Showing 1 words to 3000 words out of 47874 words

Chapter 1 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf

16 Mar 2025

2614

[4:21PM, 11/19/2016] Fadeela lamido: MIJIN MARAINIYA


story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed


Bismillahir rahmanir rahim

1-3

Zaune take a dan ma tsakaicin gidan su tana ta faman share hawaye wata dattijuwan mata ce
ta fito daga daki tana fadin , kin fara ko, dama ke idan tsohon munafunci ki ya tashi ba mutunci
gareki ba, wlh uwarki ta bar miki mugun gado, ki zauna kiyi ta kuka salon iya ta ce ana miki
wani abu, matsuwa tayi ta rike mata kunne tace ai baki ga komai ba safna sai rada na koreki
gidan nan , zakiyi kuka, yadda uwar ki tasani kuka ta tura min bakin ciki kema sai na tura miki
bakin cikin da zai kashe ki .

Safna taji zafin wannan ruko, fitsari ne yake bin kafafun ta, tace goggo dan allah kiyi hakuri
, indai kuka ne na daina.
Kar ma ki daina dan jakar ubanki, tashi maza ki wanke kafafunki ki dauki rake , kuma karki
dawo gidan nan sai ya kare.

Jiki na rawa safna ta mike ta dauki bukiti taja ruwa a rijiya ta shiga bayi, cikin sauri safna ke
wanka dan gudun fadan goggo.

goggo na tsaye safna ta fito da bukitin wanka a hannun ta goggo ta bita da harara , da sauri
tashiga dakin ma haifiyar ta, wanda a yanzun ita kadai take kwana acikin sa, cikin sauri ta jawo
ledan kayan ta, ta fara cirowa tana dubawa duk tsun mukara ne , masu dan kyan goggo ta
kwashe tayi kyauta dasu, haka dai ta dauki daya daga ciki ta saka, tadauki raken goggo ta
kama hanya.

tafe take tana hada hanya domi ita bata iya tallah ba sai dai idan mutun ne yakira ta ,haka
tai ta tafiya ko nera ba tayi ba, ta gaji ta koma gida.

goggo na zaune a tabarma ita da yaran ta guda biyu iro da salma, safna ta shigo , goggo
ta mike yanzun nan dawo min da raken nan kikayi , iro tashi kaba yarinyar nan kashi rashin
duka ke damun ta.

Kamar jira yake yamike da sauri ya fara kai mata duka daga kar she ma dukkan su suka

taron mata wannan na duka wannan nayi , sai da suka ga bata iya motsi suka bar ta

WAIWAYE
malam musa mutumin kirki ne matan sa biyu goggo itace uwar gida, sai mahaifiyar safna wanda
suke kira Inna, tunda malam musa ya auri goggo ta haifi iro bata kara haihuwa ba dan haka iya
mahaifiyar malam musa ta matsamai ya kara aure, duk inda malam musa yaje neman aure ba a
bashi saboda masifar matar shi, wata rana malam musa na cikin tafiya akan tsuhuwar mashin
dinsa yaci karo da wata bafulatana batafi shekara sha biyar ba tana tafiya tana kuka, tsayawa
yayi ya tam baye ta lfy take kuka, sai da ta share hawaye sannan tace wata yaya tace tayi aure
a binni tunda mijin ya tafi da ita har yau bamu sake ganin ta ba, shine muka fito neman ta su
baffah suka ce na jira su karkashin wata bishiya tunjiya har yanzun basu dawo ba, malam yace
ina ne garinku , kame kame takama malam dai yagane bata san sunan garin su ba, goya ta yayi
abayan mashin din sa dan su kara duba wajan ko iyayan ta sun dawo, suna zuwa suka duba
babu kowa awajan , dan haka malam musa yace ma wani abukin sa dake zaune a waja
bayanin cewa ko da iyayan ta sun dawo ya kawo su gidan shi.

malam musa gidan iya ya wuce da yar fillo saudatu dan yasan halin matar sa, iya ta kar
beta hannu biyu tare da mamakin wauta irin na filani, sai da saudatu tayi shekara biyu awajan
iya ba labarin iyayan ta ,dan haka iya ta matsawa malam musa ya auri saudatu, malam musa
yabi umarnin ma haifiyar shi dan shima yafara tunanin haka. bayan an daura musu aure da wata uku goggo ta sake haihuwan salma itako amarya
saudatu sai da ta shekara biyu sannan ta haifi safna , saudatu tasha wahala a gun goggo dan
ma tana samun kariya agun malam safna nada shekara sha hudu tafiya ta kama malam zuwa
kauyen su iya dan kai masu ziyara, iya tace atafi da saudatu tunda bata taba zuwa ba.
lokacin safna nazuwa makarantar primary tana aji shidda dan haka suka barta gun goggo,
bayan wani dan lokaci da tafiyan su labari ya same su, motar da suka shiga ta kone kurmus
babu wanda yayi rai, haka su kai ta kuka a yanzun haka shekaran su daya da rasuwa inda
goggo tahana safna makaranta sai tallan rake.
Abduljalal
wani matshin yaro ne me ji da kanshi daka ganshi kaga dan gata bazai wuce shekara ashirin da
bakwai ba, dogo ne sosai yanayin tsawan shi sai ka zaci ya wuce shekarun shi haka fari ne tas,
bashi da yawan fara,a.

Idan kaga jalal na dariya to da ummin sa ne , ko kuma cikin abokan sa, zuwa yayi ya
samu ummin sa zaune a falo, yaje ya fada jikin ta yana fadin ummi yinwa nake ji.

ummi tace jalal karfa ka karya ni, wai kai baka san ka girma bane.
haba ummi wanni girma nayi ne, kodan kinga kin samu wata.
tace ba haka bane jalal ya kamata ka fahimci cewa ka girma yanxun fan ba da bane, ga
abinci nan kaci , karani gida hajiya sahura.
cokali daya ya kai bakin sa yace ummi na gaji zo ki bani abaki.

gargiza kai ummi tayi ta matso ta fara bashi abaki sai da ya koshi yace ummi bar shi haka
na koshi.
sai da ummi ta shiga ta gama gyara wa sannan ta fito, ta samu jalal na zaune a falo kanan
kaya ne a jikin shi yayi kyau sosai, idan kaga jalal da ummin sa sai ka rantse yayar sa ce, jalal
ne ke jan motan ba, suna tafiya suna hira .
sunyi nisa sosai sun shiga unguwan su hajiya saratu abduljalal ya hango wata yarinya
tana tafe tana kuka ga kuma rake akan ta, yace ummi ji wata yarinya yar karama an daura mata
talla, yanzu dan Allah ummi wa zai sha wannan raken kofa kan kare shi ba,ayi ba.
ummi tace kai kake ganin haka jalal kazamai yan uwan ta zasu sha.
jalal na kawowa kusa da yarinyar ya tsaya ya kira ta da gudu ta karaso, yace me yasa
meki kike kuka?
tace idan na koma gida raken nan be kare ba duka, duka za,ayi min, jalal ya tausaya mata ya
kalli jikin ta yaga shedan bulala, yace ummi zan saya raken nan.

da sauri ummi tace amman dai ba a mota ta zaka zuba wannan kazamin raken ba.
yace sai ta bawa almajirai , ya sunan ki ya tam baye tace safna sai da ya maimaita sunan
sannan yace raken na nawa ne?
tace nera dari, dari biyu ya ciro ya mika mata, tamiko hannu zata karba , ummi ta daka
mata tsawa taja baya da sauri, jalal yace ummi me tayi ?
yaro ban yadda ku hada hannun da yarinyar nan ba ka aje mata akasa sai ta dauka
[1:22PM, 11/23/2016] Fadeela lamido: MIJIN MARAINIYA


story
&
written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed


4-6

Jalal yace haba ummi ai ba taba ta zanyi ba, bata kawai zan yi.
ummi tace ashe tsaftar ka ta banza ce , idai ka bawa yarinyar nan da hannun ka kuwa.
juyawa yayi ya ajewa safna kudin akasa, da saurin ta ta tsuguna ta dauka tana ma jalal
godiya, ummi ko hararar ta kawai take.

bayan sun dawo gida ummi ta lura jalal fushi yake da ita, dan haka ta bishj har dakin sa,
tace jalal me ya same ka, kake ta fushi?
abduljalal be iya boye wa ummi komai dan haka yace ummi yarinyar nan ce take bani
tausayi, ummi da,a kwai yadda zanyi dana tai make ta.
ummi hada rai tayi tace yaro halin ka yana bani mamaki in banda abinka ina ruwan ka da
yayan talakawa da har zaka damu kan ka, akan wata banza yarinya kazama, da kikiya.

ummi bazaki gane ba nasan da dady ne zai fahimce ni, ummi raken nera dari ne fa akanta,
ummi kuma gashi yarinyar kyakyawa da ita.
zoro ido ummi tayi tace yaro kai ne kuwa, kaga yarinya mumuna kace kyakyawa ko dai
gamu kayi ne, to naji kyakyawa ce me kake nufi yan zon.

ummi ni ba abinda nake nufi kawai dai inason ki tai maka mata ne.
kaga jalal karna kuma jin manar yarinyar nan abakin ka, ta mike da sauri tabar wajan.

itako safna zuwa tayi gurin wasu almajirai tana raba musu, iya na daga gefe tana kallon safna,
saida ta gama ta juya zata tafi iya ta kwala mata kira , ai tana ganin iya ta roga da gudu ta
kamkame ta, cikin rudu iya ta daga kan safna tace a ina kika samu rake kike rabawa Jama,a?
Safna ta kwashe labari kaf ta fadawa iya, salati iya ta shiga yi, tana fadin ina can zaune za,a
lalata min jika, wanne dan iskan ne, yabaki kudi?
iya nima ban san shi ba kawai gannin su nayi amota.
be miki komai ba dai ko?
ba abinda yayi min, iya tasa keyar safna tayi tace muje na samu goggon taki, in kaskiya ne ta
daurawa salma mana.


suna shiga iya ta fara fada taita fada tundaga ranar rokon safna yadawo hannun iya, safna
dadi takeji sosai agurin iya babu ta kura, iya duk ta. hada dan kudin da take da shi ta mai da
safna makaran ta, haka iya tai ta wahala da safna ana haka safna ta gama primary schools,
gashi iya nason safna ta ci gaba da karatu kuma bata da kudi Dan haka ta fara toya kosai a
kofar gida, iya bata barin safna tazo gurin tuyan kosan ta sai dai aikace aikacen cikin gida duk
da cewa iya ba wani karfi gareta ba, amman safna ta murje tayi kyau kamar ba ita ba.

a yanzun safna tana J S2 dan haka iya ta fara tunanin aurar da safna dan duk da cewa
safna bata wuce sha bakwai ba, itako safna babban burin ta shine ta tayi karatu me zurfi.

ana cikin haka rashin lafyya ya kama iya dan kosan da take yi ya gagara, safna ta rasa ya
zatayi , tana kuka ta nufi gidan goggo, ta gaya mata iya babu lafiya.
fada ta fara tana fadin aiga irin ta nan, kina nan muna neman kudi tazo ta dau ke ki, sai
yanzun da ciwo yakama zaki taho to bamu da kudi, wacce ki bani waje karna kara ganin ki
gidan nan, haka safna ta juya tana tafe tana kuka.

haka safna ta dawo ta samu iya kwance cikin amai, ta shiga gyara wajan bayan ta gama ta
fara tunani yadda zata samo ma iya abincin da zata ci, tashi tayi ta fita ta gama bulayin ta bata
somo komai ba ba yadda zatayi dole ta koma wurin goggo sai da ta gama zagin ta sannan ta
bata ragowar tuwan jiya da sauri ta nufi gida tana ta sauri , tun kafin ta isa kofar gidan ta hango
muta ne tana shiga gidan kara kamkame tuwan ta tayi ta sheka da gudu tana shiga taga an
lulube ta da zani, safna fadawa tayi jikin ta tana kuka.

Wata makociyar su iya ta taho ta dafa safna tace kiyi hakuri safna ki daina mata kuka

Allah ya karbi abinsa kuma ya fimu santa dan haka sai muraka ta da.ardu,a haka safana taita
kuka har aka kai iya makwanci ta safna bata bar kuka ba.

bayan anyi bakwai da yamma goggo ta hada kayan ta ko salama batawa safna ba ta wuce
gida, gidan iya kuwa safna ce ka dai aciki sai ta tsince kanta cikin matsanan cin tashin hankali,
haka safna ta kwana ita kadai acikin gidan, safna na tashi hankalin ta kara tashi yayi
musamman da ta leka dakin iya taga wayam dan haka ta tsoguna abakin kofar iya ta saki Kara.
makociyar iya baba dije taji kukan safna aguje ta zagawo tace Ina goggonki .
safna tace ta tafi tunjiya
au yanzu nan nufinta baza ta rike kiba, lalai abin nata babba ne, tashi ki hada kayanki na
rakaki .

cikin tashin hankali safna ke hada kayan ta tana ganin ita meye amfanin ta tuda ba iyayen
ta iyar ma da take takama da ita ta tafi ta bar ta itama da mutuwar kawai tayi.

suna shiga gidan goggo suka same ta tana tankadan garin tuwo, tana ganin safna ta hada rai,
bayan sun gaisa tace yazaki tafi kibar yarinya ita daya acin gida.
cin sauri goggo ta fara rantse rantsan ita sam bazata rike safna, baba dije ta fahimci da gaske
ta keyi tace to naji to me zai hana ki kaita gun dangin iya.
cinkin sauri goggo tace ina naga kudin motan da zan kai ta.
kwance haban zanin ta tayi takwaso gudin wajan duk ta mikawa goggo ta sannu ta karba harda
fadin yauyau zan kai ta.

goggo bata tashi kai safna ba sai gaf da mangariba tace dauko kayanki mutafi , safna ta
dauki kullin kayanta suka kama hanya, motar cikin gari suka hau , safna tace azuciyar ta dama
motar garin su iya acikin gari ake hawa ,take farin ciki ya rufeta ko banza yau zataga gidaje
masu dan banan kyau . suna isa aka sauke su garin kamar rana saboda fitilun da suke haka ko,ina gidaje kuwa fadan
kyansu bata lokaci.

suna ta tafiya taki karewa ita dai safna bin goggo kawai take suna zuwa gurin wata katuwar
bishiya, goggo tace safna zoki zauna anan naje na dawo , haka banzayen kakannin ki sukama
uwarki har ta mutu bata kara saka su a idon taba.
[2:05PM, 11/24/2016] Fadeela lamido: MIJIN MARAINIYA


Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed

7-9

Itako safna bata fahimci me goggo ke nufe ba dan bata da wannan labarin , haka tai ta zaman
jiran goggo har ta gaji tun tana ganin wucewan mutane daidai har ta daina gani dan haka tsoro
ya shige ta, mikiwa tayi tabi hanyar da goggo tabi , tana tafiya tana dubawa ko Allah zai sa su
hadu da goggo.
wata mota ce ta shigo layin tun daga nesa motar ke hasko ta, dan haka ta tsora ta , motar
na zuwa kusa da ita ta tsaya, wani dake cikin motar yace yace ke ina zaki da daddaren nan,
kisan ko karfe nawa kuwa?
cikin kuka me ban tau sayi ta girgiza kai wanda ke mazauni direba yace kabir ina ruwan ka da
ita ne kasani ko aljana ce yanzun 12:15 pm fah ,yace yarinyar ar zikice za aganta a waje
awannan lokaci, kabir yace kuma fah haka ne aboki na, motar su kaja suka mike layin.

Safna ko babu abin da take ban da kuka, gaba tayi kadan ta samu wani dan dutse ta
zauna sautin kukan ta kawai kake ji awajan wasu samari ne suka zo wucewa su uku irin yan
shaye shayen nanne sun sha sun bugu daya daga cikin su yace kai kunga wata baby danya, da
sauri suka isa wajen ta suka fara ja mata dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login