Showing 1 words to 2373 words out of 2373 words
Chapter 1 - TURABAR GASKIYA Part 2 By Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf
TURABAR GASKIYA
Part 2 littafin Yaki
Writing by
MADAKI
"An ya kuwa ya shugaba, amma tun da idanuwanka sun hanga maka ba zan yi maka musu ba,
amina da wuya hakan ta faru, domin ko yanzu na duba duk jama'ar da muka taho dasu."
Yarima Zaiyan ya ce, "Kada ka damu na san ba lallai ka iya gano hakan ba domin dama a boye
take kuma ba zata taba bayyana fuskarta ba.
Da jin haka sai Likita Zauwad ya yi shiru Zaiyan ya yi gaba yana duba yanayin jama'ar da suke
ta faman aikace aikace, shi kuma zauwad na biye da bayansa, duk tantin da suka nufa suka ji
motsi sai Yarima Zaiyan ya ce, "Ayi sallama da na cikin a haka har suka wuce Tantuna kusan
goma, ana sha daya ne, Yarima Zaiyad ya tsaya duk da babu motsin kowa a ciki amma sai
Yarima ya dubi Zauwad ya ce
"Su waye a cikin wannan Tantin.?"
Likita Zauwad ya yi shiru batare da ya ce komai ba. Domin kuwa ya san
cewar Shadilat ce da Lushmaira a cikin, koda Zauwad ya yi shiru sai Yarima ya kara yi masa
tambayar.
Likita ya ce, Babu mamaki su Haisara ce matar Sarkin yaki."
Yarima Zaiyan ya dube shi cikin rashin fahinta ya ce, "Kamar ya ya kana ji, dama akwai wani
tanti da baka san ku su waye a ciki ba.?"
Likita ya dan yi murmushi ya ce, "Ya shugaba abunne da yawa, amma haka ne wannan tantin
Haisara ce, mun kuma barota tana girki a baya."
Zaiyan ya dan matsa kusa da dakin ya ce, "Tun da babu kowa bari na leka domin ina zargin
wani abu daga cikin wannan tanti, yanda ya zama shiru akwai alamar sirrin boye a cikinsa
saboda tunda muka taho nake nazarin tantuna idan babu mazauna cikinsa akwai dalilin akwai
masu zama, amma shi wannan ya yi kurum kamar kurma, dan haka bari na duba.
TURABAR GASKIYA-3
MADAKI
Gadan-gadan Yarima Zaiyan ya nufi cikin Tantin ya leka kansa, shi kuwa Zauwad sai ya yi tsaye
sak domin ya riga ya san a sirin Shadilat da Lushmaira ya gama tunowa, bisa mamakinsa sai
yaga Yarima ya dawo da kansa waje ya ce. "Da mamaki ace, an kafa tanti babu kowa a ciki
haka zalika babu alamar kowa din.?"
Da jin wannan batu sai farin ciki ya kama Likita Zauwad domin ya fuskanci bai yi sa'ar ganinsu
ciki ba, nan ya yi hamdala ya kuma dubi Yarima ya ce, "Babu damuwa zan binciki masu zama a
cikin kafin mu bar gun"
Kafin Yarima ya kara cewa wani abu sai suka ji karar ihun namun dawa daga can bayansu,
koda juyawar Yarima sai yaga an wani zaki ya yi sufa a sama ya nufi wani bangare na da
koramar nan take, batare da ya jira kamai ba sai ya zare makaminsa ya nufi gurın gauan gadan.
Cikin tsananin fusata koda ya isa gurin sai ya daka tsalle ya fada farfajiyar gurin ya yi tsaye cikin
tsananin mamaki domin koda ya isa sai yaga babu komai a gurin sai gawar wata Kada da zaki
da aka soke shi a makoshi.
Nan take mamaki ya cika masa zuciya ya fara waige-waige amma bai ga kowa ba, ya isa inda
zakin yake kwance matacce sai ya lura da mashin tabbas mashin irin mashin da aka sana'anta
shi ne daga kasar su, to waye ya yi wannan aikin.
Ga jini yana zuba daga jikin zakin ita kanta Gadar jini ne yake malala a jikinta alamar yanzu
yanzu aka aika dasu barzaho.
Nan take zargi ya shiga ransa ya fara kewaya gurin sai da ya kusa rabin sa'a yana zaga bakin
ruwan nan amma bai ga kowa ba, a sannane Likita Zauwad ya kara so gurin shima ya taya shi
dubawa. Ha yarima Zaiyan ya juya zai bar gun sa kawai ya hango wasu suturu a maƙale a jikin
wata bishiya
Koda ganin wadannan suturu sai mamaki ya kama shi take ya nufi suturun ya saka hannun ya
dauka kayan mata ne dogayen riguna irin na matan da suka fito da su, nan take hankalinsa ya
dugunzuma ya nunawa Zauwad kayan ya ce.
"Shin za ka iya shaida masu wannan kayan.?
Zauwan ya girgiza kai cikin alamun rashin sani ya ce, "Ya shugaba tabbas kayan kaya ne irin na
matan da muka zo da su, amma ba zan tantance kayan wacece ba.
Zauwad ya gane ko wane kayane ba kayan kowa bane face kayan Lushmaira nan da nan
shima ya shiga tsananin mamaki ya dubi Yarima ya kara da cewa "Abinda ya kamata, yanzu ka
shaida kayan ko wacece zata zo ta dauka ka ga idan ka gansu a jikinta zaka ganota watakila ita
ce wacce kake zargi da satar hanya ta biyo bayanmu."
Koda jin wannan ba tu sai Yarima Zaiyan ya girgiza kai ya ce, "sam haka ba zai yiyiwu ba domin
kuwa idan na bar kayan nan a nan dole zata dauka ta canza musu kama, amma yanzu idan na
tafi dasu, koda a ce wacce ta biyo ce dolenta ta hakura ta koma tunda ba zata ci gaba da biyo
mu tsirara ba, koda ma ta biyo m farat daya zamu shaidata dan haka mu wuce mu koma cikin
al'umma"
Koda gama fadan haka Sai Yarima ya yi gaba abinsa shi kuwa Zauwad sai ya bi bayansa cikin
matsananciyar damuwa da mamakin Lushmaira da ta iya karawa da wannan narkekiyar
dabbobin masu hadarin gaske.
Al'amarin Sarki Abu Zaiyan kuwa tun sa'ar da ya nufi saman tsauni ya ga wasu dakaru da
Sarkin yaki Safwan ya barsu dan su kula da lafiyar tsaitsaye sai
kasa, koda saukar su sai Sarki ya dubi can nesan saman tsauni sai ya lura a she wasu gungun
Zakuna ne sun kai kimanin sun goma sun yi cirko cirko suna kallonsu, ashe abinda ya hane su
da zuwa inda wadannan dakaru suke ganin dogayen masu a hannunsu dan haka suna sauka
sai suka tada jijiyoyin wuya suka fara harbin iska suna gurnani."
Shi kuwa Sarki da yaga haka sai ya fasa shiga cikin tantin ya tsaya yana dubansu, duk irin
jarumtaka da Sarki yake takama da shi sai da ya ji shakkar wadannan zakuna domin kananun
cikinsu zasu iya kai girman dan marakin jaki, kuma su biyu ne kananun sauran manya kuwa
kowanne zai iya kai girman bajimin Sa.
Babu abinda yafi abinda yasa ya kara jin shakkarsu sai ganin yanda suke bude bakunansu
wasu irin tsaratan kaifafan hakura suna haskaka masa fuska,
ga wani yawu yana dalala, koda suka kusa kara sowa sai ya duba jikinsa ashe ya sha'afa ko
'yar karamar wuka bai hawo da ita ba.
Aikuwa sai suka kara kaimi suna zagaye shi, wannan al'amari ba karama tada hankalin Sarki ya
yi ba amma saboda tsananin jarumta sai yaki ya sauka kasa ya nemi agajin dakarunsa, duk da
cewa yasan daga inda yake zuwa saman tsaunin akwai nesa sosai, bare ma ko ba nisa ba zai
taba neman taimakonsu ba, nan take sai ya sauke ajiyar zuciya ya dubesu kwanon abincinsa
da ya taho dashi sai ya ajiye shi a gefe.
Ya murda jikinsa ya bada wani sauti karas. Kafin ya yi aune wadannan Zakuna sun taso masa
haikan kuma su duk.
Cikin tsananin zafin nama shima ya yi kansu, nan take suka kaceme suka hargitse da tsananin
hargitsi mai munin gani, duk irin wannan gunji da suke
jama'ar kasa basa ji duk da cewa Sarkin yaki Safwan yana zaune a kasan domin ya tabbatar da
tsaro amma koman basa jin sai shiru da yalwata a tumaninsu ma yanzu haka Sarki ya yi barci
Abin da basu sani ba ashe Sarki na can yana artabu da zakuna masu tsananin jin yunwa da da
kishirwa, dama haushinsa suke ji sun zo sun mamaye musa guri.
Da farko Sarki ya fara kokarm wajen kai musu bugu da hannunsa amma da tsamari ya kai
tsamari sai ya fara tsille musu, domin koda ya doke su sai sun yage shi a hannunsa, ko kuma
su bangaje shi wanda idan suka bangaje shi sai ya ji kamar wani katon dutse ya bangaza, dan
haka cikin kankanin lokaci suka dimauta shi suka dugunzuma masa lissafi.
Ya yi danasanin rashi zuwa Takobi domin da akwai takobi a tare das da tuni ya gama dasu, ko
mai gama da su
ba da tunanin su faman jin tsananın azaba Babbar cikinsu ita ce mai tsananin dabara yaki da
iya fada, domin sai kananun sun yunkura suna fafatawa dashi, sai ita kuma ta ja da baya ta
dako tsalle sai dai ya ji ta bangaje shi, haka nan suka dinga wannan dabara har Sarki ya fara
fita daga haiyacinsa.
Da kyar ya samu ya kama Wata zakanya da ta take kokarin cafkar masa hannun ta cinye ya yi
tsalle ya dokar mata fuska, ta yi wata kara ta kara nufo shi ya kara yin karfin hali ya kara
nausarta nan take ta yin laushi, amma saboda tsananin naci sai da ta kara nufo shi koda ganin
irin wannan taurin ran nata sai ya shammace ta na zuwa ya dagata sama ya cillata can nesa da
nan take ta rikito izuwa kasa gurin wannan koramar ruwa da Gimbiya Lushmaira take
A Lushmaira wannan lokaci Gimbiya da Shadilat suna boye a
Jiikin katangar tsaunin nan sai kawai suku ga wannan zakin ta rikito Rasa kuma ta fadi kasa
matacciya, sai hankalinsu ya yi sama suna daga kawunansu sai suka hango Sarki Abu Zaiyan
yana fafatawa da Zakuna a lokacin da ya yi tsananin jigata da kyar yake iya daga hannu ya kare
kansa, nan take suka daka salle suka dauke makamansu suka haye saman tsaunin da gudun
gaske.
Koda suka isa tuni Sarki ya gama galabaita ya zamana da kyar yake iya bude idanuwansa,
koda suka hawo saman tsaunin sai suka farwa wadannan Zakuna da suka da sara kafin kace
meye wannan tuni sun karar dasu, lokacin da suka gama yakar wadannan dakaru Sai Shadilat
da Lushmaira suka nufi hanyar sauka dan kada Sarki ya gane su domin ko a lokacin da suke
kwafsawa da wadannan Zakuna suna yi suna rufe fuskokinsu.
Har sun bi hanyar sauka sai
Sarki ya ce "Ku dakata ya ke 'yata."
Koda suka ji maganar Sarki suka tabbatar ya gane su sai suka tsaya suka jiyo a hankali da
yake a lokacin Shadilat ta cire dankwalin kanta ta bawa Gimbiyar Lushmaira ta yane jikinta dasu
dan haka ba a iya hango jikinsa dai dai kaurikanta.
Koda suka tsaya sai Sarki ya mike tsaye da kyar ya ce, "Ku bani labarin yanda aka yi kuka biyo
bayanmu alhalin a cikin lissafin tafiyarmu babu ko, kuma bana son dayarku ta yi min karya ku
sanar da ni iyaka gaskiyarku.
da Koda Shadilat Gimbiya Lushmaira suka ji wannan batu daga Sarkin sai suka durkusa bisa
gwiwoinsa sannan suka ce, "Ya shugabana muna rokanka alfarma a bisa kyata maka doka da
muka yi ka yi sani ba mu yi haka dan komai ba sai dan mu je zuwa wannan filin daga domin
idanuwanmu ya gane mana irin jarumtakar da Jarumi Zaiyan da kuma kai zaku nuna, a wannan
gurin
Koda Sarki ya ji su da wannan ba tu sai ransa ya yi mutukar baci ya dube su ya ce. "Amna dai
kun cika sakarala wanne dalili ne kuna mata ma'abota rauni zaku biyo sawunmu zuwa wannan
bakin yamutsin da ko a tarihin ban taba jin urin azababbin yakin da zamu yi mu da wadannan
Sakarai uku da suka hadu a kanmu, tabbas sai kun koma gida domin kuwa bazan taba lamunta
na yi tafiya daku zuwa wannan yaki ba."
Koda yazo nan a batunsa sai su duka suka sauke kawunansu kasa suna masu nadama zuwa
dan su taimakawa masa hakan ya jawo masa asarar tafiyarsu
Sim sim suka juya suka sauka daga kan tsaunin, cikin rashin kwarini jiki.
Sarki ya biyo bayan su, duk jikinsa yakushe ne gaa jini koda Sarkin yaki Safwan ya ga
kyawawan 'yan mata daga saman tsaunin sun sauko kafin ya gane
su wayo sai ya zare makami koda suka yi kasa ya gano su Lushmaira ne sai ya yi sak ya kuma
cika da tsananin mamaki, kafin su iso kasa sai ga Sarki shima ya nufo su koda ya hango Sarki
cikin mawuyacin halin sai ya nufo shi
"Ya shugabana lafiya mai ya faru da kai haka.?"
Sarki Abu zaiyan ya dube shi batare da ya tsaya bata lokaci ko inda inda ba ya kwashe duk
abinda ya faru a tsakaninsa da zakuna da kuma taimakon da su Shadilat da Lushmaira suka
kawo masa, amma sai ya rufe Sarkin yaki da fadan yanda a ka bar su Shadilat da Lushmaira
suka biyo bayansu.
Nan da nan Sarkin yaki ya kama rantsuwa yana nuna rashim saninsa da wannan allamari ana
wannan abu sai ga Zaiyanu ya iso gurin ganin su Lushmaira da Shadilat ya yi mutukar ba shi
mamaki
kai tsaye ya dubi Sarka gamu halinda yake ciki ya ce.
"Ya mahaifina shin mai yake faruwa da kai haka ina dalilin ganin rasrika a jikinka, kuma
wadannan daga ins suke?"
Koda Sarki ya ji wunnan be tu sai ya ce, "Bana son Su Shadilat su kara koda sa'a daya anan
lallai a shiryzsu su koma can gida domin kuwa ba zamu yi warinan tafiya da su
Koda jin wannan ba tu sai yarima ya dube shi cikin tsawa ya ce, "Mai yasa kuka biyo mu, ta
wace hanya kuka hiyo bayanmu, koda ya kurawa Shadilat idanı sai ya ce, "Tabba na gane ki ba
ta ko wace hanya ko ka biyo ba face ta hanyar Likita Zauwad ba kuma na nufin shi ya yi muku
hanyar biyo mu ba kun bata cikin jama'arsa kun biyo mu."
Su dai basu iya cewa komai domin dukkanin zuciyoyinsu cike suke da fargabaa, da tashin
hankali muddin suka
koma cikin birnin to babu shakka cuta damuwa zata iya sanadin haifar musu da wata matsalar.
Mu hadu a part 3 littafin yaki