Showing 66001 words to 69000 words out of 108136 words

Chapter 23 - Matar Malam Complete Book free By Mai Dambu .txt

08 Nov 2024

17189

Husaina, Aunty Mummy Ya Abubakar duk sun zuba mata idanu bata hanya sukayi a falo ta zauna tana ajiyar zuciya tare da ɗaukar goran faro tasha kusan rabin ruwan,


Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.
"Ina nazarin maida yarinyar nan gaban ahalinta kozata samu saukin damuwarta ko me kuka ce "


"Ummana korata kike daman baki son ganina ko toh shikenan sai nafadawa Imamu kina korata ni wallahi babu inda zanje sai kunemo min Mijina," a razane suka juya basuyi tsamanin ganina ba shigewa tsakiyarsu nayi naje nayi pillow da cinyar Umma ina kuka, suma tausayina ya hanasu magana sai kallona suke,
"Shi kenan A'isha bazaki je ko ina ba,kinji zamu zauna a nan har sai an nemo miki mijinki, wa yace miki umma bata son ganinki" Ya Abubakar ya faɗi haka cike da tausayi,


Ya ali ya girgiza kai cikin karfin hali dan masifaffene amma yana da raunin zuciya,dukda likitane shi amma haka zaka ganshi yasa mara lafiya agaba yana kuka, yau ma haka yayi yana son min magana amma ya rasa yanda zaiyi sabida kukan da taci karfin shi mikewa yayi yabar falo ya shige ɗakin matarsa yana kuka kamar karamin Yaro,
Hassan ne yasaka hannunshi a aljuhu ya ciro chocolet ya mika min kallon abin nake kamar dodo girgiza mai kai nayi nace.
"Abu khalil ya hanani sha, kuma dan baya nan bazan sha ba, nidai ku nemo min shi ina jin yunwa."


Ranar nasasu kuka ainun dan naki cin kome na koma tankar mahaukaciya, kaina ya juye baki ɗaya idan ba imamu ba bana tunanin kome abinda ke kara dagula min lisafi ba kome bane sai gizon da yake min, haka zan wuni ina rigima da fita abokin hirana kenan Khalil wanda shima yake fama da rashin kanwarshi......




Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba duk inda ake tsamanin abu yaci tura dole aka shiga min alluran bacci ina samu hutawa, suma suna hutawa...... Ana cikin haka Innaji da Baba da Ya Ishak suka zo ganin halin da nake ciki basu zauna ba suka musu jaje sannan suka ɗauke ni sai gida,


Ayya Umma ashe lalurata ce ta ɓoye ta umma bayan tafita hawan jini da Sugarta ya tashi, karshe Abuja Ya Abubakar ya tafi da ita Khalil ya koma hannun Ya Abba lawan.


Ni kuma Innaji suka dufufa min rokon Allah da kaine asibiti abin kan ba daɗi fa......






«»
*Mu koma baya*
Lokacin da su Imamu suka rasa jirginsu suka shiga na dubai har suka sauka Hauwa na makaƙe dashi kaman dai yanda muka zauna na wancan lokacin haka wannan karo, tana fakonshi tun airport ta zare wayarshi ta jefa a bin shara, koda suka sauka a masauki ya lalubi wayarshi da niyyar kira yaji wayam, yayi niman duniyan nan bai samu ba gashi yayi asaran abubuwa masu matukar muhimmaci a cikin wayarshi da nafasa, bai damu ba amma ɓatar wannan wayar itama sai da ta fuskanci matsala gaggaruma dan kaman zai maketa yake ji dan yafi tunanin like masa da tayine wayar ta fadi gashi yana son kirana, ko har ynz fushi nake......








Ya fita niman koda karama ce amma sabida tsadarsu yasa ya hakura, lokacin tafiyrsu na cika suka tafi tashar girjin anan ake nuna suka ga labaran hatsarin da akayi take hankalinshi ya tashi, ya ɗauko jakar laptop ɗinshi abin mamaki tayi rugurugu, screen ɗinta kamar zaiyi hauka aka yaji a ranar haka suka tafi yana tunanin hanyar da zai tura sako.




Koda suka isa london yasamu sakon post mail a kofar gidanshi makarqnta ya tafi bayan ya buɗe mata gida, bai dawo ba sai dare tun daga ranar abubuwa suka sha kanshi bayi da lokacin kowa har ita kanta dalilin da yasa bai nemi gida ba kenan ga karatu ga aiki, abubuwan sunyu masa yawa wani lokacin goma yake komawa gida, Ga Riyya tasashi agaba da fitina yar lebonis ce,tana matukar son Imamu shi kuma yaki bata fuska..... Karshe fatafata yayi mata yace mata yana da mata har biyu shine ta kyaleshi........








«»
Yanzun an sami wata hudu kenan da faruwa al'amarin dan har an shiga na biyar, saka iyayena nayi agaba da kuka lokacin da na fahimci ramlata rasu nayi kuka sosai karshe nace su maidani gida kawai.............








2009word kuka samu


Share/Voter/Comments
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*
*Wattpad:Mai_Dambu*




*_Dominki Sister Nana ta grp ɗin Musha karatu_*


_Fatan Alkhairi ga Mom littel Tambayarki ta jiya amsarki tana cikin wannan shafin_
```Bayan wani jinkiri ban sake ban sake litafin da ya wucce page talatin da biyar ba Sai matar malam, shin ya abu Yake```😂
*:~•35*
Not edit🔨
Kam'kameni yayi yana sauke ajiyar zuciya akai akai, ɗago fiskarshi nayi cikin rawan murya nasake tambayarshi waye ya rasu.


Sassauta riko da yake min yayi cikin murya yace
"Fatima ce taɓa jiya sun kirani sun faɗa min ana nimanta, toh har gari yawaye ba'a sameta ba, sai ɗazun aka ga gawarta a cikin magudar dattin cikin gidanmu, Allah sarki yarinyar batasan dadin uwa ba, Allah yayi mata rahama"


D'an kwanakin da nayi a shashin Umma yarinyar dakyar tasake dani, asalima ita tsoron mutane take, abin tausayi niman kukana nayi narasa, yau nice mai rarrashin imamu can wani zazzaɓi ya rufeshi, amma dukda haka yana rungume dani, dakyar nasamu ya kwanta naja masa bargo muka kwanta ya bani tausayi ainun.




Ina son tashi amma ya kisake ni, dole na gyara kwanciyana muka kwanta,ina shafa bayanshi cikin tausayi a hankali na aro wasu kalmai na shiga faɗa masa, wanda zasu kwantar masa da hankali.... A cikin ikon Allah sai gashi yana salati da hailala tare da tasbihi,... Dakyar na lallashi nasamu na ciro wayata daga chaji niman layin Umma dakyar ta ɗauka cikin sanyi murya nayi mata ta'aziya nan nake gaya mata ai shima imamu bai shida lafiya amma yasamu yin bacci.


Mun jima kaɗan a wayar sannan mukayi sallama,ranar a haka muka wuni da shi ina jinyarshi, sai magrib yafita sallah bai dawo ba sai bayan isha, ina kan sallaya, koda ya shigo ɗakina ya shigo nan na shafa addu'ar da nake na tareshi har ya zauna ina masa sannu kallonshi nayi akaro na biyu nace.
"Mi kake so adafa maka, ya dace kaci wani abu ba daɗi xama da yunwa."


A hankali ya ɗago kanshi yace.
"Ki bani black tea da brown sugar kawai ya isa."


Jikina narawa na nufi kicin na haɗa masa sabida akwai ruwan zafi a flask, kayan ganyen tea na haɗa na zuba ruwan zafi a cikin tukunya, sannan nasaka citta da kanunfari, ganye da kayan kamshin na dafuwa na juye a karamin flask na ɗauko kofi na nufo ɗakin a kishingiɗe nasame shi yana addu'a har gabanshi naje na mike xan bar gurin ya riko hannuna cikin sanyi murya yace..
"Zoki zuba min, idan kin gama ki haɗa min ruwa zanyi wanka."


Gyaɗa masa kaina nayi cike da kunya, na zame hannuna daga rikon da yayi min nayi masa yanda yace sannan na mike na shige bayi,na haɗa masa ruwan wanka sannan nafito na zare hijab ɗina na zauna ina jiranshi ya shiga wankan nima nayi na kwanta,


Yana gamawa ya shige ni kuma na fita zuwa ɗakinshi na ɗauko masa, kayanshi nazo na zuɓe masa a nan , can yafito nima na shiga nayi nafito sai dai matsalar ina ɗaure da towel, dakyar nafito nasameshi yayi kwanciyarshi,kaya nasa nima na kwanta a gefenshi na kwanta.


Janyoni yayi zuwa jikinshi tare muka sauke ajiyar zuciya, sannan yace min.
"Kwanta kiyi bacci kinji."
Haka muka kwana har zuwa asuba sannan muka tashi a gida yayi sallah, komawa mukayi bacci yayi gaba damu,


Sai karfe sha ɗaya muka tashi dukanku babu me kuzari haka muka wuni har zuwa ranar monday......


Ya tafi mkrnta daga can ya wucce aiki ko ya akayi sai gashi wurarren karfe biyu ya na rana ya shigo ko zama baiyi ba yasake fita da passport ɗinmu, bai shigo sai goma na dare, yana shigowa yayi wanka tea ya bukata, kafin nakawo masa har yafito daga wanka dan dama zai shiga wanka ya umurceni da na haɗa masa, koda yafita yasa kaya ya zauna yasha tean kwanciya yayi dan har na fara bacci matsowa yayi jikina ya kwanta,....




«»
Washi gari da kanshi ya haɗa min kayana ina kallonshi kukane ya kwace min dan banga alamun zan dawo ba kome nawa sai da ya tattara min bai kalleni ba balle na karyar masa da zuciya zuwa nayina rungumeshi tabaya ina kuka,


Nace. "Daman baka hucce ba ko, kayi hakuri zan gyara kurakuraina."


Dawo dani gabanshi yayi sannan ya zaunar dani ganin yanda nake kuka mika min tissu yayi na goge kwallar dake fuskana sannan yace.
"Kiyi hakuri,kema nan da wata uku masu zuwa zaki dawo adalci nake son na kwatanta a tsakaninku, A'isha ina matukar sonki amma dole na ki koma gida Yar uwarki tazo itama."


Rikice masa da kuka kaman zan shiɗe ina rokonshi da yabani dama amma ina yaki saurarona haka naci kukana har na godewa Allah take naji raina ya ɓacci naji nima ina son komawa gidan tunda ya gama har yace min mutafi, ko kallonshi nayi alkawari ba zan sake nunawa na damu dashi ba da yardan Allah.




Koda muka isa kaman mu ake jira, muka shiga......




«»
Ranar talata da dadare muka iso lagos a nan muka kwana, washi gari muka bar lagos, yaso yaja ni a jiki amma naki na ɗauke masa wuta, har muka iso yobe,


Tunda muka shigo gidan na tare a shashin Umma, na zauna abuna akacigaba da zaman makoki dani, hankalinshi bai tashi ba sai da mukayi kwana uku bai sani a ido ba dan ko naji muryanshi zan silale na gudu, wancan kan tunda miji yazo take rawan kai, shima da dare a wajenta ya kwana, ina jin Umma khadi tana mita da hausa kafin ya juya harshe, raina kara ɓacci. Satinmu guda bayan anyi addu'ar bakwai suka shiga, shiri da ita nan kuwa kanta ya fara rawa, shima yagaji da wasan ɓoyar da muke ya nime na koma ɗakina banki ba na koma, anan yazo min da sunan miji nayi masa fitsara son raina nace.
"Kaje gurin mace ni kam kasan bani da lafiyar ɗauka namiji, kuma zanje ganin gida, cikin ruwan sanyi kabarni na tafi inba haka ba zan haɗaka da Umma."


Zuwa yayi inda nake ya tureni na faɗi a bakin gado, raina ya kara ɓaci mikewa nayi zan ratsa gefenshi na wucce, ya fincikoni, ya shiga kallon cikin idanuna, yace.
"Allah ya dawo dake lafiya,"


Daga haka yafita koda zasu tafi ban leko ba kwanciya nayi abuna nayi baccina, dan na kudiri a niyyar sai Imamu yaji a jikinshi, cikin bacci naji ana lasar bakina ɓuɗe idanu nayi mukayi ido huɗu a raina nace.*Jarababbe kaida kake da wata matar zakuje ku cinye kanku shine yazo yana lasar bakina kai kasani magulmaci.* Zuba min ido yayi cikin mamaki yace.
"A'Isha nine jarababbe kuma magulmaci ko wallahi badan ina sauri ba dana nuna miki jarabata murarin, amma Allah ya hadamu kuma na hanaki zuwa kt, naga abinda zakiyi."


Juya masa baya nayi sabida bana son kallonshi, haka ya karaci surutunshi yayi tafiyarshi nace.
"Kar naje katsina ɗin ai ba mutuwa zanyi ba kuma nace ɗin jarababben"


Wallahi nazata ya tafine ashe yana bakin kofar ɗakin ranshine ya ɓaci ya dawo a zafaffe, janyoni yayi da karfin tsiya ya yaga min rigar jikina, yashiga min abunda baxan iyace ga ma'anarshi ba kuka na fashe masa dashi tabbas yau ran yan maza ya ɓaci dan, sai da yazo kamala, aikinshi sai yaganin like da pad😂 tsaki yayi yace.
"Zamu haɗu sai nacire miki tsiwar nan naki in Allah ya yarda tunda baki iya da harshenki ba."


Yana gama faɗin haka yafita abunshi idanunshi sun kaɗa jajjur, dukda ranshi a ɓace yake amma yaji daɗin wannan karan batta har yafita yana murmushi gefe guda kuwa yana mamakin yanda akayi na rainashi haka amma zaiyi maganin abin, falon Umma yaje sukayi sallama sannan yace.
"Umma nan da sati me zuwa ki tura A'isha katsina, tayi iya adadin watanin da zatayi amma karta wucce biyu dan a wata na uku zan dawo da Hauwa."




"Allah yakiyayye hanya Ubangiji ya kaiku lafiya."shine adɗu'ar da tayi masa cikin farin ciki yafita Hauwa tana bakin kofa, a choge taki shigowa aka khalil yayiwa Babanshi sallama.


Sun tafi maiduguri acan suka wucce lagos, sai aka samu akasi jirgin da zasu tafi ya tashi karshe kwana sukayi, washi gari suka tashi.




«»
Ina kitchen nagama abin karyawa kenan na ɗauka a basket na nufi cikin gida dashi, abin mamaki ganin mutane nayi cirko cirko, suna tsaye cike da jimami kuma sunki kallona ina shiga falon Umma ta mike tabar falon sai nashiga raba idanu, duk mutanen falon kowa fita yake, duba a goge nayi naga tara saura.....


Ihu najiyo tana cewa.
"Allah ya isa min Batula kinyi sanadin da yatafi min da Y'a ashe ba zamu sake ganawa ba Innalillahi....."


Lekawa nayi naji Ya mansur yana cewa.
"A'A hajja babu tabbacin suna cikin jirgin da Yayi haɗari fa daɓ ace jirgin da ya tafi lond...."


Karan fashewar abu suka ji a falo koda suka shigo nice na fadi jikin kayan abincin da na kawowa Umma flask ɗin Kunun da nayi ya faɗi shine yayi kara tushhh.......


*_Ya naga baku ɗaga min darajata fa anya xancigaba babu alamar vote_*🙆

*Rest In Peace Imamu da Hauwa*😭
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳


*Na:Mai_Dambu*
*Wattpad:Mai_Dambu*



*Jazakallahu Alkhairi My Wattpad Fans nagode da Comments & Votings kuyi hkr da rashin maganata abun sai a hankaline amma zan dubaku Insha Allah Nagode sosai*




Wannan pagen na kune
Fatima Magaji
Yusrah M Sadan
Maman Iman
Feenert
Maman Fatima
Yan grp ɗin A'isha sadan Michika nagode da comments ɗinki......


```Wata Rigimar mai armashi sai ka leka zauren Mai_Dambu Ina muku fatan alkhairi baki ɗayanku```


_Kuma sauran grps ɗin nagode da bibiyar matar malam_






*:~•37*




Tsaki Innaji tayi cikin jin haushin ta,zabga min harara sannan ta rufe idanunta ta hau bala'i inda take shiga ba nan take fita ba, tace.
"Mara kunya ke amaidake ɗakinki ke daɗi miji."



Kaman zan fasa ihu nace.
"Innaji nikan wallahi guduwa zanyi tunda nasan hanya, gwara kawai kibarni natafi."


Murmushi Baba yayi yana kallon dramanmu can yace.
"Ki shirya jibi a maidake."


Murmushi nasake wanda yayi dai dai da zubowar kwalla daga idanuna nace.
"Babana nagode Allah yaja kwananku."


Ina gama faɗin haka na koma ɗaki nashiga haɗa kayana da duk wani abuna sai da natattara tsaf jibi nake jira kawai.




«»
Aikuwa kaman yanda Baba yace haka ta faru shake min mota akayi da kayan tsaraba, Ya Ishaq ya maidani, ni kuwa dalilina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login