Showing 1 words to 1996 words out of 1996 words
Chapter 1 - GUGUWAR ANNOBA Book 3 by Madakin Gini.docx
GUGUWAR ANNOBA -> Madakin Gini
08137237071
arewanovels.com.ng
Koda Sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa ya rungume Yarduza ya fashe da kuka.
Al'amarin da ya karyar da zuciyar Yarduza ke nan shima ya kama kukan. Sai da suka dade a zaune rungume da juna suna kukan sannan suka mike tsaye ya raka Sarki har cikin turakarsa yaje ya kwantar da shi akan gadonsa.
Haka dai suka rabu kowannensu na zubar da hawaye, Yarduza na fitowa daga cikin turakar Sarki sai ya koma dakinsa ya ajiye kayansa ya cire batun barin gari daga ransa.
Bayan kwana biyu da faruwar wannan al'amari Sarki ya mutu., Bayan an gama bikin binne Sarki da kwana biyu sai 'yan majalisa suka kirawo gagarumin taro a fada.
Jama'a kuwa suka zo daga birane da kauyuka aka cika fada makil ya amana cewar babu masakar tsinke a ko ina.
! Bayan kowa ya hallara ne aka kirawo yarima Kuraisu da yarima Yarduza aka sanar da su wasiyyar da Sarki ya bari ta cewar sai sun fafata yaki a tsakaninsu wanda duk ya kai wani kasa shi ne zai zama Sarki".
Koda jin wannan batu sai yarima Kuraisu ya kyalkyale da dariyar mugunta da farin ciki domin ya yi matukar mamaki da jin hakan, kuma ya san cewa a banza zai sami garabasa.
Shi kuwa yarima Yarduza dama ya san da wannan batu, don haka bai yi mamaki ba. Abinda ya baiwa yarima Kuraisu mamaki shi ne, ko kadan babu alamr tsoro a tare da Yarduza, kuma a shirye yake ayi wannan gasa da shi, harma ya yi shigar yaki ya dauki garkuwa da takobi ya rike.
Nan take shima yarima Kuraisu ya sa aka kawo masa takobi da garkuwa ya rike, sannan ya shiga tsakiyar fadar ya tsaya ya daga takobinsa sama sai fadar ta rude da shewa aka hau yi masa jinjina da kirari.
A sannan ne shima yarima Yarduza ya shigo cikin tsakiyar fadar. Koda ya zo kusa da Kuraisu ya tsaya, sai ya zamo dan mitsitsi tamkar an ajiye 'yar karamar Akuya a gaban katuwar Kura, domin sai ya daga kansa sama yake sannan yake iya kallon fuskar Kuraisu.
Kuraisu ya matso daf da Yarduza ya ce da shi, "Yau na sami dama da zan kasheka gaba daya na huta da fargabar wanzuwarka a doron kasa, don haka ba wai kaika kasa ne a gabana ba, sai kayi
kokari ka ceci rayuwarka!"
Koda gama fadin hakan sai Kuraisu yaja da baya ya koma gefe daya ya tsaya yana jiran a basu umarnin fara yakin.
Shima Yarduza sai yaja da baya ya tsaya a wannan lokaci zuciyar Yarduza daka take domin ya san cewa ko ba a gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza.
Nan take aka buga gangar fara yaki, sai Yarduza da Kuraisu suka tunkari juna, kowannensu rike da takobi da garkuwa. Nan take suka ruguntsume da azababben yaki tamkar makiya a filin yaki, suka rinka kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta.
Al'amarin da ya burge kowa ke nan a fadar aka rinka yi musu tafi da jinjina.
Koda aka sami dan dogon lokaci ana wannan gmurzu sai yarima Yarduza ya fara raina kansa domin ta kai cewa ya kasa ci gaba da kai martani face kokarin kare kansa saboda Kuraisu ya kara karfin saransa da kyar yake iya tarewa.
Wani lokacin ma har ja da baya yake ko kuma ka ga ya durkushe bisa gwiwoyinsa amma sai yai sauri ya mike a ci gaba da bakin artabu.
Hakika duk wanda ya ga yadda ake wannan
gumurzu ya san cewa Yarduza ba karamin kokari yake ba, domin a tarihin sadaukantakar yarima Kuraisu a gaba dayan Birnin Kaluza ba a taba samun jarumin da ya tareshi gaba da gaba ba suka gabza yaki bare ma har a su jima suna fafatawa face yarima Kuraisu ya kaisu kas.
Sau tari ma idan Kuraisu zai jarraba jarumtaka sai an tara manyan sadaukai guda arba'in sannan ya yakesu shi kadai ba tare da ya rike makami ba, su kuwa da makamansu a hannu. Har a gama yakin dayansu ba zai sami damar koda lakutar jikinsa ba saboda tsananin zafin namansa. Amma yau gashi mutum daya jal ya gagareshi duk da cewa da makami a hannunsa kuma ya fishi karfi, jarumtaka da zafin nama.
Ana cikin wannan bakin artabu ne Kuraisu ya sami nasarar yankar Yarduza a hannu, har jini yai tsartuwa.
Yarduza yai ihu ya ja da baya da sauri amma sai Kuraisu ya bishi ya sa kafa ya doki kirjinsa.
Yarduza ya tafi luu! zai fadi kasa da bayansa, amma sai yai sauri ya dafa kasa da daya hannunsa mara takobi ya mike zumbur tamkar sifirin.
Gaba dayan 'yan kallo sai da suka mike tsaye suna ihu domin a zatonsu Kuraisu ya ci gasa, amma da aka ga Yarduza ya mike tsaye sai kuma aka zazzauna cikin tsananin mamaki, aka ci gaba de kallo.
Koda Kuraisu ya ga yarima Yarduza bai je kasa ba sai ya fusata ainun ya ruga kansa suka ci gaba da kazamin yaki. Wannan karon sai ya tattara karfinsa gaba daya ya zuba akan Yarduza har ya sareshi sau biyu.
Saran farko a kirjinsa. Duk da cewa Yarduza ya yi kokarin gocewa, amma sai da kaifin takobin Kuraisu ya fasa sulkensa ya datsa fatarsa, jini yai feshi, inda da tsautsayi ya sami kashin kirjin ma shi ke nan tasa ta kare.
Yarduza ya kwala ihu ya juya da baya da nufin ya matsa baya, sai Kuraisu ya dankara masa wani saran a gadon bayan.
Wannan karon sai da Yarduza ya kwala ihu domin bayan nasa ya dare, jini mai yawa yai tsartuwa da feshi, ya durkushe kasa bisa gwiwoyinsa a cikin wani irin mugun yanayi mai kama da suma.
Koda Kuraisu ya ga ya sami wannan nasara sai ya daga hannayensa sama ya yi kururuwa irin ta mazaje, ya yin da suka sami nasara a filin daga.
Jama'a suka kaure da shewa aka hau yi masa jinjina. Nan take Kuraisu yaji wani irin girman kai ya shigeshi, kawai sai ya ci gabo da kuri, har yana tofiawa Yarduza yawu a Siska yana yi masa dariyar mugunta
Su kansu 'yan kallon sai jikinsu ya yi sanyi bisa mamakin yadda Kuraisu ya wulakanta dan uwansa Yarduza. Haka kuma da yadda ya yi masa wadannan munanan sara guda biyu wadanda da gani ka san cewa rayuwarsa yake nema kawai ba gasar ce ba kadai a gabansa.
A wannan lokaci ne Yardoza ya dawo cikin haiyacinsa, kawai sai ya shiga tunanin abinda ya faru tsakaninsa da mahaifinsa sa'adda yake karfara masa gwiwa ya ce da shi.
"Nasara ta danganta akan se'a da dakewar zuciya! Ka sa a ranka cewa ta kowanne hali sai ka sami nasara domin ceton kasarka da jamaarka".
Koda Yardura yazo dai-dai nan a tunesinsa sai yaji wani irin sabon karfi ya shigeshi, jihinsa ya kama karkarwa.
Ba zato ba tsammani sai aka ga Yarduza ya mike tsaye ya fuskanci Kuraisu kuma yai wurgi da takobinsa da garkuwarsa ya yafito Kuraisu da hannu yana mai kiransa.
Shi kansa Kuraisu sai da ya cika da mamaki,amma sai ya bushe da dariyar mugunta
A dai-dai wannan lokaci ne hadari ya gangamo, kafin a ankara ruwa ya fara zubowa kadan-kadan, amma sai mutane suka kasa watsewa saboda kawai suna son su ga yadda karahen wannan gasa za ta kasance, gashi ana tsawa da walkiya mai firgitarwa.
Kuraisu ya daga takobinsa sama ya rukem da hannu biyu ya nufi kan Yarduza gadan-gadan da nufin ya tsargeshi gida biyu.
Yarduza ya taaya cak a inda yake ko motsawa bai yi ba. Koda Kuraisu ya zo daf da shi ya kawomasa wawan sara sai ya goce cikin zafin nama ya sunkuceshi da hannu biyu ya dagashi sama ya dinga hajijiya da shi.
Kuraisu ya yi kokarin ya subuce daga hannun Yarduza amma ya kasa. Al'amarin da ya matukar baiwa kowa mamaki ke nan.
Yarduza ya ci gaba da yiwa Kuraisu hajijiya a sama har sai da duk su biyun jiri ya debesu sannan ya makashi da kasa, shima ya durkushe kasa ya baje a sume.
Nan take fadar ta rude da shewa, jama'a suka rugo da gudu suka daga Yarduza sama yana sume ba a sani ba ana tayashi murna ana ta yi masa jinina da tayashi murnar cin wannan gasa ta sarauta.
Kashe gari da sassafe fada ta sake cika makil da jama'a, aka shiga shagalin bikin nadin sarautar. Har aka dora Yarduza akan karagar mulki aka bashi sandar mulki ya rike bai ga dan uwansa Kuraisu ba kuma sai dube-dube yake da hange-hange yake ko zal ganoshi.
Bayan an gama bikin nadin sarautar ne makada da yan rawa suka fara baje kolinsu aka fito da abinci da kayan shaye-shaye kowa ya shiga baiwa bakinsa hakkinsa.
Ana cikin tsaka da wannan hali ne Yarduza ya hango yarima Kuraisu tare da matarsa sun fito daga cikin gidan sarautar deuke da kayansu bisa dawakai biyu za su fita.
Cikin sauri Yarduza ya mike tsaye don yaje garesu, amma sai yaji rauaikan da ke jikinsa sun kama ciwo kamar ba zai iya tafiya ba.
Cikin Karfin hali ya daure ya tafi da sauri yn aha gabansu ya rike dokin Kursisu yn ce, "Habu ya kai dan uwana ya ya za ko tafi ka barni alhalin kaine kadai ka rage a gare i? Abinda nake so da kai shi ne, ka zauna mu yi mulki tare ka zama wazirina, kuma ka fadin duk abinda kake bukata na baka ko na yi maka."
Koda jin wannan batu sai Kuraisu ya yi murmushi sannan ya ce, "Ya kai dan uwana, kayi sani cewa ba zan iya zama ba a cikin wannan Birni namu ina kailon karagar mulki, amma bani ne a kanta ba, domin tuni na nada kaina a matsayin Sarki, kuma ka san cewa ba a yin Sarki biyu a cikin gari guda.
Wannan shi ne kalamina na karshe a gareka. Duk ranar da na sake dawowa garin nan to ka tabbata a wannan rana ne zan hau karagar mulki, na kwanta akan gadon sarauta, na ci abincin sarsuta kuma na sanya tufafin sarauta kamar yadda mahaifirmu ya yi kafin ya gushe.
Koda gama fadin haka sai Kuraisu ya kada linzamin dokinsa yai gaba, itama matarsa sai ta bishi da sauri tana mai waigowa tana kallon gidan sarautar hawaye na zuba a idanunta, domin ta san cewa shi ke nan ba za ta sake dawowa mahaifarta ba
Daga wannan rana ba a sake jin duriyar yarima Kuraisu da matar sa ba, kuma babu irin neman da ba a yi musu ba, amma ba a gansu ba". Sa'adda gunki Salkar yazo dai-dai nan a labarinsa sai yai shiru gami da ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ya kai wannan Sarki kayi sani cewa daga wannen
lokaci ne mahaifinka ya ci gaba da sarauta har tsawon shekara arba'in.
A ranar da ka shekara takwas a duniya ne mahaifin naka ya rasu, kuma dama da sunansa ake kiranka. Yanzu dai a takaice ka fahimci cewa wannan kyakkyawar budurwa da ka hadu da ita a daji, wato Sharlisa ita ce 'yar da yarima Kuraisu ya haifa tare da matarsa wadda yai Hijirah tare da ita.
A halin yanzu Sharlis ta taso da tsananin jarumtaka fiye da mahaifinta, kuma tayi alkawarin sai ta cika masa burinsa na hawa karagar mulki tsawon kwana bakwai.
Ina so ka sani cewa idan ka cika mata alkawarinta za ka aureta har ku haifi wanda zai gajeka, idan kuma baka cika ma ta burinta ba har abada ba za ka sami magaji ba, koda kuwa za ka auri dukkan matan duniya, kuma ba za ka taba gama mulkinka lafiya ba.
Babbar illar ga yin aurenta shi ne, kana ji kana gani matarka za ta rinka tafiyar da harkokin mulki tamkar ita ce mai sarautar, wato sai dai ka zama dan kallo.
Shawarata a gareka ita ce ka hakura da auren Sharlisa domin ka tsira da kimarka da mutuncinka
Mu hadu a littafi na 4 don jin cigaban labari
08137237071