Showing 6001 words to 9000 words out of 17719 words
Chapter 3 - FATAUCIN BAYI Book Complete by Mansur Usman Sufi.txt,
Muryar Hushaibu na rawa ya ce "An gama ya shugabana, yana gama faɗin hakan sai ya miƙe tsaye ya fice daga cikin lambun da sauri.
Jim kaɗan sai ga Yesiran ya bayyana gareshi, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance SADAUKIN SADAUKAI, mai tarwatsa maza a filin daga.
Sarki ya dubi Yesiran ya ce "ya kai Yasiran ka yi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi izuwa wani birni dake iyaka da tekun Baharul-sawara, ana kiran birnin da suna DARUL-IMFAL
ina so gaba daya mazajen birnin su zamo matattu, sannan ka kawo min matayensu da dukiyoyin su cikin ƙoshin lafiya,
sai dai ina son kayi sani cewa kuɓucewar ɗaya daga fursunonin dai-dai yake da rasa rayuwar ka baki ɗaya''.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Uhaisu sai Yesiran ya ce "ya shugabana ai wannan aiki abu mai sauƙi a gare ni tamkar kurɓar ruwa, na rantse da ƙarfi mulkin ka sai na kawo maka matayen birnin DARUL-IMFAL cikin ƙoshin lafiya'';
Koda jin wannan batu daga bakin Yesiran sai Uhaisu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Kafin sarki Uhaisu ya sake furta wani abu Yesiran ya miƙe tsaye zumbur ya fice daga lambun.
Kamar yadda sadauki Yesiran ya yiwa sarki Sarki Uhaisu alƙawari haka al'amarin ya kasance, a in da yana fita ya ɗebi dakarun yaƙi guda dubu hamsin, suka durfafi hanyar da za ta sada su da birnin DARUL-IMFAL bisa wani makeken jiragen ruwa.
Da la'asar sakaliya, sadauki Yesiran da rundunar mayaƙanshi, suka iso gaɓar tekun Baharul-sawara sakamakon hango kofar birnin DARUL-IMFAL da su kayi.
A wannan lokaci jama'ar birnin DARUL-IMFAL na gudanar da ayyukan su na yau da kullum cikin walwala da jin daɗi, hakan ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji ihu da kururuwar dakaru masu tsaron ƙofar gari, kafin ka ce me, gari ya hargitse da guje-gujen jama'a gami da ifice-ifice, yara da manya mata da maza,
Nan take dakarun sadauki Yesiran suka afkawa jama'ar birnin da masifaffan yaƙi, nan fa mazaje suka dunga yin MUTUWAR JARUMTA, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, ƙarar karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne.
Kaico! Haƙiƙa yaƙi abin tausayi ne in da a ce mutum zai ga yadda dakarun Yesiran ke hallaka mazajen birnin ba ji ba gani, dole ne ya zubar da hawayen tausayi domin hatta ƙananan yara maza kashewa suke yi, koda kuwa jariri ne sabuwar haihuwa ba su ƙyale ba.
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN KARFI sai ya zamana dakarun Yesiran sun kashe gaba ɗaya mazajen birni ɗayan su bai tsira da rayuwar shi ba. Nan fa ƙananan yara da mata suka dunga rusa kuka mai matuƙar ban tausayi da narkar da zuciya, wasu na kuka ne bisa rasa mazajensu, wasu 'ya'yensu, wasu 'yan uwansu.
Bayan sadauki Yasiran ya kashe sarkin dake mulkin birnin wani dattijo mai suna Sha'aran sai ya yi umarni aka kwashe baki ɗaya dukiyar dake birnin, aka sanya matayen birnin da suka rage a raye sasari na baƙin karfe, bayan an fice daga birnin sai waɗansu dakaru suka bankawa gidadanjiin birnin wuta, take aka nufi gaɓar teku aka sanya ɗora dukkanin jama'ar a bisa wannan makeken jirgin ruwa.
Lokacin da aka ɗora su jama'ar a bisa jirgin ruwan suka hango yadda birninsu ke ci da wuta, kuma an mayar da da yawa daga cikin su zaurawan yara kuwa sun zamo marayu.
Sai suka fashe da matsanancin kukan takaici da baƙin ciki.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba sadauki Yesiran ya yi umarni aka tuƙa jirgin ruwan a aka cigaba da tafiya zuciyarshi cike da matuƙar farin ciki da samun wannan nasara.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya sarki Uhaisu ya farauto su jaruma Nabihat daga birnin DARUL-IMFAL dake iyaka da tekun Baharul-sawara.
BABI NA UKU
Al'amarin shugaba Yesiran kuwa, lokacin da ya gabatar da su Nabihat da sauran jama'ar birninsu gami da dukiyar ganima a gaban sarki Uhaisu sai sarki ya dube shi a lokacin da yake durƙushe a gaban shi ya buɗi baki cikin alfahari da BAƘAR IZZA ya ce
''ya kai Yesiran haƙiƙa kayi aiki mai kyau yadda na buƙata saboda ina mai tabbatar maka da cewa zaka samu gwaggwaɓan kaso daga cikin ganimar dukiyar da aka farauto. Yanzu abin da nake ya kamata ayi shine a tafi da dukkanin fursunonin izuwa kurkuku a ajiye su a ɓangaren BAUTAR MUTUWA".
Koda yarima Zafiyar da ya kafa idanuwanshi akan jarumai jaruma Nabihat dake cikin halin suma, ya ji wannan batu daga bakin mahaifinshi sai ya yi caraf ya tari numfashin shi ya ce "ya abbana ina neman alfarma a gare ka da abar fursunonin a hannuna har izuwa lokacin da za'a yanke hukunci akan su."
Da jin wannan batu daga bakin yarima sai sarki ya juya ya dube shi yana mai fahimtar wani abu akan fuskarshi, sannan ya yi tattaunawar murmushi a gare shi ya ce "ya abin alfaharina kuma muradin zuciyata kayi sani cewa babu wani abu da zaka nema a gare ni face na baka shi koda kuwa raina ne, amma akwai buƙatar ka ba ni lokaci na yi nazari, domin bisa binciken da na gudanar ya tabbatar min da cewa a cikin jama'ar za a samu wanda zai kawo ƙarshen mulki na".
Sa'adda yarima ya ji wannan batu daga bakin sarki sai ya gyaɗa kai cikin alamun matuƙar damuwa, domin wannanne karo na farko a rayuwarshi da ya ji ya kamu da matuƙar tausayin bayin da mahaifinshi ke farautowa.
Koda gama wannan tattaunawa sai shugaba Yesiran ya huce kai tsaye izuwa hanyar da za ta sada su da kurkukun birnin, koda isowar su sai masu gadin suka wangame makekiyar ƙofar shiga, suna masu risinawa ga shugaba a gare shi.
Daga ciki kurkukun ya kasance tafkeke tamkar gari guda, katangun shi sun kasance masu matuƙar tsawo da aka yi su da zallar duwatsun wuta masu ƙwarin gaske.
Duk inda mutum ya kai duban shi a ciki bayi ne maza da mata, yara da manya na ta gudanar da ayyukan bauta nau'i daban-daban, waɗansu na aikin farfasa duwatsun wuta da manyan gudumun ƙarfe, wasu na ɗinka kayan adon dawakai da tufafin sarauta.
Koda shigowar shugaba Yesiran cikin kurkukun sai gaba ɗaya bayin su ka dunga a jiye aiyukan su suna zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa a gare shi, cikin hanzari shugaban dake kula da kurkukun ya karɓi su jaruma Nabihat ya yi umarni aka rarraba jama'ar su a cikin waɗansu ɗakunan na musamman.
Koda jama'ar dake wajen suka ga cewa an shigar da su jaruma Nabihat izuwa ɓangaren da ake yiwa laƙabi da BAUTAR MUTUWA, sai suka cika da matuƙar tausayin su. Domin kuwa duk wanda aka shiga da shi izuwa ɗakin BAUTAR MUTUWA baya fitowa a raye sai daigawar shi.
Sa'adda jama'ar su Nabihat suka tsinci kansu a cikin ɗakunan sai suka fashe da kukan baƙin ciki mai matuƙar tsuma zuciya.
Wannan shine abin da ya faru da su Jaruma Nabihat ya yin da aka isa da su izuwa kurkuku.
Al'amarin wannan yarinya fursuna da ta fafata yaƙi da shugaba Yesiran a ƙarƙashin tekun Baharul-sawara kuwa, bayan ta samu nasarar datse nashi hannunshi ɗaya, shi kuma ya samu nasarar yi mata miyagun raunuka, ɗaya a gadon bayanta na biyu a cinya na ukun kuwa a damtsen ta na hagu.
Saboda yawan jinin dake zuba a jikinta take numfashinshi ya ɗauke, kuma ta taso izuwa saman tekun igiyar ruwa ta cigaba da tafiya da ita, har ta kawo ta izuwa gaɓar tekun ta ɓangaren yamma maso kudu.
A dai-dai wannan lokaci ne wani mafarauci da matarshi suka nufo gaɓar tekun ɗauke da bahon ɗibar ruwa.
Sa'adda suka yi arba da ita kwance babu alamun rai a tare da ita ga manyan raunika a jikinta sai suka yi turus! cikin kaɗuwa suka matsa inda take.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba suka ajiye bahon ruwan dake hannunsu, mafaraucin ya ɗauki yarinyar ya saɓa ta a kafaɗarshi.
Cikin hanzari suka juya suka durfafi hanyar da zata sada su da dajin da suka fito.
Tafiyar daƙiƙa latalin kacal suka yi suka iso wani gida a dajin. Gidan an gina shi ne da zallar duwatsun wuta, kai tsaye suka kunna kai izuwa gidan.
Daga ciki gidan ya kasance mai kyawun tsari yana ɗauke da ɗakuna guda biyu da makewayi ɗaya sai wani madaidaicin fili da aka kafa turken dabbobi wata saniya guda ɗaya fara sol tana cin ciyawa a cikin wani bawon kaba.
Cikin hanzari matar mafaraucin ta shimfiɗe yarinya Lazimat a bisa wani madaidaicin gado da aka yi shi da zallar itace aka shimfiɗe shi da kilishi mai taushi, bayan ta kwantar da ita sai ta shiga danna ƙirjinta cikin matuƙar tashin hankali.
Shi kuwa mafaraucin sai ya fice daga ɗakin, jim kaɗan sai ga shi ya dawo ɗauke da tafashasshen ruwan zafi gami da tacecciyar madarar shanu, a ɗayan hannunshi kuwa yana ɗauke da wata jakar fata, kawai sai ya shiga ɗauko waɗansu magunguna a cikin jakar ya na haɗa su a cikin wani akushi mai ɗauke da ruwa.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya Lazimat bata farfaɗo daga dogon suman da tayi ba.
Sai daga bisani ne ta buɗe idanuwanta tana mai jan gwaron numfashi, nan fa suka cika da matuƙar farin ciki bisa ginin farfaɗowarta, ba tare da wani ɓata lokaci ba matar ta shiga sanya mata magani a raunikan ta.
Bayan ta kammala ne sai ta tashe ta zaune ta shiga bata wannan madarar shanu a baki tana kurɓa, sai da tasha ta ƙoshi sannan ta bata waɗannan magunguna da maigidanta ya haɗa a cikin wannan akushi.
Kana daga bisani mafaraucin ya dubi matarshi fuskarshi cike da annuri gami da tsantsar so da kauna ya ce "ya uwar 'ya'yana ina mai ba Ni farin ciki, kiyi sani cewa ina ji a jikina wannan yarinya da muka tsinta za ta maye mana gurbin da raɗaɗin 'yarmu da muka rasa.
Kuma na ji a jikina cewa za ta zamto silar da zamu ɗauki fansa akan sarki Uhaisu".
Koda jin wannan batu daga bakin mai gidannata sai ta cika da matuƙar farin ciki ta ce "maganar ka haƙƙun ya abin bege na tabbas alamun nasara sun fara bayyana a gare mu";
Mafaraucin ya ce "yanzu zan ɗan shiga izuwa daji, domin na farauto mana abin da zamu yi kalaci sai ki kula da ita har naje na dawo".
Yana gama faɗin hakan sai kawai ya miƙe tsaye ya fice daga ɗakin ya na mai waigen matarshi suna jifan juna da tsantsar so da ƙauna, yana fita ya sake kunna kai izuwa cikin daji .
Jim kaɗan bayan shuɗewar waɗansu daƙiƙu matar mafaraucin na zaune a gaban Lazimat ta ƙura mata idanu sai kawai ta jiyo ƙarar takun sawaye gami da gurnani mai matuƙar ban tsoro, ya cika dajin baki ɗaya.
Koda jin hakan sai kawai ta ɗauko wata takobi a gefen gadonta ta miƙe tsaye zumbur ta ruga izuwa ƙofar gidan, ai kuwa tana fita sai tayi arba da waɗansu irin ayarin gabza-gabzan birrai su kimanin guda ɗari biyu.
Birran sun kasance masu matuƙar tsawo, girma, kwarjini gami da muni, a hannayensu na ɗauke da wani irin sungumi mai waɗansu irin tsinika a jikin shi tamkar zarto,
Wannan shi ne abin da ya faru da mafarauci da matarshi da suka tsinci yarinya Lazimat.
Kallo ne ya wakana tsakanin kilimat matar wannan mafarauci da ayarin gwaggwan birran na ɗan wani lokaci.
Daga can sai birran su kayi wani mahaukacin gurnani mai matuƙar ban tsoro mai ɗimauta duk wata halitta numfashi, bishiyu suka dunga rangaji suna karairayewa suna faɗuwa kasa.
Wani daga cikin birran wanda alama shi ne shugaban su ya daka masu wata tsawa dake nuna cewa su afkawa matar, ai kuwa sai su ka yi ɗauki kanta suna masu daga makamansu suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Shi kuwa shugaban birran sai ya samu wani ɗan faffaɗan dutse ya zauna a a kai yana mai harɗe kafafuwanshi yana mai zuba idanu domin ya ga yadda artabun zai wakana.
Koda ganin hakan sai uwar gidan mafaraucin ta ɗaga takobinta sama sannan ta ruga izuwa kan birran tana ihu da kururuwa mai firgitarwa ta far masu da sara da suka, su kuwa suka shiga kai mata duka da bugu da sungumin su cikin wani irin zafin nama, duk sa'adda takobinta ta sari jikkunan birran sai ta ji kamar dutse ta sara domin ko gezau ba su yi
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan, yazamana ta canza salon fadan ta a in da ta dunga saran su gami amfani da hannunta ɗayan tana gabza masu naushi da bugu da dukkan ƙarfin ta.
Gaskiyar masu iya magana da suka ce "Idan kiɗa ya canja dole ne rawa ma ta canja, nan fa ya zamana cewa ta fara samun galaba akan birran, domin duk wanda ta gabza masu naushin sai ka ji ya tsandara ihu ya ya faɗi ƙasa yif!.
Koda ta fahimci cewa ƘARFIN DAMTSE ya fi tasiri akan su sai kawai ta yi jifa da takobinta ta shiga amfani da hannayenta duka biyun gami da kafafu wajen kai farmaki. Duk in da ta sanya a gaba sai dai kaga gawarwakin birran na zube kasa matattu.
Wohoho! Tabbas ƙarfi da jarumtaka ba a siyan su da kuɗi face baiwa daga Allah,
Komai tsakanin hassadar mutum idan ya ga yadda kilimat ke ragargazar birran dole ne ya jinjina mata ya san cewa ta ciri tuta a cikin jerin manyan JARUMAN DUNIYA.
Nan fa kururuwa gami da hargagin su ya cika dajin baki ɗaya, jini ya dunga tsartuwa yana kwaranya a kasa, haƙiƙa waɗannan birrai suna ganin tashin hankalin da basu taɓa ganin irin shi ba.
Domin ta zame mssu alaƙaƙai, kuma ƙadangaren bakin tulu, cikin abin da bai gaza daƙiƙa ɗari biyu ba ta kashe fiye da kaso biyu bisa uku na birran.
Sa'adda shugaban birran ya ga irin muguwar ɓarnar da matar mafaraucin ke yi mashi sai ya cika da matuƙar mamaki kuma ya fusata ainun, domin fiye da shekaru ashirin suna zaune a wannan daji ba su taɓa ganin bil'adama da ya yi masu hasara kamar haka ba.
Nan take zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone, kawai sai ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da sanya bishiyu suka dunga ƙarye suna faɗuwa ƙasa, duwatsu suna karo da juna su na yin bindiga,
kawai sai sauran birran da ke yaƙin suka zubar da makaman su suka ruga izuwa bayan bishiyu su ka ɓuya
A lokaci guda shugaban ya tsuke bakinshi sannan ya dako wawan tsalle daga inda yake zaune ya durfafi inda take, ya yin da ya isa gare ta nan take ta zamto 'yar mitsitsiya tamkar an ajiye ɓera a gaban giwa, saboda matuƙar tsawo da girman shi.
Kafin ta yi wani yunƙuri shugaban ya shammace ta ya gabza mata wawan naushi a fuska da hannunshi ɗaya.
Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da tayi katantanwa a sama sau uku sannan ta faɗo ƙasa tim! A matuƙar galabai ce,
cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta miƙe tsaye da nufin ta mayar da martani amma sai ya damƙe ta da hannunshi ɗaya ya matse ta ya shiga yi mata lugudan naushi a fuska nan take fuskarta ta kumbura, tayi kaca-kaca da jini da majina kuma numfashinta na fita samas-sama.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai ya ji ta ƙwalla ƙara ta suɓuce daga hannunshi sannan ta gabza mashi naushi a idonshi ɗaya.
Take ya fashe wani koren ruwa gami da jini ya dunga kwaranya da ga ciki, nan fa shugaban ya dunga ihu da kururuwar neman taimako, kafin ya sake wani yunƙuri matar mafaraucin ta cire wata 'yar karamar wuƙa ta caka mashi a maƙogaronshi, nan take ya faɗi kasa rikica! Yana shure-shuren mutuwa kafin wani lokaci ya sheƙa barzahu.
A dai-dai wannan lokaci ne mai gidanta ya rugo izuwa wajen, koda ya yi arba da gawarwakin birran sai kawai ya rungume matarshi cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa bisa ganin cewa tana raye bata mutu ba.
Sai daga can ne ya janye jikinshi daga na ta, a lokacinne ya