Showing 1 words to 1993 words out of 1993 words
Chapter 1 - DUHUN DAJI Part 1 Littafin Yaki By Abdulaziz Madakin Gini .pdf
DUHUN DAJI
MADAKI
arewanovels.com.ng
Lokacin da Bawa Shamsil yazo nan a labarinsa sai Sarki Jalaluddeen yaji ya kamu da tsananin
tausayin mahaifinsa. Nan take hawaye ya zubo masa ya dubi Shamsul ya ce "Hakika
mahaifiyata ta zalunci mahaifina ba akan hakkinsa ba. ta kashe dukkan zuri'arsa nima data
haife ni a cikinta tana so ta kashe ni to kuwa in dai ina numfashi a doron kasa bazata taba
samun wannan nasara ba.
Sa'adda Bawa Shamsil yaji wannan batu sai nan take shima idanunsa suka ciko da kwalla har
hawaye ya zubo masa. Ya ce " yana son shugabana ni dai wata alfarma guda daya nake so na
nema a wajenka ina ka danne zuciyarka kada ka kuskura kace zaka tsani mahaifiyarka ko kace
zaka kasheta koda kuwa ka sami damar hakan."
Sa'adda Sarki jalaludden ya ji wannan batu sai ya yi murmushi ya ce "Na gode da wannan
shawara taka amma ka sani cewa daidai da rana daya ban taba jin na tsani mahaifiyataba
kuma ban taba tunanin na dauki fansaba a kanta bisa kisan da ta yiwa mahaifina. Ni ma burina
shine ta gane gaskiya kuma zata yi nadamar abin da ta aikata"
Shimsıl ya yi doguwar ajiyar zuciya ya ce "Tabbas zata ga wannan gaskiya kuma zata yi
nadamar amma a lokacin da nadarnar bata da wani amfani".
Haka dai Sarki da Shamsil suka yi ta hira har dare ya raba sosai basu sani ba daga bisani sai
suka fara hamma. Anan wajen suka bingire suka kama barci.
Lokacin da asuba ta yi hadimai suka zo suka ga Sarki are da Bawa Shamsil kwance a kasa a
falo suna ta faman shara barci, sai suka cika da tsananin mamaki saboda ko shi Sarki marigayi
ba'a taba ganin ya kwana tare da bawa Sitamsil ba. sai dai su raba dare supa hira sannan kowa
ya tafi izuwa turakarsa. Nan dai aka tashi Sarki da Shamsil daga barci suka shiga shirin tafiya.
Kafin cikar sa'a guda Sarki Jalaludeen, Bawa Shamsil da ragowar hadimai guda biyar sun gama
kimtsawa kowa ya hau kan ingarman dokinsa dauke da isasshen guzuri.
A wannan lokaci fadawa da jama'ar gari sun taru jingim a kofar gidan Sarautar sun yi
jugum-jugum um tamkar zaman makoki ake yi.
Kowa da ka dubi fuskarsa sai kaga kamar kadan yake jira ya fashe da kuka. Ba komai ne ya
janyo hakan ba face tsananin damuwa akan tafiyar Sarki Jalaludeen kowa hankalinsa ya
dugunzuma saboda tunanin eewa idan har yayi wannan tafiya ma hadari to fa sai ya riske
ajalinsa.
Tun da Sarki Jaluludeen ya hau kan karagar mulki komai ya sauva a kasar ya zamana cewa
rayuwar takalawa ta inganta fiye Ga zamanin mahaifinsa sahoda an rage haraji kimanin kaso
sittin cikin dari manoma sun sami tallafi ma yawa daga masarauta, kasuwan ya bunkasa kuma
adalci ya karu.
Hakance ta karawa Sarki Jalaludeen mafukar farin jini a wajen talakawa. Bugu da kari yanzu
idan Sarki Jalaludden ya mutu to fa abune mawuyaci su sake samun kamarsa tunda a zuri'ar
gidansuma babu ko mutum
daya da ya rage sai dai a zabo wani daga cikin majalisa.
لد Lokacın da Sarki Jalaludden ya fito daga cikin gidan sarautar yayı arba miliyoyin talakawansa
a tsaitsaye jugum jugum, duk sun fito saboda shi kuma suna bakinciki rabuwa da shi kai mata
kuwa musamman yan mata da zawara duk wanda ka kalla sai kaga ta caba ado na kure adaka
amma kuma ta: Баа adon da kuka domin hawayene ke shatata akan kumatuwanta saboda
tsananin so da began Jalaludden dake addabar zuciyarta.
yan mata da yawa 'ya'yan attajırai, sarakai da masu fada aji da yawa a birnın Istanbul sun shiga
mugun yanayi sakamakon
kamuwa da son Sarki Jalaludden amma saboda sanin cewa shi ya tsani mata kuma baya yarda
ya kusance su, sai suka dauki hakuri da dangana. Tun da wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa. In
da Allah ya taimaki Sarki Jalaludden shine bai taba ganin 'ya mace wacce yaji ta burge shi ba
bare yaji ya kamu da sonta.
Sarki Jalaludden ya sauko daga kan dokinsa ya fuskance jama'ar gari ya gaishesu sannan ya
ce "Ya ku jama'ata ku yi snai cewa bani da wani zabi wanda yafi na yi wannan tafiya domin
kawar da fargabar dake cikin raina har abada, amma ina mai yi muku alkawari ceawr lalali zan
dawo. gareku a raye kuma cikin koshin lafiya."
Koda jin wannan batu sai jama'a suka rude da shewa gami da tafi tare da bata wani lokaci ba
Sarki yayi bankwana da kowa sannan ya hau dokinsa ya wuce gaba Bawa Shamsil da hadimai
biyar na biye da shi.
Kawai sai Sarki ya zaburi dokinsa da gudu. Cikinm hanzari Sharnsil da sauran Hadıman ma
suka yi ko yi dasu. Aikuwa sai jama'a suka zuba musu idanu tun ana hangosu har sai da ya
rage Kurarsu kadai ake iya hangowa. Sannu a hankali kurar tabi iska ta dusashe.
Nan dai su Sarki Jalalluden suka yi ta tsala gudu bisa kan
dawakai har sai da suka fice daga cikin gari gaba daya suka nausa cikin daji sannan suka fara
tafiya hankali
A dai-dai wannan lokacine Jalalludeen da Shamsul suka jera suka fara hira inda Shamsil ya
dube shi ya ce "Ya shugabana wai shin menene dalilin da yasa kakki dauko dakarun yaki masu
yawa wadanda zasu bamu kariya?"
Sarki yayi Murmushi sannan ya ce "Hakika ka yi mini tambaya mai kyau kuma mai ma'ana. Ka
μα dai duk dakarun da zan dauko ma auratane, wadanda ba su da aure kuwa a cikinsu suna da
dangı ko zuria. Wannan tafiya da zamu da matukar hadarı tana dukkaninsu iya Tasa
rayukansu Idan suka mutu akwai jama'a da yawa danda zasu yi kuka da rashi."
Koda jin wannan batu sai Shamsil yayi tsaki ya ce "To me kake nufi mu daga sama muka fado
kenan idan muka mutu babu wanda zai yi kuka kuma babu wanda yayı rashi?"
Dajin haka sai Sarki ya bushe da dariya ya ce "Kwarai kuwa ni da kai duk marayune bamu da
kowa. Kai dai ko budurwa baka da ita bare kace kana shirin yin aure, ni ma bani da ita bare
wadannan Hadimai nawa wadanda suka kasance bayi basu da ikon komai face da iznina".
Shamsil ya gyada kai ya ce "Ba haka bane ka yi kuskure. A
yanzu kana da dan uwa nima ina da dan uwa tunda mutum gudane ya rainemu kuma a gida
daya muka taso, ban trafia ganin mahaifinka va muna mini wani banbanci ba a tsakanina da kai.
Tabbas ko kaso ko kaki ni da kai 'yan uwan juna ne duk da čewar babu wata alaka ta jini a
tsakaninmu. Wai shin ma a yanzu wanene ya shaku da kai sama da ni kuma waye kake iya
gayawa dukkanin sirrinka in ba ni ba?"
Koda jin wannan tambaya sai jikin Sarki yayi sanyi kuma nan take kwallar farin ciki ta zo masa
saboda sanin cewa yana da sauran mutum daya jal a duniya wanda zai kallah a matsayin dan
uwansa wato Shamsil. Gaba dayansu sai
suka yi shiru babu wanda ya Kara cewa uffan har sas da suka shafe sa'a tara suna tafiya
sannan suka yada zango a bakın wata korama a lokacin da rama ta soma alamun faduwa. Nan
take aka kafa tantuna aka ci abinci. So Hadimah su hudu suna can gefe daya suna cin masu
abincin Sarki da Shamsil na cin nasu abincin tare a cikin akushe guda.
Sai da Shamsil ya kai loma uku cikin bakinsa sannan ya juyo ya dubi wannan Hadimai su hudu
Koda ya ga suna cin abinein cikin nishadi har da darya da tafi sai Shamsil ya bushe da dariya.
Al'amarin da ya batwa Sarki Jalaludeen mamaki kenan ya ce "Mnene kuma ya baka dariya?"
Shamsil va co Wadancan shashun ne suka bani dariya, dubi yadda suka sha'afa suka
sakankance har suke busa dariya, sun mata da cewa mugun daji muka nufa mai taken DUHUN
MUTUWA, Rare kukanka, tarkon Ajali kuma bakin kabarı."
Koda jin wannan batu sai Sarki ya bushe da dariya ya ce "Ni inda kake burge ni kenan kana da
basirar yiwa abu Kirari. Yanzu ga shi a cikin dakiku kadan ka sawa wannan dajı sunaye hudu."
Shamsil yayi caraf ya ce "Yauwa ni kuwa dam atun dazu nake son na yi maka wata tambaya."
Wai shin yaya batun Boka Jardas ne? Menene dalilin da yasa ka
sauya shawara bamu tahi tare da shi ba?
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Jalaluddden vayi murmushi ya ce "Waye ya gaya maka
cewa ba tare da mu?"
Kafin Shamsil ya sake budar baki yace wani abu sai kawai ya ga Boka Jardas a can gefe daya
kwance bisa wata shimfida ya zubo musu idanu fuskarsa cike da murmushi.
Cikin kaduwa Shamsil ya mike tsaye zumbur ya ce "Ashe dai da gaskene suma Hadiman hudu
da suka ga Boka Jardas sai suka firgice suka kamu da tsananin mamaki.
A sannanne Boka Jardas ya taso daga kan shimfidar yana
mikewa tsaye sai shimfidar tasa ta rikide ta zama doki kai tsaye Boka Jardas ya tunkaro inda su
Sarki suke
Da isowarsa sai ya risina ya kwashe gaisuwa ya ce "Ya shugabana daga yanzu na daina Боус
kaina ga sauran abokan tafiyarmu.
Sarki ya gyada kai cikin murmushi ya ce "Ai ba ban so ka baiyana kankaba yanzu sai anan
gaba idan mun fara shiga cikin mugun dajin da muka nufa. Wai shin ma tafiyar kwana nawacc
ta rae mana mu riski dajın? D ajin wannan tambaya sai Boka Jardas yayi murmushi ya "Ya
shugabana wai shin me kake cine na baka na zubowa kasa? Ai yan kwanakine gaba daya ma tafiyar ta mu don haka nanda kamar kwanako hudu kacal zamu shiga
duhun dajın.
Da jin wannan tambaya sai Boka Jardas yayi murmushi ya ce "Ya shugabana wai shin me kake
cine na baka na zubowa kasa? Ai yank wanakine gaba dayama tafivar tamu don haka nan da
kamar kwanaki hudu kacal zamu shiga Duhun daji, da jin ba a shigarsa a fito lafiya komai
jarumtakar mutum da karfin sihirinsa
Koda jin wannan batu sai cikin hadiman nan hudu ya duri ruwa, hankalinsu ya dugunzuma. Nan
take jikinsu ya kama kyarma saboda tsoro har gumi na tsattsafo
musu shi kuwa Bawa Shamsil ko a jikinsa an mintsini kakkaura.
Al'amarın da ya baiwa Bo Jardas da Sarki Jalaludden mamaki kenan. Jardas ya dubi Shamsil
ya ce "Wai kai menena takamarkane, kai 'ba jarumta ba kuma kai ba matsafi ba amma ko
kadan baka jin wani abu wai shi tsoro ba tun daga ranar da Sarki ya yı furucin wannan tafiya
kawo i yau din nan banji ka girgiza ba bare ka ji tsoro harkokinka kaci gaba da yi kawai tamkar
babuw ata masifa a gabanka. Ni kaina dana kasance gawurtaccen matsafi ko barcin kikrı bana
iya yi da daddare haka shi ma Sarko ko cikin daren farkawa yake yi ya zauna yayi ta tumani
amma kai
idan ka kwanta ko kyakkyawan motsi baka yi sai gari ya waye.
na Sa'adda Boka jardas yazo nan a jawabınsa sai Bawa Shamsil ya bushe da dariya sannan
yace "Ta yaya yaron da tun yana karami ya ga yadda ake sara da suka jikin Sil'adama, jini
fallatsi da kwarara a kasa zai zamo matsoraci? Ta yaya yaron da mayaki kuma gawurtaccen
jarumi ya rena zai zama mai tsoro? A rayuwata sau daya na taba jin tsoro ranar da mahaifin
Sarki ya rasune na ji tsoro a zuciya tabisa tunanin na rasa babban masoyi wanda bazan taba
samun kamar saba. Amma yanzu da na sami magajinsa kuma naga yadda yake nuna mini
kulawa da da kauna fiye da wanda mahaifinsa ya bani sai na ji da wannan sauran jin tsoro.
Mu hadu a part 2 don cigaban wannan labari
arewanovels.com.ng