Showing 30001 words to 33000 words out of 111068 words
Chapter 11 - THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt
skin ɗinta wani haɗaɗɗan lotion mai ƙamshi,lumshe idanunta tayi sabida sanyin lotion ɗin da taji a fatarta,tana kammalawa ta ɗauki wani parfume ta fesa a lungu da saƙo na jikinta da kuma gaɓoɓin jikinta,duk inda turare yafi zama nan ta saka sosai tayi missing ɗin parfume,tana kammalawa ta saka sabon pant daman beriza ba damunta tayi ba,wani red ɗin fakistan ta saka mai riga da wando,kana ta yane kanta da vail ɗin fakistan ɗin,ya salam kamar wacce ta haɗa jini da indiawa faɗin ƙyan da tayi wasting time ne,sosao farar fatarta ta amshi red colour ɗin fakistan ɗin,tana gamawa ta shimfiɗa ladduma tare da gabatar da sallan raka'atul fijir,bayan ta idar tayi sallah asuba da aka shiga yanzu,sosai tayi lazumi tare da addu'a Ubangiji ya dubi niyarta ya bata nasara akan abinda ke shirin tunkarota,sannan ta nemi zaɓin Allah tsakaninta da Lil prince wanda ta farajinsa a ranta.
Tilawan al'kurani tayi kana ta kishingiɗe bacci yayi gaba da ita,bata farkaba sai wajan 11 "Ya rabbi wannan baccin fa"ta faɗa tana murza goshinta wanda yayi mata nauyi,a gaggauce ta faɗa toilet ta wanke fuskarta da bakinta kana ta gyara zaman vail ɗin jikinta,cikin sauri ta fito daga bedroom ɗin ta nufi parlour ganin babu kowa tayi saurin gyarawa tare da fesa air freshener nan parlour'n ya ɗauki ƙamshi.
Kichen ta huci ta fara soya masa pilantain and egg soup,sai coffee,tana gamawa ta fita bata 5minutes ta dawo ɗauke da zogala a hannu,cikin sauri ta haɗa ƙwaɗon zogalan da yaji timatir da almasa da dafaffan ƙwai sai ɗan lemon tsami data matsa,plate ta nema ta zoba sannan ta ƙwashi kayansa tayi parlour,zaune ta samesa yana latsa waya,daga shi sai three gauter haɗi da singlet wacce ta kama jikinsa,sai a lkcn ta fahimci baiwar suma da ALLAH yayi masa ko'ina na jikinsa soma ce,musamman santala-santalan cinyoyinsa wanda sukai ƙwance luff.
A sanyaye ta ƙarasa tare da jera beakfast ɗin akan table,kana ta sunkuyar da kanta ƙasa ta shiga wasa da yatsun hannunta,lumshe idanunta tayi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake fita a jikinsa,numfashi taja kana ta ware idanunta haɗi da soma juya laɓɓanta da ƙyar ta lalobu kamar.
"Good morning"
ƙara lafewa yayi jikin lumtsumemiyar kujerar yana fidda wani zazzafan huci ta cikin hancinsa,lumshe idanunsa yayi wanda hakan ya zama ɗabi'arsa,kana yayo pouting lips ɗinsa,yayi lamo yana sauraran bugun zuciyarsa wacce ke fita da saurin-saurin,a sanyaye ya sanya hannu ya dafe saiting zuciyarsa tare da murza wajan a hankali,a tunaninsa hakan zai saka ya daina jin zafi da raɗaɗin daya keji a zuciyarsa.
Jin yayi shuru ya tabbatar mata bazai taɓa yin magana ba,hakan yasa ta ware idanunta ta zoba a kan ƙirjins inda yake murzawa ta naji tamkar tace ta taimaka masa,juyawa tayi kicthen ɗin tare da ɗauko plate ɗin zogalan ta fito zuwa parlour,dicret hanyar ficewa daga sashin tayi.
Idanunsa ya ɗaga tare da saukeso kan mai dai²cin hip ɗinta dake juyawa cikin kayan,can ƙasan maƙoshi yace.
"ina zaki?"ya faɗi maganar yana pouting lips ɗinsa.
Tsayawa tayi tare da juyowa ba tare data kallesa ba tace "wajan Mai babban ɗaki"ta bashi amsa a taƙaice,lumshe idanunsa yayi ba tare da yace komai ba,few minutes ya buɗe laɓɓansa yace.
"kada ki daɗe"shine abin yace a taƙaice kana ya ƙwanta lamo saman sofa yana sauke numfashi,mamakin jin kansa take shi komai wahala yake masa hatta magana,juyawa tayi tabar parlour'n tare da nufar sashin Mai babban ɗaki.
A bakin ƙofa ta samu Bafade Kamal tana zuwa yasa remote ya buɗe mata ƙofa,sabida tun jiya Mai babban ɗaki tayi masa bayani a kanta,tana zuwa ta sameta a zaune saman wata lumtsumammiyar sofa ke fatan kuma Hadima Kaltume ce zaune tana yi mata tausa,cikin nutsuwarta jiki a sanyaye tayi sallama tare da tsayawa tana jiran umarnin shiga,wani tattausan murmushi Mai babban ɗaki tayi kana ta janye ƙafanta tace.
"yau ɗiyata ta zama dogari mene yau kikazomin dashi,ohh ya zonan"ta ƙarasa maganar tajan casbahar hannunta.
Ɗan murmushi Zarina tayi cikin tafiyarta mai sanyi ta ƙarasa wajanta,tana zuwa ta ajjiye plate ɗin hannunta tare da shige jikin Mai babban ɗaki cikin murna tace.
"barka da hutawa Ammi yaya ƙarfin jikinki?"ta ƙarasa maganar tana zare jikinta ta soma matsa mata ƙafarta,jinjina kai Mai babban ɗaki tayi sannan tace.
"Ɗiyata jiki sai godiya,Kaltume jeki zan kiraki idan Ɗiyata ta tafi"
"A'a Ammi ta kin barta sabida ance yanzu na dawo kada na daɗe,daman Ƙwaɗon zogalan na kawo maki"ɗan haɗe rai Mai babban ɗaki tayi kafin tace"waye haka mai baki umarni kamar wata ɗiyarsa,nida nakeso Azumi na zuwa ki dawo nan naga wata ya kusa kamawa?"ɗan raurau tayi da idanun kafin taja numfashi tace.
"Amma wani sabon sojane da yazu mai kula da Mai martaba toni ke kula dashi wajan abinci da gyaran wajan baccinsa,kuma fa Ammi baya magana wlh miskilanci garai"ta ƙare maganar tana turo baki gaba alamar jin haushi.
Wani tattausan murmushi Mai babban ɗaki tayi sannu a hankali ta lumshe idanunta tana jin wani irin yanayi na saukar mata a zuciya da gangar jikinta,fasali taja kana tace.
"maza je kiramin shi naji dalilin miskilancin kinsan soja baisan wargi halan tsoransa dai kawai kikeji,amma kafin ki tafi bani ƙwaɗon zogalan"jin jin daɗi Zarina ta miƙa mata zogalan sannan ta miƙe tsaye tare dayi mata sai anjima idan ta kirasa,tana fita Bafade Kamal ya zoba mata idanunsa na wani lokaci kafin can ya ɗauke idanunsa ya maida ga zoben hannunta wanda yake ta sheƙi,ganin kallon daya kewa ring ɗin yasa tayi saurin ɓoye hannunta tare da barin wajan da ɗan sassarfa.
Tana shan wata ƙwana ta haɗu da Hadima batul,washe baki tayi tace "ƴar baiwa yanzu Fulani kilishi tace na kira mata ke"wani tsoro da fargaba ne suka dira zuciyan Zarina kasa amsa Batul tayi sai runtsa idanunta da tayi tana jin zuciyanta nayi mata zafi,gaba ɗaya tsoro da firgici ya gama kamata,idan har bata manta ba Kilishi itane mahaifiyar Lil prince,to mene tayi mata haka take nemanta,ko Lil Prince yakai ƙararanta,jin tayi shuru ya sanya Batul cewa.
"Zarina mene kike tunani aike kakanki ta yanke saƙa wallahi,nifa ina son Prince sosai dama ni Allah yayiwa wannan liɗifin keman ƴar baiwace ke,daga zuwanki gidanan abin arziƙi ya sameki,wlh ni...."
"ohh ya Allah kina hutawa hakanan mana"Zarina ta katseta da faɗin hakan.
Washe baki Batul ta ƙarayi,kafin ta leƙa ko'ina taga babu kowa cikin sauri ta kama hannun Zarina tace.
"kisan Mai martaba ya taɓa.."saurin haɗiye maganar tayi ganin Lil prince tsaye a bayanta,hararan daya watsa mata yasa tayi saurin barin wajan,gyara tsaiwarsa yayi tare da zoba mata rikitattun idanunsa wanda sukai jaa,saurin ja baya tayi sabida warin giya daya duki hancinta,cikin mayen giya ya kalleta ya saki murmushi yace.
"Ohh..My Zarina...you are very beautiful..i love you."ya ƙare maganar a rarraɓe sabida jirin dake ƙwasanshi,ƙara matsawa baya tayi cikin sauri ganin yana ƙoƙarin ƙwara mata amai a jiki,da ɗan sassarfa tabar wajan zuciyarta fal tsoransa.
Da sallam ta shiga sashin fulani kishi a zaune ta sameta kuyangu wajan goma a kanta,wasu nayi mata tausa wasu nayi mata fita gefe guda kuma wata nayi mata messges a kanta,tsayawa tayi ta zobawa sarautar Allah idanu,lallai wannan tafi Mai martaba son mulki,kasa ƙarasawa wajan tayi sai zoba masu idanu da tayi tana kallon kowa cike da mamaki.
"Wakik tsayawa a nan?"taji magana daga can nesa da ita,sunkuyar da kanta tayi tare da lumshe idanunta ta shiga taune laɓɓanta tamkar zata rabasu gida biyu,jiki a mace ta ɗaga ƙafar tare da ƙarasawa inda take ta durƙosa gefenta,cikin murya mai sanyi tace.
"batul tace na amsa kira"
Kallonta Kilishi tayi tana sakin dariya kafin ta tace "Eh tabbas na kiraki,daman Batul ta gayamin kin karɓi zogala wajanta ɗazon mene kikai dashi?"
Hamadali tayi a ranta jin ba wani abune,kafin ta saki ajjiyar zuciya a fili,laɓɓanta ta soma mamula hakan alamune da yake tunana cewa ƴar ƙinƙinar da take da ita ya tashi,amma mutane da yawa basa fahimtar hakan suna ɗaukan sbd ado take yin hakan sbd wani ƙyau da hakan keyi mata,da ƙyar ta samu damar faɗin.
"Mai baban ɗaki nayimawa ƙwaɗo"ta mata amsa a daƙaice.
Cikin jin daɗi Fulani kilishi tace "Masha Allah kice ta amince da mai kula da ita kennan yanzu? To da ƙyau naji dadi dukkan abinda kikeso zakiyi mata kizo wajena zan baki,daman ga azumi dai kama aƙwai kayan abinci na musamman da aka ware dominta idan an shiga azumi sai kizo ki amsa wajena"ta ƙare maganar tana sakin wani murmushin gefen baki.
Da "to" kawai Zarina ta amsa mata dashi kana ta miƙe tare da ficewa daga cikin sashin nata,a nutse take tafiya kanta a ƙasa tana tafe yatsanta a baki,yadda take kaɗai zai tabbatar maka ita ɗin yarinyace mai ƙarancin shekaru,tana isa harabar masarautar ta hango tsaye waya manne a kunnansa,ya haɗe cikin ƙananunsa masu ƙyau,yau picap kawai ya saka ta uniform ɗinsa.
Idanunsa lumshe yana sakin murmushi da dukkan alamu yana jin daɗin wayan da yake.
A hankali ya shafi cikinsa tare da lumshe idanunsa,juyowa yayi tare da sauke idanunsa a kanta,jinjina kai yayi murya ƙasa yace.
"Abbuna Ramadan zai kama ina son ganinka nayi kewanka sosai"ya ƙare maganar yana pouting lips ɗinsa,daga can ɓangaren Abbu yace.
"My luv sam baka girma,ba kace wata 5 zakai ka dawo ba,mene abin takura muna waya muna chart muna vedio call amma luv na baka girma rigimanka kullum yawa yake"
Jinjina kai Saifu kana ya ƙara ƙasa da muryarsa yace "ok Abbuna bye i luv u"yana gama faɗin hakan ya ƙatse wayan,kallon kana yayi mata alama tazo da hannunsa.
Kanta a ƙasa ta shiga takawa zuwa inda tana zuwa taja ta tsaya tare da soma wasa da hannunta,taɓe yayi tare da ɗauke kansa daga gareta,wajan 5minutes bai tankata ba,gajiya da tsaiwarta da tayi ne ya sata faɗin.
"daman nemanka nake"ta ƙarasa maganar ta cilla yatsanta a baki tsora mata idanu yayi yazu daf da ita murya ƙasa yace.
"Duk sanda kika ƙara shan yatsa gabana sai na tsotse shi tas naji abinda kikeji sakalya kawai"ya ƙare maganar yana watsa mata harara.
Wata kunyace ta kamata cikin sauri ta zare yatsan kana tace.
"Mai babban ɗaki na nemanka yanzu"ta ƙare maganar tana lumshe idanunta,wani ƙawataccen murmushi yayi cikin nutsatsiyyar murya yace "ohhh muje naga wannan Mai babban ɗakin"..
_Kada a fitar da littafi waje keda kika siya kene mai alhakin karantawa,idanma kin fitar ƙarin costomer ne,_
_Gamai buƙatar yin payment zai turo kuɗinsa ta Accout ɗina mai som nrml grp 200, mai buƙatar vip grp wanda zai samk duka littafan tana rubuta na kuɗi zai biya 500,zaku turo kuɗin ta wannan accout ɗin 0116886423 Sulaiman Na'ima S Union bank sai proof of payment ta wannan number 08119237616👉🏼keda kika fitar keda ALLAH.
BY
*NIMCYLUV*
*31-32*
#Heart cry
Yadda ya faɗi sunan Mai babban ɗaki a taushashe zaka fahimci ya ƙai ƙarshe wajan yin magana mai tsaye,lumshe idanunsa yayi tare da fesar da wani zazzafan numfashi,a duk sanda ya tuna abinda Mai martaba ya shirya akan Mai babban ɗaki yana jin zuciyarsa na zafi da raɗaɗi mai taba tunanin aƙwai mutum mara imani kamar haka ba,zuwa yanzu babu abinda yake tunani irin yadda zai ya kuɓutar da Mai babban ɗaki harta tsira da ranta,tabbas da ace Mai martaba yasan cewa yasan komai da tuni ya ɗauki mataki a kansa,yana sharesu ne ya nuna tamkar bai san me suke aikatawa ba,ƙara jan idanunsa yayi ya lumshe.
Kusancin da sukai da juna yasa ta shiga cikin wani yanayi mara misaltuwa,zuciyarta ta shiga harbawa da sauri,a duk lokacin data tuna kalmar tsotsan yatsanta da yace zaiyi sai taji tsigan jikinta na tashi wani irin abu nayi mata yawo a kan skin ɗinta,numfashi taja mai ƙara wanda ya tawo da daddaɗan parfume ɗinsa wanda ta kejinsa sanyinsa har cikin ranta,tabbas tasan cewa tana jin wani abu game dashi,musamman idan tayi la'akari da yadda take yawan tunaninsa,sosai ta kejin wani abu game dashi a kansa rauninta yake bayyana,zuciyarta da gangar jikinta ne suka kaɗaitu dasan ganinsa amma ta hana kanta haka,sabida ba tason ta jefa zuciyarta cikin damuwa sbd tana neman jafeta cikin tsaka mai wahala,lallai idan soyayyar Saifudeen ce ta shige zuciyarta ba tayi mata adalci ba,sbd ta kaita wajan da za'aci *ZARAFI* nta kuma a wulaƙanta,ta fahimci shiɗin mutum ne wanda bai damu da kowa ba sai kansa,sosai miskilancinsa ke damunta,tasan cewa bata damu da magana ba,amma kunnunwa cike suke da ƙwaɗayin son jin zazzaƙar muryarsa mai daɗin sauraro,mai cike da nutsuwa da kamala,duk yadda tasu ta hana zuciyarta da idanuwanta da suke ƙwaɗayin ganin ƙyaƙƙyawar fuskarsa kasawa tayi,idanunta ta runtse da ƙarfi ta shiga taune laɓɓanta,sosai take tsoran buɗe idanunta sbd tsoran kallon da zai watsa mata a wanna karan.
Gajiyayyun idanunsa ya ɗaga wanda hakan ya haddasa ɗagawar eyes lashes wanda suke ƙwance luff saman idanunsa,idanunsa ya manna saman innocent face ɗinta,ɗan rolling eyes ball ɗinsa a saman fuskarsa,a hankali ya soma ƙarewa ƙyaƙƙyawar fuskarta kallo,sai a lkcn ya fahimci ƴar ramar dake tattare da ita,yadda take sauke ajjiyar zuciya yasa ya fahimci tana cikin yanayi na tsoro da kuma fargaba,lips ɗinta ya zobawa idanun ganin yadda ta jiƙesu da saliva sbd taunesu da take tamkar zata rabasu gida biyu,pouting lips ɗinsa yayi ganin zata buɗe idanunta yayi saurin kawar da kansa tare daya mutsa fuska.
Bata da wani zaɓi face bin abinda zuciyarta keso,hakan shine kawai samun nutsuwar ranta da gangar jikin,a hankali ta soma buɗe idanunta zuwa kan fuskarsa,wani wahalallan numfashi ta sauke tare da sakin ajjiyar zuciya a lkcn guda,wani sanyi da nutsuwa ne suka soma ratsa duk wani sassan jikinta,ƙyaƙƙyawar sajen fuskarsa wanda yasha gyara ta zobawa idanu,shiɗin na musammanne komai nasa abin sone da birgewa,amma dole ta hana son zuciyarta kasgata abinda ta keson ƙwaɗaita mata,bata san shine ba amm yadda fresh skin ɗinsa take a murje ta tabbatar hutu da ƙwanciyar hankali sun gama ratsashi,wannan dalili yasa take tunanin yayi mata nisa,nisa mai yawan gske shiɗin ba ajinta bane,dole zuciyarta da gangar jikinta da kuma idanuwanta su hqr da abinda sukeso daga garesa.
"halan bodyguard ɗinki na zama ko? Zaki huce kosai na ɓalla wannan sili-silan ƙafafuwan naki..!" ya ƙare maganar cikin ɗan ɗaga murya.
A hankali ta janye idanunta daga garesa wata kunya ta kamata sbd kamata da yayi tana kallonsa,a sanyaye ta juya ta soma tafiya ba tare data tanka saba,bayanta yabi da kallo tare da watsa mata harara,kana yaja tsaki kaɗan tare da lumshe idanunsa kana ya shafi lafaffan cikinsa,kana ya mara mata baya cikin tafiyarsa mai cike da nutsuwa da kamala.
A hankali suke tafiya tana gaba yana bayanta duk takunta ɗaya akan idanunsa yake time to time yakan janye idanunsa tare da lumshe haɗi da taund lips ɗinsa,komai nata cikin sanyi jiki take yinsa hatta ga maganarta tafiyarta aikinta duk cikin kasala take aiwatar dasu,ƙarancin shekarunta a bayyane yane idan tayi wani abun,yana lura da ita ko magana zatai sai tayi kamar tai kuka wani lkcn har hawaye ke sakko mata kafin tayi maganar,a hankali ya fesar da wani huci mai zafin gaske tare dajan fegen dake manne a haɓarsa,a ƙasalance ya yasa hannu ya shafi gefen cikinsa dake masa ciwo sama-sama baya fatan ace ciwonsa ne zai tashi,jin ta tsaya yasa a buɗe gajiyayyun idanunsa wanda suke a lumshe kamar mai jin bacci.
Wajan ya zobawa idanu ganin wani haske na musamman na haske wajan tare da cikin idanunsa,zuwansu sashin Mai babban ɗaki ya haddasa fitowar wani sihirhattaccen haske ya soma fitowa ta cikin zoben dake sanye a yatsan ko wannansu,hashekene mai sanya idanu ƙarfi tare da bawa gangar jikin kuzari,Bafade Kamal dake zaune yana gyara wata baka yayi saurin miƙewa tsaye sabida ƙarfin hasken da yaso kashe masa idanu,cike da mamaki yashiga ƙarewa yatsan ko wannansu idanu,kasa ko motsi yayi sbd tsantsar mamaki da kuma abin al'ajabi,dukkan abinda ring ɗin wannan yayi sai ɗayan yayi abu tamkar magic cikin ransa yace.
" ya rabbi Save them help them Ubangiji ka karesu daga abinƙi,yabbin rahama ka basu nasara a rayuwar,Ubangiji idan maƙiyansun fito ka hanasu fitowa,lallai suɗin GARKUWA ne wa al'ummar Bilhas,sharrin mutum aljan ka karesu,naji zuciyata ta amince dasu a karo na farko kuma tsahun shekaru kusan 20 kafin ta yarda da wani sai yau"cikin rawar jiki ya sanya remote buɗe masu tangamemen glass get ɗin,wanda aka ƙawata zallar a zurfa,ba tare da yayi masu magana ba yayi saurin shigewa ɗakinsa wanda suke parcing da sashin Mai babban ɗaki.
Zaune suka sameta ta fuskancin gabas tana lazumi da alama sallar zuhur da idar domin tun suna waje akai kira,da ɗan sassarfa Zarina ta ƙarasa shiga cikin haɗaɗɗan parlour'n nata,tana zuwa ta nufi inda take zaune kana cikin kulawa ta turo baki gaba tare da langwaɓe kai gefe guda tace.
"Ayya Ammi nabarki jira ko,halan Kaltume ta kula dake ko?"tayi mata tambayar yayinda zuciyarta ke fidda tsantsar tausayin Mai babban ɗaki.
Wani ƙawataccen murmushi Mai babban ɗaki tayi tare da ajjiyar casbawar hannunta,cikin jin daɗin kulawan da Zarina ke bata tace.
"Halan sojanne ya ƙarayi maki laifi,shiyasa ya kasa ƙarasuwa ya amshi hukuncinsa"ta ƙarasar maganar tana sakin wani murmushi kasan cewarta mace mai fara'a da faran-faran da mutane.
Shiguwarsa cikin parlour'n faɗuwar gabansa ta tsananta,kansa ya soma juyawa dukkan ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa,gargasar cikinsa ce ta soma mimmiƙewa wani sanyi ya samu nasarar soma rasa kan fatarsa zuwan cikin ƙashin kafin a hankali ya samu nasarar ratsa cikin ɓargwansa,lallai zuciyarsa nasan tuna masa wani wanda bai sanshi ba,shin mene hakan?teeths ɗinsa yasa ya datse laɓɓansa wanda suka soma yin rawa sabida tsananin sanyin daya gama ratsa gabɓan jikinsa,a hankali ya runtsa idanunsa tare da lalobar jikin bango ya jikin gina jikinsa,wani zazzafan zazzaɓine ya soma maye gurbin sanyin daya addabi jikinsa,a hankali jijoyin kansa suka fito tare dayin raɗa-raɗa saman forehead ɗinsa,wata zuface ta shiga karyo masa cikin yanayin daya samu kansa ya soma fitar da wani huci ta cikin hancinsa,a galabaici ya sanya hannu tare da ɗorashi bisa mararsa wacce take murɗa masa tare dayi maza zogi,saukar muryarta yayi dai² da ɗaukewar numfashinsa na wani dakiƙo,cikin wani hali na fitar hayyaci ya samu nasarar buɗe manyan gajiyayyun idanunsa wanda lkc guda suka sauya kala zuwa jaa,a karo na biyu ya ƙara fitar da wani zazzafan numfashi ta cikin bakinsa saɓanin hancinsa,raguwar ƙarfin daya ragema da kuma jarumtar dake cikin zuciyarsa ta ƙarfafawa gangan jikinsa samun kuzari,kallo guda zakai masa kasan cewa shiɗin namijin duniya wanda yake da juriya da kuma danne abinda ke cikin