Showing 1 words to 3000 words out of 50228 words

Chapter 1 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf

*RAYUWATA CE*

*Na*

*Khadeejah sani (journalist)*

*Kainuwa writers association*

(United we stand and succeed; our ambition to entertain and motivated the mind of readers)


*Assalamu alaikum inayiwa Allah subhanahu wata,ala godiya daya bani ikon kammala littafina
rayuwar gidan kawuna sannan yakara bani damar fara wani sabon bookdin nawa mai suna
RAYUWATA CE Allah yabani ikon fadakarwa da nishadan tarwa*

*Allah ya yafemin dukkan wani kuskure dazanyi sannan Allah yabani ladan abinda zanfada
Ameen*

*Wanna littafi k`irk`i rarren labari ne banyi shi doncin zarafin wani ba Kuma banyi shi Don
muzan ta wani ba na k`irk`iri labari nane Don fada karwa da nisha dan tarwa Allah yabani ikon
kamalawa Ameen*


*Sadaukarwane gareki mahaifiyata Allah yaja da ranki Ameen*

*1-2*




Suya, nakeyi ta awara" akofar gida ga maza sun kewaye ni, sunata hirar su jinai wani daya
daga cikin su yace
"Nafisa tund`a zu nake Miki magana Amma kinyi shiru Kuma kina jina". d`ago kaina nayi cikin
sanyin murya nace
"Uhm banji bane tanawa za,a baka. murmushi" yayi san nan yace
"Kibani awara ta naira hamsin"
"Kawo kudin"
"Kefa dadina dake y`ar'rainin wayo ce guduwa akace Miki zanyi ne dallah bani naci yunwa
nakeji wallahi" kallon shi na karayi nace
"Kaga Musa kasaba yimin haka kawai ka gudumin da kudina. kasan nidai bazan ta binka ba"
dallamin harara" yayi sannan yace
"Hmm shiyasa nafiso naje wajen hinde Mai awara wallahi nasiya kawai dandai takin tafi Tata

dadine Amma ita har dakina take bina kuma kije ki tam bayeta wallahi ina bata indai taje
shiyasa kema nake fada miki kijecan kikarb`a amma ke kauyanci yayi miki yawa" ya k`arasa
fada Yana dallah min, wata hararar.

Banza nayi dashi inaci gaba da sallamar wadanda suka bani kudi. idnn da sabo nasaba da
wadan Nan magan ganun awurin yan'iskan unguwar mu. don haka kullum kafin nafita sai innata
tayimin fada a kansu karna yarda nabi mutum akan baiba ni kudi ba nabarshi da Allah.

Haka naketa sallamar mutane suna tafiya wasu kuma suna zuwa,
Ana haka Musa da abokan shi suka zauna dan nesa da wurin dana ke kadan amma ina iya
jiyo magan ganun su, na tabbata basu san inajiba wani abokin sane yafara cew
"Nifa wallahi Musa inason wannan yarinyar ina mugun Sha,awarta tunda nafara ganin ta gashi
naji kace bakauyiya ce ita bata iya harka ba yaza,ayi kenan don gaskiya na matsu najita ajikina"
dariya suka kwashe da ita gabaki da yansu wani aciki yace
"Shege zaki wallahi kamar kasan abinda ke raina nima don haka gaskiya asan abinyi kawai"
zakin ne yace
"Kai kasanfa bana son wulakanci nace inason wata sannan kace kanasonta wallahi zan yanka
Maka rigar mutunci tam.
Haka daya fadane yasaka su yin tsit Babu Wanda yakarayin magana,

Tashi yayi yamatso kusa dani yace
"Baby sannu da aiki ya garin"
Dago kaina nayi na kalleshi kawai najuya naci gaba da aikina ina haka naji an dafani dasauri
na dago nayi tunanin koshine sainaga kawata ce farida don haka na saki fuska muka fara
gaisawa da ita.


*My fans inayimuku fatan alkairi dafatan kuna lafiya*

*Agaskiya wannan sabon book din nawa zanfada muku yawan comment yawan typing don
agaskiya banason turomin wadan Nan sticks din kokuma*❤ *bawai bamajin dadiba idon
aka turo wannanba a,a munaji saidai munfi bukatar comment akan komai, ina godiya sosai my
fans Allah yabar kauna* ❤❤

*By*


*Khadeejah(Ummu Fu,ad & Afnan)*


*RAYUWATA CE*

*Na*

*Khadeejah sani (journalist)*


*Kainuwa writers Association*
*Dashin Allah*

(United we stand and succeed our ambition to entertain and motivated the mind of readers)

*Sadaukarwa gareki sisternah masoyiyata Ayshat m zazzau Allah yabar kauna*❤


*5 _ 6*


Mahbub ne yafito daga cikin gida dagudunsa yayi wurin da wannan mutumin yake ganin Babu
motarshi yasakashi kallo wurina naji yace
"Anty uncle tafiya yayi naga bayanan?" Banza nayi dashi yakara kwadamin wani Kiran nanma
banza nayi dashi harya gaji yakaraso wurina wurgamai harara nayi tare da fadin
"Baka da hankali ko kakeyimin irin wannan Kiran Kumar baka San wurin danake zauneba
nagode" ina fadar haka najuya naci gaba da aikina,

Komawa yayi gida zuwa can saigashi yakara zuwa ya tsogunna yace
"Anty innarmu tace kije kibani suyar tana kiranki" cikin tsoro da fargaba nace
"Mahbub mekace mata nayi maka?"nafadane kawai bawai Ina tunanin hakanba nasan abinda
zata tambayeni,
Cikin sauri ya zaro Ido yace "wallahi anty Babu abinda nace mata kawai tace kijene" bankara
maganaba saidai na Mike nayi cikin gida cike nake da fargabar abinda zatacemin,

Tsaye natadda innarmu tana jirana kallonta nayi naga fuskarta ahade don haka nakoma baya
baya da ita inadan yake baki irin murmushin Nan da akewa lakani da kafi kuka ciwo nace
"Innarmu gani" wani kallo ta watsamin sannan tace
"Waye wannan mutumin?"
Dafe kirjina nayi nace
"Wanne innarmu banganeshiba" harara tskara yimin tace
"Mai siyan awara nake nufi wayeshi nafisa banason munafurci kifadamin gaskiya wayeshi
Kuma meye tsakaninki dashi" ai cikinane yayi wata irin murdawa datasakani dafeshi sannan
nafara fadin
"Wallah Allah innarmu bansanshiba kawaidai Yana zuwa siyan awara Amma baya ga wannan
Babu wata alaka tsakanina dashi sai sai........" Shiru nayi Inna raba idanu dakamin tsawa tayi
tace
"Saime kibude baki kiyimin bayani banason munafurci fah kinsani"

Jikina Banda rawa Babu abinda yakeyi don innarmu tahanani karbar wani abu ahannun wani
don haka atsorace nake wata uwar tsawa data dakamin tasakani dawowa daga duniyar tunanin
dana lula don haka nadawo hankalina nafa fada mata abinda ya faru dazu danaje wajen
registration din jamb har zuwa tahowa danayi da kudin da zummar idon nazo gida yazo karbar
awara zan bashi abinsa nafada mata Kuma yadda mukayi dashi Dana kaimasa shiru nayi ina
jiran amsar da zata bani,

"Uhmm wato saboda baki maidani bakin komaiba shine baki fadaminba kika Kama bakinki
kikayi shiru karkiga kamar Ina takurakine akan Hulda da maza wannan dakikaga inayi miki
shine tarbiyya Kuma shine dacewa shine Kuma daidai agareki 'ya mace don haka wallahi kikula
duk talaucin damuke ciki banyarda da wannan shashancin ba ki kiyaye Kuma gobe idon yazo
kifada Masa inason magana dashi don bazamu karbi kudinba saiyazo zanbashi kudinsa
mungode da taimakonsa garemu ko wannan awarar dayake siya tawadatar basai yayi
dawainiya damuba kije Allah yayi miki Albarka" cikinsu kuka nadurkushe kan gwaiwowuna
nafara Bata hakuri Nan tadagani tace Babu komi inje Allah ya tsare,


Saida na wanke fuskata sannan nadawo naci gaba da Sana,ata,


***********

*Wacece nafisat*


Sunana Nafisa Adam jiggo maifina su biyune agurin iyayyensu suntaso cikin kulawa saidai
mahaifinsu Wanda akewa lakani da jiggo talakane ahaka suka taso suna zuwa makaranta Boko
da Allo har sukayi sauka yayan babana mai Isa isya shine yafara zuwa wajen want mai hali
alayin nasu yake binsa kasuwa ahaka harya Fara samu awurinsa sosai shikuma babana Yana
sanar Saida rake da gurji akofar gida suna haka wani bawan Allah yazo wurin Ahj jiggo yace
yanaso yabashi yaronsa Wanda ke Saida rake yadunga bisa kasuwa don bashida yaro Kuma
ya yaba da hankalinsa ikon Allah Babu want musu ya amince da batun Nan yafara zuwa
kasuwa shekararsa biyu da rabi wannan bawan Allah yakara bunkasa akayi lissafi yaga riba
sosai don haka yabawa abbana kudi mai yaw yace yayi jarin kanshi,

Alhamdllh wannan kudi daya bashi shine yadunga bankarashi harya zama wani ahaka ya
hadu da innarmu itakowa itadayace agidansu mahaifi ta ya rasu sai mahaifiyarta wadda ke ruke
da ita haka akafara shirye shiryen biki ba Bata lokaci akayi bikin tare Dana Dan,uwansa
yayansa aka hada abbana ya Gina gidanshi shikuwa yayanshi baigina gidaba Amma alonacin
yasiyi fili yace bayan biki zaifara gini ahaka suka fara rayuwarsu matar baba isya itace tafara
haihuwa tahaifi danta namiji lokacin innarmu batada ciki ahaka akasha shagalin suna,

Saida tayi kusan shekara uku sannan innarmu tasami ciki ta haifi yarta mace Amma tazo Babu
Rai alokacinne itama matar baba isya takara haihuwa tahaifi namiji,

Bayan shekara takara haihuwa akasami Yaya yaci sunan babanta Khalil shine muke kiranshi
da yaya,
Yaya yabani suekara shidda lokacin da innarmu takeda cikin mahbub lokacinne kuma Allah
yayiwa abbanmu rasuwa munji mutuwarshi sosai don lokacinma bani da wayo sosai don haka
mahbub baisan abbanmu ba sai a hoto,

Nikuwa tsakanina da mahbub shekara gomane don yanzu inada shekara 19 shikuwa shekara 9
bamu Jima da fara awaraba da innarmu tana saida kayan miyane taga abin sai ahankali shine
bayan nayi candy nabata wannan shawarar ta awara akofar gida da taki amincewa saikuma
daga baya ta amincewa dakyar don ko Yaya baisan munayiba yatafi neman kudi Legos.
***************

*Cigaban labari*




*By*


*Khadeejah (Ummu Fu,ad & Afnan)*





[8/29, 7:24 AM] Hayat: *RAYUWATA CE*

*Na*

*Khadeejah Sani (Journalist)*

*Kainuwa writers Association*
*Dashin Allah*

(United we stand and succeed; our ambition to entertain and motivated the mind of readers)


*Sadaukarwa gareki masoyiyata abar alfaharina kisani dukkan addu,o,inki Ina jinsu kuma Ina

godiya Allah yasaka da mafificin Alkairi yabar kauna wannan page din nakina nabaki kyauta kiyi
yadda kikeso da abinki Sai Wanda kikayi niyyar bawa nasan kinsan kanki antynah FAREEDAH
AUWAL Ina yinki*❤❤

*9 _ 10*



Shiga nayi nasami nafisat zaune tana duba wani littafi don ita harta fara zuwa makaranta kuma
tare mukagama secondary sallama nayi ta tashi da sauri tare da rungumeni Tana fadin
"Wallahi yau din Nan magama tunaninki nace kokinyi registration din jamb kokuwa bakiyiba?"
Murmushi nayi nace
"Wallahi nayi dazu da safe naje fce nayi harmace kilama kina makaranta yanzu"

"Aikuwa kamar kinsani inacan din"
"Ayyah bansaniba danaje mungaisa dake kuma aima bansan ajinba ai"
"Eh saidai hakan kuma aikece haryanzu bakida waya da kinada ita dasaiki kirana don Allah
kiyi waya ko tanan arunga zumunci haba saikace ba buduruwaba" murmushi kawai nayi nace
"Allah y hore zanyi insha Allah"
"Ameen ammadai banajin dadin rashin wayar Nan naki Allah"

Wucewa nayi cikin dakin Ina fadin "komai lokacine takwarata kibari Allah zai bada yadda
yadda yadda,ayi Amma ana takai wayake ta kaya"

"Indai hakane to nikuma bari nabaki dayar wayata dake ajiye bana amfani da ita ammafa
karamace"
Hijjab din dake jikina nacire tare da fadin
"Kedai baki rabuwa da surutu lokacin sallah yayi kuma baba Yana dawowa Daga masallaci zai
nemeni karyaji ban idar da sallah bah yayimin fada" Ina gama fada nashige toilet din dake
dakina,

Bayan mun idar da sallah Ina zaune ta tashi ta bude wata jaka tadakko wayar tadawo kusa
Dani tare da zama tace "yawwa gashi saiki siya layi naira darine ko Dari da hamsin don Allah
karkice bazaki karbaba nasan halinki yanzu zakice Inna indai kikace mata nice nabaki nasan
bazatace komaiba kitaimaka ki karba please my lovely sister karkiyimin haka" takarasa
maganar cikin rausayar dakai gefe,
Kallo kawai nabita dashi bankai ga maganaba naji mama na kirana tashi nayi batare Dana
karbaba nayi falon don dakinta Dana Mama Dana afalo Daya suke,
Ina shiga bakina dauke da sallama na tadda baba yadawo Yana zaune saikuma Yaya dake
gefansa dakuma Mama itama Tana zaune karasawa nayi na zauna akasa tare da kara gaidasu
Saida na gaida baba sannan mama sannan Yaya dake wurin dakyar ya it's amsawa nidai nace
kaika Sani yaddama yakemin yauyafi na kullum don haka banwani damuba tunda yasaba, Babane yafara magana hakan yadawo Dani Daga tunani nabada hankalina Nita fara yiwa

tambaa wadda tabani mamaki yace
" Nafisa kinada Wanda kike some yanzu haka Wanda kikayi alkawarin aure dashi?" Dagow
nayi cike da Al ajabin tambayar da naji yayimin dorawa yayi da fadin
"Karkiji nayi Miki wannan tambayar inasone nacika alkawarin Dana daukarwa Dan,uwana
yabani amanarku baki Daya yafadamin narikeku kamar yarana don haka nakeso na aurar daku
dake da nafisa da yayyannaku baki Daya nafisa tun kwanaki nagane sun daidaita da yayanki
shikuma wannan" ya nuna Yaya dake zaune yace "Naga haryanzu bai fidda wataba shine
nakiraki kema don naji ya abin yake" sunkuyar dakaina nayi zuwa can nace
"Baba Babu kowa damukayi alkawarin dashi"
"To Masha Allah inason don Allah dukkanku kuyimin afuwa dajin abinda zan fada kugafarceni
inason had a zumunci tsakaninki da yayanki kuyi hakuri kudaure karku bani kunya" Banda
faduwa Babu abinda gabana yakeyi Jin abinda baba yafada mamaki tsoro fargaba dakuma
tunanin mehakan yake nufi nidai nasan yadda baba yake bawani damuwa yayi damuba haka
kuma tunda abbanmu ya rasu zan,iya cew baifi sau biyu ko uku yazo gidanmuba baya want
nuna Mana kulawa Amma yau kawai yazomin da zancen hadani aure da yaronsa bayan bama
jituwa tsakaninmu,
Cikin tunanin naji yace "nasan zakuyi mamakin Jin abinda nafada ba abun mamaki bane
tunkafin Dan,uwana ya rasu munyiwa kanmu alkawarin hada yaranmu aure to Sai Allah yayi
Shibamai tsayin kwana bane, ajiya nakwanta bacci bayan sallahr asubah nayi mafarkin
Dan,uwana yakara jaddadamin zancen had a zuri,armu aure hakanne yasakani taraku don
nafada muku abinda yake raina kuma burinmu na farko da mukeso muga muncika" shiru wajen
ya dauka nawasu lokuta zuwacan Yaya yafara magana
Cikin yanayin da bazaka ita gane abinda yake cikiba yace
"Allah yasaka hakane yafi Alkairi yabamu ikon cika muku burinku" Ameen suka amsa dashi
nidai shiru nayi nama rasa baking magana babane yayimin magana yace
"Nafisa bakice komaiba" cikin dauriya da hadiye kuka nace
"Allah yabamu ikon rike Alkawarin da muka dauka" Ameen suka Kara amsawa dashi nan baba
yace
"Insha Allah gone zanzo wurin innartaku zamuyi magana da ita" to nace tare da mikewa nace
"baba zantafi dare yanayi" mamace wadda tunda aka fara magana batace komaiba tace
"Kibari ayi sallahr Isha,I Sai yayanku yakaiki amotarshi Kinga dare yayi ga garin Nan Sai
ahankali" to nace tare da komawa dakin nafisa Ina shiga ta rungumeni tace
"Wayyo Dadi naji dadin amincewarku keda Yaya Masha Allah" kallonta nayi nace
"Wai dama kuna tare da Yaya shine baki taba fadaminba kuma bantaba ganewaba wallahi"
dariya tayi tace
"Wallahi cewa yayi karna bari kisani Amma ai innarmu tasani hakama mama da baba"
"Hmm lallaine wato ni akabari abaya kenan" dariya takarayi tace
"Kinga kusa yadda kikayi wani mugun dacewa keda Yaya Allah yabar kauna wayasanima ko
kuma anata soyewa bamu saniba" murmushi kawai nayi bance komaiba,

Kiran sallah akayi hakan yasa natashi nayi sallah tunda inada alwallah nazauna Ina tunani
Amma Inka ganni zakayi tunanin addu,a nakeyi,

Nafisa Bata dakin Mama tayi kiranta saigata tashigo da faranti dauke da abinci shinkafane da
taliya damiya da nama ta ajiye tare da zaunawa tace
"Mama tace kiyi sauri muci kafin yadawo kutafi" kallonta nayi Ina niyyar yin magana tace
"Wallahi idon bakiciba saina fada mata nasan yanzu Zaki wanice kinkoshi" kallonta nakeyi abin
mamaki kamar tasan abinda zanfada Sai kawai nafasa maganar,

Mungama cin abincin sannan mama takirani tace infito muwuce yashigo nace to
Dakko wayar tayi ta biyoni da ita tanata magiya har mukakai falo inda Mama ke zaune shikuw
gogan naku Yana waje Yana jirana,
Ganin naki karba yasakata fadawa mama Nan mama tasaka baki har Saida nakarba nayi
godiya tare da yimata sallama nafisace ta rakani harwaje,
Zaune yake cikin motar mukayi sallama sannan naje nakama niyar bude baya don banason
zama kusa dashi yayita yimin kallonta banza jinai arufe nakara budewa naji arufe jin
maganarshi nayi yace
"Me kika maidani dazaki shiga baya lallai raini yashiga tsakanina dake" Jin hakan yasakani
komawa nabude gaba nazauna hararata yakeyi sannan yatada motar muka tafi,

Tafiya muke Babu Wanda yayi magana Sai zuwacan yace
"Inamai baki shawara kiyiwa kanki adalci ki ceci kanki kije kisami baba kicemasa bakisona
kinada Wanda kikeso don wallahi aurena dake Babu abinda zaija Miki Sai wahala da rashin
kwanciyar hankali kinsani tunda nake dake kallon kirki baitaba shiga tsakanina dakeba kuma
bantaba Jin zan ita rayuwar aure dakeba ke Koda zama irin wanna acikin mota bana fata
mukarayi dake balle zaman aure don haka kije kifada Masa bakya Sona inkunne yaji jiki yatsira"
Saida nadauki lokaci sannan nadauke kaina gefe nafara magana nace
"Inaso kasani nima bana sonka kuma haka bana kaunar zama dakai matsayin mini da mata
haka kuma Ina fatan Allah karya nunamin ranar dazan aureka harna zauna dakai gida Daya
wallahi idon yanzu za,azo atambayeni ace nazaba Dana aureka Dana mutu cewa zanyi gwara
na mutu dana aureka, kuma naji kayi maganar naje nafadawa baba inaso kasani ni inada
hankali haka kuma inada tarbiyya bazan ita zuwa nafada Masa hakaba don haka Kaine yafi
cancanta kaje kafada Masa baniba" Ina kaiwa Nana nabude nafita nabar motar don dama
munzo kofara gida,

Zaune yayi Yama rasa abinyi wannan yarinyar shizata kalla tafadawa wannan maganar tan lallai
batada kunya Amma zaiyi maganinta,


****************


Bangaransu Musa kuwa haka suka Kari zamansu basuga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login