Showing 1 words to 3000 words out of 50006 words
Chapter 1 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
06/05/2022 à 15:31 - Les messages et les appels sont chiffrés de bout en bout. Aucun tiers, pas
même WhatsApp, ne peut les lire ou les écouter. Appuyez pour en savoir plus.
06/05/2022 à 15:23 - Sœur Amih:
06/05/2022 à 15:33 - Mom Lateef:
06/05/2022 à 15:36 - Sœur Amih:
06/05/2022 à 15:39 - Mom Lateef:
06/05/2022 à 15:52 - Sœur Amih:
06/05/2022 à 21:22 - Mom Lateef:
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_1_
Cike da murna ya shiga ba wa yaran hannu suna tafawa yana fad'in "Yaran kirki kenan, amma
fa kunyi k'ok'ari."
Cike da zumud'i *Hameeda* da ba za ta wuce shekara bakwai ba tace "Abba, to za ka siya
mana kyautar da ka yi alk'awarin siya mana idan mu ka yi k'ok'ari?"
Da fara'a a fuska dattijon yace "Dole na ma, ai ina fita daga nan zan kawo muku kyautarku."
*Hadeeya* dake zaune kusa da shi ne tace "Amma dai Abba ai na fi su k'ok'ari ko? Dan haka
kyautata za ta fi ta su kyau."
Hararanta Hameeda tayi tace "Ka ji yarinya, ke da ma ko jarabawar ba'a muku ba, ku fa yara
ne."
Kyakyawar matashiyar matar dake zaune gefe da su tana kallonsu da murmushi a fuskarta ce
ta bud'a baki cike da gayu a harshen faransanci tace "Calmez-vous les enfants, votre Papa
offrira a chacun le bon cadeau (ku kwantar da hankalinku yara, Mahaifinku zai ba ko wa kyautar
da ta dace)."
Wani kallo ya jefa mata cike da so da k'auna yace "E toi, me za ki basu?"
Wani mahaukacin fari ta masa da ido kafin tace "Ce une secret entre eux et moi (sirri ne
tsakanina da su)."
'Yar k'aramar cikinsu wato *Hamdeeya* ce ta k'arasa kusa da mahaifiyarta cike da shagwab'a
da kuma yarinta tace "Momma, ni ma za ki siya min kyauta?"
D'agata tayi ta d'ora a cinyarta tace "Sosai ma yariyata, ai ke ce ma gaba kafin kowa."
Duk farin ciki da murnar nan da ake *Haleematu* na tsaye gefe tana kallo, ganin dai ita ba'a
ambaceta ba yasa ta matsowa kad'an kusan mahaifin tace "Abba nima za ka siya min?"
Wani mugun kallo ya watso mata daga sama zuwa k'asa kafin ya d'auke kai yace "Da wannan
sakaran sakamakon da kika kawo ne zan kashe miki kud'ina?"
Sunkuyar da kai tayi a marairaice tace "Dan Allah Abba, ko k'arami ne ka siya min."
A tsawace ya kalleta yace "Matsa ki bani wuri, ba zan siya d'in ba *Saleema*."
Dake sunan mahaifiyarshi gareta sai suke kiranta da sunan Saleema, d'ago kanta tayi ta zuba
masa idonta da suka cika taf da hawaye tace "Abba, to idan na yi k'ok'ari a zango na k'arshe za
ka siya min?"
Saida ya sake hararanta sannan ya yatsina baki yace "Watak'ila."
Murmusawa tayi tace "Tozan yi Abba."
A sukwane ta nufi inda mahaifiyarta ke zaune wacce ka rantse bata falon, sai dai tana zaune
tana kallon komai dake faruwa, duk da ranta na suya amma ba ta da yanda za ta yi da ya wuce
hak'uri, Saleema na k'arasawa ta zauna kusan Mamanta tana mik'a mata takardar (bulletin)
sakamakon, karb'a tayi a raunane tana duba sakamakon, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke
ganin sam ba wani k'ok'ari da Saleema ta yi, dan ko a yawan yan ajinsu mutum uku kad'ai ta
bari a bayanta.
Uwarsu Hadeeya kam dake cike take da farin cikin dake d'awainiya da ita mik'ewa tayi ta nufo
inda *Alhaji Yusuf Jiji* ke zaune, *Safeeya* na ganin haka ta yi saurin d'auke kanta dan ta san
me amaryar za ta yi. Ai kam *Ardayi* na zuwa d'an rank'wafawa tayi ta d'ora hannunta a
kafad'arshi sannan ta sumbaci labb'ansa, daga ita har shi ba wanda ya ji kunyar yaran, dan
hakan ba sabon abu bane a wajensu.
Saida suka aikawa junansu wani kallo da su kad'ai suka san ma'anarshi kafin ta tattara
hannayen yaran ta rik'e a hannunta, d'an juyawa tayi ta harari inda Safeeya da 'yarta suke tare
da fad'in "Alajina zan shiga ciki, kasan yau ina cikin farin ciki saboda nasarar da yarana suka
samu, ka san fa abun da ka jini ne, gado sukayi."
Da wani murmushi a fuskarshi ya bi bayanta da kallo cike da so da k'aunarta, kamar yanda
soyayya ta sa ya aureta haka yake da matuk'ar son farar mace, dalilin da ya sa ma kenan ya
kutsa ya shiga lungu da sak'o ya zab'o buzuwa da ta amsa sunanta, gashi kuma kwalliya ta biya
kud'in sabulu tunda har ta zama fitilar gidansa mai haska masa duk wani duhu.
Saida suka ga shigewarta kafin ya d'an gyara zamanshi yana matse fuska ya d'an kalli inda
Safeeya take ya ga ko tana kallonshi ne, idansu na had'uwa ya szke had'e fuska kamar zai
fashe, shi a dole kar ta kawo masa wargi duk da kuwa ya fi kowa saninta akan hak'uri da kau da
kai. Murmushi kawai tayi ta d'anyi gyaran murya tace "Abban Hajia, ina ganin me zai hana ka je
makarantarsu yaran nan ka ji me ye matsalar Saleema, ta yiwu akwai wani abun da bata
ganewa?"
Cike da basarwa ya d'an kawar da kai yace "A idonki dai ba k'ok'arin da bana yi akan karatunsu,
har malami na musamman na d'aukar musu da ke zuwa gida yana sake musu bitar abinda aka
koya musu, a k'alla kowane dare yana d'aukar awa biyu a gidan nan, to idan ba ta fahimta
yanzu ba sai yaushe?"
Jinjina kai tayi alamar gamsuwa tare da sassauta muryarta sosai tace" A kawo maka abinci
ne?"
" Sai na yi wanka." Ya fad'a ba yabo ba fallasa.
*Bayan wani lokaci*
Rashin damar zuwa da yau malamin na su bai samu ba yasa Alhaji Yusuf zaman dirshen yana
koya musu karatun saboda jarabawar da zasu fara gobe ta zangon k'arshe, allon (ardoise)
Saleema ya karb'a ya fara mata da lissafi, sosai ya rik'e allin kafin ya rubuta mata 4 a tara da 4
nawa zai bayar?
Cikin ikon Allah sai Saleema ta k'urawa rubutun ido tana kallo sam ta ji ta manta da komai ta
yanda ta kasa fad'a da sauri, da yatsunta take ta k'idayawa yayin da yatsanta d'aya ke cikin
bakinta tana ta motsa bakin. Kafin ta ankara Alhaji Yusuf ya d'auke fuskarta da wani
mahaukacin mari yana fad'in "Dan ubanki wannan d'in ne ba zaki iya fad'a ba? Bari ki gani..."
Jawo k'afarta yayi bai kulada kukan data fashe da shi ba saboda girman da marin ya ma
shekarunta guda goma ya matsata daf da shi, sake nuna mata rubutun yayi yace "Nawa ne nan
dan uwarki?"
A kid'ime cike da son k'watar kanta tace "Biyar."
Wani marin ya gaura mata yace "Wannan d'in ne biyar? Ubanki ke da biyar d'in."
Kallon Hamdeeya yayi dake k'arama a cikinsu kuma yar shekara hud'u yace "Idan na tambayi
Hamdeeya ta fad'a min wallahi ci miki uwa zan yi."
Nunawa Hamdeeya yayi yace "Autata nawa ne nan? 4+4?"
D'an jim tayi sai kuma ta furta "8."
Bai jira komai ba kam ya shiga jibgawa Saleema allonta tare da kikkifa mata mari yana fad'in
"Me yake shiga kanki ne? Ke baki ji kunya ba yanzu? Wannan fa k'anwarki ce ta uku ma, ke ce
babba a cikinsu amma ke ce dak'ik'iya mai k'walwar kifi."
Da sauri Safeeya ta fito daga d'akinta gabanta na fad'uwa, ganin yanda yake dukanta ta ji ba
dad'i sosai, a sanyaye tace" Haba Alhaji, a haka ta ya za ta fahimci abinda ka ke koya mata?
Dukan ya yi yaw..."
A tsawace ya nunota da yatsa yace" Ke rufe min bakinki, dama na jima da fahimta ke kike
d'aure mata gindi kina sakata lalaci, duba fa ki gani abinda ta kasa fad'a sai k'aramar k'anwarta
ce ta fad'a, wannan ba abun kunya ba ne ?"
Ardayi da fitowarta kenan daga d'akinta ita ma tana jinme ke faruwa ta fito tana fad'in" Ta fad'i
haka mana saboda bata so a koya mata ilimi, burinta 'yarta ta zama kamar ita, wannan ma ai
abun kunya gareka a ce kana fama da iyalinka akan karatu."
Girgiza kai tayi cike da kissa tace" Karfa ka manta siyasa kake, ta ya za ka nuna iyalinka a haka
bayan ba sa gane komai."
Ta k'arashe tana hararen Safeeya, kallonta Safeeya tayi tace" Saboda ba 'yarki ba ce ake duka
ko? Ta hakane za' a koya mata ana mata dukan mutuwar? Ko kuma a ganin ta hakane za ta
fahimta?"
A hassale Yusuf yace" Koma dai menene ai gaskiya ta fad'a, saboda hakane fa yasa ko nunaki
bana so na yi a matsayin iyalina, ba yanda zanyi ne tunda iyayena ne suka had'ani da ke,
amma 'yata dole na d'orata akan irin tsarina."
Tsamm! Safeeya tayi tana kallonshi da mamakin kalamanshi, bai tab' a kwatanta fad'a mata
haka ba sai yau, me ya yi zafi daga magana har yake cizgata haka? Hawayen da suka malalo
mata ne yasa ta saurin juyawa da sauri ta koma d'akinta, da harara ya bita tare da d'auke
kanshi ya mayar kan Saleema wacce ke kuka kamar ranta zai fita, sake gyara zama ya yi
alamar dai za sucigaba daga inda suka tsaya.
*Bayan sati d'aya*
A shirye dukansu suka fito cikin kyakyawar shiga, sai dai duka yaran na Ardayi riga da wndo ne
na siket a jikinsu yayin da kawunansu ke bud'e sai dogon gashinsu da aka mishi fasalin kitso
mai kyau. Daga cikin mota yake hangen yaran na tunkaroshi, tabbas ya fi son 'ya'yan Ardayi,
sai dai bai san me yasa ya fi son su ba, saboda kyawonsu da farar fatarsu ne? Ko kuma dai
saboda ilinmunsu ne? Maida kallonshi yayi kan Saleema dake bayansu cikin shigarta ta
doguwar rigar shadda da kyakyawan hijab d'inta, ba za ka kirata bak'a ba saboda tana da d'an
haske, sai dai idan ta jera da su Hadeeya bak'a take komawa saboda haskensu, kyawu kuma
ba'a magana dan ba wani kyan fuska gareta ba, shi mamaki ma yake wasu lokutan yanda
Saleema ta zama jininshi, duba da shi dai yayi tashen kyawu a zamanin k'uruciyarsa, kuma har
yanzu da yake da shekara arba'in da yan kai, sannan mahaifiyarta ma kyakyawa ce dan ta wata
fuskar ta fi Ardayi kyau, duhu ne kawai gareta na fata wanda kuma yake k'ara fito da kyawunta.
Amma Saleema ba kyan fuska ba hasken na fata, wanda daga shi har uwarta da ta yo d'aya
daga cikinsu to fa da ita ma kyakyawa ce, ga kuma wani munin na daban wato rashin ilimi.
Drebanshi ne ya bud'e musu inda mahaifin na su ke zaune duk suka shiga, da fara'a ya amsa
musu da "Kun gama shiryawa?"
"E Abba." Suka fad'a kusan a tare, a hankali dreba ya fara jan motar suka fita a harabar gidan,
cikin sanyayyar murya Saleema ta kalli mhaifin na ta tace "...
_Yan uwa barkanmu da sallah, da fatan Allah ya karb'i inadunmu yasa muna cikin 'yantattun
bayi, Allah ya gafarta mana zunubanmu._
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_2_
Cikin sanyayyar murya Saleema ta kalli mahaifin na ta tace "Abba ka min alk'awarin siya min
kyauta nima idan na yi k'ok'ari?"
Ba tare da sakin fuska ba yace "Idan kin yi k'ok'arin zan siya."
Washe baki tayi da farin ciki tace "Na yi ma Abba."
Wata harara Hadeeya ta jefa mata ta ja tsaki, a tausashe Saleema ta kalleta tayi k'asa da kanta,
ba wanda ya sake magana a motar har suka isa makarantar, tsabar farin ciki da sakawa ransa
'ya'yansa za su ciri tuta ko tun yaran basu gama shagali ba ya dawo d'aukarsu, hakan yasa
saida ya d'an jirasu na wasu mintoci.
Hadeeya da Hameeda na gaba sun taho da gudu da fara' a a fuskarsu, bud'e motar sukayi suka
shiga suna rige-rigen mik'a mishi sakamakon kowace na fad'in "Abba ka ga ni nayi ta farko."
Karb'a yayi tare da kyautukan da aka basu a makarantar yana dubawa, yanda bakinshi ya kasa
rufuwa tsabar farin ciki yasa shi kasa furta komai, sai da Hamdeeya ta shigo fuskarta da alamar
damuwa, jawota yayi yace "Ya ne autata ?"
Dariya Hadeeya ta k'yalk'yale da ita tace "Abba wai dan ba'a bata kyauta ba ita ma, na fad'a
mata ta yi hak'uri idan ta kai ajin CI (pramary 1) ita ma za'a bata."
K'ara jawota yayi jikinshi zai yi magana sai kuma ya tuna da babbar 'yarsa wacce ta fara kiransa
da sunan Abba kafin duk wad'annan, da sauri ya d'aga Hamdeeya daga jikinshi ya kalli
Hadeeya yace "Hadee, ina mai sunan Hajia?"
Saida ta yatsina fuska kamar ta ga abun k'yama kafin tace "A aji na barota ba'a kira sunanta
ba."
Maida dubanshi yayi ga k'ofa yana fad'in "Me ya hana ku jir..."
Bai k'arasa fad'a ba suka hangi Saleema na tahowa ta rufe fuskarta da hijabi da alamar kuka
take, wata mummunar fad'uwa gabanshi ya yi da tunanin ko lafiya? Abun da ya fara zuwa masa
shine, kar dai sakarcin Saleema ya kai k'adamin da ta fara bayan gida a jikinta da har yaran nan
ke biyarta suna mata ihu da tafi? D'an sauke madubin dake b'angaren shi yayi tare da bud'e
motar da niyyar fita.
Sai dai wak'en da kunnuwansa suka tsinkayo ana ma babbar 'yarsa yasa shi dakatawa tare da
rintse ido, a rayuwar duniya bai tab'a tsammanin haka za ta faru ga ahalinshi ba, a matsayinshi
na wanda k' ok'arinshi ta sa gwamnati d'aukar nauyin karatunshi har ya keta hazo saboda
iliminshi, yake alfahari da kasancewarsa d'an Alhaji *Saddi Jiji* wanda har turawa suka shaida
iliminsa ya kuma karb'i lambobin girma ta fannin ilimin kimiya, a matsayinsa na wanda ya tashi a
ahalin da babu wanda gwamnati ba ta wa rana ba, hakan yasa ko a gari aka fad'i ahalin Jiji ake
musu inkiya da ahalin *bariki* ba dan komai ba sai dan sanin mutane a kan su cewa su d'in
mutane ne da suka san darajar boko kuma suke bata hakk'inta yanda ya dace, daga shekara
ashirinda ta wuce zuwa yanzu da wuya ka samu wanda ba ya aikin gwamnati, ba wai dan sun
dogara da ita ba, sai dai a ganinsu ta hanyarta ne kad'ai iliminsu da alfaharinsu zai bayyana
jama'a su sani. Amma yau gashi kunnuwanshi na jiyo mishi ana ma babbar 'yarsa da saboda
k'auna ya saka mata sunan mahaifiyarshi wacce ita kanta ta kasance likitar da a lokacin tana
d'aya daga cikin mata biyu da suka fara tiyata a k'asar Niger, yau gashi ana ma takwararta d'an
kira da wacce ta zo ta kusa da k'arshe a ajinsu.
Dakatawa ya yi daga shirin fitar ya d'aga madubin ya rik'e hab'a cike da jimami, dreban da ya ga
yara na bin Saleema ne ya tsawatar musu ya bud'e mata gidan gaba ta shiga ta zauna tana ci
gaba da shashek'ar kuka.
Suna isa gida a fusace ya fita a motar ya nufi d'akin Safiya ba tare da ya bi ta kan kowa ba,
Saleema dake kuka da sauri ta zagaya bayan gidan ta lab'e kusa da tagar d'akin mahaifiyarta
dan tunaninta dukanta zai yi, sai dai daga nan inda take ta juyo muryar mahaifin na ta sanda ya
fad'a d'akin Safiya yana fad'in "Na sha fad'a miki ki dinga kula da karatun yarinyar nan amma ba
kya ji, yanzu dubi abinda ta jawo mana, na je d'aukarsu amma yara na binta suna mata ihun
jaka."
A razane Safiya ta mik'e tana kallonshi a mamakance tace "Jaka kuma?"
A hassale yace "Jaka mana, idan ba jakar ba mecece? Wacce ke zuwa k'arshe a komai,
yarinya ban da majina ba komai a kan ta."
A raunane ta girgiza kanta ta sanyaya murya tace "To yanzu da kake fad'a min ya kake so na
yi? Na bud'a k'wak'walwarta na tusa mata ilimi? Ko kuma na kasheta saboda bata ganewa?"
Dafe k'ugu yayi yace "Au ! Haka ma za ki ce?"
Jinjina kai yayi yace "Ya yi kyau."
Juyawa yayi ya fice a d'akin, wata nauyayyar ajiyar zuciya Safiya ta sauke ta koma ta zauna
tana dafe k'irjinta dake doka mata da mugun k'arfi.
*Washe gari*
Da gudu yaran suka tarbeshi inda ya dinga rumgumesu a jikinshi