Showing 1 words to 3000 words out of 4297 words

Chapter 1 - MUTUM DA ALJAN Book 3 By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

".MUTUM DA ALJAN
Littafi Na Uku (3)
Part B.
Author: Abdul aziz M Gini
Rubutawa : Al amin Ahmed Misau
Nickname: Guyson ko shagala
Contack me: 08064594218
Gargadi: Ban yarda wani yayi edit na wannan post ba ba tare da izinina ba..
.
Labari ya isowa Guyson cewa
Face mutum biyo, wato sarki da yarima kamsus
tsawon yan dakiku suna tsaye suna kallon
yadda ake ta shirye shiryen tafiyar dayansu
bai ce uffan ba daga can sai sarki yayi
gyaran murya ya dubeshi a cikin murmushi
yace'' hakika ka baiwa namrita shawara
mai kyau dakace da ita su manta da
batun daukar fansa a kaina''
koda jin wannan batu sai zuciyar yarima
kamsus ta buga da karfin gaske ya firgita
ainun kuma ya kamu da tsananin mamaki
kuma yayi shiru baice komai ba sarki
ya sake yin murmushi a karo na biyu yace
idan namrita da dan uwanta zaihas sun
dauki shawararka sun daina farautar
rayuwata nima zan kyalesu amma nayi maka
alkawarin duk ranar da suka sake yin gangancin
kawo min hari a wannan lokaci zan zare
musu ruhin numfashinsu wannan shine
kashedi na karshe kuma sakone nake baka
yanzu ka isar dashi.
Alfarma daya zan iya yi musu idan har suka
zo gareni bisa lumana zan rokesu gafara
bisa abinda na yi na kashe musu mahaifi
ba akan laifinsa ba
ka sani cewa a ka idar sarauta kisa a wajan
sarki ba laifi bane saidai a kirashi kuskure
saboda duk harkace ta mulki duk sarki
na gari mai cikakken iko da isa gami da
kamala baya durkusawa wani ko da kuwa
dan uwansa sarki ne'
koda sarki Alkasim yazo nan a zancensa
sai ya kwalawa wani hadiminsa mai suna kailub kira
yace maza ka janyo min dokina nan take
kailub ya ruga zuwa inda dokin sarki yake
kafin yazo da dokin tuni sauran hadimai
sunkimtsa sarki sun daura masa damararsa
an kawo masa takalmansa an ajiye a gabansa
ya sanya kuma an shirya masa kayan yakinsa
a jikinsa koda ganin haka sai shima yarima
kamsus ya ruga zuwa nasa tantin ya
shiga kimtsawa da sauri nasa hadimin na taimaka masa.
Lokacin da sarki Alkasim ya gama shiri ya hau
bisa ingarman dokinsa mai launin ruwan
kasa ya zauna saiya wuce kan gaba gaba
daya miliyoyin jama ar dake cikin tawagar
sai suka biyoshi a baya duuuu.... Kai kace
mutanen duniyar ne kaf sukayi hijira
zasu koma wata nahiyar daban'' wohoho''
hakika masu iya magana sunyi gaskiya
da sukace dole ne ace da mijin iya BABA.
domin duk wanda yaga sarki Alkasim a wannan
lokaci saboda kwarjininsa cika idonsa da
kuma irin gagarumar shigar yakin da ya
yi dolene ya tsorata da al amarinsa saboda
ya zama tamkar zaki Uban dawa
kallo daya mutum zaiyiwa sarki Alkasim
yaji zuciyarsa ta buga da karfi saboda
kirarsa gaba daya irin ta zakice kaida gani
kasan cewa dolene ya kasance masifaffen
kakkarfa hm Guyson nake magana
sarki Alkasim ya kasance dogon mutum
mai murdadden jiki cike da kwanji gami
da jijiyoyi yana da yalwataccen kirji cike
da gashi kuma a fuska ya kasance kyakkyawa
abin kwatance amma kusan ko yaushe
fuskar tasa a murtuke take tamkar bai taba
yin dariya ba
tabbas barewa bata gudu danta yayi rarrafe
yarima kamsus ya gado mahaifinsa a sura da cikar zati sai dai
zuciyarsa bata da tauri irin ta mahaifinsa
ma ana yafi sarki Alkasim walwala da annurin
fuska kuma ya fishi tausayi gami da jin kai,
sai dai suna tsananin kama da junansu
tamkar hassan da usaini kawai shekaru ne
ya banbantasu gami da tsohon kashi
shidai sarki yana da saje mai kauri gemu
mai tsawo da gashin baki mai yawa shi
kuwa yarima kamsus bash da saje da gemu
sai dan siririn gashin baki wanda ya yiwa
lebensa da habarsa kawanya abin gwanin
ban sha awa kuma ko yaushe yana tattare
dogon gashin kansa ya tattareshi ya daure
su zube bisa gadon bayansa yan matan kasar
birnin misra da yawa sun dimauce a cikin
soyayyar yarima kamsus saboda kwarjininsa
kyawunsa da kuma baiwarsa ta jarumtaka
kai wasu ma saida suka zama kamar zautattu saboda
yawan begensa da ambatonsa amma ba a taba samun
wacce ta burgeshi ba bare ma yayi soyayya
shi kansa a halin yanzu da yaji zuciyarsa na begen
jaruma namrita kamuwa yayi
da tsananin mamaki har yana
tambayar kansa a cikin zuci yana mai cewa
akan wane dalili nake tunanin namrita
alhalin na sha haduwa da matan da suka fita kyau
matsayi da daukaka amsar da ya kasa baiwa kansa kenan a duk lokacin da wannan tunani ya bijiro masa
to wai shin yadda naji na kamu da son namrita haka itama al amarin yake a ranta kuwa?
Ta yaya zan gane hakan alhalin har yanzu
bamu fito kuru kuru mun bayyanawa junanmu komai ba
ai ita ce ya kamata ace ta fara bayyana min sirrin zuciyarta tunda ni dan sarkine ita kuwa ba yar kowa bace
haka dai yarima kamsus yake ta irin wannan tunani da wasu wasun zuci mara kan gado a duk sa adda tunanin namrita ya bijiro masa.
Kamar yadda sarki Alkasim ya fada haka al amarin ya kasance wato tunda aka fara wannan tafiya babu sassauci ba ayada zango sai bayan kwanaki uku uku kuma dare da rana a cikin tafiyar ake hatta abinci akan ababan hawa ake ci kuma ko bukatace ta kama mutum
ba a tsayawa a jirashi saidai a barshi a baya ya kawai da bukatar idan ya kammala ya ruga da gudu ya riski tawagar
kai ko barci ne ya kama mutum sai dai yayi akan dokinsa ko rakuminsa
ko alfadaransa sau tari sai dai kaji tum mutum ya fado kasa daga kan abin hawansa saboda magagin barcin sai dai ya mike tsaye zumbur a firgice ya sake dane abin hawan nasa
hm Al amin Ahmed Misau Guyson..
Wani babban abin mamaki shine babu wanda yake jin gajiyar tafiyar a jikinsu har sai an yada zango bayan cikar kwanaki ukun .
Haka dai darare suka ci gaba da shudewa har ya zamana cewa saura kwanaki uku kacan a iso birnin sarki masarul anjana
wanda ke nahiyar kasar Sin inda aka yada zango a cikin wani
babban daji wanda ake kira da suna DARUL SAMJUL.
Shidai wannan daji na darul samjul masana matafiya da masu bincike
sun tabbatar da cewa babu wani daji mai girmansa tarin ni imominsa da kuma yawan dabbobi babu tamkarsa a duk fadin duniyar nan don haka yana da hadarin gaske saboda
babu irin kalar mugayen halittun da babu a cikinsa kai sai mafarauci ya cika babban barde yake iya shiga cikinsa yayi farauta inba haka ba kuwa sai dai a dauko gawarsa a ciki
koda aka iso farkon wannan daji sai sarki Alkasim dake kan gaba ya ga dokinsa yayi turjiya
yana mai haniniya gami da daga kafafunsa na
gaba sama kuma yaja da baya kadan cikin
alamun firgici tamkar wanda ya hango
wani mugun abu a gabansa
ai kuwa nan take sauran dawakai
da sauran alfadarai da rakuma
sukayi koyi da wannan doki na sarki aka
rasa dayansu wanda zai kara gaba koda
taku daya ne koda ganin abinda ya faru
sai farin ciki ya lullube sarki Alkasim ya
bushe da dariyar farin ciki a lokacinda
kowa ke firgici aka yi tsit ana kallonsa kawai
cikin al ajabi kawai kuma sai aka ga sarki
Alkasim ya sauko daga kan dokinsa ya tsuguna
kasa bisa gwiwarsa guda ya debi kasa ya shinshina cikin
hanzari da murna ya juyo ya dubi
sarkin yaki da yarima kamsus yace tabbas mun iso
dajin darul samjul dajin da na dade ina
burin son zuwansa domin nayi farauta a cikinsa
maza mu yada zango a nan a kafa tantuna tunda dare ya soma
sai gobe da safe saimuyi shirin shiga farauta cikinsa
yakai sarkin yaki ka zabo manyan jarumai
a cikinmu guda arba in ka shirya mana gasar farauta
a cikin wannan daji na darul samjul lallai
ka sa kanka da yarima a cikin wannan gasar
koda jin wannan batu sai mamaki da tsoro ya
kama gaba dayan jama ar dake cikin wannan tawaga
sarkin yaki da yarima kamsus ne kadaibasu
yi wani gezau ba
Saikuma Ni Al amin Guyson.
Wanda na kasance Jarumi.
Ba komai ne ya firgita jama ar ba face
kowa ya dade yaana jin wannan dajin darul samjul ana cewa komai
hatsabibancin boka ko mafarauci ko kuma jarumi yana shakkarsa
akwai abubuwa masu tsananin wahalar gaske
wadanda ba a samunsu sai a dajin darul samjul
kuma mutane da yawa sun hallaka a kokarin nemo wadannan abubuwa
a cikin dajin
kai ance ma komai yawan ayari kona fatake idan sukazo
giftawa ta cikin dajin darul samjul to sai kaso biyu cikin ukunsu
sun zama gawa kaso dayan ma sai sun kasance
zakwakuran mayaka matsafa da jarumtaka sannan zasu tsira kuma
duk da hakan ma sai da yawansu sun samu mugayen raunuka a jikinsu
ba tare da bata wani lokaci ba aka yada sansani a bakin wannan daji na darul samjul
aka shiga kafa tantuna aka shirya kayayyaki sai dai
mutane da yawa a firgice suke musamman mata hadiman da aka taho dasu
saboda jiyo sautin kukan mugayen dabbobi da tsuntsayen dajin duk da cewa suna can nesa dasu
saboda kukane mai irin wani bakon sauti wanda kunnuwa basu saba ji ba
bayan an gama kafa tantuna anci abinci ana zaune ana hutawa kowa ya samu nutsuwa
yarima kamsus na zaune a cikin tantinsa tare da wadansu kuyangi guda
uku suna debe masa kewa daya daga cikinsa na bashi labari mai dadi
na ban dariya sai ga sarkin yaki ya shigo cikin tantin nasa
koda ganinsa sai kuyangin suka barsu su biyu
sarkin yaki ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya dauko wata
takarda daga cikin aljihunsa wacce akayi rubutu
akan ta da bakar tawada ya mika masa yace ya shugabana
wannan takarda na dauke da sunayan jarunamu guda arba in
wadanda sarki ya umarceni dana zabosu domin shiga gasar farautar daya ce
nau shirya mana a gobe da safe koda jin
wannan batu sai yarima ya karbi takardar da sauri ya fara dubawa inda ya fara yin arba da sunan sarki sannan nasa da na sarkin yaki
a can karshen sunayen kuma da yaga sunayen wadansu jarumai guda biyu wadanda ake kira RAMJUS DA HATYAN sai ya dago kai ya dubi sarkin yaki
cikin mamaki yace saboda me zaka sanya ramjus da hatyan a cikin wannan gasa alhalin suna jinyar raunikan da suka samu a yakin da sarki ya turasu watanni hudu da suka gabata??
Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaki yayi murmushi sannan yace.
Ya shugabana ai duk sun samu lafiyarsu kuma kowannansu ya amsa min da bakinsa
cewar zai iya shiga wannan gasa ba kaga yadda ma suke farin ciki da yin wannan gasar ba
yayina yarima yaji wannan batu sai al amarin ya sake daure masa kai saboda shi dai a saninsa irin raunikan da ramjus da hatyan suka samu ana iya yin shekara guda ana jinyarsa
ya za ayi ace har sun warke a cikin watanni hudu kacal?? Kawai sai yarima ya kada kai ya dubi sarkin yaki yace to menene yanayin wannan gasar ina so naji yadda aka tsarata
sarkin yaki yayi gyaran murya sannan yace abinda na tsara shine gaba dayanmu mu arbain din zamu shiga cikin dajin
darul shamjul a kasa bisa kafafuwanmu mu yi farautar dabbar farko wacce mukayi arba da ita
.
.
Dokar gasar itace ba za a harbi dabbar ba ko kuma a sareta da makami
sai dai a kure mata gudu a kamota da karfin tsiya koda mutum
ya samu nasarar kamata shi kadai sauran jaruman
gasar zasu iya kwaceta daga hannunsa sai dai karfinsa da basirarsa da zafin namansa su kwaceshi
ya dawo da dabbar a hannunsa har izuwa nan sansanin namu shine ya tabbata ya lashe gasar
koda jin sarkin yaki yazo nan a zancensa
sai yarima kamsus yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dubi sarkin yaki yayi masa dan guntun murmushi yace
tabbas ka iya shirya gasa mai matukar wahala aiko sarki da kansa sa ace zata iya bashi nasara a wannan gasa ba wai karfinsa da dabararsa ba
sai dai ka manta da abu guda a cikin gasar
cikin mamaki da doki sarkin yaki yadubi yarima yace menene abin da na manta dashi?
Yarima yace ka manta kace a cikin dokar gasar babu amfani da karfin sihirin tsafi hakanne kadai zai hana sarki dani lashe wannan gasar a saukake
yayinda sarkin yaki yaji wannan batu sai yayi murmushi yace tabbas kazo min da babbar shimfidarsa ya kishingida yace inka fita ka toromin kuyangina suci gaba da debe min kewa saboda bana zaton zan iya yin barci da wuri
sarkin yaki yace haba ya shugabana kai kuwa menene zai hanaka barcin alhalin baka daya daga cikin
masu tsoron wannan daji na darul shamjul?
Yarima yace kaga mai daki shi yasan inda yake yi masa yoyo tafi ka bani wuri dajin haka
sai sarkin yaki ya juyo da sauri ya fice
daga cikin tantinsa fitarsa ke da wuya sai ga kuyangin yarima sun dawo
nan dai sukaci gaba da debe masa kewa har saida suka ga barci ya saceshi sannan suka mike
tsaye suka fice suka tafi izuwa nasu tantin
suna tsegumi da gulma inda daya daga cikinsu ta dubi sauran tace
wai shin anya kuwa yarima lafiyayyen namiji ne ko da jin wannan tambaya sai sauran kuyangin biyu suka bushe da dariya sanna
guda tace kece bakuwa a cikinmu shi yasa baki san halayansa ba to ki sani
mu tare dashi muka taso tun kuruciya yarima bai damu da mata ba kuma bai taba yin soyayya ba mun sha yin barci
tare dashi mu kwana daki guda amma bai taba nuna sha awarsa akan
dayarmu ba akwai ranar da muka taba yi masa
irin wannan tambayar da kikayi mana yanzu
amsar da ya bamu itace ya daukarwa kansa
alkawari cewar ba zai taba sanin wata ya mace
ba face matar da ya aura
koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke wannan kuyanga ta jinjina kai tace ai kuwa duk
macen da ta auri yarima ta gama dace da samun babbar sa a domin ya tara baiwa mai yawa irin wacce mazaje da yawa basu da ita da wannan kami kuyangin suka rufe hirarsu
kowacce ta samu wuri ta kwanta suka kama barcinsu...
.
Nima kuma da wannan kalami nawa Guyson naji barci ya fara neman zuwa sbd haka nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe zamu ci gaba
Amma kafinnan...
Nidinne dai
Al Amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
MUTUM DA ALJAN
Littafi Na Uku (3)
Part C.
Author: Abdul aziz M Gini
Rubutawa : Al amin Ahmed Misau
Nickname: Guyson ko shagala
Contack me: 08064594218
Gargadi: Ban yarda wani yayi edit na wannan post ba ba tare da izinina ba..
.
Labari ya isowa Guyson cewa

da wannan kalami kuyangin suka rufe hirar tasu kowacce ta samu guri ta kwanta
suka koma barci abinsu,lokacin da gari yaw aye da sassafe bayan anyi kalaci
jama’a suka sake taruwa a bakin tantin sarki Alkasim inda aka jere jarumai talatin
da takwas wadanda zasuyi gasar farauta a cikin dajin darul samjul , a cikin wadannan
jarumai hard a sarkin yako, sauran jama ar tawaga kuwa sunyi dandazo a gefe
guda suna jiran fitowar sarki Alkasim ana ta kace nace kowa na fadin albarkacin
bakinsa akan wannan gagarumar gasa da za ayi wasu suna mamakine akan
daliin da yasa sarki ya shirya wannan gasa alhalin ana kan hanyar zuwa birni
n sarki masarul anjana , wasu kuwa suna mamakin yadda aka zabo ,mutum
arba’in kacal alhalin ga jarumai nan da yawa wadanda aka taho dasu dubunnan
don su nuna jarumtakarsu acan birnin sarki masarul anjana domin su burge
gimbiya zulfulaifa ko tayi dariya.Jim kadan sai ga sarki Alkasim tare da dansa yarima kamsus sun fito daga cikin tantinsu.
A wannan lokaci duk su biyun sunyi gagarumar shigar yaki mai matukar
kwarjini daban sha awa wadansu bakaken
rigunan fata matsatstsu masu gajeren
hannu suka sanya gami da dogon wando
shima na fata matsatstse gaba dayan
surar jikinsu ta bayyana a fili takalmin
da suka sanyama fata ne dogaye iya
guiwa masu madauri kowannansu ya rataya
zabgegiyar takobi a bayansa kuma ya
saba kwari a bayansa ga baka ruke a hannunsa.
Wohoho duk wanda yaga wannan da da
uba a wannan lokaci dole ne su burgeshi kuma
dolene su firgitashi saboda yasan cewa su
biyun kacal zasu iya tashin gari guda domin
da gani babu tambaya ansan kura zataci
mutum
Guyson nake magana sunana kenan dan misau
babban abin da zai fi burge mutum shine
yadda kamanninsu tsawonsu da kuma kaurin
jikinsu da surarsu ta zamo iri daya sak
tamkar tagwaye kawai a fuskane za a gane
banbancin shekarunsu
ba tare da bata wani lokaci ba sai sarkin
yaki ya risina ya gaida sarki da yarima kamsus
sannan ya dubi sauran jama ar tawagar
su ma yagaishesu nan take yayi jawabin
yadda za ayi wannan gasa da kuma dokokinta
koda jin hakan sai gaba dayan jama a suka
kama yiwa sarki Alkasim kirari gami da
jinjina ana cewa ai tabbas shine zai lashe
wannan gasa sun manta dani guyson a gefe
nan fa sarki alkasim yaji wani irin farin ciki
gami da girman kai ya shigeshi baisan
sa adda ya kama yin murmushi ba yana dagawa
jama a hannu
a dai dai wannan lokacine yarima kamsus
ya hango jarumi Ramjis da hatyan tsaye a gefe
daya cikin jaruman gasar suna kallon sarki
suna murmushi alamar cewa suna da ja akan
cewa babu tabbacin cewa shine zai lashe
wannan gasa fiye da shekaru ashirin da biyar
baya a birnin misra idan aka yi gasar farauta
ramjis ko hatyan ne daya daga cikinsu ke
lashe gasar saboda dama can sune 'ya'yan sarkin
mafarauta wato gado sukayi ba haye ba
ko sau daya sarki Alkasim ko yarima kamsus
dayansu bai taba shiga wannan gasa ba
don haka yau Al amarin ya zama sabo
ba a san yadda zata wakana ba
kawai sai
yarima kamsus ya baro inda sarki ke tsaye yazo
inda su ramjis ke tsaye ya dubi ramjis yace
tayaya kuka samu lafiyar jikinku da sauri haka
har kuka iya shiga wannan gasa? Koda
jin wannan tambaya sai ramjis da hatyan suka yi yar
dariya sannan ramjis ya dubi yarima cikin
murmushi yace tabbas ya kamata ace mun
samu wata bakwai zuwa takwas muna
jinyar jikinmu kafin mu sake fita yaki ko
farauta amma saboda an shigo fagenmu na
farauta dolene mu fito don kada a yi mana
gori ko kuma a kwace mana matsayinmu
da muka gada tun iyaye da kakanni
koda jin haka sai yarima ya gyada kai yace
gaskiya ne kun burgeni amma kuma kunyi
ganganci domin ko yaya aka fama wannan
rauni naku shi kena9 an dawo daku baya don
sai kun sake maimaita watannin da kuka shude
na warkewa
idan ba zaku damu ba ina son ku kwaye min
raunikan naku na gani
kafin yarima ya gama rufe bakinsa tuni
ramjis da hatyan sun janye kafar wandonsu
sai5a tabon manyan sara akan cinyoyinsu
shi ramjis akan cinyarsa ta hagu aka yi masa
wani lafcecen sara shi kuwa hatyan akan
kaurinsa ne na hagu
gashi dai duka raunukan an dinkesu kuma
saura kiris wajan ya gama kamewa amma
akwai alamun cewa idan aka fama ciwukan zasu
iya dawowa sababbi koda yarima yaga
wadannan raunuka sai ya cika da mamaki kuma
ya fara tunani a cikin ransa cewa abin fa da
yake zargi ba haka bane
ba wani abu yarima ke zargi ba face yana tunanin
cewa ramjis da hatyan basu bane ba a zahirin
suuka shiga wannan gasa jaruma namrita da dan uwanta
jarumi zaihas ne suka juye izuwa kamanninsu
to yanzu dai gashi ya duba da idanunsa yaga
kuma basu bane domin ida sune din da dole
ne ya ganesu saboda wannan rauni da suka
samu tsawon watanni hudu da suka gabata
kafin yarima ya dubi su ramjis ya sake cewa wani abu sai sukaji an

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login