Showing 1 words to 1414 words out of 1414 words
Chapter 1 - BASARAKE BOOK 1 COMPLETE BY MANSUR USMAN SUFI .pdf
BASARAKE
LITTAFI NA FARKO
Shekarar Rubutu 2025
©️ Haƙƙin Mallaka :- SUFI
Rubuta Labari
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
BABI NA FARKO
Ƙasaitacciyar kasuwar ta cika ta batse da manya da ƙananan fatake, maza da mata
haɗe da ayarin baki daga birane da manyan ƙasashen duniya.
Duk inda mutum ya kai duban sa zai ga jama'a na ta kai komo suna hada-hadar siye da siyarwa
cikin kwanciyar hankali da lumana.
Fiye da shekaru ɗari bakwai wannan kasuwa ta kasance cibiyar cinikayya a yankin ƙasashen
Larabawa baƙaƙen fata, shekarun da suka shuɗe kasuwar tana ci ne duk bayan wata shida,
ma'ana a shekara sau biyu kenan, amma kasancewar FATAKE na yin tafiya mai nisan zango,
daga sassan duniya hakan ya sanya aka canja tsarin ya zamto cewa a duk lokacin da wani
ayari suka iso birnin Zawatul-dinar za su iya gudanar da cinikayyar su. Sai dai duk shekara ana
cin kasuwar ƙarshen zango.
Bakomai ne ya sanya birnin Zawatul-dinar ya samu wannan shahara ba sai bisa dalilai
guda huɗu.
Na farko shi ne sun bunƙasa a arzikin noma da kiwo, yawan al'umma masu kyawun ɗabi'u,
tarin ZARATAN JARUMAI masu Juriya a FILIN DAGA, abu na ƙarshe shi ne samun adalin sarki
mai jiɓintar damuwar al'ummarsai.
Sarkin dake riƙe da sarautar birnin ana yi masa laƙabi da Hubrul-Zaman. Sarki Hubru
kasance kyakkyawar saurayi ma'abocin kwarjini, ƘARFIN DAMTSE kuma mashahurin attajiri.
A wannan lokaci gaba ɗaya ƙasashe da biranen dake nahiyar sun shaida cewa babu
MASHAHURIN SARKI kuma GWARZON MAYAKI tamkar sa.
Duk waɗannan abubuwa da sarki Hubru ya mallaka dukiya, ƙarfin rundunar mayaƙa sun
zamo tamkar kumfar kogi, domin kuwa ba sa da magaji da zai zamto halifansa.
Bai taɓa soyayya ba kuma bai yarda da ita ba, yana ganin cewa babu komai a cikin soyayya
face shirme da shashanci.
'Ya'yan manyan sarakuna, bokaye haɗe da attajirai sun bayyana sirrin zukatansu na buƙatar
mallakar Hubru a matsayin abokin tarayya, amma sai ya sanar da su cewa ba zai taɓa yin
soyayya ba har ƙarshen rayuwar sa.
Bisa al'adar sarki Hubru duk lokacin da yake cikin nishaɗi ya kan yi ɓadda-kama ya shiga
izuwa daji domin ya yi farauta.
Wata rana daga cikin ranakun da Huburul-zaman ke fita farauta, tafe yake a bisa ingarman
doki, yana sanye cikin baƙaƙen tufafi ya rufe fuskarsa da rawani idanuwansa kaɗai ake gani.
A gadon bayansa yana rataye da wani rantsattsan KWARI DA BAKA a kwiɓin cinyarsa yana
makale da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta.
Ya wanzu yana ratsa wani daji mai cike da duhuwar bishiyu, duwatsu, ƙoramu da sarƙaƙiya.
Lokacin da ya iso wata bishiya sai ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak! Ya sauko ƙasa ya ɗaure
sa a jikin bishiyar sannan ya sake kunna kai izuwa cikin dajin yana mai zare bakansa.
Sannu-sannu sarki Huburul-zaman ya shafe tsawon rabin sa'a yana tafiya ba tare da ya ji
motsin koda ɓera ba ballantana ya ji kukan tsuntsu, al'amarin da ya yi matuƙar ba sa mamaki
kenan kuma ya ɗaure masa kai kenan, domin tsawon shekaru goma yana fitowa wannan
farauta hakan bai taɓa faruwa ba ya ce a ransa, shin ko dai halittun dajin sun farga da shigowa
ta shi yasa suka nemi maɓuya. Wani ɓangaren a zuciyarsa kuma ya ce da shi anya kuwa ba
maƙiyin ka ba ne ya yi maka tarko domin ka faɗa.
Amsar tambayoyin da Huburul-Zaman ya kasa bawa kansa kenan, kawai ya ci gaba da
kutsa kai cikin dajin har yazamana ya shafe sa'a ɗaya cif! A dai-dai wannan lokaci ne ƙishi da
yunwa suka fara addabar shi, amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta GWARZON ƘARNI sai
ya ƙara himma. Yana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ya hango wata kyakkyawar barewa ta sunkuiyar
da kanta ƙas tana shan ruwa a ƙorama.
Nan take farin ciki ya cika zuciyarsa ya zare kibiya guda ɗaya a cikin kwanson dake rataye a
gadon bayansa ya saka a cikin bakansa ya ja ya taɓe da dukkan ƙarfin sa sannan ya harba.
Kibiyar ta tafi cikin matsanancin gudu tana mai keta iska ya durfafi barewar, lokacin da ya
zamana tazarar dake tsakanin kibiyar da ita bai huce kamu huɗu ba, kwatsam! Sai wata kibiyar
daban ta bayyana ta kaɗe ta Huburul-Zaman.
Al'amarin da ya fargar da barewar kenan ta ranta a na kare.
Al'amarin da ya fusata Huburul-Zaman kenan ya fusata ainun cikin takaici ya rufa ma barewar
baya suka tasa tsere.
Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce inda babu ƙasa nan ake
gardamar kokowa.
Ana fara wannan artabu ne wani abun mamaki ya fara wakana, ya zamana cewa duk irin ƙarfin
gudu na sarki Hubru amma ya kasa cimma barewar.
Lokacin da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu ana wannan tsere nan take Ƙarfin gudun
sarki ya fara raguwa saboda yunwa da ƙishi da suka ƙara tsananta gare sa.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ya ji hucin hucewar wata kibiya ta saman kansa. Kafin
ya farga ta soke wannan barewa a gadon bayanta ta wuntsila ƙasa matacciya ko shurawa ba ta
yi ba.
Al'amarin da ya sanya Huburul-Zaman ya ja ya tsaya ya yi turus cike da matuƙar al'ajabi,
yana mai duba gabas, yamma kudu da arewa ko zai ga makashin barewar ya bayyana amma
shiru kake ji.
Kawai sai ya durfafi inda gawar barewar take domin ya sarrafa naman ta ya yi kalaci ko ya yi
maganin yunwar da ta addabe sa
Kwatsam! Sai ya ji busassun ganyayyaki na motsawa, alamun dake nuni da cewa akwai wani
abu mai rai da yake shirin bayyana gare sa.
Daga can sai wani jarumi ya yi fitar burgu daga cikin duhun bishiyun dajin daf da inda barewar
take tamkar an harbo sa daga cikin baka.
Jarumin yana sanye da tufafin fatun dabbobi da aka yi su da fatar damisa tun daga ƙasa har
sama, ya rufe fuskarsa da baƙin yanki idanuwansa kaɗai ake gani, a gadon bayansa yana
rataye da wata rantsattsiyar KWARI DA BAKA da aka sana'ata ta da wani itace na musamman.
Koda bayyanar jarumin sai ya tsugunna ƙasa ya zare kibiyar dake jikin barewar ya goge
jinin dake jiki a ƙasa, ya mayar da ita izuwa cikin kwansonta.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jarumin da sarki Huburul-zaman har na tsawon daƙiƙa
talatin, daga can sai Huburul-Zaman ya dakawa jarumin tsawa ya dube sa cikin matuƙar fushi
ya ce "ya kai wannan jarumi shin wane ne kai da zan farauto dabba, ka zo ka ce za ka yi min fin
ƙarfi? Maza ka amsa min tambaya ta kafin na yanke maka hukunci dai-dai da laifin da ka aika ta
min?"
Koda jin wannan tambaya daga bakin Huburul-Zaman sai jarumin ya yi gum da bakinsa ba
tare da ya ce uffan ba.
Al'amarin da ya fusata Huburul-Zaman kenan ya sake maimaita masa tambayar a karo na biyu.
Sai a lokacinne jarumin ya buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarewa ya ce "ai ni
ya fi dacewa ka bawa amsar waɗannan tambayoyi domin ba zai yiwu ace "kura da shan bugu
gardi da ƙwace kuɗi ba".
Sa'adda sarki Huburul-zaman ya ji wannan batu daga bakin jarumin sai ya cika da matuƙar
mamaki ainun kuma ya fusata. Abin da ya ba shi mamaki shine jin muryar 'ya mace a lokacin da
jarumin ya fara magana. Sai a lokacin ya kuma ya lura cewa surar halittar JARUMIN sun fi
karkata zuwa na 'ya mace wato gashin kai da kuma tudun ƙirji. Abin da ya fusata shin kuwa shine a iya tsawon rayuwarsa babu wani mahaluki da ya taɓa
GABA DA GABA da shi har suka yi musayar yawu da shi ba sai a yau.