Showing 1 words to 3000 words out of 113443 words
*WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
*Alhamdulillahi I'm back after a long break...*
*©All right reserved... No individual, group or organization is allowed to copy, translate, publish or read this content on the public space, radio station, YouTube, social media or any other outlet without the authorization of the original writer, Aisha Muhammed Alto.*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
__________________________
*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*
*SADAUKARWAR SO!!!*
*Sun taso tun yara tare...Iyayensa sun fifitasa akansa shima yafi fifita buƙatun ɗan goggonsa fiye da buƙatunsa, a tasowarsu kowa halayyarsa ta bambanta yana jin daɗi da sha'awar ganin rayuwarsa cikin barkwanci saɓanin shi daya kasance magana ma wahala take mai...Rana tsaka dalilin maƙotaka wata yarinya ta ratso rayuwarsu ya fara sonta ba tare daya sani ba, ashe shima ɗan uwansa ya kamu da soyayyarta, bashi da zaɓi illa yin SADAUKARWAN SO...!*
*Ba tare da kowa yasan yana sonta ba...Ya binne abun a ranshi bai taɓa koda wasa wani daga cikinsu ya fahimci abinda ke cikin zuciyarsa ba...Kamar yadda yayi SADAUKARWAN SO haka shima akayi mai SADAUKARWAN SO...!*
Shin wace irin Ƙauna ce haka a tsakaninsu da har zai iya ma ɗan uwansa SADAUKARWAN SO...?
Nasan kuma dole zaku yiwa kanku waɗannan tambayoyin, kuma zaku zaƙu da son jin amsarta..To tambayar taku ɗaya ce amma amsoshinta suna da yawa kuma ba'a ko'ina ne zaku samu amsarta ba sai a cikin wannan shahararren labarin SADAUKARWAR SO wanda shahararriya kuma fiƙrarriya zaƙaƙurar marubuciya ta rubuta wato *JAMILA UMAR JANAFTY* kuma zaku iya samun duk wannan garaɓasar da romon daɗin labarin ne akan farashi mai rahusa kamar yadda ta saba muku:
*Zaku biya kuɗin karatu ₦300 ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*
*KO*
*Katin MTN ₦400 ta wannan lambar 09069067488*
*Ƴan Niger kuwa zaku iya tuntuɓarmu akan wannan lambar +22794775574*
Karku sake ayi babu ku domin wannan tafiyar miƙaƙƙiya ce mai nisan zango mai neman ƙarin bayani sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 09069067488 muna maraba daku masoya sai kunzo🤝
___________________________
*KADUNA STATE*
*Igabi Local Government*
_Area Rigasa..._
1️⃣
Alarm ɗin daya saka domin ya riƙa tadashi ƙarfe huɗu da rabi na asuba, shine ya fara bugawa cikin ƙaramar wayarsa ƙirar Nokia.
Da hanzari ya miƙe zaune daga barci mai nauyi daya kwashesa tun na daran jiya sakamakon ya gaji ɗakin da duhu amma haka ya laluba gefen katakon gadon ya lalubi wayarsa ya kashe alarm ɗin lokaci ɗaya yana kunna fitilar dake jikin wayar haske ya gauraye ɗakin.
Ƙafafunsa ya zuro ƙasa lokaci ɗaya yana miƙa da kuma bayyana salatinsa tare da addu'an tashi daga barci gefensa ya kalla lokaci ɗaya ya miƙe yana gyara zaman bakin dogon wandon dake Jikinsa, daman babu riga, tana kwance ta nannaɗe cikin bargo tana sharar barcinta cikin kwanciyar hankali ya daɗe yana kallonta kafin kawai ya kaɗa kai yana tuna irin rigiman da suka tafka jiya kafin su kwanta bai san yaushe ne FADWA zatayi hankali ba.
Fita yayi daga cikin ɗan madaidaicin ɗakin ƙaramin kichin ɗin dake tsakar gidan ya shiga ya fito da ƙaramin murhun gawayi, sai da ya fito dashi waje kana ya ɗibi ruwa a buta ya shiga ƙaramin makewayin da aka karesa da langa langa ya kama ruwa bayan ya fito ne ya duƙufa hura gawayin da ledojin daya fito dasu, da ƙyar ya hura gawayin duk idanuwansa sunyi jawur da ƙyar ya samu ya ɗora wata ƙaramar tukunya ya cikata da ruwa kana ya koma ya ɗauki tsintsinya ya fara sharan ƙaramin tsakar gidan mai shimfiɗe da siminti ya share tas ya kwashe kana ya ɗauki manyan botikai ya fita waje can gangaran layinsu ya riƙa ɗebo ruwa yana zuwa yana dawowa sai da ya cika duka manyan bombun Fadwa har guda uku kana ya dakata ganin har 5 tayi na asuba ruwan wankan ya duba yaga yayi zafi ya ɗiba sai ya ƙara ruwan ya sirka ya shiga wanka bai wani jima sosai ba ya fito ya shiga ɗakin har lokacin Fadwa bata tashi ba bai mata magana ba sai da ya shafa mai ya buɗe ƙaramar jakarsa ya ɗauko wata jallabiyarsa mai ruwan toka ya saka da hularsa.
Har ya sa ƙafa zai bar ɗakin sai ya fasa ya dawo da baya ya isa jikin gadon yana buga katifar cikin sanyin muryarsa yake faɗin "Fadwa...Fadwa..ke Fadwa...." Yake faɗa yana buga gadon ganin ko motsi taƙi yi yasa ya daki ƙafarta yana ƙara kiran sunanta cikin takaici da ƙunƙuni Fadwa ta motsa tana yamutsa fuska kamar taga kashi cikin ɗaurewar tuska ta waigo tana kallonsa daga hasken fitilar maƙarfin daya kunna acikin ɗakin.
Cikin haɗe rai yace "Ki tashi kiyi alwala ki yi raka'atanil fijir kafin a tada sallar asuba...." Ko gama rufe baki bai yi ba taja wani uban dogon tsaki da ƙarfi ta juya ta ƙara dunƙulewa, abun sosai ya bashi mamaki duk da yasan halin Fadwa duniya kaɗai ta sakama gaba bata ma damu da sallar ba sai ya matsa mata sosai take sallar asuba sauran sallolin kuwa bai san ko tana yi ko bata yi ba tunda baya wuni a gidan ita kanta ma ba zaman gidan take yi ba.
Kamar zai ƙyaleta sai kuma yaji ai bai kamata ya barta tai ta barcin asara ba da sauri ya duƙa ya fizge bargon jikinta cikin wani wawan fushi ta waigo tana watsa masa kallon banza kafin ta tashi zaune tana mutstsike ido kanta duk ya hargitse yayi buzu buzu saboda ba kitso akan nata cikin wani takaici ta kallesa daga sama har ƙasa tana faɗin "Meye haka Malam...? Dillah ni bani bargona kasan dai ni na siya abuna da kuɗina bada guminka na siya ba...."
Bai damu ba illah kai daya girgiza yana faɗin "Wallahi bazan baki ba komai zaki ce...Malama ki tashi lokacin sallah yayi...." Taso mai tayi da faɗa tana faɗin "Ce maka nayi bazan yi sallar ba...? Kai fa wallahi mugun ɗan rainin hankali ne tsiyata da kai kenan aikin riya komai sai ka nuna kai na Allah ne...."
Ransa ya ɓaci sosai da kalamanta cikin takaici yace "A'uzubillahi Allah ya rabani da aikin riya Fadwa...matsawar da kika ga ina miki kuma saboda sauke hakkin ki dake kaina ne na baki tarbiya na kula dake, ke matata ce ina da ikon dawo dake kan hanya in naga zaki karkace Fadwa...." Hannu ta ɗaga mai tana faɗin "Naji ubana sarkin tarbiya nidai bani bargona kai talaka da kai faƙiri baka da ko sisi har kake faɗin zaka iya tarbiyantar dani...to ta ina ma....?" Ta ƙarashe maganar cike da rashin kunya tana harararsa.
Bai damu ba illah juyawa da yayi yana faɗin "Bazan baki ba..sai fa kin tashi kinje kinyi sallah Malama...." Baki ta tura kawai tana kallonsa sanin halinsa na taurin kai da nacin tsiya yasa ta zuro ƙafarta ta sauko daga kan gadon ƙaramar rigar barcinta iya gwiwa ta bayyana miƙa tayi tana hamma lokaci ɗaya cikin takaici ya kalleta yana faɗin "Sau nawa zan gaya miki ki dinga salati in zaki yi miƙa ki kuma riƙa rufe bakin ki in zaki hamma amma kalli abinda kika yi yanzu wannan ai ba ɗabi'a bace ta ɗan musulmi na ƙwarai...."
Ko kallonsa ba tayi ba ta raɓa ta gefensa zata fita ya riƙo hannunta yana faɗin "Ya zaki fita haka...? Kalli ƙaramar rigar jikinki fa...? Kanki kuma ko ɗankwali babu, safiya batayi ba kada ki manta ko sallar asuba ba'a tada ba..." Haushi ya ƙara kamata ta waigo azafafe zatayi magana ya girgiza mata kai yana faɗin "Don Allah ba don ni ba kada ki fita a haka ki suturta jikinki Fadwa...." Ya faɗa lokaci ɗaya yana langwaɓe mata kai alamun roƙo bata da yadda zatayi dole tayi shiru cikin ƙufula ta koma ciki tana ƙunƙuni ita kaɗai yana kallonta ta ɗauko zani ta ɗora saman rigar barcin jikinta ta kuma ɗauki ɗankwalin doguwar rigarta baƙa ta saka tana ɗagowa suka haɗa ido dashi, ido ta waro masa tana faɗin "Sai kuma me....? Ka ce sai na tashi kuma na tashi kace na suturta jikina kuma nayi yadda kace bibiyar ta isa haka a ajiye min bargona don Allah a ƙara gaba a daina ƙuramin ido haka nan kamar za'a cinye ni...."
Maganarta sai ta bashi dariya sai da ya murmusa ya ajiye mata bargonta saman gado yana gyara zaman hularsa yana faɗin "Ni na tafi masallaci in zaki yi wanka ruwan wankan yana kan gawayi na ɗora miki..." Bata ma tsaya sauraransa ba ta raɓashi ta wuce ɗauke da wayarta wacce ta kunna fitila bayanta yabi suka fita tare yana kallonta ta zari buta ta shige banɗaki kai tsaye ko addu'a batayi ba, kai kawai ya girgiza kafin a fili ya furta "Allah ya shirya min ke Fadwa..."
Daga haka ya fice daga gidan bayan ya zare sakatar ƙofar daya fita sai ya sakayata ganin anguwan shiru sai ɗai ɗaiɗai kun mutanen dake wucewa zuwa masallacin dake gaba kaɗan.
Tana jin fitarsa daga cikin bayin ta saki tsaki tana faɗin "Gaskiya nidai an haɗani da aiki ga shegen talauci ga takura...." Ta faɗa dai dai lokacin data ke fitowa daga banɗakin, tsakar gidan ta ƙare ma kallo lokaci ɗaya ta taɓe baki domin ita bazata iya tuna yaushe ne ma ta taɓa sharan gidan nan ba tunda aka ɗaura mata aure da YA AZEEZ.
Batayi alwalan ba kamar yadda tace ɗaki ta koma ta ƙara hayewa gado ta kwanta tana faɗin "Sai na tashi nayi sallar..." Ta faɗa tana ƙara duƙunƙunewa a cikin bargon tana ta sakin tsaki ita kaɗai kamar wata tsaka, daga nan barci ya ƙara kwasheta bata ƙara sanin komai ba sai da taji maganar Azeez asaman kanta kana ta buɗe idanuwanta cike da barci tana kallonsa sanye yake cikin riga da wando na wani yadi mai saukakkan kuɗi daga ganin yadin yaji jiki amma kuma yana wanke ne kuma agoge sai hularsa taɓani kaji Hadisi.
Sama da kasa take kallonsa tana kuma ƙare mai kallo aranta kuwa faɗi take ga namiji har namiji sai dai talauci ya mai cikas, Ya Azeez kyakkyawa ne ajin farko domin dogon namiji ne mai cikar zati da haiba ba baƙi ba ne chocolate colour ne irin mai ɗan hasken nan, ga dogon hanci har baka wanda ya dace da kyakykyawar fuskarsa ga sajensa wanda ya zagaye ƙaramin bakinsa ya ke ƙarawa fuskarsa kyau da cikar zati da kamala Abdulazeez mutum ne na gari mai dattako da sanin ya kamata uwa uba ga haƙuri da kawaici, mai wadatar zuciya mai tsantseni da iyawa talaucinsa bashi da hange hange ko duban na gabansa, abinda ya sani kawai neman na kansa.
Ganin ta shagala da kallonsa yasa ya duƙa ya tallabi kumatunta yana faɗin "Yau kuma ni ake son gani Fadwa...?" Sai lokacin ta dawo daga duniyar tunanin data faɗa cikin basarwa ta kauda kai tana faɗin "Ummhh..na kalli wa...? Dama kana da kuɗi ne sai nace ka mori kyanka amma kalle ka..kullum da safe sai ka fita kayi gararanba a gari kake samo abinda zamu ci..kai Allah karabamu da ƙangin talauci da auran talaka wallahi...." Ta faɗa cikin bayyanar tsantsar takaicinta.
Bai damu da kalamanta ba ya kaɗa kai yana saka makullin napep ɗinsa cikin aljihun wandonsa lokaci ɗaya yana faɗin "Sai ki tashi kiyi sallar...ni fita zan yi..ga kayan tea nan na shigo miki dashi...." Mamaki ya kamata na ya akayi ya gane batayi sallar ba, bai bi ta kanta ba ya zura takalminsa na roba yana faɗin "Ga ɗari biyu nan saman gado..kiyi cefene ki dafa wani abun..duk da na tabbata ba girkawan zaki yi ba amma hakkin ki ne shiyasa nake baki saboda kada Allah ya kamani da hakkinki wata rana...."
Bai tsaya saurarenta ba ya fice ta rakasa da tsaki kafin ta miƙe zaune tana bin ɗakin da kallo banda gadonsu dake cikin uwar ɗakan sai ɗan madubinta da ledan tsakar ɗaki a falo ba wani abun ƙwarai sai akwatunan kayansu ita dashi ɗakin fayau yake babu wani abun arziki aciki, tsaki ta saka kafin ta sauko daga kan gadon waje ta fita ta duba ruwan wankan da Ya Azeez ya saka mata ta juyo sauri sauri take sai da ta fito wanka kana tayi alwala ta koma ɗaki tayi sallar lokacin wajen ƙarfe 7:50am ne na safe bata damu ba tana idar da sallar ta fara tsara kwalliya cikin burgewa domin ba ƙarya ita kanta Fadwa ba baya ba wajen kyau da jikin mata.
Tunda itama doguwa ce kuma tana da haske bata da munin fuska ga dogon hanci a fizge suna yanayin kama da AZeez ɗin ta ɓangaren yanayin tsarin fuskarsu sai dai ita fara ce sol, taci mintina sunfi talatin wajen tsara kwalliya kafin ta gama akwatinta ta jawo ta buɗe ta ɗauki wani leshinta mai kyau da tsada wanda kawarta Hajiya Labiba ta ɗinka mata ne cikin lokaci Fadwa ta fito tsaf kamar wata matar Alhaji gyalen kayan ta ɗauko ta saka sai jakarta mai kyau da ita lokaci ɗaya tana jefa ƙaramar wayarta a ciki ɗari biyun daya bar mata ta ɗauka tana yamutsa fuska kamar zata yi kuka ta jefa cikin jaka tana faɗin "Allah rabamu da auren matsiyacin namiji...ana harkar Dubai da Saudi amma ni harkar Nigeria Hayin Rigasa kawai nake ƙasƙanci zalla, ace kamata miji na bani 200 kuɗin cefene...." Bata tsaya gyaran ɗakin ba ballatana tayi kaye kayen kayan tea ɗin daya siyo mata wanda ko kallonsu batayi ba ta fito ta saka kwaɗo ta rufe ɗakin tsakar gidan tabi da kallo harta da murhun gawayin bata kauda shi ba ta saka ƙafa ta fita ta bar gidan bayan ta saka ƙaton kwaɗo ta kulle gidan tana ta wani ɗaure fuska domin tama fi jin ɗadin ganin gidan tana cikin gidan da sai ta fita ta kalli gidan sai taga Abba ya gama cutanta daya haɗata zama da makiri irin Ya Azeez.
Tafiya ta farayi tana taku ɗaya bayan ɗaya duk wanda yaga Fadwa a lokacin sai ya ɗauka matar wani ƙusa ce ita, tafe take tana tsaki tana faɗin "Kai Allah rabamu da talauci...ni kam rayuwata ba cigaba na taso cikin baƙin talauci ubana na fama da mashin ƙarfe ƙarfe ƙawayena duk sun fini, ina tunanin in nayi aure zan huta ashe ba haka bane an riga an gama cutata kamata ina auran mai keke napep kullum yana gararan ba a gari da ace yau wani mai daula nake aure da daga gida mai kyau zan fito cikin lafiyayyan mota direba na jana Ac a gida Ac a mota, amma kalleni ina tafiya a ƙasa kamar wata wulaƙanttaciyar almajira...kai Allah ka azurtamu da azurtawarka ka rabamu da tsiya...."
Take faɗa tana ƙara jin kamar igiyar auran ya Azeez dake kanta wani bala'i ne tana cikin wannan tunanin ta isa bakin titi ta samu mai Napep ta shiga bayan ta gaya mai inda zataje ya ja suka fara tafiya.
Bai direta ko'ina ba sai ƙofar wani tangamemen get ɗin gida mai kyau da tsari fitowa tayi ɗari biyun data ɗauko ita ta bashi kuɗin keke napep ɗinsa ta nufi bakin get ɗin ta fara ƙwanƙwasawa bata jima ba megadin ya leko daman tun kafin ya leko yasan ba wani mai zuwan sassafe sai Fadwa yana ganinta A ɗage yace "Kai..jama'a yau ma dai...?"
Wani kallon banza tayi mai kafin tace "Eh yau ma..ko zaka hanani shiga ne tunda gidan uban ka ne...?" Bai mata magana ba ya buɗe mata ƙofa yana faɗin "A'a wane ni na hanaki shiga...nima fa cin arziki nan nake..." Ƙaramin tsaki taja tace "Tunda kasan haka ka tsaya iya matsayinka..." Ta faɗa tana wucewa kamar zata tashi sama da kallo ya bita a fili ya furta "Kowaye mijin matar nan..wallahi bai yi sa'ar mata ba ko kaɗan..ace mace kullum bazaki zauni gidanki ba kina tafe kamar leda...."
Ita kuwa batama jinsa tana ta kallon motocin dake harabar gidan lokaci ɗaya ta saki dariyar jin daɗi tana faɗin "Alhajin na ciki inaga...." Ta fada tana nufar ƙofar da zai sadata da cikin falon gidan.
Yadda ta shiga cikin falon kanta tsaye babu wani jira zaka san ta saba zuwa gidan daga ganin falon zaka san ma mallakan gidan sun tara dukiya ko daga kujerun da suka zagayen falon zaka gane hakan, Fadwa ta riƙa bin ko'ina da kallo tana ƙarawa ko'ina yayi neat sai ƙamshi mai daɗi ke tashi gyalenta ta cire ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon jakarta ta ajiye tana faɗin "Ikon Allah..arziki na inda yake..ji Hajiya Labiba suna ma sama abunsu ita da Alhajinta basu ko tashi ba ji gidanta duk ƴan aiki kota ina sun gama mata komai..kai Allah ka rabamu da auran talaka wanda bai da ko sisi ka bamu mai wadata....."
Ta faɗa tana wani ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya kafin ta ɗaga baki tana faɗin "Rabi..! Rabi..!!.." Rabi mai aikin Hajiya Labiba taji muryan Fadwa na kiranta fuska ta ɓata tana faɗin "Toh fa..su jarabatu iyayan kwaɗayi an zo kenan...." Sai da tace haka kana ta amsa kiran ta fito da sauri kamar zata kifa, har ƙasa ta duƙa tana mata sannu da zuwa cikin wani banzan kallo Fadwa take kallon Rabi kafin tace mata "Ke wuyanki har yayi kaurin da ina kiranki sai kin ga dama zaki amsa...?"
Cikin kawo rantsuwa Rabi zata fara magana Fadwa ta ɗaga mata hannu tana wani jijjiga ƙafa kamar matar gidan kafin tace "Ban ce ki rantsemin ba Malama..ina so dai kisan matsayinki anan gidan aiki kike ana biyanki ba wata tsiya ba...." Rabi kanta na ƙasa tace "Haka ne Hajiya ki gafarceni..."
Fadwa ta wani taɓe baki tana faɗin "Naji..tashi kije ki haɗo min breakfast..ki haɗo min tea mai kauri kada ki saka lipton, ki soya min ƙwai kamar guda huɗu da dankalin turawa nasan Hajiya Labiba bata rasa pepper chickens ki haɗo min dashi..." Da sauri Rabi ta miƙe tana faɗin "An gama Hajiya..." Ta faɗa tana wucewa kichin da sauri Fadwa ta bita da kallo tana wani sakin tsaki.
Tana nan zaune sai ga Rabi ta dawo da faranti shaƙe da kayan karyawan da Fadwa tace a haɗo mata, kan Center table ɗin dake tsakiyar falon taja ta ajiye mata kana ta fita ta bar Fadwan na gyara zama kamar matar gidan haka ta zauna ta ci ta ƙoshi kana ta kora da lemo tayi gatsa tana faɗin "Alhamdulillahi...kaga inda ake harkar arzki...irin wannan karin shi nake fatan na dinga karo dashi duk