Showing 1 words to 1878 words out of 1878 words

Chapter 1 - MULKIN ZALUNCI Book 1 Part A By Adam Tukur Miyatti .pdf

MULKIN ZALUNCI
Rubuta Labari Adam Tukur Miyatti
Sarkin Samarin Marubutan Afrika
arewanovels.com.ng


Sarki KADDARU ya dubi dattijon dake tsugunne a fadar tasa da ita kadai ta isa a kirata da
aljannar duniya domin kuwa duk wani kayan ado dana more rayuwa an mallaka a cikin wannan
luntsumememiyar fada mai cike da kawatuwa. Kuma ta gaban kwatance domin tsayawa
zayyana abubuwan da wannan fada ta kunsa zai iya zama kauyanci.
Yakai "tsoho RAUWAKU kayi sani cewa baka isa ka tsira daga sharrina ba na rantse da karagar
mulkina sai na kasheka da kisa mafi muni domin ya zama darasi ga dukkan wani mutum mai
shirin aikata irin abinda ka aikatamin ko kuma bijirewa umarnina. Koda yazo nan a jawabinsa
sai yai ajiyar numfashi sannan ya cigaba da bayani kamar haka "kazabi daya a cikin uku wane
hukunci zan yanke maka, hukunci na farko shine
zan yi jima'i da matarka da kuma jikarka sai na yafe maka laifin da ka aikata

Hukunci na biyu kuma shine zan daureka a cikin dakin ukuba a kullin za a dinga gana maka
azaba daban daban ko kuma nae daukeka na kaika zuwa KURKUKUN SHADIDUL MAUT.
Koda tsoho Rauwaku yaji wannan hukunci da sarki kaddaru ya yanke a kansa sai ya takarkare
ya kurma uban ihu sannan ya fashe da kuka yai tayi wiwi tamkar ransa zai fita daga jikinsa
zuciyarsa ta turnike ya rasa nutsuwa a ransa tamkar zai zauce a ransa ya soma sakawa yana
warwarewa yana cewa tabbas mudai mun kasance mutane amma bamu da maraba da dabbobi
wadanda ake cin kashi kansu.kuma wadanda basu da iko akan kansu balle su taimaki waninsu.
Lalle idan mukaci gaba da wannan matacciyar rayuwa tabbas waťaran za a wayi gari bamu
gaba daya kuma sai yanzu na kuma tabbatarwa cewa a duk duniya ba
azzalumin sarki kamar sarki kaddaru.
Nidai na mutu da sauran raina dama gidauniyar mutuwa tazo ta daukeni na huta da wannan
bala'i.

Yana cikin wannan yanayine yaji an daka masa tsawa ana mai cewa kai karamin dan iska ka
cikan kunne wane kazaba ne acikin hukuncin dana yanke maka. Koda yaji haka sai yai tsit
tamkar daukewar ruwan sama sannan ya dago kai da luhu luhun idanuwansa wadanda suka
dade da yin jajir yace dashi ya shugabana kamin afuwa ka kuma yimin karka azabtar dani da
hukuncin dabazan iya daukaba domin hukuncin daka yankemin duk sun yimin tsauri ya
shugabana ina mai rusunawa agareka da neman sassauci duk da nasan nine da laifi kuma na
cancanci karbar duk wani hukunci daka yanke a gareni.

Koda sarki kaddaru yaji haka saiya mike tsaye a fusace kamar wanda zai shakoshi amma sai
ya takarkare ya bushe
Mulkin Zalinci Miyatti

da wata mahaukaciyar dariya tamkar mahaukaci sabon kamu ya dade yana kyakyatawa daga
bisani kuma ya murtuke fuska tamkar wani annuri bai taba kusantar fuskar ba sannan ya dubi
tsohon yace dashi nayi maka sassauci bisa hukuncin dana baka zabi uku kace duk summa
tsauri to a yanzu zan yanke maka hukunci na karshe wanda dagashi bazan kuma yima
sassauci ba.

Hukuncin shine zansa a gutsure maka kafa daya hannu daya da kunne daya dan haka wannan
hukunci dana yanke maka ba sassauci a cikinsa.

Koda dattijon yaji wannan hukunci daga bakin sarki kaddaru sai ya cika da dumbin farin ciki.
Sarki kaddaru ya karbi takobi ya cire mai hannun hagu da kafar dama da kunne na barin hagu
ya tsandara ihu ya fadi a sume daidai lokacin da jini yai fitar burtu daga hannunsa da cinyarsa
da aka cire.
To mai karatu shin wanene sarki yayiwa kaddaru, kuma shin wanene rauwaku.sannan kaddaru.
me tsoho sarki

Sarki kaddaru shine sarkin dake mulkin birnin kufa a wannan zamani, sarki kaddaru shine sarki
na sittin da takwas amma hasashe ya nuna cewa a wannan zamani duk duniya babu sadauki
tamkarsa bai taba aure ba saidai yana da wata 'va davake mutukar ji da ita a duk duniya babu
yar dayake so sama da wannan 'ya to ko a ina yasamo ta oho kuma tayaya tazama yarsa sarki
kaddaru dattijane mutum dan kimanin shekaru saba'in da bakwai yahau kan karagar mulkinne
yanada shekaru talatin aduniya.

A da mutanan birnin kufa suna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali amma tun daga lokacin da
sarki kaddaru yakarbi karagar mulkin sai suka kasance cikin tashin hankali da rashin nutsuwa.

Harkawo wannan lokaci dasuke ayanzu sarki kaddaru sadauki ne kuma kakkarfa mai karfin
allah ya isa domin duk wanda ya zalunta saidai ya hakura koda kuwa sarki ne domin idan sarki
yana takama da dakaru baikaishi ba kuma inkarfine ma haka domin shi ko rumawa ma
tsoranshi suke saboda tsagwaron karfin dantse duk girman kasa idan ya durfafeta sai ya
rusheta akan dakikun da basu wuce sa'a guda ba, sankar sa a filin yaki kuwa tamkar saukar
aradu ne domin da zarar ya iso sai ya yamutse dakaru komin yawansu.

Sarki kaddaru duk inda yake yana tare da gimbiya LASHMIRA koda kuwa fada ne saidai yasa
doka mai tsanani akanta dokar kuwa itace duk wanda ya kuskura ya hada ido da ita to
hukuncinsa cikun biyu daya ne kodai ya kawo matarsa ko kanwarsa ko kuwa jikarsa ko kuma a
kaishi kurkukun shadidul maut a rufe a kaf tarihin ya nuna baja taba yin

ganin halin da nake ciki sannan suka ce da ni nazo inji sarki, da naji haka sai na dube su nace
dasu dubi halin da nake ciki kwakkwaran motsi ma bana iyawa domin tun jiya ban rintsa ba don
girman abin bauta ku koma ku shaidawa sarki banda lafiya bazan iya zuwaba. Koda dakarun
sukaji haka sai naga sun zaro idanu a tare daya daga cikinsu yace dani kayi hakuri vakai

safwan dole mubi umarnin sarki kaddaru dan gudun halaka domin bazai barmu ba in har muka
shaidamai baka da lafiya don haka kayi hakuri da hukuncin dazan yanke maka koda yazonan
jawabinsa sai yai shiru kamar bazai ce komai ba daga bisani kuma sai naga ya mirgina kai
alamun dakarun su daukeni nan take suka cika umarnin shugaban nasu suka ciccibeni sukai
waje dani suka azani bisa wani ingarman doki suma suka have nasu dawakan muka nufi fadar
sarki kaddaru muna isa ne mamaki matuka ya kamani ganin yanda fadar ta cika makil ba
masaka tsinke tamkar zaai wa wani

hukunci karasawarmu keda wuya dakarun suka ajiyeni a tsakivar fada sannan suka rissina a
gaban sarki suka ce gashi mun kawoshi ya shugaba. Koda sarki kaddaru yaji haka sai va
dubesu sa,annan ya dubeni ina lavi va takarkare ya bushe da dariva yadan tsawon lokaci yana
darawa sannan ya tsuke bakinshi kamar bashi ne me dariyar ba sannan ya dubi shugaban
dakarun da suka kawoni yace yakai dabaru shin nace ka kamoshine ba cewa nayi kace yazoba
dabaru ya bude baki zaiyi magana sarki kaddaru ya dakatar dashi yace bana bukatar jin wani
furuci daga bakinka tunda kuwa ka karya doka to hukuncinka kaida yaranka shine zan kaiku
dakin ukuba harna tsawon kwanaki talatin sannan na fito daku koda sukaji haka sai duk suka
zube suna rokonsa gafara da yayi musu sassauci koda yaji haka sai ya kuma bushewa da
dariya harda buga kafa daga bisani saiya tsuke baki yace na gode da tayin da kukai min domin
kun nunamin cewa hukuncin dana yanke muku na kaiku

take zai halakashi. Ya shiga halwar tsafinsa yana cikin wannan bincike ne kwatsam ba zato
bare tsammani sai yaga dakaru tsaye a kansa yayin da yarazana ainun da ganin dakaru ashirin
cikin halwar tsafinsa kuma ya rasa ta inda suka shigo cikin halwar tashi tunda shidai baiji karar
bude kofa ba kuma baiji motsin. suba bare yace ko dama suna ciki. Abinda bai saniba shine
dakarun ba mutane bane sun kasance aljanu ne suka rikida suka zomai a suffar mutane kuma
su duka sun. kasance hadiman abokinsa wato sarki kaddaru va bude baki da niyyar ya musu
magana daya ya cafki wuyansa ya dankaramai naushi a makoshi saukar naushin keda wuya
tsoho rauwaku ya sume bai farfado ba sai a fada gaban sarki kaddaru a durkushe.

Bayan wannan sarki kaddaru ya sake kafa dokoki da dama a cikin birninsa doka ta farko da
sarki kaddaru ya kafa itace duk wani manomi in ya noma zai

raba amfanin gonarsa kaso uku ya dau dava sannan dayan ma ba,a yarda ka ajiye a gida ka
ciba saidai ka fita kasuwa ka siyar in ka siyar ka raba abinda ka samu kaso uku ka bawa
gidauniyar sarki kaddaru daya haka shima dan kasuwan daya siya saiya raba hatsin uku yadau
biyu ya bawa sarki kaddaru daya. Haka zalika in zakayi siyayya shima sai ka cire kason sarki
kaddaru ka bayar shima dan kasuwan haka. Wannan hukunci shi ya rinka karya manyan
attajiran da yan kasuwan garin gami da fatake masu zuwa birnin kufa kasuwanci har suka soma
ja da baya domin duk karfin dukiyarka sai ta narke in ka shiga da ita birnin na kufa. Hukuncin
sarki kaddaru ba,a kan manoma ya tsayaba har masunta duk masuncin dava kamo kifi ko
kadanne saika raba biyu ka bawa sarki kaddaru kaso daya sannan sai ka fitar da kaso daya ka
siyar dashi kasai abin masarufi shima kuma akwai harajinsa. Bayan haka

inkai makadi ne inka samu kudi a wajen biki ko suna toh nan ma akwai kamashonsa. Bayan
haka kuma ya kafa doka ta biyan haraji cewa babba da yaro duk wanda ya kwana a cikin
birninsa sai ya biya dinari daya ba ruwansa da talaucinka ko arzikinka bayan haka duk wanda
aka mai rasuwa sai ya biya dinare bakwai sannan ya binne gawar koda kuwa a cikin gidansa
za,a binne ta in ba hakaba kuwa saidai su dauwama da gawar domin baza a binne ba. Koda
sarki kaddaru va kafa wannan doka kuma jama,arsa suna sulalewa su gudu don barin birnin
kufa sai ya sa dokar cewa duk wanda ya kuskura ya bar birnin kufa sai ya halakashi ko kuma ya
kaishi kurkukun shadidul maut kuma hukuncin bashi kadai ya shafa ba har danginsa kaf.

Tun daga wannan rana jama,ar birnin kufa'suka kasance tamkar matattu domin kuwa babu mai
jin dadin
rayuwarsa. Sarki kaddaru duk wannan tsawon shekaru nasa bai taba aure ba.

***

Tsoho rauwaku bashi ya farfado ba daga suman da yayi sai bayan ya shafe sa,a uku.yana
farfadowa sai ya tsinci kanshi a dakin bada magani likitoci nata kokarin ceto rayuwarsa suna
manne raunin guntun hannun da wasu korayen ganyaye. Koda tsoho rauwaku ya farka ya
ganshi a wannan matsanancin hali sai ya fashe da kuka, ya dade yana kuka gami da surutai
yana cewa" dama mutuwa nayi na huta da wannan bala,I da masifa da nake ciki wai ace kamar
yanda muke da sarki kaddaru yamin irin wannan danyen hukunci na cin zarafi". Yana cikin
wannan sambatu sai yaji an dafa shi ta baya gami da kiran sunanshi, yakai rauwaku ka daina
irin wannan surutan domin basu dace da kaiba kuma kai ai ta zoma da sauki


Mu hadu a littafi na ɗaya Part 2
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da koyaushe
Adam Tukur Miyatti
Sarkin Samarin Marubutan Afrika

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login