*WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* *Alhamdulillahi I'm back after a long break...* *©All right reserved... No individual, group or organization is allowed to copy, translate, publish or read this content on the public space, radio station, YouTube, social media or any other outlet without the authorization of the original writer, Aisha Muhammed Alto.* *Bismillahir Rahmanir Rahim* __________________________ *TALLA! TALLA!! TALLA!!!* *SADAUKARWAR SO!!!* *Sun taso tun yara tare...Iyayensa sun fifitasa akansa shima yafi fifita buƙatun ɗan goggonsa fiye da buƙatunsa, a tasowarsu kowa halayyarsa ta bambanta yana jin daɗi da sha'awar ganin rayuwarsa cikin barkwanci saɓanin shi daya kasance magana ma wahala take mai...Rana tsaka dalilin maƙotaka wata yarinya ta ratso rayuwarsu ya fara sonta ba tare daya sani ba, ashe shima ɗan uwansa ya kamu da soyayyarta, bashi da zaɓi illa yin SADAUKARWAN SO...!* *Ba tare da kowa yasan yana sonta ba...Ya binne abun a ranshi bai taɓa koda wasa wani daga cikinsu ya fahimci abinda ke cikin zuciyarsa ba...Kamar yadda yayi SADAUKARWAN SO haka shima akayi mai SADAUKARWAN SO...!* Shin wace irin Ƙauna ce haka a tsakaninsu da har zai iya ma ɗan uwansa SADAUKARWAN SO...? Nasan kuma dole zaku yiwa kanku waɗannan tambayoyin, kuma zaku zaƙu da son jin amsarta..To tambayar taku ɗaya ce amma amsoshinta suna da yawa kuma ba'a ko'ina ne zaku samu amsarta ba sai a cikin wannan shahararren labarin SADAUKARWAR SO wanda shahararriya kuma fiƙrarriya zaƙaƙurar marubuciya ta rubuta wato *JAMILA UMAR JANAFTY* kuma zaku iya samun duk wannan garaɓasar da romon daɗin labarin ne akan farashi mai rahusa kamar yadda ta saba muku: *Zaku biya kuɗin karatu ₦300 ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* *KO* *Katin MTN ₦400 ta wannan lambar 09069067488* *Ƴan Niger kuwa zaku iya tuntuɓarmu akan wannan lambar +22794775574* Karku sake ayi babu ku domin wannan tafiyar miƙaƙƙiya ce mai nisan zango mai neman ƙarin bayani sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 09069067488 muna maraba daku masoya sai kunzo🤝 ___________________________ *KADUNA STATE* *Igabi Local Government* _Area Rigasa..._ 1️⃣ Alarm ɗin daya saka domin ya riƙa tadashi ƙarfe huɗu da rabi na asuba, shine ya fara bugawa cikin ƙaramar wayarsa ƙirar Nokia. Da hanzari ya miƙe zaune daga barci mai nauyi daya kwashesa tun na daran jiya sakamakon ya gaji ɗakin da duhu amma haka ya laluba gefen katakon gadon ya lalubi wayarsa ya kashe alarm ɗin lokaci ɗaya yana kunna fitilar dake jikin wayar haske ya gauraye ɗakin. Ƙafafunsa ya zuro ƙasa lokaci ɗaya yana miƙa da kuma bayyana salatinsa tare da addu'an tashi daga barci gefensa ya kalla lokaci ɗaya ya miƙe yana gyara zaman bakin dogon wandon dake Jikinsa, daman babu riga, tana kwance ta nannaɗe cikin bargo tana sharar barcinta cikin kwanciyar hankali ya daɗe yana kallonta kafin kawai ya kaɗa kai yana tuna irin rigiman da suka tafka jiya kafin su kwanta bai san yaushe ne FADWA zatayi hankali ba. Fita yayi daga cikin ɗan madaidaicin ɗakin ƙaramin kichin ɗin dake tsakar gidan ya shiga ya fito da ƙaramin murhun gawayi, sai da ya fito dashi waje kana ya ɗibi ruwa a buta ya shiga ƙaramin makewayin da aka karesa da langa langa ya kama ruwa bayan ya fito ne ya duƙufa hura gawayin da ledojin daya fito dasu, da ƙyar ya hura gawayin duk idanuwansa sunyi jawur da ƙyar ya samu ya ɗora wata ƙaramar tukunya ya cikata da ruwa kana ya koma ya ɗauki tsintsinya ya fara sharan ƙaramin tsakar gidan mai shimfiɗe da siminti ya share tas ya kwashe kana ya ɗauki manyan botikai ya fita waje can gangaran layinsu ya riƙa ɗebo ruwa yana zuwa yana dawowa sai da ya cika duka manyan bombun Fadwa har guda uku kana ya dakata ganin har 5 tayi na asuba ruwan wankan ya duba yaga yayi zafi ya ɗiba sai ya ƙara ruwan ya sirka ya shiga wanka bai wani jima sosai ba ya fito ya shiga ɗakin har lokacin Fadwa bata tashi ba bai mata magana ba sai da ya shafa mai ya buɗe ƙaramar jakarsa ya ɗauko wata jallabiyarsa mai ruwan toka ya saka da hularsa. Har ya sa ƙafa zai bar ɗakin sai ya fasa ya dawo da baya ya isa jikin gadon yana buga katifar cikin sanyin muryarsa yake faɗin "Fadwa...Fadwa..ke Fadwa...." Yake faɗa yana buga gadon ganin ko motsi taƙi yi yasa ya daki ƙafarta yana ƙara kiran sunanta cikin takaici da ƙunƙuni Fadwa ta motsa tana yamutsa fuska kamar taga kashi cikin ɗaurewar tuska ta waigo tana kallonsa daga hasken fitilar maƙarfin daya kunna acikin ɗakin. Cikin haɗe rai yace "Ki tashi kiyi alwala ki yi raka'atanil fijir kafin a tada sallar asuba...." Ko gama rufe baki bai yi ba taja wani uban dogon tsaki da ƙarfi ta juya ta ƙara dunƙulewa, abun sosai ya bashi mamaki duk da yasan halin Fadwa duniya kaɗai ta sakama gaba bata ma damu da sallar ba sai ya matsa mata sosai take sallar asuba sauran sallolin kuwa bai san ko tana yi ko bata yi ba tunda baya wuni a gidan ita kanta ma ba zaman gidan take yi ba. Kamar zai ƙyaleta sai kuma yaji ai bai kamata ya barta tai ta barcin asara ba da sauri ya duƙa ya fizge bargon jikinta cikin wani wawan fushi ta waigo tana watsa masa kallon banza kafin ta tashi zaune tana mutstsike ido kanta duk ya hargitse yayi buzu buzu saboda ba kitso akan nata cikin wani takaici ta kallesa daga sama har ƙasa tana faɗin "Meye haka Malam...? Dillah ni bani bargona kasan dai ni na siya abuna da kuɗina bada guminka na siya ba...." Bai damu ba illah kai daya girgiza yana faɗin "Wallahi bazan baki ba komai zaki ce...Malama ki tashi lokacin sallah yayi...." Taso mai tayi da faɗa tana faɗin "Ce maka nayi bazan yi sallar ba...? Kai fa wallahi mugun ɗan rainin hankali ne tsiyata da kai kenan aikin riya komai sai ka nuna kai na Allah ne...." Ransa ya ɓaci sosai da kalamanta cikin takaici yace "A'uzubillahi Allah ya rabani da aikin riya Fadwa...matsawar da kika ga ina miki kuma saboda sauke hakkin ki dake kaina ne na baki tarbiya na kula dake, ke matata ce ina da ikon dawo dake kan hanya in naga zaki karkace Fadwa...." Hannu ta ɗaga mai tana faɗin "Naji ubana sarkin tarbiya nidai bani bargona kai talaka da kai faƙiri baka da ko sisi har kake faɗin zaka iya tarbiyantar dani...to ta ina ma....?" Ta ƙarashe maganar cike da rashin kunya tana harararsa. Bai damu ba illah juyawa da yayi yana faɗin "Bazan baki ba..sai fa kin tashi kinje kinyi sallah Malama...." Baki ta tura kawai tana kallonsa sanin halinsa na taurin kai da nacin tsiya yasa ta zuro ƙafarta ta sauko daga kan gadon ƙaramar rigar barcinta iya gwiwa ta bayyana miƙa tayi tana hamma lokaci ɗaya cikin takaici ya kalleta yana faɗin "Sau nawa zan gaya miki ki dinga salati in zaki yi miƙa ki kuma riƙa rufe bakin ki in zaki hamma amma kalli abinda kika yi yanzu wannan ai ba ɗabi'a bace ta ɗan musulmi na ƙwarai...." Ko kallonsa ba tayi ba ta raɓa ta gefensa zata fita ya riƙo hannunta yana faɗin "Ya zaki fita haka...? Kalli ƙaramar rigar jikinki fa...? Kanki kuma ko ɗankwali babu, safiya batayi ba kada ki manta ko sallar asuba ba'a tada ba..." Haushi ya ƙara kamata ta waigo azafafe zatayi magana ya girgiza mata kai yana faɗin "Don Allah ba don ni ba kada ki fita a haka ki suturta jikinki Fadwa...." Ya faɗa lokaci ɗaya yana langwaɓe mata kai alamun roƙo bata da yadda zatayi dole tayi shiru cikin ƙufula ta koma ciki tana ƙunƙuni ita kaɗai yana kallonta ta ɗauko zani ta ɗora saman rigar barcin jikinta ta kuma ɗauki ɗankwalin doguwar rigarta baƙa ta saka tana ɗagowa suka haɗa ido dashi, ido ta waro masa tana faɗin "Sai kuma me....? Ka ce sai na tashi kuma na tashi kace na suturta jikina kuma nayi yadda kace bibiyar ta isa haka a ajiye min bargona don Allah a ƙara gaba a daina ƙuramin ido haka nan kamar za'a cinye ni...." Maganarta sai ta bashi dariya sai da ya murmusa ya ajiye mata bargonta saman gado yana gyara zaman hularsa yana faɗin "Ni na tafi masallaci in zaki yi wanka ruwan wankan yana kan gawayi na ɗora miki..." Bata ma tsaya sauraransa ba ta raɓashi ta wuce ɗauke da wayarta wacce ta kunna fitila bayanta yabi suka fita tare yana kallonta ta zari buta ta shige banɗaki kai tsaye ko addu'a batayi ba, kai kawai ya girgiza kafin a fili ya furta "Allah ya shirya min ke Fadwa..." Daga haka ya fice daga gidan bayan ya zare sakatar ƙofar daya fita sai ya sakayata ganin anguwan shiru sai ɗai ɗaiɗai kun mutanen dake wucewa zuwa masallacin dake gaba kaɗan. Tana jin fitarsa daga cikin bayin ta saki tsaki tana faɗin "Gaskiya nidai an haɗani da aiki ga shegen talauci ga takura...." Ta faɗa dai dai lokacin data ke fitowa daga banɗakin, tsakar gidan ta ƙare ma kallo lokaci ɗaya ta taɓe baki domin ita bazata iya tuna yaushe ne ma ta taɓa sharan gidan nan ba tunda aka ɗaura mata aure da YA AZEEZ. Batayi alwalan ba kamar yadda tace ɗaki ta koma ta ƙara hayewa gado ta kwanta tana faɗin "Sai na tashi nayi sallar..." Ta faɗa tana ƙara duƙunƙunewa a cikin bargon tana ta sakin tsaki ita kaɗai kamar wata tsaka, daga nan barci ya ƙara kwasheta bata ƙara sanin komai ba sai da taji maganar Azeez asaman kanta kana ta buɗe idanuwanta cike da barci tana kallonsa sanye yake cikin riga da wando na wani yadi mai saukakkan kuɗi daga ganin yadin yaji jiki amma kuma yana wanke ne kuma agoge sai hularsa taɓani kaji Hadisi. Sama da kasa take kallonsa tana kuma ƙare mai kallo aranta kuwa faɗi take ga namiji har namiji sai dai talauci ya mai cikas, Ya Azeez kyakkyawa ne ajin farko domin dogon namiji ne mai cikar zati da haiba ba baƙi ba ne chocolate colour ne irin mai ɗan hasken nan, ga dogon hanci har baka wanda ya dace da kyakykyawar fuskarsa ga sajensa wanda ya zagaye ƙaramin bakinsa ya ke ƙarawa fuskarsa kyau da cikar zati da kamala Abdulazeez mutum ne na gari mai dattako da sanin ya kamata uwa uba ga haƙuri da kawaici, mai wadatar zuciya mai tsantseni da iyawa talaucinsa bashi da hange hange ko duban na gabansa, abinda ya sani kawai neman na kansa. Ganin ta shagala da kallonsa yasa ya duƙa ya tallabi kumatunta yana faɗin "Yau kuma ni ake son gani Fadwa...?" Sai lokacin ta dawo daga duniyar tunanin data faɗa cikin basarwa ta kauda kai tana faɗin "Ummhh..na kalli wa...? Dama kana da kuɗi ne sai nace ka mori kyanka amma kalle ka..kullum da safe sai ka fita kayi gararanba a gari kake samo abinda zamu ci..kai Allah karabamu da ƙangin talauci da auran talaka wallahi...." Ta faɗa cikin bayyanar tsantsar takaicinta. Bai damu da kalamanta ba ya kaɗa kai yana saka makullin napep ɗinsa cikin aljihun wandonsa lokaci ɗaya yana faɗin "Sai ki tashi kiyi sallar...ni fita zan yi..ga kayan tea nan na shigo miki dashi...." Mamaki ya kamata na ya akayi ya gane batayi sallar ba, bai bi ta kanta ba ya zura takalminsa na roba yana faɗin "Ga ɗari biyu nan saman gado..kiyi cefene ki dafa wani abun..duk da na tabbata ba girkawan zaki yi ba amma hakkin ki ne shiyasa nake baki saboda kada Allah ya kamani da hakkinki wata rana...." Bai tsaya saurarenta ba ya fice ta rakasa da tsaki kafin ta miƙe zaune tana bin ɗakin da kallo banda gadonsu dake cikin uwar ɗakan sai ɗan madubinta da ledan tsakar ɗaki a falo ba wani abun ƙwarai sai akwatunan kayansu ita dashi ɗakin fayau yake babu wani abun arziki aciki, tsaki ta saka kafin ta sauko daga kan gadon waje ta fita ta duba ruwan wankan da Ya Azeez ya saka mata ta juyo sauri sauri take sai da ta fito wanka kana tayi alwala ta koma ɗaki tayi sallar lokacin wajen ƙarfe 7:50am ne na safe bata damu ba tana idar da sallar ta fara tsara kwalliya cikin burgewa domin ba ƙarya ita kanta Fadwa ba baya ba wajen kyau da jikin mata. Tunda itama doguwa ce kuma tana da haske bata da munin fuska ga dogon hanci a fizge suna yanayin kama da AZeez ɗin ta ɓangaren yanayin tsarin fuskarsu sai dai ita fara ce sol, taci mintina sunfi talatin wajen tsara kwalliya kafin ta gama akwatinta ta jawo ta buɗe ta ɗauki wani leshinta mai kyau da tsada wanda kawarta Hajiya Labiba ta ɗinka mata ne cikin lokaci Fadwa ta fito tsaf kamar wata matar Alhaji gyalen kayan ta ɗauko ta saka sai jakarta mai kyau da ita lokaci ɗaya tana jefa ƙaramar wayarta a ciki ɗari biyun daya bar mata ta ɗauka tana yamutsa fuska kamar zata yi kuka ta jefa cikin jaka tana faɗin "Allah rabamu da auren matsiyacin namiji...ana harkar Dubai da Saudi amma ni harkar Nigeria Hayin Rigasa kawai nake ƙasƙanci zalla, ace kamata miji na bani 200 kuɗin cefene...." Bata tsaya gyaran ɗakin ba ballatana tayi kaye kayen kayan tea ɗin daya siyo mata wanda ko kallonsu batayi ba ta fito ta saka kwaɗo ta rufe ɗakin tsakar gidan tabi da kallo harta da murhun gawayin bata kauda shi ba ta saka ƙafa ta fita ta bar gidan bayan ta saka ƙaton kwaɗo ta kulle gidan tana ta wani ɗaure fuska domin tama fi jin ɗadin ganin gidan tana cikin gidan da sai ta fita ta kalli gidan sai taga Abba ya gama cutanta daya haɗata zama da makiri irin Ya Azeez. Tafiya ta farayi tana taku ɗaya bayan ɗaya duk wanda yaga Fadwa a lokacin sai ya ɗauka matar wani ƙusa ce ita, tafe take tana tsaki tana faɗin "Kai Allah rabamu da talauci...ni kam rayuwata ba cigaba na taso cikin baƙin talauci ubana na fama da mashin ƙarfe ƙarfe ƙawayena duk sun fini, ina tunanin in nayi aure zan huta ashe ba haka bane an riga an gama cutata kamata ina auran mai keke napep kullum yana gararan ba a gari da ace yau wani mai daula nake aure da daga gida mai kyau zan fito cikin lafiyayyan mota direba na jana Ac a gida Ac a mota, amma kalleni ina tafiya a ƙasa kamar wata wulaƙanttaciyar almajira...kai Allah ka azurtamu da azurtawarka ka rabamu da tsiya...." Take faɗa tana ƙara jin kamar igiyar auran ya Azeez dake kanta wani bala'i ne tana cikin wannan tunanin ta isa bakin titi ta samu mai Napep ta shiga bayan ta gaya mai inda zataje ya ja suka fara tafiya. Bai direta ko'ina ba sai ƙofar wani tangamemen get ɗin gida mai kyau da tsari fitowa tayi ɗari biyun data ɗauko ita ta bashi kuɗin keke napep ɗinsa ta nufi bakin get ɗin ta fara ƙwanƙwasawa bata jima ba megadin ya leko daman tun kafin ya leko yasan ba wani mai zuwan sassafe sai Fadwa yana ganinta A ɗage yace "Kai..jama'a yau ma dai...?" Wani kallon banza tayi mai kafin tace "Eh yau ma..ko zaka hanani shiga ne tunda gidan uban ka ne...?" Bai mata magana ba ya buɗe mata ƙofa yana faɗin "A'a wane ni na hanaki shiga...nima fa cin arziki nan nake..." Ƙaramin tsaki taja tace "Tunda kasan haka ka tsaya iya matsayinka..." Ta faɗa tana wucewa kamar zata tashi sama da kallo ya bita a fili ya furta "Kowaye mijin matar nan..wallahi bai yi sa'ar mata ba ko kaɗan..ace mace kullum bazaki zauni gidanki ba kina tafe kamar leda...." Ita kuwa batama jinsa tana ta kallon motocin dake harabar gidan lokaci ɗaya ta saki dariyar jin daɗi tana faɗin "Alhajin na ciki inaga...." Ta fada tana nufar ƙofar da zai sadata da cikin falon gidan. Yadda ta shiga cikin falon kanta tsaye babu wani jira zaka san ta saba zuwa gidan daga ganin falon zaka san ma mallakan gidan sun tara dukiya ko daga kujerun da suka zagayen falon zaka gane hakan, Fadwa ta riƙa bin ko'ina da kallo tana ƙarawa ko'ina yayi neat sai ƙamshi mai daɗi ke tashi gyalenta ta cire ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon jakarta ta ajiye tana faɗin "Ikon Allah..arziki na inda yake..ji Hajiya Labiba suna ma sama abunsu ita da Alhajinta basu ko tashi ba ji gidanta duk ƴan aiki kota ina sun gama mata komai..kai Allah ka rabamu da auran talaka wanda bai da ko sisi ka bamu mai wadata....." Ta faɗa tana wani ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya kafin ta ɗaga baki tana faɗin "Rabi..! Rabi..!!.." Rabi mai aikin Hajiya Labiba taji muryan Fadwa na kiranta fuska ta ɓata tana faɗin "Toh fa..su jarabatu iyayan kwaɗayi an zo kenan...." Sai da tace haka kana ta amsa kiran ta fito da sauri kamar zata kifa, har ƙasa ta duƙa tana mata sannu da zuwa cikin wani banzan kallo Fadwa take kallon Rabi kafin tace mata "Ke wuyanki har yayi kaurin da ina kiranki sai kin ga dama zaki amsa...?" Cikin kawo rantsuwa Rabi zata fara magana Fadwa ta ɗaga mata hannu tana wani jijjiga ƙafa kamar matar gidan kafin tace "Ban ce ki rantsemin ba Malama..ina so dai kisan matsayinki anan gidan aiki kike ana biyanki ba wata tsiya ba...." Rabi kanta na ƙasa tace "Haka ne Hajiya ki gafarceni..." Fadwa ta wani taɓe baki tana faɗin "Naji..tashi kije ki haɗo min breakfast..ki haɗo min tea mai kauri kada ki saka lipton, ki soya min ƙwai kamar guda huɗu da dankalin turawa nasan Hajiya Labiba bata rasa pepper chickens ki haɗo min dashi..." Da sauri Rabi ta miƙe tana faɗin "An gama Hajiya..." Ta faɗa tana wucewa kichin da sauri Fadwa ta bita da kallo tana wani sakin tsaki. Tana nan zaune sai ga Rabi ta dawo da faranti shaƙe da kayan karyawan da Fadwa tace a haɗo mata, kan Center table ɗin dake tsakiyar falon taja ta ajiye mata kana ta fita ta bar Fadwan na gyara zama kamar matar gidan haka ta zauna ta ci ta ƙoshi kana ta kora da lemo tayi gatsa tana faɗin "Alhamdulillahi...kaga inda ake harkar arzki...irin wannan karin shi nake fatan na dinga karo dashi duk safiya a gidana amma bana samu...." Ta karashe faɗa cikin takaicin tuna abun. Rabi ta kwalawa kira tana zuwa tace ta kwashe komai ta gama jikin Rabi na rawa ta kwashe komai zuwa kitchen domin yadda Fadwa ke tafiyar dasu ko Hajiya Labiba da ta ɗauke su aikin albarka shiyasa dole suke kiyaye mata. Fadwa tafi awa ɗaya da zuwa kana taji takun takalma faga sama ana saukowa ta ɗago idanunta ta sauke cikin na Hajiya Labiba da mijinta Alhaji Zayyanu Wakili suna riƙe da hannun juna Hajiya Labiba farar mace alkyabbar mata jikinta cikin kayan alfarma wuyanta da hannayenta cikin gwala gwalai, haka ma mijin nata cikin shigar gezner fara tas mai kyau da yarari. Sai da suka sauko kana Hajiya Labiba ta lura da Fadwa cikin mamaki tace "Lah Habibi kalli Fadwa..yaushe kika zo ban sani ba...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallonta da mamaki. Fadwa ta gyara zama tana faɗin "Sannun ku da fitowa..Alhaji barka da safiya..." Ya amsa cikin sakin fuska yana faɗin "Yauwa Hajiya Fadwa sannu da zuwa, shine kuma kika zo baki yi magana ba kike zaune ke kaɗai..." Kan Fadwa na ƙasa kamar wacce take gaban ubanta tace "Ahh ba komai Alhaji...ai da yake ba yanzu zan tafi ba..." Hajiya Labiba tace "Haba ƙawata ai ko da haka da sai ki kirani a waya kice kin iso...." Fadwa Tace "Ayi haƙuri ƙawa..." A tare suka saka dariya mijin Hajiya Labiba ya juya yana faɗin "Shikenan ni zan fita..Fadwa agaida gida...." Da sauri Fadwa tace "Adawo lafiya Allah ya tsare ya kiyaye hanya...." Cikin farin ciki yace "Ameen Allah yasa..." Hajiya Labiba ta kalli Fadwa tana faɗin "Ƙawata bari na raka Habibi na dawo Rabi kuwa ta kawo miki abun karyawa...?" Fadwa tace "Eh..ta kawo min har naci..." Hajiya Labiba ta juya tana faɗin "Ok ina zuwa bari nayi rakiya in dawo...." Fadwa ta bita da kallon sha'awa ji take dama ace itace Hajiya Labiba da tafi kowacce mace dacewa duniya da lahira. *Aisha Alto...* [12/23, 10:15 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI..* *Wattpad: Aishaalto09* __________________________ *TALLA! TALLA!! TALLA!!!* *SADAUKARWAR SO!!!* *Sun taso tun yara tare...Iyayensa sun fifitasa akansa shima yafi fifita buƙatun ɗan goggonsa fiye da buƙatunsa, a tasowarsu kowa halayyarsa ta bambanta yana jin daɗi da sha'awar ganin rayuwarsa cikin barkwanci saɓanin shi daya kasance magana ma wahala take mai...Rana tsaka dalilin maƙotaka wata yarinya ta ratso rayuwarsu ya fara sonta ba tare daya sani ba, ashe shima ɗan uwansa ya kamu da soyayyarta, bashi da zaɓi illa yin SADAUKARWAN SO...!* *Ba tare da kowa yasan yana sonta ba...Ya binne abun a ranshi bai taɓa koda wasa wani daga cikinsu ya fahimci abinda ke cikin zuciyarsa ba...Kamar yadda yayi SADAUKARWAN SO haka shima akayi mai SADAUKARWAN SO...!* Shin wace irin Ƙauna ce haka a tsakaninsu da har zai iya ma ɗan uwansa SADAUKARWAN SO...? Nasan kuma dole zaku yiwa kanku waɗannan tambayoyin, kuma zaku zaƙu da son jin amsarta..To tambayar taku ɗaya ce amma amsoshinta suna da yawa kuma ba'a ko'ina ne zaku samu amsarta ba sai a cikin wannan shahararren labarin SADAUKARWAR SO wanda shahararriya kuma fiƙrarriya zaƙaƙurar marubuciya ta rubuta wato *JAMILA UMAR JANAFTY* kuma zaku iya samun duk wannan garaɓasar da romon daɗin labarin ne akan farashi mai rahusa kamar yadda ta saba muku: *Zaku biya kuɗin karatu ₦300 ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* *KO* *Katin MTN ₦400 ta wannan lambar 09069067488* *Ƴan Niger kuwa zaku iya tuntuɓarmu akan wannan lambar +22794775574* Karku sake ayi babu ku domin wannan tafiyar miƙaƙƙiya ce mai nisan zango mai neman ƙarin bayani sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 09069067488 muna maraba daku masoya sai kunzo🤝 _____________________________ 2️⃣ Hajiya Labiba bata daɗe ba sai gata ta dawo gefen Fadwa ta zauna tana faɗin "Ya akayi ne ƙawata yau na ganki wata iri dake kamar baki da lafiya...?" Ajiyar zuciya Fadwa ta sauke tana ƙara bin Hajiya Labiban da kallo wacce ta tsargu da kallon da take binta dashi ta ƙara kallon kanta kafin tace "Ya dai Fadwa...? Da matsala ne...?" Fadwa ta ƙada kai tana faɗin "Ke kam Labiba ta ina kika haɗa hanya da wata damuwa ballatana matsala..? Ai matsala da damuwa tana ga irin mu talakawa waɗanda suka taso cikin talauci kuma suka kare a cikinta Labiba..." Hajiya Labiba tayi murmushi kawai domin indai ira iran waɗannan maganganun ne ta saba da jinsu a bakin Fadwa duk sanda tazo gidanta ko kuma suka haɗu a wani waje. Kai ta kaɗa tana faɗin "Zaki fara ko ƙawata...? Ni banga wani talaucin da kike kira ma kanki ba Azeez ɗinki fa cikakken namijin duniya ne duk da bai dashi bai zauna ba yana neman na kansa kuma dai-dai gwargwado yana miki iya ƙoƙarinsa kece dai bakya gani kike kushewa Fadwa..." Wani ƙaton tsaki Fadwa taja tana ƙara gyara zama lokaci ɗaya tana faɗin "Haba ƙawata ya kike son koda yaushe ki dinga bin bayan Ya Azeez ne alhalin kinsan komai me yake min...? Me yake dashi..!? Kalle ki fa ƙawata kalli gidanki kalli mijinki..? Ki duba da kyau ki ga irin rayuwar da kike ciki zaki taɓa haɗani dake ni da nake auran faƙirin matsiyaci mai tuƙin keke napep wanda saiya fita ya gama gararambarsa akan titi sannan zai samo na sakawa a bakin salati, ta ina zaki haɗa kanki dani keda kike kwance komai sai ƴan aiki sun yi miki store ɗinki cike da kayan abinci nau'i nau'i kala kala sai, sai kiyi shekara ma baki san babu ba...." Ta faɗa cikin bayyana tsantsar takaicin da take ciki, Hajiya Labiba tayi murmushi tana faɗin "Kina da damuwa Fadwa kada fa ki manta ko hannayenmu ba dai-dai suke ba Fadwa wani yafi wani ne kai kuma kafi wani... A kullum ina ƙara gaya miki ki daina faɗin haka, a hakan da kike raina Azeez ɗin naki mata nawa ki kafisu dace da jin daɗi Fadwa...! Wani irin bauta ne Azeez baya miki, nifa da kaina nasha zuwa gidanki naga ya dage yana miki aiki harda wankin kayan sawanki cangal bakya mai Fadwa ko ta wannan fannin bazaki godema Allahn daya baki miji mai haƙuri da kuma neman na kansa ba, uwa uba Wadatar Zucci, sai fa ya samu kuɗi keda kanki kike faɗa min bai ma kansa komai ba ya kwashe ya baki kayan nan kina dasu dai-dai gwargwado na shiga ƙawaye ni kaina na gaya miki in kina da wata mtsala ki sameni kai tsaye Fadwa wallahi zan taimaka miki indai bai fi ƙarfina ba amma don Allah kidaina faɗin irin waɗannan kalaman ga mijinki hakan ba dai-dai bane sam bana jin daɗin jin hakan...." Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana dafa kafaɗar Fadwa wacce ta haɗe rai tana wani tsuke fuska Hajiya Labiba ta girgiza kai tana faɗin "Kinji dan Allah ƙawata...?" Fadwa ta gyaɗa kai tana faɗin "Naji shikenan..Aike daman baki son laifin Ya Azeez bansan dalili ba...." Hajiya Labiba tace "Bai da wani aibun da zaki zauna kina zaginsa ne Fadwa..mutum ne nagari kinsani nasani Azeez ya kai duk inda ake neman namiji mai zati da kyawawan hallaya..." Fadwa ta saki ƙaramin tsaki tana faɗin "Amma kuma bai da ƙumbar susa ko...? Shi kaɗai yayi mai cikas nima ban ce yana da wata illah ba...." Hajiya Labiba tace "Oh....ƙawata baza dai ki daina maganar ba ko...?" Fadwa tace "Ni me nace...? Gaskiya ce kawai na faɗa namiji in har ba shi da ƙumbar susa ai ni bana masa kallon cikakken namiji wallahi..." Hajiya Labiba tace "Shikenan...Yanzu ki tashi mu shiga ciki na ɗauko miki ankon ƙanwar Lubna wanda na siya mana ni dake...." Fadwa ta washe baki tana faɗin "Da gaske ƙawata....? Kai Allah ya barni dake ta hannun damana, shiyasa duk cikin ƙawayen mu nafi sonki saboda baki manta zaman tare ba kullum cikin alheri kike ba irin su Lubna ba, suna da dukiyar amma ba hannun alherin...." Ita dai Hajiya Labiba dariya kawai take tana faɗin "Nidai tashi mu shiga ciki...." Fadwa ta miƙe tana ɗaukan jakanta da mayafinta tabi bayan Hajiya Labiba kichin suka fara shiga ta bama Rabi umarnin tayi musu ferfesun kayan ciki ta kawo musu suna sama, Rabi ta amsa cikin ladabi kana daga nan suka haura sama bedroom ɗin Hajiya Labiba mai kama da aljannar duniya kan lafiyayyen gadonta suka baje Hajiya Labiba ta buɗe ƙaton wardrobe ɗinta ta ɗauko wata babbar jaka ta ajiye ta gaban Fadwa dake kan gado tana faɗin "Gashinan harda jaka da takalmin da zamu saka wajen Dinner, less ɗin Dinner ɗin na ba wani telan Hajiya Lubna ya ɗinka mana. Less ɗin yinin biki kuma gashinan sai ki kaima telanki na baki kuɗin ɗinkin...." Ta faɗa tana zama kusa da ita. Fadwa baki yaƙi rufuwa, tana buɗe kayan tana jinjina kai ganin tsadan kayan da haɗuwarsu yasa ta sakin wani ƙayataccen murmushi cikin fara'a ta ɗago kanta tana faɗin "Kai ƙawata...Na gode ƙwarai....Bansan da wace kalma zan gode miki ba wallahi...." Hajiya Labiba na buɗe ƙaramar jakarta dake gefen gadon tana faɗin "Haba ƙawata..Mun wuce wannan stage ɗin faa...." Fadwa dai sai santi take Hajiya Labiba ta miƙa mata rafar ƴan dubu dubu sababbi fil tana faɗin "Ga 20k nasan zai isheki kuɗin ɗinkin...." Fadwa ta wangame baki tana kallon Hajiya Labiba duk da ba yau ta saba mata kyautan kuɗaɗe ba amma abun akwai jin Kunya kullum kai sai dai ka zauna abaka ba dai kai kabama wani ba, nan da nan yanayin fuskarta ya sauya ta kasa saka hannu ta karɓi kuɗin ganin haka yasa ta kama hannunta ta damƙa mata tana faɗin "Bana son wata magana...." Fadwa ta kaɗa kai tana faɗin "Dole zanyi magana Labiba kifa duba wannan rayuwar tare fa muka taso tun muna yara mukayi makaranta tare amma yau kalli rayuwarki kullum ke ke bani badai ni na baki ba haka zan dauwama Labiba ba wani cigaba...?" Hajiya Labiba tace "Fadwa dan girman Allah ki daina faɗin haka kinsan me Allah zai yi agaba ne...? Ƙilama wata rana ke matar gwamna ce fa Fadwa babu abinda Allah ba yayi da bayinsa..." Taɓe baki Fadwa tayi tana faɗin "Uhmm..Daman wannan mafarkin naki zai tabbata fa...? Sai dai nasan bazai taɓa zama gaskiya ba in ba auran Ya Azeez dake kaina ya saukemin ba ban ƙaryataki ba domin wallahi ko matar gwamman garin nan da nake gani a poster bata fini kyau da cika ba kema kanki kin sani Ya Azeez matar manya ya samu a sama ya aura...." Dariya Hajiya Labiba ta sheƙe dashi kafin ta dakata tana faɗin "Hakane ƙawata...amma shima kansa Azeez ɗin ai ba baya ba..kema kinsani dan ko kyan banza ya fiki..." Yamutsa fuska kawai Fadwa tayi bata ƙara magana ba, sanin gaskiya Labiban ta faɗa kawai sai ta bangarar da zancen suka ci gaba da hirar bikin ƙanwar Hajiya Lubna da zai gudana nan da sati biyu. Suna nan zaune suna hira Rabi ta shigo musu da farfesun nan suka sauko suka ci suka ƙoshi suka ƙara komawa suka ci gaba da hirar su sai da aka kira sallah suka tashi sukayi kana suka sauko ƙasa lokacin su Rabi sun gama lunch nan suka ci farar shinkafa da miyar kaji Fadwa yadda kasan gidanta haka ta saki jiki ta baje tama manta da wani wai miji ko gidanta. Sai bayan la'asar kana suka fita da Hajiya Labiba zuwa kasuwa ta rakata ta siya kayan kwalliyanta sun ƙare nan itama Hajiya Labiban ta siya mata daga nan ta rakata saloon dukkansu aka wanke musu kai suna fitowa ana kiran sallar magriba da motan Hajiya Labiba ta ɗauketa zuwa gida suna tafe suna hira cikin tsantsar shaƙuwa da ƙawancen su mai cike da yarda da juna. Tun daga nesa suka hangesa tsaye a ƙofar gidan ya jingina jikin ƙofar gidan ya harɗe duka hannuwansa a aljihu lokaci bayan lokaci yana duba agogon roban dake ɗaure a hannunsa yafi awa ɗaya da dawowa, sai da yaje ya kai kekensa gidan bulo ɗin da yake ajiyeta kana ya nufo gidan sai dai kamar kullum yau ma gidan yana kulle ne ganin zai yi zaman banza yasa ya gangara masallaci yayi sallar magriba ya sake dawowa yana zamam jiran Fadwa amma shiru bata dawo ba mutane sai wucewa suke suna binsa da kallo in da sabo sun saba ganinsa kullum yana tsaye zaman jiran Fadwa domin ba ranar da bazata fita ba yayi yayi ta bashi key ɗin ƙwadon amma Fadwa taƙi bashi tafi son kullum ya dinga zaman jiranta a ƙofar gidan kamar maigadi. Sai da aka kira Isha'i kana ya ƙara komawa masallacin yayi sallar Isha'i ya sake dawowa ya iske har lokacin bata dawo ba, ransa ya ɓaci sosai yaji ya kamata Fadwa ta gane yana haƙuri da ita ne kawai saboda iyayensu amma ita tayi kaɗan ta zauna tanayi mai wannan cin kashin. Hajiya Labiba ta waigo gefenta tana kallon Fadwa da tunda ta hango Azeez ta haɗe ranta ta ɗaure fuska cikin damuwa Hajiya Labiba tace "Kinga abunda nake ta gudun miki ko Fadwa...? Ga mijinki can ya dawo kuma daga gani ya daɗe da dawowa, Allah kaɗai yasan iya tsawon lokacin daya ɗauka yana zaman jiranki bakya gida ina amfaninsa....?" Fadwa ta saki tsaki tana faɗin "Toh sai me Labiba..nace sai me...? Ko ina gidan me zan mai...? Kada ki damu daman ya saba zaman jiran...." Ta faɗa cikin halin ko in kula Labiba ta girgiza kai kawai bata ƙara magana ba har ta ƙarasa ƙofar gidan Fadwa inda Azeez yake tsaye yana kallonsu tun daga nesa ya shaida motar Hajiya Labiba ce ƙawar Fadwa kuma yana da tabbacin Fadwan na ciki. Sai da suka ƙaraso gabansa ya ɗauke kansa kamar bai gansu ba har dukkansu suka buɗe motar suka fito Fadwa na riƙe da ƙatuwar ledarta tana saɓa jakarta a kafaɗa cikin dakiya ta kalli Hajiya Labiba tana faɗin "Na gode ƙawata sai munyi magana..." Hajiya Labiba ta kaɗa kai tana faɗin "Shikenan...Barka da dawowa Azeez..? Mun wuni Lafiya...?" Ta fada tana kallon Azeez ɗin daya kalli can gefe guda kamar bai gansu ba jin Hajiya Labiba na gaishesa yasa ya waigo cikin ɗan sakin fuska yana amsa mata da cewa "Yauwa...sannu Labiba Alhamdulillah..." Ya faɗa yana sauke hannayensa daga ƙirjinsa kana lokaci ɗaya ya tashi daga jikin ƙofar ya matsa gefe. Labiba taji tausayinsa ya kamata da takaicin ƙawarta Fadwa wacce ke tsaye tana wani ɓata fuska cikin sanyin jiki Hajiya Labiba tace "A ƙara haƙuri dan Allah ni na tsaidata tun ɗazu ta rakani kasuwa..." Cikin murmushinsa na koda yaushe yace "Ah haba ba komai fa...." Labiba ta kaɗa kai tana faɗin "Na gode..sai da safe ƙawata sai munyi waya..." Ta faɗa tana buɗe murfin mota ta shiga Fadwa ta ɗaga mata hannu dukkansu suna tsaye ba wanda ya motsa har motar Hajiya Labiba ta ɓace daga layin, kana Azeez ya maida kallonsa kan Fadwa wacce take wani cika tana batsewa kamar wacce akayi ma wani laifi bai ce mata komai ba illah haɓa daya riƙe yana binta da kallon mamaki ita kuma tana ganinsa yana mata wannan kallon yasa taƙi yarda su haɗa ido ta fara laluban jakarta domin ɗauko makulli tana ɗaukowa ta matsa jikin ƙofar tana faɗin "Bani waje na buɗe ƙofar mana...." Azeez bai ce komai ba ya ƙara matsawa yana ƙara binta da kallo, domin in dai halin Fadwa ne ko Abba ba zai gaya mai wacece ita ba. Yafi kowa saninta in bata da gaskiya haka take wannan borin kunyan bai mata magana ba har ta buɗe gidan ta tura ƙofar ta shiga bata ji takunsa ya biyo ta, sai ta tsaya lokaci ɗaya ta juyo tana kallonsa yana tsaye ya ƙurawa wani waje ido cikin ɗan tausayinsa daya shigeta tace "Bazaka shiga gidan bane...?" Bai kalleta ba ya sauke numfashinsa ya raɓa ta gefenta ya shige gidan ya barta nan tsaye, da kallo ta rakasa kafin taja ledarta ta mara mai baya, ɗakin ma sai da ya jirata ta buɗe kana ya shiga ko ta kanta bai ƙara bi ba ya cire kayansa ya fita ruwa ya ɗiba ya shiga ya watsa ya fito yana shiga ɗakin ya sameta tana ɗaga jaka da takalmin da Hajiya Labiba ta siyamata ganin ya shigo ne yasa ta kallesa tana nuna mai kayan lokaci ɗaya tana faɗin "Kaga abun arzikin da Hajiya Labiba ta min ko...? Less biyu ta ɗinka min ɗaya na can wajen ɗinki ta bada a ɗinka mana ga ɗaya nan kuma zan kaiwa Idris telana, na bikin ƙanwar ƙawarmu ne Hajiya Lubna...." Yana daga gaban jakar kayansa yace "Kin gode...." Daga haka bai ƙara cewa komai ba ya zaro wata baƙar jallabiyarsa ya zura, tura baki Fadwa tayi tana maida kayanta cikin ledar tana faɗin "Uhmm koma mutum yace an gode koma kar yace ban damu ba...Komai dai baƙin cikin tanda sai munci waina ni ƙashin arziki gareni ko ana so ko ba'a so ehe....! Duk yana jinta amma bai ƙara cewa komai ba ya zura silifas ɗinsa bayan ya laluba aljihun wandon daya cire ya ɗauki kuɗi ya fice ta rakashi da taɓe baki har ta gama maida kayanta cikin leda ta diɓi ruwa taje tayo wanka dayake ma garin da ɗan zafi zafi tana fitowa ta saka kayan barcinta tabi lafiyan gado domin cikinta acike yake dam da daɗin dataci daga gidan Hajiya Labiba ta kwanta ba daɗewa taji dawowarsa da rufe gidan da yayi tana jinsa ya shigo ɗakin ya kulle ƙofa daga kwancen take kallonsa ta hasken fitilar wayarsa domin ta kashe fitilan da zata kwanta, ledar daya shigo da ita guda biyu ya tura ɗaya can gefe ɗayan kuma ya jata ya buɗe daga kwancen ta hango tsire a cikin takarda da hanzari ta miƙe lokaci ɗaya ta dirko daga kan gadon sai gata gabansa cikin washe baki tace "Shine ko ka tadani kasan fa ina jin yunwa...." Cikin mamaki yake kallonta ta janye ledar gabansa har ta fara tura tsiran bakinta cikin sanyin muryarsa ya tsame hannunta yana faɗin "Na zata kin ci kin ƙoshi daga inda kika fito...?" Tana cika bakinta da naman tace "Eh naci na ƙoshi amma kasan bana bama nama kunya...." Bai ƙara mata magana ba ya miƙe bayan ya tura mata ɗayan ledar Youghrt ɗin dake ciki kaɗai ya ɗauka ya miƙe yana faɗin "Gashi nan na bar miki duka in zai isheki ki cinye...." Ba kunya ta ƙara jan ledar gabanta tana kallonsa tace "Madaran fa...?" Murmushi kaɗai yayi yasha kaɗan ya miƙa mata da sauri ta ƙarɓa tana faɗin "Yauwa ko kai fa...." Take faɗa tana shan Youghort ɗin tana wani sauke numfashi ganin in ya tsaya kallonta zai ɓata ransa ne a banza yasa ya buɗe ƙofa ya fita yayo alwala ya dawo yazo ya ƙara kulle ɗakin tana nan zaune ta yi rashe rashe tana cin naman tana korawa da madaran kallo ɗaya yayi mata ya girgiza kai ya shimfiɗa darduma ya daidaici gabas ya tada sallar shafa'i da wuturi. *Aisha Alto..* [12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* ____________________________ *TALLA! TALLA!! TALLA!!!* *SADAUKARWAR SO!!!* *Sun taso tun yara tare...Iyayensa sun fifitasa akansa shima yafi fifita buƙatun ɗan goggonsa fiye da buƙatunsa, a tasowarsu kowa halayyarsa ta bambanta yana jin daɗi da sha'awar ganin rayuwarsa cikin barkwanci saɓanin shi daya kasance magana ma wahala take mai...Rana tsaka dalilin maƙotaka wata yarinya ta ratso rayuwarsu ya fara sonta ba tare daya sani ba, ashe shima ɗan uwansa ya kamu da soyayyarta, bashi da zaɓi illa yin SADAUKARWAN SO...!* *Ba tare da kowa yasan yana sonta ba...Ya binne abun a ranshi bai taɓa koda wasa wani daga cikinsu ya fahimci abinda ke cikin zuciyarsa ba...Kamar yadda yayi SADAUKARWAN SO haka shima akayi mai SADAUKARWAN SO...!* Shin wace irin Ƙauna ce haka a tsakaninsu da har zai iya ma ɗan uwansa SADAUKARWAN SO...? Nasan kuma dole zaku yiwa kanku waɗannan tambayoyin, kuma zaku zaƙu da son jin amsarta..To tambayar taku ɗaya ce amma amsoshinta suna da yawa kuma ba'a ko'ina ne zaku samu amsarta ba sai a cikin wannan shahararren labarin SADAUKARWAR SO wanda shahararriya kuma fiƙrarriya zaƙaƙurar marubuciya ta rubuta wato *JAMILA UMAR JANAFTY* kuma zaku iya samun duk wannan garaɓasar da romon daɗin labarin ne akan farashi mai rahusa kamar yadda ta saba muku: *Zaku biya kuɗin karatu ₦300 ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* *KO* *Katin MTN ₦400 ta wannan lambar 09069067488* *Ƴan Niger kuwa zaku iya tuntuɓarmu akan wannan lambar +22794775574* Karku sake ayi babu ku domin wannan tafiyar miƙaƙƙiya ce mai nisan zango mai neman ƙarin bayani sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 09069067488 muna maraba daku masoya sai kunzo🤝 ____________________________ 3️⃣ Koda ya idar ya jima zaune a gurin yana addu'o'i kafin ya shafa ya miƙe tsaye lokaci ɗaya yana naɗe darduman ya ajiye kana ya zare jallabiyar dake jikinsa ya haye gado yay kwanciyarsa ya juya mata baya. Watsawa bayansa wata uwar harara tayi lokaci ɗaya tana taɓe baki kafin ta ɗauke kai ta ci gaba da shan Youghort ɗinta, sai data shanye abunta tas kana ta miƙe ta ɗauki buta ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita tsakar gida taje ta wanko hannunta sannan ta dawo ta sake kulle ƙofar ta wuce uwar ɗaka ta ajiye butar, bata ko kalli ɓarayinsa ba ta haye gado abinta tai kwanciyarta itama ta matsa nesa dashi ta juya masa baya lokaci ɗaya tana sakin gyatsa haɗe da tsaki, duk yana jinta amma yay luf bai ko motsa ba ballantana tasan cewa idonsa biyu, haka tai ta juye juye tana sukur sukur a gadon kamar wata tsutsa duk yana jinta yay banza da ita, sai ma sake matsawa da yayi can ƙarshen gadon ya bar mata sauran filin. Ta jima tana mutsu mutsun kafin zuwa can ya fara jin saukar numfashinta a hankali a hankali alamar tayi bacci, sai da ya bari baccin nata ya ɗan yi nisa tukunna ya juyo ya matso kusa da ita a hankali ya ɗora kansa akan filon da kanta yake cikin natsuwa ya kwanta a gefenta ya juyo da fuskarta suna fuskantar juna ya zuba mata idonsa ƙirr yana ƙarewa ɗan madaidaicin ƙaramin bakinta kallo, kamar ana fizgarsa zuwa gareta haka ya dinga matsar da fuskarsa a hankali a hankali kamar mai jin tsoron kar wani ya kamashi, da haka har ya ɗora bakinsa akan nata ya fito da harshensa ya soma lasar saman lips ɗinta cikin wani irin salo da muradi. Fadwa kuwa cikin baccin daya ɗan soma ɗaukarta ta fara jin ɗumin wani tattausan abu mai ɗan tsantsi tsantsi da laushi akan lips ɗinta, duk a zatonta mafarki take dan haka ta buɗe baki cikin magagi da shauki, aiko bai yi wata wata ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya zura tattausan harshensa ya kamo nata ya shiga tsotsa cikin wani yanayi mai daɗi haɗe da muradi mai girma, tana jin haka itama ta cafki nasa ido rufe ta shiga basa wani lafiyayyen tsotsa mai cike da zallan shauki da nishaɗi. Sosai ya zage ido rufe ya tsotse bakinta iya son ransa, wanda shi kansa ya sani inda ace idonta biyu babu yadda za'ayi ta barsa ya matso kusa da ita balle har ya samu damar taɓa wani sassa na jikinta irin haka, shiyasa daya samu wannan damar ya zage ya dama abinsa iya yanda ransa yakeso. Sai daya gama yamutsata iya son ransa dan sai daya gaji don kansa sannan ya ƙyaleta ya koma gefe ya kwanta yana maida numfashi lokaci ɗaya da ajiyar zuciya, ba daɗewa kuwa wani bacci mai masifar daɗi yayi awon gaba dashi, itako Fadwa gaba ɗaya ba tasan abinda yake faruwa ba, dan ita duk a zatonta mafarki kawai take kuma a cikin bacci komai yake faruwa, ga wani shegen daddaɗan bacci mai cike da nishaɗi daya sake kwasheta cikin ƙanƙanin lokaci sai take jin kanta kamar tana yawo a sararin samaniya ne don daɗi, shiyasa gaba ɗaya bata san abinda ya wakana ba a tsakaninsu. Da asuba tun misalin ƙarfe 5am. Ya tashi ya lalubo wayarsa ya kunna fitila ya haska fuskarta tana ta sharar bacci abunta hankali kwance ta ƙanƙame filo a ƙirjinta, ɗan murmushi yayi kana ya shafa kumatunta lokaci ɗaya yana faɗin "Rigimammiya kawai...ji ɗan bakin rashin kunyar...." Ya faɗa yana zuro ƙafafuwansa ƙasa ya sauko daga kan gadon bayan ya ajiye wayar a gefen gado yaje ya ɗibi ruwa a bokiti sannan ya ɗauki buta ya fita ya shiga banɗaki yayi wanka kana ya ɗauro alwala ya fito ya dawo ɗakin ya zura wata jallabiyarsa ruwan madara ya fesa turare kana ya ɗauki casbaha ya fita ya tafi masallaci. Koda aka idar da sallan bai fito daga masallacin ba ya zauna ya ɗauki Kur'ani ya soma karatu cikin daddaɗar muryarsa mai sanyi da daɗin saurare, sai da gari yayi haske sosai sannan yayi addu'a ya shafa kana ya rufe Kur'anin ya maida gurin da ake ajiyewa ya ajiye kana ya fito ya nufo gida. Sosai yayi mamakin ganinta riƙe da buta ta fito daga banɗaki, dan shi duk a tunaninsa zai zo ne ya isketa kwance akan gado tana sharar bacci kamar yadda ta saba bai taɓa zaton zai dawo ya iske ta tashi har ta ɗauki buta tana ƙoƙarin yin alwala ba, ya ɗauka idan ya dawo sai yay ta tashinta ya dinga nacin taje tayi alwala tazo tayi sallah tukunna ya samu da ƙyar da suɗin goshi ta tashin, amma sai yaga saɓanin hakan, wai yau Fadwa ce da kanta ta tashi ta fito tunda sanyi safiya ba tare da ya dawo yasha wahalar tashinta ba, kai gaskiya abun ya faranta ransa sosai yaji daɗi. Ina ma ace zata ɗore a haka..? Aiko da babu wanda zai kaisa farin ciki. Fadwa kuwa ganin irin kallon ƙurullar da yake mata ne yana sakin wani makirin murmushi cike da jin daɗi yasa ta kallesa a yatsine tana watsa masa harara tace "Wannan kallon fa Malam lafiya....?" Ya Azeez ya sauke numfashi yana faɗin "Lafiya ƙalau wallahi, kawai dai naji daɗin ganinki ne yau kin tashi da wuri zakiyi sallah shiyasa murnata ta kasa ɓoyuwa...." Saboda takaici Fadwa bata samu daman magana ba ta raɓa ta gefensa ta wuce can nesa dashi ta nemi waje ta tsugunna ta fara alwala, da sauri ya ƙarasa kusa da ita ya tsaya yana ƙare mata kallo cikin mamaki kafin ya miƙa hannu ya karɓe butar dake hannunta lokaci ɗaya yana faɗin "Wai kin ma yi wanka kuwa da kike niyyar yin alwala....ko kuwa ke a naki haukan zakice bakiji wani sauyin yanayi a tattare da jikinki ba wanda ya cancanci ace dole sai kin...." A zafafe ta fizge butar a hannunsa tana faɗin "Don Allah Malam ni bani inyi alwala ta bazanyi wankan ba ko dole ne...." Ta faɗa kai tsaye tana watsa masa kallon banza. Murmushi yayi kawai kana yace "Aiko dole ne sai kinyi wanka Malama tunda ya kamaki, dan haka ki tashi kawai kije kiyi wanka sannan sai kizo kiyi alwala kiyi sallah. Dan wallahi bazan taɓa bari kiyi sallah a haka da najasa a jikinki ba tare da kinyi wanka ba...." Tsabar takaici da baƙin ciki da suka turnuƙe Fadwa kasa cewa komai tayi kawai ta juya da nufin ci gaba da ɗaura alwalarta, taji ya sake fizge butar a hannunta yana faɗin "Ai wallahi duk abinki bazan taɓa bari kiyi sallah a haka ba sai kinyi wanka, dan ni ba jahili ba ne...." Yana gama faɗin haka ya juya da butar a hannunsa ya shige ɗaki, ba jimawa ya sake fitowa da butar a hannunsa wacce yaje ya cikota da ruwa yazo ya dire a gabanta yana faɗin "Gashi nan ki tashi kije kiyi wanka sai kiyi alwalar kiyi sallah...." Ya faɗa lokaci ɗaya yana juyawa ya wuce ya barta nan. Fadwa data daskare a tsugunne tana kallonsa cikin mamaki da al'ajabin dagewar da yayi kan dole sai tayi wanka kafin tayi sallah, tai ɗan jim cikin nazari kana ta sauke numfashi a hankali tana faɗin "Kutt kar dai ace dama ba mafarki nayi ba a zahiri ne abun nan ya wakana..to idan a zahiri ne ta ya hakan ta faru..? To idan kuma mafarkin ne ma ta ya akayi zai sani har ya matsa yace dole sai nayi wanka, ai kuma koda mafarkin ne ma ya zama dole ne sai nayi wankan...kanbuu kar dai kuma ace sakar mai jiki naje nayi yay yadda yake so dani tunda nasan halinsa kamar maye yake....?" Ta faɗa a fili tana miƙewa tsaye cike da baƙin ciki kafin tace "Tabɗi aiko daya gama dani, ni kuma da na cika banza shashasha sauna wallahi...." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana duban jikinta. Haka tai ta juyi tana ƙara nazarin jikinta, amma duk bata gano komai ba ta ja wuyar rigar baccin dake jikinta data kasance mai faɗi ta leƙa ƙirjinta nan ma bata ga alamar komai ba. Rasa abun yi tayi kawai sai ta ɗauki butar ta wuce banɗaki taje tayo wankan kana ta ɗauro alwala ta fito tana zagin Ya Azeez a zuciyarta ta shiga ɗaki, a falo ta iskesa zaune yana ta danne danne a ƴar wayarsa bata ko kalli inda yake ba ta dangwarar da butar ta wucesa fuuuu ta shige cikin uwar ɗaka, ko ɗago kai baiyi ya kalleta ba shima ya ci gaba da abinda yake yi. Sai data ɗaura zani akan rigar baccin dake jikinta kana ta zura hijabi ta shimfiɗa darduma ta tayar da sallah, bayan ta idar ta daɗe a zaune kafin ta tashi ta linke darduman ta sagaleta a jikin ƙofa ta fita falo, har lokacin yana nan zaune a inda ta barsa, sai dai yanzu ba danna wayar yake ba tana ajiye ne a gefensa ya jingina da bango ya lumshe idanunsa kamar mai bacci, ba tare da tunanin komai ba ta ƙarasa ta tsaya a kansa ƙerere tana faɗin "Nifa yunwa nake ji Malam kaji dani..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana watsa mai wani kallon sama da ƙasa. Shiru yayi bai tanka mata ba, ya buɗe idanunsa a hankali ya ɗauki wayarsa yana duba lokaci ƙarfe 7:49am. Ya gani sai da ya maida wayar ya ajiye kana ya ɗago kai ya kalleta cikin natsuwa yace "Yi haƙuri ina zuwa bari inje in haɗo miki kayan tea..." Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa, da sauri ta matsa gefe tana wani kumbura baki cike da shagwaɓa tace "Nidai dan Allah ya Azeez yau ɗaya ka ɗan haɗo min har da soyayyen kwai dan Allah kaji....?" Ta ƙarashe maganar a shagwaɓe tana harararsa a fakaice. Bai ce komai ba ya ratsa ta gefenta ya shige uwar ɗaka bai wani jima ba ya fito ya fice daga ɗakin ba tare da ya kalleta ba ya zura silifas ɗinsa ya fice daga gidan. Ɗan taɓe baki tayi kana ta samu guri ta zauna lokaci ɗaya tana ƙarewa falon kallo a ranta tana ji kamar ta ɗora hannu akai ta rushe da kuka saboda tsabar baƙin ciki da takaici, wai kamar ita ace wannan fankan fayau ɗin shine falonta, ba kujeru ba komai sai kace wani zauren almajirai. Tana nan a zaune ya dawo da baƙar leda riƙe a hannunsa ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama ba tare daya jira amsawarta ba ya nufeta direct ya dire mata ledar a gabanta yana faɗin "Gashi nan na haɗo miki har da ruwan lifton, sai ki haɗa tean kawai...." Ya faɗa yana juyawa ya shige cikin uwar ɗaka. Da kallo kawai ta bishi ba tare da tace komai ba ta miƙe ta bi bayansa taje ta ɗauko kofi da cokali ta dawo ta zauna ta buɗe ledar ta fito da abubuwan dake ciki, washe baki tayi cike da murna ta yagi wainar kwan ta tusa a bakinta ta fara taunawa tana wani lumshe idanu cike da jin daɗi kafin ta ɗaga murya ta yadda zai iya jiyota daga can cikin uwar ɗakan tace "Allah sarki Ya Azeez gwarzon Fadwa, na gode Allah ya ƙara dalili, lallai yau litinin ɗin tawa ce Allah ya kawo arziki lodi lodi kai ta siyo min kayan daɗi ina ci...." Ta faɗa tana ƙara yago kwan ta haɗa da biredi ta danna a bakinta. Yana jinta bai tanka mata ba ya girgiza kai kawai, ya ɗauki bokiti ya cikasa da ruwa ya fito ya ɗauki soson wanka ya fice, da wata ƙatuwar harara ta rakasa tana sakin tsaki ƙasa ƙasa tace "Ji ina masa magana yayi banza dani sai kace kurma, mutum sai shegen faɗin rai da girman kan tsiya kamar wani mai faɗa aji...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana jawo kofi ta juye ruwan lifton ɗin a ciki kana ta zuba madara da milo ta haɗa tean ta mai kauri ta jujjuya ta soma kurɓa tana wani lumshe ido. Bai wani jima sosai ba ya fito tana cikin karyawa ya shigo ɗakin ya wuceta ya shiga ciki sai daya shafa mai sama sama kana ya ɗauki wata rigar T-shirt ɗinsa blue mai gajeren hannu da baƙin wandon jeans ya saka kana ya ɗan fesa turare ya ɗauki makullin keke napep ɗinsa ya fice, har yasa kai zai fice ya dawo da baya da sauri ya ƙarasa kusa da ita yana faɗin "Ni zan fita aiki, zuwa anjima da rana idan Allah ya kaimu zan dawo in kawo miki kuɗin abinci kiyi haƙuri yanzu ba ko sisi a hannuna dama wanda zan bar miki ɗin ne dashi na siyo miki kwai, kinga ni ko karyawar ma ban samu na yi ba sai na fita tukunna..dan haka kiyi haƙuri zan dawo in kawo miki...." Ko gama rufe baki bai yi ba ta ɗago kai tana faɗin "Ba damuwa saika dawo ɗin...." Ya amsa yana ƙarasa ficewa daga ɗakin, kamar kuwa daman jira take ya fice ta ɗaga kofin tean da sauri ta ƙarasa shanyewa a gurguje ta cinye kwan kana ta ƙulle sauran buredin ta miƙe ta tsallake kofin da ledojin ta barsu nan ta wuce taje ta ɗauki bokitin daya fito wanka ta diɓi ruwa ta ɗauki kwandon soso ta wuce banɗaki. A gurguje tayo wankan ta fito tazo ta shafa mai ta zauna ta tsantsara kwalliyarta mai kyau da burgewa kana ta buɗe akwatinta ta ɗauko wata baƙar doguwar rigarta wacce tasha kwalliyar duwatsu masu walwali tun daga sama har ƙasa ta zura kana ta yana gyalen a kanta ta ɗauki ƙaramar hand bag ɗinta ta sagala a kafaɗarta ta ɗauki kwaɗo ta fice tana taku ɗai ɗai. Sai data fara kulle ƙofar ɗakin sannan ta juya ta nufi ƙofar gidan cikin wani irin taku ta fice ta jawo ƙofar gidan itama ta kulle, kana ta jefa ɗan makullin a cikin jaka ta wuce ta nufi bakin titi, mai napep ta tare ta hau bayan ta gaya mai inda zai kaita yaja suka wuce. Gaban wani tangamemen haɗaɗɗen gida mai ɗauke da wani ƙaton gate ruwan madara a cikin unguwar Rimi Gra Fadwa ta nuna ma mai napep ɗin yayi fakin ta fito ta buɗe jakarta ta ɗauki ɗari biyar cikin irin kuɗin da Hajiya Labiba ta bata jiya ta miƙa masa kana ta juya cikin iyayi da yanga ta tura ƙaramar ƙofar ta shige, security's ne kota ina suna ta zagaye a fankacecen harabar gidan. Haka ta dinga wucesu tana ratsesu ba tare da tsoron komai ba suma kuma babu wanda yabi ta kanta dan sun santa ƙawar matar gidan ce tana yawan zuwa akai akai shiyasa duk suka ganeta. Direct ƙofar da zata sadata da shiga babban falon gidan ta nufa kai tsaye ta danna wani abu a gefe yayi ƙara zuwa can sai ga wata ƴar matashiyar budurwa wacce da ganin mai aiki ce tazo ta buɗe mata, tana ganin itace ta saki ƙaramin tsaki ƙasa ƙasa yadda bazata jita ba a daƙile tace "Sannu da zuwa Hajiya shigo...." Ta faɗa tana matsawa daga hanya, wani kallon sama da ƙasa Fadwa ta watsa mata a wulaƙance tana faɗin "Dama fa tsiyar talaka kenan bai iya samun guri ba, ni dalla matsa min a hanya in wuce bake nazo gani ba da wasu shegun koɗaɗɗun kayanki kamar na masu sharar titi...." Ta faɗa tana tureta gefe ta shige ciki. Da kallo kawai budurwar ta bita kafin ta girgiza kai ta maida ƙofar ta rufe ta juya ta wuce kichin abinta tana ƙunƙunai da zagin Fadwan a zuciyarta. Fadwa kuwa duk bata san tana yi ba tana can gurin ƙarewa haɗaɗɗen falon mai kama da aljannar duniya kallo wanda ya gaji da haɗuwa ya tsaru iya tsaruwa kamar fadar wani hamshaƙin sarki ko shugaban ƙasa, dan kaf cikin ƙawayensu ta sani babu wacce gidanta ya kai kwata kwatan haɗuwan na Hajiya Kalsoom duk da ta kasance yaya ce a gurin ƙawarta Hajiya Lubna hakan bai hana Fadwa zarya gidanta akai akai ba domin ko kaɗan matar bata da matsala akwaita da son mutane ba kamar ƙanwarta Hajiya Lubna ba mai shegiyar rowar tsiya da iyayi, duk daya kasance Hajiya Kalsoom ɗin tana auren mataimakin gwamnan jihar Kaduna ne kuma gashi shahararren ɗan kwangila wanda ake damawa dashi a yanzu amma hakan bai sakata girman kai da ɗagawa ba. Sai data gama ƙarewa falon kallon tsaf tukunna ta samu waje kan luntsuma luntsuman kujerun da suka yiwa katafaren falon ƙawanya ta zauna tana ƙurawa faskeken talabijin ɗin daya kusan mamaye rabin bangon falon ido wanda duk ranar da tazo gidan sai ta yi masa irin wannan kallon ƙurullan dan har ta saba ko gajiya bata yi abun ya gama bin jikinta. Tana nan zaune wata hamshaƙiyar mace kyakkyawa black beuty ta sauko cikin shiga ta alfarma jikinta sanye da tsadadden leshi wanda aka tsantsarawa ɗinkin Abuja bubu ta sha adon gwala-gwalai hannu da wuyanta sai walwali take tana sheƙi, fuskarta ɗauke da fara'a ta ƙarasa saukowa cikin falon tana murmushi take faɗin "Barka da zuwa Hajiya Fadwa, ina ta cigiyarki dama kwana biyu na ɗauka ko bakya ƙasar ne da naga baki zo ba....?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana zama a kusa da ita. Washe baki Fadwa tayi cike da fara'a tana faɗin "Wace ni Aunty Kalsoom...Ina nan babu inda naje kwana biyu ne abubuwan sai a hankali, ya shirye shiryen bikin....?" Hajiya Kalsoom tace "Alhamdulillahi gashi nan anata yi, fatan dai kinyi ankon....?" Fadwa ta sauke numfashi tana faɗin "Eh Hajiya Labiba ta siyan min har ta kai mana gurin ɗinki sauran kuma ta bani gobe insha Allahu zan kaiwa telana...." Hajiya Kalsoom ta kaɗa kai lokaci ɗaya tana faɗin "Ok ba matsala Allah ya kaimu goben lafiya...." Ta faɗa tana gyara zamanta kafin ta ƙwallawa mai aikinta Halima kira, ta fito daga kichin da sauri tazo ta durƙusa a gabanta cike da ladabi tace "Gani Hajiya..." Cikin bada umarni Hajiya Kalsoom tace "Kije ki haɗowa Hajiya Fadwa abinci ki kawo mata...." Ta faɗa kai tsaye tana kallon Fadwa da ta wani yatsine baki tana watsawa mai aikin kallon banza tace "Inda akwai abinda kikeso a haɗo miki dashi ki gaya mata..." Saurin girgiza kai Fadwan tayi tana faɗin "A'a babu Aunty Kalsoom, ta kawo min ko mene ne ya isa....Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziki...." Cikin jin daɗi Hajiya Kalsoom ta amsa da Ameen tana sakin murmushi, kana tace "Halima tashi ki je ki kawo mata..." Tace "Toh Hajiya..." Ta faɗa tana miƙewa ta wuce kichin, ba jimawa ta dawo falon hannunta ɗauke da babban faranti ta ajiye a gaban Fadwa bayan ta janyo ƙaramin tebur ta ɗora akai, sai data zuba mata komai ta aje mata kana ta bar gurin. Nan Fadwa ta zage ta buɗe ciki ta kwashi abinci tana ci suna hira da Hajiya Kalsoom sai da taci tai nak abinta, kana ta kora da sassanyan lemun abarba wanda yaji madara da kayan haɗi. Sai da taji cikinta ya cika taf sannan ta ture farantin gefe ta zari tsinken sakace ta saka a baki ta saki gyatsa kana ta sake yin balans a kujera bayan ta zare gyalen dake kanta sanyin Ac na ratsata yana shigarta ta ko'ina ta lumshe idanu tana ƙara godewa Allah daya sa tasan su Hajiya Lubna da Hajiya Labiba a rayuwarta, dan silarsu gashi tasan mutane da dama waɗanda ko ba dasu ba idan taje gidajensu babu mai wulaƙanta ta. Wani bacci mai daɗi Fadwa taji ya fara ɗaukarta dan haka ta zame nan kan doguwar kujerar tai kwanciyarta abinta, ganin haka yasa Hajiya Kalsoom ta tashi ta koma sama ta shiga ɗakinta ta barta nan. ********* A ɓangaren Ya Azeez kuwa tun misalin ƙarfe 12pm. Na rana ya koma gida domim ya kaiwa Fadwa kuɗin abinci kamar yadda yayi mata alƙawari, amma sai me...? Yana zuwa ya iske ƙofar gidan nasu a kulle da ƙaton kwaɗo alamar matar gidan bata nan, ya daɗe tsaye a ƙofar gidan yana kallon hanya amma babu ita babu alamarta, yafi awa ɗaya tsaye a ƙofar gidan kafin ya haƙura ya shiga keke napep ɗinsa yaja ya wuce ya koma bakin sana'arsa, zuciyarsa cike taf da baƙin cikin irin halin da Fadwa ta jefa kanta a ciki. ********** Fadwa kuwa tana can gidan Hajiya Kalsoom inda taci baccinta ta ƙoshi hankali kwance babu abinda ya dameta, sai bayan la'asar sannan ta tashi ta shiga ɗakin baƙi dake nan cikin falon ta ɗauro alwala tayi sallar azahar da la'asar kafin ta fito falo ta zauna ta kunna kallo. Haka tai ta zama a gidan har bayan sallar magriba sannan bayan ta ci abinci Hajiya Kalsoom ta haura sama ta ɗauko kuɗi ta bata tace ta biya kuɗin ɗinki kana ta kira direbanta tasa ya maida ita gida, Fadwa bakinta ya kasa rufuwa sai fara'a take tana faman washe baki ta tura kuɗin ta a jaka tana ta yiwa Hajiya Kalsoom godiya kamar zata ari baki. Haka ta rakota har gurin mota direban ya buɗe mata gidan baya ta shiga ta zauna tana ƙara jin kanta wani iri ta hakimce tana wani saki ƙayataccen murmushi, lallai arziki yayi a rayuwa yau itace a cikin wannan danƙareriyar motar za'a kaita gida. Lallai dole talaka ya ƙara tashi tsaye gurin roƙon Allah kan yayi masa tsari da talauci, dan babban ƙalubale ne mai tarwatsa rayuwa. Suna karyo kwanan layinsu tun daga nesa ta hangosa zaune a kan wani ɗan dakali da ƴar wayarsa a hannu yana daddannawa, dan haka tace direban ya tsayar da motar ɗan nesa kaɗan da gidansu daga can gefe, ta ɗauki jakarta ta buɗe motar ta fito tana yi masa godiya ta wuce tana wani ƙara tamke fuska alamar bata san raini. *Aisha Alto...* [12/23, 10:15 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* _Ina mai bawa makaranta littafin nan haƙuri a bisa jina shiru da ku kayi kwana biyu, hakan ya faru ne ta dalilin rashin mahaifina da nayi, to Alhamdulillahi mun gode Allah yanzu na dawo zanyi ƙoƙari in ƙarasa muku kamar yadda na fara. Nagode matuƙa Allah yabar zumunci da Ƙauna. Son So FISABILILLAHI🤝_ 4️⃣ Kamar ance ya ɗago kai ya hangeta tana tahowa cikin wani irin taku tana rangaji, tsam ya mike tsaye lokaci ɗaya yana maida wayarsa cikin aljihu ya matsa jikin ƙofar gidan ya tsaya yana jiran ta ƙaraso, Fadwa kuwa ganin haka yasa ta ƙara wani shan mur ta nufosa tana zuwa ko kallonsa ba tayi ba ta zura hannu a cikin jakarta ta lalubo makulli ta buɗe ƙofar ta tura lokaci ɗaya ta buɗe ta shige ciki abinta ba tare data waigo ta kalli inda yake ba. Sosai lamarin nata ya ƙara ɗaure mai kai ya bashi mamaki amma sai bai ce komai ba ya kaɗa kai yabi bayanta zuwa cikin gidan, koda ya shiga ya iske har ta buɗe ƙofar ɗakin ta shige abinta, dan haka ya ɗaga labulen shima ya shiga cikin ɗakin. A falo ya isketa zaune tayi rashe rashe ta miƙe ƙafafuwanta ta cire gyalen doguwar rigar dake jikinta ta wurgar gefe, tana ganinsa ta miƙe da sauri zata shige uwar ɗaka. Cikin zafin nama ya fizgota da ƙarfi ta dawo da baya ya hankaɗata ta tafi taga taga kamar zata kifa Allah ya taimaketa tayi saurin dafe bango, ta ɗago a tsorace lokaci ɗaya tana watsa masa wani mugun kallo cike da masifa tace "Malam lafiya zaka wani fizgoni haka kamar wata tsumma..ko kana bina bashi ne ko kuma so kake ka ji min ciwo ne....?" Bai tanka mata ba illa shan gabanta da yayi ya tsareta da ido yana faɗin "Bana binki bashin komai Fadwa amma daga ina kike shine kawai abinda nakeso inji, domin wannan shegen yawon naki mara dalili ya isheni na gaji bansan ya kikeso in yi da raina ba....?" Ya ƙarashe maganar cikin sanyin muryarsa lokaci ɗaya yana kallonta. Sakin tsaki kawai Fadwa tayi ta raɓa ta gefensa ba tare da tace komai ba ta shige cikin ɗaki ta barsa nan tsaye sake da baki yana aikin binta da kallo cikin tsantsar takaicinta, dan Allah ya gani lamarin Fadwa ya gama isarsa ya fara gajiya da abubuwan da take masa, amma yasan yadda zaiyi da ita matakin gyara mata zama kawai zai ɗauka sai yaga yadda zatayi, gajiya yayi da tsaiwar ya kaɗa kai ya juya shima ya fice daga gidan ya nufi bustop ɗin unguwarsu. Gurin mai soya doya da kwai ya fara zuwa ya siya na ɗari biyu ya biya kuɗin sannan ya juya ya nufi gurin mai tsire shima ya siya na ɗari uku kana ya siyan mata madarar holandia yoghut mai sanyi shi kuma ya siyan ma kansa pure water guda biyu ya nufo gida. Sai daya tsaya a wani shago nan kusa dasu ya siya maganin sauro da ƙyandir kasancewar unguwar tasu suna da matsalar rashin wuta, dan sai suyi kusan kwana uku huɗu har biyar ma ba'a kawo musu ba, kuma yasan Fadwa bata son zama a duhu, shiyasa kullum sai ya siya idan zai shiga gida. Dan yasan halinta sai tai ta complain tana masifa tace ya barta a cikin duhu. Sai daya rufe ƙofar gidan yasa sakata, sannan ya wuce ya shiga ɗakin ya iske falon tsit alamar har lokacin bata fito ba tana can cikin uwar ɗaka, sai da yayi sallama kana ya ɗaga labulen uwar ɗakan ya shiga. Ko ɗago kai ba tayi ta kallesa ba, ballantana yasa ran zata amsa mai sallamar da yayi, tana zaune tayi rashe rashe a tsakiyar ɗan madaidaicin gadon six by six ɗinsu na katako, da kuɗi zube a gabanta tana ƙirgawa cike da jin daɗi sai faman washe baki take tana ƙara lissafa kuɗin cike da farin ciki. Sosai lamarin nata ya bashi matuƙar mamaki, gefe guda na zuciyarsa kuwa, sai ya shiga tambayar kansa da cewa ina ta samu waɗannan kuɗi masu yawa haka, waye ya bata, me tayi da aka bata su...ko dai...ko dai...? Da sauri ya kori sheɗan da banzan tunanin da yake son bijiro masa dashi akanta. Kafin ya fara takawa a hankali a hankali har ya ƙarasa kusa da ita bayan ya ajiye ledar dake hannunsa cikin nutsuwa ya zauna a bakin gadon kusa da ita ya zuba mata ido ƙyam yana kallonta, ganin irin kallon tuhumar da yake aika musu dashi ne lokaci ɗaya ita da kuɗin dake zube a gabanta yasa ta ɗago kai tana harararsa kafin cikin tsiwa tace "Lafiya dai ko aka zo aka wani tasani gaba ana ƙare min kallo...?" Bai tanka mata ba, sai ma ƙara tsareta da yayi da ido ƙirr yana kallonta, kafin kawai taga ya miƙa hannu kan kuɗin zai kwashe, aiko da sauri ta buge hannunsa, ta tattare kuɗinta ta ɗaga cinyarta ta tusa a ƙarƙashinta ta danne, kana ta ɗago tana aika mai da wani mugun kallo tana faɗin "Ina ruwanka da kuɗina da zaka taɓa min..? Ko kuma ka ajiye kuɗin da suka kai yawan wannan ne anan ɗakin baka gansu ba da kake tunanin naka ne na kwashe...?" Ta faɗa kai tsaye tana wani tsatstsaresa da idanu cike da fitsara. Ba tare daya kulata ba ya sake kai hannu a karo na biyu zai janyeta gefe domin ya kwashe kuɗin, ta riƙe hannun nasa ta matsa gefe da sauri tana faɗin "Oh ni Fadwa! Yau ina ganin wata lukutar masifa, wai dan Allah meye nufinka dani ne, ina ruwanka da kuɗina...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana watsa mai wata muguwar harara kamar ƙwayar idanuwanta zasu faɗo ƙasa. Ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke kana ya dubeta cikin natsuwa yana faɗin "Akwai ruwana har da tsakina Fadwa, tunda dai a ƙarƙashin ikona kike..kinga kuwa duk wani abu da yake naki shima ya zama a ƙarƙashin ikona, kuma dole ne idan na ganki da abu ko menene in tambayeki a ina kika samu, balle abinda na san baki dashi kuma nima da ya kamata in baki bani dashi, kinga kuwa dole zan tuhumeki inji a inda kika samesu..." Daga haka ya sake miƙa mata hannunsa lokaci ɗaya yana kallonta cikin ido yace "Ciro kuɗin ki bani su nan, kuma sannan ki gaya min gidan uban da kikaje da kuma aikin da kikayi musu, wanda ya kai su ɗauki wannan uban kuɗin haka su baki....?" Wani mugun kallon haushi Fadwa ta watsa masa tana ƙara haɗe fuska take faɗin "Gidan Hajiya Kalsoom naje yayar ƙawata Hajiya Lubna kuma ai kana ganin irin motar da aka saukeni a ciki zaka san ba daga gidan matsiyata nake ba, kuma kuɗi ma daka gani itace ta bani su dubu hamsin gasu cas tace in kai ɗinkin less ɗin da Hajiya Labiba ta siyan min na ankon ƙanwarsu Lubna ƙawarmu, sannan zan siya takalmi da jaka da gyale mahaɗin leshin da sauran abubuwa, dan haka akan me zaka wani tsareni kace sai na baka..? Ni wallahi Allah ya gani bazan iya ɗaukar kuɗina ina baka ba, ina dalili...! Ta faɗa lokaci ɗaya tana watsa mai wani kallon banza cikin nuna tsantsar jin haushinsa. Ɗauke kansa yayi da sauri ya haɗe fuska bai ce komai ba. Ganin bai sake tanka mata bane yasa ta miƙe da sauri ta tattare kuɗinta ta kwashe ta buɗe jakarta dake rataye a ɗakin ta zuba aciki, kana ta dawo ta zauna tana rarraba ido. Kafeta da ido yayi kawai yana kallonta kafin ya tashi, tana ganin ya miƙe itama ta miƙe zumbur ta matsa gurin jakarta ta riƙe ƙugu ta tsaya, dan ita a tunaninta jakar zai ɗauke. Shiko ko kallonta bai sake yi ba. Ya juya yaje ya ɗauko filet guda biyu a kwando ya dawo ya buɗe ledar daya shigo da ita ya ciro ƙunshin tsiren ya juye kana ya fito da ɗayar ledar itama ya juye doya da kwan dake ciki a ɗayan filet ɗin sannan ya fito da holandia ya ajiye, kana ya miƙe ya ɗauki buta ya fita waje yaje ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna, duk hakimar na nan tsaye ta zuba mai ido tana kallonsa, ɗaukar filet ɗin tsiren yayi ya tura gabanta yana faɗin "Gashi nan ki zauna kici karya huce, dan idan ya huce ba zai yi miki daɗin ci ba..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana matso da ɗayan filet ɗin doya da kwan gabansa ya saka hannu ya fara ci. Ba kunya kuwa Fadwa ta dawo kusa dashi ta zauna ta jawo filet ɗin gabanta ta saka hannu ta fara ci hankali kwance, tana korawa da madarar holandia yoghut ɗin. Shi dai sai kallonta kawai yake bai ce komai ba. Sai da ta kusan cinyewa dan ɗan sauran daya rage bai wuce yanka uku ko huɗu ba sai ƴar diddigar ƙuli ƙuli dasu albasa, sannan ta cire hannunta ta tura mai filet ɗin gabansa lokaci ɗaya tana suɗe hannunta take faɗin "Alhamdulillahi ya Allah ka ƙara wadatamu da wadatarka ka yaye mana talauci, gaskiya arziki yayi a rayuwa Ya Azeez talauci mugun ciwo ne, yanzu da kullum ina samu kana kawo min irin wannan kayan daɗin ai da babu abinda zai dameni...amma nasan na jiya da yau ne kawai ƙila kuma sai nan da tsakiyar wata kafin in sake samun wani irin haka, gashi ni kuma bakina ya riga ya saba da cin daɗi, shiyasa kwata kwata bana iya haƙuri nake tafiyata gidan ƙawayena inci abun da raina yakeso in ƙoshi, saboda nasan ba samu nake a gidana ba su kuwa komai na jin daɗin rayuwa akwai a gidajensu suna dashi, kuma komai nakeso idan naje shi ake yi min, shiyasa a kullum nake ƙara godewa Allah daya dubeni ya bani ƙawaye na gari ƴaƴan masu arziki kuma matan masu kuɗi, kaga nima da haka na samu ai da nafi kowa sa'a a duniya da jin daɗi...." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana ƙoƙarin miƙewa bayan ta ɗauke kwalin holandia yoghut ɗinta ta ƙarasa shanyewa kana ta ajiye masa fankon kwalin agabansa, ta fice zuwa falo ta ɗauki buta ta fita tsakar gida taje ta wanke hannunta kana ta dawo ta zauna a falo, ɗan jim tayi kafin ta tashi tana jan siririn tsaki a fili tace "Kai! Wallahi talauci bai yi ba, haba ina tsiya taga rana wannan wace irin masifa ce...ace yanzu ko ɗan irin talabijin ɗin nan na zamani da mutum zaiyi kallo ma babu, ballantana akai ga maganar wata shegiya fanka da generator, wanda idan zafi ya ishi bawa yadda bamu da wutan nan zan ɗan dinga kunnawa ina ɗan shan iska ko na rage wani raɗaɗin...? Ta faɗa cike da baƙin ciki kana ta bankaɗa labule ta shige cikin ɗakin ta wucesa ta haye gado ta kwanta abinta tana jan tsaki. Shiko dama tunda ta ajiye masa filet ɗin tsiren a gabansa bai ɗaga kai ya kalla ba ballantana yayi tunanin ɗauka ya kai bakinsa, ya cigaba da cin doya da kwansa hankalinsa kwance, sai daya cinye abunsa tsaf yasha pure water ɗaya yayi hamdala, kana ya tattare kayan ya ɗauke ya matsar dasu gefe ya ajiye, sannan ya miƙe yaje ya ɗaurayo hannunsa a waje, ya dawo ɗakin ya tsaya a kanta lokaci ɗaya yana ɓalle maɓallan gaban rigar dake sanye a jikinsa yake faɗin "Kinyi magriba da isha'i ne da kika kwanta zakiyi bacci, ko kuwa kin manta da anayi ne tunda ba damunki dama sallar tayi ba..?" Ya faɗa yana ƙoƙarin cire rigarsa bayan ya gama ɓalle maɓallan. Banza tayi dashi bata kulasa ba, sai ma lumshe idanuwanta da tayi kamar mai bacci, kaɗa kansa kawai yayi kafin yace "Malama ki tashi kiyi sallah kafin ki kwanta, dan kinsan ba barinki zanyi kiyi bacci ba alhalin nasan bakiyi sallah ba...dan haka gara kawai ki tashi tun kan ranki ya ɓaci kiyi sallah kafin ki kwanta.." Ya faɗa yana ƙarasa cire rigarsa ya ajiye kafin ya cire dogon wandon dake jikinsa, yayi saura daga shi sai ɗan gajeren wando ya ɗauko bokiti ya cikasa da ruwa sannan ya ɗauki brush ya matsa makilin akai kana ya ɗauki kwandon soson wanka ya juya zai fice daga ɗakin bayan ya sake jaddada mata kan cewa ta tabbatar ta tashi tayi sallolin da ake binta kafin ya fito wanka ya dawo ɗakin. Tana jinsa tayi banza dashi ta sake gyara kwanciyarta abinta. Tsawon mintuna talatin yayi da fitarsa a ɗakin kafin ya dawo ɗauke da bokiti da kwandon soso a hannunsa da alamun yayo wanka ne, dan jikinsa duk ruwa ya shigo cikin ɗakin, kamar yadda ya barta haka ya dawo ya isketa a kwance, ransa ya sake ɓaci sosai, wato ta gama rainasa shiyasa ko ya gaya mata magana bata ji amma zai fara maganinta tunda magana ɗaya bata taɓa yi mata zai fara gwada mata ta yadda zata gane, dan ba zai taɓa ɗaukar rashin sallah a gidansa ba, cikin haɗe fuska ya ƙarasa kusa da ita ya tsaya a kanta yana faɗin "Wato da nace ki tashi kiyi sallah sake gyara kwanciyarki kikayi da kika ga na fita kika ƙi tashin ko Fadwa..? Wai dan Allah me kikeso ki zama ne, ke burinki kullum shine kawai ki baƙanta min rai ki muzguna min ko...? Sallah fa nace ki tashi kiyi Fadwa ba wani abu ba, amma da yawace yawacen gidajen ƙawaye ne b..." Kafin ma ya ƙarasa maganan ta tashi zaune a zafafe tana ɗaga masa hannu lokaci ɗaya tana faɗin "To cewa nayi bazan yi sallar ba da zaka wani zo ka dameni, ko kuwa idan nayi sallar ladan kai za'a ba bani ba da kake isata...? Tunda kai kayi taka ai saika saurara min nima inyi tawan ko..? Amma duk kabi ka wani takura min kana nema ka hana kanka sukuni kamar wanda idan nayi sallar ladan tare za'a raba mana...." Daga haka kawai ta sauka daga kan gadon ta wucesa taje ta ɗauki buta ta zuba ruwa ta fita tsakar gida tana surutai. Shima kaɗa kansa kawai yayi yabi bayanta ya fice, tana tsugunne a tsakar gidan ta tasa buta a gaba ta zuba uban tagumi ya fito, ko kallon inda take bai yi ba ya nufi zaure yaje ya kullo ƙofar gidan ya dawo, har lokacin tana nan a tsugunne ta tasa buta gaba ya sake wuceta ya shige cikin ɗaki. Da kallon haushi kawai take bishi har ya shige ya turo ƙofa kafin ta ɗauke kanta tana sakin ƙaramin tsaki. Allah ya sani ba don tana da babban buri a rayuwarta na son auren sanannen mai arziki ba da babu abinda zai hanata kwantar da hankalinta ta zauna da Ya Azeez lafiya cikin aminci, saboda Ya Azeez ya gama haɗa komai da ko wacce irin mace duk taƙamarta da jan ajinta zataso ace ta samesa a matsayin mijinta, dan sosai ya gama haɗuwa kota ina. Acan ƙasan ranta tana jin kamar tana ɗan sonsa kaɗan kaɗan, amma saboda talaucin da yake fama dashi ya masa katutu yasa bata jin zata iya gwada masa tana sonsa, domin a rayuwarta bata kaunar ta haɗa hanya da talauci sai dan babu yadda zatayi, amma talauci babbar tsiyace. Shiyasa bata son ta nuna masa yana da wani abun burgewa a tattare dashi dan ma karya ce zai saki jiki da ita ya sakankance dan ita ba mazauniya bace a gidansa, Allah ma ya sani takurawar mahaifinta ce kawai tasa take zaune dashi har kawo yanzu tsawon watanni tara da aurensu take ta haƙuri, amma ba wai dan tana so ba, sai dan babu yadda zatayi. Duk da tasan ko a cikin ƙawayenta da suke auren manyan mutane masu kuɗi babu wacce take auren mijin da ya kai nata kyau da nagarta, ballantana su fishi nasaba, uwa uba kuma yarinta da dattako da kamewa, sai dai kawai su gwada masa arziki, hutu, jin daɗin rayuwa da hawa manyan manyan motoci, amma ko ilimin addini dana boko bata tunanin sun fishi sai dai ma su fishi tsufa da manyantaka. Amma ita kanta ta sani *AbdulAzeez Naseer Abdullah Arabi* Cikakken namijin duniya ne wanda ya amsa sunansa namiji, Allah ya mai kyakkyawar ƙira mai ban sha'awa haɗe da zati da kwarjini masu tsantsar burgewa da mazantaka, gashi da ingarman jiki da haiba, wanda burin ko wace mace ne taga ta mallakesa a matsayin mijinta duk kuwa da taƙamar mace da ajinta kuma komai mulki da gadara da ji da kanta in ta kallesa sai taji ta raina kanta, da duk wata gadararta, wanda kuma ita da kanta shaida ce kan cewa Ya Azeez ba sa'an aurenta bane nesa ba kusa ba, domin ya gama haɗa komai da ita kanta idan ta kallesa wani lokacin takan ji wani irin alfahari da isa aranta, wanda wani lokacin har ji take kamar ta haƙura ta rungumi mijinta su zauna lafiya, amma kuma idan ta tuna da burinta sai taji kwata kwata bazata iya haƙuri ta dawwama cikin tsiya da talauci ba, dan ita ɗaukar kanta take matar manya ba matar ƙanana marasa galihu irinsa ba. Wannan ƙasƙantacciyar rayuwar gidan nasa bata dace da ita ba, saboda haka bazata iya da ita ba dole ne ta nemawa kanta mafita. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta gyara tsugunnonta ta fara alwala, sai data gama ta miƙe riƙe da butar a hannunta ta shiga ɗaki. Yana nan zaune akan darduma ya idar da shafa'i da wutiri yana jan casbaha ta shigo, bata kallesa ba ta ɗauko ɗayar darduman ta fita falo ta shimfiɗa kana ta dawo uwar ɗakan ta buɗe akwatinta ta zaro wata doguwar rigar baccinta mara nauyi ta zira sannan ta ɗauki hijabi ta saka ta fice falon. Sai data ɗaura zani akan rigar baccin dake jikinta sannan ta hau kan darduman ta daidaita tsayuwarta ta tayar da sallah. *Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya🤲* [12/23, 10:15 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 5️⃣ Bayan ta idar bata wani zauna yin addu'a ba ta miƙe ta cire hijabin jikinta ta linke kana ta ɗauke darduman ta shiga cikin ɗakin. Yana zaune a bakin gado da robar mai a gabansa yana shafawa ta shigo, yi tayi kamar bata gansa ba ta wuce taje ta ajiye hijabin da darduman kana ta cire zanin jikinta ta ajiye, ta buɗe ƙaramar durowar gadonta ta ɗauko wata ƴar ƙaramar kwalbar turaren humra mai ƙamshi wacce Hajiya Labiba ce ta kawo mata ita tsaraba lokacin da suka je Dubai ita da mijinta, wanda tunda ta bata bata taɓa yin amfani da ita ba ta ajiye, yau ne taji tana sha'awar tayi amfani dashi, rigar jikinta ta tuɓe yayi saura daga ita sai ɗan pant da bra ajikinta, kana ta buɗe kwalbar ta tsiyaya humrar a tafin hannunta ta murza tabi ko'ina lungu da saƙo a jikinta duk ta shafa. Shiko gogan kasa ci gaba da shafa man yayi ya ture robar gefe, ya dinga satar kallonta ta gefen ido, itama fahimtar da tayi gaba ɗaya hankalinsa yana kanta ne yasa da wani irin taku ta ƙarasa gaban akwatinta ta buɗe ta zaro wata ƴar ɓingilar rigar baccinta kalar ja mai kyau da ɗaukar hankali, sai data cire bra da pant ɗin jikinta sannan ta saka rigar duk yana kallonta, dai-dai iya cinyarta rigar ta tsaya amma sakamakon shara shara rigar take kuma gata irin mai roban nan ce sai ya kasance tabi jikinta ta lafe komai na jikinta ana iya gani, sake tsiyaya turaren tayi a tafin hannunta ta kuma shashshafe jikinta dashi har kan ƙirjinta tana yi tana mai wani irin kallo da idanuwanta masu cike da tsantsar wayewa tana juyi lokaci ɗaya haɗe da sauke numfashi cike da tsokana, tasan halinsa sarai indai a irin wannan fannin ne baya taɓa iya jurewa, kuma kome tai masa na ɓacin rai baya iya dogon fushi da ita, dan koda yayi ɗin idan dare yayi kuma sai ya lalubeta, shiyasa ita da kanta wani lokacin take ɗan ɗaga mai ƙafa, tunda ya iya tarairayar mace da nuna mata tsantsar kulawa a shimfiɗa wanda cikin mintina ƙalilan duk taƙamar mace da izzarta zata mance da ko ita wacece. Ita dai kawai babbar matsalarta dashi babu ce, Allah ya sani itace kuma babbar damuwarta. Buɗe handbang ɗinta tayi ta ɗauko wani cingum ɗinta mai ƙamshin fruit ta ɓare ta jefa a cikin bakinta ta fara taunawa a hankali a hankali tana wani karkashe masa ido cikin nuna tsantsar ƙwarewa a bariki. Aiko kafeta yayi da ido shima cike da zallar sha'awa, yadda take wani banƙaro masa ƙirjinta yana rawa yasa hankalinsa gaba ɗaya ya sake tashi, har ya kasa ɗauke idanuwansa daga kanta, cikin wani irin taku ta ƙaraso gabansa ta ɗan duƙa cikin wani salo tana leƙen kyakkyawar fuskarsa cikin wata irin murya ƙasa ƙasa tace "Ya Azeez ya nayi maka kyau ne...?" Wani jan numfashi yayi sakamakon daddaɗan ƙamshin cingum ɗinta data buɗe baki ya bugi hancinsa, sai lokacin ta kalli cikin ƙwayar idanunsa daya ɗago taga yadda suka kaɗa ta saki wani malalacin murmushi kafin ta saka hannu ta ɗago haɓarsa tana kallon cikin ƙwayar idanun nasa da wani irin ruwa ruwa suka kwanta a ƙasansu, cikin wata irin murya tace "Ya Azeez ɗina...kayi haƙuri kaji ai kafi kowa dai sanin burina da kuma yadda nake matuƙar son jin daɗin rayuwa, amma kake zaune dani har kawo yanzu ko..? To dan haka ina roƙonka ka daina wani damun kanka a kaina mu cigaba da zamanmu kawai a yadda nakeso ni kuma zan dinga ƙoƙarin faranta maka, ina ganin ban tauye maka hakkinka ba kaji...?" Ta faɗa tana mai wani irin kallon cikin ido. Saurin rumtse idanuwansa yayi kafin ya buɗe yana kallonta yace "Fadwa bazan iya barinki kina yin abinda kika ga dama ba a matsayinki na matar aure, amma komai kikeso dai zan iya miki shi dai-dai karfina, kuma ko a ina yake indai har bai fi ƙarfina ba zan nemo miki shi...." Ya faɗa lokaci ɗaya yana janye hannunta dake riƙe da haɓarsa, dan ya gama fahimtarta indai taga yana buƙatarta to ta dinga shigo mai da wasu buƙatunta kenan tana neman ta maidashi wani sakaran namiji wanda bai san ciwon kansa ba, saboda tasan shi mabuƙaci ne sai take amfani da irin wannan damar a kuma dai-dai irin wannan lokacin ta nuna tana da buƙatar wani abu a garesa, bata san tuni ya gama ganota ba, dan shi dai ba wawa bane da zai biye mata yabarta tai ta gararanba da sunan tana zuwa gidan ƙawayenta ko biki da sunan ƙannen ƙawayenta ba. Amma bari zai nuna mata ya isa da ita, kuma ita ɗin halalinsa ce dan haka yana da iko da damar yin duk abinda yaso kuma yake da muradin yi da ita, a kuma duk lokacin da yaga dama, babu kuma wanda ya isa ya hana ko yace masa don me. Buɗa idanunsa yayi sosai a kanta yana aika mata da wani shu'umin kallo wanda yasa da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, kafin lokaci ɗaya ta soma ƙoƙarin tashi ta matsa daga gurin, fahimtar hakan da yayi ne yasa shi saurin riƙe hannunta ya fizgota da ƙarfi gaba ɗaya ta faɗo jikinsa ya zagaye hannayensa a ƙugunta ya riƙeta ƙam ƙam, a tsorace ta ɗago tana faɗin "Haba Ya Azeez m..." Saurin katseta yayi da faɗin "Hakkina kawai zaki bani, shi nake da muradin karɓa..." Daga haka ya fara ƙoƙarin cire mata rigar jikinta, da sauri ta riƙe mai hannu lokaci ɗaya tana ɓata fuska take faɗin "A ina hakkin naka yake da zan baka...?" Bai kulata ba yasa hannu ya fara shafa cinyoyinta yana hura mata iskar bakinsa a cikin kunnenta, kafin ya ɗago yana ƙoƙarin haɗa bakinsu waje ɗaya, ganin haka yasa ta kauda fuskarta da sauri ta dumtse bakinta taƙi bashi damar hakan, tsirawa fuskarta idanu yayi yana aika mata da wani sihirtaccen kallo kafin ya matso da ita sosai jikinsa ya soma lasar wuyanta zuwa bayan kunnenta kana a hankali ya zira harshensa cikin kunnenta yana mata wani irin salo, ajiyar zuciya ta dinga saukewa a hankali a hankali kafin ta fizge da sauri tana ƙoƙarin janye jikinta daga nasa tana mutsu mutsu lokaci ɗaya tana faɗin "Ni dai gaskiya ka bari bana so...Ya Azeez dan Allah ka bari ni dai bana sha'awar komai yau, ka bari sai na shirya tu...." Bai bari ta ƙarasa ba yayi caraf ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya shiga tsotsar bakinta cikin wani irin salo, hannunsa daya tallabo kanta dashi ta riƙe gam tana faman girgiza mai kai tana shushshura kafafuwanta, ƙara manne bakinta yayi cikin nasa lokaci ɗaya yana shashsafa bayanta zuwa cinyoyinta. A hankali ta dinga sauke numfashi tana wani irin miƙa kafin ta fizge da ƙarfi zata sauka, ya sake rarumota ya rungumota da sauri yana wani jan numfarfashi cikin wani irin shauki da muradi yana faɗin "Ki natsu mana..." Ya faɗa can ƙasan maƙoshi kana ya miƙar da hannayenta a hankali ya zame rigar jikinta ya yar a ƙasa, wani irin shigewa jikinsa tayi da sauri tana harɗe kafafunsu guri ɗaya, har lokacin bakinsu na haɗe yana cigaba da tsotsar harshenta kamar zai haɗiye ta. Ya daɗe yana tsotsar bakinta kafin ya janye bakinsa yana sakin nishi a hankali, ita kuwa jin ya cire bakinsa a nata yasa ta matsa da sauri ta jawo zanin gado ta rufe ƙirjinta wanda nonuwanta dake tsaye ƙyam babu alamar risinawa a tare dasu suke kallonsa ta zabga mai harara, ganin haka sai ya saki murmushin mugunta yana kallonta cikin ido ya matsa ya kamota ya matso da ita jikinsa sosai ya fara shafa wuyanta lokaci ɗaya yana hura mata iskar bakinsa a fuskarta yana faɗin "Ina zaki bayan na gaya miki ina da buƙatarki...?" Ya faɗa kai tsaye yana janye zanin gadon data rufe ƙirjinta dashi ya kifa kansa a ƙirjin nata, sai gashi duk ƙoƙarinta na son ta ƙwace kanta a gurinsa ta kasa, sai kawai ta wani ƙara lafewa ta shige jikinsa tana wani jan numfarfashi, saurin matsar da ita baya yayi ya kwantar da ita sosai akan gadon kana ya bita ya 🤐, ya ƙara ƙanƙameta lokaci ɗaya ya cigaba da abinda yake yi a ƙirjinta.🥱 Sosai ya zautata da sabon salon wasaninsa masu gusar da tunani sai da ya bari ta gama kamuwa tazo hannu dan har wani buɗe ƙafarta take yi da kanta tana daɗa kamosa jikinta tana cusa kanta a ƙirjinsa tana jan numfashi sannan ya ɗago kai lokaci ɗaya ya ƙara haɗe bakinsu waje ɗaya, cikin wani irin bege ta kamo kansa itama ta shiga kissing ɗinsa ba ƙaƙƙautawa kamar zata cinye mai baki. Wata irin zallar soyayyarsa mai cike da shauki haɗe da muradi ya shiga nuna mata, sai da ya bari ta gama kaiwa ƙololuwa sosai gurin buƙatuwa dashi kafin cike da tsokana ya ɗan janye jikinsa a nata, aiko cikin fitar hayyaci ta kai mai wata raruma da sauri tana nishi. Kafeta yayi da ido yana kallonta kafin ya janyeta kaɗan ya matsa ya zame gajeren wandonsa ya cire kana ya sake ƙanƙameta har lokacin bakinsu na haɗe suna kissing ɗin juna. Sakin nishi tayi tana ƙara cafkar harshensa cikin shauki tana tsotsa, ya ɗago kansa a hankali yana kallon fuskarta, idanuwanta a lumshe suke amma sai jujjuya kanta take tana kiran sunansa can ƙasan maƙoshi, wani kyakkyawan murmushi ya saki kana ya buɗe ƙafarta a hankali ya fara ƙoƙarin saita kansa. (Sisina tace kar in wuce haka🥱🤣 Sosai ya zage yana ta aikin abu guda duk yadda taso da ya ƙyaleta ta huta haka nan ƙi yayi har da kukanta riris, amma yay banza da ita kamar bai ji ta ba, haka tana ji tana gani ta kasa kataɓus, dan haka ta rabu dashi tana jinsa yayi yadda yake so da ita ya gama, sosai abun ya baƙanta mata rai yadda ya wani zage ya gurjeta iya son ransa kamar ya samu abinci ba imani balle yaji tausayinta, take taji wani bala'in haushinsa ya turnuƙe mata zuciya, kuma ta yiwa kanta alƙawarin daga yau ba zata sake bari ya samu fuskar koda riƙe hannunta ba ne. Ballantana abun ya kai ga har ya samu damar yace zai kusanceta tunda shi dai mugu ne bai da tausayi. ********* ******** Washegari bayan ya dawo daga masallaci sallar asuba, ya ɗebi ruwa a bokiti yaje yayo wanka ya dawo a gurguje ya fito da mangal tsakar gida ya zuba gawayi ya ɗauko ashana ya hura wuta, sannan ya koma cikin ɗakin ya ɗauko tukunya ya ɗauraye ya zuba ruwa da citta da kanumfari da lifton, kana ya ɗan zuba sigari kaɗan ya rufe ya miƙe hannunsa riƙe da robar dakakkiyar cittan haɗe da kanumfari, sai ɗan ƙullin siga a leda da kwalin lifton ya koma cikin ɗakin dan ya shirya kafin ruwan tean daya ɗora ɗin ya tafasa. Tana kwance tayi ɗai ɗai akan gadon tana ta sharar bacci abinta hankalin kwance, cike da ɓacin rai ya ƙarasa kusa da ita, kallonta yake cike da baƙin ciki wani takaicinta na cika mai zuciya yanzu ace tunda aka kira sallar asuba ya tasheta yace ta tashi tayi wanka ta tsarkake jikinta sannan tayi sallah ashe bata tashin ba, amma shi gashi har ya tsarkake jikinsa yaje masallaci yayi sallah har ya dawo ya sake wani wankan ita duk tana nan a kwance tana baccin asara. Kayan hannunsa ya ajiye ya isa kusa da ita ya zauna a gefenta lokaci ɗaya yana dukan cinyarta cikin takaicinta yana faɗin "Ki tashi kiyi wanka ki sallah tunda ke haka rayuwarki take bakin san abinda ya dace da wanda bai dace ba, wankan tsarki da sallahn ma dole sai an matsa miki ance ki tashi kiyi sannan zakiyi, saboda ke sam baki san ciwon kanki ba..." Cikin jin ɗacin kalamansa ta buɗe ido lokaci ɗaya tana watsa mai wani banzan kallo kafin ta yunƙura ta tashi zaune tasa hannu ta ture hannunsa dake kan cinyarta, kana cikin muryar bacci da jin haushin katseta da yayi tana baccinta mai daɗi tace "Naga ai kai da kasan ciwon kanka ɗin kayi naka wankan tsarkin da sallar ko..To meye kuma ni da bansan ciwon kaina ba kake takura kanka gurin matsa min kace in tashi inyi sai kace a kanka nake ko idan nayi tare za'a raba mana ladan...?" Ta faɗa tana watsa mai wata muguwar harara, wani baƙin ciki da haushi yaji a ransa, kawai sai ya miƙe yana kaɗa kai yace "To kiyi haƙuri tunda na tasheki a bacci, amma ai ko yanzu ma kina iya komawa ki cigaba da abinki tunda dama sallar ba wani damunki tayi ba, kina ƴar musulma amma ibada sai an matsa an takura miki kike yinta da ƙyar, ke abun ma ko kunya baya baki, koda yake ai ba sanin muhimmancin sallar kikayi ba ballantana dan bakiyi ba kiji wata kunya..Allah ya shiryeki..." Aiko tana jin abinda yace ta hayayyaƙo masa da masifa ta shiga faɗan mai maganganu. Dama wani bala'in haushinsa take ji kan rashin imanin daya gwada mata a daren jiya, sakamakon haka yasa ta rufe ido ta dinga ruwan bala'i, shi dai ko ta kanta bai sake bi ba ya buɗe jakar kayansa ya zaro wata farar riga da baƙin wandon jeans ya zura kana ya ɗauki turarensa mai ɗan sauƙin kuɗi ya fesa, sannan ya ɗauki kofi da abun tace ruwan tea ya fita, sai daya kashe gawayin sannan ya sauke tukunyar ya tsiyaya ruwan tean iya yanda zai yi masa, kana ya rufe sauran ya ɗauki na kofin ya koma cikin ɗakin, har lokacin tana cikin ɗaki tana ta zazzaga ruwan masifa tana kumfar baki, dan haka sai yayi zamansa a falon bayan ya ɗauko sauran bredin daya siyo mata tun shekaran jiya wanda ko taɓashi bata yi ba ya soma karyawa abunsa hankali kwance. Yana cikin karyawan ne ta fito da buta da bokiti cike da ruwa a hannunta ta fice tana sakin tsaki, shi dai ko a jikinsa bai kulata ba, har ya gama karyawarsa ya miƙe yaje ya ɗauraye kofin ya dawo dashi ya kife sannan ya ajiye mata gudar ɗari biyar a bakin gado, ya ɗauki makullin keke napep ɗinsa yasa kai ya fice. A tsakar gidan ya isketa tsugunne tana brush, bai kalleta ba yace "Nina fita sai na dawo..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakai zai fice, jin tayi shiru bata tanka masa bane yasa shi ya dawo da baya ya ƙaraso gabanta ya tsaya lokaci ɗaya yana dubanta kai tsaye yace "Ni dai ina roƙonki dan girman Allah Fadwa ba dan halina ba yau ki daure ki zauna a gidanki karki fita ko'ina, dan Allah ki zauna a ɗakin mijinki ki kula da gidanki ki daina hangen gidan wasu da kalar rayuwar da sukeyi a gidajen mazajensu, kema ki fuskanci taki rayuwar dan Allah..." Ya ƙarashe faɗa yana tsatstsareta da idanu, ko kallonsa ba ta ɗaga kai tayi ba ballantana yasa ran zata amsa masa, sai ma cigaba da wanke bakinta da tayi tana ƙara haɗe rai, ganin haka yasa ya girgiza kai kafin yace "Ni dai kinji maganata kuma a matsayina na mijinki ɗan uwanki wanda ya isa dake nake baki wannan umarnin, dan haka ko ki ji ko kar kiji wannan ya rage naki nidai ban ce ki fita ko nan da ƙofar gida ba domin ban baki izini ba, duk da dama fitar da kike yi ɗin kai tsaye kike yin abarki ba tare da izinina kike yinta ba, dan haka daga yau na soke kuma idan kika kuskura kika fita bada yawuna ba ban yafe miki ba tunda ke naga alamar lallashi da lallaɓawa basa taɓa miki dole sai an bi dake ta tsiya tsiya sannan ake shiryawa dake, saboda haka wallahi ki kiyaye ni karki sake ki ƙureni na gaya miki...." Daga haka kawai ya juya yasa kai ya fice daga gidan gaba ɗaya ya barta nan. Da wata ƙatuwar harara Fadwa ta rakasa kafin ta ɗauke kai lokaci ɗaya tana sakin ƙaton tsaki kamar bakinta zai faɗo ƙasa tace "Aiko wallahi sai na fitan, sai dai kayi duk abinda zakayi ɗin, haba! Mutun sai shegen fi'ili da iyayin banza da wofi sai kace wani uban abun yake ajiye min na azo a gani a cikin gidan da zai wani hanani fita inda naga dama saboda samun waje...Lallai kuwa aiko wlh sai na fita kuma a lokacin dana so naga dama, tunda ba zamansa nake yi ba, dan ni wannan ƙaddararran auren nasa ban wani ɗaukesa a bakin komai ba ji nake kamar ma zaman kaina nake yi ba zaman wani ba, har da zai wani zo ya isheni da wasu surutansa marasa tushe ballantana makama, faƙirin banza kawai faƙirin wofi direban napep...." Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana kuskure bakinta da ruwa, kafin ta soma ɗaura alwala tana kumbura fuska tana ƙunƙunai. *Allah ya gafartawa iyayenmu da kakanninmu yasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu🤲* [12/23, 10:15 AM] Janafty: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DXDyWhc0O3LCKZVYVT5N3M *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 6️⃣ Koda ta idar da sallahn miƙewa tayi jikinta sanye da hijabin sallar bata cire ba, ta buɗe jakarta ta ɗauki dubu ɗaya acikin kuɗin da Hajiya Labiba ta bata ta fice daga gidan. Can bakin layinsu taje wani babbba shagon provision ta haɗo kayan tea irinsu madara, milo, sigari kana ta siyo kwai da buredi saboda bata jin zata iya cin wannan bushasshen buredin daya siyo ya kawo tun shekaran jiya ya ajiye. Sai da mai shagon ya gama haɗa mata komai da take buƙata sannan ta biyasa kuɗinsa ya bata canji ta kamo hanyar komawa gida a ranta tana mitar duk wannan siyayyar fa bai kamata ace kamarta sai ta fita yinta ba, kamata yayi ace tana da komai ajiye a gidanta sai dai kawai tasa ƴar aikinta tayi mata duk abinda take so tana daga zaune, amma ina zata samu haka tana a irin wannan faƙirin gidan. Bayan ta koma gidan gawayi ta sake haɗawa ta kunna bayan ta shiga ɗaki ta ɗauko kaskon suyan kwai a kwando da wani ɗan silba da cokali sannan ta haɗo da wata yar gora da Ya Azeez yake siyo musu man gyaɗa a ciki ta dawo tsakar gidan ta fasa kwan data siyo ta kaɗa sannan ta ɗora kaskon ta zuba man gyaɗa, sai lokacin ta tuna bata ɗauko maggi ba ta miƙe taje ta ɗauko nan taga tsiren data rage jiya ta ɗauko abunta ta zuba a cikin kwan ta yanka albasa sannan ta zuba a kaskon. Sai data gama soya abunta tsaf ta juye a filet, kana ta sake maida ruwan lifton ɗin da Ya Azeez ya dafa ya ƙara tafarfasa sannan ta sauke ta juye a kofi ta ɗauka ta kai ɗaki ta ajiye, kana ta zuba ruwa a tukunyar ta sake ɗorawa a mangal ɗin sannan ta koma ta zauna inda ta haɗa tean ta mai kauri wanda yaji madara da milo. Wani irin tsananin farin ciki yau take ji a ƙasan ranta dan haka cikin jin daɗi ta zauna ta fara karyawa abunta hankalinta kwance babu abinda ya dameta. Tsaf ta gama cinye abunta tas bata rage komai ba, ta ɗauki pure water ta sha ta saki gyatsa, sai data ɗan yi jim kaɗan sannan ta tashi ta tattare kayan ta kwashe ta kai uwar ɗaka ta ajiye, kana ta cire kayan jikinta ta ɗaura fallan zani ta ɗauki bokiti da soson wanka ta fita zuwa tsakar gida. Ruwan zafin data ɗora ta juye ta ɗauka ta shige banɗaki dan Allah Allah take tayi ta gama shiryawa taje ta kai ɗinkinta, a gurguje tayo wankan ta fito ta shiga ɗaki sai data goge jikinta tsaf kafin ta ɗauko lotion ɗinta ta ɗan shafa sama sama, bayan ta gama ta ɗauko akwatin kayan kwalliyarta ta zauna zaman dirshan ta shiga tsantsara kwalliyarta kamar wacce zata gurin taron biki, ta ɓata lokaci sosai gurin yin kwalliyar gaba ɗaya ta gama canjawa ta fito tai wani irin fes fess da ita, abunka da farar fata sai ta sake zama kamar wata balarabiya. Sai data kama shafe shafenta tsaf kana ta tashi taje ta sauko da babban akwatinta dake shaƙe da kaya ta buɗe ta zaro wata sabuwar atamfarta Chiganvi wacce ƙawarta Hajiya Lubna ta ɗinka musu dukansu sukayi anko ita da sauran ƙawayensu ranar sunan yayarta Hajiya Kalsoom data haihu suka saka. Sosai kuwa atamfar tayi mata mugun kyau, kasancewarta fara atamfar kuma ta kasance kalar blue ce da yellow a jiki, anyi mata ɗinkin riga da siket wanda ya zauna a jikinta sosai ya fito da shape ɗinta tayi wani fayau da ita a ciki, sai data gama feshe jikinta da turare ko'ina ya ɗauki ƙamshi sannan ta ɗauko ɗan madaidaicin yellown gyalenta ƙarami ta yafa a kanta dan bata so ta ƙara ɓatawa kanta lokaci gurin tsayawa ɗaurin ɗankwali, a mugun ƙagare take ta ƙosa ta bar gidan jinta take kamar tana kan ƙaya, shiyasa kawai ta bar ɗankwalin akan gado ta ɗauki blue ɗin handbag ɗinta bayan ta zura takalmanta masu tsinin dunduniya suma kalar blue kana ta kwashe kuɗin dake cikin waccan jakar data fita da ita jiya ta zuba cikin wanda zata fita da ita yau kafin ta ɗauki ledar leshinta da zata kai ɗinki, kafin ta ɗauki kwaɗo ta fito ba tare data sake bi takan komai ba tasa kai ta fice abunta, dan ko ɗari biyar ɗin ma daya ajiye mata bata kalla ba saboda bata jin akwai abinda zata yi da ita tunda Allah ya hore mata kuma ya rufa mata asiri ya hore mata tana da kuɗi. Sai data kulle ƙofar ɗakin kana ta fice daga gidan tana wani irin taku cikin yanga ta kulle ƙofar gidan ta jefa ɗan makullin cikin jakarta sannan ta fara takawa zuwa bakin titi tana yatsine fuska cikin wani taku irin nasu na manyan mata masu ji da kansu tana wani rausaya jiki kamar ba matar aure ba. A haka tazo ta wuce ta gaban gungun mazan dake zaune akan layin inda suke haɗa ƴar ƙaramar majalisarsu da safe kafin kowa ya kama gabansa ya tafi gurin aikinsa, haka idan suka kuma dawo da dare ma sukan ɗan zauna su taɓa ƴar hira kafin kowa ya shiga gidansa, aiko tana gittawa ta gabansu duka suka bita da ido yadda take wani yauƙi da yarari da yawa a gurin sai data tafi da hankali da natsuwar su, ita kuwa ko ajikinta tayi gaba abunta tana ci gaba da takunta ɗaya bayan ɗaya cike da ginshira ta barsu da shaƙar daddaɗan ƙamshin turarenta mai matuƙar daɗi da sanyaya zuciyar duk wanda ya shaƙesa. Tana gab da fita daga cikin layin nasu ne ta hau kan titi wani mai keke napep ya taho aguje yazo yaci burki a gabanta, cike da iyayi da yanga ta ɗaga kai tana kallonsa kafin ta juya cikin iyayi tana faɗin "Bawan Allah ban tsaidaka ba ai...kana iya ƙarawa gaba..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana matsawa gaba kaɗan ta tsaya tana yatsina fuskarta kamar taga kashi. Zuro kansa waje yayi daga cikin keke napep ɗin yana dubanta fuskarsa cike da mamaki yace "Haba Hajiya...naga ai kamar abun hawa kike jira shiyasa na tsaya, kuma dan na tsaya ki shiga ai ba laifi bane...kamar ma na taimaka miki ne tunda baki sani ba kila kita jira kizo baki samu ba, kinga sai ki ɓatawa kanki lokaci tunda daga gani kamar gurin aiki zaki..." Daga haka ya sake gunguro keken nasa ya ƙaraso gabanta ya tsaya lokaci ɗaya yana faɗin "Muje Hajiya...ina za'a kaiki...? Wani ƙululun baƙin ciki ne da takaici lokaci ɗaya ya turnuƙe Fadwa ta ɗago a zafafe tana watsa mai harara cikin ɓacin rai take cewa "Wai wannan wane irin naci ne..? Nice na tsayar da kai da zaka dameni ko kuwa hawa keken naka dole ne da zaka takura min ko yaya...?" Cike da mamaki mai keken ya zuba mata ido kafin yace "To laifi ne dan naso taimaka miki...?" Cikin zafin rai tace "Ba laifi bane amma ka dubeni da kyau ka gani nafi ƙarfin kace zaka taimaka min, sai dai ni ka nemi taimako a gurina in taimaka maka, domin kaine kake a wahale kake neman taimako...." Cike da mamaki ya riƙe baki yana kallonta kafin yace "Ikon Allah..ashe kuma taimako yana juyewa ya zama masifa da bala'i ban sani ba...?" Fadwa da kalmar taimakon da yake ta maimaitawa ta fara ɓata mata rai tace "Wai kai kaga nayi maka kama da wacce zata nemi taimako a gurinka ne..ko kuwa nice na tsayar da kai nace dole saika ɗauke ni da zaka buwayeni...?" Kaɗa kai mai keke napep ɗin yay kafin yace "A'a baki ce ba Hajiya, amma Allah ya baki haƙuri...." Da sauri Fadwa tace "Ameen Ameen, sai kuma ka ƙara gaba. Haba ina dalili haka kawai daga ganina zaka wani ci burki a gabana ka dameni da sai na hau wani shegen ruɓaɓɓen kekenka...Sai kace saboda ni kaɗai yau ka fito..? Haka kawai ka shafa min masifa..ƙilan ma ƙararren kwana gareka inzo in hau keken naka kaje kayi hatsari ka mutu ni injijji ciwo ka barni da bala'in neman kuɗin magani ina zauniyata lami lafiya, ko kaje can ka watsar dani a gefen titi ka ɓata min lafiyayye jikina da tabbai. Dan ni tunda naga wannan shegen nacin naka nasan ba haka nan bane, shiyasa ma ni bana taɓa hawa keken da nasan bani na tsayar dashi ba, dan yawancinku masu rawar jikin ku ɗauki mutum ɗin nan duk masu tafe da tsautsayi ne wasu da ƙarar kwana, haka kawai suje su mutu su barka da wahalar rayuwa..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da jan tsaki, kafin ta wuce ta ƙara gaba ta barshi nan sake da baki yana bin bayanta da kallon al'ajabi da mamaki, sai da ta ɗan yi nisa kafin ya kunna mashin ɗinsa ya wuce. Itako Fadwa sai data ƙarasa bustop inda take hawa napep wani lokacin sannan ta hau bayan ta gaya masa Unguwar Rimi zai kaita inda shagon telanta yake kafin yaja suka wuce. Koda suka ƙarasa ta iske shagon telan nata a kulle bai riga ya fito ba, gashi ba waya a hannunta balle ta kirasa, dan tunda wayarta ta samu matsala ta jefar da ita bata sake bi ta kanta ba, dan bata jin zata iya gyara waya kuma sannan taci gaba da amfani da ita a ganinta tafi ƙarfin hakan. Dan haka kawai sai ta samu benci ta zauna a bakin shagon da nufin zata jirasa har zuwa lokacin da zai fito. Gurin ƙarfe 9am dai-dai kuwa sai ga wani matashin saurayi irin ƴan gayun nan ya iso akan farar mashin ɗinsa wayyo kuɗina, yana ganinta ya sauka daga kan mashin ɗin bayan yayi parking ɗinsa a gefe guda ya ƙaraso gabanta da fara'arsa yana faɗin "A'a Hajjaju yau kece tunda sassafe...meyasa baki kirani a waya nazo gida na ƙarba ba...?" Sauke numfashi Fadwa tayi tana yatsine fuska kafin tace "Wayan ne ya lalace kuma har yanzu ban siya wani ba, amma insha Allahu kwanan nan nake so in siya sabuwa..." Ta faɗa tana ɗaukar ledan da tazo da ita ta miƙa masa kafin taci gaba da faɗin "Gashi ai kana da measurement ɗina kayi amfani dashi ba sai ka sake gwadani ba, amma inaso ka ƙure basirarka kayi min ɗinki na garari da ɗaukar magana, dan so nake in cinye gurin da kwalliyata saboda manyan mata isassu za'a haɗa agurin bikin inaso idan na isa gaba ɗaya kallo ya dawo kaina gaba ɗaya in ɗauke hankalin mutane gurin..ka dai gane ai..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana buɗe jakar hannunta ta ƙirgo kuɗi dubu goma sha biyar cif ta miƙa masa, cikin murna ya karɓe yana faɗin "Insha Allahu karki damu Hajiyata zan finfaki sai kin fi kowa a gurin nan nayi miki wannan alƙawarin..." Cikin jin daɗi Fadwa tace "Yauwa Sadeeq shiyasa bana jinka, ina alfahari da kai ta wannan fannin..." Ta faɗa tana maida jakarta ta rufe kana ta miƙe tsaye tana faɗin "Ƙarfe nawa ne yanzu duba min..kasan ba waya a hannuna kuma gashi inata sauri ban tsaya na saka agogo ba na fito..." Agogon fatan dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba kafin ya ɗago kai yana faɗin "Ƙarfe tara da kwata yanzu Hajjaju..." Jinjina mai kai Fadwa tayi tana gyara zaman gyalen dake kanta lokaci ɗaya tana faɗin "Yauwa bari kawai in ƙarasa ƴan majalisu gidan Hajiya Lubna, dan nasan zuwa yanzu ita mijinta ya daɗe da fita..." Ta faɗa kai tsaye tana yin gaba, da sauri ya biyo bayanta shima domin yayi mata rakiya, a bakin titi suka tsaya, sai data tari keke napep ta gaya masa inda zai kaita sannan ta shiga sukayi sallama da telan akan nan da kwana uku ko huɗu ta zo ta karɓi ɗinkin ko kuma ya kawo mata gidan Hajiya Labiba, tunda yasan gidan wani lokacin ma tare yake musu ɗinki ya kai musu har gida. *Allah ya gafartawa iyayenmu da kakanninmu yasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya🤲* [12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad Aishaalto09* 7️⃣ Ƙofar wani haɗaɗɗen gida mai ɗauke da tangamemen farin gate ta nunawa mai Napep ɗin ya tsaya ta sauka, ta buɗe jakarta ta zaro ɗari biyar ta miƙa mai, ba tare data tsaya karɓan canjinta ba ta juya ta fara takawa a hankali ta ƙarasa bakin gate ɗin ta fara ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar a hankali. Ta jima sosai a tsaye tana ƙwanƙwasawa amma babu motsin wanda taji ballantana tayi tunanin za'a zo a buɗe mata, tun tana bugawa a hankali har ta fara gajiya ta koma bugawa da ƙarfi tana jan tsaki, gajiyar da tayi da tsaiwar ne yasa ta yanke shawarar ta juya kawai ta tari Napep ta wuce gidan Hajiya Labiba tunda nan basu da niyyar buɗe mata balle tasa ran zata shiga ciki, to ko dai itama Hajiya Lubnan yau basu tashi da wuri bane..? Tunanin hakan da tayi ne yasa kawai ta juya ranta a ɓace ta fara tafiya da niyyar ƙarasawa bakin titi don ta tari Napep, har ta kusa bakin titin taji an buɗe gidan da sauri ta juyo ta koma tana jin wani baƙin ciki a ranta, tana zuwa taga maigadin a tsaye ya babbake hanya yana watsa mata wata muguwar harara, a ɗage itama take kallonsa kafin ta saki tsaki lokaci ɗaya tana faɗin "Dalla Malam ni matsa ka bani hanya, ka wani babbake ka tsare hanya sai kace gidan ubanka..ni matsa ka bani guri da shegun idanuwanka sai kace na jemage..." Ta ƙarashe maganar a zafafe tana watsa masa wani banzan kallo. Shima kallon banzan ya watsa mata kafin yace "Bazan matsa ba ai kema nan ɗin ba gidan naki uban bane da zaki nemi ki gaya min maganar banza kwaɗayayya kawai ƴar maula..." Wani zabura Fadwa tayi tana kallonsa kafin ta matsa kusa dashi a fusace tana faɗin "Yau ni kake kira da ƴar maula...? Kasan matsayina a gurin matar gidan da zaka kirani da ƴar maula...? Lallai Habu yau ƙarshen gadinka anan gidan ne yazo, tunda kai baka gaji arziki ba zan nuna maka na fika rashin mutunci ɗan iska kawai maigadi..." Ta faɗa tana kumfar baki, yayinda ranta yake cike da jin haushinsa na kiranta da yayi da sunan ƴar maula, wai ita Fadwa yau maigadi yake kira da ƴar maula. Jinjina kai kawai yayi kafin yace "Ai na sani ba abinda kika haɗa da ita face ƙawance, in kuma bayan haka akwai wani abu sai ki gaya min idan yar uwarki ce kullum da zaki wani dinga zaryar zuwa mata gida kullum kina takurawa mutane da shegen yawace yawacen maularki kina wani iyayi da salo sai kace gidan mijinki, ke ko kunyar abun ma ba kyaji...." Ya faɗa yana jan tsaki cike da takaicinta, dan shi da yasan itace ma da babu abinda zai sashi ya buɗe mata ƙofa, shi haka nan matar sam bata taɓa masa ba bala'in haushinta ma yake ji saboda yadda take nuna musu iyayi da salo idan tazo shiyasa ya tsani tazo gidan, ita kuwa gashi ko a jikinta kusan kullum sai tazo sai kace gidan ubanta. Horn din da aka saki daga cikin gidan ne yasa ya juya da sauri yana faɗin "Sai ki kauce kiba masu gidan guri zasu wuce..." Ya faɗa yana komawa ciki da sauri ya fara ƙoƙarin buɗe tangamemen gate ɗin yana sakar mata harara. Itama Fadwan hararar ta sakar masa tana taɓe baki kafin ta ɗan matsa gefe ta tsaya tana jiran motar ta fito kafin ta samu ta shige ciki, dan ta rantse tunda wannan ɗan iskan ya mata wannan cin mutuncin sai ta shiga ta gayawa Lubna duk abinda yayi mata, dan ta yiwa kanta alƙawarin cewa sai ta haɗa masa sharrin da sai an koresa daga gidan sannan hankalinta zai kwanta tunda shi ɗan iska ne bai da kunya, wanda a ƙalla tana zaton ta girmesa nesa ba kusa ba, dan tayi ƙani dashi. Amma har ya iya kallon tsabar idanunta ya gaggaya mata maganganu iya son ransa har yana kiranta da ƴar maula saboda shi ga tantirin ɗan iska mara kunya, aiko zata nuna masa itama ta fishi rashin mutunci. Tana nan tsaye tana saƙawa da kwancewa wata hadaddiyar baƙar mota ƙirar Bugatti ta silalo ta fito daga cikin gidan, a hankali ta ɗago kai tana kallon motar wacce gaba ɗaya ta gama tafiya da imaninta, har wata ajiyar zuciya ta sauke da taga yadda motar take wani silalowa tana tafiya a hankali a hankali, ita dai Allah ya sani tana matuƙar ƙaunar ta ganta a cikin galleliyar mota irin haka ace dai wannan tata ce kota mijinta ranar bata san irin farin cikin da zata kwana tana yi ba, ƙara gyara tsaiwarta tayi ta kafe motar da ido ƙirr tana kallo. Kasancewar akwai tintek a jiki yasa bata gano waye a cikin motar ba sai daya iso gab da ita sannan ya sauke gilashin motar a hankali wani magidanci ne kyakkyawa fari tas tas wanda a ƙalla shekarunsa zasu kai arba'in da biyar zuwa da shida yaji hutu sosai, da ganinsa kasan kuɗi da jin daɗi sun gama zauna masa, yana sanye da wata ubansun shadda fara ƙal sai maiƙo take da yarari tana shaining, shigar tayi masa mugun kyau. Leƙo da kansa yayi fuskarsa ɗauke da murmushi lokaci ɗaya yana dubanta tun daga sama har ƙasa yace "A'a Hajiya Fadwa manyan mata yau kece a gidan namu tun da safe, to meyasa baki shiga ciki ba kike tsaye a nan waje sai kace wata baƙuwa ai ƙawar taki tana ciki babu inda taje..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana tsaida motar a gabanta. Cikin sauri Fadwa ta ɗauke kai dan kar ya fahimci yadda take ƙare masa kallo ta juyo a hankali ta ɗan risina tana faɗin "Barka da safiya ranka ya daɗe, har an fito kenan...?" Ta faɗa cikin tsantsar ladabi tana yin ƙasa da murya. Sai da ya ƙara ƙare mata kallo a fakaice kafin yace "Allah ya nufa Fadwa mun fito za'a tafi ƙwadago..." Cikin yin ƙasa da murya kamar wacce take gaban ubnata Fadwa tace "To Allah ya tsare yasa an fito a sa'a, Allah ya taimaka kuma ya bada sa'a..." Ta faɗa tana sakin ɗan murmushi, shima sake faɗaɗa murmushin nasa yayi, kafin ya buɗe wata yar loka a gaban motar ya zaro yan ɗari biyar biyar bandir guda ya miƙa mata yana faɗin "Gashi in kin tashi tafiya kya hau mota, na gode sosai kuma naji daɗin addu'arki Allah ya saka da alkhairi..." Ya faɗa tare da miƙa mata kuɗin hannunsa, aiko zaraf ta miƙa hannu ta karɓe tana washe baki cike da murna take faɗin "Na gode Alhaji Allah ya ƙara maka buɗi da arziki mai albarka da amfani, na gode Allah ya raya maka zuri'a kyakkyawar rayuwa mai albarka...na gode ƙwarai Allah ya biyaka ya ƙara dalili..." Ta faɗa cikin zumuɗi tana ƙara yashe baki, kaɗa kai kawai yayi yana faɗin "Ameen Ameen...Ameen ya Allah Fadwa na gode sosai da sosai ki gaida maigidan naki..." Cike da farin ciki itama ta sake risinawa kamar zata kifa tana cewa "Nike da godiya Alhaji, Allah ya saka ya bada lada, Allah ya barku da ƙawata Lubna..." Ya amsa mata da Ameen ya Rabbi kana ya ja motar ya ƙara gaba abinsa. Jujjuya kudin Fadwa ta dinga yi a hannuta lokaci ɗaya tana bin bayan motar tasa da kallo har sai da ya ɓacewa ganinta, sannan ta ɗauke idanunta ta buɗe jakarta ta jefa kuɗin a ciki tana sakin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, kana ta juya ta ƙarasa bakin gate ɗin inda Habu ke tsaye yana ta kallonta fuskarsa ɗauke da matsanancin mamaki, bata bi ta kansa ba ta tura ƙaramar ƙofar tayi shigewarta ciki ta barsa nan tsaye sake da baki yana bin bayanta da kallo. Har ta kusa isa ƙofar da zata sadata da shiga babban falon gidan ta dakata ta juyo tana kallonsa kamar yadda shima ya tsareta da ido har lokacin yana kallonta, wani dogon tsaki taja kafin ta watsa mai wata muguwar harara ta kallesa sama da ƙasa ta watsar kafin tace "Ba yadda mutum ya iya dani dole ana ji ana gani a barni in shiga, idan kuma ba haka ba a koma gidan mai dattin hula a cigaba da cin arne da kwot. Ƙaramin mara kunya kawai ɗan iska..." Daga haka ta juya ta cigaba da tafiya tana wani irin taku da rausaya ta shige korido ɗin da zai sadata da ƙofar shiga falon gidan. Bata tsaya wani ƙwanƙwasawa ba dan tasan Hajiya Lubna bata cika kulle ƙofar babban falon gidanta ba, ba kamar Hajiya Labiba ba da sai kai ta faman tsayiwa kana ƙwanƙwasawa kafin da ƙyar wannan mummunar mai aikin nata tazo ta buɗe maka ba, aiko tana turawa ƙofar ta buɗe ta shige ciki bakinta ɗauke da sallama. Wata kyakkyawar mace ce black beauty ƴar duma duma hakimce akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman lafiyayyun kujerun da suka yiwa haɗaɗɗen ƙayataccen falon nata da yasha kayan alatu ƙawanya, taci uban kwalliya sai kace wacce tayi shiri zata gasar sarauniyar kyau jikinta sanye da wani tsaddaden leshi maroon colour wanda akayiwa ɗinkin bubu gown sannan aka ƙawata gaban rigar da stone work wanda aka jajjerasa tun daga sama har ƙasa gwanin sha'awa, gashi ta zuba gwala-gwalai jikinta sai sheƙi yake da ɗaukar ido. Jin sallamar Fadwa yasa ta juyo a hankali cikin wani irin salo ta amsa mata da wata irin murya kafin ta miƙe cikin iyayi da yanga tana faɗin "Barka ƙawata..daga ina kuma haka tun da sanyi safiya aka doko mana irin wannan uban sammako...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallonta. Sanin halinta da Fadwa tayi ne yasa hakan bai wani dameta ba, sai ma washe mata baki da tayi tana faɗin "Wallahi daga gurin Sadeeq tela nake na kai masa ɗinki, shine nace bari in ƙaraso mu gaisa dan mun kwana biyu bamu haɗu ba..." Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana zama kan kujerar da take facing din wacce Hajiya Lubnan ta tashi akai. Ɗan taɓe bakinta Hajiya Lubna tayi kafin ta koma ta zauna itama tana faɗin "Ok yayi kyau, to ya gidan..ya kuma mai keke napep ɗinki an fita hayis ɗin kenan....?" Ta faɗa cike da rainin wayau lokaci ɗaya tana kallonta. Taɓe baki Fadwa tayi itama kafin ta zare gyalen dake jikinta ta ajiye tana faɗin "Aiko kamar kin sani ƙawata ɗan wahalar ya fita tun sassafe, ana can kuma ana yawon gararanba a kwalta...." A wulaƙance Hajiya Lubna take dubanta tana wani yatsine fuska tace "Ai dama abinda ya kamaceku kenan tunda dama tun asali ba wani abun arziki ke gareku ba kema dan kinƙi natsuwa ne a guri guda ki maida hankalinki kan mijinki ki zauna lafiya shiyasa kika kasa gane abinda ya kamaceki. Kwaɗayinki da son abun duniya ne ya gama rufe miki ido shiyasa kullum kike gantali a titi kin kasa zama guri guda balle ki natsu ki kama kanki ke kenan yawon bin gidajen ƙawaye kina naniƙe musu, kamar kema ba miji nan gareki ba duk kin bi kin hana kanki sukuni kina wahalar da rayuwarki a banza kin gama ƙasƙantar da kanki a wofi...." Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana jan tsakin takaici kafin ta ci gaba da faɗin "Amma fa kiyi haƙuri idan maganata tayi miki zafi kinji ƙawata....?" Ta ƙarashe maganar tana watsa mata wani kallon gefen ido, kana ta shiga kwallawa mai aikinta Adama kira ta fito daga cikin kichin da sauri tazo gabanta ta duƙa tace "Gani Hajiya..." Ba tare data ɗago kai ta kalleta ba tace "Jeki haɗowa ƙawata abun kari dan nasa da wuya idan ma ta karya daga gidanta ta fito, yi sauri kije ki haɗo mata...." Ta faɗa cikin halin ko in kula kafin ta juyo ta fuskanci Fadwa data jingina kanta da jikin kujera ta lumshe idonta ko a jikinta, tace "Bari a kawo miki breakfast dan nasa ƙila haka nan kika fito ba tare da kin tsaya kinyi karin kumallo a gidanki ba....?" A mai makon Fadwa ta nuna taji haushin maganar da Hajiya Lubnan ta gaya mata, amma sai bata nuna komai ba, kawai ta share ta saki murmushi lokaci ɗaya tana faɗin "Wallahi kamar kuwa kin sani ƙawata..ruwan lifton kaɗai na sha na fito, dan wani matsiyacin buredi ne ya siyo ya kawo ya ajiye min tun shekaran jiya waccan yau kusan kwanansa uku kenan a haukansa wai ni zanci, ni kuwa ina zan iya wannan rayuwa ta wulaƙanta kai. Dan ma Allah yasa ina daku a garin nan da na shiga uku da uƙubar rayuwa..." Ita dai Hajiya Lubna bata tanka mata ba ta ɗauki remote tana canza tashoshi daga Tauraruwa Tv zuwa MBC Bollywood. *Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu, kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya🤲* [12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad Aishaalto09* 8️⃣ Amma abun mamaki duk wannan ɗaure ɗauren fuskar da shan ƙamshin da Hajiya Lubna take bai wani ɗaɗa Fadwa da ƙasa ba ballantana ya dameta, abinda zaiyi matuƙar baka mamaki da takaici ma bai wuce nunawa da tayi ko a jikinta babu abinda ya dameta ba. Saboda a ganinta ta daɗe da sabawa da halinta na wulaƙanci da nuna kai ba komai bane a gurinta, dan ma wai ita ɗin Fadwan ƙawarta ce kuma tana sonta shiyasa bata cika nuna mata halinta na rashin son wani ya raɓeta ba take ɗan dannewa wani lokacin ta nuna ana tare. Amman duk da haka wata rana a fakaice take gaggaya mata maganganu akan kwadayinta da son abun duniyarta, itako Fadwa sai ta nuna ko a jikinta abun baya damunta saboda in da sabo yaci ace zuwa yanzu ta daɗe da sabawa da halin ƙawar tata. Tana nan zaune mai aikin ta shiryo mata abun kari a ɗan madaidaicin faranti ta kawo mata har gabanta, sai data jawo ƙaramin tebur ta ɗora mata akai kana ta ɗauki filet ta fara zuba mata soyayyen dankali da kwai sannan ta zuba mata souce ɗin hanta a gefe ta ɗora mata da cinyar kaza ta ajiye a gabanta, ta ɗauki kofi tana ƙoƙarin haɗa mata tea ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu tana cewa "A'a jeki barshi wannan ma ya isa...." Ta faɗa tare da ɗaukar fork ta fara cin soyayyen dankalin hankalinta kwance ba tare data ko ɗaga kai ta kalli inda Hajiya Lubna take zaune ba, saboda taga take takenta so take ta dinga mata abinda zaisa tayi zuciya tace ta daina zuwa gidanta, ita kuma bata ga wannan ranar ba. Dan ko dukanta tayi ta mata korar kare sannan ta haɗa mata da har da zagi ta uwa ta uba ba zai hanata zuwa gidanta ba sai tazo ko dan daɗin da take ci, ga kuma haɗaɗɗun suturu da ɗinkunan kece raini da suke mata ita da Hajiya Labiba. Aiko dan wannan ta ƙara daurewa ta cigaba da jure wulaƙancinta tayi ta bibiyarsu kafin itama lokacinta yayi burinta ya cika taga ta samu abinda take so. (Lallai wannan shi ake kira da inda kwaɗayi dole ka jure wulaƙanci😂) A ɓangaren Hajiya Lubna kuwa ta wutsiyar ido ta dinga ƙarewa Fadwa kallo wacce ta zage tana ta tura dankali da kwai sai kace wata mayunwaciya ko wacce ta kwan ta wuni bata ci komai ba, sakin tsaki tayi cike da takaicinta kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Kinje gidan Hajiya Labiba kuwa..ko can ɗin ma kin kwana biyu baki leƙa ba...?" Fadwa data cika bakinta da naman kaza ta ɗago tana girgiza mata kai kafin tace "Jiya ma ai can na wuni abuna muka sha hirarmu da ita...kinsan ita akwai son mutane shiyasa da wuya kiga nayi kwana biyu ban leƙata ba, kullum ina kan hanyar zuwa gidanta saboda ita mai jama'a ce...." Ta faɗa cike da tura haushi tana kallonta, itama Hajiya Lubnan fahimtar da tayi magana ce kawai Fadwan ta gaya mata a fakaice yasa ta jinjina kai lokaci ɗaya tana murmusawa kafin tace "Aiko kin kyauta, Allah ya bar zumunci da ƙauna..." Cikin taɓe baki Fadwa ta amsa mata da "Ameen Ameen dai...." Daga haka gaba ɗaya sukayi shiru babu wanda ya sake magana a cikinsu, har Fadwa ta kammala cinye dankalinta tas kana ta sha ruwa mai sanyi, ta saki gyatsa kafin ta soma ƙwallawa Adama mai aikin Hajiya Lubnan kira ba ɓata lokaci tazo ta risina a gabanta tace "Gani Hajiya..." A yatsine Fadwa ta nuna mata farantin dake gabanta ba tare da tace komai ba tayi mata alama da ta kwashe kayan, da sauri ta tashi ta tattara kayan ta kwashe ta wuce ta kai kichin kana ta cigaba da aikinta. Ita kuwa Fadwa komawa tayi ta jingina da jikin kujerar tana wani lumshe ido alamar cikinta ya cika taci tayi hani'an. Ita dai Hajiya Lubna kallon ikon Allah kawai take tana ƙara mamakin Fadwa da ƙarfin halinta, baki ta taɓe kafin ta miƙe tsam tana girgiza kai ta wuce ta haura sama inda ɗakinta yake. Ba jimawa sai gata ta fito hannunta riƙe da wani ɗan madaidaicin gyale da jaka a hannunta wanda suka shiga da kayan jikinta, saukowa tayi zuwa cikin falon ta ƙaraso inda Fadwa take kishingiɗe akan doguwar kujera ta zuba mata ido tana kallonta. Ganinta cikin shirin fita ne yasa Fadwan ta tashi zaune da sauri daga kishingiɗar da tayi tana faɗin "Zaki fita unguwa ne ƙawata...?" Gyaɗa mata kai Hajiya Lubna tayi lokaci ɗaya tana saƙala jakar handbag ɗinta a tsintsiyar hannunta take faɗin "Eh inaso zan shiga kasuwa ne akwai abubuwan da nake so in siya zanyi amfani dasu anjima kafin Alhajina ya dawo...ko zakije ne...?" Ta faɗa tana duba agogon tsadaddiyar wayarta ƙirar iPhone 11 pro max dake hannunta. Tashi zaune Fadwa tayi da sauri tana faɗin "Aiko nima shawarar shiga kasuwar dama nake ina so zan siya waya bari in tashi mu tafi tare daga can kawai sai in wuce gidan Ƙawata..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa ta yafa gyalenta kana ta ɗauki jakarta ta sagala tace "Muje ko...?" Ta faɗa tana yin gaba, Hajiya Lubna kuwa kichin ta wuce inda ta iske Adama na wanke wanke ta sanar mata da cewa zata fita ta kula da gidan, sannan ta fito ta bi bayan Fadwa wacce tuni ta daɗe da fita daga falon. A sabuwar Prado ɗin Hajiya Lubnan wacce mijinta ya siyan mata ko sati ba ayi ba suka fita, wanda tunda suka fita tafiya kawai suke kamar kurame ba wanda ya tanka ma wani a cikinsu har suka shiga kasuwa. Royal Plaza suka fara zuwa inda Fadwa ta siya wayarta ƙirar Infinix smart 5 sabuwa dal a kwalinta ta lale kudinsu ƙyal dubu hamsin ta basu, ita dai Hajiya Lubna sai kallonta kawai take cike da al'ajabi tana mamakin inda ta samu kuɗi haka, amma da tayi wani tunani sai ta kaɗa kai kawai ba tare da tace komai ba, amma tabbas tasan babu wanda zai iya bata waɗannan kuɗaɗen sai Hajiya Labiba ko Aunty Kalsoom domin sune suke ɗaure mata gindi akan komai take yadda take so. Daga nan cikin kasuwa sukayi inda ta raka Hajiya Lubna gurin ƴar Sudan mai tutaren manyan mata, tai mata haɗin turarukan data saba haɗa mata masu tsada kana daga nan kuma suka wuce wani haɗaɗɗen babban shagon saida jakunkuna da takalma masu tsada ta zaɓi duk kalolin da takeso, sannan tace itama Fadwa ta zaɓi jaka da takalmi kala ɗaya irin wanda takeso, aiko Fadwa kamar bakinta zai yage saboda tsabar murna tai ta washe baki. Sosai suka daɗe a kasuwar dan sai gurin gab da la'asar sannan suka bar kasuwar suka nufi gida, dan sai da Hajiya Lubna ta gama duk wata siyayyar da zatayi wacce duk abinda ta siya sai tace Fadwan itama ta ɗauka, saboda tasan halinta ba ƙaramin aikinta bane tai ta terere da ita tana gayawa ƙawayensu tace ta rakota kasuwa amma taƙi sai mata komai shiyasa hatta da sababbin kayan baccin data siya sai data siyan mata itama kana suka bar kasuwar. Tun a hanya kafin su ƙarasa gida Fadwa tasa Hajiya Lubna ta sauketa a Laventis Round About ta hau napep ta nufi Gwamna Road gidan Hajiya Labiba, ita kuma Hajiya Lubna ta wuce gidanta. Ana kiran sallar la'asar ta isa gidan sai da ta fara saka chajin sabuwar wayarta sannan tasa Rabi ta zubo mata lafiyayen abincin data gama girkawa taci ta ƙoshi tayi hani'an sannan ta tashi ta haura sama ɗakin Hajiya Labiba taje tayi sallah inda ta haɗa azahar da la'asar kafin tana idarwa suka sake saukowa falon ƙasa tare. Nan suka zauna sukai ta hira har wayar Fadwan ta cika suka kunna, sai murna take bakinta yaƙi rufuwa. Da rawar jiki ta ɓare sabon layinta na MTN data siya tun a kasuwa ta saka kana ta zaro tsohuwar wayarta ƙirar Aitel a cikin handbag ɗinta ta buɗe ta zare tsohon layinta na Airtel a ciki ta saka a sabuwar wayar, sai data jira layukan duka suka gama hawa kana ta kwalawa Rabi kira tazo ta miƙa mata tsohuwar wayar tace "Gashi nan kema sai kije ki gyara kya ƙarasa ta..." Cike da murna kuwa ta ƙarba tana ta zuba godiya har da duƙawa lokaci ɗaya kamar zata kifa ƙasa saboda farin ciki, domin ta daɗe dama tana ƙaunar waya ƴar dangwale amma tsabar maƙo da son abun duniya ya hanata siya saboda bazata iya cire maƙudan kuɗaɗe ta siya waya ba, duk ko da irin kuɗaɗen da Hajiya Labiba take biyanta duk wata naira dubu talatin bata jin zata iya cire ko rabi ne ta siya waya, shiyasa take ta fama da ƴar ƙaramar nokia ɗinta mai touch light, amma yanzu tunda ta samu an bata zata iya ƙuru ta cire kuɗi ta bada a gyara mata. Sai da komai na wayar ya gama saituwa kana nan take Hajiya Labiba ta ɗauki wayarta tai mata vtu transfer na dubu uku direct daga bankinta ta siyan mata data na wata ɗaya, ba ɓata lokaci ta buɗe mata Facebook da WhatsApp da Instagram dake dama duka tana yin abun ta tun kafin tayi aure. Sai data gama yi mata saitin komai dan har a group ɗinsu na Isassun mata wanda nasu ne yasu yasu class mates ɗin juna waɗanda sukayi karatu tare, sai da ta yiwa admin ɗin magana kana ta maidata saboda dama tana ciki da aka buɗe mata sabon WhatsApp ɗin ne sai tayi left a group ɗin. Komai na gama saituwa Hajiya Labiba ta miƙa mata wayar lokaci ɗaya tana faɗin "Barka My Ƙawa an dawo online..sai chat kuma, dama kowa sai tambayarki yake ina kika shiga kwana biyu ba'a ganinki a online....?" Cikin sauri Fadwa ta gimtse fuskarta tana faɗin "Amma dai baki ce musu wayata ce ta lalace ba ko...dan kar su rainani...?" Ta faɗa tana wani tsatstsareta da ido. Tsareta da nata idanun itama Hajiya Labiban tayi tana kallonta kafin ta girgiza kai lokaci ɗaya tana faɗin "A'a ban gaya musu ba, kawai cewa nayi kin gaji da chatting din ne shiyasa kika daina hawa sai kin huta..." Ta ƙarashe maganar da murmushi akan fuskarta tana kallonta, sai a lokacin Fadwa ta saki murmushin itama kafin tace "Ai dama nasan bazaki taɓa gaya musu ba saboda ke ƴar amanata ce, da dai waccan zaƙwai akuyar Zulai ɗin ce Lubna nasan tsaf zata gaya musu tace wayata ce ta lalace, ta zubar min da kima da mutuncina a gurinsu suji daɗin rainani...." Kai tsaye Hajiya Labiba tace "Tsaf kuwa indai Lubna ce kaɗan daga aikinta ne wannan tsaf zata iya...." Ta faɗa tana dariya, itama Fadwan dariyar tayi kafin daga haka suka ci gaba da hirar group ɗin nasu. Suna nan zaune har ƙarfe 6pm. Ta buga amma Fadwa bata da niyyar tashi ta tafi gidanta, sai ma sake gyara zama da tayi ta cigaba da chatting din da suke a group tana kwasar dariyar labarin da wata ƙawarsu Azima ke basu akan mijinta, daga ƙarshe da abun yayi mata daɗi ma bata san har lokaci ya wuce haka ba, dan har an idar da sallar magriba duk bata sani ba. Sai da Hajiya Labiba ta taɓa ta ta nuna mata lokaci a wayarta sannan ta farga ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi akan kujera tana jan tsaki lokaci ɗaya tana faɗin "Kai wallahi hirar tayi min daɗi sosai, shegiya Azima ashe itama haka ta iya tsiya...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara fashewa da dariya kafin ta sake ɗaukar wayar zata ci gaba da chatting ɗinta hankali kwance, fizge wayar Hajiya Labiba tayi a hannunta tana faɗin "Kin kuwa ga time Fadwa...fast 8pm fa yanzu..? Ya kamata gaskiya ki tashi kiyi shirin tafiya gidanki dan kila zuwa yanzu mijinki ya daɗe da dawowa ke kina nan...." Cikin ɓacin rai da takaici Fadwa ta kalleta kafin ta miƙe ta ɗauki jakarta da gyalenta lokaci ɗaya tana faɗin "Wallahi na tsani takura a rayuwata, ba dan ba dan ba da babu abinda zai hanani kwana yau a gidan nan Allah na rantse..." Ta ƙarashe maganar tana jan tsaki. Jinjina kai Hajiya Labiba tayi kafin tace "Kisha kuruminki ai wata rana dole zaki kwanan tunda gashi an kusa fara bikin ƙanwar Hajiya Lubna, kinga ai dole zai barki ki zo nan ki kwana biyu har sai an gama biki sannan ki koma gida..." Cike da jin daɗi Fadwa ta washe baki tana faɗin "Allah ya kaimu ya nuna mana, ai wallahi ko bai amince ba sai na taho..." Ta faɗa tana yin gaba yayinda Hajiya Labiba ta miƙe itama tabi bayanta don yi mata rakiya, dan yau bata jin zata samu damar kaita gida, saboda tasan mijinta yanzu haka yana kan hanyar dawowa gida tunda yau ma anan gidanta yake, kuma ita bata son duk abinda zai hanata bawa mijinta cikakkiyar kulawa ɗari bisa ɗari a kwanaki biyun da yake zuwa yana yi a gidanta, saboda ta sani tana da kishiya ba ita kaɗai bace shiyasa take kiyaye duk abinda zaisa ta shiga hakkin mijinta ballantana har ya hanata bashi kulawar da ta dace. *Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya🤲* *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 9️⃣ Ƙarfe 9pm dai-dai mai keke napep ɗin daya ɗaukota daga gidan Hajiya Labiba ya sauketa a ƙofar gidanta bayan ta biyasa kuɗinsa ta juya ba tare da fargaban komai ba ta nufi gidan, tun kafin ta ƙarasa ta hango ƙofar gidan nata a buɗe an wangale ƙofar saɓanin a rufe da kwaɗo kamar yadda ta barshi ɗazu lokacin da zata fita, cike da mamaki ta ƙarasa bata ko bi ta kan tsohuwar mashin ɗin da ta gani fake a ƙofar gidan ba ta shige tana tambayar kanta ko dai ɓarayi ne suka shigo musu gida suka kwashe mata kaya, wannan tunanin daya bijiro mata ne yasa da sauri ta afka ta yaye labulen ɗakin kai tsaye kafin a fili ta furta "Aiko dana shiga uku na lalace..dan na gama yawo na tashi aiki...." Ta faɗa cikin tashin hankali tana zare ido. Kamar daga sama ta jiyo muryar mahaifinta daga cikin ɗakin yana faɗin "Baki shiga uku ba tukunna Fadwa, tunda abinda kika zaɓarwa kanki kenan..." Wani matsanancin faɗuwa gabanta yayi kafin da sauri ta saki labulen a tsorace tana dafe ƙirjinta cikin zaro ido tana faɗin "Na shiga ukuna...ashe Abba ne..to yaushe yazo gidan...?" Daga cikin ɗakin ta sake jiyo muryarsa a karo na biyu cikin bada umarni yana faɗin "Shigo ciki..." Ɗaga ƙafarta tayi cikin sanyin jiki ta fara ja da baya da baya tana dafe bakinta lokaci ɗaya tana girgiza kanta kafin ta juya da sauri jiki na rawa zata fice daga gidan, dan tabbas in da tasan cewa mahaifinta yana cikin gidan da babu abinda zai sata tayi sha'awar shigowa sai dai tayi ta tsayuwarta a waje har ya gama zamansa ya fito ya tafi, dan tafi kowa sanin halinsa kaɗan ne daga cikin aikinsa ya zage ya gurjeta yay mata shegen duka kuma babu mai iya ƙwatarta a hannunsa. Ji tayi an fizgota ta baya da mugun ƙarfi an wancakalar da ita gefe guda, a zafafe ta ɗago tana huci lokaci ɗaya tana ƙoƙarin miƙewa, ganinsa tsaye a kanta yana watsa mata wani irin mugun kallo ne yasa ta zabura da sauri ta miƙe tsaye tana aika mai da wani banzan kallo sama da ƙasa kafin cike da masifa tace "Wannan wane irin iskanci ne da wulaƙanci da zaka wani fizgoni ka watsar dani sai kace wata mage...wannan ai tsabar mugunta ce da mugun hali salon kaje ka karya ni ka illata ni ka kashe min rayuwa tunda baka da asara ai...." Marin da aka ɗauketa dashi ne ya hanata ƙarasa maganar da tayi niyyar faɗa, da sauri ta dafe kuncinta ta ɗago tana kallonsa, kafin ta farga idanunta ya gama buɗewa ta samu gano wanda ya maretan ta sake jin saukar wani zazzafan marin wanda har yafi na farkon azaba haɗe da raɗaɗi a karo na biyu. Matsawa baya tayi da sauri tana sosa kumatunta da yayi mata wani irin cik saboda mugun shigarta da marukan sukayi, kafin ta duƙe a gurin cikin rawar jiki har lokacin kuma tana tallabe da kumatunta dake mata mugun raɗaɗi sakamakon marin da mahaifin nata yayi mata wanda yasa gaba ɗaya fuskarta ta ɗauki zugin azaba. Kyakkyawan farin Dattijo ne da shekarunsa a ƙalla zasu iya kaiwa 65 tsaye a gefen Ya Azeez fuskarsa ɗauke da matsanancin ɓacin rai yake dubanta kafin ya juya yana duban Ya Azeez wanda ya duƙar da kansa, cikin nutsatstsiyar muryarsa mai cike da tarin kamala da dattako haɗe da ɓacin rai yace "Kana tsaye kana kallonta take gaggaya maka irin waɗannan maganganun amma ka kasa yi mata komai...? Wannan wace irin zuciya ce gareka da bazata iya baka shawarar hukunta iyalinka idan tayi maka ba dai-dai ba...? Kenan nufinka kafi son ta cigaba da duk abinda takeso kana kallonta ko...?" Ya faɗa yana tsaresa da ido, da sauri ya girgiza kansa yana faɗin "A'a Abba ba haka bane...." "To idan ba haka bane yaya ne....?" Ya faɗa yana ƙara kafesa da idanu. Rusunawa yayi cike da girmamawa kafin yace "Wallahi Abba ina mata faɗa sosai idan naga tayi ba dai-dai ba kum...." Saurin katsesa yayi da faɗin "Kana mata faɗa idan kaga tayi ba dai-dai ba amma kuma take cigaba da aikata ba dai-dai ba ɗin...baka tunanin cewa har yanzun baka mata irin hukuncin daya dace da irin laifin da take aikatawa bane....?" Ƙwarjinin dattijon ne yasa ya kasa magana kawai ya duƙar da kansa ƙasa yana kallon Fadwa wacce ta takure a guri guda ta matse kafafunta tana matsar ƙwalla. Wata uwar tsawa ya buga mata wacce tasa jikinta ya sake ɗaukar rawa da kakkarwa ta zaburo babu shiri ta matso gabansa da rarrafe cikin rawar murya take faɗin "Ab..ba...dan Allah kayi hakuri wallahi tallahi bazan sake ba...dan girman Allah wallahi daga yau zan dinga jin maganar Ya Azeez na rantse da Allah bazan sake fita ko nan da can ba sai da izininsa...." Ta ƙarashe faɗa cikin rawar jiki tana matsar ƙwalla. Wani murmushin takaici kawai Ya Azeez ya saki kafin ya kaɗa kai a zuciyarsa kuwa cewa yayi zaki gane baki da wayau ne yarinya ba dai kince bakya jin magana ba, zamu zuba nida ke aga wanda zai ci riba. Fadwa kuwa sosai take shassheƙar kuka tana matsar ƙwalla kamar gaske, shi dai Ya Azeez kawai girgiza kansa yake yana kallonta, dan yasan babu wani kukan da take kawai tsabar bariki ce da iya kwarewa a munafunci yasa take haka. Shi kuwa Malam Jabir kallon Fadwa wacce ke zube a gabansa tana kuka yayi kafin ya ɗauke kansa lokaci ɗaya yana kallon Ya Azeez wanda ya duƙar da kansa yana faɗin "Ayi mata haƙuri Abba...insha Allahu bazata sake ba...." Cike da ɓacin rai yake dubanta kafin yace "Daga yau idan ta sake fita ko nan da ƙofar gida ne bada izininka ba ka kirani, kuma duk wasu abubuwa da take maka marasa kyau idan har bata daina ba ta cigaba ka gaya min, ni kuma zanyi maganinta tunda ita tace faɗa baya taɓa yi mata to ni nasan ta yadda zan bi da ita...." Yana ƙarashe maganar ya juya ba tare da ya sake ko bi ta kanta ba ya tsallaketa ya fice daga gidan yayinda Ya Azeez ya rufa masa baya da sauri don yi masa rakiya. Sai data jiyo ƙarar tashin mashin ɗinsa kafin ta iya lallaɓawa ta miƙe a hankali tana sake dafe fuskarta da har lokacin take mata mugun raɗaɗin azaba ta ɗauki jakar handbag ɗinta dake yashe a ƙasa ta zuge da sauri ta fito da sabuwar wayarta da take cike da fargabar ko ta fashe sakamakon cillar da jakar da tayi lokacin da taji shigar marin da Abbanta ya ɗauketa dashi. Sai data duba taga babu abinda ya samu wayar sannan ta kaɗa kai ta maida ita cikin jakar ta koma ta jingina da ƙofar ɗakin nata tana sauke numfashi haɗe da ajiyar zuciya. Tana nan a zaune ya shigo bayan ya kulle ƙofar gidan ya saka sakata ya ƙaraso gabanta ya tsaya tare da zuba hannuwansa duka cikin aljihun wandon jeans ɗin da yake jikinsa ya zuba mata ido yana ƙare mata kallo, a hankali ta ɗago kai tana dubansa kafin ta sakar masa harara cike da jin haushinsa kana ta fara ƙoƙarin miƙewa, saurin ɗagota yayi cike da mugunta ya haɗeta da faffaɗan ƙirjinsa ya fara kissing ɗin wuyanta zuwan cikin kunnenta. Fizge jikinta tayi da sauri ta matsa gefe tana zafga masa harara, ɗan ɗaga kafaɗarsa yayi alamar ko a jikinsa, kana ya tsura mata idanu yana kallonta ta cikin ɗan hasken wutar solar daya hasko cikin gidan nasu kafin ya miƙa hannunsa cikin tamke fuska ya fincikota ta ƙara faɗowa jikinsa ya haɗeta da ƙirjinsa lokaci ɗaya ya ɗago fuskarta yana kallon cikin ƙwayar idanunta dake cike da ruwan hawaye ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi wanda bashi da maraba dana mugunta. Cike da jin haushinsa ta galla masa harara, amma ko a jikinsa sai ma ya kashe mata idonsa ɗaya yana ci gaba da yi mata murmushin. A ranta tace "Mugu kawai dole kayi min dariya mana tunda ka haɗa min munafunci kasa an mareni..." Kamar yaji abinda tace kuwa ya ɗago yana tureta daga jikinsa ya yatsine fuskarsa lokaci ɗaya yana faɗin "Ya mukayi dake ɗazu da safe kafin in fita...me nace dake....?" Ya faɗa lokaci ɗaya yana tsareta da idanuwansa. Wani banzan kallo ta watsa mai kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Na manta...." Ta faɗa kai tsaye ba tare da fargabar komai ba. Murmushi yayi kafin yace "To naji wuce kije kiyi sallah dan nasan da wuya idan kinyi daga can inda kike, tunda ko a gidan ne ma dole sai an matsa miki sannan kike yi..acan kuwa ai babu mai matsa miki tunda duk shegiyar ɗarin ce..." Ya ƙarashe maganar yana wucewa ya shige cikin ɗaki ya barta nan tsaye a gurin tana binsa da wata ƙatuwar harara kamar idanunta zasu faɗo ƙasa. Ta daɗe a tsaye tana saƙa maganganun Abbanta a zuciyarta kafin ta saki ƙaramin tsaki ta shige ɗakin tana ƙunƙunai, zaune a falo ta iskesa yana danne danne a ƴar wayarsa, ba tare data kallesa ba ta wuce ta shige uwar ɗaka sai data fara cire kayan jikinta ta ɗaura zani a ƙirjinta sannan ta ɗebi ruwa a bokiti ta ɗauki kwandon soso ta fita. Har ta cire zaninta ta sagale a jikin katanga ta tsugunna zata fara wankan, ta tuna da jakarta data bro akan gado, aiko da sauri ta rarumi zaninta ta sake ɗaurawa ta fito da gudu. Yana nan zaune a inda ta barshi yaga ta afko cikin ɗakin da gudu tana haki kamar wacce aka koro, a tsorace ya ɗago kai yana kallonta dan har ga Allah ta bashi tsoro, itako kota kansa bata bi ba ta wuce cikin uwar ɗakan, sai data ɗauke jakarta ta ɓoye a cikin kayanta sannan ta fito ta sake ficewa, shi dai binta kawai yake da ido lokaci ɗaya yana girgiza kansa har ta fice kafin ya ɗauke kansa ya maida kan wayarsa ya cigaba da abinda yake yi. Yana cikin waya da Ummansa ta shigo ɗakin da bokiti ta ajiye kana ta ɗauki buta ta sake fita, koda ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin ta iske still dai yana kan waya da Umman tasa suna ta hira, haka tazo ta sake wucewa ta gabansa taje ta ajiye butar. Tana cikin shafa mai ya shigo da wayar a hannunsa ya miƙa mata lokaci ɗaya yana faɗin "Gashi ku gaisa Umma ce..." Banza tayi dashi ta miƙe ta raɓa ta gefensa ta wuce ta ƙarasa gurin akwatinta ta buɗe ta fara ƙoƙarin ɗauko kaya, matsawa yayi gabanta ya sake miƙa mata wayar yana faɗin "Ƙarɓa mana Fadwa Ummana ce fa..." A zafafe ta ɗago kai tana watsa masa kallon banza kafin tace "To don Umman cefa...uwata ce ko kuwa dole ne akace sai na gaisa da itan...?" Ta faɗa cikin nuna zallar rashin mutunci da rashin kunya. Bai damu ba yace "Amma ai Ummana tamkar uwa take a gareki ko..kuma dan nace ku gaisa ai naga ba aibu bane tunda kema mahaifiyarki ce...?" Hayayyaƙo masa tayi cike da fitsara take faɗin "Allah ya kyauta min wallahi ni ba mahaifiyata bace babu abinda na haɗa da ita, mahaifiyata tana nan a inda take amma ni bana kalar uwar wasu ince mata tawa haka kawai saboda shisshigi...gaisawa ne dai kuma nace bazan gaisa da itan ba dan ba'a dole dan haka sai a kauce a bani guri..." Jin tijara takeson yi masa ne yasa da sauri ya maza ya kashe wayar dan kar mahaifiyar tasa taji abinda take faɗi, saboda ko kaɗan baya buƙatar tasan irin zamantakewar auren da suke gudanarwa a tsakaninsu. Fadwa kuwa tsaki ta saki kafin ta ɗauki kayan baccinta ta matsa gefe ta fara ƙoƙarin sakawa, tsayawa kawai yayi galala yana kallonta ta zura rigar wanda ya kasance doguwar rigar bacci ce irin mai kaurin nan kana ta ɗauki hijabi ta saka ta zari darduma ta shimfiɗa shi dai kawai binta da ido yake, sai da yaga ta tada sallah sannan yaja ƴan ƙafafuwansa a sanyaye ya fice ya koma falo ya zauna ya dafe kansa yana tunanin matakin da ya kamata ya ɗauka akan Fadwa. Dan har ga Allah ba zai taɓa iya haƙuri ya zuba mata ido yana kallo ta raina mahaifiyarsa ba, zai iya jurewa ya ɗauki komai nata indai zai tsaya a iya kansa ne, amma baya jin zai iya daurewa ya ɗauki raininta akan Ummansa, domin gaskiya bashi da wannan haƙurin kuma baya jin zai iya samunsa indai akan mahaifiyarsa ne domin bai da wanda ya kaita duk faɗin duniyar nan saboda haka bai haɗata da kowa ba kuma baya jin zai iya haɗa matsayinta da kowa, balle har ya bari wani ya nemi taka masa ita ko waye shi kuwa kuma komai matsayinsa a duniya. Motsinta daya jiyo daga cikin ɗakin ne yasa ya miƙe da sauri ya faɗa ɗakin tana tsaye a gaban madubi tana fesa turare ya tsaya a gabanta fuskarsa a haɗe tamkar bai taɓa dariya ba. Ganin yadda gaba ɗaya yanayinsa ya sauya ne lokaci guda yasa gaban Fadwa ya tsananta faɗuwa taja baya da sauri cikin dakiya tana galla masa harara, bai yi wata wata ba ya fizgota ya haɗata da jikin bango ya matseta da iya ƙarfinsa ya zare mata idanu cikin wata irin murya yace "Maimaita abinda kika faɗa ɗazu akan Ummata....ki maimaita nace....?" Ya faɗa a fusace yana shaƙe mata wuya. Zaro idanuwanta waje tayi cike da tsoro tana faɗin "Ni ba wani abinda na faɗa akanta...ka sakar min wuyana...." Ta faɗa cike da ƙarfin hali tana ƙoƙarin cire hannunsa dake wuyanta. Sake matse mata wuyan yayi da kyau yana huci yace "Ba dai ke kince baki da kunya ba kuma baki da mutunci...? To yau kuwa zan koya miki hankali har ki ɗauki darasi tunda kince bakyaji....." Ya ƙarashe maganar tare da saka ɗayan hannunsa ya kama bakinta cike da mugunta ya matse da ƙarfin bala'i yana huci. Ƙarar azaba Fadwa ta saki sakamakon wani mugun raɗaɗin azaba da ya ziyarceta lokaci guda dan gabaki ɗaya ji tayi tamkar numfashinta zai ɗauke ya bar gangar jikinta saboda tsabar wuyar da yake gana mata. Shiko babu ko ɗigon tausayinta a ransa ya sake matse mata baki haɗe da shaƙe mata wuya yana faɗin "Daga yau ko ba Ummata ba zakisan irin maganar data kamata ki faɗa akan babba ko wane iri ne....kuma wallahi kika sake gigi ko kuskuren sake faɗar wata mummunar kalmar rashin kunya ko wani raini akan mahaifiyata agabana wallahi kinji na rantse sai nayi miki abinda har ki mutu bazaki taɓa mantawa dani ba ƙarshe ma sai kinyi da kin sanin sanina a rayuwarki dan sai na canza miki kamanni...." Cikin rawar jiki ta shiga gyaɗa mai kai cike da azaba dan babu bakin magana, maƙoshinta da bakinta gaba ɗaya azaba suke mata. Ya Azeez kuwa ko kaɗan bai ji wani tausayinta ya ɗarsu a ransa ba, sai daya gama gana mata azaba ya wajigata iya son ransa, ya tabbatar data gama wajiguwa a hannunsa tukunna dan bakinta har ya tasa sannan ya wancakalar da ita ya watsar gefe guda ya juya ya fice daga ɗakin. *Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya 🤲* [12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 1️⃣0️⃣ *ASALIN TUSHE...* Malam Abdullah Arabi da goggo Fatime sune asalin kakannin su AbdulAzeez da Fadwa waɗanda suka haifi iyayensu, wanda ya kasance su ɗin dukkaninsu haifaffun garin Babura ne dake a jihar Jigawa. Sai dai kuma tun asali dukkansu sun fito ne daga tsatso ɗaya kuma dama auren zumunci ne tsakanin Malam Abdullah da goggo Fatime. Daga Malam Abdullah har goggo Fatime ɗin dukkaninsu marayu ne gaba da baya kasancewar duk sun rasa iyayensu tun bayan watanni da yin aurensu, bayan haka kuma dangin nasu da suka sani basu da yawa, gashi wasu duk sun mutu sai ƴan ƙalilan ne suka rage su ma kuma kowa ya kama kansa da yawa duk sun bar ƙauyen sun koma cikin gari wasu kuma sun lula kudu neman kuɗi, sai ya kasance su kaɗai ne suka rage a garin Babura basu da wani babba nasu a tare dasu. Basu shekara biyu da yin aure ba Allah ya basu Naseer, sai da Naseer ya shekara huɗu a duniya kana goggo Fatime ta sake haihuwar wani mai suna Jabir bayan shekara ɗaya kuma tai mai bi masa Adama daga nan sai Hauwa'u sai Zainab itace auta, kasancewar tun daga kanta Allah bai sake basu haihuwa ba. Malam Abdullah Arabi wanda jama'a da dama su kafi kiransa da Baffa Arabi wasu kuma suce Malam Arabi sanannen malamin Addini ne mai tsantsar dattako da kiyaye dokar Allah, wanda a ɓangaren ilmin addini yayi gwagwarmaya da dama yayi koyarwa a manyan makarantun islamiyoyi da dama dake cikin garin Babura da ma sauran jihohin dake makwabtaka dasu, bayan shekarunsa sun ɗan fara ja ne sai ya daina zuwa ko'ina, ya buɗe shagon dake zauren gidansa dattijan unguwar suna zuwa kullum da daddare bayan sallar isha'i idan ya dawo daga kasuwa inda yake sana'ar saida kayan miya kamar su tumatur, albasa, tattasai, attarugu, latas, kabeji, doya da dankalin hausa, da dai sauransu. Yana koyar dasu karatun Alkur'ani mai girma da sauran littattafan addini duk ƙarshen wata suna biyansa. Malam Abdullah Arabi mutum ne mai kyakkyawar zuciya da jajircewa yaga ya nemi na kansa, uwa uba tsoron Allah da taqawa da son kiyaye dokokinsa, haka itama matarsa goggo Fatime mace ce mai tsananin kirki da hangen nesa gata da zumunci da son mutane. Duk da sun kasance ba masu ƙarfi bane amma yayi ƙoƙari sosai gurin kyautata rayuwar ƴaƴansa, ya jajirce sosai gurin baiwa ƴaƴansa ingantaccen ilimin zamani duk tsadarsa tun daga kan Naseer da sauran ƙannensa babu wanda bai yi karatun boko ba, haka a fannin karatun addini duk sunyi saukar Alkur'ani mai girma da sauran litattafai wannan yasa suka samu ingantacciyar tarbiyya wanda yasa iyayensu suke matuƙar alfahari dasu. Naseer tun yana da shekaru goma sha uku a duniya ya gama primary school ɗinsa yana kammalawa mahaifinsa yayi masa cuku cuku ya samu shiga SS1 yayinda shi kuma Jabir a lokacin yake da shekaru tara a duniya kuma yake aji huɗu a primary, haka sauran ƙannensu mata suma dukkansu a lokacin suka fara daga primary 1, ko kafin Jabir ya gama secondry tuni Sa'ad yana Federal University Dutse inda yake karantar Business Adminstration wanda gwamnati ta ɗauki nauyinsa, shi kuma Jabir a lokacin yana gama secondry dole karatunsa ya tsaya sakamakon rasuwar Baffa Arabi sai ya kasance shine ya cigaba da kula da ƴan harkokin kasuwancinsa na yau da kullum dashi suke ɗan samu suna rufawa kansu asiri da haka har suke samu suke cin abinci har yake iya biyan kuɗin makarantar sauran ƙannensu da sauran harkokin cikin gida. A haka suka cigaba da manejin rayuwarsu har kawo lokacin da suka aurar da ƙannensu duka wanda lokacin Naseer na shekarar ƙarshe a haɗa digree ɗinsa na biyu a SLU goggo Fatime ta matsa masa tace dole dole sai yayi aure kafin ta mutu dan ta samu ganin kwansa a duniya, wannan dalilin yasa babu yadda ya iya haka yasa ta neman masa auren ƴar wani maƙwabcinsu Hafsatu, wanda cikin lokaci kaɗan akayi komai aka gama, sai bayan an gama komai ne Jabir ya tafi Zaria ta jihar Kaduna inda ya cigaba da zuwa yana saro kayan miya dasu kabeji da dankali acan yana kawowa nan ƙauyen na Babura, shi kuma Naseer yana zaune a gidansu ɓangaren da aka gyare masa kafin lokacin tafiyarsa service yayi ya tafi ya bar matarsa Hafsatu mai kunya da kawaici tare da goggo Fatime ya tafi Kano inda aka turasa can yaje yayi service ɗinsa. Watansu goma da aure cif ta haifi kyakkyawan ɗanta mai tsananin kama da ubansa sak aka saka masa suna AbdulAzeez. Bayan shi sai bata sake haihuwa ba, lokacin ne kuma itama goggo Fatime Allah yayi mata rasuwa wanda kowa sai daya kokawa rashinta, sakamakon mutuwar Baffa Arabi data sake dawo musu sabuwa. Tun bayan rasuwarta sai abubuwa suka fara canzawa wanda tun daga nan yanayin rayuwa yasa shima Jabir ya fara tunanin neman aure dan ji yayi gaba ɗaya gidan yayi masa girma kasancewar shi kaɗai ne yanzu yake rayuwa aciki dan tun bayan arba'in ɗin goggo Fatime da kowa ya watse shima Naseer ya ɗauke matarsa Hafsatu da ɗansa suka koma Kano da zama inda a yanzu yake gudanar da harkar kasuwancinsa acan, sai shi kaɗai ya rage yake rayuwa a cikin gidan. Sai da AbdulAzeez ya shekara bakwai a duniya kana Jabir ya samu mata a garin Kaduna yayi aure inda yake da gida acan bayan Alhaji Naseer Arabi ya bashi kuɗi sosai ya kuma ɗorasa kan kasuwancinsa da yake dama motoci yake saidawa ƴan kwatano sannan yana shigo da kayan ginin kamfanoni da gidaje. Matar Jabir Maryama itama ba ƴar kowa bace face ƴar talakawa ce futuk irinsa, dan mahaifinta asalinsa shima malamin zaure ne haka mahaifiyarta itama wankau take zuwa tana bin gidajen masu kuɗi tana yi ana biyanta, sai dai Maryama irin matan nan ne masu bala'in son abun duniya waɗanda basu da godiyar Ubangiji ko kaɗan, gata da mugun son jin daɗin rayuwa duk da kasancewarta ta fito daga tsatson talakawa futuk hakan bai saka ta rage wasu manyan burikan data ɗauka ta ɗorawa rayuwarta ba, shekararsu uku da rabi da aure ta haifi ƴarta mace wacce aka sakawa suna Fadwa, wanda ita da kanta ta zaɓi sunan kuma tace shi takeso a kasawa ƴarta dan tafi so komai nata ya kasance na ƴan gayu dan yazo daban a gurin mutune. Sosai Fadwa taga gatan duniya a gurin mahaifiyarta Maryama dan tana tutiya da ita kaɗai ce Allah ya bata, shiyasa ta gama sangartata dan har ta cire rai da sake samun haihuwa saboda haka tun Fadwa na ƴar ƙarama Maryama ta ɓata ta da irin muguwar huɗubarta shiyasa bata ganin kowa da kwalli a idonsa ballantana tayi maka kallon mutunci, a haka rayuwarta ta taso da mugun buri a zuciyarta, gata dai jikar talakawa kuma mahaifinta bai da wani tarin dukiya amma kwata kwata a rayuwarta bata ƙaunar gamuwa da talaka ko a hulɗa ne bata son duk wani abu da zai haɗata da talaka tun tana ƴar ficiciyarta ta yiwa talaka mummunar tsana a rayuwarta. AbdulAzeez nada shekara sha biyar a duniya lokacin har ya kammala makarantar primary ɗinsa, Hafsatu wacce take amsa Umma a yanzu ta haifi kyakkyawar ƴarta mace mai suna Khadija suna kiranta da Imaan, wacce AbdulAzeez yafi iyayensa murna da ɗokin haihuwar Imaan. Tafi tafi sannu a hankali rayuwa na daɗa nisa har zuwa lokacin da AbdulAzeez ya kammala secondry school ɗinsa a wata tsadaddiyar makarantar secondry dake cikin birnin garin Kano. Kuma a dai-dai wannan lokacin ne kwatsam sai ga Maryama da ciki a lokacin Fadwa tana ƴar shekara takwas cif a duniya wannan karon ma mace ta sake haifa aka saka mata sunan goggo Fatime sai suke mata alkunya da Ilham, bayan shekaru biyu da haihuwar Ilham ta sake haihuwar Amatullah. AbdulAzeez tun yana ɗan ƙaraminsa yaro ne mai tsananin ƙwazo da son karatu dan haka koda ya kammala secondry school ɗinsa bayan ya karɓi takardunsa mahaifinsa bai wani sha wahala ba ya samar masa gurbin karatu a jami'ar BUK, kai tsaye ya nema masa admission bayan ya zaɓar masa irin course ɗin da yayi wato business Adminstration domin yana matuƙar sha'awar AbdulAzeez ɗin yayi karatu sosai ya zama wani abu kodan ya taimakesa akan harkan kasuwancinsa, wanda ta kai yanzu sosai yayi suna a duniya babu inda zaka zaga ka ambaci sunansa ba'a sanshi ba, gashi mutum mai taimako duk sai da ya taimaki ƴan uwansa especially ma mahaifin Fadwa, dan hatta da ita kanta Maryama a lokacin kusan koda yaushe tana kan hanyar zuwa Kano gidansu AbdulAzeez bata sati ba tare taje ta dangwali arziki taci mai kyau ta kwana a mai kyau sannan ta danƙaro abun arziki da kuɗaɗe ta dawo ba. Haka yasa itama Fadwan data ɗan fara zama budurwa a lokacin take matsawa Abbanta tace akaita gidansu AbdulAzeez itama taje tayi kwanakinta ta samo abun arziki ta dawo. Sannu a hankali ya fara karatunsa cikin nasara da jin daɗi cikin ƙudurar Ubangiji har ya kai matakin haɗa Masters ɗinsa, dai-dai lokacin da yake gaɓan da zai ci amfanin karatunsa kwatsam wata ranar litinin suka wayi gari cikin wani mummunan tashin hankali sakamakon ƙullawa mahaifinsa Alhaji Naseer Arabi sharri aka saka mai hodar ibilis a kaya aka kamasa dalilin da yayi sanadiyyar da komai nasa ya ƙare baƙin cikin hakan yasa ya samu paralays bai shekara yana ciwo ba Allah yayi masa rasuwa bayan duka kadarorinsa sun ƙare ga jinya ga abubuwa komai yabi ya runcaɓe musu, a dalilin haka ne mahaifin Fadwa wanda shima ya koma bai da komai sai sana'ar faci da yake a bakin titin layinsu ya ɗauko AbdulAzeez ɗin ya dawo dashi gidansa yana zaune har ya nema mai aikin tuƙin keke napep. Ita kuma Fadwa zuwan AbdulAzeez gidan sai bai yi mata daɗi ba ko kaɗan sai ya kasance duk lokacin da AbdulAzeez yake guri bazaka taɓa iske Fadwa a gurin ba, duk da a lokacin tana ƴar shekara ashirin ne abun ya faru shi kuma a dai-dai lokacin AbdulAzeez yana da shekara talatin cif, amma idan Fadwa tayi maka wani abun sai ka zata ƴar shekara ashirin da biyar ce ita, sai ya kasance duk wata taɓara da sangarta da take yi a gidan shine ke taka mata burki kafin kace me tuni wata muguwar tsanar AbdulAzeez ta shiga zuciyar Fadwa, wannan yasa Maryama wacce suke kira da Mama nuna tsanar AbdulAzeez ɗin ƙarara itama domin bata da abar farin ciki irin Fadwa dan har yau ji take tamkar ita kaɗai ce ƴarta guda ɗaya tal data haifa a duniya, shiyasa ta gama sangartata komai sai tayi mata bata taɓa la'akari da cewa ita macece dole wata rana gidan wani zata, wannan abun na baƙanta ran AbdulAzeez sosai yadda Fadwa babu mai gaya mata taji tun tana ƙaramarta yarinya ce mai yawace yawacen bala'i da tara tarkacen ƙawaye gata da mugun kwaɗayi da son abun duniya, ga shegen son tara ƙawaye ƴaƴan masu kuɗi ita dai ace wannan ƴar wane ce kuma ƙawarta ce tun tana ƙaramarta jikinta har rawa yake in taji ance gidansu wane ana biki, dan ko ba biki bane idan ta saka ƙafa ta fita daga gida tun safe sai yamma liƙis sannan take dawowa, dan sai taje ta gama yawon bin gidajen ƙawayenta inda take zuwa kwaɗayi kullum sannan, mahaifiyarta kuma ita ke ƙara bata dama wani lokacin ma Abbanta ke taka mata burki ya hanata fita kuma ta haƙura da yake tana tsoronsa. Ana cikin haka ne AbdulAzeez yaje Kano ya ɗauko Ummansa da Imaan ƙanwarsa ya dawo dasu inda suka samu wani tsohon gida a unguwar K/Mashi bayan ta siyar da sauran ƴan kunnenta da awarwarayen da suka rage masu daraja a lokacin suka biya kuɗin gidan suka shiga. Shiko mahaifin Fadwa zuwa lokacin tuni ya gama gajiya da halayenta saboda maganar da take ja masa a unguwar bata zama a gida kullum yawo shine ya yanke shawarar yace zai haɗata aure da AbdulAzeez, shi kuma AbdulAzeez a nashi ɓangaren bai taɓa jin son Fadwa ba ko kaɗan, amma kawai saboda yadda mahaifinta ya riƙesa tsakani da Allah yasa yaji bazai taɓa iya watsa mai ƙasa a ido ba ya amince yace zai auri Fadwa. Hakan yasa ba'a ɗau wani dogon lokaci ba cikin wata biyu aka gudanar da bikinsu cikin kwanciyar hankali aka kaita gidan daya kama haya a unguwar Hayin Rigasa, wanda Fadwa da mahaifiyarta tamkar zasuyi hauka haka abun ya kasance musu, dan Fadwa har shirya guduwa tayi amma ta fasa dan sanin an riga da an ɗaura auren yanzu a matsayin matar aure take, dan haka koda ta gudun babu abinda guduwar zata ƙareta dashi, saboda haka ta ƙuduri aniyar ƙuntata masa tare da huɗubar mahaifiyarta da take ƙara zugata tana ingizata kan ta wulaƙantasa ta muzgunawa rayuwarsa, hakan yasa ta sake buɗe sabon shafin jin daɗin rayuwarta a gidansa domin koda akai auren bata fasa yawace yawacen bin gidajen ƙawayen da take yi ba sai ma abinda ya ƙaru, amma abun bai taɓa bashi mamaki ko ya ɓata mai rai ba, dan tuni ya riga da ya gama sanin halinta farin sani shiyasa kwata kwata bai ɗorawa kansa damuwa akan abubuwan da take mai ba, domin yana da tabbacin cewa dole wata rana ita da kanta koda an biyo mata ance ta tashi ta tafi yawon zatace baza taje ba, shiyasa ko kaɗan hakan bai damunsa dan yasan komai take wata rana zata daina. Sai gashi ko sati uku basuyi da aure ba AbdulAzeez ya fara tantance halayen Fadwa ashe da can da shi ba sanin halinta yayi ba, kawai ganinta yake yi, saboda ko girki tunda sukayi aure Fadwa bata taɓa yi ba, sai dai shi idan ya dawo ya girka tana daga zaune ya gama ya bata taci ta ƙoshi, wannan yasa Fadwa ta sake sakankancewa ta miƙe ƙafa tana zuba iskancinta yadda taga dama a gidan, saboda ita a nata haukan ɗauka take soyayyarta ce tasa baya taɓa ganin laifinta shiyasa yake mata komai kamar jin tsoro saboda kar ranta ya ɓaci. Watansu uku da aure al'amuran Fadwa suka ƙara taɓarɓarewa sakamakon idan ta saka ƙafa ta fita daga gida tun da sassafe bata dawowa sai dare, kuma kullum idan ta tashi fita sai ta kulle gidan ta tafi da makullin kuma bata taɓa sanar dashi ga inda zataje, haka zai dawo yazo ya zauna a ƙofar gida yana jiran dawowarta, haka zai ta zama har zuwa lokacin da taga dama ta dawo sannan ta buɗe mai ƙofa ya shiga. AbdulAzeez da yake haƙuri garesa ko tayi wani abun bai cika mata magana ba saboda haƙuri da miskilacinsa, uwa uba kuma matsayin mahaifinta a garesa da irin taimakon da yayi masa a rayuwa yasa baya jin zai iya wulaƙanta ta, amma tabbas zamansa da Fadwa akwai cutarwa haƙuri kawai yake saboda babu yadda zaiyi. A haka dai rayuwa ta cigaba da gangarawa da daɗi ba daɗi har kawo yanzu da suke wata tara da aure babu abinda ya sauya. *Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya 🤲* [12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 1️⃣1️⃣ Wani tarin azaba ne ya sarƙe mata wuya babu ƙaƙƙautawa nan da nan idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir saboda tsabar raɗaɗi da zafin da maƙoshinta yake mata, a hankali taja jikinta ta matsa ta jingina da jikin bangon ɗakin lokaci ɗaya tana shafa wuyanta kana ta fashe da wani matsanancin kukan azaba da tsantsar baƙin cikin irin rashin mutunci wulaƙancin da Ya Azeez yayi mata. Sosai ta zauna take rusa uban kuka kamar zata shiɗe sai sauke ajiyar zuciya take da numfashi lokaci ɗaya, gefe guda a ranta kuwa mamakin tsantsar rashin tausayi da imaninsa take yadda ya zage ya rufe idonsa ya karta mata rashin mutunci. Wai shine yau har da shaƙeta kawai dan tace baza ta gaisa da uwarsa ba..? Lallai idan kuwa ta barshi ya cigaba da mata irin wannan iskancin wata rana akan abu ƙalilan sai dai kawai ya rufeta da duka, aiko da ranar sai yasan ko ita wacece wallahi dan sai ta nuna masa asalin kalarta. Da ƙyar take iya haɗiyar miyau saboda yadda maƙoshinta yake raɗaɗi da zugin azaba. Jin yadda bakinta yake mata raɗaɗin azaba ne shima yasa ta miƙe taje ta ɗauko ƙaramin madubi ta kunna fitilar torch light ɗinsu da suke haska ɗaki ta zauna a bakin gado tana haska fuskarta tana kallon kanta ta cikin ɗan madubin, wani masifaffen kuka ta saki lokacin da taga yadda bakinta ya suntume yayi wani dam kamar ganda ga fuskarta tayi jajir abunka da farar fata wuyanta kuwa inda ya shaƙeta har da shedar farcensa duk ya fito gashi yayi jajir alamar ba ƙaramin matsar azaba wuyan nata yasha a hannunsa ba. Tunawa da tayi cikin satin nan ne zasu fara bikin ƙanwar Hajiya Lubna yasa ta sake rushewa da kukan takaici da baƙin ciki, sai yanzu ne ta sake tabbatar da cewa Ya Azeez mugu ne na ƙarshen zamani ya iya salon mugunta iri iri. Wani uban kuka ta saka kafin ta ɗan rage sauti cikin murya ƙasa ƙasa tana faɗin "Wallahi bazan taɓa yafewa ba, mugu kawai mara imani...Allah ya isana kuma uwarka ɗin anƙi a gaishe tan kayi duk abinda zakayi mamugunci kawai munafiki...." Ta ƙarashe faɗa da ɗan ƙarfi ta yadda zai iya jiyota daga inda yake zaune a falon. Karaf kuwa sai a kan kunnensa ya taso da sauri ya faɗo cikin ɗakin tana ganinsa ta zabura ta matsa gefe, ya matso gabanta ya tsaya a kanta cikin haɗe rai yana watsa mata wani mugun kallo yace "Sake maimaita abinda naji kin ce....?" Tsit tayi taƙi tanka masa, a zafafe ya sake matsawa gabanta kamar zai kai mata duka yana faɗin "Nace ki maimaita abinda kika faɗa ko...?" Nan ma Fadwa tayi gum taƙi kulasa sai ma ta duƙar da kai ta hau ƙifƙifta idanu kamar wacce ta yiwa sarki ƙarya. Ganin yadda tai wani tsumu tsumu ne a zaune tana zazzare ido yasa ya fahimci cewa duk a tsorace take da tsaiwar da yayi a kanta, ya zafga mata wata uwar harara lokaci ɗaya yana sakin tsaki kafin ya gyaɗa kai yana cewa "Ashe dai ke ƙaramar mara kunya ce mara mutuncin banza da wofi kawai, ashe iskancin naki kaɗan ne bai wuce cikin cokali ba, baki iya komai ba sai rashin kunyar ƙarya da fitsara..fitsararriya kawai...." Ya ƙarashe maganar a fusace lokaci ɗaya yana ɗaga hannu kamar zai kai mata mangari. Ɗif tayi tana matsar ƙwallah tare da harararsa ƙasa ƙasa kafin ta ƙara matsawa gefe tana faɗin "To ai nidai babu abinda kaji nace...kuma ma ina ruwanka dani, mutum da bakinsa za'a hana masa magana ne kaji min wata lukutar masifa haka kawai. Allah ya yagawa mutum baki sai a nemi a hana mai magana saboda nuna iko da zalunci...?" Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana murguɗa mai baki ƙasa ƙasa yadda ba zai gani ba. Bai tanka mata ba ya raɓa ta gefenta ya wuce yana kaɗa kai, ya nufi inda jakar kayansa take yaje ya buɗe ya ɗauko wani farin wandon tree quarter mai kyau a ciki kana ya maida jakar ya rufe ya ajiye wandon akai sai daya cire kayan jikinsa yayi saura daga shi sai ɗan gajeren wandonsa baƙi ya ɗauki bokiti ya cika da ruwa ya fice daga ɗakin. Da wata ƙatuwar harara Fadwa ta rakasa yana fita ta ɗauke kai lokaci ɗaya tana jan tsaki kana ta tashi da sauri taje ta ɗauko jakarta ta ciro sabuwar wayarta aciki ta kunna data, lambar Hajiya Labiba ta lalubo sai dai tayi rashin sa'a bata hau online ba, amma duk da haka sai da ta bar mata massage kana ta rufe datan ta saka wayar a silent ta mayar da ita cikin jaka ta ajiye, ko ta kan kayan bacci yau bata bi ba ta kwanta da zurmemiyar rigar da tayi sallah a jikinta tana sauke ajiyar zuciya. Bata jima da kwanciya ba ya shigo ɗakin da bokiti a hannunsa ya ajiye sannan ya ɗauki ƙaramin tawul ɗinta wanda take amfani dashi idan ta fito wanka ya shiga goge jikinsa, tana jinsa tayi banza dashi bata motsa ba, shima bai sake bi ta kanta ba ya ci gaba da goge jikinsa sai da ya gama duk abubuwan daya saba yi kafin ya feshe ilahirin jikinsa da turarensa mai daɗin ƙamshi da sanyaya rai kana ya zura wandonsa ya haye gado ya kwanta a gefenta. Tana jinsa a kusa da ita ta zabura kamar wacce ta ga dodo, tayi sauri ta matsa can ƙarshen gadon ta juya masa baya tana kumbura baki tare da takure jikinta guri ɗaya tana rarraba idanu. Shi dai ko kulata bai yi ba ya shiga karanto addu'ar kwanciya bacci ya gama ya shafe ilahirin jikinsa kana ya ja bargo ya lulluɓe jikinsa lokaci ɗaya yana lumshe idonsa, dan wani irin bacci ne sosai a idanunsa saboda yau gaba ɗayansa a gajiye yake tuɓus dan yasha aiki gashi ko abincin kirki bai samu yaci ba tun karin safe da yayi kafin ya fita shine har yanzu a cikinsa kasancewar lokacin daya dawo gida da nufin ya ɗan huta sannan ya samu ya ɗan ci wani abun shine ya iske gidan a kulle lokacin Fadwan bata nan, haka ya sake juyawa ya nufi gidansu dake can Unguwar Mu'azu a tunaninsa ko can ta tafi, yana zuwa can ɗin ma kuma ya iske mahaifinta a ƙofar gida ya dawo daga masallaci sallar magriba inda ya tabbatar mai da cewa Fadwa bata zo gidan ba kwata kwata yau, dan rabonta da zuwa ma kusan sati biyu kenan, abun ya matuƙar bashi mamaki sosai dan shi duk a zatonsa nan ɗin tazo bai ɗauka duk abinda ya gaya mata da safe kafin ya fita zai bi ta bayan kunnenta ya wuce bane bai shiga kunnen nata ba. Shi kuwa Abbanta dama yana ganin Ya Azeez ɗin a irin wannan lokacin yasan tabbas akwai matsala dan haka ya matsa masa da tambayar abinda ke faruwa amma Ya Azeez yaƙi faɗa masa komai sai cewa yayi ba komai dama sunyi da ita ne zata zo gidan ta wuni shiyasa ya biyo dan ya ɗauketa su koma gida. Ƙin yarda yayi da abinda ya faɗa ɗin dan haka yace masa ya jirasa ya shiga gida ya fito sai su wuce gidan tare yaga abinda ke faruwa, saboda yayi yayi dashi kan cewa ya gaya masa gaskiyar abinda yake faruwa amma yaƙi, shiyasa yace to ya tashi su tafi gidan tare saboda yasan abinda ke faruwa, domin gaba ɗaya zuciyarsa bata kwanta da abinda Ya Azeez ɗin ya faɗa masa ba. Haka dole ba dan yaso ba yana gani ya hau mashin ɗinsa shi kuma ya shiga keke napep ɗinsa suka kamo hanyar zuwa gidan. Aiko nan suka iske har lokacin Fadwa bata dawo ba, haushi da takaicinta yasa Abbanta yace da Ya Azeez ɗin ya buge kwaɗon su shiga cikin gidan su zauna su jirata har zuwa lokacin da taga dama ta dawo, dan ba zai tafi ba har sai yaga dawowarta. A hankali ya sauke ajiyar zuciya kana ya sake shigewa cikin ɗan yalolon bargon nasu lokaci ɗaya yana gyara kwanciyarsa, kafin ya matsa kusa da ita ya saka hannuwansa duka ya juyo da ita gaba ɗaya ya sakata cikin jikinsa, a hankali ya ɗago kanta ya ɗan sumbaci goshinta kana ya ƙanƙameta sosai yana sauke numfashi. Fadwa dake idanuwanta biyu duk tana jin abubuwan da yake mata amma tayi ɗif kamar mai bacci bata motsa ba. A hankali a hankali tana jinsa yake ɗan shasshafa bayanta yana hura mata iskar bakinsa a cikin kunnenta da haka har bacci ya ɗaukesa ta fara jin saukar numfashinsa a gefen wuyanta, sai data bari baccin nasa yayi nisa sosai sannan a hankali ta zare jikinta a nasa ta matsa can ƙarshen gadon ta gyara kwanciyarta bayan ta lumshe idanunta da haka itama baccin yayi awon gaba da ita. Washegari kuwa da ƙyar Fadwa ta iya tashi sakamakon wani zazzafan ciwon kai daya saukar mata tun cikin dare sai nishi take, wuyanta da maƙoshinta kuwa zafi suke mata, bata ko iya haɗiyar miyau saboda shaƙa da matsar da Ya Azeez yayi mata, a daddafe ta ita gabatar da sallar asuba wacce sai gurin ƙarfe 8am na safiya sannan tayi ta wanda shima saboda takurawar Ya Azeez da matsawarsa ne yasa ta lallaɓa ta tashi ba dan taso ba taje tayo alwala tazo ta gabatar da sallahn, tana idarwa kuwa ko hijabin jikinta bata tsaya cirewa ba ta koma gado ta kwanta ta ƙudundune tana jan ajiyar zuciya, ba jimawa ta sake komawa wani baccin. Sai ƙarfe 11am sannan ta tashi lokacin shi kuwa Ya Azeez ya daɗe da ficewa gurin sana'arsa, gaban madubi taje ta tsaya tana ƙarewa bakinta kallo wanda har lokacin yake a suntume bai koma dai-dai ba, ga wani azababben raɗaɗin azaba da yake mata, hannu ta kai ta shafa saman inda yayi suntum ɗin kamar zata fashe da kuka tace "Wallahi Allah ya isana bazan taɓa yafewa ba, mugu kawai azzalumi mai baƙin hali..." Ta faɗa tare da fashewa da wani matsanancin kuka, kana ta wuce taje ta ɗauki bokiti ta ɗebi ruwa ta fice daga ɗakin zuwa banɗaki. A haka tayi wankan tana ta mita da masifar yadda ya suntume mata baki ta koma kamar wacce aka naushe gurin kokawa, bata ƙara tsinkewa da lamarin ba kuwa sai lokacin da tazo yin brush taji wata azaba ta ziyarceta ba tasan lokacin da wasu sabbin hawaye suka soma silalowa kan fuskarta ba, dan ji tayi kamar ta ɗora hannu akai ta rushe da kuka saboda baƙin ciki. Haka nan dai ta daure ta lallaɓa ta wanke bakin tsaf sannan ta tashi ta koma ɗaki. Sai data gama shafa mai sannan ta ɗauko wata atamfarta Avogan wacce aka yiwa ɗinkin doguwar riga da tasha adon stones a jiki kalarta brown da milk ne sai ɗan ratsin orange kaɗan a jiki ta zura, kayan sun mata kyau sosai sun zauna a jikinta sun mata ɗas, dan ɗinkin rigar irin mai ɗan matsewar nan ne daga sama daga ƙasa kuma ya buɗe, bata ɗaura ɗankwalin kayan ba ta fesa turare kawai ta ɗauki wayarta ta fita falo. Wata ɓaƙar leda taci karo da ita ajiye a tsakar dakin sai wani ɗan madaidaicin ƙaramin kofin flas, ɗan taɓe bakinta tayi tare da watsawa kayan harara kafin ta zauna ta janyo kofin flas ɗin gabanta ta buɗe ruwan lifton ne a ciki sai titiri yake yana tashin ƙamshin kanumfari da citta, sakin tsaki tayi kana ta tashi taje ta ɗauko kofi da cokali sannan ta dawo ta zauna ta zuba lifton ɗin kana ta rufe flas ɗin ta jawo ledar ta buɗe, buredi da ƙosai ta gani a ciki sai wata ƴar guntuwar siga kaɗan a farar leda. Sai data zuba sigan ta jujjuya kana ta ɗaga ta kai bakinta ta fara sha tana haɗawa da buredi da ƙosan, a haka ta cika cikinta taf sakamakon mugun daɗin da taji lifton ɗin yayi mata sosai dan sai data ƙara cika kofi ta shanye tas sannan taji cikinta yayi mata dam ta saki gyatsa kana ta ture flas da kofin gefe ta sake gyara zamanta sannan ta ɗauki wayarta ta lalubo numbern Hajiya Labiba ta danna mata kira. Tana ta ringing bata ɗauka ba, haka har sai da ta kira kusan sau uku tana yankewa ba'a ɗauka ba, ana huɗun ma ta jima tana ringing dan har sai da ta cire rai dan tana gaf da tsinkewa taji an ɗaga cike da farin ciki ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin "Hello Ƙawata kintashi lafiya..Allah yasa dai bani ce na tasheki ba..dan naga tun ɗazu nake ta kira baki ɗauka ba....?" Daga can ɓangaren kuwa Hajiya Labiba wacce kiran wayar Fadwan ne ya tasheta daga bacci tana kwance akan makeken gadonta da yaji shimfiɗa da wani haɗaɗɗen lallausan zanin gado sai wani tattausan bargo data lulluɓe rabin jikinta dashi tayi luf ga sanyin Ac kota ko ina yana kaɗawa a cikin haɗaɗɗen bedroom ɗin nata wanda ya gaji da haɗuwa. A hankali tayi juyi ta sake manna wayar sosai a kunnenta lokaci ɗaya tana ƙara gyara kwanciyarta kafin cikin muryar bacci da ƙosawa tace "Aiko dai kece kika tasheni da wannan shegen nacin kiran naki wallahi...." Ta ƙarashe faɗa tana sakin hamma alamar baccin bai gama isarta ba aka katse mata shi. Murmushi kawai Fadwa tayi kafin tace "Ai wallahi na kasa haƙuri ne Ƙawata, duk na ƙagara in gaya miki abinda wannan azzalumin yayi min shiyasa nake ta kiranki, amma kiyi haƙuri ban san kina bacci ba na tasheki nasan bakyaso ana tashinki idan kina bacci...." Da sauri Hajiya Labiba ta tashi zaune kafin tace "Kamar ya...? Ban gane ba meya miki kuma...kar dai ace fara dukanki yayi Azeez ɗin...?" Fadwa da taji wasu hawayen baƙin ciki da ɓacin rai sun cika mata ido tasa hannu da sauri ta share kana ta girgiza mata kai kamar tana ganinta tace "A'a marina yayi kuma ya shaƙe min wuya ya matse min baki da maƙogwaro kamar zai kasheni sannan ya dinga zagina yana ta ce min kwaɗayayya mai bin gidajen ƙawaye maula, ba kiji cin mutunci ba iri iri haka ya dinga min, har yanzu wuyana kuwa in banda zugi da raɗaɗi babu abinda yake min, gashi bakina ya suntume leɓena yayi ƙato baki gani ba kamar ganda...wallahi mutumin nan mugu ne na bugawa a jarida, ba kiga irin muguntar da yayi min ba..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da fashewa da kuka. Wani uban ashar Hajiya Labiba ta mulmulo cike da ɓacin rai tace "Dan kutumar ubansa ance masa ke ɗin jaka ce da zai ware ƙwanjinsa a kanki kamar wata tsararsa saboda shi ɗan iska ne mugu salon yaje ya raunataki ya illata miki rayuwa, shine ya rasa inda zai gwadawa muguntarsa a jikinki sai fuskarki tunda yana baƙin ciki da kyaun da Allah yayi miki har da kumbura miki baki...? Ni da har ina tausaya masa ki gansa wani simi simi dashi kamar na Allah ashe shima ƙwallon shegen ne a ƙunshe ba'a sani ba, To wai uwar me ma kikayi masa da zai miki irin wannan rashin mutuncin...? Aiko wanda ya isa da gidansa ma bana jin zai iya yiwa matarsa wannan iskancin, ke ko zaginsa kikayi ba ki cancanci yayi miki wannan muguntar ba, banza kawai wawa..." Ta ƙarashe maganar cike da masifa tana sauke numfarfashi. Fadwa kuwa wani mugun daɗi ne ya lulluɓeta lokacin da taji irin masifar da Hajiya Labiba take yi akan irin abun da Ya Azeez yayi mata, dan tana bala'in son taga ana tausaya mata akan irin zaman ƙunci da takurar da takeyi a gidan aurenta, domin ita har ga Allah ba ko da yaushe bane take ɗaukan kanta a matsayin matar Ya Azeez, ita gaba ɗaya ma auren gani take kamar bata dashi. Saboda haka ta sake marairaice fuska kamar tana gabanta tace "Wallahi idan kika ga irin wulaƙancin da yayi min jiya sai kin tausaya min, ke saboda tausayina da zakiji wallahi har kuka sai kinyi min...kamar fa wata jaka haka ya dinga matse min baki yana shaƙe min wuya kamar zai kasheni, kuma wai duk don kawai nace bazan gaisa da uwarsa ba shikenan sai masifa, sai kace gaisawar da ita ance dole ne, aiko na ƙi nace ai ba uwata bace kuma bazan gaishe tan ba, na kafe na nuna mai kalan nawa taurin kan na ƙeƙashe naƙi karɓan wayar nai ta faɗar maganganu kuma nasan duk makirar uwar tasa tana jina, itama munafuka mai fuska biyu. Ni wallahi Allah ma ya gani bana ƙaunar matar nan kwata kwata kamar yadda bana ƙaunar ɗan....." Ƙamshin turaren data shaƙa ne yasa ta ɗago kai a razane ba tare data ƙarasa maganar da tayi niyyar faɗa ba, ido huɗu sukayi dashi yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe duka hannuwansa duka a ƙirji ya zubo mata ido, zabura tayi ta matsa baya da sauri tare da zaro idanu waje cike da tsoro, kafin cikin firgici da tashin hankali ta soma ƙoƙarin tashi tsaye jiki na rawa ta saki wayar dake hannunta ta fara ja da baya da baya tana girgiza kai cike da matsanancin firgici da tashin hankali. *Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya 🤲* [12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 1️⃣2️⃣ A hankali ya shiga takowa inda take yana ƙara kusantarta yayinda kuma har lokacin idanunsa ke tsaye ƙam a kanta ko ƙiftawa ba ya yi. Ita kuwa Fadwa hakan yasa ta ƙara gigicewa ta kiɗime ta fara ɗaga hannayenta sama a tsorace tana faɗin "Nidai ai ba da kai nake ba kuma baka ji nayi maganarka ko na ambaci sunanka ba, kuma wallahi Allah ma ya gani iya abinda nasan kayi min jiya shi kawai nake bada labari....amma shine zaka wani zo ka tsatstsareni da ido kamar ka kama wata mai laifi....to kai mema kaji na faɗa tsakani da Allah nidai gaskiya karka ce zaka sake matsemin baki ko ka shaƙe min wuya in ba haka ba wallahi na rantse gidanmu zan tafi dan bazan zauna kaita min mugunta ba kamar ka samu jaka...." Ta ƙarashe maganar a tsorace tana galla mai harara. Ba tare daya tanka mata ba ya ƙarasa gabanta kawai ta ga ya duƙa ya ɗauki wayarta dake yashe a ƙasa ya ɗago a sanyaye yana jujjuya wayar a hannunsa cike da mamaki yayinda gefe guda a ransa kuwa tsantsar al'ajabinta ne ya ƙara cika masa zuciya, ɗago kai yayi a hankali yana kallonta dai-dai lokacin kuma kiran Hajiya Labiba ya shigo wayar, ga mamakinta kawai sai gani tayi ya miƙo mata wayar ba tare da yace mata komai ba ya juya ya matsa gefe guda yana yi mata alama data ɗauki kiran. Tsaye kawai Fadwa tayi riƙe da wayar a hannunta tana binsa da kallo mai cike da mamaki, har kiran ya yanke ta kasa ɗagawa haka aka sake kira a karo na biyu nan ma ta kasa ɗagawa, duk yana kallonta da ya fahimci ganinsa ne ya hanata amsa wayar kawai sai ya saki murmushin yaƙe kafin ya juya lokaci ɗaya yana faɗin "To ni dai zan koma gurin sana'ata tunda naga jikin naki da sauƙi dama na dawo ne in duba jikin naki saboda naga kamar bakya jin daɗi ɗazu da safe kuma har na fita daga gidan baki tashi ba shiyasa na dawo in dubaki kuma inji ko kin sha magani...." Ya faɗa lokaci ɗaya tare da zaro gudar dubu ɗaya daga cikin aljihunsa ya ajiye agabanta kana ya juya zai fice daga ɗakin yana faɗin "Sai na dawo, ki kula da kanki Allah ya ƙara lafiya...." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da ficewa daga ɗakin. Wata zazzafar ajiyar zuciya Fadwa ta sauke kana ta koma ta zauna lokaci ɗaya tana dialing numbern Hajiya Labiba, kamar kuwa jira take kiran na shiga ta ɗaga cike da masifa tana faɗin "Wai ina kika shiga ne dan tsabar iskanci da wulaƙanci ina ta kiranki a waya kin ƙi ɗagawa...?" Ta faɗa a hasale tana sauke numfashi. A hankali Fadwa ta sauke numfashin itama kafin cikin ƙasa ƙasa da murya tace "Shine ya shigo shiyasa kika jini ɗif wallahi..amma kiyi haƙuri..." A fusace Hajiya Labiba ta katseta da faɗin "Dan ya shigo sai akayi ya ya...nace sai akayi ya ya...? Oh ashe dama tsoronsa da kikeji ne yasa har yake takaki yake samun damar yi miki duk iskancin da yaga dama...? Lallai yau na sake raina wayonki ashe dama duk bakinki na banza ne da wofi ban sani ba Fadwa....? Wallahi yau kin bani mamaki na raina ajinki..." Daga haka ta shiga zazzaga mata masifa tana ta faffaɗan mata maganganu akan ta daina jin tsoronsa idan ya zare mata ido itama ta zare masa tunda shi lusarin namiji ne babu abinda yake tsinana mata a gidan da har zaisa ta dinga jin wani tsoronsa haka kawai, ta dage ta kwatarwa kanta ƴanci ta kuma tsaya tsayin daka itama ta nuna masa cewa dashi ko babu shi zata iya cigaba da rayuwarta babu abinda zai sameta. Fadwa kawai sakin baki tayi tana sauraren masifar da Hajiya Labiba take ta surfa mata sai kace wata uwarta, kawai sai taji duk ranta ya ƙara ɓaci da abinda Ya Azeez yayi mata jiya, taji kamar ta dawo da hannun agogo baya ta yadda zata zagesa ta gaggaya mai magana iya son ranta. Lallai Hajiya Labiba tayi gaskiya ita banza ce shashasha kuma bakinta ma na banza ne da wofi dole a raina wayonta yanzu ji yadda ya barta da kumburarren baki ya tafi harkokinsa, ita kuma ya barta tsuru a gida kamar wata mayya tana ji tana gani bata da halin fita taje ko'ina, lallai ya kamata ta tashi tsaye domin ta ƙwatarwa kanta ƴanci sannan ta nunawa Ya Azeez cewa itama tasan takan tsiya. Maganar da Hajiya Labiba ta ci gaba da yi ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula ta sake manna wayar sosai a kunnenta kafin tace "Wallahi duk abinda kika faɗa gaskiya ne ƙawata, kuma dole zan tashi tsaye in kwatarwa kaina ƴanci in bi hanyar da nasan zata ɓullar dani, domin kuwa idan na bari muka ci gaba da tafiya dashi a haka ba ƙaramin la'anta min rayuwata zaiyi ba. Wallahi a kullum shiyasa nake ƙara ƙaunarki a raina nake kuma ƙara ganin kima da mutuncin ki a idanuna saboda burinki ako da yaushe shine kiga kin ɗaukaka darajata a ko'ina kin kuma fifita ni fiye da kowa a gareki, na gode ƙawata kuma insha Allahu bazan taɓa baki kunya ba zan gyara daga yau nayi miki wannan alƙawarin dan sai na nuna masa cewa ni ba kanwar lasa bace kamar yanda yake zato, sannan in nuna masa mata ma suna suka tara sannan ruwa ba sa'an kwando ba ne, ko an zubasa sai ya tsiyaye...." Ta ƙarashe faɗa tana sauke numfarfashi kamar wacce ke shirin kokawa. Daga can ɓangaren kuwa Hajiya Labiba da ta gama saurarenta taja ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗi kafin tace "Alhamdulillahi dama haka nake son ki zama ƙawata, to yanzu kuma ya maganar shirye shiryen biki ƙanwar Hajiya Lubna kinsan fa ranar juma'ar nan ne bikin yau saura kwana uku kuma tun yau ne za'a fara programs, ga ankon Dinner ɗinki nan ma a hannuna ɗazu na aika direba yaje gidan Lubnan ya karɓo mana ƙarfe 5pm za'a fara a Hall ɗin dake Ahmed Musa Garden, ya za'ayi kenan...?" Ba tare da tunanin komai ba Fadwa tace "Haba ba damuwa ai dole zanzo ƙawata kema kin sani, ina nan tafe tun ƙarfe uku ki jirani..." Hajiya Labiba tace "Yauwa to Shikenan, Allah ya kaimu anjiman lafiya sai kinzo ina jiranki...." Cikin rashin tunani Fadwa ta amsa mata da "Toh sai kin ganni..." Daga haka kawai suka yi sallama akan sai sun haɗun kafin suka yanke kiran. Sakin baki kawai Fadwa tayi a zaune tana saƙawa da kwancewa kafin ta miƙe da sauri ta shiga uwar ɗaka ta ɗauko gyalenta wanda ya shiga da atamfar jikinta tayi rolling ɗinsa akanta bayan tayi dabara ta janyosa har zuwa kan bakinta ta naɗesa ta yadda zai rufe bakinta da yake a kumbure suntum har lokacin, ta ɗauki jakarta da wayarta cikin sauri ta fice, sai da ta fara kulle ƙofar ɗakin ta jefa ɗan makullin a cikin jakarta sannan ta juya kai tsaye ta fice daga gidan gaba ɗaya, yau ko tsayawa ma batayi ta kulle ƙofar gidan ba, kawai ta janyo ƙofar ta sakaya ta ƙara gaba abunta. Tana fita dai-dai kan layinsu ta tari ɗan acaɓa ta ɗare abunta dan bata jin zata iya ƙarasawa bustop ɗinsu yau gurin masu keke napep shiyasa kawai ta hau mashin bayan ta gaya masa unguwar da zai kaita ya tada mashin ɗin yaja suka wuce. Ƙofar wani ɗan madaidaicin ƙaramin gida ginin bulo da bulo mai ɗauke da fenti kalar ruwan madara tasa mai mashin ɗin daya ɗaukota ya ajiyeta, ta sauka ta buɗe jakarta ta zaro kuɗinsa ta bashi kana ta juya ta shige cikin gidan bakinta ɗauke da sallama. Wata kyakkyawar mata ce wacce a ƙalla shekarunta zasu kai arba'in zuwa da bakwai zaune a ɗan filin tsakar gidan da babu sumunti ko kaɗan sai ɗan diddigen ƙasa ga ƙaton baho girke a gabanta wanda ke cike da curarriyar tunkuza da aka murza, sai wani ɗan katakon mulmula da wasu manya manyan farantan silba wanda idan ta cura tunkuzar ta mulmula take jerawa akai, jin sallamar ƴar tata ne yasa ta ɗagowa da sauri lokaci ɗaya tana washe baki ta amsa mata sallamar haɗe da faɗin "Oyoyo kuɗina..Ƴar halak kenan kin ƙi ambato, yanzu fa muka gama maganarki nida Ilham nake cewa kwana biyu na jiki shiru ban ganki ba Allah yasa dai lafiya...." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana ƙare mata kallo. Wani rau rau Fadwa da tayi da idanu kamar zata fashe da kuka kafin ta yatsine fuska cike da shagwaɓa tana faɗin "Wallahi lafiya ƙalau Mama muna ta shirye shiryen bikin ƙanwar ƙawata ne Hajiya Lubna, shiyasa kika jini shiru gaba ɗaya kanmu ya ɗauki zafi, muna ta zirga zirga kullum ina kan hanyar zuwa gidan Hajiya Labiba da Hajiya Lubnan, kwata kwata bana samun zama sai dare sannan nake komawa gida kuma dana koma kwanciya kawai nake yi saboda na gaji shiyasa ko samun damar kiranki ma bana yi...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana janyo kujera ƴar tsugunne ta zauna akai. Baki Maman ta washe cike da fara'a tana faɗin "Ikon Allah kice har bikin ya matso...? Amma kuwa gaskiya Fadwa baki kyauta min ba ko kaɗan da kika ƙi gaya min tunda wuri dan in samu in tanadi sabon ɗinkina na kece raini in shiga taron manyan mata nima in samu a fantama dani...koda yake ai duk da haka ma bata ɓaci ba yaushe ne za'a fara bikin dan in san abinda zan tanada...?" Take faɗa tana kallon Fadwa da take ƙoƙarin cire gyalen jikinta kafin ta cigaba da cewa "Kinga sai ki haɗani kawai da ita uwar Hajiya Lubnan nima mu dinga mutunci abun mu kinga zumunci ya ƙara ƙulluwa kenan a tsakani...." Fadwa data linke gyalenta ta ɗora akan jakarta dake ajiye a gabanta ta ɗago kai tana faɗin "Aiko Hajiya Turai akwai ta da jin kai da ɗagawa Mama, da wuya ku shirya da ita saboda akwai ta da gadara sosai dama dai Hajiya Kalsoom ce ita babbar yayar su Hajiya Lubnan..." Mama kuwa da taji abinda Fadwa tace dan da nan ta gimtse fuskarta tana faɗin "To sai me nidai kawai ki haɗani da ita, duk wata ɗagawarta ba damuna zatayi ba nidai kawai in dangwali arziki kuma in barshi a mazauninsa atoh..shine kawai..." Ta faɗa tare da ɗaga hannuwanta sama alamar ko a jikinta ita dai kawai a kaita. Gyaɗa kai Fadwa tayi tana faɗin "Aiko zaki ga matan manya Mamana, dan wallahi har da matar gwamnan jihar Kaduna zata zo bikin, ni ba dan ma wannan algungumin ya kumbura min bakina ba ai da tun tuni ina can abuna muna ci gaba da shirye shirye, amma da yake azzalumi ne mugu ji yadda yayi min da baki sai kace wacce tayi kokawa da ƙatti..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara jin zafi da tsanar Ya Azeez ɗin a ranta. Da sauri Maman ta kalli bakin ta ga yadda ya wani suntume yayi jajir abunka da farar fata gashi har lokacin bai saɓe ba yana nan a yadda yake sai ma ƙara hawa da yake tayi yana ƙyalli, take taji gabaki ɗaya ranta ya gama ɓaci gwiwarta tayi sanyi tace "Meya faru kuɗina...wane ɗan iskan ne ya nemi ya canza min kyakkyawar hallittarki lokaci ɗaya da duka haka...? Kuma dan saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci ya rasa inda zai kai hannu ya doka a jikinki sai bakinki saboda yana baƙin ciki da kasancewarki mai magana ba kurma ba kome...?" Cike da tsantsar takaici Fadwa dake jin wasu irin zafafan hawaye masu raɗaɗi na shirin ziraro mata tace "Ya Azeez ne fa ya matse min baki ya shaƙe min wuya ya dinga gana min azaba da mugunta iri iri haka kawai ba abinda nayi masa, kuma bayan yaje ya haɗo min munafunci a gurin Abba ya ɗauko Abba suka zo har gida ina dawowa na samesa a gidanmu ya mammareni sannan shi kuma ya ɗora min da nasa...dubi yadda ya maida min bakina kamar wata mara galihu....." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana matsar ƙwalla, a fusace Mama ta miƙe tsaye cikin tsananin tashin hankali da masifa take faɗin "Kan uban nan kai...lallai Malam ya shahara da mugunta, yanzu saboda tsabar mugun abu yaje har gidanki ya ware wannan kafcecen hannun nasa mai kama da guduma babu tausayi ballantana imani ya kafta miki shi a tattausar fuskarki haka kawai...? To wallahi anzo dai-dai inda ba zan iya haƙuri ba, kuma tunda abinda suka tsiro dashi kenan bazaki koma gidansa ba kin barosa kenan sai dai suyi duk wacce zasuyi, amma bazan taɓa zuba idanu ina kallo a ƙara kassara min rayuwarki ba bacin wanda akayi na farko, bari Malam ɗin ya shigo ina nan ina jiransa za'ayi duk wacce za'ayi amma auren wannan matsiyacin kam kin barshi har abada kin gama shi dan bazan lamunci mugunta ba..." Fadwa ta buɗe baki zatayi magana kenan suka tsinkayi muryar Abbanta dake tsaye tun ɗazu a bakin ƙofa kamar daga sama yana faɗin "Ai kuwa aure tsakanin AbdulAzeez da Fadwa yanzu aka farashi, dan haka ban ga wanda ya isa ya guntulesa ba har sai lokacin da Ubangijin al'arshi yaso kuma yaga dama, dan haka ki sakawa zuciyarki haƙuri da salama kawai ki cire bakinki a maganar aurensu, in kuma ba haka ba to tabbas zaki iya jawa kanki matsala..Ke kuma..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana kallon Fadwa da tai wani tsumu tsumu a zaune tana muzurai yace "Ki tashi cikin mutunci ki koma ɗakin mijinki tun kafin ranki ya ɓaci, kuma daga yau kar in sake ganin ƴar ƙafarki a gidana indai ba tare da mijinki zaku zo ko da wani ƙwanƙƙwaran dalili ba..." Gaba ɗayansu suka zaro idanu a tare suna kallonsa cike da mamaki, ganin irin banzan kallon da yake binsu dashi ne yasa gaba ɗaya jikin Fadwa ya ƙara yin sanyi ta shiga ƙoƙarin miƙewa lokaci ɗaya ta ɗauki jakarta da gyalenta ta yafa a sanyaye tana zumɓuro baki ta juya zata wuce, Mama tai caraf ta riƙe mata hannu tana faɗin "Wallahi babu inda zakije tunda gidan ubanki ne nan dan haka babu wanda ya isa ya koreki daga cikinsa sai dai a haɗa har dani uwar data haifeki a kora atoh..." Ta faɗa cike da masifa tana karɓe jakar a hannunta. Fadwa kuwa ji tai wani tarin baƙin ciki ya ƙara cika mata zuciya, ta fizge jakarta a zafafe tana faɗin "Mama nidai dan Allah ki barni in tafi tunda yace in bar masa gidansa..." Mama tana numfarfashi take faɗin "Ai wallahi bai isa ba indai ni uwarki ina cikin gidan nan dole zai ganki a cikinsa, sai dai nima idan zai sallameni ne in kama gabana kinga ba wanda zai sake gani a cikinmu kuma sai in tayi dalili, yo me zai ma kawo wani dalilin da har zaisa mu haɗu dashi ko a hanya ne..? Ai kuma hanyar jirgi daban ta mota daban tunda babu haɗin fura da kashi..." Tamke fuska Fadwa tayi tana faɗin "Ni dai ki daina faɗin haka dan Allah Mama, kawai bani jakata in tafi zan kiraki a waya idan na isa gidan bikin..." Ƙin bata jakar Mama tayi, ta sake riƙeta ƙam ta rungume tana harararta kafin ta juya shima ta ƙara galla masa harara, duk yana kallonta amma bai ko saurareta ba ballantana ya tanka mata. Hakan kuwa ya ƙara ƙular da ita ta fizgi hannun Fadwan da ƙarfi tana faɗin "Muje in rakaki ki tafi ƴar albarka ta..." Ta faɗa lokaci ɗaya tare da ɗauke kai tana wani harare harare. Shi dai Abba ko kaɗan bai sake tanka musu ba yayi gum da bakinsa har suka ƙaraso inda yake tsaye, suna ƙarasowa gabansa Fadwa ta ɗan zame hannunta ta rusuna a gabansa tana faɗin "Abba na tafi sai anjima..." Ɗan dubanta yayi a hankali yana kaɗa kai, kafin yace "Toh madalla Allah yayi albarka ki gaida gidan dashi AbdulAzeez ɗin..." Yana gama faɗin haka kawai yasa kai ya wucesu ya nufi ɗakinsa. A zafafe Maman ta ƙara fizgar hannunta tana faɗin "Dalla muje ni in rakaki ki wuce ki tafi inda zai fissheki, kin tsaya sanabe da iyayi..." Ta faɗa tare da janta da sauri suka fice daga gidan. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 1️⃣3️⃣ Har zauren gidan nasu Maman ta rakota suka tsaya ta miƙa mata jakarta ta ƙarba ta buɗe ta zaro kuɗi ƴan ɗari biyar biyar sababbi fil guda goma ta miƙa mata, da sauri tasa hannu ta karɓe lokaci ɗaya tana washe baki take faɗin "Allah yayi miki albarka ɗiyar ƙwarai, shiyasa akoda yaushe nake ƙara alfahari dake ke ɗin ta musamman ce. Dama kamar kin sani ɗan jarin ƙuli ƙulin da kayan miyan nawa duk mun taru mun cinye nida ƙannenki da mahaifinki, jarin ya karye ɓagas saboda wani lokacin a ciki muke zarar wani abu muke yin cefane mu samu mu ci abinci dan ni ban ga amfanin facin da mahaifinki yake yi ba, wani lokacin fa sai a fi wata da watanni bai shigowa da ko asi gidan nan amma koda yaushe yana kan hanya yana gararanba a tsohon mashin zuwa bakin titi sai kace wani abun azo a gani yake tsinanawa kansa da iyalinsa, wallahi abun bala'in bata min rai yake, kinga yanzu dai wannan ƙulin da nake curawa nan da zuwa anjima ina soyawa zaki ga har an siye ya ƙare amma ƙarshenta sai kiga ban tsira da ko sisi ba na kwashe kuɗin duk mun yi cefane saboda rufawa kai asiri amm...." Fadwa tai saurin tarar numfashinta da faɗin "To ai rufin asirin kenan dama Mama, yanzu da baki yin sana'ar ai da ba'a san kuma wane irin hali zaku shiga ba, amma a hakan ma ai sai a ƙara godewa Allah ko...?" Take faɗa cikin takaici da jin haushin irin maganganun da Maman ke faɗi akan mahaifinta. Tasan mahaifiyarta farin sani shegen kwaɗayi gareta da rashin godiyar Ubangiji ga bala'in son abun duniya, shi kuwa mahaifinta tuni tayi masa kyakkyawan sani shi mutum ne wanda ke da tsantseni da WADATAR ZUCCI kuma baya taɓa hangen abun hannun wani, amma ita sam ba ta san ya kamata ba shiyasa wani lokacin take jin haushin abinda take yi. Ƙaramin tsaki Fadwan taja kana ta juya lokaci ɗaya tana ƙoƙarin fita daga zauren take faɗin "Ni zan wuce ki gaidasu Ilham da Amatullah idan sun dawo..." Tana gama faɗin haka kawai tasa kai ta fice daga zauren ba tare data tsaya sauraren addu'ar da Maman ke mata na fatan sauka lafiya ba ta wuce abun ta. Maman kuwa ko a jikinta ta juya itama ta koma cikin gidan tana mita da faɗin "Ai sai kiyi kuma, baƙin rai kuwa sai ki ta yi kin daɗe baki yi ba zaki gaji ne wata rana..haba ina dalili yarinya sam bakya so a faɗi laifin ubanki. Ke kenan indai ana so a ga ɓacin ranki to a ambaci ubanki yayi ba dai-dai ba kuma ya yin sai kawai aƙi faɗi saboda jin tsoro, ai kuwa kin daɗe sai dai kije kiyi ta ƙuncinki da nunƙufurcinki dan ni dai kam sai na faɗa kuma koda a gabanki ne..Atoh....." Take faɗa cikin masifa da jin haushin yadda suka rabu da Fadwan, dan ita so tai suyi magana tai mata kwatancen gidansu Lubna dan jibi ta cakare ta tafi biki, amma daga maganar gaskiya ta bi ta murtuke fuska tana ta faɗin maganganu har da su tsaki. Tana cikin masifar Abbansu Fadwan ya fito daga cikin ɗakinsa riƙe da buta a hannunsa zai yi alwala ya kalleta ya ɗauke kai bai ce mata komai ba ya wuce ta gabanta ya shige banɗaki abunsa. Sai da ta kallesa ta watsar kafin ta bi bayansa da wani banzan kallo ta ɗauke kai lokaci ɗaya tana jan tsaki ta kwanto haɓar zaninta ta ƙulle kuɗin da Fadwa ta bata kana ta jawo kujera ta zauna ta ci gaba da curin ƙuli ƙulinta hankali kwance. Haka koda ya fito ma bai kalli inda take ba ya matsa can gefe guda ya tsugunna ya ɗaura alwala bayan ya gama ya miƙe riƙe da butar a hannunsa ya ƙarasa gabanta ya ajiye kana ya juya yana warware hannun rigarsa daya nannaɗe gurin alwala yana faɗin "Ni zanje masallaci sai na dawo..." Yana gama faɗin haka yasa kai ya fice yana kallonta tana aikin curin ƙuli ƙulinta ko ɗagowa ba tayi ba ballantana ya saka ran zata amsa masa, kawai ya kaɗa kai ya fice abunsa. Fadwa kuwa haka tai ta tafiya a ƙasa kasancewar tafiyar akwai ƴar tazara sosai tsakanin gidansu da bakin titin unguwarsu, gashi rana ta ƙwallare zufa sai tsattsafo mata take, a haka har ta kai bakin titi sannan ta samu keke napep ta hau ta gaya masa ya kaita unguwarsu Hayin Rigasa dan bata jin zata iya zuwa Gwamna Road gidan Hajiya Labiba kamar yadda ta ƙudurta a ranta, dan yadda ta kwashi ranan nan gaba ɗaya duk ta haɗa uwar zufa fuskarta tayi jajir zaifi idan ta koma gida ta sake sabon wanka da sabon shiri kafin ta tafi gidan. Koda ta isa gidan sai da tayi wanka kana ta gabatar da sallar Azahar sannan ta shirya ta cancaɗa kwalliyarta dai dai gwargwado kamar yadda ta saba, kana ta zura haɗaɗɗiyar baƙar abayarta wacce ta karɓi jikinta sosai ta sake fito da hasken farar fatarta. Sai data feshe ilahirin jikinta da Arabian Oud ɗinta masu daɗin ƙamshi kana ta ɗauki mayafin rigar tayi rolling ɗinsa a kanta ya fito da farar fuskarta sosai sai tayi kamar wata balarabiyar ƙasar Oman. A gurguje ta ɗauki wata baƙar jakar handbag ɗinta mai kyau ta zira wayarta a ciki kana ta sagala a tsintsiyar hannunta ta fice daga ɗakin, haka ta fito tsakar gidan tana wani irin yauƙi da taku ɗai ɗai ta jawo ƙofar ɗakin ta saka kwaɗo ta rufe babu ko ɗar a ranta tasa kai ta fice daga gidan kamar wata tauraruwa. ********** A ɓangaren Ya Azeez kuwa lokacin da ya fito daga gida direct cikin gari ya nufa da keke napep ɗinsa dan can yafi shiga da rana yayi sana'arsa hankalinsa kwance, amma yau sai ya kasance kwata kwata bashi da natsuwar zuciya da sukuni komai baya masa daɗi, zuciyarsa gaba ɗaya a cunkushe take sosai da baƙin cikin Fadwa da ɓacin ran da take ta ƙunsawa zuciyarsa, kwata kwata ya rasa me ke masa daɗi shi kam ya sani bai yi dacen matar aure ta ƙwarai ba. Amma koda wasa bai taɓa tunanin cewa al'amarin Fadwa har ya kai ƙwarin haka ba gaba ɗaya kansa ya gama ɗaurewa da mamakinta, gashi idanunsa da zuciyarsa sun kasa goge hoton tsadaddiyar wayar da ya gani a hannunta tana amfani da ita, babbar damuwarsa yanzu kawai itace a ina take samun kuɗin da har ta siyi wannan wayar dan ya sani kaf cikin danginsu babu wanda yake da kuɗin da zai iya cirewa a yanzu ya bata ta siyi wannan tsadaddiyar wayar, kowa ta kansa yake yi, ba kamar da da suka fi karfin komai ba yanzu komai ne yafi ƙarfin su. A haka ya kusan wuni a cikin gari yana ta faman gararanba cikin takaici da ƙunar zuciya har lokacin sallar azahar ya wuce bai sani ba gashi ya kasa tsinanawa kansa komai tunda ya fito dan ko tsayar dashi mutane sukayi a bakin hanya baya iya tsayawa sai dai kawai ya wuce yace ba tafiya ba ne, haka har la'asar tayi bai sani ba sai da yazo wucewa ta Abakwa dai-dai bakin wani masallaci ya ga mutane suna ɗaura alwala nan ya tsaya ya faka keke napep ɗinsa a gefen masallacin, ya fito da sauri bayan ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe 3:50pm dai-dai. Sosai yaji baƙin cikin subuce masan da sallar azahar tayi da bai samu yin ta akan lokaci ba ya tokare masa zuciya, cikin sanyin jiki ya ɗauki buta yaje ya tari ruwa a famfon dake gurin ya ɗaura alwala kana ya shiga cikin masallacin. Ya daɗe zaune a cikin masallacin bayan ya idar da sallolin, amma ya kasa tashi ya tafi yana kallo mutane suka dinga fita ɗaya bayan ɗaya amma shi ko motsi ya kasa yi, sai ma matsawa da yayi ya jingina da jikin bango ya lumshe idonsa yana ci gaba da tasbihi a zuciyarsa. Haka kowa ya gama ficewa aka barsa tsuru shi kaɗai ƙwal a zaune. Yana nan zaune a cikin masallacin har gurin ƙarfe 5:40pm. Sannan ya tashi ya fito ya shiga kekensa ya zauna yana tunanin inda kuma ya kamata ya nufa. ******* Fadwa kuwa lokacin data isa gidan Hajiya Labiba ta iske bata nan sai mai aikinta kaɗai dake ta aikace aikacen haɗa abincin rana a kichin, ita ke sanar mata cewa Hajiya Labiban bata nan taje gidan Hajiya Lubna amma ba zata daɗe ba yanzu zata dawo. Ɗan sauke numfashi Fadwa tayi kafin tace "Ita tace miki bazata daɗe ɗin ba zata dawo, ko kuma wani iyayin ne da tsarinki kawai yasa kika faɗa...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallonta. Saurin kaɗa kai tayi tana faɗin "Eh itace da kanta ta gaya min tace bazata daɗe ba saƙo kawai zata kai mata ta dawo, shiyasa kikaji nace yanzu zata dawo..." Fadwa bata sake magana ba ta juya ta shiga cikin falo ta samu waje ta zauna akan kujera ta ajiye jakarta lokaci ɗaya ta kashingiɗa tana faɗin "Bari in jirata har ta dawo ɗin..." Ta faɗa a hankali tana lumshe idanunta. Ita dai Rabi bata ƙara magana ba ta wuce ta koma kichin ta ci gaba da aikin girkinta. ********** A natse ya ɗaga labulen buhun da ya kasance shine a matsayin ƙofar gidan ya shiga ciki bakinsa ɗauke da sallama, wata kyakkyawar dattijuwa ce fara sol sol da shekarunta a ƙalla zasu iya kaiwa hamsin da biyu zaune a ɗan madaidaicin filin tsakar gidan nasu wanda ya kasance ginin jar ƙasa ne mai kyau irin na da, sai dai duk ya gama jin jiki gefe gefen katangar duk ya zaizaye wani gurin ƙasan ma duk ta rufta sai buhu da aka kewaye wani gefe gurin yay kamar katanga gashi an share ko'ina har ɗan filin tsakar gidan nasu da yake ƙarami yay fes fes gwanin ban sha'awa. Ita kaɗai ce zaune a tsakar gidan da faranti a gabanta tana tankaɗen garin tuwo, tana jin muryarsa ta ɗago kai fuskarta ɗauke da fara'a take faɗin "Masha Allah maraba da ɗan albarka...yanzu kake tafe da yammacin nan...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana ajiye rariyar hannunta ta miƙewa da sauri ta shiga cikin ɗaki ta ɗauko mai tabarma ta fito har lokacin fuskarta ɗauke da farin ciki tazo ta shimfiɗa masa a kusa da inda take tankaɗen kana ta wuce gurin randa tana faɗin "Zauna ina zuwa bari in kawo maka ruwa..." Ta faɗa cikin dattako tana ɗaukar kofin silba a kwando taje ta ciko masa shi da ruwan randa mai sanyi ta kawo ta ajiye a gabansa kana ta koma ta zauna ta ci gaba da tankaɗenta tana kallonsa. Sauke numfashi Ya Azeez yayi a hankali kafin ya ɗan ɗago kai ya kalleta, sai ya ga ta kafesa da idanuwanta ƙirr bai ce komai ba ya ɗauki ruwan data ajiye masa ya kafa kai, bai sauke ba sai da ya shanye tas kana ya sauke kofin ya ajiye lokaci ɗaya yana sauke numfashi kafin yace "Na gode Ummana Allah ya biyaki da mafificin gidan aljanna fiddausi..." Ya faɗa cike da tsantsar jin daɗi lokaci ɗaya yana gyara zamansa, tare da ɗan waigawa ya leƙa ɗakin dake kusa dashi yana faɗin "Wai ina Imaan ne taje data barki ke kaɗai a gidan kike yin aikin da kanki...?" Murmushin daya ƙara fito da tsantsar haiba da kwarjininta ta saki kafin tace "Tana nan maƙota gidan Malam Sabo na aiketa siyan kayan miya yanzun nan zaka ganta ta dawo..." Ta faɗa tare da ɗan tsura masa idanu cike da nazari da son gano yanayinsa da yake ciki. Kaɗa kai kawai yayi a hankali ba tare daya ce mata komai ba, ya juya ya ci gaba da kallon wani guri can daban. Fahimtar da tayi kamar yana da damuwa ne a ransa yasa ta ajiye rariyar tankaɗen ta miƙe daga inda take ta dawo kusa dashi kan tabarman ta zauna tana fuskantarsa, sunkuyar da kansa ƙasa yayi da sauri cikin ƙoƙarin danne abinda yake ji a ransa yana taso masa yace "Ummana har kin gama tankaɗen..ko kin gaji ne in ƙarasa miki...?" Girgiza masa kai kawai tayi tana faɗin "Kayi haƙuri kaji..nasan akwai abinda yake damunka amma bana buƙatar ka gaya min, ka gayawa Allah ko mene ne sannan ka bar masa ikonsa, kuma duk abinda yake damunka kayi ƙoƙari ka danne ka jure ka barwa zuciyarka daga Allah sai kai karka sake duniya ta hango gazawarka har ta saka ido a kanka, ka zamo jarumi akoda yaushe kuma a kowanne irin hali karka sare, komai yayi tsanani maganinsa Allah..kuma komai yana da farko haka yana da ƙarshe wata rana sai labari..." Take faɗa cikin taushin murya da nuna tsantsar kulawa da tawakali. A hankali Ya Azeez ya ɗago ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa yake faɗin "Umma ina cikin tsananin damuwa komai bai min daɗi, Fadwa ta hana zuciyata sakat bani da natsuwa da sukuni ballantana in samu kwanciyar hankali..gaba ɗaya a tsorace nake bana so Allah ya kamani da hakkin Fadwa Ummana na rasa inda zan saka kaina da rayuwata inji daɗi..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana share ƙwallar data soma zubo masa. Wani irin sanyi Umma taji lokaci ɗaya jikinta ya ɗauka, a hankali ta juyo ta kallesa kafin ta ɗan saki murmushin yaƙe tana faɗin "Insha Allahu Allah ba zai taɓa kamaka da laifin komai ba a kanta, kayi haƙuri ka ci gaba da yi mata nasiha kuma ka dage da addu'a, duk abinda yafi zama alkhairi tsakanin kai da ita Allah ya zaɓa muku. Amma ban so kake nuna damuwa akan duk abinda zata yi maka ko kaji haushinta, saboda kar ka manta Fadwa dai jininka ce ƙanwarka ce kuma har yanzu akwai yarinya a tattare da ita, dan haka ka dinga haƙuri da ita wata rana da kanta zata gyara kaji...?" Sosai Ya Azeez ya ƙara haɗe fuskarsa yana faɗin "Umma wace irin yarinta kuma, yanzu kamar Fadwan ce za'a ce akwai yarinta a tattare da ita har yanzu tana ƴar shekaru talatin da wani abu a duniya...?" Kallonsa kawai Umma ke yi tana ɗan murmusawa kafin tace "Eh mana a kanka ai ita yarinya ce ko...?" Bai ce mata komai ba dan tsabar takaici, ya ɗauke kansa lokaci ɗaya yana ƙara jinjina kalaman Umman tasa akan Fadwa wai akwai yarinta a tattare da ita, sai kace wata ƴar jaririya. Fadwan ce take da yarinta..? Lallai kuwa Umma har yau har gobe ba tasan wacece Fadwa ba ganinta kawai take amma bata san ita ɗin wacece ba. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 1️⃣4️⃣ Umma kuwa a zuciyarta tana sane ta gaya masa hakan, saboda tasan dalilin abinda da yasa yake ta wannan kumburin yana ƙara jin haushin Fadwan a ransa, ba zai wuce ƙin amsar waya da batayi bane jiya ta gaisheta, ita kuma ko kaɗan hakan bai dameta ba, domin indai Fadwa ce tasanta farin sani ita da uwarta dama ba wani shiri sosai sukeyi da ita ba saboda yanayinsu kwata kwata ba ɗaya ba ne da nata, rashin kunyar Fadwa kuma ta daɗe da saninta iri iri tunda ko jiyan ma duk maganganun data gaggaya masa a kanta tana jiyota ta cikin wayar duk taji komai amma ko a jikinta hakan bai dameta ba. Umma ta ƙara gyara zama sosai tana fuskantarsa tace "Nidai ina ƙara tunasar da kai muhimmancin haƙuri a rayuwa AbdulAzeez, kuma ina roƙonka akan kome Fadwa zatayi ka kasance mai yi mata uzuri a matsayinta na ƙanwarka, sannan ka dinga nusar da ita akoda yaushe kana yi mata nasiha a matsayinta na ƴar uwarka kuma matarka, ka daina ɗaukar zafi da ita har kayi fushi kaji..." Ƙara sunkuyar da kai yayi a hankali yana faɗin "Insha Allahu Umma..." Suna cikin haka wata matashiyar budurwa wacce a ƙalla shekarunta ba zasu wuce sha tara ba ta shigo gidan bakinta ɗauke da sallama tana riƙe da ledar kayan miya a hannunta, tana ganinsa kuwa ta washe baki cike da fara'a tana faɗin "Laaah Ya Azeez kaine..yaushe kazo...?" Take faɗa tana ƙarasowa gabansa ta duƙa ta ajiye ledar dake hannunta kana tace "Sannu da zuwa Ya Azeez, ya Aunty Fadwa ya aiki...?" Ta faɗa tana sakin murmushi wanda kallo ɗaya idan kayi mata zaka hango tsantsar kamanninsu sosai da Ya Azeez ɗin, tun daga kan dogon hancinsu zuwa ɗan madaidaicin ƙaramin bakinsu, da kalar fatarsu duk iri ɗaya sai dai da yake ita ɗin mace ce sai ta ɗan fishi hasken fata kaɗan, amma hatta da yanayin yatsun hannayenta dana ƙafarta duk irin nasa ne. Ɗago kai yayi yana kallonta da murmushi akan fuskarsa yace "Alhamdulillahi Aunty Imaan sarkin surutu, ya makaranta..ana dai maida hankali gurin karatun ba'a wasa ko...?" Da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin "Eh ina yi sosai Ya Azeez, jiya ma muka kammala zana jarabawar Ssce ɗin mu..." Cikin farin ciki Ya Azeez ya dafa kanta yana faɗin "Masha Allah lallai autar Umma an kusan zama ƴan matan jami'a kenan..ko kuma aure zakiyi idan kin kammala secondary school ɗin...?" Ya faɗa cike da tsokana fuskarsa ɗauke da murmushi. Imaan a kunyace ta rufe fuskarta tana girgiza kai take faɗin "A'a Ya Azeez nidai karatu zan ci gaba da yi abuna, ko Ummana...?" Ta faɗa tana duban Umma dake sauraran diramar tasu tana ta murmusawa, jin ba tace komai ba ne yasa Imaan ta shagwaɓe fuska tana faɗin "Kai Umma kice eh mana..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana kwaɓe baki kamar zatayi kuka. Umma tace "Toh nace eh autar Umma sai ta gama jami'a sannan zatayi aure shikenan...?" Ta faɗa tana kallon Ya Azeez daya kaɗa kai yana ta dariya. Itama Imaan ɗin dariyar tayi kana ta miƙe ta ɗauki ledar kayan miyan data siyo ta ɗauko roba mai faɗi ta juye a ciki kana ta zuba ruwa ta wanke, ta shiga ɗakinsu ta fito da ƙaramin turmin su na jajjagen kayan miya tazo ta jajjaga ta kwashe ta ajiye. Umma da Ya Azeez na zaune suna ta hira, har tayi talge ta tuƙa tuwon ta kwashe sannan ta ɗauko tukunya ta ɗora miya. Tana kammala aikin gaba ɗaya ana kiran sallar magriba, dan haka gaba ɗayansu suka miƙe domin yin alwala Ya Azeez ya fita zuwa masallaci, su kuma suna yin alwalar suka shiga ɗaki dan gabatar da tasu sallar. Koda ya dawo daga masallacin sai daya zauna ya ci tuwon da ya tarar Umman ta saka masa ya ƙoshi yasha ruwa kana ya wanke hannunsa yayi musu sallama Umma ta tashi ta rakosa har bakin ƙofar gidan tana ta saka masa albarka ya shiga napep ɗinsa ya tada duk tana tsaye, sai da taga wucewarsa kana ta juya ta koma cikin gidan. ********** A ɓangaren Fadwa kuwa tun ƙarfe 6pm. Suna can Ahmed Musa Garden cikin wani haɗaɗɗen Hall daya sha decorations kiɗa sai tashi yake ga manya manyan jiga jigan mata kota ko ina a zazzaune cikin shiga ta alfarma wannan na wane wannan, ga uban gwala-gwalai a wuya da hannuwansu kamar waɗanda suka zo wajen gasar nuna gwal da auna gram ɗinsu. Fadwa kuwa itama tasha tata kwalliyar ta kece raini tana sanye da ankonsu na wani Maroon ɗin leshi mai tsada a jikinta wanda akayi mata ɗinkin riga da siket da ya zauna sosai a jikinta ya fito da kyakkyawar surarta, kanta kuwa wani irin ɗaurin zamani akayi mata da head kalar golding aka wani turosa gaban goshinta ya karkace sai aka ɗan jashi baya kaɗan hakan ya bawa baƙin gashin dake kwance luf luf a gaban goshinta damar fitowa. Zaune tayi abunta ta kame tana ta wani yatsine yatsinen fuska tana kallon mutane ɗai ɗai ita a dole hamshaƙiya, wanda duk abunka idan ka kalli Fadwa kaga yadda tasha gwala gwalan da ƙawarta Hajiya Labiba ta ara mata a wuyanta da hannuwanta itama saika ɗauka cewa matar wani shahararren ɗan siyasan ce ko wani babban ɗan kasuwa dan ko kaɗan ba tayi kama da matar mai jan keke napep ba, gaba ɗaya ta saje dasu ga wani haɗaɗɗen make-up ɗin da akayi mata wanda ya ɓoye bakinta da har lokacin yake a ɗan kumbure bai gama saɓewa ba. Sai kai kawo take tana ɗaga kai tana wani hura hanci dan jin kanta take yau wata daban, itace gata ga uwar gidan gwamnan jihar Kaduna da kanta da take gani a talabijin da fostoci a cikin gari yau gasu zaune a waje guda teburinta na kallon nata suna kallon juna har ana ta ɗaukarsu Video da hotuna a tare, kanta har wani girma taji ya ƙara. Sosai idan ta kalleta take ƙara jin wani alfahari da nishaɗi haɗe da tsantsar farin ciki aranta, yau ɗin ta kasance babbar rana ce ta musamman a gareta, ganinta tsamo tsamo cikin taron manyan matan ƴan siyasa da ƴan kasuwa ga gogaggun ƴan boko ya fiye mata komai farin ciki da jin daɗi a rayuwarta, sai wani shisshige musu take tana naniƙe musu dan ita wannan babban ci gaba ne agareta a ganta tare da matan manya. ******* A ɓangaren Ya Azeez kuwa lokacin da ya baro K/Mashin gidan Ummansa bai biya ko'ina ba direct gidansa ya nufa, yana shiga unguwar tasu kuwa ana kiran sallar isha'i dan haka sai daya tsaya yayi sallah a masallacin dake bakin layinsu kana ya fito ya ƙarasa shagon masu sayar da fura dake kusa da gurin yasa aka damawa Fadwa sannan ya fito ya siyan mata kankana dasu abarba da apple ya biya sannan yaja kekensa ya wuce ya nufi gida. Yana isa ƙofar gidan nasu ya faka napep ɗinsa a gefe kana ya fito riƙe da leda mai layi layi da makullin napep ɗin a hannunsa, yana ƙarasawa ya iske ƙofar a sakaye yasa hannu ya tura ya ga ta buɗe cike da ƙwarin gwiwa yasa kai ya shiga gidan bakinsa ɗauke da sallama, kasancewar ba wani samun wutar nefa suke sosai ba a unguwar yasa ya zaro wayarsa ya kunna fitila ya haska ƙofar ɗakin. Sosai Ya Azeez yaji gwiwarsa tayi sanyi sakamakon tozali da yayi da ƙaton kwaɗon dake garƙame a jikin ƙofar ɗakin, cikin mamaki yace "Kenan yarinyar nan yau ma sai data saka ƙafa ta sake fita daga cikin gidan nan..toh ina kuma taje ita da bata da lafiya...?" Ya faɗa a fili cike da al'ajabi lokaci ɗaya yana zama kan wani ƙaramin dutsen siminti dake ajiye a bakin ƙofar ɗakin nasu ya yi tagumi. Gefe guda a ransa kuwa faɗi yake "Ya Allah kaji ƙaina ka tausaya min ka yafe min laifukan da nayi maka wanda na sani da ma wanda ban sani ba, Ya Allah kaga zuciyata kaga abinda ke cikinta Allah ka dubeni ka yaye min abinda nake ji a zuciyata ka musanya min da mafi alkhairi..." Yake faɗa lokaci ɗaya yana jin tsiyayowar wasu hawaye masu ɗumi da raɗaɗi saman kumatunsa. ******* Fadwa kuwa a dai-dai wannan lokacin tana can gaba gaba a tsakiyar filin rawa tana ta cashewa abunta hankalinta kwance, ko ajikinta babu abinda ya dameta dan ko tunanin gida ba tayi kawai sha'anin gabanta take. Ta zage sai kwasar rawa take har da kaiwa ƙasa, ƙawayenta kuwa duk sun baibayeta suna ta mata ɓarin sababbin kuɗi ƴan dubu dubu, ita kuwa ta dage sai juyi take tana ta wani kakkarya jiki kamar zata karye. Sai gurin ƙarfe 11:30pm dai-dai sannan aka tashi daga Dinnern mutane suka soma fitowa daga hall ɗin kowa yana nufar inda motarsa take fake, a hankali a hankali duk mutanen suka fara watsewa da haka kowa ya kama gabbansa harabar gurin ta zamo ba kowa sai iya security ɗin dake aiki a gurin. A hankali Hajiya Labiba ke jan motar tana tuƙi cikin ƙwarewa da natsuwa yayinda Fadwa ke zaune a gefenta tana kallon hanya suna taɓa hirar yadda Dinnern ta kasance sama sama suna shewa cike da nishaɗi, da haka har suka shigo unguwarsu Fadwan. Dai-dai lokacin Ya Azeez ya dawo daga gidan bulon da yake kai ajiyar kekensa ya iske motar Hajiya Labiban fake a ƙofar gidan nasu yayinda suka buɗe duka ƙofofin motar lokaci ɗaya suna ƙoƙarin fitowa, abunka da dare gaba ɗaya muryar Fadwa duk ta karaɗe layin inda take ta kwasar dariya cike da nishaɗi tana faɗin "Ai wallahi ji nayi kamar kar a tashi Dinnern nan yanzu ƙawata, abun yayi masifar yi min daɗi ji nayi dama a kwana anayi wallahi bazan gaji ba, kai harkar arziki tayi ina tsiya ta ga rana ai talauci babbar masifa ce, shiyasa Annabi yace mu nemi tsari da talauci..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana fitowa daga motar tare da rataya jakarta a gefen kafaɗarta. Hajiya Labiba data fito daga motar itama tana kallonta cikin dariya tace "Ai biki ma ba'a fara ba tukunna ƙawata, ƙila har sai kin gaji da zirga zirga kin daina zuwa kinsan biki indai na gidansu Lubna Sambo ne saika gaji da zaryar zuwa party dan akwaisu da son raƙashewa..kamar ƴaƴan dujal...." Fadwa ta saki dariyar jin daɗi tana faɗin "Tabɗi aiko bazan taɓa gajiya ba ƙawata kema kinsani indai irin wannan harkar ce mu ne kan gaba gaba dan bama taɓa bata kunya..." Hajiya Labiba ta buɗe baki kenan zatayi magana Azeez dake tsaye daga can gefensu yana sauraren su ya ɗaga murya yana faɗin "Muje ki buɗe min ƙofar ɗakin tukunna sai ki juya ku koma inda kuka fito kuje ku ci gaba daga inda kuka tsaya..." Da sauri dukkansu suka juyo suna kallonsa ganin irin banzan kallon da yake binsu dashi ne yasa gaba ɗayansu suka ɗauke kai cikin wani irin yanayi, Hajiya Labiba ta kama murfin motarta ta buɗe kana ta waigo tana faɗin "Toh ƙawata kuje ki buɗe mai ƙofar, sai mun sake haɗuwa goben, Allah ya huta gajiya..." Tana gama faɗin haka ta juya ta watsa mai harara kana ta shige motarta ta zauna ta kunna tayi ribas ta fice daga layin a guje ta barsu nan tsaye suna kallon kallo. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad:Aishaalto09* 1️⃣5️⃣ Ya Azeez daya daskare a tsaye kawai kallon Fadwa yake cikin mamaki da al'ajabinta dan tunda sukayi aure zai iya cewa wannan shine karo na farko da ta taɓa irin wannan fitar ta kuma kai har wannan lokacin haka a waje dan haka abun yayi bala'in ɗaure masa kai da mamaki. A hankali ya matso kusa da ita lokaci ɗaya yana ƙare mata kallon sama da ƙasa kafin cikin sanyin muryarsa yace "Yanzu tsakaninki da Allah Fadwa abinda kike yi kin kyautawa kanki kenan..? Yanzu wannan itace irin rayuwar da kika zaɓarwa kanki a matsayinki na matar aure...? Wannan wace irin fitina ce haka kika ɗorawa kanki..ko an gaya miki talauci hauka ne da zaki bi ki takura rayuwarki ki hana kanki sukuni da kwanciyar hankali a banza da wofi...? Yanzu ke hakan da kike yi yayi miki dai-dai kenan a matsayinki na matar aure ace ki saka ƙafa ki fita ki bar gidanki bada sanin mijinki ba tun da sauran safiya ki tafi gidan ƙawaye kije ki miƙe ƙafa ki ta zama kina zubarwa da kanki mutunci kamar wacce bata da mafaɗi...Yanzu ke hakan shine dai-dai a gareki...?" Ya faɗa lokaci ɗaya yana ƙureta da ido, gaba ɗaya Fadwa sai taji gwiwarta tayi sanyi ta ɗago kai tana dubansa cikin wani yanayi tace "Meya faru kuma daga dawowata da tsohon daren nan zaka tsareni da wasu kalar maganganu marasa tushe ballantana makama...ko nayi maka wani laifin ne...ko kuma gidajen ƙawayen nawa da kake ta nacin maimaita ina zuwa naka ne ko na wasu ƴan gidanku da abun zai dameka...?" Ta faɗa kai tsaye tana aika masa da wani mugun kallo cike da jin haushinsa, kafin ta saki tsaki lokaci ɗaya tana faɗin "Idan naka ne ko na wani daga cikin danginku daga yau don girman Allah Ya Azeez ka hanani zuwa, ko kasa idan naje su wulaƙanta ni suyi min korar kare suce kar in sake zuwa kaji....?" Tana gama faɗin haka kawai taja wani dogon tsaki ta wuce tana harararsa. Har ta kusa shiga gidan ya tafi da sauri ya sha gabanta ya tsaya yana watsa mata wani mugun kallo kafin ya fizgi hannunta da ƙarfi a fusace ya jata ƙiiii kamar kayan wanki suka shige cikin gidan, Fadwa data cika da mamakinsa ta zaro ido waje cike da tsoro ta shiga ƙoƙarin ƙwacewa a hannunsa tana ta tittirjewa amma yaƙi sakinta har sai daya sadata da tsakar gidan sannan yayi wurgi da ita can gefe guda ya watsar har sai da kanta ya gwaru da bango ta saki ihun azaba lokaci ɗaya ta dafe kanta cike da tsoro dan ba ƙaramin buguwa kan nata yayi ba. Wani kallon banza ya wurga mata ba tare da yace komai ba ya fara matsawa gabanta, tana ganin haka ta ƙara gigicewa jikinta ya ɗauki rawa da kakkarwa, a gigice ta soma matsawa tana ja da baya da baya a tsorace tana faɗin "Dan girman Allah Ya Azeez kayi haƙuri..wallahi tallahi gurin bikin ƙanwar Hajiya Lubna mukaje daga can muke..na rantse da Allah ba yawo naje ba idan kuma baka yarda ba ka kira Hajiya Labiba ma ka tambayeta kaji wallahi duk muna tare dasu acan..." Ta ƙarashe maganar cike da tsoro tana kallonsa, gaba ɗaya yanzu yanayinsa tsoro yake bata, tun abinda yayi mata jiya ta ƙara shiga taitayinta take kuma ƙara jin tsanarsa a ranta, Ballantana kuma yanzu da taga ya bala'in fusata, sai take ji a ranta kamar rufeta kawai zaiyi da masifaffen duka. Dan haka ta samu hantar cikinta da kaɗawa ga wani tsananin tsoron muguntarsa da firgicin da suka ziyarci zuciyarta lokaci guda, a ruɗe ta ja da baya da sauri ta matsa gefe. Sake ɗaure fuskarsa yayi tamau kamar wanda bai taɓa dariya ba yace "Amma kin tambayeni lokacin da zaki fitan, ko kin taɓa gaya min zakije bikin ƙanwar ƙawarki...?" Bakinta na rawa tace "A'i nasan kona tambayeka bazaka taɓa barina inje ba ne, shiyasa nayi tafiya ta..." Ta faɗa cike da gadara haɗe da tsoro tana harararsa ƙasa ƙasa, dan Allah ya gani al'amarin nasa ya fara bata haushi, ta ya zai wani tasota gaba ya tsareta da wasu shegun koɗaɗɗun tambayoyinsa kamar wani alƙali. Duk yana kallonta amma bai ce komai ba ya kaɗa kansa kawai ya juya cikin raɗaɗin zuciya yana faɗin "Ok hakan yayi dai-dai, muje ki buɗe min ƙofar ɗakin dan Allah inaso zanyi wanka..." Ya faɗa cike da takaici wanda da gani kasan ransa a matuƙar ɓace yake, wata irin dakiya taji tazo mata ta wani kallesa tun daga sama har ƙasa a wulaƙance kafin ta fashe da wata irin dariya wacce kana jinta kasan ta tsantsar rainin wayau ce da son turawa mutum haushi tace "Uhmmm Ya Azeez kenan nida zaka taimaka min ma kayi min adalci ka sahale min wannan ƙaddararren auren naka mara amfani wallahi daka gama min komai ka taimaki rayuwata dan Allah ya gani kamar ina zaune ne akan ƙaya haka nake jina..wai muje ki buɗe min ƙofar ɗakin inaso zanyi wanka, sai kace wani ɗakin azo a gani ko wanda yake da haɗaɗɗen toilet ɗin wanka a ciki ni wallahi wani lokacin ma dariya kake bani idan naga kana wannan taƙamar da wani nuna isa da gadara sai kace wanda ya isa da gidansa ya kuma mallaki komai na jin daɗin rayuwa...nan ko hotiho ne fankan fayau..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana sake fashewa da dariya kana ta miƙe ta ɗauki jakarta da tayi wurgi da ita can gefe ta zura hannu ta lalubo ɗan makullin ta bi bayansa, yana nan tsaye a bakin ƙofar ɗakin ta raɓa ta gefensa ta tsaya sai data kallesa ta wani taɓe baki sannan ta zura makullin ta buɗe ta tura ƙyauren lokaci ɗaya ƙofar ta buɗe kana ta matsa gefe ta bashi hanya tana faɗin "Na buɗe ranka ya daɗe..." Ta faɗa tana ƙara sakin wani shu'umin murmushi. Ko kallonta bai yi ba ballantana tasa ran zai tanka mata haka yasa kai ya shigewarsa cikin ɗakin ya barta nan tsaye tana hararar bayansa. Ɗaga kafaɗarta tayi alamar ko a jikinta kana tabi bayansa ta shige ɗakin itama, tsaye yake a tsakar ɗakin yana ƙoƙarin tuɓe kayan jikinsa ta shigo ta wucesa ta shige uwar ɗaka, har ya ɗaga rigar jikinsa zai cire ya tuna da ledar fura dasu fruit ɗin daya siyo mata tun ɗazu suna tsakar gidan ya manta dasu, ya juya da sauri ya fice yaje ya ɗauko mata furar kuwa har ta gama saki salaf ba sanyin ko kaɗan saɓanin lokacin daya siyota ƙarara dan har da ƙanƙara aka saka a ciki, ya dawo ɗakin hakimar tana zaune a bakin gado ya shiga uwar ɗakan ya dire mata ledojin a gabanta ba tare da yace mata komai ba ya sake juyawa ya koma falo. Ko kallonsa ba tayi ba ballantana ta kalli ledar daya ajiye matan, haka ta miƙe ta tsallake su tana sakin tsaki ta fara ƙoƙarin cire kayan jikinta, sai data cire sarka da ƴan kunnen da Hajiya Labiba ta ara mata da awarwarayenta tsaf ta zuba mata a cikin jaka sannan ta tuɓe kayan jikinta ta janyo zani ta ɗaura ta haye gado ta kwanta lokaci ɗaya ta lumshe idanunta tana sauke numfashi. Tana nan kwance ya shigo cikin ɗakin ya ɗauki soson wanka da gajeren wandonsa ya sake ficewa, zuwa can kuma har bacci ya soma ɗaukarta sama sama ta jiyo motsinsa a falo ta miƙe da sauri ta sauka daga kan gadon ta ɗaga labule ta ɗan leƙa. Hangosa tayi yana ƙoƙarin shimfiɗa tabarma a tsakar ɗakin, da sauri ta ƙarasa gabansa tana faɗin "A'a Ya Azeez ya haka ba dai nufinka a nan zaka kwana ba...?" Ko ɗaga kai bai yi ya kalleta ba yace "Haka nake nufi Fadwa yau anan nake sha'awar kwana..." Ya faɗa kai tsaye ba tare daya kalleta ba, ya ƙarasa shimfiɗa tabarman kana ya juya ya koma cikin ɗakin yaje ya ɗauko wani ƙaramin bargonsa da Ummansa ta bashi tun lokacin yana karatu a BUK yazo ya shimfiɗa akan tabarman ya haye yayi kwanciyarsa abunsa ya juya mata baya, kallonsa kawai Fadwa take yi cike da mamaki kafin ta saki tsaki tana hararar bayansa ta juya tayi komarta cikin ɗaki ta haye gado tayi kwanciyarta hankalinta kwance taja bargo ta lulluɓe jikinta ta ƙudundune tana faɗin "Ni dama Allah zaisa kayi zuciya ka sawwaƙe min wannan munafukin ƙaddararren auren naka daka taimakeni wallahi, sai inje in duƙufa da yi maka addu'a ina roƙon Allah ya haɗaka da dai-dai kai wacce zata dace da yanayin talaucinka dan ni dai kam ai nayi maka nisa kowa ya sani kawai an shiga hakkina ne babu yadda zanyi...." Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana jan tsaki kana ta sake lafewa a gadon ta lumshe idanuwanta wanda suke cike da baccin gajiya, dan har wani lumshewa suke yi suna mata wani yaji yaji saboda tsabar rashin samun isasshen baccin da bata yi ba, ga kuma gajiyar da tayi tuɓus gaba ɗaya jikinta a sake yake kamar wacce aka yiwa shegen duka ƙafarta kuwa har wani ɗib ɗib take mata saboda tsabar taku da raye rayen da ta sha yau. Bata jima da kwanciyar ba, wani daddaɗan bacci mai cike da zallar natsuwa da jin daɗi yayi awon gaba da ita. Ya Azeez kuwa ya daɗe idonsa biyu ya kasa bacci yana ta juye juye da tunane tunanen rayuwa zuciyarsa kamar zatayi bindiga saboda tsabar baƙin ciki da takaicin Fadwa, gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idanuwansa sai wani irin tafasa da ƙuna zuciyarsa take yi. Ganin tunanin yana neman hanasa sukuni da natsuwar zuciya ne a banza yasa ya tashi ya ɗauki buta bayan ya kunna glove ɗin ɗakin haske ya gauraye ko'ina kasancewar akwai wutar nefa da suka kawo tun ƙarfe 12:30am. Basu ɗauke ba ya fita tsakar gida yaje ya ɗauro alwala ya dawo ɗakin ya shimfiɗa darduma ya hau ya daidaita tsaiwarsa ya tada sallah. Ya daɗe a sujjadarsa ta ƙarshe yana kai kukansa ga rabbil izzati cikin ƙasƙantar da kai da nuna tsantsar tawakali da tsoron Allah, kafin ya ɗago daga sujjadar yana mai ƙara miƙa dukkan lamuransa ga Sarkin sarakuna mai ji kuma mai gani wanda yake shi kaɗai bashi da wani abokin tarayya. Ya daɗe zaune akan darduman yana ta yiwa Allah kirari kafin ya ɗora da salatin Annabi (SAW) daga nan ya shiga kwararo addu'oi kan Allah ya zaɓa musu dukkan abinda yafi zama alkhairi a tsakaninsa da Fadwa sannan ya tashi ya shiga cikin ɗakin ya ɗauko Alkur'ani da cashaba ya dawo ya zauna ya fara karatu a hankali cikin daddaɗar muryarsa mai sanyi da sanyaya zuciya da saukar da shauki ga duk wanda ya saurara. Yana nan akan darduman bai tashi ba har 4:30am. Na asuba dai-dai ta buga a alarm ɗin daya saka cikin wayarsa domin ya riƙa tadashi, sai da yayi addu'a ya shafa kana ya miƙe cikin kuzari da wani irin farin ciki da yake ji tun daga can ƙasan zuciyarsa yana taso masa wanda baya rasa nasaba da addu'oin da yayi, linke darduman yayi ya ajiye akan tabarman daya shimfiɗa sannan ya mayar da Alkur'anin uwar ɗaka ya ajiye a inda ya ɗaukosa, kana ya fita daga ɗakin yaje ya buɗe ɗan kichin ɗinsu ya ɗauko murhun gawayi ya fito dashi tsakar gida sannan ya koma ya ɗauko ƙaramar tukunyar da suke dafa ruwan wanka da tsintsiya ya fito, sai daya haɗa gawayin wanda ya samu da ƙyar ya rure har ya kama sannan ya zuba ruwa a tukunyar ya ɗora ya rufe, kana ya ɗauki tsintsinya ya hau sharan tsakar gidan kamar yadda ya saba. Sai daya share ko'ina yayi fes fes gwanin sha'awa ya kwashe sharar ya zuba a abin zuba shara kana ya ɗauki manyan bokitan da yake zuwa ɗebo ruwa dasu ya fita, sai daya ciccika ko'ina kamar yadda ya saba duk bayan kwana uku, koda ya gama lokacin ruwan daya ɗora yayi zafi sosai ya juye a bokiti ya sake zuba wani ya ɗora sannan ya sirka wanda ya juye ya shiga cikin ɗakin ya ɗauko kwandon soso ya fito ya ɗauki ruwan ya shiga banɗaki, bai wani jima sosai ba yayo wanka ya fito ya zuba ruwa a buta ya ɗaura alwala kana ya koma ɗaki har lokacin gimbiyar na nan a ƙudundune tana sharar bacci, bai ko bi ta kanta ba ya buɗe jakarsa ya ɗauki riga da wandonsa na wani farin yadi mai sauƙin kuɗi ya saka sannan ya shafa mai sama sama kana cikin sauri ya fesa turare a gurguje ya ɗauki casbahansa ya fice ya zura takalmansa ya nufi masallaci dan lokacin har ƙarfe 5am tayi da ƴan mintuna dan har wasu masallatan ma sun tada sallah. Yau bai wani zauna a masallacin ba ana idar da sallah ya fito ya nufo gidan yana zuwa ya iske ruwan daya ɗorawa Fadwa yayi zafi sosai har yana shirin tafasa bai sauke ba ya shiga ɗakin direct ya wuce uwar ɗaka, bai yi wani mamaki ba ganin har lokacin tana nan kwance tana ta sharar bacci bata tashi ba, kaɗa kai kawai yayi ya ɗauki makullin keke napep ɗinsa dake ajiye a saman jakarsa kana ya ɗauko wandon daya cire ya laluba aljihun ya zaro kuɗi ya ciri ɗari biyar ya ajiye a kusa da ita sannan ya zura sauran cikin aljihun wandon da ke jikinsa, har ya juya zai fice daga ɗakin sai yayi wani tunani ya fasa ya dawo da baya ya tsaya a kanta yana kiran sunanta a hankali yake faɗin "Ke Fadwa...Fadwa..." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa lokaci ɗaya yana ɗan dukan ƙafarta. Kamar a mafarki Fadwa taji muryarsa a sama yana kiran sunanta, cike da takaici ta saki tsaki kafin ta juya tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta da suke cike da bacci har lokacin. A hankali har ta gama waresu fes a kansa yana tsaye kyakkyawar fuskar nan tasa a haɗe tamau kamar wanda bai taɓa dariya ba, sai ta ga ya ƙara mata wani kwarjini na musamman ya cika mata idanu, kayan daya saka sun karɓi jikinsa sosai sai suka ƙara fito da zallar kyawunsa da kamalarsa a fili, uwa uba haiba da tsantsar natsuwarsa. Da sauri ta tashi zaune tana binsa da wani mugun kallon sama da ƙasa kana taja tsaki a zafafe tana faɗin "Wai lafiya Malam zaka kashe min dodon kunne da wannan ƙatuwar muryar taka, ko kana bina wani bashi ne...?" Ta faɗa tana wani ƙara haɗe rai lokaci ɗaya tana galla mai harara, ga tarin mamakinta sai ta ga ko kallonta bai yi ba, sai ma ɗauke kai da yayi gefe ya juya yana ƙoƙarin ficewa yake faɗin "A'a bana binki bashin komai, dama dai zan sanar dake ne ga kuɗi nan na ajiye miki ki siya abun kari sannan ga ruwan wanka can idan kin tashi sai kiyi, ni na fita..." Daga haka kawai yasa kai ya fice daga ɗakin ya barta nan zaune sake da baki tana binsa da kallo cikin sanyin jiki da tsantsar mamakin sauyawarsa lokaci guda, ji yadda yake mata magana kai tsaye ba wani tausasawa ko lallashi kamar ba Ya Azeez ɗin data sani nata mai haƙuri da tsananin tausayinta ba. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* *WADATAR ZUCCI* *Wattpad:Aishaalto09* 1️⃣6️⃣ Ta daɗe zaune tana bin ƙofar daya fice da kallo kafin ta kaɗa kai lokaci ɗaya tare da waigawa tana ƙarewa ɗakin kallo, cikin mamaki da al'ajabi take faɗin "To wai meya faru ne daya sauya lokaci guda irin haka...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana tsurawa guri guda idanu cikin nazari, kafin a hankali kuma ta sauke numfashi tana faɗin "Can da matsalarka wallahi ni dai a sani na babu abinda ya haɗani da kai balle inyi tunanin ko nice na ɓata maka rai, dan haka babu abinda ya dameni ballantana yasha min kai nida zaka taimakeni ma daka sahale min wannan auren naka in rabu da ƙaya, kaima kuma ka huta nauyin yayi maka sauƙi kaji da kanka..da wannan ƴar ya ƙunanniyar uwar taka..." Ta faɗa tana hararar jakar kayansa kamar shine yake zaune a gurin, kana ta saki tsaki tana zuro ƙafarta ƙasa ta sauko daga kan gadon tana gyara ɗaurin zanin dake ƙirjinta ta fice daga ɗakin zuwa falo, bokitin daya fito wanka dashi ta ɗauka ta juye ruwan daya ɗora mata ta sirka sannan ta kashe gawayin dan babu abinda zata ɗora. Komawa tayi cikin ɗaki ta ɗauko sabon shower cream ɗin da aka raba musu jiya gurin bikin kanwar Hajiya Lubna sannan ta dawo ta ɗauki bokiti da soso ta shige banɗakin. Sai data kwashe kusan awa guda a cikin banɗakin tana dirzar jikinta kamar wacce zata canza fata, dan har sai da ta soma jin fatar jikinta na mata raɗaɗi da zafi kafin ta haƙura ta fito, ta wanke bakinta sannan ta ɗaura alwala lokacin ƙarfe 7:40am. Dai-dai ta shiga ɗaki ta tayar da sallah. Koda ta idar bata bi takan neman abun karyawa ba ta ɗauko kayan kwalliyarta ta zauna bayan ta shafa mai ta murje ko'ina na jikinta da wata humrarta mai daɗin ƙamshi da tsadar gaske wacce Hajiya Labiba ce ta kawo mata ita tsaraba lokacin da sukaje Maiduguri gaishe da mahaifiyar mijinta. Shafa hoda tayi sama sama kana ta shafa wet lips ta miƙe ta buɗe akwatinta ta zabo wata doguwar rigar abaya purple mai kyau wacce tasha adon stones manya manya a jiki, sai data fara saka pant da bra farare masu kyau, sannan ta zura rigar a jikinta ta naɗe kanta da mayafin. Tana ƙoƙarin fesa turare a jikinta taji ƙarar wayarta dake cikin jaka, da sauri ta ƙarasa inda jakar take rataye ta buɗe ta ciro wayar, sunan Hajiya Labiba ta ga yana yawo akan screen ɗin wayar, da hanzari ta ɗauka ta manna a kunnenta tana faɗin "Ƴar halak kin ƙi ambato, yanzu fa nake zancenki a zuciyata na gama shiri kenan zan taho gidanki..." Daga can ɓangaren Hajiya Labiba tace "Yauwa ƙawata yi sauri ki taho dan Allah tun ɗazu nake ta zuba ido ina saurarenki na jiki shiru ba labari, shiyasa nace bari in kiraki kinsan yau dai muna da abubuwan yi da yawa dan har ƙunshi nake son ayi mana, gashi zamu shiga kasuwa inaso zan ƙarasa siyayya sannan zamuje gidan Hajiya Kalsoom dan acan ne yau za'ayi bridal shower ɗin..." Ajiyar zuciya Fadwa tayi tace "Ok gani nan zuwa yanzun nan insha Allahu mashin ma zan hau dan yafi min sauri..." Hajiya Labiba tace "Ok sai kin ƙaraso nima bari in tashi in shirya kafin ki iso..." Ta faɗa tana katse wayar, a gurguje Fadwa ta ƙarasa fesa turaren kana ta ɗauki handbag ɗinta ta sagala a gefen kafaɗarta, wayarta kuma ta riƙeta a hannu ta fice daga gidan bayan ta jawo ƙofar ɗakin ta kulle haka nan ba tare data saka kwaɗo ba, dan saboda yau ma tasan suna da abubuwan yi da yawa wataƙila bazata dawo gidan da wuri ba sai dare, shiyasa kawai ta bar mai ƙofar ɗakin data gidan duka a buɗe bata kulle ba, domin bata son ta dinga dawowa kullum tana iskesa tsaye a ƙofar gida yana dakon jiran dawowarta kamar wani almajiri. ******* A ɓangaren Ya Azeez kuwa yana fita daga gida direct cikin gari ya nufa inda ya saba shiga yayi sana'arsa, sai dai yau abun yazo masa da wani irin salo mai matuƙar ban mamaki da al'ajabi dan tunda ya fito daga gida yake ta haɗuwa da jama'a kota ko'ina gashi tunda ya tashi yau yake jin kansa wani iri kamar bashi ba, dan duk wani ƙunci da baƙin ciki da damuwa daya kwana dasu a ransa daren jiya tuni sun kau, sai wani farin ciki da walwala da yake ji from no were da jin daɗi suna taso masa tun daga can ƙasan zuciyarsa har zuwa cikin ransa. Sosai yau ɗin ta kasance mai ta musamman dan tunda ya auri Fadwa bai ƙara tsintar kansa a irin wannan yanayin mai daɗi ba, irin na yau gashi tunda ya fito yake ta aiki bai samu ya huta ba, dan har rana ta fito bai samu ya tsaya ba ballantana ya huta har ya samu ya ɗan ci wani abu, gashi yau ko karyawar daya sabayi a gida kullum kafin ya fito bai samu yayi ba, haka ya dinga zirga zirga a tituna da unguwannin dake cikin garin har ƙarfe 1pm. Ta buga aka kira sallahn azahar, sai a lokacin ne ya tsaya ya samu wani masallaci dake kan titin Raɓa Road ya shiga yayi sallah kana bayan an idar ya fito ya tsallaka gefen masallacin inda ya hango wani mai shagon provision ya shiga ya siya biredinsa babba da coke ɗinsa mai sanyi sosai, ya fito ya zauna kan bencin dake bakin shagon ya dinga yagar biredin yana korawa da coke ɗin, sai da yasha yayi nak abinsa sannan ya ɗan zauna jim na ƴan wasu mintoci ya huta kafin ya tashi ya yiwa mai shagon sallama kana ya tsallaka inda ya ajiye keke napep ɗinsa a bakin masallacin yaja ya wuce abinsa. **** Fadwa kuwa dasu Hajiya Labiba da Hajiya Lubna gaba ɗayansu suna can wani haɗaɗɗen shagon saloon na isassun mata dake cikin gari ana yi musu gyaran jiki, sai da aka gama musu gyaran jiki da na kai tsaf sannan aka kira mai ƙunshi tazo ta tsantsara musu lafiyayyen ƙunshi mai kyau da burgewa, kana aka yi musu fixing eyelashes da nails ƴan dai-dai masu kyau da ban sha'awa. Ana cikin wankewa Fadwa ƙunshin ƙafarta ne Sadeeq telanta ya kirata a waya yake sanar da ita cewa gashi a gidan Hajiya Labiba yazo kawo mata ɗinkinta amma mai aikinta ta sanar dashi basa nan dukkansu sun fita, ya jirata ne zasu dawo yanzu ko ya bar wa mai aikin Hajiya Labiban kayan ne kawai ya wuce..? Ɗan jim Fadwa tayi kafin tace "Ok ba damuwa Sadeeq ka bar mata kayan kawai ka wuce abinka, na gode sosai sai mun sake haɗuwa..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana katse wayar, Hajiya Lubna dake zaune a gefenta ana ƙarasa saka mata nails a yatsun ƙafarta ta ɗago tana kallon Fadwa lokaci ɗaya tana ƙare mata kallo kafin tace "Gaskiya ƙawata kinyi masifar yin kyau..ke kin ganki kuwa wallahi na tabbata yau idan Azeez ɗinki ya ganki da wuya ya iya ganeki saboda komai naki ya canza kin ƙara wani haske da kyau kamar wata tauraruwa..." Fadwa da taji kanta ya ƙara mata wani girma ta washe baki cike da jin daɗin yabon da Hajiya Lubnan tayi mata tana faɗin "Dan Allah fa ƙawata..amma ai ban kaiku ba..." Ta faɗa tana duban Hajiya Labiba wacce ta sakar mata harara tana faɗin "Lallai ne ma ƙawata, ai wallahi da nice nake da kyaunki da yanayin tsarin halittar jikinki da ba ƙaramin abu zanyi ba..dan ko miji ne wallahi sai na zaɓi haɗaɗɗe wanda yaci naira ya tada kai da ita sannan zan yarda in aura, dan irin wannan haɗaɗɗen jikin naki bana talaka faƙiri bane..." Fadwa ta saki tsaki cikin tsantsar baƙin ciki da takaici tana faɗin "Uhmmm ki bari kawai ƙawata ai ni kam an gama cutata da aka haɗani da jigari jigarin miji wanda bai da wani abinda ya mallaka duk faɗin duniyar nan sai keke napep wanda itama ba tasa bace tausayinsa kawai akaji aka ara masa dan ya dinga samun ɗan na kashewa da siyan abinci..amma dan Allah ki dubeni yanzu waye zai ganni yayi tunanin cewa ni matar ƙaramin mutum ce irin Ya Azeez..? Gaba ɗaya an gama kashe min rayuwata da kuncin talauci, ɗan kyaun da nake taƙama dashi ma so ake aga ya dusashe sannan za'a san zaman da nakeyi dashi kwata kwata bai kamace ni ba kuma duk da hakan wai mahaifina ya kasa ganewa, shi dai babban burinsa kawai in cigaba da zama dashi in ƙarashe rayuwata cikin baƙin talauci da ƙuncin rayuwa..yanzu anyi min adalci kenan dan Allah...?" Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya da sigar tambaya tana wani kwaɓe fuska kamar zata fashe da kuka, saurin girgiza mata kai Hajiya Lubna tayi tana faɗin "Gaskiya kam har ga Allah ba'a kyauta miki ba Fadwa, amma kiyi haƙuri ki ci gaba da zama dashi a yanda yake wataƙila Allah yayi masa kyakkyawan tanadi wanda yafi wannan a nan gaba, kema sai kiga wata rana kin tsinci ribar haƙurinki..domin gaba ɗayanmu nan babu wanda yasan me gobe zata haifar, ballantana muyi wani hasashe a kansa da abinda zai faru da rayuwarsa nan gaba..." Wani dogon tsaki Fadwa taja lokaci ɗaya tana hararar Hajiya Lubna kafin tace "Oh ashe ke har wani tunanin kyakkyawar rayuwa kike yi masa a nan gaba...?" Cikin sauri Hajiya Lubna ta kaɗa mata kai cike da tabbatarwa tana faɗin "Of course..ko kin manta ne a dare ɗaya Allah kanyi bature...?" Fadwa ta girgiza kai cikin takaici tace "Amma yana a faƙirin matsiyaci wanda bai ajiye komai ba kuma bai ba wani ajiya ba har kike tunanin zai iya zama wani abun arziki a nan gaba...?" Ta faɗa cike da mamaki tana kallonta, cikin yaƙini da sake tabbatarwa kuwa Hajiya Lubna ta kaɗa kai tana faɗin "Sosai kuwa wallahi wata rana sai kinyi mamakin yadda Azeez ɗinki zai zama a rayuwarsa nan gaba, domin duk ɗan hakin daka raina wata rana shi zai tsole naka ido..shiyasa nace kibi komai a sannu dan dole wata rana in dai muna raye komai zai zamo labari, ke dai ki jira lokaci..." A zafafe Fadwa ta taso mata da faɗa tana faɗin "Eh saboda ke kina cikin daula kina jin daɗin rayuwarki kina zuba mulkin da kika ga dama a gidanki ba..ai dole ni kiyi min fatar dawwama cikin tsiya da ƙuncin rayuwa, to insha Allahu ta Allah ba taki ba..kina nan mugun bakinki zai biki dan nima Allah ya kusa kawo min mafita ta alkhairi sai dai ɗan baƙin ciki ya mutu..." Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana huci. Ran Hajiya Lubna ya ɓaci sosai da kalamanta amma sai bata kulata ba tayi banza da ita. Ita dai Hajiya Labiba duk tana jinsu amma bata tsoma musu baki ba, sai ma wayarta data fito da ita daga cikin jaka take ta latsawa tana sakin murmushi. Dan ita Allah ya sani bata ganin laifin Fadwa ko kaɗan akan irin tsanar da ta yiwa Azeez saboda an tauye mata hakki da yawa an durƙusheta sosai an hana mata ci gaba, shiyasa take bala'in jin tausayinta domin zama da matsiyaci sai wanda ya daure ya kai zuciyarsa nesa. Haka har aka gama musu babu wanda ya sake magana a cikin su, suka miƙe ko wacce ta ɗauki jakarta Fadwa sai hararar Hajiya Lubna take tana sakin tsaki, ita ko Hajiya Lubna ko bi ta kanta bata sake yi ba ta wuce taje ta biya duka bill ɗin komai da akayi musu kana suka fice daga saloon ɗin. Kasancewar dama dukkansu a motar Hajiya Lubna suka je saloon ɗin dan koda sukaje gidan Hajiya Lubnan Hajiya Labiba acan ta bar tata motar, shiyasa direct daga saloon ɗin suka wuce gidan Hajiya Lubnan sai da Hajiya Labiba ta ɗauki tata motar kana suka wuce kasuwa ita da Fadwa dan Hajiya Lubna tace bazata je ko'ina ba zata tsaya a gida ta ƙarasa wani aiki. *BAYAN AWA HUƊU* Fadwa ce tsaye a tafkeken ƙayataccen bedroom ɗin na Hajiya Labiba tana shiryawa cikin wani haɗaɗɗen lufaya mai tsadar gaske yellow mai flowers blue ajiki sai rigar da tasa long sleeve itama blue sannan tasa takalmi mai tsini blue shima sai ƙaramar jakarta ƴar madaidaiciya data sagala a tsintsiyar hannunta mai kyau kalar blue itama. Bata yi wani kwalliya sosai a fuskarta ba yau sai hoda kaɗai da janbaki da ta ɗan shafa amma idan ka ganta sai ka ɗauka wata shuwa arab ce saboda bala'in kyaun da shigar tasu tayi mata ga ƙunshin ƙafarta da hannayenta ya sake fitowa raɗau yayi jajir dashi sai tayi sharr da ita kamar wata sabuwar amarya. Hajiya Labiba dake gefenta a tsaye tana ƙoƙarin naɗa lufayan itama a jikinta ta buɗe baki galala kawai tana kallonta, cikin wani irin taku Fadwa ta ƙaraso gabanta ta tsaya fuskarta ɗauke da wani ƙayataccen murmushi take faɗin "Nayi kyau kuwa ƙawata...?" Hajiya Labiba tayi murmushi kana tace "Haba ana magana ma! Ai kinyi masifar yin kyau tawan..na tabbata yau kinfi jiya haɗuwa da tsaruwa dan baki ga yadda kike wani walwali da ɗaukar ido bane..kamar a saceki a gudu..." Cikin tsananin jin daɗi Fadwa tace "Na gode tawan, wallahi har kinsa kaina ya ƙara wani girma da wannan yabon naki..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara jin wani alfahari da farin ciki suna mamaye zuciyarta, murmushin itama Hajiya Labiban tayi tana faɗin "Ai kinfi duk yadda zan kwatanta ki aminiyata, dan ke ɗin ta musamman ce wallahi..samun irinki a wannan zamanin zaiyi matuƙar wahala saboda ke mai tsada ce sai mai babban rabo, shiyasa nake tayaki baƙin ciki da takaicin kasancewarki matar talaka faƙiri mai jan keke napep wallahi..." Ɗan taɓe baki kawai Fadwa tayi ba tare da tace komai ba ta matsa inda wani haɗaɗɗen ƙaramin show glass yake ta buɗe, turaruka ne kala kala masu matuƙar tsada ƙamshi jere reras a ciki ta ɗauki turaren sweet baby da lovely ta feshe ilahirin jikinta dasu tsaf kana ta ɗauki wayarta ta zura cikin jaka sannan ta kwashi awarwarayen gwal manya manya guda huɗu da Hajiya Labiba ta zube mata yau ma ta zura a hannunta, kana ta juya tana kallon Hajiya Labiba dake fesa turare a jikinta tana faɗin "Muje dan Allah ƙawata, wallahi duk na ƙosa mu isa gurin in ga irin manyan jiga jigan matan da Hajiya Kalsoom ta gayyata dan nasan tabbas taron yau sai yafi na jiya tara manyan mata saboda ita mai tarin jama'a ce..." Hajiya Labiba tace "Ai kuwa dai kamar kin sani yau gidan na can cike maƙil da jama'a sai wanda ya gani..." Ta faɗa tana duƙar jakarta itama kalar flowern jikin lufayanta ta riƙe a hannunta tace "Muje ko..?" Ta faɗa tana yin gaba yayinda Fadwa ta rufa mata baya suka fice daga bedroom ɗin, haka suka fita harabar gidan gaba ɗayansu suna baza ƙamshin turare irin na manyan mata masu aji da yarari, direba yana ganinsu ya taso da sauri ya iso gabansu kamar zai kifa ya rusuna yana faɗin "Barka da fitowa Hajiya..fita zamuyi ne...?" Fadwa dake kallonsa sama da ƙasa a wulaƙance tace "A'a ba fita zamu yi ba, zamu zauna ne a bakin ƙofa..." Ta faɗa tana jan tsaki kana taja hannun Hajiya Labiba tana faɗin "Muje dan Allah ni kar ya ɓata mana lokaci muna da abun yi mai muhimmanci a gabanmu..." Cikin sauri yace "Allah ya huci zuciyarki ƙawar Hajiya..." Ya faɗa yana wucewa da hanzari yaje ya buɗe musu wata dalleliyar sabuwar mota baƙa wuluk ƙirar Bugatti. Cikin rawar jiki Fadwa ta ƙarasa da sauri ta shige zaraf ta zauna lokaci ɗaya tana ƙarewa motar kallo dan sosai ta gama tafiya da imaninta, itama Hajiya Labiban kanta ganin yadda Fadwan tayi sai data kalleta ta murmusa kana ta girgiza kai ta shiga ta zauna a kusa da ita, sai da ya rufe musu ƙofar kana ya juya cikin sauri ya shiga gurin zamansa ya zauna ya tada motar yaja maigadi ya wangale musu get ya silala motar a hankali suka fice daga gidan. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 1️⃣7️⃣ Abba ne zaune a ɗan filin tsakar ɗakinsu ya zuba uban tagumi yana kallon Mama dake riƙe da wani ɗan madaidaicin madubi a hannunta tana shafa hoda a fuskarta, lokaci ɗaya tana ƙara kallon kanta a madubin tana sakin murmushi. Kaɗa kai Abba yayi a hankali yana kallonta kafin ya juya cike da takaicinta ganin ta ɗauko janbaki zata shafa a leɓenta yayi murmushin da yafi kuka ciwo yana sake kallonta cikin mamaki da al'ajabinta yake faɗin "Yanzu Maryama rayuwar da kika ɗaukarwa kanki kina ganin mai ɓullewa ce..kamar ke ace kina babba dake tsofai tsofai amma kina abu sai kace wata ƙaramar yarinya...?" Da sauri ta ajiye madubi da janbakin dake hannunta tana yatsina fuskarta cikin ƙosawa tace "To rayye me kuma nayi maka nida bana girma da laifi a gurinka...?" Ta faɗa cikin taɓe baki tana harararsa, shiru yayi yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa kafin yace "Yanzu ina zakije kike irin wannan kwalliyar kamar wata ƙaramar yarinya..anya kuwa kin san abinda kike shirin aikatawa Maryama...?" Fuska ta ƙara tamkewa tana watsa mai harara kafin tace "A'a ban sani ba kazallaha saika sanar dani..." Ta faɗa cikin gatse tana watsa mai wani mugun kallo mai kama da harara. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Ai indai zakice irin wannan muguwar ɗabi'ar taki ta kwaɗayi da son abun duniya zaki ɗore da ita har ƙarshen rayuwarki to kuwa kina da babban aiki ja a gabanki, dan wallahi wata rana sai kinyi danasani mara amfani a nan gaba...kina tsofai tsofai dake ko kunya babu kice ke babu abinda kika iya sai kwaɗayi da son abun duniya..yanzu dan Allah da kike wannan shirin ina zakije...?" Ɗaure fuska tayi sosai kafin tace "Ikon Allah wai tsofai tsofai dake, a'a kwan lafiya ce ni ƙarewar tsufa, kuji min ɗan mutumi da baƙin ciki da hassada sai kace a kanka nake kwaɗayi da son abun duniyan da zai dameka..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana ɗaukar ƴar ƙaramar wayarta ƙirar Aitel dake ajiye a kusa da ita, cikin lokaci kaɗan ta lalubo numbern Fadwa wacce tayi saving ɗinta da *KUƊINA.* Shiru yayi yana bin ta da kallo, ta danna mata kira lokaci ɗaya tana kallon ɗan agogon dake maƙale a bangon ɗakin, ƙarfe 5pm ta gani har ta wuce. Wayar ta shiga haka ta dinga ringing har ta katse bata ɗauka ba, bata haƙura ba ta sake kiranta nan ma har ta gama ringing ta katse bata ɗaga ba haka ta dinga kira har kusan sau biyar bata ɗaga ba, tsaki taja ta kife wayar tana harararsa kamar shine ya hana Fadwan ɗaukar wayar tata, shi dai bai tanka mata ba da ido kawai yake ta bin ta bai ce komai ba. Haushin haka ne yasa ta sake ɗaukar wayar a fusace tana faɗin "Duk baƙin cikin mutum dai yau sai naje bikin gidan masu arziki, sai dai ƙyashi da hassada su kashe ɗan baƙin ciki...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana sake danna mata wani kiran a karo na shida. Daga can ɓangaren Fadwa dake gefe cikin wani haɗaɗɗen ƙayataccen garden dake gidan Hajiya Kalsoom daya cika da manyan mata ana ta shagalin biki gurin ya kaure da hayaniya, sai sautin kiɗan dj ke tashi, shigowarsu tsakiyar fili kenan ita da Hajiya Labiba da wata hamshaƙiyar ƙawarsu Hajiya Zalika wacce ke auren wani babban ɗan kasuwa a jihar Kano, zasu fara yiwa amarya liƙi kenan, taji vibration ɗin wayarta dake cikin jaka wacce dama ta sakata a silent ne gudun kar a dameta da kira, ba tabi ta kanta ba sai da suka gama liƙin suka fice daga cikin filin kana ta zura hannu a jakarta ta ɗauko wayar, ganin sunan wacce ke kira ne yasa tayi murmushi kafin ta ɗaga kiran tana faɗin "Hello Mamana...kina jina....?" Daga can ɓangaren Mama da taji muryar Fadwa ta ɗaga kiran ta washe baki cike da farin ciki gefe guda tana hararar Abba daya saki baki galala yana kallonta kafin tace "Ina jinki ƴar albarka, ya taron...kuna can gurin bikin kenan dan naji hayaniya...?" Murmushi Fadwa tayi kafin tace "Muna can tun ɗazu guri yayi guri Mama manyan mata an haɗu ana ta shagali sai kin gani wallahi abun gwanin ban sha'awa...." Da sauri ta katseta da faɗin "Yauwa dama abinda nakeson ji kenan shiyasa nake ta kiranki, aiko nima banga ta zama ba yanzu nan zan taho ayi dani insha Allahu ki gaya min sunan unguwar kawai yanzu yanzu zan shirya dan bazan ta zama a gida in cuci kaina ba atoh...." Fadwa tace "Toh..." Nan ta gaya mata sunan unguwar daga haka suka yanke kiran, cikin sauri Mama ta ajiye wayar ta miƙe ta fara ƙoƙarin shiryawa cikin wata atamfarta mai sauƙin kuɗi wacce Fadwan ta ɗinka mata ita tun ƙaramar sallahn data wuce, inda tasa Sadeeq telanta yayi mata ɗinkin doguwar riga Ashape mai kyau wanda yaji stones irin na zamani masu walwali da ɗaukar ido ta saka, kana ta ɗauki ɗankwalin atamfar ta zauna ta saita madubi ta kafa ɗaurin Maryam Babangida a kanta wanda ya zauna daram, sannan ta wani turosa gaban goshi ta ɗan karkata shi yayi gefe irin na ƴan matan zamani. Shi dai Abba sakin baki kawai yayi yana kallon ikon Allah, dan sosai zuwa yanzu lamarin na Mama ya fara bashi tsoro, domin yaga alamar abun nata ƙara gaba gaba kawai yake kwata kwata babu alamar wata saduda a tattare da ita, Mama kuwa ko a jikinta shirinta kawai take yi abin ta ko kallon inda yake bata yi. Sai data gama shiryawa tsaf har ta yafa gyalenta kana ta ɗauki ƴar jakar pos ɗin da take zuba cinikin ƙuli ƙuli da kayan miyanta ta buɗe ta jefa wayarta a ciki ta riƙe a hannunta lokaci ɗaya tana gyara zaman gyalenta tana wani yatsina fuska. Abba dake ta kallonta cikin ƙufuluwa da baƙin ciki yace "Wai yanzu kina nufin da gaske bikin ƙanwar ƙawar ƴarki zaki kama hanya ki tafi gotai gotai dake Maryama saboda rashin tsoron Allah....?" Ya faɗa cikin son kwantar da fushinsa duk da ya kasance mai tsananin haƙuri da yakana. Banza dashi tayi tasa kai zata fice daga ɗakin, da sauri ya miƙe yana faɗin "Babu fa inda zakije Maryama...kuma a matsayina na mijinki nake baki wannan umurnin, dan haka ki dawo ki zauna tun kafin ranki ya ɓaci...." Ta buɗe baki a fusace zatayi magana kenan wasu kyawawan ƴan mata guda biyu masu tsananin kama da ita suka shigo ɗakin hannuwansu rungume da litattafai wanda da ganin alamu daga makarantar islamiyya suka dawo, dan dukkansu sanye suke da dogayen hijabai har ƙasa iri ɗaya. Ganinsu baisa ta fasa abinda tayi niyya ba sai ma ƙara buɗe murya da tayi ta taso mai cikin masifa da bala'i tana faɗin "Wallahi sai na tafi sai dai duk abinda zai faru ya faru...kai ya ma daɗe abun bai faru ba, sai naje ɗin kayi duk abinda zakayi kaji...!?" Ta faɗa kai tsaye tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa ta wuce, cike da mamaki ƴan matan suke kallonta kafin ɗaya daga ciki tace "Haba..Mama wannan wace irin rayuwa ce kika zaɓarwa kanki tsakani da Allah...? Wannan abun da kikeyi fa sam bai dace ba har ga Allah nidai na gaji da ganin irin wannan wulaƙancin da kike yiwa mahaifin mu tunda ba'a kansa kaɗai aka sauke talaucin duniya ba kuma ba wai Allahn da ya yishi baya sonsa bane daya barshi a haka...idan kuma kin gaji da zama dashi ne sai ki nemi ya sawwaƙe miki ba ki dinga cin zarafinsa a gaban ya'yansa kina neman zubar mai da mutunci ba...." Ta ƙarashe maganar kai tsaye tana kallon cikin ƙwayar idanunta cike da rashin kunya, zaro idanu waje ta kusa da ita tayi cike da tsoro kafin cikin sanyin muryarta tace "Subhanallahi Ilham ki daina mata rashin kunya mana dan Allah, kar fa ki manta ita ɗin mahaifiyar mu ce bai kamata kina gaya mata duk maganar data fito daga bakinki ba...." Cikin baƙin ciki da damuwa wacce aka kira da Ilham ɗin tace "Amma baki ji itama mahaifinmu ne take gayawa duk maganar data fito daga bakinta ba....?" Bata bata zarafin magana ba ta cigaba da faɗin "Dan haka ki ƙyaleni dole zan faɗa Amatullah! Kaf unguwar nan babu uwa kamar tamu, sam ba wanda kake jin kansa da mijinsa a cikin gidansa sai ita itace duk abinda akayi bazata barwa cikinta ba sai ta amayar...kina kallo dai komai mahaifin mu yayi a cikin gidan nan sai ta nuna bai isa ba saboda tsabar rashin godiyar Ubangiji da kwaɗayi haka take ta zubar mai da mutunci a gurin mutanen unguwa ake kallonsa wani iri....amma wallahi Amatullah kowa ya sani mahaifin mu bai da zuciyar kwaɗayi da son abun duniya, yana da WADATAR ZUCCI da jajircewa yaga ya nemi na kansa..amma Mama kullum hakan baya yi mata akoda yaushe ita gazawarsa take gani, meye laifinsa Amatullah...shine ya ɗaurawa kansa talaucin ko akwai wanda yafi ƙarfin shima Allah ya ɗora masa ne....? Bansan kuma me takeso yayi ba....." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya ƙwallar tausayin kansu dana mahaifinsu na taruwa a idanunta. Wani mugun kallon banza Mama ta watsa mata a wulaƙance tana faɗin "To kisa ya sakeni mana dan uwar ubanki ki gani idan zan ƙara ko second ɗaya ne a wannan ƙaddararren baƙin gidan nasa....shegiya kawai mai matacciyar zuciya wacce ta kwaso mugun halin dangin ubanta na baƙin talauci da muguwar zuciya...." Ta buɗe baki kenan a tsiwace zata sake bata amsa Abba ya ɗaga mata hannu cikin sanyin muryarsa yana faɗin "Fita ku tafi ɗakin ku Ilham, kuma daga yau kar in sake ji idan muna magana da mahaifiyarku wani daga cikinku ya sake saka mana baki...domin wannan ba itace irin tarbiyyar da muka yi muku ba kunji ko....?" A sanyaye duk suka gyaɗa mai kai kana suka juya ba tare da sun sake cewa komai ba suka fice daga ɗakin. Cikin ɓacin rai Mama tace "Kash ai da baka katse mata hanzari ba da ka barta ta ƙarasa zagina tunda ita tantiriya ce ƴar iska gantalalliya...." Lokaci ɗaya Abba yaji wani abu na taso mai tun daga ƙasan ransa ya tokare mai maƙoshi ya tsaya mai ƙyam a ƙahon zuciya, shi dai Allah ya sani bai yi dace da uwar ya'ya ta gari ba, cikin ƙoƙarin danne fushi da ɓacin ran da yake ji suna taso masa yake kallonta kafin yace "Kull! Daga yau karki sake jifan ƴaƴana da wata mummunar kalma makamanciyar wannan, domin kome sukayi miki kece kika jawo...saboda a gurinki suke ganin komai kuma kece ke ɗaurasu akan hanya...." Wani ƙasƙantaccen kallo ta watsa masa tana faɗin "To ko zaka kirata ta dawo ne sai ku rufeni da duka gaba ɗayanku tunda naga kamar hakan shine zai sanyaya muku zuciya da kai har itan...?" Ta faɗa cike da masifa tana kumfar baki, ko tanka mata bai yi ba ya raɓa ta gefenta zai fice, har ya kai bakin ƙofa ya tsaya ya juyo yana kallonta kafin cikin bada umarni yace "Ban baki iznin fita ko nan da can ba kuma idan kika fita bada izinina ba ban yafe miki ba tunda ke bakin san abinda ya dace ba...." Daga haka yasa kai ya fice daga ɗakin ya barta nan tsaye tana binsa da kallon mamaki. Wai yau itace Abban Fadwa yake gayawa irin waɗannan maganganun...Yanzu har ta kai lalacewar da zai tasata gaba yana gindaya mata wasu shegun sharuɗansa marasa tushe ballantana makama..? Aiko wallahi sai yasan yayi da Maryama ɗiyar Malam Audu da Fulera in ma yana tunanin tayi sanyi ne to tana nan daram a yadda ya santa tun tali tali kuma sai ta nuna masa kuskurensa. Da wannan tunanin ta cire gyalenta ta koma ta zauna a tsakar ɗakin bayan tayi wurgi da ƴar pos ɗin dake hannunta gefe ta rafka tagumi cike da baƙin ciki, Allah ya sani yau taci burin zuwa gidan bikin nan sosai dan har ta gama tsara irin abubuwan da zatayi a gidan idan ta isa, amma gashi yanzu a karin banza an rusa mata tsari. ******* A ɓangaren Ya Azeez kuwa ƙarfe 5:30pm nayi ya wuce kasuwa domin ya yiwa Ummansa da Fadwa siyayyan kayan abinci kamar yadda ya saba yi musu duk bayan sati biyu zuwa uku, Ummansa ya fara haɗawa komai da yasan zata buƙata na kayan abinci, sannan ya siyawa Fadwa taliya da indomie itama kana ya siya kwai rabin kiret ya haɗa mata har da kayan tea kasancewar yasan sune kawai abinda take iya ci a gidan suma kuma dan tasan ba wani wahalar dafawa zatasha sosai ba domin ko ruwan lifton wani lokacin ganin ƙyashin ɗorawa take a gidan ballantana akai ga dahuwar indomie ko wata taliya da take ganin ɓata lokaci ne kawai indai itace zata tsaya ta dafa da kanta to ta gwammace ta wuni da yunwa ko ta tafi gidan ƙawayenta taje can ta ci lafiyayyen abincinta wanda ranta yake so tayi hani'an, in kuma da safe ne kafin ya fita sai dai shi da kansa ya ɗora tukunya ya dafa mata tana zaune tana kallonsa ya gama ya ɗauka ya kai mata ba kunya ba tsoron Allah tasa hannu ta ƙarɓa kuma taci ta ƙoshi abin ta hankali kwance ba godi bare na gode. Sai daya gama haɗa mata komai da yasan tana buƙata dan har cornflakes da yaga tana yawan sha, sai daya siyan mata sannan yaje gurin masu kayan miya nan ma yasa aka haɗa masa mai ɗan yawa ya biya kuɗin yasa aka raba masa gida biyu ko wanne aka ɗaure a ledarsa daban daban, ya kwashi kayan ya zuba a napep ɗinsa ya wuce. Daga nan direct K/Mashi ya wuce gidan Ummansa yaje ya kai mata nata, sosai taji daɗi ta dinga saka masa albarka kafin ta tashi ta zubo masa jallof ɗin shinkafa da wake da tayi saura da suka dafa da rana ta kawo masa, kana ta ɗebo masa ruwan randa mai sanyi ta ajiye masa ya zauna ya ci ya ƙoshi yasha ruwan yayi hamdala. Sun daɗe suna tattaunawa da Ummansa akan rayuwa kafin ya koro mata zancen Fadwa da abinda take yi mai wanda har yanzu bata canza ba, sai da ta bari ya kai ƙarshe sannan tace "Toh yanzu me kakeso kuma ince maka...?" Ta faɗa tana kafesa da ido, rausayar da kai yayi kana ya ƙara matsawa gabanta sosai ya tanƙwashe ƙafafuwansa, kafin cikin sanyin muryarsa yace "Umma Fadwa ta gama rainani bata ganina da mutunci ko kaɗan, ban isa in gaya mata magana taji ba duk abinda ta ga dama shi take yi babu ruwan ta da zaiyi min daɗi ko ba zai yi min ba..ta fita duk lokacin da taso ta dawo lokacin da ta ga dama, tamkar wacce take zaman kanta haka Fadwa ta maida rayuwarta babu abinda ya dameta da damuwata. Kullum idan ta saka ƙafa tun da sassafe ta fita tabar gidanta sai can dare sannan zata dawo, ko cikin kwanakin nan sai ƙarfe 12am na dare take dawowa wai suna bikin ƙanwar ƙawarta..taya hakan zaiyi min daɗi har hankalina ya kwanta Umma...?" Ya ƙarashe maganar yana duƙar da kansa ƙasa, shiru Umma tayi tana kallonsa kafin tace "Naji Yayan Imaan..amma dole yau ma haƙurin dai shi zan kuma baka, tunda bayan hakan babu abinda zan iya gaya maka..." Ta faɗa fuskarta cike da tausayinsa, murmushi yayi ganin yadda ta nuna jin tausayinsa a fili ƙarara kafin yace "Toh shikenan Umma na gode kuma insha Allahu zan cigaba da haƙuri da halayen Fadwa kamar yadda kikace har zuwa lokacin da Allah zai kawo min mafita..." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa yana kallonta, kaɗa kai tayi a hankali kafin tace "Da yardar Allah kuwa Allah zai kawo maka kyakkyawar mafita ta alkhairi anan gaba wacce sai kowa yayi mamaki, kai dai kai ta haƙuri kana nuna komai ba komai bane insha Allahu wata rana sai labari..." Ta faɗa a sanyaye cike da tausayinsa, dan ita kanta ta sani ɗanta yana da bala'in haƙuri sosai shiyasa bata fatan ace haƙurinsa ya gaza wata rana zuciya ta ɗebesa ya yanke hukuncin da bai kamata ba. Haka suka daɗe suna hira har Imaan ta dawo daga islamiyya ta samesa a gidan, yana nan zaune sai ƙarfe 7pm bayan yayi sallar magriba sannan ya bar unguwar. ******* Yau ma kamar kullum Fadwa sai dare sannan ta baro gidan bikin ta koma gidanta shima sai da Hajiya Lubna ta haɗata da yayar ta Hajiya Kalsoom ta kirata tayi mata faɗa sosai sannan tace ya kamata ta tafi gida haka nan dare yayi kar mijinta ya riga ta komawa gida ya iske bata nan ransa yazo yana ɓaci gobe tana son fitowa kuma ya hanata, domin kwata kwata ita bata san irin zaman da Fadwan takeyi da mijinta ba shiyasa take hasashen hakan, wanda ita Fadwa anata son ran so tayi ta kwana a gidan Hajiya Kalsoom ɗin, amma ganin babu yadda ta iya yasa ta haƙura ba dan taso ba ta tashi Hajiya Kalsoom da kanta tasa direbanta ya ɗauketa a motarta ya kaita gida. Ƙarfe 11:50pm. Dai-dai direban Hajiya Kalsoom ya dire Fadwa a ƙofar gidanta kamar yadda ta kwatanta masa, sai dai sosai tayi baƙin cikin kasancewar unguwar tasu shiru cikin layinsu babu kowa mutane duk sun shige gidajensu sun kwanta sai ƴan tsirarun dake bakin titi suna harkokinsu amma taso ace koda mutum ɗaya ne ta haɗu dashi a lokacin dan ya ƙarar a gaba cewa ya taɓa ganinta a motar matar mataimakin gwamnan jihar Kaduna sukutum an kawota gida ko banza za'a daina mata kallon matar matsiyaci a dawo ana mata kallon ƙawar matar mataimakin gwamnan jihar Kaduna daga nan darajarta ta ƙara ɗaguwa a idanun jama'ar unguwa a dawo a riƙa mata kallon hamshaƙiyar mace ƙawar manyan mata masu faɗa aji. Yana yin parking ya fito da sauri yaje ya buɗe mata tana ta wani yauƙi da iyayi ta zuro ƙafafuwanta waje cike da yanga sannan ta fito riƙe da wayarta da ƙaramar jakar handbag ɗinta a hannunta kana ta juya ta ɗauki ƙatuwar ledan data cikota da kayan ciye ciye iri iri danginsu snacks da drinks kala kala da gasassun kaji waɗanda aka rarraba a gurin bikin sister's day ɗin ta riƙe a ɗayan hannunta ta juya ko waiwayen direban ba ta tsaya yi ba kawai ta ɗaga masa hannu tasa kai ta shige cikin gida abin ta, shima direban bai ce komai ba ya shiga motar yaja yabar unguwar. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya*🤲 [12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 1️⃣8️⃣ Ya Azeez kuwa koda ya baro gidan Ummansa bai tsaya a ko'ina ba direct ya wuce unguwarsu, dan sosai ya gaji gaba ɗaya jikinsa ciwo yake yi tamkar wanda aka yiwa dukan tsiya, shiyasa ya ƙosa ya isa gida ya watsa ruwa a jikinsa ko zai ɗan ji dama dama ga wani azababben ciwon kai mai tsanani daya saukar masa lokaci guda, yana neman ya hanasa sukuni. Yana fitowa dai-dai kan babban titin Gwamna Road zai juya ya ɗauki hanyar unguwarsu ya hangi wata matashiyar budurwa wacce bazata wuce sa'ar Imaan ƙanwarsa ba tsaye a bakin titi daga gefe tana ɗaga mai hannu, da kamar ba zai tsaya ba har ya wuce sai kuma yayi wani tunani ya dawo da baya da baya a hankali ya gangara gefen titi ɗan nesa kaɗan da ita yayi parking ya tsaya ba tare daya fito ba ya dafe kansa dake tsananin sara masa dan har wani irin jiri jiri yake gani daga zaunen kamar zai kifa ya faɗi. Cikin sauri ta ƙaraso kusa da napep ɗin ta tsaya daga gefe tana ɗan leƙensa tace "Dan Allah Malam taimako muke nema motarmu ce ta lalace gashi bamu san ko'ina ba mu baƙi ne yau ɗin nan muka shigo garin ga dare ya fara yi bamu san inda zamu dosa ba..dan Allah ka taimaka mana..." Cikin natsuwa ya ɗan juyo da fuskarsa yana kallonta kafin yace "To yanzu ni wane irin taimako kukeso inyi muku nida ba bakanike ba...?" Ya faɗa lokaci ɗaya yana ɗauke kansa, ɗan taɓe bakinta tayi kafin tace "Taimaka mana kawai zakayi ka kaimu inda kasan zamu samu bakanike ya duba mana pls...." Ta faɗa kai tsaye tana zumɓura baki, dan ta ga alamar mutumin miskili ne na ƙarshe gashi da alama yana da taƙama da jin kai domin ko magana ta ga da ƙyar yake yin ta yana wani basarwa kamar basarake. Shiru yayi bai ce mata komai ba, ganin haka yasa ta rausayar da kai tana faɗin "Pls ka taimaka mana dan Allah..." Ɗan jim yayi yana kallonta daga sama har ƙasa kafin yace "Ina motar taku take...?" Cikin murna tace "Gata can gurin..." Ta faɗa tana nuna mai wata dalleliyar farar mota sabuwa dal dake fake a gefe sai ɗaukar ido take tana sheƙi, cikin mamaki ya juyo ya kalli inda motar take kafin ya sake juyowa yana kallonta yace "Ok shiga muje can bakin tsallaken mu duba ko za'a samu bakanike a gurin sai a kirasa yazo ya duba muku..." Ya faɗa yana ƙoƙarin tada keken, da sauri ta dakatar dashi da faɗin "Yi haƙuri bari in kira Auntyna mu tafi tare kar mu barta a nan ita kaɗai tana zaman jiranmu..." Ta faɗa ba tare data tsaya sauraren amsarsa ba ta juya da sauri ta nufi gurin motar da ɗan gudunta. Tsintar kansa kawai yayi da fitowa daga napep ɗin ba tare da tunanin komai ba yabi bayanta, domin haka nan kawai ya samu kansa da jin wani mummunan faɗuwar gaba a tare da shi, haka ya dinga bin ta a baya har suka ƙarasa gurin motar a tare yaja ya tsaya a gefe ya zubawa gilas ɗin motar idanu ƙirr kamar wanda akace idan ya ƙifta idon wani abun zai iya faruwa. Suna ƙarasawa ta zagaya ta gefe mai zaman banza dai-dai saitin inda ya tsaya ta ƙwanƙwasa gilas ɗin motar, a nutse ta sauke gilas ɗin lokaci ɗaya tana gyara kishingiɗar da tayi tamkar wata sarauniya ƙamshin haɗaɗɗen turarenta mai matuƙar tsada ya huro ta ɗago a hankali cikin wata zazzaƙar muryarta mai daɗin saurare tace "Ya akayi autar Ummi an samu bakaniken ne...?" Ta faɗa cikin muryarta mai matuƙar sanyi da sanyaya rai. Lokaci guda Ya Azeez yaji gwiwarsa tayi masa wani irin sanyi ya ɗago kai da sauri, a cikin kyawawan idanuwanta masu matuƙar girma da haske nasa suka sauka domin hasken motocin da suke ta wucewa sun hasko gurin da kyau ga kuma hasken solar dake nan burjik akan titi, hakan sai ya bashi damar ƙarewa kyawawan brown ɗin ƙwayar idanunta kallo, wani irin dam yaji gabansa ya buga yayinda zuciyarsa ta hau bugawa da sauri da sauri da wani irin mugun gudu dan lokaci guda yaji yana neman rasa natsuwarsa, ganin yadda ya wani ɗauke kai da sauri ne ya juya zai wuce yasa ta rausayar da kai tana duban ƙanwar tata dake tsaye tana kallonta tace "Wannan shine bakaniken...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙarewa bayansa kallo a fakaice, da sauri ta girgiza kai tana faɗin "A'a fa Aunty bashi bane...wannan mai keke napep ne na roƙesa zai taimaka mana ya kaimu inda zamu samo bakaniken shine nace bari in kiraki sai muje tare..." Cikin natsuwa tace "Ok aiko mun gode sosai Malam Allah ya biyaka...?" Ta faɗa kai tsaye tana ƙoƙarin buɗe motar ta fito. Ƙarar tsadaddiyar wayarta ƙirar iPhone 12pro max dake riƙe a hannunta ne ya dakatar da ita daga ƙoƙarin fitowa da take daga cikin motar, ta ɗago a tsorace tana zaro manyan idanuwanta waje tace "Oh my God...Zahra Abbie ne yake kirana...mun shiga uku yau..." Ta faɗa fuskarta cike da tsoro ƙarara tana kallon ƙanwar tata, a tsoracen itama ta kalleta kafin tace "To ki ɗauka mana Aunty kiji abinda zaice miki...." Saurin girgiza kai tayi kafin tace "In ɗauka fa kikace Zahra...to mezan gaya masa idan na ɗauka ɗin...?" Ta faɗa tana tsareta da ido, ɗan ɗaga kafaɗarta tayi kafin tace "Sai kice masa kawai muna hanya mun kusa isa Abujan...nasan ai bazai yi mana faɗa ba sai dai kawai zaiyi faɗan meyasa muka tsiri yin doguwar tafiya mu kaɗai ba tare da direba ba alhalin munsan baya son fitarmu ko cikin gari ne mu kaɗai irin haka ba tare da wani babba a tare damu ba...ki ɗaga kawai insha Allahu bazai yi miki faɗa ba dan nasan abinda kike tsoro kenan..." Murmushi ta saki saboda tasan wayon Zahra so kawai take ta ɗauka taji abinda Abbie ɗin zaice musu dan haka ta ɗauka kai tsaye tana cewa "Barka da dare Abbie ya Um...." Tsit tayi tana zaro dara daran manyan idanuwanta waje cike da tsoro, kafin ta cire wayar a kunnenta ta miƙawa Zahra tana gyaɗa mata kai, a sanyaye ta ƙarɓa ta manna a kunnenta itama ta ɗan saurara, can sai ta kaɗa kai tana turo baki a shagwaɓe tace "Ayya Abbie wallahi har fa mun kawo Kaduna motar mu ta lalace shine muka tsaya za'a duba mana, amma da tuni mun isa, kuma babu abinda ya faru damu..." Ɗan jim ta sake yi tana sauraren maganar da ake mata ta cikin wayar kafin ta sake shagwaɓe fuska kamar zata fashe da kuka tana faɗin "Ai Aunty Shatu ce tace mu tafi kawai kuma har mun gayawa Aunty Salma ma muna hanya..." Sai a lokacin Ya Azeez ya ɗago da sauri ya kalleta, dan tun lokacin da ta fara wayar ya matsa gefe ya zaro wayarsa daga cikin aljihu yana dannawa, a hankali yaga Zahran ta ciro wayar daga kunnenta ta miƙa mata amma sai taƙi ƙarɓa ta watsa mata harara tana ɗauke kanta gefe, sake maida wayar tayi kunnenta tana faɗin "Abbie taƙi ƙarba sai hararata take..." Da sauri ta fito daga motar ta fizge wayar a hannunta tana watsa mata harara kafin ta manna a kunnenta cikin zazzaƙar muryarta tana cewa "Sharri fa take yi min Abbie...ni bance mata bazan karɓa ba..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara galla mata harara, sun ɗan jima suna magana kafin suka yanke wayar ta mayar da ita cikin jakar dake hannunta ta ɗago tana kallonta tace "Ai shikenan kuma hankalinki ya kwanta, sai ki wuce mu tafi an fasa zuwa Abujan Abbie yace mu bar motar anan zai yi magana da abokinsa Alhaji Mudi ya turo direbansa ya ɗauki motar, mu kuma muje mu kama hotel mu kwana gobe da sassafe mu koma gida..." Ta faɗa tana dungure mata kai, saurin matsawa tayi gefe tana turo baki kafin tace "Ai kece kika ja tunda wayarki ya kira kuma kina sane kika ɗauka..." Ta faɗa tana kwaɓe fuskarta kamar zata fashe da kuka, cikin mamaki take kallonta kafin tace "Oh haka ma zakice..amma ina ce ke kikace in ɗauka inji me zai ce...?" Cikin sangarta da shagwaɓa tace "Amma ai ni ban matsa miki nace dole sai kin ɗauka ba kika ɗauka..ko Malam...?" Ta ƙarashe maganar da sigar tambaya tana kallon Ya Azeez dake tsaye ya harɗe duka hannuwansa a ƙirji yana kallon diramar tasu cike da nishaɗi, itama juyowar tayi ta kallesa da idanuwanta masu kashe jiki da saukar da kasala tace "Amma ai kana ji lokacin da tace in ɗauka ko tsakani da Allah...?" Rasa abin cewa yayi kawai ya juya ya fara tafiya yana faɗin "Muje nidai in kaiku inda za'a samu bakaniken dare yana ƙara yi inaso inje gida in huta..." Ya faɗa yana yin gaba da sauri, bin bayansa itama Zahra tayi da sauri tana faɗin "Aunty Shatu muje dan Allah wallahi dama na gaji na ƙosa in samu inda zan ɗan kwanta in huta..." Banza da ita tayi ta danna wani ɗan madanni dake jikin makullin motar boot ɗin ya buɗe ta zura hannu ta ɗauko wani ɗan madaidaicin ƙaramin akwatin matafiya ja mai kyau ta dire a ƙasa kana ta sake dannna madannin boot ɗin ya rufe ta kulle motar ta ɗauki akwatin tabi bayansu, har sun shiga cikin napep ɗin yana ƙoƙarin kunnawa ta ƙaraso ta shiga itama ta zauna a kusa da Zahra tana harararta, ɗauke kanta tayi da sauri tana faɗin "Nidai Allah ya baki haƙuri Aunty Shatu..." Banza tayi da ita bata tanka mata ba sai ma ɗauke kai da tayi cike da jin haushinta, duk yana kallonsu ta madubin dake jikin napep ɗin. Ganin ya kunna keken amma ya tsaya bai tafi ba yasa ta ɗago karaf kuwa idanunsu ya sarƙe cikin na juna da sauri ta duƙar da kanta dan haka nan kawai taji jikinta ya ɗauki rawa ta kasa jurar kallon ƙwayar idanunsa, wani yawu yaji ya sarƙe masa maƙoshi a hankali yayi gyaran murya cikin wani yanayi kafin yace "Ina mukayi yanzu neman bakaniken zamu ko...?" Tsagal Zahra tace "A'a Hotel mai kyau zaka kaimu mu kama ɗaki ko Aunty Shatu na...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallonta, banza da ita tayi bata tanka mata ba. Shima kallonta yayi kafin yaja keken a hankali ya juya suka koma ta kan titin Gwamna Road. Wani haɗaɗɗen Hotel dake cikin gari ya kai su suka kama ɗaki, bayan ta biya suka fito ta tsaya daga gefe tana kallonsa yana cikin keke napep ɗin a zaune yana ta faman danna ƙaramar wayarsa, kallon Zahra tayi dake gefenta tace "Kije ki ɗauko mana akwatinmu kar mu tsaidashi sannan kiyi masa godiya ki kuma tambayesa nawa ne kuɗinsa mu biyasa ya tafi kar mu sake ɓata masa lokaci..." Haɗe fuska Zahra tayi tana kallonta kafin tace "Haba Aunty! Muje dai tare kiyi masa godiya daga nan saiki biyasa hakkinsa tunda kinga yayi mana ƙoƙari sosai ya taimaka mana, ya kamata mu nuna masa jin daɗin mu..." Shiru tayi tana kallonta kafin ta kaɗa kai tace "Ok muje..." Daga haka suka nufi gurin keke napep ɗin Zahra ce a gaba kafin ita, a hankali take tafiya har suka ƙarasa, Zahra ta zagaya ta gefen da yake ta ɗauko akwatinsu dake bayan napep ɗin ta dire a ƙasa kana ta juya tana kallon Auntyn tata dake tsaye tana faɗin "Aunty Shatu kizo kiyi masa godiyan mana ya wuce abinsa kar mu sake ɓata masa lokaci..." Ɗago kyakkyawar fuskarsa yayi ya kalleta da idanuwansa masu cike da gajiya wanda itama dai-dai ta ɗago kai ta kallesa suka haɗa ido tayi saurin ɗauke kanta tana jin faɗuwar gaba kafin cikin zazzaƙar muryarta tace "Mun gode da taimakon da kayi mana...Allah ya saka maka da mafificin alkhairinsa ya biyaka da gidan aljanna fiddausi...mun gode sosai..." Ta faɗa tana ɗan matsawa gefe tayi shiru. Jin bata sake cewa komai ba ne yasa Zahra ta ɗago ta kalleta kana cikin yin ƙasa da murya tace "To baki tambayesa nawa zamu bashi ba Aunty Shatu...kuma kinyi shiru...?" Har lokacin kallonta yake yi ƙirr ya kasa ɗauke idanuwansa daga kanta, ɗagowa tayi ta saci kallonsa itama karaf suka sake haɗa ido da sauri ta sauke kanta ƙasa tana faɗin "Nawa zamu baka...?" Jin yayi shiru bai yi magana ba yasa ta sake cewa "Ina nufin kuɗin kawo mu nan da kayi...nawa ne...?" Ta faɗa tana kallon Zahra data zuba mata ido ƙirr tana kallonta, watsa mata harara tayi kafin ta ɗauke kanta a ranta tana faɗin "Kyaji dashi dai munafuka..." Jin ya tada napep ɗin ne yasa ta juyo da sauri tana kallonsa amma sai ta ga ya kauda kai shima da sauri ya juya gurin Zahra yana faɗin "Ku barshi bazan karɓa ba na yafe muku..sai da safe...." Ya faɗa yana ƙoƙarin jan napep ɗin zai wuce. Cikin sauri Zahra ta karɓi jakar hannun Auntyn tata ta buɗe ta zaro wayarta dake ciki ta cire code ɗin ta miƙa masa tana faɗin "Gashi ka saka mana numbern wayarka saboda gobe da safe idan muka tashi tafiya in kiraka ka kaimu tasha...ko Aunty Shatu tunda kinga dole goben a motar kasuwa zamu koma gida...?" Ta faɗa kai tsaye fuskarta ɗauke da murmushi tana kallonta, gyaɗa mata kai kawai tayi ba tare da tayi magana ba ta ɗauki akwatin ta wuce ta barta nan tsaye tana mamakin shegen rawar kan tsiya irin na ƙanwar tata daga haɗuwa da mutum duk tabi ta damu dashi sai wani shisshige masa take tana neman zubar mata da mutunci. Ita kuwa Zahran ko a jikinta sai daya gama karanto mata numbern ta kwashe ta loda acikin wayar tayi saving ɗinta kana tayi masa godiya ta juya da gudu tabi bayan Auntyn tata wacce ta daɗe da shigewa ciki. Shima sai daya ga shigewarta cikin hotel ɗin kana yaja napep ɗinsa ya wuce yana mamakin kansa da ɓata lokacinsa da yayi akansu haka kawai ba tare da ya sansu ko ya taɓa ganinsu ba. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 1️⃣9️⃣ Fadwa kuwa lokacin data shiga gidan ta iske komai yana nan a yadda ta barsa babu abinda ya sauya alamar dai tunda ta fita ga dukkan alamu Ya Azeez bai dawo gidan ba kwata kwata, kasancewar tana da tabbacin in har da ya dawo gidan tun daga ƙofar gida zata fara gano hakan dan tana shigowa cikin unguwar zata hangi keke napep ɗinsa fake a ƙofar gidan nasu yana zaune a gefe yana dakon zaman jiran dawowarta tazo ta buɗe masa ƙofa, amma sai gashi yau da ta bar masa gidan a buɗe ta fita taje inda zata har ta gama duk abinda zata yi ta dawo amma shi bai dawo ba. Ɗaga kafaɗarta tayi alamar ko a jikinta hakan bai dameta, ta tura ƙofar ɗakin ta shige abin ta tayi wurgi da ƴar jakar dake hannunta kana ta cire kayan jikinta ta jawo zani ta ɗaura ta ɗebi ruwa a bokiti ta ɗauki sabulun wankanta da soso ta fice zuwa banɗaki, wanka tayi haɗe da alwala tazo tayi sallah, sai data rama duk sallolin da ake bin ta tsaf tukunna, kasancewar dama ko azahar bata samu tayi ba sakamakon aiki daya kacame musu suna ta hidima, sai a lokacin ta haɗa duka har da la'asar da magriba da isha'i tayi kana ta tashi taje ta buɗe ƙaramin akwatinta ta ɗauko ƙananun kayan shan iska kasancewar garin akwai ɗan zafi zafi ta saka kana ta ɗan fesa turare sama sama ta sha ruwa ta haye gado ta kwanta dan ta gaji sosai kuma bata jin yunwa saboda sai data ƙara cin abinci a gidan Hajiya Kalsoom tayi nak abin ta sannan tayo guzurin wani ta taho dashi gida. A ɓangaren Ya Azeez kuwa koda ya isa unguwarsu lokacin ƙarfe 12:30am dai-dai na dare, cikin layinsu babu kowa duk ƙafafuwa sun ɗauke ko'ina yayi tsit sai hasken solar kawai daya haske ko'ina yayi fayau, ganin hakan yasa bai nufi gida ba direct ya wuce kai tsaye gidan bulon da yake kai ajiyar napep ɗinsa ya kai ya ajiye kana ya kwashi kwalayen indomie da taliya da sauran kayan cefanen da ya siyowa Fadwa ya nufo gida. Lokacin daya isa gidan ya iske Fadwa ta daɗe da yin bacci, dan haka yana shiga shima ya ajiye kayan dake hannunsa ya fita yaje ya kullo ƙofar gidan yasa sakata sannan ya dawo ya tuɓe kayan jikinsa ya ɗebi ruwa a bokiti yaje yayo wanka ya ɗauro alwala kana ya dawo ɗakin ya zura jallabiya ya shimfiɗa darduma ya hau ya daidaita tsaiwarsa ya tada sallah, sai da yayi shafa'i da wuturi kana yayi adduoinsa ya shafa ya miƙe ya linke darduman ya ajiye sannan yayi shimfiɗarsa yau ma a nan falon yayi kwanciyarsa ba tare daya sake bi takan Fadwa dake uwar ɗaka tai ɗai ɗai abin ta, tana sharar baccinta hankali kwance ba tare da tasan ya ma dawo gidan ba. ******* Washegari da misalin ƙarfe 10am na safe Zahra ce zaune akan makeken gadon dake ɗakin da suka kama a cikin Hotel ɗin, shirye take tsaf ta yana ɗan madaidaicin ƙaramin gyale a kanta, tana riƙe da faskekiyar wayar Shatu a hannunta tana ta faman latsawa, yayinda ita kuma Shatun ke tsaye a gaban ƙaton madubin dake ɗakin ta gama shiryawa cikin wata tsadaddiyar doguwar riga ƴar Oman mai mugun kyau wacce taji stones tana ta sheƙi da walwali, tayi rolling ɗin gyalen rigar a kanta tayi kyau sosai ta fito kamar wata balarabiyar ƙasar Saudiya, dan rigar sosai ta karɓi jikinta ta fito da faffaɗan hips ɗinta masu kyau da ɗaukar hankali saboda rigar irin mai shape ɗin nan ce gashi ta ɗan kamata kaɗan sai tayi mata kyau ta ƙara fito da zallar kyaunta da yarintarta, sai data fesa turare a jikinta kana ta ɗauki ƴar jakar handbag ɗinta ta riƙe a hannunta ta jawo akwatinsu ta ƙaraso gaban Zahra dake nan zaune ta haɗe fuska tana ta faman latsa waya tana sakin tsaki, tsayawa tayi tana dubanta kafin ta zauna kusa da ita tana faɗin "Wai lafiya kike ta faman ɗaci kina wani ɓaɓɓata rai sai kace wacce akayiwa wani laifi..ko dai baki son komawa gidan ne yau sai in kira Abbie in gaya masa kinga ni sai in tafi kawai in barki a nan ɗin, tunda haka kika fi buƙata...?" Banza tayi da ita bata tanka mata ba, ta sake danna wata lamba ta kai wayar kan kunnenta, jim kaɗan ta sake sauke wayar daga kunnenta tana sakin tsaki kafin cikin ƙosawa tace "Ikon Allah to ko dai ba asalin numbernsa bace dama ya bani...? Ƙila ma numbern wani garjejen ƙaton ce ya karanto min ni kuma na kwashe, amma ai in da numbernsa ce da yanzu dana kira ya ɗauka ko....?" Cikin mamaki Shatu ke kallonta kafin tace "Wai numbern waye kike ta kira da yaƙi ɗauka ne haka duk kika damu...?" Ta faɗa tare da tsareta da ido tana kallonta. Ɗan taɓe baki Zahra tayi kafin tace "Numbern mai keke napep ɗin mu na jiya mana...." Ta faɗa kai tsaye tana wani ɗauke kai. Wani sabon mamakin ne ya ƙara kama Shatu tace "Ban gane mai keke napep ɗin mu na jiya ba...kina nufin kice wanda ya kawo mu nan kika karɓi numbensa...oh daman da gaske kike karɓar numbern tasa kikayi Zahra....?" Cikin ɓacin rai Tace "Eh mana dama ai nace miki zan karɓi numbernsa in kirasa yau yazo ya kaimu tasha mu shiga mota ko kin manta ne....?" Wani kallon banza Shatun ta watsa mata tana faɗin "Amma shine dan iskanci da wulaƙanci ki rasa wayar da zaki karɓi numbernsa a ciki sai tawa...to ke ina taki wayar take da baki ƙarba a ciki kin kirasa ba....?" Ta faɗa cike da jin haushin kiransa da tayi da wayarta tana harararta. Tura baki Zahra tayi ta ɗauke kai gefe kafin tace "Ai tawa tana can a kashe ne ta ɗauke shine na barota a mota...." A fusace ta miƙe tsaye ta fizge wayarta a hannunta tana faɗin "To bani tawa don ubanki sai kije ki nemo wacce zaki kira mai keke napep ɗin naki da ita..." Ta faɗa tana ƙoƙarin zura wayar a cikin jaka, da sauri Zahra ta miƙe ta riƙo hannunta tana marairaice fuska kamar zatayi kuka take faɗin "Please dan Allah Aunty Shatu ki bani in ƙara kiransa yazo ya kaimu tashan kinji...wallahi mutumin yana da kirki sosai kiga fa irin taimakon da yay mana jiya amma yaƙi karɓan ko sisin mu...?" Harara ta watsa mata tana faɗin "Amma ai kina gani dai bani na hanasa karɓan kuɗin ba ko...? Shine yaga dama kawai yaƙi ƙarba don kansa ba nice na roƙesa ba...." Ta faɗa tana komawa ta zauna a bakin gadon, da sauri itama Zahran ta zauna a kusa da ita tana faɗin "Dan darajar iyayenki nidai ki kawo in sake kiransa kinji Aunty Shatuna...?" Sake ɗaure fuska Shatu tayi kafin tace "Wai dan Allah ke wace irin yarinya ce mai shegen mita da rawar kan tsiya ne...Nace ni bazan bada wayata ba..bazan bada ba ko dole ne...?" Ta faɗa cikin ƙosawa tana watsa mata harara, zaro idanu waje Zahra tayi tana cewa "A'a ba dole bane Aunty Shatu riƙe wayarki Allah ya baki haƙuri..." Ta faɗa tana matsawa can ƙarshen gadon ta zuba tagumi, da mamaki Shatu ta juyo ta kalleta kafin ta girgiza kai lokaci ɗaya tana buɗe jakarta ta zaro wayar ta wurga mata tana faɗin "Gashi nan sai kije ki ta kiransa mai shegen naci da rawar kan tsiya...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana jan tsaki kafin ta miƙe ta koma kan sofar dake ɗakin ta zauna ta zubo mata ido tana kallonta. Cikin sauri Zahra ta ɗauki wayar ta lalubo numbern Ya Azeez ta sake danna masa kira a karo na shida. Dai-dai lokacin shi kuma Ya Azeez fitowarsa daga ɗaki kenan cikin shirin fita, yau ɗin shigar ƙananan kaya ce yayi dan kusan duk ƴan kayan sawan nasa sunyi datti kuma gashi bai samu zama ba ballantana ya haɗa har da na Fadwa da yaga itama natan sun taru ya wanke musu, yana daga tsaye a ƙofar ɗakin ya gama ɓalle boturan gaban rigarsa lokaci ɗaya yana ƙoƙarin zura takalmansa wayarsa dake cikin aljihun wandonsa ta ɗauki ƙara da sauri ya zarota yana duba mai kiran dan a tunaninsa ko Ummansa ce saboda kullum da sassafe idan ya tashi sai ya kirata sun gaisa yaji ya suka tashi kafin yake fita, amma yau saboda ya makara kuma gashi bai da kati ko na flashing a wayar shiyasa bai samu ya kiratan ba ya bari idan ya fita ya saka katin sai ya kirata. Cikin mamaki yake kallon fuskar wayar tasa ganin ba Ummansa bace ke kira still dai special numbern da ake ta kiransa da ita ce tun ɗazu ya sake gani tana yawo akan wayar dan haka ya danna ya ɗauka ya kai kunnensa cikin sanyin muryarsa yana faɗin "Assalamu alaikum dawa nake magana pls...?" Ya faɗa tare da ɗan saurarawa cikin son ya gano muryar mai kiran nasa. Daga can ɓangaren kuwa Zahra dake riƙe da wayar a hannunta ta danna handsfree da sauri ta ajiye wayar akan cinyarta tana faɗin "Waalaikums salamu..ina kwana an tashi lafiya...?" Jin yay shiru bai amsa ba, yasa ta juya ta kalli Shatu dake zaune har lokacin ta zubo mata ido ƙirr tana kallonta, cikin basarwa ta harareta a fakaice ta ɗauke kai tana cewa "Ka ganeni kuwa Malam...Zahra ce wacce motarsu ta lalace jiya da daddare ka taimaka musu ita da yayarta...?" Ta ƙarashe faɗa tana wani washe baki kamar tana ganinsa. Daga ɗaya ɓangaren Ya Azeez ya buɗe idanuwansa sosai yana sakin ƙaramin murmushi kafin yace "Oh Allah sarki na ganeki ƴan mata, ya gajiyan tafiya ya kuma kwanan Kaduna...?" Ya faɗa gefe guda na zuciyarsa yana mamakin kansa da biye ma shirmenta da yake so yayi. Ƴar dariya ta saki kafin tace "Ai dama nasan zaka ganeni da nayi magana saboda muryata bata taɓa ɓoyuwa..." Ta faɗa tare da juyawa ta saci kallon Shatu wacce ta kauda kai daga kallonta tana sakin tsakin takaici lokaci ɗaya tana ji kamar ta tashi taje ta rufeta da mugun duka dan baƙin ciki. Ɗan yatsina fuskarta tayi tana taɓe baki kafin tace "Ga Auntyna ma tana gaisheka...tace ayi maka ban gajiya...mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana hararar gefen Shatun, a zabure Shatu ta miƙe tsaye tana zaro manyan idanuwanta waje tare da dafe ƙirjinta, kafin cikin sanyin muryarta tace "A gidan ubanki nace kiyi masa ban gajiya Zahra don uwarki...?" Ta faɗa cikin ɓacin rai tana zafga mata harara, ko ajikinta bata damu ba ta ci gaba da faɗin "Yanzu ma ita tace in kiraka in gaya maka mun gama shiryawa kazo ka kaimu tasha dan Allah kar muyi dare a hanya..." Ta faɗa kai tsaye tana kallonta. Daga can ɓangaren Ya Azeez kuwa wani irin mugun sanyi yaji a zuciyarsa lokacin da Zahra take cewa Auntynta tace a gaishesa ayi masa ban gajiya, take yaji wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarsa lokaci ɗaya ya samu kansa da sake maƙala wayar sosai a kunnensa kafin ya buɗe baki cikin daddaɗar muryarsa mai sanyi da daɗin saurare yana faɗin "Ok gani nan zuwa Zahra ku jirani yanzun nan zan ƙaraso insha Allahu...." Ya faɗa daga haka ya yanke kiran yana kallon wayar kafin ya saki murmushi ya maida wayar cikin aljihun dake gaban rigarsa ya juya ya koma cikin ɗakin ya ajiyewa Fadwa dake ta sharar bacci ɗari biyar a kusa da ita, kana ya fito yasa kai ya fice daga gidan da sauri hannunsa riƙe da makullin keke napep ɗinsa. A ɓangaren su Zahra kuwa Shatu na jin ya yanke wayar tayo kan Zahra dake ƙoƙarin aje wayar akan gado a fusace ta fizgota da ƙarfi ta miƙar da ita tsaye lokaci ɗaya tana watsa mata wani mugun kallo da idanuwanta wanda suka fara tara ƙwallar ɓacin rai take faɗin "Tsakaninki da Allah Zahra yaushe kikaji nace kiyi masa ban gajiya har da godiya...yanzu saboda Allah mutuncina kikeson ki zubar min a idanun wannan mutumin..meyasa kikeson haɗani dashi ne...Ke meyasa rawar kanki tayi yawa...? Wai haka kawai daga haɗuwa da mutum duk kinbi kin addabi kanki da rayuwarki sai wani shisshige masa kike kina neman zubarwa da kanki mutunci sannan hakan bai yi miki ba shine dole sai kin haɗa har dani nima kin zubar min da nawa mutuncin...? To wallahi ba kiji da kyau ba, dan ni ba ƴar iska bace da zaki dinga neman haukatani..." Ta ƙarashe maganar cikin fushi lokaci ɗaya tana tureta ta faɗa saman gadon. Sakin baki kawai Zahra tayi daga kwancen tana kallonta kafin ta miƙe lokaci ɗaya tana gyara zaman gyalen dake kanta tana faɗin "Nidai ai ba wani abu nace akan ki ba gani nayi abun arziki yayi mana bana tsiya ba, kuma ni naga cancantar mu ƙara yi masa godiya ba shine zaiyi mana ba...amma tunda abun ya miki zafi to Allah ya baki haƙuri insha Allahu bazan sake ba...." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana matsar ƙwalla kamar gaske, dan tasan babu abinda Shatun ta tsana a rayuwarta irin ta ganta cikin damuwa balle har ta kaita ga zubar da hawaye, ballantana kuma idan itace ta ɓata mata rai yanzun nan zaka ga duk ta ruɗe ta hau lallashinta tana bata haƙuri. Saboda ita Allah ya yi ta da mugun son ƴar uwarta balle daya kasance Zahran ita kaɗai ce ƙanwarta dan su biyu ne kacal iyayensu suka haifa shiyasa gaba ɗaya ta ɗauki son duniya ta ɗaura mata. Gaba ɗaya Shatu sai taji gwiwarta tayi mata sanyi cikin muryar lallashi tace "To me kuma nayi miki kawai daga miki faɗa sai ki hau kuka...to naji kiyi shiru na haƙura bari ya ƙaraso sai ya kaimu tashan kinji....?" Ta faɗa tana zama a kusa da ita ta kamota tana share mata hawayen fuskarta tana ƙara lallashinta da bata baki, itako Zahra sai ƙara narkewa take ajikinta tana ƙananun kuka duk ta gama ruɗata sai faman lallashinta take kamar wacce tayi mata wani ƙaton laifi. ******* A ɓangaren Fadwa kuwa sai gurin ƙarfe 11am na safe sannan ta tashi daga bacci ta miƙe da sauri ta lalubo wayarta dake ajiye a gefen filo ta latsa, misscalls ta gani rututu daga ƙawayenta daban daban akan screen ɗin wayar da sauri ta miƙe bayan ta ajiye wayar ta sauka daga kan gadon ba tare data da tabi ko takan kuɗin da Ya Azeez ya ajiye mata a gefen gadon ba ta ja tsaki lokaci ɗaya tana sakin hamma alamar baccin bai isheta ba, ta hau cire kayan jikinta ta jawo zani ta ɗaura kana ta ɗebi ruwa a bokiti ta fice da sauri zuwa banɗaki. Agurguje tayo wanka ta fito sannan ta ɗebi ruwa a buta ta ɗauro alwala, sai da tayi sallah kana ta hau shiryawa cikin wata irin shadda gezner mai ruwan toka ɗinkin riga da siket, sai ɗaurin Zahra Buhari data cokashi ta tsikarosa gaban goshi, fuskarta ba wata kwalliya sai hoda kaɗan data ɗan shafa ta saka kwalli da janbaki, ko gyalen bata tsaya yafawa ba ta sagalashi a gefen kafaɗarta ta ɗauki jakarta da wayarta ba tare da tunanin komai ba tasa kai ta fice daga ɗakin. Yau ma bata tsaya kulle ɗakin ba ta jawo ƙofar kawai ta sakaya ta fice daga gidan tana taku ɗai ɗai kamar yadda ta saba, amma kallo ɗaya idan kayi mata zaka fahimci cewa bata da wata damuwa ko kaɗan a ranta. ******* ******* Koda ya isa hotel ɗin ya daɗe a harabar gurin amma ya kasa kiran layin da Zahran ta kirasa dashi, sai da yaga yana ɓatawa kansa lokaci ne kawai a banza, yasa yayi shahada ya zaro wayarsa ya danna numbern data kirasa da ita ɗazu, ba ɓata lokaci ta ɗaga haɗe da yin sallama, cikin sanyin muryarsa ya amsa mata kafin yace "Idan kun shirya ku fito ina jiran ku a waje...." Ya faɗa daga haka kawai ya yanke wayar. Cikin murna Zahra ta miƙe tsaye ta kama hannun Shatu dake zaune har lokacin a kusa da ita tana faɗin "Tashi muje Aunty Shatu kinji ya ƙaraso yana waje...." Ta faɗa tana jan akwatinsu ta kama hanyar ficewa daga ɗakin tana ci gaba da faɗin "Dan Allah ki taso muje kar mu tsaidashi yay ta zaman jiranmu kinga ba daɗi...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙarasa ficewa daga ɗakin. A sanyaye Shatun itama ta miƙe tabi bayanta suka fice tare, suna fita tun daga nesa ya zuba mata ido, ganin yadda take tafiya cikin natsuwa dole ya ɗauki hankalinka, sosai ya shagala da kallonta har suka ƙaraso bakin napep ɗin bai sani ba, sai da suka shiga suka zauna sannan Zahra ta ɗan zuro da kanta ta gefensa ta kallesa da kyau kafin tace "Allah yasa dai ba tunanin budurwarka kake yi ba har muka ƙaraso baka sani ba...." Ta faɗa tana kallon gefen fuskarsa inda lallausan baƙin gashi ya kwanta yay luf luf gwanin sha'awa, ajiyar zuciya ya sauke cike da kunya kafin ya waigo ya ɗan saci kallon Shatu data duƙar da kanta tana latsa wayarta dake hannunta yace "Barkanku da ƙarasowa to Hajiya Zahra...." Ya faɗa yana kallon Shatu da har lokacin kanta ke duƙe taƙi ɗagowa ta kallesa. Ƴar dariya Zahra tayi kafin tace "Yauwa Ya....uhmm Ya wama zance....?" Ta faɗa cike da tsokana tana kallon Shatu, banza da ita tayi bata tanka mata ba sai ma ci gaba da tayi da latsa wayarta tana harararta ta gefen ido. Cikin wani irin yanayi ya kalleta kafin yace "Cikakken sunana AbdulAzeez Naseer Abdallah Arabi...amma matata da ƙanwata Imaan suna kirana da Ya Azeez....Ummana kuma tana kirana da Yayan Imaan...kinga kema sai ki zaɓi suna ɗaya da zaki dinga kirana dashi a ciki...." Ya faɗa a hankali yana ƙoƙarin tada napep ɗin, da sauri Zahra ta kallesa kafin ta juya ta kalli Shatu data wani haɗe rai tace "Kai amma gaskiya sunanka yayi daɗi sosai, amma ni daga yau Ya Abdul zanna dinga kiranka dashi...ko Aunty Shatu ai yafi daɗi....?" A hankali ta ɗago ta saci kallonsa, karaf kuwa ƙwayar idanuwansu suka haɗu waje guda, rass gabanta ya buga ta juya da sauri cikin rashin abun yi ta hau gyara wuyan rigar abayar dake jikinta, kafin ta ɗago lokacin har sun fara tafiya ya fice daga cikin hotel ɗin ya ɗauki hanyar tashar Kawo, ta ɗan kamo gefen rigar Zahra ta jawota, da sauri Zahran ta kalleta ta ɗaga mata gira kafin ta saki wani ƙaramin murmushi tana harararta tace "Taɓ amma Aunty Shatu gas..." Da sauri ta katseta ta hanyar toshe mata baki tana zaro manyan fararen idanuwanta waje kamar zasu faɗo ƙasa. Hakan yasa Zahran taja bakinta ta tsuke tayi tsit har suka ƙaraso babbar tashar Kawon bata sake magana ba, shi kuwa duk abinda sukeyi yana kallonsu ta madubin napep ɗin daya saita yana ta murmusawa abinsa amma bai tanka musu ba, haka har suka ƙarasa cikin tashar. Shatar sharon suka ɗauka tun daga nan har Kano daga ita sai ƙanwarta su biyu kaɗai ta biyasu kuɗin, yana nan sai da yaga tashinsu kana ya juya ya shiga keke napep ɗinsa shima yaja ya fice daga tashar. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣0️⃣ *KANO STATE* Ƙarfe 2pm. Dai-dai suka shigo garin Kanon dabo, inda direct mai motar ya nufi tsararriyar unguwar ta Nasarawa GRA dasu, kamar Zahra dake zaune a bayan motar kusa da Shatu tai ta kwatanta masa. Bakin wani tafkeken haɗaɗɗen gida na gani na faɗa, mai ɗauke da tangamemen gate na kece raini suka yada zango. Inda direban yana yin parking suka buɗe ƙofofin motar suka fito, bayan sun sallami direban Zahra ta buɗe boot ɗin motar ta ɗauko akwatinsu, kana shi kuma direban yaja motar ya wuce. A hankali su kuma suka ƙarasa bakin gate ɗin gidan suna isa Zahra ta ƙwanƙwasa ba jimawa sai ga wani farin dattijo ɗan kyakkyawa dashi wanda da gani kasan maigadi ne yazo ya buɗe musu ƙaramar ƙofar yana ganinsu ya washe baki cike da farin ciki yana yi musu maraba, cikin fara'a duk suka amsa masa kana suka shige ciki. Wani lafiyayyen ginin gida ne na kece raini kamar a turai, harabar gidan shaƙe take da haɗaɗɗun motoci kala daban daban wasu duk suna rufe an lulluɓesu da tampol yayinda wasu kuma suke a buɗe sai ɗaukar ido suke suna sheƙin sabunta, ga wasu manyan manyan bishiyoyin ya'yan itatuwa dogaye masu kyau da tsari sun kewaye gidan, ga wasu fulawowi suma kala daban daban da aka ƙayata jikin ginin gidan dasu sai ɗaukar ido suke sunyi shar gwanin sha'awa. Suna gab da shiga ɗan koridon da zai sadasu da babban falon gidan ne, Shatu taja ta tsaya tana kallon Zahra data wuce da sauri zata shige ta tari gabanta tana watsa mata harara tace "Naga kina ta wani rawar jiki kin ƙosa ki shiga kije ki kai rahoto ko...? To saura idan mun shiga ki cewa Ummi ni na matsa nace mu tafi Abuja jiya, dan nasan halinki wannan shegen bakin naki kamar na Parrot yake wallahi idan ki ka ƙulla min sharri sai kin san sauran..." Ta faɗa tana fizge wayarta dake hannun Zahran lokaci ɗaya tana ƙara haɗe fuskarta. Kallonta Zahra tayi sama da ƙasa tana faɗin "Haba mana Aunty Shatu wai dan Allah me kika maidani ne...? Nifa babu abinda zan gayawa Ummi kuma mu shiga kiji idan zan gaya mata wata magana Allah kuwa...." Ta faɗa tare da kamo hannunta tana cewa "Muje Aunty Shatuna wallahi bazan ce komai ba, tsit zanyi da bakina..." Ɗago kai Shatun tayi ta galla mata harara tana cewa "Ai nasan halinki ne indai kece tsaf zaki zame jikinki ki ɗora min laifin duka ki barni a ciki..." Ɗan murmushi Zahra tayi ta kalleta kafin tace "Babu abinda zance na rantse kuma muje kiji..." Wucewa tayi ba tare data sake magana ba ta nufi ƙofar da zata sadata da makeken falon gidan Zahran na biye da ita a baya. Makeken ƙaton falo ne haɗaɗɗe na gani a bada labari wanda aka tsarashi iya tsaruwa fiye da tunanin mai tunani, ga wasu manya manyan luntsuma luntsuman kujeru masu girma da taushi na alfarma da aka kewaye falon dasu, sai wani tattausan kafet mai tsananin laushi da nutse ƙafafu da aka malale falon dashi tun daga bakin ƙofar shigowa har zuwa cikin tsakiyar falon ya mamaye ko'ina. Gefe guda kuma ga wani sassanyan ƙamshin turaren wuta mai bala'in daɗi daya gauraya da sanyin Acn dake tashi a falon yana yi maka maraba, sai ya haɗu ya bada wani daddaɗan ƙamshi mai sanyaya rai da tsayawa a zuciya. Cikin natsuwa dukkansu suka shigo falon bakinsu ɗauke da sallama, Babu kowa a falon sai wani tangamemen talabijin da yake maƙale a jikin bango yana ta aiki shi kaɗai yana faman ɓaɓatu, a gajiye Shatu ta ƙaraso kan ɗaya daga cikin kujerun da suka yiwa katafaren falon nasu ƙawanya ta zauna tana faɗin "Wash Allahna..wallahi duk gaɓoɓina ciwo suke, jikina kamar an min dukan tsiya haka nake ji, Zahra pls jeki dauƙo min ruwa mai sanyi a fridge in ɗan sha, sai mu haura sama gurin Ummi..." Amsawa tayi da "Toh..." Kana ta wuce taje ta ɗauko mata ruwamai sanyi haɗe da kofi ta kawo mata, kaɗan ta tsiyaya ta sha ta ajiye sauran kana ta miƙe ta zari jakarta tayi gaba Zahra ta biyota suka haura sama har zuwa falon Umminsu dake can. Wani tafkeken haɗaɗɗen falo ne nan ma wanda har yaso yafi na farkon da suka baro kyau da tsaruwa, suna shiga wata hamshaƙiyar mace kyakkyawa ajin ƙarshe a cikin manyan mata ta fito daga wani ɗaki da faskekiyar waya riƙe a hannunta tana latsawa, jikinta sanye cikin wani tsadadden leshinta wanda aka yiwa ɗinkin Abuja bubu taci ɗaurin ɗankwalinta wanda ya ƙara fito da tsantsar hutu da haibarta ga wasu uban gwala gwalai datayi ado dasu a jikinta sai walwali take da ɗaukar ido tana sheƙi, sai dai a kallo ɗaya idan kayi mata zaka hango tsantsar kamaninta da Shatu kamar an tsaga kara babu inda ta barta, dan hatta da yanayin tsarin dirin jikin Shatun da yanayin tafiyarta sak irin na mahifiyar tata ne sai ɗan banbancin abinda ba'a rasa ba, tsaye kawai sukai a tsakiyar falon gaba ɗayansu suka zubo mata idanu, a hankali ta fara saukowa cikin falon lokaci ɗaya tana washe baki cike da fara'a take faɗin "Oyooyo My lovely daughters Oyooyo barkanku da zuwa you are welcome...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙarasa saukowa daga saman benen cikin natsuwa ta ƙaraso gabansu lokaci ɗaya ta jawosu jikinta ta rungume tana shafa bayansu cike da murnar ganinsu tana faɗin "Alhamdulillahi tafiya tayi riba ƴan mata Ummi sun dawo gida cikin ƙoshin lafiya barkanku da dawowa...." Murmushi Zahra ta saki kafin tace "Thanks my Ummina...." Ta faɗa itama tana ƙara rungumeta, kafin ta ɗan janye jikinta a nata lokaci ɗaya tana duban Shatu data wani kwaɓe fuska cike da shagwaɓa ta matsa daga kusa dasu tayi can gefe tana turo baki tace "Ummi kishin mutuniyar taki fa ya motsa...ji yadda aka wani ja gefe ana turo mana baki kamar zai taɓo bango, da alamar dai nan fushi akayi mana bamu sani ba..." Ta ƙarashe maganar cike da tsokana lokaci ɗaya tana nuna Shatun da bakinta tana ƴar dariya. A hankali Shatun ta ɗago kai ta watsa mata harara kana ta ƙarasa gaban mahaifiyar tasu ta rusuna a gabanta ta kamo hannayenta tana ɗan murzawa a hankali a hankali kana cikin murya ƙasa ƙasa tace "Ummi kina can kina ta autarki ni kam kinyi banza dani a gefe kuma nayi missing ɗinku keda Abbie na..amma na dawo kuma baki kulani ba sai ta autarki kawai kike..." Ta faɗa a shagwaɓe tana hararar Zahra da tunda ta fara maganar ta riƙe baki kawai tana kallonta a ranta kuwa faɗi take "Kai Allah ya yayewa Aunty Shatu wannan mugun kishin nata...ita kenan komai sai tayi complain ɗinsa abinda bai kai ya kawo ba sai ta nuna tana kishi akansa, anya kuwa zata iya auren mai mata ta zauna dashi...?" Ta faɗa a ƙasan ranta kafin kuma ta fashe da dariya a fili tana cewa "Tabɗi aiko akwai aiki ja agabanki...Ummi kiji mai hali..lallai gaskiyar hausawa ne da suke cewa mai hali baya taɓa fasa halinsa kiga daga dawowa dai har ta fara kawo ƙorafi, wallahi har kinsa na fara tausayawa mijin da zai aureki indai yana da mata dan babu halin ya raɓi matarsa kenan sai kin nuna halinki, wannan ai bazaki bar gidansa ya zauna lafiya ba dan ba zai taɓa yin adalci a tsakaninku ba..." Shatu da tunda ta fara maganar take kallonta a fusace ta miƙe tayo kanta gadan gadan tana faɗin "Ummi kiji mugun bakin da yarinyar nan take min agabanki wai zan auri mai mata...wai nice zan zauna da kishiya...Ummi dan Allah kiji min wani mugun fata fa da take min..." Ta ƙarashe maganar a shagwaɓe tana zumɓuro ɗan ƙaramin bakinta lokaci ɗaya tana ƙoƙarin fizgo Zahra data maƙalƙale a bayan Ummin ta ruƙunƙumeta suna mata dariya. Cikin ƙulewa Shatu tace "Ummi kema harda tayata kuna min dariya ko..kenan kema fatan in auri mai matan kike min....?" Ta faɗa cikin rawar murya kamar zatayi kuka, sake kwashewa sukayi da dariya ta ƙara ƙulewa a fusace ta juya zata wuce da sauri Ummi ta riƙo hannunta tana ƙoƙarin danne dariyarta take faɗin "Haba mana ƴan matan Ummin ta meye na fushin kuma...ni yaushe kikaji nace zaki auri mai mata har ki zauna da kishiya...?" Ta faɗa tare da jawota jikinta ta rungumeta tana shafa bayanta alamar lallashi tana cewa "Ƙyale autar Ummi kinji, ki kwantar da hankalinki insha Allahu da ke kaɗai mijinki zai zauna ba zai taɓa haɗaki da kowacce mace ba, amma banaso kikesa hakan aranki har abun yazo yayi tasiri a zuciyarki...nafi son ki barwa Allah yinsa kawai komai yayi akanki shine dai-dai kinji ƴan matana..ki daina nuna zaɓinki akoda yaushe kice ke dole dole sai lallai abinda kikeso kuma kike buri shi Allah zai baki, ki sani shi fa Allah ba'ayi masa dole, ki bar masa komai shi kaɗai yasan irin tanadin alkhairin da yayi ma rayuwarki kinji...?" Ta ƙarashe maganar cikin lallashi da lalama lokaci ɗaya tana share mata hawayen da suka fara zubowa kan fuskarta, a hankali ta gyaɗa mata kai cikin sanyi jiki kana tace "Insha Allahu Ummi na daina bazan sake ba...." Da sauri Zahra ta kaɗa kai tace "Yauwa gara dai ki daina ɗin ko Ummi tunda babu kyau kuma bakisan wanene mijinki ba....? Ƙila ma mai mata uku ne kece zakije a ta huɗu...." Wata dariya ce ta kubcewa Ummi lokaci ɗaya tana riƙe hannun Shatu data kawowa Zahra duka a gefen kafaɗarta ta janyeta da sauri tare da turata baya tana cewa "Ki gudu nidai babu ruwana idan ta kamaki tunda ban ce ki tsokaneta ba...." Ta faɗa tare da kamo hannun Zahran ta nuna mata saman bene alamar ta gudu kar Shatu ta kamata, aiko da sauri Zahra ta tattare siket ɗin jikinta taja shi sama kana ta juya a guje ta fara haurawa matattakalar benen da gudu ta haye tare da yiwa Shatu dake bin ta da kallo gwalo tana faɗin "Kina taɓani wallahi saina gayawa Abbie ince kin samu miji a Kaduna kuma...." Maganarta ce ta katse lokacin da taga Shatun tayo kanta cikin fushi tana faɗin "Bari in taɓakin sai kiji daɗin faɗa masa ɗin dan ubanki...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana haurawa saman da sauri itama, ko kafin ta ƙarasa gareta tuni Zahra ta buɗe wani ɗakin dake kusa da ita ta faɗa ciki da sauri ta mayar da ƙofar ta rufe tana sauke numfashi. Ƙwaffa Shatu tayi, kafin cikin ƙufula ta sauko daga saman benen tana kumbura fuska ita a dole an ɓata mata rai. Ummi dake tsaye har lokacin tana kallon diramar tasu ta kamo hannunta tana dariya take faɗin "Haba mana ƴan matan Umminta inda sabo ai yaci ace zuwa yanzu kin gama sabawa da halin tsokanar Zahra, amma ke kullum sai ki dinga biye mata ku dinga abu sai kace wasu ƴan ƙanana yara...? Idan fa kikaci gaba da biyewa halin Zahra wata rana koda kinyi aure idan ta kai miki ziyara gidanki haka zata dinga miki, dan sai tasan yadda tayi ta tsokaneki kika biye mata kuka raba hali har a gaban mijinki ita babu ruwanta, dan haka ki daina kinji ƴan matana....?" Shatu ta kaɗa kai ba tare da tace mata komai ba, hakan yasa Ummi ta ƙara kamota tana faɗin "Haba to ki ɗan saki fuskar taki mana tunda ya wuce ai bazata ƙara ba, yanzu kije ki watsa ruwa a jikinki kiyi sallah sannan saiki sauko kizo kuci abinci, dan nasan ma da wuya idan kun karya kuka kamo hanya..." Da To Shatu ta amsa mata still tana kumbura baki, kana ta wuce ta haura sama zuwa ɗakinsu, yayinda ita kuma Ummin ta juya ta shige kichin ɗinsu dake cikin falon domin ta haɗo musu abincin kafin su gama shiryawa su sauko. ******* Misalin ƙarfe 4pm. Ya Azeez ne zaune a cikin keke napep ɗinsa dake fake a gaban wani masallaci, wanda fitowarsa daga cikin masallacin kenan inda ya gabatar da sallar la'asar ya daɗe a zaune shiru gabaki ɗaya ya rasa meke yi masa daɗi kasancewar tun ɗazu da ya baro tasha inda ya kai su Shatu suka shiga motar Kano, ya dawo gabaki ɗaya ya kasa natsuwa zuciyarsa kwata kwata ta hanasa sukuni sai faman hasaso masa wasu manyan abubuwa masu matuƙar jan hankali take a game da ita, a hankali ya sauke ajiyar zuciya cikin son kawar da tunaninta a zuciyarsa ya zaro makulli a cikin aljihunsa ya tada napep ɗin yana ƙoƙarin ja kenan wayarsa dake cikin aljihun gaban rigarsa ta ɗauki ƙara, zaro ta yayi daga cikin aljihun yana duba mai kiran numbern Fadwa ce ya gani wacce yayi saving ɗinta da MY FADWA. Shiru yayi yana bin wayar da kallo dan haka kawai da yaga kiran nata ya tsinci kansa da samun mummunar faɗuwar gaba, da kamar ba zai ɗauka ba amma sai yayi wani tunani ya saki murmushin takaici kana ya ɗaga kiran ya kara wayar a kunnensa yayi shiru ba tare da yayi magana ba. Daga can ɓangaren Fadwa kuwa tana gefe cikin babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport dake Abuja, wanda saukarsu kenan ita da gogaggun ƙawayenta da wasu manyan mata masu faɗa aji tana tsaye a jikin wata doguwar mota baƙa wuluk ƙirar Lemoxin sabuwa dal mai kyau sai ɗaukar ido take irinna sabunta, sanye take da doguwar riga na wani arnen leshi mai kyau da tsada kalar baƙi sai head ɗin kanta kuma golding color fuskar nan taci uban make-up sai kace wata amarya. Jin ya ɗaga wayar amma yayi shiru yaƙi magana, yasa ta ƙufula cikin ƙosawa tace "Ka ɗaga wayar amma shine kayi shiru saboda ga mai kuɗin banza ta kiraka ko...?" Ta faɗa tana hararar wayar kamar tana kallonsa, shiru yayi yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa kafin yace "Ai kece kika kirani bani na kiraki ba, saboda haka kece ya kamata ki fara faɗin abinda ke ranki tunda bansan dalilin kiran naki ba...." Haɗe rai tayi tai kicin kicin da fuska tace "Nidai bana kiraka dan inji ƙorafinka bane dama na kiraka ne kawai dan in sanar da kai cewa mun tafi Abuja kai amarya dan haka koda ka koma gida karkace zaka tsaya jiran dawowata inzo in buɗe maka ƙofa na bar maka ita a buɗe kawai kana zuwa ka shige abinka ka kulle karka tsaya jirana, dan ban san ranar dawowata ba domin anan ɗin ma wani sabon bikin yau za'a fara kuma sai nan da kwana uku za'a gama sannan idan muka kai amarya gidanta Asokoro washegari sai mu kamo hanya mu dawo gida, saboda haka sai nan da kwana huɗu ko biyar zan dawo..." Cikin baƙin ciki da ɓacin rai yace "Kin kuwa san abinda kike faɗi Fadwa...Abuja fa kike gaya min kin tafi kai amarya ba tare da sanina ba...?" Ƙaramar dariya ta saki kafin tace "Oh daman kai duk a naka haukan ɗauka kake dole sai da saninka sannan zan fita inje duk inda zanje...tabɗi ashe bani da ƴancin fita inda naso naga dama kenan sai da yardarka...?" Bata bashi damar magana ba ta cigaba da faɗin "To idan ɗaukar hakan kake kayi maza ka sauke dan ni ba irin matan nan bane marasa sanin ciwon kansu waɗanda suke zaman rashin ƴanci a gidajensu ba..nidai Allah ya sani na fita hakkinka tunda na gaya maka nayi tafiya kuma na gaya maka inda naje dan haka sai na dawo...." Daga haka ta yanke kiran tana sakin wani ƙaton tsaki tace "Matsiyaci kawai faƙirin banza...." Ta faɗa tana jefa wayarta cikin jaka bayan ta kasheta gaba ɗaya dan ma kar yayi tunanin sake kiranta ya dameta. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣1️⃣ Wani ƙatoton abu ne mai tsananin baƙin ciki da ɓacin rai Ya Azeez yaji yana taso masa tun daga ƙasan zuciyarsa ya tsaya masa cak a maƙogoro ya kasa wucewa, wayar yabi da kallo cikin sanyin jiki da mamaki kafin ya soma jujjuyata a hannunsa yana sakin ajiyar zuciya. Tabbas sai yau ne ya sake tabbatar da cewa Fadwa ta gama rainasa, ta maidashi banza wofi mara amfani wanda bai san ciwon kansa da abinda yake damunsa ba. Amma tabbas kam a wannan karon an kawo dai-dai inda ba zai iya haƙuri ba dole sai ya ɗauki mataki akanta, saboda ya gaji da waɗannan mugayen halayen nata domin Allah ma ya sani kuma ya gani yayi iya bakin ƙoƙarinsa a kanta dan ta gyaru amma bata gyarun ba, dan haka anzo dai-dai gaɓar da dole zai san abun yi domin ba zai taɓa yarda haka kawai ya zuba mata ido ta maidashi wani lusarin namiji mara iko da isa da gidansa ba. Kunna napep ɗin yayi ya tada kana yaja ya soma tafiya a hankali a hankali cikin sanyin jiki yana ƙara nanata maganganun da Fadwan ta gaya masa a zuciyarsa yana ƙoƙarin bawa kansa haƙuri. A haka da wannan tunanin ya ƙarasa gidan Ummansa, koda yaje sai bai nuna mata komai ba ya saki jikinsa ya zauna sukai ta hira da ita kamar babu abinda ke damunsa. Nan ko zuciyarsa danƙare take taf da baƙin cikin abinda Fadwa tayi masa, nan yai ta zaune har bayan sallar Isha'i suna tare da Ummansa da ƙanwarsa Imaan suna ta hira abun su gwanin sha'awa, Umma ta gama girkin dare ta zubo masa yaci ya ƙoshi kana ya tashi yayi musu sallama ya fita ya ɗauki keke napep ɗinsa ya wuce ya nufi gida. ******* *KANO* Lafiyayyen ɗaki ne mai bala'in kyau wanda za'a iya kiransa da aljannar duniya, an ƙayatashi da duk wasu abubuwa na ƙayata ɗaki dan more rayuwar duniya da jin daɗin ya'yan gata, ga wata luntsumemiyar doguwar kujerar sofa mai shegen laushi da taushi dake tsakiyar ɗakin, sai ga kuma wani ƙaton Royal bed dake ɗauke da shimfiɗa na wani lallausan zanin gado na alfarma mai kamar bargo ɗaya ƙarawa ɗakin haske da kyau, ga kuma wani sanyin Ac mai haɗe da ƙamshin daddaɗan turaren wuta dake tashi kaɗan kaɗan a cikin ɗakin. Shatu ce tsaye a gaban tangamemen madubin dake ɗakin, wanda da alama fitowarta daga wanka kenan tana ɗaure da wani ɗan madaidaicin ƙaramin tawul kalar pink a jikinta wanda yake ɗan ɓingil dashi dan ko gama rufe cinyoyinta bai yi ba, sai wani ƙarami dake riƙe a hannunta tana goge ruwan fuskarta dashi, a hankali take ƙarewa kanta kallo ta cikin tangamemen madubin dake jingine da bangon ɗakin wanda ke shaƙe da tsadaddun kayan kwalliyarta da kalolin turarukanta masu tsananin tsada sai wasu manya manyan kwalaben turarukan humra dake jere a gefe cikin wani ɗan madaidaicin show gilas, a hankali ta janyo kujerar gaban madubin ta zauna lokaci ɗaya tana ɗan zame tawul ɗin dake jikinta ta ɗan jashi sama kaɗan wanda hakan ya bawa santala santalan fararen cinyoyinta dake sheƙi da ɗaukar ido damar bayyana. A hankali ta miƙa hannu gaban madubin ta ɗauko robar tsadadden lotion ɗinta Makari ta buɗe ta tsiyaya a tafin hannunta ta murza kafin a nutse ta soma shafawa lallausar fatar jikinta cikin wani irin salɓi da yanga, ta ɗauki kusan mituna ashirin tana shafa man a jikinta kafin ta gama ta mayar ta ajiye kana ta ɗauko turaren body spray ɗinta na Smart Black ta fashe ilahirin jikinta dashi, kana ta ɗauki turarukan arabian oud ɗinta kala daban daban ta goga a kowanne lungu da saƙo na jikinta. Cikin lokaci ƙalilan kuwa ɗakin ya ƙara ɗaukar wani sassanyan ƙamshi mai tsananin daɗi da sanyaya rai. Bayan ta gama fesa turaren ne, ta ɗauki lipgloss ta ɗan goga a lallausan pink lips ɗinta wanda suke nan sirara dasu masu ɗan faɗi kaɗan, sai suka ƙara fitar da tsantsar kyaun fuskarta sosai. Miƙewa tayi daga kan kujerar ta wuce ta ƙarasa gaban wani kafcecen wardrobe ɗinta daya kusan mamaye rabin bangon ɗakin ta buɗe, kaya ne kala kala jere reras a ciki, kama daga kan less, atamfa, materials, shadda, english wears da dogayen riguna haɗaɗɗu irin na larabawa da na turawa suma kaloli daban daban kowanne da ɓangarensa, a hankali ta shiga duba ɓangaren inda dogayen rigunanta suke, tsayawa tayi shiru tana ƙarewa jerin kayan dake cikin wardrobe ɗin kallo kafin ta miƙa hannu ta zaro wata tsaleliyar doguwar rigarta mai kyau ƙirar Armani kalar ja ta saka, kana ta naɗe kanta da ɗan ƙaramin mayafin rigar, ta sake feshe jikinta da turare kana ta ɗauki wayarta dake aje kan bedside drower ta zura bedroom silifas ɗinta ta fice daga ɗakin lokaci ɗaya tana duba agogon dake jikin wayarta, ƙarfe 7pm dai-dai ta gani da sauri ta ƙarasa sauka daga matattakalar benen ta nufi cikin falon inda take jiyo muryar Zahra, wacce gaba ɗaya surutanta ya cika falon sai karaɗi take tana zuba labari kamar an kunna tsohuwar radio. Ƙarasawa tayi cikin falon bakinta ɗauke da sallama, wani farin dattijo ne kyakkyawa wanda a ƙalla shekarunsa zasu iya kaiwa 62 zaune saman ɗaya daga cikin manyan luntsuma luntsuman kujerun da suka yiwa katafaren falon nasu ƙawanya, jikinsa sanye cikin shigar tsadaddiyar shaddar gizner fara ƙal wacce aka zubawa uban aiki irin na manyan ƴan kasuwar dake garin Kano, wanda ya ƙara fito da haiba da kwarjininsa na musamman daya cika falon. Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai kenan kamilin mutum mai cikar zati da kamala mai fara'a da son mutane, ga dattako da son taimakon na ƙasa dashi. Sallamarta ce tasa Zahra yin tsit kamar anyi ruwa an ɗauke ta fara zare ido, ita ko Shatu ko kallon ɓarayin da take ma ba tayi ba ta tsallaketa ta isa gabansa cikin murna da ɗokin ganinsa ta duƙa kusa dashi tana faɗin "Abbie ashe ka dawo tun ɗazu shine ba'a gaya min ba...?" Ta faɗa a shagwaɓe tana marairaice fuskarta. Ɗago kansa yayi ya kalleta fuskarsa ɗauke da wani kyakkyawan murmushi wanda ya sake fito da zallar dattako da hutunsa, a hankali ya miƙa mata hannunsa cikin nuna ƙauna irinta ɗa da mahaifi ya riƙo nata, bayan ya amsa mata sallamar tata cikin nuna tsantsar kulawarsa da jin daɗin ganinta da yayi yace "Zo nan kusa dani uwata maganin kukana..." Ya faɗa tare da ɗagota ya zaunar da ita a kusa dashi, duƙar da kanta ƙasa tayi tana ɗan murmushi take faɗin "Na gode Abbie na..." Ta faɗa tare da ɗagowa ta watsawa Zahra harara. Saurin ɗauke kanta tayi gefe tana zumɓuro baki kafin tace "Yauwa Aunty Shatu dama fa ke nake ta jira ki fito, ki ɗan bani aron wayarki in kira Ya Abdul in sanar masa mun sauka gida lafiya...dan kar yaji mu shiru ya ɗauka ko wani abun ne ya faru damu...ko ba haka ba Ummi...?" Ta ƙarashe maganar da sigar tambaya tana kallon Ummi dake ƙoƙarin shirya abinci akan dinning, juyowa Ummin tayi ta kalli Shatu data wani haɗe rai tana hararar Zahra tace "Gaskiya kam kinyi tunani mai kyau auta ya kamata ku kirasa ku sanar dashi kun sauka lafiya, saboda yaron yayi muku abun alkhairi bai kamata ku manta dashi da wuri haka ba..." Abbie wanda yaji zancen nasu daga sama sam bai gane inda suka dosa ba, juyowa yayi ya dubi Ummi cikin rashin fahimta yace "Wai waye ake cewa za'a kira ɗin ne..me kuma yayi musu...?" Dama kamar jira Zahra take tayi tsagal tace "Wani bawan Allah ne mai kirki a Kaduna yake Abbie. Jiya shi ya dinga ɗawainiya damu ya k..." Katseta Shatu tayi a fusace da faɗin "Dalla rufewa mutane baki mai shegen surutun tsiya kawai, faɗi ba'a tambayeki ba kin saki baki kina wani zaro zance sai kace wata mai bada lectures...." Ta faɗa cike da jin haushin Zahran tana harararta. Baki kawai Abbie da Ummi suka saki suna kallon ikon Allah, kafin Abbie yace "To ke uwata gaya min abinda ya faru tunda kin hana auta ta faɗa min...." Ɗif Shatu tayi ta ɗukar da kanta ƙasa ta kasa cewa komai, ganin yadda ta yin ne kuma yasa Abbie ya juya yana kallon Zahra da tai zaune tsumu tsumu yana faɗin "To ke gaya min auta wanene Ya Abdul ɗin kuma tunda ita uwata ta kasa min bayani...." Juyowa Shatu tayi da sauri tana faɗin "Allah zan gaya maka Abbie, jira nake dama sai mun gama ci abinci tukunna...." Ta faɗa fuskarta a haɗe babu alamar fara'a, dariya Abbie yayi irin tasu ta manya kana yace "To wai me yake faruwa ne nifa ban gane ba...ko dai suruki aka samo min ne a Kadunan uwata shine ake jin kunyata ba'a so in sani, domin na lura bakin nan na auta akwai daddaɗan labari da akeson fesa min....?" Ya faɗa tare da kallon Shatu data miƙe da sauri ta nufi hanyar dinning area inda Ummi ta gama jera musu abinci saman makeken tebur ɗin dake gurin taja kujera ta zauna lokaci ɗaya tana turo baki tace "Abbie nidai dan Allah ku taso muci abinci wallahi yunwa nake ji sosai..." Ta faɗa a shagwaɓe tana ƙoƙarin buɗe kular farfesun dake gabanta. Tasowa sukayi dukkansu suka nufo dinning area ɗin kowannen su yaja kujera ya zauna kana Shatu ta miƙe ta fara zuzzubawa kowa nasa, tuwon shinkafa ne miyar taushe wacce taji naman rago da kayan miya sai tashin ƙamshi take, gefe guda kuma ga farfesun kayan cikin rago da sassanyan kunun aya wanda yaji madara da kayan ƙamshi, turawa kowannen su abincin tayi gabansa, kana itama ta zuba nata taja kujera ta zauna a kusa da Ummi bayan sunyi bismillah kowa ya fara cin na gabansa. Koda suka kammala cin abincin Zahra ce ta fara miƙewa ta tattare kayan da suka ɓata ɗin ta kai kichin, kana Abbie, Ummi da Shatu suma duk suka tashi suka koma cikin falo suka zauna, ita kuwa Zahra koda ta kai kayan kichin bata barsu haka ba sai data tsaya ta wanke su tsaf ta maida kowanne ma'ajiyarsa kana ta dawo tazo ta goge kan dinning table ɗin sannan ta koma falon inda ta iske Abbie da Ummi suna ta hira yayinda Shatu kuma ke zaune a gefe guda riƙe da wayarta tana chatting. Zama tayi a kusa da Ummi tana faɗin "Barkanku da hutawa Ummina da Abbiena..." Ta faɗa tare da jingina kanta a kafaɗar Ummin, ɗan shafa kanta Ummin tayi kana tace "Yauwa autar Ummi sannu da ƙoƙari Allah yayi muku albarka...." Da Ameen suka amsa dukkansu kana Abbie ya dubi Zahra dake faman satar kallon Shatu ta gefen ido yana faɗin "Auta kefa nake ta saurare dan na lura bakin nan naki akwai kyakkyawan labari mai daɗi da akeson a labarta min, shiyasa duk na ƙosa nima inji ko mene ne..." Kamar dama kuwa jira Zahra take ta shiga zayyane masa komai daya faru a Kaduna da irin taimakon da Ya Azeez yayi musu har zuwa kawo su tasha da yayi suka hau mota babu abinda bata zayyane ba sai wanda ta manta. Shatu kuwa tunda ta fara zayyane labarin ta tsaya tsam ta bar abinda take yi ta zuba mata ido kawai tana aikin kallonta, gaba ɗaya lamarin Zahra yanzu bala'in takaici yake bata, ita a nata ganin bata ga dalilin da zaisa a damu da yayata labarin wannan mutumin ba. Kawai dan saboda ya taimaka musu shikenan za'a wani damesu da maganarsa sai kace wanda suka ɓata ya tsintosu ya dawo dasu gida. Mamaki da takaicin Zahran bai gama sakinta ba ta tsinkayi muryar Abbie yana faɗin "Ina numbern tasa take auta maza jeki ɗauko wayata a ɗaki ki saka min in kirasa ayi masa godiya, wannan ai bai kamata a kyalesa haka ba tare da mun yaba masa mun nuna masa farin cikinmu kan abun arzikin da yayi mana ba, maza maza tashi kije ki ɗauko wayar ki saka min numbern in kirasa kar dare ya ƙara yi...." Ko kafin ma ya gama rufe baki Zahra ta miƙe da sauri ta nufi bedroom ɗinsa, Shatu kuwa gaba ɗaya ji tayi kamar ta tashi ta bita ta rufeta da duka saboda tsabar takaicinta. ******* A ɓangaren Ya Azeez kuwa koda ya koma gida kasa aiwatar da komai yayi duk jikinsa a sanyaye yake gaba ɗaya al'amuran Fadwa sun gama hargitsa masa tunani, dama ɗan zaman da yayi ne a gidan Ummansa yasa duk wata damuwa da baƙin cikin zuciyarsa suka kau, amma tunda ya dawo ya shigo cikin gidan ya fara jin komai yana dawo masa sabo kamar yanzu ne Fadwan ke sanar dashi cewa tana Abuja sai nan da kwana huɗu ko biyar sannan zata dawo, a hankali ya sake yin juyi akan shimfiɗarsa yayi rigingine ya tsurawa saman silin ɗin dake ɗakin idanu, yanzu fa shikenan haka zai zuba idanu yana kallon Fadwa tana abinda takeso amma babu damar ya kwaɓa mata..? Yana cikin wannan tunanin wayarsa ta ɗauki ƙara, cike da mamaki yayi saurin tashi zaune ya lalubo wayar dake aje gefen filonsa, kallon fuskar wayar yayi a hankali ganin baƙuwar special numbern da ake kiransa da ita ne yasa ya ƙara cika da matsanancin mamaki, to shi wa yake dashi da zai kirasa a wannan daren..? Idan Ummansa ce ai numbernta ya kamata ya gani. Fadwa kuwa dama ita yasan babu abinda zaisa ta kirasa haka kawai ballantana yayi tunanin ganin kiranta a dai-dai wannan lokacin, alhalin yana da tabbacin ta riga ta gama gaya masa duk abinda take da niyyar gaya masan, dan haka yake da yakinin babu abinda zaisa ta kuma kiransa. Agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakin ya kalla ƙarfe 9:20pm ya gani dan haka yayi ta maza kawai ya daure ya kawar da al'ajabinsa ya ɗaga kiran lokaci ɗaya ya kai wayar kunnensa cike da ƙoƙarin ɓoye damuwarsa duk da bai san waye takamaiman me kiran nasa ba yace "Assalamu alaikum..." Daga can ɓangaren kuwa Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai yayi saurin saka wayar a handfree bayan ya amsa masa sallamar kafin ya ɗora da faɗin "Barka da dare Abdul..." Wani banbarakwai haka Ya Azeez yaji sunan a kunnensa, dan haka yayi shiru bai amsa ba. Ɗan murmushi Alhaji Bello yayi daga can ɓangaren kana yace "Ko ba da AbdulAzeez nake magana ba ne....?" Ajiyar zuciya ya sauke a natse kafin yace "Nine inaji, ina wuni...?" Ya faɗa tare da ɗan yin jim kaɗan cikin nazari. Daga can ɓangaren kuwa Alhaji Bello juyawa yayi ya kalli Zahra da tai wani zaman dirshan a gabansa ta tanƙwashe ƙafafuwa ta zubo masa idanu tana faman washe baki. Ɗan murmushi yayi kafin yace "Nasan baka gane mai kiranka ba ko..? To sunana Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai kuma nine mahaifin Zahra da Aisha ƴan matan daka taimakawa jiya da daddare a garin Kaduna..." Cikin tsananin mamaki Ya Azeez ya waro kyawawan idanuwansa waje yana kaɗa kai, kafin ya sauke numfashi cike da kunya yace "Barka da dare Alhaji...ina wuni..fatan sun sauka gida lafiya...?" Ya faɗa lokaci ɗaya yana duƙar da kansa kamar yana gabansa. Ƴar dariya Alhaji Bello yayi kafin yace "Bakanmu dai yaron kirki, Alhamdulillahi wallahi sun dawo gida lafiya mun gode Allah, dama na kiraka ne domin inyi maka godiya bisa ga irin taimakon da kayi mana saboda ba dan Allah ya kiyaye kuma ya haɗaka dasu ba, da bamu san abinda zai faru a jiyan nan ba, sakamakon dukkan mu babu wanda yasan lokacin da suka ɗauki mota suka fita daga gidan nan, sai dai kawai dubawa akayi sama ko ƙasa akaga babu su babu alamar su a gidan wai sun tafi Abuja. Nidai babu abinda zan ce maka sai godiya da fatan alkhairi, Allah ya biyaka ya rabaka da iyayenka lafiya..." Cikin tsananin jin daɗin addu'ar tasa Ya Azeez ya amsa da Ameen Ameen, kana daga nan suka yi sallama bayan yace agaishe dasu Zahra da Shatu da sauran mutanen gida. Wanda basu sauke wayar ba har sai da Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya cewa Ya Azeez ɗin yayi saving numbernsa shima zaiyi saving ɗin tasa a wayarsa domin su riƙa gaisawa, kana daga haka suka yanke wayar. Ajiye wayar Ya Azeez yayi ya koma ya kwanta kana yaja ɗan yalolon bargonsa ya rufe ƙafafuwansa lokaci ɗaya yana gyara kwanciyarsa cikin tarin nazari da tunanin rayuwa. Cikin haka bacci mai daɗi ya kwashesa ba tare da ya bar zuciyarsa ta samu sukunin tuna wata aba can Fadwa ba. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣2️⃣ Tunda suka fara wayar Shatu ta tashi tsam ta bar falon, kai tsaye ɗakinsu ta wuce tana shiga ta tuɓe kayan jikinta ta ɗaura tawul ta wuce toilet, a gurguje ta ƙara watso ruwa domin taji daɗin jikinta, bata jima a toilet ɗin ba ta fito ƙirjinta ɗaure da tawul kai tsaye gaban wardrobe ɗinta ta nufa ta saka hannu ta buɗe ɓangaren inda kayan bacci suke gasu nan kala kala a jere gwanin sha'awa da burgewa. Cikin kayan baccin ta zaɓo wasu riga da wando farare tas masu taushi da tsari ta zura a jikinta, kana ta ɗauki wata hular net baƙa ta zura akanta, matsawa tayi gaban madubin dake ɗakin ta ɗauki turarenta mai sanyin ƙamshi ta fesa kaɗan a jikinta kafin ta bar gaban madubin ta wuce ta haye saman gado ta kwanta lokaci ɗaya taja tattausan bargon dake ajiye a gefen gadon ta lulluɓe rabin jikinta dashi tai luf ta lafe tare da lumshe idonta tana jin wani irin yanayi a tattare da ita. Rabin hankalinta gaba ɗaya yana can falo inda ta rasa dalilin zuciyarta na azalzala mata da son ƙara jin muryarsa, tsaki ta saki ta ƙara ƙudundune kanta a cikin bargon ta runtse idonta da ƙarfi a ƙoƙarinta na son barci ya ɗauketa koda da ƙarfin tsiya ne, saboda bata jin zata iya biyewa zuciyarta akan gurguwar shawarar da take son bata na ta tashi ta koma falon. A ɓangaren Zahra kuwa bata shigo ɗakin ba sai gurin ƙarfe 10pm kuma har lokacin Shatu idonta biyu ta kasa bacci sai faman juyi take tana tunane tunane marasa tushe ballantana makama, a haka Zahra ta shigo ɗakin ta isketa inda tana jin motsin shigowar Zahran ta lumshe idonta da sauri kamar mai bacci, wanda abinda bata sani ba Zahran na lura da ita tuni ta gama ganowa idonta biyu ba baccin take ba. Kallonta tayi tana mamakinta dan ita duk a zatonta yau idan tazo kwanciya mai rabata da ita sai Allah, saboda tasan halinta farin sani ba'a taɓa cin bashinta sai an biya, amma yau abun mamaki sai ta ga saɓanin haka. Taɓe bakinta tayi a hankali tana sauke numfashi kafin ta shiga tuɓe kayan jikinta ta wuce toilet direct itama taje ta watso ruwa a gurguje ta fito, gaban ɗayan wardrobe ɗin dake ɗakin ta ƙarasa ta buɗe, wasu kayan bacci ne masu kalar ruwan madara ta zaro da sauri ta zura a jikinta kana ta ɗan fesa turare, ta lallaɓa ta haye gado kusa da Shatu ta kwanta kana taja bargo a hankali ta rufe ƙafafuwanta zuwa cikinta, ganin kamar bacci ya ɗauketa ne yasa ta ƙara matsawa kusa da ita sosai tana karanto musu addu'ar bacci ta shafa kafin ta shafawa Shatun a jikinta itama, sannan ta koma ta kwanta ta ƙudundune lokaci ɗaya tana runtse idanuwanta masu cike da baccin gajiya. Wanda a ɓangaren Shatun itama hakan ce ta kasance da ita bayan Zahra ta shafa mata addu'ar baccin dama kamar jira take wani daddaɗan bacci mai cike da wasu irin mafarkai masu tsananin daɗi yayi awon gaba da ita. ********* Washegari Misalin ƙarfe 1:20pm Shatu ce tsaye cikin wasu tausasan riga da wandon Palazzo masu bala'in kyau da sheƙi. Inda riga da wandon suka kasance kalar royal blue da ɗigon fari fari a jiki, sai rigar kimono data ɗora akai fara itama mai ɗan zane zanen fari da yarfin royal blue ɗin a jiki wacce bata wuce gwiwarta ba, sosai shigar tayi mata masifar kyau ta kuma fito da zallar wayewarta da kalar fatarta mai kyau da ɗaukar hankali, ta zura tsadadden half cover ɗinta fari ƙirar kamfanin Italy, kana ta ƙaraso gaban madubi ta ɗauki turaren Smart Black cikin jerin tsadaddun turarukanta dake gaban madubin ta fesa wanda ya haɗu da ƙamshin body mist ɗinta na white mist suka bada wani daddaɗan ƙamshi mai sanyi da sanyaya rai. Tana ƙoƙarin yafa ɗan siririn farin gyale a kanta Zahra ta shigo ɗakin itama cikin shirinta na wata pink ɗin atamfa ɗinkin riga da siket wanda suka dace da jikinta da kalar fatarta, ta yana ɗan madaidaicin ƙaramin gyale itama akanta, ta nufo inda take gaban madubin ta tsaya tare da dubanta tun daga sama har ƙasa tana faɗin "Masha Allah ƴan matan Ummi, kin ganki kuwa..? Gaskiya kinyi kyau sosai ba ƙarya wallahi..." Ido Shatu ta lumshe tare da sakin ƙaramin murmushi kana tace "Amma ai ban kai autar Ummi kyau ba ko, domin ita komai tasa a jikinta kyau yake mata...?" Ɗan shagwaɓe fuska Zahra tayi tare da juyar da kanta gefe tana faɗin "A'a nidai ba ruwana ki daina wani haɗa kanki dani saboda kin fini kyau da komai da komai nesa ba kusa ba, amma sai ki wani dinga yaudarata kina cewa wai na fiki kyau, ko a ina ne na fiki kyau ɗin oho..." Ta ƙarashe maganar a shagwaɓe tana ɓata fuska. Wani ƙayataccen murmushi Shatu ta saki tana cewa "To na daina Aunty Zahra shikenan ko...?" Murmusawa kawai tayi ba tare data kuma cewa komai ba ta ƙarasa gaban madubin ta sake gyara kwalliyar fuskarta kana ta juyo tana duban Shatu tace "Ni kam na gama shiryawa ke kawai nake jira..." Wayarta kawai ta ɗauka da Atm card ɗinta ta saka cikin wata ƴar madaidaiciyar handbag fara ta saƙala a hannunta tayi gaba Zahra na biye da ita a baya suka fito, kai tsaye cikin babban falon gidan suka nufa, Shatu na gaba, Zahra na biye da ita tana lallatsa wayar dake hannunta. Shigowar su cikin falon ce tasa Ummi dake fitowa daga kichin hannuta riƙe da wani babban farati ta saki wani lallausan murmushi dake bayyana tsantsar ƙaunarta ga ƴaƴan nata, tace "Masha Allah my baby's gaskiya kunyi kyau sosai tubarakallah, amma ya kamata ku bari muci abincin rana dai kafin ku tafi shopping ɗin nan, tunda na gama girkin tun ɗazu..." Ta faɗa tana wucewa kai tsaye dinning area ɗin ta ajiye farantin, kafin ta shiga jera abincin lokaci ɗaya tana faɗin "Maza kuzo kuci sai ku wuce, saboda nasan idan na biye muku baci zakuyi ba, sai dai kuyi ta min hanya hanya tunda dama can abincin ba wani damunku yayi ba, dan haka idan na kyaleku ba ci zakuyi ba..." Jin abinda tace ɗin ne yasa dukkansu sukayi ƴar dariya kana suka wuce zuwa dinning area ɗin kai tsaye. Bayan sun zazzauna ne Ummi tayi sarving ɗinsu, inda ta zuba musu farar shinkafa da miyar kaji zuƙu zuƙu da tayi, sai haɗin coslow da pepper chicken data sakawa kowannen su a wani ɗan ƙaramin bowl, ta turawa kowa filet ɗin gabansa, kana taja kujera itama ta zauna tana faɗin "Maza kuyi ku kammala ku tafi, kafin rana ta ƙara kwallewa kuje ku kwaso zafi ku dawo min gida a galabaice kuce kuma kai na ciwo..." Ta faɗa tare da ɗaukar cinyar kaza ta kai bakinta ta soma ci, ɗago kai Shatu tayi ta kalleta kafin ta ɗan turo baki a shagwaɓe tana faɗin "Wai ina Abbie ni ban ganshi ba ko har ya fitan ne...?" Kai Ummi ta gyaɗa kana tace "Ya fita tun ɗazu, saboda yau suna da ɗaurin auren yaron wani abokinsa Alhaji Sale Musawa da za'ayi a Kundila shiyasa ya fita tunda wuri, saboda ya samu ya halacci ɗaurin auren, amma yace ba zai jima ba ana gama ɗaurawa zai dawo gida..." Jinjina kai Shatu tayi kana tace "Allah ya sanya alkhairi ya dawo dashi lafiya..." A hankali Ummin ta amsa da "Ameen ya Allah..." Kana daga haka suka ci gaba da cin abincinsu, Zahra kuwa murmushi kawai tayi ta ci gaba da danna abincinta dan ita dama bata taɓa wasa da cikinta ko a ina ne zagewa take ta ci abincinta hankali kwance babu abinda ya dameta. Ganin yadda ta zage take cin abincin ne yasa Shatu da Ummi haɗa idanu suka yi murmushi, yayinda ita kuwa Zahra ko ajikinta bata san suna yi ba, aikawa cikinta abinci kawai take tare da korawa da sassanyan juice. Shatu kuwa ko data kammala cin abincin wanda ko rabi bata ci ba, ture filet ɗin tayi ta matsar gefe kana ta miƙe tsaye ta ɗauki wayarta dake aje kan dinning ɗin, kafin ta yagi tissue ta goge bakinta, kana ta juya ta kalli Zahra dake riƙe da wani kofin gilas a hannunta tana shan juice tace "To nidai na kammala saura ke kiyi ki ƙarasa mu tafi..." Ta ƙarashe maganar tare da ficewa daga dinning area ɗin ta nufi falo, kai kawai Zahra ta kaɗa kana ta dire kofin dake hannunta da sauri ta miƙe tsaye ta yagi tissue ta goge bakinta da hannunwanta, kafin ta suri jakar handbag ɗinta ta wuce tana faɗin "Ummina mun tafi sai mun dawo, me kikeso in taho miki dashi tsaraba...?" Ta faɗa tana ƙarasa saukowa daga dinning area ɗin ta nufi cikin falo inda Shatu ke tsaye tana jiranta, Ummi kuwa dake tsaye a dinning ɗin tana ƙoƙarin tattare kayan da suka kammala cin abinci dasu ne ta ɗago ta kallesu tana sakin murmushi take faɗin "A'a bana buƙatar komai ƴan matana kuje dai Allah ya dawo min daku lafiya, ni kam zanyi online shopping abuna..." Da sauri Shatu tace "No Ummi kar kiyi dan Allah ki gaya mana abinda kikeso kawai mu siyo miki..." Ta faɗa a shagwaɓe tana kallonta, ɗan taɓe baki Ummi tayi kana tace "Alright shikenan...perfumes kawai nakeso da turaren ɗaki..." Ɗan murmushi Shatu tayi tana cewa "Ashe ma duk buƙatar tamu ɗaya ce Ummina, nima turarukan fa nakeso in siya, sai kayan bacci da nakeson canza sababbi saboda nawa duk sun tsufa ina buƙatar wasu..." Ta faɗa tare da juyawa ta kama hannun Zahra tana faɗin "Muje auta, Ummi mun tafi sai mun dawo..." Kallonsu Ummi tayi cikin kulawa kafin tace "To a dawo lafiya Allah ya tsare..." Da "Ameen..." Suka amsa kana cikin jin daɗi suka sakai suka fice daga falon. ★★★ Acan Kaduna kuwa Ya Azeez ne tsaye a ƙofar su, inda yake ƙoƙarin kulle ƙofar ɗakin da kwaɗo, a hankali ya juyo lokaci ɗaya yana saka ɗan makullin a cikin aljihun wandon shaddar dake sanye a jikinsa, ɗan kallon tsakar gidan nasu yayi ya kaɗa kai kafin yasa kai zai fice daga gidan, har ya kai bakin ƙofa wayarsa ta ɗauki kara ya dakata ya zura hannu cikin aljihun dake gaban rigarsa ya fito da ita, ganin Ummansa ce yasa da sauri ya zauna saman wani ɗan dutse dake jikin ƙofar gidan nasu ya jingina bayansa da bango kana ya masa kiran cikin girammawa haɗe da tsantsar biyayya yace "Assalamu alaikum..Ummana Barka da rana..." Daga can ɓangaren kuwa Umma dake zaune a tsakar gidanta tana gyaran shinkafa, sai Iman dake gefenta a zaune tana gyara kayan miya, ta saki murmushi cikin nuna jin daɗi tace "Waalaikums salamu ɗan gidan Ummansa, ya aikin har an fitan ne...?" A hankali ya saki murmushin shima kana yace "A'a ban fita ba Umma sai yanzu ne dai na fito nake shirin zan fitan..lafiya dai ko...?" Ya ƙarashe maganar tare da ɗan saurarawa. Numfashi ta sauke a hankali kafin tace "Dama na kiraka ne inji kasan yau ake bikin Fahad abokinka ɗan gidan Alhaji Sale Musawa amma shine ko kaɗan baka taɓa gaya min ba...?" Da sauri ya zaro idanuwansa waje cike da mamaki kafin yace "Wane Fahad ɗin kuma Umma..ba dai Fahad nawa dana sani ɗan gidan Alhaji Sale abokin Abbana ba...?" Cikin sanyi tace "Shi ɗin dai Fahad na Kano AbdulAzeez shi nake nufi yau ake ɗaura masa aure..." Cike da tsantsar mamaki yace "Amma shine bai gaya min ba Umma..? Kuma fa ko jiya sai da ya kirani da yamma mukayi waya dashi, yake tamabayata yaushe zan shigo nace masa sai ƙarshen watan nan..." Umma tace "To ka daina mamaki nima yanzu Hajiya Zabba'u ta kirani take tambayata ya bata ganni a gidan biki ba, shine nake tambayarta bikin wa tace na Fahad, nace ai ban sani bane tace aiko yau ne ɗaurin aurensa amma ɗaurawa kawai za'ayi yau ɗin, taron bikin kuma sai nan da sati ɗaya za'ayi, shine nace bari in kiraka inji koka sani shine baka gaya min ba. Ai da naje wallahi ko dan saboda Hajiya Fiddausi mutuniyar kirki matar akwai ta da mutunci da son mutane gata da fara'a, tun lokacin da abun nan ya samu mahaifinka bata taɓa gajiyawa da yi mana abun arziki ba ita kenan kullum akan hanyar kawo mana abun alkhairi, ita da mijinta suna da karamci sosai wallahi, inda da hali da ka halacci bikin nan idan aka gama komai saika dawo..." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Insha Allahu kuwa Umma zanje, za'a san yadda za'ayi. Amma yau..." Saurin katsesa tayi da faɗin "Amma da so samu ne Yayan Imaan daka tafi tun yau ɗin kawai sai dai su ganka kwatsam..." Ɗan jim kaɗan yayi kafin yace "Amma Umma kinsan ɗaurin auren safe Kano sukeyi nasan yanzu an riga da an gama ɗaurin auren, kawai dai dana bari zuwa nan da sati ɗayan sai in tafi ayi bikin dani a gama sannan in dawo..." Ɗan gyara zama Umma tayi daga can ɓangaren tana cewa "Nidai inda hali ka tafi yau ɗin kawai dan Allah..." Ta faɗa kai tsaye cikin bada umarni. Idonsa ya lumshe fahimtar da yayi cewa umarni ne kai tsaye mahaifiyar tasa take bashi, dan haka cikin sanyi yace "Insha Allahu duk yadda kikace hakan za'ayi Ummana, ina nan zan biyo idan na shirya, zanzo muyi sallama kafin in wuce..." Cikin jin daɗi tace "Toh shikenan ina jiranka saika ƙaraso, amma kayi sauri ka shirya kar yamma tayi kasan yanayin hanyar sai a hankali. Ka gaida Fadwa Allah yayi muku albarka yasa a gama lafiya..." "Ameen Ameen Ummana, Ameen ya Allah..." Ya faɗa cike da jin daɗi, kana daga haka sukayi sallama ta kashe wayar. Ya jima a tsaye shiru yana tunani kafin ya juya da sauri ya buɗe ƙofar ya koma cikin ɗakin, kasancewar dama bai wani daɗe da yin wanka ba yasa ya tuɓe kayan jikinsa a gurguje, ya buɗe jakarsa ya zaro wata shaddarsa mai kyau kalar sky blue wacce bata wani sha jiki sosai ba ya hau shiryawa cikin sauri sauri, sosai shaddar tayi masa bala'in kyau ta haska fatarsa, yana gamawa ya ɗebi ƙananan kayansa kala biyu da jallabiya guda ɗaya, ya haɗa da abubuwan da yasan zai buƙata ya saka a wata ƙaramar jaka irin ta matafiya ya sagala a gefen kafaɗarsa, kana ya ɗauki wandon kayan daya cire ya kwashe kuɗaɗen dake ciki wanda basu wuce dubu huɗu da ɗari biyar ba ya zuba a cikin aljihunsa sannan ya ɗauki makullin napep ɗinsa ya fice daga ɗakin. Kulle ƙofar ɗakin ya soma yi kafin yasa kai ya fice daga gidan gaba ɗaya yaja ƙofar ya kulle ta can waje, kana ya nufi kekensa inda yayi parking daga can gefe guda ya shiga yaja, gidan bulon da yake kai ajiya direct ya nufa yaje ya ajiye keken acan haɗe da basu ɗan makullin kana daga nan ya fito ya tari mashin ya hau, bayan ya gaya masa inda zai kaishi yaja suka wuce. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣3️⃣ Koda mai mashin ɗin ya saukesa a kofar gidan Umman bai wani daɗe sosai ba, dan ko zama baiyi ba daya shiga, suna ƙara gaisawa kawai yayi mata sallama ya fito ya sake tarar mashin ya hau kai tsaye ya nufi tasha. Yana isa can ma bai wani jima sosai ba ya hau motar Kano suka kama hanya. ★★★★ *4pm.* Ummi ce zaune saman ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun da suka zagaye katafaren falonta sukayi masa ƙawanya, riƙe take da remote control a hannunta tana canja tashoshi, tashar Sunnah TV ta kamo inda taga an sako wa'azin mutuminta Malam Aminu Daurawa wanda yake bada fatawa akan haƙuri da juriya a zamantakewar aure, kasancewar tana tsananin son wa'azinsa yasa gaba ɗaya ta natsu ta maida hankalinta kacokan kan talabijin ɗin, ta ƙara gyara zama lokaci ɗaya ta ƙaro volume tana saurare. Buɗe ƙofar falon da akayi ne yasa ta ɗan juyowa a hankali, taga Zahra ce ta gyara zama da sauri ta kalleta, ƙaramin murmushi ta saki kafin tace "Welcome my princess an dawo..." Ta faɗa tare da ajiye remote ɗin hannunta ta buɗe mata hannuwanta alamar tazo gareta. Ɗan kwaɓe fuskarta Zahran tayi kana ta fara takowa a hankali ta ƙaraso gabanta tazo ta dire shopping bags ɗin dake hannunta kafin ta faɗa saman kujera lokaci ɗaya tana faɗin "Wash Allahna Ummi na gaji sosai wallahi..." Cikin sauri Shatu dake shigowa cikin falon itama hannunta riƙe da wasu shopping bags ɗin tace "Aikin uban me kikayi da har kika gajin..? Ummi kiji min wannan ragguwar autar taki da wani iyayi fa...?" Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana dire jakunkunan a gaban Ummin, kafin ta ɗago tana cewa "Sannu da gida Ummina..." Ta faɗa tare da zama a kusa da Zahra data wani dafe kai tana yamutse fuska. Watsa mata harara Shatu tayi kafin ta saki tsaki ta miƙe tana hararar Zahran take faɗin "Mutum sai shegen rakin tsiya abu ba abu ba duk kibi ki damu mutane da ƴan ƴan ƴan..wai ke a dole kin gaji sai kace wacce ta ɗauko Sahad Store gabaki ɗaya a kanta..." Ummi dake kallonsu tana dariya tace "A'a fa ƴan mata, ya kamata ki tausaya mata tsakani da Allah, tun fa ɗazu kuka fita kusan awa uku kenan ga zafin gari ga rana, taya za'a ce mutum ba zai jigata ba dan Allah...?" Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi tana hararar Shatu. Ɗan taɓe baki Shatu tayi ta harari Zahran kana ta ɗauki handbag ɗinta data ajiye tana faɗin "Ummi nidai bari inje inyi sallahr la'asar, lokaci har ya wuce muna gurin siyayyar kaya..." Ta faɗa tana wucewa da sauri ta haura sama zuwa ɗakinsu. Miƙewa itama Zahran tayi lokaci ɗaya tana faɗin "Nima bari inje inyi Sallah Ummi, idan na idar na ɗan watsa ruwa zan sauko..." Ta faɗa tana ɗan yatsine fuskarta alamar gajiya. Kaɗa mata kai Ummin tayi tana faɗin "Ok a sauko lafiya, amma ki gayawa Shatu nace idan tayi sallah maza ta sauko falo karta sake ta kwanta, dan nasan halinta ba takamaiman lokacin bacci gareta ba ko wane lokaci tayi ra'ayi kwanciyarta kawai take yi..." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar remote ɗinta tana ƙaro volume, gyaɗa mata kai Zahra tayi kana ta ɗauki wayarta itama tayi gaba, cikin natsuwa ta fara hawa matattakalar benen tana takawa a hankali a hankali har ta haura saman ta nufi ɗakinsu. ******* Ƙarfe 4:40pm. Dai-dai na yamma direban daya ɗauko su Ya Azeez tun daga Kaduna ya shigo garin Kanon dabo, wanda kuma bai diresu a ko'ina ba sai a Na'ibawa Ƴan Lemu. A hankali ya buɗe murfin motar ya fito riƙe da jakarsa a hannu, kafin cikin natsuwa ya lumshe kyawawan idanuwansa masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Kana a hankali ya sauke numfashi yana sake shaƙar iskar garinsa mai cike da ɗimbin tarihi a rayuwarsa. A hankali yake jin wani irin mugun farin ciki yana ratsa ruhi da gangar jikinsa, wanda yasa yake jin kansa cikin wani irin yanayi mai masifar daɗi, yayinda a nutse zuciyarsa ta dinga tariyo masa wasu abubuwa da dama waɗanda suka shuɗe a lokacin da mahaifinsa yake a raye. Cikin sanyin jiki yasa hannu ya share ƴar ƙwallar dake shirin zubo masa ya girgiza kansa a hankali kafin a fili ya furta "Allah ya gafarta maka Abbana, Allah yasa kana kyakkyawan matsayi a cikin aljanna fiddausi maɗaukakiya..." Ya faɗa yana rataya jakarsa a gefen kafaɗarsa ya juya cikin takunsa mai cike da zallar natsuwa ya fara kutsawa cikin mutanen dake ta kai kawo a gurin suna ta hada hada, har ya isa inda masu daidaita sahu suka faka a gefen titi, ya tsallaka ya tare wani ya shiga bayan ya faɗa masa unguwar da zai kaisa yaja suka kama hanya. Koda suka ƙarasa cikin unguwar ta Medile, gaban wani katafaren ƙerarren gida mai ɗauke da tangamemen gate kalar ruwan madara ya nunawa mai adaidaita sahun yace ya tsaya. Fitowa yayi daga cikin adaidaitan ya biyasa kuɗinsa, kafin ya juya a hankali cikin natsuwa ya tunkari gate ɗin gidan lokaci ɗaya yana gyara zaman jakarsa dake rataye a gefen kafaɗarsa, ƙarasawa yayi bakin gate ɗin ya tsaya daga ɗan gefe kaɗan dai-dai inda ƙaramar ƙofar take, kai tsaye ya saka hannu ba tare da tunanin komai ba ya fara ƙwanƙwasa ƙofar a hankali yana ɗan waigawa bayansa lokaci bayan lokaci yana kallon cikin unguwar dake nan tsit babu motsin mutane ko kaɗan, sai ƴan ɗaiɗaikun motocin dake ɗan giftawa jefi jefi suna wucewa zuwa gidajensu. Dai-dai lokacin kuma aka wangale tangamemen gate ɗin wata mota ƙirar Benz baƙa wuluk ta silalo a hankali ta fito daga farfajiyar gidan, wani irin wawan burki mai motar ya taka a gabansa, ɗago kansa yayi a hankali yana kallon motar da sauri wanda ke cikin motar ya buɗe ya fito, wani kyakkyawan saurayi ne irin black beauty ɗin nan, wanda a ƙalla shekarunsa zasu iya zuwa ɗaya dana Ya Azeez ɗin. Sanye yake da wata tsadaddiyar shaddar gezner fara sol mai masifar kyau da yarari sai ɗaukar ido take tare da zuba wani irin sheƙi na musamman, kai da ganin yanayin shigar da yayi tun daga sama har ƙasa da yadda fuskarsa ke ɗauke da murmushi take kuma fitar da wani annurin farin ciki na musamman zaka fahimci cewa shi ango ne. Cikin sassarfa ya iso gaban Ya Azeez ɗin wanda tunda yayi masa kallo ɗaya ya wani ɗauke kai gefe yasha mur kamar bai gansa ba. Fuskarsa ɗauke da matsanancin mamaki ya zaro idanu waje yana faɗin "Laaaa AbdulAzeez Naseer Arabi..." Ya faɗa cike da tsananin farin ciki, da kuma mamakin ganinsa a dai-dai wannan lokacin yana kallonsa. "Wai dan Allah da gaske kai ne Arabi...?" Ya faɗa cike da al'ajabi yana ƙoƙarin kamo hannunsa, saurin janye hannunsa Ya Azeez yayi tare da watsa masa wani mugun kallo cikin ɓacin rai ya ɗauke kai yana cewa "A'a bani bane mai kama dani ne..." Bai bashi damar magana ba ya ci gaba da faɗin "Wallahi ka bani matuƙar mamaki Fahad, wai ace duk yadda muke da kai yau aurenka amma koda wasa baka taɓa faɗa min ba..kuma kusan kullum sai munyi waya da kai amma saboda bani da komai yanzu bani da abinda zan iya baka amatsayin gudunmawata, kuma ni ba kowa bane, ban kuma mallaki komai ba shiyasa kaƙi sanar dani aurenka saboda ban cancanci zuwa bikinka ba..? Ko kuma kar inzo in zubar maka da kima da mutuncinka a idanun abokanka saboda ni ba ɗan kowa bane sannan ban tara komai ba ko...?" Ya ƙarashe maganar cikin ƙunar rai da tsakanin jin zafin abinda Fahad ɗin yayi masa na ƙin gaya masa aurensa da bai ba, wanda shi lokacin da nashi auren da Fadwa ya tashi sai da ya kirasa ya faɗa masa kuma yaje har garin Kaduna akayi komai dashi kuma ya bashi abun arziki sannan ya dawo, amma saboda shi ba komai bane yanzu basu da wani mai tallafa musu sai mahaifinsa shiyasa zai yi masa haka..? Shi kuwa Fahad gaba ɗaya ji yayi gwiwarsa tayi bala'in sanyi, ko ba komai bai kamata ya yiwa AbdulAzeez haka ba, duba da irin zaman amana da mutuncin da iyayensu sukayi, da irin shaƙuwar dake tsakaninsa dashi kansa AbdulAzeez ɗin, wanda a duk faɗin garin Kano da cikar ta bashi da wani amini ko shaƙiƙi da ya kai masa AbdulAzeez ɗin, haka kuma shima AbdulAzeez ɗin a nasa ɓangaren bai da wani amini da ya kai masa Fahad ɗin duk faɗin garin Kano da kewayenta. Har ga Allah shi da kansa ya sani bai kyauta masa ba, kuma ba yayi hakan da wata manufa bane a ransa kawai yayi ne domin kar ya takura masa, saboda yasan halinsa shi mutum ne mai bala'in kawaici da takura kai dan kawai yaga ya farantawa wanda yake tare dashi, shiyasa ya barshi bai gaya masa ba, amma ko kaɗan bai san abun zai ɓata masa rai har haka ba.. "Kai ni gurin Mami nidai inyi mata Allah sanya alkhairi, in kama hanya kafin dare yayi min..." Maganar Ya Azeez ta katsewa Fahad ɗin tunanin da yake yi da sauri ya ɗago kai ya kallesa, kafin cikin sanyin jiki yace "Dan girman Allah aboki ka fahimceni..wallahi banyi hakan da wata niyya ba, amma idan kana ganin kam..." Ɗaga masa hannu Ya Azeez yayi da sauri yana faɗin "Nidai ba saboda kai dama nazo ba, idan kuma gidan ma bazaka iya bari na in shiga bane to sai in koma inda na fito..." Ya faɗa kai tsaye yana dubansa. Saurin kallonsa Fahad ɗin yayi kafin ya juya lokaci ɗaya yana faɗin "Ai ban isa ba aboki kaima gidanku ne, amma please nidai ina ƙara roƙonka ka yafe min dan girman Allah ba dan ni ba..." Ya faɗa yana riƙe hannunsa lokaci ɗaya suka fara tafiya, banza dashi Ya Azeez ɗin yayi ya ɗauke kai gefe, ganin haka yasa Fahad ɗin sake dubansa fuskarsa cike da damuwa yace "Please mana abokina..." Wani banzan kallo Ya Azeez ɗin ya sake ɗago kai ya watsa masa kana ya juya cikin sauri ya isa bakin gate ɗin gidan ya tura ƙaramar ƙofar kai tsaye ya shige ciki, da hanzari shima Fahad ɗin yabi bayansa ba tare daya sake ko bi ta kan motarsa daya bari fake a gurin ba ballantana har ya kula da cewa abokansa da suka fito tare suna ciki ba, ya bishi suka shige gidan a tare yana ƙara yi masa magiyar ya tsaya ya sauraresa, amma ko waigowa Ya Azeez bai yi ba sai ma sauri daya ƙara ya nufi ƙofar da zata sadashi da shiga babban falon gidan. Da sauri wani kyakkyawan matashin saurayi dake fitowa daga cikin falon ya nufosa cike da farin ciki yana faɗin "Oyooyo Ya Azeez, ina ka baro min Umma da Imaan ɗina...?" Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana karɓan jakar dake rataye a kafaɗarsa, yana cewa "Muje ciki Mami tana nan..." Ɗan shafa kansa Ya Azeez yayi a hankali yana murmushi yake faɗin "Masha Allah su Ibrahim yaron Mami an ƙara girma, sai kuma aure tunda an gama karatu ko...?" Ya faɗa cike da tsokana yana kallonsa, da sauri ya rufe fuskarsa da hannuwansa alamar jin kunya kafin yace "Kai Ya Azeez ni fa ba yanzu zanyi aure ba har sai Imaan ta gama makaranta tukunna sai muyi atare..." Ya ƙarashe maganar yana wucewa da sauri yayi gaba, shima Ya Azeez ɗin da Fahad dariyan sukayi kaɗan kana suka bi bayansa a nutse suka nufi ƙofar babban falon gidan. Wani haɗaɗɗen falo suka shiga mai tsananin kyau da tsari, wanda aka kewayesa da wasu rantsatstsun kujeru na alfarma. Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga cikin falon, inda suka iske wasu hamshaƙan manyan mata zazzaune kota ina a cikin falon kowaccen su taci uban ado na kece raini, suna ganinsu kuwa suka hau faɗin "Oyooyo ango..oyooyo ango kasha ƙamshi..." Suka faɗa a tare suna dariya, a hankali suka ƙarasa gabansu duk suka rusuna suna gaishesu, shi kuwa Ibrahim da sauri yayi gaba yana kiran "Mami..Mami kizo ga Ya Azeez yazo..." Wata kyakkyawar hamshaƙiyar mata ce mai matsakaicin tsaho ta fito daga wani ɗaki da sauri cikin fara'a tana cewa "Ina AbdulAzeez ɗin yake...?" Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki tana kallon Ibrahim ɗin. Da sauri Ya Azeez ya miƙe ya isa gabanta cikin nuna tsantsar farin cikin ganinta da yayi ya ɗan rusuna a gabanta yana faɗin "Mami ina wuni mun sameku lafiya...?" Ya faɗa cikin sanyin murya lokaci ɗaya yana sakin murmushi. Cikin tsantsar so da nuna kulawa Mami tace "Lafiya Alhamdulillahi AbdulAzeez, ya Hajiya Hafsatu da Imaan ɗin, fatan duk kuna lafiya ko...?" Cikin natsuwa ya amsa mata da faɗin "Duk suna lafiya Mami Alhamdulillahi, sunce ma agaisheki..." Gyaɗa kanta tayi kafin tace "Masha Allah, ina ita iyalin naka ko ba tare kuka zo ba...?" Ta ƙarashe maganar tana ɗan leƙa cikin falon. Saurin girgiza mata kai yayi da sauri yana faɗin "A'a tana gida can na barota, ba tare da ita muka zo ba..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana jin wani irin ɗaci da bala'in haushin jin sunan Fadwa da Mami ta ambata ya ƙara cika masa zuciya. Dai-dai lokacin kuma Fahad ya ƙaraso gabansu yana faɗin "Mami dan Allah ki tayani ba aboki haƙuri, nayi masa laifi kuma na bashi haƙuri amma yaƙi fahimta ta..." Ya faɗa cikin marairaice fuska yana kallon Ya Azeez daya wani ƙara haɗe rai ya ɗauke kai gefe. Mami kuwa riƙe baki tayi da sauri tana faɗin "A'a rufa min asiri kunfi kusa, nima tare na ganku, kuje can ku ƙarata..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana murmushi kafin ta juya tana duban Ibrahim dake tsaye har lokacin da jakar Ya Azeez sagale a kafaɗarsa tace "Kaje ka kai masa jakar ɗakin yayanku mana ya samu yayi wanka ya ci abinci, sai ya ɗan huta kafin kuma Abbanku ya dawo ko...?" Ta faɗa tare da kallon Ya Azeez ɗin tana ci gaba da faɗin "Tashi ku shiga ciki ka watsa ruwa, yanzu za'a kawo maka abinci..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da juyawa ta nufi kichin. Koda suka isa ɓangaren Fahad ɗin wanda ƙofar shiga cikinsa ke kusa da falon mahaifinsa, ajiye jakar Ibrahim yayi ya wuce toilet yaje ya haɗa masa ruwan wanka kana ya fito ya fice daga ɗakin da sauri dan zuwa ya karɓo masa abinci kafin ya fito wankan. A hankali ya miƙe tsaye ya fara ƙoƙarin tuɓe kayan jikinsa dan ya samu ya ɗan watsa ruwa kafin yazo ya gabatar da sallar la'asar data kuɓuce masa, wanda kuma a dai-dai lokacin Fahad ya shigo cikin ɗakin da sauri shi da wani abokinsa, ya zauna saman wata sofa guda ɗaya dake tsakiyar ɗakin ya dafe kansa cike da damuwa. A hankali Ya Azeez ya waigo ya kallesa kafin ya matso kusa dashi ya riƙo hannunsa cikin nuna kulawa wanda kuma har a lokacin fuskarsa take ahaɗe yace "Meya faru kuma..ko wani abun akayi maka...?" Da sauri Fahad ya riƙe hannunsa yana faɗin "Wallahi na rasa ta yadda zanyi ne in fahimtar da kai dalilina na ƙin sanar da kai ɗaurin aurena da ban yi ba, na san nayi maka kuskure ban kyauta ba, amma..." Saurin rufe masa baki Ya Azeez yayi lokaci ɗaya yana fashewa da wata irin dariya wacce ya daɗe rabon da yayi irinta, sakin baki kawai galala Fahad da abokinsa sukayi suna kallonsa, kana suka juya suka kalli juna, kafin kuma cikin wani irin rauni Fahad ɗin yace "Amma dai kai ɗan iska ne ko aboki..to meye abun dariyan kuma...?" Bai kulasa ba sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita yana faɗin "Shege Dude..ai dama nace yau sai nayi maganinka ɗan iska tunda kai baka da mutunci, amma ni komai ya riga ya wuce a gurina, dama ban riƙeka ba tuni na manta. Amma idan ka ƙara ko...?" Ya faɗa tare da yin ƙwaffa kafin ya ci gaba da faɗin "Sai na bala'in ɓata maka rai wallahi..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana wani ƙara haɗe fuska irin ya ci serious ɗin nan. Dunƙule hannunsa Fahad yayi ya kai masa duka a ƙirji yana sakin murmushin farin ciki, kafin ya faɗa jikinsa lokaci ɗaya suka rungume juna atare suna ƙara fashewa da dariya. Ya Azeez ne ya fara janye jikinsa a hankali yana murmushi, kafin yace "Ina zuwa bari in watsa ruwa idan nayi sallah sai ka kaini gurin amaryar tamu in ganta..." Ya faɗa tare da juyawa ya shige toilet. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣4️⃣ Yana fitowa daga wankan ana kiran sallahr Magriba, da sauri ya sake komawa cikin toilet ɗin ya ɗauro alwala kana ya fito shima Fahad ya shiga yayo, sannan abokinsa. A gurguje ya buɗe jakarsa ya zaro wata farar jallabiyarsa ya zura kana ya ɗan fesa turare ya ɗauki casbaha ya fice daga ɗakin yayinda Fahad da abokinsa ke biye dashi a baya zuwa masallacin dake cikin unguwar. Basu dawo ba sai da suka sallaci sallar isha'i sannan gurin ƙarfe 7:40pm suka shigo gidan. Koda suka shigo sun iske Ibrahim ya kawo abinci yana ajiyewa suna shigowa cikin ɗakin, da sauri Fahad ya nufi ɗan madaidaicin teburin da Ibrahim ɗin ya jera abincin akai ya zauna, filet ya ɗauka tare da spoon ya buɗe kular farfesun kayan cikin rago dake ta tashin ƙamshi ya fara zubawa yana faɗin "Zoka zauna kaci abinci aboki, dan nasan tun kafin ka taho ƙila rabonka da abinci..." Ya faɗa yana ƙoƙarin zuba masa farfesun, a hankali Ya Azeez yazo ya zauna a ƙasan kafet ɗin dake malale a tsakiyar ɗakin tare da tanƙwashe ƙafafuwansa lokaci ɗaya yana kallon tarin kulolin dake jere kan ɗan teburin cin abincin kafin ya juya ya kalli gefen da abokin Fahad ke zaune yana faman danna waya yace "Ya ka koma nan kuma..? Matso mana kaima kaci abincin..." A hankali ya taso shima ya ƙaraso ya zauna kusa da Ya Azeez ɗin kana ya tanƙwashe ƙafafuwansa kamar yadda yaga Ya Azeez ɗin shima yayi. Fahad ne yayi Sarving ɗinsu da kansa kana ya turawa kowa filet ɗin abincin gabansa, kafin shima ya ajiye nasa agabansa suka fara ci shida abokinsa, shi ko Ya Azeez bai ko kalli abincin da Fahad ɗin ya zuba masa ba, ya ɗauki kofi ya soma ƙoƙarin haɗa tea, ɗagowa Fahad yayi ya kallesa kafin yace "Ya haka kuma aboki, tea naga kana haɗawa abincin kuma fa...?" Ɗan kwaɓe fuskarsa Ya Azeez yayi ya lumshe idanunsa kafin yace "Tea ɗin kawai zan iya sha Dude, shi kaɗai ya isheni..." Ya faɗa kai tsaye yana ɗaukan kofin daya haɗa kakkauran tean a ciki ya kai bakinsa. Kai Fahad ya ɗan jinjina ba tare kuma da ya cewa komai ba, ya ci gaba da cin abincinsa, saboda yasan halinsa farin sani tunda yace tea ɗin kawai zaisha to shi ɗin kuwa zaisha ba zai ci abincin ba. Koda suka kammala cin abincin Ya Azeez ne ya fara miƙewa tsaye lokaci ɗaya yana kallon Fahad cikin tarin gajiya yace "Kawai mu bari sai zuwa gobe muje gurin amaryar nan tamu dan yanzu kam dare yayi kusan 8:30pm ake nema, kuma duk a gajiye nake wallahi baka ji jikina ba ko'ina ciwo yake min, mu bari goben kawai..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana nufar hanyar toilet ya shige, a hankali Ibrahim ya turo ƙofar ɗakin ya shigo yana kallon Fahad dake tsaye a tsakar ɗakin yana ƙoƙarin tuɓe kayan angoncin dake jikinsa ya ɗago ya kallesa kafin yace "Yauwa dama yanzu nake shirin kiranka ka kwashe kayan nan ka fita dasu..." Ya faɗa yana ƙarasa tuɓe babbar rigar shaddar dake jikinsa ya sagale a cikin wardrobe ɗinsa, shi kuwa Ibrahim duƙawa yayi ya soma tattare kayan yana faɗin "Dama Mami ce tace inzo in kira mata Ya Azeez yazo su gaisa da Abba ya dawo tun ɗazu yana falonsa..." Buɗe ƙofar toilet ɗin da Ya Azeez ɗin yayi ne ya dawo da hankalin Ibrahim ɗin kansa inda yake faɗin "Yauwa Ya Azeez dama Mami ce ta aikoni wai kazo Abba ya dawo yana falonsa..." Da sauri Ya Azeez yace "Ok muje..." Ya faɗa tare da yin gaba da hanzari yayinda Ibrahim ɗin kuma ke biye dashi a baya hannunsa riƙe da babban farantin daya kwashe kwanukan da suka gama cin abinci dasu suka fice daga ɗakin. Ƙofar wani haɗaɗɗen falo dake can tsakiyar babban falon gidan suka nufa, tsayawa Ibrahim yayi daga bakin ƙofar ya buɗe Ya Azeez ya kutsa kai cikin lafiyayyen falon bakinsa ɗauke da sallama, yana shiga shi kuma Ibrahim ɗin ya juya ya nufi kichin dan kai kayan dake hannunsa ya ajiye. Wani kyakkyawan mutum ne mai cikar haiba da kamala ke zaune a tsakiyar falon kan wata ƙatuwar darduma da aka shimfiɗa, gabansa wani babban farati da aka jere masa kulolin abinci akai, sai gefensa kuma Mami ce zaune cikin shiga ta alfarma tana ƙoƙarin zuba masa abinci, ganin shigowar Ya Azeez ɗin ne kuma yasa Alhaji Sale Musawan ɗagowa fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi ya buɗe masa hannayensa cikin tsananin farin ciki da jin daɗin ganinsa yana faɗin "Barka da zuwa yarona, yaka nan..." Yake faɗa yana ƙara sakin murmushin jin daɗin ganinsa da yayi. Da sauri Ya Azeez ya ƙarasa gabansa ya rusuna tare da faɗawa jikinsa cikin tarin farin ciki da wata tsananin kewar mahaifinsa da yake ji lokaci guda tana bijiro masa yace "Barka da dare Abba, fatan na sameku lafiya...?" Ya faɗa tare da yin tsam a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali, kafin kuma ya janye jikinsa a hankali ya matsa gaban Mami yana faɗin "Sannu da gida Maminmu..." Jinjina masa kai Mamin tayi tana murmusawa kafin tace "Yauwa sannunmu yaron kirki, ya gajiyar tafiya...?" Ta faɗa tana ƙarasa haɗawa Abban abincinsa ta tura gabansa kana ta sake ɗaukar wani filet ɗin ta fara ƙoƙarin haɗa wani tana faɗin "Me za'a zuba maka AbdulAzeez...?" Da sauri yace "Wallahi a ƙoshe nake taf Mami, yanzu ba daɗewa muka gama cin abincin da Ibrahim ya kai mana..." Ya faɗa lokaci ɗaya tare da ɗan shafa cikinsa yana sakin murmushi. Dariya Abba yayi irin tasu ta manya kafin yace "Da dai ka daure ka ƙara ci ɗin, tunda naga alamar so Mamin taku take taga kayi ƙatoton tumbi ƴan mata su dinga gudunka, suna basa son mai tumbi..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da yin dariya, itama Mamin dariyar tayi kafin tace "Aiko babu budurwar da duk haɗuwarta zatayi tozali da yarona tsalele dashi santalele ta kushesa, sai dai idan bata kula da kyau ta kallesa ba. Amma irinsu kam ai su ake kira da one in town nake gaya maka..." Ta ƙarashe maganar da iya gaskiyarta tana murmusawa. Kallonta Abba yayi da murmushi akan fuskarsa yana faɗin "Banda dai cika baki atoh, kuma suzo suyi kwantai anan gaba, duk da shima wancan ɗayan tuzurun an samu da ƙyar da suɗin goshi yau an ɗaura, dan har gwara wannan ɗin ma yana da nashi iyalin tun tuni..wai ina take nema..ko ba tare da ita kuka zo bane...?" Ya faɗa tare da kallon Ya Azeez ɗin daya sunkuyar da kai yana murmushi. Suna cikin haka Fahad ya shigo cikin falon bakinsa ɗauke da sallama wanda dawowarsa kenan daga rakiyar abokinsa da yayi ya tafi, da sauri ya ƙaraso gaban Abban ya rusuna cikin girammawa ya yiwa Abban nasa barka da dare haɗe da yi masa ban gajiyar taro, kafin ya juya ɓarayin Mami itama yayi mata. Amsawa sukayi dukkansu cike da kulawa, kafin kuma Abban yace su tashi su koma babban falo su jirasa idan ya kammala zai fito akwai maganar da yake so dama zaiyi dasu. Jinjina kai sukayi dukkansu kana suka miƙe atare suka fice daga falon zuwa babban falon gidan kamar yadda Abban ya umurcesu. Suna nan zaune Abban ya fito sanye da farar jallabiya ajikinsa wanda da alamu sai daya sake yin wanka kafin ya fito, ƙarasowa yayi ya zauna saman ɗaya daga cikin kujerun falon yana fuskantar su. Wanda da sauri dukkansu suka zamo daga saman kujerar da suke zaune akai lokaci guda suna daidaita zamansu a ƙasan kafet ɗin dake tsakiyar falon cike da girmamawa suna yi masa barka da fitowa. Amsawa yayi cike da kulawa, kafin ya ɗago kai a hankali ya kalli Ya Azeez daya sunkuyar da kai yana wasa da zoben azurfan dake hannunsa. Yace "AbdulAzeez ya gurin aikin naka, ina fatan dai komai yana tafiya dai-dai yadda ya kamata ko, ba wata matsala...?" Da sauri Ya Azeez ɗin ya ɗago kai jin irin tambayar da Abban yayi masa, kafin yace "Eh Abba Alhamdulillahi komai yana tafiya dai-dai yadda ya kamata mun gode Allah..." Jin irin amsar da Ya Azeez ɗin yaba Abban ne kuma yasa Fahad juyowa da sauri yana galla masa harara kafin yace "Wallahi ƙarya yake Abba, babu wani aikin da yake yi kawai ɓoye maka yake saboda bayaso kasan takamaiman abinda yake yi acan ɗin..." Wani kallon banza Ya Azeez ya ɗago kai ya watsa masa yana faɗin "Malam bada kai ake magana ba kayi mana shiru..faɗi ba'a tambayeka ba..." Ya faɗa lokaci ɗaya tare da zafga masa harara. Abba da tunda suka fara maganar ya kafesu da idanu kawai yana sauraren su, yayinda shi kuma Fahad ya ƙara matsawa gaban Abban da kyau yana faɗin "Wallahi Abba ƙarya yake yi kek..." Da sauri Ya Azeez ya katsesa da faɗin "Ka kiyayeni wallahi ka fita daga harkata, tunda ba kai aka tambaya ba, saboda haka ka barni inyi mai bayani da kaina..." Fahimtar da Abba yayi cewa akwai abinda Fahad ɗin ke son sanar dashi ne amma Ya Azeez ke ta kakkarewa yana hanasa, yasa ya ɗago kai ya kalli Ya Azeez ɗin da yay sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa yana faɗin "Sharri kawai yake son ƙulla min a gurinka Abba kum..." Ɗaga masa hannu Abban yayi yana faɗin "Ina jinka Fahad..." Ya faɗa kai tsaye cikin tsare gida yana kallonsa. Ɗan kallon gefen da Ya Azeez ɗin yake Fahad yayi kafin ya gyara zamansa da kyau lokaci ɗaya yana faɗin "Bai aikin komai fa Abba, keke napep kawai Abban Fadwa ya ƙarban masa a hannun wani mutumi yake ja..kuma tun..." Ɗaga masa hannun shima Abban yayi cikin ɓacin rai kafin yace "Amma tunda nake da kai ka taɓa sanar dani irin aikin da yake yi acan ɗin kenan...?" Da sauri Fahad ya girgiza masa kai cikin sanyi jiki kafin yace "A'a ban taɓa gaya maka ba Abba, amma shida kansa ya hanani yace kar in gaya maka..wai baya so ya takuraka kuma..." Wata uwar tsawa Abba ya daka masa a fusace yana faɗin "Tashi ka fita ka bani guri..mutumin banza kawai..." Ya faɗa a zafafe lokaci ɗaya yana nuna masa ƙofa, cikin sanyi jiki Ya Azeez ya ɗago kai da sauri yana kallonsa, kafin cikin hanzari ya ƙara matsawa gabansa ya duƙar da kai yana faɗin "Dan girman Allah Abba kayi haƙuri ka gafarceni, wallahi ba laifinsa bane laifina ne nine na hanasa ya gaya maka, amma kayi haƙuri ka fahimceni ban yi hakan da wata niyya ba, sai domin bana son in sake ɗora maka wani nauyi akanka bayan wanda kake fama dashi..." Ya ƙarashe maganar a sanyaye yana ƙara sunkuyar da kansa. Abba da tunda ya fara maganar ya kafesa da ido baya ko ƙiftawa, gaba ɗaya jikinsa sai yayi bala'in yin sanyi da maganganunsa. Domin tabbas yasan indai har AbdulAzeez cikakken ɗan Alhaji Naseer Arabi ne kuma jininsa yana yawo a jikinsa, to dole zaiyi gadon halayyarsa na rashin son dogaro da kowa sai Allahn daya haliccesa, shi dai burinsa a kullum a kuma koda yaushe shine ya nemi na kansa ya tsaya da ƙafafunsa baya son ya kasance mai dogaro da wani ɗan Adam balle har ya zame masa kaya ya ɗora masa nauyin kula da wasu al'amuransa, wanda kwata kwata hakan ba ɗabi'arsa ba ce kuma har ya koma ga mahaliccinsa bai taɓa damun kansa da neman wani abu a gurin kowa ba sai a gurin Allah. Lallai yau ya ƙara tabbatar da cewa AbdulAzeez jajirtaccen namijin duniya ne mai ƙwazo, da son dogaro da kansa. A hankali ya kalli Ya Azeez ɗin cikin natsuwa kafin yace "Na fahimceka AbdulAzeez..sai dai kuma inaso zan yanke wani hukunci a kanka, wanda nake fatan zai faranta maka kuma zaka karɓesa hannu bibbiyu bazaka taɓa yi min musu akai ba...?" Ya faɗa kai tsaye yana tsaresa da idanu. Kai Ya Azeez ɗin ya jinjina masa tare da cewa "Insha Allahu Abba, babu hukuncin da zaka yanke min wanda har zan ƙi karɓarsa koda kuwa hakan bai yi min ba..." Kai Abba ya jinjina shima cike da gamsuwa kana yace "Alhamdulillahi naji daɗin kalamanka, kuma tabbas hakan na min nuni da cewa ka ɗaukeni tamkar mahaifinka..dan haka kai tsaye nake roƙonka daka ajiye wannan ƙudirin dake zuciyarka a gefe ka karɓi abinda nake son gaya maka yanzu..." Ya faɗa a hankali yana mai ƙara nazarin hukuncin daya yanke a zuciyarsa yanzu, kuma yake son furtawa a fili. A hankali ya gyaɗa masa kai tare kuma da sunkuyar da kansa ƙasa yana faɗin "Insha Allahu Abba..." Sake kallonsa Abban yayi da kyau yana ƙara nazarinsa, kana kuma cikin tausasa murya yace "Akwai wasu sabbin shaguna na guda huɗu dake kasuwar Kurmi, sannan akwai guda biyu kuma dake kasuwar Kwari, ka haɗa duka na mallaka maka su halak malak sun zama mallakinka, kuma koda bayan raina zan faɗa kuma zan barshi a rubuce babu su a cikin lissafin dukiyata, wannan naka ne nine na baka su kyauta, dama kuma na gama ordern komai da za'a buƙata a shagunan, kuma insha Allahu ƙarshen watan nan kayan da nayi ordern zasu iso Nigeria dan haka ka zauna cikin shiri, sannan zan saka a ƙara gyara muku gidan motocina dake cikin gari, dan inaso zan ƙara muku jari kai da Fahad ku riƙa shigo da motocin kwatano da China, kamar yadda muka din gayi da mahaifinka lokacin da yana raye...." A razane Ya Azeez ya ɗago kai yana kallonsa, kafin ya juya da sauri ya kalli Fahad dake ta washe baki cike da farin ciki yana faɗin "Aboki kaji abinda Abba yake faɗa kuwa...?" Ya faɗa cike da matsanancin mamaki da al'ajabi yana kallonsa. Cike da tsananin farin ciki kuwa Fahad yace "Naji mana aboki ina matuƙar tayaka murna..." Ya faɗa fuskarsa ɗauke da tsananin farin ciki da jin daɗi. Ya Azeez kuwa gaba ɗaya rasa abun cewa yayi saboda tsabar farin ciki, wai yau shine ake maganar yi masa kyautar shaguna ɗai ɗai ɗai har guda shida sukutum a cikin garin Kano, kuma hakan duk bai isa ba har sai da aka ƙara masa da jarin motoci da gidan motocin kansa ɗungurungum duk dan ya ƙara inganta rayuwarsa. Kawai sai ya samu kansa da jin saukar wasu zafafan hawaye masu matuƙar ɗumi daga cikin idanunsa suna kwaranyowa saman kyakkyawar fuskarsa, da sauri Abba ya kallesa yana girgiza masa kai kafin yace "Da kasan irin tarin abun alkhairin da mahaifinka yayi min a rayuwa AbdulAzeez da bakayi mamakin duk abinda zanyi maka ko in mallaka maka ba, saboda duk wani arziki da zan samu yanzu ko in samesa a nan gaba to mahaifinka shine sanadi..domin shine ya koya min harkar kasuwanci sannan kuma ya nuna min yadda zan juya biyar ta zama goma, ashirin ta zama hamsin, a haka har na mallaki manyan shaguna na tara abun duniya fiye da zato da tunanin mai tunani. Amma duk da hakan dai-dai da rana ɗaya bai taɓa gwada min baƙin ciki ko hassada ba, haka zalika bai taɓa min gori ko ya nemi wani abu a gurina ba. To ni kuwa taya zan iya manta halaccin wannan bawan Allah a gareni..? Taya zan iya mantawa da iyalinsa har in gaza tallafawa rayuwarsu alhalin kuma suna neman taimakona...?" Wani irin miƙewa Ya Azeez yayi da sauri ya faɗa jikin Abba ya rungumesa ƙam ƙam tare da fashewa da wani matsanancin kuka lokaci ɗaya yana faɗin "Wallahi nama rasa bakin magana Abba, bansan da wane irin baki zan iya gode tarin alkhairanka a garemu nida mahaifiyata da ƙanwata ba, kai mutumin kirki ne Abba..kai mutumin kirki ne..." Yake faɗa yana ƙara fashewa da kuka. A hankali Abba yake bubbuga bayansa alamar lallashi, kafin kuma ya ɗagosa daga jikinsa yana share masa hawayen fuskarsa cikin tsananin nuna ƙauna da kulawa yake faɗin "Ya isa..ya isa ka daina kukan haka nan dan Allah, nidai fatana shine Allah ya tayaka ruƙo ya kuma baka damar kula da al'amuran kasuwancinka yadda ya kamata..." A hankali dukkansu suka amsa da "Ameen ya Allah Abba..." Suka faɗa a tare suna murmushi, kafin Fahad ya ƙara matsowa gabansu yana faɗin "Abba muna godiya sosai Allah ya saka da mafificin alkhairi ya ƙara girma da nisan kwana..." A hankali Abba dake murmushi irin nasu na manya ya masa da "Ameen ya Rabbi..sai a kula sosai, Allah yayi muku albarka yasa kuma a gama lafiya..." "Ameen Ameen..." Suka ce kana daga haka kuma suka ɗora da hirar kasuwanci. Sun daɗe dashi a falon suna tattaunawa, dan sai gurin ƙarfe 11:45pm. Sannan suka bar ɓangaren Abban, sukayi mai sai da safe suka wuce ɗakin Fahad, koda suka shiga basu wani tsaya komai ba sakamakon dukkansu dama kowanne jallabiyar da yayi sallah ce a jikinsa, dan haka kawai suka haye gado kowa ya nemi gurin bacci suka kwanta. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣5️⃣ Washegari 9am. Dai-dai gabaki ɗayansu zaune suke akan makeken dinning table ɗin gidan suna breakfast, Abbie, Ummi, Shatu, sai auta Zahra. A hankali kowa ke cin abincin dake gabansa cike da natsuwa, amma ban da Shatu wacce tunda ta zauna a gurin babu abinda ta iya ɗauka ta kai bakinta, gaba ɗaya ta rasa abinda ke damunta tunda ta tashi ta rasa gane kanta, sai faman jujjuya cokalin dake hannunta kawai take tana ɗan satar kallon Zahra dake zaune a kusa da Ummi tana cin abincinta hankali kwance babu abinda ya dameta. ****** A ɓangaren su Ya Azeez kuma dai-dai lokacin fitowarsu kenan daga ɗakin Fahad, cikin shirinsu tsaf, inda suke sanye da wata dakakkiyar farar shaddar gezner mai maiƙo da yarari a jikinsu ɗinkin samarin zamani masu ji da kansu. Kansu sanye da hular zanna bukar mai kalar brown irin zaren aikin dake jikin shaddar, sai agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannuwansu shima na kamfanin Rolex ne, ƙafafuwansu kuma duka sanye suke da rufaffen takalmin fata. Sai dai a kallon farko idan kayi musu zaka fahimci tsantsar kyau na musamman da shigar tafi yiwa Ya Azeez sosai, gashi dai komai anko suka saka domin ɗinkin da Fahad ɗin ne yayi musu wanda zasu saka ranar taron bikin, amma idan ka kallesu a lokaci guda zaka hango tsantsar zati da haibarsa uwa uba kyau da nasabarsa ga kuma wani kwarjini na musamman, fuskarsa na ta fitar da wani annurin farin ciki wanda yake jin yana taso masa tun daga can ƙasan zuciyarsa a hankali kuma yana mamaye illahirin ƙirjinsa. A hankali suka ƙarasa saukowa cikin falon inda suka iske Abba da Mami da Ibrahim zaune a dinning suna karyawa, cikin natsuwa suka ƙarasa suma kowanne yaja kujera suka zazzauna. Inda cikin tsananin kulawa Mami dake kallonsu fuskarta ɗauke da murmushi tace "Masha Allah tagwayen Abba da Mami, kunsha kyau abinku kun fito sak angwaye sai zuba ƙamshi kuke..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙarewa shigar tasu kallo kafin ta juya ta kalli Abba dake riƙe da kofin kunun tsamiya a hannunsa yana sha tace "Alhaji baka ga angwaye bane..banji kace komai ba...?" Ta faɗa still fuskarta ɗauke da wani ƙayataccen murmushi tana kallonsa. Murmushi Abban yayi shima kafin ya ajiye kofin dake hannunsa yana faɗin "Ai ni tun kafin ma su fito naji gabaki ɗaya falon ya gauraye da ƙamshi mai daɗi, baki ga har wani haske da walwali ko'ina ya ƙara ɗauka ba sai wani shaining muke muma mun samu tabarrakin sabbin angwaye...?" Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya cike da zolaya yana murmushi. Nan ma dukkansu murmushin suka sake yi kafin kuma Ibrahim ya kallesu a tare yana faɗin "Gaskiya kunyi kyau sosai my brothers, idan Aunty's ɗina suka ganku yau na tabbata sai sun ƙara ruɗewa sosai a kanku..." Dariya duk sukayi yayinda Abba yace "Ina zakuje ne haka da akasha irin wannan haɗaɗɗen wankan...?" Ya faɗa cike da yanayin barkwancin daya saba musu yana kallonsu. Ɗan juyawa sukayi suka kalli juna kafin daga bisani Ya Azeez yace "Gurin amaryarmu zamuje Abba amma bazamu daɗe ba insha Allahu yanzu zamu dawo..." Kai kawai Abban ya jinjina ba tare kuma da ya sake cewa komai ba, ya ci gaba da shan kununsa, kana suma suka soma cin soyayyen plantain da dankalin da Mami ta saka musu kana kuma suna haɗawa da tea. Bayan sun kammala ɗin ne Ibrahim ya miƙe ya wuce ɗakinsa domin yayi shirin tafiya makaranta, saboda yau yana da lecture ƙarfe 11am. Inda su kuma gaba ɗayansu suka miƙe suka koma cikin falo yayinda Abba da Mami kuma suka wuce sama inda ɗakin Abban yake. Suna nan zaune sai ga Abban ya sauko yayinda Mamin ke biye dashi a baya tana riƙe da brief case ɗinsa a hannunta, da sauri duk suka miƙe yayinda Ya Azeez ya matsa kusa da ita ya karɓi jakar hannunta, kana suka juya atare suka fice daga falon. Suna tsaye a farfajiyar gidan Abba ya fito ya samesu, suna ganinsa da sauri suka buɗe masa bayan motarsa ya shiga ya zauna, yayinda direbansa kuma ya taso da sauri yazo ya shiga gaban motar, ya kunna suna ɗaga masa hannu yaja, maigadi ya wangale musu gate suka fice daga gidan. Sai da suka ga fitarsu daga gidan kana suma suka ƙarasa inda motar Fahad ke fake daga gefe suka shisshiga inda Ya Azeez yaja motar a hankali suka fice suma daga cikin gidan. ******* Acan ɓangaren Shatu kuwa gaba ɗaya ta rasa meke mata daɗi, haka kawai take jin kanta cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, a haka har kowa ya gama breakfast ɗinsa duk suka miƙe, yayinda Abba ya wuce falonsa, Ummi da Zahra kuma suka wuce kichin, aka barta ita kaɗai ƙwal a dinning area ɗin, tayi zaune zuru ta tasa abinci a gaba, amma ta kasa kai koda loma ɗaya ne bakinta. Ganin duk sun tashi sun barta ita kaɗai ne yasa haka nan ta daure ta ɗan tsakuri dankali da kwai kaɗan taci, tasha ruwa kana ta miƙe ta tattare kayan ta kai kichin inda ta iske Ummi na ƙoƙarin ɗora girkin rana yayinda Zahra kuma ke gefe tana wanke wanken kwanukan da suka gama cin abinci suna taɓa hira sama sama. A hankali ta ƙarasa shiga cikin kichin ɗin ta ajiye filet da kofin dake hannunta, kana ta matsa gurin Ummin bayan ta yi mata sannu, ta fara ƙoƙarin tayata aikin da take yi. Ganin yanayinta ne yasa Ummin ta ɗan kalleta cikin nazari, kafin tace "Wai me yake damunki ne yau naga duk kinyi wani iri dake kamar mara lafiya, ko akwai abinda yake damunki ne dan tun ɗazu nake lura da yanayin ki, kwata kwata yau bakya cikin walwala, ko akwai inda ke miki ciwo ne...?" Jin abinda Ummin ta faɗa ne yasa tai rau rau da idanu kamar zata yi kuka kafin tace "Wallahi nima haka kawai nake jina wani iri Ummi, kamar bani da lafiya amma kuma babu inda ke min ciwo, daga ƙirjina ne dai kawai nake jin wani irin nauyi mara daɗi kamar wani abu zai sameni..." Cikin sauri Zahra ta bar abinda take yi ta juyo lokaci ɗaya tana kallonsu, kafin ta ɗan saki murmushi tace "Toh Allah yasa dai alkhairi ne Aunty Shatu, kuma ina fatan idan ma alkhairin ne Allah yasa haɗuwarki ne da tsantsareren saurayi wanda zai kasance mijinki abin alfaharinki a nan gaba, dan naga ko a novel ɗin hausa irin wannan yanayin da kikace kina ji, ake cewa anaji idan za'a haɗu da haɗaɗɗen saurayi mai kyau na nunawa a cikin taro ko Ummi...?" Ta faɗa da dukkan gaskiyata tana kallon Ummi data saki baki galala tana kallonta, kafin ta juya ta kalli Shatu data wani haɗe rai tana watsa mata harara tace "A'a a'a ni kam babu ruwana ban taɓa karanta littafin hausa na ci karo da hakan ba...." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana dariya. Zahra itama dariyar tayi tana faɗin "Allah kuwa Ummi haka ne, kinsan ance idan abun alkhairi zai sameka kana ji a jikinka, haka idan sharri nema, shiyasa akoda yaushe akeso ka dinga yiwa kanka addu'ar Allah ya haɗaka da dukkan alkhairin duniya da lahira..." Gyaɗa kai Ummin tayi cike da gamsuwa tana cewa "Ƙwarai kuwa uwata, haka maganarki take, to Allah ya haɗamu da dukkan alkhairinsa duniya da lahira..." Da Ameen duk suka amsa mata, kana Shatu ta ɗauki tumatur ɗin da Ummin ta fito dashi daga cikin fridge ta matsa gaban sink ta kunna fanfo ta fara wankewa a hankali, yayinda kuma a lokaci guda maganganun Zahra suke ta kai kawo a zuciyarta. ********* A dai-dai wannan lokacin kuma Ya Azeez ne da Fahad zaune a cikin wani ƙayataccen falo na gani a bada labari, dake cikin wani haɗaɗɗen gida mai rai da lafiya, gabansu kuwa wani ɗan madaidaicin ƙaramin teburi ne mai kyau da aka cikasa da abubuwan ciye ciye da juices masu sanyi kala kala. A hankali wata kyakkyawar budurwa da bazata wuce shekaru talati ba ta shigo falon yayinda a bayanta kuma wata matashiyar budurwa ce ke biye da ita ɗauke da wani babban farati a hannunta, wanda da ganinsu kasan cewa ƴaƴan manyan mutane ne, cikin natsuwa dukkansu suka ƙaraso cikin falon, inda direct babbar ta nufi gurin Fahad dake hakimce akan kujera ya zubo mata ido, cikin wani irin takun salo da iyayi irin na sangartattun ƴaƴan gata ta isa gabansa tana faɗin "Your welcome love, barkanku da zuwa..." Ta faɗa tare da zama a kusa dashi lokaci ɗaya tana sakin wani ƙayataccen murmushi. Basma Jada kenan kyakkyawar budurwa kuma ƴar gata a gurin iyayenta. Murmushin jin daɗi Fahad yayi tare da yi mata wani sassanyan kallo yace "Nagode amaryata..." Ya faɗa cikin nuna tsananin jin daɗi yana murmushi, kafin kuma ya juya ɓarayin da Ya Azeez ke zaune yana latsa wayarsa yace "Aboki ga fa amarya tamu ta iso..." Sai a lokacin ne Ya Azeez ɗin ya ɗago kai ya kallesu kafin kuma ya juya lokaci ɗaya ya harari ɗayar budurwar da tun da suka shigo falon ta tsura masa idanu ƙirr tana ta ƙare masa tun daga saman kansa har zuwa ƙasan ƙafarsa kamar zata cinyesa ɗanye, watsa mata harara yayi a fakaice kafin ya ɗan ja tsaki ƙasa ƙasa yana faɗin "Nifa na tsani kallon ƙurulla a rayuwata, haba mutum sai kace maye..." Ya faɗa cike da tsantsar takaici yana harararta. Karaf kuwa sai a kunnenta, aiko take taji wata masifaffiyar kunya gaba ɗaya ta dabaibayeta, da sauri ta miƙe tsaye bayan ta ajiye farantin data shigo dashi, ta juya da sauri cikin hanzari ta fice, kamar zata kifa. Wata muguwar harara ya rakata da ita har ta ƙarasa ficewa daga falon, kafin ya saki tsaki, kana ya juyo lokaci ɗaya yana kallon Fahad da amaryarsa da gaba ɗaya suka zubo masa idanu suna kallonsa, ɗan taɓe bakinsa yayi shima ya kallesu kana kuma ya saki ƙaramin murmushi yana faɗin "Barka da fitowa amaryar mu, ya taro kuma..." Ya faɗa tare da watsawa Fahad daya kasa ɗauke idanunsa daga kanta harara yace "Toh maye ai sai ka barta haka kuma da wannan mayataccen kallon naka, ka barta ta huta..." Dariya Fahad ɗin yayi yana faɗin "Ina ruwanka sa'idawa idan ma cinyeta nayi ai tawa ce ko Baby...?" Gyaɗa mai kai tayi a hankali tana murmushi, kafin kuma cikin nuna tsantsar wayewarta tace "Daga gani dai ba sai na tambaya ba wannan shine, amininka Azeez Arabi da kake ta bani labari na Kaduna ko...?" Da sauri Fahad ya gyaɗa mata kai yana faɗin "Shine kuwa Baby kin canka dai-dai..." Murmushi kawai tayi ba tare data sake cewa komai ba, suna cikin haka ne kuma wayar Ya Azeez ɗin ta ɗauki ƙara, da sauri ya zarota daga cikin aljihun wandonsa ya duba, ganin da yayi Ummansa ke kira ne yasa ya miƙe da sauri ya nufi hanyar waje tare da barin kiran nata ba tare daya ɗauka ba, har ya katse, sannan ya sake bin bayan kiran. Sun daɗe sosai a gidan dan sai gurin ƙarfe 11am. Sannan suka fito bayan sun shiga cikin gidan sun ƙara gaishe da iyayenta da sauran baƙinsu da basu gama tafiya ba, kana suka fito ta rakosu har gurin motarsu kafin suka yi mata sallama suka wuce. Tafe suke a hankali suna hirar abinda ya shafesu, inda anan ne Ya Azeez ke tambayar Fahad dalilinsa na matsawa a ɗaura masa aure ba tare da biki ba, kamar wanda ya auri bazawara alhalin kuma shi da kansa ya gaya masa cewa Basman budurwa ce ba bazawara ba. Idanu Fahad ɗin ya ɗan runtse a hankali kafin ya juyo gaba ɗaya yana fuskantarsa yace "Wallahi babu yadda na iya ne Aboki, ban san yadda zanyi da yarinyar nan ba. Inda dan ta nine wallahi da tun jiya a gidana zata kwana amma bani da yadda zanyi ne kawai saboda anfi ƙarfina, kuma tun farko da aka buƙaci hakan a gurina ban yi wani tunani ba na amince, shiyasa dole na cika alkawarin dana ɗauka, amma ka sani wallahi bada son raina bane hakan ta kasance, saboda ina matuƙar son Basma kawai dai babu yadda na iya ne..." "Ban gane ba, kamar ya babu yadda ka iya...?" Ya Azeez ya tambayesa cike da rashin fahimtar inda zancen nasa ya dosa. Fahad Yace "Wallahi nida kaina bansan haka abun zai zama ba aboki da tun farko ban amince da tsarinsu ba, amma gaba ɗaya nine da laifi, kuma ban san haka abun zai zo ya dameni ba daga baya da ko kwatanta yi ma banyi ba..." Fahad ɗin ya faɗa cikin tsananin damuwa da tashin hankali, dan gaba ɗaya sai yanzu ne yake daya sanin abinda yayi. Cikin rashin fahimta Ya Azeez ya sake cewa "Kai nifa duk ban gane nufinka ba har yanzu, ka fito fili kayi min bayanin abinda ke faruwa dalla dalla, dan in fi ganewa sosai da sosai..." Fahad kuwa da yaji gaba ɗaya har ya fara muzanta a gaban abokin nasa yace "Wallahi nine nayi sakaci aboki har hakan ta faru, da tun farko da iyayenta suka ce sai ta gama karatu sannan zasu aurar da ita inda nayi haƙuri da duk hakan bata faru ba, amma yanzu dana nace ai kaga gashi nan ina ji ina gani za'a mayar dani sauna kullum inta jerangiya a titi ina gararanban zuwa wajenta kuma wai da sunan tana a matsayin matata kuma amarya amma tana gidansu, har sai ta kammala karatunta sannan za'ayi biki ta tare a gidana, wannan wace irin lukutar masifa ce...?" Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya cike da damuwa yana kallon Ya Azeez daya wani taka burki da sauri ya gangara gefen titi ya tsaya kawai, yana kallonsa cike da tsantsar takaici yana ji kamar ya rufesa da masifaffen duka saboda tsabar baƙin cikin abinda yayi. Shi kuwa Fahad ganin yadda Ya Azeez ɗin ke masa wani mugun kallo ne yasa yasha jinin jikinsa, duk ya wani dabarbarce kana kuma cikin sanyi jiki yace "Toh ai na gaya maka ne dan ka bani shawara amma naga ka wani tsaya kana ƙare min kallo, ko har yanzu dai baka fahimci abinda nake nufi bane, saboda naga kamar sai kallon tuhuma kake min kana ƙara sanyaya min jiki...?" Ƙwaffa kawai Ya Azeez ɗin yayi ba tare kuma da ya ce masa komai ba, ya fara ƙoƙarin tada motar su wuce, a fusace Fahad ya riƙe hannunsa lokaci ɗaya yana harararsa yake faɗin "Wannan wane irin abu ne haka..ya na gaya maka magana kuma amma ba kace komai ba kuma kake ƙoƙarin shareni, ko nufinka maganata bata da wani amfani kenan...?" Idanu Ya Azeez ɗin ya buɗe sosai a kansa yana faɗin "Ashe ka gane nufina kenan, danni kaf a maganarka banga abun kulawa ba, wanda har mutum zai damu kansa da sai ya baka wata shawara akan wannan shirmen naka na banza da wofi..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da jan tsaki, kafin ya zura key da sauri ya tada motar, yayinda kuma yana ƙoƙarin ja, Fahad ɗin ya riƙe masa hannu da sauri yana girgiza masa kai lokaci ɗaya yana faɗin "Haba abokin, dan Allah karka yi min haka mana, kasan dai bani da wani abokin shawara duk faɗin garin nan sai kai, kuma bayan Ubangijina kai kaɗai nake dashi wanda zan iya faɗawa damuwata, dan girman Allah ka tsaya ka saurareni ka kuma nuna min inda kuskurena yake, wallahi zan gyara..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya cikin sanyin jiki yana kallonsa. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣6️⃣ A hankali kuwa Ya Azeez ɗin ya kallesa shima yana faɗin "Wallahi ka bani mamaki Fahad, ace kamar kai da tunaninka da komai amma har ka iya biyewa son zuciyarka ka aikata irin wannan wawancin, dan wannan ai babban wawanci ne da rashin lissafi, to wai kai mema ya shiga kanka ne da har ka biye musu aka aikata wannan ɗanyen aikin da kai...?" Bai yi magana ba illa sunkuyar da kai kawai da yayi yana sauke ajiyar zuciya. Ajiyar zuciyar Ya Azeez ɗin ya sauke yana ƙara runtse idanunsa cike da takaicin Fahad ɗin, kafin kuma ya jingina kansa da jikin kujerar motar yana ƙara haɗe fuskarsa yace "Wallahi kayi wauta Fahad, kayi rashin tunani, idan tsoron kada ka rasata ne kuma yasa ka aikata hakan, to kuwa na tabbata ita a gurinta ka gama zubarwa da kanka mutunci ne, dan wallahi anan gaba dole sai abinda take so kuma taga dama shi zatayi a cikin gidanka kuma kana kallo baka isa ka tsawatar mata ba, tunda tun farko kai ne ka nuna mata cewa duk abinda take so ko tayi shine dai-dai a gurinka. Amma inaso ka sani indai mata ne wallahi nan gaba sai kayi bala'in dana sanin biye matan da kayi, saboda kai shaida ne ban taɓa ɗora Fadwa akan irin wannan hanyar ba, amma yau fa wane irin zama muke yi da ita, aya ta ɗauke ni..meta maidani..? Duk fa kasan waɗannan abubuwan saboda babu abinda nake ɓoye maka kasan komai, wanda kuma a yanzu haka maganar da nake maka Fadwa na Abuja da sunan ta tafi bikin ƙanwar ƙawarta, kuma koda wasa ban san ta tafin ba, saboda bata gaya min ba sai da suka sauka sannan ta kirani take gaya min wai tana Abuja, wanda kai da kanka ka sani a duniya bani da wata damuwa sai Fadwa, Fadwa itace babbar matsalata kuma kasan wannan. Amma ban san meya shiga kanka ba har ya kaika ga sha'awar aikata irin wannan, wanda na tabbata tun farko daka nuna musu cewa zaka iya rayuwa ko babu ita, da tuni sunbi yadda kakeso, amma saboda shaukin soyayyarta ya gama rufe maka idanu ya hanaka ji da ganin komai sai ita, shiyasa ka yanke wannan hukuncin ba tare da tunani ko wani lissafi ba, kuma nayi mamaki da har su Abba suka iya biyewa wannan shirmen naka, basu taka maka burki ba..." Fahad ya saki ajiyar zuciya kafin yace "Wallahi duk na sani aboki, kuma ko Abba da kansa ma sai daya so nusar dani a lokacin ya nuna min rashin dacewar hakan, amma na dage na nuna masa ni na amince kuma babu komai, wallahi banyi tunani ba aboki ban yi lissafi ba. Sai yanzu gaba ɗaya na ke ji a raina ban kyautawa kaina ba, kuma banyi abinda ya kamata ba, amma yanzu meye abun yi..ya zanyi in nuna ni jajirtaccen namiji ne wanda zai iya nuna isa a gidansa..? Dan Allah aboki ka gaya min taya zan gyara kuskurena...?" Sai a lokacin ne Ya Azeez ɗin ya sake gyara zamansa da kyau yana fuskantarsa kafin yace "Uhmmm ai kamar yadda ka nuna musu cewa ka amince tun farko, to yanzu ɗin ma haka zaka koma ka sake nuna musu cewa baka amince ba, kawai tunda an ɗaura kana buƙatar matarka ta tare a gidanka, idan yaso ka yarda ta ci gaba da karatun acan gidanka, amma wannan tsarin nasu karka sake ka yarda yayi tasirin da komai sukace dole shi za'ayi, ka gyara tun kafin lokaci ya ƙure maka..." Gyaɗa kai Fahad yayi kafin yace "Insha Allahu kuwa aboki hakan zanyi, kuma tun yau zan fara yiwa Abba magana idan muka koma gida, dan Allah ya sani bazan iya haƙurin har nan da sati ɗaya zuwa biyu ba nima, dole ne za'a san abin yi..." Ya faɗa yana dafe kansa. Ya Azeez bai yi magana ba illa sauke ajiyar zuciya da yayi, ya kunna motar lokaci ɗaya ya tada suka soma tafiya a hankali, yayinda kuma suke ci gaba da tattauna maganar a tsakaninsu. ★★★★★ Acan ɓangaren su Shatu kuwa bayan sun kammala girkin ne ta fito ta koma ɗakinsu, tana shiga ta wuce toilet direct ta ƙara watso ruwa ajikinta ta fito. Kasancewar garin akwai ɗan zafi zafi ne yasa ko mai bata tsaya shafawa ba, ta buɗe wardrobe ɗinta ta zaro wata laloluwar doguwar riga kalar ruwan madara mai hannun shimi ta saka, kana kuma ta ɗan fesa turare kaɗan ajikinta. Koda ta gama shiryawan kuwa gado ta haye tai kwanciyarta abunta tai luf da nufin ta ɗan huta, kafin kuma lokacin sallar Azhar yayi ta tashi tai sallah. ********* A ɓangaren su Ya Azeez kuwa basu nufi gida direct ba, cikin gari kawai suka wuce gurin abokanansu, inda suka kusan wuni acan, dan sai gurin ƙarfe 4pm. Da wani abu sannan bayan sunyi sallar la'asar sukayi musu sallama, suka kamo hanyar gida. Wanda kuma suna ƙarasowa gidan ne suka iske Abba da Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai zaune a wata ƴar madaidaiciyar baranda mai kyau dake gefen koridon da zai sadaka da shiga cikin babban falon gidan, a hankali sukayi parking ɗin motarsu a farfajiyar gidan kana suka buɗe lokaci ɗaya suka fito atare suka nufi gurin su Abban, inda suna ƙarasawa dukkansu suka rusuna agabansu cike da girmamawa suna gaishesu. Juyowa Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai yayi ya kalli Ya Azeez dake durƙushe a agabansa yana gaishesa, domin a yadda yaji muryar tasa, da yanayin yanda yake gaishesan, sai take yi masa kama da wata muryar daya taɓa ji amma ya rasa tuna ko a ina ne ya taɓa jinta, amma kam tabbas ya taɓa jin irin kwatankwacin wannan muryar sak sai dai ya kasa tuna a inda ya jitan. Haka har suka gama gaishesu duk suka miƙe suka nufi cikin gida, amma Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya kasa ɗauke idanunsa daga kan Ya Azeez, wanda kuma har zuwa lokacin bai iya tantance a inda ya taɓa jiyo ko da mai kama da irin muryar ta Ya Azeez ɗin ba ne kawai dai hasashe yake, haka yay ta binsu da kallo har sai da yaga shigewarsu cikin gidan kana ya iya ɗauke idanuwansa daga kansu yana mai ƙara nazarin abun a zuciyarsa. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke tare da kallon Abba fuskarsa ɗauke da tsananin mamaki yake faɗin "Ni kuwa Alhaji sai nake ganin wannan yaron kamar ɗan wajen amininka Alhaji Naseer Arabi, dan naga kamar tasu tayi yawa ne har ta ɓaci wallahi...?" Murmushi Abba yayi ya kallesa kafin yace "Babban ɗansa ne mana AbdulAzeez, akwai kuma ƙanwarsa Imaan itama tana can Kaduna tare da mahaifiyarsu..." Cikin tsananin mamaki ya juyo yana dubansa, kafin kuma cikin sanyin jiki yace "Allah sarki Alhaji Naseer mutumin kirki, Allah yayi mishi rahama ya yafe masa kurakuransa..wallahi har yau na kasa manta karamcin wannan bawan Allahn, Allah yasa halinsa na gari ya bishi..." Da "Ameen..." Abba ya amsa masa, kana daga haka suka ci gaba da tattaunawa akan harkar kasuwancinsu. Sai gab da magriba kana bayan sun gama tattaunawan, Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya miƙe tsaye sukayi musabaha da Abba wanda ya rakasa har gurin motarsa sukayi sallama, direbansa yaja suka fice daga gidan. Yayinda shi kuma Abba ya juya kai tsaye ya wuce cikin gidan ya nufi ɗakinsa, domin ɗauro alwala ya wuce masallaci, dan yaji har an fara kiran sallar magriba. Wanda kuma a tare suka fito daga cikin gidan shi dasu Ya Azeez da Fahad har ma da Ibrahim dukkansu suka nufi masallacin, koda aka idar da sallar magriban kuma gaba ɗayansu basu fito daga cikin masallacin ba har sai da suka sallaci sallar isha'i kana suka fito a tare suka dawo gida. Inda direct kuma suna shigowa cikin falon dukkansu kai tsaye suka wuce dinning area, inda Mami ta gama shirya musu lafiyayyen girkinta suka zazzauna, Mamin da kanta ta miƙe tayi sarving ɗinsu inda ta zuba musu haɗaɗɗiyar jalop ɗin da tayi musu wanda taji hanta da kayan haɗi sai pepper meat, ta turawa kowannen su filet ɗin abincin gabansa, kafin itama ta zuba nata ta koma ta zauna a gefen Abba. Bayan sun kammala cin abincin ne kuma suka miƙe dukkansu suka yiwa Abba da Mami sai da safe, yayinda Ibrahim shima yayi musu ya wuce ya tafi ɗakinsa, kana su kuma suka haura sama zuwa ɗakin Fahad. ******* Washegari kuwa tunda sassafe Ya Azeez ya gama shirinsa tsaf, cikin wasu riga da wando masu kyau a cikin kayan daya taho dasu, sosai kayan sukayi masa kyau dai-dai gwargwado dan basu wani sha jiki sosai ba, gashi sun ƙara fito da asalin kyau da kwarjininsa a fili, uwa uba wani haɗaɗɗen ƙamshi mai daɗi dake tashi a jikinsa. Cikin natsuwa ya ƙarasa saukowa cikin falon yayinda kuma Fahad dake biye dashi a baya yake riƙe da jakarsa, kai tsaye suka ƙaraso gaban Abba da Mami dake zaune saman kujerun dake falon, yayinda Abba ya saki baki cike da mamaki yake kallonsu, kafin kuma ya juya ya kalli jakar dake hannun Fahad yana faɗin "Ba dai har ka fito ba kenan, tunda sanyin safiyar nan sai kace ana koranka...?" A hankali Ya Azeez ɗin ya durƙusa a gabansa yana faɗin "Eh Abba inaso ne dama in isa gida da wuri dan in samu damar yin magana da Umma dan ban riga na gaya mata yadda mukayi da kai ba, so nake sai na isa gidan tukunna..." Kai Abba ya jinjina cike da gamsuwa yana faɗin "Hakan yayi dai-dai kuwa, Allah ya tsare ya kiyaye hanya Allah kuma ya saukeku lafiya..." Da "Ameen..." Duk suka amsa atare, kana kuma daga haka Ya Azeez ya sake gyara zamansa cikin girmamawa yana faɗin "Abba dan Allah muna ƙara roƙon arziki ayi haƙuri a dubi buƙatar mu, wallahi Abba abin bai yi tsari ba kwata kwata kuma su iyayen yarinyar sune suka yanke hukunci ba tare da sun yi tunani ba, amma t..." "Amma me AbdulAzeez..? Abba ya faɗa a kausashe yana kallonsa, kafin ya ci gaba da faɗin "Kai a naka ganin kawai sune suka yanke hukunci ba tare da amincewarsa ba kome...?" Ɗan ƙara duƙar da kansa Ya Azeez ɗin yayi yana faɗin "Amma ya kamata su duba abinda ya dace da wanda bai dace ba kafin su zartar da hukuncin, wannan ai yana nuni da cewa su ba manyan mutane bane sam, saboda babu ta yadda za'ayi babban mutum da yasan ciwon kansa yayi irin wannan shirmen..." Da kallo kawai Abba ya bishi kafin ya ɗan saki murmushi a fili yace "Ka daina ganin laifinsu AbdulAzeez, ga ƙaton mai laifin nan tunda shine ya azalzala ya matsa yace dole sai an ɗaura auren kamar yadda yake so..dan haka laifinsa zaka gani ba nasu ba..." Abba ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana nuna Fahad da yayi kasaƙe yana kallonsu. Sai a lokacin ne kuma Mami tayi magana inda ta kalli Ya Azeez daya fututtuke ya dage wai dole sai an je an samu iyayen Basma amaryar Fahad an gaya musu cewa ya fasa jiran sai ta gama makaranta kafin ayi biki atare, kawai shi yanzu yake buƙatar matarsa, tunda an riga da an ɗaura auren kawai a kawo masa abarsa. Baki Mami ta taɓe cikin ɓacin rai tace "Toh wai waye kuka maida ƙaramin mutum ɗin da zai je yayi muku wannan aikin, ko kun haifemu ne da zaku dinga juyamu kamar waina kuna abinda kukeso...?" Ta faɗa a zafafe tana hararar Fahad ɗin daya duƙar da kai yana sauke numfashi. Abba kuwa miƙewa tsaye yayi yana faɗin "Ki barsu dai Fiddausi, ai nace zamuje anjima nida Alhaji Bello muji yadda zamuyi da iyayen yarinyar, idan ma basu yarda ba sai mu barsu da abinsu, su ida ƙarasa abinda suka fara, tunda mun riga munyi mai wuyar an ɗaura, sai su san abin yi kuma..." Ya faɗa tare da raɓewa ta gefensu ya wuce, miƙewa Mamin tayi tana faɗin "Aiko dai wallahi, tunda duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka, kuma duk abinda mutum ya zaɓa shi zai gani..." Ta faɗa cike da jin haushi tare da juyawa ta wuce tabi bayan Abba daya haura sama zuwa ɗakinsa. A sanyaye duk suka bisu da kallo, har suka shige, kana suka miƙe cikin sanyin jiki suma suka fice daga falon, yayinda Ya Azeez ke ta ƙara kwantarwa da Fahad hankali, yace ya natsu kar ya damu insha Allahu komai zaiyi dai-dai. A hankali suka fito farfajiyar gidan nasu, wanda ganin fitowarsu ne kuma yasa direban Abba tasowa da sauri ya ƙaraso gabansu, jakar dake hannun Fahad ya ƙarba ya saka a boot, kana ya buɗe masa gidan baya ya shiga ya zauna, kafin ya ɗan leƙo da kansa yana faɗin "Pls Dude ka kwantar da hankalinka, insha Allahu nan bada jimawa ba komai zaiyi dai-dai..kaji...?" Kai kawai Fahad ɗin ya ɗaga masa cikin sanyin jiki kafin yace "Insha Allahu aboki, Allah ya tsare ya saukeka lafiya ka gaida min dasu Umma. Sai mun yi waya..." Ya faɗa cikin ƙaƙaro murmushi tare da ɗaga masa hannu. Har motarsu ta fice daga cikin farfajiyar gidan Fahad na tsaye yana ɗaga musu hannu, har sai da maigadi ya mayar da ƙofar gate ɗin ya rufe sannan ya juya cike da kewa ya koma cikin gidan. ********** A ɓangaren Shatu kuwa, yau ɗin wani irin sakayau take jin kanta, zuciyarta babu nauyin komai, dan haka tunda ta tashi da asuba tayi sallah, ta koma bacci, bata tashi ba sai gurin ƙarfe 10am. Tana tashi kuma ta faɗa toilet tayo wanka ta fito, a gurguje ta hau shiryawa cikin wani rantsatstsen leshinta mai tsananin tsada da kyau kalar ja da baƙi, wanda aka yiwa ɗinkin doguwar rigar fitted. Koda ta gama shiryawa bata tsaya wata kwalliya ba, ta ɗan shafa hoda kawai a fuskarta, ta ɗan saka kwalli sannan ta shafa lipstick a laɓɓanta. Ba tare kuma data sake shafa komai a fuskarta ba, ta ɗauki fashion ɗan kunne ta saka a kunnenta, kana ta yafa wani ɗan siririn gyale kalar ja a kanta, ta sanya tsadadden takalminta mai tsinin dunduniya shima ja, sannan ta ƙarasa gaban madubi a gurguje ta fesa turare, ta ɗauki wayarta dake aje agurin ta fice daga ɗakin. Fuskarta ba wata kwalliya amma kuma duk abinka idan ka kalleta a lokacin saika so ka ƙara kallonta, saboda wani sihirtaccen kyau da shigar tayi mata, ta ƙara fito da zallar natsuwa da wayewarta. Koda ta sauko ƙasan kuwa Ummi kaɗai ta iske zaune a falon tana kallo, ganin kuma irin kallon da Ummin take mata ne, yasa ta wani ɓata rai ta juya tana faɗin "Ummi nayi kyau kuwa...?" Kaɗa kai Ummi tayi kafin tace "Ana ma magana ƴan matana..? Sosai kikayi kyau wallahi tubarakallah Masha Allah, sai ina kuma tunda safiyar nan akaci wannan uban gayun haka...?" Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana ƙare mata kallo. Ɗan kwaɓe fuskarta tayi kafin tace "Gidansu Basma Jada zani Ummi, ashe wai an ɗaura aurenta tun shekaran jiya, amma shine babu wanda ya gaya min sai jiya da daddare ne muna chat da Husna Baita take faɗa min, amma wai ɗaurawa kawai akayi ba'a yi bikin ba tukunna, sai nan da sati mai zuwa sannan za'a yi biki ta tare..." Gyaɗa kai Ummi tayi tana faɗin "Masha Allah Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya, Allah kuma ya nuna mana na ƴan baya lafiya..." "Ameen ya Allah..." Shatu ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa daga falon. Da sauri Ummi tace "Wai kina nufin a haka zaki fita ba tare da kinyi breakfast ɗin ba, ga can kuma abincinki akan dinning fa tun ɗazu har muka gaji da jiranki muka karya baki fito ba..." Fuska ta kwaɓe kafin tace "Ummi a ƙoshe fa nake, idan na dawo zanci..." Harara Ummin ta galla mata tana faɗin "Aiko babu inda zakije sai kinyi breakfast..." Ta faɗa cikin haɗe rai tana watsa mata harara, ganin babu yadda ta iya ne yasa ta juyo ta koma cikin falon kai tsaye ta nufi dinning area ɗin tana turo baki taja kujera ta zauna. Tea kawai tasha sai farfesun kaza data haɗa dashi, tana kammalawa kuma ta miƙe tsaye tana goge bakinta da tissue, saurin kallonta Ummi tayi tana faɗin "Ba dai har kin gama ba..." A hankali ta gyaɗa mata kai kafin tace "Na ƙoshi Ummi..." Ta faɗa a shagwaɓe tana shafa cikinta, kafin ta wuce ta nufi ƙofar fita daga cikin falon tana faɗin "Ummi na tafi sai na dawo..." Ta faɗa tare dasa kai da sauri ta fice daga falon. Tana fita harabar gidan kuwa direban su dake zaune akan benci ya taso da sauri ya ƙaraso ya buɗe mata wata farar mota ƙirar Vibe dake fake a harabar gidan ta shiga ta zauna kana ya mayar da ƙofar ya rufe, ya zagaya shima ya shiga mazaunin direba ya tada motar, maigadi ya wangale musu gate lokaci guda ya silala motar suka fice daga cikin gidan. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣7️⃣ Ƙarfe 2pm. Dai-dai Ya Azeez suka shigo garin Kaduna, direct gidan Ummansa suka nufa kamar yadda ya kwatantawa direban. Suna isa ƙofar gidan direban kuwa yayi parking, Ya Azeez ya buɗe motar a hankali ya fito, kafin cikin natsuwa ya juya ya kalli direban dake ƙoƙarin tayar da motar ya wuce yace "Ba dai nufinka tafiya zakayi ba tare daka tsaya ko ruwa ne ka ɗan sha ba...?" A hankali direban ya jinjina masa kai yana faɗin "Eh yallaɓai so nake in koma da wuri, saboda bana so inyi tafiyar dare, shiyasa nake so in juya da kafin duhu yayi saboda hanyar ba kyau..." Ɗan kwaɓe fuska Ya Azeez ɗin yayi yana faɗin "Aiko baka isa ba saika tsaya kasha ruwa ka huta kafin ka wuce..." Murmushi Nuhu direban yayi kana ya buɗe motar ya fito yana faɗin "Toh yallaɓai..." Ya faɗa tare da ɗaukar jakar Ya Azeez ɗin kai tsaye suka nufi cikin gidan a tare bakinsu ɗauke da sallama suka shiga. Umma ce zaune akan tabarma ita kaɗai a tsakar gidan yayinda take riƙe da littafin Husnul Muslim a hannunta tana karantawa, jin sallamarsu ne yasa ta ɗagowa da sauri fuskarta ɗauke da murmushi take faɗin "Waalaikums salamu, maraba da baƙin Kano..yanzu kuke tafe da ranan nan...?" Ta faɗa cike da kulawa tare da ajiye littafin dake hannunta, ta miƙe lokaci ɗaya tana ƙara yi musu barka da zuwa tace "Ku zauna mana..." Ta faɗa tana wucewa ta shiga cikin ɗaki da sauri ta ɗauko wani sabon kofin jug da ƙananan kofinansa guda biyu, ta fito taje ta ɗebo musu ruwan randa mai sanyi ta kawo gabansu ta ajiye, kana ta ƙara komawa cikin ɗakin ta ɗauko wata ƴar madaidaiciyar kula da suke zuba abinci, ta haɗo dasu filet da cokula ta kawo musu. Sai data zuzzuba musu kana ta koma gefen tabarman ta zauna suna ƙara gaisawa, yayinda take tambayar ya suka baro su Abba da Mami, suka amsa mata da lafiya ƙalau sunce ma agaisheta. Har Nuhu direba ya kammala cin abincinsa yasha ruwa, amma Ya Azeez shi ko taɓa cokalinsa bai yi ba, ganin haka yasa Umma juyawa ta kallesa, kafin cikin kulawa tace "Kaci abincin mana karya huce, idan ya huce bazai maka daɗin ci ba..." A hankali ya kalleta kafin yace "Zanci Umma, so nake in ɗan ƙara hutawa tukunna..." Kaɗa kai kawai Umman tayi ba tare da tace komai ba, yayinda shi kuma Nuhu direba ya miƙe yana faɗin "Yallaɓai zan wuce..kar dare yayi min a hanya..." Ya faɗa tare da ɗan duƙawa yana yiwa Umma sallama, bayan tayi masa fatan alkhairi da addu'ar sauka lafiya ne kuma ta ƙara yi masa godiya kana tace ya gaishe mata dasu Mami da Abba dasu Fahad da Ibrahim, ya amsa mata da Toh, kana Ya Azeez ya miƙe domin yi masa rakiya suka fice daga gidan. Ya Azeez kuwa sai da yaga tafiyarsa kafin ya dawo cikin gidan, kusan Umma ya ƙaraso ya zauna yana sauke numfashi. Ɗagowa Umman tai ta kallesa kafin kuma cikin kulawa tace "Ya hanya, ya ka baro mutanan gidan...fatan anyi biki an ƙare lafiya...?" Cikin sanyin muryarsa yace "Alhamdulillahi su Mami duk suna gaisheki, Abba ma yace a gaisheku da Imaan..." Ya ƙarshe maganar lokaci ɗaya yana jayo filet ɗin abincin da Umman ta rufe masa ya buɗe, ya ɗauki cokalin ya soma cin abincin a nutse hankalinsa kwance, yayinda gefe guda kuma suke taɓa ƴar hira a tsakaninsu. Suna tsaka da hirar tasu ne kuma aka kira la'asar, dan haka ya miƙe ya ɗauki buta, yaje ya ɗauro alwala ya fice zuwa masallaci, koda ya dawo ya iske Umma itama har ta idar da tata sallar tana zaune akan tabarma jikinta sanye da hijabin da tayi sallah. Dan haka yana zama suka cigaba da hira, inda a nan ne kuma Ya Azeez ɗin ke gaya mata irin kyautar abun arzikin da Abba yayi masa, har kawo jarin da yace zai ƙara musu shida Fahad su haɗa hannu gurin ƙara yalwata harkar kasuwancinsu, da yace ya basu gidan motocinsa su dinga saro motoci daga Kwatano da China suna shigowa dasu gida Nigeria. Umma kuwa tun kafin ya ƙarashe bayanin da yake mata idanuwanta suka cika taf da hawayen farin ciki, dama ashe akwai ranar da farin cikinsu zai dawo garesu..? Ashe akwai wanda zai tallafi rayuwarsu ya agaji maraicin ƴaƴanta..? Lallai wannan mutumin kirki ne, ita kam bata san da wane irin baki zata iya gode tarin alkhairansa a garesu ita da ƴaƴanta ba. Da mamaki tace "Yanzu duk wannan abun alkhairin wa kai kaɗai bawan Allahn nan yayi su Yayan Imaan...?" Ta faɗa cike da tsananin farin ciki da mamaki tana kallonsa. Ɗauko jakarsa yayi tare da buɗewa ya zaro wata ɓaƙar leda a ciki ya miƙa mata yana faɗin "Gashi wannan ma ke yace in kawowa..." Zaro idanu tayi da mamaki tana ƙara kallon ledar, kafin tasa hannu ta ƙarɓa ta warware tana faɗin "Allah sarki shidai baya taɓa gajiya da abun arziki...mun gode..mun gode Allah ya saka masa da mafificin alkhairi ya ƙara masa buɗi..." Ta faɗa tare da warware ledar tasa hannu tana ƙoƙarin fito da abinda ke ciki, baki ta buɗe sakamakon ganin kuɗi ne rafar ƴan ɗari biyar biyar sababbi fil fil har guda huɗu a ciki, ware ido tayi cike da tsananin mamaki tana faɗin "Ikon Allah, kaga ashe kuɗi ne aciki..." Ta faɗa cike da tsantsar mamaki tana nuna masa kuɗin, zaro ido yayi cike da mamaki dan shima karan kansa bai san kuɗi ne a ciki ba, dan yadda ya bashi a kanannaɗe a leda haka ya saka a jakarsa ba tare daya buɗe yaga ko mene ne a ciki ba, dan shi irin mutanen nan ne waɗanda basu iya shisshigi ba kwata kwata, kuma basa so ayi musu. Da sauri yasa hannu ya karɓi kuɗin ya jujjuya a hannunsa, kafin ya saki murmushi yana faɗin "Allah sarki Abba, wallahi Umma mutumin nan akwai kirki, har dubu ɗari biyu fa..? Wannan ai sai dai kija jari kawai kita kasuwanci abinki..." Gyaɗa kai kawai tayi ba tare da tace komai ba, ranta fari tas kyautar naira dubu ɗari biyu ƙyal ba tare da aikin komai ba, itako dame zata iya biyan wannan bawan Allah..? Sosai bakin Umma yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki, dan rabonta da riƙe kuɗi irin haka tun kafin karayar arzikin mijinta, dan tunda komai nasu ya ƙare bata taɓa tunanin ko a mafarkin zata riƙe dubu hamsin nata na kanta bane a lokacin, ballantana kuma a nan gaba. Sun daɗe suna tattaunawa akan kuɗin, tare da yanke shawarar abinda ya kamata Umman tayi dasu. Inda Ya Azeez yace ta cigaba da saro atamfofi da lesuka ta dinga saidawa kafin kuma aga abinda Allah zaiyi, kuma itama tayi na'am da wannan shawarar sosai, dan haka tace washegari da kanta zata shiga kasuwa ta samu shagon ƴan sari inda zata dinga zuwa da kanta tana saro kayanta. Haka Imaan ta dawo ta samu wannan kyakkyawan labarin, tayi matuƙar murna sosai itama, kuma ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari akan shawarar da Ya Azeez ɗin nata ya kawo. Nan ya kusan raba dare suna ta hirar duniya, dan sai gurin ƙarfe 11pm. Sannan yayi musu sai da safe ya tashi ya wuce gida. Washegari kuwa tun ƙarfe 10am Umma ta shirya ta tafi kasuwa, inda akayi mata kwatancen shagon Ɗan Fulani wani mai sayar da atamfofi da lesuka akan farashi mai sauƙi da rahusa, direct aka rakata har shagonsa inda tayi sa'a kwanansa biyu kenan da dawowa daga Lagos ya kawo kaya sosai. Nan ta zage ta zaɓa aka haɗa mata komai da komai, sannan ya bata akan farashi mai sauƙi yadda idan ta siyar itama zata samu nata akai. Koda ta dawo daga kasuwar da kanta ta shisshiga gidajen maƙotansu ta kai musu kayan ta gaya musu duk mai so tana saidawa, kuma komai mutum yake so ya faɗa ko menene idan bata dashi ma zata ɗauko masa. Kan kace me, tuni kasuwanci ya fara haɓɓaka dan ta kai yanzu kome ake so tana gida daga zaune zata kira ɗan fulanin a waya ta gaya masa duk abinda takeso, ya haɗa komai yaba yaron shagonsa ya kawo mata har gida. ******** ********* A ɓangaren Fadwa kuwa yau kimanin satinta biyu kenan cif a garin Abuja, kuma duk wannan tsawon kwanakin bata taɓa koda kiran Ya Azeez a waya bane, haka kuma shima tun ranar da suka tafi data kirasa bai ƙara koda kwatanta kiran layinta bane har yau tsawon kwana goma sha biyar. Wanda ita Fadwa anata ɓangaren tun ranar data kirasa ta sanar mai da tafiyar tata bata ƙara kunna wayarta ba har yau, ballantana tayi tunanin kiransa ta bashi haƙurin jinta shiru da yayi bata dawo ba har tsawon kwanaki da yawa haka. Gararin gabanta kawai take yi babu abinda ya dameta, shima kuma ana shi ɓangaren haka ne, dan ko kaɗan bai taɓa ɗorawa kansa damuwar rashin dawowar tata ba har lokacin, wanda shi a nashi ganin ma gwara ya zuba mata idanu kawai yaga iyakar gudun ruwanta. Wanda kuma ko kaɗan rashin jin ɗuriyar tasa da batayi bai taɓa damunta ba, abinda taso taga dama kawai shi take yi abinta. Sashe guda aka ware musu a cikin rantsatstsen gidan suke zaune su kaɗai abinsu, gashi kullum rana ta duniya sai direba ya kwashesu sun fita yawon zaga gari, duk wani gurin shaƙatawa sai sun leƙa shopping mall kuwa iri iri babu wanda basu shiga sunyo siyayyan kaya ba. Fadwa an samu abinda akeso dan haka ko maganar komawa gida bata so ayi mata, shiyasa koda Hajiya Labiba da Hajiya Zalika suka shirya komawa Kaduna tun washegarin da aka kai amaryar cikinsu babu wanda yabi ta kanta balle suyi mata maganar komawa gida, kuma itama bata yi musu ba. Haka kuwa tana kallo suka gama shiryawa, abin takaicin kuma har da ita a ƴan rakiyarsu zuwa airport, tana kallo kuma suka shiga jirgi dan komawa amma ko ajikinta, sai ma ɗaga musu hannu da ta dinga yi tana faɗin "Allah ya tsare ya saukeku lafiya ƙawata, sai mun dawo muma agaidasu Alhajin..." Hajiya Lubna dai kawai da ido take binta, dan ita zuwa yanzu al'amarin Fadwa gaba ɗaya ya daina bata mamaki, tsoro yake bata. Kamar kullum yau ma tunda safe suna gama karyawa direba ya kwashesu suka fice, yau ɗin wani haɗaɗɗen gurin shaƙatawa sukaje, daga can kuma suka wuce Sahad Store inda suka danƙaro siyayyarsu. Sai yamma liƙis suka nufo gida. Washegari kuma tunda sassafe suka tashi da shirin komawa gida, dan haka yau tunda Fadwa ta tashi take ta wani kumbure kumburen fuska da baki. Hajiya Lubna kuwa duk tana lura da ita kuma taga take takenta amma ko kaɗan bata tanka mata ba, dan ta fahimceta so take kafin su bar garin su raba abun faɗe a gaban ƙanwarta da mijinta, haka kawai tasa ta barwa kanta abun gori, shiyasa tayi banza da ita taƙi kulata, har tai ta gama ba tabi ta kanta ba. Ƙarfe 3pm. Dai-dai suka gama shiryawa direba ya kwashesu zuwa airport. ********* Ƙarfe 6pm. Dai-dai dawowarsa kenan daga cikin garin inda ya faka napep ɗinsa a ƙofar gida ya fito ya nufi cikin gidan, yau ɗin a gajiye yake tuɓus, dan haka ya tashi aikin tunda wuri ya nufo gida dan ya samu ya ɗan watsa ruwa ajikinsa ko zaiji daɗi, ɗaki ya shiga ya ɗauko bokitin wanka ya ɗebi ruwa ya fito ya shige banɗaki. Koda ya fito jallabiyarsa kawai ya zura ya ɗan fesa turare, ya ɗauki casbahansa da wayarsa ya fito, yana ƙoƙarin kulle ƙofar ɗakin ne ya juya ya kalli tsakar gidan, wanda ya haɗa uban ƙura ko'ina yayi bututu saboda rashin samun gyara kwana biyu da baiyi ba, dan yanzu kullum idan ya tashi tunda sassafe ya gama ƴan aikace aikacen da yake yi irinsu gyaran ɗaki da ɗebo ruwa, baya samun tsayawa yin sharar tsakar gidan yake ficewa, kuma baya dawowa gidan sai dare, shiyasa baya samun lokaci sosai saboda abubuwa sunyi masa yawa, ga kuma shirye shiryen tafiyarsu China shida Fahad sai ƙara matsowa take. Sosai yau yake ƙara jin tsananin takaici da baƙin cikin rashin Fadwa a cikin gidan, dan ko babu komai mutum ma rahama ne, koda kuwa bazai yi maka aikin komai ba, idan kana jin motsinsa zaka dinga jin daɗi. Ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yayi kamar yadda take bunne a zuciyarsa, amma Fadwa kam ta gama kaishi bango, kuma dole zai ɗauki mataki akanta. Haka har ya gama kulle ƙofar ɗakin ya fita zuwa masallacin dake kusa dasu zuciyarsa tafasa take. Koda aka idar da sallar magriban bai fito daga masallacin ba, har sai da aka kira isha'i yayi sannan ya fito riƙe da casbahansa a hannu ya nufo gidan, yayinda yake tasbihi a zuciyarsa. A hankali ya shiga layin nasu wanda kuma yana shanyo kwana tun kafin ya kai ga isa ƙofar gidan ya hangi wata tsaleliyar farar mota fake a ƙofar gidan, cak ya tsaya daga ɗan nesa kaɗan yana kallon motar, yayinda a zuciyarsa kuwa mamaki yake da tambayar kansa, waye yazo yayi masa banzan parking haka ya rufe masa ƙofar gida ruf..? To ta ina zai shiga gidan kenan..? Ganin an buɗe gidan baya ne an zuro ƙafa mai ɗauke da haɗaɗɗen takalmi mai tsini ana ƙoƙarin fitowa yasa da sauri ya ƙaraso gurin yana kallon wacce ke ƙoƙarin fitowar, wanda ta cikin motar itama take ƙare masa kallon tsaf, kafin kuma ta ƙarasa fitowa cike da gadara tana wani irin yatsine fuska a wulaƙance tana kallonsa. Ganin yadda yake mata wani ƙasƙantaccen kallo ne yasa tasha jinin jikinta sosai, amma ta dake bata nuna ba, sai ma juyawa da tayi cike da yanga ta zura kanta cikin motar ta ɗauko jakarta da ɗan madaidaicin akwatinta sai wata ƙatuwar farar leda dake cike da tarkacen siyayyarta, kana ta matsa tana yiwa direban sai da safe, kafin kuma ta juya cikin takunta na isa da taƙama ta raɓa ta gefensa ta nufi cikin gidan. Wanda yana ganin haka shima ya rufa mata baya da sauri yana faɗin "Karki sake ki shigan min ɗaki, kizo ki koma inda kika fito...." Ya faɗa da kakkausar murya yana nuna mata ƙofar gidan. Juyowa tayi tana watsa masa wani mugun kallo kafin tace "Kamar ya in zo in koma inda na fito, ban gane nufinka bane....?" Ta faɗa cikin tsantsar rainin hankali tana watsa masa harara. Bata gama rufe baki ba, ya sake daka mata wata uwar tsawar data gigitata lokaci ɗaya ta zaburar da ita, ta juyo da hanzari tana kallonsa, a fusace ya watsa mata wani ƙasƙantaccen kallo yana faɗin "Nace karki sake ki shigar min ɗaki, ki koma inda kika fito Fadwa bana buƙatar ganinki acikin gidana ki fita ki tafi...." Ya faɗa a zafafe yana nuna mata ƙofa. Wani wulaƙantaccen kallo ta aika masa tana ƙara haɗe fuskarta kafin tace "Sai me dan ka hanani shiga wannan ruɓaɓɓen ɗakin naka, wanda babu komai a cikinsa sai tarkacen komatsai kamar zauren Almajirai, nace sai me AbdulAzeez...!?" Ta faɗa tana huci haɗe da zafga masa harara, kafin kuma ta juya lokaci ɗaya tana ƙoƙarin tura ƙofar ɗakin. Wani ɓacin rai ne mai tsananin zafi ya tokare zuciyar Ya Azeez, idanuwansa sun rufe gabaki ɗaya ko gani baya iya yi, a harzuƙe ya damƙota, sai ji tayi ƙiiiii ya jawota baya da ƙarfi ya fizgota kamar wata tsumma ya hankaɗeta tayo baya a tsorace tayi taga taga zata kifa, da sauri ta kama kyauren ƙofar ɗakin ta riƙe. Cike da tsananin mamaki da al'ajabi take binsa da kallo kafin tace "Wai me yake damunka ne haka AbdulAzeez...?" Ta faɗa a tsorace tana binsa da kallo, bai kulata ba illa sake nuna mata ƙofa da yayi yana faɗin "Nace ki bar min gidana bana buƙatar ki a cikinsa, ki koma inda kika fito kije kici gaba da duk abinda kika ga dama babu abinda ya dameni..amma gidana kam kin bar ƙara ko kwana ɗaya ne a cikinsa, yau ba sai gobe ba zaki bar min gida ki kama gabanki..." Baki kawai Fadwa ta buɗe galala tana kallonsa kafin ta saki tsaki tace "Toh wai sai me idan na bar gidan naka, sai kace wani gidan arziki daka damu mutane da abar maka gidanka, abar maka gidanka sai kace gidanka kona uban...." Bata ƙarasa ba taji saukar wasu zafafan maruka har biyu masu azabar raɗaɗi da zugi Ya Azeez ya wanke fuskarta dasu dama da hagu, lokaci guda kamar gilmawar walƙiya haka taji saukar marukan akan fuskarta. Wanda saboda tsabar azaba bata san lokacin data faɗi zaune a tsakar gidan ba ta dafe kumatunta dake mata mugun raɗaɗin azaba, tana bin Ya Azeez ɗin da kallo mai cike da tsantsar tsoro yayinda kuma hawaye ke shatata a fuskarta kamar an buɗe famfo. _______________________ #Barkan mu da juma'a hajji babbar rana, Allah ya sadamu da dukkan alkhairin dake cikin wannan rana, ya kuma karemu ya kiyaye mu daga sharrin dake cikinta.. ________________ *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 2️⃣8️⃣ Ko bi takan kukan da take bai yi ba, ya ƙara matsawa gabanta lokaci ɗaya yana nuna ta da yatsa yace "Wannan shine na farko kuma na ƙarshe Fadwa, duk abinda zakiyi karki sake gigin sako iyayena a ciki, kuma ko wace irin rashin kunya ce akanki ki dinga taunata kafin ki yarda ta fito daga bakinki kice zaki furtata, ni nan da kike gani ba lusarin namiji bane da zaki maidani shashasha mara tunani, duk abinda kikeyi ina sane kawai ƙyaleki nake yi, ba kuma wai dan ina tsoronki bane yasa nake ɗaga miki ƙafa kawai ina miki haka ne saboda darajar mahaifinki, amma ke kanki kin sani bayan shi baki da wani amfani a wajen AbdulAzeez, ke ba komai bace a cikin rayuwarsa face banza, baki da wani amfanin da kike yi masa...." Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya da hargowa. Wani kukan baƙin ciki da takaici Fadwa ta fashe dashi kafin ta miƙe itama cikin ihun kuka tana faɗin "Sai me AbdulAzeez...nace sai me..nima ai ba amfanin komai ɗin kake yi min ba, wanene kai..? Meye kai ɗin da har Fadwa zata damu da rashinka a rayuwarta...meye kai me kake dashi, dame kake taƙama wanda har zanyi takaicin ace yau na rasaka..? Kai ɗin banza kai ɗin wofi me ka taɓa tsinana min a zamana da kai..me na ƙaru dashi duk tsawon wannan watannin da nai a tare da kai..? Ka sakeni tunda bani da wani amfani a wajenka, ka sakeni ka gani AbdulAzeez idan zan ƙara ko da second ɗaya ne a wannan matsiyacin ruɓaɓɓen gidan naka, da kake tutiya dashi kake wani ɗaga hanci kana tinƙaho da ɓaɓatu sai kace naka, ka sakeni ka gani idan daga yau rayuwar Fadwa zata wulaƙanta kota ƙasƙanta...AbdulAzeez ka sakeni nace...!" Ta faɗa a zafafe cikin hargowa tana ƙara fashewa da kuka. Da kallo kawai Ya Azeez yake binta lokaci ɗaya kuma sai jikinsa yay bala'in sanyi, wani irin tafarfasa zuciyarsa ke yi idanuwansa kuwa sun kaɗa sunyi jajir saboda tsabar baƙin ciki da tashin hankali, kai kawai ya kaɗa kafin ya juya da sauri zai fice daga gidan, ganin haka yasa Fadwa tashi da sauri tana kuka tasha gabansa tana faɗin "Ina zaka tafi kuma ba tare daka sakeni ba...?" Ta faɗa kai tsaye cikin tsantsar rashin tsoro da bushewar zuciya tana watsa masa mugun kallo. Matsar da ita gefe yayi a hankali yana ƙoƙarin danne ɓacin ran dake taso masa, ya raɓa ta gefenta zai wuce, da sauri ta sake shan gabansa tana watsa masa wani mugun kallo da idanuwanta da suka kaɗa jajir saboda tsabar kukan data sha, kafin kuma cikin tsananin ɓacin rai tace "Wallahi babu inda zakaje saika sakeni AbdulAzeez, indai kai cikakken ɗan halak ne kuma cikin uwarsa da ubansa ba shege ba, to yau ka sakeni ka sawaƙe min wannan ƙaddararren munafukin auren naka nima in huta da wannan masifaffiyar jarabar ko zanyi rayuwar ƴanci da salama..." Sosai ran Ya Azeez ɗin ya ƙara ɓaci, dan hatta jikinsa rawa ya ɗauka. Ƙasa yayi da kansa yana ƙara jin wani ɗaci da tsananin baƙin ciki a cikin ransa, ɗagowa yayi yana kallon Fadwa da idanuwansa da suka ƙara runewa da zallar ɓacin rai da tsantsar damuwa, jikinsa har rawa yake, saboda tsabar baƙin ciki da tashin hankali, yayinda a lokaci guda kuma maganganunta suke ƙara kai kawo a ƙwaƙwalwarsa, cikin ƙaraji kunnuwansa ke masa amsa kuwwar muryarta tana ƙara maimaita masa. "Indai kai cikakken ɗan halak ne kuma cikin uwarsa da ubansa ba shege ba, to ka sakeni ka sawaƙe min wannan ƙaddararren auren naka nima in huta da wannan masifaffiyar jarabar ko zanyi rayuwar ƴanci da salama...!!! Sosai idanuwansa suka ƙara kaɗawa jajir, jijiyoyin kansa suka fito raɗa raɗa agaban goshinsa, da ƙyar ya buɗe baki cikin tsananin ɓacin rai ya furta "Kije na sakeki saki ɗaya Fadwa, ki fita ki bar min gida..." Ya faɗa muryarsa cike da amon sauti mai cike da tsantsar takaici da ɓacin rai. Rass rass rasss! Gaban Fadwa ya yanke ya faɗi, yayinda a kuma lokaci guda fargaba da tsananin tashin hankali suka ziyarceta, amma sai bata nuna ba tayi ƙoƙarin ɓoye fargabarta da tashin hankalinta. Murmushin yaƙe ta saki a ƙoƙarinta na son ɓoye razanarta tace "Sai me dan ka sakeni AbdulAzeez..Nace sai me..? Mena tsinta a gidan naka dama in banda baƙin ciki da ƙuncin rayuwa..? Kuma da kake maganar in fita in bar maka gidanka ai naga nan ɗin ba gidanka bane kaima haya ka kama, kuma duk abinka dai dole kaima ka fita ka barwa masu gida gidansu tunda bana gado bane..." Wani ɓacin rai mai zafi ne ya ziyarci zuciyar Ya Azeez, haɗe fuska yayi ba tare kuma da ya ce komai ba ya juya kawai yasa kai ya fice daga cikin gidan. Ganin haka yasa ta bishi da sauri har ƙofar gidan, sai dai ko kafin ta cimmasa har ya sha kwana yabi ta lungun bayan gidansu ya fice daga layin gabaki ɗaya. Dawowa tayi cikin gidan a ƙofar ɗakin ta tsaya, sai a lokacin ne kuma wani kukan nadama ya taho mata, mai cike da tsantsar danasani da baƙin ciki. "Yanzu fa shikenan Ya Azeez ya saketa ta zama bazawara kenan..? Yanzu ta tashi daga sahun matar aure ta koma bazawara..." Wani gefe na zuciyarta kuwa cewa take "Toh ai farin ciki ya kamata kiyi Fadwa ba baƙin ciki ba, tunda dama abinda kike muradi kenan, kuma anyi miki kamata yayi ki murna ki nuna jin daɗinki ba ki tsaya kuka ba banza kina ƙara ɓatawa kanki lokaci ba..." Saurin gyaɗa kanta tayi tana sakin murmushi, kafin ta jinjina kai a hankali tana faɗin "Tabbas kuwa, kuma yanzu ne nake da iko da lasisin da zanyi duk abinda nakeso kuma nake buri..." Ta faɗa a fili yayinda kuma a lokaci guda take jin wani irin sanyin daɗi na ratsa zuciyarta. A sanyaye ta shiga cikin ɗakin, direct ta wuce uwar ɗaka ta fara harhaɗa kayanta a babban akwatinta, sai data cika akwatin taf da kayanta, sannan ta gyara zaman gyalen dake kanta ta ɗauki ƙaramar jakarta da wayarta ta zura flat shoe a ƙafarta saɓanin ɗazu data dawo da mai tsini a ƙafarta. A hankali take jawo akwatin har ta fito dashi daga cikin ɗakin, sai a lokacin ne kuma ta samu zarafin duba agogon wayarta ƙarfe 9:20pm ta gani, saka wayar tayi a cikin jakarta kana ta ratayar jakar a kafaɗarta. Cikin sanyi jiki take jan akwatin da ƙyar, da haka har ta samu ta fice daga cikin gidan. Koda ta ƙarasa bakin titi ta daɗe a tsaye kafin da ƙyar ta samu napep, sai da ta gaya masa inda zai kaita sannan ta hau yaja suka wuce. Sai da taga mai napep ɗin ya shiga cikin unguwarsu, sannan ta fara jin tsoron ƙarasawa gidan, zuciyarta ta fara raya mata tana shiga Abbanta korarta zaiyi yace ta fitar mai daga gida, take ta tuna da kalaman daya gaya mata ranar da taje zuwanta na ƙarshe gidan, yayinda wani ɓangare na zuciyarta kuma ke raya mata ba ta yadda za'ayi ya koreta, tunda bata da inda ya fiye mata nan, dole zai yi haƙuri ya barta ta zauna. Misalin ƙarfe 9:55pm. Mai napep ɗin ya direta a ƙofar gidansu, a hankali ta fito daga cikin napep ɗin bayan ta sauko akwatinta ƙasa ta buɗe jakarta ta zaro ɗari biyar ta miƙa masa, kana ta ja akwatin da ƙyar a hankali ta shige cikin gidan. Tana gaf da shiga zauren gidan ne kuma sai taja ta tsaya tana tunanin idan ta shiga to meza tace..? Take wani bala'in tsoron haɗuwarta da Abbanta ya cika mata zuciya, ganin tsaiwar tata babu amfanin da zata ƙara mata, sai ma wani laifin da zata ƙarawa kanta yasa tayi shahada kawai tasa kai ta shige cikin gidan kai tsaye. YA AZEEZ Acan ɓangaren Ya Azeez kuwa sai da yaga fitarta daga gidan, sannan ya fito daga maɓoyarsa ya koma cikin gidan da tunanin Allah yasa dai gida ta nufa, kar kuma tace zata tafi gidan ƙawayenta a wannan daren, ɗakin ya shiga ya zauna a falo ya dafe kansa yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa, sake ɗago kansa yayi yana kallon tsakar ɗakin kafin kuma ya sake matsawa sosai ya jingina kansa da jikin bangon ɗakin ya ɗaga kansa sama yana jin nauyin daya dabaibaye zuciyarsa lokaci ɗaya yana sauka a hankali a hankali. Sai daya daɗe a zaune yana saƙawa da kwancewa sannan ya fara tunanin da wane ido zai kalli Abba..? Me zai faɗa masa..? Taya zai fara tunkararsa yayi masa bayani..? Anya zai fahimcesa kuwa..? Toh idan ya tuhumesa dalili me zai faɗa masa..? Yace masa bata zaman gida ne ko kuwa tun matsalar da ya sani dai tun farko itace dalilin da yasa har ya kasa haƙuri ya saketa..? Ko kuwa zai faɗa masa cewa ta tafi bikin ƙanwar ƙawarta ne tayi kwana da kwanaki, shi kuma haushin hakan yasa ya saketa..? Can sai ya miƙe tsaye da sauri ya fara kai kawo yana zagaya ɗakin, sai a lokacin ya ƙara shiga kogin danasani. Tabbas bai kyautawa Abba ba, bai kuma cancanci irin wannan sakayyar daga garesa ba, to shi me ma ya harzuƙasa ne da har ya yanke wannan hukuncin ba tare da yayi tunani mai zurfi ba, bai kuma duba abinda zai je ya dawo ba..? Da sauri ya girgiza kansa yana ɗan saurarawa kafin kuma cikin sanyin jiki ya furta "Iyayena fa ta zaga, tace idan ni cikakken ɗan halak ne cikin uwarsa da ubansa ba shege ba, in saketa..." Ya faɗa a fili lokaci ɗaya yana ƙara jin wani tsantsar ɓacin rai da baƙin ciki na sake bijiro masa tamkar a lokacin Fadwa ke zagin iyayen nasa. FADWA Tana saka ƙafarta cikin gidan tai arba da Abba da Mama dake zaune a tsakar gidan kan tabarma suna hira. Cikin rashin kuzari ta taka a hankali ta isa gabansu ta durƙusa, da sauri duk suka ɗago kai a tare suka kalleta, kafin kuma Abba ya juya da sauri ya kalli akwatin data shigo dashi, girgiza kansa kawai yayi cikin tarin takaici da tsantsar damuwa yana faɗin "Lallai yau da ganin alamu Fadwa kin ƙure haƙurin AbdulAzeez, tunda gashi har ya gaji da halinki ya sakoki..." Cikin rashin jin daɗin maganarsa Mama tace "Haba Abban Fadwa wannan wace irin magana ce kake yi haka, daga tafiya fa ta dawo yau, ka sani ko dare ne taga yayi yasa ta taho nan ta kwana gobe da sassafe sai ta wuce gidanta..? Amma shine saboda baka son zaman lafiya daga ganinta zaka fara mana jaye jayen wata lukutar masifa da daddaren nan kana son jajibo mana ja'iba...?" Maman ta faɗa tare da kallon Fadwa data sunkuyar da kai lokaci ɗaya tana jin jikinta na ƙara yin sanyi. Da kallon takaici Abba ya bisu lokaci ɗaya yana ƙara nazarin Fadwan, bai dai ce komai ba ya kaɗa kai kawai ya miƙe tsaye ya wucesu da sauri ya nufi ɗakinsa ya shige ya turo ƙofa. Ganin haka yasa Fadwa matsawa da sauri ta zauna a kusa da Mama tana sauke numfashi kafin kuma cikin yin ƙasa ƙasa da murya tace "Mama da gaske fa Ya Azeez ya sake ni..." Ta faɗa tare da juyawa lokaci ɗaya ta kalli ƙofar ɗakin da Abban ya shige. Zaro idanu Mama tayi cike da tsantsar mamaki tace "Ya sake ki..shi AbdulAzeez ɗin ne ya sake kin Fadwa...?" Da sauri Fadwa ta rufe mata baki da hannunta tana girgiza mata kai, kafin kuma cikin yin ƙasa da murya tace "Kai Mama kiyi a hankali dan Allah kar Abba ya jiyoki..." Ta faɗa tare da sake waigawa tana zare idanu, kafin ta juyo a hankali tana gyaɗa mata kai tace "Wallahi kuwa Mama Ya Azeez ya sakeni kuma sakin wulaƙanci, wai saki ɗaya, gashi har da marina wai in fita in bar mai gida, sai kace wata karya, baya son ganina bani da wani amfani a gurinsa, dama darajar ubana nake ci kuma ya gaji, in tafi baya son ƙara ganina..bakiji cin mutunci ba iri iri, wallahi yau Mama nayi mamakin abinda Ya Azeez ya rufe ido yayi min, ban taɓa zato ba..." Taɓe baki Mama tayi tana faɗin "Ai kaɗan kenan daga iskancin talaka, dan shi jaki koya kikayi dashi sai yaci kara, amma in ba dan haka ba har AbdulAzeez ya isa ya kalleki yace wai darajar ubanki kike ci, ai shi ya kamata a gayawa haka ba ke ba banzan bazara kawai matsiyaci, bai san dama can rufa masa asiri mukayi kawai kike zaune dashi ba, amma inda yayi tunani ai daya gano cewa ruwa ba sa'an kwando bane dan ko an zubasa sai ya tsiyaye, daƙiƙin banza da wofi kawai ɗan iska..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana kumfar baki. Haka dai suka zage sukai ta zagin Ya Azeez, wanda yana can gida shi bai ma san me sukeyi ba. Mama nata aibantasa tana ta faɗan maganganu marasa daɗi akansa da mahaifiyarsa, Fadwa kuwa sai biye mata take itama tana tayata suna zaginsa. Sai da suka gaji dan kansu sannan suka miƙe, Mama taja akwatin Fadwan ta shigar mata dashi ɗakin kannenta, kana ta fito ta ɗauki bokiti ta cika mata shi da ruwa ta kai mata har banɗaki ta fito ta sake ɗaukar soso da sabulu ta kai mata, ta dawo ta bata zani ta ɗaura bayan ta tuɓe kayan jikinta tace "Jeki ɗan watsa ruwa ko kyaji daɗin jikinki, kafin ki fito na gyara miki gurin kwanciyan..." Ta faɗa tare da ficewa zuwa ɗakinta, kafin itama Fadwan ta fice zuwa banɗakin dake tsakar gidansu domin tayo wankan. ********* A ɓangaren Ya Azeez kuwa ya daɗe idonsa biyu ya kasa bacci, gaba ɗaya idanuwansa sun gama bushewa zuciyarsa kuwa har lokacin tafarfasa kawai take saboda ɓacin rai. Sai juyi yake yana ta tunane tunane yana jin wani abu mara daɗi na masa yawo a zuciya, ta wani ɓangaren kuwa har lokacin tunani yake ta yadda zai iya tunkarar Abba ya iya kallon idonsa idan yasan cewa ya saki Fadwa, ƴar cikinsa duk irin halaccin da yay masa. Sake juyawa yayi a hankali yana sakin tsaki, kafin a fili a furta "Abba ka gafarceni na kasa control ɗin kaina da zuciyata ne akan irin abubuwan da Fadwa ke yi min, kuma ina fatan ka fahimceni insha Allahu zan dawo da ita ɗakinta, kuma nayi alƙawarin kome tai min zan daure in jure in cigaba da zama da ita a yadda take..." Ya ƙarashe maganar tare da gyara kwanciyarsa lokaci ɗaya ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya. ********* Washegari misalin ƙarfe 8am. Ya Azeez ya fito cikin shirin fita, sai daya kulle ƙofar ɗakin sannan ya fita daga gidan, da ƙafa ya taka yaje gidan bulon da yake kai ajiyar napep ɗinsa ya ɗauka, bayan ya fito ya nufi unguwar Mu'azu. Tafe yake a cikin napep ɗin sai saƙe saƙe yake a ransa, tunani kawai yake yadda zai fuskanci Abba idan ya isa gidan, dan sosai yake matuƙar jin matsananciyar kunyar Abban a zuciyarsa, anya kuwa zai iya fuskantarsa..? Ko dai ya juya ne yaje ya ɗauko Umma su taho tare..? Haka har ya isa gidan bai gama yanke shawarar ba, ya fasa zuwa gidan ne ko kuma ya koma ya ɗauko Umman..? *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* _Nagode ƙwarai da sharhinku ina matuƙar jin daɗin yadda kuke nuna kulawarku akan littafina, nagode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi ina godiya sosai Allah yabar Ƙauna._ 2️⃣9️⃣ Koda ya shiga cikin gidan Ilham kaɗai ya samu a tsakar gidan tana shara, yayinda Amatullah kuma ke kichin tana ƙoƙarin dama musu koko. Ganinsa ne yasa Ilham ɗin ajiye tsintsiyar dake hannunta da sauri ta matso gabansa, dan tana ganin yadda ya shigo gidan tasan ba lafiya ba, domin tun bayan aurensa da Aunty Fadwa ba kasafai yake zuwa gidan ba balle kuma yau ɗin data ganshi tunda sassafe, aiko ba lafiya, tunda taga ita karan kanta Aunty Fadwan jiya a gidan ta kwana. "Ya Azeez ina kwana...?" Ta faɗa a sanyaye bayan ta amsa sallamarsa. Ƙarasowa yayi cikin gidan bayan ya amsa mata gaisuwar tata, kafin kuma ya ɗora da faɗin "Abba ya tashi kuwa...?" Ya faɗa tare da ɗan juyawa yana kallon ƙofar ɗakin nasa. Gyaɗa masa kai tayi kafin tace "Ya tashi tun ɗazu, yana cikin ɗaki karatu yake, bari inyi masa magana..." Ta faɗa tare da juyawa da sauri ta nufi ɗakin, ba daɗewa sai gata ta fito tace "Yace ka shiga..." Ta faɗa tare da wucewa ta ɗauki tsintsiya ta cigaba da shararta. Shiko Ya Azeez a hankali ya ƙarasa ƙofar ɗakin yayi sallama, inda daga ciki Abba ya amsa masa tare kuma da bashi iznin shigowa. Cikin natsuwa ya ɗaga labulen lokaci ɗaya ya saka kansa cikin ɗakin, karaf kuwa idonsa ya sauka ana Mama dake zaune a gefen Abba, kauda kai yayi da sauri tare da ƙarasawa gaban Abba dake zaune akan darduma ya rusuna yana faɗin "Barka da safiya Abba..." Ɗagowa Abba yayi da murmushi a fuskarsa yana faɗin "Barka dai AbdulAzeez, lafiya dai ko na ganka yau tunda sassafe...?" Ya faɗa cikin fargaba, yayinda ya tsaresa da idanu lokaci ɗaya gabansa na faɗuwa, domin haka nan tun jiya da yaga Fadwa hankalinsa ya gaza kwanciya zuciyarsa kuma gabaki ɗaya taƙi natsuwa da zuwan nata shiyasa yanzu da yaga Ya Azeez ɗin tunda sassafe zuciyarsa ta ƙara shiga ruɗu da tashin hankali. Mama kuwa zabga masa wata muguwar harara tayi ba tare kuma data amsa gaisuwar da yake mata ba tace "Yo ba dole ka ganshi a gidan tunda sassafe ba ya dako uban sammako, tunda yasan tsiyar daya ya tsula maka..." Ɓata fuska Abba yayi kafin yace "Wace irin tsiya kuma, wai ke meyasa kwata kwata rayuwarki babu lissafi da tunani ne..? Ana zaune lafiya ke dai dole sai kin jajibo abinda za'a yi fitina sannan hankalinki zai kwanta, yanzu tsakani da Allah wace irin tsiya yayi miki daga zuwansa...?" Fuskar Mama ba walwala tace "Sakin ƴata yayi ya mayar min da ita ƙaramar bazawara..." Ta faɗa kai tsaye tana harararsa. Galala Abba yake kallonta kafin kuma ya juya ya dubi Ya Azeez wanda ya duƙar da kai ƙasa yace "Da gaske ne ka saki Fadwa AbdulAzeez...?" A ƙufule Mama tace "Yo ya saketa mana, meye na wani bin ba'asi kuma...?" Ta faɗa tana wani kumburo baki sai kace wata ƙaramar yarinya. Shiko Ya Azeez gaba ɗaya ji yayi ya gama muzanta a gaban Abban, gabaki ɗaya ya rasa da wane ido zai iya kallonsa me zai ce masa..? Riƙo hannunsa da Abban yayi ne yasa ya ɗago kai da sauri ya kallesa, kafin kuma ya sake duƙar da kansa dan baya jin zai iya kallon cikin ƙwayar idanunsa saboda tsabar kunyarsa da yake ji gaba ɗaya ta gama lulluɓesa. Bai gama jin kunya ba sai da ya jiyo muryar Abban kamar daga sama yana faɗin "Na fahimceka AbdulAzeez kuma bazan taɓa ganin laifinka akan duk irin hukuncin daka yanke akan Fadwa ba, domin ina sane da duk irin zaman ƙuncin da kayi da ita na tsawon watannin nan har zuwa yanzu, saboda haka bazan sake tauyeka akanta ba. Kuma bazan taɓa ƙullatarka da wani mugun nufi akanta ba, amma tabbas banji daɗin rabuwar aurenku da Fadwa ba, domin zamanta a gidanka shine kwanciyar hankalina da farin cikina, amma babu yadda zanyi tunda aikin gama ya riga daya gama, kuma ni bazan taɓa matsa maka lallai dole saika maida Fadwa ɗakinta ba, sai dai in tayaka da addu'ar Allah ya zaɓa maka duk abinda yafi zama alkhairi a rayuwarka..." Da sauri Ya Azeez yace "Abba dan Allah kayi haƙuri, wallahi sharrin shaiɗan ne, amma tun jiyan na maida ita ɗakinta, yanzu ma nazo ne in ɗauketa mu koma, sannan kuma in ƙara bada haƙuri..." Girgiza kai Abba yayi cikin takaici kafin yace "Uhmm AbdulAzeez kenan, koda ka maida Fadwa zaman nan naku bazai taɓa yin dai-dai ba, domin tun farko abinda ta saba yi maka shi zata cigaba da yi, bazata taɓa sauyawa ba. Kuma komai da kake ganin take yi daga tushe ne domin da haka ta taso, shiyasa take ganin kamar duk abinda take aikatawa mai kyau ne, kuma daga ita har me zugatan bazasu taɓa ganewa ba sai lokaci ya ƙure musu. Saboda haka a matsayina na mahaifin Fadwa ina mai baka umarni daka janye maidata da kayi ɗakinta ka barta har zuwa ranar da tayi hankali ta gane abinda take yi sannan ta banbance idan mai kyau ta aikata ko akasinsa, sannan idan tana da wata dama ta gyarawa a lokacin sai ka maida ita ɗakinta, idan kuma babu dama sai ka ƙyaleta da abinda take ganin shine dai-dai da ita..." A wulaƙance Mama ta kallesa dan ta gane maganganun nan duk da yake kawai tsabar cin fuska ne da neman zubarwa ƴarta da mutunci a gaban Ya Azeez ɗin, kauda kai tayi kafin tace "Ai bama zata taɓa komawa gidansa ba itama, ta barosa kenan bari na har abada, sai dai kuma abi wani sarkin, amma Fadwa kam yadda tabar nonon uwarta haka tabar auren wannan mara mutuncin wanda bai san abinda ya kamata ba..." Ta faɗa a ƙufule tana harararsa. Wani mugun takaicin Mama ne ya ƙara kama Abba, shiko Ya Azeez sake duƙar da kansa yayi da sauri yana ƙara jinjina halin rashin mutuncin Mama a zuciyarsa. Haka shima Abba bai sake cewa komai ba ya miƙe tsaye, ya kamo hannun Ya Azeez da shima ya miƙe suka juya atare suka fice daga ɗakin. Suna fita Mama ta bisu da wani ƙaton tsaki tana faɗin "Aikin banza kawai aikin wofi, wai sharrin shaiɗan ne..yo akwai wani babban shaiɗani ne bayan kai shege almuri, mai ƙirar samudawan zamanin daa, wai yanzu ma nazo ne in ɗauketa mu koma sannan kuma in ƙara bada haƙuri...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana kwaikwayon maganar Ya Azeez ɗin, kafin ta miƙe tana cigaba da mita tana faɗar maganganu, ta zare hijabin sallar dake jikinta ta fice daga ɗakin ta nufi ɗakinsu Ilham. Tana shiga ta samu Fadwa har lokacin tana ƙudundune a saman ƴar yaloluwar katifarsu Ilham ɗin tana ta sharar bacci abinta hankali kwance, wanda da ganin alamu ko sallah bata tashi tayi ba. Ganin haka ne yasa Mama ta juya ta fice daga ɗakin, ta nufi kichin inda ta iske Amatullah har ta gama dama kokon ta wanke tukunyar tana ƙoƙarin ɗora musu ɗumamen tuwon jiya. A ɓangaren Ya Azeez da Abba kuwa koda suka fita sun daɗe tsaye a ƙofar gida suna tattaunawa akan abinda ya faru, inda Abba ke ta bawa Ya Azeez ɗin haƙuri akan abinda Mama tayi masa, da irin rashin mutuncin daya labarta masa Fadwan tai masa jiya, kana daga bisani sukayi sallama bayan Ya Azeez ɗin ya gaya masa cewa zai tafi Kano cikin satin nan domin cigaba da shirye shiryen tafiyarsu China, da kuma neman waɗanda zai wakilta acan ɗin domin su dinga kula mai da shagunan da Abban Kano ya bashi. Sosai ran Abba yayi fari tas tas yaji gabaki ɗaya ɓacin ran da ya fito dashi ya kau, yay ta murna yana yi masa addu'a, kana daga haka kuma suka sake yin sallama ya shiga napep ɗinsa ya wuce, shi kuma Abban ya juya ya koma cikin gida, yayinda zuciyarsa ke cike da tsananin baƙin ciki da takaicin rasa nagartaccen miji irin Ya Azeez da ƴarsa Fadwa tayi, wanda kuma yake da tabbacin cewa nan bada jimawa ba ita da kanta sai tayi kukan rashinsa a rayuwarta. Ya Azeez kuwa koda ya bar gidansu Fadwa direct gidan Ummansa ya wuce, sai dai kawai Umma ta gansa kwatsam, wanda koda Umma ta tambayesa lafiya ta ganshi da sassafe, bai ɓoye mata komai ba, ya kwashe komai da yake faruwa tun daga farko har ƙarshe ya gaya mata, sai dai ya ɓoye zagin da Fadwan tai ma iyayensa bai gaya mata ba. Wanda kuma tunda take dashi yau ce rana ta farko data taɓa yarda har ta sauraresa ya kwashe duk abubuwan dake faruwa tsakaninsa da Fadwa ya labarta mata, dan a baya koda yazo mata da maganar tausarsa take tai ta lallashinsa tace yayi haƙuri Fadwan yarinya ce, ya ƙyaleta yarinta ke damunta wata rana zata bari. Mamaki ya kama Umma sosai, dan bata taɓa zaton cewa Ya Azeez ɗin yana da haƙurin da zai iya jure duk wani rashin mutuncin Fadwa ba, shiyasa abun yayi matuƙar ɗaure mata kai. Amma kuma duk da haka sai bata ji daɗin sakin da ya yiwa Fadwan ba, ko dan saboda mahaifinta, dan haka ta yanke shawarar anjima da yamma da kanta zataje gidan tayi bikonta ta dawo da ita ɗakinta. Shi dai Ya Azeez jinta kawai yake, amma bai hanata ba, dan yasan koda ya hanata ɗin ma sai taje. Shiyasa kawai ya bita da Allah ya tsare, amma yasan kam da kamar wuya Maman Fadwa ta saurareta a yadda ta ɗauki zafin nan, ballantana har ta bar Fadwan ta dawo. 3:10pm Mai napep ɗin daya ɗauko Umma daga gidanta ya ajiyeta a ƙofar gidansu Fadwa ta sauka, ta buɗe jakarta ta ɗauko kuɗinsa ta bashi, ya ƙarba ya bata canji, sannan ta juya kai tsaye tasa kai ta shige cikin gidan. Dai-dai lokacin kuma Fadwa da Mama na zaune a tsakar gida kan tabarma, yayinda Mama ke bawa Fadwan labarin zuwan Ya Azeez da maganganun data gaggaya musu shida Abba, bata rage komai ba sai data kwashe tsaf ta gaya mata. Dariya ta kama Fadwa tana cikin yi ne kuma Umma tayi sallama fuskarta ɗauke da murmushi ta shigo cikin gidan. Cak Fadwa ta tsaida dariyar tata tana kwaɓe fuska lokaci ɗaya tana bin Umman da wani mugun kallo a wulaƙance kamar taga kashi. Mama kuwa itama watsa mata wani ƙasƙantaccen kallon sama da ƙasa tayi a wulaƙance tana faɗin "Baiwar Allah lafiya kuwa zaki faɗowa mutane cikin gida haka kai tsaye, ba tare da neman izini ba..ko akwai wanda kike bi bashi ne a gidan da zaki diro mana haka kwatsam sai kace dirar yesu..?" Ta faɗa a wulaƙance tana mata wani ƙasƙantaccen kallon sama da ƙasa. A sanyaye Umma ke kallonta kafin kuma ta ƙaƙaro murmushin yaƙe tace "Ayi haƙuri, amma nayi sallama sai dai in bakuji bane..." Ta faɗa tana ƙoƙarin zama a kusa da Fadwa da tayi saurin matsawa gefe tana watsa mata harara. Kauda kai Mama tayi itama kafin tace "Ayya Allah sarki, to sannunki da zuwa fa, Allah kuma yasa dai lafiya..? Saboda irinku ba kasafai mutum ke buƙatar ganinku a gidansa ba..." Ta faɗa tare da juyawa ta kalli Fadwa data juyar da kai can gefe guda tana harare harare tace "Kuɗina wai baki ga sarakuwarki tazo biko bane.? Tashi ki ɗebo mata ruwa mana tasha, dan da ganin alamu tashawo rana, dan yadda ake ƙwalla ranar nan kam nasan maƙoshi ya bushe sai an kora ruwa mai ɗan sanyi sanyi za'a samu salama..." Asakarce Fadwa ta juyo ta kalleta kafin tace "Ina sarakuwar tawa take kuma Mama, ko har kin manta da cewa ɗanta ya sakeni ne yanzu zaman idda nake da kike dangantata dani...?" Girgiza kai Mama tayi taja tsaki kafin tace "Oh ai na ɗauka zakiyi mata irin ɗan na mutunci nan ne, saboda zaman da kikayi da ɗanta na wata da watanni..." Dariya ta ƙara ƙwacewa Fadwa tace "Kai Mama, sai kace wata wadda tayi zaman jin daɗi a gidan ɗan nata, da zan dinga wani ɓare ɓare akanta...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallon Umma a wulaƙance ta wutsiyar ido. Ita dai Umma tsit kawai tayi a zaune kamar ruwa ya cinyeta, dan gaba ɗaya ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki saboda tsananin kunyar wulaƙancin da Mama da Fadwa suka tasata agaba suke mata. Wanda dama tun kafin ta taho sai da Ya Azeez ya gaya mata kuma ya sake jaddada mata dan yaso ma ya hanata amma sanin bazata hanun masa bane yasa kawai ya ƙyaleta ba dan yaso ba ta taho. Amma bata taɓa zaton ko Fadwa zata iya mata haka ba ballantana kuma Mama karan kanta da take ganin tafi ƙarfin wulaƙanci a gurinta. Haka sukai ta faɗan maganganu Umma dai na zaune tana jinsu amma babu wanda ta tankawa a cikinsu, har sai da suka gaji dan kansu sukayi shiru sannan Umma ta samu ƙwarin gwiwar bayyana musu abinda ya kawota gidan, nason a bata bikon Fadwa ta maida ita ɗakinta tunda Ya Azeez ɗin yace tun a daren jiyan da yayi sakin ya maidata ɗakinta. Zaburowa Mama tayi cike da bala'i tana faɗin "Allah ya kyauta ƴata ta koma gidan ɗanki wallahi, ai tunda ya yarda ya saketa kuma ta bar wannan ƙaddararren auren nasa kenan har abada, banga abinda zai kuma maida ita wannan ƙasƙantacciyar rayuwar mara ƴanci ba, gida ne dai ta barshi kuma bari na har abada da ikon Allah dan banga mai mata dole ba ya maida ita, dan haka ku daina wani damun mutane da maganar kome kuna cewa ya maida ita dan bata maidu ba, atoh na gaya mikk..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana harararta. Galala Umma tayi tana kallon Mama data rufe ido tana ta zazzaga mata masifa kamar bata santa ba, Fadwa kuwa ta gefen ido take ta kallon Umman yayinda a ranta kuma take ta jin daɗin rashin mutuncin da Maman ke yiwa Umman kamar ta kurma ihu saboda tsananin murna da farin ciki. Ɗago kai Umma tayi a hankali ta kalli Mama data wani haɗe rai tana harararta tace "Yanzu Maryama dan nazo bikon Fadwa sai ya zama abun tsiya da son tada zaune tsaye..? Tsakani da Allah duk waɗannan maganganun da kike faɗi kina ganin sun cancanta da ki gaya min..? Me nayi miki da zafi..? Aiko ni nasa AbdulAzeez ɗin ya saki Fadwa iya abinda zakiyi min kenan, amma ban san hawa ba bansan sauka ba daga zuwa abun arziki sai ya zama na tsiya...?" Kai tsaye Mama tace "Na tsiya tsiya ma ya zama ba tsiya ba, nace na tsiya tsiya ya zama ba tsiya ba..." Ta faɗa a zafafe tana watsa mata harara. Kaɗa kai kawai Umma tayi tana kallonta kafin tace "To shikenan Allah ya huci zuciyarku ya kuma baku haƙuri, amma ni bansan..." Ɓata fuska Mama tayi kafin ta katseta da faɗin "Dan Allah nidai tashi ki tafi mun gode Allah ya saka da alkhairi, amma Fadwa dai bazata koma gidan wannan basamuden ɗan naki ba mara mutunci da bai san ciwon kansa ba..." Da sauri Fadwa tace "Gaya mata dai Mama hanyar jirgi daban ta mota da daban wallahi, kowa kuma yaje yaji da kansa, amma ni kam bazan taɓa komawa gidan Ya Azeez ba, na barshi bari na har abada. Yaje can ya auri dai-dai shi ya cigaba da manejin rayuwarsa kamar yadda ya saba, amma ni ba komawa gidansa zanyi ba, dan daso samu ne ma daya ƙarashe tsige sauran igiyoyin sai kowa ya huta ko ya kikace Mama....?" Ta ƙarashe maganar hankali kwance tana kallon Mama. Da sauri Maman ta gyaɗa mata kai tana faɗin "Sosai kuwa, dama kamar akan ƙaya muke duk mun ƙagara a samu masalaha, to yanzu kuma Allah ya kawo mana ai baza muyi wasa da damar mu ba...." Ta faɗa a wulaƙance lokaci ɗaya tana kallon Umman. Umma bata mata magana ba illa kallon Fadwa da take yi kafin tace "Kiyi haƙuri da abinda yayan Imaan yayi miki kinji dan Allah, ba zai sake ba insha Allahu nayi masa faɗa...? Amma dan Allah na roƙeki ki koma ɗakin mijinki dan girman Allah..." Jin haka yasa Mama sakin tsaki ta miƙe tsaye tana faɗin "Kinga dan Allah tashi tashi ki tafi, haba mata sai kace mayya, yarinya tace bazata koma gidan ɗanki ba bazata koma ba, amma kin wani ishisshire kin zauna kina neman matsa mata haka kawai sai kace ana kome dole..ina dalili..? Dan Allah tashi ki fitar mana a gida tun kafin raina ya ɓaci..." Ta ƙarashe maganar tare da nuna mata ƙofar fita. Miƙewa Umma tayi a hankali ta ɗauki ƴar pos ɗinta ta riƙe a hannunta, kafin ta juya lokaci ɗaya tana faɗin "Toh Allah ya huci zuciyarku ya baku haƙuri na gode..." Ta faɗa tare dasa kai cikin sanyin jiki ta fice daga gidan. Da ido Mama da Fadwa suka bita, kafin Maman ta rakata da ƙaton tsaki tana faɗin "Agayas dai Allah ya raka taki gona almunafunfun..." *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* *Mum Khairy, Ummin Sauban, Aysher Umar Yaro, Maman Abba, Ummu Shuriem. Ina matuƙar jin daɗin sharhinku, kuna sakani nishaɗi sosai nagode matuƙa Allah ya saka muku da mafificin gidan aljanna fiddausi🤝* 3️⃣0️⃣ Koda Umma ta koma gida zaune tayi tana ta saƙe saƙe da tunanin abinda Fadwa da Mamanta sukai mata, sai a lokacin ne kuma take ƙara gasgata haƙuri da kawaicin da Ya Azeez yayi na zama da Fadwa har tsawon wannan lokacin, sai taji tsananin tausayin Ya Azeez ɗin ya ƙara kamata. Sosai abun ya tsayan mata arai, sai dai ko Imaan bata sanarwa ba saboda bata son ta haddasa mata tsanarsu Maman da Fadwa aranta tazo ta dinga jin haushinsu. Haka ta kwana da juyayin abun aranta, amma bata iya gayawa kowa ba. Washegari da safe da suka tashi sai da ta bari Imaan ta gama shirin makaranta ta tafi, sannan ta samu zatafin kiran Ya Azeez ta sanar masa tana son ganinsa. Ko cikakken awa ɗaya ba tayi ta kiransa ba kuwa, sai ga Ya Azeez ɗin ya iso gidan cikin gaggawa, koda ya shigo ya samu Umman zaune a tsakar gida ita kaɗai ta zafga uban tagumi da hannu bibbiyu tayi kasaƙe alamar tayi zurfi a cikin tunani. Ganinta haka yasa jikinsa ƙara yin sanyi ya isa gabanta da sauri ya durƙusa cikin damuwa yana faɗin "Umma lafiya kuwa..meyake faruwa...?" Murmushin yaƙe ta ƙaƙaro tana ƙara jin tausayin ɗan nata a ranta, kafin kuma ta ɗago tana nuna masa gurin zama akan tabarman dake shimfiɗe a tsakar gidan tace "Toh zauna mana ɗan gidan Umma..." Da sauri ya zauna yana ƙara nazarinta kafin yace "Dan Allah Umma meyake faruwa ne, na ganki ba'a yadda na saba tarar dake ba, kuma tun kiran da kikayi min a waya yanayin muryarki kaɗai na gano akwai abinda yake faruwa, mene ne Umma...?" Ya faɗa cikin tsantsar tashin hankali yayinda kuma yake jin wani irin ɗaci aransa. Nan Umma ta gyara zama ta zayyane masa komai ta kwashe tun daga farko har ƙarshe na abinda Fadwa da Mamanta sukayi mata ta gaya masa, bata rage komai ba, kuma bata ƙara musu komai ba. Duk irin rashin mutuncin da sukayi mata sai data gaya masa, babu abinda ta ɓoye masa. Aiko ba ƙaramin ɓaci ran Ya Azeez yay ba, jikinsa har wani irin tsuma ya ɗauka saboda tsabar baƙin ciki da ɓacin rai, mamaki ya kamasa ko kaɗan bai taɓa zaton Mama zata iya rufe ido ta yiwa Ummansa irin wannan wulaƙancin ba, dan har gwara Fadwa dama yasan zata aika har ma fiye da haka indai itace. Sosai Ya Azeez ya jinjina al'amarin kuma ba domin komai ba, sai irin yadda suka iya kallon tsabar idanun Ummansa suka iya gaggaya mata maganganu masu zafi irin haka yaga ƙoƙarinsu sosai, amma bai ga laifin kowa ba, sai laifin kansa saboda shine yaja mata domin duk ta dalilinsa ne aka samu zarafin yi mata irin wannan cin mutuncin. Ran Ya Azeez ya ɓaci ya dinga sauke numfashi, Umma tace "Dan Allah kar kasa abun a ranka yazo yana damunka, suma kuma nasan sharrin shaiɗan ne da ɓacin ran abinda akayi musu yasa suka aikata hakan, shiyasa banso ka saketa ba wallahi dan babu yadda zanyi da kai ne amma da ka ci gaba da haƙuri kamar yadda nake gaya maka da duk hakan bata faru ba..." Cikin tsananin ɓacin rai Ya Azeez ya ɗago yana kallon Umma kafin yace "Amma nayi matuƙar mamakin Mama sosai wallahi, dan ni a uwa na ɗauketa ba matar ƙanin mahaifina ba, taya Mama zata iya rufe idanu su ci mutuncinki ita ƴarta wacce take a matsayin suruka agareki hakan bazai min zafi ba, wanda koda wasa ni bazan taɓa iya kwantanta yi mata hakan ba...?" Ya ƙarashe maganar kamar zai fashe da kuka, saboda baƙin ciki. Ajiyar zuciya Umma ta sauke a hankali tana faɗin "Ka barsu kansu suka yiwa kuma insha Allahu sai sunji kunyar abinda suka aikata..." Ƙasa yay da kai yana ƙara jin wani ɗaci a cikin ransa, Umma kuwa kawai runtse ido tayi tana girgiza kai, yayinda kuma take ƙara tausar Ya Azeez ɗin kan yayi haƙuri ya cire abun a zuciyarsa ya manta dashi. Haka dai ya dinga ƙoƙarin yakice duk wani ɓacin ran da yake ji a zuciyarsa, ya nuna mata komai ya wuce, kafin ta tashi ta kawo masa abin karin kumallo, bayan ya gama karyawa ne kuma suka shiga hirar business ɗinta, wanda yanzu komai ya daɗa kankama dan babu abinda bata kawowa har su kayan kichin da sauran tarkacen kayan aikace aikacen gida, kome ka gaya mata kana so ko baka da kuɗi zata kawo maka ga kayanta da sauƙi, kuma bata zuwa ko'ina, duk mai so har gida ake biyota a siya. Ya daɗe a gidan suna tattaunawa kana daga haka kuma suka gangaro kan zancen tafiyar Ya Azeez ɗin Kano jibi da zaiyi. Bai bar gidan ba kuma sai gurin ƙarfe 12:20pm, kafin yayi mata sallama ya tashi ya tafi. ************* Acan Kano kuwa ta ɓangaren su Fahad yanzu komai ya gama daidaita, domin zuwa yanzu hankalinsa a kwance yake tunda amaryarsa Basma ta tare, bai da wata sauran damuwa kuma. Gabaki ɗaya hankalinsa yanzu kacokan ya tattarasa ne gurin shirye shiryen buɗe shagunan Ya Azeez da kammala shirin tafiyarsu China. Wanda duk wani shiri da ya kamata suyi Abba ya riga da ya gama musu sai ɗan abinda ba'a rasa ba kuma wanda sune zasuyi da kansu, amma hatta da Visa da Epassport ɗin Ya Azeez ɗin gaba ɗaya suna hannu an riga an gama haɗawa, sai zaman jiran lokacin tafiyar tasu kawai suke. ************ A ɓangaren Shatu kuwa yau tunda wuri ta gama shiryawa domin tafiya makaranta, saboda yau ɗin ƙarfe 9am. Suke da text ɗin Sociology. Bayan tayi breakfast ta gama ne kuma ta miƙe ta ɗauki ƴar ƙaramar jakarta yayinda take duba haɗaɗɗen agogon fatan dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, ƙarfe 8:30am. A gaggauce ta sauko daga dinning area ɗin zuwa cikin falo inda Ummi da Zahra ke zaune ta ƙaraso inda suke, a hankali ta ɗan duƙa tare da faɗin "Ummi zan wuce saina dawo..." Ta faɗa tare da nufar ƙofa zata fice, ganin haka yasa Zahra miƙewa da sauri bayan ta ɗauki laptop ɗinta da jakarta tana cewa "Aunty Shatu jirani dan Allah tare yau zamu tafi...." Ta faɗa tare da nufar ƙofar da sauri itama tana faɗin "Ummina bari muje sai mun dawo ayi mana addu'a..." Ta ƙare maganar tana bin bayan Shatu da tuni ta fice daga falon. Kai Ummin ta jinjina, tare da ɗan ɗaga murya ta yanda zasu iya jiyota tace "Allah ya tsare ya dawo min daku lafiya, agaishe da ƴan makarantan..." Da "Ameen Ameen..." Zahran ta amsa kana tasa kai ta ƙarasa ficewa daga cikin falon. Suna fitowa harabar gidan nasu kuwa suka iske Ribadu direbansu tsaye a jikin mota yana jiran fitowarsu. Ganinsu ne kuma yasa da sauri ya buɗe musu gidan baya, suka shiga suka zauna, sai da ya rufe kana shima ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna, a hankali kuma ya tada motar maigadi ya wangale musu gate yaja suka fice daga cikin gidan, kai tsaye suka nufi BUK, kasancewar acan ne dama dukkansu suke karatu sai dai kowanne da ɓarayinsa, inda Shatu ke 400 level dan tana matakin ƙarshe ne na kammala B.Sc ɗinta. Yayinda ita kuma Zahra take 100 level, wanda ita sai yanzu ne ma ta fara. ********** Fadwa ce zaune a tsakar ɗakin Mamansu, inda ta tasa robar soyayyar awara da yaji a gabanta tana ci sai kwalban coke mai sanyi dake aje a gefe guda, ci take a hankali yayinda kuma take korawa da sassanyan coke ɗin jifa jifa kuma suna ɗan taɓa hira sama sama da Maman, ɗago kai tayi a hankali tana kallon Maman dake zaune a ƙofar ɗaki tana jajjagen kayan miya a turmi, ganin kuma ta ɗauki daddawa ne zata saka a turmin yasa Fadwan ta wani kwaɓe fuska kafin cikin nuna ƙyankyami tace "Haba Mama me kuma za'ayi da wannan abun mai warin tsiya da naga kina ƙoƙarin sakawa a turmin...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana toshe hanci tare kuma da yi mata nuni da daddawar. Fuskar Mama ba walwala tace "Zan jajjaga ne mana Fadwa, kinsan miyar kuka zamuyi kuma kuka ba daddawa ai bata shawuwa da daɗi, sai dai asha da haƙuri..." Ɓata fuska Fadwa tayi tana faɗin "Miyar kuka kuma Mama, yau ma tuwon za'a ci kenan...?" Kauda kai tayi da sauri tana yatsine fuska kafin tace "Haba Mama! Kullum tuwo kullum tuwo..tsakani da Allah ku ko gajiya bakuyi da cin tuwo, kullum kuci da daddare sannan ku ɗumama kuma da safe ku ci...? Nidai har ga Allah bazan iya ba na gaji da cin tuwo atoh..." Ta faɗa kai tsaye ko a jikinta. Galala Mama take kallonta kafin tace "Toh ya muka iya Fadwa..? Ya zamuyi da ranmu..? abinda muka samu ya kawo kenan kuma da babu ai gwara ba daɗi, amma wallahi ni karan kaina na gaji da cin tuwon nan kullum mu kenan cin ƙarza sai kace wasu ƴan iska, bamu da halin sauya girki kullum mu kenan girka abu guda, idan kinga mun samu canji to ya ɗan yi buga bugarsa ne ya samo wasu ƴan kuɗaɗen sai ya auno mana shinkafa ƴar Buhari mu dafa, amma in ba haka ba kuwa tuwon nan shi zamuyi ta ci kullum, ranar da ba'a samu na yin tuwon ba kuma kowa sai yasha ruwa ya kwanta..." Wani irin kallo Fadwan ta aika mata tana faɗin "Wallahi yau bazamu ci tuwo ba Mama, dan ni na gaji tsakani da Allah, jiya kun bani tuwo da daddare an bani da safe, sannan yau kuma ace za'a ƙara min..? A'a bazan iya ba wallahi wannan ai sai ruwan jikin mutum duk ya tsotse idan yana cin irin wannan cimar..." Dariya Mama tayi kafin tace "Toh ya muka iya mu kam Fadwa..? Haka nan muke daurewa mu ci, kafin zuwa lokacin da Allah zai haɗaki da babban rabo muma mu huta..." Da sauri Fadwa tace "Aiko insha Allahu lokacin ya kusa tunda anyi mai wuyar na rabu da wannan mummunar ƙaddarar..." Ta faɗa tare da tashi taje ta ɗauko jakarta ta buɗe ta zaro dubu uku aciki, kana ta mayar da jakar ta rufe ta ajiye, ƙarasowa tayi gurin Mama ta miƙa mata kuɗin tana faɗin "Gashi ayo cefane a dafa mana shinkafa da miya da nama, yau muma mu samu canji..." Da rawar jiki Mama ta saka hannu ta karɓe kuɗin tana washe baki cike da tsantsar farin ciki, kafin tace "Masha Allah lallai yau zamu ci daɗi a gidan nan, kai Allah yayi miki albarka ya rabamu da talauci, bari ki gani in tashi inje inyo mana cefanen da kaina dan ma kar in aika su Amatu suje suyo shirme..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana zare taɓarya a turmin ta jingine, kafin ta miƙe tsaye da sauri tana kakkaɓe jikinta, kana ta leƙa ɗaki ta ɗauko hijabinta dake sagale a ƙofa ta zura a gaggauce ta juya da sauri ta fice daga gidan. ********** ********** 2:30pm. Shatu ce zaune tare da ƙawayenta akan wasu fararen kujeru dake ƙarƙashin wata ƙatuwar bishiya a cikin makarantar tasu suna hira, wanda kuma fitowarsu daga Lecture Theatre ɗin kenan bayan sun kammala text ɗinsu. Husna Baita ce a gefenta suna magana akan text ɗin da sukayi yau ɗin, yayinda Basma Jada kuma ke zaune daga gefe guda da waya manne a kunnenta tana magana ƙasa ƙasa wacce dukkansu babu mai jin abinda take cewa a wayar, sai faman wani narkewa take tana shagwaɓe fuska. Juyawa sukai lokaci ɗaya suka ɗan kalli juna kana kuma suka sake juyawa a tare suka kalleta, kafin kuma suka saki tsaki lokaci guda a tare suna harararta, wanda ita ko kaɗan bata ma san sunayi ba, dan hankalinta kacokan yana kan wayar da take da mijinta, tana ta wani narke mai tana zuba mai shagwaɓa da sangarta. Zuba mata ido gaba ɗayansu sukayi suna ta kallonta, kafin Shatu ta saki tsakin takaici ta miƙe tsaye lokaci ɗaya tana ɗaukar jakarta da wayarta ta juya tana faɗin "Nidai nayi nan sai munyi waya Hussy..." Ta faɗa tana ƙoƙarin wucewa, saurin miƙewa itama Husnan tayi tana faɗin "A'a jirani mana nima ai ba zaman zanyi ba..." Ta faɗa tare da ɗaukar jakarta itama ta rataya, kafin ta kalli Basma data zubo musu ido tana so taga iya ƙarshen rashin mutuncin su, ganin da tayi da gasken sukeyi wucewar zasuji su barta ne yasa ta katse wayar da sauri tana kallonsu tace "Wai meye nufinku ne, naga duk kun ɗauki jaka kuna shirin tafiya ku barni anan ne, ban gane ba...?" A karkace Shatu ta juyo ta kalleta kafin tace "Me kika gani halan...?" Basma tace "Wucewa mana naga zakuyi baku min magana ba..." Tsaki Husna taja kafin tace "Ai munga kina ta waya da angonki ne shiyasa, bama so mu takura miki ne dan karmu shiga hakkinku..." Ta faɗa kai tsaye tana harararta. Tsaye Basma ta miƙe lokaci ɗaya kuma tana fashewa da wata irin dariya kana tace "Kutt lallai ma yaran nan, oh dama saboda ina waya da love shiyasa kuka haɗa kai zaku tafi ku barni..? To wai waya hanaku yin auren nan ne kuma kuje kuji yadda akeji...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana watsa musu harara. Ɗaure fuska Shatu tayi tana faɗin "Kisha kuruminki amaryar ƙarshen zamani muma mun kusa zuwa dai-dai gurin insha Allahu, me kike ci na baka na zuba ne..? Ai wallahi ko dan saboda gorin nan da kike mana kullum ya zama dole muma muyi zuciya mu fito da mazaje ayi mana aure, dan muje muji abinda kikeji da yasa duk kika wani susuce kika zama wata mara kunyar ƙarfi da yaji..." Tsaye kawai Basma tayi tana kallonsu, dan ita fa Allah ya gani mantawa take da kowa da komai in tana tare da Fahad balle har ta tuna da wasu Shatu da Husna, dafe kai tayi kafin tace "Wai laifina kuke gani ne...?" "Of course..ba dole muga laifinki ba, gabaki ɗaya tunda kikayi aure duk kin sauya sai kita wani shasshare mu irin ke kinsan abinda bamu sani ba ɗin nan, idan ana hira sai ki ƙi saka baki, ki koma gefe ki kira mijinki kuyita hira a waya mu ki barmu a gefe irin yanzu kin wuce da sanin mu ɗin nan, haka fa kike mana iskanci kala kala sai kace a kanki aka soma aure..." Husna ta faɗa tana watsa mata harara. Basma tace "Toh kuyi haƙuri ƙawayena na daina, amma wallahi bazaku gane bane kuma sai kun shiga kunji yadda akeji tukunna..." Ta faɗa tare da yin dariya, kana ta miƙe ta ɗauki jakarta itama tace "Ku muje Cafeteria mu ɗan ci wani abun dan Allah, wallahi yunwa nake ji sosai...." Shatu tace "Ni dai bana jin yunwa ruwa kawai zan sha...." Haɗa baki Husna da Basma sukayi gurin faɗin "Ok muje to..." Haka suka kama hanyar zuwa Cafeteria ɗin suna hira suna dariya, kamar basu ne yanzu suka gama balbale juna da faɗa ba. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 3️⃣1️⃣ Ƙarfe 5pm. Dai-dai Shatu da Zahra suka dawo daga makaranta a gajiye tuɓus suka shigo gidan. Suna shigowa cikin falon kuwa Shatu tai saurin zare gyalen abayar da tayi rolling akanta, tare da faɗawa saman kujera lokaci ɗaya tana dafe kanta da take jin yana sara mata kaɗan kaɗan. Dai-dai lokacin kuma Ummi ta fito daga kichin, hannunta riƙe da jug wanda ta zubawa Abbie juice ɗin kankana data haɗa masa aciki. Ganinta yasa Zahra ta miƙe ta rungumeta tana faɗin "Barka da gida Ummina, ya aiki...?" Ta faɗa tana sakinta tare kuma da ƙarban jug ɗin dake hannunta ta nufi dinning area ɗin taje ta ajiye kana ta dawo. Koda ta dawo falon kuwa bata zauna ba direct kichin ta wuce dan ta ɗan samu abun taɓawa, dan ita bata taɓa iya zama shiru ba tare data ji bakinta na motsi tana cin wani abun ba. Shatu kuwa miƙewa tayi a hankali ta ɗauki jakarta tana faɗin "Bari inje in ɗan watsa ruwa Ummi, yanzu zan sauko..." Ta faɗa a gajiye tana ɗan yatsine fuskarta. Kai Ummin ta gyaɗa mata kafin tace "Ok sai kin fito, nima bari in ƙarasa aiki a kichin..." Ta faɗa tare da juyawa ta koma cikin kichin ɗin, yayinda Shatu kuma kai tsaye ta wuce ta haura sama zuwa ɗakinsu dan yin wanka. *A TAƘAICE* Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai mutumin kirki ne kamili mai kwarjini da son jama'a, Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai su biyu ne rak a gurin iyayensu, Alhaji Muhammad da Hajiya Aisha. Shine babba sai ƙaninsa Alhaji Abubakar da ake kira da Baffa Buba, kuma shine auta kasancewar tun daga kansa Allah bai sake basu haihuwa ba. Asalinsu ƴan garin Mubi ne ta jihar Adamawa wanda kusan gabaki ɗaya danginsu duka suna can, inda kuma iyayensu ba masu ƙarfi bane, amma kuma sun jajirce sosai gurin basu ingantaccen ilimin addini dana zamani. Kasuwanci ne kawai ya kawosa garin Kano, inda kuma a yanzu haka yake da manyan manyan shaguna a kasuwannin dake cikin garin Kanon. Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai matarsa ɗaya Hajiya Khadija, haifaffiyar ƴar ƙasar Chadi ce, marainiya ce iyayenta duk sun mutu tun suna ƙanana ita da ƙanwarta Salma wacce a yanzu take auren wani babban ɗan siyasa a garin Abuja ruƙonsu ya dawo hannun kakarsu Ata, sun haɗu ne kuma da Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai a bikin wani babban abokinsa Alhaji Baballe da sukaje ƙasar Chadi. Hajiya Khadija macece mai kyaun hali da mutunta mutane, gata kamila mai dattako da sanin ya kamata, bata da ƙyama ko hantara, ita kowa nata ne. Ƴaƴan ta biyu Aisha wacce ake kira Shatu itace babba, sai kuma mai bi mata Zahra. Wannan kenan. ************ Duk yadda Ya Azeez yayi ƙoƙarin sakin ransa ya yakice tunanin abunda Mama da Fadwa suka yiwa Ummansa abun yaci tura, koya ya tuna irin cin fuska da cin mutuncin da sukayi mata sai yaji gaba ɗaya ransa ya baci, yaji kamar ya ƙarashe cikashewa Fadwa sauran saki biyun da suka rage su zama saki ukun cif, saboda tsabar baƙin ciki da takaicin abunda sukayi. Ko kaɗan a ranar bai samu baccin kirki ba, saboda tsabar tunani da saƙe saƙen daya wuni ya kwana yana yi. A haka washegari da safe kuma ya tashi da shirin tafiya Kano, dan gaba ɗaya komai na tafiyarsu ya gama kammala yau da daddare jirginsu zai ɗaga zuwa ƙasar China. Koda ya gama shiryawa bai samu biyawa gurin Abba ba saboda baya so lokaci ya ƙure masa, a waya kawai ya kirasa sukayi sallama yay masa fatan alkhairi. Kana ya nufi gidan Ummansa yayi mata sallama itama, kana kuma daga can direban da Abba ya turo daga Kano ya ɗaukesa suka kama hanya. 7pm. Dai-dai kuwa tayi musu ne a Mallam Aminu Kano International Airport, inda Abba da Mami har ma da Basma sukayo musu rakiya a motarsu har Airport ɗin, sai Ibrahim dake riƙe da ƙatuwar jakar sababbin kayan Ya Azeez ɗin wanda Abba ya saka Fahad ya siyan masa su masu matuƙar kyau da tsada. Yayinda kuma suna isa airport ɗin ko cikakken minti talatin basu yi ba, jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar China. Wanda su Abba basu dawo ba, sai da suka ga tashin jirginsu, kana suka dawo gida tare dasu Basma wacce zuciyarta ke cike da tsananin kewa da muradin mijinta. Su Ya Azeez kuwa sai gab da asuba jirgin ya saukesu a Shanghai Pudong International Airport. Bayan sun sauka ne kuma suka tari taxi, Fahad ya gaya mai ya kaisu hotel mafi kusa, inda direct ya nufi wani tsadadden hotel A Marriott Hotel dasu. Koda suka shiga cikin hotel ɗin kuwa booking ɗin ɗaki suka fara yi, kafin kuma sukayi wanka suka gabatar da sallar asuba, kasancewar kuma garin bai gama wayewa bane sosai yasa kawai kowannen su ya nemi gurin kwanciya suka kwanta bacci, saboda gaba ɗayansu a gajiye suke tuɓus. ************** Shatu da Zahra ne zaune a babban falon gidan kowa na sha'anin gabansa, Shatu na daga gefe guda ta harɗe a saman kujera ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana latsa wayarta, yayinda kuma Zahra ke kwance a ƙasan kafet ɗin dake falon da laptop a gabanta tana kallo. Dai-dai lokacin ne kuma Abbie da Ummi ke saukowa daga saman bene inda kwannensu ke sanye da shiga ta alfarma sai zuba ƙamshi suke. Cikin dattako suka ƙarasa saukowa cikin falon, inda da sauri Zahra ta rufe laptop ɗin da take kallon ta tashi zaune lokaci ɗaya tana ɗan sosa gefen wuyanta kafin kuma cikin yanayin rashin gaskiya tace "Barka da fitowa Abbie..." Juyowa Ummi tayi ta kalleta, kana ta harareta tana cewa "Oh saboda baki da gaskiya shiyasa kikayi saurin rufe laptop ɗin dan kar aga abinda kike yi ko...?" Kallonta Abbie yayi kana ya juya ya kalli laptop ɗin yana faɗin "Hala game takeyi ko...?" Ya faɗa yana kallon Ummi data wani haɗe rai tana hararar Zahran kafin tace "A'a ina wannan take da lokacin wani game, kallon films ai shi yafi shige mata zuciya yayi kane kane, dan indai zaka ganta da laptop a hannu to ba komai take yi da ita ba sai kallo, dan bana tunanin tunda aka siyan mata ita ta taɓa karatu ko wani assignment kullum cikin duba sabbin film ɗin India take da Korean Drama take, sai kace aikin da aka kawota yi kenan..." Ummi ta ƙarashe maganar cikin faɗa tana hararar Zahran. Haɗe fuska Abbie yayi yana faɗin "Oh dama abinda kikeyi kenan..? Ashe kice asarar kuɗina kawai nake babu karatun da kikeyi...? Toh kodai aure kikeso ne ayi miki...?" Sai lokacin ne Shatu ta ɗago kai da sauri ta kallesu, kafin kuma ta sauke numfashi ta sunkuyar da kai ƙasa lokaci ɗaya tana jin faɗuwar gaba. Zahra kuwa baki ta turo gaba a shagwaɓe tana faɗin "A'a Abbie nidai bana son aure, karatu zanyi a fara yiwa Aunty Shatu auren tukuna..." Ta faɗa tana kwaɓe fuska kamar zata yi kuka. Wani mugun kallo Shatu ta watsa mata tana faɗin "Ni sa'arki ce da zaki dinga haɗa kaina dake, ko kuwa ni abokiyar wasanki ce da ana miki magana zaki kauce ki sako sunana...?" Cike da mamaki Zahra ke kallonta, kafin ta taɓe baki tace "Ai dai dole kema zakiyi auren ko, tunda ba zamanki ba kenan a gida ba aure..." Zaburowa Shatu tayi a zafafe tayo kanta tana faɗin "Dan ubanki ba sai ki kawo min mijin in aura ba, tunda ina wasa dake ne da zaki dinga cewa zanyi aure zanyi aure, ko kin taɓa ganina da wani saurayi ne da zaki damu mutane da maganar aure aure, sai kace a kanki nake...?" Salati Ummi ta fara tana faɗin "Yau na banu ni Khadija, daga fatan arziki sai ya zama na tsiya..? Alhaji ka jini da wannan masifaffiyar yarinyar dan Allah, na rasa meyasa gabaki ɗaya halinta ya fita daban dana sauran mutane, kaji kuma wai auren ne take jin haushin dan ance zatayi...?" Kallon Shatun Abbie yayi kafin yace "Uwata zancen auren ne yanzu baki so yasa kike wannan haƙilo da tada jijiyoyin wuyan..?" A shagwaɓe Shatu tace "Inaso mana Abbie amma nifa ko saurayi bani dashi ne, kuma shine zata wani dinga yi min zancen aure alhalin tasan cewa ko mai zuwa gurina bani dashi, taya zanyi aure a haka...?" Ta ƙarashe maganar a sanyaye tana hararar Zahran. Da hanzari Ummi tace "Ai bakiso auren bane, amma ai ko Suhaib ɗin Baffanku Buba yaso ku daidaita kece kika ƙi masa daɗin hannu, ki kai ta botsarewa kina zille zille. Gashi nan har ya samu mata yayi aurensa har da ƴaƴansa biyu abinsa, ke ko kina nan jaɓe in banda son girman tsiya babu abinda kika iya..." Abbie kuwa murmusawa kawai yayi yana gyaɗa kai, kafin ya dubi Shatu yace "Kina dai son auren ko Mamana...?" Da sauri ta gyaɗa mai kai tana faɗin "Eh Abbie inaso, Amma sai na samu mijin tukunna ko...?" Ta faɗa a hankali tare kuma da rufe fuskarta da hannuwanta alamar jin kunya. Idanu Abbien ya ɗan tsura mata, kana kuma cikin nazari yace "Allah ya zaɓa maku abinda yafi zama alkhairi a rayuwarku baki ɗaya..." Da Ameen duk suka amsa kana kuma daga haka Abbien yasa kai ya fice daga falon, yayinda kuma Ummi ta rufa masa baya domin yi mai rakiya zai wuce kasuwa. ******** *BAYAN SATI BIYU* Yau ɗin ta kama Asabar ba makaranta, wanda kuma tun ƙarfe 10am. Dai-dai Shatu ta tashi daga baccin data sake komawa tun bayan sallar asuba. A hankali ta tashi zaune ta zuro ƙafafuwanta ƙasa kafin kuma ta miƙe tsaye lokaci ɗaya ta sauko daga saman gadon kai tsaye ta wuce toilet. Koda ta fito mai kawai ta ɗan shafa a jikinta, ba tare kuma da ko hoda ta kalla ba ballantana tayi tunanin shafawa fuskarta ba, ta ƙarasa gaban wardrobe ɗinta ta zaro wata rantsatstsiyar ɓaƙar abaya, mai tsananin kyau da taushi ta zura a jikinta. Sosai kuwa rigar tai mata mugun kyau a jikinta ta fito das gwanin sha'awa. Sassanyan turarenta ta fesa a jikinta, kana ta yana gyalen rigar a kanta, ba tare kuma data tsaya komai ba ta ɗauki wayarta tasa kai ta fice daga ɗakin. Tana sako kai kuwa ƙofar ɗakin suka kusan cinkaro da Zahra data taho da sauri zata shigo cikin ɗakin. Jada baya da sauri Zahran tayi tana dubanta sama da ƙasa, kafin ta saki murmushi tace "Kai Masha Allah My Aunty kinga yadda kikayi wani masifaffen kyau kuwa..? Gaskiya kin haɗu ba ƙarya wallahi..." Murmushi Shatu tayi ta kalleta kafin tace "Toh faɗi ba'a tambayeki ba, ni matsa ki bani guri in wuce..." Ta faɗa tare da raɓawa ta gefenta zata fice daga ɗakin, ajiyar zuciya Zahran ta sauke tana faɗin "Aiko ni fa Abbie yayi yace in kiraki ki samesa a falonsa..." Ta faɗa a hankali tana ɗan turo bakinta, kai kawai Shatun ta jinjina ba tare kuma da tace komai ba ta sauka ta nufi falon Abbien. Koda ta isa falon kuwa Abbie kaɗai ta samu zaune a saman kujera yana kallon TV, bayan ta durƙusa ta sake gaishesa ne kuma ya nuna mata gurin zama, ɗan nesa kaɗan dashi ta matsa ta zauna a saman kafet ɗin dake falon. Tsawon mituna goma ta kwashe a zaune shiru, kanta a sunkuye ba tare da Abbie yayi mata magana ba, yayinda kuma falon ya ɗauki shiru babu motsin komai a ciki, dan tun lokacin data shigo ya ɗauki remote ya rage ƙarar volume ɗin Tvn yayi ƙasa dashi sosai, ta yadda ba zai damesu ba. Jin shirun tayi yawa ne kuma yasa ta ɗago kai a hankali da nufin ta kalli Abbien taga me yake yi, wanda take ganin kamar mantawa yayi da tana zaune ne yasa bai ce komai ba. Ɗago kan nata kuwa yayi dai-dai ne da ɗagowar da Abbie yayi lokaci ɗaya yana gyara zamansa cikin tsantsar dattako da nuna manyantaka yana faɗin "Gyara zamanki da kyau Mamana, magana nake so zanyi dake mai matuƙar mahimmanci wanda kuma nakeso ki natsu da kyau ki saurareni...." Da sauri ta ɗaga kai ta kallesa, kafin kuma lokaci ɗaya ta gyara zamanta da kyau tana fuskantarsa. "Aishatu...." Abbie ya kira sunanta cikin sanyin murya mai cike da son bada umarni. A hankali ta amsa kana lokaci ɗaya ta ɗago tana kallonsa, sakamakon kiran sunanta da yayi sak ba tare da wani sakaye ba kamar yadda ya saba mata, wanda kuma tun tasowarta bata taɓa jin ya kira koda wata mai irin sunanta bane kai tsaye kasancewar sunan mahaifiyarsa gareta sai dai yace Mamana ko uwata, ballantana ita da tun tana ƙarama ta gama sabawa da kiranta da yake da uwata, amma yau sakamakon kiran sunanta da yayi dangas sai abun yazo mata a wani irin yanayi na daban. Gyara zamansa yayi a hankali, kana kuma cikin sanyin murya da nuna tsantsar kulawa yace "Inaso ki natsu da kyau kiji abinda zan gaya miki, sannan duk abinda zan gaya miki inaso ki natsu da kyau kuma ki bani gamsashshiyar amsa wadda zata gamsar dani..." A hankali ta gyaɗa mai kai kafin kuma cikin sanyin jiki tace "Insha Allahu Abbie..." Jinjina kansa Abbie ɗin yayi, kafin kuma yace "Kin dai san aurene ya haifeki ko..? Kuma duk wata ɗiya mace mai cikar kamala burinta shine aure...? Amma ke meyasa baki so ko maganar auren ayi miki....?" Rass rasss haka gaban Shatu yayi wani mugun bugawa, runtse idanunta tayi a hankali yayinda take jin yadda gaba ɗaya jikinta yake son ɗaukar rawa. Abbie kuwa maida hankalinsa yayi gabaki ɗaya kanta ya zuba mata idanu ƙirr yana kallonta cikin nazartar yanayinta. Sakin murmushi yayi kafin ya ƙara tsura mata idanu yana faɗin "Ina saurarenki..." Ya faɗa kai tsaye yana kallonta. Saurin girgiza mai kai Shatu tayi lokaci ɗaya tana ƙoƙarin haɗiye wani kakkauran yawun daya daskare mata akan harshe, kafin kuma a hankali ta tattaro jarumta cikin in ina tace "A'a Abbie...ba..ba haka bane..bani da saurayi ne kuma ma ni kwata kwata ban taɓa..yin wani saurayi ba shiyasa...." Tai maganar a rarrabe tana sunkuyar da kanta. Ɗan guntun murmushi Abbie yayi tare da gyara zamansa kafin yace "Amma kinsan cewa dole wata rana komin daren daɗewa zakiyi aure tunda ba haka zan ta zuba miki idanu ina kallonki a cikin gida kina jera kafaɗa da kafaɗa da mahaifiyarki kuna kaiwa da kawowa a tare kanku ɗaya ina kallonku ba ko Mamana...?" A sanyaye Shatu ta sake gyaɗa mai kai tana jin taruwar wasu hawaye a idanunta tace "Zanyi insha Allahu Abbie ku tayani da addu'a Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi..." Ta faɗa lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta da zuciyarta na mata wani irin bugu da take jin zuciyar tata kamar zata fasa ƙirjinta ta fito waje. Da Ameen ya Allah Abbie ya amsa mata kana ya ɗora da faɗin "Insha Allahu kuwa kyakkyawan zaɓi mafi alkhairi Allah zaiyi muku, tashi kije in kin fita ki turo min Ummin ku..Allah yayi muku albarka yasa a gama lafiya..." Ya faɗa cikin tsantsar kulawa da dattako. A hankali Shatu ta miƙe lokaci ɗaya tana ƙara rusunawa tace "Na gode Abbie Allah ya ƙara girma da nisan kwana..." Ta faɗa tare da juyawa tasa kai ta fice daga falon. Tana fita kuwa ba jimawa Ummi ta turo ƙofar falon ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Yanayin yadda taga Abbien nata sakin murmushi ne kuma yasa ta sakin wani lallausan murmushin itama, kafin ta ƙaraso ta zauna a kusa dashi tana kallonsa. Gyara zama Abbie yayi yana fuskantarta kafin ya soma zayyano bata duk yadda sukayi da Shatu, kamar yadda Ummin da kanta ta bashi shawarar ya titsiyeta ya tambayeta ta fito da miji, sosai mamaki ya kama Ummi dan ita har ga Allah tana burin taga auren babbar ƴar tata, shiyasa duk ta ƙosa taga ta gama makaranta ko taji anyi sallamar neman aurenta saboda ita duk a tunaninta karatun da Shatun ke yi ne yake hanata saurarar samari. Fatan samun na gari tayi mata, kafin daga haka suka cigaba da tattaunawa akan yanayin karatun Shatun. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 3️⃣2️⃣ A ɓangaren su Ya Azeez kuwa yau kimanin watansu biyu kenan cif a ƙasar China. Wanda kuma zuwa lokacin tuni har sun kammala siyan dukkan abinda ya kai su ƙasar, inda kuma wani abokin kasuwancin Abba Mr Yuang da Abban ya haɗasu dashi ne wanda asalinsa ɗan ƙasar Chinan ne, shi ya dinga yi musu jagoranci yana kaisu kamfanonin da suke siyan nagartattun motocin da suke shigowa dasu ƙasar ta Nigeria. Sai da suka kwashe watanni biyu cif har da kwana goma a ƙasar, wanda zuwa lokacin kuma tuni kayansu sun jima da isa ƙasar Nigeria. Inda kayan sun isa ne da kwana biyu suma suka fara shirin dawowa gida. Ƙarfe 5pm. dai-dai na yammacin yau ɗin ne kuma jirginsu ya ɗaya zuwa gida Nigeria. *BAYAN SATI BIYU* Yau kimanin sati biyu kenan da dawowarsu, wanda kuma zuwa yanzu komai na tafiya dai-dai musamman ta ɓangaren shagunan Ya Azeez ɗin da gidan motocin su, dan zuwa yanzu kam an gama tsara komai da komai lokaci kaɗan gidan motocin nasu zai fara aiki. Sai da sukayi sati huɗu cif da dawowa gida sannan suka buɗe gidan motocin wanda kafin kace me har sun fara samun jama'a kota ina. Bayan sun zuba ma'aikata ne kuma da masu kula da gurin da dukkan wani ciniki dake shiga da fita, wanda tuni dama shi Fahad Abba yasa ya barwa Ya Azeez garamar kula da komai na gurin a matsayin manaja, murna sosai Ya Azeez ɗin yayi ya dinga yiwa Fahad da Abba godiya har da kwallarsa. Haka Umma da Ya Azeez ɗin ya kirata ya gaya mata sai data zo har Kano tai ma Abban godiya, kafin Ya Azeez ɗin da Fahad suka ɗauketa a danƙareriyar sabuwar motar da Abban ya siyawa Ya Azeez ɗin ƙirar Mazda CX-30 fara sol suka kaita har kamfanin motocin da shagunan Ya Azeez ɗin dake cikin kasuwa ta gani, kafin ta kwana washegari Abba yasa direbansa ya maida ita Kaduna. Alhamdulillahi Ya Azeez ya fara kasuwancinsa da ƙafar dama, kuma komai yana tafiya dai-dai akan tsari, dan zuwa yanzu hatta da Umma Ya Azeez yanzu ya huttasheta bata zuwa kasuwa, shi ke tura mata da kaya ta mota har Kaduna. Kafin kace me dan da nan Ya Azeez ya canza lokaci guda yay wani irin kyau na musamman har da ƴar ƙiba ya ƙara, ga kuɗi nata shigo masa kota ina, basu rufe wata uku da fara harkar kasuwancin su ba abubuwan alkhairi suka soma shigo masa kota ko ina, Allah ya sakawa kasuwancinsa albarka dan da nan shagunansa suka yi fice a faɗin kasuwannin, wanda kasancewarsa kuma mutum mai taimako da rangwame akan kayansa yasa dan da nan sunansa yayi fice a garin Kano, wanda bama ga ƴan kasuwa kaɗai ba hatta da kamfaninsu na siyar da motoci komai tuni Allah ya sakawa nemansu nasibi. Abu na farko kuwa da Ya Azeez ya fara yi da abubuwa suka fara warware masa shine taimakon danginsa, yan uwan Abbansa dana Ummansa tamkar yadda mahaifinsa yayi lokacin da yake raye, wanda a tashin farko Babura ya fara zuwa kai tsaye yaje yay musu sha tara ta arziki, inda daga nan kuma yasa aka neman mai babban shagon saida zannuwa a Chechenia Market dake garin Kaduna, ya zubawa Abban Fadwa kaya kama daga kan less, atamfa, shaddoji da yadikan maza dana mata, sai abayoyin mata, da jallabiyoyin maza. Sai daya cika masa shagon taf da kaya sannan ya mallaka masa ƙaramar mota ƙirar Camry domin zirga zirgar yau da kullum ta zuwa kasuwa da dawowa. Lokacin da motar ta isa ga Abban Fadwa kuwa yayi matuƙar murna sosai da farin ciki, dan har ƙwalla sai da ya zubar saboda tsantsar farin ciki da jin daɗi. Yau kwanan motar biyar kenan da kawota amma koda wasa Abba bai taɓa gayawa Mama ba, sai dai kullum da safe idan zai tafi kasuwa yaje gidan wani Alhaji dake nan ƙasan layinsu ya ɗauki motar ya tafi, haka idan ya dawo da yamma ma sai yaje ya kaita gidan ajiya sannan yake takowa da ƙafa yazo gida, shiyasa har yau Mama da Fadwa basu taɓa sanin wani sauyi da Abban ya samu ba, ballantana har su san halin da yake ciki, wanda su har yau a tunaninsu faci yake. Dan kullum cefanen da ya saba shigowa dashi gidan har yau haka yake musu babu abinda ya canza, sai dai tun bayan da Fadwa ta dawo gidan har yau basu ƙara cin tuwo ba, dan koda ya kawo garin tuwon da kayan miya basa amfani dashi sai dai su ajiye. A haka rayuwa tai ta tafiya, yayinda kuma zuwa yanzu ɗan kuɗin da Fadwa ke samu tana kashewa take kuma badawa ayo musu cefane su yi cima mai daɗi sun fara ƙarewa, dan ta kai yanzu tunda taga kuɗin sun fara ƙarewa, kullum da sassafe zata shirya ta caɓa uban kwalliya ta fita abunta kai tsaye babu abinda ya dameta, idan ta fita kuma bata taɓa dawowa gidan sai dare kuma kullum idan zata dawo da manyan ledoji cike da kayan ciye ciye take shigowa gidan. Amma koda wasa Mama bata taɓa tambayarta a inda take samosu ba, sai dai kullum idan ta kawo jiki na rawa tasa hannu ta karɓe tana washe baki suyi kasafi su raba su ci abunsu suyi hani'an babu abinda ya damesu. Ana cikin haka wata ranar juma'a da daddare Fadwa ta dawo daga gidan bikin ƙanwar ƙawarta Hajiya Zalika wanda aka yi anan Kaduna. Tana zaune a tsakar gida ita da Mama dasu Ilham da Amatullah da suka ɓararraje suna ta ciye ciyen abubuwan da aka raba a gurin bikin da tazo musu dashi, lokaci ɗaya kuma tana basu labarin yadda manyan mutane masu ji da kuɗi da kansu suka halarci taron bikin. Suna cikin haka wani almajiri yayi sallama yace ana sallama da Fadwa a ƙofar gida. Da sauri Mama ta yafito yaron tana washe baki tace "Kai waye ya aikoka...?" Yaron yace "Wani Alhaji mai mota ne yana ƙofar gida..." Ko kafin yaron ya ƙarasa Mama ta miƙe da rawar jiki tana kabbara tace "Allahu Akbar! Yaro maza jeka kace tana zuwa yanzun nan..." Ta faɗa cikin zallar farin ciki tana bin bayan yaron har zuwa zauren gidan. Laɓewa tayi a bayan ƙofa tana leƙa ƙofar gidan, ganin wata tsaleliyar ɓaƙar mota ƙirar Benz da tayi ne fake a ƙofar gidan yasa ta juyowa da sauri jiki na rawa ta koma cikin gidan tana kwalla kiran sunan Fadwa dake cikin ɗakin tana ƙoƙarin canza kaya, da sauri ta fito tana faɗin "Gani nan Mama..." Cikin rawar jiki da tarin farin ciki Mama tace "Lallai yau kinyi gam da katar ƴar albarka, wallahi ba kiga tsaleliyar motar da yazo a cikinta ba. Yi ki shirya ki fito yana jiranki, kar kuma ya gaji da jira ya tafi..." Ta faɗa da sauri tare da faɗawa cikin ɗakin ta ɗauko turare ta hau feshe mata jiki dashi sama da ƙasa, sai data gama mata ruwan turare a jikinta sannan ta ɗauko wani ɗan siririn gyalen daya shiga da rigar leshin dake jikinta ta sagala mata a gefen kafaɗarta. Ɗan ja da baya tayi da sauri tana ƙara ƙare mata kallon sama da ƙasa, kafin ta jinjina kai tare da ɗaga mata babban yatsa tace "Komai yayi maza jeki. Adawo lafiya..." Ta faɗa tare da kama hannunta suka fice daga gidan, suna zuwa zaure ta sakin hannunta tace "Allah ya tsare adawo lafiya..." Ta faɗa tana komawa bayan ƙofa ta laɓe tana leƙensu. Cikin wani irin takun yanga Fadwa ta ƙarasa gurin motar ta tsaya, lokaci ɗaya tana ƙarewa motar kallo cike da ɗokin son ganin mamallakin motar. A hankali ya buɗe motar ya fito cikin isa da ginshira yake ƙare mata kallon tsaf, kafin ya ɗan saki wani malalacin murmushi yace "Ya akayi ne Baby..?Ƙaraso mana..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana kallonta tun daga sama har ƙasa. Ƙarasowa gaban motar tayi ta tsaya tana jin kamar ta daka tsalle dan murna da farin ciki. Ɗan karkace kai tayi gefe, kafin kuma cikin iyayi tace "Ina yini yallaɓai...?" Ta faɗa da rawar jiki tana ɗan rusunawa. Jingina yayi da jikin motar yana kallonta sama da ƙasa kafin yace "Fadwa ko...?" Ya faɗa a hankali yana ɗan sakin murmushi, kaɗa kai tayi kafin cikin ƙaƙalo wata siririyar murya tace "Eh yallaɓai nice..sunan kenan..." Murmushi mutumin yayi kafin ya ɗan kalleta yana faɗin "Ok ni kuma sunana Muhammad Al'ameen Zailani kuma nine shugaban majalisa ta Kaduna, kuma na ganki ne a gurin bikin abokina Alhaji Hannafi Mamadi da akayi yau, bari dai in barki haka kar in cika ki da surutu, in ba damuwa inaso ayi min iso zan shiga in gaida Mama..." Mama kuwa dake laɓe ta kaso kunne, jin abinda yace yasa ta juyawa cikin gidan da gudu ta faɗa ɗaki ta ɗauko wata sabuwar darduma wacce ko Abba bai taɓa ganinta ba ta shimfiɗa a ƙofar ɗakinta, bayan ta kori Ilham da Amatullah tace duk shige ɗaki ta koma ta canjo hijabin jikinta ta dawo ta zauna a gefen darduman tana jiran shigowar su. Ganin shigowar Fadwan ita kaɗai ne kuma yasa ta ɗaure fuska ta kalleta tana faɗin "Ya haka kuma, ina baƙon yake...?" Ta faɗa tana kallon bayanta, wani irin faɗowa jikinta Fadwa tayi tana faɗin "Mama kinsan waye kuwa...?" Girgiza mata kai Mama tayi tana faɗin "Ai da gani ma ba sai an faɗa ba dama wannan mutumin shine irin mijin daya cancanci mallakarki Fadwa, shine irin mutumin da muke ta dakon jiran zuwansa tun tuni, sai gashi yau ɓagatatan Allah ya jefo mana shi, dan haka maza jeki shigo mana dashi ɗan albarkan..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana katseta daga abinda take shirin gaya mata. Miƙewa Fadwan tayi da sauri ta juya ta ta fice daga cikin gidan. Ba jimawa kuwa sai gasu sun shigo cikin gidan, yana biye da ita a baya suka ƙaraso har gaban Mama dake ta faman yage baki tana mai barka da zuwa cike da tsantsar murna da farin ciki. Matsawa yayi ya zauna ɗan nesa kaɗan da Mama akan darduman, suka gaisa kafin ya gabatar mata da kansa, inda tunda ya fara maganar Mama ta zuba masa ido tana kallonsa sama da ƙasa, ganin irin mashahuriyar shigar alfarmar dake jikinsa ne ya ƙara gigita mata tunani. Wani irin tsananin farin ciki mara misaltuwa yau Mama take jin kanta a ciki. Karkacewa yayi gefe ya zura hannu cikin aljihun wandon tsadaddiyar shaddar dake jikinsa ya zaro kuɗi masu yawa ya zube a gabanta yana faɗin "Ga wannan ba yawa ayi haƙuri, sai na da ɗa zagayowa..." Ko kafin ya gama rufe baki Mama ta fara tattare kuɗin tana faɗin "Haba ba komai wallahi, mai yawan kenan wannan ai kyautar manya ce..." Ta faɗa kai tsaye, kafin kuma ta shiga kwallawa Ilham da Amatullah kira tana faɗin "Amatu.. Ilham Ina kuke ne..? Maza kuzo ku gaida yayanku zai wuce..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana tattare kuɗin da hanzari ta tura a hijabinta. Fitowa su Amatullah ɗin sukayi suka gaishesa, da murmushi a fuskarsa ya amsa musu, ganin ya zura hannu a aljihu yana ƙirgo kuɗi ne yasa Mama sake washe baki tana zuba masa godiya kamar bakinta zai yage saboda tsantsar farin cikin da take ciki. Kuɗi masu yawa ya damƙo a hannunsa ya miƙa musu, da sauri Mama tasa hannu ta karɓe tana faɗin "A'a ranka ya daɗe kuma har da ƙarin wata wahalar haka..? Mun gode mun gode Allah ya saka da alkhairi, Allah yasa a gama da duniya lafiya mun gode..mun gode Allah ya raya zuri'a yayi musu albarka..." Miƙewa yayi zai tafi, Mama ta miƙe da sauri itama tana ƙara kwarara masa godiya, a hankali ya zura takalmansa da tunda ya zauna Mama take gyara mai zamansu ta matsar mai dasu dai-dai gurin ƙafarsa ta yadda zai zura cikin sauƙi, miƙewa Fadwa tayi itama cikin rawar jiki ta rufa masa baya, Mama kuwa sai data rakosa har cikin zaure, sannan ta juya ta koma cikin gida cike da tsananin farin ciki, su kuma suka fita shida Fadwa. Jiki na rawa Mama ta zauna ta miƙe ƙafafu bayan ta zube kuɗin duka a gabanta ta hau ƙirgawa. A ɓangaren Fadwa kuwa koda suka ƙarasa gurin motarsa bai wani tsaya dogon zancen da ita ba ya buɗe mota ya shiga ya zauna kana ya buɗe mata ɗayan gefen itama yace ta shigo, ba tare da wani tunanin komai ba kuwa ta zagaya da sauri ta shige tana ji tamkar ta taka rawa saboda tsabar murna. Juyowa yayi ya ɗan kalli fuskarta da har lokacin take ɗauke da fara'a, kafin a hankali ya kamo hannunta ya riƙe a nasa wanda kamar dama Fadwa jira take ya riƙe hannun nata, ta ƙara matsawa jikinsa sosai ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, ɗan murmushi yayi tare da ƙara damƙe hannunta a nasa kafin kamar daga sama taji muryarsa yana faɗin "Baby ina matuƙar sonki ina ƙaunarki, zaki aureni...?" Ya faɗa cikin wani irin salo da shine kaɗai yasan ma'anarsa. Zaro idanu Fadwa tayi cike da tsantsar mamaki da kaɗuwa tana faɗin "Why not ranka ya daɗe..me zai hana...?" Ta faɗa kai tsaye tana tsaresa da manyan idanuwanta waɗanda ke cike da tsantsar farin ciki da jin daɗi. Numfashi yaja a hankali kafin ya zame hannunsa a nata yana faɗin "Ok ba matsala, ni zan wuce ki bani numbern wayarki zan kiraki sai mu ƙarashe maganar a waya...." Jinjina masa kai tayi cike da farin ciki tana washe baki, kafin taga ya buɗe wani guri a cikin motar ya ɗauko kuɗi sabbi fil rafa guda ya miƙa miƙa mata yace "Gashi ki siya kati da kayan kwalliya, kafin insa ayo miki odern wasu daga Dubai..." Karɓa tayi tana masa godiya tamkar zata zube ƙasa dan farin ciki, fitowa tai. daga motar ta nufi cikin gida yayinda shi kuma yaja motar ya bar unguwar. Da ihun murnarta ta shigo cikin gidan, Mama dasu Ilham suna zaune har lokacin a tsakar gida Mama nata lissafin kuɗi. Murmushi kawai Fadwa tayi ta zauna tana duban Ilham da itama itan ta tsare da idanu tana kallonta. Kwaɓe fuska Fadwan tayi ta taɓe baki kafin ta juya ta miƙawa Mama kuɗin dake hannunta tana hararar Ilham data tsare ta ido, tana faɗin "Kinga inda ake harkar arziki ko Ilham...? Amma kullum ki damu mutane da zancen in koma gidan Ya Azeez duk kibi ki damu mutane da zancen sa saboda baki san ɗumbin alkhairin dake kirana ba kikeso ki ƙara turani gurin tsiya sai kace wata uwar abun na tsinta a auren nasa da har kike min sha'awar komawa in cigaba da zama dashi, shegiya mai baƙin halin tsiya da munafunci. To kiga dai harkar arziki yau yau ɗin nan daga ganina mutum ya biyo ni har gida ji bi abun alkhairin da yayi mana nida ku..? Amma sai ki ta damun mutane da maganar wani banza can Ya Azeez sai kace ƙanin uwarki kona ubanki..." Ta ƙarashe maganar a zafafe tana watsa mata harara. Kauda kai kawai Ilham ɗin tayi ba tare kuma da ta tanka mata ba, ta miƙe tsaye ta zura takalmanta ta wuce ɗaki tana mai tsananin takaici da baƙin cikin halin kwaɗayi da son abun duniya irin na mahaifiyar tasu da Auntyn su. Ita kuwa Mama ko bi ta kansu ma ba tayi ba tana can gurin hidimar lissafa kuɗin da Fadwa ta shigo dasu, zaro idanu tayi tare da kama hanci lokaci ɗaya ta saki guɗa, kafin kuma cike da tsananin farin ciki tace "Kan uban nan kai..kinji inda ake harkar arziki, Lallai yau munyi gamdakatar..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana barbaje kuɗin a gabanta tana kallo, ganin yanda kuɗin sukai wani caa agabanta ne yasa ta ƙara zaro idanunta waje tace "Kiga tsabar kuɗi dan Allah kiga irin wannan abun arziki..? Wuri na gugar wuri naira na gugar naira har naira dubu ɗari cif cif, ga kuma wanda ya bani dubu hamsin sai wanda yabawa su Amatu suma dubu ashirin, dubu ɗari da saba'in fa kenan a daren nan..? Kai!! Amma wannan mutumi yayi wallahi yayi ba ƙarya..." Ta faɗa cikin fara'a da tsananin farin ciki tana washe baki. Tashi Amatullah tayi itama ta bar gurin tana mai musu addu'a da fatan shiriya a zuciyarta ta wuce ɗakinsu. Su ko su Mama da Fadwa ko a jikinsu babu wanda yabi ta kansu, haka sukai ta murnar kuɗinsu suna jin daɗi. Kafin daga bisani Mama da taga lokacin dawowar Abba gida yayi ta tattare kuɗin ta shige dasu ɗakinta taje ta ɓoye a cikin kayanta sannan ta dawo suka cigaba da tattaunawa akan sabon saurayin a Fadwa. ********** Washegari Misalin ƙarfe 4pm. Dai-dai na yamma zaune yake a tsararren falonsa dake cikin gidan Abba yana latsa tsadaddiyar wayarsa ƙirar iPhone 12pro max. Sanye yake da wata tsadaddiyar shaddar Bazan mai kyau da yarari kalar ruwan toka, sai rufaffen takalmin ƙafarsa daya kasance baƙi, haka hular kansa zanna bukar mai zanen baƙi ce. Sai kyakkyawan haɗaɗɗen agogon baƙin fatan dake ɗaure a hannunsa na kamfanin Rado, sosai shigar tayi masa bala'in kyau, dan shi karan kansa daya gama shiryawa kafin ya fito, sai daya kai dubansa ga madubi ya ɗan murmusa, domin shi a karan kansa sai daya yaba da tsantsar kyau na musamman da yaga shigar tayi masa. Sannan ga wani irin masifaffen ƙamshi na musamman da daɗin shaƙa da yake fitarwa a jikinsa, lallausan sajen nan nasa kuwa ya kwanta luf luf sai ya ƙara fito da ainihin kyaun fuskarsa da zallar haiba da kwarjininsa, sai sheƙi yake kamar wani sabon ango. A hankali ya gyara zaman hular dake kansa yana duba agogon dake hannunsa, kafin ya saki tsaki lokaci ɗaya yana miƙewa tsaye da wayarsa riƙe a hannunsa yasa kai ya fice daga falon. Direct sashen Fahad dake can wani ɓangare daban a cikin gidan ya nufa, cikin takunsa na isassun maza masu ji da kansu, da sassarfa ya ƙarasa ƙaramar ƙofar gate ɗin gidan ya tsaya yana ɗan ƙwanƙwasawa. Jin shiru ba'a buɗe bane yasa ya tura ƙofar a hankali ya shiga kai tsaye yana ƙarewa ɗan madaidaicin ƙaramin filin tsakar gidan da aka ƙayatasa da shukar furanni masu ƙamshi da ɗaukar ido. Yana isa dai-dai ƙofar da zata sadashi da shiga falon gidan ne kuma ya fara jiyo dariyar Fahad ɗin daga can cikin falon yana faɗin "Pls pls pls Baby..kiyi haƙuri bazan daɗe ba yanzu zan dawo kinji...?" Kansa ya ɗan girgiza tare da lumshe idanunsa, kafin kuma a hankali yasa hannu ya fara ƙwanƙwasa ƙofar falon. Buɗe ƙofar falon da Fahad ɗin yayi ne yasa ya tamke fuska yana harararsa kafin juya yana faɗin "Idan ka fasa zuwa ne ai da tun tuni ka sanar dani in wuce abuna, amma saboda ka maidani ɗan iska shine zaka wani shanyani ka barni ina ta zaman jiranka, kai kazo ka wani rashe ka miƙe ƙafafu ka barni acan inata kiranka ma ka ƙi ɗauka..." Ya faɗa da alamun gajiya da zaman jiran nasa da yayi. A karkace Fahad ya kallesa kafin yace "Kasan abinka dame iyali, wallahi hanani fita tayi sai dana lallasheta na lalaɓata tukunna. Kuma lokacin da kake kira ina kallon kiran naka amma bani da lokacin ɗagawa ne saboda ina kan lallashi iyalina..." Ya faɗa cike da tsokana yana ɗaga masa gira. Sakin baki galala kawai Ya Azeez yayi yana kallonsa, kafin ya kaɗa kai ya juya ba tare da ya tanka mai ba ya kama hanyar ficewa daga cikin gidan, saboda yasan halin Fahad idan ya biye masa yanzun nan zai fara mai terere yana mai gorin bai da mata dan haka ya barshi ya kula da tashi matar, tunda shi yanzu gwauro ne baida mai lallaɓasa. Shiko Fahad ganin ya fice ne bai ce mai komai ba, yasa ya bi bayansa da sauri yana ƙoƙarin danne dariyar dake taso masa. Koda ya ƙarasa ya iske har ya buɗe motarsa ya shiga ya zauna, yana ƙoƙarin tada motar, da gudu ya ƙarasa ya buɗe ɗayan ɓangaren ya shiga ya zauna, ko gama rufe ƙofar kuwa bai yi ba Ya Azeez ɗin yaja motar da gudu ya tunkari gate, zaro idanu Fahad yayi cike da tsoro yana faɗin "Aboki meye haka ne wai...?" Ya faɗa da mamaki yana kallonsa, hararansa Ya Azeez ɗin yayi kafin yace "Sauka ka hau taka motar, sai mu haɗe acan tunda kasan gidan..." Ya faɗa tare da taka motar a guje bayan maigadi ya buɗe masa gate ya fice daga cikin gidan. Kallonsa Fahad yayi kafin yace "Wai meye na duk wannan fushin ne kake ta wani cin magani, daga faɗar gaskiya kawai sai cibi ya zama ƙari...?" Kai tsaye Ya Azeez yace mai "Nima ka jira lokaci ka gani yaro, na kusa in baka mamaki. Kai ƙaramin ɗan iska ne sabon shiga..." Kallonsa Fahad yayi kafin yace "Kan uban nan kai, ni kake kira da yaro..? Ina shirin zama Daddy amma saboda tsabar tsaurin ido irin naka shine kake kirana da yaro...?" Ko kallonsa Ya Azeez bai yi ba yace "Kaji dashi dai..." Wani kallo Fahad ya watsa mai kafin yace "Gwauro kawai..." Ya faɗa cike da jin haushin kiransa da yaro da yayi. Bai tanka masa ba yayi banza dashi, ya ci gaba da tuƙinsa cikin ƙwarewa a haka har suka shiga tsararriyar unguwar ta Nasarawa Gra. Suna isa dai-dai tangamemen gate ɗin gidan Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai, Ya Azeez yayi horn da hanzari maigadi ya taso ya wangale musu gate, cikin natsuwa ya sako hancin motarsa cikin gidan kafin a hankali ya ƙarasa inda aka tanada domin ajiye motoci ya faka motar. A kuma Dai-dai lokacin ne direban Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya zuba horn a bakin gate ɗin gidan nasa, inda da sauri maigadin ya tashi yaje ya wangale masa ƙofar gate ɗin kafin a hankali direban ya silalo motar ya shigo cikin gidan. Bayan ya gama daidaita parking ne kuma maigadin ya ƙaraso da sauri ya buɗe masa murfin motar yayinda lokaci ɗaya kuma ya ɗan rusuna yana yi masa barka da dawowa, a hankali ya fito daga cikin motar yana mai kallon motar su Ya Azeez dake fake a kusa da tashi, wanda kuma har lokacin suna ciki basu fito ba. Ganin Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ɗin ne kuma yasa Fahad saurin buɗe motar ya fito yana ƙarasowa gabansa ya rusuna yana gaishesa, ganin haka ne kuma yasa Ya Azeez buɗe motar shima ya fito cikin natsuwa ya ƙaraso gabansu ya ɗan rusuna yana gaishesa. Da fara'a Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya amsa musu, kana kuma cikin tsananin farin ciki da jin daɗin ganinsu ya ɗago su atare yana riƙe da hannayensu suka nufi cikin gidan kai tsaye. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 3️⃣3️⃣ A tare dukkansu suka shiga cikin falon yayinda Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya sake riƙe hannun Ya Azeez ƙam a cikin nasa, wanda kuma a zuciyarsa yaje jin wani irin tsananin nishaɗi da tsantsar farin ciki mara misaltuwa. Suna ƙarasowa tsakiyar falon kuwa Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya shiga kwallawa Ummi kira yana faɗin "Khadija..! Khadija..!! Ina kike ki fito mun yi baƙi..." Ya faɗa cikin ɗan ɗaga murya ta yadda duk inda Ummin take zata jiyosa. Kasancewar kuma suna kichin ne ita da Zahra yasa cikin hanzari suka bar abinda sukeyi suka fito a tare da sauri zuwa babban falon. Ummi ce akan gaba sai Zahra dake biye da ita a baya, tana faɗin "Ko daga ina kuma baƙin suka zo da yamma nan oho..." Ta faɗa cikin ƙagara da son ganin baƙin nasu. Da Fahad ta fara arba zaune a saman kujera yana sakin murmushi, kafin kuma idonta ya sauka akan Ya Azeez dake zaune shima a gefen Fahad ɗin hannunsa riƙe da makullin mota da wayarsa yana kallonta. Tsayawa tai cak tana kallonsa kafin ta washe baki lokaci ɗaya ta taho da gudu tana faɗin "Laaa Ya Abdul kaine..dama kasan gidan mu ne yaushe kazo...?" Ta jero masa tambayoyin duka a tare cikin matsanancin farin ciki da mamaki tana kallonsa. Ya Azeez kuwa dake zaune fuskarsa ɗauke da tsananin farin ciki da kuma mamakin ganin Zahran da yayi a gidan, ya sake faɗaɗa fara'arsa yana kallonta still kuma fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Dama nan ne gidanku..ina Auntynki...?" Rausayar da kai Zahra tayi kafin tace "Aunty Shatu tana ɗaki yanzu ta haura sama, bari inje in kirata tazo ku gaisa..." Ta faɗa kai tsaye tare da juyawa da sauri ta haura sama zuwa ɗakinsu domin kiran Shatun. Murmushi Abbie da Ummi sukayi tare da juyawa suna kallon Zahra data ƙarasa haurawa saman da gudu tana kwallawa Shatu kira, kafin kuma lokaci ɗaya su dawo da kallonsu kan Ya Azeez wanda shima Zahran yabi da kallo yana sakin wani lallausan murmushi daya ƙarawa kyakkyawar fuskarsa kyau da haiba. Sake kallonsa Abbie yayi fuskarsa ɗauke da fara'a yana faɗin "Au ashe kama sansu tunda gashi naji kai tsaye Zahra ta ambaci sunanka...?" Jinjina mai kai Ya Azeez ɗin yayi, kana ya buɗe baki kenan zai bashi amsa. Dai-dai lokacin kuma Shatu da Zahra suka sauko a tare zuwa cikin falon, yayinda ganin fitowar Shatun kuma tasa gabaki ɗaya hankali da tunanin Ya Azeez ɗin sukutum ya tafi gareta, wanda a ɓangaren ta itama hakan ce ta kasance. Idanunsu gaba ɗaya suka zubawa juna, yayinda lokaci ɗaya Ya Azeez yaji wani irin abu ya daki ƙirjinsa, sakamakon kallon kyakkyawar fuskar Shatun da yayi. Wani irin tsantsar mamaki ne ya lulluɓe Fahad, yayinda yaga yadda Ya Azeez ɗin ya tattara gabaki ɗaya hankali da natsuwarsa kacokan ya ɗora akan Shatu wacce gaba ɗaya itama ta shagala da kallonsa lokaci ɗaya tana sakin wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Matsawa kusa dashi Fahad yayi kana cikin dabara ya zunguri gefen kafaɗarsa yana galla masa harara, kafin kuma cikin yin ƙasa ƙasa da murya yace "Dalla Malam ka natsu ka dawo hayyacinka..ka wani saki baki da hanci kamar gaula sai ƙarewa ƴar mutane kallo kake sai kace wani maye, kai ko kunyar iyayenta ma bakaji ba..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana yi masa nuni da Abbie daya zuba musu ido yana kallonsu. Wani kallon banza Ya Azeez ya juyo ya watsa mai kafin ya ɗauke kai yana faɗin "Ina ruwanka dani...? Kai uban me ya kai idonka kanta da har kasan ina ƙare mata kallo in banda tsabar gulma da shegen sa idonka...?" Ya faɗa tare da haɗe rai yana zafga masa harara. Dariya ce taso kufcewa Fahad amma sai bai bari ta fito fili ba, yayi sauri ya haɗiyeta kafin yace "Allah ya huci zuciyar gwarzon mazaje angon Hajiya Fadwa..." Ya faɗa cikin tsokana yana cigaba da danne dariyarsa, banza dashi Ya Azeez yayi bai tanka masa ba, saboda ya fahimci take takensa so yake ya biye mai su raba hali a gidan mutane, shi kam bada shi ba. Ba zai yarda ya barshi da jin nauyi da kunyar mutanen gidan ba, duk da bai san dalilin Abba na turo su gidan da yayi ba, kawai yace suzo ne su gaishe da Abbie da Ummi, sannan ya gaisa da babbar ƴar Alhaji Bellon kuma ya ganta idan tayi masa. Ita kuwa Ummi tuni ta koma kichin da hanzari domin ta kawo musu abun motsa baki. Ba jimawa kuwa sai gata ta fito riƙe da wani ɗan madaidaicin farati ɗauke da juices da ruwan gora mai sanyi sai wani ƙaramin filet data zubo fruit masu sanyi akai tazo ta ajiye a gabansu kana ta koma kusa da Abbie ta zauna, tana kallonsu Zahra da Shatu da sukai cirko cirko a tsaye, Zahra sai faman washe baki take kamar wacce aka yiwa bushara da gidan aljanna, Shatu kuwa juyawa tai da sauri ta wuce ɗakinsu da hanzari yayinda a zuciyarta kuwa har lokacin take cike da matsanancin mamakin ganinsa a gidan nasu, wanda kuma hakan yasa har ta manta da yanayin shigar da ke jikinta ta fito a haka. Inda take sanye da wasu tausasan riga da wando masu kamar sleeping dress marasa kauri, sosai kayan sukayi masifar bin jikinta musamman ma wandon daya bayyana shape ɗin cikakkun hips ɗinta masu faɗi, sai kuma rigar data kasance mai ɗan faɗi kaɗan wacce ta ɗan kamata ta bayyana tudun cikakkun ƙirjinta. Gaba ɗaya sha'afa tayi ta manta lokacin da Zahra taje kiranta ta biyota a yadda take gashi kanta ko ɗankwali babu sai lallausan baƙin dogon gashinta dake ta sheƙi daya zubo har kan kafaɗarta, domin ita duk a zatonta ƙarya kawai Zahran take da tace mata Ya Abdul ɗin yazo gidansu shiyasa ta fito da sauri dan taga zahiri. Bin ta sukayi da kallo dukkansu har sai data ɓacewa ganinsu kafin Ya Azeez ya iya ɗauke manyan idanunsa daga kanta yana sauke numfashi. Ita kuwa Zahra sai murmushin jin daɗi take yi wanda ke bayyana tsantsar farin ciki da jin daɗin da take ciki. Abbie ne ya kallesu yace "Ku saki jikinku sosai dan Allah nan ma gidan ku ne kunji..? Ke Zahra maza zuba musu lemun su sha..." Abbie ya fada cikin kulawa yana duban Zahran. Da sauri Zahra kuwa ta matsa gabansu ta buɗe robar juice ɗin ta soma zuba musu cikin wasu kyawawan kofunan tangara kana ta ajiyewa kowa agabansa kafin ta ɗago tana murmushi tace "Na gode Allah ashe da rabon zamu ƙara ganinka Ya Abdul, wallahi na ɗauka shikenan baza mu sake haɗuwa ba tunda kana Kaduna mu muna Kano, ashe kai ɗan uwan mu ne ma bamu sani ba..ko Abbie...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallon Abbie dake murmushi yana faɗin "Ɗan uwanku ne mana, dama kun sanshi ne dan naji ɗazu kin ambaci sunansa kai tsaye da alamu kun daɗe da saninsa ma..." Baki ta washe cike da fara'a tana faɗin "Sosai ma Abbie, ai shine mai keke napep ɗin nan ɗaya taimaka mana a Kaduna, kuma da muka dawo har kukayi waya dashi...?" Ta ƙarashe maganar da sigar tambaya tana kallon Abbien. Wani irin mamaki ne ya lulluɓe Abbie, yayinda Ummi kanta sai da ta kallesa ta dubi yanayin shigar dake jikinsa kafin tace "Allah mai girma ashe kice ma ɗan gida ne shi baku sani ba...?" Ummi ta ƙarashe maganar tana ƙara kallon Ya Azeez da ya duƙar da kai yana murmushi. Abbie kuwa gaba ɗaya farin ciki ya gama cika masa zuciya, ashe kunnuwansa basuyi masa ƙarya ba ranar daya fara ganinsa a gidan Alhaji Sale Musawa yaji muryarsa yake jin kamar ya taɓa jinta a wani guri, ashe dai da gaske ne ya taɓa jin muryar tasa. Lallai Allah da iko yake ashe yaron da tunda ya gansa yake jin wani al'amari mai girma a kansa shine ya taɓa taimakon ƴaƴansa wanda har yake burin duk ranar daya haɗu dashi sai yayi masa kyakkyawan alkhairi domin ya nuna masa tsantsar jin daɗinsa akan irin taimakon da ya yiwa ƴaƴansa. Ɗagowa Abbie yayi cikin tsananin farin ciki da jin daɗi yake kallon Ya Azeez ɗin kafin yace "Naji daɗin ganinka sosai AbdulAzeez, dama ina ta ƙoƙarin son inga na haɗu da kai, ashe ban sani ba ma kai ɗana ne. Lallai kai mutumin arziki ne babu abinda zan ce da kai kuma sai godiya da fatan alkhairi, Allah ya gafartawa mahaifinka yasa kuma ka rabu da mahaifiyarka lafiya..." Da Ameen duk suka amsa, kana daga haka kuma Abbie ya hau bawa Ummi labarin Alhaji Naseer Arabi mahaifin Ya Azeez, da irin taimakon da yayi musu lokacin da yana raye. Nan take kuwa Ummi ta shiga kwararo masa addu'a da fatan alkhairi tana faɗin "Ashe ma kai ɗan gida ne, lallai Allah da hikima yake. Aiko mun gode ƙwarai da gaske Allah ya saka maka da alkhairi yasa ka gama lafiya..." Amsawa sukayi da Ameen dukkansu, kana kuma daga haka Ummi ta miƙe ta koma kichin dan sauke miyar stew ɗin da take yi, wanda kuma dai-dai lokacin aka soma kiraye kirayen magriba a masallatan dake cikin unguwar. Shatu kuwa tunda ta baro falon take jin zuciyarta na tsananta bugawa, wanda duk taku ɗaya idan tayi sai gabanta ya faɗi. Hakan ne kuma yasa tana shiga cikin ɗakin kai tsaye ta faɗa saman lafiyayyen gadonsu daya sha shimfiɗa da wani uban sun haɗaɗɗen zanin gado na alfarma, ta kwanta ruf da ciki lokaci ɗaya tana mai dafe saitin zuciyarta da take jin tana ƙara tsananta bugawa tamkar zata faso ƙirjinta da fito waje. Ta daɗe kwance a tsakiyar gadon tana dafe da saitin zuciyarta wanda har lokacin bai daina bugawar da yake mata ba, yayinda daga gefe guda kuwa ƙwaƙwalwarta ke ta tariyo mata kamannin Ya Azeez da irin tsantsar kyau da kwarjinin da taga ya ƙara, da sauri sauri zuciyarta ta hau bugawa, musamman a yanzu da take ƙara hasaso tsananin kyau da wani annuri da ta hango a saman kyakkyawar fuskarsa. Haka tai ta tunane tunane haɗe da lissafa siffofin Ya Azeez wanda gaba ɗaya kamanninsa da zatinsa suka kasa gogewa a idanuwanta. Juyawa tayi wanda kuma dai-dai lokacin ta soma jiyo kiran sallar magriba da akeyi a masallacin dake jikin gidansu, miƙewa tayi a hankali ta wuce toilet dan ɗauro alwala, wanka ta fara yi agurguje sannan ta ɗauro alwala ta fito. Acan ɓangaren su Ya Azeez kuwa har akayi sallar Isha'i suna tare da Abbie, wanda kusan a tare ma sukaje masallacin sukayi sallar magriba da Isha'in. Yanzu ɗin ma zaune suke a falon inda Abbie ya matsa musu dole yace sai sunyi dinner kafin su wuce. Haka nan babu yadda suka iya Ummi ta zubo musu abincin ta kawo musu har nan cikin falon inda suke suka ci tare da Abbien. Bayan sun gama ne kuma Abbie ya ɗauki wayarsa ya danna numbern Shatu wacce dai-dai lokacin ta idar da sallar isha'i kenan tana zaune a gaban madubi tana shafa mai a jikinta kiran Abbie ya shigo wayarta dake ajiye a gaban madubin. Da sauri ta ajiye robar man dake hannunta ta ɗauki wayar bayan ta ɗaga kiran ne kuma ta ƙara wayar a kunnenta. "Ki sauko ku gaisa da baƙi zasu wuce..." Abinda Abbien ya faɗa mata kenan ba tare kuma daya jira cewarta ba ya katse wayar. Ba tare data tsaya ƙarasa shafa man ba kuwa ta ajiye wayar ta miƙe da sauri ta ƙarasa gaban wardrobe ɗinta ta buɗe ta zaro wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar material wanda tasha ɗinkin fited gown mai kyau da tsari, saka rigar tayi a jikinta wacce ba ƙaramin kyau tayi mata ba, gaba ɗaya ta fitar da kyakkyawan dirin jikinta mai kyau da burgewa, wanda kuma haka kawai ta tsinci kanta da son yin kwalliyar da tasan zata burge Ya Azeez ɗin. Ko ɗan kunne bata tsaya sakawa ba ta ɗauki wani siririn gyale mara nauyi ta yafa akanta, kana ta zura wani flat shoe mai kyau a ƙafarta ta ɗan fesa turare a gurguje ta fice daga ɗakin. A hankali ta fara saukowa ƙasa tana kallon cikin falon, inda gabaki ɗaya Ya Azeez ya karkata hankali da natsuwarsa kacokan a kanta. Tsumammun idanunsa ya lumshe a kanta a hankali yana sauke wata irin sassanyan ajiyar zuciya. Tabbas da kafin yanzu yana jin zuciyarsa na matuƙar tafarfasa tamkar zata fasa ƙirjinsa, sai dai kuma yanzu lokaci ɗaya yaji zuciyar tasa nayi masa wani irin sanyi, yayinda a hankali a hankali yake jin duk wani duhu daya mamaye zuciyarsa yana yayewa ya koma haske. Ƙarasowarta cikin falon kuwa yayi dai-dai da miƙewar Abbie da Ummi a tare suka wuce falon Abbie ɗin kai tsaye. Ganin haka ne kuma yasa Shatu zama a kujerar dake kallon wacce Fahad da Ya Azeez ɗin ke zaune akai ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa da zoben azurfan dake maƙale a yatsanta, da sauri Zahra ta kalleta kana ta juya ta kalli Ya Azeez da har lokacin ya kasa ɗauke idanunsa akanta tace "Kai Masha Allah gaskiya fa kun dace sosai Ya Abdul ina matuƙar tayaku murna..." Ta faɗa kai tsaye tana kallon Shatu data ɗago kai da sauri tana watsa mata harara. Shiko Ya Azeez Fahad ya kalla tare da nuna masa Shatun da idanunsa, kafin kuma ya juya yana yiwa Zahra alama data ɗan basu guri, aiko da sauri ta miƙe zaraf kamar daman jira take ta buga wani uban tsalle, kafin kuma cikin karaɗi tace "Abu dai ya tabbata da ikon Allah, Ya Abdul ina tayaka murna wallahi, Aunty Shatu kinyi sa'ar miji..." Ta faɗa cike da tsantsar farin ciki tana haurawa sama da gudu. Dariya Fahad yayi, kafin ya kalli Ya Azeez daya wani tsare Shatu da idanu yayi masa alama daya matsa gurinta mana. Wanda ita kuwa Shatu gabaki ɗaya kunyar kalaman Zahran sun gama kasheta a zaunen da take, kota ina kunyar su ta gama lulluɓeta ji take kamar ta nutse dan tsabar kunya da takaicin Zahran. Wai abu dai ya tabbata sai kace yace yana sonta ne, har da wani cewa Aunty Shatu kinyi sa'ar miji. Shegiya kawai cakwaikwaiwa mai baki sai kace reza. Tana cikin tunanin ne kuma taji daddaɗan ƙamshin turarensa mai tsada ya cika mata hanci, gabanta ne ya yanke ya faɗi ras rass, wanda har sai data dafe saitin zuciyarta, motsin zamansa a kusa da ita ne kuma ya ƙara haddasawa zuciyarta tsananta bugawa, tsam yayi da idanunsa akanta yana ƙare mata kallo, itako ganinsa a kusa da ita ne yasa ta ƙara ruɗewa duk ta daburce bakinta na rawa ta furta "Bar...Bar..ka...da dare..." Lumshe kyawawan idanunsa yayi sakamakon wani sassanyan daɗi da yaji ya ziyarci zuciyarsa, bai taɓa tunanin anan kusa zai iya riskar irin wannan farin cikin mai daɗi da tsayawa arai ba. Sassanyan murmushi yayi kafin kuma cikin daddaɗar muryarsa yace "Barkan mu dai Eishatuna..." Cak ta ɗauke numfashinta ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya, kafin ta ɗago still dai har yanzu idanunsa tsaye suke ƙyam akanta yana ƙare mata kallo, wani irin zirr zirr taji ƙarar saukar wani sassanyan sauti mai tafe da daddaɗan yanayi ya ziyarceta "Eishatuna..." Haka tai ta maimaita sunan a zuciyarta tana ƙara jin wani irin mugun daɗi a ranta, wanda tunda Ummi ta haifeta bata taɓa jin wanda ya kirata da irin sunan kai tsaye cikin daddaɗan lafazi mai sanyaya rai irin haka ba. Buɗe idanunta tayi karaf ko suka ƙara haɗa ido, jikinta ne ya fara rawa ta damƙe hannunta lokaci ɗaya tare da runtse idonta, saurin matsawa yayi kusa da ita yana faɗin "Eishatuna pls buɗe idanunki da kyau ki kalleni kinji...?" Sunkunyar da kai tayi ba tare data buɗe idon ba, kallonta yayi yana tunanin wani abu kafin kai tsaye ya sake cewa "Pls Eishatuna ki ɗago magana zamuyi a matsayin mu na masoyan juna, ba'a matsayin mai keke napep daya taɓa taimaka muku ba..." Jin haka yasa ta ɗago da sauri tana kallonsa, gyaɗa mata kai yayi alamar tabbatarwa. Lumshe kyawawan idanunta tayi kafin ta ɗan ƙara matsawa gefe tana kallonsa. Ya daɗe yana ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo zuwa ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da jajayen laɓɓa masu taushi da santsi, kafin kuma ya sauke idanunsa kan zara zaran yatsun hannunta farare tas tas masu kyau da ɗaukar hankali. Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama ƙare mata kallon tsaf kafin ya lumshe tsumammun idanunsa ya kira sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya mai haɗe da muradi yace "EISHATUNA..." Amsawa tayi ba tare da ta ɗago kai ta kallesa ba, shi kuwa idanunsa ya buɗe sosai a kanta yana kallonta kafin yace "Sosai na yaba da zaɓin Abba, kuma insha Allahu kema ina fatan ki yaba dani sannan ki karɓe ni hannu bibbiyu a matsayin masoyinki wanda zaki yi rayuwar aure dashi ta har abada. Saboda haka nidai na amince dake a matsayin matar da zan aura, dan da nasan kece ma matar da Abba yace inzo in gani, da ba sai na bawa kaina wahalar zuwa ba kawai zan sanar dashi cewa kin yi min kawai a ɗaura, amma duk da haka yanzun ɗin ma bata ɓaci ba. Insha Allahu ina yiwa kaina kyakkyawan fata na samunki a matsayin matar aurena...." Jin kalmar daya faɗa ta ƙarshe ne yasa ta ɗago kanta lokaci ɗaya wani kyakkyawan murmushi na shirin suɓuce mata, amma nauyi da kunyarsa sun cika mata ido. A hankali ta ɗan jinjina kai ba tare da tayi magana ba. Ɗan murmusawa yayi kafin yace "Meye ra'ayinki...? Dan Allah karki ɓoye min ki gaya min duk abinda ke zuciyarki a game dani..." Ya faɗa cikin nuna alamar shirun nata ya damesa. Ɗago kanta tayi ta kallesa kafin tace "Nima..." Sai kuma tayi shiru ba tare data ƙarasa ba. "Kema me...?" Ya faɗa a tsorace yana jin wata mummunar faɗuwar gaba. Girgiza masa kai tayi a hankali kafin tace "Yanzu dare yayi ka ɗan bani lokaci zamuyi magana insha Allahu..amma yanzu ya kamata ku tafi gida domin abokinka ya baro min ƙawata a gida ita kaɗai...." Ɗan kwaɓe fuskarsa yayi yana faɗin "A'a Eishatuna ya tafi shi kam ga makullin mota, amma ni ina nan sai mun gama magana..." Ya faɗa kai tsaye yana jefawa Fahad da waya ke manne a kunnensa suna magana da Basma makullin motar yana faɗin "Gashi nan ka tashi ka tafi gurin matarka, nima ka barni da tawa matar zamu yi sirri..." Kallonsa Fahad yayi a karkace kafin yace "Toh meye na wani korata, kaima ai dole ka taso mu tafi tunda ba'a riga an ɗaura auren ba. Sai ka bari idan an ɗaura an kai maka ita ne sai ka faɗi haka..." Harararsa Ya Azeez yayi kafin yace "Aiko insha Allahu nan kusa za'a gama komai, sai dai ka mutu munafuki..." A ɗage Fahad ke kallonsa kafin ya juya ya kalli Shatu data duƙar da kai tunda suka fara ja'injan tana dariyar diramar tasu yace "Ƙawarmu kiyi masa magana ya tashi mu tafi, gobe ya dawo shi kaɗai ku ƙarashe, dan ni kam na bar sake rakosa yau ne na farko kuma na ƙarshe..." Wani kyakkyawan murmushi Shatu tayi kafin ta kalli Ya Azeez ɗin daya tsareta da ido kamar zai cinyeta, kana kuma cikin lalama tace "Ok Ya Abdul tashi to ku tafi zamuyi waya idan kuka isa gida kaji, pls kuje..." Ta faɗa cikin taushin murya tana kallonsa. Saurin kallonta yayi yana jin wani irin farin ciki lokaci ɗaya yana mamaye zuciyarsa, kafin ya miƙe tsaye yana mata wani sassanyan kallo kana cikin kwaɓe fuska yace "Nidai da kin ƙyaleni Eishatuna shi ya wuce, dan ni ban gaji da ganinki ba. Pls ki barni in ɗan ƙara ganinki anjima sai in tafi kinji...?" Ya faɗa yana tsareta da ido. Hakan yasa ta gano nufinsa kwata kwata baya son tafiyar ne, kawai dai babu yadda ya iya ne saboda ita tai masa magana da kanta, amma da babu inda zaije sai sun gama daddale magana. Ita kuwa Shatu ganin yaƙi tafiya ne ya tsaya yasa ta miƙe tana ƙara lallaɓasa kafin ya yarda ya juya tabi bayansa wanda kuma tuni Fahad shi har ya fice daga falon dan yaga take taken abokin nasa yau gabaki ɗaya sai a hankali, sai wani rawar ƙafa yake yana wani rawar jiki kamar wanda aka ce an ɗaura masa aure da Shatun ta zamo tasa. Har wajen da motarsa ke fake ta rakosa inda nan ma da ƙyar Ya Azeez ya barta tayi musu sallama ta juya ta koma cikin gida, yayinda su kuma suka shiga motar wanda a wannan karon Fahad ne ke jan motar suka fice daga cikin gidan. Sai ƙarfe 10:20pm suka isa gida, wanda koda suka dawo su Abba tuni sun daɗe da rufe sashensu sun kwanta, suma ba su bi ta kansu ba, Ya Azeez ya shige ɓangarensa ya garƙame ƙofa, yayinda Fahad shima ya wuce nasa ɓangaren yana mai jin haushin Ya Azeez kan ɓata masa lokaci da yayi bai dawo gida da wuri gurin amaryarsa ba. A ɓangaren Ya Azeez kuwa yana shiga bedroom ɗinsa kai tsaye ya wuce toilet bayan ya tuɓe kayan jikinsa ne kuma ya sakarwa kansa shower. Inda ya ɗauki kusan mintuna sha biyar a cikin toilet ɗin yana wankan, bayan ya gama ne kuma ya ɗauraye jikinsa yayi brush ya fito ɗaure da tawul a ƙugunsa, sai wani ƙarami dake riƙe a hannunsa yana tsane ruwan dake kansa. Sai daya gama goge jikinsa tsaf kana ya ɗan shafa mai sama sama ya fesa turare, kana ya saka wani tattausan riga da wando na wani yadi mai tsantsi da sheƙi. Kafin ya ƙarasa gaban haɗaɗɗen gadonsa da yasha shimfiɗa da wani lafiyayyen zanin gado mai kalar ruwan ƙasa ya haye ya kwanta bakinsa ɗauke da addu'a, kana yaja lallausan bargonsa ya lulluɓe jikinsa. Ɗan juyawa yayi ya ɗauki wayarsa dake aje a gefen gadon cikin lokaci kaɗan ya nemo numbern Shatu wacce Zahra ke kiransa da ita, wanda Allah ya taimakesa ya daɗe da yin saving ɗinta bai dai taɓa kira bane, sai yau da yake ta zumuɗin kiran. SHATU Sake rungume hannuwanta tayi a ƙirji tana ƙara ƙudundunewa a cikin lallausan bargonta. Wanda a ƙalla ta kai kusan mintuna sha biyar zuwa ashirin tana so bacci ya ɗauketa amma ko kaɗan babu shi a idanunta. Duk yadda ta kai da runtse idanunta kuwa hoton Ya Azeez kawai take gani ko ya ta ƙifta idanuwanta, yayinda a cikin jikinta kuwa gaba ɗaya wani baƙon al'amari take ji a ko wane lungu da saƙo na ilahirin gangar jikinta. Haka nan ta samu kanta da sakin wani ƙayataccen murmushi. Lumshe kyawawan idanuwanta tayi tana ƙara ƙanƙame jikinta waje ɗaya, wanda kuma tana cikin haka ne wayarta dake aje gefen Zahra dake ta sharar baccinta hankali kwance ta soma ƙara. Da sauri ta tashi zaune tare da miƙa hannu a hankali ta ɗauko wayar, ganin sunan dake yawo akan screen ɗin wayar ne yasa ta sakin wani malalacin murmushi mai cike da tarin farin ciki kafin ta shiga maimaita sunan aranta kamar mai ƙoƙarin haddacewa. "YA ABDUL..." Ta sake maimaita sunan tana kallon screen ɗin wayar, haka wayar ta dingi ringing tana kallo amma har ta katse bata ɗauka ba, bai haƙura ba ya sake kira, nan ma har ta ƙarashi ringing ta katse bata ɗaga ba. Bai daddara ba ya sake danna mata kira, haka har sai da yayi mata misscall biyar amma duk bata ɗauka ba, kuma duk tana kallo amma ita kanta ta rasa dalilinta na ƙin ɗaukan kiran nasa. A ɓangaren Ya Azeez kuwa gaba ɗaya rashin ɗaukan wayar nata sai ya saka masa wani tunani da kokwanto a zuciyarsa, wanda nan take ya shiga fargaba da tsananin tashin hankali. Ya ɗauki sama da mintuna kusan talatin yana tunane tunane da saƙe saƙe a zuciyarsa, kafin ya haƙura ya ajiye wayar ya sake gyara kwanciyarsa lokaci ɗaya yana ƙara jin matsananciyar fargaba a zuciyarsa. Haka ya kwana juyi cike da fargabar kar Shatu ta juya masa baya ta canza shawara tace bata sonsa. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 3️⃣4️⃣ Washegari kuwa haka ya tashi sukuku dashi gaba ɗaya zuciyarsa ba tai masa daɗi. Daga gefe guda kuwa duk da kasancewar ransa baya masa daɗin amma hakan bai hanasa jin wata irin masifaffiyar ƙaunar Shatu mai matuƙar ratsa zuciya da gangar jikinsa na daɗa yaɗuwa tana kuma mamaye ilahirin lungu da saƙon gangar jikin nasa ba. Wani irin yanayi yau ɗin ya tashi dashi wanda bai taɓa jin irinsa ba, kasancewar a iya tsawon rayuwarsa banda mahaifiyarsa da Imaan bai taɓa jin son wata halitta irin kwatankwacin son da yake yiwa Shatu ba, tunda ya taso kuma bai taɓa haɗuwa da wata macen da ta taɓa burgesa har ta tafi da natsuwarsa lokaci guda irin Shatu ba. Dan ko Fadwa ya dai aureta ne kawai saboda ya sharewa Abba hawaye akan abubuwan da take yi a lokacin, amma tunda yake bai taɓa jin sonta ba dai-dai da ƙwayar zarra a zuciyarsa, kuma a haka ya zauna da ita ba tare da koda wasa ya taɓa nuna mata cewa baya ra'ayintan ba. Idanunsa ya ɗan lumshe da sauri sakamakon tunawa da yayi da yanayin surar jikinta da yadda komai nata yake da kyau da matuƙar ɗaukar hankali tamkar itace ta tsarawa kanta komai. A hankali ya fesar da wani zazzafan numfashi mai cike da zallar shauki da muradi. Ajiyar zuciya ya sauke saboda wani irin daddaɗan yanayi da yake ji yana yi masa yawo a cikin jikinsa, kafin a hankali kuma ya lumshe idanunsa tare da harɗe hannuwansa ya sake gyara kwanciyarsa a saman doguwar kujerar dake falonsa, wanda kuma tun dawowarsu daga masallaci sallar asuba ne shi dasu Abba ya kwanta anan ɗin yana ta saƙe saƙe, ya kasa tashi ya koma cikin bedroom ɗinsa. A haka yana ta nazari da tunane tunane har wani daddaɗan bacci yayi nasarar ɗaukarsa, saboda rashin isasshen baccin da bai samu yi ba a daren jiya. SHATU Kwance take a saman makeken gadonta wanda yasha shimfiɗa da lallausan zanin gado na alfarma, irin kwanciyar nan ta rigingine ce tayi idanunta na kallon saman ɗakin, yayinda take sanye da wata ƴar shimi mai shara shara mara nauyi a jikinta. Kyawawan idanuwanta ta lumshe a hankali tare da waresu lokaci ɗaya tana sauke wata sassanyar ajiyar zuciya mai cike da tsantsar farin ciki da jin daɗi. Juyawa tayi a hankali tana mai saƙawa da kwancewa a zuciyarta, inda yanzu kuma gabaki ɗaya duk haushin kanta take ji. Can kuma wani sashi na zuciyarta ya fara hasaso mata wasu manya manyan abubuwa dake tattare da Ya Azeez ɗin. Lallai tabbas ita ɗin mai sa'a ce a rayuwarta, har yanzu kuma ganin abun take tamkar a mafarki, sake juyawa tayi a hankali ta mirgina ƙarshen gadon kana ta cigaba da tunani. To wai mema ya hanata ɗaukar wayarsa ne jiya daya kirata, gashi yanzu rashin kiran nasa kuma duk ya dameta..? Toh ko dai yaji haushi ne da bata ɗauki kiran nasa jiyan ba..? Ɗan jim kaɗan tayi tana tunani, kana kuma can sai ta saki ƙaramin murmushi kafin kuma a fili ta ba kanta amsa da cewa "Jan aji mana, kuma ai hausawa sunce mai son ɗan tsuntsu shike binsa da jifa, saboda haka ina kyakkyawan zamana zai nemeni da kansa..." Ƙarar wayarta dake aje a gefen filonta ne ta katse mata tunanin da take yi, wayar ta ɗauka ganin kuma sunan Ya Abdul ne ke yawo akan screen ɗin wayar yasa ta sakin wani ƙayataccen murmushi kafin cikin hanzari ta ɗaga kiran ta manna wayar a kunnenta tayi shiru ba tare da tayi magana ba. Daga can ɓangaren Ya Azeez kuwa jin ta ɗaga wayar ne yasa shi sakin wata sassanyan ajiyar zuciya kafin kuma cikin wata irin daddaɗar murya mai taushi yace "Ki fito ina harabar gidanku ina jiranki..." Ya faɗa kai tsaye kana daga haka kawai ya katse wayar. Da sauri ta buɗe idanunta dake lumshe tare da tashi zaune cike da tsantsar mamaki tana duban agogon dake maƙale ajikin bangon ɗakin, ƙarfe 9am dai-dai ta gani. Zuro ƙafafuwanta ƙasa tayi da sauri ta sauka daga kan gadon ta zura bedroom silifas ɗinta kana ta juya tana ƙoƙarin kwance igiyoyin rigar baccin dake jikinta lokaci ɗaya tana sake duban agogon bangon dake ɗakin. Tuna abinda yace ne kuma yasa ta juyawa kai tsaye ta shige toilet da sauri dan yin wanka. Sanin da tayi cewar yana jiranta ne kuma yasa bata wani ɓata lokaci a wajen yin wankan nata ba ta fito. Koda ta fito kuwa mai kawai ta ɗan shafa ajikinta, sai ƴar hoda kaɗan da ta ɗan mutstsuka sannan ta shafa lipstick a kyawawan laɓɓanta masu taushi da tsantsi. A gurguje ta feshe ilahirin jikinta da sassanyan body spray ɗinta masu sanyin ƙamshi da sanyaya zuciya. Ƙarasawa tayi gaban wardrobe ɗinta ta buɗe inda ta zaro wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar material na yadin roba roba mai kyau kalar sararin samaniya ta zura ajikinta, kana ta saka wani takalmi mai tsini fari a ƙafarta, sannan ta yane kanta da wani ɗan madaidaicin gyale shima fari. Murmushi ne ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta, saboda ganin irin kyaun da kayan suka yi mata lokacin data kalli kanta a cikin madubi. Wayarta ta ɗauka ta riƙe a hannunta kana ta juya ta fice daga cikin ɗakin, a falo ta samu Ummi da Zahra a zaune suna hira, wanda bayan sun kammala breakfast ne kuma suka dawo falon suka zauna suna hira. Ƙarar takun takalminta da suka ji ne kuma yasa su juyowa a tare suka zubo mata idanunsu gaba ɗaya suna kallonta. "Masha Allah Aunty Shatu kinyi kyau sosai, wallahi kamar kin sauko daga Saudiya..." Cewar Zahra da ta wani hangame baki da hanci tana kallon Shatun. Ita kuwa Shatu ƙarasa saukowa cikin falon tayi tana hararar Zahran da har lokacin bakinta ke hangame tana kallonta. Ganinta cikin shirin da sukayi ne kuma yasa Ummi cewa "Ina zakije haka kuma tunda sassafe ko karyawa ba kiyi ba...?" Ɗan kwaɓe fuskarta tayi tana ƙarasowa gaban Ummin ta ɗan rusuna, kafin a kunyace tace "Zan ɗan fita ne gurin Ya..uhmm Ya Abdul tun ɗazu yazo yana jirana...." Wani tsalle Zahra tayi ta miƙe tsaye cikin tsananin farin ciki tana faɗin "Innalillahi kai Aunty Shatu amma shine baki gaya min ba inje in gaishesa..? Gaskiya baki kyauta min ba nidai ban ji daɗi ba..." Ta faɗa a shagwaɓe tana turo baki. Zafga mata harara Shatu tayi kafin tace "Ba dole in gaya miki ba, tunda gurinki yazo..." Ummi kuwa har a cikin ranta Allah ya sani taji daɗin abun sosai, dan haka da saurin ta ta miƙe tsaye tana faɗin "Zahra tashi maza ki ɗauki key kije ki buɗe masa falon baƙi ki kaishi, ke kuma ƴan mata tsaya ki tafin mai da breakfast..." Ta faɗa tana wucewa kichin da sauri. Itako Zahra da gudu ta haura sama taje ta dauko makullin falon baƙin tazo ta fice da hanzari, Shatu kuwa tana nan tsaye Ummi ta fito riƙe da ɗan madaidaicin farati a hannunta, ƙarba Shatun tayi kana tasa kai ta fice daga falon. Tana ƙarasawa falon kuwa tun kafin ta shiga take jiyo surutun Zahra duk ya cika gurin, girgiza kai kawai tayi kafin ta tura ƙofar lokaci ɗaya ta shiga cikin falon bakinta ɗauke da sallama. Dai-dai lokacin kuma Ya Azeez wanda ke zaune akan ɗaya daga cikin kujerun dake facing ɗin ƙofar shigowa falon ya ɗago kansa kenan fuskarsa ɗauke da murmushin dake ƙara masa wani tsantsar kyau da haiba yana kallon Zahra. Karaf kuwa idanunsu suka sarƙe a cikin na juna, da sauri ta maida kanta ƙasa dan bata jin zata iya jurar kallon cikin ƙwayar idanunsa masu matuƙar kashe mata jiki su saukar mata da kasala. Tunda ta duƙar da kanta bata ƙara ɗagowa ba daga bakin ƙofar ta coge ta sunkuyar da kanta, Zahra kuwa ganin haka yasa ta miƙe ta matsa kusa da ita ta karɓi farantin dake hannunta taje ta ajiye a gabansa, kana ta ɗago ta kallesa tana faɗin "Ya Abdul bara na shiga ciki tunda amaryar ta ƙaraso idan ka fito sai muyi sallama, Aunty Shatu a fito lafiya..." Ta faɗa tana ficewa daga cikin falon da hanzari tana dariya. Sun kusan mintuna goma a haka tun bayan fitar Zahra Shatu bata ɗara daga inda take ba, ganin kuma bata da niyyar ƙarasowan ne ta zauna yasa Ya Azeez miƙewa a hankali ya ƙaraso inda take, wanda kuma Shatu kwata kwata bata san da ƙarasowar tasa ba kawai sai jin amon daddaɗar muryarsa tayi haɗe kuma da sassanyan ƙamshi turarensa daya gauraya da numfashinta suka saukar mata da wani daddaɗan yanayi mai wuyar fassara. Cikin wani irin yanayi yake kallonta shima kafin kuma ya ƙara matsawa kusa da ita sosai yana faɗin "Pls mana Eishatuna, dan Allah horon ya isa haka, ki sassauta min ba dan halina ba..." Ya faɗa cikin marairaice murya yana kallonta. Wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyarta, wanda hakan kuma yasa ta ɗagowa da sauri tana lumshe kyawawan idanunta, a cikin ranta kuwa faɗi take "Nima dauriya kawai nake, amma tuni soyayyarka ta riga da ta gama min kamun kazar kuku ta fatattaka zuciyata, tayi mata dalla dalla..." Ta faɗa tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba kamar zatayi kuka. "Pls na roƙeƙi ki daina wahalar dani ta hanyar yiwa kunnuwana rowar jin daddaɗar muryarki dan Allah Eishatunaaa..." Ya ƙare maganar cikin wata iriyar kasalalliyar murya da shi kansa bai taɓa sanin zai iya irinta ba. Shatu kuwa jin abinda ya faɗa ɗin ne yasa ta sake yin ƙasa da kanta, tare da lumshe idanunta, kafin kuma ta ɗan buɗe a hankali tana faɗin "Ina kwana...?" Idanunsa ya ɗan lumshe saboda wani irin abu na musamman da yaji ya taɓa zuciyarsa kana a hankali kuma yana ratsa dukkan ilahirin lungu da saƙon gangar jikinsa. Ɗan ƙaramin bakinta ya kalla kafin kuma cikin kasalar da muryar tata ta saukar masa yace "Lafiya Alhamdulillahi Eishatuna, yasu Ummi da Abbie...?" A hankali ta amsa da Lafiyarsu ƙalau, kana kuma tace "Muje ka zauna in zuba maka abincin kar yayi sanyi..." Ta faɗa tare da wucesa ta ƙarasa tsakiyar falon inda Zahra ta ajiye farantin abincin ta zauna a ƙasan kafet ɗin daya mamaye falon bayan ta tanƙwashe ƙafafunta ta buɗe kulan tare da ɗauko filet ta zuba mai soyayyen dankali da kwai, sai source ɗin hanta da taji albasa kaɗan da ta ɗan zuba mai daga gefe guda, kana ta haɗa mai tea mai kauri ta aje a gabansa. Ƙarasowa yayi ya zauna akan kujerar dake kallonta, kana ya ɗauki kofin data haɗa masa kakkauran tean a ciki ya kai bakinsa ya soma kurɓa a hankali a hankali yana lumshe idanunsa cike da nishaɗi. Shatu kuwa har lokacin kanta na ƙasa bata ɗago ba sai faman wasa take da yatsun hannunta. Bai wani ci dankalin sosai ba kaɗan kawai ya ɗan tsakura ya ci, sai tean daya shanye tas. Bayan ya gama ne kuma ta tattare kayan ta matsar da farantin gefe kana ta koma kujarar kusa dashi ta zauna ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da adon zaren dake jikin gyalenta. Ajiyar zuciya Ya Azeez ya sauke, kana kuma cikin tsananin so da ƙaunarta yace "Ɗago kanki ki kyalleni pls..." Ya faɗa cikin taushin murya yana kallonta. Ɗagowa tayi a hankali ta kallesa, kafin kuma ta maida kanta ƙasa tana jin wani baƙon yanayi mai saukar da farin ciki yana ziyartarta. Kallonta Ya Azeez ɗin yayi kafin yace "Pls mana Eishatuna kinji...?" Ya faɗa cikin wata irin narkakkiyar murya kana lokaci ɗaya yana sakar mata manyan idanuwansa. Da sauri Shatu ta ɗago kai tana kallonsa, kafin kuma kai tsaye ta tsinci kanta da furta "Na daina bazan sake ƙin ɗaukar wayarka ba, kayi haƙuri..." Ta faɗa a hankali tare da rufe idanunta tana murmushi. Saurin riƙo hannunta yayi ya matso kusa da ita ya zauna a gefenta yana faɗin "Nagode Eishatuna..." Ya faɗa cike da tsantsar farin ciki yana kallon kyakkyawar fuskarta. Ɗan janye jikinta tayi a nasa ta matsa gefe tana murmushi, ganin kuma yadda tayi ne yasa shi ɗan matsawa gefe shima yana murmushin. Wanda kuma a dai-dai lokacin wayarsa dake cikin aljihun rigar tsadaddiyar shaddar jikinsa ta ɗauki ƙara, zaro wayar yayi ganin sunan Fahad yasa ya kwaɓe fuska kafin ya ɗauka ya manna a kunnensa yayi shiru ba tare da yayi magana ba. Daga can ɓangaren Fahad kuwa jin ya ɗaga wayar yayi shiru ne, yasa ya hau faɗa yana cewa "Wai dan Allah kana ina ne, tun fa ɗazu ina ofis ina jiranka amma har yanzu baka fito ba, kuma ka sani yau zamu gana da baƙin mu da suka zo daga Lagos ƙarfe 10am amma shine har gashi yanzu ƙarfe 9:45 baka fito ba, kuma Abba da Mami sun tabbatar min da cewa tun ɗazu ka fita, amma shine har yanzu baka ƙaraso ba..to wai gidan uwarwa ma ka tsaya ne, ina kaje tunda sassafen nan...?" Ɗan kwaɓe fuska Ya Azeez yayi kafin yace "Karka cika min kunne dan Allah Malam ina gurin amaryata..." Ya faɗa kai tsaye kana daga haka ya katse wayar ya mayar cikin aljihu. Shatu kuwa da tunda ya fara wayar take ta kallonsa tana murmushi sakamakon duk ta jin abinda Fahad ɗin ya faɗa, kasancewar kuma a handfree Ya Azeez ɗin ya saka wayar, yayinda kuma ganin ya gama wayar ne ya ƙara gyara zama alamar bai da niyyar tafiya yasa tace "Pls mana Ya Abdul tashi kaje ana jiranka..." Juyowa yayi ya ɗan kalleta kafin kuma cikin kwaɓe fuska yace "A'a nidai ba inda zanje yau ina nan tare da Eishatuna..." Kallonsa tayi kafin tace "Pls mana Ya Abdul kaje dan Allah ai zamuyi waya..." Ta faɗa cikin magiya tana kallonsa, ganin yadda ta wani marairaice masa ne kuma yasa ya miƙe ba dan yaso ba gashi sai faman narke masa take tana ƙara kashe masa jiki da zuciya da salon soyayyarta mai matuƙar tsayawa arai da zuciya. "Kin tabbatar dai zamuyi waya ko...?" Ya Azeez ɗin ya faɗa murya a sanyaye yana tsura mata idanu. Gyaɗa masa kai tayi cike da tabbatarwa kafin ta miƙe tsaye tana cewa "Insha Allahu da kaina ma zan kiraka karka damu..." Cike da jin daɗi ya amsa da Toh ina jira, kana daga haka ya juya suka fice daga falon, har gurin motarsa ta rakosa wanda sai da taga ficewarsa daga cikin gidan sannan ta juya bayan ta ɗauko farantin ta kulle falon da key ta wuce cikin gida. FADWA Sosai suke shan soyayyarsu ita da sabon saurayinta, wanda yanzu kusan kullum sai yazo gidan taɗi gurinta, yayinda kuma kullum idan zaizo sai ya taho musu da kayan ciye ciye iri iri ya kawo musu. Duniya sabuwa a gurin Mama da Fadwa, an samu abinda akeso babu abinda ya damesu yanzu sha'anin gabansu kawai sukeyi. A ɓangaren Fadwa kuwa yanzu burinta ya gama cika ta gama samun abinda takeso, shiyasa yanzu da gayya take shiga cikin ƙawayenta tana fankama saboda yanzu gaba ɗayansu babu wacce zata nuna mata wani abu, dan hatta da tsadaddiyar wayar da take riƙewa irin ta hannun Hajiya Lubna ce da Hajiya Labiba, shiyasa yanzu ko bi ta kansu bata cika yi ba. Dan har gwara gwara Hajiya Labiba ma ta kan ɗan je gidanta wani lokacin, amma Hajiya Lubna kam tun ranar da tayi mata faɗa tace ta koma gidan Ya Azeez domin shine rufin asirinta, Fadwa ta rufe ido tayi mata kaca kaca, kuma tace daga yau ta fita harkarta babu ruwanta da ita kowa yayi ta kansa, saboda ita a ganinta yanzu duk wanda zai ga irin cigaban da take ciki yazo yana mata maganar komawa gidan Ya Azeez to ba masoyinta bane, cikakken maƙiyinta ne, domin ya nuna mata tsantsar hassada da baƙin ciki. Toh tun daga wannan ranar da sukayi haka kuwa basu sake haɗuwa ba, sai wata rana da tasa Alhajinta ya kaita gidan Hajiya Labiba suka haɗu da Hajiya Lubnan acan, tana shiga kuwa ko zama ba tayi ba ta juya ta koma gida, dan acewarta bata son duk wani abu da zai sake haɗata inuwa ɗaya da Hajiya Lubna da take yi mata kallon babbar maƙiyiyar a yanzu. Wanda kuma duk waɗannan abubuwan da suke faruwa Abba bai da masaniya ko kaɗan akai, dan kullum idan ya fita kasuwa tun safe baya dawowa gida sai dare, inda kuma zuwa lokacin sosai harkar kasuwancinsa ya ƙara haɓɓaka, dan zuwa yanzu gaba ɗayansu sun san cewa ya samu aikin tsaron shago a kasuwa, dan ko da wasa bai taɓa gaya musu cewa shagon mallakinsa bane ballantana kuma su san cewa Ya Azeez ne ya samu kuɗi har ya buɗe masa shi. Sai dai kuma zuwa yanzu yanayin samun Abban yana matuƙar ɗaure musu kai da basu mamaki, domin yanzu duk wata yake siyo musu tilin kayan abinci ya kawo ya aje musu sannan ya siyo musu komai da yasan zasu buƙata, ga abubuwa sosai daya canja musu a cikin gidan, dan hatta da makarantar boko da islamiyya yanzu ta kuɗi su Ilham da Amatullah suke zuwa, sannan duk abinda yasan zasu buƙata ba sai ya jira sun tambaya ba haka yake siyowa yazo ya ajiye musu, shiyasa yanzu babu abinda suka nema suka rasa. Wanda kuma hakan kwata kwata bai taɓa ɗaɗa Mama da ƙasa ba, domin duk wannan kyautatawar da yake musu ko ajikinta bata gani, ballantana taga ƙoƙarinsa. Ita kawai babban burinta yanzu shine taga Fadwa ta auri Alhaji Zailani, shine kawai hankalinta zai kwanta idan tasan cewa ƴarta na gidan arziki tana auren mai kuɗi suna damawa yadda suke so suna abinda suka ga dama. Shiyasa ma tuni ta watsar da sana'ar ƙuli ƙuli da kayan miyan da take yi, dan yanzu gani take tafi ƙarfin wannan sana'ar ta wuce da saninta kuma, yanzu jira kawai take idan komai ya gama daidaita tsakanin Fadwa da Alhaji Zailani yayi mata Visa ta dinga fita ƙasashen waje tana harkar Saudi da Dubai, itama ta faso gari tana damawa da manyan mata. ********* *BAYAN WATA UKU* Zuwa lokacin haka abubuwa sukayi ta gudana da daɗi ba daɗi. A ɓangaren Shatu da Ya Azeez kuwa komai yana ta tafiya dai-dai, domin yanzu har ta kai basu iya ɓoye irin tsananin soyayyar da suke yiwa junansu ko a gaban waye. Wani lokaci ita kanta Zahra har mamaki take idan taga Shatu na yin wasu abubuwan, ballantana idan taga yadda take faman rawar jiki akan Ya Azeez abun har ɗaure mata kai yake yi. Haka kuma shima a ɓangaren Ya Azeez ɗin gaba ɗaya ya gama susucewa akan Shatun. Sosai suke gudanar da tsaftatacciyar soyayyarsu hankali kwance babu abinda ya damesu, waya kuwa a rana sai suyi ta yafi sau ashirin, har wata shaƙuwa suka ƙara yi ta musamman a tsakaninsu, domin basu iya yin awa ɗaya ba tare da sunji muryoyin junansu ba. Yayinda gefe guda kuma ga harkar kasuwancinsu Ya Azeez ɗin da zuwa yanzu komai yake ƙara haɓɓaka, wata bakwai gidan motocin su yayi da buɗewa, amma lokaci kaɗan ya yiwa sauran zarra wanda kuma dama Ya Azeez haka yake komai ya sakawa hannu sai abun yayi albarka. Wanda kafin kuma wannan watannin Abba da Fahad na matuƙar alfahari da samun Ya Azeez ɗin saboda tsantsar maida hankalinsa akan kasuwancin nasu. Haka ma Ummansa dan zuwa wannan lokacin tuni ya siyan mata wani haɗaɗɗen gida mai kyau a cikin unguwar Mashi Road, sannan ya zuba mata ababen more rayuwar duk wani jin daɗin duniya, da motar hawa mai kyau da tsada sannan ya ɗaukan musu direba saboda zirga zirgan kai Imaan makaranta da ɗaukota, sai kuma idan Umma zata fita unguwa itama ya kaita kuma ya dawo da ita, sannan duk wata yake biyasa. Haka Abban Fadwa shima sha tara ta arziki Ya Azeez yake masa, wanda bama shi kaɗai ba kaf dangin su da suka rage na Babura suna matuƙar alfahari da samun Ya Azeez, saboda shi kwata kwata bashi da burin tara wani abun duniya, burinsa kawai shine ya yiwa jama'a hidima ya kuma kyautata musu tamkar yadda mahaifinsa ya dinga taimakawa mutane yana tallafawa rayuwarsu kafin rasuwarsa. Sannu a hankali abubuwa suka gama daidaita a tsakanin Shatu da Ya Azeez ɗinta, dan ta kai yanzu har Abba ya samu Abbie da kansa yayi masa magana, inda kuma kai tsaye Abbien ya basu dama yace su turo, sosai Abba yayi matuƙar farin ciki. Inda kuma yana komawa gida ya samu Ya Azeez ɗin ya sanar masa da duk yadda sukayi da mahaifin Shatun. Sosai shima Ya Azeez ɗin yayi farin ciki matuƙa, dan har sai daya kasa ɓoye farin cikin da yake ciki a gaban Abban, wanda kuma da kansa ya kira Ummansa ya sanar da ita abinda ke faruwa, sannan kuma yace ta gayawa Abba Fadwa jibi zai turo direbansa da mota yazo ya ɗaukesa domin su haɗu da Abban Fahad aje nema mai auren Shatun, saboda yana so cikin lokaci kaɗan ayi komai a gama. Inda kuma anan ne Umman ta sako masa zancen Fadwa, wanda shi har ga Allah ma tuni ya daɗe da shafe babinta a rayuwarsa, dan tun daya samu Shatu kuma bai tunanin akwai wata mace da zai iya so ko yaji tana burgesa a duniyarsa, balle kuma daya fahimci cewa Shatu na da tsananin kishi a kansa gashi ta tsani ayi mata zancen kishiya ballantana ace ya taɓa aure, ranar ta dinga fushi dashi kenan tana ɓata rai, sai yay ta aikin lallashi da ban baki sannan yake iya shawo kanta. Shiyasa koda Umma tayi masa zancen yace ta ɗan bashi lokaci zasu yi maganar daga baya, tun daga haka kuwa bai ƙara tada mata zancen ba, itama kuma Umman tun da taga haka sai bata ƙara tunkararsa da maganar ba ta zuba mai ido kawai tana so taga iya gudun ruwansa. Kwana biyu da maganar kuwa Ya Azeez ya tura direbansa Kaduna yaje ya ɗauko Abban Fadwa, nan suka haɗu gabaki ɗaya dasu Abba da Fahad da wani abokin Abban sukaje gidansu Shatu inda suka samu Abbie da ƙaninsa Baffan su Shatu da yazo daga Yola suka yanke magana inda akayi komai a mutunce da girmama juna Abba ya bada komai da ake buƙata kana aka tsaida rana wata ɗaya kacal, dan a cewar Abban gwara ayi komai a gama cikin lokaci saboda azumi dake gabatowa. Nan dai suka haɗu suka gama tsara komai cikin mutunta juna, suka yanke shawarar yadda abubuwan zasu kasance. Kafin daga bisani suna gamawa kuma Abban Fadwa yayi musu sallama dan yace a yau ɗin yake son komawa Kaduna, dan haka yake so ya koma da wuri saboda bayaso dare yayi musu akan hanya. Daga nan kuwa ko gidan Abban bai koma ba dan ko Ya Azeez ɗin ma ta waya ya kirasa sukayi sallama, kafin ya shiga mota direban Ya Azeez yaja suka ɗauki hanyar komawa Kaduna. Inda kuma a daren ranar ne bayan Abban ya dawo gida da daddare bayan sallar isha'i iyayen Alhaji Zailani suka zo tambayar auren Fadwa, wanda kuma sai a ranar ne ma Abban yasan da zancen cewa Alhaji Zailanin yana nemanta, saboda duk abubuwan dake faruwa a gidan ko kaɗan Mama bata taɓa gaya masa ba, haka kuma itama kanta Fadwan bata taɓa yi masa maganar ba. Amma duk da haka Abban bai nuna musu komai ba ya karɓe su hannu bibbiyu suka gama magana, bayan kuma sun bada sadaki da komai da komai ne. Kuma suka sanarwa da Abba cewa angon da kansa ya riga da ya tsaida rana sati biyu kacal saboda yace baya so aja wani lokaci mai tsawo dan yana so ana gama biki zai ɗauketa su wuce Saudiya, nan take kuwa Abba yace hakan yayi dai-dai babu wani abu, Allah ya kaimu lokacin lafiya, daga haka kuwa sukayi sallama suka rabu a mutunce. Abba na shiga gida kuwa ya zubewa Mama kuɗin da iyayen Alhaji Zailanin suka kawo, kana kuma ya sanar da ita lokacin bikin kamar yadda angon ya tsara. Sosai kuwa Mama da Fadwa sukayi farin ciki, dan Fadwa har ji ta yi kamar sati biyun da aka saka ɗin sunyi mata nisa, dan ita ba ta ƙi ma ace yau ɗin ne aka ɗaura auren ba. Shi dai Abba kawai kallonsu yake da ido ba tare da yace musu komai ba, na shi kawai ido ne, kuma su ɗin ya saka musu. Tun washegarin ranar kuwa Fadwa da Mama suka soma shirye shiryen biki kota ko'ina balle da suka ji zancen ana gama biki Fadwa da angon nata zasu wuce Saudiya. Kan kace me kuwa tuni Mama ta fara yayatawa ƴan unguwarsu cewa Fadwa zata auri shugaban majalisa kuma ana gama biki zasu tafi Saudiya. Ƙawayen Fadwa kuwa koda sukaji labarin zata auri mai kuɗi sosai suka tayata farin ciki, dan a cewar masu zuciya da hali irin nata sai yanzu ne ta samu dai-dai da ita. Nan suka hau shirye shiryen biki ba kama hannun yaro, ankon dinner kuwa leshi mai tsada suka fitar na kece raini sannan ga event kala kusan biyar da suka shirya yi. Tun ana saura sati ɗaya biki kuwa gidansu Fadwa ya soma cika maƙil da mutane ta ɓangaren Mama, amma a ɓangaren Abba babu wanda yazo domin babu wanda ya gayawa, dan ko dangin su dake Babura babu wanda yasan da labarin auren Fadwan a karo na biyu ballantana kuma Umma da kwata kwata ma bata san abinda ke faruwa ba. Mama kuwa sai kaiwa da kawowa take tana ta fankama tana hura hanci ita a dole ga surukar shugaban majalisa sukutum da guda. Fadwa kuwa tana jin yadda ƴan uwan Mama ke ta labarin haɗuwar gidanta da Alhaji Zailani ya aiko da mota aka kaisu sukaje suka gani, sai yabawa suke suna faɗar irin gyaran da yayi mata da yadda ya zuba mata abubuwan more rayuwar jin daɗi da hutu, Mama sai saka masa albarka take tana kwararo mai addu'oi, saboda dama yace baya buƙatar komai gashi ya zuba mata komai da ake buƙata har fiye da yadda ake zato. Sai dai wani abu dake ƙara ba Fadwan tsananin mamaki da takaici tun da aka fara zancen auren nasu sau ɗaya kawai Alhaji Zailanin yazo gurinta suka haɗu dashi, shima kuma ranar wayar hannunta yazo ya karɓa yace zai sake mata sabuwa, kuma tun daga ranar sai bai sake zuwa ba gashi kuma babu wayar da zata kirasa, wayar Mama kuwa ko ta kirasa da ita ma bata shiga. Sai dai kusan kullum ya aiko direbansa yace yana gaisheta. Ranar yau ta kama Asabar ranar da ake ɗaurin auren Fadwa, gaba ɗaya gida ya kacame sai hidimar biki ake kota ko'ina a cikin gidan, Mama da ƴan uwanta da wasu daga cikin makwabtan su da a yanzu suke matuƙar ganin girmanta da kimarta, sune suke ta kai kawo a tsakar gidan suna aikace aikace, yayinda su Ilham da Amatullah waɗanda suka sha ankon su na wata atamfa mai kyau suma suke ta nasu kai kawon a cikin gidam. A ɓangaren uwar gayya Fadwa kuwa tana can cikin ɗakin Mama ita da gogaggun ƙawayenta dukkansu sun sha kwalliya ta kece raini suna ta tasu hidimar. Ƙarfe 2pm. Dai-dai kuwa aka ɗaura auren a masallacin dake bakin layinsu, inda kuma ana gama ɗaurawa ango yace yana buƙatar a bashi amaryarsa ya tafi da ita, saboda a yau ɗin yake so su kammala shirin tafiyarsu. Aiko Abba da kansa ya shiga har cikin gidan ya sanarwa da Mama cewa maza Fadwa ta fito mijinta naso zai tafi da ita gidanta da kansa. Nan ko Mama tai tsalle ta dire tace ba tasan zancen ba, dole yayi haƙuri sai dare kamar yadda ake kai kowacce amarya itama akawo motoci na kece raini akaita. Abba dai bai sake tanka mata ba yasa kai ya fice daga gidan ya koma kasuwa abinsa, inda a nan gida kuwa Mama itama bata sake bi takan zancen Abban ba suka cigaba da hidimarsu. Bayan sallar magriba kuwa lokacin gidan ya ƙara cika da mutane maƙil ƴan zuwa kai amarya, inda kuma kowa burinsa shine kawai yaje yaga gidan da za'a kai Fadwa domin ya ƙaras da bada labari. A lokacin da aka sanar da cewa motar ɗaukar amarya ta iso ne kuwa mutanen suka dinga fita bakin titin unguwar domin samun motar shiga. Fadwa kuwa tana can tare dasu Hajiya Labiba dasu Hajiya Zalika da Hajiya Lubna da wasu sauran ƙawayensu da Mama da itama ta shirya ta saka hijabi tace dole da ita za'a tafi kai amaryan. Fitowa sukayi a hankali yayinda hannun Mama ke riƙe dana Fadwa, tafiya suke Mama nata faman washe baki cike da tsantsar farin ciki, jama'ar unguwar na biye dasu da sauran ƴan biki suna ta shewa suna guɗa, Fadwa kuwa sai wata dariyar farin ciki take da nishaɗi tana jin daɗi. A dai-dai lokacin suka isa bakin titi, nan take kuma kallo ya koma sama Mama ta hau waige waige tana zare ido, da mamaki ta saki hannun Fadwa ta ƙarasa inda wata mota ƙirar 207 ke fake ta tsaya tana tambayar wani dattijo dake tsaye a gurin tace "Malam ina motocin ƴan kai amaryar suke ne...?" Ta tambaya cike da tsananin mamaki tana kallonsa. Ɗan kallonta dattijon yayi kafin yace "Ga dai nan motar da amaryar zata shiga nan domin ita kaɗai akace in ɗauko..." Ya faɗa tare da nuna mata motar da ya jingina da ita ɗin. A take kallo ya ƙara komawa sama, dan ba Mama ba hatta Fadwa da sauran ƴan biki sai da suka shiga tsananin shock da mamakin kalaman mutumin, ba ma kamar Fadwa da take ganin kamar mafarki take ba gaskiya ba, wayar hannun Hajiya Lubna ta ƙarɓa da sauri ta kunna fitila ta ƙarasa gaban mutumin ta haska fuskarsa, ganin kuma mutumin da Zailani ke aikosa wajenta ne yasa ta sakin wani ƙaramin murmushi lokaci ɗaya tana sauke numfashi, kafin ta juya gurin Mama tana faɗin "Kai Mama ashe fa Baba Salahu ne direban Alhaji shine baki ganesa ba, dama kinsan yace ana gama ɗaura auren ranar zamu wuce Saudiya, ƙila tafiyar dare ce zamuyi ne shiyasa..." Ta faɗa cikin ƙoƙarin danne tashin hankalin da take jin yana bijiro mata, kafin kuma ta buɗe bayan motar kai tsaye ta shiga ta zauna sannan ta yafito Mama dake tsaye har lokacin jikinta a sanyaye tace "Mama ku shigo kuyi mana rakiya koda zuwa airport ne keda Hajiya Labiba, daga can sai a dawo daku gida..." Ta faɗa tana matsawa Maman ta shigo ta zauna, kana itama ƙawarta Hajiya Labiban ta shiga wanda itama tsantsar mamaki da al'ajabi suka kusa kasheta. Haka sauran dandazon mutanen suka tsaya suna gani aka ja motar dasu Mama da Fadwa da Hajiya Labiba kaɗai ke ciki aka wuce. Nan fa unguwa ta ƙara ɗauka Fadwa ta auri hamshaƙin mai kuɗi an tafi Saudiya har dasu Mamanta, wasu nata faɗin dama rabon auren mai arzikin ne ya rabota da auren Ya Azeez, wasu kuma suce Allah yasa dai na ƙwarai ne, wasu kuwa har da ƙari akan abinda basu sani ba. Mama dai kam gaba ɗaya cikinta ya gama ɗurar ruwa, kwata kwata ta rasa wane irin tunani zata fara yi, ita dai gata a cikin motar ana ta tafiya da ita amma gabaki ɗaya ba tasan inda aka nufa dasu ba. Hajiya Labiba kuwa kawai miƙa wuya take ta cikin motar tana ƙarewa layukan da suke ta wucewa kallo, wanda kuma tunda take a garin Kaduna bata taɓa sanin akwai irin waɗannan jagwalallun unguwannin ba, wai kuma da sunan mutane ne ke rayuwa a cikinsu. A haka har suka shigo cikin wata kwaraɓaɓɓiyar tsohuwar unguwa wacce kai da ganinta kaga tantagaryar unguwar talakawa futuk, wanda kuma duk a zaton Fadwa dasu Hajiya Labiban wucewa za'ayi ba tsayawa ba, basu ankara ba kuwa suka ga yaci burki a gaban wani ruɓaɓɓen gida mai gajeruwar katanga da kwata faca faca kota ko'ina. *Ina matuƙar godiya masoyana🙌* *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 3️⃣5️⃣ Wani irin kallon yagalgalallen gidan suke cikin tsananin mamaki da al'ajabi, kafin Hajiya Labiba tayi ƙarfin halin buɗe baki cikin tarin mamaki tace "Kai Malam gidan Alhaji Muhammad Al'ameen Zailani fa zaka kaimu shugaban majalisa, ya kuma ka kawo mu nan...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tare da buɗe ƙofar motar ta fito tana ƙara ƙarewa gidan kallo. Buɗe motar yayi ya fito shima yana faɗin "Nan ne gidan nasa ai Hajiya..." "Nan ne gidan fa kace...?" Hajiya Labiba ta tambayesa cikin tsananin mamaki da al'ajabi tana kallonsa. Daga cikin motar kuwa Mama da Fadwa gaba ɗayansu kallon kallo suka hau yiwa juna, kafin daga bisani Mama tayi ƙarfin halin buɗe ƙofar motar ta fito itama cikin sanyin jiki tana faɗin "Wai ina ne gidan ne daka zo ka wani tsunburemu anan sai kace wasu marasa galihu, kodai motar ce ta lalace ne...? Toh ka kira Alhajin mana ya turo da wata motar kar mu ɓata musu lokaci har jirgin ya tashi bamu isa airport ɗin akan lokaci ba..." Mama ta faɗa tana fitowa daga motar. "Munzo ai nan ne gidan Baaba..." Mutumin ya faɗa kai tsaye yana kallonta. Wani irin zaro ido Mama tayi tare da dafe ƙirjinta, kafin tace "Nan ne gidan wa ɗin..? Wannan kufan ne gidan Alhaji Zailanin kome kake nufi ne..? Ban gane maganarka kai tsaye ba yi min gwari gwari ta yadda zan gane..." Ta faɗa cikin tsananin tashin hankali tana kallonsa. Ganin yadda Mama tayi ne kuma yasa Fadwa buɗe motar itama ta fito tana kallonsu, wanda kuma ganin Fadwan ne yasa Mama saurin matsawa gabanta ta riƙo hannuwanta cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa tana faɗin "Ke Fadwa dama wai wannan shine gidan da Alhaji Zailanin yace zai ajiyeki, nan ne kuma gidan da ƴan uwana sukaje suka gani har suka koma suna yabawa...?" Numfashin Fadwa ne ya soma rawa yayinda kuma zuciyarta ta hau dokawa tana tsalle tamkar zata faso ƙirjinta ta fito waje saboda tsantsar tashin hankali da ɗimuwa. Sake girgizatan da Mama ne tayi tana ƙara tambayarta yasa ta dawo daga duniyar tunanin data lula. A hankali ta girgiza kai kafin tace "A'a Mama ba wannan bane, wancan a Millonion City yake ya taɓa kaini na gani..." Ta faɗa tare da juyawa tana kallon mutumin daya kawo sun kafin tace "Wai Baba Salahu ya haka ne, ya zaka kawo mu nan ka zube sai kace wasu dabbobi, ina shi Alhajin yake...? Wanda ta kira da Baba Salahu yace "Hajiya ai nan ne gidan naki, kuma Alhaji yana nan zuwa ya tsaya ne ya ƙarasa sallamar baƙinsa, amma yace ki shiga ciki ki jirasa yanzun nan zai ƙaraso..." Jada baya da sauri Fadwa tayi tana girgiza kai kafin tace "Wannan wace irin magana ce kake yi haka Baba Salahu, nan ne fa gidana kace shi wancan gidan kuma daya taɓa kaini na gani fa na waye shi ina yake...?" Ta faɗa cike da tashin hankali tana kallonsa. Ɗan ɗaga kafaɗarsa Baba Salahun yayi kafin yace "Ki dai shiga daga ciki Hajiya, idan yazo da kansa zaiyi miki bayanin komai..." Fadwa taja da baya da sauri tana riƙe da hannun Mama tace "A'a ba dai wannan gidan zan shiga ba Baba Salahu, ka dai sake kiransa kaji, amma ba dai nan gidan ba..." Yace "Hajiya nan ne gidan fa..." Mama ta watsa masa wani mugun kallo tana faɗin "A'a kaiko bawan Allah taya zakace mutum mai tarin arziki kamar Alhaji Zailani zai ajiye amaryarsa a irin wannan matsiyacin gidan, ka dai sake kiransa ɗin kaji, amma wannan zancen naka yayi kama da ƙanzon kurege..." Ta faɗa cikin ƙara tabbatar da zancen nata, domin ita a ganinta bazai taɓa yiwuwa ace mutum kamar Alhaji Zailani mai tarin dukiya da manyan motoci ya aje matarsa a wannan ruɓaɓɓen gidan ba, mutumin da yake shugabantar majalisa sukutum da guda taya za'a ce ma yasan irin wannan tsinanniyar unguwar balle ace wannan gidansa ne. Ita dai Hajiya Labiba tana tsaye daga gefe tana ta kallonsu, amma gaba ɗaya jikinta ya gama yin sanyi da lamarin. Fadwa kuwa wani irin tsantsar tashin hankali ta tsinci kanta a ciki, ita fa sai yanzu ne ma take son yiwa kanta wasu tarin tambayoyi da tun a baya ta gaza yiwa kanta su sakamakon rufewar da idanuwanta sukayi a lokacin. Sai data gama kallon ƙazantar bolar da kwatamin dake ƙofar gidan, sannan ta juya cikin sanyin jiki tana kallon Mama da faɗar irin tsananin tashin hankalin da take ciki itama ɓata baki ne, domin abun yayi matuƙar gigita tunaninta har yana neman fitar da ita daga hayyacinta. "Mama ya zanyi ne..ta ina zan fara fuskantar wannan ƙasƙantacciyar rayuwar...? Nifa gaba ɗaya kaina ya kulle..." Fadwa ta faɗa cikin tsananin tashin hankali tana duban Maman da itama ta zuba mata ido tana kallonta, sai a lokacin ne kuma Hajiya Labiba ta ƙaraso garesu ta dafa Fadwa da zuwa lokacin take ji tamkar ta ɗora hannu bibbiyu akai ta fashe da ihu tana dukan kanta saboda tsantsar damuwa da tashin hankalin da take ciki. Juyowa Fadwan tayi ta kalleta kafin tace "Dan Allah ki tasheni daga wannan mummunan mafarkin da nake yi kice dani ƙarya ne ba gaskiya bane abinda Baba Salahu yake faɗa, dan Allah kice ba gaskiya bane wasa yake min..." Ta faɗa cikin matsanancin tashin hankali gwanin ban tausayi. Rufe mata baki Hajiya Labiba tayi tana faɗin "A'a ba mafarki kike yi ba Fadwa a zahiri ne kike ganin duk abinda ke faruwa kuma gaskiya ne, amma fa nima kaina duk jikina yayi sanyi ban san me zance ba..." Wani irin mugun kallo Mama ta watsawa Hajiya Labiba kafin tace "Babu wani sanyin jiki, domin indai Alhaji Zailani ne da aka ɗaurawa Fadwa aure dashi ba wannan ne gidansa ba, saboda babu yadda za'ayi ace babban mutum kamarsa da irin manyan motocin da yake hawa ace wai nan ne gidansa, mtsww zancen banza kenan..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana jan dogon tsaki kafin tace "Ku mu ƙarasa cikin gidan dai dan mu ƙara tabbatar da abinda yake nufi, kafin mu zartar da hukunci..." Ta faɗa kai tsaye tare dasa kai cikin ƙwarin gwiwa ta shige cikin gidan, yayinda kuma Fadwa da Hajiya Labiba suma suka rufa mata baya cikin sanyin jiki suka doshi cikin gidan. Basu raina kansu ba sai da suka tsinci kansu a ɗan tsukakken ƙazantaccen tsakar gidan, inda gaba ɗaya ko'ina yake rakwacam da kwatami ga wani ɗoyin bandaƙi dake busowa tsakar gidan yana yi maka sallama. Ja da baya da sauri Mama tayi ta tsaya tana zaro idanu, kafin ta fara bin tsakar gidan da wani ƙazantaccen kallon ƙyama da ƙyanƙyani bayan ta toshe hanci tace "Kutumar uban nan kai, wai me suke nufi damu ne mutanen nan...?" Maman ta faɗa tare da juyawa da sauri ta fita waje, can sai gasu ita da Baba Salahu sun shigo, kamar kuwa dama jira Mama take su shigo nan ta rufesa da masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, sai faman zuba masa ruwan bala'i take tana cewa ya kira mata Alhaji Zailanin yazo, wannan wane irin tsabar wulaƙanci ne da iskanci da rainin hankali, taya zaisa akawosu wannan ruɓaɓɓen gidan ace anan ƴarta zata zauna, wallahi bai isa ba bazata taɓa saɓuwa ba sai dai idan ya sakar mata ƴa amma wannan gidan kam ko minti talatin ƴarta bazata iya yi a cikinsa ba, maza maza ya kirasa yazo ya sallamesu an fasa auren tunda abun nasu duk rainin wayau ne da rainin hankali wallahi yau sai ya sakar mata ƴarta, bazata yarda tana ji tana gani ƴarta tayi rayuwar ƙasƙanci a irin wannan matsiyacin gidan ba. Shi dai tunda ta fara faɗan bai tanka mata ba, hasali ma sunkuyar da kansa ƙasa yayi kawai yana saurarenta, sai da tayi faɗan ta gama sannan ya fito da wayarsa ƙirar Nokia mai tocila ya danna wata number kafin ya kara wayar a kunnensa. Cikin lokaci kaɗan kuwa aka ɗaga kiran, yayi sallama kafin ya ɗora da faɗin "Munzo gidan amma Mamanta tace bazata zauna ba, sai dai in kiraka kazo ka saketa su koma gida..." Kasaƙe Mama tayi tana saurarensa amma duk basu jin mai ake cewa daga ɗaya ɓangaren, sai dai kawai gani sukayi ya sauke wayar daga kunnensa yana faɗin "Toh shikenan saika ƙaraso ɗin..." Ya faɗa tare da kashe wayar ya mayar cikin aljihu yana kallon Mama da Fadwa da Hajiya Labiba da sukayi mai caa da idanuwa suna kallonsa. Tsaki Mama ta saki cikin takaici kafin tace "Ni wallahi sam ban yarda nan gidansa bane, domin ba ta yadda za'ayi a danganta Alhaji Zailani da wannan matsiyacin gidan, sai dai in da wata a ƙasa da mu bamu sani ba..." Hajiya Labiba ta rausayar da kai tana faɗin "Kiyi haƙuri Mama, mu jira har ya ƙaraso ɗin, sai muji dalilinsu na yi mana hakan..." Wani wawan tsaki Maman ta saki kafin tace "Muna nan muna jiran isowarsa ɗin ai yazo ayi duk wacce za'ayi..." Hajiya Labiba tace "Adai yi haƙuri Mama abi komai a hankali..." Dan takaici Mama bata ƙara magana ba ta koma gefe ta jingina da jikin bango tana sauke numfashi, itako Fadwa dama duk maganganun da suke tana jinsu amma bata da lokacinsu ne ballantana ta tanka musu, saboda a ganinta ita damuwarta tafi gaban tsayawa ta biyewa wannan shirmen surutan nasu na banza ballantana har ta tayasu. Suna nan tsaye cirko cirko a tsakar gidan kowa na saƙawa da kwancewa, Fadwa dai na tsaye da tunani barkatai a ranta daya cunkushe mata zuciya, domin a yanzu ta fara ɗiga ayar tambaya akan Alhaji Zailani da dalilinsa na sawa a kawosu nan gidan, sai dai kuma bata fatan abinda zuciyarta ke zargin ya tabbata har ya zamo gaske. Suna nan tsaye kuwa sai ga Alhaji Zailanin ya shigo gidan faram faram yana tattare babbar rigar shaddarsa ta ɗaurin aure. Ganinsa ne yasa Mama matsowa da hanzari tana washe masa baki tana faɗin "Yauwa gwara da Allah ya kawoka Alhaji, kaga wannan matsiyacin gidan direbanka ya kawo mu ya zube wai nan kace Fadwa zata zauna, kuma ance ba wancan gidan da ƴan uwanta sukaje suka gani bane shine abun yake bamu mamaki nace a kiraka kazo saboda inaga shi bai san wancan sabon gidan da ka ginawa Fadwan bane shiyasa ya kawo mu nan..." Wani irin kallo Alhaji Zailanin ya watsa mata kafin yace "Ita Fadwan tafi ƙarfin zama a wannan gidan kenan kike nufi ko me...?" Ya faɗa kai tsaye yana watsa mata wani ƙasƙantaccen kallon da yasa Maman saurin matsawa gefe tana kallonsa. Zaro idanuwa Mama tayi cike da tsoro kafin tace "Amma baka ga yanayin gidan bane..? Ai kaima kanka kasan babu ta yadda za'ayi Fadwa data saba da rayuwar jin daɗi ta zauna a irin wannan matsiyacin gidan balle har ta iya yin wata rayuwa a cikinsa ba..." Cikin matsanancin ɓacin rai Alhaji Zailanin ya kalli Mama kafin yace "Dame gidan uban ita Fadwa ɗin yafi wannan amma har ta iya rayuwa a cikinsa na tsawon shekaru, sai wannan ɗin ne saboda tsabar rainin wayau da rainin hankali zakice bazata iya rayuwa a cikinsa ba, dame gidan nata uban yafi nawa da har kike faɗin haka...?" Ya faɗa cikin tsawa yana tsatstsareta da idanu cike da rashin kunya. Wani irin rawa da kakkarwa jikin Fadwa da Mama ya ɗauka lokaci ɗaya yayinda suke kallonsa fuskokinsu ɗauke da tsananin mamaki da al'ajabin yanayinsa, ganin irin kallon da suke masa ne kuma yasa shi ƙara tamke fuska, kafin kuma cikin tsantsar rashin mutunci da rashin kunya yace "Ki buɗe kunnuwanki da kyau ki jini wannan gida da kike gani shine asalin gidan da Fadwa ƴarki zata zauna a cikinsa kuma zama na har abada, domin aurena da ita babu saki babu yaji kuma ban da wannan gidan bani da wani gida da ya kai min shi ballantana har ya fishi, saboda haka ku kama hanya ku fita ku bar min gidana tun kafin in fito miki a ainihin Ya'u na, sannan in nuna miki asalin kalata, domin ni ɗin nan da kike gani kallon kitse kike yiwa rogo ko ince kuna yi min kallon biri ne ni kuma ina yi muku na ayaba, dan ni ɗin nan da kike gani cikakken ɗan jagaliya ne na bugawa a jarida kije kuma ki tambayi duk wanda zaki tambaya tun daga kan farkon unguwar nan har zuwa ƙarshenta, kice musu waye Ya'u mai kifi daga yaro har babba babu wanda bai sanni yasan tarihina ba kuma babu wanda ba zai gaya miki asalin waye ni ba, saboda haka sahunki a likafa ki fita ki bar min gida, amarya dai tawa ce tunda na biya sadaki an ɗaura mana aure shaidu sun shaida kuma kun kawota gidan mijinta, saboda haka ga hanya fita ku kama gabanku kuma daga yau kar in sake ganin ƙafar ko waye daga cikinku a gidana, domin ni jajirtaccen namiji ne dan haka bazan ɗauki irin iskanci da wulaƙancin da kuka dinga yiwa wancan mijin nata na farko da kuka raina ba, ni ɗin nan na isheku riga da wando har da ƴar ciki. Saboda haka ga hanya nan maza ku fice min daga cikin gida kowacce ta kama gabanta..." Ya ƙarashe maganar cikin tsawa da hargowa kamar zai kaiwa Maman duka. Daga Mama har Fadwa da Hajiya Labiba kuwa gaba ɗaya jikinsu rawa ya ɗauka, kafin Mama ta iya ƙarfin halin buɗe baki cikin tsananin kaɗuwa da tsoro tace "Wane irin magana ne..wa.. wannan Alhaji..? A maimakon muga ɗorewar daɗi da farin ciki kamar yadda ka faro mana sai kuma kwatsam rana ɗaya yau ka canza mana gabaki ɗaya kamar baka sanmu ba...?" Watsa mata harara yayi kafin yace "Dawa kuke tunanin ɗorewar daɗi da farin ciki a tare dashi..? Kin ko san ma dawa kike magana kuwa..? Kai ga dukkan alamu dai har yanzu baki fahimci inda maganata ta dosa ba, amma bari in yi miki gwari gwari saboda kar in barki a duhu..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakin wani munafukin murmushi kafin ya ɗora da faɗin "Ni ɗin nan da kike gani ban je neman auren ƴarki dan ina sonta ko domin tana burgeni ba, hasalima naje nemanta ne domin in bata shawara sannan in nusar da ita illar abubuwan da take yi wanda har ya jawo mata rashin samun kwanciyar hankali a gidan mijinta sannan kuma cikin hikima in ganar da ita babban kuskuren data tabka a rayuwarta na rabuwa da mijinta da tayi, amma sai me..? Tun a zuwan farko da nayi gidanku na fahimci maganar da mutanen unguwar ke faɗa a kanku ke da ita na tsantsar kwaɗayi da son abun duniya da rashin wadatar zuciya gaskiya ne, wanda hakan yasa na sake komawa na yo sabon shiri kafin na sake dawowa da ƙarfina da nufin siye zuciyarta da taki gabaki ɗaya, kuma sai gashi ban sha wata wahala ba domin dukkanku kun kasance masu kwaɗayi da son abun duniya, shiyasa tun a ranar farko na ƙara fahimtarku na gano inda kuka dosa da yanayinku gabaki ɗaya, wanda ni kuma hakan yasa na ƙara zage damtse na shiga na fita na aro duk wani abu da nasan zai ƙara dulmiyaku har ku shagala da son gano ko ni ɗin wane ne na gama siye zuciyarku da bakunanku da abu mafi soyuwa a gareku wato kuɗi. Saboda nasan idan naje gidanku a yadda nake bani da komai da wuya ki saurareni saboda dogon burin da kuka ɗauka ke da mahaifiyarki kuka ɗorawa kanku. Hakan yasa naje nayo aron haɗaɗɗiyar mota da kuɗaɗe masu yawa nazo har ƙofar gidanku na aika akayo min sallama dake, sannan nace kiyi min iso inaso zan shiga in gaida mahaifiyarki..." Ya faɗa yana sakin wani makirin murmushi kafin ya cigaba da faɗin "Nayi mamaki sosai na irin tarbar dana samu a gun mahaifiyarki, domin ko kaɗan bata tambayeni waye ni da sana'ata ba, kawai ina zube mata kuɗi ta hau rawar jiki tana yaƙe baki, tun daga nan na ƙara tabbatar da ku ɗin ko su waye. Daga nan na dinga ƙoƙarin son inga na burgeki, wanda hakan yasa kina gaya min kina son waya naje kai tsaye na aro waya mai tsada a gurin wani na kawo miki. Wanda kuma a ranar na haɗu da mahaifinki mutumin kirki ya tambayeni waye ni sannan meye sana'ata duk na faɗa masa gaskiya, cewa ni mai cin kasuwar ƙauye ne inda nake siyo dabbobi da kayan miya ina siyarwa, sannan ina soya kifi a bakin titin layinmu ban ɓoye mai komai ba, duk a tunanina mahafinki bazai yarda in aureki ba sai gashi kai tsaye yace ya bani ke in turo magabatana a tsaida magana. Ban taɓa zaton zan sameki cikin sauƙi haka ba, shiyasa tunda aka ɗaura aurena dake yau nake cikin tsantsar farin ciki duk da yake babu mutum ko ɗaya a cikin dangina da iyalina da yasan cewa na ƙara wani auren a birni, domin ban sanar dasu komai ba, amma duk da haka ina cikin matuƙar farin ciki da jin daɗi sosai..." Ya ƙarashe faɗa yana murmushi mai cike da tarin ma'anoni. Fadwa kuwa tunda ya fara maganar jikinta ya ɗauki wata matsananciyar kakkarwar tashin hankali da ɗimuwa, lokaci guda gaba ɗaya kunnuwanta suka daina jiye mata sautin muryarsa sai shuuuuuu kawai da suka ɗauka ji take kamar ba gaske ba, dama ranar yau ɗin ta zame mata tamkar a mafarki ba gaske ba. Jan kumatunta tayi da ƙarfi ta shafa fuskarta yanzu kam ta tabbatar da ba mafarki take ba, da gaske ne komai dake faruwa a gabanta, sai dai bata san me zatayi ba kukan baƙin ciki ko nadama..? Idan na baƙin ciki ne anya ya dace ta tsaya tunanin abinda ya kamata da wanda bai kamata ba..? Idan kuwa na nadama ne ya dace ta tsaya saurarar zantukansa wanda furtasu yake dai-dai da yankewar numfashi daga gangar jikinta ta yanke jiki ta faɗi ƙasa..? Wani irin mummunan bugawa zuciyarta tayi da mugun ƙarfi ta zame ta zauna daɓas a ƙasa tana dafe kai cike da matsanancin tashin hankali kafin tace "Wane irin laifi nayi maka dana cancanci irin wannan sakayyar daga gareka, mena yi maka daka zaɓi ka muzgunawa rayuwata ka wulaƙantani a idon duniya irin haka..mena tsare maka dan Allah wane irin zunubi na aikata maka da zakayi min sakayya irin wannan..me nayi maka da zafi haka...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana jin saukar wasu zafafan hawaye daga cikin idanunta. Cikin damuwa Hajiya Labiba tace "Nima dai tambayar da nake son yi masa kenan kika rigani..." Mama kuwa baya taja tana dafe ƙirji gaba ɗaya ta gama cika da mamakinsa hakan yasa bakinta yayi mata nauyi ta gaza iya furta komai sai faman kallonsa kawai da take tana jinjina kai cikin matsanancin mamaki da al'ajabi, a hankali take ƙoƙarin tattare maganganunsa tana aunawa a mizanin da zata iya fassarawa da yaren da zata iya ganewa domin maganganun nasa sunyi mata kama da saukar aradu nauyinsu yayi mata yawa. Shiko Ya'u ko kaɗan bai ji tausayin Fadwa ba, sai ma sake matsawa da yayi gabanta yana murmushi ya kai hannu yana ƙoƙarin riƙota tai saurin ja da baya ta miƙe tsaye tana girgiza masa kai hawaye na ƙara zubo mata. Sake matsawa yayi kusa da ita zai kamota, sai ta fashe da wani matsanancin kuka tana girgiza kai kafin tace "Na roƙeƙa da girman Allah ka barni ka rabu dani, na haɗaka da girman Allah..." Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka mai ƙarfi. Ya'u ya bita da kallo kafin kuma ya maida kallonsa kan Baba Salahu dake tsaye yana ta kallonsu cikin al'ajabi, taɓosa Ya'un yayi yana faɗin "Kwashesu ka mayar dasu gida dare na ƙara yi..." Kallonsa Mama tayi kafin tace "Ban gane a kwashemu a mayar damu gida ba, ita Fadwan kuma fa, kana nufin anan zamu barta kenan ko me kake nufi...?" Wani irin banzan kallo ya juyo ya watsa mata kafin yace "Abinda nake nufi kenan, ku fita ku bar mana gida inaso zan huta da amaryata, idan kuma kika zaɓi akasin haka to ki tabbatar da a yau ba sai gobe ba zaku biyani duk abinda na kashe muku tun daga ranar dana fara zuwa gidanku har kawowa yau da aka ɗaura mana aure, komai da komai yana nan a rubuce tsaf a takarda na gama lissafawa, idan kuka biyani yanzun nan zan saki ƴarki ku ƙara gaba, zaɓi ya rage naki..." Ya faɗa kai tsaye yana kallon cikin ƙwayar idanunta. Baki Mama ta rufe cikin kaɗuwa tana faɗin "Yanzu ashe dama baka da mutunci ban sani ba, ashe abinda ka tanada zakayi mana kenan ko..? To wallahi bazan taɓa ƙyaleka ba, kuma wallahi sai kasan mu ka wulaƙanta..." Wani kallo Ya'u ya sake watsa mata kafin ya nuna mata hanyar fita yana faɗin "Fitar min daga cikin gida tun kafin in sauya tunanina a kanki, idan kuma kina ganin wasa ne ki jira ina zuwa..." Yana gama faɗin hakan ya fizgi hannun Fadwa dake duƙe tana rusa uban kuka ya jata tana tutturjewa tana ihun kuka ya shige da ita wani ɗaki kafin ya mayar da ƙofa garam ya rufe yana faɗin "Karku yarda in sake fitowa in iskeku a cikin gidana, idan ba haka ba kuwa duk abinda nayi muku kune kuka jawa kanku..." Tsayawa akai kallon kallo tsakanin Hajiya Labiba da Mama, kafin Hajiya Labiba tayi ƙarfin halin riƙo hannun Mama dake tsaye kamar an dasata tace "Mama muje dan Allah kar ya sake fitowa ya iskemu yayi mana rashin mutunci, dan naga alamun bai da kunya zai iya aikata abinda ya faɗa..." Ta faɗa tana janta da hanzari suka fice daga gidan, yayinda Baba Salahu shima ya rufa musu baya da sauri suka fice tare. Koda suka fito waje kuwa da ƙyar Hajiya Labiba ta iya lallaɓa Mama data toge a bakin motar ta kafe tace babu inda zataje har sai Ya'u ya sakar mata ƴarta. Sai da ƙyar da ya Allahu sannan Hajiya Labiba da Baba Salahu sukayi da gasken gaske kafin ta haƙura ta shiga bayan motar ta zauna tana ta sauke numfarfashin wahala da tashin hankali, kafin itama Hajiya Labiba ta zagaya ta shiga ta zauna a kusa da ita kana Baba Salahu shima ya shiga yaja motar suka bar unguwar. A ɓangaren Fadwa kuwa sosai hankalinta yay mugun tashi, sai tutturjewa take tana ihun kuka amma ko kaɗan Ya'u bai ji ɗigon tausayinta a ransa ba, haka ya wancakalar da ita a saman wata ƴar yaloluwar katifa mai kamar tabarma dake tsakar ɗakin. Fashewa tayi da wani sabon kuka tana faɗin "Dan girman Allah na haɗaka da Allah da Manzonsa kayi haƙuri ka rabu dani na tuba ka taimaka min..." Take faɗa tana jan ajiyar zuciya tamkar numfashinta zai ɗauke yabar gangar jikinta, saboda tsabar tashin hankali da tsantsar damuwar da take ciki. Miƙewa tsaye yayi yana murmushi ya cire babbar rigar shaddar dake jikinsa ya aje gefe, kana ya kai hannu ya kamo hannunta yana shafawa cikin wani irin salo yana faɗin "Haba mana amaryar Alhaji Muhammad Al'ameen Zailani, kiyi haƙuri ki rungumi angonki mana..." Fizge hannunta tayi ta miƙe tsaye da sauri tana zaro ido lokaci ɗaya tana girgiza masa kai. Murmushi ya sakar mata yana ƙoƙarin sake kai hannu ya riƙota ta ƙara matsawa can gefe ta manne a jikin bango tana kakkarwa da tsiyayar hawaye. "Dan darajar iyayenka ka ƙyaleni, na roƙeƙa dan Allah..." Ta faɗa tana ƙara matsawa baya tare da haɗa hannayenta guri ɗaya alamar roƙo. Matsawa yayi da sauri ya riƙota lokaci ɗaya ya haɗeta da ƙirjinsa ya ruƙunƙumeta yana sauke numfarfashi haɗe da ajiyar zuciya. Mutsu mutsu ta hau yi tana ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ina ya riƙeta gam gam babu ta yadda za'ayi ta iya ƙwatar kanta. Haka ta gaji da mutsu mutsun dan kanta ta haƙura ta lafe a jikinsa yayinda take ƙara fashewa da wani kuka mai ƙarfi da matuƙar ban tausayi, da sanyaya jikin duk wanda ya saurara. Itako Mama koda ta koma gida banda sannu da zuwan da ƴan uwanta sukayi mata babu abinda ya sake shiga tsakaninta da kowa, haka ta shige ɗakinta ta haye gado ta kwanta tana ta juye juye ranta fal da tunanin makomar rayuwar Fadwa a gidan Ya'u mai kifi. Tambayan duniyan nan kuwa Abba yayi mata amma tace mai lafiya ƙalau babu komai, kawai gajiyar biki ce take nuƙurƙusarta, daga ƙarshe dai haka Abba ya zura mata ido kawai ya ƙyaleta ba tare daya sake tanka mata ba. Ita kuwa Hajiya Labiba tun a daren ta dinga kiran wayar ƙawayensu tana gaya musu abinda ya faru. Inda Hajiya Lubna sosai abun ya taɓa ta ta, wanda da yawa kuma daga cikin ƙawayensu dariya suka dinga yi suna jin daɗin abinda ya faru da Fadwa, dan dama tuni take basu haushi da wannan iyayin nata na banza da wofi. Washegari Fadwa ce durƙushe gaban murhu ta haɗa itace tana ta hura wuta da bakinta, yayinda kuma idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir hawaye sai tsiyaya suke daga cikin idanunta suna mata wani mugun raɗaɗin azaba, kwana ɗaya tak tayi amma duk tai wani wujiga wujiga da ita gwanin tausayi. Gefe kuma Ya'u mai kifi ne tsaye daga shi sai gajeren wando a jikinsa yana riƙe da mafici yana fifita sai wani banzan kallo yake jefa mata. A hankali ta miƙe taje ta ɗauko tukunya tazo ta zuba ruwa tana ƙoƙarin ɗaurawa akan murhun ya karɓe tukunyar yana faɗin "Dalla ki hura wutar ta kama tukunna kafin ki ɗora tukunya, ko a gidanku haka wannan tsohuwar uwar taki ta koya miki ɗora tukunya ba tare da ice ya kama ba...?" Bai bata zarafin magana ba ya cigaba da faɗin "Ko da yake ba abun mamaki bane tunda babu abinda ke gabanta sai son abun duniya, bai zama lallai ma ta tsaya koya miki girkin ba tunda in banda son kuɗi babu abinda ta saka a gabanta..." Kuka Fadwa ta fashe dashi ta ɗago tana kallon Ya'u, wanda ya kauda kai da sauri yana watsa mata harara. Hannunsa ta kamo cikin sanyin jiki tana faɗin "Dan Allah idan akwai abinda nayi maka da yasa kake da niyyar azabtar dani da irin wannan wulaƙancin, kayi haƙuri ka yafe min ba dan halina ba na tuba ka gafarceni..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana jin taruwar wasu zafafan hawaye a idanunta, jikinta kuwa sai faman rawa yake da kakkarwa, dan zuwa yanzu ji take tamkar tai ta ihu da ƙarfi ko zataji sauƙi da sassaucin baƙin ciki da tashin hankalin dake azalzalar ruhi da zuciyarta. Bai tanka mata ba ya raɓa ta gefenta ya wuce ɗaki, haka ta zauna ta ci kukanta har ta gaji ta share hawayenta, sannan ta miƙe ta cigaba da aikin girka tuwon daya sata a matsayinta na amaryar da aka kawo gidan miji jiya, wacce ya kamata iyanzu ace tana cikin ɗaki akwance tana hutawa, amma saboda rashin gata yasa babu yadda ta iya dole ta fito, tayi abinda ya sata. Bayan Kwana biyu Zaune take a ɗan filin tsakar ɗakinta wanda babu komai a cikinsa sai tarkacen kayan robobin cin abinci da tukunyar da take dafa musu abinci sai bunbun zuba ruwan sha, wanda kuma ko arzikin ledar tsakar ɗaki ɗakin bai samu ba, sai wata ƴar yaloluwar katifar da suke kwanciya akai wanda ko arzikin zanin gado itama bata samu ba, sai kuma wani ɗan ƙullin kaya da aka ɗaure a ɗankwali wanda shine a matsayin filo. Tsuru tayi kawai tana kallon ko'ina a cikin ɗakin kafin a hankali ta kai bayan hannunta ta goge wasu sababbin hawayen da suke ƙara zubo mata. Wanda kuma tun da take bata taɓa shiga tashin hankali irin wanda take ciki a yanzu ba, duk wani abu da take tunani kuwa ada lokacin da take gidan Ya Azeez sai ta tarar na yanzu yaci ubansa. Dan tun da take da Ya Azeez bai taɓa zagin iyayenta ba koda wasa, kuma kullum burinsa shine yaga ya kyautata mata, bai taɓa barinta cikin damuwa, kuma koya ta nuna tana son abu ko mene ne shi kuma koda yafi ƙarfinsa ne sai ya nemo mata koda kuwa zai takura kansa ne sai yasan yadda yayi ya samo ya kawo mata. Bai taɓa barinta tayi aikin komai indai har yana gida, ko girki shi ke yi mata da kansa ya kuma bata taci, amma bai taɓa nuna gajiyawarsa ba, hasalima a kullum burinsa shine yaga ya faranta mata rai ya mata abinda takeso. Amma wannan kam yau kwana uku da kawota gidansa har ta fara tantance tsakanin aya da tsakuwa. Allah sarki Ya Azeez, ashe akwai ranar da zataji kewarsa a ranta har taji dama ace tana gidansa bata fito ba..? Lallai sai yanzu take ƙara yarda da maganar Abbanta, inda yace yayi matuƙar baƙin cikin rabuwarta da Ya Azeez kuma ya tayata baƙin ciki domin da wuya ta ƙara samun kamarsa, kuma haka zatai ta kokawa rashinsa a rayuwarta. Saboda shi ɗin na musamman ne kuma samun irinsa a wannan lokacin zaiyi matuƙar wahala. Kuma gashi tun kafin aje ko'ina da rabuwar tasu abubuwa sun runcaɓe mata. A Haka dai rayuwar Fadwa ta dinga gudana a gidan Ya'u mai kifi. Inda a cikin kwana huɗu zuwa biyar duk ta rame ta jeme kana ganinta kasan tana cikin matsananciyar damuwa. Shiko Ya'u a cikin ƴan kwanakin har wata ƴar ƙiba ya ƙara yayi kyau abinsa yay ɓul, alamar dai bai da wata damuwa, dan tunda akai auren bai fita wajen suyan kifi ba, koda yaushe yana nan naniƙe da ita a gida yana gurzarta kamar tuwo ko gajiya baya yi. Gaba ɗaya Fadwa ta gama galabaita irin muguwar galabaitan nan duk ta fita a hayyacinta, wanda kuma a cikin kwanakin duk wanda ya ganta da wuya ya iya ganeta, saboda wata iriyar muguwar rama da tayi ga wani uban baƙi da tayi kullum ita kenan baki a bushe ƙayau gwanin tausayi. Allah ya sani ta kasa sabawa da yanayinsa gabaki ɗaya, amma ya kasa tausaya mata. Gashi babban abinda yake matuƙar ɗaga mata hankali kullum shi kenan aikin abu ɗaya, ba dare ba rana. Wanda kuma a gidan Ya Azeez sam bai saba mata da hakan ba, gashi kwata kwata shi bai iya tarairaya da lallashi da tausasawa ba. Saɓanin Ya Azeez ɗinta dake komai cikin nuna tsantsar kulawa da soyayya uwa uba kuma tausasawa da lallashi, ga tarairayarsa mai matuƙar tsayawa mutum a zuciya, wanda kuma a lokaci guda sai yasan yadda yayi ya fitar da kai daga hayyacinka ya ɗaukaka maka tsananin so da shaukin kasancewa dashi cikin kowanne irin yanayi a lokacin. Saɓanin wannan kuma da kullum burinsa kawai ya hayeta ya biya buƙatarsa babu ruwansa da wani lallashi ballantana wata tausayawa, shi dai kawai yaji ya gamsu kuma buƙatarsa ta biya shikenan zai tsallake ya barta. Wannan yanayi yana matuƙar yiwa Fadwa ƙunci da baƙin ciki, tana matuƙar azabtuwa domin ta riga ta saba da yanayin Ya Azeez ɗinta cikin watanni taran da sukayi tare, gashi tun tafiya ba tayi nisa ba har ta fara tsanar kanta da nadamar abinda ta dinga yiwa Ya Azeez wanda a lokacin idan yazo mata da buƙatarsa bata saurararsa sai dai tai ta kawo masa uzururrukan ƙarya ƙarshe kuma ta nuna masa bata ra'ayi. Shi kuma dake yana tsananin gudun ɓacin ranta a lokacin sai ya haƙura koda kuwa zai cutu ne ba zai taɓa takura mata ba. Amma wannan tana ji tana gani kuma ko tana ra'ayi ko bata yi, haka zai zage ya sasiƙeta iyakar son ransa, wata rana kuma yana yi yana zagin mahaifiyarta haka zaiyi ya gama kuma ya tsallake ya barta nan. ************* Bayan Sati Ɗaya Acan Kano kuwa tuni shirye shiryen bikin Shatu da Ya Azeez yake ta ƙara kankama, Shatu da ƙawarta Husna Baita kuwa tunda bikin ya ƙarato kullum cikin zirga zirga suke basu nan basu nan, dan har gidansu Ummi taje ta roƙi mahaifiyar Husnan akan a barta ta zauna a gidansu har sai an gama biki, dan ita kanta Zahra bata samun zama yanzu kullum tana kan hanyar zuwa kasuwa yin siyayya. Haka a ɓangaren Ya Azeez kuwa shima yana cikin tsananin farin ciki, shirye shirye kawai suke shi da Fahad da sauran abokanansu. Biki ne kuma suke shiryawa na kece raini irin na manyan ƴaƴan gata. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 3️⃣6️⃣ A haka shirye shiryen bikin yake ta ƙaratowa, gashi har yau saura sati biyu, shirye shirye kuwa kota ina yinsa akeyi, ta ɓangaren gidan su Shatu kuwa suma suna ta yin nasu. Haka a ɓangaren gidansu Ya Azeez suma duk da Umma ba a garin take ba, amma Abba yaba Mami manyan kuɗaɗe ita ta shige gaba akan komai kamar itace uwar angon, domin shi kansa uban gayyar yana daga ɓangaren Mamin da ita yake dukkan wasu shawarwari da shirye shirye, hatta da kuɗin kayan lefe da komai da komai kuwa ita Ya Azeez ɗin ya turawa ta account ɗinta bayan kuma wanda Abba ya bata shima ta haɗa, suka je Dubai ita da Basma da wata ƙawarta Hajiya Turai suka haɗo komai. Ɓangaren gidansu Shatu ko suma suna can suna ta nasu shirin bikin na kece raini irin na ƴaƴan manyan mutane. ********* Zaune take a saman kujera mai cin mutun uku dake cikin falonsu, wayarta ce a hannunta suna video call da Ya Azeez, wanda baya gari yau kwanansu uku kenan a Lagos shida Fahad, sunje siyo motoci, inda kuma sati ɗaya zasuyi acan kafin su dawo. Sanye take da wata doguwar rigar jallabiya baƙa, wacce ta dace da kyakkyawan surar jikinta, kanta kuma kitson kalaba ne ƙanana ƙanana da Husna ƙawarta ta kama mata, gyalen jallabiyar ne a kanta wanda ya zame kaɗan, sai hakan ya baiwa lallausan baƙin gashin dake gaban goshinta damar bayyana gashi kalaban ya kamu sosai gashin kuma yasha gyara sai sheƙi yake, fuskarta tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tai ba, sai ƴar hoda kaɗan da lipstick da ta ɗan goga, amma fuskarta tayi kyau matuƙa sai sheƙi take. Daga tsakiyar falon kuma Husna ƙawarta ce zaune a saman kafet ɗin dake shimfiɗe a falon ta tanƙwashe ƙafafunta ta jingina bayanta da jikin kujera tana ta faman latsa wayarta. Shatu kuwa sosai tayi nisa ta shagala da video call ɗin da sukeyi da Habibyn ta, sai zuba masa shagwaɓa take tana wani narke masa wai ita ala dole nan tayi missing ɗinsa, shi kuma duk ya wani susuce mata sai lalaɓata yake yana lallashinta. Ƙara gyara zama tayi tana kwaɓe fuska cike da wani irin salon shagwaɓa da sangarta, wanda har gyalen kanta ya zame gaba ɗaya kalaban kanta ya bayyana. Daga can ɓangaren Ya Azeez kuwa dake kwance a saman wani makeken Royal bed dake cikin wani katafaren hotel da suka kama a garin Lagos, juyi yayi yana ƙara ƙanƙame filon dake rungume a ƙirjinsa ya tsura mata ido ta cikin screen ɗin wayar kafin yace "Pls Eishatuna ki ɗan sassauta min kar ki zautani in kasa aiwatar da abinda ya kawo ni..." Ya faɗa cikin wata irin kasalalliyar murya dake bayyana tsantsar shauki da muradin da yake ciki, kana yana wani lumshe manyan idanunsa yana sakin numfashi. "Ni kuma Habiby..." Ta faɗa a sanyaye tana karyar da wuyanta gefe a sangarce. Saukar muryarta a kunnuwansa da yadda tayi maganar da wani irin daddaɗan salo ne kuma yasa shi jin wani irin yanayi mai cike da shauki da muradi mai girma na sauka da yawo a cikin jikinsa. Wanda kuma hakan yasa a hankali ya rungume wayar a ƙirjinsa kana ya ɗago lokaci ɗaya yana ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo ta cikin screen ɗin wayar, kafin kuma ya kwaɓe fuska cikin wani irin salo na musamman yace "Pls ki barni haka Eishatuna, zamuyi waya anjima, yanzu Fahad na jirana zamuje wani guri dashi idan na dawo zan kiraki..." "Nifa Habiby ban gaji da jin muryarka ba, pls kace masa ya tafi shi kaɗai, ya barni in ɗan ƙara ganinka kaji..." Ta faɗi maganar cikin sigar shagwaɓa, tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Tausasan laɓɓan nata ya kalla, still kuma yana ƙara jin wani irin abu nayi masa yawo a cikin jikinsa yace "Idan na dawo zan kiraki ai, bazan daɗe ba kinji...?" "Uhmm..." Ta amsa masa a hankali tare da ɗan tsura masa ido ta cikin screen ɗin wayar tana kallon kyakkyawar fuskarsa, kafin ta ɗaga masa hannu alamar bye, kana kuma ta katse kiran. A hankali ta ɗago kai tana murmushi karaf kuwa idanunta suka sauka a cikin na Husna dake ta galla mata harara, ganin irin kallon da take mata ne yasa ta zamewa ta kwanta a saman kujera tana faɗin "Kyaji dashi dai..." Ta faɗa tana wani lumshe idanunta a hankali tana sauraran yadda zuciyarta ke bugawa da tsananin son Ya Azeez da ƙaunarsa. Husna kuwa ganin sharetan da tayi ne yasa ta miƙe tsaye tana faɗin "Idan kinga dama sai ki tashi mu tafi dan wlh idan kika bari na kwanta duk nacinki babu inda zanje, sai dai ki tafi ke kaɗai ko ki haƙura da fitar sai gobe, amma idan na shige na kwanta kuwa ba inda zanje na rantse..." Kanta ta ɗan dafe a hankali kana ta tashi da sauri saboda tunawar da tayi cewa Basma na can na jiran zuwansu domin su tafi kasuwa suyo siyayya. A hankali ta miƙe tsaye tana ɗaukar wayarta kafin tace "Muje ni karki cinyeni da baki, almasifatu..." Ta faɗa tare da yafa gyalen jallabiyar a kanta, kana taja hannun Husnan lokaci ɗaya suka fice daga falon. A farfajiyar gidan suka ci karo da Ummi da ƙawarta Hajiya Zakiya da tayo mata rakiya, suna ta hira taƙi ƙarewa tun daga cikin gida. Cikin natsuwa suka ƙaraso kusa dasu suka rusuna suna gaishe da Hajiya Zakiyan, ta amsa musu fuska a sake kana tana kallon Shatu cike da tsokana tace "Ƴata amarya lallai har kin fara kyallin goshin amarci, wannan irin kyau haka sai ina kuma da yamman nan...?" Shatu tai murmushi tana sunne kai, Ummi ta harareta cikin wasa tana faɗin "Ina zasu kuwa daya wuce kasuwa yo siyayyar biki, ai kinsan ƴaƴan yanzu ba kunya ce dasu ba, ko irin ƴar kunyar nan ma su basu ji kawai shirye shiryen su suke tayi da kansu babu abinda ya damesu, marasa kunya kawai..." Ta ƙarashe maganar tare da zafgawa Shatun hararara. Da sauri Shatu ta kamo hannun Husna suka wuce da hanzari suna dariyar maganar Ummin. Hajiya Zakiya kuwa kai ta kaɗa tana dariya kafin tace "A'a barsu suyi Hajiya Khadija lokacin su ne, Allah yasa ayi taro lafiya a tashi lafiya..." Ummi tace "Ameen ya Allah Hajiya..." Daga haka suka ƙarasa inda direban Hajiya Zakiyan yayi parking motarta ta buɗe gidan baya ta shiga, kana suka ƙara yin sallama da Ummi, direban yaja bayan maigadi ya buɗe musu gate ne kuma suka fice daga cikin gidan, yayinda direbansu Shatu shima ya rufa musu baya suka fice daga gidan a tare. Washegari Ranar ta kama saura kwana sha ɗaya dai-dai bikin Ya Azeez da Shatu. Aunty Salma kuwa takanas ta ɗauko wata mai gyaran jiki da tsumi tun daga ƙasar Niger, wanda kuma ba ƙaramin kuɗi aka kashe ba wajan zuwanta nan ɗin. Koda ta iso kuwa wani lafiyayyen ɗaki na daban aka ware musu a cikin gidan, baka jin komai kuwa sai ƙamshi, gadon da aka ajiye domin baccinta kuwa tamkar anyi ɓarin turare akai. Kullum da safe za'ayi mata turaren jiki dana tsugunno dana wanka, sosai ake gyarata ciki da wajenta. Ga haɗin kayayyaki kala kala, tun daga kan na gyaran jiki har na turaruka da kayan mata. Haɗi akayi mata na musamman irin na amaren zamani. Tsumi ne na musamman irin na buzaye akewa Shatu, gyara ciki da wajenta dashi, sai tsumata ake, yanayin turaren da ake turara mata jiki da tufafi dashi kuwa lokaci guda wani daddaɗan ƙamshi ya soma bin jikinta duk inda ta gitta kuwa ƙamshi take bari awajen. Kullum mai yi mata dilka da halawa sai tazo, ga wani sihirtaccen kyau data ƙara, haskenta ya ƙara fitowa fuskarta ta ƙara wani fresh tai kyau gwanin ban sha'awa. Yayinda kuma a kullum Aunty Salma da kanta take sakata gaba tana bata haɗe haɗen da Hajiya Mariam Buzuwa ta haɗa mata, wanda kuma saboda tsabar son zaƙinta bata taɓa yi mata musu, haka take karɓewa ta shanye abinta tass hankalinta kwance. Wanda hakan yasa a wuni sai ta canza pant uku, saboda yadda take tsiyaya, sakamakon gyaran ya kamata sosai. Ana saura sati ɗaya biki kuwa su Mami da wasu manyan ƙawayenta suka kawo akwatuna guda goma sha biyu cif shaƙe da tsadaddun kaya ƴan gasken na kece raini. Sannan kuma Fahad ya bada makullin danƙareriyar mota ƙirar Ferari fara sol wacce aka zubo kayan akwatinan acikin yace kyautarsa ce a kawowa amarya. An karɓe su hannu bibbiyu domin ƙawayen Ummi manyan mata sun cika gidan, ga kuma tawagar Aunty Salma suma dan haka akayi musu tarba ta mutunci da karamci. Sosai suka ga kara da karramawa, sai yamma liƙis sannan suka koma gida bayan an cikasu da abin arziki har da tukuicin kuɗi mai tsoka. Inda kuma ana saura kwana uku ɗaurin aure ne Umma da Imaan suka zo daga Kaduna, nan gidan iyayen Fahad ɗin dai suka sauka, wanda kuma ta ɓangaren ango a nan ne za'ayi komai na taron bikin. Ɓangaransu Shatu kuwa yau ne suka fara gabatar da events ɗinsu wanda kuma gaba ɗaya duk na mata zalla ne babu namiji ko ɗaya, wanda kuma yanzu tsakanin Shatu da Ya Azeez waya ne kawai ke haɗasu sai chat, saboda an hanata fita sakamakon gyaran da ake mata. Shiyasa sosai suke kewar junansu, ba kamar Ya Azeez da yake cike da tsananin ƙaunarta da begenta, haƙuri kawai yake yana daurewa saboda babu yadda zaiyi, amma ji yake kamar yayi shekaru ne bai ganta ba. Ranar da akayi Bridel Shower kuwa wasu ƴan uwan Abbie dana Ummi suka iso, washegari kuma akayi buɗan kai da kamu wanda idan ka kalli Shatu kuwa a ranar saika ƙara kallonta saboda tsantsar kyawun da tayi, kuma a ranar ne ƴan uwan Abban Ya Azeez dana Ummansa suma duk suka iso garin. Sai ana gobe ɗaurin aure ne suka had'u lokacin da za'aje dinner, Ya Azeez kusan zaucewa yay sakamakon kyaun da yaga Shatu tayi masa sosai, idanu kawai ya zuba mata acikin motar, amma baiyi gigin ko kama ɗan yatsarta ba, saboda yasan bazai taɓa iya jure hakan ba. Shatu ma a nata ɓangaren gani tayi Habibyn nata ya canza mata sosai ya ƙara mata wani masifar kyau, lokaci ɗaya ya sake tafiya da imaninta, gefe guda kuwa sai take ganin tamkar yafi ƙarfinta, kawai ta tsinci dami akala ne, amma ba sa'anta bane. Bayan anyi dinner lafiya an tashi, Ya Azeez kasa zaune da tsaye yayi sabida yadda haɗuwar Eishatunsa da ƙamshinta suka gigita masa tunani, ai kuwa ranan ya addabeta da kira dan kusan raba dare sukayi suna hira. Haka ya kwana a falo kasancewar Abban Fadwa ya iso shima tunda rana, wanda kuma a nan ɓangaran Ya Azeez ɗin ya sauka shiyasa ya keɓe kansa a wani guri daban yana ta waya da Eishatunsa. Washegari kuwa misalin 11am. Dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren ABDULAZEEZ NASEER ABDULLAH ARABI da amaryarsa AISHA BELLO ƊAN ƘWARAI akan sadaki mafi daraja. Sosai ɗaurin auren ya samu halartar manyan mutane, kama daga kan ƴan kasuwa, ƴan siyasa, manyan Malamai da sauran masu faɗa aji dake garin Kanon duk halarci taron ɗaurin auren. Faɗar irin tsananin farin cikin da Abban Fadwa yake ciki kuwa a wannan lokacin ɓata baki ne. Sai faman washe baki yake yana ta gaggaisawa da mutane, ga manyan manyan ƴan kasuwa kota ko'ina, har da ma waɗanda bai taɓa tunanin zai gansu ido da ido ba a wannan ranar duk sai da ya gansu. Inda kuma ana gama ɗaurin auren aka tafi walimar cin abinci wani katafaren babban hotel aka gabatar da liyafar, wanda sai abinda ranka yake so shi zaka ci. Kusan kuma duk wanda yake jigo a gurin amarya da angon sai daya halarci liyafar. Zahra kuwa ba zama sai kai da kawowa take, ga tawagar ƙawayenta itama data gayyato sai hidima take dasu. Farin ciki kuwa a fuskar Ya Azeez kasa ɓoyuwa yayi, sai faman doka murmushi yake zuciyarsa tai fari tas tass tamkar bai taɓa shiga wata damuwa ko tashin hankali ba a rayuwarsa. Haka dai akayi yinin biki na kece raini, Masha Allah anci ansha biki yayi a duk yadda akeson ganin bikin ƴaƴan gata, biki yayi armashi sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya. Wanda kuma anan gidansu Shatun bayan an ɗaura aure, da yamma Ummi tai nata bikin tare da ƙawayenta, sai kuma amarya da aka fito da ita filin walimar inda aka ɗauko wata shahararriyar Malama da aka ɗauko tun daga garin Bauchi tana gabatar da wa'azi akan zaman takewar aure. A wannan lokacin kuwa babu wanda zai yiwa Shatu kallo ɗaya ya iya ɗauke idonsa akanta, saboda tsananin kyawun da tayi. Farin lashi ne tass a jikinta mai zanen golding, da alkyabba golding colour mai kyau da ɗaukar ido. Ana cikin wa'azin ne kuma Umma ta shigo gurin tare dasu Mami da Imaan da wasu daga cikin danginsu Ya Azeez ɗin na Babura. Ummi da kanta ta miƙe ta tarbosu ta basu gurin zama na musamman a inda take zaune tare da tawagarta. Sosai Umma ta dinga jin wani irin girma da tsananin daɗi da farin ciki yana mamaye zuciyarta, tana ta kallon Shatu wacce a lokaci guda taji ta shiga ranta, wanda kuma a gefen Shatun itama hakan ce ta kasance, dan tana ganin Umman taji gabaki ɗaya matar ta gama kwanta mata arai. Saboda daga ganinta tasan bata da matsala. Sai wajen ƙarfe 5pm. Aka tashi bayan kuma an rufe taron da addu'a ne aka shiga rabon takeaways, masu cike da kayan daɗi, sai kuma wata jaka mai kyau dake ɗauke da hotunan amarya da ango da aka zuba abubuwa kala kala a ciki. Koda aka tashi daga gurin walimar kuwa sai data sake wani sabon wankan sannan aka tsantsara mata kwalliya, sosai tayi masifar kyau sai haskawa take, gashi ta sha jan lalle ɗau daya zanu ya ƙara fito da kyakkyawar farar fatarta tamkar domin ita kaɗai aka ƙerosa. Sai da aka gama yi mata hotuna da iyayenta daƴan uwanta kafin nan aka shiga da ita ɓangaren Abbien ta, Ummi tayi mata faɗa sosai kana shima Abbie ya ɗora mata da nasa. Koda suka fito daga ɓangaren Abbien kuwa kwance tai akan cinyar Ummi tana ta hawaye, sai a lokacin ta fara jin wani tsananin kewar Ummin da Zahra, wanda kuma tunda aka fara bikin bata yi tunanin zataji tana missing ɗinsu irin haka ba. Bama kamar Zahra da ƙawarta Husna Baita, da kuma Umminta da Abbien ta, domin duk nasihar da Ummin ke mata na tayi biyayya wa mijinta ne, ta kuma bishi sau da ƙafa. Daga ƙarshe dai Ummi ta ƙarashe da yi mata bankwana itama tana nata hawaye. Misalin ƙarfe 6:30pm. Bayan an idar da sallar magriba Abban Fadwa da Abban Fahad da Abbie, su suka ɗauki Shatu a sabuwar motarta da Abbien ta ya bata ba tare da ɗan rakiya ko ɗaya ba. Wanda kuma daman tuni Abban Fahad yace Ya Azeez da Fahad ɗin suje can sabon gidan Ya Azeez ɗin da ya ƙera a unguwar. Tarauni G.R.A su jirasu. Ƙerarren gini ne irin na zamani wanda yaji ababen more rayuwar duk wani jin daɗin duniya, babu ce kawai ba'a saka ba acikin gidan. Bayan sun kaita ne sukai musu nasiha mai ratsa jiki da addu'ar zama lafiya, kana suka miƙe sukayi musu sallama suka tafi. Fahad shima yayi musu nasiha mai ratsa jiki da zuciya sosai kana daga bisani kuma yaja Ya Azeez ɗin suka fita inda aka bar Shatu da Basma matar Fahad ɗin da ƙawarsu Husna, nan suka tashi suma suka shisshiga ko'ina a cikin gidan suka zazzagaya suna ta yaba kyawu da tsaruwarsa. A hankali Shatu ke biye dasu suna ƙara ƙarewa gidan kallo, yayinda su kuma suke ta ƙara kutsawa ko'ina suna kuma ƙara yaba tsantsar haɗuwa da tsaruwar da gidan yayi. Dai-dai sun iso wani gefe daga tsakiyar gidan ne kuma idanunta suka sauka akan wani madaidaicin swimming pool mai kyau wanda aka ƙawatasa da wani irin nau'in ruwa mai kalar blue mai kyau da ban sha'awa, sosai gurin yayi mata mugun kyau. Daga can gefen swimming pool ɗin kuwa wasu kyawawan furanni ne masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, wanda aka kewaye gefe da gefensu da wani kalar wuta mai fidda kala kalan haske mai kyau da burgewa. Ita kam bata ma san dame zata iya tsara haɗuwa da tsaruwar da kuma tsantsar kyawun gidan ba. Haka suka gama zagaye ko'ina a cikin gidan, kana suka dawo falon da shima ya gaji da tsaruwa ya amsa sunansa falo, wanda aka narka uban dukiya mai tarin yawa a cikinsa, suka zauna suna ƙara yabawa tsantsar ƙoƙarin da Ya Azeez ɗin yayi. Su Ya Azeez da Fahad kuwa basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i suka shigo da manyan ledoji masu ɗauke da gasassun kaji masu zafi sai su fresh milk masu sanyi da sauransu. Nan Husna da Basma suka ce bazasu bar amarya ba sai anyi siyan baki dole Fahad da Ya Azeez suka siya baki, inda da ƙyar suka yarda suka karɓi dubu ɗari da hamsin, wai tayi musu kaɗan. Daga ƙarshe dai Fahad kama hannun matarsa yayi suka fita, Husna ta bisu itama domin su sauketa a gidansu dan bada motarta tazo, bayan duk sun fice ne aka bar Ya Azeez kawai da Eishatunsa a cikin gidan. A hankali ya ƙara matsawa kusa da ita sosai kana ya kai hannu cikin natsuwa ya ɗaga mayafinta, hawaye yaga suna sakko mata domin ji tai gaba ɗaya duk wata murna da farin ciki da take tuni ya kau a zuciyarta, saboda sai yanzu ne ta gane cewa tabbas ta rabu da kowa nata ta koma sabuwar rayuwa, idanunsa ya tsura mata yana ta kallon kyakkyawar fuskarta da ta sha kwalliya, hawaye sai zubo mata suke babu ƙaƙƙautawa, gani yayi ayau ɗin tafi masa kyau fiye da kullum da ko yaushe ma, domin har wani annuri da haiba yaga take saboda tsabar tsananin kyaun da tayi. "Masha Allah..." Ya furta yana ƙara kallon yadda Ubangijin talikai ya ƙera mata tsantsar kyawu gwanin ban sha'awa da burgewa, kuka take ɗan ƙaramin bakinta kuwa sai rawa yake yana wani irin shacking da motsi kamar tana son yin magana. Matsawa ya ƙara yi kusa da ita sosai ya yaye mayafin gaba ɗaya ya rungumeta. A hankali yake yi mata raɗa a kunnenta, cikin wani irin tattausan lafazi yake faɗin. "Nasan dole zakiyi kukan rabuwa da Ummi da Abbie, amma bai kamata kiyi kuka a irin wannan ranar mai cike da ɗimbin tarihi da farin ciki a garemu ba, ranar da mutane da dama suke fatan gani a rayuwarsu amma Allah bai basu damar hakan ba, ranar yau rana ce mai matuƙar muhimmanci a rayuwar mu, pls na roƙeki karki ɓata mana ita da ƙunci kiyi mana giɓin farin cikinmu..." Ƙara lafewa tai sosai a jikinsa ta kwantar da kanta a saman faffaɗan ƙirjinsa dake ta tashin ƙamshin daddaɗan turarensa mai matuƙar daɗi da sanyaya zuciya. A take kuma taji kukan ya yanke mata ɗif, sai wani matsanancin farin ciki dake neman mamaye ilahirin ruhi da gangar jikinta. Hannunsa ya kai ya kamo nata tattausan hannun daya sha jan lalle ya riƙe gam a nasa yana kallon ƴan siraran yatsunta da sukai wani irin mugun kyau da jan lallen ya ƙara musu. A hankali yake wasa dasu yayinda kuma yake ta shafa bayanta da ɗayan hannunsa. "Yau fa ke ƴar gata ce, matsayinki ya ƙaru sosai akan wanda kike dashi, daga yau za'a dinga ruɓanya miki ladanki saboda aikin ladan da zaki riƙa yi koda yaushe...ai nasan kina so ko...?" Ya faɗa a hankali cikin wata iriyar kasalalliyar murya data sake kashe mata jiki da zuciya lokaci ɗaya ta saukar mata da kasala. A hankali ta kaɗa kanta tana faɗin "Alhamdulillahi na gode Allah..." Kyakkyawan murmushinsa yay mai kyau daya ƙara bayyana tsantsar kyawu da haibarsa, a hankali ya ɗago kanta daga saman ƙirjinsa yana ƙara kallon kyakkyawar fuskarta dake ƙara dilmiya zuciyarsa a tafkin ƙaunarta. A hankali ya fara matso da fuskarsa kusa da tata a tunaninta ɗan gutun hawayen da suka rage zai share mata, hakan yasa ta saki jikinta, kawai sai ji tayi ya haɗe bakinsu waje ɗaya lokaci ɗaya kuma ya kama tausasan laɓɓanta yana tsotsa a hankali, kana ya saka hannayensa duka biyu ya riƙe ƙugunta ƙam ta yadda bazata iya zamewa a jikinsa ba. Abunka kuma da an daɗe ba'a haɗu ba, sai gashi tun yana yi a hankali a hankali har ya zage yana ta tsotsar bakin nata da zafi zafi yana sauke zafafan numfarfashi haɗi da ajiyar zuciya. Ƙoƙarin ƙwatar kanta take amma ina ta kasa, sai mutsu mutsu take amma yaƙi sakinta, har sai daya gaji dan kansa sannan ya janye bakinsa a nata ya ɗago fuskarsa yana kallon tata fuskar data kwaɓe cikin shagwaɓa da sangarta tana shirin yin kuka. Saurin matsawa gefe tayi tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tana faɗin "Habiby bacci nake ji..." Yana jin haka ya miƙe da sauri yana kallonta cike da tsananin sonta da begenta yace "A'a ki bari sai muci abinci munyi sallah tukunna sai mu kwanta..." Kai Shatu ta girgiza kana kuma cikin sanyin murya tace "A'a na ƙoshi kuma munyi sallahn magriba da isha'i tun ɗazu dasu Basma..." Murmushi kawai yayi ya matso dab da ita ya zura hannunsa ya fara zirya da yatsunsa a wuyanta yana sauke wasu irin tagwayen numfarfashi a hankali cikin kunnenta yana kuma kallon gefen wuyanta inda wasu ƙananun gashi masu laushi suka kwanta luf luf gwanin sha'awa. "Yanzu ki shiga toilet kiyi alwala, idan mukayi sallah muka ci abinci sai mu kwanta..ko ƴan matana...?" Ya faɗa cikin wata iriyar kasalalliyar murya, kana kuma yana ci gaba da shafa wuyanta da yatsunsa. Saurin janye jikinta tayi tana turo baki kafin tace "Ina da alwalata tunda nayi sallar isha'i bata karye ba..." Murmushi yayi kafin yace "A'a shiga dai ki sake wata..dan wannan kam da ƙyar in bata karye ɗin ba..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana ɗan kama gefen kunnenta ya ɗan ciza kaɗan, kana kuma yayi kissing ɗin wuyanta, sannan ya ɗago yana kallonta da idanuwansa da suka koma kamar na mai jin bacci. Bai sake cewa komai ba ya miƙe tsaye ya saka hannayensa ya ɗauketa cak ya ɗagata sama, da sauri ta saka hannayenta ta zagaye bayan wuyansa kana ta kwantar da kanta saman faffaɗan ƙirjinsa tana murmushi. Murmushin shima yayi yana sakar mata kiss a saman idanunta, kafin ya nufi saman bene da ita, ya tura ƙofar haɗaɗɗen bedroom ɗinsu suka ratsa har cikin toilet ya kaita sannan ya direta a gaban fanfo. Kallon kanta tayi ta cikin madubin dake toilet ɗin, a hankali ya matso ta bayanta ya tsaya, kana ya zuro hannuwansa ta saman ƙirjinta ya ƙara matso da ita sosai jikinsa ya haɗa bayanta da ƙirjinsa. A hankali ya saka hannu ya cire mata ƴar siririyar sakar gwal ɗin dake wuyanta tare da kissing ɗin bayan wuyanta da gefe da gefen kunnuwanta, kana kuma a hankali ya saka yatsun hannunsa biyu ya ɗago kanta suna fuskantar juna ta cikin madubin. A hankali kuma cikin murya ƙasa ƙasa yace "Yanzu kiyi alwala sai nima inyi muje muyi sallah ko...?" Gabanta taji ya faɗi, lokaci ɗaya tsoro ya kamata, ganin haka yasa ya ƙara matsowa a kunnenta ya raɗa mata "Kar kiji tsorona kinji...?" Ya faɗa tare da zura hannu ya kunna fanfon, shiru tayi bata ce komai ba. A haka dai sukayi alwalar kana suka fito daga cikin toilet ɗin, yana riƙe da babbar rigar tsadaddiyar farar shaddarsa, ya ɗorata saman makeken gadon daya kusan mayaye ɗakin, sannan ya nufi tafkeken wardrobe ɗin dake ɗakin ya buɗe ya ɗauko mata wani dogon hijabi ya kawo mata, sai data ƙarba ta saka, sannan ya ɗauki darduma ya shimfiɗa musu kana suka daidaita tsaiwarsu cikin natsuwa suka tayar da sallah. Bayan sun sallame yay musu addu'a sannan ya juyo ya kama kanta ya riƙe ya shiga karanto mata addu'a, kamar yadda Annabi S.A.W ya koyar damu. Shatu dai gaba ɗaya gabanta sai faɗuwa yake, dan haka nan take ganin take takensa kamar ba zai ɗaga mata ƙafa ba a yau ɗin. Sai daya gama mata tambayoyi ta bashi cikakkiyar amsa yadda ya dace, sannan ya tashi ya nufi falo yaje ya ɗauko ledojin da suka shigo dasu ya kawo gabanta ya ajiye, kana ya sake sauka ya shiga kichin ya ɗauko filet da kofuna guda biyu ya dawo ɗakin, da kansa ya zuba komai ya matsa kusa da ita ya ajiye. A hankali ya gutsuro naman ya kai bakinta, kasa buɗe bakin tai ta ƙarɓa saboda haka nan kawai take jin fargaba da tsoro sun cika mata zuciya. A haka cikin dabara ya samu ya ciyar da ita da ƙyar, wanda duk da haka bata ci wani abun kirki ba tace ta ƙoshi, ya bata fresh milk itama tasha kaɗan, kana kuma shima ya samu ya ɗan ci naman kaɗan yasha fresh milk ɗin. Bayan sun gama ne kuma Shatu ta miƙe ta shiga toilet ta wanko bakinta ta fito, kana shima ya shiga ya wanko bakinsa ya fito. Shatu idanu ta zuba masa ganin yana ƙoƙarin cire rigar shaddar dake jikinsa. "Meza kayi kuma zaka cire riga...?" Ta tambaya jikinta na tsuma. "Kayan bacci zan saka, kema ki cire naki sai in saka miki..." Ya bata amsa yana ɗan sakin ƙaramin murmushi. Shatu idanunta ta runtse ganin ya cire rigar jikinsa gaba ɗaya surar jikinsa ta bayyana, murmushi yayi ya saka rigar baccinsa kana ya canza wandon shaddar ya saka na bacci, kana ya taka ya isa inda makunnar wutan ɗakin yake ya kashe ya kunna wata kala mai kyau mara haske sosai. Jin motsinsa ta bayanta yana ƙoƙarin cire mata riga yasa tsoro ya ƙara cika mata zuciya. Wata shegiyar rigar bacci mai masifar kyau ya ɗauko ya saka mata wacce bata ɓoye komai na jikinta, luff tai a jikinsa tana ƙara shaƙar daddaɗan ƙamshinsa mai sanyaya zuciya, jin yana ƙoƙarin saka hannunsa cikin rigar baccinta ne yasa ta fara ƙoƙarin zamewa daga jikinsa tana riƙe mai hannu. Jikinsa na rawa ya ɗagata cak ya shimfiɗeta a saman tamfatsetsen gadon baccinsu, daya sha shimfiɗa da wani lallausan zanin gado fari ƙal mai kyau da ɗaukar hankali. Shatu kuwa duk ilahirin jikinta ɓari yake yi, jin Ya Azeez ya rungumeta ƙam ajikinsa ne yana ƙoƙarin cire mata riga yasa ta riƙe masa hannu a tsorace tana girgiza mai kai. Bata gama tsorataba sai da taji yana lasar fuskarta zuwa wuyanta, yana yawo da hannuwansa a sassan jikinta, lokaci ɗaya kuma yana mata raɗa tare da gaya mata kalaman soyayya masu daɗi da kashe jiki. Jikinta banda tsuma babu abinda yake. Baki ta buɗe da zummar magana yayi maza ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Ya dinga wasa da harshensa a cikin bakinta yana mata wata irin tsotsa cikin fitar hayyaci. Shatu banda hawaye ba abinda take, jin irin yadda Ya Azeez yake sarrafata yana juyata ne, ga wani irin wasa da yake da ƙirjinta wanda tun bata jin abun har ta fara jin daɗin yanayin amman tsoro ya hanata ta nuna jin daɗinta a zahiri. A zafafe yake kissing ɗinta yana shafa bayanta sai wani yarrrr yarrr take ji tana jin wani baƙon al'amari na kusantar sabuwar duniyarta, ya jima yana tsotsar bakinta kafin ya janye ya tashi zaune yana ƙoƙarin cire rigar baccin jikinsa, sai daya cire sannan ya koma ya kwanta lokaci ɗaya yana ƙara jawota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayanta tare da jan hannunta ya kai kan fuskarsa yana shafawa a hankali a hankali har ya sauko dashi kan faffaɗan ƙirjinsa da taji babu riga. A hankali ya kai hannunsa yana ɗan shafa gefen fuskarta yana wani lumshe ido, shiru tai tana jin duk abinda yake mata amma bata da ikon hanasa saboda yadda ya gama kashe mata jiki da salonsa, mai cike da tafiyar da tunani. Hakan yasa ta sakar mai jiki sosai saboda tana jin daɗin abubuwan da yake mata, duk a tunaninta kuma iya hakan za'a tsaya sai ta ƙara sakin jiki ta lafe tana karɓan sakwannin da yake aika mata dasu cikin tsantsar kulawa da ƙwarewa. Sai daya gama shagaltar da ita da wasanninsa masu matuƙar tsayawa a zuciya, sannan ya soma ƙoƙarin isar da kansa gareta, cikin shauki haɗe da muradi mai girma. A lokacin ne ta ƙara tsorata ta hau rirriƙesa tana kuka. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lumshe idanuwansa ya kai laɓɓansa saman goshinta ya manna mata wani sassanyan kiss, sannan ya gangaro da bakinsa kusa da kunnenta a hankali cikin murya ƙasa ƙasa sosai ya fara karanto addu'ar saduwa da iyali, kafin tayi wani yunƙurin ceton kanta tuni taji har ya ɗauki hanyarsa cikin hikima da tausasawa, kana kuma a hankali ya ƙara saka bakinsa cikin kunnenta a sanyaye ya soma hura mata iskar bakinsa a kunnenta dan ƙara son ɗauke hankalinta. A hankali ya ƙara gyarawa ya buɗe ƙafafuwanta da kyau, kafin ya sake yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa ya cigaba da neman hanyarsa. Ɗiff tayi tana saurarensa, kafin ta ware idanuwanta da suke a lumshe ta sauke a kansa a hankali tace "Wayyooo Allahna zafiii..." Ko bakinta bata gama rufewa ba ya ƙara ƙanƙameta ya mata riƙo irin na ƙam ƙam ɗin nan, wanda bazaka iya ƙwatar kanka ba, kafin ya ƙara daidaitawa da ƙarfinsa cikin dabara ya samu da ƙyar ya shiga. Ihuuu ta saki da ƙarfi tana faɗin "Dan Allah Ya Abdul na tuba wallahi zafi kasheni zakayi..." Bakinsu ya haɗe yaci gaba da neman hanyarsa har yayi nasarar shiga gaba ɗaya da ƙyar yana haɗa zufa. Duk zantuka da ihun da take bai jinta balle ya tausaya mata, abunka kuma da an daɗe ba'a haɗu ba, ga kuma gyaran da tasha. Cikin natsuwa da wata irin gigitar da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba tunda yake, sosai yake jin wata irin natsuwa da tasha bambam da irin wacce ya saba ji a lokutan baya, tabbas yaji bambanci sosai wanda bai taɓa jin irinsa ba. Ita kuwa Shatu kuka kawai take tana jin tamkar yana yanka mata naman jikinta ne. Shi kuwa ko kaɗan baya jinta banda sambatu da kwasar gara ba abinda yake lokaci mai tsayi ya ɗauka yana juyata yadda ransa yake so kafin ya samu natsuwa ya dawo hayyacinsa. Zuwa lokacin kuwa Shatu tuni ko motsin kirki bata iya yi, hawaye kawai yake tsiyaya a idanunta. Mirginawa yay gefe yana sauke numfarfashi a jere a jere, kafin ya lumshe idanunsa yana faɗin "Allah ya miki albarka na yafe miki duk wani laifi da zakiyi min a duniya, da wanda na sani da wanda ban sani ba daga nan har mu koma ga Allah..na gode na gode Allah yayi miki kyakkyawan sakamako da gidan aljanna fiddausi..." Ya ƙarashe maganar yana buɗe lumsassun idanuwansa ya rungumeta sosai a jikinsa, ganin hawaye suna gangarowa ta gefe da gefen idanunta ne yasa ya ɗago fuskarta yana kallon cikin idanunta wanda sukayi jajir saboda tsabar kukan azabar da tasha. Cikin rawar murya yace "Wayyo nine ko...?" Kai Shatu ta ɗaga cikin shasheƙar kuka kafin tace "Ya Abdul ruwa zansha ƙishi nake ji..." Ta faɗa cikin wata iriyar murya mai cike da rauni. Jikinsa na rawa yace "Ina zuwa..." Ya miƙe da sauri ya sauko daga saman gadon ya ɗauki gajeren wandonsa da sauri ya saka, sannan ya shiga toilet ya haɗa ruwa mai zafi, kana yazo ya ɗauketa cak yaje ya sakata acikin ruwan. Kuka ta Saki tana rirriƙe hannunsa. "Kiyi haƙuri bari na kawo miki ruwan kisha..." Kai ta jinjina tana ciza laɓɓanta. Cikin rawar jiki ya fito, sai a lokacin ne kuma idanunsa suka sauka a saman zanin gadon wanda yake fari tass amma yanzu ya ɗan ɓaci da jini kaɗan. Cikin sauri ya ciresa ya ɗauko wani ya shimfiɗa musu, kana ya naɗe wannan ya koma cikin toilet ɗin ya saka a kwandon wanki, kana ya fito ya sake ficewa daga bedroom ɗin ya sauka ƙasa. Robar ruwan da ya siyo jiya ya ɗauko ya dawo ya tsugunna a gabanta lokaci ɗaya ya tallafo kanta ya manna mata robar ruwan a bakinta. Cikin rawar jiki kuwa ta buɗe bakin ta hau kwankwaɗa tana sauke ajiyar zuciya. Sosai kuwa tasha ruwan fiye da rabi. Cikin tsananin tausayawa da kulawa da kuma nuna tsantsar so da ƙaunarta yay mata wanka haɗe dana tsarki, kana ya naɗota a towel kamar wata ƴar baby yazo ya shiryata tsaf ya kwantar da ita, kana ya manna mata kiss a saman laɓɓanta yace "Ina matuƙar sonki da ƙaunarki Eishatuna, ina zuwa bari inyi wanka nazo kinji..." Bata dai ce mai komai ba, sai turo baki gaba da tayi tana wani lumshe idanunta. Murmushi yay kana ya juya ya koma cikin toilet ɗin, wankan tsarki yayi ya fito ya shafa mai a gurguje kana ya shirya cikin wasu sababbin kayan bacci farare masu taushi da kyau ya fesa turare, ya kashe wuta ya haye saman gadon ya kwanta lokaci ɗaya ya rungumota jikinsa yaja bargo ya lulluɓesu. Lamoo tayi ajikinsa, tana ji yana mata wasu daɗaɗan zantukan soyayya, a haka har wani daddaɗan bacci ya dauketa. Shima daga baya baccin yay cike da nutsuwa yana jin a ransa ba namijin da ya kaisa dace da samun macen data haɗa komai kota ko'ina irin Eishatunsa. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 3️⃣7️⃣ Dai-dai lokacin kuma Fadwa na kwance akan ƴar yaloluwar katifarta. Sosai ta gaji tana son tai bacci amma gaba ɗaya tunanin duniya yayi mata rufdugu ya cunkushe mata zuciya, wanda hakan yasa ta rasa sukuni, sai juyi take tana sakin tsakin takaici, ga kukan sauro duk ya addabeta a ɗakin sai faman cizonta suke kota ko'ina, ta rasa inda zata tsoma ranta taji sanyi. A zafafe ya turo ƙofar ɗakin ya shigo kamar an jefosa, direct inda take ya nufa kai tsaye ya haye saman katifar, kwanciya yayi ya rungumota jikinsa, bai yi wata wata ba kuwa ya hau shasshafata kamar wani mayunwacin zaki yana yi yana wani ƙara ƙanƙameta a jikinsa. Cikin tsananin tashin hankali Fadwa ta zabura lokaci ɗaya tana janye jikinta tace "Dan Allah na roƙeƙa ka barni in huta na gaji wallahi na gaji, gaba ɗaya jikina ciwo yake min, bana jin daɗin komai, dan Allah ka barni inji da guda ɗaya..." Cikin wata mayaudariyar murya yace "Kiyi haƙuri ɗan kaɗan zanyi kawai bazan takura ki ba..." Da sauri tace "A'a nidai dan Allah Ya'u ka ƙyaleni, wallahi bazan iya ba idan kace zakayi mutuwa zanyi na roƙeƙa ka ƙyaleni ba dan halina ba..." Ganin idan ya tsaya roƙonta ɓata masa lokaci zatayi, yasa ya jawota da ƙarfi a zafafe ya fara fizge kayan jikinta kamar mahaukaci. Kokawa suka fara ganin da gaske take bata so ya kusanceta ne yasa ya ɗauketa da mari, kana ya matseta da ƙarfin tsiya bayan ya fizge kayan jikinta ya fara biyawa kansa buƙata cikin tsantsar rashin tausayi da imani, yana yi kuma yana zagin mahaifiyarta babu ko kunya balle tausayi. Sosai Fadwa ke rizgar kuka kamar ranta zai fita wanda duk rashin tausayi da imaninka idan kaji yadda take kukan a wannan lokacin dole saika ji tausayinta, dan kuka ne da take yi da dukkanin zuciyarta, wanda kuma yake fitowa tun daga can ƙasan zuciyarta mai cike da rauni da tsantsar tausayin kanta. Sosai ya ɗauki dogon lokaci a kanta yana aikin abu ɗaya, kafin ya sauka ya koma gefe yana sauke numfarfashi, Fadwa kuwa rakuɓewa tayi gefe guda tana kuka mai cike da rauni da tsantsar tausayin kanta da rayuwarta. Bayan shuɗewar wasu mintuna a tsakani kuma ya sake wawurota cikin tsantsar rashin tausayi ya ƙara haike mata, wannan karon ba tayi masa musu ba ta buɗe masa ƙafafu. Saboda tasan halinsa kota nuna bata so ɗin ba ƙyaleta zaiyi ba, ƙarshe ma sai dai yayi mata rashin mutunci sannan kuma yayi bata isa ta hanasa ba. Dan haka ta ƙyalesa ta zuba masa ido, ya gama bidirinsa ya sauka. Tashi tayi da ƙyar tana dafa bango, zaninta daya yasar a ƙasa ta jawo ta ɗaura kana ta ɗauki buta tana tafiya da ƙyar tana buɗe ƙafafunta a haka ta samu ta fice daga cikin ɗakin ta nufin banɗaki. Tana shiga banɗakin kuwa ta zame ƙasa a hankali ta jingina da jikin bango lokaci ɗaya tana sakin wani maraitaccen kuka mai cike da rauni da tsantsar nadama da tausayawa kai gwanin ban tausayi. Kuka take sosai kamar zata siƙe gaba ɗaya duniyar tayi mata duhu, tunda take bata taɓa tunanin koda wasa zata iya tsintar kanta a irin wannan rayuwar da take ciki a yanzu ba. Tabbas tasan ta aikata babban kuskure a baya, domin kuwa Allah yayi mata ni'imomi masu tarin yawa a rayuwarta amma bata gode masa ba, shiyasa duk iya tarin dukiyarka indai baka da wadatar zuciya bazaka taɓa ganin yawan arzikinka ba sai dai ka hangi na wani, a baya tana cikin jin daɗi da kwanciyar hankali lokacin da take gidan Ya Azeez, amma saboda rashin wadatar zucci irin nata sai ta dinga hange waɗanda suka fita, a ƙarshe ga yadda rayuwa ta maida ita. Yanzu ido rufe take fatan dama ace rayuwar ta baya ta dawo da ta gyara kuskurenta, amma ina tasan bakin alƙalami tuni ya riga daya bushe, amma duk da hakan zata gwada sa'arta saboda tasan Ya Azeez akwaisa da tausayi kila zai dubeta a karo na biyu idan ta nuna masa tayi nadama ya maida ita ɗakinta, dan ba zata iya zama a cikin wannan ƙasƙantacciyar rayuwar ba, insha Allahu sai tasan yadda tayi ta kashe wannan ƙaddararren masifaffen auren ta koma gidan mijinta na asali mai sonta da ƙaunarta tsakani da Allah, saboda yanzu ta gano kuskurenta kuma da ikon Allah zata gyara. A haka tai wankan tsarki ta tsarkake jikinta, tana wannan tunanin bayan ta gama ta fito ta koma ɗaki. Lokacin kuwa tuni Ya'u ya daɗe da yin bacci sai sakin munshari yake, dan haka itama tana shiga ɗakin kawai riga ta saka ta haye katifa ta kwanta tana ci gaba da tunanin neman mafita a ranta. A haka itama baccin ya ɗauketa mai cike da mafarkin rayuwarta a gidan Ya Azeez. ********** Acan ɓangaren su Eishatu da Habibyn ta kuwa. Da asuba ma da ƙyar tai sallah, sai kukan sangarta take masa tana faɗin bayanta da cinyoyinta duk ciwo suke mata, gaba ɗaya ta addabesa da rigimarta, motsi kaɗan sai ta fashe masa da kuka tana zafi cinyoyinta ƙirjinta da bayanta kuma kamar zasu rabe gida biyu, duk ta gigitasa da koke kokenta kamar wata ƙaramar yarinya. Shiko sai lallashinta yake yana lalaɓata, ganin ta kasa sakin jikinta ne yasa yaji tausayinta ya ƙara kamashi, ya jawota jikinsa ya rungumeta yana lallashinta da kalamai masu daɗi da sanyaya rai. Abincin da Mami ta aiko musu ma bata wani ci na kirki ba, sai tea daya haɗa mata shima kaɗan tasha tace ta ƙoshi. Haka ya lalace a gurinta yana ta lalaɓata bini bini kuma yace suje toilet ya gasata, tun tana nonnoƙewa kuwa har ta saki jikinta, shiko ya zage ya dinga gasa mata jiki yana ƙara tarairayarta yana lalaɓata tamkar kwai, ko kaɗan bai son ya matsa daga kusa da ita, duk inda take yana nan naniƙe da ita. Kusan wunin ranar kuwa haka suka kusan cinyesa tana ta zuba mai shagwaɓa da sangarta kala kala. Bai bar gidan ba sai gab da la'asar shima saboda mutanen dake zuwa ganin amarya ne, duk wanda ya ganta kuwa sai yasan tasha kuka domin gaba ɗaya fuskarta da idanuwanta sun nuna, dan ma baƙin duk ƴan uwanta ne, sai Imaan da ƙannen Abban Ya Azeez ɗin ƴan Babura, sai yamma liƙis sannan suka tafi, aka barta dasu Basma da Husna. Kamar kuwa dama jira take baƙin su tafi, ta fashe da kuka ta hau labarta masu Basma irin muguntar da Ya Azeez yay mata daren jiya. Nan fa Basma ta hau tsokanarta tana ta mata dariya, itako Husna gaba ɗaya tausayin ƙawar tata ne ya lulluɓeta, yayinda kuma lokaci guda taji tsoron auren ya cika mata zuciya, wanda har sai da taji kamar tace ta fasa, dan ma tana ganin Suhail ɗinta mai haƙuri ne bai da matsala, tasan zai ɗaga mata ƙafa idan anyi auren. Suna gidan tare da ita har bayan sallar magriba, bayan sunyi sallah ne kuma Basma ta ƙara bata shawarwari kan yadda zata kula da mijinta ta tarairayesa sannan ta ƙara da karfafa mata gwiwa kan tattali da jure duk wasu buƙatunsa. Kafin daga bisani kuma sukayi mata sallama tayo musu rakiya suka tafi kana ta koma cikin gida. Basu daɗe da tafiya ba kuwa shima ya dawo, tana jin motsin shigowarsa ta miƙe da sauri tana yi masa barka da zuwa. Ƙarasowa yayi kusa da ita ya zauna a saman kujera ya jawota jikinsa ya ɗorata akan cinyarsa. "Bari in kawo maka ruwa..." Ta faɗa kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta. Girgiza mata kai yayi alamar a'a, kana ya ƙara kwantar da kanta a jikinsa ya rungumeta. Sun jima a haka tana rungume a jikinsa, kafin ya ɗagota yana kallon kyakkyawar fuskarta dake fitar da wani annurin kyau na musamman, kana ya miƙe da ita a hannunsa suka haura sama zuwa bedroom ɗinsu. Wani irin mummunan faɗuwar gaba taji lokacin daya direta a saman lafiyayyen gadonsu da sauri ta tashi zaune tana gyara rigar leshin dake jikinta, kafin ta ɗago ta kallesa ganin kuma yana tuɓe kayan jikinsa ne yasa ta saukowa daga saman gadon, kai tsaye ta nufi ƙofa da sauri zata fice, cikin zafin nama yayi taku ɗaya ana biyu ya riƙota ya ɗagata cak ya nufi toilet da ita. Duk noƙe noƙenta kuwa haka ta haƙura tana ji tana gani ya cire mata kayan jikinta tas yayi mata wanka da kansa, kana ta ɗauro alwalar sallar isha'i da ta jiyo ana kira ta fito, sannan shima yay nasa wankan ya ɗauro alwalan ya fito. Duk a tsorace take dashi, shiyasa suna idar da sallar isha'in ta haye gado ta kwanta ta ƙudundune a cikin bargo ta juya masa baya. Ganin take takenta ne kuma yasa koda ya hau gadon shima bai taɓata ba, ba dan kuma baya buƙata ba, sai dan kawai yana tausayinta. Itako Shatu a nata ɓangaren gani take wayau kawai yake mata so yake sai tayi bacci sannan ya lallaɓa ya sake maimaitawa, dan haka ko baccin kirki ba tayi ba, sai can cikin dare kafin wani daɗaɗan bacci mai masifar daɗi ya kwasheta. Haka suka kwana bai mata komai ba har gari ya waye, tun daga nan ta ɗan ji sanyi a ranta, har ta saki jikinta, ta ci abincin da Zahra ta kawo musu washegari da safe. Sosai ta saki jiki taci ta ƙoshi abinta, suna gamawa ya goge mata baki kana ya riƙe hannunta suka dawo cikin falo ya zauna, kana ya zaunar da ita a kusa dashi. A hankali ta ɗaga kai ta kallesa ganin shima ita yake kallo yasa ta sunkuyar da kanta da sauri tana murmushi. Sake ɗago kanta yayi ya matso da ita kusa dashi yana faɗin "Ina matuƙar sonki da ƙaunarki Eishatuna..." Murmushi tai ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke ajiyar zuciya. Shafa bayanta yayi yana murmushin shima, kafin ya ɗagota yana tsura mata idanu yace "Allah yayi miki albarka, yasa mu rayu tare har ƙarshen rayuwar mu..mai daɗina..." Ya faɗa a kunnenta cikin raɗa yana ƙara ƙanƙameta. Ranar wuni sukayi tun safe har dare yana naniƙe da ita kamar wanda akace za'a ƙwace masa ita, wanda kuma ko toilet zata shiga tare suke shiga, bai yarda ta matsa ko nan da nan. A hankali a hankali yanayin ya fara bin jikinta, kafin sati ya kai idan zata zauna sai dai a kusa dashi ko akan cinyarsa, haka a wajen bacci sai ya ƙanƙameta sannan yake iya runtsawa. Wanda kuma zuwa lokacin tuni ta gama sabawa da yanayinsa, tun tana ɗan jin zafi sama sama har ta dawo yanzu bata jin komai sai daɗi, dan haka ta ƙara sakewa dashi sosai ta saki jikinta. Bayan sati ɗaya ya canza mata sabon layi ya canza mata waya, ya saka mata numbern Umma data Imaan. Aiko tun da ya bata numbern kusan kullum da safe sai ta kira Umman sun gaisa, haka Imaan itama koda yaushe sai sunyi waya da ita. Satinta biyu a gidan kuma Ya Azeez ya ɗauketa daddare ya kaita gidansu Fahad ta gaishe da Mami da Abba. Nasiha sosai Mami tai mata, haka Abba shima yayi mata nasiha sosai sannan yace ta bi mijinta sau da ƙafa. Daga nan kuma direct sashen Fahad kuma suka shiga, inda suka daɗe suna hira da Basma wacce Shatu tai mamaki sosai da ta ganta da ciki wanda har ya fara girma ya fito sosai, dan ya kai kusan wata huɗu zuwa biyar, amma bata taɓa lura ba. Nan ma sun daɗe, da suka tashi tafiya kuma Basma ta bata turarukan humra masu ƙamshi da sinadari tace ta dinga amfani dasu. Sai wajen ƙarfe 11pm. Suka baro gidan inda kuma a hanya suna tafiya yake sanar da ita cewa cikin satin da za'a shiga zasu Kaduna su gaishe dasu Umma. Wanda saboda tsabar murna bata san sanda ta ruƙunƙumesa ta sakar mai zazzafan kiss a laɓɓansa ba. Washegari kuma gidansu ya kaita da kansa ta wuni inda Ummi tai ta nan nan da ita tana riritata, abinci kuwa an dafa mata ya kai kusan kala biyar idan taci wannan sai taci wannan. Ganin haka kuma yasa Zahra tace itama zata gayawa Abba ta gaji da karatun a fitar mata da miji tayi aurenta itama ta huta taji abinda ake ji. Dan tunda taga yadda Aunty Shatun ta tai wani irin fresh ta ƙara kyau sosai tasan ba ƙaramin daɗi take ji a gurin Ya Abdul ɗinta ba, dan haka itama auren nan zatayi hankalinta kwance ta huta abunta. Shatu da Ummi sukayi ta mata dariya, inda kuma anan Ummi ta dinga yiwa Shatun nasihar kula da miji da irin abubuwan da ya kamata ta dinga yi masa da wanda basu kamata ba. Sosai Shatu ta ƙaru da abubuwa da dama a gurin Ummi, wanda har ji tayi ta ƙosa Ya Azeez ɗinta yazo ya ɗauketa suje gida ta fara gwada masa abubuwan da Ummin ta koyar da ita a ranar. Sai dare sannan Ya Azeez ɗin yazo gidan ya ɗauketa suka koma gida. A ranar kuwa Shatu kusan zautar da Ya Azeez tayi da salonta, domin gaba ɗaya susuce mata yayi ya dinga sambatu da sakin layi yana saka mata albarka. Itama kuma sosai taji daɗin yanayin duk da tasha wuya sosai a hannunsa, amma haka nan ta daure ta gwada masa jarumtarta, hakan kuwa shima sosai yanayin yayi masa daɗi, ya kuma sa ya ƙara ganin kima da mutuncinta na ƙara hauhawa a idanunsa. Bayan Sati Biyu Zaune suke a falo ya kanainayeta a jikinsa tana ta zuba mai shagwaɓa, hannunsa ya zura cikin rigarta yana shafar cikinta a hankali yana faɗin "Ina ne yake zafin..nan ne..ko nan...?" Ya faɗa cikin wani irin yanayi yana shafo ƙasan mararta haɗi da ɗan dannawa kaɗan. Saurin riƙe hannunsa tayi tana faɗin "Wayyo Habiby akwai zafiiii..." Ta faɗa cikin sangarta tana janye hannunsa daga gurin. Kumatunta yaja a hankali yana faɗin "Ina ne yake zafin to, nuna min...?" Hannunsa ta kama ta kai dai-dai kan mararta ta ɗora tana ɗan shafawa a hankali a hankali. "Nan ne...?" Ya faɗa tare da saka yatsunsa biyu ya danna gurin da ɗan ƙarfi. Wata irin zabuwa tayi ta ƙara ƙanƙamesa kafin a shagwaɓe tace "Wayyo Habiby nan ne..." Yace "Ayya sorry..." Ya faɗa yana sake danna cikin a hankali, kafin kuma ya ɗago kai ya kalleta yace "Nan ma yana zafin...?" Shagwaɓe fuskarta tayi ta gyaɗa mai kai, sai kuma ta rufe idanunta tana dariya. Hannuwanta duka biyu ya kamo ya sumbacesu, kafin ya tashi ya miƙar da ita tsaye yaja hannunta suka nufi dinning table. Da kansa yaja kujera ya zauna, kana ya zaunar da ita saman cinyarsa ta zauna ta zuba musu abincin, shi ya dinga bata da kansa tana ci, kana itama ta dinga bashi a baki yana ci, a haka dai suka ciyar da junansu har suka ƙoshi. Koda suka gama kuwa kayan ta kwashe ta kai kichin, sai data wanke ta maida komai ma'ajiyarsa sannan kuma ta fara ƙoƙarin ɗora girkin dare. A daren kuma sukaje wata babbar super market suka yowa Umma da Imaan siyayyan kaya masu yawa kala kala, kana ta haɗawa Imaan dasu chocolate da biscuits har dasu sweet da cingum kayan ƙwalama dai iri iri ta haɗa mata. Sosai dai sukayi siyayya mai yawa kana suka dawo gida. Washegari kuwa tunda sassafe ta gama haɗa musu breakfast, bayan sun ci ne kuma ta wanke kwanukan kafin suka haye sama suka shiga toilet suka sake sabon wanka. Koda suka fito kuwa shiryawa sukayi cikin wasu tsadaddun kaya masu matuƙar kyau da tsada, inda Ya Azeez ɗin ke sanye da wata haɗaɗɗiyar shadda mai tsada ruwan sararin samaniya, yayinda kuma Shatu ke sanye da wani tsadadden leshi ja sai gyale da jaka da takalminta kuma suma duka kalar sararin samaniya ne. Sosai shigar tayi mata masifar kyau ba kaɗan ba, kayan dake jikinta kaɗai sun isa su sakata tayi kyau balle kuma kwalliyar da tasha kamar wacce zata tafi gurin gasar sarauniyar kyau ta Nigeria. Yana zaune a falon ƙasa yana waya da Fahad, ta soma saukowa a hankali yayinda kuma takalmin ƙafarta ke bada wani irin sautin ƙwaras ƙwas ƙwas, ɗagowa yayi da sauri yana kallonta, kafin ya miƙe da hanzari yana faɗin "Ina zuwa Fahad zan kiraka..." Ya faɗa tare da katse wayar lokaci ɗaya yana tsura mata idanu cike da zallar so da ƙaunarta, domin kusan kullum gani yake kamar ana ƙara mata kyau ne. A hankali ya furta "Masha Allah Eishatunaaa kin ganki kuwa..? Gaskiya kinyi kyau sosai tubarakallah Masha Allah..." Murmushi tayi kafin ta ƙarasa saukowa har ya ƙaraso gabanta ya riƙo hannuwanta duka biyu lokaci ɗaya ya jawota jikinsa ya ƙanƙameta yana juyawa da ita a tsakiyar falon. "Zautani zakiyi da salonki ƴan matana, ina matuƙar ƙaunarki ina sonki..ina sonki..ina sonki..." Ya ƙarashe maganar yana ƙara ƙanƙameta ajikinsa ƙam yana juyi da ita. Itama ƙanƙamesan tayi tana faɗin "Nima ina sonka ina sonka ina sonka masoyina..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ɗago kai ta haɗe bakinsa da nata waje ɗaya ta shiga bashi wata irin salon tsotsa mai matuƙar ɗaukar hankali da gusar da tunani. Sai data tsotsi bakinsa iya son ranta kafin ta janye ta sauka daga jikinsa ta rungumesa tana wani irin shafa gefen wuyansa. "Muje Habiby wallahi duk na ƙosa mu isa inga Umma..." Ta faɗa tare da sumbatar kumatunsa. To yace, kana ya ɗauketa cak suka fice daga cikin falon. Sai daya sakata a cikin mota ya rufe, kana ya dawo ya kashe wutar falon ya kukkulle ko'ina, sannan ya dawo ya shiga motar direbansa ya kunna bayan yayi horn maigadi ya wangale musu tangamemen ƙofar gate ɗin ya silala motar suka fice daga cikin gidan gaba ɗaya. Koda suka isa airport ɗin kuwa direban ajiye su yayi ya dawo da motar gida. Ƙarfe 10am. Dai-dai kuwa jirginsu ya ɗaga zuwa Kaduna, suna sauka acan kuma direban Umma yazo ya ɗaukesu zuwa gidan Umman. Zo kaga nuna ƙauna gurin Umma, kamar zata haɗiye Shatu saboda tsabar murna da farin cikin ganinsu. Sai mamaki take yadda taga Ya Azeez ya canza cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙara wani kyau da haske na musamman. Imaan ma tana ta murnar ganin yayanta da matarsa da take ji tamkar ta maida ita cikinta saboda son da take mata. Sai yamma sannan suka sake yin wanka suka shirya cikin wasu tsadaddun kayan da har sukafi wanda suka zo dasu ajikinsu kyau da tsada, dan Ya Azeez kam duk wanda ya gansa indai ba kyakkyawan sani yayi masa ba da wuya zai ganesa lokaci guda, saboda tsantsar kyau da kwarjinin da kayan sukayi masa. Har da Imaan direban Umma ya ɗaukesu zuwa unguwar Mu'azu gidansu Fadwa. Dai-dai ƙofar gidan Abban Ya Azeez ya nunawa direban yace ya tsaya. Sannan a hankali ya buɗe motar ya fito kana ya zagaya ɗaya ɓangaren ya buɗewa Shatu itama ta fito, Imaan ma dake kusa da direba ta buɗe itama ta fito. Nan suka bar direban a cikin motar yana jiransu suka nufi hanyar da zata sada su da shiga cikin gidan, Imaan da Shatu na riƙe da ledojin tsarabar turaruka da manyan shaddojin da suka yowa Abban a hannayensu. Cikin zauren gidan ya tsaya ya kira Abba yana sanar dashi cewa sun iso suna gidan, yayinda kuma Shatu da Imaan kai tsaye suka nufi cikin gidan bakunansu ɗauke da sallama suka shiga. Fadwa da zuwanta kenan tana zaune a ƙofar ɗakin Mama tana cin wake da shinkafan da Maman ta dafa ta zubo mata, wanda kuma tunda aka ɗaura mata aure da Ya'u mai kifi, yau ce rana ta farko daya taɓa barinta fita har tazo gidan, shima kuma sai data haɗa masa da ƙaryar cewa Abbanta ne bashi da lafiya shine ya yarda tazo ta gaishesa, har da bata ɗari biyu yace ta siyan mai lemu da ayaba ta tafi mai dashi, wanda ɗari biyun ma da ita tai kuɗin mota tazo gidan. A yunwace take cin abincin, domin rabon da taci abinci mai daɗi irin haka tun ranar bikinta da Ya'u mai kifi. Ta ɗago da nufin kai kofin ruwa bakinta ne kuma idanuwanta suka sauka cikin na Shatu da Imaan da suke tsaye a tsakar gidan hannayensu riƙe da manyan ledoji suna kallonta. Ganin kallon da suke mata ne yasa a kunyace ta dire kofin ruwan ta miƙe tana janye kwanon abincin gefe tace "A'a Imaan kune..? Sannunku da zuwa ku ƙaraso ciki mana..." Ta faɗa cikin rawar jiki tana tsallake abincin ta shiga ɗakin Mama ta ɗauko musu sabuwar darduma tazo ta shimfiɗa musu tace su zauna, kafin ta fice da hanzari ta nufi kichin ta kira Mama suka dawo cikin ɗakin atare. "A'a Imam ashe dai ke ɗin ce da gaske..to sannunku da zuwa sannunku..ke Fadwa ungo ki siyo musu ruwa mai sanyi maza..." Maman ta faɗa cikin rawar jiki tana miƙawa Fadwa hamsin ɗin dake hannunta, wanda kuma a dai-dai lokacin ne Ya Azeez da Abba suka shigo cikin gidan. Miƙewa Fadwa tai zata fice da sauri Imaan ta dakatar da ita tana faɗin "A'a Aunty Fadwa ki barshi, wallahi Mama daga gida muke sai da muka ci abinci muka sha ruwa kafin mu fito..." Rausayar da kai Mama tayi tana faɗin "Ko dai anan ɗin ne baki son kusha ɗin ko...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon suturar jikinta tana mamakin sauyawar da Imaan ɗin tayi cikin lokaci ƙanƙani da bata ganta ba. Imaan ta buɗe baki kenan zatayi magana Abba da Ya Azeez suka sako kansu cikin ɗakin yayinda Abba ke gaba Ya Azeez kuma na biye dashi a baya. Wani mummunan faɗuwa gaban Fadwa yayi jin daddaɗar muryar Ya Azeez ɗinta ne ke sallama, Mama kuwa daɓas ta koma ta zauna a tsakar ɗakin tana kallon Abba da bakinsa ya kasa rufuwa saboda tsabar murna da farin cikin ganinsu Ya Azeez ɗin. Cikin rawar murya data jiki kuwa Mama ta hau inda inda tana nuna Ya Azeez cikin tsantsar mamaki tana faɗin "Wane..ne wann..an nake gani kamar AbdulAzeez, kai anya kuwa shine ko dai ɗan wanda ka kewa tsaron shago ne kasuwa Abban Fadwa...?" Ta faɗa cikin tsananin mamaki da al'ajabi tana kallon Abba daya kamo hannun Ya Azeez ɗin ya zaunar dashi kusa da Shatu da tunda ya shigo ta ɗago kai tana kallonsa suna aikawa juna da wani sihirtaccen kallon tsantsar ƙauna da soyayya kana suna sakarwa junansu kyakkyawan murmushi mai tsayawa a zuciya. Kallonta Abba yayi, kana ya juya ya kalli Ya Azeez daya ɗan jingina da jikin Shatu kaɗan yana yi mata raɗa a kunne, kafin yace "Ɗana ne AbdulAzeez dai kike gani..." Wani irin zaro idanuwa Mama da Fadwa sukayi a tare suka kalli Abban kafin kuma suka juya suna kallon Ya Azeez wanda gaba ɗaya hankalinsa baya kansu, yana can duniyar shaƙar daddaɗan ƙamshi matarsa yana wani lumshe idanu cike da tsantsar ƙaunarta. Tsura masa idanu Fadwa tayi tana ƙare masa kallo, kafin kuma ta ware ido sosai tana faɗin "Wallahi Mama Ya Azeez ɗina ne, shine wallahi..." "Shine fa kikace Fadwa...?" Mama ta tambaya tana wani zaro idanuwa waje, kamar wacce taga wani abun tsoro. Jinjina mata kai Fadwa tayi tana faɗin "Wallahi tallahi Mama Ya Azeez ne ya dawo, kiyi addu'a Allah yasa maidani ya dawo yayi ɗakina wallahi Mama komawa zanyi bazan koma gidan Ya'u ba..." Fadwa ta faɗa cikin fitar hayyaci tana kallon Mama data wani tsaya ƙam ta saki baki galala tana faman kallon Ya Azeez kamar mai son gano wani abu a cikin jikinsa. Ganin irin kallon da Maman ke masa ne yasa ya ɗago kai ya kalleta, kafin kuma cikin sanyin muryarsa yace "Mama ina wuni mun sameku lafiya...?" Da sauri Fadwa ta fito da idanu waje tana kallonsa, dan ita da kanta sai yanzu ne take ƙara tabbatar da cewa Ya Azeez ɗinta ne dai data sani, tabbas shine zaune a gabanta ba ƙarya ba, kuma ba gizo idanuwanta suke mata ba. *Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲* [12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI* *Wattpad: Aishaalto09* 3️⃣8️⃣ "AbdulAzeez kai ne dai da gaske, Fadwa duba dai da kyau ki gani, anya kuwa ba idanuwanku bane suke yi muku gizo...?" Mama ta faɗa lokaci ɗaya tana nunashi jikinta na tsuma, ji take abun kamar a mafarki wai AbdulAzeez ne haka a gabanta cikin kyakkyawar shiga wacce kana gani kuma kasan kuɗi sun gama zauna masa, ga jikinsa yay wani irin lukwi lukwi tamkar na jinjirai, gaba ɗayansa ya koma wani hamshaƙi na musamman. Yunƙurawa tai zata tashi amma tsantsar kaɗuwa da mamakin abinda take gani ya hanata samun karshashin hakan, kawai sai ta koma daɓas ta zauna a ƙasa tana zare ido. Abba dai guri ya samu ya zauna shima yana ta kallon Mama dake ta kaɗa kai tana faɗin "Ikon Allah ni kaga Imaan kaɗai na gane tsaf, amma kai ko kaɗan ban ganeka ba, dan wannan ma ni ban taɓa ganinta ba, ko ƴar uwar Ummanku ce...?" Girgiza mata kai Ya Azeez yayi yana murmushi kafin yace "A'a matata ce sunanta Aisha..." "Matarka...?" Fadwa da Mama suka haɗa baki gurin faɗa a tare suna kallon Shatu data sunkuyar da kai ƙasa tana murmushi. Jinjina kai Imaan tayi kafin tace "Eh Mama matarsa ce yau suka zo daga Kano..." Imaan ta faɗa tana kallon Ya Azeez ɗin da Shatu tana murmushi, girgiza kai Mama tayi tana kallonsu kafin ta gyaɗa kai tana faɗin "Ikon Allah! Lallai arzikin bawa na tare dashi, kuma hausawa sunyi gaskiya ɗan hakkin daka raina wata rana shi zai tsole maka idanu, wallahi yanzu kam na yarda da maganar nan gaskiya ce na yarda, yanzu AbdulAzeez kai ne haka kuma wannan matarka ce...?" Ta faɗa cikin kuka tana kallon Abba da yay zaune ya zubo mata idanu yana kallonta. Wata iriyar mummunar bugawa zuciyar Fadwa tai, yayinda lokaci ɗaya kuma taji wani abu mai tauri ya sarƙe mata maƙoshi yana barazana da numfashinta, zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata tamkar wacce ake hurawa wuta. Idanu kawai ta zubawa Shatun tana kallonta tun daga kan kyakkyawar fuskarta kuwa har zuwa kan tsadaddiyar suturar dake jikinta da wayar dake hannunta, haka take binta da kallo har kan babban ɗan yatsar ƙafarta sosai take ƙare mata kallo. Kafin kuma a hankali ta mayar da idanuwanta gam ta rufe tana jin taruwa wasu azababbun hawaye masu matuƙar raɗaɗi da ƙunar zuciya na tsiyayowa daga cikin idanunta. Tabbas yanzu kam Ya Azeez yayi mata nisa, nisan da ko anyi kiransa ma bazai taɓa jiyowa ba ballantana ya amsa, kuma ganin Shatu a matsayin matarsa kaɗai ya isheta babban darasi, domin ita kanta ta sani ko da gami bazata haɗa kanta da ita ba, balle kuma tayi tunanin zata so haɗa matsayinta da nata. Dan haka bazata taɓa raudarar kanta da zuciyarta ba dole tayi ƙoƙarin goge mafarkinta na son komawarta gidan Ya Azeez, domin ita kanta ta sani wutsiyar raƙumi ta riga da tayi nesa da ƙasa, dole tayi haƙuri ta fuskanci rayuwarta ta yanzu. Wani irin bugawa Shatu taji zuciyarta tayi, saboda ita sai a yanzu ne ma take tunawa da labarin Fadwa da Mamanta da Ya Azeez ɗin ya taɓa bata. Ganin kuma irin kallon da Fadwan ke mata ne yasa ta ɗago kai ta watsa mata harara kana ta saki tsaki ƙasa ƙasa, tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, yayinda a kuma gefe guda na zuciyarta take mitar Allah ya gani da tasan cewa idan suka zo zasu samu wannan abar a gidan da babu abinda zaisa ta yarda mijinta yazo, saboda ita in ba dole bama bata yadda za'ayi Fadwa ta ƙara ganin mijinta koda ko akan hanya ne sai dai ko a hoto, shima a hoton inda hali sai ta gogesa a inda tasan zata iya gani ɗin. Shiko Abba gyara zamansa yayi lokaci ɗaya yana bin kowa da kallo kafin kuma ya maida kallonsa kan Fadwa da har lokacin take ta kallon Shatu kamar zata haɗiyeta yace "Kunga dai hukuncin Ubangiji ko...?" Ya faɗa tare da juyawa lokaci ɗaya ya kalli Mama data zafga uban tagumi ta tsurawa Ya Azeez da Shatu idanu tana tsiyayar hawaye, kafin ya ci gaba da cewa "Dama haka Allah ke ikonsa ya kuma wanzar da lamarinsa yanda yaga dama babu kuma mai ce masa a'a, shiyasa hausawa ke cewa duk abinda ya baka tausayi wata rana shi zai baka mamaki, haka kuma duk abinda ya baka mamaki wata rana zai baka tsoro. To kunga dai yadda Allah ya juya lamarinsa akan AbdulAzeez a lokacin da baku taɓa zato ko tsammani ba, shiyasa akeso duk halin da kaga bawa a ciki walau daɗi ko akasinsa karka taɓa tunanin zai ɗore masa, domin shi daɗi baya taɓa ɗorewa haka wuya ma duk tsananin da zaka tsinci kanka a cikinta akwai lokacin da Allah zai kawo maka ɗauki ya yaye maka halin ƙunci da baƙin cikin da kake ciki..dan haka karka sake kaga wani a cikin wata matsala ko wani mummunan yanayi kayi zaton zai ɗore a cikinsa har abada, domin duk wanda kika gani a duniyar nan Allah yasan da zamansa, haka kuma duk a halin ƙunci da baƙin cikin da mutum zai tsinci kansa a ciki to akwai ranar da komai zai wuce har ya zamo kamar bai taɓa faruwa ba. Kai dai ka riƙe Allah kawai ako wane irin hali zaka tsinci kanka aciki, ka kuma saka a ranka cewa shine yake badawa a duk lokacin da yaso ya kuma kwace a lokacin da yaga dama, kuma babu wanda ya isa ya tuhumesa don me...saboda haka idan har ka kaɗaita Allah ka kuma riƙe wannan to tabbas zaka zauna lafiya a duniya babu abinda zai dameka..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana kallon Mama da Fadwa da tunda ya fara maganar hawaye ke faman zubo musu babu ƙaƙƙautawa. Girgiza kai kawai yayi kafin ya ci gaba da faɗin "Tun lokacin da kuka dinga nuna ƙiyayarku ƙarara akan AbdulAzeez da halin daya tsinci kansa a ciki nake ta son nusar daku amma kuka nuna min kunyi nisa, bazaku taɓa jin kirana ba. Wanda kuma a lokacin so nayi in tunasar daku sannan in tuna muku abinda kuka manta, amma kuka nuna min ni bansan komai ba, dan haka bazaku taɓa saurarata ba, shiyasa daga ƙarshe nima na ƙyaleku kawai na zuba muku idanu, gashi kuma yanzu wa gari ya waya...?" Ya tambayesu fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallonsu. Bai kuma basu zarafin magana ya ci gaba da faɗin "Lokaci guda dukkanku kuka nuna kun manta taimakon da mahaifinsa yay muku lokacin da yake raye, sannan kuka rufe idanuwanka kuka nuna tamkar baku taɓa saninsa ba a rayuwarku, alhali ku kanku kun sani mahaifinsa yayi mana komai a rayuwa, amma daga baya da Allah ya jarrabesa sai kuka shafe komai kuka manta da duk abubuwan da suka faru a baya, sannan kuka rufe idanuwanku ku a dole kanku kawai kuka sani baku san kowa ba..." Sai ya girgiza kai kana kuma ya cigaba da faɗin "Sai gashi da yake shi Allah ba azzalumin sarki bane sai dai kai ka zalunci kanka, cikin lokaci ƙanƙani ya juya duk wasu al'amura ta yadda baku taɓa zato ko tunanin zasu kasance ba..." Nan ya fara basu labarin abubuwan da suka faru tun daga kan komawar Ya Azeez Kano da zama, da fara kasuwancinsa zuwa shagunan daya buɗe masa anan garin Kaduna da motar da ya siya masa, da farkon haɗuwarsa da Shatu har zuwa aurensu babu abinda ya ɓoye musu, sai gashi tun Mama na zaune har ta koma jikin bango ta jingina tana sauraren Abba. Fadwa kuwa sai kuka take har da shassheƙa, Imaan ko ta rafka uban tagumi tana ta kallonta. Ya Azeez da Shatu kuwa ido kawai suka tsura musu suna ta kallonsu. Har ya kai ƙarshe Mama da Fadwa kuwa kuka suke tamkar ransu zai fita. Abba kuwa share hawayen da suka cika masa idanu yayi, kana ya ci gaba da faɗin "Cikin hukunci da buyawar Ubangiji sai gashi Allah ya dubi zuciyarsa da maraicinsa, da kuma kyawawan halayensa na kirki ya buɗe masa kaɗan daga falalarsa da rahamarsa lokaci guda ya mayar dashi abun kwatance ta yadda wani daga cikin mu bai taɓa zato ba balle tsammani. Shiyasa ko a baya lokacin da abubuwan suka dinga faruwa nayi ta ƙoƙarin inga na fahimtar daku kun gane amma ina sam kuka ƙi saurarata, shiyasa na ƙyaleku duniya ta fahimtar daku ta kuma bi daku ta yarda zaku fi ganewa, sai kuwa gashi cikin hukuncin Ubangiji duk abinda kuke zaton kuma bashi ɗin ne ya faru a kanku ba, sai wanda baku taɓa zato da tsammanin ba shine ya farun. Kunga wannan shine hukunci Ubangiji Buwayi gagara misali wanda ba'ayi masa dole..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana share hawayen dake ƙara taruwa a cikin idanunsa. Cikin kukan nadama da tsantsar danasani Mama tace "Na roƙeƙa ka yafe min AbdulAzeez nayi nadamar abinda na aikata maka, ban kyautawa kaina ba..tabbas idan na mutu da irin halin nan sai Allah ya hukuntani, domin na kasance cikin mutane masu saurin manta alkhairi a rayuwarsu, ban kyautawa kaina ba, nayi nadamar butulcin da nayi a rayuwata..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara fashewa da wani kuka mai ƙarfi da nadamar abinda ta aikata, dan dama tunda akai auren Fadwa taga yadda abubuwa duk suka runcaɓe musu cikin lokaci ƙanƙani, tun daga nan ta tsorata da lamarin duniya, shiyasa duk ta watsar da komai take kuma ƙoƙarin daidaita al'amuranta da zamantakewarta da kowa a yanzu. A hankali kuma cikin rauni da sanyin murya itama Fadwa tace "Wallahi ban taɓa jin nadama da danasani a rayuwata ba irin na yau Abba, nayi baƙin cikin kasancewata a raye har na tsawon wannan lokacin da zanga tashin hankalin abubuwa iri iri waɗanda ban taɓa tsammatan zan fuskancesu ba a rayuwata, na tafka babban kuskure a rayuwata nayi kuskure Ya Azeez na roƙeƙa ka yafe min ba dan halina ba dan Allah..." Ta faɗa tare da rushewa da wani irin kuka gwanin ban tausayi, domin a lokaci guda ta ji gaba ɗaya komai ya tsaya mata cak, saboda ko a lokacin da aka kaita gidan Ya'u mai kifi bata ji zafi da raɗaɗin baƙin cikin da take ji yanzu a zuciyarta ba, gabaki ɗaya duniyar tayi mata duhu dinɗim lokaci ɗaya sai abun ya zame mata biyu kukan zuci dana fili, domin tasan yanzu Ya Azeez yayi mata nisa ta rasashi kenan har abada, ga kuma zama da mugun mutumin da Allah ya haɗata dashi a yanzu. Ya Azeez kuwa jin abinda Fadwan ta faɗa ne yasa shi juyawa a hankali ya sauke idanunsa akanta, wanda kuma tunda ya zauna ɗin sai yanzu ne ya kalli inda take. Sosai yay mamakin ganin yadda ta koma, duk ta rame ta wani ƙarmashe, sai ɗan wuya bakinta kuwa duk ya bushe, ga wasu koɗaɗɗun kaya da take sanye dasu a jikinta duk sun soshe, gaba ɗaya ta zama abar tausayi. A hankali kuma ya janye kallonsa daga kanta, tare da runtse idanunsa kana cikin nuna tsantsar tausayi da kulawa yace "Ki bar faɗin haka Fadwa, komai daya faru dama tuni Allah ya ƙaddara hakan sai ta faru, dan haka ni ban riƙeku a zuciyata ba. Na daɗe da manta komai daya faru ya wuce..." Ya faɗa yana ƙara riƙe hannun Shatu dake cikin nasa yana ɗan murzawa a hankali. Cikin tsananin jin daɗin maganarsa Abba yace "Allah yayi maka albarka, Allah yasa ka rabu da mahaifiyarka lafiya, Allah ya albarkaci rayuwar aurenka ya baku zuri'a ɗayyiba..." Da sauri Mama ta amsa da Ameen ya Rabbi, kana kuma ta ɗora da faɗin "Kaga dai yadda duniya ta mayar damu AbdulAzeez..ni na dinga uzzurawa Fadwa na dinga goyon bayan ƙinka da take, ina ƙara ƙarfafa mata ƙiyayarka a zuciyarta na dinga bata shawarwarin banza da wofi, sai gashi duk fatan sharrin da nake binka dashi ya ƙare akaina da ƴata, kai kuma kana cikin alkhairi, gashi kuma duk da haka ban isa hana abinda Allah yaso ba, yanzu ga ijabar Ubangiji nan ina gani akan Fadwa. Dama kuma duk wanda za'a yiwa hassada ko a cutar dashi to zaiyi ta samun cigaba ne a rayuwarsa, kuma zai ga ribar haƙuri tun a duniya kafin kuma ya iske ladan lahira..." Abba yace "Allah yasa mudace..." Dukkansu suka amsa da Ameen, kana daga haka kuma suka cigaba da hira har zuwa wani lokaci, kamar wani abu bai taɓa haɗasu ba, suna gidan kuma har lokacin dawowar su Ilham da Amatullah daga makarantar islamiyya yayi suka dawo. Koda suka ga Ya Azeez kuwa suma sunyi matuƙar mamaki sosai, dan Ilham har da kukan farin ciki sai da tayi. Suna gidan kuwa har bayan sallah isha'i, bayan Abba da Ya Azeez sun dawo daga masallaci ne kuma Ya Azeez ɗin yace Shatu da Imaan su tashi su tafi, amma Abba ya hana yace sai an gama abinci sunci kafin su tafi, dan haka babu yadda Ya Azeez ya iya ya koma ya zauna suka ci gaba da hirar yadda abubuwa suka kasance musu, inda anan ne kuma Abban ke labarta musu yadda auren Fadwa da Ya'u mai kifi ya kasance. Wanda kuma zuwa lokacin tuni Abban ya kora Fadwa yace ta tafi gida kar mijinta ya koma gidan ya iske bata dawo ba, haka nan kuma ba dan taso ba ta tashi ta tafi, dan ɗan zaman da sukayi da Shatu kuwa har taji Fadwan ta shiga ranta, dan haka koda ta tashi tafiya Shatu da Imaan dasu Ilham ne suka rakata har soron gidan, sai bayan da Fadwan ta wuce ne kuma Shatun taba Ilham kuɗi da zasu haura dubu hamsin tace ta kaiwa Fadwan gida ta fara sana'a. Sosai Abba da Mama sukai tai mata godiya, dan Mama kam har da kwallar murna sai da tayi. Koda suka tashi tafiya kuwa Ya Azeez kayan daya kawowa Abba ya bashi, ita kuma Mama ya bata kuɗi masu yawa kana kuma ya ba su Ilham suma yace su siya kayan kwalliya su kuma sake uniform ɗin islamiyyarsu. Suna gidan har kusan ƙarfe 9:30pm. Sannan bayan Mama ta gama girki sunci sun ƙoshi sukayi musu sallama Abba yana ta saka masa albarka yana masa addu'a har da kwallarsa, dan har lokacin idan ya tuna ya kan ji baƙin cikin rabuwar Ya Azeez da Fadwa, dan dai babu yadda zaiyi ne kawai dole sai haƙuri. Koda suka koma gidan Umma kuwa, Ya Azeez sashensa dake gidan ya buɗe shida Shatunsa suka shige, dan dama sai fargaba yake kar Shatun tace zata kwana a ɓangaren Umma, sai gashi kuwa ba tayi musu ba ta biyosa sukayi kwanciyarsu abinsu. Washegari kuwa Ya Azeez tunda wuri ya fita shida direban Umma, suka shiga cikin gari suka haɗo kayan abinci masu yawa ya aika direban da kayan da kuɗi aka kai can unguwar Mu'azu gidan Abba, sannan kuma ya kira Abban a waya ya gaya masa a ɗebi kayan abincin da kuɗin daya aiko direban dashi a haɗa duka a kaiwa Fadwa. Kwanansu biyu a garin kuma Shatu ta matsawa Ya Azeez yasa direba ya kaita gidan Fadwan, karku so kuga yadda Fadwa tai murna da ganin Shatun. Can ta wuni ranar sai dare sannan Ya Azeez ɗin sukaje da direba suka ɗaukota suka dawo gida. Da daddaren ranar kuwa Shatu da zazzaɓi mai tsanani ta kwana, sai faman kuka take tana ta nuƙurƙusarsa, ko kanta bata iya ɗagawa saboda tsabar zafin da jikinta yay mata, sai da yaje ɗakin Umma ya karɓo mata magani tasha sannan ta ɗan samu zazzaɓin ya lafa mata, bayan sallar asuba har ta ɗan samu bacci. Satinta guda tana jinya sannan ta samu sauƙi sosai ta warware, sai rashin ƙwarin jiki kawai da take ɗan fama dashi. Washegarin ranar kuma suka bar Kaduna zuwa Kano. Bayan sati biyu da tafiyarsu Shatu da Ya Azeez ne kuma Fadwa da mijinta Ya'u mai kifi sukaje har gida suka yiwa Abba da Mama sallama kan zasu koma Birnin Kebbi garin mijin da zama, wanda kuma zuwa lokacin tuni Ya'un yayi sauƙi ya rage wasu abubuwan da yake mata sosai, shiyasa yanzu itama ta saki jikinta suna zaune lafiya basu da wata matsala, Umma kuwa koda Fadwan taje mata sallama tayi mata nasiha sosai sannan ta bata kuɗi masu yawa tace idan sukaje can garin ta kama sana'a. BAYAN WATA BIYU A haka dai rayuwa tai ta gangarawa da daɗi ba daɗi, haka abubuwa sukayi ta canzawa yau daɗi gobe kuma akasinsa, zuwa yanzu kam komai ya gama daidaita a zaman Fadwa da Ya'u mai kifi. Domin kuwa yanzu sana'ar kayan koli take sosai da zannuwa, cikin unguwar da suke a can Birnin Kebbin kuwa da maƙotanta babu wanda bai santa ba, shiko Ya'u tuni ya daina sana'ar siyar da kifi shima yanzu sana'ar siyar da dabbobi yake yi, kuma dukkansu sana'ar ta karɓarsu suna ganin buɗi sosai. Dan Fadwa kam zuwa yanzu har ƙiba tayi ta murmure abinta, alamar dai bata tare da wata matsala hankalinta kuma a kwance take gudanar da sana'arta bata jin damuwar komai a ranta tana zaune da mijinta lafiya da abokiyar zamanta. *********** A ɓangaren Ya Azeez da Shatunsa kuwa suma hakan ne ya kasance, dan duk wani jin daɗin rayuwa babu wanda basu jiyar da junansu. Hakan yasa har wata shaƙuwa ta musamman suka ƙara ga wani ji da juna da sukeyi tamkar zasu haɗiye kansu saboda tsabar ƙauna, kuma ko a gaban waye basu iya ɓoye tsantsar soyayyar da suke yiwa junansu shiyasa mutane da dama suke sha'awar yanayin zamansu, wasu kuma suke koyi da kalar soyayyar su mai matuƙar burgewa. Yau ɗin ta kama Lahadi Ya Azeez yana gida bai fita ko'ina ba, duk da Fahad nata damunsa da kira kan ya fito ya rakasa gidansu Basma zaije ganinsu ita da yaronsa, wanda watansa biyu kenan da haihuwa, amma yaƙi da yaga ma zai damesa da kira ya takura masa kawai sai ya kashe wayar gaba ɗaya ya ajiye, domin yau hutawa yake so yayi a gida tare da iyalinsa, dan haka baya jin zai fita ko nan ne da ƙofar gida, ranar yau ɗin gaba ɗayanta ta Eishatunsa ce, shiyasa baya buƙatar takura. Shiko Fahad a nashi ɓangaren jin abokin nasa ya kashe wayarsa ne yasa ya kaɗa kawai ya shiga motarsa ya nufi gidansu Basman, yana tuƙi yana mitar ya gaji da zamanta a gidansu daga zuwa wankan gida taje ta wani rashe ƙafafu tai zamanta, ko damuwa da lamuransa ma ba tayi balle tayi tunanin dawowa gida, sai dai kullum yay ta zarya akan hanya ba dare ba rana. A shirye ta fito cikin wasu haɗaɗɗun tausasan riga da wandon English wears masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, sosai kayan suka karɓeta sukayi mata masifar kyau, ta kama dogon gashinta da ribbon sai ta fito kamar wata ɗiyar indiyawa, ga cikinta ɗan wata uku daya fara fitowa yay ɗas a jikinta gwanin ban sha'awa. A hankali ta ƙaraso kusa dashi ta zauna lokaci ɗaya tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. "Babyna zaki zautani fa da wannan kyaun naki..." Ya faɗa tare da sumbatar kumatunta duka biyu, yana faɗin "Kinyi kyau sosai, gaskiya dole zan biya kuɗin kwalliyar nan da akayi min ta musamman..." Murmushi tayi tana kallonsa kafin ta sumbaci kumatunsa shima tana faɗin "Na gode Habiby na..." Ta faɗa tare da ɗan shafa gefen wuyansa tana kallonsa, kana kuma cikin shagwaɓa tace "Habiby zan sha fura da gyaɗa, da gwaiba da yalo..." Saurin ɗauke kai yayi daga kallonta ya kalli gefe yana dariya. "Fura da gyaɗa da gwaiba kuma har da yalo Baby...?" Ya faɗa lokaci ɗaya yana tsura mata idanu. Rausaya kai tayi tana turo bakinta gaba kafin tace "Eh su nake sha'awar ci yau..." Murmushi yayi tare da kai hannu ya lakace mata hanci yana dariya, haka take masa kullum musamman idan taga yana zaune baya komai ta dinga ƙaƙale ƙaƙale kenan duk dan ta sakasa aiki, wata rana kuwa har wanka sai shi zatace yay mata. Babu ranar kuma da bazata sashi zuwa nemo mata abubuwan ciye ciye da kwaɗayi irin na masu ciki ba, haka zata tashesa cikin dare tace zata ci abu, idan bai nemo mata ba kuma ta tasashi a gaba tai ta kuka kamar wata ƙaramar yarinya, wani lokacin idan yaga dare yayi kuma sai ya lalaɓata yace ta kwanta zai nemo mata, da haka zai samu da ƙyar tai shiru har bacci ya ɗauketa, wani lokacin kuma haka zai fito ya gama bulayinsa ya dawo bai samo abinda take son ba. Bama kamar yanzu da cikin yake ƙara girma, gashi kuma kullum kamar ƙara mata son yawo ake, idan kuma yace zai hanata nan ma wata rigimar ce zai tsokalowa kansa, yau ma da ƙyar ya hanata zuwa gidan Husna ƙawarta, wacce akayi bikinta sati uku da suka wuce. Dan har ta shirya yace ba inda zataje, tunda shima yau a gidan zai wuni ba inda zaije. Abun mamaki kuma sai yaga ba tayi gardama ba ta haƙura ta zauna a gida, shine yanzu kuma aka fito za'a bashi aikin nemo fura dasu gwaiba da yalo. Tsadadden agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ɗaga ya kalla, ƙarfe 5pm. Dai-dai ya gani. Sanin kuma yanzun nan zata iya dasa mai rigima ne yasa ya riƙota jikinsa ya rungumeta sosai, kana a sanyaye yace "Kinga dai yau gaba ɗaya bana jin daɗi duk jikina ciwo yake, ko zamuje kidan daddanna min jikina ko zanji daɗi, idan yaso daga baya sai inje in siyo miki, ko bazaki iya ba...?" Da sauri kuwa ta girgiza mai kai tana ƙara cusa kanta a tsakiyar faffaɗan ƙirjinsa, kana kuma cikin yin ƙasa da murya tace "Zan iya mana, Habiby ina matuƙar sonka fa..." Manyan idanuwansa ya lumshe sakamakon jin daɗin kalamanta, domin yana matuƙar son yaji kalmar a bakinta tana matuƙar yi mai daɗi ta kuma sanyaya masa rai. A hankali ya raɗa mata a kunne "Nima ina matuƙar ƙaunarki sosai Habeebtyna..." Murmushi tayi kana a hankali tace "Shikenan muje inyi maka tausan..." A hankali ya miƙe tsaye da ita a jikinsa suna tafiya cikin natsuwa suka nufi bedroom ɗinsu. Cak ya ɗagata ya ɗorata saman gadonsu, ya kwantar da ita lokaci ɗaya yana zura hannunsa cikin rigarta kana kuma cikin raɗa yana furta mata "Zaki iya kuwa Babyna...?" Ɗaga masa kai tayi a hankali tana wani lumshe idanunta, sake matsa hannunsa yay akan abinda yafi so, kana ya girgiza mata kai yana wani lumshe manyan idanunsa murya ƙasa ƙasa yana faɗin "Kin tabbatar dai bazan takura Babyna ba ko...?" Sake ɗaga mai kai tayi cikin fitar hayyaci da muradi mai girma, kana ta ɗago kanta cikin sauri ta haɗe bakinsu waje ɗaya, sannan ta jawosa gaba ɗaya ya faɗo kanta ya zamana tana ƙasa shi yana samanta, sannan ta ja musu lallausan bargo ta lulluɓesu. *ALHAMDULILLAHI* *ALHAMDULILLAHI* *ALHAMDULILLAHI* Daga nan na kawo ƙarshen wannan labari mai suna *WADATAR ZUCCI* Ina roƙon Allah ya yafe min kurakuran da nayi a cikinsa, ya kuma bani ladan abinda na rubuta dai-dai a cikinsa. Masoyana aduk inda kuke ina matuƙar godiya Allah ya barni daku, ina muku fatan alkhairi, sai mun sake haɗuwa idan mai kowa mai komai ya amince. Sannan ina roƙon duk wanda ya karanta wannan littafin ya yiwa mahaifina marigayi Alhaji Muhammad Alto addu'a, Allah ya sanyaya makwancinsa yasa aljanna fiddausi maɗaukakiya ta zamo makoma agaresa da dukkanin sauran musulmi baki ɗaya Nagode. *22-12-2021*