Showing 1 words to 3000 words out of 155127 words
Chapter 1 - Siradin rayuwa 1-2-3-4 Book Complete by Takori .pdf
Ummi Tandama: ________________
»SIRADIN RAYUWAâœ
*@Takori*
Da Karfe Shidda Na Yamma Agogon Garin Miami
Dr. Al’ameen Bello Makarfi, ke kwance cikin sofa mai juyawa dama zuwa hagu, idanun shi a
rufe suke tamkar mai barci, amma a zahiri ba barcin yake ba, shi kadai ya san hakikanin abin
da ke damunsa. Alal hakika rigimar matar shi IHSAN ne ya ishe shi a yau. Shi kam tun barin sa
kasar haihuwar shi bai sake waiwayar ta ba balle ya tuna ta da sunan zama na din-din-din ba.
America, ta bude wani shafin rayuwa mai dimbin tarihi da nasarori a tare da shi, ta maida shi
wane, ta zamo silar dukkanin nasarorinsa a rayuwa ta warkar da bakin cikin kuruciyar da ya zo
Miami da shi ta kuma shafe rayuwar shi ta baya, ta wanke tsanar kan shi da yake a da can, shin
a kan me zai bar ta?
Sai dai wani bangaren na zuciyarshi sam, ya ki amince mai da hakan. Idan ya yi hakan ya
tabbata hakkin yarinyar kadai na iya wargaza masa farin cikin da yake takamar ya samu a
Miami; Shekaru goma kenan cif da rabuwarta da iyayenta, shi kuma goma sha biyar cif in har
lissafin da yake daidai ne bai rage ba, sun turo ta karatu sun sarke da soyayyar da har ta kai su
ga aure ba tare da sanin iyayen ko dayan su ba.
Ta jure rashin soyayyar nan ta iyaye a tare da ita tsayin shekarun nan wadda ta fi komai dadi da
muhimmanci ga dan adam, idan shi namiji ya iya ya jure, ita Ihsan mace ce, ya kuma tabbatar
ta yi hakuri kan hakuri ba don komai ba sai don masifaffen son da take masa. To shi don me ba
zai nemo mata wannan soyayyar ba, ko don albarkacin wadda take masa? Shi kansa ya san a
yanzun zuciyarsa ta yi sanyi da takaicin kuruciyarsa ta gida.
Tunanin Daddy din shi ya addabe shi, ko an harbe shi? Ko har yanzu yana kulle a kurkuku
(Prison)? Zuciyarsa ke bijiro masa da cewa, yanzu ne ya dace ya je ya tallafi mahaifiyarsa da
‘yan uwansa duk da ya san a kowanne hali mahaifiyarsu za ta iya kula da su, kasancewarta
mace mai dumbin arziki. Yana ganin yanzu ne ya dace Hajiyarsu ta huta da guminsa, shi a
yanzu ya san Allah ya yi masa ludufi da nasibi ta kowanne fanni a rayuwa;
Bar ta kasancewarsa mamallakin shahararren asibitin kwakwalwa wato “MERITIME� da
ke cikin birnin Miami, hakan nan shi ne babban likita a sashen kwakwalwa (consultant) a
babban asibitin garin Miami (Jackson Memorial) da ke Florida. Har ila yau, Dr. M.A.B (Senior
lecturer) ne da ke daukar daliban “Medical Psychology� a jami’ar da ya yi karatu
(University of Miami), kuma masani a kan duk wata larura da ta shafi kwakwalwa. Don haka
kasar America ke ji da shi, suna lailayar shi da ruwan arziki kasar su na amfana da dumbin
baiwa da fasaharshi. Baya ko tuna kasar shi ta haihuwa (Nigeria) balle iyayen shi da ya tafi da
niyyar barin su har bada, don yana ganin ba abin da zai masu, ‘ya’ya irinsa ba abin
bukata ba ne, don haka bashi da amfani a gare su. Ga ingantacciyar kauna da kulawa daga
matarshi abin kaunar shi Ihsan, yalwataccen gida a Miami, motocin hawan da ko a U.S. sai
wane da wane.
Kenan duk wani buri da dan adam zai iya ciwa rayuwar duniya, ya samu. To amma zai so ya
mutu ba tare da sanin halin da iyayen shi ke ciki ba? Ba tare da ya kara sa wani jinin shi a
idanun shi ba? Bai sake sanin halin da kanwarsa SARATU-INTISAR ke ciki ba, shakikiyarsa
kuma kanwarsa da ya NAKASTA?
Mafarke-mafarken da yake na Daddy a dan tsukin kadai na tayar masa da hankali, ya kasa
nutsuwa kwata-kwata wanda hakan ya janyo masa yi wa wani mara lafiya (Patient) rubutun
magungunan da ba su dace da lalurarsa ba, ba don Ihsan ta lura ba da an yi mamakin shi
M.A.B ne da wannan danyen aikin. To haka ko rubutu yake yana daburcewa ya rasa me zai
rubuta?
Gaba daya hankalinsa ya yi gida ya kuma tabbatar kwanciyar hankalinsa kadai ya bude ido ya
gan shi a gida.
Baya jin zai sake samun nutsuwa bai baro Turai haka nan ba. Anya ma kuwa babu hakkin Dady
din shi a kan shi? Mutumin da ya wanzar da ran shi da lafiyar shi cikin wahala, domin nema
masu farin ciki, anya ya cancanci hukuncin da ya yanke masa?
Bar ta so da gatan da yake nuna masa throughout sauran kannensa to haka Hajiyarsa, ya tuno
yadda a kullum take gaya masa ba ta son ya yi nisa da ita, ya fiye mata duk sauran
‘ya’ya taran da ta haifa a duniya! Sai ya ji kansa ya yi wani irin gingiringim, idanuwansa
sun yi mai nauyi, baya ko iya bude su. Ya lumshe ido cikin wani sabon yanayi a tare da shi.
Allah kadai ya san halin da zuciyarsa ke ciki.
Ihsan ta karaso rike da tambulan mai garai-garai cike da danyar madarar shanu mai sanyi
(fresh) wadda shan ta ya zamewa likita Ameenu lazim a duk yammaci, a gida ne ko ofis. Sanye
take cikin fararen kayan wanka (bikini), gashin kanta ke digar da ruwa tabbacin daga wanka ta
fito. Ganin yanayin da Al’ameen ke ciki sai ta ja dan karamin tebur da ke gabansa ta ajiye
kofin.
Sannu a hankali ta kwanta jikin Al’amin sannan ta marairaice kamar za ta yi kuka ta ce,
“Ameenu isn’t this enough? America is not our motherland�. Don Allah mu koma
gida…� Sai kuka.
Shiru ya yi cikin tunani, shi kam bai san ma abin da zai ce mata ba ma. Zuwa gida? Ai shi ne
mai cewa a je ba ita ba yanzun. Bai ce komai ba, baya ga dora hannu cikin gashin kanta, don in
ta soma yi mai wannan rigimar ta “a dawo gida…� da kyar yake iya samun kanta. Hakika
tana ba shi tausayi, dole su baro MIAMI a wannan watan.
*****
1 GA WATAN SAFAR (HIJRIYYAH)
Jirgin American Airways ya sauke su a birnin Ikko da karfe tara daidai na safe. Sai da kowa ya
fita amma Al’ameen da Ihsan ba su ko motsa daga “seat� dinsu ba. Gaba dayansu
jikkunan su sun yi sanyi, domin a take zazzafan zazzabi ya rufe Ihsan, ba su san da fuskokin da
za su aro su dubi iyayensu ba.
Sai da wata ma’aikaciyar jirgin ta yi masu magana cewa za a rufe jirgin, sannan ne
Al’ameen ya tuna cewa shi fa namiji ne, ya rungume matarsa da hannunshi na dama a
yayin da na hagun ke rike da ‘yar kyakkyawar jakarta ‘Japanese� a haka suka soma
tako matattakalar jirgin cikin nutsuwa har suka taka kasarmu mai dimbin albarka.
Dole idan ka kalle su sai ka maimaita su kuma yi bala’in ba ka sha’awa. Kwarjini da
cikar zati irin na Al’ameen da ke sanye cikin edpensive Italian suit, kalar baki da ratsin fari
sol sun taimaka ainun wurin kara fiddo ilhama da cikar zatin shi, ya saya kwayar idon shi cikin
bakin dark-spaces da ganinsa dai ka ga bakon Ba’amurke. To haka itama Ihsan din tamkar
aljana take don kyau, baby face gareta mai dauke da kayatattun idanu tare da kyakkyawan
dogon karan hanci da gassun gira mai tsari. Yarinya ce ‘yar gajeriya mai jiki kuvul-kuvul,
kamar na tarwada saboda tsabar hutu tamkar ba bakar fata ba, domin tun fil’azal ita brown
ce, sai kuma zaman kasar sanyi da jin dadin samun gwarzon miji irin Al’ameen Bello, da
suka kara wanke ta tas.
Dr. M.A.B zai yi wuya ka fassara daga kabilar da ya fito a lokaci daya, kamannin shi na da ruda
tunani da sanya shakku, bi-ma’ana (by appearance) ba za ka kira shi Bahaushe ba
sam-sam duk da cewa ya fi son yin magana da harshen Hausa a kodayaushe fiye da duk wani
harshe da ake magana da shi a duniya. Hakan nan ba za ka ce shi din Balarabe ba ne, domin
baya da tarin nannadaddiyar suma irin tasu kullum kansa cikin saisaye yake, amma ya bar
siririn saje a gefen fuskarshi abin nan da ake kira Man’s pride. Mutum ne dogo siriri, don
tsayi har ya rankwafa, wanda mutane da dama ke (kuskuren tsammanin) cewa yanayi ne don
kwalisa, amma Al’ameen Bello komai nashi natural ne babu artificial. Idanun shi abin so ne,
ba ga mata kadai ba har maza ‘yan uwansa will not keep wishing they were like him (Ba za
su bar fatan ina ma a ce sune shi ba).
Idanuwa ne manya kuma lumsassu, tamkar kuma an diga masu zaiba har wani maiko-maiko
suke. Bai kama da Turawan ma sam-sam shi dai kawai Al’Ameen ne, haka Allah ya yi sa.
Da wuya ka karanci zuciyar Al’ameen Bello, ko matar shi ba ta iya gane wasu
al’amuran shi. Mutum ne murdadde mai yin komai straight forward (kansa tsaye) ba tare da
tunanin illar da abin zai haifar ba, mai tsayawa a kan mgana daya, ba kankanin abu ke sa shi
canza ra’ayi ba. Kuma mutum mai tausayi da masifaffar kyauta. Ya sha sauka daga mota in
ya ga wani a gefen titi yana jiran bus a Miami, ya kira shi ya danka mai mukullin ya ce,
“Tafi.� Shi kuma ya sayi wata.
Tun Ihsan na masifa har ta gaji ta kyale shi don ta lura abin a cikin jinin shi ne. Ita kanta ba
karamar barna yake wa kayan ta ba wurin baiwa masu karamin karfi dake tareda su. Sau tari,
tana kwance a mike ya kan dafa mata abinci, ya dauko ya kawo mata yana sanya mata a baki,
yana mai lallashinta ta ci sosai.
Cewa yake wannan hakkinshi ne ya ciyar da matarshi, tunda a Alkur’ani mai tsarki babu
inda aka ce mace ta ciyar da mijinta hakan nan bai son mata suke wahala, domin su ne uwayen
al’umma duk wata wahala a wuyan su take. Idan suna nakuda ji yake kamar ya taya su.
In yana fada mata irin wannan kallon shi kawai take ta yi dariyarta mai isar ta ta ce wata rana
zai daina ne, don yana ganin ba su da kowa ne a nan inda suke sai junansu. Shi wani irin
mutum ne da bai bambancewa cikin mu’amalarshi da kowa, abin nufi, mai kudi da mara
kudi, mace ko namiji. Dr. Al’ameen Bello kowa nasa ne.
Don haka ya sha fama da mata iri-iri a zamanin karatunsa, daga Turawan zuwa ‘yan sauran
kasashen duniya da karatu ya hada su. Ihsan A.A kadai Allah ya bai wa sa’ar koda yake
zan iya cewa, Al’ameen ya auri Ihsan ne domin ceton ta daga masifar son shi da ta sanya
kanta, amma ba wai don wani mashahurin so na Allah ko na Annabi ba.
Ihsan Abubakar Argungu, ‘ya daya tal ga mataimakin Governor na (Central Bank of Nigeria),
Dr. Abubakar Argungu. Iyayenta mazaunan Abuja ne na din-din-din duk da cewa dukkansu aiki
ne ya kawo su a garin, daman an ce wai birnin Tarayyah ne. Kasancewar Ihsan ‘ya daya jal
ga iyayenta ya sanya duk wani buri na Dr. Argungu da mahaifiyarta Ann Hathaway wadda ta
kasance Kirista ‘yar uslin Birnin Gwari, akan Ihsan yake.
Mahaifiyarta Ann ce mamallakiyar bankunan Savannah da ECOBANK da ake damawa dasu a
halin yanzu a kowacce jiha ta Najeriya, don haka gaba da baya Ihsan ‘yar gata ce ta karshe
gun iyayenta baya ga watsi da ta yi da su kan son Al’Ameen Bello.
Iyayenta sun turo ta karatun medicine ne a University of Miami, inda ta hadu da Al’ameen,
wanda a lokacin ke ba da lacca cikin makarantar bangaren masu karantar lafiyar kwakwalwar
dan-adam.
Tun daga wannan lokacin Ihsan ba ta kara nutsuwa ba sai da ta zamo friend din Aminu. A
hankali a hankali ta yi amfani da hilarta wajen jan ra’ayinsa gare ta tana bayyana masa
yadda take son shi wani zubin har tana kuka take rokon shi ya aure ta gudun kar ta sanya kanta
cikin gurbatacciyar rayuwa.
Ga Al’ameen mutum mai tsananin tausayin mace, tun ba in tana fidda mai hawaye ba, sai
dai sam a lokacin bai da ra’ayin aure, tunda kuwa zai sada shi ne da gidan da ya baro baya
ko son tunawa. Yaya ma za ai ya yi aure, ba tare da sani da yardar mahaifansa ba da baya da
kamar su? Don haka ya rungumi Ihsan suka tsunduma watsewarsu ba tare da tunanin illar da
hakan zai haifar ba.
Wannan ya fi komai dadi ga Ihsan domin dama ita ba auren ne a gabanta ba, illa tana tsoron
idan ta bijiro mai da irin soyayyar da ta zaba musun ba zai amince ba, kasancewarsa mutum
mai tsananin kamewa daga barin jin dadin rayuwar Turai a ko’ina kuma a cikin kowanne
hali ya sami kansa, duk zalamar yarinya kuwa haka za ta ga Aminu Bello ta kyale domin abin da
ya kai shi kadai yasa a gaba.
To itama Ihsan din kowa da ke tare da su ya yi mamakin yadda ta samu Ameenun haka a
hannu, ba mamaki, domin an ce kowacce ‘ya mace da kissarta ake haifarta, hakan nan Ihsan
tun tana mitsitsiyarta take koyan kissa gun uwarta har girmanta iri-iri ba wadda ba ta iya ba, don
haka duk saurayin da ta kimsawa kanta sha’awarsa ta same shi ta gama kuma da kyar ne
yake kubuta daga tarkonta.
To haka shi ma Al’ameen, ta tabbatar sha’awarshi ya fi son shi yawa a tare da ita kamin
su yi aure, sai dai a dan zaman da ta yi da shi ta koyi kaunarsa saboda wasu kualities nasa da
ke burge ta da ba duk maza Allah ya mallakawa ba.
Don haka ne ma duk wulakancin da yake mata in ya bushi iska ko ya yi sabuwar girlfriend take
hakuri tana shanyewa, don ta tabbatarwa kanta tana samu nutsuwa 100% and beyond a tare
da Al’ameen fiye da duk wasu maza da ta taba mu’amala da su gida da wajen. Hakan
nan tana ganin Al’ameen ko a cikin maza daban ne wurin nuna kauna. Samun maza irin su
a matsayin MIJI sai mai sa’ar gaske. Ba ta taba haduwa da namijin da ke gamsar da ita ba
har ya kure ta kamar Al’ameen ba. Ba ta taba haduwa da namijin da ya san darajar diya
mace kamar Al’ameen ba.
Don haka ta kara manne masa ta like masa tare da kara zage damtse wurin nuna masa
ingantacciyar kauna da kulawar da ta sa shi dole ya so ta, ta kuma shiga yakar macen duk da ta
gani tare da shi ba tare da shi din ya sani ba ma. Ta kuma alkawartawa ranta, ruwa ko iska
baya raba su.
Daga baya ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa Musulmi ne, da kuma irin horon da Daddy
dinsu ya yi masu, wanda da a ce yana tare da shi, hakan ba zai taba faruwa da shi ba.
Ya roki Allah ya yafe masa ya kuma nemi Ihsan da ta yi Istibra’i su yi aure, ita kuma ganin
lokacin Aminun na sonta kamar me ta ce ba ta san wannan ba, jin hakan shi kuma ya fita
harkarta kwata-kwata, ko a tunaninta kuma ko a mafarkinta a lokacin ba ta kawo Al’ameen
zai iya rayuwa ba tare da ita ba.
Ta kuma tabbatar gab yake da ya shafe ta kwata-kwata a babin rayuwarsa in har bata amince
su yi auren ba, ta amince ta saduda cewa shi din mai ra’ayin kansa ne, don haka ba ta isa
ta sashi ko ta hana shi ba.
Suka yi auren su mai tsafta ba tare da sanin iyayen ko dayansu ba.
Daga baya ne ita Ihsan ta aikawa Ann cewa ta yi aure da wani likita Al’ameen. A lokacin
hanyoyin sadarwa basu yi kamarin da suka yi yanzu ba. Ann din ta aiko mata da zagin cin
mutunci ta waya da e-mail kan don me ta auri Musulmi ba ta auri dan Addininta ba, bayan ta yi
mata alkawarin muddin ta tashi aure Kirista za ta aura, don wai sun fi rikon aure. Shi kuma
mahaifinta ya ce kwata-kwata ba ta kyauta musu ba ta dauke su ba a bakin komai ba tunda
kuwa har za ta iya ta yi aure ba tare da sani da amincewarsu ba, don haka ta je Al’ameen
din ya maye mata gurbinsu.
To Ihsan ranta ya baci sosai da iyayenta a ganinta gata ta yi wa rayuwarta ai, domin shi kansa
auren ai mutunci ne ko bature yana daraja aure, da dai ta ci gaba da gurbatacciyar rayuwar
turai da babu komai cikinta sai lalacewa, kuma ba su yi mata uzuri da soyayyar da ta rinjaye ta
ba sun manta an ce luv is overall, wato soyayya tana gaba da komai.
Wannan ya faru shekaru uku da suka gabata, tun daga lokacin Ihsan ba ta kara waiwayarsu ba,
duk da cewa daga baya su din sun neme ta amma ta share su, don tana ganin son Ameenu ya
fiye mata komai, ko in ta sauraresun me za su yi mata? Za su hana ta aurensa ne? To gara ita,
shi din ko sanar da su bai yi ba, tunda kuwa a lokacin ya riga ya shafe gida kwata-kwata daga
kundin tarihinsa illa sabuwar rayuwar da ya gina a gaba. Sai suka hade abinsu suka dunkule
junansu wuri guda suka bude sabon shafin rayuwa cike da soyayya mai ban sha’awa.
Daga Al’ameen har Ihsan kowa na son Da, musamman ita Ihsan da take ganin haihuwa da
Ameenu ne kadai zai dorar da dangantakarsu. Tana ganin in ta haihu da shi zai mallaka mata
dukkan so da kaunarsa da har yanzu kwakwalwarta take gaya mata bata mallaki