Showing 1 words to 3000 words out of 163126 words
*TKGB30A1*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
A hankali na riƙa buɗe idanuwana da suka yi mini wani nauyi. Da farin POP da a ka yi rufin ɗakin na fara cin karo, a hankali na juya dama da haunina amma na rasa fahimtar a in da nake, kamar dai ƙaramin ɗaki ne sai da idanuwana suka sake washewa sannan na soma fahimtar in da na tsinci kaina.
Da ƙyar na miƙe zaune, ina sake bin ɗakin da kallo in har idanuwana sun ganin min daidai in kuma ba mafarki na ke yi ba tabbas ina asibiti kuma a gadon asibiti. Sakamakon ɓarayin hannun damana da na kalla sai na ga hannuna saƙale da abin ƙarin ruwa da na ɗaga idanuwana sama kuma sai na ga ruwa ake ƙara mini. Ɗis! Ɗis haka na ƙura ma saukan ruwa ta cikin ma zubar sa zuwa cikin jikina idanuwana jikina na bi da kallo sai na ga ba kayan da na baro gida da su ba ne jikina ba. Wata doguwar riga ce a jikina wanda in dai ban yi kuskure ba kayan Amina ne a jikina.
"Me ya faru da ni?
Na faɗa a sarari saboda na kasa tuna komai. Na kasa tuna lokacin da na tsinci kaina a gadon asibiti. Ɗakin ba kowa sai ni kaɗai kamar irin daƙunan ne na VIP. Kaina na dafe da hannuna na hagu jin ya ɗan saramai ina tunanin lokaci na ƙarshe kafin a hankalina ya gushe. Tabbas a gidan Amina na tuna ina cikin Toilet ɗin ta ina amai daga nan sai na ga jini. E tabbas na ga jini daga nan ne na fita hayyacina ban ƙara sanin in da kaina ya ke ba sai yanzu da na tsinci kaina a gadon asibiti.
"Innalillahi."
Na faɗa Daidai lokacin da na shafa kasan marata na ji kunzugu. Da gaske ne na yi zubar jini amma me ya kawo mini zubar da jini? Damuwa ce da firgici suka kawo min zuwan period ba tare da lokacin sa ya yi ba. Haka na faɗa ma kaina a cikin zuciyata. Yanayin lokaci nake so na fahimta amma na kasa ganewa. Sakamakon ɗakin akwai wutar lantarki sannan window ɗin ɗakin ya na nesa da ni. Sai dai duk da haka na ɗan fahimci akwai haske daga waje kenan duk abin da ma ya same ni bai daɗe ba tun da har yanzu dare bai yi ba akwai sauran rana.
Na muskuta kenan na gyara zama daidai lokacin aka buɗe ƙofar ɗakin a ka shigo. Na bi wacce ta shigo da kallo Nurse ce domin fararen kaya ne a jikinta wata yar mai ƙiba da ita.
"Sannu ya jikin na ki?
Ta faɗa bayan ta ƙariso gaban gadon da na ke zaune.
"Yauwa. Da sauƙi"
Na bata amsa a hankali ita kuma sai ta saka hannu ta dauƙo wani fayel da ke saman ɗan teburin da ke gefen gadona ta buɗe ta na dubawa.
"Don Allah wa ya kawo ni nan?
Sai da ta kalleni kafin ta cigaba da duba fayel ɗina na ma ɗauka ba ta ji ba ne.
"Dr Ibrahim Aliyu."
Sai na kalleta amma na kasa mgana saboda na kasa tuna waye na sani mai wannan sunan.
"Jiya tare da wata mata suka kawo ki."
"Jiya?
Na faɗa cikin mamaki har ina waro ido.
Ijiye fayel ɗina ta yi lokaci ɗaya ta na cire min ƙarin ruwan da ke hannuna kafin ta cigaba da faɗin.
"Yes. Sun kawo ba kya cikin hayyacin ki. Kin farfaɗo amma muka sake mai dake da alluran barci."
Kallonta kawai na ke yi na kasa magana. Tun jiya na ke asibiti ban sani ba? Me ya same ni haka?
"Na cire miki ki ɗan huta. Zuwa an juma sai a mayar miki da shi"
Har ta juya za ta tafi na kasa haƙuri.
"Sister don Allah me ya same ni?
Sai ta juyo ta na kallona kafin ta kaɗa kai ta na faɗin.
"Miscarriage
"Miss cra gge."
Na maimaita a rarrabe.
"Yes. Kin samu ɓarin ciki ne a jiyan."
Ta na gama faɗin haka ta juya ta na faɗin" Matar da suka kawo ki jiya ita ta kwana da ke. Ta je gida ta dawo nan ba daɗewa ba."
Tana gama faɗin haka ta fice lokaci ɗaya ta na jawo min ƙofar ɗakin har sai da ta ɗan ba ta sauti.
"Ɓari? Wani irin ɓari kuma?
Domin sai na ji tunani ya tsaya cak na kasa fassaran ma'anar maganar Nurse ɗin.
"Daman ana ɓari ba a samu ciki ba?
Tambayar da na yi ma kaina a fili kenan kafin na samu amsar ta an sake buɗe ƙofar ɗakin an shigo. Da rinannun idanuwana da suka yi min nauyi da na ɗaga ina kallon mai shigowa.
Amina ce a kan gaba sai megidanta biye da ita ɗauke da kwando a hannunsa ita kuma riƙe da ledoji guda biyu suka shigo ɗakin sai da na gan su ne sannan na tuna da sunan da Nurse ta faɗa min. Tabbas mijin Amina ne Dr Ibrahim Aliyu malami ne a jami'ar Kaduna. Da ya ke kuma sai da ya haura arba'in san da ya auri Amina shi ya sa duk wanda ya gan sa zai san ba yaro ƙarami ba ne.
"Ya Sadiya kin tashi?
Amina ta katse mini tunanina sai na kalleta ta zauna a gefen gadon ta na mai riƙo hannuna mara kanular.
"Ya jikin na ki? Jiya kin ba ni tsaro wallahi."
Ta faɗa ta na yar dariya lokaci ɗaya ta na kallon mijinta.
Kallonta kawai na ke yi na kasa mgana domin sai na ji bakina ya yi min wani irin nauyin da na kasa furta harafi ɗaya daga bakina.
"Maman Jidda ya ƙarfin jikin na ki?
Sai a lokacin na ji na yi magana bayan na kalle shi.
"Da sauƙi Dr. "
"Ma sha Allah. Allah ya ƙara lafiya."
Na amsa da Amin a saman leɓe na. Ita kuma Amina sai ta miƙe ta nufi kwandon da suka shigo da shi ta na tambayana me zan ci? Dr na gefe ya ce ta fara haɗa min tea ne ya warware min ciki tun da tun jiya ban ci wani abu ba.
"Kenan da gaske ne tun jiya na ke asibtin cikin rashin hayyaci?
Tambayar da na yi ma kaina kenan ban samu amsarta ba Amina ta haɗo min tea ta kawo min na karɓa hannuna na ɗan rawa sai Amina ta taya ni riƙewa da hannayenta ta na faɗin.
"Har yanzu jikin na ta ba ƙarfi."
"Kin san daman sai a hankali."
Dr ya amsa mata lokaci ɗaya yana duba wayarsa da ke hannunsa.
Ina ta taimakamin ina shan tea ɗin da cokali, Dr ba daɗe ba ya ce zai shiga cikin makaranta Amina ta sakar min kofin ganin saura kaɗan ta miƙe domin yi masa rakiya.
"Allah ya ƙara lafiya Maman Jidda."
"Amin Dr. Na gode da ɗawainiya da ga zuwa baƙun ta na zo muku da hidima."
"Haba bakomai. Ai lalura ce Allah ya ƙara afuwa."
"Amin"
.
Na amsa a hankali, sun fice ina mai bin su da kallo kawai sai ina hakaito kaina ni da Yallaɓai. Yanzu itama Amina watan wata rana Dr zai iya nuna mata halin su na Maza ranar da ya yi aure. Wata ƙila shi kuma ba irin Yallaɓai ba ne, wataƙila shi ya san me ake kira hallaci. Duka na shanye tea ɗin domin ina jin jikina fayeu kamar takarda kuma ina jin yunwa kaɗan amma ba da yawa ba sai dai kuma ruwan zafin ya taimaka wajen farfaɗo da bushewar da cikina ya yi tare da maƙogwaro na har da saman labɓana.
Ji na yi marata kamar ta ƙulle ina jin fitsari sai na yi ƙoƙarin miƙewa tsaye a hankali, sannan na ijiye kofin saman drewer ɗin gefen gadon da na ke kwance. Sai a lokacin na fahimci ko hijabi ma babu a jikina daga ni sai rigar nan sai ɗankwali Allah ya sa bai saɓule ba tsabar halin da na kr ci na manta da rufe jikina a gaban suruki. To su da suka kawo ni asibiti cikin rai ƙwakwa mutuwa me ye ya yi saura kuma? Da ƙyar na iya taka kafafuwana zuwa tiolet ɗin cikin ɗakin ji na yi kamar in faɗi jikina kamar fallen takarda saboda rashin ƙwarin jiki.
Tabbas jini ke zubar min tun da ga shi a jikin pad ɗin da ke jikina. To ko dai maganar Nurse ɗin gaskiya ne na samu ɓari? Amma abin tambaya anan daman ina da ciki ne? Dawowar Amina ɗakin ne da ta ga ba ta ganni ba sai ta ƙwala min kira shi ya sa na yi tsarki na fito ina faɗin.
"Gani nan Amina."
Da sauri ta zo ta kamani ganin ina faman da fa bango ta maida ni har saman gado na zauna sannan ta koma gefe na kamar ɗazu ta zauna.
"Ya Sadiya jiya kin ba ni tsoro"
"Me ya faru? Na kasa tuna komai"
Na faɗa ina kallon ta.
"Suma fa kika yi a cikin tiolet ga shi kina ta zubar da jini. Na ƙwalla ƙara ina ta ihu ba mai jina. Ƙwatsam sai ga shi Allah ya aiko min da Baban Yunma shi ya taimaka min muka kawo ki asibitin nan, ko da muka zo kin fita hayyacin ki tun jiya sai yau kika farfaɗo "
Ina kallonta amma na kasa mgana, sai ta cigaba da faɗin" Jiyan kin farfaɗo da daddare amma sai kika koma bayan sun yi miki alluran barci."
"Da gaske ne tun jiya na ke kwance a nan?
Amina ta ɗaga min kai kafin ta ce" E nan kika kwana tare da ni da safen nan ne na koma gida na yo abin karyawa sannan na taho miki da wasu kaya."
Ta mike ta na nuna min kayan sawan ta da ta zo min da shi ganin pant da pad a cikin kayan ya sa na gasgata zargina.
"Me ya same ni? Me ya sa na ke zubar da jini?
Sai ta dawo kusa da ni again ta sake zama ta na faɗin" Ya Sadiya ɓari kika yi fa?
Ƙura mata ido na yi ba tare da na yi mgana ba sai ta riƙe hannuna guda ɗaya ta na faɗin.
" Wallahi Ya Sadiya. Na ce ashe ciki gare ki ban sani ba?
"Nima ban san da shi ba Amina."
Na faɗa wasu hawaye masu zafin da ban da taruwan su ba suka kece mini. Hawayen baƙin ciki. Hawayen takaici, hawayen nadama da dana sanin da na biye ma Yallaɓai ya yi sanadiyar na rasa wani abu mai muhimmaci da na daɗe ina neman tsawon shekaru goma na cikin rayuwar da ubangiji ya ba ni.
"Wallahi Ya Sadiya kin zubar da jini shi ya sa likitan ya ce ki riƙa shan ko cin a baben ƙarin jini."
"Wata nawa ne cikin?
Na faɗa ina kallonta cikin kuka. Sai a lokacin ita ta farga ma kuka na ke yi da sauri ta dafa kafaɗata lokaci ɗaya ta na faɗin.
"Ƙarami ne likitan ya ce sati huɗu bai ma gama cika ba ƙila shi ya sa ma ba ki san da shi ba "
Wasu hawayen ne suka ƙara ke ce min ban sani ba. Ban taɓa kawo ma kaina ciki gare ni ba, ko da period ɗina ya tsallake min wata ban yi tunanin haka ba, sanin daman ya na yi min haka sai dai ban saka lissafin da cewa tun da na sha mganin lokacin al'ada ya gyaru ba kawai sai na yi tunanin ya dawo da yi min wasan da ya fara min a baya ne. Ashe ashe ciki ne Allah ya ba ni bayan na fidda rai da yaƙinin zan sake haihuwa. Ban san ina kuka har da shessheƙa ba sai da na ji Amina na bubbuga bayana ta na mai faɗin.
"Ki daina kuka Ya Sadiya. In sha Allahu Allah zai kawo wani da gaggawa. Allah kuma ma ya taimaka cikin ya fita duka ba su yi miki ma wankin ciki ba."
Amina na kallah itama ni ta ke kallo kawai sai na fashe da kuka mai sauti na kwantar da kaina a saman cinyarta ina kuka ina ma tana lallashina amma har muryanta ta fara rawa.
"Ni kaina Ya Sadiya sai da na yi ƙwalla da aka ce ciki ne da ke amma kin samu ɓari. Na ce Allah sarki Ya Sadiya abin da ta daɗe ta na nema ga shi ta samu amma Ubangiji ya yi ikon shi. Ki yi haƙuri za ki samu wani da ikon Allah."
Ba wani Ubangiji da ya yi ikon shi. Yallabai ne ya yi sanadiyar da na rasa ɗana gudun jinina. Domin shi ne ya saka ni cikin cikin baƙin cikin da har ya yi sanadiyar ɓarin cikina. Cikin da na shafe tsawon shekaru goma ina fafutukan samun sa sai ga shi ya samu ɗin amma tun kafin na ma san da wanzuwar shi ya bi rariya. Kuka na ke yi da ƙarfi da dukkan zuciya ta. Kukan rasa gudan jinina. Kukan baƙin ciki da wani kullutun abu da ya tokre min a ƙirji na jin wani irin haushin Yallaɓai da ban taɓa jin irin shi ba sai yau.
Na yi kuka sosai kukan rasa gudan jinina. Lallashin Amina bai sa zuciya ta ta yi sanyi, sai da na yi kuka sannan na ɗan ji sanyi sanyi amma wannan taɓon da Yallabai ya saka min ba na jin zan iya mantawa. Idanuwana sun yi jajir sun tasa saboda kuka Amina faɗi ta ke yi Allah zai ba ni wani na daina kuka jin ta kawai na ke yo. Ko na samu wani ba shi zai goge taɓon na samu kafin shi kuma ya zuɓe ba, kuma ba shi zai taɓa goge taɓon sanadiyar baƙin ciki Yallabai na rasa abu mafi soyuwa gare ni a karon farko ba.
Da ƙyar Amina ta lallasheni na ci abinci fanten doya da hanta na ci na ɗora da maltina sai na ji na fara samun ƙarfin jiki na komawa na yi na kwanta ina kukan zucci sai ga Likita ya shigo duba ni ya yi min tambayoyi na amsa masa cikin raunin zuciya. Ledan ruwa ya sake rubutamin sannan ya umarci Nurse ɗin da suke tare ta mai da ruwan da ya rage da aka cire da safe ya ida sa shiga jikina.
"Madam kin samu misscarrge so za mu riƙe ki a nan kwana uku saboda jikin ki ya samu karfi. Hop za ki bamu haɗin kai ki riƙa cin abinci saboda kina bukatar jini sosai."
Sai na gyaɗa masa kai, sai ya jinjina min kai shima kafin ya ce. "Good. Allah ya ƙara lafiya."
Daga nan ya fice tare da zugan Nurse ɗin da ke bayan shi takardan da ya rubuta Amina ta karɓa itama ta bi bayan su da cewa bari ta je ta siyo. Ba daɗewa ga shi ta dawo da kwali a hannunta a jikin kwalin ne na ga sunan asibitin GARKUWA HOSPITAL.
Amina ta daɗe a tare da ni sannan ta ce min za ta koma gida ta yi girki sannan ta taho min da ruwan zafin da zan yi wanka.
"To."
Na amsa mata da farko sannan na ce" Ina su Yumna?
"Suna makaranta. Jiya da babansu suka kwana da safe ma shi ya yi musu shirin makaranta."
Sai na yi mirmishi ban yi mgana ba.
Ta haɗa kayan da za ta koma da su sannan ta yi min sallama ta ce sai anjuma za ta dawo.
"To sai an juma ɗin."
Ta faɗa ta na rike hannuna mara ƙanula.
"Sai anjuma."
Na faɗa a hankali ina jin kamar barci na son ɗauka ta.
Har ta kama hanyar fita sai ta dawo da sauri ta na faɗin.
"Laa kin ga na manta ga wayarki "
Ta faɗa lokaci ɗaya ta na fiddo wayata daga jakarta ta miƙa min na saka hannuna mai lafiya na karɓa ina juyata cikin mamaki sannan ina kallon Amina.
"A cikin jakar ki na gani shi ne na saka miki ita chaji. In kina bukatar wani abu ki kirani shi ya sa na taho miki da ita. Ko in za ki kira Baban su Jidda ki faɗa mai halin da ake ciki."
"Ba zan faɗa masa ba."
Na bata amsa da sauri sai ta tsaya ta na kallona cikin nazari.
"Ba shi ba, har can mutanen gidan kar ki sake ki faɗa ma kowa ko da sun kira ki."
"To me ya sa?
"Haka nan kawai ai na ji sauƙi ba buƙatar a tashi hankali kowa."
Na faɗa ina kallonta.
"To ko Yallaɓai ba za ki kira ba?
Wannan karon kai na girgiza mata alamun a'a sai ta zakuɗa kafaɗa kafin ta ce shikenan kayan hannunta ta duka ta ɗauka sannan ta yi min sallama ta fice daga ɗakin na bi ta da kallo sai da ta ficen sannan na danna gefen wayar haske ta kawo. 12:30pm na rana ne agogon wayar ya nuna ita Amina ta ɗauka rashin chaji ne ya sa wayar ta mutu ba ta san ni na kashe ta da kaina ba tun jiya ɗin nan ba wanda ya kirani.
Wanda na ke tunanin ya kiran kuma ni na san ba zai kira din ba kamar zan sake kashe wayar sai kuma na fasa na bar ta a kunne bayan na tura ta ƙasan filon da na ke kwance.
Kamar a jikin ƙarin ruwan an yi min allura barci ban daɗe ba barci ya tafi da ni mai nauyi sosai wanda har ina jin nauyin sa a yadda jikina ya saki gabaɗaya ko ɗan ya tsana na kasa ɗagawa saboda nauyin barcin da ya kwasheni.
*****
Kwana huɗu na yi a asibiti sannan a ka sallame ni. Kuma duka abin da a ka kashe na asibitin nan Dr ya biya ga shi asibitin na kuɗi ne amma haka suka yi ta ɗawainiya da ni.
Na ji sauƙi kuma na samu ƙarfin jiki amma dai na ɗan yi rama, sannan likita ya yi ta jadaddamin na riƙa cin abincin da zai ƙara min jini, sannan na riƙa cin abinci da ganye da wake sannan na yi ta shan maltina da madara. Sannan suka rubutamin mugungunar da zan rika sha na wanke