Wane ne marubuci :- Abdul'aziz Sani Madakin Gini An haifi marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini a jihar Kano a shekarar 1969 a unguwar gwangwazo. Ya yi makarantar allo a garin na kano inda daga nan kuma ya yi karatun firamare a unguwar Yalwa dake birnin Kano wato Yalwa primary school, daga ya koma technical wudil, sai ya tafi kuma ya yi federal technical Bichi dake masarautar Bichi . Bayan kuma yanzu ina aiki a karamar hukumar Dala. Na fara rubutu a 1983 kuma abin da ya ja hankalina shi ne yawan karance-karance na littattafan yaki tare kallon fina-finai. Sai tunani na ya fara bani cewa ya kamata ni ma na shigo cikin duniyar marubuta domin na jarraba hikimar da Allah ya bani. Wannan dalili shi ne ya sanya na fara rubutu littafi. Shi rubutu baiwa ne ba a koya wa mutum. Babu wanda yake koya min. Na fara rubuta littafina na farko a 1995, Wato littafin IDANIYAR RUWA. Kuma littafi ne na soyyya kamar yadda sunan ta bayyana. Kuma littafin yana fita ya samu haskawa a duniyar marubuta, bayan wannan kuma na rubuta wani mai suna DUNIYA RAWAR YA MATA. Sai kuma littafin YAUDARA KO BUTULCI. Babu wani littafi da marubucin ya wallafa da aka yi sa a gaske dukkanin ƙirƙira ne. Marubucin ya rubuta littattafai fiye da guda dari biyu. Kuma marubucin shine mafi shahara a Duniyar marubuta littattafai yaki cikin harshen Hausa Marubuci abdul'aziz Sani Madakin Gini ya rubutu littafin sa na yaki na farko mai suna RINJAYE Kuma littafin ya shahara sosai inda aka sanya sa a tsarin nazarin ɗaliban makarantun primary. Kamfanin da ya buga littafin shine JAKARA CITY BOOKSHOP dake birnin Kano. Har yanzu dai Littafin rinjaye ya samu karɓuwa inda shahararren mai karatun littattafan a rediyo ya karanta sa wato malam Muhammad Umar kaigama. Wani abun farin ciki ma ta dalilin wannan littafi marubuci abdul'aziz Sani Madakin Gini ya gida gidan da yake zaune littattafan marubucin mafiya shahara sune KUNDIN TSATSUBA MAZAN JIYA GALLABAR MAZA SARKIN SARAKAI RIJIYA GABA DUBU JELAR DAMISA Duk da cewar a wannan lokaci akwai littattafan marubuta da suka shahara. A wani bangare kuma marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini Ya rubutu fina-finai da dama tun farkon wanzuwar masana'antar kannywood Kamar shahararren fim mai suna JUYIN MULKI Daga cikin fina-finan da marubucin ya yi aiki da kasuwanci da kan sa shine kamar haka:- MARAICI za a dinga samun littattafan marubucin akan shaguna kamar haka:- Madakin Gini Bookshop Yahya SO Bookshop Jakara City Bookshop Al'amin Bookshop Da sauransu Jerin sunayen littattafan marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini RINJAYE YAUDARA KO BUTULCI RAMIN MUGUNTA IDANIYAR RUWA GALLABAR MAZA MAKASHIN MAZA SADAUKI ZOBEN SIHIRI RUGUNTSUMI RUGUNTSUMIN RUGUNTSUMI JELAR DAMISA DAMISA KI SABO GABA DA GABANTA KUNDIN TSATSUBA MATSATSUBI MIFTAHUL ZARBIL KARO DA DUBU ZOBEN SIHIRI RUWA DA ISKA ZARATAN JARUMAI FARMAKI MUTUWAR YAWA FILIN DAGA DARE UKU TSUBURIN ZAKARAN MAYAKAN ASALI HASKE DA DUHU DARUL MUHUK DODON MAZA FARAUTAR BAYI YAKIN SHAHADA NAMIJIN DUNIYA KUNDIN LABARAI HIKAYOYIN AL'AJABI JARUMI DAN BAIWA WASIKAR JINI SARAUNIYAR DAJI MUTUM DA ALJAN RIJIYA GABA DUBU KARAGAR MULKI KWARI DA BAKA BIRNIN AZZALUMAI SAIFUL ISLAM MUMINA DA AZZALUMA MAGOGIN KARFE TURNUKU FADAN IBLISAI MURUCIN KAN DUTSE KARFI DA KARFE KAIFI DA TSINI JINI DA KASA SARA DA SUKA SAIFUL LUJARA TAKOBIN SIHIRI ZAGE DAMTSE SANSANIN AZABA ZALUNCI MACE MAI KAMAR MAZA KARO DA MAZA INUWAR MUTUWA GOGA SHA YAKI RINTSI DA TSANANI RAGAYAR TSAFI TAFARKI GABA TSINI BAYA SIYAKI SADAUKI TSUBURIN ZAKARAM SAIFUL MAUT MAMAYAR BAZATO DUGUNZUMA MUGUWAR GASA JARUMIN JARUMAI TASKAR AJALI TURBAR GASKIYA FARAUTAR BAYI ZALUNCI HIKAYOYIN ABU SHAJJAR RUNDUNAR AJALI TSIBIRIN ZAKARAM