Showing 3001 words to 6000 words out of 134297 words
Chapter 2 - So Da Buri part 1 Complete Hausa Novel By Bulama.pdf
da
makarantar da take zuwa ta gwamnati ce…da alama tanada wani muk’amin a makarantar tasu
domin d’an kwalin kanta yellow ne ba Fari ba ba kuma kore ba,ta zaro shi daga cikin hijabin
nata tayi daurin ture kaga tsiya ta saman hijabin….daga makaranta take amman ta rambada
uban jan jambaki,sannan ga idon nan yasha kwalli ya sake fitowa rambad’au!!!! tubarkalla,y’ar
k’aramar jakarta da ba za ta ci littafi biyu ba na sakale a gefen hannun damanta.
Ido suka had’a da Mama wadda ta gama fitowa daga d’akinta yanzun hakan yasa ta jan wani
dogon tsaki had’i da tofar da cingum d’in bakinta kafin tace”Ni fa na tsani kallo.”
Sannan ta yi hanyar shiga d’akin Ummansu.
“dakata Jalila, magana za mu yi dake”
Mama ta fad’i hakan tana k’ok’arin K’arasowa inda take.
Juyowa ta yi ta zuba mata ido ta gyara tsayuwarta tare da nad’e hannuwanta akan k’irjinta irin
ina jinki d’innan.
Kallon ta Mama ta yi sannan tace”yanzu Jalila saboda Allah dukan da kike sakawa yayanku
Ja’afar yana yiwa y’ar uwarki ba tare da hakkinta ba kina ganin ya dace kenan? Ke kenan
kullum ba za ki ja k’anwarki a jiki ku zauna lafiya ba?
Ki duba fa
saboda Atule d’in fa da kike sakawa Yara suna yi mata kullum hakan ya sanya dole Babanku
ya chanza mata islamiyya aka maida ita ta dare da asabar da lahadi na safe.
Yarinyar da ta taso da k’aunarki acikin ranta kina k’ok’arin maida mata rayuwa kurkuku?Meyasa
kike hakane Jalila?mai ya faru kika chanja?”
Umma ce ta hankad’o labule ta fito daga dakinta cikin masifa tace
“Kawai kinga munafuka ki fito fili b’aro b’aro kice tunda na dawo gidan nan na chanjata,akan
wanne dalilin za ki tasa mini y’a a gaba kina wani cewa ta chanza hali? To bari kiji in gaya miki
Allah ne ya tsameta a cikin munafukai ya dawo da ita cikin masu gaskiya,kuna abu simi sumi da
ke da y’arki nankuwa kunfi kowa iya munafurci da cin dunduniyar mutum!.” Juyawa Mama ta yi ta kalli Jalila wadda ta ga ta yi shiru tana kallon gefe kamar bata wajen,a
tunanin Mama nutsuwa ce ta zowa Jalilan,
Juyawa tayi ta kalli Umma wadda har yanzu take fad’a baki da kumfa tace mata
“kinga Sadiya ba dake nake ba, ya Ina shirin shirya tsakanin Yara ke kuma kina k’ok’arin kiga
kin b’ata?ki daina shiga fad’an y’an uwa fa dan wataran za ki ji kuny.....”
“In sha Allah ke ce za ki ji kunya ba dai Ummana ba!”
maganar Jalila ta katse ta,
“kuma da kike ta cewa wani wai y’an uwa da ni da Huda shin wai Ubanta ne d’an uwan Baba?
ko kuwa ke uwarta ce y’ar uwar Umma???”
Shiru Mama ta yi tana kallon Yarinyar da ta rena ta goya a bayanta ta ci kashinta taci fitsarinta
tana rera mata rashin kunya.
Cikin son fahimtar da ita Maman tace
“Jalila ai ko babu y’an uwantaka ke kin san Hudan k’anwarki ce.”
“Chan ki je ki nemo y’an uwanta wallahi ba dai ni ba.”
Jalila ta fad’a cikin d’aga mata Hannu kafin ta d’aura da cewa”kiganni nan kaf y’an uwana na
dangin Ummana da Babana suna da nasabarsu kuma suna amsa sunan iyayen su!…da za ki
ce wani Ummana za ta ji kunya dan kawai ke kinji kunya shine za ki so kowa ma ya ji?kinje kin
Haifo shegiya kin kawo ta cikin gidanmu still za ki yi ta lak’aba mini ita kina wani y’ar uwartace
ita?
Idan ba tsoroba ki nuna ubanta mana ki kaita wajenshi Yarinyar da ko sunanta Babanta ba ya
so yaj.....”
Jalila bataga k’arasowar Mama daff da ita ba sai kawai wani haske da ta gani sakamokon marin
da Mama ta d’auke ta da shi,ai kuwa batai wata wata ba itama ta d’aga hannunta za ta mari
Mama.
Ji ta yi an rik’e hannun hakan
ya sanya da sauri ta juyo,nan suka had’a ido da Junaidu ya had’e rai. Matse hannun nata yai da
k’arfi sai da tayi k’ara sannan yace mata
“baki da hankali Mama za ki mara?”
Nan Umma daga bakin d’akinta toyo wata super tayi kan Junaidu ta rufe shi da duka tana
cewa”saketa ta rama ka saketa nace!!”
duk irin dukan da Umma take yiwa Junaidu hakan bai saka ya saki hannun Jalila da taketa
tsalle tana k’ok’arin fizge hannunta ba tana kallon Mama tana”Ya Junaidu ka cika mini hannu in
rama Allah yau Mama kin tab’o tsuliyar dodo,idan sama da k’asa za ta had’e sai na rama!!”
duk ta birkice ta tada k’ura tana k’ok’arin fizge hannunta a cikin na Junaidun.
Junaidu da ya ga dambe ma take shirin yi da shi ne yasa ya fizgo ta ya juyo da ita ya d’auke ta
da wani irin gigitaccen mari
yace
“ke ki nutsu!”
ya daka mata tsawa,ganin haka yasa Umma tayi kan Mama ta d’aga hannu zata mareta Mama
tai saurin rik’e hannun ai kuwa gida ya kacame Umma kawai k’ok’arin ta ta mari Mama ta yi
dambe da ita ita kuwa ta k’i bata daman yin hakan ta dai rik’e mata hannu shi kuma Junaidu
yana gefe yana fama da Jalila.
“kai!kaii!!kaiii!!!!,lafiyarku kuwa?”
sukaji muryar Baba wanda ya gama parking machine d’in sa a soro yana k’arasowa cikin gidan
da d’an sauri ga leda a hannunshi da alama yanzu dawowarsa kenan.
Umma ce ta saki hannun Mama cikin fushi tace”Alhaji gara da Allah ya dawo da kai yanzu,dan
yau za ayita ta k’are a cikin gidan nan,matar nan ta kwashi k’afa ta kai k’arar mu gurin
kaka,kaka ya goya mata baya an hanamu ni da Jalila ko kallon banza mu yiwa Huda,shine
yanzu ni ta d’aga hannu ta zabgawa Jalila mari saboda Allah duba fuskar Yarinyar nan.” Ta finciko Jalila daga gaban Junaidu da ya sake mata hannu ta hankad’ata wajen da Baba yake
tsaye,aikuwa kamar jira take ta fashe mishi da kuka,lallashinta Baba ya shiga yi cikin rawar jiki
kafin a fusace ya d’ago ya hau Mama da fad’a,Umma ce ta katseshi ta hanyar cewa
“Ai matar nan ta raina ka,tun ranar da ka hanamu shiga harkar Huda a cikin gidan nan muka
daina bi takanta,amman ita da ka ce in an hukunta Hudan kar ta yi magana
shine saboda tsananin raini yau tun safe bata barmu mun sha ruwa ba a cikin gidan nan,saboda
an tab’a y’ar gwal kalla yadda ta mari Jalila saboda Allah.”
Junaidu ne ya kalli Baba sannan ya juyo yana kallonta yace “Umma ba fa hakane ya faru
ba,yau tun safe Ina cikin gidan nan babu inda naje,a idona aka yi komai, ita Jalila ce bat...”
Tsawar da Umma ta daka masa ne ta sanya shi yin shiru
“Junaidu!! Bar nan”ta nuna mishi hanyar fita da yatsarta manuniya,baki ya bud’e zai yi magana
ta sake daka mishi tsawa tace
“bar nan nace!!”
sum sum haka ya juya ya fita ba yadda ya iya.
Juyowa ta yi ta kalli Baba tace “Alhaji a bi mana hakkinmu.”
Shiru ya yi yana kallon Mama wadda ta yi k’asa da kanta,
...Harga Allah yana son Mama, babu abinda ya chanza daga soyayyar da yake yi mata tun suna
Yara amman idan ya tuna da yadda ta yi fatali da soyayyarshi saboda waninshi sai yaji wani
haushin ta yana shiga masa rai yadunga jin babu abinda yakeda Buri sama da ya cusguna
mata itama ta d’and’ana ta ji ya zafin cusgunawan yake... Umma ce ta katse masa nazari ta hanyar cewa
“Alhaji muna sauraronka.”
Takawa yayi inda Mama take ya tsaya,yai mata nuni da yatsunshi guda biyu sannan ya fara
magana
“Maryama a cikin zab’i guda biyu da zan baki yanzu ki d’auki d’aya….
na farko ko ki tsaya Yarinyar nan ta rama marin da ki ka yi mata na biyu ko kuma ki bata hakuri
tare da alk’awarin ba za ki k’ara ba, kuma muddin kika k’ara to tabbas a bakin zaman Huda a
cikin gidan nan!.”
a razane Mama ta d’ago kai tana kallon shi da idanuwanta da suka kawo kwalla…tausayinta ne
ya kama shi tashi d’aya yaji zuciyarsa tana neman yi mishi gardama
dan haka cikin sauri ya juya ya daina kallonta yana me cewa “zab’i ya rage naki.”
Jalila da Umma kuwa zuciyoyinsu sun yi fess sai faman murmushi sukeyi,Jalila har da tattare
hijabinta ta yi gaba d’aya ta jefa shi baya ta wajen wuyanta tana hurawa hannun damanta iska
ta matso daff da Mama…
ganin da Mama tayi Jalila na neman kifa mata mari, ne ,ya sanya ta yi saurin runtse idanunta
tace
“Jalila na mareki tsautsayi ne ki yi hak’uri na yi alk’awarin ba zan sake ba!.”
Da sauri kafin su Jalila su ce wani abun Baba yai saurin cewa “barka to!! kin shafama kanki
lafiya,wuce ki tafi d’akinki.”
Jalila kuwa ta b’ata rai za tai magana Umma ta yi saurin rik’o hannunta tai mata alamun ta yi
shiru kafin ta juya ta kalli Baba tace
“Alhaji mun gode da adalci”
Daga haka ta ja hannun Jalila suka yi d’aki.
Suna k’arasa shiga d’akin Jalila ta wafce hannunta a cikin na Umma sannan tace
“haba Umma!!mai yasa kika hanani yin magana?”gashi yanzu ban rama marina ba,harfa Ya
Junaidu sai da shima ya mareni,kuma abun haushin ni Baba ya hanani dukan Hudan da a kanta
zan huce,ni dai gaskiya da kawai kin barni nace ban hak’ura ba na rama marina! yanzu Ina
kikeso in kai wannan d’acin da zuciyata take yi mini??” Ta yi maganar tana mai zama da dukkan k’arfinta a kan y’ar kujerar su two seater da take ita
d’aya a d’akin duk ta yayyage.
Murmushi Umma ta yi kafin ta zo ta gabanta a hankali ta d’aura dukka hannayenta akan
kafad’arta sannan ta durk’usa a gabanta tare da sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“ta Yaro kyau takeyi bata kwari, ai Jalila ko da ace ta zab’i ki rama marin nan da ta yi miki to fa
da ni da kaina ba zan bariba,saboda zab’i na biyun nan da Alhaji ya fad’o shi ji na yi kamar an
tsunduma ni a cikin aljanna”
Shiru Jalilan ta yi tana kallon Umma sak’ak’e alamun tana buk’atar k’arin bayani, fahimtar hakan
da Umma tayine yasata sauk’e numfashi sannan tace “menene babban burinmu a yanzu??”
Shiru ta yi na y’an sakanni sannan tace
“in auri mai kud’i kuma mu ga bayan Mama da Huda”
Murmushi Umman ta yi kafin tace “yanzu idan Hudan ta bar gidan nan tanada wajen zuwa?
Girgizama Umman nata kai tayi kafin Umman ta sake cewa
“wane hali kike tunanin Maryam za ta shiga?”Babu b’ata lokaci Jalila tace”tashin hankali”sannan
ta kyalkyale da dariya sai da tayi mai isarta tukunna tace
“Umma idan na fahimceki so kike in sake yi mata abunda zai b’ata mata rai har ta kai ga sake
mari ko dukana”
“Abinda nakeso kenan”
Umma ta fad’a tana murmushin jin dad’i mai had’i da dariya kafin ta mike tsaye tana kallon k’ofa
kamar mai tunanin wani abun tace
“Jalila ki tuna ata dalilin matarnan na bar gidan nan na rabu dake naje nai rayuwar wahala,
itakuma ta dinga gallaza miki azaba
ki tuna da cewa bakiji dad’in tashi a gaban uwa ba kamar ko wacce y’a
ki tuna yadda ta ci amanata ta aure mini miji,
ki tuna! ki tuna!! ki tuna!! dayawan abubuwan da ta yiyyi mana.”
Murmushi Jalila ta yi sannan tace”Ummana kar ki damu, zan tattaro gaba d’ayan abunda na san
bataso in yi ta zuba mata har sai ta kai ga tab’a ni,kuma na riga na gano abinda yafi b’ata mata
rai
shegiyar y’artan nan ce bataso akira da shegiya ni kuwa yanzu na fara….”
Zuciyar Umma fess ta dawo ta zauna kusa da Jalila sukaci gaba da k’ulla yadda za su
k’untatawa Mama…..
A chan d’akin Mama kuwa tana shiga ta saki kukan da take ta k’ok’arin rik’ewa,da sauri Hudan
ta taso ta zo ta rungumeta itama kawai sai ta fashe da kuka kowa ya kasa lallashin d’an
uwanshi,sai da sukayi mai isarsu tukunna Mama ta d’ago da fuskar Hudan tace mata “mai
ya saki kuka?”
Shiru tayi kafin tace “Mama gani nai kina kuka kuma naji abinda ya faru a tsakar gida”
Sharemata ragowan hawayen nata tayi kafin tace “bakomai ki kwantar da hankalinki”sannan ta
mik’e tayi kan gado ta kwanta ta lumshe idanunta….ganin hakan ne yasa itama Hudan ta mik’e
taje ta kwanta a kusa da ita tana sauk’e ajiyar zuciya kafin bacci ya yi awon gaba da ita….
SHARE PLS.
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
03
A hankali Mama ta bud’e idanunta da suka d’an kumbura ta juyo tana kallon fuskar Hudan kafin
ta kai hannun a hankali ta shafa kumatunta tausayinta yana sake shigar mata zuciya.
Nasarawa GRA, Kano.
Wani dogon dattijo ne ke tsallako titin da sauri had’e da d’an gudunshi,hannunsa na dama rik’e
da agwaluma guda uku a cikin farar leda,na hagun kuma yana amfani da shi wajen mayar da
y’an chanjin sa cikin aljihun gabar rigarsa,da alama agwalumar ya tsallaka siyowa.
K’ara saurin gudun nasa yayi sakamokon ganin har motocin da ya hango sun iso bakin
mahaukacin gate d’in makeken estate d’in.
Da saurinsa ya zaro wani d’an k’aramin makulli a cikin aljihun gefen wandonsa ya isa gaban
wata had’add’iyar k’ofa wadda ke a ta gefen makeken gate d’in wadda colour d’inta da design
d’in exactly irin na gate d’in ne, cikin sauri ya zura mukullin a ramin mukulli sannan ya murza
k’ofar ta bud’u ya tura da sauri ya shiga har yana tuntub’e, shigarsa ke da wuya waennan
motocin da ke jiransa a ta wajen gate d’in suka fara danna masa horn babu k’akk’autawa…tashi
d’aya duk ya bi ya rikice hakan yasa ya yi sauri ya fad’a d’akinsa na mai gadi ya d’aga k’asan
pillow ya d’auko mukullin babban gate d’in ya fito yanata sauri ya k’araso jikin gate d’in ta baya
ya bud’e padlock d’in sannan ya bud’e wani lock kafin ya durk’usa k’asa ya zare wata makekiyar
sakata tukunna ya mik’e ya fara k’ok’arin tura gate d’in jikinsa duk yana rawa kana ganinsa ka
san a rikice yake gashi an k’ara rikita shi da uban horn d’in da ake ta maka masa babu
k’akk’autawa… ,
Bai kai ga k’arasa tura gate d’in ya bud’u duka ba motar farko k’irar benz G wagon Bak’a wuluk!
ta danno kai da mugun gudu ta biyun na binta a baya, ba don ya yi hanzarin barin wajen ba da
babu abunda zai hana gilashin motar tafiya da y’ar sharar jikinsa.
Ganin motocin sun shige ne yasanya shi K’arasowa bakin gate d’in ya fara turawa domin
rufewa, da kyar yake iya turawa saboda tsabar girma da nauyi.
Wani gate d’in motocin suka nufa a cikin jerin gidajen estate d’in da a kalla sun kai 15 kuma
gaba d’aya ginin gidajen yanayin tsarin 3D ne masu hawa biyu,tsayuwa fad’an haduwar ginin
gidajen b’ata lokaci ne.
Wani kakkauran mutumi ne zaune a bakin gate d’in da suka nufa,sanye cikin uniform d’in
sojoji,da alama shi ke gadin wannan particular gate d’in, mik’ewa ya yi sakamokon hango
motocin sannan ya shiga ta k’aramar k’ofa ya bud’e musu gate d’in wanda hakan ya bawa
farfajiyar gidan damar baiyyana..mahaukacin makeken mansion ne yanayin tsarin ginin 3D
shima…
Ma sha Allah aljannar duniya kenan domin kuwa ya had’u har ya gaji da had’uwa da tsaruwa ga
kyau ga girma duk ya had’a.
Wajen da aka tanada domin ajijiye motoci suka nufa sannan suka yi parking.
Wani mutum ne ya bud’e motar farko,ta wajen mazaunin driver ya fito ya zagayo ta wajen
owners corner da d’an saurin shi ya bud’e murfin motar ya koma gefe ya tsaya .
....K’afarshi ta dama wadda ke sanye cikin had’add’en black d’in covershoe mai tsananin tsada
ya fara zurowa waje, kafin ya sauk’o da d’ayar sannan ya mik’o ya fito gaba d’ayansa, ba
matashi bane ba ko magidanci ko kuma dattijon Alhaji, tsohon mutum ne ,tukuf da shi!!
Sanye yake cikin wasu zazzafan suit,ash colour, kai kana ganin yanayin kayan ka san ya kai
kud’in jarin mai k’aramin k’arfi,idanunsa sanye cikin wani farin glasses wanda kana gani ka san
na k’arin k’arfin gani ne,walking stick d’in dake rik’e a hannunsa for sopport ma kanta abar
kalloce!! Ka na gani ka san an zuba mak’udan kud’ad’e wajen siyar ta,ga wani had’add’en Rolex
watch a hannunsa,
Tsohone amman skin d’insa glowing yake yi wanda kana gani ka san tsabar hutune..to cut it
short dai,every part of him is screaming ‘I’M RICH!!’.
Sandar hannunsa ya d’aga domin yin tafiya har ya d’an tura k’afarsa gaba sai kuma ya yi
amfani da ita ya juyo ya tsaya yana kallon motar da suka shigo tare.
Wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga mazaunin driver da alama shi ya tuk’o motar da
kansa, yana d’an fizgen kama da tsohon sannan kalar fatar su iri d’aya ce.
Ganin da Auwal ya yi kakan nasa ya kafeshi da idanune ya sanya shi K’arasowa wajensa da
d’an sauri, tukunna ya d’an rissinar da kansa yana mai kallon k’asa kafin yace”Garanpa,u need
something??.”
Ya yi masa tambayar ba tare da ya kallesaba .
Juyawa Grandpa d’in ya yi ba tare da ya sake kallonsa ba,har zuwa lokacin da drivern d’insa ya
d’auko suitcase d’inshi ya gama rufe motar yana taka mishi baya….
yana tafiyar ba tare da ya tsayaba cikin muryarsa ta tsofaffi yace”Go and give iliyasu 50k,ask
him to leave this house foreva,he is fired!!