutum me kuɗi ki aura, amma kinga Ammar talaka ne sosai kalli suturar da yake sawa, bashi da komai kinyi garajen zaɓarsa a matsayin miji" Zuba masa ido tayi kawai ta fashe da kuka cikin kuka tace "Niba kwaɗayayyiya bace, ni ba kuɗi nake so ba Yaya Ammar nake so, ban san Ya akayi na fara soyayya ba, ban san ya akayi nake sonka ba bayan ko damuwa bakayi dani ba, ni kuɗi basa gaba na" Sosai take kuka hada sheshsheƙa, Ammar yayi ƙasa da murya yace "at your age is too early ace kin fara soyayya zuciya ce kawai take ruɗarki, ni anya ba jumping aka yi miki a baya ba, dan kamata yayi ace kina Jss2 ko 3 yanzu" A ranta tace " ka manta kamata yayi ace ina ciki ba a haifeni ba ƙarewar Jss3 " A fili kuma tace " ni ba'aimin jumping ba shekara ta ɗaya aka sani a makaranta saboda mama tace ina surutu sosai " Ammar seda ya ɗanyi murmushi dan komai na yara take yi yace "No wonder you are still baby, bakifi a saka zani a goyaki ba amma kince ke aure zakiyi meyasa kika zaɓi yin aure yanzu akan karatu? Aure akwai challenges masu yawan gaske da ba lallai ki iya ɗauka ba a shekarun ki " Ta zumɓura baki fuska duk hawaye tace "tunda ni Baby ce seka dinga goyani ai" "Waye ze goya kin?" "Yaya Ammar ɗina" girgiza kai kawai yayi yace "baki gayamin meyasa kika zaɓi Aure akan karatu ba?" "Nifa da nafi son in fara karatu, kawai na haɗu da kai naji tsoron kar wata ta rigani auren ka shikenan fa" tai maganar tana son ganin reaction ɗin sa Ikon Allah ita abunda ke ranta kenan Ammar yace "Amma bani da kuɗi fa kuma gani mummuna nayi miki girma" "Nifa ko gurgu ne kai a haka nake sonka, ni duk mazan duniya da nagani babu me kyan Baba na da kuma Yaya Ammar ɗina, kuma ai Arziki na Allah ne, dama dai ni nasan ba sona kake ba" Murmushi yayi tare da girgiza kai yace "kinga goge ragowar hawayen nan kar wani yazo wucewa yace wani abun nayi miki" Tasa hannu ta goge hawayen fuskarta, Ammar yace "me kike shiryawa na bikin naki?" "Bikinmu dai" ta mayar masa "Waike ba kya jin kunya ne?" Kallon sa tayi ta ɗan lumshe ido tace "wai kunyar wa zanji? Aiba ƙarya nayi ba bikinmu ne nida Yaya Ammar" Tunda take Ammar be taɓa zuwa gurin ta ya daɗe haka ba sunyi hira me tsawo, amma yau Ammar hada murmushi dan haka ta saki jiki take ta masa yarin ta, dan ta ƙudurce wa zuciyar ta da ƙuruciyar tata zata yi amfani ta mallake shi. Ammar yasa hannu a Aljihunsa ya ɗakko kuɗi ya ajiye mata yace "ga wannan nasan ana party kokuma kamu na Amarya, sekuma yayi shiru daga baya yace" ke sam be kamata a kiraki wata amarya bama" Ta kalleshi tace "to me za'a kirani? Ƙwaila ko?" Kallon ta yayi bece komai ba ya cigaba da magana "gashi nan ki ɗauka ki ƙara kiyi wani abun" Ya kuma sa hannun sa a Aljihu ya ɗakko wasu kuɗin yace "wannan Halima tace min ana bada kuɗin ƙunshi da sauransu dai ban san kan abunba gashi nan kiyi abunda ya kamata kuɗin ba yawa kin san ni talaka ne" Ƙura masa ido ta ɗanyi sannan tace "banda abunka Yaya Ammar kai da kake fama da hidima meye na bani wannan kuɗin haka? Ni angama shirya komai a gida ba abunda muke buƙata ka barsu kawai kayi wani abun dasu" Haɗe rai yayi sosai sannan yace "kin raina ko?" Da sauri ta girgiza kai tace "A'a ni ban raina ba" "idan na kuma baki abu kikace Bazaki karɓa ba sena ɓata miki rai ai ba roƙa ta kikayi ba" Mufeeda tace "to Allah ya bada haƙuri nagode Allah ya ƙara buɗi" Ammar ya miƙe yace "zan tafi" "Se yaushe?" ta tambaye shi "se ranar ɗaurin aure" shi da yayi maganar ma kunya ce ta kama shi, waida wannan 'yar mitsitsiyar abar za' a ɗaura masa aure Haɗe rai tayi tace "bazaka zo kaga kwalliya ta ba na biki?" Kwaɓe fuska yayi yace "ke in an miki kwalliyar ma ba kyau za kiyi ba" Cikin shagwaɓa tace "ni wallahi ba mummuna bace" Ammar yace "Auke tunanin ki kyaune dake? To ban sani ba wataƙila nan gaba idan kika girma kika zama mace kiyi kyau amma a yanzu dai kam se a hankali" Ji tayi kaman tayi dariya Ammar ya gama raina ta saboda wulaƙanci ma wato ba ta kai mace ba lallai zata bawa Ammar mamaki, amma ta maze tace "to ni mece inba mace ba?" "Aike ƙwaila ce" "wai dan Allah Meye ƙwaila?" "Ke kin isheni da surutu bana son yawan magana seda safe" Mufeeda aran ta tace "bari in nunawa mutumin nan ƙwailar ma mace ce" Ta kashe murya sosai ta kalle shi cikin shagwaba kaman 'yar yarinya tace "Mijin Jaririya ban gaji da ganin ka bafa dan Allah ka tsaya in ƙara kallon ka" Ya haɗe rai yace "ke bana son shirme fa" "waini komai nayi shirme ne, muje in raka ka ni ban gaji da ganin ka ba" Haka ta biyo shi wajen gate yace "koma gida rakiyar nagode haka" "to My love, ka gaida gida ka gaishemin da Mama, ina sonka Yaya Ammar ɗina" ta kashe masa ido ɗaya ta koma gida. Girgiza kai yayi ya nufi Napep ɗin sa, yana ƙara jinjinaa yarintar mufeeda. Shi mamakin kansa ma ya dingayi yadda ya tsaya yana sauraren shirmen ta. Ammar ya dinga ji a ransa ina ma Mace ze aura, inama Auren kirki zeyi ba wannan auren shirirtar ba, Yarinyar da sam ba zaman Auren ne a gaban ta ba ita dai tace zata yi aure ne saboda tana sonsa, sam besa ran wani zaman Aure da Mufeeda ba kawai zeyi aurene ya ƙarasawa Mama raino. Ɗakin Baba ta shiga da sallama ta tarar dashi zaune tare da Mama, Baba yace "Autar Baba kuma Amarya to be" Murmushi Mufeeda tayi ta ƙarasa ta miƙawa Mama kuɗin da Ammar ya bata, Mama tace "wannan kuma na menene?" "Bani yayi wai inyi haƙuri bashi da kuɗi in ƙara inyi wani abu, sannan inyi kitso da ƙunshi a ciki" Mama tace "roƙon sa kikayi kenan?" "Ni kin san bana Roƙo shi yace sena karɓa" Suna cikin maganar ne yaro yayi sallama ya kawo viva yace "Ammar yace a bawa Mufeeda" Mufeeda ta karɓo ta shigo ɗakin Baba Kayane ɗinkakku shadda ce blue da leshi se takalmi da jaka na Amare, ita dai Mufeeda kasa magana tayi se kallon kayan take. Baba yace "A jikina ina jin Insha Allah yaron nan ze kulamin da Auta, akwai shi da ƙoƙari, yanzu bayan kayan lefe hadda wata hidimar ta daban" Mama tace "lallai yaron nan akwai ƙarfin hali, bayan hidimar lefe da yayi hadda wata ɗawainiya daban, kuma gashi an riga an sai mata kayan da zata yi fitar biki" Mufeeda tai farat tace "ni gaskiya na Yaya Ammar zan sa" Mama tace tashi ki bar ɗakin nan mara kunya kawai, ban taɓa ganin mace mara kunya kamar ke ba, ana maganar aurenki kina tsoma baki shashasha kawai. Hausawa sukace rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, kwanci tashi asarar rai satin bikin Mufeeda ƙwaila da Oga Ammar ya kama (😜😜😜) Tunda satin biki ya kama jikin ta yayi sanyi komai a hankali take yi kaman kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Yaya Amina da fati sune suka zama tamkar manyan ƙawayen ta. Tasha lalle anmata gyaran kai tayi kyau matuƙa ga fatarta se sheƙi take yi, Mama daurewa kawai take yi dan har cikin zuciyar ta take jin rabuwa da Autar tata, dukda kullum cikin faɗa suke. An kama mata gurin kamu, tayi shigar gargajiya anmata simple make up tayi kyau sosai, 'yan gulma se cewa suke wannan amarya' yar yarinya se kace auren ƙauye, hada masu Anya ba magana ta ɗaukowa iyayen ba shiyasa suke so su lallaɓa su aurar da ita ba, kowa da abunda yake faɗa, akayi kamu da sauran Al'adun gargajiya aka watse. Abokan Ammar sunyi bajinta, suka haɗa kuɗi suka sai masa ƙaramin inji, suka sai masa dish suka bashi kuɗi naira dubu saba'in, da yake Shima Ammar meyi ne, duk wanda sha'anin sa ya tashi dukda bashi da shi sosai amma ze daki jikin sa yayiwa mutum alheri, gashi shi babu wani babban sha'ani daya taɓa taso masa balle suyi masa kara, shiyasa wannan karon suma suka jajirce suka yi masa wannan abun Alkhairin. Ammar yaji daɗin kuɗin nan matuƙa, dan haka ya samu Abba ya nuna masa kayan da abokan sa suka bashi, Abba yaita murna yana samu su Albarka. Ammar ya bawa Abba dubu hamsin yace "ga sadakin sa nan da za'a bawa Mufeeda" Abba yace "Madalla Allah yayi maka Albarka, Allah ya Sanya muku Alkhairi" Yaya jidda na gidan Ammar ya bawa Abba kuɗin sadakin. Ta dinga mita tana masifa "wannan 'yar mitsilar yarinyar za' a bawa sadaki har dubu hamsin saboda Almubazzaranci wallahi Ammar ni har ka fara bani kunya duk wannan izzar se kashewa ƙaramar yarinya kuɗin ka kake, wallahi zakayi dana sanin auren wannan abar dan banga abunda zaka samu a jikin ta ba, banda abun namiji ga mace kaman Zainab amma ka ɗakko wannan 'yar mitsilar abar" Ammar yace "Komai girman ta komai ƙanƙantar ta tunda Auren ta zanyi dole in kashe mata kuɗi tunda itama 'yace mutane ne suka haife ta, tunda Auren ta zan yi kulawar ta dole ta dawo ƙarƙashina dole in nema in kashe mata tunda kema naki mijin yana nema yayi miki" Umma tace "jidda karki ƙara shiga sabgar abunda Ammar zeyiwa Mufeeda, Allah ya riga ya ƙaddara baze auri Zainab ba Mufeeda ze aura" Duk Events ɗin da akayi babu wanda Ammar ya halarta, Amma danginsa sunje, Amma Amarya dai2 gwargwado tayi kyau matuƙa, Mufeeda tana da kyau ba laifi (Amma oga yace bata kai mace ba dan haka se a hankali, se anyi rainon ta😂). Ayimin haƙuri may be zaku ɗan jini shiru kwana biyu Share please More Comments More typing Ayshercool 07063065680 [23/06, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 9 Tunda aka fara bikin nan ko waya Mufeeda basu yi da Ammar ba, kan Mufeeda ya ɗau caji sosai, ana i gobe ɗaurin Aure Mufeeda ta fara kuka, ji take kaman tace ta fasa kuka sosai, Mama tun tana rarrashin ta harta bata haushi tace "da Ubanwa yace kice ke Auren kike so, ki rufemin baki ko in zane miki jikinki" Yaya Amina ce taje ta samu Baba ta gaya masa ga Autar sa can tana kuka Mama tace zata zane ta, Baba yasa aka kira masa Mufeeda, Ya dinga rarrashin ta yana mata nasiha ƙarshe a ɗakin Baba ta kwana. Kasancewar bata samu bacci ba sosai daren jiya yasa bayan sallar Asuba tai kwanciyar ta tana bacci, Baba kuma ya hana a tashe ta har ƙarfe tara na safe aka kafa rumufunan ɗaurin Aure tana bacci. Da ƙyar Baba ya bari aka tashe ta ta karya, sama sama aka mata kwalliya shima tana yi tana kuka. Ammar ya sha shaddrsa fara ƙal yayi kyau kaman a sace shi a gudu se zuba ƙamshi yake, Amma se wani cin magani yake kaman wanda za'ayiwa auren dole, Aminu yace "gaskiya Ammar ka saki ranka ba ze yuwu muje gurin ɗaurin auren nan kana wannan hade ran ba, se mutanen nan suce azabtar musu da 'ya zakayi, yau ranar farinciki ce a gareka" Ɗan tsaki Ammar yayi yace "nikam bana farincikin saboda dani da wanda da wanda ba aure zeba duk ɗaya, ni garama in zauna ba auren, na ɗauki wannan Auren a matsayin ƙaddara ta ne kawai" Jabir yace "Ammar be kamata ka ɓata Auren ka da bakin ka ba, dukda ƙaramar yarinya ce idan kasa gidan Auren ka ze zame maka dausayi na farinciki, yarinyar nan kai take so zata iya zama da kai a kowane yanayi na rayuwa, dan Allah ka saki ranka ka dena wannan ɓata ran" Haka suka ci gaba da lallɓa Ammar har suka tafi gurin ɗaurin Auren. Aka ɗaura Auren Mufeeda da Ammar akan sadaki har Naira dubu hamsin, Mutane sun yi mamaki musamman magulmata, Yaya Fadila ta shigo ɗaki ta samu Mufeeda tace "Auta buri ya cika an auri Ammar, an zama matan Aure su Mufeeda yanzu nidake mun zama ɗaya fa ko?" Banza Mufeeda tai mata taƙi ko kallon ta. Fadeela tace "Yarinya zaki ga abunda muke jiye miki, seki tashi an ɗaura, ki tashi kije za'ayi hotunan ɗaurin Aure" Kuka Mufeeda ta saka tare da noƙe kafaɗa, Fadila kuwa ta dinga mata dariya tana cewa "Yarinya da an gayamiki Auren abune me sauƙi? Ai ki adana kukan ki" Seda Mama tazo tai fama da ita Sannan aka gyara kwalliyar ta fito, Angwaye sun shigo anata gaisawa Mufeeda ta fito. Tunda ta fito yake kallon ta da alama tana cikin damuwa amma tayi kyau, irin shaddrsa ce ya kawo mata itace a jikin ta, me hoto yazo anata ɗaukar hotuna, dukda haka wasu anayi tana kuka, kallon ta Ammar yake sam kuka ba yamata wahala ko meye na kukan kuma yanzu oho? Daga cikin abokan Ammar ne wani Faruk yace "haba boss ka rarrashi babyn taka mana, kana kallo tana kuka" Wata uwar harara Ammar ya watsa masa, ya maze. Abokan Ammar suka sasu gaba wai za'a musu hoto tare, Mufeeda taƙi tsayawa, Jabir yace "dan Allah ka rarrashi Amaryar nan taka ayi hoton nan" Ammar ya ɗanyi ƙasa da muryarsa yace "wai ba zakiyi shiru ba? Kukan me kike haka waye yace kice kina son Auren? Kidena wannan kukan ko a fasa hoton, maza goge hawayen nan" Abokan Ammar se ihu suke suna "kunga wani salon Soyayya" Mufeeda tana kuka amma ta zumɓura baki daidai kunnen Ammar tace "ka bani handkerchief in goge" "bazan bayar ba in bazaki dena ba kiyi tayi" "wallahi in baka banba da babbar rigarka zan goge" Da sauri ya ɗago ya kalleta, babbar rigar sa fara ƙal tasha aiki, Amma tace da ita zata goge hawaye, yanayin kallon da yayi mata ne kaman na soyayya, aka dinga ɗaukar su hoto. "Ka bani mana Allah zan goge da rigar ka" girgiza kai yayi baya son yayi wani abu daze nuna rashin kyautawa a gaban mutane, amma tabbas yasan zata aikata abunda tace ya ɗakko handkerchief ya miƙa mata ta karɓa ta goge hawayen fuskarta, handkerchief ɗin se tashin ƙamshin turaren Ammar yake. shi dai Faruk ji yake inama shi ya samu damar da Ammar ya samu, yarinya ƙarama gata me kyau ga shagwaɓa abunda yake matuƙar burgeshi da mace kenan ya samu mace shagwaɓaɓiya. Nan ma aka dinga surutu 'yan matan layin su Mufeeda da suke ji da kansu su kaita gulma wata tace "Taɓɗijan wannan yarinyar ya zata yi da wannan mutumin ai yayi mata girma, kalleta' yar mitsitsiya da ita jishi a murɗe kaman ɗan dambe" Ɗayar tace "ke Amma wallahi ya haɗu koni na samu wannan Auren sa zanyi wallahi yana da kyau, wannan beyi kalar auren 'yar mitsitsiyar yarinya ba, Amma se wani cin magani yake ko fara' ar kirki ba yayi kaman wanda akayiwa auren dole" "Ke wallahi da na ganshi lokacin da yake zuwa zance ni zanyi ƙoƙari in cusa kaina, amma wannan ai da irin mu ya dace ba wannan fitsararriyar ba" Ɗayar tace "Allah ya kiyaye in auri me Napep nafi ƙarfin nan" "A'a wallahi ni banfi ƙarfi ba, ba gamu a zaune a layi ba, ita kuma tayi wuf dame napep wallahi indai zanci in sha na samu kaman wannan tafiya zanyi gamu a zaune ai yarinyar da aka haifa a gaban mu ta shige muna zaune" haka suka ci gaba da surutunsu da gulmace gulmace Haka aka gama shagalin biki a wunin ranar, Amma uwar gayya kanta har ciwo yake saboda kuka, bayan magariba motocin ɗaukar Amarya suka zo, maƙota suka dinga cika motocin nan suna tafiya zasu je suga ƙwal uwar daka suje ganin gidan mufeeda. Kusan duk an watse Mufeeda ake jira a tafi da ita amma ta maƙale a jikin mama tana ta kuka, Mama ta aurar da yara mata amma bata taɓa zubda Hawaye danta aurar da 'ya ba se wannan karon tana cikin yiwa Auta nasiha mufeeda ta ƙanƙame ta tana kuka, kawai se Mama itama ta hau kukan, duk faɗan da suke yi da Mufeeda tana matuƙar ƙaunar' yar tata, suka rungume juna suna kuka, Yayan mufeeda ya shigo yace "Mama dan Allah kidena kukan nan ki ƙyale yarinyar nan akaita ɗakin ta, tun ɗazu su gwaggo sahura na mota ita suke jira amma kin ƙanƙameta kuna kuka, haba Mama baki taɓa kuka dan zaki aurar da 'ya ba se Mufeeda" Su Anty Murja sukai tayiwa mama mita, Sosai Mama taƙi saurara su ta ƙara rungume auta. Seda Baba yazo da kansa, ya zauna ya ƙara yiwa Mufeeda nasiha me ratsa zuciya sannan yace ta tashi ta tafi a raka ta, amma Mufeeda tai mursisi ta sake hayewa kan gado bayan Mama tana kuka, Mama ji take kaman tace a ƙyale mata 'yar ta, Mufeeda tayi ƙanƙanta da fara fuskantar ƙalubalen dake cikin rayuwar aure, Amma tana mata addu'a Allah yasa Ammar ya riƙe ta Amana. Baba ne yace "yaki Auta na zo da kaina zan raka ki ɗakin ki, duk yayyan ki ba wadda na raka, amma dole in raka auta taho muje" Baba yasa hannu ya kamo na auta, ta sakko daga kan gadon amma ta riƙe hannun Mama, shi kansa Baba daurewa yake yadda suke kuka gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi. Baba yace "Sarah dan Allah kiyi hakuri kiyi mata fatan Alkhairi" Mama ta goge hawayen ta tace "yi shiru Auta na kinji, kiyi hakuri haka dama rayuwar 'ya mace take, kedai ki riƙe nasihohi da muka yi miki zaki zauna lafiya da kowa a rayuwa Insha Allah, jeki Auta na Allah ya bada sa' a Allah ya sanya alkhairi yasa gidan zamanki ne, Allah ya Sanya alkhairi da haske a rayuwar auren ki Allah ya bada sa'a" Daƙyar Mufeeda ta saki Mama, Baba ya riƙe hannun ta yasa ta a mota ya tafi kai Autarsa da kansa ɗakin miji. *************** Ammar ya kammala shiryawa se zuba ƙamshi yake, abokan sa na waje suna jiran sa, gidan su Ammar wasu duk sun tafi gidan Amarya, yayin da wasu ke ƙarasa Wanke-Wanke da gyaran gida, Ammar ya shiga ɗakin Abban sa ya tarar da shi zaune da shi da Ummansa yaje ya durƙusa gaban su yace "Abba zan tafi" Abba yai murmushi yace "Ango ka sha ƙamshi, ubangiji Allah ya Sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, dan Allah dan Annabi Ammar yadda suka baka 'yar su cikin mutunci ka girmama musu yarinya ka kula da ita, ka sauke dukkanin haƙƙoƙin ta dake wuyan ka, ka rage wannan zafin zuciyar naka da izza da wannan yawan faɗan naka, kaga yarinya ce ƙarama ka kula da ita Ammar " Ammar ya jinjina kai yace " Insha Allah Abba " Umma tace "to Ammar duk abunda zan gaya maka na riga na faɗa maka a baya, kuma mahaifin kama ya gaya maka, yarinyar nan da iyayen ta sun mana halacci, kaji tsoron Allah ka riƙe musu yarinyar su Amana, sannan ka tuna kaima akwai 'yan uwanka mata dake aure a gidan wasu, idan ka muzgunawa' yar wasu to tabbas kaima za'a cuzguna ma naka, ka riƙe ta da amana sannan kuma kayi haƙuri, kayi haƙuri rayuwar aure gaba ɗayan ta haƙuri ce, Allah ya baku zaman lafiya " Ammar kasa cewa komai yayi, a hankali yace " Abba a zaman mu daku nasan baza'a rasa abubuwa marasa daɗi da nayi muku ba ina roƙon afuwar ku" Abba yace "Aini dama matsala ta da kai ɗaya, rashin Aure ga miskilanci, amma duk wannan ba komai bane akan tarin alkhairan ka a gare mu, mun yafe maka Allah yayi maka albarka" Ya amsa da Ameen, sannan ya miƙe jiki a sanyaye ya fito tsakar gida, sauran 'yan biki suka dinga masa guɗa suna masa fatan Alkhairi, wasu har sunje sunga gida sun dawo. Yayar sa Maryam wadda ita yake bi ta ja shi gefe tace "To ɗan uwana ina maka fatan Alkhairi, Allah ya Sanya albarka yasa anyi kenan, sannan abunda nake so in gaya maka shine, ka kula sosai karka fifita matarka akan iyayen ka, sannan karka fifita buƙatun mu 'yan uwanka akan Na matarka, mu a gidan mazajen mu muke, duk wadda tazo maka da buƙatar ta indai bata da wani mahimmanci ka ƙyale namu buƙatar ka sauke haƙƙin matar ka, dan Allah ze tambaye ka akan amanar da ka ɗakko, Sannan Ammar tsakanin ka da iyayenka da mu 'yan uwanka daban, tsakanin ka da matar ka daban, dan haka ka yi wa matar ka abu ba lallai se mun sani ba, haka dan ka yi wa iyayenka abu base lallai ta sani ba, hakan ze toshe kafar samun matsala, Sannan kasan Auren nan naka yana da maƙiya mussman a gurin bikin nan na ƙara gani, kasan Yaya jidda bata son Auren nan, Sannan karka manta ko kuma in baka sani ba yanzu in gaya maka, Fa'izar Kawu Bala tana ɗaya daga cikin masu ƙaunar ka, ƙiri Ƙiri take nuna adawarta tareda kushe Auren nan, dan haka seka kula sosai, Allah ya baku zaman lafiya ƙanina" Mamakine ya kama Ammar sosai, wai Fa'iza Yarinyar da ko gaisawar kirki ba sayi ace itake sonsa, da yake duk cikin 'yan uwan sa yana jituwa da maryam sosai dan haka yace "Shikenan Sayyada Maryama, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah ya huta gajiya" Yai gaba tana ɗaga masa hannu. Yana fita nan ma abokan sa suka dinga tsokanar sa, daga nan suka hau abun hawa zuwa gidan Ammar. Mutane kusan duk an watse, suka je suka tarar da Mufeeda da mahaifin ta yana jiran isowar Ammar. Suna ganin mahaifin Mufeeda suka nutsu suka dena wannan rawar kan da suke, suka nemi guri suka zauna, Ammar da Mufeeda na gaban Baba, Baba yai musu addu'a da nasihohi irin na dattawa, ya kama hannun Ammar yasa na Mufeeda a ciki yace "Ammar ga Amanar Auta na nan, ayi haƙuri da halin ta yarinya ce ƙarama, tana da tarbiyya daidai gwargwado amma akwai yarin ta, Mufeeda ga Mijin ki nan ki kula da amanar Auren ki banda rashin ji, kinji Autar Baba" Jinjina masa kai tayi tana goge Hawaye. Baba yace "Allah ya baku zaman lafiya" Yana gama faɗin haka ya miƙe ze tafi, yana jiyo kukan auta amma yayi waje, yana jin babu daɗi a ransa yana jin rabuwa da autarsa har cikin ransa. Aminu yace "haba Mufeeda burinki ya cika Yaya Ammar ɗinki ya zama naki, meye na kuka kuma?" Faruk yace " ai da alama wannan Amaryar shagwaɓaɓɓiya ce, Ammar zaka sha daru fa" Jabir ya katse hirar ta hanyar yi musu fatan Alkhairi suka miƙe zasu tafi, Ammar yayi musu rakiya suka yi sallama Faruk yace "To Oga Ammar abita a sannu dai Yarinya ce ƙarama" Haushi ya fara kama Ammar akan wannan zaƙewar da Faruk yake, amma ya basar suka yi sallama suka tafi, Yayin da Ammar ya rufe ƙofa ya dawo, tana nan zaune inda ya barta, tana ta goge Hawaye, tsayawa Ammar yayi yana Kallon Mufeeda dan besan ta inda ze fara ba, kaman shi a ce wannan 'yar yarinyar ce matar sa, wannan sunan yayi aure ne kawai amma shida wanda beba duk ɗaya. "Ke wai bakya gajiya da wannan kukan ne? Se kanki yayi ciwo" Shiru tayi masa ta ci gaba da goge Hawayen ta hada sheshsheƙa. Tsaki yayi yace "sekiyi tayi ai, in kin gaji ko kin gama ga leda nan ki ɗauka kaza ce a ciki" Yana gama faɗin haka. ya wuce ɗaya daga ɗaku nan dake cikin falon, yaje ya rage kayan dake jikin sa ya watsa ruwa ya canza wasu kayan. Fitowa falo yayi da niyyar ya kashe fitilar falon, kawai ya tarar da Mufeeda inda ya barta bacci ya ɗauke ta, girgiza kai yayi tare da jan tsaki "ita wannan yarinyar banda yarin ta ma hadda taurin kai na damun ta" Ya ƙarasa inda take yace "Ke, ke!" amma sam bata san me yake yi ba, hannu yasa ya bubbugi jikin kujerar da take jiki, amma bata motsa ba sema ajiyar zuciya data sauke alamar baccin ta yayi nisa. Hannu yasa ya ɗago ta amma baccin ta take, bashi da zaɓi illa ya ɗauke ta zuwa ɗaya ɗakin da yake gado biyu akayi mata, yasa hannu ya ɗauke ta kaman wata 'yar shila se wani irin ƙamshin turare take zubawa. Yana zuwa ya shimfiɗe ta akan gadon ya tsaya ya ɗan zuba mata ido, fuskarta harta kumbura saboda kuka, ya zare mata mayafin jikin ta, tare da gyara mata kwanciya, idonsa ya sauka akan zara zaran yatsunta da suka sha adon lalle ja da baƙi, zuba mata ido yayi na wani ɗan lokaci yana saƙaa abubuwa daban daban a ransa sannan ya miƙe ya kashe mata fitila ya tafi ɗayan ɗakin. Mama kam kasa bacci tayi tana ta tunanin koya ya zata kaya wa autar ta? Wani hali take ciki? Kasancewar wannan ce ranar ta ta farko a gidan miji? (🙄🙄 bafa abunda ya faru mama ki kwantar da hankalin ki) Gaba ɗaya ta kasa sukuni bacci kam se ɓarawo ne ya ɗauke ta Kiraye kirayen salla ne yasa Mufeeda farkawa, tana tunanin koya akai ta dawo nan oho ita dai tasan a falo take tana bacci Ammar ya je da niyyar ya tashe ta salla ya ji motsin ta a toilet alamun ta tashi dan haka ya fice masallaci. Tunda Mufeeda ta koma bacci bayan Asuba bata farka ba se bayan ƙarfe tara, ta farka da wani irin ciwon kai saboda kukan da tayi. A hankali ta miƙe ta dudduba cikin kayan ta ta ɗako brush da toothpaste tayi brush, toilet ɗinta da famfon ruwa dan haka tayi wanka ta saka wasu kayan, Yunwa take ji sosai ga kanta yana ciwo haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito, Ammar ta hanga zaune akan three seater yana danna wayar sa. A hankali ta fara takowa inda yake, ya ɗan ɗaga kai ya kalle ta, ta ɗan rame ga idon ta a kumbure saboda kukan da tayi, ta ƙaraso inda yake ta zauna a kusa da ƙafafuwan sa tace "Yaya Ammar ina kwana?" "lafiya ƙalau uwar kuka" ya amsa mata yana dannan wayar, ɗan ɗaga kai tayi ta kalle shi ta sauke kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannun ta. Shiru ne ya ratsa na wani ɗan lokaci cikin shagwaba tace "nifa Yunwa nake ji" Ammar Yace "ai na ɗauka ba kya ci, je kitchen ki duba" Ta miƙe ta tafi kitchen, Tana zuwa ta tarar da kayan tea har ruwan zafi ya dafa, ba tayi wata2 ba ta haɗo tea ta dawo falo, ta zauna tana yin breakfast ɗin ta. Ta kalli Ammar tace "yaya Ammar ɗina kayi breakfast kuwa?" Kallon ta yayi yace "ke kici naki mana ina ruwan ki dani?" Tace "to Allah ya bada haƙuri" ta cigaba da cin Abincin ta. Daga nan shiru ya ƙara ratsawa tsakanin su, Ammar ya maida hankalinsa sosai akan wayar sa. Tana cikin cin Abincin, aka kira Ammar a waya bata san waye ba se ji tayi yace "A'a base kunzo ba bacci take yi, kuyi zaman ku kawai" Buɗe baki tayi za tayi magana, ya galla mata harara taja bakin ta tai shiru ya kashe wayar sa ya ci gaba da danna waya. Cikin shagwaɓa tace "Wai su waye za su zo kace kar suzo?" Shiru yayi mata yaƙi kula ta, ta ture kayan Abincin tana tura baki. "ni ka wani zauna kaƙi kulani ance za'azo kace baza suzo ba ni gaskiya kace suzo dan Allah" Wata uwar harara yai mata wanda ya tilasta mata yin shiru. Ta miƙe ta kai kwanukan data karya kitchen ta ajiye, ta dawo ta zauna ta zubawa Ammar ido. Har yanzu kanta yana mata ciwo, Ammar ya maida kai sosai akan wayarsa yana game. Kallon sa take yi yayi mata kyau sosai, inama ze kulata suyi hira a ranta tace "a sannu zan sauke wannan halin naka in dai nice" Fashewa tayi da kuka, Ammar ya ɗago da sauri yace "Ke lafiya? Meye haka?" Ta lanƙwasa "Nifa kaina ne yakemin ciwo" Ammar yace "shine zakimin kuka? Wannan koke koken da kike yi ba dole kanki yayi ciwo ba, kiyi min shiru ni in duba magani in baki" Yai maganar yana miƙewa, yana tafiya tayi murmushi, bayan tafiyar sa ɗaki tayi kwanciyar ta akan kujerar da ya tashi, ya dawo da magani a hannun sa da ruwa ya miƙa mata "ni gaskiya bana son magani ka ƙyaleni ze dena" Haɗe rai yayi yace "kika kuma Yimin kuka sena ɓata miki rai tashi ki karɓa" Ta tashi zaune tasa hannu ta karɓa, ta ɓalli ɗaya zata ƙara ɓalla yace "ke baki da hankali, maganin har nawa zaki sha?" "to manya ba guda biyu suke sha ba?" ta faɗa kaman za tayi kuka Hararta yayi yace "suwaye manyan?" Yasa hannu ya karɓe na hannun ta data ɓallo ya raba biyu ya miƙa mata rabi yace "ungo" tsayawa tayi tana kallon sa tace "rabi fa ka bani" "eh rabin, baki kai ki sha guda ba, ƙarama dake zaki sha magani har biyu saboda shirme, da masu chemist sun fito yanzu da na ruwa zan siyo miki" yai maganar in very serious tone yana wani haɗe rai. Wata uwar dariya ce ta kama Mufeeda, Ammar yayi mugun raina mata hankali itace ya kamata tasha magani na ruwa sekace jaririya ta gimtse dariyar ta a ranta tace "lallai Yaya Ammar muje a haka, ka shirya ganin ƙuruciya samfur samfur da yarinta zaka gane kacemin yarinya kuma ƙwaila dani kake zancen, zan maka aikin yara kala kala" . Masu Comment da addua ina godiya Allah ya bar ƙauna Domin shawara, gyara ko kuma sharhi Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S **Daddy, Baba, Abba, Appa, papa, Yaya, Abee, babi, father, Abbu ❤️❤️❤️* *I want tell you that we love you 😍😍😍* *HAPPY FATHER'S DAY* _Baba kuɗin mota, school fees, nepa bills, saloon, rapper everything father, father, father_ _we rest in your shoulders in every moment,_ __every day is yours but today is special day for you, i will use this opportunity to tell you that we all loves you endlessly our dads we really appreciate your efforts toward us especially in this very period of hardship, on behalf of every female daughter we wish you a very happy moment, we wish you a very long healthy life, more strength, joy happiness and halal money in your account. May Allah_ _subhanahu wata'ala crown your efforts towards us with countless rewards_ _Your female daughter's really loves you 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃_ _ _For those that thier father's pass away, we pray for them Allah's Rahma and Janna, may their gentle souls rest in perfect peace may Allah subhanahu wata'ala gives them a highest rank in jannatul fiddausi Ameen _ _I dedicated this page to all fathers all over the world thank you 😍 😍 😍 for your love*_ *Your female daughters really loves you* ❤️❤️ Page 11 Haka Ammar ya kwanta yana mamakin Mufeeda. Da gari waye Ammar be tashi da wuri ba, bacci yake har kusan takwas na safe. Mufeeda ta shiga kitchen ta dafa tea tun dare Ammar ya shigo da bread, tayi amfani da ƙwan nan da albasa da kuma naman jiya da suka kasa ci ta sarrafa bredin nan ta gasa, har ta gama Ammar be tashi daga bacci ba. Ɗakin ta tafi domin tayi wanka kafin ya tashi, amma harta fito ta kintsa jikin ta bacci yake, ɗakin sa ta tafi, tana zuwa ta tarar yana ta baccin sa. Kan gadon ta hau ta ɗan tsura masa ido a fili tai murmushi tace "Masha Allah mijina yafi na kowa kyau" Ta ɗan daki fulon da yake kai, tana faɗin "Mijin So, ka tashi haka baccin ya isa fa" A hankali yake buɗe idon sa har ya buɗe su duka ya sauke akan Ƙwailarsa, bakin ta raɗau da jan Jambaki, tayi ɗare ɗare akan gadon sa, ƙura mata ido yayi ba tare da yace komai ba ga ƙamshin turaren ta me daɗi yana ratsashi, se sake lumshe ido yake. Murmushi tayi tace "good morning Baby, na dafa ruwan wanka, in kayi seka fito mu karya" Yadda ta fita daga ɗakin sa a zuciye daren jiya beyi zaton zata kulashi ba, wani ƙarin mamakin wai har tasan ta dafa masa ruwan wanka. Yanayin kallon da yake mata ne yasa ta tsarguwa, dan haka Ta juya ta sauka ta bar ɗakin, ta koma falo tana jiran sa, koda ya fito falon ƙamshi ne daban daban yake dukan hancin sa, ya samu guri ya zauna harta jere komai na breakfast ɗin. Ta kalle shi a shagwaɓe tace "Nagaishe ka amma kaƙi amsawa ko" "to sannu, lafiya ƙalau" ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin janyo flask ɗin shayi. "No tsaya in zuba maka" Ta haɗa masa tea, gurin zuba Madara tana zuba spoon ɗaya yace "Ya isa haka" "taɓ spoon ɗaya, gaskiya ni spoon ɗaya yayi min kaɗan" shiru yayi ya fara shan tea ɗin sa ya kalle ta yace "Ina bredin ne?" Plate ta miƙo masa ɗauke da bredin da ta sarrafa, ya kalli bredin yace "meye Wannan?" "kaci kaji mana" "bredin kika wulaƙanta ya koma haka?" "ni ban wulaƙanta ba, kaci kaji da daɗi" Girgiza mata kai yayi yace "bazan ci ba" Hannu tasa ta ɗakko bredin ta matsa kusa da Ammar ta kwantar da muryar ta sosai tace "dan Allah Yaya Ammar kaci, na yadda idan babu daɗi na wulaƙanta maka Abinci kamin duk hukuncin daya dace dani, dan Allah" Yadda tai maganar ne cikin sanyin murya yasa ta bashi tausayi, hannu yasa ze karɓa, ta ɗan girgiza masa kai ta miƙa masa bakin sa, ya buɗe baki ta saka masa. Ai ba ƙarya bredin nan ba ƙaramin kaiwa Ammar yayi ba, dan yayi test sosai a bakin sa, Mufeeda tasan idan tayi magana ze iya mazewa ya fasa ci dan haka ba tace komai ba ta ƙara miƙa masa wani, ba kunya ya amshe abun sa ya taune ba tare da yace komai ba. Zata kuma gutsurowa yace "banni inci da kaina, zuba naki kici" Murmushi kawai Mufeeda tayi tace "Shikenan zanci, gama cin naka" Ammar yaci bredin nan sosai dan ba ƙaramin daɗi yayi ba, se yaji da'aka sarrafa bredin zuwa wani abun daban yafi bredin daɗi ma, amma be iya buɗe baki yace yayi daɗi ba. Ya kammala ci ta miƙa masa tissue ya goge hannun sa da bakin sa, har ze tashi ta kalle shi cikin salon kashe murya tace "Mijin baby ba kace komai ba, yayi daɗi kuwa?" Ɗan kallon ta yayi ya maze tare da ɗan tsuke fuska yace "ba wani daɗi na dai cine kawai maganin Yunwa" Murmushi tayi tace "Tunda dai har ya wuce cikin ka ba kayi amai ba ai shikenan" tai maganar tana murmushi, ta tattare Kwanukan taje kitchen ta wanke. Ta dawo ta tarar da shi a zaune a falon be tashi ba "Yaya Ammar ya haka ba zaka fita bane?" "Se an jima zan fita" ya bata amsa "shikenan Allah ya kaimu anjiman, ai gara ka zauna in ta kallon abuna ko?" tai maganar tana kashe masa ido ɗaya. Hararar ta yayi ya kauda kansa daga kallon ta, tai murmushi ta zauna tana facing ɗinsa, lokaci lokaci suna haɗa ido se yayi sauri ya kau da kansa. Ta tattara attention ɗin ta tana ƙoƙarin gano meya hana shi fita yau da wuri, kullum yana gama karyawa yake fi cewa, Amma yau yaƙi fita kuma yana zaune a falo, abun mamakin kuma se satar kallon ta yake, sake ɗaga ido yayi suka haɗa ido, ya ɗan maze yace "lafiya kike min wannan kallon ƙurillan?" A ranta tace "sekace shiba ni yake kallo ba" amma seta ta taso daga inda take tazo kusa da shi ta zauna ta kalle shi tace "Kasan menene? So nake in taɓa gemun ka, shike tsolemin ido" Ɗan buɗe baki yayi yana kallon ta, lallai yarinyar nan ta mugun raina shi, kawai ya ɗauke kansa yace "tashi daga kusa dani mara kunya" ƙara narkewa tayi a jikin sa tace "dan Allah Yaya Ammar sau ɗaya fa zan taɓa dan Allah" Juyowa yayi yana kallon bakin ta, wanda yayi raɗau da jan baki, se ɗaukar ido yake, dukda kitson kanta ya fara tsufa amma har yanzu yana ɗaukar hankalin Ammar, Yadda take maganar very serious kamar 'yar yarinya. Ta kuma cewa "in taɓa dan Allah ?" "Tashi kije kiyi breakfast seki zo ki taɓa" Murmushi tayi tace "to" Ta miƙe tana fara' a ta haɗa breakfast ta zauna tana karyawa, ta nayi tana kallon sa tana murmushi, ta kammala ta tattare Kwanukan, tana dawowa ta tarar ya ɗakko mukullin sa ze fita. Ta ɗan ɓata fuska tace "haba Mijin bebi, haka muka yi da kai? Banfa taɓa ba" "Ke bana son shiririta, ni fita zanyi Ungo wannan" ya miƙo mata kuɗi ɗari biyar "Me zanyi da wannan? Naga ka siyo komai na amfani ai" "Eh baki nayi ko zaki sai wani abun" "ni babu abunda zan siya" "Ke ki karɓa meye haka?" ya ɗanyi maganar a hasale. Durƙusawa tayi tasa hannu biyu ta karɓa tace "Nagode Allah ya ƙara Arziki, yaja da ran su Umma" "Ameen" Suka yi Sallama ya fice. ********************** Fa'iza ce keta kaiwa tana komowa a ɗakin ta tarasa meke mata daɗi, tana ƙoƙarin tuna menene mafita akan halin da take ciki tabbas tana son Ammar kuma tunda har ya iya Aure ƙaramar yarinya kaman wannan to tabbas itama zata iya jarraba sa'arta akansa amma ta yaya? " Fitowa tayi falo ta tarar da Maman ta tayi baƙuwa, ba tare da ta kalli inda baƙuwar take ba tace "Mami dan Allah zan fita anguwa, zanje gidan su Nasreen" "To kiyi sauri karki daɗe, bana son babanku ya dawo yaita min mitar ba kwa nan" (Nasreen ɗin 'yar ƙanin mahaifiyar Fa' iza ce) "Ok" Baƙuwar tace "Ahh Fa'iza ba magana?" Fa'iza ta ɗan juyo ta kalli matar tace "Ohh sannu" a ƙalla matar tayi sa'ar mahaifiyar Fa'iza, bata kuma bi takan Matar ba ta wuce ɗakin ta. A gurguje ta watsa ruwa ta shirya ta fice daga gidan, ba ta tsaya ko ina ba seda taje gidan su Nasreen, ta shiga da sallama tayi sa'a Nasreen ɗin tana tsakar gida tana mopping, Nasreen na ganin ta tace "hajiya fa'iza wannan zuwa haka babu waya, anjima nake tunanin in zo gidan ku fa" "Kinga gurin ki nazo dan Allah ina Umma?" "ba ta nan tana Islamiyya" "Muje ɗaki dan Allah ina cikin damuwa" Ɗaki suka shiga kaman yadda Fa' iza ta buƙata. "Nasreen wallahi nayi sakacin kasa ga yawa Ammar abunda yake cikin raina, saboda ina ganin baze soni ba, se gashi ance yarinya ƙarama ya aura" Nasreen tace "Wallahi yarinya ce sosai, ai ke baki je gurin dinner ba, mu munje munga komai wallahi yarinyar nan bata fi shekara sha shida ba, 'yar ƙarama da ita se iyayi in gaya miki tsaf zaki iya goya wannan' yar abar" "dan Allah ba wannan ba meye abunyi yanzu? Wallahi Nasreen baki ji yadda nake ji a raina ba, ina son Ammar sosai fa ba da wasa ba" "Aikuwa seki ɗau haƙuri tunda ya riga yai Aure" Hararar ta Fa' iza tayi tace "haba Nasreen Ammar mijin mace huɗu ne fa, dan me zan haƙura?" "to da sana'ar Adaidaita sahun ze riƙe ku ku biyu, kiyi tunani mana Fa'iza" "Taɓɗijan ubanwa ya gaya miki mu biyu zamu zauna, ta isa in zauna da ita inyi kishi da 'yar mitsitsiyar Yarinya, wallahi sena fara da korar ta daga gidan tukuna, in saka Daddy na ya bashi aikin yi, dan bazan aure shi a dinga miji na ɗan a daidaita sahu bane" "ta yaya?" Nasreen ta tambaye ta "koma ta ina ne, sena fara da kora ta tukuna ni kuma zan shige" "Naji amma kin san meze faru?" "A' a sekin faɗa" "Yanzu ki bari se an jima, ki shirya muje gidan su Yaya Ammar, semu sa Halima ta raka mu gidan sa dan nima banje gidan sa ba, muje kiga yarinyar muga yanayin kamun ludayin ta daga nan semu san ta ina zamu fara" "Yawwa Nasreen naji daɗi Sosai, ina nan bazan koma gida ba, gama abunda kike, bari in ɗora girki idan yasa anjima se mu tafin" "shikenan bari in samo Almajiri yai mana cefane kafin Umma ta dawo". Haka kuwa akayi, bayan sun gama girki Maman su Nasreen ta dawo suka yi mata sallama cewar za suje gidan Yaya Ammar. Maman Nasreen tace "Aikuwa kwa gano min gidan dan dama ban samu naje ba nima, dan Allah kuce ina gaishe su kafin inzo" Nasreen tace "to Umma zamu gaya musu Insha Allah" Daga nan suka fice basu tsaya ko ina ba se gidan su Ammar. Mahaifihar Ammar taji daɗi da taji sunce gidan Ammar zasu je, da iyayen su da mahaifin Ammar uwa ɗaya uba ɗaya, Dan haka Umma tasa Halima ta shirya ta raka su gidan nasa, ta bada kayan kuka da su zogale tace akaiwa Mufeeda. Sam Su Fa'iza basu nuna akwai wani abu a ƙasan ransu ba game da zjwan su gidan Ammar dan haka Halima ba taji komai ba ta shirya domin ta raka su. ************************** Koda Mufeeda ta kammala gyaran gidan ta, ba wani abu da zata yi bata da tabbacin Ammar ze dawo da rana ko baze dawo ba dan haka ta gyara masa ɗakin sa ko ina tsafa se ƙamshi yake, ta samu takadda ta rubuta masa "My love to you is endless Baby, good night, have a very sound sleep tonight i will be with you in your dreams, I Love you, mijina" ta ajiye masa a kan gadon sa Daga nan ta nemi guri ta zauna ta fara tsifar kanta dan a ganin ta ya tsufa. Ta fara tayi nisa a tsifar dan harta tsefe rabi taji ta gaji, ta tufke rabin data tsefe, ta ajiye tsifar tayi kwanciyar ta a falo, bacci ne ya ɗauke ta bata farka ba se ƙarfe ɗaya, ta tashi taji tana jin Yunwa dan haka ta haɗa cornflakes ta sha sannan ta tafi yin Salla. Tayi raka'a biyu taji ana buga gate ɗin, bata yanke sallar ba ta ci gaba da sallar ta, seda ta idar sannan ta ɗakko Hijjabi ta tafi buɗewa. Har sun fara zage2 "wai dan wulaƙanci tana ji suna buga ƙofa amma anyi banza da su an barsu a waje" Halima tace "wataƙila tana wani abunne" Ta ƙaraso cikin sassanyar muryar ta tace "Waye?" Halima tace "Mune Anty Mufeeda" ai gaba ɗaya suka kalli Halima "Anty kuma?" Mufeeda ta buɗe ƙofar, Halima ta gane a cikin su dan tazo gurin bikin ta ranar kamu da kuma dinner, ta faɗaɗa murmushin fuskarta tace "Bismillah ku shigo" Suka shiga tai musu jagora zuwa falon ta, suna tafe suna hararar bayan ta. Tai musu jagora har cikin falon ta, ko ina na gida ƙal da shi, se ƙamshi ne ke ratsa kafofin hancin su. Suka nemi guri suka zauna suna kuma ƙarewa falon nata kallo a wulaƙance, Kayan kujerun ta suka kalla hakan ya tabattar musu da Mufeeda ba 'yar matsiya ta ce ba, dan kayan ta masu tsada ne. Mufeeda tace "Sannun ku da zuwa kun kwaso rana, Yaya Halima naita sa ido inga kinzo amma baki zoba se yau ko? Nikam nayi fushi" Halima tai murmushi tace "haba Anth Mufeeda washegarin da' ak kawo ki Umma ta bada Abinci akawo muku, har mun shirya zamu zo, na kira Yaya Ammar amma yace kar muzo bacci kike" Mufeeda tai murmushi tace "Hmm Yaya Ammar kenan, bari in kawo muku ruwa kun kwaso rana" Ta tashi ta tafi kitchen, ita kam fa'iza mamaki da baƙin ciki ne suka haɗu suka hana ta magana, duk yadda ake faɗin yarintar matar Ammar bata zaci zata ganta a haka ba, ga Yarinyar da kyau ga wani iyayi da take yi abun haushi. Mufeeda ta ɗakko musu ruwa da lemo me sanyi a fridge, ta ɗebo musu snacks ta kawo musu tace "ku fara da wannan bari in shiga kitchen in ɗora muku girki" Ta koma kitchen tana ƙoƙarin ɗora musu girki, Nasreen tace "Ya kika ga kamun Luda yin ta, kinga dai matar Ammar" Fa'iza tace "Nagan ta kam, amma Ammar ya bani kunya duk wannan jiji da kan nasa kalli abar da ya auro" "ba wannan ya kamata ki duba ba, mafita ya kamata ki nema" Halima tace "wai Yaya fa'iza me kuke yi hakane? Ya zamuzo har gidan ta ku dinga munafuncin ta" Nasreen tace "dalla rufewa mutane baki, ina ruwanki kema munafuka wai Anty Mufeeda meye wani Anty, wallahi kin girme ta" "to dan na girme ta ai ƙanin mahaifiya ta take aure, kuma nima ai tana bani girma na dukda haka, ni banga aibun ta ba wallahi" Fa'iza tace "dalla ƙyaleta mu ci gaba da zancen mu" Ana haka Mufeeda ta fito daga kitchen ta dawo tace "bari in kunna muku yv kafin abincin ya dahu" Halima tace "to Anty Mufeeda ko in taso in kama miki wani abun ne, mun saki aiki rana tsaka" "laa kinji Yaya halima da wani batu wai kun sani aiki ba wani aiki" Ta tafi tana kunna tv, sarai Mufeeda ta lura da wank irin mugun kallon banzar da Fa'iza da Nasreen suke mata, Amma ta maze ta kunna tv ta dawo ta zauna tace "nikam Halima wannan Antyn nawa ban gane taba" ta faɗa tana nuna fa'iza sanna ta nuna Nasreen tace "har gara wannan na ganku tare ranar kamu amma na manta sunan ta, Amma ita ban gane ta ba" Halima tace "wannan Antu Fa'iza ce, wannan kuma Anty Nasreen duk cousin's ɗin Uncle Ammar ne" Mufeeda tace "Masha Allah, Sannun ku fa" Nasreen ta ɗan taɓe baki sannan tace "yawwa" Mufeeda a ranta tace "ashe cousins ɗin sane, wannan wani abun ne ya kawo su, akwai wani abu a ransu, amma bari inga iya gudun ruwan su, zan ɗago inda suka dosa kafin su tafi " Fa'iza tace "Nikam a jinki nawa akayi miki aure haka?" Mufeeda tai murmushi tace "Jss 2 nake" Nasreen tace "da alama kam, ke gidan ku ba'a karatu ne? Aka miki aure da ƙananun shekaru? Sekace a ƙauye" "anayi mana nima har zan ci gaba da karatuna amma Allah beyi ba, Allah ya haɗa ni da Yaya Ammar yace na ƙarasa in muna tare tunda muna son juna baze iya jira in gama ba, kuma duk wanda yaje Islamjyya yasan origin ɗin Auren wuri, ai ba wai ɗabi'a ce ta mutanen ƙauye ba, yana da asali a addinin musulunci, bari in dubo girki na karya ƙone" Kallon juna Fa'iza da Nasreen suka yi tare da jinjina kai. Ta kammala dafa farar taliya dama tana da Miya, dan haka ɗumama miyar kawai tayi ta zubo musu. Ta kawo musu manyan kuloli da cokula ta ajiye, Fa'iza tace "Ke duk wannan Abincin kika dafa? Abincin naki kuwa ze ciyu?" Mufeeda tace "indai har Yaya Ammar zeci Abincin dana dafa to komai matsayin mutum zeci wannan Abincin, sedai kuma in mutum be niyyar ci ba, Yaya Halima sakko muci Abinci naga su Anty Nasreen ba Yunwa suke ji ba" Halima sam bata ji Daɗin abunda su Nasreen ɗin sukayi ba, da ta san haka za suyi da bata rako su ba, ta sakko suka kwashi girki it da Mufeeda, Nasreen taga kaji a miya kuma ranta ya biya dan haka ita ma ta sakko, ita kuwa Fa'iza se haɗe rai take. Se la'asar suka shirya zasu tafi, Nasreen tace "kin san da'aka kawo ki bamu zo ganin gida ba, zo ki nuna mana, ta shiga dasu ko ina amma tai mirsisi ta hana su shiga ɗakin Ammar. Fa'iza hadda baƙaƙen maganganu Amma Mufeeda tace baza su shiga ɗakin mijin ta ba, da dai sunzo kafin akawo tane shikenan, Amma tunda Ammar ya fara kwanciya a ɗakin babu wanda ze shigar masa ɗaki ko waye kuwa. Haka suka tafi, Halima taji daɗin abunda Mufeeda tayi sosai, ɗari Biyar ɗin da Ammar ya bata kafin ya fita ita ta takurawa Halima ta karɓa. ****************** Yauma Ammar se bayan isha'i ya shigo gidan, yauma da kaya niƙi niƙi a hannun sa ya shigo, Mufeeda tayi masa sannu da zuwa ta taya shi shiga da kayan, ya zauna a falo akan carfet ya mimmiƙe ƙafafuwan sa, dan ya gaji sosai. Ta kawo masa ruwa me ɗan sanyi ta bashi ya karɓa ya sha, yana lumshe ido saboda gajiya. Mufeeda ta zauna wajen ƙafafuwan sa tana ja masa yatsun ƙafan Tace "Sannu mijin bebi" jinjina mata kai yayi yana jin daɗin yadda take jan yatsun ƙafafuwan nasa. "Nasan kayi salla a waje, a kawo Abinci ne?" Ammar yace "yanzun ma wani girkin kika kuma yi?" Ta miƙe tsaye tace ina zuwa, taje kitchen ta kawo masa Abinci, ya kalli taliyar tana ta tururi a cikin flask, bece komai ba, ta zuba masa ta miƙa masa ya karɓa ya jujjuya taliyar yana kallo sannan ya fara ci, aikuwa turawa kawai yake, yaji daɗin taliyar nan sosai, gashi tunda ya fita ruwa kawai ya iya siya ya sha. Mufeeda kallon sa take yi, tausayinsa ne ya kamata da ganin yadda yake cin Abincin kasan yana jin yunwa sosai, tun safe yake yawo a gari neman halak ba tare da ya dawo gida ya huta ba, dole duk inda ya samu yayi bacci. Ta ture ɗankwalin kanta gefe dan zafi ya ishe ta, ya kalli kan yaga ta tsefe rabi, kitson da yake matuƙar so, ajiye fork ɗin yayi yana kallon ta, seda tace "ya dai naga kana kallo na? Ko nayi laifi ne?" da sauri ya basar yace "kwashe kayan Abincin nan na ƙoshi" Murmushi tayi masa tace "to Mijin so" Ta kwashe kayan ta shiga ɗakin ta, ta fito da kibiya da mataji zata ci gaba da tsifa dan tuni Mufeeda ta gano Ammar yana matuƙar begen kitson kanta, wanda shi sam besan ta gane ba. Ta fito falo ta zauna ta fara tsifa, Ammar yace "me kike yi hakane? Me yasa kike tsefewa?" "ya tsufa ne, dama kuma na gaji da tsifar dan Allah ka tayani tsefewa" tai maganar tana miƙa masa comb. "ke na miki kama dame saloon ne? Ta yaya zan iya wani tsefe miki kai? Ni bazan taɓa wannan ƙazamin kan naki ba, ban iya wani tsifa ba" Tura masa baki tayi tace "Aini kaine me Saloon ɗina, kuma zaka dinga tayani tsifa wallahi ko in bar kan yaita zama a haka bazan ƙara tsefe ko guda ɗaya ba ko ze shekara" "Saboda kin iya ƙazanta ko. Idan kuma gashin ya zube fa?" "Shikenan na huta dama damuna yake da zafi, ji nake kaman in ɗan rage shi da almakashi aini yarinya ce Allah ze yafe min, au ni namanta ma na kulaka bayan ɗazu da safe nace zan taɓa gemunka ka hanani" Ɗan taɓe baki Ammar yayi ya miƙe tsaye, wannan Yarinyar bata rabo da Rikici. Ta jingina da kujera tace "Yau bazaka sha shayin naka bane? Ko so kake kayi Tumbi? Kaci Abinci fa yanzu kuma za kaje ka kwanta" "bazan sha ba" ya bata amsa. Har ze shiga ɗakin sa yaji tace "Mijina Dan Allah Wacece Fa'iza a family ɗinku?" Ji yayi gaban sa ya faɗi ya waigo da sauri yace "kamar Yaya wace Fa'iza?" "Ɗazu suka zo suda Yaya Halima, mun daɗe dasu anan tare" Be amsa mata ba ya shige ɗaki abunsa, ƙyale shi tayi dan taga alamar gajiya a tare da shi, amma ta barwa ranta dole Ammar ya gaya mata matsayin fa'iza da Nasreen a gurin sa. Yana zuwa ze kwanta yaga takaddar data ajiye, ya ɗauka ya karanta, ɗan murmushi yayi ya ajiye takaddar a akan side bed ya kwanta. **************** Motsin da Ammar ya dinga ji a banɗakin sane ya sa shi farkawa daga baccin da yake yi. Shiru yayi ya lumshe ido yana tunanin meye yake motsi a toilet ɗinsa, be gama tunanin ba Mufeeda ta fito jikin ta ɗaure da towel kan ta babu ɗankwali ta gama tsefe kanta ta wanke shi. Ammar ya buɗe ido da sauri yace "Ke meye haka? Me ya kawo ki banɗaki na?" Murmushinta me ƙayatarwa tayi masa tace "tap ɗina ne yaƙi zuwa, ni kuma bazan iya kai ruwa toilet ɗina ba kaga ni ƙarama ce bazan iya ɗaga babban bucket ba shiyasa nazo nan nayi wankan" Tsaki yayi yace "to jeki maza fitar min daga ɗaki" maimakon ta fita seta girgiza gashin kanta da yake jiƙe da ruwan wanka, ai kuwa ruwan har fuskar Ammar "Wai Mufeeda meke damunki ne, ya haka?" Cikin kalar Halayar Yara tace "Yi haƙuri kanne ya jiƙe, shine nake jijijjigawa dan ruwan ya fita, ka dubamin idan kan ya fita dama jiya kace kaina ƙazamine" Girgiza kai Ammar yayi ya ja bargo ya rufe kansa ya juya mata baya. Murmushi Mufeeda tayi a ranta tace "Yaya Ammar kenan ai ka gamu da yarinta kenan" Ta zaga gurin ƙafar sa da ya bari a waje, taja yatsansa na tsakiya tace "ai ka bar ƙafar ka a waje" Banza yai mata yaƙi kula ta, yana ji tana jan yatsun ƙafarsa, kawai Mufeeda ta kalli gashin ƙafarsa ta ja ɗaya be kula ta ba, ta ƙara jan wani ai ba shiri Ammar ya miƙe zaune yace "Meke damunki ne?" Ta ɗan kwaɓe fuskarta tace "bakomai fa, so nake ka tashi ka karya" "Naji amma yanzu fita kije kisa kaya, sannan karki ƙara zuwarmin ɗaki kiyi wanka in zaki yi wankan ki gayamin in kai miki ruwan" "to shikenan naji zan tafi, Amma in ka fito sena taɓa gemunka dan ban manta ba" Ta kashe masa ido, ta juya ta fice tana girgiza gashin kanta yana fidda ruwan dake jikin sa. Yayin da Ammar yabi bayan ta da kallo zuwa kan santala santalan ƙafafuwan ta, tunda ga kan gashinta har ƙafafunta ɗigar da ruwan wanka suke. Ammar ya dafe kai yace "kai wannan 'yar mitsitsiyar Yarinyar se rigimar tsiya, wai gemu na zata taɓa, wani lokacin kamar me hankali amma shirmen ta yayi yawa, dama nasan nikam na auri ƙuruciya da rawar kaine kawai, ni da ko ɗaukar ƙana nan yara ba nayi, amma wai gemuna zata taɓa" Domin gyara, sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 12 Ammar ya sakko daga kan gado ya shiga a gurguje yai wanka ya fito falo, kamar ko yaushe falon ta tasaf tayi turaren wuta, ta ajiye kayan breakfast a falon, se dai ita bata falon zama yayi ya haɗa ya fara karyawa, har ya kammala bata fito ba abun ya bashi mamaki, yana daf da fitane sannan ta fito cikin doguwar rigar ta, ta atamfa ta tsikara ɗaurin ɗan kwali a gaban goshin ta, masha Allah, Ba ƙaramin kyau tayi ba dukda bata saka jambaki ba yau fuskarta ba kwalliya amma tayi kyau, kaman Ammar yayi magana amma ya fasa. "Hubby har kayi breakfast kai kaɗai, shiryawa fa nake yi amma har kayi shirin fita?" "Eh na makara yau, zan tafi" "Amma nifa yau kai zaka bani Abinci, amma zaka tafi gashi ko ganinka ban gama yi ba" tai maganar cikin sigar shagwaba da rararshi, ta ƙaraso gaban sa ta riƙo hannayen sa tace "please My Ammar ka tsaya inyi breakfast seka tafi, Allah ban ganka ba sosai" "Ke wai duk wani salon damun mutum kin sani, ni tafiya zanyi ba kiga na makara ba" Tura baki tayi ta ɗan haɗe rai "dan Allah Yaya Ammar ka zauna inyi breakfast seka tafi, in ka tafi Allah bazan ci ba" Ammar yace "karki ci ɗin cikin kine ai ba nawa ba" Ya ƙwace hannun sa ze tafi, ta riƙe shi gam, idon ta har ya fara kawo ruwa za tayi kuka, Ammar ya girgiza kai yace "Shikenan ni karki min kuka, muje ki zuba in kuma ba kiyi sauri ba zanyi tafiya ta ne" Murmushi tayi tace "zanma yi saurin" Haka Ammar ya dawo ya zauna, ta haɗa breakfast ta nayi, rigar ta cif a jikin ta kaman a jikin ta tela ya ɗinka. Haka Ammar ya zauna jaririyarsa ta gama cin Abincin ta, seda ya miƙe ze fita ta cire ɗankwalin kanta taje gaban sa tace "Yaya Ammar ka dubamin idan gashi na ya fita" dama gashin nan ya daɗe yana tsolewa Ammar ido. Ajiyar zuciya yayi yace "Ke na gaji, ki bari idan na dawo zan duba miki" yayi waje da sauri, Yayin da Mufeeda ta bishi tai masa addu'ar da ta saba yi masa. A ƙasan zuciyar sa yana jin dama ya taɓa gashin nan, dan har ya bushe ta shafe shi da mai. ************ Su fa'iza kam bayan sun tafi jiya suna tafe suna zagin Mufeeda suna tsine mata. Daddare suna chatting ita da Nasreen, Nasreen tace "ke yanzu na samo mana wata mafita" Cikin zaƙuwa Fa'iza tace "wace mafita ce haka?" "Kin san Anty jidda ma ba son Auren nan take ba" "haba dai?" "Wallahi dagaske nake, yanzu abunda za muyi shine, muje gidan ta mu zigata, muce Yarinyar tayi mana wulaƙanci mu dai ɓata ta sosai a gurin ta, tunda kinga ba zamu tunkari umman sa mu gaya mata ba mussman inda wannan banzar haliman" "haka za'ayi Nasreen, Allah ya kaimu gobe gidan Jidda zamu je". Haka kuwa akayi Washegari haka suka wanke ƙafa zuwa gidan Jidda, tayi murnar ganin su suka baje ana ta hira Fa'iza tace "Anty jiya fa mukaje gidan Yaya Ammar, wallahi Anty Ammar ya bada maza ke kinga matar tasa kuwa? Jidda tace "na ganta mana ya zan masa tunda shi ya zaɓo ta" Nasreen tace "haba Anty jidda me wannan 'yar yarinyar zata morawa Ammar banda abun namiji dai?" Jidda tace "ba shi yace yana so ba, itace ta ganshi ta nace masa sekace mayya seda ya aure ta, da akwai wata bazawara nan kusa dani ita yake so, amma ya koma ya auri wannan yarinyar" Kallon juna Nasreen da Fa'iza suka yi, suka maze Nasreen tace "'hmm ai baki ga abu ba Anty, kinga wulaƙanci da tayi mana? Munfi minti goma sha biyar a ƙofar gida muna bugu taƙi buɗewa, ke kinga kallon banza da take mana wai taga dangin miji" Fa' iza tace "ba wannan ba anty jidda, data bamu Abinci baki ga kaji a ciki ba manya manyan yanka, nace Allah sarki su Abba su basu ci ba amma daga aure ya saiwa matarsa kaji fal, banda na kitchen wanda ba'a soya ba" Anty Jidda ta jinjina kai tace "hmmm Allah sarki, se anyi magana yace shi bashi dashi sana'rsa ba wata babbar sana'a bace, Amma har ya iya saiwa matarsa kaji iyayen sa ko oho, wallahi ze gamu dani ai zanje gidan" Nasreen tace "ai gara dai kije wallahi Anty Jidda dan in ba'a ɗau mataki akai ba ana mata kallon ƙaramar yarinya gaida su Abban ma seya dena zuwa balle ya basu wani abu" (Abunka da mata, wanda mune maƙiyan junan mu) haka suka dinga ziga jidda suna gaya mata abunda akayi da wanda ba'ayi ba, seda suka tabbatar sun kunna ta ta hau sosai sannan suka bar gidan. ***************** Yau Ammar da Yamma ya dawo be kai dare ba kaman yadda ya saba, yana komawa yaga Mufeeda da wasu shigar dukda be gaya mata ze dawo ba, kayane Pakistan a jikin ta kanta ba ɗankwali, Mufeeda tayi murnar dawowarsa, sedai kaman kullum yauma a gajiye yake, ta jera masa sannu ba a dadi, kafin taje ta kawo masa Abinci ya zare rigar jikin sa ya bar vest da dogon wando. kafin Mufeeda ta dawo iskar fanka dake busa shi har ya jingina da kujera ya fara gyangyaɗi. Mufeeda na fitowa daga kitchen taga Ammar yana bacci, bata taɓa ganin sa da vest ba, kodai yasa shirt ko kuma Jallabiya. Ganin sa haka yasa ta ga yaƙara mata wani uban kwarjini, da ka ganshi kaga ƙaƙƙarfan namiji, ga gashi kwance a ƙirjinsa bacci kawai yake abunsa Mufeeda na matuƙar Tausayin Ammar, neman halak akwai wahala, hartazo ta ajiye Abincin be buɗe ido ba. A hankali cikin fargaba da tsoro taje kusa da shi, a hankali ta riƙo hannun sa cikin nata tace "Yaya Ammar ka tashi kar wuyan ka yayi ciwo fa, ga Abincin na kawo maka" Ɗan buɗe idon sa yayi ya mayar ya lumshe, ƙurawa fuskarsa ido tayi, sannan ta kai hannun ta zata taɓa masa gemu caraf ya riƙe hannun ta yace "ai ina kallon ki" dariya tayi me cike da ɗaukar hankali tace "kana jina amma kaƙi kulani seda zan taɓa gemun ka ko? Ka bari in taɓa sau ɗaya mana" Ya ɗan kalle ta yace "A'a ba yanzu ba" A shagwaɓe tace "se yaushe?" "Sekin girma" ya bata amsa Tura baki tayi tana ɗan harararsa "ni wallahi na girma tunda baka taɓa goyani ba, ko Abinci ma da kaina nake ci ba kai kake bani a baki ba" "Ke yanzu na baki Abinci a baki seki ci?" "Au meze hana? Kaima fa rannan na baka a bakin nan kaci" Tayi ƙasa da muryar ta daidai kunnen sa tace "Kuma da'akaci ba'ayi min Comment ba, Yayi daɗi ko akwai abunda zan gyara a Abincin ba'a gayamin ba" Ammar ya ɗanyi murmushi yace "Aini har yanzu ina tunanin anya ke kika dafa? Saboda ci kawai nake saboda ina jin Yunwa amma ba daɗi" Yau ba ƙaramin mamaki Mufeeda take ba, Ammar yana mata hira kaman a mafarki, Mufeeda ta riga ta gama gano Ammar a ɗan zaman su ta gano abubuwan da yake matuƙar so, dukda magana seya ga dama yake yi amma actions ɗin sa in tayi wani abu yasa take gane abubuwan da suke birge shi. Mufeeda tace "to ko zamu shiga kitchen ɗin tare?" "kin isheni da surutu fa, kuma ni bacci nake ji" "yanzu la'asar fa tayi zakayi bacci" "eh kwanciya zan in huta" "Abincin fa?" "Se an jima zanci, ɗakko min pillow guda biyu a ɗaki" ba musu ta miƙe taje ta kawo masa pillow, ya jere pillows ɗin ya kalle ta yace "oya ga naki nan kwanta" "Aini bana jin bacci" "eh kwanta, nasan muddin na kwanta bazaki bari inyi baccin ba damuna zakiyi" Kallon sa take yi, sekace wata yarinya 'yar shekara biyar ɗin nan. "ni gaskiya Yaya Ammar wanki ne dani, zan wanke kaya na da bedsheets, na haɗasu a ɗaki se kuma inyi bacci? Bayan ina da aiki" Ya kalleta yace "kece zaki wanke kaya su fita? kiyi jiƙa jiƙa dai, ba fita za suyi ba" Zata kuma magana, ya janyo ta ya kwantar da ita akan pillow yace "kar in ƙara jin bakin ki" dan yasan Mufeeda bazata taɓa bari yana bacci ita kuma idon ta biyu ba, wannan bakin nata ma ya isa ya hana shi bacci. Haka ta kwanta tayi shiru, shima ya kwanta a nasa pillow, babu daɗewa Mufeeda ta fara ajiyar zuciya bacci ya ɗauke ta, shi kuma ya kasa baccin ƙamshin man gashin ta da tuararen jikin ta suka kashe masa jiki amma ya kasa bacci, baƙin gashin ta ya zubawa ido da yake ta sheƙi. Jin ta fara sauke numfashi ne alamun bacci ya sashi a hankali ya kai hannun sa kanta, ya taɓa gashin nata. Sam bata san yana yi ba, haka ya dinga shafa gashin nata a hankali na wani lokaci, a hankali Ammar ya miƙe daga inda yake kwance ya shiga ɗakin ta, ko ina tsaf dashi a ɗakin nata. Drower ɗinta ya buɗe yaga kayan data naɗe na wanki, yasa hannu ya ɗauka ya wuce ta a falo ya fita tsakar gida. A zamansu da Mufeeda na ɗan lokacin nan, akwai halayen ta da suke matukar burgeshi, duk rikicin ta da shagwaɓarta tana matuƙar bashi girma, dama Ammar mutum ne me matukar son girma, komai ya bata komai ƙanƙantar sa ta dinga godiya kenan tana masa addu'a shida iyayen sa, dukda shi in tayi abu baya yabawa, amma yana jin daɗin addu'ar da take masa, da nuna tausaya masa da take yi. Se magariba ta buɗe ido, ta juya taga babu Ammar a gurin, ta miƙe ta duba taga ya fita beci Abincin ba, tana fitowa tsakar gida taga ya haɗa kayan sa da nata ya wanke, ya wanke napep ɗinsa a tsakar gida, mamaki ne ya cika Mufeeda, taje tai alwala tayi sallar magariba sannan Ammar ya shigo gida. Falo ta fito ta sameshi ya zuba Abincin sa ya fara ci. "Mijina wanki fa naga kayi min" shiru yayi mata yana danna remort, tare da tauna Abincin sa. "Yaya Ammar ka wankemin kayana, yanzu idan akazo aka tarar kamin wanki ace matarka bata da imani, ka fita ka nemo Abinci sannan ka dawo kamin wanki" Ya ajiye spoon din yace "ni za'acewa bani da Imani na bar wannan 'yar Yarinyar tana wanke kayan ta, hadda abun shimfiɗa ta" "Amma Yaya Ammar... " Ke Yimin shiru, kin isheni da surutu, ga leda can ki ɗauka naki ne" yai maganar ransa a haɗe dan karta kuma magana, ta ɗakko ledar ta duba popcorn ne a ciki da tarkacen chocolate. Murmushi tayi tace 'Nagode Baby" Harararta yayi tai saurin cewa "yi haƙuri ashe fa nice babyn, mijin baby, babyn ka ta gode Allah ya ƙara maka buɗi na alkhairi" "Ameen" ya amsa. Seda ya gama cin Abincin tace "Yaya Ammar dan Allah ka dinga dawowa da rana kana cin Abinci, ka dena wuni a rana". Kaman baze magana ba se kuma yace "Idan ban wuni a rana na nemo ba, me zan baki? Me zan kaiwa su Abba?" "Allah sarki Minjna, gobe insha Allah za'a kawo mana gara se a ɗebarwa su Umma, muma mu samu seka ɗan huta na kwana biyu" "Gara kuma? Me yasa za'a kawo gara?" "ai duk wanda aka aurar a gidan mu Baba yana masa gara" "ya bani 'ya, ya rangwantamin kayan aure, Sannan kuma ya bani gara abun yayi yawa ai, zan iya baki Abinci dai dai ƙarfina amma baza' a ɗora masa ɗawainiya ba, hakan tamkar na gaza ne" Taje jikin Ammar ta kwanta a hannun sa tace "tabbas Yaya Ammar ko ƙasa kake ɗauka ka bani zan karɓa inci ba tare da nayi ƙorafi ba, saboda nasan abunda kake da shi zaka bani, ba gazawa ce tasa Baba yake bamu gara ba, sedan sanin cewa maza kuna kashe kuɗi lokacin Aure, dan Allah yaya Ammar karka ce A'a bazaka karɓa ba" Shiru yayi bace mata komai ba, wayarsa ce ta fara ringing, Jidda ne ke yawo akan screen ɗin wayar sa, ɗagawa yayi tare da yin sallama. Suka gaisa sama sama, shi izza da rashin son raini, ita kuma jidda a fusace take da shi. Jidda tace "idan baka komai ina son ganinka gobe in Allah ya kaimu" Ammar yace "zan duba inda lokacin zanzo" daga nan ya kashe wayar sa. "Yaya Ammar wacece wannan"? "kin fiye tambaya fa" "Yaya Ammar kenan yanzu laifi ne dan na tambaya?" "Yaya tace" ya bata amsa a taƙaice. "Amma baka bani mun gaisa ba?" tai maganar tana saka popcorn a bakin ta "zaku gaisa wataran" "Hmm wacece kuma Fa'iza?" "ƙanwa ta ce, cousin ɗina ce" Ta gyara kwanciyar ta a jikin sa tace "Wadda ta kira ka rannan fa da daddare?" "Ke ɗagani ban sani ba, kin fiye tambaya" Murmushi tayi masa tace "Yaya Ammar kenan, daka san abunda mace take ji idan taga mijin ta da wata mace daban, da baka ce na fiye tambaya ba" Kare mata kallo yayi cike da rainin hankali yace "wace ce macen?" Wani irin kallo tayi masa, ta miƙe tsaye har zata wuce ɗakin ta ta dawo ta bayansa ta sunkuyo da kanta kunnen sa "kowace mace, mace ce komai girman ta komai ƙanƙantar ta, tunda ɗaurin kallabin wata yarinyar yana iya zaunar mata da mutum a gida, ai nima na kai acemin mace baby na, kishin ka ne yasani nake abunda nake" tayi kissing ɗin sa a goshin sa tace "I love you baby" Ta juya ta tafi ɗakin ta, Yayin da Ammar yabi bayan Mufeeda da kallo. Wannan yarinyar me take nufi ne? Ɗaurin kallabin ta yake zaunar mata da mutum a gida, to wata ke nufi kenan. Miƙewa yayi ya tafi ɗakin sa kaman wanda ƙwai ya fashewa a ciki, yai shirin bacci ya kwanta, amma ya kasa bacci, haka kurum yau yake jin Nishaɗi, wanda ya rasa na menene, gaba ɗaya duk inda ya juya ƙamshin turaren mufeeda ne ke tashi a jikin sa, lumshe ido yayi yana tuna yadda ya farka ya ganta a ɗakin sa, da yadda ya dinga shafa gashin ta kaman kar ya dena. Sosai Ammar ya kasa bacci, ya dinga juyi akan gadon, Seda ya fito ya sha tea sannan ya koma ya iya bacci. ******************* Yauma yana baccin safen sa tazo ta tashe shi, "Mijin baby ka tashi zanyi wanka" Ya buɗe ido yace "dan zakiyi wanka se kinzo kin tasheni?" "kaifa kace in zanyi wanka in maka magana ka kaimin ruwan, kace kar in sake shigar maka toilet, toilet dina ba ruwa" Tsaki yayi ya miƙe, ya fita tsakar gida ya ɗebo ruwa a bucket ya kaimata toilet, harze fita taje gaban sa ta juya masa bayan ta "Yawwa mijina ɗan aljanna, Allah ya barmin kai saura ka zugemin riga ta" Ƙara tsuke fuska yayi, da kamar ya share ta, amma a ransa yace "bari in zuge mata karta zaci wani abu a ranta" Cikin fushi Ya kama zip ɗin da nufin ya zuge mata da sauri ya fita, tana sane ta ƙwala ihu wai ya haɗa da fatar ta, kuma ƙarya take, ɗan Riki cewa yayi yace "Subhanallah, tsaya in gani ban sani ba na haɗa da jikin ki" Ƙin tsayawa tayi ya duba, ta dinga tsalle tana kuka wai ita bayan ta zafi, Ammar yace "yi haƙuri zo in ƙara sa zuge miki, ba ina sane na haɗa da jikin ki ba" Fuskarta harta fara hawaye, gaba ɗaya Ammar yaji ba daɗi, zata ga kaman yana sane yai mata "A'a ni bana so, dama tunda naga ka haɗe rai baso kake ba ka zugemin da baya na, ni ƙyaleni in ƙarasa abuna". Tafara kici kicin cire rigar ta, ai ba shiri ya juya ya bar mata ɗakin, yana fita ta zauna ta sha dariyar ta sannan ta shiga tai wankan. Da ta fito falo taƙi kulashi wai ita lallai haushin sa take ji, ko hirar ma yau ƙin yi masa tayi tai zamanta a kujera tana tura baki. Haka ya gama karyawa yana yi yana kallon ta, da sassafen nan maimakon ta karya chocolate take sha, kaman yayi magana amma ya ƙyaleta. Ya gama karyawa ya kalle ta yace "zan tafi" Ta kalleshi tace "adawo lafiya" ta ci gaba da cin popcorn ɗin ta, sabon da Ammar yayi in ze fita seta raka shi tana masa rangwaɗa tare da addu'a, yau da bata yi ba seya ji babu daɗi, yana fita kafin ya kunna babur ɗin sa ta tura masa "I love you my soul, Allah ya tsaremin kai ya albarkaci neman ka, ya wadata mu da halal" Ɗan murmushi yayi ya tura mata "bana so, ai kina kallo har na fita kika ƙi kulani" Tana ganin message ɗinsa ta miƙe tana murna, tare da faɗin Yaya Ammar kazo hannun ƙwaila. ****************** Kai tsaye gidan Anty Jidda ya nufa don yaje yaji kiran me take masa haka, yai sa'a tana nan, haje suka gaisa se wani haɗe rai take Ammar yace "kince kina nema na Allah yasa lafiya" Jidda tace "hmm Ammar kenan ina fa lafiya, tun yanzu daga yin auren naka beje ko'ina ba, za'a fara wulaƙanta mana dangi" "kamar yaya ban gane me kike nufi ba" "Ahh dama ai bazaka gane ba, yanzu tsakani da Allah ace su Nasreen suje gidanka amma a wulaƙanta su" Nan ta dinga zazzagewa Ammar, wai ya fara wulaƙanta iyayen sa da 'yan uwan sa akan wannan' yar ficikar yarinyar mara mutunci, wadda bata san darajar manya ba. Sosai suka yi faɗa da Jidda, yace "karta ƙara zagin Mufeeda baya tunanin mufeeda zata aikata abunda ta faɗa" Ya tashi yai tafiyar sa, wunin ranar gashi nan ne dai kawai, yana tunanin anya Mufeeda zata aikata haka? Wani sashin na zuciyar sa yana gaya masa Mufeeda tana da tsiwa, kuma ba'a shedar mutum. Mufeeda tana ta murna ta gyara gida ko ina fes ta sha kwalliya, tun da rana taiwa Halima waya cewar taje, da Halima taje ta bata Abinci cikin flask ya sha nama wanda Yaya Amina ta kawo mata a miya, tace wa Halima ta kaiwa Su Umma, amma sam bata gayawa Ammar tayi hakan ba. Har wajen tara Ammar be dawo ba, har Mufeeda ta fara shiga damuwa akan ina Ammar ya tsaya haka be dawo ba? Se wajen tara da Rabi sannan ya dawo, tana jin ya shigo da babur ɗin sa ta fita da sauri tana "Mijin baby yau ina aka tsaya ne, tun ɗazu na kasa nutsuwa ban san inda ka shiga ba, na kira ka bata shiga" Banza yayi mata ya wuce ɗakin sa, tsayawa tayi tana tunanin me akayiwa Ammar haka ya sashi yin fushi haka, bata karaya ba tabi bayan sa zuwa ɗakin sa, ta tarar yana cire agogon hannun sa, ta tsaya a gaban sa tace "Yaya Ammar wai meya faru ne?" Har yanzu bece mata komai ba ya nemi guri ya zauna akan gadon sa, gefen sa ta koma ta zauna ta riƙo hannun sa tace "Yaya Ammar dan Allah ka gayamin meya faru?" Tureta yayi daga jikin sa yace "karki ƙara kwanciya a jikina, saboda wulaƙanci 'yan uwa na suzo gidan nan amma ki musu wulaƙanci, me suka yi miki? To bari kiji in gaya miki wani abu, dan ina aurenki baze yuwu ki wulaƙantamin' yan uwa ba, ni bana son rigima kinsa sunje sun gayawa Yata kin musu wulaƙanci se faman jaraba take min, ni bana son tashin hankali na gaya miki, tashi ki barmin ɗaki na" Tunda Ammar ya fara maganar Mufeeda ta sunkuyar da kanta ƙasa, yaita banbamin sa ya gama ba tace masa uffan ba, seda yayi ya gama sannan ta ɗago ta kalle shi, ta kuma riƙe hannun sa tace "Kayi haƙuri dan Allah, Insha Allah bazan sake aikata makamancin hakan ba, Sannan suma ka basu haƙuri akan laifin da suka ce na musu, bisa kuskure ne ni ban san nayi musu ba, Insha Allah zan kiyaye" Ta ƙarasa maganar hawaye na bin fuskarta, ta miƙe zata bar ɗakin, har zata fita ta waigo tace masa "Ga Abincin ka can a falo, sannan na dafa maka tea ɗinka, akwai ruwan wanka a ɗaya flask ɗin. Daga nan ta juya ta bar ɗakin da sauri tana sheshsheƙar kuka. Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 13 Mufeeda tana komawa ɗaki ta kwanta akan gadon ta tana zubar da hawaye "ashe wannan ƙalubalen Mama take jiye min tace nayi ƙanƙa ta da fara fuskanta, Allah ka bani ikon cin wannan jarrabawa" haka Mufeeda ta cigaba da zubda Hawaye. Ammar kam ya ɗanji babu daɗi kukan daya ga tana yi, amma tunda har take bada haƙuri to tabbas tayi ne, kuma ze nuna mata kuskuren ta, 'yan uwan sa nada mahimmanci a gurin sa, baze taɓa bari ta wulaƙanta suba. Haka yai kwanciyar sa beci Abincin ba, da safe haka ta tarar da Abincin yadda ta ajiye masa, haka ta ɗauka ta kai fridge tai masa girkin safe ta gyara ko ina kaman yadda ta saba. Fuskarta harta ɗan ɗaga saboda tayi kuka sosai, ƙarfe takwas Ammar ya fito har ta kammala komai. Tana ganin sa tace "Yaya Ammar ina kwana" Kallon ta yayi ya ɗauke kai, yana ƙoƙarin fita, taje ta sha gaban sa tace "Yaya Ammar dan Allah kayi haƙuri, kazo muje kaci Abincin, karka zauna da yunwa" "bazanci ba na ƙoshi" ya faɗa a hasale yai waje, falo ta koma ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta dinga kuka kasa cin Abincin tayi itama. Can da Rana tana kwance abun duniya duk ya dame ta, taji ana buga gate haka ta miƙe jiki babu ƙwari taje ta buɗe, kamanin matan da Ammar ne yasa ta gane 'yan uwan sa ne, murmushinta ta faɗaɗa ta musu barka da zuwa, Maryam ce da Amina Yayyen Ammar, Mufeeda tana ta ɗan ɗari ɗari karta yi wani abun da za' a ƙara zuwa a cewa Ammar tayi, amma se taga su sam bahaka bane, suna ta mata hira kaman ƙanwarsu, a hankali ta ɗan saki jiki dasu suna hira. Suma tayi musu girkin Abinci, suka zauna suna hirar duniya da yanayin rayuwa, cikin hirar Maryam ta dinga yiwa Mufeeda nasiha tace "Mufeeda naji daɗin yadda na ganki 'yar gayu dake ga tsabta, kaman kin san Ɗan uwan namu akwai son gayu" Murmushi Mufeeda tayi ta sunkuyar da kai, Amina tace "Amma halin sa sekin haɗa da haƙuri, mutum ne me sauƙin kai se dai yana da wahalar sha' ani wani lokacin, kiyi hakuri" Maryam tace "maybe mune yake nunawa wahalar sha'anin ita ba haka ake mata ba" Ita dai Mufeeda sedai tayi murmushi tana sunkuyar da kai. Maryam ta kuma cewa "Kiyi haƙuri Mufeeda da yanayin Rayuwar kinji, babu Auren da bashi da ƙalubale, amma kiyi hakuri ki fuskanci mijinki, sannan karki kuskura wani yasan sirrin auren ki kinji?" Mufeeda tace "Insha Allah Anty nagode sosai" Mufeeda taji daɗin zuwan su, sun ɗebe mata kewa sosai dukda ƙasan zuciyar ta a cunkushe yake, se bayan la'asar suka yi mata sallama suka tafi. Koda Ammar ya dawo bebi takan ta ba balle ta gaya masa 'yan uwan sa sunzo. Kusan kwanaki biyu kenan Ammar baya shiga sabgarta, duk wani abu da ya shafi cin Girkin ta, ko zaman falo ya dena, gaba ɗaya a takure take. Tana kwance akan gado tana ta tunani, 'nikuma kalar tawa ƙaddarar kena dangi miji su dinga haɗamin makirci a gurin miji, dan ta Ammar wannan me sauƙi ne, amma duk namijin da yasan ciwon kansa baze taɓa bari matarsa ta ci zarafin' yan uwan sa ba, shiyasa bata ganin laifin Ammar, ita burin ta a yanzu ya dena fushi da ita, Amma ya zama dole ta ci gaba da rarrashin sa harta shawo kansa. ********************* Shi kansa Ammar baya jin daɗin yadda ya share ta, yayi missing ɗin fitinar ta da kuma Addu'oin da take masa, amma baze nuna mata karaya da wuri ba seta gane tayi kuskure tukuna seya tabattar mata da 'yan uwan sa ba abun wulaƙantawa bane. Yana zaune a falo da daddare yazo da Abincin sa daga waje yana ci, Mufeeda bata gaji ba tazo da plate ɗauke da Abinci akai tazo gaban sa ta ajiye tace "dan Allah Yaya Ammar kayi haƙuri kaci Abincin dana dafa" Shiru yayi mata ya ci gaba da Cin Abinci, "Yaya Ammar dan Allah ka gayamin mezan maka wanda zesa ka huce, ni ko cewa kayi inje in basu haƙuri zanje, indai zaka haƙura please" Ammar baya son ɗaga ido ya kalleta, amma hawayen da take zubarwa har cikin ransa yake jin kukan nata babu daɗi. Kasa jurewa tayi ta faɗa jikin sa ta ci gaba da kuka, jikin ta wani irin ƙamshi yake fitarwa, gaba ɗaya yaji jikin sa yayi sanyi, yadda ta ruƙunƙume shi da hannayen ta ya saukar masa da kasala, zuciyarsa nata harbawa sannan tana ta raya masa abubuwa daban daban, ji yayi kaman ya ƙara rungume ta a jikin sa, amma yin hakan yana nufin wani abun daban kenan, dan haka yasa hannu ya ture ta yace "kin san bana son kuka ko? Karki ƙara kwanciya a jikina" ya tashi ya bar mata falon. Kukan ma yanzu kasawa tayi, wace irin zuciya ce da Ammar haka wanda baya jin magiya? Haka taja jiki ta koma ɗakin ta gwanin ban tausayi. Ammar kam ya shiga yanayi me wuyar fassara, wannan rungumar da Mufeeda tayi masa. Da safe kafin ta tashi ya fice ya bar gidan, sam Mufeeda ko Abinci bata iya ci saboda damuwa. Kai tsaye ya wuce unguwar su domin yaje ya gaida su Abba, A soro ya haɗu da Abba yana shirin fita, ya tsaya suka gaisa suka ɗanyi hira, Ammar ya ciro dubu biyu a aljihun sa ya miƙawa Abba, Amma Abba yace "Ammar ka bar kuɗin ka, nauyin iyaline yanzu akan ka, bakomai ni ina da kuɗi a jikina" Yadda Ammar yake da kafiya haka Abban sa yake se haƙura yayi ya ƙyale shi ya shiga cikin gida. Guri ya samu ya zauna suka sha hira da Umma, Yace a bashi Abincin safe yaci Umma tace "ka baro gidan ka sannan mu kazo ka cinye mana Abinci, maimakon ka taho mana dana Amarya" Ɗan murmushin yaƙe yayi yace "Umma kenan yau naku nake son ci" "A'a kodai akwai matsala ne?" "A'a babu wata matsala Umma" Umma tace "Halima ɗakko masa fulasan Mufeeda ya tafi dasu" Ammar ya kalli Umma sororo yace "flasan Mufeeda kuma?" Halima tace "Eh mana Yaya Ammar, sau biyu tana kirana a waya na karɓo mana Abinci, wallahi ta iya girki sosai, ran da mukaje gidan ka baka nan, Su Yaya fa'iza suna ta mata wulaƙanci wai matar ka 'yar Yarinya amma tana zubo mana Abinci tsit kake ji" Shiru Ammar yayi bece komai ba, ya karya a gida, daze tafi ya bawa Umma kuɗin da yayi niyyar bata dana gurin Abba yai musu Sallama ze tafi yace "Halima biyo ni da Kwanukan nan" Umma tace "to Ammar kace ina gaida 'yata, ya kamata kuma ka kawo mana ita, ko seta haihu munje barka" Da sauri ya kalli umma, a ransa yace "ji umma da wani zance, wai seta haihu aka ga wannan' yar yarinyar da ciki ai naji kunya" A fili yace "zan kawo tane, na tafi" "to shikenan ka gaishe ta dan Allah, kace mata nagode sosai, Allah yayi albarka, Su Maryam ma da sukaje shekaranjiya suna ta ƙara yaba Sirikartawa, ka gaishe ta dan Allah, Allah yayi muku Albarka" "Ameen" ya amsa Tunani daban daban ne suka ziyarci zuciyar sa, ya akayi aka samu banbanci da abunda Anty Jidda ta gaya masa? Halima tabi bayan sa da flasai, seda suka fita suka je gurin a daidaita sahunsa Ammar ya kalleta yace "yaushe kukaje gidana keda su Fa'iza?" "wancan satin ran Asabar" ta bashi amsa "Da kukaje akwai abunda ya faru da ku kaje ne?" "A'a ba abunda ya faru, sedai su Yaya Nasreen ne suka dinga gaya mata baƙar magana, da zamu tafi suka ce zasu ga gida, ta shiga dasu ko ina tace ba zasu shiga ɗakin da kake kwana ba, shine suka dinga zagin ta, kuma bata kulasu ba, tace dai kome za suyi suyi ba zasu shiga ba" Jinjina kai Yayi yace "Shikenan jeki, se an jima" daga nan ya hau Napep ɗin sa ya tafi. A hanya ya haɗu da Aminu, ya tsaya suna gaisawa, Aminu yace "lallai mutumin nan wato tunda Allah yasa aka kaimaka ƙwailar ka, ko neman mu baka sake yi ba, kaga yadda kayi wani shar da kai dan Allah me take baka ne?" Ammar yace "ban sani ba, na shigo rannan naje gidan ka baka nan, Jabir ma kunyar sa nake ji, ina so muje gidan sa nida Mufeeda sannan kaima in kaita gidan ka, tunda Jabir yai Aure sau ɗaya naje gidan sa se dai mu haɗu a unguwa" Aminu yace "Kai Ammar ƙyale wannan Auren na Jabir, ƙaniyar sa kawai yake ci, Allah ya kiyaye kar auren nan ya mutu" Da sauri Ammar yace "haba dai, saboda me auren da befi watanni huɗu ba zuwa biyar ba, shine ze mutu?" "Ammar abun ne ba'a cewa komai, su matan se a hankali muma mazan hakan take, kasan halin Jabir shi kawai kyau da body structure na yarinyar yabi ya aure ta, amma she's not wife material at all, Sam bata ganin girman sa, rannan yake gayamin faɗa cikin dare shi da ita zagi in zaga" "Subhanallah garin yaya haka ta faru da Jabir, sam bemun zancen ba" "Ai zancen ne babu daɗi dan haka ba lallai yai maka ba, sedai mun haɗu zancen nada tsayi, Amma Jabir na buƙatar mafita" Hama sukayi sallama da Aminu, Ammar ya tafi yana tunani a ransa, yayi zagi in zaga da mace kuma ya ci gaba da zama da ita baze yuwu ba, yana daga cikin illar Auren yaran nan da basu gama hankali ba. Wunin ranar haka yai ta saƙe saƙe, gefe yana tunanin yaze warware matsalar sa da Mufeeda. Bayan sallar isha'i ya koma gida, Tana jin dawowarsa amma bata fito ba, yana ta tunani me yakamata yayi ne, yana son ya ganta amma sam bata fito falon bama balle ya ganta. Yayi tunanin ze iya zama makircin su Nasreen ne abunda suka faɗawa Jidda, Amma baze iya tunkarar Mufeeda ya bata haƙuri ba, idan yayi hakan zata raina shi, ko kuma ta samu damar wulaƙanta su anan gaba, Amma yadda take kukan nan ya kamata ace ya ganta. Tashi yayi ya nufi ɗakin ta, ya tura ƙofar ɗakin a hankali, akan dadduma ya hango ta ta duƙunƙune a cikin hijjabi, da alama kukan take, tausayinta ya mamaye zuciyar sa, ya ɗanyi gyaran murya yace "ba'asan na dawo bane?" Juyowa tayi ta kalle shi a sanyaye tace "bana so in fito kaƙi kulani ne" tai maganar wasu Hawayen na fitowa daga idon ta. "Azo a bani Abinci, ina jin Yunwa" Ai da sauri ta miƙe tsaye ta cire hijjabin jikin ta tare da ƙaƙalo murmushi tana goge hawayen ta tace "dagaske ka haƙura zaka ci Abincin?" Jinjina mata kai yayi alamar "Eh" Cikin sauri tace "bari inje kitchen in ɗora yanzu zan gama" "Shikenan ina falo ina jiranki" ya juya ya yafice daga ɗakin, farinciki yasa ta kasa dena kukan da take, ta fito falo ta ɗakko masa ruwa da cup ta kai masa kaman yadda take masa in ya dawo. Yasa hannu ya karɓa sannan ya zaunar da ita a kusa dashi, yasa hannu yana goge mata Hawayen fuskar ta, yace "kin san bana son kuka ko?" Jinjina masa kai tayi, yace "to me yasa kikeyi dan ki ƙara ɓatamin rai?" "Ai kaine kake fushi dani kuma na baka haƙuri kaƙi haƙura" "to ai yanzu na haƙura, sedai abunda nake so dake, ko a nan gaba karki kuskura kiyiwa wani wulaƙanci a cikin 'yan uwana, sannan duk wanda ya wulaƙanta ki ko ya miki wani abu ki gayamin zan ɗau mataki akai" Girgiza masa kai tayi tace "A' a Yaya Ammar idan sunmin wani abun ma ni bazan gaya maka ba, bana son in dinga ɓata maka rai ko wani abu na ɓacin rai ya shiga tsakanin ka dasu na ɓacin rai saboda ni, kuma ni ba wani abu da suka yi min da zesa in kawo ƙararsu gurin ka, ni ɗinma da suka ce na musu ba daidai ba, ba ina sane bane kuma nace ka basu haƙuri " Gaba ɗaya mamakin maganganun ta yake, ga wani tausayinta da ya kama shi, ita dai kar ransa ya ɓaci shine babban burin ta. Ya kalle ta yace "kina cin Abinci kuwa? Naga kin rame" Shiru tayi ba tace komai ba se kallon sa da take yi. "je ki ɗora mana Abinci ina jin Yunwa kwana biyu nayi missing jagwalgwalonki, Umma tace a gaisheki wai jagolgwalon Abincin ki da daɗi" Murmushi tayi tace "Yawwa gara da umma ta faɗa ai, nasan Abinci na da daɗi ai" Ɗan Murmushi yayi yace "dama kin kai musu Abinci ban sani ba? Ai shikenan tunda an wareni suna ta godiya, nima nagode sosai naga kaman ma sunfi sonki yanzu akai na" "Idan na kuma yiwa su Umma abu kayi min godiya, zamu ɓata da kai zan dena kula ka, ni su Umma iyaye na" tai maganar tana ɗan zumɓura baki. Ammar ba ƙaramin jin daɗin abunda ta faɗa yayi ba. Yau taƙi zuwa ta zauna kusa dashi sosai balle ya shaƙi wannan dadaɗan ƙamshin turaren na jikin ta. Ta miƙe da sauri tace "bari inje in ɗora Abincin nasan kana jin yunwa sosai" Ta tafi kitchen ta ɗora sanwa, cike da farincikin yau mijin ta ya sakko daga fushin da yake da ita, yana nan zaune ya kallo wayarsa ta fara ringing baƙuwar lamba ce dan haka ya ɗaga tare da yin sallama, Muryar Zainab ce ta amsa sallamar, haɗe rai Yayi yace "ya akayi?" "Shikenan Ammar bazan kira ka mu gaisa ba? Har yanzu ina nan ina dakon soyayyarka a raina na kasa mantawa da kai" "baki san nayi Aure bane zaki dinga kirana duk lokacin da kika ga dama?" Mufeeda dake kitchen ce ta fito zata je tsakar gida ta ɗakko tsintsiya, karaf taji yana waya da mace, turus tayi ta tsaya tana kallon sa, shima ɗaga kai yayi suka haɗa ido, wani banzan kallo tayi masa ta fice ta ci gaba da aikin ta, dukda jikin Ammar Yayi sanyi da irin kallon da tayi masa, amma be kawo komai a ransa ba ya ci gaba da wayar sa. "Look zainab bana son shirirta, idan Allah ya baki miji kiyi haƙuri kiyi Aure kawai, ni bani da halin riƙe mata biyu" zata kuma magana ya katse kiran. Mufeeda da ta koma kitchen kawai ta tsinci kanta da zubda Hawaye, dukda kasancewar ta yarinya ƙarama kuma me kawaici tana da matukar rauni a ɓangaren kishi. Ta kammala ta zubo masa Abincin ta kawo gaban sa ta ajiye masa komai ta juya zata tafi, yace "ke ba zaki ci Abincin ba?" "Na ƙoshi" ta bashi amsa tana ƙoƙarin tafiya ɗakin ta. "idan ba zaki ci ba, zoki ɗauke Abincin ki nima bana ci" Dawowa tayi ta zauna, ta zuba masa Abincin ta miƙa masa. Nasihar Mahaifinsa ya tuna akan yayi haƙuri ya kula da Matarsa ƙaramar Yarinya ce, kar ya dinga nuna mata wannan yawan fushin nasa. Ammar neman shiri yake da Mufeeda dan haka ya Karɓa ya matso kusa da ita, ya ɗebo Abincin a cokali ya kai bakin ta "maza ungo karɓi kici, nasan kema kina jin Yunwa" Girgiza masa kai tayi hawaye na bin idon ta tace "Ni na ƙoshi" "Haba Ƙwailar kar muyi haka dake mana, kince bana baki Abinci a baki, nace zan baki kuma kince ba kya so" ya kuma kai cokalin bakin ta, Amma ta ɗauke kanta tana kuka. Sosai ta komawa Ammar ƙaramar Yarinya, har mamaki take bashi ace Yarinya kaman Mufeeda take kuka haka saboda kishi, ajiye spoon ɗin yayi ya ɗan zuba mata ido, sannan ya janyo ta jikin sa yace "kiyi shiru bana son kukan nan, in baki ci Abincin nan ba, nima bazan ci ba" A hankali cikin raɗa yace mata "ina da chocolate a aljihuna in kika ci zan baki, kinji Jaririya ta" ganin Ammar duk jin kan nasa ya zage yana rarrashi ne yasa ta saki fuskarta tayi murmushi, Ammar ne ya bata Abincin cikin salo na rarrashi, gaba ɗaya ta manta da ɓacin ran da take ciki, dan ita wannan rarrashin nata da yake da bata Abinci yasa ta manta da komai. Seda ya tabbatar taci da yawa ta ƙoshi, Sannan ya ƙyaleta shima yaci nasa, karshe a jikin Ammar tayi bacci, ya ɗauke ta ya kaita ɗakin ta ya kwantar da ita. Seda ya tsaya ya ɗan zuba mata ido, haka nan yake jin tausayinta, she's simple minded ita dai burin ta kar yayi fushi da ita, ya daɗe yana kallon ta sannan ya tashi ya tafi ɗakin sa, da yaje ɗakin nasa ma tsaf da shi ta canza masa bedsheets, ta rubuta masa takadda ta ajiye masa, takaddar ɗauke take da kalaman soyayya dana ban haƙuri. Ɗan murmushi yayi yace "She's so kind" ya ajiye takaddar a ƙasan filon sa ya kwanta. Da safe Ammar yana ta shirin fita ya buɗe wardrobe ɗinsa ze ɗauki kaya, Mufeeda ta shirya masa wardrobe ɗin tsaf, amma bega inner wears ɗinsa ba, wayarsa ya ɗauka ya kira Mufeeda tana kitchen taga kiran Ammar, ta ɗaga wayar tace "Hello Baby na ka tashi lafiya?" "lafiya ƙalau, Amma Niba baby bane, ina kika ajiyemin inner wears ɗina?" "Ina kitchen ne, zanzo in ɗakko maka" "Ok" suna gama Waya Ammar ya shiga wanka. Seda ta kammala ta tafi ɗakin Ammar zata ɗakko masa kayan da yake nema, tana zuwa ta duba wardrobe ɗinsa ta ɗakko masa "Hmm Yaya Ammar kenan ga kayan anan kusa amma wai be gansu ba, ko ina ya duba oho" Tana ɗagowa taga ya fito daga wanka, boxers ne kawai a jikin sa yana goge ruwan wanka. Tsorata Mufeeda tayi ta zare ido, bata taɓa ganin namiji a haka ba, wasu zara zaran gashi ne a jikin sa, tun daga kansa ƙirjinsa zuwa ƙafafuwan sa, taga yayi wani irin girma da kwarjini, nan ta shiga zazzare ido. Ammar sarai ya ga tsoro a fuskar Mufeeda Ammar yace "Yawwa kin ɗakko min?" Jinjina masa kai kawai tayi tana kallon sa, yace "miƙomin su nan, ni ba'a nan nake ajiyewa ba" Jiki a sanyaye tana kallon sa tana ɗauke ido, ta ƙaraso ta miƙo masa kayan, maimakon ya karɓi kayan seya riƙe ta, ƙara zare ido tayi tana jan numfashi. "Me kike Kallo" girgiza masa kai tayi tace "bakomai fa" tai maganar kaman za tayi kuka "A'a sekin gayamin me kike kallo?" "wallahi bakomai, ba kallon ka nake ba" "ki gayamin ba abunda zan miki" "Wallahi bango nake kallo ba kai ba" Murmushi ya ɗanyi a ransa yana tuna yadda take masa rangwaɗa da shagwaba ashe ma matsoraciya ce haka. Ya ɗan kashe mata ido yace "ko zaki taɓa gemun ne?" "A'a aikace ba yanzu ba" "A'a na canza ra'ayi ki taɓa mana" Noƙe kafaɗa tayi tace "A'a Abinci na ze ƙone" Sakin ta yayi ta fita da sauri hada haɗawa da gudu, sosai ta bawa Ammar Dariya. Har ya shirya ya fito bata son kallon sa sosai, ko surutun yau babu, da taga zasu haɗa ido seta sunkuyar da kai, idan kuwa suka haɗa ido se Ammar yace "ko in zone? . Da sauri take cewa A'a Haka ya karya ya fice yana dariyar yadda tayi da ido daya riƙe ta. Domin sharhi, Gyara ko Shawara Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 14 Ammar be kai dare ba yau tun azahar ya dawo gida, amma yana zuwa ya tarar da Mufeeda a falo kwance akan kujera, da ƙyar ta iya amsa masa sallamar sa ya kalleta yace "ya dai?" tace "bakomai ya naga ka dawo da wuri yau?" "kince in dena kaiwa dare, na dawo da wuri kuma kina tambaya ta" Ɗan murmushi tayi tace "ai ban san zaka dawo yanzu ba, ban girki ba" "haka kike zama da yunwa in ba na nan, salon Ace bana baki Abinci?" "Ai bana jin yunwa ne, kuma ga cornflakes can, idan naci ya isheni, Abincin yafi daɗi idan ina ci ina kallon ka" Murmushi yayi yace "yanzu me zaki ban, ina jin Yunwa" "ina da miya, bari inje kitchen ɗin in gani" Ammar ya lura da ita kaman jikin ta babu ƙwari, a hankali take komai, ta dafo masa Abinci ta kawo masa, ta koma kan kujera ta kwanta. Ammar yace "wai meke damunki ne?" "Ciki nane yake min ciwo fa" "Shine kike ta faman haɗe rai haka, wannan ciye ciyen naki ma ya isa su saki ciwon cikin ai" Shiru tayi masa ta lumshe idon ta, ya kalle ta yace "ki sakko kici Abinci seki sha magani" Girgiza masa kai tayi alamar A'a,. Ammar yaci Abincin sa ya ƙoshi, ya ture Kwanukan gefe, ya ɗakko wayarsa yana game, a tunanin sa Mufeeda ba dagaske take ba. Can ta ɗan fara juyi tana riƙe cikin ta, tana numfarfashi. Ya kalleta yace "idan banɗaki zaki shiga ki tashi ki tafi mana" Haushi ne ya kamata, tana fama da kanta amma yana mata wata maganar daban, a hasale tace "Idan banɗakin zani ai na sani, ko na taɓa fitsari a falo ne? In haka kake gudu seka dinga samun pampers kar in ɓata maka guri tunda dama ni Jaririya ce" Mamaki ne ya kama Ammar, ko da wasa be taɓa tunanin Mufeeda zata gaya masa baƙar magana ba. Ƙara riƙe cikin ta tayi tana rintse ido, Ammar binta yake da ido kawai, miƙewa tayi tana durƙusawa ta tafi ɗakin ta. Ɗan taɓe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, idon sane ya sauka a inda Mufeeda ta tashi, tayi staining na jini a gurin, ɗan zare ido yayi, dama Mufeeda ta isa fara period ne? 🙄 Miƙewa yayi ya samo ruwa da Omo ya goge gurin, da yake bada yawane inda ta ɓata ɗin ba, shi da farko ya ɗauka kawai rigima take ji, se yanzu ya tabattar bata jin daɗi ne. Ya bita ɗakin dan ganin halin da take ciki, yana shiga ɗakin nata ya tarar ta cire kayan jikin ta, daga ita se underwear hatta ribbon ɗin kanta ta cire shi, gashin ta a wargatse tana durƙushe a gaban gado, ta tattaro bedsheet ɗin kan gadon ta tada kai dashi tana kuka, ga fanka se gudu take amma ita ta haɗa gumi sosai se kace me naƙuda. Daidaita nutsuwar sa yayi, ya ƙarasa da sauri ya ɗago ta, ya ƙare mata kallo, Mufeeda ba farace tas ba amma chocolate ce me haske, fatar ta tana da matukar ɗaukar ido se sheƙi take, ga wannan sassanyan ƙamshin da take me kashe masa jiki A hankali yace " sannu ban zaci abun ya kai haka ba, daure kisa kayan ki se muje Asibiti" Ɗan ƙura masa ido tayi sannan ta ƙara kwanciya a jikin sa tace "bazan iya tafiya yanzu ba, ka bari ya lafamin, kuma ma daka ƙyaleni ze dena fa" "No gara muje Asibitin dai" Ɗan lumshe ido tareda yamutsa fuska alamar tana jin jiki, a hankali kaman me raɗa tace "bari ya ɗan lafamin, yanzu ina jin ciwon sosai" "shikenan sannu" Bata iya amsawa ba se lumshe ido da tayi, a hankali Ammar ya kai hannun sa kan gashin ta yana shafawa, zuciyar Ammar ta shiga bugawa da ƙarfi tana raya masa abubuwa da dama akan Mufeeda, Amma wani ɓangaren na zuciyar sa na ƙoƙarin kawar masa da tunanin da yake. Ɗan yamutsa fuska ta kuma yi tana miƙe ƙafafuwan ta tace "Yaya Ammar Ciwo" Ya riƙe hannayen ta yace "Sannu ze dena Insha Allah" Gaba ɗaya tausayi take bashi, yana tuna wani littafi daya taɓa karantawa me suna (MATA A LOKACIN HAILA) Mata na shiga mawuyacin hali a wannan lokacin, wani yanayi ne wanda inba wanda yake jinin ba baze gane ba, sukan shiga halin takura, yawan ƙunci, kasala tashin zuciya, yawan faɗa da saurin fusata, kwaɗayi kaman masu ƙaramin ciki, yawan kuka ko san kaɗaici da dai sauran su, ga uwa uba Wannan ciwon da wasu matan kan yi, ciwo ne me wahala matuƙa wata duk lokacin da za tayi seta kwanta rashin lafiya sosai, ciwon mara me haɗe da ciwon ciki da gudawa, ko kuma ciwon baya da ƙafafuwa, wasu kuma hada amai da zazzabi ƙuraje su fito su ɓata musu fuska, wannan ma ya ishesu shiga damuwa, wata idan tana wannan ciwon kaman zararriya haka take, wata harta gama Al'ada bata san saka kaya, se dai marasa nauyi, wata kuma komai sanyi zata dinga kwanciya a guri me sanyi ko cin abu me matukar sanyi, da dai sauran su. Dan haka yake da mahimmanci miji kokuma wanda yake tare da Mace ya gane idan mace tana irin wannan yanayin ayi mata uzuri, ba kowane lokaci mata suke wani abun suna sane ba, sedai dan kusan gaba ɗaya rayuwar su cikin yanayi ne na hormones da suke sauyasu lokacin al'ada, lokacin da suke da ƙaramin ciki ko kuma idan cikin ya tsufa. Kallon ta ya ci gaba daya, bacci ne yayi gaba da ita, dan haka Ammar yasa mata filo ya kwantar da ita ya fita. Se la'asar sannan ta farka, ta shiga tayi wanka ta samu ta saka kaya a jikin ta, ta gyara gadon ta ta nemi guri ta zauna. Ammar ya dawo ɗakin yaga har tayi wanka ta canza kaya, ya kalle ta yace "ya jikin?" "Da sauƙi Alhamdilillah" "Saka hijjabinki kizo mu tafi" Kaman tace masa A'a amma ta fasa saboda yanzu seya ɓata rai, haka ta saka hijjabi ta fito. A hankali take tafiyar, Ammar ya riƙo ta suka fito zuwa cikin a daidai ta sahunsa, Matan layin da yake sana'ar su ce leƙen ƙofar gida suna gulma, suna ganin Ammar ya riƙo Mufeeda sun fito gaba ɗaya hankalin su ya koma kansu, yasa Mufeeda a babur ɗin ya zagaya ya zauna a mazaunin direba ya kunna suka tafi. Suna tafiya matan layin suka dasa gulmar su, wasu suna itace matar gidan, wasu suna ba ita bace ba sedai ko baƙuwa suka yi ko 'yar uwassa ce, da yake basu san itace matar gidan ba. Wani Clinic na kuɗi ya kaita, suna zuwa ta samu guri ta zauna Ammar yaje aka buɗe mata file, sannan suka shiga gurin ganin likita. Suka gaisa da Likitan, ya kalle su yace "to kai ta kawo ko kai ka kawo ta" Ammar yace "itace ba lafiya" Likitan ya kalleta yace "meya ke damun ki ne?" Kallon Ammar tayi tai shiru, Ammar yace "kiyi magana mana" "Ciki nane yake min ciwo" Ammar yace "ba ciki ba dai mara ko?" Kunya ce ta kamata tai shiru tare da sunkuyar da kai. Likitan yai murmushi yace "Nagane, menstrual cramp ne, yaushe kika fara?" "haka yake min idan zanyi" "Yaushe kika fara menstruation?" "four years back" Ba Likitan ba har Ammar seda ya kalleta Ammar yace "are you sure?" "Very sure" ta bashi amsa Likitan yace "Ok hakan ba wani abun damuwa bane, mata suna shiga wannan yanayin idan suna Al'ada, sedai a kula da ita da abubuwan da zata ci, Sannan idan ta samu ma nemi a mata Aure, idan akayi musu Aure in akayi sa'a wasu yana raguwa koma su rabu dashi baki ɗaya" Ita dai Mufeeda ba tace komai ba. Likitan yace "tsakanin magani da Allura wanne kike so?" Kafin tayi magana Ammar yace "Allura zaka rubuta mata" Zare ido tayi tace "Haba Yaya Ammar wallahi bana son Allura, dan Allah kar ayimin" "Likita rubuta mata Allura, Allura tafi quick Action, in ba haka ba muka koma gida zuwa zata yi ta cigaba da lanƙwashewa" Mufeeda tuni ta fara kuka, liktan yace "We have to respect her autonomy, tunda magani take so a rubuta mata" Ammar yace "No Allura zaka rubuta mata" Haka likitan ya rubuta mata Allura da sauran magungunan, ya kalle Mufeeda yace "Sorry Baby Allura ba zafi fa, Wannan Yayan naki yace se an miki Allura" Basu kuma kulashi ba, Ammar ya sunkuya yace mata "gobe ma ki ƙara min rashin kunya, ina sane nace a miki Allura" zumɓura baki tayi suka fito daga OPD ɗin, Ammar yace ta zauna ya siyo maganin, ta zauna tana jiran sa. Bayan ya siyo maganin ne yaci karo da Faruk, suka gaisa Faruk yace "Ahh mutumina me kake anan?" "Mufeeda ce bata jin daɗi na kawo ta A duba ta" "Allah sarki, nima nazo in duba wasu patients ɗina ne da na yiwa CS jiya, muje semu gaisa tunda kuka tare ko leƙoku ban kuma yi ba" Suka tafi tare suna hira, Faruk yaga Mufeeda ta ƙara ƙiba, dukda kuka take amma tayi wani fresh da ita, Faruk yace "Madam har yanzu ba'a dena rikici ba? Hala laulayi ne?" Ammar yace "Haihuwa zata yi ba laulayi ba" Ganin irin kallon da Faruk ke mata yasa Mufeeda tace "Na gaji Mu tafi" Ammar yace "to Faruk se anjima se munyi waya" ya kama hannun Mufeeda suka tafi Injection room. Fafur Mufeeda taƙi shiga Nurses suyi mata allurar, Ammar ya fara ƙulewa ya janyo ta zuwa cikin gurin, kuka take sosai kamar wadda za'a yanka. Ammar yace "haba Autar Baba sonake ki warke da wuri shiyasa nace ayi miki allurar ai, hug me you won't feel the pain" Ya buɗe mata hannayen sa, a hankali ta ƙarasa ta kwanta a jikin sa, ya riƙe ta, Nurse ɗin tace "Ikon Allah, dan Allah ƙanwarka ce ko matar ka?" da yake babbar mace ce dan haka Ammar ya bata amsa "Mata ta ce" "gaskiya ran haihuwa da kallo, Allura kawai tana wannan abun, Allah ya ƙara maka haƙuri ɗan nan, kana fama da shagwaba" murmushi kawai Ammar yayi. A hakan ma da ƙyar ta tsaya aka yi, Hawaye sharkaf fuskarta, maimakon da'aka gama ta tashi sema ƙara narke masa da tayi a jiki tana kuka. Ammar yace "ya isa haka harfa an gama, Insha Allah yanzu zaki dena jin ciwon" "Wallahi Allurar da zafi sosai" "to ai zafin kaɗan ne akan ciwon da kike ciki" Nan ta shiga zabga shagwaɓarta, ƙarshe nurse ɗin se fita tayi tabar musu room ɗin. Ammar yace "ki tashi mu tafi kinji an fara kiran sallar magariba" Noƙe masa kafaɗa tayi, "idan munje gida zan baki biscuit ai zaki ci ko Jariri ya ta?" Murmushi tayi masa tana lumshe ido, a hankali ta miƙe ta biyo shi suka fito, suka hau babur ɗin su zuwa gida. Da sukaje gida Mufeeda tace ita ba zata iya tafiya ba, ƙafar ta ta sage jikin ta babu ƙwari, ƙarshe seda Ammar ya ɗauke ta ya kaita har kan gadon ta a ranta tace "tunda kasa akamin Allura se kayi jinya kaima" Ammar yaje yayi salla, ya dafo mata tea ya kawo mata, ta karɓa ta sha sannan ya miƙo mata ledar pharmacy yace "gashi nan pampers ɗin da kika ce in sai miki ne" ta kalle shi tace "Pampers kuma?" "Eh mana ko kin manta ne?" Karɓar ledar tayi ta duba, pad ce guda uku da sababbin pants guda biyar, wata kunyace ta kama ta, banda abun Ammar panties ɗinta kona lefe bata taɓa ba amma ya sai wasu. Sunkuyar da kai tayi taƙi ɗagowa su haɗa ido. Yace "zanje masallaci idan nayi sallar isha'i zan ɗan za gaya, kinga yau ban samu nayi aiki ba yadda yakamata" "Shikenan amma karka yi dare sosai dan Allah" Jinjina mata kai yayi, ya miƙe ya fita. Bayan ya idar da Sallar isha'ine Aminu ya kira shi yace "yana so su haɗu za suje gidan Jabir" Haka kuwa akayi a gidan Jabir suka haɗu, Jabir yayi farincikin zuwan su, Yace "Kai Ammar Mufeeda ta ɓoye ka, ko a hanya sam bama haɗuwa, ga yadda kayi kumatu" Yaita zolayar Ammar sannan yai musu iso zuwa cikin gidan, falon sa ya kaisu suka zauna suka dinga hira, Can Ammar yace "Jabir abar hirar nan muyi abunda ya kawo mu? Ina matar gidan ne?" Jabir yace "tana gidan ɗakin ta" "a gaskiya naji wani labari dabe min daɗi ba game da auren ka, Jabir ya'akayi haka ta faru?" Jabir yace "bari Ammar ai nayi zaɓen tumun dare dana san haka Auren yake da banyi ba, wallahi mata basu da mutunci nayi dana sanin Auren Saima" Ammar yace "Dana sanin mene?" "Yarinyar nan sam bata da Mutunci bata ganin girma na, bata da tarbiyya Sam, ban isa in gaya mata taji ba, wallahi badan ina tsoron abunda iyayena zasu ce ba da tuni na sake ta" Aminu zeyi Magana sega Saima ta fito, tana ganin su ta faɗaɗa murmushin ta tace "Manyan Baƙi aini har nayi fushi, sau ɗaya kuka zo mana tun bayan bikin mu, Ammar ina Amaryar?" "tana gida, idan ma baku zoba zan kawo ta Insha Allah" Saima tace "Insha Allah ai zanzo har gida mu gaisa, Jabir baka gayamin sunzo ba ai be kamata abar baƙi babu ko ruwan sha ba, bari in baku ruwa" Ta wuce ta nufi kitchen, Jabir yaja wani uban tsaki yace "Munafukar Banza" Aminu yace "Subhanallah, haba Jabir a gaban mu kake kiran ta Munafuka" "mece idan ba Munafukar ba, danta ganku take nuna ita ta Allah ce, Amma tafi sheɗan iya rashin mutunci" Saima ta dawo da lemuka da ruwa faranti da kofuna, ta ajiye Musu a gaban su. Saima ta kalli Su Ammar idon ta fal Hawaye tace "Aminu wallahi Abokin ku Azzalumi ne, dan Allah ku gaya masa idan mutum ya auri mace baya na nufin ya auro baiwa bane, Jabir Jahili ne besan darajar ɗan Adam ba" Miƙewa Jabir yayi yana zare ido, ya fara narko mata Ashar, Saima tace "Wallahi ba iyaye na ba sedai naka" Da sauri Aminu ya miƙe ya riƙe jabir yace "Jabir meye haka? Matarka ta Aure kake wa wannan mummuna ashar agaban abokan ka?" Saima tace "baka ga komai ba a gurin sa, dana san haka yake wallahi bazan Aure shi ba, mutanen kirki suka fito suna sona na liƙe nabi soyayya nace seshi, amma bayan Auren mu, shine kullum cikin chatting da 'yan mata, ba dare ba rana lokacin da nake buƙatar lokacin sa lokacin ne yake chatting, idan nayi magana seya ce wai na taɓa ganin anyi campaign bayan zaɓe? Da ina haƙuri ina ƙyale shi, Amma Ba damar inyi masa laifi se ya fara zagarmin iyaye, wallahi baka isa ba iyaye basu fi iyaye ba kakuma zagarmin iyaye sena zagi naka iyayen " Ammar yace "Saima yi haƙuri ki koma ɗaki, zamuyi magana da Jabir " Haka ta wuce ɗaki tana kuka, Aminu yace "gaskiya Jabir kaine mafarin samar da matsala a cikin gidan ka, ta yaya zaka dinga ce mata ba'a campaign bayan zaɓe, hakan fa na nuna bata da wani mahimmanci a gurin ka, haba dan Allah Jabir kaman ba wayayye ba kaima fa kana da ƙanne mata baza kaso ayi musu haka ba, kuma wallahi in gaya maka kaida ta ƙara ganin mutuncin ka har gaban abada sedai tayi pretending, amma a matsayin ka na namiji daga lokacin da ka buɗe baki ka zage ta ka zagi iyayen ta mutuncin ka ya zube a idon ta musamman idan ta buɗe baki ta rama, Jabir meye Amfanin hulɗa da 'yan matan daba Auren su zakai ba bayan ga matarka ta halal a gefen ka? Kawai ka zauna fadi banza faɗi wofi a haka har sheɗan ya kawo muku wani tunani na daban" Ammar shiru Yayi yana tunani, ya tuna Yadda Jabir yake Soyayya da Saima kaman babu wata mace da tai Saura a duniya sama da ita. Ammar yace "tabbas Jabir kana da laifi, ba kowane ze iya jure ka zagi iyayen sa yai maka shiru ba duk mutuncin ka da yake gani, karka manta da haƙoran ta bayan iyayen ta sun gama ɗawainiya da ita ka ganta ka aura, babu yadda zata iya jure cin zarafin su gaskiya, kaman yadda bamu da juriya da jarumta irin na iyayen mu haka suma matan basu da haƙuri da biyayya kaman na iyayen mu duk sedai muyi haƙuri da juna, amma batun chatting da 'yan mata lokacin da matarka ke buƙatar lokacin ka, to tabbas idan me raunin Imani ce hakan zesa itama ta fara tunanin fara chatting da wasu mazan" Suka dinga yiwa Jabir Nasiha, zasu tafi ne Saima ta fito idon ta jawur saboda kuka ta miƙawa Ammar turaren wuta, da humra tace "Ammar gashi ka kaiwa Amarya a bata haƙuri, Insha Allah ina nan tafe mu gaisa, Kaikuma Aminu se Fiddausi ta haihu ma haɗu" Ammar yace "to mungode zan gaya mata Insha Allah, sannan Adinga haƙuri ana kai zuciya nesa saima, a unguwar mu babu wanda be san Soyayyar ku da Jabir ba, be kamata ace daga yin Auren ku hakan tana faruwa ba" Murmushi me ciwo Saima tayi tace "Ammar kenan, Soyayyar nan duk a baki ce ya nunamin, kudai ina muku fatan Alkhairi ku gaida gida" ta juya ɗakin ta tana sharce hawaye. Ammar yake tunanin ita kuwa wani irin pain take ji a zuciyar ta har take wannan kukan haka. Su kayi wa Jabir sallama suka tafi, seda Ammar da Aminu suka ƙara tattaunawa akan batun, Ammar yace "gaskiya Aminu lamarin rayuwar nan akwai ban tsoro, shiyasa naita gudun yin Aure a baya" "Ammar kenan, ai abun dace ne, kaga ni babu wata babbar matsala da nake fuskanta tsakanina da fiddausi se tarkacen ƙawaye da yawon maƙota, sune babbar matsalar ta, nayi nayi ta dena taƙi, Amma ta wani ɓangaren idan na duba alkhairan ta se in share ta kawai inyi haƙuri tunda nima haƙuri take dani" Suka gama taɗinsu sannan Ammar ya nufi gida, ya ɗan tsaya a hanya yaiwa Mufeeda siyayya, sannan ya tafi gida, tunani yake tayi ya gano me Mufeeda take yi wanda baya so, amma ya kasa ganowa se yai tunanin ko dan Yarinya ce, ko kuma tana jin tsoro nane yasa bata min wasu abubuwan? Ko dan bamu daɗe tare ba? A'a wannan Yarinyar da tana jin tsorona da bata tunkareni ta kalli tsabar idona tace tana sona ba wata zuciyar ta bashi amsa. Da wannan tunane tunanen yaje gida, se daya duba agogonsa yaga sha ɗaya na dare. Aikuwa yana shiga tana falo a zaune tana rarraba ido, tana ganin sa ta miƙe "Yaya Ammar ina ka tsaya haka? Har na fara tsorata ko wani abun ne ya same ka" "Sarkin tsoro, ba abunda ya sameni gani na dawo" "gaskiya ka daɗe sosai" "Ai gani na dawo dai, ya jikin naki?" "Naji sauƙi Alhamdilillah" "Haka ake so, ungo gashi nan ki samu Kisha, tunda yau baki ci Abun kirki ba" Ƙatuwar Jarkar yoghurt ce a ciki, Murmushi tayi tace "Masha Allah, Nagode sosai mijina Allah ya baka Aljanna maɗaukakiya, Yasa ka gama da duniya lafiya" "Ameen" Ta ɗakko kofi ta zubawa Ammar ta bashi yace shi baya sha, ita dai ta sha ya sata a gaba ta sha sosai sannan ta ajiye sauran. Ta kalle shi tace "Mijina meke damunka ne? Naga kaman akwai damuwa tare da kai" Kallon ta yayi da mamaki ya akai ta gane yana da damuwa. Ya maze yace "gajiya ce ni babu wata damuwa dake raina" "idan gajiya ce kawai take damun ka ina ganewa, yau yanayi ya nunamin bayan gajiya akwai damuwa" Miƙewa yayi yace "jeki kwanta seda Safe" Bayan sa tabi da kallo daga bisani ta miƙe ta tafi ɗakin ta, yau ta sha baccin rana, saboda rashin lafiyar ta, dan haka ta kasa bacci, tana ta tunanin meke damun Ammar? "dole inyi wani abu kar ya kwana da damuwa. Ta ɗakko wayar ta tura masa saƙo "My love, hau online kaga wani abu" Ya tura mata "me kike baki Bacci ba?" "Nakasa baccin ne, ka hau ka gani" Ya buɗe data ɗinsa ya shiga what's App, hoton ta ta tura masa, tayi wa gashin kanta ado, ga wata body hook ce a jikin ta pink, leɓen ta raɗau da jambaki se shining yake, ta ɗan turo baki ta lanƙwasa wuya, a haka ta ɗau hoton ta ɗora waƙa me daɗi akan hoton. Ammar na buɗe hoton besan lokacin da ga tura mata "Wow Masha Allah" Wani murmushi tayi tana daga kwance ta tashi zaune, ta tura masa "Nayi kyau?" "Ba laifi kin kusa yin kyau, dama kin girma ne da se yafi kyau" Sosai Mufeeda tayi dariya, baze ce tayi kyau ba sedai ya kushe ta. Ta tura masa "Mijin baby wani jambaki yafi min kyau?" "kowanne" ya bata Amsa. "shikenan gobe idan na saka zaka ce nayi kyau?" "ba tabbas dan ba wani kyau kike ba idan kin saka, seki koma kaman 'yar ƙauye" ya rubuta yana murmushi. Emoji ɗin haɗe rai ta tura masa tare da "nice mummuna ko? Sena gayawa Umma kana cemin mummuna" "Ke ki kwanta dare yayi fa" "to My love, you do your task very well today ka kula da Jaririyar ka, nagode sosai Allah ya ƙara Arziki, da naso inyi fushi saboda kasa anmin Allura, amma bazan iya ba nagode sosai da kulawar ka miji nagari, Allah ya barmin kai har ƙarshen rayuwa ta" "Me a daidaita sahun kike so har ƙarshen rayuwar ki?" "Ko sana'ar da kake bata kai ta a daidaita sahu ba, ai halal kake nema, kuma ni ba sana'arka ce a gabana ba, kai nake so Ammar ɗina" Tayi mai voice message kaman me raɗa take cewa "I love you my Ammar have a nice dreams" Shiru Ammar yayi yana jujjuya wayar a hannun sa yana kuma duba chatting ɗin sa da Mufeeda. Murmushi yayi ya kwanta wani daddaɗan bacci yayi awon gaba da shi. (to su Yaya Ammar ko an faller ne🙄🙄🙄) Ina godiya da ƙauna da kulawar ku. Ƙofata a buɗe take, domin gyara sharhi, ko kuma shawara nagode sosai 😍 😍 😍 Ayshercool 07063065680 .✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 15 Da Safe Ammar ya fito, se dai Mufeeda bata saka jambakin ba kaman yadda yayi tsammani, haushin kansa ne ya kama shi, komeya na son ganin ta da Jambakin ma oho, haka sama sama ya tambaye ta ya jiki, Sarai ta gane abunda yasa shi haɗe rai Tace "Jiki da sauƙi Alhamdilillah tunda Mijina yana tare dani" Ƙin kula ta yayi ya karya abunsa yana wani basarwa. Da ya gama ya kalle ta yace "ya kamata ki shiga ku gaisa da maƙwabta, ɗazu mun haɗu da maigidan dake kallon namu, yace min baki shiga kun gaisa da matan su ba, kuma haka ake yi" "to idan naje me zance musu?" "nima ban sani ba" ya bata amsa. "ce musu zanyi nice matar gidan nan, kokuma Jaririyar Yaya Ammar?" shiru ya mata tare da yi mata wata uwar harara. Mufeeda tace "shikenan zan shiga Insha Allah" "Sannan kuma ba cewa nayi kuma kidinga shige2 ba da tarkacen Maƙota ba, cewa nayi kawai ku gaisa bana son shige2" "Shikenan insha Allah zan kiyaye, dama niba me shige shigen bace, saboda bana son takura da sa ido" Ya gama karyawar sa ya shirya ya fita, yana ƙoƙarin tada babur ɗin sa ya fita da shi ne Mufeeda ta ƙaraso da sauri ta riƙe ƙarfen Babur ɗin, cikin shagwaɓar ta ta tace "Wai fita zakayi?" "A'a zama zanyi, in kinji yunwa ki dafani ki cinye" "idan na dafa ka na cinye na zauna da wa? Wani abu nake son baka ne" Juyowa yayi yana kallon ta, ba zato ba tsammani ta sumbace shi a kumatun sa na hagu tace "take a good care of your self My love, Allah ya kiyaye hanya, ya wadata mu da halal" tsayawa yayi yana kallon ta, yayin da ita kuma ta koma gida. Seda ta kammala aikace2 da zata yi a gidan sannan ta shiga maƙota suka gaisa kaman yadda Ammar ya urmace ta, wasu sun bayyana mamakin su kan cewar itace matar gidan, yayin da wasu kuma suka ɓoye hakan, ita kuwa ko a jikin ta, tai musu sallama ta koma gida. Ta koma gidan ta babu daɗewa Yaya Usman ya kira ta a waya yace "ke buɗe mana ƙofa muna waje. Aida gudu ta miƙe ta tafi gate ta buɗe, gurin Baba ta tafi da gudu ta rungume shi, Baba ya shafa kanta yace "I really miss you Auta na" Mama tace "Baban ki kaɗai kika gani ko? Ni baki ganni ba" Ta ɗan tura baki tace "Aini duk fushi nake, tunda aka kawo ni masoyyiya Amina ce kawai tazo gidan nan" Yaya Usman yace "mu koma kenan?" Tai murmushi tace "ni bance ba" Mota biyu suka yi, duk Yayyen ta da yaran su, haka suka zo. Mufeeda ta rasa inda zata saka ranta dan murna, nan suka shiga shigo da kayan Abinci na garar Mufeeda. Yaya Fadeela tace "Auta naga kin ƙara haske ko dai an gamu ne?" "Eh na gamu dake mana" Anty Murja tace "Lallai Autar Baba, wallahi kin ƙara nutsuwa" Suka dinga tsokanar ta. Taji daɗin ganin 'yan gidan su, nan suka dinga hira, tana raha. Sedai ba' azo da Yaya Amina ba cikin ta ya tsufa. Mufeeda tace "Mama bari in kira shi, yazo ku gaisa" Mama tace "A' a, ƙyale shi kar a takura masa" Iyayen Mufeeda sunji daɗin yadda suka ga Mufeeda ƙalau da ita, alamu sun nuna gidan Ammar ba yunwa yana iya ƙoƙarin sa. Se la'asar sannan suka yi mata Sallama, da zasu tafi Baba ya bawa Mufeeda Naira dubu goma taita godiya, suka ce ta gaida Ammar, sannan suka tafi. Mufeeda taga uban kayan garar da Baba yayi mata, ta dinga murna tace "Allah ya biya ka da Aljanna Baba na, kwana biyu Yaya Ammar ya huta" Bayan la'asar Ammar ya dawo, seda ta bari yaci Abinci ya huta take gaya masa su Mama sunzo. "meyasa baki kirani kin gayamin ba?" "Baba ne yace in ƙyale ka, maybe kana aiki kar a takura maka" "Gaskiya banji daɗi ba, naso a ce nazo na tarar dashi" "Dukan su suka zo harda su Anty Murja gaba ɗayan su" "Naso mun haɗu dasu, but insha Allah very soon zamuje" "duk suna gaishe ka" "Ina amsawa" Yana zaune yana kallo, yaga Mufeeda tana cin wani abu, ya kalleta yace "me kike ci? Se an jima ki lanƙwashe kice ciki na ciwo ko?" "gullisuwa ce fa" Ammar yace "Madarar kike gullisuwa da ita, za'a raba madara kowa ya ɗau tasa, in kika ƙarar da taki seki koma shan tea baƙi ko kuma cin cornflakes ba madara" Ɗan tura baki tayi tace "idan na shanye semu koma shan taka" "Seki sha ɗin in gani" "Ai da kanka zaka bani, saboda bazaka iya shan shayi da madara ni kuma ka bani ba madara ba" Hararta yayi ya ɗauke kansa Wani cup ta ɗakko me kyau da murfin sa a jiki ta miƙa masa kofin tace "ungo naka" Ya kalleta yace "meye wannan?" "taka gullisuwar ce" "Ni bana shan wannan kayan shiriritar da yarinta, kedai kije kiyi tayi" "da daɗi fa ka ɗanɗana kaji" Girgiza mata kai yayi yace "Ke nace bana so" Ta ƙyale shi bata kuma takura masa ba, se bayan ya dawo daga sallar magariba Mufeeda tace "Yaya Ammar zo kaga" Tana ɗakin tsakar gida, dan haka ya leƙa ɗakin, kayan Abincin daya gani a ɗakin ne ya sashi yin turus, yace "Wannan fa?" "Kayan gara ne dasu su Baba suka kawo mana" Shiru yayi yana kallon kayan yace "Amma wannan kayan ai sunyi yawa ya zamuyi dasu, ni badan ina tsoron kar Baba yaji babu daɗi ba gaskiya da bazan karɓi kayan nan ba" "Haba Yaya Ammar meye sa? Ai bamu kaɗai zamuyi Amfani da kayan ba, za'a ɗibarwa su Abba, Su Yaya Maryam ma duk a basu, Baba zeji ba daɗi idan kai magana akai" Ɗan girgiza kai Ammar yayi yace "Kayan nan sunyi Yawa fa" "Yaya Ammar babu wani yawa da suka yi, da Baba baze iya ba baze takura kansa yace se yayi ba, dan Allah kawai ka bar zancen nan, muci Abincin mu kawai ko?" Tai maganar tana leƙa fuskarsa, wani ɗan murmushi yayi wanda iya kacinsa leɓensa, ya koma falo, ya kalleta yace " Ni zan kwanta seda safe" "Amma ina fatan ba ranka ne ya ɓaci ba akan kayan nan?" Girgiza mata kai yayi yace "A'a inajin Bacci ne kawai" "shikenan Allah ya tashemu lafiya" Yace "Ameen" ya wuce ɗakin sa itama ta wuce nata. Harta kwanta taji kawai bata ji daɗin yanayin yadda ya tafi kwanta ba, dan haka ta miƙe ta fito ta tafi ɗakin sa. Har ya kashe fitila ya kwanta, ta shiga da sallama sannan ta kira sunan sa Amsa mata yayi sannan yace "Ya a kayi?" Gadon ta hau ba tsammani yaji Mufeeda a jikin sa, a hankali yace "lafiya kuwa?" "Yaya Ammar zuciya ta ta kasa samun nutsuwa, gaba ɗaya yanayin ka tun jiya zuwa yau baya mun daɗi, dan Allah idan laifi nayi maka kayi haƙuri" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ni nace kin min laifi ne?" "Yanayin ka ke nuna kaman na maka laifi, bana jin daɗin ganin ka a haka, idan kuma akan kayan nan ne se in kira Yaya Usman yazo a mayar da su" Tai maganar jikin ta a sanyaye, gyara kwanciyar sa yayi yace "ni babu abunda kika yi min, kawai dai ɗan Adam dole wataran ya tashi babu daɗi shikenan kawai" Kwanciya tayi sosai a jikin sa tace "Duk da haka yana da kyau in san damuwar mijina, dukda Mijin nawa yana ganin Yarin ta ta, Amma bazan so in ganshi cikin damuwa ba" Nannuyar Ajiyar zuciya Ammar ya sauke, yace "Naji zan dena damuwa, tashi kije ki kwanta seda safe" "Zan tafi Amma buɗe bakin ka" "Me yasa zan buɗe bakina" Yana maganar ne ta saka masa Gullisuwa a bakin sa, shiru yayi yana tunawa, tayi masa daɗi Sosai dukda shi irin wannan abubuwan basa gaban sa yana ganin kaman shirita ne. Wata ta kuma saka masa a bakin sa, ƙamshin turaren jikin ta, da yadda ta kwanta a jikin sa ya sashi cikin wani farinciki dabe san dalilin sa ba. A hankali cikin raɗa tace masa "da Daɗi kuwa?" "Babu daɗi kaman inyi amai" Murmushi tayi tace "koma babu daɗi tunda ka riga ka sha shikenan za'a raba madara dai dai, kuma tawa seta fi Yawa" "Naji tashi ki bani guri, mara kunya ji yadda kika biyoni har ɗaki kika wani kwanta min a jiki" "Ba jikin mijina bane, kuma dai naga ni Yarinya ce" Kasa cewa komai yayu, Ƙasan zuciyar Ammar kuwa bugawa yake da ƙarfi yana saƙawa yana kwance abubuwa daban daban game da matar tasa da yake mata kallon tayi ƙanƙanta da Aure. Miƙewa Tayi daga jikin sa, ta sumbaci goshin sa tace "Honey seda safe, I love you Baby" Riƙe hannayen ta yayi, kaman ya hana ta tafiya, se wata zuciyar tace masa "She's still young, Yarinya ce raini ze shiga tsakani na da ita, tayi ƙanƙanta" Sakin hannayen ta yayi kaman an masa dole yace "Seda Safe" ya juya mata baya. Dukda a cikin duhu ne bin bayan sa Mufeeda tayi da kallo tareda ɗan girgiza kai, Ammar akwai taurin kai da izza. Ta koma ɗakin ta, Ammar kam baccin sa rabi da rabi ne, juyi kawai yake akan gadon har Asuba. Da safe yana fitowa yai tozali da ita akan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana ta kaɗa ƙafa ta sha kwalliya ta kashe ɗauri, bakin ta se shining yake da jambaki, ga ƙamshin girki dana turare ya gauraye falon, gani yake kaman tana sane take wannan abubuwan. A hankali ya tako falon kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki, ya samu guri ya zauna, ta ɗago ta kalle shi tare da yi masa murmushi, ta taso daga inda take tazo gaban sa ta durƙusa ƙasa tace "Barka da Safiya Yallaɓai" kallon ta yayi tayi kyau sosai, yana jin daɗin yadda lokuta da yawa take bashi girma, wani lokacin kuma ta maida shi kaman ƙaramin yaro, yace "lafiya ƙalau prof. Kin tashi lafiya?" Miƙewa tayi ta zauna a kusa dashi ta ɗan tura baki tace "Bayan jiya dan naje ɗakin ka ka koreni" Murmushi ya ɗanyi bece komai ba, ji yake kaman yace mata tayi kyau, amma ya fasa. Ta jingina a jikin sa tace "A kawo breakfast ne?" "Bari se anjima kaɗan" "yau bazaka fita da wuri bane?" "Eh se lokacin salla yayi zan fita" Mufeeda a ranta tace "Yaya Ammar manya maganin ƙanana, na gane Lagon ka sarai, Jambakin nan da gashin nan ba ƙaramin tafiya suke da kai ba" Ta kamo hannun sa tace "Yau Friday ya kamata a yanke maka farce" bece komai ba ita kuma ta ci gaba da wasa da yatsun hannun sa, can ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa takai hannun ta fuskar sa tace "in taɓa?" "in kika taɓa sekin biya" "dan Allah sau ɗaya fa" "kika isheni sena aske gemun nan" "aikuwa idan ka aske na dena kulaka, dan ina son gemun nan sosai" Ammar yace "tashi ki kawomin Abinci" Ta tashi ta kawo masa Abinci, ta haɗa musu Tea, zata sa masa Madara yace "bar madarar nan ki shanye abarki, naga ta kusa ƙarewa" "Se insha tea da Madara kai kuma ka sha ba Madara?" "Eh kece 'yar gayu ai, ni ban damu da shan me Madara ba, kiyi Addu'a Allah ya hore kafin ta ƙare in siyo wata" Shiru tayi tana kallon sa, duk faɗan Ammar yana da sauƙin kai Sosai, kuma yana matukar ƙoƙarin ganin ya wadata da Abinci, baya bata Abinci mara daɗi, ko alawar da tayi jiya da madarar be mata faɗa ba. "Allah ya ƙara maka Arziki na halal My love" "Ameen" ya amsa mata. Suka kammala karyawa, ta ɗakko nail cuter ta yanke masa farce tsaf. Ammar yace "in Allah ya kaimu ranar Saturday zamu ɗan fita, Umma nata mita har yanzu ban kaiki ba" "Wayyo Allah daɗi, Allah ya kaimu lafiya nima na ƙagu ka kaini in gansu" Wasa2 Ammar seda ya kusa makara zuwa masallaci saboda yadda Mufeeda ta narke masa a jiki take ta zuba taɓarar ta iri2. Se azahar sannan yai wankan juma'a ya fita salla. ****************** Fa'iza taga abubuwa sunƙi tafiya yadda take so, ta kuma wanke ƙafa ta tafi gidan Yaya Jidda, suna ta hira Fa'iza fa sako maganar gidan Ammar "Nikam Yaya Jidda kinje gidan Yaya Ammar kuwa?" "hmm ina fa naje, idan naje gurin wa zani gurin wannan ƙwailar Yarinyar kokuwa? Bani da lokacin su daga shi har ita" "Amma ai gidan ɗan uwan ki ne Yaya Jidda ya kamata ku dinga zuwa kiga a wani hali hake ciki? Idan kuma ya tattara ya koma gurin ta gaba ɗaya fa, ku kuma ko oho kenan?" "Aini bana son zuwa inga abunda ze ɓata min rai, ranar da nayi masa magana akan wulaƙancin da tayi muku, seda mukayi faɗa dashi ya kare ta" Fa'iza tace "kinji abunda nake gaya miki ko Yaya Jidda wallahi ki dinga zuwa, idan ba haka ba ana ganin ƙanƙantar ta da haka zata raba shi da kowa, tunda tun yanzu ya fara goyon bayan ta" Jidda tace "kuma fa hakane, zanyi ƙoƙari inje gidan nasa, zan kuma yiwa umma maganar ta ja masa kunne, akan ya kula da 'yan uwan sa, dan nasan ita zata gaya masa yaji ko kuma Maryam, in be ga dama ba idan Maryam ta faɗi magana ze rusa maganar uban kowa ya ɗau tata, duk wannan masifar tasa ita baya yi mata" Fa' iza tace "haba dai Yaya Maryam ɗin?" "ita fa, ai baya shiri da kowa a cikin mu kamar ita, indai Maryam na san abu ze hana kansa ya hana uban kowa ya bata" Jinjina kai Fa'iza tayi, a ranta tace "dole inje in ziga Yaya Maryam itama, zata taimaka min" Suka ci gaba da hirar su daga nan suka yi sallama. A hanya Fa'iza tana tafe tana zancen zuci akan ya zata ɓullowa lamarin Ammar, taji ana mata horn tsayawa tayi ta juya, me motar yazo dai2 inda take sannan ya sauke baƙin gashin motar yace "Manya maganin ƙanana, ke kuwa talaka na ganin ki" Murmushi tayi tace "Ba gashi ka ganni ba, yaushe rabon da in ganka?" "Shigo motar se muyi magana" ba musu ta zagaya ta buɗe gaban motar ta shige. Ya kalleta yace "Ni ko a bikin Ammar ban ganki ba ina kika shiga haka?" Tsaki ta ɗanyi tace "me zanje inyi masa a gurin bikin, dan abun kunya kuna gani kuka barshi ya auri wannan 'yar mitsitsiyar Yarinyar, bayan a duniya ya tsani Auren ƙaramar Yarinya" "kinfi kowa sanin Halin sa ɗan uwan ku ne, ke zaki gayawa wani halinsa, shekaranjiya na haɗu da shi da matar tasa ya kaita Asibiti se zuba shagwaba take yi, Wallahi Yarinyar nan za tayi saurin tafiya da Imani namiji, duk jin kan Ammar lallaɓa ta yake ranar, ina ga ko ciki ne da ita " Wani dogon tsaki ta ja tace "dan Allah ka dena ɓata min rai, dan abun kunya 'yar wannan Yarinyar Ammar zewa ciki, mtseww" Dariya sosai Faruk yayi yace "Kai Fa' iza, to shi kna ruwan sa, Wallahi tun ranar ɗaurin Aure da naga yarinyar nan na kasa samun nutsuwa, wallahi dana ga Yarinyar nan kafin bikin su da bazan taɓa bari Ammar ya aure ta ba, Idan naga Yadda take wa Ammar shagwaba wani irin kishi ne yake kamani, Wallahi ina jin ƙaunar yarinyar nan har a cikin zuciya ta" Wani irin Murmushi Fa'iza tayi tace "dagaske kana son ta" "Wallahi Fa'iza ina mata so bana wasa ba, ni ko ban Aure ta ba kawai dai in same ta, kin gane ai balle ma ina son in Aure ta, wallahi tunda naganta mata ta dena birgeni" Jinjina kai tayi tace "Me ze hana mu haɗa kai mu taimaki juna?" Ya gyara zama yace "kamar Yaya kenan?" Murmushi tayi tace "zamuyi waya" ******************** Kasa nutsuwa Yaya Jidda tayi, dan haka ta tambayi mijin ta zata fita unguwa, shiryawa tayi ta tafi gidan su Ammar. Koda Mufeeda ta buɗewa Jidda ƙofa taga kammanin ta da Ammar, sannu da zuwa tayi mata tai mata iso ciki, wani irin kallon banza take bin Mufeeda dashi. Tun kafin Jidda ta shiga falon idon ta ya sauka akan jibgin kayan Abincin dake ɗakin tsakar gida, tayi ƙwafa suka shiga falon. Ta kalli Mufeeda tace "Ina Ammar ɗin?" "be daɗe da fita ba kuma, yana gida tun ɗazu, amma se in kira shi a waya" "Ammar ɗin da yake fita tun farar Safiya shine yake zaune a gida har bayan azahar sannan ya fita" Shiru Mufeeda tayi tace "bari in kawo miki ruwa" "Ke dawo bana son gulma, ni bazan sha ruwan ki ba, sannan ki buɗe kunne da kyau ki jini, Wallahi daga yau idan wani daga dangin mu yazo kika kuma masa wulaƙanci sekin bar gidan nan dan baze yuwu ba, 'yar mitsitsiya dake kin san wulaƙanci, su Fa' iza sa'anin kine da zasu zo ki musu rashin mutunci, ko gidan uban kine? " Mufeeda ta girgiza mata kai alamar A'a, Mufeeda a ranta tace" wannan ce Jidda kenan? " " to ko yanzu yai niyya ze iya sakinki ya auri wata, 'yan uwa kuwa ba' a canza su, ance miyar ki hadda kaji alhalin be kaiwa namu iyayen ba, shafaffiya da mai, ni ina tunanin kin haɗawa Ammar da ƙulumboto dan Ammar ba sakaran namijj bane, daga zuwan ki ki kainainaye shi, kalli uban kayan Abincin daya tile miki a ɗaki, Amma iyayen mu ko oho, se anyi magana yace bashi da kuɗi ina ya samu kuɗin daya siya miki wannan kayan haka? Algunguma baki isa ki rabamu dashi ba" Jidda taiwa Mufeeda cin mutunci tsaf, Sam Mufeeda bata tanka mata ba, se dai zuciyar Mufeeda kaman ta fashe, ga Jidda ta girme ta sosai balle tace zata rama. Seda ta gama sannan ta tashi ta tafi, bayan tafiyar ta se da Mufeeda tayi kuka dan ba ƙaramin jin zafin abunda Jidda tayi mata tai ba. Ammar ne ya dawo ya tarar da ita a falo, ba haka ya saba ganin ta haka ba in ya dawo, amma ya basar ya miƙo mata leda yace "gwada wannan takalmin in gani ɗazu na ganshi yayi kyau na siyo miki" Ƙoƙarin maida hawayen idon ta take, Ammar ya ga idon ta da ƙwalla, ya ɗan haɗe rai yace "kukan me kike yi?" "bakomai bafa kuka nake ba" "bana son ƙarya, meke damunki?" "bana jin daɗi ne" A fusace yace "ƙarya kike lafiyar ki ƙalau, meya same ki? Bana son ƙarya" Domin sharhi, gyara ko shawara Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 16 Ƙura mata ido yayi, a hankali tace "bafa wani abun damuwa bane, radio nake ji aka faɗi wani labari daya bani tausayi, shikenan fa bari in gwada takalmin nan dan tun kan isa na hango ƙafa ta tayi cif a ciki" Ammar yabi Mufeeda da kallo ba dan ya yadda da abunda tace ba, amma ƙiri ƙiri ta basar da zancen ta karɓi takalmin ta saka, na zaman tsakar gida ne amma kalar pink ne me tudu yayi kyau sosai, ta miƙe ta ɗanyi juyi tace "yaka gani yayi min kyau kuwa?" Gyaɗa mata kai yayi, tace "Nagode mijina Allah ya baka gidan Aljanna" "Ameen ya Allah" ***************** "Maman Sadiq maƙociyarki me kallon gidan ki ta shigo miki kuwa? " Maman sadik tace "Hmm ta shigo min maman Amir ke kin ganta wata 'yar yarinya da ita, amma mijin ta baki ganshi ba ƙato da shi, ni ba dan na ganta kalar wayayyu ba da cewa zanyi a ƙauye ya auro ta" Ɗayar tace "dan Allah ta shigo muku? Ranar da ta shigo muku ina ga bana nan, kaddai' yar Yarinyar da naga ya sata a a daidaita sahun sa ce matar?" Maman Amir tace "Wallahi itace maman Nur" "Taɓɗijan niko zanso in ƙara ganin ta" Maman Sadiq tace "ke kina ganin ta 'yar Yarinya se shegen ji da kai, watan ta guda a unguwar nan fa sannan ta shigo mana, tana wani jin kai a gurguje ta tafi, nace kin gamin yarinya da kinibibi,' yar da da auren wuri aka min na haifeta" Maman Nur tace "Kedai bari da mijin nata wata tsiyar ne da shi da ta ɗaga mana kai, amma duk layin nan shi ne matsiyaci ɗan adaidaita sahu ne fa" Maman Ameer tace "kema dai kya faɗa" Maman Sadiq tace "Maman Nur ya kamata akaiwa maƙociyar tamu ƙyallen Ankon sunan ki na haihuwa" Maman Amir tace "wallahi kuwa mu kai mata muga meza tace" Maman Nur tace "haka za'ayi ɗakko ƙyallen muje" Suka ɗakko ƙyallen Atamfa suka nufi gidan Mufeeda. Tana tsakar gida tana aikace aikacenta aka buga ƙofa cikin ƙaramar Muryar ta tace "waye?" Suka amsa da "mune". Ta buɗe musu ƙofa suka shigo, tun daga tsakar gidan suka fara ƙarewa gidan nata kallo basu yi zaton cikin gidan ta yana da kyau haka ba. Tai musu iso cikin falon ta suka gaisa, ta kawo musu ruwa da ɗan abun motsa baki na garar ta, nan suka dinga ci suna zuba surutu, ita dai Mufeeda sam bata da saurin sake wa da mutane dan haka sedai ta kallesu tayi murmushi kawai. Can maman Amir tace "yawwa Mufeeda dama ƙyallen ankon sunan Maman Nur ne muka kawo miki ko mai gidan ze sai miki" Mufeeda ta karɓi ƙyallen ta gani tai murmushi ta miƙa musu tace "Aikuwa Atamfar tayi kyau sosai, se dai ni da ban daɗe da Aure ba kayan lefe na na nan ko taɓawa banyi ba, sedai ince Allah ya rabaki da cikin lafiya, idan kika haihu zan sako abunda Allah ya horemin in shigo inyi miki barka" Ɗan buɗe baki maman Nur tayi tace "kodai me gidan ne baze miki ba, amma Atamfar fa babu tsada dubu biyar ce fa" Mufeeda tace "Anty kenan aike yanzu kinfi buƙatar Addu'a fiye da wannan Atamfar, kuma insha Allah zan saki a Addu'a Allah ya raba ki da cikin nan lafiya" Maman Sadiq tace "ai insha Allah zata rabu da cikin nan lafiya, duk 'yan layin nan za suyi fa anko zamuyi, mene dan ya miki lefe kwanan nan, ke yarinya bari kiji mazan yanzu ba' a tausayin su, ki zage duk abunda kike so ki sashi gaba seya miki" Murmushi sosai Mufeeda tayi tace "to nikam se an jimanku zan shiga kitchen, nagode sosai da shigowar da kuka yi" Ta tashi ta barsu a falon, suka fito suna mamaki gami da zage zage. Maman Sadiq tace "yau naga kinibabbiyar yarinya, wani wai kinfi buƙatar addu'a akan anko ji munafuka" Maman Nur tace "ke niba wannan ba ina mijin ta ɗan a daidaita sahu ne, kawai base naga saman fridge ɗin ta da kayan shayi ba hadda su butter ga biscuits da kayan daɗi, naga dai bata haihu ba amma data buɗe fridge zata ɗakko mana ruwa hadda chocolates a cikin fridge ɗin, wallahi raina ya biya, bari gobe in Allah ya kaimu aikawa zanyi ta sanmin milo" Maman Amir tace "hmm kedai bari muda mazajen namu suke da sana'oi da suke samun kuɗi rabona da baban Amir ya saimin kayan shayi tun haihuwar Amir yanzu yara na uku, danma ba kiga ɗakin nan na tsakar gida ba ke kinga kayan Abinci kamar a kanti?" Maman Nur tace "wallahi shiga gidan zan dinga yi nida yara, a dinga shan madarar nan damu" Maman Sadiq tace "in kinga fuska muma semu biyo ki" Suka cigaba da gulmar su dai ********************** Mussaman Jidda ta shirya ta tafi gida, domin ta ziga Umma akan Auren Mufeeda da Ammar. "Umma wallahi Idan ba'a tsaya akan Ammar ba, wallahi ze zama mijin tace, su Fa'iza basu gaya miki abunda yarinyar nan tayi musu ba" Umma tace "A'a nidai sunzo nan Halima ta rakasu gidan Sa amma ba su dawo ta nan ba" "to sun biya gida na, sun gayamin yadda ta dinga musu wulaƙanci" Halima tai farat tace "Wallahi ƙarya sukeyi, tare fa muka je ba wani wulaƙanci da tayi musu" Jidda tace "dan ubanki dake nake magana? Ko kuma ƙanwar uwaki ce da zaki goyi bayan ta?" Tura baki Halima tayi tace "ai ni gaskiya na faɗa" Umma tace "to ni Jidda na kasa gane inda maganganun ki suka dosa sam, wani irin wulaƙanci ne haka?" "wallahi Umma rashin mutunci ta dinga yi musu, kuma da naje gidan ta baki ga kayan Abinci ba kamar abun banza, kashe mata kuɗi yake kaman kaman me amma ku nan baya kawo muku, se anyi magana yace ba shi da kuɗi" Umma tai Murmushi tace "To meye a ciki dan ya kashe mata kuɗi matar sa cefa, kuma Ammar ko be mana a yanzu ba a baya yayi mana balle har yanzu Ammar yana iya ƙoƙarin sa akan kyautata mana, Jidda lokacin da mahaifinku yake da shi na wata ya ya kashe min kuɗi kaman babu gobe, shi ba mace ce ta haife shi ba? Ko kuma lokacin da yake kashe mana kuɗin meyasa ba kiyi complain cewar be kyauta ba? Ina yanzu keda 'yan uwanki kuma' ya'yan wasu kuke aure kuma suke muku hidima, dan me za kuce ɗan uwan ku baze wahaltawa wata ba? Ai abun Alfaharinku ne ace ɗan uwan ku ya auro 'yar mutane kuma yana iya riƙe ta, nikam Alhamdilillah Ammar har yanzu yana ƙoƙarin kyautata mana, kuma ni ina ƙaunar ta, Dukda murɗaɗen hali irin na Ammar duk da yadda bashi da tarin dukiya tace tana sonsa a haka ni ta gama yi min komai ina ƙaunar ta" (ƙalubale gareku iyaye, haka ya kamata ku zamo masu adalci ga matayen 'ya' yan ku, dukda wasu sirikan basu da kirki, amma da yawan lokuta ƙannen miji da yayye suke jawowa matar ɗan uwansu a gurin iyayen su, su faɗi abunda akayi da wanda ba'ayi ba suce anyi, ku kuma iyaye babu binki ce babu komai ku hau kai ku zauna, Allah ya kyauta) Jidda tace "Shikenan Umma tunda baki yadda ba, zaki gani da kanki wataran ai" ******************** Ammar ya dawo ya shiga ɗakin sa, ƙaton flower Mufeeda ta zana da sunan sa da Nata, gefe tayi rubutun kalaman Soyayya ta ajiye masa akan gado ɗan girgiza kai Yayi a ransa yace "sam Yarinyar nan bata rabo da shiriri ta" Ya fito falo ya tarar da Abincin sa sedai be ganta ba, yayi tunanin ko tana wani abun ne, dan haka ya zauna ya fara cin Abincin sa, sam Abincin baya masa daɗi saboda babu Mufeeda a kusa dashi balle taita masa wannan shirirtar tata, yana gama ci har ya tafi ɗakin sa ya dawo ya duba yaga ko tana lafiya, yana buɗe ɗakin ta ya tarar tayi ɗaiɗai akan gado tana bacci, ta tafi ƙarshen gado wanda idan tayi ƙwaƙwƙwaran juyi zata iya faɗowa, kome ya sata bacci da wuri haka oho? A hankali yaje gaban gadon nata da niyyar ya gyara mata kwanciyar, yana ɗagota ta firgice ta saka ihu. Rirriƙeshi tayi tana zare ido, yace "Ke menene haka? Nine fa" Ajiyar zuciya tayi ta lumshe ido tace "wallahi ka bani tsoro, wani ɗan jaririn ƙadangare ne ya shigo gidan nan shiyasa na taho ɗaki fa" tai maganar tana kwanciya a jikin sa. "Yanzu Jaririn ƙadangaren ne yasa kika dawo ɗaki kika kwanta hadda rufe ƙofa?" "eh mana idan kuma ya shige min ɗaki fa?" "Shikenan cikani zanje in kwanta" Ta ɗan kalle shi tace "kaci Abinci kuwa?" "Naci kwanciya zanyi yanzu" Ta langaɓar da kai tace "nifa yau ban ganka sosai ba" "Nifa bana son rigima, cikani ki koma baccin ki" Wani irin kallo take masa, lumshe ido take alamar akwai bacci akan ta sosai amma Ammar gani yake kaman da gayya take masa wannan kallon. "I love you sweetheart" shine abunda ta furta masa a hankali. "Naji, karki manta gobe in Allah ya kaimu ki shirya da wuri zamu fita" Jinjina masa kai tayi tana lumshe ido, ya zame ta daga jikin sa, ya kwantar da ita sosai akan filo ya fita ya koma ɗakin sa. Daya koma ɗakin ma tuni ta dafa masa ruwan wankan sa kafin ta kwanta, da zafi sosai ya haɗa ruwan yayi wankan, sannan ya samu guri ya kwanta, tunani yake da ƙoƙarin sama wa kansa mafita akan zaman sa da Mufeeda, baze yuwu su ci gaba da zama a haka ba dan ba ƙaramin cutuwa yake ba, yana mata kallon Yarinya ƙarama amma a lokuta da dama kasancewar su tare yana ƙara jefa shi cikin wani hali, lallai salon da take amfani da shi yana matuƙar tasiri ga zuciyar 'yan mazan. Haka yaita tunani har yayi bacci. Da safe Mufeeda tana ta ɗoki zata fita, watan ta biyu a gidan nan amma sau ɗaya taje Asibiti sekuma maƙota data shiga, Suna gama breakfast ta saka Ammar a gaba suka ware kayan Abincin gara da su rarraba da wanda zasu tafiwa da su Umma, har na su Yaya Maryam seda da su Jidda seda ta ware masa, ta rarraba kayan zaƙin nan na alkaki ta warewa kowa nasa hadda wanda ze bawa abokan sa su Jabir su bawa matan su. Ammar ya kalle ta yace "Ai wannan kayan da kika rarraba sunyi Yawa, saboda ke aka kawo be kamata ki kwashe ki rabar ba, wanda zaki bawa su Umman ma ya isa nagode" "Abunda kaci kashi ne wanda ka bayar shine rabon ka, ka sani ko dalilin bayarwar da mukayi Allah ya ninka mana, ai abun duniya ko ka bayar ko baka bayar na seya ƙare" "Amma babu wanda zaki bawa a family ɗin ku? Be kamata ace kin rabar da kayan nan haka ba" "Ai kowa seda aka bashi kafin a kawomin, kaga wannan ai ya ishemu kaima kwana biyu seka huta, Allah dai ya ƙara maka buɗi babban mutum, ciyarwa ba aikin rago bane, kana ƙoƙari sosai seka huta kafin su ƙare" "maganar hutu ai babu shi tunda na riga na ajiye ki, dole in fita in nemi abunda zan riƙe ki, kaman yadda yake a shari'a" Miƙewa tayi tsaye tace "kana ƙoƙari mijina, Allah ne kawai ze biyaka ladan ɗawainiyar da kake, Allah ya ƙara Arziki, bari inje in shirya karmuyi rana" Ya jinjina mata kai, ta koma ɗakin ta ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, tayi to match da mayafin ta da Jakarta, Mufeeda akwai Gayu, da ta fito falo Ammar be fito ba ta bi shi ɗakin sa, tana zuwa ta tarar ya shirya yana ƙoƙarin saka links ɗin hannun rigar sa. Da sauri ta ƙarasa inda yake, ta fara ƙoƙarin saka masa tace "Babban mutum kayi kyau sosai kaman in sace ka in gudu" Kallon ta kawai yake ba tare da yace mata uffan ba, amma itama tayi kyau sosai, amma sam ba tayi kama da matar Aure ba. Ta ɗakko turare ta feshe masa jikin sa, tace "Allah ya barni da abun sona har ƙarshen Rayuwa ta" ita dai duk wani motsi da zata yi se tayi masa Addu'a kokuma tayi masa kirari, kota nuna masa irin soyayyar da take masa, lokuta da dama har mamaki take bashi. Haka ya shiga gaba tana binsa a baya, suka kulle gidan suka fita, Ammar idan ya fita tare da Mufeeda baya ɗaukar passenger. Seda tasa Ammar ya tsaya suka saiwa su Abba Fruit sannan suka tafi, Basu tsaya ko ina ba se gidan su Ammar, Mahaifin Ammar yana tsakar gida yana jin radio suka shiga da Sallama. Abban Ammar yana ɗaga ido, Mufeeda ya fara kallo ganin su tare da Ammar yasa ya gane itace Sirikar sa, Murmushi yayi yace "barka da zuwa Yarinyar kirki sannu da zuwa sirika ta" Har ƙasa Mufeeda ta durƙusa tana murmushi ta gaida Mahaifin Ammar, shima cikin dattaku ya amsa mata, yace "Zauna mana sirika ta" gefen tabarmar Abba ta zauna Ammar ya ɗanyi gyaran Murya yace "tunda ni baka maraba da zuwa na, bari in koma" Abba yai Murmushi yace "ni ai ka daɗe muna tare, ni nayi 'ya dama ba a Auta da namiji babarka tayi Auta da kai, ni yanzu ga auta ta nan" Ammar yace "Aikuwa zaka ga halin Auta kam" Murmushi Mufeeda tayi tace "dama shima ɗan auta ne?" Abba yace "ƙannensa uku ne suka rasu, kinga kuwa shi ne ɗan Auta" Dariya Mufeeda tayi, Umma ce ta fito daga ɗaki hannun ta ɗauke da carbi, alamar sallar walha ta yi, tace "Yau Allah yayi an kawo min Mufeeda kenan? Tun ina magiyar har na gaji" Nan ma cikin girmamawa Mufeeda ta gaida Umma, ana haka Halima ta shigo daga aiken da aka yi mata, tana ganin Mufeeda ta fara murna tace "Anty Mufeeda ashe zaku zo ɗin tun ɗazu nake kallon hanya" "Yaya Halima ni na makarar damu ai, Amma ai gashi munzo" Duk rashin saurin Sabon Mufeeda yadda iyayen mijin ta suka karɓeta ba ƙaramin yi mata daɗi yayi ba, sun nuna mata karamci da dattako, jinsu take kaman iyayen ta, sosai ta sake suna hira, anan Har hira ta kawo Abba yake gaya mata yana kiwon dabbobi a kangon jikin gidan sa, nan suka shiga hira sosai har Mufeeda take nuna sha'awar ta akan kiwo. Yadda take hira da iyayen sa cikin mutuntawa kaman iyayen ta ba ƙaramin burge Ammar yayi ba, Ammar ya miƙe yaje Napep ɗinsa ya kwaso kayan Abincin da suka zo dasu da Yadda aka kasafta kayan. Abban Ammar yace "A ina ka samo wannan kayan haka Ammar?" "Dama kayan garar Mufeeda ne" Abba yace "gara kuma Ammar? Ina fatan ba zuwa kayi kace se an maka gara ba, dan nasan halin ku matasan yanzu akan gararar nan se kuyi wa mace gori dan abin kunya" Abba ya ɗanyi maganar a hasale. Wato Abba halinsu ɗaya da Ammar, sam basa son aga gazawar su, musamman akan abunda yake haƙƙin su ne suyi shi. Mufeeda tace "A'a Abba, da cewa yayi ma baze karɓa ba, Baba ne ya kawo haka yake yi duk wadda ya aurar ya bata gara, Amma dan Allah kayi haƙuri ba shi yace a kawo ba" Abba ya kalleta ganin kaman ba taji daɗin yadda yayi wa Ammar ɗin ba, yace "Hmm zaki kare mijinki ko? To ni a yanzu yamin laifi zan iya zane shi ma" Sunkuyar da kai Mufeeda tayi tana murmushi, daga nan yayi musu Nasiha da Addu'oi. Seda Mufeeda tabi Abban Ammar ya nuna mata yadda dabbobin sa da yake kiwo suke, a cikin maganar sa zaka gane tsohon ɗan boko ne, Ga Mufeeda da shegiyar tambaya, duk abunda ta tambaye shi se yayi mata bayani dalla-dalla. . Bayan tafiyar Mufeeda Abba yace "Ammar kana surutan cewa Kai tayi maka Yarin ta, to a manyan da kake hange da wuya ka samu Yarinya me hankalin ta, dukda nagani tana nuna ƙuruciyar wasu lokutan amma ka bita a hankali Yarinya ce me biyayya, ina jin nauyin ta ne amma ba dan haka ba seka koma da kayan Abincin nan, ka kula da matar ka, ka sauke dukkanin haƙƙoƙin ta da yake kanka" Ammar yace Insha Allah suka yi Sallama da Abba ya bar Mufeeda a gidan su. Bayan tafiyar Ammar ya kira Halima a waya, tana ɗagawa yace "kiyi wa Mufeeda kitso kafin in dawo ɗaukar ta" Ta amsa masa da "to" Mufeeda da Halima ne suka zage suka tsiri alkubus, Yadda Mufeeda take aiki ba ƙyuya babu ganda ba ƙaramin bawa Mahifiyar Ammar mamaki tayi ba. Da azahar suka kammala girki, suka gyara ko ina, aikuwa sunyi santin girkin nan sosai, Halima tayi wa Mufeeda kitso ƙanana masu kyau ba tare da ta gaya mata Ammar ne yace ayi mata ba, Bayan sun gama kitson Kuma tai mata jan lalle, kaman wata amarya tayi kyau sosai. Ta samu food flask ta ɗibarwa Ammar Abincin, ta ajiye masa se bayan sallar isha'i sannan Ammar yazo ɗaukan ta, taji daɗin wuni a gidan su Ammar dan sun mata kara suka nuna tamkar su suka haifeta, sosai suka karrama Mufeeda. Da zasu tafi Abba ya kira Ammar ya nuna masa Akuya Aure ɗaya da kaji masu ƙwai yace ya bawa sirikarsa, za'a cigaba da kula mata dasu anan. Ammar yace "ba shakka an gode, to ni wanne ka bani?" Abba yace "kai sau nawa ina baka dabba, idan kaza ce ka yanka ka cinye abarka, ai bazan kuma baka ba" Mufeeda tai murmushi har ƙasa ta durƙusa tana yiwa mahaifin Ammar godiya. Abba yace "bakomai 'yar Auta, Allah ya baku zaman lafiya ya ƙara muku ƙaunar juna, muma mungode sosai" Umma ma seda ta haɗawa Mufeeda su tsintsiya da manyan jakar omo, sannan suka yi sallama. Seda Ammar ya biya da ita gidan Yaya Maryam ta gaishe ta, taita mita akan meyasa be kawo ta da wuri ba se a daren nan, suka bata nata kayan da suka kawo mata sannan suka tafi gida. Suna komawa Mufeeda ta gabatar masa da Abincin da tazo dashi, seda Ammar ya kwashi girki ya ƙoshi sannan yace "waye yayi girkin nan?" "Nice" ta bashi amsa Ya basar yace "shiyasa beyi daɗi ba" Ta kalle shi tace "Abba dai yace yayi daɗi" "Ai dan karki ji babu daɗi ne yasa shi cewa yayi daɗi, amma babu daɗi" Seda yaga ya ƙoshi ya wani fara beyi daɗi ba, tattare Kwanukan ta fara yi tana tura baki, se yanzu ya lura da hannun ta da yayi Jawurrr da lalle, ƙurawa hannayen ta ido yayi, ta kwashe Kwanukan ta, ta kai kitchen ta wanke tai tafiyar ta ɗaki. Ƙin zama tayi a falo, shi kam Ammar dariya ma ta bashi, ita a dole fushi take. Har ƙarfe goma Ammar yana falo yana kallon wani Film a Bollywood, ba zato babu tsammani yaga Mufeeda ta ɗare cinyar sa, shi a zaton sa tuni tayi bacci, se ƙamshin turare take, rigar ta ta bacci iya gwiwar ta, kanta babu ɗankwali se bakin ta da take shan sweet. Ammar yace "Ya haka?" "Na kasa bacci, kuma naji kana kallo shi yasa na fito" Ammar kaman ze kuka yace "kinga ɗagani banyi shafa'i da wuturi ba" "in muka gama kallon base kayi ba" "waike baki san yanzu lokacin sanyi bane? Ba'a son yawan taɓa ruwa ba?" "to ba se in dafa maka ruwan alwala ba" A ransa yace "wannan 'yar yarinyar in banyi dagaske ba yauma seta hanani bacci" Dan haka ya haɗe rai yace "Malama ki ɗaga ni" Maimakon ta ɗaga shi, sema ta gyara zaman ta ta miƙe ƙafafuwan ta akan nasa, kaman yadda yayi ta jingina bayan ta a ƙirjinsa ta ci gaba shan alawarta da zuwa yanzu bakin ta ya zama ja jawurrr saboda kalar alewar. Daskarewa yayi a gurin ya kasa magana balle ya motsa, lallai yau ya ƙara tabbatar da tsagwaron yarinta akan Mufeeda, Ammar yayi ƙam dashi kaman gunki, sun kusa mimtuna goma a haka, ko a jikin ta kallon ta kawai tame. Ta fara taune alawar nan a bakinta, sekuma ta janye ƙafafuwan ta ta juyo ta kalle shi tace "Au naman ta ban maka bismillar alewa ta ba gashi na taune ta, bari in tafi dan na fara jin bacci" Ta miƙe da nufin ta tafi amma ba zato ba tsammani Ammar ya janyo ta. Abunda yayi ne yai matuƙar bata mamaki, dan ko a mafarki batayi zaton hakan ba. Seda Ammar yasa baki ya shanye alawar da ta tauna a cikin bakin ta tsaf, sannan ya cika ta ya miƙe kamar beyi komai ba ya wani maze ya haɗe rai yai tafiyar sa ɗakin sa (🙄🙄 to su Yaya Ammar manya) Ashe dai kuna son littafin nan haka? Ai ban sani ba seda nayi tsallaken update na rana ɗaya nasha tambaya. To yaseen in ba Comments posting se Allah ya kaimu Monday. Ina godiya masoya da addu'oinku da kuma shawarwari. Domin gyara, sharhi ko shawara ƙofata a buɗe take Ayshercool 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 17 Binsa tayi da kallo har ya shige ɗakin sa, tashi tai ta koma ɗakin ta, tana ƙara mamakin abunda Ammar yayi mata. Da safe harta tashi ta gama breakfast be fito ba, tana ƙarasa gyara gida ne ya fito yana wani basarwa, Mufeeda ta kalle shi tace "barka da Safiya Babban Mutum" Be amsa ba se jinjina mata kai da yayi, ya nemi guri ya zauna, ya fara breakfast ɗin sa yana wani mazewa, murmushi take yi tasan abunda ya faru jiya ne yasa yake ta wannan basarwar. Seda ya gama ta koma kusa dashi tace "Hubby kalli lalle na yayi kyau kuwa?" Kallon hannun yayi da zuwa yanzu ya fara zama maroon, ya gyaɗa mata kai, amma bece komai ba. Ta kawo masa breakfast ɗinsa ya fara yi, yanayi yana wani mazewa gaban sa taje ta zauna ta zuba masa ido ya ɗago idon sa ya sauke a nata yace " Se kinsa na ƙware kike min wannan kallon haka?" "A'a bazaka ƙware ba, kallon Soyayya ne sedai ka ƙara jin daɗin Abincin, A bani a baki mana duk randa ka ciyar da ni da hannayen ka masu tarin Alkhairan nan nafi ƙoshi fa" Hararar ta yayi yaci gaba da antaya loma, tayi ƙasa da murya tace "haba Autan Abba mijin Autar Baba, ba dan halina bafa kaga ni Yarinya ce zanyi maka kuka fa" "ga guri nan maza zauna kiyi kukan, tunda ke a rayuwar ki Kuka kamar jin daɗin sa kike yi" Tura baki tayi ta riƙe hannun sa "dan Allah baby ka bani a baki, nice fa Jaririyarka ce seka barni da yunwa?" Kallon ta yake yadda take ta zuba taɓara. Ammar ya haɗe rai yace "kinga idan baki bari ba zan tashi yanzun nan in bar miki gidan" "Allah in baka bani ba zanƙi cin Abincin yau" "to karki ci mana cikina ko naki?" "cikina ne, Amma ni bazan iya zama ina kallon abun ƙauna ta beci Abinci ba, dama nasan baka sona" "Dama na taɓa cewa ina sonki ne?" "Baka taɓa cewa kana sona ba, Amma nasan ana sona ko ba a gayamin ba na riga na sani" Kallon ta yayi ta ɗago itama ta kalle shi tare da kashe masa ido. "Ni dai bance ina so ba, saboda a yanzu dai raino kawai nake yi, ni banga abun so a gurin ƙwaila ba, banda rawar kai da Yarinta babu abunda kika iya" Ta gyaɗa kai tace "Shikenan nagode, Nikam har zuciya ta idan nace ina sonka, to ina nufin abunda na faɗa" Ta miƙe ta koma kan Kujera tai shiru, ƙarshe ma ta kwanta ta rufe idon ta, Yanayin yadda yaga ta yine ta ɗan bashi tausayi, Amma dai bece mata komai ba ya kammala breakfast dinsa, kaman ya miƙe yaje yai haramar Fita, se yaga be kamata ya tafi ya barta tana fushi ba duba da Yadda take shiga damuwa idan taga baya walwala. Hannunsa ya Miƙa ya ɗan ja yatsan ƙafar ta, a hankali ta buɗe ido ta kalle shi, "Sakko in baki Abincin, kar inje kice bana baki Abinci" Ba tace komai ba ta Sakko tazo gaban sa ta zauna, Yanayin Fuskarta ya nuna ƙirirs take jira tayi kuka, dan ba ƙaramin haushin abunda Ammar ya faɗa taji ba. Ya haɗa mata abun karyawa ya kalleta yace "dawo nan" ya nuna mata inda zata zauna daf dashi, ta matsa ta zauna ya fara bata Abincin a baki tana ci. Ya ɗan girgiza kai yace "Rigumammiya kawai se kace 'yar Yaye" Tura baki tayi tana sosa gefen fuskarta, tamkar irin shagwaɓaɓɓun Yaran nan. "Na ƙoshi fa" "kin ƙoshi wa kike nufi ya cinye ragowar ki?" "To ai na ƙoshi cikina ya cika" "ɗan wannan Abincin ne kika ƙoshi, oya buɗe bakinki ki cinye sauran" "Allah in kace se naci zan iya yin Amai" Haɗe rai Yayi yace "kenan ɗan wannan Abincin kikeci shiyasa ba kya ƙiba, sekin cinye" Hannu tasa ta ɗaga rigarta tace "kalli fa cikina ya cika sosai" "Nagani rufe" ta sauke rigar ya ɗan ƙura mata ido sannan yace "Allah ya shirye ki" "Mekuma nayi?" "A'a bakomai Addu'a kawai nayi miki" Ƙarshe Ammar ne ya tattare Kwanukan, dan yau rikici take ji sosai. Yana shirin fita ne yaro yayi Sallama da yake yau gidan a buɗe yake, Mufeeda ta amsa ta fito tsakar gida, ta kalli yaron tace "Ya akayi ne?" Ya miƙo mata kofi yace "wai gashi inji Umman mu wai dan Allah ki ɗan zuba mata madara da milo zata sha tea, idan kina da Butter ki ɗan san mata taci bredi" Mufeeda tace "ayya ka koma kace mata dan Allah tayi haƙuri, bani nake siyan kayan ba, me gidan ne yake siya kuma bana bayar da abu seda izinin sa" Yaron yace "to" ya juya ya tafi. Ta koma falo tana tsaki,Ammar da yaji yadda suka yi da Yaron yace "Meyasa baki basu ba? Kefa kikace abunda ka bayar shine rabon ka" "hmm Yaya Ammar kenan, ina sane na hanasu, kai baka san wannan rainin hankalin na wasu matan ba, ranar suka shigo nan suka nemi su rainamin hankali dan sun ganni ƙarama, Yanzu dana basu shikenan sun Sami gurin zuwa, duk abunda ka siyo tare zamu yi amfani da shi, duk nasan irin wannan abubuwan tun a unguwar mu" Ammar yace "Kinga kowa rainaki yake saboda ke Baby ce, kowa yana miki kallon Yarinya, waini gayamin ma me yasa kika ce kina son Aure ne a shekarun nan naki?" "Saboda nima Mutum ce, kuma ina son kasancewa da abunda nake so, zuciya ta ta makance bata ganin kowa a wannan lokacin in ba kai ba, ni dai nasan ina sonka sosai, kuma bazan iya cewa ga dalilin da yasa nake son naka ba, koda yake na maka ƙanƙanta kuma baka sona amma shi so babu ruwan sa, karka makara rana ta fara yi fa, Adawo lafiya " Ta juya ta koma ɗakin ta, Shiru Ammar yayi na wani ɗan lokaci daga baya ya miƙe ya fita sam beji daɗin yadda sallamar su ta kasance yau ba duk se yaji babu daɗi. Koda yaro ya koma ya gayawa Maman sa Saƙon Mufeeda take bala'i "Jimin 'Yar matsiyata babu a house anzo gidan miji an samu shine zata yiwa Mutane Iskanci, bata san mune masu unguwar ba, in ba tayi wasa ba sena sauke mata wannan wulaƙancin da take ji dashi se zaman unguwar nan ya gagare ta" haka ta zauna ta dinga mita tana Masifa. Daga ƙarshe dai haka ta saka Mayafin ta ta fita yin cefane, gurin me kayan miya taje ta tarar da mutane sosai a gurin ta samu guri ta zauna. Seda ya ɗan sallami Mutane sannan ya kalleta yace "uwar biyu me za'a zubo miki ne?" Ta gaya masa abunda ze haɗa mata, sunayi suna hira da Sa'idu me kayan miya. Sa'idu Yace "Amma Maman Nur wannan ne watan haihuwar ki naga da ƙyar kike tafiya" "Wallahi kuwa sa'idu a wannan watan nake sa ran haihuwa duk na gaji da cikin nan wallahi" "Ai se haƙuri tunda kin kusa saukewa, mudai fatan mu ki haihu Asha suna muci shinkafa" "Hmm Anya shinkafar nan kuwa, ai abun se Addu'a kasan Baban Nur da wulaƙanci wani lokacin, yaci basussuka sun masa Yawa, muna ta rigima da shi akan abunda ze bani na taro waishi bashi da kuɗi, ni ko ba abunda ya dameni so nake in fita kunya, kaga su Maman Amir ɗin nan ba ƙananan munafukai bane, Alla Alla suke in haihu suga abunda zanyi kallon su kawai nake, ina zan bari suga walle na" Sa'idu yace "gaskiya kam be kamata ba" Yana cikin haɗa mata kayan miyan ne sega Maman Amir itama tazo yin cefanen. Suka gaisa ta kalli Maman Nur tace "Maman Nur ina su Nur ɗin kika fito cefane da kanki?" "wallahi suna makaranta, ga gidan ba kowa kin ganni ko karyawa banyi ba na fito kafin kayan miyan su ƙare" Maman Amir tace "maman Nur kidena zama da yunwa fa, kina ɗauke da ciki kina wasa da Abinci" Me kayan miya yace "gaya mata dai" "Hmm kin san me maƙwaciya ta tayi min? Wai na aika ta sanmin Milo in sha tea, amma ta hanani" "Haba dai ke dama seda na gaya miki Yarinyar nan ba Mutunci za tayi ba" Me kayan miya yace "Wai wace Yarinyar ce ne?" Maman Nur tace "wata 'yar mitsilar Yarinya ta jikin gida na, matar wannan me a daidaita sahun, banza bata saba sha a gida ba, anzo birni ana iskanci" Suka haɗu suka dingayi da Mufeeda suka zage ta tsaf a teburin me kayan miya (Mata kenan Allah ya shirya) ********************* Yau Ammar be dawo da azahar ba, se bayan sallar isha'i ya dawo, ya ɗauka ze dawo ya tarar da ita yadda ya barta amma yana dawowa ta ɗan tsuke fuska cikin shagwaba tace "shine se yanzu ko? Ina ka tsaya yau baka dawo da wuri ba?" "inda kika aikeni" ya bata amsa Tayi murmushi tare da duƙar da kanta tace "Allah ya bada haƙuri, Allah ya huci zuciyar Manya" Ɗan Murmushi yayi yace "ban Abinci, tunda na fita banci komai ba" "Bana hana zama da yunwa ba?". Tai ƙasa da muryar ta tace "idan aka ƙara se nayiwa mutum abunda baya so" Ya kalleta yace "Mene bana son?" "Idan ka kuma zanyi ka gani, ko in maka tausa ne? Naga ka gaji da yawa" Da sauri yace "A'a bana so" "Tausar tawa ce baka so? Zaka rage jin gajiyar" "A'a nagode kawomin Abinci inci, ina so mu ɗan fitane zaki rakani unguwa" Ta kawo masa Abinci shima ta nayi tana damun sa. "Yaya Ammar naga kaman gemun ka ya ragu fa" "Eh na rage sumar kaina ne, akamin gyaran fuska" "to kuma se a rage maka gemu?" Ɗan tittiraza ƙafa tayi tace "Ni gaskiya dan Allah kar a ƙara rage wa, haba dan Allah ni ina son gemun fa" " zanje kuwa a aske shi gaba ɗaya" "da bazan ƙara kallon ka ba se ya fito" tai maganar tana miƙewa. Seda ya kammala cin Abincin sa sannan suka shirya zasu fita ya kalleta yace "Idan anyiwa mutum haihuwa me ake bashi?" "Waye ya haihu?" ta tambayeshi "Matar Aminu ce ta haihu har anyi suna ma, ni namanta ya gayamin" Mufeeda ta jinjina kai tace "zaka iya sai musu rigar Baby, Amma riga tana tsada sosai indai me kyau kake son basu, amma kaman ka basu kuɗin kawai ina da turaren wuta, se in bata nima" Ammar ya jinjina kai sannan suka gama shiri sannan suka fita. Kaman haɗin baki suna zuwa suka tarar da Saima da Jabir a gidan. Saima na ganin Ammar tare da Mufeeda tace "Gaskiya munji kunya, kamar in gudu yau gani ga Amaryar Ammar ban taɓa zuwa ba" Fiddausi tace "Ai nidai zatamin uzuri saboda nayi nauyi ne lokacin" Mufeeda dai ba tace komai ba se Murmushi da take yi ta zauna suka gaisa da su Aminu da Matansu. Aminu yace "Ammar se yau zaka zo kaga Jaririyar ko? Yau kwana tara da haihuwa" Ammar yace "to komu koma ne? Ai badan Fiddausi ba ba zanzo ba, kai kaje gida nane?" Aminu yai murmushi yace "Allah ya bada haƙuri" Tunda suka zo Jaririyar take kuka, aka miƙawa Ammar Jaririyar, Amma sam be iya ɗaukar Yara ba, yanayin yadda ya riƙe yarinyar kasan be iya ba. Mufeeda taje kusa da shi tace "Yaya Ammar ai ba zata yi shiru a haka ba, kalli yadda ka ɗauke ta fa, kawo ta ka gani" tasa hannu ta karɓeta, tana jijjiga yarinyar amma ba ta dena kuka ba, wuyan Yarinyar yayi ƙananan ƙuraje saboda zafi kuma yarinyar nada jiki, Mufeeda tace "Maman Baby dole taita kuka fa, zafi take ji" Mufeeda ta cirewa Yarinyar kayan jikin ta, ta shafe ta da Hoda sannan ta ki fata akan cinyar ta tana shafa bayan ta tareda jijiya yarinyar, shiru Yarinyar tayi dukda ba bacci take ba, Jabir yace "Ikon Allah, To ke Fiddausi ya akayi baki iya raino ba, Mufeeda karki yadda ko koya masa yadda ake raino in bahaka ba idan naku Babyn yazo kudinga yi tare" Saima tace "Mufeeda kina son Yara Allah yasa nan da 'yan watanni muzo mu ɗau naki" "Taɓɗijan nima Yarinya ce har yanzu rainona ake, ban isa inyi raino ba" Tai maganar kaman' yar Yarinyar, Ammar ya Harare ta, ita kuma tai masa Murmushi, Jabir yace "Babbar magana" Aminu yaja su Ammar suka koma part ɗinsa suna hira, suka bar su Mufeeda a tare. Ammar yace "Jabir ya batun matsalar ka da Saima kuwa? Ina fatan yanzu komai ya daidaita" Jabir yace "ba dai komai ba, Amma da ɗan sauƙi" Aminu yace "Jabir kenan, ai kamata yayi komai ya daidaita ka dena wayar da 'yan matan kokuwa?" "A' a fa inayi amma na dena yi a gida sosai, zamana nake a waje insha wayata sannan in dawo, dukda haka shima be mata ba ƙorafi take" Nasihar dai suka ci gaba da yiwa Jabir. Mufeeda ta ɗan saki jiki da su Saima suna hira Sama sama, Saima tace "Nima Allah ya nuna min na rabu da nawa cikin lafiya, amma ina jin tsoron haihuwa" Fiddausi tace "Wallahi da wahala, amma in har kika kwantar da hankalin ki, kika kula da cimarki da shan magani zaki rabu da shi lafiya insha Allah" Saima tace "Ai abunda yake bani tsoron be wuce duk lokacin da naje Awo se a cemin jinina ya hau ba, harfa sun ɗorani akan maganin hawan jini" Mufeeda tace "Subhanallah, Allah ya sawwake kuma ba'a son hakan, Allah ya baki lafiya" Fiddausi tace "Amma meyasa jinin ki yake hawa?" Saima tace "to ya zanyi Fiddausi, nifa ba dan anyi test na gano da cikin nan ba to da sena kashe auren nan, nayi haƙuri ne saboda bana son Abunda zan haifa yayi irin rayuwar wahalar da nayi saboda rashin uwa a gidan, to yanzu ga hawan jini ina tunanin ko zanyi rai idan nazo haihuwar oho"tai maganar kamar za tayi kuka Mufeeda tace "Amma Anty Saima meyasa zaki kashe auren ki? Naga Yaya Ammar yace min saura watanni bikin mu akayi naku" Ajiyar zuciya Saima tayi tace "Bari Mufeeda babu komai a rayuwar Auren da nayi se nadama, Unguwar mu ciki harda mijin ki babu wanda be san soyayyar mu da Jabir ba ciki hadda mijinki, mutane na ganin tsaurin Ammar sosai duk cikin su ukun nan babu me sauƙin kan Jabir, ina ta murna nayi dacen Mijin Aure wanda ze sharen kuka na, Amma me bayan Auren mu komai ya canza, har ƙarfe biyu seya kai yana chatting, ko yaya nayi masa laifi se zagi da ashar yana cin mutuncin iyayena na rasa me nayi masa tun ina haƙuri na fara ramawa, ga gori wai ni 'yar matsiya ta ba akwoni da abun kirki ba, bayan Jabir yasan halin da nake ciki a gidan mu, a hannun kishiyar uwa na tashi kuma mahaifina bame ƙarfi bane, ya zama bani da mutunci a idon sa se dare yayi yana buƙata ta, na kasa jure cin mutunci da wulaƙanci da yake min na fara ramawa, na dena saurarasa na dena masa duk wani abu na biyayya kona kyautatawa baya jin ko ɗar ya wulaƙantani ko a gaban waye nima bana jin komai nake ramawa" ta ƙarasa maganar tana hawaye Gaba ɗaya jikin Mufeeda yayi sanyi, tace "Anty Saima be kamata ki dinga biye masa ba, tunda kika riga kika yi Aure, idan kika kashe Auren kika koma gida baki da wata makoma a gida, idan har kukayi faɗa kika biye masa kikace sekin rama to tabbas kece zaki sha haushi, shi ze fita ya sha iska ya manta kunyi, amma ke kina gida ke zaki cigaba da shan takaici, kuma ƙin kula dashi zesa 'yan matan su cigaba da jansa a jiki, amma kiyi ƙoƙarin kwantar da hankalin ki kodan lafiyar ki" Fiddausi tace "ni na rasa ma abun cewa" Saima ta goge Hawayen ta tace"zan Jarraba Mufeeda, Amma abun babu sauƙi fa" Suna cikin hirar ne Aminu ya shigo yace "Mufeeda Ammar yace ki fito ku tafi dare yayi" Seda Mufeeda ta sake ƙanƙame Jaririyar kaman kar ta bayar, sannan tabawa Fiddausi ita, ta bata abunda zata bata na barka, sukayi Sallama Mufeeda ta fito. Jabir yace "Gaskiya Ammar Amaryar nan tana son Yara, yakamata kuyi zuciya fa" Banza Ammar yayi masa yace "Mukam seda safenku" Sukayi Sallama suka fito, Ammar ya lura gaba ɗaya Mufeeda bata walwala dan tunda suka kama hanyar gida ko uffan bata cewa har sukaje, ya ɗauka kawai ta gaji ne tana jin bacci amma idan ya kalleta ta mirror se yaga kaman tunani take. Haka suka koma gida gaba ɗaya bata walwala, suna komawa tace masa seda safe ta tafi ɗakin ta, gaba ɗaya halin da saima ke ciki ne ya hana ta sukuni, ta kwanta da nufin tayi bacci amma baccin ya gagara zuwa, ƙishirwa take ji dan haka ta fito dan ta sha ruwa, Ammar yana falo har wannan lokacin, kusan sha biyun dare ko me yake oho? Bata kulashi ba, Seda taje ta sha ruwan ta dawo zata koma ɗakin ta, taji yace "Zo ina son ganin ki" Juyowa tayi jiki a sanyaye ta zo gaban sa ta zauna tare da sunkuyar da kai. Ya kalleta yace "Meke damunki ne?" Girgiza masa kai tayi tace "bakomai" "Kalleni, Bana son ƙarya, naga tunda muka taho mood dinki ya canza" cikin sanyi jiki tace "Yaya Ammar I give up" "you give up on what?" "Duk yadda ake gayamin akwai ƙalubale a Aure ban zaci ya kai haka ba se yau da Anty Saima ta bani labarin Auren ta, ita da tai Auren Soyayya kenan, ni meye tawa makomar da ya kasance ni kaɗai nake son mijina, ina tunanin ni wani irin ƙalubale zan fuskanta, na karaya sosai har na fara tunanin dama banyi Auren ba" Ta riƙo hannun Ammar tace "dan Allah Yaya Ammar idan saɓani yazo tsakani na da kai karkamin irin hukuncin da Jabir yakewa Anty Saima, bazan iya jure zagi ko in ganka kana mu'amala da wasu 'yan matan daba Auren su zakai ba" Kallon ta yake yadda take sharɓar Hawaye sosai hadda sheshsheƙa. Ajiyar zuciya yayi dan ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, janyo ta yayi jikin sa, ta kwanta sosai akan ƙirjinsa tana ci gaba da kuka, a hankali yace "Sunan sa Jabir, ni kuma Ammar dan haka ba lallai halin mu ɗaya ba, kinyi ƙanƙanta da fara damuwa ko tunani, ki sha chocolate ɗinki kiyi wasanki kiyi bacci kawai shi ya daxe dake a yanzu ba tunani ba" Sam Ammar be ɗauki abunda take faɗa so serious ba Cigaba tayi da kukan ta, Ammar yace "kiyi shiru, zan baki chocolate ai kina so ko?" "A'a Yaya Ammar let's be serious please" "kinga dare yayi, maza yi bacci" Noƙe masa kafaɗa tayi ta cigaba da kuka. "zamuyi faɗa fa, ki dena kuka ko kina so muyi faɗa?" Ta girgiza masa kai "to Yimin shiru, kowa ya aikeki shiga cikin manya oho, gobe kikuma shiga zancen manya sekin jiyo abunda ze hana ki bacci" "Ai nima babbar ce tunda ina da Aure ai" Ammar ya kalleta yace "Au haba? Ashe matar Aure ce, yaushe kika zama matar Aure?" "ranar daka bada Sadaki aka ɗaura mana Aure" Ammar yace "Amma ai baki biya sadakin da kika ci ba " Sarai ta gane inda zancen sa ya daosa amma tace "Dama in anci sadakin biya ake? Ni ban taɓa jiba" Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna kallon juna yace "Hmm baki taɓa ji bako? Idan na kuma cewa ke Yarinya ce kikamin Musu sekin biyani Sadaki na" "Se inje ince Baba ya biya ka, amma ni ban taɓa ji ba se yau a gurin ka" "Ke kika ci dan haka ke zaki biya" Shiru tayi masa ta lumshe ido ta ƙara shigewa ta kwanta a jikin sa. A hankali yake shafa gashin kanta, zuwa jimawa ta fara sauke ajiyar zuciya alamar tayi bacci. Ammar a ransa yace "Allah karkasa na zama daga cikin Azzalumin maza" Dukda yana mata kallon Yarinya, Amma she's so Simple gata da Biyayya sedai rikicin ƙuruciya. Domin gyara, sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 .✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 18 Baccin ta take hankali kwance a jikin Ammar, yasa hannu ya ɗago nata hannun, lallen hannun ta ya ƙara dark sosai gwanin sha'awa, a hankali ya kai hannun ta hancin sa ya shaƙi ƙamshin lallen, haka ya dinga wasa da da yatsun hannun ta, bacci yake ji sosai amma kasalar da yake ji ta hana shi motsawa dan haka ya zame ya kwanta a kan carfet da Mufeeda a jikin sa bacci yayi awon gaba dashi. Se Asuba sannan ya farka, yaje yayo alwala sannan ya tashe ta, ba ƙaramin mamaki tayi ba kenan a falo ta kwana. Miƙe wa itama tayi taje tayi salla ta koma baccin ta. Bata farka ba se wajen ƙarfe goma na safe, da sauri ta miƙe ta shiga tai brush ta fito a gurguje bata san ya akayi tayi bacci haka ba. Ammar baya falo ta nufi kitchen da sauri ta tarar, ya dafa tea ya zuba a flask ya shirya komai kaman yadda take yi, fitowa tayi tsakar gida ta tarar ya haɗa kan kayan sa da nata ya wanke, duk ya shanya yana wanke adaidaita sahunsa. Da sauri ta nufi inda yake tace "Yaya Ammar dan Allah kayi haƙuri, ban san ya'akayi ban tashi da wuri ba yau" "to ni nace kinyi laifi ne?" "A'a amma bekamata ace kai kayi aikin gida ba yau" Ɗan kallon ta yayi ya ɗauke kansa ya ci gaba da aikin da yake yi, rigar bacci ce a jikin ta iya gwiwar ta. "Allah dai yasaka maka da Aljanna mijin so, har wanki kayi mana ni har kunya nake ji idan naga ka wanke min kaya na, ni yakamata in wanke naka" Ya ɗago ya kalle ta yace "Nakin ma in kin wanke ba fita za suyi ba, balle ki wanke nawa" Murmushi tayi tace "bari inzo in tayaka wankewa" "No nagode kije kiyi breakfast ɗinki rana tayi" Ƙarasawa tayi ta riƙe duster da yake goge ruwan jikin Napep ɗin tace "My love wai baka son in dinga samun ladane? Komai seka hanani yi" "Aike ba afara baki lada ba, in kinyi abun kirki sedai a rubutawa su Mama" Wani irin kallo tayi masa, wanda seda ya sashi yin murmushi be shirya ba yace "Au Sorry namanta ashe fa ta isa afara rubuta mata lada da zunubi, ni shedane ma" Zumɓura baki tayi tana kallon sa, aikin sa ya cigaba da yi, ya ɗago yaga still tana tsaye "waiba cewa nayi kije ki karya bane?" Juyawa tayi ta koma, taje ta zauna ta karya, seda ta gama sannan ya shigo falon ya kalleta yace "Prof a haɗa min ruwa zanyi wanka" Ba tace komai ba ta miƙe, taje kitchen ta ɗakko ruwan zafi ta shiga ɗakin sa, ya tuɓe gajeren wando ne a jikin sa, ya tsuguna a hanyar da zata wuce yana duba wani abu, ɗagowa yayi ya kalleta yace "Wuce mana" Se wani Sunkuyar da kai take kamar mara gaskiya. Ta wuce shi ta shiga toilet, ta haɗa masa har zata fito yace "tsaya inzo in duba, nafi son shi da zafi sosai" Sauri take ta fito daga banɗakin ta bashi guri, amma ya riga ya shiga, ya kalli ruwan yaga yana tururi ya taɓa yaji da zafi, ya ɗago ze mata magana yaga tana ta sunkuyar da kai bata son kallon sa. "duba kan Mirror ki bani sabulu" Da gudu gudu ta fice daga banɗakin dan a matuƙar tsorace take, Ammar yana kallon yanayin ta, da ta ɗakko sabulun ƙofar toilet ɗin taje ta tsaya, kaman za tayi kuka ta ɗan zira sabulun tace "gashi" "Idan ba zaki miƙomin ba ki mayar bana so" "to ai gashi ina miƙo maka" Shammatarta yayi ya janyo ta cikin banɗakin. A firgice tace "Wayyo Allah na Mama" Ya riƙo ta gam yana kallon ta, gaba ɗaya a firgice take, jikin Ammar lulluɓe yake da gashi, ƙato ne na gaske, jikin sa a murɗe yake, kallo ɗaya zaka masa kasan ƙaƙƙarfan Namiji ne. A hankali yace "wai meye hakane?, se wani sunkuyar da kai kike kaman kinga abun tsoro?" Zazzare ido take tana ta sauke numfashi, "Dan Allah Yaya Ammar ka cikani kayi wankan ka, ni bana son ganinka a haka" "Meye ba kyason ganin?" "dan Allah ka cikani" Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, Kaman yayi dariya yadda take rarraba ido, amma ya maze yace "Ki jirani a ɗakin nan, idan kuma kika sake kika tafi nida kene" Haka ta fito ta zauna a gefen gadonsa tana maida numfashi. Ammar ya daɗe sannan ya fito, yana fitowa kaman ɗazu ta ɗauke idon ta daga kansa, basarwa yayi yaje ya ci gaba da shirin sa, juya masa baya tayi ta rintse idon ta ita a dole karta kalle shi. "taso kizo" Ta juyo a hankali taga ya saka dogon wando da shirt, tasowa tayi ta nufi inda yake tana raɓe raɓe, ya dube ta yace "Mara kunya kawai, lokacin da kike yawo da underwear da nace kidena cewa kika yi sedai a raba falo, shine yau kike wani sinne kai, to ai nan ɗakina ne dole insa abunda nake so" Zumɓura baki tayi, yace "ni kike zumɓurawa baki?" Da sauri ta girgiza kai tace "Nifa ba zumɓura baki nake ba" "ƙarya nayi kenan?" Da sauri ta girgiza kai tace "A'a yi haƙuri" Mufeeda akwai bada haƙuri, da ance tayi laifi za tace Allah ya bada haƙuri. "zo nan ki zauna" ya nuna mata bakin gado. Ta ƙarasa taje ta zauna, ya durƙusa ya buɗe drower ɗin jikin Mudubinsa ya fito da wata leda. Wata jaka ce silver me matuƙar kyau ya ciro ya miƙo mata, yace "Wannan ce Jakar da kika saka a status ɗinki?" Zare ido tayi tace "Amma Yaya Ammar ai ba cewa nayi ka saimin ba" "tambayar ki nayi itace?" Jinjina masa kai tayi alamar Eh, idon ta cike da hawaye. Ammar Yace "to gata nan a kashe lafiya, lokacin da kika saka bani da kuɗin ta ne, Amma a kwanan nan Alhamdilillah idan na fita ina samun ciniki sosai" Kasa magana tayi, kawai ta faɗa jikin sa ta rungume shi "Allah ya biya ka da Aljanna mijina, Allah ya ƙara sutura da Arziki, Allah ya ƙara wa su Umma lafiya da nisan kwana, nagode, nagode" Ji yayi kaman ya rungume ta sosai, se ya tuna za'a iya samun matsala dan haka yace "to sarkin kuka, ke komai ma sekin masa kuka, godiyar ta isa haka" Girgiza kai tayi tace "ai babu kalaman da zanyi Amfani dasu da zasu nuna godiya ta a gare ka Hubby na" "Wai kin gama jin tsoron nawane da kika rungume ni? Mara kunya" Cikashi tayi tana rufe ido, haka suka yi sallama ya fita. Abunda ta lura shi ne duk lokacin da tayi wa Ammar wani abu da ya ji dadi baze nuna mata ya ji dadi ba, sedai zeta ƙoƙarin yi mata kyauta, ko wani abu da zeta farinciki. Kamar yadda ya mata Alƙawari sati ya zagayo, ta shirya ya kaita taga gida, Kaman Yadda Mufeeda ta tsara a ranar suka shirya zasu haɗu da yayyen ta a gida. Ammar ya shiga da niyyar su gaisa dasu Baba, ya shiga ya gaida Baba, sun daɗe suna hira da Baba sannan ya fito ya shiga falon Mama, Su Yaya Fadeela, Anty Murja da Yaya Amina duk suna falon, Ammar ya shigo har ƙasa ya durƙusa ya gaida Mama Mama tace "Sannu Ammar ya gida, ya haƙuri da Auta?" Murmushi yayi yace "Alhamdilillah" Suka gaisa da su Anty Murja ma, an ɗan taɓa hira da shi kaɗan, yace ze tafi, Mufeeda ta tashi ta bi bayan sa Seda sukace gareji tace "Hubby yaushe zaka dawo mu tafi?" "Se magariba insha Allah, yau ki huta sosai a gida" Tai murmushi tace "to ya za'ayi da Abincin rana fa?" "Don't mind me, sena dawo ɗaukar ki" "Shikenan I will miss you for the whole day Honey, take a good care of yourself" Juyawa yayi yana murmushi ya fice. Ta koma cikin gidan, tana zuwa Yaya Fadeela tace "Shegiya Auta se da kika samu jakar nan, waye ya saimiki?" "Mijina mana" Yaya Amina tace "kai Auta Jakar nan fa da tsada amma kika takura masa ya saimiki" "Yaya Amina kema kin san bazan takura masa ba, gani yai na ɗora a status, kawai shekaranjiya ya bani" Anty murja tace "Lallai 'yar gatan miji, gwangwajewa, kuma dan Allah yana sakin jiki ya miki hira? Baya son Magana" "Nida sauran Mutane ɗaya ne da ba zamuyi hira ba?" Yaya Fadeela tace "Oh ni Fadeela Allah rahimi, wai yau Autace a cikin mu ake hirar miji dake, Allah me iko" Nan suka dinga hirar yaushe rabo, daga Auren ta zuwa yanzu ta ƙara ƙiba sosai kamar ba ita ba. Cikin hikima Mama take bugun cikin Mufeeda don taji yanayin zaman ta da Ammar, amma yadda Mufeeda ke mata bayani ya tabattar mata Mufeeda na cikin kwanciyar hankali. Mama tace "Mufeeda mijin ki akwai tsatstsauran ra'ayi, ranar da yazo gidan nan ya gaishe mu, na bashi bushashshen kifi da Nono da aka kawo daga munjibir ya kawo miki, amma yaƙi karɓa wai basu kawo ba baze karɓe mana ba" Mufeeda tace "to aini be gayamin yazo gidan nan ba" "Yazo ya gaishe mu, ya kawo mana kayan miya fal" "hmm be gayamin ba, Haka halin sa yake baya son aga gazawarsa ta ko ina, inaga ranar ne ya zomin da ƙaton kwalin madara, ko a zaton sa nina tambayeki" "aini yaron ya birgeni, haka ake son magidanci ya zama me wadatar zuci, sannan kema tunda kinsan halinsa ki kiyaye duk wani abu da zakiyi daze nuna ya gaza miki a wani abun" "Insha Allah Mama zan kula, kuma kinsan ni bame kwaɗayi bace" "hakane amma duk da haka ya kamata ace na ƙara gayamiki" Mufeeda ta tafi gurin Baba, nan ma ta shan take sukaita hira da mahaifinta wadda ke nuna yadda suka yi kewar juna, seda Baba ze fita da azahar sannan ta baro ɗakin sa. Gurin su Anty murja ta koma suka ci gaba da hirarsu, taji daɗin haɗuwa da 'yan uwan ta yau, Ga masu ƙaramin ciki ga ƙananan yara haka aka dinga ɗora tukunya ana saukewa, Mama tasha hidima da' ya'yanta da kuma jikokin ta. Ammar be dawo ba se bayan isha'i yazo ɗaukar Mufeeda, Mama tace aje ace masa "ya shigo yaci Abinci sannan su tafi" Bahaka yaso ba dan yana matuƙar jin kunya, haka ya shiga sitting room ya zauna, Mufeeda ta kai masa Abinci. Ammar yace "Nifa gaskiya inajin nauyi inci Abincin nan anan, kizo mu tafi gida se inci a can" Haɗe rai tayi tace "nice mara kunya da naje gidan Umma har na zage na dafa na ci ko, Bansan me yasa kake haka ba Yaya Ammar, Iyayena ɗa suka ɗauke ka ba sirirki ba, kaman Yanda su Umma suka ɗaukeni 'ya, basa jin daɗin yadda kake yi ɗin nan fa" Ɗan Ajiyar zuciya yayi yace "bahaka bane, ni tun asali irin wannan yana bani wahala, kuma ina matuƙar jin nauyin su ne, ba wani dalili yasa nake hakan ba" "to yanzu dai in koma ince mata kace ba zaka ci Abinci a gidan ta ba?" "zuba inci" Ta zuba masa Abincin, Amma da ƙyar yaci se kace mace. Mufeeda tayi shirin tafiya ta haɗa bagco guda na shirgi zata tafi da shi, kome ta gani a gida seta ɗauka tana so sukai ta faɗa da Yaya Fadeela akan seta ajiye kayan data ɗiba amma taƙi. Mama tace "dan Allah ki ƙyaleta karku yi faɗa, ke se kace kece sakuwar ta ba Amina ba" "Mama kenan da wani ne a cikin mu bazaki bamu ba, amma da yake Auta ce ai kin bata" Mufeeda tace "baki ji ba auta fa kika ce" Ammar yai Sallama a ƙofar falon yace "Mama zamu tafi" Mama tace "shigo mana muyi sallama" Ya shiga ya zauna a gefe Mama tace "Ammar naji daɗin yadda naga Mufeeda Allah ya ƙara muku zaman lafiya, Amma dan Allah idan muka bada abu daga gidan nan, ba mun bayar bane saboda ka gaza, da kai da Mufeeda duk 'ya' yan mune, A cigaba da haƙuri" Ammar yace "To Mama Insha Allah, nagode sosai" Fadeela ji take kaman tayi dariya idan ta kalli Mufeeda wai Ammar ne mijin ta, koya take da shi oho?. Ta ɗakko kayan ta, ta fito guri ta samu ta zauna zata saka takalmi da yake takalmin me igiya ne ga tsini, ganin da Ammar yayi zata ɓata masa lokaci yasa ya durƙusa yana taya ta saka takalmin, ya gama samata sannan ya ɗagota tsaye suka fita. Anty Murja ce ta fara hango su ta window ta nunawa Amina, sun sha dariya sosai, Amina tace "ai nasani indai da Mufeeda ze zauna duk wannan izzar ze dena ta ne" ********************* Kwanci tashi asarar rai, Mufeeda ta cika watanni huɗu cif a gidan Aure, a zaman ta da Ammar ta gama karantar sa fiye da yadda yake tunani, ta san fushinsa tasan farincikin sa, Ammar be tsaya iya sana'ar tuƙa a daidaita sahu ba duk wata sana'a da yasan zeyi ya samu kuɗi yana yi, iya yinsa yake ƙoƙarin ganin ya sauke duk wasu buƙatun gidan sa dana gidan iyayen sa. Dukda a fari baya son Auren yana ganin Matar tasa tayi ƙanƙanta da Aure, Amma a ransa yana jinjina tarbiyya da haƙurin ta, bata da damuwa sam ita dai kullum burin ta ta jadadda masa tana sonshi, laifi ko ita tayi koba ita bace, idan taga ya ɗau zafi se tayi shiru, kuma ta bashi haƙuri dan a zauna lafiya kuma dan kar ransa ya ɓaci, dukda a wasu lokutan shike da laifin ba ita ba amma seta karɓi laifin. 'yan kwanakin nan Ammar ya lura kamar akwai abunda Mufeeda take shiryawa, amma ya kasa gano menene, be takura mata baya son yawan damunta, da tana so ya sani da tuni ta gaya masa. Aka sanar dashi Jidda babu lafiya, ta kwan biyu a kwance, dan haka yasa Mufeeda ta shirya suje su duba ta, dan tunda yasan Jidda bata ƙaunar Mufeeda beyi gangancin kaita gidan ta ba. Koda suka je gidan Ammar ya tsaya gyara parking din Napep ɗinsa ita kuma ta riga shi yin gaba ta shiga gidan. 'Ya'yan Anty Jidda ta tarar a falo, se wata mata a zaune a falon, Jidda tana bedroom din ta . Mufeeda ta gaida matar dukda matar ma ba wata babba bace, Matar se kallon ta take. Babu tsammani Jidda ta fito daga ɗaki taga Mufeeda, aikuwa take ta wani haɗe rai kamar taga kashi. Mufeeda tace "Anty Jidda ina wuni" "Lafiya" "Ya jikin naki?" "lafiya kalau" Jidda ta kalli ta falon tace "Zainab gafa Amaryar ku, matar Ammar" Ai da sauri Zainab ta kalli Mufeeda tace "Wannan ɗin? To ai wannan da Auren wuri Ammar yayi da ya haifeta" "to gata nan dai" Zainab tace "to aini Anty Jidda banga abun so anan ba, wannan ai bata kai macen da Ammar ze kalla ba balle ya aura, amma dai a ƙauye take ko?" Jidda tace "A'a 'yar cikin birni ce, wataƙila ta gallabi iyayen ne shiyasa suka aurar da ita" "Amma dai Ammar ya bada maza wallahi, meze samu a jikin wannan' yar kaman mutum mutumi? Kalleta fa" Da farko Mufeeda tai shiru taƙi kula su, amma ta fara ƙuluwa dan haka ta zumɓura baki tace "Abunda ake samu a jikin ko wace mace" Zainab tace "ke karki sake kimin rashin kunya wallahi, yanzun nan se in tattaka ki, aini wallahi Anty Jidda wannan abun kunya ne inyi kishi da ita wallahi" Sallamar Ammar ce ta katse Zainab dan sam basu san tare suke ba. Yadda Zainab take Zaune jikin ta babu mayafi da wata pitted shirt haka Ammar ya shigo ya same ta bata rufe jikin ta ba, Mufeeda ta koma gefe ta haɗe rai. Ya samu guri ya zauna a gefen Mufeeda, Ya kalli Jidda yace "Sannu ya jikin naki?" "Da sauƙi Alhamdilillah nama warware" "To Allah ya ƙara lafiya" Zainab ta kalle shi tace "Ammar ina wuni" Ɗaga kai yayi ya kalleta yace "lafiya kalau, ya me jikin?" "gata nan taji sauƙi Alhamdilillah, Amma ta sha jiki" Ammar yace "banga alama ba dan ƙiba ma tayi" Jidda tace "a hakan ne ban rame ba, ai kuwa na rame sosai" Zainab tace "Haba Ammar ka kalleta fa da kyau, Allah Anty na ta rame sosai, kalli fa na fita ƙiba yanzu" tai maganar tana wani girgiza jikin ta Ammar yace "mhmm hakane" Ya kalli inda Mufeeda take ta haɗe rai tai kicin kicin, tsagwaron kishi ne kwance a fuskar ta, ya ɗan matso kusa da ita yace "Ya dai? Meke damunki ne?" "Bakomai" ta bashi amsa Ƙara ƙasa yayi da muryar shi yana leƙa fuskarta yace "gayamin a kunne na meyafaru ne? " Girgiza kai tayi tana tura baki. "ko chocolate ɗince?" yai maganar yana murmushi. Sam Ammar yama manta ba a gida suke ba, ba Zainab ba hatta Jidda kallon Ammar take da mamaki, Ammar ya zauna yana wannan murmushin sedai in a cikin abokan sa yake. Mufeeda cikin shagwaba tace "ni mutafi gida" "Anƙi a tafin, se da magariba zamu tafi, ga Zainab nan seta ta yaki hira" Wata uwar harara tayi masa, ta yunƙura zata tashi ya riƙe ta yana dariya. Ɗaga kai yayi yaga yadda Jidda da Zainab ke hararar su. Miƙewa yayi yace "bari mu tafi, Allah ya ƙara afuwa, ga wannan ki sai wani abun" ya ajiyewa Jidda kuɗi. Jidda kasa cewa komai tayi se binsu da kallo, Mufeeda tace "Anty Jidda, Allah ya ƙara sauƙi" Tai waje abun ta. Zainab ce ta biyo su da sauri tace "Ammar dan Allah ina son muyi magana" Yace "yi sauri ina jinki, Prof ta fara gajiya" Harar Mufeeda tayi ta tabe baki, kallon su Mufeeda tayi tai tsaki tai gaba abun ta. Ba tasan me Zainab ta cewa Ammar ba, ya fito daga soron ya kunna Napep din suka tafi. Suna zuwa gida ta fice daga a daidaita sahun tai tafiyar ta ɗaki, bata ko tsaya ta saurare shi ba. Abincin daren sa a falo ta ajiye masa bata ko bi ta kan sa ba. Da safe ma be sata a idon sa ba, dan haka ya bita ɗakin ta, tana kwance tayi rigingine tana kallon roofing ɗakin. Ya kalleta yace "Azo a taimakeni da ruwan wanka in ba damuwa" Juyowa tayi ta kalle shi, ba tace komai ba ta fito ta wuce shi, taje kitchen ta dafa masa ruwan ta kai masa banɗakinsa, ta fice seda ta tabbatar ya shiga banɗakin sannan ta koma ɗakin nasa tana gyara masa dan yayi ƙura. Wayarsa ce take ta ringing, bata damu ba balle ta duba me kiran, Ammar ya fito daga banɗakin yana goge ruwan jikin sa yace "bakyajin wayata tana ringing ne, miƙomin tunda ke bazaki ɗaga ba" Ganin sunan Zainab akan screen ɗin wayar yasa ta ɗakko wayar hannun ta na rawa ta jefa masa a ƙirjinsa ta fice. Binta yayi da kallo yana jinjina wannan kishi na Mufeeda, ɗaki ta tafi taje taita kuka saboda ɓacin rai, gani tayi kuka baze fishesheta ba dan haka ta fito falo tayi aikace aikacen ta. Amma ta tarar Ammar yana waya a falon, ta daure ta tafi kitchen, ta kuma fitowa taga still waya yake, kuma alamu sun nuna da mace yake wayar, har tayi gaba kawai ta juyo a zuciye ta fizge wayar daga hannun sa ta buga ta da ƙasa. Ɗagowa yayi a matuƙar zuciye cike da Masifa, ya kalle ta se huci take Hawaye na bin fuskarta. Share please Domin sharhi, gyara ko shawara Ayshercool 07063065680.[08/07, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 19 Binta da ido Ammar yayi, a fusace yace "baki da hankali ne? Meye hakan kikayi? Ɗazu kin jefomin waya na ƙyale ki yanzu kuma kin fasamin waya kin kyauta kenan? Wace irin Yarinya ce ke haka? Wane irin hali ne wannan? " Ta ɗago manyan idanun ta ta kae shi tace "Nice bani da hankali ko? Nagode bani da hankali na Yadda" ta juya da sauri tabar masa falon, binta yayi da kallo yana mamaki, ta masa laifi kuma tayi fushi (Nikam nace ashe babu daɗi, mutum yayi lefi ya maze ya ɗorawa abokin zamansa laifin da gangan" Har Ammar ya kammala shirin sa ya fice be kuma ganin ta ba, shima da ya fita be dawo gida ba se bayan magariba, bayan magariban ma daya dawo bega Mufeeda ba, ta ajiye masa duk abunda ya kamata wanda ze buƙata, amma bata falon. ************* Washegari bayan fitar Ammar sannan Mufeeda ta fito falon, ta kammala ayyukan gidan ta zata ɗora girki amma taga bata da kayan miya, gashi bata kula Ammar ba balle ta gaya masa babu kayan miya, shiryawa tayi ta fita yin cefane, tunda ta fito kan babban layin taga Wata ƙatuwar Mota tana binta, bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da tafiya. Taje gurin Sa'idu me kayan miya domin Siyayyar kayan miyan, Sa'idu yace "ko kece Amaryar kusa da gidan Maman Nur?" "Eh Nice" ta bashi amsa a taƙaice. "Allah sarki, da alama naga ke ba irin halinku ɗaya ba, kina da nutsuwa da hankali, amma yakamata ki kula sosai kiyi taka tsantsan dasu dan basu da kirki sam basu san ciwon kansu ba" "to ni jna ruwa na? Ko tambayar ka nayi?" "A'a naga kina da nutsuwa ne, shiyasa nace bari in miki magana kiyi hankali da su" "Malam dan Allah bana buƙatar jin wannan maganganun naka, ka sallameni in tafi dan Allah" "to shikenan, amma ni gaskiya na gaya miki" Tsaki Mufeeda tayi ta karɓi kayan miyan ta tace "Riƙe gaskiyar ka bana so" tai gaba abunta. Biyo bayan ta me motar nan ya ci gaba dayi yana mata horn, juyowa tayi domin ganin dalilin da yasa ake mata horn bayan ta bashi hanyar daze wuce. Parking me motar yayi, me ya buɗe murfin Motar ya fito, Babban Mutum ne a ƙalla ze shekara Arba'in da biyar, ya ƙaraso inda Mufeeda take yana wani ƙarama ta kallo yana murmushi, Sanye take da dogon Hijjabi tun daga Sama har ƙasa, ya gyara tsayuwar sa yace "Baby tun ɗazu nake binki, ina ƙoƙarin yi miki magana amma ban samu dama ba" Banza tayi masa tana ƙoƙarin wucewa, Ya kuma shan gaban ta kaman zasu haɗe yace "Haba 'Yar kyakywa, ya ina miki magana kinƙi saurara ta, ki tsaya kiji dame nazo mana" "Malam meye hakane? Nifa matar Aure ce ka dena bi na dan Allah" Kallon ta yayi daga Sama har ƙasa yace"Ke ɗince matar Aure? Nima ai mijin Aure ne, dan Allah ki bani lokacin ki two minutes kawai Beb, Akwai saƙo me girma da nake ɗauke dashi daga zuciya ta zuwa gare ki dan Allah ki saurareni mana, Kyakywar Baby kamar ki nasan bazaki wuce your sixteen age ba, baki dace da tafiya a wannan ranar ba" A fusace ta kalle shi tace "Tir da Wannan saƙon naka, mara mutunci Ka kiyaye ni na gaya maka ina da Aure dan me zaka dinga bina haka? Wallahi zan maka tijara in taraka mutane a gurin nan na gaya maka, dalla ban hanya wuce dattijon banza kawai, wanda be san darajar Aure ba" Ganin Mufeeda ta haƙiƙance ne yasa ya bata hanya karta tara masa jama'a, aikuwa da gudu2 sauri2 ta ƙarasa gida se haki take. Duk abun nan daya faru akan idon Sa'idu me kayan miya, riƙe baki yai yana jinjina kai, Yace "Au dama duk ustazancin nata na ƙarya ne, ance me Napep ne mijin ta me kuma ya haɗa ta da wannan me motar? Taɓɗijan mata na abunda suke so a duniya, Fuska biyu da rana tsaka lallai yau akwai zazzafar Jarida a majalissa" Nan ya ci gaba da ƙanan surutan sa. Koda ta koma gida, mita ta ci gaba dayi da mamakin maganganun wannan shashashan mutumin mara mutunci, Seda tayi salla ta huta sannan ta ɗora girki, loka2 idan ta tuna abunda mutumin nan yai mata ta kan yi tsaki. Sosai take missing ɗin Ammar, tayi kewar murmushin sa, da sauran Nishaɗin da yakan sata, amma idan ta tuna abunda Zainab ta dingayi masa ranar, da kuma Yadda take kiran sa a waya se haushi ya kamata. Yauma ya gaji sosai bayan isha'i ya dawo gida, gaba ɗaya kwanakin nan da Mufeeda ta watsar da shi se yaga gidan yayi masa faɗi, gidan baya masa daɗi, kosan fitowa falon ba yayi ko Abincin ya fara ci se yaji baya masa daɗin ci, gashi yanzu duk wanda ze bashi Abinci inba na gidan sa ba ba yajin daɗin sa. Abunda yake ƙara bashi mamaki be wuce Yadda take takatsan tsan gurin kiyaye ɓacin ransa ba, Amma ƙiri Ƙiri tayi masa laifi amma ta maze tana fushi, to zuwa ze ya rarrashe ta ko kuwa? Wata zuciyar tace "kai aikuwa daka faɗo wannan 'yar Yarinyar zaka bawa haƙuri, ita fa tayi maka laifi" Wata zuciyar kuma tace masa "But at least ya kamata kasan halin da take ciki" haka yaita saƙe2 a ransa. Seda yayi Sallar isha, har ya zauna ze ci Abincin ya fasa ya miƙe ya nufi ɗakin ta, ya tarar da ita tana zaune a tsakiyar gado tana wasa da gashin kanta data tsefe, yai Sallama ta amsa ba tare da ta kalle shi ba, tunda ya shigo ɗakin yaji yana tashin wani sasanyan ƙashi me daɗin gaske. Ya tako a hankali ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita, yayin da ta maze ta basar dashi kaman yadda yake mata a wasu lokutan idan yana fushi da ita. "Wai Fushin me kike yi hakane?" "Bakomai" ta bashi Amsa "Kin min laifi kin koma kina fushi, Allah ya shiryeki, tashi muje kici Abinci" "Ni na ƙoshi" Haɗe rai yayi ya ƙura mata ido, juyawa tayi ta sakko daga kan gadon tana tura baki, ta fice falo. ɗan girgiza kai yayi yabi bayan ta. Ammar ya takura ta ta dinga cin Abincin nan badan ranta yana so ba dan har ƙwalla tayi, yace idan tai masa kuka ze ɓata mata rai sosai. Suna cikin haka Wayar sa ta fara ringing, Idonta ya sauka akan Sunan Fa'iza da ke screen ɗin ƙaramar wayar sa, miƙewa Yayi ya tafi ɗakin sa Amsa wayar. A ɗan hasale ya ɗaga wayar yace "Ke lafiya kike kirana yanzu? Meye hakan kikayi?" "Bakomai Yaya Ammar bugowa nayi in kwashi gaisuwa kawai, Sannan kwana biyu baka zo gidan mu ba" "Abunda zaki gayamin kenan ya hana ki kirani tun rana?" "to ai nasan lokacin kana aiki" "Yanzu kuma ina hutawa ne, karki ƙaramin haka na gaya miki" yayi tsaki tare da kashe wayar sa yace "Wannan wace irin takura ce? Mutum yayi Auren ma be huta ba? Da suke damuna da kira ni ina naga halin kuma Auren wata macen? Yanzun ma inji da rigimar wadda nake tare da ita mana" yai ta mita ya fito falo Koda ya dawo falon ya tarar bata nan, Kwanukan yadda ya tashi ya barsu haka itama ta barsu a gurin, shi ya tattare Kwanukan ya kai kitchen, ya tsaya yana wankewa dan ya lura bata barin ko cokali ya kwana bata wanke ba. Yana kammala wanke wanken akan ɗauke wuta, harze wuce ɗakin sa ya ƙyaleta ya jiyo sheshsheƙar kukan ta ta Window. Ƙofar ɗakin ta ya tura ya shiga, ya kunna fitilar ƙaramar wayar sa ya haske ta, duk tayi jifa da fulullukan dake kan gadon ta, ta baje gashin kanta se sheshsheƙar kuka take, haushi ne ya kama shi, daze balbaleta da Masifa se ya tuna tunda suke bata taɓa masa makamancin haka ba, idan har ya ƙyaleta a haka be kyauta ba gata Yarinya ƙarama. (Gareku Maza, ya kamata a dinga yiwa Mata Uzuri a wasu lokutan, idan har ya kasance mace tana kaman ta kyautatawa, wani lokacin ta birki ce saboda ɓacin rai ayi haƙuri a kai zuciya nesa, kar kace zaka hau ka ƙara mata tension, ka danne taka damuwar hankalin ta ya kwanta tukuna) Ammar yaje ya kwaso fulullukan da tayi watsi dasu a ƙasa ya mayar da su kan gadon sannan ya hau gadon. zuba mata idanu Yayi yana haskata yama rasa ta ina ze fara. Gajiya tai da kallon da yake mata, ta zame ta kwanta ta juya masa baya, kashe fitilar wayar Yayi shima ya kwanta ya matsa kusa da ita dai dai Kunnen ta Yace "Waike wace irin rigimammiya ce haka? Kinmin laifi baki bani haƙuri ba, kika fasa min waya bayan baki san da wa nake waya ba" Gaba ɗaya jinta tayi wani iri Yadda suke kwance a guri ɗaya yake mata magana. Ta dake tace "Nasani mana, da 'yan mata kake waya" "Shine kike fushi dan nayi Waya da 'yan Mata? Ai bani na kira su ba, su suka kirani fa" Banza tayi masa ta ƙara matsawa gaba. Aikuwa Ammar ya ƙulu yasa hannu ya fizgota yace "Ni kike wa wulaƙanci dan ina lallaɓa ki, ranar da nake Waya da Maryam nake magana, kije kiyi abunda kika ga dama" Jiki a sanyaye ta riƙe Hannun sa "Yaya Ammar ɗina, Nasan nayi maka laifi amma ban san a wannan karon me yasa na kasa haƙuri in karɓi laifina ba, Yaya Ammar ina shiga damuwa idan naga wata ta raɓeka, ina iya jure komai amma banda wannan, dan Allah kayi haƙuri bazan ƙara ba, Wayar ka ma dana Fasa kayi haƙuri please, ka karɓi tawa kasa layin ka seka bani ƙaramar in riƙe, kayi haƙuri kaji " " bana son wayar ki, ai bani na sai miki ba" "Eh nidai naji ka karɓi tawa please" Shiru Yayi bece mata komai ba yama rufe idon sa, miƙewa Zaune tayi tace "Dan Allah Yaya Ammar badan halina ba, kayi haƙuri Insha Allah ko dawa zakayi waya bazan ƙara maka haka ba, yanzun ma sharrin sheɗan ne" tai maganar tana riƙe hannun sa, ɗisar Hawayen ta yaji a hannun sa ya ɗan kalleta, dukda a duhu ne tayi kalar tausayi, tayi regretting har zuciyar ta. A hankali ya janyo ta jikin sa yana taɓa gashin kanta dake matuƙar birge shi, amma bece mata komai ba. "Yaya Ammar ka haƙura?" Shiru ya kuma yi mata. Cikin Muryar Shagwaba me cike da Yarin ta tace "Dan Allah kace ka haƙura" Still bece uffan ba, shiru tayi bata kuma cewa komai ba, ji tayi gaba ɗaya ta takura da yadda suke ɗin nan, Yanayin ya mata wani iri banbarakwai, dan haka ta Yunƙura zata miƙe taji ya riƙe ta gam, a hankali taji yace "Turaren wa kika shafa?" "Turare na ne" "Hmm ba irin wannan kike sawa ba" Yai maganar a hankali tare da Ajiyar zuciya Ɗan tura baki tayi tace "Yaya Amina ce ta bani ranar da ka kaini gida" Jinjina mata kai Yayi. Cikin shagwaba tace "Yaya Ammar bacci nake ji" "to yi mana ai ba hanaki nayi ba" "to ka cikani mana ka tafi ɗakin ka" Ɗan Murmushi yayi yace "Ni kike kora? To ai gida nane a inda nake so anan zan zauna" Ammar yana jin yadda zuciyar ta ke harbawa da sauri sosai, gaba ɗaya ya takura ta. Gajiya tayi da ƙoƙarin barin jikin sa tai shiru, amma ta kasa bacci tana jin Yadda yake sauke Numfashi ta ɗauka bacci yayi. A hankali ta kai hannun ta ta taɓa gemun sa dake matuƙar birge ta, ji tayi ya riƙe hannun ta, ɗan zaro ido tayi tace "dama idonka biyu wai?" bece komai ba se ɗan murmushi da yayi yace "Yau hankalin ki ya kwanta ko? Gobe zan aske shi" "Idan ka aske ko hmm ni nasan me zan maka". A hankali bacci me nauyi ya ɗauki Mufeeda, bugun zuciyar ta ya koma normal, Tunda Ammar ya shiga ɗakin ta zuciyar sa ke saƙawa tana warwarewa, ya rasa abunyi gaba ɗaya, wani gefen na zuciyar sa yace "Yarinya ce tayi ƙanƙanta" Amma Cikin bacci Mufeeda taji abunda bata saba ba dan haka da ɗan ƙarfi tace "Yaya Ammar meye haka ne? Nifa bacci nake ji, dan Allah ka koma ɗakin ka" Ƙarshe Ammar be gama yanke shawara ba, se bayan da komai ya lafa ya dawo hankalinsa, dafe kai Yayi tare da faɗin "Subhanallah, what the Fucking shit i did" Yama rasa me ya kamata Yayi, ya dafe kansa yai shiru, Yayin da kukan Mufeeda ke fita ƙasa2, ta shi Yayi a hankali ya kunna fitilar wayar sa ta dunƙule a cikin bedsheet tana kuka, gaba ɗaya tausayin ta da haushin kansa suka kama shi, wai yau shi ne ya kasance da wannan 'yar mitsilar Yarinyar da yake wa kallon me ƙuruciya. Ya miƙe ya fita, yaje ya kunna gas ya ɗora ruwa, Allah ya temake shi aka dawo da wuta, ɗakin ya dawo ya same ta yadda ya barta, yama rasa me zece mata. A hankali yace "Can I help you? Ga ruwa can na kai miki toilet" Sanin Halinsa yasa ta ɗan juyo ta tashi zaune tace masa "bakomai zan iya kula da kaina" Ta sakko daga kan gadon ta nufi toilet tana taka wa a sannu a hankali ya riƙe ta har ƙofar toilet, Ammar yace "but do you know how to take the ritual bath?" Juyowa tayi ta Harare shi a ranta tace "Sekace da shi yake min?" Amma a fili tace "An ko yamana a Islamiyya" Seda ta shiga toilet Sannan Ammar ya canza mata zanin Gado ya fita da wancan. Bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya yaji kamar ya koma ya kuma duba ta, kuma se yayi tunanin karta raina shi, wani kallo zata yi masa idan ya koma? ( Yo Yaya Ammar raini na nawa kuma? 🤔🤔 bayan..... 😜) Ya nemi guri ya kwanta. Wani irin farinciki ne ke ratsa Ammar wanda ya rasa na mene ne? A zahiri yana matukar raina Mufeeda yana ganin ƙanƙantar ta amma ta bashi mamaki fiye da yadda yake zato matuƙa, lokaci lokaci se ya ɗanyi murmushi wani lokacin kuma yayi tsaki a hankali zazzaɓi ya dinga rufe shi, tare da wani bacci me daɗi yayi gaba da shi. Da ƙyar Mufeeda ta iya bacci, dan har bacci ya ɗauke ta kuka take tana kiran wayyo Mama a hankali. *************** Da safe wata uwar makara yayi, dan bayan Yayi sallar Asuba har goma da rabi bacci yake, a hankali ya buɗe idon sa da suka yi masa nauyi ga kansa na sarawa, Ya miƙe ya shiga toilet ya wanke bakin sa ya fito. tunani yake idan ya fito ta ina ze fara haɗa ido da ƙanƙanuwar Yarinyar da ya kasa controlling ɗin kansa a kanta. Ita kuwa Mufeeda gajiya tayi da kwanciyar, dukda Jikin ta babu ƙwari tashi tayi ta sake wanka ta sha kwalliya ta shiga kitchen. Ga mamakin Ammar yana fitowa yaji ƙamshin Abinci, tana kitchen tana aikin ta, lallai Yarinyar nan wani lokacin akwai ƙarfin hali sannan ya jinjinawa juriyar ta, a hankali ya taka zuwa ƙofar kitchen ɗin, ta bawa kitchen ɗin baya dan haka bata san yazo ba. Ƙura mata ido Yayi yana kallon ta. Waya take yi da Yaya Amina, tasa wayar a hansfree ta ajiye tana waya. Mufeeda tace "Yaya Amina wai dan Allah wani irin turare kika bani ne?" "Turare ne kawai Amma meya faru?" "A'a bakomai tambayar ki kawai nake" Dariya Yaya Amina tayi tace "Kai Auta ki labarta min mana" "Uban me zan labarta miki? Keda Allah kawai Yaya Amina" Dariya sosai Yaya Amina take, suka yi sallama ta ci gaba da aikin ta. Seda Ammar yayi dariya mara Sauti da yaji tace wa Yaya Amina ita da Allah. babu tsammani ta juyo taga Ammar ta ɗan razana ta ce "Haba Yaya Ammar ni gaskiya ka bani tsoro, ban san kazo ba fa" Ya wani maze yace "Kingama girkin ne? Na makara zan fita" "yi haƙuri saura kaɗan" ya jinjina mata kai ya koma falo, dama ita tasan za'ayi haka, mazewa ze tayi kamar be komai ba. Har Yanzu da ta taho kawo masa kayan breakfast a hankali take tafiya tana yamutsa Fuska, wani irin tausayin ta ne ya kama shi, amma shi sam gani yake idan ya buɗe baki yai mata magana akan abunda ya faru koya mata sannu zata raina shi. Yana lura da ita Abincin ma bata ci ba Sosai, kaɗan taci ta barshi, seda ya gama ta miƙe zata kwashe kwanukan Kaman an masa dole cikin basarwa yace "Yi zaman ki kawai" Da yake yasan yayi aika aika, duk wani aiki na gidan shi yayi, amma ya buɗe baki Yace mata Sannu ya gode ne baze iya ba. Har Mamaki Halayen Ammar suke bata wani lokacin Yana dai ta kula da dukkanin Moves ɗin ta. Mufeeda ma kuwa ta nuna masa kaman babu abunda ya faru tunda haka yake so, har wani respect na musamman ta shiga bashi ko da wasa bata nuna masa sauyi saboda abunda ya faru jiyan ba. Wuni yayi a gida beje ko ina ba, Duk shi ya dinga ayyukan gidan, duk da shima baya jin daɗi, Mufeeda kam bakin ta yau mutuwa yayi, wuni sukayi kaman kurame, kusan akan kujera ta wuni gaba ɗaya jikin ta babu daɗi ciwo yake mata, Amma sedai Ammar ya kalleta ya ƙi ce mata komai. Daddare tea ya dafa mata ya sha Madara da Milo ya kawo mata, ɗan yamutsa Fuska tayi za tayi magana ya haɗe rai yace "ki karɓa ki ci Abinci kawai" Tana tura baki taci Abincin seda ya tabattar ta ƙoshi sannan ya sata a gaba ta tafi ɗakin ta ta kwanta, shima ya tafi nasa. Wayar ta ta ɗauka ta tura masa saƙo "Yaya Ammar bani da lafiya fa" "Meke damunki?" yai mata reply Emoji ɗin kuka ta tura masa tace "Ai kafini sanin meke damuna" "Ai ba jikin mu ɗaya ba da zan san meke damunki, ki gayamin mene ne, idan ya kama muje Asibiti semu tafi" "Shikenan tunda haka kace, Seda Safe have a nice dream Hubby, I love you" Juya message ɗin nata yaita yi, wani irin tausayin ta ne ya kama shi, tabbas yasan yayi mata ba daidai ba, dan shi kansa ya yabawa dauriyar ta, dan ta bashi mamaki, Amma baze iya zuwa yace mata wani abu ba, to idan yaje meze ce mata? Mufeeda harta rufe data zata kwanta aka kira ta a waya, ganin dare beyi sosai ba ta ɗaga, muryar Namiji taji suka gaisa tace "ban gane me magana ba" "Muffy beb, nasan bazaki gane waye ba, Amma me ƙaunarki ne, mezan samu ne daze sani nishaɗi" "Dalla Malam Saurara, ina da Aure meyasa zaka dinga kirana, ko so kake ka kashemin Aure?" "ƙwarai kuwa nasan ke Matar Aure ce, Amma kyakywar mace kamar ki baki dace da zama da Ammar ba, meze hana ki Auri wanda zaki huta kaman sauran 'yan uwanki?, zan baki zaɓi guda biyu ne, ko dai ki kashe Auren ki ki Aureni, ko kuma ki Amince mu dinga Soyayya muna hutawa ko kuma nida kaina ina kashe Auren, zaɓi ya rage naki" Mufeeda ta tashi zaune tace "Allah ya shiga tskanina da kai, yayi min maganin ka, Kuma koma waye kai Na barka da Allah ya nuna maka ikon sa, Kuma nida Ammar Mutu ka raba" Ta kashe Wayar ta, tayi blocking ɗin lambar, what's App ta koma taga Yaya Amina a online, nan ta gaya mata abunda ya faru da wanda ya kira ta yanzu da wanda ya biyo ta ɗazu. Amina tace "Anya Mufeeda ba duk mutum ɗaya bane, inaga wanda ya biyo ki ɗin nan ne, kuma da ƙyar in be sanki koya san Ammar ba, Abunda ya kamata shine ki gaya masa" Mufeeda tace "Kai Yaya Amina nasan halin abina, ƙyaleshi kawai idan, nayi blocking ɗin lambar sa" "Amma kina ganin babu matsala idan baki gaya masa ba?" "Zan gaya masa amma ba yanzu ba". Ɓangaren Ammar har ya kwanta yaji saƙo ya shigo wayarsa, da sauri ya ɗakko ya duba yayi zaton Mufeeda ce "KASA IDO SOSAI AKAN MATAR KA, DAN TANA AIKATA WANI ABU A BAYAN IDON KA, DAGA ME ƘAUNAR KA!!! In an karanta amin share zuwa wasu groups ɗin dan Allah Ayimin afuwa ba Editing Domin sharhi gyara ko Shawara Ayshercool 07063065680 [11/07, 8:43 PM] Ayshercool: ..✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 20 Shiru Ammar yayi yana sake juya message ɗin, tsaki Yayi ya ajiye tare da sawa ransa wrong Number ne kawai. Ya ajiye Wayar da niyyar yayi bacci amma ya dinga tunanin Message ɗin, Halayen Mufeeda ya dinga tunawa na kirki, dan haka ya ƙara tabattar wa da kansa cewar wrong Number ne, tunanin daren su na jiya ya tsaye masa a rai, yana tuno wasu abubuwan da suka kasance tsakanin su, ɗan murmushi Ya dinga yi tare da rungume filon sa, Tunani yaita yi a ransa ko ya jikin ta? Me ya kamata yayi mata ko ya bata wanda zesa taji daɗi, yana wannan Tunanin wani nannauyan bacci ya ɗauke shi. Da safe ma fitowa Yayi ya tarar tana ta aikace aikacen ta ya kalleta ko rigar bacci bata canza ba tana mopping "Sannu agogo sarkin aiki, ki dinga sassautawa kanki da wannan aikin mana" Ɗagowa tayi tare da yin murmushi ta ɗan risina tace "Ina kwana Yallaɓai" "Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?" "Alhamdilillah" "masha Allah" Yaje ya nemi guri yana zauna, ta kammala aikin ta, ta kalle shi tace "in kawo Abinci ne ko se an jima, ina so inje in wanka ne" "Je kiyi ki fito semu ci" Ta kalle shi ta lanƙwasa kai tace "za'a bani a baki?" "Je kiyi wankan ki dawo dai" Taje tai wanka ta canza kaya, sannan ta fito ta gabatar da kayan breakfast din, kaman Yadda ta buƙata Ammar ke bata Abincin a baki, yana ci yana bata. Mufeeda ta so tayi masa zancen wanda ya kira ta amma se taga Ammar yayi mata kwarjini bata san a ya ze kalli abun ba. Ɓangaren Ammar kuma tausayinta yake ji Sosai, yana son ya tambaye ta ya jikin ta? amma Izzar sa ta hanashi ji yake yin hakan tamkar ya faɗo ne a idon matar tasa. Se da suka kammala yana ƙoƙarin tashi yaje ya shirya, tazo ta kwanta a jikin sa. Ammar yace "Ya haka? Fita fa zanyi rana ta fara yi" "Nifa bana gajiya da ganin ka, ka bari in ƙara ganin ka mana" "Kinga ɗagani ina sauri" "Me kake so in girka maka kafin ka dawo?" "Kome kika dafa zanci" "Shikenan bari in jira ka anan ka shirya semu yi Sallama" "Zo muje ki tayani in shirya" Zumbur ta miƙe daga jikin sa ta koma gefe tare da tura baki "A'a ina nan ka shirya seka fito" Ammar ji yayi kaman yayi dariya amma ya basar ya shige ɗakin sa. Tana nan zaune a falo ya fito ya shirya tsaf ze fita, wani murmushi tayi masa daya sa Ammar ƙura mata ido, ta tafi inda yake tsaye tace "Kayi kyau sosai babban mutum, Allah ya kiyaye min kai ya ƙara mana Arziki, Allah yai maka jagoranci Namijin duniya" Ɗan murmushin gefen baki Ammar yayi yace "Ameen" sannan ya fice. ************** Mufeeda na zaune na aikace aikacen ta, yaro yayi sallama tai masa izinin ya shiga dan gidan Maman Nur ne ya gaishe ta ta amsa cikin sakin fuska, Yaron yace "Wai cewa akayi inzo in gaya miki umman mu ta haihu" Mufeeda tace "masha Allah, kace ina mata barka kafin in shigo" tai masa kyautar sweet sannan ta Sallame shi ya tafi. *********************** Nasreen zaune suna hira da Fa'iza , Nasreen tace "Fa'iza wai ya ake ciki da mutumin ne? Ina fatan zuwa yanzu dai kinyi wani ƙoƙari?" "bari kawai, ina ta up and down a gidan Anty Jidda ina kushe ta ina ƙara tura mata tsanar ta, in gaya miki anan naga wata guzuma wai ita ce tsohuwar budurwar Ammar wadda ze aura da, na maze in gaya miki ban nuna musu komai ba, Amma itama zata gane kuskuren ta, yanzu ba ta tata nake ba, ina nan ina shiryawa matar Ammar tarkon da ba zata fita ba se Auren nan ya mutu " Nasreen tace "Shikenan Allah ya taimaka, amma dai abi komai a sannu dan wallahi Fa'iza yarinyar ta fara bani tausayi, Yarinya ce ƙarama ga Sanyin Hali" Tsaki Fa'iza tayi tace "ki koma bayan ta kenan?" "A'a nina isa in koma bayan ta in bar 'yar uwa ta, bata isa ba ina bayan ki har yanzu" "In dai kina bayana to ki cigaba da goyan baya" "Karki wani damu ana mugun tare" Suka yi shewa tare da tafawa. ******************** Mufeeda ta kira Ammar a waya ta gaya masa anyi haihuwa zata shiga barka yace mata to. Da Yamma Ta shirya ta fita da niyyar yiwa Maman Nur barka, amma tana zuwa aka ce mata ai, an tafi da ita Asibiti tana ta zubar da jini Jaririn ma kaman bashi da lafiya. Mufeeda ta Jajanta musu ta fito, akwai surprise ɗin da take shiryawa Ammar dan haka ta miƙe ta tafi titi shagon da take son yin siyayyar da take buƙata. Seda tai siyayyar ta ta gama ta kama hanyar komawa gida. shan gaban ta akayi da Napep taji ance "Ke 'yan mata daga ina?" Ɗagowa tayi a fusace zata yi magana seta ga Ammar ne, Murmushi tayi tace "Nice' yan matan? To ɗan Saurayi siyayya na fito" Ammar yace "kin cemin zaki shiga maƙota barka amma in ganki anan, me kike yi?" "Allah ya bada haƙuri, Siyayya na ƙaraso titi nayi, kuma nayi niyyar gaya maka dama" "Shikenan shigo mu tafi" Ta ɗan kashe masa ido tace "Nawa zan biya?" Ɗan murmushi yayi saboda haɗuwar su ta farko ya tuna. Shiga tayi yaja babur ɗin, maimakon su tafi gida kai tsaye seda yayi zagaye da ita sannan suka nufi gida, a hanyar su ta komawa gida Mufeeda tace "Yaya Ammar zan sai Kayan miya a gurin me kayan miyan kan layi" Ammar ya jinjina mata kai, Kafin su ƙarasa bakin layin taga motar wannan mutumin da ya biyo ta ranar a ƙofar wani katafaren gida. Tunani ta fara yi a ranta "Kenan mutumin nan a unguwar nan yake kenan?" Ammar ya kalle ta ta mirror yace "ya dai? Akwai magana ne?" Saurin girgiza masa kai tayi alamar A'a. Suka tsaya gurin Sa'idu me kayan miya, suka sai kayan miya sannan suka yi gaba. Mijin Maman Amir na gurin me kayan miyan shima yaje siyayya, Sa'idu me kayan miya yace "Taɓɗijan Iska na wahalar dame kayan kara" Mijin Maman Amir yace "kamar yaya?" "Hmm ai Matan yanzu se Addu'a, wannan maƙocin naku me A daidaita sahun nan, baka ga Yadda yakewa gidan sa hidima ba, kusan kullum cikin cefane yake, ko ya shiga shagon Sunusi me kanti siyan madara, ƙwai bredi, kusan duk ɗan cinikin nasa a haka yake tafiya, Amma rannan da tsakar rana ba kunya na ganta ita matar tasa tana zance da wani Alhaji me mota, seda na ƙura ido naga ashe Wannan Alhajin ne na bayan layin nan, Alhaji Idris " Buɗe baki Baban Amire Yayi yace " Kai haba dai? " " Wallahi dagaske nake, Allah ya nunamin Annabi kamar yadda na gansu " "Taɓɗijan amma wannan anyi sakaryar mata, To Allah ya tona mata Asiri, shegiya da idon ta kamar an soya Aya, ashe munafuka ce, ai shiyasa mutum ya zama tsayayye a gidan sa, ni mata ta isa taimin wannan shirmen? A haka kalle shi kamar namijin gaske sakarai ni har ya ban haushi" Haka Baban Amir ya ci gaba da zazzga tare da zage zage shikuma me kayan miya yana ziga shi. Seda baban Amir ya tafi Sa'idu yace "Aikin banza ji yadda yake wani cika baki waishi ya isa da gidan sa, Kamar ba nan matar tasa take yawo kwararo kwararo tana fallasa Asirin sa ba, anan gurin nan suke zama take zazzage sirrin sa ba waishi ke ya isa da gidan sa, aikin banza, ni ina nan gefe ayi dai mu gani" ******************** Da safe Ammar ya tashi daga bacci ze fito ya ɗakko wayarsa ya kunna, saƙo ne ya shigo wayar sa yana dubawa saƙon Mufeeda ne na birthday wishes ya shigo wayar sa, saƙon cike yake da nuna fatan Alkhairi da kuma tsantsar Soyayya a ciki, Murmushi yayi ya ajiye wayar har ya miƙe wani saƙon ya shigo wayar sa "KA SA IDO AKAN MATARKA, TANA AIKATA RASHIN GASKIYA A BAYAN IDON KA" Mamaki ne ya kama Ammar shiru yayi yana tunani, yana sake juya saƙon, wani irin rashin gaskiya ne Mufeeda zata aikata a bayan idonsa? Tunani yake akan Yadda take masa biyayya iya yinta, taya za'ace tana aikata wani abu a bayan idon sa? Amma zeso yasan wanda yake ya turo masa wannan saƙonnin. A hankali ya ajiye wayar ya miƙe jiki a sanyaye ya fito falon. Yana fitowa ya tarar da Mufeeda ta saka mini Skirt da wata 'yar ƙaramar riga shara shara bata ƙarasa rufe mata cikin ta ba, tayi parking ɗin dogon gashin ta, ta saka hular hat tana rawa a falo tana juya jikin ta a hankali tana bin sautin waƙar dake tashi a talabijin ɗin dake falon, ba tsammani ta juyo taga Ammar a tsaye yana kallon ta, da Sauri ta ƙaraso inda yake tsaye tana faɗin "Happy birthday to you Hubby" Kallon ta kawai yake yi, ta riƙo hannun sa zuwa falon ya samu kujera ya zauna ta cire hular kanta ta dube shi tace "barka da zagayowar ranar haihuwar ka Mijina Allah yayi wa rayuwar ka Albarka" "Ya akayi kika san yaune ranar zagayowar haihuwa ta?" "Barwa zuciya abunda take so Hubby, ina son yin wani abu daze faranta maka kawai na samu labarin wannan kwanan watanne na haihuwar ka, shiyasa na maka barka da zagayowar ranar haihuwar ka" A hankali ya janyo ta jikin sa yana shafa gashin kanta da yasha gyara ya kwanta yana ta tashin ƙamshin mayuka, tunani yake akan saƙon da aka turo masa, yana cikin tunanin yaji muryar ta tace "Abun sona naso mu kasance cikin farin ciki yau, Amma naga kamar baka walwala, Allah ya sa ba laifi nayi maka ba"? Tai maganar jiki a sanyaye, Ajiyar zuciya yayi yace "muyi breakfast ko?" Jinjina masa kai tayi, har suka kammala Mufeeda na kallon sa tana tunanin meke damun sa? Sosai kayan da ta saka suka karɓi jikin ta tayi kyau sosai, Amma tunanin da yake yaƙi barin sa ya kalleta sosai. Ya shirya tsaf ze fita Mufeeda ta bishi Cikin sanyi jiki tace "Allah ya kiyaye hanya, Amma gaba ɗaya inajin babu daɗi da yanayin da kake yau, ban sani ba ko be kamata inji damuwar taka ba, Amma idan ni nayi maka laifin kayi haƙuri dan Allah" Bece mata komai ba ya fice. Gaba ɗaya Mufeeda haka ta wuni babu daɗi, ta shirya masa abubuwa da dama yau amma taga kaman baya cikin farin ciki, haka ta dake ta ci gaba da abunda ta shirya masa. Ɓangaren Ammar ma yana tunanin wani irin Abu Mufeeda zata yi haka a bayan idon sa, wani sashe na zuciyar sa na ƙara yadda da matar sa akan babu wani abu da zata iya aikatawa na rashin gaskiya a bayan idon sa, a zaman da suka yi ya yadda da amanar ta. Da daddare ya dawo gida a matuƙar gajiye, tunda ga falo yaga ta sauya tsarin falon, ta canza gurin zaman kujerun, ko ina se ƙamshi yake a gidan. Fitowa tayi daga ɗakin ta tayi simple make up, yanzu ma English wears ne a jikin ta, murmushi tayi masa tace "Birthday man sannu da zuwa, shine ka fita ka daɗe ko? Ko ka leƙo gida ai shikenan, zomu je ɗakina am having a surprise for you, na shiryawa wannan ranar sosai fa" A ɗan hasale yace "Ke ni ki ƙyaleni, bana son duk wannan abubuwan shirmen naki, ki rabu dani" Gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi ƙwalla ta cika idon ta tace "Yi haƙuri, Allah ya baka haƙuri, ban san baka so ba, dana san baka so da ba zanyi ba Insha Allah bazan sake ba, Allah ya huci zuciyar ka, Allah yabaka haƙuri" tai maganar muryar ta na rawa hawaye na bin Fuskar ta. Da sauri ta juya ta koma ɗakin ta ta rufe ƙofa. Jikin Ammar ne kuma yayi sanyi da abunda yayi matan, a hankali ya nufi ɗakin sa shima, yana buɗe ɗakin yaga shima tayi masa ado, ga zane zane na heart da tayi me ɗauke da sunan su a jiki da kalaman Soyayya dana fatan Alkhairi. Ga balloons data hura ta ƙawata ɗakin se ƙamshi yake, gefe ga cake me fari da pink ta saka HAPPY BIRTHDAY HUBBY, ga lemuka da alawoyi data shirya, tausayin ta ne ya kama shi, besan adadin lokacin da tayi tana wannan shirin ba, be san adadin kuɗin da ta kashe akai ba dan kawai ta sashi farinciki, amma lokaci ɗaya ya Gwale ta. Rage kayan jikin sa yayi ya shiga yai wanka yana ƙara kallon ɗakin yadda yai matukar kyau, fitowa yayi ya nufi ɗakin ta. Yana zuwa yaga ta cire kayan adon da tayi, ta zauna a tsakiyar gado idon ta sharkaf da Hawaye ta hargitse gashin kanta tana kuka. Ƙarasowa yayi ya kalle ta yace "Taso muje a bani cake ɗin" Ɗagowa tayi tana kallon sa hawaye na cigaba da bin idon ta, "Taho mana" yai maganar yana ƙara kallon ta, a hankali ta matsa inda yake zata sakko daga kan gadon, tausayin tane ya ƙara kama shi, bata iya fushi da shi, banda lokacin da tayi fushi harta fasa masa waya, bata iya fushi dashi ko tayi ma ita ke fara sakkowa ta bashi haƙuri. Kafin ta sakko daga kan gadon yasa hannu ya ɗauke ta, kamar wata 'yar yarinya kuwa ta kwanta tai lamo a jikin sa. Ɗakin sa ya nufa da ita, ya ajiye ta a bakin gado ya kalleta yace "waye ya koya miki zane ne?" "bakowa kawai iyawa nayi" jinjina kai yayi, kayan snacks ta gabatar masa, ai kuwa Ammar yaci sosai, shi irin wannan abubuwan basu dameshi ba shi dai kawai yaci Abinci ya dena jin Yunwa, wani abunma zama da Mufeeda yasa shi iya cin sa. Ta yanka cake ɗin nan takai bakin sa, buɗewa yayi tasa masa, tunda Ammar yake be taɓa cin cake ɗin birthday ba, jin cream ɗin nan yayi har kansa dan daɗi. "A ina kika siyo cake ɗin nan?" "Ni nayi fa" "A'a gayamin gaskiya dai" Taso ta tsokane shi tace santi yake, amma ta tuna ze iya dena ci in tace haka dan haka ta ƙyaleshi, gaba ɗaya Ammar ya manta da abunda yake damun sa kuma yaji daɗin abunda ta shirya masa sosai, Amma kunsan halin mutumin bazece ya yaba ba. Seda suka gama ciye ciyen su, Sannan Ammar ya nemi gurin kwanciya, har zata tafi ɗakin ta, ta fasa ta dawo ta hau kan gadon tace "Yaya Ammar har yanzu baka gayamin laifin da nayi maka ba yau, gaba ɗaya yau haka na wuni raina babu daɗi ka gayamin dan Allah" Juyowa yayi ya zuba mata ido ba tare da yace komai ba. "Kayi Magana mana, kabarni a cikin damuwa fa" Maimakon yace wani abu sema janyo ta da yayi jikin sa yace "meyasa kika ɓata gyaran gashin da kika yi?" "Ai cewa kayi baka so" "Ni nace bana so? Bance bana so ba" A hankali Ammar ya canza akalar hirar zuwa wani abu daban, tun tana jurewa harta fara kuka, A hankali ya ɗagota amma taƙi kallon sa, miƙewa yayi yaje yai wanka ya dawo yai kwanciyar sa a gefen ta, bata da zaɓi itama ta shiga banɗakin sa tai wankan, maimakon ta tafi ɗakin ta, seta haye gadon sa tai kwanciyar ta, seda ya tabbatar tayi bacci sannan ya juyo ya ƙara rungume ta a jikin sa yana fatan Allah yasa message ɗin da ake turo masa ƙarya ne. Da Asuba da ya dawo daga salla seya kwanta a falo, Mufeeda kuwa da tayi sallar Asuba kwanciyar ta ta kuma yi a gadon sa tana bacci. Seda gari yayi haske sosai sannan ta farka, tashi tayi ta fito ta tarar da shi yana bacci akan carfet, zuwa tayi kusa dashi ta kwanta tana ƙarewa fuskarsa kallo, A hankali ya buɗe idon sa ya kalle ta ya mayar ya lumshe. A hankali ta ɗora hannun ta a ƙirjinsa dai dai inda zuciyar sa ke bugawa tace "Yallaɓai ina da saƙo ka bawa zuciyar ka" Buɗe ido yai yana kallon ta Mufeeda cikin salon muryar tausayi ko wanda ya karaya da wani abu ttace "ka gaya mata akwai zuciyar da take matuƙar begen ta ba dare ba rana, Akwai zuciyar da ke son kasancewa da ita har ƙarshen rayuwar ta, ta zama me yiwa wannan zuciya da take son ta afuwa, idan tayi ba dai dai ba tayi mata uzuri kasancewar wannan zuciya me rauni ce, kuma 'yar jaririyar zuciya ce dake girma yanzu, zuciya ce dake girma da soyayya ba zata iya ɗaukar tsatstsauran hukunci daga gurin ta ba, ina fatan saƙon zuciya ta ze isa ga zuciyar Abun so na, zuciya ta bata ganin kowa se kai, ban taɓa son wani ba in bakai ba akanka na fara, kuma daga kai na gama, ina roƙon ka kamar yadda kake min kallon yarinya Koma ince Jaririya ina fatan idan na maka laifi ka duba ƙanƙanta ta kamin hukuncin da Jaririyar zuciya ta zata iya ɗauka, ina fatan saƙona ze isa ga zuciyar ka kai tsaye nagode Hubby na" ta sumbaci fuskarsa ta miƙe. Bayan ta yabi da kallo harta shige kitchen yana sake tunani daban daban a ransa. ************** Wajen ƙarfe goma na dare dan har sun fara shirin kwanciya, dan Mufeeda har ta masa Sallama ta tafi ɗakin ta, aka fara buga musu gate, Ammar ne yaje buɗe ga mamakin sa yaga Faruk ne da yarinyar sa, se kuma Fa'iza abun ya bashi mamaki matuƙa ganin Faruk da Fa'iza a tare a wannan lokacin haka, amma ya ɓoye mamakin sa yace "kune kuke tafe yanzu?" Yai musu iso har cikin gidan, zuwa falo Faruk yace "Ai gani nai rashin kirkin nawa yayi yawa, dan haka naje har gida nace Fa'iza ta rakoni gidan ka dai inga Amarya har gida kafin in kawo Madam" Ammar kallon tuhuma yakewa Fa'iza amma ya dake yace "Aikuwa ka kyauta bari in kira ta ku gaisa, dan harta kwanta" Yaje ya taso Mufeeda suka taho tare, suka gaisa Fa'iza se wani mugun kallo take mata, hirar babu gaira babu dalili Faruk yake, gaba ɗaya Mufeeda ta tsani Faruk ɗin nan musamman irin kallon da yake mata. Yarinyar da suka zo da itane Jawahir ta fara kuka, tausayin Yarinyar ya kama Mufeeda taje ta haɗo mata cornflakes tana bata. Faruk yace "Kai Amarya akwai san yara, ina fatan dai kun kusa kiran mu mu ɗau Baby" Yai maganar yana mata wani irin kallo. Fa'iza tace "Ai ka tausaya mata tayi ƙanƙanta ace tayi ciki ai" Wani mugun kallo Ammar yayi wa Fa'iza, Fa'iza tace "Kinga dan Allah idan da cornflakes ɗin nan ɗan haɗamin dan nima Yunwa nake ji" "Cornflakes Abincin yara ne, kamar Yadda kika faɗa Mufeeda Yarinya ce saboda ita nake ajiye irin wannan Abincin ba dan baƙi ba, da kunzo da wuri ne da se ko wani abun ta girka muku, Amma tunda kuka kai kamar wannan lokacin nasan kunci Abinci, Sannan Faruk gaskiya banji daɗin yadda ka ɗakko 'yar uwa ta kana yawo da ita a gari a wannan daren ba, raina ya ɓaci gaskiya kuma zanje in samu Mama se naji dalilin da yasa kika fito kika biyo shi a wannan daren, maza ka tashi ka gaggauta maida ita gida na gaya maka" Fa"iza tace "Yanzu Yaya Ammar bani da Alfarmar da zanci wani abu a gidan ka? Har inzo amma ka koreni" "Gidanki ne ko gida na? Ko kuma ya dace kizo min gida a irin wannan lokacin" Faruk yace "Amma Ammar gaskiya..... "Shut up get out from here please, kekuma zamu gauraya dake" Haka ta tashi sum suma suka fice Amin Afuwa abubuwa ne sunmin yawa sosai Domin gyara, sharhi, ko Shawara Ayshercool 0706306568 [14/07, 8:19 AM] Ayshercool: ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 21 Bayan tafiyar su Faruk gaba ɗaya jikin Mufeeda yayi sanyi, ta kalli Ammar zatayi magana, Amma yai sauri yace "kar inji wata magana daga bakin ki, tafi ɗakin ki kije ki kwanta" haka tai shiru ta wuce ɗakin ta cike da Fargabar kar Fa'iza taje ta kunno mata wata wutar a gurin 'yan uwan Ammar. Ammar tunani ya dingayi wace irin Alaƙa ce tsakanin Faruk da Fa'iza, da har zesa su dinga yawo a wannan daren su biyu se ƙaramar Yarinya, iyayen Fa' iza suna da tsauri akan tarbiyya amma me zesa abar Fa'iza ta fita a wannan daren? Meye alaƙar ta da Faruk? Da wannan tunanin yai bacci. Da safe Mufeeda na ta kallon Ammar, tana so ta gaya masa abunda ke faruwa game da halin da take ciki da wanda yake kiran ta, Amma sam Ammar baya walwala ransa a matukar ɓace yake tun zuwan su Faruk jiya da daddare, babu alamar ze tsaya ya saurare ta be kamata ma ta tunkare shi da zancen ba ganin yadda yake cikin ɓacin rai, dan haka bata gaya masa ba ta lallaɓa yai breakfast ya fice. ***************** Maƙotan Mufeeda' yan layin su suka shirya zasu tafi duba Maman Nur, suka biyo wa Mufeeda wai in zata je. Mufeeda tace "dan Allah kuyi haƙuri idan kunje kuyi mata sannu, baya nan ban tambayeshi ba kunga be kamata in fita ba" Wata maƙociyar su tace "ke yanzu dan dai dubiya muje yanzu mu dawo shine sekin wani tambayi miji, yanzu fa zamu dawo" Mufeeda tace "A'a bekamata in fita be sani ba" Maman Amir ta kwaɓe baki tace "Aikin banza sannu daɗi miji, dama seda nace muku karmu biyo mata, Yarinya 'yar ƙarama se girman kan tsiya da nuna tafi kowa tsoron Allah, tsoron Allah a baki, zuciya baƙi ƙirin" Mufeeda binsu tayi da kallo suka gama surutan su suka fita suna mita. Har suka je Asibitin nan Maman Amir Mita take, suka je suka tarar Maman Nur an gama sama ta jini, Jaririn data haifa ɗinma yana Nursery Unit saboda bashi da cikakkiyar lafiya. Suka mata Sannu, Maman Nur tace "wai Maman Amir mitar me kike hakane?" "Wannan banzar Yarinyar mana, muka biya mata tazo muzo duba ki amma taƙi wai bata tambayi mijin ta ba, 'ya se girman kai kamar wata matar gwamna, Da mijin nata wani shege me a ƙasar nan inaga da seta kore mu daga unguwar" Wata Yayar Maman Nur me suna Hadiza tace "to ai da gaskiyar ta, ya zata fito bata tambayi mijin ta ba, ai tayi gaskiya" Maman sadik tace "Anty hauwa bari kawai, ta fiye iyayi ne, ita fa ko ɗam shiga maƙotan nan a Saba da juna ba tayi ga rowar tsiya ta jaraba" Anty Hauwa tace "Wallahi banga laifin ta ba hakane daidai, ta zauna inda mijin ta ya ajiye ta kuda kuga zaku iya yawo se kuyi tayi" Maman Amir tace "wallahi Anty hauwa ba wani bin miji, to jiya Sa'idu me kayan miya ne ya gaya wa Baban Amir yace ganin idonsa ya ga tana zance da wannan Alhaji Idris ɗin na bayan layin mu da ranar Allah" Maman Nur tace "ke dan Allah dagaske?" "Wallahi tallahi dagaske, dan har Baban Amir yace ze tari mijin nata Amma ya fasa" Nan suka salallami suna ƙara jagwalgwala maganar, Anty hauwa tace "ban taɓa sanin munafuncin maza ya kai haka ba, kinga ku kiyayi wannan me kayan miyan, kuma wallahi in sharri kukayi mata se Allah ya tambaye ku" Maman Sadik tace "ba wani sharri, nifa rashin lafiyar Maman Nur ma ina zargin ta, don in baku manta ba ranar da muka kai mata anko se cewa tayi, Ai maman Nur tayi Addu'ar Allah ya sauke ta lafiya yafi wannan ankon da take rabawa, Jama'a kunga Yadda Maman Nur ta ƙare a Asibiti, ta haihu lafiya amma kalli " Maman Nur ta zare ido tace "Wallahi hakane maman sadik, na haihu lafiya, Amma naita zubar da jini, nikam kar dai ace mayya ce" Maman Amir tace "ai cire kamar ɗin, itace kawai se kowa ya kula da kansa, bayan bin maza hadda maita" Nan suka haɗu suka saka gulmar Mufeeda suka dinga zagin ta gami da tsine mata bata san suna yi ba, laifin ta ɗaya taƙi yadda ta zama irin su, mata masu gantali da yawon kwararo kamar ba matan Aure ba, Matan da basu ɗauki sirrin mazajen su a komai ba duk inda suka zauna sesu tone shi. **************** Mufeeda tana zaune tana karanta Al'qur'ani mai girma, cikin nutsuwa ji tayi ana mata wani irin mahaukacin bugu da seda yasa ta miƙe tsaye a tsorace, kasa matsawa tayi ta tsaya tana rarraba ido dan firgick, gashi dai Yamma ce amma bugun ya tsorata ta, kamar mara gaskiya haka ta fito tsakar gidan ta nufi gate cikin murya me cike da tsoro tace "Waye?" "Mune ko ba zaki buɗe ba?" babu ko tantama muryar Jidda ce, buɗe ƙofar tayi bata ko ƙarasa buɗe ƙofar ba Jidda ta danno ƙofar da ƙarfi ta shigo, ita da Fa'iza ne da wasu Yara, wanda 'ya' yan Anty Jidda ne. Tun daga tsakar gidan ta fara faɗa tana masifa, "Ke har kin isa wani daga dangin mu yazo gidan nan ki hanashi wani abu, ina ɗan uwan mune yake siya ya ajiye, 'yar ƙanƙanuwa dake se rashin mutunci" Fa' iza tace "wallahi Anty Jidda idan ba'a ɗau tsatstsauran mataki akan wannan yarinyar ba, wallahi se ta raba shi da kowa, baki ga zagin cin mutunci da yayi min saboda ita ba, akan shege cornflakes aka wulaƙanta ni, ta wani haɗe rai tace gaskiya ya sallameni za ta yi bacci " " tunda da uban ta aka haɗa kuɗi aka gina gidan ai dole ta faɗi haka mana, ku shiga kowa ya ɗau abunda yake so, Ammar ne ya siya" Mufeeda ta koma gefe ta zubawa sarautar Allah ido, kayan garar Mufeeda da suke ci yasa Ammar yake samun rararar kuɗi, ya ɗanyo siyayyar kayan buƙatu, Amma Fa'iza ta shiga kitchen ta ɗakko ƙaton kwano da cokula, tazo suka dinga zazzage cornflakes ɗin nan suna antaya Madara cike da mugun ta suna ci suna zubarwa, suka gama Fa'iza ta shiga kitchen ta buɗe mata fridge ta ɗebi abunda ranta yake so, suka wulaƙanta mata falo Abinci har kan kujerun ta, Mufeeda tayi tagumi ta zuba musi ido. Anty Jidda tace "Wallahi duk ranar da wani namu ya kuma zuwa gidan nan kika masa wulaƙanci, ko kika saka Ammar ya wulaƙanta shi sekin koma inda kika fito, Yarinyar banza data wofi kawai" Tabbas Anty Jidda ta haifi Mufeeda, kuma taci darajar Ya yar mijin ta ce, banda haka ba abunda ze hana Mufeeda ta sawa falo key da mata duka da muciya, sedai Hausawa suka ce Ana barin halak dan kunya. Tana nan zaune Fa'iza ta shiga kitchen ta dafa Abinci fiye da yadda zasu iya cinyewa, ta ci kowa yaran nan kwano suka ci suka jagwalgwala sauran, 'Yar Anty Jidda Haseena wadda zata shekaru ɗaya da Mufeeda ita ce tace "Amma Anty Fa' iza wannan almubazzaranci ne, Abincin nan yayi yawa, muma idan Abbnmu ya dawo yaga an wulaƙanta masa Abinci Faɗa yake mana" Fa'iza tace "Rufemin baki ko in make ki, ji gulmamiya, wancan Abbanku ne yake siya wannan kuma uncle ɗinki ne ya siya, kici iya cinki ki bar sauran" Suka yiwa Mufeeda kaca kaca da gida, ga zagi da cin mutunci da suka zazzage mata sannan suka tafi. Zama Mufeeda tayi tai shiru tana Hawaye, ta rasa me tayi wa bayin Allah nan suka tsane ta haka. Wayar ta ce ta fara ringing, tasa hannu ɗaga ta kai kunnen ta. "Amarya ba kya laifi shine kika yi blocking ɗina a what's App ko? To ai ba zaki taɓa gujemin ba, baze yuwu inta Azabtuwa da ƙaunar ki ni kaɗai ba, kuma idan ba kiyi wani abu a kai ba to ina tabattar miki dani zanyi, ki huta lafiya abar sona" Ya katse wayar sa, Mufeeda ta kasa ko motsawa daga inda take ta rasa me ya kamata tayi, tayi tunanin ko ta gayawa Mama halin da take ciki, se kuma taga yayi wuri ace ta fara gayawa Mama ga matsalolin da take ciki, dama Abunda Maman taita jiye mata kenan, ina ma na bi abunda Mama ta faɗamin wataƙila da hakan bata faru ba, wata zuciyar tace ai duk daren daɗewa ai zanyi Auren kuma ƙaddara ta ba zata canza ba. Tayi nisa sosai a cikin tunanin dan haka ba zato ba tsammani taji Ammar yana ƙoƙarin buɗe ƙofar falo, dan sam ba taji tsayuwar babur ɗinsa ba, zumbur ta miƙe da nufin tattare kayan da su Fa'iza sukayi kaca kaca da su, Amma Ammar ya riga ya shigo, turus yayi yana bin falon da kallo, Anyi kaca kaca da Madara a tsakiyar falon ga kwalin cornflakes da jarkokin lemo komai an zubar da shi a wulaƙance, da sauri ta ƙara so inda yake tana masa sannu da zuwa ta miƙa hannu da nufin karɓar kayan hannun sa ya kalle ta yace "Meye haka a falon ki? Abincin Akayiwa haka?" "A'a Yaya Ammar dama baƙi nayi shine.... " Shut up " ya mata tsawa. " baƙi kikayi shine za'a wulaƙanta min Abinci haka, kalli falon nan fa ji almubazzaranci kuma kina kallo? Kin sani saboda ke nake ajiye wannan abubuwan ni ba damuna suka yi ba, Amma kika bari a ka wulaƙanta haka, kalli Abinci har a tsakar gida an ajiye shi fal a bakin tap, da yake baki san zafin nema ba ko shiyasa kike wulaƙanta wa, bazan ƙara siyo wa ba, zan ajiye Abinci ne kawai, in kinyi hankali na siyo a nan gaba amma ko Madara ba zan sake siya ba, sakarya kawai " ya watsar da ledar da ya shigo da ita a falon ya wuce ɗaki Fuuuuu. Jiki a sanyaye ta durƙusa ta shiga gyara inda ya ɓaci a gidan, gaba ɗaya ta rasa mafita akan lamuran nan, Allah ya temaki Mufeeda hankalin Fa'iza be kai kan Flask ɗin Abincin Ammar ba, dan haka seda ta gyara ko'ina sannan ta ɗau Abincin ta bishi ɗakin sa. Ya kwanta yayi rigingine yana kallon ceiling da alama tunani yake yi, ta ajiye Kayan Abincin tace "Yaya Ammar ga Abinci na kawo maka" Banza yayi mata yaƙi kallon ta, cikin sanyin Jiki tace "dan Allah kayi haƙuri, zan kiyaye insha Allah dan Allah kayi haƙuri" A fusace yace "ɗauke Abincin ki ki fitar min daga ɗaki" "Dan Allah kay..... "ki ɗauke Abincin ki nace na ƙoshi, idan baki fita ba ni zan bar miki ɗakin" Cikin hanzari ta ɗauke Kwanukan ta fito. Ɗakin ta ta koma ta kwanta, ta rasa me ke mata daɗi "ya Allah idan abunda bayin nan naka sukemin da mugun ta sukemin Allah kayi musu abunda suka yi min" ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata, "har zuwa yaushe zan cigaba da ɗaukar laifin da ba nawa ba, babu Amfani in gaya masa abunda sukemin dan ba abunda hakan ze haifar se wata rigimar da tashin hankali, Allah ka bani mafita" Haka ta ci gaba da Hawaye tana surutai. Kiraye kirayen sallar magariba ne yasa ta tashi taje ta ɗaura alwala ta daɗe akan sallaya har kusan ƙarfe sha ɗaya tana ta Addu'a tana kaiwa Allah kukan ta, kamar yadda taga Mama ta nayi a lokuta da dama. Da gari ya waye farkawa kawai tayi taji ƙarar Napep ɗin Ammar yayi ficewarsa, ji tayi gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi bata ƙaunar ganin ya share ta. Idan ya fice tun safe baya dawowa se sha ɗaya kuma yana dawowa ɗakin sa yake wucewa, ko kula ta baya yi balle ya ci Abincin ta, Ammar be iya fushi ba sam, gaba ɗaya idan yana fushi tsoro yake bata dan wani irin kwarjini yake mata, ko tunkarar sa bata son yi, dan idan ya mata tsawa ba ƙaramin firgita take ba. Yau tana idar da sallar Asuba bata koma ba ta fito, ta shiga aikace aikace, aikuwa ƙarfe bakwai ya fito ze fice, tana kitchen ta fito da sauri tana kiran sunan sa, be saurare ta ba yayi gaba, cikin sauri ta bishi amma ta bige goshin ta da ƙofa da sauri ya tsaya ya juyo, ƙarar da ƙofar tayi zesa kasan ta bugu sosai ya kalle ta yace "ke komai ba zakiyi a hankali ba, da kinjiwa kanki ciwo fa?" Bata kula da me yake cewa ba tayi kneeldown akan gwiwowin ta, ta riƙe rigar sa tana kuka tace "ba dan hali na ba dan girman Allah kayi haƙuri, Insha Allah bazan sake wulaƙanta maka Abinci ba ko in bari wani ya wulaƙanta maka ba, kayi haƙuri dan Allah mijina ka dena fushi dani komai ya denamin daɗi saboda kana fushi dani, kayi haƙuri dan Allah" Jin kukan nata yayi har cikin zuciyar sa, ya kalleta yace "shikenan get up" "A'a dan Allah kace ka haƙura se in tashi" "Ninace ya wuce ai" "ka haƙura?" tai maganar wasu hawayen na bin fuskarta, ya jinjina mata kai alamar eh. Ya juya ze fice tai sauri tace "dan Allah Yaya Ammar, ka tsaya in dafa Abinci kaci ba dan ni ba dan Allah" "Shikenan muje" Har Mufeeda ta kammala girkin kuka take, ta kawo ta ajiye masa tana ƙoƙarin haɗa masa ya kalleta yace "Kukan be isa haka ba? Se kanki yayi ciwo?" Ai kaman ya tunzura ta, ta sake fashewa da kuka hadda sheshsheƙa. "Idan kuka za kiyi zan fasa cin Abincin" Kasa denawa tayi tasa hannun ta, ta toshe bakin ta tana ci gaba da kukan, zubawa sarautar Allah ido yayi, seda tayi me isar ta sannan ta koma gefe ta dinga sauke Ajiyar zuciya, bece mata komai ba ya shiga cin Abincin sa ya nayi yana kallon ta, har ya kammala ya fita, tunani ya dingayi a ransa anya ba wani abu ne yake damun Mufeeda ba, ace dan yana fushi da ita ne zesa taita wannan kukan? Ba yadda zeyi ya zama dole idan tayi ba daidai ba ya hukunta ta. Kamar Yadda Ammar ya gaya mata be ƙara siyo duk wani abu da ya saba siyowa domin ita, ya dena ajiye mata kaman Madara, Milo tarkacen buscuit da lemo da yake ajiyewa duk ya dena sedai yayi cefanen abunda zaa'a ci kawai, Sam bata nuna masa ta damu da hukuncin ba, Sedai har yanzu sama sama yake da ita ko sakar mata fuska ba yayi, haka take gaba ɗaya a takure sedai idan ta bashi Abinci ze ci, idan ta gaishe shi ze amsa mata. Tana son shiga maƙota tayi wa Maman Nur ya jiki taji ance ta dawo dan haka tun kafin ya fita ta tambayeshi yace seta dawo. Seda rana tayi sanyi bayan la'asar sannan ta saka hijjabin ta ta rufe gida ta shiga gidan Maman Nur, duk maƙotan nan na layin su wanda ta sani da wanda bata sani ba sun cika gidan suna ta shewa, Mufeeda tai Sallama ta shiga ta samu guri ta zauna suka gaisa, tace musu "ina me jegon ne?" Banza suka yi mata, Wannan Yayar Maman Nur ɗin ce Anty hauwa tace mata "ta shiga wanka amma yanzu zata fito" Mufeeda ta zauna zaman jiran Maman Nur ta fito, Yayin da Maman Amir se wani binta take da kallon banza. Su Maman Sadiq na gefen ta taji suna ƙusƙus da wata maƙociyar su, Maman Sadiq tace "Kin san wani abu Hafsa jira nake inga Yadda maman Nur zatayi ranar suna, ta ishi mutane hadda fidda anko wai za'ayi shagali ta dinga tatsar mijin ta kuɗi tana hana yaranta Abincin kirki tana tara kuɗin cefane dasu fa dama zata yi taron sunan, to yanzu ta haihu kuɗin data ƙulle za ta birge 'yan unguwa su ta ɗakko akayi mata magani, Mijin ta yace bashi da kuɗi " Wadda aka kira Hafsa tace " Dama abun nata duk burga ce da ƙaryar banza, gani take kamar duk layin nan mijin ta yafi kowa kuɗi " " Dalla duk ƙarya ce, shegen ƙaryace da ita ga roƙe roƙen tsiya ita kuma ga rowa " Mufeeda dai na jinsu ba tace komai ba, Maman Nur ce ta shigo ta fito daga wanka, dama Mufeeda duk ta gaji da zaman, a tsakanin su da suke tare ma suna zagin juna ina ga ita da ba sayi da ita. Mufeeda tace " Maman Nur ya jiki? " se lokacin Maman Nur ta lura da Mufeeda ya tsine fuska tayi tace "Naji sauƙi da ba kije dubani bama na warware" "Nima ba haka naso ba, lokacin da suka biyo min muzo duba ki baya nan ban tambaye shi ba, kuma ni ba wani sanin kan uguwanni nayi ba, baya barina in fita nika ɗai" Wata uwar shewa suka saki, Maman Nur tace "Allahu Akbar masu miji kaga masuyi dan Allah" Maman Sadiq tace "Taɓ kaga matar so, dama ina ze bari kifi ta ke kaɗai duniya ba yadda" Mufeeda ta basar da su tace "A bani Babyn in ganshi" Har za'a miƙa mata Jaririn Maman Nur tace "gaskiya Anty hauwa karki bata ɗana" Anty hauwa tace "saboda me?" "Haka kurum, daga zuwa gidan ta, in kai mata ankon suna se cewa tayi inyi fatan in haihu lafiya ba rabon anko ba, ƙarshe na haihu lafiya amma seda na dangana da Asibiti" Anty hauwa tace "to ai gaskiya ta gaya miki, yanzu kingama rabon anko amma kin ƙarke babu lafiya" Mufeeda ta miƙe tsaye tace "Bakomai, Allah ya baki lafiya, ya raya abunda aka haifa" "Bana buƙatar Addu'ar ki, inkina da gaskiya ai bekamata da nayi wannan zancen ki tashi kice zaki tafi ba, Yarinya se girman kan banza, ga sana'ar Mijin ta yafi na kowa lalacewa a tsukin nan" Har Mufeeda zata fita daga ɗakin ta tsaya ta kalli maman Nur tace "Allah sarki matar mangal, se gashi kina aike gidan direban a daidaita sahu atemaka miki da abunda attajirin mijin naki ba ya iya ajiye miki, ashe ma dai wani kuɗin ƙaryar banza ce, kuma karki ƙara sa kamin mijina a shirmen ki Jahila 'yar ƙauye kawai" Maman Nur ce ta antayo wata zazzafar Ashar "Ke kin isa kizo gidanta ki zage ta" "Na zage ta ɗin uwata ce? Tun da nazo layin nan nake baku girman ku Amma bakwa ganewa, wallahi babu matar da zata min in ƙyaleta, kuji da kanku ku ƙyaleni inyi rayuwa ta" Anty hauwa ce ke ƙoƙarin sasanta abun amma ina suka haɗe kai suka dinga zagin Mufeeda. Mufeeda tace "Anty kwantar da hankalin ki yanzu zan tafi, Amma duk wadda ta zageni ta zagi iyayen da suka kawo ta duniya, kuma wallahi kaf cikin mazan su babu me karamci da girman mijina, kar wadda ta sake zagar mana sana'a babu wadda nazo gidan ta yin barar abunda zamu ci " Maman Amir tace " Dalla rufe mana baki karki ƙara haɗa faƙirin mijin ki da mazajen mu" "Aini banga alamar kuɗin mazajen naku a jikin ku ba, dan da mijin naki kuɗin nasa na Arziki ne da be barki da wannan koɗaɗɗen zanin da rigar ta ɓarke daga hammata ba" Ai Mufeeda na faɗar haka kowa ya kalli Maman Amir, aikuwa sega riga a ɓarke ta hammata aikuwa aka ƙyalƙyale mata da dariya. Mufeeda tai ficewarta a hasale tana jin zafin yadda ake cin zarafin sana'ar mijin ta. Kanta ne yake wata irin sarawa kusan kwana uku kenan, ta miƙe layin su domin zuwa ta siyo ko paracetamol ne ta sha, amma kafin ta kai ƙarshen layin sega wannan mutumin da ya biyo ta rannan, basarwa tayi zata wuce yace "'haba adon gari, ina murna yau kayana ya tsinke a gindin kaba na sake tozali da wannan zuƙeƙiyar halittar amma zaki basar dani ki wuce " "Wai dan Allah malam kai baka tsoron Allah, baka tsoron kaima wani yayi maka abunda kakewa wani?" "Na gane ke matar Aure ce, dan har gidan ki nasani, rannan ta ƙofar gida na kuka wuce keda mijin ki, Amma fa kinga a wannan zamanin kowa samawa kansa mafita yake, ki ƙyale wannan faƙirin mijin naki, kizo mu jone zan sakar miki kuɗi kiyi yadda kike so, dukda ina da mata huɗu zan saki ko dukan sune idan kina so dan in Aure ki " " Auzubillah talakan mijina ya fiye min wawan dattijon banza irin ka, gara talauci sau dubu da Arziƙin daya fito daga hannun Asararre irin ka dukiyar taja da in akabi diddigi ta Haramce" "Haka kika ce?" "Na faɗa ko zaka yi wani abu akai?" "shikenan bari mu gani, zan tabattar miki da talauci masifa ne" Mufeeda fasa zuwa siyan maganin tayi ta koma gida tana tunanin meyasa wannan masifun suke bibiyar ta haka?. Ammar na zaune yana kallo da daddare Mufeeda na zaune a ƙasa, itama idon ta akan talabijin yake amma tunanin ta sam baya tare da ita, tayi nisa a tunani, ƙwanƙwasa gate ɗin da aka yi ne yasa Ammar ya tafi ya buɗe. Mijin maman Nur ne, suka gaisa da Ammar, "dama zuwa nayi dan Allah ka jawa matarka kunne, daga sallamo mata ta dsga Asibiti ta shiga ta tayar min da hayaniya a gida dan Allah a jama ta kunne karta sake" Wani banzan kallo Ammar yai masa yace "Gaskiya bana tunanin mata tace, idanma itace wani abun suka yi mata dan sam bata da neman rigima" "A'a sufa matan nan na yanzu ba shedarsu ake ba, be kamata in kawo maka ƙara ka goyi bayan ta ba" "Naji amma ni nafi kowa sanin halin ta, idan ba wani abun suka yi mata ba haka kurum ba zata je gidan ka tana hayaniya ba, Amma hakan ba zata sake faruwa ba, Allah ya bata lafiya" (wato Ammar yace Allah ya bada haƙuri ne baze iya ba) motsin shigowar sane yasa Mufeeda ta buɗe idon ta. Ammar ya samu guri ya zauna ya zuba mata ido, seda gaban ta yai mummunar faɗuwa kallon da yake mata dan na tuhuma ne. "Ina kika ce min zaki ɗazu?" "maƙota na shiga yin barka" "Da kin cemin zaki barka kika ɓuge da neman rigima a gidan mutane ko? Yanzu wanne wanda yayi Sallama dani maƙocinmu ne yace daga sallamo matarsa daga Asibiti kin shiga kin tayar musu da rigima, wai matar dama ance jinin ta ya hau, ke wai dama haka kike ne?" Shiru Mufeeda tayi ta sunkuyar da kanta, Ammar yai faɗansa iya son ransa Ya gama sannan ta ɗaga kai ta kalle shi tace "Allah ya baka haƙuri bazan kuma ba" Wasu lokutan wannan halin na Mufeeda ba ƙaramin haushi yake Bashi ba duk laifin da zece tayi bazata taɓa musa masa ba, sedai taita bashi haƙuri ko kuma taita kuka. Ta miƙe a hankali jiri na ɗibar ta ta tafi ɗaki, ƙirjinta yai mata nauyi se kokawa take da numfashi, tana shiga ɗaki ta samu guri ta kwanta ta rintse idon ta tana maimaita Innalillahi wa inna ialaihi raji'un. Se ƙarfe goma Ammar ya miƙe ze tafi ɗakin sa yaga wayar Mufeeda akan kujera tana vibrating. Masoyan Mufeeda ayimin afuwa labarin ne yazo a haka, ban fara rubuta shiba seda na kammala tsarashi, ayi haƙuri a bini a sannu dan ganin yadda zata kaya. Bana son wannan stickers ɗin ko kuma thanks kawai Comments nake so dan Allah Dan Allah in kin/ka karanta atemaka a dinga tayani sharing saboda masu bina pvt suna tambaya ta wasu pages ɗin abubuwa sunmin yawa. Masu bina private suna sanar dani ƙorafi su ko shawara ina godiya daku da masu Comment Fansa ɗina na watpad don't forget to vote Har yanzu ƙofa ta a buɗe take domin gyara, sharhi ko kuma shawara Ayshercool 07063065680 [16/07, 10:00 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP __Happy marriage life to my lovely friend_, __MARYAM MUSA ƁAIDU_I WISH YOU A VERY HAPPY MARRIAGE LIFE DEAR_ ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 22 Har Ammar ze share wayar ya tafi ɗakin sa se kuma ya ɗau wayar ya nufi ɗakin Mufeeda. Yana zuwa ya tarar har tayi bacci ta dunƙule a guri ɗaya ko kayan jikin ta bata canza ba da alama dai baccin ba shiri ya ɗauke ta, fuskarta duk hawaye se ajiyar zuciya take. Ɗan girgiza kai Ammar yayi ya zauna gefen gadon ya ɗagota ya cire mata hijjabin jikin ta, a wasu lokutan Mufeeda na da nauyin bacci sosai dan haka ya rage mata kayan jikin ta data kwanta da su, ya ƙura mata ido ta ɗan rame sosai, Amma tubarkallah tana da kyau dai dai gwargwado, musamman idan tana bacci se yaga ƙuruciyar ta ta ƙara fitowa, iya goshin ta ya ɗau zafi sosai yayin da sauran jikin ta yayi sanyi saboda kuka. Ammar ya daɗe yana kallon ta yana jin wani abu na masa yawo a jikin sa ba tare da ya tabattar dame hakan ke nufi ba, a hankali ya janyo pillow ya kwantar da ita a kai yana cigaba da kallon fuskarta, sosai yake jin tausayinta be kamata ya cigaba da yi mata faɗa any how ba, hakan yana sata a cikin damuwa sosai, gefe guda wayar Mufeeda na ci gaba da vibrating, har ya miƙe ze bar ɗakin yaga vibration ɗin wayar ze iya tashin ta dan haka ya dawo ya sunkuya ya ɗau wayar, baƙuwar lamba ce babu suna ya danna alamar amsawa ya kai kunnen sa zeyi magana, shiru yayi yana sauraren abunda me wayar yake faɗa, kunnuwan Ammar ba zasu iya jure jin abunda wannan la'anannen dabe san darajar Aure yake faɗa ba, Idan kunnuwan sa ba ƙarya suka jiye masa ba to tabbas kalaman soyayya ne wanda ya kiratan yake faɗa "tun ɗazu nake kiran ki saboda inji daddaɗar muryar ki ko da zagina kiyi in samu inyi bacci cikin kwanciyar hankali, Amma kinƙi ɗaga waya ta, kice wani abu mana mufeeda, Shikenan tunda ba zaki magana ba ɗaga wayar da kika yi ma ya tabbatar min kina lafiya, Ina son ki fiye da yadda wannan mijin naki me girman kai da baki da tabbacin yana sonki" A hankali Ammar ya ajiye wayar, zuciyar sa tana wani irin bugu da ƙarfin gaske tamkar zata tsaga ƙirjin sa ta fito, gashin jikin sa duk ya mimmiƙe saboda ɓacin rai, ya kalli inda Mufeeda take kwance tana bacci, se faman sauke ajiyar zuciya take she's looking so innocent. Da ƙyar Ammar yaja ƙafar sa ya bar ɗakin yana ci gaba da jin Yadda zuciyar sa take bugawa. Ɗakin sa ya koma ya samu gefen gado ya zauna ya dafe kansa da yake jin tamkar ba nasa ba, yanzu duk iƙrarin Soyayyar da Mufeeda take masa ƙarya take, zata iya cin Amanar sa tayi soyayya da wani a waje da Auren sa a kanta, lallai mata ba abun yarda bane. Yana wannan tunanin message ya shigo wayar sa "KA SA IDO AKAN MATARKA TANA AIKATA RASHIN GASKIYA A BAYAN IDON KA" Wannan shi ne ire iren saƙon da'ake yawan turo masa "to Amma waye wannan yake turo masa saƙon? Ya akayi me turo saƙon ya samu lambar sa har yasan Matarysa tana aikata rashin gaskiya a bayan idon sa?" Yadda Ammar ya ga dare haka ya ga rana, bacci ya ƙauracewa idanunsa. ********************* Ƙarfe biyu da rabi na dare Saima ce kwance tana bacci yayin da gefen ta Jabir ke kwance yana chatting, A hankali ta buɗe ido tana kallon sa ba tare da yasan tana kallon sa ba, voice message ɗin da aka turo masa ya buɗe yana saurarar, amon muryar mace ne ya fara tashi "My Jabir i can't wait to see you as my husband, na ƙagu lokaci yayi ni kaɗai nasan me make ji akan ka, Amma ni matsala ta ɗaya gaskiya bana son zama da kishiya, bazan iya sharing ɗin ka da wata 'yar talakawa ba, Daddy ze baka gida ya canza maka mota wataƙila ma har muƙami yayi maka a cikin kamfanonin sa, Amma gaskiya ni batun zama da wata ne akwai damuwa" Jabir yayi ƙasa da muryar sa yace "My love karki ji komai ni kaina na ƙagu in mallake ki, dan babu wani farinciki da nake tsinta a Auren nan, Mata ta babu abunda ta iya, Ni ban san wani irin tsautsayi ya kaini na Aure ta ba, bayan ga irin ki, yanzu dai so nake ta haihu tukuna kar ace na sake ta da ciki, Amma da zarar ta haihu zan san abun yi" Ba shiri Saima taji abunda yake cikin ta yayi wata irin juyawa saboda maganganun da Jabir yake yi, A hankali ta miƙe zaune saboda nauyin cikin dake jikin ta, Jabir yana kallon ta haka ta dinga bin bango da ƙyar ta shiga banɗaki, tana shiga ta durƙushe ta dinga zubar da Hawaye tana tuna yadda ta ƙaunaci Jabir, lokacin da take hasashen tayi dacen miji, take tunanin duk cikin mane manta Jabir ne ze riƙe ta ya kula da maraicinta, se gashi Jabir ɗin nata ya sauya komai ya dagule mata, babu wanda zata kaiwa kukan ta se Allah, ba uwa ba Uba, a hannun ƙanin mahaifinta ta girma, cike da tsangwama da bautarwa basu da burim da ya wuce suga ta wulaƙanta dan haka batun ta kai kokenta gidan su be taso ba, ta daɗe a banɗaki tana kuka sannan ta fito, yanzu ma a durƙushe ta dawo ta sa hannu ta ɗau fulo ta kwanta a ƙasa Jabir yana kallon ta amma be ce mata uffan ba ya ci gaba da Chatting ɗin sa. Bacci ya ƙauracewa idanun Saima, har ƙarfe uku na dare Sannan Jabir ya kwanta, a hankali ta kuma jan jikin ta zuwa banɗaki tayi alwala ta koma ɗaya ɗakin ta shimfiɗa sallaya, nafila tayi ta idar ta ɗaga hannun ta zata yi Addu'a amma ta kasa se kuka me taɓa zuciya da ta dinga yi. ******************* Babban abunda ya bawa Mufeeda mamaki be wuce yadda tun Asuba da Ammar ya fita salla be ƙara dawowa ba kuma be fita da babur ɗinsa ba, har ƙarfe sha ɗaya na safe babu shi babu alamar sa, Wayarta ta ɗauka ta kira shi amma sam yaƙi ɗagawa daga ƙarshe ma ya kashe wayar sa ta dena shiga. Addu'a Mufeeda ta dinga yi na Fatan Allah yasa na lafiya dan be taɓa yin hakan ba, Mufeeda ko karyawa ta kasa yi, dan damuwar da take fama da ita kwanan nan, da yawan kukan da take yi yasa take fama da ciwon kai dan sam ko Abinci ba ta iya ci. Wasa wasa har Azahar babu Ammar babu ɗuriyar sa, da ƙyar ta dafa tea ta sha kaɗan ta ajiye gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake. *************** Maman Nur ta saka mijin ta a gaba "wai ni da kaje ka samu wannan me Napep ɗin game da abunda matar sa tazo tayi min me yace maka, baka yi min bayanin komai ba fa" Baban Nur yace "to me zance miki labarin bame daɗi bane, dan naga alamar baya son laifin ta, cemin yayi wai ba yadda zata tayar da faɗa idan ba wani abun akayi mata ba, shi matar sa ba fitinanniya bace" "kan bala'i haka ma yace, to kai me kace masa?" "Me kuwa zance masa? Nace masa dai ya ja mata kunne" "Amma wallahi ka fiye abun haushi, wato kaine baka kishi na ko? maimakon kayi masa rashin mutunci ka nuna masa ɓacin ranka akan abunda tayi, kawai se kace yaja mata kunne, be yadda tayi laifi ba ta ina ze ja mata kunne? Tunda kai ba zaka iya ba ni zanyi, wallahi se fitowa da rana ya gagari yarinyar nan dani take zancen zan sauke mata wannan girman kan nata" "Akan me zaki hana ta fitowa da rana? Ke kika ajiye ta?" "kaga ba ruwan ka dan Allah kasa ido kawai, zata gane bata da wayo zan koya mata hankali yadda gaba in ance idan ta ganni tayi min rashin mutunci seta gudu da ƙafar ta" ****************** Mufeeda ta tsorata sosai da rashin dawowar Ammar gida, gashi har magariba tayi amma babu shi babu alamar sa, waya ta ɗauka tana ƙoƙarin kiran Umman Ammar ta sanar mata abunda yake faruwa amma wayar taƙi shiga, shiru tayi ta fara tunanin ko wani abunne ya same shi, Alamar buɗe gate taji, dama idan ya dawo yana da key, yake sawa ya buɗe kawai. Da sauri ta tashi ta fito tsakar gida, Ammar ne ya shigo fuskar nan tasa tamkar kumurci babu alamar Afuwa, tana ganin yanayin sa gaban ta ya faɗi, Amma ta dake tace "lafiya kuwa Yaya Ammar daga tafiya sallar Asuba na neme ka na rasa? Hankalina fa ya tashi sosai" Wani mugun kallo yayi mata dase da 'ya' yan cikin ta suka juya, ya wuce ta ya shige falo, da ya shiga ɗinma be tsaya a falon ba ɗakin sa ya wuce kai tsaye. Bata karaya ba tabi bayan sa dukda irin mugun kallon da yayi mata. "Mijina dan Allah ka gayamin ina ka tafi haka?" "get out from here" yai mata wata irin tsawa da ta razana ta matuƙa. "Yaya Ammar daga tambaya sekamin tsawa haka?" "Ki fita tun ban tattaka ki a gurin nan ba, ki fitar min daga ɗaki nace" Gaba ɗaya jikin ta rawa yake, ga Yunwa ta wuni ba taci Abinci ba ga ɓacin rai ga wannan masifar da Ammar yake da bata san dalilin ta ba, wani irin jiri ne yake nema ya kada ita ƙasa dan haka ta dafe kanta ta fita. Gaba ɗaya hawayen ma yaƙi zubowa se zafi da ƙirjinta yake yi, bata taɓa tsammanin halin Ammar ya kai haka ba, bata taɓa tunanin zafin zuciyar sa ya kai haka ba? Shikenan laifi wanda tasan tayi da wanda ba tayi ba se ya ɗora mata yaita faɗa, ko'a ɓata masa rai a waje yazo ita ya sauke mata, abun ya fara damun ta. ******************** Sosai Saima take dana sanin sanin Jabir a rayuwar ta, gaba ɗaya taji Aure ya fita daga ranta, ta ɗauki shawarar Mufeeda idan Jabir yana mata rashin mutunci ƙyale shi take bata tanka masa, tsanar da tayi wa Jabir a yanzu harta kai ga taji bata ƙaunar cikin dake jikin ta, dan haka ta ƙudurce a zuciyar ta ranar data haihu zata karɓi takardar sakin ta daga hannun Jabir tun kafin yaci zarafin ta ya kore ta akan 'yar masu kuɗin da yake hari, yake ganin zasu yabke masa talauci idan ya auri ' yarsu, sannan ta ajiye masa abunda ta haifa idan yasa kowa ze Auro tazo ta kula masa da ɗansa amma ba zata shayar da abunda ta haifa ba, Abunda Jabir yake mata yasa gaba ɗaya haushin maza take ji ta ƙudurce a ranta ba zata ƙara yin wani Auren a rayuwar ta ba, idan har Jabir da suka shafe shekaru suna soyayya ze mata haka bayan Aure to bazata sake Aure ba dan babu sauran wani namiji me imani da yayi saura duk haka halin su yake. ******************* Mufeeda tana ta fama da damuwa ta kasa gayawa kowa dan gani take hakan tamkar tona Asirin Auren tane, kuma koda ta gayawa iyayen ta aka sasanta komai ze iya wucewa a gurin ta, Amma ba lallai ya wuce a gurin iyayen ta ba. Tana kwance akan kujera bata jin daɗin komai aka ƙwanƙwasa ƙofa, jiki ba ƙwari ta tashi taje buɗe, tana buɗewa taga Anty Maryam ce, Yayar Ammar, murmushin dole Mufeeda ta ƙaƙalo tayi wa Anty Maryam tare da yi mata maraba. Suka gaisa Maryam tace "kin ganni unguwa naje na dawo naga na biyo ta layin unguwar ku nace bari inzo mu gaisa" "Aikuwa naji daɗi Anty Maryam, dama baya nan duk kaɗaici ya dameni, bari in dafa miki Abinci" "A'a Mufeeda ba sekin wahalar da kanki ba, kin ganni seda na cika cikina na fito" Nan suka shiga hira da Mufeeda, Amma Anty Maryam ta karanto damuwa ɓoye a bayan murmushin da Mufeeda take yi, ta ɗan dube ta tace "Mufeeda baki da lafiya ne?" "A'a Anty Maryam lafiya ta ƙalau" "Amma naga kinyi wannan ramar haka? Kodai wani abun yana damunki ne?" Wani murmushin dolen Mufeeda ta kuma yi tace "Ba abunda yake da muna fa ke kika ga na rame, amma komai lafiya" tana magana ne yayin da ƙasan zuciyar ta ji take kaman ta fashe da kuka. "Mufeeda idan kinsan akwai matsala ki gayamin, idan wani abun yake miki ki faɗa tun wuri ayiwa tufkar hanci, nasan halin Ammar sarai ɗan uwana ne amma zama dashi se me haƙurin gaske ki gayamin idan akwai matsala" Shiru Mufeeda tayi sannan ta ɗago ta kalli Anty Maryam tace "Anty Maryam gaskiyar kenan na gaya miki ki yarda dani" tai maganar tana ƙoƙarin maida ƙwallar dake ƙoƙarin zubo mata, ganin Mufeeda bata da niyyar gaya mata abunda ke damun ta yasa ta ƙyaleta, aka jima tai mata sallama ta tafi. Kusan gaba sosai Ammar yake da Mufeeda ba tare da tasan laifin da tayi masa ba, ko haɗa hanya suka yi, idan yayi mata tsawa se tayi dana sanin haɗuwar da suka yi. Gaba ɗaya ya zame mata tamkar wani dodo, duk da jin kansa amma yanayin yadda suke kasancewa tare, suci Abinci tare yanayi ne da yake matuƙar sata nishaɗi, Amma ƙirƙiri yanzu fargabar ganin sa ma take yi balle su haɗa hanya, gashi ita bata san laifin da tayi masa ba. Duk wani abu da ya kama na ciyar wa be fasa ba, Amma ba zata dafa yaci ba ko gaisuwa bata haɗa su. Sosai zaman da suke yi yake damun ta ya kamata ace idan laifi tayi masa ya gaya mata, dan haka ta yanke shawarar zuwa ta same shi taji laifin da tayi take fuskantar wannan hukuncin me matuƙar tsauri. Ɗakin sa taje ta same shi yana shiri ze fita, ɗagowa yayi ya kalleta ya ɗauke kansa, jiki a sanyaye tace "Yaya Ammar ka dubi zatin Allah ka gayamin laifin da nayi maka kake min wannan hukunci" Banza yayi mata ya ɗau wayarsa ya saka a Aljihu yana ƙoƙarin kewaye ta ya wuce, tare shi ta kuma yi cikin kuka tace "Yaya Ammar zuciya ta ba zata iya ɗaukar wannan hukuncin ba, dan Allah ka gayamin me nayi maka haka?" A fusace yace "get out from my sight bana son wannan salon yaudarar taki, 'yar ƙanƙanuwar yarinya dake amma kin iya yaudara" Zubewa tayi akan gwiwoyin ta tace "Naji na yadda amma dan Allah kayi haƙuri dukda ban san laifin da nayi maka ba, Amma kayi haƙuri" Ture ta yayi daga gaban sa yasa kai ya fice, da gudu ta kuma binsa falon tana riƙe rigar sa tana kuka. Fizge rigar sa yayi yace "Karki ƙara riƙe min riga munafuka mayaudariya, seda na yadda dake zaki tozartani ki bani kunya" "Yaya Ammar me yayi zafi kake kirana da wannan miyagun maganganun? Wani laifi ne haka na aikata? A zaman mu da kai bana tunanin na aikata wani kuskure dana cancanci wannan kalmomin daga bakin ka" "Tambaya ta ma kike yi? Da Aurena a kanki kike Soyayya da wani a waje, kin san zaki yi soyayya da wani dan me kika dage sekin Aureni kike yaudara ta da cewar kina sona, kinsan me kuɗi kike burin Aure meyasa kika Aureni kikemin daɗin bakin cewar ni kike so ba abun hannu na ba? An kiraki a waya na ɗaga wani ɗan iska yana faɗin yayi missing ɗinki, na fita sallar Asuba an tareni ance an ganki ƙiri ƙiri da wani me mota kina zance, akan me zakimin haka? Har yanzu zuciya ta ta kasa Amincewa zaki min hakan, sakamakon kalaman yaudara da kike Amfani dasu akaina, nasan da mace na Aura me hankali da inaga duk hakan bata faru ba, nayi nadamar Auren ki da nayi " Shiru tayi seda yayi ya gama ta ɗago idanun ta da suka koma Jawur ta kalli Ammar tace "Ba dan sharrin Soyayya ba Ammar babu abunda zesa in soka in zauna da kai da wannan halin naka, Yaya Ammar ko a kotu Alƙali yana bawa mai laifi damar kare kansa koda kuwa a gaban Alƙalin me laifi ya aikata laifin, ba kai ya kamata ka yi dana sani ba, ni ya kamata inyi dana sanin yin Aure, A iya zamana da kai na gane abubuwan da mahaifiya ta da 'yan uwana suke jiye min, Yaya Ammar ko dan Darajar Soyayyar da nake maka ya kamata kayi min Adalci ban cancanci jin wannan kalaman daga bakin ka ba, a zaman mu da kai a Alkhairaina guda nawa ka yaba? Amma yau akan kuskuren da baka da tabbas na Aikata ka hukunta ni da kalamai masu muni, kalaman da bazan manta ba har in koma ga Allah, Shikenan Nagode sosai, sannan bazan gajiya ba Allah ya baka haƙuri, idan ka sakko daga Fushin nayi maka bayanin abunda ya faru, Adawo lafiya Allah ya kiyaye hanya " Tana gama maganar ta tafi ɗakin ta tana shehssheƙar kuka me tsuma zuciya, seda Mufeeda tai wannan maganganun sannan Ammar ya dawo hayyacin sa ya fara tunanin Anya kalaman da yayi Amfani da su sun dace? Take kuma yaji kamar be kyauta ba gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, tabbas ya kamata ya bincika kafin yayi mata hukunci, haka nan ya ɗau key ɗin babur ɗin sa ya fice. Bayan fitar sa Mufeeda gaba ɗaya ji tayi ta tsani zaman gidan, gaba ɗaya ta rasa abunda yake mata daɗi ga zuciyar ta da take ta faman bugawa da ƙarfi, miƙewa tayi tasa hijjabin ta ta ɗau wayar ta ta fice, tafiya kawai take dan wani matsanancin ciwon kai ne ke damun ta ga Jiri da take ji dan haka kawai jefa ƙafar ta take, tana fita bakin titi ta tare me Napep ta gaya masa unguwar daze kaita ta faɗa ciki tana goge Hawaye. Akan idon Sa'idu me kayan miya hakan ta faru, dan haka ya jinjina kai yace "Yau akwai zazzafar Jarida" Me Napep ɗin daya ɗauki Mufeeda kuwa tsoro ya fara ji karta mace masa a Babur, dan wata irin shaƙuwa take tana sauke numfashi da ƙyar, seda ya kaita har ƙofar gidan Yaya Amina, Mufeeda ta fito daga A daidaita sahu abu ya faskara dan harta fara fita daga hayyacin ta da ƙyar take numfashi. Ƙwanƙwasa gate ɗin Yaya Amina me Napep ɗin yayi, akayi sa'a Yaya Amina ce ta buɗe, suka gaisa dame Napep sannan yace mata "dama waccan baiwar Allah na ɗakko tace nan zan kawo ta, kuma gashi munzo ta kasa fitowa kamar bata da lafiya" Aikuwa Yaya Amina na leƙawa ta hango Mufeeda a cikin Napep ɗin ta riƙe ƙirji, da Sauri Yaya Amina ta koma cikin gida ta ɗakko mayafi suka fito tare da mijin ta, Mufeeda na ganin Yaya Amina ta sake fashewa da kuka, suka ɗakko ta daga A daidaita sahu zuwa cikin gidan, mijin Yaya Amina ya sallami me Napep. A tayani Share ba dan halina ba 😍😍😜 NAGA NAFARA ƁATAWA 'YAN TEAM ƊIN MUFEEDA RAI, ANA CEWA HAƘURIN MUFEEDA YAYI YAWA, GA WATA TAMBAYA, DA MUFEEDA BATA KASANCE ME HAƘURI BA WANI IRIN ZAMA KUKE TUNANIN ZATA YI DA WANNAN MIJI NATA ME BAUƊAƊƊEN HALI? IDAN BA TAYI HAƘURI BA TAZAMA ME YAWAN ƘORAFI YANA HAƊA SHI FAƊA SA 'YAN UWAN SA A SANNU WATARAN SE IYAYEN MIJIN TA SUN FARA JIN HAUSHIN TA. AYIMIN HAƘURI LABARIN NE YAZO A HAKA DAN HAKA KU BIYONI SANNU A HANKALI DAN JIN YADDA ZATA KAYA KISSA BATA NUFIN KWALLIYA DA KWARKWASA BANE, AKWAI HAƘURI DA JURIYA. Taku har Kullum Aisha Humaira, Daddy's girl ko ince Ayshercool, ina godiya sosai da ƙauna da kuma bibiyar littafin da kuke Domin sharhi gyara ko shawara 07063065680 ✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP __Happy marriage life to my lovely friend_, __MARYAM MUSA ƁAIDU_I WISH YOU A VERY HAPPY MARRIAGE LIFE DEAR_ ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 22 Har Ammar ze share wayar ya tafi ɗakin sa se kuma ya ɗau wayar ya nufi ɗakin Mufeeda. Yana zuwa ya tarar har tayi bacci ta dunƙule a guri ɗaya ko kayan jikin ta bata canza ba da alama dai baccin ba shiri ya ɗauke ta, fuskarta duk hawaye se ajiyar zuciya take. Ɗan girgiza kai Ammar yayi ya zauna gefen gadon ya ɗagota ya cire mata hijjabin jikin ta, a wasu lokutan Mufeeda na da nauyin bacci sosai dan haka ya rage mata kayan jikin ta data kwanta da su, ya ƙura mata ido ta ɗan rame sosai, Amma tubarkallah tana da kyau dai dai gwargwado, musamman idan tana bacci se yaga ƙuruciyar ta ta ƙara fitowa, iya goshin ta ya ɗau zafi sosai yayin da sauran jikin ta yayi sanyi saboda kuka. Ammar ya daɗe yana kallon ta yana jin wani abu na masa yawo a jikin sa ba tare da ya tabattar dame hakan ke nufi ba, a hankali ya janyo pillow ya kwantar da ita a kai yana cigaba da kallon fuskarta, sosai yake jin tausayinta be kamata ya cigaba da yi mata faɗa any how ba, hakan yana sata a cikin damuwa sosai, gefe guda wayar Mufeeda na ci gaba da vibrating, har ya miƙe ze bar ɗakin yaga vibration ɗin wayar ze iya tashin ta dan haka ya dawo ya sunkuya ya ɗau wayar, baƙuwar lamba ce babu suna ya danna alamar amsawa ya kai kunnen sa zeyi magana, shiru yayi yana sauraren abunda me wayar yake faɗa, kunnuwan Ammar ba zasu iya jure jin abunda wannan la'anannen dabe san darajar Aure yake faɗa ba, Idan kunnuwan sa ba ƙarya suka jiye masa ba to tabbas kalaman soyayya ne wanda ya kiratan yake faɗa "tun ɗazu nake kiran ki saboda inji daddaɗar muryar ki ko da zagina kiyi in samu inyi bacci cikin kwanciyar hankali, Amma kinƙi ɗaga waya ta, kice wani abu mana mufeeda, Shikenan tunda ba zaki magana ba ɗaga wayar da kika yi ma ya tabbatar min kina lafiya, Ina son ki fiye da yadda wannan mijin naki me girman kai da baki da tabbacin yana sonki" A hankali Ammar ya ajiye wayar, zuciyar sa tana wani irin bugu da ƙarfin gaske tamkar zata tsaga ƙirjin sa ta fito, gashin jikin sa duk ya mimmiƙe saboda ɓacin rai, ya kalli inda Mufeeda take kwance tana bacci, se faman sauke ajiyar zuciya take she's looking so innocent. Da ƙyar Ammar yaja ƙafar sa ya bar ɗakin yana ci gaba da jin Yadda zuciyar sa take bugawa. Ɗakin sa ya koma ya samu gefen gado ya zauna ya dafe kansa da yake jin tamkar ba nasa ba, yanzu duk iƙrarin Soyayyar da Mufeeda take masa ƙarya take, zata iya cin Amanar sa tayi soyayya da wani a waje da Auren sa a kanta, lallai mata ba abun yarda bane. Yana wannan tunanin message ya shigo wayar sa "KA SA IDO AKAN MATARKA TANA AIKATA RASHIN GASKIYA A BAYAN IDON KA" Wannan shi ne ire iren saƙon da'ake yawan turo masa "to Amma waye wannan yake turo masa saƙon? Ya akayi me turo saƙon ya samu lambar sa har yasan Matarysa tana aikata rashin gaskiya a bayan idon sa?" Yadda Ammar ya ga dare haka ya ga rana, bacci ya ƙauracewa idanunsa. ********************* Ƙarfe biyu da rabi na dare Saima ce kwance tana bacci yayin da gefen ta Jabir ke kwance yana chatting, A hankali ta buɗe ido tana kallon sa ba tare da yasan tana kallon sa ba, voice message ɗin da aka turo masa ya buɗe yana saurarar, amon muryar mace ne ya fara tashi "My Jabir i can't wait to see you as my husband, na ƙagu lokaci yayi ni kaɗai nasan me make ji akan ka, Amma ni matsala ta ɗaya gaskiya bana son zama da kishiya, bazan iya sharing ɗin ka da wata 'yar talakawa ba, Daddy ze baka gida ya canza maka mota wataƙila ma har muƙami yayi maka a cikin kamfanonin sa, Amma gaskiya ni batun zama da wata ne akwai damuwa" Jabir yayi ƙasa da muryar sa yace "My love karki ji komai ni kaina na ƙagu in mallake ki, dan babu wani farinciki da nake tsinta a Auren nan, Mata ta babu abunda ta iya, Ni ban san wani irin tsautsayi ya kaini na Aure ta ba, bayan ga irin ki, yanzu dai so nake ta haihu tukuna kar ace na sake ta da ciki, Amma da zarar ta haihu zan san abun yi" Ba shiri Saima taji abunda yake cikin ta yayi wata irin juyawa saboda maganganun da Jabir yake yi, A hankali ta miƙe zaune saboda nauyin cikin dake jikin ta, Jabir yana kallon ta haka ta dinga bin bango da ƙyar ta shiga banɗaki, tana shiga ta durƙushe ta dinga zubar da Hawaye tana tuna yadda ta ƙaunaci Jabir, lokacin da take hasashen tayi dacen miji, take tunanin duk cikin mane manta Jabir ne ze riƙe ta ya kula da maraicinta, se gashi Jabir ɗin nata ya sauya komai ya dagule mata, babu wanda zata kaiwa kukan ta se Allah, ba uwa ba Uba, a hannun ƙanin mahaifinta ta girma, cike da tsangwama da bautarwa basu da burim da ya wuce suga ta wulaƙanta dan haka batun ta kai kokenta gidan su be taso ba, ta daɗe a banɗaki tana kuka sannan ta fito, yanzu ma a durƙushe ta dawo ta sa hannu ta ɗau fulo ta kwanta a ƙasa Jabir yana kallon ta amma be ce mata uffan ba ya ci gaba da Chatting ɗin sa. Bacci ya ƙauracewa idanun Saima, har ƙarfe uku na dare Sannan Jabir ya kwanta, a hankali ta kuma jan jikin ta zuwa banɗaki tayi alwala ta koma ɗaya ɗakin ta shimfiɗa sallaya, nafila tayi ta idar ta ɗaga hannun ta zata yi Addu'a amma ta kasa se kuka me taɓa zuciya da ta dinga yi. ******************* Babban abunda ya bawa Mufeeda mamaki be wuce yadda tun Asuba da Ammar ya fita salla be ƙara dawowa ba kuma be fita da babur ɗinsa ba, har ƙarfe sha ɗaya na safe babu shi babu alamar sa, Wayarta ta ɗauka ta kira shi amma sam yaƙi ɗagawa daga ƙarshe ma ya kashe wayar sa ta dena shiga. Addu'a Mufeeda ta dinga yi na Fatan Allah yasa na lafiya dan be taɓa yin hakan ba, Mufeeda ko karyawa ta kasa yi, dan damuwar da take fama da ita kwanan nan, da yawan kukan da take yi yasa take fama da ciwon kai dan sam ko Abinci ba ta iya ci. Wasa wasa har Azahar babu Ammar babu ɗuriyar sa, da ƙyar ta dafa tea ta sha kaɗan ta ajiye gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake. *************** Maman Nur ta saka mijin ta a gaba "wai ni da kaje ka samu wannan me Napep ɗin game da abunda matar sa tazo tayi min me yace maka, baka yi min bayanin komai ba fa" Baban Nur yace "to me zance miki labarin bame daɗi bane, dan naga alamar baya son laifin ta, cemin yayi wai ba yadda zata tayar da faɗa idan ba wani abun akayi mata ba, shi matar sa ba fitinanniya bace" "kan bala'i haka ma yace, to kai me kace masa?" "Me kuwa zance masa? Nace masa dai ya ja mata kunne" "Amma wallahi ka fiye abun haushi, wato kaine baka kishi na ko? maimakon kayi masa rashin mutunci ka nuna masa ɓacin ranka akan abunda tayi, kawai se kace yaja mata kunne, be yadda tayi laifi ba ta ina ze ja mata kunne? Tunda kai ba zaka iya ba ni zanyi, wallahi se fitowa da rana ya gagari yarinyar nan dani take zancen zan sauke mata wannan girman kan nata" "Akan me zaki hana ta fitowa da rana? Ke kika ajiye ta?" "kaga ba ruwan ka dan Allah kasa ido kawai, zata gane bata da wayo zan koya mata hankali yadda gaba in ance idan ta ganni tayi min rashin mutunci seta gudu da ƙafar ta" ****************** Mufeeda ta tsorata sosai da rashin dawowar Ammar gida, gashi har magariba tayi amma babu shi babu alamar sa, waya ta ɗauka tana ƙoƙarin kiran Umman Ammar ta sanar mata abunda yake faruwa amma wayar taƙi shiga, shiru tayi ta fara tunanin ko wani abunne ya same shi, Alamar buɗe gate taji, dama idan ya dawo yana da key, yake sawa ya buɗe kawai. Da sauri ta tashi ta fito tsakar gida, Ammar ne ya shigo fuskar nan tasa tamkar kumurci babu alamar Afuwa, tana ganin yanayin sa gaban ta ya faɗi, Amma ta dake tace "lafiya kuwa Yaya Ammar daga tafiya sallar Asuba na neme ka na rasa? Hankalina fa ya tashi sosai" Wani mugun kallo yayi mata dase da 'ya' yan cikin ta suka juya, ya wuce ta ya shige falo, da ya shiga ɗinma be tsaya a falon ba ɗakin sa ya wuce kai tsaye. Bata karaya ba tabi bayan sa dukda irin mugun kallon da yayi mata. "Mijina dan Allah ka gayamin ina ka tafi haka?" "get out from here" yai mata wata irin tsawa da ta razana ta matuƙa. "Yaya Ammar daga tambaya sekamin tsawa haka?" "Ki fita tun ban tattaka ki a gurin nan ba, ki fitar min daga ɗaki nace" Gaba ɗaya jikin ta rawa yake, ga Yunwa ta wuni ba taci Abinci ba ga ɓacin rai ga wannan masifar da Ammar yake da bata san dalilin ta ba, wani irin jiri ne yake nema ya kada ita ƙasa dan haka ta dafe kanta ta fita. Gaba ɗaya hawayen ma yaƙi zubowa se zafi da ƙirjinta yake yi, bata taɓa tsammanin halin Ammar ya kai haka ba, bata taɓa tunanin zafin zuciyar sa ya kai haka ba? Shikenan laifi wanda tasan tayi da wanda ba tayi ba se ya ɗora mata yaita faɗa, ko'a ɓata masa rai a waje yazo ita ya sauke mata, abun ya fara damun ta. ******************** Sosai Saima take dana sanin sanin Jabir a rayuwar ta, gaba ɗaya taji Aure ya fita daga ranta, ta ɗauki shawarar Mufeeda idan Jabir yana mata rashin mutunci ƙyale shi take bata tanka masa, tsanar da tayi wa Jabir a yanzu harta kai ga taji bata ƙaunar cikin dake jikin ta, dan haka ta ƙudurce a zuciyar ta ranar data haihu zata karɓi takardar sakin ta daga hannun Jabir tun kafin yaci zarafin ta ya kore ta akan 'yar masu kuɗin da yake hari, yake ganin zasu yabke masa talauci idan ya auri ' yarsu, sannan ta ajiye masa abunda ta haifa idan yasa kowa ze Auro tazo ta kula masa da ɗansa amma ba zata shayar da abunda ta haifa ba, Abunda Jabir yake mata yasa gaba ɗaya haushin maza take ji ta ƙudurce a ranta ba zata ƙara yin wani Auren a rayuwar ta ba, idan har Jabir da suka shafe shekaru suna soyayya ze mata haka bayan Aure to bazata sake Aure ba dan babu sauran wani namiji me imani da yayi saura duk haka halin su yake. ******************* Mufeeda tana ta fama da damuwa ta kasa gayawa kowa dan gani take hakan tamkar tona Asirin Auren tane, kuma koda ta gayawa iyayen ta aka sasanta komai ze iya wucewa a gurin ta, Amma ba lallai ya wuce a gurin iyayen ta ba. Tana kwance akan kujera bata jin daɗin komai aka ƙwanƙwasa ƙofa, jiki ba ƙwari ta tashi taje buɗe, tana buɗewa taga Anty Maryam ce, Yayar Ammar, murmushin dole Mufeeda ta ƙaƙalo tayi wa Anty Maryam tare da yi mata maraba. Suka gaisa Maryam tace "kin ganni unguwa naje na dawo naga na biyo ta layin unguwar ku nace bari inzo mu gaisa" "Aikuwa naji daɗi Anty Maryam, dama baya nan duk kaɗaici ya dameni, bari in dafa miki Abinci" "A'a Mufeeda ba sekin wahalar da kanki ba, kin ganni seda na cika cikina na fito" Nan suka shiga hira da Mufeeda, Amma Anty Maryam ta karanto damuwa ɓoye a bayan murmushin da Mufeeda take yi, ta ɗan dube ta tace "Mufeeda baki da lafiya ne?" "A'a Anty Maryam lafiya ta ƙalau" "Amma naga kinyi wannan ramar haka? Kodai wani abun yana damunki ne?" Wani murmushin dolen Mufeeda ta kuma yi tace "Ba abunda yake da muna fa ke kika ga na rame, amma komai lafiya" tana magana ne yayin da ƙasan zuciyar ta ji take kaman ta fashe da kuka. "Mufeeda idan kinsan akwai matsala ki gayamin, idan wani abun yake miki ki faɗa tun wuri ayiwa tufkar hanci, nasan halin Ammar sarai ɗan uwana ne amma zama dashi se me haƙurin gaske ki gayamin idan akwai matsala" Shiru Mufeeda tayi sannan ta ɗago ta kalli Anty Maryam tace "Anty Maryam gaskiyar kenan na gaya miki ki yarda dani" tai maganar tana ƙoƙarin maida ƙwallar dake ƙoƙarin zubo mata, ganin Mufeeda bata da niyyar gaya mata abunda ke damun ta yasa ta ƙyaleta, aka jima tai mata sallama ta tafi. Kusan gaba sosai Ammar yake da Mufeeda ba tare da tasan laifin da tayi masa ba, ko haɗa hanya suka yi, idan yayi mata tsawa se tayi dana sanin haɗuwar da suka yi. Gaba ɗaya ya zame mata tamkar wani dodo, duk da jin kansa amma yanayin yadda suke kasancewa tare, suci Abinci tare yanayi ne da yake matuƙar sata nishaɗi, Amma ƙirƙiri yanzu fargabar ganin sa ma take yi balle su haɗa hanya, gashi ita bata san laifin da tayi masa ba. Duk wani abu da ya kama na ciyar wa be fasa ba, Amma ba zata dafa yaci ba ko gaisuwa bata haɗa su. Sosai zaman da suke yi yake damun ta ya kamata ace idan laifi tayi masa ya gaya mata, dan haka ta yanke shawarar zuwa ta same shi taji laifin da tayi take fuskantar wannan hukuncin me matuƙar tsauri. Ɗakin sa taje ta same shi yana shiri ze fita, ɗagowa yayi ya kalleta ya ɗauke kansa, jiki a sanyaye tace "Yaya Ammar ka dubi zatin Allah ka gayamin laifin da nayi maka kake min wannan hukunci" Banza yayi mata ya ɗau wayarsa ya saka a Aljihu yana ƙoƙarin kewaye ta ya wuce, tare shi ta kuma yi cikin kuka tace "Yaya Ammar zuciya ta ba zata iya ɗaukar wannan hukuncin ba, dan Allah ka gayamin me nayi maka haka?" A fusace yace "get out from my sight bana son wannan salon yaudarar taki, 'yar ƙanƙanuwar yarinya dake amma kin iya yaudara" Zubewa tayi akan gwiwoyin ta tace "Naji na yadda amma dan Allah kayi haƙuri dukda ban san laifin da nayi maka ba, Amma kayi haƙuri" Ture ta yayi daga gaban sa yasa kai ya fice, da gudu ta kuma binsa falon tana riƙe rigar sa tana kuka. Fizge rigar sa yayi yace "Karki ƙara riƙe min riga munafuka mayaudariya, seda na yadda dake zaki tozartani ki bani kunya" "Yaya Ammar me yayi zafi kake kirana da wannan miyagun maganganun? Wani laifi ne haka na aikata? A zaman mu da kai bana tunanin na aikata wani kuskure dana cancanci wannan kalmomin daga bakin ka" "Tambaya ta ma kike yi? Da Aurena a kanki kike Soyayya da wani a waje, kin san zaki yi soyayya da wani dan me kika dage sekin Aureni kike yaudara ta da cewar kina sona, kinsan me kuɗi kike burin Aure meyasa kika Aureni kikemin daɗin bakin cewar ni kike so ba abun hannu na ba? An kiraki a waya na ɗaga wani ɗan iska yana faɗin yayi missing ɗinki, na fita sallar Asuba an tareni ance an ganki ƙiri ƙiri da wani me mota kina zance, akan me zakimin haka? Har yanzu zuciya ta ta kasa Amincewa zaki min hakan, sakamakon kalaman yaudara da kike Amfani dasu akaina, nasan da mace na Aura me hankali da inaga duk hakan bata faru ba, nayi nadamar Auren ki da nayi " Shiru tayi seda yayi ya gama ta ɗago idanun ta da suka koma Jawur ta kalli Ammar tace "Ba dan sharrin Soyayya ba Ammar babu abunda zesa in soka in zauna da kai da wannan halin naka, Yaya Ammar ko a kotu Alƙali yana bawa mai laifi damar kare kansa koda kuwa a gaban Alƙalin me laifi ya aikata laifin, ba kai ya kamata ka yi dana sani ba, ni ya kamata inyi dana sanin yin Aure, A iya zamana da kai na gane abubuwan da mahaifiya ta da 'yan uwana suke jiye min, Yaya Ammar ko dan Darajar Soyayyar da nake maka ya kamata kayi min Adalci ban cancanci jin wannan kalaman daga bakin ka ba, a zaman mu da kai a Alkhairaina guda nawa ka yaba? Amma yau akan kuskuren da baka da tabbas na Aikata ka hukunta ni da kalamai masu muni, kalaman da bazan manta ba har in koma ga Allah, Shikenan Nagode sosai, sannan bazan gajiya ba Allah ya baka haƙuri, idan ka sakko daga Fushin nayi maka bayanin abunda ya faru, Adawo lafiya Allah ya kiyaye hanya " Tana gama maganar ta tafi ɗakin ta tana shehssheƙar kuka me tsuma zuciya, seda Mufeeda tai wannan maganganun sannan Ammar ya dawo hayyacin sa ya fara tunanin Anya kalaman da yayi Amfani da su sun dace? Take kuma yaji kamar be kyauta ba gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, tabbas ya kamata ya bincika kafin yayi mata hukunci, haka nan ya ɗau key ɗin babur ɗin sa ya fice. Bayan fitar sa Mufeeda gaba ɗaya ji tayi ta tsani zaman gidan, gaba ɗaya ta rasa abunda yake mata daɗi ga zuciyar ta da take ta faman bugawa da ƙarfi, miƙewa tayi tasa hijjabin ta ta ɗau wayar ta ta fice, tafiya kawai take dan wani matsanancin ciwon kai ne ke damun ta ga Jiri da take ji dan haka kawai jefa ƙafar ta take, tana fita bakin titi ta tare me Napep ta gaya masa unguwar daze kaita ta faɗa ciki tana goge Hawaye. Akan idon Sa'idu me kayan miya hakan ta faru, dan haka ya jinjina kai yace "Yau akwai zazzafar Jarida" Me Napep ɗin daya ɗauki Mufeeda kuwa tsoro ya fara ji karta mace masa a Babur, dan wata irin shaƙuwa take tana sauke numfashi da ƙyar, seda ya kaita har ƙofar gidan Yaya Amina, Mufeeda ta fito daga A daidaita sahu abu ya faskara dan harta fara fita daga hayyacin ta da ƙyar take numfashi. Ƙwanƙwasa gate ɗin Yaya Amina me Napep ɗin yayi, akayi sa'a Yaya Amina ce ta buɗe, suka gaisa dame Napep sannan yace mata "dama waccan baiwar Allah na ɗakko tace nan zan kawo ta, kuma gashi munzo ta kasa fitowa kamar bata da lafiya" Aikuwa Yaya Amina na leƙawa ta hango Mufeeda a cikin Napep ɗin ta riƙe ƙirji, da Sauri Yaya Amina ta koma cikin gida ta ɗakko mayafi suka fito tare da mijin ta, Mufeeda na ganin Yaya Amina ta sake fashewa da kuka, suka ɗakko ta daga A daidaita sahu zuwa cikin gidan, mijin Yaya Amina ya sallami me Napep. A tayani Share ba dan halina ba 😍😍😜 NAGA NAFARA ƁATAWA 'YAN TEAM ƊIN MUFEEDA RAI, ANA CEWA HAƘURIN MUFEEDA YAYI YAWA, GA WATA TAMBAYA, DA MUFEEDA BATA KASANCE ME HAƘURI BA WANI IRIN ZAMA KUKE TUNANIN ZATA YI DA WANNAN MIJI NATA ME BAUƊAƊƊEN HALI? IDAN BA TAYI HAƘURI BA TAZAMA ME YAWAN ƘORAFI YANA HAƊA SHI FAƊA SA 'YAN UWAN SA A SANNU WATARAN SE IYAYEN MIJIN TA SUN FARA JIN HAUSHIN TA. AYIMIN HAƘURI LABARIN NE YAZO A HAKA DAN HAKA KU BIYONI SANNU A HANKALI DAN JIN YADDA ZATA KAYA KISSA BATA NUFIN KWALLIYA DA KWARKWASA BANE, AKWAI HAƘURI DA JURIYA. Taku har Kullum Aisha Humaira, Daddy's girl ko ince Ayshercool, ina godiya sosai da ƙauna da kuma bibiyar littafin da kuke Domin sharhi gyara ko shawara 07063065680...✨✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 23 A falo Su Yaya Amina suka kwantar da Mufeeda, mijin ta ya kunna fanka, Yaya Amina ta ɗakko ruwa tana shafawa Mufeeda a goshin ta, har yanzu Mufeeda sauke ajiyar zuciya take tana jan numfashi da ƙyar, kusan mintuna Ashirin wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, zuba mata ido suka yi gaba ɗaya kafin Yaya Amina tace "Hubby ina tunanin me yasa mu Mufeeda haka harta fito a wannan yanayin? Ko shi Ammar ɗin yana ina oho?" "Nima nayi wannan tunanin, Amma dai karki sanarwa da kowa mu bari ta tashi muga yadda hali zeyi, idan ta kama mu tafi Asibiti ne semu tafi a duba ta dan na tsorata gaskiya" Jinjina kai Yaya Amina tayi suka cigaba da dakon farkawar Mufeeda. Ammar kuwa bayan fitarsa abunda ya faru tsakanin sa da Mufeeda ya tsaya masa a rai, Yanzu yake tuhumar kansa akan me yasa yayi amfani da wannan Kalmomin masu nauyi akan Matar tasa, Kalaman sunyi zafi da yawa, Yayin da gefe guda kuma wata zuciyar take gaya masa me yasa zata yi masa haka, akan me zata yi Soyayya da wani a waje alhalin da Auren sa a kanta? Ace har a iya tararsa a waje a gaya masa a ganta tana zance a layi, ga wayar da aka kirata yaji da kunnen sa ga messages ɗin da ake turo masa akan ta gaba ɗaya kansa ya kulle, Alkhairan ta ya shiga tunawa wanda ita dai kullum burin ta ta ƙara Jaddada masa tana sonsa, Idan har tana sonshi kamar haka ya za'ayi ta aikata wannan aiki haka? " Mufeeda ta daɗe tana wannan baccin sannan ta tashi, koda ta tashi seta ji sassauci a zuciyar ta, Yaya Amina ta kai mata ruwan wanka tayi wanka ta kawo mata Abinci Amma tace ba zata ciba Mijin Yaya Amina yace " Haba Autar Baba ya zaki ce ba zaki ci Abinci ba? Kinzo a mawuyacin Yanayi gaba ɗaya mun tsorata da halin da muka ganki a ciki, dan Allah kici Abinci kinji" Girgiza kai tayi tana goge Hawaye tace "Na ƙoshi Yaya Auwal" Auwal yace "Amina ko zaki tambaye ta idan wani abun take so a siyo mata" Saurin girgiza kai Mufeeda tayi tace "Nifa na ƙoshi" Yaya Amina tace "wai ke meye hakane, ya za'ayi ta fama dake kici Abinci kamar wata Jaririya" Auwal yace "A'a My love mu bita a hankali tana cikin damuwa ne, be kamata kiyi mata faɗa a wannan yanayin ba" Da ƙyar suka takura Mufeeda ta sha tea da slides na dankali ta ture tace bata ci. Seda Mijin Yaya Amina ya tabattar babu wata matsala Mufeeda ta samu nutsuwa Sannan ya koma ɗakin sa dan ya basu guri, dan inda Amana Mufeeda ta hannun daman sa ce baze manta Yadda ta tayashi campaign a gurin neman Auren Amina ba. Bayan tafiyar sa Amina ta kalli Mufeeda tace "Auta bana son wannan halin naki na zurfin ciki da ɓoye ɓoye, kiyi min bayani me yake faruwa?" Shiru Mufeeda tayi ta sunkuyar da kai wasu hawayen na bin idon ta amma taƙi magana. Ba yadda Amina ba tayi ba akan Mufeeda tai mata bayani amma taƙi, Yaya Amina tace " shikenan tunda ba zaki gayamin ba bari in kira Mama in mata bayani, wataƙila ita zaki iya gaya mata" Da sauri Mufeeda ta riƙe hannun Yaya Amina tace "Yi haƙuri dan Allah zan gaya miki, Amma kiyi min Alƙawarin ba zaki gayawa Su Mama ba ko Anty Fadeela, kinga ke kaɗai ce abokiyar Sirri na wadda zata tausaya min, idan kuma Mama taji zata ji babu daɗi" "Shikenan naji babu wanda zan gayawa, gayamin meyafaru ? Kuma bance ki ragemin komai ba indai kin yadda ni yayar kice kuma abokiyar shawarar ki" Nan Mufeeda ta zauna ta warwarewa Yaya Amina yadda suka yi da Ammar da yadda take fama da Wasu daga cikin 'yan uwan sa, ɗan shiru Yaya Amina tayi sannan tace "Amma gaskiya Mijin ki bashi da kirki, se kace bashi da' yan uwa mata, ko dan keba ƙanwarsa bace ba uwa ɗaya uba ɗaya kuke ba shine ze dinga miki rashin mutunci? ko kuma yana ganin ya Aure ki a ɓagas seya dinga wulaƙanta ki, a da na goyi bayan ki Aure shi saboda naga yadda kike sonsa, Amma ya bani kunya wallahi zega tsiya tunda bashi da mutunci " Ɗan tura baki Mufeeda tayi tace " Ni gaskiya ki dena zagarmin mijina " Buɗe baki Yaya Amina tayi dan mamaki sannan tace " Dan kin samu baki hallaka ba, kin manta yadda kika zomin rai a hannun Allah shine kike wani in dena zagin sa, an zage shi ɗin bashi da mutunci, kema kuma sokuwa duk surutun naki da rashin kunya akan 'yan gari ya ƙare ki zauna yana neman ya kashe ki da ƙuruciyar ki" Yaya Amina ta harzuƙa sosai, tana da haƙuri dan tafi duk su Mufeeda haƙuri, Ba ƙaramin abu ne yake ɓata mata rai ba. "Yaya Amina nice fa a ƙarƙashin sa, Idan har nace zanyi masa rashin kirki ban kyauta ba, duk abunda mutum yayi maka na laifi akwai buƙatar kayi masa Adalci, Yaya Ammar yana kula dani fiye da tunanin ki, in bani da lafiya ze kaini Asibiti na kuɗi in shine yaje na gwamnati, ya yadda ya hana kansa ko yaci Abinci mara daɗi ni inci abunda nake so, Saboda shi na dena ɗora kayan ƙyale ƙyalen mata akan status ɗina, ko in ajiye su a waya ta, da ya gani, komai tsadar su indai ze iya seya nema ya siyamin indai ze iya, ko a hira na faɗi wani abu idan yana da kuɗi se ya saimin abun nan, ba abunda na nema na rasa a gidan sa se Soyayyar sa da kuma yawan fushi da rashin bincike idan akace masa nayi laifi" Ta ƙarasa maganar tana kuka hadda sheshsheƙa, Yaya Amina ba ƙaramin tausayawa Mufeeda tayi ba, gaskiya Ammar halin sa seshi, tayi mamaki da suke zaune da Mufeeda ma, Saboda babban abunda yake haɗa Mama da Mufeeda ko a gida yawan Faɗan ta da rashin ɗaukar raini, Amma yanzu Allah ya haɗa ta da murɗaɗɗen Namiji wanda tilas yasa ta ajiye nata rawar kan. Yaya Amina ta numfasa sannan tace "Shikenan ya isa haka, Amma Gaskiya Mufeeda kinyi wauta, seda na gayamiki, ki gaya masa abunda yake faruwa amma kika ƙi" "Yaya Amina ba ƙi nayi ba a lokacin ma sama sama yake dani, maƙota na sun kawo masa ƙara ta" Yaya Amina tace "Maƙota kuma? Me kuma ya haɗaki da maƙota zasu kai masa ƙarar ki?" Nan ma ta zauna ta warwarewa Yaya Amina komai, Yaya Amina ta jinjina kai lallai ƙanwar ta tana ganin ƙalubale a cikin rayuwar Auren ta, Yaya Amina ta riƙe hannun Mufeeda tace "ki kwantar da hankalin ki kiyi haƙuri Insha Allah komai ze wuce ze daidaita, amma sena koyawa wannan mijin naki hankali, waima uban waye ya gaya masa ya ganki kina zance da wani?" "Wallahi ban saniba Yaya Amina, Amma akwai wani mutumi da yake bina a unguwar wai yana sona, hana da kuɗi sosai, Amma wallahi Yaya Amina rashin mutunci nayi masa nace ni matar Aure ce, ban san waye ya gaya masa hakan ba" "to ke uban me ya hana ki gaya masa ga abunda mutumin yake miki?" "Hmm Yaya Amina kenan, me ɗaki ai shi yasan inda yake masa yoyo, Nasan halin mijina tsaf kallo ɗaya yakewa abu yai masa hukunci ba tare da dogon bincike ba, koda na gaya masa se yaga laifina nima" "Shikenan ya isa, ki dena kukan haka nan" A hankali Yaya Amina ta dinga janta da hira domin ta rage damuwar da take ciki. ********************* Gaba ɗaya idan Ammar ya tuna abunda yayiwa Jaririyar matarsa da yadda take kuka se yaga be kyauta ba, ya tuna yadda ya baro ta a yanayi mara daɗi dan haka ya yanke shawarar komawa gida don yaga halin da take ciki. Koda ya koma gida be san ta ina ya kamata ya fara ba, zuwa ɗakin ta zeyi ya duba ta kokuma yaya? Tuno irin maganganun da yaji ana yi mata a waya yayi nan da nan yaji ransa ya ƙara ɓaci ya nemi guri ya zauna a falo, shiru shiru be ji motsin ta ba, ya fara mamakin anya kuwa taji dawowar sa, ko yana fushi da ita idan ya dawo seta fito ko baze kulat ba za tayi masa sannu da zuwa, a hankali idon sa ya kai kan inda hular ta ta faɗi lokacin da ta biyo shi tana bashi haƙuri, se yanzu ya lura da yadda ya fita ya bar gidan haka ya dawo ya tarar da shi. Da sauri ya miƙe ya fara leƙe leƙe amma komai yana nan yadda yake, ya nufi ɗakin ta da sauri ya buɗe ƙofar amma bata ciki ga ƙofar wardrobe ɗinta a buɗe, ya buɗe banɗaki nan ma bata ciki, a gaggauce ya dinga duba lungu da saƙo na gidan nan amma babu Mufeeda babu alamar ta. Hannu yasa a Aljihun sa ya ɗakko wayarsa ya fara kiran layin ta, Mufeeda na kwance a ɗakin da Yaya Amina ta sauke ta wayar ta ta fara ringing, kallon inda wayar take tayi taga sunan My lovely Bae akan screen ɗin wayar. Ƙurawa wayar ido tayi tana ci gaba da ringing, idan ta katse ya sake kira ya kira ya kai sau takwas, Amma Mufeeda taƙi ɗagawa kuma ta kasa kashewa, Yaya Amina ce ta jiyo ringing ɗin wayar ta shigo ɗakin tace "Auta ba wayar kice ke ringing ba?" "Waya tace Yaya Amina, Yaya Ammar ne yake kira na" Yaya Amina tace "maza yi rejecting ɗin kiran nan ki kashe wayar" Girgizawa Yaya Amina kai tayi tace "bazan iya rejecting ɗin kiran sa ba" Wata uwar Harara Yaya Amina tayi mata, ta fizage wayar tayi rejecting ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta cillawa Mufeeda wayar. Hankalin Ammar ya tashi da yaji ya kira taƙi ɗagawa ƙarshema ta kashe wayar, nan da nan gumi ya fara tsatstsafo masa, yanzu ina Yarinyar nan ta shiga? Me zance wa Iyayen ta? Gaba ɗaya kansa ya kulle ya rasa abunyi, idan Yace zeje gida ya gayawa iyayen sa halin da ake ciki to tabbas ze fuskanci ɓacin rai musamman a gurin mahaifinsa, dama Yaya Jidda ba'a maganar ta dan babbar banza ce, ita kuwa Yayarsa Amina da suke cewa Ummi 'yar ba ruwana ce, har gara Maryam wadda yake bi tafi su fahimta, dan haka ya yanke shawarar yaje gidan Yaya Maryam yaji ya zasuyi dan gaba ɗaya ya rasa abunyi. A sukwane ya rufe gidan ya ɗau babur ɗin sa ya tafi gidan Yaya Maryam, tayi mamakin ganin sa a wannan lokacin amma yanayin sa ya nuna mata Akwai matsala akwai abunda yake damun sa, Yaya Maryam ta kalleshi tace "lafiya kuwa Ammar?, naganka kamar ba a nutse ba, meke faruwa ne?" "Akwai matsala ne fa" "Matsala kamar yaya? Allah yasa ba wani abun kayi wa Mufeeda ba" Ammar ya ɗan sosa kai, cikin jin nauyi yace "A kanta ne" "ina jinka" Nan Ammar ya kwashe komai ya sanar mata, shiru tayi tana kallon Ammar seda ya gama tsaf ta jinjina kai tana ci gaba da kallon sa, can tace "Amma Ammar ban taɓa tunanin rashin hankalin ka ya kai haka ba wallahi" Haɗe rai yayi yace "ya za'ayi dan nazo na gaya miki matsala ta ki kirani da mara hankali" Babban abunda yasa Ammar yake shiri da Maryam shine yadda take girmama shi, daman akwaishi da son girma, Be taɓa zaton zata kira shi da mara hankali ba. A fusace tace "Na faɗa mara hankali, dama da naje gidan ka wancan satin yarinyar nan tana cikin damuwa nayi nayi ta gayamin idan akwai matsala amma tace babu ashe cutar ta kake" "Ya zaki ce ina cutarta ni bance ta cutar dani ba da Aure na take kula maza a waje" "Karka ƙara cewa tana kula wasu mazan a waje tunda baka gani ba, baka da tabbas ashe duk Nasihar da Baba suka dinga yi maka lokacin da aka baka Auren Yarinyar nan da wadda nayi maka duk baka ɗauka ba, iyayen ta sun baka ita a mutunce da girmamawa amma kayi haka, kai a marrar nan ka samu Yarinyar da harta san tayi laifi ta baka haƙuri, amma kake wulaƙan ta ta, niba abunda zan iyayi maka akai, kaje ka samu Su Baba kayi musu bayani aje gidan su a duba, in tana can in taga zata dawo shikenan, ko dayake ma ai babu Aure a tsakanin ku tunda har zargi ya shiga ciki " Zaro ido Ammar yayi yace " Ubanwa yace miki zargin ta nake, ko duk duniya zasu taru akan Zata aikata zina zan ƙarya ta kowaye, Yanzun ma na yadda ne saboda da kunne na na ɗaga wayar naji, kuma ita mace ce me son kulawa da soyayya sosai " Yaya Maryam tace "Eh Mace ce me son kulawa da Soyayya, kai kuma bazaka iya nuna mata soyayya da kulawa ba kana ganin yin hakan kaman ka faɗo ne ko? Shiyasa ka yadda za tayi Soyayya da wani a waje, ai in gaya maka kaɗan da aikin mace idan har zatayi abu ba zaka yaba ba tayi ta burge wasu a waje, ai ita mace tana so a yaba mata kai kam nasan bazaka iya ba" Ammar ya ɗan kalleta ya ɗauke kai, "Nasan halinka ai Ammar, Yarinyar nan tana sonka bekamata kayi mata haka ba, da kaji wani ya kira ta bincike ya kamata kayi, Idan tana chatting ne a social media akwai sakarkarun maza marasa tarbiyya da suke bin lambar mutane su dinga kira, zata iya yuwuwa a cikin su ne, kuma me ya kaika ɗaga mata waya? Da har kaji wannan maganar" Cikin damuwa Ammar yace "Amma fa har message ake turomin akan in saka ido akan ta tana aikata rashin gaskiya a bayan idona da ban yadda ba amma abun ya fara ɗauremin kai" "Taɓɗijan to waye yake turomaka?" "Nima ban sani ba, anyi hiding ɗin lamabar" "to tabbas me turomaka saƙon yana da Alaƙa da wanda ya kira ta a waya in ba haka ba ya akayi yasan tana aikata rashin gaskiyar? Kuma me yasa ya ɓoye lamba, ai kamata yayi ku zauna ku tattauna, ko ka yi bincike a ɓoye ka gane gaskiya kafin ka yanke mata hukunci " Shiru Ammar yayi ya dafe kai yana tuna lokacin da Mufeeda ta biyo shi tana riƙe rigar sa tana kuka, yadda bata son ɓacin ransa sam, gaba ɗaya tausayin ta da nadama ya kama shi, Jiki a sanyaye yace "Yanzu meye abunyi? " "Abunyi kaje ka samu Abba kuyi maganar" "Haba Yaya Maryam, idan har zan gayawa Abba meye amfanin zuwa gurin ki, Abba bazemin da daɗi ba, inason sanin takamaimai tana ina, na kirata yafi a ƙirga bata ɗauka ba, ƙarshe ma ta kashe layin ta gaba ɗaya" "Koma menene dai kai ka janyo shi, dan ka kaita bango ne shiyasa ta tafi ta bar maka gidan ka, da alama ka daɗe kana muzguna mata, yanzu abunyi shine kaje gida zuwa gobe in Allah ya kaimu se asan yadda za'ayi" Zare ido yayi yace "har zuwa gobe? Ban san inda ta tafi ba kuma bansan a wani hali take ba?" "to seka fita kaje ka neme ta ai, kasan da haka amma kai mata wulaƙanci" Jiki a sanyaye Ammar ya tashi ya koma gida, gaba ɗaya ya shiga damuwa tare da tunanin ina ta tafi haka? Abunda zesa Mufeeda taƙi ɗaga wayarsa ba ƙaramin abu bane, lallai indai tana cikin ƙoshin lafiya ba ƙaramin fushi take da shi ba, ɗakin ta ya kuma komawa yana dubawa kota dawo amma still bata nan, Ammar ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ya shiga tunanin idan Mufeeda wani gurin tayi da wani ido ze kalli iyayen ta, Abun duniya ya ishe shi gidan yayi masa faɗi, daren ranar sam bacci ya ƙauracewa idon sa, yayi zurfi a tunanin ina ze gano 'yar mutane. Ɓangaren Mufeeda ma tunanin sa take yi, tasan hankalin sa yana tashe besan inda ta tafi ba, A ranata tace "Allah yasa kar yaje gida nemana bana son su Mama su san abunda ke faruwa" Ji take kaman ta kunna wayar ta ta kira shi saboda tasan ze shiga tashin hankali rashin ganin ta, amma da ta tuno kalmar mayaudariya munafuka da ya kira ta da su se wasu zafafan Hawaye su zubo mata, ƙoƙari ta dinga yi ta manta da shi amma abu ya faskara, dan wani tausayin sa ne ya mamaye zuciyar ta dan tasan tabbas Ammar baze iya bacci ba yau. Wasa2 kwana uku babu Mufeeda babu labarin ta, hankalin Ammar ya gama tashi, ko Abinci baya iya ci, yaje gidan su Mufeeda ya fake da gaishe su yaje yi Amma ya tarar bata nan, kuma bega wata alama a fuskar Mama da yake nuna wani abu ba, Ammar ba bacci babu cin Abincin kirki saboda tunani da fargaba, Yayi niyyar ya nemi Aminu koda shawarar daze bashi se kuma ya fasa, sam Ammar ya rasa kwanciyar hankali. Yaya Maryam ma nata ƙoƙarin trying lambar Mufeeda amma taƙi shiga. Har yanzu Mufeeda tana fama da damuwa ga shi bata da lafiya har yanzu, Mijin Yaya Amina yace idan ya dawo zasu tafi Asibiti. Yanzu ma Yaya Amina ta saka Mufeeda a gaba akan tayi breakfast, gaba ɗaya mufeeda bata jin daɗin Abincin ta riƙe cokali tayi shiru tana zancen zuci, Yaya Amina tace "Kinga Auta karki wa kanki illa da wannan tunanin ki maida kai kici Abinci kafin Ya dawo mu tafi Asibiti" Mufeeda ta ajiye cokalin ta kalli Yaya Amina tace "Yaya Amina wallahi tunanin Mijina nake, besan inda nake ba hankalinsa ze tashi sosai, kuma ma ko yaci Abinci yanzu? Nasan ba lallai yana cikin nutsuwar da zeci Abinci ba" "Sannu Tattabara uwar ƙauna, ko ince sarkin Aure, ke ba kiga halin da kike ciki ba saboda shi, amma tausayin sa kike ji baki da zuciya" "Ba rashin zuciya bane Yaya Amina, abun da Yaya Ammar yayi shi duk wani Namiji da yake son matarsa zeyi, tun ɗazu na kunna wayata kiran sa yake shigowa, Zuciya ta na rayamin in ɗaga nasan zuwa yanzu yana cikin nadama" A fusace Amina tace "Wallahi kika ɗaga wayarsa sena gayawa Mama abunda ke faruwa" Wayar Mufeeda ta fara ringing, tana dubawa taga Anty Maryam ce, ta kalli yaya Amina tace "Yaya, Anty Maryam ce Yayar Ammar" Yaya Amina tace "bani wayar nan" ta karɓi wayar tare da yin sallama, suka gaisa da Anty Maryam. Anty Maryam tace "dan Allah Mufeeda nake nema" "Ba ita bace Yayar tace" "Masha Allah, gurin ki ta taho kenan?" "Eh muna tare, nan ta taho" "Dan Allah ki temaka ki gayamin inda gidan ki yake zanzo muyi magana" Yaya Amina tayi mata kwatancen gidan ta, befi awa ɗaya da rabi ba sega Anty Maryam, Yaya Amina tayi mata kyakywar tarba, Kallo ɗaya Anty Maryam tayi wa Mufeeda taga ta rame sosai kuma kana ganin ta kasan bata da lafiya, Anty Maryam tacce "Mufeeda ran da naje gidanki ba yadda banba ki gayamin in akwai matsala amma kika ƙi" Yaya Amina tace "Ai ba zata gaya miki ba, yanzu ma dan taga ta kusa mutuwa ne yasa ta zo gidana, dan lokacin da tazo ko numfashi bata iyayi" Nan Yaya Amina ta zauna ta gayawa Anty Maryam komai kamar Yadda Mufeeda ta gaya mata, kallon jinjina take wa Mufeeda tace "Sannu Mufeeda Allah ya baki ladan biyayya da haƙuri, amma maganar gaskiya koni bazan iya wannan haƙurin da kikayi ba, Amma ku ƙyaleni dashi ze gane kuskuren sa, yanzu Alfarma ɗaya nake so kiyi min, ki bani ita in tafi da ita, zan kaita Asibitin ta zauna a gurina na wani ɗan lokaci, bana son wani daga iyayen mu yasan hamin da ake ciki, amma tabbas zan koya masa hankali " Da farko Yaya Amina bata yadda ba, se daga baya ganin Yadda Anty Maryam wadda ta girmesu gaba ɗaya keta magiya yasa ta Amince, ita dai Mufeeda bata da ta cewa, Yaya Amina ta bawa Mufeeda wasu daga kayan sawarta da yake ba tazo da kaya ba sena jikin ta tabi Anty Maryam gidan ta. Ammar kam seya raba dare a falo a zaune, idan yayi salla kuwa bashi da Addu'a se Allah ya bayyana masa Matarsa yasa tana lafiya, idan ya zauna a falon nan ya dinga tuna yadda take tattalin sa tana kula dashi, be taɓa tunanin ya shaƙu da Mufeeda haka ba se yanzu, ji yake duniyar tayi masa zafi rashin ganin giftawar ta a gidan. Kwanan Mufeeda biyu a gidan Anty Maryam kulawa take bata kamar ƙanwarta da suke ciki ɗaya, tana kula da ita, ita da mijin ta suka kai Mufeeda Asibiti, aka bata magunguna aka tabbatar musu da jinin ta ya hau, ta rage damuwa ga ulcer da tayi mata mugun kamu saboda rashin cin Abinci, Mijin Anty Maryam se mita yake yace "Ummu Iman wannan ƙanin naki Halinsa se shi, Ya samu yarinya me haƙuri amma ze wasa da damar sa yana nema ya kashe musu 'ya" Anty Maryam tace "ƙyaleshi zega tsiya sena koya masa hankali" Da sassafe Ammar ya shirya ya tafi gidan Anty Maryam, gaba ɗaya yana cikin kiɗima yace "Maryam na rasa inda zan saka zuciya ta rashin ganin Mufeeda, wallahi ina cikin tashin hankali" "Illar Fushi kenan da rashin bincike, seka kiyaye gaba" "Maryam yanzu ba lokacin wannan bane, na yanke shawarar inje in gayawa Abba, tun kafin lokaci ya ƙure in karɓi duk hukuncin daze min" Har ya juya ze tafi Anty Maryam tace "badan halinka ba na gano inda take" Da sauri ya juyo a gigice yace "dan Allah tana ina?" "Babu ruwan ka da inda take, Amma na ganta har munyi magana" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdilillah dan Allah ki bar batun wasa tana ina?" "Sanin inda take bashi da Amfani a gurin ka, dan tace min ita da gidan ka har Abada ba zata koma ba" "Ƙarya ne ba dai Mufeeda ce ta gaya miki haka ba, ba zata taɓa faɗin haka ba" PLEASE IF YOU READ IT HELP ME TO SHARE IT, DON'T FORGET TO VOTE AND COMMENT JIYA NA KUSA CIN DUKA A WAJEN MASOYA MUFEEDA 🤣 Domin Sharhi gyara ko shawara you are free to contact me via my what's App Number Ayshercool .. ✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment ELEGANT ONLINE WRITER'S Page 25 Mufeeda tana fama da laulayi Sosai, har gwara 'yan kwanakin nan ta ɗanji sauƙi, Ammar kam kullum cikin sintiri yake gidan Anty Maryam, Amma bata saurarar sa duk lokacin da yaje haka ze dawo gwiwa ba ƙwari. Yanzu ma Sallama yayi sedai yau Anty Maryam bata nan, Mufeeda ce kawai se 'yar Anty Maryam wadda ba tafi shekaru uku ba suna kallo da Mufeeda a falo, A hankali Mufeeda ta amsa Sallamar Ammar ɗin, ya shigo falon da suke ya tarar da Mufeeda a falon, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai. Ɗan Murmushi Ammar yayi yace "Lallai Auta Sauƙi ya fara samuwa, yau kina falo wannan kwalliya haka" Bata ce masa komai ba sema maida hankali da ta sake yi akan Tv, 'yar Anty Maryam Ammar ya bawa biscuit yace "Amrah ina Umminki?" Cikin maganar yara tace "ta tafi unguwa ta bammu nida Anty Mufeeda" "Shikenan maza jeki ɗaki kici biscuit ɗinki keda teddynki" Cikin murna yarinyar ta tashi ta tafi ɗakin su na Yara tana murna, Yaran Anty Maryam duk suna makarantar kwana ne (boarding) , daga ita se Yarinyar ta ƙarama. Ammar ya zauna a kusa da Mufeeda yana ƙare mata kallo, ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tayi taƙi kallon sa. "Mufeeda nine bakya son gani ko?" Tura baki tayi taƙi kallon sa. "you look so beautiful Masha Allah" Da sauri ta kalle shi tace "Ka manta ne ƙwaila fa kake wa magana kar in rainaka fa naji kana cewa nayi kyau" Ƙasa yayi da murya yace "Eh nasan ƙwailar ce, Nace kiyi hakuri please mu koma gida, nima fa bani da lafiya koda yake naga kin dena sona Amma ayi haƙuri dan Allah" Cikin tsiwa tace "Dan Allah nika matsa daga kusa dani, na gaya maka daga gidan nan se gidanmu zan wuce, bazan sake zama da kai kanamin faɗa kullum ba" "Mufeeda nine fa" Shiru tayi tana zumɓura baki, Janyo ta yayi yana ƙoƙarin kissing ɗin ta, ta dinga ture shi tana girgiza masa kai. Sallamar Anty Maryam ce tasa shi sakin ta yana maida numfashi, miƙewa Yayi Da Sauri, Anty Maryam ta kawo kai ɗakin ta tsaya tana yiwa Ammar kallon tuhuma. Basarwa Yayi yabi gefen Anty Maryam ya fice ba tare da ya kula ta ba, ta kalli Mufeeda da tayi kicin kicin da fuska tace "Lafiya kuwa Mufeeda?" "lafiya ƙalau" "Kodai Akwai matsala ne?" Girgiza mata kai Mufeeda tayi, bata son ci gaba da takura mata dan haka ta ƙyaleta. ********************* Bayan barin Mufeeda gida wata mata ta sake tarewa a jikin gidan Mufeeda, tunda ta shiga gidan Su Maman Amir taga take taken basu da mutunci, basu da Aiki se gulma da zagin mutane, kuma da wata ta tashi a cikin su zasu hau yi da ita. Ammar yana kwance a falo yaji ana knocking, kamar kar ya tashi amma ya miƙe yaje ya buɗe, yana buɗewa yaga Fa'iza a tsaye, Murtuke Fuska yayi yace "Malama lafiya?" Murmushi tayi tace "laa Yaya dama kana gida? Ziyara na kawo maka" "Nagode, Amma bata nan dan haka zaki iya tafiya" "Amma Yaya Ammar ai ko ruwa ka bari Insha, na kwaso rana da gajiya wallahi" "Baki da hankali ne? Bakije me nace ba? bata nan, ya zaki shigo gida Alhalin matar gidan bata nan, daga ni seke? Ki tsaya anan in miƙo miki ruwa amma ba zaki shigo ba" Haka tabi Ammar da kallo ya rufe ƙofar sa ya shiga gida ya miƙo mata ruwa ya koma. Jinjina kai Fa'iza ta shiga yi kafin daga bisani ta bar gurin tana wani tunani a ranta. Bayan Su Anty Maryam sun kammala cin Abincin dare, ta lura kamar akwai magana a bakin Mufeeda, ta kalle ta tace "Mufeeda ya akayi ne?" Ɗan shiru Mufeeda tayi sannan tace "Dama Anty.. Inn.. Ina so in koma ne" "Kin gaji da zaman nan kina kewar mijin ki ko?" Saurin girgiza mata kai Mufeeda tayi tace "A'a Anty Maryam, naga bashi da lafiya ne ko Abinci ba yaci, kuma ya bani haƙuri yayi nadamar abunda yayi" "ki gayamin gaskiya, ko dai shi ne ya takura miki yace sekin koma?" "A'a Anty be takuramin ba sam, kawai dai.." Anty Maryam ta katse ta ta hanyar cewa "Shikenan naji, amma karki gaya masa zaki koma, zanga yadda za'ayi ki koma ɗin, koba komai ai mun hora shi" ***************** Wasa2 Saima rashin lafiya take sosai, Amma Jabir kawai cewa yake rakine irin nata, ta kumbura sosai ga damuwa tayi mata Yawa komai da ƙyar take yi, Jabir kam yana ta rawar ƙafa akan Fatiyya dukda kasancewar ta 'yar masu kuɗi hakan be hanashi yin bajinta yana kashe mata kuɗi ba, yayin da tsakanin sa da Saima se ido, kullum yana kan waya ko chatting, gani yake gaba ɗaya Saima ta koma masa wani iri, ta dena kwalliya kullum cikin larura take, gashi ta raina shi shiyasa sam baya saurararta. Yanzu ma yana zaune yana chatting ɗin sa se dariyar sa yake, Saima ta kalle shi tace "Jabir yanzu haka zamu ci gaba da zama? Tsakanina da kai se ido ina fama da rashin lafiya ko a jikin ka sedai ka kalleni, ko kuma ka zauna kayi chatting da mata, babu ruwan ka da halin da nake ciki? Jabir kaji tsoron Allah" "kinga Malama ya isheki, me kike so in miki? Zan cire miki ciwone? Ko kuma ni na ɗora miki? Kuma kina batun ina chatting da Mata danme ba zanyi ba? Kalli yadda kika koma kin Zama wata ƙatuwa kwalliyar ma kin dena, Kullum ke kenan cikin ciwo, nan ciwo can ciwo kaman akan ki aka fara ciki, nace kije gidan ku idan kika haihu seki dawo amma kin nace kinƙi tafiya, ya kike so in miki? Ba dai Abinci kikeyi wa ba, gashi nan na siya na ajiye kiyi taci" Share Hawaye Saima tayi tace "Jabir da ina da gata da tuni na barma gidan ka, kasan bani da kowa se Allah se kai, da na sa ran na samu mijin marainiya ashe ba haka bane, kake zancen kullum cikin ciwo nake bana kwalliya, da a haka ka ganni kace kana so? Kaifa ka maidani haka, kuma da kayi haƙuri na ɗan lokaci ne dana haihu Insha Allah zan koma yadda nake, Amma ina rabaka da Auren kwaɗayi Jabir, wallahi kaji tsoron Allah " " Ubanwa yace miki Auren kwaɗayi zanyi? " " karka sake ka zagi Ubana, kuma ba uban wani ne ya gayamin ba da kunne na naji, za'a baka gida da Mota saboda rashin zuciya, duk Ni'imar da Allah yayi maka kana da gidan kanka, kana da Mota Amma kana hange, wallahi Jabir haƙƙi na baze barka ba" "Oho ke kika sani, 'yar baƙin ciki dan kinga faƙiran' yan gidan ku basu kawo ki da wani abun Arziki ba shine kikewa wasu Hassada, ko gishiri da Sunan gara ba'a kawo ki da ita ba" "Yanzu Jabir hadda Gori zakayi min? Amma ai haƙƙin ciyar dani a wuyan ka yake" "Dalla rufemin baki, Aure ne se nayi kuma chatting yanzu na fara" "Shikenan Jabir kayi abunda kake so, Amma wallahi se Allah ya sakamin, dan bazan taɓa yafe maka ba, Azzalumi mayaudari ka lallaɓani ka Aure ni da daɗin baki da Komai, Shine yanzu ka samu abunda kake so, zaka Auro wata har tana ba zata zauna dani ba, kaje ka yi indai kaine gaka gata nan, dana haihu ka sawwaƙemin yadda za kuji daɗin zama" Tsaki yayi ya wuce ya barta a falon tana kuka. **************** Ammar har baya so ya tunkari komawa gida, musamman idan ya tuna Mufeeda bata gidan. Yanzu ma ba yadda zeyi ne, haka nan ya tunkari gidan yana komawa ya shiga da Napep ɗinsa harabar gidan yayi parking, Amma se yaji kaman ƙamshin turaren wuta, da sauri ya ƙarasa cikin falon ya tararar da komai tsaf se tashin ƙamshi falon yake, Ajiyar zuciya yayi ya lumshe ido yace "ta dawo kenan" ya nufi ɗakin Mufeeda da Sauri, yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin Amma yaga bata nan. "Mufeeda" ya kira sunan ta da ɗan ƙarfi. Gyaran murya tayi masa alamar tana banɗaki. Guri ya samu ya zauna a gefen gadon ta yana jiran fitowar ta. A ƙalla ya kai mintuna goma sha biyar a zaune sannan Mufeeda ta buɗe ƙofar toilet ɗin ta fito. Ba tasan yana ɗakin ba dan haka daga ita se towel ta fito, tana fitowa suka haɗa ido, ɗauke idon ta tayi tai gaba abun ta, shikam Ammar binta yayi da ido, tun daga sama bayan ta ƙugunta zuwa ƙafafunta, se sheƙi fatar ta take kamar wata tarwaɗa, kasa Magana Ammar yayi, Mufeeda ta tafi gaba wardrobe ɗinta ta ɗakko zumbulelen Hijjabi ta zura ta nemi guri tayi zaman ta. Mamaki Ammar yake, Yarinyar da wata shigar idan tayi wataran sedai yabar mata falo, shine yau ta wani basar tasa Hijjabi, sharewa Yayi yace "Ashe kin dawo?" maimakon ta amsa masa seta kalle shi kawai. "Dakin min Waya nazo na taho dake, tunda baki da lafiya" "Hmm to koma dai mene ne, ai gani na dawo" "Ki tashi kisa kayanki mana, kinsa Hijjabi kin duƙunƙune ko har yanzu jikin ne?" "toni kazo kana ta kallona, a haka zansa kayan?" Ammar yace "Hmm shikenan bari in baki guri, ko akwai abunda kike buƙata in siyo miki?" Girgiza masa kai tayi alamar A'a, ya tashi ya fice. Yana zuwa ɗakin sa ya tarar da Abinci, wani murmushi yayi yai salla, sannan ya zauna yaci Abincin, rabon da yaci Abinci haka har ya manta, yayi missing ɗin Abincin ta sosai. Har yanzu Mufeeda basar da Ammar take, taƙi sakin jiki dashi kamar da, yana rage mata ayyukan gida sosai saboda tana fama da laulayi sosai, Amma a hakan kafin ya dawo take masa girki ta gyara ko'ina. Sam Mufeeda bata iya cin Abinci se 'yan kame kame yana matuƙar tausayin ta yadda take fama da laulayi amma ko inda take bata so yaje. Yau Ammar be dawo da wuri ba dan se dare ya koma gida, yana komawa ya tarar bata falo ya bita ɗakin ta, yana zuwa ya tarar ta kwanta dan harta fara bacci, gaban gadon ta ya ƙarasa ya durƙusa yana kallon fuskarta data faɗa sedai fatar ta data ƙara haske, Zuba mata idanuwan sa yayi yana kuma ƙare mata kallo, Sosai Ammar yake jin Mufeeda a ransa, ƙamshin turaren Ammar ne yasa ta farka, A hankali ta buɗe nata idanuwan da suka yi mata nauyi saboda bacci kallon sa ta ɗanyi ta mayar da idon ta ta lumshe. "Sannu ya jiki?" "Da sauƙi" ta faɗa ba tare da ta buɗe idon ta ba. "Ki tashi ga Maltina da fruit na kawo miki ko zaki iya ci, tunda ba kya iya cin Abinci" girgiza masa kai tayi tace "Na ƙoshi" Gaba ɗaya Ammar baya jin daɗin wannan Mood ɗin nata, ya kuma ƙasa da murya yace "har yanzu baki huce ba fushi kike dani ko?" Girgiza masa kai tayi. "to dan Allah ki tashi kici Abinci, bana jin daɗin yanayin da nake ganin ki, nayi nadamar maganganun dana gaya miki, Amma kiyi haƙuri bazan sake ba Insha Allah" "Ai nima ya wuce a gurina" "Banga alamar hakan ba tunda har yanzu bakya kulani kamar da, kin dena Yimin Addu'a, kin dena sakin jiki dani, ko sena bada cin hanci ne? Biscuit ko chocolate, gayamin wanne kike so?" Yai maganar yana sake langaɓar da kai cikin sigar rarrashi Murmushi tayi tace "Ai am still under punishment, ko kaman ta ne?" "Baki haƙuran ba kenan?" Miƙewa zaune tayi ta kalle shi "eh gaskiya ban haƙura ba" "Meyasa?" "Saboda baka sona" Ɗan zaro ido yayi yace "Nine nace bana son ki?" Cikin shagwaɓa tace "to ka taɓa cewa kana sona ne?" Murmushi yayi yace "Hmm wayo zakimin ko? Ni dai kiyi hakuri kidena wannan fushin" Faɗawa tayi jikin sa ta rungume shi tace "Nifa ya wuce" Yasa hannayen sa ya ƙara rungume ta a jikin sa yace "I miss you ƙwailata" Murmushi tayi tace "bazaka dena cemin ƙwaila ba ko?" "Eh mana har yanzu ke ƙwaila ce" "Hmm zan rama ne" Daga nan suka jone abunsu ya sata a gaba yana bata Fruit (Note: kayan marmari mussaman ga mace me ciki yana da amfani da kuma ƙara mata lafiya, yana dawo da test ɗin baki da sukan rasa mussman a first trimester wato watannin ukun farko) Ammar yace" Anty Maryam ta wahal dani, nasan da dagani seke ne zamu sasanta da wuri, please idan mun samu Saɓani ki bari mu dinga gyarawa a tsakanin mu base wani yaji ba" "Yaya Ammar nima ba haka naso ba, naso ka saurareni a lokacin amma kaƙi, kuma bayan fitarka naji kamar zan mutu shine na tafi gidan Yaya Amina" "Hakane raina ne ya ɓaci sosai, nasan kina haƙuri da ni amma ki ƙara kinji Jaririya ta, ban san ina sonki haka ba seda na zauna a 'yan kwanakin nan babu ke, kin mun wayo kin shiga raina ba tare da na sani ba" Murmushi tayi masa tare da kwanciya a jikin sa tace "Yaya Ammar nima nasan kana haƙuri dani, duba ga yanayin ƙuruciya ta da kuma shirme na wani lokacin, Allah ya ƙara mana haƙuri da juna" "Ameen, Amma ya aka yi haka ta faru baki sanar dani ba, hankali na ya tashi sosai akan abunda ya faru" Nan ta zauna ta warware masa abunda ya faru tsaf tun daga ranar da aka fara kiran ta, Sannan ta ɗora da cewa "Abunda yasa ban gaya maka ba, nasan halinka Yaya Ammar kallo ɗaya kake wa abu kayi masa hukunci, baka fiye tsawaita bincike ba, kana Amfani ne da abunda zuciyar ka ta gaya maka ko abunda idonka ya gani" Ammar yace "shikenan abunda za'ayi zaki bani layin da kike Amfani da shi, zan canza miki wani Insha Allah, Sannan zan duba matakin da zan ɗauka, Sannan gobe insha Allah zan maida ke Asibiti gaskiya, rashin cin Abincin nan yana damuna" Haka suka shirya suka jone abunsu, dukda rashin lafiyar Mufeeda, be hana Ammar shan Shagalin sa ba, he show's her how much he miss her, Mufeeda kam taga ta kanta, yana ce mata ƙwaila Amma a hakan.... 🤭🤭, seda ya nutsu ya dawo hankalin sa, sannan kuma yaga yadda ya tara mata gajiya, ya taimaka mata ta gyara jikin ta ta kwanta sannan ya tafi ɗakin sa. ***************** Saima se tayi Sati ba ta riƙe naira ɗari biyu ba, Jabir baze kaita Asibiti ba dan haka befi sau biyu taje awon ciki ba, yauma da ta tashi maimakon yadda take ji ana faɗa daga alamomin Naƙuda akwai zubar ruwa se ita taga Jini, bata ɗauka matsala bane dan haka ta ci gaba da harkokinta sama sama, Sosai Marar ta ta fara ciwo, ga baya ya riƙe se jiri da take ji idon ta yana mata duhu, Jabir ya fito falo yana gyara links ɗin rigarsa, kunnen sa ɗauke da wayar salula yana magana "Haba my Fatiyya, kiyi haƙuri dan Allah, yanzu zaki ganni zanzo in kaiki da kaina, kina dani meye sekin jira driver ɗinku, ki jira gani nan yanzun nan zaki ganni" Saima tace "Jabir dan girman Allah ka kaini Asibiti, wallahi ina ga haihuwa zanyi, bayana kamar ya ɓalle" "to uwar ciwo, baki ma tabattar da naƙudar bace, ina EDD ɗinki se ƙarshen wata za kice wani naƙuda kike, ga ɗari biyu kije Asibitin in haihuwar ce se kimin waya" Shiru tayi tana binsa da ido ya ɗau mukullin motar sa ya fice, duhu ta ci gaba da gani a idon ta dan haka ta nemi guri ta kwanta akan kujera ****************** Mufeeda taƙi yadda Ammar ya maida ita Asibiti tace ita likita yace se cikin ta yayi wata huɗu sannan zata fara zuwa Awo haka ya haƙura ya ƙyale ta. Bayan fitar Ammar sega su Maman Amir sun shigo mata. Fuska ba yabo ba fallasa Mufeeda ta karɓe su, Maman Amir tace "Mufeeda ashe baki da lafiya kina gida? Hankalin mu ya tashi kwana biyu bama ganin ki, shine muka tambayi mijin ki yace mana kina gida babu lafiya" Mufeeda tace "Eh banji daɗi bane ba" Maman Sadiq tace "Allah sarki sannu, munso muje gidan naku duba ki ai, to kin san halin Mijin naki bashi da fuska shiyasa bamu tambaye shi ba" Mufeeda tace "Ai na warware ma Alhamdilillah" Maman Amir tace "Aikam dai mijin ki bashi da fuska, ai Sa'idu me kayan miya ne ya gaya mana a gaban sa kika wuce kika hau A daidaita sahu kaman ba kya hayyacin ki, kina ta kuka bayan fitar shi mijin naki, shine hankalin mu ya tashi muka ce bari mu biyo muga ko lafiya, shine ya gaya mana ai baki da lafiya kina gida " Mufeeda tace " Sa'idu me kayan miya kuma? " Maman Amir tace " Eh wallahi munje cefane yake ga yamana " Jinjina kai Mufeeda tayi ba tace komai ba, suka ƙaraci soki burutsun su, ciki hadda yi da Maman Nur wadda ta kasance a cikin su, Mufeeda ba tace musu komai ba, ganin Mufeeda bata da niyyar kulasu yasa su kayi mata sallama suka fita. Ta biyo su tana ƙoƙarin rufe gate ɗinta taga ɗan gidan Maman Nur ya zubara mata da ƙanzo a ƙofar gida, kanta tsaye babu fargabar komai a gaba su Maman Amir, dukda tasan zasu gayawa uwassa tace seya kwashe, idan ya kuma zuba mata ƙanzo a ƙofar gida seta zane shi, haka yaron ya durƙusa ya kwashe yana kumbura fuska yace "nifa ba barmu ce tace inzo in zubar anan" Mufeeda tace "ka koma ka gaya mata ƙofar gidana ba bola bace, ta dinga zubarwa a ƙofar nata gidan da yafi kama da bola akan nawa, idan na kuma ganin ka zuba min ƙanzo a ƙofar gida sena mareka" Mufeeda tana sane ta faɗi wannan maganganun dan tasan se sun gayawa Maman Nur, tana shirin rufe gate ɗinta sega wata mata, za tayi shekaru Ashirin da bakwai ta kalli Mufeeda tace "Baiwar Allah, kece Matar gidan nan dan Allah?" Mufeeda tace "Eh nice" Matar tace "Yawwa dama nice na tare a nan kusa da gidan ki, nazo mu gaisa bakya nan suna na Hajara" Mufeeda tayi murmushi tai mata maraba suka shiga cikin gidan, suka zauna a falo, suka ɗan taɓa hirar rayuwa da hirar gida, Matar tace "Amma sam banji daɗin zuwa na unguwar nan ba wallahi" Mufeeda tace "Saboda me?" Hajara tace "kwata2 matan layin nan kaman Awaki haka suke, naga basu da kintsi sam, tunda nazo suke ƙoƙarin shigemin nagane duk take taken su, idan basu yi wasa ba se nawa mace shegen duka da taɓarya" "Subhanallah haba Anty Hajara, ai baza akai ga haka ba, maganin abun kawai ki fita sabgar su" Mufeeda tayi ƙoƙari ta karkatar da hirar tasu, a yanayin maganar Hajara zaka san tayi gwagwarmaya rayuwa, bata da tsoro kuma a tsaye take, Mufeeda ta lallaɓa suka yi sallama. Gaba ɗaya batun wai Sa'idu me kayan miya ne yake yamaɗiɗin ya ganta ta bar gidan ta tana kuka shine ya tsaya mata a zuciya, ina ruwan sa da ita daze mata haka, zuciyar ta ji take kaman taje taci uban sa, amma seta ga hakan ba mutuncinta bane a matsayin ta na matar Aure, da tana budurwa ne ba uban daze hana tayi masa tijara, da se tayi watsi da kayan miyar nan da cinikin da yayi sedai a kwao ƙarar ta Baba ya biya. ***************** Tun daga tsakar gida Jabir yake Sallama amma Saima bata amsa ba, hakan yasa ya harzuƙa ya shiga falon da niyyar ya zazzaga mata rashin mutunci, amma me yana shiga ya tarar da Saima a ruf da ciki a ƙasa. "ke Saima baki da hankali, wannan wace irin kwanciya ce haka? Sekin kashe min ɗa" Shiru bata amsa masa ba, dubawa yayi se yaga Jini face face a ƙasan ƙafar ta da sauri ya ƙarasa ya ɗago ta, gaba ɗaya bakin ta ya karkace bakin ta duk bushashiyar kumfa tare da jini da ta daddatse harshen ta da alama jijjiga tayi babu alamar rai Sam a tare da ita. "Na shiga uku SAIMA!!!" **************** Mufeeda tayi deciding ko tayi wa Ammar maganar Sa'idu me kayan miya, fasawa tayi dan ta san halin Ammar ba haƙuri amma abun ya dame ta, ina ruwansa da ita? Ita ba shiga sabgarsa take ba amma har ya iya gayawa mutane ga a halin da ya ganta, dana sanin fita ta shiga yi a wannan yanayin daya ganta. Haka Ammar ya dawo ya same ta, ya takura ta da tambaya akan meke damun ta, amma taƙi gaya masa. Tana zaune a kusa da shi, yana cin Abinci ita kuma tana cin Aya danba ƙaramin daɗi Ayar take mata ba. Ƙwace ledar Ayar yayi yace "Mufeeda wai ba zaki Abinci ba se wannan tarkacen? Ni bana son wannan kayan shiritar da kike ci me zasu ƙara miki?" Ya janyo ta jikim sa ya dinga ɗura mata Abinci ta naci tana kuka dan sam bata jim daɗin Abincin, aikuwa yana gama bata Abincin ta amayar dashi gaba ɗaya, Ammar shiru yayi ya rasa abunyi shi be taɓa zaton haka mata ke shan wahalar ciki ba, haka ya zage ya wanke kayan da tayi aman a jiki ya bata wasu ta canza. Mufeeda ta kalle shi tace "Yaya Ammar ko in koma gida ne kaima ka ɗan huta, idan na samu sauƙi se in dawo kana wajan dayawa" "Na nuna miki na gaji ne? Lokacin dana Aure ki ai ba'a haka aka auramin ke ba, da lafiyar ki na Aure ki, ni yakamata in kula dake ba 'yan gidan Kuba, nifa Impact bana son kowa yasan da cikin nan, nafi so in kin haihu a gani" Da sauri ta kalle shi tace "Amma me yasa? "Au meyasa ma kike tambaya? Haba ai da kunya a ganki da cikin nan, and am responsible for it, se aganni wani iri" Kallon sa tayi da tana so ta gaya masa magana amma ta fasa, ya kalle ta yace "Ya dai?" "bakomai ta bashi amsa" Wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga yayi sallama, Aminu ne cikin tashin hankali yace "Ammar, Jabir ya kashe Saima" A firgice Ammar yace "Kamar ya ya kashe Saima?" Aminu yace "toni mema zance maka ne? Ya fita ya barta taita jijjiga a gida ba kowa se ita kaɗai, ya kirani yanzu muna Asibiti, da naje gidan ko motsi ba tayi, a Yanzu babu me tabbacin tana raye" Da ƙarfi Mufeeda tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un" Ammar yayi jifa da wayar yace "Mufeeda ki kwantar da hankalin ki bata mutu ba ai, likitoci na duba ta" AYI HAƘURI NAYI DOGON PAGE AMMA BANYI EDITING BA. MASHA ALLAH, INA ME FARINCIKIN MIƘA SAƘON BARKA DA SALLA GA ƊAUKA AL'UMMAR I NA DUNIYA, FATAN ALLAH YA MAIMAITA MANA. WANDA SUKA KIRANI DA WANDA SUKA TURAMIN SAƘON BARKA DA SALLA NA GANI INA GODIYA, ALLAH YA BAR ƘAUNA In an karanta a tayani share please Don't forget to Follow Vote and Comment Ayshercool 07063065680✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment ELEGANT ONLINE WRITER'S NOT EDITED Page 26 Ƙoƙarin ci gaba da kwantarwa da Mufeeda hankali Ammar ya cigaba dayi, Amma kuka take Sosai tana nanata "Innalillahi wa and raji'un" Ammar yace "Mufeeda, Saima fa ba mutuwa tayi ba, likitoci suna ƙoƙarin ceto ranta ne, ki dena kukan nan" "da kunne na fa naji ance Jabir ya kashe ta" "Ai bashi ya kashe ta ba, bata da lafiya ne kawai, ki bari gobe Insha Allah zanje Asibitin in ga abunda yake faruwa" Da ƙyar ya dinga rarrashin ta, ya samu ta sassauta kukan da take yi, bacci ne ya fara ɗaukan ta, ba zato ba tsammani suka ji ana buga ƙofar falo da ƙarfi ana masifa, se yanzu Ammar ya tuna ne rufe ƙofar gida ba, da sauri ya miƙe yaje yaga wani mara hankalin ne yake musu wannan bugun? Yana buɗewa yaga Maman Nur tana bala'i "Waye uban ta a garin nan da har za tace zata dakarmin ɗa? Ita ta haifa min shi ko tare muka haife shi, wallahi in yarinyar nan ba tayi wasa ba sena mata dukan tsiya a layin nan" Kallon da Ammar yayi mata ne yasa ta nutsu tana kame kame, cikin ɓacin rai Ammar yace "tinkiyar inace ke zaki shigo min gida ƙarfe goma na dare kina zaki daki mata ta? Me tayi miki?" "Am... Ammm... Dama yarona tace zata daka nazo inji ba'asin me yayi mata zata dakarmin ɗa" "shine za kizo kinamin hayaniya kamar tashin duniya bama ta daki ɗan naki ba zaki zo kina ɗagawa mutane murya kamar ba matar Aure ba, Wallahi na kuma ganin ki a gidana sena ɓata miki rai, fice ki barmin gida mahaukaciya kawai" Yanayin Yadda Ammar yake maganar ne ya tabattarwa da Maman Nur ya ƙulu matuƙa dan haka sum sum ta fice. Ɗakin Mufeeda ya koma, ya tarar da ita a zaune, bugun ƙofar da'akayi yasa ta tashi, ya ƙaraso ya zauna kusa da ita yace "wai dan Allah meye haɗin ki da matar nan ne?" Mufeeda tace "wallahi babu wani abu tsakanina da ita, kawai ta tsane ni ne, tun ranar da tace in bata Madara na hana ta, ta sakani gaba a layin nan wallahi badan darajar Aure na ba, wallahi da sena koya mata hankali, bana son biye mata ne kawai, sabon Aurena shine mutunci na, da zarar na biye mata mun raba abun faɗa mutunci na da naka ze zube a idon mutane " Mufeeda kenan dukda tarin ƙuruciyar ta akwai kaifin tunani. Ammar yace " Shikenan, ki cigaba da haƙuri ba ruwan ki da ita, duk abunda tayi miki na ba dai dai ba ki gayamin, idan ba tayi wasa ba sena kaita gurin 'yan sanda, mahaukaciyar banza kawai " " A' a Yaya Ammar base ka kaita gurin 'yan sanda ba, aishi maƙoci haƙuri ake dashi, Allah ya shirya ta kawai, ni yanzu hankali na yana kan Anty Saima" "Ki kwantar da hankalin ki, Insha Allah zata warware". ******************** Da Safe Ammar ya shirya yace zeje Asibiti yaga halin da Saima take ciki, Mufeeda tace seta bishi, yayi yayi ta zauna a gida tace ba zata iya zama ba binsa zata yi, "Kinga kiyi haƙuri bekamata in tafi dake ba yanzu, ki bari inje inga halin da take ciki se inzo muje ki duba ta kinji Jaririya ta" "Shikenan Allah yasa tana raye ya bata lafiya, muje in raka ka" Ammar ya wuce gaba tana binsa a baya, suna fitowa tsakar gida ta shaƙi ƙamshin ɗumamen miyar kuka, ta kalli Ammar tace "Yaya Ammar ba kaji ƙamshin miya ba?" "Naji mana, meyafaru?" "Kaman daga gidan Anty Hajara nake jin ƙamshin" Ammar yace "Maybe" Marairaice Fuska tayi tace "dan Allah Yaya Ammar in baka kwano kace ta sanmin ko loma biyu ne?" Wani irin kallo Ammar yayi mata yace "Idan tuwon kike so ki dafa mana, kawai se inje da kwano ince a baki tuwo se kace bana baki Abinci, naga ma dai ba shiri kike da maƙotan nan ba, kawai se inje in fara roƙon Abinci" "Dan Allah Yaya Ammar, ita wannan da zaka karɓo min a gurin ta ba irin su bace, niko loma ɗaya ta bani" Ammar ya fara ƙuluwa, haushi ya cika shi yaja babur ɗinsa yai waje ya barta a gurin, ɗaki Mufeeda ta koma tana kuka ji take kamar taci babu, ji take inba tuwon nan ba ba zata iya cin komai ba. ***************** Ammar yana tashi gidan Aminu ya fara zuwa suka tafi Asibitin tare, bayan sun gaisa Ammar yace "Aminu wai dan Allah meyafaru ne? Jiya hankali na ya tashi sosai da abunda ka faɗa, kuma Mufeeda taji gaba ɗaya ta birki cemin da koke koke" Aminu yace "Hmm Ammar ni nama rasa ta inda zan fara, wallahi duk Faɗan da muka yi wa Jabir sam baya ji, Jinin ta ne ya hau taita Jijjiga. jiya dai har na baro Asibitin likitocin basu ce komai ba, yanzu da Safen nan kuma na kira shi bata shiga" Ammar yace "Allah ya kyauta, bari muje muji" Koda suka je Asibiti suka tarar da Jabir a zaune a reception duk yayi wani iri, suka gaisa suka yi masa yame jiki?. Ammar yace "Jabir wai ya akayi haka ta faru meyasa meta ne?" Jabir yace "Wallahi da zan fita ne ta cemin kanta na ciwo, na ɗauka kawai rakine irin nata shiyasa ban kula ba na fita, kawai ina komawa gida na tara da duk jikin ta jini" Wata Nurse dake reception ɗin tana cike files ta ɗago ta kalle su tace "Eh ai da yake ba 'yarka bace dole kace haka mana, kudinga girmama larurar mace me ciki koda kuwa tana da raki, da yake cikin ba' a jikinka ba yake ba dole kace tana da raki ai, ai gashi nan ta kusa rasa ranta, ko Awo bata zuwa ga jinin ta yayi mummunan hawa, bata shan magunguna da'ake rubutawa masu ciki, dan Allah ku dinga girmama larurar mata masu juna biyu komai ƙanƙantar ta ko kuma buƙatun su" Aminu yace "Ayi haƙuri ranki ya daɗe yanzu wani hali take ciki?" Nurse ɗin tace "ku jira likitan safe yazo tukuna, Amma tana ICU kuma a rubutun da likitoci suka yi a file ɗin ta, Jinin ta ya hau batasan ma waye a akanta ba sakamakon jijjigar da tayi, an rubuta muku hoton ƙwaƙwalwa zakuje ku biya, masu kula da ɓangaren zasu zo suyi mata, sannan likitoci zasu ranar daza'ayi mata aiki, dan ba zata iya haihuwa da kanta ba" Aminu yace "Jabir kayi wauta wallahi, bekamata ace haka ta faru da Saima saboda kai ba" Ajiyar zuciya Jabir yayi ya kasa cewa komai, haka suka dinga sintiri zuwa wajen biyan kuɗaɗe da'aka nema, 'yan dubiya suka dinga zuwa amma babu damar ganin Saima saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman. ******************* Rashin samun tuwon nan ba ƙaramin ɓatawa Mufeeda rai yayi ba dan seda tayi kuka tukuna, kuma taƙi cin komai ita kanta wannan abubuwan suna damun ta sosai, ga tunanin ko wane hali Saima take ciki daya dame ta, waya ta ɗakko ta kira layin Ammar, kafin ta tsinke ya ɗaga yasa a kunnen sa "Yaya Ammar ya jikin Anty Saiman" Ammar yace "Jikin ta da sauƙi Alhamdilillah, dan yanzu haka ma bacci take" Ajiyar zuciya Mufeeda tayi tace "Masha Allah, Allah ya bata lafiya" "Ameen, nima yanzu nake sa ran in taho, me zan taho miki dashi" Zumɓura baki tayi kamar yana kallon ta tace "Ni bana san komai, dama dana samu tuwon nan ne da se inci, tunda ban samu ba na sha ruwa kawai" "Ke wato tunda na fito baki ci Abinci bako? Keba kya tausayin kanki" "Nima ban san me yasa nake haka ba, Amma ni wallahi tuwon nan nake so" "to ni karkiyi min kuka, ko tea ki haɗa Kisha, zan san yadda za'ayi kafin in dawo" Ammar ya dage yana rarrashi a waya, gaba ɗaya ya manta da Aminu a gurin, Aminu yace "Kaga mijin ƙwaila an dage ana rarrashi da alama an gamu kenan?" "Aka gamu dame?" "Ban sani ba, gaskiya wannan ƙwailar she deserves to be saluted, Kai Ammar ka wani kwantar da murya kana rarrashi, kai da kace raino zakayi ya akai ka haɗa ta da raino kuma?" Ɗan Murmushi Ammar yayi yace "ba zaka gane ba that girl is so funny and romantic, ban san yadda akai komai ya canza ba" Dariya Sosai Aminu yake yana tsonakanarsa. Suka ƙara yiwa Jabir jaje suka bar Asibitin. ****************** Maman Nur suna zaune suna tafe ita da Maman Amir suna hira suka je gurin Sa'idu me kayan miya, nan suka tsaya suna munafuncin nasu da suka saba, Munafuncin Maman Sadiq suke yi, wai mijin maman Sadiq ke son ƙanwar Maman Nur, ita maman Sadiw ɗin bata sani ba, ya saiwa ƙanwar Maman Nur wayar dubu tamanin ya bar maman Sadiq da wayar dubu uku me fasashshen screen, Nan Maman Nur ta dinga zuba tana faɗar irin hidimar da yake musu, Sa'idu se zigata yake, suna cikin hirar Hajara tazo yin cefane, ko kallon su ba tayi ba ta gama cefanen tayi gaba. Tana tafiya Sa'idu yace "Wai ita wannan 'yar waye girman kai kamar matar me A daidaita sahu, kuma kamar ita kaɗai take zaune a gidan" Maman Nur tace "Nifa banga alamar tana da miji ba, kamar zaman kanta take" Sa' idu yace "zaman kanta take to se ku killace yaran ku, dan kar ƙarti su fara muku sintiri a layi" Nan suka yi ta gulmace gulmacen su sannan suka tafi. ***************** Fa'iza ta shirya ta tafi gidan su Ammar, tayi sa'a kuwa Umman tana nan, Umma na ganin tace "Fa'iza yau kece a gari haka?" "wallahi kuwa Umma, ina Halima ne?" Umma tace "Halima ta tafi Makaranta" Fa'iza tace "Umma naje gidan Yaya Ammar fa" "Allah sarki ya kika baro su? Mufeeda har ta gaji da mitar banje ba, ina jin kunyar zuwa gidan Ammar, bana son ka dinga zarya a gidan yara, karka takura musu" Kwaɓe baki Fa'iza tayi tace "Nifa Umma ƙara na kawo miki" "to ƙarar wa kuma?" "Ranar da naje gidan Yaya Ammar wallahi a waje ya barni wai Mufeeda tana bacci bazan shiga a tashe ta ba, wallahi a waje yaimin korar kare" Shiru Umma tayi tace "Ammar ɗin ne yayi miki haka?" "Wallahi haka yayi min, ranar ma munje da daddare amma baki ga korar karen da yayi min ba, tunda Mufeeda ta nuna bata sona yake min wulaƙanci" Shiru Umma tayi sannan tace "Amma basu kyauta ba, kiyi haƙuri Insha Allah zan musu magana, Amma Mufeeda mutuniyar kirki ce" "Hmm kudai take wa kirki ni ban san me nayi mata ba, kuma goyon bayan ta yake, yafi sonta akan mu 'yan uwansa" Umma tace "Haka naji Jidda tana ƙorafi akai, Amma ni dai ba tayi min nagani ba, Amma Insha Allah zan masa magana, kiyi haƙuri" "bakomai Umma na dai gaya miki ne dan kisan me' ake ciki" Haka Fa'iza ta ci gaba da ɓata Mufeeda a gurin Umman Ammar, Sannan tai mata sallama ta tafi. Ammar yana ta sauri ya koma gida, se kuma yayi tunanin bari yaje gida ko ze samu Umma tayi tuwo ta bashi ya kaiwa Mufeeda. Sedai yana zuwa ya tarar kamar ran Umma a ɓace, Umma tace "Yawwa Ammar naji daɗin zuwan ka, dama ina son ganin ka" Ammar yace "to Umma Allah yasa lafiya" "Ammar ɗazun nan Fa'iza ta bar gidan nan, ta kawomin ƙararka akan abunda kayi mata, tazo gidan ka amma kaƙi bari ta shiga gidan ka, wannan wane irin haline? Bekamata ka dinga fifita Matar ka akan 'yan uwanka ba, bance karkaso Matar ka ba amma dai ka kula da' yan uwan ka" Ammar yaso yayi ƙoƙarin kare kansa, Amma wani abu daya koya a gurin Mufeeda shine, muddin lokacin da babba yake maka magana kayi ƙoƙarin yin magana da niyyar kare kanka, to hakan na iya tunzira mutum, dan haka Ammar yayi shiru Umma ta gama faɗan ta, sannan ya ɗago kai yace "to Umma Allah ya baki haƙuri, Insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba" Umma tace "Yawwa ina Mufeedan tana lafiya?" Ammar yace "lafiya ƙalau tana gaishe ki, bari in koma in Abba yazo kice ina gaishe shi" "to tsaya ina da gyaɗa me gishiri da aka kawomin bari in baka ka kai mata, sannan ka gaya mata akuyar ta ta haifi yara uku" Bece komai ba se shiru da yayi zuciyar sa na tafasa, yana tunanin wane hukunci zeyiwa Fa'iza ya huce Ɓacin ran da Ammar ya tarar ya hana shi gayawa Umma batun tuwo da rashin lafiyar Saima ba, ya karɓi gyaɗa harda tsintsiyar laushi ya tafi. Ransa a ɓace sosai ya fito daga gidan ze tafi, Halima ce ta dawo daga Islamiyya taga Ammar yana ƙoƙarin tafiya "Yaya Ammar Ashe kazo? Ina Anty Mufeeda?" "tana lafiya" Ammar ya bata amsa ya shige A daidaita sahunsa ya tafi. Halima tayi mamakin ganin Ammar ya fito daga gida ransa a haɗe haka, ta ƙarasa ta shiga gidan. "Umma wai me kikayiwa Uncle ne? Na ganshi da zan shigo kamar ransa a ɓace" "me kuwa zanyi masa? Na dai yi masa faɗa ne Fa'iza da Jidda suna yawan kawo ƙorafi akan yana fifita matarsa akan 'yan uwansa, kin san duk abunda Baki yayi yawa, ɗazuma Fa' iza tazo ta kawomin ƙarar sa shine na ɗan Ja masa kunne dai shine yake fushi" "Umma kenan kuma a ce duk yawan Family ɗin mu su biyu kawai yakewa haka? Sudai suna da wata manufa a ransu amma wallahi Yaya Ammar baya nuna banbanci, kuma ita Anty Jidda ina itama nata mijin se abunda take so yake yiwa 'yan uwan sa" Umma tace "to nidai ban zaɓi ɓangare ba kawai dai nayi masa magana ne" **************** Fa' iza seda ta gama gantalin gidan ƙawaye sannan ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da motar Faruk a ƙofar gidan su, tsaki tayi zata shiga gida Faruk ya fito da sauri yace "Ke kina ganina amma kika wani basar zaki wuce, lambar yarinyar nan fa ta dena shiga idan na na kira dole ki samo mana wata" A fusace Fa'iza tace "toni ina ruwana? Ba na gaya maka kowa yayi ta kansa ba, na gaji da shirirtar da kake babu wani kyakkyawan result, dan haka kowa yayi ta kansa" "Ke kin isa mu fara abu tare yanzu ki zame, ai ta inda aka hau ta nan ake sauka, Yadda muka fara tare haka zamu ci gaba" "Baza'a sauka ta inda aka hau ɗinba, dalla ja jiki ka bani guri in wuce, niko uban me ya kaini ma haɗa kai da kai tun farko oho" Faruk yace "Hmm wallahi baki isa ki zame ba, in ba haka ba in watsa komai" "inka fasa shege ne kai, ka tsaya ka jira in nayi nasara na fidda ita daga gidan kaje ta ƙare muku can, Amma a yanzu kowa yayi ta kansa" "Ni kike gayawa haka?" "An gayamaka waye kai? Banda banza wofi" Tas, Faruk ya ɗauke ta da mari, kallon sa tayi idonta fal Hawaye tace "Nika mara?" "Na mareki ɗin, kin isa ki cemin banza wofi in ƙyale ki" "Wallahi baka isa ba, zaka gane baka da wayo sena ɗaura maka sharrin da baka isa ka kwance ba, bunsuru me bin matan mutane kawai" "inkin Fasa min sharrin keba 'yar halak bace, munafuka koma meye dawa mu keyi inba tare ba" Hankalin mutane ne ya dawo kansu, mutane suka fara taruwa. Fuuu Fa'iza ta shige cikin gida tana kuka, tana zuwa ba tayi tunanin komai ba ta gayawa Mahaifiyar ta cewar wani ne ya mareta a waje. "Mari kuma? Waye ya marekin?" "wani Faruk ne abokin Yaya Ammar" Se kuma da ta faɗa tayi wani tunani. Mahaifiyar ta tace "lallai to ke me kika yi masa daze mareki akan me? To wallahi baze yuwu ba, bari Yayanki yazo gurin 'yan sanda zan kai ƙarar sa, ko kuma shi Ammar ɗin in nemeshi ya gayamin dalilin da yasa Abokin sa ya mareki" Fa'iza tace "A' a Umma ki ƙyaleshi kawai nasan matakin da zan ɗauka" Umma tace "Saboda me zan ƙyale shi, baze yuwu ba" ************** Ammar a zuciye ya koma gida, gaba ɗaya ransa a ɓace yake, Mufeeda tana ta jira Ammar ya dawo taji ya jikin Saima, Amma yanayin sa ya nuna mata ransa a ɓace yake. Ya dire mata gyaɗa da tsintsiyar laushi, murmushi tayi tace "da gani ba tambaya wannan saƙon Umma ne, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" Shiru yayi be amsa ba se ƙara haɗe rai da yake yi "Mijina ya na ganka a hakane? Kodai Jikin Anty Saiman ne?" "A'a jikin ta da sauƙi" "to kowani abun aka kuma cewa nayi?" Kallon ta yayi kamar ya gaya mata kawai ya fasa yace "A'a bakomai" Ƙyaleshi Mufeeda tayi ta zubo masa Abinci, ya kalle ta yace "A haka kika yi girkin?" "Naji zan iyane shiyasa na girka maka" Ammar yace "ke kuma me kikaci?" "bakomai amma ga Gyaɗa nan da Umma ta bani se inci, amma Allah yau da baka karɓo min tuwo ba seda nayi kuka" Hararta yayi yace "kawai se in ɗau kwano in tafi maƙota roƙon Abinci kamar Almajiri" "Allah ya baka haƙuri, ci Abincin ka" Haka ya maze ya ci Abincin sa, Amma ransa babu daɗi. Sallar isha'i ma a gida yayi, Mufeeda tana lura dashi, ya kwanta a falo yayi shiru abubuwa da yawa suna damun sa a rai. Mufeeda tazo ta zauna a kusa dashi, ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa tace "Abun so na, dukda nasan nayi yarinta daka gaya min abunda ke damunka amma ganin ka a wannan mood ɗin yana sani a damuwa" Shafa gashin kanta yayi yace "Waye yace miki ina cikin damuwa?" "Hmm ai kallo ɗaya nake maka in san a wani yanayi kake, farinciki baƙin ciki ko makamancin hakan duk ina iya ganewa" Ɗan murmushi yayi yace "kinmin wayo da yawa, ya akayi na bari duk kika gane ni haka?" "Yaya Ammar gobe in Allah ya kaimu zaka kaini inga jikin Anty Saiman?" "Ai ko kinje ba zaki ganta ba, likitoci ne kawai suke shiga inda take, amma insha Allah sunce gobe in Allah ya kaimu zuwa jibi idan jinin ta ya sauka za'a cire mata abunda ke cikin nata" "to Allah ya raba su lafiya, Amma fa harna tsorata da haihuwa" "Ai komai na Allah ne, kuma Insha Allah ina ta Addu'a ki rabu da cikin nan lafiya" Ƙasa ya kuma yi da muryar sa yace "kefa Jaruma ce, tsoro ba naki bane tunda 'yar Jaririya dake kike ɗauke da Jaririn Ammar a jikin ki" yai maganar ya shafa cikin nata da kaikace ko kayan ciki babu a ciki. "Kaga cikani inje in kwanta inajin Bacci ne" "zomuje ɗakina mu kwana a can, kinji ƙwailata" Zaro ido tayi kaman zata yi kuka tace "taɓ gaskiya ni A'a wallahi" "meyasa ba zaki ba?" "Nifa Yarinya ce dan Allah ka ƙyaleni wallahi hanani bacci ka keyi" Sosai ta bawa Ammar dariya, "you are ready for it, that's why you choose marriage" Zumɓura baki tayi tace "ba wani ni kawai dan ina sonka ne" ɗaga ta yayi yana dariya tafi da ita ɗakin nasa. *************** Da sassafe Ammar yana ta shirin fita Maman Fa'iza ta kira shi a waya, ya ɗauka itama mitar zata yi masa, dan haka ya amsa cike da basarwa bayan sun gaisa tace "Ammar a cikin abokan ka wani ya mari Fa'iza waishi Faruk, yanzu hakan na kai maganar gurin 'yan sanda, dan Allah in ba zaka damu ba ƙarfe goma kaje police station ɗin ayi maganar" Ammar yace "gaskiya Anty kiyi haƙuri, kinga ina da aiki da yawa, ita tasan meya haɗo su kuje can ku warware abun a station ɗin" Ya katse wayarsa ya fice. **************** Rana tayi sosai Mufeeda tana tsaka da wani bacci me daɗin gaske, dan kwanan nan Mufeeda tana fama da kasala da yawan bacci, tana cikin baccin taji ana hayaniya a waje kamar ana yaƙi a gigice ta miƙe ta saka hijjabi ta leƙa ƙofar gida, tana leƙawa taga su maman Nur ne suke ta Masifa suna faɗa a bakin layi, Maman Sadiq taje ta gayawa maman Amir cewar Mijin ta na soyayya da ƙanwar maman Nur, nan suka dinga tonewa juna Asiri, dambe ne ya kaure a tsakiyar layi aka yagawa Maman Nur riga ko vest babu a jikin ta aka danna kanta a kwata. Da sauri Mufeeda ta mayar da ƙofarta ta rufe, ta koma cikin gida dan ita abun kunya ne a gareta a zo wucewa ace anganta tana kallo ana dambe a layi, gaba ɗaya matan layin nan suka firfito suka dinga tonawa juna asiri kuma wani abun in aka gangaro daga gurin Sa'idu me kayan miya magana ta fito. Hajara ce ta fito itama jin Hayaniya tayi yawa, taje tana ƙoƙarin rabawa. Maman Amir ta juyo kanta zata daka, Hajara tace "Wallahi kika taɓani sena karya ki gida biyar na bawa karnuka, nafiki rashin mutunci" Maman Amir tace "Aikin banza keda a gurin sa'idu me kayan miya ake bada labarin baki da miji zaman kanki kikeyi, karuwa kawai" Hajara tace "Yawwa dama irin wannan ranar nake jira da zaku taɓoni, zan nuna muku wace Hajara yau 'yan unguwar nan babu me rintsawa wallahi, zaku ga tsiya Tofa!!! Share please Domin sharhi gyara ko shawara Ayshercool 07063065680.✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment ELEGANT ONLINE WRITER'S NOT EDITED Page 27 Sun ɗauka Hajara ƙarya take, Maman Amir tace "ke ɗin banza ki hanamu bacci, uwarmu ce ke? Ko kuma halittar mu kikayi?" Maman Nur kam gida ta shiga ta sako wasu kayan ta nufi gurin Sa'idu me kayan miya tana ruwan Ashar, Hajara tace "tunda kuka ce zaman kaina nake wallahi sena nuna muku zaman kaina nake, A bariki aka haifeni kuma a bariki na girma" Gurin Sa'idu me kayan miya Hajara ta fara tafiya, tana zuwa ta tarar da wasu matan daya haɗawa munafunci suna ta zagin sa, ko a jikinsa yana siyarwa da wasu kayan miya ya maida su kamar wasu banzaye. Hajara na zuwa tafara fatali da kayan miyar nasa, ya kalleta a fusace yace "ke mahaukaciyar ina ce meye haka?" "Mahaukaciyar gidan ubanka ce, kai ni zakayiwa munafunci, kace ina zaman kaina, baka da aiki se tara matan mutane suma jakuna su biye maka, kaita haɗa gulma kuna zagin mutane daga yau in ance ka sake ba zaka kuma ba" Ta cigaba da fatali da kayan Sa'idau, nan aka saka wawa, har ɗan cinikin nasa na ranar, wannan matar tace yace kaza waccan ma haka guri ya hargitse da hayaniya. Mufeeda kam Amai ne hana ta sakat, gashi cikin ta ba komai ga amai se taso mata yake, jin layin nasu yayi tsit ne yasa ta ɗauka sun watse dan haka tasa hijjabin ta, tafi ta ko guava ta samu ta siya. Aikuwa tana fitowa bakin layi inda Sa'idu me kayan miya ke siyar da kayan miya ta tarar da mata sunyi dandazo a gurin, ga wasu kayan miyan na iyo a kwata, wasu an tattake. mata sun sashi a tsakiya suna zagin sa tare da tsine masa har zata wuce Maman Nur tace "Yawwa Mufeeda gara da Allah ya kawo ki, ga munafukin da yaje yana yamaɗiɗi a unguwa wai ya ganki kina zance da wani, har mijin ki aka tara aka gayawa, lokacin da kika tafi gida ba lafiya yace auren ki ne ya mutu" Mufeeda tace "to ni ina ruwana? Me kike so ince ko zan manta yadda ni kika sani a gaba da sharri da cin mutunci a layin nan, a fakaice har maita kika ɗoramin yanzu da ta kwaɓe muku zaki dinga gayamin, kuje Allah ne ya kama ku" Mufeeda tai wucewarta ta tafi gurin me guava, tana tsaye tana cinikin guava, sega Alhaji Idris yayi parking a motar sa, Sam Mufeeda bata ganshi ba seda me guava yace mata "Hajiya ana magana" tana juyawa Alhaji Idris yace "me guava zubawa babyn nan ko ta nawa take so in biya" Banza tayi masa tace "me guava ban ta iya kuɗina" Me guava Ya zuba mata kamar yadda tace ya bata ta nufi hanyar gida, aikuwa Alhaji Idris ya biyo ta, ta ratse tabi ta lunguna dan ta guje masa, Amma yayi parking ɗin motar sa ya bita. Sosai Mufeeda tasa gudu yana binta yana ta tsaya taji, da ƙyar ta kai gida tana zuwa ta buɗe ta shige ta rufe ƙofar ta, a tsakar gida ta zube tana ta haki, ya daɗe a gurin yana buga gate ɗinta wai ta fito suyi magana ko nawa take so ze bata, hawaye ne ya fara bin idon ta, wannan wace irin masifa ce daga yin Auren ta zuwa yanzu ta haɗu da ƙalubale daban daban wanda bata san iyakar sa bama, wani irin zamanine wannan ace dattijo kamar Alhaji Idris yana bin yarinyar da yayi jika da ita kuma yasan matar Aure ce. Tana cikin wannan tunanin taji ƙarar harbin bindiga, ai da gudu ta shige ɗaki ta ƙule a gado jikin ta na cigaba da tsuma. Hajara ce tayi waya ta kira sojoji, Ashe baban ta babban General ne na Sojoji, mijin ta ma babban soja ne tunda aka haife ta a barrack take, aka turo mijin ta aiki kano tace ta gaji da zaman barrack tana so yakama mata gida ta zauna a wajen barrack, suna shirye2 dawowa kanon aka tura shi yaƙi Maiduguri, dan haka se yasa abokin sa ya kama mata gidan ta dawo ta zauna, dan haka tai waya aka zo hadda Sojoji mata aka tattare mata su Sa'idu da su Maman Nur da suka yi wa juna jina jina saboda duka, dan har jaririn da Maman Nur take goyo aka fasawa kai saboda dambe. ********************* Maman Fa'iza taji hasuhin abunda Ammar yayi matuƙa da yace babu ruwan sa akan lamarin, ita kanta Fa'iza taji daɗi da yace ba ruwan sa dan tana tsoron Asirin su ya tonu. Faruk yana gurin aikin sa 'yan sanda sukazo suka tafi da shi, Yayan Fa' iza Abubakar shi ya kai ƙarar sa gurin 'yan sanda akan marin da yayi wa Fa' iza. Maman Fa'iza ta kira Maman Ammar a waya ta gaya mata abunda ya faru da yadda suka yi da Ammar, Umma ta bata haƙuri tace za tayi masa magana Umma ta kama mita tana "Nikam na rasa wannan hali irin na Ammar, meye a ciki dan yaje ya taimakawa 'yar uwarsa, kawai yaje station aji ba' asin meyasa ya mareta ayi musu tsakani tunda Abokin sane shine baze iya ba, kai Allah ya shirya Ammar. Abba yace " Banga laifin sa ba, tunda bashi yayi marin ba kuma ba shi yace ayi ba, da alaƙar kirki ce tsakanin ta da Shi Farukun da baze mareta ba, babu yarinyar da zata kama kanta wani ya mare ta a banza" Umma tace "dukda haka dai, tunda har Maifiyar Fa'iza ce ta nemi yaje ai se yaje, inda mutunci ai itama uwarsa ce" Abba yace "hakane" Umma ta kira Ammar a waya, yana tsaka da tuƙi sega kiran umma, Yayi parking ya ɗaga wayar, bayan ya gaishe ta umma tace "Ammar kai duk maganar da za'a gaya maka sedai ta shiga ta dama ta fita ta hagu ko? Yanzu abunda kayiwa Maman Fa'iza ya dace? Meye laifi dan kaje police station anji ba'asin da yasa ze mareta? Aiba raguwa zakayi ba" "Umma kenan, Allah ya baki haƙuri, amma ni dai nasan Faruk abokina ne, Amma bansan wace irin Alƙace a tsakanin su da har yasa ya mareta ba" Umma tace "koma dai wace iri ce, kaje kaji kodan Mahaifiyar ta" "shikenan zani Insha Allah" "Ai ba zaka ba kaje yanzu suna police station ɗin unguwar su Fa'iza na nan babban titi" "to Umma" Ya katse wayar, ita dai Umma indai akan lamarin 'yan uwane setaita cusashi, abunda ya shafe shi da wanda be shafe shi ba. Ya ajiye wayar kenan ya nufi unguwar su Fa' iza aka kira shi da baƙuwar lamba, ya kuma tsayawa ya ɗaga, ko gaisawa basu yi ba balle yasan wake magana yaji ance "Kai maza ka koma gidan ka, Sojoji sunzo unguwa suna ta kwashe matan mutane suna tafiya da su" aka katse wayar Ai a gigice Ammar yabi lambar amma shiru, ya kira Umma yace "Umma dan Allah kiyi haƙuri ba zan samu zuwa station ɗin nan ba, yanzu aka kirani wai sojoji sunje suna kwashe matan mutane a unguwa" Umma tace "Subhanallah,ƙ Allah yasa lafiya shikenan Allah ya kiyaye kai maza ka koma, zanyiwa maman Fa'izan bayani" Ammar ya kashe wayar ya tafi, aikuwa yana zuwa ya tarar unguwar tasu tun daga titi kamar anyi ɗan ƙaramin yaƙi kowa ya kulle a gida ss hayaƙi unguwar take. Har yaje ƙofar gidansa bega kowa ba, yasa key ya buɗe gidan ya shiga da sauri ya shiga yana ƙwalawa Mufeeda kira, ya nufi ɗakin ta da sauri yana zuwa ya tarar da ita ta ƙule akan gado tana kuka, a gigice ya ƙarasa kan gadon nata ya ɗagota yace "Mufeeda lafiya meyafaru? An kirani a waya wai Sojoji na kwashe matan mutane a unguwar nan meyafaru?" Mufeeda ta gaya masa duk abunda ya faru gaba ɗaya a unghwar na dambe da tons tonen Asiri da suka yi hadda zubarwa da juna jini, shiru Ammar yayi yace "Alhamdilillah da Allah yasa baki zama daga irin su ba Mufeeda, da yau bansan wani baƙin ciki zanyi ba ace anyi dambe da mata ta a layi, dambe na tashanci hadda keta sutura kuma ace sojoji sun tafi dasu Allah kaɗai yasan meze faru, Allah yayi miki Albarka" Mufeeda ta goge Hawayen ta tace "Yaya Ammar wai ashe me kayan miya ne yaita cewa ya ganni ina zance da wani, har akazo aka tare ka aka gaya maka?" Ammar yace "bansan waye ya fara zancen ba, amma maƙocinmu ne ya tareni bayan sallar asuba ya gayamin" "shikenan ai koba komai Allah ya sakamin yanzu" "hakane kam, kiyi haƙuri ki dena kuka kinji, ni mema yasamin ke kuka haka?" Nan ta kwashe abunda ya faru tsakanin ta da Alhaji Idris ta gaya masa data fita ɗazu, nan da nan Annurin fuskar Ammar ya ɗauke, wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa, gaba ɗaya gashin jikin sa ya miƙe. " meyasa baki gayamin tun tuni ba? " "saboda ina gudun ɓacin ranka" "Wannan ba hujja bace" ya faɗa a ɗan hasale. "Allah ya baka haƙuri, Yaya Ammar nasan halinka fiye da yadda kai kasani, na ɗauka ze dena bina amma yau kam da gudu ma ya biyo ni har ƙofar gidan nan" A hankali ya raba Mufeeda da jikin sa ya miƙe, cikin zafin nama ta riƙe shi tace "Yaya Ammar kabi komai a sannu, mutumin nan yana da kuɗi sosai kar yasa ayi maka wani abun" Ammar ya ƙwace hannun sa ya fita da sauri, yana fita ya tarar Mazajen wanda aka kwashe sun daddawo suna salallami, babu wanda yasan inda aka tafi da matan nasu, gashi Hajara bayan an tafi dasu ta rufe gidan ta ta ƙara gaba. ********************** Faruk yana police station a bayan kanta yana rarraba ido, tun safe Su Fa'iza basu je ba se bayan la'asar da suna jiran Ammar kuma beje ba. Lokacin da suka je suka yi sa'a D. P. O yana nan, aka buɗe file ɗin da aka rubuta ƙorafin da su Fa'iza suka shigar, aka kalli Faruk akace "Kai me wannan baiwar Allah tayi maka ka mareta?" Faruk yace "Yallaɓai saɓani ne muka samu, amma dan Allah ayi haƙuri hakan ba zata sake faruwa ba" Abubakar yace "Yallaɓai ba wani ayi haƙuri ya faɗi wani irin saɓani ne yasa har ze mari ƙanwa ta?" D. P. O yace "waima tsaya meye a tsakanin ka da ita?" Faruk yace "ƙanwar Abokina ce" "ina Abokin naka?" Nan Maman Fa'iza ta faɗi dalilin rashin zuwan Ammar, D. P. O yace "yanzu dai sulhu ya kamata ayi, tunda shi sulhu duk inda yake Alkhairi ne" Zumɓura baki Fa'iza tayi tace "bawani sulhu kawai a fitar min da haƙƙina dan baze mari banza ba" " D. P. O yace " ke nutsu, idan kika yi min rashin kunya zan saka a saki bayan kanta kema, waima meye dalilin Yin marin ne, dan ba yadda za'ayi da mutuncin ki, abokin Yayanki ya mareki" Faruk yace "Yallaɓai zagina tayi" "to zagi yana fitowa a jiki ne? Banda shashanci da nusaranci meya kaika dukan mace banda ragwanci" Nan maman Fa'iza suka zage akan lallai se an fitarwa da Fa'iza haƙƙin ta basu yadda da sulhu ba, ganin da Faruk yayi ze kwana a ciki dan sunyi masa taron dangi, ya kwashe abunda ya faru tsaf tsakanin sa da Fa'iza ya gaya musu. D. P. O yace "to Hajiya kinji, kina ta zaƙewa a Bima ta haƙƙin ta da kin haƙura anyi sulhu da haka bata faru ba, kinga yanzu dole mu haɗa da ita saboda abunda suka yi babban laifi ne kuma dole a hukunta su tare" Maman Fa'iza tace "Fa'iza abunda kikayi kin kyautatawa kanki kenan, duk yadda na rarrashe ki akan ki haƙura da batun Ammar baki haƙura ba shine zaki kashe masa Aure, Yarinyar da babu ruwan ta baiwar Allah tsakanin ta mutane girmamawa, shikenan kije dan kanki, duk hukuncin daya dace ai mata ayi mata officer " Abubakar yace " A'a Mama be kamata a barta a nan ba tunda mace ce, abamu belin ta amma dole Ammar yazo gurin nan ku gaya masa abunda kukayi, wallahi kaji kunya Faruk kaci Amanar Ammar " **************** Ammar daya fita, gidan Alhaji Idris ya wuce yasa aka yi masa sallama dashi, Koda Alhaji Idris ya fito yaga Ammar ya wani yatsine fuska, Ammar be kula da yadda Alhaji Idris ke masa kallon ƙyama ba yace " Dama nazo ne muyi magana ta fahimta da kai, na samu labarin kana bibiyar mata ta wai kana sonta, kuma ta gaya maka matar Aure ce ita, da farko naso in kaika hukuma kai tsaye amma naga gara inzo muyi magana nida kai, a matsayin ka na dattijo be kamata inyi maka haka ba, shiyasa nazo da kaina gurin ka dan Allah ka fita harkar mata ta, nine mijin ta tana da Aure dan Allah ka fita harkar ta" Wata irin dariyar ƙet irin na riƙaƙƙun 'yan duniya Alhaji Idris yayi, sannan yace "hmm yaro man kaza, ai ita duniya faɗi ne da ita meye a ciki dan naga matar da bata dace da kai ba nace ina so? Ai ba wani abu dan tafi da cewa dani dan..... " Rufemin baki tsohon banza dana wofi, nazo maka da niyyar muyi magana ta kirki amma kaƙi i will show you what am capable of doing, Wallahi badan da hukuma ba da da kaina zan illa taka, an gaya maka mata ta irin sakarkarun matan banzan da karnuka irin ka suke bine? Wallahi inba Allah daya bani ita ba babu me iya rabani da ita, kuma bari kaga hukuma ce zata rabani da kai" Alhaji Idris yace " Nikuma zan nuna maka tasiri, da kuma ƙarfin da dukiya take dashi, zanyi Amfani da hukumar da dukiya ta in wulaƙanta ka, kana kallo matar da kake taƙama da ita talauci seya sa ta tsere ta barka, ba dai ni kazo ƙofar gidana kana ɗagawa murya ba, zaka gani sena jefa ka cikin talaucin da babu me ciro ka" "ƙarya kake munafuki, Allah baya barin zalunci kuma idan taƙamar ka dukiya wanda yayi ka ya baka dukiyar shize maganin ka" Ammar ya juya ya bar gurin cikin zafin nama da tafasar zuciya. Wasa2 har ƙarfe takwas na dare, babu labarin Inda aka kai su Maman Nur, mazajen su na ta yawo gidajen radio suna sanar da sojoji sun kwashe musu mata basu san inda aka kaisu ba, wadda tasa aka kwashe su an nemeta an rasa shikenan anyi kidnapping ɗin matan su. Se wajen sha ɗaya na dare aka bada sanarwar cewa, ba wanda ya sace su Sojoji da suka zo suka tafi dasu State CID, sashen kula da manyan laifuka, ana zarginsu da tada tarzoma a unguwa da yunƙurin yin kisan kai ta hanyar dambe da illata junan su da suka yi harda karya ƙafar Jariri da dasa masa kai. Haka mazajen su da 'yan uwan su suka ɗunguma suka tafi State CID amma aka hana su shiga akace su koma dare yayi. Inda aka kaisu Maman Sadiq kamar kabari, ga matsi ga sauro na Jaraba a gurin nan ko juyi ba zaka iya yi a ciki ba, ga gurin se tsami yake yana wari, ko Abinci babu wadda taci haka suka dinga kuka a gurin nan, Sa'idu kuwa Hajara tace a kai shi barrack a koya masa discipline idan ya kwana bakwai a miƙawa 'yan sanda shi suyi binkice a kai shi kotu a tuhume shi akan haɗa fitina da bibiyar matan mutane. Aikuwa Sa' idu yaga masifa, dan ba ƙaramin tumurmusa yasha a hannun sojoji ba, gashi gaba ɗaya cinikin sa an kwashe a gurin dambe, an watsar masa da kayan miya, ɗan babur ɗinsa na can, ga duka daya sha gashi an sashi tsallen kwaɗo ko iya tashi ba yayi. Ammar Yana zuwa gida ɗakin sa ya wuce ba tare da ya kula Mufeeda ba, tana ganin haka tasan a zuciye yake, seda ta bari kamar awa ɗaya da dawowarsa sannan ta tafi ɗakin nasa bakin ta ɗauke da Addu'oi. Ya ƙule akan gado zuciyar sa tana ta tafasa, wai shi wannan tsohon banzan ze kalli tsabar idonsa yace wai yana son matar sa, matarsa ta Aure (ba dai kace ƙwaila bace? Ai wani ƙwailar yake so 🤭🤭🤭) Kan gadon sa ta hau cikin murya me sanyi tace "Mijina koba ka faɗamin ba nasan a cikin damuwa kake, shiyasa tun a baya na kasa gaya maka abunda ke faruwa, idan ina ganin damuwa a fuskar ka ji nake tamkar zuciya ta tayi bindiga" Ta matsa kusa da shi ta rungume shi ta fara shafa sumar kansa, kaman me raɗa tace "dan Allah ka kwantar da hankalin ka, karka sani cikin damuwa dan ina kana fushi gani nake kamar a duniya nika ɗai aka tsana, kayi haƙuri Mijina Allah yana tare damu, kayi haƙuri, Allah yana son bawan sa me haƙuri kuma baya barin zalunci nasan baze wuce gurin wannan mutumin kaje ya ɓata maka rai ba, sam mutumin nan babu Allah a ransa" Ƙara rungume Mufeeda yayi a jikin sa kamar wani ze ƙwace masa ita, ya dinga shaƙar ƙamshin turaren ta kamar me koyar magana yace "Mufeeda kina sona?" "Surely, with all my heart, karka manta Soyayya ce tasa na Aure ka a lokacin da bana zaton kai kana sona" "Mufeeda" ya kuma kiran sunan ta "Na'am abun sona" ta amsa masaz "zaki iya rabuwa dani?" "Babu wani dalili bayan mutuwa da ze rabani da kai, in ba da ƙwaƙwarar dokar Addini ba" Ya ƙara rungume ta yace "Mufeeda ban taɓa Soyayya ba se akanki, ban taɓa sanin haka Soyayya take ba, Mufeeda" "Na'am My Ammar" "Ban san meye kishi ba seda na zauna dake, ke kika koyamin Soyayya, seda na fuskanci meye Soyayya sannan na gane na fara sonki ne ranar da na fara ganin ki, na ɗakko ku a babur ɗina, Salon ki na daban ne, na riga na saba da komai naki, bana tunanin akwai wanda ze iya jurewa zama dani kamar ki, na saba da ƙuruciyar ki, Nishaɗinki, haƙurin ki, ladabin ki, da kuma kawaici bana tunanin akwai macen data haɗa dukkanin abunda kika haɗa, ko akwai ta nike kawai nasani, Mufeeda komai naki yana burgeni, komai kikayi looks beautiful to me" Shiru Yayi yana sauke ajiyar zuciya, yayin da hannayen Mufeeda ke cigaba da shafa sumar kansa tare da mamakin jin wannan kalamai da suke fitowa daga bakin Ammar, ko wane lokaci tayi abu dan ta birge shi baya kulawa, Ashe yana jin daɗin abubuwan da take masa tankawa ne baze ba se yau data ciyo shi. Tana cikin tunanin ne ya sake kiran sunan ta, bata gaji ba ta sake amsa masa Ammar ya ɗora da cewa "Rayuwar Ammar ba zata cika ba idan babu ke, Mufeeda ban san haka kishi yake ba, wanda na nuna a baya ashe shirme ne, seda wani ya tsaya a gaba na yana gayamin wai yana son abunda yake mallaki na, sannan na gane menene kishi, wallahi zuciya ta kamar tayi bindiga, badan ina tsoron abunda ze biyo baya ba da sena illa tashi sedai kome ze faru ya faru" Tana jin yadda jijiyoyin kansa suka miƙe, jikin sa ya ɗau zafi ga bugun zuciyar sa dake fita da sauri saboda ɓacin rai. "Mufeeda takace kai kaɗai mijina, bana ganin kowa idan ba kai ba, Yaya Ammar Allah daya haɗani da kai shine kaɗai na yadda ze rabamu, ina maka so irin wanda baki be isa ya bayyana ba, ka kwantar da hankalin ka dan Allah, ni kai nake so ba wani mahaluki daze iya raba mu" Ta ƙara kwantar da murya cikin sigar shagwaɓa da rarrashi tace "dan Allah ka kwantar da hankalin ka, karka illa ta min kanka, kaji fa Babyn ka ma yana cewa sorry Daddy we loves you " Duk da a cikin ɓacin rai Ammar yake seda yayi murmushin abunda ta faɗa yana shafa cikin nata. Mufeeda tayi iya yinta gurin samarwa da Ammar farinciki tare da gusar masa da dukkanin damuwar da yake ciki, suka nunawa juna tsantsar soyayya da ƙaunar juna. ***************** Da safe Ammar ya tashi da farinciki yadda Mufeeda keta ƙara bashi kulawa duk dan ya saki ransa, gefe ɗaya idan ya tuna Alhaji Idris se yaji kamar yaje ya ɗau doka a hannun sa, Amma dole in ya fita yanzu yaje Hisba ko gurin 'yan sanda ayi masa tsakani da shi da iyalinsa. Mufeeda kam idan ta tuna irin kalaman da Ammar yak mata jiya seta jita tamkar a wata sabuwar duniyar masoya, bata taɓa tunanin jinsu daga bakin Ammar ba, bata taɓa zaton yana jin daɗin abubuwan da take masa ba se jiya. Yanzu ma da kanta take bashi Abinci tana masa hira, ya saki jiki yaci sedai ita Mufeeda ba wani ci tayi ba. Ya janyo ta jikin sa yana shafata yace "ƙwailata dan Allah kj dinga cin Abinci karki haifo min yaro a rame" Ta tura baki tace "Nifa ban gane ba ana cemin ƙwaila kuma a dinga mazewa a zomin ɗaki in dare yayi ba" Dariya Ammar yayi yace "tunda kika ce ke Aure kike so ai so kike ki zama babba, gayamin me kike so in siyo miki" Da sauri tace "ɗanyen mangwaro" Ɗan tsuke Fuska yayi yace "meye wani ɗanyen mangwaro ina maganar arziki kina wani ɗanyen mangwaro" "Aini maganar Arziki a gurina yanzu ka baani ɗanyen mangwaro" "kin taɓa ganin mangwaro lokacin sanyi ne? Kinga ɗagani na sai miki wasu kaya idan na dawo zan taho miki dasu, ga kayan Abincin mu sun ƙare ban siyo ba kuma ya kamata in fara tanadi saboda haihuwa" Za tayi magana aka kira Ammar a waya, ya ɗaga, Umma ce ke kiran Suka gaisa Umma tace "Ammar fatan dai komai lafiya ko, ina mufeeda?" "Umma tana lafiya muna tare ma" "Yawwa masha Allah, ɗazu munyi waya da Maman Fa'iza tace lallai kaje police station, Ana neman ka" "Umma me nayi ake nemana? Me nayi nifa bani nasaka Faruk ya mare ta ba" "Nima bata gayamin ba Amma dai kaje" Ajiyar zuciya Ammar yayi yace "Shikenan zani Insha Allah" Ha ajiye wayar tare da dafe kansa, Mufeeda tace "Ya dai?" "Abubuwa sunmin yawa Mufeeda, ni ban sanma wanne zanyi ba, wai lallai inje police station akan zancen Fa'iza" "Kayi haƙuri kaje kaji menene? Kaga 'yar uwakka ce kuma yakamata a nunawa Faruk kuskuren sa" "Ni masan meye a tsakanin su da ya mare ta?" "yi haƙuri, ka daure kaje" ****************** Ƙarfe Goma aka shirya Saima za' a shiga da ita tiyata, za'a cire abunda yake cikin ta, an shiryota cikin blue ɗin kaya na theater, Nurses na turo gadon da take, idon ta a buɗe Jabir ya taho da gudu shida ƙanwar maman Saima, dan tunda aka kaita Asibiti be ganta ba se yanzu, ko magana ba tayi Amma da Jabir ya tafi kanta kan a shigar da ita ta kalle shi A hankali tace "Jabir nasan idan shiga dani aikin nan ko in mutu ne ko inyi rai, dan ban zaci ma zan ƙara buɗe ido a duniya ba, abun da nake so in gaya maka shine nagode da irin riƙon da kayi min, Allah ya baka matar da zata maka abunda kayi min, idan na mutu a gurin theater nan, ina fatan Allah ya karɓi shahada ta, sannan ya fitarmin da haƙƙina akanka, idan kuma na rayu ka tabbatar kafin in farka ka ajiye min takaddar sakina, Azzalumi kawai" Share please Domin sharhi, gyara ko kuma shawara Ayshercool 07063065680.✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment ELEGANT ONLINE WRITER'S NOT EDITED Page 28 Shiru Jabir yayi yana bin Saima da kallo Nurses suka tura ta zuwa ɗakin theater. Reception ya koma ya dafe kansa yana tunani, gaskiya Saima ta so shi kamar babu sauran ɗa namiji da ya rage sai shi kuma shima ya so ta, idan yasake ta a yanzu duniya zata zage shi ace beyi mata Adalci ba, Amma harga Allah yana son Fatiyya, saboda yana kwaɗayin abunda ze samu idan ya Aure ta. Ammar ba dan ransa yaso ba ya nufi station ɗin da su Fa'iza suke, yana zuwa ya tarar da Abubakar da maman Fa'iza, Faruk se sunkuyar da kai yake, Ammar ya gaisa da su ya fuskanci DPO yace "Yallaɓai Me yasa aka takura lallai sena zo, Allah yasa ba laifi nayi ba?" DPO yace "ba laifi kayi ba sedai ma ince kai akayiwa laifi" Ya waiga ya kalli Faruk yace "Kai munafuki ɗago kayi masa bayanin abunda kukayi" Cikin jin kunya Faruk yace "Amm... Inmm... Da farko dai ina me baka haƙuri Ammar, dan... "Ka gaya masa me kuka yi nace idiot" DPO Yai maganar a Hasale, Faruk ya gyara zama yace "Ammar tun lokacin da muka je ɗaurin Aure naga Mufeeda naji ina son ta, yanayin yadda take nuna maka Soyayya yayi bala'in burgeni, se naji kana cewa kai ba sonta kake ba dandai ba yadda za ka yi ne Allah yayi hukuncinsa, tun daga lokacin nake tunanin tunda baka sonta me zanyi wanda zaku rabu ni in Aure ta, kawai se ranar na haɗu da Fa'iza take gayamin ai itama tana sonka mu haɗu mu haɗa kai ka saki Mufeeda, ni in Aure ta kaima ka Aure ta, ta dinga zuwa gidan yayar ka tana zigata, suje gidan ka suyi tayi wa matarka wulaƙanci, ta samomin lambar matarka nake kiran ta, ita kuma take hiding ɗin lamba tana turomaka saƙo akan ka sa ido akan matar ka, wallahi Ammar sharrin sheɗan ne kum........ "Enough!!!" Ammar ya faɗa a Hasale ya ɗau mukullin babur ɗinsa ya bar station ɗin, ransa cike da baƙin ciki. Duk zurfin cikin Ammar ji yayi baze iya jurewa ba, dan haja Kai tsaye gidan su ya nufa yana zuwa ya tarar da Jidda a gida ta saka Umma a gaba tana ta kuka kamar ƙaramar yarinya, fuskar Umman ɗauke sa damuwa, da gani Matsala Jidda ta kawowa Umma, dan haka yaga be dace ace shima ya faɗa mata matsala ba, dan haka ya gaida Umma yai tafiyar sa. Zuciyar sa ce ta ci gaba da tafasa, ya rasa inda zesa ransa, baze ji daɗi ba idan har be amayar da abunda yake ransa ba, dan haka ya tafi gidan Anty Maryam. Yai sa'a tana nan tana ta ɗinki, kallo ɗaya tayi masa taga damuwa ƙarara a fuskar sa, "Allah yasa dai lafiya, na ganka kamar an koroka, Allah yasa ba wata matsalar ka kuma kunnowa ba tsakanin ka da Mufeeda" Girgiza mata kai yayi yace "Lafiya muke sedai mutane daga waje dake ta kunna mana matsala, yanzu daga gida nake, naje in gayawa Umma abunda ke faruwa na tarar da Anty Jidda a gida tana kuka, naga bekamata in ƙara mata damuwa ba kawai na taho nan" Anty Maryam tace "Mhmm ai Anty Jidda reshe ne ya juye da mujiya, mijin ta ne ze ƙara Aure tabi ta ɗaga hankalin ta" Ammar yace "shine taje ta saka Umma a gaba tana kuka kamar wata ƙaramar yarinya, seta ɗaga mata hankali" "to nima dai haka nagani, itama me gayawa wasu ce, su Khalil ɗinta ds mata ne aida tuni ta aurar dasu, amma take wannan, mata nawa akayiwa suka jure, shekara Ashirin da uku dayi mata Aure amma be ƙara Auren ba se yanzu, amma tabi ta ɗaga hankalin ta da nasa" Ammar yace "Yaya Maryam wallahi duk wanda ya hana ɗan wani zaman lafiya a gidan Auren sa shima baze zauna lafiya ba, Anty Jidda yaya tace, Amma maganar gaskiya ta cutar da mata ta" nan ya warwarewa Maryam duk abunda yake faruwa, daga bisani yace "wallahi Maryam ina matuƙar jin nauyin Mufeeda, ta dinga ɗaukar laifukan da bana ta ba, naita mata faɗa sedai tayi kuka ta bani haƙuri, bata taɓa gayamin abunda suke mata ba, naji kunya Maryam" Yaya Maryam Tace "Abunda nake gaya maka kenan, saurin zuciyar nan taka da izza ba zasu haifar maka da ɗa me ido ba, dan ma yarinyar ta samu kyakkyawar tarbiyya ba dan haka ba Wallahi da bazata zauna da kai ba, ka dinga cewa kai ba sonta kake ba, me za ka yi da ita, raino zak.... Ammar ya katseta ta hanyar cewa "dan Allah ki dena tuno wannan abubuwan, wallahi ina matuƙar jin kunyar abunda nayi, Mufeeda 'yar Aljanna ce Insha Allah" "Kaji da shi dai, seya zame maka izina Ammar, Addu'ar iyayece ta rabaka da Zainab ka Auri Mufeeda, dan wallahi wannan Zainab ɗin ba zata yi maka biyayyar da Mufeeda take maka ba" "se bayan na Auri Mufeeda nima na gane haka, tana min Biyayya fiye da yadda bakya zato, laifi ko ita tayi koba ita tayi ba har ƙasa zata durƙusa akan gwiwowinta tana bani haƙuri, indai ana samun Aljanna a gidan miji Mufeeda ta samu Insha Allah" Murmushi Yaya Maryam tayi tace "gaskiya ƙwaila ta iya kissa, tunda har tasa 'yan maza suka zubar da makaman su na muzurai da haɗe rai, suka afka duniyar soyayya" "Maryam kenan, kafin inyi Aure ne nake ganin' ya mace bata isa ta juyani ba, seda na Auri Mufeeda nagane duk izzar namiji da mulkin sa ya Auri mace tagari kamar Mufeeda dole ya duƙa, ai WATA KISSAR SE MATA" Dariya Sosai Yaya Maryam ta dingayi wa Ammar sannan tace "wani mataki ka ɗauka akan su Fa' izan?" "matakin me zan ɗauka? Na barsu a hannun hukuma su da Allah, wallahi ban yafe haƙƙin ƙaramar yarinya da suka ɗauka ba, suka sa na dinga gaya mata miyagun maganganu, tana kuka ta biyoni tana bani haƙuri, wallahi Allah yasaka mata, nida Fa'iza har abada wallahi Shikuma Faruk shima ya je shi da Allah " Ammar yayi maganar kamar zeyi kuka saboda baƙin ciki da takaici. Anty Maryam Tace " ka dai bi komai a sannu kayi haƙuri, se kaje ka maida hankali ka ƙara riƙe matar ka hannu biyu da mutunci, abunda kake rainawa kake ganin kafi ƙarfin sa wani nan duniya shi yake so" Ammar ya dinga yabon Mufeeda yana jinjinawa ƙoƙarin ta game da haƙurin ta, lallai ta cancanci yabo. Anty Maryam ta ci gaba da yi masa Nasiha. Wayarsa ce ta fara ringing ya ɗaga ya duba, Maman Fa'iza ce take kiran sa Kamar kar ya ɗaga se kuma ya ɗaga "Ammar ka tafi ba kace komai ba, kan case ɗin nan" Ammar yace "mezan ce Mama na barsu da Allah kawai, shi ze sakamin kuma anfi cutar da Mufeeda ita ya kamata abawa haƙuri, a madadin ta kuma mun barwa Allah kawai" ya kashe wayar sa yana kuma jin tsanar Fa'iza da Faruk. Yayiwa Anty Maryam sallama ya tafi, yana tafe amma tunani daban daban sun cika masa kwanya yama rasa wanne ya kamata yayi. A can police station kuwa, da ƙyar DPO ya bada belin su saboda Ammar yace ya barwa Allah komai. *************** Ƙarsfe sha ɗaya na safe aka fito da Saima daga theater, anyi cikin nasara sedai Jaririn yazo babu rai, haka aka kaita ɗakin ta tana bacci, Jabir ya ƙura mata ido duk tayi wani iri gwanin ban tausayi. Haka Ammar ya koma gida jiki a saɓule, yauma yana komawa Mufeeda ta karanto damuwa a kyakywar fuskar sa, ɗan ƙyaleshi tayi tai masa sannu da zuwa, se binta yake da kallo yana tuna lokacin da yake mata faɗa akan wasu laifukan amma ba zata taɓa kare kanta ba sedai ta bashi haƙuri. Hakanan yaji kunyarta tana kama shi, ya tuna lokacin da take nuna ita a duniya babu wani namiji da take so seshi yaita Gwaleta, tayi abu danta burgeshi amma yai banza kamar be san me tayi ba, amma bazata karaya ba gobe ma se tayi wani abun da zesa yaji daɗi. Gaba ɗaya tausayinta ya sake kama shi. "Wai na canza kamanni ne? Naga ana ta kallo na" "gani nayi kin ƙara kyau" Murmushi tayi tace "Kyau se Yaya Ammar amma ni ina naga wani kyau" Ammar yace "eh nagode, ko baki faɗa ba nasan ai ni mummuna ne" "Idan ka kuma cewa mijina mummuna sena ɗau mataki akan ka" Kallon ta Ammar ya ci gaba da yi sannan yace "Am sorry Mufeeda" Kallon sa tayi cikin rashin fahimta tace "Sorry for what?" "Nasan kinyi haƙuri dani a zamanmu, nayi miki abubuwa da dama na rashin kyautawa, ina neman afuwar ki Mufeeda, ina jin kunyarki mussman idan na tuna abubuwan da suka faru a baya" Juyowa tayi ta tattara dukkanin hankalin ta akan Ammar, ta riƙo hannayen sa a nata sannan tace "Mijina Alkhairanka sunfi kura kuranka yawa da matsayi a idona, a zamana da kai nima haƙuri kake dani ai, idan harna manta alkhairin ka na kalli kuskurenka bazan taɓa yi maka Adalci ba, kasawa zuciyar ka ni babu abunda kayi min, Ni jina nake nafi kowace mace sa'ar miji, Allah ya barni da abun sona" Tai maganar tare da sumbatar hannun sa. Murmushi yayi yana kallon ta Mufeeda akwai hikima da iya kalaman kwantar da hankali "Ina sonki Mufeeda" "I love you more my heart, amma gayamin kace ranar daka fara ganina ka fara sona how comes?" Murmushi yayi yace "Ranar da na fara ganin ki, wannan iyayin naki da shagwaɓa har raina naji sun burgeni, a fili kuma abun ya ban haushi, ƙaramar yarinya kamar ke kina wannan abubuwan? Da na koma gida duk abunda zanyi sena tunoki, idan na kwanta bacci se in dinga mafarkin ki, lokacin da kike turomin saƙoni kullum nagani se naji daɗi, duk ranar da baki turo ba se inta fushi babu dalili " Dariya suka dingayi tare, ta shafa gemun sa tace " Gayamin meke damunka ne? " Girgiza mata kai yayi yace " Babu komai " "ƙarya ba hakinka bace Mijina, duk yadda ka kai ga ƙoƙarin ɓoyemin damuwar ka ina ganewa, gayamin meke damunka? Ko har yanzu nayi ƙanƙanta in san damuwar Mijina" Girgiza mata kai yayi ya ɗan lumshe ido yana tuna irin abunda Faruka ya aikata shida Fa'iza, a hankali yace "Family issues ne Mufeeda, karki damu" "Shikenan, amma kabi komai a sannu kaji mijina" Ya jinjina mata kai, sannan yace "ki shirya Anjima da daddare insha Allah zamu je ki duba Saima, yau aka yi mata aiki, munyi waya da Jabir yace babyn yazo ba rai" "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, ai da sauƙi tunda ba ita ta mutu ba" Murmushi yayi yana ƙara riƙe hannun ta a nasa yace "Allah ya raba ki da cikin nan lafiya, Jaririya ta" "Ameen Babyn Jaririya" Suka yi murmushi gaba ɗaya. ****************************** Su Maman Nur kuwa aka karɓi Jaririn ta aka kai shi Asibiti, su kuma akaƙi sakin su, Hajara tace kotu take so akai su sunyi mata ƙazafi ga tada tarzoma a unguwa, da ƙyar aka shawo kanta ta yadda aka sake su, amma sunji a jikin su dan kamar 'yan gudun Hijira haka suka koma, wasu babu takalmi haka aka kamo su. Abun kunya ace an kama matar Aure akan dambe da tada tarzoma ki bar gidan mijin ki ki tafi yawan gulma, abun takaicin ace harsa namiji baligi wanda ba muharraminsu ba suke zama a teburin sa suyi hira (Mace kenan, wata ko me kifi ta tare zata siya ta dinga masa rangwaɗa kenan tana kashe murya tana yayana, dan yayi mata ragi wanda ba lallai tayi wa mijin ta ba, Mata aji tsoron Allah, a dinga kama kai) Aure dayawa ya mutu a sanadin wannan tashin hankali da akayi a unguwar su Mufeeda, da ƙyar aka sake su yayin da aka miƙa Sa'idu ga 'yan sanda domin tattara bayanai a gurfanar da shi a kotu, sakamakon tara matan daba muharramansa ba yake hira da su, yana haɗa husuma. ****************** Se la' asar Saima ta farka daga nannauyan baccin da take yi, ƙanwar mamanta ce a gurin ta, ta temaka mata ta zaunar da ita, da yake an samu ci gaba a yanzu likita yace a bawa saima tea, saɓanin da da idan akayi theater se ace se mutum yayi tusa za'a bashi Abinci. Ta gama shan tea ɗin tana kashingiɗe tana jin yadda wani irin zafi ke ratsa inda aka yanka ta, dan Allurar harta sake ta, cikin zuciyar ta kuma na ƙunar rashin Jaririnta, seda ta haihu take jin da ɗan yana da rai Jabir kome zeyi ba zata barmasa ɗanta ba kamar yadda ta faɗa a baya ba, se dai yaje wadda ze aura ta haifa masa. A hankali ta lumshe ido hawaye na bin kuncin ta, zuciyar ta na mata raɗaɗi, muryar ta can ƙasa tace "Jabir duk a sanadin ka har yankamin ciki aka yi, amma nice abar wulaƙantawar ka" Sunkuyar da kai tayi tana ci gaba da share hawaye. Ƙanwar maman ta tace "wai Saima bazaki dena wannan kukan ba, ki fawwalawa Allah mana, kima gode Allah da ya barki da ranki da lafiyar ki, Allah ya kaimu baɗi iyanzu ki kuma haifo mana wani" "Ba Ameen ba Gwaggo, bazan koma gidan Jabir ba" "Meyasa?" "Gwaggo ni kaɗai nasan abunda nake fuskanta a gidan nan, bar masa gidan sa shine mafita baze ƙarasa hallaka ni ba" Suna cikin maganar ne mariƙin Saima ya shigo da matansa duba ta, bayan sun gama yi mata ya jiki sun zauna ana ɗanyin hira, sega Jabir ya shigo hannun sa ɗauke da leda, kamar na Allah ya durƙusa ya gaida 'yan uwan Saima, ya ƙarasa gaban gadon ta yace "Saima ya jikin naki?" "Ban sani ba da sauƙi ko babu sauƙi be shafe ka ba malam ina fatan kazo min da takaddata ta saki?" Mariƙin ta cikin fushi yace "ke Saima meye haka? Mijinki nefa kike gaya masa wannan maganganun, ya sake ki akan me?" "Kawu duk abunda ya sameni Daga Allah ne, Amma Jabir ne Sila, wallahi na koma gidan sa kasheni zeyi da baƙin ciki, dama ko bance ya sakeni ba yace ze sakeni dazarar na haihu, ya auro wadda zeyi Arziki ta sanadin ta" Maimakon kawun Saima ya tsaya yaji ba'asi kawai ya balbale Saima da Faɗa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, ya zage ta tsaf harda gori a gaban Jabir, yace seta koma gidan ta dan baze iya ci gaba da riƙe ta ba wanda yayi a baya ma Allah ya Amfana. Seda wata metron tazo ta kori duk na cikin ɗakin saboda hayaniyar da suke, aka bar gwaggon Saima kawai, bayan fitar su Saima ta samu ta zayyanewa Gwaggon ta halin da take ciki. "Allah sarki marainiyar Allah ina gefe ai ban san halin da kike ciki ba, ban san irin zaman da kika yi a gidan kawun naki ba kenan" "Dan Allah gwaggo kisa baki, wallahi ba zan iya zama da Jabir ba" "Shikenan kwantar da hankalin ki, nima ban goyi bayan kikoma ba, bari inje in samu kawun naki muyi magana" Kusan mintuna Ashirin da fitar Gwaggo bata dawo ba, turo ƙofar ɗakin aka yi Mufeeda ce da Ammar, sekuma Fiddausi da mijin ta Aminu. Saima na ganin su tayi murmushi tace "Sannunku da zuwa, maraba" Fiddausi tace "yana ganki ke kaɗai babu kowa?" "sun reception suna magana, ga guri ku zauna, Mufeeda naso mu haɗu kafin in haihi Allah beyi ba" Mufeeda ta ƙarasa gaban gadon Saima ta zauna tace "Bakomai Anty Saima sannu ya jikin naki?" Nan suka gaisa suna mata sannu, Mufeeda tace "Amma jinin naki ya sauka ko?" "Eh Alhamdilillah, Jijjiga nayi shine aka yimin aiki" "Allah sarki Anty Saima sannu" Tai maganar cikin tausayawa tana riƙe hannun Saima. Ammar yace "Nida ta tayarmin da hankali ranar da Aminu ya kirani yace wataƙil ma kin mutu, ta kasa zama ta kasa tsaiwa, to gashi dai Anty Saima tana raye. Suka yi murmushi ana ta hira da Saima, taji daɗin zuwansu, sun ɗebe mata kewa, ta samu sassauta daga ɓacin ram da take ciki. Mufeeda tace "Anty Saima babyn ba rai ko? Allah ya kawo mafi Alkhairi" "Babu rai yazo Mufeeda" Tai maganar tana goge ƙwalla. Mufeeda tace "Anty Saima ya zakiyi kuka? Ki gode Allah da kina raye Allah ya baki wani" "Mufeeda kenan dole inyi kuka, wata tara yaron ma ciki na na saka rai, Amma Allah yayi ikon sa" Fiddausi tace "kiyi haƙuri Saima, ki kwantar da hankalin ki, kin san baki da cikakkiyar..... Ai ba ta ƙarasa maganar ba kawun Saima ya shigo yana banbami yace "ba dai baki da mutunci ba kin dage sekin kashe Aurenki, to idan ya sake ki ki nemi gurin zama ba gida na ba, dan bazan ƙara riƙe ki ba wahalar da nayi dake a baya ta isa" Gwaggon Saima tace "ka dai ji kunya, dama can ba wata tsiyar kuke tsinana mata ba, tayi zama ne tamkar baiwa a gidan ka, a matsayin ta na 'yar ɗan uwan ka, nayi imani da Allah da' yar ka ce bazace ta koma ba, shima shegen yaron kwaɗayayye ashe 'yar gidan Alhaji Saminu Kwangila ce yake ƙuzun Aure, ai nasan yaran gidan maza yaje ya kwasa, nidai tunda ya sakarmin ' yata yaje ya ƙarasa, fuskarsa ta nuna dama haka yake so" Mufeeda ta silalae ta bara ɗakin dan ba zata iya jure kallon wannan wulaƙancin ba, kowane tarkace sedai a ɗora shi akan mata. Ammar ma bayan ta ya biyo ya kunna babur ɗinsa suka tafi, shi kansa ransa a ɓace yake, yana jinjina wulaƙanci da rashin mutunci irin na Jabir, sesa Mufeeda tayi kuka saboda tausayin Saima. Haka suka tafi kamar kurame, a daidai danja 'yan sanda suka zo suka kewaye babur ɗin su Mufeeda, suka sa hannu suka kashe babur ɗin suka zare key, ɗaya ya kalle shi yace "Ammar ko?" Ammar yace "Eh nine Yallaɓai amma me nayi?" "dalla rufewa mutane baki, kalle ka kamar mutumin kirki ashe ma cuci ne, ana haɗa kai da kai anyiwa Fasinja fashi fito yai dubunka ta cika" "Kai Yaya Ammar ɗin? Wallahi bashi bane ba, ba yaya Ammar ɗina bane, wallahi bashi bane baze aikata haka ba" Shikam gaba ɗaya kan Ammar ya kulle, yama rasa meze ce, shi dai ba da wani suke exchanging ɗin babur ɗinba, balle ace shine shi a iya sanin sa ko fitinar nan ta ƙuruciya beyi ba balle yanzu da girman sa. "zaka fito ko sena ɓaroka munafuki" Ammar jiki a sanyaye ya fito daga babur ɗin, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko kuɗaɗen dake ciki ya kalli Mufeeda yace "Mufeeda kinga dare yayi, karɓi kuɗin nan maza ki tafi gida, Insha Allah da safe zan dawo, tunda nidai nasan ban aikata laifin komai ba" Mufeeda ta fashe da kuka ta riƙe rigar Ammar tace "Wallahi sedai a haɗa dani, ni Ammar ɗina mutumin kirki ne Officer dan Allah, wallahi bashi ake nufi ba" "Yi haƙuri 'yan mata maza ki tafi gida, yana division ɗin gangare zamu tuhume shi" "Maza ki tafi gida dare yanayi, sannan karki sanar da kowa se zuwa gobe in Allah ya kaimu inga yadda hali zeyi" Aka saka Ammar a motar ' yan sanda, suka tuƙa Napep ɗinsa suka tafi da shi. Kai masha Allah, ban san haka kuke son book ɗin nan kuke following ɗinsa ba, kwana biyu da ban posting ba nasha kira a waya, ina godiya ta musamman Allah ya bar ƙauna, kar' amanta in an karanta ayimin share dan Allah ba dan halina ba 🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏 Wanda sukamin magana akan voting na gasar dana shiga, se an kammala gasar ne za'a bada link ɗin da fans zasu shiga suyi mana voting, nagode da kulawar ku Domin gyara, sharhi, ko shawara, ƙofa ta a buɗe take Ayshercool 07063065680..✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment ELEGANT ONLINE WRITER'S NOT EDITED Page 29 Gaba ɗaya jikin Mufeeda rawa yake, ji take tamakar a mafarki, wace irin masifa ce wannan? Daga wannan se Wancan "Ya Allah ka fitarmin da mijina" Haka ta tari Abun hawa ta tafi gida, unguwarsu baƙi ƙirin saboda duhu, har ƙofar gidanta me Napep ya kai ta. Safa da Marwa Mufeeda ta dinga yi a ɗaki ta rasa me ya kamata tayi, se sharce hawaye take tana tunanin ya Ammar ze iya kwana a ceil, waye yai masa wannan sharri haka? Tayi tunanin ko ta kira Baba a waya ta gaya masa, seta tuna Ammar yace karta gayawa kowa. babu Alamar Bacci a tattare da Mufeeda, tai alwala dinga salla tana kai kukan ta ga Allah, har dare ya raba kuka Mufeeda take sosai ga tsoro da take ji. Tana zaune a tsakar ɗaki ta dunƙule a guri ɗaya tana kuka, ji tayi ana buga gate ɗin gidan, da sauri ta miƙe ta koma kan Gado tana rarraba ido, cigaba da bugun aka yi, wata zuciyar tace idan kuma Ammar nefa ya dawo, da sauri ta sakko daga kan gadon ta buɗe falon ta fito tsakar gida cikin sanɗa. Buga ƙofar aka cigaba dayi, cikin sanɗa take tahowa ta tsakanin gate da garu Mufeeda ta leƙa yanayin inuwar wanda yake tsayen ba tayi kama data Ammar ba. Da gudu ta koma ta rufe falon ta, ta koma ɗaki ta kulle ƙofa, ta hau gadon ta ta dinga Karanto Addu'oin da suka zo bakin ta. Yadda Mufeeda taga rana haka taga dare, cikin tashin hankali ta wayi gari. A gurguje tai wanka ta shirya, ta girka Abinci ta rufe gida ta fice. Station ɗin da'aka kai Ammar ta tafi, tun ƙarfe takwas na Safe ta tafi, taita Jira a station ɗin, se ƙarfe Goma aka fito da Ammar daga shi se dogon wando da vest, da alama an dake shi ma, sedai cikin Jarumta yai mata murmushi yace "meyasa kikayi Sammako haka?" Kuka ta fashe da shi Sosai, ta kalli ɗan sandan tace "Yallaɓai wai baku gama binciken ba? Dan Allah ku sake shi wallahi Yaya Ammar mutumin kirki ne" Ɗan sandan yace "Ke kije gida kizo da wani Babba daga gidan ku, ko baban ku ko wani babba, 'yar mitsitsiya dake ba dake za muyi magana ba" Mufeeda tace "haba Yallaɓai cewa kukayi zakuyi bincike ku sake shi, wallahi mijina mutumin kirki ne" Zare ido ɗan sandan yayi yace "Miji kuma? Ke yanzu wannan ne mijin ki, kai Ashe banda tuhumar da muke maka, akwai buƙatar Human right su bincike ka, wannan ai child Abuse ne Wannan Yarinyar ce matarka?" Banza Ammar yayi masa ya kalli Mufeeda yace "Ina fatan kinyi bacci jiya, dan nasan halinki" "Wallahi yaya Ammar banyi bacci ba, aka dinga bugamin gida jiya a tsorace na kwana ga hankalina yana kanka" tai ƙarasa maganar tana kuka. "ki kwantar da hankalin ki, ki kira Aminu a waya ki gaya masa ina nan" "Yaya Ammar, Har yanzu basu gama binciken ba? nasan ba zaka aikata haka ba" "Mufeeda ni kaina na kasa gane kan lamarin nan, har yanzu banga fasinjojin da ake zargin nayiwa fashin ba, sun tirsasani in amsa laifina naƙi, Amma ki kira Aminu" "Yaya Ammar, ba zamu gayawa su Baba ba" Girgiza mata kai yayi yace "ba yanzu ba, kina gaya musu hankalin su ze tashi, ki bari mu ga yadda hali zeyi" Haka Mufeeda ta koma harabar station ɗin ta kira Aminu ta sanar da shi halin da'ake ciki, Aminu ya kaɗu sosai da jin Abunda Mufeeda ta gaya masa Yace "ki kwantar da hankalin ki Mufeeda, gani nan zuwa Insha Allah, Amma abun da mamaki gaskiya" Befi mintuna Arba'in ba sega Aminu yazo station ɗin. Ya shiga ya samu officer on duty, suka gaisa Aminu yace "Yallaɓai nazo ne akan case ɗin ɗan uwana da aka kama" Ɗan sandan yace "Eh mun kama shine saboda muna zarginsa da haɗa kai da 'yan iska suka yi wa fasinjansa fashin waya da kuɗaɗen sa, munyi2 yaƙi ya amsa laifin sa" Aminu yace "Amma Yallaɓai ai se mutum ya aikata laifi sannan ze amsa yayi, sannan wanda kuke zargin nan da iyalinsa da mutuncin sa beyi kama da wanda ze aikata wannan laifin ba kag..... "Kai zaka koyamin yadda zanyi aikina ne? Su mutanen banza a fuska ake gane su?" ɗan sandan ya katse shi Aminu yace "A'a Allah yabaka haƙuri, yanzu meye abunyi? Ina so abani belin sa" "zamu bada belinsa amma zaku biya yaron da akayiwa Fashi kayan sa, yaron ɗan makaranta ne yana school yanzu amma in anjima zezo, in bahaka ba mu miƙa ku kotu" "Amma yallaɓai abunda ba'a tabbatar ba, har a yanke masa wannan hukunci haka" "kaga idan baku shirya karɓar belinsa ba, zamu tura ku kotu a satin nan kuma kasan hukuncin fashi da makami za'a yanke masa" Aminu yace "Shikenan ina jinka meye abunda za'a biya yaron?" "Naira dubu ɗari da goma ne abunda za'a biya" Da sauri Mufeeda ta ɗago kai ta kalli ɗan sandan, idon ɗan sandan kawai ze nuna maka rashin imani, yanzu ace da ire iren wannan bara gurbin 'yan sandan a cikin Al' ummar mu ta ina za'a zauna lafiya. Mufeeda tace "Yanzu kai ko tsoron Allah ba kaji ba, dubu ɗari fa saboda mugunta, wallahi se Allah ya saka mana, duk wanda yake da hannu a cikin yiwa mijina sharri se Allah ya wulaƙanta shi, idan da haɗin bakin ku Insha Allah sekun rasa aikin" "Ke ni kike gayawa haka? A gaban hukuma fa kike" "Hukumar banza da Wofi, Allah ya Tsinewa hukumar indai irin wannan ce, Azzalumai kawai" "Ke idan baki wasa ba sena saki a ceil na koya miki hankali, mutuniyar Banza kawai" Aminu na ƙoƙarin rarrashin ɗan sanda, amma Mufeeda ta hasala ƙarshe tace "Kai ka isa kasani a ceil, wallahi ka sani a ceil seka rasa aikin ka har gaban Abada, indai Alfarma ce nima inada wanda zasu tsayamin a fitar da mijina, sannan a hukunta ku" Da ƙyar Aminu yasa Mufeeda tayi shiru yasa ta tafi gida, dan indai tana nan ƙarshen ta Ammar baze fita a yau ba, seda aka kai ruwa rana Aminu yaita fama sannan aka bari Aminu yaga Ammar, Aminu ya gaya masa abunda suka ce, Ammar yace "shikenan, Mufeeda ta ɗau wayata tayi maka transfer ɗin dubu tamanin da biyar, su kenan a Account ɗina, dama ina tara kuɗinne saboda in fara yiwa Mufeeda siyayyar haihuwa, ka ciro ka basu in bar gurin nan, na barwa Allah" Mufeeda na Adaidaita sahu zata koma gida tana ta kuka a Napep ɗin, Aminu ya kira ta ya sanar da ita abunda Ammar yace, tace "to bari in ƙarasa gidan, se in turo maka" A titi ta sauka ta biya me Napep kuɗin sa, ta fara tafiya sedai tana zuwa bakin layin taci karo da motar Alhaji Idris yana zaune akan motar, yana ganin ta ya sakko da Ƙaton cikin sa yana wangale mata baki yace " 'yan matan daga ina haka? Naga kamar kina kuka, da safe naga fitar ki, shine na zauna ina jiran dawowarki" Shiru tayi masa tana ƙoƙarin raɓawa ta gefe ta wuce, amma ya sha gaban ta yace "Naji labarin ashema mijin naki ɗan ta' adda ne, yana hannun 'yan sanda, matsalar Auren mutane irin mijin nan naki kenan, ki kwantar da hankalin ki, kici Arziki ki barshi a inda yake, ni me ƙaunar kine, tunda an riga an kama shi ki manta da shi kawai" Cike da ɓacin rai Mufeeda tace "Kaji labari ko kuma kasa aka kama min Miji saboda son zuciyar ka? , kuma kasan baya gida kazo gidana cikin dare kana ƙwanƙwasamin ƙofa, kasa an cajemu kuɗi masu yawa, to insha Allah Ammar baze ƙara kwana a hannun hukuma ba, ze fito, kuma kasani shi Allah baya bacci idan har dasa hannun ka akan abunda ya samu mijina, ko bance komai ba Allah yana kallon ka" Ta ƙarasa maganar cikin hawaye, ta raɓa gefen motarsa ta wuce, ya girgiza kai yace "wannan Yarinyar akwai shegen taurin kak, baki da rabo amma muje zuwa da kanki zaki kawo kanki, dan talauci masifa ne, sannan bazan iya haƙura da yarinyar nan ba" Mufeeda tana zuwa gida ta turawa Aminu kuɗin nan, tana kuka gami da tausayin Ammar ta tura kuɗin nan. Ammar yana matuƙar ƙoƙari da gwagwarmayar neman halak, ya tara kuɗinsa da ƙyar beci ba be sha ba, A banza an raba shi da haƙƙin sa, sosai ta dinga kuka tana tunanin wannan wane irin zalunci ne haka? Bayan ta tura kuɗin ne ta shiga kitchen ta duba me zata girkawa Ammar kafin ya dawo, kayan Abincin su duk sun ƙare, ranar daza'a kama shi yace mata tayi masa list ɗin abunda ya ƙare ya siyo, Amma wannan ƙaddarar ta haushi. Aminu ne ya cika kusan dubu Arba'in sannan kuɗin suka cika ya biya, da zasu taho daga station ɗin Ammar yace a bashi mukullin Babur ɗinsa, amma suka ce ba zasu bashi ba, zasu riƙe Babur ɗin se sun kammala bincike. Mufeeda ta shiga tana duba kitchen, Taliyace da ita guda biyu ta ɗauki ɗaya ta dafa, tana da sauran miya ta gyara ta, ta zuzzuba a Flask ta ajiye masa tana dakon dawowarsa, se la'asar sannan taji ana knocking ɗin gate, da sauri ta tashi taje ta buɗe, Ammar ne shida Aminu, suna shigowa Mufeeda ta rungume Ammar tana kuka tace "Allah ya saka mana Yaya Ammar, Allah ya ƙwatar maka haƙƙin ka, duk wanda yayi maka sharrin nan Allah ya saka maka" Sosai suka bawa Aminu tausayi, Mutum me ƙaramin ƙarfi kamar Ammar ya tara 'yan kuɗaɗen sa da ƙyar Amma lokaci ɗaya a raba shi dasu abun da tausayi. Aminu ya Jajanta musu, Sannan yace Insha Allah ze cigaba da bibiyar case ɗin a samu Ammar ya karɓi babur ɗinsa, Ammar yayi masa godiya da irin gudunmuwar da ya basu. Ammar yayi wanka ya fito amma Mufeeda kuka take bata dena ba, ya zauna ya dinga rarrashinta, shi yanzu babban abunda ya dame shi shine babur ɗinsa da'aka riƙe, da Allah ya dogara da babur ɗin nan ya dogara, gashi kusan komai nasu na Abinci ya ƙare, ya daɗe yana tara kuɗaɗen sa gashi dare ɗaya babu su. ******************* Saima ta fara samun Sauƙi, tunda akayi wannan sa'insar tsakanin kawunta da gwaggonta, gidan mariƙanta babu wanda ya sake zuwa duba ta, gwaggonta ce kawai a gurin ta take ta kula da ita se sauran wanda ba'a rasa ba, Jabir ma ya ɗauke ƙafarsa ya dena zuwa, ya samu Nutsuwar ci gaba da neman Auren Fatiyya. Da'aka Sallameta tabi gwaggonta gidan ta, dukda itama me ƙaramin ƙarfice ga nata marayun Amma haka ta tafi da Saima tace Allah baze hanata yadda zata yi ta riƙe su gaba ɗaya ba. ****************** Rayuwa ta fara yiwa su Ammar wahala, da ƙyar yake iya samo abunda zasu ci inya fita, wataran sedai ya samo abunda Mufeeda zata ci shikuma ya haƙura. Duk wata Sana'a da Ammar zeyi ta ƙarfi dan ya samu ya riƙe gidan sa yanayi komai ƙasƙancinta, Cikin Mufeeda ya shiga wata na biyar, ga wani irin yawan cin Abinci da take yi. Duk Abunda ya kawo ya bata, bata raina wa hannu biyu take karɓa da murna tana Godiya koda kuwa abun be mata ba. Itace ma take ƙoƙarin kwantar masa da hankali. Gari ya waye da Safe, Ammar yana kallon ta ta ɗakko tuwon masara ta yayyankashi ƙanana tasa masa gishiri ta zauna tana cin Abunta da uwar safaiyar nan, saboda babu abunda zasu ci da Safen, tana yi tana kallon bollywood da suke wani shiri, yadda aketa sarrafa Naman kaji, tai shiru tana kallo gwanin ban tausayi da alama tana son ci ne. Ammar ji yayi kamar yayi kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi. Ammar a rayuwar sa idan akwai abunda ya tsana be wuce ya keta bullensa yayi roƙo ba, tun yana ƙarami yake da wannan ɗabi'ar, idan har kaga ya nemi taimakon wani sedai idan ya rasa yadda zeyi ne abubuwa sunyi matuƙar ƙure masa A hankali ya kalli ta yace "Mufeeda" Ta juyo ta kalle shi, tare da yi masa murmushi tace "Na'am my sugar" "Dan Allah kiyi haƙuri, ni kaina bana jin daɗin halin da muke ciki, a halin da kike ciki be kamata ace kina cin wannan Abincin da sassafen nan ba, Dan Allah ki ƙara haƙuri Mufeeda, sannan naji daɗi da kika rufamin Asiri baki gayawa kowa halin da muke ciki ba, Insha Allah komai ze wuce" Ya ƙarasa maganar kamar zuciyar sa ta fashe dan ɓacin rai. Mufeeda tayi masa shiru ta cigaba da cin Abincin ta, tuwon data ci ma ba ƙoshi tayi ba, taci ta ƙarasa da ruwa, ta kalle shi tace "Mijina, idan har na gujeka kona ɗaga maka hankali saboda yanayin da muke ciki Allah ma baze barni ba, duk abunda ya same ka ni ya sama, lokacin da kake samu dukda ba ƙarfi ne da kai ba, daidai gwargwado babu abunda baka bani na jin daɗin rayuwa iya ƙarfin ka, to wani dalili ne zesa in ɗaga maka hankali a yanzu, Jarrabawa ce Allah ne ya jarabce mu ina fatan Allah ya kawo mana mafita " Shiru Ammar yayi yana kallon ta, ya kasa cewa komai. "Yaya Ammar rufin Asirin ka nawa ne, Ina sonka Yaya Ammar fiye da yadda kake tunani, zan iya zama da kai a duk halin da kake ciki,saboda haka duk abunda ka kawo ka bani zan karɓa inyi Amfani da shi komai ƙanƙantar sa, sannan ina Amarya lokacin da su Baba suka zo sun ban dubu Goma, ban gaya maka ba saboda nasan zakamin faɗa kace meyasa na karɓa, shiyasa na haɗa da kuɗin da wanda kake bani kusan dubu goma sha biyar na bawa Yaya Amina nace ta yi Business dashi, idan ina buƙata zan mata magana, yanzu nayi mata magana na bata Account Number ɗinka zata sakomin kuɗin, seka ɗau dubu goma ka bani biyar tunda fridge ɗina biyu ne kuma ana samun wuta se in fara saida kayan sanyi, Amma me kace? " Ajiyar zuciya yayi yace "zaki iya sana'a a haka? Karki wahalar da kanki fa" "zan iya Yaya Ammar, zaman haka baze yuwu ba, kaga da ina Sana'a da abun yazo mana da sauƙi" "Shikenan, Amma be kamata in karɓar miki kuɗi ba, sedai ko rance in Allah ya hore in mayar miki" Haɗe rai tayi tace "Niba rance zan baka ba, kyauta zan baka kayi abunda ya dace dasu, kaga da Abba ze yadda a cikin dabbobi na ya baka ka siyar da wasu ka haɗa" "A'a kin san halin Abba, baze yadda ba, Naji daɗi Sosai Mufeeda Nagode, Nag..... "Shhhhh babu wannan tsakani na da abun sona, dan Allah Yaya Ammar ka kwantar da hankalin ka kaji, ni ba zan ɗaga maka hankali ba, mubi komai A sannu, Allah yasa haka shine mafi Alkhairi" Ya amsa mata da Ameen, sannan yace "ranar Litinin ya kamata ki koma awo, amma baki je ba, Amma in Allah ya kaimu sati me zuwa zaki koma Awo ina sane, Insha Allah" Jinjina masa kai tayi tana masa murmushi. ******************* Mijin Jidda ya dage kai da fata seya ƙara Aure, duk wani abu data san zata yi ta tayar masa ds hankali tayi amma kamar tana ƙara ziga shi, haka ta haƙura ta shiga gyare2, ya gina sabon gidan sa inda zasu koma gaba ɗaya ya haɗe su. Tana so ta koma da sababbun furnitures, tace ya canza mata yace bashi da kuɗi, ita kuma kuɗinta ba zasu kai ba, tace bari taje tasa Ammar a gaba ya cika mata. Sedai da taje ta tarar Ammar baya nan, Rashin mutuncin nata dai data sabawa yiwa Mufeeda bata dena ba, taita zuba ido Mufeeda ta zubo mata Abinci amma shiru nan ma ta samu nayi, ita dai Mufeeda ko uffan ba tace mata ba, ana haka Ammar ya dawo ya tarar da Jidda. Se wani harare hararw take tana hura hanci ita ga me ɗan uwa, Bayan sun gaisa ta gaya masa abunda takeso yayi mata. Ammar yace "A gaskiya Jidda sedai kiyi haƙuri, bani da hali a yanzu bani da kuɗi, naga kayan kujerun naki aiba wani abun suka yi ba, ki tare dasu mana" "dalla Yimin shiru, kace dai bazaka bani ba, ka taɓe a gindin mace se abunda take so, tunda kayi Auren nan ko ɗan Alherin da kakewa Mutane ka dena, Saboda wannan lotsatsiyar Yarinyar mara hankali" "Ya isheki Yaya Jidda, a baya da ne miki babu nauyin kowa a kaina, kuma kinsan ina miki, yanzu kuma Akwai Nauyin Mufeeda a kaina, A yanzu idan na tauye haƙƙin ta nayi miki se Allah ya tambayeni, balle kuma bani da shi" Abun ya nemi ya koma musu faɗa suka yi baran baran ta koma ta zage Mufeeda tsaf, Ammar yana tare mata, da haka ta bar gidan. Ammar yaita rarrashin Mufeeda yana bata haƙuri akan irin abubuwan da Jidda take mata, Mufeeda tace "Bakomai Yaya Ammar, ai wataran se labari nasan ze wuce" "Yawwa 'yar Aljanna, ɗazu bayan fita ta Amina ta turo kuɗin nan, amma dubu Ashirin da biyar ta turo'" Mufeeda tace "Eh munyi waya da ita, wai a ribar data samu ne nima ta sanmin, seka bani dubu goma ka siyomin ruwan leda, se in rubuta maka kayan lemon da nake buƙata, in sanar da mutane na fara saida kayan sanyi" Ammar yayi murmushi yace "Shikenan, Allah yasa Albarka, Gobe in Allah ya kaimu da sassafe zan shiga kasuwa ana sauke kaya daga trailer, inje abunda na samu in ƙara da kuɗin hannu na se in siyo ko Omo ne da Sabulu a hannun 'yan sari in fito bakin kasuwa in siyar" Idon Mufeeda fal ƙwalla tace "Yaya Ammar zaka iya wannan aikin me wahala kuwa?" Murmushi yayi yace "Nifa namiji ne, da aikin soja zan tafi dan dai Baba baya so ne, karki damu zan iya kije ɗakin tsakar gida na siyo miki nama kici, ki ƙara haƙuri Mufeeda Insha Allah komai ze wuce" "Yaya Ammar seda ka siyo Naman nan" "Eh mana nasan kina so, kin daɗe baki ciba" Allah sarki Ammar, harda fruit ya haɗa ya siyo mata, duk yadda tayi dashi yaci ƙi yayi, Amma yaji daɗin ganin murmushi a fuskar ta, sanadin wannan Nama data ci. Tun Ammar yana sintiri akan Napep ɗinsa har ya haƙura, Kullum da sassafe yake tafiya kasuwar singa, haka ze zage yaita sauke manyan buhunhunan kayan Abinci, abun da ya samu haka ze haɗa da kuɗin hannun sa ya sai ƙanan abubuwa kamar Omo da su Sabulu a hannun 'yan sari ya fito bakin kasuwa ya siyar. Ammar duk sana' ar daya san zeyi ya samu kuɗi babu ruwan sa yin abarsa yake, wataran ya samu riba wataran ya faɗi amma hakan baya hana gobe ma ya fita. Kamar wasa Mufeeda ta fara Saida kayan sanyin nan, dama kafin su fara seda taita gayawa Allah, abu kamar wasa wuni ake zuwa siyan ruwan sanyi da lemo, randa babu wuta ta bayar a siyo mata mai ta kunna inji, Sosai take ciniki. Ranar da taga ta samu riba da yawa bayan Ammar ya dawo ya huta tace "Yaya Ammar ya kamata ka siyo mana banki, kullum mudinga ajiye ɗari biyu, duk sati dubu ɗaya, zasu temaka mana wataran" Ammar yace "hakane kin kawo shawara Jaririya ta, Insha Allah zan siyo mana mudinga ajiyewa" Duk wannan hali da suka shiga Babu wanda suka gayawa, tare suke ta faɗi tashin su, randa suka samu suci me kyau randa babu suci abunda ya samu. Allah yasa musu Nasibi akan sana'ar, Mufeeda tana daga gida amma tana cinikin ta sosai. Kwana biyu Ammar beje gida ba saboda bashi da kuɗin daze musu alheri idan yaje, ranar wata Asabar yasa Mufeeda ta shirya suje, su fara zuwa gidan su Ammar idan yaso da Azahar, se suje gidan su Mufeeda. Haka kuwa aka yi, suna Zuwa gidan su Ammar suka tarar da Abba a tsakar gida, suka gaisa. Abba yace "Aikuwa Halima tana Islamiyyar safe, ita kuma taje wata barka nan ƙasa amma yanzu zata dawo, Ina A daidaita sahun naka ne?" Ammar yace "tana gurin gyara, Amma zan karɓo Insha Allah " Abba yace "To Allah ya dafa, 'yata fatan kuna lafiya?" "Lafiya ƙalau Abba" "Masha Allah, tunda Allah yasa yau kinzo kafin ku tafi kya je kiga dabbobin ki" Mufeeda tace "To Abba nagode sosai Allah ya ƙara girma" Abba yace "Bakomai Mufeeda, Allah yayi muku Albarka, ni zan fita nasan ba daɗewa zata yi ba, zata dawo" Ammar yace "Shikenan Abba adawo lafiya" "Allah yasa Ammar" Abba ya fice Mufeeda da Ammar suka zauna suna Hirar su, ɗakinsa na gwauranta dake cikin gidan ya buɗe musu suka shiga, Mufeeda tace "Yaya Ammar wannan ƙatuwar katifar fa kamar ta Amarya?, bari in kwanta akai" Ammar yace "Yi a hankali karki lotsamin katifa da wannan ƙaton cikin naki" "Sena lotsa ɗin, ai da bani da nauyi, kaika mayar dani me nauyin" Dariya yake mata yazo ya kwanta a kusa da ita yace "Allah sarki Jaririya ta, ta kusa zama Mum koya zata yi raino" "Ai baka tuna ni Jaririyar bace, ka haɗani da aiki" Hirar su suka dinga yi cike da ƙaunar juna, wani lokacin Ammar yana kallon yadda cikin yake motsawa mussman idan tana bacci, ya ɗora hannun sa akan cikin nata, yana jin yadda yake ɗan motsawa, Da haka bacci ya ɗauke su. Koda Umma ta dawo tayi mamakin ganin gidan a buɗe ba kowa, tana shigowa ta tarar da ɗakin Ammar a buɗe ga takalma a ƙofar ɗakin, tai magana kusan sau uku taji shiru, ta ɗaga labule, bacci suke sosai Umma ta sauke labulen tana ɗan murmushi. Aikace2 ta shiga yi, Ta ɗora girki Amma duk su Ammar basu san tana yi ba, Mufeeda bata samun bacci sosai, tana raba dare gurin Ibada da kaiwa Allah kukan su, sannan idan tayi sallar Asuba bata komawa bacci saboda Ammar da wuri yake fita, wani lokacin shida da rabi ya bar gida, da rana ta ɗan ɗaga kuma an dinga sintirin siyen ruwa da lemo kenan, dan haka basa samun ishashen bacci, mussman Ammar da yake Aikin ƙarfi. Jiddace tayi sallama idon ta Jawur kamar wadda aka koro, Umma ta kalleta tace "Jidda lafiya kuwa?" Fashewa da kuka tayi, tace "Umma na shiga uku, Baban su Haidar wai Zainab ze Aura ashe? Ɗazu na samu labari, na shiga uku Umma, ta gama sanin Sirri na ta shisshige min, na yadda da ita Amma taci Amana ta, Nusaiba na taje har gida ta mata rashin Mutunci baki ga dukan da da baban ta yayi mata ba, na shiga Uku Umma. Wata ta biyo ni private tace "Gaskiya baiwar Allah kin fiye tsananta masifa" 🤣 🤣 🤣 🤣 🤣 Sorry labarin ne yazo a haka. Ina godiya da Comments da shawara. Ina Masoya na, lokaci yayi da zaku min kara ku nunamin ƙauna, kamar yadda kuka sani na shiga Gasar Matasan marubuta 2021, A gobe in Allah ya kaimu Asabar, 31 ga watan July rukuni na 7,wanda shine rukunin da nake ciki zamu saki litattafan Gasarmu, masu ɗauke da kalmomi 2500. Na shiga gasa da littafi na me suna BAƘIN TABO, ku kasance dani domin ji ya taka ya a cikin wannan gajeren labari, ina fatan idan lokacin zaɓen labarin Gasar Yayi, zaku zaɓi labarina na BAƘIN TABO, https://chat.whatsapp.com/J3lB9LvDu174M3yeR56BoK Mata kawai banda maza Ina Alfahari daku Masoya a duk inda kuke. Domin Sharhi Gyara, ko Shawara Ayshercool 07063065680 ✨✨✨ *WATA KISSAR...... * ✨✨✨✨✨ ( *Sai Mata* ) *PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞 ( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪) /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P.W.A✍️ *_A SHORT LOVE STORY_* *Story and written by* '''AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) The experience writer of ABDUL JALAL''' Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba Watpad @ Ayshercool7724 What's app 07063065680 Gmail Www.ayshertadam@gmail.com Please follow me on Wattpad, vote and Comment ELEGANT ONLINE WRITER'S NOT EDITED Page 30 Hargowar Jidda ce tasa Ammar ya farka, yai shiru yana sauraron abunda Jidda take faɗa, rungume Mufeeda ya sake yi a jikin sa yana tunani, a ransa yace "Allah nagode maka da ba Zainab na Aura ba, da ita na aura nasan tabbas ba zata iya haƙuri da halin da nake ciki ba" ya cigaba da shafa kan Mufeeda yana kallon ƙanƙantar ta, Amma akwai haƙuri da hangen nesa, tana yiwa Ammar so na gaskiya da zuciya ɗaya. A hankali Mufeeda ta fara motsawa itama sakamakon kukan Anty Jidda, ta kalli Ammar tace "Yaya Ammar su Umma sun dawo" Ammar yace "tun ɗazu suka dawo ai" "amma me yasa baka tasheni ba? Yanzu an gan mu tare muna bacci, yanzu ya zamuyi mu fita?" Murmushi yayi yace "Ya zakiyi ki fita dai, ni ficewa ta zan yi" Ta kalli agogon dake ɗakin ta ɗan zare ido tace "Yaya Ammar lokaci ya ja fa, kalli Azahar tayi" Ammar yace "Eh tashi muje muyi salla" "Yaya Ammar kunyar fita nake ji, Amma kamar muryar Anty Jidda nake ji fa" "Eh ita ce" ya bata Amsa Mufeeda tace "Kamar kuka fa naji ta nayi" Ammar bece komai ba ya miƙe, ya basar ya fito tsakar gida, ya gaida Mama yai alwala ya fice masallaci. Da ƙyar Mufeeda ta fito cike da jin nauyi, Jidda na ganin ta, wani baƙin ciki ya tokare mata zuciya. Mufeeda ta durƙusa tace "Umma ina wuni" "Lafiya ƙalau Mufeeda, kin tashi ashe?" Cike da jin Kunya Mufeeda tace"Eh Umma" Umma ta fuskanci Mufeeda nauyin ta take ji sosai dan haka tace "to yi salla kizo kici Abinci" Mufeeda tace "to Umma, Anty Jidda ina wuni" Banza Jidda tayi da ita, Mufeeda ta tashi ta tafi yin Alwala. Umma ta kalli Jidda tace "Ke kina jin matar ɗan uwan ki tana gaishe ki amma baki amsa ba" "Umma ba dole in mata banza ba, yarinyar nan ta cuceni ba dan Ammar ya Santa ba da tuni Zainab ya aura, Amma yanzu kalli ya Aure ta, ni kuma zata Auremin miji na shiga uku Umma" "Haba Jidda, da bakin ki kike cewa kin shiga uku? Ki fawallawa Allah lamarin ki mana, sannan kija girman ki, karki shiga sabgar ta balle inya aurota ta raina ki" "Haba Umma ya kike wannan maganar, yarinyar Zainab nan ba sirrina da bata sani ba, wataran a gida na take wuni, kawai seta ci Amana ta" Duk haƙurin Umma seda ta ƙule tace "to Ubanwa yasa kike gaya mata sirrin ki? ashe har yanzu baki da hankali, kina girma kina shiga dawa, waya gaya miki ana haka? Ai koni da nake mahaifiyar ki ba komai yakamata in sani ba game da zaman Auren ki, Amma kinje kina gayawa wata sirrin Auren ki, watanma bazawara, yanzu kinzo kinamin kuka, ai kinyi kuskuren da baze taɓa gyaruwa ba, kuma karki ƙara zargin Mufeeda ba ita tayi miki ba, dama can Allah ya rubuta Ammar ita ze Aura" Mufeeda ta fito daga banɗaki tazo ta tada Salla, ana haka Sega Yaya Maryam tazo, tana zuwa ta tarar da Mufeeda ta idar da salla suka shiga Hirar su, tamkar bata san halin da Jidda take ciki ba, suka cigaba da hira hadda Umma suka ƙyaleta. Jidda tace "Wai Maryam baki san hakin da nake ciki bane?" Maryam tace "koma na sani mezan iyayi akai? Tun farko ni dama wannan Zainab ɗin ba tayi min ba, na baki shawara shaƙuwarki da ita tayi yawa, Amma kika ƙi ji, Abunda haƙuri be baki ba rashinsa baze baki ba, kuma wallahi in baki nutsu ba Abba yaji labarin yadda kike ɗagawa mijin ki hankali kin san sauran" Sallamar Ammar ce ta hana su ci gaba da Hirar, ya shigo ɗakin ya zauna, ya kalli Yaya Maryam yace "Sarakan yawo, daga Yaya Jidda tazo shine kema kika taho ko?" Anty Maryam tayi dariya tace "A'a zuwan ta daban nawa daban, kawai mun haɗu ne, Ai bansan tare kuke da Mufeeda ba, banga babur ɗinka a waje ba" "Eh yana gurin gyara ne" Ya kalli Umma yace "Umma me kika dafa ne, muna jin Yunwa fa, daga nan wani gurin zamu tafi" Jidda tace "Ammar shine kazo ka kula kowa, Amma ni ka shareni kamar baka ganni ba, balle ka tambayi halin da nake ciki, koda yake ba abun mamaki bane, tunda ka fi ƙaunar matar ka a kanmu, damuwar ta itace damuwa 'yar gwal" "Wallahi tafi gwal" Ammar ya bata Amsa kai tsaye cike da basarwa. "Ni kake gayawa Matar ka tafi gwal ko?" Shiru yayi mata yaƙi bata Amsa, a fusace tace "Ai dama nasani, ba yau kasaba wulaƙantani ba akan Yarinyar nan, ƙiri ƙiri naje gidanka da buƙata amma kaƙi saurara ta, ko Abinci ya gagara a bani a gidan ka, kuma kana kallo ba kace komai ba" Shiru Ammar yayi yana mamakin wani irin hali ne haka da Jidda. Yaya Maryam tace "Haba Yaya Jidda, kema fa ɗan wasu kike Aure, kuma Yayan wasu, sannan ƙanin wasu, shekaru Ashirin da biyu yana miki bauta ya wahalta miki kamar besan ciwon nema ba, shikenan ke kuma wata ba zata mori ɗan uwanmu ba? Mu yiwa kanmu Adalci mana, me Ammar yake dashi wanda yake wahaltawa Mufeeda da har kike iƙrarin ya tare a gurin ta? Ita kin san halaccin da take masa? Kin san ita ɗawainiyar da take da shi, ai macen ma da zata iya Zama da ɗan uwan mu da irin halinsa na Fushi da zuciya, Yabo ya kamata ta samu" gaba ɗaya Mufeeda ta takura taji babu daɗi abubuwan da suke faruwa duk a dalilin ta, Umma kuwa ta hau yiwa Jidda Faɗa, jiki a sanyaye Mufeeda ta bar ɗakin dan bekamata ta cigaba da zama ana rigima a kanta ba. Tana fita Ammar ma ya miƙe yabi bayan ta, Abinci ya zubo ya jata ɗakin sa suka zauna yana bata, sedai sam hankalin ta ba'a kan Abincin yake ba. Yana bata yana mata hira, Amma sam taƙi sakin Jiki, ganin haka yasa Ammar yace "Shirya muje kiyi musu sallama, mu tafi" Ta jinjina masa kai, haka aka yi jiki ba ƙwari Mufeeda taje tayi wa su Umma Sallama, ta zaci Umma zata canza mata Fuska ko wani abun, Amma taga saɓanin hakan. Mufeeda tasa hannu a Jakarta ta ɗakko dubu uku tace "Umma ga wannan, ki ɗau dubu ɗaya a ajiyewa Abba dubu biyu" Girgiza kai Umma tayi tace "A'a Mufeeda, Nagode Allah yayi Albarka, Amma ai sunyi yawa, ki riƙe Abun ki, ga hidima tana tunkarar ku Allah ya raba lafiya" Kunya ce ta kama Mufeeda, dan ba tayi zaton Umma ta gane tana da ciki ba, saboda bata cire hijjabin jikin ta ba. Ammar kam ba kunya caraf ya amsa da "Ameen ya Allah Umma" Mufeeda a ɗan Shagwaɓe tace "Amma Umma meyasa idan Yaya Ammar ya baki kike karɓa? Nawane bakya so ko?" Gaba ɗaya Jidda ta tsani yarinyar nan, duk wani salon bariki ta iya. Umma tai murmushi irin na manya tace "Aishi wannan ƙyale shi, suyi ta nemowa suna bamu muna cinyewa" Ammar yace "yau dai na ganku a rana keda Umman" Mufeeda tace "Dan Allah Umma karfa yayi mana dariya, Anty Maryam kisa baki mana" Anty Maryam tace "Gaskiya Umma kar kisa Yayi mata dariya mana" Da ƙyar Umma ta karɓa, tana ta mata Addu'a dasa Albarka kamar ta bata duniya, suka yi Sallama suka tafi. Seda suka shiga Ammar ya nuna mata dabbobin ta, suna ta hayayyafa gwanin sha'awa, Sannan suka tafi. Bayan fitar su Mufeeda Anty Maryam ta bawa Umma labarin abunda su Fa'iza suka yi wa Mufeeda, da yadda ta zauna a gurin ta bayan sun samu Saɓani, Abun ya daki zuciyar umma, tayi tayiwa Ammar faɗa idan Fa'iza tazo tace ya mata wulaƙanci. Maryam tace "Wallahi Jidda ba kowace mace bace zata iya abunda Mufeeda tayi ba, na haƙuri da Ɗan uwan mu, Muddin kikayi dalilin kashe masa Aure wallahi kin cuce shi, kuma baze manta ba, nan ma Umma tai kan Jidda da faɗa, da taga alamun babu me goya mata baya, ta miƙe tai haramar tafiya, ranta a ɓace. Ammar yaji daɗin Abunda Mufeeda tayi, dan be san zata basu ba, suna tafe a hanya yace "Mufeeda Nagode sosai, Amma kuɗin da kika bawa su Umma yayi yawa, karki kwashe jarin naki fa" Wata uwar harara tai masa wanda hakan ya shashi yin shiru, suka tari abun hawa zuwa unguwar su Mufeeda. Suna yin Sallama ta tarar da Baba ze fita, ai da gudu ta tafi ta rungume shi, seda Ammar yaji tsoron karta jiwa kanta rauni, ko nauyin cikin bata jiba take wannan tsallen. "Autar Baba naga kin zama ƙatuwa, Ammar me kake bata ne? Ta cinye maka tuwo ko?" Murmushi Ammar yayi suka gaisa da Baba, Baba yace "tunda 'ya' ya na sunzo bari in zauna muyi hira" Ammar yabi Baba ɗakin sa, Mufeeda ta ƙarasa gurin Mama, Ta tarar da Yaya Fadeela, Yaya Fadeela ta hangame baki tana bin Mufeeda da kallo, Mufeeda ta rungume Mama tana Shagwaɓa. "Mamana ina Missing ɗinki sosai" Fadeela tace "Auta wannan ƙiba haka? Ke kuwa me kike ci haka?" "Abunda kike ci mana" Hira suka shiga yi, Fadeela tace "Auta a cire hijjabin mana, kowani salon ne kuma haka?" "bazan cire ba ɗin" "Autar Baba kodai kodai" Hararta Mufeeda tayi tace "Kodai me?" Ammar yai sallama a falon Mama suka gaisa, sannan yace ze tafi bayan la'asar zezo su tafi. Mufeeda ta tashi ta tafi rakashi, suna fita Fadeela tace "Mama kinga abunda nagani kuwa?" Mama tace "A ina?" "Kamar ciki ne da Yarinyar nan fa" "Hmm Fadeela kenan, nagani mana se fatan Allah ya raba lafiya" Mufeeda ta dawo falon suka cigaba da hira, tunda Mufeeda ta cire hijjabin ta Fadeela taga cikin Mufeeda har ya fito, ta dinga tsokanar ta. "Mufeeda ni zan miki wankan Jego fa in kin haihu" "Allah ya kiyaye, wallahi ba zaki minba" "Ohh ni Fadeela, wai Mufeeda da ciki" "Eh ya ranki? Shiyasa nake raina ki takuramin kike" Haka Mufeeda suka wuni suna hira, Fadeela tana ta tsokanar ta, duk lokacin da Mufeeda tazo gida idan tana hira Mama tana fuskantar Mufeeda na cikin kwanciyar hankali, Ammar ya isa da gidan sa, ta dinga tuna lokacin da take ƙoƙarin hana Auren nan, yadda mazan yanzu suke se a hankali samun kamar Ammar se an tona. ********************** Wata ɗaya da sakin Saima Jabir yana ta shirin Aurensa, Saura Sati biyu a fara biki, Amma Ammar, da Aminu sam basa goyon bayan Auren Jabir, dan haka sam besa su shirgin Auren sa ba. Saima kam tana murmurewa, ta siyo form ɗin makaranta ta cike zata koma, dama tayi N. C. E, ta sai D. E Form zata koma Jami'a, ta tura aka kwaso mata kayan ta tsaf daga gidan Jabir, dukda gwaggonta ba wata me ƙarfi bace, Amma sam bata tsangwamar Saima, Saima ta iya ɗinki dan haka ta cigaba da sana'ar ta, suna rufawa juna Asiri, nan da nan ta fara dawo da ƙibarta kamar ba ita ba. Sa'idu me kayan miya aka yanke masa hukunci zaman shekara uku a gidan yari ƙarƙashin wata kotun Addinin musulunci, tunda Abun nan ya faru layin su Mufeeda suka zauna lafiya, ba gantali ba tashin hankali kowacce tana gidan ta, idan suka haɗu da Hajara a hanya har guduwa suke su ɓuya Ammar ya dage sosai da zuwa kasuwar nan, da safe ya sauke kaya a biya shi, ya siyo wani abun ya fito bakin kasuwa ya siyar, ɓangaren Mufeeda ma likkafa ta cigaba, yanzu har manyan kuloli take cikawa da kayan sanyi, Almajirai suzo su ɗauka sukai mata kasuwa Da yake Mufeeda tasu ta ɗanzo ɗaya da Hajara, ta bata shawarar ta dinga haɗawa da snacks za tayi ciniki, dan sune Abincin shaf shaf mussman ga ma tafiya, Aikuwa Mufeeda ta shawarci Ammar ya bata goyon baya, a hankali ta fara haɗawa da snacks ɗin. Wataran se Ammar ya dawo da daddare yake temaka mata ta haɗa kayan siyarwar, saboda cikin ta ya tsufa. Duk abun nan Sam Ammar besa mata ido akan abunda take samu ba, ba ruwan sa sannan babu abunda ya fasa yi na hidimar gidan sa. ********************* Satin bikin Jabir ya kama akai biki aka sha shagali, aka yi ɓarnar dukiya, kamar yadda akayiwa Jabir Alƙawari aka bashi gida da mota, aka sake masa Aiki a kamfanin Mahaifin Fatiyya. Sedai tun a ranar farko da ta tare Jabir ya gane Fatiyya tasan Maza, Amma ba shi da ikon magana ko dan wannan daular da'aka sa shi a ciki, haka nan ya haƙura bece komai ba. Ammar sun gama sauke kaya a kasuwa, yana shirin tafiya Wani hamshaƙin Alhaji da suka gama sauke masa kaya, yasa aka kira masa Ammar,Ammar yazo suka gaisa. Ammar a nutse yake sam baya wannan rawar jikin da sauran suke idan sunga Alhajin, Alhajin yace "Dan Allah in ba zaka damu ba kuɗi nake so ka kaimin banki" Ɗan zare ido Ammar yayi, shi dai yasan ba ma'aikacin Kamfanin Alhajin bane, kawai aikin sa idan ya shigo kasuwar za'a sauke kaya ya sauke a biya shi, Amma me yasa yace masa ya kai masa kuɗi banki? Alhajin yace "Dan Allah ka temaka, in bazaka damu ba, na yaba da hankalin ka ne, depositing kawai zakayi min, ga kuɗin can a mota, me kaimin ne baya nan, million biyar ne" Kallon rashin yadda Ammar yake wa Alhajin, Alhajin ya miƙa masa mukullin motar, jiki a saluɓe Ammar ya karɓa yakasa cewa komai, Ya rubuta masa Account details ɗin ya bashi. Hakanan Ammar ya tsinci kansa da kasa musawa Alhajin saboda dattijantakar sa. Ammar ya kai kuɗin ya karɓo receipt ya dawo kasuwa Amma Alhajin baya nan ya fita amma ze dawo. Ammar ya zauna ya jira ko gurin tasa sana'ar beje ba, se bayan la'asar sannan Alhajin ya dawo, yana zuwa ya tarar da Ammar, yace "Yi haƙuri Ammar, na zaunar da kai, da kasani ka tafi, ka kawomin receipt ɗin daga baya" Ammar yace "A'a gara dai dana jira, gashi, kuɗin million bakwai ne ba biyar ba" Ya miƙa masa receipt, yasa hannu ya karɓa ya dinga juya receipt ɗin yana kallon Ammar, yana nazarinsa, yace "Nagode sosai Ammar, na ɗauka " ya zura hannu a Aljihu ya ɗakko bandir ɗin kuɗi naira dubu ɗari ya bawa Ammar. "A'a bazan karɓa ba, ba seka biyani ba" "Ammar ba biyan ka nayi ba, kyauta ce fa" Girgiza kai Ammar yayi yace "Nagode, Amma ka barsu" daga nan ya juya ya tafi. Jabir ya fara gane kuskurensa, dan satin Fatiyya biyu bata girki sedai suci takeaway, ga yawo kamar masifa, bashi da ikon ya tambaye ta ina taje? Ko ina zata? Data raya mata seta fice abun ta, sekuma ya ganta, be isa tayi abu yayi magana ba seta balbale shi da masifa, ga rashin kunya da ƙazanta, zata gyara jikin ta Amma banda mahallinta, ga gayyar ƙawaye kowa ƙawar ta ce, Abun duniya ya fara damun Jabir, da yana ganin Saima bata iya komai ba, se gashi Fatiyya kamar rainon gaɓaye jaka take, ko magana bata iya ba, ga rashin kintsi. A hankali Alhaji Haruna yake karantar Ammar, Ammar ba ruwan sa da kowa, da yaje kasuwa abunda ya kaishi kawai yake yi, dan ko Abokai bashi da su. Alhaji Haruna duk lokacin da ya tashi Aiken kuɗi seya aiki Ammar, kuɗi bana wasa ba maƙudan kuɗi masu nauyin gaske. ************* ********* Ammar kafin ya fita se yayiwa Mufeeda aikin gida, da daddare ma idan ya dawo haka, wataran kuma ya kira Halima a waya yace tazo ta taya Mufeeda aiki, Ammar yace idan cikin ya cika wata tara ze maida ita gida koda Naƙuda zata tashi baya nan. Ranar data shiga wata na tara, Cikin dare kusan ƙarfe biyun dare labor ya kama Mufeeda, tashin Ammar tayi a gigice tana jin ciwon har cikin kanta. Gaba ɗaya Ammar ya ruɗe, tausayinta ya kama shi, kamar ze kuka yace "Sannu Mufeeda, bari in fita inga inda zan samo abun hawa" Riƙe shi tayi gam ta hana shi fita ko ina, se salati take, vest ɗin Ammar kuwa da ta riƙe ta seda ta tale har cikin sa. Ta dinga sintiri a ɗakin, Ammar ya kasa fita, gani yake daya fita wani abun ze sa meta, se Addu'a yake Allah ya raba ta da cikin lafiya, tun tana iya tafiya harta durƙushe tana ambaton Allah. Waya Ammar ya ɗakko a gigice yana ƙoƙarin kiran waya, kawai yaji kukan Jariri yana ɗaga kai yaga Mufeeda ta haihu yaro Jariri yana ta tsala kuka. Jifa yayi da wayar ya taho kanta da sauri, ya riƙo hannun ta yace "Sannu Mufeeda" murmushi tayi masa tare da gyaɗa kanta, ta nuna masa Akwatin da ta shirya kayan haihuwar ta, kamar yadda Mama ta gaya mata, ta nunawa Ammar yadda ze yanke cibi da komai. A ƙarshe dai Ammar ne ya gyara komai, hatta kayan jinin data ɓata da ɗakin shi ya zage ya gyara su tsaf. Dama Mama ta koyawa Mufeeda komai, in case haihuwa zata ka mata babu wani a kusa. Kamar ba Mufeeda ce tayi labor ba, ya dafa mata ruwa tayi wanka ta kintsa jikin ta, Jaririn ƙato dashi se kuka yake yi. Haka Ammar ya rungume Mufeeda da Jaririn yana godiya ga Allah, wai Yau ƙwailarsa ce ta haifa masa Jariri, waze maka wannan kyauta inba Allah ba, Ga mace ta gari ga ɗa. Da safe duk wanda suka kira suka ce Mufeeda ta haihu se yaita mamaki, Mussman idan akace ita kaɗai ta haihu, kafin kowa yazo gidan Ammar ya share ko ina ya dafa Abinci taci. Da Mama taje gidan tayi mamaki taga ko ina tsaf, Mama tace "Auta dan Allah ke kaɗai kika haihu?" "Hajiya Mama kenan, wallahi da gani se Yaya Ammar, Allah ya bani da sauƙi ko ciwon mara da kikace banji ba lokaci ɗaya ciwon ya taso min cikin dare" "Sannu Autar Mama, ga farfesu nan na taho miki dashi ki samu kici" "A ajiye se an jima, Yaya Ammar ya dafa Abinci naci" "Ikon Allah, lallai Allah yasaka wa yaron nan da Alkhairi" Kwana uku da haihuwa Ammar ya shigo da wata ƙatuwar Akwati, wanda suke ɗakin Mufeeda suka fito suka basu guri. Ammar ya kalle ta yace "Ƙwaila ta Ammar" Ta tura baki tace "Ai wallahi na zama mace, tunda na haifi wannan me kukan" Murmushi yayi yana jan hancin ta, ya turo mata Akwatin gaban ta, ya karɓi yaron ya kwantar da shi, Sega Ammar yana ɗaukar Jariri, da baya ɗauka dan gani yake yayi ɗan mitsitsi dayawa. Cikin Mamaki ta buɗe Akwatin, kayan Jariri ne, duk abunda ake buƙata kayan wanka diapers ba abunda babu, itama ga sabon kaya kala uku da turaruka da sabon takalmi da Jaka. "Kayan robobin kuma suna ɗakin tsakar gida, na siyo fulawa da shinkafa, abun hakika kuma Abba ya bayar, sannan kuɗin da muke tarawa na bar miki nawa da nakin, seki haɗa ayi hidimar suna" "Yaya Ammar, ina ka samu kuɗi haka muna fama da kanmu? Yaya Ammar meyasa ka takura kanka" "ba takura bace, haƙƙina ne inyi, kuma na daɗe ina tara kayan, Anty Maryam nake bawa kuɗin ta siyo, fatana Allah ya barmin ke, sannan ya raya mana Ibrahim Khalil a tafarki madaidaici ina Alfahari dake Mufeeda" Rungume Ammar tayi tana kuka tace "Allah ya ƙara Arziki Mijina, Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira, mungode, mungode, we loves you Abu Khalil" "Mentioned it not sweetheart, ni yakamata inyi godiya" Ta tattare kayan ta kira Mama tace "Mama ku tayani godiya, kinga siyayyar da Yaya Ammar yayi mana" Nan ma Mama taita Addu'a da saka Albarka. Yaya Fadeela tace "Mufeeda gaskiya ki bani sirrin wannan soyayya haka, Allah sarki nan muka dinga surutan kinyi ƙanƙanta da Aure yayi miki girma, kawai se mu gaki da ɗa, ohh Auta manya" Mufeeda tace "kyaji dashi dai" ******************** Abun duniya ya ishi Jabir, Fatiyya tasa shi gaba da rashin mutunci ga gori na masifa, gashi ba damar ya kai ƙararta gidan su, ba akaiwa iyayen ta ƙara ɗan su, gantali ga Almubazzaranci, daga iyayen sa har 'yan uwan sa basu isheta kallo ba. Ɗaure take da towel ta fito daga cikin banɗakin dake cikin ɗakin hotel ɗin, ta kalli mutumin dake kwance akan gado yayi ɗaiɗai, ta ɗan yamutsa fuska tace "Alhaji ka tashi kayi wanka ka maida ni inda ka ɗakko ni, bana jin daɗi" Washe baki yayi yana shafa cikin sa yace "Fatiyya manyan mata, nifa banƙi mu kwana anan tare ba" Haɗe rai tayi tace "Kafiye wasa, dan Allah ka tashi jini nake zubarwa fa" Zaro ido yayi yace "jini kuma? meya haɗa ki da zubar da jini?" "Inaga ciki ne dani fa, kamar ɓari zanyi" Alhaji Idris yace "ke se kace ba wayayyiya ba, tun abaya da muke tare da ke baki yi ciki ba se yanzu? Daga yin Auren seki bari kiyi ciki" "Kaga nifa ban san da cikin nan, dan Allah kayi ka maidani, dan banzo da mota bane da bazan tsaya jiran ka ba" "Kai Amma ban gama shagali na ba kin katsemin jin daɗi" "Koma meye ai kaine ka janyo shi, dan Allah Alhaji Idris kayi sauri" Haka ya tashi ya shiga yayi wanka, sedai me yana fitowa ya tarar da ita a kwance kamar ba rai a jikin ta jini ya malale a gurin. A gigice ya zaro ido, ya dinga jijjigata yana kiran sunan ta Amma shiru, bata Amsa ba, da gudu yasa rigar sa ya fice, fitar tasa tayi dai2 da kawo Abincin da suka yi order, yaga Alhaji Idris ya fice da sauri, da sauri ma'aikacin yabi bayan Alhaji Idris yaga ya shige mota ya, aikuwa ya haddace lambar motar sa. Ya koma ɗakin ya tarar da Saima a kwance cikin jini male male. Ranar suna Jariri yaci suna Ibrahim Khalil, Dai2 gwargwado anci ansha, Ammar yayi bajinta daidai ƙarfin sa. Mufeeda ta samu Alheri sosai. Anty Murja ce ta zaunawa Mufeeda saboda jego, Sam Ammar da Mufeeda basa jin kunyar Anty Murja, su barta da rainon ɗa su shige ɗaki suyi ta cin dariyar soyayyar su, Anty Murja tayi mamakin yadda Ammar yake barkwanci da dariya haka, yadda yake haɗe rai da miskilanci idan za'ace yana magana ma seka Musa, Amma wataran a falo suke soyayyar su shida Mufeeda, ba ruwan su da idon Anty Murja. Ranar da Ammar ya koma kasuwa Alhaji Haruna yasa aka kira masa shi, Ammar yaje suka gaisa. Alhaji Haruna yace "Ammar kwana biyu baka shigowa kasuwa lafiya kuwa?" "lafiya ƙalau, me ɗakina ce ta haihu shiyasa" "Masha Allah, Amma babu Labari, Allah ya raya abunda aka samu, Amma gaskiya zanzo har gida in ga Jariri" Ammar yace "to Nagode sosai, Allah ya kawo ka" Bayan Alhaji Idris ya bar hotel ɗin nan ya gudu ya bar gari, yana ta shirye2 barin ƙasar aka kira shi a waya aka sanar masa hukumar custom sun kama kayan da yayi order, Nigeria bata buƙatar irin wannan kayan, gaba ɗaya ya gigice ya rasa abunyi, gaba ɗaya dukiyarsa ya narka akan kayan nan Amma wai custom sun kama kayan. yana ƙoƙarin kiran abokin kasuwancinsa 'yan sand suka zo suka kama shi a gurin. Jabir ya shiga tashin hankali jin A hotel aka ga matarsa tayi ɓari, kuma abokin iskancin nata ya gudu, Jabir yayi kuka, dan yasan Alhakin Saima ne ya kama shi. Ya shirya ya tafi gidan Gwaggon Saima, yasa aka yi masa Sallama da ita, ba tasan ko waye ba ta fito, tana ganin Jabir ta haɗe rai tace "malam me kake mana a ƙofar gida?" Jabir ya fashe da kuka yace "dan Allah Saima kiyi haƙuri ki yafemin, Alhaji kine yake ɗawainiya dani, dan Allah kizo mu koma mucigaba da rayuwar mu, wallahi na canza hali" "Allah sarki, kuma gashi ka makara, dan ko baka makara ba babu ni babu komawa gidan ka, sedai ina maka Albishir ranar Asabar za'a ɗauramin Aure, zan Auri sirikin ka wato mahaifin Saima, sedai ni ba Auren Jari zanyi ba" Ta juya ta shige ta bar Jabir a tsaye, abun takaici yana komawa gida ya tarar da Saima yai mata rashin mutunci yace tabar masa gidan sa tace sedai ya bar gidan, dan gidan uban ta ne bana uban sa ba. Jabir yai mata saki uku sannan ya bar gidan. Baban Fatiyya ya shigar da ƙarar Alhaji Idris akan ya sace masa 'ya yai mata Fyaɗe, aka hana shi kare kansa yanaji yana gani aka kulle shi. Bayan ya Auri Saima haka Fatiyya ta koma gida, duk yadda babarta take juya mahaifin ta ƙarshe' yan kallo suka zama dan se abunda Saima take so akeyi. Alhaji Haruna yaje gidan Ammar yaga Jariri yayi masa Addu'a sannan yace "Ammar babban dalilin zuwa na gidanka shine, A baya na jarrabaka gurare daban daban, Na lura kana da Amana sannan ka birgeni saboda rashin girman kanka da Amanarka, wadda tayi ƙaranci a yanzu, shi ne nace Akwai branch da zan buɗe na saida kayan masarufi da nake yi, zan zuba kayan million Ashirin, ka riƙe gurin ka ɗau ma'aikata ku riƙe gurin, idan shekara tayi zaka dinga raba riba biyu kana biya na, a hankali har shagon ya zama mallakinka" Zare ido Ammar yayi yace "Aini ban taɓa kasuwanci ba, ta yaya zan iya juya dukiya me yawa haka?" "zaka iya Ammar, ina so in taimake kane, dan a rayuwa ta ina son inga na temaki na ƙasa dani shima ya tsaya da ƙafar sa, na jinjina maka dan har unguwar nan nazo nayi bincike akan ka naji daɗin yabon da naji ana maka" Ammar yayi shiru yace "to zamuyi shawara da Madam, abun da muka yanke shikenan" Alhaji Haruna yayi murmushi yace "Kai wannan Madam ana ji da ita, ko dai in baka 'yane, naga ka iya riƙe gida" Ammar yace "daga ita ba ƙari ai" "shikenan Ammar, da wasa nake maka, sena jika" Mufeeda tayi farinciki da jin labarin, tace "Yaya Ammar mahaƙurci mawadaci, wataƙila da sana' ar A daidaita sahu kake ba lallai ka samu wannan Ni'imar ba, Ammar da yake Allah me hikima ne, seya raba ka da Napep ya maida kai kasuwa, yanzu dai muyi ta istikhara tukuna inda Alkhairi Allah ya tabattar, sannan kayi shawara dasu Abba " Haka kuwa akayi, bayan yin Addu'oi da Neman shawara, Ammar ya Amince ya karɓi shagon, Allah yasanya masa Albarka ya dinga ciniki, nan da nan Ammar ya zama hamshaƙi. Da Khalil ya isa yaye, ya kaiwa Umma shi ya nemo wa Mufeeda Admission, ta shiga makaranta, seda Ammar ya cika Alƙawarin da yayi wa Baba akan karatun Mufeeda. A hankali Ammar ya gama biyan Alhaji Haruna kuɗin sa, shagon ya zama mallakin sa, ya canza gida ya sai mota, kullum cikin neman taimako ake a gidan Ammar, duk me wata buƙata in dai ya biyo ta gurin Uwargidan Ammar anyi ta an gama, dan Mufeeda bata taɓa cewa abu yaƙi, 'yan uwa da abokan Arziki babu wanda baya morar Arziƙin Ammar. Faruk ya haɗu da ciwon sugar, gaɓoɓin jikin sa suka dinga gutsurewa suna zubar da ruwa. Fa'iza kuwa har shekara talatin babu wanda ya Aure ta. Ammar ya zama hamshaƙin ɗan kasuwa, ya buɗewa Mufeeda Ƙaton gidan gona, aka ci gaba da yi mata kiwo, ta zama wata uwar mata. A duk lokacin da aka tashi yin interview da Ammar, idan aka tambaye shi meye matakin Nasarar ka a rayuwa? Waye wanda kake kwaikwayo, waye ya baka ƙarfin gwiwa akan harkar kasuwanci? Amsar ɗaya ce yake bayarwa "Mata tace" Duk lokacin da ya zauna zeyi misali se ya bada misali da Mufeeda, ya kance "A baya ina raina Mata, ina ganin babu macen da zata iya sauyamin ra'ayi, seda na Auri Mufeeda na gane 'WATA KISSAR SE MATA' Allah yayi musu baiwa da hikima, na sarrafa zukatan maza, idan Allah ya baka mace tagari kamar Mufeeda ka gode Allah, dan Mufeeda 'yar Aljanna ce Insha Allah " Mufeeda ta haifawa Ammar yara huɗu, seda ta zama professor akan harkar sadarwa, mata da yawa sukanzo mata da matsololinsu ta basu shawara, mussman take gabatar da shirye2 a kafafen watsa labarai, sannan ta mallaki personal blog ɗinta da take wayar da kan mata akan sha'anin zamantakewa. Kullum a kamata tambaya ko zata bada misali da Ammar take bayarwa "Mijina ɗan Aljanna ne Insha Allah, da dukkanin maza zasu sauke haƙƙoƙin dake kansu, su kuma mata suyi biyayya da tabbas mutuwar Aure zata ragu, kuyi koyi da hali irin na Alhaji Ammar" Ire iren wannan hirarrakin nasu yana matuƙar burge mutane. Tammat bihamdillah, Masha Allah, Alhamdilillah, Rabbigfir zanbi kullahu, diƙƙahu, wa jillahu, sirrahu, wa alaniyatuhu. ANAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN GAJEREN LABARIN ME SUNA WATA KISSAR... SAI MATA, INA FATAN AN AMFANA DA DARUSAN DAKE CIKI. ABUNDA NA RUBUTA NA DAIDAI DAGA ALLAH NE, AKASIN HAKA KUMA DAGA NINE INA FATAN ALLAH YA YAFEMIN. SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! Haɗaɗen littafin nan dana fara kawo muku na dakata da kuka daɗe kuna jira me suna AƘIDA TA insha Allah yana nan tafe a watan September, ku kasance tare da Alƙalamina domin jin me littafin ke ɗauke dashi, idan kina daga cikin wanda basu karanta littafin ABDUL JALAL ba kuwa, to ki garzaya ki nemi naki, domin jin cakwakiyar dake cikin sa, Insha Allah bayan AƘIDA TA, Akwai sauran daɗaɗan litattafan da suke daf da isowa gareku domin faɗakarwa, da nishaɗantar da ma'abota fahimtar wannan harshe namu na Hausa. Karku manta link ɗin voting na zaɓen gasar dana shiga yana nan tafe, ina fatan zakumin kara in lokaci yayi ku zaɓi labari BAƘIN TABO gajeren labarin gasa Ina buƙatar jin ra'ayoyinku akan wannan littafi dana kammala, domin gyara, sharhi, ko kuma shawara, kai tsaye a tuntuɓeni ta wannan lambar Ayshercool 07063065680 Ku asancni a cikin sabon littafina da zd e zo muku a 1st september insha Allah mai suna AƘIDA TA