Showing 3001 words to 6000 words out of 14779 words

Chapter 2 - HAMMAD ZAIRAH BOOK COMPLETE BY BOOS LADY .txt

09 Dec 2024

2970

nan ya basu hakurin rashin samun shi da har yanzu ba'ai ba amma har yau ana cigaba da neman shi.






........ alhamdulilahi yanzu buɗi ke ta zuwa masu ta inda basu tsammani ba, ta koma sana'a tana sai da sobo kunun aya tana shinkafa da wake saboda kusa dasu an buɗe wata makaranta Aliyu kuma ya koma makaranta, tana zaune baba sabo ya shigo cikin gidan kai tsaye ko sallama ita gaban ta ma faduwa ya yi saboda ganin mutum ba tai tunani ba.




Ya ce" naji wani labari wai kina sai da abin ci mereeh ba dai zaki fidda miji ba dai ko?"


A'a baba sabo ina wuni ya su gwaggo? Ehh muna sai da abincin ne domin rufa ma juna asiri..


Ko haka zaki ce ance min har masu motoci suna tsayawa don ki basu Kunun aya' ban yarda da cewa shi kaɗai suke karba ba harda wani abun dai to ki shirya na maki miji akwai wani malam Musa abokina nane sosai yana da mata uku yara kuma guda 47 ne nan da sati biyu nake san ai bikin sai ki sai abinda ya kamata!


Ƙwalla ce ta zubo mata ta furta billahillazi bazan aure shi ba, ai yanzu ba'a auren dole tabbas Dole baba sabo kabar wannan zancen tana cikin wannan magana sai ga Aliyu daga makaranta ganin shi ya sa ya haɗe fuska kamar bai taba dariya ya ce mai ya kawo ka gidan mu malam?


Ohh yara dai rashin kunya kuka koya dai cewar baba sabo to nazo ne batun auren yayar ka da na mata miji nan da sati biyu masu zuwa..


Kutt mar duma du kenan' duk duniyar nan Uban waya isa ya mata auren dole ai sai mahaifanta kuma basu raye' don haka ka daina wannan batu kada ma rai ya ɓaci mai kasani game da ita cin ta shan ta suturar ta sai kawai muga mutum daga sama ya zo da zancen banza, bari kaji sabo sai batun ya ba shi mamaki. Yau ba baban mun fidda kai a matsayin ɗan uwan uba kowa ya yi hidimar shi...




" Duk zancen da yake mereeh kuka ta ke sai yanzu ne tasa baki da taji furucin Aliyu wai sun fidda shi ta ce don Allah Aliyu kai shiru haka"




Dalla can Aunty mereeh idan ke baki da baki ne zaki tsaya a cuta Maki nine Yanzu zan rinƙa tare maki duk wani shege zan iya dashi ko waye wallahi ya fizgi hannun ta ya tura daki ya yawo ƙofar ya rufe, ya juyo gun baba sabo tare da nuna mai kofar fita ya buga mai woning kada su ƙara ganin kafar shi gidan!






....baffa ya mai wanka ya canza mai kaya shi dai bin su yake da ido ko magana sukai mai sai dai ido baffa dai yana ta mai magani kuma suna ganin sauki sai dai Maganar ce da har yanzu ya koma kamar karamin yaro, kamar kullum yau ma sun gana shan fura baffa ya tafi daji ita kuma ta kaɗa shanu suka tafi kiwo sun je inda shanu zasu sha ruwa sai taji Muryar ƙaramin yaro ya ce canu lale yana tsalle!!


Da sauri ta juyo don ganin waye wannan kaɗo ta gani ba ta tabbatar ba sai da taji ya kuma canu lale sannan da murna tace su koma gida sun isa gida ba da jimawa ba baffa ya dawo ta laburta mai komi ya ji daɗin haka ya fara magana...




Taliya baffa ya fita garin yayi cefa ne ya dawo domin ta dafa masu "habu dake zaune ya amsa ya ce cannu da cuwa baffa" da yake sunan da suke kiran shine habu, murmushi baffa ya yi ya ce kai ma ƴar kanwarka ta dafa mana"!


Da gudu ya shiga cikin gidan mutum har mutum amma ba hankali ya ce" baffa ya ce na kawo maki yana waje"


Amsa tai ta daura masu.... minti 30 ta gama komi ko wajen cin abinci mai sai da habu ya bata kayan shi




























Please contuie
Ku riƙa share fisabidillahi redear saboda suma wasu su gani






Masu comments ina godiya




Phone number 08160647868


Boos lady taku ce




6️⃣🔸🔟




Alhamdulilahi suna ganin alamun sauki sosai sai dai ya koma yaro abin da suka ci karo dashi bai masu daɗi ba saboda mai gari ya ce" kaɗo ba zai zauna mai gari ba tabbas sai dai ya bar garin ko su tafi tare ba, duk garin babu mai magani gargajiya irin baffa amma akai mai wannan wulakancin Saboda kaɗo ya samu masu gina yar bukka aka gina mashi mai daki biyu shi da kaɗo ita kuma fatsume ita kaɗai, mai gari bai tunanin zai yarda ya bar garin ba gashi ko ya yi nisa da garin sosai don sai kayi ƴar tafiya sosai zaka iske gidan baffa" sun tare Lafiya lau baffa kuma ya cigaba da bada maganin shi sai dai a same shi can ƴan kuɗin da yake tarawa na magani ya siyo ma habu kaya kala biyar na gwanjo ita ma fatsume ya sai mata kala biyar shi ko bawan Allah kala biyu ne nashi haka suka cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa kamar kullum yau ma habu ne zai tafi kiwo saboda yanzu ya iya yana zuwa shi kaɗai ya dawo lafiya"..




"Cikin dake jikinta nake so malam a zubar min saboda iddar ta takare a zaman gidan da take don ya mai da ita"
Cikin ta zai fita amma kinsan ai sakamakon abin ko?


Ɗan zare ido tai saboda tasan mai yake nufi ta ce" idan wannan ne ban da damuwa malam idan har ya fita ni kuma zani baka shi". Wani magani ya bata ya ce ta tabbatar ko da a cikin lemo ne tasha shi tabbas idan har tasha komi zai waka yadda take so..


Murna ce fall ranta saboda ta samu abin da take so idan "jannat ta har ta bar gidan ko da asiri ne sai ta auri sameer kuwa, ta mike tare da mai godiya tana wani ban ƙare kirji shi kuma yana taɓa su kamar wani tsohon maye"


________________
Mereeh tashin hankali tana cikin shi duk tasa ma kanta damuwa da abin da baba sabo ya mata gashi cikin lokacin da ya ɗiba mata har anci kwana takwas ranar na tara ne "malam Musa yazo mata zance babban mutum ne mai kimanin shekaru 67 bakin shi duk ya ci goro haƙora sunyi ja kamar barkono, suka gaisa ta ce baba kunun aya ɗin za a kawo"


Malam Musa ko duk ya ruɗe da yaji muryar mereeh ya ce" baba kuma mu da muke shirin zama ma'aurata zaki kira da baba ƴar nan mijinki ne ni da sabo ya maki"


kallon mamaki take mashi lalle mutumin nan bai da ma kunya ko kaɗan a ƙalla zaiyi jika tanawa da ita amma wai ita ce zai yi mata da ita cirr yana cin jalala kuwa!!


"Kikai shiru baby na"


Da sauri ta ɗago don kallon bakin da ya kirata da baby ta ce" Malam wai ko kunya babu wai baby Allah ya kyauta gaba"






Sameer kwance kan gadon jannat shi da budurwar shi suna watsewar su hankali kwance ita kuma ya mata duka wai ta ɗaura masu girki tun kafin ya ƙara mata wani haka ta tafi kitchen ɗin don ta mai abinda ya sata..




....... tunda nasa akai mai kurciya yanzu ni ai ban da damuwa wallahi' Fulani take faɗi hankali ƙwance ko fargaban wani yaji ma bata yi duk maganganun da take hanan ƙanwar hammad najinta amma matar nan bata tsoron Allah ko kaɗan tana ganin yadda ake ta fama da mummy bata lafiya amma ko ajikin ta lalle gidan sarauta ana abu mara hankali sai da taji wani zancen kofin hannun ta ya faɗi ƙasa ji kake tassss ya fashe lokacin Fulani ta juyo don ganin waye a gun hanan ta gani ta ruga da gudu tana kuka innalillahi wallahi sai nayi maganin ki banza zan mai dake kurma yadda ko maganar ba bazaki ba wallahi mara hankali..




Ko da hanan ta koma part ɗin su kuka take Kamar mai "mummy sai ta bata hakuri tare da bata umarnin ta tashi tunda suna da class yau ta tafi makaranta, haka ta shirya jiki ba ƙwari ta tafi driver bai nan ita zata tuka kanta ta shiga ciki tun da ta hau titi ta lura akwai masu Binta a wata baƙar mota ba ta tabbatar da hakan ba har sai da ta ƙara gudu ta ga suma sun yi kanta canza titi tai ta hau na zoo road suka bita sai da sukai nisa motar ta ta fara jaking salati tasa ta tsaya zata buɗe ta gudu sai ganin mutane tai zagaye da motar sun rufe ta wani tsumma suka sa mata a hanci wanda daga nan bata kuma sanin inda kanta yake ba"




Dare ya tsala sosai irin ƙarfe 2 na dare mutane ne kan katan gan gidan "Malam Musa suka dura basu zame ko ina ba sai ɗakin shi mari suka falla mai ihun ya yi suka nuna shi da wuka ya masu shiru ya ce don Allah mai na maku da zaku zomin banda kudi ni talaka mai ci da ƙyar"


Wata irin dariya ɗayan su ya yi yace kana ci da ƙyar amma kake shirin ƙara aure Musa?


Aure kuma ni bazan yi Aure ba matana mun isheni ga yara ga jika, ina zan saka matar... Oho kai da kake neman ɗiyar sabo fa da ina zaka saka ta??


Nafasa wallahi kunji na rantse na fasa indai don ita ce kuka min haka, da safe in sha kallahu zan faɗi mai na janye..


Wani yace in sha Allah ake cewa ba in sha kallahu ba...








Please ku hakuri da wannan banda caji




🕊️ HAMMAD ZARAH 🕊️






BY boos lady
Phone number
08160647868




Bismillahir rahamanir rahim






Mikiya writer's asso.....




Dedicated to fan's of convention room hammad zairah masu comments only 🥰🙏godiya Mai tarin yawa love You so much.






"Wani bakin ɗaki aka saka hanan wanda ko hannun ka baka Isa kagani ba balle kaga na kusa dakai, kan wata katifa mai laushi suka ajeta tare da rufe ɗakin suka fito cirko cirko suke saboda kadafa asirin su ya tonu wannan aikin shine na farko da suka fara gashi sun fara da mai hatsari sace ɗiyar sarki lalle sun taro match idan asiri ya tuni, babban su ya ce dalla ku kwantar da hankalinku ai samu akai ba wai haka nan bane don ra'ayin kan mu"




Bangaren jannat kuwa tasamu da ƙyar"sameer ya maida ita sai dai sharaɗin da ya mata na yadaina bata abinci ta nema da kanta kawai dai sunan tana aure amma duk wani abu da miji zai ma mata bazai mata ba, kuma a haka taji ta amince rana ta farko da mai da ita duk wani Kayan abinci ya kwashe Allah ya taimaka mata tana ɗinki to sai ta zuba asusu wasu kuɗin dashi ta ɗauka ta siyo kullum ɗari gyaɗa ta 50 suga 50 ta samu ta haɗa a nepa ta jona ta sha, da rana ko garin kwaki tasha da kuli haka ta cigaba da rayuwa ga ciki tana Tare Da shi iya wahala tana shan ta gashi Wajen hakkin shi sai ya amsa ko bata so!!


Kamar kullum yau ma tana zaune ya shigo cikin gidan ko sallama babu Amma haka nan ta mai sannu da zuwa, ko kallo bata ishe shi balle ya amsa mata ya wuce ciki tasan lokacin dawowar shi ruwan wankan shi na a haɗe ya shiga ya yi yana cikin ɗaki ne ya ji sallamar auntyn jannat gaban shi ne ya tsinke ya faɗi ta gaida ita amma ko ta amsa ta furta jannat lafiya kika kode kikai baƙi kamar ba jannat ƴar gayu ba Lafiya kuwa??




Kan jannat ta bada amsa ya yi wuff ya fito ya mata sannu da zuwa ya ce" Aunty nikaina abin na ban mamaki wallahi bata da lafiya munje asibiti an bata magani amma bata sha bata san cin abinci ko kaɗan yanzu ma fama nake da ita ta tashi ta shirya mutafi asibiti amma ina ko kallo na ta ki balle nasan zata".. salati Aunty tasa ganin irin abin da ƙanwar ta take ma mijinta tace anya jannat kina san rahamar Allah? Mijin naki kike na musu lalle tabbas kin canza Daga Yadda kike yaushe kika fara mai wannan iskancin zaki tashi ko sai na buge ki a nan!!




Kuka ne ya ci ƙarfin" jannat ganin sharrin da sameer ke san mata lalle ya iya makirci tayi wanka doguwar riga tasa mara nauyi ta sa hijabin ta suka fito don tafiya asibitin"




Baffa don Allah kabar ni naje kallon shadi Yau kaga na dade banje ba ina so yau cewar fatsume!


Shaɗi kuma fatsume? Bana san fitar yamma kinsani amma ke da wa zaki?
Dama dama haka ta dinga faɗa Saboda ba gaskiya..




Tafi maganar ki kai tsaye mana fatsume haba.. baffa nida yayana zani mu kalla mudawo!


Shi ya ce yana san zuwa ne to a dawo Lafiya ya faɗa tare da cigaba da kulla maganin shi......ta fito tare da cewa yaya ya ce mu tafi.




Aliyu Yanzu kaga saukar ku nazuwa alhamdulilahi gashi ka kammala school mun samu cigaba da karatun ka kyauta tunda gwamnatin mu ta ɗau nauyi yanzu sai mu fara shirin zuwa University ko ta faɗa tana dariya..


Cush "Aunty mereeh nidai sai second term sannan zan yi rijistar ma Allah karatu da wahala sosai fa". Ware hannu tai irin na mai mamakin nan ta ce a'a ai so kake kaji no wahala komi? Tab kasan haka nasha fama gashi an gama ba aiki sai addu'a amma in sha Allah Aliyu gadanga zai sami aiki da zai kula da yayar shi".. uhmm ai yanzu aiki sai wanda Allah ya cida kalli dai ƙawarki don baban ta kusa ne a gwamnati shine tasamu da yanzu kema tare kuke amma Allah ya ban kuɗi na gina maki asibiti ta kanki.




Ameen ta faɗa dai-dai lokacin kuma an kira sallar mangariba ya tashi don tafiya masallaci.




...... innalillahi ta furta ganin ko hannun ta bata gani ta kurma ihun azo a taimaka mata wannan shi ake kira da ihun ka banza' saboda gun ba kowa suna kan su sun fita suje su dawo tashi tai tana lalube ko zata samu hanya amma ina ta duƙe tana kuka kamar ranta zai fita ba wanda take tausai Kamar mummy tana can hankalin ta a tashe yanzu..


tashi tai tare da laluba bangon ɗakin amma babu alamun da fitila haka ta koma ta kwanta tare da kiran sunan Allah.


Hajiya gaskiya wannan aiki da kika samu mai wahala ne babba!
Fulani dake gefen su ta ce Please bana san kuna cewa haka ina so ne nan da sati sannan ku saketa amma kada ku mata komi, kada naji wani zance daban..


OK ma! Babban cikin su ya amsa kudi ne masu uban yawa ta ce wannan ku fara rikewa kafin ku gama aikin ku na sallame ku, kuma abinci mai dadi nake so a rinka bata.


Suna gama magana ku san minti 30 ta wuce gida rai fes...


.____________asibiti ciwo ne har ya ci karfin ta ga ciki na barazanar barewa ga yunwa ta kama mata hanji sosai, kwantar da ita sukai sai ta samu sauki sosai ko zasu sallame ruwa suka sa mata tare da mata allurar bacci ta samu relief, aunty ta koma gida don ta sanar ma su umma tana tafiya sameer ya fita shima gida ya koma ya kira kawar jannat suka sheke ayar su a dakin ta na sunna bai koma asibiti ba har sai wajen karfe 5 na yamma ya shiga kamar wani munafuki, ga gaida umma da wasu yan uwan nata suka tashi don su zanta da matar shi suna fita ko ya matso kusa da gadon ta ya ce munafuka saboda karya an hada baki da likita dan kawai a ci mun kudi to zan nemi sallama mu tafi gida ba!!




"Allah ya sani Meer ina ƙaunar ka saboda san ka cikin jinin jikina yake Allah ne ya daura min tawa kaddarar a haka, gashi ka canza min kamar ba auren soyayya mu kai ba tabbas zuciyata tana fada min an canza min kai ne". Wata dariyar mara kunya ya mata ya ce nine dai sameer ba wani canza ni akai ba harda wani munafunci wai Meer nace bana san wannan sunan!


Ƙwallar da take shirin zubo mata ta goge saboda bata san tai kuka, idan tai tasan sameer ya samu nasara tace "abba ya aiko mun da dubu hamsin nasha lemo kafin ya zo"




Tsaki ya buga mata mtsssss wai Lemo kawai dai ki ban su na sai mana kayan abinci malama ya fada da wani jan idon shi shi ga oga..


Kallon mamaki ta bishi da shi tace"sameer ka manta rabon da kaban abinci yau wata nawa?? Da kanka ka furta min kai yanzu ba zaka rinka ban abinci ba na nema yanzu kudin mai kuma kake so na baka haba don Allah a sa tunani ciki mana Meer, tana gama magana ta juya mai baya"


Shake mata wuya ya yi yana don uban ki sai kin bada su wallahi ko na illa taki, daidai nan aunty ta turo kofa sai ya wa yin ce yana sannu beb bari naje ko nama ne a restaurant sai a sai maki....


Banaso ta ce.


Aunty tace har yanzu dai kina mai rashin kunyar nan ashe kina kwance gadon asibitin ma zaki ci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login