Showing 1 words to 3000 words out of 44623 words
[30/04, 5:37 PM] UMMU AFAN :
Bissimillahir Rahmanir Rahim
Ya Allah kamar yadda nafara wannan novel lafiya kasa nagama lafiya
Wannan novel hakkin ummu afan ne mallakarta ne kuma banyarda wata ta juyashi zuwa nata
book dinba
Dedicated this page to
GORGEOUS WRITERS FORUM
GORGEOUS WRITERS FORUM
G.W.F
HOME OF GORGEOUS, INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS,
WE ARE THE BEST AMONG THE REST
AKWAI LOKACI
PAGE 1 to 5
Alhaji abubakar dankoli shahararan Dan kasuwa ne Wanda yashahara gida da wajen kasan nan
Allahji abubakar d'an asalin garin Kaduna ne dake zaune a anguwar tudun wada
Ficeccene a duniya duk inda kuke tunani sunan shi yaje
Alhaji abubakar shikadai ne agurin mahaifiyarshi kuma amma agurin mahaifinsa su goma sha
hudune
Mahaifiyarshi amina itace amarya agurin mahaifinsa kuma ita kadai Allah yaba d'a namiji
wannan dalili yasa kishiyoyinta suke mugun matsa mata
Bama iya kishiyoyi ba harda 'yan uwan alhaji abubakar duk ba mai sonta kasancewar Allah
yawa Dan uwansu arziki
Kofaduwa yayi yamutu suna da kaso mai tsoka acikin dukiyar tunda bashida da namiji
Sai kuma gashi kwatsam ya auro matarshi ta hudu kuma karamar yarinya tahaihu da namiji
Shikuma alhaji shuaib dankoli yayi murnar samun magaji da yayi
Ranar suna yaci sunan Abubakar
Tunda aka haifi abubakar mahaifiyarsa batada ishashan lafiya
Uwargidanta hajiya suwaiba da maibinta suka je gurin wani hatsabibin boka shine yabasu
magani sukasa mata a abinci ranar sunan abubakar
Haka tayi ta fama da ciwo
Abubakar na da shekara daya aduniya Allah yayi wa mahaifiyarsa amina rasuwa
Rikonshi yakoma hanun uwargida hajiya suwaiba
Hajiya suwaiba yaranta biyar mata
Babbar yarta rukaiya sai kannata hudu
Rukayya tadau komai na bakin halin mahaifiyarta
Dan haka kawai itama tadauki tsanar duniyar nan ta daura akan abubakar
Gashi duk yadda zasuyi abubakar yabar duniya sunyi amma Allah yace basu isaba
Cikin tsanani da kunci abubakar ya rayu agidan mahaifinsa
'Yan uwan Alhaji shuaib ma sunfi nuna mishi tsana karara
Bayan shekaru 30 abubakar anzama saurayi kuma mai jini ajika
Mai Neman nakamshi duk da yawan dukiyar mahaifinsa hakan baisa ya nade hannu ba
Yayi karatu sosai inda yakai matsayin babban a karatunsa
Bayanwata biyar da kammala karatun professor abubakar ne
Mahaifinsa ya mishi maganar aure yace ba yanzu ba sai yasamu matar da ta dace dashi
Hajiya suwaiba uwargidan allahji shuaib tasameshi da zancen Yakama ta ya matsawa abubakar
akan yayi aure Dan duk abokanshi yanzu suna da matayensu
Alhaji shuaib yace mata tunda yace abashi lokaci abashi mana suwaiba
Ran hajiya suwaiba yabaci tace wallahi alhaji kana bata yaron nan dayawa yanzu auren ne sai
yagada ma zaiyi
Tashi yayi yabata guri Dan baicika San surutuba
Hajiya suwaiba taje tasamu kishiyarta maibinta tafada mata yadda sukayi da allahji akan
abubakar
Hajiya larai tace aikema dai wasa kika tsaya
Mai zai hana muje musami baffa kisan shima mafa ba kaunar yaron nan abubakar yake
Sai muji shawarar dazai yanke
Hajiya suwaiba ta amince da shawarar hajiya larai
Sukayi gidan baffa sunci sa akuwa suka sameshi agida
Nan yazauna bayan sungaisa sukace fada mishi abinda ketafedasu
Yace aikin banza shi shaaibun ne yake daure masa gindin Dan na lura da hakan
amma badamuwa zanyi maganinsu
Zan hada shida hafsat kunga kenan kawar dashi aduniya bazai mana wuya ba
Cikin jindadi sukace hakan ma yayi baffa Dan wallahi muddin yaron nan yana gidan nan fa
bawani morar dukiyar Dan uwanku zakuyi
Dan komai nashi abubakar yakesawa akai yanzu kamai na kadarorin alhaji abubakar ne
jagoransu
Baffa yace nima abin yana damuna
Komai yazo karshe ita wannan yarin hafsa zata gama mana dashi
Nan dai su hajiya suwaiba murna yakamasu
Sukayi sallama sukatafi gida
Bayan kwana biyu baffa yasamu kaninshi alhaji shuaib da maganar hada yaransu auren
zumunci
Alhaji shuaib yace abashi lokaci yayi magana da abubakar tukun
Baffa yace lalle ma shuaibu Ashe maganar da mutane suke fada akanka dagaske ne nawan wai
yaronka yafi karfinka
Alhaji shuaib yace yaya kenan
Wannan kuma wani maganane na mutane Wanda idan mutum yanajin irin wannan jita jitar
bazaiyi abinkashi ba
Baffa yace kwarai kuwa shuaibu dole kanunamin ban isa da kai ba balle danka
Duk abunda kefaruwa akunnen abubakar
Yashiga cikin falon yadurkusa harkasa yace wa babanshi abbu na amince
a aura min wace baffan yakeso abbu dalilina bazanso kasaba wa 'yan uwan kaba Allah yasa
haka shine mafi alkari
Alhaji shuaib yace Allah yamaka all albarka abubakar Allah yarabaka da sharrin duniya da na
lahira Allah kuma yakareka daga sharrin mutum da aljan
Abubakar yace ameen abbu
Baffa yace kagani ba Dan naka ma yafika hangen nesa idan bamu hadasu zumunci tun yanzu
sai bayan ranmu zasuyi
Alhaji shuaib yace tunda ya amince ai shikenan
acikin yaran nawa
Wacece za ahadsun
Baffa ya wage baki yace hafsatu mana
Alhaji shuaib yace Allah yasanya alkari
Sukace amin
Baffa yace saika shirya kaje kufahimci juna ko abubakar
Abubakar yace insha Allah baffa zanyi kokari naga nasamu lokaci naje
Baffa yace yauwa hakan ma yayi kyau
Yace nizanwuce
Abbu yace tun yanzu yaya
Baffa yace tunda nayi abinda yakawoni zama ai banawa bane
Abbu yace hakane kagaida gida yace gida zaiji
Bayan tafiyar baffa abbu yakalli abubakar yace nidai hankali na baikwanta da wannan auren ba
abubakar
Abubakar yayi murmushi yace karka damu abbu kasa albarka kawai aciki
Hajiya suwaiba da kishiyarta hajiya larai sunji dadin wannan Abu koba komai idan abubakar
yamutu suna da kaso maitsoka cikin dukiyar alhaji shuaib
Hafsa yarinyace ga baffa kuma itace babbar yarshi
Hafsat kyakkyawace ajin farko Dan danginsu sungaji kyau ne Dan shima Abubakar ba bayaba
gurin kyau
Hafsat tana da zafi Dan ita bata son raini ko kannata ba kasafai tafiye sake musu fuska ba Dan
karsu rainata
Ko a school ba mai taka ta barshi sai dai kuma tana da wani hali Wanda ko agidansu ba asanta
nadashi wato tausayi da son 'yan uwanta
Kwatata bata nunawa dan tasan halin iyayen nata
Lokacin da zancen hadasu aure da Abubakar yazo kunnen ta hafsat tayi murna sosai
amma sai ta bar abinda acinkinta
Ba Wanda ya fahimceta
******
Bayan auren abubakar da hafsat tun abubakar baya kulata irin kyautatawar da take mishi yasa
yafara sakin jikinsa da ita
Soyayya sosai suke inda kasan auren soyayya sukayi
Bayan shekara daya da aurensu
Ranar asabar hafsat tana zaune kusa da abubakar tasa mishi ido kawai tana kallonshi yace
yadai madam
Tace wallahi dama sonake kabarni naje gida na wuni yau kaga nafi wata banjeba
Abubakar yace shikenan bukatar tace shikenan
Da kanshi yashirya hafsa ma ta shirya suka shiga mota yajasu sai gidansu su hafsat
Suna zuwa yasauketa yabata kudi masu yawa yace tashiga shi sai yazo daukarta zaishiga
Tace Allah yadawo da kai lafiya
Yace ameen matar kirki tayi murmushi tashiga gidansu
Kannanta na murna ga adda hafsat ga adda hafsat tayi murna ita ma da ganinsu
Taci sa akuwa YAU suna da babbar bakuwa wato rukayya babbar yarinyar hajiya suwaiba
Wato yayar abubakar kenan
Nan akagaisa Rukayya tace anya hafsat kina amfani da maganin da akebaki kizubawa
abubakar a abinci
Maman hafsat dinta ce nima dai abin yadameni wallahi ace duk wata sai munkashe makudan
kudi akan sa munkarbo maganin
amma sai muji sajinkanya kuwa kina yin yadda akesaki kuwa
Hafsat ta zumburo baki tace inayi mana kawai dai shifa yana da addua sosai ajinkinshi Dan
infada muku gaskiya ma baicika bacci ba saboda makiyansa
Rukayya tace a lalle wato mune ma makiyansa ko
Ashe bakida kunya hafsat
Hafsat tace kai nifa barin fito muku a mutum ina son mijina
Kuma koda banasonshi bazan taba kashe mutum ba balle ma Dan uwana kuma mijina
Salati sukasa tare da tafa hanu suna salati cikin tsananin kaduwa da maganar hafsat dasukayi
Hafsat batayi aune aune ba taji saukar bugu kota inta
Bakowa bane yake dukanta illa mahaifinta baffa yace ai wanna yarinya da haihuwarki gwamma
barinki
Ashe bakya son cigaban mu kinje soyayya ya rufe miki ido ko
Maman ta tace to wallahi ko kiyi abinda mukace ko na tsine miki
Cikin tsananin tashin hankali hafsat tace mama babu biyayya ga aikata sabo
Barin taba aikata abinda kukeso ba sai dai kuhada dani da shi kukashe gaba daya
Nan ma baffa da maman ta suka rufu mata da duka dakyar rukayya takarbeta
aikuwa tana samun anbarta tadauki Jakarta da gudu tabar gidan takal manta a hanu
Tayi bakin titi ta tari keke nafef
Sai gidanta tana shiga tayi dakinta tayi kuka mai isarta kafin
Ta bakanta hakuri takudiri aniyar koza a kasheta bazata barisuyi galaba akan abubakar ba
Takira abubakar tafada mishi ya wuco gida kawai tadawo
Yana zuwa yasameta ba kaman yadda suka rabu ba
Yace meyasameki madam tace bani da lafiya ne shiyasa ma baffa yace na dawo gida
Yace ashsha maza tashi muje asibiti
Tace a a basainaje asibiti ma jikinda sauki yace shidai baiyarda ba
Bata son mishi gardama sosai
Cikin ikon Allah kuwa kitoci sukayi mata tambayoyi
Tayi ta bada na karya
Daga karshe dai suka mata pregnancy test aikuwa aka sameta da ciki na sati hudu
Itakam ma bata sani ba Dan bata laulayi komai
Cikin farinciki abubakar yayi wa Allah godiya
Bayan sundawo gida ne abubakar yatafi hargidansu yafada wa abbu mahaifinsa cewan hafsat
na da ciki
Abbu ma yayi murna sosai daga karshe yayi fatan alkairi
Labarin cikin hafsat yabaza ko ina duk dangi asan da cikin dake jikin hafsat
Hajiya suwaiba da kishiyar ce cikin tashin hankali suke tattaunawa
Hajiya suwaiba tace amma larai kinsan baffa ya mugun raina mana wayo
Hajiya larai tace nima nayi tunanin haka kinga gashi yarinyar zata haihu idan ta haihu
musamman akasamu namji fa shikenan kashin mu ya bushe
Shikuwa baffa jika za ahaifar mai kinga koba komai za anfana tanan
Nan dai suma suka hau kulla kullansu
Bayan wata tara hafsat tahaifi danta kyakkyawa namiji fari Sol dashi kaman atsaga jini yafito
Yaro sonkowa kin Wanda yarasa
Ranar suna yaro yaci sunan ABDUL HAKEEM
ana kiransa da HAKEEM
Hakeem yataso cikin soyayyar iyayensa ga wayo ga farinjini
Tako inta Hakeem ya hadu
Mujezuwa taku ummu afan ce
Sai mun hadu a next page
Comments & share
[30/04, 5:40 PM] UMMU AFAN :
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN
DEDICATED THIS PAGE TO UMMY KHALEEL
GORGEOUS WRITERS FORUM
G.W.F
HOME OF GORGEOUS ,INTELLIGETAND EXPERT WRITERS
WE ARE THE BEST AMONG THE REST
AKWAI LOKACI
PAGE 6 to 10
Please masu karatu karku rikice shuaib shine baban alhaji abubakar
******
BAYAN SHEKARA ASHIRIN
Hakeem yaro Dan kwalisa Wanda yagaji kyau tako ta ina kama daga kan uwa uba dangi da
dai sauransu
Duk wani kulla kulla yafaru acikin shekaru ashirin nan
amma Allah bai ba wa makiyan alhaji abubakar nasaran cin galaba akanshi
Tare da gudumawar uwargida ran gida hajiya hafsat
Kwatata taki bada hanyar da za a cutar mata da miji ko danta
Dan yanzu mahaifinta wato baffa ya saduda tunda yaga samu tunda an Haifa mishi jika namiji
Hajiya suwaiba tare da hajiya larai sune basu yarda ba su sai sunga bayan alhaji abubakar da
iyalanshi
Yayar alhaji abubakar wato hajiya rukayya itama fa tana nan akan bakanta
Naganin kanin nata yabar duniya da iyalansa
amma hakan ya gagara .
Hajiya hafsat zaune makeken falonta tana duba wani littafin ahalarine
Sai taji sallamar dan nata Hakeem
Tadaga kai ta kalleshi tace Dan albarka yace na am abin alfaharina ki tashi lafiya ,
Hajiya hafsat tace lafiya qalau Dan albarka daman kainake jira kamin dauri akan inda nake jiya
Hakeem yayi murmushi yace da fatan dai d'alibartawa zata kawo hadda
Idan bata kawo hadda ba yau ba dori
Mummyn shi tayi murmushi tace tunda kaga yau baka kirani ba kaima nakejira aikasan nawuce
gun
Hakeem yayi murmushi yace a a fa mummy bagirin girin ba tayi mai fa
Mummy tace mai sosai makuwa
Yace muje zuwa inajinki d'alibata
Nan mummy hafsat tafara karatun da ya Dora mata najiya tiryan tirya.
Tana gamawa yace allahuakbar yaufa gaskiya daliba tayi kokari
Nan yaci gaba da Dora mata
Duk abinda suke daddynshi abubakar yana kallonsu cike da sha awa
Dan Allah ya daura mishi son iyalanshi da
Akullum ya kallesu yana godewa wa Allah daya bashi family kaman Wanda yake dashi a yanzu
Yana alfahari da hafsat
Saukowa yayi falon tare da sallama Hakeem yaje ya Rungume dad din nasa
Dan kullum haka suke gaisuwa kaman wasu larabawa
Baban yace Allah yamaka albarka Hakeem
Mummy tace ameen daddyn Hakeem
Nikam ina da tambaya daddyn Hakeem yace inajinki mummyn Hakeem inajinki yi tambayarki
Tace kullum saika tasawa Hakeem albarka Dan wani lokacin sainaji jikina yana sanyi saikace
mai bankwana
Alhaji abubakar tayi murmushi manya yace hafsat kenan a duk lokacin da kalli Hakeem
inajinsane harcikin raina kullum son d'ana karuwa yake acikin zuciya
Sai nakeganin ba Kalmar da dace dashi sai aduk lokacin da na kalleshi nasamishi albarka
Daddy yace tukun nama badai kishi kike bako
Mummy hafsat tayi murmushi tace kishim ma ai sainayi daddyn Hakeem kafin na haifi Hakeem
duk ni kama irin wannan abubawar amma tunda aka haifeshi karage
Komai naka Hakeem
Hakeem yayi dariya yace wato ma d'aliba kishi kike dani ko zamuzo karatu zan fanshe ai
Daddyn Hakeem yayi dariya yace gaskiya kam yakamata kadau mataki
Mummy hafsat tace inkuwa hakane Nima saina dau maki
Nima Baku abinci d'an kadan
Kasan danka da ci kaman gara
Gashi bayacin abincin kowa sai na mummyn shi
Haka dai sukayi ta hira cikin nishadi
Hakeem tun yana shekara shabiyar yagama secondary school
Kuma ashekarar mahaifi sa yakaishi Saudi Arabian karatu ,
Duk shekara Hakeem yake da wowa gida Hutu.
Wannan shekarar ma yadawo ne har yanasa ran komawa nan da sati daya
Islamic law ne acan saudiya
Karatu yake sosai bakama kafar yaro wancen da wowar dayayi ne yayi service dinshi a
Kano
Kafin yakoma Dan hado degree dinsa nabiyu wato masters
Yanzu yake da shekara ashirin aduniya cas
Hajiya rukayya yayar alhaji abubakar suna zauna da mahaifiyarta
Tazo gida tace nikam hajiya maizai hana muhada su Hakeem da laila aure
Kinga dai laila kam kanwar lasa bace zata iya komai akasata
Hajiya suwaiba tace amma kinsan baza a wa Hakeem aure yanzu bako
Duka duka fa shekararsa ashirin
Kuma kakansa ya yarda ko babanshi ya yarda kinsanshifa da taurin rai
Dakyar ya yarda aka aura wa abubakar hafsat
amma Kinga yadda tazama bata jin maganar kowa
Hajiya rukayya tadubi uwartata tace hajiya tunda kekika rike abubakar ,
Ki aika akira miki shi kinsan shi da biyayya har kuka kisamishi akan lalle kina son a hada auren
laila da Hakeem inyatashi komawa karatu yatafi da matarshi ,
Kinga idan kika gama kama kafar abubakar na Abba ba maiwuya bane saboda Abba yana son
abubakar Kuma yana jin maganar shi ,
Hajiya suwaiba tace naji dadin wannan shawarar taki rukayya
Allah yamiki albarka 'ya mai kishin uwarta ,
Nan hajiya rukayya tace wa uwarta zata wuce gida dan taje tasamu laila tafara gaya mata
abinda suke