Showing 1 words to 2042 words out of 2042 words
Chapter 1 - SADAUKI MAI ZAKI Part 2 littafin Yaki By Mu'awiyya A Muhammad .pdf
SADAUKI MAI ZAKI
Mu’awiyah A Muhammad
arewanovels.com.ng
"Ya kai shugaban Bokaye ta ya ya zan zama sadaukin da babu kamarsa a fadin duniya, idan
har kuwa na zama babu abin da zai hanani in ninka zaluncin da nake yi sau dubu. Sai na yaki
dukkanin biraneń da suke kusa da Birnina yadda zan karawa Birnin Zalmura girma ya dawo
babu kamarsa, sannan na saka dandazon mazajen fama bataliya guda a cikikn fadata". Ko da
Sarki Bałwanu ya ze nan a zancensa sai Boka Kurbasu ya bushe da wannan dariya tasa mara
dadin sauraro, sannan lokaci daya ya turbune fuskarsa ya ce, "Wannan shine gwajin farko da
na yi maka don naga iya zurfin da kayi a bangaren zalunci, kuma
na lura kai ba karamin azzalumi bane, saboda haka yanzu take zan baka wata damara ta tsafi
wadda idan ka daurata a jikinka zaka zamo sadaukin sadaukai.
Yadda ko doki bai isa ya dauke ka ba sai dai toron giwa, itama idan ka yi tsalle ka dira a kanta
sai ta fadi matacciya, idan kuwa ka shiga cikin dandazon mayaka komai yawansu ba za su yi
sa'a daya a gabanka, sai dai ita wannan damara tana da wasu sharudda kadanda idan ka
aikata tsafin da ya ke jikinta zai lalace.
Sharadi na farko shine idan ka sanya ta kada ka yarda ka tausayawa wani, duk wani abin
tausayi kada kaji tausayinsa koda kuwa kai kanka.
Sharadi na biyu kuma ba'ayin adalci ka zamo mai zaluntar kowa, idan ka yarda ka aikata
tausayi tasirin tsafin da sihirin da yake jikinta zai karye. Wadan nan abubuwa biyu ka gujesu
idan ka sanva wannan damara. Sannan kuma idan ka daurata ke nan ta manne a jikin fatarka
ba zata taba fitava bare makiyanka suyi tunanin rabaka da ita"..
Sarki Balwanu ya sake cewa da Boka Kurbasu, "Na amince da duk sharadın da ka furta kuma a
shirye nake da kiyaye su".
Boka Kurbasu ya yi murmushi, sannan ya daga hannunsa sama yana mai furta manyan
dalasuman tsafi, nan fa wata walkıya da tsawa suka gauraye kogon dutsen, kai kace zai
rugajene baki dayansa. Shi kansa Sarki Balwanu sai da ya toshe kun nuwansa bisa jin karar
tana barazanar lalata ma sa dodon kun nen. Daga cikin tsawa da walkiyar sai ga wata damara
nan ta bayyana hannun Boka Kurbasu, lokaci daya kuma sai tsawa da walkıyar suka dauke.
Boka Kurbasu ya mikawa Sarki Balwanu damarar yana mai yi ma sa izinin daurata. Hannun
Sarki Balwanu yana rawa da karkarwa ya karieta, sannan ya mike tsaye ya daura damarar
kamar yadda Boka Kurbasu ya umarceshi Yana sanyata sai, yaji ta manne da fatar jikinsa,
sannan yaji gumi yana karyo ma sa tako ina a jikinsa wanda bai san dalilin hakan ba
Sannan yaga jikınsa yana kumbura yana kara guma kwanji ya ciko hannayensa har sai da
alkyabbar da take sanye a jıkinsa ta yage jikınsa ya mummurde kamar an daure nakiya,
idanunsa suka juya kamar na kyanwa, tsayinsa ya karu fiye da farko, kai hatta takalmin da ya
ke sanye a kafarsa sai da ya fashe saboda kumburar da kafarsa ta yi.
A takaice sai da tufafin da suke jikinsa suka zube kasa a yayyage Sannan sai wasu
mahaukatan tufafi suka bayyana a jıkin nasa wadanda suka ka
sance bakake jikinu skwal manyan takubba guda hiyu ma su girman gaske, ko days daga kin
wadan nan takubba aka a jiye a kata naal en tara barada goma sannan za su iya rabata da
kasa amina hasu isa sun sarrafala ba
A kafarsa kuma wani takalmin fatar Zaki ne ya hayyana tamkar sai da aka duha kafar samman
aka hadashi
Maza) hakika idan mulum ya kai duban sa ga Sarki halwanu a wannan lokacı dole yasan za'a yi
zunzurutun karfin damise a tare dashi, kuma dole ya zamo DODON MAZA
Shi kansa a lokacin wani masifaffen Karfi yake ji a jikinsa wanda bazai misaltu ta baki ha sai dai
kawai a fadi abin da ya samu jiasa yake tamkar zai iya daukar kogon dutsen na Darul Sibir, ko
kuma zao iya yaki da sadaukan duniya bakı dayansu, kai yana jin ko duniyarce ta taru a kansa
zasiya murkusheta.
Boka Kurbsa ya mike tsaye daga kan dutsen da yake zaune ya dala kalar Sarkı Balwanu ya ce
ma sa, "Ya kai wannan Sarki shin ko zaka yi furata min inn karfin da kake ji a jıkınka?"
Ko da jin wannan tambaya sai Sarki Balwanu ya bushe da wata hatsabihiyar mahaukacıyar
danya wadda hargowa da rurinta ya cika kogon dutsen
dariyace irinta manyan sadaukai ma su takama da Kartin damtse, sannan ya ce, Ya kai
shigaban Bokaye na rantse kartin dans mallaka a yanzu han san a yadda zan fasalta sadaukan
takar dana keji a jikina yanzu ba
Sai dai a karanci ina jin ko za's yi ruwan Giwaye daga sama zan iya binsu ina cafewa" Ko da jin
abin da Sarki Balwanu ya ce, sai
Boka Kurbasu ya yi murmushi shima ya ce, "Na san da baka ya Balwanu, yanzu abin da nake
so ka sani shine tuni nayi tsafi yadda kafin SADAUKI MAI ZAKI ya iso Birninka sai ya yr tafiyai
kwanaki ashirin tukunna a maimakon sa'a goma shatakwas, kaga kafin lokacin ka gama tsara
yadda zaka tareshi duk da na san bazai bata maka lokaci ba wajen kasheshi, sannan a hanyar
tafiyar tasa zan dinga tura ma sa da masifu ta alkaluman tsafi da sihirina, na san cewa bai isa
ya tsallake sharrinsu ba, tunma kafin ya iso Birnınka zan hallakashi ka huta da fargabarsa ke
nan"
Sa'adda Sarkı Balwanu yaji abin da Boka Kurbasu ya ce, sai ya yi shiru na tsawon want lokaci,
sannan ya ce, "Ya kai uban Bokaye, banso ka kara ma sa nisan tafiyaba na so ka harshi ya iso
da wuri yadda zanyı ma sa kisan kiyashi, sannan kuma kana nufin kace min ya taho zuwa
Birninane
da nutin ya hallakani?"
Boka Kurbasu ya amsa masa da cewa, Tabbas yana shirin ya taho Birminka don daukar fansar
mahailinsa kamar yadda yaji labarin kai ne ka kasheshi a wajen mahaifiyarsa
Nan da kwanaki bakwai zai yi shiri ya taho, amma kamar yadda na furta maka da farko zanyi
maka maganinsa tun kafin yazo gareka"
Sarki Balwau ya sake cewa, "Ta yaya suka san zan yankewa Tsoho Shalfanu da iyalansa
hukunci da har ya kawo mu su dauki, sannan ya ya akayi mahaifiyarsa da kuma shi kansa suka
rayu alhalin sun nausa cikin daji wanda su kansu basu san inda sukayi ba?"
Boka Kurbasu ya ce, "Na san cewa zaka yı mamakin hakan, to amma gangancın da ka yi shine
lokacin daka kashe Sarki Salmir ka dawo gida maimakon kasa tsohuwa Amrishatu ta binciko
maka inda matarsa da dansa suka yi ka tura baradanka su hallakasu amma sai ka yi shiru da
al'amarin, yanzu gashi yaron ya girma yana neman kawo barazana ga rayuwarka.
Batun yadda akayı sadauki mat Zakı ya san zaka yankewa Tsoho Shalfanu hukunci shine,
lokacin da Sarki Salmir ya isa wannan Birnin da suka kaiwa Sarkin Birnin ziyara anan wani
Boka ya
basu want madubin tsafi vadda duk abin da suka su sani idan suka shafeshi da hannunsu suka
fura wasu dalasuman tsafi take komai zai bayyума garesu. Madubin tsafin yana hannun Zulfira
kuma bata tuno dashiba sai kwanaki uku da suka shude tana fadar dalasuman tare da shafashi,
nan take taga dukkanin abın da yake faruwa, shine ta kirawa danta sadauki mai Zaki ta nuna
ma sa fuskokinsu ta ce yaje ya ceto rayuwarsu.
Sai bayan ya dawone take bashi tarihin mahaifinsa, kuma yanzu haka ya daura damara dos
zuwa ya yakeka ya rusa daular mulkinka, to amma abin da bai sani ba shine tuni mu mun riga
munga nasa bayan kuma mutuwa ta zamo dole a gareshi"
Gaba dayansu suka bushe da dariya har da Bokanya Amrishatu wadda take zaune tana
sauraronsu, sai da suka jima suna dariyar, sannan Boka Kurbasu ya ci gaba da cewa, "Daga
yanzu mun zama daya ni daku zamu hada kari da karfe don ruguza adalci da ma su tausayı, ba
zamu dakata ba har sai munga gaba daya duniya babu kowa sai azzalumi. Na sallameku sai
lokacin da kuka sake dawowa gareni"
Koda Boka Kurbasu ya zo nan a zancensa sai ya koma kan dutsen nan ya zauna tare da
lumshe idanunsa kamar yadda suka tarar dashi da farko,
Nan take wannan sıniyar iskar ta sake zuke Sarkı Balwanu da matsafiya Amrishatu ia kawosu
wajen kogon dutsen. Tana a jiyesu kuma sai wannan hayakin ya bayyana, suna shakarsa sai
hankalinsu ya gushe hasu tsinci kansu a ko ina ba sai a cikin turakar tsohuwa Amrishatu, ita
tana kwance akan gadonta, shi kuma yana zaune a gelen gadon cikin gagarumar shigar
yakınsa kuma tigijim dashi kamar bakın ifntu
Matsafiya Amrishatu ta dubeshi ta ce, "Ya kai wannan Sarki tafi abinka kaci gaba da mulkın
zalunci babu wanda ya isa ya kawo maka mishkila a lamarinka, tashi lafiya ka isa lafiya ya
hamshakin sadaukın da babu kamarsa"
A duk lokacin da matsafiya Amrishatu ta kewa Sarki Balwanu wannan kırarni ya kanji girman kai
yana shigarsa bare kuma yanzu daya samu gagarumin karfin dantse, sai yaji kamarshi kadai zai
iya yakar duk halittun doron kasa. Nan da nan ya mike tare da yiwa tschuwa Amrishatu sallama
Sa'adda ya fito daga cıkın turakar yana tafiya, sai karlin takunsa ya dinga amsawa tamkar na
toron Giwa, nan da nan kuyangin da suke kai kawo suka dinga juyowa suna kallonsa, duk
wadda ta hada idanu dashi kuma taga siffat da jikınsa ya koma sai su dinga ja da baya cıkin
alamun tsoro da firgita Shi kuwa ganin hakane yasa ya kama kyalkyala dariya wadda sauraronta ma zai hallakar da
dodon kunne
Lokacin da ya iso Kofar gidan ya iske Sarkis yakı da sauran Dakarun da suka yi masa rakiya,
suma koda suka yi arba dashi sai suka bude bakunansu cıkın matukar mamaki, kai marasa
karfin zucıya daga cikinsu har yankurin guduws suka so suyı, amma da suka ga Sarkin yakı
Zamrus bai gudu ba sai suma suka daure suka fasa yunkurin nasu.
A zahiri dai Vun san cewa Sarkı Balwanu ne don kanmanninsa ko kadan basu jurkita ba, to
amma ya ya akayı jikınsa ya kumburu haka, alamomin Karfi suka bayyana a jikın nasa, sannan
ina tufalin daya shiga dasu gidan wadanda suka kasance na sarakai, yanzu kuma ya fito da
sabaninsu wadanda su kuma sun kasance na shigar yaki tare da wasu miyagun makamai a
jikinsu
Shi kansa Sarkin yaki badan ya kasance sadaukın gaskeba da babu ahın da zai hana shi
juyawa da gudu. Nan dai ya yi karfin hali ya matsowa da Sarkı Balwanu dokinsa, shi kuwa Sarki
Halwanu sai kama dokin da niyar ya hau kansa yana da newa sai kafafun dokin daka suka
karye dokin ya zube Rasa yana hanıniya kamar zai mutu Sai fa dukkanin Dakarun suka sake cika da
mamaki harma wasu suka fara elyanawa anya kuwa Sarko Halwanu ne wannan. Amma koda
suka tuno cewa daga gidan matsaliya Amrishatu ya fito sai mamakın nasu ya katse don sun san
san anys amfani da Karfin sihirine wajen mat da Sarki Sacki Balwana mai kirar sadaukai, to
amma idan yadda kırar jikınsa take haks karfin dantsensa yake baza'a samu sadaukin daya isa
ya gwabza fada dashi ba
Shi kuwa Sarkı Balwanu ganin yadda kafafun dokinsa suka karye, sai ya dubi Sarkın yaki
Zamrus ya ce masa, "Ya kai Zamrus ka yı hanzari zuwa inda ake kiwan namun dawa na gidan
sarautata ka zabo toron Giwa ka kawota nan, ita kadaice zata iya daukata
Sarkin yakı ya amsa sannan ya juya ya sakarwa dokinsa linzamı
Lokacin da ya iso inda ake kiwon dabbobin daji na gidan sarautar kai tsaye sai ya wuce garken
Giwaye, ya tadda mai kula dasu ya fada masa sakon Sarki na cewa a zabo katuwar Giwa a
kaita can gidan matsafiya Amnshatu Cikin hanzan mai kula da garken Giwayen ya zabo wani
Toro daga cikin Giwayen ya haye kan giwar yas nufi gıdan tsohuwa Amrishatu.
Mu Hadu a babi na uku
Mu’awiyah A Muhammad
arewanovels.com.ng