Showing 1 words to 3000 words out of 7219 words

Chapter 1 - ALLON SIHIRI Book 5 Compelet by Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

ALLON - SIHIRI
Littafi na Biyar (5)
Part A

Ku ziyarci Shafin www.rumbunlabarai.com domin samun littattafai masu daɗi da debe kewa

__LOKACIN DA Yarima Mangul da Barde Ruhaisu
suka
ruguntsume da azabbaben yaki mai tsananin
muni,sai wani abin mamaki ya afku domin kuwa
gashi a zahiri Yarima Mangul yafi barde Ruhaisu
karfin damtse da iya yaki,domin da kyar ma
barde
Ruhaisun ke iya kare saransa saboda nauyin
saran,amma da yake Barde Ruhaisu nada
matukar
zafin nama gami da juriya da mugun naci sai
Yarima
Mangul ya kasa cutar dashi.Saida suka shafe
sa'a
guda cur suna wannan mugun artabu amma
dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin dayan
ba.Al'amarin daya fusata su kenan kowa yaja da
baya suka tsaya suna kallon kallo suna haki
kamar
zakaru.Koda Yarima Mangul ya karewa Barde
Ruhaisu kallo ya fahimci cewar ba sa'ansa bane
a
kallah Barde Ruhaisu zai iya girmarsa da tazarar
shekaru kusan goma sai takaici ya kamashi yaga
cewa ai yakamata yayi ace tuni ya gama da
wannan
JARUMI tunda yafishi kuruciya,idan kuwa kafi
mutum
kuruciya zaka iya finsa kuzari,saidai kawai ya
nuna
maka tsohon kashi.Gama aiyana hakan keda
wuya
sai Yarima Mangul ya daga hannunsa sama yana
mai baiwa dakarunsa inkiyar su afkawa su barde
Ruhaisu.Ai kuwa shima Barde Ruhaisu sai ya
baiwa
nasa dakarun umarnin su taresu.Nan fa kowacce
RUNDUNA ta ruga da rugu izuwa kan dayar ana
haduwa a tsakiya aka ruguntsume da azababben
yaki.Karar karafa gami da ihun mazaje ya cika
dajin
gaba daya.Jini ya rinka fallatsi da fantsama sai
gashi
al'amarin ya rinciba a tsakanin dakaru dubu da
guda
dari.Kodaga nesa ne mutum ya zuba ido yana
ganin
abinda ke faruwa bazai iya gane bangaren
mutum
zai zuba ido da kyai a cikin lura zai gane cewa
anfi
ragargazar dakarun Yarima Mangul.Lokacin da
aka
fara wannan gumurzun ne Yarima Mangul ya
sami
damar matsawa kusa da inda Yazarina ke
tsugunne
saboda duk Badakaren Barde Ruhaisu da yazo
gabansa kwaf daya yakeyi masa.A lokacin Barde
Ruhaisu ya shiga cikin tsakiyar dakarun Yarima
Mangul yana ta ragargazarsu yana yi musu sarki
ya
hana dawa tsayuwa.Hakan ne yasa ya sha'afa ya
bar
daidai wajen da Yazarina ke tsaye.A wannan
lokaci
da yakin yai tsamari ne Yazarina ta dimauce
kuma ta
firgice saboda wannan ne karon farko a
rayuwarta
da akayi yaki a gabanta.Koda taga an sare wani
Badakaren ya fado a gabanta jininsa yai feshi
akan
fuskarta bata san sa'adda ta kurma uban ihu ba
ta
daka tsalle sama.Faruwar hakan keda wuya sai
rawanin fuskarta ya subuce ya fadi
kasa.Kyakkyawan
dogon gashin kanta ya tarwatse a sama ya zubo
kasan kafadunta.Koda Yarima Mangul yayi arba
da
fuskar Yazarina yaga itace sai ya kamu da
tsananin
mamaki ya daka tsalle sama ya dira a bayanta
yasa
takobinsa a wuyanta ya ritsata kuma ya daka
tsawa.Take aka daina yakin kowa ya juya ya
dubeshi.Take aka daina yakin kowa ya juya ya
dubeshi.A sannan ne Barde Ruhaisu ya hango
abindake faruwa sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun.Yarima Mangul ya bushe da dariyar
farinciki a
lokacin daya dora yankakken hannunsa akan
kafadar
Yazarina ya sumbaci wuyanta yace,marhaban da
ganinki ya abar kaunata.Tabbas nayi matukar
farin
cikin sake saduwa dake a wannan lokaci da ban
taba
zata ba.A tsammani sai na karbi karagar mulkin
ubana sannan zan sami damar sake ganinki na
kashe mijinki Lubainu koda yana raye domin na
mallakeki amma sai gashi yanzu na sameki a
banza
ba tare da wata matsala ba.Ki sani cewa yanzu
ina
gama kashe wadannan abokan tafiya naki zan
tafi
dake can sansani na a daura mana aure bisa
dole..Kafin Yarima Mangul ya gama rufe bakinsa
tuni
Yazarina ta tofa masa yawu a fuska sannan tace
karyarka tasha karya saidai ka auri gawata
amma
bani ba.Yaza'a yi na auri azzalumin daya lalata
rayuwar wani saboda son zuciyarsa?Ka sani
cewa ni
yanzu bana tsoron mutuwa tunda kasa mijina ya
tafi
izuwa inda zai iya rasa rayuwarsa gaba
daya.Idan
kuwa har Lubainu ya mutu to nima banga
amfanin
tawa rayuwar ba saidai na bishi.Koda Yazarina
tazo
nan a zancenta a lokacin da jikin su Barde
Ruhaisu
duk yayi sanyi sun sauke makamansu kawai suna
kallon abin da ke faruwa tsakanin Yarima Mangul
da
Yazarina cikin alamun tsananin tsoro da
fargaba.Har
izuwa wannan lokaci Yarima Mangul bai cire
kaifin
takobinsa daga kan wuyan Yazarina ba don haka
sai
ya sake bushewa da dariya,kuma yayi amfani da
dan
yatsansa guda daya ya lakuci yawun bakin
Yazarina
data tofa masa akan fuskarsa ya lashe a bakinsa
yace,ban taba jin abu mai zakin yawun bakinki ba
yake MASOYIYATA.Yana gama fadin hakan sai
ya
dubi Barde Ruhaisu ya daka masa tsawa yace
maza
ku bude fuskokinku kaida yaranka kuma ku zubar
da
makamanku ko yanzu nan na shaftare
makogwaron
yazarina.Har su Barde Ruhaisu zasubi wannan
umarni sai Yazarina ta daka musu tsawa
tace,kada
ku yarda ku aikata hakan domin bazai kasheni ba
saboda bashi da burin dayafi ya mallakeni a
rayuwarsa.So yaje kawai ya yaudareku ku zubar
da
makamanku yasa a kasheku a banza.Koda ma ya
kasheni din bani da asara ko nadama,domin
babban
bakin cikina shine ya mallakeni din.Ku ci gaba da
yaki har sai idan karfinku ya kare,domin ku
zamto
masubin umarnin sarki.Zaku iya bude fuskokinku
domin ko baku bude ba su ba yanzu yasan cewa
ku
dakarun sarki Sailur ne.Koda Yazarina tazo nan a
jawabinta sai Barde Ruhaisu da dukkan sauran
yaransa kimanin mutum saba'in suka bude
fuskokinsu kuma suka daga takubbansu sama
suna
masu niyyar cigaba da yaki.Koda Yarima Mangul
yayi arba da fuskar Barde Ruhaisu sai ya jinjin
kai
yace,tabbas babu mamaki domin banda sarki
yakin
garinku da Yarima Lubainu babu wanda zai iya
tarata muyi GUMURZU na tsawon wannan lokaci
ba
tare dana sami nasarar hallakashi ba face kai.Ai
kuwa dayanmu bazai bar wannan
wuri ba a raye saidai a dauki gawarsa!Yarima
Mangul na gama fadin hakan sai ya wurga
Yazarina
izuwa hannun sarkin yakinsa ya cafketa ya
dubeshi
yace,mazaka ka tafi da ita izuwa sansaninmu a
tsareta kuma ka dawo nan tare da dakari dubu
goma.Koda jin wannan batu sai Barde Ruhaisu
ya
falfalo da azababben gudu izuwa inda Yazarina
take
ya kutsa ta tsakiyar dakarun Yarima Mangul yana
karkadesu da karfin sara da suka domin ya isa
inda
sarkin yakin Yarima Mangul yake a lokacin daya
ja
Yazarina da karfin tsiya izuwa kan wani
doki.Koda
ganin haka sai shima Yarima Mangul ya falfalo
da
gudun tsiya da nufin yasha gaban Barde Ruhaisu
ya
hanashi isa inda su Yazarina suke.Koda ya rage
saura baifi taku goma ba tsakanin Barde Ruhaisu
da
Yarima Mangul sai Ruhaisu ya daka wawan tsalle
a
sama ya tsallake Yarima Mangul ya doki gadon
bayan sarkin yakin nasa.Ba shiri sarkin yakin ya
saki
Yazarina ya fadi can gefe daya.Kafin Yarima
Mangul
ya juyo baya da gudu yazo ya riskesu tuni Barde
Ruhaisu ya daka tsalle sama ya haye dokin dake
gabansa.Kawai sai ya mikawa Yazarina
hannunsa ta
kama ya dagota sama cak ya dorata a bayan
dokin
kuma ya zaburi dokin da gudu izuwa cikin
daji.Koda
ganin haka sai shima Yarima Mangul ya ruga
izuwa
inda nasa dokin yake ya daneshi kuma ya
zabureshi
da gudu yana mai bin bayan dokin su
Ruhaisu.Nanfa
filin yakin ya watse kowacce runduna hankalinta
ya
tafi izuwa tafiya neman shugabanta tamkar ma
an
manta mummunan yaki da ake fafatawa.Lokacin
da
Barde Ruhaisu ya sami nasarar gudu da Yazarina
akan doki suna tsala gudu a cikin daji ba tare da
sanin inda suka dosa ba sai suka jiyo sukuwar
doki
a bayansa.Cikin firgici Yazarina ta waigo baya
kawai
sai taga ashe Yarima Mangul ne ya biyosu kuma
tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku ashirin
da
biyar ba,kuma dokin nasa gudun bala'i yake yi
yana
rike da linzaminsa da lafiyayyen hannin nasa sai
dada zungurar dokin yake da kafafunsa yana kara
masa kaimi ga zabgegiyar takobinsa rataye a
bayansa.Cikin tsananin firgici Yazarina ta juya
tace,yakai Ruhaisu kayi sani cewa wannan
azzalumin
makiyi makiyin namu yana daf da riskarmu.Koda
jin
haka sai shima Barde Ruhaisu ya karawa nasa
dokin
kaimi.Nanfa dawakan suka cigaba da kasa
mugun
gudu,tseren gudu na ban al'ajabi.Koda karfin
gudun
dokin Ruhaisu ya karu sai Yazarina taji tana
neman
fadowa kasa don haka ba shiri tasa hannayenta
biyu
a zagayen cikin barde Ruhaisu ta rukeshi gam
gam
da kyau ta kwantar da kanta akan gadon
bayansa.Haka dai aka cigaba da wannan tseren
gudu
na tashin hankali har izuwa tsawon sa'a
guda.Kwatsam sai dokin Barde Ruhaisu dana
Yarima
Mangul din suka iso wani wuri mai tudu wanda
basu
ankara dashi sukayi tuntube suka zube kasa
gaba
dayansu har su Barde Ruhaisu.Cikin gaggawa
Barde
Ruhaisu ya mike tsaye zumbur ya kama hannun
Yazarina ya tasheta tsaye suka sake
ruguntsumawa
da gudu izuwa cikin daji.Shima Yarima Mangul a
dimauce ya mike tsayen da sauri yabi su a guje
suka kasa sabon tseren gudu kafafunsu tamkar
zasu
tashi sama saboda karfin gudu.Faruwar hakan
keda
wuya sai Yazarina ta sare ta fadi kasa kuma a
lokacin tazarar dake tsakaninsu da Yarima
Mangul
bata wuce taku ashirin ba.Koda Yarima Mangul
yaga
Yazarina ta fadi kuma gashi babu makami a jikin
Barde Ruhaisu sai yayi wuf ya zaro sharbebiyar
takobinsa yayi kansu da nufin ya riskesu kafin
Barde
Ruhaisu ya tasheta tsaye ya sare masa
kai.Amma
sai yaga Barde Ruhaisu yayi wuf cikin wani bakin
zafin nama da bajinta ya suri Yazarina tamkar
sillan
karah ya daga ya goyata a bayansa.Ita kuma ta
rukunkumeshi ya cigaba da falfala azababben
gudu.Sai gashi sun ci gaba da tseren gudun nasu
tamkar mai kaya ya biyo barawo.Yarima Mangul
ya
dage iya karfinsa domin ya cimmusu amma sai
abu
ya gagara.Al'amarin daya daurewa Yarima
Mangul
kai kenan ya cika da tsananin mamakin yadda
akayi
ya kasa cimma Barde Ruhaisu duk da cewa yana
fama da nauyin Yazarina wacce ke goye a
bayansa.Barde Ruhaisu na cikin wannan gudu ne
ya
riski wani katon tsauni mai fadi,girma da tsawon
tsiya a gabansa,kuma babu wata hanya da zai
iya
ratsewa tsaunin dole ne yabi ta kansa in ba haka
ba
kuwa saida ya tsaya ya jira isowar Yarima
Mangul
ayi wacce za'ayi.Ta yaya zan fuskanci Yarima
Mangul alhalin babu makami a hannuna?Tabbas
bani da wani zabi wanda yafi na hau kan wannan
tsauni.Ya bawa kansa amsa a cikin
zuciyarsa.Yaba
gama aiyana hakan sai ya hau kan tsaunin goye
da
Yazarina a bayansa yana cigaba da gudun.Shima
Yarima Mangul yana isowa bai tsaya jiran komai
ba
sai yabi shi izuwa kan tsaunin a guje yana ruri da
kururuwa mai ban tsoro,cikin murna domin gani
yake kamar ma ya gama samun nasarar kashe
Barde
Ruhaisu gami da mallakar Yazarina.Nanfa duka
cigaba da gudu akan tsaunin tun sunayi da
karfinsu
da guzarinsu har saida suka sare suka fara
faduwa
kasa suna mikewa da kyar suna haki.Saida suka
shafe sa'a daya da rabi suna gudu gudu,tafiya
tafiya
akan tsaunin sannan suka iso can kokoluwar
karshensa.Koda Yazarina Da Barde Ruhaisu suka
leko kasan tsaunin wanda saboda tsananin nisan
zurfinsa mutum baya iya hangi abinda ke xan
kasan
nasa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,a
lokacin
da suke ta fama haki saboda tsananin gajiya
tamkar
ransu zai fita.A daidai wannan lokaci ne shima
Yarima Mangul ya iso kusa dasu da kyar yana
haki
da layi rike da takobinsa.Koda yaga cewa ai sun
iso
karsshen tsaunin sai ta dubesu ya bushe da
dariyar
farin ciki duk da cewa makogwaronsa a bushe
yake
saboda muguwar kishirwa gashi babu ruwa a
kusa.Suma su Yazarina haka suke jin tsananin
kishirwa tamkar zata kashesu domin yawun
bakinsu
ma daukewa yake
kamar babu shi.Yarima Mangul ya gyara
tsayuwarsa
irin ta wadanda suka sami nasara ya dora
zabgegiyar takobin tasa kan kafadarsa ya dubesu
cikin izaa yace,yanzu kuma ta yaya zaku iya guje
mini tunda gashi kunzo makura?Tabbas yanzu
zan
kasheka yakai Barde Ruhaisu,amma fa ka
burgeni
domin kayi jarumtakar da ban taba zaton kana da
ita
ba,kuma dole ne na rubutaka a cikin KUNDIN
TARIHIN rayuwata,saidai kash,jarumtakarka taka
ta
zama ta banza tunda baka cika aikin sarki Sailur
ya
baka na kare Yazarina kuma gashi zaka mutu a
banza.Koda Yarima Mangul yazo yazo nan a
zancensa sai Barde Ruhaisu ya tari numfashinsa
yace,kaicinka yakai wannan azzalumin dan sarki
wanda rayuwarsa ta gama tarwatsewa.Ka tuna
cewa
ka rasa masoyiyarka yazarina kuma ka rasa
abokinka amininka YARIMA LUBAINU,Kuma ka
cutar
dashi bisa son zuciyarka don kawai ka rabashi da
wacce ya riga ka SO da KAUNA kun zama
ABOKAN
GABA!Yanzu gashi ka rabu da mahaifinka ka rabu
da
matsayinka na Yarima tunda Mahaifin ya zama
abokin gabarka,kana hada runduna ta YAN
TAWAYE
domin kaje ka kashe shi,kaga kenan kai yanzu
abin
tausayi ne tunda baka ga tsuntsu ba bakaga
tarko
ba.Baka da komai bakada kowa sai mafarkin
zuciya
wanda ina tabbatar maka da cewa har abanda ba
zai
taba tabbata gaskiya ba.Da wannan furuci nake
yi
maka bankwana domin ko zaka sami nasarar
mallakar Yazarina saidai ka mallaki
gawarta.Nima
saidai ka tusa gawata amma ba dai ka kasheni
da
hannunka ba!!!Barde Ruhaisu na gama fadin haka
sai ya juya da sauri ya daka tsalle ya fado kasan
wannan tsauni mai zurfi shi da Yazarina suka
kurma
ihu saboda sun san cewa mutuwarsu ce tazo.
Just now · PublicALLON-SIHIRI
Littafi na Biyar (5)
Part B
Suka kurma ihu saboda sun san cewa mutuwarsu
tazo.Shi kuwa Yarima Mangul sai bakin ciki ya
turnukeshi ya durkuse kasa bisa guiwoyinsa
sannan
ya wangame baki shima ya kwarara uban ihu
kuma
ya fashe da matsanancin kuka saboda yasan
cewa
shike nan har abada bazai sake ganin Yazarina a
raye ba.Kafin Yazarina da Barde Ruhaisu su kai
rabin nisan tsaunin tuni sun sume saboda karfin
iskar dake kadasu da kuma jirin daya kwashesu
don
haka sa'adda suka iso can karshen tsaunin sun
zama tamkar gawarwaki sai ji kake tunjum...!sun
fado cikin kogi.Lokaci guda suka nutse kasa
amma
sai suka taso sama igiyar ruwa ta rinka kadasu
cikin
tsananin sa'a da rabon sauran rayuwa ta kaisu
can
gefe kogin ta watsar.Saida suka shafe kusan
rabin
sa'aa kwance a gefen kogin a sume basu
farfado
ba,iska mai sanyi ce ta rinka kadawa a wajen ta
yadda utace ta zamo sanadin farfadowarsu daga
dogon suman da sukayi.Koda suka bude
idanunsu
suka kalli juna suka tabbatar da cewa suna raye
basu mutu ba sai suka kamu da tsananin mamaki
suka kama kyalkyala dariya.Saboda tsananin
farin
ciki Yazarina batasan lokacin data rungume
Barde
Ruhaisu ba.Faruwar hakan keda wuya ta tuna
cewa
ita fa matar Yarima Lubainu ce,kawai sai tayi
saurin
janye jikinta daga cikin na Barde Ruhaisu ta
sunkui
da kanta kasa ta budi baki cikin rawar murya da
kunya tace ka gafarceni.Take shima Barde
Ruhaisu
yaji kunya ta lullubeshi yama rasa abinda zaice
da
ita.Kawai saiya juya mata baya ya fada kogin
tunanin
abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi
yana
mamakin al'amarin da ya kasance hakan.Wannan
shine abinda ya faru tsakanin Barde Ruhaisu Da
Yazarina a lokacin da suka baro Birnin Zamrul
domin neman Yarima Lubainu.
쇼쇼쇼 쇼쇼쇼 쇼쇼쇼
AL'AMARIN SU Bakon Jarumi kuwa lafiya sumul
suka kwana a cikin fadar Boka Darbusa kuma
dukkaninsu suka wayi gari cikin koshin lafiya ba
tare
da fuskantar wata matsala ba.Da sassafe bakon
jarumi da bawansa Dazyan suka shiga daji suka
farauto wani katon tsuntsu suka zo suka fisgeshi
sannan suka gasashi.Da naman wannan tsuntsun
kowa yayi kalaci.Bayan an gama kalacin ne
bakon
jarumi ya dubi Dazyan yayi masa inkiya shi kuwa
sai
ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima
Lubainu
da Sarki Darmanu yace,yaku abokan
tafiya,maigidana yace na gaya muku cewa zamu
cigaba da tafiya gaba dayanmu izuwa kogin
BAHAR
IMFALkamar yadda akayi alkawari da farko
domin
ya nuna muku karfi da iko na ubangijin musulunci
amma badon ya yarda da tsafinku ba.Zai baku
dama
ku tsirar da rayuwarku da karfin ababan bautarku
da
karfin sihirigami da karfin damtsen ku har sai
yaga
kun kasa kare kan naku sannan zai taimakeku da
taimakon ubangijinsa.Yace na dada jaddada
muku
cewa idan fa har aka isa can kogon Bahar Imfal
aka
samo abinda akaje nema da taimakonsa to dole
ne
ku karbi addininsa ko kuna so ko bakwa so,in ba
haka na kuwa zaku zamo abokan gabarsa babu
abinda zai rabaku face yaki!Daga yanzu zai ci
gaba
da ajiye ALLON SIHIRI a wajensa har izuwa
wannan
lokaci don haka tun yanzu kuna da sauran damar
da
zakuyi shawara bisa abinda kuke ganin cewa
shine
zai fissheku.Koda Dazyan yazo nan a zancensa
sai
su Yarima Lubainu suka dubi junansu suka rasa
abinda zasu ce kawai sai Yarima Lubainu yajasu
gefe daya ya dubesu cikin nutsuwa yace,abinda
nake
so daku shine,kada dayanku ya bigire sharadin
wannan bakon jarumi domin yanzu a hannunsa
muke sai yadda yayi damu,idan muka ce zamuyi
masa tawaye dayanmu bazai tsira da rayuwarsa
ba
bare ya cika burin rayuwarsa.Ko kuwa akwai mai
korafi a cikinku akan wannan shawara dana
kawo?
Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul
Sauwara da sarki Darmanu suka budi baki a
lokaci
guda sukace bamu da wani korafi face bin
sharadinsa.Dajin haka sai farin ciki ya lullube
Yarima
Lubainu yaja su suka koma wajen bakon jarumi
ya
sanar dashi cewa sun amince da dukkan
sharadinsa
kuma basu da wani korafi.Da jin haka sai bakon
jarumi ya mike tsaye ya dubi Dazyan yayi masa
zancen kurame shi kuma ya dubi su Yarima
Lubaiun
yace,shugabana yace kowa ya debo kayansa
zamu
cigaba da tafiya yanzu.Dajin haka sai kowa ya
ruga
izuwa cikin fadar Boka Darbusa ya dauko jakar
guzurinsa ya dora akan dokinsa kuma ya hau kan
dokin nasa ya zauna.Saida kowa ya gama
kimtsawa
sannan bakon jarumi ya hau nasa dokin ya wuce
gaba,Dazyan ya jere dashi.Sarauniya Akisatul
Sauwara ce ke biye dasu sannan Yarima
Lubainu,Sarki Darmani ne na karshe.A wannan
lokaci bakon jarumi ya lullube ALLON SIHIRI a
cikin
wani babban mayafi ya dora akan wuyan dokinsa
ya
daureshi tamau.Ana fara yin wannan tafiya ne
sarauniya Akisatul Sauwara ta waigo ta dubi
Yarima
Lubainu sai taga ya sunkui da kansa kasa yana
tunani mai zurfi.Koda ganinsa a wannan hali sai
ta
tsayar da dokinta har saida taga ya iso daf da ita
sannan suka cigaba da tafiya a tare a jere,a
sannan
ne ta dubeshi cikin alamin tausayawa tace,yakai
Yarima menene yake damunka ne?Tun jiya na
lura
da kai baka yin magana sosai,kuma baka cin
abinci
kamar yadda ka saba,sannan ko yaushe sai naga
kayi shiru kana tunani mai zurfi ina dalilin hakan?
Koda Yarima Lubainu yaji wannan tambaya daga
bakin sarauniya Akisatul Sauwara sai ya kawo
gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubeta
yace,yake wannan sarauniya mai daraja,kiyi sani
cewa tun jiya ne naji zuciyata tana yawa bugawa
da
karfi haka kawai ba tare da nasan dalili
na,sannan
kuma a daren jiyan nayi wani mafarki mai ban
tsoro.A cikin mafarkin an nuna mini katon bakin
kumurcin maciji yana bin inuwata da gudu a cikin
daji har inuwar rawa tana yin tuntube tana
faduwa
amma a karshe
sai inuwar tawa ta yanke jiki ta fadi kasa ta kasa
cigaba da gudu har macijin yazo daf da ita ya
fasa
kai.Yana shirn saranta ne na farka daga barci a
cikin
daren naji jikina na kyarma saboda firgita danayi
kuma gaba daya jikina a sannan ya jike sharkaf
da
gumi tamkar abinda na gami a mafarki ya faru ne
a
gaske.Lokacin da Yarima Lubainu yazo nan a
zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi
ajiyar
zuciya sannan tace,indazaka tuntubi bakon jarumi
akan wannan mafarki naka da zai iya gaya maka
fassararsa.Koda jin haka sai mamaki ya kama
Yarima Lubainu yace yaya akayi kika san cewa
ya
iya fassara mafarki alhalin bashi da bakin yin
magana?Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ji
nayi
wancan bawan nasa dan wada Dazyan ya bashi
labarin wani mafarki dayayi shi kuma ua fassara
masa mafarkin a cikin yaren kurame,al'amarin
daya
bani sha'awa kenan na tambayi Dazyan nace
yakai
Dazyan naji kana gayawa shugabanka cewa kayi
mafarkin wata kaza wacce tayi kwaikwaye biyu
kala
daban daban.Kwan farko data sako FARI ne fat
na
biyu kuma JA ne,kawai sai tayi kwanci akan farin
ta
kyankyashe UNGULU da kuma tayi kwanci akan
jan
saita kyankyashe ZABUWA.To waishin menene
fassarar dayayi maka akan wannan mafarki
naka?
Lokacin da Dazyan yaji wannan tambata dana yi
masa sai yace,fassarar da maigidana yayi mini
itace,Allah ne yakeyi mini nuni dana nutsu nayi
hankali da duniya.Wannan kasa itace
duniya,kwan
farko ya kasance FARI shine hali nagari idan
mutum
ya rikeshi zuciyarsa zata zama fara mara
mugunta
da kyakkyawan nufi.Kwai na biyu data
kyankyashe
wanda shine JA alama ce ta mugun hali.Ai bakaji
karshen mafarkin nawa ba saboda a cikin yaren
kurame na karasa bashi labari.Cigaban labarin
kuwa
shine,bayan kazar ta kyankyashe kwaikwayen
biyu
sai unguku taka jewa.Koda tazo giftawa ta gaban
zabuwar sai zabuwar ta cafko kanta ta gutsure
mata
kai,kuma ta hau bayanta ta zauna.Wannan alama
ce
ta cewar mutane a yanzu sunayin UNGULU da
KAN
ZABO!Ma'ana idan sukaga yan'uwansu masu
kyawawan halaye sai su jasu a jiki kamar suna
koyi
dasu,amma a karshe sai suyi amfani da wannan
dama su turmushesu su hallakasu.Sa'adda
maigidana yazo nan a jawabinsa saina dubeshi
cikin
alamun mamaki nace,to yanzu menene matakin
daya kamata na dauka don kada irin haka ta
sameni?Maigidana sai yace,kayi gaskiya,amana
da
rikon alkawari.Idan kayi hakan Allah zai kareka
daga
sharrin dukkan mai son cutar dakai.Koda
Sarauniya
Akisatul Sauwara yazo nan a jawabinta sai
Yarima
Lubainu yaji gaba dayan tsigar jikinsa ta
tashi,take
yaji a cikin ransa cewa lallai akwai alamun
gaskiya a
cikin wannan addina na bakon Jarumi saboda jin
irn
wannan hikima da aka zuba a cikin mafarkin dan
wada Dazyan.Kawai sai Yarima Lubainu ya dubi
Sarauniya Akisatul Sauwara yace,ai kuwa duk
sa'adda muka yada zango zanje na sami bako
jarumi na sanar dashi nawa mafarkin don naji irin
fassarar da zaiyi.Waishin ke bakiji wani abu a
ranki
ba ko a jikinki sakamakon labarin wannan mafarki
mai dauke da dumbin hikima da basira.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta numfasa tace,tabbas naji
gaba
dayan tsigar jikina ta tashi kuma zuciyata ta
daskare
tamkar na tsomata a cikin ruwan kankara.Koda
kin
wannan batu sai mamaki ya turnuke Yarima
Lubainu
yace,ai nima irin abinda naji kenan sak da
naki.Anya
kuwa wannan addini na bakon Jarumi bashi ne
ADDININ GASKIYA BA?Koda jin wannan tambaya
sai
sarauniya Akisatul Sauwara ta gyada kai tace,ai
kuwa ita gaskiya bata buya har abada,idan har
shine
ADDININ GASKIYAR to da sanni zamuga babbar
shaida dazata tabbatar mana da hakan.koda jin
wannan batu sai Yarima Lubainu ya girgiza kai
yayi
shiru bai kara cewa komai ba aka

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login