Showing 30001 words to 33000 words out of 55242 words

Chapter 11 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

22 Feb 2025

3155

awa uku cikin gumurzu, wadda nake ji a raina na hakura da komai na rayuwa na ha?ura da duk wasu burikana, ro?o nake yi Allah ya dauki raina ko na samu na huta. Abun da ke tokare da makoshina ya sake tasowa, hannun da ke dafe da kuguna na yi gaggawar dagowa na rike wuyana, Maman Yunus kuka take da idanuwanta domin ba ta taba ganin wata mai haihuwa a irin halin da nake ciki ba, a daidai lokacin kuma na ji kuguna da wasu ?asusuwana da na kasa tantance na wane bagire ne sun motsa lokaci daya, tsananin radadin ya wuce duk wani sanina, tamkar an cire min wani abu na ji a makoshin hakan ya ba ni damar furta, "Innalillahi wa inna ilaihi raji un," da tsananin ?arfi, a daidai lokacin kuma na ji abun kaunata ya ratso jikina da taimakon Maman Yunus ya ?arasa dirowa a cikin duniyarmu, duniyar ruWani da rikici.
Wani irin nannauyan numfashi na sauke, haWe da ajiyar zuciya, na yi baya luuu kafin na iya ba wa kaina taimako na ga wani duhu mamaye ganina.

&
BAYAN WASU AWANNI

A hankali na fara bude idanuwana, biji-biji na fara gani ga tsananin nauyi da suka yi mini, sake rufe su na yi zirr na ji saukar hawaye, hannuna na yi ?o?arin Wagowa shi ma jinsa na yi ya yi mini nauyi, ware idanuwan na yi sosai a kanshi, ganinsa na yi sakale da zaren karin ruwa, Wayan hannun na Wora kan cikina, jinsa silib ya sa ni zabura sai dai cikin matu?ar gudu irin na ?wa?walwa abinda ya faru da ni ya soma dawo mini, "Abun?aunata," na faWa da sauri tare da yunkurawa da nufin tashi zaune, daidai lokacin Maman Yunus ta shigo, da saurinta ta karaso ta mikar da ni zaune.
"Sannu Amatallah, sannu." Jinjina kai na yi, da hannu na yi mata nuni ina abun kaunata? Da rai ma kuwa ya zo ko ba rai? Mace ce ko namiji?"
Murmushin da Maman Yunus ta yi min ya ba ni tabbacin da ransa ya zo. "Nutsu Amatallah, Abun?auna da ransa ya zo, kuma namiji ne, kyakkyawan yaro kaman balarabe..." ta ?are zancen tana ?ara gyara mini zamana.
"Alhamdulillahi," na Waga hannunwana sama ina yi wa Allah godiya. Juyawa ta yi baya da ni kadan, gani na yi ta juyo da jariri cikin wani hadadden farin showel mai matukar kyau, fiddo shi ta yi daga cikin shawul din ta juyo mini da fuskarshi, "Kin ganshi ko Amatullah,"
"Na ganshi," na faWa hawaye na sakkowa daga idanuwana, hannuwa na bude da nufin karbarshi, sai dai Maman Yunus ta wuce hannuwan ta dora mini shi kan ?irjina, zuciyata ta hau bugawa da sauri wani irin sanyin dadi da babu kwatankwacin ya ratsa lungu da sakon zuciyata ya cigaba da zagaye sassan jikina, hannu na sa na dafe shi, "Abun kaunata& " na fada hawayen jin dadi na cigaba da sintiri daga idona. Maman Yunus ta duko ta sumbace ni ta sumbaci abun kaunata, hawaye ne ita ma cike fal da idanuwanta, cikin raunanniyar murya ta ce, "Abinda nake so ta in ji kenan, jiya na ji kin yi magana na kasa tantancewa ina tunani ko gizo kunnena ya yi mini ashe da gaske ne, Alhamdulillah."
Jinjina kai na yi na kasa tsaida hawayena, "Ni ma na ji tamkar hakan Mama," dago abun kaunata na yi daga kan ?irjina, kallonsa nake yi cikin shaukin soyayah, cikin shaukin so da kaunar da ban taba yi wa wata halitta makamancinta ba, na zuba mashi idanuwa ko ?yaftawa bana yi, barci yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, gashi linkib a kansa ya yin da wani ya yi mashi kwalliya a goshinsa, hancinsa da bakinsa daidai wa daida, tabbas duk wanda ya san AbuDalib kallo Waya zai yi masa ya gane gudan jininsa ne, cikin muryata da ba ta gama fita ba na ce, "AbuDalib," sannan na sumbaci goshinsa da fuskarsa.
Maman Yunus ta ce, "Amatullah sannu kin ji, kin sha wahala sosai." Murmushi na sakar mata, domin ji nake duk wata wahala da ?uncin zuciyata ya yaye.
"Amma Alhamdulillah, tunda ke da Abun?aunarki kuna cikin koshin lafiya. Yanzu kafin ki ci wani abu shi ma ki ba shi na shi abincin saboda tun Wazun ba abinda aka ba shi, ga shi yanzu kimanin karfe huWu na yamma. "Toh Mama," na furta ban yi gardama ba.
Hannu ta sa cire ?arin ruwa da ke sar?afe da hannuna, kasantuwar rigar da na bude idanuwa na ganta jikina babban wuya gare ta Maman Yunus ta gyara zaman Abun kaunata jikina, sannan ta ba ni umarnin na fiddo Mamanshi na ba shi, kiciniyar yadda zan yi na fara, hannunta ta sa ta fiddo sannan ta ce, "Ki yi bismillah ki sa ma shi bakinshi."
Bismillah na yi kamar yadda ta ba ni umarni, zukar maman ya yi kamar ya saba da shi, wanda sai da na ji har cikin kaina. Alhamdulillah Rabbil alamin, na fada, ga abun kaunata a gabana ga maganata da na mance yadda ake yin ta ta dawo. "Allah nagode maka, Allah nagode maka," na fada cikin muryata mai cike da jimami da kuma farin ciki.
Sai da Maman Yunus ta kintaci ya koshi ta karbe shi ta ajiye shi kan gadon da duk su ne suka dauki dawainiyar siyo shi. Maman Yunus ta ce, yanzu sai ki shirya a je a yi wanka, ko kuma za ki sha tea. Jikina ya yi wani kala hakan ya sa na fara zaSar wankan. Mikewa na yi cinyoyina na ta rawa, abun ya zo in ji mai haihuwar fari ni ma abun ya zo kenan. Saboda rashin karfin jikina Maman Yunus ta kama ni har toilet muka je, kamar yadda Uwa ke kula da 'yarta a wannan lokaci da ta shiga wata sabuwar chapter ta rayuwarta haka Maman Yunus ta wanke ni tass da ruwan zafi wanda aka kare wankan da koke-koke na har da ihu. Fitowa na yi na nemi wuri na zauna, kayan shafa tun daga kan mai powder, turaruka da kayan sawa Maman Yunus ta kawo mini, tabbas ba abinda zan ci gaba da yi wa Allah sai godiya domin shi ya hada ni da Yunus da Mamansa suka tallafi rayuwata. Shiryawa na yi tsaf cikin doguwar rigar atamfa, sannan Maman Yunus ta haWa mini hadadden shayi mai kauri da zafi tare da wata gasashhiyar kaza, sam na kasa ci da yawa, amma ta tsare ni sai da ta tabbatar cikina babu kwarin yunwa a cikinsa sannan ta bar ni na huta. Fita ta yi za ta duba marasa lafiyarta, hakan ya ba ni damar zuwa wurin abunkaunata, barci yake cikin kwanciyar hankali Wauko shi na yi na koma mazaunina, juya shi ina sake yi masa kallon ?wa?waf, ba shi da wata tawaya jikinsa ciff yake sannan yana da cikakken kuzari da koshin lafiya.
A shake na ce, "Abun kaunata, barka da zuwa zuciyata, abun ?auna ga ka ga Amminka, Allah ya kare min kai, Allah ya raya min kai, Allah ya ba ka rayuwa mai albarka, ina sonka abun kaunata." Hawayen tausayinmu ni da shi suka ziraro min. A daidai lokacin na ji ?wan?wasa kofa, cikin dakakkiyar muryarsa ya ce, "Mu shigo." Mayafi na sa na lulluSe jikina, sannan na ce ku shigo.
Yunus ne fuskarsa cike da annuri da murmushi, tamkar shi ne Uba ga Abun?aunata, tamkar shi ne aka yi wa haihuwar. Cikin girmama shi na ce, "Ina wuni." KaWa kai ya yi, "Ama, Masha Allah Ama kin dawo magana." Jinjina kai na yi, mi?a mashi Abun?auna na yi, karSar shi ya yi cikin bayyanan nan jin daWinsa, "Ama na ga abun?auna, na ma riga ki ganinsa." Murmushi na yi ina du?ar da kaina, saboda kallon da Yunus ke yi mini tamkar ranar ya fara ganina.
"Mun yi ta barka Amatullah, abun ?auna ya zo duniya lafiya. Ban tambayi izininki ba Wazu na zo wajen 7:00am kina ta barci, na yi masa ta'ani?i na yi masa addu'o'i Allah ya raya mana shi."
"Duk abinda ka yi masa daidai ne, kai ai Uba ne a gare shi."
"Nagode," ya faWa yana sakar mini murmushin da ya kasa barin fuskarshi.
"Ya kamata a yi masa huWuba, wane suna za a saka mashi?"
A sanyaye na ce, "A saka mashi Abu?alib." Sunan da na faWa ya sa hawaye zubowa daga idanuwana.
"Okay, amma waye Abu?alib ba za a saka mashi Muhammad ba?"
"A saka mashi Abu?alib Yaya Yunus, amma za a ri?a kiransa da Nadir."
"Shi ke nan Ama." ?ago Abun?aunata ya yi, ya saita bakinsa kan kunnuwansa ya fara rera mashi kiran sallah, sai da ya gama masa huWubar sannan ya mayar da shi kan gadonsa.
"Bara na je Ama, ki kwanta ki huta, kin sha wahala sosai."
"Nagode muku, Allah ya saka da alkhairi." KaWa kai kawai ya yi, ya mi?e ya fice daga Wakin. Mi?ewa na yi na koma kan gadon na kwanta, kasantuwar akwai tarin gajiyar wahalar da na sha ban jima ba ina ta tunane-tunane kan rayu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wata barci ya yi awon gaba da ni.


&&&


Inna Uwale ce tsaye kan Umma, Rumaisa ta yi kuka har ta gode ma Allah ganin Umma cikin yanayin da ba ta taba ganinta ba, duk da sun yi gaggawar zuwa asibiti, amma likita sai cewa ya yi ba su ga komai ba jikinta, hatta zargin da suke na cutar kansar mahaifa da ta same ta ba su ga komai ba, hakan ya sa za su iya cewa ma babu wani abu da ke damunta hawan jininta da damuwa ta sabbaba mata shi.
Bude idanuwa ta yi da kyar ta kalli Uwale. "Uwale, a yau ina jin kewar Wana AbuDalib, na ji zuciyata da kwayar idanuwana tana son ganinsa, amma kuma kamar na makara saboda ina gab da kushewa, ku kira mani shi ko da a gabar numfashina na karshe ne in ganshi, na fada mashi abinda ke raina."
Rumaisa ta kama hannunta, "Umma wallahi babu abinda zai same ki, ba za ki mutu ki bar mu ba Insha Allah."
"Rumaisa, ina ji a jikina lokacin yankewar wannan wahalar da bakin cikin ya yi." Wani dan tari ya taso mata da ya sa jikin Rumaisa ya hau karkarwa. "Ya Ubangiji kar ka dauke Ummana, ya Allah kar ka dauke Ummana, Allah ka raya ta."
Inna Uwale ko hawayen kawai take yi yayin da ta kasa furta komai. Hannu Umma ta sa ta lalaubo hannun Rumaisa, "Mutuwa gaskiya ce, kuma ita ke raba kowa da masoyinsa, har jinjiri ma ta raba da uwarsa a kan me kike wannan ihun kukan?"
"Umma ni dai ba na son ki tafi ki bar ni." Wani murmushin ta yi mai ciwo, "Ki saurare ni da kyau zan ba ki wasiyya ki nutsu ki rike da kyau a ?wa?walwarki."
"Na san idan AbuDalib ya samu labarin mutuwata dole zai zo wurin jana iza da zaman gaisuwata. Idan ya zo ki shaida mashi, na yafe mashi duk abinda ya yi mini, amma na tafi da bakin cikin kazafin da suka yi wa diyata, zan yafe masa wannan laifin ne idan ya nemo ta duk inda take cikin fadin duniyar nan, ba zan yafe mashi wannan zunubin ba in har bai nemo ta ya wanke ta daga wannan zargi da sharrin."
Shuru ta yi hawaye na zubo mata tana jin dacin abinda ya faru kamar yanzu ne yake faruwa. Tari take saboda mikin da ya samu wuri cikin zuciyarta ya zauna ya motsa. Sallamar Malam Saleh cikin dakin asibitin ya sa Inna Uwale juyawa ita ko Rumaisa ta hada kai da gwiwa tana wani irin kuka mai cin rai. Umma ta ji sallamarsa sai dai ta yi shuru domin rauni ya ida lullube ta, shi ma kula da yanayin da suke ciki ya sa shi zarcewa kawai inda Umma take. Ko gaisuwa ba su yi ba ya ce, "Uwale tare muke da Baban Rumaisa." Kallon shi ta yi a dan razane, bakinta na rawa ta ce, "Baban Rumaisa kuma?"
"Ehh, idan kun ba da izini yana son ya shigo."
Umma ta kada kai, "Don Allah ku bar shi a waje ba na bukatar shi nan."
"Bilkisu ki yi hakuri ki yi afuwa domin Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, kuma lada mai yawa tana ga mai yafiya da afuwa a kan laifin da aka yi masa."
Da ?yar ta ce, "Shi ke nan ka ce mashi ya shigo." Shigowa ya yi cikin Wakin kallo daya za ka mashi ka tabbatar yana cikin wani yanayi marar fassaruwa, cikin nauyin harshe ya ce, "Umma ki taimake ni ki yafe mani, domin na san kuskuren da na yi maki ko a wurin Allah babban laifi ne." Shuru ta yi zuciyarta na suya, "Kin ji Umma..." Sallamar Doctor cikin Wakin ya katse zancen da ya fara. Kasantuwar asibitin private ce kuma suna Wakin mutane masu muhimmanci, (VIP room) hakan har ya ba su damar shiga.
Doctor ya kalli Uwale cikin nuna Sacin rai ya ce, "Na ce a bar ta ta huta, saboda hypertension da ya tasar mata."
Inna Uwale ta ce, "Ka yi ha?uri Doctor."
"Okay, ina so zan yi aikina ku Wan ba mu wuri."
Gaba daya suka fice yayin da Rumaisa da ke ta aikin kuka ta kasa bari, shi ma Babanta duk da kasancewar shi babban mutum shi ma kwallah yake yi.
Fitowa suka yi daga waje, Inna Uwale ta nisa a sanyaye ta ce, "Malam jiya ban samu zuwa ba saboda jikin Umma da ya rikice."
"Haka ne, ina ji a jikina rikicewar jikin Umma ya tallaka ne da kiran da na yi maki. Kuma yanzu ma da Likita zai ba mu sallama da mun je an yi mata rubutu da addu o i ta cigaba da sha za ta warware Insha Allah."
"Malam, akwai wani abu a ?asa ne?"
"Jinjina kai ya yi alamun eh. "Amma a nan zancen ba ya yiyuwa, ga wannan rubutun da na zo da shi a ba ta tasha yanzu. Idan aka sallame ku, za mu yi bayanin komai na fi son a yi komai a gaban Umma," ya kare zancen yana fito da rubutu daga cikin aljihunshi.
"Inna Uwale ta nisa ta ce to shi ke nan, amma jikin Umman ne& " kukan da ya taso mata ya hana ta ?arasa zancen.
"Ba wani abu Insha Allah, kin san cuta ba mutuwa ba ce ko? Haka ciwo ba shi ke nufin ajali ya zo ba, wani lokacin ma idan ajalin ya zo ko ba ciwo tafiya ake yi. Wannan abun da ke faruwa warwara ce da samun sauki daga kunci da tsananin da aka shiga Insha Allahu."
"Allah ya sa haka Malam." Rumaisa da take jin zantukansu a kunnenta, ta daga hannunwanta sama tana kiran, "Ya Allah ka raya mani Ummana."
Malam Saleh ya ce, "Rumaisa babu abinda zai same ta Insha Allahu." Zama suka cigaba da yi jugum-jugum bayan likitan ya fito Inna Uwale da Rumaisa suka koma ciki. Kasantuwar sun samu tana barci ya sa Malam Saleh da Baban Rumaisa tafiya, tare da jaddada zancen kashe garin ranar za su koma.


SH 13

Wuraren ?arfe bakwai na safe jirginsu ya sauka filin jirgin Malam Aminu Kano, tunda suka taho haka suke zaune kamar kurame, kowa da tunanin da ke ?unshe cikin zuciyarsa. Kai tsaye Abu?alib tashar mota suka nufa, takaici zuciyar Badiyyah tamkar ta yi bindiga domin ta shafe babin hawa motar haya a cikin kf Win rayuwarta.
Motar kwankwasiyya ya Wauka drop kai tsaye ta kai su har birnin Dikko Wakin kara. Fitowa Badiyyah ta yi daga motar tana yamutsa fuska, Abu?alib bai bi ta kanta ba, sai ma abun da ya yi na in ba ki yi ba ni wuri da ya yi, da sassarfa ya tari mai achaSa domin ya kai shi gidansa da ke Modoji. Har bakin ?ofar gidan ya kai shi, ma'aikatan gidan da suka ganshi bagatatan sun cika da mamaki sosai. Da sauri ya isa ?ofar babban falo, abu Waya yake so ya tabbatar wanda Badiyyah ta faWa mashi, shi Abu?alib ya saki matarsa Lilbirrah saki uku ?warara, shin da gaske ne ko kuma zafin kishi ne irin na mata ya sa ta faWar hakan. Cikin falon ya tsaya yana kallon hanyar da sashenta yake cike da tsammanin ganinta, cikin fara'a da annushuwarta, ganin babu ita babu alamarta ya sa shi faWin "Lilbirrah?" da ?arfin gaske. Falon tsit yake sai sautinsa da ya karaWe shi, ?ara kiranta ya yi da sunan da babu mai kiranta da shi sai shi kaWai, "Khouhar," sam bai ji da alamun za a amsa ba. Gudun zuciyarsa ya ?aru fiye da gudun da yake yi, a hanzarce ya nufi sashenta, hannu ya sa ya murWa handle Win ?ofar Wakinta, falon ya yi ?ura da har yana ganin sawayenshi a ?asa, hakan ya ?ara tada hankalinsa sosai. "Innalillahi, kenan da gaske ne abinda Badiyya ta faWa mani?"
Bai tsaya wani abu ba ya fice daga Wakin, kai tsaye gidansu da ke yammawa ya nufa domin ya samu Ummansa ya sani ita kaWai ce za ta warware masa zare da abawa ta fitar da shi daga ruWanin da yake ciki. Mai mashin na aje shi ya fiddo takardar Dollar da ke aljihunsa wanda da ita ya biya kuWi tun daga Kano har zuwa kan mai mashin Win da ya sauke shi. Cikin mamaki mai mashin din ya ce, "Malam Dollar ce ka ba ni?"
"Je ka kawai rabonka ne." Ya faWa yana shigewa cikin gidansu.
"Salamu Alaikum," sallamarsa ta ratsa cikin gidan. A guje matasan ?annensa suka fito da gudu, Waya daga cikinsu ya rungume shi Wayan kuma tsaye yake yana masa kallon mamaki.
Babansa Malam Abdulhadi ya fito yana masa kallon yaushe rabo, Wayan Wakin kuma Antinsu Rashida ita ma ta fito tana ?are masa gani, su duka kallonsa suke kamar yau ne suka fara ganinsa. Sakinsa ?anin nasa ya yi, "Yaya Abu?alib..." Ya faWa yana sakin murmushin jin daWi, sai kuma hawaye suka ziraro daga idanuwansa.
"Yaya Abu?alib, da ma za ka sake shigowa duniyarmu?" Shi ma kallonsu yake cikin tsananin mamaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login