Showing 9001 words to 12000 words out of 14779 words

Chapter 4 - HAMMAD ZAIRAH BOOK COMPLETE BY BOOS LADY .txt

09 Dec 2024

2968

ce"bangane ba mai hakan ke nufi''


Kinga sunan ki meerah' mijin ki imran idan aka hada karshen sunana da farkon naki shine zai bada meeran!


Dariya tai sosai, sannan tai mashi sallama....... Abban mubeen ya saman mata aiki a asibitin da yake aiki fannin mata shi kuma yana fannin masu c,s ne!!


...... Kai yaro yanzu ita '' meerah ɗin ce ta turo min kai saboda bata da kunya? To ai ni na fita daga matsayin uban ta ta nemi wani uban"


İmran ya aje mashi kuɗi masu yawa sannan yace mai zan tafi ni yanzu!


Har ya tashi ya kusa kofar fita ganin wannan kudi yasa baba sabo cewa yaro dawo mana!
Zama ya yi '' baba sabo ya furta a hankali kamar wanda ke jin tsoron wani yaji ya ce yaushe kake san ai auren? Ni ko gobe kace ma alhamdulillah sai a daura''........ A'a baba sabo daman nazo magana ne ina son na turo iyaye na don jin magana.
To shi kenan ai sai sun zo haka ya mai sallama ya fito ya kunna mota tare da kiran meeran bugu uku ta dauka tare da yin sallama!


Jin sallamar ya yi har cikin ran shi ya ce'' zuciya ta nazo baba sabo bai kalleni ba dole kinga zamu tafi funtua kun dangin mama''..... Uhmm in dai shine zai maka fiye da haka ma, amma kai ta addu'a funtua kuma gaskiya.... Sai kuma tai shiru kamar tana jin tsoro.


Ya ce'' fadi mainene bazaki bane? ''


Noooooo ta fada a hankali.... Sai da ya gama jan aji sannan ya fada mata gaskiya har cikin zuciyar ta taji dadin abin da ya faru!!




...... Tashi ya yi da sauri ya rungume ta ta baya yana mai wani irin numfashi tai saurin farkawa tare da ture shi tace a'a yaya habu lafiya?


Bai bari ta idasa ba ya hada bakin su waje daya yana shafa wani sassan jikinta..... Kwalla ce take ta zuba mata tana so ta kwace amma ta kasa rigar jikinta ya yaga tare da kwantar da ita kan gadon.....
























Tofa fans ku biyo ni don jin cigaba


08160647868


🕊️HAMMAD ZAIRAH🕊️




BY boos lady












Mikiya writer's asso...








Alhamdulilahi wannan shafin naku ne masoya na a duk inda kuke sanku na cikin raina💘🔓




Bismillahir rahamanir rahim




2️⃣1️⃣▶️2️⃣5️⃣


"Bangaren abban mubeen kuwa baida aiki da ya wuce tunanin mereeh kullum haka yake, ya tashi aiki ya nufi gidan hajiya domin su gaisa da ita daga can ya wuto da mubeen yana shiga cikin gidan da sallama a bakin shi mubeen ya taso da gudu yana ga abba ga abba hajiya dake gefen shi ta ce dawo daga nin mutum sai kace kasan shi" murmushi ya mata tare da gaida ita ya ce akwai abinci kuwa?


Akwai mana mai zai hana ni ɗaura tukunya nida ba ma'aikaciyaba imrana ai wannan aikin sai ma'aikata.. tunda yaji wannan maganar sai ya yi shiru ita kuma ta shiga ta zubo mai jolop ɗin taliya taji kifi sosai ya gyara zama tare da ci yana ci yana santi ya ce" hajiya kinsanme mainene na samu mata mai hankali da nutsuwa fa ina san ƙara aure''


Ta washe baki Allah abban mubeen?? Ina ka same tane? Yar gidan waye? Allah ya sa dai mai mutumci ce ba irin hamdiya ba?


Yace noo "mereeh ai mace ce wadda tasan mai take wallahi ga ladabi Hajiya yarinyar ta haɗu sosai sai dai ai min fatan nasara' nan ya kwashi labarin mereeh ya faɗa mata duka aiko taji tausan ta tare da karfafa mai gwiwa sannan ya fito gidan Cikin farin ciki ya nufi gida, ko da ya isa sai da ya gyara gidan sannan ya zauna tare da kiran gimbiya mereeh don jin ya take"




....................
Mai mata hidima ce ta shigo tare da faɗin ranki ya daɗe' ga wata mai magani nan tazo don gwada sa'ar ta!
Ta girgiza kai tare da cewa kice mata ta shigo...tunda mai martaba ya sanar cewa duk wani mai magani da ya ma yar shi magani tadawo daidai suna da kyauta mai tsoka masu magunguna suke zarya idan sunyi basu iyawa shikenen' shiga tai cikin ɗakin tace a samo mata rushi ta fara hayaki nan ɗaki ya ɗauki kauri su ka fara tari haka tai ta yan dabaru amma babu Sa'a Sannan ta tafi..


Hanan tai mata nuni da hannu wai kada a ƙara bari wani mai magani yazo bata so karya ce suke yi ba magani ba!
Murmushi mummy tai tare da faɗin a'a ai sai kiga an dace...


.......kai nake jira fa "Aliyu ka tashi kai wanka muci abincin nan Please ina san fita ne yau aiki na na rana ne fa"
Ohh wai yau ma danadawo Aunty mereeh sai kinje aiki? Ki hakura yau dai kawai tunda gobe asabar a haɗe a monday!
Tai sakato tana kallon shi saboda ita sai taga don mai bazata ba haba, da ƙyar ta lallaba shi ya yi wanka ya fito zaman cin abincin shima nan sai da ya ɗauki lokacin mai tsawo ya fita.....ganin mutum tai ya dafe kai tare da faɗin wash Aunty kaina ya faɗa kan kujerar dake kusa dashi da sauri tayi kan shi ta na duba shi shiru, ta nufi daki dan ɗauko akwatin taimaka mai' yana ganin haka ya buɗe ido tare da dariya yace ai yau no aiki zo kisamun ruwa ko naji karfin jiki na ma ai nasha tafiya!






........
Fatsume tunda ta sume bata farka ba sai sanyin asuba da ya tashe ta' da ƙyar ta buɗe idon ta da ya mata nauyi ta ja jikinta ta ɗauko robar da baffa ya bata ta watsa mai ruwan idan haka ta faru shikenen' ta na zuba mai sau ɗaya amma ba motsi sai da ta zuba sau uku sannan ya tashi ita kuma ta jawo zanin gadon tare da rufe jikin ta' da sauri yayi kanta tare da rungume ta saboda ya tuna mai ya aikata mata yana mata sannu ɗaukar ta zaiyi tasa ƙara tare da faɗin was Allah hamma habu zafi nake ji...


Haka dai ya lallaba ta ya ɗaura gado tare da rufe mata jiki' ɗan gas ɗin da baffa ya siya masu ne ya ɗaura ruwan wanka roban su yaje ya fara tare da zuba wasu ya dinga saka ta a robar tana kukan zafi a haka ya gyara ta ta kwanta gado, ya gyara karamin gadon tare da zuwa ya kwanta bayan ta, zuwa safe jiki ya gashe da zazzabi


(Ga yan comments room sun zuba ido ganin ƙwaf)


________________________
"Fulani sai jin daɗi take maganin na aiki gashi yanzu tai wanda za'a a kori mummy gidan ma ga baki ɗaya tabbas malamin nan nata da tai sabo yana aiki yadda ya kamata, tana zaune ya ce kije kice subarmiin gida kafin nan da dare" ta zaro ido ta ce ranka ya daɗe' ai wannan aikin kane saboda sai a ga kamar nice nasa hakan ta faru!!


Ya wani shafin gefen fuskar ta ya furta duk wani da yace kece ki kawo shi fada yaga aiki na!!
Haka mai martaba ya fita tare da masu korar wulankaci, mummy tasa mai mata aiki nemo mota suka kwashe kayan tsaf suka fito tana wayeyen gidan tana ƙwalla .....




.......an sai da kujerun "jannat masu rai da lafiya amma ba wani tsada gashi an kori sameer Saboda rashin gaskiya da ya yi masu na cin kundin ma'aikata shi ne dalilin tunda yaga ta saida suka dawo zama Lafiya kamar bashi ne mai mata duka ba, ita kuma ta ɗauka ya gyara halin shine yanzu ya daina kawo yan mata gidan sai dai su haɗe can waje kamar kullum yau ma tunda ta tashi ta gyara gidan yayi kyau ta ɗaura masu abincin safe zuwa 7 daidai ta gama komi ta tashe shi ya yi wanka suka karya ta ce ina san zuwa gidan Aunty na"
Jannat ba wai bana san kina zuwa gidan bane a'a sai taga kamar ina Cutar ki...


No my "meer bazata ce haka ba kasan dai Aunty ma nasanka Please kai hakuri bazan daɗe' ba" meer kuwa Cikin zuciyar shi daɗi yake ji Saboda yau yasha sha'anin shi yadda yake so yace to kikai dare sai nazo mu taho tare!


Rungume shi tai tare da mai kiss ta tashi tasa hijabi da jaka ta fito tare da mai sallama daman tasan dai ita ce zata ma kanta kuɗin mota..


......ruwa tasa mai aiko barci ya ɗauke shi tana Cikin cin abinci ne kiran abban mubeen ya shigo suka gaisa yaji Muryar ba dai-dai ba yace Lafiya sarauniya??


kukan dake boyewa ne ya fito ta faɗa mai Aliyu ne bai da lafiya yanzu ma ruwa take samai' sannu ya mai tare da faɗin anjima zai zo ya kashe wayar!


Hamdiya da tadawo aiki Yanzu kuma taji wayar da yake ta shigo a fusace tare da faɗin uban wacece gimbiya ɓacin gani??


Murmushi ya yi tare da riko mata hannu yana zauna mana "maman mubeen haba ya da zagi haka Please, ƙanwar kice ai da zan kawo don kula da gidan kinga ke aiki kike". Ta mike da sauri tace lalle Imran sai yanzu ne tabbatar da kai ma yaudari ne na gaske....


A'a hamdiya kina Min girki gyaran gidan nan ɗaki na kula da mubeen kina yi ko??


Ta share ƙwalla tare da faɗin ai nace a nemi mai aiki kace kai baka so to kaga ko sai dai ka kawo ta matsayin yar aiki ba da aure ba!!


No no no yadda kike aure ita ma haka zatai sai dai ita ce mai kula da miji da yaro yai gaba abin shi tare da sa ma kofa mukulli..


Da safe sai ga "baffa da koko da kosai ya kawo masu ƙofar bukar su ya kira fatsume sai habu ya taso yace barci take yana ganin habu yasan komi ya wakana ya bashi kokon tare da gaisawa shi kuma ya koma ciki inda ya tada ita ya bata tasha da ƙyar, robar maganin su na gargajiya ya nemi magani ya bata ta koma ta kwanta gashi shi kuma magani bai sake shi ba.....
(ya haɗa da Yan comments room)




Mai aikin ta ce" mummy ina zai kaimu?" Ta share ƙwalla tare da faɗin muje gidana dake tudun Wada Wanda ba kowa ɗin nan, can suka nufa mai kofa ne haka matasan layin suka tunda shiga da kayan cikin gidan ta biya mai mota suka shiga daki uku ne sai kitchen bayi ɗaya amma akwai bayi a ɗaki suka cigaba da gyara zuwa mangariba sun kammala komi mummy ta bada kudi a siyo taliya su dafa!!




Wow ganin Yadda ya fito yadi ne pink yai kyau ya fito don tafiya "hamdiya tace ina ya ture ta gefe ya fito mota ya tada mai gadi ya buɗe mai gida ya fita, sai da ya sai kayan dubiya sannan ya shiga cikin layin nasu, ya kira ta gashi nan zai shigo ta sa hijabinta sai gashi ko da sallama a bakin shi ya shiga inda ta amsa tare da shigar dashi cikin ɗakin don duba Aliyu sai taga ya wartsake suna ta fira da shi anan ne yake faɗa daman yayi haka ne don kar taje aiki"


Aiko abban mubeen ya mun tsine mai kunne tare da faɗin sannu idan ka kuma ma sarauniya ta haka zan rama mata!


Ya tashi ya shiga cikin dakin inda ya barsu anan suna fira..




....... hamma habu dai sai laluben fatsume yake tana ture mai hannu saboda jiya tasha wahala yanzu ma mai yake nufi? Murya na rawa tace don Allah kayi hakuri idan laifi na maka ka daina hukuntani ta haka na rokeka.


Jin Muryar ta yake kamar tana kara zuga shi ya danne ta tare da magana a hankali ki hakuri fatsuma na sau daya zanyi!!




tace...........








Please contuie
08160647868






HAMMAD ZAIRAH🕊️


BY boos lady


Mikiya writer's asso....






2️⃣6️⃣⏹️3️⃣0️⃣


Mummy komi ya sauya mata inda Allah ya taimaka mata tana da gidan da take bada su haya Sannan akwai wasu kuɗi a account ɗin ta nan ne ta samu sauƙi ta maida mai aikin ta kamar yarta komi tare suke' hanan ta daina damuwa yanzu ta bar ma Allah komi amma har yanzu tana tuna Fulani gashi ba bakin faɗa baiwar Allah, suna zaune mummy ta kalli mai masu hidima tace Binta ko dai shago zamu buɗe a kofar gidan nan kinga kafin aje kasuwa sai a rinƙa yi nan??


Kuma haka ne "mummy Allah ya taimaka mana a samu dacewa cewar Binta, haka sukai ta shawara dai har suka saida magana ɗaya harda na aune ma zasu rinƙa yi"




......... Aunty Wallahi ban cuta mai hasali ma zaune muke Lafiya nida shi.
Jannat bance kina cuta mai ba' amma don Allah duk wani hakki nashi kada ki rinƙa danne mashi kinji yar ƙanwata ta faɗa tare da da fata!!


Murmushi tai tare da faɗin tom aunty, suka cigaba da firar zumunta sai ƙarfe 8pm Sannan sameer yazo don su tafi ko da zata tafi Aunty wajen dubu hamsin ta bata sukai mata sallama tare da fitowa..


"Mereeh na Please kidaina mun hukunci da irin wannan abu don Allah ko so kike na haukace akanki". Ita abun ma kunya ya bata ta furta noo hibban am sorry amma sai gobe zan shigo aiki wallahi yau ƙanwar mama tazo ta funtua kaga ba halin zuwa" ......lah kinga asirin ki ya tuno da bazaki faɗa ba nazo na gaida ita ba ko? Idan na taso aiki zanzo!


Uhmm... Uhmmm hibban rigima daman zam faɗa maka' to shikenen gata ku gaisa kafin kazo!!


Bata wayar tai suka gaisa tai masu fatan alheri sukai sallama...




________
Kullum fatsume tana Cikin zulmi saboda abin ya zama kamar wani mara kai' a ƙalla sai yayi awa wajen ɗaya ko biyu gashi kullum ba daga kafa tunda akai auren nan basu haɗu da baffa ba yau kwana biyar da bikin gashi sai anyi goma kafin ya dawo normal ta bushe ta rame, sai ta ƙara ƙyau da tai ramai hancin ya fito kamar biro tana zaune taga alamun dai so yake ya yi tace hamma bayi zani....


Ɗaukar ta yayi cak ya kaita bayin ya taho ɗaki idan ta gama buƙatar ta sai ta kira shi, tana gama fitsarin ta fito a hankali take tafiya har ta wuce shashin nasu ta tafi can inda rafi yake ta zauna tana cilla dutse Cikin ruwa!!


Bangaren hamma habu kuwa yana ɗaki injiniya ta damaisa' ya fito domin yaga ta gama ya yi magana shiru sai ya leka mai zai gani babu ita ya tafi wajen baffa don yaga ko can ta tafi yana zuwa suka gaisa ya tambaye shi fatsume ya sosa kai tare da faɗin tana Lafiya ya gama zaman shi bata ba labarin ta yayo daki don ganin ko ta dawo...



Fulani Yanzu abu yaci gaba saboda har mata yan lasbian gare ta, yanzu ma bikinta ake ita da wata ita ce ango....mai martaba bai gari sai ita kaɗai da hadimai ko cikin hadiman ma wasu nata ne sun fi samun albashi mai tsoka sama da Wanda basu bata kansu basu da albashi mai tsoka wasu ma ta ko resu daga aikin!!


Fatsuma tana jin tafiyar hamma habu ta lallaba ta fito bayan gari ta nufa inda rafi yake' ta zauna tana mai jefa dutse Cikin ruwa tana yar wakar ta carman dudu carman duduwa haka take tana ta nishadi sosai kuwa, murmushi tai da ta tuna ta guduma hamma ne kusan awa uku tana gun wajen la'asar sai ga hamma wajen don ya duba ko tana gun tun daga nesa ya gane ita ce murmushi ya yi ya isa tare da rufe mata ido ta baya jin hannun shine yasa taji sanyi har taji tsoro fa tace nagane hamma ne...


"Uhmm shine kika gudu ko?"


A'a ba gudu nayi ba kawai dai nazo rafi ne!


yasha fuskar ta tare da faɗin abun ba gaiya na raka ki? Ko da yake nasan mai kike ma gudu yarinya.
Dariya tai tare da rufe fuska taji kunya ta ce" hamma kaine ba daga kafa kullum abu ɗaya, ni kuma zafi nake ji fa sosai"


Ohh Allah sarki "fatsume na duk lokacin da zan ganki wata zumar kaunar ki ce kesa har naji ina ƙwadayin na kasance dake a zumfiɗa ɗaya ba wani abu ba amma ki hakuri, kinga ko anan ma kiban kaɗan"


Ware ido tai kamar zatai kuka ta ce" bakin rafi fa muke ko ka manta ne?"


Idanun shi suka Kada tare da yin ja kamar barkono ya furta a hankali cikin sigar lallashi yace'' sanyin ido na ki tashi mu tafi gida na gaji da zama nan wallahi"...... Ba dan taso ba haka tashi suka tafi abin da bata so ɗin dai sai da ya faru!




....................


Ƙarfe tara na dare yazo suka tafi gida sai da suka gama watsewar su can sannan ya taho suka tafi, abin gwanin tausaya ma jannat harda Aunty ta bata dubu hamsin suna kan mota ta bashi kuɗin aiko ya biya ya sai masu kaza ɗaya da yogout suka wuce gida....idan yau taji daɗi gobe akasin shi haka take rayuwa a gidan ta..




Kiran ta yayi tare da faɗa mata gashi a ƙofar gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login