Showing 9001 words to 12000 words out of 56747 words
Chapter 4 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na bakwai.Ga
masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni
mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata
(SUMAYYA NA'IGE)
Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike
bani.
*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*SHAFI NA BAKWAI*
Tsananin mamaki ya kama shi ganin yadda Juwairiya ta gan shi amma sai ta yi tsaye ta na
kallon shi, ba tare da nuna wani tashin hankali a fuskar ta ba ko tsoro.
Ya ɗan ƙare mata kallo cikin mugun nufin sa amma sai ya ga duk da ramar da ta yi,ta ƙara mishi
kyau ɗan tafiyar da ya yi.
Juwairiya da tsaya ko zai ce wani abu amma ganin ya yi shiru,ya sa ta nufi hanyar shiga ƙofar
gida za ta shige.Da dauri ya sha gaban ta a ransa ya na mamakin dai na tsoron shi da ta yi,tun
ranar da ya nemi haɗa jiki da ita.
"Da ga gidan uban wa kike?"
Ya tambayeta da fuskar shanu y na zare mata idanunsa da suka kaɗa suka yi ja,saboda tsabar
fitina da ya saka ma kansa.Ta ɗan ja ta tsaya tare da matsawa nesa da shi ganin yadda ya
matso daf da ita.
"Ba na hanaki yawon maula ba,shi ne don kin ga ba na nan kika mai da shi sana'ar ki?"Ya
tambayeta tamkar zai kai mata bugu.
"Ni ba maula naje yi ba,aikatau na samu nake yi domin na ciyar da kammu."Ta faɗa mishi ba
tare da jin tsoro ko shakku a ranta ba.
Wani irin azababben mari ya wanka mata wanda ya sa ta yi taga-taga za ta faɗi,amma ta dake
duk da azabar da ta ji kamar za tai fitsari a tsaye sai ba ta nuna mishi ba,don a shirye take ta
shirya tsaf!Ko kasheta zai yi.
Matuƙar mamaki ya kama shi wai yaushe ya yi sake har ta raina shi haka,amma sai ya ƙara
ɗaure fuska yace."Na ga kwana biyu kin raina ni Juwairiya saboda na nuna miki manufa ta a
kanki,to wallahi har yanzu ina kan baka na saina cika muradina gara ma ki amince ki sami
maslaha a rayuwarki." A wannan lokacin ta ji wasu tagwayen hawaye sun cika mata fuska,zuciyarta ta amince da
lai-lai shi ba mutum bane don ta yi tunanin rasuwar mahaifinta zai saka ya haƙura da ƙudirin sa.
"Ka sani ko mutuwa zan yi ba zan lamunce ka biya buƙatar ka a kaina ba!Ina matuƙar kaico a
rayuwata da ka fito a matsayin ƙanin mahaifina.Ko mutuwa zan yi sai dai na mutu."Tace mishi ta
na ƙoƙarin shigewa gida.
Sororo ya yi lai-lai ya yi sake tunna har taga wallar shi ta na faɗa mishi mugayen kalamai,masu
tsauri a cikin idanunsa ba tare da shakku ko shakkar sa ba.
"Tun da kika ce haka mu zuba ni dake,bari na tuna miki akan ki zan iya komai tun da kika girma
na ɗora kwaɗayina akanki Ki kuka da kanki zan iya komai don na cimma manufata."
Ta buɗe baki za ta yi magana wani irin takaici ya toƙare mata maƙogaro,sai hawaye da suka
fara turereniya a fuskarta da ta tuna ƙanin mahaifinta yake mata wannnan halin,sai ta ruga a
guje ta shige cikin gida ta na kuka.
Mama dake ƙoƙarin hura wuta a murhun gawayi idanunta duk sun yi ja, suna zubar hawaye
saboda wutar taƙi kamawa sai saka leda take yi.Sai ganin ta ta yi ta shigo da kuka ta shige cikin
ɗaki ta buɗe baki da nufin ta yi magana,duk da cewa ta san dalilin kukan saboda ta ji dirin motar
sa sanda ya dawo sai kuma ga shi ya shigo.
"Saboda ba na nan shi yasa kika saka ta ta na yawon maula ta samo muku abinci ko?Na rasa
wani hali kike so ki koya mata shi yasa na tsaneki saboda mugun halinki."
Ta yi shiru ba tace komai ba dama ɗabi'ar ta kenan duk sanda zai yi mata rashin mutunci ba za
ta tanka ba,haka ma yanzu mutuwar Yayan sa bai saka ta canza ba.
Har ya gama bambamin sa ya fice bata ce ƙala ba,amma ta na jin gara su haƙura kawai da
tashin hankalin da zai jawo musu.Bayan ta gama kukan ta ta share kamar kullum don Mama ba
za ta taɓa lallashinta ba.
"Juwairiya ina ganin a haƙura da aikin nan kawai."Tace cikin ƙunar zuciya ta na kallon
ta."Gaskiya Mama sai dai kiyi haƙuri,amma ba zan haƙura tunna shi ba taimaka ma na yake
ba."
"Amma kina ganin tijarar da yake mana ko?Kin san halin shi ba shi da kirki,ni fa bana son tashin
hankali ya dinga jibgar ki a banza."
Juwairiya shiru kawai ta yi a ranta ta saka komai zai faru sai dai ya faru,amma aikin Anty Naja
yanzu ta fara.Hankalin Mama ya tashi da safen ranar da ta gama hutun ta bayan Juwairiya ta yi
sallah ta tafi aikin ta,ba ta kula da kiran da Mama take ƙwala mata ba.
Da yamma da ta dawo Baba Sani ya shigo da bulalarsa ya yi mata duka,har bata iya tashi
amma ba hana washegari ta koma aikin ta ba.Ganin irin dukan da yake mata Mama ta hana ta
aikin,sai dai wannan karan ta bijire ma umurnin ta don ta rantse ko kashe ta zai yi ba za ta bar
aikin ba.
Tsakanin ta da mijin Anty Naja ba ruwanta da shi tun da ta fara aikin so uku ta gan shi,duk
sanda ya shigo ya ga yaran a kusa da ita sai ya fara musu faɗa ya kora su cikin ɗaki ya na
harararta ya na mazurai,a yadda yake mata ta lura ya matuƙar tsorata da halin masu aiki.
Ganin haka ta ƙara kame kanta ta na mamakin yaran duk da suna zuwa islamiya amma ba su
wani iya karatu ba,don ko babban dake da shekaru tara ko alhamdu bai iya cikakka bare ya
damu da sallah ba,sai kallon catoon da suke yi kullum ba ƙauƙautawa,ganin haka ta dage da
koya musu da saka su su yi salla,abin da ya ƙara saka Anty Naja son ta a cikin zuciyar ta.
Ganin ƴan canjin da yaransa suke samu abin ya burge shi har yake amsa gaisuwar ta a
sake,wani lokacin har kyauta yake mata na kuɗi yace ta kaiwa mahaifiyarta don Anty Naja ta
gaya mishi mahaifinta ya mutu.
Kusan kullum Juwairiya ta dawo sai taci na jaki a gurin Baba Sani jikin ta duk shatin duka
ne,amma hakan bai saka ta karaya ba ta ci gaba da aiki don yanzu suna ci ga Mama dake
sana'ar ta rayuwar su ta na tafiya cikin rufin asirin Allah sai dai takurawar da Baba Sani yake
mata,wanda hakan ya na damin Mama ga shi taƙi ta dai na aikin. A haka rayuwa take gara musu yau fari gobe tsumma,yayin da kullum burin Baba Sani ya cika
burinsa amma Allah bai ba shi damar ida mugun nufin sa a kanta ba.Ganin haka sai ya ɓullo
mata da nuna mata kuɗi ya na jan ra'ayin ta akan ta amince mishi ko sau ɗaya ne,amma taƙi
duk ta gan shi sai ta nemi tsari da sharrin sa don ganin sa take kamar wani sheɗani.
Ta ɗauki tsawon shekaru biyu ta na aiki a gidan Anty Naja,a lokacin ta girma ta ƙara wayewa ga
hankali da natsuwa kullum cikin hijabi take bata cirewa sai in mutanen gidan ba sa nan,ko ita
Anty Naja ba za ta ce ga yanayin jikin ta ba,don tun kafin takai haka da Baba Sani ya saka mata
ido ta yi tunanin ko jikinta yake ruɗarsa,bare yaanzu da ta zama ƴan mata ta cika ta batse ga
Anty Naja da take ba ta kaya masu kyau kuma ta ba cin me kyau,har mai na shafawa da na
wanke kai take siyar mata.
Maza da dama sun sha bayyana soyaryarsu gurin ta wasu kuma suje gurin Baba Sani,amma
sai ya taƙarƙare yace Juwairiya ƴar mace ce sannan ba ta da kamun kai har kwana take a
waje.Ya faɗi mugun abu da ba ta mata suna ya gaya musu,wasu suna jin haka za su tafi wasu
in suka nace ya yi musu korar kare don ya rantse,in har ba ta amince mishi ba to ita da aure sai
dai ta ga ana yi ko kuma in ya mutu.
Juwariya yarinya mai kimanin shekaru sha tara.Ta na da haske amma ba can ba,fuskarta mai
kyau irin zagayayen fuska gareta,da dogon hancin ta haƙoran ta masu kyau ga ƴar wushiryar ta
a tsakiya,wanda in ta yi dariya yake ƙara ma kyau matuƙa!Da dimful ɗinta.Bata da jiki amma a
kwai shafe sannan doguwa ce ba can ba,amma ta na da tsawo wanda yake ƙara mata kyau.
Ƙirar jikinta me kyau ne ko ita ta na alfahari da hakan wato irin jikin nan ne mai ɗaukar hankali
waɗanda ko wane namiji yake burin samu mace mai irin sa.Wannan dalilin ya sa kullum take
cikin hijabi do ko ƙawayenta suka shigo suka gan ta ba hijabi,sai su yi ta zuzuta ta su na yaba
kyawun jikinta.
A wata ranar litinin da safe bayan mutanen gidan sun gama karyawa suka wuce gun
aiki,kasancewar da garin a kwai zafi sannan Anty Naja ta tura mata da tsako a cikin wayarta me
botira da ta siyar mata,don ta din ga kiran ta ko kuma in ta tafi aiki da wuri ta gaya mata abin da
za ayi,don yanzu girkin su ya dawo hannunta saboda Baban Abnaj yafi son girkinta. Waina da miyan karas za'a yi da farfesun rago,ganin ta na da aiki ya sa ta zage damtse ta na yi
tun ta na cikin hijabi har ta cire ta na ta aikin ta,ta kunna wayarta ta na sauraron karatun kur'ani
cikin suratul ma'ida.Ta shafa'a ta na ta aikin ta sai ƙanwar Abnaj mai suna Ibtihal ta danna
remote ta ɓata saitin tibin,Abnaj ɗan shagwaba ya saka kuka ya zo ya na sanar da Juwairiya
akan ta zo ta gyara musu.
Hannunsa ta kama suka nufi falon da nufin ta gyara mishi,ta na tsaye a gaban tibi ta na ta
ƙoƙarin yadda za ta gyara amma ta kasa gashi ita ba ta san yadda ake yi ba,sannan gashi har
sun fara kuka akan a gyara musu.
A hankali ya buɗe ƙofar ya shigo da sallama a bakinsa,Juwairiya da hankalin ta ke kan tibi ba ta
san ya shigo ba,ko in ce dukan su sai bayan ya ɗauki tsawon lokaci ya na kallonta cikin mamaki
a ransa ya na mamakin dama a kwai wannan halittar a gidan sa?Don shi zai rantse bai taɓa
mata kallo ko na sakan bane ya san dai ta na da kyau a fuska.
"Oyoyo Daddy!"Abin da yaran suka ce kenan wanda ya ɗauki hankalinta ta miƙe a razane ta yi
diri-diri,tamkar za ta shige cikin ƙasa yayin da wani irin kunya ya lulluɓeta.
Ganin yadda ta diririce sai ya shige ɗakin sa akan ya ɗauko abin da ya saka shi ya dawo
saboda mantuwa da ya yi,wato wasu fayal da ya ije da nufin ya tafi dasu sai gashi ya manta da
su kuma ana buƙatar su.Ashe da rabon ya yi gam da katar!Don shi ya ga matar aure dama tuni
ya yaba da hankalinta.
Ko da ya shiga cikin ɗakin wani irin kasala ya ji y rufe shi ya faɗa kan gadon shi ya na jin wani
irin shauki na ta ya na zagaye ilahirin jikin shi.Ko da ya shiga ɗakin faɗa kan gadon sa ya daɗe
ya na jin wani girmar lamari har na tsawon lokaci,sannan daga bisani ya miƙe ya ɗauki fayal ɗin
ya fito.
Kawai sai ya tsinci kansa da bin hanyar kicin ɗin ya ɗan tsaya nesa da kicin ɗin zuciyar sa na
bugu da ƙarfi,take yake jin lamura suna sauya mishi har ya fara dana sanin dawowar sa gida
gashi komai na son ya canza musamman akan yarinyar da take ba shi girma
"Abnaj fito na gyara muku tibin ku barta ta yi aikin ta,kun dame ta da surutu."Yace da yaransa
da suke kicin ɗin suna ta zuba da Anty Juwairiya kaza,ita kuma ta na ta yi musu dariya ba yan
ta basu kwan da ta soya musu.
Yaran suka bi shi suna murnar zai gyara musu tibi,bayan tafiyar sa ziciyar Juwairiya ya buga
dam!Da ta kalli ƙwayar idanunsa cikin rashin sani ganin yadda ya kafa mata idanu lokaci
guda,abin da ta hango ya matuƙar tsorata ta wanda bai yi kama da so ba sai tsantsar sha'a
warta da ta hango.In ko haka ne abincin ta ya ƙare a gidan.
Bayan fitar sa ta ɗaga labule ta na kallon farfajiyar harabar gidan,sai kawai ta ji hawaye ya na
sauka a kan ƙuncinta bai yi kama da mutumim banza ba saboda ya na da dattako.To me
ƙwayar idanunsa suke nuna mata?Ita kuma irin na ta jarrabawar kenan?
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na takwai.Ga
masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni
mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata
(SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da
irin taimakon da kike bani.
*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*SHAFI NA TAKWAS*
Tun daga wannan ranar Juwairiya ta ga canji a tattare da shi,ya sakin mata sosai kuma ya na
matuƙar kyautata mata,ko hira yake da matar shi sai kiji ya tsoma ta ciki yace"Wai haka aka yi
Juwairiya ita za ta faɗi gaskiya."
Ranar da ya fara mata hakan ta yi matuƙar razana ta kalli Anty Naja ta ga ko me za tace amma
sai taga sai dariya take ta na jin daɗi har ta na ƙara tambayar Juwairiya,wani tsabar takaici kaɗa
kanta kawai ta yi ta shige kicin ɗin wanda dama shi ya ƙwala mata kira don kawai ya tambaye
ta.
Bayan sati ɗaya sai gashi ya dawo gidan da wuri da yake a ranar matar sa na gurin akin ta na
night duty acan za ta kwana.Bayan ya yi sallar magariba ya kulle ko ina na gidan ya shigo,tun
da taga ya dawo da motar sa ya wuce masallacin kofar gidan sa gabanta ya faɗi hankalinta ya
tashi,domin ita canjin da ta gani a gurin sa ya na tsorata.
Bai fito ba ya na karatun kur'ani har kiran sallar isha ya tafi masallaci,sannan bayan ya yi sallah
ya dawo ya zauna a falo shi da yaransa suna kallo shi kuma ya na aiki a laptop ɗin sa.
"Abnaj je ka kira min Antyn ka Juwairiya kace ta zo ta bani abinci."Yace mishi ba tare da ya
kalle shi ba,burin sa ya ganta ya san ta ɓoye kanta a ɗaki don kar ya ganta.
Yaron ya ruga da gudu zuwa can ya dawo yace."Ga ta nan zuwa."Ya ci gaba da kallon sa bata
jima ba ta fito da dogon hijabin ta har ƙasa.Ita sai yanzu dake matuƙar dana sanin gadin mijin
wata da yaran ta da take,don a a kwai haramcin haka a cikin addini mace baliga da namiji ba
muharramai ba dama na ukun su sheɗan ne.
Nesa da shi ta tsaya kamar za ta yi mishi magana sai kuma ta juya ta shige kicin ta ɗauko
abincin shi ta ije mishi za ta juya."Ba kiji ba Juwairiya."Yace da ita ganin za ta shige ɗakin da
take kwana har ta na haɗawa da gudu-dugu.
Tsayawa ta yi bata re da ta juyo ba ta na watsa da yatsun hannunta gani take kamar zai haiƙe
mata kamar yadda ƙanin mahaifinta ya yi mata,amma sai ta ga ya ƙaraso ya tsaya ɗan nesa da
ita ya miƙa mata sabuwar waya mai kyau a kwali ya ɗan daure fuska."Ga shi na ji Antynki tace
Abnaj ya saka miki waya a ruwa ta lalace shine na hutar da kuɗin ta,amma fa ki kiyaye ki dai na
basu don nan gaba in kika bari suka lalata sai na haɗa da bulala kafin na canza miki wata."Yace
ya na kashe mata ido.
Zare ido ta yi ganin wayar da ya siya mata irin wanda take gani a hannun su masu kyau da
tsada,ina