Showing 1 words to 2225 words out of 2225 words

Chapter 1 - GUGU WAR ANNOBA Book 4 Littafin Yaki By Madakin Gini.pdf

GUGU WAR ANNOBA -> Madakin Gini
arewanovels.com.ng
08137237071


Wannan ba umarni bane a gareka, kana dazabi.
Ka tuna cewa yau kwananka daya jal da hawa karagar mulki, bai kamata ace da hawanka ka yi
aure ba, kuma matar da ka aura ta more jin dadin sarautar fiye da kai."

Sa'adda gunki Salkar yazo nan a zancensa sai hankalin Sarki Yarzusa ya dugunzuma, yai shiru
yana tunani har izuwa lokaci mai tsawo".

Daga can sai ya dago kai ya dubi gunki Salkar ya ce, "Me ya sa aka sa mini sunan mahaifina?"

Gunki Salkar ya bushe da dariya sannan ya tsuke bakinsa a lokaci guda ya ce, "Duk Sarakunan
da suka yi mulki a gidan nan irin sunanka ne da su, ba a taba samun canji ba, shi yasa duk
ranar da aka samu sauyi shi ke nan sarautar ta bar irin gidan. Wannan shi ne dalilin da ya sa
mahaifinka ya dage akan cewa kaine za ka gajeshi, kuma haka abin ya samo asali tun daga
Kakanka na farko".

Ya yin da Yarduza yaji wannan batu sai ya jinjina kai sannan ya ce, "Shi ke nan zan je na
aiwatar da abinda nake ganin zai fissheni". Gama fadin hakan ke da wuya sai Yarduza ya mike
tsaye ya juya ya fice daga cikin dakin.

A wannan rana dai Sarki Yarduza bai sami sukuni ba saboda yawan tunani bisa hukuncin daya
kamata ya yankewa kansa akan auren Sharlisa ko barinsa, har dare ya raba Sarki Yarduza bai
rintsa ba.

Lokacin da ya ga ya kasa barci sai yasa aka kawo masa giya aka zuba banju a cikinta ya
kwankwade tulu guda.

Ai kuwa bai ma gama shanye giyar ba ya bingire akan gadonsa ya kama barci. Wannan shi ne
abinda ya faru ga Sarkı Yarduza bayan ya gana da abin bautarsa gunki Salkar

AL'AMARIN SHARLISA ma'abociyar Akyawu kuwa, lokacin da ta rabu da Sarki

Yarduza sai ta daka tsalle sama ta kama wannan doguwar jijiyar bishiya ta tafi shuu! a sama ta
dinga dira akan bishiyoyi, sai dai ka ga ta hau wannan ta sauka, ta hau waccan ta sauka

A haka har sai da ta bi ta kan bishiyoyi a kalla guda ashirin da uku, sannan ta dira akan wani
dogon tsauni mai tsananin twon tsiya, wanda idan mutum ya tsaya daga kansa ya kalli sama sai
ya hango abinda ke kan tsauni ya zama dan mitsitsi.

Bayan Sharlisa ta dira akan tsaunin sai ta cigaba da tafiya akansa har sat da tayi 'yar doguwar
tafiya sannan ta iso inda wadansu dogayen bishiyoyi suke a cunkushe a waje daya sun haifar
da duhuwa saboda yawan ganyayensu masu fadi. Komai jarumtakar mutun sai ya yi shakkar
ratsawa ta cikin duhuwar bishiyoyin saboda kwarjinin wajen domin gani zai yi cewa lallai ba za a
rasa wani mugun abu ba a cikin wajen.

Kai tsaye Sharlisa ta kunna kai ta tsakiyar bishiyoyin ta sake yin wata 'yar doguwar tafiyar sai
gashi ta iso gaban wani dan karamin daki wanda aka yi shi da zallan itatuwa. Sharlisa ta sa
hannu ta bude kofar dakin ta kunna kai

Daki ne mai fadi daga cikinsa wanda aka ajiye gadon kara a tsakiyarsa, wanda aka yi masa
shimfida mai kyau irin ta sarakai.

A gefe daya an ajiye wani katon gunki mai siffar wata mace. Gunkin ya sassaku matuka kamar
zai yi magana. Zaunc a gaban gunkin wani mutum ne tsoho tukuf fuskarsa da kansa cike da
farin gashi ya kurawa wannan gunki idanu yana zubar da hawaye.

Kallo daya mutum zai yiwa tsohon ya san cewa hakika jarumin gaske ne ada, domin har yanzu
akwai kirar sadaukantaka a tare da shi, Wannan ya kasance zabgegen mutum ga tawo kauri.

Koda jin an turo kofar dakin sai tsohon ya juyo da sauri. Yana yin arba da Sharlisa ya ga
fuskarta cike da annuri sai ya bude hannayensa ta fada kan Kirjinsa suka rungume juna.

Tsohon ya janye jikin nasa daga cikin nata ya ce, "Ya ke 'yata bani labari, na ga alamar cewa
yau akwai magana a bakinki".

Sharlisa tayi murmushi ta ce, "Tabbas akwai labari mai dadi a tare da ni".

Nan take ta kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninta da Sarki Yarduza ta shaida masa.

Koda jin wannan labari sai tsoho Kuraisu ya cika da tsananin farin ciki ya ce, "Tabbas burina zal
iya cika a ko yaushe daga yanzu".

Koda gama fadin hakan kuma sai ya bushe da dariyar murna. Lokaci guda kuma ya hade fuska
idanunsa suka ciko da kwalla ya fara zubar da hawayc.

Al'amarin da ya matukar girgiza hankalin Sharlisa ke nan ta kama kafadun tsoho Kuraisu ta ce,
"Ya kai Abbana, ina dalilin zubar da hawayen nan naka kuma, alhalin burinka na daf da cika?"

Koda jin wannan tambaya sai Kuraisu yai
ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ya ke 'yata kiyi sani cewa ba komai bane ya sani zubar da wannan
hawaye ba face ganin cewa zan zauna akan karagar mulkın garinmu a lokacin da na tsufa ba
sa'adda nake ji da samartaka ba.

Wannan babban abin bakin ciki ne a gareni. Dalili na biyu da ya sani zubar da hawaye ba zan
iya gaya miki ba a yanzu sai bayan bukatata ta biya.

Abinda nake so da ke shi ne kiyi shiri gobe da sassafe ki koma inda kika hadu da Yarduza, lallai
shima zai zo, kuma zai amince da sharadin da kika kafa masa.

Alfarma daya nake so ki yi mini. Bayan kin auri Sarki Yarduza ki dauki wannan gunki na
mahaifiyarki ki tafi da shi can gidan sarautar kuma ki tabbata kin ajiyeshi a cikin wani daki na
musamman, dakin da babu mai shigarsa face mijinki".

Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Sharlisa ta ce, "Ya kai Abbana saboda me kake son
na kai gunkin cikin wannan daki alhalin nima ina son na dinga yawan kallonsa tunda shi ne
kadai yake debe mini kewar mahaifiyar tawa?

Ka tuna cewa rabona da ita tun ina da shekara
bakwai a duniya?"

Kuraisu ya yi ajiyar zucıya sannan ya ce, "Ya ke 'yara kiyi sani cewa na yi bincike na gano cewa
anan gaba wasu shekaru masu dan yawa da za s zo za a yi wani gagarumin yaki a Birnin
Kaluza, za a yi asarar miliyoyin rayuka, kuma za a kona gaba dayan gidajen Birnin, wannan
daki guda daya da Sarki ke shiga a sirrance shi kadai ne zai yi saura a fadin Birnin duka.
Ina son gunkin mahaifiyarki ya wanzu tare da ke da kuma abinda za ki haifa nan gaba har izuwa
wadansu shekarun masu yawa da za su zo gaba."

Koda gama wannan jawabi sai tsoho Kuraisu ya mike tsam daga gaban wannan gunki ya kome
kan wannan gadon kara ya yi kwanciyarsa ya lumshe idanu.

Ita kuwa Sharlisa sai ta mike taje ta fara kokarin shirya musu abincin da za su ci.

K ASHE GARI da safe Sarki Yarduza ya yi shirin fita farauta shi kadai kamar yadda ya saba

Bayan ya debi makamansa an kawo masa doki ya hau zai fita daga gidan sarautar ke nan sai
ya ga 'yan majalisa sun taho gareshi da sauri.

Da isowarsu sai suka sha gabansa. Waziri ya dubeshi cikin girmamawa ya ce, "Ya shugabana
ya kamata yau ace kayi zaman fada domin ka gabatar da harkokin mulki kamar yadda iyayenka
da kakanninka suka yi a bayanka".

Koda jin wannan batu sai Sarki Yarduza yai murmushi sannan ya ce, "Ya kai Waziri kayi sani
cewa kima da darajar Sarki bata tabbata face yana da matar aure. Wannan fita da zan yi yanzu
zan fita farautar matar da zan aura ne.

Ina so ka sani cewa zaman fada baya ga cikin abinda ya dameni. Babban abinda ya dameni shi
ne ci gaban kasar nan da kwanciyar hankalin talakawana.

Wannan aure da zan yi shi ne zai tabbatar da wadannan abubuwa biyu".

Koda gama fadin haka sai Sarki ya sakarwa dokinsa linzami ya zabureshi da gudu ya fice daga
cikin gidan sarautar ya durfafi cikin daji.

Sarki Yarduza ya ci gaba da tafiya sannu-sannu har ya iso bakin dogon tsaunin nan mai santsi
inda suka hadu da kyakkyawa Sharlisa.

Da isowarsa sai ya hango Sharlisa akan tsauni mai santsi ta harde kafafu tana yi masa
murmushi
wanda ya dimautashi yaji kamar ya ruga izuwak tsaunin ya rungumeta.

Cikin hanzari ya sauka daga kan dokinsa daga kansa sama ya dubeta ya ce, "Ya ke Sharli 'var
yarima Kuraisu maza ki sauko mu tattauna bi alkawarin da ke tsakaninmu".

Koda jin wannan batu sai Sharlisa ta had fuska, hankalinta ya tashi, kuma ta cika da tsanan
mamaki bisa yadda aka yi Yarduza ya san ko wace co.

Jikinta gaba daya ya yi sanyi ta kasa saukowa daga kan tsaunin, kawai sai ta kurawa Yarduza
idanů ta kasa cewa komai.

Koda ganin haka sai Yarduza yai murmush sannan ya durfafi tsaunin kai tsaye. Da zuwalisa daf
da tsaunin sai ya dubi tsaunin da kyau ya y nazarin jikin tsaunin da kyau, kawai sai yai tsall ya
kama tsaunin ya ci gaba da hawa kansa tamka Kadangare na tafiya akan katangar duwatsu.

Saboda mamaki Sharlisa bata san sa'adda mike tsaye ba ta ci gaba da kallonsa domin ta se
cewa ita kanta da ta saba da hawa wannan tsauni za ta iya yi masa irin wannan hawan ba.

Cikin kankanin lokaci Yarduza ya isa ka tsaunin yaje daf da Sharlisa ya tsaya yadda har suna
iya jin numfashin juna ya ce, "Ya ke Sharlisa ki saki jikinki da ni, ki tuna cewa ke 'yar uwata ce ta
jini, kuma na yi gadon mahaifina a komai.

Kamar yadda mahaifina ya Kaunaci mahaifinki a matsayin dan uwansa guda daya jal da ya
rage a duniya, dole ne nima na kaunace ki haka, ba zan taba cutar da ke ba.

Kamar yadda kika taso baki girma tare da mahaifiyarki ba, nima haka na taso ban san ta ba. Ya
zama wajibi a gareni na tausaya miki a rayuwa. Ina mai sanar da ke cewa na amince da
sharadin da kika gindaya mini, don haka yanzu a shirye nake ki dauko mahaifinki mu tafi da shi
izuwa can gidan sarauta domin ki cika masa burinsa.

Idan ma zai iya ci gaba da tafiyar da harkokin mulki ni mai iya hakura da mulkina ne na bar
masa".

Koda Sarki Yarduza yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa Sharlisa, nan take taji ta kamu
da tsananin son Yarduza, bata san sa'adda ta rungumeshi ba.

Tsawon 'yan dakiku suna manne da juna, sannan Sharlisa ta janye jikinta daga cikin nasa suka
fuskanci juna ta ce, "Ya kai Yarduza, kayi sani cewa mahaifina ya bani labarin mahaifinka da
duk irin kaunar da ya nunawa mahaifina ammad ya ki yarda da shi saboda kishi da bakin cikin
cinye shigasa ta neman karagar mulki.
A ullum idan mahaifina ya tuno mahaifinka sai ya yini yana kuka da bakin ciki b rabuwarsu.
Kafin na kaika inda mahaifina y yanzu shin za ka iya sanar dani yadda aka yi ka ko ni wace ce
bayan mun rabu?"

Koda jin wannan tambaya sai Yarduzay murmushi ya ce, "Ba wani bane ya sanar da komai
akanki ba face Ubangijina da nai bautawa".

Da jin haka sai Sharlisa tayi ajiyar zuciya, tay shiru bata kara cewa komai ba. Daga can kumas
ta dago kai ta dubi Yarduza ta ce, "Wai shin me ne sunan ubangijin naka, kuma ta ya ya kake
bau masa?".

Koda jin wannan tambaya sai Yarduza y hade rai sannan ya ce, "Babu wanda zai iya sanz
amsar wannan tambaya taki face wanda aka don masa hular mulkin Birmin Karluza, ya zama
Cikakken Sarki ta hanyar cancanta. Kin ga ke ne har abada ba za ki ji amsar wannan tambaya
b
face idan kece kika zama Sarauniyar Karluza. Yanzu sai mu tafi izuwa inda mahaifinki yake
mu daukeshi mu tafi can fada domin yanzu haka fadawa da mutanen gari suna jirana".

Ba tare da garamar komai ba Sharlisa ta sauko daga kan tsaunin, Yarduza ya biyota da sauri.

Kawai sai ta dubeshi ta ce, "Duk abinda ka ga nayi, kaima ka yi".

Gama fadin hakan ke da wuya sai ya ga ta daka tsalle sama, ta kamo jijiyar bishiya. Jijiyar ta
tafi da ita a sama shuu! izuwa kan saman wata bishiya.

Cikin zafin nama shima Yarduza ya daka tsalle ya kama jijiyar tayi sama da shi ya dira a inda ta
dira.

Haka suka yi tayi, duk inda ta dauke sawunta sai nasa ya dira, har suka isa inda bishiyoyin nan
suke masu duhuwa. Suka kutsa ta cikinsu suka isa dakin da Kuraisu ke ciki.

Hakika Yarduza ya yi matukar mamakin yadda aka yi dan adam ya rayu a wannan wuri tsawon
shekara da shekaru, domin wuri ne mai ban soro, mai kwarjini wanda babu wanda zai taba
tsammanin cewa akwai mutum a cikinsa.

Da shigarsu cikin dakin sai Yarduza ya yi arba da Kuraisu tsaye a tsakiyar dakin ya kura masa
idanu, idanunsa cike da kwalla.

Mu hadu a littafi na 5 don cigaban labari
08137237071

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login