Showing 1 words to 2609 words out of 2609 words
Chapter 1 - SADAUKI MAI ZAKI Part 1 Littafin Yaki By Mu'awiyya A. Muhammad .pdf
SADAUKI MAI ZAKI
Mu'awiya A. Muhd
arewanovels.com.ng
Sadauki Nazmir ya dawo da inda dubansa
Mahaifiyarsa Zulfira da su Tsoho Shalfanu suke ya ce mu su "Babu makawa sai na dangana da
fadar Sarki Balwanu na yi masa kisan gilla sannan na karbi gadon mahaifina, sai na cikawa
mahaifina burinsa na rusa duk wata daula ta azzalumai daga karshe na shimfida adalci a
cikinta."
Lokacin da Nazmir ya zo nan a zancensa sai Zulfira ta dafa kafadarsa tare da cewa, "Ya kai
dana abin so yuwa a raina tuni na san cewa idan na baka labarin ko waye mahaifinka sai ka
daura damarar zuwa daukar fansar kisan da akayi ma sa, ni kuwa zaka samu karfin guiwa daga
wajena ta hanyar yi maka fatan samun nasara, za ka yi shiri ka tunkari Birnin Zalmura ka da ka
saurarawa duk wani azzalumi da ka gamu da shi akan hanya.
Sannan ka ji tausayin duk wani abin tausayi, ka taimakawa wanda ya ke bukatar taimako, daga
karshe kada ka bata lokacinka a yawan ya da zango a daji. Tabbas nan da kwanaki bakwai
zaka kama hanyar ko mawa Birnin Zalmura kai da Zaki Jummar."
Sa'adda zulfira ta zo nan a zancenta sai shima
Tsoho Shalfanu ya dora da cewa, "Ya kai Nazmir ina son ka sani ni haifaffen Birnin zalmura ne a
nan na girma har na yi aure na samu shekaru kusan hamsin a cikin Birnin don haka babu inda
ban sani ba kuma na san sirrinsa, kafin ka tafi zamu zauna da kai na gaya maka irin shigar da
za ka yiwa Birnin da kuma yadda za ka bi hanyoyin da zaka samu nasara."
Tsoho Shalfanu ya na rufe bakinsa sai Zulfira ta mike tsaye tana mai cewa, "Ya kamata mu
baku dama ku kwanta ka sancewar duhu ya mamaye ko ina idan gari ya waye sai dana Nazmir
ya samo itacen da za'a hada wata bukkar saboda zamu zauna a wannan daji ne har saj lokacin
da ya dawo daga Birnin Zalmura."
Tsoho Shalfanu da sadauki Nazmir sai suka mike suka fice daga cikin bukkar su ka yi shimfida
a waje suka kwanta. Zulfira da Salzirat da kuma Sumairat su kuma sai suka kwanta a cikin
bukkar.
Wannan shine abin da ya faru a dajin da yake bayan Birnin Zalmura bayan sadauki mai Zaki ya
ceto rayuwarsu Tsoho Shalfanu ya kawo su dajin.
***
Lokacin da rana ta zo tsakiya la sararin samaniya,
shine ya zo dai-dai da lokacin da Sarki Balwanu ya gama kimtsawa a turakarsa, domin babu
abin da yake ransa a wannan lokaci illa ya isa gidan matsafiya Amrishatu don su tafi kogon
tsafin Boka Kurbasu.
Yana gama kimtsawa ya fito daga turakarsa ya nufi kofar gidan sarautar, duk inda ya gifta sai
dai kaga Dakaru suna zubewa tare da kwasar gaisuwa, shi kuwa ko duban inda suke ba ya yi.
Tafiyarsa kawai ya ke yi cikin takama da izzah.
Yana isowa kofar gidan sarautar sai ga Sarkin yaki nan, ya gabato gareshi ya kwashi gaisuwa,
sannan ya ce, da Sarki Balwanu, "Ya shugabana ina zaka tafi haka ba tare da ka sa ni na shirya
mun tafi tare ba don tabbatar da tsaron lafiyarka?".
Ko da jin wannan tambaya sai Sarki Balwanu ya yi murmushi, sannan ya ce, "Ya kai Sarkin yaki
na baka umar nin ka shirya Dakaru hamsin wadanda za su yi min rakiya zuwa gidan Bokanya
Amrishatu kafin cikar dakika talatin". Sarkin yaki ya amsa da cewa, "Ya kai Sarkin sarakuna
dakika talatin ta yi yawa na rantse da karfin sadaukan taka ta a dakika goma za su iso nan."
Yana gama fadar haka sai ya mike sannan ya kama dokinsa ya haye ya sukwaneshi da gudu,
kafin cikar dakika shida sai gashi tare da wasu
barada cikin shigar yaki. a dai-dai wannan lokacine wani bawa ya iso wajen yana rike da
linzamin dokin da Sarki Balwanu yake hawa. Sarki ya kama okin ya haye tare da sakar ma sa
linzami, sauran baradan hade da Sarki yaki suka take ma sa baya.
Lokacin da suka shiga cikin Birnin sai ya zamana duk inda taron jama'a suke da sun hango
Sarki Balwanu da mukarrabansa sai kowa ya tarwatse tamkar sun ga mutuwa, ma su
kasuwancima ba'a bar su a baya ba don suma hade kayansu suka dinga yi, tare da rugawa
gida jensu. Idan kuwa mutum bai yi saurin debe kayansa ba har baradan Sarki Balwanu suka
tarar dashi, take za su dniga dukansa da wata doguwar bulala mai tsayin zira'i ashirin da biyar
har sai sunga ya daina motsi, kayan kasuwancin nasa dawakansu subi ta kansu.
Ba kowane ya sa wadan nan barada aikata wannan zalunci ba illah Sarki Balwanu domin a
cewarsa duk wanda ya hangoshi daga nesa bai dakata da duk abin da ya ke yiba to ya nuna
taurin kai a gareshi, wannan da liline ya sa akewa duk wanda aka tarar wannan wulakanci.
Kafin cikar wani lokaci gaba daya Birnin na Zalmura ya yi shiru kowa ya shiga gidansa, wasu
kuma sun buya a wani wuraren.
Ko da Sarki Balwanu yaga yadda jama'a suke gudunsa tamkar sunga wani dodo sai ya
takarkare ya bushe da wata mahaukaciyar dariyar mugunta, sannan ya shiga yiwa kansa kirari
tare da kuranta kansa, su kuwa baradan da suke bayansa sai suka shiga amsawa abin da ya ke
fada, sai da ya jima yana kirarin sannan ya ci gaba da tafiya.
Ya yinda suka iso gidan matsafiya Amrishatu sai Sarki Balwanu ya ja linzamin dokinsa ya tsaya
cak! sannan ya sauko daga kan dokin, har Sarkin yaki ya yunkura shima zai sauko daga kan
nasa dokin sai Sarki Balwanu ya dakatar dashi ta hanyar daga ma sa hannu, ya ce, "Ku jira ni a
kofar wannan gida har tsawon sa'a uku saboda zamu tattauna da uwar. Bokaye, ku tabbata kun
bawa gidan nan tsaro yadda babu wata halitta da zata iso kusa dashi bare harta shiga". Ko da
jin abin da Sarki Balwanu ya ce, sai Sarkin yaki ya dukar da kansa yana mai cewa, "Zamu cika
umarninka kamar yadda ka fafa".
Daga nan Sarki Balwanu ya nufi cikin gidan, kafin ya karaso kofar gidan tuni Dakarun da suke
gadinta sun budeta, sannan suka zube kasa don nuna girmamawa, shi kuwa Sarki Balwanu sai
ya danna kansa zuwa cikin gidan.
Kamar yadda Sarki Balwanu ya taradda
matsafiya Amrishatu a kwance akan gado a wan can karon hakama ya sameta a yanzu, sai dai
sabanin da aka samu shine ta mike zaune tana mai dube-dube a jikin madubin tsafinta.
Shigowar Sarki Balwanu ita tasa ta dago da kanta don ganin wanda ya shigo, koda tayi arba da
Sarki Balwanu sai ta saki murmushi sannan ta fara cewa, "Mar haban da babban Sarki Dodon
sarakuna Hadari sa gabanka inda kake so. Ka zamo gindin kuka kafi runguma sai sara, kaine
kwado mai kwacewa kunama koto, hamshakin Sarki kake mai bawa sarakuna umarni subi ko
suna so ko basa so. Kai ina wani azzalumi ga babansa, kaine abul zulmu, sahibul zulmu mai
koyar da darasin zalunci.
Kara, so gareni don mu gaggauta tafiya zuwaga uban Bokaye Kurbasu Ibn Zalmur wanda zai
biya mana bikatarmu."
Sarki Balwanu yaji girman kai yashiga cik 1 kokan kansa bisa jin kirarin da matsafiya Amrishatu
ta yi ma sa, sai ya tako har zuwa kusa da gadonta ya zauna, sannan ya fuskanceta ya ce, "Ya
ke Amrishatu uwar Bokaye kina nufin kice min kin gama shiryawa ni kika jira?".
Matsafiya Amrishatu ta jinjina kanta tana mai cewa, "Ai damanni a shirye nake tun a jiya, dalilin
da yasa nace sai yau zamu tafi saboda na san kai
Sarkine kana bukatar nutsuwa a kwakwalwarka idan nace a jiyan zamu tafi hankalinja zai rabu
kashi-kashi ka dinga tunaní a zuciyarka, kuma hakan yana da matukar matsala muddin mukaje
gaban Boka Kurbasu a haka, domin zai yi maka wadansu tambayoyi wadanda idan ka bashi
amsa dai-dai zai biya mana bukatar idan kuma ka kuskure ba zai taba amincewa damu ba, don
haka ya zama dole ka nutsu. Yanzu na kirawo abokin tafiyarmu wanda zai kaimu har kogon
Boka Kurbasu a sa'a daya kacal! idan ka shirya sai mu tafi B
Lokacin da Amrishatu ta zo nan a zancenta sai Sarki Balwanu ya mike tsaye tare da gyara
alkyabbarsa yana mai cewa, "Nima na gama shiryawa zamu iya tafiya".
Yana rufe bakinsa sai Amrishatu ta dauko wata kwalba me dauke da shudin ruwa a cikinta. Ta
bude murfin kwalbar tana mai karanta wasu kalmomin tsafi, nan take wani hayaki ya dinga
fitowa daga cikin kwalbar yana taruwa a waje daya, shi kuma ruwan kwalbar yana raguwa a
hankali. Har sai da ruwan ya kare, sannan hayakin ya daina fitowa, a sannan ne hayakin ya
bada siffar Aljani.
Kafin Sarki Balwanu ya yi wani yunkuri tuni
hayakin ya nufoshi, yana shakarsa sai hankalinsa ya ģushe bai san kuma abin da ya faru dashi
ba.
Lokacin da hankalin Sarki Balwanu ya dawo jikinsa sai ya tsinci kansa a tsakiyar wani
kungurmin daji mai yawan ciyayi, a kusa dashi kuma Bokanya Amrishatu će a zaune a kasa
tana mai yi ma sa murmushi, daya dawo da dubansa zuwa dajin sai ya yi arba da wani katon
kogon dutse mai tsananin girma da kuma duhu, kai da ganin wannan kogon dutse ka san babu
mai iya zama a ciki walau mutum, dabba ko aljan sai wanda ya yarda da kansa, kasancewar
kogon yana tsakiyar wannan dajin wanda shi kadai ma abin tsorone.
Sarki Balwanu ya dubi matsafiya Amrishatu ya ce, "Ya ke uwar Bokaye wannan kuma wane
dajine, kuma me yasa kika ajiyemu a kusa da wannan kogon dutse?".
Koda jin wannan tambaya sai matsafiy a . Amrishatu ta bashi amsa da cewa, "Wannan shine
dajin Zailuma, shi kuwa wannan kogon dutse shi akewa lakabi da Darul Sihir wanda ya kasance
mazaunin Boka Kurbasu. Yanzu zamu shiga cikinsa domin mu gana dashi".
Sa'adda Sarki Balwanu yaji abin da tsohuwa Amrisuatu ta ce, sai ya yi shiru yana mai fadawa
kogin tunani. Daga can sai ya dago da kansa da sauri yana mai cewa, "Yanzu ke nan duk da
kasancewar kogon dutsen nan yana da matukar duhu amma zamu shiga cikinsa, kina ganin ba
zamu samu barazana ba daga halittun dake cikinsa?".
Tsohuwa Amrishatu ta yi murmushi tare da cewa, "Haba ya kai Sarkin sarakai ka manta kana
tare da nine ai babu wata halitta data isa ta cutar damu a wannan kogo in banda Boka Kurbasu,
zan samar da haske a cikin kogon yadda zamu iya ganin komai dà idanunmu".
Matsafiya Amrishatu tana gama fadar haka, sai ta runtse idanunta tana mai karanta dalasuman
tsafi tare da yin nuni da hanunta zuwa kofar kogon dutsen.
Sai da ta sami rabin sa'a tana wadan nan surutai don ganin haske ya samu a kogon amma ko
alama babu, kai daga karshema sai da ta hada gumi sharkaf tamkar wadda aka cirota daga
cikin ruwa. Numfashinta ya'fara sarkewa idanun su ka yi jajir, hannun ta ya fara fitar da wani
turiri. Abu kamar wasa sai da sa'a biyu ta shude haske bai samu a cikin kogon ba. A sannan ne
Bokanya Amrishatu ta zube kasa tana mai fitar da numfashi sama-sama. Sarki Balwanu ya ruga
da gudu ya tashe ta zaune
yana mai tambayarta dalilin faduwarta.
Daga cikin kogon dutsen suka ji wata kakkausar murya ta bushe da dariya tamkar rugugín
hadari. Dariyar ta ci gaba da hauhawa tana karin sauti kamar wanda ya ke yinta bazai daina ba,
amma kuma bisa mamaki sai aka tsaya cak da yinta, sannan aka fara da cewa, "Lallai
Amrishatu kinyi kuskure kuma zanyi miki gyara akansa, shin kin manta duk halittar data shigo
wannan dajin tsafinta baya tasiri sai idan ya fita daga cikinsa, saboda karfin sihiri na yafi na
kowa, kuma ina da sanin da kafin a samu matsafi kamarni za'a sha matukar wuya".
Lokacin da muryar nan. tazo nan a zancenta, sai tsohuwa Amrishatu tace ina neman a fuwarka
ya shugabana cilia Bokaye, tabbas nayi kuskure kuma hakan ba zata sake faruwaba.
Nasan. cewa kasan abinda muke tafe dashi, muna neman taimakonka tun kafin makiya suga
bayanmu su rusą daular zalinci".
Sa'adda matsafiya Amrishatu ta zo nan a zancenta sai Sarki Balwamu ya jinjina kansa dan sai a
lokacin ya gane ko waye wannan mai magana ba kowa bane fa ce Boka Kurbasu. Sarki
Balwanu ya ce, a zuciyarsa,
Ashe a duniyar nan akwai wani matsafi da
uwar Bokaye Amrishatu zata risina a gareshi a matsayın shugabanta. Lallai wannan Boka ya
cika uban Bokaye".
A dai-dai wannan lokacinne kogon dutsen ya haskake da'wani haske wanda basu san daga
inda yake ba, sannan muryar nan ta ci gaba da cewa, "Ni mai taimakonku ne a duk inda kuka
sa gaba. Ku shigo don na sanar da ku hanyoyin da zamubi mu rusa duk wasu masu shirin
kawar da zalunci daga doron kasa".
Ko da muryar ta zo nan a zancenta sai Sarki Balwanu ya mike tsaye da nufin ya goya tsohuwa
Amrishatu su shiga cikin kogon, sai kawai suka ga wata siririyar iska ta taho ta zukesu shida
Amrishatu ta shigar da su cikin kogon.
Ba su tsinci kansu a ko inaba sai gaban wani mutum wanda ya ke zaune a kan wani faffadan
dutse. Ya tankwashe kafafunsa tare da rufe idanunsa. Mutumin ya kasan ce mai kasumba
wadda ta cika duk ilahirin fuskarsa, hanci da idanunsa ne kawai a waje, amma hatta bakinsa
gemu ya rufe shi. Sannan yana da katon ciki tamkar tulu kai da ganin wannan ciki kasan yana
cin abincin bila adadin. Ko kadan babu riga a jikin mutumin illa wani wargin fata da yake daure a
kugunsa.
Sa'adda suka tsinci, kansu a gaban wannan mutumin wanda ba kowa bane face Boka Kurbasu
sai matsafiya Amrishatu ta duka takai ma sa gaisuwa, sannan ta bude baki da niyar ta yi
magana, amma sai Boka Kurbasu ya daga ma ta hannu yana mai yi mata nuni da tayi shiru
kada ta yi magana, don haka sai ta kame bakinta kamar yadda ya umar ceta sai da suka shafe
rabin sa'a ba tare da wani daga cikinsu ya ce komai ba, sannan Boka Kurbasu ya bude jajayen
idanunsa, sannan ya dubi Sarki Balwanu wanda yake zaune yana kallonsa tare da tsohuwa
Amrishatu ya fara ce musu, "Ya kuwadan nan masu son dasa daular zalunci a doron kasa.
Hakika na san duk abin da yake tafe daku, kuma zan share muku hawayenku yadda babu wata
halitta da zata sake yunkurin kawo muku mamayar ba zato.
Sai dai matsalarmu guda da yace ba kowane matsalar ba face SADAUKI MAI ZAKI, wanda idan
har bamuyi da gaske ba zai iya rusa daular zalunci, saboda yana da karfin dantsen da samun
kamarsa yana da wuya.
Ya kai wannan Sarki zaka zamo sadaukin maza mai tarwatsa rundunar barada, zanyi amfani da
karfin sihirina ka zamo hamshakin gwarzo wanda duk fadin duniya baza'a samu mai karfin
dantsen ka ba, babu wani sadauki da zaku hada kwanji dashi baka murde masa hannu ba koda
kuwa hannun karfene dashi, ta hakane zaka koma can Birninka ka yi rayuwarka a cikin
kwanciyar hankali, na, rantse da karfin sihirin tsafina ko sadaukik mai Zaki ne zai zo zaka iya
hallakashi a sa'a daya, kacal, sannan ka murdewa Zakin nasa wuya, daga karshe ka je ka kamo
mahaifiyarsa da Tsoho Shalfanu da matarsa ka yi mu su muguwar hallaka, ita kuma 'yarsa ka
aureta kamar yadda ka so ka yi da farko".
Mu hadu a na biyu
arewanovels.com.ng