Showing 42001 words to 45000 words out of 51634 words
mata a
kunanta menene, gaya min me akayi miki?
Yaya ba kaine kayi tafiyarka ka barni ba, har
kwana bakwai?ya rinka shafa bayanta, shikenan
yi shiru, bazan kuma tafiya na barki ba. Shikenan
yi shiru kada kanki yazo yana ciwo.
Mansura tazo kansu tana huci, tace, ai saika
mayar da ita ciki, karewar shagwaba da sangarta,
ko kuma ka sakata a jaka, ka rinka yawo da ita
du inda zaka je.
Kuma wallahi rashin adalci da ake yi min na
daina yarda, bazan kuma zama anan ka dauketa
ku tafi abuja ba, kana tura mata kudi kana kashe
mata kudi acan, taci abunda du ranta yake so, ka
kalli yanda kuka canja kamar masu rayuwa a
turai.
To wallahi ko mu rinka tafiya abujan gaba daya,
ko kuma wananan intaje tayi watanni wannan ma
taje.
Ya daga mata hannu ya isheni, tunda ke baki iya
sannu da zuwa ba, sai kananan maganganu kika
iya.
Ta tafi tana kunkuni a dakeka a hanaka kuka,
nidai bazan yarda da zalunci ba, ko gware kuka yi
kuka fito karewar 'yan uwantaka.
Ta bar wajen. Aliyu ransa ya baci, ya rinka huci
yana kokarin tashi, zainab ta sake langabewa
ajikinsa, tana shafa kirjinsa, yayana menene dan
Allah?
Ka huce kada damu yayana.
Da safe zainab tasha kwalliyarta da wata ganila
shadda bulu tayi kyau, Aliyu ma yasha wata
lallausar farar shadda, sai kyalli takeyi kamar
boyal, sai tashin kamshi suke yi, kamshin da yake
tsoratar da mansura, ta rasa wani irin kamshine
dasu.
Du da ya hanata yin komai amma ranar girkinta
bata iya hakuri saita yi masa girki.
Yau ma ita ta hada break din suna kan tebir din,
shida mansura suna ci amma ita ta kasa cin
komai.
Aliyu yace zeeyta kici mana.
Tace, yaya bazan iya ci ba.
Nasa talatu ta gasa min hanta ita kawai zanci.
Ya ajiye kofin tea din, yace, bakya jin dadi zeey,
tun jiya ina kula dake, taso na kaiki asibiti.
Tace, yaya bana jin ciwon komai
bakina ne kawai ba dadi.
Mansura ta tabe baki ta yamutsa fuska, tace
kyaji da gulmarki, haihuwa dai ba abar wasa
bace, in kin tsaya iyayi kyasha wahalarki ke
kadai.
Aliyu yace Allah zai rabata da wahala, lafiya lau
zata haihu, na samu jaririn dana dade ina
mafarkin samu.
Mansura tace Allah sarki wane dare ne jemage
bai gani ba? Ai sai daran mutuwarsa.
Talatu tayi sallama ta shigo ta kawo mata gashin
hantarta, Aliyu ya karba ya yanka yasa wa zainab
a baki, ta rinka tauna tana yamutsa kamar mai
cin magani.
Shi kuma du ya damu, sai lallabata yake yi da
taci, mansura kuwa ta kumbura tayi tim, haushi
da takaici suka cikata.
Ni'ima tayi sallama ta shigo tana dauke da
yaronta hanif, zainab ta kama dariya, Oyoyo 'yar
uwa naji dadin zuwanka, bani yarona naji
duminshi.
Aliyu yayi saurin karbarsa yana cewa, zeey ai
bazaki iya daukansa ba, tubarkallah yayi nauyi.
Aliyu ya rinka yi masa wasa yanata dariya, ni'ima
ta gaishe da yayan nasu.
Ta juya tana gaishe da mansura, ta amsa a ciki,
ni'ima ta shareta don intana cikin wannan
yanayin bada sauraronta.
Ni'ima ta fito da atamfar super hollan da les
masu kyau, tace zainab ga ankon suna mun fito
dashi.
Zainab tace yaya ni'ima har wani anko za ayi?
Tace ke kada kimanta dan autarmu nefa da
babban yaya, ai dole muyi abubuwan da zasu
kayatar masa da taron sunan dan dangi (kuji
ni'ima da tsokana)
zainab ta debi kayan ta mikawa mansura, aunty
ga ankon suba nan su yaya ni'ima sun fitar.
Ta watsar da kayan ta doka mata tsaea, dan
Allah can yimin shiru kwaji da munafuncinku,
maga dai abunda za a haifa ko dan gwal ne ma
gani.
[8:02AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**5
Aliyu ya dago kansa yayi mata wani mummunan
kallo, ya rinka wani huci na bacin rai, mansura ta
juya ta shige bangarenta.
Aliyu ya mike zai bita zainab ta rikoshi ta
marairaice fuska, kamar me shirin yin kuka, tace
yaya don Allah kayi hakuri, kaji ka huce, bani
break din zanci.
Ya koma ya zauna, yayi ajiyar zuciya, ya rinka
bata break din du da ba dadinsa takeji ba, amma
ta daure taci sosai, don ta kwantar masa da
hankali.
A yangace tace, yaya na koshi, yayi murmushi, ai
naji dadi ma da kika ci wannan din, hankalina har
ya kwanta.
Ya mike ya dauki makullin mota, bari naje ofis, na
tabbatar da kayan da suka iso jiya, an gama
jibgesu a sito.
Ta mike a hankali ya riketa, kiyi zamanki ki huta,
ta makale kafada, tace um-um nidai saina
rakaka.
Ta dauko masa jakarsa, suka jera suna hira cikin
nishadi, suna murmushi, suna zuwa kofar falon ya
karbi jakan yace, ta koma ciki, ta rinka daga
masa hannu yana daga mata, har ya shige mota,
ita kuma ta dawo falon, ni'ima ta mike suka yi
bangarenta.
Ni'ima tace wai ke zainab ke wacce irice? Ta
rinka yi miki abu iri-iri bazaki dau mataki ba,
kuma ki rinka hana yaya yi mata komai.
Tace haba yaya ni'ima, Allah du abunda take yi
baya sakamin bacin rai, ko daya a zuciya.
Kuma in na mace zan ringa biyeta, ai kullum yaya
bazai samu kwanciyar hankaliba, du inda yaje
yana tunanin halin da gidansa yake ciki.
Yanzu kuwa ko ina yaje hankalinsa kwance,
yasan bazan saurareta ba, kuma dan habaici tai
tayi mana, nasan ko giyar wake tasha bazata kai
hannu ta dake ni ba. Hayaniya kuwa taita yi,
wata rana zata gaji ta daina, dan karfe daya baya
amo.
Ni'ima tace hakane.
Suka ci gaba da hirar abunda ya shafesu.
**** **** *****
mansura tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta
bugawa tayarta saratu.
Hello! Mansura ya akayi ne?
Tayi tsaki hum yaya saratu, gaskiya matsalolin
gidan nan sun fara isata.
Tace menene kuma meya faru?
Tace, um mutumin nan du ya wani rikice akan
cikin yarinyar nan, saika ce wanda bai taba
haihuwa ba, zaita lallbata tana wani yanga da
yamutsa ga shagwabar tsiya (komai girman
namiji wani lokacin yana son ana masa
shagwaba), ta kama kukan gulma ya rikice
yanata rarrashinta, sai kace wata 'yar kwai.
Yarinya ina ganinta gidahuma kamar ba
wayayyiya ba ina ganin bazata iya aikata abunda
take yi ba, kinga yanda take zama dakyar ta tashi
da dakyar amma du ranar girkinta, ita zata yi
masa du wani abun da kanta.
Kuma shima da yake munafikine, ranar girkina
idan kuku yayi girkin iyakacinsa yaci cokali biyu,
ko uku ya ture. Ranar girkinta kuwa ta sashi a
gaba tana loda masa abinci yana ci yana santi
tana dariya, sai yaci dayawa.
Baki ga yanda yake daukin cikin nan ba, kullum
addu'arsa da fatansa ta haihu lafiya inda kika san
ba a taba yi masa haihuwa ba.
Gashi ya mayar da Ahmad din irin makarantar
dasu zainab din suka yi, bazai dawo ba sai shidda
na yamma wannan ai zalunci ne.
Gashi ya debi yayunta ya dorasu akan dukiyarsa,
wannan kamfanin nasa fa a hannunsu yake, daya
darakta daya manaja.
Saratu ta katseta to ina ruwanki ba 'yan uwansa
bane? To idan 'yan uwansa ne ni bazaiyi min
kara ba?
Kamfaninsa na motoci ya daura kannensa, da
suke uwa daya uba daya da ni'ima su biyu da
nasa kannen biyu. Shi kenan arzikinsa saide suci
su isu? Ni banda nawa dangin kenan?
Saratu tace kedai mahaukaciya ce wallahi, ki
jawowa kanki abunda zai sakeki, kizo mu sake
zama.
Kina kallona gashi miji yaki samuwa, kuma kice
yana yiwa danginsa banda naki.
Kina ina ya dauki rabi'u da hamisu
ya kaisu kamfanin nasa ya basu aikin yi. Ko kin
manta da zaman banza suke yi.
Gashi yana zuwa yana gaida iyayenmu, ya kawo
musu kudi da kayan abinci. Du ya dauke wasu
sabgogin gidan nan ba tare da kin sani ba ko yayi
shawara dake.
Nidai bazan gaji da baki shawarar ki rike mijinki
da kishiyarki ku zauna lafiya.
Mansura tace, kai yaya saratu abunda nake nuna
miki daban abunda kike hange daban.
Sai anijima tunda kinki ganewa.
Bayan sati daya da dawowan Aliyu daga dubai,
ranar a dakin zainab ya kwana. Da safe ya
taimaka mata tayi wanka, da kwalliyarta ya bata
break taci.
Ta langabe ajikinsa, ya dago kanta, menene zeey,
tana limshe ido tace bacci, yace bai isheki ba
baccin?
Ta daga kai alamar amsawa.
Ya kwantar da ita a hado a hankali ya rinka
matsa mata jikinta, da bayanta data fi yawan
kuka dashi saboda ciwo ya rinka murza mata shi,
sannu-sannu tayi bacci, yayi ajiyar zuciya ya
mike ya fara shiri ya gama shirinsa yana fesa
turaruka.
Wayarsa tayi kara ya dauko yana amsa wayar ta
bude ido tana kallonshi.
Ya gama wayar yasa a aljihunsa, ya dauki
makullin motarsa yazo ya durkusa a gabanta,
yasa hannu yana shafa kanta, yace, an
shammaceni anyo min waya, kararta ta tasar min
dake, da nasan za a yo wayar nan da falo zan
fita.
Da baki tashi ba, bana so ki samu matsala kanki
yazo yana ciwo.
Tace yaya bakomai, normal nake jina, tace yaya
ina zakaje?
Ofis din su Abba znje kona zauna?
A'a yaya kaje Allah kiyaye hanya, ya dawo dakai
lafiya.
To koma baccinki ya rinka lallaminta yana jijjigata
kamar karamar yarinya harta koma bacci
[8:03AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**6
Yarinka lallaminta yana jijjigata kamar karamar
yarinya, harta koma bacci, sannan ya mike ya
tafi.
Be dade da jan motarsa ya tafi ta farka da wani
gigitaccen ciwon baya da mara, ta farka tana
salati, ta matsa kararrawar kiran talatu shiru bata
shigo ba ta tuna fa ashe tun dazu ta tafi gidan
yarta.
Ta taso a hankali tana dafe da kugu, tana salati
ta fito babban falo.
Mansura tana zaune tana kallo, ta jiyo salatinta
da nishinta, ta juyo tana kallonta, ta tabe baki ta
juya taci gaba da kallonta.
Zainab ta durkusa a gabanta ta daura kanta akan
cinyarta, tana salati. Aunty dan girman zatin Allah
ki taimaka min ki tallafawa maraicina, ki dubi
girman Allah aunty kinsan abunda nakeji.
Saita ji jikinta yayi sanyi, taji tausayin yarinyar ta
tuna irin gigicewar dayi sanda tana nakudar
Ahmad, da yanda yarinyar tai ta kuka.
Ta juyo ta kalleta, ta murkususu a jikinta, ta
dauki waya ta bugawa direban gidan, tace maza
ya fito da mota.
Ta taimakawa zainab din, saida suka shiga direba
ya dauki hanyar asibiti data ke zuwa awo.
Mansura ta fito da wayarta tana neman layin
Aliyu amma bata sameshi ba, har suka isa
asibitin, ana kokarin shigar da ita dakin haihuwa,
ta samu lambar Aliyu ta shiga.
Ringin uku ya dauka, hello! Aliyu muna asibiti da
zainab ba lafiya.
Kafin ta karasa cikin kara yace mata what? Tayi
saurin cire wayan daga kunnenta, don jin yana
barazanar tsorata mata dodon kunne.
Daga nan ya hawo motarsa ya nufo asibiti, ya
tarar da ni'ima da sadiya dasu umma sunata
zarya a kofar dakin data ke ciki.
Yana zuwa bai tsaya ba ya banka dakin haihuwar
tayi wujiga-wujiga tana salati, wata likita tana
tsaye a kanta.
A galabaice ta rinka miko masa hannu, tana cewa
wayyo yayana zan mutu, yaya ka yafemin, yaya
haka mamana tayi shiyasa ta rasa ranta.
Yazo ya zauna a gefen gadon ya rungumeta, yana
rarrashinta kiyi shiru zainab, kita addu'a Allah zai
saukeki lafiya kinji?
Ya rinka murza mata bayanta, yana karanata
addu'o'i ya tofa a ruwa ya bata tasha.
Taji ciwon ya lafa mata, ta bingire a jikinsa ta
fara bacci, can wani gigitaccen ciwo ya farkar da
ita, cikin lokaci kankani ta rikice da salati ta
kankame Aliyu likitan tana taimaka mata, katuwar
'yarta ta fado fara tas da ita.
Wata irin dariya Aliyu ya saka, tare da jerawa
ubangiji kirari, yana nuna godiyarsa ga Allah.
Ya dauki 'yar ya rungumeta, yanata aikin kallon
babyn, likita tana gyara zainab, kamar wanda aka
mutsina yayo waje da gudu yana kiran umma,
mama, ummi, gaba daya suka yo kansa suna
masu farin ciki.
Ummi ta karbeta, kai tubarkallah masha Allah. Su
ni'ima da sadiya sai lekenta suke yi a hannun
ummi, su naso su dauketa, amma Aliyu ya hana,
wai kada a jagwagwalaa, ko ya manta suma sun
a haihune.
Likita ta fito cikin kalmar turanci take ce masa
likita baka tsoro bebyn tayi mura ne, ka fito da
ita take shakar iska?
Aliyu yace ato ku kawota.
Ya karbeta da sauri yayi cikin dakin da ita. Su
umma duk suka bishi don ganin jikin zainab din.
Zainab tana ganin su umma ta rufe idonta wai
kunyarsu take ji, ni'ima da sadiya sunata yi mata
dariya.
Mansura kuwa tana tsaye a gefe tana mamakin
irin murnar da Aliyu yake yi, kamar wanda bai
taba haihuwa ba.
Mansura ta fito daga dakin, don bazata iya kallon
takaici ba.
Ya wani zauna dirshan a gadon zainab din, jikinsa
yana gogar nata, kamar zai rungumeta, sai wani
dariya yake.
Ta dauko wayarta ta buga, hello yaya saratu,
yarinyar nan fa ta haihu yanzu,
haba dan Allah meta haifa? Um du wannan iyayi
da akeyi ta bige da haihuwar mace.
Saratu tace "A me bambacin mace da
namijin,kema ai yaya saratu kinsan mace da
namiji akwai bambanci. Ai namij shine magajin
gida bare ahmad shekara takwas fa kenan, a
hada da 'ya mace ta mintuna amma kinga yanda
shida kannensa da iyayensa yanda suke ta wani
murna da farin ciki.
Saratu tace gaskiya mansura sai anyi miki uzuri,
wannan hali naki sai an taimaka miki da addu'a,
ni kinga bazan iya sauraran wadanan kananun
maganganu naki ba, ta kashe wayar.
A ranar aka sallamesu saboda mai jego da baby
lafiyarsu kalau.
Ummi itace a gun zainab.
A ranar da dare saida ta kori Aliyu bangarensa, da
asuba talatu ta girka garwa kan kuka gas, ruwan
ya tafasa ta kwashe, ummi tayi wa zainab
cikakken wakan jego, tana zillewa tana wash a
haka aka gama.
Zainab tana shiryawa ummi tana yiwa baby
wanka talatu tana goge lokaci daya du suka
gama.
Me jego da baby sun fito dagwas shar dasu, gaba
daya bangaren nata ya rikice da kamshi me rikita
zuciya.
Karfe takwas Aliyu ya shigo, ya durkusa ya gaida
ummi, ya karbi babyn a hannunta, yace ummi
zeey din tana ina?
Tana daki.
Ya mike da babyn a hannunsa ya shiga dakin ,
sai yaji kamshin da dakin yake yafi na ko ina
dadi.
Tana zaune a gefen gado ya shiga da dariyarsa,
me jego kinsha kamshi.
Tayi murmushi yazo ya zauna kusa da ita.
Ta durkusa kasa, yaya ina kwana?
Lafiya lau, yaya babyn ta kwana?
Gata nan ka ganta.
Ya dago zainab din ta zauna a jikinsa, zainab
kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya daukeni?
A daure anayin comment please
[8:04AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**7
Zainab kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya
daukeni?
Saboda me yaya?
Wallahi tunani babyn nan tawa 'yar kyakywan nan
ta zauna min daram a rai, tunda na taso ranar da
aka haifeki, na ganki kika zauna daram a
zuciyata, ban taba tunanin za a samu abunda zai
kuma shiga zuciyata ya zauna min irin haka ba,
sai gashi kin haifa min kyakyawan diyata da tafi
komai shiga zuciyata.
Zainab ta kalleshi cikin shagwaba tace, yanzu
yaya kafi sonta dani?
Yayi murmushi ya shafi fuskarta, yace ai ke
dabance zeeyta, kaunar danake miki bata da
misali, amma kinga bebyn nan tawa ma ta maye
ruhina gaba daya.
Zainab kin gama min komai da kika haifomin
bebyn nan, bani da bakin da zan miki godiya, bani
da abunda zan baki.
Babbar addu'a da zan miki Allah ya miki tukuici
da gidan Aljannah
amin yayana.
Bebyn ta dan motsa, ya balle marfin swan water,
ya tsiyayo kadan a kofin azurfa ya bata tasha.
Yace bata nononta tasha.
Yaya wallahi data kama jiya, baka ji zafi ba.
Yi hakuri ki bata a hankali zai daina zafin.
Zainab din taba bata tana cije baki
tare da cewar wash.
Lallabata yakeyi yana cewa, yi hakuri zeeyta,
tasha ta koshi, yauwa bata dayan.
Da haka babyn tasha ta koshi, ya karbeta ya
dorata a kafada, yana shafa bayanta har tayi
gyatsa taci gaba da baccinta.
Zainab ta dora kanta akan cikinsa, yana
tambayarta me da me take so ayi shagalin suna?
Suka jiyo karadin ni'ima da sadiya suna buga
kofa yace su shigo.
Suka shigo, sadiya tace yaya ka hade zeey din da
bebyn du ka rikesu anan ga jama'a ga jama'a
can sunata zuwa barka ba me jego ba beby.
Yace nifa bana son yawan daukan nan fa, saboda
shi yake kawowa yara ciwon jiki.
A fitar da kan gadonta falon a sakata a ciki, a
rufe da net din, du wanda yazo ganinta ya ringa
lekata kawai, a ganta haka basai sun dauka ba.
Ranar kwana hudu aka kawo kayan barka
akwatuna shidda uku na beby akwatuna uku na
mai jego fadan kayan da suke cikin akwatin bata
lokacine.
Mansura ta mike fuu tayi bangare Aliyu, ta banko
kofar dakinsa, babu sallama ta tsaya masa
tsegege aka, yana kwance akan gado yana
kallonta.
Tace Aliyu nagaji da wannan rashin adalci naka,
ni bazan iya zama ba, kana nuna min iyakacina,
ka dubi uban kaya daka jibgawa zainab da
jaririyarta, ni wallahi bazan yarda ba saide kome
zai faru ya faru,
ya daga mata hannu ki saurara kada kiyi min
hayaniya aka, fita ki bani waje.
Ta fito ta kwashi akwatunan daya bata ita da
Ahmad tasa aboot din motar da ya bata da
akwatunan ta tafi gidansu.
Mansura tana isa gida, tasa kannanta suka shigo
mata da akwatunan, iyayenta suna falo da saratu
da hauwa, suka tareta da lafiya?
Tace wallahi Alh na gaji da rashin adalcin
mutumin nan, ka dubi 'yan kayan da ya bamu
nida Ahmad, amma ita ya hada mata akwatuna
shidda ita da 'yarta kuma ya bata irin motar da
ya canja min.
Saratu ta bude kayan tana gani, super da holland
da les da material da shadda ganila ga takalma
jaka da sarkar gwal.
Akwatin Ahmad ma kananan kaya masu tsada,
sai shadda da boyel masu tsada sun sha aiki,
kala goma sha daya, ga takalma da huluna masu
kyau da tsada, harda glas mai ruwan gwal
suka gama gani, saratu ta rufe kayan, hajiya tace
mun gani Allah ya saka da alkhairi, ubangiji ya
kara buda masa.
Mansura tace, hajiya nifa na taho gida, ku kirashi
kuyi masa fada bazan iya zama da wannan
rashin adalcin nasa ba....
Kafin ta rufe bakinta Alh ya wanke mata fuska da
mari, hajiya ta rufeta da duka.
Dabbar yarinya mara hankali, dazunan ya
kawomin makullin mota sabuwa kar.
Ya aikowa da mahaifiyarki katon injin kankara
don ta rinka sana'a dashi shine kike kokarin
tozarta kanki, da yake bakisan abun arziki ba, to
du ranar da kika sake zuwa gidan nan kika
kawomin karar mijinki, saina karyaki, bare kuma
kiyo yaji, wannan kasheki zanyi murus har lahira.
Fita ki bani waje, ya biyota tayi waje da sauri,
kananta suka mayar mata da akwatunan cikin
mota, taja ta koma gida tana hawaye, fuskarta da
yatsun babanta daya mareta.
Tazo ta wuce ta babban falo tana kuka Aliyu
yana zaune yana kallo, ko kallonta baiyi ba, ta
wuce bangarenta.
Ranar suna aka sawa jaririyar sunan maman
zainab, suna kiranta da ihsan.
Taron suna yayi kyau angama lafiya aka watse.
Kyaututuka da zainab ta samu baza su lissafuba,
daga kawayenta, abokan Aliyu 'yan uwa da
abokan arziki, kayan kamar a bude sito dashi.
Yaya ni'ima tace, kinsan kuwa yau shekarar ku
uku cif da aure da yaya. Shida yayi alkawari
saikin shekara uku sannan zai kusanceki, sai
gashi shekara uku tazo da 'yar diyarku ko?
Zainab tace ke kika jiyo, ni ba ruwana.
Suka sa mata dariya.
*** *****
kwanci tashi rayuwa ta mika, zainab tuni sunyi
arba'in, harta koma abuja, taci gaba da
karatunta.
'yar diyarta saida daddynta ya nema mata tsari
sosai, saboda kyan Ihsan du wanda ya bude baki,
sai yace hu! Wannan yarinyar da kyau take.
Ihsan watanta shidda kenan tayi 'yar kubibi abun
sha'awa da 'yan hakoranta biyu abakinta, tayi
sabo da Aliyu du sanda ya dawo gida, yana tare
da ita, don haka data ganshi tana bayan talatu
zata rinka zillo.
Ya karbeta ya rungumeta, yana murnar ganinta...
via # Abdul azeez muhammad
Ina 'yan gidan nan kowa ya fito ya bani Happy
sallah nah
[8:05AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**8
Ya karbeta ya rungumeta, yana murnar ganinta,
yasata a gaban mota, yaita yawo da ita.
Tanada wata takwas ta fara takawa, dadi ya ishi
Aliyu, komai ya gani sai ya siyo wa ihsan.
Ihsan tana sanye da dan jeans din dogon wando
da 'yar riga yalo ta dan kama mata jiki, anyi
mata indomie akanta, ansa mata kananan ribon
yalo. Da takalminta yarinyar tana ta kamshi, tana
tura 'yar motarta a falon, tana binta.
Aliyu yayi sallama ta taho da gudu tana cewa
Abba! Har tana kokarin faduwa.
Ya sureta ya rungumeta ta Abba.
Zainab ta fito cikin kayataccen kwalliyarta ta
kananan kaya, ta sake komawa yarinya sharaf,
saboda hutu ya kara samuwa.
Ta taryeshi ta