Showing 1 words to 3000 words out of 12054 words

Chapter 1 - MALAMIN MATA HAUSA NOVELS BY MOM ISLAM.txt

06 Dec 2025

1528

*✿❥MALAMIN MATA❥✿⁠ *
(Romantic and love story)


Mom Islam


Page 1-2
Ƙarfe goma na dare. Driving yake yi, cikin yanayi na damuwa gami da rashin walwala shimfiɗe a saman fuskarsa, Hannunsa dake ɗaure da agogon hannu yasa ya shafi sumar kansa, yana jan dogon tsaki mtswww, yaci gaba da driving ɗin yana tsaki lokaci-lokaci, wani wawan birki ya taka sakamakon yin ido biyu da wata ƙaramar yarinya da yayi wacce bazata wuce shekaru takwas a duniya ba, kuka takeyi iya ƙarfinta, tana tsaye a gefen hanya bakinta na fitar da jini, yayinda jikinta yake ta karkarwa, Habibullah ya haska ta da fitilar motar, kana yai parking a nesa da yarinyar, jiki a sanyaye ya ƙarasa inda yarinyar ke tsaye, cikin taushin murya yace "ke..me kikeyi anan?"
Bakinta na rawa tace "an...an...anty..an...ti.. Hanifah ce tace ina jirata tana zuwa, kuma har yanzu bata dawo ba"
Habibullah ya ƙarewa yarinyar kallo cikin tausayawa yace "meye sunanki, wacece Hanifah?"
Hawaye nabin kumatun yarinyar, sai rawar sanyi takeyi, kasancewar garin yayi sanyi sosai, dan ba'a daɗe da ɗauke ruwan sama ba, kuma har yanzu ana yayyafi kaɗan-kaɗan, yarinyar tace "Hurrah.."

Bai sake tambayarta ba, ya ɗagata cak ya rumgumeta a jikinsa ya sata a cikin mota, kana ya zagaya shima ya shiga mazaunin Driver, kafin ya yiwa motar key yace "zaki iya gane gidanku?"
Hurrah tace "eh" bayan yayiwa motar key, a hankali ya hau hanya, driving yake yi amma ƙirjinsa na dukan uku-uku, shi kansa ya rasa dalilin da yasa yake fuskantar hakan, sunyi nisa sosai, Habibullah ya ɗan juyo ya kalleta har yanzu tana rawar sanyin yace "wace anguwa zamu je, sannan zaki gane gidanku"
Hurrah ta gyaɗa masa kai da sauri bakinta na rawa, suwaitarsa dake a saman kujerar da yake zaune ya lulluɓa mata, a hankali ta gyara kwanciyarta, koda ya ɗan ƙara yin gaba, ya juyo domin ya tambayeta, sai yaga tuni tayi barci, dafe goshinsa yayi, yana tunanin yanzu ina zai kaita..
Yana cikin tunani wayarsa ta katse masa tunanin saboda rurin neman agaji da ta farayi, Habibullah ya sake jan dogon tsaki yana ci gaba da driving, can Anjima wayarsa tayi ruri na alamun an turo saƙo, bai kalli wayar da ya ajiye ba, driving yaci gaba dayi har ya iso wata anguwa wacce shiru ya yawaita sosai, a bakin wani tangamemen baƙin get ya danna horn, mai gadi yai saurin buɗe masa, Habibullah ya kutsa hancin motar ciki kana yai parking motar a gurin ajiyar motoci, sannan ya buɗe murfin motar ya fito, kana ya zagaya ya ɗauko Hurrah da tuni tayi nisa a barci, rungumeta yayi a kafaɗarsa, kana ya lulluɓa mata rigar sanyinsa a bayanta, sannan ya fara tafiya zuwa cikin gidan.
Sallama yayi kana ya murɗa handle na ƙofar sannan ya shiga ciki, babu kowa a parlor, dan haka ya shige ciki, kai tsaye hanyar da zata sada shi da bedroom ɗinsa ya nufa, wata matashiyar mata wacce bazata wuce shekaru 25yrs ba ta iso gabansa tare da riƙe Kwankwaso kamar wacce tayi gudu take kallonsa tana sauke numfashi tare da shan gabansa, dogon tsaki yaja "mtswww" kafin ya gyarawa Hurrah kwanciya a kafaɗarsa, muryarsa na nuni da yanayin gajiyar da yake ciki yace "Fareedah ki matsa min Please"
Tana sauke numfashi tace "wlhi Habibullah Bazan matsa ko ina ba, so nakeyi ka gayamin matsayina a gurinka?"
Bai ce da ita komai ba ya tureta ya wuce, koda ya shiga bedroom ɗinsa ya yiwa ƙofar key tare da kwantar da Hurrah a bed ɗinsa, ya nemi guri ya zauna kusa da ita yana ƙare mata kallo, Hurrah kyakkyawa ce sosai, fara ce sol tanada dogon hanci, sannan gashin kanta dake a cikin hula dogo ne har gadon baya, a taƙaice dai Hurrah tana Kama da shuwa Arab, sannan kayan dake jikinta baya nuni da tana cikin wani hali,
Tashi yayi tsaye, ya fara zagaye ɗakin, sautin muryarsa na fita ƙasa-ƙasa, yace "wacece Hanifah, sannan meye dalilinta na sake Hurrah a bakin titi?"
Ya daɗe yana zagaye bedroom ɗin yana maimaita tambayoyin da bashi da wanda zai bashi amsarsu.
Nannauyar ajiyar zuciya Habibullah ya sauke, kana ya fara rage kayan jikinsa daga shi sai boxes sannan ya shiga toilet, ruwa ya sakar wa kansa kafin ya fara wanka, bayan ya gama ya fito ɗaure da towel cikin sauri ya buɗe drowa ya Ciro farar jallabiya da gajeren wando yasa sannan ya zauna a bakin gado, sai yanzu tunanin Fareedah ya faɗo masa, murmishi yayi wanda iya karsa gefen baki, ledar daya ajiye ya ɗauko, ya Ciro takeaway da spoon, ajiye takeaway ɗin yayi a saman bedsite, kana ya miƙe yaje inda madaidaicin fridge ɗin dake ɗakin yake, ya ɗauko bottle water sannan ya dawo ya zauna ya fara cin abincin, shinkafa ce jollof taji kayan lambu da naman kaza dasu salad, sai dai sam baya jin daɗin abincin kawai yana Turawa ne saboda yau ma kar ya sake kwana da yunwa, ajiye ragowar yayi, sannan ya shiga toilet yai brush kana ya dawo kan bed ɗin, yasa haƙarƙarinsa zai kwanta kawai yaji shi luntsum a cikin fitsari, da sauri ya tashi yana ambaton innalillahi wa inna ilahir raji'un, yai saurin komawa toilet ya watsa ruwa, kana ya fito yana duban Hurrah da take barcinta cikin kwanciyar hankali, yama rasa me zeyi mata, kawai ya ɗauko blanket ya shimfiɗa a ƙasa saman carpet sannan yasa pillow ya kwanta, ba wani barci mai nauyi ne ya ɗaukesa ba, kawai dai rayuwar ce baya jin daɗinta, a hankali ya ɗaga kansa idanunsa suka sauka a kan wani makeken frame dake ɗauke da hoton wata kyakkyawar mace wacce bazata Gaza shekaru Ashirin da biyar ba, fuskar matar dake jikin hoton yalwace da murmishi, kamar zaka kirata ta amsa, Muryar Habibullah kamar ta mai shirin yin kuka yace "Allah yayi miki Rahama Salma"
Ya mayar da kansa kan pillow ya kwanta, bugun ƙofar da aka farayi ne babu ƙaƙƙautawa ya sashi runtse idanunsa yana mai jin takaici da irin hali na Fareedah,
Cikin ɗaga murya bata tsoron dare take cewa "Yah Habibullah ka buɗemin na kasa barci acan.."
Yai mata banza, dan yasan abinda ya kawota, kuma yasan inhar ta shigo ɗakin bazata fita lafiyaba, har sai ta nemi fitina,
Bugun ƙofar yayi yawa, dole ya miƙe baya son Hurrah ta tashi, ya buɗe ƙofar kaɗan, da sauri ya fito yana kulle ƙofar, wani irin haɗaɗɗen ƙamshin turaren dake tashin ƙamshi a jikinta ne ya bugi hancinsa, wanda yau ta taho dashi daga gida, koda ta fara lura da yanayinsa a cikin zuciyarta tace "Yaji zuwa gida yayi min rana ai wallahi inhar maganin nan yai aiki Yah Habibullah sai na gwara kanka kamar inda kake gwara nawa, har wacece wata Salma wacce tuni ta riga ta daɗe da barin duniya amma kake..."
"Fareedah lafiya..?"
Habibullah ya tambayeta.
"Am Uhm lafiya mijina dama so nake in kwanta a ɗakinka.."
Fareedah tayi maganar tana shafo gabansa cikin wani irin salo....!


08141799224

✿⁠ ✿⁠ ❤✿✿
*✿❥MALAMIN MATA❥✿⁠ *
(Romantic story)


Mom Islam

Page 3-4
Habibullah ya bige hannunta da sauri, cikin fushi yace "meye haka?"
Fareedah ta taɓe baki gami da cewa "ban gane ba, nida mijina sai akace kar inzo neman haƙƙina a gurinsa, Yah Habibullah nifa na fara zarginka wlhi, sannan wannan yarinyar daka shigo da ita wacece?"

Fareedah kin daɗe baki zargeni ba, nace kin daɗe baki zargeni ba, yarinyar wacece ko ita wacece duk babu ruwanki, ki kama gabanki tun kafin jikinki yayi tsami"
Habibullah ya faɗa yana yi mata nuni da hanyar fita, dogon tsaki taja tare da komawa bedroom ɗinta, har idanunta sun ciko da ruwan hawaye, tai saurin ɗaukar wayarta, a daren ta kira number Ummanta, ringing ɗaya Umman ta ɗaga, kafin tace "Fareedah lafiya kika kirani a cikin darennan?"

Fareedah ta fashe da kuka ko hawaye babu, tace "Umma har yanzu yaƙi ya kusanceni bare in samu cikin.."
Umma dake kwance a saman katifa ta tashi zaune, da sauri tace "Fareedah inaga dai bakiyi amfani da maganin nan inda ya kamata ba ko?"

"Nayi Umma, duk abinda malam ya faɗa babu wanda nayi kuskure gurin yinsa"

Umma ta ja dogon numfashi kafin tace "kuma bakiga yanayinsa ya sauya ba?"

Fareedah na gyara zaman wayar a kunnenta tace "ɗazu da naje gurinsa ya ɗan fara sauyawa daga baya kuma ya koma inda yake"

Umma tace "ki kwantar da hankalinki zaki samu Habibullah cikin ruwan sanyi, Allah ya kai mu gobe insha Allah sammako zanyi zuwa gidan Malam"

Fareedah ta ajiye wayar, Sam barci ya kasa ɗaukarta, koda ta kwanta lumshe idanunta tayi, dan bata san lokacin da barcin ma yai nasarar ɗaukarta ba,

Acan ɓangaren Habibullah barci rabi da rabi yayi, kasancewar firgita da Hurrah ta dinga yi, a firgitar nata ne ya gano Yarinyar tana cikin wani hali, saboda cewa take "Momy zata kasheni, Momy kizo ki taimakeni wuƙa ne a hannunta, sai da ya dinga karanto mata adu'oi kafin tayi barci, sai wajen asbha ta farka tana neman abinci, shikam ba ma'abocin shiga kitchen bane, Dan haka ya ɗauko takeaway ɗin da ya rage abinci, Allah ya taimaka ma abincin beyi komai ba, ya bata ta fara ci kamar zata haɗa da takeaway ɗin, kallonta kawai yake yi cikin tausayawa da tunanin idan gari yayi haske dole zai tafi da ita saboda ta nuna masa gidansu,
Toilet ya shiga ya ɗauro alwalah bayan ya fito ya shimfiɗa prayer mat ya kabbara sallahar nafila, har sai da aka kira sallahar Asbha sannan ya ninke prayer mat ɗin ya wuce masallaci, ana idar da Sallah ya dawo, dan yana son su fita da wuri, lokacin da ya shigo Hurrah ta tashi daga barci, tana zaune a saman bed sai rarraba idanu takeyi, tana ganinsa ta duro daga saman bed ɗin tace "uncle zaka mayar dani gida koh?, amma kar ka kaini gurin Anty Hanifah"
Habibullah yace "insha Allah ba zan kaiki gurinta ba"
A hankali ya fara cire mata kayan jikinta ya rage daga ita sai pants, a ɗan tsorace ya kalli shatar bulalar dake a jikinta, yakai hannunsa ya taɓa gurin yace "Hurrah....malamin makaranta ne yayi miki wannan dukan?"
Hurrah ta girgiza kai tace "anty Hanifah ce, take dukana kullum"
Habibullah ya girgiza kai yana mai tausaya mata, toilet ya shiga ya haɗa mata ruwan wanka bayan ya dawo ya ɗauketa ya kaita yayi mata wanka ya naɗota a towel, bayan ya goge mata jiki ya sa shafa mata Vaseline, sannan ya fara tunanin wane kaya zai saka mata bayan tayi fitsari a wanda ya cire mata?,
A waya ya kira wanda yake yi masa wanki da guga, yace kafin ya ƙaraso ta taho masa da kaya na yarinya kamar ƴar shekara takwas, mai wankin masa yace "an gama" bai wani ɗauko dogon lokaci ba ya shigo gidan hannunsa riƙe da leda wacce kayan yake ciki, a bakin ƙofar parlor ya tsaya, kana ya kirasa a waya bayan ya ɗaga yace ya iso, Habibullah ya fito ya karɓi kayan sannan ya tambayesa nawa ne?,
Mai wankin yace 15k, Habibullah ya bashi 20kk kana ya miƙa masa kayan wanki da bedsheet ɗin da Hurrah tayi fitsari yace ya wanke, mai wankin yayi masa godiya, koda ya dawo ciki ya sameta tana zaune a gefen bed ta takure, ya ƙarasa gurinta fuskarsa ɗauke da murmishi yace "Hurrah ga kaya kisa sai mu tafi.." da sauri ta miƙa hannu tana yi masa murmishi, wanda yasa poin ɗin dake kumatunta ya loɓa , fito da kayan yayi yana zaune saman bedsite ya duba su, riga da dogon wando ne ƴan kanti, masu ado mai kyau da mayafinsa siriri, da kansa ya saka mata kayan, ya bata mayafin a hannunta kana yace jirani.
Kayan da zai sauya ya ɗauka a drowa kana ya wuce toilet, bayan ya gama wankan yasa kayan sannan ya fito, ya shafa mai ya ɗauki takalmi da hula da abubuwan buƙatunsa, bayan ya fesa turare ya riƙe hannunta suka fito parlor, Fareedah na zaune ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta kallesu ta watsar har yayi hanyar fita cikin ɗaga murya tace "ikon Allah karuwa tafi matar gida daraja kenan?"
Wannan maganar da yayi ta mugun dukansa sai dai yasa kai ya fice ko saurarenta beyi ba, kai tsaye parking space ya wuce ba motar da ya shiga jiya ya buɗe ba, wata da bance, bayan Hurrah ta shiga ya zagaya shima ya shiga sannan ya yiwa motar key, bayan an buɗe masa get ya fice daga gidan.
Fareedah na ganin fitarsa tai saurin ɗaukar wayarta ta danna number Ummanta, kamar jira Umman take yi, ta ɗaga tare da cewa "walhi na kira Malam yace "dole sai dai mu tafi tare dake" Fareedah tace "Umma ai babu wata damuwa, tuni ya fice da wata shegiyar yarinya nidai nafi tunanin ƴarsa ce ta waje dan wallhi kinga inda yake nan nan da ita kuwa?"
"Umma tace "duk ba wannan ba idan kika zo mukazo gurin Malam duk sai kiyi masa bayanin koma meye"
Fareedah tace "insha Allah Umma"
Da sauri ta wuce bedroom ɗinta ta cire kayan jikinta ta, tayi wanka, bayan ta fito daga wanka, ta fara tunanin wane irin kaya ya kamata tasa, daga ƙarshe dai ta Ciro wani rantsatsen leshi mai kyau da tsada yasha ado, bayan tasa bra da under tasa doguwar rigar leshin anyi mata ɗinkin buba, kasancewarta mai kyan diri kayan yayi mata cif ɗaurin ɗankwali tayi wanda shima ya sake ƙawata adon nata, ta ɗauki Mayafi ruwansa irin ratsin adon leshin, kana tasa ɗankunne da sarƙa da warwaro ta fesa turare, sannan ta ɗauki handbag ɗinta irin takalminta cover shoe, kana ta ɗibi kuɗaɗe ta saka a cikin da wayarta, sannan ta wuce kitchen, yunwa take ji sai dai abinda take son amayarwa bazai taɓa barinta ta zauna cin abinci ba, a gurguje ya dafa indomie leda huɗu hungry man, sannan ta juye a warmer mai kyau ta ɗauki leda babba tasa a ciki, sannan ta fito, sai da ta kulle bedroom ɗinta da ƙofar parlo kana ta fita zuwa compound, driver ta ƙwalawa kira, bayan yazo tace masa ya kaita gidansu, kai tsaye ta shiga backside ta ajiye abincin a gefe driver ya shiga sannan yayiwa motar key...!

Mom Islam
*✿❥MALAMIN MATA❥✿⁠ *
(Romantic story)


Mom Islam

Page 5-6

A ƙofar wani madaidaicin gida wanda yake da ƙofar katako driver yai parking motar, Fareedah ta fito daga cikin mota tana wani yauƙi, "kaje zuwa ƙarfe uku ka dawo ka ɗaukeni"

Ta faɗa ba tare da ta jira amsar da zai bata ba ta buɗe ƙofar tare da yaye labulen buhun dake a bakin ƙofar gidan nasu ta shiga da sallama, Umma dake bakin rijiya tana jan ruwa, ta washe haƙora tana cewa "sannu da isowa nima na shirya ruwan sha nake ɗiba zan zuba a randa sai mu wuce"

Ɗakin Umman ta shige, sannan ta nemi guri a bakin ƙaramin gado ta zauna, ta rasa mai yasa yau ɗinnan take jin farin ciki na musamman, Umma ta shigo ta ɗauki Mayafi da goronta sannan tace "mu tafi.."
A tare suka fita daga gidan, Umma ta kulle ƙofar ta waje suka wuce bakin titi, dan ba'a cika samun abin hawa anan ba.
Koda suka isa bakin titi cikin sa'a suka samu mashin wanda zai kaisu gidan malam, sukayi ciniki sannan kowacce ta hau nata suka wuce, sunyi tafiya mai nisa sosai sannan suka iso gidan, madaidaicin gida ne, tsakar gidan yana malale da siminti, gidan Malam ɗin yasha fenti yayi fes, koda su Umma suka tura ƙofar da sallama suka shiga, gidan a cike yake da matan aure da tsofaffi da zawarawa da ƴan mata, kowacce da damuwar daya kawota, dan haka sai da su Umma sukabi layi tukuna, dan Fareedah batayi tunanin zasuyi irin wannan daɗewar har haka ba, sai wajen sallahr la'asar bayan an dawo sallah kafin suka samu damar shiga gurin malamin, zaune yake a saman kujerar ƙarfe hannunsa riƙe da babban carbi irin mai dubu ɗinnan, ɗakin ya tara kayan aikinsu na malunta, Umma ta gaishesa lokacin da suke zama a gabansa, Fareedah na ta gaishe sa, ya amsa kafin ya kalli Fareedah yace "Fareedah ko?"
Ta gyaɗa kai da sauri sannan tace "Malam mijina ne ya juyamin baya tun bayan da ya samu labarin an taɓa zubar min da ciki kafin aurenmu kuma wlhi auren soyayya mukayi, bayan haka ma a halin da ake ciki yanzu ya kawo ƴar karuwarsa gidan hankalinsa gabaki ɗaya yana kanta"
Malam yayi murmishi kafin yace "ki kwantar da hankalinki, insha Allah zanyi iya bakin ƙoƙarina dan ganin kin zauna lafiya keda mijinki, sannan zan shafe masa wannan tambarin da yake ganinki dashi, ita kuma wannan yarinyar dole zamu san abinyi amma kafin nan barin haɗa miki wasu magungunan" cikin zumuɗi Fareedah tace "Malam kana haɗa irin maganungunan mu na mata ne?"
Malam yayi murmishi kafin yace "mezai hana ai har dashi zan haɗa miji"
Bayan ya gama zuzzuba mata magungunan ya faɗa mata inda zata yi, ta tambayi nawa zata bada abin sadaka, yace ta bada duk abinda ya samu, ya nuna Umma kana yace "wannan baiwar Allahan ai bana ciniki da ita" Fareedah ta Ciro kuɗi mai yawa ta ƙirga 20k ta basa, yace ta ɗaga wani ƙoƙo ta ajiye, bayan ta ajiye sukai masa sallama yace nan da kwana biyu su dawo, sannan yace kar wanda ya shigo yanzu..
Kamar inda yai umarni babu wacce ta sake shigowa har sai ya buƙata, bayan fitar su Fareedah, Malam ya riƙe Dick ɗinsa sosai yana shafawa ya kallo wandonsa ya riƙeta gam sakamakon wani miƙewa da tayi kamar zata faso wando, sai da ya gama mulmulawa kana ya shiga toilet ɗin dake a ɗakin ya fito sannan yai Umarni wasu su shigo, a haka har ya sallami mutane.
Tun safe Habibullah yake yawon neman anguwarsu Hurrah da gidansu amma bai samu ba, ita kanta ta kasa tuna sunan anguwar tasu, koda suka gaji da yawo ya wuce restaurant sukaci abinci kamar inda sukayi da safe, yayi takeaway biyu, da nata da nasa, kasancewar yanzu kiran sallahar la'asar ake yi, kai tsaye ya dawo da ita gida, extra key ɗin dake a hannunsa yasa ya buɗe ƙofar parlon sannan suka shiga, kai tsaye bedroom ɗinsa suka wuce, ya yi mata nuni da ta zauna saman carpet wanda yake a tsakiyar ɗakin, bayan ta zauna shima ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login