Showing 123001 words to 126000 words out of 149432 words

Chapter 42 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

11 Jun 2024

31457

haka ka tashi kabar gidan nan sannan zuwa gobe ina buƙatar takardar sakin da kayi mata, don tabbas sai ka sake ta ba zata koma ba."


Kuka ne ya kufce masa ba tare da sanin kuka na zuwa ba, kamar ƙaramin yaro ya dinga kuka wai yana roƙonsu da su bar masa matarsa amma ina kowa ya tafi yabar masa wurin, sarrafawa yayi inda Inteesar ke shirin barin wajen zata bi bayan Gwaggo, Ƙasar abyar ya riƙon yana kallonta da idanunsa suka rikiɗe zuwa ja ya ce,


"Inteesar kada ki rabu dani wallahi yanzun sonki nakeyi da gaskiya, bazan cutar da ke ba tunda nake a rayuwa ta ban taɓa jin tsananin soyayyar wata ƴa mace kamar yadda nake jinki a cikin zuciya ta, kada ki rabu dani ki nuni muje mu gina sabuwar rayuwa mai cike da jin daɗin da kwanciyar hankali."


Gwaggo ce ta buge hannunsa daga jikin Inteesar taja hannunta suka shige ɗakinta suka barshi nan durƙushe yana kuka.


Haka ya zauna wajen ya cigaba da kuka, yana roƙonsu da su bashi matarsa, Mummy ma kam sai da taji tausayin yaronta sosai, dan kamar ta zubar masa da ƙwallon take ji, ɗanta namiji d take jinsa a ranta fiye da kowa yau gashi durƙushe a gabansa yana kuka akan mace ba wanda ya saurare shi.


Ya kwashe awa ɗaya a wajen ba wanda tabi takansa, har Dady ya fito daga part ɗinsa yazo zai fita bani takansa ba yayi ficewarsa ko kallonsa baiyi ba, ƙarshe haka ya tashi har yana jin ciwon kai da jiri haɗa hanya yake idan yana tafiya, har ya ƙara da wajen motarsa ya tada yabar gidan.


Tsaye take a kitchen tana yanka alayyahu yayin da Mummy ke tuƙa tuwon shinkafa suka ji sallamar Jabeer yana gaida Gwaggo


"Assalamu alaikum Gwaggo Barka da warhaka"


"Jabiru lafiya naganka haka kamar wanda aka jefo daga sama?"


"Ina fa lafiya Gwaggo ga Muhdeen can yayi accident yana kwance a gadon asibiti."


Jin haka yasa Inteesar ta saki ƙara tare da yarda wuƙar hannunta jini na tsiyaya daga hannunta, bata san ta lokacin da ta yanke ba sakamakon jin magamar da Jabeer ke faɗawa Gwaggo, ita dai Mummy bata ji maganar Jabeer da Gwaggo ba sai jin ihun ƙarar Inteesar da ta yanke hannu da saki wuƙa, da sauri Mummy ta ƙaraso wajen tare da kallon hannun Inteesar ta ce,


"Subhanallahi garin yaya kikayi muguwar yankewa haka da wuƙa?"


Girgiza kai tayi sai a lokacin Mummy taji muryar Gwaggo na ƙwala mata kira


"Fatima! Fatima!! Fatima!!!"


Jin yadda Gwaggo ke ƙwala mata kira tasan ba na lafiya bane, da hanzari ta fito kitcheen ɗin tare da Inteesar na biye a bayanta


"Na'am Gwaggo meke faruwa"


Kuka Gwaggo ta saka yana cewa


"Na shiga uku yanzun haka ɓacin ran abinda muka masa ne yasa yayi hatsari, wayyo Allah na."


Jabeer ne ya kalli Gwaggo ya ce,


"Gaskiya kam Gwaggo indai akwai abinda kaka masa a gidan nan da ya ɓata ransa to shine ya jefa sa cikin wannan halin."


Jinjina kai Jabeer yayi ya ce,


"Gaskiya kam da alamar haka, domin mutanen da hatsarin ya faru a idanunsu sun tabbatar da cewa tuƙin motar kawai amma ba a cikin hankalinsa yake ba ababen hawa da ke kan tatin ma wasu sauka sukayi daga kan tatin ganin yanayin tuƙin nasa, sai daiAllah yasa ba bugu kowa ba motar ce dai ta kufce masa take da daki wata bishiya."


Mummy ce ƙwalla ya cika mata ido ta kalli Jabeer ta ce,


"Yanzun wani hali yake ciki."


"Da sauƙi za'a ce amma yana can baisan wa ke kansa ba"


Inteesar ce ta fashe da kuka ganin cewa duk alhakin faruwar abun akanta yake ita ce silar komai da ya same shi,Jabeer ne ya kalli hannunta dake zubar da jini ya nufi ɗakin Muhdeen ya fito da kayan aiki yazo yayi mata treatment na hannunta sannan ya kalli Gwaggo ya ce,


"Dawa zamuje ne? tun ina asibitin na kira Dady na sanar da shi."


Mummy ce ta kalli Inteesar ta ce,


"Daughter ki tsaya muje mu dawo ke da Mufida ku tsaya a gida ita tana barci."


Kai Inteesar ta girgiza tana kuka ta ce,


"Mummy wallahi bazan iya tsaya ba zan biku mu tafi domin naga halin da yake ciki."


Tana magana tana kuka, kafin ma Mummy tayi magana har ta shiga ɗauki ta ɗauko hijabinta don zuwa Asibitin, dole suka ƙyale ta suka tafi da ita inda aka bar Mufida tana kwance a ɗakinta tana barci.


Ko a cikin motar ma kuka take Jabeer dake driving Ya ɗan juyo ya kalle ta ya ce,


"Please kibar kukan nan haka insha Allahu zai warware anyi masa alluran barci ne, saboda yaƙi yarda a duba sa da kyau ga rauni a jikinsa amma amma sai cewa yake a barshi ya tafi wanda hakan yasa dole muka yi masa allurar."


Kasancewar Mummy ce a gaba gefen Jabeer Gwaggo da Inteesar suna baya, Gwaggo ce ta kalli Inteesar ta ce,


"Ke nifa bani son damuwa, duk kinbi kin cikawa mutane kunne da hayaniyar kuka."


Jabeer ne ya ce,


"Ba dole tayi kuka ba mijinta na cikin wani hali."


Taɓa baki tayi tare da cewa


"Ni ban gane kukan da take yi ba, mijin da ba wai sonsa take ba neye na ɗaga hankali? sai da na tambaye ta tana sonsa zata koma gidansa ta ce bata sonsa ba zata koma ba, to yanzun daga jin yayi hatsari tabi ta rikice har tana yanke hannunta da wuƙa bata damu da ciwon hannunta ba ta shi kawai take, ni gaba ɗaya na kasa gane inda yarinyar nan ta dosa, wato ke sawun keke ce ba'a gane gabanki ba'a gane bayanki, sonsa kike ko tausayin halin da yake ciki ne ban sani ba."


Tura baki tayi tace,


"Nifa kwai tausayinsa nake ji, gani nake nice silar komai shiyasa nake kuka ba don komai ba, kuma ko waye zan iya masa kuka indai ya shiga wani hali saboda ni."


Daga nan ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa Asibitin, bayan Jabeer yayi parking suka fito suka bi bayansa.








*Daga alk'alamin*✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*DON NEMAN ƘARIN BAYANI*


09065327995




Love you oll😍😘


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






Idan kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na buɗe wannan duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne.




*GARGAƊI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinin na ba




*SANARWAR*


Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi da cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce Ni bada niyyar yin hakan nayi ba, rashi ne mai kashe auren wawa.






*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*




Page6️⃣9️⃣


Daga nan ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa Asibitin, bayan Jabeer yayi parking suka fito suka bi bayansa.


Yana kwance yana barci sai rauni da ya ji a kansa, Jabeer ne ya turo ƙofar sai Inteesar da ke bayansa sai Mummy da Gwaggo, a guje Inteesar ta ƙarasa jikin gadon bata san lokacin da ta riƙo hannunsa ba tana kuka, Jabeer ne ya kalle ta ya ce,


"Kada ki tayar da shi ana son ya samu isashshen barci kada ki damu zai tashi, zuba masa ido tayi tana tuna lokacin da ya riƙe ƙasar rigarta yana roƙonta da cewa, Inteesar kada ki rabu dani wallahi yanzun sonki nakeyi da gaskiya, bazan cutar da ke ba tunda nake a rayuwata ban taɓa jin tsananin soyayyar wata ƴa mace kamar yadda nake jinki a cikin zuciya ta ba, kada ku rabu dani ki bini muje mu gina sabuwar rayuwa mai cike da jin daɗi da kwanciyar hankali.


Haka ta dinga tuna kalamansa da a cikin zuciyarta tana jin tausayinsa har cikin ranta.


Mummy kuwa ita kaɗai tasan yadda take ji a zuciyarta tana tausayin halin da ya ke ciki akan mace, dan yanzun da daina jin haushinsa akan ƙuntatawar da yayiwa Inteesar a baya, dan yanzun ta fahimci cewa yayi nadama.


Ɓangaren Gwaggo ma bata ji daɗin faruwar hakan ba duk da ita ce ta tunzura shi, amma tayi haka ne dan ta ƙwayar wa Inteesar ƴancinta a wajensa Sakamakon azabar da uƙuba da ya nuna mata a gidansa, duk da ya sauya amma yana da kyau ya gane kuskure da ya aikata kuma yasan mahimmancin da take da shi a wajensa.


Nan dai Jabeer ya kwantar masu da hankali sannan ya nufi office ɗinsa, zama yayi ya ɗauki wayarsa tare da cewa


"Bari na kira abokanmu na sanar da su halin da abokinsu yake ciki."


Bayan yayi dialing number Salisu ya sanar da shi ne, sai ya lalubo ma Biliyaminu shima ya kira sa ya sanar da shi sannan ya lalubo number Bashir shima ya danna masa kira.




Kwance suke a ɗakin hotel ɗin ba kaya a jikinsu suna kulluɓe cikin bargo, ta kwantar da kanta a ƙirjinsa kallonta yayi yana murmushi ya ce,


"Yakamata ki tashi kiyi wanka ki koma gida kafin mijinki ya dawo ya tarar baki gida."


Yamutshe fuska tayi tare da cewa


"Ba yanzun ba don na gaji wallahi sai na huta"


Wayarsa ce tayi ringing ya duba tare ɗagawa ya ƙara a kunne da ya ce,


"Hello Jabeer yau ka tuno da ni ne?"


Ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa


"Abokinka fa ba lafiya yayi accident?"


"Subhanallahi wane daga ciki Muhdeen ki Salisu ko..."


Kafin yakai ƙarsen zancensa ne yaji muryar Jabeer na cewa


"Muhdeen"


Ita dake kwance a saman ƙirjinsa kasancewar ta ji muryar Jabeer cikin wayan ya ambaci Muhdeen da sauri ta miƙe zaune tare da cewa


"Na shiga uku nala..."


Kafin takai ƙarshen zancenta Bashir yayi saurin rufe mata baki da hannunsa ya ce,


"Asibitinsa yake kwance?"


"Eh"


Ya bashi amsa a taƙaice daga nan ya aje wayar.


Bashir ne ya kalli Sumayya sannan ya cire hannunsa daga bakinta ya ce,


"Meye haka daga magana kina neman tona muna asiri idan ya gane muryarki fa?"


"Kasan yadda naji ne?mijina fa aka ce yayi accident ya bazan ruɗe ba?"


"Bari nayi sauri na tafi Asibitin"


Ta ƙarasa magana tana sauka daga kan gadon, kallonta yayi tare da cewa


Tunda basu kira ki suna sanar da ke ba yanzun idan kika je aka tambaye ki waya sanar dake me zaki ce? ni zaki ce ?idan suka tambaye ki ina muka haɗu na sanar da ke fa?


Sai a lokacin ta tuna ta dawo ta ɗauki wayoyinta tare da kunna su ta ce,


"Na mance na kashe wayoyi na duka kila ma ya kira ni bai samu ba"


Tana kunnah wayar kuwa sai ga kiran Jabeer ya shigo kamar jira yake da sauri ta ɗaga tare da karawa kunnenta duk da cewar da wayar Muhdeen ya kira ta don baida number ta, ko ranar da ta kira shi ya roƙi Muhdeen ya barta akan ta cigaba da zama a gidansa baiyi served number ta ba, kallon Bashir tayi da ya zuba mata ido ta ce,


"Da number Mijina ya kira Ni wayar na hannunsa ne."


Ɗagawa tayi tare da cewa


"Hello my sweet"


Da sauri Jabeer ya ce


"Bashi bane bani da number ki ne yasa na duba wayarsa na kira ki."


"To Allah dai yasa lafiya da naga ka Kira da wayarsa hankali manya tashi."


"Kina ina ne?"


Gabanta ne ya faɗi kada dai ace yahe gidansu bai gabata bane, kafin tayi magana ta ji ya ce,


"Kizo Asibitinsa muna nan"


"Lafiya me ya faru da shi ne?"


"Kada ki damu kizo kawai"


Daga nan ya katse kiran yana girgiza kai.


Suna nan zaune a ɗakin Dady ya shigo don duba halin da Muhdeen ke ciki, daga nan ya je office na Jabeer inda ya nemi jin ƙarin bayani daga bakinsa nan Jabeer ya kwantar masa da hankali cewa ba komai zai warware insha Allahu, sai dai akwai damuwa. zuciyarsa kuma samuwar akan Inteesar ce don haka ya dinga sambatu yana kiran sunanta kafin barcin yaɗauke sa, nan Jabeer ya ƙara jaddada wa Dady cewa su basa matarsa don gaskiya Muhdeen yabcanza, yanzun son Inteesar yakeyi da gaskiya ya kamu da matsancin soyayyar Inteesar, bazai taɓa cutar da ita ba ko ya bari wani ya cutar da ita, nan dai ya cigaba da masa bayani kuma Dady ya gamsu da bayanin Jabeer sannan sukayi sallama ya fita.


Suna nan zaune a ɗakin sa aka kwantar da Muhdeen bayan tafiyar Dady sai ga Sumayya ta faɗo ɗakin kamar wacce aka jefo, ganin su Mummy da Gwaggo yasa ta shan jinin jikinta kunya ce ta dabaibaye ta, don tunda ta auri Muhdeen bata taɓa zuwa ta gaida su ba, lokacin da idonta suka sauka akan na Inteesar sai da gabanta ya tsananta faɗuwa, taji ƙiyayyar da take wa Inteesar ce ta dawo sabuwa a cikin zuciyarta, musamman da taga idanunta alamar tayi kuka kuma tana riƙe da hannun Muhdeen ta zauna a gefen gadon, take sai taji kishin mijinta ya taso mata, ga kuma kunya tana ji na abunda ta aikata na yunƙurin kashe Inteesar kallon Gwaggo tayi ta ce,


"Ina wuni Gwaggo?"


Kauda kai Gwaggo tayi tare da cewa


"Bari na fita ɗakin nan kada Allah ya tashi turo ma wata bala'i ya shafe ni."


Ta ƙara maganar tana kallon Mummy da Mufida tana masu alamar da suzo su tafi, Sumayya ta ƙalli Mummya ta ce,


"Ina wuni Mummy?"


Ba yabo ba fallasa ta amsa mata da


"Lafiya lau ya gidan?"


"Alhamdulillah"


Gwaggo ce tayi saurin sawa gadon taja hannun Inteesar suka tafi zuwa waje, wani wuri suka samu suka zauna saman kujeru dake ajiye a wajen.


A can cikin ɗakin kuwa turo ƙofar akayi tare da yin sallama, Salisu ne da Biliyaminu, sai Bashir, durƙusawa sukayi suka gaida Mummy tare da tamabar ta ya mai kiki, ta amsa da Alhamdulillah sannan Sumayya ta gaishe su suka amsa mata inda Bashir ya kashe mata ido ɗaya da sauri ta kauda kanta daga kallon sa don ta lura Bashir ba kunya ne da shi ba, yanzun sai ya nemi tona masu asiri bayan 'yan mintuna sai ga Gwaggo da Inteesar sun shigo ɗakin, yayin da Bashir ya kafe Inteesar da wani kallon ƙurilla ba wanda ya lura da hakan sai Sumayya da idanunta ke kansa, gyaran murya tayi ya kalle ta ta galla masa harara sosai kai yayi tare da gaida Gwaggo ta amsa suma sauran suka gaishe ta amsa masu.


Bayan kamar mintuna goma ne Bashir ya miƙe ya ce


"Bari naje na ɗauko abu a mota."


"Salisu ya ce


"Okay"


Yana ƙoƙarin fita ne sukayi kiciɓis da Jabeer suka ƙara gaisawa sukayi sannan sannan ya fice, bayan fitar da da mintuna biyar Sumayya ta tashi ta fice,


Yana zaune a cikin motarsa gani kawai yayi an buɗe murfin motar kafin yayi magana har ta shigo ta rufe murfin motar, da mamaki ya kalle ta ya ce,


"Sumy! lafiya kuwa?"


Kauda kai tayi tana taunar cingum ta ce


"Ƙalau"


"To me zaisa ki biyo NI har cikin mota idan wani ya hannu fa akwai matsala."


"Yaushe kasan yarinyar can da naga kana binta da wani mayataccen kallo?"


"Wata yarinya?"


Kauda kai tayi bata ce komai ba sai a lokacin ya tuna cewa lokacin da yake kallon Inteesar Sumayya ce kaɗai ta kula da hakan, dan haka ya ce,


"Oh Inteesar?"


Taɓe baki tayi ba tare da ta ce komai ba


"Ai Inteesar ta daɗe da shiga raina, ranar da akayi reception na aurenki da Muhdeen ne na fara ganinta ita da Jabeer wai daga tashi reception matarsa ta kira sa tana son agwaluma suka kai mata, to bayan sun dawo ne na ganta har na cewa Jabeer zan aure ta don banga maccen da ta haɗa abubuwan da nake so kamar Inteesar ba, gani na na biyu da ita munje gidan baki nan lokacin kina London tana amarya munje cin girkin amarya, munta ta santin daɗin girkinta sai Salisu ke bani labarin wai da kike amarya sunzo cin girkin ki wai kinyi masu daɗɗaɗan girki irin taki ba, wai taki ta musamman ne basu taɓa cin girki mai daɗinsa ba, sanin cewa tsokanarta yake yasa ta ɗaga hannayenta biyu tana kai masa dukan wasa riƙe hannunta yayi, kamar daga sama suka ji ana knocking glass ɗin motar da sauri suka juya cikin fargaba dan ganin waye.








*Daga alk'alamin*✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*DIN NEMAN ƘARIN BAYANI*


09065327995




Love u oll😍😘




Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a






*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na buɗe wannan duk abu ɗaya ne, sannan idan kisan cewa bazakyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne.




*GARGAƊI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.




*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*




Page7️⃣0️⃣


Kamar daga sama suka ji ana knocking glass ɗin motar, da sauri suka juya cikin fargaba dan ganin waye.


Sauke glass ɗin motar yayi sai yaga ɗaya daga cikin security na Asibitin ne ya a tsaye, kallonsa Bashir yayi tare da cewa


"Lafiya?"


"Yallaɓai dan Allah ka gayara parking ɗin motarka."


Jinjina kai yayi tare da cewa


"Okay"


Sai a lokacin ya lura da inda yayi parking ashe ya a hanaya ne, kuma motocin da ke gabansa dole sai ya bada hanya kafin su wuce, don haka ya gyara parking ɗin motar sannan ya juya ya kalli Sumayya.


"Waya ta na manta a motar shine na fito ɗauka yakamata ki fita ki koma kiyi jinyar mijinki ko?"


"Ni wallahi tunda na ƙyallara ido naga yarinyar nan a Asibitin nan sai naji gaba ɗaya raina ya ɓaci, musamman da ta haɗu da waccan jarababbiyar tsohuwar Gwaggo, Wallahi na tsane su a rayuwa ta."


"Me sukayi maku da kika tsane su?"


Yamutshe fuska tayi tare da cewa


"Ita wannan tsohuwar tun lokacin da na fahimci baya ƙauna ta ne, ita kuma waccan yarinyar haka nan kawai tun ranar da na fara ganinta a gidansu Muhdeen na tsane ta, Ni dama na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login